𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 _TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_ https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy _TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_ https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K _TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_ https://arewapen.com/u/prettys01 *✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽* _In the name of Allāh the Entirely Merciful, the Especially Merciful._ _Godiya da yabo su ƙafa tabbata ga ubangiji talikai mamallakin sammai da kasai Allah❤️._ _Tsira da amincin Allah su Kara tabbata ga fiyayen halita annabi Muhammad (s. a. w)❤️_ *GODIYA MARA IYAKA* _Ga dumbin mabiya litattafaina a duk inda kuke cikin kasar Allah. Ina matukar alfahari daku, kuma ina kaunarku kamar yadda kuke kaunata 😍💃 nima PRETTY SK Ina ƙaunarku har cikin raina 💋❤️._ > “I will succeed. Not immediately. But definitely.” in shaa Allah. *GARGAƊI* _Wannan littafin mallaka nawa ne *Pretty SK ✍️* , Ina Gargaɗin kar wani ya sauyamin komai dake cikin littafin nan, sannan kar a sanya min shi a YouTube ko wani website ba tare da izini ba, ga duk mai son karantawa ko wasu daga takadduna to direct ya min mgana._ > 07038436703 \ 08126151523. _WANNAN ZAZZAFAN SHIRIN MAI TAKEN 𝒀𝑨𝑹 𝑵𝑶𝑳𝑳𝒀𝑾𝑶𝑶𝑫 ZAI ZO MUKU DA SABON SALO MAI BAN MAMAKI, HARGITSI MAI CHAKWAKIYA, ƘADDARA MAI RADAƊI, FARINCI MAI YANKE WA DA HAƘURI MAI CUTARWA......HMMM DUKKA DAI A CIKIN LITTAFIN NAN *ƳAR NOLLYWOOD*._ *_ITA SAM BA KANNYWOOD TAKE SO BA, HOLLYWOOD TAKE SO AMMA GANIN YA MATA NISA KUMA AKWAI MATSALA YASA TA KOMA SON NOLLYWOOD GADAN-GADAN, BA TA JIN DUK DUNIYAR NAN AKWAI MAI HANATA FILM ƊIN NOLLYWOOD......... HMMMM KU DAGA NAN KUSAN AKWAI MATSALA NA MUSANMAN._* ______________________________________ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* _Jarumta shine taken mu, Rubutu shine madubin mu, basira shine aikin mu, motsa zuciyar masu karatu shine baiwar mu, mun rungume alƙalami dan haskaka al'umma_ ______________________________________ *𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅* *Dream – Love – Rebellion – Evil – Drama & Hatred* Story and writing✍️ ```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊 ``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️* _BOOK ONEIS FREE🥰_ _E.P________1️⃣⏩2️⃣_ “ACTION” Faɗin wani ƙaton baƙin mutum dake zaune kan kujerar roba. Yana sanye ne da riga t-shirt da wando three-quarter, wiyarsa na ɗauke da sarƙan cross, sai p- cap da ke kansa, a kallo ɗaya za ka fahimci babban arne ne, duba da shigarsa da kuma fuskarsa da babu hasken musulunci ko kaɗan. Take masu cameras suka fara ɗaukan video na wani saurayi dake tsaye shi da wata budurwa. Saurayin shi dai dogon wando ne jikinsa da riga mai dogon hannu, sai macen dake tsaye gabansa, riga ce iya gwiwa ke jikinta, ta matseta sosai, ya bi jikin ta ko ina, sannan ga kanta wanda ta sanya attachedment kai ka ce kashin tane dan yarda ya zauna. A karo na ba adadi na yi murmushi, ina tsaye daga gefan Director, duk na ƙosa a ban dama da na shiga filin nima. A lokacin da ya kalleni alamun zai yi min sign na shiga filin, take wani duka ya shiga fatata, wanda ya sa na tsala ihu ina dawowa duniyar gaskiya, baki na yana faɗin. “Director see meeeee." A ɗan gigice na tashi daga barcin da ya ɗauke ni a mota. Tsaki na ja mai tsayi wanda babu wanda zai ce daga ƙaramin bakina ya fito, take na kalla gefan da na ji wannan dukan. Sai idanuna suka haɗu da na ƴaƴanta da ke dallamin harara. “Shashasha!, fitar min a mota, saboda ke na yi latti, yanzu 8:12am, ni da zamu shiga Lecture 8:00am. Fitar min a mota, in banda hauka daga gida zuwa nan shine za ki yi barci, harda shegen mafarkin nan ne hauka.” ta faɗa cike da ɗaga murya, murmushi na ɗan yi dan wallahi ina so naga ina ɓa ta mata rai. “Stop insulting my dream ehe, because it means more to me than anything else in life.” Murmushi kallon mahaukaciya ta yi min. “Hmmmm yaro man kaza, fita kafin na makeki, kuma wallahi idan ba ki bar wannan maganar ba sa na faɗa ma Dad." “Uhmmmm a huce haka Ashenty." Na faɗa ina buɗe motar. Makarantar mu na kalla wanda manyan motoci ne ke ta sauke yara, har na fara tafiya na tsaya cak da jin abin da take cewa. “So you left your lunch bag with me, right?." Dan nasan sai 6pm zan koma gida shi yasa na koma baya tare da ɗaukan lunch bag ɗina. Ga ƙaton jakka ga lunch bag, ɗauka na yi sannan na marairaice fuska, kallon yayata nake wacce muke maka da ita, sanye take da dogon hijabi ɗinkin Jalbab, maroon colour, ta yi ƙyau sosai, fara ce mai dogon hanci, ga ƙaramin baki, sannan ga fararen idanuwa masu ɗaukan hankali, ba ƙyarya muna da ƙyau mai sunan ƙyau, dan Dad ɗin mu shuwa ne Mom kuma buzuwa ce. “Uban me kika tsaya yi, rifomin ƙofata.” ta faɗa tana son ta da motar. Fiƙi-fiki na yi idanuwa sannan cikin ladabin da nake yafa ma kai na idan ina bukatar abu a wajen ta nace. “Auntyna.....Aunty Aishataahhh." Murmushi ta yi dan tasan sauran. “Please give me some money for break.” Na faɗa cikin salon magiya. “A gabana Mom ta baki ₦500, to kuɗin me zan kuma baki?." Tsaki na ja a cikin raina, amma da yake ina so sai na ce. “Wallahi bayarwa zanyi, wata yarinya zan ba kyauta.” “Hmmmm.” ta faɗa tana ciro ₦500 daga jakkarta, bani ta yi, na amsa ina washe baki har dimple ɗina na lotsawa. “Ko duk duniya za su taru bazan yadda ke ce za ki yi ƙyautar kuɗi ba, hmmm na sanki fa." Da haka ta figa mota da gudu dan dama ita gwanace da iya wasan mota. Murmushi na yi ina ɗaga kafaɗa, dan ko a jikina, da haka na nufa bakin get, har an fara taran latti, amma da yake ansan ban yin latti sai suka bar ni na wuce. Babban makaranta ne wanda a ido kasan na masu kuɗi ne. Duk wasu masu ji da kuɗi to yaransu a school ɗin nan suke. School ne wanda akwai Musulmai da kiristoci, uniform ɗin mu, blue and white ne, Rigar blue mai gajeran hannu zuwa gwiwa, sai farin riga ta ci mai dogon hannu da ƙwala. Musulmai mukan sanya legis a ciki, sannan gaba ɗaya bama sanya hijab, sai hula. To Ni wani lokacin ma nawa na jakka, haka nake yawo na da gashin kaina. A lokacin islamiyya ne kawai muke sanya hijab blue har ƙasa . Tafiya na fara yi cikin babban makarantar, har na hau stairs, bene na ƙarshe a can S.S section yake, ina hawa na nufa S.S.3, hamdala nayi ganin babu teacher, shiga na yi kai na tsaye, bayan na yi signing da rubuta time ɗin da na shigo, akan wani book dake kan desk na teacher, dan haka tsarin yake shiyasa ko wani class akwai agogo babba daga saman whiteboard, Dan kana shigowa ka duba tare da rubuta lokaci. Da mazan dake set ɗin gaba muka fara gaisawa ta hanyar tafawa, haka muka dinga kashe tafi muna cewa. “Hey/Hello.”. Haka sai da na bi kowa na ajin, mu 24, maza goma mata sha-huɗu. Sit ɗin ƙarshe na nufa wanda a nan nake zama, kowani desk mutum biyu ne, akwai wajen aje bag da lunch bag, ajewa na yi ina gaisawa da wacce take gefena, wato mutumiyata. “Jennifer, how are you?.” “Am fine Dear Rose.” murmushi na yi dan sunan na a school kenan *Rose*, saboda ina son sunan. Yau dai ban cire hula ba na barshi, daga lokacin teachers suka fara shigo ma na, har zuwa lokacin break, dama lokacin nake jira, ƴan class ɗin wasu suka fita wasu kuma suka zauna. Ni dai nishaɗi nake sosai ba dan komai ba sai dan abin da Jennifer ta fito min da shi, *Waya* ce, ƙirar tecno spark 4, Wanda yake mallakina, babu wanda ya san ina da shi sai Jennifer, na sha wahala sosai kafin na haɗa kuɗin wayar, sannan kullum in na zo ina ba ta 500 na data. “Thank you so much jennifer.” na faɗa dan ganin wayar a 100%. Murmushi ta yi tana cewa. “Yesterday, *To Kill a Monkey* Episode 5 was released." Take na buga desk ɗin gabana, tare da ɗan ihun murna sannan da yi mata waƙan Auta waziri. “Ahhhh, ki sani komai, nisan-nisa ba zana barki baaa......ba za na ɗauki watanki in ijiyeki anan baaaaa....” na faɗa ina nuna zuciyata, dariya muka yi harda tafawa, ƴan aji kuma suka yi murmushi dan yarda na yi waƙan ba magana, har wani action na yi fa. “Me too I love you Rose.” Da haka ta yi waje ni kuma na toshe kunnuwa na hau kallon *Nigeria Film* kamar yarda na saba, downloading nake yi wani lokacin kuma Jennifer ke turo min. Ni dai Allah ya yi da son fina-finan 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅Saboda shi, yasa na siya waya, na sha wiya sosai kafin na haɗa 35k, kullum aka ban kuɗi nake tarawa, sannan na yi ta ƙarerayin, daga in ce. “Zan sai abu - Wata ba lafiya zamu siya mata abu, - an sake abu a class ɗin mu, to ance duk sai mun haɗa kuɗi, amma Dad na ce ni zan biya dukka.” Hmmmmm da haka na siya wayar, so nake da mun gama secondry school, na ta fi University a wani state, a can zan zama *ƳAR NOLLYWOOD*, wanna shine burina kuma muradina, ban jin akwai mai shiga tsakanin wannan burin nawa. Film biyu na kalla sannan aka dawo class, haka muka kuma shan karatu, nifa duk wasana nice first class, Banda wasa akan karatu, ban ta ɓa cin second position ba, ko dan idan na je shiga Film na shiga da class. Sai 2:00pm aka tashi, sai da muka yi Sallah sannan muka ci abinci sai muka koma part ɗin Islamiyya, ƙawata Kirista ce ta wuce gida, sam ban jin daɗin Islamiyya saboda banda ƙawa, kuma ina sa wasa sosai, zan iya cewa ko Exam ban wani yi na islamiya, gaba ɗaya sai a hankali dai. Kamar kullum sai 6:00pm aka tashi, Driver na be da lafiya shi yasa Ashenty ke kawo ni da ɗauka ta, ina tsaye daga bakin get ta cikin school, sai gata nan ta faka, sai da ta fito muka yi signing tare sannan muka bar bakin school ɗin, dama dokace idan student ya shiga shi zai yi signing, in kuma aka tashi sai wani nashi ya zo su yi signing da rubuta number. Na gaji sosai shi yasa ban ne ma faɗar ta ba, ita ma Driving kawai take yi a natse. Bayan mun ɗan yi tafiya muka shiga layin mu, bayan mun kai bakin get ɗin mu, ta yi horn. Sai da me gadi ha buɗe get sannan muka shiga gidan, sai da ta daidaita parking sannan na fito, da gangan na bar lunch bag ɗina. Tafiya nake yi cikin sauri-sauri harda ɗan gudu duk dan karta kirani. Babbane gidan mu sosai, wanda ya gaji da haɗuwa dan kuwa mahaifina mai suna Alhaji Musa babban mutum ne wanda yake cikin siyasar ƙasar nan, sanan yana da kamfanoni Barkatai, a taƙaice dai yana da kuɗi sosai. Gidan mu mai hawa biyu ne, akwai ɗakuna masu yawa a ciki amma kaɗan daga ciki ne muke amfani da shi. Mu huɗu ke rayuwa a ciki bayan masu aiki, Dad, Mom, Ashenty da kuma Ni. Dukda ba mu kaɗai suka haifa ba, an fara haifan Muhammad wanda shekara ɗaya ya yi ya rasu, sannan aka haifa wani Usman shi kuma tun yana jariri ya rasu, sai Ashenty, kafin ni ma an haifa Sadiq sai dai shima ba mai tsawon rai bane, ko shekara be yi ba ya bar duniya sai kuma Ni, hmmm mazan suke sheƙawa suka barmu, Allah dai ya jiƙasu. Ina shiga babban falon namu na yi kan Mom wacce ke kallon labarai a N.T.A, rungumeta na yi ina murmushi. “I'm back Dear." Na faɗa ina sakin ta. “My Daughter you're welcome.” sai na zauna gefanta ina cire hijab ɗin islamiyya, idanunwa ta zuba min dan kuwa kaf gidan mu na zarce kowa a ƙyau. Mom fara ce sosai wanda yayi sirki da ja-ja, tana ƙyau sosai, ga jiki masha Allah, nakan rasa tsakanin ita da Dad waya fi ƙyau haka kuma da A'isha, amma dukkansu suna cewa na fisu ƙyau sosai. “My beautiful girl, Kullum ƙara ƙyau kike yi, balle yanzu da aka fara zama ƴam mata.” ina jin ta faɗa haka na miƙe ina ina gudu-gudu, tare da dariya, a nan na bar hijab ɗin da jakkata. Murmushi ta yi tana ɗan girgiza kai. “Inayah akwai kunya.” da haka ta mai da kanta ga tv. Ni kuwa stairs na hau, ɗakin farko shine nawa amma na wuce na shiga na gaba wato na Ashenty, ina san zuwa room ɗin ta saboda tana da tv, ai kuwa Ina shiga na kunna tare da hayewa kan bed Ina zaɓan channel. (African zone) shina shiga wani Nigeria Film suke yi mai suna *Two father* . Ina cikin kallo Hajiya mai ɗaki ta shigo tana dallamin harara dan kuwa ta tsana na shigar mata room saboda ɓata mata nake yi kuma ban gyarawa. “Shine kika bar min lunch bag ɗin ko? Hmmmm Inayah bansan yaushe ki ka raina ni ba.” ta faɗa tana cire Jalbab ɗin jikinta. Maimakon na bata amsa sai na ce. “Aunty Aisha yanzu za'a gama, Please ki bari ya ƙare, ban fara daga farko ba amma so nake nasan waye real father ɗin.” “Hmmm lallai kam.” ta faɗa tana kashe Tv. Tashi na yi daga gadon ina tafiya tare da cewa. “Very soon za ki fara gani na a ciki, ko meye abin damuwa akan haka, Insha Allah very soon zan......” ban gama faɗin abin da ke bakina ba ta janyo ni zuwa baya, sannan da sauri ta tasha gabana tana kulle ƙofar harda murza key amma ta bar key ɗin jinkin ƙofar. Kallona take cikin ido kamar yarda nima nake kallonta cikin ido, har ɗan wani hawa na yi kamar wacce za ta fashe, ba ko tsoro na tsaya gabanta muna kallon juna, har da ɗan ɗaga mata gira na yi dan neman ƙarin bayanin akan abin da ta yi min, A'isha kuwa kallona take kamar da rufeni da duka, sai dai yarda ba za ta iya ba saboda tana mugun sona......................✍️ END. > The beginning 🤭🤭🤭🤭 > 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 > A yi haƙuri da Update na riga na raba su a haka. *PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇: 📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥* #LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️🔥 *𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅* _TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_ https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy _TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_ https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K _TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_ https://arewapen.com/u/prettys01 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* *BOOK ONE IS FEEE, WHILE BOOK 2 IS ₦500* *𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅* Story and writing✍️ ```PRETTY SK``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ _E.P______________3⃣⏩4️⃣._ _Previous_ > Kallona take cikin ido kamar yarda nima nake kallonta cikin ido, har ɗan wani hawa na yi kamar wacce za ta fashe, ba ko tsoro na tsaya gabanta muna kallon juna, har da ɗan ɗaga mata gira na yi dan neman ƙarin bayanin akan abin da ta yi min, A'isha kuwa kallona take kamar da rufeni da duka, sai dai yarda ba za ta iya ba saboda tana mugun sona......................✍️ _Continuotions_ __________________“Inayah, magana zan yi dake.” ta faɗa tana zama kan sopa, ganin ta sake rai nima na sake nawa ina zama a kan dressing mirrow, sai da ta furzar da iska daga bakinta sannan ta ce. “Sherunki nawa?." Jin tambayar da ta min yasan na ɗan murmushin basawa sannan na ce. “Shekarun ki a cire 3 kacal, ke 21 ni kuma 17 kinga kusan mate muke.” wani kallo ta watsi min shi yasa na ɗan natsu. “Hmmm, be serious. I don’t want madness.” sai na gyara zama ina ƙara ware mata dara-daran idanuwana masu haske da ƙyau. “Me yasa kike son zama ƴar Film?.” sai da na yi fari da manyan idanuna, sannan na ce. “Coz I love it.” “Ke yanzu rayuwar Ƴam matan Hausa Film ne ke burgeki.......” da sauri na katseta. “Nifa ba kannywood nake so, *NOLLYWOOD* nake so.” Hannu ta ɗaga min alamun na yi shuru. “Ke fa Musulmace. Dad da Mom ba su da burin da ya wuce ki zama Doctor, amma......” “Nifa bance ba zan zama doctor ba, dukka zan haɗa.” da sauri ta miƙe tsaye, sannan ta nufa tvn dake jikin bango ta kunna. Channel ɗin ɗazu ne in da ake wani film, ɗaga gani zai yi daɗi har na fara murmushi sai na ji ta ce. “Yanzu wannan kike so? Yanzu irin wannan iskancin kike so ki din ga yi.” ta faɗa a daidai in da aka nuna club, mata da maza suna rawa, mata da wasu tsinannun kaya, yawanci saman ƙirjinsu duk a waje, Mazan dai sun fi shiga mai ƙyau, yawan ci suna jikin juna, suna rawa abun dai ba tsari. Wani aka hasko wanda ga alamun star ɗin Film ɗin ne, shi da wata budurwa ne suka riƙe da juna, magana ya fara mata tana yin murmushi, sai kuma ta raba jikinsu za ta wuce da saurin saurayin ya juyo da ita tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Da sauri na kauda kai na daga Tvn. “Ki kalla mana. Ba irin wannan kike so ba.” cikin ɗaga murya kamar yadda ta yi maganar nima na ce. “Ni sam ba haka ba, ba zan yi irin wannan ba, kuma Ni a maid nake so na fito, a ban kaya ne mutumci zuwa ƙasan gwiwa kamar dai wannan uniform ɗin nawa.” shiru ta yi tana girgiza kai tare da min wani irin kallo. “Fita...... Fita.” ganin yadda ta haɗe fuska yasa na fita da sauri, dan Ni ko a jikina, ko tsoron ta faɗa masu Dad ban yi saboda nasan tana sona ba za ta so ta ga ina kuka, kuma Ni Ko sun sani babu mai hanani film ɗin NOLLYWOOD 🔥. ********** ********** ****** *★GIƊAƊO MANSION★* _______Babban gida ne wanda yake da get guda huɗu, cikin gidan kuwa kai ka ce gari ne guda, dan kuwa Mansion ɗin ba ƙarami bane, gida ne mai hawa huɗu. Masu gadi kuwa a ƙalla sun kai 40 kowanne suna riƙe da bindigu, sannan duk wanda zai shiga sai an yi bincike kuma sai wani daga gidan ya tabbatar da wajensa zai je. Parking lot kuwa motoci ne ajere kala-kala masu tsaɗa. Masu gadi ne suka buɗe get ɗaya sannan wata mota ta kunno kai zuwa cikin gidan, a hankali motar ta faka a jerin motocin dake wajen, sannan aka buɗe, wata budurwar falullata ce ta fito tana kulle motar, farace masha Allah, a ƙalla ba za ta wuce 21yrs ba, cikin gidan ta nufa tana taunar chewing gum a natse. Ƙofar mai aiki da nunfashi ne, ya jin an matso yake buɗe wa, shiga ta yi wani tanƙameman falo mai ɗauke da kujeru ba iyaka, ga dukkan alamu gidan Family House. “Sarah." Da sauri ta juya dan jin muryan mahaifiyarta. Ilai itace murmushi ta yi tana nufan ɓangaren da take. “Ya makarantar." Mahaifiyar ta faɗa cike da kulawa. Ko ba'a faɗa ba ana ganinsu anga jini ɗaya, dan suna kama da macen dake zaune, Babbar mace mai jiki masha Allah, ga haske ga ƙyau, kana ganinta kasan jinin Fulani ne tsantsa. “Alhamdullah.” budurwar ta faɗa cikin sanyin hali. “To masha Allah, je ki huta.” sai ta miƙe har ta fara tafiya sai ta ji muryan wani saurayi daga stairs na uku. “Darling.....Darling.” tsayawa ta yi cak sannan ta ja ƙaramin tsaki ta na ɗaga kanta, da fuskarsa ta fara cin karo yana mata ɗan iskan murmushi. “Ki jira ni ina zuwa." Ya faɗa yana fara saukowa, daga in da yake zuwa wajenta akwai nisa sosai, amma tsayawa ta yi cak har sai da ya sauko. Saurayi ne wanda a kallo ɗaya za ka gane ɗan Allah ya shirya ne, dan kuwa shigarsa ma ya bayya haka, riga da wando ne jikinsa ƙananan kaya, sai wasu sarƙoƙi a wiyarsa kusan guda uku, haka hannunsa ma akwai su banda sosai, harda ɗankunne yake da shi a kunnuwan biyu. yana da ƙyau sosai, gashi dogo mai cika ƙirji, Babban star ne na fina-finan NOLLYWOOD, kuma tantairin mara jin magana dan kuwa kaf gidan shine babban ɗan Allah ya shirya, har zanen tattoo yana da shi a gefen wiyarsa ɓarin dama har ƙasa, ina da ka mai wani lafiyayyen zanen wata dabba. “Darling ya kike?.” ya faɗa da zazzaƙar muryarsa kuma cikin ɗan taushi. Saurayine ƙyaƙƙyawa dogo mai hasken fata sosai, sai dai shigarsa yana rage masa ƙyau sosai. “Lafiya." Ta faɗa da ɗan rawar murya. “Nasan kin gaji, je ki huta zuwa an jima zamu haɗu .” ɗaga mai kai ta yi sannan ta fara tafiya har da gudu-gudu ta hau stairs. A hawa na biyu ta yi kwana room 25 nan ta buɗe ta shiga. Tana shiga ta kulle da murza key. Hijab ɗin jikinta ta cire tana zama a ƙasa, ɗabas, ita har ga Allah ta tsana rayuwar *GIƊAƊO MANSION,* domin kuwa irin matsalolin dake cikin gidan, ji take dama Allah ya sa an haifota a talaka masu rayuwar kunci da ya fi mata akan rayuwar gidan *GIƊAƊO MANSION* Gida mai yawar al'umma, mai mabanbanta mutane da halaye, family ɗaya ne dukka amma yadda kasan gidan haya ko gidan yari, haka ake rayuwa a wahale babu damar rabuwa saboda wata *WASIYYA* guda ɗaya da ya zama silar zamansu a gidan, wato *WASSIYAR GIƊAƊO* wasiyyar da ya zama suka zama tsintsiya wanda bai da madauri kwata-kwata. Sai da ta jima sannan ta miƙe ta shiga bayi, wanka ta yi sannan ta sauya kaya, ba ta fita har sai da ƙarfe 8:00pm ta buga wanda lokacin cin abincin dare ya yi, ko ba ka jin yunwa dole ka hallaci cin abinci safe da dare, wannan dole ne, da safe ƙarfe 7:30am dole kowa ya fito ko da ba za ci komai ba, sai ka fito. Doguwar riga ne jikinta sai ta yafa vail sannan ta fita. A hankali take tafiya kamar wanda ƙwai ya fashe nawa, dama ita haka take da sanyi. Ji ta yi an bangajeta da sauri ta riƙe ƙarfen stairs ɗin da sauri, tana bin wacce ta buge ta da kallo. Girgiza kai ta yi tana ƙarasa sauka, sun saba da irin rayuwar nan a cikin gidan, balle ƴan ɗakinsu. Daga ko wani ɓangare sauka ake yi zuwa wajen cin abinci, ita ma nan ta nufa. Babban Dining area ne wanda yake da kujeru 50, kowa zama yake a nasa, gaba ɗayansu su 47 suka halarta wajen, babu mutum ɗaya, dan gaba ɗaya ƴan gidan su 46 ne yara da manya. Manya da yara duk suna zaune, amma babu wanda ya fara cin komai. Sarah tana saukowa ta zauna gefan mahaifiyarta tana ɗan yaƙe kamar yadda ta saba. “Ina Ayan? Shi kullum sai ya ɓa ta lokaci, salon ayi ta zaginsa” Bafullatanar dake gefen Sarah ta faɗa tana haɗe fuska. “Ummee ku mai uzuri, zai fito yanzu." Sarah ta faɗa tana mai kallon wanda ke zama a gefan ta, Ahmad ne wanda aka kira da A.G. murmushi yake sakin mata har da kashe mata ido. “Ummee Barka da dare." Ya faɗa yana kallon mahaifiyar Sarah. “Yauwa." Ta faɗa tana kauda kanta da kuma jin tsanar Ahmad a cikin ranta, kaf gidan shine ɗan Allah ya shirya, kuma aka rasa duk cikin samarin gidan wa za'a Sarah da shi sai shi. Manya maza guda huɗu uwaye 6 kowanne matansa biyu, amma biyu sun rasu, sannan kowa suna da yara mata da maza. *GIƊAƊO* shine kakan wannan dangin wanda yaransa biyu ne kacal Yusuf da Yunus sai yaran ƙannin sa wanda ya mai da su na shi, Adam da Musa, gaba ɗayansu ya raina cike da so da ƙauna. *GIƊAƊO* mutum ne mai tsatstsaurar ra'ayi, sai Allah ya bashi yara masu matukar biyayya. Shi ya gida wannan tangamemen gidan kuma anan ya yi rayuwa har mutuwarsa. Sai dai ya mutum ya bar *WASIYYA, kan cewa, so yake duk su aura mata biyu, su haihaifa, kuma su dinga haɗa aure a tsakanin su, ko da wasa kar wani nasu ya auro bare, ya zamana jininsa shine a cikin zuri'arsa.* Da haka yaransa suka ɗau wannan wasiyyar da muhimmanci, kuma ba su yi wasa da shi ba, ƴan dangi suka auro dukka, suka haifafa kuma suke haɗa aure, ko mutum ya so ko bai so ba haka nan yake yarda, a wasa-wasa, an yi aure 8 na yaran gidan. Yaron Musa ya aura yarinyar Yusuf, sannan yaron Yusuf ya aura yarinyar Adam, sai yaron Yunus ya kuma auren yarinyar Adam. Haka suke haɗa wa, kuma a gidan kowa ke rayuwa, yanzu mata huɗu suka rage da maza biyar, sai kuma yara masu tasowa. “Ina Ayan?." Faɗin Baba Adam wanda shine mahaifin Ayan da Sarah da wasu biyu. “Kunsan halinsa ai, sai ya gama ɓa ta mana rai zai fito." Matar Yusuf ta faɗa wacce ita ce mahaifiyar Adam (Ammee), kuma ƴan ɗakinta sun fi kowa rashin mutumci da iskanci, duk dan Ammee tana ganin ai dukiyar GIƊAƊO ta su ce, ba ta su Adam ba, dan su yaran ƙaninsa ne. Abubuwa dai a gidan babu daɗi sam, ga uban dokoki mara sa tsari. Sai dai babu wanda yake da ikon furta komai idan Iyaye maza huɗun nan suka yanke. Gaba ɗayansu ƙyawawane sai dai wasu sun fi wasu haske, amma gaba ɗaya jini ɗaya ne a jikinsu na cikakkun Fulani. Cike da izza da kamala yake takowa, tafiya yake kaman wani basarake ko yarima, ƙyakykywan saurayi ajin farko, dogo mai cikar haiba da kalama, wanda a kallo ɗaya za ka fahimci tarin ni'ima da Allah ya yi mai, yana cikin faɗin ƙirji, ƙyawawan idanuwa masu rikata mata, Ayan kenan, gagara kowa a gidan sai mahaifansa. Shine mutum ɗaya, wanda yake faɗa da tsarin gidan, be da wasa ko kaɗan, abu idan ba ya zama dole ba, ba ya magana, sam be da surutu haka yake, gashi shine duk yafi mai da hankali akan GIƊAƊO'S INDUSTRIES duk da ba kullum yake zuwa ba dan Lectural ne na Islamic studies anan Kad-poly. Sai dai duk da haka yake da mahassada a gidan. Amma shi sam be damuba ko ta kansu baya bi dan rayuwarsa kawai yake yi, yana da tsare-tsaren sa ba irin da gidan ba duk da wasu lokutan iyayensa na taka mai burki, da yake mutum ne ma mai biyayya sai yake musu biyayya kamar yarda suke so, badan yana so ba...................✍️ END. > Kunfa ji Jama'a. AYAN, AHMAD (A.G) DA SARAH, da alamun kuna cikin taurarin labarin🥺. > GIƊAƊO MENTION 😬😬 > WASIYYA 🙆 > Mu haɗu dan yi wa Inayah karatun natsuwa🤣, ga duk kan alamu a bauɗe take. *PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇: 📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥* *𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅* _TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_ https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy _TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_ https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K _TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_ https://arewapen.com/u/prettys01 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```PRETTY SK``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P5️⃣⏩6️⃣ _______Sai da ya gaishe da kowa sannan ya zauna gefan Ummee wacce ke sakar mai murmushi. “Kai kullum sai an jiranka?." Sai ya shafa tarin gashin kansa mai tsayi da laushi sannan ya ce. “I'm Sorry Abba." Ɗan tsaki Abba ya yi sannan ya ce. “Ina Daughter?.” take fuskar Ayan ya haɗe dan shi a duniyar nan ya tsana ganin Daughter (Ruma.) “Abbana ganin nan." Kusan gaba dayansu suka kalla in da suka ji muryan na ta. Sarah a cikin ranta ta ja tsaki, domin kuwa Ruma ba ta hankali sam, wani wando da riga ne ta sanya wanda sun matseta kamar ba ƴar Fulani ba, mutane masu ado da kunya, ita kam sam ba ta da kunya, sanya ƙananun kaya a wajen ba komai bane, kuma babu mai yi mata magana. A haka ake so a haɗa ta Ayan, shi kuma baya santa, sai dai aurenta shi zai kawo kusanci tsakanin Umminsu da Ammeen Ahmad dan kuwa Ruma ƙawar Ahmad ce. “Daughter zauna.” Abba ya nuna mata waje kusa da Ayan wanda nan ne muhallinta. “Ruma ba kunya, za ma ta yi fa a can tana jiran shi." Ahmad ya faɗa yana kallon Ayan, shi ai Ayan be ma san yana yi ba sam. “To ina ruwanka kai kuma.” faɗin Baba Musa. Daga haka suka yi addu'an cin abinci sannan aka fara ciki, abinci ne kala-kala sai ka za ɓa, kowa da wanda yake so kuma shi yake ci. Sarah ta kalla agogo 8:38pm, at least an ɓa ta sama da 39mnt ana taruwa kafin a fara ci. Daga masu cin abincin sai masu tsakura sai masu aika wa juna kallon soyayya, da masu aika wa juna na ƙiyayya, haka dai kowa ya gama sannan aka yi addu'a aka tashi. Babu abin da ya ci a wajen dan kuwa a ƙoshe yake, ya dai zaune ne kamar yadda ya zama wajibi ga kowa. A hankali ya ke tafiya yana hawa stairs, da sauri ya ji ansha gabansa, ko be kalla ba yasan Ruma ce. Ƙasa yake kallo dan haka da fararen ƙafafunta ya fara cin karo, murmushi gefan baki ya yi, muryansa mai cike da amo da sauti ga sanyi ya ce. “Matsa min daga hanya.” cike da salo ta ɗan ƙara matsawa dab da shi. “Baby me yasa kake min haka? Karka manta nice matarka ta gobe, idan ba mu saba tun yanzu ba sai yaushe?.” tsaki ya ja sannan ya kewayeta yana ci gaba da tafiya. Ƙwafa ta yi sannan ta sauka babban falon. Sarah kamar ta fashe da kuka, dan kuwa ta cika ta yi fam, barci take ji gashi tana da assignment amma Ahmad ya hana tashi. Tun ɗa zu yake mata hira wanda ko fahimtarsa ba ta yi. Ita sam ba ta yi da ce ba, ta so ace Mubarshir aka zaɓan mata sai dai Ahmad ya nuna maitarsa akan ta, shi ne aka bashi ita. A lokacin hauka ne kawai ba ta yi ba. “My Heart, bara na barki ki je ki kwanta." Da sauri ta miƙa tsaye, sai ya sa hannunsa ya mai do ita kan kujera, yana gab da ita, har suka jin numfashin juna suke, shi dama besan kunya ba, dan kuwa a finafinan da yake yi, har kiss ɗin ah-lul kitab yana yi, ga shi duk Film idan ya yi sai ya tura mata ko kunyar irin baɗalar da yake ba ya yi, ba ya ji, in ta yi magana sai yace wai “Akwai lession a ciki, karki damu faɗa karawa muke yi.” A lokutan sai ta ji kaman ta rufesa da duka amma babu dama. “Tell me something special." Ya faɗa har da kashe mata ido ɗaya. Tasan Idan ba ta faɗa mai kalaman soyayya ko ɗaya ba ce to za su kwana anan. “I love You." Ta faɗa a hankali. Murmushi ya yi. “So nake ya fito daga zuciyar ki.” ya faɗa yana juyo da fuskarsa sai tin na sa. “I love you." Ta kuma faɗa har da hawaye. “Me too. Mai da hawayen nan ko wallahi na lashesu da harshe n....” da sauri ta haɗiye kukan, hannun ta ya saki ai kuwa da gudu ta haura sama, dama sun saba in da suka zauna taɗi da kuka take wucewa....... (Pretty ta ce ku ji wani bala'i.) *********** *********** Ina cikin ƙaton bargo duk da ba sanyi ake ba, jin ana buga ƙofar room ɗina, yasa na dafe ƙirji na ina fatan ba Mom ba ce. “Inaya ki buɗe, nasan kina jina." Na ji muryan Mom, haɗiye miyau na yi sannan na yaye bargo. “Ina babban tauraruwa ace ba zan iya kafcen Film ba." Na faɗa ina sauya mood ɗina, dama na ƙware wajen basaja. Ƙofar na buɗe tare da yin miƙa da hamma. Ko da Mom na harararta ban sauya ba duk da gaba na yana faɗi. “Ban wayata?.” Mom ta faɗa sai na zaro ido ina dafe kai. “Mom dama ban dawo miki da shi ba!?." Da haka na juya wajen extension ɗin ɗakin, wayar Mom na jikin chargi, dan kuwa tun jiya na sato shi, kallo nasha sosai. “Na manta ne, dan da wuri na gama assignment." Na faɗa ina miƙa mata wayar, fizga ta yi. “Bance ki dena ɗau min waya ba, sai kin tambaye Ni." Da sauri na rungumeta ina murmushi, lokaci guda kuma ina muryan kuka. “Ki ya ƙuri, assignment ɗin da wuya ne, amma ba zan sake ba, kuma na ce kima Dad magana ina son waya amma kin ƙi." Na kai nan ina ƙaƙalo kuka, take kukan ya zo harda uban hawaye ka ce dukana aka yi. Mom jikinta ne ya yi sanyi, sai ta sake ni tana sharemin hawaye. “Ki dena kuka, kuma kinsan waya sai kin gama secondry, ki daure saura kadan kinji shalele." Na ɗaga kai Kamar wata mai ladabi. “Kin yi salla?." Na ɗaga kai duk da ƙarya nake yi. “Yauwa shi yasa nake sonki, shirya kafin A'isha ta cinye min ke da faɗa." Da haka Mom ta fita. A'isha dake bakin kofana ta shigo tana min wani kallo. “Hmm Mom na ruwa, ba ta san ƴar basaja ta haifa ba.” hararar ƙasan ido na yi mata, ina share hawayen. Ganin jikina a mace ya sa ta ƙaraso tana ta ɓa Ni. “Dama kukan gaske kike? Me aka miki?." Ta faɗa tana zama gefena, take na sake fashewa da wani kuka mai motsa zuciya. Jikinta ne ya yi mugun sanyi dan kuwa A'isha na mugun so na. Take ita ma hawaye suka fara cika idanunta dan ko da wasa ba ta son wani ya sani damuwa. “A..A... Auntyna.." na faɗa ina rungumeta. “Me aka miki?.” ta faɗa tana raba jikinmu. Kallonta na yi sosai ganin hawaye tab idanunta, sai na tsaya da kukan. Take na fashe da wani mugun dariya ina dafe cikina, harda kwanciya kan gado. Kallon mahaukaciya ta yi Galala, sannan ta tureni. “Dama na ƙarya ne?.” ta faɗa tana miƙewa tsaye kuma a fusace. Sai da na yi dariya mai isata sannan na miƙe ina dafa ciki. “Wayyo daɗi, haka zan dinga tsuma masu kallona a tv, kinga baiwa ko?." Na faɗa ina share hawaye, ga kuma dariyar ya ƙi barina. “Amma ya kika ga scene ɗin ya bada citta.......” da wani irin zafin nama ta yo kaina, dama a ready nake. Da gudu na shige restroom Ina murza key. Ina ji tana dukan ƙofar Ni kuma na ci gaba da dariya kamar sabon kamu. Wanka na yi tare da alwala, na ƙosa Driver na ya dawo dan bansan tuƙin A'isha, ya yi tafiya ne na sati ɗaya, shi yasa take kai ni school. Bayan na fito wanka na kullu room ɗina sannan na yi sallah, bayan na idar na shafa mai. Uniform na sanya, riga da ƴar ciki, sai legis sannan na tsaya gaban mirrow. Gashin kai na mai tarin yawa na ta je sannan na ƙulle, hular na sanya wanda wasu suka ce idan na sa yafi min ƙyau, amma da gangan nake cirewa. Sai na fito fes kamar a sace Ni, na yi ƙyau sosai dan Allah ya ban ƙyau na musamman. Jakkata na ɗauka sannan na fita, Dining area na nufa, abinci na gani yana tiriri, take na hau ci wanda bansan na waye ba, amma ga dukkan alamu na A'isha ne, dan ita ke cin Indomi sosai kuma wannan girkin na ta ne. Da gayya na hau ci da sauri-sauri, yana ƙonani, sai da na cinye eggs ɗin, sannan na ci iya cina duk na jakwalkwala Indomie. “Wayyo! Indomie na ya huce ai.....” haɗiye sauran maganar ta yi tana kallona ina kai loma bakina. “Inayah, waya ce ki taɓa min abinci na?." “A...Auntyna na za ci Rabi (mai girki) ita ta aje min." Na faɗa ina jin cikina ya cika amma saboda neman rigima na kuma kai wani bakina. “Lailai ba ki da .....” “Aisha." Mom ta faɗa tana daga falo. “Mom Indomie na girka na tsaya nemo yaji shine ta cinye min.” “Ki ya ƙuri kinsan yarinya ce, duba kaman Doya aka yi, sai ki ci ko yayane." “Na ƙoshi.” ta faɗa tana dungure roba yajin makan shi ya yi mata laifin. Ganin ta yi waje nasan wucewa za ta yi ai da sauri na miƙe, Rabi ta miƙo min lunch bag ɗina na amsa ina komawa falo. “Za ta wuce." Na faɗa ina amsar ₦500 wajen Mom. “A dawo lafiya." Na ɗaga mata kai ina gudu, ga nauyin jakka, ga ciki ya cika sannan ga abinci. Ilai ta kunna motar tana zuba horn ajere kai ka ce wani ne ya biyota. shi kuma me gadi yana bude get, ai da sauri na buɗe motar ina shiga baya ban gama kulle motar ba ta figesa. Da sauri na kulle ina addu'a, dan kuwa Aisha da figa motar ne da wani irin gudu. Ganin gudun bana wasa bane, sai faman kutsa motoci take, tana cin taya, yasa na fara ihu, ina mata magiya. “Aunty karki kashe ni....wallahi za ki yi ma Dad and Mom asara.......za ta kashe babbar tauraruwa......dan Allah ki min rai......Aunty wayyo." Nai ta faɗa amma a banza dan kuwa sai kutsawa take yi kamar mun yi sata an biyo mu. Kafin ka ce me sai gamu a school, jikina duk ya yi tsami dan ko zaman kujera ban yi ba, haka na fito ina sauke ajiyar zuciya, kallonta na yi ina cewa. “Insha Allah gobe Driver na zai dawo, na dena hawa motar....." Take ta baɗe ni da ƙurar motarta tana ƙara hawa titi kamar wacce ta bugu. Girgiza kai na yi, sai na nufa cikin school raina a ɗan ɓa ce, da abin da ta yi min, ina kumbure-kunbure dan ma Allah ya kawo mu lafiya.............✍️ END > Ƴar NOLLYWOOD 🔥 > Fatan yana zuba sweet 😍 > Update ba yawa ko..... I'm sorry everyone, na riga na rarraba ne kunji. #LIKES👍 #SHARING☹️👌 #COMMENTS🙏👌 *𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅* _TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_ https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy _TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_ https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K _TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_ https://arewapen.com/u/prettys01 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```PRETTY SK``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P7️⃣⏩8️⃣. __________Abu kaɗan ke ɓata ma A'isha rai, dama ga ta uwar fushi, haka ta shiga school ɗin su, parking ta yi ta fito, tana jin yunwa amma taurin kai ba zai barta ta ci komai ba, department ɗin su ta nufa. Ko da ta shiga zama ta yi, gaisuwa ke haɗata da kowa, haka aka gama lecture biyu tana aji amma ba ta fahimci komai ba. ________Ajin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Take student suka gaishe sa sai ya amsa yana nufan wanjen zaman malamai, a hankali ya kai ƙyawawan idanunsa kanta, da sauri ya janye yana jin wani ɗa ci a cikin ransa, zai iya cewa tunda ya fara koyarwa yau shine karo na farko da ya shiga class ɗin ba ta kallesa ba, duk da ta ji an kira sunan sa. *Sir M.D* amma ba ta ɗago ta kallesa. Haka ya gama Lecture hankalinsa na kan Aisha wacce har ya gama ba ta kallesa ba. Yana fita ta sauke nan nauyan ajiyar zuciya tana lumshe idanunta, kifa kanta ta yi a kan desk, tana kallon bayanin da ya yi a jikin board. Wata budurwar ce ta shiga ga dukkan alamu ba musulma ba ce saboda shigar dake jikinta. Tana shigowa ta nufa Aisha sannan ta ce. “Hey Sis, Sir M.D ya kiran ki, ya ce ki sa me sa a office ɗin sa." Ji ta yi gabanta ya yanke ya faɗi, sai a lokacin ta dawo cikin hankalinta, miƙewa ta yi sannan ta yi waje. Haka ta taka har zuwa bakin office ɗin sa, sai kuma ta tsaya dan gani take makar ƙarya ne, duk da wacce ta kirata ta santa sosai, mamaki take akan kiran na sa, dan kuwa Sir M.D be kula mata, ba ya magana da su privacy. Sai dai ita tun da ta fara ganinsa ta kamu da soyayyar da ba ta san ya shigeta ba, tana da samari masu yawa amma hankalinta yana kan M.D, idan ya shiga class ɗin su to da idanunta yake fara cikin karo ta na aika mai tsadaddan murmushi, haka duk in da za ta gansa a school ɗin nan take zuwa. Ta sha wahala kafin ta samu numbersa amma ranar da ta yi gigin kirarsa, ranar ya sameta ya yi mata faɗa sosai, maimakon ta rage bibiyarsa sai ta ƙara, kullum sai ta tura mai saƙon, safe, rana da dare, na kulawa da tambayar ya ci abinci, ba ta damuwa da rashin reply amma ya zama mata aikin yi na kullum. Wai shine kuma a yau ya ce a kirata. Knocking ta yi. “Yes coming." Ta ji zazzaƙan muryarsa ta faɗa. A hankali ta tura ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, sai dai har lokacin fuskarta na haɗe duk da kuwa bazatan da Sir M.D ya yi mata. “Ina kwana....sir wai kana nema na?.” ta faɗa daga can nesa. A karo na farko da ya yi mata murmushi kenan sannan ya ce. “Eh, zo ki zauna." Ba musu ta ƙara sa ta zauna a ɗan ɗarare. Ya ɗau kaman minti 3 yana kallon fuskar, tabbas A'isha ƙyakƙyawa ce, wacce ta cika gaba ɗaya abubuwan da ake nema ga budurwar mace, ƙyau, ilimi, hankali, natsuwa, mu'alama mai kyau da mutane, ƙyautta ma kowa da sauran abubuwa wanda ya bincika da kansa. “Me aka miki?.” ta jin tambayar kamar daga sama. Ɗago idanunta ta yi suka haɗa ido ta sauri ta kauda kanta. “Sir ba komai....." “Ƙarya ba ɗabi'ar ki ba ce... Tell me.” sai ta saki fuskarta, dan kuwa abin da Inayah ta yi mata ne kawai yake ɓata mata rai. “Sir ba wani abu bane.” “Ina so na sani, nasan wa ya ta ɓa min ke.” ya faɗa hankalinsa kwance, mamakin abin da ya ce ta yi amma sai ta share. “Kawai ƙanwata ce ta ɓa ta min rai amma ya wuce.” ta faɗa tana jin tasirin idanunsa akan fuskarta, ji take kaman ta nitse a ƙasa. “Me ta miki?” murmushi ta ɗan yi sai ta ce. “Ba wani serious abu bane......” “Ina so na sani." Ya faɗa a ɗan zafafe. “Kawai na gama ɓa ta lokaci na yi wa kaina breakfast, shine ta cinye, kuma tasan ban iya cin duk wani abu da wani zai dafa sai nawa, shine na ji haushi, kuma na ɗauke ta zuwa school, ta dinga min hauka a cikin mota.” ta kai maganar cike da shaƙwabar da ba tan ta yi ba, murmushi ya yi sannan ya tashi daga kujerar, a hankali ya za gayo in da take sai ya zauna a gefan ta. Take daddaɗan turarensa ya cika ƙofofin hancinta lumshe idanunta ta yi sannan ta buɗe. “Ki faɗa mata na ce, duk ranar da ta sake ɓa ta miki rai zan haɗu da ita. Please ki koma yarda na sanki mai yawan murmushi, kinfi ƙyau." Dariya ta ɗan yi. “Aisha." Ya faɗa a natse sai ta kallesa tana amsawa. “Na'am." “Magana zan yi da ke mai muhimmanci.” “Ina jinka, fatan ban yi laifi ba?." “Hmmm, ko ɗaya, Kinsan Ni sosai, zan iya cewa tunda nake ban ta ɓa tsayawa da mace na yi hira da ita kamar yarda nake yi yanzu, kinsan dalili?." Sai ta girgiza kai. “Saboda soyayyar da kike nuna min...... A'isha, kina nuna kulawarki a kai a kodayaushe, saƙon nin ki ba su ta ɓa makaraba, Ni kuma ban taɓa gajiya da karanta su, ko da na sameki na yi miki faɗa, maimakon ki dena sai ki ka ci gaba, daga lokacin Ni kuma na fara bincike akan ki, na samu abubuwa masu yawa kuma masu daɗi wanda ko wace mace take fatan a sameta da shi........ke kin samu, zama na yi nai tunani akan ki, kuma a yanzu zan iya ce miki na amsa Soyayyarki.” ya faɗa yana mata murmushi, ita kuwa saboda maganganunsa sai ta kasa natsuwa, ji take kaman ta fashe da ihun murna. “Na yarda da wani abu, duk mai sonka ko yayane ka so shi. Ban ta ɓa soyayya, amma har ga Allah ina Ƙaunarki A'isha saboda halayenki.” take hawaye ya gangaro daga idanunta na murna. Murmushi ya yi sannan ya miƙe, hawayen ta share tana ce wa. “Tabbas a yau ka farantamin. Ya Allah ka faranta mai shima. Alhamdulillah alhamdulillah." Ta faɗa tana fita cikin sauri harda gudu. Dafe kansa ya yi yana mamakin irin soyayya da A'isha ta faɗa. Shi kansa ya ɗau lokacin kafin ya zauna dan kuwa zuciyarsa ce ta yanke mai wannan shawarar, yana zama ya rintse idanunsa, be mata ƙarya ba, be ta ɓa soyayya, sai dai sau ɗaya wata yarinya ta taɓa burgesa, ya so ko sau ɗaya su sake haɗuwa amma be samu dama ba. (A lokacin da ya je Abuja, wani school an gayyace sa Quiz competitions na makarantu, ya je kuwa, a cikin yaran da suka wakilci wata makaranta ya ga yarinyar, duka da ƙarama ce sosai amma ta burgeta sosai, kuma a gaba ɗaya Quiz ɗin ita ce ta ci, be manta sunan da ake kiran ta da shi ba *QUEEN ROSE* sannan shi ya ba ta ƙyautarta, aka musu hoto. Bayan da ya dawo Kaduna, ya yi ta bincike a makarantar mai wannan sunan sai aka ce ta fita a school ɗin, da haka ya bar maganar amma kullum yana tunawa da ita.) Yasan al'adar gidansu amma shi so yake ya aura mace daga waje, so yake ya aura bare, ko dan tsallake auren *Ruma* . Tsaki ya ja dan tuna sunan Ruma da ya yi. A yanzu A'isha zai aura duk da ba ya sonta amma yana ƙaunarta, zai aureta dan ya faranta mata sosai, shi sai yau ya ga kaman ta mai kama da yarinyar da yake nema. _____Ko da ta fito motarta ta nufa kai tsaye, ciki ta shiga ta kulle, sai da ta sha kuka ta gode ma Allah, sannan ta jin gina da kujerar tana jin daɗi a ranta. Take wayarta ta hau ringing tana dubawa ta ga M.D cikin sauri ta ɗauka tana kaiwa kunninta. “Please ki samu ko biscuits ne ciki kin ji.” ya faɗa cikin wani salo da ƙwantar da murya. “Insha Allah, Sir M.D thank you Soo much." “By now a dena cemin Sir pls." Murmushi ta yi. “To me zance?." Ta ji bakinta sun furta ba tare da izinin ta ba. “Uhmmmm *AYAN* ." “To Yaya Ayan." Sai ya yi murmushi. “Take care." Da haka ya katse kirar, bin wayar ta yi da kallo cike da mamaki.......✍️ END. > Hmmmmm wallahi zafin 🔥 labarin nan, na daban ne. Wato Sir M.D shine AYAN na Familyn *GIƊAƊO MANTION* hmmmmmm 🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔 muje dai GUY'S. > GIƊAƊO'S FAMILY Rayuwar ku sai ku kam 😓. > Wacece ROSE? Kuna tunanin abin da nake tunani kuwa........🙆🙆🙆🙆🙆🙆. #LIKES👍 #SHARING☹️👌 #COMMENTS🙏👌 *𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅* _TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_ https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy _TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_ https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K _TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_ https://arewapen.com/u/prettys01 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```PRETTY SK``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P9️⃣⏩🔟 ________Inayah, yau makarantar bai min daɗi ba saboda, Jennifer ba ta zo school ba, haka dai school ɗin ya zama min lami, ko da A'isha ta zo ɗauka ta ban yi mata magana ba har muka koma gida, na dai lura sai faman murmushi take yi, sai nima na shareta saboda abin da ta yi min na ɗazu ya ɓa ta min rai sosai. Bayan ta yi parking na fito fuskana babu yabo ba fallasa. Ina shiga falo na nufi Kitchen aje lunch bag ɗina na yi sannan na fito sai na ga mom na saukowa daga stairs, murmushi take yimin sai dai Ni na kuma ɗaure fuska. Jakkana na ɗauka na yi hanyar room ɗina , har zan wuceta sai ta riƙon. “Waya ta ɓa shalele?.” ta faɗa tana dawo dani gabata, shuru na yi ban yi magana ba, sai ta ɗaga mun fuskanta na kalleta. “Me aka miki?.” ta faɗa dan yanayin da na koma. “Babu komai..........ina zuwa." Na faɗa ina wucewa, bina ta yi da ido dan kuwa yanayin na wa ba magana abin ka da kullum ina nishaɗi. “Ke kin yi ma Shalele wani abu ne?." Mom ta tambaya A'isha wacce ta zauna a falo bayan shigowar ta. “Haka na ganta, ko magana ba mu yi ba, sai dai ko tun faɗar safe da muka yi ne." Sai ta ɗaga kai tana zama a kujera, sai dai jikinta ya yi sanyi, dan Inayah sam ba haka take ba. “Hajiya, yau fa Shalele ba ta ci komai ba, da alamun ko buɗe lunch bag ɗin ba ta buɗe ba. Sannan ga wannan a ciki" Mai aikin su wato Rabi, ta faɗa tana miƙa ma A'isha ₦500, sai A'isha ta yi mata alamar ta wuce da shi, sai ta yi godiya tana koma wa Kitchen. Mom ta kalla A'isha da ta ɗan zaro ido, a ce tun safe mutum be ci komai yanzu ana shirin kiran sallar magrib. “Da matsala me aka mata?.” A'isha ta faɗa cike da damuwa. “Muje room ɗin." Da haka suka nufa room ɗin Inayah. Ina shiga ɗakina na kulle ko ina sannan na kashe haske, kwanciya na yi kan gado ko takalmi ban cire ba, gaba ɗaya haushin kowa na ke ji, so nake yau a gidan kowa ranshi ya ɓaci dan kuwa abinda A'isha ta min ya ɓa ta min rai, sannan ga Jennifer da ta ƙi zuwa school, sai abu ya haɗe min, shi yasa ko magana banyi da kowa ba. Jin ana buga min ƙofa yasa na yi wani murmushi sannan na yi magana a hankali. “Ai yau sai hankalin kowa ya tashi, hmmm." Na yi ƙwafa ina toshe kunnuwana. Mom da hankalinta in ya yi dubu ya tashi ta kira Dad a waya akan Inayah ba lafiya. Sun bubbuga ƙofar kamar me amma na kasa tashi. Nikam wani wahalalliyar barci ne ma ya ɗauke ni. Dad a ɗan ruɗe ya shigo gidan dan kuwa Allah ya dasa musu soyayyata kamar me. Lokacin har an yi sallar isha'i, dan daga office ɗin sa zuwa nan akwai nisa, ina jin muryan Dad na tashi daga kwancen, bayi na shiga na yi wanka tare da alwala, lokacin dana fito na dena jin motsin kowa a wajen, sallah na yi magrib da isha'i sannan na zura kayan barci, yunwa nake ji sosai dan haka na buɗe ƙofar na fita ina ƙara haɗe rai. Ga yunga da ya cinye Ni hakan yasa tafiyata ta koma kamar mara lafiya. Mom, Dad, da A'isha suna tsaye kaman wa'inda aka yi wa mutuwa, sai suka ganni a falon, da sauri Mom ta nufoni tana riƙeni dan ganin kaman zan faɗi. “Inayah....Inayah....." Mom ta faɗa sai na kalleta. “Meke damunki?.” ta tambaya idanunta na cika da hawaye, a cikin raina kuwa nishaɗi ya kamani dan kuwa yau *Film* ake yi a gidan nan, tun yanzu ƙwanda na dinga practice. “Shalele ba ki jin muna dukan ƙofar ɗakin ki bane?.” A'isha ta faɗa tana riƙoni. Har lokacin na ƙi magana. Dad sai ya riƙo ni yana kwantar da murya. “Tell me My bloodline. What's wrong with you?.” sai ga hawaye ya zubo min sai ya sa hannunsa ya sharemin. “A....A...abinci.” na faɗa da ƙyar, ai da sauri A'isha ta nufa Kitchen, Tea ta haɗo min sannan Dad ya ban a baki, sai da na ƙoshi sannan na ce. “Ku kwantar da hankalinku, kawai wani abu ne ke damuna....." Na faɗa cikin sanyin murya. “Shalele faɗa min meke damunki, ko kina wa'inda suka fimune?.” na girgiza wa Mom kai. A cikin raina kuwa dariya na ke yi, sai daurewa nake yi saboda karta kuɓuce min. “Kuna so na zama Doctor ko?." Suka ɗaga mun kai. “Ra'ayin ku shine nawa, akwai wata ƙawata, tare muke, ina sonta sosai, to ra'ayin mu ya zo ɗaya, ita dama a can wajen iyayenta za ta ƙarasa, shine jiya suka ɗauke wai a can za ta yi waec....... So nake mu yi University ɗaya......dan Allah ku taimaka.........” sai na fashe da kuka, kallona kawai suke yi dan ba su fahimci in da na nufa ba. “Yanzu me kike so?." Dad ya tamabaye ni. “*University College of Medicine (LASUCOM)*......” da sauri Mom ta ce. “You mean Lagos State University?." Na ɗaga mata kai. “Alfarma ce kawai, amma in ba ku so shike nan, dama kawai ina so ne mu yi karatu tare.” da haka na miƙe tsaye ina son na wuce, ga wani ɗan jiri da ke ɗibana. “Ki yi ƙoƙari a weac Ni kuma zan kai ki.” sai na rungume Dad. “Dad har Legos....gaskiya a'a?." Faɗin Mom, ita dai A'isha kallon mu kawai take. “Shike nan, in dai ɗayan ku bai so ba za Ni ba." Na faɗa ina barin falon, da ido suka bini har na ɓa ce musu. “Inayah problem, yanzu duk makarantu sai na can? Kuma akan wannan ne ta hora kanta da yunwa.” Mom ta faɗa sai A'isha ta ce. “Kunsan halinta ai, akwai sa abu a rai, Allah dai ya ƙyauta, duk da ɗaga wa mutane hankali a banza.” A'ishah ta faɗa tana nufan Kitchen dan haɗa ma kanta abinci, ita haka Allah ya yi ta, tun tana ƙarama in aka dafa abu aka ba ta ba ta ci sai dai in Mom ta yi, tana ƙara girma kuwa ita ke girka ma kanta abinci, haka take ko ina ta je ba ta cin abu sai in da ita aka yi making. Ina shiga room ɗina na daka wani tsalle sai gaba mirrow, dariyar ce ta ƙwace min, ai kuwa nai ta yi kaman mahaukaciya, sannan na ce. “Hmmm ai ƙwanciyar hankalinku shine ku turani *Lagos State University College of Medicine (LASUCOM)* Hahahahahah ga ni ga NOLLYWOOD...... Sai ni ƳAR NOLLYWOOD insha Allah.” na faɗa ina sumbatar kai na ta mudubi. Ni fa tun ainiyi *HOLLYWOOD* shi nake so, amma nasan ba zan samu daman zuwa U.S ba balle na shiga *HOLLYWOOD* har na yi Film, sai kawai buri na ya dawo *NOLLYWOOD* kuma insha Allah ko Film ɗaya ne sai na yi. _______Aisha complex ta haɗa, anan ta sha dan ita ba wani abinci take ci sosai ba, tana gamawa ta koma room ɗin ta, a al'adance kullum sai ta yi wanka da daddare, sannan ta yi sallah kafin ta kwanta, haka yau ma bayan ta gama komai ta kwanta, take yau ɗin ta ya faɗo mata, tabbas yau rana ce da ba za ta manta da shi ba. Jin sautin S.M.S ya sa ta duba, ganin M.D ya mata reply da. *GOOD NIGHT It’s just been a day that you are gone and already it feels like ages. There’s no reason left to wake up in the morning, please come back soon. Thank you so much Eeshert.* Murmushi ta yi sannan ta kalla wanda ta tura mai. *Hello! My name is Night. I came here to kidnap your stress; Kill your strain. My weapon is deep sleep and my path is Sweet Dream. So please kindly co-operate and handover yourself! Good Night My.....*. Murmushi ta kuma yi sannan ta lumshe idanunta, tana hasasho fuskar Ayan, ƙyaƙyƙyawan sauri mai Capacity. take barci ya ɗauke ta cike da zazzafan soyayyar Ayan........................✍️ END > Ƴar NOLLYWOOD 🙆🙆🙆 Inayah gagara kowa kenan, hmmm ko ya za ta kasance......???? > Ba ku yi comments da Likes shi yasa Update yake zuwa a haka. Na so kuban haɗin kai da a 2week za mu kammala........😏😏😏. #LIKES👍 #SHARE😁 #COMMENTS🥰👌 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```PRETTY SK``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣ *BAYAN WATA BIYU* A'isha ta ƙara shiga tafkin soyayyar Yaya Ayan, ba shi kulawa take kamar me, wasa-wasa shima yake kulata sosai, amma har zuwa lokacin ba ya jinta a zuciyarsa, sai dai yana so ya aureta ɗan abu biyu, na farko da soyayyar da take mai, na biyu ko dan ya kauce ma auren Ruma. *GIƊAƊO MANSION* ____________Gaba ɗaya sun yi shuru suna sauraran Baba Musa dake tsaida lokacin auren su, su 8, an sanya nan da wata biyar ne kacal. Ayan dake kallon iyayen nasa rai a haɗe ya ce. “Baba ina da magana.” “Ayan ina jikin ka, yarona.” Sai da ya sosa kansa sannan ya saci kallon kowa ganin yarda suke binshi da ido, dakewa ya yi sannan ya ce. “Kunfi kowa sani cewa banson Ruma...........wallahi banson ta da aure, sai dai ina sonta a matsayin ƙanwa, Ni ina da wacce na yi ma alƙawarin aure.” ya kai nan yana shirin miƙewa da sauri Baba Yusuf ya mai da shi ya zauna. Idan ransu ya yi dubu ya ɓaci, balle ma Ruma da Mahaifiyarta. “Me ka ce?.” baba Yusuf ya tambaya ransa a haɗe. “Akwai wacce na yi ma.......” wani sanyayyar mari ya ji Abba ya sauke mai a kuncinsa. “Kar ka mai da mu mutanen banza, wallahi idan na kuma jin irin wannan furucin a bakinka sai na saɓa maka. So kake mu yi watsi da wasiyyar mahaifin mu ko ya ya?.” ya kai nan yana ɗan huci. Ayan dake dafe da wajen, ya ɗan yi murmushi sannan ya miƙe tsaye. “Shike nan, amma idan har wani abu ya bayya wa ƴan jaridu, kune sila, ina so na kare mutuncin gidan nan ne, amma tunda haka kuka ce shike nan.” da haka ya miƙe, yana musu kwarjini sosai, babu wanda ya dakatar da shi har ya fita, kowa cikin maimaita maganarsa suke yi dan kuwa babu abin da suka fahimta. Sun dai riƙe. “Ƴan Jaridu, mutumci." Babu dai wanda ya yi magana a cikinsu. Ruma kuwa tuni hawaye sun fara gangaro mata masu zafi..... Cikin wannan takun nasa wanda kai ka ce sarki ne ko shugaban ƙasa, haka yake taku ƙasa na amsawa. Direct motarsa ya nufa sannan ya bar gidan, yau Sunday Babu school dan haka ya nufa gidansu Aisha wacce ta yi mai kwantan ce. A bakin get ɗin gidan su ya yi parking, sannan ya kira wayarta. “Ina ƙofar gida." “Okay ganin zuwa.” ta furta, da haka ya aje wayar yana ji kamar an yi mata abu dan yarda ta yi maganar kaman ranta na ɓa ce. Ilai sai ga ta fito fuskarta babu annuri duk da suprice ɗin da ya yi mata na zuwa babu notice. Ta yi ƙyau cikin dogon Blue Black na hijab har ƙasa, fuskarta babu komai dan be ta ɓa ganin ta yi makeup ba. Ba yarda ta iya ko dan rana ma sai ta shiga motar tana sallama, murmushi ya saki kafin ya amsa. “Aisha bazata na miki amma naga kina cikin damuwa meya faru?.” ya tambaya yana jin babu daɗi da ganinta a haka. Kai ta girgiza mai. “No faɗa min dai kin ji.” sai ta saki ranta dan dai komai ya wuce. “Yaya Ayan ba komai walla...........” da sauri ta tsaida da maganar sakamakon ya sanya hannunsa ya kulle mata baki. “Shhhhhh. Magana na zo mu yi mai muhimmanci amma idan ba ki faɗa min abin da aka miki ba, wallahi ba zan faɗa ba, kuma sai na.....” “Shike nan zan faɗa maka.” ta faɗa tana gyara zamanta, shi kuma ya zuba mata fararen idanunsa akanta. “Shalele ce.” sai ya yi murmushi, be ta ɓa ganin Shalele ba amma yasan akwaita da rashin ji, babu rana da za ta wuce ba tare da ta ɓata ma A'isha rai ba. “Nikam wannan Shalelen duk randa na ganta sai na sa an rataye min ita, tana takura miki da yawa, me ma ta yi miki?.” murmushi ta ɗan yi sannan ta ce. “Yau Sunday tana gida, wallahi tun asuba ta fara damuna, yanzu ta mun abu jima haka ta yi wani, kuma ban da ikon mata magana yanzu sai Mom ta ce *ina takura mata* kalla yarda ta fasamin yawa, wallahi da ganganga ta yarda shi, da na yi mata magana sai ta hau kuka wai natseta, shine ta faɗa ma Mom, sai Mom.................” “Yi shuru na fahimta.” ya katseta dan kuwa gab take da yin kuka, a zamansu abu abu ya sani dangane da A'isha shine saurin Fushi ga ɗaukan abu da zafi. “Zan siya miki waya shike nan.” “A'a na gode, ai tsaga ne kawai.” ta faɗa tana kallon wayar da ya fashe sosai, har ya taɓa screen ya yi baƙi gefe ɗaya. “Gobe insha Allah zan tawo miki da waya. Yanzu dai babban magana ne ya kawo ni.” sai ta mai da hankalinta a kansa. “Aisha.” ya faɗa cike da rauni mai haɗe da taushi. “Na'am.” “Nasan kina sona sosai, balle a yanzu da nake baki lokaci na, sai dai aure tsakanin mu abu ne mai wahala saboda wata *WASIYYA* ” Take ya ba ta taƙaitaccen labarin *Giɗaɗo Family* tare da abin da aka yanke a gidansu yanzu. Wani abu ta ji ya doki zuciyarta, ta sauri ta rintse idanunta tana maimaita duk abin da yace. “Yanzu......a...a...aure za ka yi?." Sai ya yi murmushi. “Nasan za ki ce me yasa na miki haka. Me yasa na fara kulaki ko?.” sai ta ɗaga mai kai. “Ni kaina banson auren.........uhmmmmmm ina da shawara amma yana da wahala sosai, in ɗai za ki iya to aure tsakanina da ke kamar an yi.” buɗe dara-daran idanunta ta yi tana kallonsa kamar yarda yake kallonta. “Akwai wahala.” ya sake faɗa kamar mai raɗa. “Koma menene shi zan yi muddin zamu yi aure.” ta faɗa tana jin zafi a ranta har lokacin. “Gidan mu suna da abu guda ɗaya, idan har akan mutumcin gida ne to za su iya komai dan ganin be zuba ba, nasan kunsan familyn sosai ko da a labarai, to akwai son riƙe mutuminci.............yanzu mu mafita ɗaya ne tak mutumcin Familyn zamu yi ƙoƙarin mu ta ɓa, idan muka musu bayani to za su yarda.” “Bangane ba Yaya Ayan.” sai ya ja dogon numfashi sannan ya ce. “Uhmmmmm........Mu'aluma matar da miji kafin aure.” zaro idanuwanta ta yi dan jin furucinsa, dan kuwa ba ta yi tsammanin jin haka daga bakin sa ba, kai ta fara girgiza mai hawaye na gangarowa daga idanunta sannan zuciyarta ta tsananta bugu cikin sauri-sauri........................✍️ END. > Duk wasan yara muke, har yanzu ba mu shiga labarin ba. Kar a manta Like 👍 and Comment. Ngd SOSAI. 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```PRETTY SK``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P1️⃣3⃣⏩1️⃣4⃣. “Na haƙura da auren.......... Wallahi bazan iya wannan abun ba, ai wannan mutumcin harda na wa, da iyayenmu, da yaranmu duk zai zube, a'a......aa....... a'a Gaskiya. ” takai nan ta fashewa da kuka. Take ya kwashe da dariya, yana dubanta, ganin irin dariyar da yake yi yasa ta kai hannu za ta fita daga cikin motan da sauri ya sa luck. “Ai sai ki tsaya kiji gaba ɗaya maganar, ke kinsan ina da ilimin addini, ba yarda zan yi na kauce hanya, balle Zina, abu mafi muni. Kawai zamu yi basaja ne akan mun aikata haka, kuma ke kince idan ban aureki ba, za ki faɗa ma duniya saboda kina ɗauke da cikina a yanzu.” zaro idanuwa ta yi tana cewa. “Innalillah, ta ya zamu yi irin wannan ƙaryan, kai ba ka ganin zai zo da matsala?.” “Ko ɗaya, ai maganar daga familyna zuwa kanmu ne kawai, nasan yarda suke son mutumcin kansu ba za su bari hakan ta faru ba, dan sun san waye Mahaifinki, abokin kasuwancin sune.” jinjina kai ta yi tana maimaita abinda ya ce, tabbas a baki ya ya sauƙin faɗa, amma kuwa yana da girma fiye da a mai da shi abun wasa. “Za ka fuskanci matsala sosai kuma nima haka idan na shiga gidan na ku haka.” ta faɗa bayan kukan na ta ya tsaya. Iska ya furzar daga bakinsa sannan ya ce. “Na sani, kuma nasan sharaɗin ɗaya ne, dole su aura min Ruma.” shuru ya yi, itama haka sai can ta katse shurun da cewa. “Hmmmmmm da in rasaka gaba ɗaya ƙwanda mu yi hakan kuma zan iya rayuwa da ita Ruma ɗin. Duk da ina da zafin kishi.” sai ta share hawayenta. “Yi min bayanin yarda tsarin yake.” ta kuma faɗa, with confidence. Murmushi ya yi sannan take ya koro mata yarda ya tsara, dan kuwa wannan tsarin na sa tun kafin ya fara sake mata ya yi shi. Ita dai jin yarda ya koro zancen ne ya bata mamaki, kaman wanda ya shekara yana tsara plane. Bayan ta fahimta ne suka canza hira zuwa na soyayya. *Inayah* ___________Tsaki na ja, ina ganin ai A'isha ta jima da fita, gashi a waje ne balle in ce tana cikin gidan nan, duk na bi na damu, kallon Mom na yi dake cin abinci. “Mom zan leƙa na dubota, karfa a ce sace ta aka yi, mu muna nan zaune” na faɗa ina nuna damuwa. “Kin iya neman rigima ne ai, amma je ki.........” ai ba ta ƙarasa ba na yi waje da sauri. Tabbas ina da neman magana dan kuwa yau tun safe nake ɓata ma A'isha rai, sai dai ba da gangan na fasa mata wayaba bisa tsautsayi ne amma A'isha ta wani hau min masifa. Me gadi na ganina ya washe baki yana cewa. “Shalele ina zuwa?.” “Baba Rabe duba Aunty zan yi kar a sace ta.” murmushi ya yi yana miƙewa. “Zauna ai ba fita zan yi ba, leƙawa zanyi.” sai ya zauna yana kai Radio wajen kunninsa. “To shalele.” ya faɗa yana lumshe idanunsa. Ta saƙon get na leƙa, wata arniyar mota na gani, kafin na yi wani yinƙuri har A'isha ta fito ta ɗayan ɓangaren. Ɓangaren dake gefana na ga an buɗe shima, take na ji abu na min yawo a ƙafata, da sauri na kalla a ɗan tsorace dan ma ban saki ihu ba, ashe igiyar riga nane, tsaki na kuma ja, ina mai da idanuwana wajen. Wani dogon namiji na gaji cikin manyan kaya har da hula, yana da faɗi sosai, kaman wanda ke ɗaga ƙarfe, ban ga fuskansa ba dan haka na taɓe ƙaramin bakina. A gaban A'isha ya tsaya yana goge mata fuska, da wani abu wanda ban tantance menene ba, sannan yana yi mata magana, wanda ban jin komai. Kallon rigar na wa na kuma yi ina jin kaman na yi dambe da rigar saboda ban samu ganin fuskar Saurayin A'isha ba, so nake na ba Mom labarin komai da na gani kuma inason na karanci yanayinsu. Ƙarar motar ne yasa na mai da idanuna wajen, ashe har ya wuce, ai da mugun gudu na bi bayan ɗakin mu, kamar wacce ta ga mugun abu. Ta ɗayan ƙofar Kitchen na shiga ina mai da nunfashi kamar wacce aka biyo. Ina shigowa falo na ƙura ma A'isha ido wacce ke ma Mom magana, dan itama shigowarta kenan. “Mom wallahi A'isha ta yi kuka, kinsan menene........dukanta ya yi a cikin mota, sannan ya mata kashedi akan dole ta aureshi. Na gaji ai, shine saboda rainin wayau ya fito yana ba ta haƙuri harda share............... ” da sauri Aisha ta janyo Ni kusa da ita, Ita dai Mom ko kallona ba ta yi ba, dan kuwa tasan halina. Zama A'isha ta yi tana riƙe da ni, zaunar da ni ta yi sannan ta ce. “Inayah, me yasa kike son ɓata min rai? Me yasa kullum kike sani magana? Ba ki sona ne ko mene, ban fahimta ba kimin bayani?." Ta faɗa cike da raunin da ya sa Mom ta mai da hankalinta akan mu. “Ki faɗa min.......ina jinki?." Da sauri na miƙe tsaye ina girgiza kai. “Aisha, ban tsane ki ba............” “Karya ne Inayah.” ta faɗa tana share hawaye wanda suka zubo mata. Da sauri na isa gabata ina mai ɗago fuskarta. *“Ban da ƙannai wanda zan sanya kuka, banda wanda zan duka ya yi kuka...........kawai ina miki wasu abun ne saboda na samu abokin faɗa, ke kuma komai da gaske kike ɗauka...........shine matsalarki............wallahi A'isha Ina miki muguwar soyayya. Na yarda ni ina sanyaki kuka, amma wallahi.......wallahi.......wallahi duk uban da ya sanya ki kuka a rayuwa, bayan ni sai na sa shi shima, duk wanda ya ɓata miki rai wallahi sai na rama miki........koda ko waye, na fita ne dan ga saurayinki, so nake na fahimci waye shi, dan wallahi bazan yarda wani ya sa ki kuka ba................wannan alƙawari na ne duk wanda ya saki kuma sai na rama miki, kisa wannan a kanki............har abada.”* Da haka ya bar musu falon, cikin zafi-zafi da ɓacin rai na haye stairs, saboda sauri, bibbiyu nake haɗawa. Da idanu suka bi ni dan kallon yarinya suke min, amma a yanzu sai suka ji maganganuna suna shiga kansu. Mom ta taso har zuwa in da A'isha take zaune, zama ta yi, da sauri suka rungume juna cikin soyayya. “Mom wacce irin ƙanwa nake da ita?, sam ba a fahimtar ta, tana da shiga rai ga gundura, wallahi ni kaina ina mugun son Inayah.” ta faɗa wani kukan na kwace mata. “Mu yi ta mata addu'a kawai, sai kace mai iska. Dama ina faɗa miki duk soyayya ce yasa take ɓa ta miki rai.” “Hmmmmm Inayah.” Sai Mom ta saketa. “Akwai in da sanya mutum damuwa ya zama soyayya?." “To ku na ku haka yake.” sai suka yi murmushi suna ƙara jin soyayyar Inayah har cikin ɓargo da jininsu.............✍️ END. > Hmmmmm karku manta furucinta dan nan gaba zai ƙara bayyana........a wata siga............ > Ayan da A'isha wannan wani irin ganganci ne, lallaikam. > Me kuke tunanin zai faru? 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```PRETTY SK``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P1️⃣5⃣⏩1️⃣6⃣. ______________________________Ina shiga ɗakina na kwanta kan gado, gaba ɗaya na ƙosa result ɗina na waec ya fito, zaman gidan nan duk ya isheni, nasan saura lokacin kaɗan na tafi Legos Wanda da ƙyar Mom ta yarda, Ina fatan komai da na tsara ya yi yarda nake so. A hankali na kulle idanunwa take wani ɓari na zuciyata ya min tambayar da tunda nake be ta ɓa min ba. “Inayah.......kina so ki jefa kanki ga halaka, *NOLLYWOOD* ba wajen zuwan mata masu kammun kai bane, tsakani da Allah haka ya dace? Ko karatun islamiya ba ki so, why?.” Shuru na yi ina maimaita maganar, da sauri na miƙe tsaye sai kuma na nufa jakkanta, takaddun Islamiya na fiddo da su, zan iya cewa na manta rabon da na yi maraja'a. Na iya Arabic sosai, dan bama yin magana da Hausa a Islamiyya. Ba laifi na yi karatun sosai, sai da na bi gaba ɗaya takaddun na, Fiƙihu, Hadith, nahwu, insha'i, sarfu da sauransu, sannan na ɗauki Alqur'ani. Na haddace izu 30 gan, daga lokacin kuma na sanya wasa sosai, har zuwa yanzu ban iya haɗa 60 ba, da yake ma be dame ni ba. (Astagafirullah 😓) Ina da kaifin hadda sosai, nan fa na fara maraja'an al'qur'ani cikin zazzaƙan muryana mai cike da taushi, ko Ni kaina nasan ina da zaƙin murya, sannan duk wanda ya sanni haka yake cewa. Duk wanda ya ji karantun nan zai rantse wata Hafiza ce wacce ta ke da cikakkiyar hankali take rerowa. Ina tsaka da karatu sai ga A'isha ta shigo tana sakarmin murmushi, da yake na kai aya sai na tsaya ina mai da mata murmushin. Zama ta yi gefan takadduna tana cewa. “Ina alfari da sabuwar ƙanwar da nake gani a yau, haka nake so ki zama, ba irin wancan ba mai son abin da Allah ya hana.” nasan me take nufi dan haka na ce. “Insha Allah na sauya daga yarda nake, kuma za ku yi alfahari da nan gaba.” na faɗa amma a zuciya kuwa cewa na yi. *‘Film ɗaya kawai zan yi, ai ba yawa.’* “Mu yi musaffa.” ta faɗa tana gyara zamanta murmushi na yi duk da nasan A'isha ƙwarowace a karatun Alkur'ani, dan shekara biyu kenan da haɗa sittin, sannan tana zuwa musabaƙa sosai, in da ta ciyo ƙyatuttuka, amma haka mu ka fara yi cikin nishaɗi. Sallah da cikin abinci ne kawai ya yake rabamu, tare muka shiga kitchen, Aisha ta dafa wa kanta taliya, muna yi muna hira wanda muka manta rabon da su yi tsabar rashin jituwa. Dining area muka koma in da muka fara cin abincin abinci, sai a lokacin Mom and Dad suka fito, suma wajen mu suka nufa, zama suka yi in da Dad ke cewa. “Congratulation my Daughter u get 200 score in your Waec.” wani irin ihu na sa ina ɗaga hannu, da sauri A'isha ta buge min kai. “Alhamdullah.” ta faɗa sai na maimaita ina miƙewa, rungume Dad na yi da Mom Ina jin daɗi. “Sai ki fara shiri dan kuwa tuni an sama miki gurbi a school, ko zuwa next week sai tafiya.” murmushi na yi a raina ina cewa. ‘Saura abu ɗaya.' a fili kuwa cewa na yi. “Dad amma ba a hostel zan zauna ba ko?." Kamar yarda na yi tsammani kallona suke yi cike da neman ƙarin bayani. “Shalele, me yasa kika ce haka?.” Faɗin Mom sai na ce “Eh to a makarantu irin haka, sai kuga mata suna ɓata ƴan uwansu, ko da wasu ba su so dole ake musu, gaskiya ni ina jin tsoron Hostel, in dai anan zan zauna gaskiya na fasa.........na haƙura.” na faɗa ina ɓoye damuwan dake fuskanta, a raina kuma ina fatan su yarda, dan wallahi ƙarya nake ba zan iya fasawa ba. “Gaskiya zan fi so ki zauna a Hostel, akwai masu tsaro sosai ba wani abu ai.” “Mom. Wallahi banso........” da sauri A'isha ta katse Ni. “Why not a kai ta gidan friend ɗin ta, sai su dinga zuwa tare da komawa gida, sai mu roƙa ta zauna da su.” Gaba na ne ya faɗi dan babu wanda na sani a can ɗin. “Shawarar nan ta yi, na yarda.” faɗin Dad sai Mom ta ce. “Nima haka.” sai na yi murmushi dan jin sun yarda. Falo muka dawo dukkan mu, A'isha na latsa waya sai murmushi take yi, Mom da Dad kallo suke yi, in da ni kuma na faɗa duniyar tunani. ‘Yanzu idan muka je Lagos, wani waje zan kai Dad? Kuma ta ya zan tsallake wannan ƙaryar? Oh Allah ka taimake Ni, ya zan yi?. So nake na zauna a gidan haya ba Hostel ba saboda babu mai takura min, na fita shooting yarda nake so.....................” “Inayah! Inayah!! Inayah!!!." Da sauri na dawo duniyar mutane, a ɗan zabure na kallon Dad dake kirana. ”Me kike tunani?." “Dad.........ba........ba komai." na faɗa ina turo baki tare sosa kaina. “Ok, je room ɗina, za ki ga wani bag da na dawo dashi ɗazu, na aje a wajen bookshelf ɗaga sama.” na ɗaga mai kai ina miƙewa. Ɗakin na shiga, ban nufa in da ya aikeni kai tsaye ba, sai gaban mirrow na tsaya nufa, na fara taɓe-taɓe, harda ƙwaɗa Jallabiyar Dad, Dan Ina son jallabiyar maza, shi yasa Mom ta hanani zuwa ɗakin, in dai na shiga saina sanya kayansa duk da sun yi min mugun yawa. “Ba ki gani ba?.” na jiyo ya faɗa da ƙarfi. “Gani nan zuwa............" Da haka na cire rigar da sauri, a wajen dana ɗauka na ajiye, sannan na nufa wajen da ya aike Ni, na ɗauka, sai na yi waje har da gudu-gudu. “Dad, wani book na gani shine na fara dubawa, gaskiya ya yi daɗi." Na faɗa ina bashi Jakkan. “Wani book kenan?.” murmushi na ɗan yi dan bansan me zance ba. “Ban duba sunan ba, kawai karantawa na yi.” ya ɗaga min kai yana buɗe jakkan. Zama na yi sai kawai na ga A'isha ta nufo ni tana murmushi da na ɗauka na mugunta ne, take na haɗe giran sama da ƙasa, aikuwa tana zuwa ta kullemin ido tana cewa. “Tashi, muje.” “Malama sake ni.” “Shalele ku zo ta nan." Dad ya faɗa, sai na yi shuru muna takawa, a gabansa muka tsaya sannan na ji ya sanya min abu a cikin hannuna. Sai A'isha ta buɗe min idanuna tana cewa. “Suprise.” Zaro dara-daran idanuwana na yi ina kallon wata haɗɗiyar waya a hannuna. Tsabar an shammace ni da min bazata, sai da na durgushe ina kallon wayar. Hawaye ne na ji sun cika min ido, da sauri na je wayar ina rungumesa tare da mai godiya wanda bansan menake furtawa ba amma nasan godiya dai nake yi. Daga shi na rungume Mom wacce ke ta murmushi. “Yanzu nawa ya huta." Sai na ɗaga mata kai, A'isha na nuna mawa tare da cewa. “Ashenty......oh Aunty Aisha, kin gani." “Tubuli-wayuklifullahu ta'ala.” ta faɗa tana kallon wayarta ƙirar Samsung. “Thanks." Na faɗa ina nufa stairs da gudu. Ɗakina na shiga tare da aje wayar kan mudubu na fara rawar murna, sai dai na yi kaman na minti 3 sannan na tsaya, sai kuma na tsaya sai na fara gode wa Ubangiji. Sai da na natsu tukun na kalla wayar da ƙyau, irin na A'isha ne wanda aka siyamata bayan da na fasa mata na ta. Murmushi na kuma yi sannan na sumbaci wayar, sai na rungumeta a saitin zuciyata, ina jin soyayyar wayar yana shiga cikin jikina. A kunne take dan haka na latsa, wayyo daɗi, ji nake kaman a mafarki na mallaka waya, dan kuwa wancan muna gama exam na bar ma ƙawata. “Allah na gode ma." Na faɗa ina shiga nan in fita nan, har da layin MTN a ciki. Jin wayar na ringing har sai da na tsorata, har ina sakin wayar kan gado. (DAD❤️) sunan da ya fito kenan, sai da na sauke ajiyan zuciya sannan na ɗauka ina washe baki. “Shalele sauko ƙasa." “To, Dad." Da haka na katse kiran sannan na mai da hulana na fito. Kamar yadda na barsu haka na sake su, sai na nufa su, a tsakiyar su Mom na zauna. “Shalele." “Yes Dad." Na faɗa ina kwantawa akan cinyar mom. “Na baki waya yanzu, dan kin kai riƙewa, ina so ki yi koyi da Yayarki, kamar yarda take yi da waya, babu kallon banza, banda chart da ƙawayen banza, no Facebook by now, sannan in ba group na education ba banyarda ba, banda waya da maza da sunan classmate. Ki kama kanki, ki kula, kin ga wannan wayar, takan jefa mutum masifar duniya da lahira, Na aminta da tarbiyyar da na baku kuma karki ban kunya.” ya kai maganar cikin rauni da lallashi. Tashi na yi na rungumesa ta gefe ina jin babu daɗi “Tabbas A'isha ba ta saɓa mana, mun yadda da ita, kema muna so ki zama haka. Duk da ke za ki yi nisa da mu amma a kodayaushe ki dinga tunawa da Allah na kallon ki, ki sa wannan a ranki, amanar kanki za mu baki, kisani idan kika ci Allah zai tambayeki, kuma ke kiwon da Allah ya bamu ne, za mu so mu rabu a duniya lafiya, mu haɗu a aljanna cikin amincinsa.” “Insha Allah Mom bazan baku kunya ba.” na faɗa ina share hawaye. “Amma Dad ai zan iya kallo a YouTube?." Na tambaya duk da wallahi babu mai hanani kallon finafinan *NOLLYWOOD.* “Eh, amma kisan me kike kalla, banda na lalata yara, kuma banda abin da be kamata ba." “Dama ni Film kawai, irin series haka." “Za ki iya but banda Nigeria Film.” A'isha ta faɗa da sigan zolaya, hararar wasa na yi mata. “Ai Nigeria Film kala-kala ne, kaman *The king -........." Da sauri na katse Dad. “Like, *Two father - How to bake - Treasure in the sky - Poor Mom and Rich Mom - To kill a monkey - Our problems - Maids - Love is blind etc. Ai is normal kallon su.” na faɗa ba tare da nasan aika-aikan da na yi ba. “A ina kika san wa'inna fina-finan?." Rintse ido na yi ina haɗiye miyau, dan kuwa wa'inna kaɗan ne daga wanda ma kalla a school. “Da ke fa nake?." Ya kuma tamabaya, dan a gida ban kallo a tv, ko na na fara za'a mai da sunna tv ko labarai. “Da........dama ranar a wayar A'isha ne na ga an yi posting a facebook, na dukka postern kuma aka rubuta, yara za su kalla." Na faɗa ina fatan ƙaryar ya fitar da Ni. “Ai banda Facebook a waya na." Aisha ta faɗa tana danne dariyar dake cinta. “To a ina kika kalla?.” Mom ta tamabaye ni. “To na manta amma a cikin wayoyin kune." “Nima banda Facebook a ciki." Sai na ji kaman Mom ta ƙwalamin abu ne a kai. Fuska na haɗe ina shirin fashewa da kuka, dan in Dad ya gane ƙwarya nake, zai amshe wayar ne, dan ya tsana ƙarya. Jin sun washe da dariya, ya sa na san wasa suke mun, ai da biyu na miƙe, ni a dole na yi fushi, na dau wayata ina hucewa da gudu. “Ku dena zolayar min Shalele." Dad ya faɗa yana mai da hankalinsa a kan Tv. Ina shiga ɗakina na kulle sannan na haye gado dan yau babu barci, sai dai babu komai akan wayar, amma akwai data, da haka na kunna na shiga Tiktok, sai dai Ni ban son kallon raye-raye da shirme na mutane, dan haka na koma Youtube, ai wani ɗan ihu na yi ganin ga fina-finai kaman hauka sun fito. “School mate." Na faɗa ina kallon poster na wasu ƴam mata da samari cikin uniform na school, sun yi ƙyau sosai, duk da fuskokinsu babu alamun wasa a ciki, da haka na shiga dan kallon Film ɗin ina ji raina fes banda wata matsala................✍️ END > Ƴar NOLLYWOOD 🔥😁, hmmmm akwai abu. > Har yanzu ba mu fara wasan ba GUY'S 🥴🥴🥴. > INAYAH an yi waya, gaskiya zan zo kallo nima. 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```PRETTY SK``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P1️⃣7⃣⏩1⃣8⃣. ______________A Kwana a tashi, haka muka dinga shirye-shiryen tafiya, munje kasuwa an yi min siyayya sosai, tare da Mom da Dad za mu je, gaban ɗaya sai na ji kaman na fasa, dan ina son rayuwa jikin iyayena amma in Ina tare da su ba zan zama *ƳAR NOLLYWOOD* ba. Ranar ba ta kyar, yau Monday, da misalin 9:30 muka nufa Airport, A'isha kuma tun safe mukayi sallama ta tafi school, har kuka muka yi kamar kar mu rabu da juna, amma haka dai ta bar gidan tana hawaye. A filin jirgin, gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, muna nan zaune muna jira a kira ƴan jirgin mu dan Flight za mu bi. *GIƊAƊO MANSION* _______Babu wani sauyi dangane da rayuwar gidan, sai dai tsanar da Ammee ke ma Ummee kullum ƙaruwa yake, haka dai suke rayuwa. Sarah ce tsaye a bakin motar Ahmad wanda zai tafi Lagos dan a can suke shooting film. “Dear gab da bikin mu zan dawo, series ɗin da muke yi saura kaɗan mu gama." Ya faɗa yana mata wani irin kallo. Sarah dake kallon ƙasa ta ɗaga mai kai, dan kuwa ba ƙaramin tsanar wannan aikin na sa take ba, babu wanda be san irin iskancin da yake ba, amma babu mai magana saboda Ameensa ta rufe ma kowa baki. Da tana da dama *NOLLYWOOD* Film za ta fara hanasa dan kuwa irin baɗalar da yake yi sai dai a yi shiru, gashi ko kunya ba ya ji, abun na ba ta mamaki sosai. “Ba ki ce komai ba?.” “A sauka lafiya." Ta faɗa a hankali. “Ki kulamin da kanki da kayan daɗi, wallahi duk na ƙosa, Ni dama Lagos ɗin zamu je tare bayan ɗaurin auren" Tafiya ta fara yi kamar ba da ita yake ba. Murmushi ya yi sannan ya yi ma Driver magana, take aka buɗe daya daga cikin gets ɗin suka nufa waje.......... *AYAN* _______Shuru ya yi a cikin mota yana tunanin abin yi, ya yi ma su Abba maganar da ya kamata su nema ba'asi amma sunƙi, sai dai kaman shirye-shiryen bikin suke yi, tsaki ya ja mara sauti, yana shirin fita daga motan. Sai ya hangi A'isha ta fito daga na ta motan ta, niƙaf ta sa yau, sai ya ɗau waya ya kirata. “Zo mu gaisa, ina mota na." Ya faɗa yana katse kiran, dan yasan za ta iya kawo mai uzuri. Motar ta nufo a natse kamar yarda take, tana zuwa ya buɗe mata, sai ta shiga. “Ina kwana?.” ta faɗa cikin ɗan rawar murya. “Sun wuce ne?." Sai ta ɗaga mai kai. “An jima za su wuce.” “Allah ya tsare su, addu'a za ki musu, ba kuka ba." Sai ta daga mai kai. “Har Ƙanwata za ta wuce karatu ba mu haɗu ba." Sai Aisha ta yi murmushi dan kuwa sau uku da Ayan ke zuwa, tana ce ma Inayah ta fito su gaisa, sai ta ce _Ba za ni ba eyehh_ da haka take ƙyaleta. “Aisha." Sai ta kallesa ta cikin niƙaf. “Daga yau wasan kwaikwayo zai fara, yau zan ƙara ma su Abba magana, to at anytime za ki iya samun kira daga wajensu. Idan har ba ki yi harda za su ɗauka da gaske ba, ba za su bari a yi auren ba, ki yi acting sosai.” “Karka damu." Ta faɗa tana jin in wannan ne ai an gama dan har kuka za ta yi, kuma za ta zuzuta komai, wannan ake kira da *Heart Flighting when you fail, it's mean......... your heart is die forever* ............ Adam ana sauke sa a airport, nan fa mutane suka an kara da shi, take aka fara mai hotuna, mutane suka zagaye sa dan kuwa A.G ya shahara sosai, babu wanda be san shi ba, ya shiga duniya gaba ɗaya. “A.G hoto ɗaya............Sa hannun ƙauna......... Please kalla nan.............. Please 1minute Sir." Haka mutane suka cikasa da tambaya, kuma suka zagayesa. Tsayawa ya yi yana yi ma wasu, signing, wasu kuma hotuna ya yi da su kwanin burgewa. Daga in da nake na hangi A.G, tauraron mai ci tashe a *NOLLYWOOD*, na kalla fina-finan sa guda 5, kuma duk sun yi daɗi, fiye da misali. Ai da sauri na miƙe tsaye. “Ina za ki?." Mom ta faɗa ganin irin yarda na zabura na miƙe. “Uhmmm.........I want to buy..... Eh gashi can a waje." Na faɗa ina ɗan yaƙe. “Take." Dad ya ban ₦1000, daban ya hangi abin da nake ambata ba, amsa na yi ina yin waje, ta glass na hangasa wanda ya raba cikin wajen da waje. Fita na yi ina buɗe ƙaramin jakkarta, pen da memo na ciro ina nufan wajen. Tun daga nesa idanunsa suka sauka akanta, Budurwar yarinya, fara mai manyan idanu, ga siririn hanci. Black abaya ne jikinta, sai ta yafa vail, ga kuma ƙaramin jakka da black ta rataya, ta yi wani masifaffen ƙyau, ga wani murmushi take sauka a fuskarta har kumatunta suna lotsawa. “Wow." Ya faɗa yana nufanta, dan mutanen sun ragu mai, ita ma wajensa take nufa. “Hey." Na faɗa ina tsayawa a gabansa. “Hello." Ya faɗa a hankali yana min wani irin kallo mai narka zuciya. “A.G, ai Ni fans ɗin ka ce. Pls your signature." Na faɗa badan iya abin da nake so bake nan. Da mamaki na ga harda phone number ya sanya min, kuma sai murmushi yake sakin min. “Gaskiya na gode sosai." Na faɗa ina son juyawa. “Ya sunan ki?." Ya tambaya. “Inayah." Da haka na wuce, na barshi tsaye yana bina da kallo, daga sama har ƙasa, har yadda nake tafiyar kai ka ce wata sarauniya ce, be ankaraba har na shige. Nannauyan ajiyan zuciya ya sauke mai shafan kansa. Ina kowa ma ciki aka kiramu, shiga jirgi muka yi, take jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya. Ina jin na fito da ƙafar dama, na fito da babban sa'a, gashi daga fitowa na samu number A.G. A V.I.P muke zaune, murmushi nake yi sosai ina daga bayan su Mom, a hankali bakina ya furta. “Nollywood gani nan zuwa............” na faɗa ina rufe idanuna tare da wani irin murmushi na musamman...............✍️ END. 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊 ``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P1⃣9⃣⏩2️⃣0⃣. ___________Ba mu muka sauka ba sai misalin 3:00pm, da yake tun daga can Dad ya gama komai, a airport muka sake haɗuwa da A.G wanda ke ta zabga min murmushi, ina mai da mai kamar irin mun saba ɗin nan. manyan motoci uku ne suka ɗauke sa, in da mu kuma wata guda ɗaya ta ɗauke mu da kayan mu. A gefan Driver na zauna ina ƙare ma Jahar Lagos kallo, da mutanen da ke ciki, murmushi na kuma yi ina tuna abin da Dad ya ce min shekaran jiya. ‘Mu je school ɗin ku, sai a duba file ɗin ƙawarki, nasan za mu samu number familyn su, in ya so su sai su bamu number ainiyin iyeyenta.’ a lokacin har wani zufa na ji ya yanko min, amma na daure na ce. “Dad ba sai mun yi haka ba, kawai mu bari in munje can sai mu nemeta." ‘Lallai ba ki da hankali, Jahar Lagos an ce miki wajen wasa ne balle unguwar Ikeja.' Mom ta faɗa, take na fara zazzaɓin ƙyarya haka aka dai fasa zuwa. “Wow" na faɗa ina kallon wani unguwa da muka shiga bayan munyi tafiya mai tsawo. Yadda kasan estate ɗin mutum ɗaya wajen, gaba ɗaya gidajen iri ɗaya kuma pentin ma iri ɗaya. Ɓangaren dake kallon wannan ɓangare kuma, wani babban gatangane wanda ya cinye tsawon wajen. Ciki muka shiga ashe nan ne school ɗin, da mamaki nake ƙare ma school ɗin kallo, dan kuwa makaranta ta fi unguwar mu girma. Ga manya-manyan gidaje, ajujuwa suma ɓangare-ɓangare, gwanin ƙyau. Ga tsirarun mata da suke sanye da fararan kaya, wasu kuma, farin riga da blue trousers, wandon ne dai kala-kala gwanin ƙyau. Hmmm kuɗi duniya ne, dan kuwa muna shiga office aka basu certificate, nan da nan Dad ya ƙarasa komai sannan muka fito haraban school ɗin. “Sir gobe da ƙarfe 7:30am, nan za ta zo, za su ba ta uniform da takaddu, sannan a faɗa masu lokacin zuwa, dan har an fara karatu." Wani wanda ga alamun, malami ne a wajen, ya faɗa. “Okay Sir thank you." Da haka suka kuma gaisawa, sai ya wuce. “Can ne Hostel." Dad ya faɗa yana nuna min ɓangaren dama. Hostel ɗin ne kam, dan kuwa har da igiyar shanya na hango, take na haɗe rai dan banson zaman ciki. Ko iya zuwan mu nan, na fahimci mugun tsaron da suke dashi, dan ga jami'ai nan ta ko ina, babu daman fita. Baki na ta ɓe ina haɗe fuska. Sai dai da mamakina muka nufa mota, hawa muka yi sannan muka bar school ɗin, a cikin jerin wa'inna gidajen, na ga mun tsaya a number U.7. Madaidaicin gida ne wanda muka shiga da mota har ciki, ba laifi yana ƙyau sosai, key Dad yasa tare da buɗewa, Ni dai binsu kawai nake yi. Ƙaramin falo ne wanda akwai komai na more rayuwa, kujeru, fridge, A.c, TV da sauransu. “Wow Dad wannan gidan ai ya yi ƙyau sosai.” sai ya ɗaga min kai yana cewa. “Allah ya so munyi magana da wuri da ba lallai mu samu ba, gaba ɗaya gidajen nan na haya ne, wanda iyaye ke haya wa yaransu. Suna da dokoki sosai wanda duk sai da na bi. Akwai security guard guda uku da na aje miki, sannan ku biyu za ku zauna ke da wata yarinya, ga ɓangaren ki can." Ya kai nan yana nuna min wani ƙofa. Ban damu da wasu guard da yace ba na rungumeshi ina mai godiya. “Sai ki kula, dan kuwa yarinyar ba ta son hayaniya, da kyar Dad ya samo yarinya irin wacce za ku ƙaru da juna.” “To Mom.” “Kuma ki kama kanki, kar kiga bama kusa ki samu daman aikata abin da be kamata ba, to ki sani Allah yana kallonki, dan mun yarda dake shi yasa muka kawo ki nan. Ki mai da hankali cikin shekara uku ki kammala, in ya so lokacin sai mu aurar da ke, a gidan mijin ki sai ki ƙarasa.” murmushi na yin gaba. Zan iya cewa ban taɓa tunanin wai ni zanyi aure ba, kwanta-kwata baya cikin tsarina nan kusa, ji nake babu wanda zai iya rayuwa da Ni, domin Ni ɗin nan sai a hankali. Ƙofar na tura tare da shiga, da wayata na yi amfani wajen kunna hasken ɗakin. Ɗakin ya yi kyau sosai, babu wasu tarkace, bed, mirrow, wardrobe da bookshelf. “Gaskiya gidan nan duniya.” na faɗa ina hawa kan gadon, daga nan na duba toilet. Komai ya burgeni, dan haka na koma falo, nasan su Dad sai gobe zamu koma Kaduna. Abinci aka kawo mana muna ci sosai, sannan suka tayani jera kayana, kayan abinci muka kai Kitchen. Komai dai ya yi need. Zaune muke a falon muna ɗan hira sama-sama dan jikina ya min tsami saboda na jima ban fita ba. “Yanzu Dad ko mai girki ba za ka ne man min ba, Ni ka rage mutum ɗaya a cikin wa'incan samudawa, a kawo mai aiki." Na faɗa ina tuna ganin da na yi musu ɗazu, wallahi manyan mutane masu kaman Samudawan. “Hmmmm da kanki za ki dinga girki dan kuwa karatu da girki na kawo ki.” sai Mom ta amsa maganar. “Akwai classes na koyar da abinci a YouTube, su za ki dinga bibiya, sai ki dinga practice kina ci, a kwana a tashi za ki iya." “Mom ta ya zan kowa girki a waya......Ni dai a'a, kinsan ban zama a gida sai Sunday shi kuna hutawa nake yi, sauran ranakun daga safe har yamma ina school, ko na dawo ban iya wani abu.” “Eh, yanzu ai kina da time, ki yi karatu ki yi girki, kuma a cikin school ɗin akwai ɓangaren da suka koyar da karatun islamiya duk weekend shima na miki register, sai ki dage dukka." Dad ya faɗa yana gyara kwanciya akan kujera mai uku. Mom na kalla na yi ina marairaice fuska, murmushi ta yi tana ce min. “Idan yanzu ba ki iya girki ba sai yaushe? Sai after 3yrs kike so ko me? Kina gamawa aure za mu yi miki, ya rage kanki ki koya ko dangin miji su zageki.” murmushi na ya ina miƙewa tare da cewa. *“Akwai uban da ya isa ya zageni ne?. Hmmmm wallahi babu dan kuwa sai na rama.”* “Ban ji me kika ce ba." “Mom ba da ke nake ba." Na faɗa ina shigewa bedroom. Anan muka kwana ni da Mom, Dad kuma a falo, washegari da safe suka rakani school, sai da aka ƙarasa min komai sannan na yi sallama da su. Kuka na yi kaman ƙaramar yarinya, gashi babu daman binsu, haka suka tafi suka barni ina ta rusa kuka, Allah ya so iya kuka ne banda birgima. Sai dai ina cikin kukan na tuna dalilin zuwa na nan state ɗin, take na yi shuru ina goge hawayena. Sai washegari zan fara shiga class, da haka na juya zan shiga gida, ɗaya daga cikin wa'inna manyan maza suka buɗe min na shiga, ina kuma fashewa da wani sabon kukan dan kuwa banson kallon su. Ina shiga room ɗin na kwanta kan kujera ina ƙara fashewa da kuka, ko ma yayane rabuwa babu daɗi, akwai zafi. Hatta su sai da suka yi kuka, dan ba su ta ɓa yin nisa da ita ba, kullum ina tare da su, ga irin ƙaunar da suke min. Mom ce ta rungume Dad tana hawaye. “Yanzu shike nan, na yi nesa da ƴa ta.......... tun farko shi yasa na ce banso amma......" Sai kuka ya ci ƙarfin ta. “Kiya ƙuri, mu daure shekara 3 ba yawa, kuma duk end of the year ana basu hutu.” sai ta kalla wayarta wanda sunana (SHALELE ❤️) Ya fito kuma shine kira na 7 da ta fara jero mata. “Sai mun koma gida zan ɗaga, bayan ta karya min zuciya shine za ta dameni da kira.” Dad murmushi ya yi yana goge hawayen da ya taru mai, ai suna hawa mota yasa wayarsa a flighmode dan yasan halin Inayah za ta damesu da kira ne kuma da zai ce ta biyo su ba za ta yarda ba..... .................✍️ END. > Update ba yawa ko... I'm sorry, ku yi comments sosai, an jima na kuma saki muku wani. > Toh fa Inayah an shiga Lagos, fatan sa'a. 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊 ``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P2️⃣1⃣⏩2️⃣3⃣. *Aisha* ___________Jikinta a mace ta wuni a school, ko bayan da ta koma gida hakan ta kasance, duk da mai aikinsu ana take kwana, ta ji duk babu daɗi. Da misalin 5:21pm wayarta ya hau ringing, tana dubawa ta ga masoyinta, ɗauka ta yi tana kai kunninta. “Aishata, iyayena sun ce na kawo ki wajensu yanzu, ya za'a yi? kinsan banson su Dad su san plan ɗin nan." Shuru ta yi sai ta ce. “Ka zo muje, zan kira Mom na ce zan ni wani waje.” “Ba matsala?.” ya faɗa a hankali. “Eh babu." Da haka ta katse kiran. Number Mom ta Kira, bayan Mom ta ɗauka, ta ɗauki permission na fita dan siyan abu, Take Mom ta yarda. Da haka ta miƙe, bedroom ta nufa, shiryawa ta yi sannan ta zura hijab ɗin ta, sai dai me, gabanta ne ya fara bugawa ninkin bugawan da yake yi. Addu'a akwai take ta jerowa duk wanda ya zo bakinta, ta dai sanar wa mai aikinsu za ta fita. Motarsa ce ke dake daga gefan gidan su, nunfashi ta ja sosai sannan ta nufa tana jin gabanta na tsananta bugu, amma haka ta daure ta isa. Buɗe wa ta yi ta shiga sa sallama. “Wassalamu alaikum Beauty.” ya faɗa yana kunna motar. Da haka ta yi shiru, ta ci gaba da addu'oi. Motar ta ɗau hanya, dan ma tsakaninsu ba wani nisa. A bakin katafaren gidansu ya yi parking, kallonta ya yi kuma ga alamu tana cikin damuwa, ya kashe kiran. “Aisha, mu koma gida kawai, ba son na cutar dake, sai dai ba mu da wani hanya sai wannan. Kina sona nima ina ƙaunarki." Take zuciyarsa ta ce. (ƙarya ne, so kake ka ƙyauce ma auren Ruma) Sai ya rintse idanunsa. “Yaya Ayan karka damu, mu shiga." Ta faɗa cikin dauriya. Horn ya yi aka buɗe mai get ɗin sannan ya shiga. Maimakon ya shiga ta babban falo sai suka kewaya suka shiga falonsu Abba. Babu komai a babban parlourn da ya haɗu kaman fadar sarki. A'isha ta san duk kuɗin Dad ba zai kai na wa'inna ba duk da su haɗaka ne. “Zauna." Sai ta zauna kan carpet. Shi kuma ya bi wata ƙofa ya fita. Tana zaune tana jan Tally counter da kullum ke yatsarta, ba'a ɗau lokaci ba, ta ji an fara shigowa ciki, sai dai ta kasa ɗaga kai ta kalla mutanen da suka shigo. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalla manyan maza guda huɗu wa'inda suka yi mata kwarjini da cika ido. Gaishesu ta yi cikin rawar murya, biyu suka amsa biyu kuwa wani irin kallo suna watso mata. Ayan kuwa kusa da ita ya koma shima ya zauna, sai a lokacin ya ji wani ɓari na zuciyarsa na, hanasa wannan ɗanyen aikin amma ina, (Yana cikin zanen ƙaddararsu wannan ƙaryar, kuma za su yi nadama a lokacin da ya ƙura musu, koda wasa ba su san hakan zai shafi rayuwar aurensu ba......😓) “Yarinya ya sunan ki?.” muryan Abba cike da kamala ta fito. “A...A'isha.” “Mai babban suna kenan, ya ce ke yarinyar Alhaji Musa ne ko?." “Eh." “Menene alaƙarki da Ayan?.” faɗin Baba Yusuf cikin ɓacin rai. Miyau ta haɗiye dan kuwa Ayan ya ce mata. _(Ni ce musu na yi, akwai babba alaƙar dake tsakanin da ke wanda in ban aure ki ba, akwai matsala, hakan zai iya ɓa ta musu suna da Martabansu.)_ Idanunta ta rufe sannan ta buɗe. “Saurayina ne." Ta faɗa cikin wani irin rauni. “Hmmm ba ki san da cewa *GIƊAƊO FAMILY*, ba su auren bare.” “Abeey........" “Shut up Ayan. Ba da kai nake ba.” Baba Yusuf ya faɗa cikin ɓacin rai. Take cikin A'isha ya kaɗa wanda har ɗan ƙara sai da ya yi (Ƙur-ƙur) “Eh na sani." Ta faɗa a natse. “Kuma shine kika ci gaba da tarayya da shi. Ko dai dukiyarsa kike kwaɗayi?." Ya watso mata maganar wanda ta ji kaman ruwan zafi aka watsa mata. Tasan suna da kuɗi, kuma da za su raba su huɗun nan, babu wanda zai wuce Dad, sai dai su zo kai da kai. Take wata irin ƙwarin gwiwa ta saukar mata dan kuwa yanzu faɗa za ta yi da soyayyar Ayan, in ma ta ɗaure ta ci, ko ta faɗi, wanda shine zai rabata da shi har abada, dole ta fuskanci wannan al'amarin da kanta. Take ta ɗaga kanta ta kalla wanda ke maganar sannan ta ce. “Ko ɗaya, badan kuɗi ba ne nake son Yaya Ayan, domin cikin kuɗi na tashi, kuma wanda suka fi shi kuɗi sun nemeni kawai........” “Kawai mene?." Baba Yunus ya faɗa shima rai a ɓace. “Ku kwantar da hankalinku, ku yi mata magana cikin taushi.” faɗin Abba. Dama Ayan ya nuna mata hoton maza biyu, Ya ce duk mai suka ce karta yi musu, amma sauran komai ta ce. “Yarinya muna jinki. Me yasa Ayan ya ce aurenki ya zama dole, kuma in be aure ki ba akwai matsala?.” A hankali ta kalla Ayan, sai ya ɗaga mata kai. “Daga gani nasan kai ne mahaifin Yayana, dan Allah duk abin da zance kar ka hukunta shi da babban abu, kuskure ne mun riga munyi cikin rashin sani. Ni ɗalibarsa ce, mai sonsa da ƙyaunarsa. Tun baya kulani har ya fara kulani, a kwana a tashi, ya fara sona, soyayya muke yi mai tsafta da shi, sai wata rana yake faɗa min dokar familyn nan, a ranar na shiga damuwa ainun, haka washe gari na je school cikin wani hali, to sai na faɗa ma ƙawata wata Gloria..................Ni bansa shirinta ba sai ta bani wani abu ta ce na sha, ban yi musu ba nasha, sannan ta rakani bakin office din Ayan................shiga na yi shima na bashi wani abu a kofi, be yi musu ba ya sha.......................Sai a lokacin na fara jin jikina......ya na......ya .............” sai ta fashe da kuka mai shiga rai. Ayan da jikinsa ya yi sanyi dan kuwa yarda yake maganar ka ce da gaske ne. “Yi shiru, ɗaure ki ƙarasa.” Baba Musa ya faɗa. Sai da ta share hawayenta sannan ta ci gaba da cewa. “Ashe maganin gushewar hankali ne da tayar da............ sha'awaaaaa.............take hankalina ya gushe, shima Ya Ayan. shine...... shine...........shine.....muka aikata al...............a....a.....al.....alfasha......” sai wani kukan ya kuma cin ƙarfinta, da sauri Baba Yusuf ya miƙe tsaye da jin furucinta. “Ƙarya ne, karku mai da mu jahilai. Wannan ai ƙarya ne, hmmmmm ba yau aka haife mu ba, munga shekaran jiya, munga jiya, kuma gamu cikin yau. Ku faɗa mana abinda zai yi dai-dai da hankalin mu." “Yusuf zauna su gama magana, yi haƙuri. Ayan ci gaba tunda kuka ya hanata ci gabawa.” Ayan nunfashin ya ja, sannan ya ɗaure ya ci gaba shima cike da tsoron da ya yafa ma kansa. “Wallahi Abba cikin rashin sani komai ya faru, ban iya tuna komai dake faruwa da ni ba sai bayan mun gama komai, anan na shiga tashin hankalin sosai, bayan faruwar haka da kyar A'isha ta bar kuka dan a tunaninta da gangan na aikata mata haka.......sai yamma sosai na kaita gida wanda har lokacin kuka take yi. Daga nan ba mu sake waya da ita ba har na tsawon sati ɗaya, dan kuwa Ni kaina banda lafiya lokacin. Sai wata rana ina zaune a office damuwa ya isheni, Ina son zuwa ganin halin da take amma ina jin tsoro abinda zai biyo baya.............sai kawai ga ta a office ɗina. Cike da mamakina na ke kallonta, dan ban ta ɓa tsammanin za ta kuma raɓata ba ta ɓa, dan a ganin laifi name................bayan ta zauna shine take bani haƙuri da faɗa min aikin Gloria ce, wai ai tasan addinin mu in an yi haka dole ake aure........” take ya yi shuru yana dafe kansa kaman da gaske. Ganin haka A'isha da tasa cikin shashsheƙan kuka. “Yaya wallahi bansan da mugun nufi ta yi ba.......Baba wallahi ban sani ba, kawai daga baya naga saƙonta akan haka, bayan na faɗa mai ya dinga kuka akan ta cucesa dan ya ɓa ta min rayuwa, Ni kuma da haka na ce mai ai dole ya aureni ko kuma na faɗa wa Dad ɗina, ba kuma zance tsautsayi bane, zance da gangan ne.........yanzu haka ina da juna biyu, shi yasa na ta da maganar dan in iyayaena suka sani..............." Sai ta kuma fashewa da kuka. Ɗakin ne ya yi tsit sai kukan ta dake tashi cikin wani irin yanayi, hatta su Baba Musa sai da jikinsu ya yi sanyi. “Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un.” shi kawai suke faɗi cike da tashin hankali. “Mahaifinki ya sani?.” Baba Musa ya tambaya. Girgiza kai ta yi. “Ayan tashi ka mai da ita gida, sannan ka nema izinin mahaifinta akan next week zamu zo maganar aurenku, ƙwanda a yi auren, in ta haihu sai a sake ɗaura muku aure.” Abba ya faɗa cikin ɗacin rai sosai. “Yanzu daga sun faɗa sai mu yarda, muje asibiti a duba ta a gani, in babu ciki, kawai su haƙura da juna, in akwai a zubar dashi ko nawane sai mu biya yarinyar. Amma maganar Auren bare be ta so ba, dan wasiyyar Baban mune.” Yunus ya faɗa cikin ɗaga murya. “Kuma kunsan akwai maganar aure tsakanin su da ƴata.” “Yusuf, za mu tattauna wannan amma mu fara ji da wannan masifar. Yaro kuje." Kafin Ayan ya miƙe Yusuf ya miƙe yana cewa. “Wasiyyar babanmu dole mu cika, dan munsan darajar sa." Da haka ya fice sai Yunus shima ya ja tsaki ya fita. “Ya Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawan.” “Ameen Musa. Kaina ya ɗaure sosai, dole dai ka aura Ruma ko ba yanzu ba, dan shine maslaha, yanzu ka mai da ita, in ka dawo za mu yi magana, Yarinya ki kwantar da hankalin ki, ba za'a zubar da cikin ba." Da sauri A'isha ta ce. “Baba dan Allah karku yi mai komai, wallahi be da masaniyar haka...........karku hukuntasa ta hanya mara ƙyau, komai da ya faru ni ce sila.” ta faɗa wani kukan na ƙwace mata. Hawaye Ayan ya share dan kuwa shima ji yake kaman komai dake faruwa gaske ne. Cikin rauni Abba ya bar room ɗin sai Baba Musa ya ƙara tausar su sannan ya sallamesu, ta ƙofar da suka shigo nan suka bi har waje. Sai da motar Ayan ta bar layin tukun ta fara jin iska mai daɗi na ratsata, a bakin wani provision ya tsaya sannan ya fita, be jima ba ya dawo riƙe da leda. Pepsi ne mai sanyi da suprite, ba ta ɗaya ya yi shima ya buɗe ɗaya. Shanye nashi ya yi ita kuma ta sha kusan rabi. Numfashi suke mai da wa a hankali. “Wallahi komai sai ya min kaman a gaske, balle yarda kika dinga zubar min da hawaye, yau na ƙara tabbatar da soyayyar da kike min, da ina da dama rungumeki zan yi in yi miki godiya sosai.....wallahi A'isha ina jin ki a cikin ruhi na. Ina sonki." Ya faɗa yana riƙe mata hannu tare da matsawa. “Nima ina sonka sosai, ji nayi kukan ya zo min.” “Hmmm mun iya acting sosai, yanzu damuwana ɗaya, cikin da muka ce, ya zamu yi?.” “Allah ma sani, kawai idan ka ga alamun za su ta da maganar zai muje asibiti mu yi na ƙarya." “Shike nan kawai, muje magrib na yi, yau za ki yi kwanan shuru babu su Dad.” ta yi murmushi kewansu na motso mata.............✍️ END. > Innalillah wa'inna ilaiyi raji'un 🙆🙆🙆🙆🙆 wannan irin ƙarya haka, hmmm anya kuwa Ayan da A'isha ba ku kira babbar matsala ba. > Kaina ya kulle akansu, hmmm muje dai amma fa da matsala ga alamu. > Acting kuma ai ke jinin Ƴar NOLLYWOOD ce 🤭, dole ki iya iri-iri 🏃🏃🏃. *📢 Assalamu Alaikum Everyone!* Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖 Idan kina son: ✅ Sabbin *updates* ✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi ✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman* To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi: 💰 *₦300 only* kafin mu gama. 🕒 Bayan an gama: *₦500* 🌟 *V.I.P Access*: *₦1000* _Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_ Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi. ```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number: 07038436703.``` ~SING BY PRETTY SK~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊 ``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P2️⃣4⃣⏩2️⃣5⃣. *INAYAH* __________Haka na wuni a gidan bani da walwala, amma da Mom ta kira akan sun isa gida, shine na ji dama-dama, ina kwance akan kujera na toshe kunnuwa da Earphone, sai ji na yi ana ƙoƙarin shigowa ɗakin. Da sauri na zabura sai kuma na tuna yau wacce za mu zauna tare za ta iso. A hankali ta turo ƙofar, trolley ɗin ta ne suka fara shigowa, sannan ta shigo gaba ɗaya. Ƙyaƙƙyawa yarinyar wanda za mu yi sa'a ɗaya, sai dai na fita ƙiba amma za ta fini tsayi, ba fara ba ce tana duhun fata sosai, sai dai Beauty ce. Atamfa ne jikinta ɗinkin doguwar riga, ya sha stones sosai. Murmushi na ga ta yi min, sai na yi mata yaƙe dan ni sai na gama karantar mutum nake sake mai. Ita da wasu ne suka dinga shigowa da kayayyakinta, na abinci da kayan sawa. “Ƴar Uwa Barka da gida." Ta faɗa sai na ɗaga mata kai dan ban ji me ta ce ba, ko ɗazu nasan sallama ta yi amma Earphone din kunni ba be bari na ji ba. “Hey, Sis.” ta kuma faɗa tana ɗaga min hannu, ga dukkan alamu dai yarinya ce mai son mutane. Earphone ɗin na cire ina kallonta, sai na ja dogon numfashi na furzar sannan na ce. “You are welcome.” “Thank you, wannan ne room ɗi na?." Sai na nuna mata da hannu. Gyalenta ta cire ta fara shiga da kayan Ni kuma ina rakata da ido. “Haba Inayah ki taimaka mata mana.” zuciyata ta faɗa min. ‘okay, nasan ko zan yi wanki za ta tayani.' na faɗa a kasan leɓe na. “Can i help you?.” sai ta juyo tana riƙe da leda. “Na gode." “No bara na tayaki na ga kayan da yawa." Murmushi ta yi. Aikuwa tare muka ƙarasa, sannan na ta ya ta shirya kayan, kayan abinci kuma muka kai Kitchen gefe guda ta zuba nata. Da alamun itama ba rashi dan kuwa ta zo da kaya masu yawan gaske. A falo muka zauna bayan mun gama, zuwa lokacin har na saki da ita. “My name is Mubina, what of you?.” “Inayah." “Wow nice name." “Thanks. Wani cost ki ke?." Sai ta kunna mana Tv. “Gynecologist." Murmushi na yi dan nima shine. “Wow, same room, same cost and same mate." Sai ta zauna gefena tana murmushi itama. “Nice to meet you." Ta faɗa, Ni kuma na mai da hankali na ga Tv in da ta sanya Star plus, in da suke yin Film ɗin *KULFHI THE SINGING STAR.* “Sis Ina son Series ɗin nan." Sai na mai da mata murmushi ina hawa Youtube dan kuwa ban juran kallon India film. Tare muka yi sallan magrib da isha'i, bayan mun gama muka shiga kitchen. “Ni dai ban iya girki ba wallahi, kuma an ƙi ɗaukan min mai aiki.” murmushi ta yi sai ta ce. “Ki ce na fiki ta wannan wajen, dan kuwa na iya wasu abubuwan. Yanzu dai me zamu ci?." Sai na buɗe wajen kayana, ina bin ko ina da kallo. Indomi na ciro guda huɗu na ce. “Nima na iya, ki dafa Indomie Ni kuma zan soya ƙwai." Dariya muka yi dukkan mu. Hanata buɗe na ta pack of Indomie na yi, nawa muka dafa sannan na soya eggs ɗin. Wallahi da gaske nake na iya siya eggs sosai. Hmmmm Allah kenan, cikin some hours jinin mu ya haɗu da abota. Sai 10:54pm muka rabu, ta shiga room dinta Nima haka. *************** Ina cikin barci na ji yo tana dukkanmin ƙofa, tsaki na ja ina tashi dan jiya sai 1:20am na kwanta. “Inayah, ki tashi 8:00am ake fara karatu, ance in mutum ya yi late wanke hostle restroom ya ke yi." Ai da sauri na wuntsulo daga gadon ina watstsakewa.. “Thank You, ki shiya ganinan zuwa." Da haka na shiga restroom Ina miƙa. 7:35am na fito cikin uniform tsaf, Farin ƙaramin hijab, sai farar riga mai tsayi, sannan dogon wando, na yi kyau sosai. Mubina ma tsaf ta shirya, sai dai ba ta sa hijab ba tana cin bread ne. Nima zama na yi ina ɗaukan bread ɗin. “Na ƙoshi ki yi sauri." Ta faɗa tana miƙewa. Tea na sha sharp-sharp, sannan muka fita kowacce da jakkanta. Ina tafiya ina ƙara sa cin bread ɗin. Masu gadin mu suka gaishe mu, muka amsa, ɗaya kuma sai da ya raka mu har class, sannan ya zauna daga can waje. Babbane class ɗin wanda zallar ƴammata ne, sai shigowa ake yi, da yake na saba zaman baya sai na ja Mubina muka zauna a can layin ƙarshe. Wayata na ciro sannan na kira number Dad. “Shalele ba ki tafi ba?." Ya faɗa daga cikin wayar. “Ina school, Good morning." “Morning Dear, what's wrong?." Sai na kalla window in da nake hangen Guard ɗina. “Dad Guard ɗaya bina yake fa, me yasa?." Na faɗa ina rage murya. “Yes, biyu masu tsaron gida, ɗaya kuma duk in da za ki zai kasance yana binki.” “Amma me yasa?.” “Saboda ina son ki.” ji na yi kaman na fashe da kuka sai na daure na ce. “I will call you later." Sai na kashe kiran. “Menene?.” Mubina ta tambayeni. “Wai wancan mutum Ni zai dinga bi.....tab da sake." Murmushi ta yi sai ta dafa kafaɗata. Kafin ta yi magana wasu malamai maza biyu suka shigo, ganin kowacce yarinya ta fara sanya I.D card ya sa muma muka sanya namu muna kallonsu. Gaishesu muka fara yi, suka amsa sannan ɗaya ya yi mana bayaninsa. Muna da sabbin zuwa, da haka aka dinga kiran sunaye suna fita kowacce tana bayanin kanta a gaban student. A ƙalla mun kai 50, dan babba ne hole ɗin. “Mubina Abubakar." Ya faɗa, sai Mubina ta miƙe tsaye. Sai da ta ƙara gaishe da ƴan aji, da kuma malaman cikin ladabi, sannan ta faɗa bayani duk cikin harshen English. Tana dawowa ta zauna, take mutumin ya ce. “Halimatu Musa! Halimatu Musa!! Halimatu Musa." Shuru babu wacce ta amsa. Haka ya kuma kiran sunan. “Halimatu Musa! Halimatu Musa!!.” Malamin dake gefe shine ya nu na sit ɗin mu yana cewa. “You come.” Mubina ta miƙe sai ya ce. “Not you, the other person." Sai na miƙe. Sai a lokacin Mubina ta kalla sunan dake jikin I.D ɗina. “Inayah dama ke ce Halimatu Musa?.” danne zuciyata na yi bance komai ba na wuce. Da yake mutumin ya gane ni, dan yasan Dad. "Aren’t you Halimatu Musa?.” ya tambayeni sai na ce. “Uhmmm, am HALEEMART MUSA." na faɗa fuskana a haɗe. Na tsana a dinga kiran sunana da Halimatu, haushi nake ji, shi yasa ban wani amfani da sunan. Murmushi su biyun suka yi. “Sorry Haleemart." Me kiran sunan ya faɗa, da alamun ba su da matsala, dan haka ya kuma cewa. “Introduce yourself." Juyawa na yi na kalla matan da suke kallona. Take na nuna haka zan dinga tsayawa gaban cameras a Lokacin shooting, sai na yi murmushi ina cewa. “At first, my name is Haleemart Musa, but I am called Inayah. I do not take offense easily, nor do I like conflict. Whoever keeps to herself, I give her respect; otherwise, I will be disrespectful. I am also your sister's. Than A woman aspiring to become a doctor, and I pray that Allah helps us all." Daga malaman har ɗaluban kowa baki ya buɗe yana kallona. Ni kuwa ko a jikina na kowa wajena na zauna. “Inayah bayani kawai akace ba ki faɗa yadda kike so ba." “Mubina, haka nake ni.” na faɗa ina lumshe idanunwa...............✍️ END. > Kai Inayah boom 🔥, Allah ya shiryeki. > Kun fa ji GUY'S. > Mubina ai kin yi sa'a da ta fara kulaki ma 🤭🤭🤭. *📢 Assalamu Alaikum Everyone!* Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖 Idan kina son: ✅ Sabbin *updates* ✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi ✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman* To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi: 💰 *₦300 only* kafin mu gama. 🕒 Bayan an gama: *₦500* 🌟 *V.I.P Access*: *₦1000* _Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_ Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi. ```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number: 07038436703.``` ~SING BY PRETTY SK~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊 ``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P2️⃣6⃣⏩2️⃣7⃣. *Adam* ________________Tun bayan shigowarsa Lagos sau biyu ya je shooting dan be da wani scene masu yawa, yana da wani target akan new year, so yake shi da kansa ya ɗau nauyin wani zazzafan Film da za su yi, labarin ya riga ga siya, so yake su kammala *LOVE AT THE FIRST SIGHT* . Zaune yake kan kujera yana shan drink, a yanzu babu abin da yake yawan tunani sai fuskar yarinyar da ta ce mai sunanta *Inayah* , gaba ɗaya ta hanashi sukuni, babu dare ba rana fuskarta yake gani tana mai murmushi. A kowani lokaci jiran kiranta kawai yake yi, sai dai har yau ba ta kira ba, kuma a ƙalla da haɗuwarsu sun kai 6days, duk sai ya ji ya damu. Har Sarah ya rage kulawa, dan kuwa Inayah ta sace zuciyarsa. Ya na so zuwa gobe ya koma Kaduna dan jiya mahaifiyarsa Ammee, ta kirasa akan akwai matsala, wai Ayan ya fasa auren Ruma, kuma yanzu wani auren zai yi. Hakan ya ɗaga hankalinsa sosai, so yake ya koma ya ji abinda ke faruwa. Wayarsa ne ya ɗau ƙara, ganin ƴan uwan aikinsa ya sa ya ɗauka. “Okay, ganin zuwa.” da haka ya miƙe ya nufa room. Wow bedroom ya haɗu sosai, be tsaya a ko ina ba sai close-set ɗin sa, buɗe wa ya yi sannan ya zaɓa ƙananun kaya ya sanya. Cikin ɗan Lokaci ya fito sanye da ƙananan kaya kamar ko yaushe. Fita ya yi ya hau motarsa sannan ya nufa in da suke shooting ɗin. Motar sa ƙirar Bugatti Veyron black ya shiga, a hankali ya dinga tafiya har ya isa, saura 2 Episode a kammala Film ɗin, so suke su sake shi lokaci ɗaya. Asibiti ya nufa dan a can ne za'a yi shooting ɗin. Da isansa bakin asibitin, wasu maza biyu suka nufosa da sauri suna takamai baya. Tun anan ya ga masu aikin Film ɗin. *Jim Iyke* shine mahaifinsa a shirin, wani ɗan babban kafiri. Zama suka yi, mai yin makeup wata Angel, ta zauna ta yi ma Jim Iyke, sannan aka ba shi wasu kayan na masu kuɗi sosai dan ya sa. A.G ma makeup aka mai amma na ciwuka dan kuwa a wancan Episode ya yi accident akan soyayyar wata yarinyar wanda mahaifinsa Jim Iyke ya hanasa aurenta, to hakan ya haifar mai da damuwa, har ya yi accident. Ana gamawa aka shiga ciki, wani room aka basu, A.G ya kwanta ya lumshe idanunsa. Sanye yake wanda jeans black da white shirt, ya cire sarƙokin jikinsa da ɗankunne, dan a yaro mai hankali ya fito. Fuskansa kaman ciwon gaske, an dai rufe waje biyu da bandage, amma har launin jini aka sanya musu, sannan an yi kaman ana ƙara mai jini. “Action." Ya ji an faɗa, yasan an fara kenan, yana kwance Mahaifinsa ya shigo a ruɗe yana kallon yaronsa cikin wani hali. Har yana tuntuɓe ya isa gaban gadon, take ya fashe da kuka kaman na gaske yana jijjiga gadon da yin magana cikin English. “My Son.... please wakeup...... my son...... Alexx, wallahi yanzu na amince da ka aura Mercy , na yarda , ka tashi na yarda, ko ma wacece kake so by now na yarda. Ko wacce ba ta da ƙafafu na yarda.........oh Jesus help me........" (Astagafirullah 😓😓) Ya kai nan kukan na fin ƙarfinsa. Take doctor ya shigo sai ga wata budurwar yarinya wacce suka yi mata shiga na talakawa, riga ce T-shirt sai mini-skirt irin na kanti, a ruɗe ta shigo, amma suna haɗa ido da Mahaifin Alexx sai ta juya, a tsorace za ta fita. “Me................Mercy, please come back.......na amince da Ya aureki yanzu.” ya faɗa yana miƙa mata hannunsa. Take director ya ce su sake wajen, haka dai aka sake sannan ya yi, bayan ta isa gaban dagon tana kuka, fuskar A.G take ta shafawa kamar t samu fuskar yaro, tana ce mai da ya tashi ta dawo. Bayan sun ɗau lokacin da director ya basu umarni. A hankali ya buɗe idanunsa kaman dama wanda yake a sume ɗin. Ya ɗan ɗau lokaci kafin ya gane suwake akanta. Nanfa mahaifin ya shaida ya amince, da auren na su. take Mercy ta rungumesa suna kuka kamar da gaske. Sai da suka tsara wajen sosai yanda zai sanya mutane zubda hawaye dan kuwa duk wanda ya kalla Film ɗin daga farko, dole ya yi hawaye, dan ya na son Mercy duk da talaka ce, sai mahaifinsa Jim Iyke, ya hana saboda yana so ya yi mai auren jari, haka dai aka gama labarin. Gobe ne shooting na ƙarshe, da haka aka tattara kayan aiki. A.G ne rike da hannu Mercy suna ɗan hira, shifa dan ta ɓa jikin mace a wajensa ba wani abu bane. Sai da suka ɗau lokaci suna hira kafin ya yi kissing na ta a kumatu suka rabu. Gidansa ya koma hankali kwance, yana shiga ya yarda carkey kan kujera ya nufa Kitchen, be jima ba ya fito riƙe da plate wanda ya zuba snacaks a ciki, zama ya yi yana kunna Tv, sai ya fiddo wayarsa, saƙonnine ta kowani App Suka fara antayowa, shi har gajiya yake da amsawa, Saƙonta ko kiranta kawai yake jira, yana so ko sau ɗaya ne ta kirasa sai dai shiru har yanzu............. *A'isha* _______Kallon screen ɗin yawarta take yi, ganin wayar ta kuma katsesa ba a ɗauka ba sai ta koma wajen sakon Yaya Ayan wanda ya shigo yanzu, sai ta shiga. ‘yanzu ko hoton ki ba za ki tura min ba.' shine a rubutu ce sai ta mai reply. ‘Ba ka ta ɓa cewa kana so ba.' tana tura mai ta fita, take kiran Shalele ya shigo. Murmushi ta yi sannan ta ɗauka ta na ajewa akan mirrow dan Video call ne. A'isha da ke sanye da hijab fari iya ciki sai shuɗin doguwar riga na yadi, murmushi ta kuma yi tana kallon ƙanwarta dake zaune kan kujera, Pjmask ne jikinta pink colour, da band wanda dogon gashinta ya zuba ta baya. “Ina kika sa wayan ne, 4 missed call na miki fa?.” “Sorry, earphone yana jikin wayar ne, shi ya sa ban ji ringing ɗin ba.” sai Aisha ta ɗaga min kanta. “Ya makaranta fatan ana gane karatun ko?." “Eh Alhamdulillah. Kun fara exam ku ai." “Eh, mun gama." “Allah ya taimaka.” take fuskar A'isha ta ɗan bayyana damuwa sannan ta ce. “An sanya ranar aure na.” murmushi na yi. “Masha Allah, wata nawa?, Allah ya sa sai ƙarshen shekara, yarda idan na zo na ci uwar ƴar fili, dan rawar da zan yi hmmmmm." Na faɗa ina ɗan mistsike idanuna. “Hmmm yau yaushe?.” “Saturday." “On Friday na satin nan, shine auren.” da sauri na zaro manyan idanuwa ina cewa. “Dad ya ba da sadakan ki ne?.” harara ta watso min. “Eh mana, wani irin aure ne za'a sanya sati ɗaya......faɗa min me yasa?.” murmushi ta yi, ita har yanzu a yarinya take kallona shi yasa ta ce. “Ayan zai yi tafiya ne, so ana ɗaurawa za mu wuce tare." Sai na ɗaga kai. “Kenan bana gida za'a yi bikinki? Gaskiya ban so ba wallahi." Na faɗa har da turo baki. “Ina zuwa Sis.” ta faɗa tana katse kiran. A'isha ji take tun yanzu ta fara na daman ƙaryan da ta yi, gaba ɗaya kwana biyun nan cikin wani irin yanayi take ciki. ‘Ki turomin na ki, da na Shalele, tinda Allah ne haɗa mu ba.’ ta karanta saƙon Ayan, take ta shiga gallery ta tura mai guda uku sannna ta yi offline. Kan gado ta koma ta kwanta tana tuna abubuwan da suka faru a ɗan kwanakin baya, wanda a dukka a cikin wata ɗaya ne ya faru......................✍️ END. > Sannu A.G, kana duniya wlh, gaskiya Sarah an cuceki 😓😓. > Aisha 🥺 bara dai mu ji me ya faru, dan ga dukkan alamu................😬😬😬 > Team of Aisha and Ayan 🧏 ba ruwan Sk. *📢 Assalamu Alaikum Everyone!* Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖 Idan kina son: ✅ Sabbin *updates* ✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi ✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman* To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi: 💰 *₦300 only* kafin mu gama. 🕒 Bayan an gama: *₦500* 🌟 *V.I.P Access*: *₦1000* _Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_ Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi. ```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number: 07038436703.``` ~SING BY PRETTY SK~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊 ``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P2️⃣8⃣⏩2⃣9⃣. _(Tunani)_ Tun bayan da suka je gidan su Ayan, ta shiga damuwa sosai, amma haka ta ɓoye masu Dad. Duk a zatonta maganar shike nan ba zai kuma tashi ba, sai dai bayan kwana biyu, Ayan ya zo ya ɗauke ta, asibiti suka je aka musu takadda na ƙarya, sannan Ayan ya biya wani doctor akan ko da sun dawo, ya musu result irin wannan. Da haka ya mai da ita gida, ita dai tun a yanzu jikinta ya riga ya mutu sosai. Again after some days, suka zo aka yi baiko, ansa tana gama exam za'a yi auren. Dad da Mom sun yi mamakin irin uzurin da suka zo da shi na auren da wuri, sai da su sun san idan lokaci ya rantse babu wanda zai iya dakatar da haka. A yanzu har sun kawo komai saura akwati kaɗai, rana kawai ake jira, dan sun ce ba su son komai daga wajen Dad. Duk ta shiga wani hali sosai, ita yanzu idan sun yi aure aka gano Babu ciki ba, duk da dama zama za su yi har ta haihu sai a kuma ɗaura musu auren, a cewar su Abba. ba ta san yarda za ta yi ba in suka gane, kullum dai Ayan ce mata yake *Kar ta damu* da haka ta ke rage ma kanta damuwa... _Ci gaba_ Murmushi ta yi wanda ke da ma'anoni da dama, ita tasan akwai ƙura bayan aure dan kuwa tun a yanzu ta ga ƙiyayya ƙarara a cikin idanunwan Baba Yusuf da Baba Yunus, hmm balle ma mutanen gida. _Ayan_ Shi komai da ke faruwa ko a jikinsa, ɓacin ran Ummee ne kawai baya so, dan ta yi fushi da shi, duk dan Ruma, yarinyar da yasan har ita Ummee ba sonta take ba. Abin da be sani ba shine, tun faruwar komai, Ammee da matan gidan dukkansu, sun ƙara tsanar Ummeensa, da ƙanwarsa Sarah, abubuwa dai yana faruwa amma be sani ba, kuma sun kasa faɗa mai, sai dai in a gaban su Abba ne shine ake nan-nan da su. Kallon wayarsa ya yi ganin hoton da A'isha ta tura sun shigo, sai ya latsa yana fara cin karo da nata. Ta yi ƙyau sosai, doguwar riga ce jikinta, sannan ta yafa gyale, tana zaune ne a kan kujera aka mata hoton, sai wani shima ta yi ƙyau sosai, sanye take da dogon hijabi. Na ƙarshen ne ya tsaya yana kallo sosai, in dai ba gizo ba, Rose ce jikin hoton nan, duk da ta ƙara girma amma ya ganeta. Su biyu da A'isha ne suka yi hoton, A'isha na baya sai ita Shalele a gaba, kayansu iri ɗaya wasu lifaya mai kyau sosai. Zooming pic ɗin ya yi yana ƙare ma fuskarta kallo sosai, murmushi ya yi sai kuma ya ce. “Allah mai iko, ashe dai ina da rabon ganinki, ashe sirikata za ki zama, kai masha Allah.” ya faɗa tana tura ma A'isha saƙo. ‘Dear gaskiya na gode, sun yi ƙyau sosai, masha Allah kawai, amma fa Shalele ta fiki ƙyau.' ya tura mata yana fita a cikin chart ɗin. Ganin new number an yi mai sallama sai ya shiga, profile ɗin da yaga wacce ke kai, tsaki ya ja dan ko jiya ya yi blocking wani numberta. Ta turo saƙo dan haka ya shiga. ‘Assalam Babyna, Ruma ce, me yasa kake yawan blocking nawa? Hmmm ka yi ka gama dan aure na da kai wallahi babu mai hanawa. Ko ita waccan ƙaruwar taka ba za ta hana na aureka ba wallahi.' shike nan saƙon. Tsaki ya ja sannan ya duba reply ɗin A'isha. ‘Nasan ta fini ƙyau.........Yanzu nake faɗa mata biki sai cewa ta yi, _Dad ne zai ba da sadaka na_ ' murmushi ya yi sai ya rubuta. “Wasa nake dan kuwa kaf duniyar nan kinfi kowa ƙyau, hmmm Shalele sai addu'a.' da haka ya kashe datan yana aje wayar, lumshe idanunsa ya yi yana ji kamar wani abu na motsa zuciyar sa...... *Inayah* Kallon Mubina da ta fitowa daga Kitchen riƙe da babban plate na jollof chicken spaghetti, yana ta tiriri. Zan iya cewa cikin sati biyu da wasu kwanaki na gama karantar Kowa na ajin mu, da ita Mubina. Na lura babu mai jin kanta na hayaƙi, sai dai a wajen karatu kowa ita so take ta fi kowa, hatta Mubina sune kan gaba wajen ba da amsa a gaba class, abin da ɓan ta ɓa yi ba, dan kuwa Ni in ba fito da ni aka yi bana yi, haka kuma ko na sani ban faɗa, sai abu na gaba, bana tamabaya, ko da kowa zai yi Ni dai ba zan yi ba, hakan yasa ƴan class ɗin suke ganin kaman Banda brain kawai English ne na fi su ƙwarewa. Ko a jikina in sun faɗa haka, dan Ni ban cika shiga irin wannan ba, da dai wata maganar ne to za a ji bakina. Ajewa ta yi tana cewa. “Inayah, me yasa ko na baki amsa, ki dinga tashi ko faɗa miki na dinga yi, wallahi ƴan ajin mu kallon..........” sai ta ga na yi murmushi. “Kaman be dameki ba." “Mubina, share kawai, yanzu muke waya da yayata wai bikinta friday, shine nake tunani, gashi ba zan samu zuwa ba.” na faɗa ina ɗaukan spoon. “Masha Allah, amma ban ji daɗi ba, ace ba ƙya gida za'a sha shagali.” “Ba'a min adalci ba sam.” na faɗa ina jin kaman da wani abu a ƙasa, A'isha ba ta faɗa min ba amma bakinta akwai magana haka kuma zuciyarta kaman a raunane take. Bansan na yawaita tunani marasa ƙyau hakan yasa na ce. “Mubina ban labarin ki mana.” murmushi tana mai cewa. “Mu gama cin abincin.” “A'a Please yanzu dai." Sai ta kuma wani murmushin ta na cewa. “Toh ni ta ina zan fara?......." “Ta ƙasa.” na faɗa ina son na manta yanayin A'isha a cikin kaina. “Uhmm, a Abuja aka haife ni, Ni kaɗai ce mahaifiyata ta haifa, to ta rasu tin Ina yarinya, a wajen kakata na girma, sai dai bayan rasuwar ta shine na koma wajen matar Babana, ba ta wani matsala, zan iya ce miki rayuwa yana tafiya min yarda nake so ne." Ta kai nan tana kai abinci bakinta. Murmushi na yi sannan na ce. “Ya batun Saurayi? Oh sorry samari zan ce." Na faɗa da sigan zolaya. Hannu takai min kaman za ta bugeni sai na kauce. “Inayah, saurayi na ɗaya, kuma ina son shi sosai.” “Masha Allah." “Da na kammala karatun za mu yi aure insha Allah, yanzu haka aiki yake yi." “Allah ya kaimu." “Ameen, to ke fa? Samarin ki nawa?." Ɗan hararan wasa na yi mata. “Banda ko ɗaya, kuma ba zan yi ba dan ba zan yi aure ba.” na faɗa be serious. “Ban gane ba!?” murmushi na yi. “Yes haka ne, banda saurayi, kuma ba zan yi ba, dan babu mai aure na nan gaba.” “Subuhanallah, Inayah wanna wani irin magana ne?." Sai na dafa kafaɗarta ina cewa. “Da gaske nake......” “Haba Inayah, Allah ya miki ƙyau mai suna ƙyau, a dire kike amma me yasa kike faɗin haka?." Sai da na furzar da iska daga bakina sannan na ce. “Saboda babu wanda zai aura Ni idan na cika burina, babu wanda zai so Ni, dama haka nake so, babu aure a agender na, babu wanda zan dinga ma biyayya kamar baiwa, babu wanda zan dinga zama yana sani aiki ko ƴan gidansu........hmmm shi ya sa ban tsamman zan iya auran kowa." Na kai nan ina latsa wayana. “Wani buri?." “Ina so na zama ƴar Film, ke a ganin ki waye zai aura wacce take film?.” da mamaki take kallo na. “Film kuma!? Ke yanzu Film kike so bayan kina karatun Gynecologist............”” “Eh." “Film ba wani tawaya bane amma yana da matsaloli sosai, a gida ma nasan ba za su barki ba." Ta faɗa tana riƙo hannayena. Kallonta na yi sai na yi murmushi. “Hajiya nifa ba kannywood zan shiga ba. NOLLYWOOD 🔥 nake so.” na faɗa ina kallon gefe. “Hmmm kinsha wani abu ne yau?." Sai na yi murmushi, tashi ta yi ta nufi room ɗin ta tana kuma cewa. “Bansan irin wasan nan please.” jinjina kai na yi dan ba ta yarda ba kenan. A hankali na furta. “Lokaci! Lokaci!! Lokaci!!! Nake jira, ina nan da saving number A.G, so nake na yi karatu na cikakken tearm kafin na fara nemansa.” sai na kalla number da na yi saving da, *NOLLY A.G* wato number A.G , sumbatar wayar na yi ina lumshe ido na dan number kaɗai sani nishaɗi take.....................✍️ END. > Toh na yi nan 🚶🚶🚶🚶🚶 *📢 Assalamu Alaikum Everyone!* Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖 Idan kina son: ✅ Sabbin *updates* ✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi ✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman* To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi: 💰 *₦300 only* kafin mu gama. 🕒 Bayan an gama: *₦500* 🌟 *V.I.P Access*: *₦1000* _Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_ Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi. ```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number: 07038436703.``` ~SING BY PRETTY SK~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️* 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅 Story and writing✍️ ```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊 ``` ~SAKINA ABDULLAHI~ > *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️ ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽ E.P3️⃣0⃣⏩3️⃣3⃣. *A.G* Zaune yake a kan sopa yana kallon last episode ɗin da aka ya sanya yanzu a YouTube, Likes ake ta zuba da Comments, da haka ya yi playing ƙarshen video ɗin in da ya fi ko ina burge masu kallo. Shi da Mercy ne zaune kan wani kujera mai ƙyau da ke cikin Hole, ga mutane ta ko ina ka ce da gaske ne, haka aka dinga shan rawa da ciye-ciye, dan a wajen an yi wasan kuɗi, sannan a ƙarshe aka ce su taka rawa shi da matarsa. Nan fa ya riƙe ƙugunta suka fara rawa kai kace da gaske shi ne mijin na ta. Mercy ɗin ta yi kyau sosai cikin red marriage gown. A ƙarshe dai ya tsugunna gabanta wani gold ring, take aka hau ihu da mai masu wasan kuɗi, dan gaskiya a labarin ana sha drama akan soyayyarsu. Yana tashi suka rungume juna, take Director ya mai alama da ya yi kissing na ta, ai kam take ya haɗe bakinsu wajen ɗaya, nan fa suka aka hau ihu................. Fita ya yi a wajen ya shiga comment section, nan fa ya dinga ganin masu comments da musu fatan alheri, wasu na cewa wai a ci gaba da series ɗin. Murmushi ya yi sai kuma ya mai da idanunsa kan ƙofa da ya ji alamun ana buɗewa. Ammee ce ta shigo sai Ruma a bayanta, kwana biyu kenan da ya zo kuma gobe zai koma. A fuskokinsu kawai ya gane akwai matsala, dan dama babban matsala ce ya dawo da shi. Ammee da Ruma zama suka yi kowa rai ɓa ce. “Ammee, me ya faru kuma? Ba an gama wancan maganar ba?.” Rai ɓa ce ta ce. “Ahmad Ina fa, wai yanzu ce wa suka yi, an soke auren Ruma da shi, za ta aura Fahad....." “What?." Ya faɗa yana kallon Ruma da idanunta suka cika da hawaye. “Wai me yasa komai Ayan ke so ake mai? Da ace Ni na ce zan yi aure a waje babu mai yarda..........hmmmmm Ni wallahi ban yarda Ayan ya yi zina da wata ba............ban yarda ba wallahi." Ya kai nan yana jin wani ɓacin rai na saukar mai, da fari an gama magana akan gobe zai aura waccan ƙaruwar, idan ga tare har sai ta haihu za su kusanci juna, bayan an sake ɗaura musu aure, sannan kafin nan da zai aura Ruma, shine yanzu aka sauke gaba ɗaya. “Damuwata ɗaya wai Fahad, Fahad..........yaron da ko gaishe Ni ba ya yi saboda ba ma wani jituwa da uwarsa. Shine wai zan bawa ƴa ta............hmmmmm............” da sauri Ruma ta katseta tare da share hawayenta tana cewa. “Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Duk ƴar iskan da ta aura Ayan ta shiga uku.............sai ta kwammaci dama mutuwa ta yi da rayuwa da Ayan ɗina...........Na tsane shi Ammee wallahi na ji ya fita min a rai...........tun.....tun ina yarinya nake sonsa.....ko sau ɗaya bai ta ɓa min magana mai daɗi ba...a...a...amma haka nake ta nace mai, kullum ce min yake Ya baya sona. To nima daga yau bazan ƙara son shi ba har abadaaaaa....." Da haka wani irin kuka ya ƙwace mata. Jikin Ammee ta faɗa tana kuka sosai, ganin haka ran A.G ya ƙara ɓa ci sosai, kafin ya yi wani motsi sai aka kuma murdo handle ɗin kofar aka shigo. Baba Yusuf ne ya shigo shima ranshi a matukar ɓa ce. Yana jin iri kukan da Ruma ke yi hankalinsa ya kuma tashi, dan kuwa a duniyar nan ba ya son ganin ɓa cin ranta ko kaɗan. “Ruma, is okay. Ni na ce na warware alƙawarin auren da ke tsakanin ku, saboda Ayan sam baya sonki. Kuma mun tabbar da maganarsa, sau biyu muna zuwa asibitoci ana kwaji kuma dukka result ɗaya ne, sannan har yarinya da ta aikata musu haka mun sameta, ta yi ta kuka akan kuskuren da ta yi........Amma ganin yarda kika shiga damuwa shi kenan zan yi ma......” da sauri Ruma ta ɗago tana cewa. “Dad wallahi ko maza sun ƙare ba zan aura Ayan ba....na tsanesa wallahi." Ta faɗa tana nufa bedroom ɗin ta da mugun sauri har tana bugewa da fridge amma ba ta sani ba. Da idanuwa suka bi ta har ta shige. “AYAN.... AYAN.....me yasa? Hmmmmm." Sai Dad ya haɗiye sauran maganar yana nufan nasa room ɗin. Tafiya yake yana ayyana abubuwa da yawa akan Ayan. “Ina zuwa." Ammee ta faɗa tana bin bayan Ruma. Dafe kai A.G ya yi sannan ya fita daga ɗakin yana fatan su haɗu da Ayan ko yayane ya faɗa mai ɓakar magana, dama ba wani shiri suke ba saboda halinsu be zo ɗaya ba sam. Ammee na shiga ta ci gaba da rarrashin Ruma har sai da kukan ya tsagaita sai faman sauke ajiyan zuciya take mai sauti sosai. “Ki bar kuka, wallahi Ayan sai yasan ya yi kuskure, sai ya san ya cuci kansa....ke kinsan kaf gidan nan gaba ɗaya iyeyenku maza sunfi sonsa da ƙaunarsa. Shi yasa tun fari na fara dasa miki soyayyarsa, to a yanzu ya ja ma kansa dan kuwa da wannan ɓacin ran zan yi amfani wajen cusa tsanarsa wajen Dad sannan da sauran ƴan gidan......a yanzu nasan babu wanda za su ba Shugabancin masana'ata shine Fahad........kuma kin ga yanzu shi za ki aura, sai ki samu ki janyo hankalinsa sosai, sauran kuma sai bayan an yi bikin.” ta faɗa tana kallon fuskar Ruma. “Shike nan, amma wallahi sai na rama abin da ya yi min, ya auro duk wacce zai aure, ai duk tsiya za ta shigo *GIƊAƊO MANSION*, sai na tarwatsa mai farin cikinsa.........sannan hatta Uwarsa da Ƙanwarsa da nake ganin su sa gemu, duk da banso ba............to ya shafesu......Balle Sarah da Ayan yake sonta hmmmm." Ta faɗa tana ƙwafa. “Karki damu ƴata ai kowa wannan al'amarin ya shafa.....auren nan kamar zubar da Wasiyyar Kakan kune." Ta faɗa tana ɗaukan mugayen alwashi akan Ƴan ɗakin su Ayan....... Baba Yusuf ne zaune a gefan gado yana jin zuciyarsa na mai raɗaɗi sosai, daa yana son Ayan sosai, dan ya fi ƙaunarsa akan yarda yake sun A.G, sai dai tun faruwar al'amarin nan ya fara fitar mai a rai, balle yau shi yasa ya ce ba zai aura Ruma ba. Wani irin kallo yake mai irin na wanda ya ci mutuncin Mahaifinsu *GIƊAƊO*. “Ayan sai na sa ka yi kuka da idanuwanka akan abin da ka yi ma Ƴa ta, sannan ka ci mutuncin Kakanku sai ka kwammaci da ba ka san ƴar iskan da za ka aura ba gobe." Ya faɗa yana rintse idanunsa tare da tafe kai, dan al'amarin ya mai zafi sosai. *AYAN* Zaune yake akan kujeran dake garden, wajen akwai tsaftatatciyar iska mai bushawa sosai, dan kuwa akwai bishiyoyi sosai. Shi kaɗai ne zaune ya ƙura ma Swimming pool ido kaman me na zarin adadin ruwan dake ciki, amma a zahiri ya tafi duniyar tunani ne. _Abubuwa sun faru wanda tun daga farko shi ya tsara komai bai san matsala za ta iya biyowa baya ba. Kamar yasani sai da ya je asibiti biyu wanda yasan tabbas ƴan gidan na zuwa. Roƙon doctor's ya yi akan idan ƴan uwansa sun zo su ce akwai ciki sannan ga adadin lokacinsa. Alhamdulillah haka komai ya ta fi mai, sannan sai da suka nema wata a department ɗin A'isha ta amsa ita ta aikata haka. Abin da yake sanya shi damuwa shine *Ummee* gaba ɗaya hankalinta a tashe yake tun bayan bayyanar komai ga ƴan gidan, ranar Ummee tasha kuka, amma saboda tasan ba da gangan ya yi ba sai ta sauka daga fushin. Amma wunin yau kuwa, babu annuri a tare da ita, sai ya ji duk babu daɗi, so yake zuwa an jima ya leƙata sai ya ƙara ba ta haƙuri.) “M.D.” jin an kira sunansa babu sakayawa ya sa ya kalla A.G dake nufosa cikin fusata da ɓacin rai. Kaf gidan babu mai kiran sunan sa saboda sunana Baba Giɗoɗa ne, shi yasa yake da farin jini, wasu sukan danganta hakan sunan da ci ne. Miƙewa Ayan ya yi, dai-dai nan A.G ya iso gabansa yana wani muzurai kamar damusa. Dama sam ba sa shiri, ko gaisawa ba ta wani haɗasu duk da zasu aura ƙannan juna ne. “Akan me yasa ka fasa auren Ruma? Eh akan me yasa? Wannan ai rashin mutumci ne, yarinya tun yaushe take sonka duk abin da kake mata haka take ci gaba da sonka amma a yau wai an sauke auren ku!!.” ya kai nan kaman wanda zai buga Ayan. Tsayinsu ɗaya amma Ayan ya fi A.G cika, da haiba, amma bayan wannan komai suna da shi ne zaratan maza, jarumai masu siffar ƙarfi da jarumta. Ayan kuwa murmushi ya yi mai sanyi sannan ya ce. “Abbeey (Bana Yusuf) da kansa ya ce anfasa, dama ni ba so nake ba, kuma da kake cewa tuntuni take sona, shin ni na aiketa? Na fita hakƙinta tun da tasan bana sonta......” “Hmmmmm nima na fasa auren ƙanwarka!.” ya faɗa duk da yana mugun son Sarah. “Wallahi da na fi kowa murna, kai kanka kasan ba sanka take ba. Hmmm wannan labarin ne mai daɗi, Bara na je na sanar ma Sarah.” da haka ya kewayeshi ya nufa Main door. Ayan be son ya jima yana magana da A.G dan zasu samu babban matsala, A.G akwai shi da naci, shi kuma be son maimaita abu ɗaya, kuma yasan A.G komai zai faru sai ya auri Sarah Dan ba ƙaramin sonta yake ba. Murmushi kawai ya yi ya shiga ciki. A.G ƙafa yasa ya buge kujerar dake gabansa, ɗan huci ya fara yi kaman wanda ya ci gudu, sai kuma ya zauna yana tunanin ta ina zai fara. “Tunda ba ka so, to wallahi sai na aureta............eh sai na aureta......Ina son Sarah amma saboda kai Ayan zan ƙuntata mata, zan sa ta sha wahala sosai, sai daga baya na ba ta haƙuri, amma yarda Ƙanwata ta yi kuka, haka zan sanya ta ka ƙanwa.” ya faɗa cikin ɗaukan alwashi sannan ta furzar da iska daga bakinsa.. ****************** Ummee ce zaune kan prayer mat tana kallon Yaranta su huɗu da Allah ya ba ta, ita da Ammee sune kawai masu yara huɗu-huɗu, amma sauran suna da yawa. Dan Baba Musa yaransa 9 maza huɗu mata biyar, duk sun yi aure a cikin gidan. Sannan shima Baba Yunus yaransa 8, 5 sun yi aure , sai Namiji ɗaya Fahad da kuma mata biyu amma su ba su girma sosai ba. Baba Yunus matansa biyu, haka Baba Musa shima, amma Abba matarsa ta biyun ta rasu tun shekarun baya, yarinyarta ɗaya, ƙanwar Sarah ce amma ita booding school. Rufaida ita ce babba a ɗakin ta aura Yaron Baban Musa na farko, sai Abdulrahman shi kuma ƴar ɗakin Baba Yunus ya aura, sai Ayan da kuma Sarah. Duk suna zaune jikinsu a mace da abin da ke faruwa. “Ummee...." Da Sauri Ummee ta ɗaga mai hannu alamun ya yi shuru. Shurun ya yi yana kallon ƙasa. “Ni ba wai auren wata ne ban so ba, kai yanzu har kana fatan ka auro wata ta shigo gidan nan?...........kai yanzu idan ka kawo ƴar mutane nan gidan ba ka cuce ta ba?............idan kana kusa babu wanda zai yi mata komai, amma idan ka fita ba?........mu kanmu ya muke a cikin gidan nan..........sannan abubuwan nan da suka faru kowa ransa ya ɓaci da kai sosai, hatta Abba shiru kawai ya yi, ni dai da ka ji nawa ka aura Ruma ɗin, ko dan ita maiyuwa mu samu wata iska mai daɗi a gidan.” ta kai tana jin babu daɗi, sannan ta ci gaba. “Kamar yarda Abbanku ya ce............*Rabo*, shine zai kawo A'isha gidan nan. Ina fatan Allah ya baku zuri'a ɗayyiba.” da haka ta miƙe ta shige room ɗin ta. Jikinsu duk ya yi sanyi, tabbas a gaba ɗaya gidan suna samun takura da matsi, dan ma suna da baki shine suke san iska. Sai gashi Ayan ya rikito musu babban aiki. “Ni yanzu Sarah na ke ji...........A ganin su Ammee za su bar maganar nan ne? Za su iya ɗaukan fansa akan Sarah." Rufaida ta faɗa cikin damuwa. “Anya Ahmad zai iya bari a cutar da ita? Yana sonta sosai.” faɗin Abdulrahman sai Ayan ya ce. “Hakane, amma kuma ba wani zama yake ba. Sai dai mu ai muna nan.” ya faɗa yana riƙo hannun Sarah. “Yaya Ayan, karku damu Ni na yarda da mutum ba zai tsallake ƙaddarar sa ba. Yanzu dai gobe ne auren na ka ko?.” sai ya yi murmushi yana mai ɗaga mata kai. “Angon da babu shiri, gidan ma kaman ba biki ba.........” “Maman Hibba (Rufaida) shi kansa angon ba wani natsuwa ga rai ba. Fatana a kawo amarya lafiya ba tare da anyi rikici ba.” “Ameen Sarah.” da haka suka sauya hiran akan na bikin duk da babu abin da za'a yi sai dai walima, haka dai suka tsara kuma suna fatan komai ya tafi lafiya dan sunsan ƴan gidan nan balle wannan shine karo na farko da za'a kawo mace cikin gidan.........✍️ END. > Ya Allah 😓, hmmmm ba zance komai ba gaskiya. > Nifa har yanzu ba mu shiga labarin ba, wasa kawai muke yi 😬😬😬. > Typing mood 😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩🥴. A nan zan katse muku dan kar na baku cittan da yawa. Sai dai ku sani bamu yi komai a labarin ba. 1. Shin ya rayuwar A'isha da Ayan za ta kasance a *GIƊAƊO MANSION* 🔥. 2. Ya *Ƴar NOLLYWOOD* 🔥 ne? Kusan dramer da zai biyo baya kuwa..........Za ta yi? Ta yaya? Idan ta yi mai zai biyo baya?........kai jama'a ku dai jiraye Ni a book 2. Ina faɗa musu kwanan Zafin na sa daban ne, dan 1 bisa 5 muka yi, wannan duk sharan fage ne, ainihin cittar yana book 2. BOOK TWO IS FIVE HUNDRED ONLY ₦500. Ga Mai so ya min maganan direct....... 08126151523/07038436703 Pretty Sk ce 😁🥰🥰🥰🥰🥰. I love You All my FAN'S 😘. Akwai wani book da zan sadaukarwa wa ku insha Allah mai suna SAKEENAT 😓, ba zan ce komai ba ku dai nema kawai 👌👌👌👌❤️ *SAKEENAT ABDULLAHI ✍️😁* ```TALLAH! TALLAH!! TALLAH!! Na Book 2.``` _________ _GIƊAƊO MANSION_ Wannan daren akwai jama'ar da suka kasa barci, wasu sun yi amma ba na daɗin rai ba, duk da akan abin da ya faru, mutane da yawa sun shirya tarwatsa farin cikin da ya rage ma Ummee da Ayan, sun shirya hargitsa rayuwar ƙaruwar da ya kawo, sun shirya haka tuggu iri-iri a cikin gidan, da dama kowa ya kwanta rai a ɓace, ya yin da suke tunanin Ayan yana can shi da ƴar iskan ƙaruwarsa suna jin daɗin juna..........✍️ ________“Uhmmm dama ina da sha'awar film ne.......duk da a yanzu karatu nake amma ina so.........shine na ce ba ra na tambaya ke. ” ina tura mai ya gani dan haka na gyara zama na sosai ina jiran amsarsa. “Ok, sai dai ni ban san wani manya a fina-finan kannywood ba, kinsa Ni NOLLYWOOD nake yi, amma zan bincika miki.” Murmushi na yi ina tura mai. “Sir A.G, NOLLYWOOD ɗin nake so.”........✍️ ______“Ƙanwata, ai na yi fushi ace ba ki ta ɓa nema na a waya ba sai yau, ko gaisuwa ai.......” da sauri ya ji ta katseshi cike da masifa tana cewa. “Ni ba gaisuwa na kira mu yi ba. A yanzu kai miji ne ga Yayata, to Kira na yi dan na yi maka fashin ɓaƙi, nasan ba lallai ka gane hausan ba idan A'isha ta faɗa maka........Amana na baka ita, ka kula da ita fiye da komai, ka sanyata farin ciki a kodayaushe, hakan zai faranta min, amma idan wani ya sanyata kuka hmmmmmm to ta na da mai kare mata wato Ni.” tana kai wa nan ta katse kiran..........✍️ ________ (_Assalamu Alaikum, Barka da wannan lokacin A.G.....sunana Inayah maybe ka manta amma kai ka ban number ka. PLS akwai maganar da nake so mu yi is very important.... thanks.-) ............✍️ _________ *Inayah* Na rasa meke min daɗi, nasan yau Yayata za ta sha kuka sosai, shi yasa ni fa banson na yi aure, haka kurin a rabani da iyaye ne, na koma wani gidan, cikin wani family ɗin, na zama kamar mai aiki, miji ya min duk abinda yake so, ya kwana da ni kuma na tashi na yi mai girki.......hmmm shiyasa ban kawo aure a jerin rayuwata sam.........✍️ _________“I'm fine the Star of NOLLYWOOD.” ganin yana online ya sa na koma na kwanta ina jiran reply ɗin sa. Ganin yana on typing yasa na ji wani sanyi yana ratsani sosai, murmushi ya ƙi barin fuskanta, sai na ji duk na ƙosa na ga saƙon da zai turo min....................✍️ _______“To ki faɗa akan menene zan yi alƙawarin.” “So nake ki yi min alƙawari, idan har wani abu ya sameki mara daɗi da mai daɗi za ki faɗa min, bance da sirrin aurenki ba, amma duk abin da ya kamata na sani, to ki faɗa min. A family house aka ce za ki zauna. Maybe akwai wanda za su yi kishi da ƙyawun da Allah ya miki. To Ni dai duk uban da ya shiga harkan ki, ki faɗa min, zan ji da kowa, nan da 8 month zan dawo, to a gidan ki zan cinye hutun, komai da za'a miki kawai ki tara in na zo zan ji da komai, dan duk wanda ya taɓa ki dole ne yi mai wankin babban bargo.” A'isha murmushi ta yi mai sauti. “Sai aka ce miki kowa ne irin ki, kowa ne mai neman faɗa. Kai wallahi na za ci wani abun ne za ki ce.”........... Jama'a mudai haɗu kawai____________₦500 ONLY. 8126151523-Opay number. Sakina Abdullahi 😁👌🥰🥰🥰🥰🥰🥰 *📢 Assalamu Alaikum Everyone!* Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖 Idan kina son: ✅ Sabbin *updates* ✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi ✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman* To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi: 💰 *₦300 only* kafin mu gama. 🕒 Bayan an gama: *₦500* 🌟 *V.I.P Access*: *₦1000* _Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_ Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi. ```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number: 07038436703.``` ~SING BY PRETTY SK~ *ALHAMDULILLAH ❣️*