Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
sirrinta, amma data tuna irin tuggun da zata shirya sai ta mayar da komai ba komai ba, ta zubawa sarautar Allah ido tayi da jiran tsammanin lokacin haihuwar Fulani Zaliha. Domin a nan ne zata aiwatar da dukkan ƙudurinta.
Bayan kwana biyu Mai Martaba na zaune a turakarsa Fulani Maryama na gefe a zaune, ta kalleshi sai dai gabaɗaya baya cikin walwala cikin kissa ta ce. "Mai Martaba wannan yanayin sam bai kamace ka ba, Allah ƙara lafiya da nisan kwana shugaba kamar kai wannan yanayin bai dace da kai ba, Bango madafar bayi idan har zaka dinga shiga cikin damuwa, to mu da sauran talakawanka ya zamu kasance." Mai martaba cikin damuwa yace. "Wallahi ina yawan yin mummunan mafarki akan ƙanwarki Zaliha ina yawan mafarki mara kyau akan cikinta" gaban Fulani Maryama ya faɗi ɓaci rai ya sauka a zuciyarta amma da yake ta iya duniyanci sai ta aro damuwa ta yafa a fuskarta ta ce. "Haba taƙamar bayi adalin Sarki mai adalci, ai zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi, ka kwantar da hankalinka Fulani Zaliha zata sauka lafiya tunda alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, nidai a iya sanina Fulani Zaliha tana cikin ƙoshin lafiya kuma zata haife mana ƙanin Yarima lafiya" farinciki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Me martaba, janyo hannunta yayi ya sumbaceta yace.
"Allah ya yi miki albarka Maryama ke ɗin ta daban ce saboda haka kike ƙara birgeni, naji daɗin yadda kika riƙi ƴan uwanki da zuciya ɗaya kuma kika riƙe girman da Allah ya ɗora miki, hakan ne yake sa nake tunanin ko bayan raina zuri'ata zata haɗa kanta." Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. "Dole ƙanwar naƙi wa ya isa ya ja da abin da Mai Martaba yake so, ai duk abin da ka nuna kana so har bada ina ƙaunarsa"Mai Martaba daɗi yaji sosai yadda take bashi kulawa akan sauran matansa. Cikin zuciyarta Fulani Maryam ta ce. "Da ikon Allah bazai zo duniya lafiya ba mu zuba mu gani"
*BAYAN WATA UKU*
Fulani Zaliha ce durƙushe tana naƙuda, gefenta Marka ce sai Jakadiya dake riƙe da ita, daga bakin zaure Shamaki ne yake sallama, da sauri Jakadiya ta fita gurinsa, ƙwarya ce da rubutu aciki ya miƙa mata yana faɗin, " Gashi Takawa ya ce a bata ta sha ashafe cikin da shi " karɓa Jakadiya tayi ta koma ciki ta ɗago kan Fulani Zaliha da ta haɗa uban gumi, a wahalce ta sha bayan ta gama sha aka Shafe cikin da sauran.
Bankaɗa labulen ɗakin akayi ko sallama babu, Jakadiya na ɗago kai tana shirin masifa suka haɗa ido da Fulani Maryama fuskar nan tata babu annuri, wani tunani Fulani Maryama tayi lokaci ɗaya ta sauya yanayin ta cikin ruɗewa ta ce, " Jakadiya ashe Fulani na kan gwiwa amma ba'a turo ansanar mun ba sai yanxu labari ya je mun " Jakadiya cikin rawar murya ta ce, " Ai wato...Nima zuwa na kenan, na fito zanje wajenki Takawa ya ayko da rubutu "
Marmushin Markirci Fulani Maryama tayi ta ce, " Bari nazo na riƙeta kije ki kawon garwashi yanxun nan ga ragowar turaren da akamun lokacin naƙudar Yarima " Suna haɗa ido Fulani ta watsawa Jakadiya mugun kallo ba shiri Jakadiya ta fice.
Fulani na shiga ta riƙe Fulani Zaliha tana mata sannu.
Jakadiya na kawo wuta Fulani Maryama ta kunce turaren wajen boka ta barbaɗa, ba'a jima Jariri ya faɗo yana tsanyara kuka, Fulani Zuwaira da Fulani Bilkisu na kawo kai suka ji kukan jariri, da sauri Fulani Bilkisu ta ce, " Lallai mun shigo a sa'a Barka da arziki " suna shigowa kowa yayi turus saboda ganin Abunda Fulani Zulaiha ta haifo, sai dai kowannen su haɗiye abinda ke ransa yayi gudun kar afuskanci halin da Suke ciki.
Bayan an yanke mabiyar angyara gun ruwa aka kawo na wankan jariri. Kasancewar Fulani Maryama ita yaro ya faɗo a hannunta ita aka bawa ruwan, fakar idanun su tayi ta damƙi garin gurin boka haɗe da ƙafar jaririn ta sa acikin ruwan wankan.
Lokacin da garin maganin ya garwaye jikin sa wani irin kuka ya fashe da shi, amma babu wanda ya kawo komai sai ma tsokarsa da Marka ta ke cikin waƙa tana faɗin, " Ka zama Jarumin maza karka zama rago mana matsoraci bashi zama gwani, jinin Aminullahi yafi ƙarfin wasa kyawun ɗan ƙwarai ya gaji ubansa"
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[12/10/2021, 19:42] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*ANYA BAIWA CE?*
Na
*AMEERA ADAM*
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
FREE PAGE 5
Fulani Maryama zuciyarta fes wani shu'umin murmushi tayi har ya bayyana a fili ta ce. "Marka ai ɗana jarumi ne kamar yadda ɗan uwansa salman yake" Jakadiya ce ta fita ta yiwa Sarki albishiri Marka ta fara ƙoƙarin gyara Fulani Zaliha. Har aka gama yiwa Jaririn Fulani Zaliha wanka bai daina tsanyara kuka ba, tana gamawa ta gyarashi sannan ta ce. "Fulani barka da arziki bari na ƙarasa ciki na bar yarima yana bacci kar ya tashi ki samu ki ci abinci ki kwanta ki huta." Fulani Zaliha ta ce. "To na gode Yaya Allah ya huta gajiya" Fulani Maryama ta wuce sashenta.
Kafin wani lokaci tuni haihuwar Fulani Zaliha ta zaga cikin gidan masarautar, sanƙira bi yake ko ina yana shelar sanar da ƙaruwar da Mai martaba ya samu , cikin lokacin ƙanƙani cikin garin Kano ta samu sakon haihuwar da aka yiwa Sarkin Kano Aminullahi.
Jaririn Fulani Zaliha tun ranar da aka haifeshi yayi wannan kukan bai ƙara wani kuka da ƙarfi yadda wani zai iya ji ba, Fulani Zaliha bata kawo komai ba saboda wannan ce haihuwarta ta farko kuma bata taɓa kawowa ranta komai ba, tafi alaƙanta haka da yaro ne shi mara rigima saboda wasu jariran basu cika rigima ba. Matan cikin masarauta da sauran bayi tsegungumi sukeyi akan Fulani Maryama na rashin nuna matsanancin kishinta akan ɗan Fulani Zaliha duk da yadda kowa yasan Fulani Maryama da matsanancin kishi. Fulani Zaliha ba ta shan wahalar rainon Jaririnta dukda akwai masu kula dashi amma sam bashi da rigima. Tun daga ranar kuma Fulani bata ƙara takawa ta leƙa saahen Fulani Zaliha ba har sai da yayi kwana uku, da wata yammacin ranar ta shirya cikin shiga ta alfarma irin ta jiƙaƙƙun matan sarakuna, tafe take cikin takun ƙasaita da taƙama kamar ba zata taka ƙasa ba. Ga duk wanda yayi arba da Fulani Maryama kallo ɗaya zai mata ya tabbatar da ita ɗin tabbas jinin masarauta ce gaba da baya, duk yadda ka kai ga kallan ƙurulla zai yi wuya ku haɗa ido da ita batare da janye idanuwanka ba kuma duk sanka da ka fahimci a wane yanayi take zaiyi wuya ka fahimci halin da take ciki. Tana tafe kunyangarta na biye da ita da Salman a hannu har suka ƙarasa sashen Fulani Zaliha, lokacin da ta shiga sashen Fulani Zaliha na zaune tayi kwalliyar ta fito shar da ita ga wani kyau da ta ƙarayi irin na masu jego, Fulani Maryama zama tayi kan lallausar shimfiɗar Fulani Zaliha baiwar ta tsaya daga rumfa.Da fara'arta Fulani Zaliha ta ce, "Barka da shigowa Yaya da fatan kin wuni lafiya ya kwanan Yarima" Fulani Maryama wani murmushi tayi mai wuyar fasaltuwa ta ce. "Lafiya kalau masu jego ya kwanan ɗannawa" Fulani Zaliha kunya taji bata amsa ba ta ƙwalawa baiwarta kira tana bata umarnin kawo Jaririn, a fakaice Fulani Maryama take ƙarewa Fulani Zaliha kallo tana ƙara jin wata irin tsanarta a zuciyarta.
Lokacin da aka kawo mata Jaririn karɓar sa tayi tana murmushi sai dai ƙasan zuciyarta har wani zafi take ji saboda yadda taga kamaninsa dana Mai martaba na ƙara fitowa, a fili ta shafa fuskarsa ta ce. "A jinjira baƙwan duniya yana rigima kuwa?" Fulani Zaliha ta ce, "Tun kukan farko da yayi bai ƙarayi ba bashi da rigima" Fulani Maryama na shirin yin magana taga hawaye na gangarowa daga idanuwansa, buɗe baki yakeyi yana ɗan juya kansa wanda yake nuna yunwa yake ji, Fulani Maryama murmushi tayi me sauti ta ce. "Ai dama bazai yi ba indai ya biyo gida kinsan Yarima ma haka nayi goyonsa, ungoshi naga kamar yunwa yake ji" a kunyace Fulani Zaliha ta karɓeshi miƙewa Fulani Maryama tayi tayi mata sallama zata wuce har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce. "Sai fa kinsa ido akansa saboda ɓoyayyun maƙiya duk yadda kika kai ga ganosu sai kin gaza a masarautar nan dan haka ki bi sannu" murmushi Fulani Zaliha tayi ta ce, "In sha Allah Yaya kinsan zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi" Fulani Zaliha zuciyarta ɗaya ta faɗi haka ita kuwa Fulani Maryama juyowa tayi amma sai ta wayence da murmushi ɗauke a fuskarta ta ce. "Kinyi gaskiya kuma nasan da haka amma duk da haka tsugunne bata ƙare miki ba amma fa shawara ce na baki." tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin.
Tun daga ranar Fulani Maryama bata ƙara shiga sashen Fulani Zaliha ba, kuma zuciyarta fes ta fita daga ɗakin saboda yadda da dukkan alama haƙanta ya cimma ruwa. Shirye-shirye ake ta gudanarwa na shagalin suna daga sassan ɓangarori na cikin masarautar. Ranar suna Mai martaba ya raɗawa Jariri sunan Saifullah suna kiransa da Saif, anyi shagali sosai ɓaki daga garuruwa suka kawo ziyara wajen taya Mai Martaba murnar samu Ɗa namiji a karo na biyu.
Anyi taron suna angama lafiya kuma daga ɓangaren Mejego da jaririnta suna cikin ƙoshin lafiya. Bayan wata uku Mai Martaba ne zaune a fada shi da Waziri, ga duk wanda ya dubi yanayim Mai Martaba zai fahimci tsantsar damuwar da yake ciki, amma da yake namiji ne jajirtacce farat ɗaya bazaka fahimci ainihin yanayin da yake cikin ba. Waziri ya ɗuƙar da kai cikin sigar girmamawa yace. "Allah ya taimaki takawa ya ƙarawa Sarki lafiya, Muna zaune aka aika da saƙon kiranmu" Sarki Aminullah ya jinjina kai sannan ya ce.
"Waziri wani abu yana damunmu kuma babu wanda muka aminta da mu tattauna dashi sai kai" Waziri ya ɗago yace. "Wannan haka haka yake" Sarki yace. "Mun lura da yaron wajen Zaliha kamar bashi da wadatacciyar lafiya, kuma na lura da yanayin Mahaifiyarsa ita kanta ta fahimci haka sai da tana shakkun sanar dani. Waziri ina san maganar nan ta zama sirrin saboda kunnuwa da idanun Fada suna bibiyar halin da ake ciki, banasan a fuskanci halin da yaron nan yake ciki inasan ka nemo min mai magani a sirrance ta yadda babu wanda zai fahimci halin da ake ciki."
Waziri ya numfasa yace. "Allah ƙadiran alamanyasha'u gaskiya akwai matsala babba dukda kasancewar ba shine Yarima ba, amma sirrantawar yana da matuƙar fa'ida. A cen garin Zaria akwai wani mai magani dana sani yana bada magunguna sosai, dan haka insha Allah zan shirya naje na karɓo maganin sai a jarraba da ikon Allah za'a dace." Mai Martaba yace. "Waziri me zai hana ya gayyato mana mai magnin ina ganin kamar hakan zaifi" Waziri yace, "Duk yadda kace haka za'a aiwatar da kai da kaya duk mallakar wuya ne" Mai Martaba yace. "A shirya tafiya gobe aje a gayyato mana shi" Waziri ya amsa daga nan ya fice daga fadar."
Da daddare Fulani Zaliha ce zaune a turakar Sarki ta zuba uban tagumi, Sarki Aminullahi ya kalleta yace."Me yake damunki Zaliha" idanunta ne suka ciko da ƙwalla muryarta na rawa ta ce. "Mai martaba Saif ne nake lura da yanayinsa bashi da ƙosasshiyar lafiya, na lura fa ko gani kamar ba ya yi, gashi har yanzu kansa baya tsaiwa hatta irin gwarancin yarannan banji yana yi ba, abu ɗaya kawai nasan yanayi idan na kira sunansa zan ga yana ɗan motsawa." Fulani Zaliha na kawo nan a zancenta ta rushe da kuka. Rungumeta yayi ajikinsa tsam kamar wani zai ƙwaceta ya fara rarrashinta, yana buga bayanta harta lafa da kukan sannan yace. "Ina lura da halin da kike ciki kuma na fahimci duk abinda kika gayamun, dan haka na aika a kira mai magani a sirrance inasan ki zama jaruma karki bari magauta su ga kukanki, Insha Allah Saif zai samu lafiya ki kwantar da hankalinki." Haka dai Sarki yayi da lallashin Fulani Zaliha har ta sauko ta daina kuka.
Bayan kwana biyu Mai magani suka ƙarasa ta ƙofar baya suka ƙaraso ɗakin sirri wacce take bayan gari, Saif na hannun Mai martaba mai maganin ya shigo hannunsa ɗauke da wata jakar fata ta magunguna, yana zuwa ya ƙurawa Saif kallo nan take ya fara tsanyara wani irin kuka, jinjina kai yayi ya ce. "Tabbas ancutar da shi da guba mai tsanani sai dai zan iya taimaka muku da yardar Allah koda kuwa bazai warke gabaɗaya ba." Mai maganin kwance jakarsa ya farayi nan take ya dafe ƙirjinsa ya fara wani irin kakari kafin wani lokaci ya yanke jiki ya faɗi ƙasa matacce.
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[13/10/2021, 18:53] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*ANYA BAIWA CE?*
Na
*AMEERA ADAM*
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
FREE PAGE 6
Hankali a tashe Waziri da Mai martaba suka kalli juna ganin abinda ya faru da mai magani, ƙanin Mai maganin da ke gefe da sauri ya faɗa kan ɗan uwansa yana kuka, Mai Martaba cikin al'ajabi haɗe da tashin hankali ya kalli Waziri yace. "Waziri a ji da bawan Allahn nan bamasan a tara mana jama'a, ashirya tafiya ƙasar Zazzau a sirrance batare da wasu sun sani ba, zan aiko da takarda akaiwa da iyalansa tare da kyautuka masu yawa." Yana gama faɗa ya juya ya fita ta ƙofar baya cikin jimami" Lokacin da Mai martaba ya ƙarasa cikin turakarsa dare yayi sosai babu komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabbobi, Fulani Zaliha na tsaye sai safa da marwa take yi da ka ga yanayinta zaka fahimci tana cikin damuwa, tana jin motsin Mai Martaba da sauri ta ƙarasa ta tarbeshi gabanta sai faɗuwa yake tunaninta ɗaya wacce amsa Mai martaba zai bata.
Ganin Mai martaba tayi ya shigo cikin shigar da yayi ta ɓadda kama, sanye yake da kayan bayi fuskarsa naɗe da rawani sai Saif dake rungume a ƙirjinsa, har kusan gware sukayi da Fulani Zaliha ta ɗan ja da baya tana kallan yanayinsa, a hankali ya taka kan lallausar shinfiɗarsa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Fulani Zaliha zama tayi a gefensa ta ƙarɓi Saif dake hannun Sarki Aminullah yana shan ɗan yatsansa, kallan ɗan nata take zuciya a karye ta ce. "Allah ya taimakeka har dace ba ko?" Sarki Aminullah yace. "Mai maganin Allah yayi masa rasuwa" a hargitse ta ɗago tana kallansa bakinta na rawa ta ce.
"Mai Martaba ɗazu kace Mai maganin yana ɗakin sirri yana jiranka" Sarki Aminullah yace. "Zaliha lamarin Ubangiji yafi gaban komai, yana gabda haɗa magunguna Allah ya karɓi rayuwarsa." Fulani Zaliha ta jinjina kai ta ce. "Allah ya fimu sanin dalilin faruwar haka. Amma gani nake larurar Saif anya babu sihiri a ciki?" Kallan da Sarki Aminullah ya yi mata ne yasa ta haɗiye wani yawu tana sunkuyar da kai ƙasa ta ce.
"Allah ya huci zuciyar Takawa a gafarceni ban faɗi haka saboda ɓacin ranka ba" Sarki Aminullah yace. "Zaliha karna ƙara jin makamanciyar irin wannan maganar daga bakinki, kina nufin yafi ƙarfin Ubangiji ya jarrabceshi da wani ciwo ne? Karki bari shaiɗan yayi tasiri a zuciyarki har ya kaiga kin fara zargin abinda ba haka bane" Fulani Zaliha kukan da take ɓoyewa ne ya ƙwace mata, wani irin kuka take me tsuma zuciya Mai martaba jin kukanta yake har cikin zuciyarsa, takowa yayi a hankali ya karɓi Saif ya kwantar da shi sannan ya rungumeta yana lallashinta, sai da ya ga ta tsagaita da kukan sannan yace.
"Zaliha dole na gaya miki gaskiya koda bazata miki daɗi ba saboda gujewa faɗawa ga halaka, zato a musulunci haramin koda ya kasance gaskiya abinda nake so da ke ki cigaba da kai kukanki gurun Ubangiji, shi zai magance mana duk abinda yake damunki, karki nufi kowa da sharri sai kiga Allah ya kare ki duk wanda ma ya nufe ki da shi koda yana nasara wata rana mugun abinsa zai koma kansa saboda ramin ƙarya ƙurarre ne. Allah ya fimu sanin dai-dai amma ni bana zargin akwai wanda zai iya cutar da abinda kika haifa a cikin masarautar nan, ki riƙi ibada kamar yadda nasanki da ita Allah zai kawo mana waraka cikin ƙudurarsa." Fulani Zaliha goge hawaye tayi tana gyaɗa kai Sarki Aminullah ya cigaba da kwantar mata da hankali.
Fulani Maryama banda zarya babu abinda take yi a soron baya cikin shigarta ta baɗɗa kama, motsin tafiya taji da sauri