Rawanin Zalinci Book 2 Complete Hausa Novels By Fatima Zahra Musa

Author :  Fatima Zahra Musa Category :  Tknovels

Chapter   78 / 118

231K to 234K   out of 352.1K words

ta yi mashi gizo, ya rinƙa jin kamar ya taɓa yin rayuwa a wata duniya ta daban, to mu je dai zuwa, lokacin zai warware mana komai.

"Hamma in tafi ne?". Ta faɗa kallonta a ƙasa, tana son ɗago idanu ta saci kallonsa dan taga me yake yi, amma ta kasa gudun kada ta tsinci yana kallonta su haɗa idanu.

Shiru shiru bai amsa mata ba, sai dai kallonta da yake ta yi yana jin ƙwaƙwalwarsa tana wani irin juyawa tamkar agogo.

One step ta yi baya kafin ta ɗan ɗago da kallonta a kansa. Ai a fujaje ta sake yin ƙasa da kai ganin ita yake kallo sun kalli juna ido cikin ido. Shi dai ba komai yasa ya ƙasa dai'na kallonta ba face wannan tunani da yake ji na daban idan yana kallonta, abin yana bashi mamaki da yasa baya son kawar da kallonsa daga kanta.

Ita kuma sarkin tsoro, ganin yana ta kalleta yana kalle kayansa, e mana kayansa tun da dai aure ya ɗauru in ji ni princess Teema taku ta amana..........😂

Yana ta kalle kayansa yasa ta tsorata, nan take kirjinta ya fara dukan uku uku, a tunaninta wani abin zai yi mata, shege shaiɗan da kuma munafukar zuciya mai sake sake sai ta fara saka mata cewa ai dama jama'a sun ce maki shi maye ne, ba ga shi yanzu yana kalle maki jiki yana neman ta in da zai fara cinye maki tsokar jiki idan ya samu dama ba.

Ai kuwa wani irin ihu ta zunduma wanda bata san ta yi ba, kamar mai wani motsi a kai, kawai zuciya ya kai ta zai barota, wlh yarinyar nan ta zaci a cikin zuciyarta ta kurma wannan ihu, bata san a fili ta yo shi ba.

Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin ihun nata, kamar wadda aka yi wa allura ko wadda aka kwalawa guduma a kai, ta wani kware baki ta zundumota, anya ma lafiya take kuwa?. Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.

Ita kuwa ihun da ta yi ya yi dai'dai da ta ɗago kai ta kallesa, ai kuwa hakan ya yi dai'dai da idanun da ya zaro dan mamakin abin da ta yi.

Habawa tana haɗa ido da shi taga ya zaro nasa me zata yi? Ai sai ta zunduma a guje ta yi wani irin juyawa da karfi ta nufi hanyar gida, kafa me na ci ban baka ba? Ai sai gida.

Bata ma san lokacin da takalmar kafafunta suka cire ba, ita dai gida kawai take burin ta shiga.

Sai dai bata kai ga isa gidan ba ta faɗi ƙasa tare da kurma ihu mai sautin gaske.

Yana dai tsaye yana kallon ikon god da wannan yarinya, yana gani ta watsa a guje bai yi wani motsi ba, sai da ya ga ta faɗi ƙasa ta kuma zunduma wani ihun ne ya ɗan lumshe idanunsa tare da jan dogon numfashi. Ni kuwa nace har yanzu dai wannan fadanci ta jinin sarautar tana nan bata rabu da shi ba.

A hankali ya fara takawa ya tinkari in da take, a gabanta ya tsugunna dan yaga me yasameta ta faɗi take yin wannan ihu kuma.

Jini ne yake zuba daga kafarta ta dama, da sauri ya kai hannu ya riƙo kafar tata, jini sosai yake zuba, sam bai iya gane me ya sameta a wajen ba, saboda jinin ya wanke wajen, shin yankace ko dai wani abin ne ya soketa har ya fasa fatar kafar haka? Jini sosai ya rufe wajen ciwo baka iya gani, ga jinin nata jajir da shi.

Dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, ta datse idanu gam, ba abin da zaka gani face hawaye dake bin ƙuncinta kamar ruwa ya faso hanya. Da alama bata ma san yana kanta ba.

Ɗan miƙewa ya yi, ya duƙa ya ɗauketa cak suka nufi cikin gida. Bappa dai yana ta ƙoƙarin gyara wajen da zasu yi bukkar kusa da ɗakinsu Mahnoor ɗin ta gefe haka.

Gabaɗaya kunya ya ji tamkar ƙasa ta tsage ya shiga ciki na ganin bappa a tsakar gidan, sai ya ji dama bai ɗauketa ba, wato shi fa wlh kunyar a jininsa take, ba wai tsiya bace kamar yadda Jawad yake tsokanarsa da shi, ai kunga ko zai ji kunyar kowa ban da Yah Jawad, so shiyasa Jawad ɗin yake ganin kamar iyashege ne ba kunya ba dan shi baya nuna mashi yana jin kunyarsa.

Ko kallon in da bappan yake yaki ya yi, yadda kuka san ya gefar da ita a ƙasa haka yake ji, sam bai yi tunanin zai isko bappan a tsakar gidan ba, da Allah ba zai ɗaukota ba sai dai ya taimaka mata ta miƙe ta taka da kafafunta su dawo.

Shi fa wlh ko da Mahreen baya son jerawa mutanen gari su gansu bare kuma bappa, kunya hakan take bashi. Allah sarki yaron Mommarsa mai alkunya.........😂

Saman wata dutse da suke zama su goge kafa idan sun fito daga wanka ya zaunar da ita, sam ɗan tahaliƙin nan yaki yarda ya juyo in da bappa yake, yana ganin kamar idan ya juyo zasu haɗa idanu ne.

Shi kansa bappa abin ya yi matuƙar bashi kunya yadda ya ɗaukota ya keta wajen nan jama'a suna wucewa ya shigo da ita, amma da yake yana kaunarta sosai sai ya danne kunyar a ruɗe ya fara tambayarsu meyafaru kafarta ke jini?.

A dai'dai lokacin Mahreen ta fito daga cikin ɗaki tana zabga uban hamma kamar zata ci babu, da alama da yunwa ta taso daga wannan barci.

Ganin abin dake faruwa yasa ta yi saurin ƙarisowa wajen tana tambayar hamman nata me ya faru?.

Bai kulasu ba ya yunƙura zai miƙe ya bar wajen, cikin jin raɗaɗin ciwo ta riƙo wuyarsa yadda ta saƙalosa lokacin da ya ɗauketa haɗe da faɗin zafi kafarta yake yi mata, su taimaka mata su cire mata zafin.

Shi kuwa kunyar bappa yasa zai bar wajen dama, baya son su haɗa ido, ba wai dan baya son taimaka mata ko bai ji tausayinta ba, aa, ko ɗaya, hasali ma ya so ya wanke mata kafar, ya wanke jinin sai ya duba menene ya ji mata ciwo a wajen.

Bappa ya lura da kunyarsa yasa Jaish ɗin yake son gudu ya bar wajen, bai san cewa shi kansa abin ya bashi kunya ba, in gaya maku Mahreen ce kawai bata ji komai ba, dan kun san ita kunya ya yi gabas ne ita kuma ta yi yamma, sam basu da haɗi.

Ganin yadda ta riƙe mashi wuya gam tana kuka haɗe da magiyar a cire mata zafin ne yasa ya koma ya tsugunna a gaban nata, a hankali ya kai hannunsa ya fara ƙoƙarin cire hannunta da ta sarkafe wuyarsa da shi.

Hakan yasa bappa ya ji ba zai iya ganinsu ba, sai kawai ya fice daga gidan ya basu waje, ya nufi gonarsa na su tomatoes dake kusa da gidan, dan ya je ha fara saro itacen da zai haɗa masu bukka da shi kafin su gama abin da suke yi.

Ganin bappan ya fice ya basu waje ne yasa sai ya fasa cire hannun nata daga wuyarsa, dama wai zai cire hannun nata ne dan ya samu ya bar wajen, yana son taimaka mata amma idan bappa na wajen ba zai yi ba, da tafiyarsa zai yi abinsa, amma tun da bappan baya nan sai ya kai hannu ya kamo kafar tata.

A gabansu Mahreen ta tsugunna, idanu jajir da su saboda barci, ga yunwa, sai daka hamma take yi, kamar zata yi kuka ta kai hannu ta saƙalo wuyarsa saman hannun Mahnoor dake wuyar tasa, lallausan kumatunsa ta shafa da ɗayar hannun nata, cikin fuskar tausayi ta ce. "Hamma meyasami Adda Mahnoor ɗita?".

Dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, hannunsa ɗaya ya kai ya shafi face dinta kafin ya yi mata alama da ba komai, sannan ya yi mata alamar ta kawo mashi ruwa.

Ba shakka akwai shaƙuwa sosai a tsakanin shi da Mahreen, shaƙu kam mai karfi ma.

Da sauri ta miƙe ta nufi cikin kitchen, ruwa ta ɗebo a cikin butar karfe irin na mutanen da ɗin nan ta dawo da shi in da suke.

A gabansu ta tsugunna ta miƙa mashi. Karɓa ya yi, hannunsa yasa a saman wajen ciwon ya fara zuba ruwan yana wanke mata jinin.

Sosai ta kara tsananta kukan nata, saboda ruwan sanyi da ya taɓa ciwon, sai ya kara azabar zafi.

Yana wankewa wata jinin tana ɓulɓula, sai dai kuma da ya wanke ya gano babbar ciwo ta ji sosai, wani kwalba ne ya fasa mata fatar har nama, ya yanketa sosai da sosai.

A hankali wani irin tsananin tausayinta ya ratsa zuciyarsa sosai, tsumma mai tsabta ya buƙaci Mahreen da ta kawo mashi.

Ɗaure mata kafar ya yi ko zai samu jinin ya ɗan tsagaita su saka magani, dan shi ma a yanzu ya san magunguna da dama na gargajiya.

Miƙewa ya yi ya ɗauketa izuwa ɗakin bappa, da sauri Mahreen ta rufa masu baya. Saman gado ya zaunar da ita, sai a lokacin ta sakar mashi wuyarsa, dan ta ɗan ji sassaucin zogin.

Juyawa ya yi zai fita sai kuma kamar wanda aka cewa ya juyo, yana jiyowa suka haɗa idanun, dan jin zai fice yasa ta yi saurin waro idanu dan tagansa kafin ya fita.

Yana haɗa idanu da ita tunanin yadda ta tashi hankalinta a ɗazun da kaska ta hau hannunsa ya faɗo mashi, ya ji daɗi sosai yadda ta ruɗe ta kuma taimaka mashi, ta nuna tsantsar tausayinta a gare shi, tuna hakan yasa ya juyo ya dawo, ya fasa ficewa.

Da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mamakin me ya dawo da shi kuma?.

Sai surutu Mahreen take zuba masu babu wanda yake iya jin me take faɗa, dan kuwa duk sun afka duniyar tunani.

A kusa da ita ya zauna yana kai hannu ya riƙo kafar tata, mamaki ne ya kusa sanyata suma, bata taɓa zaton hakan ba. Ita dai Mahreen sai tambayar ina Nenne take take yi, ba wanda ya bata amsa, ni kuwa princess Teema na ce Nenne ai ta saki kanta da kanta, bappa dai ba ruwan, ta haɗa kaya sai gidan Arɗo abinta, dan dai bappa namu na gargajiya kam bai sake ta ba, kuma bai ce ta tafi gidan Arɗo ba, rashin albarka ne irin tata da rashin ilimin sanin darajar miji, kai ita bama tasan me ake nufi da miji ba, kan fanko ne.

Alama ya yi mata da hannu a kan har yanzu wajen yana yi mata zafi?. Mamaki ya hanata iya amsawa, ta yi suman zaune, kanta a ƙasa ta kasa iya ɗagowa.

Ya fahimci ita ma kunya ce da ita sosai kamar shi, hakan yasa ya saki kafar tata tare da miƙewa ya nufi waje da nufin ya je ha tsinko magunguna ya zo ya haɗa mata, sam baya son su haɗu da bappa a yau ɗin nan, dan haka yana fitowa ya bi ta baya dan karsu haɗu.

Ai kuwa ya gudu bai tsira ba, dan kuwa bai yi zaton bappa yana wannan gona na su tomatoes ɗin ba, can kuma ya shiga dan ya ciro abin da zai ciro. Yana sanya kai unexpect suka yi ido huɗu, ai wani irin kunyar da ya ji tamkar ya ce ƙasa ta tsage ya shige ciki, sai ya ji kamar ya juya ya fasa shiga, gabaɗaya sai ya ji ya rasa sukuninsa.

Shi kam bappan da yake yasan halin kayansa sai ya kawar da kansa kamar bai gansa ba, dan baya son ganin ɗan nasa a cikin takura, bayan son yaga ya takure kansa saboda kunya, sai ya matsa can cikin gonar ma ya bashi damar shiga ya yi abin da zai yi ba tare da ya takura kansa ba.

Ya fahimci sarai bappa ya gano yana tsananin jin kunyarsa, ya fahimci da gangan ya wuce can cikin gonar ya bashi waje, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ƙarisawa wajen bishiyar zogale, dan ganyenta yana tallafawa wajen tsayar da jini, idan jinin ya yawaita over wajen zuba to yana ragesa, idan kuma ba dayawa sosai bane yana ɗauketa gabaɗaya.

Bari na baku magunguna biyu zuwa uku dangane da zogale domin mu karu da juna kafin na wuce. Ina masu ulcer? To zogale takuce, ku matso kusa. Komai karfin ulcerki idan kika samu furen zogale, ki gyarata ki wanketa tsab, sannan ki zuba a tukunya, ki sanya ruwa kada ya wuce litter ɗaya, sai ki ɗaurata saman wuta, idan ta tafasa sosai, ki sauƙeta ki tace, sai ki zuba zuma a cikin ruwan ki sake ɗaurata a wuta ta tafasa na minti uku zuwa biyar, sai ki sauke, da ɗan ɗuminta zaki rinƙa sha, da izinin Allah zaki rabu da ulcer.

Magani na biyu, ki yi wa ganyenta shanyar inuwa, idan ta bushe ki dakata ta yi laushi sosai, ki samu nonon shanu mai kyau, sai ki rinƙa zuba tea spoon uku na garinta a cikin nonon kina zuba zuma tea spoon biyu, ki garwaya sosai ki sha, wlh yana matuƙar saukarwa da mace ni'ima, yana kuma maganin sanyin ciki sosai.

Na uku, ki rinƙa dafa ganyen zogalen kina tace ruwan, ki zuba zuma ki sha, yana matuƙar wanke jini, yana kashe kwayoyin cutar sanyi na ciki, tana matuƙar saukarwa da mace ni'ima sosai, ki gwada zaki sha mamaki In Sha Allah.

Kina iya dafa ruwan ganyen, ki zuba a cikin buta kina tsarki da shi, yana matuƙar gyara wajen sosai, yana kashe kwayoyin cuta, sannan yana ɗauke duk wani wari. To ya isa haka mu koma kan karatunmu, sai kuma wani lokacin.......... A karshen littafin nan da izinin Allah zan baku wasu sirrika, ina matan da mazansu ke biye biyen matan banza a waje? Ina iyayen da suka fuskanci jarabawa na ƴaƴansu suna shaye shaye da bin matan banza? Ina iyayen da ƴaƴansu basa jin maganarsu? Sun bijire masu basa ji? Ina iyayen da suke fuskantar matsalolin tsakaninsu da ƴan uwan miji? Baki yi masu komai ba su ɗauki karan tsana su ɗaura maki? Ina matan da mazansu suke wahalar da su ba tare da kina da hakkinsu ba? Baki yi wa namiji komai ba kawai ya rinƙa azabtar dake yana cusa maki bakinciki? Ina masu son mallake zuciyar mai gida? To duk ku matso, a karshen littafin nan zan baku wani sirri na musamman, amma ki tabbatar da cewa tsakaninki da Allah kike zaune da kowa, kada ki cutawa kowa, sirri ce ta musamman, magani ne irin ta addinin Musulunci, in dai zaki yi shi yadda yake to da izinin Allah duk wata damuwarki zata warware, zaki samu waraka da yardan Allah, sai dai ina kara haɗaku da Allah da ku zauna da kowa da zuciya ɗaya, domin da ki cuci mutum gara shi ya cuceki, kada ki je Allah ya mallaka maki zuciyar oga kuma ya zamana kina da kishiya ki cuta mata! Ki ji tsoron Allah ki sani akwai mutu, ni dan saboda iyayen da yaransu ke biye biyen mata, da matan da mazansu ke biye biyen matan banza a waje ma yasa zan bada, a dai ji tsoron Allah na faɗa na kara faɗa, wlh duk wadda tasan da kudurin niyar cutar wata ko wani a ranta ya Allah kasa ko zata yi sau miliyan kada bukatarta ta biya ato, babu ruwana, In Sha Allah a karshen littafin nan na yi maku tanadi na musamman, fatana dai Allah ya kaimu da rai da lafiya, ina kaunarku my people's.......💘

STORY 🔥

Sinko dik abin da zai buƙata ya yi, ya dawo cikin gidan.

Kai tsaye bappa room ya nufa, zaune ya iskota ita da Jumma ƴar Inna Rabi, sun yi wa Mahreen wayo sun koreta, sai suka kama hira a kan aurensu, Jumma tana kara bata shawarar ta yarda ta zauna da Jaish, kun san fa ita Jumma ta ɗan waye, dan tana zuwa cikin birni tallar nono, so ta fi Mahnoor wayo nesa ba kusa ba, ta san wasu abubuwan na duniya, sannan bugu da ƙari mamarta malamar addini ce sosai, ta koyar da su daidai gwargwado, so yanzu sai ƙoƙarin wayarwa da Mahnoor kai take yi a kan ta yarda ta zauna da shi zata ji daɗi.

Aikota fa Inna Rabin ta yi a kan ta zo ta kira mata Mahnoor ɗin, dan Innar ma ta samu labarin auren da aka ɗaura wa Mahnoor ɗin, shi ne ta ce ta kira mata ita tana son yin magana da ita. Shi ne da ta zo ta samu ta ji ciwo a kafa sai ta samu waje ta yi zamanta suka kama hira a kan gidan miji, yara sun girma Inna Rabi bata sani ba.

Wani irin tsoro ne ya kama Jumma na ganin yau gata ga Jaish a ɗaki guda, ta kafeshi da idanu tamkar zata cinye shi, shi kuwa da bai san da wata halitta a wajen ba, abin da yake gabansa kawai yake yi, a kusa da ita ya tsugunna tare da kamo kafar tata, cikin nutsuwa yake murje ganyayyakin magungunan da ya tsinko yana sanya mata a ciwon.

Sai washe take faɗa, sai ma da ya sa hannu ya buɗe ciwon nata da kyau zai ɗiga ruwan ganyen zogale da ya murje ya matse, datse idanu ta yi tana kuka a hankali hankali.

Jumma kam tamkar zata sume, abin ya yi matuƙar burgeta yadda yake yi wa matarsa magani cikin nutsuwa da takatsantsan ga tsantsar kula, sai dai kuma a tsorace take, dan har yau har gobe yana ruɗar da ita idan taga kyansa.

Ba ita yake yi wa magani ba, amma it ce jikinta yake kerma.

Bayan ya gama abin da yake yi ya mayar da tsummar ya ɗaure mata kafar, dik da jinin ya tsaya da zuba hakan bai sa ya cire tsummar ya jefar ba, saboda yana son maganin ta nutsa ciki ciwon sosai.

Miƙewa ya yi tare da ɗan ɗaura hannunsa a kanta alamar sannu ya yi mata, daga haka ya nufi waje.

Kamar jira take yi ya fita, yana kurewa ganinsu ta yi maza ta ce. "Amma gaskiya Mahnoor baki da hankali!".

Cikin jin zafin ciwo ta zaro idanu kafin ta ce. "Mekuma na yi na rashin hankali Jumma?".

"Mema baki yi ba! Yanzu dan tsabar rashin hankali da

78 / 118