Rawanin Zalinci Book 2 Complete Hausa Novels By Fatima Zahra Musa

Author :  Fatima Zahra Musa Category :  Tknovels

Chapter   1 / 118

1 to 3K   out of 352.1K words

❤️🤍 RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🤍




𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥





❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/9/2024.....✍️📚🌹




For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.






اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




💘STEP TWO....✍️📚🔥


E__________________1🔥


GIDANSU KHADIJAH 😥💔

Daga Zainab har mamanta an ransa wanda zai kalli ɗan uwansa ya ce ya yi shiru, sun shiga tsananin tashin hankali. Basu ƙara tsorata bama sai da suka kalli baban Zainab ɗin ya dai'na motsi, ya yi tsit alamar rai ya yi halinsa.

Wani irin ihun da Maman Zainab ɗin ta kurma mai sauti sai da yasa Zainab ta tsorita sosai ta miƙe tsaye. Daga wannan ihun da ta kurma bata sake yin kwakkwaran motsi daga in da take ba, kawai ta sulale ƙasa ne, kan ka ce me ta dai'na numfashi, numfashinta ya ɗauke diff alamar ta sume.

Da gudu Zainab da diro ƙasa daga saman gadon, har lokacin kuma jini na cigaba da malala daga cikin babanta, yadda kuka san hanyar ruwa ta fashe, kuma babban abin takaicin ma faɗuwar da ya yi yana murkusoso sai ya kwanto a kan wukar dake cikin nasa, hakan yasa wukar ta kara lumewa a jikinsa, shiyasa jinin ya yawaita sosai, dan ba ƙaramin ciwo ya ji ba, ga shi a tsakiyar cikin nasa ta caka mashi wukar, abin ya munana sosai!!.

Waje Zainab ta nufa domin ta duba Khadija, ta rasa me zata yi wa iyayen nata ne yasa ta bi bayan yar uwarta.

A takaice dai maman Zainab bata tashi farkawa ba sai da ta ɗauki awa uku masu kyau a sume, an zuba ruwa an zuwa ruwa, amma shiru bata farfaɗo ba, daga karshe suka kyaleta suka zubawa sarautar Allah ido.

Lokacin da ta farfaɗo kuwa sai ganin kanta ta yi a wani irin ɗaki mai kama da cell na ƴan'sanda. A hankali ta fara bin saman celling da kallo, idanunta sun kumbura luhu luhu, sun kuma yi jajir kamar jini ne kwance a cikinsu.

Tunanin baban Zainab ne ya faɗo mata a ranta, hakan yasa ta yunƙura zata miƙe da zafinta kuma a ruɗe. Sai dai kash ta kasa iya miƙewar, sakamakon jikinta duk ciwo yake yi mata, gaɓɓanta sunki koda motsawa.

Hakura ta yi ta cigaba da kwanciya a saman tabarman da take ɗin. A hankali ta fara sauko da kallonta da kallon celling da take yi izuwa ƙasa dan taga a ina take a kuma wani hali take! Wasu irin siraran hawayen takaici haɗe da danasani mai girma ne suka fara zirara daga idanunta izuwa saman ƙuncinta.

Kwatsam ba zato ba tsammani tana sauke idanun nata ƙasa sai saman kofar shigowa wanda yake kofa ce ta burglaris, wato kofar cell kenan.

Zaro idanu ta yi a tsorace, jikinta har kerma ya fara yi, cike da mamaki take tunanin ina su Khadija da baban Zainab ɗin? In da take ɗin babu kowa bare ta yi tambaya. Sake yunkurin miƙewa ta yi a karo na biyu, cikin tashin hankali da ruɗani take. Jikinta sai kerma yake yi, idanunta sun cicciko da kwallah sosai ga kuma wasu na zuba.

A wannan karon ma kasa miƙewar ta yi, saboda jikinta duk a mace yake, ga bala'in ciwo da yake yi mata. Tunani ta fara yi a kan me ya kawota cell kuma? Me ta yi?.

Rasa mai bata amsa ta yi, hakan yasa bata gaji ba ta sake yunkurin miƙewa a karo na uku, sai a lokacin ta fahimci cewa kafarta na ɗaure da wani sarka irin na ɗaure manyan ɓarayi. Kara zaro idanu ta yi tare da fara ƙoƙarin tunawa ko zata iya tunano abin da ya faru a baya?!.

A can gida kuwa sai kuka Zainab take ta yi, ta ƙunshe kanta a cikin ɗaki tun bayan da ƴan'sanda suka tafi da mamar ta su.

Abin da ya faru shi ne, fitar da Khadija ta yi domin zuwa kiran mutane su zo su taimaka masu, tana fita bakin gidan nasu bata ga kowa ba, babu mutane, dukka mazan unguwar tasu sun tafi masallacin jumma'a, dan lokacin an fara sallar jumma'a.

Ganin hakan yasa a ruɗe ta nufi hanyar fita daga unguwar nasu izuwa bakin titi ko zata haɗu da wasu su taimaka mata, basu da nisa da titi. Bata ƙarisa fita ba wata dankareriyar mota kirar Bugatti la voiture noiro baka kirin sai kyalli take yi ta faka a gabanta.

Tana ƙoƙarin kaucewa motar ta raɓa gefenta ta wuce sai gani ta yi an buɗe kofar motar. Wasu maza biyu kyawawa farare tas tas masu sanye da suit ash color ne suka ɓalle kofar motar suka fito. Daga ganin mazan nan ba Nigerian mens bane, daga gani daga ƙasashen masu jajayen kunnuwa suke, dan kuwa jajir suke kamar ka taɓa jini ya fita, ba irin farin Nigeria bane, ga kyakkyawan gashin kai bakin kirin, sannan idanunsu tas kamar an ɗiga zaiba, kwayar idanun kuma bakin kirin har wani ɗan kyalli yake yi, suna da kyau kam masha Allah, matasane da ba zasu wuce 25 years ba a duniya.

Sai dai da kallo ɗaya zaka yi masu ka san basu da imani, saboda fuskokinsu babu alamarta ko kaɗan, a turnuke fuskokin nasu suke sosai. Ga su dai dirarrun maza ne sosai sosai, kira kamar su suka yi wa kansu.

Da yake tana cikin ruɗani da tashin hankali sai bata ma bi ta kansu ba, hasalima bata ɗaga idanun ta kalli koma su waye bane, kai tsaye ta raɓa gefensu zata wuce, kamar wata mahaukaciya haka ta zama.

Bata kai ga wucesu ba suka damketa suka wurga cikin motar tasu, ga motar da tinted a jikinta. Ihu ta fara kurmawa da karfi karfi. A hanzarce suka faɗa cikin motar suma, suna shiga kuma bayan sun rufe kofar ji kake tsit Khadija ta dai'na wannan ihu, kamar waɗan da suka yi mata wani abin...... To fa, su waye su?.

Cikin kwanciyar hankali suka yi reverse na motar tasu, a hankali suka takata suka bar unguwar, suka miƙi hanya.

Abin da yasa kenan su Zainab suka ga ta jima bata dawo ba, ita kuma Zainab ɗin bayan mamarta ta suma sai ta fito a guje kamar mahaukaciya, dan ta nemo jama'a da kuma ƴar uwarta.

Kasancewar ta fito a guje kamar mahaukaciya yasa ta shiga gaban wani mai mashin da ya ɗauko wata mata, ai kuwa bata ankara ba sai jinta ta yi a ƙasa. Ko kaɗan bata wani damu ba, da yake Allah ya takaita mashin ɗin bai ji mata ciwo sosai ba, tureta kawai ya yi ta faɗi ƙasa, ƴar kwarzanewa ta yi a hannunta sakamakon wani dutse da yake a kusa da ita ta faɗa kansa.

Baiwar Allah hankalinta baya a jikinta, sai ta miƙe cikin kaɗuwa da tashin hankali. Da gudu ta nufi bakin titi. Mai mashin da yake ƙoƙarin banka mata ashariya saboda shiga gabansa da ta yi, kafin ya buɗe baki ma ta miƙe da gudu ta barshi da baki a buɗe, bai san me take ji ba, bai san bala'in da yake kanta ba.

Bata ƙarisa isa ga bakin titi ba sai jin jiyar motar ƴan'sanda a gabanta ta yi, birki ta ja ta tsaya da nufin idan sun wuce sai ita ma ta nufi bakin hanyar, kasancewar hanyar fita daga unguwar tasu zuwa bakin titin babu wani faɗi sosai.

Ganin Hauwa a gaban motar ƴan'sanda ne yasa Zainab ɗin bata san lokacin da ta juya ta fasa isa ga bakin hanya dan neman mutane ba, ta juya ta bi bayansu, dan tasan cewa definitely gidansu wannan mota ya nufa tun da ga Hauwa a ciki....... Ashe ƴan'sanda Hauwa ta je tattarowa.

Suna isa bakin gate ɗin suka fara dirowa ƙasa daga saman bayan motocinsu, ba tare da ɓata lokaci ba suka nufi cikin gidan, ƴan'sanda shidda ne cif suka zo, sai Hauwar da ta kirasu, shegiya ko ɗan'kwali babu a kanta.

Ita ta yi masu jagoranci har izuwa ɗakin nasu in da maman Zee ta kashe baban Zainab ɗin. Suna shiga suka sami maman Zee a sume, duk da take a sumen kuma bai hana sun tafi da ita ba, hands gloves suka sanya a hannayensu kafin su taɓa baban Zainab ɗin, sai da suka ɗauke shi a hotuna kala kala ma kafin su taɓa shi. A takaice dai wannan shi ne abin sa ya faru.

Zainab tana kuka kada su tafi mata da mamarta, amma haka suka wuce da ita tana sume bata san me yake faruwa ba, sannan suka tafi da Hauwar ma, dan kara gudanar da bincike, shi kuma baban Zainab wasu ƴan'sanda ne na daban suka zo suka ɗauki gawarsa izuwa asibiti, dan a yi gwaje gwajen da za'ayi.

Hauwa a police station ɗin ne da suka je ta kira Hajiyarsu baban Zainab da wayar baban Zainab ɗin ta sanar mata da cewa maman Zainab ta kashe baban Zainab, gawarsa tana police hospital, dan haka su zo.

Ai kuwa babu ɓata lokaci sai gasu sun hallara a station ɗin bayan Hauwar ta gaya masu a division ɗin da suke.

Ƴan'sanda sun yi sun yi maman Zainab ta farfaɗo daga sumar nan da ta yi sun ƙasa, sun yi ta zuba mata ruwa, amma bata farfaɗo ba. Hakan yasa suka yi duk gwaje gwajen da zasu yi ɗin tana sume.

Shatin zanen hannunta ne a jikin wukar dake lume a cikin baban Zainab ɗin, suna gwajin farko ya tabbatar masu da hakan, hakan yasa suka gasgata dukkan zantukan da Hauwa ta gaya masu, sun yarda, duk wani bincike da zasu yi ya tabbatar masu da lallai maman Zainab ce ta yi wannan kisan kan, wannan dalilin yasa suka jefata cell tun kafin manyansu su iso kan case ɗin.

Ita kuwa Hajiyarsu baban Zainab ɗin da take ta faman kuka tun da ta zo, ƴan'sanda sun ce ta koma gida, kin yarda ta koma ta yi, faɗi take sai maman Zainab ta biyata ran ɗanta, azzaluma ta kashe masu bangonsu, da shi kaɗai suka dogara, shi ne mai yi masu komai, dan haka wlh sai ta biyata ɗanta, maman Zainab dake sume bata san wainar da ake toyawa bama baiwar Allah, sai banka mata ashariya kala kala suke yi tana sume. Maman Haidar kam ma har da wani cewa wlh ba zasu yarda ba dole ita ma a kasheta kamar yadda ta kashe shi azzaluma kawai.

Da kyar dai aka samu ƴar'sanda mace ta ja Hajiyar suka tafi zata mayar da ita gida, haka su Maman Haidar suka bisu, Maman Hanif kam ta ƙasa iya furta ko kala bayan ruwan hawaye da take yi, banda ruwan hawaye babu abin da take yi, ita dai tasan maman Zainab ba zata taɓa kashe baban Zainab haka kawai da gangan ba, dan ita ta san soyayyar da yake a tsakaninsu, ta san irin yadda baban Zainab ya rinƙa jigila a tsakanin Kano da Kaduna saboda ita, sannan ta san yadda maman Zainab ɗin ma take son shi, so ita bata ma yarda cewa maman Zainab ɗin ce ta kashe shi ba, zargin Hauwa ce ta yi hakan take yi a ranta, dan ita fa kwata kwata bata kaunar Hauwa, amma Hajiyarsu da Maman Haidar fa suna kaunar Hauwar duk da balai'n da take surfa masu, da alama ta kai sunansu wajen bokanta ne, sai dai aikin bai kama maman Hanif ba, dan dai ita kam babu son Hauwar ko ɗigo a ranta, sai ma zallar tsana da take yi mata.

Ko da aka mayar da su gidan baban Zainab ɗin, a bakin kofar gidan suka isko Zainab a zaune tana tikar kuka kamar ranta zai fita, ta rasa ina zata sanya rayuwarta, babu uba yau, sannan ƴan'sanda sun tafi da mamansu, ga kuma Khadija shiru bata dawo ba.

Ƴar'sanda da ta rakosu ta dawo da su gidan tana juyawa suka fara halin nasu, tana barin gidan maman Haidar ta fara surfe da nikar bala'in a kan wlh ba zasu taɓa hakura su yafewa maman Zainab ba, dole a kasheta kamar yadda ta kashe masu bangonsu ma jingina.

(Ni kam na ce sai yanzu kenan suka san cewa shi ɗin bango ne a gare su?🤔)

Kasancewar har da Hauwa ƴan'sanda suka saki da nufin idan wani abin ya taso zasu nemeta, hakan yasa ita ma ta fara rera nata kukan munafurcin tana faɗin wlh haka ne ba zasu yafe jinin baban Zainab ba.

Dama fa ita Hauwa idan baku manta ba dukiyar baban Zainab ɗin kawai take so ba shi ba, so ita mutuwar tasa ma rage mata hanya ya yi, ya zame mata tsanin da zata taƙa ta cinma burinta ne, dama ko maman Zainab bata kashe shi ba ita Hauwar ta shirya yadda zata sanya a ɓatar mata da shi bayan ta gama kwasan abin da zata kwasa, so ita wannan kasheshi da maman Zee ta yi hanya ta rage mata, wani dama ne ta samu, yanzu tunanin da yake a cikin ranta kawai shi ne ta yadda zata yi ta rufe bakin kowa ta kwashe komai na marayun Allahn nan Khadija da Zainab ta gudu abinta, shiyasa ma kuka ga ta yi saurin zuwa ta kira ƴan'sanda domin su tafi da maman Zainab, tasan idan maman Zainab ɗin tana cikin cell abubuwa zasu tafi mata yadda take so saɓanin idan tana gidan, bokanta ya gaya mata asirinta ba zai ci maman Zainab ɗin ba, ba zata iya rufe mata baki ba, domin a yanzu maman Zainab ta tsaya tsayin daka a kan ibada, ta koma ga Allah sosai, hakan yasa babu wani aiki da zai iya kamata.

Sanin hakan yasa Hauwar ta yi azaman jefata a cell, dan in tana gidan zata katse mata duk wani abin da ta shirya, kuma bata isa ta ɗauki ko tsinke a gidan ba, amma yanzu kunga maman Zainab tana cell, iyayen baban zee ɗin kuma ta sanya an yi masu aikin cusa masu kaunarta, saura mata aiki ɗaya shi ne ta rufe bakunansu ta yadda zata gudanar da komai babu wanda zai iya ce da ita uppan........ E lallai akwai kura, ina Khadija? Sai Allah kaɗai yasan su waye suka ɗauketa, ina kuma zasu kaita baiwar Allah.

Wani irin tsananin tsana Hajiyarsu baban Zee ta ji take yi wa maman Zee da ƴaƴanta gabaɗaya...... Ni kuwa nace to me laifin ƴaƴan nata? Su suka yi laifin ne? Ko a wajen Allah laifin wani baya shafar wani, amma jahilci yasa Hajiyarsu ta haɗe da su dukka ta tsana kamar ta kashesu, sai faɗi take maman Zainab ta gama da su ta tona masu asirin da Allah ya rufa masu, shikenan sun shiga uku sun lalace.

Maman Hanif kam har izuwa yanzu ta kasa iya furta ko uppan. Banda zagi babu abin da maman Haidar take surfawa Zainab dake zaune a bakin kofa tana tikar kuka, yarinyar nan kamar ranta zai fita, kuka take yi ba ji ba gani, idanunta har ƙanƙancewa suka yi, sun kumbura sun yi jajir, idan ka ganta sai ta baka tausayi, sai kuma ka tsorata da ganin idanun nata, saboda yadda suke jazur da su.

Ko sannu bata ce da su ba, duk zagin da maman Haidar take yi mata bata ko ɗago idanu ta kallesu ba, hasalima hankalinta baya a tattare da ita ne, bata jin me ma suke faɗe.

Maman Haidar na zagi Hauwa na ƙara ingizata, har da kara cewa ai dama maman Zainab ta kai sati tana cewa sai ta kashe baban Zainab, dan haka wlh har su Zainab ɗin ma kada su bari, ai suma mugun iri ne, dan halin uwarsu suka ɗauko.

Ita fa Hauwa fama take yi taga yadda zata yi ta kawar da su Zainab ɗin, sannan ta rufewa kowa baki ta kwashi dukiya ta yi pacakanta da su son ranta, ta haɗa kayanta ta koma Kaduna....... Gaskiya ba karamar mayyar son abin duniya bace Hauwar nan, ba kuma ƙaramar azzaluma bace ba.

Da dai suka ishe Zainab da zagi kamar zasu cinyeta ɗanya, sai ta miƙe ta nufi cikin ɗakinsu, ji take kamar zuciyarta na ƙonewa da wuta, su barta ta ji da abin da take ji mana, amma suna kara mata wani.








Ko da ta shiga ɗakinma ba su barta ba, maman Haidar ta ce ta fito daga ɗakin nan munafuka, yadda kuka san ba jininsu ba ce, kamar ba jinin baban Zainab ɗin ne yake gudu a jinin Zainab ɗin ba, suka murje idanu, suka sanya yarinya a gaba da zagi da baƙaƙen maganganu kamar ita ta aikata laifin ba mamanta ba.

Da maman Hanif ta yi ƙoƙarin basu hakuri su rabu da ita, ai kuwa ita ma maman Haidar ta hau zaginta babu kakkautawa, wai bata kishin jinin ɗan uwanta, kamar ba yau bawan Allahn nan ya rasu ba, sun zauna sai kace nace suke yi, tun ruhinsa bai gama sauka a masaukinsa ba sun fara walaƙanta bayansa, sun fara cin zarafin ƴaƴansa kamar ba nasu ba.

A takaice dai Zainab da ta ga ba raga mata zasu yi ba, sun isheta da magana, sai ta kama hanyarta ta nufi barin gidan. Maman Haidar ce ta ce ina zata je munafukar banza.

Ko sannu bata ce masu ba, bata ma sake ɗaga idanu ta kallesu ba, abin da take ji a cikin zuciyarta ma ya isheta, haka ta yi banza da su ta nufi waje, sai magana suke ta yi mata, ina ko waigowa bata yi ba, sai kiranta suke yi.

Tana fita ta fara neman ina Khadija take, tana tafiya tana hawaye bibbiyu, wani na bin wani gwanin ban tausayi.

Ni kai'na na tausayawa maman Zainab da ƴaƴanta wlh, kowa da kalar tasa ƙaddara a rayuwa, ba ta yadda Allah baya jarabtar bawa, amma kuma my people's ina son ku san wani abu, duk wanda kuka ga yana shiga cikin kaddarori to wlh Allah ya fi sonsa, Allah yana jarabta imanin bawa ne kawai idan yana kaunarsa, kada ki ga kina shiga cikin wasu matsaloli ki yi tunanin ko Allah

1 / 118