L UU LUU BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS BY HUGUMA ZAFAFA.txt

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  Tknovels

Chapter   77 / 99

228K to 231K   out of 294.4K words

Sanda motar ta miqa saman kwalta,wani shuru mars hayaniya ya wanzu a motar,sanda system dinsa ta daidaita ya kuma shiga bangaren saqonnin,sai ya motsa labbansa da wata irin nutsuwa data zame masa dabi'a

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)


"Ban karbi aurenki don ina hada rayuwata da taki ba....ban aureki kuma don na murqusheki ba......baki zama cikin lissafina ba tun daga farkonsa har qarshensa......ki kwantar da hankalinki,idan kin zabi tafiya ba tare da rikici ba.....zan zareki cikin lissafina cikin sauqi kamar bamu taba haduwa ba,idan komai ya daidaita,zan barki kamar yadda na sameki.....amma kuma daga yau....sunan da kike dauke dashi.....da sunan da zaki ci gaba da dauka zuwa wani lokaci duka ba naki kadai bane.......bana buqatar soyayya domin na kare mutuncin aure na da sunana.....wata kariya ce ta gajeran lokaci". Maganarsa ta gilma sosai cikin kanta,ba abinda kuma ta sake bude mata sai linking da tayi da maganar mammina.

Kalamansa suna sake bata tabbacin auren yarjejeniya ne.....saidai wasu alamu suna neman qaryata mata hakan. Yadda yake magana da ita cikin kwanciyar hankalinsa ya sanyata daga idanu,saidai bata iya kallon qwayar idanunsa ba.

"Kada ka rudi kanka,ban nemi shiga cikin lissafinka ba,kuma bazan tsaya jiran a zareni ba.....nima nasan inda zan tsaya......kamar yadda nasan lokacin da zan fice" Ta furta cikin tsiwar da takejin zataso kallon qwayar idanunsa ta masa ita kai tsaye.

Zare idanunsa yayi daga system din sanda ya bude wani email na manager din kamfanin turarensa dake Ethiopia wanda baima kai ga karantawa ba. Idanu ya zuba mata sosai,har sai dataji kallon har bargonta,sai da taji kamar ba wani sauran space daya rage mata da zata iya cikakken motsi. A wannan yanayin kuma,ya sake matsowa dab da ita.....ba kuma don ya samu kusanci da ita ba.....don sai ya ajiye mata nauyin maganar sosai a qirjinta.

"Qaddarar wasu tana zuwa musu ne daidai da yadda sukayi sakaci da rayuwarsu......daidai da yadda basu iya tabukawa rayuwarsu komai sai abinda xaren tunanin wasu ya qulla a kansu......da zaki dan sanya haquri kadan na zuwa wani lokaci zamu gani......kina cikin wadanda qaddara take basu zabi?,ko kuma qaddarar ce take zabarsu......duk da banajin ke kina cikin wadanda take bawa zabin.....don inda tana baki zabi da baki kasance a wannan bigiren ba gimbiya akhnan" Yana kaiwa qashe ya koma da baya a nutse yana relaxing bayansa jikin fuskar kujerar yana maida idanunsa ga email din,saidai ko daya fara karantawa har yakai qarshe baiji ya fahimci komai ba.

Ya zuqo qamshin turarenta sosai a hancinsa wanda yaci gaba da kaiwa da kawowa tsakanin kwanyarsa da hancin nasa. Yadan lumshe idanu kadan yana mamakin yadda zuciyarsa ke bugawa sosai,bugawar da baisan dalilinta ba.

Daidai sanda taja nata numfashin d qyar tana daidaitashi itama. Qarin taku daya da yayi a tsakaninsu sai taji kamar ya zuqe iskar motar gaba daya,kamar ya tare mata duk wani sarari. Wani abu taji yana sauka a gabbanta sanda ta shaqi iska sosai wadda ke cakude da fitinannen tutarensa.

Ya dauki wasu sakanni kafin ya bude idanunsa a hankali a hankali,fararen idanun da suka kada kadan suka kuma sauya launi,ya saukesu kawai saman saqon,wanda sunan da abbakar yayi highlight akai shine abinda ya fara jan hankalinsa.

*_prince khadeeja muhammad hammud of agadez_* kaman zai daga idanunsa ya kalleta sai kuma ya fasa,ya maido saqon farko yana duban abinda ya qunsa.

Neman iri ne na turaren da yasan shi kadai ya mallaki irinsa,da kuma tayin kudade ga kamfaninsa,da kuma bada damar yiwa turaren dukka price din da sukaga dama muddin zai samu.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


*BOOK 02///PAGE 109*



Cikin wani yanayi da salo na kallon mutum ya saci kallonta kadan. Fuskar nan a hade cikin miskilanci,wanda ya tabbatar da cewa tana jin wannan izzar ne a ranta,tana jin kamar an takura mata aurenshi,auren da baya nufin komai dashi a gurinsa,auren da inda tasan haqiqanin me yake cikinsa tabbas da zatayi gudu ne saboda rayuwarta......quruciya ne?ko rashin dabara ke damunta.

Ya sake saukar da idanunsa kadan,saidai still ita yake kalla,yadda take basarwa saika rantse da Allah ba ita ke neman turaren dake jikinsa a yanzu haka ruwa a jallo ba,tana nema......amma batasan wa take nema ba. Ya janye idanunsa kadan wani boyayyen murmushi yana subuce masa,sannan ya fara maidawa abbakar amsar da yake buqatar su tura mata.

_Akwai qamshin da ba'a qerashi don kasuwa ba,ba kowa ke dacewa dashi ba,wasu suna ganinsa abu ne me sauqi,amma gaskiyar itace qamshi ne dake neman wanda zai zauna dashi,idan ya dace dake zaki sake jinmu ba tare da kin nema ba_

_sashen gudanarwa_

Turawa abbakar yayi,ya kuma bashi umarnin ya turashi kai tsaye kamar yadda ya tura masa yanzu yanzu. Ya sake dora masa da cewa idan sun sake magana akai kafin ya amsa musu ya fara shaida musu,kada ya yarda ya daga kira,musayar saqonni kawai tsakaninsu.

Yana kaiwa nan din ya soma shutting down system din da rufe duk wani guri da yasan ya shiga. Haka kawai yakejin bashi da energy din yin komai,ya xubawa system din idanu yana kallonta sanda take kulle kowanne sashe da kanta da kanta kamar yadda ya budeta daya bayan daya a dazun,daidai sannan wani sassanyan ring tone ya kada.

Kadan ta motsa,tana yamutsa fuskarta. Ta sanya hannunta a jaka tana ciro wayar data katse mata tunani da lissafin ME YASA YA BUDE MATA MOTA?,ME YASA YA HANA TARIN HADIMANTA MAZA BUDE MATA QOFAR?. Wataqila wani salon makircinne,ko ba komai ko banza kuma mutane da yawa dake gurin zasu tayashi shaida gurin sultane kan yana bata kulawa,ta yadda ko yaya tayi wani abun laifin zai zama nata ita kadai? Ta yiwa kanta tambaya.

Shehnaz ce take kiranta,kamar kada ta daga amma kuma darajarsu tafi gaban taqi daga wayarsu.

"Hello" Ta furta da wani sauti daya sauka a hankali.....wani sauti dake cike da yauqi.....gayu da kuma sarauta. Idanunsa ya maida a hankali ya lumshe,shurun da tayi yana zarcewa gaba daya ilahirin motar,kafin a hankali sautin muryarta da yake da wani taushi da tsari ya sake ratsa shurun.

"Dites-moi votre excuse directement,ne perdez pas mon temps(Ki fadi uzurinki kai tsaye,karki batamin lokaci)". Wani dariyan shaqiyanci shehnaz ta saki,a hankali cikin nishadi tace.

"Me zai hana ki magana da yaren abzinanci ko hausa?" Ta maida mata da yaren France. Qaramin tsaki taja,itama dai cikin harshen France tace mata

"Voilà ce que je veux être ahjourdh'hui(haka na zabi na zama yau)".

"Oh.....ba laifi ai,amma akhnan......wai idona kemin gizo,ko zallar munafurcin hadimai da bayin gidan nan ne?,naga kamar a mota daya kuka fita da sheikh muhammad dinmu.....yawon amarci ne ko shan iska?" Ta fada tana qunshe dariya. Dariyar data qular da akhnan sosai,wato har ya zama wani topic na tattaunawa fitarsu tare dashi a yau?,ta diga masa ta goga masa wata daraja tata kenan da har aka fara maganan?.

"Zan shayar daku mamaki.....baku kadai ba harshi din. Na nema mu fita ne don ya ganewa kansa da kansa tazarar dake tsakaninmu......inaso ya kunyata gaban kowa da kowa a sanda zai kasa magana cikin harshen qasarmu.....kuma na shirya nayita yi masa haka har sai da kansa ya banbance matsayina da nasa......shehnaz,bashi da abinda zai ja zuciyata dashi,kyanshi baya rudata baya kuma burgeni sam" Ta qarasa maganan da harshen faransanci tana daga idanunta a hankali ta zube saman fuskarsa kamar meson tabbatar da managarta ta qarshe da gaske ta fadeta ko kawai fita tayi a abakinta don ta gamsar da shehnaz.

"Biftu?,tozarci fa kenan?"

"Yakai kalar tozarcin da yayimin na sakani amsa sunan matar malam?.....ku zuba ido kawai labari zai dawo muku"

"Idan kuma labarin ya sauya salo fa kinga ai shikenan ko?". Wani tsaki akhnan taja sosai kamar ta tsinke harshenta.

" Ai sai kiyita yi.....idan na yar ai zaki iya dauka kem halal ne" Daga haka saita yanke kiran. Haka kawai ta sake samun kanta da daga idanunta ta zube a kansa,saidai dukka hankalinsa yana kan wayarsa yana dannawa,ta janye duban nata daga kanta tana jan tsaki mara sauti.

Rashin sani ai masifa ne,a zage mutum tas amma bai fahimci ma cewa dashi ake ba?. Ko ita da ba rainon english ba amma tana ji tana kuma maidawa sosai,iya wannan kawai ya isa ya gaya mata hausa ce kawai a bakinsa,itama bata fita yadda ya kamata,to wai shi menene yarensa?. Amsar data sanyata sake waiwayowa tana dubansa. Kyakkyawar fuskar nan cikin nutsuwa take ci gaba da kallon screen din wayarsa,ganin ya motsa saita kauda idanunta da hanzari,tana gudun kada ya ganta irin na wancan lokaci yayi alfahari ko ya dauka tana kallonsa ne da wani abu.

Wani irin murmushi kawai yake saukewa qasan ransa,zuciyarsa tana sake jaddada girman kai da stubbornness irin nata.

Ya tura saqon qarshe wa beeno wanda ya tura masa duk details na gurin taron,awannin da zaa kwashe a gurin,su waye suka halarta,dame dame za'a gabatar,dama tabbacin cikakken tsaro da gurin ya samu,wanda shi ya bada umarni a tabbatar da hakan a gurin.

Daidai sanda ya sauke wayar daga idanunsa motocinsu suka iso bakin gurin. Cikin girmamawa da mutuntawa aka wangale musu babbar qofar shiga gurin.

Hannu ta sanya zata bude qofar don ta qagauta ta sauka.....ta matsu a fara gudanar da taron don ta samu mission dinta ya fara cika,amma sai taji kawai an danna locked dukka qofofin motar suka maida kansu suka kulle.

Da sauri ta waiwayo tana dubanshi cike da mamaki,shima ita yake kalla,ya zuba mata wadannan idanun nasa masu tsananin kwarjini da sanya mutum ya rusuna komai taurin kanshi. Ta dauka zata iya ci gaba da kallonsa,amma sai taji ta kasa,dole ta tattare tsiwar data taso mata ta maidata cikinta,sannan ta dauke idanunta a hankali tana maidawa farfajiyar gurin.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)


Wani abu ta hadiye,tana jin ba zata karya izzarta.....ba zata karya martabartabarta gurin tambayarsa dalilin saka lock a qofofin,gashi alamu suna nuns dukka guard din da dogarai da suka musu rakiya sunyi gaba abinsu.

A hankali ya zare idonsa daga kanta yana sake ganin wannan izzar a tattare da ita. Baisan me yasa takejin kamar tafi dukka sauran matan duniya ba.....baisan meye nata daya banbanta da sauran mata ba daya sanya takejin izza har haka ba,sai ya maida idanunsa ya lumshe yana saka hannunsa ta gefe yadan kwantar da kujerar kadan,abinda zai bashi daman yin relaxing sosai cikin nutsuwa.

A mamakance take kallonshi da gefan idanu,yadda yayi relax cikin kwanciyar hankali,hasalima earpiece taga ya jawo ya sanya a kunnensa,sannan ya maida idanunsa ya lumshe yana sauraren karatun qur'ani cikin suratu taubah.

"Kai" Ta fada cikin ranta tsananin mamaki yana cinta. Me malamin nan yake nufi?,fitar ce ba zatayi ba kwata kwata?,ko kuma sanda yakeso?,sai sanda yaga dama?,sai sanda ya bata izini?. Magana yakeso tayi?,idan haka ne kuwa ya makara.

Babu ta yadda za'ayi ta nema ALFARMA daga gareshi,don kuwa bashi da ita,shi kansa alfarmar tata yakeci.

Shuru yaci gaba da wanzuwa cikin motar,saboda dukka gilasan motar a rufe suke ruf. Mintina suka ci gaba da harbawa suns niyyar hada awa guda. Zuwa sannan zuciyarta ta gama tunzura,ranta ya gama baci,ta daga idanunta zuwa ga glass din gaban motar,sai taga qananun yayyafi sun fara sauka,abinda ya sake tunzurata kenan,har taji kamar zata fashe,sai kawai ta fidda wayarta ta soma kiran shehnaz kai tsaya.

Bugu biyu aka dauka,cikin muryarta da ko fushi takeyi ba zakaji ta kaurara ko ta canza salo maras dadi ba.

"Shehnaz kinga abinda mutumin nan yayimin?,ya kulleni a mota yana jiran saina karya girmana na masa magana?".

"To meye a ciki biftu,karyowa miji faduwa ne ko asara ce?" Muryar aisa ta mamayi kunnenta a madadin shehnaz data kira. Sosai akhnan taji ta hasala

"Kinsan abinda yakeyi ne yanzu aisa?,ya kulleni a mota kamar wata yarinyarshi?,wai ba'a gayawa malamin nan wadda ya aura bane?" Maganar ta tsaya a zuciyar aisa,ta kuma sauka a kunnen haisam daya saki boyayyen murmushi. WANNAN IZZAR.....WANNAN GIRMAN KA?. Ya fada can qasan zuciyarsa.

"Akhnan.....miji ne wannan.....ba ordinary malami ba akhnan......"

"Wai me yasa ba zaki gane ba aisa?,tozartani yakeson yayi aisa......yana kwance abinsa yana lumshe idanu kaman ban wanzu a gurin ba". Tana iya jin dariyar shehnaz ta cikin wayar,wadda ita abun ma dadi yayi mata. Zataso ace tana gurin,ta tabbatar yadda yanayinsan nan yake cike da miskilanci idan baiso ba da aji abun zai dadin kalla. Shi qasaita ita izza.

"Nice scene" Ta fadi daga kunnen aisa har sai da aisan ta juya ta tureta.

"Akhnan,ki tambayeshi me yasa yayi hakan,ta yuwu akwai dalili...."

"Bazan tambayeshi ba Allah aisa......bazan bashi wannan nasarar ba" Sai ta gintse wayar kawai don ta fuskanci ita aisa ma sam bata fahimtar abinda take fada......kamar aisa haisam ta sani,dukkansu ma ba wanda yake ta tata,kowa kaman goyon bayansa yake.

Wani miskilin murmushi na qasan zuciya ya saki,tana magana hankalinta kwance bisa dukkanin tsammanin baya jin yaren France,hakan ma yayi masa,kuma zaici gaba da barinta cikin duhunta.

Motsawa yayi a nutse yana duba kiran beeno.

"Obbo.....gurin yayi clear,komai yana a daidai,nan da mintuna talatin taron zai iya tashi"

"Okay" Kawai ya furta ta hanyar motsa kyawawan labbansa,muryarsa can qasa da wani irin zurfi da nutsuwa.

Da cikakken kuzarinsa ya miqe yana zama sosai,yadda ya zauna cikin zafin nama yaja hankalinta,amma saitaqi waiwayawa ta dubeshi,saboda idanunta dake cike taf da hawaye. A wannan lokaci ita kanta ta yabawa kanta qoqarin da tayi na riqe kukanta. Bata qaunar abinda zai sanya aga faduwarta ko kasawarta,wannan dalilin ya sanya bata taba yarda wani yasan rauninta bare ya cusguna mata har yaga hawayenta.

Ya riga ya tsada yadda zai fara mata karatun da zata san rayuwarta a yanzun ba daidai yake data baya ba. Ya sani,wani aiki ne da dole sai ya yishi,a kafiyarta da taurin kanta zai iya zame masa me wahalar gaske.....amma ya shirya fahimtar da ita da dorata bisa tsarin tarbiyya. Ya kamata tasan cewa zuwa yanzu tana da iyaka,ba komai ne zataci gaba da yinsa yadda takeso ba da kuma yadda ta tsara....akwai umarni ko hani daga wani da zai iya zuwa mata kowanne lokaci,dole ta koyi saurara,ta koyi bin tsarin da zai ci gaba da zaba mata.....zata fahimci kuma ba duk inda takeso zata dinga tafiya ba......saidai izininsa da amincewarsa. Dole ya riqe martabar igiyar aurensa,koda auren kwana daya ne tal!.


*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira 1,000 kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


*BOOK 02///PAGE 110*



A nutse ya bude idanun nasa,sannan a hankali ya miqa hannunsa ya cire lock din.

Sai daya zura qafafunsa dake saye cikin tsadajjen royal half shoe din qafarsa sannan ya furta kalaman a jejjere cikin izza.

"Idan zaki shiga ki shiga yanzu,lokutana masu muhimmanci ne,bazan sake tsayawa ba" Sai ya qarasa fita waje yana tsaiwa saman qafafunsa gami da barin qofofin motar duka a bude.

A nutse yake gyara rigar jikinsa,yana kuma qarewa gurin kallo. Da a haka takeso su shiga?,sanda gurin yake a yamutse da mutane?,daidai mintunan data bayar don isowarsu gurin?. A lokacin ya tabbatar kowa yana qagauce da ya ganta,tunda wani abune da bata taba yi ba. Cikin kwanaki uku ya binciki komai daya shafeta,mu'amalarta da mutanenta dama komai. Yaji wani abu kadan daya burgeshi a halayenta,duk da ita bada wannan manufar tayi ba BATA DA YARDA SAM bata kuma yarda da abinda zai taba izzarta. Abune me kyau gurin mace,ki zama me izza.....ki zama maras yadda amma akan MAZA KAWAI. Dabi'a ce ta jin isa daga jininta,amma kuma siffa ce me kyau ba tare da ita tasan da hakan ba.

Kusan wannan shine karo na farko ma da zata bayyana a taron jama'a irin haka. Ba kowa bane yasan fuskar princess akhnan din ba,ya tabbatar akwai dimbin masu jiran ganin bayyanuwar fuskarta,abinda idan ya tuna hakanan sai yaji kamar su

77 / 99