Author : Mansur Usman Sufi Category : Arewa Pen
suna na shubairu ibn mauzur mahaifina mashahurin boka ne da yayi shura a yankin nahiyar larabawa,
Duk cikin ya'yan mahaifin mu ni ne kaɗai na gaje shi tun banfi shekara goma sha biyar ba da rasuwar sa,
Game da amsar tambayar ki ta biyu kuwa zakiji amsar acikin bayanin da zan yi miki,
Binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na ya tabbatar mini dacewa tun mahaifin ki yana raye ya ziyarci bokaye da dama domin samo maganin lalurar ki amma abu ya ci tura,
Yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa har abada bazaki taɓa warkewa daga wannan lalura taki ba face kin sha wani tsumin tsafi dake ajiye a cikin wata salka a fadar Sarkin bokayen duniya,
Bincike ya kara tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki da ya isa yaje fadar Sarkin bokaye ya ɗauko tsumin tsafi face wani hatsabibi kuma taƙadirin jarumi da ake yiwa laƙabi da SARKIN SADAUKAI,
Hibairu wani irin mutum ne da yake rayuwa ta daban domin ya taso ne a cikin dabbobi da aljanu tun yana jariri, bai taɓa ganin wani bil'adama ba ballantana ya iya Yaren su,
An kira sa ne da SARKIN SADAUKAI saboda tsanin jarumtakar sa ya huce hankali,
Bazai taɓa fitowa daga dajin Baitul-shamshan ba face ya kammala karanta waɗansu dalasiman tsafi dake jikin wani ZOBEN SHIRI dake hannun sa wanda adadin sirrikan tsafin shine adadin dabbobin dake cikin dajin,
Game da amsar tambayar ki ta uku kuwa akan mene ne riba ta idan na taimaka miki wajen samun maganin lalurar ki shine
Sai domin na gano cewa kece kaɗai wacce zata taimaka mini wajen biyan tawa Bukatar,
Kamar yadda kike ɗauke da lalurar tsagin jiki
Ni ma ina da irin ta sak amma a tsagin dama kuma na samu tawa lalurar ne alokacin da nake fafata artabu da yan uwana a ƙoƙarin su na rabani da muhimman sirrikan tsafin mahaifin mu,
Bisa wannan dalili ne yasan ya nake so mu haɗa karfi da karfe domin mu sadu da sadauki Hibairu a lokacin da zai fito daga dajin Baitul-shamshan domin mu bayyana masa buƙatar mu ta zuwan sa fadar Sarkin bokaye,
Koda tsuntsun ya zo nan azancen sa sai kawai ya rikiɗa izuwa wani zabgegen kyakkyawan saurayi ba ya sanye da riga ko wando face bantai na fatar damisa da ya rufe al'aurar sa zuwa kwaurin sa,
Sa'adda sarauniya Abidatul-auliya tayi arba da saurayin nan take taji zuciyar ta buga da karfi kuma tsikar jikin ta ta tashi,
Bakomai ne yasanya sarauniya Abidatul-auliya taji zuciyar ta ta buga da karfi ba sai domin tunda take a rayuwar ta bata taɓa ganin wani ɗa namiji mai kwarjini da kyan diri tamkar saurayin ba,
Abinda yasanya tsikar jikin ta ta tashi kuwa shine Yayin da ta kalli saurayin sai taga barin jikin sa na dama na zubar da wani ruwan mugunya na kuturta,
Daga can sai saurayin ya sake rikiɗa izuwa wannan kyakkyawan tsuntsu ya buɗe baki a karo na uku yace "Na barki lafiya ya sarauniyar kyawawa sai mun sake saduwa a ranar da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI zai kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI a dajin Baitul-shamshan,
Koda gama faɗin hakan sai ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Nan take sarauniya Abidatul-auliya ta cika da matukar farin ciki maral misaltuwa yazamana cewa a kullum idan dare ya tsala sai ta zauna a wannan baraba ta Turakar ta koda wannan tsuntsun zai sake bayyana gareta wato shubairu ɗan boka mauzur
Wannan shi ne abinda ya faru da sarauniya Abidatul-auliya ya birnin Tehran dake yammacin duniya.
Kwatsam bazato babu tsammani sai saurayi Hizmal da mahayin suka ji ƙarar alamun zare sakatun wannan ƙofa daga ciki,
Daga bisani sai ƙofar ta bude sai ga wani irin haske da kamshi mai nan sha'awa ya ratso daga ciki
Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa mahayin ya kunna kai izuwa ciki saurayi Hizmal yayi koyi dashi goye da yaro Humair a gadon bayan sa,
Su na kammala shiga sai ƙofar ta mayar da kanta ta rufe ruf!.
Adai dai wannan lokaci ne sarki shazwan waziri Rufyan Sarkin bokaye da sauran tawagar su suka bayyana a wajen bayan buɗewar ƙofa ta huɗu,
Sa'adda suka bayyana sai sarkin bokaye ya dubi sarki shazwan cikin matukar takaici yace"ya shugaba na haƙiƙa munyi babban rashi da har mu kayi kuskure su saurayi Hizmal suka ƙetare kofa ta biyar suka shiga izuwa gidan tsira
Bisa tsarin wannan gida babu wanda ke da ikon shiga cikin gidan tsira matukar akwai wanda ya ƙetare kofa ta biyar har sai nan da kwanaki uku,
Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai kowa ya cika da matukar takaici, shi kuwa Sarki shazwan saboda matukar takaici bai san sa'adda ya takarkare ya kurma wawan ihu ba wanda ya firgita duk wata halitta dake wajen har da boka Dargas,
Sai Daga bisani ne ya turɓune fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi Sarkin bokaye a lokacin da idanuwan sa suka kaɗa su kayi jawur tamkar garwashin wuta cikin kakkausar murya yace"ya Sarkin bokaye ina so kayi ma za ka gudanar da bincike gano mini shin mene ne abin da ke faruwa a birni na,
Koda jin wannan umarni daga bakin sarki shazwan sai idanun Sarkin bokaye suka zazzaro su dube sa cikin ladabi yace"ya shugaba na shin ka manta ne cewa abisa ƙa'ida da dokar wannan gida sihiri baya tasiri,
Idan kuwa har ka naso na gudanar da binciken dole sai dai mu koma da baya,
Sai dai ina da wata shawara,shawarar kuwa ita ce mu kasu guda biyu kaso na farko su jira anan har zuwa nan da kwanaki uku domin su samu damar shiga izuwa kofa ta biyar su cimma su saurayi Hizmal,
Ni kuma da wasu zamu koma izuwa birnin mu domin mu kai ɗauki jikina ya bani cewa tabbas bayan tafiyar mu wani mummunan al'amari ya faru sai dai bazan iya sanin ko mene ne ba tunda bani da halin gudanar da bincike,
Yayin da sarki shazwan yaji wannan shawara daga Sarkin bokaye sai yayi shiru yana nazari Daga bisani kuma ya dubesa yace"Ka kawo shawara mai kyau saboda ka tafi kai da sauran Yan uwan ka bokaye mutum biyar,tare da waziri Rufyan
Ni kuma da Sarkin yaƙi zamu zauna nan mu jira cikar kwanaki uku domin mu cimma su saurayi Hizmal.
Koda jin wannan umarni daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye ya juya da baya ya shige izuwa cikin wannan kofa ta huɗu da suka fito waziri tare da bokaye biyar suka mara masa baya,
Suka bar su sarki shazwan a tsaitsaye cirko cirko fuskokin su cike da matukar damuwa,
Wannan shi ne abinda ya faru da su sarki shazwan da su saurayi Hizmal a cikin gidan tsira,
****. *****. *****
Daji ne ma'abocin kwarjini,da ban tsoro, ya tara bishiyoyi, duwatsu,koramu haɗe da kwazazzabai,gami da manyan tsaunuka,
Komai rashin tsoron Mutum idan ya yaga yadda dajin yakasance dole ya razana,
Domin da gani dole ne a samu miyagun dabbobi ko aljanu a cikin sa,
Tsananin shirun da ya wanzu a wajen ya ishi ya firgita Mutum
Sai dai abinda zai bawa mai kallo mamaki shine duk yadda dajin ya tara wadannan abubuwan ban tsoro amma sai gashi wani bil'adama ya wanzu a cikin sa amma babu alamun tsoro ko razani a tare dashi
Kyakkyawan saurayi ne ɗan kimanin shekaru sha biyar yana sanye da bante iya gwiwar sa, babu riga a jikin sa,
Hakan ne abinda ya bayyana surar jikin sa ta jarumtaka , jikin sa a murɗe yake tamkar na ƙarfe,yana da faffaɗan kirji tamkar duwatsu aka cuccusa masa a ciki,gashin kansa baƙi ne siɗik mai kyalli ya zuba akan fuskar sa da kirjin sa,
Kafar sa ko takalmi babu, a hannun sa yana riƙe da wani dogon mashi mai baki tamkar zarto mai kaifi tamkar takobi,
Kallo ɗaya za ka yiwa saurayin ka fahimci cewa yana da karfi na Allah ya isa,
Tafiya yake a dajin cikin ƙasaita yana mai ratsa duwatsu koramu da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi tamkar yana cikin turakar sa,
Yana cikin wannan tafiya ne ya jiyo alamun motsi a bayan,. Koda ya waiga bayan sa sai yayi arba da wata zakanya da mijin ta suna tsere cikin nishaɗi,
Idan namijin ya ba wa macen tazara sai macen ta zage damtse ta tsere masa, ta mai yimasa gurnani dake nuna cewa ta samu nasara ,
Sa'adda saurayin yaga abinda zakanyar da mijin ta ke yi sai ya kalle su yayi murmushi har suka zo suka gifta ta gaban sa suna matsanancin gudu suka yi nisa sosai har yazama dakyar yake iya hangosu.
Sai kawai shima ya takarkare ya falfala da azababban gudun mai ban al'ajabi daban mamaki,
Domin ƙorama, duwatsu da bishiyoyi basa tsaida sa,
Duk faɗin ƙarama tsallake ta yake yi.
A wasu lokutan sai kaga ya daga tsalle sama yana yana mai rike rassan bishiyoyi tamkar wani ɗan biri,
A wasu lokutan ma idan yaga bishiya zatayi masa waigi sai kaga ya sanya hannun sa ɗaya ya naushe ta ta faɗi ƙasa ya bi ta kanta ya huce,
Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa goma sha biyar ba sai gashi ya dira a can gaba ɗaya inda zakunan suke,
Ya yin da su kayi arbda da saurayin sai suka ja suka suka tsaya cak,
A kayi kallon kallo sai bisani sai zakanyar da mijin ta suka dako sufa izuwa kan saurayin yayin da suka hada kirji da juna sai su duka biyun suka faɗi ƙasa tim,
Amma saurayin ko da ƙafarsa bata motsa ba ballantana yayi gezau,
Sai da akayi haka har sau goma, koda zakunan suka ga cewa sun kasa samun nasara sai kawai suka risina da kawunan su ƙasa suka durƙusa alamun dake nuna cewa sunyi MUBAYA'A ga saurayin,
Ba wani bane wannan saurayi ba face jarumi Hibairu wato SARKIN SADAUKAI.
Yayin da Hibairu yaga zakunan sun risina agareshi sai kawai ya juya ya cigaba da tafiya a dajin hannun sa riƙe da wannan mashi mai baki biyu,
Wannan shi ne abinda ya faru da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI a cikin dajin Baitul-shamshan.
Al'amarin su saurayi Hizmal kuwa sa'adda suka samu nasarar shiga izuwa gidan tsira sai suka tsinci kan su a cikin wani kasaitaccen gida da aka kawata sa da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin duniya, gaba ɗaya ginin gidan anyi sane da zallar duwatsun zubar daju yana sheƙi da walwali, ko ina an kawatashi da furanni da furanni da shuke-shuke gwanin ban sha'awa.
Gidan yana ɗauke da manyan falo guda arba'in kowanne na ɗauke da kayan alatun jin daɗin duniya daya bambanta da ɗayan,
Haƙiƙa babu wani Basarake ko attajiri da zai tsinci kansa a cikin gidan face ya raina kansa ya tabbatar dacewa ya shiga cikin maƙurar aljannar duniya,
Bayan su saurayi Hizmal sun sauka a cikin wata ƙasaitacciyar turaka sai kowa ya shiga kimtsa cikin sa bayan an kammala an samu nutsuwa ne sai Hizmal yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye ya dubi mahayin nan yace"ya kai wannan jarumi ma'abocin karfin damtse lokaci yayi da ya kamata ka bani amsar tambayoyin da nayi maka a baya,
Koda jin wannan batu sai Mahayin ya ɗora hannun sa a kansa ya cire rawanin sa fuskar sa ta bayyana a fili ƙarara,
Sa'adda saurayi Hizmal yayi arba da fuskar mahayin sai ya cika da matukar al'ajabi da mamaki,
Bakomai ne ya basa mamaki ba sai bisa ganin cewa mahayin yakasance tsaleliyar kyakkyawar budurwa,
A iya tsawon rayuwarsa bai taɓa ganin mace mai kyan diri tamkar mahayin ba,
A karon farko Hizmal yaji soyayyar ya mace ta shiga zuciyar sa,
Kyakkyawar budurwar ta jefi Hizmal da wani irin kayataccen murmushi mai ɗauke da alamar tambaya,
Sannan ta buɗi baki cikin zazzakar murya mai daɗi tamkar sarewa tace"yakai Hizmal a yanzu na bayyana maka wace ce ni
Yanzu kuma zan sanar dakai dalilin da ya sanya taimaka maka wajen ceton rayuwar yaro Humair,
Da farko dai suna na Husnaila bintu ishwar, mahaifina ƙasurgumin matsafi ne kuma ƙasaitaccen sarki da yayi shura a yankin ƙasashen yamma ta tsakiya,
Dalilin rabuwa da mahaifina da ƙasar mu kuwa shine ,
****. *****. *****
Kimanin shekaru arba'in bayan shuɗewar KARSHEN ƘARNI na shida da yin YAKIN DUNIYA na biyu,
An yi wata ƙasaitacciyar ƙasa da ake yiwa laƙabi da Baitul-Mausul,
Ƙasar Baitul-Mausul ta bunƙasa a harkar kasuwanci,noma da kiwo daɗin daɗawa sun tara zaratan Jarumai masu juriya a filin daga,
Sarautar ƙasar na karkashin mahaifina sarki ishwar,
Sarki ishwar yakasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga, ya na da tarin dukiya,gami da sanin ilimin tsafi,
Mutum adali mai tausayin talakawan sa, bisa wannan dalili ne yasan ya jama'a ke matukar kaunar sa da yi masa biyayya,
Kuma sarakunan dake nahiyar suke shakkar sa basa yunkurin kawo masa farmaki,
Mahaifina yana da matan aure guda huɗu kuma dukkanninsu sun haifa masa ya'ya
Yarima ubaiyu shine babba, sannan Hushriba,yarima Zaiyum sai ni yar autar su Husnaila,
A kaf cikin ya'yan mahaifin mu ni kaɗai ce na gajeshi a fagen halaye na kwarai, saɓanin yan uwa na su yarima ubaiyu,
Yayin da yan uwana suka ga cewa sarki da ma sauran juma'ar gari sun ɗora soyayyar agareni kuma suna nuna cewa nice zan gaji karagar mulki sai yan uwa na suka fara bayyana mini ƙiyayya,
Sau babu adadi sun kawo mini hari domin su cutar dani amma sai na tsalleke,
Haka ma a bangaren mahaifiyata tana fuskantar tsangwama daga kishiyoyin ta
A wasu lokutan haka zamu zauna ni da ita suna kukan baƙin cikin abinda ake yi mana
A kwana a tashi wata rana sai mahaifin mu ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da aka kasa gane kanta,komai na jikin sa ya daina motsi sai dai idanunsa da bakin sa da yake iya magana,
Nan fa manyan bokayen ƙasar suka dukufa gudanar da bincike domin su gano musabbin abinda ya haddasa cutar da kuma maganin dazai warkar da cutar,
Amma mahifina bai taɓa sani ɗaya daga cikin matayen su sun sa abin da binciken ya bayar ba,
Wata rana tunda dukun safiya ni da sauran Yan uwa na muka shiga turakar mahaifin mu domin mu duba sa,
Da shigar mu mu ka tarar dashi kwance abisa kan gadon sarauta,
Kai idan ka gansa sai kayi tsammanin cewa gunki ne domin komai na jikin sa ya daina motsi idan ka cire idanuwan sa dake kiftawa,
Sa'adda mu kayi arba da halin da mahaifin mu ke ciki muka shiga zubar da hawaye
Tsawon daƙiƙa hamsin a cikin wannan hali sannan Daga bisani muka miƙe tsaye domin ficewa daga Turakar,
Yarima Ubaiyu ne a gaba sannan Gimbiya Hushriba yarima Zaiyum sai ni a ƙarshe,
Har na sanya ƙafa ta ɗaya a waje sai naji bisa mamaki mahaifina ya yi gyaran murya yace"ya yata dawo izuwa gareni domin in sanar dake wani sirri,
Koda jin wannan batu daga bakin mahaifina sai na dawo da baya nazo na tsugunna a gaban mahaifina,
Kawai sai abbana ya buɗi baki ya karanto waɗansu dalasiman tsafi take wani haske ya bayyana yaje ya shiga jikin kofofi da tagogin turakar take suka rufe kansu,
Kana haske ya dawo ya cure waje guda ya rikiɗa izuwa wata fitilar haske,
Nan fa Turakar ta gauraye da wani irin haske na ban mamaki wanda koda allura ce ta faɗi mutum yana dubawa zai ganta.
Kana daga bisani mahaifina ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai tattare daban tausayi yana mai cewa "ya yata abar alfahari na kiyi sani cewa bakomai ne ya sanya na keɓe da ke ba sai domin na sanar dakai wani boyayyen sirri guda ɗaya game da wannan cuta da ta same ni,
Ya yata kiyi sani cewa binciken da bokayen wannan ƙasa su kayi ya tabbatar dacewa wannan cuta tawa Yan uwan ki su yarima ubaiyu ne suka yi mini Shirin tsafi domin su hallaka ni su gaji karagar mulki na,
Saboda da mugun shirin da su kayi mini ne yasan ya na umarci waziri daya tura ku izuwa sassan duniya domin ku nemo mini maganin cutar,
Duk wanda ya samu nasarar nemo maganin shine zai gaji karagar mulki na,
Ya yata kiyi sani cewa kece kaɗai na fi kauna a cikin yan uwan ki da mahaifiyar ki,
Saboda haka ne nake so na sanar dake maganin dazai warkar dani daga wannan cuta,
Domin ina son ki gajeni bayan raina na ta tabbata cewa jama'a zasu samun farin ciki da zaman lafiya har abada, saɓanin yan uwan ki,
Maganin dazai warkar dani daga wannan cuta shine sihirtaccen DAMARAR SIHIRI ta Sarkin bokayen duniya dake sanye a ƙugun sa DAMARAR SIHIRIn na dauke da waɗansu sirrika na sunayen Ubangijin wadansu ma'abota wani addini da ake kira da suna Musulunci,
Ina da ace JARUMAN DUNIYA zasu taru waje guda baza su iya raba Sarkin bokaye da wannan DAMARAR SIHIRI ba matsawar yana tare da ita
Ya yata kiyi sani cewa bazaki taɓa samun nasarar mallakar ɗamarar ba face kin nemi taimakon wani hatsabibi jarumi da ahalin yanzu yake zaune a dajin Baitul-shamshan,
Ana kiran jarumin Hibairu bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu Hibairu shine SARKIN SADAUKAI na duniya domin babu jarumi mai karfin damtse kamar sa,
Hibairu bai taɓa ganin bil'adama a rayuwarsa ba domin ya na rayuwa ne a cikin dabbobi da aljanu, don haka ya taso da wani yare da wanda ya iya yinsa a duniya face yaro Humair makaho,
A halin yanzu makahon Yaron yana ajiye a hannun saurayi Hizmal yana kula da https://youtu.be/bq_-9I3FtnA sa tun bayan mutuwar mahaifan sa,
Lokacin da mahaifina yazo nan a zancen sa sai yace ya yata na umarci da kika kara matsowa kusa da ni
Koda jin hakan sai na daɗa matsa kusa dashi
Kawai sai abbana ya buɗe bakin sa take wani dunkulallan farin haske ya fito daga bakin sa da girman sa bai huce na kwan jimina ba
Take hasken ya dunga shiga jikina lokacin da hasken ya kammala shiga,
Take naji wani irin gagarumin karfi ya shige ni naji tamkar zan iya yaƙar duniya baki ɗaya,
Mahaifina yayi guntun murmushin ƙarfin hali sannan yace ya yata Kiyi sani cewa ahalin yanzu kina ɗauke da sirrikan tsafina guda miliyan biyu,
Haƙiƙa babu wani al'mari da za ki sanya a gaba face kin samu nasara,
Saboda haka sai ki jira nan da kwanaki domin kiji bayanin da waziri zai bayyana.
Sa'adda mahaifina yazo nan azancen sa sai hawaye suka shatato daga idanuwan sa
Al'amarin daya sanya na rungume mahaifina kenan na fashe da kuka saboda da mutukar tausayi,
Sa'adda jaruma Husnaila bintu ishwar