Author : Mansur Usman Sufi Category : Arewa Pen
an dauko wannan littafi ne Daga shafin
www. Littafanyaki.com.ng
SARKIN SADAUKAI 1
Sarkin marubuta littattafan yaƙi
MANSUR USMAN SUFI
Wthapp number &;call
08137237071
kyakkyawan saurayi ne nagaban kwatance ɗan kimanin shekaru ashirin da ɗoriya sanye da tufafi fatatun dabbobi riga da wando, takalmin dake kafarshi na fatar Damisa ne, Gashin kanshi ya zuba izuwa kafadunshi.
A Kafaɗarshi yana rataye da wani yaro mai kimanin shekara biyar.
Yana ta faman tsala matsanancin gudu babu a cikin kasaitaccen daji mai dogayen bishiyu,duwatsu,koramu, Da kananan tsaunuka,saboda gudun da saurayinn keyi sai jbgasai kaga har tsallake yan kananan duwatsu yake yi koda ya shafe sa,a daya
yana gudun sai karfin gudun nasa ya ragu ainun gajiya ta fara kamasa .
kwatsam bazato babu tsammani sai yaga wadansu irin masifaffun kibiyoyi suna sauka adajin tamkar ana ruwan sune daga saman,
koda ganin hakan sai saurayin ya shiga shiga yin amfani da hikimar sa yana zillewa kibiyoyin cikin matukar zafin nama naban al,ajabi tamkar daukewar ruwan sama aka daina harbo kibiyoyin
koda ganin hakan sai saurayin ya nufi wata sarkakiya mai cike da duhuwa adajin ya ciro wannan yaro daga kafadar sayan sa acikin duhuwar ta yadda babu wanda zai iya ganinsa sannan ya juya yayi kamar taku hudu daga inda yake
sannan yaja ya tsaya yana mai jiran yaga abinda zai faru yana waige waige da dube dube,kwatsam sai ga wadansu irin girda girdan dakaru masu kirar samudawan farko mara sa adadi suna firfitowa daga duhuwar bishiyoyin dajin dakarun suna da girma tamkar toran giwa agaba
dayan su suna sanye cikin matsananciyar shigar yaki mai matukar kwarjini daban tsoro fuskokin su asanye suke cikin hular karfe
jajayen idanuwan su kadai ake gani ahannayen su suna rike da miyagun makamai dangin su gatari,takobi,sungumi,majaujawa
da sauran su kafin saurayin yayi wani yunkuri dakaru sun rugo izuwa kansa suna ihu da kururuwa mai firgitar wa ana haduwa aka kacame da azababban yaki ana cikin wannan yaki ne wani badakaren ya shammaci sajurayin ya gabza masa navshi afuska ya bazar dashi akasa
sai shugaban dakarun ya uwarci wasu dakaru suka duba cikin duhuwar dajin sai gasu sun fito da yaron kawai sai shugaban
dakarun ya cillawa badakaren dake rike da yaron wata wuk,ya cafe shi kuma ya dora kaifin wukar akan wuyan yaron domin
yamasa yankan rago wani barde akusa dashi ya tara wani farin kasko domin jinin
yaron ya zuba a cikin sa.
Lokacin da wannan badakare ya dora KAIFIN TAKOBIn sa akan wuyan yaron da nufin yayi masa yankan rago
kwatsam! bazato babu tsammani sai wani mahayi yayo fitar burgu daga cikin duhuwar bishiyoyin daji kafin badakaren yayi wani yunkuri
mahayin ya zare wata sharbebiyar takobi agadon bayansa ya sare wuyan
badakaren kansa yayi futar burgu gangar jikin ta fadi kasa rikica sa.adda sarkin yaki lahmar yayi arba da gawar badakaren
sai ya dakawa sauran dakarun tsawa yana mai yi musu nuni dasu afkawa mahayin alokaci guda dakarun sukayi
dauki kan mahayin ana haduwa da juna aka kacame da azababban yaki mai matukar muni ban tsoro daban al,ajabi nan take karar karafniyar karafa ta cika dodan kunne ihu da kururuwar mazaje ta cika dajin gaba daya
duk inda badakaren yasanya agaba sai dai kaga mazaje na zubewa kasa matattu tamkar ana sassabe agonar
auduga dakarun suna kaina mahayi miyagun hare hare cikin matukar zafin nama, sa,adda wannan yaro makaho yaji wajen
ya kacame da artabu sai kawai ya durkusa kasa ya kama rarrafe ya boye abayan wani dutse, kafin shudewar dakika
saba,in mahayin ya kashe fiye da kaso shida bisa goma na dakarun, al,amarin da yayi matukar firgita sauran dakarun kenan
suka fara kokarin cika wandonsu da iska shi kuwa sarkin yaki lahmar koda yaga irin muguwar barnar da mahayin yayi masa sai
ya fusata ainun duk wannan fafatawa da akeyi saurayin dake kokarin ceto rayuwar yaron yana kwance magashiyan
yana kallon abinda ke wakana tsakanin mahayin dasu sarkin yaki zuciyarsa cike da matukar mamaki yana mai cewa acikin ransa
ya.akayi wannan mahayi yasan cewa ina cikin bukatar taimako?
amsar tambayar daya kasa bawa kamsa kenan lokacin da sarkin yaki yaga cewa mahayin ya kusa karar da dakarunsa
sai kawai ya sai kawai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye
tamkar an harboshi daga cikin baka yana saman ya zare wadansu zaratan takubba agadon bayansa ya dira adaf da inda mahayin yake alokacin da sauran dakarun sukaja da baya aka fara kallon kallo tsakanin su.
Abin tambaya anan shine anan shi ne daga ina wannan saurayi da wannan yaro suka fito,
Ku ma mene ne dalilin da ya sanya wadannan dakarun ke farautar rayukan su,
Dalilin hakan kuwa shi ne kamar haka.
**** ***** *****
Fiye da shekaru dubu biyu da arba'in da hudu a yammacin gaɓar tekun Bahar maliya anyi wani ƙasaitacciyyar kasa da ake yiwa laƙabi da zawatul-ifdal
Kasar madinatul-ifdal ya bunƙasa a arziki f
annin noma da kieo,siye da siyarwa, daɗin daɗawa kuma sun tara ZARATAN MAYAKA masu juriya a filin yaƙi
Sarkin dake mulkin birnin yakasance gawurtaccen jarumin jarumai,kuma shararren MATSAFI, shekarun bazasu haura hamsin ba,
Ana yi masa laƙabi Shazwan ibn zamaran,
Sarki Shazwan yana da matar aure guda ɗaya jal wacce ta haifa masa ya guda ɗaya mai suna sulairat,
Gimbiya sulairat takasance kyakkyawar gaske da labarin kyawun ta ya watsu a nahiyar baki ɗaya
Ta gaji mahaifin ta sarki Shazwan a fagen sadaukantaka da ilimin tsafi,
Mutanen kasar madinatul-ifdal suna zaune lafiya babu tashe tashen hankula sai kash akwai wata matsala guɗa ɗaya da take ci musu tuwo a kwarya,
Wannan matsala bata bace face bayyanar wata GOBARAR DAJI,
Da kan bayyana duk bayan wata shida, ma,ana dai a shekara sau biyu take zuwa
Gobarar tana taso wane daga wani daji dake makwabtaka da kasar,
Duk sa'adda da annobar ta bayyana tana haddasa rasa rayukansu jama'a,dukiyoyi na miliyoyin nairori,
Gami da rushewar gine-ginen jama'a
Bokayen nahiyar gami da masu bincike sun ce GOBARAR DAJI n tana bayyana ne sakamakon waɗansu hatsabiban matsafan aljanu,
Wasu kuma suka ce wani shuumin boka ne ke haddasa GOBARAR DAJI ma,ana dai babu matsaya guda ɗaya ingantacciya game da annobar
Sa,adda Sarki Shazwan yaga cewa wannan annoba taki ci taƙi cinyewa kuma ya ziyarci manyan bokaye amma babu wata mafita,
Sai kawai ya yanke shawarar ya tara gaba ɗaya bokayen sa kowannen su ya shiga gudanar da bincike na tsawon mako biyu domin nemo bakin zaren ,
A ranar da mako biyun ya cika bokayen suka hallara a wani daƙin sirri bisa jagorancin shugaban bokayen wani dattijo ma, abocin kwarjini mai suna Dargas ibn Aumal,
Sa,adda Sarki Shazwan yaga cewa dakin taron yayi shuru,
Sai kawai ya katse shirun daya wanzu ta hanyar buɗar baki yayi gyaran murya yace"yaku waɗannan bokaye masana ilimin tsafi shin ina sakamakon da binciken ya baku? Game da mafitar abinda yatara mu anan
Koda jin wannan batu sai bokayen sukayi shiru wannan ya kalli waccan,wancan ya kalli wannan aka rasa wanda zai ce kala a cikin su,
Daga can sai sarkin bokaye Dargas ibn Aumal ya mike tsaye ya fuskanci ya fuskanci sarki sannan yayi gyaran murya gami da gyara riƙon kwagirin dake hannun sa cikin kakkausar murya yace
"Ya shugabana zance mafi rinjaye da bincike ya tabbatar mana shine
Babu wani matsafi ko wasu miyagun aljanu dake haddasa GOBARAR DAJI face wani hatsabibin jarumi dan baiwa mai tattare da abubuwan al'ajabi
Da a halin yanzu babu wani GWARZON MAYAKI kamar sa atsakanin duniyar mutane da aljanu ana yi masa laƙabi da HIBAIRU IBN SHARWAZ ma'ana SARKIN SADAUKAI,
HIBAIRU yana rayuwa ne a cikin daji bashi da abokin ma'amala da ya huce aljanu da dabbobi tun yana jariri mahaifiyar ta rasu bayan ta haifesa a cikin dajin
Wannan dalili ne yasanya gaba ɗaya ɗabi'un sa irin na dabbobi ne yana da jarumtaka domin komai girman bishiya idan ya naushe ta take zata jijjigo har jijiyar ta ta faɗi ƙasa,
Yana iya saɓa zaki,ɓauna da damisa a kafadar sa yayi gudun daga bakwai baare da ya gaji ba,
Batun yaƙi kuwa komai tsananin yawan abokan gaba a cikin abinda bai gaza daƙika ɗari biyu ba yana iya karar dasu,
Wani abin mamaki ga HIBAIRU shi ne dudu du shekarun sa basu haura sha bakwai ba,
GOBARAR DAJin kuwa tana Bayyana ne a lokacin da Hubairu ke bawa wani tsuntsun tsafin sa horan yaki,
Horan yaƙin da Hubairu ke bawa kansa yana yi ne kawai domin kare martabar dabbobin dake dajin domin a ganin sa sune zuri,ar sa da danginsa
Domin bai taɓa ganin wani bil'adama a rayuwarsa ba
Sa'adda shugaban bokaye Dargas yazo nan ajawabin sa sai sarki Shazwan ya cika da matukar mamaki da al ajabi,
Shugaban bokaye Dargas yaci gaba da cewa
Bincike ya tabbatar dacewa SARKIN SADAUKAI zai bayyana a wannan duniya tamu ma,ana zai shigo cikin yan uwan sa bil,adama
Amma sai bayan ya kammala bawa tsuntsun tsafin nasa horan yaƙi,
Tare da kammala karanta waɗansu dalasiman tsafi dake jikin wani zoben sihiri dake sanye a hannun sa na hagu
A dadin sirrikan tsafin dake jikin zoben shine iya adadin dabbobin dake dajin
Bincike bai bayyana a yau shene zai kammala karanta sirrikan tsafin ba
Sai dai akwai hanya guda ɗaya da zamu bi wajen kawo karshen GOBARAR DAJI hanyar kuwa ita ce.
08137237071
Yazama wajibi a yanka yaro makawo Maraya ba uwa babu uba,
Za,ayi amfani da jinin sa ne wajen zubawa a cikin rijiyar bauta dake tsakiyar birnin mu
Wannan shi ne Abin da mafi yawan binciken sauran yan uwa na bokaye ya tabbatar,
Sa,adda sarkin bokaye yazo dai dai nan a zancen sa sai sarki Shazwan ya cika da matukar farin ciki maral musaltuwa amma sai ya dubi boka Dargas alokacin da yakoma kan kujerar sa ya zauna yace buɗi baki yace dashi
"Yakai masanin ilimin tsafi naji dukkan bayanin ka sai dai ina da tambaya guda biyu,
Da farko ina so nasan a ina zamu samu yaro makaho kuma maraya,
Sannan ta Wace hanya zamu tsira daga sharrin SARKIN SADAUKAI a lokacin da zai fito daga dajin Baitul-shamshan?
Ko dajin wannan tambaya sai sarkin bokaye yayi shiru yana mai zurfafa cikin kogin tunani,
Daga can ya cigaba dacewa
Ya shugabana ahalin yanzu yaron da za'a yanka yana cikin dajin kasar ka tare da wani jarumi daya ke kula da Rayuwar sa tun bayan rasuwar mahaifan sa,
Game da amsar tambayar ta biyu kuwa bayani ne mai tsawo da yake buƙatar bincike da dogon nazari,
Yanzu dai abinda yafi muhimmanci da zamu gabatar shine,
Farautar yaro makaho domin magance GOBABR DAJI,
Dake tunkaro mu nan da mako shida,kasan masu iya magana nace wa idan duka yayi yawa naka ake karewa
Yayin da boka Dargas yazo dai dai nan azancen sai sarki Shazwan ya cika da matukar farin ciki,
Take bokayen suka yi bankwana,
Su rabu akan cewa zasu sake gudanar da bincike a karo na biyu akan gano mafita game da SARKIN SADAUKAI bayan sun ɓace cikin alkalumman sihiri,
Sai sarki Shazwan ya shafi wani kambun a damtsen sa da hannun sa na hagu ya ɓace bat tamkar bai taɓa wanzu wa ba,
Bai bayyana a ko ina ba sai a cikin turakar sa,
Koda bayyanar tasa sai ya kwallawa wata kuyangar sa kira,
Kuyangar ta bayyana a gaban sa ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa,
Sarki Shazwan ya dube ta yace"ya Sunaila ina so ki tafi izuwa gidan Sarkin yaƙi kice masa ina son ganin sa yanzu cikin gaggawa,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Shazwan sai kuyanga Sunaila ta sake risina wa tace "An gama ya shugaba na,
Tana gama fadin hakan sai ta mike tsaye ta fice daga turakar da sauri,
Kawai sai sarki Shazwan ya dunga kai komo acikin turakar ya kasa zaune ya kasa tsaye,
Yana cikin wannan hali ne Sarkin yaki ya bayyana agare sa ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin ladabi,
Sannan ya buɗi baki yace"Gani gare ka ya shugabana me kake da buƙata?
Sarki Shazwan yayi gyaran murya sannan ya ce"Yakai Sarkin yaki lahmar kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi zuwa dajin dake ƙasa ta ka farauto mini wani yaro makaho dan shekara biyar,
Farautar yaron shine zai tseratar da rayuwar gaba ɗaya al'ummar birnin mu daga GOBARAR DAJI,
Zaɓi biyu gareka kodai ka kawo mini yaron a raye ko kuma ka yankashi ka kawo mini jinin sa,
Koda jin wannan umarni sai sarkin yaki lahmar ya ce "An gama ya shugabana cikin wannan zaɓi biyu da ka bani Dole ne ɗaya yakasance,
Koda gama faɗin sai sarkin yaƙi ya mike tsaye ya nufi kofar fita daga turakar,
Kallo ɗaya zakayi wa sarkin yaki ka fahimci cewa ya cika mai karfi na Allah na isa,
Duk da kasancewar sa saurayi amma yana da kirar samudawan farko,ya tara kwanji mai cike da curi curin tsoka tamkar duwatsu aka cuccusa masa a ciki yana da doguwar fuska mai kyawu da kwarjini
Da saje da gemu bakake sidiƙ,
Idan ka ɗauke sarki da gimbiya a gaba ɗaya Birnin Madinatul-ifdal babu gwazon mayaki kamar sa
Kuma ya gaji sarautar ne awajen mahaifin sa ma,ana sarautar ta su gado ce,
Koda ficewar Sarkin yaki lahmar sai ya ɗebi dakarun yaƙi guda dubu talatin bisa dawakai suka fice daga cikin birnin madinatul-ifdal,
Sa,adda suka fice sai suka wanzu suna nausawa cikin daji suna lafiya cikin hanzari,
Yar gajeriyar tafiya su kayi suka fara hango wata yar bukka a dajin guda ɗaya jal,
Don haka sai suka kasu huɗu, wadansu sukayi bangaren yamma,gudu,gabas wasu arewa, suna masu yiwa bukkkar kawanya
Cikin azama Sarkin yaki ya umarci wadansu dakaru Mutum dubu hudu suje su bude wannan bukka su fito da abinda ke cikin ta
Yayin da dakarun suka zo dai dai bukkkar sai suka kewaye ta wadansu mutum ashirin daga cikin su suka kunna kai izuwa ciki,
Kaico hakika rashin sani yafi dare duhu domin inda waɗannan dabaru sun san abin da zai biyo baya da basuyi gangancin shiga bukkkar ba.
Dakarun dake tsaitsaye suna jiran fitowar yan uwan su sai kawai suka ga an wurgo gawarwakin dakarun daga cikin bukkkar,
Al'amarin da ya fusata sauran dakarun kenan suka dunga kunna izuwa ciki,
Nan ma sai yazamana gawarwakin su ake ta jefowa waje koda ihu basa yi
Kafin wani lokaci fiye da rabin dakarun sun sheka barzahu,
Koda ganin hakan sai Sarkin yaƙi lahmar ya fusata ainun ya tako da kafafafun sa har izuwa bakin kofar bukkkar yana mai dakawa sau ran dakarun tsawa dakarun suka ja da baya,
Sannan ya yunƙura da nufin ya kunna kai izuwa cikin bukkkar,
Kwatsam bazato babu tsammani sai kawai yaji an gabza masa wawan naushi a fuska saboda karfin naushin sai da yayi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim!,
Kafin Sarkin yaki ya yi wani yunkurin mike wa tsaye sai kawai akaga wani kyakkyawan saurayi yayo fitar burgu daga cikin bukkkar kafadar sa rataye da wani ƙaramin yaro ,
Sa,adda dakarun suka yi arba da saurayin sai kuwa suka ce dawa Allah ya haɗa mu
Kawai sai suka zare makaman su suka rufa masa baya suna ihu da kururuwa mai firgitar wa,
Koda ganin hakan sai saurayin ya falfala da azababban gudu i zuwa cikin dajin,
Nan fa dakarun suka dinga kai masa hare hare ta ko ina amma sai yazamana saurayin yana tsallake wa
Duk yawan kibiyoyin da suke harba masa sai yazamana yana zille musu cikin gwanintar yaki
Ana cikin wannan hali ne saurayin ya bace musu daga gani ya shige cikin duhu.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya waɗannan dakaru ke biye da wannan saurayi mai ɗauke da ƙaramin yaro domin ya hallaka shi.
koda sarkin yaki yayi arba da idanun mahayin sai yaji zuciyarsa
ta buga da karfi abinda ya fado masa azuciya shine duk da cewar bai ga
fuskar mahayin ba amma yaji ajikinsa cewa tabbas ya taba ganin fuskar mahayin sai dai abin tambaya anan shine a,ina
yataba ganin mahahin kuma mace ce.ko namiji amsar tambayoyin
da sarkin yaki ya kasa bawa kansa kenan kawai sai ya daga takubbansa
sama ya falfala da azababban gudu izuwa kan mahayin yana kwarara ihu
koda ganin hakan sai mahayin ya dako wawan tsalle daga inda yake ya kaiwa sarkin yaki lahmar wawan sara da takobinsa
da nufin tsinke masa wuya cikin zafin nama sarkin yaki yasanya takobinsa ya kare saran sannan suka rugunntsume da
masifaffan yaki suka wanzu suna kaiwa kaiwa juna sara da suka cikin matukar zafin nama juriya da bajinta ta gaban kwatance
wohoho! tabbas jarumtaka da sadaukantaka baiwa ce daga Allah komai hassadar mutum idan yaga yadda gwanayen biyu ke tsallakewa.
miyagun hare-haren
juna dolane ya jinjina musu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA
azahiri ga wanda yake kallon yadda artabun yake wakana zai fahimci cewa
sarkin yaki yafi mahayin karfin damtse sai dai mahayin ya fishi tsagwaron sanin salon yaki nanfa yazamana cewa jaruman biyu har daka tsalle sama su keyi suna kaiwa jhna hari wohoho!
tashin hankali ba.a
samaka rana GOBARAR ANNOBA kuwa idan ta taso babu mai dauke ta face Allah,
Nanfa yazamana cewa bama bishiyoyi da duwatsun dake dajin ba hatta sauran dakarun
suna cikin matukar tashin hankali domin bishiyoyi dake karairayewa
sakamakon artabun jarman biyu suna yunkurin murkushesu bashiri suka kama guje-guje gami da ifice-ifice ana cikin wannan artabu ne
mahayin yayi tunani tunanin kuwa shine matukar aka cigaba da wannan artabu wannan jarumi dake kwance magashiyan.
zai iya rasa rayuwarsa koda gama tunanin hakan sai kawai ta shammaci sarkin yaki ya gabzamasa wawan naushi a kirji saboda karfin naushin sai da yayi katantanwa asama sau hudu sannan ya kife akasa
Kafin yayi yunkurin mikewa mahayin ya karanto wadansu dalasiman tsafi ya rikida izuwa wata bakar guguwa ya tashi izuwa
sama ya keta gajimare ya bace bat! sarkin yaki ya mike tsaye zumbur
kawai sai yaga wajen wayam babu mahayin da saurayin da wannan karamin yaro cikin matukar takaici gami matsanancin
fushi ya takarkare ya kwarara wawan ihu acikin wannan hali ne kwatsam!
sai sarki shazwan,sarkin bokaye Dargaz,waziri Rufyanda wadansu zaratan dakaru suka rugo izuwa wajen abisa dawakai sukayi tirjiya
Sarki shazwan yakama linzamin dokin sa ya sauko ƙasa, Sarkin bokaye, waziri,da sauran dakaru suka yi koyi dashi,
Sa'adda Sarkin yaƙi lahmar yayi arba dasu sarki shazwan sai gabansa ya faɗi, cikin matukar razana ya sunkiyar da kansa kasa na alamun jin kunya a