Author : Hassana Bamalli Oum Aphanan Category : Read Hausa Novels
kawai"
"Ni bazani ba mu tafi gida"
"Allah sai mun je, Nari ga da na ganoki tunda if baki yarda da had'ubar shed'aniyar nan ba ,da
banga kina mun asaran hawayenki ba a banza"
Gaddaman nan bai k'areba har Saida sukazo asibitin koyarwan dake kusa da company d'insa.
Don dole ta bisa saboda itama tana buk'atar sanin dahir d'insu ko zuciyarta zata natsu.
Saida aka d'auki blood sample d'insu kafin akace suje su jira a reception.
Cikin k'ank'anin lokaci result yayi out, likitan hannu ya kawo sukayi musabiha "congratulations
result is negative so bakuda wata matsala... Amma in kuna tantama still zaku iya dawowa
bayan wata uku ,sai ku k'ara sakeyi."
Sayayyar tsarabar da ba ayi ba kenan,tace abarshi in sunje can adamawan a siya.
******
Tunda suka isa hanyar garinsu take ganin certain changes .
Koina solar ga kwalta shar har rugarsu ,tuk'atuk'a har biyu ,banda wutar nefa da aka jawo masu
Cikeda murna da mamaki take kallon julayb
"Hmmm bae jibi,aikin da mukasamu wannan gomnatin ta tuna damu...mun zama kamar cikin
gari ,kai allah ya shiwa wannan gomnatin da albarka"
"Amin ,amin baby gaskiya kam waje yayi kyau"
Suna fitowa mutanen k'auyen sukayi masu caaaa
Kowa nayi wa julayb godiya tareda shi masa albarka.
Kallon rashin fahimta tayi masa.kawai sai ya kauda Kai,ya mik'a mata Jakarta da ya cika mata
da 'yan dubu² vatareda ta sani ba,don yasan zataso rabon kud'i.
"Kishiga daga ciki ganinan shigowa nima,sai ayi mun iso"
Dalo ido tayi,to ai ba gidan namu
"To ki fita ki tambaya"
"Na shigesu kardai iyayena sun Mutune gomnati ta gine filin mu"
"Come on ,nan shine gidan baba nima nasha mamaki da nazo naga ya chanza"
"Kai yaushe kazo baka sanar daniba"
"Baby kije zan gaisa da mutane kinga suna taruwa"
Jan jakarta tayi ,tafito waje sukuku , cikin tsoro da mamaki
'yan gidansu ne sukaji labarin zuwansu aiko saigasusu fito da gudu ,kaci6is sukayi da ita
Da sauri suka kar6a jakanta cikin d'oki sukayi cikin gidan dashi
Shikuwa saida yagama rabon kud'insa na k'aida kafin ya kirata waya ,wai tazo ta shigo dashi.
Lokacin kuwa an gama koro mata labarin aikin da yayiwa k'auyen Ashe duk shine yagyara garin
ya kuma k'era ma babanta wannan k'erarren gidan .
Cikin zakuwa taje ta shigo dashi ,kafin ayi haka angama cika mata gabansa da cimmakatai iri iri
,banda soyayyen naman zabbi da dafaffen k'wai.
Yaci sosai kafin ya bi d'aki d'aki ya gaishesu ,sannan yayi masu sallama with intention gobe zai
zo da wuri su wuce.
Har taxi d'in da sukayi tasha ta rakasa dukda bata kai ga yimasa godiya abunda yayi masu
ba,kawai she reserve it ,sai sunje gida.
Anyi firar yaushe gamo ,saida suka k'ure a daki da mamanta kafin take shaida mata sun zo
yimasu sallama ne zasuje gayar da dangin mijin ta da hutun amarci.
Shiru maman tayi tana jujjuya abun a ranta ,tsoronta d'aya Kar zancen mutane ya
tabbata,dasuke cewa sun yi cinakin 'yarsu sun kar6i kud'in harda canji
Ta6ata tayi "mama akwai damuwa ne?"
"Aah , dama dai inata jin tsorone ,amma kiyi hak'uri zan fad'a maki ,amma karki zargeni da
rashin yiwa mijinki adalci watau abun ne yina bugamun kai,mun zama abun tsegumi a cikin
karkaran nan ,nima kuma na fara tsoro saidai inda Allah ba komai...watau kinsan meke
faruwa...yanzu haka bayan wannan gyaran garin da yayi Mana,ya bud'ewa babanki k'atuwar
masana'anta daga wajen gari...ana fidda madaran shanu ana maidashi ta kanti ana d'urewa a
buhu...man jikin sa d'inma suna wasu amfanin dasu na davam... Ya zuba masa maaikata harda
wainda ba 'yan kasan nan ba ,wai duk a k'ark'ashin sa suke ya bashi wajen halak malak,yanzu
haka babanki gini yike yi daga cikin garin yola wai zamu tashi anan mu koma can yanda zai fi
masa kusa da wajen aikinsa.
Anya haka zatayiwu babanki jahilinsa dashi ,ba zaginsa nike son yi ba amma a basa irin
wannan waje ,ai dole mu shiga zargi ...shikuwa ko a jikinsa fantamawansa kurum yikeyi...amma
bakomai na barwa Allah za6insa.
"Ayya mama na yarda da julayb dari bisa dubu ,saidai mugu bayida kama,don haka zan hak'ura
da tafiyan nan kurum,ni dama bason zuwa wajen danginsa nikeyiba,don na lura basu sona"
"Akul d'inki...kije ba abunda zai faru inshallah, sannan gameda danginsa zan baki addu'oin tsari
da na mallaka amma ki tunamun in zaki tafi zan rubuta maki wannan zantuttuka da mukayi , Ina
so suzamar mana sirri"
"Shikenan mama allah ka shige mana gaba."
*****
Washegari suka wuce Lagos cikin kewar iyayenta ,kwana biyu tsakani suka wuce egypt tanan
suka fara ,dama yayi masu scheduling daga Egypt ne su wuce America,sai Australia ,china sai
su sauka a dubai daga nan su wuce saudiyya...tunda Egypt yafi kusa damu Africa ne,sai ma su
tsaya suyi umrah da aikin hajji kafin su dawo.
Aikuwa maryam ta shana taga gari sun 6arji soyayya ,anan ne tayiwa julayb godiyan duk
kyautatawan da yayiwa iyayenta batareda ko sanin taba.duk ko k'asar da sukaje sai tayi hotuna
tayo tsarabar irin abubuwan k'asan da ita kanta... status kam kullum yina kar6an sababbin pix
na amarya da ango.
Saida sukayi sati biyu da kwana hud'u kafin suka wuce sa'udiyya ,a lokacin batajin ko shayin
turanci , abunda ta gane shine ka kwakwa6a indai zaa gane ai shikenan.
Garin sa'udiyya
'karfe goma na daren garin suka sauka a k'asar.
Ouk Aphnan
[3/14, 07:13] Bamalli✌️: *JARABABBEN NAMIJI*
*89 - 90*
Amma tantarwai ko ina yike kamar rana,ga yara 'yan k'anana dake ta wasanninsu a k'ofar
gidajensu ...kasa daurewa maryam tayi saida ta 6ara tayi magana "baby kajibi yara k'arfe nawa
na dare suna wasa a waje basu tsoran a sace masu yara,kaf cikan sufa ba mai shekaru bakwai
. Ga gari ko ina duwarwatsu ni tsoroma zanji in na d'aga kaina kalli wainnan bak'ak'en
duwarwatsun."
"Hhh babe akwai tsokana to aibaki saniba da darana mukazo mutum 1 bazaki ganiva sai masu
hidimar gidaje saboda garin akwai bala'in zafi ,bama iya fitowa,anjuyane yanzu shine lokacin
mu,tamkar rana muke kallon sa,kuma sa'udiyya ba kamar sauran k'asashe bane akwai tsaro
sosai"
Jinjina kai kurum tayi"lallai duniya juyi juyi,haka kowa da kiwon da ya kar6esa."
Sun samu karramawa ta musamman ilahirin mutanen gidan suna falo zaman jiransu,suna
sallama kuwa,d'uuuu sukayo kansa suka rungume kotakan ta basu biba...sai Abby ne ya
kamota
"Kun kamo wannan garjejen kun rungume, Kun bar bakuwa sagale da hannu."
Gabadaya yaranne suka yo kanta ,banda uwar gayyan
"Ayyah anty we are sorry. ..yayan ne mun dad'e bamu gansa ba"
Murmushi tayi tana satan kallan ummy raudha "ayyah bakomai"
Jan hannunta sukayi bayan an gaggaisa suka kaita d'akinsu
"Anty ki zauna anan tare damu ko?"
"Uhm "
Zaro ido sukayi "uhm what? Me uhm yike nufi? Baki yarda ba " "no i agreed" tsalle sukayi suka
rungumeta
"Shikenan munajin dad'inmu...anty kiyi wanka and freshing up,kizo muci abinci mu fita yawo"
"To sarakan yawo ba inda zataje baku ganin ta gajine...yanzufa mukazo k'asar,ai kwa bari sai
gobe ...."
Duddurke k'afa suka shiga yi "Yaya mune mayawatan?"
"Yes a ba mata na waje ta kintsa"
Fita sukayi suna tsallen murna kamar k'ananun yara. . ada suna jin haushin ta amma yanzu
kallon farko sukaji sonta a cikin ransu
D'aga ido sama tayi tanayuwa Allah godiya
"Nasamu kar6uwa a wajen 'yan gidan duka ,saura uwar gidan"
Matsowa kusa da ita yayi ya rungumota..."baby ya kika ga family na?" "Hmm sun burgeni ina
sonsu"
"Kowa yaganmu sai ya so mu , haka kuma kema kike"
"Aah ni awa? Ga larabawa me za ayi dani bak'ar fata"
"Come on, karki wulakanta mun ke" sassauta murya yayi "baby inaso zan ci?"
"Hmmm zakaci me?"
Kashe mata ido d'aya tayi kafin ya shafo mararta "nan nike nufi"
Zubut ta mik'e "wa? Kai baka gajiya? A gidan mutanen? To bazan iya ba"
Dariya ya saki zai magana aka turo kofan ,dan sunkuyar da kai yayi yina sosa k'eya .
Dallara masa harara tayi
"Sai ka barta tazo d'akina mu gaisa a tsanake kawani zo ka kanainayeta"
"Mom kin daina sona ashe?"
"Eh d'in tafi bani waje,kinga d'iyata zo muje"
A sullu6e ta taso ta biyota.
Rungumo kafad'arta tayi suka wuce can part dinta
K'ulhuwallahu ta tofe ta dashi k'afa uku
Da li'ilafiy
Tambayoyi kam tasha shi Kala da kala ,wani tasan amsa wani tayi murmushi ta duk'ar da
kai,saita harbitsa mata ingausan larabci da turanci .
Tayi observing d'inta tas tayi, akwai lack of knowledge a tare da ita saidai tanada kunya da
kawaici ,sosai tayiwa julayb sha'awarta...abunda ya Kamata shine a bata training
Don haka dole ta zauna tare da ita kamar yanda bazata bar yaronta ya kuma tafiya ya barta ba
Topah ya kenan,mairo tazo sa'udiyya ba hanyar komowa .......
Oum Aphnan
[3/14, 07:14] Bamalli✌️: *JARABABBEN NAMIJI*
*BONUS PAGE*
*91 - 92*
_Wannan page d'in bonus ne ga kaf masoyan julayb da mairo,ku tayasu murna sunyi abun
kai,duk masoyan mairo da julay kai dama littafin jarababben namiji gaba daya ,in wannan fejin
ta riskeki ki turawa wasu wainda basu samu biya ba su karanta,ko k'wanyarsu ta fad'a din
nasan akwai mak'ek'e masu jiran na kyauta....lolz 09065990265_
Twins d'insu julayb ne suka shigo Asim da Asib daka gansu kaga kamanni ,saidai shi asir
muskiline original asim kuwa warkam sai dai sune 'yan gayun sa'udiyya...kallon farko dole ya
fizgeka dukda komai nasu iri d'ayane saidai banbancin rawar kai
"Hyy mumy we are back" sukaje da gudu suka rungume ta at the same time.tareda kowa yina
rege regen yimata kiss.
Dariya tayi kafin ra riko hannunsu a tare,suka zauna aside to side d'in ta.
"My loves bakuga antynku bane?"
Waiwaigawa sukayi,kafin suka hango ta kan resting chair tana aika masu da sakon murmushi
har ranta take k'aunar wainnan 'yan biyun...saidai ita tambayerta shine laylerh da nihla suma
twins ne ,ko ko gwarne momy tayi? This is difficult to ask
"Wow what a surprise? Antyyy?"
Suka zo da gudu suka fad'a a jikinta
"Heheheyy stop,manyan kawai girma ba hankali, karkuyi muna asara , have nt you see , she's
conceived"(baku ganin tanada cikine?)
"Wayyo dad'i finally zamu samu baby muna zuwa dashi club da masallaci tare,muna sa kaya iri
d'aya komaida shi...sorry anty ina akhy?"
Murmushi tayi ,amma tayi mamakin rudewarsu da murna da sukayi dakuma maganar baby da
taji sunayi
Turo kofar yayi dagashi sai gajeran wando da singlet
"Gani abani matana ,in rarrasheta tayi barci,don nasan yau tasha squeezing kowa ya
damuk'eta"
"Hooopp bros ka ganka kuwa?..."cewar Asir ,kafin duk su biyun su d'auka magana a tare "you
look fresh,giant nice looking handsome,so awesome like your darling wife"
Wani bok'are baya yayi ,cikin bragging (kuri) "Ah to ya san ranku , Yara aure kenan ,kuma kuyi
maza ku k'ara girma ,ku gama makaranta kuzo ku samo mata musha biki...ni kunga na zama
cikakken mutum abunda ya rage mun shine madam ta samu ciki ...oushhh ta sulluro muna fine
fine kids"
Wurgo masa throw pillow tayi "D'an nema zoka fad'amuna kaid'in matarka nada ciki ,to ai ko
baka fad'a ba mun gane ehem ...kuma we must to celebrate"
Zaro ido yayi waje kawai yayi dawara ya kalli mairo data kulle ido da sauri ,sai yanzu ta gane
zancen
Kan ummah raudha yayi da gudu ya rungumeta
"Momy are you serious?...to ya akayi banganeba ...uhhhhh rejoice"
"To yakamata ku gane banbancin tsohon hannu da sabon hannu,ni ku kyaleta ma ta huta
hakanan ,duk ku fita zatayi barci"
"Yawwa mom gara ki fad'a masu asim ku barta ta huta ,baby zo muje kinji" yawani denying
kamar bai fahimci mai take nufi ba
"Wuce bani waje,har kai nike nufi ,anan zata kwana don baa haik'ewa mai yaron ciki ,kaje kayi
mana asara"
"Yawwa fada masa Oumma saidai duk mu tafi mubarta" ganinfa da gaske take yasashi 'daure
fuska,idonsa ya wani kad'a
"Oum da gaske kike, to wa zaki bari da abbey d'in?"
"Aah mai ruwanka, lokacin mu kula da surukanmu ne yanzu oya wuce zo kaimata sallama ka
tafi"ta fada tana hankad'a su asim waje.duk dariya sukayi su ka wuce side d'insu nihal su
k'yank'yasa masu albishir.
Itakuma ta shige wani corridor dazai linking d'in ta da personal kitchen d'in ta,taje ta hau har
had'a mata kayan ni'imarsu na larabawa a d'an k'aramin kofi .
Zallar madarar ruwa ta zuba a kofin amma mai d'umi sai d'an zuma cokali d'aya,ta barbada
garin kanunfari shima cokali ,sai ta d'ebo wani magani ta tsiyaya ta hau bugashi da cokali.
Sarau sarau yayi kamar tsumi yina tashin k'amshin dad'i.
Julayb kam Zuwa yayi kusa da mairo ya zauna ,da sauri tad'an matsa ,mintsinin ta yayi.
Cikin rad'a yace "kiji tausayi na ki taso mu gudu a matse nake wallahi yanzunnan muke tareda
abokina saad yazo muna murna ya bani wani tab nasha ,yanzu haka na fara jina some how
bansaniba ko maganin k'ara sha'awane ya bani ,ya fara dissolving a jikina yanzu"
dariya tai masa tareda gwalo , sannan ta nok'e kafad'arta.ta bude baki zatayi magana kenan
saiga su Layla sun shigo da gudu
"Antyyyyyy ?"
Suka k'wala kiran sunanta kafin duk sukayo kanta zasu fad'a mata a jiki
Wani mugun tsawa ya daka masu kafin yace "kuna ta6ata zan shek'e mutum da mari ,bakuda
hankaline eheee"
K'am sukaja suka tsaya rik'e da hannu .
Ido yayi rau rau zasuyi kuka.
Mom ce tafito da sauri Jin tsawansa ,tana rayawa a ranta "mai hali bayi fasa halinsa"
"To...to.... what's going here ... haven't you hear the fines?" Ta kalli julayb tana
tambayarsa.shikuwa kya6e fuska yayi tareda girgiza kai.
"Ohk shine zaka fanshe haushinka akan auta da jikalle(tana nufin Layla da take jikan yayarta
duk da a Indonesia suke hutune ya kawo ta wajen nihla da kullum suke lik'e da juna in wannan
yazo hutu wannan karon wata karon d'ayan ta tafi k'asar d'ayar)
To ba wanda zanbaka fuska ka wulakanta mun inama laifin sunzo tayaku celebration...kinji
maryerm taso muje"
Ta jawo hannunta suka wuce hanyar corridor d'in
Buga kansa a lallausan cushion d'in yayi "Ohhhhh shit mum zata k'ure mun maleji"
Dariya suka saki kafin Layla tace "uncle sorryyyy"
Suka k'alk'ala waje a guje.
Biyosu yayi da gudu yina ciccillo masu throw pillows , bam suka 6amo k'ofar.
Dawowa yayi ya samu waje ya rafka tagumi d'insa tana jan ruwa yina dad'a
kumbura...zabura ya shigayi abu na tsunguninsa.
"Ai wallahi bazan yarda ba ,bara nasan abunda zanyi" ya mik'e ya nufi corridor d'in da yaga sun
shiga ita da umman.
Oum Aphnan✍️
[3/14, 07:14] Bamalli✌️: *JARABABBEN NAMIJI*
*93 - 94*
A can d'akin kuwa oum tasa mairo tayi ta shanye maganin da ta had'a mata
"Daughter from now a kowanne dare kina shan wannan had'in da nayi maki ,har zuwa cikin ki
yayi k'wari for at least 3 months, inba wannan ba,zuma ma da ruwan zafi kad'ai ya isah banda
inserting unnecessary abubuwa da ka iya janyo maki matsala kin jini ko?"
A kunyace ta gyad'a mata Kai.
Yanzu bara in d'akko maki kayan had'in ,ki adanasu kafin nan sai in aiki su nihal su d'auko maki
night dress d'inki.keda had'uwa da julayb sai kun tare a gidanku"
Jinjina kai tayi kafin tace "Nagode ummah" amma ranta na mata rawa,sai mun tare a gidanmu?
Bayan gidan da muke dashi a lagos?... can't understand.
Tana bada baya julayb na shigowa
Yina zuwa ya sureta ,ya d'aga cak kamar 'yar tsana
"Zaki sani ne yau,kina sane ina jiranki ,kinsan condition d'ina amma had'uwa da 'yan gidan nan
ya koya maki rashin tausayi na ko?"
Cuno baki tayi "ni ka saukeni ko in kira ummah"
"To saime ? Mutum da matarsa a hau yi maka seizing kamar wanda yayi laifi? Kita kiranta"
Haka har suka kai bakin k'ofa,hannu tasa ta Ri'ke k'ofan
"Habawa d'an arziki shirin albarka...kayi hak'uri kar ka jamun abun kunya gidan surukai...kaji
d'an kirki na?" Ta fada cikin kalailaya murya , kamar wacce take rarrashin babyn da akeso yayi
barci
"Nak'i wayon saki mutafi"
"Kwalla Kiran sunan mumy tayi cikin sigar wasa bata san muryarta zaiyi k'ara ba" aikuwa sai ga
mum ta dawo da sauri tana Kiran "Na'am ya akayine 'yar albarka?"
Kawai sai gashi tayi kici6is dasu a bakin k'ofa
"Kai lafiya cikata mana"
Sauketa yayi a hankali kamar wanda ya tallafo k'wai kar ya fashe
"Umma plz ki barta tazo muje ,wallahi nagaji da yawane , massage kawai zatai mun ta
dawo...just few minutes"
"Hmmm massage? Lallai julayb ni kake,kallo kana fad'amun zakaje da matarka taima
tausa?...yau ka fara dawo wa daga tafiya eheee?....to amma tunda kun nuna mun k'ok'on usuli
,ja matarka ku tafi" ta fad'a tana tafa hannu.
Fyallawa da gudu mairo tayi ciki "Oumma ba ruwana,ni na fi sonki a wajenki zan kwana"
"Kajimun yaran zamani,ni zaku had'awa plan ? Sarai nasan kin fison kwana da mijinki zo ku
wuce allah bamu lafiya"
"Kinji ummah d'in nan ku haka akayi maku?" Ya fad'a cikin k'unk'unai
"Me kace?"
Sosa k'eya yayi "momy i just said thank you" ya wuce yaje ya janyo hannunta ,aikuwa zugwui
zugwui tabi bayansa suka fita
"Hmmm i love this couples allah ya k'ara masu zaman lafiya amin"
*****
Washegari wani babban Asibitin dake garin suka tafi shi da ita.
Serum test akayi masu anan aka tabbatar da shigar ciki na sati biyu