BUZU YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA/002) Bright pens 3rd batch. (2025) Bismillahirahmanirrahim. *Labarin BUZU ƙirƙirarren labari ne, duk wani sashi na labarin na iya faruwa a gaske, idan ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne.* ⚠️ Labarin mallakina ne, ban yarda wani ko wata, su yi amfani da shi ta kowace irin siga ba, sai da izina. AISHA ADAM (Ayshercool) 08081012143 Arewabooks; Ayshercool7724 Watpad: ayshercool7724 Page 1 Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka. Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta. Gefe da gefen hanyat baki ɗaya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huɗu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado. Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi. "Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?" Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba" "Dans  quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)". "Bai fi awa ɗaya ya rage ba" "Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka" Ya yi maganar yana haska fuskar wani matashin mutum, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai  yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar. Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin matashin, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take bugawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito dummm!. Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ƙara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi" Lauwalli ya jinjina kai yana ƙara gudun motar. ***** Misalin ƙarfe shida da mintuna goma sha biyar na safiyar ranar asabar, ɗaki ne madaidaici, wanda ya samu kyakkyawan ginin ƙasa ma ƙwarin gaske, duk da kasancewar sa na ƙasa, amma adon da aka yi masa ya bayyanar da darajarsa. Can daga kusurwar ɗakin wata matashiyar mace ce, kwance a kan matsakaiciyar katifa ta yi ɗaiɗai ta na bacci, zaninta ne kawai ya kare bayyanar tsiraicinta, amma idan ta yi kyakyawan yinƙurin za ta yi tsirara. Iya ƙarfinta take ƙoƙarin tashi daga baccin, amma abu ya gagara a sakamakon sleep paralysis, wanda a hausance da kuma fahimta ta mutane suke kira da dannau, a cewar mutane wani aljani ne mai suna dannau, yake danne mutum ya kasa motsi, alhali idanunsa biyu, kamar a zahiri haka ta din ga ganin abubuwan da suke faruwa da ita, amma ta kasa motsawa. Tamkar an cire mata wani abu mai nauyi, haka tayi firgigit ta tashi zaune, ta na mayar da numfashi, a sakamakon fafutukar da ta sha, kafin ta samu ta iya farkawa daga nannauyan baccin da take yi mai kama da na mutuwa. Ware ido tayi, ganin yadda gari ya yi haske, ba tare da ta gabatar da sallar asuba ba. Ta yinƙura za ta sauka daga kan katifar, ta ji duk gaɓoɓinta na yi mata ciwo, jikinta kamar wadda aka yi wa dukan tsiya, zanin jikinta ya yaye. Shiru ta yi ta na ƙoƙarin tuna abin da ya faru a daren jiya, a iya saninta ninkin kaya take yi, ba ta kai ga kwanciya ba, daga nan ba ta san abin da ya faru ba. Ita dai ta san sanye take cikin suturarta, amma yanayin da take ganinta a ciki, yana sanya mata wasi-wasi. A hankali ta tashi ta gyara zaman zanin ta nufi banɗakin da yake cikin ɗakin, domin ta kintsa jikinta ta gabatar da sallar asuba. ***** Sannu a hankali yake buɗe idanunsa, da suke yi masa wani irin zugi saboda hasken da ya cika masa su, sai ya ji tamkar hasken wani baƙon abu ne a cikin idanun nasa. Yanayin ya yi masa kama da farkawa cikin wata duniya ta daban. A hankali ya daina jin zugin da idanun suke yi masa, ya buɗe su tanagrau, ya ƙurawa wurin da yake ido, yana ƙoƙarin gano a ina yake. Wani dogon mutum ne baƙi, fuskarsa ɗauke da jan rawani hannunsa rike da ɗan ƙaramin kofi, ya shigo cikin tantin. Jifa yayi da kofin hannunsa, ya nufi mutumin da yake kwance da matuƙar hanzari. Taimaka masa yayi ya tashi zaune, fari ne amma ba tas ba, irin mai sirkin yellown nan, ya na da ɗan siririn hanci, dai-dai da siririyar fuskarsa, sai gashin baki kaɗan da ya haɗe da ɗan madaidaicin gemunsa, sai kuma manyan idanuwa da yake da su, da su ka kaɗa su ka yi jawur tamkar jini zai kwararo daga cikinsu. Zaman da ya yi, ya bawa gashin kansa damar kwanciya a kafaɗarsa zuwa bayansa, tamakar mace. A hankali ɗayan ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Sannu ya jikin naka?" Maimakon ya bashi amsa, sai ya yi shiru ya na bin sa da kallo. "Akwai abin da yake yi maka ciwo ne?" A hankali ya motsa bakinsa ya ce "Ina ne nan?" Baƙin ya kalli gurin sannan ya mayar da idonsa kan shi ya ce "Mun shigo Nigeria ne yanzu haka" "Nigeria?" Ya maimaita. "Eh Nigeria" ya amsa masa. Ya yi shiru ya na ƙoƙarin tuna a ina ma ya taɓa jin sunan. "Ya na ga ka yi shiru ne? Ka gane ni ma kuwa?" Ya ɗago ya kalle shi a hankali ya girgiza masa kai alamar a'a. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ba ka sanni ba ka ke nufi?" Ya jinjina masa kai. "To ka san sunanka?" Yayi shiru yana ƙoƙarin yin tunani, amma ya gaza tuna komai, sai ma wani irin rugugi da ya ji a cikin kansa tamkar an yi aradu, hakan ya tilasta masa dafe kansa yana rintse idanunsa. "Shi kenan ya isa, ba sai ka tuna ba, amma ka san alwala da salla?" Ya ɗaga masa kai alamar eh, ba tare da ya yi magana ba. "Sallar asuba raka'a nawa ce?" Ya ɗaga masa yatsunsa guda biyu. "Azahar fa?" Ya nuna masa huɗu. "Ka san salla, amma ba za ka iya tuna komai ba bayan haka?" "Eh" ya amsa a taƙaice. "Shikenan, ka zo ka yi alwala sai ka rama sallolin da suke kanka, ka yi ƙasaru, tun da mun yi tafiya mai nisa daga Nijar". Shiru ya yi ya na son tuna a ina kuma ya taɓa jin sunan Nijar, sai kawai ya bar shi a sunan da ya ji ya faɗa ɗazu ne Nigeria. Cif ya jera sallolin kamar yadda wanda suke tare da shi, ya gaya masa waɗanda su ka tsere masa. Ya ɗaukko abinci ya bashi, ya saka hannu ya karɓa ya fara ci. Bayan ya kammala cin abincin, ya tsiyaya masa shayin da ya dafa a cikin ɗan ƙaramin kofi ya miƙa masa. Ya karɓi shayin ya fara sha, hakan ya sanya shi fara ƙoƙarin tuna wani abu, amma abu ya ci tura. Bayan ya gama shan bunun, ɗayan ya fito da wani ƙyalle ya tattare masa dogon gashinsa, ya naɗe masa shi, sannan ya naɗa masa rawani ya kamo hannunsa su ka fito daga cikin tantin. Tsayawa yayi, ya yi wa wurin ƙuri da ido, jeji ne babu kowa a wurin, sai bishiyu sai kuma wani raƙumi da yake gefe a ɗaure ya na ta taune-taune. Ya tafi ya kwanto raƙumin, ya janyo akalarsa zuwa gabansa, ya kalle shi ya ce "Ka san menene wannan?" Ya jinjina kai. "Mene ne shi?" "*Le chameau*" (Camel/ raƙumi ne) Yayi sassanyar ajiyar zuciya ya ce "Hau mu tafi" ya taimaka masa, ya hau kan raƙumin, shi kuma ya ja akalar raƙumin su ka tafi. ***** Tafe take sannu a hankali, ta na ratsa matsakaitan gidajen da su ka haɗu suka samar da rukunin gidajen da suka samar da wani ɓangare na unguwar. Mamakon ruwan saman da aka tafka kamar da bakin ƙwarya awanni kaɗan da suka shuɗe, ya wanko datti da ƙazanta daga mabanbanta wurare, sai dai rashin kyakyawar hanya da magudanan ruwa, ya sanya ruwan shiga gidajen mutane, wani kuma ya kwanta a cikin layuka, ta yadda ba a iya banbance kwata da hanya, duk sun haɗu sun shafe. Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, abin da take tsoro da fargaba ta tarar, tun da hadarin nan ya taso aka fara ruwa, hankalinta ya kasa kwanciya. Daga in da take ta na hango tsakiyar tsakar gidansu, a sakamakon fiye da rabin katangarsu ta zube. Ta lallaɓa ta ƙarasa, duk mutanen gidan su na tsaye sun yi cirko-cirko su na jajanta abin da ya faru. Sai dai abin da ta tarar ya fi wanda ta hanga daga nesa, domin ƙarasawarta gidan ke da wuya, ta tarar rijiyar gidan ta burma, ta haɗe da masai kasancewar daf da juna suke, daga in da aka yi rijiyar babu tazara. Wani babban mutum ne ya fito daga cikin banɗakin, ya dubi matashiyar ya ce "Nana kin dawo?" Jiki a sanyaye ta amsa ta ce "Eh Baba" "Kin ga abin da ya faru ko" Nana ta ce "Eh baba, tun ina makaranta da aka fara ruwan nan, hankalina yake tashe nake a tsorace" "Ai mu na cikin jarrabawa, yanzu lalubawa zaki yi, ɗan abin da aka samu a hannunki, ki kawo a samu ko katangar a fara tayarwa". Saroro Nana ta yi baki buɗe tana bin Baba da kallo, duk da ba abin mamaki bane ba, jin hakan daga bakinsa, cikin ƙarfin hali ta ce "Baba dubu bakwai ne fa albashin nawa, kuma yau goma sha ɗaya ga wata, ko sisi ba ni da ita ka manta dubu biyar ka karɓa ka bani dubu biyu" "Kai Nana, ina ki ke kai kuɗi ne? kullum da an taɓa ki babu, ai shikenan sai ku zauna haka, duk wanda ya ji turotso sai ku bi maƙwabta ko ku tafi jeji ku yi, ni ba ni da yadda zan yi" Wata mata da tun da su ka fara maganar ba ta yi magana ba, sai yanzu, ta kada baki ta ce "Ai kuwa sai ka san yadda za ka yi, haka zamu dauwwama mu na gantalin yawon kashi a maƙwabta kai ko kunya ma ba ka ji, Nana ka tsare ka na ta baka kuɗin da zaka ɗaga katangar gidanka, kai fa take miƙawa albashin nata, dubu bakwan nawa take, ka bi ka kashe zuciyarka, wallahi dole ka nemi yadda za ka yi" Nana dai ba ta sake cewa komai ba, ta nufi hanyar wurin kwananta, ta na jiyo ɗaya daga cikin yaran gidan ya na cewa "Abu mai sauƙi, a samu ƙaton bokiti kawai, kowa ya din ga juyewa a ciki, a tara a sayar zazzafan taki ne fa, tsaf za a samu kuɗin ɗaga katangar gidan nan, gwargwadon ƙwazonmu wurin tarawa da yawa gwargwadon..... "Za ka rufe mini baki, ko sai na daka ka a wurin nan, shashasha mara tunani kawai" Baba kuwa waje ya yi, saboda tijarar da mama ta fara yi masa, maƙwabta duk sun fito waje, ana jajanta ɓarnar da ruwan yayi a layin, tare da jajantawa su Baba abin da ya faru da su. Jiki a sanyaye ta shiga wani ɗan madaidaicin ɗaki, bakinta ɗauke da sallama. 'yan mata biyu ne a kwance su na danna waya, da ƙyar ɗaya ta amsa, ɗayar kuwa ko ɗagowa ba ta yi ba. Nana ta ajiye jakar hannunta tare da faɗin "Jamila, ashe ruwa ne yayi mana gyara haka?" Jamila ta ce "Aikam, ɓarna ma ba ƙarama ba, kin ganni nan lissafi nake yi yadda zan tsallake na bar gidan nan, wannan abin kunya da mai yayi kama, ace in da zaka tsuguna ka juye najasarka babu, sai dai ka bi maƙwabta, wannan gidan Allah kaɗai ya san lokacin da za a gyara shi". Nana ta nemi wuri ta zauna ta ce "Idan kin bar gidan nan, ina za ki je?" Cike da takaici Jamila ta ce "Ko ma ina ne, tun kan jarabar talauci ta kashe mutum, kullum gida babu cigaba ba a ɗauki ɗawainiyarka ba, amma ana nema a wurinka" Nana ta girgiza kai ta ce "To, Allah ya sa mu dace, ya bamu mafita". "Amin, kalli wurin kwanciyar ki ma duk ya jiƙe, nan wurin ma zuba yake yi". Nana ta kalli wurin tare da yin ajiyar zuciya, ba tare da ta ce komai ba. Haka gidan su Nana suka kwana, rabin katanga a zube, kowa ya zo wucewa ya na kallon cikin gidan. Washegari da asuba da 'yan kame-kame su ka kama ruwa, wasu su ka zagaya maƙwabta wasu kuma suka yi a wani wurin, su ka yi alwala su ka gabatar da sallar asuba. Tun daren da abin ya faru maƙwabta suke shigowa yi musu jajen abin da ya faru. Jamila sai masifa take yi tana mita, "Wallahi na san ikon Allah ne kawai zai sanya a gyara katangar nan, haka zamu ci gaba da zama da zubabbiyar katanga, ni matsalar banɗakin nan ba ta dame ni ba sama da katangar nan, duk asirinmu a tone, kodayake wane asiri ne ma da mu, banda damin talauci da tsiya" Nana ta na jin ta ba ta ce uffan ba, ta ɗaukki Alqur'aninta tana dubawa. ***** Tsura masa ido yayi, yana nazarinsa, sannu a hankali yake cin abincin gabansa, ya gama ya wanke hannunsa, ya gyara zaman rawaninsa ya rufe fuskarsa. Habu ya dube shi ya ce "Ka ƙoshi?" Ya jinjina masa kai alamar eh. "Yanzu za ka iya tuna sunanka?" Ya girgiza kai alamar a'a. Habu yayi ajiyar zuciya yana sake jinjina lamarin, ya sake kallonsa ya ce "Babu abin da yake iya zuwa kanka ka tuna?" "Eh" ya faɗa a taƙaice. "Shikenan, kar ka matsawa kanka sai ka tuna wani abu, amma a duk lokacin da ka tuna wani abu ka sanar mini, dole in fara tunanin nema maka magani kafin yin komai, amma sai mun samu wurin masu amana" shi dai yayi shiru bai ce masa komai ba. Ya saka hannu a aljihun babbar rigarsa, ya ɗaukko waya, ya duba wata lamba, ya kara wayar a kunnensa. Mintuna kaɗan ya amsa sallamar sannan ya ɗora da cewa "Mun iso Nigeria tun jiya, yanzu mene ne abu na gaba?" Ya ɗan yi shiru tsawon wasu mintuna sannan ya ce  "Ka tabbatar babu matsala? Ba na son azo a samu matsala, dole ayi taka tsantsan da lamarin nan, kafin mu san ma in da za mu nufa neman maganin" ya sake yin shiru sannan ya ce "Shikenan, ina sauraronka" har ya kammala wayar bin sa yake yi da ido, kamar zai yi magana amma bai ce komai ba. ***** Kwanaki uku suka shuɗe ana tsilla-tsillar makewayi a gidan Malam Isa, wato gidansu Nana, ƙarshe katanga sai buhu aka saka aka rufe ta. Cikin ikon Allah, maƙwabta su ka yi ta kawo masa gudunmuwa, sai dai idan kuɗi ne sai ya karɓa ya saye abin sa, tun da matarsa rabi ta fuskanci haka, ta sanya shi a gaba da tijara, da masifar ya fito da kuɗi a san abin yi. Nana ta na ɗaki tana shafa mai, amma hankalinta yana kan su Baba sa suke ta faɗa. "Amma rabi da kuɗaɗen gudunmuwar nan, nake ta baku kuɗin cefane, kuɗin nan fa ba isa za su yi ba ayi aikin katangar nan" Ta hayyaƙo masa cikin ɗaga murya ta ce "Wane cefanen, ba wata tsiyar ka bamu ba, makewayi ya gagari mutum, kamar mun fi kowa talauci a tsukin nan" Nannauyar ajiyar zuciya Nana ta yi, ta tashi ta ƙarasa shirinta, ko sallama ba ta yi wa su Baba ba ta fice, dan wannan rashin girmamawar da suke yi wa juna ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba. Kamar yadda ta saba, tana ƙule a gefe guda, tana dudduba cikin Alqur'ani, yayin sa sauran 'yan ajin suke ta tilawarsu daban. A hankali ta fara jin jikinta yana wani irin sanyi, ta fara jin tamkar daga wata duniyar take jiyo karatun 'yan ajin nasu. "Nana" ta ji muryar Amira ƙawarta. Tayi jarumta ta ɗaga kai ta kalleta, Amira ta zauna a kusa da ita ta ce "Na biya miki makaranta, ashe abin da ya faru kenan, Allah ya mayar da alkhairi ya tsare gaba, na tarar da baba yana ta faɗa, wai kowa ya nemi in da zai tafi kafin Allah ya hore masa abin da zai gyara gidan" Sai Nana tayi da gaske take fahimtar me Amira take faɗa, ganin yadda Nana ta ƙura mata idanu ko ƙiftawa ba ta yi, ya sanya ta ɗan matsa baya kaɗan ta ce "Nana lafiya kuwa? Ko baki da lafiya ne?" Ta girgiza mata kai, ba tare da ta ce komai ba. Amira ta koma gefe ta ɗaukko Alqur'aninta, ta koma nesa da Nana. kamar wadda ake zarewa laka, take ji, wani irin sanyi jikinta yayi zuciyarta ta din ga bugawa cikin matsanancin tsoro da fargaba, numfashinta ya dinga sama-sama kamar zai bar gangar jikinta, ji tayi kamar ta kurma ihu, sai dai jikinta babu wannan ƙwarin, ji take kamar ajalinta ne ya risketa. Alqur'anin gabanta take kallo, zuciyarta ta din ga raya mata, ta yi jifa da shi. Ganin yadda yanayinta ya sauya, ya sanya 'yan ajijsu darewa suka koma gefe daga kusa da ita. Malam Auwallu ne ya shigo, 'yan ajin duk suka yi shiru, hankalinsa ne ya sauka a kan Nana, da take ta fizgar numfashi idanunta sun yi jawur. Girgiza kai ya yi ya ce "Nana Asma'u" kamar wadda aka jonawa shocking, haka ta ja da baya a razane, tare da sunkuyar da kanta. Ya janyo kujerarsa zuwa gabanta, ya ce "Yau haddar ki zan fara ji, matso ki karanto mini, kin san ina son ƙira'arki" ba ta yi magana ba ta ci gaba da sunkuyar da kai tana haki. Ya kalli ta kusa da ita ya ce "Amira dawo nan gefe ki fara ke" Cikin damuwa Amira ta tashi, tana kallon Nana cike da tausayawa, hatta 'yan ajin kallon Nana suke yi cike da tsoro, su na jiran kyat su falla da gudu su na iface-iface. Amira na zama a gaban malam Auwal ta fara karatu, a haka ya ci gaba da sauran karatun ɗaliban ɗaya bayan ɗaya. Nana tana gefe a zaune tana ta gursheƙen kukan da ita kanta ba ta san dalilin sa ba, adadin yadda suke karatun ya ingiza bugun zuciyarta, tare da jin jikinta na ci gaba da yin sanyi. Malam Auwal na fita amsa waya, Nana Asma'u ta tashi ta fice ta bar ajin, ba tare da wani ya yi yinƙurin tare ta ba, har ta yi nasarar barin cikin makarantar. Ayshercool 08081012143 BUZU YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA) AISHA ADAM (AYSHERCOOL) Arewabooks Ayshercool7724 P2 Kiraye-kirayen sallar magariba ake yi, Baba ya shigo gida da nufin ya yi alwala ya tafi masallaci. "Nana, Nana" "Baba ba ta dawo ba fa" matashin yaron da bai wuce shekara goma sha biyu ba ya bashi amsa. "Ba ta dawo daga ina ba?" "Makarantar islamiyya" "A yanzun da magaribar nan, ke Jamila, Sa'adatu wai kuna ina ne ina ta magana kun mayar da ni mahaukaci?" Jamila ce ta fito tana yamutsa fuska ta ce "Baba ba ta dawo ba fa" "To tana ina? Ina ta tafi? Ko an aiketa ne?" Rabi ce ta fito ta ce "Wai Nanan yarinyar goye ce ne da ka ke ta wannan haƙilon saboda ita? Idan ta gama yawon nata za ta dawo ai" Guntun tsaki ya yi ya ce "Kai sani da aka tashe ku daga islamiyyar ba ka ganta ba?" Sani ya ce "Ban ganta ba, kuma mu ne ƙarshen tafiya, yau na makara aka sakamu kwashe butocin alwala muka gama aka kulle makarantar" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba bankaɗawa ta yi, tayi wani wurin ba" "Ko kuma yawon watsewa ta tafi ba" "Allah ba zai nuna mini watsewa a kan 'ya'yana ba" yayi maganar yana ficewa daga gidan. Nana kuwa tun da ta fita daga islamiyyar, babu wanda ya ganta, dan haka ta ci gaba da tafiya ba tare da ta san in da take sanya ƙafafuwanta ba, ba ta iya tantance rana ce ko dare ma, sai dai tana jin yadda zafin rana yake ratsa ƙafafuwanta da kuma tafin ƙafarta, da take takawa babu ko takalmi. Ita dai burinta ta yi nesa da in da take, ko ta fita daga halin da take ciki, ko kuma tserewa abin da take jin tamkar ajalinta ne yake tunkarota. Wani matsakaicin gida ta tunkara, babu sallama babu neman izinin masu gidan, kawai ta afka ciki. Ɗaya daga cikin jerin ɗakunan ta shiga, ta cire hijjabin jikinta na islamiyya, ta cukuikuye shi, ta yi fulo da shi, ta kwanta. Kusan mintuna goma sha biyar, da shigarta babu motsin kowa a gidan. Wani matashi ne yayi sallama, ya ji shiru, ya sake sallama ya ji shiru. Saka kai yayi ya shiga ciki yayi tozali da Nana a kwance tana bacci. Turus yayi yana kallonta, yana tunanin ita kuma wannan daga ina. Shaiɗan ne ya shiga ƙawata masa kyakkyawar baƙar fatarta mai sheƙi, da kuma ilahirin jikinta. A hankali cikin sanɗa ya shiga ɗakin, yana cigaba da ƙare wa ƙirjinta kallo. Ɗan dukan gefen carfet yayi, dan ya tabattar da idonta biyu ko bacci take yi. A hankali yake ƙoƙarin kai hannu jikinta, kwatsam! Ya jiyo muryar matar gidan a ƙofar gida tana gaisawa da maƙwabta. Cikin hanzari yayi baya ya dawo tsakar gida ya tsaya. Sallama tayi tare da yara ƙanana, ya amsa yana mazewa. "Saleh, zuwa babu sanarwa haka?" Ya ɗan sosa kansa ya ce "Wallahi kuwa, ina ta sallama amma gidan shiru babu kowa" Ta kalli gidan ta ce "Ikon Allah, kuma yarinyar maƙwabta na bari a gidan, ta jire mini na je ɗaukko su hafsa daga makaranta shi ne ta bar mini gidan a buɗe haka?" Saleh ya ce "Aikuwa ta yi ganganci da ta bar miki gidan babu kowa haka" "Aikam yaushe ka shigo garin ne?" "Shekaranjiya da daddare na ce yau bari na ɓullo mu gaisa" "Aikuwa ka kyauta" ta yi maganar tana ɗaga labulen ɗakin. Turus tayi, tana maimaita"Innalillahi wa innalillahi raji'un" ganin mutum a kwance. Ya kalleta ya ce "Lafiya kuwa?" Ba ta amsa masa ba, ta ƙarasa tana ƙare mata kallo, ta kai hannu ta taɓa ta ta ce "Nana" sai dai shiru ba ta amsa ba. Ta kalli ƙafafuwan Nanan, futu-futu, har da jini alamar ta taka abubuwa a hanya. "Subhnallah, kar dai da ƙafa ta taho Nana, Nana tashi mana" sai dai ba ta motsa ba. Cikin basarwa Saleh ya ce "Anty lafiya kuwa? Wace wannan ɗin dama da mutum a gidan nake ta sallama ba a amsa ba?" Yayi maganar yana ƙare mata kallo, dan shi gaba ɗaya ma bai lura da raunin da yake ƙafarta ba. Anty ta ce "Ƙanwata ce wallahi, ba ta da cikakkiyar lafiya ne, ga wayata ta lalace balle in kira gida in ce tana nan, kuma ni Wallahi ban haddace lambar kowa ba, balle na kira na gaya musu" Suka ci gaba da jimantawa, Nana kuwa ta ci gaba da baccinta, mai kama da suma. Baba yayi sintiri zuwa islamiyyar su Nana babu adadi, tun yana yawon neman ta har ya gaji. Suwaiba ta ce "Wataƙila mutanenta ne su ka yi wani wurin da ita" "Ba wasu mutanenta, ayi ta fakewa da sheɗanu tana rashin mutunci, ta taɓa yin irin haka ne? Allah ne kaɗai ya san gidan uban wanda ta tafi" Baba ya ce "A'a ba na tunanin za ta je wani wurin ba mu sani ba, tun da ba ta taɓa yin hakan ba, amma ina Jamila ma?" "Ta na gidan uwa ɗakkinta ɗin nan, maman khairat, tun azahar tana can" Baba ya ce "Kuma haryanzu goma saura na dare, ba ta gida uban me take yi a gidan mutane?" Mama ta ce "A'a yau na ga abin tsiya, to malam ba abincin safe babu na rana, ba dole yarinya ta tafi in da za ta samu ta ci ba? Ai gara ita an san in da take, 'yar ka fa? Shi ya yi nasa wuri, ita ma gashi ta kama gabanta" Baba yayi shiru bai sake cewa komai ba. Shirun sa ke da wuya, Jamila ta yi sallama, suka amsa baki ɗaya, Baba ya ɗaga kai zai yi magana, sai yayi shiru ganinta da babbar leda. "Mama na dawo" "Sannu jamila, ya ki ka barota?" "Lafiya kalau Alhamdilillah, baba sannu da gida" Baba ya ce 'Yauwwa Jamila, amma ina ki ka tafi haka ba kya gida?" Jamila ta taɓe baki ta ce "Baba Allah ya gani na gaji da raragefen shiga banɗaki ne, ga yunwa ina ji shi yasa na tafi gidan maman khairat na wuni a can" Baba ya ce "Ku yi ta haƙuri ku na addu'a, in sha Allah za a gyara katangar nan, kuma a gyara masan, mutanen unguwar nan ne ma, babu haɗin kai da zuciyar taimako, amma yadda iftila'in nan ya afko mini, ai kamata yayi ayi gidauniyar da za a tallafa mini" Mama ta ce "Kai wa ka ke tallafawa idan matsalarsa ta tashi?" "Rabi wai babu damar na yi magana, sai ki nemi tozarta ni a gaban yara" Ta girgiza kai ta ce "Ba wani tozarci gaskiya ce" Bai bi ta kanta ba, ya kalli Jamila ya ce "Jamila, Nana fa ba ta dawo gidan nan ba, tun ɗazu ake neman ta ba a ganta ba" Jamila ta tsaya da juye abincin da take yi ta ce "To ina ta tafi?" "Wallahi ban sani ba, an rasa in da ta shiga " Jamila ta ce "Kuma ita ba waya ba, balle a kira ta kuma dai na ga ba ta taɓa yin irin haka ba" "Wallahi kuwa. Kai Sani ɗaukko kwano a zuba mini abincin nan nima na saka a cikina, dan rabona da abinci tun safe, ashe akwai sauran masu zuciyar taimako a unguwar nan, irin wannan abinci haka Jamila" Haka Baba ya karkace aka lamushe abinci da shi, har ya nemi ya manta batun ɓatan 'yar sa Nana. ***** Misalin ƙarfe tara na safe, Nana ce a zaune, tana kurɓar kunun tsamiya, duk da babu sukari a cikinsa, amma ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, ga dankali da aka take mata kwano da shi, wanda rabonta da ta ci ta ƙoshi haka har ta manta. Ummi ta dube ta ta ce "Nana, wai garin yaya aka yi ki ka taho gidan nan a ƙafa haka? Tun jiya kin ƙi magana" Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban san ya aka yi ba, ni dai kawai ina islamiyya na ji duniya ta yi mini zafi, kamar zan mutu shikenan ban san meyafaru ba, na dai ji ina bacci, kawai na farka na ganni a nan" Ummi ta ce "Ohh wannan larura taki Allah ya yaye miki Nana, an gode Allah ma da ki ka yo nan ba wani wurin ki ka yi ba, in ƙara miki dankalin ne?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a na ƙoshi Alhamdilillah" "Nana ina kyautata zaton mutanen nan ne, suka hana miki samun mijin aure har yanzu, ga Habibu, rumi-rumi an fara magana aka fasa, ni a yanzu ma akwai wani a ƙasa kuwa?" Nana ta girgiza kai alamar a'a. "Wallahi Nana ina yi miki fatan ki yi aure, ki bar wannan gidan namu, da ba a iya amfana maka komai, idan ba uwarka ce ta yi maka ba, kin ganni nan duk da yau da daɗi gobe babu, yau mu ci gobe mu yi haƙuri, ga azabar dangin miji, amma ya fiye mini wannan gidan namu, da kamar a cikin sa aka yi wahayin babu, ke kanki a yunwace ki ke, ga Baba ya damu ki yi aure, dan Allah kalli wata breziya a jikinki, dan masifa duk kin ƙuƙƙuleta, wallahi da na shiga banɗaki na tarar da phant ɗinki, na za ta tsumma ne da yarwa zan yi, wannan wace irin rayuwar azaba ce?" Nana ta sunkuyar da kai ta yi shiru, dan duk abin da ummi take faɗa gaskiya ne, amma waye zai aureta da wannan larurar a haka? Malam Auwal na islamiyyar su, na ta nuna mata alamar soyayya amma ta yi burus, dan ta san yau da gobe sai Allah, babban fatanta ta rabu da wannan larurar, duk da tana burin yin auren, dan ita kaɗai ta san masifar da take ciki. "Kin san wani abu Nana, akwai wani mai magani da na ji maƙwabciyata su na magana rannan, zan yi mata magana ta kwatanta mini wurin, anjima mu kama hanya mu je ko Allah ya sanya a dace, daga nan na je na duba idan an gyara mini wayata sai na raka ki gida" To kawai Nana ta iya cewa, ta cigaba da shan kununta a hankali. ***** "Alhajin Allah" "Na'am malam" ya amsa yana tattara nutsuwarsa a kan mutumin da yake zaune, a kan tabarma, gefensa ga carbi mai dubu, ga wani ɗan farantin katako da ƙasa a kai. Yayi shiru ya na nazartar ƙasar da ya yi wa zane-zane a gabansa. "Malam me ka gani ne?" "Eh to, buƙata zata biya Alhaji Zailani, amma gaskiya za a sha gwagwarmaya, ga magauta ko ta ina a tattare da kai, arziki zai ninku fiye da yadda ka ke zato, amma gaskiya zaka sha wahala, ƙila ma ka iya rasa ranka, kuma a gidan huɗu ga wata kujerar siyasa nan ko ta mulki da zaka iya samu, sai dai gidan uku ya nuna shi ma akwai bala'i, da tarin ƙalubale" Alhaji zailani ya yakice gumin da yake tsatsafo masa daga goshinsa ya ce "Yanzu malam menene abin yi, dan ko a yanzu kasuwancina harkokin sun fara ja da baya" Ya sake zazzana ƙasa, ya ɗago ya ce "Eh ga wani ƙulli nan a binne a kusurwa huɗu na mararraba, a kanka, amma warware wannan ba zai yi wahala ba, yanzu mafita ɗaya ce da za a samu mai burujin aƙrabu, ko hutu ko surdanu da zai dace da burujin ka, kuma za su taimaka maka ka kai ga ci, ba tare da ka fuskanci ƙalubale ba" Alhaji Zailani ya tattara hankalinsa, ya gyara zamansa ya ce "Malam Gambo to tayaya zan gane su, kuma a ina za a same su, ko nawa ne zan bayar a samo" "Ba samo su za ayi ba, ka samu mace mai ɗaya daga cikin waɗannan burujan, ka kwanta da ita, zaka samu buɗi ta in da ka zata da in da baka zata ba, taurarinta za su haskaka naka da suke ƙoƙarin disashewa, sannan za ta ɗauke wannan wahalar da zaka sha, kafin ka cimma muradinka" Ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "In dai mata ne gasu nan kamar jamfa a jos, tayaya zan gane wadda ka ke nufi?" Malam Gambo ya numfasa ya ce "Wadda namiji bai taɓa kusanta ba ake so, kuma idan aka samo ta sai na duba ranar sa'ar burujanku. Kuma ba a fuska za a gane mai irin tauraron da nake faɗa ba. A samo mai suna Nadiya, ko ɗausiyya, ko badariyya" Alhaji zailani ya ce "Ni yanzu malam ina zan samo waɗannan sunayen?" "Bincikawa za ka saka ayi, ko Asma'u ma zai yi, amma shi ma da sharaɗi, idan aka samo ɗin sai na lissafa adadin sunanta da na mahaifiyarta na tabattar da haɗuwar aikin" "Shikenan malam, in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina, zan samo in sha Allah, ga wannan ba yawa" yayi maganar yana ajiye masa kuɗi a kan shimfiɗarsa. ***** Ummi ce ta kalli Nana a ɗan fusace ta ce "Wai nuƙu-nuƙun me ki ke yi ne haka Nana?" "Wallahi Anty ummi ba na son zuwa wurin maganin nan ne, idan ki na da niƙab ki bani na saka, kar na je wanda suka sanni su ganni" Sheƙeƙe ummi ta kalli Nana ta ce "Au to sai me, ba neman lafiya ki ka je ba, duk wanda ya ce ya sanki shi uban me ya kai shi? Ki wuce mu tafi dan Allah" Jiki a sanyaye Nana ta bi Ummi, sai dai gaba ɗaya ranta babu daɗi, sai dai ta wani ɓangaren tana ƙarfafar zuciyarta a kan wataƙila ta dace da maganin. Maƙil suka je suka tarar da gidan mai maganin, tamkar ana rabon gafara, mata ne suke ta shiga suna fita. Suka samu wuri suka zauna, wasu a shigo da su a rirriƙe, wasu kuma da ƙafafuwansu. Ga manyan mata masu shigar alfarma da kuma yaku bayi. Wasu na ta tumamin iskokai, wasu na kwancez Nana dai ta raɓe ta yi shiru a gefen ummi, kasancewar Ummi ba halinsu ɗaya da Nana ba, tuni ta saki jiki suna hira da matan wurin, wannan ta ce matsalar yara ce ta kawota, wannan ta ce matsalar miji, wasu kishiya wasu larura, wasu su ce mayu ne suka kama su, wasu kuma matsalar rashin mijin aure ne ya kaisu. Nana ta din ga nazarin matsalolin daki-daki, ita a tunaninta matsalar rashin lafiya ce kawai za ta kai mutum wurin mai magani, wadda suke samun saɓani da miji maganin me za a bata, ban da ta kai wa Allah kukanta? Ummi da wayo da dabara, da iya daɗin baki da hira, ta yi wa matan nan wayo, ta ce Nana zata shigar a gani ba ta da lafiya, kwananta uku ba ta magana, kasancewar tun da suka zo ba ta ce uffan ba. A tsanake yake ƙare masa kallo, yadda ya zauna ya tanƙwashe ƙafafuwansa, yake ta wasa da yatsun hannunsa, yaƙi ɗagowa su haɗa ido. Ya mayar da idanunsa kan Habu, da yayi shiru yana jiran bayani daga bakin mutumin. "Wannan ciwon nasa gaskiya ba zan ɓoye maka ba, idan na matsa ni zan shiga matsala, sai dai ku bincika wani wurin" Cikin damuwa Habu ya ce "Yanzu babu yadda za ayi ace ko sunansa ya tuna? Ya san duk wani abu da ya shafi rayuwar yau da kullum, amma ya manta duk wani abu da ya shafe shi" Mutumin da yake zaune a kan sallaya, "Ka san wa ka kawo mini kuwa? Anya ka san waye?" "Na sani" Habu ya amsa cike da ƙwarin gwiwa, cikin gurɓatacciyar hausar sa" Mutumin yayi murmushi ya ce "Ka san dai abin da ka sani, ka bar shi a haka kawai kar ka matsa sanin abin da yake a ɓoye" jiki a sanyaye habu ya kalle na zaunen ya ce "Tashi mu tafi" ya yinƙura ya tashi, ya tsaya ya kalli malamin ya saki murmushi ta cikin rawaninsa suka fice. Babu tsammani Nana su na tsaye a ƙofar shiga wurin mai magani, wasu mutane suka fito, ƙafafuwansa kawai ta kalla ta ji jikinta ya saki, zuciyarta ta tsinke ta sulale za ta faɗi a wurin, Ummi ta riƙe ta da sauri tana salallami. A hankali Nana ta bi bayansa da kallo kasancewar ya riga ya wuce, zuciyarta ce ta raya mata ta bishi da gudu ta ga waye, daina ganin kowa ta yi sai itakaɗai a cikin sahara, sai kuma shi wannan mutumin da ba ta ga kowaye ba, yana tafe yana jan akalar raƙumi ya yi nesa da ita, tana hango shi a can nesa sai kuma manyan sawayen raƙumin da nasa. "Nana" ta ji muryar ummi a kunnenta, ta buɗe ido ta kalle ta a hankali ta kalleta. "Sannu Nana kin tashi" ba ta amsa ba ta ɗaga kai ta gansu a gidan Ummi. "Anty yaushe muka dawo?" Ummi ta ce "Hmm tun ɗazu, ai tun kafin mu shiga wurin mai maganin, ki ka sume, ya ce manyan dakarun aljanu ne a kewaye da ke, mu na shiga ya gansu" Cikin mamaki Nana ta ce "Ya ga su wa?" "Aljanun mana" ta bata amsa cike da ƙwarin gwiwa. "Dama mutum yana iya ganin aljani a suffarsa?" "Ban sani ba, tambaya dawanau, yanzu ga magunguna nan da hayaƙi kowane zan nuna miki yadda za ki yi amfani da shi, ki ci abinci muje na raka ki gida" Nana ta jinjina mata kai kawai, amma bakinta akwai tarin tambayoyi. Da yamma Ummi, ta taso Nana a gaba domin ta rako ta gida. Ko da suka je gidan, mamaki ne ya cika Nana, ganin an zube kayan aikin gini a ƙofar gidansu, a iya tunaninta Baba ba shi da wata hanyar da zai samu kuɗaɗen da za ayi musu wannan gyaran. "Nana, haka gidan ya koma? Ummi ta yi maganar cikin mamaki. "Eh, sai ma kin shiga, rijiya ta haɗe da masai, amma na ga an kawo kayan aiki ban san a ina aka samo su ba" Da haka suka shiga gidan da salallama, Suwaiba da take wanke-wanke ta ɗago ta kalle su, ta ce "Too yau kuma Allah ya yi miki dawowa daga yawon kenan?" Ummi ce ta ce "Wane irin yawo kuma?" But Mama ta fito daga ɗaki ta ce "To ina ta tafi idan ba yawon ba? Wa ta gaya wa za ta je wani wurin? Kwana biyu babanku ya hana mu sakat, saboda ba a ganta ba, ana ta cigiya a unguwa, dama na gaya masa wani wurin ta yi" Har Ummi ta ɗauki numfashi za ta yi magana, Baba ya yi sallama. Suka amsa masa baki ɗaya, baki sake ya bi Nana da kallo, ya ce "Nana daga ina ki ke? Ina ki ka tafi baki gaya mini ba? Ko wurin uwartaki da ba ta san muhimmancin ki ba ki ka wanke ƙafa ki ka tafi?" Ummi ta girgiza kai ta ce "Haba Baba, dan Allah ka tsaya ka ji mana, ka san halin da take ciki na rashin lafiya, shekaranjiya na je ɗaukko yara daga makaranta, ina komawa gida na tarar da ita, a baje a ɗaki ƙafafuwanta duk jini ko takalmi babu, ba ma ta cikin hayyacinta. Ni kuma wayata ta lalace, babansu kuma ba ya gari, shi yasa ban kira na sanar muku ba. Mama ta yi farat ta ce "Wallahi ƙarya ne, ki na nufin tun daga nan ta tafi gidanki a ƙafa? Ƙarya ki ke yi Ummi, ki faɗi gaskiya idan ma, yawon ta zubar ta tafi ki ke kareta" A fusace Ummi ta ce "Allah ba zai nuna mana mai yawon ta zubar a cikin zuriyarmu ba, baƙin bakinki ya faɗa miki kanki da 'ya'yanki..... "Ke ummi rufe mini baki kafin na kwaɗe ki" Baba ya katse ta cikin fushi. Ya ɗora da cewa "Mara kunya wuce ki tafi gidan ki, Allah ya ba da lada" Nana ji ta yi tamkar ta bi bayan Ummi su koma tare, saboda karɓar da aka yi musu, ko arzikin abin zama ba su samu ba, balle a bawa ko ummin ce ruwa, haka ta kasa magana ta bi bayan ummi da kallo yadda ta fita a fusace. Ayshercool 08081012143 BUZU Ayshercool YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA/002) BRIGHT PENS 3rd BATCH. P3 Nana ta tsaya jiran abin da Baba zai ce, bayan fitar ummi, amma ba ta ji ya ce komai ba. "Wai haka zaka ƙyale yarinyar nan, ba zaka tuhumi ina ta je ta kwana biyu ba?" Mama ta yi maganar tana tsare Baba da ido. "To rabi ya ki ke so na yi, kin san a cikin larura take, ni wannan larurar ta ta ta ishe ni, Allah ya kyauta kawai" Tun da Baba ya faɗi haka, mama ta dasa mita da bala'in baya ganin laifin Nana. Nana kuwa ɗakinsu ta shiga, tana jin yadda maganganun mama ke ratsa zuciyarta, da sanya mata wani irin raɗaɗi da zafi a cikin zuciyarta. Haka ta wuni sukuku, ba wanda ta kula ta ƙule a ɗaki kamar yadda ta saba. Sai dai wunin ɗakin nan, ya ƙara sanya zuciyar Nana a cikin ƙunci, haka kurum kewa da son ganin mahaifiyarta ya bijiro mata. Sai daf da magariba Jamila ta shigo gidan, ta ya da zango a tsakar gida, da abin da ta zo da shi daga gidan uwar ɗakinta. Ƙamshin abinci har cikin ɗaki in da Nana take, ga yunwa tana ta sakaɗar cikinta, kamar ba ta taɓa cin abinci ba, haka take jin cikinta. A lokacin ta tsinkayi hirarsu, wai ashe mijin maman khairat, uwar ɗakin Jamila, shi ne ya ɗauki gabarar gyara musu gidan. Tun tana fahimtar hirar ta su, har ta faɗa duniyar tunani, ba ta iya jin me suke cewa. "Laa Nana yaushe ki ka dawo ke kuwa?" Firgigit Nana ta kalli Jamila, ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce "Tun ɗazu, Anty Ummi ce ta rako ni" "Kuma na zo da abinci amma ki na ƙule a ɗaki, kuma na ga alamar yau gidan ba harka, bari Nasiru ya zo ya sayo miki gurasa" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a a ƙoshe nake, na ci abinci a gidan ummi" Jamila ta ce "Gidanta ki ka gudu kenan? Kin taimaki kanki, kya rage wata kafar, wannan gida namu da kullum cikin indararon talauci ake, ni ma tun da Allah ya sa na samu wurin fakewa, na riƙe wuta" Murmushin nan na ta da ta saba, shi kawai ta yi wa Jamila. Ta ɗan numfasa ta ce "Dan Allah Jamila idan wayarki da kuɗi, ara mini zan yi kira. Jamila ta miƙa mata wayar ta fice, wata lamba Nana ta danna, ta din ga kira, a ƙalla sau biyar amma ba a ɗaga ba, jiki a sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta, tare da zuba wa wayar ido, ko za a biyo amma shiru, har aka fara kiraye-kirayen sallar magariba. Sai da ta fita yin alwala, ta tuna babu damar shiga banɗaki, sai dai ta raɓa ta kama ruwa, haka nan ta shiga banɗakin da dabara, ta kama ruwa ta fito ta yi alwala ta shiga ɗaki ta tayar da salla. Tana jiyo yadda yaran gidan, suka tattara a tsakar gida, tare da mahaifiyarsu, sai ɓaɓɓaka dariya suke yi suna hira, ita kuwa tana ɗakinsu a zaune tsuuruu, 'yar fitilar ma da ta kunna, babu batir ta disashe babu haske, ga uban sauro da yake ta yi mata majalisi a ka. Tana nan zaune aka yi kiran sallar isha'i, ta tashi ta gabatar da sallar, ta idar ta fara tasbihi, ita dai ta san ta fara tasbihi, amma ba ta gane kan lissafin abin da take faɗa, ta tafi wasu tunane-tunanen daban. Wuri ɗaya ta tsurawa ido, yadda inuwar wani ƙwaro, yake ta shawagi a ɗan iya in da hasken fitilar da ta kunna yake. Sai dai sannu a hankali, inuwar ta din ga rikiɗewa zuwa wasu halittun daban. Tsoro ya mamayeta, amma a zahiri ta kasa motsi, duk iya ƙoƙarinta, na tuna wasu daga cikin adduo'in da ta iya domin ta yi, abu ya gagara. "Ke Nana!" Suwaiba ta kira sunanta cikin tsawa. A wahale cikin sauke numfashi, Nana ta amsa tana zare ido. "Dan wulaƙanci ana ta yi miki magana, kin yi wa mutane banza, kuma ki na ji, ki je wai ana sallama da ke a waje" Nana ta waro ido ta ce "Ni ɗin kuma?" "Ban sani ba" Suwaiba ta ba ta amsa, tare da ficewa ta bar ɗakin. Ɗan shiru Nana ta yi, tana mamakin waye wannan ya zo wurinta, dan rabonta da wani ya biyo ta ya ce yana so, kusan shekara ta biyu kenan, tun da aka fasa aurenta da Suleiman. Jin abin take kamar a mafarki, haka ta tashi jiki a sanyaye ta fito. Tana jin maganganun Mama sama-sama, amma ba ta iya fahimtar me take faɗa, dan haka kawai ta saka kai ta fita. Duk da babu haske sosai, amma daga yanayin tsayuwarsa, ta gane waye, cikin azama da ladabi, ta durƙusa har ƙasa ta ce "Ya sayyadi ina wuni?" "Lafiya ƙalau Nana, tashi" yayi maganar yana mata alama da hannunsa, ta miƙe tana sunkuyar da kai cikin jin nauyi. Cikin kulawa ya ce "Nana ina ki ka tafi aka yi ta faman neman ki, ba a san in da ki ka je ba? Hankalin kowa ya tashi, daga fita na bar ku a aji, na dawo aka ce mini wai kin fita, sai ɗazu ƙaninki ya ce mini a gan ki" Gaba ɗaya jikin Nana yayi sanyi, ta san ba kowa za ta gaya wa abin da ya faru, ya yadda ba, amma ba ta sare ba ta ce "Wallahi ya sayyadi ni ban san ya aka yi ba, kawai ganina na yi a gidan yayata Ummi, ita ta riƙe ni a gidanta kwana biyu, amma daga nan ba in da na je wallahi" tayi maganar muryarta na rawa cike da karayar, shi ma babu lallai ya gazgata abin da take gaya masa. Cikin tausayawa malam Auwal ya ce "Ba wani abu, kar ki yi kuka, Ubangiji Allah ya yaye miki Nana, ya kawo miki mafita, amma ki na yin dukkanin azkar ɗin da yakamata?" Ta jinjina kai ta ce "Ina yi" "Yauwwa to ki ci gaba, sannan ki yawaita zama da alawala, kamar yadda nake yawan gaya miki, ki riƙe Alqur'ani Nana, Alqur'ani waraka ne" Cikin sheshsheƙar kuka ta ce "Ko hadda ba na iyawa ko na yi mantawa nake yi" Cikin tausasawa ya ce "Ki yi haƙuri, jarrabawa ce, ki ci gaba da gaya wa Allah, kuma kar ki daina ƙoƙarin yin haddar. Ayatu shifa'a ɗin nan da na gaya miki, ki din ga karanta su a ruwa ki na sha" ta jinjina masa kai tana share hawayenta. Baba ne ya tinkaro gidan, dan haka suka yi shiru, ya ƙaraso, Nana tana yi masa sannu da zuwa, malam Auwal na ƙoƙarin gaishe shi. Baba ya amsa sannan ya ɗora da cewa "Ina fatan ta gaya maka, ni ba a zuwa gidan nan yin dogon zance? In dai da gaske ka ke ka turo magabatanka, ni ba na buƙatar komai da wani ƙaƙale, ku kawo kuɗin aure, a ɗaura aure ba sai ka yi lefe ba, ka yi mata kayan ɗaki dan ni ba ni da halin yi mata kayan ɗaki" Take ran Nana ya ɓaci, wannan soki burutsun da Baba yake yi, duk na mene ne? Idan ma da gaske saurayin nata ne, haka zai yarfata, ta yinƙura za ta yi magana, malam auwal ya riga ta ya ce "To Baba in sha Allah duk ba zai gagara ba, zan yi magana da magabatan nawa in sha Allah" Baba ya ce "Yauwwa Allah ya yi albarka" yayi maganar yana shigewa cikin gida, Nana tamkar ta kasa da gudu ta bi bayan baba saboda matsananciyar kunya. Malam Auwal ya ce "Bari na tafi gida, tun da Baba ya dawo, ki shiga gida ki ci gaba da addu'a " cikin girmamawa ta risuna ta ce "Na gode sosai ya sayyadi". Cikin tausayawa ya ce "Allah yayi miki albarka ya baki lafiya Nana" Ta amsa da "Amin ya Allah" ta nufi hanyar shiga gida. A tsakar gida ta tarar da Baba yana tambayar Mama, dama akwai wanda yake zuwa wurin Nana ba a gaya masa ba. "Babu fa wani wanda yake zuwa wurinta, ni rabon da ace an zo wurinta, tun da aka fasa wancan auren nata, kamar an buga mata hatumin jaɓa, malaminsu ne na islamiyya ba wani ba, kuma Auwwalun gidan  mai koko ne ba wani ba, malaminsu ne na islamiyya" Bab ya ce "Oho ko ma ɗan gidan mai ƙosai ne, na ce ya yi wa iyayensa magana, su zo ayi maganar aure" "To ce maka yayi yana sonta?" Baba ya ce "Koma ba sonta yake yi ba, tun da ya zo wurinta ƙofar gida, ai sonta yake yi, tun da ba karatu yake biya mata ba, in samu in aurar da su na huta da wannan wahalar ta ishe ni, riɗa riɗa da su a zaune a gida, mussaman ita ma, ni duk yarana babu wanda yayi daɗewar su ba su yi aure ba". Mama a zafafe ta ce "A'a itan dai, ta fi uban kowa kwantai, sai an yi magana ace aljani ne ya hanata aure" Baba ya ce "Ko kuma kece aljanar ba, tun da kin taka muhimmiyar rawa wurin fasa wancan auren nata" "A'a ka saka munjaye dai, mun taka muhimmiyar rawa zaka ce, ba wai ka ɗora mini laifin nikaɗai ba" raɓawa Nana tayi, tana bin bango za ta wuce ɗakinsu, dan ba ta son ma wani ya ga wucewar ta, amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba, Baba ya hangota. "Yauwwa ke Nana, ki fara shirin ki, dan in dai da gaske yaron nan yake, ko wata guda ba za  ayi ba, ki tattara ki tafi ɗakinki, ki samu nutsuwa nima a rage mini wahala" Nana ba ta iya cewa komai ba, sai tsayawa da ta yi tana wasa da yatsunta a cikin hijjabinta, tana jin yadda zuciyara ke bugawa da matsanancin ɓacin rai da damuwa. Wayar Jamila ce take ringing, Baba ya koma kanta da masifar, ta ɗaga wayar nan ta cika masa kunne. "Hello" Jamila tayi maganar cikin iyayi, ganin baƙuwar lamba ce, a zatonta ko saurayi ne. "Assalamu alaikum" muryar babbar mace ta amsa a wayar. Ta yamutsa fuska ta ce "Wace ke magana?" Matar ta ce "Kira na gani da wannan layin, bana kusa da wayar ne" Jamila ta ce "Anya wannan lambar kuwa? Amma wa ke magana?" "Maijidda ce" Jamila ta ɗan yi jimm ta ce "Maijidda kuma? Auuu Nana ce dai ta yi kira da wayar ta yi maganar tana miƙewa ta nufi Nana domin bata wayar. A hasale, Baba ya fizge wayar cikin ɗaga murya ya ce "Halima babu ke babu 'ya ta, kar ki sake kiran waya ki na neman ta, zan yi ƙarar ki wallahi" Nana ta fashe da kuka ta ce "Baba dan Allah ka yi haƙuri, ni na kira ta" Ya jefar da wayar ya yo kanta, kamar zai rufeta da duka, ya ce "Da ki ka bar gidan nan wurinta ki ka tafi ko Nana?" "A'a Baba ba wurinta na tafi ba" tayi maganar tana kuka. "Wato duk yadda na bi na raba ki da matar nan, ba zaki rabu da ita ba ko? Yadda take mutuniyar banza haka zata lalata miki rayuwa, da tana ƙaunar ki ba za ta tsallake ta bar ku ta tafi ta yi wani auren ba, babu abin da zata tsinana miki, idan kuma ba haka ba sai dai ki zaɓa ko ni ko ita" Sosai Nana take kuka, tamkar ranta zai fita, ta rasa dalilin da ya sanya abin da ya haɗa su, ya shafe ta yake aibata mata uwa a gaban kowa, yana cin mutuncin ta, ita fa uwa uwa ce, mece ce ribarsa idan ya raba alaƙarta da mahaifiyar ta?. Wucewa ɗaki ta yi tana ci gaba da kuka, masifa goma da ashirin, ga yunwa ga yarfata da Baba yayi a gaban ya sayyadi, ga kuma abin da ya fi ci mata tuwo a ƙwarya, cin zarafin mahaifiyar ta. Ko hijjabin jikinta ba ta cire ba, kawai ta kwanta tana kuka, ji take tamkar ta kurma ihu ko za ta ji sanyi a ranta, shiru ta yi hawaye na zuba daga idanunta, tana sheshsheƙar kuka, ga kanta ya fara sara mata da wani irin matsanancin ciwo. Ba ta san iya adadin lokacin da ta shafe a haka ba, ta ji Jamila ta taɓa ta, ta ɗago ta kalli Jamila. "Ungo rabu da shi, kirata ku yi magana" Jiki a sanyaye ta girgiza wa Jamila kai, alamar ba zata karɓa ba. Jamila ta yi ƙasa da murya ta ce "Ya tafi ya kwanta fa, ki kira ta bari na kira miki ita, ai ban san ki na da lambarta ba, ai da kin din ga karɓa ki na kiranta" tayi maganar tana danna lambar, sai dai layin yaƙi shiga. "Ba komai Jamila na gode sosai kar ki damu" ta koma ta kwanta. Ƙoƙarin yin tunani take yi, amma kanta ya ci gaba da sara mata, ba ta san ya aka yi ba, bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ta ba. Tana tsaye a wani ɗakin library, amma yanayin wurin kamar a wani zamani ne na daban, litattafan wurin duk sun yi ƙura, wasu litattafan duk yana ta yane su, ga ƙauri wurin yake yi, da ta kasa gane wani irin ƙauri ne. Tari ta fara yi saboda ƙaurin ya fara damunta, babu tsammani ta ɗaga kai ta ga wani zanƙalelen mutum, da tsawonsa ya kusa danganawa da rufin ɗakin. Sai yanzu ta lura, ginin ɗakin ma tsawo ne da shi sosai. A hankali yake tafiya, yana zazzaro litattafai yana duddubawa. Duk iya ƙoƙarin da Nana tayi, domin karanto addu'a, ta kasa ta fara ja da baya tana waige-waige ko za ta samu hanyar guduwa, amma ta kasa samu. Ta sake ɗaga kai a dubi in da yake, amma taga ba ya wurin, ta yinƙura za ta tashi, amma ta ji tamkar an ɗaureta a cikin sarƙa. Ajiyar zuciya ta ji an yi a gefenta, ta waiwaya da sauri, ganinsa ta yi zaune a kusa da ita. Zuciyarta ce take dukan uku-uku, "Kwana da yawa" yayi maganar yana sanya dogayen faratansa a gefen wuyanta, ya tsaga jini ya fara tsatstsafowa. Ta kalle shi, amma ta kasa kallon idanunsa. Yayi gyaran murya ya ce "Yaya maganarmu ne, har yanzu babu abin da ki ka yanke a kai? Kar malaminku ya shiga gonata, saboda shi kashe shi zan yi, ba iya korarsa zan yi ba. Ba na son alaƙar ki da shi" Cikin ƙwarin gwiwa ta ce "Wallahi ba zan yi abin da ka ke so ba, kuma ba ka isa ka hana Ubangiji ikonsa a kaina ba, ko da me ka ke taƙama kuwa" tayi maganar tana jin kamar zuciyarta za ta fito. Ya ɗan ɗage kafaɗarsa ya ce "Ke ko kewata ba ki yi ba ne? Yaushe rabon da na kawo miki ziyara, na je na yi jinyar abin da ki ka yi mini, na dawo da ƙarfina, mu ci gaba da fafatawa" A raunane ta ce "Wai dan Allah me na yi maka, me ka ke nema a wurina ne?" "Kin fi ni sani Nana" "Ni ba zan yi abin da ka ke so ba, ka nemi wani yayi maka, ni ba zan iya ba" "Ke aka bani, dan haka ke za ki yi aikin Nana, idan har ki ka amince, zan daina damun ki, zan ma iya barinki ki yi auren ki, amma idan ki ka ci gaba da gardama, wallahi wataran zaki iya tsintar kanki a gidan mahaukata, sai na haukata ki tuburan na hana kowa ya raɓe ki" Nana tana kuka ta ce "Ba zan yi abin da ka ce ba, ni ba zan yi shirka ba" "Ni ban ce ki yi shirka ba, bayar da magani za ki yi, wannan shi ne gado da sana'ar gidanku. Waɗannan litattafan duk tarihi ne, na waɗanda na yi wa aiki. Kakar mahaifinki 'yar  bori ce, kuma duk wanda aka haifa da irin burujin ki, sai ya yi wannan aikin, ba a samu wanda yake da irin burujin ba wato mai irin tauraronki ba, sai a kanki, abin da baki sani ba, na sadaukar da mahaifina domin kare ki, baban ki yana matuƙar ƙaunarki, a 'yan uwansa waɗanda ba sa shiri, an bayar da jininki a yi masa tsafin kuɗi da ke, muka yi yarjejeniya da aljanin da aka sadaukarwa da jininki, na bashi mahaifina da ya tsufa a matsayin bawa, ya rabu da ke, ke kuma yanzu ki ce ba zaki yi abin da na kare ki saboda shi ba? Ba zai yiwu ba" "Wallahi ƙarya ka ke yi, dama ai ku babu gaskiya a cikin zantukanku" "Na yadda, amma ni ba ƙarya nake yi miki ba, samun kyakyawar rayuwarki, yana hannunki Nana" yayi maganar yana kai hannunsa jikinta. Iya ƙarfinta take kai masa duka, tana son ta yi addu'a amma ta kasa sai gurnani, da surutun"Allah ya fika, ba zaka yi galaba a kaina ba, kuma Allah ya isa tsakanina da wadda ta gada mini wannan masifar ni ba mushrika ba ce ba". A hankali ta buɗe idonta, ta ganta tana ta kaiwa iska naushi tana surutu a fili. Shiru tayi tana waige-waige, ta duba shimfiɗar su Jamila ta ga basa nan, ta ga ƙofar ɗakinsu a rufe, wani irin zafi ta ji a wuyanta, ta kai hannu ta shafa, ta ga jini, a gurin da ya karce ta da farcen sa. Ta nufi ƙofar ɗakin da nufin ta buɗe, amma ta ji a rufe, ta jijjiga amma taƙi buɗuwa. Gari ya yi haske ba ta yi sallar asuba ba. "Suwaiba, suwaiba, mama dan Allah ku buɗe mini ƙofa, waye ya kulle ni, ban yi sallar asuba ba fa" shiru babu wanda ya amsa mata. "Nasiru wai ba kowa a gidan ne, dan Allah ku buɗe mini ƙofa, ban yi salla ba" Nasiru ne ya leƙo daga soro, ta jiyo muryar Mama daga ɗaki tana faɗin "Kai Nasiru ba ka na leƙowa ba, wallahi ka buɗe mata sai na ci ubanka" Nasiru ya ce "Mama wallahi ta dawo daidai, ba ki ji tana maganarta normal ba" "Wallahi ba zaka buɗe ta tana wannan tamɓmelen ba" A raunane Nana ta ce "Dan Allah mama salla zan yi fa" banza ta yi mata, Nana ta gaji ta koma ta nemi wuri ta zauna, ta na tuna mafarkin da ta yi. Sallamar baba ta ji a tsakar gida, da alama shi da wasu ne, saboda ba muryarsa kawai ta ji ba. "Ga ɗakin nan malam, wallahi bamu yi bacci ba, daga mu har maƙwabata, kwana ta yi tana iface-iface, dan kawai na yi mata faɗa kafin ta kwanta, da 'yan shekarun nan, abin nata ya lafa, amma kwanan nan, abin ya dawo tuburan dan kwananta biyu ma, bamu san in da ta tafi ba" "Kar ka damu, in sha Allah koma menene a jikinta, yau sai ya fita" Ita dai Nana ta zubawa ƙofa ido, tana jiran abin da zai faru. Aka buɗe ƙofar, ta ga Baba da wani malamin makarantar allo, da garadan almajirai mutum uku, da wata irin zabgegiyar bulala a hannun malamin, ba shiri ta miƙe tsaye tana zazzare ido ta fara ja da baya. Malamin ya kalli Nana ya ce "Zaka gane kurenka munafuki, yau sai ka fita daga jikinta, ya tunkaro Nana da wannan zabgegiyar bulala. A gigice ta ce "Baba, dan Allah lafiyata ƙalau dan Allah kar ka bari ya dake ni, wallahi ni ba aljani ba ce." Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM (AYSHERCOOL) YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002) P4 Baba ya tsaya daga bakin ƙofa, yana leƙowa. Kuka Nana ta fara yi, tana "Dan Allah kar ka dake ni, wallahi  a hayyacina nake nice" "Ƙarya ka ke yi, babu irin aljanin da ban yi karo da shi ba, duk wani siddabarunku na sani" yayi maganar yana riƙe kan Nana, ya fara tofa mata ayoyin Alkur'ani. Nana ta rasa me yakamata ta yi, ita dai ta san a hayyacinta take, ba ta da zaɓin da ya wuce, ta nutsu ta yi shiru, kar ta yi wani abu, ace aljanin ne. Sai dai jikinta yana ta tsuma, dan tsoron kar malam ya dake ta da bulalar nan. Sai dai ba ta tsira ba, babu tsammani ya zuba mata bulalar nan a jikinta, sai da ta gantsare ta kurma wani irin gigitaccen ihu, ta zube a ƙasa ta gigice. Yana karanta mata Alqur'ani ya ƙara zuba mata bulalar nan tamkar ta dukan doki. Ta yinƙura zata gudu, gardi ɗaya ya danƙo ta yayi ciki da ita, suka kewaye ta su na yi mata karatu, malam yana zuba mata bulala yana cewa "Zaka yi magana ko ba zaka yi ba?" Cikin kuka da ƙaraji ta ce "Ni ba aljani ba ce ba, nice a hayyacina nake, Baba dan Allah ka taimake ni ka ce ya daina duka na" sai jikin Baba yayi sanyi ya ce "Malam ɗayyabu, ba za ayi karatun nan babu duka ba, na ga kamar ita ake duka" Malam ɗayyabu ya ce "A'a kar ka damu, ka yi haƙuri ka je ka jira mu a waje, ai wannan aikina ne, ba ita ake duka ba, ka jira mu mu gama" ganin Baba zai tafi ya bar ta a cikin maza daga ita sai su, ya sanya ta ƙara fashewa da kuka, ga raɗaɗin bulala da fatarta take yi. Tana ji tana gani, malam ya saka almajiransa, suka rirriƙe ta, suna yi mata karatu, malam yana shafa mata man gelo a fuska, yana zuba mata wani ruwa a jikinta, ga kuma bulalar da yake ta zuba mata tana ihu. Babban abin da ya ɗaga mata hankali, bai wuce yadda a wayance ɗaya daga cikin yaran malam, yake goga mata jikinsa yana naniƙar ta ba, kuma yana sane. Tun tana kuka muryar ta na fita, sai da ta yi laƙwas ta kasa motsi gaba ɗaya, kukan ma ta kasa sai ajiyar zuciya da take saukewa, ji take da da makami a kusa da ita, sai ta illata wanda yayi mata rashin ɗa'ar nan, sai ta daina jin zafin bulalar, sai na baƙin cikin tozartar da ta yi. A banza wanda ba muharramanta ba sun daddaneta, babu ladduban ruƙiyya babu komai. Malam Ɗayyabu ya ce "Ina ga aljanin ya tafi, duk na ga gardamamme ne, bai yi magana ba, amma ya kau. Ku tashi muje zan bawa babanta magungunan da zata din ga yi" Nana tana daga kwance tana ji suka fita, hannayenta da suka banƙare suka riƙe kamar ba a jikinta suke ba, ga fatarta kamar an sakata a cikin wuta saboda raɗaɗi. Ta jima a kwance tana numfarfashi, daga baya ta ja jikinta a hankali, ta fita tsakar gida ta yi alwala, ta idar kenan Baba ya shigo da ƙullin baƙar leda a hannunsa, ya ce "Kin farfaɗo kenan?" Ta ɗaga kai ta kalli Baba, ta mayar da kanta ta sunkuyar, wani mugun haushin Baban ya kamata, ba ta ce masa uffan ba, ta shiga ɗakinsu. Tana kallon suwaiba tana raɓe raɓe, za ta shigo ɗakin, ba ta kula ta ba ta tayar da salla. Da ƙyar ta yi sallar, ga yunwa ga zafin duka. Ta zame rigar jikinta, tana haska jikin nata da mudubi, wani wurin har jini ne ya fita, ita kanta ta san ba ƙaramin dakuwa ta yi ba, a take wasu hawayen suka ci gaba da zubo mata. Hankalinta ya kai kan raunin da yake wuyanta, ta shafa wurin ta yi shiru tana tuna mafarkinta da tayi jiya. Jamila ta shigo ɗakin da sallama, Nana ta amsa a hankali. Cikin tausayawa ta ce "Sannu Nana, subhnallah haka duk suka ji miki ciwo?" Tayi maganar cikin tausayawa, ganin yadda fatarta tayi ruɗu-ruɗu. Ga buredi da ƙosai ki samu ki karya. Sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta karɓa ta ce "Na gode sosai" Tuni masu aiki suka fara aikin gyaran gidan su Nana. Jamila na shirin fita, mama ta tsare ta a ɗaki ta ce "Ke magana nake son mu yi da ke" "To mama, ina jinki" "Gidan maman khairat ɗin za ki tafi?" Jamila ta jinjina kai ta ce "Eh mana, idan ban je ba me zamu samu mu ci?" Mama ta gyara zamanta ta ce "Zuwa la'asar ki dawo, kin san ba a bori da sanyin jiki, duk da tana yi miki alheri, matar nan tana ƙaunar ki, amma dole mu bi ta wurin malamai, a ƙara yi mana aiki a kanta, yadda zata ƙara sakar mana hannu, ai ni tarewar matar nan alkhairi ne a gare mu" Jamila ta ce "To mama, duk yadda ki ka ce, amma duk da haka ai tana yi mini ƙoƙari sosai fa, kalli abubuwan da take yi mana" "Ke dalla can ba a zama haka, idan ta kama mijinta ma, ba sai a shiga a fita, ayi wadda za ayi ba" Jamila ta ce "Ahh haba mama, banda auren mijinta, butulci kenan ai" "To na ji, ita ɗin dai a ƙara mallake mana ita, ta ƙara sakar mana hannu, daga ita har mijin nata" Jamila ta gyara zaman gyalenta, ta ce "Shikenan, sai na dawo" "To Allah ya tsare yarinyar kirki, duk abin da ki ka ci dai ki tuna da ni, Allah ya yi albarka" "Amin" Jamila ta amsa ta nufi hanyar ficewa. Haka Suwaiba ma ta shirya, tana ta baza ƙamshi, cikin matsatsun kaya ta fice. Nana ta ɗan girgiza kai, su waɗanda suke shigar banza, su wuni jin kaɗe-kaɗe, ba Qur'ani ba azkar, aljanu ba su bi su sun takura musu ba, sai ita da take ƙoƙarin killace jikinta da ƙoƙarin yin addu'oi. Saurin katse tunanin ta yi, ta fara istigfari. Ta lallaɓa jikinta ta fita tsakar gida, ta fara kaye-kaye, ta tattara kwanukan wanke-wanke, ta koma gefe dan ta wanke. Dan bayan da larurar nan ta waiwayota a 'yan kwanakin nan, su na tsoron taɓa ta, da akan wanke-wanke sai a ci mata mutunci, har ma a haɗata da Baba ya yi mata nasa cin zarafin. Kafin yamma tuni an gama da gyaran katangar gidan su Nana, har ma an ci ƙarfin aikin, gyaran masan gidan da na rijiya, mama sai alfahari take tana hura hancin albarkacin 'yarta aka ci, aka yi wannan gyaran, dan da ta malalacin mai gidan ne, sai dai a zauna a haka. ***** "Wata guda kenan, haryanzu shiru babu wani labari, an yi addu'ar, an yi duk abin da yakamata, amma haryanzu babu wani ƙwaƙwƙwaran labari a kan ina ya tafi. Kuma babu wata shaida ko alama, ko saƙo da zai bayar da damar gano in da yake. Amma kai a naka binciken me ka gano?" Mutumin ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ni abin da na gani, ya yi nesa da gida sosai ma, yana kudu da nahiyar nan ma" Matar ta dubi mutumin cikin rashin fahimta ta ce "Me ka ke nufi?" "Ina nufin, koma a ina yake ya riga yayi nesa da gida sosai da sosai" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu mene ne abin yi? Ina mamakin dalilin da zai sanya, ya yi wannan shirmen, kawai ya tafi ya bar gida ba sanarwa ba komai?" Mutumin ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Allah masani" "To kai yanzu mene ne abin yi, dole dole ana buƙatar sa a gida, a wannan ƙadamin da ake ciki, banda tsabar wulaƙanci da baƙin ciki, kawai sai ya kama ya bar gida? Kawai ayi masa kiranye ko gidan uban wa ya je ya dawo" Da sauri ya ce "A'a, na so na bayar da wannan shawarar, amma na duba na ga akwai matsala idan aka yi masa kiranye za a samu matsala, idan bai dawo ba zai yi hauka tuburan, abin da yafi dai ayi tunanin wata mafitar" Tayi shiru tana tunani, daga bisani ta numfasa ta ce "Shikenan babu laifi, zaka iya tafiya " ya jinjina kai ya tashi ya fice. ***** Tun da Baba ya yarfa Nana, a wurin malam Auwal, take matuƙar jin nauyinsa, shi kuwa har cikin zuciyarsa ya ji ya aminta da abin da baba ya faɗa. Yana zaune a ofishin malamai, yana marking wani assignment da ya bayar, ya hango Nana ta shigo makaranta a makare, ya zuba ido ya ga wani mataki malam Nura zai ɗauka. Ya tattara hankalinsa a kansu, baya son a daki Nana, duk da ya san duk makarantar babu wanda bai san matsalarta ba. Tayi wiƙi wiƙi da ido, tana tsoron kar malam Nura ya daketa. Cikin ikon Allah, sai bai daketa ba, ya sanya ta ɗebo ruwa a rijiya ta zuzzuba a butocin alwala. Yayi ajiyar zuciya, ya ci gaba da makin ɗin sa, kawai zuciyarsa ta raya masa, idan kuma wani abu ya sameta a gaban rijiyar fa? Ba shiri ya tashi da hanzari ya tafi. Tana gaban rijiyar tana jan ruwa, yayi gyaran murya. Tana waiwayawa, ta ganshi, risunawa tayi tana gaishe shi, bai amsa ba, ya ƙarasa ya ce "Bani gugan ki tafi aji" ta zaro ido ta ce "Ya sayyadi Nura ne ya.... "Ni kuma na ce ki kawo ki taf... A ɗan raunane ta ce "Ya sa... Auwal ya ce "Za ki bani, ko sai na jefa ki a rijiyar" murmushi ta yi, tana kallon rijiyar ta ce "To bari na janyo gugan" tayo maganar tana janyo gugan daga rijiya. Ta juye ruwan, ta ajiye zata tafi ya ce "Nana" ta tsaya cak ta ce "Na'am" ya ce "Ya jikinki kuwa?" Take annurin fuskarta ya ɗauke, ta ce "Na ji sauƙi" Auwal ya ce "To Alhamdilillah, Allah ya ɗorar da lafiya, ki ci gaba da addu'a da azkar ɗinki" ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah" "Amm goge wannan abin na bakinki, sai ki tafi aji" kallonsa tayi, man leɓe ne kawai a bakinta, ba jambaki ba, shi aka hana sakawa. Ba tayi musu ba, ta goge. "Maza jeki, anjima zan zo gida in sha Allah" ji ta yi gabanta ya faɗi, amma ta kasa magana, ta ja ƙafafuwanta a hankali ta tafi aji. Auwal su na gaban su Nana sosai, lokacin da take yarinya sosai suka yi sauka, bayan sun yi sauka ya ci gaba da koyarwa, ko da ya tafi karatu ya dawo, ya ɗora da koyarwar a islamiyyar. Tunani take yi, kar dai malam Auwal, da gaske ya yadda da abin da Baba ya gaya masa. Ganin yau tana cikin hayyacinta, ya sanya 'yan ajinsu, suka sake da ita, tare suka zauna da ƙawarta Amira, a wuri ɗaya suka ɗauki karatu. Amira ta so tambayar Nana, ina ta tafi aka yi ta nemanta, amma ta fasa, saboda kar ta tsokanota ta burkice. Duk damuwar da Nana take ciki, da zarar ta fito makaranta, aka yi karatu, ta haɗu da ƙawayenta, sai damuwar ta ragu, sai ta kamo hanyar gida tukuna. Sai dai tana jin babu daɗi yadda wasu lokutan ƙawayen nata, suke gudunta, saboda larurarta. ***** "Yanzu kai Habu yaya zamu yi da wannan mutumin, kana ganin mutum kamar katako, baya gane komai, ni anya ma ba hauka ne yake damunsa ba?" Habu ya ce "Ashsha! Na gaya maka ɗan uwana ne, ba shi da cikakkiyar lafiya ne, magani nake nema masa, da ya warke shikenan" "Ikon Allah, Allah ya bashi lafiya, ga mutum har mutum a haka, amma ba ya gane komai, Allah ya bashi lafiya" Habu ya amsa da Amin, tare da kallon wurin da wanda suke maganar a kansa yake. Yana ta wasa da zobunan hannunsa, manya manyan azurfa, da kuma tagulla. A hankali ya saka hannunsa ya ɗago layar da take wuyansa, wadda ta sauka a cikinsa. Ya zuba mata ido yana jujjuyata. Cikin hanzari Habu ya matsa kusa da shi, ya ce "Ka gane mene ne wannan ɗin?" Ya ɗaga manyan idanunsa ya kalli Habu, amma bai yi magana ba. "To ka tuna wani abu ne? Waye ya baka ita?" Bai yi magana ba, ya tattare ta, ya zura ta a cikin rigarsa, ya kawar da kansa gefe daga kallon in da Habu yake. Habu yayi ajiyar zuciya, ƙasan zuciyar sa, yana fatan Allah ya taƙaita wannan al'amari, kamar kullum ƙara rikicewa yake yi, yanzu ba ya magana sai dole, kuma maganar ma galibi shirme ce kawai. ***** Abin da Baba yayi, tamkar ya share wa Auwal hanya wurin bayyana wa Nana abin da yake zuciyarsa game da ita, sai dai jikinta yayi matuƙar sanyi, da ya ce mata ya daɗe yana tausayinta, hakan ya sanya take tambayar kanta anya so ne? Ko dai tausayin ne kawai, duk da ya daɗe yana nuna mata alamun so. Gefe ga tsoro da fargabar abin da zai biyo baya yana damunta, dan kullum ta kwanta sai ta yi mummunan mafarki a kan malam Auwal, abubuwa na tashin hankali sun faru da shi. Ajiyar zuciya tayi, bayan kwashe dogon lokaci malam Auwal, na ta yi mata bayani, ba tare da ta ce "Uffan ba" "Nana" ya kira sunanta a hankali. "Na'am" ta amsa tana sake sunkuyar da kanta ƙasa. Ya ɗan marairaice ya ce "Ina ta zuba nikaɗai, ki ce wani abu mana" Har yanzun dai ba ta yi magana ba, saboda matsananciyar kunyarsa da take ji, banbarakwai take jin abin, wai yau malaminta ne kuma yake sonta, yake ta tsarata da kalamai na soyayya. Jin taƙi magana, ya sanya ya canza akalar hirar, zuwa ta karatu sai a lokacin ta saki jiki, tana amsa masa. Bai wani daɗe ba, ya ce "Bari na tafi, tun da dai ba za a kula ni ba, amma ki sani duk lokacin da na zo wurinki, a matsayin Muhammad Auwal na zo, ba ya sayyadinki ba" murmushi ta yi, ta cigaba da sunkuyar da kai. "Ungo saka mini lambar wayarki" Ta girgiza kai ta ce "Ai ba ni da waya" "Haba dai? Ke haryanzu baki girma ba kenan, to shikkenan za'a nemo waya in sha Allah, ki gaida Baba, ki sanar masa ina nan tafe, za a zo ayi magana in sha Allah" shiru Nana tayi, ba ta yi murna ba, ba ta ji haushi ba, dan ita ba ma ta tantance tana son sa ko a a ba, ita dai ta san ba dan tana jin tsoron abin da ka iya faruwa ba, da ta so ya aureta, tana matuƙar ƙaunar muryar malam Auwal mussaman idan yana karatun Alqur'ani. "Sai da safe, ki shiga gida, ki yi ta addu'a, idan kin yi azkar ɗin kwanciya bacci, ki yi ta nanata *Wa hifzan min kulli shaɗanin marid*" A hankali ta ce "In sha Allah, na gode sosai" Ya ce "Yauwwa ungo wann, kya sai farar ƙasa, dan naga yadda ki ke shanta a makaranta"  yayi maganar yana miƙa mata kuɗi. Ta ɗan kalle shi ta ce "Ya sayyadi ni ɗin?" "Au ƙarya na yi? Ba kya sha ne?" "Ina sha amma kaɗan" ta faɗa tana mamakin yadda saka mata idon da yake yi, har ya gane tana shan farar ƙasa. "Karɓi mana" yayi maganar yana sake miƙa mata. Ta girgiza kai ta ce "A'a ka bar shi, na gode" Haɗe rai yayi ya ce "Bana son jayayya, karɓi" jikinta na ɗan rawa ta haɗa hannayenta biyu, ta risuna ta karɓa ta ce "Na gode sosai, Allah ya ƙara buɗi" "Amin, shiga gida ina kallon ki" ta juya ta shiga gida, sannan ya juya ya tafi. ta juya a hankali ta shiga cikin gida tana murmushi. Abin har mamaki yake bata, wai ya sayyadi Auwal ne yake sonta, ganin abin take kamar almara. Duk da damuwar, abin da take fargabar faruwarsa, na ci gaba da addabar zuciyarta, amma wani sashin na zuciyarta, na kwantar mata da hankali, saboda a ganinta malam Auwal masanin addini ne, mai riƙo da addini dan haka babu abin da zai faru da shi. Tana sallama Baba ya tsare ta, ya ce "Yauwwa dama ke nake jira, tuntuni" Ta tsaya, tana sauraron abun da Baba zai ce. "Yaya maganar turowar? Ni fa ba na son a tsaya a ɓata lokaci a waje ana shashancin nan, ya kawo abin da Allah ya sa yake da shi, a ɗaura auren nan ki tafi, ko a rage mini wata wahalar" A yanzu dai Nana ba zata iya tuna, rabon da Baba ya mora mata wani abu ba, amma da an motsa sai ya yi ta mitar wahala ta yi masa yawa. Ta numfasa ta ce "Ya ce na ce maka, ka yi haƙuri, yana kan tattaunawa da magabatansa ne, in sha Allah za su zo" "Yauwwa ya dai fi. Na ce babu abin da ya baki ne? ƙanen ki sai kuka suke yi, sun ci abinci amma ba su ƙoshi ba, dama wanda Jamila ta zo da shi ne, suka karɓa suka cinye" Nana ta ce "Gashi ya bani" ta miƙa wa Baba kuɗin da ba ta san ma nawa ne ba. Ya saka hannu ya karɓa, ya duba naira dubu biyu ce. "To shi wannan saurayin naki kuma da haka ya zo, ka zo wurin budurwa ka ɓuge da bata dubu biyu kamar abin tsiya. Wancan saurayin naki Sule ya fi abin arziki. Ungo ga wata naira ɗari nan a aljihuna kya sai awara, wannan kuma ayi 'yan dabaru a ci abincin dare" Nana ta karɓi naira ɗarin ta ce "To Baba na gode sosai" Shigarta ɗaki ke da wuya, Suwaiba ta ja uban tsaki ta ce "Wallahi Nana ba zaki taɓa kan gado a rayuwar ki ba, yanzu kuɗin duk ki ka ɗauka ki ka ba wa Baba, alhalin kin wuni daga ke sai ruwan koko a cikinki, kuma dai duk wannan abin da ki ke yi, dan ya ce kin fimu ƙaunarsa, amma ba tausayinki yake yi ba, haryanzu kallon ki yake yi da laifin babar ku" Tabbas maganganun Suwaiba haka ne, amma har ga Allah tana tausayin mahaifin nasu da gaske, ba ta ƙaunar gori da wulaƙancin da mama take yi masa a kan riƙe gida, amma ita ta lura ko a jikin sa, hakan baya wani damun sa. "Nana, wai da gaske Auwwalun gidan mai koko ne yake zuwa wurinki? Wannan na ajin saukar, lokacin mu na zuwa islamiyya?" Cike da ƙwarin gwiwa Nana ta ce "Eh shi ne, meyafaru?" "Lallai Nana, me na sama ya ci balle ya jefowa na ƙasa? Ban da koyarwar nan fa, ban ce yana da wata sana'ar ba" "Suby arziki ai na Allah ne, kuma ni 'yar waye da zan ɗaga kai na ce sai wani?" Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce "Lallai kam" Nana kuwa a zuciyarta, tana addu'a Allah ya tabattar mata da alkhairi, ko a daji malam Auwal yake rayuwa, muddin zai rabata da rayuwar wannan gidan na su, ta samu farin ciki haka take fata. Ta cire hijjabin jikinta, ta saka wani ta fita tsakar gida ta tarar da mama su na ta dambarwa da Baba a kan dubu biyun da ta bayar. Kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ta ce "Baba dan Allah zan je bakin layi, idan maimuna tayi waina na sayo" Baba ya ce "To hanzarta, ba na son fitar daren nan, mussaman da ba lafiya ce da ke ba, ki hanzarta" ta nufi hanyar fita cikin takunta mai kama da na ƙasaita. Dai-dai lokacin da yayi sallama yake shigowa, ita kuma ta saka kai za ta fita, suka yi kiciɓis, gabanta ya yanke ya faɗi, ta ja da baya cikin tashin hankali da bugun zuciya mai tsanani. Ayshercool 08081012143 What's app only please. BUZU Aisha Adam (Ayshercool) YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/002) BRIGHT PENS 3rd batch arewabooks ayshercool7724 Watpad Ayshercool7724 08081012143 P5 Daga tsakar gida Baba ya ce "Muryar wa nake ji haka, kamar Gaddafi?" Kallon kallo Gaddafi suka yi da Nana daga bisani ya ce "Za ki matsa, ko sai na bi ta kan ki?" Jikinta na tsuma, ta ja da baya ta bashi hanya. Sai da ya ja tsaki, sannan ya shiga cikin gidan. "Kai kuwa Gaddafi ya da zuwan dare haka, kamar mara gaskiya?" Ya numfasa ya ce "Na tsaya wani uzuri ne a hanya, fatan na same ku lafiya?" Baba ya ce "Lafiya ƙalau, ya ikkon?" "Lafiya kalau, amma ya na ga gidan duk ya canza?" Baba ya kalli gidan ya e "Damunar nan, ruwan ƙarshe da aka yi ne, ya yi mana gyara, ya zubar mana da katanga, masai ta haɗe da rijiya... Cikin alfahari mama ta karɓe zancen, da bashi labarin cewa mijin uwar ɗakin Jamila ne, ya sanya aka gyara katangar gidan. Ko da Nana ta dawo, duk su na tsakar gida, sun kewaye Gaddafi, ana hira ya ajiye musu ledojin da ya zo da su. Ɗakinsu ta shiga ta zauna, ta cinye wainar fulawan, da bai fi loma huɗu ta yi ba, kuma babu in da ta je mata sam. Ƙasan zuciyarta, tana ta addu'a, Ubangiji Allah kar ya kawo abin da zai haɗata da Gaddafi, saboda karon su ba ya yi mata daɗi. Tana zaune Nasiru ya shigo ya kawo mata abin da aka raba aka bata, ta karɓa tayi godiya, ta ajiye a gefenta ta kwanta, ba tare da ta buɗe, ta ga ko mene ne ba. Sannu a hankali Malam Auwal yake nufo in da da take yana murmushi, ita ma murmushin take yi, tana jiran ƙarasowarsa, sai dai kafin ya ƙaraso in da take, ya bayyana cikin ainihin suffarsa mai tsayin gaske, ya shiga tsakiyarsu. A hankali ya din ga rage tsawonsa ya dawo daidai da tsawonsu. Danƙo malam Auwal yayi, ya zura hannunsa a cikinsa, yana zaro kayan cikinsa, yana watsarwa a ƙasa, ya ƙarasa har maƙogwaronsa, ya zura faratansa zai zaro maƙogwaronsa. A fusace Gaddafi ya fito tsakar gida yana bala'i ya ce "Wai wannan 'yar abu kazan uban, ba ta daina wannan iskancin ba dama?" Mama da suka fito tare da Baba daga ɗaki a burkice, suka yi burki a tsakar gida, su Suwaiba tuni sun yo waje daga ɗakin, cikin rige-rige. Nana kuwa na cikin ɗakin, tana ta uban kuka da gurnani, tana ihu iya ƙarfinta. "Gaskiya na fara gajiya da wannan bala'in, kullum sai bawa ya sanya haƙarƙarinsa a ƙasa ya kwanta, ya fara bacci, sannan ta fara ihu, gaskiya na fara gajiya." Mama ta yi maganar a ƙufule. Ɗakin Gaddafi ya nufa a fusace, Baba cewa yake "Gaddafi ka bi ta a hankali dan Allah, ka tofa mata abin da ya sauwwaƙa". Yana shiga ya tarar da ita, tamkar ana girgizata, yatsun ƙafafuwanta duk sun ƙandare, kamar kuturwa. Ƙafa ya saka yayi ball da ita, tamkar abar banza, yana zabga mata ashariya. Sai dai ba ta san yana yi ba, iya ƙarfinta take ƙoƙarin karanta addu'a a cikin baccin, amma ta kasa. Gaddafi ya danƙo ta, ya fito da ita tsakar gida, ya watsar da ita a wurin, ya ce "Ku wuce ku kwanta, idan ta gama iskancin ta tashi, ba wani aljanu iya shege ne kawai, kowa ya koma ɗaki ya yi kwanciyar sa". Jikin Baba ya yi sanyi ganin halin da Nana ke ciki, ya ce "Ba iya shege bane, na kira ma an yi mata karatu fa, kalli yadda jikinta yake yi" yayi maganar yana tsugunawa a kanta, duk da wannan abun na Nana shi kansa ya ishe shi. Wasu lokutan, sai yayi tunanin ko ƙarya take yi, amma idan ya yi la'akari da wasu abubuwan, sai ya ga normally mutum ba zai iya haka ba. Sanyin Asuba, da zafin cizon cinnaku ne, ya sanya Nana farkawa, daga nannauyan baccin da take yi, da babu komai a cikinsa ban da azaba da wahala. Ba ta damu da yadda ta ganta a tsakar gida ba, a tunaninta ita ta fito da kanta ta kwanta a gurin, dan yanzu ba ta mamakin yadda wasu abubuwan suke faruwa da ita. Alwala tayi ta shiga ɗakinsu, ta yi salla, sannan ta tashi su Suwaiba. Cike da farin ciki ta tashi, dan yau ɗin ta kama litinin ce, za a koma hutun makarantar boko. Domin tana koyarwa a wata private school, da Nanny ta nema a makarantar, sai malamar da take koyar da 'yan kindergarten ta koma garinsu, aka bata riƙon ajin, kasancewar tana da kwalin sakandare, sai dai ƙoƙarinta da sabon da tayi da yaran, ya sanya suka ƙyale ta, suke ba ta dubu bakwai a wata. Tana matuƙar jin daɗin, yadda take shiga cikin ƙananan yaran, su yi ta tsalle-tsalle da wasa tana koyar da su. Sai dai ta tsananta addu'a, Allah ya rufa mata asiri, kar ciwonta ya tashi a makarantar, ta cutar da 'yan yaran. Tana ta hanzari, ta gama abin da zata yi, ta shirya ta fita, Gaddafi ya shigo da buta a hannunsa, da alama sai a lokacin zai yi sallar asuba. Yana ganin Nana ya tsaya ya ce "Yauwwa ke Nana, dan abu ta kaza kazanki, idan ki ka kuma tashi cikin dare, ki ka hana mutane bacci kina yi mana ihu, sai na yi miki shegen duka, dan wallahi sai na karya ki na gaya miki. Mahaukaciyar banza maƙaryaciya" Duk da ba wannan ne karon farko, da ake kallon ƙaryar ciwon take yi ba, amma tana mamakin yadda za ace, tana wulaƙanta kanta a gaban mutane, ta hanyar yin wasu abubuwa tamkar mahaukaciya. Ba ta fatan ko maƙiyinta, Allah ya jarrabe shi da irin larurarta, ba dan haka ba da ta roƙi Allah ya jarrabi Gaddafi da jarrabawar da ya daɗe yana ƙaryata ta, a kai. Ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da gudanar da aikinta, ba ta damu da rashin samun abin da za ta karya ba, duk ta ga an yi abin karin kumallon, ta kammala shirinta ta fice. Nana akwai ƙoƙarin sammako, dan haka kusan hatta malaman, duk a makarantar suka tarar da ita, ta ji daɗin ganin yaran sosai, kamar yadda su ma suka ji daɗin ganinta, suke ta murna tamkar sun ga mahaifiyarsu. ***** Ƙurii ta yi masa da idanu, yadda yake ta jujjuya kofin kokon hannunsa, ya kalli yarinyar da take kwance a kan katifa ya ce "Ita wannan ba ta tashi rashin lafiya ba, sai da aka koma makaranta?" Babbar macen da take gefe tana karyawa ta ce "Dama rashin lafiya ana saka masa lokaci ne? Larura ce Allah ya kawo mata" ya jinjina kai ya ci gaba da cakalar abincin. "Wai Auwwalu me yake damunka ne?" Auwal ya numfasa ya ce "A ina?" "Ka ƙi cin abinci, sai jujjuya kofin kawai ka ke yi" ya jinjina kai ya ce "Mama magana na ke son yi, amma ban san yaya za ki kalli abin ba" Ta ajiye kofin hannunta, ta ce "Ko ma a yaya zan kalle shi, gaya mini ina sauraron ka" Ya tattara hankalinsa, cikin nutsuwarsa da kamala ya ce "Mama dama akwai wata yarinya ne, da nake zuwa wurinta, to shi ne mahaifinta ya ce in tura magabatana ayi magana" Tayi masa ƙuri da ido, sai da ya kammala, sannan ta ce "Me ka taka haka ne Auwwal, da zaka ɗaukko maganar aure? Fili ne fa kawai da kai a ƙasa, babu muhalli ba wata uwar da ka ke yi tun da ka kammala makaranta, bayan koyarwar nan sai 'yan kame-kame, abin da ka ke samu mu kanmu bai ishe mu ba, balle ka yayimo mana wata a bar maganar nan, kar ka sake tayar da ita yanzu maganar aure, ba nan ba ce" Auwwal yayi shiru, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ba ya son mutuncinsa ya zube a idon Nana, da mahaifinta. Har cikin ransa yake son ya taimaketa, mussaman da ya fuskanci ita sam ba ta da buri, kamar na sauran 'yan matan zamani. **** A wannan karon ma, Alhaji zailani ne a zaune a gaban Malam, fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Wanda aka samu ka ce duk ba su yi ba, abin ba zai yiwu da su ba, na rasa abin yi gaba ɗaya" "Alhajin Allah, ai ci gaba da duddubawa za ayi, za a samu dai ba za a sare ba, sai kuma ɗaya aikin da na baka, yaya ake ciki yau kwana ashirin da huɗu da fara shi ko?" Alhaji zailani ya ce "Eh, na kusa kammala shi wannan, kuma na fara ganin alamun nasara" Mutumin yayi dariya ya ce "In dai zaka yi biyayya, to za ka samu duniya yadda ka ke so, shi wanda ka ke maganar a kansa, shi ma ba a zaune yake bane ba, wani shu'umin aljani nake so ya yi mana aikin nan, zai iya dan yana da juriya da baƙin naci, amma fafur yaƙi" Alhaji zailani ya tattare babbar rigarsa ya ce "Dan Allah ka tambaye shi, ko me yake so zan yi masa, ba ni da burin da ya wuce, na ga bayan fatuhu, gaba ɗaya shi ya hana arzikina haɓaka, ba a faɗar sunan kowa sai nasa" "Ai duk wani tayi, da mu kan yi wa aljani, domin mu saka shi aiki yayi, na yi masa ya ce ba zai yi ba, akwai aikin da yake yi. Makirin aljani ne, idan na matsa masa zai iya ɓata mini wasu ayyukan, amma ka ci gaba da waɗanda na baka, sallar asuba da la'asar sai kwanakin da na ɗibar maka sun cika, sannan za ka ci gaba. Zan so ace kafin lokacin a samo yarinyar nan, aikin zai fi tafiya dai-dai " "In sha Allah, zan ci gaba da ƙoƙarin hakan, za a samo yarinyar duk in da take" "To shikkenan, kai nake sauraro" yayi maganar yana ci gaba da zazzana ƙasar gabansa. ***** Shigar Nana gida babu daɗewa, Baba ya ce mata, taje gidan da Jamila take zuwa, ta kira masa ita. Nana ta ji daɗin hakan, domin a zatonta Baba zai tsawatar wa Jamila ne, saboda yadda take zuwa ta shantake a gidan, ta wuni kamar a gidan ubanta. A ƙalla Nana tayi sallama ya kai sau huɗu, sannan aka amsa aka ce ta shiga. Jamila ta tarar a zaune a falo, tare da matar gidan maman khairat, sai kuma wata hamshaƙiyar mata a gefe, su na ta hira. Rashin dacewar hakan Nana ta gani, bai kamata ace Jamila tana tsakiyar su, su na ta uwar hira har tana sallama ba sa jin ta ba. Nana ta kalli maman khairat ta ce "Ina wuni?" Cikin sakin fuska ta ce "Lafiya ƙalau Nana, ke ba kya zuwa gidana, Jamila ce kawai 'yar ɗakina" Nana tayi murmushi, ta kalli matar da tun da ta shigo, ta ƙure ta da ido. Haka kurum gaban Nana ya faɗi, amma ta dake ta gaishe ta. Cikin ƙasaita ta amsa mata "Lafiya ƙalau 'yan mata ya ki ke?" Nana ba ta iya amsawa ba, jikinta ya hau rawa har bakinta ya nuna ta ce "Ja.jam..jamila Baba yana kiranki" tana faɗar haka kawai ta juya ta fice. Maman khairat ta ce "Jamsy, meya samu yayarki ne?" Cikin ko in kula ta ce "Wallahi ban sani ba, kin san tana da aljanu ba wuya ta burkice, kamar sun taɓa mata ƙwaƙwalwa ma" Maman khairat ta ce "Subhnallah, ƙwaƙwalwa kuma?" Jamila da ta tashi tana ɗaukar mayafinta ta ce "Wallahi Anty, to sai ta tashi cikin dare tana kurma ihu, ranan fa kwananta biyu ba ta gida, babu ma wanda ya san in da take ba, kullum cikin ciwo take" Matar da take gefe ta ce "Allah sarki, har ta bani tausayi, amma ta burge ni a nutse take masha Allah. Masu irin larurarta na buƙatar tausayawa da ja a jiki, kar ku ƙyamace ta, abin zai yi mata yawa" Jamila ta ce "Ai ko ba ka ƙyamace ta, ka yi gudun ceton ranka, duk da ba ta duka, amma idan ta fara ihu cikin dare da gurnani, layin nan ba wanda zai rintsa. Yanzu hatta ƙawayenta sun daina zuwa wurinta, saboda tsoron kar su kwasa" Jamila ta daɗe tana ba su labarin Nana, sannan ta tafi gida. Nana kuwa tun da ta baro gidan, jikinta yake wata irin tsuma, zuciyarta take bugawa, haka kurum jikinta ya din ga bata akwai wani abu na ba daidai ba, a tattare da gidan, ko kuma matar da ta tarar a gidan. "Hasbunallah wa ni'imal wakil. Wa hifzan min kulli shaɗanin marid " ta din ga maimaitawa cike da fatan Allah ya daidaita mata nutsuwarta. Gaza cigaba da addu'a ta yi, bayan da ta jiyo Baba yana tambayar Jamila, wai gidan uwar ɗakin nata, ba su gama abinci ba, yunwa yake ji, Gaddafi ya bayar da kuɗin cefane, amma an yi girki an hana shi. Wani malulun takaici, ya turnuƙe Nana, duk wani salo na zubar da kai, Baba ya iya shi, kuma hakan shi sam baya damunsa ko kaɗan. Tun da Gaddafi ya dawo, Nana take iya ƙoƙarinta, wurin ta kaucewa yin duk wani abu da zai haɗa su, amma hakan ba ya sanya wa, ta tsira daga zagi da cin mutuncinsa. Wannan bai dame ta ba, kamar yadda malam Auwal ya rage shiga harkar ta, zuwan ma ya daina yi gaba ɗaya, sosai abin yake damunta, zuciyarta na ta son gazgata cewar Aljanin da yake bibiyarta ne, ya shiga tsakaninsu amma wata zuciyar ta hana ta yadda da hakan, domin malam Auwal mutum ne mai addini, kuma ta yadda duk abin da ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, Aljani bai isa ya hana Ubangiji ikonsa ba. Duk da ya hanata yin kwalliya a lokacin zuwa makaranta, ko da kuwa man leɓe ne, dan haka yau ta saka jam baki, ko zata samu ya kula ta. Ta riga kowa zuwa a ajinsu,  ta ɗauki tsintsiya, ta fara share ajin, ta shimfiɗa musu tabarma, ta fito harabar makarantar ta share iya in da za ta iya. Tana shirin komawa ajinsu, Auwal ya shigo makarantar, jinkirta tafiya aji tayi, ta tsaya ya zo zai gifta ta, ta ce "Yaya Auwal ina wuni" wani zirr ya ji a jikinsa, yanayin yadda ta gaishe shin, ya ce "Lafiya ƙalau" ya wuce ta zuciyarsa cike da damuwa, kamar ya waiwayo ya kalleta, sai jikinsa ya ba shi: shi take kallo, dan haka ya fasa waiwayowa. Tana ɗan jima a wurin a tsaye, daga bisani ta nufi ajinsu, gwiwa a sanyaye tana tunanin meyafaru Auwwal ya canza lokaci guda. Tana ta kallon Alqur'aninta, tana son ta yi tilawa, amma zuciyarta na ta gargaɗinta, da tunatar da ita, halin da za ta iya shiga, muddin ta ce za ta karanta. Tana nan zaune, 'yan ajinsu, suka taru suka fara tilawa. Malam Auwal ne ya shigo yayi musu ƙarin Alqur'ani, sai dai da ta ɗaga kai, sai su yi ido huɗu da shi yana kallonta. Sai dai kafin ya kammala ƙarin, ƙafafuwanta sun riƙe gam, su na yi mata wani irin zugi kamar ana karyata. Gwargwadon ɗaga muryarsu a karatun, gwargwadon raɗaɗi da zugin da ƙafafun nata suke yi mata. Ba a tashi ba, ta ɗauki jakarta ta bar makarantar, da ƙyar ta nufi gida, tana taka ƙafafuwan nata da kyar. Ummi ta tarar a gidan, tare da Baba a tsakar gida. Amsa sallamar Nana suka yi, suka tattara hankalinsu a kanta. Ummi ta ce "Ummi ya dai na ga kina bin bango, kina tafiya a hankali?" Ummi ta kalli ƙafafuwanta ta ce "Ƙafafuwana ne suke yi mini ciwo, ba a tashi ba ma na taho gida" Baba yayi caraf ya ce "Haka dai, kullum cikin ciwo ki ke Nana, yau ƙafa in anjima ciwon kai, gobe kuma ciwon ciki, idan ki ka ƙoshi kuma sai ihu da kururuwa, ni wannan lamarin ciwon naki ya ishe ni wallahi. Can a dangin babarki ki ka kwaso wannan jarabar, ni dangina babu irin wannan" Ummi ta ce "Baba aka ce mahaifiyar Inna 'yar bori ce " "In ji uban wa? Ƙarya ne bayar da magani kawai tayi" Ummi ta yi murmushi, ta ce "Nana ƙaraso magana zamu yi" Nana ta so wucewa ɗaki, ta kwanta, duk da ta yi murnar zuwan Ummi gidan, amma soki burutsun da Baba ya fara ya sanya duk ta ji komai yayi mata zafi. To idan ubanta mahaifi ya gaza da larurarta ina ga miji, da za su haɗu rana tsaka su yi aure?" Ta zauna a hankali, tana jin yadda ƙafafuwan nata suke yi mata zugi. "Yaya magungunan da muka karɓo a wurin mutumin nan, kin yi su kuwa?" Nana ta jinjina kai alamar eh. "To yaya ki ka ji, akwai sauƙi?" Da ƙyar Nana ta ce "Eh akwai" Baba ya ce "Ina fa wani sauƙi, babu sauƙi ko kaɗan sai wurin Allah. Nan na ɗaukko malamin nan na almajiran gangare, yayi mata ruƙiyya wai aljanun suka ƙi magana, ba ki ga dukan da ta ci ba, sai da ta ba ni tausayi amma jiya i yau. Shiyasa duk na damu na aurar da ita, ko na huta. Ai ni wannan zancen da ki ka zo mini da shi, ba ƙaramin daɗi yayi mini ba, Allah ya tabattar da alkhairi tun da shi wancan yaƙi cewa komai". Cikin mamaki da rashin fahimta, Nana ta ce "Wane zancen ne?" Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM (Ayshercool) Arewabooks Ayshercool7724 Watpad Ayshercool7724 YOTA 002 BRIGHT PENS 3rd batch P6 Ummi ta yi murmushi, ta tura wa Nana wata leda gabanta. Nana ta kalli ledar, daga saman ledar take iya hango sabulun wanka da man shafawa. "Saleh ne ya aiko ni, tun ranar da ki ka je gidana, yake bibiyata shi fa son ki yake yi, auren ki zai yi" take Nana gabanta ya faɗi, damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarta ta ce "Anty Ummi, Saleh kuma?" Baba ya ce "Shi fa, ƙanin mijin Ummi ba yaron kirki" Jiki a sanyaye Nana ta ce "To Baba Auwwal ɗin fa, da ka ce masa ya turo?" Sai Baba ya hau faɗa ya ce "To ina na ganshi? Tun da na ce ya fito ɗin ya fito? Da a bawa bare ke, ba gara shi ba, tun da ya san larurar ki, idan aka yi auren ba ruwanmu da kayan ɗaki, ya ɗauke ki ya tafi da ke can Ikkon, wurin neman kuɗinsa ba, ɗaki ɗaya ya ishe ku kafin Allah ya yassare masa ku tara zuriya ba. Nana wannan iskokan duk aure ki ke buƙata da kin yi shikenan za su daina damun ki". Har Nana za ta yi shiru, amma ta kasa ta ce "Baba to idan iyayen malam Auwal ɗin suka turo fa?" Ummi ta ce "Nana wai ƙanin mijin nawa ne ba kya so ko kuwa?" Gaddafi da yake gefe, tun da ake maganar bai ce uffan ba, ya na ta faman gyara wata radio ya ce "Ai dama ke Ummi ke ce ki ke tausayin yarinyar nan, ita ba tausayin kanta take yi ba" Nana ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ya ma za ayi Ummi ta yi mata haka, ta ce zata haɗa ta da wani Saleh, mutumin da ba nutsuwa ce da shi ba, ga shaye-shaye da yake yi, askin da yake kansa kaɗai ya isa ya bayyana maka, abin da yake aikatawa a Lagos ɗin. Ummi ta taɓa ta ta ce "Nana kin yi shiru" "To me zan ce, Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi" Baba ya amsa da Amin. Nana ta miƙe ta nufi ɗakinsu, zuciyarta babu daɗi, addu'a take yi da fatan, Ubangiji Allah ya sa Auwal ya fito, amma Saleh kam, ba ta tunanin ko me za ayi mata, zata iya aurensa. Dan ko Suleiman da aka fasa aurensu ya fi dama dama a kan Saleh. Ji tayi jiri yana ɗibar ta, dan haka ta samu wuri ta kwanta, ta din ga yi wa Allah kirari, tana magiyar Allah ya daidaita ta da Auwwal ya fito ya turo iyayensa. Ummi ta leƙo tayi mata sallama, amma ta ganta a kwance, ta ce "Nana bacci da yammacin nan, ni dai na tafi, in sha Allah zai zo ku gaisa". Nana na jin Ummi, amma tayi banza da ita. Shikenan dan ana so ka yi aure, sai a ace ka auri mutumin banza. Ranar dai haka ta ƙarasa wunin ranar sukuku, dare ma yayi bacci ya ƙaurace wa idanunta, sai wani azababben ciwon kai da ya kama ta. A hankali ta din ga juyi a kan shimfiɗarta, amma babu bacci babu alamarsa, sai wannan ciwon kan, da take jin tamkar ana sara mata kan da gatari. A hankali kuma ta din ga jin, tamkar ana ɗaɗɗaureta da sarƙa, ambaton Allah take ƙoƙarin yi, amma ta kasa sai a zuciyarta. Ta saka hannun tana laluben hularta, domin ta saka a bakinta ta toshe, kar ta yi ihu cikin dare, ta hana mutane bacci. Ji ta yi an kira sunanta a tsakar gida, duk da ba ta san muryar ba, amma ta amsa a wahale. Jin an ci gaba da kiran sunanta, ya sanya ta yinƙura da ƙyar ta tashi, kanta babu ɗankwali, ta fito tsakar gida neman mai kiranta. Kallon tsakar gidan tayi, taga duhun ya ninka na dare, ba ta iya gane komai a tsakar gidan. Ta juya don ta koma cikin ɗaki, amma ta rasa hanya, saboda duhu ba ta ganin komai. Ji ta yi an ci gaba da kiran sunan ta, kawai ta hau tinkarar wurin da take jin ana kiranta. Gaddafi yana shagonsa a ƙofar gida, ya ji an buɗe gida, ya duba agogon wayarsa, ƙarfe biyu saura mintuna tara na dare. Tashi yayi ya leƙo, ya ga Nana ta fito, daga ita sai zani da vest kanta ko ɗan kwali babu. Sai da ya bari ta yi nisa, sannan ya fito ya bi bayanta, a zaton sa ko wani yawon banzan take, sai dai ga mamakinsa kawai tafiya take yi. Ganin tafiyar ta ƙi ƙarewa ya sanya ya ce "Ke dan ubanki ina za ki je a tsohon daren nan?" can kamar a wata duniyar, haka take jiyo muryarsa. Ba ta tsaya ba, kuma ba ta yi magana ba, ta cigaba da tafiya. Danƙo hannunta yayi, ya din ga  jan ta har zuwa gida, sai dai ba ta yi masa musu ba, bin sa kawai take yi, dan ta kasa tantance bacci take yi, ko kuma a zahiri ne. A tsakar gida ya hankaɗa ta, ta faɗi ƙasa, cikin ɗaga murya, yake tambayarta gidan uban wa za ta a wannan daren. Shiru tayi, ta ci gaba da laluben hanya tana ƙoƙarin tashi. Ya saka ƙafa ya hankaɗa ta ta sake bajewa a wurin. Wata 'yar ƙaramar ƙara ta saki, ta sake yinƙurawa za ta fita, wannan karon da azama ta yinƙura, sai dai tamkar ya samu namiji ɗan uwansa ya sake janyota yayi jifa da ita. A wannan karon, ba ta ji muryar komai, sai dai zafin buguwar da take yi. Baba ne ya fito daga ɗaki, yana tambayar Gaddafi ko lafiya. "Wannan mahaukaciyar yarinyar ce, ta buɗe gida ta fita a haka, na bi bayanta na kamo ta". Baba ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ni Wallahi lamarin nan na Nana ya ishe ni, kula Gaddafi za ta sake fita". Baba yayi maganar yana nuna masa Nana, da ta kwaso da gudu za ta nufi hanyar fita. Ƙafa Gaddafi ya saka mata, ta faɗi a wurin, amma cikin ƙarfin hali, ta sake tashi. Fizgo ta ya sake yi, ya wanka mata mari har sau biyu. Amma ko gezau ba ta yi ba. Baba ya ce "Gaddafi daina dukanta, ba fa ta hayyacinta, ba ta san me ka ke yi ba" "Wallahi ƙarya take yi, iskanci ne kawai, buɗe idonki ki kalle ni" dan sai a lokacin ya lura duk abin nan idanunta a rufe suke. "Gaddafi tofa mata abin da ya sauwwaƙa, ni tsorona kar ta fita tayi wani wurin ba a sani ba" "Ni me na iya da zan tofa mata?" Baba ya ce "Jeka kawai, bari na zauna na ga jikinta ya saki, kar ta sake fita. Dan Allah ko da bacci zai ɗauke ni, idan ka ji motsinta ta buɗe gidan, ka riƙota" "A'a wallahi ban yi alkawari ba, bacci zan yi" Baba ya ciro zanin mama da yake kan igiya, ya rufawa Nana da take baje a wurin kamar abin banza. ***** Washegari da safe, Nana sai haƙura ta yi da zuwa makaranta, saboda yadda jikinta yake yi mata ciwo, dan har targaɗe ta yi a hannu. Da safe Jamila take gaya mata abin da ya faru. Shiru Nana tayi ba ta iya cewa komai ba, ita kanta dan babu yadda za ta yi da ƙaddararta ne. Ƙugin da cikinta yake yi na yunwa bai dameta ba, ta nemi wuri kawai ta kwanta tana goge hawaye a ɓoye. ***** Fuskarta babu annuri take kallon mutumin, kamar ta fasa ihu ta ce "Wai kana nufin babu abin da ya sauya kenan?" "Ƙwarai kuwa, komai yana nan yadda yake" Ta sake tsuke fuska ta ce "Kuma kai babu wani abu da zaka iya yi a kai, gaskiya ba zan iya zuba ido, duk aikin da na yi tuƙuru, kuma ace ba zan mori wahalata ba, ba fa zai yiwu na zama a ƙarƙashin maƙiyana ba" Yayi murmushi ya ce "Bar ganin mu na kauce hanya, akwai abin da bamu isa mu yi wani abu a kai ba, ko kuma mu canza ba, ke za ki yi duk iya ƙoƙarin da za ki yi, sai mu ga ta ɓangarenmu me za mu iya yi. Amma taurarinta su na da haske sosai, duk wanda ya raɓe ta, za ta iya haska na su tauraron" Guntun tsaki matar ta ja, ta ce "Ka ga duba mini wani abun, ka bar maganar nan kawai" Can gida babu wanda ya matsa Nana ta fito ta yi aikin gida, ita ma kuma ba ta yi ba. Sai dai abin da ya ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta ji Baba su na magana da Mama da Gaddafi ba, wai akwai wani mai magani a tsanyawa, idan aljanu suka gagara, har kwantar da mutane yake yi, a tafi a bar shi, sai ya warke ya sallame shi. Babu tunanin komai ta ji Baba ya amince, za a kaita. Rasa abin yi ya sanyata fashewa da kuka. Sallamar Jamila ce ta sanya ta goge hawayenta. "Nana ya jikin?" "Da sauƙi" ta amsa a hankali. "Ungo wannan naki ne" tayi maganar tana miƙa mata leda. Ba ta karɓa ba ta ce "Mene ne wannan?" Jamila ta gyara zama ta ce "Kin tuna ranar da ki ka je kira na, a gidan maman khairat" Nana ta jinjina kai, ba tare da ta yi magana ba. "Kin tuna matar nan da ki ka gaisar a falo" "Na tuna" "To ita ce ta ce a baki, atamfa ce da turaruka, kin san 'yar kasuwa ce" "Meyasa za ta bani, ta sanni ne?" Jamila ta ce "A'a ranar da ki ka je ne, ta ga duk kin rikice da kuka gaisa, bayan kin tafi ta tambaye ni ko ta yi miki wani abin ne; na ce mata a'a baki da lafiya ne, shi ne ki ka bata tausayi". Ita dai Nana ta yi ƙuri da ido, tana kallon Jamila. "Nana ki karɓa mana, ba a mayar da hannun kyauta baya" ta saka hannu ta karɓa ta ce "To na gode sosai" ba dan ta so ta karɓa ɗin ba, ita abubuwan da suka dame ta a yanzu, sun hanata jin daɗin komai na duniya yanzu. Ji take yi tamkar ta kashe kanta ta huta kawai. Kullum cikin addu'a take, babu dare, babu rana, akan Ubangiji Allah ya bata lafiya, sai dai haryanzu Allah bai karɓa mata ba. Wasu lokutan har shagala take da roƙo lahirarta, saboda yadda take fatan lafiya ido rufe, sai dai idan ta tuna ta yi ta istigfari. ***** Ranar laraba, ta shirya ta tafi makarantar da take koyarwa, sai dai zuwanta ke da wuya, aka sanar mata da director yana son ganinta. Ta san a rina, dan haka ta tsananta addu'a, ta nufi ofishin nasa. Ta tarar da shi tare da wani babban mutum, zaune kirim a kan kujera. Ta gaida mutumin ba tare da ta kalle shi ba, ba kuma ta jira ya amsa ba, ta gaida director. Ɗan ƙaramin yaron da yake zaune a jikin mutumin, ya saukko daga jikinsa, cikin gwarancin yara, ya nufo Nana yana faɗin "Anti Nana" ɗagowa ta yi tana murmushi, dan gaba ɗaya da ta shigo, hankalinta ba a jikinta yake ba, dan haka ba ta lura da yaron ba ma. Ta buɗe hannayenta ta rungume shi. Director ya ce "Kin ga wannan shaƙuwar taki, da yaran nan ne, ya sanya haryanzu ban sallame ki ba daga makarantar nan. Babu wadda take iya ɗaukar rigimarsu kamar ki, amma ki na ta wasa da damarki. Kwata-kwata yaushe aka dawo makarantar da har za ki yi fashin kwana biyu, ba tare da kin sanar da hukumar makaranta ba?" Cikin nutsuwarta da kamala ta ce "Dan Allah sir ka yi haƙuri, ba ni da lafiya ne, ba a son raina na yi fashi ba" A ƙule ya ce "Wai wace irin rashin lafiya ce haka, da kullum ba ki da lafiya, idan ba zaki iya ba, ki ajiye aikin mana dole ne?" Mutumin da yake zaune ya ce "A'a ba za ayi haka ba, ayi mata uzuri musamman duba da yaranmu suke ƙaunarta. Ka ga ba zuwa makarantar nan nake yi ba, na fi shekara rabon da na zo, amma na san Anty Nana a bakin Muhsin, duk abin da yake yi, idan aka ce za a gaya mata sai ya daina. Ina nema mata afuwa dan Allah" Director ya ce "Alhaji ba zaka gane ciwon kan da yarinyar nan take bamu ba. She's very hardworking lady, yarinya ce mai ƙoƙari da juriya, amma wannan fashin nata, kullum cikin ciwo shi ne yake ɓata mini rai wallahi" Mutumin ya kalli Nana ya ce "Anty mene ne rashin lafiyar taki ne?" Nana tayi shiru ta rasa abin cewa. Bai damu ya sake tambayarta ba ya ce "Kuma ki na zuwa asibiti?" Ta jinjina kai alamar eh. "Allah ya sarki, to Allah ya baki lafiya yanzu dai ki tashi ki je, na roƙa miki afuwa " Nana ta sake risunawa cikin girmamawa ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Director ya ce "Tashi ki tafi" ta tashi jiki a sanyaye, hannunta riƙw da na Muhsin, da bakinsa yaƙi rufuwa yana ɗagawa babansa hannu. Duk da ranta ba ya son faɗan da ake yi mata, yanzun ma ba ta ji daɗin faɗan ba, amma da tuna laifinta ne, haka nan ta haƙura, ta danne damuwarta ta shiga cikin ɗalibanta, tare da ƙoƙarin samarwa kanta nishaɗi da nutsuwa tare da yaran. Amma sai ya zamana yaƙe kawai take yi, ƙasan zuciyarta tamkar ta fasa ihu, ga batun kaita gidan mai magani, duk da ba a kuma zancen ba, ga kuma maganar Saleh, ga malam Auwal ya juya mata baya baki ɗaya. Da ta dawo daga makaranta, ta yi sa'a, ta tarar da wata guntuwar shinkafa, an ajiye mata, sai dai ko maggi babu, ta barbaɗa gishiri, ta ci ta tafi islamiyya. Duk da ta san tayi sammako da yawa, hakan bai dame ta ba, saboda zaman gidan na su ne ba ta so, bata ƙaunar duk wani abu da zai ƙara dagula mata lissafi. Kamar yadda ta saba, ta share duk wuraren da taga zata iya sharewa, ta shiga wurin ajiye tabarmi, ta hangi Auwal a cikin ofishin malamai, yana duba wasu litattafai. Ɗauke kanta ta yi, kamar ba ta ganshi ba, ta shiga ta ɗaukko tabarmar 'yan ajinsu, ta fito. Ba ta sanya ran zai kula ta ba, dan sati guda kenan, ko gaishe shi ta yi, sama-sama yake amsawa. "Nana" ya kira sunanta ba tare da tayi tsammanin haka ba, ta waiwaya tare da tunanin ko ba shi ba ne ya kirata. Amma ta ga yana kallonta, tabbacin shi ne yake kiranta. Sharewa tayi, ta fice ta tafi ajinsu. Tana tsaka da shimfiɗar tabarmin ya shigo ajin, ya ce "Nana, ki na ji ina kiran ki ki ka yi share ni, Yaushe ki ka zama haka?" Ta miƙe sosai tana kallonsa, ta haɗiye wani abu mai ɗaci da ya tsaya mata a maƙogwaronta. "Me yasa ba ka yi wa baba bayani ba, kuma ka hanani na yi masa; cewar kai malamina ne ba wanda yake so na da aure ba? Dama ka ce tausayina ka ke ji, ni kuma kasancewar wanda yake ruwa, ko takobi aka miƙa masa kamawa zai yi, na kawar da tunanin komai, na fara sonka ina tunanin ko yaya zan samu afuwa. Amma sai halayenka suka sha banban da abin da ka ke koya mana. Ina ma baka ce ana so na ba, na ci gaba da kallonka a matsayin malamina mai tausayina. Jiki a sanyaye cike da borin kunya ya ce "Ki yi haƙuri Nana, na san ban kyauta miki ba, babu yadda zan yi ne, matsala aka samu, na rasa ta yadda zan yi miki bayani. Ina ta ƙoƙarin shawo kan matsalar ne, amma ban ce ina sonki dan na yaudareki ba, ko na yi wa mahaifinki wasa da hankali ba". Shiru ta yi masa, ta ci gaba da gyara tabarmin, dan ba ta ma san meyakamata ta sake ce masa ba. "Nana, ki ɗan bani lokaci kaɗan, ina daf da shawo kan matsalar" "Tom" ta faɗa a taƙaice, ba tare da ta ko kalle shi ba. Bai taɓa zaton Nana tana fushi har haka ba. Ya kalli yadda take ta jan tabarmin, ba tare da wani dalili ba, ya durƙusa a kusa da ita ya ce "Kalli ki ga" ta ɗaga kai ta kalle shi. "Tabarmar ta shimfiɗu haka, ba ita ta yi miki laifin ba, ni ne amma ki yi haƙuri" Ta kalle shi da idanunta, masu kama da za ta yi kuka, har za ta yi magana, sai kuma ta haɗiye ta fasa. "Kin haƙura?" Yayi maganar yana tsareta da idanunsa shi ma. Murmushi ta yi, ba tare da ta shiryawa hakan ba. Shi ma murmushin yayi mata ya ce "Barakallahu fik, ki ci gaba da yi mana addu'a, in sha Allah komai zai daidaita amaryata". Sunkuyar da kai ta yi, bakinta ya kasa rufuwa saboda murmushi. "Ya jikinki, ina fatan ki na kula da duk adduo'in da nake baki" Ta jinjina kai ta ce "Eh, ina yi" "Yauwwa ki ci gaba da kula, Ubangiji Allah ya baki ingantacciyar lafiya" "Amin na gode sosai" ya fice bar ajin. A hankali ta ji zuciyarta ta yi sanyi, daga zunzurutun damuwar da take ciki. Aka yi karatun Alqur'ani da ita lafiya ƙalau, sai da lokacin fita salla yayi, ta tashi abu ya gagara ta ji gaba ɗaya tamkar an saka sarƙoƙi, an nannaɗe mata ƙafafuwanta. Duk wani ƙoƙari da za ta yi domin ta tashi abu ya gagara, kawai ta fashe da kuka. Amira ta dubeta ta ce "Nana, menene ki tashi an tafi salla". Cikin kuka ta ce "Amira na kasa tashi ƙafata ciwo take yi mini, kamar ana karya ni" Ganin yadda Nana take kuka, sai jikin Amira yayi sanyi, a baya da yawa ana zaton Nana ƙarya take abubuwan da take yi, amma yanayin da take ciki yanzu dole mutum ya tausaya mata. Amira ta fita ta kirawo malam Auwal, suka dawo tare, ko da suka dawo suka tarar ta mimmiƙe tamkar gawar da ta jima da rasuwa. Cike da tausayawa shi ma ya tsuguna a kanta, ya kalli bakinta na ta fitar da kumfa, yatsunta daga na hannu har na ƙafa, sun lanƙwashe. Ayoyin suratul jinn, ya fara karantawa yana tofa mata, ya idar ya koma ayoyi biyar ɗin farko na suratul baƙara, ya ɗan jima yana yi mata karatu kafin jikinta yayi saki, sai dai ba ta tashi ba. Sosai tausayin Nana yake ratsa Auwal, Nana tana buƙatar kulawa ta musamman daga namiji mai addini, da haƙurin gaske, idan Allah ya taimake ta tayi aure, tasirin larurarta zai ragu idsn aka dagewa addu'a da kulawa sosai. Kwanakin nan jikinta ya tsananta, kusan kullum ba ta da lafiya. Ganin ta yi bacci, ya sanya ya cewa Amira ta tafi wurin salla, su ƙyaleta ta huta. Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM (AYSHERCOOL) YOTA(002 7 Wunin yau Nana, a ɗaki tayi shi, ta ɗauki azumi tana tawasalli da azumin da fatan Ubangiji Allah yaye mata larurar da take damunta ya ba ta lafiya. Saboda ita kanta yanzu lamarin yana matuƙar ba ta tsoro. A tsakar gida take ji yo radion mama, wani likita yana ta bayani, a kan cutar depression cutar damuwa, anxiety disorder cutar fargaba, shaye-shaye da farfaɗiya. Shiru tayi, tana nazarin alamomin cututtukan baki ɗaya, cike da fatan ta gano wanne ne yake damun ta a ciki. Sai ta ji tana da wasu daga cikin alamomin anxiety disorder, wato cutar fargaba, sai kuma ta ga wasu alamomin na ciwon damuwa ne yake damunta. Tabbas akwai abubuwa da dama na ƙaluble daa suke binne a cikin zuciyarta, wanda galibi marasa daɗi ne. Ba ta tunanin akwai wani abu na farinciki da ya faru da ita, da za ta ce ba zata manta ba, gaba ɗaya rayuwarta a kan siraɗin ƙaddara take. Sai dai ta na godewa Ubangiji, da ya bar ta da imaninta. Haka kurum sai ta ɗan ji salama a ranta, ta fara saka ran larurarta ta asibiti ce, idan ta je za ta samu mafita. Tayi ajiyar zuciya, ta lumshe idsnaunta, kawai ta ji an bushe da dariya. Ta buɗe idonta da sauri, ta waiwaya ba ta ga kowa ba. A take ta tuna da ire-iren mafarke-mafareken da take yi, da yadda mutumin nan yake tilasta  mata yarda da sharaɗinsa na sai ta bayar da magani. Ta tuna ire-iren gane-ganen da take yi, a zahiri kuma ba ta ji likitan ya yi bayanin makamantan wannan alamomin a cikin bayanin cututtukan da ya yi ba, a take ta karaya ciwon dai da ba ta son ace shi ne da ita ya tabbata shi ɗin ne dai, ko ta na so ko ba ta so aljanu ne  suke damunta. Ko ta yi yinƙurin kawar da tunanin, sai ta tuna yadda take ganin mutumin nan a mafarki, da irin maganganun da suke yi da shi. Kawai ta fashe  da kuka, babu wanda zai iya gane halin da take ciki, sai wanda ya tsinci kansa a halin da take ciki, dan wasu sun gaza yadda ciwo ne Allah ya jarrabe ta, kawai ta ɗorawa kanta ne, dan samun attention ɗin mutane wato hysteria a turance. Ta tashi ta ɗaukko bagcon kayanta, ta din ga ciro magungunaa, kala-kala da ake ba ta, da sunan maganin aljanu, leda-leda ta din ga fito da su. Ta gama tattare su wuri guda, ta fita tsakar gida ta din ga tura su a murhu ɗaya bayan ɗaya. A take gidan ya kaure da ƙauri da hayaƙi mara daɗin shaƙa. Mama ce ta fito tana faɗa "Ƙaurin meye haka mara daɗi kamar gidan 'yan bori?" Ta tarar da Nana a bakin murhun ta na ci gaba da ƙona kayan. "Ke meye haka? Uban me ki ke tura mini a murhu?" Nana ta ɗago ta kalleta, ta yi shiru ta ci gaba da abin da take yi. Tari mama ta hau yi, ta ce "Idan ma uwarki ce ta aiko miki da wata tsiyar ki ke babbaka mini, to baƙar aniyarku ta koma kanku, dan na fi ƙarfin ku daga ke har ita" gaba ɗaya hankalin Nana ba ya kan Mama, zancen zuci kawai take yi, tana kallon yadda kayan ke babbakewa a cikin murhu. Ganin Nana ta mayar da ita mahaukaciyar ƙarfi da yaji, ya sanya ta koma gefe ta zauna, ta na cigaba da ƙananan maganganu. Ko da Nana ta yi buɗa baki, kunun tsamiya kawai ta samu ta sha, hakan bai dame ta ba, ta mayar da hankali sosai wurin roƙon Allah samun lafiya, da miji na gari. Yaro ne yayi sallama, ya ce ana kiran Nana a waje. Jamila ce ta ce masa ya ce tana zuwa. Nana ta fito ƙasan zuciyar ta cike da murnar, malam Auwal ya dawo, akwai yiwuwar ya fito ayi auren, tun da ya dawo. Sai dai tayi turus, da hasken fitilar wutar lantarki ya haske mata fuskar Saleh, ƙanin mijin Ummi. Wani takaici ne ya kama ta, amma ta dake ta ƙarasa fuskarta babu yabo babu fallasa. "Hajiya Nana, barka da fitowa ya ki ke ya gida?" "Lafiya ƙalau, ya su Anty Ummi?" Saleh ya ce "Duk su na nan lafiya" ya ɗan yi shiru, sannan ya numfasa ya ce "Na san dai Ummi, ta yi miki bayanin komai ko?" Nana ta kalle shi ta ce "Wane bayanin kenan?" Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ba ta kawo miki kaya ba, ta ce in ji ni?" "Ohh na tuna, na gode sosai da sosai" Yayi murmushi ya ce "Ai ba wani abu, ta ce Baba ya ce ba sai na wahalar da kaina ba ma, na yi miki kayan ɗaki kawai ba sai an yi lefe ba. Kin ga faɗuwa ta zo daidai da zama, sai mu tafi can lagos tare wurin sana'ata, akwai ɗakin da nake haya komai akwai a ciki na buƙata" Nana ta sake kallonsa ta ce "Baban bai gaya maka ba ni da cikakkiyar lafiya ba?" Ya gyara tsayuwarsa ya matsa kusa da ita ya ce "Ai duk wannan ba wani abu ba ne ba, muddin za a samu fahimtar juna da ni da ke. Wallahi a matse nake ne Nana, ni ko wannan juma'ar ta jibi, a ɗaura ki tare a gidanmu kan na gama shirin tafiyarmu ikko" yayi maganar cikin numfarfashin rashin gaskiya, yana ƙoƙarin ya kai hannunsa jikinta. Ja da baya ta yi, cike da takaici sai dai kafin ta yi magana, ta hango Auwal a tsaye, hannunsa riƙe da leda ya tsaya sak yana kallonsu. Ta kalli Saleh da yake ƙoƙarin kuma matsowa, ta kalli in da Auwal yake, kawai ta juya ta shiga gida, gabanta yana faɗuwa, ba ta san ma me yakamata ta yi ba. Kawai ta shiga ɗaki ta kwanta. A waje kuwa Gaddafi ne ya tarar da Saleh, suka gaisa Gaddafi ya ce "Mutumina yau kai ne a gidan namu?" Saleh ya ce "Wallahi kuwa, na zo wurin Nana, kuma mu na cikin magana ta shige gida, ba ta ce mini komai ba" "Ita Nanan?" "Eh wallahi, ina so mu fahimci juna da ni da ita, ayi a wuce wurin kawai" "Ka kwantar da hankalinka, kamar ka aureta ka gama ne, har wani zaɓi take da shi, kai da zaka taimaka mata. Ka manta da ita kawai ka turo a kawo kuɗi" Saleh ya washe baki ya ce "Allah mutumina" "To me za a jira, kawai ayi abin da ya dace" Nan ya tsaya suka ci gaba da hira, saboda Gaddafi ma a Lagos yake neman kuɗi, kuma su na haɗuwa da Saleh sosai. Sai da suka gama hirar, sannan suka yi sallama, Gaddafi ya shiga cikin gidan, ya dira wa Nana bala'i da cin mutunci a tsakar gida. " 'yar gidan uban waye ke, da za ki hurawa mutane hanci, ke da da za a taimakawa, mahaukaciyar banza da ta wofi. Ki na yawo a kwararo ki na wannan tamɓelen ki hana jama'a bacci, kowa ya san mahaukaciya ce ke a unguwar nan, kin samu ana sonki, amma ki bujire. To wallahi ba ki isa ba dole ki auri Saleh, ki fita ki bar gidan nan ƙila ma rashin aure ne ya sanya ki ke wannan haukan " Nana ta toshe kunnneta, saboda zafi da tururin da zuciyarta take yi, ji take tamkar ta ɗura masa ashariya, ta rama cin mutuncin da yake yi mata, amma ta din ga maimaita Innalillahi wa innalillahi raji'un. Baba ne yayi sallama, ya tarar da Gaddafi yana bala'i, da ya tambaye shi ba'asi, ya ji da Nana yake, sai ya karɓa ya ɗora shi ma. Nana ta rasa wannan jaraba, babu wanda aka tsangwama yayi aure a gidan sai ita, saboda su ga babarsu a gidan, ita kuma ga rashin uwa, ga larura ga shi duk wata hanya da za ta samu mahaifiyarta ko a waya, Baba ya datseta, har yana nema ya yi mat baki. 'meye na damuwa ma, matar da ko in da ku ke ba ta zuwa, ta ga halin da ku ke ciki, balle ki gaya mata halin da ki ke ciki, ta saka ki a addu'a, ko kuma t nema miki magani' wata zuciyar tayi mata tunin, abin da ba ta so, domin in dai tana ire-iren waɗannan tunanin, ta na jin zafin mahaifiyarta a ranta. "Ke Nana, zo ga waya Atine za ta yi magana dake" maganar Baba ta dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula. Gabanta ne ya faɗi, wata sabuwa in ji 'yan caca, ba ta ƙaunar duk abin da zai haɗata da matar nan a rayuwarta. Ba tare da ta amsa ba, ta tashi ta fita. Baba ya miƙa mata waya, ta karɓa hannunta na rawa ta saka a kunneta, ta yi shiru. "Ke ma'u ki na ji na?" "Eh" ta amsa a cunkushe. "Dan ubanki sai ki yi mini shiru, ko gaishe ni ba za ki yi ba, har kya yi wa mutane ƙaryar iskancin aljanu, mu da a ka yi gadon bori a gidanmu. Nana ta yi shiru, tana mamkin yadda jahilci, ya sanya yaya Atine alfahari da harkar shirka, da shi ne musababbin gadar mata da bala'i, kamar yadda mutumin da take mafarki da shi, yake iƙrari. "Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, ranar asabar ki yi kuɗin mota, ki taho gidana, akwai gidan wani mai magani da zan kai ki. A baki maganin aljanu da na farin jini, aure dole ki yi shi babu fashi, ko shi wanda ba kya so ɗin ko wani daban. Ke wannan baƙin jinin kamar an jiƙa hatimin jaɓa an baki, daga nonon babarki ki ka shawo shi. Mu zuriyarmu farin jini ne da su wallahi, babu mai nauyin jini" "Yaya atine, idan ni a nonon uwata na sha, su suwaiba a naki nonon suka sha? Tun da Uwar tawa ba ta nan, menene na sakota a zancen ki, koma wani bala'in ne ya same ni, ba duk a dalilin shirka da iyayenku suka yi ba ne, da har ki ke alfahari da ita" ita kanta Nana ba ta san yaya aka yi, suke fita daga bakinta ba, saboda yadda ranta ya ɓaci zuciyarta take tafasa fiye da kima. "Ma'u ni ki ke gaya wa haka?" Gaddafi ne ya yi kan Nana, amma Baba ya tare shi, ya ce "Rabu da ita, ka na taɓa ta babu lallai, mu yi bacci mai daɗi a gidan nan, wataƙila ma ba ita ba ce ba, ƙyale ta" Ta ajiye wa Baba wayarsa, ta koma ɗaki. **** Cike da damuwa Auwwal ya koma gida, 'yar tsarabar da ya yi wa Nana, ya bawa ƙannensa, wani irin kishi ya addabi zuciyarsa, sai dai kuma yanayin kallon da ya ga tana yi wa wanda suke tsayen ne, bai gama gane kansa ba. "Auwwalu" Umma da ta gama kasa gurasa da naman gabanta. Ya kalleta ya amsa da "Na'am Umma" "Magana nake son mu yi da kai ta fahimtar juna. A matsayina na mahaifiyarka". Ya tattara mata hankalinsa baki ɗaya cike da ladabi. "Ka zo mini da maganar aure, na ce maka ka dakata, ba yanzu ba tukuna. Karo na farko abin da ba ka taɓa yi mini ba, ka kai ƙarata wurin kawunka ƙanin mahaifinku. Ya zo har gidan nan baka nan, mun yi magana ta fahimta da shi sosai na kuma fahimce shi, har ya gaya mini ka gaya masa sunan yarinyar da gidan mahaifinta. Na ce masa to ya ɗan saurare ni. Na zo da kaina na saka ayi mini bincike, shi ma kawun naka na saka yayi ta nasa ɓangaren. To magana ta domin Allah ba zan yadda ka auri wannan yarinyar ba, ashe ita ce wadda ka ke bani labari mara lafiyar nan. 'yan unguwarsu sun tabattar da ba ta da wata matsala sai wannan iskokai, kuma ana kyautata zaton kakaninta 'yan bori ne, ni kuma gaskiya ba zan yadda a ɓatawa tsatsonmu suna ba, a sa a gada wa zuriya masifa ba. Dan haka mun gama magana da shi, shi ma zai neme ka ya kuma yi maka magana. Ya ce mini ya saka wani abokinsa ya yi naka hanyar tafiya Qatar ko Allah ya sa a dace da kyakyawar sana'a. Idan Allah ya sa ka tsaya da ƙafarka ka samu wata yarinyar mai kyakyawar nasaba da lafiya ka aura. Ba cin mutunci ba amma an ce yaran gidan ma galibi su ne suke ciyar da kansu, uban ba ya sana'ar komai, yarinya budurwa kuwa duk in da aka bari ta ciyar da kanta, ai an samu matsala. Dan haka ka cire ta daga zuciyarka" da ƙyar Auwwal ya haɗiye wani abu mai zafi da ya tsaya masa. Mama tana da gaskiya amma idan aka ce waɗannan abubuwan kacokan za a duba a ɗora mata laifi shikenan ba za a aure ta ba kenan? Nan aka zo neman auren ƙamwarsa aka ce ba za a aureta ba, 'yar mace ce, aka yi ta ɗauki ba daɗi kafin auren ya yiwu, amma Umma ta manta da wannan, ita ma tana hango aibun da ba ya cikin jerin abin da zai iya hana aure a shari'a a yanzu". "Auwalu ka yi shiru, ko baka yarda ba zaka bujire ne?" "A'a subhnallah, na amince Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi, amma Umma, da a bar maganar Qatar ɗin nan, idan Nana ce na haƙura amma.. Ta tari numfashinsa ta ce "Ai mun gama yanke hukunci, biyayya ce kawai taka Auwal" Ya risuna ya ce "Shikenan Allah ya wuce mana gaba" ya tashi jikinsa a sanyaye ya bar ɗakin Umma, ya koma shagonsa. Washegari da safe, ta je gaida Baba, bayan ta shirya za ta tafi wurin aiki, amma ya ƙi amsawa, ya ma tashi ya bar wurin. Cikin damuwa ta koma ɗakinsu, ta ɗauki jakarta, ta kalli Jamila, da ke ta danna waya ta ce "Jamila, dan Allah ko kin san laifin da na yi wa Baba, ya ƙi amsa gaisuwata?" Jamila ta ɗago ta ce "Lallai Nana, jiya da ki ka gaggaya masa magana, da shi da yaya Atine, ko har kin manta?" Shiru Nana ta yi, ta fara jin wata ƙara a cikin kanta, ta jingina da bango ta dafe kanta ta ce  "Subhnallah" Jamila ta tashi zumbur, ta ja da baya ta ce "Ya dai?" "Wallahi Jamila, ban san ya aka yi hakan ta faru ba, da na tashi daga bacci, tunanin abin nake yi kamar mafarki ba a gaske ya faru ba, gaba ɗaya na kasa gane kan rayuwata, amma shikenan" kawai ta fita daga ɗakin, ta saka takalmanta ta fice. A ƙofar makarantar, danƙareriyar motar ta yi parking, gilasanta baƙaƙe ne ƙirin, ba a ganin wanda yake cikin motar. Yaro ne ɗan shekaru uku, ya fito daga cikin motar, ya zura hannunsa ya ɗaukko akwatin abincinsa, bai tsaya rufe motar ba ya nufo wurin da Nana take tsaye, yana washe baki cike da murna. Sakin fuska ta yi, ta ƙarasa ta ɗauke shi, ta ɗaga shi tana murmushi. Sai dai yayi shiru yana kallonta, ganin alamun damuwa a fuskarta. Ta shiga da shi cikin makarantar, ta fara tafiya da shi aji, in da take ajiyewa ɗaliban nata, kwanukan abincinsu, ta juyo za ta kama hannunsa su fita, amma ya ƙura mata ido. Cikin harshen turanci ta ce "Muhsin let's go" (Muhsin mu tafi) "Anty sorry" (Anty ki yi haƙuri) ya furta cikin damuwa. Kallon sa tayi ta ce "Meyasa ka ke bani haƙuri?" "Anty waye ya dake ki, ki ka yi kuka?" Ya faɗa cike da yarinta. Haɗiye hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata tayi, ta ce "Atishawa na yi, mu tafi assembly ground" Ko da suka je wurin assembly, an yi tsit ana addu'a, amma ɗalibanta na ganinta, suka fara tsalle, su na kiran sunanta. "Anty, ko ki saka 'ya'yanki su yi mana shiru, ko ki ja su ku tafi" vice principal ya gargaɗeta. Cikin hikima ta sanya yaran yin shiru, yaran da take jin ƙaunarsu, har cikin zuciyarta. Lokacin tashin yaran, duk an zo an ɗauke su, saura muhsin da ta biyewa, take yi masa lilo, kafin a zo ɗaukarsa. Daga ita sai shi a harabar wurin nishaɗin yara, ta ɗora shi a wannan lilon ta sauke shi a wancan. "Laa Anty kin ga Daddy" yayi maganar yana nuna bayanta. Ko da ta waiwaya, mutumin nan ne da suka haɗu a ofishin director, ta sauke muhsin, ya nufi wurin babansa da gudu, ita kuma ta ɗaukko masa jakarsa da lunch box ɗin sa. Har ƙasa ta risuna ta gaida shi, ya amsa cikin sakin fuska ya ce "Ya yaran naki, ya ƙoƙari?" Ta amsa da "Alhamdilillah" "Madalla mu na ta goɗiya, mun yaba da ƙoƙarin da ki ke yi wa yara, Allah ya saka da alkhairi" "Amin na gode sosai" Har zai juya su tafi ya ce "Amma yaran naki, sun tashi gaba ɗaya ko?" Ta ce "Eh, sun tafi dama Muhsin ne ya rage, zan tafi nima" "To mu je, sai mu sauke ki a hanya mana" Nana ta ɗan yi turus ta ce "Bakomai na gode, ai babu nisa sosai" "A'a bakomai, ai ni na ce muje sai mu ajiye ki a hanya" sai ta ji mutumin yayi mata kwarjini, ta ci gaba da jayayya da shi, amma har cikin zuciyarta ba ta so hakan ba sam. Su na tafe a hanya, yana yi mata tambayoyi, kan matakin karatunta, da makamantansu. Ta din ga bashi amsa sama-sama a tsorace, dan haka kurum ta ji ya takura mata da yawa. Sai dai ya din ga yaba mata, da ƙoƙarin da take yi da yara. A bakin titi ta ce za ta sauka, ya ɗauki kuɗi dubu biyar ya ba ta, ta ce masa ba zata karɓa ya ce ba zata sauka daga motar ba, sai da ta karɓa, sannan ya buɗe, ta yi masa godiya ta nufi hanyar gida. A ƙofar gida ta hangi Baba, yana zaune a ƙasan bishiya, sai hamma yake yi, idanunsa jawur. Ta nufi inda yake, ta je ta durƙusa tana gaishe shi. Da ƙyar ya amsa mata yana kawar da kai gefe. Ta ɗaukko dubu uku a kuɗin nan ta miƙa masa ta ce "Baba ga wannan, yaran da nake kula da su ne, baban wani ya bani" sai ya waiwayo da sauri ya saka hannu ya karɓa. "Masha Allah, ai yakamata dai dama iyayen yaran nan, su din ga yi miki ihsani, tun da dai yaran nan na su da ki ke yi musu wahala, ba wani biyanki ake yi da kyau ba. Ko suturar jikinki suka kalla ai sun san mabuƙaciya ce ke, ba sai an ce su baki ba" Nana ta basar da zancen, dan ba ta son ire-iren waɗannan zantukan na Baba, masu cike da son zuciya ta ce "Bari na shiga na shirya, na tafi Islamiyya" "Zauna nan mu yi magana kafin ki shiga gidan" Nana ta zauna sosai tana sauraren Baba. "Nana duk abin da ki ka ga ina yi, ƙoƙari nake yi a kanki. Ki daure ranar talata ki je gidan yaya Atinen, a jarraba mai maganin wurinta ko za a dace. Idan bai yi ba sai fa mun dangana da mai maganin da Gaddafi ya bani labari, idan ba haka ba babu lallai ki iya zaman aure ki yi haƙuri  shi wancan malamin naku dama ba sonki yake ba, tun da ya gudu bai turo iyayensa ba. Tun daga wannan ba sai ki haƙura ayi da shi ba, nima a rage mini ɗawainiya ba. Yanzu ba a auren soyayya, ko wani zurfafa bincike duk bayi ake ba. Ki tashi ki shiga kar ki makara" Ba ta ce uffan ba, ta tashi jikinta a sanyaye ta shiga gida, gaba ɗaya kalaman Baba babu na ƙwarara gwiwa sai na kashe jiki da cire wa mutum tsammani. ***** Gaba ɗaya Auwal ya daina shiga makaranta, wanda hakan ya ɗagawa Nana hankali, ta na ta son su haɗu da shi, ta yi masa bayanin abin da ya gani ranar da ya je gidansu, amma ba ta samu ganinsa ba. Ita ba waya ba balle ta kira shi, abin duniya duk ya dameta. Ranar asabar da sassafe, Baba da kansa ya tashi Nana, ya sanyata shiryawa, ta tafi gidan yaya Atine. Babu yadda ta iya Baba, zuciyarta ta din ga raya mata, kar ta je, amma ta tabattar idan ba ta je ba, fushi zai yi da ita. Tun da Allah ya sa ta je gidan, bayan sun gaisa yaya Atine take masifa, wai ta ƙi tsayawa a nema mata magani ta wahalar mata da ɗan uwa. Nana dai ba ta ce uffan ba, Yaya atine ta yi ta faɗanta. Ta shirya ta saka Nana a gaba, suka tafi wurin mai magani. Ayshercool 08081012143 BUZU Ayshercool YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002) P8 Kallon farko da Nana ta yi wa mai maganin, takaici ya kama ta duƙun-duƙun da shi kamar wakilin sarkin dauɗa. Yana zaune a cikin wasu tarin shirgi da ta rasa ko na uban mene ne. Ɗakin sai azabar ƙauri yake yi, da tsamin wasu abubuwa da ta kasa tantance ko na mene ne. Jikin bangon ɗakin, an zana wasu irin hatimai, kuma an saƙale ƙahunhuna da layoyi. A take zuciyar Nana ta bata wannan mutumin boka ne, ba malami ba, ko kuma malun malun. Ya ƙare wa Nana kallo, ta kawar da kai ta ƙi kallonsa, Yaya Atine ta gyara zama za ta fara yi masa bayani, ya dakatar da ita, ya ce "Ɗan saurara tukuna Hajiya. Ba ki ga ta kasa haɗa idanu da ni ba? Ai sun zo shegun sun ƙaraso, tare ku ka shigo da su ai, ku na tafe su na biye da ita runduna guda, manya da yara tsofaffi da matasa, yanzu haka kusa da ke ma duk su ne a zazzaune makaran nata, sun cika gurin nan" Yaya Atine ta zabura ta tattare ƙafafuwanta ta ce "Innalillahi. A nan ɗin malam?" "Eh fa, yi a hankali kar ki hau kan wani" Nana kuwa waiwaya ta yi, domin ƙara tabattar da a kan wa yake maganar ne?. Ya gyara zama, ya juya ya ɗaukko wani ruwa, a wata tasa ruwan duk yayi gansa kuka, baƙi ƙirin da shi, ya ɗebo a hannunsa ya watsowa Nana. Take Nana ta ɗan ja da baya, saboda idan wannan ruwan dauɗar ya zuba a hijjabinta jirwaye zai yi. Ya ce "Kin gani ko, ga su nan za su yi magana, sun ji ruwan azaba, wane su dan uban su. Waye ya zo kanta za ka yi magana ko kuwa?" Nana ta ɗago kai baki buɗe tana kallon ikon Allah, tana tsoron ta yi wani abin, ya ce Aljanun ne suka zo, kar ta je ya zane ta. Sai dai ta ga idan ba ta yi da gaske ba, sai ya yi mata wanka da ruwan dattin nan, aikuwa ta tashi tsaye ta ja da baya. Yaya Atine ta miƙe da sauri, ta yi baya cike da tsoro da fargaba. "Ba za ku yi magana ba?" Yayi maganar yana zare mata ido, tare da miƙewa. Nana ta ce "Wai suwaye za su yi maganar ni ce fa" Ya ce "Da alama wannan makaran nata, su na da azabar taurin kai, sai an yi aiki tuƙuru a kansu. Yanzu zan yi mata wani ƙaramin aiki, somin taɓi idan kuma da kuɗi a hannunki ki bayar da dubu goma sha biyar, za a sayo turarukan da za ayi mata aikin da su. Ranar Litinin kafin hudowar alfijir, ake yin aikin, za ki kawo mana namijin goro guda bakwai, da zuma farar saƙa, kuma da wuya idan ba sai an yi yanka ba, kin ga sun ƙi magana". Yayi maganar yana ƙarasa sheƙa wa Nana ruwan hannunsa, hakan ya sanya hijjabin Nana, kwanciya a jikinta ya fito da surar da Allah yayi mata. Takaici ya isheta, tun da suka zo, mutumin nan bai ambaci Allah ba, ko ayar Alqur'ani sai shirme da soki burutsu. Warin ruwan da ya zuba mata duk ya cika mata hanci. Kawai ta nufi hanyar fita ta bar ɗakin. Yayi wuf ya riƙo hijjabinta. A fusace Nana ta juyo ta ce "Meye haka, ka sakar mini hijjabina ba na son haka" Mutumin ya dubi Yaya Atine da ke zare ido ya ce "Hajiya za su yi magana yanzu, ba ita ba ce ba" Nana ta saka ƙarfinta za ta fizge hijjabinta, ya saka ƙarfinsa ya hankaɗata take ta faɗa kan shirgin da ke cikin ɗakin, wani azababben wari, kamar na ruɓewar wani abu, ya daki hancin Nana, ga ƙume ƙeya da ta yi, wanda gudun kar ta yi ihu, ya sake fakewa da haka ya yi mata wani abun, ya tilasta ta yin shiru. Tana ƙoƙarin ɗagowa, ya shaƙa mata wani abu a hancinta, ta kawar da kanta ba ta sheƙa da yawa ba, amma ta ji wata irin gigitacciyar azaba ta ratsa hancinta zuwa kanta. Ba ta san lokacin da ta kurma ihu ba, jin azabar ta danne mata hanyar fitar numfashi. Ya kalli Yaya Atine ya ce "Hajiya jeki waje zan yi aikina" Yaya Atine ta ce "Ka na ganin ba wani abu na je?" "Eh mana, idan ma kin tsaya babu abin da za ki iya yi, idan ba haka ba idan suka zo fita su shige jikinki" ai cikin azama ta bar ɗakin. Sai da ya leƙa ya tabattar ta bar wurin, sannan ya dawo kan Nana, da take ta layi a ƙasa. Kan Nana ya yi, yana ƙoƙarin kai hannayensa ƙirjinta duk biyun, ta yinƙura ta juya tana takaicin yadda Yaya Atine ta iya tafiya ta bar ta, daga ita sai wannan zindiƙin mara tsoron Allah. Ƙoƙarin juyo da ita yayi, yana laluben yadda zai saka hannu a cikin jikinta, tayi wani kyakyawan yinƙuri, ta fizgo wani ƙaho da ke rataye daf da ita, ta raɗa masa a daidai tsakiyar kansa. Afujajan ya tashi tsaye, yana zazzaro ido, ya gigice saboda yadda ta yi masa dukan a bazata, dan a zatonsa hankalinta ya gushe. Ya kasa tsayuwa, ya nemi wuri ya zauna, saboda azabar raɗaɗi. Ta tashi da ƙyar, tana tangaɗi, ya yinƙura ya yi kanta domin hanata fita, kar ta tona masa asiri. Amma ta sake ɗaukan wata ƙwarya wadda take cike da ruwa, yayi baƙi ƙirin saboda tarkacen da yake ciki, ta sheƙa masa a fuska, sannan ta tattara ɗan kuzarin jikinta, ta yi masa ɓarin makauniya da ƙwaryar a fuska sai da ƙwaryar ta ragargaje. Ganin Nana ta fito tana tangaɗi, ya sanya Yaya Atine tashi ta nufe ta, mutanen wurin na ta yi mata sannu. "Ke Nana lafiya, ke ce ko aljanun naki ne? Wani mugun kallo ta yi wa Yaya Atine, ta ɗauki takalmanta a hannu ta riƙe. Yaya Atine ta koma ɗakin mai maganin, ta tarar da shi hanci na zubar da jini. Cikin tashin hankali ta ce "Malam lafiya kuwa?" "Artabu muka yi da aljanun nata, ba aljanu ne a kanta ba, baƙaƙen iblisai ne, shaiɗan ne da zuriyar sa" ya yi maganar yana shafo jinin da yake fita daga hancinsa. Sai hankalinta ya rabu biyu, tana ƙoƙarin ta tambaye shi, abin yi, kuma ga hankalinta a kan Nana. Ta koma in da ta bar Nana a tsaye, wanda suke zaune suka ce mata ai ta fita. Ta fita da sauri, amma ko alamar Nana ba ta gani ba, ta bi hanya tana salati da fatan ba wani wurin ta yi ba. Sai da ta ƙarasa titi, ta hangota zaune a gefen hanya, takalmanta a hanunta tana ta layi. Su na yin ido huɗu, kafin Atine ta tsallaka, Nana ta tashi ta shige wani adaidaita sahu, ya ja sun tafi. Salallami da salati, Atine ta hau yi, ta tari wani adaidaita sahun, ta tafi gidansu Nana. Baba na ganinta a rikice ya ce "Atine yaya dai? Lafiya kuwa?" "Ina fa lafiya Isa, mu na wurin mai magani, sun yi karambatta da aljanun nata, kawai ta fita ta haye adaidaita sahu, ai na za ta nan ta yo" Gaddafi da yake wanki, ya ja tsaki ya ce "Wallahi lamarin yarinyar nan har da iskanci, kuma da gangan take ƙin yin auren nan, a kaita gidan mutumin nan da na gaya maka Baba, idan ba gaske ne, idan ma ƙarya take yi duk zai faɗa babu wani aljani da ya gagare shi" "To yanzu a ina za a ganota?" Baba ya ce "To wa ya sani, kwanaki fa kwananta biyu ba ta nan, sai daga baya suka zo da Ummi, wai kawai ganinta ta yi a gidanta, idan ma da gaske take, idan ma ƙarya suke yi oho musu. Ni wallahi na gaji da sabgar yarinyar nan shi yasa nake Alla-Alla a samu mai so ya aura na huta. Kuma ga wannan ƙanin mijin Ummi ta tsaya tana iyayi" Babu tsammani, sai ga Nana ta shigo, Jamila ta riƙota tana ta tangaɗi, da takalmanta a hannu. Gaba ɗaya suka yi kan Jamila da tambaya "A ina ki ka ganta?" "Gidan maman khairat zan je, kawai na hangota tana ta tangaɗi kamar ma ta kasa gane hanyar gida ne" Mama da take ɗaki, tana jin su, sai yanzu ta yi but ta fito ta ce "Jamila, ban hana ki naniƙar yarinyar nan ba, sai kin kwashi masifa da bala'i" Atine ta ce "To 'yar nema, da ki na jin duk abin da ake yi, ki ka ƙule a ɗaki?" Mama ta ce "Ya shafe ni ne da zan fito, ba zaki cikata ba?" "Mama faɗuwa za ta yi fa idan na cikata" "Dan ubanki ki rabu da ita aka ce, duk ranar da ta ji miki rauni, ta sabauta ki ai kya shiga hankalinki" Gaddafi ya yi maganar cikin ɗaga murya. Duk da abin da mai maganin nan, ya shaƙa wa Nana, bai gama sakinta ba, amma tana jin duk abin da suke faɗa. Ta zame hannunta daga jikin Jamila, ta dafa bango ta nufi ɗakinsu. Tana jin Baba yana tambayar ta, dan me ta baro wurin mai magani, tayi masa shiru dan ko buɗe baki, wahala yake yi mata balle doguwar magana. Tana jin yadda Yaya Atine ta cafe, take yi masa bayanin, bataliyar aljanun da ke kan Nana, har da ƙara abin da ba a yi ba, kamar yadda mai maganin yayi mata bayani. Tun tana jin su sama, har wani abu mai kama da bacci ya ɗauketa. Kamar a zahiri ta daina jin komai a duniyar da take ciki, ya zauna a gabanta yana kallonta, kafin ya ƙyaƙyace da dariya wani irin baƙin hayaƙi yana fita daga bakinsa. Sam dariyar babu daɗin ji, ta saka hannu ta toshe kunnuwanta, amma ba ta fasa jin dariyar ba. "Igiyar ƙaddara, ta ɗaure ki ta ko ina, kuma kina da damar kwanceta, amma azabar baƙin taurin kanki, ya hana ki saduda ki karɓi ƙaddararki" Nana ta numfasa ta ce "Shirka ba ta cikin ƙaddarata, komai za ka yi mini, ba zan karɓi abin da ka ke buƙata na yi ba" Ya ɗago dogwayen yatsunsa, ya kai fuskarta ya lakuto gumin da take ta yi, ya kalli gumin a hannunsa ya ce "Ki daina cika baki, lokaci zai fayyace komai" Daga haka ya ɓacewa ganin Nana. Bayan farkawar Nana, ta tashi da wata azababbiyar yunwa, ga sallolin da ake bin ta. Ta tarar da Ummi ta zo, ta gaisheta amma ta amsa mata sama-sama. Ba a damu ba, ta yi sallolinta ta koma tsakar gida ta ce "Mama akwai abinci kuwa?" "Babu" ta bata amsa kai tsaye. Ummi ta ce "Mhmm Nana kenan, ai in dai irin wannan abubuwan ne, yanzu ki ka fara gani, tun da zaman gidan bai ishe ki ba, shi wancan na farkon Allah bai ƙaddara an yi da shi ba. Shi malamin naku an ce ya fito yaƙi, amma duk da larurarki, Saleh ya ce yana sonki amma sai wulaƙanci ki ke yi masa. Ya je ai ya gaya mini duk abin da ki ka yi masa" Nana ta yi kunnen uwar shegu da Ummi, kamar ba da ita take ba. "Mun yi magana da Baba, aure babu fashi, ya ce a gaya masa iyayensa su turo" Nana ta kalli Ummi ta ce "Yanzu za ki so hafsa ta auri mutum irin Saleh? Kin san fa ɗan shaye-shaye ne, kuma a Lagos ɗin kin san ina ne wurin sana'arsa da suwa yake tare? Duk ba kwa duba mini wannan?" "Nana ke ma fa kina da aibun nan, amma ya runtse ido ya ce ya ji ya gani, ita fa rayuwa yanzu idan ki ka samu mai sonki, duk wani tone-tone ba naki ba ne ba" ba ta sake kula Ummi ba, har ta gama abin da za ta yi ta bar gidan. Tunanin yadda Allah ya ƙwaceta daga hannun mai maganin ɗazu take yi, da tuni ya cuceta ya cuci rayuwarta, ita kanta ta san Allah ne kawai ya ƙwaceta, amma ya riga ya bugar da ita. 'wataƙila ga in da addu'oinki suke yi miki amfani, amma ki ke garaje da ɓacin rai' wata zuciyar ta tunatar da ita, a take ta yi ta istigfari. Sosai Baba ya ɗauki maganar Saleh da muhimmanci, Nana kuma ta na ta kai kukanta ga Allah, duk da neman lafiya da take roƙa ya rinjayi duk sauran adduo'in da take yi. Gashi duk da shirun da take yi wa Saleh idan ya zo, ba ya zuciya sai ya kuma dawowa, dan babban abin da yake saka shi zuwa ba yau ba gobe, bai wuce tozali da ƙirar jikin Nana ba, da yake jin kamar zai ɗimauce, idan bai kai hannunsa jikinta ba. Ta kan ƙare masa kallo, tana mamakin yadda Baba ya rintse ido, daga ganin aibun Saleh, kama daga kan askin banzar da yake kansa, zuwa suturar da yake sakawa da sunan gayu. Kodayake dama gayu idan ya haɗu da jahilci hauka ne tuburan, duk soki burutsun da zai yi mata babu maganar Allah a ciki sai shirmensa. Gefe guda ga kewar malam Auwal da ta dameta, tabbas ba dan mutunci da kamewarta, na ɗiya mace ba da babu abin da zai hanata zuwa gidansu ta tuntuɓi ko lafiyarsa ƙalau. Sai dai duk da haka sai da ta tambayi abokinsa malam Nura, ya tabbatar mata da lafiyarsa ƙalau ayyuka ne su ka yi masa yawa kawai. Kimanin makwanni biyu kenan, ba ta ga malam Auwal ba, zuciyarta na raya mata, karɓar lambarsa a wurin malam Nura, ta ari waya ta kira shi, amma ta kasa. Kwatsam su na cikin karatu a aji, ta jiyo muryarsa a waje. Ta kasa riƙe kanta, ta tashi ta fita. Kafin ta isa, har ya shiga cikin ofishinsa, yana cikin tattara litattafansa, kawai ya waiwayo ya ga Nana. "Yaya Auwal meyasa ka ke guduna? Ina ta son mu haɗu na yi maka bayani, amma ka daina zuwa ma gaba ɗaya" "Babu malami a ajinku ne?" "Eh, tilawa muke yi" "Ki koma aji" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba. Ta marairaice ta ce "Amma Yaya Auwal, magana nake son mu yi, dan Allah ka fahimce ni ba abin da ka gani, ba abin da ka ke tunani ba ne... "Ki tafi aji na ce Nana, ba sai kin yi mini bayanin komai ba" yayi maganar cikin tsawa. Tsayawa ta yi tana kallonsa, bayan tayi nasara sun haɗa ido. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta tafi ba kuma ba ta ce komai ba, sai dai idonta ya cika da hawaye. Sai ya tausasa murya ya ce "Ki je aji Nana, ba na son gardama" Ta girgiza kai ta ce "Koma me ka ke ɓoye mini ka gaya mini. Kai malamina ne, kuma abin koyi na, ka karantar da ni nagartattun halayen fiyayyen halitta Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Wanda ya haɗa da gaskiya, da kuma haƙuri. Ka gaya mini ko ma mene ne a ranka dan Allah" Jiki a sanyaye ya ɗan sunkuyar da kansa, sannan ya kalle ta ya ce "Nana kin san komai nufi ne na Allah, maganar aure tsakanina da ke, ba zai yiwu ba yanzu haka Qatar zan tafi da wani ɗan ƙanƙanin lokaci" Murmushi ta yi, duk da hawayen da ya cika mata ido, ta ce "Ko kai fa, ka ga yanzu da ka gaya mini gaskiya zan fi samun nutsuwa sosai da sosai. Ina yi maka fatan alkhairi amma dan Allah ka ci gaba da yi mini addu'a, na san larurata ce ta saka ka fasa aurena, ka yi mini addu'a Allah ya bani wanda zai iya aurena da larurata a haka" "A'a Nana, idan baki manta ba, tausayinki da halin da ki ke ciki, ya sanya na ce zan aure ki, ban ƙi auren ki saboda larurar ki ba" Ta share hawayenta ta ce "Eh, da fari tausayina, daga baya ka koma so na, dama na san zaka rabu da ni, dama na fi so na ji daga bakin ka ne, tun lokacin da aka ce ba zaka iya riƙe aure ba, na ga komai a bacci, har rabuwar nan tamu na yi mafarki na gani, ba zaka aure ni ba. Hakan ba ya nufin zan manta tarin alkhairin ka a gare ni, Ubangiji Allah ya baka mace ta gari lafiyayyiya" Zai yi magana ta girgiza kai, ta fice daga ofishin, zuciyarta na zafi hawayen da take ƙoƙarin dannewa, su ka ƙi dannuwa. Auwal bai taɓa tunanin yana son Nana har haka ba, sai da Umma ta hana shi aurenta, kuma abin bai tsaya a nan ba, sai da Umma suka tura shi Qatar. Nana ta tafi rijiya, ta ɗebi ruwa ta wanke fuskarta, sannan ta koma ajinsu aka ci gaba da tilawa da ita. Sosai rabuwa da Auwal ya shigi Nana, duk da ta yi mafarkin hakan, amma ba ta bari ta gasgata hakan ba. Har aka tashi daga makaranta, hankalinta ba ya kan abin da aka ƙara musu sam. Da daddare, bacci ya gagari idanun Nana, sai tunani da zancen zuci, ya din ga ziyartar zuciyarta, har ta rasa wane tunani ya kamata ta yi. Jamila ce ta zo da abinci daga gidan maman khairat, ta cewa Nana ta tashi ta ci, amma ta ƙi. Sai da ta takura mata, sannan ta ci kaɗan, ta sha lemon ta kwanta, sai dai abincin ya tsaya mata yaƙi wucewa. Tana daga kwance, tiryan-tiryan, yadda aka fasa aurenta na farko ya dawo mata, yadda take samari, su na tafiya, duk da galibi mutanen banza ne suke bibiyarta. Amma Suleiman ya zo da gaske zai aure ta. Sai dai Baba ya din ga zubar mata da mutunci a idonsa, ta hanyar roƙe-roƙen kuɗi, kuma wani abin mama ce take ziga shi yake yi, har ita ma wasu lokutan sai ta tura ta ce ya bata kuɗi, sun wuni ba su ci abinci ba. Tun yana bayarwa da marmari, har ya gaji ya fara mita. Ya san da Nana ba ta da cikakkiyar lafiya, duk da a lokacin abin ya lafa, amma mama ta zaunar da shi, ta din ga karanta masa Nana aljanu har sun fara haukata ta. Matarsa ta zo har gida ta ci mutuncin Nana, har da an gaya musu babarta ce take biye-biyen bokaye, abin ya koma kanta take fama da aljanu. Duk da dama Mama ta saba faɗar wannan maganar, idan ta so cin mutuncinta, amma abin yayi mata zafi ya mata ciwo. Wuni ta yi tana kuka, Suleiman da kansa ya je gida ya ba wa Nana haƙuri, bayan ya samu labarin abin da matarsa ta zo ta yi mata, sai dai tun da matar ta koma gida, ya aka rasa gane kanta, ta kwanta rashin lafiya. Ta din ga fama da matsanancin ciwon kai, idan ta fara sai ta fita hayyacinta ko gani ba ta iya yi, suka je asibiti ba a ga komai ba. Ya koma gidansu Nana, ya ce idan ta san wani abu ta yi wa matarsa, ta bari uwar 'ya'yansa ce, ba zai so lafiyarta ta taɓu ba, tun da ai ya zo ya bata haƙuri. Nana ta din ga rantse-rantsen ita babu abin da ta yi mata, ƙarshe dai matar kamar za ta haukace, ya zo ya ce a dawo masa da kayan aurensa, tun a waje Nana ta cutar da iyalinsa, ina ga idan ya aureta, dama kuma an ce masa mahaifiyarta na biye-biye. Duk yadda Nana take son ta yi aure, ko dan saboda tarin ƙalubalen da take fuskanta, amma fasa aurenta da Suleiman bai wani dame ta ba, domin tana fargaba mussaman yadda aka gama zubar mata da mutunci a wurinsa. Ajiyar zuciya ta sauke da ta zo nan a tunaninta, sai da kanta ya sara, ta sauke ajiyar zuciya. Ga abubuwa da dama su na cin zuciyarta, tana buƙatar abokin shawara da tattaunawa, amma rashin yardarta bai sanya ta bawa wani damar, hakan a rayuwarta ba. Mutanen da suka cancanci hakan a rayuwarta duk ba ta ita suke yi ba. Babbar damuwarta a yanzu, bai wuce yadda ta san ko ba ta so, Baba sai ya ƙaƙaba mata Saleh ba, dan ta fuskanci zamanta ne kawai ba a so cikin gidan, duk ga su Suwaiba da Jamila, su babu wanda yake takura musu a kan aure sai ita. Sosai take jin zafin rashin Auwal, ko ba komai mutum ne ma'abocin Alqur'ani da kuma riƙo da addini, ta san abu ne mawuyaci a iya cutar da shi, ta sanya ran idan tana tare da shi, za ta samu sauƙin wasu abubuwan. "Ke baiwar Allah" ta ji an kirata. Ta ɗaga kai, ta hangi wata mata bararoji a tsaye, ta yi kwalliya da tarin tsummokara, da wasu irin tarin sarƙoƙi na zare a wuyanta, da ƙullin kaya a hannunta, ta burtso da gashin ta gaban goshin ta. Nana ta ɗaga kai ta ganta a wani wuri, da ba ta san ina ne ba. Matar ta ce "Zo na baki magani" Nana ta ce "magani kuma, na me?" Matar ta sauke mayafin da ta rufe fuskarta, ko ina tsagu ne a fuskarta, har baka iya tantance kamaninta, saboda azabar billayen da ke fuskarta. Matar ta ciro wani magani a cikin, ƙullin kayanta ta ce "Ki zuba a tafin hannunki, ki lashe" Nana ta ce "To ai ba ki gaya mini na mene ne ba?" "Idan ka sha, ba zaki ganin Ƙaisar ba, zai daina bibiyar ki yana takura wa rayuwarki, zai rabu da ke har gaban abada. Dukkanin damuwar ki za ta kau, babu wanda zai sake zuwa auren ki, yayi nasarar korarsa ko ya saka miki wani ciwo. Dan yan daf da fara kashe mutane, domin wata ƙungiyar asiri ce suke nemansa ido rufe yayi musu aiki. Idan suka sadaukar masa da jini, zai fara kisan mutane ne, kuma zai fara da mutane mafi soyuwa a gare ki" Jiki na rawa Nana ta miƙa mata hannu, domin karɓar maganin. Matar ta yi murmushi, haƙoranta suka bayyana baƙaƙe ƙirin da su, ta kama tafin hannun Nana, ta zuba mata maganin, da yawa. Tana kama hannunta, Nana, ta ji tamkar an zare mata lakar jikinta, jikinta yayi wani irin sanyi, da ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. Ta kai garin maganin bakinta ta fara sha... Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM AYSHERCOOL YOTA/002 P9 Ko da Nana ta sake lasar maganin, sai ta ga fuskar matar tana komawa baƙa ƙirin, tana ta fito da dogon harshe, tamkar na macijiya, wani abu mara kyan gani na futa daga bakin nata. Iya ƙarfinta Nana take son ta yi addu'a, idan mafarki take ta farka, amma ta ji tamkar an saka dutse an tokare maƙogwaronta zuwa huhunta. Babu tsammani, ta ga wata irin guguwa ta haɗu, Ƙaisar ya bayyana a tsakaninsu yayi wani irin mugun cilli da matar a gefe. Yayo kan Nana, ya zubar da sauran maganin hannunta, ya shaƙe mata wuya. Wani irin kakari ta din ga yi, ta na amai dunƙunlen jini yana fitowa ta hancinta da bakinta. Ji ta yi numfashinta na neman ɗaukewa. Ita ma Nanan, ya yi jifa da ita gefe, ta riƙe wuyanta tana numfashi da ƙyar. Ya kalle ta a zafafe ya ce "Idan ki ka ci gaba da irin wannan gangancin, za a kashe ki a haka, babu wani mahaluki da zai iya raba ni da ke. Guba ta baki za ta kai jininki ayi tsafi da ke saboda tasirin taurarinki. babu wanda zai iya baki wani magani ya raba ki da ni, idan ki ka ci gaba da yinƙurin rabuwa da ni, za ki kashe kan ki da kan ki" yana maganar tartsatsin wuta na fitowa daga jikinsa, yana ƙona Nana. A hankali ta buɗe idonta, ta ganta a kan shimfiɗarta, ta takure jikinta yana ta rawa, numfashinta yana fita da kyar. Wuyanta sai raɗaɗi yake yi mata, haka ma jikinta. Ta kai hannu ta ɗauki fitilarta ta kunna, tana haska ɗakin, ba kowa a ɗakin sai ita kaɗai. Jikinta ya ba ta wani abin tayi, su Jamila suka gudu suka bar ta a ɗakin. Ta yinƙura da azama ta tashi tsaye, amma jikinta sai raɗaɗi yake mata, kafaɗunta kamar ba a jikinta suke ba. Ayatul kursiyyu ta din ga karantawa, ta fita ta ɗauki buta, ta shiga banɗaki. Tana fara fitsari ta ji ƙarnin jini, tana dubawa ta ga fitsarin jawur, jini a maimakon fitsari. Gashi ko kwana bakwai ba ta yi da gama al'ada ba. Ta wanke jikinta tayi alwala, ta koma ɗaki, gaba ɗaya ta kasa yadda har yanzu ba a cikin mafarki take ba. Da safe ta fito ta yi aikace-aikace da za ta yi, Jamila ta ce "Nana me ya same ki haka?" "A ina?" "Jiya da daddare ki na ta kakarin amai, ki na kuka a bacci, yanzu kuma kalli jikinki, kamar an zane ki da bulala" Baba da ya fito daga banɗaki, shi ma ya kalli Nana. Jikinta duk kwanciyar bulala, gashi ta ɗashe ta yi haske, kamar mara jini a jiki. Nana ta kalli jikinta, ta ɗan taɓe baki ba ta ce komai ba, ta ɗebi ruwa ta shiga banɗaki domin yin wanka. Sai dai wannan karon ma, fitsarinta jini ne kawai yake zuba. Kawai ta jingina da jikin banɗakin, ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta sannan ta ta fara yin wankan. Sai dai tana zuba ruwan a jikinta, ta ji kamar fatarta za ta zazzago, jikinta ya hau kyarma. Duk da a cikin banɗaki ta yi, haka ta furta a'uzubillah, ta cigaba da zuba ruwan a jikinta tana wanka, har ta kammala ta fito. Ta yi alwala, ta shiga ɗaki ta shirya, tana kallon Baba yana kallonta, amma ba ta gaishe shi ba, haka kurum ta tashi da matsanancin ɓacin rai, ko ganin Baban ba ta son yi. Ba ta kula kowa ba, ta fice ta tafi makaranta. Gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga jiri tana fama, dan haka a cikin aji ta yi zamanta, ta kifa kanta a kan tebur, tana ta kewar rashin Auwal. ***** "Safiyya" "Na'am Hajjaju" "Yaya kin yi magana da Jamila kuwa?" "A'a yanzu dai nake saka ran zuwanta" "Dan Allah, ki ɗan bugi cikinta ki ji, yarinyar nan ta sha lemon kuwa?" Maman khairat ta ce "In sha Allah, zan bugi cikinta zamu yi magana da ita" "Amma ina fatan, ba ki gaya mata ko na mene ne ba" "A'a haba Hajiya, ya ma za ayi na gaya mata, ai kin ce ko wani ma ya ci ba komai, ita ɗin dai ake so ta ci, zan tambaye ta idan ta zo" "To shikenan, na gode sai na ji ki" ***** Ƙamshin turare ne ya cika wa Nana hanci, sai dai ba ta motsa ba ko ta buɗe idanunta ba. Teburin da take kai, ya ɗan bubbuga, sai a lokacin ta buɗe idonta a hankali. Dishi-dishi ta fara gani. A hankali idonta ya washe, ta ɗaga kai ta kalle shi. Yayi murmushi ya ce "Anty ya dai ki ke bacci, ko babu lafiya ne?" A hankali ta tashi zaune, ta kalli agogon ajin nata ƙarfe biyu. Tunani ta hau yi, tun da ta shigo da safe take wannan baccin, ko kuwa? Maganar Muhsin ce ta dawo da ita hankalinta ya ce "Anty kin ga na gama" yayi maganar yana nuna mata littafin sa, da ya cika page guda da A. "Afuwan Anty Nana, direbansu ya yi tafiya ne, mahaifiyarsa babu lafiya, ni kuma ba ni da isasshen lokaci, na shiga wani meeting ne, shi yasa na daɗe ban zo ɗaukarsa ba, ki yi haƙuri na ɓata miki lokaci". Jinjina kai kawai ta yi ta tashi, ya ce "Mu je sai mu sauke ki a hanya" sai dai haryanzu ba ta yi magana ba, ta bi shi su ka tafi. Jamila na zaune, tana ta zaman kashe wando a gidan maman khairat, kamar yadda ta mayar da hakan ibada, tana tayata aiki su na hira. "Ni kuwa jiya kin ci abincin jiya Jamcy?" Jamila ta ce "Lallai ma Anty Safiyya, me zai hana ni ci, na yi abincin kuma na kasa ci?" "Wallahi ni gaba ɗaya kasa cin abincin na yi, na ce da na sani, na ce ki tafi da shi duka" Jamila ta ce "Subhnallah, ko dai Khairat za a yi wa ƙani" Tayi murmushi ta ce "Rufa mini asiri, wallahi sai da ki ka tafi na ga kamar abincin ba zai ishe ku ba, kuma har su Nana duk sun samu sun ci?" Sai da Jamila ta yi mamakin tambayar, amma ta ce "Eh mana, Nana ce ma babu lafiya, ba wani ci ta yi ba, kin san 'yar ƙi faɗi ce, sai na je da abu sau shurin masaƙi amma babu lallai ta ci" "Eyya, to ai ba komai, mun riga mun zama ɗaya Allah ya ba ta lafiya, ta sha lemon ma?" "Eh amma ba da yawa ba" Safiyya ta jinjina kai ta ce "Dan Allah ki yi mata sannu" Jamila ta ɗan taɓe baki ta ce "To, za ta ji, kin san ita kullum cikin ciwo take ne, abin nata ba na ƙare bane ba" Suka ci gaba da hira, ƙasan zuciyar Safiyya, cike da farin ciki ***** Ƙarfe huɗu da rabi na yammaci, sannu a hankali yake ƙarewa garin kallo, duk ya kwana biyu baya garin, amma ba wani abu ne ya canza ba, amma har cikin zuciyarsa yake jin kewar Kanon dabon. Tun daga can babban titi ya sauka, ya saɓo hanya, domin ya samu isashshiyar damar ƙarewa garin kallo, yadda yake so. Dandazon mutane ya hango a wani wuri, mutane na ta surutu da hayaniya. Har ya yi gaba, kawai ya dawo da baya domin ganewa idanunsa abin da ya tara wannan cincirindon al'ummar. Ya din ga kutsawa, yana ture mutane. Kawai ya tarar da wata matashiyar budurwa a kwance a wurin, sai dai ta juyar da fuskarta ba a iya ganin fuskarta. Ya taɓa wani mutum ya ce "Malam lafiya, me ya faru don Allah?" Mutumin ya ce "Wallahi tun azahar, muka ganta a kwance a wurin nan, an zata ma ko ba ta da hankali, ko kuma ba ta da lafiya, amma jikinta fes babu datti ba alamar hauka a tare da ita. An yi anyi ta tashi ko motsi ba ta yi, kuma tana da rai. An duba jakarta babu waya sai maka da kuɗi, yanzu ma dai an kirawo 'yan sanda". Bai ce uffan ba, cikin azama ya nufi kanta, mutane na ƙoƙarin hana shi, amma bai saurari kowa ya je kanta ya ɗago ta. Idanunta a rufe, sai dai hawaye da yake ta fita ta gefen idonta, ga jikinta zafi tamkar wuta. A sanyaye ya ce "Nana" shiru ba ta amsa ba. Miƙewa yayi yana ƙoƙarin ɗaukarta, wani ya ce "Malam lafiya, ina zaka kaita?" "Ƙanwata ce" ya faɗa a taƙaice, ya fita ya taro adaidaita sahu. Bai sake tsayawa yi wa kowa bayani ba, ya saɓa Nana ya shiga adaidaita sahu, ya tafi da ita. Mama na tsakar gida tana tankaɗen tuwo, sai ganinsa tayi a tsakiyar tsakar gida. Suwaiba da take jan ruwa ya kalla ya ce, "Shimfiɗa mini tabarma a tsakar gida" Ta ajiye gugan, ta ɗaukko tabarma, ya kwantar da Nana a kai. Ya ɗebo ruwa a kofi, ya zo ya zauna a kusa da ita, yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta rame sosai da sosai. Cirko-cirko mutanen gidan suka yi, su na bin sa da kallo, kowa da magana a bakinsa, amma babu damar furtawa. Ya tofa ayatul kursiyyu, da falaqi da nasi, kowacce da bismillah, ya shafa mata ruwan a fuskarta, da tafukan hannayenta. A hankali yake bin jikint da kallo, yana mamakin shaidar duka ce, ko ta ƙonuwa a jikinta. "Nana" ya kira sunanta. Cikin sa'a sai ta buɗe idonta a hankali, ta sauke a kan fuskarsa. Shiru ta yi tana kallon sa, kamar ba ta taɓa ganin sa ba, zuciyarta na raya mata kawai tarkacen mafarkin da take yi ne. Ta yi shiru, ta tuna ta shiga motar baban Muhsin, su na tafe a hanya, a kunnenta ta ji ana ce mata, ga Auwal can a marrraba, nan da mintuna goma tirela za ta taka shi. Babu shiri ta tsayar da baban Muhsin, bai gama parking ba, ta buɗe motar ta fita daga nan kuma, sai ta ɗimauce ta rasa gane gaba da baya. Mayar da idanunta tayi ta sake lunshewa. "Ma'u" ya kuma kiranta yana matsa hannunta. Ta sake kallonsa a hankali ta ce "Wai da gaske kai ne?" "To da waye? Dama haryanzu ba ki warke ba, ki na wannan ciwon Nana? Kuma uban waye ya dake ki duk jikin ki ya tashi haka?" Ta yinƙura ta tashi zaune, kawai ta fashe da kuka. "To kukan uban me ki ke yi kuma? Na ce uban wa ya dake ki?" "Ba dukana aka yi ba" ta bashi amsa tana share hawayenta. "To me ya kai ki yin bacci a titi, maza sun baibaye ki, kamar ƙudaje sun ga mangwaron Binta suga" Ba ta bashi amsa ba, ta ci gaba da kuka. Ya tsuke fuska ya ce "Dalla yi mini shiru, ina yi miki magana ki na wani kukan banza" "Me yasa ka tafi ka bar ni?" Ta yi magana cikin kuka. Guntun tsaki yayi, ya ce "To dai ba ga ni na dawo ba? Uban me ake tsinana mini a gidan idan na zauna, yanzun ma tunaninki ne ya addabe ni, nake ta mafarkinki shiyasa na taho, kuma ina zuwa na tarar da dandazon mutane, ina dubawa na ga ke ce. Allah dai ya tsinewa wannan matsiyatan aljanun naki banzaye marasa imani" Za ta yi magana, Baba yayi sallama suka amsa, sai dai ya ja tunga ya tsaya, ganin wanda bai taɓa zato ba a gidan. "Kai imrana, uban me ka ke yi mini a gida? Me ya kawo ka gidana?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Kamar yaya? Ya ka ke magana kamar wani shege ba kai ka haife ni ba? Gidan ubana na zo, kuma wurin 'yar uwata na zo" "Ban yi maka iyaka da gidana ba? Ki na me ki ka bari ya shigo mini gida?" Yayi maganar yana kallon mama. A ƙufule ta ce "Au to kokawa ka ke so na yi da shi? Ko saɓa shi zan yi na jefa waje, tun da kai ka dawo sai ka fita da shi ai" Ya sake kallon imrana ya ce "Ba magana nake yi maka ba? Ban hanaka zuwar mini gida ba?" Cikin rashin ɗa'a Imaran ya ce "Sai ka ce wani gidan kirki, to ka mayar da ni in da na fito, cikin uwata ta mayar maka da ni" Nana ta ce "Imarana Baba ne fa" "Shi ɗin, shekaru uku ba ka ga ɗanka ba, da haka yakamata ya karɓe ni komai girman laifin da na yi masa? Ba azabtarwa da ake yi mana ne ya tilasta mini barin gidan nan ba" Gaddafi ne ya shigo, bayan dawowarsa ya jiyo hayaniya daga cikin gidan ya shigo, domin duba abin da yake faruwa. Shi kansa mamaki ne ya kama shi, ganin Imran a gidan. Baba kamar ya fashe da kuka ya ce "Imrana ni ka ke gaya wa haka? Ka tashi ka fita ka bar mini gida na ce maka" "Idan na bar gidan shege nake, wallahi sai na gama kwanakin da zan yi. Ke Nana ga jakata nan zan je na dawo. Nana ta tashi ta ɗauki jakar, ta nufi ɗakinsu da ita, Baba ya daka mata tsawa ya ce "Bashi jakarsa ya bar mini gida" Cikin kuka Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah Baba ka yi haƙuri, tun da ya ce idan ya gama kwanakinsa tafiya zai yi. Shekara uku ban ganshi ba, dan Allah ka yi haƙuri" "Au Nana kin fi son ɗan uwanki da ni ko? Amma yana sane da mu, ya kama gabansa ya tafi gantalinsa har shekaru uku, yana gararamba bai waiwayo gida ba, sai yanzu saboda ya mayar da ni ɗan iska zai dawo mini gida?" Imaran ya nufi Nana, ya karɓi jakarsa, ya kaita wani ɗan lungu ya ajiye, ya fice ya bar gidan. Shi kansa Gaddafi kasa magana ya yi, saboda tsagwaron zunzurutun tsageranci kawai yake iya ganowa a cikin idon Imran ɗin. ***** "Hajiya Sa'a aiki ya lalace fa" "Ban gane ba, kamar yaya?" "Akwai wani hatsabibin shaiɗani a tattare da yarinyar nan, ya lalata mana aiki gaba ɗaya. Ba a samu adadin jinin da ake buƙata a jikinta ba" Dafe kai Hajiya Sa'a tayi, ta ce "Yanzu mene ne abin yi, ka ce akwai sa'a a tattare da yarinyar yanzu babu wata dabarar kuma? Yarinyar ce wata irin majanuniya, har kaya na bayar a kai mata, babu yadda ban yi a sake kawo mini ita gidan yarinyat Safiyya ba, dama a can na ganta wai ta ƙi yarda. Ni kuma na abin na je gidansu ba, ba na son zargi da saka ido" "Aikuwa neman mafita ya ganki, domin wani baƙin sheɗani ne a tattare da ita, babu lallai ya bari wani ya raɓe ta, saboda wasu dalilansa, 'yar aiken tamu ma ya ƙona ta. Yanzu dole ki san yadda za ki yi, a sake ba ta maganin zamu sake tura wani ɗan aiken" Hajiya Sa'a ta jinjina kai ta ce "Amma, ba yadda za ayi a samo jininta nata, dole sai an bata wani abin ta ci?" "Eh dole ne, idan ba haka ba babu ta yadda za a samu jininta, ba zai bari a tunkare ta ba. Kuma ko ba haka ba, idan ba ta hanyar abincin da za a bata ba, ba kowane aljani zai iya raɓarta ba, saboda tana zama da alwala, kuma tana adduo'i shi kansa aljanin jikin nata, ba ƙaramar azaba yake sha ba. Dan haka yanzu ko dai a samu jininta ta wannan hanyar ko kuma ki janyo ta ƙungiya" Hajiya sa'a ta ce "Ba abu ne mai sauƙi ba hakan, muguwar miskila ce, ba kamar 'yar uwatta ba, da ɗayar ce ko nan ka ce na kawo maka ita, zan kawo ta, amma babu komai zan san abin yi, dole haƙata ta cimma ruwa" "Babu laifi" **** A hankali jikin Nana ya ci gaba da yi mata raɗaɗi, tamkar ana kunna mata wuta, ta daure ta din ga nanata suratul jinn, tun daga farko har ƙarshe a zuciyarta. Imaran ne ya dawo bayan sallar isha'i, hannunsa riƙe da ledoji. "Nanawo, sannu ya jikin?" Yayi maganar bayan ya ja kujera ya zauna. "Jiki Alhamdilillah" "Kai Nasiru ɗaukko faranti" yayi maganar yana kallon Nasir. Ya je ya ɗaukko faranti, ya zazzage musu gurasa da nama fal a kai. Ya kalli Nana ya ce "Ina Jamila ne? Tun da na dawo Suwaiba kawai na gani, ko an yi mata aure ne?" Nana ta ce "A'a tana maƙwabta" Ya tsuke fuska ya ce "Har bayan sallar isha'i, kamar gidan ubanta?" Yana rufe baki ta yi sallama. Sai dai ta tsaya da ta ga Imaran, ta ce "Imran dan Allah kai ne ko gizo idona yake yi mini?" "Ban sani ba, tun la'asar ba kya gida kina can kina gantali a gidajen mutane" "Haba ai ka bari mu gaisa, ina ka tafi shekara uku ba wanda ya san inda ka ke?" "In da ki ka aike ni. ware ki wanko hannu ku zo mu ci abinci" Ta ce "Yanzu ma kuwa" Cikinsu ya shiga, suka rufarwa gurasar, yana kallon Nana, da ƙyar take ci. A haka Gaddafi ya shigo ɗaukar abincin dare ya tarar da su. Imran ya kalli Nana ya ce "Wai ba za ki ci ba ne?" "Imrana ba a ɗebarwa Baba ba, Mama ba a bata ba" Haushi ne ya kama shi ya ce "Wallahi ba zai ci ba, da na zo ko ruwan gidansa ya bani, ba kora ta ma ya yi ba? Kar Allah ya sa ki mayar da hankali ki ci" Abinka da 'yan uwa, haka suka kewaye Imran. Jamila ta ce "Wai dan Allah tsawon wannan lokacin, ina ka tafi?" "Duniya na shiga mana, tun da an kore ni an ce ba a buƙata ta a gidan" Baba yayi sallama, suka amsa masa gaba ɗaya. "Imarana ban ce ka bar mini gida ba wai?" "Wallahi Baba ba zan bar gidan nan ba, sai na gama abin da nake yi" A fusace Gaddafi ya ce "Wai kai baban  ka ke yi wa magana a haka?" Imran ya kalle shi ya ce "Kai kuma ina ruwanka da ni? Kai a yaya ne baka yi masa magana, ya taɓa korarka ne? Ka ga tun da na zo ban kula ba kar ka shiga harkata ehee" A fusace Gaddafi ya yo kan Imran, Imaran ya miƙe tsaye ya ce "Wallahi yanzu ba da ba ce, wallahi ka taɓa ni sai na soka maka ƙarfe". Baba ya tare Gaddafi ya ce "Rabu da shi, kar ya yi maka rauni, alamu sun nuna haryanzu yana shaye-shaye" "Wallahi Baba ko uban me yake sha, dai-dai nake da shi, ka bari na sauke masa tsagerancin da yake kansa" "A'a gara dai ya riƙeka, dan wallahi ka taɓa ni sai na buga ka da ƙasa ba abin da ya dame ni" ya kaɗe rigarsa ya fice. Nana ta dafe kanta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, tun tsaowar su Baba ba sa shiri da Imran ko kaɗan, tabbas a baya babu wanda suke tsoro sama da Gaddafi sun daku a hannunsa, saboda ya ce babar su ce ta yi sanadin da aka saki babarsa, kuma har ta mutu Baba bai dawo da ita ba. Ta yi alwala ta yi sallar isha'i ta kwanta, ba dan tana jin bacci ba. Kwanciyarta ke da wuya, ta lumshe idanaunta, ta lula duniyar tunani, ta buɗe idonta domin juyi ta gyara kwanciyarta, kawai ta ganta a bakin wani ruwa a zaune. Ta ɗaga kai ta waiwaya, ba kowa a wurin, sai dogwayen bashiyu koraye shar, ruwan gabanta kuma sai tambal-tambal yake yi tamkar zai yi ambaliya. Ta kalli jikinta, ta ga babu kaya a jikinta, sai wani ɗan mayafi da aka rufe mata ƙirjinta, zuwa al'aurarta. Jikinta duk ya ɗuri ruwa, ya kwaile saboda ƙuna. Ta yinƙura za ta ja ƙafafuwanta, ta tashi ta gansu ɗaure a jikin sarƙa. Free pages na daf da ƙarewa. Contact me to subscribe yours. Ayshercool 08081012143 BUZU YOTA/002 AYSHERCOOL P10 Ta waiwaya jin maganganun su Suwaiba, a kusa da ita, har su na faɗa a kan charger, amma ba ta ganinsu sai ita ƙwal a wurin. Ta rintse idanunta, tana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah" Ji ta yi an taɓa ta, ta buɗe idonta tana tsammanin ganinta a ɗakinsu, amma ta ganta dai a wurin a zaune. Ya durƙusa ya kwance sarƙar ƙafarta, sannan ya kalleta, ba ta iya kallonsa, duk da a suffar mutum ya bayyanar mata, duk da dogwayen yatsunsa masu ɗauke da zaƙo zaƙon farata sun fallasa bambancin da yake da shi da bil adama. "Kalli jikin ki, kalli irin raunukan da suke jikin ki, saboda azabar taurin kan ki da dan halin ki zan bi, da sai dai ciwon nan yayi ajalinki" Nana ta ɗan kalle shi, ta kawar da kanta ta ce "kai ne fa ka yi mini raunin, da tartsatsin wutar da ya din ga fitowa daga bakinka" Ya dube ta ya ce "Ba zan yi miki irin wannan illar ina sane ba, kafofin da za a din ga zuƙar jininki ake so. Ina sake jaddada miki ki karɓi abin da ƙaddara ta zana miki. Ni hadiminki ne zan zama mai biyayya a gare ki, idan kuma ki ci gaba da bujirewa zan ci gaba da azabtar da ke, dan rayuwata ba za ta salwanta a banza a kan ƙoƙarin kare ki da baiwarki ba, ba wannan aikin na karɓi yi daga wurin kakaninki ba". Ta ɗan ɗago ta ce "Wani irin aiki ka karɓa a kaina, kuma meyasa ka dage lallai ni zan yi harkar bori? Kai ba ka ga ilimin addini ya yawaita ba yanzu? Su ma na yi imani da Allah, rashin ilimi ne ya sanya su ka yi wannan harkar. Kuma duk sauran mutanen dangin babu wanda za ka matsawa ya yi harkar shirka sai ni?" "Ba ni da lokacin da zan tsaya yi miki wani dogon bayani, amma ina mai tabbatar miki tashin hankali da masifun rayuwa yanzu a ka fara, ko ƙafa ba ki saka ba domin ba ayi komai ba". Nana ta ce "Abin da Allah ya ƙaddara ya zai same ni ne kawai zai faru da ni, na zan taɓa yadda da duk wata tatsuniya da za ka karanta mini ba" "Shikenan, ba na buƙatar dama ki yarda, zan cire hannuna na ja da baya na zura miki ido, da kan ki za ki neme ni". "Da ni da kai duk bayin Allah ne, dan haka babu yadda za ayi na nemi taimakon ka. Ko da ka tare mini wani abu, Allah ne ya tare mini kai sila kawai za ka zama" Ta yi maganar cike da ƙwarin gwiwa. Yayi mata shiru, ya juya ya kalli ruwan nan, ya fara fito da wata baƙar iska daga bakinsa yana hurawa ruwan. A take iskar ta dinga tafasa ruwan har da tururi. Ya kwantar da Nana, ita kuwa ta zuba wa sarautar Allah ido. Ya ce "Maganin da matar nan ta baki ki ka sha, ta samu damar tsinka wata jijiya a mararki, shi ne ki ke wannan fitsarin jinin kuma sun samu sun tara, duk da bai ishe su ba. Wannan ciwon na jikinki, ba ƙonuwa ba ce ramuka suka yi miki, jininki na zubowa ta ramukan sai dai ba za su iya amfani da shi ba, saboda yana jikin fatarki ne kuma ba za su iya raɓarki a haka ba" Nana jin sa kawai take yi, ba wai dan tana yadda da maganganun na sa ba. Ya din ga ɗebo ruwan tekun nan, yana zuba wa Nana a jikinta. Ta rintse idanunta tana jin yadda wani irin zafi yake ratsata har cikin ƙashinta. Ya zira hannunsa a cikin bakinsa, ya zaro wata doguwar allura, ya shammaci Nana ya caka mata a mararta. Ta kurma ihu sai da gaba ɗaya dajin ya ɗauka. A zahiri kuwa, tun da ta lumshe idonta, jikinta yake rawa haƙoranka suna karo da juna, idanunta suka kakkafe. Su Jamila suka fito suka bar mata ɗakin, zuba mata ruwan nan da ƙaisar yake yi, a zahiri ihu take yi. Gaddafi ya je ƙofar ɗakin ya tsaya yana bala'i. "Wallahi ko ki rufe mana baki, ko na yi miki mugun duka, dan abin naki zunzurutun iskanci ne na za ki hana mutane bacci ba". Amma a banza dan ba ta san ma yana yi ba, sai wani irin gurnani da take yi kamar an yanka sa. Ya nufi wurin da aka sayo ice aka ajiye, ya samo wata sanda dai-dai lokacin ta fito daga ɗakin za ta fita waje. Babu tausayi babu imani, ya fara shirga mata icen nan a jikinta. Nasiru tun da Nana ta fara wannan gurnanin, ya fita majalissar da ya ga Imarana, ya ce masa ya zo ya ga abin da Nana take yi, zuwansu yayi daidai da dukan da Gaddafi yake yi wa Nana. Imran ya hankaɗe shi ya ce "Kar ka sake dukanta, wani irin azzalumi ne kai, da wanne za ta ji? Dama abin da ku ke yi mata kenan" hankaɗe shi Gaddafi ya yi yana ƙoƙarin sake dukan Nana, Imran ya ɗaukko ƙaton itace a murhu yana wuta yayi kan Gaddafi zai jirga masa gadan-gadan. Da ƙyar Baba ya raba faɗan ya ce "Gaddafi na ce ka daina dukan yarinyar nan, tun da ka ga nima na saduda ba ciwon ƙarya take yi ba, ba ta da lafiya da gaske. Kuɗin auren da na ce yaron nan Saleh ya kawo, su nake jira mu kaita can in da ka ke ba ni labarin nan, amma tun da abin ya kai haka ma dole ko rance ayo a kaita wannan jaraba ta ishe ni. Kai kuma jarababbe ɗan nema, kai ba aljan ba amma ka fi sheɗan shaiɗanci, wallahi aljanun Nana sun fiye mini hatsabibancin ka nesa ba kusa ba Imrana." Imran bai kula Baba ba, ya durƙusa ya ɗago Nana, matsanancin tausayinta ya mamaye zuciyarsa. Suka ci gaba da hayaniyarsu, shi kuma ya mayar da hankali kan tofa wa Nana ayatul kursiyyu, a fuskarta. Miƙa ta yi a hankali, sai kuma ta riƙe hannunsa tana ajiyar zuciya. "Nana" "Na'am Imran, ka tsaya a kusa da ni, tsoro nake ji" "Na sha gaya miki, ki daina jin tsoro, kar wani abu ya din ga ba ki tsoro. Babu wani abu da ya isa ya cutar da ke sai abin da Allah ya ƙaddara zai same ki" Ta jinjina masa kai, tare da ƙara jin ƙwarin gwiwa. Ya ɗaukko ruwa pure water ya bata ya ce "Yi bismillah ki sha ruwa" ta karɓa ta yi bismillah ta fara sha. Ta kammala sha, ta ce "Alhamdilillah" "Amma Nana ki na addu'a kuwa?" Ta jinjina masa kai ta ce "Eh" "Lamarin nan yana damuna Nana, da kafin na tafi kamar abin ya lafa miki" "Eh, tun da aka saka mini rana ta farko abin ya dawo, har zuwa yanzu" Imran ya ce "Ba komai akwai Allah" "Imran" ta kira sunansa a hankali. Ya amsa da "Na'am" "Tun da ka tafi, ka je wurin babarmu ne?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Ai ni da sake zuwa in da take har abada" Cike da damuwa Nana ta ce "Saboda me? Mahaifiyarmu ce fa, ni ko a waya ba na samunta, ga Baba ya hana duk wata hanya da za ta sada ni da ita" "Nana, ki yi focusing a kan rayuwarki. Duk duniya babu wanda dan ya cire hannunsa daga rayuwarki za ki kasa rayuwa. Uwa na haifar jariri ma, ta mutu a take ya girma ya rayu, balle ke da wayon ki da girman ki, ki ci gaba rayuwarki kawai. Ta fi son mijinta da yaran da ta haifa yanzu a kanmu, ban da haka ai ya kamata ta waiwayo mu, ta ji halin da muke ciki, amma tana can tana rayuwarta cikin kwanciyar hankali" Hawaye na bin idon Nana ta ce "Ba haka ba ne Imran, babarmu tana sonmu, Mijin da take aure ne ba ya son mu je in da take, nan ma idan ta zo ka san Baba wulaƙanci zai yi mata". "Kin ga mu bar wannan maganar, ki je ki yi alwala ki nemi wuri ki kwanta kawai" fafur Imran ya ƙi yarda su ci gaba da maganar. ***** Buzaye ne su uku, zaune a cikin jeji, mai ɗauke da manyan bishiyu, iska sai kaɗawa take yi. Dukkaninsu sanye da rawani. Shikaɗai ne a gefe, ya zuba shayi a kofi , yana sha yana lumshe idanunsa, alamar yanayin yana yi masa daɗi. Cikin damuwa Habu ya ce "Souley, na rasa abin yi, kaina ya kulle fa" Souley ya ce "Nima hakan take Habou, anya ba za ka mayar da shi Nijar ba, tun da an kasa samun magani?" Da sauri Habu ya girgiza kai ya ce "A'a, ba zan mayar da shi Nijar ba yanzu, akwai wani mai magani da na ji labari, har kwantar da mutane yake yi, ina jiran cikakken adireshin gurin ne, shi ma za mu jarraba" "To ai ni tsoro nake ji ne Habou, kar a garin yawon neman maganin nan a samu mushikila, ka na kallo kullum abin nasa babu wani ci gaba, duk in da aka je sai dai ace mana babu mafita. Kawai ka tsinci mutum ka yi ta wahala da shi, ka je in da ka tsinto shi ka mayar da shi kawai mu huta" Habu ya kalli Sule cike da takaici, kawai ya tashi, ba tare da ya sake tanka masa ba ya nufi in da ɗayan yake. "Taso mu tafi" yayi maganar yana kallonsa. Sai dai bai motsa ba, ya ci gaba da tsiyayo shayin da yake cikin buta yana sha. Habu ya miƙa masa hannu, ya sake cewa "Taso mu tafi" sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalli Habu, ya ƙarasa shanye shayin, ya tashi tsaye. Sule ya ce "Habou kalli fa ko magana a 'yan kwanakin nan ba ya yi, sai a shafe kwana da kwanaki bai ce komai ba, haka zamu ci gaba da wannan aiki haka?" Habu bai tanka masa ba, ya riƙe hannunsa suka yi gaba. ***** Dawowar Imran gidan malam Isa, ya sanya kullum cikin rigima ake da shi, kullum sai sun yi faɗa da Baba ko Gaddafi. Ba ya kwana a gidan, amma garin Allah na wayewa zai zo. Nana ta samu afuwa sosai da dawowar Imran. Saboda ba ta taɓa zama da yunwa, sau ukun nan sai ta ci abinci a rana. Sai dai ta kasa tunanin Auwwal, tun ranar da suka rabu, ba ta sake ganinsa ba. Ga Baba ya fara addaba mata da maganar Saleh, wanda ko sunansa ba ta ƙaunar ji. A can makaranta da take koyarwa, mahaifin ɗalibinta Muhsin, ya fara damunta, kullum ya zo ɗaukar Muhsin, sai ya ce zai rage mata hanya. Ga shi ba ta da damar tafiya, sai an gama zuwa ɗaukar yaran gaba ɗaya, kuma kullum Muhsin ne ƙarshen zuwa ɗauka. Yau bayan ta dawo daga islamiyya, Yamma liƙis, Baba ya shigo fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce "Ke Nana, ki je ga Saleh can a waje yana jiranki" gaban Nana ya faɗi. Imran ya tashi ya nufi hanyar fita, Baba ya ce "Kai malam ba kai fa kai na ce ba" Ya waiwayo ya kalli Baba ya ce "Ni akwai gurin da zan je" ya fice. "Ke kuma Nana ba magana nake yi miki ba?" Jiki a sanyaye ta ce "Ina zuwa, kaya zan canza" Imran kuwa yana fita ya tsaya ya ƙarewa Saleh kallo, ya ce "Kai ai kamar na sanka a gidan Ummi" Saleh yayi murmushi ya ce "Ba kama ba ce ba ni ne ai" Imran ya ce "Bala'i ashe idan na je neman aure nima za a bani, duk da ana ganin ba ni da saiti. Kai yanzu saboda ka raina wa kanka hankali gurin ƙanwata za ka zo neman aure a haka? Kalli wani shegen wando a jikinka ba ka san saukakkiyar Alqur'ani ba ce, kuma mahaddaciya ba?" Saleh yayi saroro yana kallon Imran. "Eh kalle ni da kyau, wallahi sai na je har gida na kasa wa Ummi warning, mai ku ka mayar da Nanan, wallahi ta fi ƙarfinka me za ta yi da ɗan jagaliya kamar ka?" "Saboda na zo ƙofar gidanku neman aure, ka ke gaya mini abin da ka ga dama?" Imaran ya ce "Malam gaskiya nake gaya maka, ba ka cikin irin mutanen da Nana za ta so da aure, a tsarinta tana son mutum mai kamala da sanya manyan kaya kuma... Shiru ya yi, ganin Nana ta fito fuskar nan babu walwala. Maimakon ya tafi sai ya ja ya tsaya, takaici ya hana Saleh magana, a girme ya girmi Imran amma ya tsaya yana gaya masa magana dan ya zo wurin ƙanwarsa. Ya maze ya kalli Nana ya ce "Gimbiyata barka da fitowa" Imran ya kwaɓe baki yana jiran me Nana za ta ce. Ta ɗago suka haɗa ido. "Amma ko za ka bamu wuri mu yi magana" Saleh yayi maganar yana kallon Imran. "In ba ku guri na je ina? Ka zo wurin ƙanwata zance da crazy jeans, meye banbanci na da kai, da ake cewa ba ni da hankali?. Kai wallahi ba za ayi zancen nan ba, ke koma gida ranar da ya shirya neman aure, yayi shigar mutunci ya zo" Babu musu Nana ta shige gida, dama haka take so. Baba na ganin ta dawo ya tambayi ko lafiya?. "Imaran ne ya ce na dawo gida" "Ki dawo ki yi masa uban me? Idan ba ki yi aure ba zai aure ki ne?" Ya nufi waje yana faɗa, ya tarar da Imran ya tare ƙofar gida yana cewa Saleh idan gidan ubansa ne, ya ture shi ya shiga da wannan shigar tsiyar. "Imrana wai ba ka da hankali ne? Meye haka?" "Baba, wai ya za a ɗauki aure a ba wa mutumin da zai zo neman aure, yayi ido huɗu da sirikinsa da yagaggen wando, da tarin suma kamar shekararren zakara. Kuma a gaya masa gaskiya Nanan nan fa ba son sa take yi ba" Baba ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imrana yaushe ka yi hankalin da ka fi ni sanin dai-dai? Shigar mutum ake dubawa ko halin iya riƙe auren? Ita Nanan ba taimaka mata zai yi ba, tun da ba lafiya ce da ita ba" Imran ya ce "Baba neman kan da ka ke yi da Nana ba daidai ba ne ba, Allah ya ɗora mata larura alhakinka ne nema mata magani, ba neman kai da ita ba, amma shikenan 'yar ka ce, duk matakin da ka ɗauka a kanta daidai ne" yayi maganar yana barin gurin. Baba ya kalli Saleh ya ce "Dan Allah malam Saleh ka yi haƙuri, yaron nan ba cikakken saiti ne da shi ba, ka san idan mutum yana shaye-shaye sai a hankali ka yi haƙuri. Nana 'ya ta ce kuma na isa da ita, ka je ka turo magabatanka kawai kar ka ɓata lokaci kamar yadda wancan yayi" Saleh ya ce "In sha Allah Baba na gode sosai" "Yauwwa yi tafiyarka, kar ya zo ya yi maka wani haukan a ka" Saleh ya so keɓewa da Nana, amma Imran ya wargaza komai. An fara kiraye-kirayen sallar magariba, Jamila ta shigo Nana ta fara nema, Nana ta ce "Wannan kiran fa ta samu ne?" "Wai dan Allah ina kayan da Hajiya ta bani na kawo miki, ko sau ɗaya ba ki saka ba, balle na yi miki hoto na tura mata, tun da na san ba za ki je ta gani ba" Nana ta ce "Zan saka ne, kawai ni ban san dalilin da ya sanya ta bani kayan ba ne, amma zan saka in sha Allah" Jamila ta ce 'Ai mace ce mai kyauta, babbar 'yar kasuwa ce fa, kwanan za ta fara bani kaya ina ɗora nawa nima, kin ga turare ta bani na kawo miki " ta yi maganar tana miƙa wa Nana wani turare. Nana ta karɓa tana murmushi, kasancewar tana son ƙamshi sosai. Ta sunsuna turaren ta kalli Jamila cikin murmushi ta ce "Amma ƙamshin turaren nan yayi daɗi sosai, ki ce mata na gode sosai" Nana ta fara ƙoƙarin fesa turaren a hannunta, amma idan ta fesa babu abin da yake fitowa, ga kuma turaren tana gani cikin kwalba. Tayi tayi amma abu ya gagara. Suwaiba da ta fito daga banɗki ta ce "Wai ke Jamila ba ki gaya wa hajiyar, ki na da 'yar uwa da ku ke uwa ɗaya uba ɗaya ba, ni ba zata bayar da komai a kawo mini ba sai wata Nana da uba kawai ku ka haɗa?" Suwaiba ta ƙaraso, ta karɓi turaren hannun Nana, ta fesa a hannunta ta sunsuna. Wurin da ta fesa turaren Nana ta ga duk ya ɓuɓɓule, kamar an caccaka allura jini ya fara fitowa. Sai dai ta ga Suwaiba normal, ba ta nuna wata alama na ta ga abin da ya faru ba, hakan ya tabattar wa Nana, ita kaɗai take gani. Suwaiba cike da mugunta, ta feshe rigar material ɗin jikinta milk. Nana ta ɗan ja da baya ganin jini, ya ɓata rigar maimakon ruwan turare. Suwaiba kuma ta ce "Amma turaren yayi ƙamshi" tana sake feshe jikinta da shi. Sai dai duk in da turaren ya taɓa a fatarta ɓulewa yake jini ya fara zubowa. Ta gama fesawa, ta bawa Nana turaren ta ci gaba da sabgoginta. Mama ma masifa ta hau yi, wai tana uwar Jamila ba a bayar da komai a kawo mata ba sai wata Nana. Jiki a sanyaye Nana ta shiga ɗakinsu, tana sake kallon kwalbar turaren. Ta buɗe ta ƙara fesawa a jikinta da hannunta, amma yaƙi fitowa. Ta ajiye turaren tana tunanin ko sharrin ƙaisar ne. Ta sake fitowa yin alwala, Baba ya zaunar da Gaddafi yana ta gaya masa abin da Imran yayi, tare da ƙorafin ya gaji da rashin mutuncin da yake aikatawa. Nana hankalinta ba ya kan abin da suke faɗa, hankalinta yana kan Suwaiba, da jini yake ta gangarowa daga hudar jikinta, kuma rigar jikinta ta rine zuwa jini. Amma normal suwaiba na ta ayyukanta. Nana ta ware a gefe, tana ta jan "wa hifzan min kulli shaiɗanin marid" Sam jikin Nana ba ƙwari ta kwanta, duk addu'a da ta zo bakinta yi take yi, ta waiwaya ta kalli in da Suwaiba take, ta jiƙe jagab da jini ga ƙarnin jinin ya cika ɗakin babu daɗin ji. Suwaiba na ta kallon kaɗe-kaɗenta a waya, har bacci ya kwashe ta. Nana ko kyakyawan ƙifta ido ta kasa yi, ganin yadda jinin ya jiƙa katifar da Jamila da Suwaiba su ke kai, ya gangaro ƙasa. Ana haka Suwaiba ta kurma wani irin uban ihu, Nana ta razana, ganin wannan bararojin da ta ba ta magani ta lasa, jikinta baƙi ƙirin ta koma kamar gawayi, fuskarta ce kawai ba a ƙone ba sai gashinta, ta tsaya a kan Suwaiba ta kafa haƙoranta a wuyan Suwaiba tana zuƙar jini. Maimakon Nana ta yi addu'a kawai ita ma sai ta saka ihu ta suma a gurin. Cikin ihu da kururuwa Suwaiba ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Mama Baba ku taimake ni, Nana za ta kashe ni, Nana tana shan jinina dan Allah ku yi mini rai Nana na shan jinina!!! Ku tuntuɓe ni kai tsaye, domin fara biyan naku kuɗin littafin. https://wa.me/2348081012143 Ayshercool 08081012143 Ko kuma ku kasance da ni a kan manhajar arewabooks @ayshercool7724 BUZU AISHA ADAM AYSHERCOOL YOTA/002 P11 Ɗungurungum, page ɗin yau naku ne, YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION, Tare da 'yan Ayshercool media, ina godiya sosai da sosai. A wannan karon Mama ce ta fito da gudu, jin muryar Suwaiba tana ihu. Sai dai ta tarar da Nana a gefe, tana bacci. Ta ɗago Suwaiba tana kiran sunanta, sai dai Suwaiba ta rirriƙe wuyanta, tana numfashi da ƙyar tana cewa "Nana ce, Mama ki taimake ni za ta kashe ni" Cikin kuka maman ta fara ƙwalawa Baba kira "Malam Isa ka zo Nana za ta kashe mini 'ya, na daɗe ina faragbar kar ta cutar mini da yara, gashi za ta kashe Suwaiba" Jamila ma tuni ta tashi, ta ja gefe, domin ita ma a tsorace ta tashi, saboda mummunan mafarkin da ta yi da Hajiya sa'a tana ƙoƙarin shaƙe ta, ta caka mata wata wuƙa. Baba ya ce "Wani irin Nana za ta kashe ta kuma? Ba ga Nanan a gefe tana bacci ba?" Cikin fushi da tsawa ta ce "To ka ƙaraso mana ka ga abin da take yi" Ya ƙarasa ya ga Suwaiba, ta rirriƙe wuyanta, idanunta duk sun fito waje sai kakari take, da ƙyar take furta Nana za ta kasheta. Baba ya ce "Suwaiban Baba, buɗe ido ki ganni, Nana bacci take yi me ki ke gani?" Cikin kuka da kakari Ta ce "Baba wallahi Nana ce, jinina take sha, ka hana ta zan mutu" Baba ya koma gurin da Nana take, ya kai hannunsa ya juyota, idanunta a buɗe, amma babu baƙar ƙwayar idonta, sai farar kawai. Jikinta kuma sanyi ƙalau kamar gawa. "Ni wannan wane irin abu ne haka?" "Ke Jamila, je ki ki taso mini Gaddafi" Jamila ta tashi jiki a sanyaye ta fita ƙofar gida, ta ƙwanƙwasa wa Gaddafi ɗaki. Tare suka dawo, yana tsaki yana bala'in shi tattarawa zai yi ya koma in da ya fito, ya gaji da wannan bala'in na gidan. Ɗan tsayawa yayi yana kallon in da Nana take, ga gefe Mama riƙe da Suwaiba tana kuka. Ya ce "Mutuwa Nanan tayi ne na ganta a haka?" Cikin kuka Suwaiba take miƙa wa Gaddafi hannu ta ce "Yaya ka taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take sha" tayi maganar tana kuka. "Wane irin shan jini kuma?" Nana kuwa tuni ta lula wata duniyar a yanayin da take ciki. Domin kuwa Ƙaisar take gani. Ya ce "Kin ga da kin sake kin fesa turaren nan a jikinki, da jininki za a sha ba nata ba. Aike ne na musamman domin ke, da na bari kin fesa turaren nan da sai dai wata ba ke ba" Nana ta kalle shi ta ce "To ni me za ayi da jinina? Kuma meyasa ba ka hana wannan mummunar matar shan jinin Suwaiba ba?" Ya tanƙwashe ƙafafuwansa ya kaɗa kai ya ce "Saboda ke ce uwar gijiyata, alhakin kula da ke ne kawai a kaina. Duk da ba jininta suke buƙata ba, amma idan 'yar aiken ta ji daɗin jinin na ta, to fa ta samu wurin zama. Ko da su can jinin bai yi musu amfani ba, to ita za ta ci gaba da amfani da jininta, domin ta warke daga ciwon jikinta, idan ba ayi wasa ba hakan zai yi ajalinta." Cikin damuwa Nana ta ce "To ka yi wani abu a kai mana" Yayi murmushi ya ce "Zan iya wani abu a kai tabbas, amma daga lokacin da ki ka fara bani umarni hakan yana nufin kin karɓi gadon gidanku. Kuma zamu yi aiki tare" Da hanzari ta ce "A'a ni ba zan iya shirka ba na gaya maka. Amma ba zan zuba ido komai ya tafi a haka ba. Idan haka ne anya ba wannan matar Hajiya sa'a da ta kawo turaren babu masaniyarta a kan wannan abun?" Murmushi ya yi ya shafi gefen fuskar Nana ya ce "Ban sani ba, amma ke ma zan shafe komai daga kanki yanzu wani binciken ba shi da amfani sam. Mussaman ke da ba za ki yi abin da ya dace ba, idan ki na tsananta bincike wataran za ki shiga gurin da ba zan iya ciro ki ba. Kalli nan ki ga, ta waiwaya domin ganin abin da yake nuna mata. Ɗakinsu ta gani, Suwaiba ta samu bacci, Jamila kuma ta ce Allah kar ta, ba zata kwana a ɗakin nan ba tsoro take ji. Mama ta ce su tarkata su koma ɗakinta, su kwana tare da yaranta a bar Nana ta ci kanta. Baba ya kalli Gaddafi ya ce "Gaddafi, gobe in Allah ya kaimu dole mu yi sammako, mu kai yarinyar nan gurin da ka faɗa ɗin nan. Ni kaina na fara jin tsoron abubuwan nan". Gaddafi ya ce "Allah ya kaimu" Nana ta dubi Ƙaisar ta ce "Ni dama gurin mamana ka nuno mini, na ganta ko na ji daɗi" "Idan na fara karbar umarninki, haka yana nufin kin amince da sharaɗina, ni kuma zan yi miki mubaya'a na zama mai hidima a gare ki" "A'a bari ba na so" tayi maganar tana girgiza kai. Ya saka dogwayen yatsunsa yana ci gaba da shafa kumatunta ya ce "Alamu na nuna, sarƙar ƙaddara ta mayen ƙarfe na ƙoƙarin janmu wani wuri, ta yi wani ɗauri mai wahalar kwancewa. Ko na ce sarƙar na ƙoƙarin sarƙe ki. Gobe za a wuce da ke gurin mai magani, 'yar uwakki ta shafa miki mugun tabo, tun da ta ce kina sha mata jini, babarta ba za ta yi shiru ba, za ta yi ta gaya wa mutane ne. Ga yayanki can ya sha ƙwayoyi yana ta bacci, gobe har ku tafi ba zai farka ba, domin na ƙarawa abin da ya sha ƙarfi. A duniya zan ga wanda ya isa ya raba ni da ke. Zan ga mai karambanin mai maganin da zai jarraba hakan". "Allah ne zai raba ni da kai" ta yi maganar a hasale. "Da zai rabani da ke, da bamu haɗu ba" ya bata amsa. Nana ta waro ido ta ce "Kaii zaka yi saɓo, ki ba musulmi ba ne? Ko da yake musulmi ba zai yi abin da ka ke yi ba" Ƙaisar ya yi dariya ya ce "Kamar ba musulmin ne ke neman jininki su yi tsafi da shi ba" Ya koma ta bayanta, ya zuro kansa gefen fuskarta, hakan ya ƙara adadin bugun zuciyarta, jikinta yayi sanyi ƙalau kamar wadda aka saka a cikin firinji. Ya ce "Bari na sake nuna miki wani abu, amma akwai buƙatar na tsaya kusa da ke, idan ba haka ba, wannan 'yar ƙaramar ƙwaƙwalwar ta ki bugawa za ta yi. Kalli can" ya nuna mata wani mudubi. Ta ɗaga kai ta kalla. Kawai ta ga Auwwal a kwance ana yi masa wankan gawa, gefen cikinsa na ta zubar da jini. Razana tayi za ta miƙe, amma ya riƙe ta ya ce "Kar ki zarge ni, babu sanya hannuna a cikin wannan abin, ya gama shirinsa gobe zai tafi Abuja, ɗazun nan masu ƙwacen waya suka tare shi, suka karɓi wayar suka caka masa ɗan buda. Yaran kuma da suka yi, abokan yayanki ne, nan da 'yan kwanaki idan bincike yayi nisa shi ma za a kamo shi". Wani irin yinƙuri Nana ta yi, domin ta ƙwace daga jikinsa amma ta ji an riƙeta. Ta ɗaga kanta kawai ta ganta a ana kiciniyar shiga taxi da ita, ta waiwaya ta ganta a tare da Yaya Atine da Baba. Ta ja ta tsaya ta ce "Wai ya na ga haka?" Baba ya ce "Ba ki da lafiya, gidan mai magani za mu je" "To Baba ai ban yi sallar asuba ba" Yaya Atine ta ce "Mu je, idan an je gidan mai magani sai ki yi sallar" Nana ta kalli sama yadda gari ya fara haske, ta ce "A'a ni a bari na yi salla" Baba ya ce "Ta dawo hayyacinta, a ƙyale ta tayi sallar" Nana ta shiga gida Yaya Atine ta bita, ta yi alwala. Yaya Atine ta ce "Rabi ki bari a tafi da Suwaiba gidan mai maganin nan a duba ta ita ma" Mam ta ce "Eh ko ba gidan mai magani ba, ta je ta ƙarasa lasheta a hanya ta kashe ta, babu in da za ta je, kuma wallahi kurwar Suwaiba ta fi ƙarfinki" ta yi maganar tana hararar Nana. Nana dai ta yi alwala, ta gabatar da sallar asuba, aka saka ta a cikin taxi, aka ja aka tafi, ba tare da ta san ina suka dosa ba. Suwaiba kuwa ba ta tashi daga bacci ba, sai bayan ƙarfe tara na safiya, kuma babu wanda ya tashe ta, domin ta yi salla. Sai a lokacin ta yi salla, ta nemi abin karyawa. Jin Mama na ta jera mata sannu ya sanya ta ce "Wai mama sannun me ki ke yi mini ne?" Mama ta ce "A'a abin da ya faru da ke jiya mana, wannan azzalumar tana neman kar ki" Cikin rashin fahimta Suwaiba ta ce "Wace ce? Ni fa ban gane ba" "Jiya kururwar da ki ka din ga yi ki na Nana za ta kashe ki, tana miki jini, ba mu yi bacci ba fa" Suwaiba ta zaro ido ta ce "Ni ɗin?" Jamila ta ce "Eh mana, kasa numfashi ki ka yi fa, kina ta kuka wai Nana tana sha miki jini" Jikin Suwaiba ya yi sanyi, ta ce "To ai ni tun da na kwanta, ko juyi ba na tunanin na yi, sai yanzu na tashi daga bacci" Jamila ta ce "Ikon Allah, kin ga kururwar da ki ka din ga yi kuwa, wai Nana na sha miki jini?" "Ni dan Allah ku daina wannan zancen tsoro ku ke bani wallahi kar na je, aljanun nata ne nima su ka shafe ni" Muryar Imran ce ya dawo da su kan tsakar gidan, yana ta kwaɗa wa Nana kira. Nasiru ya ce "Nana fa sun tafi gurin mai magani, bayan sallar asuba" "Kamar yaya ita da wa?" "Asubar farko, aka je aka taho da Yaya Atine daga gidanta, a taxi ɗin malam Shehu, gari yana fara haske suka tafi. Jiya ne Suwaiba ta din ga ihu cikin dare wai Nana tana sha mata jini, shi ne suka tafi da sassafe" "Kuma shi ne ba a gaya mini ba, ina ne garin mai maganin, kar aje a kai ta gurin bokaye" "Wallahi ban sani ba" Imran ya ce "Ke Suwaiba, ya aka yi Nanan ta sha miki jini, ita ba mayya ba, kar ki ja a ɓata mata suna, ni ba na son ƙananan maganganu ki bar ta ta ji da halin da take ciki mana" A fusace Mama ta ɗaga labule ta fito ta ce "Ban gane ba, za ta yi mata ƙarya ne? ko dan kai ba a gidan ka kwana ba, ba ka san a halin da ta kwana ba" "Eh Alhamdilillah, na ji daɗin hakan ma, ai da gani ku ke yi Nana tana sane, duk abubuwan da yake faruwa da ita, tana sane ita ta yi wa kanta ƙarya take yi. Yanzu idan ma ƙarya take idan ma gaske ne, ai kwa gani, kuma wallahi na ji wata magana a unguwa ta cin zarafin Nana, ko yi mata ƙage wallahi sai na saka an ɗaure mutum igiya ta yi saura" Jamila ta ce "Mama dan Allah rabu da shi, kar ya yi miki rashin kunya" *** Nana kuwa rarraba ido kawai take yi a hanya, tana ta ƙoƙarin tuna wasu abubuwa a ƙwaƙwalwarta, amma abu ya gagara. Abin da take iya tunawa, kawai hango Suwaiba tana zubar da jini, amma ta kasa tuna takamaiman yadda aka yi ta ga jini a jikin Suwaiba. Gaba ɗaya ta nemi kuzarinta ta rasa, jikinta yayi sanyi ƙalau, ko ƙwaƙwƙwaran motsi, sai ta yi da gaske take iya yin sa. Sannu a hankali, ƙwaƙwalwarta ta fara fassara mata maganganun da ta jiyo Baba yake yi. Wai ana idar da sallar asuba, ya kira Saleh a waya ya ce masa wai idan akwai kuɗi a hannunsa, ya turo wani abu za a nema mata magani. Wani irin takaici ya kama Nana, sam Baba ba ya gudun abin kunya da duk wani abu da zai zubar musu da kima. "Atine, ai yakamata tun yanzu yaron nan, ya fara ƙoƙartawa shi ma, tun da dai aurenta zai yi, duk wata hidima da za a yi mata, ya saka hannu a yi da shi" Babu kunya Yaya Atine ta ce "Gaskiya ne, ai kamata yayi ace ya ɗauke maka wasu nauye-nauyen". Baba ya ce "Sosai fa, kuma kin ga hakan zai ƙara tabattar masa da gaske zan ba shi aurenta. Ai mu na dawowa daga gurin maganin nan kawai iyayensa su zo a wuce gurin" Nana ta rintse idanunta, tana fatan bacci ya ɗauke ta, ba ta tunanin akwai wani wanda zai aureta ta yi mutunci a idonsa, da irin wannan halin na Baba, na son jinginawa wani ɗawainiyar da shi yakamata ace ya yi abarsa. Sun sha doguwar tafiya sosai, kafin su isa wani surƙuƙin ƙauye, sai da suka yi nisa sosai da sosai, suka daina ganin gidaje. shige da ficen ababen hawa ne, ya sanya suka tabattar da akwai mutane a gurin, domin kuwa hatta kwalta babu a gurin, sai uwar zangarniya. Yanayin surƙuƙin gurin, sai parking ɗin motar suka yi a bakin hanya, suka saukko domin takawa su ƙarasa, sai dai ƙafar Nana ta ƙi takuwa sai ma lanƙwashewa da ta yi, kamar mai shan inna. Sun daɗe a gurin, Nana ta kasa taka ƙafafuwanta, sai da ƙyar ta ɗan saki, ta takawa a hankali. Tun da suka doshi hanyar da aka nuna musu, aka ce a nan gidan mai maganin yake, Nana take ganin garke garke na Raƙuma su na fitowa daga hanyar, jajaye da farare. Yaya Atine ce ta riƙe ta suke tafe a hankali, saboda da ƙyar take taka ƙafafuwanta. Nana ta ce "Yaya Atine dama akwai baƙin raƙumi?" Yaya Atine ta ce "A ina?" "Ga su nan su na ta wucewa, ba ki gansu ba?" Yaya Atine ta ja ta tsaya ta ce "Kai Gaddafi, ku na ganin raƙuma ko kuma nima abin nata ne zai shafe ni, nice ba na ganinsu?" Baba ya ce "Raƙuma kuma a ina?" "Yo ai ji na yi tana zancen baƙin raƙumi, ni kuma ko kofato ban gani ba balle raƙumi. Kai zo ka riƙe 'yar ka, kar na gano abin da ba shikenan ba" Nana na jin haka, ta zame hannunta daga na Yaya Atine ta ci gaba da takawa a hankali. Daga nesa suka hango gidan, mutane na ta shiga su na fita. Ja da baya Nana tayi da sauri tana kare fuskarta. Baba ya ce "Me kuma ya faru?" Cikin damuwa Nana ta ce "Baba wai ba ka gani, baƙin raƙumin nan ne yake feso mini wuta fa" Cikin takaici Gaddafi ya ce "Dan Allah Baba ku daina biyewa yarinyar nan, ku zo mu ƙarasa." Su na tunkarar gidan, amma raƙuman na ƙara yawa, Nana ta fahimci ita kaɗai take ganinsu, su ba sa ganinsu. A haka har suka ƙarasa ƙofar gidan, Ko da su ka shiga gidan, jikin Nana ya hau rawa, sai dai hakan bai hanata gode wa Allah da halin da ga tsinci kanta. Saboda yadda ta ga wasu a cikin mari su na hauka tuburan, ban da masu ciwon galhanga, shan inna da sauransu. Ɗaki ɗaki ne a gidan, ma'aikatan gidan, duk su na sanye da jajayen kaya, kamar ma'aikatan jinya a asibiti. Hankalin Nana yayi mugun tashi, da ta ga ana yi wa wasu daga cikin marasa lafiya sakiya. A saka kibiya a cikin magani, sannan a sakata a cikin wuta, sai ta yi ja sannan a soka a gurin da yake da larura. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, hankalinta yayi mummunan tashi. Su na ƙoƙarin shiga ƙofar da za ta sada su, da ainihin gurin da mai maganin yake ganin marasa lafiya, idon Nana ya sauka a cikin na ɗaya daga buzaye ukun da suke ƙoƙarin fitowa daga cikin gurin. Ji ta yi tamkar an watsa mata wuta a cikin idanunta zuwa jikinta, ƙara ta saki ta dafe kanta ta faɗi a gurin. Taku uku ya yi, ya ja ya tsaya ya waiwaya ya kalli gurin da Nana ta faɗi. Habu ya kama hannunsa suka yi waje. Ma'aikatan gurin, su ka zo su ka ɗaga Nana, su ka shiga da ita gurin mai magani, su Baba su na biye da su. Mai maganin ya fito sanye da rigar fatar damisa, sai warki a ƙugunsa idanunsa Jawur tamkar garwashi, baƙi ƙirin da shi. Da sauri ya ƙarasa kan Nana, tamkar likitan da aka kawowa mara lafiyan da yake buƙatar agajin gaggawa. Ya sunkuya a kanta yana kallonta sai kuma ya ɗago a gigice ya ce "Baushe, maza bi buzayen nan ka dawo da su, wataƙila ga makarin na sa ciwon a nan, maza hanzarta kar su tafi" Su Baba dai su ka tsaya sororo su na bin sa da kallo. Nana kuwa tari ta hau yi, tamka ƙirjinta zai buɗe, ganinta ta yi a cikin ƙura, ko tafin hannunta ba ta iya gani saboda yadda ƙurar ta turnuƙe gurin. Bayan wani lokaci ƙurar ta lafa, ta ɗaga kanta ta na kallon gurin, ita kaɗai ƙwal a cikin sahara. Waige-waige ta hau yi, sai dai babu tsammani ta ga mutum a tsaye a bayanta, sanye da baƙin rawani da shigar fararen kaya na buzaye, hannunsa riƙe da akalar raƙuminsa. Sai dai duk ƙoƙarin Nana a kan ta gane kamaninsa, abu ya gagara fuskarsa a rufe take da rawani. Miƙa mata hannunsa yayi, mai ɗauke da dogwayen yatsu. Duk da a tsorace take, ta fara takawa a hankali, har ta ƙarasa gurin da yake, ta miƙa masa nata hannun. Yana kama hannunta, ta ji an zuba mata ruwa mai matuƙar sanyi a jikinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke, tare da buɗe idonta. Su Baba ta gani a zaune tsuuruu, kamar mara gaskiya a hannun hukuma. "Sannu Nana Asma'u" mai maganin ya yi maganar cikin sakin fuska. Nana ta tashi zaune, ta koma jikin Baba, tana jin yadda haryanzu jikinta yake a sanyaye. Mai maganin ya zura mata ido, sannan ya sake murmushi ya ce "Manya gatan wasa, wa ya isa ja da ku, idan ba wawa ba? Tuba nake uban duƙusa" dubawa Nana take ta ga da wa yake. Ya ci gaba da cewa "Asma'u, ki na ganin wani mutum a mafarki, ku na magana ko?" Nana ta yi shiru ba ta ce komai ba. "Za ki iya tuna me da me yake ce miki?" Still ta yi shiru ba ta yi magana ba. Ya sake murmusawa ya ce "Malam, gidanmu wanzamai ne, na kuma yi ƙarfa-ƙarfa a kan farauta, duk da mahaifiyata sun gaji farauta . Na daɗe ina hatsabibanci, har na zo na fara bayar da magani, na daɗe ban ga abin mamaki ba kamar yau. Aljanin da yake ɗawainiya da yarinyarka hadiminta ne, tun zamanin kakaninka ai 'yan bori ne. Kuma tun daga kansu ba a kuma samun haihuwar mai irin tauraronta ba, sai da aka haifeta dan haka dole ya yi mata hidima, ita kuma taƙi yadda shiyasa yake ta azabtar da ita. Duk ba wannan ba yanzun nan aka tafi da wani buzu, shi dama na gaya musu ba ni da maganin larurarsa, sai dai a shigowar ku, na ga wani abin mamaki da na daɗe ban gani ba, ina kyautata zaton wataƙila maganin nasa ciwon na da alaƙa da nata. Kodayake ba a kan wannan gaɓar muke ba. Yanzu ita Nana Asma'u za ku bar ta a nan, sai bayan kwana goma sha huɗu zaku dawo, aljaninta sai dai ayi sulhu da shi idan aka takura shi, ba ita ba ni kaina zai iya halaka ni." Kallonsa Nana tayi, gaba ɗaya maganganun mutumin nan ko gaske ne, mushiriki ne shi ma, jira take ta ji me su Baba za su ce, ko me za ayi ba za ta yarda a bar ta a gurin nan ba. Baba ya ce "Mu tafi mu bar ta har mako biyu kuma, itakaɗai?" Gaddafi ya ce "Ba magani ake mema ba? Ma samu mu huta kwana biyu mu ma, da wannan tamɓelen da take yi ai gara a batta ɗin, Allah ya kaimu makwanni biyun" Yanayin Baba ya nuna ba haka ya so ba. Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ta ji kamar an saka dutse a maƙogwaronta, tayi tayi amma magana ta gagara. Ta dage iya ƙarfinta ta miƙe tsaye, amma jiri ya kwashe ta, tana ji tana gani, masu jajayen kayan nan, suka zo suka ɗauke ta, tana fizge-fizge tana komai aka kaita wani ɗaki aka kulle. Littafin BUZU 1k ne a telegram. 0069685771 Aisha Adam Stanbic ibtc Sai shaidar biya https://wa.me/2348081012143 Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM AYSHERCOOL YOTA/002 (Bright pens 3rd batch) P12 Imaran tun yana jiran dawowar su Baba da daɗin rai, har ransa ya gama ɓaci, zuciyar sa ta din ga tafasa. Mama kuwa tuni ta din ga kiran 'yan uwanta tana gaya musu, abin da ya faru da Suwaiba. Suwaiba kuwa ko a jikinta, sabgoginta kawai take yi. Ƙarshe ma da yamma, ta sha wanka za ta fita zance, ta ga turaren nan a kan kayan Nana, ta ɗauki abin ta ta ƙara fesawa ta fice. Bayan sallar magariba, Imran yana zaune a waje, sai ga taxi har ƙofar gidansu, su Baba sun dawo. Bai motsa daga gurin da yake ba, sai da ya ga duk sun fito daga motar, amma babu Nana. Su na shiga gida, ya tashi ya bi bayansu. "Wai ina Nanan take? Ya ku ka dawo babu ita?" Daga Baba har Gaddafi babu wanda ya kula shi. Ransa ya fara ɓaci ya ce "Baba ka yi magana, ina ku kai mini Nana?" "Tana gidan Atine" ya bashi amsa a gajiye, saboda sun kwaso gajiya. "To me yasa za a kaita gidan Yaya Atine? Me yasa ba ku dawo da ita gidan nan ba?" Ganin Baba ba zai ba shi cikakken lokacinsa ba, balle ya yi masa bayani, kawai ya fice ya nufi gidan Yaya Atine. Yaya Atine, ta mimmiƙe tana cin tuwon dare, saboda wahalar da suka sha. Kamar an jefo Imran ta ji sallamarsa. Ta amsa masa, ba tare da ya ko gaisheta ba ya ce "Ina Nana?" Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Nanan?" "Baba ya ce mini tana gidan nan?" "Kuma saboda rashin ɗa'a, ko gaishe ni ba za ka yi ba, ka zo kana tambayata wata Nana, to mun sayar da ita" Ya ce "Yi haƙuri, a ruɗe nake ne" Yaya Atine ta ce "Ba wani haƙuri da zan yi, gidan uban wa ka tafi tsawon shekarun nan?" Duk da ya fara ƙuluwa ya maze ya ce "Kudu na tafi neman kuɗi, tana ina?" "Kai ban sani ba, ni ba ta gidan nan, ka koma ka tambayi uban naka" Imran ya kalle ta ya ce "Kamar yaya? Shi fa ya ce mini tana nan" "A'a tana gidan mai magani, sai nan da mako biyu za aje a taho da ita" Ashar Imaran ya yi ya ce "Wane irin magani ne, sai an kai mutum a baro shi, to ai ko asibiti ana barin ɗan jinya, balle wani shashasha da bai shiga aji ba, aje a ajiye masa yarinya shi ba muharamminta ba". "To ai ubanka za ka je ka yi wa ba ni ba. Kuma ba fin mu hankali da tunani ka yi ba, gurin akwai ma'aikata mata da suke kula da mata marasa lafiya " Imran ji ya yi kamar ya kifa wa yaya Atine mari, wannan ai ganganci ne da rashin hankali. Takalmansa ya shura, ya fita daga gidan zuciyarsa kamar ya fashe saboda takaici. Gida ya koma cikin takaici, sai dai ya tarar Baba baya nan. Labarin mutuwar malam Auwal ya karaɗe ciki da wajen unguwar su Nana, saboda an san shi sosai, saboda ya kan ja salla a masallatai daban-daban. Ga koyarwar da yake yi a islamiyya, kowa yayi masa shaidar mutumin kirki ne shi. 'yan unguwa suka yi alwashin tsayawa tsayin daka, gurin bibiyar jam'i an tsaro da tabattar da an kama waɗanda suka aikata masa haka. Cike da jimami Nasir ƙanin su Nana yake ta nanata mutuwar malam Auwal, ya ce "Allah sarki Nana, ko ya za ta ji idan aka ce mata malam Auwal ya mutu an kashe shi?" Duk da Baba yana cike da takaicin wasa da hankali da malam Auwal ya yi masa, na ƙin fitowa ya auri Nana, amma hankalinsa ya tashi bayan dawowarsu daga kai Nana gurin mai magani ya samu labarin mutuwar. Yana tsaka da jimamin mutuwar, ana tattaunawa a masallaci bayan sallar isha'i, Nasiru ya zo ya kira Baba ya ce ana nemansa a gida. Ko da ya je gida, ya tarar an daddane Suwaiba, tana ta kurma ihun Nana na sha mata jini. Cikin kuka mama ta ce "Ka gani ko? Kalli halin da Suwaiba take ciki, wallahi an cuce ni ban yafe ba, kuma wallahi ko ka ɗauki mataki ko ni na ɗauka. Dan baƙin bala'i a gaban saurayi ta faɗi tana wannan kururwar fa" Cike da damuwa ya ce "Wai Rabi ya ki ke so na yi, ki na gani domin neme wa Nana magani, a can gurin mai magani na baro ta, kuma na ce a tafi da Suwaiban ki ka ƙi yarda" "Ni wallahi ka san yadda za ka yi, dan ba zan yarda a kashe mini 'ya ba" Imaran ne yayi sallama, yana watso takalmansa da suka tsinke ya ce "Yauwwa Baba na je gidan Yaya Atine, ta ce Nana ba ta gurinta wai a gidan mai magani aka baro ta. Baba ko fa asibiti ana bar wa mutum ɗan jinya, ya za ayi a kaita gurin da babu idon wani nata da sunan neman magani? Ina ne gurin da aka kaita gaskiya zuwa zan yi na ɗaukkota" Baba bai yi magana ba, Suwaiba ta ci gaba da kakari "Baba ku taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take lasa tana sha, dan zatin Allah ku hanata jikina zafi yake yi mini" Imran ya ce "Wace Nanan? Nanan da bata gidan nan?" Mama ta ce "Amma dai a yanayin da take ba za ta yi wa Nana ƙarya ba" Imran ya ce "To Nana dai ba mayya ba ce, abin da ku ke zunɗenta ne Allah ya jarrabe ku. Ni dai dan Allah Baba ka gaya mini in da ku ka kai Nana, ni fa hankalina ba zai kwanta ba ina nan tana wata uwa duniya da ban sani ba" A fusace Baba ya ce "Ban sani ba, ba zaka iya rayuwa tana wani guri ba, da ka tafi gantalinka shekara nawa tana nan ka na can gantalinka?" Cike da ƙwarin gwiwa Imran ya ce "Amma ai na san tana gida a gabanka, ni gaskiya ban ji na gamsu da wannan tsarin ba" Ga dai Nana ba ta gida, amma yadda suka ga rana haka suka ga dare, Suwaiba na ihun Nana na sha mata jini. **** A hankali Nana ta ja jikinta ta zauna, duhu kawai take gani ba ta iya gane komai, ko tafin hannunta ba ta gani. Ta shafa bayanta ta ji alamun bango, ta ja jikinta ta jingina da bangon tana sauke ajiyar zuciya. Cikin damuwa ta haɗa kanta da gwiwa, zuciyarta sam babu daɗi yau kuma nan Allah ya kawo ta. Jin ƙarar buɗe ƙofa, ya sanyata ɗago kanta. Wasu mata ne biyu sanye da uniform su ka shigo ɗakin. Suka bubbuɗe tagogi sai ga haske ya ratso ɗakin. Duk da yanayin hasken ya nuna rana na daf da faɗuwa. Ɗaya daga cikin matan ta ce "Ta ce taso" babu musu Nana ta tashi, ta bi su suka fita, sai ta ga kamar ba gidan da aka kawota ba. "Za ki yi salla ne?" Ɗaya daga cikin matan ta tambayeta. Da sauri ta jinjina kai alamar eh. Aka janyo mata ruwa a rijiya, aka nuna mata banɗaki. Ta yi alwala ta fito aka mayar da ita ɗakin nan ta yi salla. Su na tsaye su na jiranta kamar wata fursina, wata matar ce daban, ta shigo ta kawo wa Nana abinci da ruwa pure water. Nana ta kalli Abincin gasashsen nama ne, amma ta kawar da kai. "Ki ci abinci mana" matar ta yi magana cikin kulawa. "Na ƙoshi" ta faɗa a taƙaice. Babu yadda ba su yi da ita ba, amma ta ƙi ci. Har sai da ran ɗaya ya ɓaci, ta fice ta tafi gurin mai maganin. "Sarkin baka, yarinyar nan fa taƙi cik abinci" "Ahh haba dai? Ta tashi kenan?" "Eh tun ɗazu har ta yi salla ma" "Na fa gaya muku yarinyar nan ku lallaɓa mini ita, ba na buƙatar a takura mata, ko ɓata mata rai. A nemo Salamatu ta tura 'yar aike cikin gari, a samo mata wani abincin" rai a ɓace matar ta amsa da to ta fita. Nana tana zaune tana tunani, sai ga wata matar daban ta shigo da kayan saƙi shuɗaye a jikinta. Sallamar da ta yi Nana ta amsa tana bin ta da kallo. Cikin sakin fuska matar ta ce "Barka da yammaci baƙuwar sarki" Nana ta bi ta da kallo ba ta amsa ba. Ta ajiye wa Nana kwanuka, ta ce "Ga abinci an saka a canza miki" "Ina su Baba?" Salamatu ta ce "Sun tafi, sai nan da makonni biyu za su dawo" "Me yasa za su tafi su bar ni a nan? Ni gaskiya gida zan tafi" "To shikkenan, amma fara cin abincin tukuna" Da ƙyar Salamatu ta lallaɓa Nana ta ci abinci, shi ma don tana jin yunwa ne sosai shi ya sa ta ci." Nana ta riƙe alwalarta, a nan ɗakin ta gabatar da sallar magariba, sai dai tsoro ya fara kama ta, ganin ɗakin ya yi duhu babu haske kuma ita kaɗai a ciki. Ba a jin amon kiran salla, sai dai ta kintaci lokaci kawai. Ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, ta rintse idanunta tana ta adduo'in da suka zo bakinta. Tana ji ana sallama, amma ta kasa ɗagowa, sai da aka taɓa ta sannan ta ɗago a razane tana sauke numfashi. Salamatu ce ta shigo da fitila, da kuma kayan abinci. Ta ce "Yi haƙuri, na tsorata ki ko? Ga abinci ki ci, ga kuma fitila idan ki na buƙatar mai taya ki kwana kuma sai mu kwana tare" Cikin damuwa Nana ta ce "Ni ba na buƙatar komai, gida nake so na tafi" "Haba Nana, ba kya so ki samu lafiya ki rabu da abin da yake damunki ne? Magani za ayi miki, babu wanda zai cutar da ke" ta daɗe tana rarrashin Nana, tana kwantar mata da hankali. Ta ɗan ci abincin sannan ta kwanta, tana ta adduo'i. Ji ta yi sanyi ya dame ta, ta dunƙule guri ɗaya, amma ba ta daina jin sanyin ba har cikin ƙasusuwanta, ta juya domin ta gyara kwanciyarta kawai ta ganta a cikin Sahara itakaɗai. Ga dare, sai dai farin wata ya haske saharar, sai wani irin sauti da kunnuwanta ke ji, kamar na tasowar guguwa amma ba ta san daga ina sautin yake ba. A tsaye ta ganshi a cikin saharar, a wannan karon ma fuskarsa a rufe a cikin rawani, sai dai a wannan karon dogo ne sosai fiye da kima. A hankali gurin ya ƙara haske duhun ya ƙara raguwa. Sai kuma ta ga tsayin yana raguwa har ya dawo na daidai mutane, ya saka hannu ya warware rawaninsa. Ƙaisar ta gani a tsaye, duk ba ta iya ƙare masa kallo, amma yadda yake bayyanar mata a mafarki cikin suffar mutane shi ta gani. Ta buɗe baki za ta yi magana, ya fara rikiɗewa ya zama tsoho tukuf, tun da Nana take a doron duniya ba ta taɓa ganin tufa kamar wannan ba, gashin kansa yana jan ƙasa fari ƙwal da shi, ga wasu irin kaya masu kama da yanar gizo gizo a jikinsa saboda tsabar tsufa. Nana ta fara ja da baya a hankali, zuciyarta na hakaito mata addu'a, amma ta kasa furtawa. Ya sake girgiza ya koma wani baƙin raƙumi mai muni, ya buɗe bakinsa ya fara feso mata wuta. Da wani irin gudu Nana ta juya, tana ihu, ma'aikatan gidan suka rirriƙeta. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Baba ka yi mini addu'a, wayyo Babana, baba Imaran, Jamila dan Allah ku yi mini addu'a na kasa yi" Cikin damuwa Salmatu da ke riƙe da Nana ta kalli mutumin da ke tsaye a kan Nana yana kallonta ta ce "Sarki ka yi wani abu a kan lamarin nan, kar fa ƙwaƙwalwarta ta taɓu" Ya durƙuso yana haska fuskar Nana ya numfasa ya ce "Ni na san za a rina. Salamatu" Ta amsa da "Na'am sarki" "Idan kin ji ana zaki bari, damisa bari faɗanku na manya wa yake shiga, sai wawa sai mahaukaci, to wannan rigimar ce. Wannan yarinyar da ki ke gani ban san ta ina zan fara yi miki bayani a kanta ba. Dole jikinta ya ƙara rikicewa saboda haɗuwarta da buzayen nan. Da ba su riga sun tafi ba, da ƙarshenta a cikin su ɗaya ya samu waraka ɗaya kuma ya mutu a haka tsakanin ita da Buzun" "Sarki ka ƙara rufe mini kai na, ban gane me ka ke nufi ba" Ya yi murmushi ya ce "Da ina buƙatar ki gane, ai gwari gwari zan yi miki salameme. Ya saka yatsunsa biyu a goshin Nana, take ta yi shiru bacci ya kwashe ta. **** Sosai Imran yake nema ya hana kowa zaman lafiya a gidan, saboda rashin Nana, ya kaɗa ya raya Baba ya ƙi gaya masa gurin mai maganin da aka kai Nana. Ɓangaren Suwaiba ma abin nata gaba yake yi, sai ana zaune lafiya, sai ta yanke jiki ta faɗi tana kururwar Nana na sha mata jini. Babu shiri Mama ta ce dole ta fita nema wa Suwaiba magani, kafin Nana ta kashe ta. Baba ya ce ta bari a kai ta gurin da aka kai Nana, amma fafur ta ƙi yarda. Washegari, bayan Nana ta idar da sallar asuba, Salamatu ta zo. A duk lokacin da ta zo gurin Nana, cikin sakin fuska da fara'a take yi wa Nana magana, hakan ya saka Nana ta ɗan fara sakin jiki da ita kaɗan, duk da ba magana take yi mata ba. "Nana taso mu je ko" babu musu ta tashi ta bi Salamatu. Suna fita daga ɗakin, ta tuna mafarkin da ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, ta fara karanto addu'oin da Malam Auwal yake bata. A take ya faɗo mata a rai, har yanzu tana jin kewarsa sai dai a wannan karon, jikinta ne yayi matuƙar sanyi. Salamatu na gaba tana biye da ita, sai da suka ɗan yi doguwar tafiya, sannan ta fuskanci a cikin gidan da aka kawo ta neman magani suke. Ta ga yadda ake jere masu taɓin hankali, wasu a cikin mari aka ba su abincin safe, lafiyayyen kunu da ƙosai. Gaba ɗaya suka zuro wa Nana ido. Masu ɗan sauran hankalinsu, su na ta gaida Salamatu tana amsa musu cikin sakin fuska. Masu rashin ji a cikinsu, su ƙi cin abinci, su na ganinta suka kama kwanukan abincinsu. A gaba kaɗan kuma ɓangaren ƙananan yara ne, masu larurar ƙwaƙwalwa, da ake iƙrarin aljanu ne su ka sanya musu. Wasu ɗauke ciwukan da a turance ake cewa (Down syndrome, autism, poliomyelitis) da sauran su wato masu shan inna, galhanga da sauran su. Suka ƙara yin gaba, suka ɓullo gurin da ake Sakiya, kamar yadda ta hango jiya da suka zo. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta yau ma kibiya ake sakawa a cikin magani, sai a ciro ta a saka a cikin wuta, ta yi jawur, aka ciro ana sokawa a cikin wani mutum da cikin ya kumbura tamkar zai fashe. An tara wata tasa wani irin koren ruwa yana kwararowa daga cikin nasa mai azabar wari. Mutumin yana zaune, tamkar ba cikinsa ake hudawa ba. Salamatu ta ce "Tsoro ki ke ji har haka? Sun je Asibiti aka ce hantarsa ta lalace, sai dai ayi masa dashen wata, su kuma iyalansa ba su da hali, aka kwatanta musu nan. Lokacin da aka kawo shi, ko tafiya ba ya iya yi, yau satinsa guda a nan yana iya takawa" Cikin damuwa, a kuma karon farko Nana ta yi mata magana kai tsaye ta ce "Ba ya jin zafi kuma? Da me zai ji? Zafin wuta ko ciwon, ko kuma huda shin da ake yi, idan ya mutu fa?" Salamatu ta yi murmushi ta ce "Ai ba da ka muke aikin ba, kamar yadda asibiti suke da anesthesia, magunguna da alluran kashe zafi, mu ma mu na da su, irin namu na gargajiya, ba ya jin komai. Ilimi ne ya bawa likitoci damar sanin cuta da magani mu ma kuma haka" Nana dai ba ta gamsu ba, ta ji ne amma ba ta yarda ba. Sai yanzu take jinjina girman gidan, su shiga nan su ɓulla can, ko ina ɗaki-ɗaki ne na marasa lafiya a gidan. Wata ƙaramar ƙofa su ka shiga, amma ta ga sun fito wani katafaren ɗaki ƙato, ba wai kayan alatun zamani ne a ɗakin ba, kawai dai an tsara shi ne. Ta kalli ƙasan ɗakin, an rufe shi da fatar dabbobi daban-daban, wata ta gane ta wace dabbar ce, wata kuma ba ta gane wacce ce ba. Hatta jikin bangon ɗakin, an yi masa ado da fatar dabbobi, ta damisa kawai ta iya ganewa da kura, su ma dan tana gani a tv ne wasu lokutan. Ga kuma ƙahunhunan dabbobi su ma, an ƙawata ɗakin da su, sai kuma jakunkunan fata suma duk an rarrataye su a ɗakin. Ga curin layoyi su ma duk an yi musu guri a ɗakin. Yana zaune a kan wata karaga, mai ɗauke da ƙwarangwal ɗin kawunan zaki, bayan karagar kuma an yi mata ado da kawunan macizai. Nana ta yi tsuru, tana tunanin anya ma a zahiri take, ko dai kawai tarkacen mafarkin da ta saba yi ne. Tasowa yayi jikinsa sanye da kayan fatar giwa, yana faɗaɗa murmushinsa ya ce "Barka da zuwa baƙuwa ta mussaman, lale da ke" Nana ta yi shiru tana kallonsa, duk da ta gane shi, lokacin da aka kawota ta ganshi, amma ba a wannan ɗakin ba, kuma yau baƙinsa ya ragu. Salamatu ta ce "Sarki ga ta na kawo ta, ta tashi lafiya ƙalau" Ya ce "Alhamdilillah Allah abin godiya, Nana Asma'u na san kin gane ni, amma ba ki sanni ba, ni ne Garba mai tagwayen baiwa, Sarkin bakar ƙasar hausa, kuma ana yi mini take da Garba ga baka ga aska. Salamatu ba ta abin zama". Salamatu ta zura hannu a wata 'yar ƙaramar jakar fata, ta  janyo wani abu da Nana ba ta gane ko mene ne ba, shi ba kujerar tsuguno ta mata ba, shi dai ga shi nan. Tana tsaka da kallon abin ta ga yana motsi, ta ƙura ido kawai ta ga kan kunkuru ya leƙo ashe kunkuru aka ba ta a matsayin abin zama. Babu shiri ta doka tsalle ta ja gefe tana kallon kunkurun. Sarkin baka ya bushe da dariya, ya ce "Tuba muke, mu je ki ga yadda muke gudanar da ayyukan gidan, ko kya saki jiki ayi abin da yakamata" Wata mata ce ta faɗo ɗakin babu ko sallama, bafulatana doguwa mai tsayi fiye da kima. Tana shigowa Nana ta ji zuciyarta ta yi wani irin gigitaccen bugu, da sai da ta zata mutuwa za ta yi. Matar ba ta ce komai ba, ta shirya ƙorran da ta shigo da su a wata ragaya. Sarkin baka ya ce "Idan kin gama, ga saƙonki can" bafulatanar ba ta ce komai, ta buɗe wata randa ta ɗebo wani baƙin abu ta sha, ta zo za ta wuce Nana ta fita, Nana ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fice daga ɗakin. "Asma'u kin ga matar da ta shigo ne?" Nana ta jinjina masa kai jikinta yana rawa. "Me ki ka gani a tare da ita?" Da ƙyar Nana ta ce "Ba ta da ƙafafuwa, a kan iska take tafiya" tayi maganar bakinta yana rawa. Ya ɗan yi shiru, Salamatu ta ce "Ya buɗe mata ido kenan tana ganin komai" Sarkin baka ya jinjina kai, ya ce "Taho muje" ya tashi ya yi gaba su ka bi shi a baya. Wani guri suka nufa, sai da suka je daf da wata ƙofa, ta fara jiyo ihu mara daɗin ji. Ya buɗe ƙofar ya shiga, sai dai Nana ta kasa shiga. Salamatu ta ja hannun Nana da ƙarfi, su ka shiga, sai gurin ya rikiɗewa Nana tamkar a film, mahaukata ne a ɗaki-ɗaki, tamkar a prison, su na ta kurma ihu sai ta ga ashe waɗanda ta gani da farko ba hauka suke yi ba, wannan ne masu yin hauka na gaske. Tamkar shirin fina-finan zombie, haka suke ihu su na ziro hannayen su. Nana tsigar jikinta ta din ga tashi, tana jin tamkar ita ma ta fasa ihu saboda rawar da jikinta yake yi, da wani irin azabar ciwo da kanta yake yi. Hatta haƙoranta da laɓɓanta rawa suke yi, ya yin da sautin ihu da kururwar mahaukatan, ya ci gaba da amsa kuwwa a cikin kunnuwanta, ta rintse idanunta tana sauraron bugun zuciyarta a cikin kunnuwanta dummm dummm da ƙarfin gaske. Tsawa Nana ta yi hakan ya sanya gaba ɗaya su ka yi shiru, su na kallonta, tamkar an yi ruwa an ɗauke, a hankali ta buɗe idanunta domin ta ga tsawar da ta yi ce ta sanya su yin shiru, ko kuwa?. Sai dai ta ga tabbas ita ɗin ce ba wani ba. Sarkin baka ya kalleta tare da sakin wani irin ƙasaitaccen murmushi da shikaɗai ya san ma'anarsa. Wannan littafin 1k ne a telegram, ta wannan account ɗin 0069685771 Aisha Adam stanbic ibtc bank Sai shaidar biya ta 08081012143 Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM (AYSHERCOOL) YOTA 002 P13 Ya sake duban Nana ya ce "Manya gatan wasa, uban duƙusa uban haɗari, ai shikenan tun da haka zamu yi da kai" Ya yi gaba yana ci gaba da murmushi, ya din ga bayar da umarnin abin da za a yi wa marasa lafiya, tare da yi wa Nana bayanin aljanun da kowanne yake ɗauke da shi, da dalilin da yasa ya kama mutum. Nana ta sha mamaki, wasu a dalilin harkar bokanci, da ta'amalli da aljanun ya sanya suka haukace, wasu kuma sun yi ƙoƙarin amfani da aljanun ne dan su yi kuɗi, su ma suka haukata su. Wasu kuma sharuɗɗan da aljanun suka saka musu, suka gaza cikawa ya sanya suka haukata su. Ya nuna mata wasu hamashaƙan 'yan kasuwa ne, da masu kuɗi a ka yi musu sihiri da aljanun da suka haukata su. Babban abin da ya bawa Nana tausayi, har da wata matashiyar budurwa, da ta zubowa Nana ido, tamkar ta haɗiye ta. A hankali Nana ta taka ta nufe ta. Ta zuro hannunta ta tsakanin ƙofar ɗakin, tana miƙowa Nana. Nana ta miƙa mata nata, ta din ga shafa hannun Nana sannan ta ce "Kin san tazarar da ke tsakanin ƙasa da iya gejin da jirgi yake zuwa a sama? Nigeria mu na da tarin karatu, goyon bayan ƙasar mu kawai muke buƙata, mu je in da zato bai taɓa zato ba. Ina da burin ina raye kafin na mutu, na kasance cikin waɗanda za su ƙera wa Nigeria jirgin sama nata na kanta. Dan Allah ki saka baki na je ƙaro karatun nan, na warke fa ki ce ya sake ni" ta yi maganar tana kuka. Sarkin baka ya ce "Kubra Yusuf, in sha Allah burin nan naki zai cika da zarar kin warke" Cikin kuka ta ce "Ai na warke dan Allah ka kira Daddy a mayar da ni gida na tafi karatun nan, kar na yi missing Flight" Cikin damuwa Nana ta ce "Dan Allah a fito da ita daga ɗakin nan, kamar ta warke fa" Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Ai ba da baki ake gane wanda ya warke ba, yanzu ana buɗe ta, sai ta kusa hallaka ki a gurin nan. Ainihin ta 'yar makaranta ce, degree ne da ita a engineering, kuma ita ce overaller a department ɗin su. Ta fita da makin da ba a taɓa samu ba a tarihin department ɗin su. Gwamnatin tarayya ta biya musu kuɗi su je su ƙaro karatu a kan fsahar ƙere-ƙere su biyar, ita kaɗai ce mace daga arewa. Shi ne aka yi mata asiri da wani baƙin aljani, aka ba shi jinin mutum, ta taso daga makaranta ta ba shi sadaka, shi yake ta azabtar da ita, a hakan ma zamanta a gidan nan, an rage ƙarfin tasirinsa. Cikin tausayawa Nana ta din ga kallon yadda ta koma gefe, ta zauna tana ta kuka da ƙarfinta. Haka suka wuce ta. Bayan sun baro gurin, suka tafi wani guri, shi kuma jarirai ake kawo wa sabuwar haihuwa, domin yi musu aski, kaciya da cire beli. Idan sarkin baka ya dunƙule hannunsa, yana buɗewa sai ka ga aska, ya yi siddabarunsa ya shafa kan yaro da askar, sai ka ga ya cika hannunsa da gashin yaro. Idan ya shafa aska a wuyan jariri, sai dai ya zira hannu a bakin yaro, ya ciro wata tsoka har ya cire belin. Haka kaciya, sai dai da gashin jariran, da belin, duk a cikin jakar zabirarsa yake zubawa. Sannan ya kan kama hannun yaran, ya ɗaura musu laya, ko ya sanya musu tagulla. Ya kalli wata mata ya ce "Ahh hajjaju an sauka ashe?" Ta washe baki ta ce "Wallahi sarki, gobe ma suna" Ya kalli yaron, da fatarsa duk ta yamutse ya ce "Ke ya aka yi ki ka bari mayya ta kama miki ɗa? Tun yana ciki matar da ta aiko miki da kunu, ki ka sha ta kama miki ɗa" Cikin damuwa matar ta ce "Innalillahi wa innalillahi raziƙuna, wallahi sarki ka ga ba ya gaba yaron nan, kullum cikin kuka ba ruwan nono na rasa yacca zan yi ohh ni Sakina, amma Allah ya isa wallahi" Daga yadda matar ta faɗi Innalillahi, Nana ta ƙara tabattar da jahilci a gurin matar, yadda suke ba wa maganganun sarkin baka ammana ba tare da musu ba har mamaki yake bata. Ya faɗi maganin da za a bata suka yi gaba. Wani guri suka shiga, shi kuma masu ciwon suga ne, ya yi musu ya jiki suka amsa. Bayan sun gama gaisawa ya kalli masu kula da su, ya ce "Yauwwa, kar a kuskura a karya dokokin da na saka, da sassafe kafin su ci komai a ba su magani, a basu zuma cokali biyu da garin habbatussauda, sai su karya kumallo da ruwan dahuwar yaɗiya mai ɗumi, sannan su ci ganyenta. Da rana a basu faten dankalin turawa da alayyahu, a sake basu zuma da habbatussauda, sai da daddare a ba su gurji da kwaɗon rama, sai a sake ba su magani. Yau maganin cikin ɓawon gyaɗa bibbiyu za a zuba musu a ruwa su sha. Shi ne jadawalin abincin da za a ba su yau" ma'aikatan suka amsa masa da to. Nana kuwa rasa bakin magana ta yi, sai kallon ikon Allah, tamkar likita a asibiti da marasa lafiyar sa. Sun zagaya sosai da sosai a cikin gidan, sannan suka koma wancan ɗakin da suka tarar da shi da farko. Bayan sun shiga, ya zura hannu a cikin zabirarsa ya din ga zaro gashin jariran nan, da belin da ya din ga cire musu, yana tarawa a cikin wata tasa, sai da ya cikata taf. Ya dubi Salamatu ya ce "Salameme zuba wa Fulani a randarta" Salmatu ta karɓa, ta je ta buɗe randar da bafulatanar nan ta ɗqzu sha wannan baƙin abun ta juye a ciki. Ya kalli Nana ya ce "Za ki iya tuna daga wani lokaci, ki ka fara ganin uban duƙusa a bacci?" "Waye hakan?" Nana ta tambaya cikin rashin fahimta. "Aljanin da yake zuwar miki" "Wai ƙaisar?" Ya yi murmushi ya ce "Shi" "Ba zan iya tunawa ba" ta bashi amsa. "Ina kallonsa a tare da ke ɗazu, shi ya yi wannan tsawar mahaukatan nan suka yi shiru, so nake ya bayyana a jikinki mu yi magana da shi, amma yaƙi. Masu ihun nan da ki ka gani, duk masu baƙaƙen aljanu ne masu taurin kai, wanda ko an ba su magani, suke lafawa su dawo daga baya. Nan gurin ɗaure su na yi, nake hukunta su da azaba kala-kala, a matsayin gargaɗi da kashedi. Akwai hayaƙin da ake yi musu safe da yamma an gama hayaƙin muka je, amma ƙaisar ya ƙi bayyana. A duniya aljanun da suke irin sa ba su da yawa". Nana ta yi tsuru tana kallonsa da saurarensa, tare da kallon maganganun sa a matsayin soki burutsu. "Amma ke me yasa ba zaki yadda ki karɓi abin da yake gadonku ba, ki ka gwammace ya yi ta azabtar da ke?" Take Nana ta tsuke fuska, ta tsani ta ji an danganta ta harkar bori da gadonsu, kamar wani abin arziki. "Ni ba zan yi shirka ba" Sarkin baka ya ce "Ba shirka ba ce ba, bayar da magani, idan bayar da magani shurka ne, Asibiti ma shirka suke yi. Ki amince sai mu haɗu mu ci gaba da gudanar da taimakon al'umma" Ta girgiza kai ta ce "Ni ba zan yi ba ba na so" "Anya? Ki yi tunani kar ki zo nan gana kina nema ido rufe fa" tayi shiru ba ta yi magana ba. "Salamatu mayar da ita ɗakinta, a bata abinci, idan tana buƙatar wani abin a bata" Salamatu ta jinjina kai, daga nan ta jagoranci Nana suka bar ɗakin. **** Zaune take a katafaren falonta, ta hakimce a kan kujera tana amsa waya "Hajiya Sa'a, ya mu ka ji da iftila'in nan da ya tinkaro mu, coustom sun riƙe mana kaya a Abuja?" "Aikam, mu na nan muna ta up and down, Allah ya sa su sakar mana a kan lokaci" "Amin ya rabb, wallahi hankalina duk a tashe yake, na haɗa kuɗin mutane da jarina duk na zuba na sayo kayan nan, ni dai fatana Allah ya sa kar su yi condeming ɗin kayan nan wallahi ban san in da zan saka raina ba, ga mutane sun fara ƙorafi" Hajiya Sa'a ta ce "Ahha haba Sadiya, babu abin da zai faru fa, ki kwantar da hankalinki ki yi addu'a" "To shikkenan Hajiya, na gode sosai da sosai" bayan sun yi sallama, Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta kalli maman khairat ta ce "Safiyya mutuniyarki ce fa, Sadiya" "Ohh Allah sarki" "Duk hankalinta a tashe yake, batun kayan da coustom suka riƙe, ni ba ta son ko kaɗan kayan nan ba a gabana suke ba" Safiyya ta yi dariya ta ce "Haryanzu ita kanta a tukunya yake kenan, ba ta san dawar garin ba?" "Ina fa ta sani, a zatonta business yake tara mini kuɗi, duk wannan abin shige mini take son yi, ta ji sirrina". "To hajjaju a shigo da ita sabgar mana" Cikin sauri ta ce "A'a tana da surutu, ga ƙaryar riƙon addini, kin san kuma ƙa'idarmu, muddin aka samu mushikila akwai matsala. Ai zatonta business ɗin nan na riƙe, har take neman yin takar da ni a wasu abubuwan. Ba ta san kare yawa ne kawai ba, da kawar da hankalin mutane". "Gaskiya ne, sabgar tana buƙatar sirri sosai" "Safiyya kin ga an sake samun matsala, yarinyar ba ta yi amfani da turaren nan ba, wanda ya yi amfani da shi daban, ya ce wani aljani ne a kan yarinyar hatsabibin gaske ba zai bari komai ya yi tasiri ba. Kuma wallahi ya tabbatar mini idan aka yi amfani da jininta, za a samu alkhairi sosai taurarinta masu haske ne. Kuma idan aka yi wannan aikin ba za a ƙara bamu wani aikin mai wahala ba. Mun riga mun wuce gurin mun samu sa'a, sai da na ce anya ba sato ta zan saka ayi ba?" "Na shige su ni Safiyya, kuma Jamila ta tabattar mini da ta ba ta turaren har ta na murna" "Wallahi ba ita ta yi amfani da shi ba, an yi amfani da turaren amma ba ita ba ce ba" "Kai wannan wace irin jaraba ce? Ga shi kuma wai ba ta nan an kaita gidan mai magani an barota a can" da sauri Hajiya Sa'a ta ce "Haba dai? A ina ne na ji ko da yadda za mu yi mu samu gurin?" Maman khairat ta ce "Wallahi ban sani ba, sai dai idan ta zo na tambayeta" "To ki yi mata cikin hikima dan Allah, ki nuna mata wata 'yar uwakki za a kai, kar mu bar wani trace da za a gane wani abu" "To shikenan hajjaju bari ta zo, it ma ina daf da jawota cikin ƙungiya, za ta yi mana amfani saboda tana da mugun kwaɗayi daga ita har iyayenta" "Aikuwa nima na gani, yanzu dai a far wannan ɗin" **** Ɓangaren Nana, ta ga abubuwan al'ajabi kala-kala a gidan sarkin baka. A kwana uku da ta yi, tana iya fita da kanta ta zagaya tana ganin marasa lafiya har ma ta yi magana da su, ta basu shawarar su din ga zuwa asibiti. Tana yawan zuwa ganin Kubra, sai dai yanayin da take tarar da ita a ciki, ba ya yi mata daɗi, saboda wataran da sauƙi wataran kuma hauka take yi tuburan. Kullum idan Sarkin baka zai zagayen ganin marasa lafiya, da waɗanda ake kawo masa su ganshi, tare yake yi da ita. Aka kawo wata mata da tsohon ciki tana tafiya da ƙyar, cikinta har rinjayarta yake yi, wai shekarar cikin goma a jikinta, wasu lokutan ya tashi, wasu lokutan ya kwanta a neme shi a rasa. Su na gama yi wa sarkin baka bayani, Nana tayi farat ta ce "Ba ku je asibiti ba?" "Mun je, duk gwajin da aka yi sai ace babu ciki" babar matar ta ba wa Nana amsa. Sarkin baka ya bushe da dariya ya ce "Asma'u ma'u, su Asibiti duk abin da suka zo muku da shi, za ku karɓa ku ce technology ne, mu kuma namu da muke yi, shi ne shirka a gurinki. Shi maganin baturen kin san da me da me ake haɗawa? Kin tabattar da ingancin halaccin sa a addinance? Shi fa ilmi siffa ce ta Ubangiji, kuma yana bayar da ita ga wanda ya so, bai keɓantar da baiwarsa ga farar fata ba kawai, ku baƙaƙen fata ne ku ka raina abin da Allah ya baku na ilmi, ku ka yi amanna da bature ne kawai ya iya" Ya mayar da hankalinsa kan mara lafiyar ya ce  "Hajiya a da idan ki na al'ada ba ruwanki, duk gurin da ki ka samu yarda ƙunzugun jinin ki ke yi. Da ƙunzugun jinin hailarki aka yi miki sihiri, saboda a raba ki da mijinki, idan ba ki manta ba, kin yi ta zubar da jini tun yana taya ki neman magani har ya gaji ya yi aure ya rabu da ke. Da ki ka ce ki na da ciki ma rigima ku ka yi ta yi ya ce ba nasa bane ba" cike da amanna ɗari bisa ɗari suka gazgata sarki. Nana ta ce "To kai ya aka yi ka sani, bayan baka nan aka yi?" Ya kalli Nana bai ce mata komai ba ya tashi ya nufi kan matar. Ya saka Salamatu ta ɗebo ruwan magani, aka bawa matar ta sha. Ya dunƙule hannunsa ya buɗe tafukansa aska ta fito, ya saka aka buɗe cikin matar, ya din ga yi mata ƙananan tsagu da askar. Wannan karon sanho ne a jikinsa, (jakar magunguna) zabira (Jakar wanzamai ta kayan aski) A wannan ƙaramar jakar, ya ciro garwashi jawur, ya ɗora a kasko ya zuba wani magani a kai. Take matar ta hau tari, ya kama cikin ya lailaya ya tattara shi guri guda, sai ga wani jini baƙi ƙirin guda-guda yana fitowa daga cikin. Sai da jinin ya gama fita, ya tattare guri guda ya zama wani baƙin muzuru. A take cikin ya baje, Sarkin baka ya danƙi muzurun ya jefa a cikin sanhonsa ya ce "Aljani ne yake ta yi mata wannan siddabarun. Salamatu a kaita gurin su 'yar ƙashi ɗaya, a tsumata zuwa jibi a sallame ta" Sai da Nana ta razana da abin da ta gani. Bayan fitarsu ya kalli Nana ya ce "Idan ki ka kuma ƙaryata ni a gaban mutane, sai na je na ɗaure ki a cikin mahaukatan nan kema" Nana ta ce "Amma ka ce ƙaisar ba zai kamu ba" Ya ce "Zai kamu, ban yi niyyar kama shi bane" Ta sake cewa "Amma ya ake ka ke wannan abubuwan haka? Ta ya ya ka ke sanin abin da baka nan aka yi?" "'yan aike ne suke gaya mini " "Aljnu kenan ko? Haramun ne fa hakan shirka kenan" "Ba shirka ba ne, taimakon al'umma muke yi" "Wallahi shirka ce, har fa tsafi ka ke yi " Dariya ya yi ya ce "A ina na yi tsafin?" "Ga shi nan ina gani kana yi, ya aka yi mage ya fito daga cikin mutum, kuma ya ake yi ka ke tura abubuwa da yawa a cikin 'yar ƙarama jakar nan?" Sarki ya ce "Aljihuna ne da yawa a cikin jakar" "To buɗe in gani" ya yi murmushi ya miƙa mata jakar ya ce "Buɗe da kanki" cike da ƙwarin gwiwa ta karɓi jakar, babu fargabar komai ta fara dubawa. Ya zuba mata ido yana dariya. Sai dai ta zazzage jakar babu komai a ciki. Ta kalle shi ta ce "Wallahi tsafi ne ina magen da ka saka a ciki ya tafi?" Ita kanta Nana tana mamakin yadda ta daina kewar gida gaba ɗaya, take jin kamar ta daɗe da sanin sarkin baka. "Idan kin yadda ki bayar da magani, zan nuna miki yadda nake komai, ki koma gida ki taimaki mutane" Ta girgiza kai ta ajiye masa jakarsa. "Ki je ki huta, anjima tare za mu fita farauta da ke, ki je ki yi bacci yanzu" Ta waro ido ta ce "Da wa za ayi farautar? Amma dai ba ni ba ko?" "Eh ba ke ba" ya bata amsa Ta juya da baya da baya, ta fita. Tana zuwa ɗakin da take, ta ga hayaƙi da wani irin ƙauri mara daɗi, cikin abin da bai fi mintuna uku ba, bacci ya kwashe ta. Da Ƙaisar ta fara tozali, zaune a kan wani dutse a cikin wani rafi, ya miƙe ƙafafuwansa a cikin ruwan masu azabar tsayi kamar itacen dogon yaro. Duk da ta riga ta saba da ganinsa, ba ta fiye razana dan ta gan shi ba, amma biyo bayan tuna mafarkin da ta yi da shi, a cikin sahara ya sanya ta zura da gudu tana neman hanyar guduwa. Ta yi gudu mai nisan gaske, ta ga wani gida, kawai ta faɗa gidan, tana addu'a a zuciyarta amma ta kasa furta ta, a bakinta. Sai dai bayan shigarta gidan, ta nemi hanyar fita ta rasa, kofofi kashi kashi a gidan, duk ƙofar da ta bi babu hanya sai dai ta sake dawowa guri ɗaya. Ta dinga buɗe ƙofofin amma ta rasa hanya. "Ina za ki ne?" Ya tambayeta bayan ya ajiye wata kwalba, jikinsa sanye da fararen kaya yana ɗigar da ruwa. "Yau kuma tsoro na baki? Ko ba ki yi zaton ganina yanzu ba?" Kuka Nana ta saka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, kar ka ƙona ni yau ma, dan Allah" "Yaushe na ƙona ki?" Nana ta ce"Ranar da ka zama tsoho ka koma raƙumi, ka yi haƙuri dan Allah" Ya girgiza kai ya ce "Ba ni bane" "Wallahi kai ne" "Ni ban yi wannan tsufan ba ai, ba ni bane" Cikin kuka ta ce "Kai na gani a sahara, ka zama raƙumi kana feso mini wuta" Ya sake cewa "Ba ni bane ba, tawagar buzayen da ki ka gani ne lokacin da ku ka shiga gidan. Ni ban yi wannan tsufan ba dudu sheruna nawa ban fi ɗari biyar da goma ba, yaro ne ni" Galala Nana ta saki baki tana kallonsa, shekara ɗari biyar da goman ne yaro. Tambayoyi ne fal a cikinta amma tana tsoron ta tambaye shi ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta. Ya ce "Kalli can" ta kalli gurin da ya nuna mata. Suwaiba ta gani tana ta ihu ana danneta, mama na kuka tana tofa mata addu'a, sai fizge-fizge take yi tana kiran sunan Nana. Cikin damuwa Nana ta ce "wai me ya sa take kiran sunana, ba fa ni ba ce ba, ni me na yi mata?" Ya watsa wani abu daga hannunsa a gurin da take ganin su Suwaiba, sai ga wannan bararojin, tana ta zuƙar jinin Suwaiba, sannan jikin Suwaiba na ci gaba da zubar da jini ta huda-hudar nan da jikinta ya yi da ta fesa turare. Ɗif ta daina ganinsu, ta juyo gurin ƙaisar cikin damuwa, sai dai ba ta yi magana ba. "Kin san dalilin da ya sa na ƙyale mutumin nan, da ki ke gidansa? Wasu dalilai ne, ki gaya masa har yanzu bai san ni ba, duk hatsabibancinsa akwai sararin da bai isa ya jefe ƙafarsa ba. Na zuba masa ido ne na ga iya gudun ruwansa, amma dole sai na nuna masa iyakarsa, kuma zan gani tsakanin ni da shi waye zai yi maganin wani, kuma wannan abubuwan da yake yi miki akwai wani abu a ransa za ki ce na gaya miki " "Mene ne a ran nasa?" "Za ki gani, ya ce yau zai tafi da ke farauta, zai ci gaba da nuna miki magunguna. Zan ga iya ƙarshen hatsabibancinsa" Nana ta yi sororo tana kallonsa, duk da tana son tambayarsa, amma tana tsoron ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta. Ya ce "Wuce ki tafi" "Ai na rasa ƙofar fita" "Bi waccan" ya yi maganar yana nuna mata hanya. Tana fita ta ganta a tsaye a ƙofar ɗakin da take tare da sarkin baka. Yana sanye da shigar hargi(irin shigar da maharba suke yi) Bayansa rataye da kwari da baka. Ba ta iya musa masa ba, ko jin tsoro ko makamancin haka ba, kawai ta saka kai ta bi shi. Daga shi sai ita yana gaba tana bin sa a baya hannunsa da fitila. Wata ƙofa suka je, ya ɗaga asabarin ya shiga, Nana ma ta bi bayansa. Suna shiga ƙofar ta gansu a dokar daji. Sai a lokacin jikin Nana ya hau rawa, tsoro ya kama ta, ta ja da baya ta domin koma amma ta ga babu ƙofar da suka shigo. Ya kalle ta ya ce "Kar ki tsorata, babu abin da zan yi miki, bari na ɗaure dajin" "Ina ne nan?" Tayi maganar cikin tsoro. "Dajin igbele ne, na jihar delta" Ta waro ido cikin kiɗima ta ce "Delta kuma? Daga Kanon mu ka zo delta?" Sarki ya ce "Eh, wata kububuwa nake son kamawa zan yi magani da dafinta. Daji ne mai haɗari ana tsafi iri iri a dajin, amma da na kama Kububuwar za mu tafi" ya yi maganar yana haɗa wuta a gurin, ya zuba wani turare yana kewaye wutar. Ita dai Nana ta yi shiru tana kallonsa. Sai da ya gama sannan ya yi gaba, ta bi bayansa. Gurin wani dutse suka nufa, daidai jikin dutsen akwai wani kogo, ya ajiye fitilarsa ya watsa wani abu a bakin kogon. Ya ciro wata raga a cikin sanhonsa ya kafa a gurin. Nana tana tsaye tana kallon ikon Allah. Ya gama ya ce "Mu je wani dajin na nuna miki wasu abubuwan" Al'ajabi ya hana Nana magana, suna tafe yana nuna mata wasu tsirran yana gaya mata amfaninsu. "Kin ga idan ki ka samu kashin giwa, da hauren toronta, wato namijin giwa, da kashin ungulu, ki ka haɗa su da kaucin kuka, da tazargade da garin ganyen kuka, da ganyen magarya arba'in ki haɗa jan miski, a haɗe su guri guda. Idan aka yi hayaƙin su, duk wani ƙaramin shaiɗani sai ya gudu, ke babban ma sai ya sha wahala wallahi, kuma aljani sai dai ya ganki ya bar ki" Nana ta dube shi ta ce "To ta yaya mutum zai samu wannan abun, duk sai mutum ya yi wannan wahalar? Najasar dabbobi ce za ta hana aljanu shafarsa? Bayan ga azkar da Alqur'ani" Sarkin baka ya yi murmushi, yana son ƙi faɗin Nana ƙwarin gwiwar ta na burge shi ya ce "Hala ke da Ƙaisar yake tare da ke, ba kya azkar da karatun Alqur'ani" Cikin damuwa ta ce "Ina yi mana, amma wasu lokutan idan ban yi ba na fi zama lafiya ma, na fara tsorata kar hakan ya sanya imanina ya yi rauni". Ya yi murmushi ya ce "Magani fa ba ƙarya ba ne ba, kin yarda bature ya baki maganin ciwon kai ki sha ki warke, wannan ba shirka ba ce ko, wannan technology ku ke wa ko?" Sai kuma ta ɗan yi shiru. Ja ya yi ya tsaya, ita ma ta tsaya, hasken wuta ta hango daga nesa, a hankali suka ƙarasa daf da gurin, suka tsaya, amma su na iya hango komai. Mutane ne tsirara sai ɗaurin ƙyalle ja a ƙugunsu, maza da mata su na kewaye wuta kowa da ɗan ƙoƙo a hannunsa. Wani mutum a tsakiya yana ta karanta wasu abubuwa, gefe wata mata a kwance ba ta ko motsi da tsohon ciki a jikinta. Ta ga mutumin nan ya nufi kan matar da wata wuƙa a hannunsa yana karanto wasu abubuwan. Razana ta yi, za ta ƙwala ihu sai kuma ta daina ganinsu, ta ga sun koma dajin da sarkin baka ya yi wa kububuwa tarko. "Idan muka tsaya, ki ka ci gaba da gani,  za ki iya rasa hankalinki" Jikin Nana na tsuma ta ce "Su suka kashe matar?" Ya jinjina kai ya ce "Eh, jaririn cikinta za su cire, jininsa za su sha, ƴan ƙungiyar asiri ne. Nan da ki ka gansu manyan mutane ne, da suka sadaukar da lahirar su domin duniya. Akwai 'yan kasuwa a cikin su, da 'yan siyasa" Jikin Nana sai tsuma yake yi, ba ta taɓa tunanin da gaske akwai ƙungiyar asiri ba, ta zata shaci faɗi ne  kawai ake faɗa. "Bari mu koma ki kwanta, da asuba zan dawo na kama macijiyar nan, naga duk a tsorace ki ke . Sai dai ina son mu yi wata magana da ke". Jiki a sanyaye ta ce "Wace irin magana ce?" "Ina son ki sadaukar mini da uban duƙusa wato ƙaisar, na din ga aiki da shi!" Littafin nan 1k ne a telegram ta wannan account ɗin 0069685771 Aisha Adam Stanbic ibtc Sai shaidar biya ta Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM (AYSHERCOOL) YOTA/002 P14 Cikin hanzari Nana ta ce "Na yarda na amince, na bar maka shi" "Ai ba da baki kawai za ki faɗa ba, akwai buƙatar yin wani aiki, idan kin amince za ki sadaukar mini da shi, za ku rabu har abada" "Eh na amince" Sarkin baka ya ce "Za mu ƙarasa maganar da safe" Kawai ta gansu a ƙofar ɗakinta, suka yi sallama ta shiga ta kwanta. Sai dai jikinta na ta tsuma da tunanin wace matar aka kashe, kuma ake ƙoƙarin cin zarafin gawarta haka. "Hmmm za ki sadaukar wa wani ni ko? Har kin yi sabo da shi haka kin yarda shi?" Ta ji maganar ƙaisar a tsakanin zuciyarta da ƙwaƙwalwarta. "Eh zan sadaukar da kai, muddin hakan zai sama mini lafiya da nutsuwa" ta yi maganar a fili. Dariyarsa kawai ta din ga ji, gidan baki ɗaya yana amsa kuwwa. Bayan ta yi sallar asuba, ta zauna tana azkar bayan ta idar, ta yi shiru tana tunani, addu'a ta din ga yi Allah ya rabata da ƙaisar, muddin abin da sarkin baka zai sakata bai saɓa wa Allah ba, za ta yi domin ta rabu da ƙaisar. Da kanta take zuwa gurin Sarkin baka yanzu, duk ta san hanyoyi a gidan. Kuma ganin ta samu sassauci daga takurar ƙaisar, da sanya mata cututtuka da sauran damuwowi ga abinci tana samu babu mai takura mata da damuwa, ga kuma sukulle da kyautatawar da sarkin baka yake yi mata, sai ta fara sakin jiki da mantawa da damuwar da take ciki. Abin mamaki, yau da Alqur'ani ta tarar da sarkin baka, bugun warshi yana karantawa, sai da ya idar sannan suka gaisa suka fita. Sai da suka fara zuwa gurin da ake harhaɗa masa magunguna, har da injin niƙa a gurin, shi ma ma'aikatan gurin daban, ga tarin saiwoyi da tsirrai. Gaggaisawa ya yi da masu aikin gurin, ya ce "An kawo saiwoyin nan kuwa?" Ya yi maganar yana kallon Salamatu. Salamatu ta ce "A'a sarki, ta rafi ake jira, ba ta kawo ba" "Aljanar nan akwai sheɗainiya, idan ta bari na nemo wani ya ɗebo mini, wallahi sai ta ɗanɗan kuɗarta" Nana ta kalle shi ta ce "Aljana kuma?" "Eh, wasu saiwoyin ai sai dai aljani ya ɗebo, ba dai mutum ba. Akwai abubuwan da a cikin ruwa muke ɗebo su, kuma akwai dai-dai lokacin da muke ɗibar su, idan ba aljani ba sai dai ka nemi masunta, su kuma idan ba su ga dama ba, ba za su baka ainihin abin mai kyau ba" Yana gama yi wa Nana bayani, ya ci gaba da maganar sa. "Akwai masu shanyewar ɓarin jiki, mutum biyu Salamatu a je a duba, idan na aljanu ne, a jira ni ki ba su taimakon gaggawa. Idan kuma na larura ne maza a haɗa musu magani, a ɗauki ɓawon kwakwa, da sassaƙen zogale, da zoɓo da ɓawon abarba, a dafa su sosai, a ƙara ruwa, a din ga basu kofi ɗaya sau uku rana. Ba cin man gyaɗa, ba cin gishiri ba cin kanwa, uzairu ya yi musu ƙaho zan zo na ga jikin nasu" cikin girmamawa ta ce "To sarki" Tun Nana tana mamakin al'amuran sarkin baka, har ta zuba wa sarautar Allah ido kawai Amma duk da haka, Nana ta kan kasa jurewa sai ta tambayi wasu abubuwan, yanzun ma ɗan gyaran murya ta yi ta ce "Sarki, su wannan magungunan da ka ke bayarwa haka da ka, ba ka tunanin ya yi wa mara lafiya illa, a asibiti akwai maganin da idan mutum yana da wani ciwon fa ba a ba shi, ku kuma nan ba tantancewa ku ke yi ba, kuma ba auna maganin ku ke yi ba" Ya gyara zaman sanhonsa ya ce "Ban da sharri irin naki, da kuma abu irin naku na 'yan boko aƙida, da ku ke cewa maganin hausa ba shi da awo, ba yanzu a kunnen ki na faɗi gwargwadon abin da za a ba su ba? Wanda ya sani fa ya sani Asma'u, wanda bai sani ba bai sani ba, galibi gurin masu neman na Abinci kawai ake zuwa, wani koya ya yi amma ba a koya masa maganin yadda yake ba, dan ba kowa ne yake yarda ya bayar da sirrin sa ba. Ni na gada kuma na koya. Bature ya yi nasa ban raina masa ba, kuma nima na yi nawa ba wanda ya isa ya raina mini. Ke shaida ce duk abin da ba ni da maganinsa ina gaya wa mutane. Kuma ni ba dan neman kuɗi nake bayar da magani ba. Ki din ga tambayata abin da ba ki gane ba zan yi miki bayani, amma muddin na ji kushen abin da nake yi, ba zan ba ki amsa ba, kuma kin yi wa kanki, dan ba ki san a ina abubuwan da ki ka koya a gurina, za su iya amfanar ki ba, ko su amfani wani ba" jin sa kawai Nana take yi, tana ganin me za ta amfani wani da wannan abubuwan da babu scientific proof ko research a kan su. Bayan sun gama da nan suka tafi ɓangaren da ba ta taɓa zuwa ba a gidan. Shi kuma garke garke ne na dabbobin dawa da na gida, wani abin ma ba ta taɓa ganinsa ba. Ya din ga nuna mata dabbobin, da magungunan da ake yi da wasu sassa na jikinsu. Yana cikin yi mata bayani, ta ga ya yi shiru ya daina magana, ta leƙa fuskarsa za ta yi magana kawai ta ga ƙwayar idonsa ta koma baƙa gaba ɗaya, jikinsa ya hau tsuma. Cikin sanhonsa ya zira hannu, sai ga shi ya fito da wani shirgegen zaka, ya gaji da riƙa cerarsa jawur da ita. Jiki na tsuma Sarkin baka ya saka hannu ya raba kan zakaran da gangar jikinsa. Ya ɗaga gangar jikin, ya tsiyaye jinin a bakinsa, ya gama ya hau cin gangar jikin zakaran a ɗanyensa da gashinsa da komai yana zazzaro ido. Ihu Nana ta saka tana karkarwa, ta juya za ta kasa da gudu, kawai ta ganta a jikin Salamatu tana shafa mata wani abu. Nana ta juya ta ga ba ta ga Sarkin baka ba, sai ita da Salamatu a ɗakin. Salamatu ta ce "Nana zamanki a gidan nan, ya ci ace kin daina tsorata a mafarki, ki koyi dakiya garin tsoron nan wataran za ki iya zaucewa fa. Shi ya sa Sarki yake nuna miki wasu abubuwan domin ki saba ki rage tsoro" Ajiyar zuciya kawai Nana take yi, cike da tsoron abin da ta gani da ta kasa tuna mafarki ne ko kuma gaske. *** Gaddafi na zaune a rumfar mai shayi, yana jiran a dafa masa noodles da ƙwai ya ci. Babu tsammani sai ga jami'an tsaro sun dira a gurin, tare da Imran. Imran ya nuna Gaddafi aka kama shi, cikin mamaki Gaddafi yake tambayar ba'asin abin da ya faru, amma ba su gaya masa ba suka tafi da shi. Sai da su ka je charge office, sannan aka ce Imran ya faɗi abin da ya kawo ƙarar Gaddafi a kai. Imran ya ce "Yallaɓai, ƙanwata ya ɗauka suka haɗa kai da yayar babanmu, aka kai ta wani guri wai neman magani. Kusan sati guda kenan na yi na yi, su gaya mini ina suka kai ta sun ƙi, kuma ita kaɗai aka baro a gurin babu ɗan jinya". Cikin mamaki da takaici Gaddafi ya ce "Amma ka cika mara mutunci, me ya hana ka saka a kama da Baban, sai ni zaka saka a kama, bayan tare muka kai ta". Imran ya ce "Eh wannan ai ubana ne, kuma Kai ka kawo shawarar a kai ta can ɗin. Ga Suwaiba nan a gidan tana aljanun ita ma, ita baku kaita ba, saboda ita ana son ta ƙanwata ce ba a so, kawai ka gaya mini ina aka kai mini ƙanwa" D.P.O ya ce "Ya isa haka, wannan maganar ta cikin gida ce, kuma shi ma yana da gaskiya, babu yadda za ayi ace an kai mutum gurin mai magani, babu wani nasa a gurin, kuma ba asibiti ba. Ko Asibiti ne?" Ya yi maganar yana kallon Gaddafi. Gaddafi ya girgiza kai. "To ka gani, shi ba ubanta ba ba ɗan uwanta na jini ba, ba ma kwa tsoron ya lalata rayuwar yarinyar. Ga ku a cikin ƙwaryar birni kamar masu hankali, amma kun yi abu kamar mutanen farko. Duk yadda ake ciki wajibi ne gobe ka wuce gaba, zan bayar da mutum biyu a nan, aje a dawo da yarinyar nan, muddin ba ku dawo da ita ba, to wani abun ku ka aikata kuma sai na rufe ku daga kai har wanda ku ka kai ta" Gaddafi ya jinjina kai tare da yi wa Imran wani mugun kallo. ***** Nana a ɗakin da sarkin baka yake bayar da magani ta tarar da shi, yana ganin wata mata da yaronta. Ƙafafuwan yaron tamkar lagwani 'yan sirara marasa ƙwari, da hannayensa. Haka kansa ma ɗan mitsitsi da kaɗan ya fi lemon zaƙi fuskarsa tamkar tsoho abin tsoro yaron. Uwar kuma sai rungume shi take yi cike da so da ƙauna. Sarkin baka ya ce "Wata rana kin kashe gizo gizo cikin dare, a banɗakin ki, lokacin ki na da ƙaramin cikin yaron nan, ba tare da kin yi bismillah ko addu'a shiga banɗaki ba, an yi haka?" Ta girgiza kai ta ce "Sarki ba zan iya tunawa ba" "To an yi, shi ya faɗi abin da ki ka yi masa, kin bugawa jaririnsu takalmi, kin nakasa shi, shi suka ajiye a jikin gizo-gizo yana wasa, ki ka dake shi da takalmi, da kin yi addu'a da ya bar jikin gizo-gizon. Dan haka yanzu ɗan su suka ajiye a jikin yaron naki, jininsa da sauran sinadaran jikin yaron ki, da za su saka ya girma, su yake sha yana girma, dan haka ko an cire aljanin mutuwa zai yi ba shi da sauran mamora sun gama lalata jikin yaron da garkuwar jikinsa" matar ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah sarki ka taimake ni" Ya girgiza kai ya ce "Magani kawai nake bayarwa, ba ni da ikon kashewa ko rayawa, zan baki magani ki koma gida, Allah ya baki wani" Nana ta ce "Ya a ka yi ka san aljanin ne a jikinsa, kuma idan ya fita ba zai rayu ba?" Buɗe ƙwaryar can, ki ɗaukko mini habbatussauda, akwai tazargade a ciki da tsakin kuka, da garin farin muski, duk ɗebo su da kan ki ki zo" babu musu Nana ta harhaɗo kayan da ya ce ta kawo masa. Ya zira hannu a jakarsa ya ɗaukko garwashi, ya ɗora a kan wata tasa, ya ɗebi haɗin nan ya zuba a kai. Ko sakan goma ba a yi ba, yaron ya mimmiƙe ya din ga tsala uban ihu. Sarkin baka ya cewa matar "Yaushe rabonsa da kuka, ko ya motsa wata gaɓa ta jikin sa?" Ta girgiza kai ta ce "Ba zan iya tunawa ba, kullum a kwance kawai yake" "To tun da ya yi kuka yanzu har da mimmiƙe wa, kin san ba ƙalau ba, baiwar Allah ki je gida, Allah ya baki wani" Nana a ranta ta ce "Yaro ya ji wannan uban hayaƙin ba dole ya tsala ihun azaba ba". Ya ce "Kamar har yanzu ba ki yarda da abin da ki ka gani ba ko?" Ta girgiza kai ta ce "A'a na yarda" " 'yar wace ɗariƙa ce ke ne?" Ta girgiza kai ta ce "Ɗariƙa ba ta cikin sharaɗin addini, dan haka ni ba ni da wata ɗariƙa" Ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne, kin san kowace ɗariƙa akwai malamin da ta ke yarda da shi, da ki na da ɗariƙa da na ce ki saurari bayanin da wani babban malami ya yi a kan aljanu, amma manta kawai kin tashi lafiya?" "Lafiya kalau Alhamdilillah" ta buɗe baki za ta sake magana ta ga bakin sarkin baka duk jini da sauran gashin zakaran da ya cinye jiya, wanda lokacin da ta shigo ba bu shi a bakinsa. Zabura ta yi ta ja da ba, dan a zaton ta a mafarki ta ga ya ci zakaran ba a gaske ba, kuma da har ma ta manta ma. Sarkin baka ya sanya hannu, ya zaro sauran gashin daga bakinsa, ya kalla ya yi murmushi ya ce "Kar ki tsorata Nana, tun a zuwan ki gidan nan da na so cutar da ke, sai na cutar da ke ta in da uban duƙusa ba zai iya ba ki kariya ba. Har ga Allah bani da niyyar cutar da ke, kuma da gaske na san ba zan iya raba ki da shi ba, amma na rage masa tasiri ta wasu fuskokin daban-daban a tattare da ke. Tabbas na cinye zakara da ransa, kuma uban duƙusa ne ya zungure ni, sai da na yi a gaban ki, dan ki cire yarda da ni kar ki yarda ki sadaukar mini da shi. Da na mallake shi zan ƙara ƙarfi da ƙarin tasirantuwar magunguna na, kuma zan kerewa sa'a tsakanin mutanenmu. Ainihina ɗan wanzamai ne, na gaji wanzanci daga nan aka kai ni bara, na samu karatun Alqur'ani daidai gwargwado sai dai babu sauran litattafai na addini. Azabar yunwa ce ta sanya na fara bin matasa daji farauta, daga baya na watsar da allo na bar gurin malamin da aka kai ni gaba ɗaya, duk mahaifiyata 'yar maharba ce, amma na fi ƙarfi ga ɓangaren wanzanci. Na yi rashin ji, na yi faɗi tashi, na yi wa harkar baka haye, har na so na fi 'yan gado ƙwarewa, hakan ya saka sauran maharba sako ni a gaba, da tsaface-tsaface da ƙoƙarin son kawar da ni. Sun sha haɗa kai domin su kashe ni. Suka yi mini shiri, na zo ba na iya kama komai idan na fita harbi, ga rashin lafiya, dole na bazama neman magani a nan na haɗu da uban gidana, a masu magani ya bani maita, wadda ita ma wasu baƙaƙen aljanu ne suke tasrifinta, ya ƙara koya mini harkar magani, ga wanda na gada na wanzanci a gida. Ya yi mini girkar aljanu na zo na gawurta, na nemi na fi shi ma ko ma na ce miki na fishi ta kaowace fuska, kawai sai ya fara neman ya kashe ni, saboda hassada. Wataran mun fita farauta tare ya rikiɗe ya koma ƙaton maciji ya yi ƙoƙarin haɗiye ni, ni kuma garin ƙwatar kaina na kashe shi har lahira. A haƙiƙanin gaskiya, ba na yadda na bawa mutum duk wani abu da zai cuci mutane a kan zalunci. Ina da tarin aljanu kala-kala da nake aiki da su. Na nemi ki sadaukar mini da uban duƙusa ne domin na ƙara ƙarfin tasirina. Rabona da maita har na manta, tana nan a jikina amma bana amfani da ita, na daina ta'amalli da aljanun maita, shi ne jiya ya zunguri maitar ta motsa mini. Yanzu haka sai na je na yi jinya, kuma zan ja dogon lokaci ban yi aiki ba, sai dai yarana su yi. Hatta Salamatu da ki ke gani ba mutum ba ce ba. Ainihin matar ba ta da lafiya sihiri aka yi mata, ba ta iya komai aka kawota nan. Na saka Salamatu a jikinta take yi mini aiki, Salamatu na fita gangar jikin za ta faɗi ta ci gaba da jinya. Shirin a jikin gawa aka yi mata, aka binne gawar ni kuma ba zan iya sakawa a ciro gawa daga makwanci domin karya sihirin ba, hakan tamkar tozarta gawar ne." Jikin Nana duk ya yi sanyi da jin labarin da sarkin baka ya bata. "Yarinyata da tana raye da ta kai kamar ke, na tafi farauta abokan adawa ta, su ka kasheta da babarta, tun daga nan ban kuma aure ba,, shiyasa na yi iya ƙoƙarin da zan yi na gagare su. Zan saka a mayar da ke gida, ba sai kin yi makonni biyun ba, domin kuwa jiya an turo mini 'yan aike, ana so a haɗa kai da ni, in bayar da jininki, kuma ina da yadda zan yi na bayar, za ayi mini musaya da wani abu mai tsoka, wanda da na so, zan karɓa na bayar da jinin naki na yi maganin uban duƙusa, amma ina jin tausayin ki, ban san gaibu ba, amma akwai yiwuwar kina daf da buɗe sabon babi na ƙaddara, dan zuwanki gidan nan tuni kin yi wa ƙaddarar mukulli" Cikin mamaki Nana ta ce "wace irin ƙaddara ce kuma haka?" "A'a ba ni da damar cewa komai, amma ki tambayi ƙaisar mene ne tarihin kakaninki, za ki ga ta in da zuwanki gidan nan ya buɗe sabon babin ƙaddararki. Babu lallai ki fahimci labarin a take sai a gaba kaɗan za ki fahimta sosai da sosai. Abu ɗaya zan iya gaya miki, nima ina da alaƙa da labarin kakaninki ta wata fuskar" "To kai ka gaya mini labarin mana" Ya sauke numfashi ya ce "Ƙarfin hali kawai nake yi, maitar da take cikina ce take ta wahalar da ni, rabona da cin wani abu da sunan maita na fi shekara goma sha, saboda na sha maganin danne ta, kwatsam jiya na ci na san sai na yi jinya" Nana har da gyara zama ta ce "To ita maitar mece ce? A addini babu maita sai dai kambun baka, to ita a ina ake samun maitar kuma ya ake yin ta" Sai da ya yi dariya, Nana akwai tambaya ba kasafai take barin kanta ya kulle ba. "Tabbas babu maita a addini, sai kambun baka. Maita tsafi ce sihiri ce, wani siddabaru ne da aljanu, da yake ƙara tasirin kambun baka. Ya danganta da wadda ka ke da ita. Akwai wadda ka ke iya ganin kurwoyin mutane, a siffofi na dabbobi, akwai wadda muke amfani da ita mu lalata abu. Idan muka kalli abu, ko ba mu tanka ba zai lalace. Mu kan zuba yawunmu idan ta taso mana a cikin abinci mu bawa mutum, sai ya yi ta rashin lafiya. Ina da jar maita ne, mai bala'in fiye da kowacce tare da wani aljani nake sarrafata, shi ne idan ya buƙaci jini yake zuwa kaina, sai na sha sai ya samu nutsuwa ya sake ni. Ina iya sarrafa maitar yadda nake so, ko shi ne Uban duƙusa ya zunguri maitar a cikina" Nana ta jinjina kai ta ce "To amma ya aka yi ya iya zuwa gurin da ka ke, bayan ka na da magungunan su?" "Ban gaya miki a cikin aljanu irin ƙaisar ba su da yawa ba? Yanzu ki je zan kwanta in huta ne" Ta jinjina kai, ta tashi ta nufi ƙofa, har ta kusa fita ya ce "Ki na ji?" Ta waiwayo ta ga har ya kwanta. "Ki ci gaba da addu'a da karatun Alƙur'ani, duk da idan kin yi kin fi shan wahala, kar ki daina. Kuma kar ki yadda wani abu ya baki tsoro, wasu lokutan da tsoron ka ake amfani a cutar da kai, ki cigaba da addu'a duk tsanani akwai sauƙi a biye. Wataƙila tsanani da ƙaddarar gobe ta fi wadda ki ke ciki yau" ta yi shiru tana jinjina maganganun sa. Ta ɗago ta ce "To na gode sosai da sosai. Ka ajiye mini naman maciji an jima zan zo in gwada ci" ya yi dariya ya ce "Kamar gaske. Zo mu ga tafin hannunki" Ta koma gurin da ta bar shi, ta durƙusa ta nuna masa tafin hannunta hagu da dama. Ya yi shiru yana kallo sannan ya ce " Ki kula sosai zanen X ɗin da yake kusa da layin zuciyarki na nuni da tsagwaron gwagwarmayar rayuwa. sannan layukan ƙasan babban ɗan yatsanki suna nuni da za ki yi wasu tafiye-tafiye, wasu daga ciki na jin daɗi wasu na wahala. Sai kuma alamar ido, da ke babbar ɗan yatsarki da alamar sarƙar da ke jikin babban yatsan akwai wani abu amma ba zan gaya miki ba, shi ma wani karatun ne daban, yana da alaƙa da aure da kuma matsalar iyali" Ta kalli Sarkin baka ta ce "Abin mamakin  ka ba ya ƙarewa sarki, bayan layuka ban ga komai a hannun nawa ba, ko kana ganin wani abu da bana gani a hannun, kuma dai sanin gaibu sai Allah ai" Ya kwashe da dariya ya ce "Wani karatun ne daban, duk da na san ji na kawai ki ke yi ba yarda ki ke yi ba. Je ki an jima ki zo ki ci naman. Na so na je da ke taron wasan maharba da muke yi duk shekara, ni ke ɗauke da kambun har yanzu, sai dai ba na iya tunanin bana za ayi wasan da ni, ƙaisar ya yi mini illa. Maza je ki sai an jima" ta tashi tsam ta nufi hanyar fita tana kallon hannunta. Wannan tsohon mai kama da Ƙaisar ta gani, cikin wannan fararen kayan nasa, tamkar yanar gizo gizo saboda tsufa. Sai kuma ya ɓacewa ganinta, a hankali ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ga baya nan, sannan ta fita, tana tafe a hankali tana duba tafin hannunta tana kallon zanukan da sarkin baka ya faɗa, da tunanin shi kuma wani kalar siddabarun ne. Ji ta yi zafin rana ya ƙaru kamar lokaci ɗaya temperature ta canza. Ta ɗaga kai kawai ta ganta a bakin layinsu. Ta waiwaya da sauri ta ga ba ta cikin gidan sarkin baka. Ta sake dubawa ta ga dai bakin layinsu ne dai. Hatta kayan jikinta ba su bane ba, dogon hijjabi ne da aka ba ta take sakawa lokacin salla, sai kuma wata jaka da take rataye da ita ta fata. Ta din ga ƙifta idanunta domin ta ji ko bacci take yi amma ta ga ido biyu ne, kawai ta nufi gida. Ko da ta shiga gidan da sallama, babu kowa a tsakar gidan. Ta sake yin sallama Nasiru ya shigo gidan da gudu ya dawo daga aike, ya ce "Laa mama Nana ta dawo" Hakan ya yi daidai da fitowar Mama daga ɗaki, hannunta riƙe da tsintsiya da abin kwashe shara. Sakin tsintsiyar ta yi tana kallon Nana kamar baƙuwar halitta. Nana ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Mama sannu da gida?" "Uban me yasa ki ka dawo gidan nan yanzu?" Cikin mamaki Nana t tsaya tana kallonta. "Ke idan ki na da kunya ma kya dawo gidan nan, duk da ta'asar da ki ka yi?" Cikin mamaki Nana ta ce "Wace ta'asar?" "Ban sani ba" ta yi magana tana ɗaukar wayarta a kan taga" Nana ta nufi ɗakinsu, amma Mama ta dako tsalle ta tare ta, ta ce "Ai kuma zamanki ya ƙare a gidan nan, abin da na yi na riƙon ki Allah ya ba ni lada. Ba za ki ci gaba da zama ki kashe mini 'ya 'ya ba" "Mama kisa kuma? Wa na kashe?" Ba ta kula Nana ba, ta fara magana a waya "Ko ma ina ka tafi, ka dawo ka zo ga Nana ta dawo, ka zo ka fitar mini da ita daga gida, dan wallahi ba zan zauna da ita ba" ta kashe wayar. Nana ta tsaya tana kallon ikon Allah, Fafur Mama ta hana ta shiga ɗakinsu, ba a fi mintuna goma sha biyar ba, sai ga Baba ya dawo gida. Cikin mamaki yake kallon Nana ya ce "Ina Gaddafin yake?" "Gaddafi kuma Baba?" Nana ta tambayi Baba cikin mamaki. "Eh mana, ba wancan jarababben ɗan nema ya kai ƙarar mu ba, wai mun kai ki inda ba a sani ba, aka haɗa Gaddafi da jami'an tsaro a je a taho da ke" Nana ta girgiza kai ta ce "Ni da kaina na dawo, ban ga Gaddafi ba" Suwaiba ce ta fito daga ɗakin Mama, sai da Nana ta tsorata, ta yi wani irin haske, duk da tana shafe-shafe, amma hasken da ta yi, da gani na rashin lafiya ne. "Ka fa san yadda za ka yi da ita, dan wallahil azim ba zan ci gaba da zama da masifa da annoba ba, shi kansa wanda aka ce an kashe ɗin nan, ina kyautata zaton ma ita ce ba wani ba, to wallahi jinin 'ya'yana ba zai shawu a sha banza ba" Baba ya ce "Wai Rabi me yasa ki ke haka? Idan ta bar gidan nan ta je ina?" "Ta koma gurin uwatta, ta je ta sha nata jinin" "Ba zai yiwu ba, har duniya ta naɗe, ba zan bawa maijidda ɗa na ba." Nana ta yi ajiyar zuciya cike da tsantsar damuwa da baƙin ciki. Ya sake kallon ta ya ce "Wai ba makonni biyu aka ce za ki yi ba, me ya dawo da ke gidan nan yau?" "Shi ne ya sallamo ni" ta amsa a hankali. Baba ya ci gaba da faɗa "Wallahi Ina takaicin haihuwar Imarana, ya haɗa Gaddafi da jami'an tsaro, shi kuma an zo nemansa a kama shi ya gudu, yanzu ma kalli 'yan sandan ne suke kirana ga kuma wannan masifar" "Baba a kama shi kuma? Me ya yi?" "Eh ai ke ce mai jin tausayinsa dama, sun haɗa kai da 'yan iskan abokansa, sun kashe wannan malamin naku, ana ta nemansa ruwa a jallo" Nasiru ya yi farat ya ce "Baba ba fa Yaya imarana ne ya yi kisan ba, abokansa ake nema, shi ne ake nemansa dan ya nuna inda suke" "Duk ba abu ɗaya ba ne dai?" Baba ya faɗa cikin takaici. Jikin Nana na rawa ƙirjinta na dukan uku-uku ta ce "Wai wani malamin namu?" Nasiru ya yi farat ya ce "Malam Auwal aka kashe da daddare, ya fita sayayya ana gobe za a kai ki gidan mai magani" Kanta ne ya yi wata irin sarawa, ta yi saurin dafe kanta tana tunanin kamar ta san zancen amma ta manta a ina. Iya ƙarfinta take kokowa tsakanin ƙwaƙwalwarta da zuciyarta a kan sai ta farka daga nannauyan baccin da take yi. Ayshercool 08081012143. 15 Suwaiba ta shiga banɗaki ta koma ɗaki, babu wanda ta kula a tsakar gidan. Mama kuwa bala'i ta ci gaba da yi. "Wallahi baban Jamila ba zan zauna da Nana ba, idan ta gama da yaran nan kaina za ta dawo, shi kansa wannan yaron an fara maganar saboda yaƙi aurenta ya rasa ransa". Baba ya ce "A'a Rabi, wannan dai zance ki ne, idan da wanda zai mutu dan bai aureta ba ai Suleiman ne, kuma duk abin da ake yi mata a gidan nan babu wanda ya mutu, dan Allah ki daina wannan maganar" Kamar ta mari Baba ta ce "Abin da ya samu Suwaiban bai ishe ka hujja ba, sai ka buɗe ido ka ga gawar ta tukuna? Ni fa wallahi sai dai ka zaɓa, ko ta bar gidan nan ko ni na bar gidan" "A'a ba za ayi haka ba, yanzu idan ki ka ce ta bar gidan nan ina za ta tafi? Haba Rabi Nanan nan fa 'ya ta ce ita ma. Kuma idan kin kwantar da hankalinki, kin san na karɓi kuɗin auren ta, nan da sati biyu za a ɗaura mata aure, ta bi mijinta Ikko, duk mene ne abin tayar da jijiyar wuya?" Nana tun da ta dafe kanta, ta sunkuya ba ta ko motsa ba, sai yanzu da ta ɗago ta fara magana iya ƙarfinta "Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah ku tashe ni daga baccin nan, ya za ayi malam Auwal ya mutu? Dan Allah ku tashe ni kafin ƙwaƙwalwata ta samu matsala, dan Allah ku tashe ni daga baccin nan" ta ɗago da idanunta suka yi wani irin ja kamar za su kama da wuta, hawaye ne tare da mijina suke rige-rigen zuba a fuskarta. Baba ya ce "Nana meye haka? Zuwa islamiyyar na banza dama ki ke yi? Ko ni na mutu ai ba kya yi haka ba" jefar da jakar hannunta ta yi, tai waje. Baba ya bita da sauri, amma tamkar walƙiya bai ga ko sahunta ba. Kai tsaye Nana rukunin ofisoshin malamai ta nufa a islamiyyar su. Malam Nura ta tunkara, babban abokin malam Auwal. Cikin yanayi na ɗimuwa ta ce "Wai an kashe malam Auwal? Dan Allah kai ma ka iya ruƙiyya ai ka na yi mini, dan Allah ka karanta mini koma mene ne ko zai sake ni na tashi daga wannan baccin." Ya ƙarewa Nana kallo, da gaske a ɗimauce take, cikin sigar rarrashi ya ce "Zauna mu yi magana" "Ba zan zauna ba, kawai ka yi mini ruƙiyya na tashi. A nan fa na same shi a ofishin sa, muka yi magana, ya gaya mini gaskiya ba zai iya aurena ba, kuma duk na fahimce shi, ya ce mini zai tafi Qatar, to kuma daga na yi tafiya sai ace mini ya mutu?" "Al mautu haƙƙun Nana Asma'u, mun yi rashin Auwal. Ɓata gari ne suka soka masa makami su ka ƙwace masa waya kafin a kai shi Asibiti rai ya yi halinsa, ki yi masa addu'a" Jikinta na karkarwa ta ce "Ya sayyadi Nura. Na yi rashi ba zan manta Yaya Auwal ba, yanzu waye zai din ga bani addu'oin? Waye zai yadda da abubuwan da nake ji a jikina na ciwo, ba tare da ya ƙaryata ni ba?" Tuni malamai suka cika ofishin, kowa da abin da yake faɗa, wasu na kuka domin mutuwar ta dawo musu sabuwa. Da yawa ba su san ya so ya auri Nana ba sai yanzu. An daɗe ana rarrashin Nana, da yi mata nasiha, ba a taɓa yi wa Nana mutuwa mai shiga jiki ba sai a wannan lokaci, Alkhairinsa kawai take tunawa. Halin da take ciki, bai hana kunnuwanta jiyo maganganun wasu malaman, su na cewa yayanta ake nema ruwa a jallo shi ya kashe Auwwal. Sauti komai ƙanƙantarsa Nana na iya jiyo shi, wasu lokutan da haka take gane ƙaisar na daf da ita. Malam Nura ya saka ta a gaba, ya tafi raka ta gida, suna tafe yana yi mata nasiha. A ƙofar gida malam Nura ya yi mata sallama, ta shiga cikin gida tana taku da ƙyar. Ko sallama ba ta iya yi ba, ta nufi ƙofar ɗakinsu, ta ga an saka tsumma an ɗaure ƙofar ɗakin. Ta ɗauki jakar da ta dawo da ita daga gidan sarkin baka, duk da har a wannan lokaci ba ta san mene ne a ciki ba. Ta fara ƙoƙarin kwance ƙofar ɗakin, jin motsi ya sanya Mama sake fitowa, tana ƙoƙarin nufo Nana tana bala'i. Nana ta ɗago a hankali ta kalli Mama, sai kuwa ta ja ta tsaya, dan ba ta taɓa ganin Nana ta yi mata irin wannan kallon ba. Gani ta yi tamkar walƙiya idanun Nana suka yi. Ta buɗe ɗakin ta shiga ta kwanta. Aka jima Baba ya dawo, dan yawon neman in da Nana ta yi ya yi. Yana dawowa suka ci gaba da faɗa da Mama a kan lallai sai ya fitar da Nana daga gidan. Nana tana ji Baba ya kira Yaya Atine yana roƙonta. Baba ba ya iya waya sai ya saka ta a hansfree, kuma sai ya ta ɗaga murya tamkar yana magana da aradu. "Atine dan Allah idan da hali Nana ta zo gidanki, ta zauna kafin a ɗaura mata aure. Rabi taƙi yadda ta zauna da ita, kin san halin da Suwaiba take ciki" "Wace Nana kuma? Ba tana gidan mai magani ba?" "Ta dawo ɗazu, wai mai maganin ne ya sallamo ta, kuma ga 'yan sanda sun tafi da Gaddafi a taho da ita, shi kuma Imarana ya gudu nemansa ake yi ana zargin sun kashe wannan yaron da ake ta magana a kansa a radio, wanda ya ƙi auren Nanan" Nana na jiyo Yaya Atine, kasancewar wayar Baba a ragargaje take kuma China ce ta na cewa "Taɓ lallai Isa Allah ya jarabce ka, wannan masifar duk a gidan ka? To mai magani ma ya kasa ya sallamo ta balle kuma ni, ya zan yi da ita ina ma na ga gurin ajiyeta? Ka yi haƙuri ta zauna a gurinka kafin lokacin bikin nata" Ya marairaice ya ce "Me nake da shi, ba wani biki aure kawai za a ɗaura su tafi, ai kin san ba shi ne da ni ba" Yaya Atine ta ce "To ai shikenan, amma ka riƙe 'yar ka, ba zan je nima na gogi bala'i ba, dan ni na fara tsorata da al'amuranta" "Amma yay... Ba ta bari ya gama maganar ba, ta kaste kiran. "Ka gani ko? Ita ba za ta karɓi bala'i ba, ni kuma a bar ni da bala'i ya ci gaba da kashe mu ba zai yiwu ba" Sallamar da ake kwaɗawa a waje, ya sanya Baba fita, ya tarar da 'yan sada tare da Gaddafi. Ɗaya daga 'yan sandan ya ce, "Yauwwa barka malam, zamu tafi da kai station ne" Baba ya ce "Saboda me?" "Mun je in da aka ce an kai yarinyar ɗanka ya yi ta raina mana hankali muna yawo, babu wani a gurin nan, kuma ga wanda ya kawo ƙarar ana nemansa ruwa a jallo" Baba ya ce "Ai bayan tafiyar ku ta dawo" Gaddafi ya ce "Ta dawo kuma? Ni fa har gurin da muka ajiye mota muka shiga, bamu ga gidan nan ba" "Wallahi ta dawo, tana cikin gidan nan" Sai da aka tafi tare da Nana har police station, aka yi rubuce-rubuce sannan aka saki Gaddafi suka taho gida. Tana jin yadda Gaddafi yake rantsuwa shi da sake shiga duk abin da ya shafe ta har gaban abada. Kwanaki biyu suka shuɗe, Nana ko rintsawa ba ta iya yi, sai da ta gwammace dama a gidan sarkin baka ta yi zamanta. Mama kuma ba su fasa faɗa da Baba a kan lallai ya nemi in da Nana zata zauna ba. Dama normally ma ba abinci ake ba ta ba sai an ga dama, yanzu kuwa tun da ta dawo Baba ne ma ya kan bayar a sayo mata kunu ko awarar naira ɗari, shi ma ba iya ci take yi ba. Dama ba su fiye shiri da Suwaiba ba, sun fi shiri da Jamila, sai dai a wannan karon tun da ta dawo, babu wanda yake shiga sabgarta, hatta ɗakin da take ba sa shigowa. Tana jin yadda idan aka yi baƙi, ko aka zo duba Nana mama take muzanta ta, tana cewa aljanunta ne suka halaka Auwal, wanda ya fasa aurenta kuma suke ƙoƙarin kashe Suwaiba. Nana tana ganin yadda wasu daga hudar jikin Nana suka fara warkewa, sai dai wasu ba su fasa zubar da jini ba. Turaren da Jamila ta kawo mata ta gani a kan tagar su, an feshe fiye da rabi. Ita dai ta san turaren nata ne, amma ta kasa tuna yadda aka yi ta same shi. Cikin dare ta kasa bacci, ta tashi zaune ta haɗe gwiwoyinta ta kifa kanta, har yanzu gani take kamar za ta farka daga bacci, ace mata Auwal bai mutu ba. Kwanakin nan da aka ɗauka kuma, ta gazagata da gaske malam Auwal ya rasu. Tana so ta je ta yi wa mahaifiyarsa ta'aziyya amma ba ta sani ba ko ta santa, ga kuma surutun da ake ta yi a kanta. "Ya Allah ka yafe mini rashin tawakalli da na yi, na bari ɗimuwa ta sanya ni yin abin da bai kamata mai imani ya yi su ba. Ya Allah Auwal bawanka ne, mai kwaɗaitar da al'umma bin ka da manzonka, mai hidima ga addini, mai ƙaunar Manzon Allah ma'abocin Alqur'ani ya Allah ka yafe masa ka yi masa rahama" ta yi maganar kuka yana ƙwace mata. Dariyar da ta ji ne, ya sanya ta ɗaga kanta. Ta ganta a zaune jikin wata bishiyar tsamiya, ita kaɗai ƙwal a daji. "Iska na wahalar da mai kayan kara, yanzu duk saboda soyayyar ki ka koma haka? Kamar gaske mutumin nan ya riga ya mutu, kuma ba fa wai son shi ki ke yi ba, shaƙuwa da tausayi ne a tsakanin ku" tashi ta ya tsaye a fusace tana waiwayen in da za ta ga ƙaisar. Domin kuwa sai a lokacin ta tuna ya nuna mata mutuwar malam Auwal, amma da ta tashi a wancan lokacin ta manta da komai. "Kai ne ka kashe shi ko?" "Idan zan kashe shin ne zan soka masa wuƙa? Kwanansa ne ya ƙare ba zan iya kashe shi ba ai, ni ba na kisan kai sai an dame ni, kamar yadda Sarkin baka ya taɓo ni, nima na taɓa shi wataƙila na karya alkadsrinsa wannan maitar wataƙila ita ce ajalinsa" Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Kenan kashe shi za ka yi? Wai kai wani irin halitta ne azzalumi mara imani? Duk wanda na mu malanta sai ka cuce shi?" "A'a ni ba na taɓa kowa sai ya taɓa ni. Ba ya fara lallaɓa ki ki sadaukar masa da ni ba? Ba ki yi tunanin ta wace hanya zai yi amfani da ni ba, kawai saboda ki rabu da ni, ki ka amsa masa kuma ke ba ki san ya ake sadaukarwar ba, ki ka amsa. Ya shiga gonata ni kuma na shata masa layi" yayi maganar yana bayyana a gabanta. Cikin kuka Nana take faɗin "Allah ya yi mini maganin ka ya saka mini, idan ka fi ƙarfina ba ka fi ƙarfin Allah ba ai. Kuma kana kallo aka kashe malam Auwal ba ka yi komai a kai ba, banda zalunta ta ta azabtar da ni ba abin da ka ke yi" Ya yi murmushi ya ce "Zuwa islamiyyar ta ki ba shi da amfani ashe, ai idan abin da ya fi haka za ayi masa ba ruwana, azabar da ya din ga saka ki na bani, na yi farin ciki da mutuwarsa, ki roƙa masa Allah gafara, dan wasu lokutan idan damuwa da gajiya ta yi masa yawa, yan shan ƙwayoyin gusar da hankali ya yi bacci mai tsawo. Sannan akwai tarin hotunan 'yan mata a wayarsa, ke har ma hirar tsakar dare a dandalin sadar da zumunta yana yi na rage zafi da 'yan mata.. "Ƙarya ka ke yi, wallahi ƙarya ne ba dai malam Auwal ba... Nana ta katse shi cikin ƙarji. Ƙaisar ya ce "Ai dama ban ce ki yarda ba, ku bil adama ma akwai wanda ya kai ku ƙarya ne. Sarkin baka kuma zan kasa zan tsare sai na ƙarasa shi, saboda ba neman sadaukar masa da ni ne kawai ya sanya na yi masa wannan hukuncin ba, wani gagarumin laifi ya taka mini da sai na ga bayansa" "Dan Allah kar ka kashe shi, mutumin kirki ne, kuma mutane wasu sun yi imani da maganinsa, marasa ƙarfin da ba za su iya jelen Asibiti ba, yana taimaka su babu ko kwabonsu" A hankali ya fara zagaya Nana ya ce "Gaba ɗaya halayyarki ba ta da saiti, kin gama kushe abin da yake yi, yanzu kuma kin ce a ƙyale shi, mutane na amfana. Idan ya mutu sai ki je ki gaje shi, tun da dama ya kai ki ya nuna miki magunguna. Kwanta ki yi bacci kafin ƙwaƙwalwarki ta samu matsala, ki shirya tarar sabuwar matsalar da take tunkarar mu daga ni har a dalilin zuwan ki gidan wannan mutumin. Za ta yi magana kawai ta daina ganin komai, sai juyi da ta yi a ɗakin da take, cikin magagin bacci. Ƙoƙarin yinƙurwa take yi ta tashi, amma wani irin bacci mai kama da fita daga hayyaci ya yi awon gaba da ita. Bayan kwanaki uku, jami'an tsaro ba su fasa zarya a gidan su Nana ba, a kan neman Imran. Ga fitina da mama take yi a kan zaman Nana, abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, sai da maƙwabta har da mai unguwa su ka shiga lamarin, aka din ga rarrashinta, aka din ga janyo mata ayoyi da hadisai, a kan tauhidi da ɗayanta al'amura. Nauyin manyan mutanen da suka haɗu, ya sanya ta ce ta haƙura Nana ta zauna, zuwa lokacin da za a ɗaura mata aure. Nana gaba ɗaya lamarin da yake faruwa a gidan na su baya gabanta, har da batun ɗaurin aurenta da ake yi, sati biyu masu zuwa. Rashin samun Abincin nan da ba ta yi, ya fara damunta dan sannu a hankali mutuwar malam Auwal ta fara sakinta, sai dai duk lokacin da ta tuna shi sai ta yi masa addu'a. Tana zaune a tsakar gida da yamma, Suwaiba na tsakar gida tana ta jin kaɗe-kaɗe a wayarta, kanta ko ɗan kwali babu. Bararojin nan ce a zaune a kusa da Suwaiba, jikinta duk ya ciko ta warke, ta zura kanta kusa da Suwaiba tana leƙa wayar ita ma. Nana ta yi shiru tana kallon Suwaiba, tana son ta yi magana, amma tana tsoron abin da ka iya biyo baya. "Ke Suwaiba, tashi ki shiga ɗaki, dan jaraba kalli yadda ta zura miki idanu, kar ta ƙarasa tanɗe ki" Mama ta yi maganar cikin haɗe rai. Suwaiba ta kashe wayar, ta yinƙura ta tashi, aikuwa matar ta haɗe rai, kafin Suwaiba ta kai ɗaki, ta hankaɗeta ta faɗi ƙasa. "Kin gani ko? Abin da nake faɗa ko? Dama na ce ba zan zauna da yarinyar nan ba, gashi dai sai ta kashe mini 'ya hankalinta zai kwanta" Kawar da kai Nana ta yi gefe, ta ci gaba da zancen zucinta, dan ba hatsaniyar gidan ce a gabanta ba yanzu. Da daddare Nana ta tsaya tana ƙarewa jakar da ta zo da ita daga gidan sarkin baka kallo, tun da ta zo da ita, ba ta buɗe ta ga abin da yake cikin jakar ba. Yau ma kwanan ihu Suwaiba ta yi, cikin ikon Allah Nana kuma, tun da ta dawo ba ta ihun nan da take yi da daddare sai Suwaiba. Washegari Monday, Nana ta shirya domin jarraba zuwa makaranta, duk da ta san za ta sha bala'i gurin director, na rashin zuwanta tsawon lokaci, amma ta tafi cike da fatan Allah ya sassauta zuciyarsa ya sanya ya karɓe ta, ya biya ta Albashinta, kuma ta ci gaba da aikinta. Sai dai ta tarar da saɓanin abin da take ta fata, domin kuwa ta tas director ya yi mata, ya ci zarafinta ya ba ta takardar kora. Jiki a sanyaye ta karɓi takardar ba tare da ta buɗe ba ta ce "To sir salaryana ka taimaka ka bani na last month" "Ba za a bayar ba, shi ma last month ɗin wani zuwan kirki ki ka yi, kullum ba ki da lafiya" Nana ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah ko rabi ne, ka taimake ni" "Ba zan bayar ba, asarar da ki ka janyo mana, na wahalar neman wata malamar a kuɗinki" Nana ta ji zafin korar da aka yi mata, duk da ta san laifinta ne, amma dai yakamata a bata hakkinta. Ko sallama ba ta yi da sauran malaman ba, dama ba cikinsu take shiga ba, saboda yadda suke yi mata kallon Nanny kawai. Dama da ƙafa ta zo makarantar, dan haka yanzu ma ba ta da kuɗin abin hawa, da ƙafarta ta miƙi hanya. Horn ɗin da aka ishe ta da shi ne, ya sanya ta tsaya, ta waiwaya. Motar baban Muhsin ta gani. Ya ƙaraso gurin da take ya ce "Anty kwana biyu lafiya kuwa? Muhsin na ta rikici ba kya zuwa makaranta shi ba zai zo school ba" "Wallahi na ɗan yi rashin lafiya ne" Cikin tausayawa ya ce "Eyya Allah ya sauwwaƙe, mun yi magana da director ya ce sallamarki zai yi, ba yadda ban yi ba, amma ya ƙi yarda ya haƙura" Nana ta yi guntun murmushi da iyakarsa laɓɓanta ta ce "Ba wani abu, rabona ne ya ƙare a gurin kawai". "Eyya babu daɗi, to hawo na sauke ki a gida" Ta girgiza kai ta ce "a'a ba komai na kusa ƙarasawa ai" "A'a da saura ai na sani, hau dan Allah" ya yi maganar yana buɗe mata ƙofar gaban motar" ta yi bismillah ta hau. "Wallahi ban ji daɗin sallamar ki da director ya yi ba, ki na da ƙoƙari matuƙa gaya." A wannan karon ma murmushin dai ta yi tana wasa da yatsun hannunta. "Ki bani takardun ki, na nema miki admission a school of legal studies, ko koma makaranta mana" Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode sosai" "Me yasa? Karatun ne ba kya so? Nana ba zan cutar da ke ba. Ba na wasa da duk abin da ya shafi yarana, yanzu haka Muhsin ne ƙarami, amma duk lokacin da nake gari ni nake kai shi makaranta, saboda yana son hakan. Da ɗa da dukiya ba ayi musu mugunta ba ka san wa zai amfane su ba. Amma ki yi tunani idan kin amince zan samar miki admission ba, ko ba duka ba zan ɗauki ɗawainiyar karatun naki." Cikin girmamawa ta ce "Ka na cikin mutanen da ba zan manta da su ba a rayuwata, ba zan so ka ɓata kuɗin ka ba, ina ga nan da wani ɗan lokaci za a ɗaura mini aure, kuma garin zan bari gaba ɗaya" "Allah sarki, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Bani wayar ki na saka miki lambata, idan lokacin bikin ya yi ki sanar da ni, zan halarci ɗaurin aure in sha Allah" Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ni da waya ai, ka yi mini addu'a na gode sosai da sosai. Sannan a cewa Muhsin ya yi karatu da kyau, Allah ya yi masa albarka" jiki a sanyaye yake kallon Nana, haka kurum take ba shi tausayi gaba ɗaya yanayinta ya nuna akwai labari mai ban tausayi a tattare da ita. Ya yi parking daidai gurin da take sauka, tana kiciniyar buɗe ƙofar motar, ya miƙa mata kuɗi, ya ce "Ga wannan ba yawa, Allah ya baki wani abin yin." Za ta yi magana ya girgiza mata kai. Ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai"  ya daɗe yana kallon yadda take tafiya da ƙyar ta shige cikin layuka. ***** Malamin Hajiya Sa'a yana zaune, ya duba wurin da yake gabansa, ya kalle ta ya ce "Hajiya a wannan karon ma babu sa'a fa, 'yan aikenmu sun makara, domin fafur sarkin baka ya hana yarinyar nan, ƙarshe ma ya mayar da ita gida, ya ce mu je can mu ɗauke ta, yanzu haka tana can" "Kai wannan wace irin masifa ce? Ni an taɓa bani aiki mai wahalar wannan ma kuwa?" Ya yi dariya ya ce "Ai na gaya miki hatsabibin aljani ne a tare da ita, kuma mutane irinmu, mu na burin mallakar aljani irinsa, domin kaf jinsin babu aljani mai tsananin juriya da kasada kamar sa, tun da sarkin baka ya mayar da ita ba tare da ya mallaki aljanin ba, na san akwai matsala. Yanzu ki bar wannan mu jingine ta zuwa wani lokaci kaɗan. Yanzu ga wani aiki mai ɗan sauƙi, 'yar aikenmu na kan waccan yarinyar da ta yi amfani da turare kuma ta warke ma. Ki duba dangi wanda yake jininki ki samo yaro da bai wuce shekara biyar ba, a sadaukar mata da shi, domin ta ƙara samun kuzari zan sanya ta yi miki wani aiki" Hajiya sa'a ta ɗan yi shiru ta ce "Akwai ɗan wa na, ba zai gagara ba" "To shikkenan, tashi ki je, Sa'a na tare da ke Hajiya Sa'a tun da ki na bibiya ga duk abin da aka saka ki. Ki je za a sanar da ke lokacin da ake buƙata" tashi ta yi tana jin daɗin yabon da ya yi mata. ***** Nana da ta koma gida, ta tarar an kai Suwaiba asibiti, daga gurin masu magani, wai jikinta babu jini an riƙe ta a asibiti. Sam Nana ba ta yi gigin bin su ba, ta dai yi wa Suwaiba Addu'a. Ta duba kuɗin da baban Muhsin ya bata dubu goma cif. Addu'a ta din ga kwarara masa da shi da zuriyarsa, saboda ta ji daɗin kuɗin nesa ba kusa ba. Da yamma Ummi ta zo gidan, ta tarar da Nana a gida. "Nana ke ba ki je asibiti duba Suwaiba ba?" "Hmm kin san da yadda ta yarda nake zaune a gidan nan ne ma? Su na cewa ina ƙoƙarin kashe Suwaiba, wai ina sha mata jini.. sauran maganar ya kakare mata saboda kukan da ya kufce mata mai taɓa zuciya. Jiki a sanyaye Ummi ta ce "Yanzun ma da na je, su na ta maganganu amma dan Allah ki manta da su. Ke dai Allah ya baki lafiya. Na zo ne a kan batun shirin bikinki, Baba ya ce ba za ayi taro ba. Amma ko ba za ayi taro ba ai kya fara gyaran jiki dai ko?" "Me zan gyara? Ni dan Allah ki rabu da ni" Ummi ta ce "Kamar yaya na rabu da ke? Aure fa za ki yi." "Auren jeka na yi ka ba? Ai kun san ba so nake yi ba, amma babu yadda na iya ne, shi ne sauran mafitar da ya rage mini" "Au Nana ba za ki daina maganar ba kya so ɗin nan ba ko? Ke ba kya tausayin kanki da wannan wahalar da ki ke ciki ko? Ki je ki ki yi ta yi, sai mutum ya tausaya miki, idan ki ka tafka wani rashin mutuncin zai gane ke ba abar tausayi ba ce. Ki je ki yi abin da ki ka ga dama, ni na cire hannuna a kan ki" "Allah yana tare da ni, na san shi ba zai cire hannu daga kaina ba" Nana ta yi maganar hawaye na gangarowa daga idanunta. Ayshercool 08081012143 P16 Sosai Ummi ta fusata, da yadda ƙarara take nuna ƙiyayyarta ga Saleh. Bayan tafiyar Ummi da magariba sai ga Saleh, Nana tana iyakar ƙoƙarinta duk da ba ta son Saleh, ta saka wa zuciyarta son aurensa, ko dan samun sassauci daga wannan takurarriyar rayuwar da take yi. Sai dai fafur ta kasa jin komai game da shi balle auren. Ga gefe tana fargabar kar shi ma wani abin ya same shi, ko ƙaisar ya cutar da shi. Har ya yi kiɗansa ya yi rawarsa, Nana ba ta tanka masa ba, har ya yi ya gama ya gaji ya tafi. Washegari da safe tana bacci, Baba ya je ƙofar ɗakinsu da kansa yana ƙwalawa Nana kira. Ta yinƙura ta taso da kyar ta fito ya ce "Nana, tun da Allah ya yi miki dawowa ba za ki koma gurin koyarwar taki ba ne? Na ga tun da ki ka dawo, ba ki je ba sai jiya, yau kuma kin naɗe a gida, ai kya gurgura ki ƙarasa ki samu ɗan abin kashewa a hannun ki, ke da za ki yi doguwar tafiya ki bar gari, duk da na san mijin naki ba zai bar ki haka ba, alamu sun nuna mutum ne mai kyauta da kirki." Tun da Nana ta ji yana ƙara yabon Saleh, da cewar yana da kyauta, ta san Baba roƙe-roƙe yake yi wa Saleh, kuma yana ba shi. "Ina magana kin yi shiru?" "Baba an kore ni" ta amsa a ciki. "Kamar yaya an kore ki?" "Baba daga makarantar mana" Sak ya yi ya ce "Ikon Allah, ke kuwa me ki ka yi haka?" "Korata kawai suka yi " ta bashi amsa tana komawa cikin ɗakin saboda wani irin azababben bacci da take ji, duniyar har juya mata take yi. Nana ta koma ta ci gaba da zuwa islamiyya da take yi, duk a fakaice tana fuskantar tsangwama, saboda yadda ake zargin da saka hannun Imran a kisan malam Auwal, wasu kuma suke zargin aljanunta ne suka yi ajalinsa. Gefe guda ta kan shiga matsananciyar damuwa, a duk lokacin da ta zo makarantar, domin kuwa yana tuna mata da malam Auwal, idan ta kalli bugiren da ya kan zauna sai ta ga kamar za ta ganshi. Dama ba sakin jiki take yi da mutane ba, dan haka nesa da ita da mutane suka ƙara yi da ita bai dame ta ba. Sai dai cikin malaman makaranta babu wanda ya canza mata. Aka sallamo su Suwaiba daga Asibiti, ta sha jini a ƙalla leda biyar, sai dai an kasa gano dalilin da ya sanya jininta yake ƙonewa. Dama zaman su a Asibiti babu ko kwabon Baba, 'yan uwar babar su Suwaiban ce kawai suke ɗawainiya da ita. Bayan sun dawo gida, yadda Mama ke tattalin Suwaiba da sauran yaranta, abin ya yi ta burge Nana yana ba ta sha'awa, ba ta damu da ƙyamar da suke nuna mata muraran a fili ba, wannan soyayyar da kulawar kawai take ƙawa. Da tuno ta su mahaifiyar sai ta ji zuciyarta babu daɗi, sam kamar ta manta da haife su a duniya, ko waiwayen in da suke ba ta yi. Duk da Baba ya ƙara yi mata gargaɗi a kan kiran mahaifiyar tasu, ta sake lalubar waya ta kira layinta amma a kashe. Yanzu wai shirin aurenta ake yi, amma Baba bai tuntuɓi kowa daga ɓangaren mahaifiyar su ba. Da akwai wata ƙanwarta da take zuwa duba su, tare da kakar su, Mama ta shiga ta fita ta saka Baba ya ci musu mutunci suka daina zuwa. Nana tana ɗaki, tana duba muktaril hadis, ta jiyo Baba a tsakar gida, rai a ɓace yana gaya wa Mama iyayen Saleh sun zo, sun nemi a sake ƙara musu sati huɗu, wai bai gama shiryawa ba haryanzu bai samu ɗakin da zai ajiye Nana a can Lagos ba. "To kuma ka yarda da hakan?" Ya ce "To ya zan yi? Ni da cewa na yi ko a ɗakinsa na samartaka a can ikkon, ya saka ta kafin ya samu ɗakin, suka ce mini a suna da yawa wanda suke kwana a ɗaki ɗaya. Na ce musu a ɗaura ko a gidan 'yan uwa sai ya ajiye ta, kafin ya samu gurin sun ƙi yarda" "Lallai ma, wannan ai zancen banza ne, amma dai ka san cewa sati biyu muka yi da kai ko? Kana kallon wahalar da nake ta fama da Suwaiba babu ko sisin ka, sai ta halaka Suwaibar sannan zaka san abin yi ko?" "Ba zata halaka Suwaiba ba, abubuwan da suke faruwa ba yin kanta ba ne na ba ita ma, kuma Suwaiba ma, wataƙila kawai zafin ciwo ne". "Au haka ka ce? Zafin ciwo ko? Wallahi duk abin da ya samu yarana ya rataya a wuyanka da nata". Zuciyar Nana na yawan ingiza ta, ta yi wa Mama martani, amma wata zuciyar sai ta hana ta. **** Kamar baƙuwar halitta haka suka zuba masa ido. Yana kwance yana sauke numfashi a hankali. Goshinsa ya haɗa gumi, idanunsa a rufe. "Da alama ya samu sauƙi, bacci ya ɗauke shi sosai" "Eh nima na gani" "To yanzu shikenan haka zai rayu, ba za a samu maganin larurar nan ba balle ya iya tuna waye shi?" Habu ya girgiza kai ya ce "A'a souley, mai rai ai baya fitar da rai, a duk inda yake. Zan ci gaba da nema masa magani, da yardar Allah na san za a dace. Yanzu idan na rabu da shi ban yi masa adalci ba, ina zai je? Kuma hannun wa zai faɗa? Duk ba mu sani ba. Gara na ci gaba da zama tare da shi, zuwa lokacin da za mu dace da maganin" Sule ya jinjina kai ya ce "Shikenan, amma ni ina jin tsoro ne, na ga hatta magana ma ya daina yi, abin gaba yake yi" "Eh duk da haka ba zamu karaya ba akwai Allah. Za mu biku na ga yanayin gurin, idan zai yiwu mu ci gaba da zama tare da ku, shikenan idan ba zai yiwu ba zamu bar gurin" "A'a babu wata matsala ma, za ku ji daɗin zaman gurin". ***** Sannu a hankali take tafiya a cikin ɗakin karatun, da ke ɗauke da tarin littattafai, kundi kundi. Ta ɗaga kanta litattafai ne iya ganinta a cikin ɗakin, sai dai sun sha ƙura, wasu ma gizo-gizo ya yi musu yana mai yawan gaske. Ta ƙarasa gaban wani tebur, ta ga wani ƙaton littafi a ajiye, gefe ga alƙalami. Bangon littafin na ɗauke da zanen wani abu mara kyan gani, da ba ta gama gane mene ne ba. Ta buɗe cikin littafin, takardar cikin littafin tamkar jemammiyar fatar dabbobi, ba kamar sauran takarda ba. "Duniya sararin subhana. Ƙudura da buwaya ta Ubangiji ta sanya ya halicci jinsi daban-daban a cikin duniya, ya sanya su rayuwa a gurare daban daban. Tarayyar wasu halittun da wasu, ta haifar da gagarumin cigaba, ya yin da wata tarayyar ɗaya ne yake morar ɗaya, ko dai ta hanyar kashe rayuwar ɗayan domin su rayu, ko kuma ta hanyar bautar da ɗaya. Zan iya cewa tun bayan wanzuwar ɗan Adam a doron duniya, al'amura suka fara canza mana kamar yadda muka samu labari, kuma muka karanta a litattafan da kakaninmu su ka rubuta dubannan shekaru da suka gabata. Sun fasalta mana bil adama, da halitta mai tsananin son kai, da hatsabibanci fiye da duk wata halitta da take yawo a doron ƙasa. Mu jinsinmu mun kasance tamkar ruhi ne, mu na iya zuwa gurin da ba sa iya zuwa, mu na ganin abin da ba sa iya gani, mu na aikata abin da ba za su iya ba, kuma mu na doguwar rayuwar da ta zarce ta su, amma duk da haka sun fi mu hatsabibanci. Dan haka mun samu gargaɗi daga gurin kakaninmu da ba mu riski zamani ɗaya da su ba, duk da doguwar rayuwar da suke yi. Sun yi mana gargaɗi da mu guji sharri da kuma kaidin ɗan Adam. Sai dai mun kalli jan kunnen na su, tamkar tatsuniya da hikayoyi, ta yaya halittar da muka keɓanta da wasu abubuwa na musamman sama da su za su iya cutar da mu?. Sai dai kash! Ashe rashin sani ya fi dare duhu, kuma yaro bai san wuta ba sai ya taka. Ku biyoni ku ji yadda bil adama, ya zama sanadin rusa rayuwarmu, da haifar da matsananciyar gaba tare da kassara zuriyarmu muka watsu a duniya, cike da gaba da ƙiyayyar junanmu, bayan kasancewar mu ahali guda." Cikin rawar jiki ta buɗe ɗaya shafin, ba tare da ko neman guri ta zauna ba, domin kuwa zuciyarta cike take da ɗoki, da son jin tayaya aka haihu a ragaya, ta yaya bil adama ya fi Aljani hatsabibanci, har ya yi silar kassara rayuwar Aljani. Allah ya bawa kakanmu tsawon rai, ya yi dubbanin shekaru a raye, har ya fara rikiɗewa ya koma fatalwa saboda tsufa. Fatalwa ba wai mamaci ne zai dawo ya din ga tsorata mutane ba, kamar kamar yadda bil adama suka zata ba, a'a riƙaƙƙen aljani da ya tsufa shi ne yake zama dodo fatalwa ko fatalwa. Kakanmu, mai suna Dirsham da ake yi wa laƙabi da Jaddul jinn, wato kakan aljanu, ya yi shekara da shekaru a bigiren da yake, ya tara tarin 'ya'ya masu yawan gaske. Ko a cikin sauran jinsin aljanu da ba namu ba, su na tsoron sa, kuma su na girmama shi. Na san da mamaki da na ce jinsin aljanu, za a yi tunanin ko gaba ɗayanmu jinsi ɗaya ne. A'a mu ma mu na da jinsi-jinsi kamar yadda bil adama, suke da ƙabilu daban daban, akwai jinnil Ashiƙ, sihir, amar, marid, uƙum, da dai sauransu, kuma yana rubuce a cikin wani littafi da nake kan rubutawa, wanda ci gaba ne da wani tsohon aljani ya rubuta, wanda haryanzu ina kan bincike, ban gama rubutunsa ba. Wannan fatalwa yana rayuwa, da iyalinsa baki ɗaya, a wani ƙasurgumin daji, a wani yanki na gabashin duniya. Tun farkon tarihin duniya, ɗan Adam bai taɓa wanzuwa a gurin ba. Yana gudanar da rayuwar sa yadda yake so da, da iyalinsa, ba tare da wani shamaki ba, adadin yawan iyalan da ya tara sai da suka fara bauta masa, wannan aljani Jaddul jinn, ya zama abin bautar su, kuma sarkin su abin roƙon su. A hankali al'ummar duniya, su ka ci gaba da yawa, da kuma faɗaɗa a cikin duniya, su na mamayar dazuzzuka suna mayar da su alƙarya. Kwatsam wataran hanya ta fara biyo da bil adama ta wannan daji, suna wucewa a kan dabbobin su, su ratse su tafi buƙatunsu da fatauci, hakan ya fara takura aljanun da suke rayuwa a gurin, domin kuwa su kan bi ta kan ƙanan yaransu, da sauran kayan amfanin su, su yi musu ɓarna. Aljanu suka kai wa Jaddul jinn ƙara, a kan abin da bil adama ke yi musu, amma sai ya ce ayi musu uzuri, ba sa ganinmu ne, dan haka kar a cutar da su, duk lokacin da suka zo wucewa kowa ya kwashe abin sa mai amfani kawai a ba su hanya. A irin son zuciya irin na ɗan Adam, kwanci tashi sai suka fara yada zango a wannan daji, da aljanu suka shafe dubbanin shekaru suna rayuwa a ciki. Daga ya da zango, kawai sai suka nemi guri suka yi zamansu, kasancewar dajin akwai dabbobi masu tarin yawa, akwai tsirrai da kayan marmari sosai a ciki. Mu kan rikiɗa mu shiga jikin dabbobi mu yi rayuwa, ko mu shiga jikin bishiyoyi ko tsuntsaye, amma ba tare da tunanin makomar sauran halittun gurin ba, saboda tsabar son kai suka din ga kashe dabbobin nan su na cinyewa, suka din ga sare bishiyoyi masu ɗauke da gidajenmu, su na ƙona bishiyoyin su na gidaje. Sannan suka din ga gayyato 'yan uwansu su na taruwa a dajin nan da muke rayuwa. A wannan lokacin, tsufan wannan aljanin da ake bautawa Jaddul jinn ya ƙazanta, bai mutu ba, kuma ba a canza sarki ba, ga rashin lafiya yana fama. Bil adama suka din ga cutar da mu, hakan ya sanya muka fara ƙoƙarin ramawa, ta hanyar kashe musu dabbobi, yaranmu su kan shiga jikin tsutsotsi su cinye musu amfanin gona. Sai dai duk da hakan, ba su fasa cutar da mu ba yadda su ka ga dama ba, hakan ya sanya sarkin nan ƙoƙarin ɗaukar mataki da kansa. Ya sanya yawunsa a ruwan shansu, dabbobinsu suka din ga sha su na mutuwa, yaransu suka din ga rashin lafiya, suka fara ganinmu muraran mu na tsoratar da su, mu na haukata wasu, mu ka hana su sukuni da kwanciyar hankali. Sai dai suka nuna mana gaba da gabanta, domin sun shayar da iyayenmu mamaki na wannan lokacin, suka samo wani hatsabibin boka, ya zo ya yi wani hatsabibancin ya kama Jaddul jinn , duk da tsufan da ya yi, babu tausayi ba tare da duba tsufan da aljanin nan ya yi ba, bokan ya gayyato 'yan uwansa bokaye, suka yi masa girkar wannan fatalwar aljani, ya zama mallakinsa, ya bautar da shi. Ya mallake da yawa daga cikin waɗanan jinsin na aljanu yake sarrafa su yadda yake so. Wannan zalunci ba zamu taɓa mantawa da shi ba, sai dai ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, shirin faɗa ne, domin kuwa ba mu ƙara waiwayar su ba, sai bayan wasu shekaru,  dan su na ji suna gani wannan boka, ya sanya babansu a cikin wata kwalba ya ajiye a rijiya, bayan da ya daina yi masa amfani. Sun zuriyar Jaddul sun  shiryo gagarumar fansa, ta ko a mutu ko ayi rai, cike da alwashin kawo ƙarshen duk wani iri-irin zuriyar wanda suka yi mana wannan cin zarafi. Jin ta gaji da tsayuwa, ya sanya cikin rawar jiki ta nemi guri ta zauna, domin ci gaba da karanta littafin, sai dai zamanta ke da wuya ta nemi littafin ta rasa. Ta ɗaga kai ta ganshi a can sama cikin litattafan da yanar gizo gizo ta rufe. "Da izinin wa ki ka ɗaukar mini littafi ki ka karanta?" Ya yi maganar yana kallon ta. Nana ta girgiza kai ta ce "Ba iznin kowa?" "Ki ci gaba, sai kin karanto ranar mutuwar ki wataran" "To mutuwa ai dole ce, Allah ya sa mu cika da imani" shiru ya yi mata ya ci gaba da gyara litattafnsa. "Amma dan Allah kai a wani jinsi ka ke na aljanun?" Shiru ya yi bai bata amsa ba. Ta ci gaba da cewa "Ina son na ƙarasa karanta littafin nan, dan jikina yana bani yana da alaƙa da abin da ka ke iƙararin kakanina sun yi. Ko su ne wanda suka gayyato bokan? Ko kuma bokan ne kakana? Dama sarkin baka ya ce na tambaye ka me kakanina suka yi maka" "Idan ki ka ci gaba da matsawa, gwargwadon sanin labarin, gwargwadon yadda za ki saka na canza na fito miki a ainihin kalata, ki bar komai a yadda yake kawai" ta buɗe baki za ta yi magana ta ji an ce "Anty Nana" muryar ɗan ƙaramin yaron nan Muhsin, ɗalibinta ta ji. Da sauri ta kalli ƙaisar ta ce "Muryar ɗalibina muhsin na ji" Cikin ko in kula ya ce "Eh shi ne, tsafi ake da sunansa, za a ba wa aljana jininsa" waro ido Nana ta yi, ta nufi gurin da take jiyo muryar yaron. Ƙaton rami ne, matar take ƙoƙarin hankaɗa shi, Nana ta ga kamar ta san matar, amma ta kasa gane wace ce, yaron ya din ga miƙo wa Nana hannu yana kuka. Gadan-gadan Nana ta nufi matar, tana ƙoƙarin ƙwace yaron. "Nana" ta ji an kira sunanta. "Na'am" ta amsa da ƙyar tare da buɗe ido. Wata Nanny da suke aiki tare a makaranta ta gani. Nana ta ce "Laaa Inna, ke ce ya aka yi ki ka san gidanmu?" Wadda ta kira da Inna ta ce "Ina fa, wucewa na zo yi ta unguwar nan, na yi ta tambaya aka nuno mini gidan nan. Na shigo aka ce mini kina nan kina bacci. Sai kuma ki ka tafi babu ko sallama" "To wace sallama zan yi, ya riga ya kore ni, bari na kawo miki ruwa" Inna ta ce "A'a yi zaman ki, dama wucewa na zo yi, na ce bari na nemi gidan su yarinyar nan na je, tun da muke tare kin sha yin rashin lafiya ban taɓa zuwa ba, ga wannan abu ya faru na ce bari na zo na yi miki jaje, harkar irin makarantun nan sai a hankali, masu karatun ma ya suka ƙare balle mu. Kin ga har gida aka je aka same ni, aka gaya mini gidan wani hamshaƙin mai kuɗi, wai 'yar sa ce za a  din ga yi wa rainon yaro. Mijinta ba ma zauni bane ba, ta koma gidansu to tana da ciki, ga kuma yaro wai za a din ga kular mata da yaron, tun safe ta je makaranta ta dawo, ga albashinka kuma ga  abinci. Amma da na je matar nan ta ƙare mini kallo, wai ban yi mata na yi tsufa da yawa, saboda iya shege irin na masu kuɗi" Nana ta ce "Amma rashin sani ya fi dare duhu, da sun san irin kirkin ki, da amanar ki da ba ta ce haka ba" Sosai Nana ta ji daɗin zuwan Inna, dan rabon da ayi sallama ace gurinta aka zo, ƙawa ko makamancin haka har ta manta, ga dai Inna dattijuwa ce amma ta na son Nana. Hirar da suka yi, sai ta ɗebe wa Nana kewa, ta kai a ƙalla awa uku a gidan, suka yi sallar la'asar, sannan Nana ta fito raka Inna. A hanya Inna ta ce "Ni kuwa Nana, me zai hana ke na kai ki, ko za ki yi wa matar nan, ki din ga yi mata rainon, tun da kin bar aikin koyarwar nan zaman haka babu daɗi, yana daga dalilin da ya sanya na ce lallai bari na nemo gidan ku na zo, na san baki da girman kai " Nana ta ɗan yi shiru ta ce "Inna zan yi, amma sai na yi magana da Baba idan ya amince" Cikin farin ciki Inna ta ce "Yauwwa Nana, ai na san ba zaki bani kunya ba, gobe in Allah ya kaimu zan zo da wuri, idan ya amince sai mu tafi kar a rigamu" "To shikenan, na gode sosai da sosai Inna Allah ya saka da alkhairi, ga wannan kya ci goro" ta yi maganar tana miƙa mata dubu ɗaya a cikin kuɗin da baban Muhsin ya bata. Inna ta kalla ta girgiza kai ta ce "A'a ke da yakamata a tausaya miki, kin rasa aikin ki, ni ba zan karɓa ba" Ba yadda Nana ba ta yi da ita ba, amma fafur ta ƙi, suka yi sallama. Haka kurum Nana ta ji tana ɗoki da fatan Allah ya sa matar ta yadda, ko ba komai ta din ga samun abinci cikin kwanciyar hankali ko sau ɗaya ne a wuni. Tun da Inna ta tafi, Nana ta duƙufa da addu'a, a kan Ubangiji Allah ya taimake ta, idan alkhairi ya tabbatar ma ya kuma kare ta daga dukkanin abin ƙi, ya sanya kuma larurar da ke tattare da ita, ta kunyata. Ba ta samu yi wa Baba maganar ba, sai washegari da safe. Ta zo gabansa ta durƙusa, ta gaishe shi ya amsa, ya ce "Wallahi ko sisi ban wayi gari da ita ba, balle na baki na koko ko naira ɗari ce, ita kuma waccan azzalumar ina ji ina gani, 'ya'yana ne suke kawowa amma sai ta ga dama za ta bani balle ta sammiki, bari Gaddafi ya shigo na karɓi kuɗi a gurinsa, sai na baki ki sai koko ki sha" Nana ta zauna sosai ta ce "Baba ba kuɗi na zo karɓa ba, magana na zo mu yi. Dama wata wadda muka yi aiki tare da ita a makaranta ce, ta zo mini da wata magana. Wani gida ne suke so za ayi musu rainon yaro, za su din ga biya ta ce ko zamu je na gani, idan za su ɗauke ni na ce bari na tambaye ka" Ya ɗan yi shiru ya ce "To ke Nana, ke da za ki yi aure? Ina ke ina wani aiki kuma?" "Baba ko yaya ne, ko na wata ɗayan ne na rage, kuma za a din ga bani abinci, kafin na taho gida" Sai Baba ya washe baki tare da gyara zama ya ce "Allahu Akbar, to ai babu laifi Nana, tun da za su ɗan din ga baki abin kaiwa bakin salati, to Ubangiji Allah ya taimaka ya sanya su ɗauke ki. In an samo abincin dai kar a manta da gyatumi, a kawo na neman albarka" Jinjina kai kawai ta yi ta tashi ta koma ɗaki. Ƙarfe tara da rabi, sai ga Inna ta zo, Nana ta sanya hijjabinta suka fito, Allah ya taimaki Nana Baba ya fita, balle ya tsayar da Inna ya yi ta yi mata surut wanda aka tambaye shi da ma wanda ba a tambaye shi ba. A hanya Inna ta ce "Nana, director fa babu lafiya, ni gaba ɗaya ma na manta wallahi, abinka da jarababben mutum kwana biyu har mun sarara a makarantun" Nana ta ce "Subhnallah me ya same shi?" "Oho masa, ranar dai da ya sallame ki, an tashi daga makaranta da yamma, ya yanke jiki ya faɗi, ɓarinsa na dama ya daina aiki. An kai shi asibiti an yi gwaje-gwaje an rasa me yake damunsa" A take jikin Nana ya yi sanyi, ta shiga fargabar kar dai ƙaisar ne ya yi masa wani abu. Inna ta ci gaba da yi wa Nana hira, kasancewarta mai surutu, hankalin Nana kuwa sam ba ya kanta. Tun da su ka doshi gate ɗin layin, Nana take kallon dogwayen gine-ginen layin. Duk a ƙasan unguwar su rukunin gidajen yake, amma ba ta taɓa zuwa ba. Su na daf da shiga gate ɗin layin, ta ga dandazon raƙuma sun fara fitowa daga layin. Rikicewa Nana ta kusa yi, amma ta fara tunanin wace Addu'a za ta yi, kawai sai ayar waraddallahu lazina kafaru, ta faɗo bakinta, aikuwa ta riƙe ta din ga maimaitawa. Sai raƙuman suka din ga darewa, su na ba su hanya, Inna kuwa ba ta san bidirin da ake yi ba, sai yarfa hannuwa take tana zuba kamar an jefe ta a ka. Nana na sanya ƙafarta a cikin gidan, ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, ta ji gangar jikinta, tamkar ba za ta ɗauke ta ba. Ta daure ta ci gaba da addu'a. Inna ta ce "Nana kalli gida na alfarma, kalli motoci arziki ya yi. Mu tamu ta ƙare ina fatan Ubangiji Allah ya tsunduma ki a tandun arziki Nana, idan kin tuna da ni ko 'yar wanke-wanke ki ɗauke ni zan yi miki." Halin da Nana ke ciki bai hanata murmusawa ba, amma ba ta yi magana ba. Har cikin falon gidan suka isa, su ka gaisa da matar gidan. Ta ce "Bari na saka a kirawo muku ita" Ta umarci wata 'yar aiki, da ta kira Shukura, sannan ta kawo musu ruwa da lemo. Ba a jima ba, aka kawo musu uban ruwa da lemo kaya guda, har da su cincin aka ajiye musu. Wata matashiyar mace ce, da a ƙalla za ta shekara ashirin da bakwai, ta fito da tsohon ciki tana ɗan yamutsa fuska ta zo ta zauna. Suka gaisa sama-sama, sannan Inna ta ce "Dama wata 'yar uwata na kawo miki, ki duba ko ita za ta yi, ta din ga rainon yaron?" Matar da suka tarar ta farko ta ce "Ahhh ni dai ta yi mini" Shukura ta ce "Mummy" "Ba wani Mummy, ba na son iyayi, wannan yaron naki mai shegen kukan tsiya ma, wannan dai ai ta yi kalar haƙuri kuwa. Idan kuma ba haka ba ki tattara ki koma gidan ki, ki ƙyale ni a gidana" Murmushi Shukura ta yi ta ce "Kai Mummy, to ai shikenan, Mummy ta ce kin yi, sai ki fara zuwa gobe in Allah ya kaimu. Sai dai gaskiya ba na son ƙazanta, kuma ba na son cin zali dan ba zan ɗauka ba. Kuma goben ba da kin zo za ki fara ba, family doctor zai zo ya ɗauki jininki, a tabattar ba ki da wani ciwo. Albashinki dubu ashirin ne, za kuma ki din ga break fast, da lunch a gidan nan. Daga safe zuwa ƙarfe biyar za ki din ga kula da shi, idan ma za ki tsaya ki ci abincin dare duk babu matsala" "In sha Allah ba zai gagara ba, kuma duk zan kiyaye" "Shikenan, za ku iya tafiya" "Su tafi ai kya ba su kuɗin mota, a kawo leda a ƙulle musu kayan nan, tun an cinye abincin safe, kuma ba a gama na rana ba" Nana na noƙewa, Inna kuwa ta karɓar musu, tana ta zuba godiya kamar wanda aka gafartawa zunuban su. Sun tashi za su tafi, har sun je tsakiyar falon, matar ta ce "Ba ki gaya mana sunan ki ba, da kuma unguwar ku" Nana ta waiwayo ta ce "Sunana Asma'u, amma Nana ake ce mini. Gidanmu a wajen makarantar ma ahad yake, gidan malam Isa Buda" "Asma'u" ya maimaita daidai lokacin da ya shigo falon. Matar ta ce "Ma sha Allah Nana, to ku gaida gida mun gode" Inna ta ce "mu ke da godiya Hajiya" Sun juya za su fita, ya ƙarasa shigowa cikin falon, dogon mutum ne mai ƙiba, ya ajiye tumbi ya sanya wata dakkakiyar shadda coffee sai ƙyalli take yi. Suna yin ido huɗu da Nana, gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ga tamkar ta san shi. Inna ce ta gaishe shi, amma hankalinsa a kan Nana. Cikin rawar baki Nana ta gaishe shi, ba ta jira ya amsa ba ta yi waje. Inna ta fito tana cewa "Nana ki na da sa'a, kin ga ke ta amince da ke, Allah ya dafa miki" "Amin" ta faɗa a hankali. A hankali Nana take takawa, ji take tamkar gangar jikinta ba za ta iya ɗaukanta ba. Su na daf da ƙarasawa bakin gate, raƙuman nan suka din ga shigowa, kala kala, Nana ta din ga mamakin wannan raƙuman na mene ne take ganinsu ne?. Ta ji jikinta ya ƙara sanyi, gabanta ya ci gaba da faɗuwa, dandazon raƙuman nan sun kewaye harabar gidan Wannan baƙin raƙumin ta gani a cikin raƙuman, idanunsa na ta hayaƙi a hankali ya girgiza ya koma wannan tsohon mai kama da ƙaisar hannunsa riƙe da wata irin sanda doguwa, ya zubo wa Nana ido. Babu abin da yake fitowa daga idanunsa sai tartsatsin wuta. Ya buɗe bakinsa yana fesowa Nana wata irin wuta, mai ɗauke da baƙin hayaƙi. Ta ja da baya ta rintse idanunta, tana maimaita "A'uzu bi kalimattilahi tammat" A hankali ta buɗe idonta, ta ga ko ina ya gauraye da duhu, ba ta iya ganin komai. A take ta karaya ta tabattar da ƙaisar ne ya bayyana. Ayshercool 08081012143 17 Addu'a ta din ga yi, Allah ya sa ba wani abun ya sanya ta aikata a gaban mutane ba. Kar ma su hanata rainon ɗan nasu. Ta laluba za ta tashi tsaye, ta ji ƙasa hakan ya tabattar mata ba a kan shimfiɗarta take ba. Wata irin walƙiyya ce mai tsananin haske, ta bayyana ta haska gurin. Wannan tsohon dai ta sake gani ya bayyana. Iya ƙarfinta ta taƙarƙare ta ƙwala ihu, tare da rintse idanunta. Ji ta yi tamkar an yi sama da ita, an jefar a gefe guda. Ta buɗe idonta tana mayar da numfashi da ƙyar. A tsakiyar sahara ta ganta da wannan mutumin da yake tsaye, hannunsa riƙe da akalar raƙuminsa. Yana tsaye ya zubo mata idanunsa. Ƙaisar ne ya bayyana a gabanta, ya kalleta a fusace ya ce "Uban me ya kai ki gidan nan na ɗazu?" Ta kalle shi ta ce "Kai da ka ke ganina ba na ganinka?, Ai bai kamata ka yi mini wannan tambayar ba" "Ina ɗakin karatu lokacin, ina wani aiki me ki ka je yi gidan?" Ta yamutse fuska ta ce "Me yasa zaka takura mini? Shi ne ka ke ta tsorata ni, saboda ka yi mini dalilin da zai sanya su kore ni, shi ne ka ke bayyana a suffar wannan tsohon ka na razana ni. Dan Allah ka rabu da ni, ka na kallon abin da zan ci gagarata yake yi, ka rabu da ni na yi aikina" "Na gaya miki ba ni ne wannan mutumin ba, ki taimaki kanki ki haƙura da aiki a wannan gidan, idan ba haka ba za ki jefa mu a cikin masifa daga ni har ke." "Na jefa mu ni da wa, meye alaƙa ta da kai? Koma mene ne kaina zan jefa, ka rabu da ni dan Allah" Cikin tsawa ya ce "Ba kan ki kaɗai za ki jefa ba, har da ni, wani abin ba zan iya baki kariya ba, idan da hali ma ki bar unguwar nan gaba ɗaya." Ya yi maganar bakinsa na fitar da tartsatsin wuta Nana ta ja da baya saboda yadda ta razana, cikin kuka ta ce "Idan ban nema ba ƙasa zan ci? Gaskiya ka rabu da ni, ka tafi ka rabu da ni, ko ma wani hali zan faɗa babu ruwanka" "Aikuwa yanzu ki ka fara ganin wannan tsohon, kuma babu lallai na iya kare ki daga farmakinsa, tun da ba za a gaya miki ki ji" Cikin ko in kula Nana ta ce "Dama Allah ne ya kare ni ba kai ba, kuma na san kai ne ka ke fito mini a suffarsa, so ka ke yi sai na yi hauka tuburan sannan zaka rabu da ni, amma Allah ya fi ƙarfin ka, kuma aiki sai na yi shi da ƙarfin ikon Allah. Ba tsoho ba idan ka ga dama ka zama fatalwar cikin littafin da ka ke rubutawa, durham yake ko wa?" Tabbas duka yau, duka gobe shi ke sanya baƙin ba'auzine yin tawaye. Gaba ɗaya yanzu Nana ta daina tsoronsa, ta saba da ganinsa, kuma har da siddabarun da sarkin baka ya din ga nuna mata, ya sanya yanzu ba ta tsoron sa kamar da. Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya tashi Nana, dan daga gidan nan, har zuwa yanzu da ta farka, ba ta san me ya faru ba. Bayan sallar asuba, ta zauna tana azkar, ta duƙufa sosai tana addu'a. Duk da wasu lokutan ta fuskanci idan ta yi addu'a jikinta ya fi ta'azzara, shi yasa wasu lokutan sai ta share ta ƙi yi. Gari na gama yin haske, ta fara shirin fita. Duk gidan yanzu daga Baba sai  Nasiru ne kawai suke shiga harkarta, duk da Mama tana tsawatar masa ta hana shi, amma ba ya ji, yana mugun ɗasawa da Nana, mussaman da ta kasance komai ta samo sai ta neme shi ta ba shi. Tana yi wa Imran addu'a sosai da sosai, tare da fatan Allah ya kare shi a duk in da yake. Bayan sun gaisa da Baba ta yi masa sallama, har za ta fita ta dawo ta ɗaura alwala sannan ta fita. Tana tafe tana yi wa Allah kirari, da neman tsari daga dukkanin shaiɗanin mutum da aljani. ***** Habu ne ya kalli Sule, ya ce "Ka ga yau jikin nasa da sauƙi, har ya tashi ya yi salla da kansa" Sule ya ce "Wallahi kuwa Alhamdilillah, sannu buzu" ya yi maganar yana kallonsa. Kallonsu kawai ya yi, amma bai ce komai ba, yanayin fuskarsa ya rame sosai. "Ko zamu fita waje ka sha iska ne?" Girgiza musu kai ya yi alamar a'a. "To za ka sha bunu" "A'a" ya furta a hankali. Cikin zumuɗi suka kalli juna, jin ya yi magana, dan rabon sa da magana ya daɗe. Tiryan-tiryan Nana ta je gidan, sai dai yau ba ta ga dandazon raƙuman nan ba. Babban abin da ya bata mamaki, bai wuce ganin layin duk buzaye ba, sun firfito sun haɗu a ƙasan wata bishiya, su na ta shan shayi, su na hira cikin nishaɗi. Gabanta ne ya faɗi, ta fara tunanin ko ita kaɗai take ganinsu. Ta kawar da kanta, ta nufi ƙofar gate ɗin gidan. Da azama ɗaya daga cikin su, ya zaburo ya zare takobinsa, cikin gurɓatacciyar hausar ya ce "Kai tsaya nan, gun wa aka zo?" Ganin mutum a tsaye da takobi tsirarta a gabanta ya sanya ta ja da baya tana ayatul kursiyyu a fili. Saboda gaba ɗayansa abin tsoro ne, sai kuma ta ga ta iya haɗa ido da shi, ta san da jama'ar su Ƙaisar ne ba za ta iya kallonsa ba. "Kai magana nike maka, za ka yi magana ko sai na fille kanka?" Yayi maganar yana kuma matsawa kusa da Nana. Sule ne ya buɗe gate ya fito, ya tarar da Nana da Wannan buzun, ya dube su ya ce "Lafiya ka tsaya a kanta da takobi haka?" Buzun ya ce "Mu na ƙasan bishiyar can, mu na ɗumama kanmu, kawai ya nufo zai abka gidan na izini, shiyasa na taso ka san an ajiyemu a gurin nan saboda kama ɓarayi" Cike da takaici Sule ya ce "Kuma wannan ne ɓarawon? Dan an saka ka gadi, sai ka din ga aza wa jama'a makami a ka?" "Ai saboda kar mu bar ɓata gari su kai wa masu gida farmaki" Guntun tsaki Sule ya yi ya ce "Yi haƙuri dan Allah, ke an na gani jiya kun zo ko? An yi mini bayani shigo kawai" Nana ta bi bayansa tana waiwayen na farkon, kar ya biyo ta ya sara mata takobin hannunsa. Tsoron mai takobi bai sanya ta tsaya ta fuskanci, ko ta shiga halin da ta shiga jiya ba da ta shigo gidan. Ta shiga falon da suka shiga jiya da suka zo da Inna. Nana ta din ga rafka sallama amma shiru babu kowa a falon. Tana nan tsaye sai ga wani matashin saurayi ya shigo falon, sanye da singlet da gajeren wando. Nana ta ɗan rakuɓe ta ce masa "Ina kwana?" Ya amsa da "Lafiya ƙalau, wa ki ke nema ne?" "Dama jiya ne aka ce na zo da wuri, zan fara rainon yaro" "Ohh ke ce mai rainon Haidar, za ki sha rigima, ga shi mutanen gidan ba su tashi ba har yanzu, have a seat zauna kafin su tashi" Nana ta zauna a kan lallausan carfet ɗin da yake tsakar ɗakin. Ya wuce gaban tv ya kunna, sannan ya bar falon. Ta daɗe a falon a zaune, ta fara jiyo taku ana saukkowa daga matattakalar benen da ke falon. Nana ta ƙara saita nutsuwa, mutumin jiya ne yake saukkowa, yana sanye da ash ɗin jallabiya, tumbinsa ya fito a cikin jallabiyar, kansa babu hula yana sanye da farin glass, hannunsa riƙe da wayarsa. Kallon kallo suka yi da Nana, Nana ta fara ƙoƙarin tuna wani abu a kan mutumin, ta taɓa ganinsa a wani guri, amma ta kasa tuna a ina ne. Tana ƙoƙarin sansano wani abu a tattare da shi, amma ta kasa tantance komai. "Asma'u ko?" Ya faɗa yana ƙure ta da ƙwala-ƙwalan idanunsa. "Eh, ina kwana?" "Lafiya ƙalau" ya yi maganar yana ƙarasowa cikin falon, ya samu guri ya zauna a kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun da ke falon. "Meye ma ki ka ce sunan babanki?" "Malam Isa" ta faɗa tana sunkuyar da kanta. "Sunan mahafiya fa?" Ya tambayeta ba tare ya sauke idonsa daga kanta ba. "Kar ki faɗa" ta ji muryar ƙaisar a kunnenta" Ta ɗaga kai ta kalle shi, ya ce "Eh jikana za ki raina, mahaifiyar sa  'ya ta ce, dan haka dole na san daga ina ki ke, kuma su waye iyayen ki?" Ta buɗe baki za ta yi magana, matashin nan ya dawo cikin falon ya ce "Daddy ina kwana?" "Lafiya ƙalau, har ka tashi?" "Eh na ɗan motsa jiki ne, na shigo kuma na tarar da baƙuwa na jiran Shukura, amma tana bacci, na je na taso ta ma" "Eh, na ga an samu mai rainon, Allah ya sa ta iya da rigimar sa" Matashin ya nemi guri ya zauna, suka ɗan yi hirar su, Nana dai na gefe, amma hankalin mai gidan a kanta. Suna cikin hirar aka kira shi Alhajin a waya, ya ɗauki wayar ya fita. Shukura ce ta shigo falon, bayanta kuma wata mai aiki ce, ɗauke da yaro da bai fi shekara biyu ba, sai uban ihu yake yi yana zillo sai ya sauka daga jikin mai aikin. Cikin girmamawa Nana ta ce "Ina kwana?" "Lafiya ƙalau. Ki ɗan jira likitan yana hanya. Ke kuma Jummai ki wuce da shi ki haɗa masa abinci, ya bi ya cika mini kunne da ihu" Yanayin yadda yaron ke zambarwar ihu, ka san ba iya abu ne na yara ba, har da sangarta, haka jummai ta wuce da shi tana jijjiga shi tare da yin yaƙe tana rarrashin sa. Shukura na zaune a falo a kawo mata kayan breakfast, ta karya ta gama ta ɗauki remote. **** Cikin sauri yake tafiya, yana kallon agogon hannunsa, ya buɗe ƙofar falon ya shiga. Tun daga bakin ƙofar yake faɗin "Ina yake ya fito na kai shi, mun kusa makara" Turus ya yi yana kallon fuskarta, ganinta itakaɗai a falon, fuskarta ɗauke da yanayin damuwa. "Lafiya kuwa? Ina boy ɗin?" "Ba shi da lafiya" A ɗan diririce Alhaji fatuhu ya ce "Kuma ba ki kira ni kin sanar mini ba, ki ka bar mini yaro ba lafiya?" Cikin damuwa ta ce "Na rasa ma ya zan yi ne, kwana muka yi ba mu yi bacci ba, yana ta ihu da surutai" "Fadila garin yaya ki ka bari sauro ya ciji yaron nan, har ya fara zazzaɓi?" "Daddy ba zazzaɓi ba ne, jikinsa babu alamar zazzaɓi ihu kawai yake yi yana razana" tsaki ya ja ya ce "Dama kina can ki na wannan baccin na mutuwa, ai har zazzaɓi ya kama yaro ya sake shi, ba ki sani ba" yayi maganar yana shiga bedroom ɗin ta. Ya kalli Muhsin da yake ta bacci, ya kai hannu ya taɓa goshin sa, a razane yaron ya miƙe tsaye yana ihu. Da sauri Alhaji fatuhu ya rungume Yaronsa, yana faɗin "Is ok, daddy is here, sannu boy" "Daddy" ya kira sunan babansa cikin razani. "Na'am boy" "Ka kai ni gurin Anty Nana" "Anty Nana kuma muhsin, ai an sallame ta daga makarantar ku" Cikin kuka yaron ya ci gaba da cewa "Daddy ka kai ni Anty Nana, tsoro nake ji" "Ikon Allah, to yi shiru bari mu fara zuwa gurin doctor Sharif ya duba ka, sai a san abin yi, sorry dear may be typhoid fever ne, ko severe malaria su ne suke saka yara irin wannan abun. Bari na kai shi asibiti kawai" Ita dai da ido ta bi shi, dan ta san duk abin da za ta faɗa, muddin ya saɓa da abin da likitoci suka gaya masa ba zai yadda ba. ***** Nana na nan a zaune, likita ya ƙaraso, yanayin yadda suka gaisa da mutanen gidan, da yadda suke jansa da hira, ya sanya Nana gane likitansu ne na iyali da yake duba su. Shukra ta ce "Ga ga nan, ita ce new Nanny na Haidar, ina son a duba a tabattar ba ta da wata matsala kamar dai yadda na gaya maka a waya" Ya ce "Ok, sai dai wasu daga gwaje-gwajen za su yiwu yanzu a nan wasu kuma, sai dai na tafi da jinin nata lab. Amma main abubuwan da yakamata a sani ɗin, Hiv ne da hepatitis, su ne main, za a yi su yanzu sauran kuma zan turo miki result ta gmail ɗin ki" "Ok gata nan a duba" Allura na cikin jerin abun da Nana ta tsana a rayuwarta, tsigar jikinta har tashi take yi idan ta ganta. Amma da yake sa kai ya fi bauta ciwo, haka ta dake. Yana saka allurar a wahale ta ce "Washhh" ya kalli yadda ta haɗa gumi, saboda ɗiban jini. Ya yi murmushi ya ce "Akwai haihuwa a gaba fa, kar ki fara yi wa allura kuka, dan haihuwa ta fi wahala, ko maman haidar?" Ya yi maganar yana kallon Shukura. Yamutsa fuska ta yi ta ce "Oho maka dai, kai ina ka san zafin haihuwa tun da ba kai ka ke yi ba, da ku ka haɗa kai da baban haidar ku ka hana ni zubar da wannan cikin, ga shi ina ta fama da wahala" Ya yi dariya ya ce "Ai saura ƙiris" "Ku kuka sani dai, daga wannan wallahi sai na yi seven years ban haihu ba, sai na yi master's na gama" "In dai kin haihun ba komai, mun yarda" Yana aikinsa su na ta hira, har ya kammala ya kalle ta ya ce "Babu matsala a wannan result ɗin, za ta iya fara aikinta" "Ok to shikkenan doctor, za ka ji alert in sha Allah na gode sosai da sosai" Ya tattara jakarsa, ya tashi zai tafi yana cewa bai ga Hajiya ba, ba su gaisa ba. Wata ɗirkekiyar mage ce ta kusa girman jaririn Akuya, baƙa ƙirin da ita, ta zo ta gindaya a tsakiyar falon. Kallon su Nana ta yi, amma ta lura babu wanda ya ankara da magen, hirar su kawai suke yi. Likitan ya zo wucewa, yana ƙoƙarin taka magen, Nana ta buɗe baki amma ta rasa me za ta ce, tuni ya taka magen, aikuwa yana taka ta ya yi tuntuɓe ya kifa a gurin. Rige-rigen sannu suka din ga yi masa, cikin dakiya ya tashi yana yaƙe, ya ce carfet ne ya saka shi tuntuɓe, kar su damu yana lafiya. Ya sake yi musu sallama ya fita. Yana yin tuntuɓen magen ta ɓace ɓat. A baɗini kuwa da kyar ya daure, bai kurma ihu ba saboda azabar raɗaɗi da zafin da ya shige shi. Ji ya yi kamar ƙashin idon sahunsa ya karkace, da jan ƙafa ya ƙarasa gurin motarsa ya ja ya fita. Shukura ta tashi ta ce Nana ta bi ta, ta yi gaba Nana ta bi ta a baya. Wani ɗaki ta kai Nana, ɗan matsakaici mai kyau, an yi wa ɗakin fenrin blue, duk in da Nana ta kai idonta teddy ne manya da ƙanana, rakwacam har sun yi yawa. Gefe ga ɗan madaidaicin gado na yara. Ta dubi Nana ta ce "Nan shi ne ɗakin Haidar, za ki din ga gyara masa kullum, dan ba kowa na yarda ya raɓi ɗa na ba." Ta buɗe wardrobe ɗaya cike da gwangwanayen madara na yar ta ce "Ba ya cin abinci, sai shayi ko madara, dan haka za ki din ga haɗa masa a kai a kai ki na ba shi. Ga wardrobe ɗin kayansa nan." Tayi maganar tana buɗe ƙofar wardrobe ɗin da aka shaƙe da kaya, ga wani sashe fal da tulin pampers. Hatta kayan wankan yaron an jere su a cikin toilet, kayan alatun rayuwa dai babu wanda babu a ɗakin nan. Ta gama nuna mata suka koma falo, ta ce a kawo wa Nana Haidar. Jummai ta shigo tare da Haidar, hannunsa riƙe da feeder, cike da shayi yana sha. Shukura ta kalli Jummai, ta ce "Yauwwa Jummai ba ta shi, Haidar ga new Nanny ɗin ka" shiru ya yi yana kallon Nana. Nana ta yi masa murmushi, tare da miƙa masa hannunta, amma ya noƙe a kusa da Jummai. Nana tana kamo hannunsa, ya daddage ya saka wani irin ihu, da sai da Nanan ta tsorata. "Ke ɗauke shi, ki tafi da shi ki rarrashe shi, ba na son wannan shegen kukan da yake yi" Nana ta ɗauke shi, ya din ga zunduma ihu, yana buga mata feeder hannun shi, yana zillo yana ƙoƙarin sauka daga jikinta, yana miƙawa Shukura hannu. Cikin tsawa Shukura ta ce "Ki tafi da shi, ki rarrashe shi, ki fara aikin ki" Nana ta nufi ɗakin da Shukura ta nuna mata, ta ce nasa ne. Ta ci gaba da ƙoƙarin rarrashin sa, amma abu ya ci tura. Duk son Nana da yara, sai da ta ƙulu da iskancin da yaron nan yake yi mata. Ta zuba masa ido, ya yi iya yin sa, ya fara lumshe idanunsa, alamar ya gaji da kuka, bacci zai yi. Ta ƙarewa ɗakin kallo, babu wani abu da ya shafi addini a ɗakin, sai uban tarkacen ABCD da teddies. Da ƙyar ya yi bacci, da azahar Jummai ta zo ta samu Nana, ta ce ta zo ta haɗa wa Haidar shayi, yana tashi ta bashi. Nana ta ce "Wai ba ya cin abinci ne?" "Ba ya cin komai, sai wannan shayin, idan kuma an yi sa'a yana cin biscuit ko chocolate" "Amma wannan ba abincin yaro bane" "To su haka tsarinsu yake, abin da yaro yake so kawai ake yi masa, ba bari ba hantara" Nana ta yi ajiyar zuciya, ta bi Jummai zuwa kitchen. Kitchen ɗin makeke ne na gaske, ɗauke da kayan alatu na sarrafa abinci, manmanyan kayan wuta na girki na zamani duk akwai su a kitchen ɗin. Aka haɗo shayi, da uban kauri, ta koma ɗakin da ta baro haidar, ta ajiye ta yo alwala ta fito ta yi sallar azahar. Tana cikin lazumin bayan salla ne, ya tashi daga bacci, yana tozali da Nana ya sake fashewa da kuka. Ta tashi ta nufe shi, cikin sanyin murya tana rarrashin sa, amma ya tubure, ta ba shi feeder amma ya yi jifa da ita a ƙasa. Ta ƙarewa yaron nan kallo, wani takaici ya zo mata wuya, ga gida har gida na masu kuɗi, amma yaron a tsumbure tamkar ƙadangare sai rungumemen kai da uwar ƙeya kamar ƙwarya. Dama ya za ayi yaro ya yi kumari? Da shayi da chocolate kayan basir. Wata uwar tsawa ta yi masa, ya gigice gaba ɗaya, ta ɗukko feeder, ta ce "Sha ko na murɗe maka kai" jikinsa na tsuma, ya karɓa ya kafa kai ya shanye. Har ta yi masa wanka, ta canza masa kaya bai sake ko ƙwaƙwƙwaran tari ba. ***** Alhaji zailani ne, yake zaune shirim a gaban mutumin, ya tattara hankalinsa a kan mutumin. "Ka tabattar sunanta Asma'u dai ko?" Ya jinjina kai ya ce "Sai da na sake tambayarta ma". "To ka samo sunan mahaifiyar ta ta?" Zailani ya ce "A'a Allah ya sa dai wannan ta yi, ina son ayi mini aikin nan wallahi. kamar yadda na gaya maka, sunan babanta kawai ta gaya mini." "To ka zo da ƙasar sawun nata?" "Eh gata a leda, ai tun da mu ka yi waya da kai jiya, na saka aka ɗebo mini" yayi maganar yana fito da farar leda, ɗauke da ƙasa a ciki. Ya karɓi ledar, ya ɗaukko ɗan wani katako mai ɗauke da ƙasa a ciki, ya zuba ƙasar sawun Nana a kai, ya fara zane-zane. Ya ɗan yi shiru, yana kallon ƙasar, ya ɗago ya kalli Alahaji Zailani ya ce "Buƙata za ta biye, wannan ta yi daidai sosai, fiye ma da abin da ake nema, za a samu a gurinta." Washe baki Alhaji zailani ya yi ya ce "Ɗan da ƙyar, har na ji sanyi, yanzu dai ta yi kenan?" Ya jinjina kai ya ce "Ɗari bisa ɗari ma kuwa. Ni nake baka tabbacin samun fiye da abin da ka ke tsammani, taurarinta masu haske ne, duk wanda ya yi tarayya da ita, bisa sharaɗin da zan gindaya masa, zai samu abin da yake so. Ana daɗewa matuƙa ba a samu masu irin tauraronta ba. Sai dai akwai wata matsala" Alhaji zailani ya ɗan ɓata fuska ya ce "Ta me kuma?" "Ban kai ga ganota ba tukuna... "Dan Allah ba sai ka gano ta ba, ni dai kawai buƙata ta ta biya" "Shikenan, an bari jeka Allah ya sa a dace" "Amin, saura kuma batun wancan ɗan iskan fatuhu, ya za ka yi mini da shi ne?" Mutumin ya yi murmushi ya ce "Na ce a kawar da shi ka ce a'a" Alhaji zailani ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar a kashe shi, so nake a naɗe shi da ciwo, komai nasa ya ƙare ya tagayyara ya wulakanta" "Ba matsala, a kawo jariri sabuwar haihuwa, a haɗo shi da zaren mahaifar da mabiyiyyar, zan yi wani aiki da shi, a binne shi da ransa, gwargwadon wahalar da zai sha kan ya mutu, zuwa lalacewar da jikinsa zai yi, haka dukiyarsa za ta lalace. Bayan kwana arba'in za a ciro ƙwarangwal ɗin, a sake aiki a kansa, a  binne a maƙera, gwargwadon yadda suke hura wutar a maƙera gwargwadon karfin ciwon da zai yi" Wata irin ƙyaƙyatawa Alhaji zailani ya yi ya ce "Na gode mutumina, idan babu kai babu ni malam. Dole fatuhu ya ɗanɗana kuɗarsa. Godiya nake" suka rabu ya tafi cikin annashuwa. **** A jikinsa yake jin daɗin jikinsa, da ɗan sauƙi, duk da cikin jikinsa yana jin raɗaɗi. A jikin tagar yake tsaye, yana jin yadda sassanyar iskar la'asar ke ratsowa, tana dukan fuskarsa. Ƙoƙarin takura ƙwaƙwalwarsa yake yi, ko zai iya tuna wani abu game da rayuwar sa, ko yaya yake. Amma ya ji tamkar an ƙara duhu a cikin ƙwaƙwalwarsa. Da ya ƙara ƙoƙari ma sai ya ji zuciyarsa na neman tsayawa da bugu, kansa kuma ya fara ciwo. Hannunta riƙe da leda, ta fito daga cikin gidan, yanayinta ya nuna a gajiye take, sai ɗan yamutsa fuska take yi. Kamar ya so ya taɓa ganinta, amma shi ma dai a wannan karon, ya manta a ina ne. Nana ji ta yi tamkar ana hankaɗa ta, wani irin nannauyan jiri yana neman ya kayar da ita a ƙasa. Kawai ta tsinci kanta a cikin sahara, wata irin azababbiyar ƙura ta turnuƙe gurin baki ɗaya. Wani irin tari ya taso mata, numfashinta ya fara barazanar barin ƙirjinta. Dafe goshinta ta yi da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma tana laluben, abin da za ta samu ta dafa, ko ta kuɓuta daga wannan iskar sahara mai ƙarfin gaske, da take neman sabauta ta. Yana daga inda yake, yana kallonta, sai dai tsananin mamaki ya cika shi, ganin dogon mutumin da yake tare da ita, duk da yana da tsawo sosai, bai hana shi ganin fuskarsa ba. Babu yadda za ayi ya manta da wannan fuskar, domin ita kaɗai ce abin da yake iya tunawa, ko dai ita ce abu na ƙarshe da ya ganu kafin barowar sa, ainihin duniyarsa. Ko kuma shi ne na farko bayan ya shigo cikin wannan rayuwar mai kama da mafarki, a sabuwar duniyar da ya shigo!. Ayshercool 08081012143 18 "La'ila ha illa anta, subhanaka inni kuntu, mina zalimin" Shi Nana take ta ƙoƙarin maimaitawa, duk da harshenta yana sarƙewa. "Lafiya kuwa? Me ya faru?" Ta ji murya a gabanta. Ta buɗe idonta, sai ta ga babu guguwar, babu kuma saharar. Wannan matashin saurayin nan ne na ɗazu da ta zo ta tarar a gidan. "Lafiya na ga ki na dafe kai?" "Amm.. kawai ji na yi kaina yana ciwo" Cikin tausayawa ya ce "Sannu, Allah ya sa ba rigimar Haidar ce ta saka miki ciwon kan ba, idan kin ga aikin da takura ba za ki iya ba, ki ajiye kawai" Da sauri ta ce "A'a ai babu wahala zan iya, kawai babu tsammani na ji ciwon ne, amma zan iya" Ya jinjina kai ya ce "To shikkenan, har kin tashi kenan?" Ta jinjina masa kai. "To sai Allah ya kaimu" Ta amsa da "To na gode" cikin sauri ta nufi hanyar waje, kuma duk wannan balahirar, ledar abincinta na hannunta. Yana kallon yadda mutumin nan, yake biye da Nana, tana zuwa giftawa gurin ɗakin da yake tsaye, mutumin da yake binta, ya zura wata sanda ta tagar ya hankaɗa shi da ita. A take ya yanke jiki ya faɗi a sume. ***** Likita ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Babu wani abu da yake damun Muhsin, malaria ce +1 sai ɗan infection a jininsa, common antibiotics ma sun isa da ɗan anti malaria" Alhaji Fatuhu ya ce "Haba doctor Sharif, ka ce babu abin da yake damunsa, ga malaria ga kuma infection, ni ban san ya aka yi aka bari sauro ya cije shi ba, matan nan sakacin su ya yi yawa" Doctor Sharif ya ce "A'a su na iyakar ƙoƙarin su fa, ɗan Nigeria ai ɗai ɗai ne, ba su da malaria. Zan rubuta magunguna in sha Allah ba wani abu". Ya yi rubuce-rubuce a kan takarda ya bawa Alhaji Fatuhu, ya ɗauki Muhsin ya je pharmacy ya sayo masa. Su na tafe Muhsin yana cewa "Daddy ka kaini gurin Anty Nana" "Muhsin Anty Nana, ta bar school ɗin ku, kuma na tambayeta lambarta, ba ta da waya, amma zan saka a nemo ta in sha Allah" Ya jinjina kai, suna tafe a hanya yana shafa kan yaron nasa, cike da so da ƙaunarsa. Wayar Alhaji Fatuhu ce ta fara ringing, ya ɗaga tare da yin sallama ya ce "Alhaji zailani kun ji ni shiru ko?" Daga can ɓangaren ya ce "Wallahi kuwa, ya gida ya iyali?" "Alhamdilillah, wallahi Muhsin ne babu lafiya, na kai shi asibiti bari na ƙaraso kawai mu yi abin da za mu yi" Cikin kulawa Alhaji zailani ya ce "Allah sarki, ɗan auta babu lafiya? Subhanallah abu bai yi daɗi ba, ayi masa sannu Allah ya bashi lafiya" "Amin Daddy mun gode, bari mu ƙaraso yanzun nan in sha Allah" suka yi sallama. **** Yamma ta yi sosai, Nana ta na sauri ta ƙarasa kafin magariba. Tana shiga layinsu, Baba ya hangota ya washe baki ganinta da baƙar leda yana faɗin "Ga Nanaz ga Nana" Ta ƙaƙalo murmushi domin ta san tatsuniyar gizo; ba wuce ƙoƙi, wannan sannu da zuwan na baƙar ledar hannunta ne. "Baba sannu da gida" "Yauwwa yarinyar kirki, sannu ya gidan aikin naki? Ina fatan babu wata matsala dai ko?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, babu wata matsala Baba" Ya jinjina kai ya ce "To ma sha Allah, haka ake so, me ki ka ƙullo a cikin ledar nan ne?" "Baba Abinci ne, ko za ka zo mu koma gidan sai ka ci?" Ya ce "Ahhh lallai kin fara aiki a sa'a, yanzu jeki gidan maza ki jira ni, bari na je na yi salla yanzu zan dawo." "Tom" ta amsa ta nufi gida. Ko da ta yi sallama, ta yi mamaki da Jamila ta amsa mata. Ta shiga ɗakinsu, ta ajiye ledarta da hijjabinta, ta fito Suwaiba na kwance kanta babu ɗan kwali, tana ta jin kaɗe-kaɗe, kanta ko ɗan kwali babu, ga shi an daf da fara kiraye-kirayen sallar magariba. Nana ta yi alawala, ta je ta zauna ta fara azkar a ɗakinsu da yanzu suka bar mata, su Jamila a ɗakin mama suke kwana, Baba kuma sai dai ya kwana a tsakar gida, ko ɗakin su Nasir da suke tsula fitsarin kwance. Idonta ne ya sauka a kan jakar fatar gurin sarkin baka, har cikin zuciyarta ta ji tana son sanin halin da yake ciki yanzu, tana son sanin halin da yake ciki ko ya warke?. Tun da ta zo ba ta taɓa buɗe jakar ba, haka kurum ta ji bata ra'ayin hakan. Shiru ta yi tana tuna abubuwa da dama, na rashin Auwal, sake guduwar Imran da haryanzu ba ta san a wane halin yake ciki ba, an kama shin ko ba a kama shi ba Allah masani. Ga uwa uba rashin mahaifiya da yake damunta. Babu maraba da ita da marainiya. Ga uwar a raye amma an nesan ta su da ita, kuma ita ma ba ta bibiya ta ji a yaya suke. Ga tarin matsalolin gidan su, da babu daɗi, ga rashin lafiyarta da ƙaddarorin rayuwa da suke bin ta kashi-kashi, kuma babu wani wanda za ta raɓa ta ji sanyi. A take ta ga duhun magaribar da ya kawo kai ya ƙara tsananta a zuciyarta. Sai ta ji tamkar duniyar ita kaɗai aka tsana. Duk da ta san idan ta yi aure, akwai yiwuwar ta samu sassauci, amma a wane irin aure ake saka ran sassauci? Auren da babu bincike babu shiri babu komai, burin mutanen gidan kawai su rabu da ita, saboda ta zame musu tamkar wani kaya ne marasa amfani da suka rasa yadda za su yi da ita. Baƙin cikinta ya ninku bayan tuna yadda mama, ta dage a kan ba zata ci gaba da zama da ita ba, ga sharri da ƙage kala-kala da suke nema su zama barazana a gare ta. Ta yinƙura da ƙyar ta tashi ta yi sallar magaribar, da ta idar ta yi tasbihi ta idar, sai ta rasa wace addu'a ma yakamata ta yi. Muryar Baba ta jiyo yana ƙwala mata kira a tsakar gida. Ta tashi ta ɗauki ledar abincin nan da yake doya ce fal da miyar ƙwai, ta kai wa Baba ta ce dama shi ta kawowa. Ya so ya tsare ta da surutu, sai dai ganin yanayinta ya sanya ya fasa, kar ya je ta burkice masa. Har aka yi sallar isha'i ma, Nana na zaune tana ta tubka da warwara. Ba ta san iya adadin lokacin da ta yi, tana zaune tana ta tunani ba. Ji ta yi mararta ta cika da fitsari, dan haka ta tashi ta fita. Tsakar gidan shiru ba kowa, alama dare yayi sosai, ta shiga ta yi fitsarin, ta fito da niyyar ta ɗebi ruwa ta yi alwala, ta jiyo Suwaiba ta fara kururwar a taimake ta, Nana tana sha mata jini. Cak Nana ta tsaya, aikuwa Suwaiba ta fito da gudu tana kurma ihu, cikin zafin nama Nana ta danƙe ta. Mama ta fito da gudu, haka ma Baba ya kaso da gudu daga ɗakin su Nasiru. Kafin su ƙaraso Nana ta shaƙe Suwaiba, cikin ɗaga murya ta ce "Kar ki ƙara kiran sunana ki ce ina sha miki jini, ko dai ki bayyana kanki, ko kuma ki ka kuma kiran sunana sai na murɗe miki wuya, ko na haɗa ki da Ƙaisar ya babbake ki" Mama ce ta yo kan su, tana ihun Nana ta cika Suwaiba, amma Nana ta saka hannu ɗaya ta ƙara shaƙe Suwaiba, aikuwa ta din ga kakari idanunta suka yo waje. "Ki gaya musu ba ni ki ke gani ba" "Dan Allah ki cika ni, wallahi ba ke nake gani ba, ki yi mini rai" "Da ba ki yi galaba a kaina kin cutar da ni ba, sai ki koma kan 'yar uwata ki saka a din ga zargina?" Cikin dasashshiyar murya Suwaiba ta ce "Ba zan sake ba ki yi haƙuri" "To bar nan gurin, ko kuma na saka a kai ki gurin sarkin baka, ya rufe ki a cikin randarsa" "T..to..tom" Nana ta hankaɗeta ta faɗi ƙasa. Baba da Mama suka yi kan Suwaiba da take ta wani irin tari, yawu mai kauri da yauƙi na wahala na fitowa daga bakinta. Nana ta nuna su da yatsa ta ce "Kullum ba ta da aiki sai jin kiɗa da shigar banza, idan ba ku yi wasa ba, sai ta kashe ta tukuna" Baba ya kalli Nana ya ce "Wace ce?" "Wata bararoji ce take zuwa kanta, tana shan jininta, amma na manta meyafaru amma dai... Ba ta ƙarasa maganar ba, ta daina ganin su Baba, sai ƙaisar. Muryar ƙaisar ta ji ya ce "A tunaninki bayanin da ki ke yi musu zai sanya su yarda da ke ne? Sai ma dai su yi miki wani sharrin. Uwar ɗakin Jamila ce suka bayar da turare a kawo miki, da kin shafa turaren nan, da shikenan jininki za a kai ƙungiyar matsafa." Cikin damuwa Nana ta ce "Meyasa a zahiri idan na tashi ba na tunawa?" Yayi murmushi ya ce "Saboda babu wanda zai yarda da ke, kuma ba ma wannan ba, muddin ki ka fara faɗar haka kin haifar da matsalar da dole sai kin samar da maganinta ne. Maganin kuma shi ne karɓar ƙaddararki." Tsaki ta ja tare da haɗe rai. Ya bayyana a gabanta a suffar wani ƙaton baƙin tsuntsu. Ya ce "Da kin amince ki na zaune, ni zan din ga kawo miki maganin, aikinki bayarwa kawai. Marasa lafiya za su din ga magana da ni ta hanyar ki" "Ban san tsawon shekaru nawa za a ɗauka ina nanata maka ba zan yi shirka ba" Ya buɗe fuka-fukansa yana shawage a gurin ya ce "Ba zan nemi yanka, ko sadaukarwar jini ba, in nemi a yi mini yanka ko makamancin haka shi ne shirka. Kuma maganin da zan bayar babu najasa a ciki, ba na cikin jerin aljanun da suke zama a cikin najasa. Ba zan ci gaba da musu da ke ba. Na san dole akwai lokacin da zai zo ki buƙace ni. Zan nuna miki wani abu, amma kafin nan ki tabattar zan hukunta ki a kan tsakin da ki ka yi mini. Kalli can" Ta kalli gurin da ya nuna mata, Muhsin ne ya bayyana a jikin mahaifinsa, yana karkarwa. Wata mata ta gani tana ta ɗaɗɗaura masa wani baƙin zare a jikinsa, amma da alama daga uban har uwar yaron babu wanda yake ganinta. Dan sai ɗura masa maganin bature suke yi, su na shafa masa ruwa a jikinsa. A take Nana ta kiɗime, sai dai kafin ta yi magana ya tari numfashinta da cewar "Kuma ina mai sake gargaɗinki da lallai ki daina zuwa wannan gidan da ki ka fara zuwa, dan kuwa ba ni da tabbacin za mu tsira daga abubuwan da suke tunkarar mu daga ni har ke" "Ni Allah ne yake kula da ni da ƙaddarata, kuma idan na bar gurin na daina zuwa, kai za ka din ga bani ci da sha? Ina duk a dalilinka na rasa aikina?" "A'a ba dalilina ba ne ba, kuma dan dai abin da za ki ci ki sha ki yi buƙatun rayuwa ba zai gagara ba. Na san inda zan kai ki, ki bayar da maganin na samar miki da komai" "Wallahi ba zan yi ba" "Shikenan, sake kallon can" Ta sake ɗaga kai ta kalli gurin, da sauri ta sanya tafukan hannayenta ta rufe idanunta. Alhaji Zailani ne, a tsaye tsirara ya gurfana yana lasar jini a wata tasa. Ƙaisar ya ce "Jinin ɗan Adam ne ɗan uwanku yake lasa, wanda duk muguntarmu a jinsinmu ba za mu yi wa junanmu haka ba. Kuma yana cikin mutanen da ku ka gani, da ke da sarkin baka, da gawar mai ciki. Sannan ki sani a gidansa ki ke aiki, kuma kema babu tabbacin za ki tsira daga gare shi" Nana ta sauke tafukan hannayenta da sauri, domin yi wa ƙaisar magana, amma ta ganta a kan shimfiɗarta a kwance, zuciyarta na wani irin matsanancin bugu, da take iya jin sa har cikin kunnuneta. Sai dai juyin duniya ta tuna me ta gani a bacci abu ya gagara, tayi-tayi, amma ta kasa tuna komai. **** Sosai su sule su ka yi mamaki yadda suka zo ɗaki, suka tarar da shi a sume. Saboda ya samu sauƙi, har ya tashi ya yi wanka ya ɗan fita ya zagaya. Duk da baya magana amma akwai alamun sauƙi a tattare da shi. Su na tunanin ko Asibiti za su kai shi, sai kuma ya farfaɗo cikin ikon Allah. Cikin harshen faransanci, Habu yake tambayarsa me ya same shi. Amma ya girgiza masa kai, ya sake tambayar sa ko akwai gurin da yake yi masa ciwo nan ma ya sake girgiza kansa. Ya tashi zaune ya jingina da jikin bango ya lumshe idanunsa. Tunani yake yi wace ce wannan yarinyar a ina take? Ba damuwarsa yarinyar ba, mutumin da suke tare, yana da yaƙinin mutumin ya san ko waye shi. ***** Wayewar garin Allah, tun bayan sallar asuba, Mama take bala'i wai a gaban Baba, Nana ta shaƙe Suwaiba, amma bai yi komai ba. Babu wanda Nana ta saurara, ta shirya ta fice shi kansa Baban, ba ta tsaya ta kula shi ba. A ƙofar gida ta haɗu da Gaddafi, bai kula ta ba, bata kula shi ba, ta tafi. Dan tun da Allah ya sa ta dawo gidan, bai ƙara ko yinƙurin shiga harkar Nana ba. Yau ma buzayen ta tarar a jikin bishiyar jiya, su na ta shan shayi, suna hira cikin nishaɗi, tana son ta ƙarasa gidan da ta zo, tana jin tsoro kar yau ma wani ya zare mata takobi, dan ita gaba ɗayansu tsoro suke ba ta, gani take kamar akwai wanda ba mutane ba ma a cikin su. Tana cikin yin wasi-wasin, kawai ta ga an buɗe gate ɗin gidan, da sauri ta nufi gurin, sai ga Habu na ƙoƙarin fitowa. A ɗan tsorace Nana ta ce masa "Ina kwana?" "Lafiya ƙalau sannu ko" Ta amsa da "Yauwwa, dama shiga zan yi" Ya ce "To bismillah" ta shiga tana ajiyar zuciya. Ta nufi hanyar cikin gidan, ta ji haushin kare, gigicewa ta yi ta ƙwala ihu. Sule ya fito da sauri, yana duba me ya saka Nana ihu. "Mene ne?" "Kare" ta yi maganar a diririce, tana jiran ta ga ta ina karen zai fito. Ya ce "Ai yana ɗaure a baya, ba za ki ganshi ba" Waige-waige take yi cikin tsoro, ba tare da ta yadda da abin da ya faɗa ba. Sai ma ƙoƙarin ja da baya ta koma da take yi. Ya ce "Mu je na raka ki" ya yi gaba ta bi bayansa tana waiwaye kar karen ya fito. A ƙofar shiga, suka yi kiciɓis da Yusuf. Ya kalle su ya ce "Lafiya?" Sule ya ce "Kukan kare ta ji take jin tsoro, shi ne na rako ta" Muryar Nana na rawa, ta ce masa "Ina kwana?" Maimakon ya amsa sai ya yi dariya ya ce "Mu da muke saka ran nan gaba, ke za ki din ga ba shi abinci. Ki kwantar da hankalinki yana kulle ai" ta jinjina kai ta kalli Sule ta ce "Na gode sosai" Ya jinjina mata kai ta shiga. Yau ma Nana ta sha fama da Haidar, gaba ɗaya yaron sangartacce ne, ba a kwaɓarsa. Ba kuma ta son saba masa da zare ido, ya koma jin tsoronta gaba ɗaya, ace muzguna masa take yi. Ga babarsa kamar dai babu yadda ta iya ne, ya sanya ta bar Nana take rainonsa, amma a zahiri take nuna mata ƙyama. Aka ce Nana ta je kitchen, ta ɗauki abincin karyawa. Bayan ta karɓo abincin, ta ɗauki Haidar, ta tafi da shi ɗakinsa. Shayi ne da soyayyen dankalin turawa, da ƙwai. Ta ajiye kwanon a tsakiya, ta kalli Haidar ta ce ya saka hannu ya ci. Da wasa da rarrashi, da hikima yana ci yana zubar da wani, tana tattarewa tana yi masa wasa da haka ya ci abincin. A hankali Nana ta samu ya ɗan fara sakin jiki da ita, har ta yi masa wasa ya yi dariya. Alhaji Zailani na zaune a cikin motarsa, a harabar gidansa zai fita, sai ga ɗaya daga cikin yarn da suke yi masa hidima a gidan ya ƙaraso, ya durƙusa suka gaisa. Alhaji Zailani ya ce ya buɗe motar ya shiga. Ya shiga motar, suka ƙara gaisawa, Alhaji ya ce "Ya ake ciki?" "Eh ranka ya daɗe na je, na kuma yi bincike a kanta da gidansu sosai, gaskiya ba su da komai, ba ka ga gidansu ba ma kamar turken dabbobi. Rabi ginin ƙasa rabi na bulo, a iya binciken da na yi ko sana'ar kirki babanta ba shi da ita. Kusan kowa a gidan shi yake kula da kansa, kuma an saki babarta ba ta gidan, babu wani gata dai balle kulawa" Alhaji zailani ya jinjina kai tare da ajiyar zuciya, ya ciro kuɗi ya bawa yaron nasa ya ce "Ga shi nan na gode sosai" ya karɓa yana godiya ya fita daga motar. Da yamma liƙis ta fito za ta tafi, yau ma hannunta riƙe da ledar abincinta na rana. Ta fito ta kullo ƙofar shiga cikin falon, tana ɗaga kai ta hango buzayen nan, zaune a cikin harabar gidan, suna ta dafa shayi su na sha, su na hira cike da nishaɗi. Tunani ta shiga yi, yadda za ta ratsa ta gabansu ta wuce, da safe idan ta zo su na gefe, amma yanzu su na cikin gidan, dole ta gabansu za ta bi ta wuce. Idanunta ne suka sauka a kansa, yana gefe shikaɗai, fuskarsa sanye da shuɗin rawani. Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faɗuwa, da sai da ta ja ta tsaya. Ta ɗan jima a tsaye, sannan ta fara tafiya a hankali ta nufi hanyar fita. Kallo ɗaya ya yi mata ya gane ta, sai dai ya yi mamakin yadda aka yi yau, bai ganta tare da wannan mutumin ba. Ganin tana tunkarar gate ɗin, tana haɗa hanya ya sanya Habu tashi, ya nufi gate ɗin shi ma. A kusan tare suka ƙarasa, ya kalle ta ya ce "Kin taso kenan" Ta jinjina masa kai kawai. Ya ce "To ki gaida gida" "Tom na gode" ta fita daga gidan da sauri, sai bayan fitar ta sannan ta ɗan samu nutsuwa. Ko da ta je gida, Yaya Atine ta tarar da Mama ga kuma Baba a gefe. Tana ganin haka ta san akwai wani abu, da ƙyar ta dake ta ce wa Yaya Atine "Ina wuni" Ta amsa da "Lafiya ƙalau, ashe kin samu aiki a wani guri" "Eh" Nana ta yi magana tana tashi tsaye tana ƙoƙarin barin gurin. Yaya Atine ta ce "Dawo nan, ai a kanki ake magana" Nana ta dawo ta samu guri ta tsuguna. Ta ɗora da cewa "Wai ya jikin naki, bayan mun baro ki a gidan mai magani ya aka yi?" Kan Nana a ƙasa ta ce "Da sauƙi" "Kamar yaya da sauƙi, sauƙi sosai ko kuwa, kuma ya ki ke jin jikin naki yanzu?" Nana ta amsa da "Lafiya ƙalau" kanta a ƙasa. A ɗan hasale Yaya Atine ta ce "Ina magana, ki na sunkuyar da kai, to matar ubanki ta kafe, a kan sai kin bar gida ba za ta zauna da ke ba, tun da har kin fara shaƙe mata 'ya. Kin san dai ko kin bar gidan nan baki da gurin zuwa. Ana ta lallaɓata ta yi haƙuri, ta saka wa ƙofar ɗakin ki kwaɗo ta ce ba za ki shiga ba, sai kin bar gidan nan, ko ita ta bari. Mu na ta bata baki a kan ta yi haƙuri zuwa lokacin aurenki, na ce shi mijin naki haryanzu ba wata magana a ƙasa? Lokacin da suka tsayar ɗin har yanzu maganar na nan ko kuwa?" Wani ƙululun takaici ya turnuƙe Nana, idanunta suka cika da hawaye ta ce "Ni bani da waya" "Ni ki ke gaya wa baki da waya? Ba ya zuwa ne?" Nana ta jinjina kai alamar eh. "To ke kuma ba zaki bibiya ki neme shi a wayar ba? Wato zaman gidan nan ne bai ishe ki ba ko Asma'u? Da ki ka samu wanda zai kwashe ki, da ke da larurar ki, amma ba za ki nutsu ki kwantar da hankalinki ba. Idan matar ubanki ta zube masa yaran nan, ta tafi, ke za ki maye masa gurbinta ne? Ki yi wa kan ki faɗa, duk gidan nan ke ki ka fara kai wa shekaru kamar naki ba ki yi aure ba" Yaya Atine ta gama yi wa Nana ta tas. Ba ta ce uffan ba, ta tashi ta nufi ɗakinsu, ta ga kwaɗo a jiki. Ta dubi Mama ta ce "Zo ki buɗe mini, zan shiga" "Ni ki ke gaya wa haka?" Ta sake cewa "Eh, ki zo ki buɗe mini ƙofa zan shiga ɗaki" Baba da bai yi magana ba tun ɗazu, sai yanzu ya ce "Nana babar taku ki ke gaya wa haka?" "Baba ya zan yi ne? Jakata zan ɗauka na fita na shiga duniya? Na karɓi zaɓin ka zan auri mutumin nan, amma ni ba na son sa, saboda na faranta muku, na yadda zan aure shi. Baba duk cikin yaranka nice kawai baka ƙauna saboda kana jin haushin mahaifiyata, kuma ba ni da cikakkiyar lafiya, Baba ya zan yi ne? Na daina zuwa Islamiyya saboda tsangwama, cewa fa ake ni na kashe malam Auwal. Gida ma babu daɗi, an ce mini mayya, an ce ina shan jini Baba ko dai tsinto ni ka yi, ba kai ne ka haife ni ba?" Da ƙyar sauran maganun nata suke fita, saboda kuka da ɓacin rai." Yaya Atine ta din ga tafa hannaye ta ce "Ma'u malam Isa ne fa baban ki, shi ki ke gaya wa wannan maganganun?" "Idan ki ka ci gaba da ƙyale matar nan, sai ta haɗa kai da matar babanku ta saka an kore ki daga gidan nan, ki je ki shaƙe ta kawai" Ƙaisar ya ci gaba da sanya mata wasi-wasi. Ta dake ta fara addu'a, amma jikinta ya hau rawa. Ayshercool 08081012143 Page 19 Baba ya ce "Atine kin gani ko, Allah ya sa ba jangwalo ta ki ka yi ba" Gaddafi da tun ɗazu yana soro, yana jin duk abinda ake yi. Duk da ya yi alkawarin fita daga shirgin Nana, ga haushinta da yake ji, amma abinka da jini ɗaya, kawai sai ya ji bai ji daɗin abin da aka yi mata ba. Sallama ya yi ya shiga, suka amsa ya kalli yadda Nana ke ta tsuma idanunta na zubar da hawaye. Ya kalli Mama ya ce "Ina mukullin ɗakin nan yake?" "Kamar yaya?" Ya ce "Mukullin ɗakin da ki ka rufe" "Ni fa ba zai yiwu na ci gaba da zama da yarinyar nan ba... Gaddafi ya katse ta da cewa "Baba zai iya canza ki, amma ba zai iya canza abin da ya haifa ba. Kuma so ki ke kamar yadda ta yi iƙirari ta ɗauki jakarta ta shiga duniya? Yadda ake zaginta a yanzu da cewar mayya ce, ana gudun larurarta, kuma ba za ku tsira ba, idan ta shiga duniya ta yi abin kunya, dan zai iya hana sauran yaran auruwa. Ki yi haƙuri kawai tun da kwanaki ya rage ta bar gidan. Idan ba haka ba kuwa Baba sai dai ka tabattar da ka sama mata gurin da za ta je ta zauna. Idan kuma ka shirya abin da wancan makakken ɗan naka zai yi maka idan ya dawo ya tarar ka kori ƙanwarsa shikenan. Dan wallahi tsaf zai kai ka human rights ya rufe ka" Jikin Baba ya yi sanyi, babu yadda ya iya, ya ce wa Mama ta bayar da mukullin ɗakin da ta rufe. Rai a ɓace ta ɗaukko ta bawa Gaddafi, ya karɓa ya buɗe ƙofar ɗakin, ya dubu Nana ya ce "Shiga, gashi nan an buɗe ɗakin" Sai dai ya ga ta ƙi gaba ta ƙi baya, tana tsaye a guri ɗaya tana ci gaba da tsuma, hawaye na zuba daga idanunta. Har zai ƙyaleta, sai kuma ya kama hannunta, ta din ga takawa a hankali ya shigar da ita ɗakin, ya kwantar da ita ya fito. Ya kalli Baba ya ce "Dan zatin Allah ko ta farfaɗo, ka da wanda ya shiga sabgarta, kar ku ja ta ƙara birkicewa, ta hana mutane bacci yau. Shi kuma batun Saleh ina da lambarsa, zan tuntuɓe shi na ji ya ake ciki" Yaya Atine ta miƙe ta ce "A'a ni bari na tashi na tafi, kar ta zo ta shaƙe ni a banza" Mama ta kwaɓe baki ta ce "Ke ma kenan da ki ke zuwa ki tafi, mu kullum a haka muke." Da haka Yaya Atine ta tafi ta bar gidan. Nana ba ta farka ba sai can dare, ta fito ta yi alwala ta yi sallar magariba da isha'i, ta ga ledar abincinta a cikin ɗakin, ta zauna ta ci ta sha ruwa, sannan ta nemi guri ta kwanta. Ta yi addu'oin kwanciya bacci. Sai dai tana rufe idonta, ta ga hoton Buzun nan kamar yadda ta ganshi ɗazu da yamma kafin ta taho gida. Dumm wannan karon ma ƙirjinta ya buga, ta buɗe idonta tare da dafe ƙirjinta. Tun daga lokacin bacci ya ƙauracewa idonta har aka yi assalatu... **** Kaiwa yake yi yana komowa a cikin falonsa, a tsakiyar dare, yana ta lissafin yadda zai ɓullowa lamarin. Yana matuƙar son buƙatar sa ta biya cikin gaggawa. Ya ma fi ƙaguwa ya cimma wannan nasarar kafin ya koma kan Alhaji Fatuhu. Saboda ya sha fama sosai, kafin kwatsam a samu wadda aikin zai yiwu da ita. Sai dai bai san yaya take ba, 'yar hannu ce za ta ɗauki haske kai tsaye, ko kuwa sai ya yi 'yan dabaru?. Haka ya yi ta wasi-wasi shikaɗai. Wayewar garin Allah, Nana ta tashi normal, sai dai bacci da take ji sosai, saboda baccin da ba ta samu yi jiya ba. Babu wanda ya tashi a gidan, ta shirya ta fita. Makarantar da ta bari ta fara zuwa, Inna tana ganinta ta din ga murna. Ta ce "Mutuniyar, daɗina da ke akwai amana, ai na zata har kin manta da ni ne" Ta yi murmushi ta ce "Haba da kuwa na kama ni an zane ni" Inna ta ce "A'a babu wanda ya isa zane ki, to yaya aikin? Ba wata matsala?" Ta jinjina kai ta ce "Babu matsala, da farko dai yaron ne rigimamme, amma daga bayan nan mun fara sabawa da shi" Inna ta washe baki ta ce "Ai dama na san za ki iya, ki na da haƙuri sosai" Nana ta sake murmusawa ta ce "Ya jikin director kuwa?" "Oho masa, an ce dai haryanzu ba ya magana, yana nan a wheelchair ake ɗora shi. Ga shi tun da ya kore ki, an rasa wanda zai iya da rigimar yaran nan" Nana ta ce "Wallahi Inna kewar yaran nan nake yi, mussaman Muhsin, shi ne na zo da kaina na gansu, mu gaisa" "Eyya Muhsin babu lafiya, ya daɗe ba a kawo shi ba" Nana ta kalli Inna ta ce "Ba shi da lafiya, me ya same shi?" "a'a ban sani ba, amma haka dai aka ce" Nana ta yi shiru tana tunanin kamar ta san abin nan, kamar ya taɓa faruwa a wani guri an ce mata yaron ba shi da lafiya, amma ta rasa a ina ne. "To Inna ba ki san gidansu ba, na je na duba shi?" "Wallahi Nana ban sani ba, ai ke ya kamata na tambaya ma, yadda babansa yake mutunta ki" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ban san gidansu ba, amma haka kurum na ji na damu, yaron nan yana matuƙar ƙauna ta. Allah ya ba shi lafiya dan Allah Inna ki ɗan bincika mini, ko Allah zai sanya a samu gidan nasu" "In sha Allah, ya na ga kin tashi har za ki tafi? Ba za ki jira yaran su zo ba, ku gaisa?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a gara na tafi kawai, kar na makara a can gidan" Inna ta raka Nana har ƙofar makarantar, suka yi sallama. Sosai batun rashin lafiyar Muhsin ta tsaye mata, duk da normally yara su na rashin lafiya, amma sai ta ji wannan kamar akwai wani abu da ba dai-dai ba. Da tuna-tunanen ta ƙarasa gidan da take aiki, sai dai yau ba ta ga buzayen a waje ba. Ta fara bubbuga gate ɗin da ɗan ƙarfi, a zuciyarta tana ta karanto Addu'oi tare da fatan Allah ya sa kar ta yi wani abu da zai saka su san ba ta da cikakkiyar lafiya. Habu ne ya buɗe mata ƙofar, ta shiga tare da gaishe shi, ya amsa mata cikin sakin fuska. Sai dai tana jin haushin kare ta ja ta tsaya. Ya kalle ta ya ce "Ya dai?" "Dan Allah ka raka ni bakin ƙofa, tsoro nake ji" Yayi dariya ya ce "Karen fa a ɗaure yake, amma muje" Yana kwance a cikin ɗaki, idanunsa a lumshe yana bacci, kamar a mafarki ya jiyo sautin muryarta. Cikin azama ya tashi zaune, ya kalli gefensa Sule ne yana ta bacci. Ya tashi ya ƙarasa gaban tagar ɗakin da suke, ya leƙa. Tare da Habu ya hange ta, sai dai a wannan karon ma, babu mutumin da ya gansu tare wancan karon. Har ta samu ta shige cikin gidan. Ya sauke ajiyar zuciya, ya dawo ya nemi guri ya zauna ya yi shiru. Shigarta falon ke da wuya, ta tarar da Alhaji Zailani kirim a kan kujera, shikaɗai a falo. Dan sai da ta ɗan tsorata. Da ƙyar ta iya gaishe shi, amma maimakon ya amsa mata, sai ya yi zuru da ido yana ƙare mata kallo. Ba ta sake yi masa magana ba, ta wuce ɗakin Haidar. Yana ta bacci, ta tashe shi, tayi masa wanka ta wanke masa baki, ta haɗa masa tea ta samo plate ta gutsutsura masa ƙosan da ta zo da shi, ta ajiye masa. Ta saka shi ya yi bismillah, sannan ya fara ci. Yana wasa, yana jagwalgwalawa, tana gyara masa a haka ya ci ya ƙoshi. Ta gyara ɗakin, ta ɗaukko shi suka dawo falo, yana ta wasanninsa, tana kallonsa tana murmushi, sai dai lokaci lokaci, idan ta tuna da Muhsin sai gabanta ya faɗi. A haka Hajiya Amina, mahaifiyar shukura ta zo ta tarar da Nana da Haidar, ta shiryo za ta fita tare da Alhaji Zailani. Ta ce "Ga Haidar ga kuma Nana, lallai ke 'yar baiwa ce, zuwan ki gidan nan, mun samu sassauci da ga rikicinsa na tsiya, me ƙaton kai kawai" Nana ta yi murmushi ta gaishe ta ta amsa. Alhaji Zailani bai ce komai ba, sai kallon Nana kamar tsohon maye. Har suka bar falon. **** Muhsin na kwance a kan gadon Asibiti, an saka masa oxygen ga ruwa ana saka masa, Alhaji Fatuhu ya yi shiru cikin damuwa, ya riƙe hannunsa cikin matsananciyar damuwa. Gefe mahaifiyarsa ce a zaune sai share hawaye take yi. Wata babbar mace ce a gefen su, ta kalli Alhaji Fatuhu ta ce "Wai Alhaji kai ma kukan za ka yi ne? Kai ka na yi ita tana yi, maimakon ayi masa addu'a." Babu wanda ya kula ta a cikin su. Ɗaya matar wadda take kama sosai da mahaifiyar Muhsin, ta ce "Kin san ƙaramin yaro da shiga rai, amma dai bai kamata ya biye mata ba". Matar ta sake yatsuna fuska ta ce "Sai ka ce shi ne kaɗai ɗansa, da zai bi ya ɗaga hankalinsa haka?. Likita ne ya yi sallama suka amsa baki ɗaya, ya ƙaraso tare da nurse, suka gaisa ya yi musu ya mai jiki, sannan ya shiga dudduba jikin Muhsin. Cikin damuwa Alhaji Fatuhu ya ce "Likita wai haryanzu babu takamaiman abin da yake damunsa?" Likitan ya kalle shi ya ce "Mu na ta ƙoƙarin ganowa Alhaji, ka yi haƙuri mu na kan bincike ne. Yanzu dai zan rubuta NG-tube, aje a sayo a saka masa, saboda a din ga ba shi abinci" "Meye shi ɗin?" "Roba za mu saka masa a hanci, a din ga ba shi abinci ta ciki" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, na shiga uku shikenan ba zai tashi ba?" Mahaifiyarsa tayi maganar cikin kuka. Likitan cikin tausayawa ya ce "A'a zai tashi in Sha Allah, ki yi haƙuri kar ya zauna babu abinci ne, amma zai warke in sha Allah" Shi kansa Alhaji Fatuhu dauriya kawai yake yi, ji yake yi tamkar ya fashe da kuka. Yana da yara biyar, Muhsin ne na shida ƙarami, 'yar sa ta biyar kusan shekarar ta goma sha biyar daga baya ya auri maman Muhsin, dan haka yaron ya shiga ransa nesa ba kusa ba. Likita ya ɗan yi amfani da kalaman kwantar da hankali, Alhaji Fatuhu ya mayar da hankali kan maman Muhsin, yana ta rarrashinta, saboda sosai take kuka, ba tare da jin nauyin mahaifiyarta da take zaune ba ma. Ɗaya matar ce ta tashi, cike da kishi ta yi waje, ba tare da ta yi musu ko sallama ba. Kakar Muhsin, ta yi gyaran murya ta ce "Ni kuwa Alhaji, na ce mai zai hana a jarraba na gargajiya. Ayo rubutu a ba shi ko Allah zai sanya a dace" A take ya haɗe rai, fiye da yadda fuskarsa take ya ce "A'a Umma, ba za a ba shi wannan ƙazantar ba, yanzu ma ana fama an rasa gane kan sa ina ga an ba shi abin da ban san ya aka yi aka wanke ba, da wani ruwa ma aka wanke ba a ba shi infection." "To ai ana rubutawa a bawa mutum, sai ya wanke da kansa, kuma ayoyin Allah za a rubuta a wanke a ba shi, ko ayi masa tofi a ruwa, a ba shi" "A'a Umma ba musu nake yi miki ba, amma ni dai a bar wannan maganar ga likitoci nan su na iya ƙoƙarin su a kansa" Umma ta jinjina kai ta ce "To shikenan" ya jima a gurin, sannan ya tashi ya tafi domin yana da abubuwan yi sosai da sosai. Yana fita Umma ta ce "Yau na ga tsiya, ko ba za a sha rubutu ba, amma ai a sha tofi, su turawan da suke yin maganin ya san tsiyar da ake haɗawa? Ke rungumi ɗanki, ki yi ta tofa masa abin da ya sauwwaƙa na Alqur'ani." Cikin kuka ta ce "Wallahi Umma ina tofa masa, shi ma yana yi masa, rubutu ne dai ko a tofa ruwa a bashi yaƙi yarda" "Tun da ya tafi tofa ki bashi, ba gara shan rubutun ba, ka san Alqur'ani ne ba, shi na yahudawan ya san da me aka haɗo ne?" Haka Umma ta ci gaba da sababi. ***** Cikin ikon Allah, tun shaƙar da Nana ta yi wa Suwaiba, ba ta sake ihun Nana tana sha mata jini ba. 'yan kuɗin hannun Nana, na gurin baban Muhsin su take ta lallaɓawa tana kashewa a hankali. Da magariba ta yi wanki ta gama duk ta shanya, su Jamila duk su na tare da Mama, suna hira. Baba ya yi gyaran murya haɗi da yin sallama, suka amsa masa, ya ƙaraso ya ce "Nana, jeki ga yaron can ya zo yau. Dama Ummi na kira na tambaya ba'asin ƙin zuwa da ba ya yi, balle a ci gaba da shirye-shirye, ta yi magana da shi ya ce "wulaƙanci ki ke yi masa, ki yi ta haɗe rai, kuma imarana na yi masa rashin kunya. Na rarrashe shi na ba shi haƙuri yanzu, kuma na gaya masa Imranan baya nan, wallahi ki ka sake ki ka je ki ka yi masa rashin mutunci, sai na saɓa miki" Ba ta ce komai ba, sai dai a duk lokacin da aka yi zancen Saleh, ranta ɓaci yake yi. Ta yi iya ƙoƙarinta a kan ta taushi zuciyarta ta fara son shi, amma abu ya gagara. A ƙofar gida ta tarar da shi, sai dai yau an yi sa'a dogon wando ne a jikinsa. Askin banzan nan dai shi ne a kansa, wanda yake haɗuwa ya ƙara masa muni. "Amaryar da ba kya nema na" Nana ta kai zuciyarta nesa ta ce masa "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau. Baba yana ta mitar ba na zuwa, balle a ci gaba da shirye-shirye. Ni kuma ke ɗin ce in dai zan gani hankalina ba ya iya kwanciya. Sai sha'awarki ta addaba mini, amma ke ko kaɗan ragewa juna zafin nan na ga alamar ba za ki yadda ayi ba. Zamanin nan in dai da soyayya fa babu abin da ba ayi, kuma ai Allah gafurun rahimu ne" Zuba masa ido ta yi, kunnuwanta na karɓa maganganun rashin ɗa'ar da yake yi, cike da jahilci da wauta. Ya ƙara matsawa kusa da ita ya ce "Yi magana mana Nanasko, wallahi in dai ina ganinki, ba zan taɓa samun nutsuwa ba, ko ɗan taɓa ki na yi, na samu sukuni" "Wallahi ka taɓa ni, sai ka yi dana sanin zuwanka duniya. Kai abin da ka ɗauka aure kenan?" Saleh ya ce "Eh mana, idan ba shi ba ne mene ne? Ni fa idan aka ɗaura aure kafin mu tafi Ikkon zan fara more angoncina, dan haryanzu ban samu ɗaki ba. Duk ɗakunan tsada suke yi. Ba na son kuma gidan haɗaka mai maza da mata ne" Nana ta ce "Ka jahilci ma'anar aure idan haka ne, maganganu ka ba sa nuna komai sai zunzurutun wauta da rashin sanin ciwon kai" Ya ce "Ba komai na ji na yadda" yayi maganar ba tare da jin zafin maganganun Nana ba. Tsaki ta yi, ta juya za ta koma cikin gida, kafin baƙin ciki ya saka ta wanka masa mari, ko ta ci masa mutunci. Kawai ya riƙo hijjabinta yana "Haba Nanasko, haka za ki tafi babu sallama irin ta masoya, ko na lalata ki fa ni ne zan aure ki, ba kuma zan guje ki ba, rungume ki kawai nake so na yi, na ji ƙirjinki a jikina" "To sannu tsinanne, sakar mini hijjabi, kafin na ci zarafin ka" Ƙara matsawa ya yi yana ƙoƙarin haɗeta da bango, ta tattaro ƙarfinta, ta hankaɗa shi ƙasa, ta juya da saurin gaske ta shiga gida, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa. "Ke Nana har kin dawo? Ya tafi ne?" "Eh" ta faɗa a taƙaice ta shiga ɗaki. Ta cire hijjabinta ta riƙe a hannunta, zuciyarta na wani irin tafasa yanzu shikenan wannan shi zai zama mijinta, uban 'ya'yanta? Ta san duk bayanin da za ta yi wa Baba, ba zai yadda ba, ba ma zai fahimce ta ba, saboda idonsa ya rufe burinsa kawai ta yi aure ta yi gaba, mussaman yanzu da Mama ke ta yi masa barazanar zube masa yaransa ta tafi. Muryar Baba ta ji a ƙofar ɗakin cikin faɗa ya ce "Ina magana kin yo gaba, bai ce miki komai ba game da shirye shiryen?" "Baba bai ce mini ba, ni wallahi Baba ba na son sa, ko ƙaunar ganinsa ba na yi, bai cancanci a ba shi aure ko ya zama uban da zaka zaɓawa 'ya'yanka ba, dan Allah Baba a fasa auren nan" ta yi magana cikin magiya, hawaye na zirarowa daga idanunta. Tsaki kawai ya ja ba tare da ya ce mata uffan ba, ya yi gaba abin sa. ***** Yanayin damuwar da Nana take ciki, bai hana ta yin murmushi da ta ga Haidar ba. Shi ma murmushin ya yi, ya saukko daga kan kujera ya nufo ta. "Ba ka ce ba" Ya durƙusa a ƙasa, cikin gwarancin yara ya ce "Anty ina kwana" kamar yadda Nana ta koyar da shi. Ta ce "Lafiya ƙalau, sai ɗayan" "Good morning" "Mornin my boy, how are you?" "I am fine, thank you" ya faɗa yana tashi tsaye, haɗe da yin tsalle. Ita dai tana son yara sosai da sosai, ko ma tana da rabon yin auren oho. Ta tambayi kanta ta bawa kanta amsa. Ƙamshin turaren Hajiya ne ya karaɗe falon. "Nana har kin zo?" Cikin girmamawa Nana ta ce "Eh, ina kwana Hajiya" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya ɗan naki?" Nana ta kalli Haidat ta ce "Haidar, ka manta?" Ya kalli Mummy, ya durƙusa ya ce "Mummy ina kwana, good morning" Baki buɗe Hajiya take kallon Nana da Haidar. "Ikon Allah, Haidar ne da gaisuwa yau? Nana ke ki ka koya masa?" Ita dai murmushi kawai ta yi, idan ba a fara koya masa abubuwa yanzu ba sai yaushe?. Bakinta ya kasa rufuwa, cikin matsanancin farin ciki, saboda duk son da suke yi wa yaron, azabar kukansa ya sanya suke ƙyale shi. Shukura ta fito tsaf za ta tafi makaranta, Haidar yana kallonta, amma bai je gurinta ba. Mummy ta ce "Shukura, Haidar fa iya gaisuwa, ka gaishe da mamin ka" Noƙe kafaɗa ya yi yaƙi ko kallonta. Nana ta ce "To ɗaga ni, mun ɓata kuma yau ba zan karanta maka littafin ba" Daga kwance ya ce "Mami ina kwana" Ɗan kwaɓe baki ta yi, ta amsa ta fice. Da yamma da Nana ta tafi, ganin da sauran lokaci, ya sanya ta hau abin hawa ta tafi gidan Ummi. Ummi na ganinta ta ce "Alhamdilillah, da gidan zan tafi ai, na kira Baba na gaya masa, ya ce ba kya nan ki na gurin aiki" Nana ta ce "Me ya faru?" "Dama game da maganar shirye-shirye ne, kuma kwatsam jiya Saleh kwana ya yi da ciwon ciki a asibiti ya kwana, ɗazun nan na dawo na ce dama yakamata ki zo mu je mu duba shi" A hankali Nana ta furta "Ƙaisar" Ummi ta ce "Me ki ka ce?" "A'a ba komai" "A'a bari na kaɗa miya, mu je ki duba shi, yana jin jiki sosai wallahi, jiya wai har da dafara ya din ga fitarwa" "Allah ya ba shi lafiya, amma ba zan je ba" "Nana, ba za ki je ba kuma? Wanda za ki aura ɗin?" "Wallahi Ummi ba na ƙaunar sa, na danne zuciyata ne na amince na aure shi, domin farantawa Baba, amma na ga alamar garin faranta masa, zan shigar da rayuwata da yarana cikin madauwamiyar nadama ne. Ummi ke kan ki kin san Saleh ba mutumin kirki ba ne na, kawai dan ku na son na yi auren nan ne" Da fari Ummi ta hasala, amma sai ya danne ta ce "Nana, ana duba miki yanayin rayuwa ne. Ko ba mutumin kirki ba ne ba, idan ya shiryu sanadin ki, sai ki samu lada. Ba da ke muka karanta littafin ƙarfe a wuta ba a gidan nan, da Jauhar ta yi juriya ba ki ga yadda ta canza mijinta ba.. "A'a fa Ummi, littafi ba gaskiya ba ne, kuma shi Vipern ai ba ɗan iska bane ba, koma ba haka ba, kin san ina da juriyar da zan iya kamanta abin da Jauhar ta yi, amma wannan misalin da wancan da ki ke bayarwa gaba ɗaya ba iri ɗaya bane ba. Ina mamakin ace a aurawa namiji mace ta gari zai shiryu, lalatacciya kuma kowa gudunta yake yi. Ke ba ki san abin da ya yi mini ba, gaskiya ba zan iya auren sa ba wallahi" "Nana, ki tsaya ki saurare ni.." Banza Nana ta yi mata, ta ɗauki ledarta, ta fice daga gidan. Washegari Nana ta koma gidan rainon yaronta. Ta riga ta saba, ko ba ta tarar da kowa a falon ba, ɗakinsa take tafiya, ko ta tafi kitchen gurin Jummai, ta taya ta aikin girki. Sai dai ta tarar Haidar baya ɗakinsa, ta dawo Falo sai ga Mummy. Suka gaisa, ta ce "Nana ba ki ga ɗan naki ba ko? Yana gurin kakansa, yau sai da Haidar ya gaida kowa, har fatiha ya fara iyawa. Kin yi ƙoƙari sosai mun gode" Nana ta ce "Bakomai" "Babansa ma da aka yi waya da shi, yana ta murna, yanzu ma kakansa ya ce ki je, yana son ganinki. Amma kafin nan akwai 'yan kayana da na Shukura da muka yi kwalema, ki duba idan da wanda za su yi miki, wannan da ki ke sakawa duk sun mutu" Nana ta ce "To" Mummy ta yi wa Nana jagora, har ɗakinta, ta ɗebo mata kayan fal, ga uban dogwayen riguna, kaya masu tsada, ba su yi komai ba wai ba a so. "Idan ki na so, kafin ki tafi, duk ki ɗiba ki tafi da su, ki canza wannan na jikin ki, ki je ɗakin Haidar sai ki saka" Nana ta karɓi doguwar rigar da Hajiya ta bata, ta tafi ɗakin Haidar. Ita kanta ta yaba kyawun da ta yi a cikin kayan, ta daɗe tana burin sanya ire-iren waɗannan rigunan, amma Allah bai bata dama ba. Ko da ta koma gurin Mummy, ta yi ta koɗa mata irin kyan da ta yi a cikin kayan. "Ma sha Allah, Nana haka ki ke tubarkallah mai kyau, kin ga diri ma sha Allah. Mu je Alhaji yana ta murna yadda ki ke kula masa da jikansa". Nana ji ta yi tamkar ta ce ba zata je ba, amma ba ta da wani zaɓi da ya wuce rufa wa Hajiya Amina baya, suka tafi sashin Alhaji Zailani. Haidar na ta tsalle-tsallensa a falon, yana kaiwa yana komowa. A hankali ya ɗaga kai ya kalli hanyar da suke shigowa. "Alhaji ga ta" Sai dai ya ƙare wa Nana kallo sannan ya ce "Ma sha Allah, zuwan ki gidan nan kin zo da kyakyawan alkhairi fa, na ji daɗi sosai da sosai, yadda ki ke kula da jikana, na yi mamakin yadda yake yadda da mutane yanzu har ya iya gaishe ni" Nana ta sunkuyar da kai, tana wasa da yatsunta ko kallon Alhaji Zailani ba ta son yi. Ita dai ba ta taɓa ganinsa ba, amma ta rasa ya aka yi take yi masa kallon sani, ta tsane shi har haka. Ya kalli Mummy ya ce "Amina, ina ga a ɗakin ki fa na bar glass ɗi na, ina ta son tura kuɗi, amma ba na gani sosai" "Ok bari na ɗaukko maka" ta yi maganar tana tashi. Tana fita ya dawo da idanunsa kan Nana, yana ƙare mata kallo yadda zai samu riba biyu a tattare da ita. Ga kyakyawar ƙirar jikin da Allah ya yi mata ga kuma taurarin ta. "Matso daga nan mana mu yi magana" yayi maganar yana nuna mata gefen ƙafarsa. Ta ce "A'a nan ma ya isa" Ya numfasa ya ce "Na ji daɗin irin kulawar da ki ke bawa Haidar. Amma nima ina da wata buƙata da nake neman agajin ki" Cikin mamaki Nana ta ce "Ni kuma? Ƙwarai kuwa" ya yi maganar muryarsa na rawa. Ayshercool 08081012143 Page 20 Dawowar Mummy ce, ta sanya shi yin shiru. "Ba a ɗakina fa ka bar shi ba, na duba baya nan" cewar Hajiya Amina tare da ƙoƙarin zama a kusa da shi. Ya ce "Too, ikon Allah ko ina na yar da shi Allah masani. Nana ko?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Nana. Ta jinjina masa kai. "Ɗauki yaron ki, ku tafi zan bayar da saƙo a kawo miki, mu na godiya sosai da sosai" Nana ta miƙe, ta kamo hannun Haidar suka fita. Duk da rigar ta ɗan yi mata yawa, saboda ta Hajiya Amina ce, amma hakan bai hana bayyanar da yadda ƙugunta yake juyawa ba. Bayan ta gama duk abin da za ta yi wa Haidar, ta tafi kitchen tana taya Jummai aiki, su na ɗan taɓa hira. Sai dai ƙasan zuciyarta tana mamakin, me mutum kamar Alhaji Zailani yake nema a gurinta? Duk da zuciyarta tana ƙoƙarin kawo mata ko wata muguwar ɗabi'ar zai nuna mata, amma sai ta kawar da wannan tunanin. Jummai ta ce "Nana dan Allah miƙa wa buzayen nan abinci, Shukura zan dafawa nata abincin, kafin ta dawo ta yi ta bala'i" Nana ta ce "To" Ta ɗauki ƙatuwar cooler abincin, tana tafe Haidar na biye da ita. Habu ta tarar ta ba shi, ya karɓa tare da yin godiya. Maimakon su koma cikin gidan, sai ta ƙyale Haidar ya yi ta wasa yana tsalle-tsallensa, tana gefe tana kallonsa, tana jin daɗin ganin yadda yake wasa cikin nishaɗi. Muhsin ne ya faɗo mata, take ta nemi annurin fuskarta ya ɗauke. Jikinta ya yi sanyi, tana matuƙar son ta san halin da yake ciki. Tashi ta yi daga inda take, ta kama hannun Haidar, da nufin su koma cikin gida, amma ya ce shi ba zai koma ba, haɗe rai ta yi ta kalle shi, ba tare da ta ce masa komai ba, a take ya nutsu ya bita suka koma. Bayan la'asar ta gama abin da take yi, ta ɗaukko kayan da Hajiya Amina ta bata, ta yi musu sallama ta fito. Da fari shayi yake sha, yana zaune a kan benci, yana facing ɗin ƙofar falon, tana fitowa ya ja rawaninsa ya mayar, ya rufe fuskarsa. A hankali take tafiya, tana ɗan rarraba ido, ko ƙifta idanunsa ba ya yi, har ta farga kallonta yake yi, suka yi ido huɗu da shi. Sai dai wannan karon ba ta ji faɗuwar gaba ba. Ta yi saurin ɗauke nata idon, ta sake ɗaga ido, ta ga still ita yake kallo, ga shi shi, ba a ganin fuskarsa sai idanunsa kawai. Murguɗa masa baki ta yi, ta harare shi, amma tamkar maye ya ci gaba da kallonta. Sai kuma tsoro ya kama ta, ta haɗa da sauri, ta ƙarasa gate ɗin, ta fara ƙoƙarin buɗewa, amma ta gan shi a rufe. Tayi-tayi amma ta ga ashe key aka saka ta ciki aka rufe gate ɗin. "Dan Allah buɗe mini ƙofa, zan tafi gida" ta yi maganar da sigar magiya. Sai dai kamar an gina shi, ko motsi bai yi ba, balle ta sanya ran zai amsa mata. "Bawan Allah dan Allah ka buɗe mini, zan tafi gida ne na tashi" ko kallonta bai yi ba, ya ci gaba da kaɗa ƙafarsa a hankali. Ajiye kayan hannunta ta yi, ta ɗan ƙara matsawa daf da shi, ta ce "Malam magana nake yi, ko baka jin hausa?" Takaici ya kama Nana, ko kurma ne ai yakamata ace ya na jin sauti, kuma tun da ya ganta a gurin ai ya san tafiya za ta yi. Sule ne ya nufo ta, hannunsa riƙe da kwanon abincin kare, ya ce "Malama kin fito?" Nana ta ce "Eh, ina ta yi wa wannan ɗan uwan naku magana, ya yi mini banza" Sule ya kalle shi ya ce "Banza ya ce miki?" "A'a ya yi mini shiru" Ya ce "Auu shiru bai yi magana ba? Ba shi da lafiya ne, ki yi haƙuri" Ta ce "Kurma ne?" Sule ya ce "A'a yana ji, magana ce ba ya yi" Maimakon ta tafi, sai ta ce "Bebe ne kenan?" Sule ya ce "Bebe me kenan?" "Ba komai, buɗe mini na tafi" Ya ajiye kwanon hannunsa ya buɗe mata, ta ɗauki kayan har za ta fita, sai ta waiwaya aikuwa karaf idanunta a cikin nasa. Ta ja kayanta ta fice ta tafi gida. ***** Cikin damuwa Mama take kallon su Jamila, Suwaiba jiki ya ɗan yi kyau kwana biyu. "Jamila, wai haka za mu ci gaba da zama babu wani ci gaba? Kun san da an aurar da yarinyar nan kanku zai juyo, kuma haryanzu kuma babu wani tsayayye na kirki, duk sai takarce" Jamila ta ce "Taɓ, ai wallahi babu wanda ya isa ya yi mini abin da ake yi wa Nana, wallahi bujirewa zan yi" "Ke dalla rufe mini baki, kafin a kai ga hakan ba sai a samu mafita ba, na gaji da kashe kuɗi a gurin malamai, babu wani saurayin kirki mai kuɗi, duk sai gayyar tsiya". Jamila ta ce "Ni fa auren nan ko na yi shi, ko kar na yi shi bai dame ni ba, ni damuwata na samu mai kashe mini kuɗi, nima na ɗana rayuwar jin daɗin nan, wannan baƙin talaucin nan na gidan nan, idan ka biye masa, haka rayuwar ka za ta ƙare, ka je kuma auri talaka irin Baba ka ci gaba da gyangyaɗa rayuwa, jin daɗi sai dai ka ga wasu suna yi" Suwaiba ta ce "A ina za a samu mai kuɗin, mu ba wani shegen kyau ba" Jamila ta ce "Kanti za mu shiga wallahi, dan ni ina ganin allura ma zan yi" Suna cikin maganar, Nana ta shigo da sallama, kasa amsa sallamar suka yi, sai bin ta da kallo, ganin kayan da suke jikinta, ga hannunta ta jakar kaya. Nana ba wani shahararren kyau ne da ita ba, sai kyakyawan diri, domin jikinta shi ne babban rashin tsaronta. Idan ta taho ta gaba duk hijjabin da ta saka, baya ɓoye ƙirƙirar ƙirjinta. Baƙa ce mai matsakaicin tsayi. Ta fito tsakar gida ta ɗebi ruwa ta yi wanka, ta yi alwala. Jamila ta kasa jurewa ta ce "Nana ina ki ka samu wannan rigar? Ta yi miki kyau sosai" Nana ji ta yi tamkar ta share ta, saboda yadda suka haɗa kai da babarsu, su ka wulaƙanta ta, suka ɗauki gaba da ita. Amma ta yi yaƙi da zuciyarta ta ce "Da gaske?" "Wallahi ta yi miki kyau sosai" "Na gode" ta faɗa a taƙaice. "Waye ya baki?" Nana ta ce "Gidan da nake aiki ne suka bani" "Zan zo a din ga bani aro" Ta jinjina kai ta ce "Idan ma so ki ke sai na baki" "A'a aron dai" Nana na shiga ɗaki, Mama ta ce "Mara zuciya, me take da shi da za ta baki? Ba ga uwar ɗakinki nan tana baki kaya ba" Nana na saka ƙafarta a ɗakinsu, ta ganta a libraryn Ƙaisar. "Meye haka kuma? Salla fa zan yi" ta yi magana tana waiwayen ganin ta ina za ta gan shi. A kan kujera ta hange shi, yana rubutu a cikin wani littafi, ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Ai ba a kira sallar ba ko?" "To me ka kawo ni nan na yi maka, a yanzu? So nake na yi azkar kafin a kira sallar" Nana ta faɗa a hasale. "Wanda za ki aura ba shi da lafiya, an ce ki je ki duba shi kin ƙi, me ki ke zato?" Ɗan shiru ta yi, sannan ta kalle shi ta ce "Kai ka saka shi ciwon ciki kenan?" Ya ajiye alƙalamin, ya rufe littafin, ya tashi ya ce "A'a, ba ni ba ne ba, miyagun ƙwayoyin da yake sha ne kawai suke tambayarsa, duk ba wannan ba, haryanzu ba ki shirya barin gidan nan ba." "Wai in bar gidan na je ina?" Ya tura littafin hannunsa, tsakiyar wasu littattafai ya ce "Yanzu ba wannan ba tukuna, kin ga da kin yadda da sharaɗinmu, da kin ceci ɗan yaron nan da yake ta ƙaunar ki" A razane Nana ta ce "Wane yaron? Ba dai Haidar ba" Ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya ce "A'a ba shi ba, kalli mudubi da kin yarda ki na da halin ceton yaron nan, amma baƙin taurin kan ki ya sanya zai rasa rayuwarsa" A gigice Nana ta ce "Wai wani yaron?" Da idonsa ya nuna mata mudubin. Muhsin ne a kwance, babu inda yake motsi a jikinsa, ga robar abinci, ga oxygen a hancinsa. Gefe mamansa ce, idanunta jawur saboda kuka. Ga kuma yar mahaifinsa Hajiya Sa'a a gefe. Nana ta gigice ta ce "Muhsin" "Eh, kin makara, an riga an bayar da jininsa ga wani aljani, mutuwa zai yi yaron" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyasa ba ka yi komai a kai ba?" Ta yi magana cikin kuka. "Ina cikin aljanu masu son zaman lafiya, dama da zan yi wani abu a kai, sai dai ta hanyar ki, kuma farkawar sa ta ƙarshe ma sunan ki yake ta kira. Kash Allah sarki, dama sunan uwarsa ya kira da take zaune kusa da shi, tna lissafa dukkanin numfashin da yake fitarwa, cike da ƙauna da kuma fatan ya ci gaba da rayuwa, ba ke ba da ba ki sam ciwon sa ba" yayi maganar yana hura iska a jikin mudubin, a take komai ya ɗauke. Nana ta rikice cikin kuka, ta rasa abun yi gaba ɗaya. "Ƙanwar babansa ce ta bayar da jininsa, aka yi mata domin ci gaban samun duniyarta. Wadda dai ta bayar da turare a kawo miki. Shikenan mun gama je ki yi sallar ki" "Nana" ta ji Baba ya kira sunanta da ƙarfi. Ta ɗago kai ta kalle shi, tana zaune a cikin ɗaki ta haɗa kai da gwiwa tana ta kuka. "Me aka yi miki? Ko wani ne ya mutu?" Ta girgiza kai alamar a'a. "To gidan aikin ne suka yi miki wani abu?" Ta girgiza kai alamar a'a. Baba ya sake cewa "To kukan me ki ke yi, an ce tun da ki ka dawo ki ke abu ɗaya ko jikin ne?" "Baba babu fa komai" ta yi magana tana tashi tsaye. Ta kalli gari ya yi duhu sosai, da alama isha ta wuce. Ta yi shiru ta tuna abin da ya sakata kuka, amma ta kasa tuna komai. Ta yi alwala ta yi sallar magariba da isha'i, tana jin wata irin matsananciyar damuwa da tashin hankali a cikin zuciyarta, amma ta kasa tuna ko a kan mene ne. Abincin da ta zo da shi ta kasa ci, ta kira Nasiru ta bashi, ya karɓa ya gudu waje kar Mama ta hana shi ci. Sai dai tun da sanya haƙarƙarinta a ƙasa take addu'a, amma bacci ya gagara, ta yi juyi, ta kuma amma ko alamar bacci babu a idonta, har aka yi kiran sallar farko, a kunnenta ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili ta zauna har aka yi sallar asuba. Har gari ya yi shaa, tana zaune. Ta tashi zata fara shirin fita, kawai idanunta suka sauka a kan jakar da ta dawo da ita, daga gidan sarkin baka. Ta ɗaukko jakar ta hau buɗewa. Sai dai ta zazzage jakar kaf babu komai a ciki. Ta yi guntun tsaki, ta ajiyeta, sai dai ta yi shiru tana tuno abubuwan da suka faru a gidan sarkin baka. Ko ba komai ya karrama ta, ya mutunta ta, tana matuƙar son sanin halin da yake ciki a yanzu. Ta gama shirinta, ta yi wa Baba sallama ta tafi gidan aikinta. A ɗaki ta iske Haidar bai ko tashi ba, kasancewar ba ta samu bacci daren jiya ba, ya sanya ta nemi guri ta kwanta a ƙasa, bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ta. Ji ta yi tamkar wani abu ba dai-dai yake ba, ga baccin tana yi, amma ba ya mata daɗi sam. A hankali ta buɗe idonta, kawai ta ga Alhaji Zailani a cikin ɗakin. A mugun sukwane ta tashi, ta ja da baya ta kalle shi ta ce "Lafiya, me ya kawo ka nan?" "Gidana ne" ya bata amsa. "Eh na san gidan naka ne, amma a cikin gidan naka akwai inda shari'a ta yi maka iyaka, tun da ba duka mutanen gidan ne iyalinka ba" Ba tare da ya amsa maganar da ta yi ba ya ce "Mun fara magana ba mu ƙarasa ba, na zo mu ƙarƙare ta yau" Cikin takaici Nana ta ce "Wace maganar?" Ya nuna mata gefen gadon Haidar ya ce "Zauna mu yi magana" "Ni ba zan zauna ba, ka gaya mini ko ma mene ne a haka" Ya nemi guri shi ya zauna, a gefen gafon Haidar yana tsareta da idanunsa. "Buƙata ce da ni a gare ki, wadda idan ki ka amince ke ma za ki samu biyan buƙatun ki" Ta ce "Ni na ce maka ina da buƙatar wani abu ne?" Alhaji Zailani ya ƙara tattara hankalinsa a kanta ya ce "Ko ba ki faɗa ba, na san ki na da buƙata kema. Kasuwancina ne ya fara yin baya, an ce mini muddin na yi tarayya da mace irin ki, taurarin ki za su haska nawa." Galala Nana take bin sa da kallo, yadda ya zauna babu kunya babu tsoron Allah, yana gaya mata maganganun banzar da babu komai a cikinsu sai jahilci da hauka. Ko a jikinsa da kallon da take yi masa, ya ci gaba da magana. "Idan ki ka amince, zan baki kuɗi, kuɗaɗe ba ƙanan kuɗaɗe ba, kuɗin da sai kin rasa yadda za ki yi da su" Cike da takaici Nana ta ce "Kai yanzu bawan Allah, ka na da kuɗin da zaka bani wanda sai na rasa yadda zan yi da su, me za ka yi da wasu kuma? Ai ina tunanin idan ka haɗa ka riƙe sun wadace ka" Ya miƙe tsaye ya ce "Ai ba a daina neman kuɗi, ki amincewa buƙatata, zan baki kalar rayuwar da ba ki taɓa tsammani ba a rayuwar ki" Nana ta ja da baya ta ce "Ba na buƙatar kuɗin ka, ko zan koma ga Allah a talauce ba zan abin da ka ke so ba, ko zan yi wannan mummunar ɗabi'ar ba zan yi da mushriki irin ka ba, Allah ya tsare ni daga sharrin ka" Alhaji Zailani ya ce "A'a ba ki da wani zaɓi fa, tunda aka kasa riƙe budurwa kamar ki a gidanku, aka bar ki, ki ka fito yawon rainon yaro. Kuma na san tunanin ki bai wuce budurcin ki ba, babu lallai wani abu ya shafi nan gurin ma. Budurcinki ba zai taɓu ba, kuma idan ki ka samu kuɗi, za ki iya rayuwar ki ba tare da wani ɗa namiji ba. Ki yi tunani a kai" ya nufi hanyar fita ya fice daga ɗakin. Jikin Nana ne yake wata irin tsuma, cike da tsoro da razani, ta dafe saitin zuciyarta da yake wani irin bugu tamkar ta fasa ƙirjinta, ta fito. Ta kalli Haidar da yake ta baccinsa hankali kwance. Jiki a sanyaye ta tashi Haidar, ta yi masa wanka ta fita da shi falo tana ba shi Abinci. "Ke me ki ke bawa ɗa na haka?" Ta ji muryar Shukura cikin ɗaga murya. Nana ta kalle ta ta ce "Ƙosai ne da kunun gyaɗa" "Ƙosai? Ki ke ba shi, a gidan uban wa ki ka samo wannan tarkacen ki ke bawa yarona?" "Kunun a nan na dama, ƙosan kuma daga gida na taho da shi, shayi ba abincin yaro ba ne" Nana ta faɗa kanta tsaye. "Shut up malama, ki kwaso jagwalgwalo daga waje ki kawo shi kina bawa yarona kashe shi za ki yi? Na san wani concoction aka haɗa a ciki ki ke ba shi, dan samun guri?" Nana kamar ta yaɓa mata magana, mussaman da take cike da takaici, da mamakin abin da babanta ya yi mata, amma ta yi shiru, ta haɗiye. Haidar dai hankali kwance, yaka ta ɗaɗɗakar kunu a cikin feeder, ta tafi a fusace za ta fizge kwanon ƙosan ta yi jifa da shi. A zuciye Haidar ya buga mata feeder hannun sa, yana ihu. Nana ta haɗe rai ta kalle shi, sai ya nutsu. "Ɗaukko kwanon da ƙosan, ka zo ka bata haƙuri, ko kuma yau na saka a kwano a kai wa kare ya cinye ka, sai wataran za a sake haifo ka" A ruɗe ya tashi ya ɗaukko kwanon ya kawowa Nana, yana cewa "Sorry Anty" "Ba ni zaka bawa haƙuri ba, maminka za ka bawa haƙuri" Mummy da take kallon duk abin da ya faru ta ce "Lallai tsakanin Haidar da Nana sai Allah. Sannan ke Shukura ban da abin ki, soyayya ce ta sanya har ta ɗauki abin ta ta bawa ɗanki. Sati biyun nan wallahi har ya yi kumari, ba nan ki ke complain na ramar sa ba? Malama ki wuce ki tafi makarantar ki, sannu da ƙoƙari Nana" "Yauwwa Mummy ina kwana?" "Lafiya kalau Nana, ya ɗan naki?" "Yana nan lafiya ƙalau" Kasancewar a fusace yake, bai gai da Mummy ba, sai da Nana ta yi magana. Nana tana ganin mutuncin Hajiya Amina, tana da kirki sosai da sosai, Nana ta din ga mamakin yadda take zaune da Alhaji Zailani da wannan mummunar ɗabi'ar da yake aitawa. Kodayake wata ƙila ba ta san yana yi ba. Wata zuciyar ta bata amsa. Abin ya din ga damunta a zuciyarta, amma ta rasa wa za ta gayawa. Tare suka yi girki da Jummai. Har na dare suka yi bayan sun kammala yau ma Jumman ta roƙe ta, ta ajiyewa masu gadi Abinci kafin ta wuce gida. Tun da ta tafi hanya take saƙawa tana warwarewa, idan ta ajiye aikin nan ba ta da wata makoma, yanzu Allah ya rufa mata asiri, ba ta da fargabar abinci ko kaɗan, dama abinci shi ne babbar damuwarta, ga kuma albashi mai tsoka da take sanya ran fara karɓa. Sai dai ga ƙoshi ga kwanan yunwa, ko dai ta ci gaba da zuwa tana fuskantar barazana daga mai gidan, ko kuma ta koma zaman gida ba ta da abin yi, yunwa ma kaɗai ta ishe ta. Duk da akwai 'yar tazara kaɗan daga gidan aikinta, zuwa gidansu, amma har ta je gida tunani take yi. Tun a ƙofar gida ta haɗu da Nasiru, ya ce "Nana kin dawo? Me muka samu yau?" Ta yi murmushi ta ce "Ba komai" "Bayan ga leda nan a hannun ki" "Shinkafa ce, ka bari sai mu ci da daddare, ko an yi girkin dare ne?" Nasiru ya ce "Tuwo ne, kuma tun da ga shinkafa ba zan ci tuwo ba, yauwwa ni na manta ma, ɗazu Baba ya yi wasu baƙi, yana ta shiga yana fita yana faɗa, ke yake jira ki dawo" Ta yi sak, ta ce "Ni kuma?" "Eh" A ɗan marairaice ta ce "To me kuma na yi?" Ya ɗan ɗage kafaɗarsa ya ce "Wallahi nima ban sani ba" Ta kalli gidan ta ji gabanta ya faɗi, sai ta ji sam ba ta ƙaunar shiga gidan ma. Ta daure a hankali, tana takawa da ƙyar, cike da fargabar rashin sanin abin da za ta tarar. Ta yi sallama babu kowa a tsakar gidan, ta shiga ɗaki ta ajiye ledar abincin hannunta. Gaba ɗaya ta rasa abin da yake yi mata daɗi, a zullumi take kawai Baba ya zo ya gaya mata me kuma ta yi a wannan karon. "Laa Nana kin dawo?" Ta ɗan zabura, ta kalli Jamila dan ba ta san ta shigo ɗakin ba. Ta ce "Eh ya gidan?" Jamila ta ce "Lafiya ƙalau, ga kunun aya can da na ajiye miki a jug, a gidan maman khairat muka yi, na san ki na son shi, shiyasa na ce bari na ajiye miki" Nana ta yi murmushin ƙarfin hali, ta ce "Amma kuwa na gode sosai da sosai, bari na yi sallar magariba na haɗa da abinci" Jamila ta ce "To shikenan, ga shi can ma an yi kira" Nana ta ce "Amm yauwwa Jamila, Nasiru ya ce mini Baba yana nemana, dan Allah ko kin san abin da na yi yake nema na?" "A'a, ai ban daɗe da dawowa ba nima" "Ok to na gode" haka dai a ɗarare ta yi sallar magariba, duk da tulin damuwar da take ciki, ta ɗauki jug ɗin kunun ayar nan, domin ta ɗan sha ta bawa Nasir sauran, dan ko sha'awar abinci ba ta yi. Shi ma dan kar Jamila ta ji haushi ne, tun da ta ga neman shiri take yi da ita. Ta buɗe jug ɗin ta kai bakinta, ta ji an ce "Kar ki sha" Ta waiwaya ba ta ga kowa ba, ta sake kaiwa bakin ta aka sake cewa "Kar ki sha" kawai ta ɗauki fitila ta haska jug ɗin. Jini ne a ciki yake ta tafasa, tamkar akan wuta. A razane ta saki jug ɗin kunun ayar ya zube. Ta din ga sauke numfashi, ta yi maza ta janyo zani ta goge gurin, dan kar Jamila ta zo ta tarar da abin da ya faru. Ba ta gama wannan taradaddin ba, Baba ya kwaɗa sallama muryarsa a sama kamar tashin hankali. Wani fitsarin tsoro ne ya kama Nana, tun kafin ta san abin da ta aikata. "Nana ta dawo ne?" Jamila ta ce "Eh tana ɗaki" Cikin hargowa ya ce "Ki na ina fito ki zo nan, magajiyar tsiya da jaraba" Dumm ƙirjinta ya sake bugawa, a karo na babu adadi, jikinta ya din ga rawa yana neman gaza ɗaukarta, ta fito jiki a sanyaye tana jiran ji abin da Baba zai ce. "Ashe kin je gidan Ummi, ta ce miki ku je ku duba yaron nan, ki ka ce ba zaki ba, ki ka ƙara nanata mata ba kya son sa. To ƙanin babansa ya zo nan ɗazu, sun ce a tattara duk wani abu da ya san ya yi miki a mayar masa. Kuɗin aurensa dubu saba'in, kuɗin da ya bayar aka kai ki gurin mai magani, da kayan shafe-shafe da ya kawo, ki na gidan mai magani aka yi amfani da su a gida, kusan lissafin dubu ɗari da sittin, sun ce a mayar musu, kuma ni ban san inda zan je na nemo wannan kuɗin ba, dan haka sai ki shiga ki fita ki san yadda za ki yi a nemi kuɗinsu a ba su." Ayshercool 08081012143 Page 21 Idan da sabo, Nana saba da ire-iren waɗannan ɗabi'un na Baba, amma na wannan lokacin sun ɗaure mata kai fiye da yadda take tunani. Duk cikin kuɗin nan, babu wanda take tunanin ta ci, hana rantsuwa sai wanda aka ce an kai ta gurin mai magani da su, hatta kuɗin auren nata ba ta san nawa aka kawo ba, kayan toshin da ya kawo kuma, bayan tafiyar ta gidan mai magani, da ta dawo ma ba ta tarar da su ba, dan tun da aka kawo su ba ta taɓa ba. Ba ta tunanin ko a tukunya, an girka kuɗin nan ta ci, amma ya haƙiƙance a kan sai ta nemo kuɗi ta biya, to a ina za ta samo wannan maƙudan kuɗaɗen har haka?. "Ina magana kin yi sukuri da kai, kamar makauniyar akuya. Nan da rana i ta yau suka ce za su dawo su karɓi kuɗinsu, ni kuma ba ni da su, kin ga kin yi wa kanki Asma'u. Babu rarrashi da ban bakin da ban yi miki a kan ki yi haƙuri, ki auri yaron nan ba, amma ki ka ƙi, sai ki ci gaba da zama a gidan ki ci uwar da ta sanya ba za ki yi aure ba. Ni wallahi na fara yadda da maganganun da mutane suke yi, shi wancan da aka fasa aurenku, duk da Rabi ta taka muhimmiyar rawa, amma matarsa ta din ga rashin lafiya sai da aka fasa, shi wancan daga fasa aure, an kashe shi har lahira, shi kuma wannan ya zo lafiya ƙalau daga komawa gida sai ciwon ciki. Nana babu irin murna da ban yi ba lokacin da aka haife ki, duk da ina da tarin 'ya'ya na gatanta ki na nuna miki so, ina yi miki kallon wadda za ta ji ƙaina, amma babu wanda yake azabtar da ni a cikin yarana sai ke Asma'u shikenan duniya ce ki je ki yi." Cikin kuka Nana ta ce "Baba baki za ka yi mini? Haba Baba ba laifina bane ba ya zan yi. Ni a ba su haƙuri ko gobe a ɗaura auren, ko ina ne ma ya kai ni, muddin hankalinka zai kwanta" "Kya ji da shi" Baba ya faɗa a ƙufule. Mama ta cafe zancen da cewa "Ahaaf a juri zuwa rafi da tulu, wallahi wataran sai ya fashe, idan an faɗa ka din ga jin haushi, gara da ka gane annobar da take tattare da ita ai, ina ƙara gaya maka muddin wa'adin da na ɗibar maka ya cika tana gidan nan, wallahi sai na tafi" "Dalla gafara rufe mini baki, ki fi ruwa gudu mana, ki bar ni da abin da ya dame ni" Nana garin komawa ɗaki, ta yanke hannu da ƙofar ƙarfen ɗakinsu, sai dai sam hakan bai dame ta ba, ta fashe da kuka, ta rasa me ma yakamata ta yi. Da gaske ita annoba ce? Anya babu ƙamshin gaskiya a kan abin da ake faɗar a kanta?. "Ƙaisar ne kai ne! Kai ka ke janyo komai, duk saboda son zuciyarka Allah ya shiga tsakanina da kai" ta yi maganar cikin ƙaraji. A library ɗin sa ta ganta. Ba ta damu ba, ta rintse ido ta ci gaba da faɗin "Ka rabu da ni, ka ƙyale ni na yi rayuwata, ka bi kakanin nawa kabari ku ƙarata, ni meye nawa da zaka din ga cutar da mutanen da suke tare da ni, ina ruwanka da rayuwata? Sai dai shiru, bai bayyana ba, kuma ba ta ji sanyi yana ratsata da yake alamta mata yana guri ba. Watso litattafan gurin ta fara ƙoƙarin yi, cikin damuwa da kuka, amma suka ƙi faɗowa, tamkar gina su aka yi a gurin. Sai ma ƙara jin ciwo da ta yi a hannunta. Babu tsammani, wani littafi guda ɗaya tal ya faɗo ƙasa. Ta ƙurawa littafin ido, sai kuma cikin azama ta ƙarasa ta ɗauki littafin, na kwanaki ne da ta fara karantawa Ƙaisarya ƙwace. Sai dai ta buɗe littafin, ta ga sai farar takarda babu komai a ciki, ta zazzage shi ta sake buɗewa amma babu komai a jiki. Sai kuma a hankali ta lura da gurin da jininta ya taɓa, rubutu ya fara bayyana a jiki. A hankali rubutu ya ci gaba da bayyana, tun yana dishi-dishi har ya yi clear. Ko da ta fara karanta wannan shafin, sai ta ga tamkar ba ci gabn gurin da ta tsaya ne, a wancan karon ba, amma saboda tsananin son jin ƙwaƙwaf, da gudun kar ya kuma ƙwace littafin, kawai ta ci gaba da karantawa a haka. Shekaru masu yawa da suka gabata, ƙauyen Buda da ke cikin ƙaramar hukumar Garkon jihar Kano. Sannu a hankali mutane sun raya gurin, su na gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, da su da dabbobin su, ba tare da wata damuwa ba. Bayan shafe tsawon shekaru, ba tare da zuriyar wannan aljani sun kuma waiwayar mutanen gurin, domin ɗaukar fansa ba, kwatsam! Rana ɗaya mutanen garin suka tashi da fari. An yi noma ana jiran ayi girbi, kawai suka je gonakin su, suka tarar da shukokin su sun ƙone ƙurmus. Su ka shiga tashin hankali mara misaltuwa, domin noma yana ɗaya daga cikin abin da suka dogara da shi, domin rayuwa. Ba su gama wannan alhinin ba, dabbobin su suka din ga kamuwa da ciwo, ga yunwa da rashin wadattacen abinci. Tsuntsayen su, suka din ga kamuwa da mura su na mutuwa su ma. Hankalinsu ya yi mummunan tashi, suka rasa menene mafita, sai mutumin da yake jagorantar wannan ƙauye, ya yi tafiya domin bincikawa, ko za a samu magani, da kuma neman maƙwabtan ƙauyuka, su tallafa musu saboda abin da ya same su. A ɗaya daga maƙwabtan ƙauyukan, ake gaya masa sun yi sake, da suka zauna haka babu wani boka, da zai iya yi musu binciken abin da ka iya faruwa, da kuma gaya musu maganin matsalolinsu. A nan take aka haɗo shi da wani boka, suka taho garin tare. Bokan ya ce a ba shi kwanaki uku, zai dawo musu da bayani. Ya tafi kan wani dutse da jakar kayansa, sai bayan kwanaki uku, ya saukko ya koma gurin mai gari. "Ba ni labari, me yake faruwa da wannan gari, muke ta afkawa cikin bala'i a jejjere haka?" Bokan ya dube shi ya ce "Ba komai ya haddasa wannan abubuwan ba, face ɗaukar fansar da wasu daga cikin aljanu zuriyar Dirsham suke yi, a kan abin da ainihin wanda suka fara zama a cikin ƙauyen nan suka yi musu." Nan ya ba su labarin abin da ya faru, duk da dama wani sun sani. "To yanzu mene ne abin yi?" "Zan yi muku aiki, amma na ɗan lokaci ne, domin kuwa za su kuma dawowa dan ba sa yafiya, abu ɗaya za ku yi wanda nake ganin shi ne mafita" Cikin zaƙuwa mai gari ya ce "Mene ne wannan abin?" "Yauwwa, za ku bada mutum ɗaya, ko biyu da za a yi wa girkar aljani, yadda zai din ga yi muku bayanin abin da ka iya faruwa wanda ba ku sani ba, sai dai za ku din ga yi wa aljanin hidima, da yi masa duk abin da yake so, shi kuma abu kafin ya faru ya sanar muku. Idan da wani mataki da za a ɗauka, duk zai din ga gaya muku". Mai gari ya ɗan yi shiru sannan ya ce "To wai mene ne girkar?" Bokan ya gyara zamansa, ya ƙara tattara hankalinsa a kan mai gari ya ce "Girka na nufin a zaunar da aljani ko kuma aljanu a jikin mutum, ta yadda za su iya zuwa kansa a duk lokacin da ya kira su. Idan aka yi haka za ku iya magana da su ma ta bakin wanda aka yi wa girkar, idan ma wani bayanin ne su yi muku" Mai gari ya ce "Taɓɗijan, Aljanu kuma? Ba na tunanin akwai wanda zai amince ya yarda ayi masa wannan abun, mu dai ka yi abin da ya kamata ka taimake mu" Ya ce "To shikenan, babu laifi sai dai maganin ba mai ɗorewa ba ne ba, ku sake bani kwana biyu kafin hudowar alfijir na ranar Alhamis zan yi aikin" Haka kuwa aka yi, bayan kwana biyu, kafin hudowar alfijir, boka ya kawo wani ƙaho, da aka naɗe shi da farin zare, aka rataya masa wasu layoyi ya ce a za a binne a tsakiyar garin. Ya saka aka gina wata ƙatuwar tukunya, aka haƙa rami aka sakata, ya zuba tarkacen tsaface-tsaface da lauyoyi, da wannan ƙahon aka binne ta a tsakiyar garin. Sun yi imani, kuma sun yarda da wannan abu da boka ya yi musu, dan haka suka zauna lafiya a garin. Sai dai ɗaya daga makusantan mai gari, ya ce masa ya dace a tara mutane a samu ko mutum ɗaya, a yi masa girka saboda gudun abin da ka iya faruwa a gaba. Ya amince da wannan shawarar, aka tara mutane aka yi musu bayani. sarkin aska ya yi farat ya ce shi ya yarda ya amince a yi masa girkar, saboda wani abu da ya ƙulle a ransa. Haka aka yi shiri, aka haɗa shi da 'yan rakiya, zuwa ɗaya ƙauyen gurin bokan nan domin yi masa girkar Aljanu. Sai dai da boka ya bashi zaɓin kalar aljanun da yake so ayi masa girkar da su, sai ya zaɓi baƙaƙen aljanu! Maimakon farare. Aka yi masa girka, ya koma Buda, su na murna za su ƙara samun afuwa da kariya daga sharrin zuriyar aljani Dirsham Jaddul jinn, sai dai kash! Rashin sani ya fi dare duhu, Sarkin aska ya yi amfani da wannan damar gurin mayar da mutanen garin tamkar bayinsa, babu wanda yake ja da shi, abin da ya faɗa tilas ayi ko ba a so saboda kar aljani ya hukunta mutum. Ya sanya wa mutane tsananin tsoronsa, hatta mai gari sai abin da sarkin aska yake so shi ake yi. Kullum mutanen garin, cikin sintirin kai dabbobinsu suke yi, domin sadaukarwa aljani duna da aka yi masa girka da shi, domin ya kare su ya kare ƙauyen daga bala'i. Ya din ga janyo wasu daga cikin aljanun da mutanen Buda suka yi wa laifi, yana canza tsarin jinsinsu, ta hanyar sadaukar musu da jini, da yi musu alkawarin taimaka musu, gurin ɗaukar fansa a kan mutanen garin. Sarkin baka na garin Buda, ya kasance cikin mutanen da suke bayar da magani, idan mutum ba shi da lafiya. 'yar sa guda ɗaya tal a duniya mai suna Lanti, duk in da za shi yawonsa da ita yake tafiya. Sarkin aska abokinsa ne, amma tun da aka yi masa girka ya canza halaye suka raba hanya. Kwatsam! Sarin aska ya ce Aljani duna ya ce kar wanda ya sake bayar da magani a garin, idan ba shi ba, kuma garin babu wani wanda yake bayarwa dama bayan sarkin baka. Sarkin baka ya ce Uban dunan ma ya yi kaɗan, balle shi kansa dunan, babu wanda ya isa ya hana shi bayar da magani. Sarkin aska ya ce akwai gagarumin bala'i, muddin ya ci gaba da bayar da magani, sarkin baka ya ce bala'in ya daɗe bai afku ba. Nan rashin jituwa ya ɓarke a tsakaninsu. Mutanen gari, duk da su na jin tsoron sarkin aska, amma sai aka rabu biyu, wasu suna bayan sarkin baka, wasu kuma sarkin aska. Kwatsam! Aka tsinci gawar sarkin baka a daji, jikinsa babu ko ƙwarzane balle a ce dabbobin daji ne suka kashe shi. Lanti ta shiga tashin hankali, ta yi kuka sosai da sosai, dan daga ita sai kakaninta sai shi ta sani, babarta ta daɗe da rasuwa, shi ne yake yi mata komai. Sarkin aska ya samu dama ya ci gaba da tsula tsiyarsa, sai da ya talauta da yawa jama'ar garin, saboda tsoron sa da ya sanya musu. Bayan wasu shekaru, Lanti ta yi aure har ta haifi 'ya mace, mutsnen Buda suka sake tashi da wata annobar, a lokacin sarkin aska ya yi bulaguro da shi da yaronsa. Aka wayi gari ƙafafuwan yaran garin yana shanyewa, ga wani irin tari da ƙuraje da suka din ga fesowa mutane. Aka rasa yadda za ayi, ga Sarkin aska baya nan, tun da mahaifin lanti ya mutu, ba ta yi gigin cigaba da sana'ar sa ba, amma ganin halin da mutane suke ciki, ya sanya ta fara ba su ɗan abin da ta sani na magani, a matsayin taimakon gaggawa. Saboda alaƙar su da sarkin aska ta ƙara yin tsami, bayan da ɗansa ya nuna ya na son ta taƙi amincewa. Ko da sarkin aska ya dawo ya tarar da abin da yake faruwa, ya yi ta bala'i a kan dan me Lanti ta bayar da magani, idan ba ta yi wasa ba Duna ya yi fushi da ita, abin da ya samu babanta ne zai same ta. Abin ya tsayewa Lanti, ta daɗe da tunanin sarkin aska yana da sanya hannu a cikin mutuwar mahaifinta. Mijinta ya ce ta yi haƙuri kar ta tanka. Kawai aka wayi gari, 'yar gurin Lanti ba ta iya tafiya ƙafafuwanta sun shanye, ita ma ta kamu da wannan larurar" Nana ta juya shafin gaba, amma ta ga wayam babu rubutun komai. Ta dudduba duk rubutun ya goge, har na baya da ta karanta. Raunin hannunta take ƙoƙarin matso jini ta kuma shafawa a kai, ta ci gaba da karantawa, ta ji wata iska mai ƙarfi na ƙoƙarin ƙwace littafin daga hannunta. Iya ƙarfinta ta saka, ta riƙe littafin, amma iskar ta haɗa da ita, ta yi sama ta fizge littafin ya shiga inda ya faɗo, Nana kuma ta dawo ƙasa tim! "Wash!" Ta faɗa jin yadda ta ji ƙashin bayanta tamkar ya buɗe. Guguwar ta rikiɗe ƙaisar ya bayyana. "Idan ba ki yi wasa ba, taurin kai zai yi ajalinki kamar yadda ya yi na kakannin kakaninki, kodayake idan ba ki yi haka ba ai ba za a ce daga zuriyar su ki ka fito ba. Saboda ke na ɓatar da rubutun jikin littafi, amma saboda baƙar jaraba, ki ka gano jinin ki ne zai bayyana rubutun. Sai kuwa kin yi jinyar jinin ki da ki ka yi amfani da shi ki ka buɗe rubutun". "To waye ya ce ka kirawo ni ina zaman zamana?" "Ai kuma na fasa faɗar abin da ya sanya na kirawo ki, fita ki ban guri" Nana ta ce "Ta ina zan bi?" "Ta kaina" Tsaki Nana ta ja ta ce "Ai ba ni na kawo kaina ba" ta yi maganar tana juyi. "Wash Allah!" Ta faɗa cikin marairaicewa saboda ciwon da bayanta yake yi. "Nana, an yi salla fa" Tashi ta yi zaune tana kallo Nasiru, da yake a tsaye a bakin ƙofa, ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Na gode Nasiru" Ta yi juyi ta ji bayanta ya ƙara riƙewa, da ƙyar ta iya tashi ta lallaɓa ta fita ta yi alwala, ta dawo ta yi salla. A wannan karon tiryan-tiryan abin da ta karanta a littafin Ƙaisar ya din ga dawowa kanta, ba ta manta komai ba, saɓanin sauran mafarkan da take manta komai. "Sarkin baka, sarkin aska, Garba ga baka ga aska, kenan sarkin baka yana da alaƙa da labarin mutanen ƙauyen Buda?' 'A'a ba zai yiwu ba kawai dai labari ne ya zo a haka. Amma ya Lanti ta yi da 'yar ta mai ciwo, kuma za ta yarda sarkin aska ya ba su magani. Mtsew ƙaisar bai yi ba. Amma da nake danganta sarkin baka da wannan labarin, wataƙila ƙaryarsa ce kawai yake rubutawa ba wai faruwa ya yi a gaske ba. Ba ta yi aune ba, ta ga lokaci ya kusa ƙure mata, ta tashi ta fara shiri a gaggauce, ta jiyo hargowar Baba, yana ta bala'i tare da jaddada ta nemo kuɗin da za a mayar wa su Saleh kafin sati ɗaya. Ita dai ba ta ce uffan ba, ta gama kintsawa ta nufi gidan aikinta. Ba ta tashi tuna abin da ya faru ba jiya sai yanzu da ta nufi gidan. Gaba ɗaya pressure Baba ta sanya ta manta da abin da ya faru jiya a gidan Alhaji Zailani. Yau gidan a buɗe yake, tana zuwa tura ƙofar kawai ta yi ta shiga. Yana kallonta har ta wuce ta shiga cikin gidan. Shukura ta tarar a falo, ta gaisheta ta amsa mata a yatsine ta ce "Yau Hajiya ba ta nan, sun fita da Jummai tun sassafe, Haidar yana gurin Daddy, idan da wani abu ki shiga kitchen ki duba ki dafa muku, ni na tafi" Saroro ta yi jin ta ce wai Haidar yana sashen mai gidan, Shukura ba ta jira me Nana za ta ce ba kawai ta fice ta tafi. Nana ta shiga kitchen, ta dafa abin da za ta bawa Haidar, da wanda za ta samu ta ci ita ma, sai dai shiru babu Haidar babu alamarsa. Ta din ga kallon agogo, ta ga yakamata ace zuwa yanzu an wanke masa baki, an yi masa wanka ya karya amma bai fito daga sashen Alhaji Zailani ba, duk da ma bai fiye yin dogon bacci ba idan gari ya waye. Abu kamar wasa har ƙarfe sha ɗaya da mintuna na rana, Haidar ɗin bai fito ba, sai ta ji ta damu ƙwarai da gaske. Ta nemi guri ta zauna, tana tunanin ko tarko ya yi mata, amma wata zuciyar ta ce ya za ayi ya haɗa baki da 'yar sa ya yi miki tarko? Tun da dama yana wasa da Haidar sosai. Kamar a cikin tunani, ta din ga jin kukan Haidar, yana ce mata yunwa yake ji. Firgigit ta tashi, kamar wadda aka mintsina, ta nufi sashin Alhaji Zailani. A ƙofar falonsa ta din ga kwaɗa sallama amma shiru, ba a amsa ba. Ta zira kai ta shiga falon amma babu kowa a falon. Sai kuma jiri ya fara ɗibarta garin ya din ga jujjuya mata. Ƙaton frame ɗin da yake ɗauke da hoton Alhaji Zailani, a hankali ya juye Alhaji Fatuhu ya bayyana a jiki, idanunsa na zubar da hawayen jini. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Innalillahi wa innalillahi raji'un" Nana ta din ga maimaitawa. Fitilun ɗakin ne suka ɗauke, wata iska ta din ga buga tagogin da ƙarfi. Muryar Alhaji Fatuhu ta ci gaba da ji yana sheshsheƙar kuka, sai kuma ta fara jin muryar Muhsin yana kiranta "Anty Nana, Anty Nana" sautun muryar Haidar ma ya fara amsa kuwwa a kunnenta "Anty yunwa nake ji" "Ƙaisar wai meye haka ne? Dole sai ka tozarta ni a gaban mutane, meye haka ka ke yi mini?" Nana ta yi maganar cikin ɗaga murya. A take ta ga komai ya koma yadda yake, sai Alhaji Zailani a gabanta. "Lafiya dai?" Ya yi maganar yana mata kallon tuhuma. Duk ta haɗa gumi sai ajiyar zuciya take yi. "Haidar zan ɗauka na ba shi abinci, lokacin cin abincin safen sa ya wuce" Alhaji Zailani ya yi murmushi ya ce "Kin damu da ba ɗan da ke ki ka haife shi ba a kan kuɗi ƙalilan, ni a kan kuɗi masu yawa nake buƙatar ki ara mini dama, amma kin ƙi. Kuɗi zan baki ba ƙanana wanda ke da talauci har abada". "Ka ce "Har abada? Kai wa ya baka wannan tabbacin? Dan Allah kar ka sake tunkarata da wannan maganar, ka rabu da ni ba na so". "Daɗina da ɗan talaka girman kai, ke ga talauci ga girman kai" "Na ji, dan Allah ka bani yaron nan na ba shi abinci" Ya yi dariya ya ce "A tunaninki, zan zuba miki ido ne, na rasa damata wallahi ko za ki mutu sai na yi amfani da ke na cimma muradina, ba zan sake lallaɓa ki ba, ta ƙarfin tsiya sai na samu abin da nake so" Jikin Nana ya hau rawa, sai ta marairaice "Dan zatin Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri bayan Allah da manzonsa mutuncina ne kawai ya rage mini dan Allah ka yi haƙuri" Shima ya kwantar da murya ya ce "A'a Asma'u, mutuncinka kuɗinka, idan kina da kuɗi miji sai wanda ki ka zaɓa. Auren ma bai zama dole ki yi ba, na ishe ki komai. Kin ga yau ne ranar sa'ar aikin nan, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ba dogon lokaci za a ɗauka ba" Dif! Dif! Dif haka zuciyarta ta ƙara ƙaimin bugawa, maimakon tsoro ya shigeta sai wata irin rawa da jikinta yake yi. "Ka bani hanya na wuce, idan ba haka ba wallahi sai na kashe ka, ka je a duba maka taurarin Shukura, wataƙila na ta sun fi nawa haske. Ka bani hanya kafin na yi ajalinka" Ganin ya ƙame kamar gunki yana kallonta, ya sanya ta hankaɗe shi, ta buɗe ƙofa ta fita. Tana fita daga ɗakin ta ƙara jin ta burkice, kamar hankalinta zai gushe. Biyo bayanta ya yi, tana gaba yana bin ta a baya yana kiran sunanta. Tun kafin ta ƙarasa gate, ta gan shi zaune a kan benci shikaɗai, addu'a ta din ga yi Allah ya sa a buɗe gate ɗin yake ta fice, domin in dai wannan ne ba kulata zai yi ba ya buɗe ƙofar. Kullum fuskarsa cikin rawani. Sai da Alhaji Zailani ya yi mamaki, domin hatta masu gadi ya aike su, duk da ga babban yaronsa mai zuwa aike a gidan. Ga mamakin Nana, kafin ta ƙaraso gurin gate ɗin, ya miƙe tsaye ya nufo su, taku biyar ya yi ya tsaya ya kafe Alhaji Zailani da ido. Ji ya yi tamkar an yi masa wani irin mugun dabaibayi ya kasa ɗaga ƙafarsa. A hankali ya juya ya nufi Nana da take ta jijjiga gate ɗin, tana neman hanyar fita. Bai ce mata uffan ba, ya buɗe mata gate ɗin ta fita ko takalmi babu a ƙafarta. Ayshercool 08081012143 P22 A hankali Alhaji Zailani ya buɗe idanunsa, ya gan shi a kan gadonsa a kwance. Shiru ya yi yana ƙoƙarin tariyo abin da ya faru. Fes komai ya dawo kansa, amma daga iya lokacin da ya biyo Nana, suka yi ido huɗu da wannan Buzun, ya kasa tuna komai. Ya tashi zaune yana ƙoƙarin saukkowa daga kan gadon, sai ga Hajiya Amina ta shigo ɗakin, hannunta ɗauke da kofin tea. "Sannu Alhaji ka tashi?" "Yaushe ki ka dawo?" "Tun la'asar, nan muka tarar da kai a sume, Haidar na ta kuka na ce Nanan ba ta zo ba ne? Amma doctor Sharif ya zo ya ce ba sai an kai ka asibiti ba, ya yi maka abin da zai yi maka, ya ce jininka ne ya ɗan hau" Ya yi shiru yana tunanin to meya same shi haka? Amma ya kasa tuna komai. **** Nana kuwa tana shiga gidansu, gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu kanta, saboda a yadda ta shigo gidan, idonta a rufe, ƙafafuwanta babu ko takalmi. Suwaiba ta ce "Jaraba" Kukan tsuntsaye ne ya gauraye ilahirin dajin, sai kuma ƙaton tafki mai ɗauke da ruwa shuɗi, sai rugugi yake yi, yana tambal-tambal. Tana tsaye tana kallon ruwan, ƙaisar ya bayyana a kan ruwan, yana shawagi yana kaɗa ruwan. "Wallahi ba ka da wani amfani a rayuwata, kana kallon za a ci mini mutunci, amma ba ka yi komai ba, ba ka da aiki sai ƙoƙarin haukata ni." Ta yi maganar a hasale. Bai yi magana ba, sai ƙara girgiza ruwan da yake yi, ruwan ya watso har sai da ya jiƙa ta, sannan ya ce "Allah ne zai tsare ki ba ni ba" Cikin kuka ta ce "Ai dama ban ce kai zaka tsare ni ba, idan ma gatse ka ke yi mini ba zan taɓa neman taimakon ka ba, amma na meye za ka din ga razana ni a gaban mutane, sai na fita hayyacina na aikata abin da zai saka a ce ba hayyacina nake ba?" "Abin da ki ka gani haka yake ko a zahiri, ba yi na yi dan na tsorata ki ba kawai" ya yi maganar yana fitowa daga cikin ruwan, da wani baƙin mayafi a jikinsa, yana jan ƙasa tare da ɗigar da ruwa. "Biyo ni" ya yi maganr yana yin gaba. Bin bayansa ta yi, suka ƙarasa gaban wani dutse, ba ta san ya aka yi ba, ta gan su a cikin libraryn sa. Ya ce "Wannan mutumin da ki ka gani yana kuka da hawayen jini, yana daf da faɗawa mawuyacin hali, a saboda abin da abokinsa zai yi masa. Abu ɗaya yake damunsa da yasa za a iya galaba a kansa, ba shi da riƙo da ibada sosai, sai baƙar aƙida da ra'ayin riƙau. Kuma ni ba na zama a guri mai ƙazanta, ko gurin da ake ta'amalli da jini, mussaman na bil'dama, ta yaya zan zo inda ki ke, alhalin inda ki ke zuwa ana ta'amalli da jinin bil'adama? Jininku ya fi jinin kowace halitta ƙarni mara daɗi, amma ya fi kowanne zaƙi da daɗi idan aka sha. Shi yasa masu aiki da jininsin aljnun da suke ta'amalli da jini, da an ba su jinin bil'adama, suke aiki cikin gaggawa, domin babu jinin da ya kai na su zaƙi da daɗi in ji masu sha". Mudubin da yake gurin ya nuna mata, ya ce "Kalli" cikin tsoro da razani, ta kalli mudubin. Alhaji Zailani ta gani tsirara, ana kwarara masa jini a jikinsa, yana buɗe baki tare da ziro harshensa waje, jikinsa yana karkarwa. Wata irin razana ta yi ta buɗe idonta, karaf ya sauka a cikin na Baba. "Uban me ya dawo da ke gida yanzu? Ko suma kin yi musu wani abun sun kore ki?" Ta girgiza kai alamar a'a. "To me ya dawo da ke gida yanzu?" "Kaina ne yake ciwo" "Ki sha magani ki koma, idan ma korar ki suka yi, ki san abin yi, dan wallahi ban san ina zan nemo kuɗin nan na biya ba" Ya gama faɗansa, ya bar ƙofar ɗakin, tana nan zaune ta ji sallamar Inna a tsakar gida. Ta amsa daga ɗaki, tare da bata damar ta shiga. "Nana ya na ganki a haka? Ba ki da lafiya ne?" "A'a me ki ka gani?" "Idonki ya yi jawur sosai fa" Nana ta yi murmushi ta ce "Lafiya ƙalau bacci na yi " Inna ta ce "Bacci kuma? Ina gurin aikin?" "Daga can nake" ta bata amsa "Wallahi da can gidan aikin zan je, kawai na fara zuwa nan". Nana ta karanto damuwa a fuskar Inna, ta ce "Meyafaru?" "Muhsin fa ya rasu yau ne uku" Wata irin zabura Nana ta yi, ta ja da baya tana bin ƙwayar idon Inna da kallo, domin ta gazagata abin da yake fitowa daga bakin Innan. "Ba Muhsin Fatuhu ba amma ko?" Nana ta yi maganar cikin tashin hankali, da ya gaza ɓoyuwa a kan fuskarta. Cikin damuwa Inna ta ce "Shi mana, idan ba kya komai ki tashi mu je ki yi musu gaisuwa, an gano gidansu mun je ma daga makaranta". Tamkar an tsinkewa Nana laka, haka jikinta ya mutu laƙwas, fatan ta a ce bacci take yi kawai mafarki ne. Can kuma sai mafarkin da ta yi da Muhsin ɗin ya dawo mata fes. Zabura ta yi tai waje, Inna ta bi bayanta, tana kiran sunan ta. Baba da yake tsakar gida ya ce "Lafiya ina za ki haka?" Inna ta ce "Ɗaya daga cikin ɗalibanta ne ya rasu za mu je gaisuwa" gaban Baba ya faɗi cikin tsoro, ya fara fargabar kar dai ta tabbata iskokan Nana ke kashe wanda take mu'amala da su?. "To Allah ya jiƙan sa" Inna ce ta amsa ta bi bayan Nana. Inna ta tare musu abin hawa, suka hau suka tafi. Sam Nana ba ta gane abubuwan da Inna take faɗa, fatanta kawai ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba. Saboda akwai kyakkyawar shaƙuwa a tsakaninta da Muhsin, saboda lokacin da aka kawo shi ma, bai kai a ɗauke shi ba, saboda ƙanƙantarsa, har goya shi Nana take yi, Allah ya sa mata ƙaunar yaron a zuciyarta. Sosai ake zaman makoki a gidan Alhaji Fatuhu, ɗan sa bai taɓa mutuwa ba, sai a kan Muhsin, shi ne ƙarami amma ya shiga ransa. Rumfuna aka kafa a cikin gidan, inda yake karbar gaisuwa, cikin gidan kuma mata ne suke karɓa gaisuwa. Gida ne katafaren gaske, ga girma ya sha kayan alatu. Alhaji Fatuhu yana tsaye yana gaisawa da wasu, ya ga wucewar Nana da Inna. Jikinsa ne ya yi sanyi, ganin yanayin tashin hankalin da yake kwance a kan fuskar Nana. Inna har falon ta raka Nana, don yi wa babar Muhsin gaisuwa. A gigice Nana ta shiga falon, kamar mai neman wani abu, ta tsaya tana rarraba ido ba tare da ta cewa kowa komai ba. Inna ta taɓa ta ta ce "Ga mahaifiyarsa ki yi mata gaisuwa" Nana ta kalli matashiyar matar da ba ta wuce shekara ashirin da huɗu ba, idanunta jawur. Nana ta ƙarasa gabanta ta risuna ta ce "Baiwar Allah wai dan Allah Muhsin ya rasu?" Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falon, suka amsa Nana ta waiwaya tana kallonsa ya ce "Nana kin samu labarin mutuwar ɗan ki ko?" Sai mahaifiyar Muhsin ta zabura ta ce "Ke ce Nanan dama? Muhsin har ya rasu kafin ya daina magana sunan ki yake kira, yana cewa a kai shi gurinki" sai a lokacin Nana ta ji kuka ya ƙwace mata, Inna take ba su labarin Nana ta je makaranta ganin Muhsin lokacin ba shi da lafiya ba ya zuwa makaranta. Cikin kuka maman ta ce "Na gode sosai da sosai, ƙaunar da ki ka nuna masa ce ta sanya, duk wanda ya san shi, zai san sunan ki a bakinsa" A wannan karon ta yarda da zancen mutane, ta fara lura da duk wanda ya shiga ranta take son shi, sai ya rasa rayuwar sa. "Wai ke ba za ki daina kukan nan ba, kamar a kan ki aka fara rashin ɗa? Wannan ai rashin tawakalli ne?" Nana ta waiwaya ta kalli mai maganar suka yi ido huɗu. Matar ta ce "Ahh wannan ba Nana ba ce, yayar Jamila" Alhaji Fatuhu ya ce "Kin santa ne? Antyn su Muhsin ce a Young talented academy" Hajiya sa'a ta ce "Na santa, ba ki gane ni ba ne?" Nana ta girgiza mata kai alamar a'a. "Ba da ke mu ka haɗu kwanaki a gidan maman khairat ba?" Nana ta sake ɗaga ido ta kalle ta, a take ta so ta nemi nutsuwarta ta rasa. Wani abu mai muhimmancin gaske take son tunawa, amma abu ya gagara sai ma wani irin sarawa da kanta ya yi. Hajiya Sa'a ta nemi ta rasa nutsuwar ta, ganin fuskar Nana tana canzawa kamar ba ta mutum ba, tana wani irin ja tamkar an shafa mata jar kala. Neman guri ta yi ta zauna da sauri, jin jiri zai ɗebe ta. A hankali Nana ta ɗauke kanta, daga kallon hajiya Sa'a, ta yi musu gaisuwa, ta tashi jiki a sanyaye ta ce tafiya za ta yi. Mahaifiyar Muhsin ta ce "Bari mu je ki yi wa kakarsa gaisuwa dan ita ma ta sanki a bakinsa. Haka Nana ta din ga yi musu gaisuwa, tana jin tamkar su ma suna zargin ita ta kashe musu ɗa, mussaman da aka ce yana ta kiran sunanta. Ta rako Nana har harabar gidan, tana ci gaba da yi mata godiya. Alhaji Fatuhu ya ƙaraso ya ce "To Nana Allah ya ƙara mana haƙurin rashin Muhsin" Ta jinjina kai amma ta kasa magana. Ya kalli maman Muhsin ya ce "Yanzu Alhaji Zailani ya kira ni, yake bani haƙuri bai shigo ba yau, ba shi da lafiya ne wai" "Ai ɗazu Hajiya Amina ta zo da safe tare da mai aikinta sun kuma yi mana gaisuwa ai ba komai sun yi ƙoƙari mun gode sosai" Gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, ba dai Alhaji Zailanin dai da ta sani ba, tuno abin da ta gani a falonsa ɗazu ta yi. Sai dai ta rasa me ma za ta ce, wataƙila ma ƙaisar ne kawai yake wasa da hankalinta. Haka suka kama hanyar komawa gida. Nana na komawa gida la'asar, kasancewar ba ta salla, sai ta shiga ta yi wanka ta kintsa jikinta. Wani abu mai ɗaci ya tsaye mata a wuyanta, har ya fara ƙoƙarin hana ta numfashi. Ba ta ko iya gani saboda azabar jiri da ciwon kai, ta kwanta ta yi shiru ta rufe idanunta, ta din ga tuna mutanen duk da suka rasa rayukansu da yanzu ita ma take kyautata zaton saboda ita ne. Ta fashe da kuka, tana "Wannan wace irin rayuwa ce, gaba ɗaya na kasa tantance ni mece ce ma gaba ɗaya. Allah ya tsinewa tsohuwar da ta gada mini wannan masifar wallahi ba zan yafe ba". ***** Malam Gambo mai allon ƙasa ne zaune a kan buzunsa, ya nutsu yana sauraren Alhaji Zailani. "Ni dai abin nan ya firgita ni malam, ni ban taɓa abu makamancin haka ba, yanayin kamar ɗimuwa ko gushewar hankali" Malam Gambo ya numfasa ya ce "Me yasa ka yi gaggawa? Wutar ciki ce da kai Alhajin Allah, ai a sannu za ka bi ta, ba kowacce yarinya za ka yi wa irin wannan tayin kai tsaye ba, mussaman idan ba ta saba ba, duk lalacewar zamani akwai na Allah" "Wallahi kuwa yarinyar ta bani mamaki, akwai taurin kai na tsiya" "Yanzu ba wannan ba, matsalar da nake gaya maka akwai, ita na duƙufa bincike a kai, kwanaki ba akwai wani wuridi da na yi maka ba, na kira wani aljani ya yi mana aiki ba ya ƙi?" Da sauri Alhaji Zailani ya ce "Eh an yi haka" "To wannan aljanin shi ne a kanta, goɗiyarsa ce" Alhaji Zailani ya waro ido ya ce "Haba, ni fa na ce, wallahi da ta buge ni ta wuce, kamar wani ingarman doki ne ya hankaɗe ni" "To ya zame maka dole ka kula ka yi taka tsantsan, ka bi a sannu burinka ya cika idan ka ci gaba da far mata zai iya ajalinka!" "Ajalina fa ka ce?" "Ƙwarai da gaske, hatsabibin matashin saurayin aljani ne, ba ya neman rigima da kowa amma idan aka taɓa shi faɗa da shi ba ya ƙarewa har abada" Alhaji Zailani ya jinjina kai cike da gamsuwa, dan kuwa a rayuwarsa babu babban abin da yake tsoro sama da mutuwa, ko zancenta ba ya so gani yake, yana da cikakkiyar lafiya da ba za ta tunkaro shi a daidai wannan lokacin ba. Sai da Nana ta shafe kwanaki uku, babu lafiya ga wani irin zazzafan zazzaɓi da take fama. A kwana na huɗu ta lallaɓa ta koma gidan Alhaji Zailani. Hajiya Amina na ganinta cikin damuwa ta ce "Nana kwana biyu lafiya kuwa?" "Wallahi Hajiya ba ni da lafiya ne" "Allah sarki, ga shi ke ba waya balle a ji halin da ki ke ciki, Haidar duk ya damu yana ta tambayar ki." Tana rufe bakinta sai ga Haidar ya fito da gudu, ya ɗane jikin Nana. Sai ta tuno da Muhsin, take wata fargaba ta shige ta, kar shi ma abin da ya samu Muhsin ya same shi, saboda sun shaƙu sosai. Jiki a sanyaye ta rungume Haidar. "Nana anya kin warware kuwa, bari na kira Doctor Sharif ya zo ya duba ki, duk kin yi zuru-zuru". Ita dai Nana ba ta ce komai ba, har mamakin kirkin Hajiya Amina take yi. Har gida doctor Sharif ya zo, ya duba Nana, ya bata magunguna da allurai, ya saka mata ruwa a gidan. Ganin Nana a kwance duk sai Haidar ya damu, ya koma kusa da ita ya kwanta shima. Nana cike da ƙaunar yaron take kallonsa, tana tuna Haidar, ta din ga addu'a Allah ya kare shi ya kiyaye shi, kar abin da ya samu Muhsin shi ma ya same shi. Kafin yamma Nana ta ɗan ji ƙwarin jikinta, har ta din ga ɗaga Haidar tana yi masa wasa, saboda yadda duk ya damu, da ganinta a kwance. Hajiya Amina ta fito falon ta miƙowa Nana waya, Nana ta saka hannu ta karɓa tana kallonta. Ta ce "Tun da shi sirikin nawa, bai kawo miki waya ba, ni ga shi na baki, ki lallaɓa da ita, bai kamata a ce budurwa kamar ki ba ta da waya ba. Ga dubu uku, idan kin fita ki tsaya ki sai layi a yi miki rijista ki saka a ciki, in sha Allah nan da kwana uku za a biya duk ma'aikatan gidan nan albashin su. Ko wani abun ne ya faru kya din ga bugo waya ki sanar" Nana ta juya wayar, da gani ba wani amfani aka yi da ita ba, sai ƙyalli take yi, har da charger. "Yanzu Hajiya wannan tawa ce?" "Eh mana Nana, ko ba ta yi miki ba?" Nana ta girgiza kai ta yi murmushi ta ce "Wallahi ban taɓa zaton zan riƙe waya mai kyau da tsada har haka ba. Allah ya faranta miki, ya kula miki da zuriyar ki, ya dauwwamar muku da farin ciki na gode sosai da sosai" Hajiya Amina ta yi murmushi ta ce "Nima na gode sosai, ina jin daɗin yadda ki ke kula da Haidar da zuciya ɗaya, na ga kina da yawan ibada da azumi, dan Allah ki yi mini Addu'a idan ina da rabo Allah ya bani haihuwa" Turus Nana ta yi tana kallonta, a wannan shekarun nata me za ta yi da wata haihuwa?. Ta yi murmushi ta ce "Kin yi mamaki ko? Ai ban taɓa haihuwa ba, ki roƙa mini, idan kuma ba ni da rabo, Allah ya ƙara mini dangana" Nana a ƙasan zuciyarta murna ta taya Hajiya Amina, na rashin haɗa zuriya da wannan majanunin mijin nata mara addini. Amma a zahiri ta ce "Ki yi haƙuri Hajiya, kin san komai rabo ne, kuma Allah ya fi mu sanin abin da ya dace da mu. Ko kin bar duniya in dai ɗan Adam zai rama halacci ire-irena da yaran da ki ka riƙe, za su yi miki addu'a. Kar ki manta ba ke kaɗai ba ce uwar mumunai Allah ya ƙara mata yarda, ba ta samu haihuwa ba amma uwa ce ga dukkanin muminai, a rashin samun haihuwar nan, ke ba ki san me Allah ya tanadar miki ba, wanda bai bawa waɗanda suka haihu ba" kai tsaye kalaman Nana suka din ga shiga zuciyar Hajiya Amina, da sai da hawaye ya cika mata ido. Ta ji daɗin kalaman Nana, na ƙwarin gwiwa, ta yi mamakin yadda Nana ta iya tsara maganganu cikin hikima. "Na gode sosai Nana, kin ƙara sawa na ji nutsuwa, Allah ya ba ki zuriya ta gari. Ka da Allah ya jarrabe ki da ƙaddarar rashin haihuwa. Duk ta tawakallinka, akwai gaɓar da mutane mussaman 'yan uwanka mata sun saka ka ji tamkar ba ka da amfani." "Amin na gode sosai Hajiya. Amma ta ki jarrabawar ki ka sani, da wata jarrabawar gara rashin haihuwa sau dubun dubu" haka su ka din ga hira da Hajiya Amina, har lokacin tafiyar ta ya yi. Tana shirin tafiya, Shukura ta dawo, Haidar yana kallonta, amma bai damu ya je gurinta ba, ya rirriƙe Nana yana cewa zai bi ta ta tafi da shi ba. Da ƙyar ta lallaɓa shi, ta fita. Habu na ganinta ya taso zai buɗe mata gate, ya ce "Malama har kin taso?" Nana ta ce "Eh malam Habu, shekaranjiya na zo zan fita, duk ba kwa nan" "Eh wallahi mai gidan nan ne ya aike mu" Ta ce "Allah sarki, yauwwa dan Allah ina wannan ɗan uwan naku?" Habu ya ce "Wanne daga ciki?" "Wannan ɗin nan" "Ya sunan shi?" Nana ta girgiza kai ta ce "Ban san sunansa ba, ɗaya ɗan uwan naku dai Sule ya ce mini ba shi da cikakkiyar lafiya, kurman nan" Habu ya kwashe da dariya ya ce "Kayya ba kurma ba ne ba yana magana" Ta ce"To ai shi kullum baya magana, fuska a rufe kamar amarya. Shi ya buɗe mini ƙofar ranar na fita" "Allah sarki, yana gane komai, kawai da larura ce a ƙwaƙwalwarsa, ba kuma wai hauka yake yi tuburan ba, wasu lokutan ma sai ya shafe sati bai ce uffan ba, yana kwance ma ba lafiya" Cikin tausayawa Nana ta ce "Allah ya sauwwaƙe, na tafi sai da safe" "To sauka lafiya, Allah ya tsare" ta amsa da Amin ta tafi. Ɓoye wayarta ta yi, saboda ta san tsaf Baba zai ƙwace wayar nan, mussaman yanzu da yake neman kuɗi ido rufe. Bayan Nana ta koma gida, Jamila take tambayarta ashe sun haɗu da Hajiya Sa'a a gidan rasuwa, amma ta ce ba ta santa ba. Nana ta ce "Ina cikin jimami da alhinin mutuwar yaron ne, shiyasa na kasa gane ta" Jamila ta ce "Allah sarki, ashe yaron ma sunanki ya yi ta kira kafin ya rasu" Nana ta kalli Jamila daga sama zuwa ƙasa ta ce "Wannan karon ma ni na kashe shi ko?" Ta yi magana tana tsare Jamila da ido. Jamila ta ce "A'a ni ban ce ba, kawai labari fa take bayarwa" Nana ta gyaɗa kai cikin gargaɗi ta ce "Jamila ina son hawainiyar matar nan ta kiyayi rama ta, idan ta ci gaba da ƙoƙarin cin iyaka ta, za ta faɗo cikin wutar da za ta ƙona ta da ita da amfanin gonarta, wannan saƙona ne a gare ta." Saroro Jamila ta yi cikin tsoro, jin yadda Nana take magana kamar an shaƙe ta. Kamar kuma wadda ta razana a cikin bacci, jikin Nana ya ɗan yi girgiza sannan ta ce "Jamila yau wainar fulawa nake sha'awa, zan sai fulawa ki sai mana manja, mu soya mana" da yake sun saba yin haka. Jamila kawai ta jinjina mata cikin tsoro. Da daddare Jamila ta samu Nana tana shirin kwanciya bacci ta ce "Nana wai Hajiya Sa'an wani abun ta yi miki ne, ki ke cewa na yi mata kashedi?" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce Hajiya Sa'a?" "Wadda ku ka haɗu a gidan rasuwa" Nana ta ce "A'a wani abin ta ce na yi mata?" "A'a to ai ke ce ki ke cewa na ce ta kiyaye ki, kuma babbar mace kamar wannan shi yasa na tambaye ki" Nana ta waro ido ta ce "Ni babu abin da ta yi mini, ni fa ko magana ban yi mata ba, me ta yi mini zan ce ta kiyaye ni?" Sai a lokacin Jamila ta fahimci kamar Nana ba ta san ta yi maganar ba sai ta ƙyale ta. Ranar da aka bawa Nana albashi, kamar ta taka rawa, ganin ta mallaki dubu ashirin ta ta, ta kanta. Ga dubu ashirin da Alhaji Zailani ya ce a bata, baban Haidar kuma ya ce a bata dubu goma, sai da ta tashi da dubu hamsin. Iya salarynta ta yi murna da shi, wanda aka ce Alhaji Zailani ya bata kuwa, ji ta yi tana ƙyanƙyamin su. Da murna ta nufo gida, tana tunanin wace bajintar yakamata ta yi a gida, yadda kowa zai amfana. Amma tana zuwa Baba ya turke ta da bala'i "Wai Asma'u ba za ki ƙuƙuta a samu komai a hannunki ba? Ƙanin uban yaron nan ya kira ni a waya, yana idan ba zan dawo da kuɗin ba, hukuma ce za ta raba mu, ba ki da asara ko a jikin ki ko?" Nana ta saka hannu a aljihun rigarta, kasancewar kuɗin dubu goma goma ne, ta ciro uku ta bawa Baba ta ce "Baba wannan ne kawai a hannuna, nima yau aka biya ni albashi". "Yauwwa ko ke fa, ba zan taɓa su ba kiran su zan yi su zo su karɓi abin su, duk da koma me aka yi mini ke ce sila, da kin haƙura kin kwantar da hankalinki shikenan, amma mugun halinki ya sanya ki ke ta yi wa yaron nan wulaƙanci, yanzu kalli halin da ki ka jefa mu" Nana ta daina mamakin ƙarfin hali da son kai irin na Baba, sai dai ta yi shiru ya gama surutansa ta tashi ta tafi. Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta juye zuwa ga babba, domin kuwa Saleh cewa ya yi ba zai karɓi dubu talatin ba, dan ko kwatan abin da ya kashe ba a ba shi ba. Dan haka ya kai Baba police station. Haka aka turo jami'an tsaro, suka tisa ƙeyar Baba zuwa gurin 'yan sanda. Sai Gaddafi aka nemo, ya bi bayan su. Gaddafi ya kalli Saleh, ya ce "Yanzu kai Saleh saboda rashin ta ido, ka rasa wanda za ka kawo gurin 'yan sanda sai mahaifina, saboda rashin kara, ko dan zaman amanar da muka yi a ikko, ga yayanka na auren ƙanwata." Saleh ya ce "Ka ga malam, a batun kuɗi babu wata kara, yarinyar nan ba ƙaunata take yi ba, har tana neman hallaka ni, ban aure ta ba zan bar muku kuɗina ne?" Duk yadda a ka yi da Saleh a yi sulhu, amma ya ƙi yarda, sai da aka yi yarjejeniya, cewar nan da kwanaki uku za su kawo kuɗinsa gaba ɗaya a ba shi". Ranar yau na ɗaya daga cikin ranakun da Nana, ba za ta iya mantawa da su ba, domin bayan dawowarta gida, Baba ya din ga yi mata bala'i tamkar zai tsine mata, har da cewar ya yi dana sanin haihuwar su da ɗan uwanta, ya yi dana sanin haɗuwa da mahaifiyar su har ya aureta ta haife su". Gaddafi ya ce "Dan Allah Baba ka yi haƙuri ka yi shiru haka mana, sai ɗaga murya ka ke yi duk maƙwabta su na jin ka, kuma ka na ta cewa ta nemo kuɗi a biya, ka san dai ba wata sana'a take yi ba, idan kuma ba hanyar banza ka ke son ta shiga ba" Cikin takaici Baba ya ce "Ka bar ni Gaddafi, ban taɓa haifar ɗan da yake neman ya yi ajalina ba kamar Nana, da me zan ji ne? Ba ta tausayina ko kaɗan duk wata hanya da zan bi na aurar da ita, ta nutsu nima na nutsu ta ƙi, a dalilinta a ka kai ni station a ke nema a rufe ni. Lokacin da aka haife ki babu farin cikin da ban yi ba, na so ki, amma kina neman ki kashe ni. To wallahi idan kuɗin nan ba su samu ba a ka rufe ni, sai kin bar gidan nan, kuma kwana ki bakwai na baki ki fito da wani mijin, ko ki koma gurin uwarki ki bar mini gida" Ayshercool 08081012143 23 Cikin maɗaukakin sauti Nana take kuka "Baba ka kashe ni ka huta, idan ma ba ka kashe ni ba, ni zan kashe kaina wai ya ake so na yi ne?" Gane nufin Nana da Gaddafi ya yi, ya sanya cikin tsananin zafin nama ya rigata isa gaban rijiyar, ya rufe ta, tana ƙarsowa ta yi karo da Gaddafi ta faɗi ƙasa. Ya kalli Baba ya ce "Yakamata ka din ga haƙuri, ka din ga tausasa lafuzanka, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya idan ta kashe kanta, kai fa abin zai dama fiye da kowa. Kuma maganar kuɗin nan, ka bar komai a hannuna ko ba duka ba za a samo wasu, ka daina cewa ta fita ta nemo kuɗi a biya. Ka daina biye shawarar da ake baka ta banza, mai baka shawarar ba za ta bari ka yi wa yaranta haka ba" Ya durƙusa ya ɗaga Nana, kawai ya ji tausayinta ya kama shi. Matsaloli sun yi wa rayuwar ta yawa. Duk da uban nauyin da ta yi, tamkar ta haɗiyi dutse, haka ya ɗaga ta ya kai ta ɗakin su, ya kwantar da ita. Har ya yinƙura zai tashi, Nana ta danƙo rigarsa, ya kalle ta, idanunta a rufe, sai ruwan hawaye da yake zuba ta gefen idonta. "Nan gaba kan tsohon nan zan cilla a rijiya, ya iya bakinsa" Gaddafi ya ce "Wane tsohon? Baban ki ke nufi?" Kawai ta tashi zaune, ba tare da ta buɗe idonta ba ta riƙe hannayensa. Ji ya yi kamar an jona masa shocking, jikinsa tamkar za fizge naman jikinsa, ga shi ya kasa motsi, ya kuma kasa magana. Ta yi murmushi ta ce "Ina fatan yanzu ka gane mai baka saƙon? Ina ƙyale ku ne saboda ku ne abu ma fi soyuwa ga uwar gijiyata." A hankali ta saki Gaddafi ta silale a gurin. Tamkar korarrare Gaddafi ya fita cikin tashin hankali, babu wanda ya tsaya yi wa magana ya fice. Tun da Gaddafi yake bai taɓa shiga bala'i irin wannan ba. Har a lokacin da ya fita, da ƙyar yake iya sarrafa jikinsa tamkar zai fita hayyacinsa. Washegari da safe tamkar babu abin da ya faru, Nana ta shirya ta gaida Baba za ta fita amma ya yi mata banza, jikinta babu ƙwari ta tafi gidan Alhaji Zailani. Inda Allah ya taimake ta, tun da wannan abin ya faru, bai ƙara yinƙurin far mata ba. A hankali take bubbuga gate ɗin, duk da ba ta da tabbacin ma, ana iya jin bugun nata. A yadda take jin duniyar ta yi mata zafi, ji take tamkar ta nemi guri ta kwanta a nan ƙofar gidan. Aka buɗe gate ɗin, tana ɗaga kai suka yi ido huɗu. Dumm! Gabanta ya yi mummunar faɗuwa, babu shiri ta sunkuyar da kanta, ita ba ta shiga ba, ita kuma ba ta koma ba. Kawai ya mayar da ƙofar zai rufe, babu shiri ta tura ta shiga, ta kalle shi tana son ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kwarjini da babu wani ɗan Adam da ya taɓa yi mata. Ƙoƙarin gane kamaninsa take yi, amma babu dama rawaninsa ya rufe ko ina na fuskarsa sai idanunsa kawai. Ta kama hanya ta nufi cikin gidan, sai da ta je tsakiyar harabar gidan, sai ga wasu irin murguza-murguzan karnuka da ba 'yan Nigeria ba, idan ta zo haushin su kawai take ji, ba ta taɓa ganin su ba, da daddare ake sakin su, da safe kuma a mayar da su keji, da guda ɗaya ne a ka ƙaro biyu. Yau kuma Sule bai samu ya mayar da su ba. A gigice ta kurma wani irin gigitaccen ihu, ta watsar da takalmanta ta zura da gudu, aikuwa suka rufa mata baya su na wani irin haushi mai ban tsoro. Yana tsaye yana kallonsu, kafin ta ƙaraso gurin da yake har ta fara fita daga hayyacinta. Cukuikuye shi ta yi tana ihu, ta daina ganin komai, sai su biyu a cikin sahara, sai kuma jin sautin haushin karnukan. Ƙaisar ne ya bayyana, ya yi wata irin girgiza, ya zama wani irin narkeken kare shi ma, haushi ɗaya ya yi sai da gurin ya yi amsa kuwwa a take karnukan suka gudu, kamar barewar da ta ji kukan zaki. Ya girgiza jikinsa ya koma yadda yake, ya miƙa masa hannu ya ce "Ko da wasa, idan ka sake yinƙurin razana ta, ko wani abu na cutarwa a gare ta, zan shafe tarihinka a duniya". Nana ta buɗe idanunta da kyar, ta kalli yadda buzun nan, ya rikiɗe ya koma tsohon nan mai kama da ƙaisar. Sai dai ko motsi ta kasa. Wata irin dariya tsohon ya din ga ɓaɓɓakawa, gurin ya din ga amsa kuwwa. "Kai ɗan samari, ka sake nazarin kalaman da ka faɗa, bayan tsawon shekaru mun sake haɗuwa, mun kuma haɗu a gaɓar da ta dace Ƙaisar" ya yi maganar yana ci gaba da dariya. A hankali ya ɗago Nana daga jikinsa da ta riga ta suma, ya kalli harabar gidan duk wannan kururwar da ta yi, babu wanda ya fito. Ya sanya yatsunsa biyu, manuniya da na kusa da shi ya daki goshin Nana sau uku. A hankali ta motsa ta ɗaga kanta, a falon cikin gidan ta ganta. Hajiya Amina ta ce "Ohh sannu Nana, haka ki ke tsoron kare? Laifin masu gadi ne da ba su mayar da su sun rufe ba, sannu ba ki ji ciwo ba ko?" Nana ta jinjina kai hawaye na zubowa daga idanunta. Alhaji Zailani ya fito falo, sai baza ƙamshi yake cikin dakkakiyar shadda. Ya tsaya a falon ya kalli inda Nana take ya ce "Lafiya kuma take kuka?" "Wallahi karnuka aka bari ba a kulle ba, suka biyo ta shi ne har da kakunta, yanzu suka shigo tare da Yusuf" Ya girgiza kai ya ce "Laifin masu gadi ne ai, bari na fita sai na dawo" Nana ta ƙura masa ido, tana son tuna wani abu a kansa, amma ta kasa, ta ci gaba da kallonsa har ya fice. Da ƙyar ta iya jan ƙafafunta, ta tafi ɗakin Haidar. Ta shiga banɗaki domin wanke fuskarta, ta tsaya ta zuba wa fuskarta ido a jikin mudubi. Ta yi shiru tana tuna tun daga tashinta, zuwa yadda ta zo gidan nan, daga lokacin da karnukan nan suka biyota, tunaninta ya hargitse gaba ɗaya, ta kasa bambance mene ne ya faru a zahiri, menene ya faru ba a zahiri ba, kuma Hajiya Amina ta ce mata, tare suka shigo da Yusuf to ta yaya? Ɓangaren kanta ɗaya ya sara, da sai da ta dafe kan nata. "Wai ko ni ma dai ba mutum ba ce ba? Ko kuma dai ƙaisar ya fara nasarar raba ni da hankalina ne?" Ta furta a hankali cikin tsoro da sheshsheƙar kuka. Jin ana bubbuga ƙofar banɗakin, ya sanya ta sauri ta wanke fuskarta ta fito. Haidar ta gani a tsaye yana mutsutsuka idanunsa. Ta kama shi ta wanke masa baki, ta yi masa wanka. ***** Alhaji Zailani ne a zaune a cikin motarsa, gefensa kuma doctor Sharif ne a ciki a zaune. "Sharif" "Na'am Alhaji" ya yi maganar cikin girmamawa. "A wannan karon ma, taimakon da ka saba nake so ka yi mini" Doctor Sharif ya ce "Babu abin da zaka nema, na kasa yi maka shi, ka faɗi ko mene ne" "Yaushe ne EDD ɗin Shukura?" Ya ɗan yi shiru ya ce, scanic biyu dai ta yi a yanzu, amma duk a cikin watan jibi ne, suka nuna za ta haihu" "To ka saurare ni da kyau, na san dole a asibitinku za ta haihu, idan ta sauka ina buƙatar jaririn" Doctor Sharif ya kalle shi da sauri, ya ce "Ban fahimta ba" "Sharif da hausa nake magana, idan Shukura ta haihu, ina buƙatar jaririn duk yadda za a yi, a yi kawai ina buƙatar jaririn. Ka tuna idan ka kuskura kalma ɗaya ta fita daga maganar da muka yi da kai, to zan iya zame kaina na barka, kuma ba ka da shaida, idan kuma ka yi shiru komai ya tafi dai-dai, zan baka abin da zatonka da tunaninka bai taɓa zata ba" Jiki na tsuma Sharif ya ce "In Allah ya yarda babu wanda zai ji, ba zan taɓa buɗe sirrinka ba" Alhaji Zailani ya ciro envelope ya bawa Doctor Sharif ya sallame shi. ***** Nana kuwa tana tunkarar gida, gabanta na tsananta faɗuwa, tabbas da tana da wani gurin zuwan, babu abin da zai sanya ta je gidan ta kwana, saboda fargabar abin da za ta tarar a gidan. A can ƙasan maƙoshinta take sallama, Mama ta kalleta ta yi mata banza, haka ma Suwaiba. Ba ta sake magana ba, ta shiga ɗaki ta jima a ɗaki sosai, sannan ta fito tsakar gida ta fara ɗan kaye-kaye, saboda yadda zama ɗakin ya ishe ta, tunani da damuwa, duk suka addabi Zuciyarta. Tana jin sallamar Baba, gabanta ya faɗi, ta miƙe tsaye hannunta riƙe da tsintsiya, dan ta san dole sai ya yi mata wani abin da ranta zai ɓaci. Sai dai ga mamakinta sai ya washe mata baki. "Yarinyar kirki irin albarka, kamar dai yadda na yi tsammani, ke ɗin ce dai maganin hawayena. A dalilinki Allah zai fitar da mu daga wannan baƙin talaucin da wahalar da muke ciki. Idan zan iya tunawa shekarar da aka haife ki an yi ruwan sama marka-marka, an samu amfanin gona mai kyau da yawa" Nana ta yi fakare da kai tana kallon Baba, duk wannan hawa da saukar da yake yi ba ta gane ina ya dosa ba. "Zo ki zauna mu yi magana Asma'u ma'ulle, maganin kukana dama na daɗe ina mafarki gani a harami, ashe ke ce za ki yi silar komai" da kansa ya jawo tabarma ya shimfiɗa, ya karɓe tsintsiyar hannunta ya jefar, ya yi mata umarnin ta zauna. Ta nemi guri ta zauna, ya kalle ta fuskarsa cike da farin ciki ya ce "An gama biyan wancan matsiyacin kuɗinsa" Kai kawai Nana ta jinjina, zuciyarta ɗauke da tambayar a ina Baba ya samu kuɗin. "Ɗazu wajen azahar, ina zaune ina ta hamma, na yi wani baƙon alkhairi. Wallahi Nana komai na duniya rabo ne, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne, wannan banzan yaron ashe ba alkhairi ne a gare ki ba, shiyasa aka yi uwar watsi da shi" ci gaba da kallonsa kawai Nana ta yi, tana jiran ya kai ƙarshen bayanan. "Yanzu dai wani bawan Allah ne ya zo neman auren ki, kuma na ce na ba shi, na yi masa bayanin halin da ake ciki da wancan matsiyacin yaron, ya ce kar na damu, dubu ɗari biyu ya bayar a biya Saleh kuɗinsa, ke kuma ya ce nan da sati biyu zai aure ki, ɗaurin aure kawai za a yi baya son kowa ya sani, kawai zai zo ya ɗauki matarsa shikenan Allah ya dube mu Nana" Idanun Nana suka kaɗa su ka yi ja, ta ce "Baba wani irin aure ne za a yi shi na sirri? Da ba a so kowa ya sani? Waye ma tukuna, sannan mece ce sana'ar sa?" A take Baba ya fusata ya ce "To dan ubanki zan yi miki zaɓen tumun dare ne? Koma wane ne za ki gani ai" "Baba na san ko waye, kuma wallahi muddin ka dage sai ka aura mini shi, wallahi zan iya kashe kaina, ko na bar gidan nan" Baki buɗe Baba ya kalli Nana, "Ni ki ke gaya wa za ki kashe kan ki, ko ki bar gidan nan?" Tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Baba wane irin aure ne, mutum zai ce, ba ya so a sani. Alhaji Zailani ne, mutumin da nake aiki a gidansa na sani." Ta yinƙura ta tashi, ta bar wa Baba gurin tana kuka. Bil haƙƙi da gaske, zuciyarta ta din ga raya mata ta kashe kanta har lahira, kawai ta huta da wannan masifar. Gani take kamar gaba ɗaya babu wanda duniya ta juya wa baya, ba ta yi da shi tamkar ita. Duk inda ta juya babu daɗi. Mama kuwa tun da Baba ya zo mata da maganar nan, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa abun da yake yi mata daɗi. Wani abu mai masifar zafi ya tsaya mata tun daga ƙirjinta zuwa bakinta. Tana ganin ya za ayi a ce, ga su Jamila a zaune, Nana ta samu hamshaƙin mai kuɗi haka. Ana yin sallar magariba Baba ya fita masallaci, ita ma ta yafa mayafinta ta fice. ***** Jamila ce a zaune a gaban Hajiya Sa'a, fuskarta ɗauke da matsanancin tsoro take kallonta. Ta dafa kafaɗar Jamila ta ce "Kin tabatta ta sha maganin da aka ba ta a kunun ayar?" "Ta ce mini ta sha, amma ba a gabana ta sha ba" "Shikenan kar ki damu, ki kwantar da hankalinki. Za mu ci gaba da ƙoƙari har zuwa lokacin da zamu samu abin da muke so. Abin da nake so da ke shi ne ki zamo mai riƙe mana sirri, za ki samu kuɗi Jamila, irin wanda ba ki taɓa zaton riƙe su, ba za ki yi rayuwar ƙunci da talauci irin na gidanku ba. Nana ita kawai muke buƙata idan ba haka ba, ba zaki zama abin da nake hangen ki zama ba" ta yi maganar cikin bawa Jamila ƙwarin gwiwa. Mama ce zaune a cikin wata rumfa, tare da wani mutum, ta tattara masa hankalinta gaba ɗaya. "Ai na gaya miki Rabi, muddin ba ki yi da gaske ba, wallahi ki na ji kina gani, sai dai ke da yaranki ku yi mata biyayya. Tasirin taurarinta ba za su bari na yaranki su haska ba." Cikin damuwa ta ce "Ai na ga alama, 'yar shegiya kwatsam mutum ya fito wai aurenta zai yi, a zuwa ɗaya ba ka ga uban kuɗin da ya bawa ubanta ba, bai gaya mini nawa ba ne ba, amma wallahi na san da yawa. Kalli aikin raino take yi, amma albashin dubu talatin aka bata, ta bawa ubanta. Wallahi ko buɗe ido ba na ƙaunar na yi na ganta. Ni dai dan Allah ka wargaza maganar nan, kar a yi auren nan. Duk da na ji tana cewa uban ba ta so" Ya yi murmushi ya ce "Ta kwana gidan sauƙi, yau zan kwana aikin, da ni da almajiraina, za a yi farraƙu mai zafi. Ki zube kuɗi kawai abin da yake hannunki a fara" Haka ta buɗe jakarta, ta ciro kuɗi ta ajiye masa. **** Tinkis-tinkis yake tafiya, kamar wani bujimin sa, ya nufi motar da zai hau ya fita, sai dai yana ƙarasawa Nana ta miƙe tsaye. Sai da ya ɗan tsorata da ganinta. Ya ce "Lafiya dai ko?" "Wani dalilin ne ya sanya ka je ka samu mahaifina, ka ce masa zaka aure ni?" Yayi dariya tare da shafa tumbinsa ya ce "Dalilin da yasa ki ka ƙi amincewa da buƙata ta, ya sanya na biyo ta in da dolen ki ki yarda. Amma na yi mamakin yadda ƙwaƙwalwarki take aiki da har ki ka yi saurin gano ni ne. Sai daga baya na gane ba iya taurarinki nake buƙata ba. Ina buƙatar aljanin da yake tare da ke ma. Kuma wannan ƙwaƙwalwar ta ki ma ina buƙatar ta" Cike da ƙwarin gwiwa Nana ta ce "Ni na yi maka kala da wadda za ta auri fasiƙi ne? Mazinaci baya auren kowa face 'yar uwassa mazinaciya, ni ba irinka ba ce ba, kuma Ubangiji mai adalci ne, ba zai yi mini wannan jarrabawar ba" Ya sake yin dariya ya ce "Akwai abin da ba a kuskurewa ƙaddara. Nima zinar da nake yi ta neman duniya ce, kafin na mutu zan tuba. Kuma tun da babanki uban kwaɗayi ne da son abin duniya, zan ta ba shi abin da yake so, domin buƙata ta biya. Tun da ke ba ki da wayo, ba ki san inda duniyar ta sanya a gaba ba." Ya buɗe motarsa ya shiga ya zauna, Nana ta bi shi da kallo cikin ɗacin rai. Ya sauke gilashin motar ya kalle ta ya ce "Ki kwantar da hankalinki, na ga kina da abubuwan da zan iya mora da yawa a jikinki, dan haka ko na aure ki zan iya zama da ke na ɗan lokaci" ya fara jan motarsa ya baro parking space ɗin. Ƙaisar ta gani ya bayyana, ya sha gaban motar, yana kallonta, babu tsammani sai ga wannan tsohon da take gani, mai kama da shi, ya keto ƙasa ya fito ya yi jifa da ƙaisar gefe. Gabanta ne ya faɗi, sai da ta dafe ƙirjinta ta ja da baya, ta ɗaga kanta ta ga har Alhaji Zailani ya bar harabar gidan, sai dai idanunta suka sauka a cikin nasa da ya ƙure ta da ido ko ƙiftawa ba ya yi. Kamar wadda ya yi wa dabaibayi ta kasa motsi. "Antyn Haidar, yau ma karen ne, na ganki a nan a tsaye" kamar wadda ta tashi daga bacci, ta kalli Yusuf ta ƙaƙalo murmushi ta ce "A'a ba karen bane, yanzu zan shiga ciki" "Ai kuwa ki yi sauri, dan mutumin naki ya tashi yana ta bin Mummy yana tambayarta ki na ina" Nana ta ce "To bari na shiga, a dawo lafiya" ya amsa mata da Allah ya sa. Ta wuce ta shiga. Hajiya Amina ce take yi wa Nana faɗa, ganin ta zubo abinci za ta ci, amma ta bar wa Haidar sai ci yake yi, ita kuma ta zuba uban tagumi. "Nana babu wanda ba shi da damuwa a rayuwar nan, kowa haƙuri yake yi, kalli 'yan kwanakin nan duk kin rame, haba Nana me yake damun ki ne" ta kalli yadda Hajiya Amina take damuwa idan ta ganta cikin damuwa, yaya za ta ji idan ta ji ta auri mijinta, sun yi auren sirri. Wasu hawaye ne masu raɗaɗi ke ƙoƙarin zubo mata, amma ta haɗiye ta ce "Rayuwa ce sai Alhamdilillah Hajiya, amma in sha Allah na daina" "Ko kefa, amma a ce da ƙanan shekarun ki, ki na damuwa tun ba ki yi aure kin tara iyali ba, ai sai wani ciwon ya kama ki" **** "Rabi ni fa ban ga Nana ba, ina ta shiga ne?" Mama ta kwaɓe baki ta ce "Ina na sani, ajiyarta ka bani ne? Tun farar safiya ta fice" "Ta fice da farar safiya? Kar fa ta aikata abin da ta ce, dan yarinyar nan ba hankali ne da ita ba" Mama ta kalle shi ta ce "Au me ta ce?" "Cewa ta yi wai ba zata auri mutumin nan ba, idan na matsa kuma guduwa za ta yi ta bar gidan" "Hmm baban su Jamila kenan, ai na daɗe da gaya maka Nana ba aljanu ne suke hana ta aure ba, tsagwaron iskanci ne wallahi. Idan Saleh talaka ne ta ƙi aurensa, yanzu ga mai kuɗi shi ma ta ce ba ta so, tana maka baƙin cikin fita daga wannan ƙangin wahalar. Kawai ka nuna mata kai ne ubanta, kai ka haife ta ba ita ta haife ka ba" Ya ja numfashi ya jinjina kai, cike da gamsuwa. "Amma ka gaya masa ciwonta?" Baba ya ce "A'a ba zan gaya masa ba, kar ya gudu, daga baya a yi wadda za a yi." Nana kuwa da taho gida, ta nemi dakalin wani gida ta yi zamanta, dan ko tinkarar gidansu ba ta son yi. Har a ka yi sallar magariba ta daidaici Baba yana masallaci, sannan ta shiga gida. Bayan ta yi sallar isha'i ta ɗaukko Alqur'ani ta ajiye a gabanta, tana so ta karanta, sai dai ta buɗe ta kasa karanta komai, ta lula duniyar tunani, ƙwaƙwalwarta ta din ga tariyo mata ƙira'ar malam Auwal. Har yanzu tana jin kewarsa, yana cikin mutanen da ba za ta manta da su a rayuwarta ba. Ko kuɗin nan da ta karɓa na albashi sai da ta yi masa sadaka. Ji ta yi ana nishi a gefenta, ga wani irin huci da yake dukan fatarta, ta buɗe idonta ta kalli gefenta, ta ga Ƙaisar a kwance, hannunsa ɗaya ya yi baƙi ƙirin, sai numfarfashi yake yi. Da sauri Nana ta nufe shi ta ce "Me ya same ka haka?" Ya ɗago hannunsa da ya yi baƙi ya ce "Ba a gaban ki a ka yi jifa da ni ba, garin in ɗauki fansar abin da a ka yi miki?" Ta ɗan waro ido ta ce "Dama akwai wanda ya fi ka ƙarfi?" Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar, sai a lokacin ta ga ya ji raunuka sosai, duk gurin da ya ji rauni shi ne ya yi baƙi sosai. "Ina ƙara nanata miki, halin da muka shiga, muddin ki ka ci gaba da zama a gidan nan, amma baƙin taurin kanki ya sanya kin nace" "Wasu lokutan, ba na gane in da ka dosa, wasu lokutan kamar ka damu da ni, amma cutarwar da ka ke yi mini ya sanya a duniya babu wanda na tsana sama da kai. Duk ka kashe mutanen da nake ƙauna, kuma alamu sun nuna da gaske haukata ni ka ke so ka yi" Ya miƙe dogwayen ƙafafuwan sa ya ce "Ni ban kashe kowa ba, duk wanda ya mutu lokacinsa ne ya yi, ni ban kashe kowa ba. Amma muddin babanki ya aura miki wannan mutumin dukkansu zan haɗa, jininsu ne zai zama jinin bil adama na farko da zan sha" "Baban nawa?" Nana ta yi magana cikin zare ido. "Shi ɗin" "Amma kuwa da... "Au ki na ji na ma ina ta baloƙoƙo ki ka yi mini banza ko?" Nana ta ɗaga kai ta kalli Baba. "Gidan uban wa ki ka je yau ba ki dawo da wuri ba?" Ta girgiza kai ta ce "Babu ko ina" "To daga yau kar ki sake zuwa gidan aikin, tun da mai abu abinsa ne ya ce ya ji ya gani yana sonki. Ya ce mini ya rage daga sati biyun nan, juma'ar nan ta jibi za a ɗaura muku aure kowa ya huta!" Ayshercool 08081012143 Page 24 "Baba dan zatin Allah, ka duba lamarin nan, wallahi ba na son mutumin nan, ba shi da kirki dan Allah Baba ka yi mini rai" "Nana duk rashin kirkinsa, bai kai talauci rashin mutunci ba, idan ki ka ga ba a yi auren nan ba, to sai dai idan wani mijin ki ka kawo, ke ko wani ki ka kawo ɗin wallahi ga dai mai rufin asiri ba zan bawa wani ke ba, gara ma ki yi haƙuri, ki tattara komatsan ki" "Ya Allah, Ya Allah Astagfirullah" ta faɗa duk a jejjere." "Mahaifinki ba zai taɓa canza hali ba, sam ta kansa kawai yake yi" Nana ta ɗaga kai a karo na biyu, da ta sake ganinta a gurin ƙaisar ta ce "Koma mene ne kai ne sila, kana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya Baba son rabuwa da ni ko ta halin ƙaƙa." Ƙaisar ya ce "Kar ki ga laifina, tun da na baki zaɓi tuntuni, ki ka tsaya wahalar da kan ki" ya yi maganar yana rubutu da hannunsa ɗaya mara ciwon. Ya ɗora da cewa "Matar babanku ta je gurin Malamin da ya zane ki rannan, a kan a wargaza maganar auren nan, dama ya kan yi mata aiki ire-iren waɗannan, idan Allah ya taimake ki aikin ya ci, sai ki ga an fasa, kalli abin da aka yi" mudubin da ya saba nuna mata, ya nuna mata. An raba wata 'yar tsana gida biyu, an rubuta sunan Nana a jikin ɓari ɗaya, ɓari ɗaya kuma Alhaji Zailani, ana ta wani surkulle. Ya ɗora da cewa "Abin da ba su sani ba su duka su ne, shi wannan mutumin ya kai matakin ƙololuwa a ƙungiyar asiri, to wani asiri ne kuma zai kama shi?" Nana cikin kuka ta ce "Wannan malamin shi ne ya zane ni rannan" Ƙaisar ya kwashe da dariya, ya ci gaba da rubutun sa. Cikin kuka ta ce "Kuma duk saboda kai, Allah ne gatana, kowa nice ba ya so kawai" ta yi magana tana ƙarewa malam Ɗayyabu kallo a jikin mudubin. Sai kuma ta daina ganin malam Ɗayyabu, sai Jamila tare da Hajiya Sa'a da kuma maman khairat. Da sauri ta kalli Ƙaisar ta ce "Wannan matar ba ita ka ce mini ta bayar da jinin Muhsin a ƙungiyar asiri ba? Amma me yasa da na tashi na manta, na ganta na kasa tunawa?" "Ashe kin san ainihin abin da ya faru, ki ke cewa na kashe wanda ki ke ƙauna?" Ta yi shiru tana satar kallonsa. "Shi ma wannan yaron na yanzu, idan ba ki yi wasa ba, ana daf da shafe tarihinsa a duniya, akwai yiwuwar 'yan ƙungiya su nemi a ba su jininsa" Cikin matsanancin tsoro Nana ta kalli Ƙaisar ta ce "A'a kar mu yi haka da kai Ƙaisar, dan Allah yaro ne fa bai san komai ba." Ya ce "Ni babu abin da zan yi da shi, kawai dai na gaya miki ne. Hatta ɗan da babarsa za ta haifa a nan gaba kaɗan, an gama shirya yadda za a yi da shi" A razane Nana ta tashi tsaye, amma sai ta ganta a tsakar ɗakinsu. Gigicewa ta yi ta nufo tsakar gida, ta ga tsakar gidan baƙi ƙirin, dare ya tsala. Sai kuma ta fara ƙoƙarin tuna abin da ya razanata, har ta fito tsakar gida, amma ta kasa tuna komai. Ta koma ta zauna jikinta yana tsuma, ta rasa ma wace addu'a za ta yi. Zuwa yanzu idan da sabo ta saba da matsanancin bugun zuciya saboda yawan razana da take yi. Ta haɗa kanta da gwiwarta, ta rasa ma wani tunanin za ta yi, kasancewar bacci ɓarawo ne, ya sanya ya yi nasarar yin awon gaba da ita. Sai dai ta din ga ganin Haidar, yana ta kuka tana ƙoƙarin rarrashin sa, amma ya ƙi yin shiru sai tsala ihu take yi. A wani ɓangaren kuma na mafarkin, ta ga Shukura a dokar daji, tana ta uban gudu da tsohon cikin nan, jikinta babu suturar kirki, duk jikinta raunika, kanta babu ko ɗan kwali, ga hannunta riƙe da Haidar sai gudu take tana kururuwa. Bayanta wani mutum ne ya rufe fuskarsa da baƙin ƙyalle yake bin ta, hannunsa riƙe da wuƙa ga jikinsa sai ɗigar da jini yake yi. Kukan Hidar sai amsa kuwwa yake yi, yana kiran sunan Nana. A wannan karon ma a razane ta tashi, da "Innalillahi wa innalillahi raji'un" daidai lokacin aka tayar da sallar asuba a masallaci. Gudu-gudu sauri-sauri, ta fita ta yi alwala, ta gabatar da raka'atanul fajar, sanan ta yi sallar asuba. Ta zauna tana tasbihi ta din ga tunanin 'yan kwanakin nan ba ta iya karanta Alqur'ani. Azkar ɗin ma sai ta shafe kwanaki ba ta yi ba, ganin ko ta yi babu abin da yake canzawa. Sai kuma ta tafi tunani, wataran a islamiyya da ta farka ta ga malam Auwal a kanta, yana ta raira karatun Alqur'ani, hakan ya tabattar mata da ƙaisar ya ziyarceta. Bayan ya sanya ta tashi, ta yi alwala ta dawo ta zauna, ya dube ta ya ce "Nana idan kin je gida kina azkar kuwa? Kuma kina karanta Alqur'ani?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To me yasa?" Cikin rauni da karaya ta ce "Ko na yi Allah ba ya kare ni, na fi shan wahala ma idan na yi" da sauri ya tari numfashinta ya ce "A'uzbillahi, waye ya gaya miki Allah ba ya kare ki? Da ba ya kare ki da Allah kaɗai ya san abin da zai faru da ke. Addu'oin da ki ke yi, da larurar da ki ke fama da ita, ba ya nufin karatun Alqur'ani da azkar da ki ke yi ba sa yi miki amfani, jarrabawa ce, daga Allah. Ke kina ganin Aljani na bibiyar marasa ji? Sun fi bibiyar nutsatsu masu addini, hakan na nufin jarrabawa ce, mai imani ba a barin shi haka babu jarrabawa. Kuma burinsu kenan ki daina ibada, su sake samu su miƙe ƙafa a jikinki, su ci gaba da azabtar da ke. Musulma ce ke, ki zama mai kyautatawa Allah zato". Ko da ta zo nan a tunaninta, sai ta ce "Astagfirullah, wa a tubu ilaihi" Ƙarfe tara da rabi na safe, Baba ya fito tsakar gida yana neman Nana. Mama ta ce "Ba fa ta nan" "Ban gane ba ta nan ba, ina ta tafi? Ba na kafa mata dokar kar ta sake fita ba, ana daf da ɗaura mata aure?" "To ka isa da ita ne? Ai ba ka isa ka gaya mata ta ji ba, ka yi kaɗan" Ƙwafa ya yi ya ce "Za ta dawo ta same ni, zan ci ubanta a cikin gidan nan wallahi" Bayan ya gama bambaminsa ya fita, Mama ta koma ɗakinta ta ɗauki wayarta ta kira Malam ɗayyabu. Sai da ta kusa tsinkewa ya ɗaga, "Malam yaya a ke ciki? An gama aikin ne?" "Eh a kan aikin muka kwana jiya" "To shikkenan, na gode sosai da sosai, baban nata fa ka yi aikin a kansa?". Ya ce "Kar ki damu, ba wanda ban yi ba fa" Ta ajiye wayar, tana kuma tunanin me yakamata ta yi. Kafin azahar ɗan aiken Alhaji Zailani ya zo, ya kawo uban kayan abinci kamar za a buɗe ƙaramin shagon sayar da kayan abinci. Bakin Baba ya ƙi rufuwa, sai shiga yake yana fita yana washe baki, yana ƙiyasata irin abin da zai yi wa Nana muddin ta bijirewa auren Alhaji Zailani. Yaron nasa ya sanar da Baba cewar, tafiyar gaggawa ta kama Alhaji Zailani, washegari zai dawo, amma ko baya nan bai dawo a goben ba, za a ɗaura auren nan ranar Juma'a, kuma ba ya buƙatar taron jama'a, waliyyai kawai sun isa. Baba yana tsuma ya tabattarwa da yaron Alhaji Zailani, mai suna Sani cewa ya tabattarwa da Alhaji Zailani ba za a samu wata matsala ba. Nana kuwa gaba ɗaya ji ta yi jikinta ya ƙara sanyi, tun da garin Allah ya waye, komai ba ya yi mata daɗi, tamkar ta mutu ta huta. Duk mutanen gidan sun koma baccin safe, ta shirya ta fice daga gidan. A hanya gari ya ƙarasa wayewa Nana, ta je ta din ga bubbuga gate ɗin, aka zare sakata aka buɗe. Sai dai maimakon ya ba ta hanya, sai ya zura mata idanunsa yana kallonta. Hankaɗa ƙofar ta yi ta shiga a fusace, ta tsani wannan ɗan iskan kallon da yake yi mata, shi kuma kullun fuska a rufe, ba a ganin fuskarsa sai dai ya yi ta kallon mutane. Burki ta ja ta tsaya, tana kallon yadda ƙosassun karnukan nan, suke safa da marwa a harabar gidan. Ta waiwayo ta kalle shi, ya kawar da kansa kamar bai gan ta ba, ya mayar da gate ɗin ya rufe ya saka mukulli, ya nufi ɗakinsu na masu gadi. Karnukan suka yi cirko-cirko suna kallon Nana, su na haushi. "Dan Allah ka raka ni bakin ƙofar shiga" ta yi maganar a marairaice. Bai kulata ba ya cigaba da tafiya. "Dan Allah idan ba za ka raka ni ba ka buɗe mini ƙofa na koma". Ganin da gaske ba zai rakata ba, kuma ba zai buɗe mata ba, ga karnuka su na nufo ta, kawai ta rufa masa baya da gudu. Ya tsaya ya waiwayo ya kalleta. Ta ja ta tsaya cikin tsananin tsoro. Sule ne ya fito yana miƙa da alama a lokacin ya tashi, ya kalle su ya ce "Nana lafiya na ganki da sassafen nan? Kuma ya na ganku a tsaye haka lafiya dai?" "Tsoro nake ji, na ce ya raka ni yaƙi, kuma ya kalle ƙofa ya ƙi buɗe mini na koma gida, kuma so suke su biyo ni su cije ni" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye saboda tsoro. Sule ya yi dariya ya ce "yi haƙuri, ni ban san dalilin da ya sanya ku ke yawan samun saɓani da Buzu ba. Jira ni na ɗaure karnukan sai ki wuce" Ta goge hawayen ta ce "To na gode sosai" Shi kuwa tuni ya shige ɗakin su, ya bar ta da Sule. Ko da Nana ta shiga cikin gidan, ɗakin Haidar ta nufa kai tsaye, yana kwance yana ta baccinsa. Ajiyar zuciya ta din ga saukewa, ta durƙusa a gabansa ta dafa kansa, tana karanto masa addu'oin da suka sauwwaƙa a bakinta. Tana ɗan tofa masa. Wata irin razana ya yi a baccin, har da ɗan ihunsa, Nana ta rungume shi, ya ƙanƙameta ta cigaba da yi masa addu'a. Yau Shukura ta na gida, sun yi hutun makaranta. Har mamaki take yi yadda Nana ba ta gajiya da abin da Haidar yake yi mata na hayyata irin ta su ta yara. Duk motsin da ya yi, ta san me yake nufi, zuwan Nana gidan ya yi ƙiba ya zama ƙato saboda yadda yake cin abinci. Ga kuma karatu da take koya masa, har da addu'oi. Nana ta ce "Shukura" karon farko da ta taɓa kiran sunanta, Shukura ta kalli Nana da mamakin tsaurin idon da ta yi. "Na san ba zan dauwwama ina kula da Haidar ba, amma dan Allah ina son ko yaya ki ajiye aƙidar boko, ki din ga jansa a jiki, kuma ki tsayawa azkar ɗin sa da kula da yi masa addu'a. Ke kanki ki ƙara ƙaimin addu'a sosai da sosai, ka na da ido ne kawai amma ba na ganin gari ba, abin da Allah ya so kawai shi muke gani" "To da na ce miki ba na addu'a ne, da za ki buɗe ƙazamin bakin ki, kina kiran sunana haka kai tsaye ni sarki ce?" Nana ta kalli Shukura ido cikin ido ta ce "Ni ki ke cewa mai ƙazamin baki! To kar ki yi abin da na ce, idan kin ƙi ji ai ba za ki ƙi gani ba" Babban abin da ya bawa Shukura mamaki, bai wuce yadda ta ji tamkar an saka mukulli an rufe mata baki ba, bayan sun haɗa ido da Nana ba, ta yi gum ta kasa cewa komai. Gaba ɗaya Nana ta manta da wani sharaɗi da Baba ya kafa mata ma, hatta batun auren Alhaji Zailani ma sai ta daina jin ya dame ta, mummunan mafarkin da ta yi da su Shukura ne kawai yake damunta. Sai kuma wata irin fargaba da ta rasa ko ta mece ce. Domin ragewa kanta damuwa, tare suka yi girkin dare da Jummai. Hajiya Amina ce ta ce "Nana ki zo ki tafi, na ga alamun hadari a garin nan, kuma tun da ba abin da ki ke yi" "A'a kar ki tafi" Haidar ya yi maganar yana riƙe rigar Nana. Nana ta kalle shi da murmushi a fuskarta ta ce "Idan na zauna zaka goya ni?" "Eh zan goya ki, ki yi bacci" ya yi maganar cike da shirirtar su ta yara. Da ƙyar a ka yi masa wayo, Hajiya Amina ta ɗauke shi, Nana har za ta fita, Jummai ta biyo ta da kular abinci ta ce "Dan Allah Nana ki ajiyewa masu gadi, na san yanzu su na can waje shan wannan shayin nasu na ibada, ba za su dawo ba sai cikin dare. ki ɗan tura ɗakinsu ki ajiye musu, idan ba su san an ajiye ba, karnuka ne suke zubar musu. Jiya da na ajiye musu a waje ba su sani ba, su ka kwance karnuka, aikuwa su na sako su, suka je in da aka ajiye abincin suka kifar, suka hau ci" Nana ta ɗan yi Jimm sannan ta karɓa ta fita. Kamar yadda Jummai ta faɗa kuwa, Nana tun kafin ta ƙarasa bakin gate ɗin, take jiyo hayaniyar buzayen a ƙofar gida, alamun duk su na waje a ƙarƙashin bishiyar da suke zama da yamma su sha shayi, su yi wasan takobuna. Amma duk da haka sai ta tsaya a ƙofar ɗakin nasu tana sallama, ko za ta ji an amsa, amma ta ji shiru. Sai ta ɗan tura ƙofar ɗakin, wani irin ƙamshin turare ya kawo wa hancinta ziyara. Ta zura flask ɗin abincin, ta yinƙura za ta tashi, kawai ta ji kukan Haidar a cikin ɗakin yana kiran sunanta. "Anty Nana, ki zo) Ba ta yi nazarin komai ba, balle tunanin ta baro Haidar ɗin a cikin gida ba, kawai sai ta ɗimauce ta hankaɗa ƙofar ɗakin ta shiga. Cak ya tsaya ya waiwayo ya kalli inda take tsaye. Daga shi sai dogon wando, hannunsa riƙe da mataji, yana taje dogon gashinsa da ya kwanta a kan kafaɗarsa zuwa dokin wuyansa. Gefensa butar shayi ce, take ta dahuwa a kan wuta, kuma da alama a cikin wutar aka zuba turaren wutar da yake tashi. Cikin matsanancin tashin hankali tsoro da razani, ta yi yinƙurin juyawa ta fita, amma ƙofar ɗakin da tagogi suka kulle, sautin wata irin guguwa ya karaɗe ɗakin. A take ya rikiɗe daga kamaninsa zuwa wannan tsohon mai kama da Ƙaisar, ya bayyana cikin suffa mai matuƙar ban tsoro, ya buɗe ƙaton bakinsa mai kama da bakin tsohuwar rijiya, ya fara fito da wata irin wuta Jawur tana wani irin hayaƙi, lamar gobarar tankar mai. Iya ƙarfinta ta dafe kanta, ta ƙwala ihu ta faɗi a gurin sumammiya. Jin ihunta ya sanya ya sake waiwayawa ya kalle ta, ya ganta a ƙasa ba ta ko motsi. Ya ƙarewa ɗakin kallo domin ya ga abin da ya razanata amma bai gani ba. Ya mayar da hankali ya ƙarasa taje gashinsa, ya tufke abinsa, ya zira rigarsa, ya shafa turare sannan ya kawo rawaninsa ya naɗa. Ya zauna a gaban shayinsa, ya fara tsiyayowa yana kurɓa a hankali tamkar shikaɗai ne a cikin ɗakin babu wata halitta kuma. Gidansu Nana tun da aka yi sallar magariba, Nasiru ya shigo gida yake tambayar ko Nana ta dawo. Suwaiba ta ce "wai kai Nasiru Nanan nan uwarka ce ne?" "Ban sani ba, idan ma uwar ta wa ce ina ruwan ki?" Cikin hasala ta ce "Idan na kama ka wallahi sai na gwara kanka" "Ba ki da wannan ƙarfin wallahi" ya yi maganar yana fita. Ya zauna a ƙofar gida yana kallon hanya, amma babu Nana babu alamar ta. Tsoro ne ya fara kama shi, kar ya je ko ta sake ɓata aljanun nata sun kai ta wani gurin. Yana zaune ya hango Baba ya nufo gida, hannunsa riƙe da manyan ledoji. Nasiru ya tashi ya karɓo masa kayan suka shiga gida. Su na shiga Nana ya fara tambayar Mama, amma ta ce ba ta dawo ba. A take hankalin Baba ya tashi, ya fara tunanin ko dai ta gudun ne? Sai a lokacin ya fara binciken ina ne gidan da Nana take aiki, tun da take zuwa bai taɓa bibiyar ina take zuwa aikin ba. Gaddafi baya nan, dan haka ya ɗauki Nasiru, suka fita neman Nana. Gurin ƙarfe tara na dare, Gaddafi ya dawo gida, ya shigo cikin gida zai wanke kayansa, yana neman Nasiru zai aike shi. Suwaiba ta gaya masa halin da ake ciki. Ya yi saroro ya ce "Yanzu har ƙarafe tara ba a san inda take ba? Kuma babu wanda ya san gidan aikin nata?" Jamila ta ce "Ni dai ta taɓa kwatanta mini, can wajen quarters ɗin markaz ne, wai gidan Alhaji Zailani" "Sako hijjabin ki mu je, mu duba" Mama ta ce "Ku je ina? Babu inda za ta je" Ya haɗe rai ya kalli Jamila ya ce "Ba magana nake yi miki ba, sai na taka wuyanki tukuna?" Ba Jamila ba ita kanta Mama sai tsuke bakinta ta yi, dan iya ashariyar Gaddafi ta ishe su. Sam ba su sha wahalar gano gidan ba, kasancewar Alhaji Zailani sanannen mutum, saboda yawan kyautar da yake yi da taimakon al'umma. A tsatstsaye suka tarar da mutane a ƙofar gidan, buzaye sai magana suke yi da yaren su. Kai tsaye Gaddafi ya kutsa suka shiga cikin gidan, mutane ne a tsaye a ƙofar ɗakin masu gadi, ga matar gidan a tsaye fuskarta ɗauke da damuwa. Gaddafi ya nufe ta, suka gaisa ya ce "Dan Allah ni yayan yarinyar da take yi muku aiki ne, Nana tun da ta fita tun safe bamu ganta ba, shi ne muka zo nan ko ta zo?" Hajiya Amina ta ce "Alhamdilillah mu na ta tunanin yadda za a yi, tun bayan la'asar muka yi sallama, ta tafi gida. yanzun nan yarona ya shigo yana gaya mini wai masu gadi sun ganta a ɗakinsu a sume, su suna waje, mutum ɗaya suka bari a ɗakin, shi kuma ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa, ya ƙi magana an rasa wanda zai taɓa ta ma. Yanzu nake tunanin ya za a yi a samo wani daga gidansu, dan ni ban san gidansu ba" Gaddafi ya ce "Ɗakin masu gadi kuma?" Ya juya ya nufi ɗakin. Nana na sume a tsakar ɗakin, gefe guda shi kuma yana zaune yana kaɗa ƙafafuwan sa, tamkar ba ya jin hayaniyar da ake yi. Gaddafi ya nufi Nana da sauri, ya ɗago ta, yatsun hannunta da na ƙafarta duk sun ƙandare kamar wadda ta daɗe da mutuwa, ga jikinta sanyi ƙalau. Ya ɗaga kai ya kalli Buzun nan da duk abin da ake yi, sabgar gabansa kawai yake yi, ya kalli Nana. Duk da ba shiri suke yi da ita ba, amma ya san Nana ba ta cikin jerin yara marasa ji, amma me ya kawo ta ɗakin masu gadi?. Hajiya Amina ce ta saka Yusuf ya ɗauki su Gaddafi ya tafi kai su gida. Cikin damuwa Habu yake dubansa ya ce "Buzu, ya aka yi yarinyar nan ta shigo ɗakinmu, me ya same ta? Me yasa kuma ba ka kira wani daga cikinmu ba?" Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Habu, a dole Habu ya ja bakinsa ya tsuke, duk da tarin tambayoyin da suke bakinsa. Cike da takaici, da matsananciyar tsana da damuwa, Baba yake kallon Nana yake maimaita a ɗakin masu gadi ka gano Nana?" "Idan an yi magana a ce aljanu ne suka hanata aure, ga haƙiƙanin abin da ya hanata aure nan ai" Mama ta din ga faɗar maganganu. Jamila ta ce "Mama ba lallai abin da ki ke tunani ba ne ba, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya" "Eh ban sani ba sai yanzu da ki ke gaya mini, rashin lafiya ne za a ganta a ɗakin masu gadi da wani?" "To ai an ce mahaukaci ne, har fa muka taho yana kallon dandazon mutane, bai yi magana ba, kuma bai fito ba" cewar Jamila, dan ta ƙi yarda zuciyarta ta bata wani mugun abin Nana take aikatawa. Kawai Baba ya tafi ɗaki, Mama ta bishi tana faɗin "Yanzu baban Jamila, baka gudun a zo a ji kunya? Wallahi tun da ta fara haka, ko an yi auren nan ba za ta zauna ba, kunyata ka za ta yi, tun da ta furta maka ba ta son auren nan, take ta wannan iskancin. Maza nawa ta ce ba ta so? ko dai ka san abin yi ko kuma abin da za ta yi a gaba sai ya fi na yanzu muni" Wata irin tafasa zuciyar Baba ta din ga yi, tafasar da tun da yake bai taɓa jin zuciyarsa ta yi ba, wata irin matsananciyar tsanar Nana ta mamaye zuciyarsa. Kamar mahaukaci haka ya fito fiuu ya yi waje. Ayshercool 08081012143 25 Ko da Baba ya fita Gaddafi ya nemo, a gurin masu shayi. Gaddafi ya ce "lafiya kuwa?" "Ofishin 'yan bijilanti zaka raka ni" "Amma a daren nan? Me ya faru?" "Mu je za ka gani" Gaddafi ya bi Baba zuwa gurin 'yan bijilanti. Baba ya shigar da ƙorafi, a kan zargin yin lalata da yarinyar sa. Gaddafi ya ce "Baba, babu tabbacin abin da ka ke faɗa fa?" "Babu tabbaci, aka same ta a ɗaki tare da shi sama da awanni?" Gaddafi ya ce "Amma ai ka san ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba" "Ka rufe mini baki Gaddafi" Gaddafi ya yi shiru, 'yan bijilanti suka bayar da mutum biyu, tare da Gaddafi aka tafi taho da Buzu. Hankalin Habu ya yi mummunan tashi, ganin wai an zo a tafi da ɗan uwansu gurin hukuma. Cikin damuwa ya ce "Wallahi ina da tabbacin babu abin da ya yi mata, ba shi da cikakkiyar lafiya ƙwaƙwalwa ne, amma ba wani abin ya yi mata ba, ai mutane sun ga a yadda muka tarar da su" Jami'in bijilanti ya ce "To ka ɗaukko takardar shaidar ba shi da hankalin, ka haɗo da ita mu tafi, ko ce maka aka yi mahaukaci ba zai iya wani abun ba" sauran buzayen ma duk hankalinsu a tashe. Haka aka tasa Buzu da Habu, da wasu daga cikin buzayen, suka tafi ofishin 'yan bijilanti. Shugaban gurin ya ce "Waye daga cikin su, aka tarar da su a ɗakin? Ina kuma ita yarinyar?" Baba ya ce "Tana gida a sume" "A sume kuma? Shekararta nawa?" "Shekara ashirin da ɗaya" "Ikon Allah, to waye a cikin su?" Gaddafi ya nuna Buzu. "Kai malam ya aka yi aka tarar da kai daga kai ita a ɗaki, tsawon awanni, sauke rawanin nan na fuskarka ina magana kana kallona" Habu ya ce "Yallaɓai ba shi da cikakkiyar lafiya fa, wallahi taɓin hankali ne da shi, ina da tabbacin babu abin da ya haɗa shi da yarinyar nan" Sule ya ce "Ba ma sa shiri da ita, wallahi rashin fahimta aka samu, na ga kwanon abinci a ɗakin, ina kyautata zaton ma abinci ta kai mana, akwai dai abin da ya faru tabbas" "Ba da ku nake magana ba, ka buɗe baki ka yi mana bayani, ko kurma ne?" Shugaban bijilanti ya yi maganar yana kallon Buzu. Amma bai ko motsa ba, balle ya yi magana. Ya sake tsuke fuska ya ce "Sauke rawanin nan kafin na saka a sauke maka shi yanzun nan, ka ƙunshe fuska kamar ɗan taliban" ƙura masa ido ya yi bai yi magana ba. Habu ya ce "Ka cire rawanin dan Allah, ka yi maganar abin da ya faru" Sule ne ya kai hannu zai sauke masa rawanin, amma ya riƙe masa hannu. "Dattijo, alamu sun nuna fa mutumin nan da gaske mahaukaci ne" Baba ya ce "Wallahi ko dawanau ce a kansa sai an bi mini hakkina, dama 'yan kwanakin nan shi ne yake hure mata kunne, sai ta kai bayan magariba a waje ba ta dawo ba. Ta ƙi aure fafur kowa ya zo ba ta so" "To kai Baba ya ka ke so a yi? Kana gani ya ƙi magana, ita yarinyar ba ku zo da ita ba, ni wannan case a bari gobe in Allah ya kaimu ku tafi gurin 'yan sanda". Baba ya ce "Duk fa wata shaida da ake nema, ta tabatta tun da abin da suke yi kenan, sai ya aure ta ya je su ƙarata" gaba ɗaya suka kalli Baba. Cikin tashin hankali Habu ya ce "Dan Allah dattijo ka yi haƙuri, wallahi ba su saba yin komai ba, wannan karon ma rashin fahimta ne, Nana mutuniyar kirki ce, shi kuma ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, dan Allah ka yi haƙuri" "Wallahi ba zan haƙura ba, daga nan har kotun ƙoli mu je, a karɓa mini hakkina na ci mini mutunci ta hanyar yin lalata da 'ya ta, ana daf da ɗaura mata aure" Gaddafi dai ya yi shiru yana kallon ikon Allah, bai ta taɓa tunanin Baba zai ɗauki irin wannan matakin ba. "Dan Allah ka yi haƙuri, ka ga nan ba ƙasarmu ba ce ba, idan aka kai mu gaban shari'a wahalar da mu za a yi, dan Allah ka yi haƙuri" Sule ya yi maganar cikin magiya. Baba ya fututtuke ya din ga bala'i, buzayen nan su na ba shi haƙuri. "Payer la dot" ya furta cikin harshen faransanci yana kallon Habu. Habu ya waro ido, shi ma ya juye harshe, suka koma magana da french. Jiki a sanyaye Habu ya kalli Baba ya ce "Nawa ne sadakin?" Gaddafi ya ce "Baba wai da gaske aura masan ita za ka yi?" "Eh mana, tun da haka ta zaɓa. Ai wallahi ba za ta zubar mini mutunci a idon duniya ba, dan na san tun da Rabi ta san maganar nan babu wanda ba zai ji a ciki da wajen unguwar nan ba, har a dangi sai ta yi ta yamaɗiɗi, tun da haka ta zaɓa ta samu" Baba ya mayar da idonsa kan Habu ya ce "Ko ma nawa ne, ku bayar da sadaki da safe ya zo ya ɗauke ta". Habu ya sake kallon Buzu, cike da damuwa ko zai canza magana, amma ya ga babu alamar hakan. Hatta 'yan bijilantin, sai da su ka ba shi haƙuri, da rarrashi amma fafur Baba ya ƙi yarda kamar wanda ake ƙara zugawa. Habu ya ce kuɗin hannunsa ba su da yawa, bari ya kira waya a kawo kuɗi. Shugaban bijilanti ya ce ba za ɗaura auren nan a ofishin bijilanti ba, sai dai a tafi gidan mai unguwa, a yi a gaban jagororin unguwa. Haka kuwa a ka yi, abin da Baba bai sani ba, da kansa ya ƙara tagayyara Nana, da yayata maganar. Naira dubu ɗari biyu Habu ya bayar, a matsayin sadakin auren Nana Asma'u ƙarfe sha biyu saura na dare. Gaddafi dai Baba ya ƙure masa mamaki, duk da ya san har da ziga a cikin lamarin na Baba. Sai dai kuma Gaddafi ya yi mamakin yadda buzaye, masu gadi suka iya biyan har Naira dubu ɗari biyu a take matsayin sadaki. Nawa ake ba su kuɗin gadin da har su ka ci suka tayar da kan biyan wannan kuɗin haka?. Can gida kuwa Nasiru ne yake ta tattaɓa Nana cikin tsoro, saboda sanyin da jikinta ya yi, kamar gawa. Sai can wajen ƙarfe goma na dare ta farka. Ta saka Nasiru ya kawo mata ruwa ƙofar ɗaki. Da rarrafe ta fito bakin ƙofar ta yi alwala. Ko yinƙurawa ba ta iya yi balle ta tashi, saboda wani irin jiri da take yi. Da jikin kaya ta jingina daga zaune ta yi salla. Ta idar ta sake kwanciya. Nasiru ya ce "Nana ba za ki ci abinci ba? Ga awara na sayo miki mai zafi" amma ya ji shiru. Ya duba sai ya ga ta koma yadda take da farko, hannunta zuwa ƙafafuwan ta duk sun ƙandare sun lanƙwashe. Sha biyu da rabi Baba suka nufo gida, Gaddafi ya ce "Amma Baba ba a yi ganganci ba kuwa? Kawai ka aura mata mutunen da baka san ma wani iri ba ne ba, dubu ɗari biyu fa suka bayar na sadaki ba ka tunanin ma ko wasu marasa gaskiyar ne?" "Gaddafi wannan abin da na yi shi ne kawai maganin abin da yarinyar nan take aikatawa. Sau nawa ana yinƙurin aurenta tana ƙi? Mutumin nan da ya fito fa cewa ta yi za ta gudu, ko kuma ta kashe kanta a kan auren, amma ta san ta je ɗaki gurin namiji. Wannan ne kawai hanyar da zan bi na aurar da ita. Muddin za a din ga saka lokaci ba za ta taɓa bari a yi ba". Gaddafi ya numfasa ya ce "Haka ne, amma ba na tunanin za ta bi maza ko makamancin haka." "Ba a shaidar ɗan yau Gaddafi. Allah ya zaunar da ita lafiya" Gaddafi yana son sake yin magana, amma ya fasa ya yi shiru. Mama tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, haka ta ji bayan da Baba ya yi mata bayanin abin da ya faru. "Wallahi ka yi dabara baban Jamila, wallahi da haka za ta ci gaba da zubar mana da mutunci a idon duniya, kuma auren ba za ta yi shi ba, duk wanda ya zo haka za ta ci gaba da korarsa. Kuma shi kansa Alhajin idan ya ji abin da ya faru ba zai yarda ya aure ta ba, ba ma ita kaɗai ba, duk wanda ya ji maganar nan ba zai yadda ya aure ta ba, amma tun da aka yi haka ka ga an yi maganin kowa ma. Kuma asiri ya rufu, tun da ta yi iƙrarin kashe kanta, ko guduwa muddin aka yi mata wannan auren". "Ai yanzu sai ta yi duk abin da ta ga dama, na yi wa tufkar hanci. Har Gaddafi yana wani cewa ba za ta aikata ba, ba zata aika ta ba uban me ya kaita ɗakin masu gadi? Ƙila ma Allah ne ya tashi tona mata asiri hakan ta faru" Mama ta ce "To Allah dai ya kyauta" Jamila kuwa jikinta ya yi sanyi sosai, sam ba ta taɓa tunanin Baba zai ɗauki wannan matakin ba. A yanayin yadda suka tarar da Nana, bai yi kama da wadda ta aikata wani rashin gaskiya ba. **** Cikin matsanancin ɓacin rai sule yake magana, "Habu yanzu da ka yarda aka yi wannan auren ya zamu yi da su gaba ɗaya?" Habu ya ce "Amma ai ka na ji, da kansa ya ce a biya sadakin ko?" "A'a ni ya za ayi na sani, tun da ba iya faransanci na yi ba, kuma da ya ce ka biya masa sadakin sai ka biye masa? Mutumin da ba hankali ne da shi ba, kai yanzu idan aka saka maka takobi a wuya, za ka iya nuna danginsa ko ahalinsa ne? Daga taimako sai jajubo mana wahala? Aure ai ɗawainiya ne, shekarata nawa a Nigeria iyalina su na can sahara, ban kawo su nan ba, yanzu ya ka ke so mu yi?" Habu ya kwantar da murya ya ce "Dan Allah Souley ka yi haƙuri, duk ba abin ɗaga hankali ba ne ba, idan aka samo wani gidan gadin, sai ya fara aikin gafin kafin a san abin yi" Tamkar ya gaurawa Habu mari ya ce "A haka zai yi gadin? Mutumin da sai ya yi sati bai ce uffan ba, aikin gadi fa ba buɗewa da rufe ƙofa ba ne kawai" "Ai ba hauka yake tuburan ba, kuma ko a nan ai mu na tafiya mu bar shi, kuma ya yi gadin, dan Allah ka yi haƙuri ka daina ɗaga muryar nan, zamu san abin yi da yardar Allah" "Ni wallahi har mamaki ka ke bani Habou, daga tsintar mutum sai wahala ka ke da shi, kamar wani tsohonka, na ga yadda za ayi ai da wannan badaƙalar" Habu ya dafa kafaɗar Sule ya yi murmushi ya ce "Babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah, kuma Allah ya na gani taimako muka yi, ba zamu wulaƙanta ba". Da ƙyar Habu ya samu ya shawo kan Sule. ***** Nana ba ta sake tashi ba, sai washegari ƙarfe bakwai na safe, shi ma Nasiru ne ya tashe ta, kamar jiya a bakin ƙofar ɗakin su ta yi alwala, ta yi sallar asuba a zaune. Yana zaune ta idar, tana idarwa ya ce "Nana kar ki kwanta, ga kokona ki sha ki daina wannan baccin, jikin ki fa sanyi yake yi" Ta girgiza kai ta ce "Na ƙoshi Nasiru, jikina babu ƙwari nima ji nake kamar mutuwa zan yi" Da sauri ya ce "Ba mutuwa za ki yi ba, yunwa ki ke ji, ki sha kaɗan" ganin yadda ya damu sosai da sosai, ya sanya ta karɓa ta sha kaɗan, ta ajiye ta fara ƙoƙarin kwanciya. Suwaiba ce ta shigo ɗakin, tare da rangaɗa guɗa ta ce "Amaryar tsakar dare, mai doki ya koma kuturi, ba a auri mai gida ba an auri mai gadi, to Allah ya sanya alkhairi". Nana ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Suwaiba, ta mayar da idonta kan Nasiru ta ce "Nasiru mafarki ne wai?" Ya girgiza kai ya ce "A'a a zahiri ne" "To me Suwaiba take cewa ne?" Cike da ƙuruciya ya ce "Wai jiya da daddare aka yi auren ki" "Aurena kuma? Kamar yaya?" Ya ce "Wallahi nima ban sani ba" Suwaiba ta cigaba da dariya, tana ɗaukar jakar kayan kwalliyar ta. Baba ne ya shigo ɗakin, ya tarar da Nana a zaune, ga Nasiru a gabanta da kofin koko. "Yauwwa kin tashi kenan? To ki buɗe kunnen ki da kyau, ki saurare ni" Ta zubawa Baba manyan idanunta, da suka yi kama da na Japanese sai dai nata manya ne. "Nana kin bani mamaki nesa ba kusa ba, duk iya ƙoƙarin da nake yi a kanku, amma ki ka zaɓi ki zubar mini da mutunci, nayi nayi kin ƙi yin aure, duk wanda ya zo sai kin kore shi kin ce ba kya so. Mutumin kirki ya fito da rufin asirinsa yana son ki da aure, amma ki ka buɗe baki ki ka iya gaya mini idan na aura miki shi, za ki kashe kanki ko ki gudu, ƙarshe kuma saboda abin kunya aka gano ki a ɗakin masu gadi Nana. Dama 'yan kwanakin nan ba na gane kanki, ba kya dawowa gidan nan sai dare. To kin kyauta sai dai nima na ɗauki matakin da ya dace, saboda mutuncina ba zai zube a idon duniya ba, na aurar da ke ga abokin lalacewar ta ki, su buzayen da ki ke zuwa ɗakinsu, idan da kun yi ba lada yanzu sai ku yi mai dalili" Jin Nana ne ya ɗauke baki ɗaya, ta daina tantance komai, bakinta tamkar an saka mata sakata, jikinta ya ƙara wani irin sanyi, sannan ya yi mata nauyi, ta kasa motsa kowace gaɓa ta jikinta." Idonta kar a buɗe ko ƙiftawa ba ta yi, hawaye ya din ga zirarowa. Baba ya ƙarasa maganar, ba tare da Nana, ta iya gane me yake faɗa ba. Idanun Nasiru ya cika da hawaye saboda tausayin Nana. Duk da ƙanƙantar shekarunsa yana fuskantar wasu abubuwan, kuma ya san ba a haka ake yin aure ba. "Nana ki daina kuka" yayi maganar cikin matsananciyar damuwa, yana kallon fuskarta. Kawai ya ga ta nemi guri ta kwanta. Baba kuwa zuwa aka yi, aka ce ana sallama da shi. Ya fita sai ya tarar da Habu da wasu buzaye guda biyu. Ya wani haɗe rai yana muzurai ya ce "Kun zo ku tafi da itan ne ko kuwa?" Habu ya girgiza kai ya ce "A'a, zuwa muka yi mu nemi alfarma" "Ta me?" Ya faɗa yana ƙara tsuke fuska. "Muna son a bamu ko mako guda ne, mu samu gurin da za su zauna, kuma a sama masa ɗan wani abin yin, yanzu idan muka ɗauke ta, babu gurin da za mu ajiye ta" Baba ya ce "Mako guda kawai, idan ku ka ƙara fiye da haka, sai na kai ku ƙara gurin hukuma" Habu ya ce "Ba za a yi haka ba da yardar Allah, mun gode sosai" suka yi wa Baba sallama suka tafi. Habu ya kasa daina ta'ajibin abin da ya faru daren jiya. Yana mamakin yadda Baba ya iya ɗaukar 'yar sa ya aura musu, ba tare da sanin ma daga ina suka fito ba, kuma har a yanzu bai tanbayi daga ina suke ba, kuma su waye danginsu ba. *** Hajiya Amina ce a zaune, tana shan tea ta kalli Shukura ta ce "Kin ga haryanzu layin Nana ba ya shiga, ina son sanin halin da take ciki, wallahi jiya ban yi bacci ba" Shukura ta kalle ta ta ce "Ba ki yi bacci ba?" "Wallahi Shukura, hankalina a tashe yake gaba ɗaya, ban takamaiman abin da ya same ta ba" Yusuf ya yi sallama, ya shigo falon ya ce "Mummy, wai buzayen nan ne, suke son magana da ke" Ta ajiye kofin hannunta ta ce "Ka ce su shigo" Ya fita ba a jima ba, sai ga shi tare da Habu da kuma Sule. Suka zauna a ƙasa suka gaisheta ta amsa musu, cikin sakin fuska. Habu ya ce "Hajiya jiya fa da daddare, an zo tafiya da ɗan uwan nan namu, mahaifin Nana ya ƙi yarda, sai da aka ɗaura mata aure jiya da ɗan uwan nan namu" ba Mummy ba hatta Shukura sai da ta zaro ido. Mummy ta ce "Saboda me?" "Ya ce lalata suke yi, kuma wallahi ɗan uwan namu ma ba shi da cikakkiyar lafiya, ai kina ganinsa kullum a gefe shi ɗaya. Shi ne dai na zo na sanar miki, kar a yi abu ba ku sani ba" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, me yasa ba ku zo kun sanar da ni ba? Haka ake yi kawai sai a ɗaura wa mutum aure a kan abin da ba a tabattar da faruwarsa ba? Yarinyar nan nutsatstsiyar yarinya ce, akwai abin da ya faru ba na tunanin Nana za ta aikata wani abu irin haka. Yanzu to ya za ku yi can ƙasarku za ku kai ta ko kuma ya ya?" Habu ya girgiza kai ya ce "A'a, zamu samu gurin da za su zauna ne, kafin mu je gida a yi wa magabatan namu bayani" Cikin damuwa Hajiya Amina ta din ga nanata "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ikon Allah wannan wane irin abu ne haka? Matakin ya yi tsauri da yawa, ai sai a fara bincike tukuna a tabattar idan ma wani abun yake zargi" Shukura duk da ba wani shiri take da Nana ba, amma al'amarin ya daki zuciyarta, a yadda take ganin Nana ta yi kalar nutsuwa sosai da sosai, sam ba ta ji a ranta Nana za ta iya aikata abu makamancin haka ba. **** "Jamila" Nana ta furta da ƙyar, saboda yadda take jin tamkar an ɗora mata wani ƙaton dutse a kanta. "Na'am" "Da gaske Baba yake yi, an ɗaura mini aure, ko kuwa mafarki ne?" Jamila ta ɗan taɓe baki ta ce "Da gaske ne mana, zai yi miki ƙarya ne?" Ta sake cewa "Kuma da buzayen nan?" "Eh fa" "Waye a cikin su?" Jamila da ta fara ƙosawa da tambayoyin Nana ta ce "Ni fa ban sani ba, tun da ba taɓa zuwa na yi ba balle na san su. Ke ma Nana me ya yi miki zafi, da za ki je ɗakin masu gadi me ki ke yi a ciki? Dama ana iƙrarin kin ƙi yin aure, yanzu ga abin da ki ka ja wa kanki nan" Sanin ko ta yi bayani ba fita za ta yi ba, ya sanya ta jan bakinta ta tsuke. Ta ci gaba da sauke numfashi da ƙyar. Tiryan-tiryan ta shiga tuno abin da ya faru, sai dai tunaninta ya tsaya cak a daidai lokacin da ta ga wannan mutumin a cikin ɗakin, har ta razana ta ƙwala ihu. Cike da dana sani take raya, da lokacin da ta firgitan nan addu'a ta yi, da wata ƙila hakan ba ta faru ba. Ta ɗaga kai a hankali, ta ƙurawa ƙofar da Jamila ta fita ido. Wani irin huci haɗi da nishi ta din ga ji, ba tare da ta san daga ina yake fitowa ba. Wata irin narkekiyar macijiaya ce, ta fito daga cikin roofing ɗin ɗakin, tana tsartuwa ta yo kan Nana. Tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsi, kuma ta kasa magana kawai ta zubawa sarautar Allah ido. Ta ci gaba da nufo ta tana tsartuwa, sai kuma Nana ta ga macijiyar ta ƙame a guri guda, tana ta wutsul-wutsul tana fasa kai, tana neman hanyar guduwa. Wani dogon hannu ta ga an zuro ta taga, an danƙi kan macijiyar, an janye ta, sai da aka janye ta, sannan Nana ta razana ta iya tashi zaune tana maimaita "Innalillahi wa innalillahi raji'un" Tagar ɗakin ta kalla, ta ga ƙaisar a tsaye, ya tattare macijiyar, ya zura ta a cikin wata 'yar mitsitsiyar kwalba. Har yanzu hannunsa ɗaya da rauni. Ya dubi Nana ya ce "Wannan ma 'yar aike ce, aka kuma aikota jininki ake so ko ta halin ƙaƙa, kuma 'yar uwakki aka bawa abin da ta zo ta ajiye a ɗakin nan, da zai bayar da damar samo jinin naki. Sai dai waccan jakar ce ta hana macijiyar ƙarasowa inda ki ke" ya ƙarasa maganar yana nuna wa Nana, jakar da sarkin baka ya bata. "Duk ba wannan ce ma ta saka na zo da kaina gurin ki, rana tsaka ba. Ina mai tabattar miki da wannan auren da mahaifin ki ya yi miki, ya jefa rayuwar ki a cikin sabon babin ƙaddara da ƙalubalen rayuwa, ba kuma ke kaɗai ya jefa ba har da ni. Sai dai na yi alwashin ba zamu wahala muka ɗai ba, sai na yi masa mafi munin azabtarwa a kansa da kuma iyalansa, duk wani farinciki da yake tunanin samu a duniyar nan, sai ya yi hannun riga da shi, ke kuma ki shirya tsaf dan wanda aka aura miki ko dai ya yi ajalina ko na yi ajalinsa! Ayshercool 08081012143 26 Jin abin Nana ta din ga yi tamkar tunani, kuma tamkar mafarki, domin da ta tashi zaune, ba ta ga ƙaisar ɗin ba, kuma ba ta ga macijiyar ba. Muryar Yaya Atine ta jiyo a tsakar gida tana faɗin "Wanda ya ƙi ji ai ba ya ƙi gani ba, sam ban ga laifin Isa ba abin da ya yi, wannan hukuncin shi ne ya dace da ita, babu irin rarrashi da ban bakin da ba a yi wa yarinyar nan, amma kowa ya zo sai ta yi burus fafur ta ƙi yarda da maganar aure, hankalinta ba ya kwanciya sai maganar ta lalace, idan wani abin da aljan wani abin tsagwaron iskanci ne kawai, dan a iya adadin yawon nema mata magani da aka yi, ai ya ci a ce ta warke" Mama kuwa tamkar ta taka rawa dan murna, duk yadda take ƙoƙarin ɓoyewa, sai da farincikin ta ya kasa ɓuya. Ta yi caraf da maganar Yaya Atine ta ce "To ai yanzu an yi mai ɗungurugum, haihuwa da hanji, ko in ce mai doki ya koma kuturi, tun da babban mutum ne mai rufin asiri ya fito yana sonta, amma fafur ta ƙi, har tana iƙirarin za ta gudu, ko ta kashe kanta, ashe ita gurin wasu take zuwa lalacewa" saurin katse maganar ta yi, bayan da suka yi ido huɗu da Nana a tsaye a ƙofar ɗakin su. "Rabi, duk abin da za ki ce na yi, ba zai dame ni ba, dan na riga na saba da duk wani ƙazafi da cin mutunci da ki ke yi mini, har ƙazafin maita kin yi mini duk abi dame ni ba, kuskure ma fi girma da za ki yi shi ne, yi mini ƙazafin zina, babu wanda ya kama ni ra'ayil aini, ina yi kar ki ƙara danganta ni da zina" Jamila ta zaburo ta ce "Nana, Maman ki ke gaya wa haka? Ki ke kiran sunanta gatsal haka?" "Ba ita kaɗai ba, kafataninku nake yi wa kashedi, kar wanda ya sake gangancin danganta ni da zina, amma idan kun ƙi ji ba za ku ƙi gani ba" Ta nufi banɗaki, tana jin Yaya Atine tana kiran ta, amma ta yi mata banza, ta shiga ta yi alwala ta koma ɗaki ta tayar da sallar azahar. Tana zaune a bigiren da ta yi salla, ta kasa addu'a ko lazumin ta kasa, haka zalika ta kasa kukan ma, ta rasa me ma za ta ce. Kawai ta haɗa kanta da gwiwarta ta yi shiru. Har yanzu ji take tamkar kawai barazana ake yi mata, amma ba da gaske ne wai an yi mata aure ba. Ga yunwa tana ji, ga jikinta a mace babu ƙwari, ga damuwa gaba ɗaya ji take kamar ma ba ita ba ce ba. Can ɓangaren Hajiya Amina kasa zaune ta yi ta kasa tsaye, ta din ga mita tana faɗa, har da cewa sai ta kai Baban Nana Human rights. Shukura ta ce "Mummy ki na da ɗorawa kai, mutumin ya yi wa 'yar sa aure, kuma ki ce za ki kai shi human rights?" "To Shukura na rasa abun da zan yi zuciyata ta yi mini sanyi ne, gaba ɗaya tausayin yarinyar nake ji. Ba na tunanin an tsaya an ji ta bakin ta. Ke ba kya gurin lokacin da aka kira ni, aka ce an ganta a ɗakin masu gadi. Gaba ɗaya ba ta hayyacinta, ba ki ga a yadda aka fito da ita ba. Kuma shi ma a buzayen wannan wanda ba ya maganar ne fa, har aka yi ta balahirar nan aka gama bai yi magana ba. Ke wait kamar fa yarinyar nan ita ma tana da mental issues" Shukura ta ce "Au ke sai yanzu ki ka gane? Ni na daɗe da fuskantar hakan, shi yasa wasu lokutan ba na sakewa da ita, ko na ganta da Haidar" Cike da damuwa ta sake cewa kuma babanta ya san mutumin da ya aura matan, yana da mental issues?" "Mummy ina zan sani ina nan?" "Oh my God" Mummy ta faɗa tana zama. Ta ci gaba da cewa "Wannan mutanen da ba sa iya zama guri ɗaya, yanzu suna nan anjima su na can, yanzu haka za su yi ta yawo da ita, ko kuma can ƙasar ta su zai kaita oho. Dan Allah Shukura, ki ɗan haɗo ɗan abin da ya sauwwaƙa mu haɗa a  kai mata, ko ma mene ne ya same ta, duk a dalilin mu ne" Shukura ta ce "A'a ba a dalilinmu ba ne, ki daina ɗora mana laifi Mummy, zan haɗa abin da ya samu, ni yadda za mu yi da Haidar kawai nake ji wallahi, dan yadda yake ƙaunar ta ba ya ƙaunata haka. Inda Allah zai taimake ni babansa cikin satin nan zai dawo, da ban san yadda zan yi ba" Mummy ta yi murmushi ta ce "Ina jin sa fa tun safe yake bin Jummai, yana ce mata ina Anty. Tana tsokanarsa tana cewa antynta ce ba ta sa ba, har da kukansa ya zo yana gaya mini, in cewa Jummai Anty Nanansa ce ba ta ta ba" "Ai sun shaƙu sosai ne, zan ga abin da zan yi a kai". Shukura ta yi maganar tana ɗaukar remote. **** Cikin ƙanƙanin lokaci labarin aure Nana, ya karaɗe dangi da unguwa baki ɗaya, Mama na ta nanata ai cikin dare aka ɗaura auren a gidan mai unguwa, jin hakan ya sanya sai mutane su tambayi ba'asin dalilin yin hakan, saboda ba abu ne da aka saba da shi ba, mussaman auren budurwa, a ce an ɗaura shi cikin dare kamar yaƙi. Sai Mama ta ce "Hmm ku dai a yi sha'ani, labarin ne babu daɗin ji" Yaya Atine ce ta bi Nana da kwanon abinci har ɗaki ta tsaya a kanta ta ce "Ki tashi ki saka wani abu a cikin ki, kina ta kwanciya kin wuni ba ki ci komai ba" Nana ta yi mata banza ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi ba. A hasale Yaya Atine ta ce "Shikkenan kin yi wa kanki" Nasiru kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, idan ya fita ya zagaya sai ya dawo ya leƙa Nana, har aka yi sallar magariba salla ce kawai take fito da Nana, babu wanda ta tankawa a gidan. Saura ƙiris Alhaji Zailani ya furzo abincin da yake ci, bayan da Hajiya Amina ta kammala yi masa bayanin abin da ya faru. Ji ya yi tamkar ta zuba masa wuta a zuciyarsa. Wannan shi ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa. A zuciyarsa ya ce amma wannan an yi la'anannen tsoho, mu gama yarjejeniyar zai ba ni aurenta burina na daf da cika, kawai sai ya aurawa wani, saboda hauka. A fili kuwa cikin ƙwarewa da iya duniyanci, ya nuna halin ko in kula ya ce Allah ya kyauta. Bayan ya kammala cin abinci ya cewa Hajiya Amina ta zauna a sashenta kawai, zai ɗan fita. "Amma na ga yaushe ka dawo, da har zaka sake fita koma mene ne ka bari sai da safe mana?" "Yaushe ki ka fara kafa mini dokoki a gidana?" Yayi maganar yana tsare ga ido, babu shiri ta ce "Allah ya baka haƙuri" Kamar zai haukace, haka ya ɗauki mota ya fita, yana tafe yana ta ɗure-ɗuren ashariya a cikin mota, yana zage-zage. Gidan malam Gambo ya nufa, gurin sha ɗaya na dare, haka ya kira shi a waya ya fito. "Alhajin Allah, lafiya kuwa ka zo a daren nan, ba yau ka dawo daga tafiya ba?" Cikin damuwa ya ce "Babu lafiya, dan kuwa an yanka ta tashi" "Too ikon Allah, me ya faru?" "Yarinyar nan, da za a ɗaura mana aure, babanta ya yarda zai bani aurenta, ina murna muradina zai cika, kawai yau na dawo na tarar wai ya aurawa ɗaya daga masu gadin gidana, saboda an ganta a ɗakinsu, wai ko yana zarginta ne oho masa, ni ko inda yake ban je ba, dan Allah meye abin yi? Ni fa ina iya saka a kashe ko ma uban wa aka aura mata, muddin muradina zai cika" Malam Gambo ya girgiza kai ya ce "A'a kar ka ja da zafi, amma tabbas aiki ya koma baya sosai. Ka bi komai a hankali kar ka yi garaje asirinka ya tonu. Ko da auren ko babu, muddin ka yi abin da na ce, buƙata za ta biya. Amma ka san ba ta yarda da kai ba ta da aure ba, babu lallai ta yarda da kai yanzu. Amma dai ka san abin yi ko kuma ku daidaita da wanda aka aura mata ɗin, ka biya shi ya sake ta." Ya shafi tumbinsa ya ce "Ni ina ma na san wanda aka aura mata a cikin nasu, shikenan dai sai ka ji ni. Amma tsaya wai babu wani abu da za ka yi mini da zai sanya yarinyar nan ta yarda?" Malam Gambo ya girgiza kai ya ce "Da da akwai, kafin ka tambaya ma zan gaya maka" Ya jinjina kai ya ce "Haka ne" ya juya ya nufi motarsa cikin matsananciyar damuwa. Wayewar gari, Nana ta tashi da wani irin azababben zazzaɓi, ta din ga jin tamkar ana ɓalla ƙasusuwanta, ta din ga tamkar an yage mata fata an cilla ta a cikin ƙanƙara, saboda azababben sanyin da take ji. Ko idanunta ba ta iya buɗewa. Nasiru dai bai gaza ba, ya zo yana tashin Nana, a kan ta tashi ta ci Abinci. A galabaice ta ce "Nasiru ka ƙyale ni ba zan ci ba, mutuwa zan yi na gaya maka" "A'a dan Allah ki daina faɗar haka, ba za ki mutu ba Nana, dan Allah ko shayin ki sha" "Kai ma jarababbe ɗan neman suna, ka ƙyale ta mana" Suwaiba ta yi masa maganar cikin tsawa. Bai kula ta ba ya je ya samu Baba ya gaya masa Nana ba ta da lafiya, amma Baba ya yi mursisi ya ce idan ta yi mushe, a yi masa magana ya yi mata sutura. Sosai Baba yake jin takaicin abin da Nana ta yi, wanda da tuni yana nan yana murna zai zama sirikin attajiri. Ya gama magana da Nasiru, sai ga motar Alhaji Zailani. Jiki na rawa Baba ya nufi motar, tun kan ya gama parking ɗin. Kallo ɗaya ya yi wa fuskar Alhaji Zailani ya sha jinin jikinsa. Ya sauke gilashin motar ya dubi Baba cike da takaici ya ce "Yanzu abin da ka yi mini ka kyauta a matsayin ka na dattijo? Cikin kame-kame Baba ya ce "Wallahi Alhaji ban yi hakan domin saɓa magana ta ba, babu yadda na iya ne, kuma da kunya a ce babban mutum kamar ka, ba zan iya cin amanar ka ba ne, shiyasa na hukunta ta dai-dai da abin da ta aikata. A ce ka na neman aurenta amma a ganta a wani guri da wanda yake ƙarƙshin ka, ai girman ka ya wuce haka, wallahi ba dan na ci amana na yi hakan ba, ya zama tamkar hukunci ne a gare ta" gaba ɗaya sai jikin Alhaji Zailani ya yi sanyi da wannan shiryayyun kalmomin na Baba. "Amma an tabattar da abin da ake zargin nata ne? An kama su ne?" "Eh to, ba na ce ba, nemanta aka yi aka rasa, aka gano ta a sume a ɗakin masu gadi dai" Alhaji Zailani ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce "Shikenan na gode" Baba ya ci gaba da ba shi haƙuri, bai saurari Baba ba, kawai ya ja motarsa ya tafi. Alhaji Zailani ya tara su Habu a harabar gidansa, yana ta bala'i a kan abin da aka ce masa ya faru a gidan, a kan ba zai lamunci haka ba, a din ga yi masa rashin ɗa'a a gida, idan ba su yi wasa ba duk sai ya kore su. Yana zaune a cikin ɗaki, yake jiyo baloƙoƙon da Alhaji Zailani yake yi, Sulei sai ba shi haƙuri yake yi. "A cikin ku, waye ne a kama tare da yarinyar?" Sule ya ce "Wallahi Alhaji ba wani abu suka yi ba, hasali ma shi ba shi da cikakkiyar lafiya ƙwaƙwalwa, yanzu haka yana bacci ne, wallahi ba wani abin suke yi ba, ko Habou?" Habu kawai ya jinjina kai. "Lallai ina son ganinsa, ba hauka ba ko a turu yake" suka jinjina masa kai. A hankali ya yinƙura ya tashi, ya nufi bakin taga, ya hango Alhaji Zailani ya nufi cikin gidan, yana baza jallabiya. Ya ɗan murza zobe hannunsa tare da jinjina kai, ya koma ya samu guri ya zauna. Sai da Baba ya ga Nana na neman mutuwa, sannan ya yadda a kaita Asibiti, ba ta ci ba ta sha, daba ɗaya ta zuge ta yi wuri-wuri, ko iya tsayuwa ba ta yi saboda jiri, ba ta iya gane komai. Tana kwance ana saka mata ruwa, ta ganta a libraryn Ƙaisar, ga hannunta ɗauke da ruwa. Yana zaune ya na rubutu. "Sannu ko" yayi maganar ba tare da ya kalle ta ba. "Idan ma kin kashe kanki, ƙaddara ta riga fata, dole ki tashi ki ƙwarara jikinki, ki ci abinci ki ware. Ko dai mu yi gaba da gaba da ƙalubalen da yake tunkaro mu, ko kuma ki amince na ɗauke ki baki ɗaya, idan ba haka ba ba zan iya cewa ga abin da zai faru ba" Nana ta ɗaga ido ta kalli inda yake zaune, ta yi masa shiru ba ta ce masa komai ba. Ya miƙe tsam ya rufe littafin, ya miƙa hannunsa can saman wani guri, ya ɗaukko wata kwalba, ya zo gabanta ya zauna, ya ƙura mata ido, take ta ji tamkar an zare mata kuzarinta. Ya watsa mata wani koren abu a fuska, babu shiri Nana ta yinƙura ta tashi zaune tana tari. Ummi ta gani a ɗakin da take a asibiti. "Zan sha ruwa" Nana furta a wahale. Aka kawo mata ruwa, ta sha sosai sannan ta koma ta kwanta. Sai da Nana ta kwana a asibiti sannan aka sallame ta, wata irin azababbiyar yunwa da ta sako ta gaba, haka ta din ga cin abinci. Sun koma gida babu daɗewa sai ga Hajiya Amina, tare da Haidar. Yana ganin Nana ya je ya maƙalƙale mata yana murna. Ita kanta Nana ta yi murnar ganin Hajiya Amina da Haidar. "Nana, duk da ni ba na zargin ki, kuma ba zan takura miki da tambayar jin abin da ya faru ba, amma ki yi haƙuri da abin da ya faru, amma idan ba kya son auren nan ki yi mini magana, a shigar da ƙara a hukumance a raba auren, kalli duk yadda ki ka rame" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Na gode sosai da sosai Hajiya, Allah ya saka da alkhairi ina fatan Allah ya sanya haka shi ne mafi alkhairi, ni ba auren ne damuwata ba, zargin da ake yi mini.. ta kasa ci gaba saboda yadda kuka ya ƙwace mata. Ta dafa bayan Nana ta din ga rarrashinta. Kaya ta kawowa Nana, har da bedsheets sabo da tsofaffi amma masu kyau, ga 'yan kayan kitchen da ta kawo mata, da Shukura ta bayar a kawo mata. Ta yi ta godiya, ta tashi za ta tafi, Nana ta ce za ta raka ta, ta ce "A'a ai ke yanzu matar aure ce, ki yi zaman ki Allah ya sanya alkhairi" ta ƙarasa maganar tana danƙawa Nana kuɗi a hannu. Maƙwabta na ta zuwa Allah ya sanya alkhairi, da biyu domin su ga halin da Nana take ciki, har da 'yan islamiyyar su, da tun da ta bar makarantar babu wanda ya bibiye ta, balle a ji dalilin daina zuwan ta. Baba sai kaiwa yake yi, yana komowa yana nanatawa Nana ta haɗa kayanta cif, ta fara shiri. Yanayin yadda take ganin duniya ta juya mata baya, ta ji ina ma ba a haife ta ba, kuma duk wannan abin babu wanda ya kira mahaifiyarta ya gaya mata halin da ake ciki. To me ye ma amfanin gaya mata, tun da ba wani abin za ta amfana miki ba, kuma kin san ba zuwa za ta yi ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita. Da daddare gari ya yi tsit, Nana tana ta juyayi da tunanin wa ma aka aura mata a cikin buzayen, tun da su na da yawa. Babu tsammanni bacci ya yi awon gaba da ita, sai dai ta din ga jin ta tamkar a zahiri ba mafarki ba. Da wata irin murya mara daɗin ji, cikin maɗaukakin sauti mai matuƙar razani da kiɗima zuciya ake yi mata magana. "Ko kin san wa ki ka aura? Mutumin da shi kansa bai tantance waye shi ba, bai san mene ne jinsa ba, mutum ne shi ko aljan. Rayuwa da shi na iya sadar da ke da ajalin ki. Lokaci ya yi da za ki biya abin da kakannin ki suka aikata, da kuma abin da ya faru a silar ki  ke ce tabbas ke za ki biya wannan bashin. Ki tsira da ranki ki bar gida, ki yi nesa da gida, ko kuma ki fuskanci rayuwa mafi muni da hatsari" A gigice Nana ta tashi, ta fita tsakar gida da gudu tana haki, jan burki ta yi duk da zuciyarta na raya mata ta zare sakata ta ruga da gudu. Wani irin zafi take ji da matsanancin tashin hankali, ji take kawai ta buɗe ƙofa ta fita shi ne za ta samu nutsuwa. Juyawa ta yi da nufin ta fice ta bar gidan, amma ta ji kamar ta na ƙwaƙƙwaran motsi, zuciyarta za ta yi bindiga saboda bugun da take yi. "Ki na ƙara ɗaga ƙafarki, zuciyar ki za ta tsaya da aiki. Sai da na gaya miki, babu irin kashedin da ban yi miki ba, ki ka yi kunnen uwar shegu da ni, wallahi da kin sake kin buɗe ƙofa kin fita, haukacewa za ki yi. Yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya" A wannan karon ta gane muryar ƙaisar ce, amma ta farkon ba ta san muryar waye ba. Zumbur ta tashi zaune, tana kallon ɗakinsu, a iya saninta dare ne ta kwanta tana bacci, amma yanzu ta ga azahar ce. Yaya Atine ta shigo ɗakin tana faɗin "Kin gama shure-shuren da ihun, kin ga dama kin tashi kenan? Wallahi tun wuri ki ajiye wannan haukan aljanun naki, ki kama kanki, ba kowa ne zai zauna kina masa wannan shirmen banzar ba, idan kin ga dama ki tashi ki wuce ki yi wanka ki zo ki ci abinci" Nana ba ta motsa ba, tana tunanin ko ta yi sallar asuba?. Ummi ta shigo ɗakin da jaka fuskarta ɗauke da mamaki ta ce "Nana" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta. "Kin ga yanzu daga fita ta, na haɗu da wasu buzaye, wai 'yan uwan mijin ki ne, suka ba ni wannan kayan wai a ba ki, sun ce , a ce ki yi haƙuri abin ya zo babu shiri, kuma ba su da isassun kuɗi. Kin ga dubu hamsin, wai a baki ki yi wani abin ga kuma kaya" Yaya Atine ta waro ido ta ce "Buzayen?" "Wallahi kuwa" "Kirawo Rabi maza a yi a gabanta" aka kirawo Mama, aka buɗe zip ɗin jakar. Danƙareriyar shadda bazin ce a farko, fara ƙal an yi mata aiki irin na buzaye, har da awarwaraye da ɗan kunne, da sarƙa. Kaya dai Atamfa set biyar, sai takalma guda biyu da turare har da na wuta. Ummi ta ce "To ke Nana ki na ta wani buntsire-buntsire da alama wannan za su kula da ke. Kalli a yadda aka yi auren fa, amma har suka yi miki wannan kayan haka." Ita kanta Mama abin ya ba ta mamaki ya tsaye mata a rai ta za ta Nana za ta tozarta fiye da haka. Ummi ta ce sai An yi wa Nana gyaran jiki an yi mata lalle da gyaran gashi, tun da har sun ƙoƙarta sun kawo wannan kayan. Da aka gaya wa Baba nuna wa ya yi ko a jikinsa, duk da cikin ransa ya ji daɗin kayan da suka kawo mata, damuwarsa kar ma a fara yi masa zancen kayan ɗaki. Dan sadakin ma naira dubu hamsin ya ware zai ba ta. **** A tsanake yake ƙare masa kallo, tun daga kansa, har zuwa kan yatsunsa da suke ɗauke da manyan zobunan azurfa. Duk da fuskarsa a rufe take, sai idanunsa kawai ake iya gani, yatsun hannunsa su ka fallasa asirin kalar farar fatarsa. "Ko za ka sauke rawanin naka mu yi magana?" A hankali ya juya ƙwayar idonsa, yana kallonsa amma bai yi magana ba. "Magana nake, ka sauke rawanin fuskarka mu yi magana" still bai sauke ba, kuma bai yi magana ba, sai ma yinƙurawa da ya yi, ya juya zai fita" cikin azama ya tashi ya sha gabansa ya ce "Ya mu na magana za ka tashi ka tafi?" "Me yasa ka kira ni?" Ya yi maganar yana tsare shi da ido. "Buƙata ce" "Ta me?" "Ina so ka gaya mini ko nawa ka ke buƙata, ka saki yarinyar nan Nana da babanta ya aura maka" Ya gyara tsayuwarsa sosai yana kallon cikin idanun Alhaji Zailani, ya ce "Je devrais divorcer?" Alhaji Zailani ya yi ƙuri da ido yana kallonsa, dan bai gane me ya ce ba. Ya taka a hankali ya je gaban Alhaji Zailani ya tsaya, sannan ya ce "Me yasa ka ke so na sake ta?" "Saboda na fi ka buƙatar ta" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ka ce ka fi ni buƙatar ta?" Kafin Alhaji Zailani ya ba shi amsa, kawai ya gansu a tsakiyar dokar daji. Ya saka hannu, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakyawar fuskarsa ta bayyana ya ce "Ka ce ka fini buƙtarta? Har ka manta da abin da na yi maka a wancan lokacin?, shi ne ka sake biyo ni da wannan maganar?" Ya saka hannunsa a wuyan Alhaji Zailani, wasu irin dogwayen farata suka tsiro a yatsunsa, a hankali kamaninsa suka gushe, fuskar wani tsoho tukuf ta bayyana. Ya ƙara tsananta shaƙe Alhaji Zailani ya ce "Ni na fika buƙatar ta, fansa ta zan ɗauka a kanta. Mallakina ce, fansa zan ɗauka, dan haka na fika buƙatar ta!! Jin numfashin sa ya yi, ya dawo iya ƙirjinsa, jini ya fara zubowa daga gurin da ya huda shi da faratansa. Ayshercool 08081012143 Page 27 "Wayyo Allah, Amina tashi Amina zai kashe ni" a razane Hajiya Amina ta tashi zaune tana waige-waige ta ce "Waye zai kashe ka?" "Haska mini wuyana jinina ya na zuba, duba mini da sauri" A sukwane cikin matsanancin razani, ta sauka daga kan gadon, ta kunna ƙwan lantarkin ɗakin. Alhaji Zailani na riƙe da wuyansa, ya haɗa uban gumi ta ko ina. Ta ƙarasa gabansa tana kallon wuyansa ta ce "To ai Alhaji ba komai a wuyanka" "Kin tabatta?" "Wallahi wuyanka babu komai, sauke hannun mu gani" ya sauke hannunsa a hankali. Ta ce "Shafa ka ji, babu komai a gurin fa" ya gyara zamansa yana ajiyar zuciya cike da razani, saboda yana jin shaƙar nan har a lokacin. "Mafarki kawai ka yi, ka yi addu'a ka kwanta" Ya ce "Ko ma ki kwanta kawai" ba ta matsa masa ba, ta gyara kwanciyarta ta kwanta. Shiru ya yi ya dafe kansa yana tunani, tabbas ya ƙuduri aniyar kiran wanda aka aura wa Nana, ya biya shi kuɗi ya sake ta, amma ya kasa tunawa ya kira shi ɗin sun yi maganar? Ko kuma sharrin mafarki ne kawai?. Tabbas ya ƙallafa rai a kan burin cikar muradinsa, dan haka ko da tsiya, ko da tsiya-tsiya sai ya yi tarayya da Nana burinsa ya cika. Bacci bai ɗauke shi ba, sai gefin sallar asuba. **** Ummi na ta shirya yara, tana ɗaukar musu kayan da za su yi amfani da shi, saboda gida za su tafi saboda wunin bikin Nana, dan a washegari za a kai ta gidanta, an samu da kyar Baba ya bayar da wani abu, a yi girki a yi mata wunin biki, shi ma sai da Yaya Atine ta saka baki, da Anty Saude 'yar autar su, ta haɗa da dubu hamsin ɗin da buzayen nan suka bayar, ta yi mata sayayya. Saleh ne ya faɗo gidan, yana ƙwala mata kira, kamar mara hankali. "Lafiya ka ke yi mini wannan kiran haka?" "Wai da gaske an ɗaura wa Nana aure?" Ummi ta ɗan taɓe baki ta ce "Eh, gobe ma za a kaita gidan mijinta" "Lallai ma, wato saboda an samu wanda ya fi ni kuɗi, shi yasa ta yi ta wulaƙanta ni?" "Ai Saleh na gode Allah ta wani fannin da ba ta aure ka ba, da na ji haushin ta, amma tun da ka iya kai Babanmu gurin 'yan sanda ba kunya babu tsoron Allah, na ce lallai ka riƙa idan aka yi auren sai abin da Allah ya yi" Ya sassauta murya ya ce "Wallahi Ummi ba a son raina ba, Hajiya ce ta dage sai an fasa an karɓo kuɗin nan, kuma na din ga ciwon cikin nan, ina mugwayen mafarkai, Hajiya ta ce dama an ce mata duk wanda zai aure ta mutuwa yake yi" Ummi ta ce "koma dai mene ne, ai yanzu ka rasa, kuma kai ka san babu inda za ka je neman aure a baka a arhar da Baba ya so baka Nana" ya zauna a tsakar gidan cike da dana sani, ya gama zamansa ya tafi ba tare da ta sake kula shi ba. ***** Kallonsa ta yi a lokacin da yake ƙoƙarin fita daga bedroom ɗin, ta tsuke fuska ta ce "Wai ina za ka je ne?" Ya kalle ta ya ce "Eh, da wuri zan fita ne, yakamata na je na duba Fadila kafin na fita" "A'a ka na azarɓaɓi dai yau ita ke da kai, jeka a sauka lafiya" Kamar wanda ya aikat laifi ya yi sororo ya ce "Haba ke kuwa? Haryanzu tana cikin jimamin mutuwar yaron nan, tun da ya rasu take fama da rashin lafiya, tana buƙatar a rarrashe ta, amma kin saka kishi a gaba ai yakamata ki tausaya mata" "Wai dan Allah a kanta aka fara mutuwar ɗa da ba za ta yi tawakalli ba? Ko ni ma ba gani da 'yar ba mara lafiya. Kullum na yi magana sai ka ce kana gurinta ka na rarrashinta, ka na lallaɓawa dai ka yi mata wani cikin, ku ƙarata" Ya ɗage kafaɗarsa ya ce "Eh haka ne maganar ki, dama yakamata a yi hakan, kuma mu haɗa da addu'a sai ki ga an dace" ya fice ya bar ta. Wani irin gululun takaici ya tsaye mata, kawai ta ja guntun tsaki. A gefen gado ya tarar da ita a zaune ta yi shiru. Sallamar da ya yi ne ya dawo da ita hayyacinta, ta amsa masa. Sannan ta ɗora da "Good morning Daddy" bai amsa ba ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, jakar makarantar Muhsin ce a gefenta, hannunta kuma littafin sa ne. Ya saka hannu ya zare littafin ya duba bangon littafin. Ya yi zanen mace a gaban allo, ya rubuta Anty Nana, duk da spelling ɗin bai fita ba, a ƙasa kuma ya zana wata ya rubuta mom sai kuma babansa. Jiki a sanyaye ya kalli Fadila da tuni idanunta suka cika da hawaye. "Haba babyna, anya Fadilana ce wannan ko dai an canza mini da wata? Ya kamata a ce mun yi tawakalli. Haryanzu ina jin raɗaɗin mutuwar boy, amma wallahi wannan yanayin da ki ke ciki ya fi ɗaga mini hankali, dan Allah ki kwantar da hankalinki ki yi haƙuri mu ci gaba da addu'a". Tamkar ya fama mata ciwon da yake cikin zuciyarta, ta ce"Daddy" "Na'am Fadila" "Ina addu'a, ina son yin tawakalli but am missing my son" ta yi maganar cikin sheshsheƙar kuka. Ya rungume ta a jikinsa, idanunsa na cika da hawaye, saboda tamkar bai taɓa haihuwa ba sai a kan Muhsin. "Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, kin ga yanzu idan ba ki kwantar da hankalinki ba, ta yaya zamu samu nutsuwar samo wani babyn?" Ya yi maganar da sigar wasa. Haka ya din ga rarrashinta, har ta ɗan nutsu, ya tattare kayan Muhsin, ya ce "Duk tattare kayansa zan yi na mayar site ɗina, tun da su suke ɗaga miki hankali ki ke kuka". Ba ta ce komai ba ta yi shiru. Ya dawo ya kwanta a jikinta ya ce "Yauwwa tun da na gama rarrashin ki, nima a rarrashe ni" a dole sai da ya saka ta dariya, dama hakan yake so. Hajiya sa'a ce ta yi sallama a falon, ta amsa mata da kyar tana cika tana batsewa. "Ke kuma lafiya ki ke ta huci haka? Ko ke da yaran ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a" "Ina fatuhun yake? Ganinsa nake son yi, Allah ya sa bai fita ba. "Yana can yana lalata" Cikin rashin fahimta hajiya Sa'a ta ce "Lalata kamar yaya?" "Gurin 'yar gwal mana, tun ƙarfe takwas ya bar sashina, ya tafi gurin matarsa wai rarrashinta yake yi, saboda a kanta aka fara mutuwar ɗa, ya ce da wuri zai fita, amma har sha ɗaya yana gidan nan, babu inda ya je yana gurinta" A fusace Hajiya Sa'a ta ce "Ni kaina fa iskancin yarinyar nan ya fara isa ta, tun lokacin zaman makokin yaron nan take ta wasu abubuwa, babu alamar tawakalli a tattare da ita, bari na je za su gane ba su da wayo" A falo ta tarar da su, Alhaji Fatuhu ya shirya zai fita, amma su na zaune a kan 3seater, sai magana yake yi mata ƙasa-ƙasa yana murmushi, ita ma Fadilan tana ta murmushi tana rufe fuska kamar wasu saurayi da budurwa. "Fatuhu meye haka? Aka ce ka na nan ka na rarrashinta, ta ƙi sakin jiki ta kwantar da hankalinta a kan mutuwar yaron nan, to idan ba za ta haƙura ba ta bi shi lahirar mana saboda ƙauna" Alhaji Fatuhu ya kalle ta ya ce "Haba Yaya sa'a, ke ma fa uwa ce, kin san dole ta shiga damuwa, kuma na san ba zai wuce Maryam ce ta zauna ta gaya miki abin da aka yi da wanda ba a yi ba" Hajiya sa'a ta ce "Wanda dai aka yi, tun da ga shi ina gani" Fadila ta kalle ta cikin mamaki, ta rasa abin da ta yi wa matar nan, tun Muhsin yana gadon asibiti tayi ta hantarar ta, wai duk ta damu mutane dan ɗan ta ba shi da lafiya . Haka da ya rasu, ta din ga hantarar ta a cikin mutane wai ba ta da tawakalli. Dama tun can ba wani shiri suke yi ba, amma abubuwan da ta din ga yi mata, sun ɗaure mata kai kuma sun saka ta ƙara tsanarta, saboda babu alamun tausayawa a tattare da Hajiya Sa'a. Tsam ta miƙe ta ce "Daddy a dawo lafiya, i will call you" Ya ce "Ok dear" "Au Fadila kin fi ƙarfin ki gaishe ni?" Alhaji Fatuhu ya ce "Dan Allah yaya ki daina yawan ƙorafin nan, ta yaya za ta gaishe ki, daga shigowar ki an zigo ki kin zo ki na faɗa" Ƙoƙarin hayayyaƙo masa ta yi, ya haɗe rai yana kallonta, ta sani sarai idan ya buɗe baki ba zai raga mata ba, hakan ya sanya ta bar maganar, ta shiga abin da ya kawo ta. ***** Sauri-sauri ya shirya, ya nufi gurin da yake ajiye mota, ya fito da motar zai fita. Sannu a hankali ya buɗe gate ɗin, komai a nutse yake abin sa, babu gaggawa ko rawar jiki kamar yadda sauran 'yan uwansa suke yi. Hankalin Alhaji Zailani yana kan waya, babu tsammani ya ɗaga kansa suka yi ido huɗu da shi, ya buɗe fuskarsa. Hantar cikinsa ce ta kaɗa gabansa ya faɗi. Shi ma ya ƙura wa Alhaji Zailani ido, da kyar ya iya jan motar ya bar gidan. **** Gidan su Nana kuwa, ranar ta kasance ranar da za a kaita, sai dai babu wanda ya san ina za a kai ta, kuma ko katifa Baba bai saya ba. Da Ummi ta yi masa magana sai cewa ya yi ba shi da kuɗi, ita ta yi mata. Abin ya ɓata mata rai, babu wanda ya san wani irin guri za a kaita, idan babu labule da katifa a ƙasa za ta zauna? Ga kuɗin sadakin Nanan har dubu ɗari biyu a hannunsa. Nana kuwa kawai dai ga ta nan ne, hankalinta ya kasu kashi-kashi, tana tunanin maganganun da ta ji da wannan muryar, ga kuma abin da ƙaisar ya gaya mata. Duk da wani ɓangaren na zuciyarta na gargaɗinta da yadda da maganganun Aljanu, wataƙila kawai wasa suke yi mata da hankali. Tana jiyo Mama tana ɓaɓɓaka dariya tana cewa yanzu idan buzayen su ka ƙi zuwa, su nuna in da za a kai Nana, ko kuma suka gudu shikenan Nana ta zama bazawara. Maganar ta sosawa Nana rai nesa ba kusa ba, wato duk bayan abubuwan da ta yi mata a baya, har ma tunani take yi, ta yi zawarci. A take Nana ta yi wa kanta alwashin ko bangon duniya wanda aka aura mata, zai ɗauke ta ya kai ta, za ta bi shi ko da kuwa zai din ga azabtar da ita ne, ta gwammace hakan da ta sake dawowa gidan nan da sunan zawarci tun da dai ibada take yi. Abubuwan da suke damunta kuwa, ta fauwwalawa Allah, ta dake ta je ta yi wanka. Ta yi kwalliya da wannan shaddar, da kayan da aka kawo mata. Kasancewar Nana tana da fata mai kyau, 'yan kayan da Ummi ta haɗo ta yi mata gyaran jiki na kwana biyu, ta yi kyau fatar ta ƙara haske. Ga zanen lalle an yi mata. Gashin kanta ma ya yi kyau, komai kyau ne da shi idan ya sha gyara. Sai da Mama ta yi saroro, da Nana ta fito cikin kayan nan, tamkar matar wani hamshaƙin mai kuɗi. Duk da ta rame sosai, amma kayan sun zauna a jikinta, tamkar tela ya gwada ta. Fuskarta babu yabo babu fallasa ta fito tana gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki. Nan gida ya ɗauki guɗa, aka din ga yi mata fatan alkhairi. Duk da ga a yadda auren ya zo mata, kuma har a lokacin ba ta tantance waye ma mijin nata ba. Amma ganin mutanen da suke ta shiga su na fita, ana cin abinci, a dalilinta. Kawai ta durƙusa ta yi sujudu shukur, ko ba komai wannan wata rana ce da kowace mace da ta san ciwon kanta, take fatan gani a rayuwarta. "Allah ga Nana, Allah ga baiwar ka. Ina godiya da tarin ni'imomin ka a gare ta" ta ɗago fuskarta duk hawaye. Suwaiba ta ce "Ji wata gulma, har da sujjada kamar auren gaske, wai a dole sai an raina wa mutane hankali. Mu dai a hanzarta a yi a bar mana ɗaki" Nana ta kalle ta ta ce "Suby kenan, ai duk ci gaba ci gaba ne, ba ɗaki ba gidan zan bar muku baki ɗaya ku sake, ina fatan aniyar kowa ta bi shi" Suwaiba ta ce "Aniyar kowa ta bi shi kamar yaya, me ki ke nufi?" Ta girgiza kai ta ce "A'a ba zan biye miki ba, ni yau ina cikin farin ciki ne a gare ni, ba zan biye miki ki lalata mini ita ba" Suwaiba ta ci gaba da faɗar maganganu. Nana kuma ta fice ta bar mata ɗakin. A hakan an sassamu wanda suka bayar da gudummawa sosai da sosai, domin kowa yana yabon Nana da halaye na gari, dan duk 'ya'yan malam Isa babu mai haƙurinta da biyayya, duk da wasu lokutan ita ma tana da faɗa, amma akwai ladabi. Ummi ta kasa ta tsare tana karɓar kaya da kuɗin gudunmawar da kanta, Ta kuma din ga ƙoƙarin, duk wani yinƙurin kawo hargitsi da Mama take ƙoƙarin yi a gurin taron ta hana. Nana ta samu kayan kitchen, da kuɗaɗe daga hannun jama'a da dangi. Da yamma sai ga Yusuf da mota, tare da Sule, Hajiya Amina ta ce a ɗauki Nana a ciki. Yaya Atine ta ce a fara zuwa su ga gurin, su san abin da za su saya, amma Yusuf ya ce babu buƙatar hakan, amarya za su ɗauka. Gaba ɗaya jikin Nana a sanyaye yake, su Yaya Atine suka saka ta sake wanka, Ummi ta bata wata lafaya da ta saya mata, ta saka ta feshe ta da turare. Ana ta rangaɗa guɗa, aka kai Nana gurin Mama wai ta yi mata nasiha. Mama ta ce "A'a ni me zan ce, ai ta san komai ba abin da ba ta sani ba, a sauka lafiya" Nana a ranta ta ce "Ko ba ki faɗa ba lafiya zan sauka, kuma sai Allah ya kunya ta ki". Baba yana ƙofar gida, aka kai masa Nana ya yi mata nasiha. Ya ƙare mata kallo ya ce "Yanzu kin ga abin da ki ka janyo wa kan ki ko Asma'u? To ki buɗe kunne ki saurare ni, babu zawarci a gidana, duk ɗan da zan aurar kin san ina jaddada wannan, ba zawarci babu yaji a gidana. Allah ya rufa miki asiri da miji na gari, amma fafur ki ka ƙi. Je ki Allah ya ba da sa'a ya baku zaman lafiya" Nana ta daskare a gurin ta kasa motsi balle ta tashi. "Na ce ki je Allah ya sanya alkhairi" ya maimaita mata. Ta ɗago idanunta a hankali ta ce "Baba... Sai kuma maganar ta maƙale ta ƙi ƙarasa fitowa, saboda kuka da wani abu mai nauyi da ya danne mata maƙoshinta. Ta yinƙura ta tashi, har sun kai bakin motar, ta waiwaya, kawai ta ga Baban ya zubo mata ido, idanunsa cike da hawaye. Kawai ta yi bismillah ta shiga motar. Ba Nana ce yarinya ta farko da Baba ya aurar ba, amma har cikin zuciyarsa ya ji rabuwa da ita, duk da tarin haushinta da yake ji. Wani sashen na zuciyarsa kuma ya fara tunatar da shi, da jin kamar bai kyauta ba abin da ya aikata. Kasancewar mota ɗaya tak aka kawo, daga Yaya Atine, Anty Sa'a sai Ummi suka tafi raka Nana. Su na tafe a hanya su na ta hirar su, Nana kuwa zubar da hawaye kawai take yi. Sosai Yusuf ya ji tausayin Nana, shi kansa ya jinjina girman wauta da rashin sanin ciwon kai da mahaifin Nana ya yi. "Kai wannan wace irin unguwa ce duk babu mutane, wannan ai sai a yanka mutum a binne ba a sani ba" Ai kuwa babu shiri Nana ta ɗago, tabbas haka ne, unguwar manyan gidaje ne sosai awon gwamanti, sai dai babu alamar akwai jama'a da yawa a unguwar. Gaban wani gida suka yi parking, mai ɗauke da doguwar katanga. Ko da suka fito, Yaya Atine ta ce "Aka ce mai gadi ne, ya na ga katafaren gida haka?" Sule ya ce "Eh gidan da zai yi aikin gadin ne, a ɗakin masu gadi za su zauna" Ta ce "To ikon Allah" ya buɗe gate ɗin suka shiga. Akwai ƙatuwar haraba a gidan, ta ko ina shuke-shuke ne, main gidan kuma yana can nesa da gate ɗin gidan. Daga nan kusa da gate ɗin kuma wani wani ƙaramin gini ne. Sule ya buɗe ɗakin ya ce su shiga. Ɗaki ne babba falle ɗaya, sai banɗaki sai ƙamshin sabon fenti da kuma turaren wuta yake tashi. Sabuwar katifa ce gal babba a ɗakin, ga labulaye da wardrobe mai guda biyu da mudubi ƙarami, ga kuma carfet a tsakiyar ɗakin. Yaya Atine ta ce "Yanzu a sati ɗayan ku ka yi wannan shirin?" Sule ya ce "Eh, wani mu muka yi, wani kuma Hajiyar da muke yi wa aiki ce, ita ta sai labulaye da abin shimfiɗar nan, da kayan ɗakin ma, abubuwa kaɗan mu ka ƙarasa" "Lallai tana da kirki sosai, bayan kayan da ta je ta kai mata gida. Amma Ummi babanku ya tafasa makaronin asara ko cokali fa bai saya wa Nanan ba" Ummi ta tsuke fuska ta ce "Babu kitchen kenan? A ina za mu ajiye mata kayan kitchen ɗin" Sule ya ce "Ai abu ne na maleji, sai dai a ajie mata a nan ɗin, tun da yana da girma sosai" Anty Saude ta ce "Bawan Allah kuma cikin gidan da mutane?" Ya jinjina kai ya ce "Eh akwai, sai dai ba ma zauna bane ba" Ya Atine ta shiga banɗaki, ta kunna famfo ta ga ruwa na zuwa, ga shi har da wearing ɗin nepa da sola na gidan a ɗakin. "To yanzu ina angon, mu fa ko sau ɗaya ba mu gan shi ba" Sule ya ce "Yana nan tafe, sai an jima za a rako shi, idan kuma za ku jira ne to shikenan" Yaya Atine ta waro ido ta ce "A ina ɗin? Wannan unguwar duk kangwaye, ku wuce mu tafi ke Nana Allah ya baku zaman lafiya" Ummi ta riƙe hannun Nana ta ce "Nana kin dai ji abin da Baba ya gaya miki, ki yi haƙuri da abin da ƙaddara ta zaɓa miki, ki yi zaman ki, ke kin san wannan gidan namu, ba gurin da idan ka bar shi zaka so koma masa bane. Ki zama mai tuna wace ce ke, kuma daga ina ki ke, sharrin da ake yi miki kawai a gidan ya ishe ki. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗayyiba. Na karɓi kuɗin sadakin ki a hannunsa, da kyar ya bayar da dubu hamsin, wai sauran da su aka yi hidimar biki. Ina son ɗan sayo miki kayan kwallita, da underwears idan kin amince, idan ba ki amince ba na baki kuɗin ki" A hankali Nana ta ce "Duk yadda ki ka yi na amince" "To shikenan, ga wata dubu ashirin ki riƙe a hannunki, a irin kuɗin gudunmawar bikin ki ce, ko za ki yi amfani da su, a sha amarci lafiya" Nana tana ji suka tafi suka bar ta ita kaɗai ƙwal. Shiru garin, ko ƙwaƙƙwaran motsin wani abin ba ta ji, ta ɗaga kai tana kallon ɗakin. A zuciyarta ta din ga addu'a, tana roƙon Allah ya shiga lamarinta. Yawan gane-gane da Nana take yi, ya sanya zuciyar Nana fara ƙeƙashewa. Ta bayan ɗakin take jin hayaniya, ana surutai da dake-dake ana hira, tamkar a irin gidan yawan nan. Kiran sallar magariba ta ji, ta tashi tsam, ta shiga banɗakin ta ɗauro alwala, ta dawo ɗakin ta yi sallar magariba. Bayan ta idar duhun magariba ya ƙara yi, sai dai ɗakin akwai hasken fitilar solar. A hankali kuma tsoro ya fara shigar Nana, ta daina jin hayaniyar da take jiyowa, ko ina ya yi tsit. Daga bisani kuma ta din ga jin bugun zuciyarta yana ƙaruwa, sai kuma hasken fitilar ɗakin ya ɗauke baki ɗaya. Ta kifa kanta a kan ƙafarta, jikinta ya fara tsuma. A hankali ta ɗago kanta, ta ganta a cikin sahara a zaune, sai sautin iska da yake kaɗa yashin saharar. A wannan karon ma yana tsaye, hannunsa riƙe da akalar raƙuminsa. Tashin sautin kaɗe-kaɗe ta din ga ji, ba tare da ta ga daga inda kiɗan yake tashi ba, ga wata zazzaƙar murya da take ta rangaɗa guɗa, muryar na amsa kuwwa a dajin. Ya taka a hankali ya je gabanta, ya miƙa mata hannu. Ta ɗago a hankali ta kalle shi, ta ɗaga hannunta za ta miƙa masa. Ta ji an yi sallama firgigit ta buɗe idonta tana kallon mai yin sallamar. Ayshercool 08081012143 Page 28 Da Sule suka yi ido huɗu, ya shigo wasu buzayen suka biyo bayansa, hannunsu riƙe da kaya. Ya kalli Nana ya ce "Afuwan mun tsorata ki ko? Ki yi haƙuri ba mu zo da wuri ba, mun tsaya mun yi salla isha'i ne. Ita dai Nana ba ta ce komai ba, aka din ga jere cartons na ruwa a ɗakin. Ita dai ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa. A hankali ta din ga jin tamkar numfashinta zai ɗauke, wani irin bugu zuciyarta take yi, sanyi yana ratsa ta. Ta ɗago kanta domin shaƙar wadatacciyar iska, kar numfashinta ya ɗauke. Fararen kaya ne a jikinsa, irin na buzaye, ya yi rawani da shuɗin yadi, ga wata ɗamara da ya yi da wani shuɗin yadin, gefen ƙugunsa kuma soke da takobi a cikin kubenta, wuyansa yana sanye da wani abu, na fata wanda ya ɗara laya girma, kuma bai kai girman jaka ba. Yatsunsa sanhe da zobunan azurfa, ga kuma ƙarfen tagulla a tsintsiyar hannunsa, ya dafe gefen cikinsa, shigar ta buzaye ce, kuma ta wata fuskar kamar ta larabawa. Yana gaba Habu yana bayansa, shi ma ya sha kwalliya cikin shigar buzayen. Wani irin daddaɗan ƙamshin turare, ya karaɗe ilahirin ɗakin, Nana ba ta taɓa jin turare mai tsananin ƙamshi kamar wannan ba. Sai kuma sauran buzayen aƙalla su biyar, duk sun sha kwalliya. Dadduma suka shimfiɗa masa ya zauna. Gaba ɗaya suka zauna a gefe, suka yi shiru. Habu ya ce "Mu yi addu'a" aka fara Addu'a. Nana ba ta san a tsakaninsu waye mijin nata ba, sai dai tana ƙoƙarin satar kallonsa, duk da kamar kullum kamar yadda ta saba ganinsa, fuskarsa a rufe take da rawani. Ba ta san me aka karanta a addu'ar ba, saboda ta lula tunani, sai muryar Habu da ta ji ya kama sunanta. "Nana" Ta ce "Na'am" "Da farko dai ina mai ba ki haƙuri a kan abin da ya faru, kin san komai Allah ne yake ƙ'addarawa. Jikina ya yi matuƙar sanyi da abin da ya faru. Na gane dalilin wannan auren ne ya sanya muka baro gida. Ki yi haƙuri bawa ba ya tsallake ƙaddararsa. Ina yi muku fatan alkhairi da fatan Allah ya baku zaman lafiya. Na san abubuwan da mu ka ba ki na aure, be kai abin da ake kashe muku na aure ba, amma ki yi haƙuri a hankali za mu duba a yi miki, kin san masu ƙaramin ƙarfi ne mu. Dama ɗan kuɗin gadin tarawa muke yi, za mu tura gida wannan abu ya bijiro, kuma kuɗin hannunmu duk ya ƙare. Dan Allah ki yi haƙuri da abin da Allah ya ƙaddara miki." Nana dai ba ta ce komai ba, ya sake nuna mata kayan da suka zo da su ya ce "Ga sayayya nan, abin wanka ne da kayan wanke baki, da ɗan abin da ba a rasa ba na kayan tsafta. Yanzu mu na sauri mu koma, ba wanda zai kula da ƙofa dole mu koma da wuri, amma zamu dawo da yardar Allah" su ka ƙara yi musu fatan alkhairi. Shi kuwa tun da ya zauna, ƙwaƙwƙwaran motsi ma bai yi ba, balle ya tofa wani abu ba. Sai da Nana ta ga sun miƙe baki ɗaya shi yana zaune, sannan ta fara zazzaro ido. Gaba ɗaya sai suka juya yare, su na yi masa magana, har suka gama maganar, shi dai bai ce uffan ba. Ɗaya bayan ɗaya suka fice, hakan ya ƙara tabattar mata da shi ne mijin nata. A take ta tuna Sule ya taɓa gaya mata ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa. 'kenan mahaukaci Baba ya aura mini?' ta tambayi kanta. Ƙoƙarin tuna wasu abubuwan take yi a kansa, amma abu ya gagara, ta ji gaba ɗaya kanta ya toshe. Ta yinƙura ta tashi, ta tafi banɗaki domin ta yi alwala ta yi sallar isha'i. Sai dai bayan ta yi alwala da ƙyar ta baro banɗakin, saboda duk taku sai ta ji tamkar zuciyarta za ta fashe. Ƙafafuwan ta su ka gaza ɗaukar ta, a dole ta zauna ta kalli gabas, ta tayar da salla. A zaunen ma jiri take yi, da haka ta yi salla. Shi dai bai kula ta ba, bai kuma tashi daga gurin da yake a zaune ba, kamar gunkin budda. Ta idar da sallar, ta koma jikin bango ta matse jikinta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ji take kamar ta kurma ihu, ga sanyin nan da take ji ƙaruwa yake yi, tsigar jikinta sai tashi take yi. "Allah ka dube ni, dan Allah ƙaisar kar mu yi haka da kai, ni hauka shi hauka ta ya ya za a yi wannan zaman" ta furta hakan a hankali. Sun shafe dogon lokaci, kamar babu halitta mai motsi da ta wanzu a gurin, Nana tana ta tufka da warwara a zuciyarta, kawai ta ga ya tashi tsaye. Zuciyarta ta ƙara tsinkewa da tsoro da razani, tare da hakaito mata miyagun abubuwa, yanzu idan ya yankata a gurin nan ya gudu fa? Mussaman wannan takobin da take gani. A hankali yake tafiya, ya tafi gefen wardrobe ɗin ɗakin, da aka kafe abin rataye kaya. Ya cire takobin ya rataye ta. Ba tare da ya waiwayo ba, ya fara kwance rawaninsa. Kasancewar ya juya mata baya, ya sanya ta zuba masa ido ko ƙiftawa ba ta yi. Ya kwance rawanin gaba ɗaya, ya ninke Nana ta zuba wa sarautar Allah ido, ganin kansa ɗauke da gashi baƙi wuluk, ya tufke shi tamkar an yi wa kan bahauhishiya saloon. Ya saka hannu ya zare rigar jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta, tana kallon gefe, kamar mara gaskiya. A hankali ta ƙara ɗagowa, ta ganshi da dogon wando, da shirt, ya ninke rigar da rawaninsa, ya buɗe wardrobe ɗin ya saka kayan a ciki. Ba ta san ya aka yi ba, kawai sai gani ta yi sun haɗa ido. A take ta tuno ganin da ta yi masa, har ta suma a ɗakin su. Da wata irin azama ta tashi, duk da bugun zuciyar da take ji da kuma jiri, ta ja da baya ta tsaya cikin tsoro da razani. Ya ci gaba da kallonta, ba tare da ko ƙifta ido ba. Kawai Nana ta fashe da kuka, ba tare da sanin dalilin da ya sanya ta kukan ba. Gani ta yi ɗakin yana juya mata, ya kawar da kansa daga kallonta, ya fice daga ɗakin. Fitarsa ke da wuya ta silale a gurin ta faɗi. A hankali ta fara juyi tana tari, a cikin kunnuwanta take jin bugun zuciyarta, ta ja jikinta ta tashi da ƙyar. Ta karkaɗe hannunta saboda ƙura, ƙaisar ta gano sanye baƙar riga tana jan ƙasa, yana shirya litattafan sa, yana goge su. Da ƙyar tarin ya ɗan lafa mata ta ce "Ƙaisar" "Ya aka yi?" Ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Tsoro nake ji, ji nake yi kamar zan mutu. Ba ka ji yadda zuciyata take bugawa ba" "Ina jin yadda take bugawa mana, ai mutuwar ma za ki yi idan ba ki yi wasa ba, tun da ke dai kin ƙware a taurin kai. Wannan mutumin ƙila shi zai yi ajalin ki. Ki kan ji bugun zuciya da sanyi ne, idan ina guri to me yasa ba na gurin daga ke sai shi ki ke jin bugun zuciyar?" Ya jefo mata tambayar. Nana ta ɗan yi shiru, sai kuma ta ware ido, amma ta kasa magana. Ya ce "Eh, ai na gaya miki ba ki da tabbacin abin da ki ka aura, mutum ne ko kuma jinsinmu" yana gama maganar ya yi gaba. A rikice Nana ta bi shi tana faɗin "Dan Allah ka tsaya ka saurare ni, yanzu ya zan yi dan Allah?" Ya waiwayo ya kalle ta ya ce "Au tambayata ma ki ke yi ya ya za ki yi? Shirka fa ki ke ƙoƙarin ko kin manta?" Nana cikin kuka ta ce "Ba haka nake nufi ba, amma wallahi tsoro nake ji idan na ci gaba da rayuwa da shi, zan iya mutuwa" Ƙaisar ya ce "Ai da da na gaya miki ba ki yadda ba" ya juya zai tafi, ta riƙo rigarsa" "Zan watsa ki ta waje, idan ki ka kuma bi na" Za ta yi magana ya ce "Sai kuma ki yi" kawai ya ɓacewa ganinta. Kawai ta koma gefe ta tsaya tare da fashewa da kuka. Yana zaune a gefen ɗakin nasu, ya na shan hantsi, sai ga Sule ya zo da kwandon kayan abinci. "Ango har ka tashi? Ya mariée ɗin ?" Ya nuna masa ɗakin, alamar tana ciki. Gaba gaɗi Sule ya nufi ɗakin da kwandon Abincin cikin hanzari Buzu ya miƙe ya tsaya a ƙofar ɗakin. Sule ya ce "Au yi haƙuri, bari na zauna daga nan" ya nemi guri ya zauna a gefensa. Nana kuma ta buɗe idonta, ta ganta kwance a kan katifar, jikinta babu naɗin lafayar da aka kawo ta da shi, sai riga da skirt ɗin ta na ciki, kanta ko ɗan kwali babu. A razane ta dubi jikinta tana tambayar kanta, ko ya yi mata wani abin ne?. Ta kalli gefen katifar ta ga lafayar a ninke a ajiye. Da azama ta yinƙura ta faɗa banɗaki, amma ba ta ga alamar an yi mata wani abu ba. Ta yi tsarki, ta yi alwala tana ta istigfari ta yi sallar asuba, cike da jin kunyar Ubangiji, yadda lokaci ya ja gari ya yi haske ba ta yi salla ba. Bayan ta idar tana jiyo Sule yana ta zuba da yaren su, shi dai ba ta ji maganar sa ba. Ta yi mamakin abin da ya sanya Sule kasa yin zuciya ya ci gaba da surutu ba tare da ana kula shi ba. Babu tsammani ya shigo ɗakin, ba tare da ko sallama ba. Aikuwa ta zabura ta ja da baya tana kallonsa. Kai tsaye ya nufo ta, ya ajiye mata kwandon Abincin a gabanta. Ya nemi guri ya zauna ya zuba mata ido, da kwandon kayan abincin a tsakiyar su. Nana ta sunkuyar da kanta, sanyi na ratsa ta. "Zan ci abinci" ta ji muryarsa kamar daga sama, ɗaga kai ta yi ta kalle shi, ji ta yi kamar ta ce masa to ya ci mana, sai kuma ta tuna ashe fa wai yanzu mijinta ne. Mamaki ne ma ya kamata, dan har a lokacin tana mamakin idan ba kurma ba ne ba. Ta janyo kwandon ta sassuke abincin, ta fara ƙoƙarin zuba masa, kawai ta ga ya tashi ya fita. Sai ga shi ya dawo da abin da suke hura wutar dafa shayi, har da butar shayin ma, da alama abin da suke yi a wajen tun ɗazu kenan, shan shayin. Ya buɗe cikin kayansa, ya ɗaukko turaren wuta, ya zuba a kan sauran garwashin. Take ɗakin ya karaɗe da ƙamshi mai daɗin gaske. Ya samu guri ya zauna, ya karɓi abincin, ya koma gefe ya sauke takunkumin rawaninsa ya hau ci. Nana kuwa kasa cin abincin ta yi, ta yi tsuru sai satar kallonsa da take yi, ya gama ci ya ɗauki kwanukan da ya ci, ya fita waje ya wanke ya dawo ya ajiye mata. Ya tsiyayi sauran shayinsa na butar, ya shanye abin sa. Ya kewaye ta, ya ɗauki pillow ya koma can gefe ya ajiye ya kwanta. An shafe tsawon lokaci, na zaune ba tare da sanin abin yi ba. Jin yunwa ta uzzura mata ya sanya ta ɗan zuba abincin ta fara ci. Tun tana cakala har ta saki jiki, ta ci gaba da zurawa kawai suka yi ido huɗu, tana ta loma. Sai kuma ta yi sak, ta ci gaba da ci ta kasa kamar wadda ta aikata rashin gaskiya, kuma ya ƙi daina kallonta. Ƙarshe sai haƙura ta yi da cin abincin, kallon da yake yi mata duk ya sanya ta damu. ***** Gidan su Nana tun a ranar kowa ya watse, dan baba faɗa ya yi ta yi, yana cewa duk wanda ya kwana sai dai ya nemi abin da zai ci, shi ba shi da abin da zai sake bayarwa a bawa mutane. Suwaiba ta ƙarewa ɗakin su kallo ta ce "Ohhh abin tsiya, ko tsinke ba ta bari ba, duk ta kwashe komai balle mu gada." Mama ta ce "Au ke har wata tsiyar ki ke saka ran gada a gurinta? Me za ki gada banda gayyar masifa, ai gara da tarkata komai ta tafi, ma sake mu miƙe ƙafa mu huta mu ma" Jamila da ta shirya tsaf za ta fita ta ce "Aikuwa dai" "To kafin hankali ya dawo kan ku, Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari 'yan uban uban su, wanda kowa sai ya koka a tashi kan munafukan unguwa da na family" Suwaiba har da tsalle ta ce Amin Mamanmu maganin kukanmu. Jamila ta yi murmushi ta ce "Ni dai sai anjiman ku" Mama ta ce "To a sauka lafiya" ***** A tsanake take kallon yadda mai gidan nata, yake ɗan yamutsa fuska bayan ya kammala cin abinci. A hankali ta ce "Daddy" "Na'am baby" "Ya dai? Jikin ne ko garin? Na ganka so silent" Ya ɗan yi miƙa ya ce "Pressure ce ta ɗan yi mini yawa wallahi, ina shirin tafka asara ne, kwana biyun da ban je kasuwa ba, har an yi mini ɓarna wallahi. Ga kaya sun iso Nigeria na gama clearance amma coustom sun ƙi sakar mini kayan" "Subhnallah, in sha Allah ba za ka yi asarar ko naira biyar ba. Allah zai warware komai, bari mu duƙufa da addu'a in sha Allah ba wani abu" Ya yi murmushi ya ce "Sweetheart, Allah ya amsa mana, ɗan duba mini paracetamol idan ki na da shi, kaina yana ciwo, ina so na je asibiti ma a duba ni ko bp na ne ya hau" Cikin damuwa ta ce "In sha Allah ba shi ba ne ba ya hau, dan Allah ka kwantar da hankalinka, mu na buƙar lafiyarka just recently fa kai ne ka ke yi mini nasiha a kan yadda da ƙaddara" Ya girgiza kai ya ce "A'a ba ma damuwar na saka a raina ba, kawai jikina ne babu daɗi" Ta tashi ta ce "Bari na ɗaukko maka" ta nufi bedroom ɗin ta. ***** Alhaji Zailani ne zaune a gaban malam Gambo, sai gumi yake yi kamar ya yi wa sarki ƙarya. "Na rasa gane abin da ya faru gaba ɗaya, ni dai na san mun yi da kai za mu yi magana da wanda ta aura ɗin, na ba shi kuɗi ya sake ta, sai dai ban san meyafaru ba na kira shi ɗin a zahiri, ban kira shi ba na kasa tunawa, ni dai kawai na ganshi a mafarki ban ma san meyafaru ba kawai na farka na ji tamkar an shaƙe ni, da ƙyar nake numfashi" Malam Gambo ya yi shiru ya ce "Kuma ka tabattar ba ka yi maganar da shi a zahiri ba?" "Wallahi na kasa tunawa" "Hakan na nufin da akwai matsala kenan, ka ɗan bani lokaci zan yi bincike" Cikin damuwa ya ce "Zuwa yaushe kenan? Ni fa duk abin da za ayi sai dai a yi, fatana kawai burina ya cika" "Kar ka manta burin naka ba ɗaya bane ba, kar ka manta bayan burinka na son haska taurarinka, na mallakar dukiya mai tarin yawa da kujerar siyasa, akwai burinka na son kawar da babban amininka, idan ka yi wasa za mu yi jifar gafiyan ɓaidu, dole ka tattara hankalinka a kowane ɓangare, muddin ba ka durƙusar da shi ba, taurarinka ko sun haska ba za ka taɓa shan gabansa ba, dan haka ka kula da kyau" Ya yi ajiyar zuciya ya ce"Na fahimta, shi ma ba mantawa na yi da nasa ɓangaren ba, shi ma na shirya komai, amma ina sauraren ka abin da binciken naka ya baka sai ka sanar da ni. Dan ko ya kama na zubar da jininsa ne zan yi domin na samu cikar muradina" "Ka dai dakata, zuwa lokacin da zaka ji daga gare ni tukuna" Da ƙyar ya lallaɓa Alhaji Zailani ya kwantar masa da hankali. ***** Cikin tsananin tsoro da razani Jamila take kallon hajiya Sa'a, jikinta na wata irin tsuma cikin faragaba da tashin hankali. Yawun da za ta haɗiye ma ya gagare ta, saboda tsoron da ya mamaye ta. "Jamila, na gaya miki sirrinmu, idan kin ga dama ki yi shiru da bakin ki, ki tara arziki ki bar shi, idan kuma kin so ki fallasa, ba ki da hujjar kare kanki, kuma sai na ƙarar da zuriyar ku, ta hanyar bayar da jinin ku ɗaya bayan ɗaya. Abin farko da nake buƙata ki taimaka mini, shi ne mu na buƙatar jinin yayar ki Nana, a baya na sha baki abu ki bata, ba tare da kin san dalilin hakan ba, to yanzu na gaya miki abin da nake so. Dan haka za ki taimake mu muma" Jamila na jan numfashi da kyar cikin rauni ta ce "Amma ba za ta mutu ba?" Safiyya ta ce "Ke ina ruwan ki da zata mutu ko ta rayu, idan aka so har babanki za a iya nema ki bayar, to dan dai wannan da ba uwarku ɗaya ba" Hajiya sa'a ta ɗaga mata hannu ta ce "ƙyale ta, dole za ta ji banbarakwai abin, ina ga sai dai mu sanya ta a wani ɓangaren, tana da tsoro sosai da sosai. Yanzu dai ki fara yi mana wannan aikin tukuna" Jamila cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Hajiya a canza mini wani, tausayinta nake ji" har maman khairat ta hasala za ta yi kan Jamila da masifa, hajiya Sa'a ta ɗaga mata hannu. Ta dubi Jamila ta ce "Ba fa kashe ta za a yi ba, ɗan kaɗan muke son jinin nata" "To ai ta yi aure, babanmu ya aura mata wani buzu" ta yi maganar hawaye na cika mata idanu. "Eh na san ta yi auren, na ga duk kin tsorata kin damu, bari na kawo miki lemo ki sha" ta tashi ta ƙiftawa maman khairat ido, ta fice daga ɗakin. Ba a jima ba ta dawo da lemo a cikin glass cup, ta miƙa wa Jamila. Jin sa da sanyi, ya sanya ta karɓa kai tsaye ta fara sha. Sai dai tun kafin ta gama shan lemon, jiri ya fara ɗibar ta. Maman khairat ta karɓe kofin lemon, Jamila kuma ta silale, cikin fita hayyaci. Suka sassaki labulaye, suka kashe fitila, duhu ya mamaye ɗakin, ta kunna kyandira, ta bawa maman khairat ta riƙe mata, ta ɗaukko wata jakar fata ta zazzageta. Wani irin tarkace ya zubo daga ciki, tare da layoyi, ta cire wa Jamila kayan jikinta, ta din ga sha mata wani irin mai jawur da shi. Bayan ta gama ta ɗaukko wata allura a cikin wata laya, ta sokawa Jamila a wuyanta. Aikuwa ta zabura jikinta ya yi wata irin girgiza. Ta juya bayanta ta kuma soka mata a ƙeyar ta. Nan ma jikin nata ya sake girgiza. Ta sake saita ƙahon zuciyar ta, ta sake soka mata. Jikinta ya din ga tsuma ba tare da ta tsaya ba. Hajiya sa'a ta din ga karanto wasu abubuwa cikin wani irin yare, jikin Jamila na ci gaba da rawa tamkar ana girgiza ta. Ta kama hannunta, ta saka mata wasu awarwaraye, sannan ta kawo wani bargo ta rufe ta da shi. **** Tamkar mujiya haka Nana take zaune a ɗakin nan, duk abin duniya ya ishe ta, yamma tana yi ya ɗauki radiyo ya fice ya bar ta a ɗakin ita kaɗai. Ta tashi ta kwance kayan da Ummi, ta yi mata sayayyar su. Ɗan kayan shafe-shafe ne, da turaruka sai under wears, duk da masu arha ne Nana ta ji daɗi sosai da sosai. Duk da tana jin haushinta, amma ta san idan ba Ummin ba, babu wanda zai tsaya tsayin daka ya yi mata wannan abin. Ta haɗa da na gurin Hajiya Amina, duk ta jere. Ta janyo drower mudubin, ta ga burshes ne da comb a ciki. Ta mayar ta rufe. Ta janyo jakar kayanta, ta buɗe wardrobe ɗin, ta ga ɓangare ɗaya shaƙe da kayansa, sai da abin ya bawa Nana mamaki. Ɓangare ɗaya ta jere kayanta, ta tsaya tana kallon kayan, duk da galibi wanda hajiya Amina ta ba ta ne, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Ta daɗe tana burin ganin kayanta a cikin wardrobe. Dan a gida, a wata tsohuwar adakar kakar su take zuba su, ƙarewa wataran talauci ya ishi Baba ya ce ta zazzage kayanta, ta ba shi. Haka ta ba shi ya sayarwa 'yan gwangwan ya sayo mata viva ya bata wai ta zuba kayan a ciki, tun da tsummokaran nata ba su da yawa. Daga baya ta koma zubawa a kwalaye, daga ƙarshe dai Jamila ce ta samo mata ghana must go ta bata, take saka kayan ta a ciki. Amma yau ga kayanta a wardrobe, kuma kaya kusan set goma sha uku, sababbi da tsofaffi, ga atamfofinta uku da ba a kai ga ɗinkawa ba. Ta ninke bargonta, da bedsheets da Shukura ta bayar a bata, ta saka su a saman wardrobe ɗin. Drower ƙasan wardrobe ɗin kuma, ta saka takalmanta guda biyu, da jakar gidan sarkin baka, da pad ɗin ta. Ta gyara kan katifar ta ɗame ta da bedsheets. Ta tashi tsaye tana kallon katifar, ita ma tsawon rayuwarta a kan wani tsohon bargon Baba take kwana, shi ma dai na kakar ta ta ne, bargon nan tamkar ya koma audigarsa saboda tsufa, amma yau albarkacin aure, ga ta da ƙatuwar katifa. Wani murmushin ne ya sake suɓuce mata, ta juyo kawai ta yi karo da shi a tsaye a bayanta. Ba ta san lokacin da ta ƙwala ihu ba, dan sam ba ta ji alamun mutum a bayanta ba. Kuma kasancewar ta ƙure da jikin katifar, razanar da ta yi, sai ta faɗa kan katifar. Taku ɗaya ya ƙara, ya tsaya a kanta yana kallonta. Ayshercool 08081012143 29 Ƙara rikicewa ta yi, ta kasa tantance abin da take gani daga cikin idanunsa. Ya sauke rawaninsa, ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗaukko wayarta ya ajiye mata a gefen ta. Tashi ta yi zaune tana kallon wayar, gaba ɗaya ta manta ma tana da wata waya, a ina ya samu wayata? Ta tambayi kanta. Ta bi wayar da kallo, ta kasa taɓa ta. Ya sake zura hannunsa a cikin aljihunsa ya ciro wata roba, ya ajiye mata, ya juya ya fita. Sai da ya fita ta ɗan samu ta nutsu, ta kai hannunta ta ɗauki wayar ta duba ta ga a kashe take, sai ƙamshi take yi. Ta kalli robar da ya ajiye mata, dabino ne fal a cikin robar lubiya. Gefe kuma ga kwanukan abinci, fulasan kawai ta kalla ta san daga gidan Hajiya Amina suke. Tana cikin tunani, ta ji sallamar mace. Ta amsa tare da kallon ƙofar ɗakin. Wata mata ce ta shigo, Nana ta yi mata maraba, ta shimfiɗa mata sallaya ta zauna. Bayan sun gaisa Nana ta ce "Ban gane ki ba" "Eh ai ba ki sanni ba, a nan baya muke, aka ce ai an kawo amarya na ce bari na zo mu gaisa" Nana ta ce "Allah sarki, dama da mutane a nan haka? Shiru nake jin unguwar duk da jiya na zo" Matar ta ce "Eh, ai a nan baya nake, sunana na Haulat, amma kin je kun gaisa da mutanen gidan" Nana ta girgiza kai ta ce "Ai ban san da mutane a gidan ba" Haula ta ce "Ai ba su fiye zama bane ba, kullum cikin yawo suke, amma yau ko gobe za su dawo." Zuwan Haulat sai ya ɗebe wa Nana kewa, su ka yi ta hira. Sun daɗe su na hirar, sannan ta yi wa Nana sallama, ta rako ta har bakin ƙofar ɗakin ta ce "Idan na fara fita, nima zan kawo miki ziyara" "To shikenan, ai a nan baya muke" Nana ta ce "Kuma da gidaje a gurin? Na ga duk kangwaye ne?" Haula ta ce "Gamu kuwa, akwai gidaje a gurin" "Allah sarki, to na gode sosai ki gaida gida" Yana zaune a kan benci, yana shan shayi a cikin ɗan ƙaramin kofin nan nasu, Nana ta jima tana mamakin kofin da suke shan shayin nan, tamkar wasan yara. A ganinta sai mutum ya sha goma bai ƙoshi ba. Tana hango shi su na fitowa da Haulat, ya rufe fuskarsa. Ta zo za ta fita ta tsaya tana gaishe shi, amma ya yi shiru, kuma bai ɗaga kai ya kalle ta ba, ta fita. Sai da Nana ta ji babu daɗi, haryanzu ita ba ta ga wata alama ta hauka a tare da shi ba, kuma jiya ya yi magana ba kurma bane ba, tsagwaron wulaƙanci ne ya sanya sai a yi masa magana amma ya yi shiru. Da daddare ma, zuwa ya yi ya saka ta a gaba, yana kallonta yana kallon kwanukan abincin da ba ta san waye ya kawo ba, ta san dai na gidan Hajiya Amina ne. Haka ta zuba masa ya ja gefe ya sauke rawaninsa ya ci abinsa, sai dai da ya gama ci, yake ɗaukar kwanon da ya ci abinci ya fita ya wanko ya zo ya ajiye. Abin da ta lura da shi, shine mutum ne mai tsafta sosai. Ita dai tana gefe sai dai ta saci kallonsa, sai dai ƙasan zuciyarta tana mamakin yadda yau ba ta jin bugun zuciyar, sai dai sanyi da take ji. Bayan ya ajiye kwanukan, ya tashi ya kwance rawanin sa, duk da wayarta take ɗan dannawa, sai da ta saci kallon gashin kansa, kawai ta ji tana son ya ware shi, ta ga adadin tsawonsa. Ya rage kayan jikinsa, ya ɗauki radion sa, da kayan shayinsa ya fice daga ɗakin. Yana fita ta ja ajiyar zuciya, ta tashi ta shiga banɗaki, ta yi wanka ta wanke bakinta, tayi alwala, ta fito ta shirya ta kwanta. A iya saninta, wayarta take ɗan duddubawa tana tunanin yadda aka yi ya samu wayarta. "Amarya ba kya laifi, ko kin kashe mai gida?" "Meye haka wai?" "A ina?" "Ni fa yanzu matar aure ce, ya zaka din ga kawo ni nan, duk lokacin da ka ga dama?" Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Ina ruwana da auren ki? Auren jeka na yi ka? Auren da haryanzu ba ki da tabbas a kansa? Haryanzu ba fa ki san me ki ka aura ba, kuma kamar an ce ma mahaukaci ne ko?" A ƙule Nana ta ce "Ko ma dai mene ne ina ruwan ka? Zan gano da kaina, koma wane ne, idan ma mutum ɗin ne ko akasin haka" Ƙaisar ya ce "Jiya fa ki ka zo nan ki na yi mini kuka, ki dai san iya abin da yakamata ki yi, da inda yakamata ki tsaya kar allura ta tono garma" "Eh, haushi ka ke ji na yi aure, ba tare da tsammaninka ba, balle ka sake hanawa" Kawai ƙaisar ya bushe da wata irin dariya, da sai da ta tsorata ya ce "Ke haryanzu ba ki san ina ki ka dosa ba, ni ba jinnil ashiƙ bane da zan hana ki aure, na baya ma mazan naki ne ba su yi mini ba, duk da wannan ma da na farga da wuri sai na ruguza shi, sai dai idan na matsa za ki iya rasa rayuwar ki baki ɗaya, shi yasa na ƙyale" Nana ta ce "Saboda me?" "Kawai" ya bata amsa. "Amma wai da gaske aljani yana auren mutum?" "Eh" "To ku ina naku matan ku ke auren na mutum?" Ya ce "To ai ni ba aljanin soyayya ba ne ba da za ki tambaye ni." Nana ta ce "Amma ka hana ni aure? Me yasa ka saka Saleh ciwon ciki?" "Ke ko duk matan bil'adama sun ƙare zan auri masifaffiya ne mai azabar taurin kai kamar ke ne?" "Eh abin nan ne, da ake cewa makaho ga ido, ya ce wari yake, na fi ƙarfin ka ne kawai" Ya ce "Ko?" "Eh mana, dan Allah ka gaya mini ya ake yi ku ke auren bil adama" "Ni ma ban sani ba, sai dai zan baki wani littafi ki karanta, soyayyar Aljani Ridwan, da bil adama" Nana ta zabura ta ce "Dan Allah, ya sarkin baka, a wane hali yake yanzu? Kuma ni ba littafin soyayya nake so ba, wannan littafin na Jaddul jinn nake so ka bani na ƙarasa karantawa" "Ba zan bayar ba, kuma ba wannan ne ya sanya na kira ki ba, duba jikin mudubi, ki zo ki gaya mini abin da ki ka gani" Nana ta ce "Wallahi ba zan kalla ba, masifa da bala'i kawai ka ke nuna mini a cikin mudubin nan, Allah ya sa ya tarwatse... "Wallahi sai kin kalla, wataƙila zuciyar ki ta saduda, ki yi abin da ya dace" Kawai ta ganta a gaban mudubin, Jamila ta gani a kwance tsirara, Hajiya Sa'a na ta tsira mata allurar nan. Tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta ta ce "Dan Allah me take yi mata? Jamila ce fa" "Ƙwarai ita ce, Matar ta umarceta ta kawo mata jininki, ta ce ba za ta iya ba, shi ne ta bi ta bayan gida, yanzu haka ta gama mallake ta, duk abin da ta ce ta yi shi za ta din ga yi, ba za ta taɓa kaucewa maganar ta ba" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu ya zan yi, kar ta cutar da Jamila, shiyasa ni tun farko ba na son yawon maƙwabtan nan da take yi. Wannan matar ba ita ta bayar da Muhsin ba?" Ƙaisar ya ce "ƙwarai ita ce, kuma ba wannan ba, bayan cin moriyar ganga, yada ƙwauron ta za ta yi. Ba wannan ba bayan ɗalibin ki da ki ka rasa, babansa ma an sako shi gaba, wataƙila nan kusa ko nesa kaɗan ya bi ɗan nasa". "A'a ba gaskiya ba ne ba Ƙaisar, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba" "Dama ai ba gaya miki nake yi domin ki yadda ba" Ta ɗan yi shiru cikin jimami da tashin hankali, ta ce "Yanzu meye abin yi, ba na son Jamila ta faɗa ga halaka" ta yi magana cikin kuka. "Kin fi ni sanin abin yi ai Nana Asma'u" "A'a ban da wannan, wannan ba mafita ba ce ba, na gaya maka ba zan yi wannan ba" Ya ce "To shikenan, sai ki zura ido mutane na cutuwa alhalin ki na da yadda za ki yi, ki taimaka musu" "A'a ƙasair" kawai ta ga tamkar ya wurgota waje. Ihu ta saka ganin tana faɗowa daga sama, za ta faɗa cikin ruwa. A razane ta tashi tana faɗin "Ya Allah" ta dafe saitin zuciyarta tana haki. Ita kaɗai ce a cikin ɗakin, ta janyo wayarta ta duba lokaci, ta ga uku da rabi na dare. Ta yi shiru domin tuna abin da ya razanata daga baccin, amma ta kasa, kawai faɗowarta daga dogon tsaunin da libararyn Ƙaisar zuwa ƙasan ruwa ta iya tunawa. Ta kalli ɗakin, fitila a kunne, amma ba ya ciki. Ta tashi a hankali, ta nufi ƙofar ɗakin, ta leƙa harabar gidan. Yana kwance a kan benci, yana bacci ya tada kansa da hannunsa. Gabansa ɗan murhun dafa shayinsa ya mutu, ga butar shayin da kofinsa. Wasi-wasi ta shiga yi, a kan ko tashin sa za ta yi. Wutar gurin ce ta ɗauke gaba ɗaya, gurin ya gauraye da duhu, aka yi wata irin walƙiya mai hasken gaske, kawai ta ga wannan tsohon a tsaye a kansa. Tamkar an dasa ta, ta kasa motsi ta kasa gaba ta kasa baya, aka sake walƙiyar nan, ta sake ganin tsohon nan a tsaye a kansa, sai dai wannan karon ya feso wani irin tartsatsin wuta da ya tilasta mata yin baya cikin matsanancin tsoro. A hankali ta buɗe idonta, kawai ta ganshi a tsaye yana kallonta, kamar taɓaɓiyya haka ta zura da gudu, ta koma kan katifa ta kifa kanta tana haki, saboda tsoro da razani. Maganganun Ƙaisar suna nema su fara zama gaskiya a kan mutumin nan. Tabbas ta fara tantamar kasancewar sa mutum. Duk da ta san ba ta da cikakkiyar lafiya ƙaisar ya saba tsorata ta, amma ya za a yi a ce mutumin da ta hango yana bacci, cikin abin da bai fi ƙifta ido sau biyu ba, ta gan shi a gabanta. A ɓangaren sa shi ma mamaki yake yi, me take yi a tsaye a bayan labule a wannan tsohon dare haka?. ***** Hajiya Sa'a ce take kallon Jamila, tana wani irin mugun murmushi ta ce "To jamsy me ki ka ce yanzu?" Jamila ta ce "Ta yaya zan samo miki jinin nata?" "Yauwwa Jamila, ba wani abu ne mai wahala ba, magani zan baki a abinci, ki kai mata ta ci, sai kuma abin da za ki ajiye mata a ɗaki" Jamila ta ce "To shikenan, babu damuwa an gama" "Kin tabattar za ki iya?" "Eh mana, me zai hana?" Hajiya Sa'a da Maman Khairat suka kalli juna, suka sheƙe da dariya, Hajiya Sa'a ta ce "Yauwwa jamcy, zan gaya miki duk yadda za a yi " Jamila ta gama wuninta a gidan, sannan ta tafi gida. Sai dai gaba ɗaya ta din ga jin ta wani iri, tamkar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tattare da ita. **** Tamkar bakin mama ya taɓo ƙeyarta, haka take washe baki, a gaban malaminta. Ta ce "Anya ka taɓa yi mini aiki mai zafin wannan? Komai ya tafi yadda ake so, wallahi yadda na tsara masa komai haka ya bi, dama abin yana cin sa a rai ƙiri-ƙiri mai kuɗi ya zo ta ce ba ta so" Ya yi dariya ya ce "Mu ɗin na wasa ne? Gangaran ne ni fa, ai duk taurin buƙata muka ɗauki allo muka hau kan buzu mun gama da ita" Mama ta ce "Ai kuwa na ga zahiri, malam saura na 'yan matana, a bamu na farin jini. Wallahi duk samarin nasu ba na arziki sai tarkace babu wata mamora a tattare da samarin nasu, ni kuma masu maiƙo nake so, inda zamu jingina mu huta, ka san rayuwar ce sai a hankali, ba zan so mu dauwwama a talauci ba, su yi gadon masifa ba" Yayi murmushi ya ce"Tabbas wahala abar gudu ce, za a san abin yi, ki bayar da kuɗi, za a sai binta sudan, da ma'u wardi, sai farin goro zan yi musu wani aiki" "To kamar nawa ka ke ganin zai isa?" Ya ɗan yi shiru ya ce "Ba da dubu goma sha biyar, akwai turarukan da zan haɗa da su ma, da wasu saiwoyi." Ganin buƙatar ta ta biya a baya, ya sanya babu fargabar komai ta amince ta ɗebo kuɗi ta ajiye masa, ta yi masa sallama ta tafi. **** Bayan sallar asuba kallonsa Nana take yi, tana tuna abin da ya faru jiya da daddare. Fuskarsa daina zahiri ba ta yi kama da ta miyagu ba, ta kalle shi daga sama har ƙasa, babu wata alama da take nuna ba mutum bane, a suffar sa ta zahiri. Amma dole tana buƙatar tabattar da waye shi, ta kalli inda yake zaune yana ta fama da radio. Akwai aikin jin radio, sai dai magana ce aiki a gurinsa. "Ina kwana?" Ya ji muryar Nana babu tsammani. Ya ɗago ya kalle ta domin ya tabbatar idan da shi take. Ta sake cewa "Ina kwana?" Ɗaga mata hannu kawai ya yi, tare da jinjina kai. Takaici ya kama Nana, maganar ce dai ba zai yi ba. Kawai ta ga ya tashi ya ɗauki ɗan kurfotin dafa shayinsa, ya zuba ruwa a cikin butarsa. Ya ɗauki wata baƙar leda ya tashi zai bar mata ɗakin. Cikin sauri ta tashi ta ce "Kawo na dafa maka" ya kalle ta ya girgiza mata kai. Ta miƙa hannu za ta karɓi butar, ya janye ya ce "A'a" Ya juya zai fita, kawai ya ji ta biyo bayansa. Ya tsaya ya waiwayo, tana ƙoƙarin tsare shi da ido, amma ta kasa. Ya kuma yin gaba ta sake bin sa. Sai ya fasa fitar, ya dawo ɗakin, ita ma ta biyo shi ta dawo. Ya samu guri ya zauna, yana kallon butar shayinsa yana kallon Nana, da ta maze. Bayan wani ɗan lokaci ya tashi ya fara shirin shiga wanka. Nana ta maze ta ɗauki wayarta tana dannawa. Sai da ya shiga banɗakin, ta bi bayansa da kallo. Hajiya Amina ta kira a waya, cikin ikon Allah kuwa bugu biyu ta ɗaga tana "Amarya kin sha ƙamshi" Cikin jin nauyinta Nana ta ce "Hajiya ina kwana?" "Lafiya ƙalau Nana, ya ki ke fatan kina lafiya? Ina ta kiran wayar ki a kashe" Nana ta yi murmushi ta ce "Sai jiya na ga wayar ne. Ina ta ganin abin alkhairi Hajiya, na gode sosai da sosai Allah ya saka miki da mafificin alkhairi. Allah ya baki abin da ki ke nema duniya da lahira, Allah ya jiƙan magabata na gode sosai da sosai" "Kai Nana kamar wadda na bawa wata duniya, kar ki damu amma yaya ki na ganin babu matsala, ba zai muzguna miki ba? Kuma baya haukan sosai ba zai cutar da ke ba?" A taƙaice Nana ta ce "A'a babu wata matsala. Ina Haidar?" "Haidar sun koma gidansu, ya hana kowa sukuni, kullum sai ya yi zancen ki, babansa ya dawo amma ya kasa sakin jiki da shi, ke kawai yake kira" "Allah sarki, wallahi Hajiya ina kewar Haidar sosai da sosai, dan Allah duk ranar da aka kawo miki shi, ki haɗa ni da shi a waya" "In sha Allah Nana, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, in sha Allah zan kawo miki ziyara har gidan naku" "To hajiya na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi" Suka yi sallama, a daidai lokacin da ya fito daga banɗakin, jikinsa na rawar sanyi. Gashin sa na ta ɗigar da ruwa, murɗaɗin damatsansa, da ƙirjinsa da yake wayam, sai kwantaccen baƙin gashi tun daga ƙirjinsa zuwa cikin sa, shi ne ya banbanta shi da mace, saboda dogon gashin da yake kansa kamar ba namiji ba. Da hanzari ya saka maɗauri ya naɗe gashin kan nasa. Ya zura rigar hannunsa, ya nufi wardrobe ɗin su gadan gadan, sai dai yana taɓa ta ya ja da baya, kamar wanda ya taɓa wuta. Ya ɗago ya kalli Nana, ya nuna mata drower ƙasan wardrobe ɗin. Tasowa ta yi tana kallon wardrobe ɗin. Ta ce "Mene ne?" Ya sake nuna mata wardrobe ɗin, ta durƙusa ta buɗe, sai ga jakar fatar gidan sarkin baka, ta bayyana a saman drower. Ya ƙurawa jakar ido. Ta ɗaga kai ta kalle shi. Da hannu ya yi mata alamar ta ciro jakar. Ta ciro jakar, ba ta ce masa uffan ba, ta canza mata guri, tana fara ƙoƙarin ƙara gazgata Ƙaisar. Ta nemi guri ta kwanta a kan katifa, ta juya masa baya, domin ya shirya a tsanake, saboda yadda ta fuskanci duk a rikice yake. Sai da ta ji motsinsa yana ƙoƙarin ɗaukar butar shayi, ta ce "Bawan Allah yunwa nake ji" cak ya fasa ɗaukar butar, ya tsaya yana kallonta. Ta sake cewa "Ina jin yunwa" magana yake son ya yi mata, amma ya kasa. Sai ya fasa ɗaukar kayan shayin, ya ɗaga labulen ɗakin, ya leƙa ya sake dawowa ya kalle ta amma bai yi magana ba. Ta sake mazewa ta ce "Bawan Allah ina jin yunwa" kallonta ya yi, amma ta ƙi kallonsa. Sai ya tafi gaban wardrobe ɗin su, ya buɗe tasa, ya sake ɗaukko robar dabino lubiya, ya zo ya ajiye a gabanta. Ta kalli dabinon ta ce "Ni ba wannan ba abinci" ta yi maganar tana kawar da kanta gefe, taƙi kallonsa. Fuskarta yake kallo, amma ta maze, ya miƙe ya ci gaba da zagaya ɗakin, kamar mai jiran wani abu. Kallonta yake amma ya ga ba ta da niyyar cin dabinon. Wani irin horn aka yi a gate ɗin, ya juya ya fita daga ɗakin, ya nufi gate ɗin. Tashi Nana ta yi, ta tafi tana leƙawa ta taga. Cikin gidan aka shige da motar, dan haka ba ta ga waye a motar ba. Yana dawowa ɗakin ta kalle shi ta ce "Mutanen gidan sun dawo kenan? Ai da na zata babu kowa a gidan" shi dai bai ce uffan ba, sai dai ya bi ta da ido. Ta koma kan katifa ta zauna, tana danna wayarta. Ƙarar tsayuwar adaidaita sahu suka sake ji, ta ga ya ɗan saki fuskarsa. Habu ne ya shigo da ƙaramin gas cylinder, da kuma kayan abinci. Harshe suka juye, suka fara magana da yaren su. Mamaki ya cika ta, tana ta magana ya share ta, amma yana ganin ɗan uwansa ya yi magana. Amma idan ta tabatta shi ba mutum bane ba, su waɗannan da yake tare da su, su ma ba mutane bane ba kenan?. Habu ya dubi Nana cikin damuwa ya ce "Nana ki yi haƙuri dan Allah, ya ce kin ce yunwa ki ke ji, na je zubo miki abin girki ne, ga abinci ma na zo muku da shi" Nana ta ce "Au dama ni ce ba zai yi wa magana ba? Kar ka damu mun gode sosai ku na ta ɗawainiya da mu" Habu ya ce "Ai dole mu kula da ku, kin auri ɗan uwanmu, amma dan Allah ki din ga haƙuri kin san na gaya miki ba shi da cikakkiyar lafiya ne. Ina kyautata zaton wannan ƙaddarar ce ta sanya mu zuwa Nigeria." Nana ta ce "Na karɓi ƙaddarata, in sha Allah, na miƙa wa Allah lamarina" A nan Habu ma ya karya, ya zauna su ka yi hira da Nana, shi kuwa da ya gama cin abincin sa, ya koma gefe ya yi musu shiru. Shi ma bai wani jima sosai ba, ya tafi. Gaba ɗaya zaman shiru ya ishi Nana, shi ba kula ta yake yi ba, sai dai ta wuni a ɗaki shiru, shi kuma yana waje, yana jin radio da aikin dafa shayi kamar ibada, ko hutawa ba ya yi, har mamaki take yi idan yana gane abin da ake yi a radion. Bayan azahar yana kwance, a ɗakin, radion ta cika wa Nana kunne, ta dube shi ta ce "Dan Allah zan shiga cikin gidan nan, na yi musu sallama, tun da na ga alamar akwai mutane a cikin gidan" ya gyaɗa mata kai kawai. Ta ɗumama ruwa a kan gas, ta shiga ta yi wanka ta fito, sanye da dogon hijjabi. Ta ɗauki kayan da za ta saka, ta koma banɗaki ta canza ta fito. Doguwar riga ta sako, hannunta riƙe mayafin rigar. Ta cire hular kanta, ta tsaya a gaban mudubi tana shafa mai. Abin ka da mace, kuma amarya, sai ta tsaya a gaban mudubin tana gyara fuskarta. Ta tsiyayo humra ta shashshafa a jikinta. Ta janyo drower mudubin, inda yake ajiya kayansa ta buɗe a hankali, ta waiwaya ta kalle shi, ta ga idonsa a rufe, ta ɗauki turaren sa, ta tsiyaya a hannunta, ta shafa a wuyanta. Yana daga kwance yana kallonta, ta ƙasan idonsa. Sai da ta gama tsaf, za ta fita kawai ya yi gyaran murya. Ta tsaya ta waiwayo tana kallonsa. Ya yinƙura ya tashi, ya nufe ta, ta tsaya ƙyam tana kallonsa. Gani ta yi tamkar zai shige cikin ta, babu shiri ta fara ja da baya, sai da ta dangana da jikin bango. Ayshercool 08081012143 30 Zazzaro ido Nana take yi, numfashin ta na neman sarƙewa, saboda tsoro da fargaba. Ya saka hannunsa ya kamo hannunta cikin nasa, wani irin sanyi ya ratso ta, tun daga tafukan hannayenta har zuwa ƙafafuwan ta. Ya kama gefen rigarsa ya goge in da ta shashshafa turare a hannunta. Ya saka hannunsa a gefen wuyanta, nan ma ya goge wanda ta shafa a nan. Na saman rigarta yake kallo, sannan ya kalli idonta. Ta yi tsuru-tsuru a ranta ta ce "Daga ɗan shafa turaren sa, shi ne yake mini wannan tijarar haka" Idonta ta saka kwalli, bakinta kuma ta saka man leɓe mai kala, sai girarta da ta gyara. Ba ta gama zancen zucin ba, ya saka hannunsa ya fara goge man da ta saka a leɓenta. Riƙe hannunsa ta yi za ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kallo da ta rasa na mene ne, babu shiri ta yi tsit. Ya goge leɓenta tsaf. Ya kalli idanunta da suka sha kwalli, ya mayar da hannun sa kan girarta, ya hargitse gashin girarta. Ya zare mayafin rigar da ta ɗora a kanta, ya ciro hijjabin da ta shiga wanka da shi, ya hau saka mata. Kamar ta rusa ihu ta ce "wanka fa na yi da shi, ba ka ga duk danshin ruwa a jiki ba?" Bai amsa mata ba, ya jefa mayafin rigar a kan katifa, ya koma gurin da yake zaune ya zauna. Wani irin takaici ya tokare Nana, kamar ta kurma ihu, saura ƙiris ta ce ta fasa fitar, amma ta tuna zaman shiru za ta zauna ta yi a ɗakin, ko ma shi ya fice ya bar ta. Ta ja takalmanta ta fice daga ɗakin tana haɗe fuska. Fasalin gidan ya yi mata kyau sosai da sosai, sai da ta zagaya ta bayan wata baranda, sannan ta gano ƙofar shiga. Tun daga barandar take ɗan jiyo hayaniya sama-sama. Ta buɗe ta shiga da sallama. Samari ne su kusan biyar a falon, su na kallon ball su na ta hayaniya. Sallamar ta ce ya sanya su yin shiru, suka amsa mata. "Sannunku, dan Allah matar gidan nake nema" Ɗaya daga cikin su mai riƙe da remote a hannunsa ya ce "Tana sama" ya yi maganar yana nuna mata upstairs. A falon saman benen ta tarar da matar, babba ce mai jiki fara tas da ita, tana shan lemo a kofi tana danna remote. Ta amsa sallamar Nana, tana yi mata kallon rashin sani. "Ina wuni?" Matar fuskarta babu yabo babu fallasa ta ce "Lafiya ƙalau, zauna mana ga kujera nan" Nana ta zauna, ta kalle ta ta ce "Dama ni ce matar mai gadinku, da muka tare, na ga tun da muka zo ba kwa nan, sai jiya na ji motsin mota a gidan, shi ne na ce bari na zo mu gaisa" "Allah sarki, sannu ko? Da maigidan ya ce mini buzaye ne" Nana ta ce "Maigidana ne buzun, ni bahaushiya ce" "Ohh Allah sarki, ya sunan ki ne?" "Nana" Ta ce "Ma sha Allah, sannun ki" Nana ta ce "Yauwwa, idan akwai wani aiki ma, idan ki na buƙata, idan bai fi ƙarfina ba, a yi mini magana zan yi in sha Allah" Matar ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai" Matar ta ɗan yi shiru tana kallon Nana. Ta yi mamakin yadda yarinyar mace kamar Nana, ta auri Buzu har yake yawon gadi da ita. Sanin da Nana ta na idan ta koma, zaman tsuru-tsuru za ta yi da wannan kurman mutumin, ya sanya ta ja ta yi zamanta, ta ci gaba da kallon Tv. Matar kuma ba ta ce mata uffan ba. Can Nana ta ce "Hajiya ba ki da 'yan aiki?" "Ina da su, ba na zama ne sosai a ƙasar, duk sun watse mun ma dai samu saɓani ne" "Ke ki ke aikin da kan ki?" "Ni da yara muke yi" Nana ta ce "Allah sarki, idan kina buƙatar aikin ma, zan din ga zuwa ina yi miki" Duk da tana basar da Nana, sai da ta yi murmushi ta ce "To in sha Allah" sai da Nana ta gama kallon, sannan ta tashi ta yi wa matar da ko sunanta ba ta sani ba sallama. Ta sauka ta fita, sai dai tana fita ta yi kiciɓis da shi, sai da ta tsorata, yana tsaye a bakin ƙofar shiga cikin falon gidan, yana jiran ta "Lafiya? Ya na ganka a nan?" Yana ganin ta fito kawai ya yi gaba ya bar ta a gurin. Ba ƙaramin ƙuluwa take yi da wannan dunkun-dunkun ɗin da yake yi ba na rashin magana. ***** Babbar mace ce a ƙalla za ta yi shekara talatin da bakwai zuwa da takwas, hannunta riƙe da waya take kaiwa tana komowa a ɗakin, ta sake kai wayar kunnenta. "Hello Yaya kina ji na? Dan Allah maganar nan da gaske ki ke?" Daga ɗaya ɓangaren matar ta ce "Oho ban tabattar ba, amma kin san babu lallai a yi jita-jita da irin wannan maganar, amma abu mafi sauƙi ki saka lokaci mu je mu tabattar" "Yanzu Yaya idan maganar nan ta tabatta, baban su Imaran ya kyauta mini? A yi auren yarinya ta amma a kasa gaya mini an yi mini adalci a haka? Ba fa shikaɗai yake da hakki a kan yarinyar nan ba" "To yaya za ki yi maijidda? Kawai mu shirya mu je shi ya fi sauƙi" Gyaran muryarsa da ta ji ya sanya ta kashe wayar babu shiri, tana faɗin sannu da zuwa. Ya ƙura mata ido ya ce "Meye haka na ganki wani iri?" Ta so ta jure zuwa ya samu nutsuwa su yi magana ta fahimta, amma ta kasa. Cikin damuwa ta ce "Labari na ji wai an yi wa Nana aure, shi ne nake son in tabattar" Nan da nan ya haɗe fuska tamkar tasowar hadari lokacin marka-marka. "Wato ba zaki fasa kiran tsohon mijinki ba ko Maijidda, ni fa na gaji ba zan lamunci wannan iskancin naki ba na shekara da shekaru" Cikin ƙoƙarin kare kanta ta ce "Ka yi haƙuri, wallahi ba kiransa nake yi ba. Da Yaya nake waya wallahi" "Bani wayar nan" Ta ɓoye wayar a bayanta ta ce "Wallahi ba da shi nake waya ba, Yaya ce" za ki bani ko sai na ɓata miki rai. Ta miƙa masa wayar tana kuka ta ce "Dan Allah baban su Walida, ka bani wayar nan, hankalina ba zai kwanta ba sai na tabattar da gaskiyar maganar nan" Ya tsaya cak yana kallonta ya ce "Allah wadaran halinki, ko kunyar Ubangiji ba kya ji, babu wata Nana da aka yi wa aure, tsohon mijinki ne ki ke bibiya, tirr da halinki" fashewa ta yi da kuka, tana sheshsheƙa mai cike da ƙunar rai. ***** "Zan yi wanka" ya yi maganar yana tsare ta da ido. Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ce "To ka yi mana" Ta yi magana tana ɓata rai, tare da mayar da hankalinta kan wayarta, da ta gano tarin fina-finai a ciki. Tun bayan da Hajiya Amina ta bata wayar, ta nunawa Nasiru, ya karɓi wayar ya fita da ita gurin abokan sa aka yi turi, ba ta taɓa sanin da su a wayar ba. Shiru ya yi yana kallon Nana, ganin ba ta gane abin da yake nufi ba. Kawai ya shiga banɗakin. Ƙofar banɗakin ta bi da kallo, gaba ɗaya ta kasa gane kansa, babu yadda za ayi ace mutumin da yake da taɓin hankali, ya din ga gudanar da al'amuransa cikin nutsuwa. Sai dai kuma wannan shirun nasa ma, yana ƙara tabattar da taɓin hankalin nasa. Duk da ma ba wannan ba, hankalinta ya fi karkata ga son sanin ainihin waye shi. Ya shafe tsawon lokaci a banɗakin, dan sai da Nana ta manta da shi ma, sannan ya fito. Jikinsa sai tsuma yake yi. Ya nufo kan katifar da Nana take kai tsaye, bai ce mata uffan ba, ya zazzageta ya janye bedsheets ɗin da yake shimfiɗe a kan katifar ya duƙunƙune a ciki. Galala ta saki baki tana kallonsa. Lallai babu alamar hankali a nan" ta faɗa a zuciyarta. Sai dai ta lura da yadda jikinsa yake ta tsuma da rawar sanyi. Ga garin babu sanyi sam, ita gumi ma take yi, amma ta ga yana ta tsuma. Ya jima sosai a haka, daga bisani ya tashi tsaye, ya nannaɗe bedsheet ɗin ya ya jefe mata a ka, ya wuce gaban mudubin. "Ya haka, me yasa ka jefo mini?" Waiwayo wa ya yi mata wani mugun kallo, ya juya ya ci gaba da abin da yake yi. Taɓe baki ta yi, ta tashi ta ɗaukko wani zanin, ta shimfiɗa ta zauna. Hannunsa ɗauke da robar mai, ya nufo ta. Ya ajiye man a gefenta, ya zauna ya juya mata bayansa. Ƙuri ta yi wa bayansa da ido, daga bisani ta ce "Me za a yi ne?" Ya ɗauki robar man, ya saka mata a hannunta, ya nuna mata bayansa da hannunsa. A ɗan tsorace ta ce "Wai taɓa ka zan yi?" Ya juyo gaba ɗayansa ya zuba mata ido. Nana ba ta taɓa ƙare masa kallo ba, sai yanzu. A hankali ta fara jin sanyi yana ratsata, bugun zuciyar ta ya fara ƙaruwa. Cikin sauri ta ce "To juya" ya juya mata. Ta ɗaga robar man ta na kallo, duk rubutun jiki da french ne, ba ta iya gane komai ba. Ta tsiyayo man, sai ƙamshi yake yi, hannun ta har rawa yake yi, ta kai hannunta bayansa. Sai dai tana ɗora hannunta ta ji tsigar jikinta ta tashi, sanyi na ƙara ratsa ta. Ta ture gashinsa gefe, ta fara shafa man a bayansa, sai dai tana shafa masa, yanayinta yana canzawa zuwa wani abu, da ta kasa tantance mene ne. Tsayar da hannunta ta yi a guri ɗaya, ta ƙi gaba ta ƙi baya, jin zuciyarta na rayo mata wani abu a game da shi. Haushin kanta ne ya kama ta, kawai ta ja da baya ta haɗe rai. Ya sake waiwayo wa ya kalle ta. Kamar wanda aka yi wa dole ya ce "Sanyi nake ji" Murguɗa baki ta yi, ta ja jikinta lungun katifa, ta yi masa shiru. Ganin ba ta da niyyar sake taɓa shi, ya sanya ya tashi ya nemi guri ya kwanta a ƙasa. Shiru ta yi tana zancen zuci, iya tsawon rayuwarta, ita ba ta taɓa kai hannunta jikin wani namiji tana sane ba. Kuma ba ta taɓa jin abu makamancin irin haka ba, a tattare da wani ba. 'ki shiga hankalinki Nana, kar wannan farar fatar ta ruɗe ki" wata zuciyar ta gargaɗe ta. Guntun tsaki ta yi, ba tare da ta shirya ba. "Ya dai?" Muryar Ƙaisar ta dawo da ita tunaninta. Ta kalle shi, yana ta haɗa wasu abubuwa a cikin kwalabe. "Kai ne ko?" Ta yi maganar a ɗan ƙule. "Na yi me?" Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba. "Ka fi ni sani ai" Ƙaisar ya girgiza kai ya ce "Sanin gaibu sai Allah ai, ban san me na yi miki ba" Nana ta ce "Ka sani" Ya ɗan kalle ta, kawai ya bushe da dariya ya tashi tsaye yana faɗin "Kar ki damu, yanayi ne da bil adama su kan kasance a ciki, ai ba ki yi wani abu ba, ba abin damuwa ba ne ba. Kuma ni bani da hannu a wannan lamarin. Sai dai ina tunatar da ke, kafin ki yi aika-aika ki tabattar da wane ne shi" Banza ta yi masa, ta nufi wata ƙofa da take buɗe. A hankali ta buɗe idonta, tana kwance a kan katifarta, ta kalli gurin da yake kwance, yana nan kamar yadda ya kwanta. Ya dunƙule jikinsa guri guda, jikinsa ko riga babu. Ta shafa jikinta ta ji gumi take yi, amma shi alamu suka nuna sanyi yake ji. Ta yinƙura da ƙyar ta tashi, ta ɗaukko bargonta a saman wardrobe, ta nufe shi. "Ka tashi ga bargo ka rufa" A hankali ya buɗe idonsa, ya kalle ta, kawai ya mayar ya lumshe. Ba ta haƙura ba ta sake cewa ga shi ka rufa tun da sanyi ka ke ji. Ta yi maganar tana ajiye masa bargon. Hankaɗe bargon ya yi gefe a zuciye, yana ƙoƙarin gyara kwanciyarsa. "Me ya sa zaka jefar mini da abu, idan ba ka so sai ka jefar mini, haka ɗazu ma ka jefa mini bedsheet a kaina, ni ka daina yi mini haka. Kawai ya tashi zaune. Me Nana za ta gani, kamaninsa sun koma na tsohon nan da take gani a tare da shi. Ihu ta kurma da ƙarfi ta suma a gurin. ***** Sanye take da doguwar rigar bacci shara-shara blue black, ta yi mata kyau sosai, ga tsohon cikinta, tana gefen gado tana shan abu a cikin kofi. Da sallama ya shigo ɗakin, ta amsa masa, ya zauna a kusa da ita. Ta ce "Ya yi baccin?" Ya ce "Ya yi da kyar, ban da labarin Anty Nana, babu abin da yake yi mini, yana ta biya mini abin da take koya masa. Babu yadda za a yi ta dawo gidan nan ne ta ci gaba da kula da shi?" Ta kwaɓe baki ta ce "Ta ina? Na gaya maka an yi mata aure da buzayen da suke gadin gidanmu" Ya ce "Ikon Allah, to dama buzaye na auren wasu wanda ba irin su ba ne?" Shukura ta ce "Waye ya san musu ma? Abin ne dai ga shi nan" "Allah ya kyauta, ni dai Haidar nake ji, da alama sun shaƙu, wai me ki ke sha a cikin kofin nan ne?" Ya yi magana yana karɓar kofin. Magani ya gani a ciki, ya tsuke fuska ya ce "Wai me yasa ba kya ji ne? Na hana ki shan wannan abubuwan, ya za a yi ki na da tsohon ciki ki din ga shan wannan abubuwan? Sai kin yi wa kan ki illa?" Shukura ta ɓata fuska ta ce "Ba fa da yawa na sha ba, kuma ai duk dan kai nake yi" "Kuma ni na ce miki ina bukatar wannan abin? Fruit bai ishe ki ba me ki ke nema kuma? Kawai sai kin illata mini yaro? Wallahi na kuma ganin kina shan wannan abubuwan sai ranki ya ɓaci" ya tashi ya fice ya bar mata ɗakin. Haushi ne ya ishe ta, kawai ta nemi guri ta kwanta. Girma da nauyin cikin jikinta, bai hanata yin gudun ceton ranta ba, tana gudun tana waiwaye, ga numfashinta na neman barin huhunta, saboda tsananin gajiya. Karo ta yi da wani mutum sanye da farar riga, miƙa masa hannu take yi, tana faɗin "Dan Allah ka taimake ni" Lokaci ɗaya abin da yake cikinta, ya yi wani irin dunƙulewa, ya na danno ta. Cikin gigita ta tsaya tare da durƙusawa a kan gwiwoyinta, tana jin nishi. Mutumin da yake bin ta ya ƙaraso gabanta, ya saka hannu ya cire abin da ya rufe fuskarsa da shi. Cikin tashin hankali ta ce "Daddy" "Ki yi haƙuri Shukura, ni za ki taimaka, ki sadaukar mini da abin da yake cikin ki" Jan jikinta ta fara yi, tana girgiza kanta, cikin kuka da azabar naƙuda take faɗin "A'a Daddy, dan Allah ka bar mini jaririna, na baka tawa rayuwar amma ka bar mini jaririna dan Allah" Ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar rayuwar ki Shukura, yaron nan kawai nake buƙata" Mutumin nan mai farar riga, ya buɗe fuskarsa, sai ta ga doctor Sharif ne. Cikin kuka take ce masa "Dan Allah Doctor ka taimake ni, ka ba shi haƙuri". Bai saurare ta ba, ya durƙusa ya yi mata wata allura, take ta yi wani irin nishi, jaririn ya faɗo. Ya ɗauke shi har mabiyiyar, ya miƙa wa Alhaji Zailani. Alhaji Zailani ya ciro wata 'yar wuƙa, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa, ƙafafuwan sa a sama. Ihu take iya ƙarfin ta, tana yi masa magiya, amma ya ɗaga wuƙar nan zai caka wa jaririn, bai kai ga caka masa ba, ta ji an kira sunanta. Tana ɗaga kai ta ga Nana. Nana ta jefa mata wata sharɓeɓiyar wuƙa, a rikice Alhaj Zailani ya yi kan Shukura, cikin sa'a ta caka masa wuƙar da Nana ta jefo mata. "Shukura lafiya? Me ya same ki? Me ya samu jaririn naki?" Ta buɗe idonta a hankali ta kalli fuskar mijinta da ke ɗauke da matsananciyar damuwa. "Meya faru?" Ya sake tambayarta. Jikinta ne kawai yake karkarwa, tana zare ido cike da matsanancin tsoro da tashin hankali. Ba ta iya yi masa magana ba, sai godiya da ta din ga yi wa Allah a zuciyarta, da ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba. ***** Da safe Nana na ta karkaɗe ɗaki tana gyarawa, ko gaishe shi ba ta yi ba, dama ba amsawa yake yi ba idan ta gaishe shi. Sai dai fes take tuna abin da ya faru jiya da daddare, yadda fuskarsa ta canza baki ɗaya. Sai dai haryanzu tana ji a ranta, sharrin Ƙaisar ne ya sanya take ganin wannan abubuwan a tattare da shi. "Zan yi wanka" ta ji muryarsa tana tsaka da gyara ɗakin. Ta kalle shi ta ce "To banɗakin zan biyo ka ko ya za a yi?" Ta yi maganar cikin tsiwa. Bakinta ya bi da kallo, rasa me zai ce mata ya yi, a wannan karon ma, ba ta gane abin da yake nufi ba, kawai ya wuce banɗakin. Yana shiga ta dira mitar abin da yake yi mata. "Wai zai yi wanka, ko bin sa zan yi na yi masa wankan, ni ban gane ba" Ta ci gaba da aikinta, yana fitowa bai tsaya wata-wata ba, ya sake yaye bedsheet ɗin da ta gama shimfiɗawa ya rufa yana rawar sanyi. A hanzarce ta ɗago a ƙule ta ce "Lafiya, meye haka wai?" Ta yi maganar kamar ta fashe da kuka, saboda a lokacin ta gama sanya zanin gadon. Jin ta tsaya masa a ka, saboda ya ɗauki bedsheet ya sanya ya miƙe, ya watsar mata da shi a gurin. Ya ɗauki kayan da zai saka ya shiga toilet ya canza, ya fito ya bar mata ɗakin. Cikin hantsi ya fita ya zauna ya takure jikinsa, ɗumin ranar yana taɓa shi. Nana ta ci gaba da mita tana ƙara gyarawa. Muryar Habu ta jiyo, ta leƙa ta taga, ta gan su tare a zaune. Yadda Habu ya yi shiru ya nutsu ne, ya sanya ta gane mijinta magana yake yi, amma muryarsa ƙasa-ƙasa, ba a jin tasa sai dai ta Habu ake iya ji. Ta saki labulen ta nemi guri ta zauna, Habu ya yi sallama a ƙofar ɗakin. Ta amsa masa. Ya ce "Na shigo?" "Eh bismillah" sai ta ga ya shigo shikaɗai. Nana ta ce "Ina kwana?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Ya rayuwar?" Nana ta yi murmushi, haryanzu hausar su wasu lokutan sai a hankali, ta ce "Lafiya ƙalau" "Ga wannan" ya yi maganar yana ba ta leda. Jiki a sanyaye ta ce "Malam Habu, abin da ya faru Allah ne ya ƙaddara, wannan ɗawainiyar ta isa haka, kullum sai kun kawo mana Abinci, ga ɗawainiya da ku ke ta yi. Zan fara girki in sha Allah" Ya yi murmushi ya ce "Kar ki damu, ai dolen mu ne mu kula da ke. Kayan miya ne a ciki da sauran kayan amfani. Duk abin da babu, akwai lambata a rubuce a gurin mijin naki, sai ku kira ni" Nana ta jinjina masa kai. Sai kuma Habu ya yi murmushi ya ce "Amm amarya, mutumin fa ya kawo mini ƙarar ki, ya ce ki na yi masa rashin kunya, ki na ɗaga masa murya. Dan Allah kamar yadda na gaya miki ki yi haƙuri da shi dan Allah. A hankali za ki fuskanci yadda za ki zauna da shi, na san abin zai yi miki wahala amma dan Allah ki yi haƙuri hakan tamkar jihadi ne, ke ma Allah ya kawo ki mu yi tare" Nana ta haɗiye maganganu da tambayoyi da ta so yi wa Habu, ta daure ta ce "Hmm ƙara ta ma ya kawo ko? To shikenan na daina" "Ki yi haƙuri amma, yanayin ciwon nasa ne ba ya son hayaniya, shi yasa" Nana ta ce "Babu damuwa in sha Allah, ina son ma na yi maka wasu tambayoyi, amma sai ka kuma dawowa" Gyaran muryar sa su ka ji, Habu ya miƙe. Buzu ya juya yare ya yi masa magana, Habu ya jinjina kai. Ya zo ya wuce ya buɗe wardrobe, ya ɗebo kayansa masu datti, da ya nannaɗe ya bawa Habu. Habu ya karɓa, ya yi musu sallama, ya tafi. Nana ta din ga kallonsa, bakinta fal magana, amma ya ƙi kallonta. "Shi ne ka ce ina yi maka rashin kunya ko? To me na yi maka na rashin kunya? Dama ashe ka na magana ni ce ba ka kulawa ko?" Ya lumshe idanunsa yana kaɗa ƙafar sa. "Idan ba ka yi mini magana, ba zan san na yi maka laifi ba, ko na san abin da ka ke so ba, da wanda ba ka so" ta gama surutunta, ganin ba shi da niyyar tanka mata ya sanya ta kama wani abin. Kayan miyar da Habu ya kawo, ta zauna ta gyara tsaf, ta yi greating ɗin su. Ta ɗora a kan gas. Tana jin yadda yake tari, saboda zafin attaruhu. Ta dafa taliya da miya. Ya din ga bin ta da ido, har ta gama. Ta zuba masa ta ajiye masa komai, ta tashi ta je ta yi alwala, ta dawo ta tayar da sallar azahar. Ta idar ta yi azkar, ta ninke dadduma, ta gan shi ya haɗa gumi, yana cakalar abincin, fuskarsa ta yi jawur, sai gumi ne yake tsatstsafo masa. "Lafiya ya na ga ka na gumi, abincin babu daɗi ne?" Ya ja numfashi ya kalle ta, hannunsa riƙe da cokali mai yatsu. Babu irin tambayar da ba ta yi masa ba, amma bai ba ta amsa ba, har ta gaji ta rabu da shi. A haka ya cinye abincin. Nana ta rasa abin da ya sanya shi haɗa wannan uban gumin. Idonta ne ya sauka a kan wayarta. A take tunanin mahaifiyarta ya ƙara faɗo mata. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta ɗauki wayar tana kallon screen ɗin. Jiki a sanyaye ta buɗe wayar, ta shiga gurin kira, ta shigar da lambobin kamar yadda ta haddace su, cike da fatan Allah ya sa wayar ta shiga. Babu zato babu tsammani, ta ji wayar ta shiga. Gyara zamanta ta yi tana fatan Allah ya sa ta ji abin da take tsammanni. Sai dai akasin haka ta ji muryar namiji, muryar mutumin da ta tsana a rayuwarta. Cikin dakiya ta ce "Baba ina wuni?" "Lafiya kalau wace ce?" Cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah me wayar nake nema" Ya ce "To wace ce ke ɗin?" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baba Nana ce, mamana nake nema" ta yi maganar cikin rawar murya, idanunta na cika da hawaye. "Ai dama na sani, wallahi na sani, na san ba ta fasa bibiyar tsohon mijinta ba, wallahi zan gauraya da ita" A ruɗe Nana ta ce "Dan Allah Baba ka tsaya ka ji, wallahi ba sa waya da Babanmu, lamba ta ce, dan Allah ka haɗa ni da ita ko muryarta na ji, dan Allah.. ƙit ya kashe wayar ba tare da ta gama faɗar abin da za ta faɗa ba. Wata irin tafasa zuciyarta ta din ga yi, cike da ɓacin rai da tashin hankali. Wasu irin hawaye masu raɗaɗi suka fara biyo fuskar ta. Ta ɗauki wayar ta yi jifa da ita, caraf ya cafke wayar. Ya kalli yadda hawaye yake fita daga idanunta. Kawai ya ga ta taso za ta fita daga ɗakin, jikinta yana rawa. Har za ta gota shi, ya danƙo hannunta ya yo baya da ita, yana ƙarewa Ƙaisar kallo da ya bayyana a gefenta yana huci!. Ayshercool 08081012143 31 Bai kula Ƙaisar ba, ya ja Nana zuwa kan katifa, ya zaunar da ita, idanunta a lumshe, har a lokacin kuma fitar da hawaye suke yi, babu ƙaƙƙautawa. Ya taɓa tafukan hannayenta, ya ji sanyi ƙalau kamar an ciro ta daga ƙanƙara. Ya ƙura mata ido yana nazarin ta, a take ya tuno ranar da ta shiga ɗakinsu, tana kiran Haidar, su na haɗa ido ta ja da baya ta ƙwala ihu ta faɗi. Haka jikinta ya ƙandare, ta din ga karkarwa, ya ga wani narkeken baƙin muzuru ya bayyana a ɗakin, yana ta zagaye ta. Ya sauke numfashi, ya sanya yatsunsa biyu, ya danna bayan kunnenta. Ya miƙe ya bar kusa da ita. A hankali jikinta ya daina rawar, ta buɗe idonta, sai dai tun da ta buɗe idon, ba ta tashi daga gurin ba balle ta ci abinci. Ya din ga satar kallonta, amma ba ta tashi daga in da take ba, balle ta ci abinci. Yana son ya yi magana amma ya rasa me zai ce mata. Ta tashi zaune da ƙyar, ta haɗa kai da gwiwa, ta yi kuka mai isar ta. Sai da aka kira la'asar sannan ta tashi ta yi alwala, ta tayar da salla. Bayan ta idar tana zaune ta yi shiru, ya dawo ɗakin, ya duba gurin da ta gama girkin, babu alamar ta ci abinci. "Ba za a ci abinci ba?" Ta ji maganar sa babu tsammani. Ta ɗaga kai ta kalle shi, kamar mai jiran ƙiris, kawai ta sake fashewa da kuka. Ya yi zuru da ido yana bin ta da kallo, bai ce ta yi shiru ba, har ta yi mai isar ta yi shiru. Duk ya damu ganin ba ta ci abinci ba, ya rasa me zai ce mata, ga shi yanayinta ya fahimci rigimammiya ce. Jin motsi a waje ana taɓa gate, ya sanya ya tashi ya rufe fuskar sa, ya fita ya duba waye. Tsayawa ya yi yana kallon su, mata ne su uku, da ƙanan yara sai wani ɗan matashin saurayi. "Sannu malam, ko kai ne mijin Nanan?" Ya tsaya tsuru yana kallon su. "Gurin Nana mu ka zo tana nan?" ya nuna musu ɗakin su. Suka wuce, Ummi tana cewa "Na yi ƙoƙari fa da na iya kawo mu gidan nan" Bayan Jamila ya bi da kallo, jikinsa na ba shi wani abu a game da ita. Wata irin zabura Nana ta yi ta rungume Ummi, ba ta taɓa tsammanin ganin su ba. Ta rungume Jamila cikin farin ciki ta ce "Dama za ku zo ba ku gaya mini ba?" Ummi ta ce "Mu ki bamu guri mu zauna" Nasiru ya ce "Hajiya Anty Nana amarya" daƙuwa ta yi masa ta ce "Gidanku" Ya yi dariya ya ce "Na yi missing ɗin ki sosai" Take ta manta da damuwar da take ciki, ta ware suka hau hira. Ta juye musu sauran abincin da ba ta ci ba, ta ce za ta ɗora musu wani. Ummi ta ce "Ke a ƙoshe muke, ga shi wannan miya ce na ɗan yi miki, tun bayan kawo ki da kwana biyu, na so yi miki, bana jin daɗi ne. Ga ɗan cin-cin da dubulan na yi miki. Ga kuma turarukan wuta da wata maƙwanciyar ku, ta bayar a kawo miki ga humra ma. Sai kuma kaya da na ɗan ƙara sayo miki" Nana ta ce "Allah sarki, na gode sosai da sosai Anty Ummi, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Jamcy ya garin ne?" Jamila ta ce "Uhumm mamaki nake yi, kamar ba ke ce ki ka gama uban kuka ba, an aura miki buzu, amma kalli yadda ki ka ware yanzu" Nana ta yi murmushi ta ce "To ba dole na ware ba, lafiyayyen ɗaki, ga wardrobe, ga katifata ga banɗakina nikaɗai ba takura ga wuta 2hrs ba yankewa" Suwaiba ta ce "Katifa ko abin da ake yi a kan katifar?" Nana ta ce "Duka ɗan sunna ai ba zai ƙi sunna ba Jamila, tun da dan haka ake auren" Ummi ta ce "Dan uban ku da yara a gurin ku ke yi mana batsa" Nana ta yi murmushi ta ce "Ya Baba, ina mama su ba za su zo ba?" Ummi ta ce "Za su zo ne, Baba babu lafiya ƙafarsa ce take ciwo" Nana ta ce "Ciwon ƙafa kuma?" "Wallahi kuwa, ba za ki kira mijin naki mu gaisa ba" Nana ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Ba kula ku zai yi ba, Nasiru ya makaranta" ta karkatar da zancen ga Nasiru. "Makaranta lafiya ƙalau Alhamdilillah" A ƙofar ɗakin ya yi gyaran murya ya tsaya, Nana ta yinƙura ta tashi, ta ɗaga labulen. Babu hijjabi a jikinta, sai doguwar rigar atamfa. Ya miƙo mata leda, ta saka hannu biyu ta karɓa, bai ce mata komai ba, ya juya ya koma bakin gate. Fura da Nono ne kaya guda, abin sai da ya bawa Nana mamaki, ba ta san a ina ya samo su ba. Ta ajiye musu suka dama, suka sha. Jamila ta miƙa wa Nana ɗan ƙaramin flask ta ce "Nana ga mutuniyar ki na yi miki wainar fulawa" Nana ta haɗiyi yawu cikin murna ta din ga yi wa Jamila godiya. Ta ce "Wannan sai dare zan dafa shayi na ci da ita" Suwaiba ta ce "Ashe fa buzu ki ke aure, ba za a gaya miki shayi ba yanzu" Nana ta ce "Kamar kin sani, ni yanzu shayi ai sai dai na koya wasu, kwana muke mu wuni shan shayi babu ƙaƙƙautawa" suka yi dariya. Har magariba su na gidan, sai da suka yi sallar magariba, Nana ta fito har bakin gate ta rako su, sai dai baya nan. Ummi ta ce "Kin ga har zamu tafi, bamu haɗu mun gaisa ba" Nana ta ce "Ina ga yana masallaci" Suka yi sallama, suka tafi Nana ta koma ɗaki. Har cikin ranta ta ji daɗin zuwan su. Ta yi wanke-wanke ta gyara ɗakin fes. Ta ɗaukko flask ɗin wainar fulawar, ta saka a gaba ta fara ci. Ba ta ci da yawa ba, Haula ta yi sallama. Nana ta amsa cikin sakin fuska, duk da ta yi mamakin ganinta a daidai wannan lokacin. "Anty Haula ba ki yi fushi ba? Haryanzu ban fara fita ba, shi yasa ban shigo miki ba" Haula ta ce "Allah sarki, kar ki damu wallahi, ashe baƙi ki ka yi?" Ba tare da Nana ta yi tunanin komai ba, ta ce "Eh, 'yan gidanmu ne su ka zo, bismillah matso mu ci abinci" Aikuwa Haula ta gyara zama ta zura hannu a kwano, ta fara cin abincin. Kafin Nana ta yi loma ɗaya ta yi huɗu da rabi, kafin wani lokaci Nana sai filin kwanon ta gani, Haula na ta suɗar baki saboda yajin wainar. Sai da ran Nana ya sosu, dan kuwa ta so cin wainar nan ta ƙoshi. Labulen ɗakin kawai ya ɗaga ya shigo, Haula ta tashi zumbur. Ta kalli Nana ta ce "Na gode sosai sai anjima" sai da Haula ta fice sannan ya shigo ɗakin. Ya zauna a gurin da ya saba zama, Nana ta ɗaukko ta sa furar da ta ajiye masa, da cin-cin da dubulan a plate, ta nufe shi. "Sannu da zuwa" ya jinjina mata kai. " 'yan gidanmu ne fa suka zo" ta yi maganar fuskarta na bayyanar da annashuwa. Ya gyaɗa mata kai. "Na gode sosai da sosai, da karamcin da ka yi mini, ga taka furar ga kuma wannan" ta yi magana tana tura masa plate ɗin dubulan. Ya saka hannu biyu ya karɓi kofin furar, Nana ta zauna a gefensa, a tsanake yake sha, ya ɗauki cin-cin ya saka a bakinsa, maimakon ya tauna yadda yakamata, amma ya din ga tauna shi a hankali kamar mai tsoron tauna dutse. "Da daɗi?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Nana ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce "Dan Allah ka din ga yi mini magana mana. Haryanzu ban san sunanka ba" ya kalle ta yana ci gaba da tauna cin-cin ɗin sa. "Ka gaya mini sunan ka" ya ajiye kofin hannunsa yana hamma, ya jingina da jikin bango yana lumshe idanunsa. Ta gaji ta ƙyale shi, ta fara shirin kwanciya, ta shiga banɗaki domin kama ruwa ta yi alwalar kwanciya bacci. A sukwane ya miƙe, duk da bacci ya fara ɗaukarsa, kwanon da Nana ta ci wainar nan ya ɗauka, ya jujjuya kwanon ya ga babu komai a ciki. Ya ajiye kwanon, ya koma gurin da yake kwanciya, ya zauna ya yi shiru. Nana kuwa tana saka ƙafarta a banɗakin, ta ganta a cikin wani gida, mai dogon gini, mai ɗauke da ƙofofi daban-daban. Ɗaya daga cikin kofofin ta bi, tana neman hanyar fita, amma da ta shiga sai ta ga ta koma ainihin gurin da take da farko. Tana cikin laluben ƙofar, kawai ta ci karo da Baba, ƙafarsa ɗaya an nannaɗe ta da sarƙa, an ɗaure ta tamau. Da sauri Nana ta nufe shi, cikin tashin hankali ta ce "Baba lafiya kuwa? Me ya same ka haka?" "Ni ma ban sani ba Nana, dan Allah ki kwance mini sarƙar nan, ina jin ƙafata kamar za ta cire, ba na iya bacci" Cikin damuwa ta ce "Ka kwantar da hankalinka, bari na gani idan zan iya kwance maka" Ta durƙusa ta fara ƙoƙarin kwance masa sarƙar, sai dai ta rasa ina ne ainihin gurin da aka ƙulle ƙafar. "Idan ki ka kuskura ki ka kwance masa, ba zai sake taka ƙafarsa ba har abada" Nana ta ɗago tana kallon Ƙaisar. "Dan me za ka ce kar na kwance masa? Ba ka ga halin da yake ciki ba, ko iya taka ƙafar baya yi ba?" Ƙaisar ya ce "Ban gaya miki sai na hukunta shi ba? Har yanzu ba ki yadda mu na cikin mummunan haɗari daga ni har ke ba, a dalilin wannan auren. Dan haka dole shi ma ya ɗanɗana kuɗarsa" Cikin ɗaga murya ta ce "Ƙaisar baban nawa? Ka kwance masa ƙafarsa" kawai tana waiwayewa ta daina ganin Baba. "Idan duniya za ta taru, babu wanda ya isa ya kwance masa ƙafar nan, idan bai yi wasa ba sai ta yi ajalinsa" yayi maganar cikin ɗaga murya. Tamkar mai shirin haukacewa ta ce "Ba zai yiwu ba, wallahi sai ka kwance shi, wai kai wane irin halitta ne da babu ɗigon imani, a zuciyar ka?" Ƙaisar ya ce "Ko ma dai mene ne, abu ɗaya za ki yi ki kwance masa ƙafar nan, wanda kin san mene ne, ba sai na gaya miki ba. Mu ajiye wannan a gefe tukuna, ban san iya adadin lokacin da za a ɗauka kafin ki san ciwon kanki ba, ki daina wasa da rayuwar ki ba. A wannan karon ma an baki abu kin ci, za kuwa ki ɗanɗana kuɗar ki, a nan na nuna miki an tsaface ƙanwar ki, amma ta kawo abu ta baki ki ka ci" Nana ta ce "Idan ma ka nuna mini, da na tashi nake manta komai, kuma ba zan taɓa yarda da maganganun ka ba, yaudarata kawai ka ke so ka yi, domin na amince da mugun nufin ka, kuma har abada ba zan amince ba, ko da ba ma jituwa da su, na san ba za su cutar da ni ba" Ya ce "Shikenan, zamu gani" A hankali ta yi kokarin yin juyi a kan katifar, amma ta ji wani irin azababben fitsari, tamkar mararta za ta yi bindiga, ga wata irin ƙullewa da mararta ta yi har cikin bayanta da ƙafafuwanta. Da ƙyar da dabara, ta tashi ta tafi banɗaki. A zaton ta da ta yi fitsarin shikenan, za ta ji marar ta saki, amma babu abin da ya canza. Da bin bango ta fito ,ta dawo kan katifar ta kwanta. Bacci ne a kanta, amma wani irin azababben ciwon mara ya turnuƙe ta. Yana kwance yana jin nishinta sama-sama, tun farkawar ta da shigarta Banɗaki, duk a kan idanunsa. Murƙususu ta din ga yi a kan katifar, tana numfarfashi. Rabonta da ciwon mara mai irin wannan azabar, tun farko-farkon fara period ɗin ta. Da idan ta fara sai an kai ta chemist an yi mata allurai. Daga baya abin ya ragu sosai, amma na yau kam, ba ta taɓa makamancin irin sa ba, ji take tamkar ba za ta wayi gari ba. Ko na minti ɗaya ciwon baya lafawa, ga shi ya haɗe mata da ciwon ciki, da na ƙirji kamar za ta bar duniya. A duƙe ta sake komawa banɗaki ta saka pad. A haka ta wayi gari, cikin mawuyacin hali, ta yi kukan ta gaji. Ta saukko daga kan katifar ta kwanta a ƙasa amma babu afuwa. Ko sau ɗaya bai ce mata sannu ba, da gari ya yi haske ma bar mata ɗakin ya yi, saboda yadda kukanta ya cika masa kunne. Tamkar za ta haihu, haka ta fita daga hayyacinta, gaba ɗaya ta manta da batun ba itakaɗai ce a ɗakin ba, ta cire kayan jikinta, ta bar vest da underwear. Rashin tanka matan da ya yi ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba. Can amai ya din ga taso mata, ga wata irin gudawa ta azaba da fitar ta kawai, yake ƙara gigita ta saboda sai cikin ya haɗu ya ƙule da marar sannan take yin ta. Ga fitarta tamkar tana zawon wuta haka take ji, ta ga duniyar tana juya mata, ta din ga salati tana ambaton Allah. Tun tana iya zuwa banɗakin a duƙe, ta koma rarrafe. Ta din ga wani irin amai, mai wari da ƙarni. Idanunta suka yi zuru-zuru, kamar ta yi wata da watanni tana rashin lafiya. Ta kwanta ta yi rub da ciki, ta lumshe idonta. Ta ji an ɗagota. Sosai ya ɗago ta ya haɗa ta da ƙirjinsa. Babu rawani a kansa, ya kwance gashin kansa, ya sauka a kan kafaɗarsa. Suna haɗa ido, ta sake fashewa da kuka, saboda ta ji zafin rashin kula ta da ya yi balle ya yi mata sannu. Ya kai dogwayen yatsunsa ya share hawayen da yake fitowa daga idonta. Ta saka hannu ta ture hannunsa, da yake share mata hawayen. Ya kama bayan hannunta ya kai bakinsa ya sumbuta, ya ɗago ya ƙura mata ido, yana matsa hannunta a hankali. Zuba masa ido Nana ta yi, sai ta ga kamar ba shi ba. Ya sake kai bakinsa goshinta ya sumbaci goshin nata. Ta sake fashewa da kuka, ya haɗa goshinsa da nata ya ce "Shhhhh" Gabanta ya faɗi, sai da ta razana jin ya ɗora hannunsa a kan marar ta. A hankali ta fara jin releif, daga wannan matsanancin ciwon da take ji. Bai ɗauke goshinsa daga nata ba, numfashin sa da yake shiga nata, jikinta ne ya saki ya mutu murus, ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. A hankali ta fara jin bacci yana ɗaukar ta. ***** Su Jamila kuwa bayan sun dawo daga gidan Nana, Baba ya tambaye su ya suka baro ta. Suwaiba ta ce "Tana nan lafiya kalau, ta ce a gaishe ka" "Ina amsawa, ya gidan nata akwai abinci kuwa?" Nasiru ya yi farat ya ce "Baba ɗaki dai, a ɗaki ɗaya take da banɗaki, amma akwai abinci a ɗakin. Har mijinta ya kawo mana fura da Nono". Baba ya ce "Ko ma dai a rami suke ba ɗaki ɗaya ba, ai ita ta jiyo, tun da Allah ya nufi ya rufa mata asiri, ya bata miji na gari na rufin asiri ta zaɓi ta tonawa kanta asiri, yanzu ta ƙare a tantalbatete" Jamila dai kawai fatan ta, Allah ya sa ta yi nasara a kan Nana. Babu kunya Mama ta saka Nasiru a gaba, tana yi masa tambayar ƙawaƙwaf da son sanin halin da Nana take ciki na daɗi ko akasin haka. **** Bangaren Shukura, duk da ta kan yi mafarkai na ban tsoro barkatai, amma bai fiye damunta ba, wasu lokutan da ta farka ma shikenan, mussaman idan tana da ciki ta fi irin wannan mafarkan. Amma a wannan karon ta kasa mantawa da wannan mafarkin da ta yi, a cikin jikinta take jin tsoro da fargaba a kan mafarkin. Duk da ba ta iya gaya wa Sagir abin da ta gani a mafarki ba, kawai ta ce masa mummunan mafarki ne, ya yi ta kwantar mata da hankali, da tabattar mata da mafarki ba gaskiya ba ne ba. Sai dai jin abin take yi, tamkar ma ya riga ya faru ne, ko kuma yana daf da faruwa, haka kurum sai ta ji gabanta ya faɗi ta razana. **** Tare da su Habu ta hange shi zaune kan wani ƙaton carfet fari tas, a cikin sahara , suna ta shan shayi su na hira cikin nishaɗi, gaban su dabino kala-kala a cikin tasoshi, yana cikin su ba ya magana sai murmushi. Ƙyam ta tsaya tana ƙare masa kallo. Karaf ya ɗago kai suka yi ido huɗu. Ya yinƙura ya nufo ta yana murmushi. Ta kawar da kanta gefe ta haɗe rai. Bai ce mata uffan ba, ya rungume ta yana ci gaba da murmushi ya ce "Ya aka yi ne?" "Ni rabu da ni, bayan ka ƙi yi mini sannu" ta yi magana cikin shagwaɓa. "Tuna dai, na yi miki fa, to yanzu ya jikin naki, me ki ke ji?" "Ba komai" "Kin tabatta?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. Ya zagayo da hannunsa, ya ɗora a kan mararta, ya sunkoyo daidai kunnenta ya ce "Hmm haka ne, na ji da sauƙi, na yi uzuri a wannan karon, amma idan aka ƙara zan ɗauki mataki" Nana ta ce "Me aka yi da zaka ɗauki mataki?" "Komai ma" Ta yi murmushi ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce "Har yanzu ba ka gaya mini sunan ka ba" Ya yi dariyar da ta ƙara masa kyau, ya ce "Sunana ki ke son sani?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Cikin raɗa ya ce mata "BUZU" "Buzu" ta maimaita a hankali tana buɗe idonta. Shiru ta yi tana jin mafarkin da ta yi a ƙwaƙwalwarta, sai kuma abun da ya faru da ya rungume ta ɗazu, ya fara dawo mata. Ta nutsu sosai ta ga shi ma a mafarki abin ya faru. Ta ƙarewa ɗakin kallo, babu kowa a cikin sa sai ita kaɗai. Sai dai ta ji mararta ta daina ciwon, ta tashi ta ɗora ruwa ta yi wanka, ta gyara jikin ta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga shi ta kasa cin abincin. Dabinon da ya taɓa bata ta ɗaukko ta hau ci. Bayan sallar magariba, ya shigo ɗakin da leda, kai tsaye ya tafi kusa da ita ya zauna. Ko kallon gurin da yake ta ƙi yi, saboda ta ji haushin yadda ya kasa kula ta duk wannan azabar wahalar da ta sha. "Ki ci" ya yi maganar yana ajiye mata ledar. Murguɗa baki ta yi ta ce "Ba na ci" ya yi shiru yana kallon ta. Ta kawar da kanta gefe tana ci gaba da ƙunƙuni. Ƙarshe ma ta tashi ta koma can gefe ta yi zamanta. Ta ɗago ta ce "Ka ci ni na ƙoshi, ba zan iya girki ba, ba na son ƙamshin abinci" kawai ya yi shiru bai ce komai ba. Ta kunna kallo a wayarta, tana yi tana cin dabinonta. "Salamu Alaikum" suka ji ana sallama a wajen ɗakin. "Wa'alaikum salam warahmatullah. Viens" ta ji ya amsa, ganin abin ta yi banbarakwai. Habu ne ya shigo da sallama fuskarsa ɗauke da damuwa. Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Hankalina duk a tashe, ya kira ni ya ce ba ki da lafiya, ba ki ci abinci ba tun safe" Nana ta waiwaya ta kalle shi, ya maze abin sa. "Ta ina ya gaya maka?" "Ta waya" Habu ya amsa mata. Ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Abin da ma bai ce mini sannu ba, kuma yana kallo na kusa mutuwa" Habu ya yi murmushi ya ce "Amma ya damu sosai ai, tun da ya kira ni kuma ya saka na tafi neman abin da za ki ci." Ya ajiye mata ledar ya ce "Ga abin da ya ce na sayo miki" Ta ce "Ni idan bai ce mini sannu ba, ba zan ci ba" Habu ya kalle shi yana murmushi, ya yi masa magana da french. Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce "Na faɗa ɗazu" "Da yaushe?" "Ki na bacci" Mamaki ne ya cika ta, jin ya yi doguwar magana, dan haka ta yi yinƙurin jan maganar. "Dama mutum ya san abin da ake yi ne, idan yana bacci, ni na ƙoshi" "Sannu" ya faɗa a taƙaice. Habu ya ce "Lallai abin mamaki, abin ya burge ni, ga kayansa nan an wanke an goge, tun da jikin naki da sauƙi, Alhamdilillah ni zan tafi" Nana ta ce "Mun gode sosai, ka gaida gida" "Allah ya sauwwaƙe ya ƙara lafiya" bayan tafiyarsa Nana ta ci gaba da kallo, ba tare da ta taɓa ledar da Habu ya kawo ba, balle wadda ya shigo da ita. Babu tsammani ta ji an fizge wayar hannunta, sai da ta tsorata, a fusace yake kallonta. "Ki ci abinci" ya faɗa a hasale. Murmushi ne ya so kufce mata, amma a zahiri sai ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka. Ya janyo ledar da ya fara shigowa da ita, ya buɗe ta kankana ce a ciki. Sai dai ta sha mamaki da ya buɗe ledar da Habu ya kawo ta ga gasashshiyar kaza. Ita dai ta san tsakiyar wata ne, a ina suke samo kuɗin da suke wadaƙa haka?" "Ci" ta kuma jin muryarsa. Sai kuma ta yi tsuru-tsuru ganin yadda ya yi mata kwarjini, saboda ya kafe ta da ido. Kamo hannunta ya yi ya ɗora a kan kankanar ya ce "Ci" kamar mara gaskiya ta ɗauka ta kai bakinta. Duk da gefe guda hankalinta na kan kazar nan, har da haɗiyar yawu, saboda sai tururi take yi ga ƙamshi. Ya tashi ya ɗauki kofi, ya tsiyayo shayi, a cikin butar shayinsa, ya zo ya ajiye a gefen sa. "Ki ci" ya kuma maganar yana zaro mata ido. Ba shiri ta tattarata nutsuwarta, duk santa da kazar, kasa sakin jiki ta yi ta ci, saboda tsoron yadda ya tsare ta da ido, sai dai tana iya hango tausayi da damuwa a cikin idanun nasa. "Na ƙoshi" ta faɗa a ɗan tsorace. Ya ɗauki ɗan ƙaramin kofin da ya zuba shayi, ya miƙa mata, a zaton ta shayi ne, sai dai tana sha, ta ji tamkar ta haɗiyi wuta. A take yanayinta ya sauya ta ji duniyar ta fara juya mata! Ayshercool 08081012143 Page 32 Gani ya yi ta rintse idanunta, jikinta ya fara karkarwa, mamaki ne ya kama shi, ya duba cikin kofin ya ga shayi ne a ciki. Ya kai bakinsa ya sha, shi bai ji komai ba. Murƙususu take yi, a galabaice tana jin tamkar ana yayyanka kayan cikinta, ta yi wani yinƙuri sai ta fara aman jini mai yauƙi. Ta ɗauki lokaci tana yi. Ta ɗaga kai da ƙyar, ta ga Buzu a tsaye a kanta, kafin daga bisani ya rikiɗe mata zuwa wannan tsohon. A razane ta fara ja da baya. Ya ja da baya ya buɗe bakinsa, zai fara feso mata wuta, Ƙaisar ya bayyana yana wani irin huci. Tsohon ya buɗe bakinsa yana dariya mai razanarwa, hayaƙi na fitowa daga bakinsa, ya ce "Na sani, na san za a rina, ta wannan hanyar ce kaɗai zan hukunta ka Ƙaisar" Cikin tsawa Ƙaisar ya ce "Kuskure mafi girma da zaka aikata, shi ne cutar da yarinyar nan, cutar da uwar gijiyata tamkar cutar da ni ne, dan haka ni da kai muke wannan rigimar babu ruwanta, domin babu ta yadda za a yi ta biya bashin da ba ita ta ci shi ba" "Ƙarya ne, sai ta biya shi, ita ce za ta biya ka sanya wannan a ranka. Ka fi kowa sanin ba ma yafiya, ba ma yafe bashin gaba, sai ta biya wannan bashin" ya ɗaga sandarsa ya nuna Nana da ita, amma cikin zafin nama, ta ji an yi sama da ita an watsar a guri ɗaya. A hankali ta ja jikinta tana tari, ƙaisar ya bayyana a gabanta, cikin ɓacin rai ya ce "Ki sanya a ranki ba a yi komai ba, ƙalubale da tarkuna marasa adadi mun din ga faɗa musu kenan, idan mun tsallake wani, wani sai mun faɗa masa" Nana ta ɗago kanta a galabaice ta kalli Ƙaisar ta ce "Wai dan Allah waye wannan tsohon? Me na yi masa, Ko shi ne na aura a suffar mutum ne?" "Sanin waye shi, ba shi da wani amfani a gare ki. Ki yi ta kanki da rayuwar ki kawai. Ko dai ki bar wannan auren mu tsira baki ɗaya, ko kuma yanzu mu ka fara wahala". Nana ta girgiza kai ta ce "Sanin waye shi yana da amfani a gare ni, waye shi? Meye alaƙa ta da shi da yake tsorata ni, laifin me na aikata masa yake iƙirarin sai na biya? Da wace hujjar zan kashe auren nan? Ko har ka manta irin ƙalubalen da na keto?" Shiru Ƙaisar ya yi mata yana karkaɗe rigarsa, har ta buɗa baki za ta yi magana, ta jiyo sautin wata ƙara a bayan wata ƙofa, kuma ta ji tamkar ta san muryar da ta yi ƙarar. "Ihun me nake ji haka?" "Je ki duba mana" ya bata amsa yana yin gaba, ya nufi kofar da sautin ƙarar yake. Yana shiga Nana ta rufa masa baya, sai dai ta yi turus da ta ga Jamila a ɗaure a jikin wani itace, jikinta babu kaya, fatarta tamkar ta ƙone, ga wasu zarurruka da aka saka, aka ɗaɗɗaure ta da su. Hankali tashe Nana ta ce "Kai Jamila, me ta yi maka? Meya same ta haka?" Ƙaisar ya ce "Me ta yi mini ki ke tambaya? Me ya faru bayan kin ci abincin da ta kawo miki? Idan Alhaji Zailani zai kassara yaran da ya haifa a cikin sa, saboda duniya ke me yasa ki ke tunanin dan kun haɗa uba ɗaya da ita ba za ta cuce ki ba? Dole ta karɓi hukuncin abin da ta aikata, ko da kuwa ya kama na kashe ta ne. Nana za ta yi magana ta ji ana taɓa fulon da take kai. Ta buɗe idonta ta ga wani irin matsanancin duhu, babu alamar haske ta ko ina. Ta yinƙura ta tashi zaune, tana faɗin hasbunallahu wani'imal wakil. Ta miƙe tsaye tana laluben hanya, ganin duhun na ƙara tsananta. Walƙiya aka yi mai tsananin haske, da ya gauraye ɗakin, ya bayyana tsaye da sandarsa yana kallon Nana. Rikicewa ta yi ta saka ihu. ta zabura za ta kasa da gudu. Tun da ta tashi tsaye a kan katifarta yake kallonta. Sai da ta yi ihun nan, ta nufi hanyar waje, ya miƙe da azama ya riƙe ta. Fizge-fizge ta hau yi cikin matsanancin tsoro da razani. "Me ya faru ne?" Ya yi magana cikin nutsuwa da kamala. Fashewa ta yi da kuka, cikin rawar murya ta ce "Tsoro nake ji, dan Allah ka daina tsorata ni" "Me na yi miki?" Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da damuwa. Ta ɗaga kai ta kalli kamilalliyar fuskar sa, ya lumshe idanunsa ya buɗe a kanta. Ta sunkuyar da kanta tana jin yadda sanyi yake ratsa ta, zuciyarta take bugawa, jikinta sai tsuma yake yi. "Zo ki kwanta" ya yi maganar yana janyo hannunta, zuwa kan katifa. Kallonsa take yi, tana tunanin waye shi? Me yake faruwa da ita, ko dai ta tabatta Ƙaisar ya fara burkita mata hankali ne, ta fara haukan da gaske?. Ya zaunar da ita a kan katifar ya ce "Yi bacci" ya yi maganar yana nuna mata shimfiɗar. Duk da tana cikin tsoro da damuwa, bai hana ta mamakin yadda yau yake magana ba. Ya sake cewa "Ki yi bacci mana" Ta girgiza masa kai ta ce "A'a" Ya ce "Me yasa?" Cikin damuwa da razani ta ce "Idan na yi bacci tsorata ni za ka yi, tsoro nake ji" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye. "Ni ba na tsorata ki, ba abin da na yi miki" Ya saka hannunsa, ya goge hawayen da yake zubo mata, a hankali ya fara hura iskar bakinsa a kan fuskarta. A hankali jikinta ya fara sanyi, gaɓoɓinta duk suka saki, wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. **** Cike da mamaki, Hajiya Amina take kallon Alhaji Zailani ta ce "Amma yarinyar nan a gidan nan ta yi mana aiki, har murna ka ke yi yadda ta kula da Haidar, mene ne a ciki dan na je na ga inda take na yi mata Allah ya sanya alkhairi?" Alhaji Zailani ya fututtuke fuska ya tsuke fuska ya ce "Na ce ba za ki je ba, ba dai raino ne ba, ta yi ta gama, dole ne sai kin yi hulɗa da ita? Shegen jajibe-jajibenki na tsiya, ki kwaso wa kanki wata masifar?" "Amma Alhaji kai ka ke faɗar haka da kanka? Duk yadda ka ke da taimakon al'umma, da son mutane kai ne kuma mai cewa ina jajibo mutane, haba... "Ya isa Amina, na ce babu inda za ki je" Hajiya Amina ta yi murmushi ta ce "Shikenan, an wuce gurin" Ya fice fuuu ya bar mata ɗakin, nasa ɗakin ya wuce, ya zauna a kan gadonsa ya yi shiru. Ya rasa ta ina yakamata ya ɓullowa lamarin nan, ammma ko ta halin ƙaƙa yana buƙatar Nana. Saboda yadda ɗari bisa ɗari ya yi amanna da samun biyan buƙatar sa ta hanyar ta. A wannan karon ma sai da ya tsinewa Baban Nana, dan shi ne silar wargaza komai. ***** Jamila ce zaune a ɗakin Mama tana ta uban kuka, saboda yadda ta wayi gari da wasu irin ƙuraje, masu ƙaiƙayin tsiya da ta sosa sai su kwailaye kamar ta ƙone, ga wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon kai da take yi. Gaba ɗaya mama ta rikice, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ta rasa yadda za ta yi da Jamila, a saka mata kaya su tafi asibiti abu ya gagara. Ga Baba shi ma yana ta fama da ciwon ƙafa, sai sayen man zafi da diclofenac yake yi, amma abu ya gagara kullum kamar turi, ji yake yi tamkar an ɗora masa dutse a kan ƙafafuwan nasa. "Ni na rasa yadda zan yi da wannan jarabar, Jamila anya ba Nana ce ta yi miki wani abin ba, wannan wane irin abu ne?" Nasiru ya ce "Kai wallahi Nana ba ta yi mata komai ba, hira fa kawai aka yi da cin abinci" Baba ma ya ce "Yarinyar nan dai ba ta ma gidan nan, balle a ce ko ita ce, dan Allah a daina wannan maganar ma" Haka Jamila ta wuni, ko ruwa ta sha sai ta yi amai, ga jikinta ya daina yi mata ƙaiƙayi sai ma wani irin zafi" Hajiya Sa'a ce a zaune da jajayen kaya, gaban malaminta. Ransa a ɓace ya ce "Hajiya Sa'a na gaya miki a din ga bin komai a hankali, ki daina gaggawa. Yarinyar nan ba za ta taɓu ta sauƙi ba. Aljaninta ya kama ɗaya daga cikin manyan 'yan aikenmu, da ki ka yi amfani shi, ya saƙale shi a jikin kurwar yarinyar ki, yana azabtar da shi ta gangar jikinta, wannan ba dai-dai ba ne ba. Da kin sani a cikin ƙanan jakadunmu ki ka haɗa ta da wani. Amma kin haɗa ta da babban hadiminmu, ya yi masa illa" Cikin damuwa ta ce "Tuba nake, a yi mini afuwa, amma yanzu mene ne abin yi?" "Abin yi, dole a je a ba shi haƙuri, a saurari sharuɗɗan da zai gindaya kafin ya saki kurwar yarinyar, dama aljanin a cikin kurwarta yake ai" "Yanzu shikenan buƙatarmu ba za ta biya a kanta ba kenan?" "Za ta biya, amma akwai lokaci. Shi ma yana kare ta ne saboda ta sa buƙatar, amma akwai wani abu da zai ɗauke masa hankali a 'yan kwanakin nan, zamu iya amfani da wannan damar, mu yi abin da muke so" Hajiya Sa'a ta jinjina kai cike da gamsuwa. ***** Da safe babu kowa a ɗaki sai Nana, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta gama ta buɗe ƙofar ta fito, ta ganshi yana gyara mata shimfiɗarta, ya karkaɗe mata. Ya ɗauki tsintsiya ya fara share ɗakin. Ya ɗago suka haɗa ido, ya kawar da kansa ya ci gaba da shararsa. Saboda daga ita sai zanin wankanta ta fito, dan ba ta san yana ɗakin ba. Nana ta ƙaraso ta ce "Ka bari, zan share ɗakin, bari na shirya" "Ba komai, ki huta ba kya jin daɗi" ta ɗan ware ido, jin ya yi magana. Ta numfasa ta ce "Ina kwana" "Wane kwanan?" "Gaishe ka na yi fa" ya ɗago ya kalle ta ya mayar da kansa ya cigaba da shararsa, ya gama ya kwashe ya je ya zubar. Ta shirya yana gefe yana aikin shan shayi, yana haɗawa da dabino yana ci. Ta bubbuɗe kazar da Habu ya kawo, ta ɗumama, ta ɗibi miya ta haɗa su ta ƙara dafawa, ta zuba ta ajiye a gabansa. Ya girgiza kai ya ce "Naki ne, ki ci" Ta ce "Ai na ci, kai ba ka ci ba" Ya girgiza kai ya ce "Na ƙoshi" Nana ta sake tura masa kwanon ta ce "A'a ba ka ƙoshi ba, dan Allah ka ci" ta yi maganar tana saka masa cokali a kan kwanon. Ya kama cokalin, ya ɗan yagi kaɗan zai kai bakinsa ya ce "Bismillah" Nana ta ɗaga kai ta kalle shi da mamaki. Jiki a sanyaye ta ce "Na san wataƙila ina yin wasu abubuwa, da za ka kasa gane kaina, kamar ba ni da hankali wasu lokutan. Na san babu lallai an yi maka bayani, ina fama da rashin lafiya ne" ta yi maganar tana wasa da yatsun hannunta. Ya ce "Aa yau ba ki yi rashin lafiya ba, kin warke ai tun jiya" sai ta ga kamar bai fuskanci abin da take nufi ba. Ta tsura masa ido, tabbas ma sha Allah, kyakyawan ne, fari ne mai dogon hanci sosai da ɗan siririn sajen sa, kuma a nutse yake. Babu babban abin da yake ɗaukar hankalinta game da shi, bayan nutsuwar sa, sai wannan kyakyawan dogon gashin da yake da shi, tamkar mace. Duk da ta kasa tantance abubuwa da dama a kansa, amma zuciyarta na ɗauke da tarin tambayoyin da take fatan bakinta ya furta. Ya ɗago shi ma ya tsare ta da nasa idanun, yana tauna a hankali. Ta sauke nata idanun ta ce "Amm ban san sunanka ba haryanzu ba fa" Kamar ba zai yi magana ba ya ce "Zan sha ruwa" tana mamakin dalilin da ya sanya yake kaucewa wannan tambayar har sau biyu, sai ta ƙyale shi, ta ɗaukko ruwan ta ba shi. "To ka bani wayata, na yi kallo" "A'a" ya furta yana tashi tsaye. ya tafi gaban mudubi, ya fara shiri. Yana tsaka taje gashin nasa, ya hango Nana ta cikin mudubin, tana kallonsa. Ya ɗaukko comb ɗin ya nufo Nana, da sauri ta sunkuyar da kai. Ya zo gabanta ya miƙa mata comb ɗin, ta tsaya tana kallon sa, ya ƙara miƙa mata. Ta saka hannu ta karɓa, ya gyara zamansa ya juya mata baya, ya ɗan yo baya da kansa. Ta yi shiru tana kallon kan nasa. "Ki taɓa, na ga ki na so" wata irin kunya ta kama Nana, haushin kanta ya kama ta, yadda ta bari har ya iya gane gashin kansa yana burge ta. Ta dafa kafaɗarsa, da nufin ta tashi, kawai ta gansu a wani ƙasaitaccen ɗaki na alfarma, maimakon ɗakin su. Ta kalli jikinta, ta ganta sanye da wasu kayan na daban. Hannunta dai riƙe da comb ɗin. Duk yadda ta yi ƙoƙarin yin magana ta kasa. Ta saka hannu, ta fara taje lallausan gashin nasa, ta gama ta tufke masa kamar yadda yake yi. Ya miƙe tsaye ya juyo ya kalle ta, ya kama hannunta ya sumbata ya ce "Allah ya yi miki albarka" Kamar wadda aka jonawa shocking ta zabura, ta ga ɗakin ba kowa, ga dai kwanukan da ya ci abinci, ya wanke ya ajiye mata. Ta tashi tsam ta je ta leƙa ta taga, ta hango shi a zaune a kan kujera, a gefen gate ya kara radio a kunnensa, gefe ga butar shayin sa. Ta dafa bango ta jingina a hankali, hawaye ya fara ziraro mata, a hankali ta ce "Ka yi nasara ƙaisar, ka burkita mini ƙwaƙwalwata fiye da baya. Na fara hauka, ba na iya tantance zahiri, tunani da mafarki. Ka cutar da ni" ta ƙarasa maganar tana sheshsheƙar kuka. Muryar Ƙaisar ta ji tana amsa kuwwa a ɗakin. "Ba ni ba ne, ko zan saka ki hauka ba yanzu ba, da sauran lokaci, ina ƙara baki lokaci ne. Abin da na yi ta yi miki gargaɗi a kai ne" "Allah yana tare da ni, ba zan bayar da magani ba Ƙaisar, ba na buƙata ka ƙyale ni na yi rayuwata dan Allah" ta ƙarasa maganar wani kukan yana kufce mata. "Nana" ta ji muryarsa a bazata. Da sauri ya sauke rawaninsa a kiɗime ya ce "Meya faru?" Kasa magana ta yi, ta ci gaba da kuka. Cikin damuwa yake kallonta, ya rasa abin da zai ce mata, ga shi da gaske kukan take mai tsuma zuciya. "Na yi wani abu ne?" Ya furta yana kallonta. Ta girgiza masa kai alamar a'a. Ya sake cewa "Ba lafiya ne?" Ta sake girgiza masa kai. Ya saka hannu ya dafa kafaɗarta, a take wani irin sanyi ya shige ta, har ƙafafuwanta. Babu tsammani ya haɗa ta da ƙirjinsa, duk da tana jin yadda zuciyarta take harabawa da sauri, amma ta yi shiru ba ta motsa ba, ba ta tunanin a rayuwarta, akwai wanda ya taɓa ba ta wannan damar. Maimakon ta daina kukan, sai ta sake fashewa da sabon kuka, sababbi da tsofaffin damuwoyinta duk suka taso mata. A hankali ta ji ya zura hannunsa a cikin nata ya riƙe. Duk da a ƙasan zuciyarta, tana jin mafarki ne, amma ta ji daɗin samun damar zubar da hawayen nan da ta samu. ***** Tamkar zai tashi sama, haka yake bala'i yana kumfar baki. "Ai dama na sani, wallahi haryanzu tana son tsohon mijinta, kuma tana magana da shi ta waya, ina da cikakkiyar shaida a kan hakan" Wata babbar mace da fuskarta ke ɗauke da damuwa ta ce "A'a Iliyasu, ba na tunanin Mai jidda za ta yi haka" "Au goya mata baya za ayi ma kenan? Ina da cikakkiyar shaida, ba na son mutuncinta ya zube ne kawai saboda 'ya'yana" "A'a ba goya mata baya zan yi ba, amma ka yi haƙuri dan Allah" "A'a a yi magana a buɗe, idan tsohon mijinta take so, to ta koma gurinsa ba dole" Maijidda na gefe tana ta sharɓar kuka, tamkar ranta zai fita, ya gama bambamin masifarsa ya fice daga gidan. Matar ta dawo da hankalinta kan Maijidda ta ce "Wai maijidda abin da Iliyasu ya faɗa gaskiya ne? Ana idar da sallar asuba fa ya kira ni a waya ya ce lallai na zo na ji abin da ki ka aikata" Cikin kuka ta ce "Wallahi Adda ba a yi haka ba, roƙonsa kawai na yi ya bani dama na je na ga halin da yarinyata take ciki, an ce mini an yi aurenta, amma ban sani ba, ko ba komai Nana da Imaran su ma yarana ne, na rasa irin wannan abu ƙiri-ƙiri an raba ni da yarana" Adda ta ce "To ke mai jidda ban da abinki, ba a gurin babansu suke ba? Ko a kan yara biyu sai ki salwantar da aurenki, da yaran nan shida saboda guda biyu ne?" Ta ɗago jajayen idanunta ta ce "Adda su ma biyun ni na haife su, ba su da kama ta, su na buƙata ta, shekara goma sha ina tattalin wannan auren, duk da ƙiyayyar da yake nuna wa 'ya'yana amma wallahi zuciyata na Kano tare da Nana da ɗan uwanta" "Aikuwa sai ki yi haƙuri, Allah ya ƙaddara abin da zai riga ya faru. Yanzu ki bari zan shirya da kaina, ki kawo abin da ki ke da shi da ki ka ajiye saboda aurenta, mu haɗa a kai mata ke dai ki yi haƙuri da zuwa, zuwa lokacin da zai saukko. Bari na kira shi a waya" Adda ta kira Iliyasu, sai da ta ta tsinke ta sake kira, sannan ya ɗaga. "Dan Allah malam Iliya ka yi haƙuri, ita ma ta ce a baka haƙuri, ba za ta sake ba" "A'a ai na daɗe ina fuskantar take-takenta ne, kuma wallahi ba za ta sake riƙe waya ba, kuma wallahi ta sake ta taka zuwa ƙafarta zuwa garin Kano, ta fake da yaranta ta haɗu da tsohon mijinta, a bakin aurenta tun da ni na ɗan iska ba ne" "Ai ba ma za ta sake ba, ta tuba ta daina ka yi haƙuri ka yafe mata" ya gama bala'insa, Maijidda na jin sa ba abin da take yi sai kuka. "Maijidda ki yi haƙuri, idan ki ka kashe auren nan saboda yara biyu ya za ki yi da na gaban ki? Duk abu gidan nan akwai ci akwai sha. Idan ki ka koma gidan Gwaggo ma, ita ba cikakkiyar lafiya ba, ga babu guri gara ki yi haƙuri. Ita yanzu tun da ta yi aure ta samu ta zo inda ki ke" Adda ta gama maganganunta, Maijidda ba ta sake tofawa ba. **** Habu ne a tsaye a ƙofar ɗakin, yana kwaɗa sallama, ya amsa masa. Ya ɗaga labulen ya shiga, kawai ya tarar da su a zaune a gefen katifa, Buzu yana fifita mata shayi a kofi, gabanta kuma ga ledar ƙosai ga kankana. Tana tauna ƙosan a hankali, fuskarta duk busasshen hawaye. Cikin damuwa ya ce "Amarya, meya faru ne? Ya kira ni hankali a tashe ya ce kina kuka, ko wani abin ya yi miki ne da ba kya so?" Ta ɗaga kai ta kalle shi, sai kuma ta ji tausayin sa ya kama ta, daga shi har Habun. Ta ce "Ba abin da ya yi mini fa" Habu ya ce "Kar ki ji komai, gaya mini idan wani abun ya yi miki ma?" "Bai yi mini komai ba" "Subhnallah, amma hankalinsa ya tashi sosai da sosai fa ya kira ni ya gaya mini, ki na kuka bai san meyafaru ba. Ko ba kya son sa ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, aikuwa ya tsare ta da ido, da alama jiran amsar sa take yi. Ta kawar da kanta gefe tana murguɗa baki. Habu ya yi shiru yana murmushi, buzu ya miƙa mata kofin shayin, ta karɓa, sai dai ta tuna wancan karon da ya ba ta abu ta sha, hankalinta gushewa ya yi, dan haka ta ci gaba da riƙe kofin a hannunta. Ganin babu wata matsala ya sanya Habu ya ce "To ni bari na tafi, amma dan Allah a daina yi masa rigima, ni bari na tafi" Suka yi magana da french, Habu ya yi musu sallama, ya tafi. Yana tafe a hanya, hana murmushi yana yi musu fatan alkhairi, domin ya ji daɗin yadda ya gan su. "To kai ma ka ci ƙosan mana" ta yi magana tana ɗaukkowa ta miƙa masa. Ya saka hannu ya karɓa, ya saka a bakinsa. Nana ta numfasa ta ce "Daga yanzu idan ina yin kuka, ko bani da lafiya, ka daina gaya musu, ka ga an saka shi yana ta zuwa, kuma da nisa daga can zuwa nan" Ya dube ta ya ce "To ki daina" "To, amma dama wai ka na magana haka, amma sai ka din ga yi mini shiru? Ba na jin daɗin hakan gaskiya" ya ɗan yi murmushi ya ce "Ɗaukewa take yi" "Me?" "Maganar " ya bata amsa. Cikin mamaki ta ce "To ta yaya maganar mutum take ɗaukewa, kamar wutar nepa?" Ya ce "Ban sani ba, wataran ma yaren naku, ɗaukewa yake yi, na manta duka" Kawai ta ɗauki kalaman nasa, a matsayin zolaya, sai ma suka bata dariya. "To ni dai ka gaya mini sunanka" "Buzu". Ta ce "Ai Buzu ba suna bane ba, sunanka na gaskiya" "Shi na faɗa" "To ai Buzu ba suna ba ne ba, kamar sunan ƙabila ne" Horn ɗin mota suka ji, a bakin gate, dan haka ya tashi ya fita ya je ya buɗe, bayan ya buɗe, ya ƙi dawowa ɗakin ya yi zamansa a waje. Sai bayan sallar isha'i ya dawo, ya ci abinci ya nemi guri ya ɗaukko wayarta, ya kunna film ɗin Indiya fassarar hausa yana kallo. Ta ƙura masa ido, duba yadda ya tattara nutsuwar sa a kan screen ɗin wayar. "Wai zuwa yaushe za ka bani wayata ne? Ina son kiran su Anty Ummi, tun da suka tafi ban kira na ji yaya suka je gida ba" ya yi mata shiru, ya ci gaba da kallon. Zaman shirun ya dame ta, ga wayarta a hannunsa, ga babu abokin hira. Ta kwanta bacci da wuri ko za ta yi bacci, amma ta kasa. Da ƙyar bacci ya ɗauke ta. Daf da kiran sallar asuba ta tashi, ta shiga banɗaki ta duba, ta ga ta samu tsarki, ta yi wanka ta yi alwala ta fito. Ta kunna fitilar ɗakin, haske ya gauraye ɗakin, ba ya cikin ɗakin. Duk da wasu lokutan idan ta kwanta bacci ba ta iya tantance mafarki ko kuma zahiri, amma ba ta tunanin da idonta ta taɓa ganin ya kwana ɗakin. Ko dai ya kwanta a farkon dare, tsakiyar dare ta neme shi ta rasa, ko farkon dare baya nan, cikin dare ta ganshi kafin asuba ta neme shi ta rasa. Har ta doshi ƙofar ɗakin, da niyyar ta ɗaga labule ta duba, ta gani ko yana waje, amma ta fasa da tuna abin da ta gani a wancan karon. Babu tsammani iska ta kaɗa labulen, ta hango shi a kan benci a kwance ya takure, yana bacci. Sai ta ji tausayin da ya kama ta. Ta tayar da salla, ta yi nafila raka'a biyu, ta zauna ta din ga istigfari da salatin annabi Sallallahu alaihi Wasallam. Bayan ta gama ta ɗaga hannayenta ta din ga tasbihi duk wanda ya zo bakinta yi take yi. La'ilahaillalahul azimul halim La'ilahaillalahul jalilul jabbar La'ilahaillalahul kabirul mut'al La'ilahaillalahu muɗɗali'i sittar La'ilahaillalahul khaliƙul laili wa nahar. Allahu Allahu rabbi, la ushriku bi hi shai'an. Allahumma inni as'aluka bi anni, ashhadu annaka antal ahadussamadu lazi lam yalid wa lam yulad, wa lam yakun lahu kufwan ahad. Sai da ta gama tasbihin kaf, sai kuma ta rasa abin da za ta roƙa. Ta sauke hannunta a hankali ta yi shiru, kawai daga bisani ta rufe da sayyidul istigfar, dai-dai lokacin an kira sallar asuba. Ƙarar zubar ruwan famfo ta ji, ta dake ta je ta leƙa, ta hango shi a durƙushe yana alwala. Ya idar ya zare sakatar gate ya fice. "Abin mamaki, mutum mai taɓin hankali ya san salla, ya san addini anma kuma a ce ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa anya kuwa?" Ta tambayi kanta. "Zan ci gaba da tunzura ka, da ƙoƙarin ƙure haƙurinka, har sai na tantance ainihin jinsin ka, sai na gano ko kai waye!" Ji ta yi an bushe da dariya mara daɗin ji, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki sautin. AYSHERCOOL 08081012143 Page 33 Ƙoƙarin dai-daita nutsuwarta ta yi, ta tattara hankalinta guri guda. Ta fara jin sanyi yana ratsa ta, ta din ga nanata Innalillahi wa innalillahi raji'un. Sai kuma ɗif tamkar an yi ruwa an ɗauke, ta daina jin sautin dariyar. Ta tafi banɗaki, ta sake yin alwala, ta zo ta yi raka'atanul fajari, sannan ta yi sallar asuba. Ta zauna a kan daddumar, tana kallon wardrobe, tana son ta je ta ɗaukko Alqur'ani, amma ta kasa tashi. Ta yi ƙoƙarin yin karatun Alqur'anin da ka, ta karanta abin da ta sani, amma ta ji tamkar an tattare komai daga cikin kanta an kwashe bar mata fanko. Ba ta san me ya ci gaba da wakana ba, ta ji an taɓa hannunta. Ta buɗe idonta ta ɗaga kanta ta kalle shi. Ta ganta zaune a kan daddumar, sai dai gari ya yi haske sosai, da alama takwas ma ta wuce. Ya nuna mata ledar hannunsa ya ce "A zo a karya, ga abinci" ƙamshin soyayyen ƙosan ya daki hancin Nana yawunta ya tsinke. Duk son ta da ƙosai ta girgiza masa kai. Ya ce "Me yasa?" "Azumi na ɗauka" "Da izinin wa?" da fari shirin tashi take yi, babu shiri ta koma ta zauna, tana bin sa da ido. Mamaki take yi har ya san sai da izninsa za ta yi azumi?. Ya kamo hannunta, ya juyo cikin tafukan hannun ya ce "Kalli, kin zubar da jini sosai, ta ya ya za ki ɗauki azumi? Ki ci abinci" Ta noƙe kafaɗarta ta ce "Ni ba zan karya ba, na riga na yi niyya, ka bari daga wannan idan zan kuma yi zan gaya maka in sha Allah" A fuskarsa ta ga alamar ya ji haushi, saboda yadda y tsuke fuskar, kawai ya gyaɗa kai ya ce "sai ki yi na gani" ya tashi daga gabanta. Ta bi bayansa da kallo, yana tashi ita ma ta tashi, ta haye katifarta saboda bacci kanta har wani nauyi ya yi mata. ***** Jamila fatar jikinta, ta warke, amma da ƙyar take tafiya tamkar tsohuwa. Hatta banɗaki sai an kai ta, komai a duƙe take yin sa. Babu shiri Mama ta ɗauki Jamila, ta kira ƙanwarta ta raka ta zuwa gurin wani mai magani, tana ta bala'in daga zuwa gidan Nana wannan masifar ta afka mata. Ta din ga faɗan ba yadda ba ta yi da su ba, a kan kar su je gidan Nanan, tun da dai alkhairi babya bibiyar ta, amma suka nace su ka tafi. Ko da suka je gurin mai maganin, ya ƙare wa Jamila kallo ya ce "Gaskiya wannan ya fi ƙarfina, sai dai na nemo Ibrahima wakilin rafi, ya duba ta. Idan da wani abu ma duk zai yi muku bayani" Mama ta ce "Waye hakan? Kuma a ina yake?" Ya ce "Kar ki damu, yanzu za ki gani, ba a nesa yake ba, yana nan kusa" Mama ta ce "To madalla, mun gode sosai da sosai " Mutumin ya tashi, ya din ga tattara shirgi a ɗakin, da tsummokara ya cika gurin da su, kamar ɗakin mahaukaci. Sannan ya buɗe wasu manyan randuna a shaƙe da ruwa, ya barbaɗa wani magani a ciki. Ya buɗa wata jaka, ya kwaso wasu tarkace, ya ɗaura wani guru a damtsensa, sannan ya saka yaronsa ya kawo masa, garwashi a cikin kasko, ya turare ɗakin da wani irin hayaƙi mai warin gaske, sannan ya nemi guri ya zauna a tsakiyar shirgin nan da ya baje. Ya sunkuyar da kansa, ya din ga karanto wasu abubuwa da ba a iya gane me yake cewa, saboda ba yaren hausa ba ne, yana yi yana kaɗa kansa. Can bayan wani lokaci ya ɗago kansa a hankali. Gaba ɗaya kamaninsa sun sauya, fuskarsa duk ta wani tattare tamkar tsoho, jikinsa kuma sai karkarwa yake yi, kamaninsa sun canza. Ba Mama ba hatta Jamila, a tsaroce suka ja da baya, su na rarraba ido. Ya ƙure Jamila da ido sannan ya ce "Wannan ai wani aljani ne yake jinya a jikinta" Ba Jamila hatta Mama cikin bala'in kiɗima da tashin hankali, ta kalli mai maganin ta ce "Aljani yake jinya a jikinta kuma, na shiga uku na lalace, ta yaya?" "A'a ba ki shiga uku ba, uban duƙusa su ka yi wa laifi da alama, ya hukunta su ne, su duka daga ita har shi a haka" Cikin rashin fahimta ta ce "Wa kenan?" "Wani aljani ne shi ma" Cikin damuwa ta ce "Ya za a yi Jamila ta ga aljani ta yi masa wani laifi?" "To wannan kuma wani abu ne daban, ba na son dai yin doguwar magana, balle dogon jawabi, amma idan ta nutsa ita ta san ta yi laifin. Yanzu dai zan baku magani, na sha da shafawa, sai kuma wanda za ta din ga sheƙa kafin ta kwanta bacci. Daga nan sai kuma a samu ƙosai mai zafi, a yi sadakarsa bayan la'asar. Amma iya ƙanan yara wanda ba su kai shekaru goma ba, su za a bawa. Za ta miƙe gaba ɗaya, ta warke. Sai kuma a nemi saurayin zakara, a yanka a fige shi a sulala, da almuru idan an gama rabawa yaran ƙosan, a tona rami a binne zakaran. Zai bar jikinta ya yi jinya a wani guri. Wanda kuma su ka ba ta aikin. ta yi musu su za su ɗauki ragamar ba wa uban duƙusa haƙuri. Ni ba ma shi nake ji ba, an riga an nakasta aljanin har abada. Ya ƙone sosai daga feshin wutar da aka yi masa. Wata ƙila ya yafe mata gaba ɗaya, wataƙila kuma shi ma ya ce sai ya rama, duk da babu lallai ya samu damar hakan ƙungiya ba za ta ba shi wannan damar ba" Cikin tashin hankali ta ce "Ni fa duk ban fahimta ba, ka na maganar ƙungiya, bayar da haƙuri, duk me ya kawo wannan zancen?" Ya ce "Ki bar shi a haka kawai yadda na gaya miki " Cikin damuwa "Ni dai malam ka taimake ni dan Allah, ka da yarinyar nan ta nakasa ita ma. Yayarta ta nan haka take ta fama da aljanun nan, da ƙyar ta yi aure tamkar za ta haukace, daga zuwa gidanta ta gamu da wannan masifar" "Kar ki damu, ba wani abu" Ya ɗaga hannunsa sama, ya dunƙule ya watsowa Mama wani ƙulli guda uku, ya ce "A je a yi mata wanka da shi, za ta ware, na baƙar takarda shi ne na shan, sai na shaƙar" Bayan ya basu maganin ya sallame su. **** Haɗuwa da kuma ƙasaitar ɗakin, ya sanya Nana sakin baki tana ƙarewa ɗakin kallo, tare da tunanin yau kuma a ina take?. Sai dai yanayin adon da aka yi wa ɗakin, ba wai ado ne irin na wannan zamanin da muke ciki ba. Ta ɗaga kai ta kalli rufin ɗakin, sai dai ga mamakinta, sai ta kasa tantance wani irin rufi ne, gini ne dogo mai matuƙar tsawon gaske. Sai da ta kalli wani sashi na jikin ɗakin, sai ta ga ya yi kama da cikin dutse,, ba wai gini ne na bulo ko ƙasa ba. Wani irin ƙamshi ya karaɗe ilahirin ɗakin, amma shi ma ƙamshin sai ta ji bai dace da wannan zamanin ba. A hankali ta kalli gadon da take kai a zane, ta shafa saman gadon, wani irin laushi na ban mamaki, bayanta ga fululluka a ajiye. Jin motsi ya sanya ta zabura ta waiwaya zuwa inda take jin motsin. Sai a yanzu ta hango wani sashi da ta sani a gurin. Gurin da ta gan ta jiya tana taje masa gashin kansa ne. Gadon ya tunkaro da kofin shayi a hannunsa yana takawa a hankali, jikinsa sanye da wata doguwar riga fara ƙal. Sai da ya zo gaban gadon sannan ya ajiye kofin a gefe, ya taka wani abu ya hawo gadon. Kallonta yake yi yana wani irin murmushi mai ƙayatarwa, ya sumbaci bakinta ya ce "que se passe-t-il?" "Ban iya ba" ta bashi amsa tana kallonsa ta ƙasan idonta. Ya yi dariya yana rungume ta a jikinsa ya ce "Me ya faru na ce" ya yi maganar yana shafa gefen fuskarta. Ta ɗan tura baki ta ce "Ni sanyi nake ji" ta yi maganar kamar za ta yi masa kuka. Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ai ina kusa da ke, kwantar da hankalinki yanzu zan ba ki ɗumin da ya dace da yanayin jikinki, wanda ba zai cutar mini da une ame(Soul/ruhinki ba). Ni ma ki bani wanda ya dace da ni, ni sanyin nake buƙata". Ya yi maganar yana rungumeta a jikinsa, cike da shauƙi. Tamkar almara haka Nana take ganin abubuwan da suke faruwa a tsakanin ta da shi, Kasa saita kanta ta yi a dalilin yadda jikinta yake wata irin tsumar da tun da aka haife ta, ko a duniyarta ta zahiri ba ta taɓa tsintar kanta a makamancin wannan yanayin ba. Ita duk yadda take tsintar kanta a mabanbantan yanayi, da gurare ba ta taɓa mafarki makamancin wannan a rayuwarta ba. Ga shi ya fi kama da zahiri ba mafarki ba. Amma duk da haka, ta bar wa zuciyarta mafarki ne, babu tunanin komai take biye masa, tamkar masoyan da suka shafe tsawon lokaci, cikin matsananciyar soyayya da ƙaunar juna. Bayan wani lokaci a hankali ya buɗe idonsa, ya ƙura mata ido idanunta a lumshe. Ta buɗe nata suka yi ido huɗu. Ta ɗan zaro masa ido, tare da murguɗa masa baki ta ce "Meye?" Ya yi murmushi ya ce "Komai ma, je suis heureux (Ina cikin farin ciki) na samu farin ciki amma ba cancan ba saura sex... Hannu ta saka ta toshe masa baki tana hararsa. "Kai ba ka jin kunya ne? Ka ke faɗar irin wannan maganat?" Dariya ya yi, yana ƙoƙarin cizon hannun nata. Ya ce "Yanzu ma ai ba mu ji kunyar ba, tun da... Ba ta bari ya ƙarasa ba, ta yinƙura ta kama kafaɗarsa, za ta cije shi, ya mirgina ta yana dariya. "Haryanzu ka ƙi ka gaya mini sunanka" ta yi maganar tana lumshe idonta "Ƙasair" ya furta a taƙaice. "Ƙaisar kuma?" Ta furta a zahiri bayan da ta buɗe ido, ta ga yadda take ƙanƙame da pillow. Juyowa ya yi daga inda yake zaune, da wani ɗan ƙaramin littafi a hannunsa, suka yi ido huɗu. Kawai ya yi wani irin murmushi yana ɗan kaɗa kai ya ci gaba da kallon ɗan ƙaramin littafin. Ta tashi tana ƙarewa kanta kallo, tana jin abin da ya faru a tsakanin su a jikinta, dan hatta ƙamshin turaren da yake yi, shi take ji haryanzu. Ita dai ba gwanar nannauyan bacci ba, balle ta ce ko abin ya faru a zahiri tana bacci. Ko da tana gurin ƙaisar da an taɓa ta take tashi. Wasu lokutan ko tsayuwa aka yi a kanta, sai ta farka. Sai dai ba ta gama razana ba, sai da ta ji ta ba a daidai ba gaba ɗaya. Da sauri ta tashi ta tafi banɗaki, cikin damuwa. Sai dai ko da ta duba, ta sha mamakin abin da ta tarar. Abin da ya faru a mafarki ta gan shi a zahiri, azumin ya karye ɗungurungum, kamar yadda ya gaya mata. Ta jingina da bangon banɗakin, al'amuran sun fara ba ta tsoro, ta yaya mutum zai biyo ta cikin mafarki, har ya aiwatar da abin da ya ce? Yaya aka yi ta iya biye masa haka, babu kunya babu jin nauyin sa, duk al'amarin baƙi ne a gare ta, kuma ta farka sun haɗa ido yana murmushi, kamar dai ya san abin da ya faru. Maganganun Ƙaisar su na ta ƙara tabatta ba ta tunanin ɗan Adam ne Buzun nan. Jiki a matuƙar sanyaye, ta yi wanka. Ko da ta fito ba ya ɗakin, ba ta ko yi yinƙurin gyaran ɗakin ba, ta zauna zaman jiransa. ***** Mama ce take zaune a ɗaki, tana ba wa Suwaiba labarin yadda aka yi a gurin malamin nan. "Ni anya ma kuwa Suwaiba, idan Jamila ta warke, ba gurinsa za mu koma ba, ya haɗa muku maganin farin jini, tun da wannan karon na ga kamar maganin malam Ɗayyabu bai yi ba". Suwaiba ta ce "To mama, a bari dai a fara ganin yanayin jikin nata, amma na yi mamaki da aka ce wai aljani ta yi wa laifi. Ni na fara zargin Nana wallahi". "Ai idan na faɗa wasu lokutan haushi ku ke ji, a zo a sayo mini waken da zan soya a yi sadakar nan, anjima kaɗan na je na sayo zakaran nan. Kar rana ta take an ce ƙosan da zafinsa ake so a bayar" Nasiru ya ce "Mama shi ƙosan ne zai ba ta lafiya? Allah kawai za.. "Rufe mini baki kafin na ragargaje ka a gurin, dama yadda ka ke shishshige mata kafin ta tafi, duk ka ko yi miyagun halayen ta". **** Nana ko karyawa ba ta yi ba, ba kuma ta da niyyar ɗora komai, ta zauna zaman jiran dawowar sa. Ba a yi mintuna talatin ba ya shigo, hannunsa riƙe da ledar buredi. Ya ajiye mata a gabanta, bai yi magana ba zai juya, ta riƙo rigarsa ta tashi tsaye. "Ina son na san waye kai? Me na aura? Na kasa fahimtar abubuwan da suke faruwa ka yi mini bayani" ta yi maganar numfashinta na fita sama-sama. "Waye ni?" Ya yi maganar cike da mamaki, yana kallonta. Ta ce "Eh shi nake son sani, ba na gane abubuwan da suke faruwa, ka yi mini bayanin waye kai? Daga ina ka ke? A ina danginka suke? Saboda na samu nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali ka gaya mini" "je ne sais pas (ban sani ba) ni ma haryanzu ban san waye ni ba" Ta buɗe baki za ta yi magana ya riga ta ta hanyar cewa "Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina ɗaga mini murya" "Ni ba ni da nufin ɗaga maka murya, amma ka yi mini bayani, ba na gane kan yadda al'amura suke faruwa, ta yaya za ka din ga bi na cikin mafarki kuma... Sai kuma ta yi shiru, ganin yana sauraren ta da mamaki a fuskar sa. "Kuma me?" "Ka din ga tsorata ni" ta ƙarasa a sanyaye. "Ni kuma? Ta yaya zan bi ki mafarki? Mafarki ba gaske bane ai, kuma wani ba ya shiga baccin wani. Kuma me na yi na.." sai kuma ya yi shiru, ya kasa ci gaba maganganun da yake son yi, suka tsaya a iya ƙirjinsa da maƙogwaronsa. A ƙoƙarin sa na ya yi maganar, kawai sai ya fara tari, ba tare da maganar ta fito ba. Sai kuma Nana ta rikice ta fara dana sanin abubuwan da ta gaya masa. A take Ƙaisar ya faɗo mata. Ta san babu abin da ba zai iya aikatawa ba, duk domin ta amince da abin da yake so. "Sannu, ko na baka ruwa?" Ya girgiza mata kai ya fita. Kawai ta zauna ta tattara hannunta, ta zabga uban tagumi ta ma rasa mene ne abin yi, a tsakanin shi da Ƙaisar waye yake raina mata hankali. Tun da take ta taso, ta fara ganin Ƙaisar a siffofi daban-daban, bai taɓa yinƙurin yin makamanciyar wannan alaƙar da ita ba, ko a farke ko kuma a bacci. Ita hasalima idan ana irin wannan zantukan har mamaki take yi, ba ta taɓa jin wani abu mai kama da feelings ba, sai da aka yi mata wannan auren, ta fara rayuwa inuwa ɗaya da wannan Buzun. Sai dai yadda mafarkin nata ya kasance, tamkar zahiri ba mafarki ba, tun da har ta farka ta tarar sakamakon abin da ya kwana a zahiri. Guntun tsaki ta ja, ta tashi da ƙyar ta fara gyaran ɗakin. Da ta gama ta shirya cikin hijjabi ta fito harabar gidan ba ta gan shi ba, kawai ta yi shigewar ta cikin gidan. A falon gidan ta tarar da matar, tana mopping, Nana ta gaisheta. Ta ɗan saki fuska ta amsa ta ce "Kwana biyu ba ki shigo ba" Nana ta ce "Ba ni da lafiya ne, kawo na yi miki" "A'a ba komai, kar ki damu zan goge" Nana ta ƙarasa ta karɓa ta ce "Bani zan goge. Masu aikin naki ba su dawo bane?" "Wallahi tsoron su nake ji ne, tun da suka yi mini sata ne, su ka gudu sarƙoƙinmu na gold kaf suka sace. Shi yasa yanzu nake ƙoƙarin mu yi komai da kanmu falon ma sai a yi sati ba shara, tun da ba yara" Nana ta karɓi mopping, ta goge ɗakin tsaf, sai dai ta din ga jin jikinta wani iri babu daɗi. Har su Tv duk Nana ta karkaɗe ta goge mata, bayan ta gama sai ga wani saurayi mai kama da matar ya shigo, da gayyar abokansa. Bayan Nana ta gama da falon ƙasan, matar ta ce "Dan Allah taimaka ki karkaɗe mini falon saman ma" Nana ta ce "Babu damuwa" ta hau saman benen, sai dai hawanta ke da wuya, ta ƙara jin jikinta babu daɗi, kamar za ta fita hayyacinta. Sai ta fara sauri ta yi ta kammala, ta kammala kafin wani abin ya faru. Ga mamakinta ta ga wata matashiyar budurwa, za ta ɗan girme mata, ta fito daga wani sashi na ɗakunan saman benen, tsiga-tsigal da siraran ƙafafuwanta ta saka mini skirt sai vest a jikinta. Nana ta kalle ta ta ce "Sannu ina kwana" Sai a lokacin ta kula da Nana ta ce "Yauwwa" ta nufi wata ƙofa. "Siyama" matar ta kira sunanta. Cak ta tsaya ta waiwayo ta ce "Na'am" "Wai Yusra ba za ta fito ta karya ba ne?" Siyama ta ɗan ɗage kafaɗa ta ce "I don't know" Matar ta ɗauki wayar ta, ta danna sannan ta kara a kunnenta. "Ki fito falo, ina son ganin ki" ta ajiye wayar, tana mita ƙasa-ƙasa. Nana a ranta ta din ga mamakin, da mata kamar wannan a gida, amma a ce saboda babu mai aiki an yi sati ba a yi shara ba. Nana ta nemi guri ta yi zamanta a kan carfet, tana kallon t.v. sai dai har ta shafe lokaci a zaune, ba ta ga wadda aka kira ɗin ta fito ba. Aƙalla Nana ta kai awa biyu, tana kallon film a MBC2 na divergent. Sai da aka gama ta yinƙura ta tashi ta ce "Na tafi" Matar ta ce "Har za ki tafi? Duba dining akwai ragowar bredi, ina ga har da sauran dankali ma ko za ku yi amfani da shi" Nana ta yi murmushi ta ce "A'a Hajiya na gode sosai, idan na tafi da shi sai dai na ajiye, a ƙoshe muke sai anjima" ba ta ma jira mai Hajiyar za ta ce ba, ta yi waje abin ta, tana jinjina rainin hankalin matar, dan wulaƙanci ma ita za a bawa ragowar buredi. A harabar gidan ta hango shi yana ta kaiwa yana komowa, ita tun da ta samu kallo ma har ta manta da shi. Wani irin kallo ya yi mata da sai da ta ɗan tsorata. A hankali take takawa tana satar kallonsa, har ta wuce bai kula ta ba, bai kuma bi ta ɗakin ba. ***** Alhaji Fatuhu ne yake zaune yana kallo, ya ɗan kalli matarsa Fadila ya ce "Kin an yi wa malamr su Muhsin aure kuwa?" Ta ce "Haba dai?" "Ƙarya na yi kenan?" Ta dafe bakinta da sauri ta ce "Afuwan" Ya ce "Haka na ji a bakin Yaya Sa'a, ashe wai ta santa" Fadila ta ce "Haka na ji ranar da ta zo gaisuwa, amma ba ta kyauta ba, abin babu gayyata" "Ni tun kwanaki ta ce mini za ta yi auren ai, na ma zata tuni an yi fa, ashe sai kwanan nan aka yi, amma duk da haka zan bayar da wani abun a bata" "Gaskiya yakamata, ni ma zan bayar, ina fatan Allah ya kawo rabo, ta yi yaronta takwara" Ya ɗan yi murmushi yana tuna yaron nasa. Ta ce "Yauwwa Daddy, ya ciwon kan kuwa?" Ya ɗan ɓata fuska ya ce "Ke dai a yi sha'ani kawai, daurewa nake yi amma duk da haka Alhamdilillah" "To sannu Allah ya ƙara afuwa" "Amin babyna" ta yi murmushi tana ɗan yi masa fari da ido. ***** Yunwa ce ta ishi Nana, ita ba azumin ba, amma ba ta ci komai ba, ta ɗora girki, sai dai fafur ya ƙi shigowa ɗakin. Muryar Habu ta ji yana ta kwaɗa sallama, ta saka hijjabi ta leƙa, ta ga Buzu ba ya gurin. Ta amsa sallamar ta ce ya shiga. Ya shiga yana sake sallama, ta amsa masa ta ce "Ina ga ya ɗan fita ne" Cikin damuwa ya ce "Ya fita kuma, ina yaje?" Nana ta ce "Nima ban sani ba, amma ai dama yana fita" "Duk da haka, kar ya din ga nisa, ki din ga hana shi fitar, kin san ba shi da cikakkiyar lafiya" Nana ta ce "Ta yaya zan hana shi fita, ni ka zo gaɓar da nake son a zo. Ni fa mutumin nan tun da aka yi auren nan, ko sunansa ban sani ba, kullum na tambaye shi sai ya ce mini sunan shi Buzu. Yakamata na san waye shi, a ina ku ke a ƙasar ku? Kuma yaushe za mu je na ga danginku. Tun da a haka tawa ƙaddarar ta zo." Habu ya numfasa ya ce "Kin yi gaskiya Amarya, shi yasa na yi ta ce miki ki yi haƙuri, ki karɓi ƙaddara, sai a yanzu na ƙara tabattar da wannan ƙaddarar ce ta haɗo mu baki ɗaya. Magana ta gaskiya, ban san waye Buzu ba, a sahara na tsince shi cikin mawuyacin hali, mai kama da gushewar hankali da ɗimuwa. Yanayin kamaninsa ya sanya na san ɗan uwa ne buzu, kuma buzyen ma kala-kala ne, na ji yana iya hausa ya kuma iya French, shi yasa na tabattar da Buzun Nijar ne. Na yi yinƙurin tafiya da shi Nijar, saboda idan na bar shi a saharar nan, zai iya rasa ransa, ban kuma san da wa zai haɗu ba, dan haka na yi nufin tafiya da shi Nijar, domin neman ahalinsa. Sai dai da na yi yinƙurin nufin komawa Nijar da shi, sai guguwar sahara ta taso, ta rufe hanyar baki ɗaya. Dole na canza hanya na nufo Nigeria, jikina ya bani akwai wani abu, domin duk wata hanya da zan bi mu koma Nijar na kasa samun ta. Ina da wasu abokai a Nigeria, su na kira suka karɓe ni, da niyyar a taimaka mini, a samo masa magani. Saboda duk abin da na tambaye shi game da shi bai sani ba, sunansa, waye shi, daga ina yake, ina za shi duk bai sani ba. Wasu lokutan zai yi miki abu lafiya kalau na cikakken mai hankali, sai dai ba zai taɓa iya ce miki waye shi ba. Wasu sai ya burkice, ba magana yana ma iya daina gane mutane gaba ɗaya. Ba ya son magana ko da yana normal, sannan wasu lokutan ya kan burkice ya din ga jijjiga. Duk gurin mai maganin da muka je a Nigeria sai a ce ba za a iya ba shi magani ba. Shi yasa tun da aka yi auren nan, za ki ga kusan kullum ina zuwa, ina kawo muku abin amfani, wallahi ina matuƙar tausayinsa ne. Ba shikaɗai ba har da ke ma" Jikin Nana ya mutu murus, ta ce "Yanzu shikenan ba ku san kowa na shi ba? Me na aura kenan?" Cikin kwantar da hankali Habu ya ce "Akwai dalilin da Allah ya sanya ya haɗa ku, da babu wanda ya sani sai shi. Ni kaina na fuskanci ƙalubale baro ahalina na taho Nigeria nema wa wanda ban sani ba magani. Idan ki ka saka hannu ki ka dafa mini a kan wannan jihadin, Allah ne kawai zai biya mu. Idan ba ki amince ba kuma shikenan babu dole, sai na wuce gaba a raba auren, dama mahaifinki ne ya matsa ya sanya aka yi auren dole". Ba su ankara ba kawai su ka gan shi a cikin ɗakin, ya ajiye abin dafa shayinsa, da kayan dafa shayin, ya juya zai bar ɗakin. Habu ya tashi da sauri yana faɗin "Tun ɗazu na zo ai, ba ka nan ga kayan dahuwar shayin nan na kawo maka" Banza ya yi masa ya nufi hanyar fita, Habu ya bi shi da sauri, ya riƙo hannunsa amma ya fizge yana yi masa wani irin mugun kallo. Ayshercool 08081012143 Habu bai yi zuciya ba, ya sake bin bayan Buzu, ya juya yare, ya tsaya yana yi masa magana, ya din ga zuba babu ƙaƙƙautawa. Nana kuma mamaki ne ya ishe ta, ganin Yadda Habu ha rikice gaba ɗaya, kuma ita ba ta ga abin da ya yi na ba daidai ba, da zai yi wannan rikicewar kamar mara gaskiya ba. Ita wasu lokutan har mamaki yake bata, kamar tsoron buzun yake ji, shi da yake taimakonsa amma ba ya ƙaunar ya ga ɓacin ransa ko kaɗan. Nana ko a jikinta, ba ta ma san yadda suka ƙarke ba. Sai dai ta yi ta jujjuya maganganun da Habu ya gaya mata. Yanzu shikenan haka za ta ci gaba da rayuwa da mutumin da ba a ma san suwaye danginsa ba? Ko a daɗe ko a jima dole tana buƙatar sanin waye shi, kuma suwaye ahalinsa. Ba ta taɓa jin lallai tana son ganin Ƙaisar ba sai a wannan lokacin. Ba shiri ta kwanta ta hau bacci, ko za ta gan shi, amma ba ta ga komai ba, har ta gama baccin ta tashi. Bayan farkawarta ta ga wayarta a gefenta, a lokacin yamma ta yi sosai da sosai. Da sauri ta ɗauki wayar, ta kira lambar Ummi, dan tun da suka zo, ba ta ji ya suka je gida ba. Sai da ta kusa katsewa, sannan Ummi ta ɗaga. Nana ta yi sallama, Ummi ta amsa ta ce "Kai, Nana a ina ki ka samu waya?" Nana ta ce "Dama ina da ita, kin san lambar ki na haddceta, saboda ke ce line 911 ɗi na" Ummi ta yi murmushi ta ce "Eh lallai kam, ya ki ke ya mai gidan?" "Alhamdilillah, ya ku ka je gida, ban samu na kira ku ba, bayan tafiyar ku na ɗan yi rashin lafiya ne" Ummi ta ce "Alhamdilillah, mun je gida ƙalau. Kai Nana daga zuwa sai rashin lafiya, a dai ciki ba ne ko?" Nana ta kwashe da dariya ta ce "Dan azaba auren kwanaki sai ciki?" "Eh mana, tun da ina jin fitsarar da ki ke yi, ranar da mu ka zo" Nana ta ce "Wallahi kawai cika baki ne, ji na yi za su raina mini hankali ne. Kuma ba na fatan ko alama, a ga ɓaraka a tattare da aurena" Ummi ta ce "Allah sarki Nana, in sha Allah auren nan, sai ya baki kwanciyar hankalin da ba ki taɓa tsammani ba. Ke Jamila fa babu lafiya fa" Nana ta dafe ƙirjinta ta ce "Babu lafiya kuma? Me ya same ta?" "Oho, ni mun yi waya da maman, ban gama gane kan zancen ba. Wai tun da mu ka baro gurin ki, washegari ta tashi ba ta iya tsayuwa, wani abu duk ya feso mata a jikinta". Nana ta girgiza kai ta ce "Hmm na san cewa aka yi ni ce ko?" "A'a wai sun je gurin wani mai magani, aljani ne yake hawa kansa ya bayar da magani, ya ce musu wai wani aljani suka yi wa laifi" Kan Nana ya sara, ta yi shiru tana son tuna wani abu, amma ta gagara tuna komai. Ummi ta ci gaba da cewa "Shi ne ya basu magani, wai ya sha sannan a yi sadakar ƙosai mai zafi da la'asar" Nana ta ce "Ita sadakar ƙosan ta mece ce, sharaɗin mene ne? Kin ga Mama ba za ta din ga kiyaye irin wannan yawace-yawacen ba ko? Wane irin sadakar ƙosai mai zafi da la'asar?" "A'a ni ina zan sani, tun da ba ni na ba su maganin ba, ina gefe labari aka bani" Nana ta numfasa ta ce "Sadaka mahaɗin Addu'a ce, amma wannan sharuɗɗan da ake sakawa ne, ni ba na gane kansu" "To ni ya za ni tsitsiye ni, labari kawai na ji, ban ma je na duba ta ba" Jikin Nana a sanyaye ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Allah ya sauwwaƙe ya jikin Baban?" "To da sauƙi, ni rabona da gidan tun biki, amma sun ce yana jin jiki, ƙafar nan tana yi masa ciwo sosai" Nana ta ce "To shikkenan, zan samu na je na duba su baki ɗaya, in sha Allah, amma jikina ya yi sanyi, na san ciwon Jamila cewa za a yi nice" "Ke rabu da su dan Allah, ni wallahi na jiye miki daɗin auren nan, Allah ya sanya shi ne mafi alkhairi, amma da zaman wannan gidan namu, ba gara auren ba, kullum cikin bala'i. Ko banza ɗakin ki a cike yake da kayan abinci" Nana ta ɗan yi shiru, kamar ta gaya wa Ummi halin da ake ciki, na rashin sanin dangin mijinta, amma ta basar. Ta ce "To Allah ya sa mu dace" na gode sosai ki gaida yaran" Suka yi sallama, Nana ta tashi ta ɗan yi gyare-gyaren ta, ta ɗauki magic coal ɗin sa da yake haɗawa da gawayi, ya kunna wutar dafa shayi, ta kunna turaren wuta. Ta ɗauki wayarta ta kunna karatun Alqur'ani. Fafur ya ƙi shigowa ɗakin, sai bayan isha'i. Ya shigo da 'yar ledarsa, ya ɗauki kwano ya zazzage fruit, ya je ya wanko abin sa, ya dawo ya zauna a gurin zamansa, ya fara ci a hankali. Nana ta na kallon sa, zuciyarta ɗauke da tunani daban-daban. Ta dake zuciyarta, ta tashi ta tafi kusa da shi ta zauna. Bai ko ɗaga kansa ba, balle ya nuna ya san tana zaune a gurin. "Ba za ka ci abincina ba ne, ka je ka sayo fruit ka ke ci?" Sannu a hankali yake tauna apple ɗin bakinsa, bai kula ta ba. "Ni mamaki ma nake yi, idan ka je da yaya ka ke sayayyar, magana ka ke yi musu, ko kuma ni ce kawai ba ka kulawa?" Ya ɓare ayaba zai kai bakinsa, ta riƙe hannun, ta sauke shi ƙasa a hankali. Ya ɗago idanunsa yana kallon ta. Ta yi saurin sauke nata ta yi murmushi ta ce "Na san na yi maka laifi, bai kamata abubuwan da na gaya maka ba, ka yi haƙuri ina cikin damuwa ne, amma ka yi mini afuwa ba zan sake ba" ya sunkuyar da kansa ya yi shiru. "Ka yi magana mana" ta yi maganar a raunane. Ture ta ya yi daga kusa da shi, ya tashi ya bar mata ɗakin. Abin ya yi wa Nana ciwo, sai dai ta tuna bayanin Habu daki-daki, tabbas wasu abubuwan da yake za ka san ba normal yake ba. Ta tashi zuciyar ta cike da damuwa,  sai dai a zuciyarta ta ƙuduri aniyar jure kowane irin ƙalubale, tun da ba duka yake ba, ba kuma zagi yake yi ba, gara zamanta a nan da shi sau dubu, a kan ta koma gidan su. Ta kunna gas ta ɗora ruwa, domin ta yi wanka kafin ta kwanta, garin akwai yanayin hadari, dan haka akwai sanyi. Tana ɗan dube-dube, da goge kan mududinta, ta ga ɗan littafin da yake yawo da shi, ko ta ga yana karantawa, da biro a cikin drower mudubi. Ta ɗauka ta buɗe, ta ga kyakyawan rubutunsa, wani da French, wani da hausa. "A ba ni kankana, da ayaba na dubu biyu. A bani buredi mai kyau babba guda ɗaya. Ina son wannan jan abin, na kuɗin da na bayar" sai da Nana ta yi dariya, wato duk a rubuce yake sayen abin da yake zuwa da shi. Tana shirin buɗe wani shafin, ta ji wutar gas ɗin na fita da yawan gaske, tukunyar kai na wata irin tafasa kamar ta diro daga kan gas ɗin. A gigice ta nufi gas ɗin ta sauke, abin ya ba ta mamaki, dan ko mintuna biyar a yi da ɗora ruwan ba, yake wannan tafasar. Ta juye ruwan a flask, ta sake ɗora wani. Yana tafasowa ta haɗa ruwan ta shiga wanka, sai dai bayan ta shiga banɗakin, ta ji ruwan ya yi mata zafi sosai, maimakon ta kunna famfo, ta ƙara sirkawa, sai ta jingina da bango tana jiran ya huce. Shiru ta yi tana ta tunani daban-daban a zuciyarta. Ɓangaren buzu bayan ya dawo ɗakin, ye nemi Nana ya rasa, ya ga littafin sa a kan mudubi. Ya ɗan yi jimm ko zai ji motsinta amma shiru. Kusan mintuna goma bai ji ko zubar ruwan famfo ba, balle ya yi tunanin tana banɗaki. Gaba ɗaya hankalinsa ya tashi, kamar yadda ya tashi ɗazu, da ya dawo ya tarar ba ta nan ashe tana cikin gidan nan ba ta gaya masa ba. Kasa jurewa ya yi ya nufi banɗakin kawai ya buɗe ƙofar. Zabura Nana ta yi, ta saki ƙara, domin ƙoƙarin cire zanin jikinta take yi ta yi wanka. Cak ya tsaya yana kallonta, ta saka hannu ta riƙe zanin da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma ta kare ƙirjinta da shi. Sannu a hankali take jin sanyi, ƙirjinta kuma ya fara bugawa. Ta sake ɗaga ido, suka haɗa ido, ko a jikinsa ya ci gaba da tsare ta da ido. Ta yinƙura da niyyar magana, amma ta ji ta kasa furta komai, ta sake sunkuyar da kanta ƙasa. A hankali ta ji ya rufe ƙofar toilet ɗin, wata irin ajiyar zuciya ta yi, jiki a sanyaye ta yi wanka, sai dai ta kasa fitowa saboda kunya. Da kyar ta iya fitowa, amma ta ga baya ɗakin, cikin hanzari take shiri, domin kwanta, kafin ya sake shigowa. Gari sai walƙiya ake yi, da wata irin tsawa hadari yana tasowa. Tana gama zura rigar ta ya shigo, bai ce komai ba, ya rufe taga sai dai yana juyowa gaba ɗaya kamaninsa sun sauya, ya koma wannan tsohon. Kallon kallo suka yi da ita, ta tsaya tana yi masa wani irin kallo, mai cike da tsoro da razani, a take fitilar ɗakin ta ɗauke, ɗakin ya gauraye da wani irin matsanancin duhu, ƙofa da tagar ɗakin su ka din ga bugawa da ƙarfin gaske. Wata irin walƙiyya ta haska ɗakin, ta ganshi sanye cikin wannan fararen kayan da take ganinsa da su, hannunsa riƙe da sandar sa, idanunsa baƙi ƙirin wani baƙin hayaƙi na fitowa daga cikin su. Ya hangame bakinsa, ya fara fito da wuta. "Allahumma ajirni fil musibati, wa aklifni kharin min ha" ta yi maganar tana sanya hannunta, ta ɗora a kanta. "Meyafaru?" Ta ji muryarsa. Ta buɗe idonta ta kalle shi a hankali. Fuskarsa ɗauke da damuwa yake tambayarta. Da sauri ta ja da baya tana girgiza masa kai. "Kar ka sake zuwa kusa da ni, ka yi mini duk abin da za ka yi mini, na gaji me na yi maka ne?" Ta yi maganar cikin kuka. Cikin mamaki yake bin ta da kallo, yana tunanin me ya yi mata take wannan kururwar. Ya taka ya ƙara matsawa kusa da ita, amma ta din ga ja da baya, tana maimaita "kar ka matso kusa da ni, ba na buƙatar ka, kar ka zo inda nake". "Kalli ni mutum ne ba abin tsoro ba, babu abin da na yi miki, le regard kalli" ya yi maganar yana nuna mata hannunsa domin ta taɓa ta tabattar. Cikin fita hayyaci Nana ta ce "Ka fita ba na son ganinka, ba za ka haukata ni a banza ba, ka fita ba na son ganin ka" ta yi maganar jikinta na tsuma da karkarwa. Cikin sauri ya nufi ƙofar fita yana waiwayen ta. Yana fita ta silale ta faɗi a gurin. Fitar sa ke da wuya, ruwan sama mai ƙarfin gaske ya sauka. **** Dare ya tsala, Fadila na zaune bacci ya gagari idonta, ta kalli kusa da ita, mijinta Sagir yana ta baccinsa hankali a kwance, ita kuwa duk dare fargabar kwanciya bacci take yi, saboda miyagun mafarke-mafarken da take yi. Tun Sagir na damuwa har ya gaji ya rabu da ita. Ta yi niyyar yin alwala ta yi nafila ko raka'a biyu ce, amma kasala ta danne ta, ga wani irin tsoro da take ji. Dama ko normal sallar farilla a zaune take yin ta, saboda yadda cikin ya tsufa sosai da sosai ga shi da girma. Ga exams tana facing, ba ta iya karatun sam. Ta dafe goshinta tana wani irin gumi, duk da sanyin A.C da ya sanyaya ɗakin. Tana jiyo surutan Haidar a cikin bacci, yana ta kiran sunan Nana. Kawai ta zuba uban tagumi hannu bibbiyu ba tare da sanin abin yi ba. **** Ko da Nana ta buɗe idanunta, da hasken fitilar ƙwan ɗakin, ta fara karo. Ta juyo da kanta, da ya yi mata nauyi tamkar zai tarwatse, kawai ta hange shi a bakin ƙofar banɗaki, yana ta sanɗa yana cire kayan jikinsa a hankali, da suke ta ɗigar da ruwa, jikinsa yana ta wata irin karkarwa. Aka yi walƙiya ta hangi yadda ruwa yake zuba ta taga. A take ta tuna abin da ya faru, da azama ta tashi zaune, ta yinƙura ta tashi, ta nufe shi. Sai a lokacin ya farga da ta tashi. Sai da ya tsorata ya tsaya cak, yana tsoron kar ta sake rikicewa ta ce ba ta son ganinsa. "Me yasa ka fita ruwa ya dake ka har haka? Subhanallah" ta yi maganar tana karɓar rigar hannunsa. Babban abin da ya tsorata ta, bai wuce yadda jikinsa yake karkarwa ba, haƙoransa suke haɗuwa da juna, su na bayar da wani irin sauti. Ta buɗe wardrobe ta ɗaukko zaninta, ta fara goge masa ruwan jikinsa. Cikin damuwa ta ce "Me yasa ka tsaya ruwa ya dake ka haka?" Kawai ya kalle ta. Ta ajiye zanin, ta ɗaukko flask ɗin da ta zuba ruwan zafi, ta shiga banɗakin ta zuba a bokiti, ta haɗa masa ruwa mai zafi. "Ka shiga ka yi wanka da shi, za ka rage jin sanyin" bai musa ba ya shiga banɗakin, ta ɗauko wando ta rataye masa a jikin ƙofar, ta rufe masa ƙofar. Ta ɗaukko bargonta, ta ajiye a kan katifar, ta duba kayanta, ta samo man zafi ta ajiye. Ta tsaya tana jiransa. Ba a jima ba ya fito, sai dai jikinsa na ta ci gaba da tsuma, yana karkarwa. Mamaki take yi, yadda dukan ruwa ya saka shi haka, ita ba ta san adadin dukan da ruwa ya yi mata ba, ko ciwon kai bai taɓa saka ta ba. Ta ɗaukko riga, ta miƙa masa, amma ya ture ta, ya nufi gurin da yake kwanciya. Ta riƙo hannunsa ta ce "Zauna a nan" ta nuna masa gefen katifar. Ya zauna a hankali yana rintse idanunsa. Ta ɗauki man zafi tana shafa masa a jikinsa, sai dai jikinsa ya ɗauki zafi rauuu. "In baka rigar ka saka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Ta gyara masa fulo ta ce "To kwanta" ya ja jikinsa a hankali ya kwanta, ta lulluɓe shi da bargo. Ta yi shiru cikin matsananciyar damuwa, ita kanta ba ta san ya aka yi yau ta gigice har haka ba. Ba ta san yadda aka yi ta rasa nutsuwar ta har hankalinta ya gushe ba, duk da abubuwa irin haka na faruwa da ita, wasu lokutan kuma ta na iya sarrafa kanta. Ji ta yi yana wani irin nishi, jikinsa tamkar ana girgiza shi. Ta ɗaga bargon cikin damuwa, ta ga yana jijjiga. Ta rikice ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, tsoro ka ke bani ne, ba ina nufin ka fita ruwa ya dake ba ne ba." Tana kuka ta ɗaukko ɗan kwalinta, ta jiƙo shi da ruwa, ta ci gaba shafa masa. Amma ta ga leɓensa har ya fashe saboda karkarwa. Ta kalli gari yadda ake ta lafta ruwa, balle ta ce a taimaka mata a kai shi asibiti. Ya yi mata alama da hannunsa ta matsa kusa da shi, ta matsa sosai a hankali ya ce "Zafi, ana ƙona ni, ƙonewa nake yi" Cikin kuka ta ce "A'a babu wanda yake ƙona ka, zazzaɓi ne ka yi haƙuri" "A'a, ƙona ni ake yi, sanyi nake so" Cikin rashin fahimta ta ce "Sanyi kuma?" "Eh, saboda ƙonewa nake yi yanzu" yayi maganar haƙoransa na ƙara karo da juna. Cikin damuwa ta ce "To mu koma bakin ƙofar ɗakin?" Ya girgiza kai ya ce "Sanyin da ki ke ji nake so" "Sanyin da nake ji kuma? Ai ba na jin sanyi" "A'a ki na ji, ki taimaka mini dan Allah, sanyin da ki ke ji nake so" "To ta yaya zan baka?" "Jikinki za ki bani, shi nake buƙata ko zan daina jin zafin wutar nan" duk da jikinsa yana rawa, amma tana fahimtar abin da yake faɗa. "To ai ni ban san ta yaya zan baka ba" Ta yi maganar a sanyaye dan ba ta san ya yake nufi ba. "Kin yarda za ki bani?" Ya yi maganar yana buɗe idonsa da suka kaɗa su ka yi jawur ya kalle ta. Ta jinjina masa kai alamar eh, cikin tsoro dan ba ta san ya yake nufi ba. Ya buɗe mata cikin bargon, ya saka hannunsa ɗaya ya janyo ta, ya mayar da bargon ya rufe., ya mirgina ta gefensa ya saka hannayensa ya ƙanƙame ta. "Wash Allah! Zafi zan ƙone" ta yi maganar a gigice, saboda wani irin zafi da yake fitowa daga jikinsa, yana ratsa fatarta, duk da akwai rigar bacci a jikinta. Ta yinƙura za ta tashi, sai dai ta kasa, saboda ya danne ta, ta kowane ɓangare. "Yi hakuri, ba za ki ƙone ba, za ki daina ji" Nana ta fashe da kuka tana girgiza kanta, shi da zafin yake fitowa daga jikinsa ya yake ji kenan?. A hankali yake shafa gashin kanta, zuwa bayanta, yana sauke numfashi a wahale. Cike da ƙarfin hali yake cewa "Yi haƙuri, na san ba zaki ƙone ba, nikaɗai nake ƙonewa" ya din ga hura mata iska a kunnenta. A hankali ta daina jin zafin, temperature jikinsa, ta fara komawa normal, ta ji ya daina wannan tsumar,  numfashin ma da yake ta saukewa ya daina. Sai ta ɗan zabura a rikice ta ɗago, ta kai hannu hancinsa. Bai buɗe idonsa ba ya ce "Ban mutu ba, ina numfashi" ajiyar zuciya ta sauke tare da gode wa Allah ganin yana raye ya kuma dawo daidai. "Sannu ka daina jin zafi?" Ya jinjina kai alamar eh. "Dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, tsorata ni ka ke yi ne, ba ina sane na yi maka ba" "Ni ma ki na tsorata ni wasu lokutan" Cikin mamaki ta ce "Ta yaya?" "An gama ruwan ko?" Ya yi maganar yana basar da wadda ya yi. "Eh an daina, amma dama ka na doguwar magana haka sosai?" "Eh" "Amma na yi ta magana ɗazu ka ƙyale ni" ta yi maganar da shagwaɓar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba. Dariya ta ji yana yi, ya ƙara riƙe ta gam. "Yanzu wai da gaske ba ka iya tuna komai game da kan ka?" Ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "Haka ne, ina iya tuna abubuwa na yau da kullum, wasu lokutan kuma ba na iya tuna komai ma. Tun da farka a cikin wannan duniyar da nake jin ta tamkar mafarki, nake iya ƙoƙarina na tuna waye ni, saboda na fuskanci babu wanda yake rayuwa shikaɗai kowa yana da ahali. Amma a duk lokacin da na yi ƙoƙarin hakan, na takura ƙwaƙwalwata, sai na ji wani duhu ya ƙara ninkuwa a cikin kaina, na ji kamar kan zai tarwatse. Kuma a ƙarshe sai na yi rashin lafiya, ko dai na ji wannan zafin tamkar ana babbaka mini wuta, ko kuma na sake manta wasu muhimman abubuwan. Amma yanzu ke ce ahalina" "Kenan ba dalilin dukan ruwan nan ne ya saka jijjiga ba?" "Ba zan iya ganewa ba, abubuwan suke saka ni hakan da yawa" Nana ta ce "To ni dai ka yi haƙuri dan Allah, ka yafe mini na gaya maka ba ni da cikakkiyar lafiya ba da son raina  ba" ta yi maganar cike da jin daɗin, yadda suke hira yau sosai har haka. Ya yi shiru, yana ƙoƙarin karkata ga wani abin daban. "To bari na tashi, tun da ka koma daidai" "A'a ban koma ba" Ƙirjinta ne ya fara bugawa cikin matsanancin tsoro, za ta yi magana muryarta ta din ga rawa. "Dan Allah" shi ne kawai abin da ya iya fitowa daga bakinta. "Shhhhhh" Wutar ɗakin ta ɗauke gaba ɗaya, duhu ya mamaye ko ina, sai ƙamshin turaren da ta ji a wancan ɗakin da ta yi mafarki da shi, ya ziyarci hancinta. Gaba ɗaya sai ƙwaƙwalwarta ta juye, ta rikice. Yau ma mafarkin ne? Ko kuma zahiri ne? Nan ta shiga dambarwa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tantance, sai dai haƙar ta, ba ta cimma ruwa ba. Ayshercool 08081012143. 35 Nana ta motsa, ta ji taushin katifar da suke kai, ta fi ta ɗakinsu. Ga ƙamshin turaren da ya sauya, ya sanya Nana sakankancewa a kan a wannan karon ma, irin wancan mafarkin ne. Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi, a wannan karon ma ta kasa sarrafa kanta da nutsuwar ta. Sai dai a wannan karon al'amarin ya banbanta da na farko. "Kai ka rabu da ni" Ta faɗa da ƙarfi, tana ƙoƙarin ture shi. "A'a" ya faɗa ƙasa-ƙasa. Tabbas ba mafarki ba ne ba, bayan Buzun mijin nata ya dangana da ita, wani bugire mai girman gaske, bugiren da ba ta taɓa kawo faruwar sa a tsakanin su ba. Ita a tunaninta tun da ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa ba ya jin komai, hakan ne ya sanya take yawonta ma babu hijjabi a ɗakin, sai ta ga ya dame ta da kallo, ta rufe jikinta. Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka ƙyale ni" "je suis désolé (ki yi haƙuri)" ya yi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa. Bayan wani lokaci da Nana ba ta iya tantance adadinsa ba, domin ta daɗe da daina gane komai. "Ma femme. (Matata)" Ya yi maganar yana ɗan murza ya tsunta. Ta buɗe idonta da ya yi jawur, da ƙyar tana kallon sa. A wannan karon fitilar ɗakin a kunne take. Sai dai fatarsa ta yi jawur. Ta sunkuyar da kanta daga kallonsa. Ya saka hannu ya share hawayen da ke fuskarta, sai dai kuma ya kasa magana. Ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta, ya kamo hannunta ma ya sumbata. Ta lumshe idanunta tana numfashi a hankali. "Merci (Na gode)" shiru ta yi tana ƙara sunkuyar da kanta. Ya saka hannunsa ya ɗago fuskarta, amma ta lumshe idanunta, ta ƙi buɗewa. "Kalle ni mana" Kwaɓe baki ta yi, ta ci gaba da kuka. Ya saki murmushi yana goge mata hawayen fuskarta ya ce "A yi haƙuri" Ya ci gaba da wasa da yatsun hannunta, daga baya ya tashi a hankali yana kallonta, sai dai ya rasa abin gaba ɗaya. Nana ta yinƙura da ƙyar, ta tashi zaune, ta ja bargon ta rufe jikinta. Su na haɗa ido ta sunkuyar da kai ƙasa, fuskarta a haɗe, hawaye na biyo fuskarta. "Yi haƙuri" ya yi maganar yana kallon ta. Kawai ta sake fashewa da kuka, har da sheshsheƙa. Shafa bayanta ya ci gaba da yi, cikin sigar rarrashi, amma ta maze ta din ga kuka. Ya ce "Ki yi shiru" Ba ta kula shi ba, ta janyo rigarta, ta saka ta yinƙura ta tashi da ƙyar, ta nufi gas ɗin ta. Ta dafa ruwa ta shiga banɗaki, ta jima sannan ta fito, a ƙofar banɗakin ta tarar da shi a tsaye. Sai da ta ɗan tsorata, ta na ƙoƙarin raɓa shi ta wuce, ya ce "Ni fa?" Ta kalle shi. Ya ce "Zan yi wanka" Ta ba shi hanyar shiga banɗakin, ya kalli hanyar ya ce "Ruwan sanyi? A a ina jin sanyi" "Bari na dafa" ya koma gefe ya zauna, ta ɗora masa ruwan, ta kalli agogon ɗakin, huɗu da rabi, ta san idan ta kwanta yanzu ba bu lallai ta samu sallar asuba. Ta shimfiɗa sallaya, ta ajiye wayarta a kai, ta ajiye hijjabinta. Yana gefenta, sai bin ta yake yi da ido. Ta kai ruwan banɗaki, ta na haɗa masa, sai a yanzu ta tuna lokacin da ya ce mata zai yi wanka, ashe ruwan sanyi ne ba ya so. Ta kashe famfon kenan, ta yinƙura ya shigo banɗakin. Ta tashi tsaye tsam tana rarraba ido. Ya mayar da ƙofar ya rufe, ta ɗago da sauri ta ce "Amm ga ruwan nan, idan zafin bai yi ba, sai ka kunna famfo ka ƙara sirkawa". "Na kasa tuna yadda ake wankan, sai kin tuna mini" "A'a wallahi nima ban iya ba" ta yi maganar idanunta a waje dan tsoro. "Amma ke ki ka yi? Ko wankan kwanciya bacci ki ka yi?" Gaba ɗaya mamaki ya cika Nana, mutumin da magana take yi masa wahala, shi ne ya ritsa ta da wannan maganganun kamar ana karanta masa. "Dan Allah ka yi haƙuri, ni ban iya ba" "Astagfirullah ba kyau ƙarya" ya yi maganar yana taɓa ruwan. ***** Doctor Sharif ne da wani likita a kan Shukura, su na gwada bp ɗin ta. Duk ta kumbura sosai da sosai. Jininta ya hau sosai da sosai, ba zai yiwu a yi mata tiyata a wannan ƙadamin a cire jaririn ba, saboda hawan da jininta ya yi. Ga shi lokacin haihuwar ta bai yi ba. Sakamakon da ya fito daga lab kuma, still ya nuna jininta ya yi ƙasa. Doctor Sharif ya fito cikin damuwa, ya dubi Hajiya Amina da Yusuf, da kuma mijinta Sagir ya ce "Wai me yake damun Shukura har haka. Normal teses ɗin suke tuk daga farkon cikin nata, amma lokaci ɗaya a ce jininta ya yi wannan mugun hawan ta kumbura har haka?" Sagir ya ce "Wallahi doctor na rasa gane kan ta, tun bai fi kwana uku da dawowa ta ba, duk ta canza. Ba ta cin abinci, bacci ma ba ta iya yi. Kullum na farka cikin dare tana zaune, na yi, na yi na tambaye ta mene ne,ta ce mini ba komai, Mummy ai har ke na gaya wa ko za ki tambayeta abin da yake damun ta. Hajiya Amina ta ce "Rigima ce kawai irin ta Shukura, duk ta ɗaga hankalinta, wai tana ji a jikinta wannan cikin mutuwa za ta yi. Ina ta rarrashinta ina ba ta haƙuri, amma ta addabi kanta kuma wallahi farkon cikin duk ba haka ta yi ba." Cikin damuwa Yusuf ya ce "Yanzu doctor mene ne abin yi?" "Zamu ajiye ta a nan, a samu jinin ya sauka, idan babu matsala za a iya barin cikin ya cika watannin haihuwar fine, idan kuma akwai matsala za a tiyata a cire cikin" Hajiya Amina ta ce "Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi" Doctor ya amsa da "Amin, dan Allah a kula, hajiya ke kaɗai za ki zauna a gurin ta, babu 'yan dubiya Please, kar a bari kowa ya je inda take, yanzu dai ta samu bacci Alhamdilillah" "To shikenan in sha Allah, za a kiyaye" Kiran Alhaji Zailani ne ya shigo wayarsa, dan haka ya bar gurin ya yi gaba ya ɗaga. "Sharif" "Na'am ranka ya daɗe" "Yaya ake ciki, Amina ta gaya mini su na asibitin ku Shukura babu lafiya, haihuwar ce ko yaya?" "A'a tukuna dai ranka ya daɗe, jininta ya yi hawan da ba zai yiwu mu yi tiyata yanzu ba, mu na dai ƙoƙarin dai-daita jinin nata ne". "To ko ma dai mene ne, kar ka manta da maganar mu" "Ban manta ba, ina sane ranka ya daɗe" "Yauwwa ya yi" ya katse wayar. ***** Jamila ce zaune fuskarta duk hawaye, a gaban Hajiya Sa'a. Hajiya sa'a ta riƙo hannunta ta ce "Kar ki damu Jamila, na san kin yi iya ƙoƙarin ki, za mu canza fasalin aikin namu, Sannan za ki samu lafiya za ki warke gaba ɗaya ma" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba. "Akwai wata tafiya da nake son na yi Abuja, idan babu damuwa ina son za ki raka ni, amma sammako za mu yi, mu je mu dawo?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Mama za ta bar ni, Baba ne babu lallai ya yadda, amma na san za ta saka baki ya bar ni, zan ma iya tahowa bai sani ba" "Yauwwa Jamsy, kar ki damu ki kwantar da hankalinki, in dai mu na tare, kuma za ki din ga yi mini biyayya babu abin da ba zan yi miki ba, kin ji yarinyar kirki?" Jamila ta jinjina kai tana ɗan sakin fuskarta. Ta numfasa ta ce "Hajiya bari na je gida" "Ban ce ki daina ce mini Hajiya ba?" "Yi haƙuri Mummy" "Good, sai kin dawo yarinyar kirki, ki gaida gida, zan saka miki kuɗin, kayan kwalliya a account ɗin ki" Ta saki murmushi ta ce "Tom Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi" Ta juya ta bar falon, tana jin wani irin nishaɗi, duk da wata irin fargaba na ratsa ta, daga ƙarƙashin zuciyarta, da ba ta san ta mece ce ba. Karo ta yi da wani matashin saurayi, yana ƙoƙarin shiga gidan. "Sannu ina wuni?" "Lafiya ƙalau ya ki ke?" "Lafiya ƙalau" ta amsa tana niyyar raɓa shi ta wuce. "Gurin Mummy ki ka zo ne?" Jamila ta ce "Eh gurinta na zo" Ya ce "Ok shikenan, ki gaida gida" "Gida zai ji na gode sosai da sosai" ta nufi gate ɗin ta fice. **** Da ƙyar Nana ta iya sallar asuba, saboda gajiya ga bacci da take ji, da ta idar da sallar ma, a kan sallaya ta jingina tana gyangyaɗi ta kasa azkar ɗin. Hannunta ya ɗan shafa, ta buɗe idonta da kyar ta kalle shi. "Bacci ne?" Ta ɗaga masa tana lumshe idonta. Ya kama hannunta, ya ɗaga ta tsaye, ya ja ta zuwa kan katifa. Ta tsaya tana ƙoƙarin cire hijjabin, ya ƙarasa cire mata ta kwanta. Ta hau katifa ta buɗe bargo ta kwanta, kawai ta ji shi ma ya bankaɗo bargon ya shigo. Zumbur ta tashi zaune tana kallon sa. A ranta ta ce "Lallai ji mutum da samun guri" za ta yi magana ta fasa ta tsaya tana kallon sa. Shi kuwa ya yi kwanciyarsa, ya lumshe idanunsa, ya bar ta a zaune tana hamma. Sai da bacci ya ci ƙarfinta sannan ta kwanta. Sai da ya ji ta kwanta sannan ya buɗe idonsa. Ya juya sosai yana kallonta. Zai iya cewa tun da ya tsinci kansa a cikin wannan duniyar da yake a yanzu, wadda yake kamantawa da duniyar mafarki, bai taɓa tsintar kansa cikin nishaɗi da farincikin yau ba. Ya kasance cikin damuwa, da tsananin ɓacin ran rashin sanin waye shi, daga ina yake? Ina zai dosa? Rashin sanin amsoshin nan, na dugunzuma hankalinsa da haifar da wani irin nauyi a ƙirjinsa, wani irin duhu ya mamaye shi, bai taɓa jin daɗin komai, ko farinciki da komai ba. Duk da dai-dai gwargwado Habu da sauran wanda suke tare su na ƙoƙari a kansa, amma sam babu abin da yake raguwa na duhu da damuwa a tare da shi. Sai bayan da ya fara kasancewa da Nana a ɗaki guda. Ganin gilmawarta kawai, yana kallon ta, yana jin daɗi. Ya kan ji kamar ya yi mata magana amma sai ya kasa, ya rasa mai zai ce mata. A wannan duniyar da ya yi wa laƙabi da duniyar mafarki, ya ga mutane na bawa ahali muhimmanci, amma shi ba shi da su, kuma ba a duba rashin ahalin nasa ba, aka aura mata shi, hakan ya kan saka ya ji tausayinta. Yanzu a wannan duniyar yana kallon Nana a matsayin ahalinsa. Duk da ba ya son hayaniya, amma muryarta mai sanyi da daɗin sauraro, ba kamar su Habu ba, sai yana cikin damuwa ko rashin lafiya, ya din ga jin muryoyin su a sama kamar kwarankwatsa ba. Ya kan ji babu daɗi idan ya ji ta shiru, yana matuƙar son ya ga tana kallon sa, idan su ka haɗa ido ta murguɗa baki tana magana ƙasa-ƙasa, komai na ta a sanyaye. Ya ƙura mata ido, yadda ta yi nisa a baccinta, ya sumbaci goshinta, ya mayar da bakinsa wuyanta ya sumbata. Ta buɗe ido ta juyo ta kalle shi, idanun na ƙoƙarin sake rufewa. Ya kwantar da kanta a kan ƙirjinsa. Ba ta yi musu ba, sai ma jikinta da ya saki. Murmushi ya yi jin yadda numfashinta yake shiga nasa, ya ji tamkar su dauwwama a haka saboda yadda yanayin ya yi masa daɗi. "Ke ce Ahalina" Nana ce ta raɓe a gefen ƙofa, tana hango ƙaisar yana rubutu, sai dai wannan karon ba a cikin Library bane ba, gurin da yake haɗa magunguna ne. Ga tarkacen kwalaban magunguna ko ina a cikin gurin. "Ya dai?" Ya tambaye ta. "Ba komai" ta faɗa a hankali, tana sinne kai. Ya ce "Na ga kwana biyu kina nema na, ba mu haɗu ba, akwai matsala ne, ko kina buƙatar wani abin ne?" Ta girgiza kai tana sinnewa. "Wai meyafaru ne na ga kin canza yau gaba ɗaya, kamar ba ke ba? Kin wani nutsu" Still taa yi shiru tana ƙifta ido. Kawai ta ji ya bushe da wata iriyar dariya, da sai da ta tsorata ta ɗan ja da baya, saboda yadda sautin dariyar ya karaɗe ilahirin gurin. Ya tsagaita da dariyar ya ce "Kar ki damu, ki kwantar da hankalinki ban ga komai ba, ba abun da na ganu" ta yi tsuru -tsuru amma ta kasa magana. Ya ce "Ki maze fa kamar babu abin da ya faru, babu abin da na gani, ai ku na cikin duhu, kuma duk da haka ma, lamari ne mai girman gaske da bai dace na ga ƙwaƙwaf ba. Sai na yi gaba abuna" ya yi maganar yana tashi tsaye. Ya nufi gurin wasu kwalabe, yana duddubawa "Ki saki ranki fa, sai dai ban sani ba ko kin gano sakamakon binciken naki, na mutum ne ko kuma aljani da ki ka iya amincewa wani abu ya faru tsakanin ku. Abin da mamaki yadda jikin ɗan Adam yake iya ɗaukar zafi kamar an saka shi a cikin wuta, kuma bai mutu ba. Kodayake ai haryanzu ban tabattar ba ko wani abun ya faru ba, tun da a cikin duhu ne, amma tsaya a tsakanin ke da shi waye ya kashe muku fitilar ne? Ko ita ta kashe kanta?" Ya sake bushewa da dariya, ya yi wata irin hajijiya, guguwa ta tashi, ta cikin guguwar muryasa ke tashi ya ce "Kamar dai yadda na gaya miki ne, ban ga komai ba ki daina sinne kai" guguwar ta yi waje ta daina jin muryarsa. Ta yi ajiyar zuciya tana tunani, ta din ga jin tamkar wadda ta aikata saɓo. Ba saɓo ki aikata ba Nana, makomar ki ki ke tunani. Wata zuciyar ta tunatar da ita. Tabbas zancen rashin sanin waye shi, yana damun zuciyarta. Amma ita ma mutum ce ba gini ba, ta yaya za ta iya tsallake dabaibayin da ya yi mata a daren. Idaonta ya sauka a kan tarin litattafan da suke gurin da ya zauna, da hanzari ta tashi ta tafi ta hau caje litattafan. Bisa tsananin sa'a ta ci karo da littafin da take ta ƙuzun son jin ci gaban sa. Da hanzari ta buɗe, sai dai tana buɗewa kawai ya kai ta daidai gurin da ta tsaya. Ta nutsu ta ajiyar zuciya ta fara karantawa. Lanti ta yi alwashin ko tilon 'yar ta, za ta rasu ba za ta taɓa kai wa sarkin aska yarinyarta ba ya bata magani. Mijinta ya rarrashe ta a kan ta yi haƙuri, su kai yarinyar ko za a dace da maganin. Cikin damuwa ta ce "Duk da yarinyar nan ce kaɗai nake da ita a yanzu, ba kuma ni da tabbacin sake samun wani ɗan, amma gara na rasa ta da na je gurin maƙiyina nema mata magani, ni na san abin yi, ka bar ni kawai" Lanti ta shirya, ta ɗauki yarinyarta, ta tafi garin da aka ɗaukko bokan da ya yi wa sarkin aska girka. Ko da ta je garin ta iske ya tsufa sosai, ga rashin lafiya yana ta fama da ita. Ta gaya masa abin da yake tafe da ita. Ta ce "Ka ga halin da yarinyata take ciki nan, ni kuma ba zan iya kai wa sarkin aska ita ba ya bani magani, saboda a duniya ba ni da maƙiyin da ya fi shi yanzu a duniya. Kuma ina son na dakatar da zaluncin da yake yi wa mutanen ƙauyenmu, da sunan Aljanu ne suke saka shi" Ya yi shiru sannan ya ce "Ni kaina na yi dana sanin girkar da na yi wa sarkin aska, kafin ke wasu da dama sun zo a kan haka, ciki har da mai garin ku, su na neman mafita. Sai dai hatta ni kaina yanzu sarkin aska ya fi ƙarfina, da na san haka ne da ban yi masa girkar nan ba". Cikin damuwa ta ce "Yanzu mene ne abin yi?" Ya ce "Babu wani abu da zan iya, sai dai ki koma gurin kakanki, mahaifin sarkin baka, ki ce masa ni na turo ki, ni boka Giyaz" "Kakana kuma? Kakana ne yake da yadda za a yi da Sarkin Aska?" "Ke dai ki je ki same shi, ki ce masa ni na aiko ki" Ta jinjina kai ta ce "To shikenan" ya bata magani, bayan kwanaki uku, ta koma garinsu. Kai tsaye gurin kakanta ta fara zuwa, bayan sun gaisa ya yi mata sannu da zuwa. "An aiko ni gurinka" Ya ce "Tun kafin ki dawo aka aiko mini da 'yan aike, suka sanar da ni zuwan mi" Cikin mamaki ta ce "Su wa kenan?" Ya yi murmushi ya ce "lokacin da aka zo da ni garin nan, ina ɗan ƙarami sosai da sosai na san wasu daga cikin gwagwarmaya da dambarwa da aka din ga yi da aljanu kafin mu samu zaman lafiya. Sai dai alƙawarin aljani ba shi da tabbas, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da muka yi, sun ƙi yarda mu zauna lafiya, su na kawo mana farmaki, lokaci zuwa lokaci. Yanzu dai ki na da burin kawo ƙarshen sarkin baka, kuma kina burin ganin 'yar ki ta warke gaba ɗaya, abu ɗaya za ki yi sai dai abin da wahala" Cikin zaƙuwa ta ce "Ka gaya mini, ko mene ne zan yi, muddin burina zai cika" "Burinki zai cika, amma sai dai ki amince a yi miki girkar aljanu, ya zamana ke ma ki na da aljanun da ki ke iya sarrafawa, sannan za ki iya ja da shi, har ma garin nan ya zauna lafiya. Amma sai dai ki samu masu ƙarfi da za su iya jayayya da na Sarkin Aska." Ta numfasa ta ce "Kakana na amince ka yi mini girkar aljanu, dole na kawo ƙarshen sarkin aska a garin nan" "Lanti, ki je ki ya shawara tukuna. Girkar Aljanu ba hukunci ne da zaka yanke kai tsaye ba tare da cikakken shiri, da nazari ba" Ta tari numfashin sa da cewa "Ba na buƙatar yin shawara, na gama yanke hukunci na amince a yi mini girkar Aljanu" Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi za ki je sai nan da sati biyu, zan haɗa tsumin da za a yi miki amfani da shi, gurin yin aikin zan shafe kwanaki ina aiki a kai, domin yi miki girkar. Sai dai ina son ja bakinki, ki yi shiru har zuwa lokacin da za a yi aikin" "To kakana, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai kai, amma ya aka yi ka iya wannan abubuwan haka?" Yayi murmushi ya ce "Kamar yadda na gaya miki, tun ina yaro aka zo da ni garin nan, lokacin ana kan ganiyar rashin zaman lafiya da ainihin aljanun da suke zaune a garin nan. Bayan na ɗan tasa na fara yawon farauta, a nan na yi karo da wani matashin saurayin, sa'ana muke shiga tare da shi daji, gurin yin farauta sai dai ya fi ni rashin ji. Shi ne ya koya mini farauta, da siddabaru kala-kala da hatsabibanci, ban san gidan su ba, kullum a hanya muke haɗuwa mu tafi Daji. Sai daga bisani na fahimci ba mutum ba ne ba. Aljani ne yake shiga jikinsa, muke wannan abotar, shi ne ya koya mini harkokin farauta da magunguna har mahaifinki ya gada. Kuma ba kowa ba ne face wannan bokan da aka kawo shi garin nan ya yi wa sarkin aska girka, wanda ki ka je gurinsa yanzu. Jikinsa aljanin yake shiga, kuma shi ya haɗa mu abota da boka Giyaz." Lanti ta jinjina kai cike da mamaki, dan duk labaran da yake ba ta, bai taɓa ba ta wannan labarin ba. Ta koma gida ta yi shiru da bakinta, ko mijinta ba ta sanarwa ba. Kakan Lanti ya shirya ya tafi daji, ya shafe makonni biyu, yana tattara saiwowayi, sassaƙe da kuma sassan jikin dabbobin da yake buƙata gurin yi wa jikarsa Lanti girkar aljanu. "Dattijo ka yi a hankali, za ka yi mini ɓarna fa" kakan Lanti ya ɗago tare da faɗin muryar wa nake ji haka, rai kan ga rai Uban duƙusa?" "Ƙwarai kuwa, na zata ka mutu ai" Kakan Lanti ya bushe da dariya ya ce "Ban mutu ba tukuna, ina nan raye ina ka tafi tsawon wannan lokacin haka? Kuma a ina ka samo gangar jikin da ka shiga haka ka zo mini?" Kyakyawan farin matashin da yake tsaye a gaban kakan Lanti yayi murmushi ya ce "Labarin dogo ne, na yi balaguro ne zuwa gabashin duniya, na samo labarai daban-daban da zan rubuta" "Yanzu neman labarin ne, kusan shekaru hamsin babu amonka" "Shekaru hamsin mu a gurinmu ai babu yawa. Bani labari na ga gari ya zama alƙarya abubuwa sun canza sosai da sosai. Saukata kenan da kai na fara karo na ce bari na bayyana na kwashi gaisuwa" "Tuba nake uban gidana, ai ni yakamata na zo kwasar gaisuwa." Nan kakan Lanti ya bawa uban duƙusa labarin abin da ya faru. Cikin damuwa ya kalli kakan Lanti ya ce "Yanzu duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi, sai da aka saɓa ta? Waye ya yi wa sarkin askar girka?" "Giyaz ne, mutane sai wahala suke yi a garin nan, saboda abin da sarkin aska yake yi. Ya sadaukarwa wasu daga ahalinku jini, ya mayar da su baƙaƙen aljanu da sunan zai taimaka musu gurin ɗaukar fansar abin da mutanen garin nan suka yi muku" Matashin ya shafi fuskarsa cikin damuwa, ya ce "Yanzu wa za ka yi wa girkar?" "Jikata ce, da nake kyautata zaton sarkin aska ne ya kashe babanta, saboda yana bayar da magani" Uban duƙusa ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne, shikenan zan je gida, zan huta kafin ranar da za ka yi mata girkar, amma ka tabattar za ta iya ɗauka? Ka san idan aka samu akasi, za ta iya haukacewa fa" "Za ta iya, tana da juriya, kuma tana fatan ɗaukar fansar abin da aka yi wa mahaifinta" "To shikenan, zan sake dawowa" "To shikenan ubangidana, ina godiya da wannan ziyara ta bazata" suka yi sallama. Kakan Lanti ya koma gida, ya shiga wani ɗaki a cikin gidansa, ya haƙa rami ya saka wata randa. Ya kawo saiwoyin da ya zo da su ya zuba a ciki, ya kawo tarkacen magunguna kala-kala ya zuba a ciki. Ya kawo ƙasusuwa da wasu sassa na jikin dabbobin daji, a zuba a ciki. Ya kawo turare ɗan goma, da farin goro duk ya zuba a ciki ya rufe randar, sannan ya mayar da ƙasar ya binne. Sai da aka kwana biyu, daren na uku da zai buɗe randar, wanda saura kwana biyu ya yi wa jikarsa Lanti girkar aljanu. Yana cikin bacci, ya ji wata irin ƙara, sanyi yana ratsa shi, ya tashi da nufin neman abin rufa, amma ya gan shi a tsakiyar daji, gurin da suka haɗu da uban duƙusa. Cikin mamaki ya ce "Ubangidana lafiya aka kira ni a wannan daren haka? Idan na yi laifi ne ina neman afuwa" uban duƙusa ya fito daga bayan bishiyoyi ya ƙaraso gaban tsohon nan ya ce "Ba ka aikata mini wani laifi ba abokina, Ina mai baƙin cikin sanar da kai mutuwar Giyaz" "Wayyo, Giyaz ya mutu?" "Ƙwarai Giyaz ya mutu, sannan na yi baƙin cikin abin da na zo na riska, galibin 'yan uwana, sun koma baƙaƙen aljanu, kuma sarkin aska yana sarrafa su ta mummunar hanyar da ba ta dace ba. Su na sanya muku miyagun cututtuka. Tabbas idan ku ka yi sake sai sun shafe tarihin mutanen garin nan. Ban ji daɗin yadda aka saɓa alƙawri da yarjejeniyar mu ba. Dan haka zan kasance tare da ku a gurin girka, dan kuwa komai zai iya faruwa, za ta iya rasa rayuwar ta ma. Kar ka kuskura ka yi mata girka da baƙaƙen aljanu, dan abin ba zai haifar da ɗa mai ido ba, sai mun haɗu a gurin. Ayshercool 08081012143 Kakan Lanti ya ci gaba da shirye-shiryen yi wa jikarsa girka. Ya samo ƙaramin ƙoƙo, da 'ya'yan wuri, tsirkiya ya haɗa garaya. Ya haɗa caki, ta hanyar samun butar duma ya fafe ta, ya zuba busassun 'ya'yan tafasa, da zogale a ciki, ya toshe bakin. Ya tsayar da ranar yi wa Lanti girkar aljanu, ya sanya ranar Lahadi. A sirrance ya aika saƙon gayyata zuwa ga bokayen maƙotan garin. Bayan almuru, yaje ya saku ƙatuwar Bishiyar kukar da ke wajen garin, ya je ya samu, ya naɗe da farin yadi. Ya koma gida, ya tono randar nan, ya ajiyeta a tsakar gida, ta kwana tsumin cikinta ya yi sanyi. Ya koma ya dafa wani magani, ya zuba a cikin kwatanniya. Mutane suka din ga mamaki wayewar gari, da suka ga wannan farin yadi a jikin bishiyar kuka, aka din ga surutu, har labari ya iske mai gari. Aka yi ta yekuwar wa ya aikata wannan abu, kar a je wata fitinar ce za ta taso. Kakan Lanti da kansa ya je ya samu mai gari, bayan sun gaisa ya ce "Ranka ya daɗe, ni ne na ɗaura wannan farin ƙyalle, yau da yamma zan yi wa jikata Lanti, girkar aljanu" Mai gari ya waro ido ya ce "Girkar aljanu kuma? Kar ka janyo mana bala'i bayan wanda muke ciki, kuma ya za mu yi idan sarkin aska ya ji, kar aljanu su fushi da mu fa?" "Babu abun da zai faru sai alkhairi, ba zamu dauwwama Sarkin aska, yana juya mu yadda yake so ba, ina son ka yi haƙuri ka bani wannan damar" Da ƙyar ya shawo kan mai gari ya amince, aka din ga shela ana gayyatar mutane, gurin yin bikin girka. Mutane suka din ga al'ajabi, tare da jiran yammacin ranar lahadin, domin ba su taɓa sanin yadda ake gudanar da girkar ba. Nana da labari har maƙwabtan garin, aikuwa jama'a suka din ga ɓarkowa cikin garin. Kakan Lanti tun safiyar ranar, ya sanya ta yi lalle dungulmi, hannu da ƙafa. Ya bata fararen kaya na saƙi, ta saka ya kawo warki, na fatar kura da aka jeme, aka saka ta a shuni, ta ɗaura a ƙugunta, sannan ya kawo wuri ya bata shi ma ta sanya a ƙugun nata. Daga bisani ya kawo wasu irin guraye, ta ɗaura a damatsenta. Ya kawo sandar dargaza ya bata, sanda ce da aka yi da itacen tsamiya, aka naɗe ta da fatocin dabbobi daban-daban, suka yi beza a jikinta. Tun daga gidan kakan Lanti, ta samu rakiyar mutane, ɗuuuu tamkar ƙudaje zuwa filin girka. Fili ya cika ya tumbatsa, aka shimfiɗa saƙi kala-kala a gurin. Ya bata wani kwalli ta sanya a gurin, ya ba ta goro da fure, ta saka a bakinta ta tauna, laɓɓanta suka yi jawur. Idanunta su ka yi rabajau da kwalli. Tuni makaɗan borin, da kakan ya gayyato daga wasu garuruwan suka jeru, suka fara kaɗa garaya da goge. Ya bawa Lanti, wannan tsumin na cikin kwatanniya ta sha, ya saka ta zauna a kan shimfiɗar nan. Ya din ga ɗebo ruwan cikin randar nan yana zuba mata, wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, har zabura take yi saboda sanyi. Ya kawo turare ɗan goma ya shashshafa mata, ya kawo wani gwado, ya rufa mata. Sannan aka koma gefe aka kunna hayaƙi. Ya koma gefe shi ma ya hau kaɗa kacakaurar da ya haɗa. An ɗauki dogon lokaci a haka, kafin ta fara murƙususu a cikin gwadon da aka rufe ta da shi, tana wani irin kakari. Shewa masu kiɗan borin suka hau yi, ana murnar aljanun sun fara hawa kanta, dan haka suka ƙara ƙaimi gurin ci gaba da kiɗan borin. A hankali ta tashi tsaye, tana wata irin girgiza, bakinta na fitar da kumfa, ta ɗaga wannan sandar ta dargaza, ta fara tangaɗi a gurin. Mutane suka ɗauki sowa, gwargwadon tashin kiɗan, gwargwadon tangaɗin da take yi, tana girgiza dogon gashin kanta. Babu tsammani, gari ya yi duhu, wani irin hadari ya haɗu, sai dai hadarin na guguwa ne. A take jama'ar gurin, suka tsatstsaya, su na kallon yadda garin ya canza, su na jiran ganin abun da zai faru. Tukunyar tsumin da aka zo da ita ta tarwatse, wata irin gigitacciyar guguwa ta turnuƙe gurin, har wani ba ya iya ganin wani. Sarkin aska ne ya bayyana tamkar an jefo shi, a hankali kuma ƙurar ta fara lafawa. Lanti kuwa cak ta tsaya, hannunta riƙe da dargazarta, ta sunkuyar da kanta ƙasa. Sarkin aska ya nufo inda Lanti take, cikin azama kakanta ya shiga tsakaninsu, ya tari Sarin Aska, wani irin jifa ya yi da tsohon a gefe. Lanti ta ɗago da kanta, suka yi ido huɗu da Sarkin Aska. Cak ya tsaya yana kallonta cike da mamaki ya ce "Uban duƙusa" "Ka durƙusa akan gwiyoyinka, ka nemi afuwar uwar gijiyata, kafin raina ya ɓaci" ta yi maganar cikin wani irin sautin muryar da ba tata ba. Sarkin aska ya ce "Kai yanzu da kai aka yi wa maƙiyanmu girka? Ka manta zaluncin da bil adama suka yi mana? Ka manta gargaɗin da kakaninmu suka yi mana a kansu?". "Ban manta ba, kuma ina bayan gaskiya har abada, ku kuka fara karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi, dan haka ba zan bi bayan ɓarna ba, dan haka ka yi abin da na ce" "Har abada. Har abada ba zamu yi maka biyaya ba, duk da kasancewarka abu mafi soyuwa a zuriyarmu." Nana ji ta yi an yarfa mata ruwa a fuska, ta buɗe idonta da sauri. Ido huɗu suka yi, ya sakar mata tattausan murmushi. Ya ajiye matajin da yake taje kansa da shi ya nufo ta, cikin hanzari ta shige cikin bargo da kanta. Ya zauna a kusa da ita, ya saka hannu ya janye bargon, ta ƙi buɗe idonta, sai ma miƙa da ta yi, saboda duk jikinta ciwo yake yi, kuma sam baccin bai ishe ta ba. Ya zuba mata ido, murmushi ya gaza barin fuskarsa. "Ina kwana" ya faɗa yana kallon ta. Kasa kallon sa ta yi, ta sunkuyar da kanta tana basarwa. "A tashi a karya" ya yi maganar murmushi ya kasa barin fuskarsa. Ta ja jikinta ta tashi zaune da ƙyar. "Bari na yi brush" ta tashi ta nufi toilet. A banɗaki ta tsaya ta yi shiru tana tunanin littafin da take karantawa na Ƙaisar, ta san yanzu kafin ta sake samun littafin sai an daɗe. Kenan da gaske dai shi ne uban duƙusa? Ya aka yi sunansa ya canza zuwa Ƙaisar? Ta wanke fuskarta ta yi brush ta fito. Har ya karkaɗe mata shimfiɗa. Ta zauna, ya ɗaukko kofi da murfi ya miƙo mata. Ta saka hannu ta karɓa, ta buɗe ta ga abu a kofin kamar madara, da ɗan wani gari gari a kai. Ta kalle shi ya ce "Sha" ta kai bakinta, ta ji babu ƙarni, ta yi bismillah ta fara sha. Babu zaƙi, sai dai akwai garɗi da maiƙo a baki, ga ɗumi kuma babu ƙarni mai damu. Sai da ya saka ta shanye tas, ta kalle shi ta ce "Wai mene ne wannan?" Ya yi murmushi ya ce "Nonon raƙumi ne" "Raƙumi kuma? A ina ka samu Nonon Raƙumi?" Ya ce "Habu na saka ya kawo miki, jikinki zai yi ƙwari, ga abinci ma sun haɗo da shi, na ce ba ki da lafiya" "Gaya musu ka yi?" Ya ce "Me?" "Abin da ya faru jiya?" "A'a ban ce musu, kin kore ni waje ruwa ya jiƙa ni saboda ki na tsoro na ba" Ta ce "Ba wannan ba" "To me?" "Ba komai" tayi maganar cikin basarwa. Ya yi dariya ya ce "Ban faɗa ba, daga ni sai ke kawai wannan" ta yi shiru wata irin kunya tana mamaye ta. Babu babban abin da yake ƙara sanya Nana farin ciki, sama da samun abinci sau uku a rana da take yi a wadace, babu geji kuma babu hantara. Ƙaton buredi ne lafiyayye, aka soya ƙwai fal, shayin ma shi ya zuba mata. Tana ci yana ƙare mata kallo. "Ka daina kallona, ko na tashi" "A'a" Ta ce "A'a me?" "Ba zan daina ba" Ta juya gefen sa, yadda sai dai ya kalli side ɗin fuskarta, ta gama ci ta koma gefe. Shi ya yi mata komai, da ta motsa sai ya ce ta zauna. Sai dai ya lura gaba ɗaya ta zama so silent yau, ba karaɗi da surutu. Duk sai ya ji hakan babu daɗi. Ita kuwa ta yi matuƙar mamaki, ganin yau bai fice ya bar ta ita kaɗai ba. Ya dawo kusa da ita ya zauna, har gashin sa yana taɓa wuyanta, kasancewar bai tufke shi ba, sakin sa ya yi. "Me ya faru?" Yayi maganar yana ɗora hannunsa a nata. Ta girgiza masa kai, alamar babu komai. "Ko ana fushi ne?" Ta ɗaga kai alamar eh. "Me yasa?" Ya tambaye ta, yana shafa jikinta. A ranta ta ce "Ikon Allah, ji mutumin nan da samun guri" "Ba ki ce mini ya jiki ba, kin kore ni ruwa ya jiƙa ni, ba ni da lafiya" Nana ta tura baki ta ce "Ba ga shi ka warke ba, kuma ba ina sane bane ba" "To ke kin warke?" Yayi maganar ƙasa-ƙasa. Cikin mamaki ta ɗago tana kallon sa, hakan ya ba shi damar haɗe bakinsa da nata. Gaba ɗaya Nana sai ta rasa bakin magana, sai rarraba ido. Yana sane yake wannan shirun, yana sunkuyar da kai, ko kuwa ya abin yake? Ta tambayi kanta. Tana jin yadda ya ƙanƙame ta a jikinsa, sai yawo yake da hannunsa a jikinta, yana neman ya sanya lissafi ya ƙwace mata. Domin har mamakin kanta take yi, yanayin da take shiga, idan su na tare ko da kuwa a cikin bacci ne. "Ammm ya aka yi yau ka ke magana sosai? Maganar ba ta ɗauke ba?" Ya ce "Mmmm, tun jiya ma na ji ina iya yi, haryanzu ban ji kaman an shaƙe ni ba ta daina fitowa. Wataran ina son na yi nake kasawa" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To yanzu baka san sunan ka ba, wane sunan zan din ga gaya maka kenan?" "Ko wanne" "In ce Buzu nima?" "Nima in ce buzuwa?" Ya tambaye ta. Ta ɗago ta kalle shi ta ce "Buzuwa kuma?" "Eh, macen buzu shi ne buzuwa ba? Idan ki na kallona zan kuma sumbutar ki ne a baki" Ta yi sauri ta sunkuyar da kanta, ya sake gyara riƙon da ya yi mata da hannayen sa. "To yanzu me zan din ga ce maka ne?" "Ki saka mini ko mene, nima zan ji daɗi, kowa yana da suna ni ba ni da shi" "To da yaya aka ɗaura mana aure ba ka da suna?" Ya ce "Habu za ki tambaya" "To ni yanzu ina na ga Habun?" Ta ɗan yi shiru, sannan ta ce "Ka ga kai mijina ne, to in ce maka Sayyid ka na so?" Ta yi maganar tana ɗagowa ta kalle shi. Sake haɗe bakinsa da na ta ya yi, na wani ɗan lokaci, sannan ya cire bakinsa ya kalli idanunta ya ce "Sayyid, j'aime ça (I like it)  ma vie" "Ni ka daina yi mini wannan yaren ba  na ganewa" ta yi maganar da sigar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba. Murmushi ya cigaba da yi, yana lumshe idanunsa. "Yau ba za ka fita ba ne? Kar su zo su na neman ka, kana nan a zaune" "Ba na son fita" Ta ce "Saboda me?" "Saboda ke" "Ni har yanzu mamaki ka ke bani, kamar an canza ka, ka yi magana ta fi guda goma sha biyar" Wannan karon sosai ya buɗe haƙoransa ya yi dariya, ya ce "Kin ƙirga ne?" Ta ɗaga masa gira ɗaya tana murmushi. "Me yasa  nake ba ki tsoro? Me na yi yake ba ki tsoro?" Shiru ta yi ta rasa abin da za ta ce masa, kenan shi ma bai san abin da take gani ba. Horn aka yi da mota, Nana ta fara ƙoƙarin zame jikinta ta ce "Ana horn, shi yasa na ce maka ka shirya ka fita, kar a zo ana buƙatar ka". A matuƙar kasalance, ya tashi ya je gaban mudubin ya tsaya. Nana ta tashi ta ɗaukko masa yin rawaninsa. Sai dai mai horn ɗin ya ci gaba da yi babu ƙaƙƙautawa. "Sayyid ko za ka buɗe musu, sai ka dawo ka saka rawanin?" Hankalinsa a kwance ya ce "Za ki iya fita ba riga?" Sororo ta yi tana kallon sa. "Idan ba za ki iya fita ba riga ba, ba zan iya fita babu rawani ba, gashina a buɗe. Yadda ki ke jin abin da ki ke ɓoyewa haka buzu yake ji, idan ya fita bai suturta gashin sa ba". "To ni dai ka bar wannan falsafar, ka yi sauri" a nutse ya naɗa rawanins, Nana na ta azalzalarsa, saboda horn ɗin ya wuce hankali. Ya gama naɗawa ya fita, ya buɗe gate ɗin. Ko ƙarasa shigo da motar ba a yi ba, ta fito daga cikin motar a matuƙar hasale cikin matsananciyar fusata ta ce "Malam bagidajen ina ne kai? Kurma ne kai ko ba ka ji ne? Wannan ai tsagwaron wulaƙanci ne?" Bagidajen da ta faɗa ya sauka a ƙirjin Nana. Kallo ɗaya ya yi wa matashiyar budurwar, ya sake gyara zaman takunkumin fuskar sa, ya nemi guri ya zauna a kan bencin da yake zama. "Ba magana nake yi maka ba? Ba za ka iya ba ni haƙuri ba?" Cikin azama Nana ta sako hijjabinta ta fito, ta nufi inda Siyama take ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, yana uzuri ne shi yasa bai fito da wuri ba" "Ni kun san meye nawa uzurin da zan ta horn over 10 minutes, amma bai buɗe ba, kuma ina magana ya yi mini shiru dan wulaƙanci?" Nana ta sake kwantar da murya ta ce "Ai ni na baki haƙuri a madadinsa, dan Allah ki yi haƙuri, ba zai sake ba" "Wawa kawai" ta furta tana juyawa t nufi gurin da motarta take. Nana ta haɗiye wani abu mai matuƙar ɗaci, ta ji zafin maganganun da aka gaya wa mijin nata. Duk da ta san ya yi laifi amma kalmomin sun yi tsauri. Ta kalli idonsa ta ga ya yi jawur, hannayen sa na rawa, launin fatarsa ya canza zuwa ja. Ta zauna a kusa da shi a kan bencin, ta ɗora hannunta a bayansa ta ce "Sayyid. Ka yi haƙuri na fika jin zafin abin da ta gaya maka, amma ka yi haƙuri ka ji?" Kawai ya jinjina mata kai. Ta sake kallon idanunsa, yadda suke ƙara rinewa zuwa launin ja, hakan ya ƙara bayyanar da matsanancin ɓacin ran da yake ciki. "Taso mu koma ciki to, tun da ka buɗe mata" ya girgiza mata kai alamar a'a. Jiki a sanyaye Nana ta tashi ta ƙyale shi, dan ya fara ba ta tsoro. Duk da yanayin da take ciki, ta ji daɗin hirar da suka ɗan yi da shi. Ta kama aikace-aikacen ta a cikin ɗakin. ***** Jamila ce take gaya wa Mama batun unguwar da Hajiya Sa'a ta ce za ta raka ta. Mama ta ce "To mene ne a ciki? Ai babu komai yadda take nuna miki ƙauna, ni ko bangon duniya ta ce za ku je, ai ba zan hana ba" "To Mama Baba fa? Ni ba na son masifar nan tasa" "Dalla rabu da shi, uwar me yake bamu a gidan, Ubangiji Allah ya haɗa ki da iyayen ɗaki masu ƙaunar ki, mu na samun alkhairi ta hannunsu, za ki din ga kawo zancen sa, ki yi tafiyar ki, ni na san abin da zan gaya masa" Jamila ta yi murmushi ta ce "To shikenan, ni dama ba na jin ki, na san za ki bar ni" Can Asibiti kuwa, likitoci sun yi deciding, tiyata za a yi wa Shukura a cire jaririn cikinta, saboda a tseratar da rayuwarta da ta abin da yake cikinta. Sai dai da Jininta ya sauka sai ya sake hawa, saboda gaba ɗaya a tsorace take, ta yanke tsammani da rayuwar duniya ba ki ɗaya. Duk da irin rarrashi da ƙoƙarin kwantar da hankalinkin da ake yi mata. Bayan Nana ta ɗora girki, ta kira Hajiya Amina su gaisa, a nan take gaya mata halin da ake ciki, cewar su na Asibiti an kwantar da Shukura. Hankalin Nana ya tashi sosai da sosai, tana son zuwa duba Baba da Jamila ma, ga kuma wannan maganar ta rashin lafiyar Shukura. Sai dai yadda ransa yake a ɓace ta san ba ta da damar yi masa magana. Tun da abin nan ya faru, bai sake shigowa ɗakin ba, ta je ta same shi a kan ta gama girki ya yi mata shiru. 'yar walwalar da ya fara yi ta gushe baki ɗaya. Gaba ɗaya abin ya dame ta sosai da sosai, ko abincin kirki ta kasa ci. Sai bayan sallar isha'i ya shigo ɗakin ya nemi guri ya zauna, ba tare da ya furta komai ba. "Sayyid ba ka ci abinci ba fa tun na safe ba ka kuma cin komai ba, dan Allah ka yi haƙuri ka ci abinci". Bai ko kalle ta ba, balle ta saka ran zai ci, ƙarshe sai haƙura ta yi ta zura masa ido. Ta gama shirinta, ta nemi guri ta kwanta, amma yana zaune. Nana ta jinjinawa girman zuciyar sa. Ya jima a zaune sannan ya tashi ya canza kayan jikinsa. Bacci har ya fara ɗaukar Nana, ta ji yana shigowa cikin bargonta, gabanta ya faɗi tuna abin da ya faru jiya, sai dai ba ta motsa ba, sai addu'a da take yi a karkashin zuciyarta. Ya matsa sosai ya rungume ta, yana yi mata numfashi a wuya. "Idan ina fushi, ki daina kula ni" ya faɗa kamar mai raɗa. Ba ta iya tanka masa ba, bai kuma sake ce mata komai ba, sai da ta ga babu alamar zai yi mata wani abu, sannan nannauyan bacci ya ɗauke ta. Tamkar wani zai ƙwace ta, ya ƙara ƙanƙame ta a jikinsa. Sai ƙamshin turaren sa take yi. A cikin baccin ta ji muryar Ƙaisar "Ba kin shige cikin bargo ba, idan ki ka kuma ɗaukar littafin nan ki ka karanta, sai na baki mamaki, sai na yi miki abin da ba ki taɓa tsammani ba" "To ina ruwanka da bargon da na shiga, ya naga kamar ka na kishi da mijin nan nawa ne?" Tsaki ya ja ya ce "Da me zan yi kishin? Haryanzu ba ki san a hatsarin da ki ke ba, wauta da shirme ne kawai yake ɗawainiya da ke. Kin ƙi ki buɗe ido ki kalli gaskiya. Gaba ɗaya kin ma manta da batun tantance waye shi, duk da irin abubuwan da ki ke gani da ya saɓa da ɗabi'ar bil adama" "A'a ba kyau zurfafa bincike, tun da Allah ya sa ina samun shinkafar da zan ci, ba ya saka ni kuka, babu tashin hankali ai gara na haƙura na lallaɓa haka. Duk wani abu da yake yi da ya saɓawa ɗabi'ar Adam wannan kuma na san kai ne, kai ka ke ƙulla komai. Na san so ka ke ka kashe mini aure, saboda kai duk yadda za ka yi hana ni jin daɗin rayuwata, shi ka ke yi" Galala yake bin Nana da kallo baki buɗe cikin mamaki. Ya ce "Gaskiya ne, idan ya gama baki jin daɗin za kuma ki ɗanɗana kuɗar ki, banda ina duba wani abu da da kaina zan bayar da jininki ga matsafan nan ki mutu uban kowa ma ya huta!" Ayshercool 08081012143 37 Nana ta saci kallon ƙaisar, jikinsa har fitar da hayaƙi yake yi saboda fusata. Ko a jikinta ta ce "Amm dan Allah ka gaya mini ya aka yi da Lanti a gurin yin girka? Ya aka yi ka hau kanta, tun da na ga ba da kai a ka fara yi mata girka ba, kuma ya aka yi ka canza sunanka? Ya aka ƙarke da sarkin aska kuma a garin? Ta yaya duk nake da alaƙa da wannan abubuwan?" Wani irin takaici ya turnuƙe Ƙaisar, ya tashi a fusace da niyyar ya yi jifa da ita, ko ya samu ya huce, sai kuma ya fasa kawai ya fice ya bar ta a gurin. Ta ce "Wallahi sai na kai ƙarshen littafin nan, ko da kuwa za ka kashe ni ne, sai na ga ƙwal uwar daka, sai na karanta har ƙarshe ko me za ka yi sai dai ka yi" Sannu a hankali yake shafa fuskarta, yana kallonta, kamar wata jaririya haka ta yi miƙa sannu a hankali, sai da ta banƙare gaba ɗaya. Ita gaba ɗaya ta manta da shi a kan katifar, a zatonta ita kaɗai ce a kan katifar, sai da ta ji ta a jikin mutum. Ta buɗe idonta ta kalle shi. Sai kuma ta ɗan tsorata, ta yinƙura da sauri. Amma ya riƙe ta yana kallon ta. "Amm lokacin salla ya yi ko?" Ya ɗaga mata kai alamar eh. "To bari na je na yi alwala" Ya cika ta tashi, ta je ta yi alwala, sai da ta fito sannan ya ce "Zan yi wanka" Ta ce "Wanka kuma? Yanzu?" Ya ɗaga mata gira daga kwance. "Ka yi da safe mana, gari da sanyi yanzu" Ya lumshe idanunsa ya buɗe, ya ce "Tare mu ka kwana a shimfiɗa, kuma ya dai kamata na yi wanka" Ba ta ce komai ba, ta yi shiru, Allah ya taimake ta, tana da ruwan zafi a tea flask ta haɗa masa. Ya yi wanka ya yi alwala ya fita Masallaci. Nana kuwa bayan ta idar da sallar asuba, ta zauna a inda take ta fara karatun Alqur'ani. Ya dawo ya tarar da ita, ya tsallake ta, ya nemi guri ya kwanta. Wajen ƙarfe takwas ya farka, tuni Nana ta gyara ɗakin yana ta ƙamshi, tana zaune a kusa da socket, tana caji tana danna waya. Ya ɗora hannunsa a kan cinyarta, ya rufe fuskar wayar, ta waiwayo ta kalle shi ya ce "Ina kwana?" Murguɗa masa baki ta yi ta ture hannunsa. Ya tashi zaune, ya matsa kusa da ita ya ce "Na yi laifi ne?" "Ai ka san me ka yi mini" Ya ce "A'a abun tun shekaranjiya ba ya wuce ba?" "Ni ba wannan ba, jiya na yi ta baka haƙuri amma ka haɗe rai ka ƙi kula ni, ka ƙi cin abinci ma" ta ƙarasa maganar tana hararsa Ya ɗan yi murmushi ya sake matsawa, tamkar zai shige cikinta ya ce "Na ce idan ina fushi ki daina kula ni" Ta noƙe kafaɗa ta ce "Ni ba zan iya ba" Murmushin fuskarsa ne ya faɗaɗa cikin matsanancin farin ciki ya kama hannunta ya ce "Ki yi haƙuri, idan raina ya ɓaci, ko bani da lafiya, bana iya magana. Wasu lokutan ina kasa magana haka kawai, amma ya fi idan raina ya ɓaci." "To ni da ba ni na yi laifin ba, sai ka daina yi mini magana? Na fi ka jin haushin abin da aka yi maka fa" "Na sani, ban san ya aka yi nake iya magana sosai ba idan ina tare da ke, ina iya yin sati ban iya yin magana ba, kuma ina son na yi amma ba ta fitowa. Amma ke yanzu ina yin magana da ke sosai, ina jin daɗi" Nana ta kwashe da dariya ta ce "Bagware idan ka yi magana dole sai mutum ya gane kai ba bahaushe ba ne ba" Yayi dariya ya ce "Na fiki iya Hausa sosai, buzuwata saka kaya muje sayo abun karyawa1" Cikin murna Nana ta ce "Yauwwa, dama ina son na fita na ga waje, tun da aka kawo ni ban taɓa fita ba". Dama ta yi wanka, ta saka hijjabi a kan kayanta, shi ma ya saka kaya, suka rufe ɗakin su ka fita. Sosai unguwar ta yi wa Nana kyau, duk da ruwan da ake yi, babu alama a unguwar saboda akwai wadatattun magudanan ruwa, ba kamar unguwarsu ba, da ruwa ɗaya sai unguwar ta shafe kwana uku maƙil da ruwa da azababben sauro. Ya saka hannunsa ya riƙo na Nana, ta ɗaga kai ta kalle shi, ya kashe mata ido. Sosai abin ya ƙayatar da ita. "Sayyid" Ya kalle ta, yana jiran jin abin da za ta ce. "Dan Allah ina son ka bani dama, na je gida na duba Baba, yana ciwon ƙafa tun bayan biki ƙanwata ma da suka zo, ba ta da lafiya. Kuma ka ga a al'adarmu yakamata mu je mu yi wa mutane bangajiya" "Mene hakan?" Ta yi murmushi ta ce "Mu yi musu sannu, saboda hidimar biki da suka yi, ka ga Shukura ma babu lafiya tana asibiti, maman yaron da nake raino" "Tom" Nana ta ce "To yaushe za mu je?" "Zan gaya miki" "To na gode sosai mai rawani" Gurin da yake zuwa sayen ƙosai suka je, Nana ta yi mamaki ganin har a manyan motoci ake zuwa gurin sayen ƙosai, da kunu gurin matar. Nana ce ta yi wa mai ƙosan magana ta gaishe ta. Matar ta ce "Laa kece matarsa ko 'yar uwassa?" Nana ta yi murmushi ba ta ce komai ba. "Allah sarki, yana zuwa sayen ƙosai ai, na nawa za a baku? Ki ce masa na ce kwana biyu bai zo sayen ƙosai ba, ban iya maganar su ba" Nana ta ce "Ai yana jin ki" Matar ta ce "Haba dai? Ba kurma ba ne?" Nana ta kwashe da dariya ta ce "Yana magana" "To ai kullum ya zo kuɗi yake bayarwa kawai, ko ya rubuta" Ya yi mirsisi kamar ba a kan shi ake magana ba, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya bawa Nana. Kamar Nana ta san matar, suka din ga hira, ta sallame su, suka nufi gida. "Sayyid dan Allah ka din ga yi wa mutane magana, ko dan saboda yanayin rayuwa. Ka ga da yawa ana ɗauka ko kai kurma ne" shiru ya yi mata, haryanzu ba ta gama fahimtar sa ba. Ba ta damu da rashin bata amsar waccan maganar ba ta sake cewa "Yauwwa, dan Allah akwai gidaje a bayan gidan nan ne? Ina son sanin gidan Anty Haula, ina son na kai mata ziyara nima" "Babu gidaje a baya" "Amma ta ce mini gidanta a bayan inda muke yake" Ya ce "Mu duba tare" ya biyo da ita ta bayan layin, wasu irin manyan gidaje ake yi, sai dai duk kangwaye ne, babu ma alamar wani gida da yake da mutane a gurin. "Ina ga ban gane kwatancen ba, idan ta sake zuwa na tambaye ta. Amma sai na din ga jin hayaniya a bayan ɗakin, kamar akwai mutane a gidan" kawai ya kalli Nana ba tare da ya ce mata uffan ba. Ko da suka gama karyawa, roƙonsa ta yi tana son shiga cikin gidan, ta gaida Hajiyar. Ya ce  "A dawo lafiya, idan kuma da maza ki dawo" ta jinjina masa kai tana murmushi. Yau ma a falon saman benen, ta iske Hajiyar gidan, tana waya a matuƙar fusace. "Ni wallahi na gaji, idan ka dawo ka san yadda za ka yi da ita. Ni me ake yi wa Yusra a gidan nan, balle a ce depression ya kama ta? Ga anti depressants ɗin nan, mun je mun ga Likita an bata, amma ta ƙi sha. Sai kuka, ba damar na yi mata magana ko nasiha ce sai ta hau kuka ta ƙule ta wuni a ɗaki" Nana ba ta iya jin abin da ake faɗa a cikin wayar, ta gama bambaminta, ta kashe wayar. Nana ta gaisheta ta amsa, ta ɗora da cewa "Yi haƙuri kin same ni ina waya ne" Nana ta ce "Babu wani abu, bari na gyara falon" Matar ta ce "Yauwwa dan Allah da kitchen ma" Nana ta ce "To" ta fara gyara ɗakin, tana cikin mopping ta fara jiyo wani sauti, da ta rasa sautin mene  ne, kamar ana buga wani abu. Ta basar ta ci gaba da aikinta amma sautin ya ci gaba da fitowa daga wata siriryar hanya. "Ƙaisar" ta furta a hankali. Kwana biyu hankalinta ya ɗan fara kwanciya, amma ta fuskanci matsalolinta na ƙoƙarin sake dawowa. Ta gama mopping ɗin falon, ta tafi kitchen ɗin, nan ma ta fara tattarewa kamar ba kitchen ɗin mata ba. Kaca-kaca ga tarkacen kwanuka wasu abinci duk ya bushe. Ta haɗa kwanukan a sink, ta fara wankewa. A hankali ta ji sautin nan ya biyo ta har kitchen ɗin, ya ci gaba da nufo inda take, ba ta waiwaya ba, ta fara karanto addu'oin da suka sauwwaƙa a bakin ta. Aka jefo mata kofi a cikin sink ɗin, mai jefowar ta nufi hanyar barin kitchen ɗin. Tamkar an dasa Nana ta kasa motsi, sai da ƙyar ta kalli ƙasan rigar matar har ta fice. A hankali Nana ta fara jin sanyi, gabanta ya fara faɗuwa, hakan ya tabattar mata da akwai matsala. Kawai ta ɗauraye hannunta ta bi bayan matar. Tamkar ana hankaɗata ta ƙarasa ta buɗe ƙofar ɗakin. Wata farar mace ta gani a ɗakin, a zaune fuskarta ta yi ja alamar ta yi kuka. Ta zubo wa Nana ido. Nana ta taka a hankali ta nufi gadon da matar take, ta zauna a kusa da ita. "Sannu" "Yauwa" ta amsawa Nana. "Shigowata ta uku kenan, ban taɓa ganin ki ba" matar ta yi ƙurii da ido tana kallon Nana. Nana ta miƙa mata hannu, da nufin su gaisa. Tamkar doluwa, matar ta bawa Nana hannu da nufin su yi musabaha. Su na gaisawa jikin Nana ya hau rawa, ita kuma launin fatar matar, ya ƙara yin jawur, idanunta ya fara zubar da hawaye. Nana ta ce "Wace ce ke?" Bakinta yana rawa ta ce "Ha...ha..Haulat" "Me yasa ki ka yi mini ƙarya? Ki ka zo mini a matsayin mutum? Kuma me ki ke yi a jikin bil'adama?" "Fansa na ɗauka, nan gidan a nan mune rayuwa da 'yan uwana, kawai su ka gina gida, hankalinsu kwance su ka yi zaman su, ba su yi tunanin akwai wata halittar a gurin ba. Da sun gabatar da karatun Alkur'ani ne ma, da mun haƙura mun tashi, amma kawai suka yi gini suka zauna" Nana ta numfasa ta ce "Kuma sai ki shiga jikin wanda bai ji ba bai gani ba ki zauna? Kun san ba ma ganin ku, me yasa za ku din ga zaluntar mu, ba za ku yi mana uzuri ba? Yanzu kin kyauta an ce matar nan ba ta ci ba ta sha, sai kuka kin yi adalci kenan?" "Nima ba a yi mana adalci ba, ramawa muke yi" Buzu yana zaune a kan benci, ya saka hanyar fitowa daga gidan, yana jiran ya ga ta ina Nana za ta fito, dan tana fita ya ji zaman ɗakin ya dame shi. Kawai ya hango ta, ta fito idanunta a rufe, ta nufo shi. Sai da ta kusa ƙarasowa, sannan ya nufe ta yana son tambayarta ko lafiya. Kawai ta tafi za ta faɗi ƙasa. Riƙe ta ya yi yana mamakin me ya same ta haka? Ɗakinsu ya shigar da ita, ya kwantar da ita, yana mamakin yadda jikinta ya yi sanyi ƙalau. Mamaki ne ya cika Nana bayan da ta ganta a tsakiyar daji, da ita da Haula. "Wace ce ke? Kuma me yasa ki ka yaudare ni ki ka zo mini a matsayin mutum?" Haula ta yi dariya ta ce "Kamar dai yadda na gaya miki, laifi aka yi mini nake ramawa. Kwatsam kuma ke ma sai na haɗu da ke. Yanzu a duniya babu abin da nake ƙauna sama da hadimin ki, shi ya sanya ma har na yi yinƙurin taimakon ki, dan na samu shiga a gurin ki" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Waye Hadimin nawa?" "Ƙaisar, tun da na buɗi ido a duniya ban taɓa ganin kyakyawan matashin Aljani mai kyau da cikar zati kamar sa ba" Galala Nana ta kalle ta, ta ce "Ƙaisar ɗin? Wannan zanƙalelen abin?" "Ƙwarai shi, saboda na burge shi na zo na cinye gubar da aka kawo miki a wainar fulawa, sai dai kash! Haƙa ta ba ta cimma ruwa ba. Ina roƙon ki, ki taimaka mini na samu Ƙaisar, ni kuma na yi miki alƙawarin barin jikin matar can, da taimaka miki da duk abin da ki ke so" "Tirrr Allah ya yi mini tsari da sake ja wa kaina wata jarabar, ta hanyar haɗa kaina da ku, shi ma maraba nake nema da shi, ido rufe, balle na sake rakito ki, ki je can Allah ya daidaita ku. A'uzu bi kalimattilahi tammat" Nana ta furta a zahiri tana hamma. Ta tashi zaune ta ga an rurrufe ko ina na ɗakin, an kuna garwashi a ɗan kaskon dafa shayinsa. "Sayyid" ta kira sunansa da ɗan ƙarfi, amma ta ji shiru. Ta yi mamakin dalilin da yasa ya rufe ko ina haka. Ta shiga banɗaki ta yi alwala, saboda an idar da sallar azahar ma. Da ya shigo ɗakin ya tarar da ita ta idar da salla, bai ce mata komai ba, ta ɗora girki tana yi masa hira, saboda ba ta iya tuna komai ba. Jin ya yi shiru ba ya tanka mata, ya sanya ta yin shiru. ***** Yaya Atine ce ta zo gida duba Baba, ta ga yadda yake tafiya da ƙyar saboda ciwon ƙafa. Ta jinjina kai ta ce "Wai Isa wannan ƙafar taka, ka je asibiti kuwa?" "Atine da wani kuɗin? Kin san auren 'ya na yi kwanan nan ai, mai nasara nake saya da aboniki sai a ji garau da nake haɗiya, shi ne nake samun afuwa na yi bacci" Ta kwaɓe baki ta ce "Yanzu kana nufin duk kuɗaɗen da ka samu, da auren Nanan babu wanda za ka je Asibiti, ni fa zuwa na yi idan zan samu wani abu ma ka ɗan bani, gidana ko ƙwayar shinkafa babu" "Haba Yaya Atine, ina su Nazifin da za ki zauna babu abinci?" "Kai ina Gaddafi, ka ke zaune a haka?" Baba ya ce "Gaddafi tun auren Nana ya tafi Ikko" "Ka ga kawai ka fito da kuɗi, idan kuma matarka ta saka ka a gaba, ta tatse ka shikenan dama ka saba abin kunya" Caraf Mama ta ce "Ina zunubin yake balle romonsa? Ina abin yake ni kar a yi mini sharri, ban ci komai ba" "Idan ma kin cin ai ba za ki ce kin ci ba, ni Wallahi kamata ya yi ka mayar da hankali su ma su Jamila ka aurar da su, ko ka samu ka huta. Ni ina suke nema tun da na shigo ban gan su ba" "Su na nan sun je gidanmu" Mama ta ba ta amsa tana tsuke fuska, saboda kar ma ta ja zancen. Ta gama surutanta, ta tashi ta tafi" **** Nana kuwa haka su ka ƙarasa wunin su, ba tare da wani yana kula wani ba, ya koma mata buzunsa. Sai dai hakan bai damu Nana sosai ba, saboda ya yi mata bayani. Duk da shirun bai yi mata daɗi ba, ɗan kulatan da yake yi, ba ƙaramin daɗi take ji ba. Sai dai tana zaune, tana addu'ar kwanciya bacci, ya shigo ya gama abin da zai yi ya ɗane kan katifa. Ya zauna ta ƙarasa addu'a ta shafa shi ma ya shafa. Yana shirin ya ga ta kwanta, amma ta ƙi kwanciya. Ya ce "Mu kwanta" Ta murguɗa baki ta ce "Ni ba bacci zan yi ba" "To mu zauna" "Ni kawai sai ka wani din ga yi mini shiru, ni ka daina irin haka ba na so" Zuciyarsa na azalzalarsa ya tambaye ta abin da yake cikin zuciyarta, saboda har wani irin zafi yake ji a ƙirjinsa, amma ya kasa furta komai. Ya rasa me ma zai yi gaba ɗaya. "Ba zaka kula ni ba ko?" "Husnahhh" ya furta a kunenta. Zirrr tsigar jikin Nana ta tashi. "Ki amsa ni" "Na'am" ta furta a tsorace. "Ni mahaukaci ne, nima ba na gane rayuwar da nake yi, rayuwata ta banbanta da yadda sauran mutane suke ta su. Ni baƙo ne a duniyar nan taku. Ke kaɗai ce Ahalina, da ke kaɗai nake gane kan wannan rayuwar. Ba zan iya zama yadda ku ke ba gaba ɗaya, duk da ke ma wasu lokutan kin bambanta da rayuwar sauran mutane. Amma ki yi haƙuri da yadda ki ka same ni" "Sayyid" Ya amsa mata da "Ma vie" "Dan Allah ka gaya mini gaskiya, zan karɓe ta a duk yadda take, dan Allah kai wane jinsi ne? Ka na tsorata ni wasu lokutan" Hannunsa bai daina yawo a jikinta ba ya ce "Na fi yadda ni halitta ne kamar ke, mutum ne ni, amma ban san ya ake yi... Sai kuma ya yi shiru, kuma ya hana Nana sake cewa uffan, ta hanyar jan su zuwa duniyar ma'aurata, mai cike da al'amura masu tsayawa a zukata da wahalar mantawa. Duk da, da faransanci yake gaya mata wasu kalamai, da ba ta san ma'anarsu ba, amma kai tsaye maganganun nasa suke shiga zuciyarta, tare da haifar mata da wata irin nutsuwa, duk da wahalar da ya bata. Ta ƙara narkewa a jikinsa, ga bacci na son ɗaukar ta, amma zuciyarta da ƙwaƙwalwarta, na kan kalaman da ko fassarar su ba ta sani ba, sai dai tsananin daɗin da suke yi mata, ya sanya ta ci gaba da sauran su. Sun shafe lokaci a haka, sannan da ƙyar ta tashi ta fara yin wanka, sannan shi ma ya tashi, sai dai kan ya dawo tuni bacci ya yi awon gaba da ita. ***** Tamkar Nana ta taka rawa yau, saboda murnar za su fita yau, ya ce mata tare za su je dubiyar. "Amma babu matsala ba za su buƙace ka ba mutanen gidan? Kar mu yi laifi" "Na gaya musu" Da wuri ta gama komai, suka shirya suka fita tare. Ta ɗaukko dubu goma a kuɗin hannunta, ta tsaya ta yi sayayya a hanya, sannan suka tafi. Asibitin da aka kwantar da Shukura suka fara zuwa. Haidar ne ya fara gano ta, ya zabura daga jikin mahafinsa ya nufo Nana da wani irin gudu, cikin matsanancin farin ciki. Caraf Nana ta ɗaga shi, ta rungume tana juyi da shi a gurin. Kawai ya ƙara ƙanƙame ta ya saka kuka. Ita kanta Nana hawaye ne ya cika mata ido, cikin sanyin murya ta ce "Is ok sweetheart, ya isa haka" ta yi maganar tana shafa kansa cike da ƙaunar sa. Yanayin kamaninsu da ta gani da Sagir, ya sanya ta gane shi ne mahaifin sa. Ta ƙarasa suka gaisa, ta ce masa "Dan Allah a wane ɗakin suke?" "Su na ciki room 2 VIP, sai dai ba sa bari a shiga" Ta ce "Subhnallah jikin har ya yi tsanani haka, Ubangiji Allah ya ba ta lafiya, Hajiyan na ciki ne?"  A fusace Sayyid ya ja hannunta, zuwa cikin asibitin. Sagir ya miƙe da sauri ya bi bayan su, saboda ga Haidar a gurin Nana, shi kuma ya ja Nana sun yi ciki ba sallama ba komai. A ƙofar ɗakin suka tsaya, Sagir ya ƙaraso ya ce "Bari na yi wa Mummyn magana" ya shiga cikin ɗakin, Nana ta dubi Sayyid ta ce "Daga tsayawa tambaya, sai ka ja hannuna mu tafi ai ba zai ji daɗi ba" Wani mugun kallo ya yi mata, da ya tilasta mata yin shiru da bakin ta. Hajiya Amina ce ta fito fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin "Ga 'ya ta, ga 'ya ta" ta rungume Nana. Nana ta durƙusa har ƙasa tana gaida Hajiya Amina. "Lafiya ƙalau Nana, kin ga yadda ki ka yi kyau tubarkallah? Haidar yau ga Nana" Ya yi murmushi yana sake riƙe hannun Nana. Hajiya Amina ta ce "Allah sarki, tare da mai gidan ku ke ashe, mu na ta ƙin abin nan da ganin an zalunce ki, Allah dai ya ƙulla lamarin. Sannu ka ji ya gidan?" Hannu ya ɗaga wa Hajjya Amina tare da risunar da kansa ƙasa cikin girmamawa, ba tare da ya yi magana ba. Nana za ta yi magana, mijin Shukura ya leƙo ya kalli Nana ya ce "Ta ce ki shigo" mamaki ya kama Nana, amma ta ɓoye hakan. Ya karɓi Haidar saboda kar ta shiga da shi, ya damu Shukura. Nana ta shiga ɗakin da sallama, babu haske sosai a ɗakin, amma ana iya ganin komai da yake ɗakin. Nana ta ƙarasa gaban gadon da Shukura take. Sai dai ta ɗan tsorata ganin Shukura duk a kumbure. "Sannu Maman Haidar, ya ƙarfin jiki?" Ta yinƙura da kyar, Nana ta taimaka mata ta jingina da jikin gadon ta ce "Jiki da sauƙi Nana, dama za ki zo duba ni?" "Haba Maman Haidar, me zai hana? Ni ban za ci za ki kawo yanzu ba ki haihu ba ma. Sannu" Ta jinjina kai ta dudduba ɗakin ta ga daga ita sai Nana a ɗakin. Ta kama hannun Nana ta ce "Na san a zamana da ke, wataƙila na yi miki abubuwa marasa daɗi, duk da ina yaba ɗawainiyar da ki ke yi da Yarona. Sai dai kowane mutum akwai irin baiwar da Allah ya yi masa, komai kallon ƙasƙancin da ka ke yi masa. Wannan maganganun nawa, ba sa rasa nasaba, da yawan miyagun mafarkin da nake yi da ke" Gaban Nana ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta kalli Shukura ta ce "Da ni kuma?" Sai kuma Shukura ta rikice, ba ta san ta ina za ta fara yi wa Nana wannan bayanin ba, amma ta dake ta ce "Mafarkai nake yi marasa daɗi, kuma ina yawan ganinki kin zo za ki taimaka mini. Ni dai kawai ki saka ni a addu'a a tsorace nake, ji nake yi tamkar zan bar duniya, ba zan rayu ba". "A'a maman Haidar, kamar ba wayayyi ba, mafarki fa ba gaske ba ne ba, duk da wasu lokutan ishara ne, amma mafarkin annabawa ne yake ɗari bisa ɗari gaskiya. Sai kuma wasu bayin Allah da a kan yi wa ishara a mafarki. Wasu lokutan shaiɗan ne kawai yake wasa da hankulanmu, amma ki kwantar da hankalinki ki saka a ranki babu wani mai yi sai Allah, kuma babu wanda ya isa ya yi miki abin da Allah bai yi miki ba. Sannan in sha Allah zan saka ki a cikin addu'a ba dan ki yarda cewa ganina da ki ke a mafarki a zahiri nice zan taimake ki ba, Ubangiji za mu nufa da buƙatunmu baki ɗaya, shi zai magance koma mene ne, ki kwantar da hankalinki dan Allah" Shukura ta jinjina kai ta ce "Haka ne, na gode sosai da sosai Nana, na gode" "Ba komai Allah ya ƙara afuwa, bari na je, na ji an ce ba a bari a shigo a gan ki" "To shikenan na gode" ta ji daɗin kalaman Nana, mussaman da ta yi ta nanata mata, mafarki ba gaskiya ba ne, wasu lokutan sharrin shaiɗan ne kawai. Nana ta fito daga ɗakin, jikinta duk a sanyaye. Hajiya Amina ta taso tana faɗin "Nana kin fito?" "Eh Hajiya, Ubangiji Allah ya bata ingantacciyar lafiya, Ubangiji Allah ya raba ta da cikin nan lafiya" "Amin ya Allah Nana" "A'a Hajiya ina Haidar ɗin?" "Babansa ne ya tafi da shi yanzun nan" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kash, ban gama ganinsa ba Hajiya" "Ki yi haƙuri, jiransa ake yi, yana tafiya da Haidar ne gurin kakarsa ake kai shi, ni kin ga ga jinya, abin zai yi mini yawa ne. Amma in sha Allah zan saka a kawo miki shi har gida." "To shikenan, ga wannan a bawa yarona, wannan kuma a saya wa Maman Haidar wani abin, ban san me take so ba" Hajiya Amina ta ce "Nana har da ɗawainiya har haka, dan Allah ki bari kar ki takura kan ki, zuwan ma da ki ka yi na ji daɗi sosai da sosai " Nana ta ce "A'a Hajiya, idan ba ki karɓa ba ba zan ji daɗi ba, dan Allah ki karɓa" Hajiya Amina fuskarta ɗauke da murmushi ta karɓa ta ce "To Allah ya saka da alkhairi, ki yi wa mijinki godiya ma ya ba wa Haidar kuɗi, Allah ya saka da alkhairi. Na ga haryanzu ba ya magana" Nana ta ɗan saci kallonsa, ta yi murmushi ta ce "Ba komai Hajiya" Ganin hirar t su ba zata ƙare ba, ya sanya shi yin gaba, Nana na ganin ya yi gaba, ta yi wa Hajiya Amina sallama a gurguje, ta nufi hanyar da ya bi. "Shi ne za ka yi gaba ka bar ni?" Ya waiwayo ya kalle ta ya ci gaba da tafiya. Ta tsaya tana yi wa Nurses ɗin gurin sallama, ya ja ya tsaya tare da waiwayowa yana hararar Nana. Ta yo gaba tana murmushi, tare da mamakin yadda yake so ta ƙarfin tsiya sai ya mayar da ita irin sa, na rashin kula mutane. Yana zuwa bakin ƙofar fita, ya ja ya tsaya, Nana ta ƙaraso tana ƙoƙarin duba, abin da ya hana shi fita amma ya tare ta, shi bai shiga ba, kuma ba dawo ba.  Ta leƙa ta gefensa, ta ga mene ne ya hana shi wucewa, kawai ta ga Alhaji Zailani, tare da Doctor Sharif, a take gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ja ta tsaya cike da razani da fargaba. Ayshercool 08081012143 38 Alhaji Zailani ma gabansa ne ya faɗin, cikin fargaba yake bin ƙwayar idon Buzun da kallo, tare da mamakin ganinsa a gurin a dai-dai wannan lokacin. A hankali Sayyid ya ja da baya, taku biyu, ya sanya hannunsa ya riƙo Nana ta bayansa, ya ba su hanya. Alhaji Zailani ji yayi tamkar an zare masa lakar jikinsa, jikin nasa ya yi wani irin sanyi, wani abu mai kama da tsoro ya shige shi. A hankali ya taka ya shigo, yana ƙoƙarin kallon Nana da ke tsaye a bayan Sayyid, amma Sayyid ɗin ya hana hakan, saboda yadda ya ƙare babbakewa ya kare ta. Ita kanta Nana ji ta yi yanayin ta na ƙoƙarin canzawa, ta saka hannu ta riƙe na Sayyid, tana addu'a a cikin zuciyarta. Wani irin baƙin ciki ya mamaye zuciyar Alhaji Zailani, ganin yanzu wannan Buzun ne mijinta, da ya aure ta ya san da yanzu buƙatar sa ta biya, wani abin yake hari ba wannan ba, amma Mahaifinta ya yi masa sagegeduwa. Doctor Sharif ya ce "Alhaji lafiya kuwa?" "Eh lafiya ƙalau" Har Alhaji Zailani ya yi gaba, ya tsaya ya sake waiwayowa, amma ya sake ido huɗu da Sayyid, ya kange Nana, ya kare ta babu yadda za a yi ya iya hango Nana yadda yakamata. Sai da Sayyid ya tabattar Alhaji Zailani ya bar gurin, sannan ya waiwayo ya kalli Nana, yadda duk jikinta ya yi sanyi, ya kamo hannunta suka fita waje. Bai dai ce mata komai ba, ta tare musu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai su. Gaba ɗaya Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ta rasa dalilin da ya sanya, gaba ɗaya ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Duk da tana zaton hakan baya rasa nasaba da mugun nufin da Alhaji Zailani ya taɓa nuna mata, amma ta rasa dalilin da ya sanya gaba ɗaya take nema ta rikice, ta fita daga hayyacinta. A hankali ta kwanta a jikin Sayyid. Cikin damuwa ya dube ta, ya dafa ta ya ce "Ba lafiya ne?" Ta ce "A'a" "To Meyafaru?" "Ba komai" ta furta a hankali kamar mara lafiya. "Ko mu koma gida ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Sannu" ta jinjina masa kai. Sai da suka je daf da titin unguwar su, sannan ta tashi daga jikinsa, tana kallon titin nasu. Suka je gurin da za su sauka, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙa wa mai Napep ɗin su ka tafi. "Sayyid" Ya waiwayo ya kalle ta. Sai kuma ta yi shiru, dan rasa me za ta ce masa ta yi. Tsayawa ya yi yana ƙare wa ƙofar gidan su Nana kallo. Ko ina faci ga uwar kwata a layin. "Bari na shiga na yi musu magana, sai ka shigo" Ya jinjina mata kai ya ce "Zan je masallaci " Ta ce "To shikenan, a yi mini addu'a" Ya ɗaga mata hannu, tare da jinjina mata kai, ita kuma ta shiga cikin gidan. Sallama ta yi, Nasiru yana tsakar gida yana goge takalminsa, yana ganin Nana ya tashi da gudu ya nufe ta. Nana ta rungume shi tana murmushi, "Nasiru ya garin?" "Lafiya ƙalau" "Ina mutanen gidan ne?" "Mama ta ɗan fita, Baba kuma ya je masallaci" Nana ta ce "Samo mini tabarma na zauna a nan, ina su Jamila?" "Jamila daga warkewarta ta tafi yawo, Suwaiba ma ba ta nan" "Ohh ya jikinta kuwa, mu ka yi waya da Ummi, ta ce mini tun da ku ka dawo ba ta da lafiya " Nasiru ya ce "Eh, amma ta warke, Mama ta ce wai me magani ya ce Aljani suka yi wa laifi. Aka yi sadakar ƙosai, aka dafa zakara aka bin... "Ammm ya jikin Baba kuma" Nana ta katse maganar Nasiru. "To ga shi nan dai, yanzu zai shigo ai ki gan shi" Nana ta ɗaukko wayarta ta ce "Nasiru ga wayata, ga kuɗi ka yo mini turin fina-finai dan Allah" ya karɓa ya miƙe tsaye tare da faɗin an gama yanzu kuwa. Nana ta tashi ta fara tattare tsakar gidan, saboda yadda aka bar shi kaca-kaca. Ta gama sharewa Baba ya yi sallama, ta ɗago ta kalle shi. Da ƙyar yake taka ƙafarsa yana bin bango. Ya tsaya sororo ya ce "Ke me ki ke yi a gida kuma?" Duk da Nana ba ta ji dadin tambayar da ya yi ba, saboda ta san yana tunanin ko auren ya samu matsala ne, amma ta yi murmushi ta ce "Baba duba ku na zo yi" Ta yi maganar tana gyara masa tabarma a tsakar gida. Ya ƙarasa ya zauna da ƙyar, Nana ta koma gefensa ita ma ta zauna ta ce "Sannu ya jikin naka?" "Jiki ga shi nan mu na lallaɓawa abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa" Ta kalli ƙafafuwan nasa ta ce "Wacce ce take ciwon a ciki?" Ya ce "Duka, sai dai wannan ta fi ciwon" ya yi maganar yana nuna mata ƙafarsa ta hagu. "To Baba ka je Asibiti?" "Da wane kuɗin zan je Asibitin? Na gargajiya zan koma, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce ta dawo da ke gidan nan?" Nana ta yi murmushi mai ciwo tana buɗe jakarta, ta fito da leda tana faɗin "Baba idan matsala ta dawo da ni, ba zaka karɓe ni ba ko? Ai ka yi mini addu'a ka ce Allah ya bani zaman lafiya, in sha Allah matsala ba za ta kawo ni ba sai alkhairi" ta yi maganar tana ɓare dafaffen ƙwan da ta fito da shi daga leda. Ta gama ɓare ƙwan, ta miƙa wa Baba, ya saka hannu ya amshe, yawun bakinsa na tsinkewa. "Baba na san ni mai laifi ce a gurinka, na ɓata maka rai a kan abubuwa da dama, mussaman na bijirewa auren waɗanda ka so na aura, amma ina son mu saka a ranmu cewa, dukkanin su Allah bai ƙaddara akwai mijina a cikin su ba. Ni yanzu babban fatana ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, na san dole na fuskanci tuhuma na abin da ya kai ni ɗakin su magadi, amma ba abin da ka ke tunani ba ne Baba, da zan lalace da ban kawo wannan lokacin ban lalace tun a baya ba." Tuni hawaye ya wanke mata fuska, zuciyarta na wani irin tafasa da raɗaɗi. Baba bai ce mata komai ba, sai karɓe ƙwan da yake yi yana lamushewa. Ta goge hawayen ta, sai da ta ɓare masa dafaffen ƙwan nan guda biyar, ta ɗebo ruwan randa ta kawo masa ya karɓa yana sha. Ta ɗaura alwala ta yi sallar azahar, bayan ta idar, Nasiru ya shigo gidan yana faɗin "Nana ga wayar ki, an ciko miki ita da fina-finai fal" Ta yi murmushi ta ce "Na gode yaron kirki" Mama ta yi sallama ita da Suwaiba, sai da suka ɗan yi turus ganin Nana a gidan babu tsammani. "Lafiya dai na ganki a gida? Ba dai auren ne ya samu matsala ba" Nana ta waiwaya ta kalle ta, ta yi murmushi ta ce "A'a ganin ku na zo yi, na gaishe ku, aurena bai samu matsala ba" Mama ta kwaɓe baki tana rataye mayafinta a kan igiya. Nana har kallon Mama take yi, tana mamakin wai ita ba ta san ƙarara a fili take nuna ƙiyayyar da take yi mata ba. Nana ta ce "Suwaiba ya ku ka zo gida?" "Lafiya ƙalau wallahi, mu na dawowa Jamila ta kwanta rashin lafiya" "Haka Ummi take gaya mini, shi yasa yau na yinƙuro na fito. Nasiru duba idan ya idar da salla, ya shigo ya duba Baban mu tafi, ban yi girki ba" Nasiru ya ce to. Suwaiba ta ce "Nana wai waye yake ba ku Abinci? Gidan da ku ke aikin ne suke ba ku?" Nana ta yi murmushi ta ce "A'a wanda ya ajiye ni ne yake kawowa, ba kuna nan ya kawo muku fura ba" Nasiru ya ce "Yana waje, na yi masa magana bai kula ni ba" Nana ta yinƙura ta ce "Bari na yi masa magana" Yana zaune a wani dakali da yake kallon gidan su Nana. Yana ganin ta fito ya miƙe tsaye yana kallon Nana. Ta ƙarasa ta ce "Sayyid, zo mu je ku gaisa da Baban" "Wai in shiga?" Ta ce "Eh, ku gaisa da Babana ka duba shi" Nana ta yi gaba ya bi bayanta, Gaba ɗaya suka zubo masa ido, sai dai kansa a sunkuye, har suka isa gaban Baba. "Sannu" ya furta a hankali yana tunanin ko haka ya kamata ya ce? "Yauwwa sannu, ya iyalin?" Ya ce "Alhamdilillah" Baba ya ce "To madalla" Nana ta ce "Sayyid, ga ƙanwata wadda su ka zo ranar, ga mamana, ga kuma Nasiru da suka zo a tare" Bai kalli inda Mama take ba, ya ce "Sannu" Yanzun ma kwaɓe baki ta yi ta ce "Ji wata irin gaisuwa, haka ake gaida sirikai?" Nana ta ce "Ki yi haƙuri, ba hausa sosai ne" Buzu dai bai tanka musu ba, ya miƙa hannu ya ɗora a kan ƙafar Baba, ya ce "Allah ya sauwwaƙe" "Amin na gode" ya ɗan jima yana kallon ƙafat, sannan ya ɗauke hannunsa, ya saka a aljihunsa, ya ciro kuɗi ya ajiye wa Baba a gefen ƙafarsa ya tashi tsaye. Nana ta bi kuɗin da kallo, ba tare da ta san ko adadin nawa ba ne ba. Baba ya ce "Duk wannan haka, to na gode sosai Allah ya yi albarka" Nana ta ce "Baba bari mu tafi gida, Allah ya baka lafiya ya ƙara afuwa, dan Allah a gaida Jamila idan ta dawo" Sayyid tu ni ya yi waje, domin shiga gidan su Nana ji ya yi tamkar ya yi tsirara, gaba ɗaya idanun mutanen gidan da bai saba da su ba ya ji ya takura masa. Suwaiba ta ce "Ke Nana wai mijin nan naki kamar dodo, baya sauke wannan takunkumin na fuskar shi, ko ba shi da haƙora ne?" Nana ta yi dariya ta ce "Biyo ni waje na saka ya sauke miki rawanin ki gan shi. Baba Allah ya sauwwaƙe idan Jamila ta dawo a yi mata sannu" Nana ta ja takalmanta ta yi waje. Tana fita waje, ta yi karo da Gaddafi. Turus Nana ta tsaya cikin tsoro, sai ma ta rasa me za ta ce masa. "Nana me ki ke yi a gida?" "Zuwa na yi duba Baba, ina wuni?" "Lafiya ƙalau, ya ki ke ya gidan?" "Lafiya ƙalau, ashe ka dawo" "Eh na dawo shekaranjiya" Nana ta yi tsuru-tsuru, tana hango Sayyid da ya tsaya yana kallon ta, ya tsuke fuska tamkar ya fashe. "Amm ai tare ma muke da shi" ta faɗa cikin kame-kame. Gaddafi ya waiwaya, ya kalli Buzu ya mayar da idonsa kan Nana ya ce "Amma babu wata matsala dai ko?" Nana ta jinjina masa kai. Gaddafi ya saka hannu a aljihunsa ya ɗaukko kuɗi ya miƙa mata ya ce "Ga wannan, kya sai wani abun" Ta saka hannu biyu ta karɓa, tana mamakin yadda duk Gaddafi ya canza. "Nana duk yadda za a yi, ki riƙe auren ki, ki ƙaddara wannan shi ne zaɓi mafi alkhairi da Allah ya yi miki, kin san zaman gidan nan namu ba daɗi ne da shi ba" Nana ta jinjina kai ta ce "Na gode sosai da sosai Yaya" Ta nufi inda Sayyid yake, idanunsa kawai suka tabattar mata da a hasale yake. Har suka je gida bai sake tanka ta ba. Su na zuwa a gurguje Nana ta yi sallar la'asar, ta ɗora girki, dan ba su ci komai ba. Shi kuwa tuni ya haɗa kayan shayinsa, yana ta tafasawa yana sha. Ta ɗaga labule ta ce "Sayyid, na gama girki, ka zo ka ci" ya ɗago ya kalle ta ya mayar da hankali ya ci gaba da shan shayinsa. Sai da ya gama jan ajin, sannan ya shigo ɗakin, ya ɗauki nasa abincin ya fara ci. ***** Mutumin yana zaune a kan kujera, a wani katafaren falo, ya ƙare wa Jamila kallo ya ce "Wannan ce yarinyar?" Hajiya Sa'a ta ce "Ita ce ranka ya daɗe" "Kuma kin tabattar za ta riƙe amana? Ba za ta tona asirin ƙungiya ba?" "Ƙwarai kuwa, na yi mata duk abin da ya kamata" Ya yi dariya ya ce "Babu laifi, wannan Shekarar da ita za mu yi taronmu na shekara" Ita dai Jamila ba ta iya cewa komai ba, sai tsananin mamaki, ganin daular da ba ta taɓa tunanin akwaita ba. Bayan Hajiya Sa'a sun gama magana da mutumin, ta ɗauki Jamila su ka fita. "Hajiya yanzu dama haka garin Abuja yake? Lallai na zaune bai ga gari ba, kalli gidaje" Hajiya Sa'a ta yi dariya ta ce "Jamila kenan, a garin nan gidajane sun fi huɗu, akwai arziki Jamila, muddin za ki yi biyayya ki riƙe sirri, to za ki samu arzikin da sai ya kankare baƙin talaucin da yake bibiyar zuriyar ku. Dan ma mun kasa samun jinin yayar ki ne, da tuni ta fashe mana tana da taurarin arziki amma ba ta san yadda za ta yi amfani da su ba ne ba" Cikin shauƙi da zumuɗi Nana ta ce "Kai in sha Allah, zan riƙe amana da sirri babu wanda zai ji komai" "Yauwwa yarinyar kirki, wannan yana ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyarmu, tun da ya amince da ke, tare da ke za mu je taron shekara, ina saka ran a karɓe ki a ƙungiya" ***** Har wajen ƙarfe goma na dare, bai shigo ɗakin ba, Nana ta kashe fitila, ta ɗaga labule, ta hange shi a zaune a kan benci yana ta kore sauro, yana shan shayi. Kawai ta girgiza kai ta nemi guri ta zauna, ta yi addu'oin kwanciya bacci, ta kwanta. Ta kai a ƙalla mintuna arba'in, tana tunanin yadda rayuwa za ta ci gaba da juyawa a haka. Zama da mutumin da ba ta san ma waye shi ba. Tana kallon ƙofa, ta ga ya shigo, ya ajiye kayan shayinsa ya tafi banɗaki. Ya jima a ciki sannan ya fito daga ciki, ya rataye kayan da ya cire, ya nufo kan katifar. A ranta take jinjina ƙarfin hali na maza, da a ƙasa yake zamansa, ko ya kwana a waje a kan benci, amma yanzu kansa tsaye yake ɗarewa katifa. Ba ta gama tunanin ba, ta ji shi a jikinta. "Me yasa ki ke kallona?" "Ya aka yi ka san ina kallon ka a duhu?" "Na sani, tun da na shigo ki ke kallona" "Shi ne tun da mu ka dawo, ka ƙi kula ni" Ya ɗan yi shiru kamar ba zai yi magana ba sannan ya ce "Ba na son na ga wani yana yi miki magana, zuciyata na yi mini ciwo. Ba na son kowa ya kalle ki, ba na son kowa ya ji muryar ki, ba na son wani ya raɓi inda ki ke, sai nikaɗai ban san dalili ba amma ina jin kamar zuciyata za ta tsaya ne, ba na so" "Amma wanda ka ganmu tare, Yayana ne fa, babanmu ɗaya da shi" Ya yi shiru bai yi magana ba. Ita ma ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Sayyid a ina ka samu kuɗi ne? Na ga ka bawa Haidar, ka bawa Baba, kuma ka na sayo mana abubuwa" "Allah ne ya bani" "Eh na sani, amma waye yake baka?" "Habu" ya amsa kai tsaye. "Shi ba shi da nasa buƙatun zai din ga kashe mana kuɗi har haka?" Ya yi shiru bai amsa mata ba. A hankali Nana ta ce "Sayyid" "Husnahh" "Dan Allah ya ake yi ka ke yin wasu abubuwan, ka san na ce maka, ba ni da cikakkiyar lafiya wasu lokutan gaba ɗaya a rikice nake ba na tantance ainihin zahiri da mafarki, amma sai na ga kana abubuwan da mutane normal ba sa iya yi" "Kamar me?" Ta ce "Ammm ka na shigowa cikin mafarkina" Kawai ta ji ya yi dariya "Dama wani na shiga cikin mafarkin wani ne? Ba mafarkinki nake shiga ba, ruhina ne yake rayuwa a cikin naki, kuma naki yake rayuwa a nawa. Na fuskanci hakan a ranar da na fara ganin ki, zuwa ranar da aka ɗaura mana aure" "Ban gane ba, ka yi mini bayani sosai" Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ƙirjina ya fara nauyi" "Saboda me?" Ya yi mata shiru. "Amma Sayyid.... "Shhhh zan yi bacci" Ta ce "Tambaya ɗaya zan yi maka dan Allah" "A'a" "Allah fa na ce" "Na ce A'a" Ta ɗan ja numfashi ta ce "To amm... Tsit ta yi dalilin bakinsa da ta ji a nata. Ya riƙe hannunta a nasa yana matsa nata a hankali. "Dan Allah ka bari yau mu samu isasshen bacci, ni dan Allah ka ƙyale ni" Ya ce "Idan ma kin yi baccin, zan biyo ki har cikin baccin naki. Na gaya miki ruhinki a cikin nawa yake rayuwa, ko fushi ki ke yi a cikin jikina nake ji". Haka ya yi ta tsaro maganganun, da suka ci gaba da dagulawa Nana lissafi, da birkita mata ƙwaƙwalwa, wanda ba ta gama warwarar su ba, har ya nufi inda yake son zuwa. ***** Tun bayar tafiyar Nana, da Shukura ta ga mahaifinta ta ji gabanta ya faɗi, ta kalle shi cike da tsoro da razani. Cikin kulawa ya ce "Sannu Auta, haka ki ka koma? Ya jikin naki?" A tsorace ta ce "Daddy dama yau zaka dawo, Mummy ba ta gaya mini ba" Cikin damuwa ya ce "Ina can hankalina ya ƙi kwanciya, na ce bari na zo na ganki, na kira Sharif ya ce mini jikinki da saura, shi yasa na ce gara na zo na gan ki" Ta dai yi shiru, gabanta na ci gaba da faɗuwa, ya gama yi mata sannu ya tashi suka fita tare da doctor Sharif. "Sharif " "Na'am ranka ya daɗe" "Muddin yaron nan zai rayu, ka yi duk mai yiwuwa a cire shi kawai, a matsa nake" "Zan yi iya ƙoƙarina, amma ka san wannan sabga ce mai haɗarin gaske, sai an yi taka tsantsan yadda ba za a bar duk wani trace da za a gane wani abu ba, zan yi setting date da komai da yadda abin zai kasance" "Better" Alhaji Zailani ya furta yana yin gaba. Gidansu Nana har ƙarfe goma na dare Jamila ba ta dawo ba, Baba yana tsakar gida yana yi wa Mama bala'i. "Yanzu Rabi sakarcin naki har ya kai Jamila ta kai bayan goma a waje? Gidan uwar wa ta tafi haka?" "Wai dan Allah Jamila za ta gudu ne? Na ga dai ba yarinya ce ƙarama ba, na ce maka za ta dawo" "Za ta dawi gidan uban ta je? Goma na dare ta riga ta wuce, me take yi a waje a wannan lokacin?" "Dan Allah ni kar ka ɗaga mini hankali, na ga dai yarinyar nan ba sauke hakkin da Allah ya ɗora maka ka ke yi ba, abinci ma ba bamu ka ke yi ba, sai ma dai ta samo ka ci" "Da ba na sana'a sai na zuba ido su lalace? Sana'ar uwar me take fita?" "Ni fa 'ya ta ba lalacewa ta yi ba, na ga dai nan Nana take nata yawo, ba ka yi magana ba" "Ai Nana na san me take fita yi, Jamila fa, na san dai tana yawon maƙota, bayan wannan uwar me take yi?" Sosai su ka ci gaba da jayayya tsakanin Mama da Baba, sai sha ɗaya da rabi na dare, sai ga Jamila ta yi sallama, hannunta niƙi-niƙi da ledoji. Duk da ledojin hannunta, sun ɗauki hankalin Baba, amma ya dake ya fara tuhumar ta daga ina take. Mama ta kankane, ta hana Jamila magana, ta din ga karewa. Ƙarshe sai haƙura ya yi, ya rabu da su. Ita kanta Suwaiba jiki a sanyaye take kallon kayan da Jamila ta zo da su, tana fargabar Allah ya sa ba kauce hanya 'yar uwarta ta fara yi ba. Sai dai Mama ko a jikinta, musamman da Jamila ta ce mata, Hajiya Sa'a ce ta saya mata, wai gidan 'yar uwatta ta raka ta. Wajen Sha biyu na dare, Jamila na ta bawa Suwaiba, labarin abin duniyar da ta gani. Suwaiba ta yi tsuru da ido tana kallon Jamila, daga bisani ta ce "Ni dai Jamila na fara jin tsoron matar nan, anya haka kurum take yi miki wannan ɗawainiyar. Jamila kar ki kai kan ki ga halaka, idan rayuwar ki ta lalace ba ki da wata makoma wallahi" Jamila ba ta yi magana ba, Gaddafi ya faɗo ɗakin ya kalli Suwaiba ya ce "Bar ɗakin nan" Jamila ta miƙe ita ma a tsorace tana kallon sa" "Fita na ce" ya yi wa Suwaiba tsawa. Jamila na ƙoƙarin fita, ya danna ƙofar ɗakin ya saka sakata, ya fito da wani irin danƙo na injin markaɗe, ya kalle ta ya ce "Gidan uban wa ki ka je, ki kai yanzu ba ki dawo ba?" Jamila ta rikice jikinta yana tsuma, amma ta kasa magana. "Ba magana nake yi miki ba?" "Babu inda na je?" "Ƙarya ki ke yi, uban waye ya sauke ki a mota?" "Hajiya Sa'a ce" "Babar ki ce ita? Meye tsakanin ki da ita?" Jin ta tsaya inda inda, ya sanya ya fara zuba mata danƙon nan a jikinta. Cikin kururuwa Mama take dukan kofar ɗakin, tana neman agajin mutane, kar Gaddafi ya kashe mata 'ya. Ya zuba wa Jamila danƙon nan, ya fi sau sha biyar, sai da ya zamana daga ita sai underwear. Sai da aka taru aka yi ta yi masa magiya, sannan ya buɗe ƙofar ɗakin ya yo ball da ita waje. Mama hankali a tashe ta nufi Jamila tana salati, saboda wahala ko kukan ba ta iya yi, sai wani yawu da yake fita daga bakinta. Baba ya ce 'Haba Gaddafi, ba kowane lokaci duka da zuciya yake aiki ba, yanzu idan ka illata ta fa, mace ce fa" Gaddafi bai saurari Baba ya ce "Wallahi ta sake sai na karairayata, ba za ta ɓata mana suna a banza ba" Cikin ƙaraji Mama ke faɗin "Wallahi ba zan yarda ba, sai na kai ka gurin hukuma" Nasiru da yake gefe ya ce "Allah sarki, Nana na can, da yanzu an ce ta hana mutane bacci" babu wanda ya saurari abin da Nasiru yake faɗa, suka ci gaba da hayaniyar su. **** Ko da Nana ta fito daga wanka, yana tsaye a ƙofar banɗaki yana jiran ta, ta murguɗa masa baki, za ta wuce ya riƙe ta yana murmushi ya ce "Meya faru?" "Ni rabu da ni, ka hana ni bacci, ga jiƙa kai sai na yi ciwon kai" "Ba dai fi na gashi ki ka yi ba" ya yi maganar yana taɓa gashin nata. Nana ta kalle shi ta ce "To yi mini gori" bakinta ya sake sumbata yana murmushi. Ta gyara shimfiɗa ta hau, shi ma ya haye yana buɗe bargo. "Ni gaskiya katifar nan ta yi mana kaɗan" Ya ce "Ya za ayi?" "Ka saukar mini daga kan katifa, ai na ga ma ba a ɗakin nan ka ke kwana ba" "Na gama yi miki amfani dole ki kore ni, ba inda zan je" ya yi maganar yana kwanciya" Nana ta ce "Na shige su, idan muka futa sai ka yi gumm, sai na yi ta yi wa mutane bayanin ka na magana, ba kurma ba ne ba, amma daga ni sai kai ka yi ta wasu maganganu" Tana jin sautin dariyar sa, cikin nutsuwar sa, da ta fi kama da Iyayi ya ce "Asma'u ke duniyata ce, tun da na farka a cikin wannan duniyar, nake jin tamkar nikaɗai ne baƙo, Habu yana iya ƙoƙarin sa a kaina, amma ba ya wadatar da ni. Fatana da burina na yi na gama mafarkin nan na tashi, na koma ainihin rayuwata. Ba na jin daɗin komai a wannan rayuwar, sai ranar da na fara ganin ki, tare da yayar ki da suka zo kun je gidan mai magani, har ki ka faɗi. Ina ganin ki na ji kamar ina da wata alaƙa mai ƙarfi da ke." "Ni ɗin? Yanzu dama kai na gani ranar da muka je?" "Mun haɗu a gidan sarkin baka ma." A zabure ta ce "Sayyid ka san sarkin baka?" Ya ce "Na sani, Habu sun kai ni, ko zan iya tuna ni waye. Ban taɓa maganar awanni biyu cikakkiya a rana ba, ban taɓa shafe sati guda ina iya magana ba. Duk sai bayan zamanmu a guri guda. Ni na ce Habu ya biya mini sadakin auren ki, tun ranar da na ganki kullum sai na yi mafarki da ke. Shi yasa da mai gidan da muke yi wa gadi ya ce na sake ki, zai biya ni na ji kamar na kashe shi. Na san ni mahaukaci ne, amma mahaukaci bai kyautu a kyautata rayuwar sa ba. Ke Duniyata ce, a tare da ke nake iya doguwar magana, na ci abinci, na daɗe hankalina bai gushe ba. Ba na son kowa ya raɓe ki, ko ya kula ki, saboda ina jin tsoron kar na buɗe ido na ga ba kya kusa da ni." Ya kwantar da kansa a ƙirjinta ya ce "Ke ce Ahalina, kuma Duniyata. Ke Duniyata ce" Haka ya din ga maimaitawa har muryarsa ta fara rawa, tamkar zai fashe da kuka. Nana ta saka hannu ta zagaye bayansa, ta rintse idanunta, sai dai ta kasa magana a dalilin sanyi da ta fara ji. Sauti ta fara ji na tasowar guguwa, ta buɗe idonta, ta gansu a cikin sahara tsakiyar dare, sai hasken farin wata da ya gauraye ko ina. Tsohon nan ta gani a tsaye a kan su, hannunsa riƙe da sandarsa. Ayshercool 08081012143 "La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin" Haka Nana ta rintse idanunta tana maimaitawa. Tana jin yadda yake sauke numfashi a jejjere, yana ƙara ƙanƙame ta. Ta sake buɗe idanunta a hankali, ta gansu still a cikin saharar. Tamkar wani zai ƙwace shi, haka ita ma ya rirriƙe shi, tana ci gaba da karanto addu'oin da suka sauwwaƙa a bakinta. Zuwa jimawa ta daina jin sanyin,  ta buɗe idanunta ta gansu a cikin ɗaki, jikinta ya gaji saboda yadda ya sakar mata nauyin shi. "Sayyid" ta kira shi a hankali. Amma shiru, sai dai tana jin yadda cikin sa yake ɗagawa yana sauka a hankali alamar bacci yake yi. Ta motsa a hankali ta gyara kwanciyarta ta ci gaba da shafa kansa, tana tofa masa addu'a. Wani irin nishi ta ji ya yi, ya yinƙura a gigice cikin ɗaga murya ya ce "Imam" Cikin azama Nana ta tare shi, duk da ya fi ƙarfinta, ta riƙe shi gam. Haki yake yi tamkar wanda aka biyo ya ƙwace da ƙyar. Ta yinƙura ta kunna fitilar ɗakin, ta dawo ta zauna a kusa da shi. Cikin sanyin murya ta ce "Sayyid. Me ya faru? Waye Imam ɗin?" Hannunta ya kamo, ya ɗora a saitin zuciyarsa, ya riƙe hannun nata yana sauke numfashi. "Sannu" ya jinjina kai. Ya sunkuyar da kansa ya yi shiru, fuskar sa na bayyanar da matsananciyar damuwa. Ta sanya ɗaya hannun nata ta dafa shi ta ce "Sayyid mene ne?" Ya ɗago da ƙyar ya kalle ta, ya buɗe baki zai yi magana amma sai ya kasa. Can tamkar an jefo maganar bakinsa ya ce "Wani abu ne yake damun zuciyata, ban san mene ne ba, amma ya yi mini nauyi, kamar zan bar duniya" "Ya isa, ya isa haka ka yi shiru, in sha Allah babu wani abu, ka yi haƙuri" ta yi maganar tana shafa gadon bayansa. Ga mamakin ta kawai ta ga hawaye na gangarowa daga idanunsa. Rikicewa ta yi cikin tashin hankali ta ce "Sayyid mene ne? Meye ya saka ka kuka?" Ya girgiza mata kai alamar bai sani ba. Tun yana yi a hankali, kukan nasa ya din ga ƙaruwa, har da jijjiga. Ganin ta rasa abin yi kawai ta fashe da kukan ita ma, ta hau taya shi. Ya janye ta daga jikinsa, ya kwantar da ita a kan pillow, shi ma ya kwanta a gefen ta, yana son ya yi mata magana amma tilas ya haƙura ya kasa ce mata uffan. ***** Hajiya Amina na kwance tana bacci, a kan carfet, a ɗakin da take jinyar Shukura, ita kuma tana kan gadon marasa lafiya tana bacci, ta ji an kama hannunta. Ta yinƙura za ta yi magana amma wani irin jiri ya ɗebe ta daga kwancen da take, duk yadda ta so ta yi wani yinƙuri ko ta yi magana, ta kasa sannu a hankali jikinta ya yi sanyi, ya mutu murus, daga nan hankalinta ya gushe baki ɗaya. ***** Fuska ɗauke da damuwa, Nana take kallon inda Ƙaisar yake ta haɗe-haɗen maganunansa, ba tare da ya dubi inda ma Nanan take ba. "Ƙaisar" "Na'am" "Karo na farko zan roƙi alfarmarka" "Ina jin ki" ya amsa ba tare da ya kalli inda take ba. "Abu na farko ina roƙon ka, dan Allah ka yi haƙuri, ka saki ƙafar mahaifina, abu na biyu dan Allah ka bar ni mu zauna lafiya da mijina, ka daina wahalar da mu har haka dan Allah ka yi haƙuri." Ya ajiye abin da yake yi, ya dawo gaban Nana ya zauna, ya kalle ta ya ce "Na riga na rantse sai na hukunta mahaifinki, mijinki ya shiga gona ta, ya kwance ƙullin da na yi wa mahaifinki a ƙafa, zai ɗanɗana kuɗarsa zan nuna masa gaba ma akwai gabanta" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Ta yaya ya kwance ƙullin da yake ƙafar Baba?" "Oho ya dai kwance, kuma zai ga abin da zan yi a kai, sannan ki daina yi mini magiya a kan wani da yake faruwa, wannan wani abu ne da ki ka amince da shi da kan ki, dan haka dole ki jure duk abin da za ki gani. Sauran tambayoyin da ki ke son yi mini kuma ki adana abin ki, dan amsa miki su, dai-dai yake da amincewa da sharuɗana" Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah Ƙaisar kar ka cutar da shi, shi kansa bai san wasu abubuwan na faruwa ba" Ƙaisar ya miƙe tare da cewa "Allah ko?" "Da gaske, bai san su na faruwa ba, dan Allah ka bar mu, mu ji da ƙalubalen rashin lafiyarsa, da rashin sanin waye shi" Wata irin guguwa ce, ta gauraye cikin Libraryn, da sauri Ƙaisar ya buɗe rigarsa, ya kare Nana. Tsohon nan ne ya bayyana a cikin libraryn, ya tsaya yana kallon Nana. Ƙaisar ya tsaya a gaban Nana ya ce "Me ya kawo ka inda nake? Da izinin wa ka shigo gurin nan?" "Ba na buƙatar izini, kafin zuwa inda farauta ta yake" "Kar ka ƙetare layin da ka iya kawo, gagarumin tashin hankali da rashin jituwa tsakaninmu" "Hannun agogo za ka mayar baya, ka gyaro ɓarnar da ka tafka, idan kuwa ba zai gyaru ba, to ba zaka hana ni, aikata abin da na yi niyya ba". "Ka aikata duk abin da ka so, amma ka taɓa uwar gijiyata a wannan karon ƙarshen rayuwarka zan kawo a doron Duniya" Jin tarin da Nana ta yi ne, ya sanya ta farkawa. A ƙasa ta hango shi, maimakon kan katifa, yana wannan jijjigar da ya yi. A rikice ta tashi ta nufe shi, tana ambaton Allah. "Sayyid jikin ne dai?" Wayarta ta ɗaukko, ta kunna karatun Alqur'ani, sannan ta ɗakko bargo ta lulluɓe shi da shi, ta zauna ta saka shi a gaba, ta zura masa ido cike da damuwa. Har gefin Asuba, sannan Allah ya sanya ya daina wannan rawar sanyin. ***** An kai ruwa rana da Mama sosai da sosai, kafin ta amince ta haƙura, amma da rantsuwa ta yi a kanz sai ta kai Gaddafi gurin 'yan sanda. Ana bata haƙuri shi kuma ya ce "Idan ba ta kai shi gurin 'yan sanda ba, ba Hudu mai ice ne ya haife ta ba" wato mahaifinta. Duk da Baba yana cikin wannan tashin hankali, amma ya lura da sauƙin da ya samu, game da ciwon da ƙafarsa take yi masa tun jiya. Sai dai damuwa da tashin hankali ya sanya, bai mayar da hankali a hakan ba, ya karkata ga son kashe wutar da ta taso a gidansa. **** Hajiya Amina na tsaye cikin matuƙar damuwa, Doctor Sharif ya ce "Hajiya ki yi haƙuri, amma a daren nan, za mu yi mata tiyata domin a ceto ta, da abin da yake cikinta. "Kuma Doctor babu wata matsala, babanta ba ya kusa, haka ma mijinta" "To Hajiya ai ba zamu bar ta haka a cikin ciwo ba, ki na kallo ba ta hayyacinta dole mu ceto ta da abin da za ta haifa". Jiki a sanyaye Hajiya Amina ta karɓi consent form, ta saka hannu, tana mamakin yadda suka kwanta lafiya ƙalau da Shukura, har likitan da ya ganta da yamma, yana faɗin za a sallame ta washegari, a ce lokaci ɗaya ta rikice, duk da ba a tara sani da Allah, kuma babu kusa babu nesa a gare shi. Haka tana tsaye aka turo Shukura a kan gado, aka shiga da ita tiyata. Ta koma gefe jikinta a sanyaye tana ta adduo'i daban-daban, tana fatan Allah ya sa ba abin da Shukuran take faɗa ne, zai faru ba, da take cewa tana ji a jikinta kamar mutuwa za ta yi, ba za ta rayu ba. Shukura a hankali ta buɗe idonta, tana kallon likitoci a kanta, ba ta san me suke yi mata ba, ita dai tana jin ana girgiza ta. Anesthetic ɗin ya ce "Kin farka?" Ta lumshe idanunta ta buɗe alamar eh. "Ɗaga ƙafarki sama mu gani" "Ba zan iya ba" ta faɗa a hankali. Ya ce "To yauwwa, suma ki ka yi ne, shi yasa saboda kar a rasa ki, a rasa babyn, ake yi miki tiyata ba zai yiwu mu ci gaba da barin ki da shi ba, sai mu rasa ku, kuma ba mu sani ba sarkinmu ne na gobe ko shugaban ƙasa" ya yi maganar da sigar wasa. Ta kasa dauke idanunta daga kan Doctor Sharif, da ya haɗa gumi suke ta ƙoƙarin ciro jaririn. **** Ƙarfe bakwai da rabi, Nana ta dafa ruwa, ta kai masa banɗaki. Ta zo kansa ta ce "Sayyid taso ka watsa ruwa, za ka ji daɗin jikinka sosai da sosai" Ya tashi ya zauna, ya ɗan jima a zaune, sannan ya yinƙura, ta bi bayansa ta raka shi ƙofar banɗakin, ta miƙa masa zanin hannunta ta ce "Idan ka gama ka lulluɓa sai ka fito" bai karɓi zanin ba, ya kalle ta, sannan ya kalli banɗakin. A take ta gane Abin da yake nufi, amma wani irin nauyin sa take ji, saboda ba su yi sabon da za a ce ta sake ta saba da shi haka ba. Amma ganin ya ja ya tsaya, ya ƙi gaba ya ƙi baya, ya sanya ta wuce shi, ta shiga banɗakin. Bayan ta ya biyo, yana bin bango, saboda jirin da yake ji, Nana ta din ga sinne kai, tamkar ta gudu saboda tsananin kunyar da ta lulluɓe ta. Kafin a gama wankan, ita ma sai da ya jiƙa ta jalaf da ruwan, tamkar ɗan ƙaramin yaron goye. Tana zuba masa ruwa a jiki yake zabura, kamar zai shiɗe, sai ya rirriƙe ta. Da dabara a hankali ta ci gaba da zuba ruwan a jikinsa. Ta gama ta goge masa jikinsa su ka fito. Da ta kalle shi, sai ta ji zuciyarta ta karaya, amma ta din ga dakewa, tana mazewa. Ta soya dankalin Hausa da suke da shi, ta dafa shayi, ta zuba masa ta ajiye masa a gabansa. "Ko na baka a baki?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Ta yi murmushi, ta saka hannu tana ba shi. Ya ƙura mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi, ya ɗage girarsa yana ƙoƙarin buɗe bakinsa. Nana ta ce "Ai na san maganar ta ɗauke, ba sai ka yi mini magana ba, na fahimta" ya sake kallon ta da mamaki. Ta ce "Ka manta ka ce mini ruhinka yana rayuwa a cikin nawa? Shi yasa nake fuskantar yinƙurinka ko ba ka furta ba" Murmushi ya yi yana jinjina kai, ya haɗa tafukan hannayensa biyu, ya ɗago su daidai ƙirjinsa, 🙏 ya risunar da kansa alamar ya gode sosai. Nana ta sauke hannun ta ce "Babu godiya tsakanina da kai, duk da ban san wace irin rayuwa ka baro a baya ba, amma kula da kai dolena ne Sayyid" Idanunsa suka cika da hawaye, ya kamo hannayenta, ya din ga sumbata, ciki da waje. Tausayinsa ya ƙara mamaye ilahirin jikinta, cikin dakiya ita ma ta sumbaci hannunsa, ta ci gaba da bashi abinci. Sai da ya ƙoshi, sannan ta saka hau kan katifar ya jingina, ta rife masa ƙafafuwan sa da bargo. Ta tashi tana gyara ɗakin, horn ɗin mota ta ji, ya ɗago ya kalli Nana. Ta ce "Ka zauna kar ka tashi" ta saka Hijjabinta ta fita waje. Matashin saurayin nan da take gani a gidan, mai tara samari su na kallon Ball ta gani a cikin mota. Ta ƙarasa inda motar take ya sauke gilashin motar ta ce "Sannu da fitowa" Ya ce "Yauwwa sannu" "Ka ga ba ya jin daɗi ne, ba shi da lafiya, bari na buɗe maka" Ya dubi Nana ya ce "Subhnallah me ya same shi?" "Zazzaɓi ne yake damun sa" "Allah sarki, wataƙila malaria ce, unguwar akwai sauro sosai. Kin ga wani magani da likita ya bani ɗaya na sha, na ji daɗin sa sosai da sosai, nake yawo da shi a mota. Ki ba shi ga paracetamol ma, zai ji daɗin sa. Je ki kawai zan buɗe ƙofar Allah ya sauwwaƙe" Nana ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce  "Na gode sosai da sosai" "Ahh ba damuwa" Nana ta ji dadin mutuntawar da ya yi mata, duk da za su yi sa'anni da shi, amma ya yi mata karamci saɓanin 'yar uwassa da ta wulaƙanta mata miji" Ya sauka ya buɗe gate ɗin ya fita, ya dawo ya rufe. Nana na shiga ɗakin, ta tarar da shi a tsakiyar ɗakin a tsaye, yana muzurai. "Ya na ganka a tsaye kuma? Ka kwnata ka huta, ga magani ma ya bayar ya ce a baka, sai ka samu ka sha" Ya koma kan katifar, ya kwanta, ba tare da ya tanka mata ba. AREWABOOKS ***** Shukura ba ta san adadin lokacin da ta shafe ba ta hayyacinta ba. A hankali ta buɗe idonta, amma sai dai dishi-dishi take gani, tana jin maganganu, amma sama-sama, ba ta gane me ake cewa. Sai sannu a hankali idanunta suka washe ta gane komai. Mummy ta taso tana faɗin "Sannu Shukura ya jikin" A wahale ta ce "Mummy" "Na'am Shukura" "Ina abin da na haifa?" "Ki kwantar da hankalinki, an kai shi nursery ne, an saka shi kwalba" Kawai Shukura ta fashe da kuka tana faɗin "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba mafarkina ne zai tabatta ba, dan Allah Mummy ni a karɓo mini ɗa na, a ciro shi daga kwalbar ba na so a dawo mini da jaririna ba na son wata kwalba" Cikin damuwa Mummy ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Shukura yanka ki aka yi fa, ko awa uku ba a yi ba, sai kin yi wa kan ki illa? Mene ne dan an kai shi nursery?" "Ni dai ba na so, ki ce su dawo mini da ɗa na, wallahi zan tashi na je na karɓo ɗa na, idan ba za ki karɓo mini ɗa na ba" "Shukura ina za ki tashi ki je, jikinki da ciwo meye haka ne?" Iya ƙarfinta take ƙoƙarin tashi da gaske, sai ta tashi sai dai ƙafafuwanta suka ƙi motsawa. Hargowar Shukura da kukanta, ya janyo hankalin ma'aikatan gurin. Suka haɗu a kanta ana ba ta haƙuri, amma fafur ta ƙi yin shiru. A dole aka yi mata allurai ta koma bacci. Sosai yake tsala gudu a kan titin, yana fatan ya isa gari ya waye. Yana yi yana kallon inda ya kwantar da jaririn a gefensa, jikinsa kaca-kaca da ƙazantar haihuwa da sauran jini, ga mahaifarsa a gefe ita ma kaca-kaca da jini a jiki. Yaron baya iya kuka, sai kaɗan-kaɗan, bakinsa sai rawa yake yi, saboda azabar sanyin da yake ji. Alhaji Zailani yana yi yana kallon yaron, sai dai ƙirjinsa ya yi masa nauyi, ya rasa dalilin hakan. Yana matuƙar ƙaunar Shukura, haka kurum ya din ga jin kamar bai kyauta mata ba. Amma da ya tuna girman buƙatar sa, na mamaye duniyar sa da samun duk abin da ya sanya a gaba, sai ya ƙara azama da ƙara gudun giyar motar. Daji ne sosai da sosai, ya yi parking ya ɗaukko jaririn, ya fita ya nausa cikin duhun duƙununun dajin. Yana tafe ya hango wuta tana ci, ya ƙarasa gurin da wutar take ci. Malam Gambo ne sanye da jajayen kaya, ya nufo shi yana faɗin "Ka kusa makara fa" "A yi mini afuwa, amma ina fatan wannan aikin zai zama daidai da sadaukarwata ta shekara". "Ƙwarai kuwa, ba za a sake neman jini daga gare ka ba a wannan shekarar" Ya miƙa wa Malam Gambo jaririn, ya saka hannu ya karɓi yaron, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa, ƙafafuwansa a sama, ya danna tafin ƙafar jaririn, a take ya tsanyara ihu, ihun jaririn ya cika dajin. Malam Gambo ya haska fitila, ya ɗaukko wani abu a cikin wata jaka, ya saka shi a wuta, ya yi ja ya juya bayan yaron, ya zana wani hatimi a jiki, ya sanya sunan Fatuhu Magaji a cikin hatimin. Yaron ya din ga tsala ihu tamkar ana zare masa rai. Suka haɗu da shi da Malam Gambo, suka tona rami, suka binne jaririn da ransa. Duk da ba yau Alhaji Zailani ya saba irin wannan abubuwan ba, amma na wannan karon shi kansa ya girgiza zuciyarsa. Malam Gambo ya ɗauki mahaifar, ya ce "Wannan na 'yan aike ne, su za su cinye ta, kai za ka iya tafiya, bayan kwana talatin za mu zo a cire ƙwarangwal ɗin, za a yi wani aikin da shi. Ka huta ka yi yadda ka ke so Alhajin Allah, in dai Duniya ce ka same ta yadda ka ke so". Suka yi sallama Alhaji Zailani, ya hau motarsa ya nufi gida. A wani irin mugun razane Nana ta tashi daga nannauyan baccin da take yi, ta tashi zaune. Tsaf abin da ta gani ya dawo mata kai fes ba ta manta komai ba. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ka duba lamarin nan, Allah ya sa shirmen mafarki ne" Tashi ya yi zaune shi ma ya ce "Me ya faru?" Ta yi ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta ce "Babu komai, maganar ta dawo?" "Eh" ya faɗa a taƙaice. "Sannu ya jikin?" "Alhamdilillah" "Ko na ɗaukko maka maganin da aka bani, ya ce yana da kyau ka jarraba sha" Ya ce "Ba na sha" ya yi maganar yana kwanciya. Ta dafa shi ta ce "Sayyid, duniya ba za ta yiwu mu rayu mu biyu ba kawai, dole wasu lokutan mu na buƙatar taimakon mutane, dan mu rayu cikin aminci mu ma. Na san haƙƙoƙinka na aure da suke kai na, dan baka da cikakkiyar lafiya ba ya nufin zan ci amanar auren ka. Na san ni Ahalinka ce, kuma wani shinge da babu wanda zai ratsa shi." Ya yi mata shiru. Ta kwanta a gefensa, tana shafa gashin sa, ta ce "Sayyid ka yi mini magana mana" "Ba ki san me nake ji ba ne" "Na sani mana, ka manta ruhinmu ɗaya ne?" Ya yi shiru ya lumshe idanunsa yana jin daɗin, yadda take wasa da gashin sa. "Sayyid" "Ma vie" "Dan Allah da gaske Alhaji Zailani ya ce maka ka sake ni?" Kamar ba zai yi magana ba ya ce "Eh, ya ce zai ba ni kuɗi. Zuciyata kamar zan mutu a ranar" Ta ce "Me ka ce masa?" "Ba zan iya tunawa ba, kawai dai na ji numfashina zai ɗauke ne, na manta meyafaru" Ta ɗan yi murmushi ta ce "Rayuwa kenan, daga ni har kai dai gamu nan kawai, Allah ya shiga al'amarinmu. Sayyid ina jin tsoron kar ka tuna waye kai, ni kuma ka manta da ni" Ta ji shiru, bai yi magana ba. "Sayyid " ta kira sunansa, amma tuni ya yi bacci. Saurin baccinsa har mamaki yake bata. Zuciyarta kuma ta ci gaba da hasko mata mummunan mafarkin da ta yi, da Alhaji Zailani, dan haka take ta fatan, gari ya waye, ta kira Hajiya Amina ta ji yaya ake ciki. Sai dai ta kasa komawa bacci, ta din ga tunane-tunane daban-daban a cikin ranta. Ba ta san adadin lokacin da ta shafe a haka ba, ta ji ya ce "Ba ki yi bacci ba haryanzu? Mafarki ba gaske ba ne ba fa" Nana ta ce "Ba mafarki na yi ba, na kasa baccin ne" "Ƙarya babu kyau, kin tsorata a mafarki. Kuma kin gaji ma yau sosai, kina ta kula da ni, na gode sosai bari na yi miki tausa" "A'a ci gaba da baccinka, daga tausar nan har a yi asuba ba zan yi bacci ba, bar ni kafin a kira salla na rage na yi baccin" Dariya ta ji yana yi ya ce "To a bari sai bayan sallar asuba" "A'a ba ni da lafiya" ya ƙara matsawa kusa da ita, ta ji shiru har ya sake komawa bacci. Ƙaisar ta gani yana ɗaure Sayyid a jikin wata itaciya. A razane ta nufe shi ta ce "Ƙaisar mene ne haka? Me ya yi maka?" "Kar ki kuskura ki zo gurin nan, ai na gaya miki tun da ya kwance ƙullin nan, sai ya ɗanɗana shi ma" Nana ta ce "Wai tayaya ya kwance ɗaurin da ka yi? Shi da ba aljani ba, kuma bai san abin da yake ɓoye ba, ka sauke shi dan Allah" "Ke ki ke ganin shi mutum kamar kowa, na gaya miki kar ki kuskura ki zo gurin nan, zan yi miki illa" Ba ta tsaya ba ta ci gaba da tunkarar sa. Hankaɗe ta ya yi gefe, ya cigaba da ɗaure Sayyid a jikin itacen nan. Ta yinƙura ta tashi da ƙyar, ta sake nufar sa, sai dai kafin ta ƙarasa, tsohon nan ya bayyana ya make Ƙaisar gefe. Da sauri Nana ta ƙarasa, ta hau kwnace Sayyid da yake a galabaice, ya fita daga hayyacinsa. Faɗa ne ya kaure tsakanin Ƙaisar da tsohon. Sayyid ya yi shiru, ya zubawa Nana ido, yana jin duk yadda take, furta abin da take gani a cikin mafarkinta a zahiri. Ya cigaba da kallon fuskarta, ds yadda gumi ya tsatstsafo mata a goshinta, ta rirriƙe shi gama tana kuka. Ya saka yatsunsa biyu a ƙyerta ya danna, a take ta yi shiru, jikinta ya saki. Da Safe yana ta bacci, ta tashi ta yi aikace-aikacen ta. Bayan tashin sa ya karya, ya yi wanka ya fita waje, sai dai tun da ya tashi bai yi magana ba. Ta gama aikinta ta fito, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi tana yi masa hira, yana jin ta amma ba ya magana. Kubra ce ta nufo inda suke zaune, tana tahowa ya sunkuyar da kai. Nana ta tashi ta ƙarasa inda take, ta ce "Sannu ina zuwa haka?" "Fita zan yi" "Ki je ina?" "Fita kawai zan yi" ta bawa Nana amsa. Nana ta miƙa mata hannu da nufin su gaisa. Ita ma ta miƙa mata suka gaisa, sai dai a wannan karon Nana ba ta ji sanyi ba. Nana ta kalle ta daga sama zuwa ƙasa, riga da wando ne na bacci a jikinta, kanta ko ɗan kwali babu. Nana ta ja ta ɗakinsu, ta shimfiɗa mata sallaya ta ce "Zauna" babu musu ta zuna. Nana ta zuba mata abinci ta ce "Na ji an ce ba kya cin abinci, bismillah mu ci" babu musu ta kama cokali ta na cin abincin. Cikin tausaywa Nana take kallonta, tana matuƙar jin tausayin mai fama da irin wannan larurar, wanda duk ba shi yake ɗauke da larurar ba, ba zai gane wahalarta ba. Mussaman idan na kusa da shi, ba su fahimci kan ciwon ba. Ta cinye tas, Nana ta ɗauke kwanon ta kalli Nana ta ce "Na daɗe ban ci Abinci da yawa ba" Cikin kulawa Nana ta ce "Me yasa?" "Ba na so kwata-kwata. Ba ma na iya bacci." "To me ki ke ji a jikin ki?" Ta ɗan yi shiru ta ce "Kawai dai ji nake mutuwa zan yi, sai na yi ta kuka" Nana ta tashi ta ɗaukko mata pillow, ta ajiye mata ta ce "Kwanta da yardar Allah za ki yi bacci" ta kwanta ta yi shiru, Nana ta kunna mata karatun Alkur'ani. Ta nutsu tana saurara, har bacci ya ɗauke ta. Farin ciki ya kama Nana, ganin ta yi bacci. Ta ce "Ya Allah, kai ka ke jarraba bayinka da larura, wasu ka haska musu maganinta, wasu kuma ka ɓoye. Ya majiɓancin lamarinmu, Allah ka yaye mana wannan larurar". ***** Misalin ƙarfe goma da rabi da safe, Baba yana ya bala'in an ba shi koko ɗan kaɗan babu sugar, alhalin an san ba isar sa zai yi ba. Mama ta ce "Da ka samu wannan ɗin ma, Jamila ce ta bayar da kuɗin gasarar, yarinyar da ka ke nufi da sharri kai da ɗan ka, sai ka bari idan ka nemo, ka fara kawowa sai ka nuna isa da iko" Sallamar da aka yi ya amsa, yana jiran ya ga suwaye, sai dai ya saroro baki buɗe yana kallon masu sallamar. Su ka shigo niƙi-niƙi da kaya a hannun su. Mama ta fito daga kitchen, ta ga suwaye, ta ce "Too ikon Allah, yau kuma da abin da muka tashi kenan?" "Lafiya yaya aka yi?" Ya tambaye su kamar ya ga annoba. "Malam Isa ai kwa bamu guri mu tsuguna tumu tsuguna tukuna" "Ba wani a baku guri ku tsuguna, ba na son fitina, meya kawo ku?" Ɗaya daga cikin su ta ce "A'a duk ba abin zafi ba ne ba ai, labarin auren Nana mu ka ji, shi ne muka zo mu tabattar" Baba ya ce "Eh, haka ne na aurar da Nana, tun da 'yata ce, kuma ina da hurumin aiwatar da hakan" Saude ta ce "Haka ne, amma mahaifiyarta da mu ma, mu na da hakki a kan ta, ai yakamata a sanar da mu" "Ba zan sanar ba, na ce ba zan sanar ba ɗin? Me sanar mukun zai amfanar?" Mama ta ce "Rakiya auren ne fa aka yi shi babu shiri, saboda magana ta nemi ta ɗaukko mana aka yi shi, ba wani taron kirki aka yi ba" "Amma duk da haka, ai ya kyautu mu sani" Baba ya taso kamar zai dake su ya ce "Kin ga ku bi hanyar da ku ka shigo mini gida ku fita". "Dan Allah Malam Isa ka yi haƙuri, abin duk bai kai haka ba, ka bari a kaimu ko gidan nata ne, mu ga ɗakinta, mu gaisa da ita, mu ba ta saƙon mahaifiyarta" "Na yi muku iyaka da 'ya ta, ba zaku taɓa ganinta ba, ba ta buƙatar ku, ku bar mini gida, kafin na yi muku ɗibar albarka" Ganin babu mutunci a lamarin Malam Isan, ya sanya suka kwashi kayan da suka zo da su, su ka fice. Ayshercool 08081012143 40 Hargowa da bala'in da Baba ya yi wa su Adda Rakiya, ya yi masifar ɓata musu rai, a zaton su duk abubuwan da suka faru a baya sun riga sun wuce, dan aure ya mutu ba ya nufin a wanzar da gaba a tsakanin yara da mahaifiyar su, ko a yanke duk wata da za su yi alaƙa da ita. Ga gajiyar tafiya da su ka sha a mota, amma Baba ya yi musu wannan mummunar tarbar. Can gidan su Nana kuwa, ana ta neman Yusra, ba a ganta ba, hankalin Hajiya Halima ya yi mugun tashi, suka fito neman ta harabar gidan tare da Siyama. Gurin Sayyid su ka nufo, Hajiyar take tambayarsa "Dan Allah yarinya ba ta zo ka buɗe mata ƙofa ta fita ba? Wata 'yar fara haka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. "Na shiga uku, ni kuwa ina yarinyar nan ta shiga haka? Kirawo mini Nuradeeni a waya, ko sun fita tare?" Siyama ta ce "Su fita tare su je ina, su da ba shiri suke yi ba, ina zai kai ta? Wataƙila tana cikin gidan nan wani gurin ta samu ta shige kawai" "To tana cikin gidan nan, mu ganta mana" "Ki yi haƙuri mu koma, mu ci gaba da duddubawa" Nana kuwa ba ta san me ake yi ba, tana zaune a gefen Yusra, tana bin karatun Alkur'ani da ta kunna a wayarta. Ta ji daɗin yadda take raira karatun yau, ba tare da ta ji kanta ya fara ciwo ba, ko ta fara jin sanyi ba. Yusra kuwa baccinta take yi da gaske. A ƙalla ta kai awanni biyu tana bacci, har Nana ta idar da karatun Alƙur'anin, ta ɗora girki. Ta kammala babu jimawa ta farka daga baccin. Nana ta saka ta yi alwala, ta ba ta hijjabi ta yi alwala ta yi salla. Ta sake zuba mata abinci ta ci, sannan ta ce "Mu je na raka ki cikin gidan, zan zubawa mijina abinci shi ma na ba shi" Ta kalli Nana ta ce "Ki na da miji?" Nana ta jinjina kai ta ce "Eh, ina da shi, shi ne a waje yake yi muku gadi" Yusra ta ce "Mhmm ni da na fara rashin lafiya, shekara biyu kenan, mijina ya sake ni, ya ma yi aure ba zai zauna da ni ba. Ba wanda ya san me nake ji, amma ke na ga kamar kin san me yake damuna, ke ba za ki ce ƙarya nake yi ba. Mami ta ce "Ina sane na kashe aurena, na ji haushi sosai da sosai" Nana ta riƙe hannunta ta ce "Ki yi haƙuri, na ki ƙalubalen kenan, tabbas na san ciwon nan, na san babu daɗi, kuma babbar jarrabawa ce a ce na kusa da mu sun kasa fahimtar mu, su din ga ganin muna sane muke yin abin da muke. Dan haka dolenmu ne, mu dage mu yi ta adduo'i da azkar domin Allah ya bamu lafiya" Ta jinjinawa Nana kai ta ce "Na gode sosai da sosai" Nana ta tashi suka fito daga ɗakin, dama Sayyid a matse yake ya shiga ɗakin, zaman Yusra a ɗakin ya hana shi shiga. "Wannan ne mijin naki?" "Eh shi ne" Ta ce "Sannu dattijo" Ya ɗago ya kalle ta, ya ɗaga mata hannu. Ta yi murmushi kawai. Nana ta ce "Dattijo kuma?" "Eh, ke matashi ki ke gani, ni kuma Dattijo nake gani, duk da kema ki na ganin haryanzu dai ki na wasi-wasi ne" Nana ta ce "Haula" Ta amsa da "Na'am uwar gijiyar Ƙaisar" "Amma me yasa za ki yi mini haka? Matar ta farfaɗo ta samu ta ci abinci, ta yi bacci kuma kawai sai ki zo za ki sake burkita ta" Yusra ta yi murmushi ta ce "Tuba nake, wallahi ba da wata manufar na zo ba, gaisuwa na zo kwasa kuma na yi sai anjima" Nana ta ɗan ƙura wa Sayyid ido, amma ya ƙi kallonta, ya tafi ɗakin su. Ta jinjina kai a hankali ta ce "Biri ya yi kama da mutum" Har cikin falon Nana, suka shiga tare da Kubra. Hajiya Halima na ganinsu ta miƙe ta ce "Laa a ina ki ka ganta? Tun ɗazu muke bulayin neman ta a cikin gidan nan" Nana ta ce "Subhnallah, wallahi ban sani ba, gani na yi za ta fita na hana ta, mu na tare da ita a ɗakina, kuma na yi ragon azancin ban zo na sanar miki ba". "Mami ta bani abinci, kuma na yi bacci ma" "Ikon Allah, yau kin yi baccin kenan?" Yusra ta ce "Eh, na yi bacci sosai mai daɗi, na ga ma Sagir a baccin" A fusace Hajiya Halima ta ce "Ba za ki daina maganar Sagir ɗin nan ba ko? Mutumin da ya riga ya sake ki, ba zai zama da ke ba, mene ne na zancen sa " Siyama kuwa da ranta ya ɓaci ta ce "Amma baiwar Allah wannan shiga hakki ne, tun ɗazu mu ke neman ta fa, kuma saboda wulaƙanci da rashin mutunci mijinki ya ce bai ganta ba, wannan ai gidadanci ne da rashin hankali" "Laifina ne, ba nasa ba ki daina zaginsa dan Allah, ba na jin daɗin hakan" Hajiya Halima ta ce "Siyama ya isa haka dan Allah, amm Nana sunan ko? Mun gode sosai da sosai" Nana ta juya za ta tafi, Yusra ta ce "Ƙawata sai anjima" Nana ta yi mata murmushi ta ce "Kar ki manta abubuwan da na gaya miki fa" Ta amsa mata da "To" ***** An ɗaga Shukura daga kwanciyar da take yi, an yi mata wanka, aka kawo mata abinci, amma ta ƙi ci, tana zaune tamkar gawa. "Shukura yanzu haka rayuwa za ta kasance mutum babu tawakalli kenan? Da Allah ya baki lafiyar ba za ki gode masa ba kenan?" "Mummy" "Naam" "Kin ga gawar abin da na haifa?" Hajiya Amina ta ce "Eh mana, awansa shida a nursery ya rasu, sai da na gan shi sannan Sagir ya tafi da shi ya binne." Hawaye ya gangaro kan kumatunta, ta ce "Amma me yasa ba a bari na gan shi ba?" "Shukura ba kya cikin hayyacinki, za a yi ta zama da gawa ne ba a binne ba? Ai ba zai yiwu ba" Ta ce "Haka ne, amma ina baban Haidar ɗin yake?" "Bai daɗe da tafiya ba ki ka tashi, kuma da na san za ki farka da wuri an jira, kin gan shi. Amma na san ya ɗaukar miki shi a hoto ai. Na tura family group ma, amma dai na ƙara gaya musu, ban da zuwa dubiya ba kya jin daɗi" Ta ce "To Mummy na gode sosai, tun da dai kin ce mini kin ga gawar babyn shikenan, Allah ya sanya mai ceto ne. Ke ma Allah ya baki ladan ɗawainiyar da ki ke ta yi da mu" Cikin jin daɗi Hajiya Amina ta ce "Amin ya Allah, ko ke fa Auta, dan Allah ki ci abincin ko na ji daɗi" "To Mummy amma saboda ki ji daɗi zan ci kaɗan, ba na son cin komai" "Ba komai, hakan ma na gode sosai da sosai Autar Mummy" Haka Shukra ta din ga yaƙi da zuciyarta, da ƙoƙarin kawar da tunanin mafarkan da take yi. ***** Har Gaddafi ya gota matan, da suke zaune a kan barandar ƙarshen layin, sai kuma ya dawo da baya ya ce "Sannun ku" Su ka amsa masa da "Yauwwa sannu" Ya ce "Kamar 'yan uwan babar su Imrana" Adda Rakiya ta ce "Laa Gaddafi kai ne?" Sai ya gyara tsayuwarsa, su ka gaisa. Ya ce "Ya na gan ku a nan?" Adda Rakiya ta so ta kare, amma Fati ta gaya masa abin da ya faru. Ya girgiza kai ya ce "Ku yi haƙuri, abu ne da ya faru ya riga ya wuce, amma an ƙi bari ya wuce, ake ta nanatawa, bari na nemo muku Nasiru, ya raka ku." Bayan tafiyar sa Rakiya ta ce "Fati, wannan ba Gaddafi ba ne ba, mai cewa zai daki Mai Jidda, yau shi ne da gaishe mu" Fati ta ce "Wallahi nima abin ya bani mamaki sosai da sosai" Su na cikin tattaunawa, Gaddafi ya kawo musu ruwan sanyi da lemo, ya nemo Nasiru, ya tarar musu abin hawa, ya biya kuɗin suka tafi. ***** "Sayyid" Ya ɗaga ido ya kalle ta. Ta ce "Ko dattijon ne?" "Wane dattijon?" "No ba komai" "Ki daina kallona, kamar ki na tuhuma ta" Ta ce "Tuhumar ta ka nake yi ai" Ya tsaya da cin abincin ya ce "Da me?" "Ci abincinka, zan gaya maka" Ya ci gaba da ci, ta sake kiran sunansa. Ya ɗago ido ya kalle ta. Za ta yi magana, su ka ji an buɗe gate ɗin gidan an shigo. "Laa a buɗe ka bar gate ɗin?" Ya ce "Eh na manta ne" Sallamar Nasiru ta ji, ta yinƙura ta tashi ta leƙa. Kasancewar jikinta babu hijjabi, ko ɗan kwali babu a kanta, kafin ya yi magana tuni ta yi wani irin ihu, ta yi waje da gudu. Tashi ya yi da sauri, ya bi bayan ta, domin ganin abin da ya sanya ta wannan ihun haka. Gani ya yi ta rungume ɗaya daga cikin matan da suka shigo tare da Nasiru. Ya koma da sauri ya rufe abincin da yake ci, ya kawar da kwanukan ya koma gefe ya tsaya. Tare suka shigo da matan, ɗayar na share hawaye ita ma. Su na shigowar ya fice daga ɗakin. Nana ta kasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Adda Saude ta ce "Nana kukan ya isa haka" "Adda ina mamanmu?" "Yanzu dai ki yi haƙuri, mu gaisa mana Nana" Ta basu gurin zama, sai dai ta kasa daina kuka, ta kawo musu ruwan roba, ta koma gefe ta zauna ta cigaba da kuka. Anty Fati ta ce "Haba Nana, ki yi shiru mana" "Dan Allah ina Maman take? Yanzun ma ba za ta zo ba?" Adda Saude ta ce "Ki yi haƙuri Nana, auren nan na ki ma ba mu sani ba, waiwai mu ka ji, tare za mu taho da ita da, amma mijinta ya hana, yanzu haka ma babanki da korar mu ya yi, Gaddafi ne ya haɗo mu da yaro ya rako mu, har ya biya mana kuɗin mota" Cikin kuka Nana ta ce "Na kira ta, Baban su Walida ya ɗauka, bai haɗa ni da ita ba" "Ki haƙuri Nana, lamarin iyayen naki ne sai haƙuri, ita kanta babu yadda ba ta yi ba ta zo, amma ya hana har da barazanar saki. Amma ga kayan aurenki nan da ta bayar a kawo miki, mu ma da abin da Allah ya yassare mana. Yanzu zamu haɗa ki da ita a waya, zan kira Lawan ya kai mata sai ku gaisa" Nana ta ci gaba da kuka, tana jin kewar mahaifiyarta, amma gaba ɗaya ba ta da maraba da marainiya. Anty Fati ta ce "Nana, mijin naki buzu ne kenan? Ke kuwa yaya aka yi ku ka haɗu har danginsa su ka bari, ya aure ki, ai ba sa auren bare da wahala. Har gara matan su, idan ka na da kuɗi za su baka, amma mazan dai ba sa auren wasu matan idan ba na su ba". Ras gaban Nana ya yi wata irin mummunar faɗuwa, amma ta dake ta ce "A gidan da yake gadi mu ka haɗu" Adda Sauda ta miƙo wa Nana waya, Nana ta karɓa jikinta yana rawa. "Salamu Alaikum Nana, ki na ji na?" "Mama" ta furta cikin rauni, tana fashewa da wani irin kuka tamkar za ta shiɗe. Maijidda ma kukan ta saka ta ce "Nana ki yi haƙuri, na san ni mai laifi ce a gurinku, dan girman Allah ku yafe mini an fi ƙarfina ne, na rasa yadda zan yi. Imrana ma ya daina zuwa inda nake" "Mama dan Allah ki zo, ni ba na son na zo na saka ki a matsala ina son na ganki, dan Allah" "Nana in sha Allah zan zo Nana, da gaske an yi miki auren ko? Kodayake daga majiya mai ƙarfi na ji, Babanku bai kyauta mini ba. Ga ɗan abin da na tara miki nan babu yawa, ki yi haƙuri Nana, ki ba wa ɗan uwanki haƙuri dan Allah ku yafe mini. Wallahi ku na raina ban taɓa mantawa da ku ba, babu yadda na iya, mijin da nake aure ba shi da fahimta, kansa kawai ya sani shi ma" Nana ta kasa magana sai wata irin sheshsheƙar kuka da take yi. Ta sake cewa "Ki na ji na Nana, ki yi haƙuri da rayuwa, jariri ma ana haihuwar sa, mahaifiyarsa ta koma ga Allah, kuma ya rayu cikin ikon Allah, ki zama mai juriya, ki yi wa mijinki biyayya. Har yadda aka yi aka yi auren ki, an gaya mini, amma ko 'yan uwana ban gaya wa ba, kowace mace ko na ce ko wane dan Adam akwai kalar tasa jarrabawar. A raina, ban taɓa jin za ki aikata, wani abu da zai tozarta ki ba. Ki yi haƙuri ki rungumi auren ki Nana, shi ne mutuncinki da suturar ki. Yaya jikin ki kuma?" "Da sauƙi" ta faɗa muryarta na fita da ƙyar. "To ki riƙe Addu'a, ki riƙe Allah. Ki riƙe auren ki da kyau, ki yi haƙuri Nana, ki yi haƙuri ku yafe mini. Dan Allah kar ki yi fushi da ni, kamar yadda ɗan uwan ki ya yi, wallahi ku na raina." "To Mama, na gode sosai, na gode" suka yi sallama, Adda Saude na ta rarrashinta da ba ta haƙuri. Gyaran muryarsa ta ji a ƙofar ɗakin, Nana ta tashi da ƙyar ta nufi ƙofar ɗakin. Zuciyarsa ce ta buga da ƙarfi, a razane ya ajiye ledojin hannunsa ya ce "Mene ne?" Nana ta yi shiru tana kallon sa. "Yi magana Husna, mene ne?" Nana ta goge hawayenta, ta ce "Babu komai fa" "A'a launin idonki ya canza, ba kuka ne kawai ba, akwai matsala ne" Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ka kwantar da hankalinka, zan yi maka bayani bari baƙina su tafi" "Zuciyata babu daɗi, ki daina kuka na roƙe ki" Cike da jarumta, ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Na daina" ya jinjina kai, ya ɗauki ledojin ya ba ta. Ta koma cikin ɗakin, su ma fruit ne, da fura da Nono ya kawo. Ta hau fafutukar ɗora musu girki, a hankali ta ɗan ware, su ka yi ta hira, Nana ta ce "Me yasa ba a zo mini da ko Walida ba, rabona da su tun su na yara sosai" Anty Fati ta ce "Wa zai ɗaukko su, ya zo ya yi ta jaraba, mussaman ya san in da aka tafi da su. Ai Maijidda ba ta yi dacen mazaje ba, daga Baban naku, har Iliyasun. Suka yi salla, Nana ta kammala girki, ta ɗebarwa Sayyid nasa, su na ta yi wa Nana hira, sai dai zuciyarta cike da damuwa. Nana ta fita ta samu Sayyid, ya miƙe tsaye yana kallon kumburarriyar fuskarta cike da damuwa. "Sayyid ka zo za ku gaisa da 'yan uwan Mamana, su ne suka kawo mana ziyara ka zo mu je ku gaisa. Amma idan da hali ka yi musu magana dan Allah" Ya ce "To, amma idan ina kallon fuskarki a haka, ba zan iya magana ba" Ta yi murmushi ta ce "Ba na son rigima, mu je to" "Ina jin kunya, wuce gaba na biyo ki" Ta yi murmushi, ta yi gaba ya bi bayan ta. Ya yi sallama sannan ya shigo, ya tsugunna, ya sauke takunkumin fuskar sa ya ce "Barkanku da zuwa, ya hanya?" Jin gaisuwar ta sa suka yi banbarakwai, amma Adda Saude ta ce "Lafiya ƙalau, mun same ku lafiya? Ya iyalin?" Ya ce "Alhamdilillah mun gode Allah" "To ma sha Allah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, bamu samu mun halarci taron biki ba, sai yanzu muka zo. Allah ya baku zaman lafiya. Sannan a yi ta haƙuri, shi aure ɗan haƙuri ne, ba farkon auren ba, sai zama ya yi zama ake gane haƙurin. Ubangiji Allah ya yi muku albarka, dan Allah ka yi haƙuri da ita ka riƙe ta amana" "In sha Allah" Anty Fati ta ce "To ina fatan dai ba za ka yi mata kishiya ba, tun da ta ciri tuta ka aure ta, tun da dai an ce ba kwa auren wanda ba ƙabilar ku ba? Dan ni 'ya ta daidai take da mata huɗu, har da ɗoriya." Miƙewa ya yi yana murmushi, ya nufi hanyar fita. Nana cikin shagwaɓa ta ce "Sayyid ba fa ka ba da amsa ba" Yatsansa manuniya ya nuna mata, ya ce "Ke kaɗai ce Ma vie" "Anty Fati ki zama shaida" Ya fice yana murmushi, Anty Fati ta ce "Ke babu ruwana, namiji na mata huɗu ne, wasa nake yi kar ki saka a hakan a ranki" Nana ta basar da maganar, dan wani irin zafi ta ji ya fara taso mata. Adda Saude ta ce "Nana an baki 'yan abubuwa kuwa na gyara, ko kuwa haka kawai su ka ninko ki, su ka kawo ki?" Nana ta yi shiru, tare da sunkuyar da kai, wa ya tsaya bin ta kan ba ta wani abu, har gara Ummi ta kawo mata, ranar da su ka zo da su Jamila, ta rubuta mata yadda za ta yi amfani da shi, amma tun da ta jefa ledar a drower, ba ta sake bi ta kan su ba, saboda pressure gabanta ta ishe ta, ba ma ta taɓa tsammanin wani abu zai shiga tsakaninsu ba. Anty Fati ta yi wa Nana tambayoyi, a kan matsalar sanyi, Nana ta ce ita ba ta jin komai na alamar sanyi. "To duk da ke kaɗai ce a gurin mijinki, amma kar ki zauna ki miƙe ƙafa Nana, kar ki ga ba shi da ƙarfi, tsaf 'yan mata za su din ga kawo masa farmaki, ki na ganinsa tubarkallah da shi. Nana ki yi addu'a, ki yi gyara kuma ki yi biyayya, za ki zauna lafiya in sha Allah. Nana ki yi kissa, kar ki zauna haka sai abin da ya zo miki, ki zama mace mai tunani Allah ya baku zaman lafiya" Suka yi ta yi mata nasiha, har aka yi sallar la'asar. Su na yin sallar la'asar, su ka ce za su tafi, saboda kar su yi dare a hanya. Nana ta ce "Bari ya dawo daga masallaci, sai na raka ku" Duk s karɓi lambobin wayar su, su ma suka karɓi ta ta. Suka shirya tsaf za su tafi, Nana ta fito ta tarar ya dawo daga masallacin. Ta ce "Sayyid, za su tafi zan raka su ko bakin titi ne, su hau adaidaita sahu, su je tasha". Ya ce "Bari mu je tare" "Idan mutanen gidan su na neman ka fa?" "Wata ta ƙone a gidan, sun tafi kai ta Asibiti" Nana ta waro ido, ta ce "Wace ta ƙone?" "Ban sani ba, kawai na buɗe gate sun ce mini za su Asibiti, wata ta ƙone da ruwan zafi" Nana ta ce "Ikon Allah, Allah ya sauwwaƙe." Su Adda Saude, su ka fito, suka tafi raka su tare da Sayyid. Su na tafe su na ci gaba da yi musu nasiha, a bakin titi, suka tarar musu adaidaita sahu. Nasiru dama tun da ya raka su, gida ya koma saboda zai je makarantar Islamiyya. Nana ta tambayi mai Napep ta ce "Nawa za ka kai su tasha" hararta Buzu ya yi, ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu, ya bawa mai adaidaita sahun. Ya sake ɗaukko baƙar leda, ya ajiye wa Anty Fati a kan cinyar ta, ya ce "Mun gode sosai" "A'a ba zamu karɓa ba, ɗawainiyar ta yi yawa" Nana ta ce "A'a Anty Fati, ba zai ji daɗi ba. A ce ina gaida Mama, ina kewar ta sosai da sosai" ta yi magana idanunta na cika da hawaye. "A'a Nana, kar fa ki je ki zauna ki yi ta koke-koken nan, idan haka ne, za mu daina zuwa" Ta goge hawayen ta ce "Na daina, ku gaida gida" Sai da su ka ja motar su ka tafi, sannan su ka dawo gida. Nana ta zuba masa Abinci, ya ce "A'a ba na jin yunwa yanzu" "Sayyid ina jin daɗin yadda ka ke mutunta 'yan uwana idan sun zo, kuma na ji daɗin yadda yau ka yi magana da su, har ka yi raha, har cikin zuciyata na ji daɗi sosai da sosai. Allah ya nuna mini 'yan uwanka haka, zan yi iya yi na, na kyautata musu nima, Allah ya sa su amince su karɓe ni a matsayin ɗaya daga cikin ahalainsu". "Na ji kin ce a gaida Mama, mamanki na nan ta bari, a ka aura miki ni?" Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ba ga Maman nawa nan ka gani ba, ranar da mu ka je duba Baba?" "Ba maman ki ba ce, kuma ko mamanki ba ta so na, ba za ta din yi mana irin kallon da waccan matar ta yi mana ba. Amma wannan da su ka zo, na ga su na murna sosai da sosai da ganina, har suka yi mana addu'a, duk da ban san me yasa ki ka yi kuka ba da suka zo" Nana ta haɗiye abu mai ɗaci da ya tsaye mata a wuyanta, ta san yanzu ba ta da wani mutum mafi kusanci da ita, sama da shi, dan haka babu buƙatar ɓoye masa komai, dan haka ta numfasa ta ce "Tabbas ba Mamana ba ce wadda ka gani a gidanmu. Mamana sun rabu da Baba, tun ban fi shekaru tara ba. Ba komai nake iya tunawa ba, kawai dai na san Mama ba sa jituwa da dangin su Babanmu, su na yawan samun saɓani. Har dai suka rabu. Ta ce Baba ya bata mu, ni da yayana amma ya hana ta. Ba ta daɗe da rabuwa da shi ba, ta yi wani auren. Abin ya ɓata wa Baba rai sosai da sosai, ya ce kamar ta sane ta kashe auren dan ta fita ta auri wani, wanda ta aura ɗin kuma an ce ya taɓa son ta, ba ta aure shi ba. Adda Saude ta zo ta ɗauke ni ta ƙarfin tsiya, ta tafi da ni, amma da ƙyar na kwana a gidan da Mama take, mijinta ya ce sai an fita da ni. Abin dai duk babu daɗi, aka sake mayar da ni gidan Baba. Na fi shekara bakwai ban ganta ba, ina kewar ta sosai da sosai" ta yi maganar tana fashewa da kuka. Ya rungume Nana a jikinsa yana shafa bayanta a hankali. "Ki daina kuka, za mu je mu ganta in sha Allah, ke gara ke a kan ni ai. Ban sani ba ma ina da maman ko ba ni da ita, ni ke kaɗai na sani" Ya jima yana rarrashinta, sannan ta ɗan tsagaita da kukan da take yi. Ta fara buɗe kayan da suka kawo mata. Ba masu tsada ba ne ba, amma ta yi ƙoƙari. Bedsheet kawai biyar ne, huɗu na gida, ɗan waje ɗaya. Ga kwanuka har da kayan sakawa. Sai da ta bari an kira magariba ya fita, sannan ta sake fashewa da kuka, ta yi kuka sosai sai da kanta ya fara ciwo,  sannan ta haƙura ta yi shiru. ***** Jikin Shukura ya yi kyau, ta warware, wannan kumburin duk ta sace, aka rubuta mata sallama. Doctor Sharif ya sha jinin jikinsa, dan sai da ya tsorata ya fara wasi-wasin ko dai Shukura ta san abin da ya aikata mata, saboda yadda ta canza gaba ɗaya. Wasa da dariyar ma da suke yi, gaba ɗaya ta daina, da ya shigo sai ta tsuke fuska. Sai dai wani sashi na zuciyarsa ya din ga ba shi, kawai yanayin da take ciki ne, na rasa ɗan ta da ta yi, ya sanya duk ta canza ta daina walwala. Hajiya Amina ta dube ta, ta ce "To Shukura yaya? Gidanki zan mayar da ke, ko gida za ki taho?" "Mummy mu je gida na ɗan huta tukuna" Sagir ya harari Shukura ya ce "Mummy, a dawo da ita kawai, ke ma ki huta da ɗawainiya tun da ta samu lafiya" Su na cikin mujadalar, Alhaji Zailani ya kira waya, ya ce "An sallame ku ne ko kuwa? Ya ce mini yau za a sallame ku" "Eh, an sallame mu, ta ce gidan zata taho, mijinta ya ce ta koma gida" "Saboda me? Ta koma ta yi masa me? A dawo mini da 'ya ta gida ta huta, kafin ta koma, me za ta je ta yi masa da yanka a jikinta". Hajiya Amina ya ce "A'a kar a yi haka, mijinta ne fa" "Ni kuma ubanta ne, ki ce masa na ce a kai mini 'ya ta gida ta huta, idan ba za ki faɗa ba, ni zan kira shi" Sagir yana ji yana gani, haka ya haƙura, aka mayar da Shukura gida, maimakon gidansa. **** Nana ta kira su Adda Saude, suka tabattar mata da sun je Bauchi lafiya, ta yi musu bangajiya. Yana ta shirin kwanciya, Nana kuma ta ƙura masa ido, zuciyarta ta yi mata nauyi, ba ta jin daɗin komai. Ya zo kusa da ita, hannunsa riƙe da kofi ya miƙa mata. Ta saka hannu ta karɓa, tana kallon sa. "Na ga ba ki ci abinci ba, madara ce na kuma karɓo miki" Ta buɗe kofin, ta kalli madarar, da wani baƙin abu a kai. "Habattussauda ne a ciki, ko na fara sha ne?" Ya yi magana yana miƙa hannunsa zai karɓi kofin. Ta kafa kai, ta fara shan madarar, sai da ta shanye ta ajiye kofin. Ta dube shi ta ce "Me yasa ka ke bani madarar nan?" "Na ji wani likita ya faɗa a radiona, yana ƙara wa mata lafiya sosai" Ta ɗan yi murmushi, sannan ta numfasa ta ce "Sayyid, da gaske ƙabilarku, ba sa auren macen da ba ta su ba?" Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sannan ya ce "Duk abin da zai fito daga bakina a yanzu, ƙarya zan yi miki, saboda ba zan iya tuna komai a kan ƙabilar tamu ba" Cikin rawar murya ta ce "To yanzu idan Allah ya sa ka tuna waye kai, da asalin rayuwar ka, ni mece ce makomata? Za ka karɓe ni a matsayin matarka kuwa?. Idan kuma aka samu akasi ka manta da ni baki ɗaya fa? Yaya zan yi? Mece ce makomata?" Ayshercool 08081012143 41 Ya yi shiru yana nazarinta, hawaye ya wanke mata fuska, har cikin ranta maganganun da suke fitowa daga bakinta. Tabbas! Tambayoyin nata a kan hanya suke, kuma sun cancanci ta samu amsar su, amma ta yaya zai bayar da amsar abin da shi kansa bai sani ba? Ya dake ya tattaro nutsuwar sa, ya ɗago fuskarta, su ka haɗa ido. "Ba na so, ganin wannan na ɗaya daga cikin abin da yake tayar mini da hankali, na rasa nutsuwa, hawayen ki zafi yake haifar mini a zuciyata, kuma yau wuni ki ka yi kuka" ya yi maganar yana share mata hawayen da yake kan fuskarta. "Sayyid ka bani amsa, zuciyata ta cika da tsoro da fargaba, da kuma wasi-wasi" Ya sassauta muryarsa ya ce "Ma vie. Idan har tunawa da rayuwata da waye ni, zai sanya na manta da ke a cikin rayuwata, ina fatan na dauwwama ba tare da na tuna waye ni ba. A jikina ina jin rayuwar da nake yi tare da ke, ita ce rayuwa mafi aminci da kwanciyar hankali. Ba ki yadda ba da na ce miki rayukanmu na cikin na juna ba? Muddin ruhinki na yawo a doron duniya, ba zai taɓa barin ruhina cikin nutsuwa ba, saboda abokan rayuwa ne" "Sayyid" "Duniyata" Wani kyakyawan murmushi ne ya suɓucewa Nana, ta ce "Kalaman ka na ƙara mini ƙwarin gwiwa, har ba na son na ji muryar ka ta ɗauke ko sau ɗaya" "Da gaske?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya sumbaci goshinta yana murmushi, mai ƙayatarwa. Sai da zuciyarta ta motsa, wani irin shauƙi ya mamaye ta, ji take tamkar ta furta abin da take ji a cikin zuciyarta, amma ta danne, sai kallonsa da take yi. Ya ce "Faɗi mana, ki furta" "Me zan furta?" "Abin da yake zuciyar ki, da ki ke son faɗa" ta girgiza kai ta ce "Babu komai" "A'a, ruhina ne a jikinki fa, ko in gaya miki abin da ki ke son cewa?" Ta girgiza kai alamar a'a. Ya saki wani irin murmushi, mai cike da ƙasaita yana kallon fuskarta. Haka ya sakankance, ya tattara duk hankalinsa da lokacinsa a kan Nana, sai da ya mantar da ita damuwar da ta shiga, wani nannauyan bacci, ya sace ta. ***** Hajiya Sa'a ce take mita iya yin ta, "Wallahi Jamila, ban da yayan ki ne ya yi miki wannan dukan, da sai na rufe shi, wannan ai take haƙƙin ɗan Adam ne. Tun da kin kai shekaru goma sha takwas, ai kin sa abin da ya dace da rayuwar ki". "Wallahi haka Mama ma ta faɗa, da police station za a kai shi, Baba ya yi ta bata haƙuri, nima na ce kar a kai shi, ta yi haƙuri" "Saboda me ki ka hana a kai shi, ai gara a kai shi, ya san cewa ke da shi akwai bambanci yanzu" Jamila ta ce "Kaii babban yayanmu ne fa Mummy" "Shi ɗin fa, shi ba dukan ki ya yi ba?" "A'a ai bai kamata ba, da kunya abun" "Ke Jamila, kalle ni da kyau. Irin wannan lamarin, dole ki sakawa kowa tsoron ki idan ki na son ki zauna lafiya ki taka duk wanda ki ke so. Ba a tausayi ba kuma a tuna danganta kan ki kawai za ki kalla, ki gina rayuwar ki. Babu wani abu da dangantaka ke ƙara wa banda koma baya da hassada da fitintinu" Jamila ta jinjina kai ta ce "Haka ne" "Dan haka duk wanda ya yi yinƙurin taɓa ki, ki yi maganinsa kawai. Ni zan fita ba daɗewa zan yi ba amma" "To a dawo lafiya" Jamila ta yi maganar tana kashingiɗa a jikin kujerar 3 seater da ke ɗakin. Har bacci ya fara ɗaukar ta, ta ji ana sallama, ta buɗe idonta ya ce "Yi haƙuri na tashe ki, Mummy ta fita ne?" Ta jinjina masa kai tana ƙoƙarin mayar da kai ta kwanta. "Ta daɗe da fita ne?" "A'a" Ya ce "Ok thanks " ta mayar da idonta, ta lumshe shi kuma ya ɗan ƙura mata ido, kan ya fice. **** Alhaji Zailani na zaune, yana jiran ta gama haɗa tea ta ba shi, kiran wayar Hajiya Sa'a ya shigo wayarsa. Ya ɗaga su ka gaisa. Ta ce "Zailani, matarka ta fi ƙarfin ta je duba Hanifah a Asibiti, har an sallame su sun koma gida" "Dan Allah ki daina kamabama abu, wane irin fin ƙarfi, ni na je, su Rauda su je, maman su ta je, duk bai isa ba? Ba ta da lafiya ne, mu na ta yawon asibiti" "Ba ta da lafiya me ya same ta?" Ya ce "We are expecting another Muhsin in sha Allah, cikin yana ta ba da matsala ne yana neman ya fita, so an bata complete bed rest ne, kin ga ba zai yiwu ta din ga yawo ba" Hajiya Sa'a ta ɗan yi jimm sanan ta ce "Yayi Allah ya raba lafiya" Uwargidan sa da ke ƙoƙarin haɗa masa tea kuwa, ji ta yi tamkar ta kurma ihu. Da ta ji batun cikin Fadila, kuma wani namijin ne. Ita nata yaran biyar duk mata ne. "Ya dai lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallon ta. Ajiye masa tea ɗin ta yi, ta bar falon saboda takaici, dan kuwa ji ta yi, tamkar ta watsa masa shayin a kansa. Ya karya abin sa a nutse, yana yi yana communicating da mutane ta waya. Tashi ya yi zai je ya duba Fadila, dan ba a gurin ta ya kwana ba, kuma ba ta jin daɗi sosai. Sai dai ya ji tamkar an ɗora masa dutse a kansa, kuma an saka igiya an ɗaure shi. Ya yi miƙa ko zai ji dai-dai, amma ya kasa jin ya dawo normal. Ya lallaɓa ya fita, kansa na sara masa ya nufi sashin ta. Ya yi iya ƙoƙarin sa, bai bari ta fahimci wani abu ba, saboda kar ya ƙara mata damuwa, ya zauna har su ka yi hira, sannan ya fita. **** Ya na zaune yana kallon Nana, ta na ta fafutukar yin breakfast, saboda ƙoƙari meatpie ta tsiri yi da safen. Ta kammala ta zuba masa nasa, ta haɗa masa tea. Ta zuba masa ido. Ya saka hannu ya ɗauka ya kai bakinsa ya ci, ya yi murmushi ya sake kaiwa bakinsa. Ta ce "Da daɗi?" Ya ɗaga mata babban yatsansa, alamar jinjina. "To ka ce Allah ya yi mini albarka" Murmushin sa ya ƙara faɗaɗa ya sumbaci goshinta, sannan ya shafa gashinta ya ce "Allah ya yi albarka" "Amin Shugabana" ta yi maganar tana dariya. "Ga Nonon can a kan mudubi, ki fara sha kan ki karya" Ta tsuke fuska ta ce "Nonon raƙuma dai ba nawa ba" A tare su ka tuntsure da dariya, har ya kusa ƙwarewa, ta ɗaukko ruwa ta ba shi ya sha. Ta ce "Ba ruwana, kar ka ƙware ka ce ni ce" Duk da ba ta da cikakkiyar masaniyar dalilin ba ta Nonon raƙumin, amma ta fara jin daɗin sa sosai da sosai a jikinta. "Sayyid, bari na kaiwa ƙawata ko za ta ci" "Wa?" "Yusra" ya jinjina kai. Ta fita ta shiga cikin gidan. Ko da ta yi sallama, a falo ta tarar da Siyama, hannunta duk ya ƙone, a ɓare mata ƙunar. "Sannu ina kwana?" Ta kalli Nana ta amsa ciki-ciki. Ba ta sake bi ta kan Siyama ba, ta haye benen. Ɗakin Yusra ta shiga da sallama. Yusra ta ɗago, amma ba ta amsa ba. Ta ganta a zaune a kan gado ta yi tagumi, amma tana ganin Nana ta saki murmushi. Nana ma ta yi mata murmushi ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita ta ce "Yayata, kin tashi lafiya?" Yusra ta ce "Lafiya ƙalau" "Abinci na kawo miki, ko kin karya?" Ta ce "A'a" "To ga wannan" ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode" Nana ta din ga yi mata hira, har ta cinye meatpie ɗin. Ta ɗan numfasa ta ce "Dan Allah Nana, kema ki na jin kin gaji da duniya, idan ki ka ga wuƙa ki ji kamar ki cakawa kanki, ko ki faɗo daga saman bene ki mutu? Irin duniyar babu daɗi ɗin nan?" Nana ta jinjina kai ta ce "Sosai, na taɓa yinƙurin kashe kaina ma, amma addu'a nake yi sosai da sosai. Ina roƙon Allah ya kiyaye ni. Kuma nake yin alwala sosai nake zama da ita" "Kin tabattar idan na yi hakan zai daina ji, idan na yi addu'a Allah ba ya karɓa, salla ma kamar ba daidai nake yi ba." Nana ta rufe mata baki ta ce "Ki daina faɗar haka, nima da ina wannan tunanin amma na yi ta istigfari. Allah ya na karɓar addu'armu, ba dan haka ba da wataƙila haukacewa zamu yi gaba ɗaya" Yusra ta ce "Haka ne, wallahi na ji daɗin zuwan ki gidan nan, duk kin san me nake ji, kuma kin san abubuwan da nake ji ba ƙarya nake yi ba" "Ai kamar yadda na gaya miki ne, mukaɗai mu ka san abin da muke ji. Ki daina damuwa sai kowa ya san halin da ki ke ciki, an fahimce ki an daina cewa ƙarya ki ke yi. Idan an kai ki gurin likita ya baki magani, ki din ga sha. A gefe kuma ki din ga addu'a ki na fatan Allah ya yaye miki" Ta girgiza kai ta ce "Ba na son maganin likitan nan, bacci suke saka ni, kuma ba na iya baccin sam, sai dai jikina ya mutu, kuma damuwa ta ƙara yi mini yawa". Nana ta din ga rarrashinta da ba ta haƙuri. Sun yi hira sosai, sannan ta ce za ta raka Nana bakin ƙofa. Su na tafe ta ce "Kin ga Siyama ta ƙone ko? Tana shiga kitchen za ta juye ruwa a flask, na sheƙe mata shi a hannunta. Nana ta tsaya cak ta ce "Saboda me?" "Ta ɓata miki rai, ni kuma muddun aka ɓata miki rai na san zuciyar masoyina sai ta sosu, ni kuma ba na fatan hakan. Dan da na ƙyale ta ma, ban san shi wani matakin zai ɗauka a kan ta ba" "Ba zaki ƙyale matar nan ta huta ba ko Haula? Ki ji tsoron Allah" Ta maze ta ce "Ai ko dan saboda ke, ina sassauta mata, ba har hira ku ke yi ba? Ina dattijon arziki?" Nana ja ta tsaya, ta ce "Me yasa ki ke kiran mijina da dattijo, alhalin matashi ne?" Ta yi dariya, ta naɗe hannunta a ƙirjinta ta ce "Ni ina ruwana da mijinki? Ba da shi nake ba, duk da na san ki na ganin komai wasu lokuta." "Ki gaya mini, me ki ka sani game da mijina? Da tsohon da nake ganin su tare, tun da na san a kan sa ki ke magana." Ta girgiza kai ta ce "Wannan wani hurumi ne da shigarsa ka iya kawo mini matsala, dama dai kin amincewa buƙata ta na taimakon soyayyata da na yi duk wata kasada da ki ke buƙata, je ki sai an jima" ta juya ta koma, Nana ta bi ta da kallo har ta ɓacewa ganinta. Tana ta saƙe-saƙe, har ta ƙarasa gurin da yake zaune a kan benci, ta zauna a kusa da shi. Ya ce "Kin dawo?" "Eh, me ka ke yi mini da waya ne?" "Kallo" ya bata amsa a taƙaice. "Yauwwa Sayyid, dan Allah gidan Anty Ummi nake son zuwa, na gaishe ta, kuma a yi mini kitso, tun da na tsefe kaina, na ban yi kitso ba" ya yi mata shiru. Jin ya yi shiru ya sanya ba ta sake maganar ba. Bayan ya yi sallar azahar, ya ci abincin rana, ta ɗaukko reza ta zauna, tana yanke masa farce. Kamar wadda aka takara ta ce "Sayyid su Habu kwana biyu ba su zo ba, Allah ya sa lafiya" AREWABOOKS Yadda ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya sanya Nana nutsuwa, da tuna katoɓarar da ta aikata. Ba shiri ta ja bakinta ta tsuke. Har ta gama yankan farcen bai sake kula ta ba. Nana a ranta ta ce "Na shiga uku, wannan baƙin kishin ya yi yawa. Daga tambaya?'. Duk wasu 'yan kame da kame, da Nana za ta yi, ya kula ta ya yi mata shiru, ya ƙi kula ta. "Allah ya haɗa ni da gamona" Ya fita sallar isha'i, ta kira Ummi, suka gaisa, take bawa Ummi labarin zuwan su Adda Saude. Ummi ta ce "Gaskiya Nana idan an kwana biyu, ki ɗauki mijinki ku je ku gaishe ta, duk tijarar da mijinta zai yi, ki rufe ido ki je ku gana, mutuwa ake ji" Nana ta sauke numfashi ta ce "Haka ne, shi ma haka ya ce min, kuma ina da wannan tunanin. Ina cikin damuwar rashin sanin halin da Imarana yake ciki ma." "Kin ga ki rabu da wannan, namiji ne ranar da Allah ya nufa, zai waiwayo gida, tun da an ce an riga an kama wanda su ka yi kisan kan" "To shikenan. Ina nan tafe zan zo ki yi mini kitso ma, kaina tun da na zo da kitson biki da na tsefe, babu kitso a kaina ne, ina lallaɓa shi ne ya ƙi bari na" Ummi ta kwashe da dariya ta ce "Au ya ƙi barin ki, har hana fita unguwa yake yi? Yana gane abubuwa dama?" Nana ta ce "Kai. Ba fa ko yaushe yake cikin halin rashin lafiya ba. Yana gane komai sai dai idan abin ya waiwayo ni faɗa ma mu ka yi wallahi ya ƙi kula ni, kuma so nake ya bari na zo wallahi" Ummi ta ce "Ikon Allah, wallahi har mamaki nake yi, mutumin da ba ya kallon mutane, balle ya yi magana, ashe yana yi. To ai shikenan idan ya bar ki a satin nan, har da gyaran jiki zan yi wa wata amarya, na haɗa da ke" "Hajiya Ummi sabga, sana'a ta kankama, to sai kin ji ni" Ta ajiye wayar, ta kunna turaren wuta a ɗakin, ta yi shirin kwanciya, tana ta lissafin yadda ta rarrashe shi, sai dai nauyin hakan take ji, da wata irin kunya tana tunanin ta ina za ta fara. Ya shigo da sallama, muryarsa ƙasa-ƙasa Nana ta amsa tana kallonsa. Ya rage kayan jikinsa, tana tsaye a gaban mudubi. "Sannu da zuwa" Bai ko kalle ta ba, ya kashe fitla ya haye kan katifa ya mimmiƙe. Yadda Nana ta faɗa kan katifar, ta danne masa hannu , ta zata zai yi magana, amma ya shiru bai ce uffan ba. Nana ta rasa me za ta ce masa, ƙarshe ma ya juya mata baya gaba ɗaya. Nana a ranta ta ce "Allah ya yaye maka Sayyid" Ta zura hannu ta warware gashinsa, "Sayyid ka din ga yi mini uzuri nima, ba na son irin wannan fushin na ƙyaliya, yana takura zuciyata sosai. Amma shikenan" ta yi maganar muryarta na rawa, kamar za ta fashe da kuka. Ta yinƙura za ta juya, amma ya riga ta juyowa. "A'a kar ki yi kuka" "To ni ka daina yi mini irin haka" "To na daina" ya faɗa yana kai hannunsa fuskarta. "Kar ki yi kuka fa" jin yadda ya shiga damuwa nan da nan, ya sanya ta ci gaba da kunna shi, ta hanyar yin taɓara iri-iri. A ranta ta ce "Ohh, wai yau ni ce ba a son na yi kuka, da uban wa ya damu idan ma rijiya zan cika da hawaye?" Ta ƙarfin tsiya ta saka ya din ga rarrashinta, da Hausa da French. Da Asuba kuwa sam bai tashi da alamar ma ya yi fushi ba, saboda kar ta yi kuka. Bayan ya dawo daga salla, tana kwance a jikinsa ta ce "Dan Allah Sayyida ka bar ni na je a yi mini kitson nan, na je gurin 'yar uwata dan Allah" "A'a" "Dan Allah Sayyid." "Idan kin tafi wa zai kula da ni?" Ta yi murmushi ta ce "Zan ajiye maka duk abin da ka ke buƙata, dan Allah ka bari na je Please. Ba dan kar na zaunar da kai ba, sai mu tafi tare ma, to ka ga bai kamata na bari ka na jira na ba" "A dawo lafiya" ta zabura ta ce "Ka yadda na je?" Ya jinjina kai. "Allah ya saka mini kai a aljanna na gode sosai Shugabana" Ya yi murmushi ya ce "Sayyid yanzu kuma Shugaba" "To ai duk abu ɗaya ne" kyakyawar sumbata ya samu a bakinsa, daga matarsa saboda tsananin farin ciki da ta shiga. Da safe ta ya ƙoƙarin gama girki da wuri, ta ɗora masa na rana, ta dafa ruwan zafi ta zuba masa a flask da duk abin da take sanya ran zai nema. Ta yi wanka ta fara shiri, su ka yi waya da Hajiya Amina, take gaya mata kwana huɗu kenan, an yi wa Shukura aiki yaron ya rasu. Nana ta ji ta damu sosai da sosai, ta yi mata jaje ta ce za ta je ta duba ta. Ko da ta ajiye wayar, ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka ji Shukura ta haihu yaron ya mutu, dan Allah zan biya na duba ta, sai na tafi gidan Ummi." "A'a" Ta marairaice ta ce "Dan Allah, kar su ga kamar wulaƙanci ne, an gaya mini abu ban je ba" Ya kalle ta ransa a haɗe, ya ce "Kar ki je gidan nan" ta tsuke bakinta, kar ta je gidan Ummin ma, ya hana ta zuwa. Har bakin hanya ya raka ta, sannan ya koma. Ta yi tunani ta ga yadda ya tsuke fuskar nan, babu lallai ya bari ta je, kuma Hajiya Amina ba ta cancanci haka daga gare ta ba. Duk da ba shiri suke yi da Shukura ba a baya, amma tana matuƙar tausayinta. Kawai ta yanke shawarar ta je a gurguje, ta duba ta ta wuce gidan Ummi. Habu ne ya buɗe mata gate, yana ganin ta, ya yi murmushi suka gaisa ya ce "Ina mutumin?" Ta ce "Yana gida, bai san zan zo ba, wata unguwar na tambaye shi, dan Allah kar ka gaya masa na zo" "A'a kar ki damu, ba zan gaya masa ba, ina fatan duk ku na lafiya?" Nana ta ce "Lafiya ƙalau, ba ka zuwar mana kwana biyu" "Ai na ga babu wata matsala ne, ku na lafiya shi yasa" "Ko kuma shi ne ya hana ka zuwa, Sayyid kishinsa ya yi yawa" Ya yi murmushi ya ce "Sayyid kuma?" Nana ta jinjina kai ta ce "To na rasa da sunan da zan kira shi, amma dan Allah da wani sunan aka ɗaura mana aure da shi ne?" "Kamar dai yadda na gaya miki ban san komai a kansa ba, kawai cewa na yi a saka Muhammad, amma ban san sunansa ba nima" Ta jinjina kai ta ce "To da gaske kai ne ka ke ba shi kuɗin da yake kashe mana? Na ga kuɗin aikin gadin ba wani yawa ne da su ba" Ya ɗan yi dariya ya ce "Ai ainihi ba gadi ne sana'ata ba. Ina safarar dabino ne, da mazarƙwaila da cukui da sassan raƙumi, daga Nijar zuwa Nigeria na rarrabawa 'yan kasuwa. A garin haka ma na tsince shi. Na fara gadi ne saboda na samu na zauna guri ɗaya, a nema masa magani, amma haryanzu ba a dace ba, masu maganin sai su ce abin ya fi karfinsu" "Amma Malam Habu, me aka ce muku yana damunsa?" Horn ɗin mota su ka ji, ya ce "Bari na buɗe ƙofa" Ta ce "Shikenan, nima bari na hanzarta" Ta shiga cikin gidan, Jummai ta din ga murna da ta ga Nana, ta yi mata jagora har ɗakin Hajiya Amina, inda Shukura take jinya. Sosai Nana ta jajantawa Shukura, tare da ba ta haƙuri, da ƙarfafa mata gwiwa a kan girma da muhimmancin tawakalli ga Musulmi. Hajiya Amina har so take Nana ta zo, ko tana cikin damuwa, ire-iren wa'azinta, a kan tawakalli da dogaro ga Allah na ƙara mata ƙwarin gwiwa. Nana ta tambayi ina Haidar, aka ce mata yana gidan kakarsa. Muryar Alhaji Zailani ta ji ya shigo ɗakin, yana kiran sunan Hajiya Amina. Gabanta ya faɗi, ƙwaƙwalwarta ta shiga fafutukar tuno mata, da abin da ta gani a mafarki amma ta kasa, duk da zuciyarta na raya mata mummunan abu ne, kuma kamar a zahiri ya faru. Saboda kaucewa zargi, Nana ta yi ta maza ta gaishe shi. Shi kansa ya yi mamakin ganin Nana, ya daidaita nutsuwar sa, ya amsa mata ya ce "Ashe amarya ce ya mai gidan?" "Yana nan lafiya ƙalau. Hajiya bari na tafi ina sauri ne, sai na sake dawowa." Cikin sauri ta ɗauki jakarta ta yi waje, Shukura na ta yi mata godiya. Ba ta tarar da Habu ba, kawai ta buɗe gate ɗin ta fice. Ganin da ta yi wa Alhaji Zailani, ta din ga jin tamkar ta aikata wani mummunan saɓo ne. Tana ta sauri, unguwar shiru babu kowa, ta ga an sha gabanta da mota. Ta ja ta tsaya ƙirjinta na dukan uku-uku. Duk wannan saurin, na ki tsere mini ne? Idan na so kamo mini ke zan saka a yi, na yi duk abin da nake so, kuma babu wanda ya isa ya ce dan me, ko ya tuhume ni. Biyo ki na yi na ƙara tabattar miki da ina nan a kan baka ta, wallahi ba zan rabu da ke ba, sai buƙata ta ta biya." Cikin dakiya ta ce "Allah ko? A baya ban taɓu ba, sai a yanzu ka ke tunanin zan taɓu? To kar ka fasa, ka ci gaba da bibiyata da mugun nufinka, kar ka fasa" ta zagaye motar ƙasan zuciyarta tana tsananta addu'a ta bar gurin. Gidan Ummi ta tafi, Ummi ta yi farin cikin ganinta sosai da sosai, su na hira ana gyara Nana. Nana ta bata wasu daga cikin kayan da su Adda Saude suka kawo mata. Aka wanke mata kai, aka yarfa mata kitso ƙanana, ta yi mata dilka ta zana mata lalle ja da baki, ta turara ta da turarukan wuta. Nana ta ce "Inyee ko ranar aurena ban samu wannan gatan ba" "Ai biya za ki yi, ki je gida ki ce ya biya kuɗin gyaran da na yi miki" "Ba zamu biya ba ɗin" ta yi maganar tana dariya. Ummi ta bata labarin yadda Saleh, duk ya shiga damuwa da tashin hankali, saboda auren da ta yi, ya tattara ya koma Lagos ma. Daga haka kuma suka koma tattaunawa a kan matsalolin gidan su, yadda Baba ya bar ragamar gida a hannun Mama, gantalin da Jamila take yi, har ta bata labarin dukan da Gaddafi ya yi mata, ga Imarana babu ma wanda yake cigiyarsa. Suka ci gaba da jajanta matsalolin na su, da a yanzu ba su san ma hanyar saita wannan gida na su ba. Gefe ɗan gidan Yaya Atine ya ce yana son Suwaiba, Mama ta ce ba za ta bawa Faƙiri 'yar ta ba. Sun daɗe su na hira, Nana ta bawa Ummi kayanta da take so a ɗiɗɗinka mata. Ummi ta duddubo mata wasu kayan kwalliya, da sauran 'yan kayan buƙatu ta rako ta titi, ta samu abin hawa ta tafi gida. Ana ta kiraye-kirayen sallar magariba Nana ta isa gida, sai dai ba ta tarar da shi ba. Ta yi salla, kasancewar ta zo da abinci daga gidan Ummi, ya sanya ba ta ɗora girki ba, ta dai kunna gas ta ɗora masa shayi. Har aka yi sallar isha'i shiru bai shigo ba, sai kuma abin ya fara damunta. Ga shi shi ba waya ba, wayarta ma tana hannunsa, ba waya ta fita. Tana nan tana kallon hanya, ta ji yana rufe gate. Ajiyar zuciya ta yi, ta jira ya shigo ɗakin. "Sayyid, duk na damu na ji ka shiru, ina ka tafi ne?" Ko kallon gurin da take bai yi ba, ya wuce ta ya shiga banɗaki. Sororo ta tsaya tana mamaki. Ta koma gefe ta jira, ya fito. Ya sake nufar wardrobe. Ta bi bayansa ta na magana. "Sayyid wai meyafaru ne? Ina ta magana ka yi mini shiru" Ya duba jallabiyar da zai saka ya kwanta. "Sayyid ka yi magana mana" Ya ajiye jallabiyar, ya kalli Nana a tsanake ya ce "Me yasa na ce kar ki yi abu ki ka yi?" Gabanta ya faɗi, ce rauni ta ce "Me na yi?" "Tambayata ki ke yi? Ban ce kar ki je gidan mutumin nan ba? Ban gaya miki ba?" Ya yi maganar cikin ɗaga murya. Cikin sauri ta girgiza kai ta ce "A'a ban... "Kar ki yi mini ƙarya kin je, me yasa ki ka je?" Ta girgiza kai tana tsuma, saboda yadda ya burkice mata. Ya Kano hannunta ɗaya ya ɗora a ƙirjinta, ya kama ɗaya ya sanya a ƙirjinsa, ta ji yadda zukatansu ke bugawa a tare. ""Haryanzu ki na tunanin ƙarya nake yi, da nace miki akwai ruhina a jikinki?" Ya saki hannayenta, ya kuma tsare ta da ido, ya ce "Me yasa ki ka je bayan na ce kar ki je?" Nana ta yi shiru ta ƙi magana. "Magana nake yi miki" ya ƙara maganar yana ɗaga mata murya. Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga gaba ɗaya ya canza, fuskar sa kamar bai taɓa dariya ba, jikinsa yana tsuma. Tsorata ta yi, ta ƙara ja da baya, kawai ta ji ya riƙe wuyanta. Ayshercool 08081012143 Idanun Nana suka yo waje, ta ji numfashinta ya yi sama, ta saka hannu ta rirriƙe nasa tana kakari. Da ƙyar ta kalli fuskarsa, gaba ɗaya ta canza naman fuskarsa sai rawa yake yi. Tsohon nan ta ga ya bayyana a gefensa, riƙe da sandarsa yana kallon ta yana dariya. Jikinta ne ya saki a hankali, ta sauke hannunta. Ya yi jifa da ita kan katifa ya yi baya, yana jin tamkar ana jan kansa. Tana durƙushe tana wani irin tari, haɗi da kakari, tana ta yinƙurin amai, amma babu abin da yake fita daga bakinta sai wani irin yawu mai yauƙi. Ta ja jikinta da ƙyar ta jingina, ta lumshe idanunta ta buɗe a hankali. Ta ga Ƙaisar ya zura mata ido. Ya gyara zamansa ya ce "Yanzu da ki ka fara ɗanɗana kuɗarki, wataƙila za ki yarda da abin da nake gaya miki. Laifi na biyu kenan da ya aikata mini, zan kuma taɓa shi a inda ba ya zato". A wahale Nana ta ce "A'a Ƙaisar,  koma dai mene ne, ni ya yi wa dan Allah ka rabu da shi, wannan tsohon na gani a tare da shi, kuma idan ka ce za ka yi masa wani abu, kai ma wannan tsohon wahalar da kai yake yi." "Ba ke za ki gaya mini abin da zan yi, ki rufe mini baki. Kuma kuskure mafi girma da ki ka aikata, bayan ƙin amincewa da buƙata ta, shi ne ɗaukar cikin da ki ka yi, ba zan taɓa lamunta a samu zuriya ta tsatsonki ba, na ci gaba da ƙuntata rayuwata ina wahalar banza a kan mutane marasa alaƙawri kamar ku ba" Nana ta kalli cikinta ta kalle shi ta ce "Ciki kuma?" "Ƙwarai, ga ɗan tayi nan a cikin ki, tun a ranar farko da ku ka kasance tare. Kin ɗauki abin da ke kan ki ba ki da tabbacin wane jinsi ne" "Mutum ne, Sayyid bil'adama ne, da aljani ne ba zai iya tarayya da ni a zahiri ba, sai dai a cikin bacci, ko ta hanyar amfani da gangar jikin ɗan Adam " "Ko?" "Eh" ta ba shi amsa. "Yaro yaro ne. Kin tabattar bil adama ne, daga ina? Daga wace nahiyar? Wane shiri ki ke da shi, a kan sanin waye shi da inda ya fito? Har ki ka sakankance ki ka amince da ɗaukar ciki?" Ƙoƙarin juyawa Nana ta yi a kan katifar, amma ta ji jikinta a ɗaɗɗaure kamar an yi mata duka. Ga wani irin azabar sanyi da yake ratsata ko ta ina, tamkar an ajiye ta a cikin ƙanƙara. A cikin kunnuwanta kuma take jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da kuma sauri. Ga wani irin nauyi da kanta ya yi mata tamkar an ɗora mata. Ga azababben ciwo da yake yi mata, tamkar zai rabe. Ta juya da ƙyar tana numfarfashi, tana son lalubar abin da za ta rufa, wani irin huci ne ya daki fatarta, ta buɗe idanunta da ƙyar, ta kalli gefenta. Yana kwance jiginsa na ta jijjiga, yana numfarfashi. Ta din ga jan jikinta a hankali, ta matsa ta hau kan ƙirjinsa ta kwanta, ba tare da fargabar zai sake yinƙurin cutar da ita ba. A hankali ta ji zafin jikinsa, ya fara ratsa ta, ta fara rage jin sanyin da take ji, wani wahalallen baccin ya sake yin awon gaba da ita. "Asmy" ta ji ya kira ta da wani sunan kuma.  Ta buɗe idonta da ƙyar ta kalle shi. Garau da shi kamar babu abin da ya faru. "Salla" ya faɗa a taƙaice, jikinsa duk danshin ruwan alwala, ya fice ya tafi masallaci. Da ƙyar ta tashi, tana daddaga bango, ta shiga ta yi alwala, ta dawo ta yi salla a zaune, ta kwanta. Ganin ba ta tashi da wuri ba, ya sanya shi fara rage aikace-aikacen ɗakin, amma ya ga babu alamar za ta tashi balle ta ɗora girki. Ya matsa kusa da ita ya tashe ta. Ta tashi zaune da ƙyar, kanta kamar ana buga mata guduma. Ya ƙura mata ido ya ga duk ta canza, sai dai ta yi masa kyau a ido sosai, ƙanan kitson kanta, sun dace ba ƙin gashinta, ga hannunta lalle ja da baƙi ya yi mata kyau sosai da sosai. Ta saukko daga kan katifar, ta ɗauki wata roba, ta ɗaukko lemon tsami ta yanka, ta fara matsawa a bakinta. A hankali tashin zuciyar da take ji, ya fara raguwa. Shi dai ya zuba mata ido. Ta gama ta sake ƙoƙarin kwanciya. "Ki ci abinci, ga ƙosai" ya yi maganar yana nuna mata ledar da ke kusa da gas. Ta girgiza masa kai ta nemi guri ta kwanta. "Kin yi mini laifi ki na fushi da ni kuma? Na ce kar ki yi abu kin yi, kuma kina fushi?" Ta kalle shi idonta fal hawaye ta ce "Kuma shi ne sai ka shaƙe ni? Har na yi maka laifin da za ka yi yinƙurin kashe ni, dama ba so na ka ke yi ba" A rikice ya zaro ido ya kalle ta ya ce "Ni? A'a ban shaƙe ki ba. Me yasa zan shaƙe ki kuma? Raina ya ɓaci ne, zuciyata ta kama da wuta, sosai da sosai amma ban shaƙe ki ba. Kamar bacci ma na yi daga lokacin" Idonta fal hawaye ta ce "Bayan ga shaidar faratanka a wuyana" Kamar ya yi kuka ya ce "A'a, kin manta kin yanke mini farce, amma ban taɓa ki ba ma, kalli hannuna" ya yi maganar yana nuna mata yatsun sa. Ya miƙa hannunsa wuyanta, dan ya duba shaidar faratan da ta ce, amma ya ji jikinta zafi rauuu. Sake rikicewa ya yi ya ce "Ma vie. (Rayuwata) tu as de la fièvre ? (Zazzaɓi ki ke yi?" Ya yi maganar a rikice. Ba ta kula shi ba ta kwanta, tana jin yadda jikinta yake ɗaukar zafi, cikin ta yake yamutsawa. Wayarta ya ɗauka ya danna, ya kara a  kunnensa. Da French ya yi magana, ya ajiye wayar a kan mudubi, ya dawo inda take ya ce "Tashi ki saka kaya, na kira Habu" "Sayyid da ba ka kira shi ba, zan warke fa"  "A'a jikin ki ya yi zafi sosai" Ya nemi guri ya zauna a musa da ita, yana ci gaba da kallonta cikin damuwa. ***** Sannu a hankali yake jujjuya wayar hannunsa, yana sake karanta saƙon da ya shigo wayarsa. An shirya tsige shi, daga shugabancin 'yan kasuwa, bisa zargin sa da yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗe, na ƙananan 'yan kasuwa. Tabbas akwai kuɗaɗen wasu a hannunsa, har da wanda kuɗinsu bai kai ba, da zai yi wa ciko ya ba su bashin kaya. Kuma ya tattara kuɗin ya yi order kayan, sai dai sun ƙara wata guda a kan lokacin da yakamata su zo, shima yana ta bibiya ne. Amma ya yi wuri a ce an ɗauki wannan matakin, duk da ba yau ya saba yi wa ƙananan 'yan kasuwan irin wannan tallafin ba, har ma da manyan, amma ba a duba hakan ba. Fadila ce ta nufo shi, hannuna da ɗan ƙaramin tray, ɗauke da fruit, ta nemi guri ta zauna. Ta ce "Daddy, ga fav ɗin ka, banana, ga kuma smoothie na yi maka, na ga kamar a gajiye ka ke" Ya yi murmushin yaƙe ya karɓa ya ce "Na gode sosai da babyna" Jiki a sanyaye ta ce "Daddy" ya kalle ta ya ce "Na'am" "Me yake faruwa ne?" Ya ce "A ina?" "Damuwa ce a fuskarka, dan Allah gaya mini, meyafaru?" Ya yi murmushi ya ce "Tsabar gajiya ce kawai, kin san yanayin harkokin namu, babu hutu" Fadila ta riƙo hannunsa ta ce "Na san wataƙila har da damuwar kayan nan, da suma suka yi delay, amma dan Allah ka yi haƙuri ka daina damuwa, yadda wancan suka kuɓuta, wannan ma da yardar Allah za su tsira. Kar ka damar mini kanka dan Allah" Maganganun nata sun ɗan ba shi ƙwarin gwiwa, shi bai damu da batun tsige shi daga shugabancin ba, shi haƙƙoƙin mutane da suke kansa, su ne suka dame shi. Yana jin daɗin tattauna matsalolin sa da Fadila. Duk da ba ta kai uwargidan sa shekaru ba, amma yau shekara bakwai da auren Fadila, ta tattara duk ta tsane shi, tana ganin ya ci amanarta, sun yi wahala tare ya ƙaro aure. Duk da duk wani abu na jin daɗi na hakkinta yana sauke mata. Ko ya gaya mata damuwarsa, sai dai ta taɓe baki kawai ta ce Allah ya kyauta, ko ma ta ce masa alhakinta ne. Fadila kuwa ko sun samu saɓani, da ya shiga damuwa, take ruɗewa har sai ya samu mafita, sai dai a wannan karon, ba zai iya gaya mata ba, saboda ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba ita ma. **** "Husnah" ta buɗe idonta ta kalle shi, lokacin agogon ɗakin ya nuna ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe. "Tashi ki saka kaya, ga Habu can ya zo, za mu je a duba ki" "Na ce ka daina gaya musu, mu daina saka su ɗawainiya" "Tashi ki daina yi mini jayayya" ya yi maganar, yana tsuke fuska. Ta tashi da ƙyat, ya taimaka mata ta saka kaya, ta saka hijjabi, a harabar gidan suka tarar da Habu. Ya yi mata sannu suka fice. Tun da ya kira Habu ya sanar masa, dama da adaidaita sahu ya zo. Wani ƙaramin asibiti suka je. Buzu yana tare da Nana, Habu ya yi ta shiga yana fita. Ya sayo kati aka duba ta, aka ba ta gwaje-gwaje. Sun ɗan jima a gurin ɗaukar jinin, ta gaji da zaman, ta zame tana ƙoƙarin kwanciya a gurin, amma ya riƙo ta tsam a jikinsa. Suka koma gaban likita da sakamakon, ya duba ya kalli Nana ya ce "Yaushe rabon ki da Al'ada?" Tamkar ya sokawa Sayyid mashi, ji ya yi ina ruwansa da zai yi mata wannan tambayar? Amma ya dake bai yi magana ba. Nana ta gaya masa, ya ce "Ok, to akwai ciki ne, sai kuma malaria++ bai kamata a ce, ga juna biyu ba kuma ga malaria ki na fama ba. A kula sosai. Zan rubuta ruwa da allurai a saka miki, za ki ɗan ji ƙwarin jikin ki in sha Allah" Ya yi rubuce-rubuce ya basu, Sayyid ya karɓa suka fito. Ya miƙa wa Habu katin, aka nuna musu inda za su kai Nana. Habu ya kalle shi ya yi masa magana da yaren su, ya cewa Habu "Tsaya" ya saka hannu a aljihunsa ya ɗaukko kuɗi ya ba wa Habu" Habu ya kalli kuɗin ya kalle shi, ya ce "Da can kuɗin yi wa Nana amfani da su. Wani ma'aikaci ne, ya shigo ward ɗin zai sanyawa Nana cannular. Nana ta miƙa masa hannun, ya kai hannu zai kama ya saka mata Buzu ya riƙe hannun Nana. Ma'aikacin ya ce "Allurai zan yi mata, zan saka mata cannula ne" ya yi shiru ya ƙi magana. Nana ta kalli yadda launin idonsa ya canza. A ranta ta ce "Allah ya yaye maka wannan azabar kishin Sayyid" Habu ya yi gyaran murya, ya "Ka yi haƙuri, a saka mata, ka ga tana shan wahala sosai. Ya yi mursisi, ya murtuke fuska, ya riƙe hannunta gam, ya ƙi saki. Sai da Habu ya zauna ya din ga yi masa bayani da yarensu, cikin tattausar murya. Ƙarshe ma'aikacin gefe ya koma, ya zubawa sarautar Allah ido. Tamkar gunki ya yi gum, ya ƙi motsi kuma ya ƙi magana. "Ni idan ba zai yarda a saka mini ba, dan Allah ku mayar da ni gida, na je na kwanta na gaji" ta yi maganar a raunane, cikin yanayin rashin lafiya. Da ƙyar ya saki hannun Nana, sai dai ya kawar da kansa gefe, saboda yadda zuciyarsa ke tafasa da ganin ya kama hannun Nana ya saka mata ruwa. Har huɗu su na Asibiti, sai dai ta ji dadin jikinta, zazzaɓin ya sauka. Aka gama saka mata ruwan, sannan suka tafi gida. Ba ya jin nauyi ko kunyar Habu, haka yake rungume da Nana yana shafa ta, kamar zai lashe ta ya mayar da ita cikin sa. Suka koma gida, Nana ta samu ruwa ta yi wanka, ta saka kankanar da ya saya mata a gaba, ta din ga sha, saboda itakaɗai ce ta ji ta yi mata daɗi. Suna harabar gidan, Habu yana yi masa magana, sai ga babar su Yusra ta ƙaraso. "Kai mai gadi, ina ka tafi baka yi wa kowa bayani ba? Zamu kai Siyama wankin ƙonuwar da ta yi, amma ka yi tafiyarka yawon ka?" Habu ya ce "Ki yi haƙuri Hajiya, mai ɗakin nasa ce babu lafiya, ba a nuste yake ba, hankali tashe mu ka tafi Asibiti ki yi haƙuri dan Allah" "Ni ma tawa 'yar babu lafiya ai, ba sai ya yi bayani ba. Tun da idan zai je wani guri yana rubutawa Jamil ba, sai Jamil ne ya buɗe mana muka tafi, ƙonuwar na ta jini" Habu ya sake cewa "Ki yi haƙuri dai dan Allah" Ko ɗaga kai bai yi ya kalle ta ba, balle ya kula ta, ko ta saka ran zai ba ta haƙuri, ya bar ta ita da Habu. "Sannu" Ta jinjina kai ta ce "Sayyid da ka sani ka ba ta haƙuri, ba na son wannan faɗan da ake yi maka" "Ya jikin? Kin daina jin zazzaɓin?" "Amma ka san mun yi laifi, bai kamata mu tafi ba su sani ba" "Da suka buɗe ƙofar sun mutu ne?" Nana ta sauke numfashi ta ce "Aishikenan, idan ka janyo aka kore mu, ka nemo mana inda za mu zauna ai" ya yi shiru, bai kuma cewa komai ba. Daga bisani ya ce "Me za ki ci?" "Ba komai, ba na son komai, kankanar nan ta ishe ni". A hankali ya kai hannunsa, ya shafa gashin ta, ya saki murmushi ya ce "Kitson nan ya yi kyau sosai, ya dawo da hannunsa kan hannunta, ya jujjuya hannun, ya kai bakinsa ya sumbata ya ce "Kin yi mini kyau" Ta kalle shi galala ta ce "A hakan da na fita hayyacina. Tun jiya na so ka kalla ka yaba ba, ka share ni ka yi ta yi mink faɗa" "Idan na ce kar a yi, to a bari ne kawai, ba na so. Me yasa zan ce kar ki je guri ki je?" Jiki a sanyaye ta ce "Na san na yi laifi, ka yi haƙuri. Za su ga kamar wulaƙanci ne, sun gaya mini abu na tashin hankali, amma na kasa yi musu jaje. Sayyid ban ji ka ce komai ba, a kan abin da aka ce" "Wanne?" "Da likitan ya ce... Sai kuma ta yi shiru. "Ya ce me?" "Ina da juna biyu, tsoro nake ji" ta yi maganar tsoron na bayyana ƙarara a kan fuskarta. "Tsoron me?" Abin da ta so furtawa daban, amma ta kauce faɗar hakan, kar ta tayar masa da hankali ta ce "Ban ga ka yi murna da hakan ba" Ya gyara zamansa ya dubi Nana a tsanake ya ce "Wata irin wutar zafin, ganin wani ya taɓa ki ne, take ci mini zuciya. Amma wallahi ina cikin murna zamu ƙara yawa, nima Ahalina zai cika, ki haifi namiji mai kama da ni. Ko kuma mace mai kama da ke" Murmushin dole Nana ta yi, ba dan ya kai zuciyarta ba ta ci gaba da tauna kankanar bakinta a hankali. ***** Yanayin yadda aka banko ƙofar gidan, sai da Baba ya tsorata kamar ya zura da gudu. Ya dai tsaya ya ce "Kai wani mara hankalin ne ya ke yi mana wannan banzan bugun haka?" Bai yi magana ba, sai ganinsa Baba ya a tsakiyar gida, tamkar ya faɗo daga sama. "Uban me ya kawo ka gidana?" "Gidan Ubana ne" ya faɗa yana ɗan rarraba ido yana kallon gidan. "To uban me ya dawo da kai? Nan ka saka 'yan sanda suka din ga yi mini sintiri a gida, ka kai Gaddafi ƙara, kuma ka gudu, da yake kai duk inda ka tsuguna babu alkhairi tsiya ce take biyo baya. Ka bar mini gida kafin 'yan sanda su zo neman ka" "Ni fa ban kashe kowa ba wanda suka yi abin ma an kama su, kawai ka wani din ga kora ta, idan na gama abin da nake yi da kaina zan bar maka gidan ai. Ka yi ta wani gidanka kamar wani gidan arziki" Baba ya ce "Tun da ba na arziki ba ne ba, zo ka fice" Imarana ya ce "Wallahi ba zan tafi ba. Ina Nana? Ke Nana" Nasiru ne ya yi sallama a gidan, hannunsa riƙe da ledar kayan miya, yana ganin Imarana ya tafi da gudu ya rungume shi. Imarana ya ce "Nasiru, na ga kana nema ka kamo ni a tsawo. Wai ina Nana ne?" Baba yana ƙiftawa Nasiru ido, amma tuni ya kwatsa wa Nasiru bayani. "Ai an yi mata aure" Turus Imrana ya yi ya ce "Kamar yaya? Uban waye ya yi mata auren ban sani ba?" "Ni ne nan ubanta, idan kuma kai ka haife ta da sai an sanar da kai sai na ji" "Kut.. aure fa, wa ka aura mata, ina fatan ba wannan ajawon bane Salisu yake ko wa?" "Ba Saleh ba ne, wani Buzu ne mai gadi" Nasiru ya sake ba wa Imrana amsa. Kai tsaye ya ƙundumo ashariya ya ce "Wane irin Buzu kuma? Kai ina ne gidan da aka kai ta?" Baba ya ce "Wallahi ka taka ka je gidanta ban yafe maka ba. Kar ka kuskura ka je ka yi mata hauka ka kashe mata aure" "Wallahi sai na je, dama kula ka ke da ni, shi ne za ka yi mini Allah ya isa ta kama ni, amma tun da ni nake kula da kaina ba za ta kama ni ba. Kai Nasiru wuce mu je ka raka ni" Baba ya ce "Nasiru idan ka raka shi, sai na yi maka dukan tsiya" "Kai mu je zan baka dubu biyu" Nasiru ya waiga yana kallon Baba, ga batun kuɗi ya ji, ya maze ya bi Imarana suka fice, Baba na ƙwala masa kira amma ya fifita dubu biyu a kan kiran Baba. Su na tafe a hanya, Nasiru yana ba wa Imarana labarin, abin da ya faru da yadda aka yi auren Nana. Ba ƙaramin fusata Imarana ya yi ba. Mussaman da ya gaya masa, gadi Buzu yake yi. "Uban me mai gadin zai tsinana mata,  Allah na tuba mu dai ba mu yi dacen uba ba wallahi  mu dai kawai ya kawo mu Duniya yana neman maraba da mu." Sayyid na zaune yana shan shayi, a harabar gidan ya ji an taɓa gate. Ya rufe fuskar sa da sauri, ya tashi ya je ya buɗe, ya tsaya yana kallon Imran, saboda tsananin kamnninsa da Nana. Babu jiran komai, Imrana ya ƙarasa hankaɗa ƙofar ya shiga, Nasiru ya bi bayansa. Nasiru ya ce "Ga mijin Nanan nan" ya yi maganar yana nu na masa Buzu. Imran ya ƙare masa kallo, ya ce "Ikon Allah, kai ka auri Nana? Tana ina?" Sayyid ya yi shiru yana kallon Imrana. "Malam magana nake yi, ko kurma ne? Ina take?" Nasiru ya ce "Kamar fa ba ya magana, amma Nanan tana cikin ɗakin nan" "Dan Allah ji wulaƙanci, ɗakin mai gadi, ba ta samun arzikin a ajiye ta a gida ba ma, sai ɗakin daga shi waje, koma mene ne ya zo ya afka mata" Nana tun tana banɗaki take jiwo, kamar muryar Imran, amma ta kawar da tunanin, a ganinta mai zai kawo shi yanzu. Ta fito daga banɗakin ya shigo, Nana ta zabura ta ce "Imrana" sai kuma ta tsaya da tuna halin Buzu a kan kishin tsiya. "Ke ashe ba ki da hankali? Ki ka zauna aka aura miki mutum kawai ki ka biyo shi yawon gadi? Gidan babanki ba mamora gidan miji ma haka? To wallahi sai kin bar gidan nan, sako hijjabinki mu tafi" "Imarana mu tafi mu je ina?" "Ko ma ina ne. Amma wallahi ba za ki zauna a gurin nan ba. Haka zamu zauna babu ci gaba?" "To ka zauna mana, ka sha ruwa ka ci abinci, sai mu yi magana. Mama ma ta yi mini aike su Adda Saude sun zo... "Dalla rufe mini baki, ina ruwana da wata? Addar wofi da can ba su zo ba sai yanzu. Ki ɗaukko hijjabinki mu tafi daga nan har human rights, na san biyayya kawai ki ka yi wa Baba ki ka auri mutumin nan, tun da dama ke ba sanin ciwon kanki ki ka yi ba" Nana ta yi shiru, tana kallon in da Sayyid yake tsaye, ya tsare ta da ido. Tsoro take ji kar Sayyid ya yi wani abun da zai tunzura Imran, dan ta san ko zai kashe shi ba zai yi shiru ba. "Imran na gode da ziyara, da kuma soyayyar da ka ke nuna mini. Amma ka yi haƙuri ina son aurena" Wani irin takaici ya kama Imran ya ce "Nana me za ki zauna ki yi a shago, ɗakin nan meye marabarsa da shago? Na san zaman gidanm ne ba kya so, ba can za ki koma ba. Harkoki sun fara buɗe mini, karatu zan mayar da ke, kyakyawar rayuwa nake so na ga kin yi" Ta sake kallon Buzu, da ya zubo mata idanunsa, Imran ya waiwaya ya ga abin da take kallo. Sayyid ya shigo cikin takunsa na kamala da nutsuwa. Ya sauke takunkumin fuskar sa, ya sakar wa Imrana murmushi, ya ce "Kun yi kama sosai, da alama ku na da alaƙa sosai" ya yi maganar yana miƙa wa Imran hannu su gaisa. "Ba zan gaisa da kai ba, ƙanwata za ka sakar mini, Nasiru ya gaya mini duk wani abin da ya sani. Ni ban ji na gamsu da wannan auren ba ko kaɗan. Ya za a yi sama ta ka a aura miki mutumin da ba ƙabilarmu ba, babu wani dogon bincike. Ni jikina yana bani wani abu, ni ban yarda da auren nan ba gaskiya." "Nima na fuskanci akwai sharuɗɗan da ban cika ba, aka yi wannan auren. Amma ko me za a yi mini, ba zan iya rabuwa da ita ba, tana ɗauke da ruhina a jikinta. Idan ka raba ni da ita, ni ya zan yi? Zan kula da ita, ka daina raina inda Allah ya ƙaddara zamana da ita, ba ka san gobe ba" Imrana ji yake kamar ya mangare Buzun nan ya huta, haka kurum ya ji bai yi masa ba. Kuma ya san wannan kyawun ne ya ruɗi Nana, har take cewa ita ba za ta rabu da shi ba. Ya sake kallon Nana ya ce "Kin zaɓi zama ko Nana?" Idonta fal hawaye ta ce "Ka yi haƙuri Imran, Allah ne ya haɗa ƙaddarorinmu, ba komai zan iya yi maka bayani ba, amma ina son aurena. Sayyid na buƙata ta a rayuwarsa". Imran ya haɗiye wata irin ƙwallar takaici. Ya zura hannu a jakarsa, ya ƙirgo kuɗi, ya tako gaban Nana, ya kamo hannunta ya saka mata ya ce "Ga wannan babu yawa, cikin abin da nake tarawa ne, domin na dawo gida na inganta rayuwar ki. Dama Saboda ke na dawo, daga nan ko gida ba zan kma ba, zan tafi inda na fito. Kai kuma tun da ta zaɓi zama da kai, idan ka ci amana na bar ka da mai hudowar rana da faɗuwar ta" Ras Sayyid ya ji gabansa ya faɗi, ya ji maganar Imran ta yi masa nauyi da yawa. Ya kalli Nasiru ya ce "Mu tafi" Nana da tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Imrana ba zaɓarsa na yi a kan ka ba.... "Shhh ba sai kin yi mini bayani ba ai, tun da ki na farin ciki da auren ki Alhamdilillah" ya juya zai fita ta sake cewa "Ka bani lambar wayar ka, da zan din ga kiran ka a waya" bai waiwayo ba ya girgiza kai, ya ce "Babu buƙata" Daga bayansa, yanayin yadda ya kai hannu fuskarsa, Ya sanya Nana gane Imran kuka yake yi. Sakin kuɗin hannunta ta yi a ƙasa ta durƙushe a gurin ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ita ma. Ayshercool 08081012143 43 Cikin matsananciyar damuwa, ya durƙusa a gabanta, amma ya rasa ta ina zai fara, ga shi ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba. Awanni kaɗan kenan da dawowar su daga Asibiti. "Ba ki da lafiya fa, ki daina kuka" Ba ta saurare shi, ba sai da ta yi mai isar ta. Ya zauna kawai ya zuba mata ido. Sai da ta yi ta gama, ta yi shiru dan kanta, sai dai ba ta iya ce masa komai ba. Ya bata magungunanta na dare ta sha, cikin sanyin jiki ya fara magana. "Duk da ban san girman alaƙar da take tsakanin ki da wands ya zo ba, amma alamu sun nuna dan uwanki ne, da yake son ki sosai. Ba zan iya jurar ganin hawayen ki ba, a dalilina. Idan zuciyar ki za ta samu nutsuwa rabuwar mu, shikenan dan Allah kar ki zauna dani alhalin za ki cutu" Nana ta gyara zamanta sannan ta numfasa ta ce "Ka yi haƙuri da halin ƙuruciya da muka nuna maka. Da zan bijirewa auren nan, da ba zan yadda na tare da kai ba. Da can ban guji auren ba sai yanzu, wannan cikin na jikina na yi yaya da shi?. Duk da na tashi a gaban mahaifina, tun mu na yara ƙanana, mahaifiyarmu ta bar gidanmu, babu wani abu da nake kallo na ji daɗi sama da Imrana. Ba ya son na yi kuka, duk da ina da yawan kuka tun ina yarinya n wasu lokutan har dukana yake yi, saboda na daina kuka ba ya so" ta faɗa tana murmushi tana share hawayen ta. Ta ci gaba da cewa "Rayuwarmu akwai faɗi tashi da kalubale da yawa, gidan yawa ga rashin uwa. Ba ni da ƙarfi sai faɗa a yi ta dukana yana tare mini. Sai ya gama tare mini mu koma gefe ya zane ni yana ce mini nusara. Yana da zafi, ana ganin ba shi da kunya, amma wasu abubuwan a kan gaskiya yake. Zaka ji maganganun nawa wani iri, kamar ina yin su ba a muhallinsu ba. Amma na sha wahala ne, ya yi juriya a kan abubuwa da dama Saboda ni. Mutum ne mai taurin kai da kasada, amma tun da ya zubar da hawaye yau, na san abin da yake ji a zuciyarsa ba ƙarami ba ne ba. Tabbas yana da buri a kaina, yana cewa in sha Allah sai mun zama abin alfahari ga ahalimu, ban san iya abin da ya yi yinƙurin yi, da shirin sa a kan rayuwar mu ba, amma abubuwa suka canza. Ka yi haƙuri da abubuwan da mu ka yi maka Sayyid, kai ma ka na da muhimmanci a rayuwata, ka yi mana uzuri dan Allah" Ya numfasa ya ce "Ba komai, daina kuka. Ni ban sani ba ma ko ina da iyaye ko ba ni da su" "Ka na da su ma in sha Allah, kuma za ku haɗu cikin aminci da yardar Allah." "Allah ya sa" Nana ta ce "Me yasa Imran ba ka ji haushin zuwansa ba, shi ba ka hana shi shigowa ba?" "A jikina na ji mutum ne mai muhimmanci a gurin ki, kuma ban ji zuciyata na tafasa da ya shigo ba" Ta gyaɗa kai kawai, ba ta sake magana ba. **** Sagir ne zaune tare da Shukura, Haidar yana ta wasansa a gefe, ya kwantar da murya ya ce "Wai dan Allah yaushe za ki koma gida ne? Na gaji da zama nikaɗai wallahi" Ta kwaɓe fuska ta ce "Ba na jin daɗi komai ne. Dan Allah tambayar ka nake son yi" Ya gyara zaman sa ya ce "Ina jin ki" "Lokacin da aka yi mini tiyata, an baka ɗan da rai ka gan shi?" "Dan Allah ki daina wannan maganar, ki na sane da jininki ya hau, managing ɗin sa ake yi" Tuni ta fara hawaye ta ce "Amma ka san ban gan shi ba, sai hotonsa kawai na gani" Ya ce "To ai kin san ba na nan aka yi tiyatar, sai da safe na zo, na lokacin an saka jaririn a kwalba, kuma dai koma mene ne ya rasu, dan Allah ki lallaɓa Daddy ki koma na gaji da zaman nan" Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah zan yi masa magana, zan dawo ka yi haƙuri" Ta lallaɓa shi da ƙyar su ka yi sallama. Yana tafiya ta tafi sashin Alhaji Zailani. Ta tarar da shi su na hira da Mummy. Hajiya Amina ta kalle ta ta ce "Ahh har Sagir ɗin ya tafi ne?" Ta jinjina kai ta nemi guri ta zauna. Alhaji Zailani ya ce " 'Yar auta ya ƙarfin jikin naki. Duk da na ga Alhamdilillah jiki ya yi kyau, sai dai kin rame da yawa". Ta yi murmushin da a iya laɓɓanta ya tsaya, saboda yadda take jin wata irin tsanar mahaifinta na kama ta. Duk da tana iya kokarin tabattar wa kanta, mafarki ba gaskiya ba ne ba, amma zuciyarta ta kasa ɗauka. "Jiki Alhamdilillah " ta yi maganar tana mayar da hankalinta, kan Hajiya Amina. "Mummy, wai dan Allah lokacin da aka yi mini tiyata, da a ka fito da ni, an baki babyn a hannunki kin gani" Hajiya Amina ta ce "Sau nawa zan yi miki bayani Shukura, ke kaɗai aka fito da ke, ba a bani jaririn ba. Doctor Sharif ya ce na ɗan jira, jaririn ne ake fama, ko ba bu wadatacciyar iska ko me, oho maganganun su na likitoci. Na dawo ɗaki gurin ki, ya shigo ya ce mini, an kai babyn Nursery, da safe na je na gan shi" Alhaji Zailani ya yi gyaran murya ya ce "Shukura, duk wani abu da za ki yi, abin da ya faru ya faru, ba za ki yi jayayya da ikon Allah ba. Kamata ya yi ki gode wa Allah, da ya baki lafiya. In dai da rai da lafiya, Allah zai baki wani mai amfani. Yanzu lafiyar ki muke buƙata, wannan damuwar ba ta dace da ke ba. Kin rasa babynki, nima ba zan so rasa tawa babyn ba, Please ki yi tawakalli na san kin sha wahala a kan cikin nan, amma ki yi haƙuri" Shiru Shukura ta yi, zuciyar ta fal wasi-wasi. Ta ƙara ƙaimi gurin yaƙar mummunan tunanin da yake ta yi mata yawo a zuciya, ta hanyar kawar da batun mafarki da ta san ba gaskiya ba ne ba. Duk mahaifiyarsu ta rasu, amma ba su tashi da zafin maraici ba, Alhaji Zailani ya yi aiki tuƙuru a kan rayuwar su, Hajiya Amina ma kuma ba ta taɓa yi musu mugunta ba, ta riƙe su da gaske tamkar 'ya'yanta. Saboda haka take ganin tamkar zuciyarta ba ta yi mata adalci ba. Amma fafur take jin ƙiyayyar mahaifin nata a cikin zuciyarta, ta kuma kasa yarda da cewa ɗan ta mutuwa ya yi ta haƙiƙa, ba wani abin ne ya faru ba. **** Kwana biyu Nana ta samu sauƙin jikinta, jikinta ya ɗan yi ƙwari babu zazzaɓin. Sai dai abinci ne ba ya ciwuwa ta daɗin rai. Ta saka Sayyida a gaba, a kan lallai sai ta yi wa gashinsa kitso, ta gaji da ganin kan a haka. Yana kwance a kan cinyarta, ta saka kibiya tana tsaga gashin nasa. Ta ce "Sayyid kishi nake da gashin nan naka, gaskiya aske shi zan yi, ya za ayi ina matarka a ce ka fi ni gashi?" Ya yi dariya ya ci gaba da kallon da yake yi da wayarta. Ta yi guda biyu ta ce "To gyara, a yi na can ɓangaren" Ya girgiza kai ya ce "Ki ƙyale ni" Ta ce "A'a sai an ƙarasa" Fafur ya ƙi gyarawa, ya ce shi fa kitson da zafi. "Dan Allah ka yi haƙuri mu ƙarasa, haba Shugaba ba ka ga yadda kitson nan ya yi kyau ba. Yauwwa nawan" ya ɗago kansa ya harare ta. Ta sakar masa murmushi tana lumshe masa ido. Ya gyara kwanciyar, ta ci gaba da kitsa gashin nasa, mai matuƙar santsi da laushi. Babu tsammanni aka bankaɗo labulen ɗakin, sai da Nana ta razana, a hankali ya ɗaga kai ya kalli ƙofar. Siyama suka gani a tsaye, Kunya ta kama Nana,yanayin da ta tarar da su. Shi kansa dogon wando kawai a jikinsa, ya ɗora kansa a kan cinyar Nana, tana yi masa kitso. "Amm dama Mami ce ta ce na zo na duba, ko Yusra ta zo ba mu ganta ba da ma. Amma shikenan" Ta saki labulen a hankali ta ja da baya, saboda yadda jikinta ya yi sanyi. Kamar babu abin da ya faru, ya ci gaba da kallon wayarsa. " Ya jikinki ya yi sanyi? Me ya faru?" "Ba komai" ta furta a hankali. Ya juyo sosai ya kalle ta, sai kuma ya fasa maganar da ya yi niyya, ya sake gyara kwanciyar sa. Dannewa kawai Nana ta yi, amma sai da ta ji tamkar ta ɗura wa Siyama ashar, saboda kawai su na masu gadi, ya ba ta damar ta shigo musu ɗaki, ba bu izini. Danne fushin ta ta yi, saboda kar ta saka shi a damuwa, amma tana ji a ranta wataran sai ta zagi Siyama. Da yamma, Nana ta yi kwalliya cikin doguwar rigar material mai taushi, da hula. Ta fesa turare sannan ta ɗora girkin dare, sannan ta kunna turaren wuta a ɗakin. Neman guri ya yi ya zauna a ɗakin ya ƙi fita, sai aikin kallonta kawai da yake yi. "Shugaba, ba zaka fita shan shayin ba ne?" Ya yi dariya ya ce "Kin yi kyau sosai da sosai, ba zan fita ba" Ta sake cewa "Ka ga yadda ka yi kyau da kitson nan kuwa? Zo ka ga" Ya yinƙura ya taso, ya zo ya tsaya a gaban ta, ta nuna masa mudubi ta ce "Kalli yadda ka yi kyau fa" Ya shafa kansa ya ce "Na zama kamar mace" Ta yi dariya ta ce "Ka yi mini kyau sosai a haka, dama nikaɗai ya dace na ga ka yi kyau". Ya sunkuyo ya yi mata kiss a goshinta. Cikin dariya ta ce "Ni idan ka na yi mini wannan abun, kunya ka ke bani" Ya ce "Wanne?" "Ko wanne" ya ƙara tsare ta da ido, da sai da ya sanya ta sunkuyar da kanta saboda kunya. "To matsa na wuce" "A'a kirana fa ki ka yi" Ya yi maganar yana haɗa bakinsa da nata. Bayan ya cika ta, ta sunkuyar da kanta tana jin kunya. Ji ta yi jikinta ya fara sanyi, ƙirjinta yana bugawa, ta kalle shi ta ga fara'ar fuskarsa ta kau, ya haɗe rai. A tsorace ta ɗan ja jikinta, tana tunanin me ta yi masa. Tana kallon mudubin ta ga duhu ya gauraye ɗakin sai iya wannan tsohon ta iya gani a cikin mudubin a tsaye, sai dai a wannan karon ci yake yi da wuta. Tattara nutsuwarta ta yi, ta fara Addu'a a cikin zuciyarta, ta waiwayo ta kalle shi. Ta ga fuskar sa ɗauke da murmushi. Ya miƙo hannunsa zai taɓa ta, ta riƙe hannunsa, ta yi yinƙurin kallon idonsa amma ta kasa, ta ji tamkar zuciyarta za ta buɗe. "Waye kai?" Ya amsa da "Mijinki mana" Ta yi murmushi ta ce "Ba Sayyid ba ne? Ai na riga na ganka. Me yasa ka zaɓi muzgunawa rayuwata ne? Da ina zargin ko Ƙaisar ne, amma na fara fahimtar kai daban shi daban. Mece ce manufarka a kaina? Me ka ke buƙata?" Wata irin dariya ya saki, ya ce "Har kin yi ƙwarin da ki ka daina razana da ganina kenan. Haka nake so fansa zan ɗauka, yanzu ne lokacin da ya dace na ɗauki fansata" "Wani laifi na aikata maka da ka ke iƙrarin ɗaukar fansa a kaina" Ba tare da tsammani ba, ya shaƙe ta, ya ɗaga ta ya yi jifa da ita, ta bugu da jikin wardrobe ta faɗi. Ɗakin ya gauraye da matsanancin duhu, ta riƙe wuyanta tana numfarfashi cikin yanayi mai kama da ɗimuwa da kuma suma. Ta daɗe a haka kan ta ji kamar daga sama muryar Sayyid. "Rayuwata bacci kuma daf da magariba a ƙasa? Ga abincinki ya fara ƙonewa" Nana ta ɗaga kai ta kalle shi suka haɗa ido, amma ba ta ji komai ba. Ta tashi da ƙyar ta ji mararta ta ƙulle, ga hannunta da ta bugu. Amma ta daure ta kashe gas din, ta shiga yin alwala. Abubuwa da dama su ka zo zuciyarta, tabbas wannan sabon ƙalubale ne a gare ta. Muddin zai cigaba da fita daga hayyacinsa yana yi mata haka, to tana tsoron wataran ya yi mata illa. Haka kurum yake jin sa cikin farin ciki, sai dai lokaci ɗaya ya lura ita ba ta cikin walwala. Su na cin abinci, ya ɗan shafa cinyarta. Ta farga ta kalle shi. Ya ce "Ba kya cin abinci mene ne?" Ta yi murmushi ta ce "Lafiya ƙalau, Abincin ne ba na so" Cikin damuwa ya ce "Na sayo miki buredi za ki ci? Ko ƙos" "A'a zan ci wannan ɗin" da ƙyar ta tilasta kanta, ta ci. Yanayin yadda yake ta bin ta da ido, ya sanya ta san akwai abin da yake so, sai dai a ɗan tsorace take. Haka ta ci gaba da addu'oi da neman ɗaukin Ubangiji. Duk da haryanzu tana jin nauyin sa, amma ta shirya cikin kayan baccinta na gwanjo, da Ummi ta ba ta ta shafa turare. Sai dai zuciyarta gaba ɗaya a tsinke take. Kwanciyarta babu jimawa, ya zo ya kwanta shi ma. "Rayuwata duk kin rage walwala" Ta ɗan ja numfashi ta ce "'yan kwanakin nan, baki ya buɗe, Ubangiji Allah ya ɗorar da lafiya" "Amin ma vie. Ina jin daɗin haka sosai" "Saura kuma, Ubangiji Allah ya sanya ka tuna waye kai. Hankalina zai fi kwanciya" Ya ɗan yi shiru ya ce "Ina wannan ƙoƙarin, ji nake kamar abin ya fi ƙarfina. Amma ko da nan gaba, idan ban tuna waye ni ba, ki nuna wa ɗa na su Habu a matsayin dangina, tun da ku kaɗai na sani" Ya yi maganar muryarsa na rawa. "Shikenan mu bar wannan maganar." Ya yi shiru bai kuma magana ba. "Sayyid fushi ka yi ne?" "A'a ban yi fushi ba" Ta din ga shafa kansa zuwa bayansa, sai dai daga ƙoƙarin rarrashin sa, ya fara ƙoƙarin zarcewa. A hankali ta fara jin wannan ƙamshin turaren, yana ratsa kafofin hancinta. "Sayyid ba ka jin wani ƙamshin turare?" "Ina ji a jikinki" "A'a ji nake kamar ba a ɗakinmu muke ba" Ya yi dariya, ya cika ta ya ce "Ba sai kin yi mini wayo ba, na ƙyale ki" Ya ɗan ja jikisa ya koma gefe, yana ajiyar zuciya. Ta ɗora hannunta a kan nasa ta ce "Ba wayo zan yi maka ba, ai ka san ba na gudun ka." "Kar ki damu, ki yi bacci" ya ɗora kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta. ***** Shukura ji take yi, tamkar za ta haukace, sai kokawa take da sashe daban-daban na ƙwaƙwalwarta, domin samawa kanta nutsuwa. Gari ya tsit amma ita sai kaiwa take yi tana komowa a cikin ɗaki, tamkar mai jiran saƙon wani abun. Ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta yi tagumi. Ta sake tashi tsaye, ta tafi bakin taga ta tsaya tana kallon waje. Ta ƙudurce a ranta, sai ta tuntuɓi doctor Sharif ta ji mene ne ya kashe mata ɗa? Haryanzu ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Alhaji Fatuhu kuwa, ƙarfin hali kawai yake yi, ji yake tamkar an daddane rayuwarsa da jikinaa gaba ɗaya. Babu abin da yake yi masa daɗi, ya daina jin daɗin komai, tamkar ya fasa ihu ko zai ji sanyi a ransa. Ƙarfin hali ya yi gurin sanya Fadila farin ciki, har ya samu ta yi bacci, tun da ta yi bacci ya raba ta da jikinsa a hankali, ya tashi zaune ya rafka tagumi ya din ga jin tamkar ana buga masa abu mai nauyi a kansa. Ya shiga banɗaki ya yi wanka, ya yi alwala ya zo ya tayar da salla, amma tunani da wasi-wasi ya mamaye shi, ya kasa nutsuwa a cikin salla. Ya din rafkanuwa. Ya din ga sallamewa yana sake tayarwa har ya gaji ya nemi guri ya zauna. Tunanin yadda kayansa za su iso, a sallami mutane ya ƙara mamaye kansa, ya rasa bakin zaren matsalar baki ɗaya, haka ya zauna har aka yi kiran sallar asuba. **** Tari ne ya sarƙe Nana, ta tashi ta ji kamar wadda ta ƙware tana numfashi sama-sama. Ta shafa ta ji Sayyid ba ya gurin, ta ji an kama hannunta an bata kofi, ta karɓa ta shanye ruwan, ta ajiye kofin saboda yadda wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Ƙaisar ta gani a tsaye yana kallonta, jikinsa duk a ƙone, bai yi mata magana ba, ya danƙi wuyanta ya zuba mata wani abu mai kama da hayaƙi a cikin bakinta. A take ta ji cikinta ya hautsuna, mararta ta ƙulle, ta kalle shi a razane ta ce "Ƙaisar me ka yi mini?". "Cikin jikinki ba shi da amfani, dole ya bar jikin ki" "Saboda me, ina ruwanka da cikina?" "Saboda ba zan ƙarar da rayuwata a matsayin bawa ga zuriyar ku ba, ki na wahalar da ni." Kafin ta yi magana, ta ji tamkar ana fizgar naman cikin mararta, ta yinƙura ta tashi a gigice. "Subhnallah, Sayyid, Sayyid" ta kira sunansa a wahale. Daga banɗaki ya fito a tsorace, ya nufo ta. Ta miƙa masa hannu, ya riƙe ta. "Kai ni banɗaki" ta faɗa tana rintse idanunta. Ya kamata ta miƙe, jini ya fara biyo ƙafafuwanta, ya kai ta banɗaki. Su na shiga ta durƙusa a kan gwiwoyinta, ta saka hannu ɗaya ta rirriƙe ƙafarsa tana girgiza kanta cikin matsanancin ciwo. Da ta ja numfashi da ƙarfi, sai ta ji jinin yana zuba da yawa. Ya rasa yadda zai yi, ga baki ya rufe ya kasa magana. Can ta yi wani irin nishi, ta ƙara rirriƙe ƙafarsa da ƙarfi, sai ga gudan jini ya faɗo. A hankali ta din ga samun releif, ta jinginar da kanta a jikin ƙafarsa ta kasa motsi. Jin yadda ƙarnin jinin ya ishe ta, ya sanya ta motsa a hankali, ta yinƙura ya kama ta, ta tashi tsaye. "Ka canza kaya ka yi sallar, bari na wanke jikina" Ya motsa baki, amma magana ta gagara, ya dage yana ƙoƙarin yi, amma gumi ya fara tsatstsafo masa. "Ya lafa mini, ka yi salla kar ka makara, zan wanke jikina" da ƙyar ya fita, ta rufe banɗakin ta wanke jikinta, duk da tana jin sauran ciwon kaɗan kaɗan. Ta fito yana salla, ta ɗaura zani, kan ya idar ta goge gurin da ta ɓata, ya idar ya ƙaraso gefen katifar da ta zauna, idanunta har sun faɗa saboda wahala. Ya zauna ya saka ta a gaba, ga magana amma abu ya gagara, ta kwanta a kan cinyarta, ga ciwon buguwar jiya, ga rashin lafiya da ba ta gama warkewa ba, ga kuma wannan matsalar da ta tashi da ita. A hankali yake shafa jikinta, yana ɗan matsa mata, ta ji daɗin hakan sosai da sosai. Wajen ƙarfe bakwai, ta kira Ummi, Ummi ta ɗaga ta ce "Lafiya, kira da sassafe?" "Kira ni kuɗina ba su da yawa" Ummi ta kira ta, ta ce "Lafiya na ji muryarki a haka?" "Ba na jin daɗi ne Ummi, dan Allah tambayar ki zan yi, idan mutum yana da ciki yana period ne?" "Wane irin period kuma? Dama ciki ne da ke? Haba ni fa in ce ranar da ki ka zo na ga alama wallahi. Meyafaru?" "An ce akwai, kuma yau na tashi da ciwon mara ina zubar da jini" "Kai, subhnallah bari na sallami yara, gani nan zuwa gidan naki" Duk da jikinta babu ƙwari, ta tashi ta saka kaya, ta kunna turaren wuta, Saboda a hancinta ba ta daina jin ƙarnin jinin nan ba. Wajen tara da rabi sai ga Ummi. Ummi ta gaishe shi, ya ɗaga mata hannu tare risunar da kansa, ranar farko da Ummi ta gan shi babu rawani, ya sha kitso a kansa jelar ta sauka a kafaɗarsa. Ta ƙarasa inda Nana take cikin kulawa ta ce "Sannu Nana ya jikin?" "Alhamdilillah" "Gaskiya ki zo mu je a yi scanic, mu tafi Asibiti" Nana ta girgiza kai ta ce 'A'a ba sai mun je ba, ni ba na son mu je, a yi ta huda ni" "To Nana lafiyarki ba ta fi komai ba, tashi mu je" Nana ta kalle shi, yadda ya tsare su da ido, ta ce "Sayyid za ta raka ni Asibiti, ka zauna kar su zo yau ma a neme ka, baka nan ya zama abin magana." Ta kalli fuskarsa ta ce "Na gane, ba sai ka yi magana ba" Ya tashi ya buɗe wardrobe ɗin sa, ya ɗaukko kuɗi, ya miƙa wa Nana. "Ka bari da kuɗi a gurina, wanda Imrana ya bani" Tsuke fuska ya yi, dole ta saka hannu ta karɓa, ya ɗauki mayafin yin rawaninsa ya yafa a kansa, ya biyo su har bakin gate, yana kallon Nana. Ta ɗaga masa hannu tare da yin murmushi, shi ma ya ɗaga mata. Su na fita Ummi ta dasa mita, ta ce "Jaraba, wannan kallon da yake yi miki, sai da na ji kamar na bar masa ke na yi tafiyata, Nana sai ka ce auren Soyayya bawan Allah duk a rikice yake. Kuma dan Allah yana magana, anya na taɓa jin maganarsa kuwa?" Nana ta yi murmushi ta ce "Yana yi mana" "To ai ban taɓa ji ya yi ba. Kai tubarkallah Nana Allah ya baki kyakyawan miji, sai ki yi ta kaffa-kaffa saboda 'yan mata. Kodayake yadda yake yi ɗin nan ma wace za ta ce tana so?." Nana ta yi murmushi. Ummi ta sake cewa "Na ji daɗin ganin yadda ya nuna damuwarsa a kan ki, Ubangiji Allah ya sanya ya ɗore. Nana idan hankalin mace a kwance yake a gidan mijinta, komai mai sauƙi ne" Da haka suka ƙarasa Asibiti, su na zuwa aka tura su scanic, da suka yi suka koma, aka tabattar da cikin ya fita. Aka ba wa Nana magunguna suka dawo gida. Yana ganin dawowar su, ya tashi. Nana ta yi masa murmushi suka wuce ɗaki. Nana ta cewa Ummi"Kar ki gaya masa, zan gaya masa da kaina" Ummi ta ce "To shikenan" ta wanke wa Nana kayan da ta ɓata, ta ƙara gyara mata ɗakin, ta yi mata girki. Duk yana waje ya kasa shigowa. Sai da Ummi ta gama ta yi wa Nana sallama, ta fito za ta tafi, sannan ya taso. Da ƙyar ya iya cewa "Na gode" shi ma sai da ya ji tamkar numfashinsa zai ɗauke. Ummi ta ce "Ba komai Allah ya ƙara lafiya". Ya shiga ɗakin da sauri, ya tarar da Nana a zaune a gefen katifa, ya zauna a kusa da ita, ya kamo hannunta, tare da tsare ta da ido. Yana jiran ta yi magana. Ta numfasa ta ce "Sayyid, ɓari na yi" Yanayin fuskarsa ya sanya ta fahimci bai gane me take nufi ba. "Cikin babu, ya fita, jinin da na zubar cikin ne ya zube" Ji ta yi tamkar hannunsa da ya riƙe ta da shi, ya yi mata shocking, saboda wani irin zirr da ta ji. A take fuskarsa ta yi jawur, ya ji tafukan hannayensa sun ɗauki zafi, jijiyoyin kansa sun mimmiƙe. Ya ci gaba da motsa bakinsa zai yi magana, amma ya kasa. "Sayyid lafiya kuwa? Ko wani laifin na yi maka?" Ya din ga murza tafukan hannayenta da ɗan ƙarfi, yana sauke numfashi. "Sayyid mene ne?" Bai yi magana ba, jin ya kasa maganar ya sanya, ya saki hannunta, ya nemi guri ya kwanta yana haki sama-sama. Abun duk sai ya ɗaure wa Nana kai, to mene ne ma'anar hakan? Me ya sanya shi canzawa haka lokaci guda? Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa. Ta ɗan matsa kusa da shi, ta taɓa jikinsa ya ji ya fara ɗaukar wannan zafin. Kafin ta yi wani yinƙuri tuni ya fara wannan jijjigar, jikinsa yana kakkafewa. Kawai ta zuba wa sarautar Allah ido, tare da rashin sanin cikakken abin yi. Ayshercool 08081012143 Ganin abun ba na ƙare ba ne, ya sanya Nana yinƙurawa da ƙyar, jikinta babu ƙwari, ga sanyi tana ji. Ta ɗauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya sauwwaƙa a Alƙur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya ɗauke daga kanta, ta kaɗa ta raya amma ta kasa tuna komai. Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana ɗaukewa tamkar ta ci screen, abin fa ba taɓa yi ba sai yau. Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi wardrobe, ta buɗe watso kayanta ƙasa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faɗo daga cikin kayan. Nana ta durƙusa ta ɗauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta ɗora masa a ƙirjinsa. Kamar ta ɗora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci. Ta saka hannu ta ɗauki jakar, tana ƙare mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo. Bayan wani ɗan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon ɗakin, ya kalle ta ya yinƙura ya tashi, ya yi alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa. Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta gyara zamanta. Ta ce "Sayyid na kasa fahimtar abin da yake faruwa, ban sani ba ko na yi wani abun da na ɓata maka rai ba." Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, na wani ɗan lokaci, ba tare da ta yi tsammani ba ya yi magana. "Duk na yi ƙoƙarin ɓoye matsanancin farin cikin da na shiga, da na ji za ki haihu. Na kasa ɓoye damuwar da na shiga, da na ji na rasa abin da yake cikinki Ban san dalili ba kawai na ji ina matsanancin son, abin da ban taɓa gani ba, kuma yanzu na rasa shi, ba tare da na yi tsammanin hakan ba". Jiki a sanyaye Nana ta ce "Sayyid idan kai ka ce haka, ni na ce me?" Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ba za ki gane ba" ya tashi ya naɗa rawaninsa, ya fice daga ɗakin. Nana duk ta gaji da kwanciyar, ta yinƙura ta fara mayar da kayan wardrobe ɗin da ta watso. Ta ɗaga labulen window, dan iska ta ƙara wadatar ɗakin, kawai ta hango Siyama ta fito, sanye da doguwar riga da ɗan ƙaramin mayafi, ƙonuwar hannunta, ko gama warkewa ba ta yi ba. Sai dai Nana ta ga Sayyid take tunkara. Ganin tana tunkaro shi, ya sanya ya sunkuyar da kansa, daga kallon gurin da take tahowa. Sai dai tana ƙarasowa inda yake ta tsaya tare da yin murmushi ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai, ba tare da ya kalli inda take ba. "Amm dan Allah magana nake son mu yi" Ya ɗaga kai ya kalle ta cikin mamaki. Ta ɗan sunkuyar da kanta ta yi murmushi, ta ce "Dan Allah a abubuwan da suka ɗan faru, na rashin kyautawa da na yi maka, nake son ka yafe mini na san na yi kuskure, ka yi haƙuri" Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, ya mayar da kansa ya sunkuyar. "Ka yi magana mana" ta yi maganar cikin iyayi. Jinjina kai ya yi, yana ƙara kawar da kansa gefe. Ta sake cewa "To ai ba zan gane ba, idan ka haƙura, ka yi magana" "Ya wuce" Ta saki murmushi ta ce "Na gode sosai" ta juya ta koma cikin gida tana murmushi. Tabbas Buzun nan, irin mutanen da idan ka ɗora kana relationship da su, za a ga ka haye, ya haɗu ta kowane ɓangare. Ta yi maganar a zuciyarta. Nana rasa abin yi ta yi gaba ɗaya, ta ji ƙirjinta tamkar ta haɗiyi kibiya, wani abu ya tsaya a tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta. Ta zauna ta yi shiru, kawai ta ji sallamar Siyama. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta, sai dai ta kasa magana. Siyama ta zauna a kusa da ita ta ce "Ƙawata kwana biyu ba ki zo ba" Nana ta kalle ta ta ce "Kina lafiya?" "Ashe kuma ba ki da lafiya? Ya jikin naki?" Nana ta kalli Yusra ta ce "Ya aka yi ki ka san ba ni da lafiya? Waye ya gaya miki?" "Sai an gaya mini, ina ganin komai ai. Ko kin manta gidanmu ne nima? Allah ya baku wani." Nana ta ce "Ina cikin damuwa, dan Allah kar ki dame ni" Yusra ta yi murmushi ta ce "Na sani, amma kin san faɗa ya kaure a tsakanin Ƙaisar da dattijo? Kuma duk a kan ki?" Nana ta ce "Waye dattijo?" "Wanda ya ke kawo muku ziyara, da ke da mijinki, idan ba ki yi wasa ba, abu mara daɗi zai iya faruwa. Kodayake kar na yi shishshigi, gurin shiga hurumin da ba nawa ba. Amma abubuwa na daf da rikicewa. Me ma ya faru kafin ki yi ɓarin cikin jikinki?" Nana ta ɗan yi shiru tana son ta yi tunani, amma ba ta iya tuna komai ba, tana ɗagowa ta nemi Yusra ta rasa. Damuwa da rashin sanin abin yi, ga takaicin abin da ta gani ya haɗu ya sanya, ta tashi ta sake watso kayan wardrobe tana gyarawa. A cikin kayansa, ta ci karo da wata 'yar ƙaramar jakar fata, mai kama da laya, sai dai ta fi laya girma, da ya kan saka a wuyansa wasu lokutan. Ta yi shiru tana kallon jakar, ta yi ƙoƙarin ta ga ta ina za ta buɗe ta, ta ga mene ne a ciki, amma ta kasa. Ta ajiye ta, ta ci gaba da gyaran kayan, ta sake ɗaga wata riga, sai ga kuɗi turmus a ciki, na Nigeria da na Nijar. Har ta kai hannu za ta ɗauka, ta waiwaya ta gan shi a tsaye yana kallonta. Ta kalli kuɗin ta kalle shi. "Wannan kuɗin fa?" "Nawa ne?" Ta kalle shi ta ce "A ina ka samu?" Wani irin kallo ya yi mata, jin tambayar da ta yi masa. "Me ki ka ce?" Ba ta ji ko ɗar ba, ta sake maimaitawa. "A ina ka samu? "A ina ma samu? A gurin Habu. Ai ya gaya miki sana'ar da yake yi ko?" "Dama shi ya gaya maka, na je gidan kenan?" Ya girgiza kai yana mayar da kayansa ya ce "A'a" Da ta tuno yadda ta ga ya kalli Siyama, wani narkakken baƙin ciki yake tokare mata zuciya, kamar ta kwaɗe shi ko ta samu ta huce. ***** Alhaji Zailani ne, tare da Alhaji Fatuhu, zaune a kan fararen kujeru a wata farfajiya. Fuskar Alhaji Fatuhu, cike da ƙwarin gwiwa yake duban Alhaji Zailani ya ce "Zailani, babu komai dan Allah ka karɓi shugabancin nan, na san za ka iya. Da a bawa wani da ba a san yanayin amanarsa ba, ba gara a baka ba?" Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Haba Alhaji Fatuhu, yaya za a yi kana abokina, aminina a yi maka wannan cin kashin, kuma ka ce na karbi shugabancin nan na yi yaya da shi?" "Wallahi za ka iya. Na fi jin tausayin ƙanan 'yan kasuwa, idan aka bawa wanda bai dace ba shugabanci, za a karya masu ƙaramin jari" "Ƙananan 'yan kasuwar, da su suka yi wannan bita da ƙullin, da rubuta takardar lallai a sauke ka daga kan shugabancin nan, su ka ke tausayawa?" Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Nima da ƙaramin ɗan kasuwa ne, kafin Allah ya kai ni matsayin da nake a yanzu. Kuma na san ba dukkannin su ne, su ka yi mini haka ba. Ni dai fatana dan Allah ka karɓi tayin riƙon ƙwaryar shugabancin nan da aka yi maka" Alhaji Fatuhu ya ɓata lokaci sosai da sosai, kafin ya shawo kan Alhaji Zailani ya amince zai karɓa. ***** Gaddafi tuni ya koma gurin neman khɗinsa, saboda takaicin abubuwan suke faruwa a gidansu, ya fara damunsa. Baba ƙiri-ƙiri haka ya zuba ido ya yi shiru, ba ya iya cewa uffan, sai dai ya zuba ido a kan lamarin gidansa. Sai ma dai idan an dafa a zuba a ba shi ya ci. Sosai al'amuran gidan su Nana, suka fara canzawa kullum sai an ɗora abinci sau uku a rana saboda hidimar da Jamila take yi da su. Ƙarewa ta saka ana ta yi musu gyare-gyare a cikin gidan. Babban abin da yake damun Hajiya Sa'a da Jamila, shi ne yadda take ta ƙoƙarin janyo ta, cikin ɗaya mummunar ɗabi'ar da suke aikatawa ta lesbian. Sai dai Jamila ta kafe da kai da fata, taƙi amincewa da hakan. Sai da Hajiya Sa'a ta yi mamaki, saboda a ƙulumboton da ta yi wa Jamila, babu yadda za a yi ta iya kaucewa duk wata buƙata da ta zo mata da ita, amma ta kasa galaba a kan Jamila. Duk wani shashashanci da suke yi tana kallo, amma sam ba ta ji abin ya kama hankalinta ba, balle ta yi sha'awar aikatawa. Ta fito harabar gidan tana shirin tafiya, sai ga Mus'ab ɗa ɗaya tilo ga Hajiya Sa'a. Yana ganin Jamila ya tsaya. Duk da ba shiga harkarsa take yi ba, amma ta yi ƙoƙarin tare shi daga shiga cikin gidan, ya yi mummunan gani. "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau Jamila. Ya ki ke?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Amm Yaya Mus'ab ko za ka ajiye ni a hanya ne, ba na jin daɗi" Ya yi murmushi ya ce "Me zai hana? Bari na kai wa Mummy saƙon nan" Da sauri ta ce "A'a ai bacci take yi, ta ce kuma kar a tashe ta" "Ok to mu je na ajiye ki" ta yi gaba ya bi ta a baya. ***** Nana kuwa ita ma a wannan karon, basar da Sayyid ta yi, ta ƙi kula shi sam. Shi ma ya maze ya share ta. Baccinta ya yi nisa sosai ta ganta a daji ita kaɗai ƙwal. Ta ɗaga kanta ta ga wani ƙaton tsuntsu yana shawagi a saman kanta. Ba ta tsorata ba, ta ɗan ja numfashi ta ce "Ƙaisar laifin me na yi maka, ka zaɓi ka hukunta ni ta wannan hanyar? Me ya sa za ka zama dalilin zubewar cikina?" Tsuntsunan nan saukko ƙasa, ya yi girgiza Ƙaisar ya bayyana. Ya zauna yana fuskantar ta ya ce "Komai ma kin yi mini, babu abin da ba ki yi mini ba, abin da ya dace nake yi" "Ba ka tsoron Allah Ƙaisar, ba ka tsoron Allah ya kama ka da hakkina, abubuwan da ka ke aikata mini na cutarwa. Kai ka yi mini, wannan tsohon ya yi mana, mijin nawa ma na fara daina gane kansa. Ya fara ƙoƙarin cutar da ni" Ya ɗan kalli saman bishiya sannan ya ce "Babu abin da ban gaya miki  ba ai. Amm kin tuna abin da na nuna miki, Alhaji Zailani yana yi wa abokinsa? Da gaske ya faru a zahiri. Kuma tsafi gaskiyar mai shi, domin kuwa al'anura sun fara juya wa Alhaji Zailani baya. Nan zuwa wani ɗan lokaci zai rasa komai nasa. Lafiyar sa da dukiyarsa." Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Dan Allah idan ka na dama ka yi wani abu a kai mana. Ka tona abin da aka yi masan" Ya girgiza kai ya ce "Ba ma shiga abin da babu ruwanmu, ko warware wani abu da aka yi wa wani, muddin ba yarjejeniya aka yi damu, aka bamu damar yin hakan ba. Zan iya taimakonsa ne kawai bisa amincewar ki, da kuma umarnin ki. Zan gaya miki inda abin yake ya saka a je a tone, ko kuma ki je ki tone. Idan ba haka ba nan da kwanaki uku rak za a tono ƙwarangwal ɗin yaron nan, a kuma yin wani tsafin da ita." Har Nana ta motsa baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa, dan tana amincewa a taimaki Alhaji Fatuhu ba ta san me zai biyo bayan hakan ba, ka iya tabbatar da buƙatar Ƙaisar a kanta. AREWABOOKS Kasancewar ba ta salla, ya sanya har gari ya waye tana bacci. Bayan ta yi wanka ta rasa abin yi, ta ɗebo kayan wankin ta, ta shiga banɗaki ta wanke. Nasa dama Habu ne yake zuwa ya ɗauka. Ta gama, ta saka hijjabinta, ta ɗaukko bokitin, ta fito daga ɗakin. Yana kan kujera a daf da gate ɗin, yana aikin dafa shayi, gefensa ga radio tana yi. Ba ta kula shi ba, ta zagaya baya, ta yi shanyar kayan nata. Ta fito ta ja ta yi turus tana kallon ikon Allah. Siyama ce a tsaye, da ɗan ƙaramin flask a hannunta. Nana ba ta san me take ce masa ba, ta ga ya sauke rawanin fuskarsa ya saka hannu ya karɓi flask ɗin, ya yi magana. Kawai ta shiga ɗaki, a ƙofar banɗakin, ta jefar da bokitin jin wani irin matsanancin ɗaci yana taso mata. Ta cire hijjabinta kawai ta tsaya ta riƙe ƙugunta, ta tsaya tana jiran ya shigo, amma bai shigo ba, zuciyarta ta din ga raya mata, yana can su na hira da Siyama. Kawai ta buɗe ƙofa ta shiga banɗaki, sai dai ta rasa uban abin da ya kai ta banɗakin ma. Ta gama tsayuwarta ta fito daga banɗakin. Tana fitowa ta gan shi a tsaye, da flask ɗin a hannunsa, ya nufo ta zai yi magana, ta riga ta ɓarar da flask ɗin. Farfesun kifi da dankalin ya tarwatse a ƙasa. Ya kalli gurin ya kalli yadda take huci, zuciya ta yinƙuro shi, sai dai ya ga Ƙaisar a bayan Nana, ya zubo masa ido. Ya haɗiye wani abu, mai ɗaci. Ya kalli Nana ya ga yadda idonta ya rufe, ta fara ƙoƙarin wuce shi ta fita. Ya riƙe ta yana ci gaba da kallon Ƙaisar. Ya kwantar da Nana a kan katifa, idanunta a rufe sai hawaye da yake fita, ta gefen idonta. Ya durƙusa ya gyara gurin ta ɓarar da abincin. Ya sake kallon yadda Ƙaisar ya jingina da bango, ya tsaya a kan Nana. "Tun da ka yi abin da ka yi, ya kamata ka bani guri" Ya yi maganar yana kallon inda Ƙaisar yake. "Gurin ka na zo ne? Idan ba gurin ka na zo ba, sai ka ƙyale ni" "Ka zubar mini da ciki, kuma saboda rashin kunya, ka zo haɗa fitina a tsakaninmu" Ƙaisar ya yi murmushi ya ce "Ina mamakin yadda Aljani yake shiga al'amuran bil adama har haka. Kai ka fara lalata cikin, ni kuma na zubar da shi." Sayyid ya shafi fuskarsa ya ce "Waye Aljanin a tsakanin ni da kai?" Ƙaisar ya ce "Ba da kai nake ba. Ka san da wanda nake" Buzu ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ka gaya mini, wane ne ni? Daga ina nake? Kuma suwaye iyayena? Me ya kawo ni ƙasar nan?" "Ba ni za ka yi wa wannan tambayar ba, zuwa yanzu na san ka bambance tsakanin ni da shi" "Haka ne, na banbance, yanzu ka tafi ka bani guri, ka bar ni da matata" "Ba zan tafi ba" Buzu ya durƙusa ya kwance rawanin kansa, ya cire rigar jikinsa, ya ɗago Nana da take cikin yanayin gushewar hankali. Ya fara cire kayan jikinta, tamkar an aiko wa Ƙaisar saƙon mutuwa ya murtuke fuska. Bai tsinke da lamarin ba, sai da Sayyid ya rungume Nana yana sumbatar bakinta. Jikin Nana ya din ga rawa, tana fatan ta saka baki a maganganun su, amma ta kasa, tana ganin duk abin da yake faruwa, amma tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsa ko da ƙaramin yatsanta. Da ƙyar ta fizgo numfashi ta tashi a zabure, ta ce "Sayyid" ya taso da sauri daga inda yake zaune ya nufo ta. Ya kasa magana, ita ma kuma ta kasa cewa komai, sai rarraba ido da take yi, ta yi zaton mafarki ne, amma ta ji ɗakin yana ƙarnin kifi, ga kuma flask ɗin da ya shigo da shi. Da ƙyar ta ce "Ina wanda ku ke magana da shi?" Ya kalli ɗakin ya ce "A ina?" Ta kalli daidai gurin da Ƙaisar ya tsaya, ta ce "Wanda ya tsaya a nan, wani dogo" "Ban yi magana da kowa ba" ya yi maganar yana girgiza mata kai. Ta yi ajiyar zuciya ta ja ta zauna, tana jin kanta yana ciwo. **** "Suwaiba" Alhaji Fatuhu ya kira sunanta. Ta kalle shi ta ce "Ya dai?" "Ba na jin daɗin jikina ne, kuma wani abu ne yake damuna" "Me ke nan?" "Ƙara ta za a kai kotu" Ta waro ido ta ce "Kotu kuma? Me ka yi?" "Kayan nan da suka yi ɓatan dabo, ranar Litinin zamu shiga kotu da 'yan kasuwa. Kujerata ma an sauke ni. Amma bai dame ni ba, kayan mutane nake tunani" Ta kwaɓe baki ta kaɗa kai ta ce "Ai Alhaji Fatuhu duk ɗan da ya hana uwassa bacci, shi ma ba zai yi ba. Babu irin wahalar da bamu sha tare ba, amma abin Duniya na samuwa, ka auro yarinya ƙarama saboda ka ƙuntata mini, ka ci duniyarka da tsinke. Ai ga shi kai ma Allah ya kama ka" Ya yi zuru da ido yana kallonta. Ta gama maganganunta ta bar masa ɗakin. Tana zuwa bedroom ɗin ta, ta rufe ƙofa, hawayen da ta maƙale ta ba su damar gangarowa. Ta hau nanata "Innalillahi wa innalillahi raji'un" Ta ɗauki wayarta ta kira Yayanta. Yana ɗagawa ya ji muryarta wani iri, ya ce "Lafiya kuwa?" "Yaya Baban su Raudah wai za a kai kotu, 'yan kasuwa su na zargin ya cinye musu kuɗi, dan Allah ka yi wani abu a kai dan Allah" "To ikon Allah, amma ba sai ki bari sai da Safe ba, kya kira ni. Amma ku kuma kin tabattar bai ci kuɗin ba?" Suwaiba ta ce "Yaya kai ma ka san shi da gudun Duniya, da abin mutane wallahi zan iya rantsuwa bai ci kuɗin kowa ba" "Ki bari zan kira ki da Safe" ta ajiye wayar jiki a sanyaye cikin damuwa. Kasancewar a sashen Fadila yake, ta fahimci damuwa a tattare da shi, sai dai fafur ya ƙi gaya mata, ya lallaɓa ta ta yi bacci. ***** Da daddare Nana ta kasa karanta Alqur'ani, amma wannan karon ta samu ta saka a wayarta, ta daɗe tana saurara tana jin nutsuwa na ratsa ta. Kasancewar jini ya ɗauke, ya sanya ta yi sallar Isha'i, ta kwanta karatun Alqur'ani yana tashi ƙasa-ƙasa a wayarta. Tana kallon Sayyid, ya shirya ya kwanta a ƙasa, gurin da yake kwanciya da. Gaba ɗaya sai ta ji ta damu. Ta daɗe idonta biyu, tana jira ta ga ko zai ta so, amma bai tashi daga gurin ba. Ta tashi a hankali ta nufe shi, har ta ƙarasa kusa da shi, ta kwanta. Ba ta ce masa uffan ba, ta caza masa hankali har ya biye mata. Bayan wani ɗan lokaci ya numfasa ya ce "Kin daina fushin?" "Ba kai ka saka na yi fushin ba? Amma ka yi haƙuri" "Me na yi miki?" "Me yasa za ka yi wannan yarinyar magana, har ta baka abu ka shigo mini da shi ɗaki?" "Ki na gurin kin san meyafaru?" Ta tashi daga jikinsa, ta ce "Ni ba na son jin meyafaru kawai babu ruwanta da kai, kar ka sake kula ta. Dan wallahi za ka iya nema ta ka rasa. Idan ka na son ta maye gurbina ba wani abu, ni zan iya tafiya ta na baku guri". "Ki daina faɗar abin da ba za ki iya aikatawa ba" "To ka ci gaba, zan baka mamaki kuwa" ta yi maganar tana tashi zaune, da nufin ta bar masa gurin." Amma ya riƙe ta gam, yana yi mata numfashi a wuya. A gurin suka kwana tare. Sai Asuba bayan ta yi wanka ta yi salla, ta koma kan katifa. Tana tsaka da bacci, ta ji yana tattaɓa ta, ta buɗe idonta ta kalle shi tana yanutsa fuska, saboda bacci ne a kan ta sosai. Wayarta ya ajiye mata a daidai kunnenta. Waƙar Ali jita ce take tashi, ta Aminiya. Shiru ta yi tana sauraren baitukan tana kallon kyakyawar fuskarsa da ya tsare ta da manyan idanunsa yana kallonta yana murmushi. Ita ma murmushin ta sakar masa, ta yinƙura ta tashi zaune, ita sam ba ta san da waƙar ma a wayar ba, kasancewar ba gwanar jin waƙa ba ce, amma har cikin zuciyarta take jin baitukan, tamkar shi ne yake rairai mata. Gaba ɗaya suka manta, da batun saɓanin da ya shiga tsakaninsu. (BAYAN MAKONNI BIYU) Gaba ɗaya Fadila ta rasa abin da yake yi mata daɗi, hankalinta ya ƙi kwanciya, tun da aka fara zaman kotu ta ji halin da ake ciki ta rasa abun da yake yi mata daɗi, yanayin yadda shari'ar ke gudana, za ka san da gayya ake yi, kawai shi ake son ya tozarta. Dan tashin farko Alƙali cewa ya yi a tsare shi, sai an ajiye wasu miliyoyi da kadarori, za a sake shi. Wasu tuhume-tuhumen ma, bai san da su ba, sai ranar da aka fara zaman kotun, sannan ya san da su. Har wasu maƙudan kuɗin, da ake zarginsa da sama da faɗi da su, a lokacin da yake shugabanci. Haka aka sayar da wasu daga kadarorinsa, aka bayar sannan aka ba da belinsa. Kotu ta yi umarnin a yi gwanjon kadarorinsa a sallami mutane kuɗinsu. ***** Alhaji Zailani, tare da Malam Gambo suka koma gurin da suka binne, jaririn nan, su ka tono ƙwarangwal ɗin sa, duk ya zagwanye. Suka saka a akwati, suka tafi da shi. Ɗakin da Malam Gambo yake tsaface-tsafacensa su ka je. Ya ɗaukko ƙwarangwal ɗin jaririn, aka babbaka wata irin wuta, aka ɗauki ƙwarangwal ɗin jaririn nan, ya rubuce jikin da sunan Alhaji Fatuhu, ya zana wasu hatimai, ya nannaɗe su a jikin ƙwarangwal ɗin aka saka a cikin wutar nan. Malam Gambo ya din ga zuba wani magani a cikin wutar, ya kawo wasu irin layoyi da ya zana hatimai daban-daban, ya din ga jefawa a cikin wutar. Alhaji Zailani kuma yana kiran sunan Alhaji Fatuhu. Sai da ƙwarangwal ɗin nan ya yi baƙi ƙirin, zaren da aka naɗe ƙwarangwal ɗin, ya kama jikin sosai. Ya kuma naɗe shi da wani zaren, sannan ya naɗe da likkafani, su ka je suka samu wata tsohuwar rijiya, suka jefa a ciki. Alhaji Zailani ya koma gida, kulle kansa a cikin ɗaki, ya din ga ɓaɓɓaka wata irin mahaukaciyar dariya, tamkar zai haukace. Ya ce "Alhaji Fatuhu ka gama yawo, yanzu sai na ga wanda za ka hura wa hanci, wai ka ga mai kuɗi kuma mai tsoron Allah, mu zuba mu gani. Wannan burin nawa ya cika, saura kuma waccan yarinyar" Alhaji Fatuhu kuwa, sun dawo daga kotu, Yayan Hajiya Suwaiba, lauyan da ya tsaya masa, yana ta yi masa nasiha a kan ya karɓi ƙaddara. Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi Barrister, na karɓi ƙaddarata. Na kuma gode wa Allah. Abu ɗaya nake tunani iyalina na saba musu da rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankali. Ina jin tausayinsu fiye da abin da ya same ni" Cikin tausaywa Barrister ya ce "Na sani Alhaji, tabbas kai mutum ne mai kyautatawa iyali. To yanzu ne ranar da za su nuna maka halacci su ma, a yi haƙuri" Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, mun gode Allah" Ji ya yi tamkar ana ƙoƙarin fizgo ƙwaƙwalwarsa. Ya yi wata irin zabura, ya riƙe kansa gam. Barrister ya ce "Alhaji lafiya dai?" Ya girgiza kai ya ce "Zafi nake ji" kafin ya kuma wata maganar, ya yanke jiki ya faɗi a gurin. Nana tamkar tana kallon talabijin, haka ta ga komai a cikin mudin da Ƙaisar yake nuna mata. Yana gefe yana rubutunsa, ita kuma ta zuba uban tagumi tana kallon mudubin. "Shigen irin wannan sihirin aka yi wa mijinki, shi ne wannan wutar da yake cewa tana ci a jikinsa. Sai dai shi nasa ya sha bamban da wannan ta wasu fannukan" Nana ta zabura ta kalle shi ta miƙe tsaye ta ce "Ƙaisar ka yi mini bayani, waye ya yi masa asirin? Kuma daga ina yake? Suwaye iyayensa?" Ya ɗago ya kalle ta ya ce "Kin manta sharaɗin ne?" Ta yinƙura za ta yi magana, ta yi ido huɗu da Sayyid, yana kusa da ita, ya zuba mata ido. Ta yi ajiyar zuciya. "Waye Ƙaisar?" Ya jefo mata tambayar babu zato babu tsammani. Ayshercool 08081012143 45 Ganin abun ba na ƙare ba ne, ya sanya Nana yinƙurawa da ƙyar, jikinta babu ƙwari, ga sanyi tana ji. Ta ɗauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya sauwwaƙa a Alƙur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya ɗauke daga kanta, ta kaɗa ta raya amma ta kasa tuna komai. Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana ɗaukewa tamkar ta ci screen, abin fa ba taɓa yi ba sai yau. Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi wardrobe, ta buɗe watso kayanta ƙasa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faɗo daga cikin kayan. Nana ta durƙusa ta ɗauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta ɗora masa a ƙirjinsa. Kamar ta ɗora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci. Ta saka hannu ta ɗauki jakar, tana ƙare mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo. Bayan wani ɗan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon ɗakin, ya kalle ta ya yinƙura ya tashi, ya yi alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa. Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta gyara zamanta. Ta ce "Sayyid na kasa fahimtar abin da yake faruwa, ban sani ba ko na yi wani abun da na ɓata maka rai ba." Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, na wani ɗan lokaci, ba tare da ta yi tsammani ba ya yi magana. "Duk na yi ƙoƙarin ɓoye matsanancin farin cikin da na shiga, da na ji za ki haihu. Na kasa ɓoye damuwar da na shiga, da na ji na rasa abin da yake cikinki Ban san dalili ba kawai na ji ina matsanancin son, abin da ban taɓa gani ba, kuma yanzu na rasa shi, ba tare da na yi tsammanin hakan ba". Jiki a sanyaye Nana ta ce "Sayyid idan kai ka ce haka, ni na ce me?" Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ba za ki gane ba" ya tashi ya naɗa rawaninsa, ya fice daga ɗakin. Nana duk ta gaji da kwanciyar, ta yinƙura ta fara mayar da kayan wardrobe ɗin da ta watso. Ta ɗaga labulen window, dan iska ta ƙara wadatar ɗakin, kawai ta hango Siyama ta fito, sanye da doguwar riga da ɗan ƙaramin mayafi, ƙonuwar hannunta, ko gama warkewa ba ta yi ba. Sai dai Nana ta ga Sayyid take tunkara. Ganin tana tunkaro shi, ya sanya ya sunkuyar da kansa, daga kallon gurin da take tahowa. Sai dai tana ƙarasowa inda yake ta tsaya tare da yin murmushi ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai, ba tare da ya kalli inda take ba. "Amm dan Allah magana nake son mu yi" Ya ɗaga kai ya kalle ta cikin mamaki. Ta ɗan sunkuyar da kanta ta yi murmushi, ta ce "Dan Allah a abubuwan da suka ɗan faru, na rashin kyautawa da na yi maka, nake son ka yafe mini na san na yi kuskure, ka yi haƙuri" Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, ya mayar da kansa ya sunkuyar. "Ka yi magana mana" ta yi maganar cikin iyayi. Jinjina kai ya yi, yana ƙara kawar da kansa gefe. Ta sake cewa "To ai ba zan gane ba, idan ka haƙura, ka yi magana" "Ya wuce" Ta saki murmushi ta ce "Na gode sosai" ta juya ta koma cikin gida tana murmushi. Tabbas Buzun nan, irin mutanen da idan ka ɗora kana relationship da su, za a ga ka haye, ya haɗu ta kowane ɓangare. Ta yi maganar a zuciyarta. Nana rasa abin yi ta yi gaba ɗaya, ta ji ƙirjinta tamkar ta haɗiyi kibiya, wani abu ya tsaya a tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta. Ta zauna ta yi shiru, kawai ta ji sallamar Siyama. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta, sai dai ta kasa magana. Siyama ta zauna a kusa da ita ta ce "Ƙawata kwana biyu ba ki zo ba" Nana ta kalle ta ta ce "Kina lafiya?" "Ashe kuma ba ki da lafiya? Ya jikin naki?" Nana ta kalli Yusra ta ce "Ya aka yi ki ka san ba ni da lafiya? Waye ya gaya miki?" "Sai an gaya mini, ina ganin komai ai. Ko kin manta gidanmu ne nima? Allah ya baku wani." Nana ta ce "Ina cikin damuwa, dan Allah kar ki dame ni" Yusra ta yi murmushi ta ce "Na sani, amma kin san faɗa ya kaure a tsakanin Ƙaisar da dattijo? Kuma duk a kan ki?" Nana ta ce "Waye dattijo?" "Wanda ya ke kawo muku ziyara, da ke da mijinki, idan ba ki yi wasa ba, abu mara daɗi zai iya faruwa. Kodayake kar na yi shishshigi, gurin shiga hurumin da ba nawa ba. Amma abubuwa na daf da rikicewa. Me ma ya faru kafin ki yi ɓarin cikin jikinki?" Nana ta ɗan yi shiru tana son ta yi tunani, amma ba ta iya tuna komai ba, tana ɗagowa ta nemi Yusra ta rasa. Damuwa da rashin sanin abin yi, ga takaicin abin da ta gani ya haɗu ya sanya, ta tashi ta sake watso kayan wardrobe tana gyarawa. A cikin kayansa, ta ci karo da wata 'yar ƙaramar jakar fata, mai kama da laya, sai dai ta fi laya girma, da ya kan saka a wuyansa wasu lokutan. Ta yi shiru tana kallon jakar, ta yi ƙoƙarin ta ga ta ina za ta buɗe ta, ta ga mene ne a ciki, amma ta kasa. Ta ajiye ta, ta ci gaba da gyaran kayan, ta sake ɗaga wata riga, sai ga kuɗi turmus a ciki, na Nigeria da na Nijar. Har ta kai hannu za ta ɗauka, ta waiwaya ta gan shi a tsaye yana kallonta. Ta kalli kuɗin ta kalle shi. "Wannan kuɗin fa?" "Nawa ne?" Ta kalle shi ta ce "A ina ka samu?" Wani irin kallo ya yi mata, jin tambayar da ta yi masa. "Me ki ka ce?" Ba ta ji ko ɗar ba, ta sake maimaitawa. "A ina ka samu? "A ina ma samu? A gurin Habu. Ai ya gaya miki sana'ar da yake yi ko?" "Dama shi ya gaya maka, na je gidan kenan?" Ya girgiza kai yana mayar da kayansa ya ce "A'a" Da ta tuno yadda ta ga ya kalli Siyama, wani narkakken baƙin ciki yake tokare mata zuciya, kamar ta kwaɗe shi ko ta samu ta huce. ***** Alhaji Zailani ne, tare da Alhaji Fatuhu, zaune a kan fararen kujeru a wata farfajiya. Fuskar Alhaji Fatuhu, cike da ƙwarin gwiwa yake duban Alhaji Zailani ya ce "Zailani, babu komai dan Allah ka karɓi shugabancin nan, na san za ka iya. Da a bawa wani da ba a san yanayin amanarsa ba, ba gara a baka ba?" Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Haba Alhaji Fatuhu, yaya za a yi kana abokina, aminina a yi maka wannan cin kashin, kuma ka ce na karbi shugabancin nan na yi yaya da shi?" "Wallahi za ka iya. Na fi jin tausayin ƙanan 'yan kasuwa, idan aka bawa wanda bai dace ba shugabanci, za a karya masu ƙaramin jari" "Ƙananan 'yan kasuwar, da su suka yi wannan bita da ƙullin, da rubuta takardar lallai a sauke ka daga kan shugabancin nan, su ka ke tausayawa?" Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Nima da ƙaramin ɗan kasuwa ne, kafin Allah ya kai ni matsayin da nake a yanzu. Kuma na san ba dukkannin su ne, su ka yi mini haka ba. Ni dai fatana dan Allah ka karɓi tayin riƙon ƙwaryar shugabancin nan da aka yi maka" Alhaji Fatuhu ya ɓata lokaci sosai da sosai, kafin ya shawo kan Alhaji Zailani ya amince zai karɓa. ***** Gaddafi tuni ya koma gurin neman khɗinsa, saboda takaicin abubuwan suke faruwa a gidansu, ya fara damunsa. Baba ƙiri-ƙiri haka ya zuba ido ya yi shiru, ba ya iya cewa uffan, sai dai ya zuba ido a kan lamarin gidansa. Sai ma dai idan an dafa a zuba a ba shi ya ci. Sosai al'amuran gidan su Nana, suka fara canzawa kullum sai an ɗora abinci sau uku a rana saboda hidimar da Jamila take yi da su. Ƙarewa ta saka ana ta yi musu gyare-gyare a cikin gidan. Babban abin da yake damun Hajiya Sa'a da Jamila, shi ne yadda take ta ƙoƙarin janyo ta, cikin ɗaya mummunar ɗabi'ar da suke aikatawa ta lesbian. Sai dai Jamila ta kafe da kai da fata, taƙi amincewa da hakan. Sai da Hajiya Sa'a ta yi mamaki, saboda a ƙulumboton da ta yi wa Jamila, babu yadda za a yi ta iya kaucewa duk wata buƙata da ta zo mata da ita, amma ta kasa galaba a kan Jamila. Duk wani shashashanci da suke yi tana kallo, amma sam ba ta ji abin ya kama hankalinta ba, balle ta yi sha'awar aikatawa. Ta fito harabar gidan tana shirin tafiya, sai ga Mus'ab ɗa ɗaya tilo ga Hajiya Sa'a. Yana ganin Jamila ya tsaya. Duk da ba shiga harkarsa take yi ba, amma ta yi ƙoƙarin tare shi daga shiga cikin gidan, ya yi mummunan gani. "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau Jamila. Ya ki ke?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Amm Yaya Mus'ab ko za ka ajiye ni a hanya ne, ba na jin daɗi" Ya yi murmushi ya ce "Me zai hana? Bari na kai wa Mummy saƙon nan" Da sauri ta ce "A'a ai bacci take yi, ta ce kuma kar a tashe ta" "Ok to mu je na ajiye ki" ta yi gaba ya bi ta a baya. ***** Nana kuwa ita ma a wannan karon, basar da Sayyid ta yi, ta ƙi kula shi sam. Shi ma ya maze ya share ta. Baccinta ya yi nisa sosai ta ganta a daji ita kaɗai ƙwal. Ta ɗaga kanta ta ga wani ƙaton tsuntsu yana shawagi a saman kanta. Ba ta tsorata ba, ta ɗan ja numfashi ta ce "Ƙaisar laifin me na yi maka, ka zaɓi ka hukunta ni ta wannan hanyar? Me ya sa za ka zama dalilin zubewar cikina?" Tsuntsunan nan saukko ƙasa, ya yi girgiza Ƙaisar ya bayyana. Ya zauna yana fuskantar ta ya ce "Komai ma kin yi mini, babu abin da ba ki yi mini ba, abin da ya dace nake yi" "Ba ka tsoron Allah Ƙaisar, ba ka tsoron Allah ya kama ka da hakkina, abubuwan da ka ke aikata mini na cutarwa. Kai ka yi mini, wannan tsohon ya yi mana, mijin nawa ma na fara daina gane kansa. Ya fara ƙoƙarin cutar da ni" Ya ɗan kalli saman bishiya sannan ya ce "Babu abin da ban gaya miki  ba ai. Amm kin tuna abin da na nuna miki, Alhaji Zailani yana yi wa abokinsa? Da gaske ya faru a zahiri. Kuma tsafi gaskiyar mai shi, domin kuwa al'anura sun fara juya wa Alhaji Zailani baya. Nan zuwa wani ɗan lokaci zai rasa komai nasa. Lafiyar sa da dukiyarsa." Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Dan Allah idan ka na dama ka yi wani abu a kai mana. Ka tona abin da aka yi masan" Ya girgiza kai ya ce "Ba ma shiga abin da babu ruwanmu, ko warware wani abu da aka yi wa wani, muddin ba yarjejeniya aka yi damu, aka bamu damar yin hakan ba. Zan iya taimakonsa ne kawai bisa amincewar ki, da kuma umarnin ki. Zan gaya miki inda abin yake ya saka a je a tone, ko kuma ki je ki tone. Idan ba haka ba nan da kwanaki uku rak za a tono ƙwarangwal ɗin yaron nan, a kuma yin wani tsafin da ita." Har Nana ta motsa baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa, dan tana amincewa a taimaki Alhaji Fatuhu ba ta san me zai biyo bayan hakan ba, ka iya tabbatar da buƙatar Ƙaisar a kanta. AREWABOOKS Kasancewar ba ta salla, ya sanya har gari ya waye tana bacci. Bayan ta yi wanka ta rasa abin yi, ta ɗebo kayan wankin ta, ta shiga banɗaki ta wanke. Nasa dama Habu ne yake zuwa ya ɗauka. Ta gama, ta saka hijjabinta, ta ɗaukko bokitin, ta fito daga ɗakin. Yana kan kujera a daf da gate ɗin, yana aikin dafa shayi, gefensa ga radio tana yi. Ba ta kula shi ba, ta zagaya baya, ta yi shanyar kayan nata. Ta fito ta ja ta yi turus tana kallon ikon Allah. Siyama ce a tsaye, da ɗan ƙaramin flask a hannunta. Nana ba ta san me take ce masa ba, ta ga ya sauke rawanin fuskarsa ya saka hannu ya karɓi flask ɗin, ya yi magana. Kawai ta shiga ɗaki, a ƙofar banɗakin, ta jefar da bokitin jin wani irin matsanancin ɗaci yana taso mata. Ta cire hijjabinta kawai ta tsaya ta riƙe ƙugunta, ta tsaya tana jiran ya shigo, amma bai shigo ba, zuciyarta ta din ga raya mata, yana can su na hira da Siyama. Kawai ta buɗe ƙofa ta shiga banɗaki, sai dai ta rasa uban abin da ya kai ta banɗakin ma. Ta gama tsayuwarta ta fito daga banɗakin. Tana fitowa ta gan shi a tsaye, da flask ɗin a hannunsa, ya nufo ta zai yi magana, ta riga ta ɓarar da flask ɗin. Farfesun kifi da dankalin ya tarwatse a ƙasa. Ya kalli gurin ya kalli yadda take huci, zuciya ta yinƙuro shi, sai dai ya ga Ƙaisar a bayan Nana, ya zubo masa ido. Ya haɗiye wani abu, mai ɗaci. Ya kalli Nana ya ga yadda idonta ya rufe, ta fara ƙoƙarin wuce shi ta fita. Ya riƙe ta yana ci gaba da kallon Ƙaisar. Ya kwantar da Nana a kan katifa, idanunta a rufe sai hawaye da yake fita, ta gefen idonta. Ya durƙusa ya gyara gurin ta ɓarar da abincin. Ya sake kallon yadda Ƙaisar ya jingina da bango, ya tsaya a kan Nana. "Tun da ka yi abin da ka yi, ya kamata ka bani guri" Ya yi maganar yana kallon inda Ƙaisar yake. "Gurin ka na zo ne? Idan ba gurin ka na zo ba, sai ka ƙyale ni" "Ka zubar mini da ciki, kuma saboda rashin kunya, ka zo haɗa fitina a tsakaninmu" Ƙaisar ya yi murmushi ya ce "Ina mamakin yadda Aljani yake shiga al'amuran bil adama har haka. Kai ka fara lalata cikin, ni kuma na zubar da shi." Sayyid ya shafi fuskarsa ya ce "Waye Aljanin a tsakanin ni da kai?" Ƙaisar ya ce "Ba da kai nake ba. Ka san da wanda nake" Buzu ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ka gaya mini, wane ne ni? Daga ina nake? Kuma suwaye iyayena? Me ya kawo ni ƙasar nan?" "Ba ni za ka yi wa wannan tambayar ba, zuwa yanzu na san ka bambance tsakanin ni da shi" "Haka ne, na banbance, yanzu ka tafi ka bani guri, ka bar ni da matata" "Ba zan tafi ba" Buzu ya durƙusa ya kwance rawanin kansa, ya cire rigar jikinsa, ya ɗago Nana da take cikin yanayin gushewar hankali. Ya fara cire kayan jikinta, tamkar an aiko wa Ƙaisar saƙon mutuwa ya murtuke fuska. Bai tsinke da lamarin ba, sai da Sayyid ya rungume Nana yana sumbatar bakinta. Jikin Nana ya din ga rawa, tana fatan ta saka baki a maganganun su, amma ta kasa, tana ganin duk abin da yake faruwa, amma tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsa ko da ƙaramin yatsanta. Da ƙyar ta fizgo numfashi ta tashi a zabure, ta ce "Sayyid" ya taso da sauri daga inda yake zaune ya nufo ta. Ya kasa magana, ita ma kuma ta kasa cewa komai, sai rarraba ido da take yi, ta yi zaton mafarki ne, amma ta ji ɗakin yana ƙarnin kifi, ga kuma flask ɗin da ya shigo da shi. Da ƙyar ta ce "Ina wanda ku ke magana da shi?" Ya kalli ɗakin ya ce "A ina?" Ta kalli daidai gurin da Ƙaisar ya tsaya, ta ce "Wanda ya tsaya a nan, wani dogo" "Ban yi magana da kowa ba" ya yi maganar yana girgiza mata kai. Ta yi ajiyar zuciya ta ja ta zauna, tana jin kanta yana ciwo. **** "Suwaiba" Alhaji Fatuhu ya kira sunanta. Ta kalle shi ta ce "Ya dai?" "Ba na jin daɗin jikina ne, kuma wani abu ne yake damuna" "Me ke nan?" "Ƙara ta za a kai kotu" Ta waro ido ta ce "Kotu kuma? Me ka yi?" "Kayan nan da suka yi ɓatan dabo, ranar Litinin zamu shiga kotu da 'yan kasuwa. Kujerata ma an sauke ni. Amma bai dame ni ba, kayan mutane nake tunani" Ta kwaɓe baki ta kaɗa kai ta ce "Ai Alhaji Fatuhu duk ɗan da ya hana uwassa bacci, shi ma ba zai yi ba. Babu irin wahalar da bamu sha tare ba, amma abin Duniya na samuwa, ka auro yarinya ƙarama saboda ka ƙuntata mini, ka ci duniyarka da tsinke. Ai ga shi kai ma Allah ya kama ka" Ya yi zuru da ido yana kallonta. Ta gama maganganunta ta bar masa ɗakin. Tana zuwa bedroom ɗin ta, ta rufe ƙofa, hawayen da ta maƙale ta ba su damar gangarowa. Ta hau nanata "Innalillahi wa innalillahi raji'un" Ta ɗauki wayarta ta kira Yayanta. Yana ɗagawa ya ji muryarta wani iri, ya ce "Lafiya kuwa?" "Yaya Baban su Raudah wai za a kai kotu, 'yan kasuwa su na zargin ya cinye musu kuɗi, dan Allah ka yi wani abu a kai dan Allah" "To ikon Allah, amma ba sai ki bari sai da Safe ba, kya kira ni. Amma ku kuma kin tabattar bai ci kuɗin ba?" Suwaiba ta ce "Yaya kai ma ka san shi da gudun Duniya, da abin mutane wallahi zan iya rantsuwa bai ci kuɗin kowa ba" "Ki bari zan kira ki da Safe" ta ajiye wayar jiki a sanyaye cikin damuwa. Kasancewar a sashen Fadila yake, ta fahimci damuwa a tattare da shi, sai dai fafur ya ƙi gaya mata, ya lallaɓa ta ta yi bacci. ***** Da daddare Nana ta kasa karanta Alqur'ani, amma wannan karon ta samu ta saka a wayarta, ta daɗe tana saurara tana jin nutsuwa na ratsa ta. Kasancewar jini ya ɗauke, ya sanya ta yi sallar Isha'i, ta kwanta karatun Alqur'ani yana tashi ƙasa-ƙasa a wayarta. Tana kallon Sayyid, ya shirya ya kwanta a ƙasa, gurin da yake kwanciya da. Gaba ɗaya sai ta ji ta damu. Ta daɗe idonta biyu, tana jira ta ga ko zai ta so, amma bai tashi daga gurin ba. Ta tashi a hankali ta nufe shi, har ta ƙarasa kusa da shi, ta kwanta. Ba ta ce masa uffan ba, ta caza masa hankali har ya biye mata. Bayan wani ɗan lokaci ya numfasa ya ce "Kin daina fushin?" "Ba kai ka saka na yi fushin ba? Amma ka yi haƙuri" "Me na yi miki?" "Me yasa za ka yi wannan yarinyar magana, har ta baka abu ka shigo mini da shi ɗaki?" "Ki na gurin kin san meyafaru?" Ta tashi daga jikinsa, ta ce "Ni ba na son jin meyafaru kawai babu ruwanta da kai, kar ka sake kula ta. Dan wallahi za ka iya nema ta ka rasa. Idan ka na son ta maye gurbina ba wani abu, ni zan iya tafiya ta na baku guri". "Ki daina faɗar abin da ba za ki iya aikatawa ba" "To ka ci gaba, zan baka mamaki kuwa" ta yi maganar tana tashi zaune, da nufin ta bar masa gurin." Amma ya riƙe ta gam, yana yi mata numfashi a wuya. A gurin suka kwana tare. Sai Asuba bayan ta yi wanka ta yi salla, ta koma kan katifa. Tana tsaka da bacci, ta ji yana tattaɓa ta, ta buɗe idonta ta kalle shi tana yanutsa fuska, saboda bacci ne a kan ta sosai. Wayarta ya ajiye mata a daidai kunnenta. Waƙar Ali jita ce take tashi, ta Aminiya. Shiru ta yi tana sauraren baitukan tana kallon kyakyawar fuskarsa da ya tsare ta da manyan idanunsa yana kallonta yana murmushi. Ita ma murmushin ta sakar masa, ta yinƙura ta tashi zaune, ita sam ba ta san da waƙar ma a wayar ba, kasancewar ba gwanar jin waƙa ba ce, amma har cikin zuciyarta take jin baitukan, tamkar shi ne yake rairai mata. Gaba ɗaya suka manta, da batun saɓanin da ya shiga tsakaninsu. (BAYAN MAKONNI BIYU) Gaba ɗaya Fadila ta rasa abin da yake yi mata daɗi, hankalinta ya ƙi kwanciya, tun da aka fara zaman kotu ta ji halin da ake ciki ta rasa abun da yake yi mata daɗi, yanayin yadda shari'ar ke gudana, za ka san da gayya ake yi, kawai shi ake son ya tozarta. Dan tashin farko Alƙali cewa ya yi a tsare shi, sai an ajiye wasu miliyoyi da kadarori, za a sake shi. Wasu tuhume-tuhumen ma, bai san da su ba, sai ranar da aka fara zaman kotun, sannan ya san da su. Har wasu maƙudan kuɗin, da ake zarginsa da sama da faɗi da su, a lokacin da yake shugabanci. Haka aka sayar da wasu daga kadarorinsa, aka bayar sannan aka ba da belinsa. Kotu ta yi umarnin a yi gwanjon kadarorinsa a sallami mutane kuɗinsu. ***** Alhaji Zailani, tare da Malam Gambo suka koma gurin da suka binne, jaririn nan, su ka tono ƙwarangwal ɗin sa, duk ya zagwanye. Suka saka a akwati, suka tafi da shi. Ɗakin da Malam Gambo yake tsaface-tsafacensa su ka je. Ya ɗaukko ƙwarangwal ɗin jaririn, aka babbaka wata irin wuta, aka ɗauki ƙwarangwal ɗin jaririn nan, ya rubuce jikin da sunan Alhaji Fatuhu, ya zana wasu hatimai, ya nannaɗe su a jikin ƙwarangwal ɗin aka saka a cikin wutar nan. Malam Gambo ya din ga zuba wani magani a cikin wutar, ya kawo wasu irin layoyi da ya zana hatimai daban-daban, ya din ga jefawa a cikin wutar. Alhaji Zailani kuma yana kiran sunan Alhaji Fatuhu. Sai da ƙwarangwal ɗin nan ya yi baƙi ƙirin, zaren da aka naɗe ƙwarangwal ɗin, ya kama jikin sosai. Ya kuma naɗe shi da wani zaren, sannan ya naɗe da likkafani, su ka je suka samu wata tsohuwar rijiya, suka jefa a ciki. Alhaji Zailani ya koma gida, kulle kansa a cikin ɗaki, ya din ga ɓaɓɓaka wata irin mahaukaciyar dariya, tamkar zai haukace. Ya ce "Alhaji Fatuhu ka gama yawo, yanzu sai na ga wanda za ka hura wa hanci, wai ka ga mai kuɗi kuma mai tsoron Allah, mu zuba mu gani. Wannan burin nawa ya cika, saura kuma waccan yarinyar" Alhaji Fatuhu kuwa, sun dawo daga kotu, Yayan Hajiya Suwaiba, lauyan da ya tsaya masa, yana ta yi masa nasiha a kan ya karɓi ƙaddara. Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi Barrister, na karɓi ƙaddarata. Na kuma gode wa Allah. Abu ɗaya nake tunani iyalina na saba musu da rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankali. Ina jin tausayinsu fiye da abin da ya same ni" Cikin tausaywa Barrister ya ce "Na sani Alhaji, tabbas kai mutum ne mai kyautatawa iyali. To yanzu ne ranar da za su nuna maka halacci su ma, a yi haƙuri" Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, mun gode Allah" Ji ya yi tamkar ana ƙoƙarin fizgo ƙwaƙwalwarsa. Ya yi wata irin zabura, ya riƙe kansa gam. Barrister ya ce "Alhaji lafiya dai?" Ya girgiza kai ya ce "Zafi nake ji" kafin ya kuma wata maganar, ya yanke jiki ya faɗi a gurin. Nana tamkar tana kallon talabijin, haka ta ga komai a cikin mudin da Ƙaisar yake nuna mata. Yana gefe yana rubutunsa, ita kuma ta zuba uban tagumi tana kallon mudubin. "Shigen irin wannan sihirin aka yi wa mijinki, shi ne wannan wutar da yake cewa tana ci a jikinsa. Sai dai shi nasa ya sha bambanda wannan ta wasu fannukan" Nana ta zabura ta kalle shi ta miƙe tsaye ta ce "Ƙaisar ka yi mini bayani, waye ya yi masa asirin? Kuma daga ina yake? Suwaye iyayensa?" Ya ɗago ya kalle ta ya ce "Kin manta sharaɗin ne?" Ta yinƙura za ta yi magana, ta yi ido huɗu da Sayyid, yana kusa da ita, ya zuba mata ido. Ta yi ajiyar zuciya. "Waye Ƙaisar?" Ya jefo mata tambayar babu zato babu tsammani. Ayshercool 08081012143. 45 Ganin abun ba na ƙare ba ne, ya sanya Nana yinƙurawa da ƙyar, jikinta babu ƙwari, ga sanyi tana ji. Ta ɗauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya sauwwaƙa a Alƙur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya ɗauke daga kanta, ta kaɗa ta raya amma ta kasa tuna komai. Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana ɗaukewa tamkar ta ci screen, abin fa ba taɓa yi ba sai yau. Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi wardrobe, ta buɗe watso kayanta ƙasa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faɗo daga cikin kayan. Nana ta durƙusa ta ɗauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta ɗora masa a ƙirjinsa. Kamar ta ɗora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci. Ta saka hannu ta ɗauki jakar, tana ƙare mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo. Bayan wani ɗan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon ɗakin, ya kalle ta ya yinƙura ya tashi, ya yi alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa. Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta gyara zamanta. Ta ce "Sayyid na kasa fahimtar abin da yake faruwa, ban sani ba ko na yi wani abun da na ɓata maka rai ba." Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, na wani ɗan lokaci, ba tare da ta yi tsammani ba ya yi magana. "Duk na yi ƙoƙarin ɓoye matsanancin farin cikin da na shiga, da na ji za ki haihu. Na kasa ɓoye damuwar da na shiga, da na ji na rasa abin da yake cikinki Ban san dalili ba kawai na ji ina matsanancin son, abin da ban taɓa gani ba, kuma yanzu na rasa shi, ba tare da na yi tsammanin hakan ba". Jiki a sanyaye Nana ta ce "Sayyid idan kai ka ce haka, ni na ce me?" Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ba za ki gane ba" ya tashi ya naɗa rawaninsa, ya fice daga ɗakin. Nana duk ta gaji da kwanciyar, ta yinƙura ta fara mayar da kayan wardrobe ɗin da ta watso. Ta ɗaga labulen window, dan iska ta ƙara wadatar ɗakin, kawai ta hango Siyama ta fito, sanye da doguwar riga da ɗan ƙaramin mayafi, ƙonuwar hannunta, ko gama warkewa ba ta yi ba. Sai dai Nana ta ga Sayyid take tunkara. Ganin tana tunkaro shi, ya sanya ya sunkuyar da kansa, daga kallon gurin da take tahowa. Sai dai tana ƙarasowa inda yake ta tsaya tare da yin murmushi ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai, ba tare da ya kalli inda take ba. "Amm dan Allah magana nake son mu yi" Ya ɗaga kai ya kalle ta cikin mamaki. Ta ɗan sunkuyar da kanta ta yi murmushi, ta ce "Dan Allah a abubuwan da suka ɗan faru, na rashin kyautawa da na yi maka, nake son ka yafe mini na san na yi kuskure, ka yi haƙuri" Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, ya mayar da kansa ya sunkuyar. "Ka yi magana mana" ta yi maganar cikin iyayi. Jinjina kai ya yi, yana ƙara kawar da kansa gefe. Ta sake cewa "To ai ba zan gane ba, idan ka haƙura, ka yi magana" "Ya wuce" Ta saki murmushi ta ce "Na gode sosai" ta juya ta koma cikin gida tana murmushi. Tabbas Buzun nan, irin mutanen da idan ka ɗora kana relationship da su, za a ga ka haye, ya haɗu ta kowane ɓangare. Ta yi maganar a zuciyarta. Nana rasa abin yi ta yi gaba ɗaya, ta ji ƙirjinta tamkar ta haɗiyi kibiya, wani abu ya tsaya a tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta. Ta zauna ta yi shiru, kawai ta ji sallamar Siyama. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta, sai dai ta kasa magana. Siyama ta zauna a kusa da ita ta ce "Ƙawata kwana biyu ba ki zo ba" Nana ta kalle ta ta ce "Kina lafiya?" "Ashe kuma ba ki da lafiya? Ya jikin naki?" Nana ta kalli Yusra ta ce "Ya aka yi ki ka san ba ni da lafiya? Waye ya gaya miki?" "Sai an gaya mini, ina ganin komai ai. Ko kin manta gidanmu ne nima? Allah ya baku wani." Nana ta ce "Ina cikin damuwa, dan Allah kar ki dame ni" Yusra ta yi murmushi ta ce "Na sani, amma kin san faɗa ya kaure a tsakanin Ƙaisar da dattijo? Kuma duk a kan ki?" Nana ta ce "Waye dattijo?" "Wanda ya ke kawo muku ziyara, da ke da mijinki, idan ba ki yi wasa ba, abu mara daɗi zai iya faruwa. Kodayake kar na yi shishshigi, gurin shiga hurumin da ba nawa ba. Amma abubuwa na daf da rikicewa. Me ma ya faru kafin ki yi ɓarin cikin jikinki?" Nana ta ɗan yi shiru tana son ta yi tunani, amma ba ta iya tuna komai ba, tana ɗagowa ta nemi Yusra ta rasa. Damuwa da rashin sanin abin yi, ga takaicin abin da ta gani ya haɗu ya sanya, ta tashi ta sake watso kayan wardrobe tana gyarawa. A cikin kayansa, ta ci karo da wata 'yar ƙaramar jakar fata, mai kama da laya, sai dai ta fi laya girma, da ya kan saka a wuyansa wasu lokutan. Ta yi shiru tana kallon jakar, ta yi ƙoƙarin ta ga ta ina za ta buɗe ta, ta ga mene ne a ciki, amma ta kasa. Ta ajiye ta, ta ci gaba da gyaran kayan, ta sake ɗaga wata riga, sai ga kuɗi turmus a ciki, na Nigeria da na Nijar. Har ta kai hannu za ta ɗauka, ta waiwaya ta gan shi a tsaye yana kallonta. Ta kalli kuɗin ta kalle shi. "Wannan kuɗin fa?" "Nawa ne?" Ta kalle shi ta ce "A ina ka samu?" Wani irin kallo ya yi mata, jin tambayar da ta yi masa. "Me ki ka ce?" Ba ta ji ko ɗar ba, ta sake maimaitawa. "A ina ka samu? "A ina ma samu? A gurin Habu. Ai ya gaya miki sana'ar da yake yi ko?" "Dama shi ya gaya maka, na je gidan kenan?" Ya girgiza kai yana mayar da kayansa ya ce "A'a" Da ta tuno yadda ta ga ya kalli Siyama, wani narkakken baƙin ciki yake tokare mata zuciya, kamar ta kwaɗe shi ko ta samu ta huce. ***** Alhaji Zailani ne, tare da Alhaji Fatuhu, zaune a kan fararen kujeru a wata farfajiya. Fuskar Alhaji Fatuhu, cike da ƙwarin gwiwa yake duban Alhaji Zailani ya ce "Zailani, babu komai dan Allah ka karɓi shugabancin nan, na san za ka iya. Da a bawa wani da ba a san yanayin amanarsa ba, ba gara a baka ba?" Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Haba Alhaji Fatuhu, yaya za a yi kana abokina, aminina a yi maka wannan cin kashin, kuma ka ce na karbi shugabancin nan na yi yaya da shi?" "Wallahi za ka iya. Na fi jin tausayin ƙanan 'yan kasuwa, idan aka bawa wanda bai dace ba shugabanci, za a karya masu ƙaramin jari" "Ƙananan 'yan kasuwar, da su suka yi wannan bita da ƙullin, da rubuta takardar lallai a sauke ka daga kan shugabancin nan, su ka ke tausayawa?" Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Nima da ƙaramin ɗan kasuwa ne, kafin Allah ya kai ni matsayin da nake a yanzu. Kuma na san ba dukkannin su ne, su ka yi mini haka ba. Ni dai fatana dan Allah ka karɓi tayin riƙon ƙwaryar shugabancin nan da aka yi maka" Alhaji Fatuhu ya ɓata lokaci sosai da sosai, kafin ya shawo kan Alhaji Zailani ya amince zai karɓa. ***** Gaddafi tuni ya koma gurin neman khɗinsa, saboda takaicin abubuwan suke faruwa a gidansu, ya fara damunsa. Baba ƙiri-ƙiri haka ya zuba ido ya yi shiru, ba ya iya cewa uffan, sai dai ya zuba ido a kan lamarin gidansa. Sai ma dai idan an dafa a zuba a ba shi ya ci. Sosai al'amuran gidan su Nana, suka fara canzawa kullum sai an ɗora abinci sau uku a rana saboda hidimar da Jamila take yi da su. Ƙarewa ta saka ana ta yi musu gyare-gyare a cikin gidan. Babban abin da yake damun Hajiya Sa'a da Jamila, shi ne yadda take ta ƙoƙarin janyo ta, cikin ɗaya mummunar ɗabi'ar da suke aikatawa ta lesbian. Sai dai Jamila ta kafe da kai da fata, taƙi amincewa da hakan. Sai da Hajiya Sa'a ta yi mamaki, saboda a ƙulumboton da ta yi wa Jamila, babu yadda za a yi ta iya kaucewa duk wata buƙata da ta zo mata da ita, amma ta kasa galaba a kan Jamila. Duk wani shashashanci da suke yi tana kallo, amma sam ba ta ji abin ya kama hankalinta ba, balle ta yi sha'awar aikatawa. Ta fito harabar gidan tana shirin tafiya, sai ga Mus'ab ɗa ɗaya tilo ga Hajiya Sa'a. Yana ganin Jamila ya tsaya. Duk da ba shiga harkarsa take yi ba, amma ta yi ƙoƙarin tare shi daga shiga cikin gidan, ya yi mummunan gani. "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau Jamila. Ya ki ke?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Amm Yaya Mus'ab ko za ka ajiye ni a hanya ne, ba na jin daɗi" Ya yi murmushi ya ce "Me zai hana? Bari na kai wa Mummy saƙon nan" Da sauri ta ce "A'a ai bacci take yi, ta ce kuma kar a tashe ta" "Ok to mu je na ajiye ki" ta yi gaba ya bi ta a baya. ***** Nana kuwa ita ma a wannan karon, basar da Sayyid ta yi, ta ƙi kula shi sam. Shi ma ya maze ya share ta. Baccinta ya yi nisa sosai ta ganta a daji ita kaɗai ƙwal. Ta ɗaga kanta ta ga wani ƙaton tsuntsu yana shawagi a saman kanta. Ba ta tsorata ba, ta ɗan ja numfashi ta ce "Ƙaisar laifin me na yi maka, ka zaɓi ka hukunta ni ta wannan hanyar? Me ya sa za ka zama dalilin zubewar cikina?" Tsuntsunan nan saukko ƙasa, ya yi girgiza Ƙaisar ya bayyana. Ya zauna yana fuskantar ta ya ce "Komai ma kin yi mini, babu abin da ba ki yi mini ba, abin da ya dace nake yi" "Ba ka tsoron Allah Ƙaisar, ba ka tsoron Allah ya kama ka da hakkina, abubuwan da ka ke aikata mini na cutarwa. Kai ka yi mini, wannan tsohon ya yi mana, mijin nawa ma na fara daina gane kansa. Ya fara ƙoƙarin cutar da ni" Ya ɗan kalli saman bishiya sannan ya ce "Babu abin da ban gaya miki  ba ai. Amm kin tuna abin da na nuna miki, Alhaji Zailani yana yi wa abokinsa? Da gaske ya faru a zahiri. Kuma tsafi gaskiyar mai shi, domin kuwa al'anura sun fara juya wa Alhaji Zailani baya. Nan zuwa wani ɗan lokaci zai rasa komai nasa. Lafiyar sa da dukiyarsa." Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Dan Allah idan ka na dama ka yi wani abu a kai mana. Ka tona abin da aka yi masan" Ya girgiza kai ya ce "Ba ma shiga abin da babu ruwanmu, ko warware wani abu da aka yi wa wani, muddin ba yarjejeniya aka yi damu, aka bamu damar yin hakan ba. Zan iya taimakonsa ne kawai bisa amincewar ki, da kuma umarnin ki. Zan gaya miki inda abin yake ya saka a je a tone, ko kuma ki je ki tone. Idan ba haka ba nan da kwanaki uku rak za a tono ƙwarangwal ɗin yaron nan, a kuma yin wani tsafin da ita." Har Nana ta motsa baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa, dan tana amincewa a taimaki Alhaji Fatuhu ba ta san me zai biyo bayan hakan ba, ka iya tabbatar da buƙatar Ƙaisar a kanta. AREWABOOKS Kasancewar ba ta salla, ya sanya har gari ya waye tana bacci. Bayan ta yi wanka ta rasa abin yi, ta ɗebo kayan wankin ta, ta shiga banɗaki ta wanke. Nasa dama Habu ne yake zuwa ya ɗauka. Ta gama, ta saka hijjabinta, ta ɗaukko bokitin, ta fito daga ɗakin. Yana kan kujera a daf da gate ɗin, yana aikin dafa shayi, gefensa ga radio tana yi. Ba ta kula shi ba, ta zagaya baya, ta yi shanyar kayan nata. Ta fito ta ja ta yi turus tana kallon ikon Allah. Siyama ce a tsaye, da ɗan ƙaramin flask a hannunta. Nana ba ta san me take ce masa ba, ta ga ya sauke rawanin fuskarsa ya saka hannu ya karɓi flask ɗin, ya yi magana. Kawai ta shiga ɗaki, a ƙofar banɗakin, ta jefar da bokitin jin wani irin matsanancin ɗaci yana taso mata. Ta cire hijjabinta kawai ta tsaya ta riƙe ƙugunta, ta tsaya tana jiran ya shigo, amma bai shigo ba, zuciyarta ta din ga raya mata, yana can su na hira da Siyama. Kawai ta buɗe ƙofa ta shiga banɗaki, sai dai ta rasa uban abin da ya kai ta banɗakin ma. Ta gama tsayuwarta ta fito daga banɗakin. Tana fitowa ta gan shi a tsaye, da flask ɗin a hannunsa, ya nufo ta zai yi magana, ta riga ta ɓarar da flask ɗin. Farfesun kifi da dankalin ya tarwatse a ƙasa. Ya kalli gurin ya kalli yadda take huci, zuciya ta yinƙuro shi, sai dai ya ga Ƙaisar a bayan Nana, ya zubo masa ido. Ya haɗiye wani abu, mai ɗaci. Ya kalli Nana ya ga yadda idonta ya rufe, ta fara ƙoƙarin wuce shi ta fita. Ya riƙe ta yana ci gaba da kallon Ƙaisar. Ya kwantar da Nana a kan katifa, idanunta a rufe sai hawaye da yake fita, ta gefen idonta. Ya durƙusa ya gyara gurin ta ɓarar da abincin. Ya sake kallon yadda Ƙaisar ya jingina da bango, ya tsaya a kan Nana. "Tun da ka yi abin da ka yi, ya kamata ka bani guri" Ya yi maganar yana kallon inda Ƙaisar yake. "Gurin ka na zo ne? Idan ba gurin ka na zo ba, sai ka ƙyale ni" "Ka zubar mini da ciki, kuma saboda rashin kunya, ka zo haɗa fitina a tsakaninmu" Ƙaisar ya yi murmushi ya ce "Ina mamakin yadda Aljani yake shiga al'amuran bil adama har haka. Kai ka fara lalata cikin, ni kuma na zubar da shi." Sayyid ya shafi fuskarsa ya ce "Waye Aljanin a tsakanin ni da kai?" Ƙaisar ya ce "Ba da kai nake ba. Ka san da wanda nake" Buzu ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ka gaya mini, wane ne ni? Daga ina nake? Kuma suwaye iyayena? Me ya kawo ni ƙasar nan?" "Ba ni za ka yi wa wannan tambayar ba, zuwa yanzu na san ka bambance tsakanin ni da shi" "Haka ne, na banbance, yanzu ka tafi ka bani guri, ka bar ni da matata" "Ba zan tafi ba" Buzu ya durƙusa ya kwance rawanin kansa, ya cire rigar jikinsa, ya ɗago Nana da take cikin yanayin gushewar hankali. Ya fara cire kayan jikinta, tamkar an aiko wa Ƙaisar saƙon mutuwa ya murtuke fuska. Bai tsinke da lamarin ba, sai da Sayyid ya rungume Nana yana sumbatar bakinta. Jikin Nana ya din ga rawa, tana fatan ta saka baki a maganganun su, amma ta kasa, tana ganin duk abin da yake faruwa, amma tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsa ko da ƙaramin yatsanta. Da ƙyar ta fizgo numfashi ta tashi a zabure, ta ce "Sayyid" ya taso da sauri daga inda yake zaune ya nufo ta. Ya kasa magana, ita ma kuma ta kasa cewa komai, sai rarraba ido da take yi, ta yi zaton mafarki ne, amma ta ji ɗakin yana ƙarnin kifi, ga kuma flask ɗin da ya shigo da shi. Da ƙyar ta ce "Ina wanda ku ke magana da shi?" Ya kalli ɗakin ya ce "A ina?" Ta kalli daidai gurin da Ƙaisar ya tsaya, ta ce "Wanda ya tsaya a nan, wani dogo" "Ban yi magana da kowa ba" ya yi maganar yana girgiza mata kai. Ta yi ajiyar zuciya ta ja ta zauna, tana jin kanta yana ciwo. **** "Suwaiba" Alhaji Fatuhu ya kira sunanta. Ta kalle shi ta ce "Ya dai?" "Ba na jin daɗin jikina ne, kuma wani abu ne yake damuna" "Me ke nan?" "Ƙara ta za a kai kotu" Ta waro ido ta ce "Kotu kuma? Me ka yi?" "Kayan nan da suka yi ɓatan dabo, ranar Litinin zamu shiga kotu da 'yan kasuwa. Kujerata ma an sauke ni. Amma bai dame ni ba, kayan mutane nake tunani" Ta kwaɓe baki ta kaɗa kai ta ce "Ai Alhaji Fatuhu duk ɗan da ya hana uwassa bacci, shi ma ba zai yi ba. Babu irin wahalar da bamu sha tare ba, amma abin Duniya na samuwa, ka auro yarinya ƙarama saboda ka ƙuntata mini, ka ci duniyarka da tsinke. Ai ga shi kai ma Allah ya kama ka" Ya yi zuru da ido yana kallonta. Ta gama maganganunta ta bar masa ɗakin. Tana zuwa bedroom ɗin ta, ta rufe ƙofa, hawayen da ta maƙale ta ba su damar gangarowa. Ta hau nanata "Innalillahi wa innalillahi raji'un" Ta ɗauki wayarta ta kira Yayanta. Yana ɗagawa ya ji muryarta wani iri, ya ce "Lafiya kuwa?" "Yaya Baban su Raudah wai za a kai kotu, 'yan kasuwa su na zargin ya cinye musu kuɗi, dan Allah ka yi wani abu a kai dan Allah" "To ikon Allah, amma ba sai ki bari sai da Safe ba, kya kira ni. Amma ku kuma kin tabattar bai ci kuɗin ba?" Suwaiba ta ce "Yaya kai ma ka san shi da gudun Duniya, da abin mutane wallahi zan iya rantsuwa bai ci kuɗin kowa ba" "Ki bari zan kira ki da Safe" ta ajiye wayar jiki a sanyaye cikin damuwa. Kasancewar a sashen Fadila yake, ta fahimci damuwa a tattare da shi, sai dai fafur ya ƙi gaya mata, ya lallaɓa ta ta yi bacci. ***** Da daddare Nana ta kasa karanta Alqur'ani, amma wannan karon ta samu ta saka a wayarta, ta daɗe tana saurara tana jin nutsuwa na ratsa ta. Kasancewar jini ya ɗauke, ya sanya ta yi sallar Isha'i, ta kwanta karatun Alqur'ani yana tashi ƙasa-ƙasa a wayarta. Tana kallon Sayyid, ya shirya ya kwanta a ƙasa, gurin da yake kwanciya da. Gaba ɗaya sai ta ji ta damu. Ta daɗe idonta biyu, tana jira ta ga ko zai ta so, amma bai tashi daga gurin ba. Ta tashi a hankali ta nufe shi, har ta ƙarasa kusa da shi, ta kwanta. Ba ta ce masa uffan ba, ta caza masa hankali har ya biye mata. Bayan wani ɗan lokaci ya numfasa ya ce "Kin daina fushin?" "Ba kai ka saka na yi fushin ba? Amma ka yi haƙuri" "Me na yi miki?" "Me yasa za ka yi wannan yarinyar magana, har ta baka abu ka shigo mini da shi ɗaki?" "Ki na gurin kin san meyafaru?" Ta tashi daga jikinsa, ta ce "Ni ba na son jin meyafaru kawai babu ruwanta da kai, kar ka sake kula ta. Dan wallahi za ka iya nema ta ka rasa. Idan ka na son ta maye gurbina ba wani abu, ni zan iya tafiya ta na baku guri". "Ki daina faɗar abin da ba za ki iya aikatawa ba" "To ka ci gaba, zan baka mamaki kuwa" ta yi maganar tana tashi zaune, da nufin ta bar masa gurin." Amma ya riƙe ta gam, yana yi mata numfashi a wuya. A gurin suka kwana tare. Sai Asuba bayan ta yi wanka ta yi salla, ta koma kan katifa. Tana tsaka da bacci, ta ji yana tattaɓa ta, ta buɗe idonta ta kalle shi tana yanutsa fuska, saboda bacci ne a kan ta sosai. Wayarta ya ajiye mata a daidai kunnenta. Waƙar Ali jita ce take tashi, ta Aminiya. Shiru ta yi tana sauraren baitukan tana kallon kyakyawar fuskarsa da ya tsare ta da manyan idanunsa yana kallonta yana murmushi. Ita ma murmushin ta sakar masa, ta yinƙura ta tashi zaune, ita sam ba ta san da waƙar ma a wayar ba, kasancewar ba gwanar jin waƙa ba ce, amma har cikin zuciyarta take jin baitukan, tamkar shi ne yake rairai mata. Gaba ɗaya suka manta, da batun saɓanin da ya shiga tsakaninsu. (BAYAN MAKONNI BIYU) Gaba ɗaya Fadila ta rasa abin da yake yi mata daɗi, hankalinta ya ƙi kwanciya, tun da aka fara zaman kotu ta ji halin da ake ciki ta rasa abun da yake yi mata daɗi, yanayin yadda shari'ar ke gudana, za ka san da gayya ake yi, kawai shi ake son ya tozarta. Dan tashin farko Alƙali cewa ya yi a tsare shi, sai an ajiye wasu miliyoyi da kadarori, za a sake shi. Wasu tuhume-tuhumen ma, bai san da su ba, sai ranar da aka fara zaman kotun, sannan ya san da su. Har wasu maƙudan kuɗin, da ake zarginsa da sama da faɗi da su, a lokacin da yake shugabanci. Haka aka sayar da wasu daga kadarorinsa, aka bayar sannan aka ba da belinsa. Kotu ta yi umarnin a yi gwanjon kadarorinsa a sallami mutane kuɗinsu. ***** Alhaji Zailani, tare da Malam Gambo suka koma gurin da suka binne, jaririn nan, su ka tono ƙwarangwal ɗin sa, duk ya zagwanye. Suka saka a akwati, suka tafi da shi. Ɗakin da Malam Gambo yake tsaface-tsafacensa su ka je. Ya ɗaukko ƙwarangwal ɗin jaririn, aka babbaka wata irin wuta, aka ɗauki ƙwarangwal ɗin jaririn nan, ya rubuce jikin da sunan Alhaji Fatuhu, ya zana wasu hatimai, ya nannaɗe su a jikin ƙwarangwal ɗin aka saka a cikin wutar nan. Malam Gambo ya din ga zuba wani magani a cikin wutar, ya kawo wasu irin layoyi da ya zana hatimai daban-daban, ya din ga jefawa a cikin wutar. Alhaji Zailani kuma yana kiran sunan Alhaji Fatuhu. Sai da ƙwarangwal ɗin nan ya yi baƙi ƙirin, zaren da aka naɗe ƙwarangwal ɗin, ya kama jikin sosai. Ya kuma naɗe shi da wani zaren, sannan ya naɗe da likkafani, su ka je suka samu wata tsohuwar rijiya, suka jefa a ciki. Alhaji Zailani ya koma gida, kulle kansa a cikin ɗaki, ya din ga ɓaɓɓaka wata irin mahaukaciyar dariya, tamkar zai haukace. Ya ce "Alhaji Fatuhu ka gama yawo, yanzu sai na ga wanda za ka hura wa hanci, wai ka ga mai kuɗi kuma mai tsoron Allah, mu zuba mu gani. Wannan burin nawa ya cika, saura kuma waccan yarinyar" Alhaji Fatuhu kuwa, sun dawo daga kotu, Yayan Hajiya Suwaiba, lauyan da ya tsaya masa, yana ta yi masa nasiha a kan ya karɓi ƙaddara. Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi Barrister, na karɓi ƙaddarata. Na kuma gode wa Allah. Abu ɗaya nake tunani iyalina na saba musu da rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankali. Ina jin tausayinsu fiye da abin da ya same ni" Cikin tausaywa Barrister ya ce "Na sani Alhaji, tabbas kai mutum ne mai kyautatawa iyali. To yanzu ne ranar da za su nuna maka halacci su ma, a yi haƙuri" Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, mun gode Allah" Ji ya yi tamkar ana ƙoƙarin fizgo ƙwaƙwalwarsa. Ya yi wata irin zabura, ya riƙe kansa gam. Barrister ya ce "Alhaji lafiya dai?" Ya girgiza kai ya ce "Zafi nake ji" kafin ya kuma wata maganar, ya yanke jiki ya faɗi a gurin. Nana tamkar tana kallon talabijin, haka ta ga komai a cikin mudin da Ƙaisar yake nuna mata. Yana gefe yana rubutunsa, ita kuma ta zuba uban tagumi tana kallon mudubin. "Shigen irin wannan sihirin aka yi wa mijinki, shi ne wannan wutar da yake cewa tana ci a jikinsa. Sai dai shi nasa ya sha bamban da wannan ta wasu fannukan" Nana ta zabura ta kalle shi ta miƙe tsaye ta ce "Ƙaisar ka yi mini bayani, waye ya yi masa asirin? Kuma daga ina yake? Suwaye iyayensa?" Ya ɗago ya kalle ta ya ce "Kin manta sharaɗin ne?" Ta yinƙura za ta yi magana, ta yi ido huɗu da Sayyid, yana kusa da ita, ya zuba mata ido. Ta yi ajiyar zuciya. "Waye Ƙaisar?" Ya jefo mata tambayar babu zato babu tsammani. Ayshercool 08081012143 CHAPTER 46. Hantar cikinta ce ta kaɗa, ta kalli cikin ƙwayar idonsa, jin yadda ya jefo mata tambayar, babu tsammani ba tare da ta shirya hakan ba. Wani irin gumin tsoro da fargaba, ya fara tsatstsafo mata, saboda ba ta san ta ina yakamata ta fara yi masa bayani ba, ba ta san ma me za ta ce masa, da zai gamsar da shi, amsar da za ta ba shi ba. Sai dai a ina ya san Ƙaisar, har yake tambayarta waye shi? Ta tambayi kanta. Ga mamakinta, sai ta ga ya tashi ya yi miƙa, ya fice daga ɗakin ba tare da jiran amsar da za ta ba shi ba, ko kuma bayanin da za ta yi masa ba. Ta tashi ta kimtsa jikinta, babu jimawa sai ga Habu ya zo, Sayyid ne ya fara ɗaga labule, ya ganta a kintse a cikin hijjabi, sannan ya ba wa Habu damar shiga. Sama-sama suka gaisa da Habu, ita ƙasan zuciyarta tana tsoron kishin Sayyid, shi ma Habun haka. Ya ajiye wani galan a gaban Sayyid, ya ce "Saƙonka nan, an kawo shi ɗazu fresh ne" Sayyid ya ce "Na Husnah ne" Nana ta saci kallonsa, ko za ta ga ya canza mata, saboda tambayar da ya yi mata, kuma bai jira ta amsa masa ba, amma ta ganshi normal. Ta ɗan yi murmushi ta ce "Me na samu?" Habu ya ce "Nonon Raƙumi ne da ake kawo miki, ga kuma dabino da zuma, fresh masu kyau da aka kawo daga Nijar" Nana ta ce "To Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai da sosai. Habu wai kai ka ke ba shi kuɗi? Na ga kuɗi masu yawa a kayansa, ya ce kai ne ka ba shi" Habu ya yi murmushi ya ce "Ba ki yadda da abin da ya faɗa ba ne? Ai mutum mai iyali dole sai da kuɗi, kuma na gaya miki mu na harkar kawo dabino, zuma, cukui kayan shayi, asuwaki mazarƙwaila daga can Sahara. Nana ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta ce "To ya batun binciken da ka ke yi, a kan danginsa, ya ce mini ka na bincike a kai." Ya ɗaga kai, suka yi ido huɗu da Sayyid sannan ya ce "Ina nan ina yi, kuma in sha Allah duk bayanin da na samo zan sanar da ke" Nana ta ce "Ma sha Allah, kuma Habu duk 'yan garinku Buzaye, su na jin Hausa? Idan ba sa ji da yaya za mu yi magana idan an gano su?" Habu ya yi murmushi ya ce "Mu ba ga shi mu na ji ba? Hausa na cikin manyan yaruka a Nijar, da kusan kowa yana jin yaren. Dan haka kar ki damu, tun da yana jin Hausa, danginsa ma na san su na ji" "To Allah ya sa su karɓe ni, idan an gano su. Ina Sule kwana biyu?" "Ya je gida, ai shi ya taho da wannan kayan ma" A wannan karon Sayyid bai kula su ba, kuma bai sanya musu baki a hirar ta su ba, har suka yi suka gama. Ta tashi ta tattaro masa kayan wankin Sayyid ta ba shi, ya yi musu sallama. Bayan ya tafi, Sayyid ya ɗauki kayan shayinsa ya koma bakin gate. Nana ma ganin babu abin da za ta yi, kawai sai ta bi shi. Ta samu guri ta zauna a gefensa, ta ɗan zuba masa ido, amma bai kula ta ba, ya mayar da hankali a kan shan shayinsa. "Sayyid" ya ɗago ya kalle ta. "In tambaye ka?" Ya jinjina kai alamar eh. A ɗan sanyaye ta ce "Yau na yi magana da Habu, na ga ba ka yi fushi ba" Kawai ya yi murmushi ya ce "Kina so na yi ne?" Ta ce "A'a, dama bai kamata ka din ga yi ba, tun da sukaɗai mu ke gani a matsayin danginka. Su Habu 'yan Aljanna ne, ina yabawa ɗawainiyar da suke yi da mu, mussaman shi, alhalin ba ku da alaƙa" "Ke ma 'yar aljanna ce, in sha Allah " "Kai ma haka" ta faɗa tana murmushi. Sai kuma fuskarta ta bayyanar da damuwa, ta ce "Sayyid, ciwon nan naka yana bani mamaki, ka san komai na rayuwa na yau da kullum amma sanin waye kai kawai ka manta. Dan Allah idan ban takura maka ba, ka gaya mini abin da za ka iya tunawa, bayan da ka buɗe ido ka ganka a wannan yanayin " Ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya kalle ta ya ce  "Kawai na ji abu ya sarƙe mini numfashi,  tari ya kama ni, ƙura tana shigar mini hancina da bakina. Na yi ƙoƙarin buɗe idona, amma abu ya gagara, saboda wata irin ƙura da na gani ta turnuƙe gurin,, da wani irin sauti da tashin ƙurar yake bayarwa. Ba na iya gane komai. Na takure jikina na lokacin da ban san adadinsa ba, daga bisani na ji shiru. Na sake buɗe idona a hankali, sai na ga ƙurar ta lafa, na ganni a cikin sahara, da wani tsoho mai matuƙar tsufa, hannunsa riƙe da sanda, gemunsa fari tas har cikinsa, ga wasu irin kaya da suka yi mugun tsufa a jikinsa. Nan na fara tunanin waye ni, ya kuma aka yi na ganni a wannan gurin, amma na kasa tuna komai. Na yi ƙoƙarin tuna sunana, da inda na fito, amma ban ji ko kusa da tunawa na yi ba. Na kalli tsohon nan, da niyyar na tambaye shi, amma na kasa magana, na yi, nayi amma na kasa ce masa komai, shi kuma bai daina kallona ba. Wata irin ƙishirwa ta kama ni, ga yunwa ina ji, amma na kasa magana. Can na hango wani mutum ya nufo ni a kan raƙumi, ya saukko daga kan raƙumin ya nufo ni da sauri. Yana ta yi mini magana, amma ba na gane abin da yake faɗa. Ya ɗago ni ya bani ruwa na sha. Sai na fuskanci kamar ba ya ganin tsohon nan, nikaɗai nake ganinsa. Ban san meyafaru ba. Na buɗe ido na ganni a wani guri, ya ce mini Nigeria ce, tun  daga nan yake ta ɗawainiya da ni" Duk wannan bayanin da yake yi wa Nana, daki-daki yake yin sa, yana yi yana hutawa, kuma a nutse babu gaggawa. Ta jinjina kai ta ce "Kenan mai ka na ganin, wannan tsohon kenan?" "Ki na ganinsa ne ke ma?" Ta jinjina masa kai, sannan ta ce "Me yasa ka tambaye ni waye Ƙaisar?" Ya yi murmushi tare da sunkuyar da kansa, ya kalle ta ya ce "Tambayoyinki sun yi yawa Rayuwata" "Dan Allah ka bani amsa Sayyid, wasu lokutan ina shiga ruɗu a kan abubuwan da suke gudana, ba na ganewa sosai, sai na ga kamar taɓin hankali ne da ni" "A'a lafiyarki ƙalau, ni ne mai matsala, ni nake da taɓin hankali na sani" "A'a lafiyarka ƙalau" Ya ɗan kurɓi shayin hannunsa ya  ce "Ai na san gaskiya, ana kuma faɗa ina ji, ba ni lafiyar ƙwaƙwalwa ina da taɓin hankali" Ta gyara zamanta, ta ce "To wai gurin masu magani da ku ka je, babu inda aka yi nasara, ko alamun nasara?" "Eh" ya amsa a taƙaice. "Amm Sayyid" "Kaiii na gaji, dan Allah ki daina tambayar nan, ba kya gajjya ne?" Ta yi murmushi ta ce "Idan zan kwana ina magana, in dai da kai ne, ba zan taɓa gajiya ba. Sannan ka yi haƙuri abin da na yi maka dan Allah, na zubar da abin da ka shiga da shi ɗakinmu, raina ya ɓaci ne, kuma na ga ban kyauta ba" "Kuma ke ta ce na kaiwa, shi yasa na karɓa" Ta ce "Makirci ne kawai na mace, amma  na ga alamar ta girgiza da ganinka, kamar ta fara son ka ne ma" Ya yi shiru bai ce komai ba. "Ba zaka kula ni ba?" "Me zan ce?" "To kar ka kulanin, kuma wallahi naga abin da raina zai sosu, sai ka neme ni ka rasa" Kawai ya sunkuyar da kai yana murmushi. "Dariya ma na baka ko? Amma idan ni ce sai ka wani haɗe rai, ka yi ta yi mini faɗa" "Ki yi shiru, ki huta" "Na ƙi yin shirun, wallahi idan sonka take yi, sai kun ga abin da ba ku zata ba" Ya ce "Ai na ma gani" Siyama ce ta nufo su, Sayyid ya yi hanzarin mahar da takunkumin fuskar ya rufe fuskar sa. Ba ta kula Sayyid ba ta ce "Nana, yau girki nake son yi, ki zo mu je mu yi" Nana ta yi murmushi ta ce "Ma sha Allah, bari na zo" ta yinƙura ta tashi, Sayyid ya bi ta da kallo. Suka shige cikin gidan tare da Siyama. Siyama na matuƙar jin daɗin hira da Nana, gani take kamar ta samu sauƙi, tun da Nana tana jin irin abin da take ji. Kuma tattaunawar da suke yi. "Kamar haka da nake yi wa Sagir girki, na zo ba na iya yi, saboda zuciyata raya mini take, na cakawa kaina wuƙa, ko na ƙona kaina da ruwan zafi" Nana ta ce "Subhnallah. Yaushe wai ki ka fara ciwon nan ne?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Lokacin da su Mami, suka tare a gidan nan, na zo ganin gida, lokacin na dawo daga umara. Kawai daga tafiyata gida, na din ga jin tsoro cikin dare. Dama da ciwon kai na tafi gida. Ina bacci sai na ji ana shafa ni da daddare. Sosai fa nake jin ana taɓa ni, idan na faɗa ba a yadda. Lokacin mijina yana neman aure. Aka ce kishi ne ya sa  dan Allah ba zan yi kishin mijina ba ina son sa Nana?" Nana ta ce "A'a dole ki yi kishi mana, tunda ki na son sa" "To daga ƙarshe, mamansa ta ce sai ya rabu da ni, wannan kishin idan ban kashe kaina ba, zan kashe shi ko matarsa. Aikuwa ya sake ni" Nana ta numfasa ta ce "Ki yi haƙuri ki ci gaba da addu'a, idan ki  na da rabo sai ki ga kin koma" "Anya kuwa Nana? Mami ta ce babu ni babu shi, ba shi da mutunci da shi da iyayensa da 'yan uwansa" "Kar ki damu fa, idan da rabo sai ki koma, amma a yanzu dai, ki fauwwala wa Allah komai" Ta jinjina kai ta ce "Haka nex Muryar Hajiya Halima suka ji, tana ƙwala wa Yusra kira. Yusra ta amsa da "Na'am, gani nan" "Me ki ke yi a kitchen ne?" Ta yi maganar tana shigowa kitchen ɗin. "Girki mu ke yi, ni da Nana" Nana ta ce "Hajiya ina wuni?" "Lafiya ƙalau Nana, lallai taku ta zo ɗaya da Yusra, na ga tana ɗan sakin jiki ta yi walwala da ke, dan Allah ki kula saboda kar ta yi wani abin da zai cutar da ita, ba ta da cikakkiyar lafiya. Ni fita zan yi" Nana ta ce "Tom, a dawo lafiya" Ta amsa da Allah ya sa, ta bar kitchen ɗin. Suka girka faten dankali da kifi, yanayin yadda Yusra ke girki, ya tabattarwa Nana, yana daga cikin abubuwan da take son yi. Su ka yi lemon mangwaro, suka saka a fridge ya yi sanyi. Bayan sun kammala, ta kalli Nana ta ce "Ki zuba kai kai wa mijinki, kar ya huce" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a mu ci kawai, zai iya gwale ni ya ƙi ci" Yusra ta ce "A'a, zai ci. Duk abin da ki ka ci, ki din ga ba shi, za ki ga ya ƙara son ki sosai da sosai. Da haka muke yi ni da Sagir" cikin tausayawa Nana take kallonta, alamu, sun nuna har da zafin rabuwa da mijinta ya sanya larurata yin gaba. Saboda aljani ya fi samun damar shafar mutum, a lokutan fushi, damuwa, ko kuma najasa. Haka ta takura wa Nana, ta zuba abincin a flask, ta fita. Yana zaune yana facing hanyar shiga gidan, ta tsaya cak tana kallonsa, hakan ya sanya shi tasowa ya nufo ta. Ya ƙaraso, ta nuna masa guri ta ce ya zauna, ya zauna ya dube ta ya ce "Kin bar ni, nikaɗai" Ta buɗe faten dankalin, ta ce "Abinci zan baka" Ya kalli harabar gidan ya ce "A nan?" "Eh mana, ba kowa ai. Bai kamata a ce kullum daga ɗaki sai bakin gate ba, canza abubuwa yana sanya nishaɗi a zukata" Ta sauke masa rawaninsa, ta ɗebo dankalin a cokali, ta kai bakinsa. Ya buɗe ta saka masa. Bayan ya haɗiye ya ce "Ba ke ki ka yi ba" "Ni na yi " "Ba ke ba ce. Babu yaji, babu tafarnuwa, bai ji maggi sosai da sosai ba" Ta kwashe da dariya, ta ce "Sayyid ko numfashi na yi, sai ka gane, ka haddace komai nawa. To na ji amma tare muka yi ai" ya ci gaba da buɗe bakinsa, yana karɓar Abincin. Tana yi tana cire masa ƙayar kifin da ba ta fita ba. Ya gama ta ba shi lemon ya shanye, ya ce "Na gode sosai" Ta kalle shi ta ɓata fuska, ta ce "Ba ka ce ba" Fuskarsa ɗauke da murmushi, ya kamo fuskarta, ya sumbaci goshinta ya ce "Allah ya yi wa rayuwata albarka" "Wannan ai wayo ne, amma shikenan na gode" gani ta yi ya tsaya cak, yana kallon guri ɗaya. Ta waiwaya sai ta ga Siyama ce a bayanta, hannunta riƙe da wayarta ta kara ta a kunnenta. Wani abu ya soki zuciyar Nana,ganin kallon da take yi masa. Bai yi magana ba, ya nufi gurin da yake zaune da farko. Nana ma ba ta kalli Siyama ba, ta wuce ta, ta shige. Hira ta je suka ci gaba da yi da Yusra. Sai dai duk wata hirar ta Yusra shirme ce, amma ta fitowa da Nana abubuwa da dama, da suke damunta. Sai dai galibin hirar ta ta,na zamanta da mijinta ne, da irin son da take yi masa. Sai da ta ji tamkar ta ce wa Hajiya Halima, su haɗa wa Yusra maganin da na gargajiya bisa doron addini. Amma yanayin yadda take ganin gidan, sun ginu a kan doron aƙidar boko, babu lallai su amince da hakan. Sai da ana daf da fara kiraye-kirayen sallar magariba, sannan Nana ta fito. Har ta wuce lungun da shuke-shuke suke, ta koma da baya ta leƙa, ta ganshi a gaban famfo, yana alwala. Ta cire takalmanta, cikin sanɗa ta nufe shi, tana zuwa daf da shi ta faɗa bayansa, ta maƙale wuyansa. "Ya aka yi ne?" "Wai ba ka ji tsoro ba?" Ya yi dariya, ya ce "Tun lokacin da ki ka fito daga cikin gidan, nake jin kina kusanto ni a jikina" "Ka daina tsorata ni, da wannan maganganun na ka" "Ɗaga ni, alwalata za ta karye" Ta noƙe kafaɗa ta ce "A'a" "Dan Allah" Ta sake cewa "A'a" ya saka hannunsa ya jawo ta daga bayansa, ya tara hannunsa a famfon, ya taro ruwa ya watsa mata a fuska. Ba shiri ta miƙe tana ajiyar zuciya. Ba ta farga ba ya ɗauki tiyon da yake bawa flours ruwa, ya fesa mata a jikinta. Tamkar ta fashe da kuka ta ce "Kuma idan na rama ka hau karkarwa ba ka son sanyi ko?" Wani irin nishaɗi ne yake ratsa zuciyarsa, a wannan yanayin da suke. Siyama na ta corridor ɗin  falon saman bene, tana hango su. Mutumin da ba ya magana, balle ya baka wata dama a tattare shi, shi ne yake wannan abubuwan haka. Ya ajiye tiyon, ya ƙarasa gurin Nana, ya rungumo ƙugunta, da jiƙaƙƙun kayan jikinta, ya fara kissing din ta. A tsorace ta ce "Sayyid, kar a ganmu fa, kuma ka ɓata alwalarka". "Bai kamata a ce kullum a ɗaki muke yi ba, yin abubuwa a wasu guararen, yana sanya wa zuckata nishaɗi" A tsorace ta ce "To ai banda irin wannan" Ya riƙo hannunta, suka nufi ɗakinsu. Sallar magariba sai da Isha'i suka haɗa su ka yi, a ɗaki wajen ma ya ƙi fita, sai dai idan an yi horn,ya je ya buɗe, ya dawo ya liƙe mata. Siyama kuwa zaman dirshen ta yi a kan ɗaya daga kujerun Falon, zuciyarta na raya mata abubuwa daban-daban, a kan Sayyid. Babu babban abin da ya tsaye mata, irin sumbatar da ta ga yana yi wa Nana. Wani irin takaici mara misaltuwa ya mamaye mata zuciya. Sam Nana ba ta dace da samun irin wannan damar ba  Tana ji a jikinta, za ta iya kashe ko nawa ne, ta raba shi da gadi, muddin za ta samu abin da take so a tattare da shi. **** Alhaji Fatuhu kuwa, al'amura sun rincaɓe, duk iya ƙoƙarin likitoci suka yi, amma suka kasa gano abin da yake damunsa. Lokaci lokaci, ya kan yi jijjiga da kururwar jikinsa na wani irin matsanancin ciwo, mara misaltuwa. Wasu na zuwa duba shi tsakani da Allah su tausayawa masa, wasu kuwa gani suke yi, zafin abin da ya faru ne. Ya gaza yin tawakalli. Ga kadarorin sa, ana ta ɗagawa ana sayarwa, da an ɗaga kadararsa, an karyar da ita, abokansa na kusa da shi, suke yin wuf su saye da arha. Sai dai duk lalacewa, ba a rasa na Allah. A hakan an samu waɗanda suka tausaya masa, suka yafe masa kuɗaɗensu, aka kafa gidauniyar neman tallafi, domin taya shi biyan basussukan da suka narke masa a ka. Gaba ɗaya Fadila ta fita daga hayyacinta, duk ba ta cikin nutsuwarta. Ba ita ba, ita kanta uwargidansa da yaransa duk hankulansu a tashe yake, duk da wani ɓangaren na Hajiya Suwaiba, ta zuba ido, dan ta san babu lallai Fadila ta ci gaba da zama da shi, tun da dama tun farko tana kyautata zaton saboda kuɗinsa ta aure shi, yanzu kuma ga jarrabawa ta zo. Hajiya Sa'a cikin damuwa ta kalli Jamila ta ce "Jamsy, ko za ki raka ni Asibiti, gurin dubiyar nan" Jamila ta girgiza kai ta ce "A'a a dawo lafiya, ba na son zuwa na ga abin tausayin nan, ranar da muka je da ke, sai da na yi kuka, gaba ɗaya iyalansa sun bani tausayi" Hajiya Sa'a ta ce "Ke yarinya, ki ko yi dakiya, ba komai zai din ga razana ki ba, ko kuma ba ki tsoro ba Ai ba a samun nasara da tsoro ko tausayi, kamar yadda nake yawan gaya miki. Na ga Abba bai tashi daga bacci ba, idan ya shigo ki ce masa na koma gurin duba kawunsa" Jamila ta ce "To a dawo lafiya" Bayan fitar Hajiya Sa'a, mata sun zo sayen kaya, kasancewar a bayan business take fakewa ta ci karenta, babu babbaka, ya sanya da yawan jama'a ba su san ainihin abin da take aikatawa ba". Wayarta ce ta yi ƙara, ta ɗaukko ta ɗaga. Cikin muryar bacci ya ce "Ƙanwata, kin shigo ne?" Jamila ta ce "Eh" "Akwai abin da zan karya ne? Ko kun cinye?" "Ai ni daga gida na karya, ka sayo buredi, na soya maka ƙwai, na san ba za a rasa shayi a flask ba" Ya ce "Ok to na gode" Kusan mintuna talatin sai ga shi ya shigo da sallama. Jamila ta kai masa kayan breakfast ɗin ɗaya falon,  kasancewar na farkon a cike yake da mutane. "Ina kwana" ta gaishe shi. "Lafiya ƙalau. Ina Mummyn ne?" "Ta tafi duba kawunka wai" Ya ce "Bari na yi, sauri nima zan je na kuma duba shi, yana jin jiki sosai " Cikin damuwa Jamila ta ce "Dan Allah ka saka baki, Mummy ta taimaka da wani abun, a biya masa bashin nan. Ko ba duka ba, na yi mata magana ta ce babu ruwana" Yayi murmushi yana ajiye cokalin hannunsa ya ce "Tun da ta ce babu ruwanki kawai babu. Nima babu abin zan iya yi a kai. Kuma kema ki iya takun ki ƙanwata, Mummy mahaifiyata ce, amma wasu abubuwan da take yi ba na gane musu" Jamila ta ɗan yi shiru, sannan ta jinjina kai ta ce "In sha Allah na gode sosai " Ya yi murmushi ya ce "Kayan nan sun yi miki kyau sosai " "Kai ma ka yi kyau, bari n sallami masu sayen kaya" ta fice daga falon. Duk da ba wani sakar masa fuska take yi ba, saboda ta fuskanci take-takensa, zai cewa yana sonta, ita kuma sam bai wani yi mata ba. Ba shi tsawo sosai, kuma ba shi da kauri, baƙi ne mai matsakaicin tsayi, sai ƙasumba da ya tara. Sai dai kuma sanyin halinsa ya sanya take ɗan kula shi. Hajiya Sa'a ta je ta tarar da ɗan uwanta a gadon Asibiti, cikin yanayi mai ban tausayi. Bayan ta gama duba shi, ta kalli Hajiya Suwaiba, ta ce "Wai ni ban ga abokiyar zaman ki ba fa" Hajiya Suwaiba, ta kwaɓe baki ta ce "Ba ta daɗe tafiya ba" "Ohh wancan zuwan da na yi, na tarar da ita hajaran majaran ai kamar gaske. Amma mu na nan mu na zuba ido, za ta zauna ne, ko kuma za ta yi gaba tun da babu abin hannu yanzu." "Oho mata, ita ta sani dai" Gaba ɗaya Hajiya Suwaiba, ta gaji da surutun da Hajiya Sa'a take yi mata, ita ba Fadila ce a gabanta ba yanzu lafiyar uban 'ya'yanta ce ta dame ta. Su na nan zaune, sai ga Fadila ta yi sallama ita da mahaifiyarta. Hajiya Sa'a ta amsa da ƙyar, Rauda babbar 'yar Alhaji Fatuhu ce ta amsa musu sosai, ta ce "Anty sannunku da zuwa" "Yauwwa Raudah, ya jikin Daddy?" "Da sauƙi, ai na zata hutawa za ki zauna ki yi? Na ga kuma kin sake dawowa" Fadila ta ce "Hankalina ya ƙi kwanciya ne, na je gidanmu na yi wanka muka taho tare da Mama" suka gaisa da su Hajiya Sa'a, sai kallon ƙasƙanci take yi wa mahaifiyar Fadila. Sai dai ba su tanka mata ba. Mutane daga gurare daban daban, su na zuwa duba shi, sai dai wasu lokutan, ba ma ya gane wanda suka zo kansa baki ɗaya. BAYAN WATANNI UKU. Nana ce a zaune, ta ja uban tagumi, tana kallon Sayyid, da fuskarsa ke ɗauke da matsananciyar damuwa. Jiki a sanyaye Nana ta ce "Sayyid dan Allah ka cire damuwar nan daga zuciyarka, ka ga nima haƙuri na yi" Ya ɗago ya kalle ta yana ajiyar zuciya ya ce "Shikenan burina na son gina zuriya tare da ke, ba zai cika ba kenan? Ba zan samu mallakar Ahali ba kamar yadda nake fata. Na uku fa kenan yana zubewa" Duk da abin a dame ta ita ma, amma ta daure ta ce "Sayyid mu yi haƙuri, mu bar wa Allah, yana sane da mu, kuma zamu samu wanda zai tsaya in sha Allah, amma ka daina saka damuwar abin a ranka ya dame ka haka" "Ba ni nake saka damuwar ba, zuwa take yi, ta yi mini nauyi ta hana ni sukuni, na rasa yadda zan yi amma abin yana taɓa ni sosai da sosai" Ta rungumo shi jikinta, tana shafa bayansa a hankali ta ce "Na sani, duk mu yi haƙuri, babu yadda muka iya da ikon Allah. Kuma ka sani ma ko yanzu akwai wani ba mu sani ba" Ya ɗan ja numfashi ya ce "Ni har fargaba nake yi, ki ce mini akwai cikin, saboda daga baya sai ki ce mini ya zube". Nana ta ci gaba da rarrashin sa, "Ka yi haƙuri Shugaba, Allah zai bar mana, in sha Allah sai na haifo maka santalele ko santaleliyar jaririya" Ya yi murmushi ya ce "Allah ya sa ma vie" "In sha Allah " ta yi maganar fuskarta, ɗauke da murmushin hali, domin kwantar masa da hankali da sama masa nutsuwa. Ya gyara kwanciyar sa ya ce "So nake mu bar gidan nan, ba na son zaman a cikin sa. Yarinyar nan tana takura mini, kuma hakan barazana ne ga zaman lafiyar da yake tsakanina da ke" "Ai na riga na fahimce ka Sayyid, ka ga haryanzu su Sule suna nema maka wani gurin ne, idan muka bar gidan nan, bamu da wani gurin da za mu tafi. Ka yi haƙuri Allah ya fi ƙarfinta ka manta da ita kawai". Ya ɗan girgiza kai ya ce "Shikenan, bari na je masallaci" Ya tashi ya yi alwala, ya fita Nana ma ta tashi ta yi salla. Ko a yanzu ma tana kyautata zaton wani cikin ne da ita, sai dai ita kanta a cikin fargaba da damuwa take. Dan da cikin ya samu ba a zuwa ko ina, yake zubewa. Abin ya dame ta sosai da sosai, kuma ta fi danganta hakan da Ƙaisar ne. Ga shi ƙawarta Siyama, da take hira da ita ta ji daɗi, ta bar gidan wai an kai ta Abuja, gidan Yayar Babanta a can za ta ci gaba da ganin likitan ƙwaƙwalwa. Tun da ta yi ɓari na farko, ta ga yadda yake, ko ta yi ma shiru take yi, ba ta sake gaya wa ko Ummi ba. Sai dai ta yi abin ta a ɗaki daga ita sai shi. Yana tafe a hanya ya nufo gida, Siyama ta yi burki da motarta a gabansa. A dole ya ja ya tsaye ya kalle ta. "Abin ƙauna, ka hau mu ƙarasa gidan, tun da can ka nufa?" Ya zagaya ya fara ƙoƙarin kaucewa motar ya wuce, amma ta sake shan gabansa da motar. "Ka hau mu tafi na ce. Duk wannan sunkuyar da kan da ka ke yi, da ƙoƙarin kaucewa buƙata ta da ka ke yi, ba zai hana na ci gaba da bibiyarka ba, da neman cikar burina ba. Ina sake gaya maka, idan ka amince da abin da nake so, zan baka kuɗi masu tarin yawa. Zaka bar aikin gadi, za mu yi rayuwa ma cike da farinciki da nishaɗi. Ita ma matar taka zan bata kuɗin da za su wadace ta, da ba za ta ji zafin rabuwar da za ku yi ba. Ka yi tunani ka duba mafitar ka" Ya ƙara takawa ya matsa daf da jikin motar, ya sauke rawaninsa ya zuba mata ido. "Na saki matata, za ki bani kuɗi ko?" Ta jinjina masa kai tana murmushi. Ya ɗan ja da baya, ya kalli layin babu kowa, kawai ya saka hannu  ya shaƙe mata wuya. Ƙoƙarin ihu take yi, amma ta kasa idanunta suka firfito waje, ta fara kokowa da numfashinta. Ta ga kamaninsa sun canza, ƙwayar idanunsa ta sauya, ya canza kamanni zuwa tsoho tukuf, tun tana ƙoƙarin ƙwatar kanta daga hannunsa, har ta gaza jikinta ya saki ya yi sanyi ƙalau. 08081012143 CHAPTER 47 Wayar hannun Nana, ce ta fara ringing, ta yi shiru, tana kallon lambar, tamkar kar ta ɗaga sai kuma, ta ɗaga tare da yin sallama. "'yan matan adon gari" Gaban Nana ya faɗi, jin muryar Alhaji Zailani ta daki dodon kunnenta. Jikinta na tsuma ta ce "Waye?" "Bai kamata ki tambaye ni ba, na san kin san waye. Kiranki na yi na ƙara yi miki tuni. Hankalina ya dawo kan ki baki ɗaya. Tun da kin bujirewa buƙatata ta laluma, to za ki biya mini ta ƙarfi da yaji. Ba zan taɓa barin ki ba sai buƙata ta biya, dama ta biyu na kira ki na baki, ko dai ki amince, ko kuma sai na tagayyara rayuwar ki, daga ke har wannan sakaran mijin naki". "Yanzu da auren nawa ka kira ni, ka ke gaya mini wannan maganganun? Da aurena me ka ke so na yi maka?" Alhaji Zailani ya ce "Babu ruwana da aurenki, buƙatata ce a gabana" Nana ta ja ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, ga fili ga mai doki, idan ka ga dama kar mu kwana a raye daga ni har mijin nawa" Ba ta gama gane me yake faɗa ba, ganin Sayyid ya faɗo ɗakin, kamar ba ya gani ma sosai. Jefar da wayar ta yi ta nufe shi, "Sayyid Meyafaru?" Ya ture ta ya nufi kan katifar, ya faɗa ya kwanta. Ta bi bayansa, ta taɓa jikinsa ta ji babu zafi, amma ya lumshe idanunsa. Ta kwance masa rawaninsa, ta ɗan gyara masa kwanciyar sa. "Sayyid" ta yi maganar tana leƙa fuskarsa, amma bai amsa ba, kuma bai yi magana ba. Ta ɗauki wayarta, za ta kunna masa karatun Alkur'ani, amma ta yi shiru tna kallon wayar, gabanta na faɗuwar, kar ta je Alhaji Zailani ya kuma kiran wayar ya ɗaga, ba ta san me za ta ce masa ba. Tun da ya ma fi ta amfani da wayar,  ita wayar ba wani damunta ta yi ba. Daga jin litattafai, sai kallo shi ma sai lokaci lokaci. Da sauri ta saka lambar Alhaji Zailani a blacklist, tare da fatan Ubangiji Allah ya tsare su daga sharrinsa da mugun nufinsa. Ga shi kwana biyu ba ta je gida ba, tana son zuwa ta gaida Baba, amma ba ta son zuwa ta tarar da damuwoyin gidansu, da ba sa ƙarewa. Ta saka Sayyid a gaba, kawai tana kallonsa, tare da tunanin abin da ya same shi, ya dawo a haka. Sai wajen sallar Isha'i ya tashi, bai ce mata uffan ba, ya yi salla ya zauna ta zuba masa abinci ta ba shi. Yana ƙoƙarin fara cin abincin, aka fara horna, ya tashi da sauri, ya fita waje. Ya buɗe gate sai ga Motar Hajiya Halima, Nuradeeni yana jan motar, Hajiya Halima na baya ita da Siyama. Nura ya ce "Ba ka san abin da ya faru ba ko? Wallahi Siyama aka gano a bayan layi, a sume a cikin mota, na raka Mami unguwa, wani maƙwabcinmu ya gano ta, ya kira mu" Ya girgiza kai cikin tausayawa, ya ce "Allah ya kiyaye" Su ka shige da motar, ya rufe ƙofa, bayan ya koma ɗakinsu, ya gama cin abincin yake ba wa Nana labarin abin da ya faru. Ta ce "A ina aka ganta?" "Ya ce a bayan layi ne" Nana ta ce "Allah sarki, abin mamaki" Sai da ya gama cin abincin sa ya ƙoshi, ya sake kallonsa ta ce "Ka gaya mini tsakani da Allah me ka yi mata?" "Wa?" "Siyama" ta bashi amsa. "Babu" Ta yi murmushi ta ce "Haba Dattijo, a duk lokacin da ka kawo mana ziyara, ina sani fa. Ka gaya mini me ka yi mata?" Ya ɗago ya ƙura wa Nana ido. Ta sunkuyar da kanta, ta ce "Ka daina kallona haka, ka san ba zan iya haɗa ido da kai ba, ka gaya mini me ka yi mata. Kar ka sanya a zo ana zargin mijina da aikata laifin da bai san hawa ba bai san sauka ba" Ya yi gyaran murya ya ce "Duk abin da zan yi, na gama aikina a kansa, ba zan bari a cutar da shi ba, sai cutarwar da na san, za ta yi miki raɗaɗi a zuciyarki da gangar jikinki, duk da na san hakan ba zai sanya na huce, daga mugun abin da ku ka yi wa zuriyarmu ba?" Magana Nana take son yi, amma tamkar an saka igiya an ɗaɗɗaure ta, ta ji bakinta ya toshe, ko magana ta kasa yi. Ta ɗauki tsawon lokaci a haka, kafin ta ji an taɓa ta. Kamar wadda aka yaye wa wani nannauyan bargo, ta ɗago a razane ta kalle shi. "Lafiya?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya saka hannunsa ya shafo gumin goshinta ya girgiza kai ya ce "Meyafaru?" "Bakomai fa. Amm Sayyid ka je masallaci ko?" "A'a a daki na yi salla, na yi bacci, ba ki tashe ni ba" "Ka haɗu da Siyama?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Eh" "Meyafaru?" Ya girgiza kai ya ce "Ba zai yi miki daɗi ba, ki bari kawai" Ta ce "A'a ina son ji, ai ni na tambaya" "Ba zan faɗa ba. Ina gaya miki za ki faɗa" Ta yi murmushi ta ce "To ya zan yi, idan ban yi kishin mijina ba, amma na bar maganar" Ya ɗan yi miƙa ya ce "Ji nake kamar ba ni da lafiya, zo ki danna mini bayana" Ta ce "To" Ya hau kan katifar ya kwanta, ta din ga yi masa tausa a hankali, tana matsa masa jikinsa, ya lumshe idanunsa ya hau bacci. Bayan ya yi bacci, ta tsallake shi, ta je ta yi wanka, ta canza kaya ta zo ta kwanta a kusa da shi. Tana kwanciya ya matsa kusa da ita, ya rungume ta. "Shugaba, baccin kenan?" Ya cusa fuskarsa a wuyanta, yana sauke numfashi ya ce "Duk baccin da nake, ki na zuwa na tashi". Ta yi murmushi ta ce "Abokin ruhina, to yaya ruhin nawa na jikinka?" Ya yi dariya ya ce "Yana nan ƙalau, cikin aminci da salama" "Ba wata salama, bayan wata na sonka" "To ai ni ba na sonta" "To idan ka fara sonta fa? Tun da fara ce, kamar kai" "Nana" ya kira sunanta. "Nana kuma? Au har ma na tashi daga rayuwar taka na koma Nanata, gatsal?" "Ai har abada ke rayuwata ce, nutsuwata, mai rayuwa da ruhina a jikinta. Idan zuciyarki ta sosu, a jikina nake ji. To ta yaya zan bar abin da zai din ga ɓata miki rai. Ita ma daga ranar da ta san ni mahaukaci ne, za ta daina son nawa" Nana ta yi dariya ta ce "Da alama hausa indiyar nan da ka ke kallo, haddacewa ka ke yi, wannan kalaman masu ɗauke da falfasa ai ba wuya za ka saka mutum ya fara sonka". "es-tu sûr(kin tabattar?" Ta ce "Yes am very sure"(Eh na tabattar) "Ma sha Allah, nice to hear that"(Ma sha Allah, na ji daɗin jin haka" Ta waro ido a cikin duhu, tamkar yana ganinta ta ce "Turanci kuma? Wai yare nawa ka ke ji ne?" "Biyar" ya bata amsa kai tsaye. "Wanne da wanne?" "Da Nana, da Asma'u, da Husna, da Asmy, da rayuwata, da Duniyata, da Ruhina. Kai ashe yarukan sun fi biyar ma" Ta ja dogon hancinsa ta ce "Wai duk lokacin da nake so mu yi magana serious, sai ka mayar da maganar wasa. Idan kuma kai ne ka ne so mu yi magana kuma, sai ka haɗe rai" Dariya ya din ga yi, da jin abin da ta faɗa ya ce "Sayyid, shugaba, ko kin manta sunan da ki ka saka mini ne?". "Shugaban da babu masarauta" "Ai a cikin Duniyata masaurata take" Nana ta ce "Wai me yasa sai dare, ka fi sakar mini fuska, ka yi ta magana ka na raha" Ya gyara kwanciyar sa, ya ɗago daga kwanciyar da ya yi ya ce "Na gaya miki?" Da sauri ta ce "A'a bar shi, ba sai ka faɗa ba" Kawai ya tuntsure da dariya, ta ce "Hmm za ka yi dariya ne, Allah ya dauwwamar da wannan kyakyawan murmushi a fuskar gangar jikin da ke ɗauke da ruhina" "Ashe ke ma kin iya, abin cikin film ɗin" Suka yi dariya tare, ya fara kashe Nana da salon soyayyarsa mai tsayawa a rai, tare da haɗa yaren Hausa da fransanci, gurin gaya mata kalamai masu motsa zuciya. Cikin rawar murya ta ce "Sayyid"ya ɗaga kai ya kalle ta. "Kana ganin abin da nake gani?" "je l'ai vu(Na gani) amma kar ki tsorata. Yi kamar ba ki gani ba" "A'a ina ne nan Sayyid? Ina yawan ganin gurin nan, ina yawan ganinmu tare a nan." Y girgiza mata kai ya ce "Nima ban san ina ne ba" "Kuma ba mafarki ba ne?" "Zahiri ne" ya amsa mata a taƙaice. "Amm..." Bai bari ta sake magana ba, ya rufe bakinta da nasa, saboda tambayoyinta ba sa ƙarewa. Bayan wani lokaci, ya rungumota daga banɗaki, sai rawar sanyi take yi. "Ba ki da lafiya ne?" Ta kalle shi ta ce "Me ka gani?" "Kamar ki na jin sanyi, kuma na da ruwan ɗumi muka yi amfani" Ta jinjina kai ta ce "Ina jin sanyi kam, mu je ka bani ɗumi" Da sauri ya ce "To mu je" "A'a ba fa abin da ka ke tunani ba ne" Ya yi murmushi ya ce "To ma na ce miki ina tunanin? Zo na baki ɗumin jikina" "Ba na so, ƙona ni ka ke yi" Kawai ya yi dariya, ya ce "Daga ni har ke, Allah ya yaye mana abin da yake damunmu" "Amin Sayyid, dama ka na ganin ɗakin nan kai ma?". "Eh amma a mafarki galibi" "To akwai ranar da ka ce azumina zai karye, na ganmu a ɗakin kuma na tashi, na ga ya karye ɗin" Kawai ya shafi jiƙaƙiyyar kalbar da take kansa, yana dariya ƙasa-ƙasa. "Ya ka ke dariya? ka bani amsa mana" "Na saka ki bacci ne, sai na taɓa ki kaɗan" "Ka yi mini me?" "Abin da muka yi yanzu" sai kuma ta yi saroro cikin jin kunya, ta kwanta za ta juya masa baya, amma ya juyo da ita, ya kwanta shi ma. Gaba ɗaya yau ya fi kullum ba ta mamaki, hirarsa ta fi ta kullum yawa, zolaya da nishaɗinsa ya fi na kullum. Duk a 'yan kwanakin nan, sun ƙara samun nutsuwa da kusanci da juna sosai da sosai. "Shugaba" "Rayuwata" "Ya ake ka ke saka ni bacci mai nauyi" Ya yi shiru bai ba ta amsa ba, ta ɗan jijjiga shi, kawai ta ga ya yi bacci. Sai dai tana sakankancewa bacci mai nauyi ya ɗauke ta, ya ƙara farkawa ya tashe ta. "Sayyid gaskiya ƙasa zan koma, na bar maka katifar nan, halak malak haba, kwata-kwata ban yi bacci ba. Kaina har ya fara ciwo. Ga zuba ruwa ga rashin bacci haba Shugaba" Bai ce mata uffan ba, ya rungume ta, ta baya, ƙirjinsa a bayanta. Ji ta yi zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. Har za ta yi magana sai kuma ta fasa, jin jikinsa ya saki alamar ya yi bacci. Siyama kuwa bayan ta farka ta ganta a gida, sai ta kasa tuna komai. Tayi-tayi amma ta kasa tuna komai. Ta tambayi Maminsu, me ya same ta, ta gaya mata a mota aka tsinto ta a sume Abin ya ɗaure mata kai ya ba ta mamaki, a iya saninta, ta haɗu da mai gadi, sun yi magana daga haka ba ta sake tuna komai ba. Abu kamar wasa sai ta din ga zabura tana tsorata haka kawai. Ta kasa zama a ɗakinta itakaɗai, ta tashi ta koma ɗakin mahaifiyarta. ***** Alhaji Zailani ne a zaune a kan kujera, yana kallon Alhaji Fatuhu, da yake zaune, ya jingina da pillow, Fadila na ta ƙoƙarin ba shi Abinci. "Sannu Fatuhu" Alhaji Fatuhu ya ce "Yauwwa Alhaji Zailani, na gode" ya furta cikin ƙarfin hali. Ya kalli Fadila, zaune ciki ya tsufa sosai da sosai. Ya ce "Babu wanda yake kula da shi, ke ga larura ga kuma ɗawainiyar jinya". "He deserves it, Daddy shi mai kulawa ne a gare mu" ta yi maganar hawaye ns zirarowa daga idanunta. "Allah sarki, sai haƙuri, ki yi haƙuri. Allah ya ba shi lafiya" kasa ci gaba da ba shi Abincin ta yi, ta ƙara fashewa da kuka. A hankali Alhaji Fatuhu ya ce "Za mu yi faɗa idan kina kuka, ai na samu sauƙi" Alhaji Zailani ya ce "Look, kukan nan ba abin da zai amfana muku. Ki yi haƙuri ki yi masa addu'a, kin ga juna biyu ne da ke. Ba zai so wani abun ya faru da ku ba, daga ke har abin da yake cikinki ba. Kin ga Shukura irin haka aka yi, ta saka damuwa mara dalili a zuciyarta. Ta zo ta haifi yaronta babu rai. Kuma ta zo ta sake shiga damuwa. Ki yi haƙuri dan Allah" Cikin rauni ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, na gode sosai da sosai" "Yauwwa babu komai, idan Hajiya Suwaiba ta zo, ta kira ni a waya, ku koma Asibitin Doctor Sharif,a din ga yi masa komai a can. Ba zai gagara ba in sha Allah" Fadila ta ce "Kar mu ɗora maka ɗawainiya, nan ma su na ƙoƙari Alhamdillah" Alhaji Zailani ya ce "kai, Fadila. Kin san waye mijin ki kuwa a gurina? Da Suwaiba ce ma ba za ta yi jayayya ba na sani. Dan Allah ku haɗa kayan ku, zan turo direba ya mayar da ku can zuwa dare in sha Allah. Abokina Ubangiji Allah ya ƙara afuwa" Ya miƙa wa Alhaji Fatuhu hannu suka gaisa, Alhaji Fatuhu ya ce "Na gode sosai da sosai, da ɗawainiyar da ka ke ta yi, na gode sosai da sosai" "Ai ka san babu godiya tsakaninmu, Allah ya sauwwaƙe". Bayan ya fito harabar Asibitin, ya din ga wata irin dariya. Ya hau motarsa yana faɗin da sauranka, tun da har yanzu ka na magna. Wannan matan ma duk sai sun gudu sun bar ka, abin da za ka ci ma sai an taimaka maka da shi. Ya ja motar ya bar harabar Asibitin. ***** Gidan su Nana kuws, duk wanda ya yi surutun, gyaran da aka yi wa gidan, da yawon da Jamila take yi. Sai Mama ta ce Maman Khairat ce ta haɗa Jamilan, da wata Hajiya 'yar kasuwa, Jamila take taya ta aiki a kasuwancinta, tana biyanta. Suwaiba kuma, abu kamar wasa jiki ya ƙi daɗi sam. Kullum cikin ciwo take, yau ciwon kai, anjima ciwon ƙafa da ciwon baya. Ga shi ta auri zaman ɗaki ba ta son fita. Idan ciwon kan nan ya tayar mata, tamkar za ta haukace, ta din ga burgima kenan tana ihu da kururuwa. Mama ba ta wani mayar da hankali ba a kan ciwon na Suwaiba, saboda hankalinta na kan abin duniyar da Jamila take kawowa, shi yasa ba ta damu sosai da sosai ba. Duk inda ta kai Suwaiba neman magani, wasu su ce Aljanu ne da ita, wasu su ce Asiri aka yi mata. Wasu su ce kambun baka ne da baki. Gaba ɗaya Suwaiba, ta rame ta yi baƙi. Idan abin ya motsa ko abincin kirki ba ta iya ci, sai aikin kuka sai bacci. ***** Can gurin su Nana kuwa, fito daga gaba ɗaya Sayyid jikinsa yake yi tamkar an zare masa laka, wata irin mutuwar jiki da ta ƙaru a kan ta jiya da yake ji. Nana ta fito daga wanka, ta ɗauro zani ta fito tana ɗigar da ruwan wanka. Ta yi fari da idonta, ta ce "Shugabana" Yayi murmushin da ya saba, tare da sunkuyar da kansa, yana kallon wayarta da ke hannunsa. Ta buɗe drowern mudubi, ta ɗaukko kibiya da comb, ta nufo shi, ya kalle ta ya tsuke fuska. Ta kwashe da dariya, ta ce "Mutumina akwai shagwaɓa, kalbar kanka ta tsufa sosai, ka bari a tsefe dan Allah. Idan ya so ma yi kitson gobe" Ya girgiza kai ya ce "A'a" "Gaskiya sai na tsefe ta, na yanke maka farce, ka yi wankan juma'a ko Rayuwata" Yana hararta, ta kwantar da kansa a kan cinyarta, tana yi masa dariya. "Rigimammen Shugabana" Tana tsifar tana yi masa hira. Yana ta shiga yana fita a cikin wayarta, ya kunn waƙr kewa, ta wani mawaƙi ɗan nijar ta kewa. Cikin nishaɗi,take bin waƙar, ta riƙo tafin hannunsa cikin nata, tana bin, baitukan waƙar. Kowa tsaneka, ni na tsane shi sanya a ranka... Zuciyata na baka, duk masu ƙin ka su daina shakka... Rayuwata na baka... Ni ta ya zan guje ka... Ka dawo gare ni dan Allah, zuciya ta bar kewa... Murmushi ya gaza barin fuskarsa, fararen haƙoransa a waje, ya juyo gaba ɗaya ya ƙanƙance idanunsa, yana yi mata wani irin kallo cikin nishaɗi. Ta ci gaba da bin waƙar, tana ɗan jan kunatunsa "Mallakina ne, kai zan kira da sheriena... Ko iyayena sun ce na bi ka mai so na... Kai jinina ne... Mahɗina ne... Ƙaddarata ne Mai yabona ne... Ashe kai ne, ashe kai ne, ashe kai ne abin so ne, abin so ne, abin so ne. Dan Allah ka dawo gare ni mai so na ina kewa... Ya ɗago hannunsa ya kalli azurfofin hannunsa, ya ciro ɗaya ya kamo hannunta ya damƙa mata. Tana dariya ta ce "Iyee gaskiya na iya waƙa, har da kyauta? Amma ya yi mini yawa ai" "Ki samo zare ki zura a ciki ki yi sarƙa da shi" Nana ta din ga tuntsura dariya. Ta ce "Riba biyu, ga tsifa na yi ga kuma kyauta an ba ni. Ya din ga kallon dariyar da take yi yana murmushi. Can zuwa la'asar Nana ta fuskanci jikinsa gaba ɗaya a sanyaye yake, kamar babu kuzari haka yake gudanar da komai. Sai dai ba ta tambaye shi ba, saboda tana tsoron ya zamana wani abu ne yake damunsa, ba ta son ganinsa a cikin damuwa sam. Su na cin abincin dare, tana yi masa hira yana amsawa muryarsa a sanyaye. Wayarta da ke caji a ɗakin, ta cika ɗakin da ƙara. Nana ta duba ta ga Hajiya Amina. Cikin rawar jiki ta ɗaga tana murmushi ta saka a hansfree ta ce "Hajiya tuba nake yi, kwana biyu ma ban kira ki na gaishe ki ba". "Alhajin ne, ba Hajiyar ba" Wata irin mummunar faɗuwar gaba, ta riski Nana, ta kalli Sayyid. Ta ga bai ko kalle ta ba, yana cin abincin sa a nutse. "Wa..wa..wane Alhajin ya aka yi? Ina mai wayar?" Zailani ya ce "Mai waya tana nan ƙalau, na ji kin saka wayar a blacklist ne, shi ne na ce bari na biyo ta inda dole ki ɗauka. Me ki ka yanke game da maganarmu? Idan kin amince zan turo miki inda zamu haɗu, mu gama na baki kuɗin ki na sallame ki, babu wanda ya ji babu wanda ya sani. Idan kuma ba haka ba zan ɗauki mataki na gaba" "Na shiga uku, zaka kashe mini aure, wannan wace irin masifa ce, ban yadda ina budurwa ba sai da na yi aure" Sayyid ya miƙa hannu ya katse kiran, ya kashe wayar gaba ɗaya. Cikin kuka ta ce "Dan Allah Sayyid ka fahimce ni, zan yi maka bayani" Ya girgiza kai ya ce "Babu buƙata, ci abinci" Sosai Nana take kuka ta ce "Wallahi Sayyid" "Don't talk.(Kar ki yi magana)" Gaba ɗaya hankalinta ya yi mummunan tashi, duk jikinta ya mutu. Amma bisa ga mamakinta, ta ga ya ci gaba sabgoginsa ko ta kanta bai bi ba. A tsorace ta raɓa shi ta kwanta, tana tsoron kar ya shaƙe ta. Ya kamo hannunta, ya ɗora kan tsefaffen gashinsa ya ce "Ki yi mana addu'ar bacci" Ta yi ajiyar zuciya, ta fara karantowa a hankali. Suratul falaƙi, Nasi, ayatul kursiyyu da ayoyin farko na Suratul Baƙara. Sai dai tana karantawa muryarta na rawa. Ta idar ta busa masa a fuskarsa. Kamar yadda ta kan yi musu, ranar da take cikin ƙoshin lafiya. Gani duk ta takure ta ƙi sakin jikinta, ya sanya ya yi ƙoƙarin kawar da damuwar da take ciki. Amma ya ji jikinsa ya ƙara nauyi, yana jan numfashi da ƙyar. Duk ƙoƙarin da ya yi, ya kasa komai, sai kokowa da yake yi da numfashi.Nana kuwa jin ya ƙyale ta, ya sanya ta yi bacci. Hatta sallar Asuba, a gida ya yi, a ɗaki. Ta sab wasu lokutan idan ba ta tashi da wuri ba, sai dai ta tashi ta ga ya sayo ƙosai ko buredi, amma yau har ta makara, ta tashi ta yi abin karyawa yana kan katifa bai tashi ba. Ta tsaya a gaban mudubi ta shirya, ta yi kwalliya. Vibrating wayarta take yi, sai da gabanta ya faɗi, saboda tana tsoron kar ta je ko Alhaji Zailani ne. Jiki a sanyaye ta ɗaukko wayar, ta kalli Sayyi, ta ga bacci yake yi. Ta ɗaga kiran gabanta na faɗuwa, ta saka a kunnenta. "Nana ba faɗa me ya kawo gaba?" Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Jamila, yau ke ce da kira na?" "Eh, tun da ba kya neman mutane ba. Rannan na wuce ta wajen gidanku, kamar na biyo na ce kar na je, na takura muku" Nana ta ce "Kashh, amma ba ki ji daɗin halinki ba, dan wulaƙanci?" "Ba wani wulaƙanci, lokacin ma Ummi ce ta ce kin yi ɓari, ai an kwana biyu da na wuce ɗin ai" "Kai Ummi sai da ta faɗa? Ina su Mama, ba ta taɓa zuwa gidana ba, Yaya Atine ma haka" "Aikuwa na ji Yaya Atine tana ta masifar, ba ki je mata ba." "Wallahi ba ya bari na fita ne, sai na yi ta fama. Ina suby ne?" "Tana gida babu lafiya, tana ta fama da matsanancin ciwon kai" Cikin damuwa Nana ta ce "Subhanallah, in sha Allah zan samu dai na zo gidan, ba ni ita dan Allah na yi mata sannu" "A'a ni ba na gida ma, na fita tun safe" "Zuwa ina?" "Gurin neman halal mana. Kin san Hajiya Sa'a nake yi tayawa saye da sayarwar kaya tana biyana". Nana ta yi murmushi ta ce "Jamila kenan, ni dai wallahi matar nan ba ta yi mini ba, ba zan ɓoye miki ba, ina iya jin alamun rashin gaskiya a tattare da ita. Na san yanayin gidanmu, dole ka nema idan kana so ka rayu. Amma Jamila ki san abin da za a saka ki ki yi, duk wani abu da zaka tara a duniya koma bayan imaninka da mutuncinka ne. Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari, masu tsoron Allah masu wadata." Jamila ta ce "Hajiya Nana sarkin manyance, dama kuma ga shi an yi aure, sai abin da ya yi gaba. To na gode sosai na ji ana sallama" "To ki gaida su Mama da Suwaiba kafin na zo" "To shikenan, sai anjima" ta kashe wayar, ta ajiye ta shashshafa turare. Ta juyo ta kalli Sayyid ta ga idanunsa kar a kan ta. "Shugaba ya dai? A tashi a zo a ci Abinci" Murmushi ya yi da ƙyar, amma bai yi magana ba, kuma bai motsa ba. "A taso mana ranka ya daɗe" ya yi shiru dai yana kallonta. Nana ta yi murmushi ta ce "Yau mulki ake ji kenan, bari na zo na ɗaukko ka, tun da tashi ya gagara" ta ƙarasa ta ɗaukko kayan abincin, ta jera a inda suke ci. Ta kunna turaren wuta, ɗakin ya gauraye da ƙamshi. Ta ga dai da gaske ya ƙi tasowa, ta nufe shi tana rangwaɗa. Ta sunkuya a gabansa, ta yi masa kiss a goshi ta miƙa masa hannu, ta ce "Bismillah taso Shugaba" Bai kama hannun ba, ya ci gaba da kallonta, sai kuma jikinta ya yi sanyi, da kallon da yake yi mata. Jiki a sanyaye ta ce "Wai Sayyid lafiya kuwa? Ko maganar ce ta ɗauke?" Ya miƙa hannunsa, ya kamo nata, ya ɗora a saitin zuciyarsa. Ta yi shiru, ta ji zuciyarsa ta buga sau ɗaya, sai kuma ta yi shiru ba ta sake bugawa ba, sai bayan wasu sakanni, sannan ta sake bugawa. A razane Nana ta kalle shi jikinta na rawa ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid meyafaru? Me ya same ka haka?" Ayshercool 08081012143 48 Bai ce uffan ba ya ci gaba da sauke numfashi. Tashi ta yi a matuƙar rikice, ta zari hijjabinta ta yi waje, cikin matsanancin tashin hankali da kuma damuwa. Ta kai a ƙalla mintuna ashirin, sannan ta dawo a rikice, ta tarar da shi a zaune ya jingina bayansa da jikin bango, ya lumshe idanunsa. "Sayyid na samo abin hawa, Asibiti za mu tafi" Ya buɗe ido da ƙyar ya kalle ta. Ta nufi wardrobe ta duba ta ɗaukko irin kuɗin da Imran ya bata. Ta buɗe wardrobe ɗin sa, ta ɗaukko masa riga jallabiya. ya tashi da ƙyar, su ka shiga banɗaki, ya wanke bakinsa. Ya fito ta naɗa masa rawaninsa, ba ta damu da ko rufe ɗakin ba, suka yi waje. Ƙarfin hali kawai Nana take yi, amma zuciyarta ta gama tsinkewa, ta karaya a mugun tsorace take. A cikin adaidaita sahun ma, a jikinta ya kwanta ya yi lamo, ya yi shiru ba ya cewa komai. Addu'a kawai Nana take yi, da fatan Allah ya kawo musu ɗauki. Amma a yanayin yadda zuciyarsa take bugawa ta yi mugun tsorata. Asibitin da suka je aka saka mata ruwa, suka je, amma aka ce musu ai weekend ne, kuma ƙaramin Asibiti ne ba sa aiki weekend. Hankalin Nana ya yi mugun tashi, yana son ya yi mata magana, amma ya kasa. Sai suka bawa ɗan sahun tausayi ya ce "Ko na kai ku Asibitin cikin gari emergency, ko wani taimakon a yi masa" Muryar Nana na rawa ta ce "Yauwwa malam, na gode kai mu dan Allah" ya ja babur suka tafi. Ya kamo hannun Nana, ya danne saitin zuciyarsa da shi, ji yake numfashinsa ma na neman ya ƙwace masa. "Sannu Sayyi, Allah ya baka lafiya, Ubangiji Allah ka dube mu, babu mai kawo mana ɗauki bayan kai, Allah ka yi mana ba dan halinmu ba" muryar Nana na rawa, take wannan addu'oin, har suka ƙarasa Asibitin. Mai adaidaita sahun ya yi mata mutunci, har zai ja babur ɗin, ya ga yadda Sayyid ya kasa tsayuwa,yana neman faɗuwa Nana kuma ba zata iya riƙe shi ba. Ya kashe babur ɗin ya fito ya ce "Ƙanwata, bari na riƙe miki shi, ba za ki iya ba" Ya saƙala hannun Sayyid a kafaɗarsa, suka taka a hankali zuwa ɓangaren emergency. Matashin ya kalli Nana ya ce "Karɓo kati, ki dawo" ta tafi da sauri gurin karɓo kati. Shi kuwa Sayyid, ƙarnin da gurin yake yi, da warin gyambo kala-kala da yake gurin, ya sanya jin numfashinsa zai ɗauke. Ya zaunar da shi a hankali a kan wata kujera, ya ce masa "Sannu" Sayyid ya jinjina kai, Nana ta dawo hannunta riƙe da kati, idanunta sun yi ja, alamu suka nuna, da ta tafi karɓo katin, kuka ta yi a hanya. Mai Adaidaita sahun ya ce "Tsaya da shi a nan, bari na duba idan da alfarmar da za a iya yi mana, a shiga da shi ya ga likita. Ta ce "To na gode" ya karɓi katin ya yi gaba. Sayyid ya riƙo hannun Nana a nasa, ya kwantar da kansa a jikinta, yana murza hannunta a hankali. "Sannu Sayyid" ya ɗaga mata kai kawai. Mintuna biyar, sai ga mai adaidaita sahun ya ce "Yauuwa bari na shigar miki da shi" Ya sake kama Sayyid, ya kai mata shi har gaban likita. Ya zaunar da shi sannan ya kalle su ya ce "To ni na tafi Allah ya ƙara afuwa." Nana ta ce "Na gode bawan Allah, Ubangiji Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi, ya jiƙan magabatanka, Allah ya buɗa maka na gode sosai da sosai" "Amin bakomai, ai yi wa kai ne, Abokina Ubangiji Allah ya baka lafiya" Sayyid ya ɗaga masa hannu, ya jinjina kai. Ta ce "Ya ce ya gode" "Ba wani abu" ya fice ya bar ɗakin likitan. Nana ta yi wa likitan bayanin abin da ya faru, ya kalli Buzu ya yi masa tambayoyi. Ta ce "Ai ba zai iya magana ba" Ya ce "Ok, to ya sauke rawanin, zan duba shi" Nana ta sauke masa. Likitan ya sanya stethoscope ɗin sa a ƙirjin Sayyid, ya saurara. Sannan ya ɗaura masa BP. Ya din ga kallon fuskar Sayyid, ya kama hannunsa ya duba pulse ɗin sa. Nana kuma ta zuba masa ido, kamar ta shiga cikin kan likitan, ta ji mai ya gano. "Hajiya tun yaushe yake da hawan jini ne?" Cikin mamaki Nana ta ce "Hawan jini kuma?" "Eh mana, jininsa ya hau fiye da kima, ko ba ki san yana da shi ba?" Ta girgiza kai ta ce "A'a ban sani ba. Sayyid ko dama ka na da hawan jini?" Yanayin kallon da ya yi wa Nana, yasa ta kalli likitan ta ce "Shi ma bai sani ba" Likita ya ce "Gaskiya dai jininsa ya hau sosai, kuma zuciyarsa babu lafiya. Bradichadia nake ji a pulse ɗin sa. So yanzu za mu yi managing jininsa da ya hau. Zan rubuta allurai da magunguna, ki sayo a yi masa. Zan rubuta muku gwaje-gwaje, idan an yi za ku dawo ranar Monday mu gani" Jikin Nana ya yi sanyi a raunane ta ce "Likita ba za a ba shi gado ba? A haka zamu koma gida har Monday, ka ji fa zuciyarsa ba ta bugawa sosai" "Ki yi haƙuri. Abin da zan iya yi masa kenan, ko na ce a ajiye ku babu gado a nan. Kuma dole sai an yi gwaje-gwajen nan tukuna, sannan zamu san abin yi. Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki. Maybe ma hawan jinin ne ya kawo rashin bugawar zuciyar sosai, amma da ya sauka za a iya samun ci gaba" Ta jinjina kai ta ce "To shikenan, na gode sosai Likita" "Babu wani abu kar ki damu, zai samu lafiya in sha Allah" Ta ce "Allah yasa, kuma Likita zai iya warkewa? Na ji an ce har abada ba a warkewa daga matsalar hawan jini da matsalar zuciya." Cikin ƙwarin gwiwa likitan ya ce "A kimiyyance, sun ce ba su da magani, sai dai a yi managing symptoms kuma a canza life style. A addinance kuma mun san babu abin da ya fi ƙarfin Allah. Babu wata cuta da ta gagari Allah ya yaye wa bawansa" Wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, bayan samun ƙwarin gwiwa daga bakin likitan. Ya rubuta allurai da magungunan da za a yi masa. Ta karɓa ta yi masa godiya. Da ƙyar Sayyid ya taka ya bar ofishin, Nana ta zaunar da shi a kan benci, ta fita ta sayo alluran da za a yi masa. Amma duk Nurses ɗin sun yi busy, aiki ya yi musu yawa. Nana ta koma gurin likitan, ta gaya masa, ya taso da kansa ya zo ya zauna ya yi wa Sayyid alluran. Yana yi yana yi wa Nana nasiha. Bayan ya gama yi masa allurar, ya saka ta bashi maganin, ya ce bayan awa ɗaya zai sake duba bp ɗin sa. Likita ya koma office, Nana ta fita ta sayo masa abin da zai ci, dan bai karya ba ga shi an fara kiran Azahar. Da ƙyar ya ɗan ci kaɗan, ya ce mata salla zai yi. Ta kai shi waje, ya yi alwala ta shimfida masa ɗan kwalinta, ya hau ya yi sallar. Bayan ya idar ita ma ta raɓa ta yi. Baya ta idar, ta miƙe masa ƙafafuwanta, ya kwanta a kai. Tana son taɓa ƙirjinsa, amma tana tsoron ta taɓa ta ji zuciyarsa ba ta bugawa sosai. Sai da suka yi kusan awa biyu, sannan Likita ya sake duba jininsa. Ya ce "Alhamdillah jininsa ya sauka, ba kamar yadda ku ka zo ba, zuciyar ma ta fi da bugawa. Yanzu ku je idan an yi wannan gwaje-gwajen, zuwa Monday sai ku kawo, ko ba ku same ni ba, za a duba shi in sha Allah" Nana ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "Mun gode sosai da sosai Likita, Allah ya sa ka ajiye aiki lafiya" "Amin Allah ya sauwwaƙe" ya miƙe ya tafi. Nana ta kalli Sayyid cikin tausayawa ta ce "Rayuwata, ya ka ke ji yanzu?" "Alhamdillah" murmushi ta yi, jin ya yi magana. "Ma sha Allah, sauƙi ya samu, zaka iya tashi mu je gida?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Ta tashi shima ya yinƙura, cikin ikon Allah, babu wanda ya riƙe shi har suka fita titi, duk da a hankali dai yake tafiyar. Su na zuwa gida, ta dafa ruwa ta yi masa wanka tsaf, ta canza masa kaya. Ta lallaɓa shi da ƙyar ya ɗan ƙara Abinci. Cikin damuwa ta ce "Sayyid, wai ya aka yi ka samu hawan jini dan Allah, ko wani abun nake yi maka da baka jin daɗinsa?" Ya girgiza kai alamar a'a. "Amma na yi mamaki. Saka mini lambar Habu, ai ya kamata na sanar masa" ya karɓi wayar, ya dannan mata lambobin, ya miƙa mata. Ta karɓa tana jiran wayar ta shiga, amma waya ta ƙi shiga. Wai layin a rufe yake. Cikin damuwa ta girgiza kai ta ce "Layin a rufe yake, bari zuwa anjima sai na sake gwadawa. Horn ɗin motar Hajiya Halima ne ya cika layin, Nana ta ɗauki hijabi ta fice. Yana ƙoƙarin yin magana amma ba ta tsaya ba. Ta leƙa ta tabattar Hajiya Haliman ce, sannan ta buɗe gate ɗin. Hajiya ta shigo da motar, Nana ta rufe ƙofar, ta dawo ta nufi motar Hajiyan, ganin ta tsaya ba ta wuce ciki ba. Nana ta ce "Hajiya sannu da zuwa" "Meye haka? Ina mai gadin da ba zai fito ya buɗe gate ɗin ba? Ina ma ku ka tafi ne, babu wanda ku ka sanarwa, ku ka bar mana gida a haka, wane irin wulaƙanci ne haka?" Cikin girmamawa Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri. Wallahi ba shi da lafiya ne, hankali a tashe muka tafi Asibiti. Mun yi kuskure ki yi haƙuri dan Allah" "To dole ne? Idan ba zai iya ba ai sai ya ajiye aikin ko? Amma ba zai yiwu na ɗauke shi aiki, ya din ga bar mini gida haka ba. Kwanaki ma haka ku ka yi mini, ya ce ke ce ba ki da lafiya, shikenan ku kullum cikin ciwo ku ke, idan ba zai iya ba ku ajiye mini aikina, na nemi wani" gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, jikinta ya yi sanyi sosai. Ta ce "Ki yi haƙuri dan Allah" Hajiya Halima, ta fizgi motar, ta yi cikin gidan. Tun da Nana ta koma ɗakin, ya ƙura mata ido, amma ta basar ta ce "Sannu Sayyid" kawai ya kawar da kansa ya lumshe idanunsa. **** Cikin damuwa Fadila take yi wa Hajiya Suwaiba magana, duk da yanayin fuskarta cikin ko in kula take amsa mata. "Ni gani nake kamar za mu ɗora wa Alhaji Zailani ɗawainiya a ce mu koma Asibitin da yake da file, ya ɗauki nauyin Daddy. Kin ga haryanzu kashe kuɗi ake yi, ba ma a gano me yake damunsa ba. Amma shi Alhaji Zailani ya dage, kina ganin babu matsala?" "To da da matsala zai ce, a kai shi ne? Tun da mun kasa affording nan Asibitin, kuɗinmu ya ƙare, idan muka koma na gwamnati, ai dariya za a yi masa. Gara mu koma can ɗin". Raudah da a baya, take biyewa mahaifiyarta ita da ƙannenta, suke zabga wa Fadila rashin kunya son ransu, yanzu gaba ɗaya ta saduda. Musamman ganin yadda Fadila ba ta da nutsuwa duk ta rame, saboda damuwa saɓanin da da suke tunanin, kuɗin mahaifinsu ne kawai ya sanya ta aure shi, kamar yadda mamansu ke nanata musu. Ta ce "Mummu Anty fa gaskiya ta faɗa, nima gani nake yi, tamkar ɗora wa Daddyn su Shukura nauyi ne, ba fa mu san ranar barin Asibiti ba" "Na saka baki da ke ne?" Rauda ta girgiza kai tare da yin shiru. Fadila ta sake cewa "Ni kuwa ya maganar kuɗaɗen kuwa? An gama biya ko haryanzu da saura?" "Da an gama biyan ai za ki ji" Fadila ba ta haƙura ta sake cewa "Dama gidan da Umma take ciki ne, shi ne ya bata, mun yi magana da ita, a sayar da shi za ta koma gidan Yaya da zama. Sai kuma gwala-gwalaina na aure, duk su na nan. A sake rage bashin, a kuma biya kuɗin makarantar su Hibba. Jiya da ya ɗan farfaɗo sai da ya yi maganar su. Ƙuri Hajiya Suwaiba ta yi mata da ido, domin ta tabattar da gaske take yi, ko kuma makirci ne kawai da iya Duniya. "Fadila" ya kira sunanta da ƙarfi. Gaba ɗaya suka nufe shi, saboda tun jiya bacci kawai yake yi, kamar sumamme. "Kar ki sayar da gidan Umma, ba ta na yi. Ni Allah zai kawo mini ɗauki" Ya yi maganar tamkar yana magana da kurame, saboda yadda yake ɗaga murya. Fadila ta ce "To, ba sayarwa za a yi ba" "Kin haihu ne?" Ta ce "A'a" "To Allah ya raba lafiya. Dan Allah ku cewa likitan nan, ya zo ya cire mini robar fitsarin nan, ta dame ni wallahi" Rauda da idanunta suka cika da hawaye ta ce "Daddy ka yi haƙuri, ka ga ba iya tashi ka ke yi ba, zuwanka banɗaki zai baka wahala. Ka yi haƙuri ka bar robar fitsarin nan " Ya jinjina kai ya ce "Shikenan Raudana, na gode" "Sannu Daddy" ta yi maganar idanunta na zubar da hawaye. A ranar Alhaji Zailani ya aiko da mota, aka mayar da Alhaji Fatuhu Asibitin su Doctor Sharif. A gaban iyalan Alhji Fatuhu, ya din ga jaddadawa Doctor Sharif, a kula da amininsa, duk abin da ya kama a yi masa, shi zai din ga biya. Suka yi ta godiya. Daga bisani ya bi bayan Doctor Sharif, suka fita. "Ka na ji na Sharif?" "Eh Alhaji" "Wannan mutumin ko me za a yi masa, ba zai taɓa warkewa ba. Kawai dai ku din ga yi masa abin da ya sauwwaƙa da duk wani abu da zai ƙara rikita masa jiki. Ka sanya ido sosai a kansa, zan din ga kiran ka, ina jin halin da yake ciki. Zan tafi umara ne." "Ba ka da matsala Alhaji" "Shikenan, za ka ga saƙo in sha Allah" **** Nana kuwa tun tana kiran lambar Habu, tana sanya ran za ta same shi, zai ɗauka har ta sare. Ga jikin Sayyid sai godiyar Allah, babu wani ƙarfi a tattare da shi. Sai dai akwai ƙarfin hali, a haka wasu lokutan yake fita buɗe gate. Jiki a sanyaye take kallon shi, ta ce "Sayyid, gobe in Allah ya kaimu, Litinin za mu je gwaje-gwajen da aka bamu, ga shi haryanzu ban samu Habu a waya ba. Ko gidan zan je na duba ko lafiya?" Ya girgiza kai ya ce "A'a" ta yi shiru tana kallonsa, dabara ta faɗo mata, ta ɗauki wayarta ta fara duba lambar Hajiya Amina. Amma ko sama ko ƙasa ta nemi lambar a wayar ta rasa. Ta duba iya in da za ta iya dubawa amma ba ta samu lambar ba. Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa, jikinta ya ba ta shi ne ya goge lambar ba wani ba. Ta koma gefe ta yi shiru, ta rasa abin da yake yi mata daɗi a ranta, gaba ɗaya a tsorace take da ciwon nan nasa. Cikin dare ba ta iya bacci, da ta fara bacci, sai ta tashi, ta duba ta ga ni ko yana numfashi, ta ɗora hannunta a kan ƙirjinsa, ta ji ko zuciyarsa na bugawa, gaba ɗaya ba a nutse take ba. Daren ranar Lahadi, Nana ta tafi cikin gidan, domin sanar da Hajiya Halima, batun komawa Asibiti da za su yi da safe. Siyama ta tarar a falo, tana kallo tana ciye-ciye. Nana ta ce "Dan Allah gurin Hajiya na zo" ko inda Nana take ba ta kalla ba, ta ci gaba da kallon Tv. Ganin Siyama ba ta da niyyar kula ta, ya sanya ta nemi guri ta zauna, ta fara zaman jira. Aƙalla Nana ta shafe awa ɗaya da rabi, ƙarshe ma Siyama ta tashi ta bar mata falon. Har Nana ta yanke tsammanni, sai ga Hajiya Halima ta saukko daga kan bene. Nana ta yinƙura ta ce "Hajiya ina wuni" "Lafiya ƙalau" ta nemi guri ta zauna. Ya kalli Nana ta ce "Ya aka yi?" "Dama Hajiya zuwa na yi na gaya miki dan Allah gobe in Allah ya kaimu, za mu yi sammako, mu je Asibiti ne an bamu gwaje-gwaje, shi ne na ce bari na zo na gaya miki kar mu yi laifi". Kamar Hajiya Halima ba za ta yi magana ba, sai kuma ta kalli Nana ta ce "Shi kuma gadin, da buɗe gate ɗin ni zan  je na zauna na yi?" Nana ba ta yi tsammanin jin haka daga bakin Hajiya Halima ba, amma ta dake ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri Hajiya, in sha Allah ba zamu jima ba, ki yi haƙuri" "Ni fa kin ga Nana, idan abin nan ba zai yiwu ba, a haƙura kawai. Na nemi wani, ku je ku nemi lafiya babu yadda za a yi ga aiki, sai dai ku bar mini ƙofa ku na can yawon Asibiti, ba fa zai yiwu ba" Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, na sani amma in sha Allah zai samu lafiya ya ci gaba da aikin, ki yi haƙuri" Hajiya Halima dai, ba ta cewa Nana su je ko kar su je ba, Nana ta tashi ta koma ɗakinsu, duk jikinta a sanyaye. Wayewar garin Litinin, Nana ta kammala komai da wuri, ta tafi cikin gidan, domin sake gaya wa Hajiya Halima, amma ta tarar ba su ma tashi daga bacci ba. Ta ga idan ta tsaya jira, za su iya makara, dan haka ta fice, ta samu abin hawa suka tafi. Nana ta ɗauka abin mai sauƙi ne, amma wuni suka yi yawo, daga nan zuwa nan, wasu gwaje-gwajen, aka ce ma ba za su fito a ranar ba, sai bayan kwanaki biyu. Ga shi duk kuɗin hannunta suka ƙare. Ƙarshe ba su samu ganin likita ba, da tasa tasan da suke hannunsu ba, saboda sai bayan la'asar liƙis sannan suka samu teses ɗin. Su na komawa Nana, ta ɗora girki, zuciyarta ta yi ta raya mata, ta je ta gurin Hajiya Halima dai, ta ƙara ba ta haƙuri, amma ta fasa saboda ba ta san me za ta tarar ba, kar ta yi mata wulaƙanci. Nana ta ci gaba da bashi magungunansa, tana kula shi, zuwa kwanaki biyun da aka ɗibar musu, komawa karɓar sakamako. Idan ana buƙatar buɗe gate, ita take zuwa ta buɗe, idan kuma ya ji jikin nasa da sauƙi, sai ya je ya buɗe da kansa. Nana ta sake zuwa ta sanar da Hajiya Halima za su koma Asibiti, nan ma ta din ga ƙanan maganganu, Nana dai ta yi ta ba ta haƙuri. Ta fito suka fita da Sayyid. Suka fara zuwa, suka karɓo gwaje-gwajen, suka koma Asibiti. Sai dai wani likitan suka gani daban. Likitan ya ce ba za su iya kula da case ɗin sa a nan ba, saboda akwai matsala a zuciyarsa, dan haka aka tura su Asibitin gaba. Can ma da suka je, aka yi masa hoton ƙirji, aka yi masa ECG, shi ma da ƙyar suka samu, dan sai da Nana ta bayar da cin hanci, sannan aka yi cuku-cuku, aka ba su result ɗin a ranar, sai dai shi ma da suka koma likitan da zai duba su, ya tafi. Nana tamkar ta ɗora hannu a ka ta fasa ihu, gaba ɗaya ma ta rasa abin yi, ga shi dakiya kawai take yi, ba ta son ta yi kuka ya gani, ta san yana yin kuka, za ta ɗaga masa hankali. Kawai ta zauna ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daɗi. "Mu tafi gida" "Sayyid ba mu ga likitan ba zamu koma?" "Eh mu tafi" jiki a sanyaye Nana ta tashi, suka nemi abin hawa suka koma gida. Sai dai su na zuwa gidan, suka din ga bugu, amma gate ɗin a rufe. Tun Nana tana sanya ran za a buɗe har ta sare. Ta zauna a kan ɗan dakalin da Sayyid ya zauna, ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Ta sake jarraba kiran wayar Habu, amma still ba ta shiga, ta damu sosai da rashin jin ɗuriyar su Habu. Ta samo ruwa suka yi salla a ƙofar gida, tana ta tunanin mene ne abun yi? Har magariba ta yi, sauro ya fara bin su, Nana tana bugun gate ɗin, amma shiru. "Sayyid yanzu mene ne abin yi?" Bai yi magana ba, sai ga motar Hajiya ta dawo, tare da Siyama. Nana ta yi ajiyar zuciya, ta tashi ta nufe su fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Hajiya ashe fita ku ka yi, kawo mukullin a buɗe" ta miƙa wa Nana mukullin, ta buɗe musu gate ɗin. Wani abu mai ɗaci ya ɗar su a zuciyar Sayyid, ganin yadda Nana ke kokawa da ƙaton gate ɗin da ya fi ƙarfinta. Ba su damu da tambayar Nana ya mai jiki ba, amma Siyama  ta ƙura masa ido, tamkar idonta zai faɗo. Suka wuce da mota, Nana kuma su ka tafi ɗakinsu. Wasu lokutan jikin nasa, sai ya ɗan samu afuwa, lokaci ɗaya kuma sai jiki ya burkice ya kasa komai. Sai ranar Juma'a, sannan suka samu su ka ga Likita. Likitan ya duba gwaje-gwajen da aka yi masa, da hoton zuciyarsa sannan ya kalle su ya ce "Maganar gaskiya Hajiya, zuciyar mijin ki akwai matsala. Yana fama da Av block stage 2" "Ni dan Allah ba sai ka yi mini bayani ba, dan Allah ya za mu yi. Mun sha wahala kafin mu ganka Doctor " Ya ce "Ki yi haƙuri, zan ɗora shi a kan magunguna, zamu din ga yi mu na monitoring zuciyarsa. Zan rubuta muku allurar da za a yi masa, saboda a kiyaye zuciyarsa daga shiga stage 3. Idan ya tafi stage 3 to 4, to sai dai a yi masa aiki, a saka na'urar da za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa." Sayyid dai ya yi shiru, ya sunkuyar da kansa. Cikin rawar murya Nana ta ce "Doctor,ni yanzu duk ba na gane wannan bayanin naka, meye abin yi? Me za a yi masa yanzu?" "Zamu yi masa allura ne, amma sai under ECG machine, to kuma gaskiya a Asibitin nan, zaku iya kaiwa wata biyu ba a yi masa ba." Cikin matsanancin tashin hankali, Nana ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Dan Allah babu yadda za a yi, a taimaka mana, yana shan wahala wallahi. Wasu lokutan ba ya iya bacci, saboda numfashinsa." Likitan ya ɗan kalli Nana sannan ya ce "Idan da kuɗi a gurinku, sai na kwatanta muku, wani Asibiti, da za ku je a yi muku" Cikin azarɓaɓi ta ce "Likita ina ne?" "Can wani Asibiti ne a by pass, za a yi masa allurar tsawon watanni ukku, duk wata za a din ga yi masa allurar, bayan an yi zai yi kwanaki uku a Asibitin, kafin ya tafi gida. Naira dubu ɗari biyu da hamsin ce, duk yi ɗaya". "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Nana ta furta a hankali jikinta a matuƙar sanyaye. Sayyid ya kamo hannunta, ta kalle shi murya ƙasa-ƙasa ya ce "Mu tafi gida" "A'a Sayyid, ba shi ne mafita ba" ta mayar da hankalinta kan likitan ta ce "Dan babu wani abin yin sai wannan?" "Gaskiya wannan ne kawai abin yi, sai dai idan ba ku da hali, ku bi layin na nan Asibitin, shi kuma dubu ɗari da Ashirin ne. Kuma idan aka bari ba a yi ba, ya ci gaba sai dai a yi masa aiki, a saka masa na'ura naira Million huɗi, kuma shi ma aikin sai a Lagos ake yin sa. Yanzu zan rubuta muku magunguna, wanda zai din ga amfani da su, zuwa lokacin da ku ka yanke shawarar abin da za a yi. Nana ji take kamar ta ɗora hannu a ka, ta rusa ihu, saboda kaf abubuwan da likitan ya lissafa babu ɗaya da take tunanin zai yiwu. Ya rubuta musu magunguna, suka tafi gida. Da wuri suka koma gida, sai dai tun da suka koma, babu wanda ya iya yi wa wani magana, tamkar kurame, haka suke zaune a ɗakin. Ta lallaɓa shi da ƙyar ya ɗan ci Abinci, ya koma gefe ya zauna ya yi shiru, babu tsammani Nana ta ga Siyama ta ɗage musu labule. Nana ta kalle ta, shi kuma ko motsi bai yi ba, balle ya buɗe idonsa. "Mami na neman ki" ta yi maganar tana satar kallon Sayyid, da yake zaune babu rawani" "Ina zuwa" Nana ta faɗa a hankali. "Shugaba, bari na je kiran da ake yi mini na dawo"ya jinjina mata kai ta tashi ta fita. Bayan mintuna kusan talatin, ta dawo ɗakin, ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da harkokinta. Sai da aka yi sallar la'asar, sannan ta dube shi cikin tausasa murya ta ce "Dan Allah Sayyid ka bari na je na sanar da Habu halin da ake ciki. Mu na buƙatar sa da gaggawa, abubuwan sun yi mana yawa mussaman yanzu da... "Ta kore mu ko?" Ya tari numfashin Nana. Ras! Gabanta ya faɗi. Ta buɗe baki za ta yi magana, amma ta kasa, sai ma hawayen da take ta maƙalewa, da suka samu damar zirarowa tamkar an kwance famfo. Ayshercool 08081012143 49 Ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na yi mata wani irin zafi da raɗaɗi. Tun da Siyama ta zo ta kira ta, zuciyarta take dukan uku-uku, har ta shiga falon, ta samu Hajiya Halima. Ta durƙusa ta gaishe ta, ta amsa mata sama, sannan ta dube ta ta ce "Amm dama, na kira ki ne, a kan tun da mijinki babu lafiya. Kin ga ba zai yiwu yana kwance babu lafiya, ku ku na yawon Asibiti, a din ga bar mini gida haka ba. Na zata abin na ƙare ne, to ban ga alamar zai samu lafiya nan kusa ya ci gaba da aikin ba. Saboda haka nake mai baki haƙuri, ga haƙƙinsa na wannan watan, dubu saba'in na ƙara muku dubu talatin, na sallame ku. Ina fatan Allah ya ba shi lafiya ya sanya kaffara ne. Na saka an nemo mini wani mai gadin ma, jibi in sha Allah zai zo ya fara aiki, sai ku kwashe kayan ku. Duk ba wani daɗewa za mu ci gaba da yi a gidan ba, mu ma zamu koma can inda mijina yake a Abuja. Mijin Hajiya Amina, da ta haɗa ni da ku ya sai gidan nan, mu ma Abuja zamu koma" Duk yadda ƙirjin Nana ya buga da ƙarfi, amma ta yi iya ƙoƙarinta, tattara nutsuwarta da nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un a zuciyarta. A zahiri kuma, ta sanya hannu biyu, ta karɓi kuɗin daga hannun Hajiya Halima, tare da sakin murmushi mai ɗauke da ma'anonin da zuciya ce kawai za ta iya shaida su. Ta ce "Mun gode sosai da sosai da wannan damar da aka bamu Hajiya. Ina fatan a zamanmu da ku tsawon watanni biyar zuwa shidda, ba mu yi wani abu da zai ɓata muku rai ba. Idan ma mun yi mu na neman afuwarku a yafe mana dan Allah. Idan kun je Abuja dan Allah a gaida ƙawata, a ce ina yi mata fatan alkhairi sosai da sosai." Hajiya Halima ta ce "Ba komai, Allah ya ba shi lafiya" Nana ta miƙe jiki a sanyaye ta fita. Nana na fita Hajiya Halima ta murza goshinta ta ce "Kai, na yi abu zai dame ni, yarinyar nan ta bani tausayi sosai da sosai. Ban so na sallame su yanzu ba, yanayin idon mijin da yadda na tarar da shi a kwance da muka dawo, ya tabattar mini da yana jin jiki. Ni ban san dalilin da ya sanya Alhaji Zailani ɗaukar wannan matakin ba, kuma ya ce kar na kuskura na gaya wa Hajiya Amina" Siyama ta kwaɓe baki, ba ta ji ta damu da korar su ba, saboda ta tsani Nana, amma tana jin kewar daina ganinsa da za ta yi. Sayyid ya ƙura mata ido, yadda take ta rusa kuka, ya saka hannu ya share mata hawayenta, ya ce "Ki daina kuka, ki je ki nemo Habu, da zan iya da kaina zan je. Amma da na fara tafiya nake jin haki" Ta jinjina masa kai, ta share hawayenta, ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta. Ta fito ta mayar da hijjabinta, ta ce "Bari na je, ko ka na da buƙatar wani abu, kafin na fita?" Ya girgiza kai ya ce "Sai dai ki kula da kan ki, ki dawo mini lafiya Rayuwata" wasu hawayen ne su ka cika mata ido, ta ƙaƙalo murmushi ta ce "In sha Allah shugaba" ta fice daga ɗakin cikin matsananciyar damuwa. Haka kurum ta din ga jin gabanta yana faɗuwa, jikinta a matuƙar sanyaye, amma ta danganta hakan, da halin da suke ciki. Sai dai duk da yamma ce, layin gidan Alhaji Zailani shiru, ba ta hango dandazon buzayen a zaune, su na shan shayi ba. Kamar yadda suka saba. Da ƙyar take jan kafarta, ta ƙarasa cikin layin. Ta je ƙofar gidan Alhaji Zailani ta fara bubbugawa. Sai da ta buga sau uku, sannan wani matashin dattijo ya buɗe. Nana ta ɗan yi turus sannan ta ce "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau yaya aka yi?" "Amm dama, gurin Habu na zo, ko Sule masu gadi a gidan nan" Ya ɗan ware ido sannan ya ce "Buzaye ko? Ai yau kwanaki huɗu da suka wuce, aka zo da wata doguwar mota, duk aka kame Buzayen layin nan kaf, aka tafi da su, babu wanda ya san inda aka kai su" Cikin matasanancin mamaki, Nana ta ce "Baba su waye suka tafi da su? Laifin me suka yi?" Ya ce "Allah masani 'ya ta. Doguwar mota ce dai baƙa ƙirin, ke motocin uku ne ma, biyu a farkon layi, duk su ka kame su, ɗaya motar dai rubutun fransanci ne a jiki, babu wanda suka yi wa bayani, suka tafi da su". "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta maimaita cikin matsanancin tashin hankali ta ce "To dan Allah Hajiya Amina tana nan?" "A'a, sun tafi Umara, tun washegarin faruwar abin" Nana ta sake cewa "To dan Allah bawan Allah, babu wani wanda zan samu wani bayani daga bakinsa a layin nan" Gaskiya ban sani ba, sai dai ki zagaya ki tambaya. Ya koma cikin gida ya rufe gate ɗin. Nana ta ji ƙafafuwanta na wata irin rawa, har suna neman gaza ɗaukar ta. Da ƙyar ta din ga ɗaga su, tana tafiya ba tare da ta san inda ta dosa ba. Ta yi shiru tana tuna maganganun Hajiya Halima, da ta ce mijin Hajiya Amina ne ya sai gidan da suke ciki. Wato yana sane ya yi abin da ya yi kenan. Ta koma tunanin suwaye suka ɗauke buzayen layin gaba ɗaya, lokaci ɗaya ko dai wata ɓarnar suke aikatawa, akwai abin da suke ɓoye mata? Tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi. Har ta je titi, ba ta tsaya da tafiya ba, ba kuma ta daina tunani ba. Idonta ya sauka a kan mai sayar da gurji da ƙuli-ƙuli. Kawai ta ji ranta ya biya, duk da damuwar da take ciki. Ta miƙa masa ɗari biyu ya bata, ta samu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai ta. Tun a napep ɗin, ta cinye gurjin tas. Tana zuwa gida aka fara kiraye-kirayen sallar magariba. Ta shiga gidan jikinta duk a sanyaye, sai dai da ta duba ɗakinsu, ba ta tarar da shi ba. Gabanta ya sake faɗuwa, ta fara tunanin ko an zo shi ma an tafi da shi, ba ta sani ba. Ba ta gama yanke hukunci ba, ta ji cikinta na hautsunawa, ta faɗa banɗaki da gudu, ta din ga sheƙa amai. Sai da ta amayar da gurjin da ta ci kaf. Tun tana yinƙuri, abu na fitowa har komai ya daina fitowa. Da ƙyar ya tsaya, ta wanke gurin, ta duba kantar abin sabulu na banɗakin, ta ɗaukko abin gwajin ciki, ta yi fitsari ta tsoma a ciki. Layi biyu ya fito raɗa-raɗa. Jikinta ya hau rawa, wani irin kuka ya kufce mata. Wani aman ne ya sake taso mata, ta din ga yinƙuri, amma babu abin da ya yi saura a cikin nata, sai kakari da yawu mai yauƙi da yake fita daga bakinta. Ji ta yi ya dafa ta, ya kunna famfon banɗakin, ya din ga taro ruwan a hannunsa, yana kai wa bakinta, tana kuskurewa.ya zuba ruwa ya wanke gurin. Ya kalli tsinken gwajin da ta yi, ya kama ta,ta tashi tsaye, jiri na kwasarta, fararen idanunta sun rine zuwa launin ja. Ya taimaka mata ta yi alawala. Suka fito daga banɗakin, sai a zaune ta yi salla, saboda yadda iya aman da ta yi ta wahala. Duk sauran cikin da suka din ga zubewa ba ta amai, amma wannan ta ji abin babu sauƙi. Bayan ta idar da sallar, ya kalle ta ya ce "Ina Habun?" Ta yi shiru tana kallonsa cikin tausayawa, ta ma rasa ta ina za ta faro masa bayanin. "Yi magana" Ta ɗan motsa bakinta, sai kuma ta yi shiru. Ya ƙara tsare ta da ido. Ta ɗan ja numfashi ta ce "Na je, wai kwana huɗu da suka wuce, an je da wata mota layin, duk an tafi da Buzayen layin, har da su babu wanda ya san inda aka kai su" sak ya yi yana bin ta da ido, tamkar bai gane me take nufi ba. Ta yi shiru tana tsoron kar abin da ta faɗa, ya ta'azzara ciwonsa. "Ba sa nan kenan? Babu wanda ya san ina suka tafi?" "Eh abin da aka ce mini kenan, kuma da alama kama su aka yi" "Hsbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta tare da sunkuyar da kansa ya yi shiru. "Dan Allah Sayyid ka kwantar da hankalinka, ka ga baka da lafiya, ina son ka warke. In sha Allah, Allah yana tare da mu. Dan Allah kar ka ɗaga hankalinka. Sonake na nutsu na ga yadda zan yi na haɗa kuɗin da za a yi maka allurar nan, ko guda ɗaya ce" Ya kalle ta cikin damuwa ya ce "A'a dan Allah kar ki damu, kar ki takura wa kan ki. Iya ɗawainiyar da na saka ki ma, ta isa. Mutuwa ce dai na sani, Allah ya sa na cika da imani, kuma ki yi mini addu'a, t... Bai rufe bakinsa ba, ta dunƙule hannunta ta dake shi a ƙirjinsa da ƙarfinta cikin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta. "Ba ka tausayina, na san dole kowa zai mutu, amma me yasa kalaman ka ba za su zama na ƙarfafa gwiwa a gare ni ba, sai dai ka kashe mini zuciya da sanya mini tsoro da razani. Ga ɗanka a cikina, ga ka babu lafiya, nan a kore mu, ga shi 'yan uwanka ba a gan su ba, kuma ka saka ni a gaba, kana gaya mini wannan maganganun. Har ka manta ka ce kowannenmu ruhin ɗayanmu ne a jikinsa? Dama faɗa ka ke yi dan jin daɗin bakinka ba ka so na, ba ka tausayina" Yanayin yadda take kukan, ya sanya ya fahimci tsagwaron damuwa ce, ta rasa yadda za ta yi, shi ne ta yi amfani da wannan damar take hucewa. Ya yi shiru ya sunkuyar da kai. Ta ci gaba da kuka tana surutu, ganin ya yi mata banza ya sanya ta haɗa hannunta, ta hankaɗe shi daga gabanta ta tashi ta fita daga ɗakin. Ƙofar ɗakin ta fita, ta samu guri ta zauna ta yi shiru. Sauro ya baibayeta da cizo amma sam, ba ta jin zafin cizon sauron, sai tunanin mene ne mafita a wannan halin da suke ciki. Ya fito daga ɗakin, kawai ya danƙi hannunta, ya mayar da ita cikin ɗakin. Ta fizge hannunta, ta koma gefe ta ja ta tsaya a tsaye. Sai ya ƙyale ta, ya tayar da sallar isha'i, ya idar ya yi kwanciyar sa. Ita ma sallar Isha'in ta yi, sai dai kuma amai ya saka ta a gaba, ta kasa sukuni. Da ta zauna sai amai, haka za ta tashi ta tafi banɗaki. Ta duba cikin kayan da take dafa masa tea, ta samu kanumfari ta saka a bakinta. Ta yi zamanta a ƙasa ta ƙi hawa katifar ma, ta kwanta a ƙasa. Sai dai bacci ya gagari idonta, tunaninta kawai mene ne mafita? Ina za su koma? Yaya za ta yi da rashin lafiyar sa. Ta kalli inda yake, idonsa a lumshe. Gani ta yi kamar ba ya numfashi. Ta yi wata irin zabura, ta nufe shi ta kara hannunta a hancinsa. Ta ji ba ya numfashi, wata irin rikicewa ta yi za ta yi ihu, ya janyo ta ta faɗo kan katifar, ya zagaye ta da hannayensa, yana numfashi sama-sama, yanayin fitar numfashin nasa, ya sanya ta ƙara tsorata, saboda ba a daidai yake fita ba. "Ka daina tsorata ni, kuma ka cika ni" "A'a ki dain fushi" "Ya zan yi na daina, bayan ba ka tausayina" "Ina yi, na daina ba zan sake ba" daga haka bacci ya ɗauke shi. Amma Nana ta kasa bacci, ko baccin ya fara ɗaukar ta, sai ta buɗe ido a rikice, ta duba ta ga yana numfashi. Sai daf da Asuba, nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Da safe Nana ta fita ta sayo ƙosai, ta dawo ta tarar ya yi wanka da kansa. Cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ba ka bari na dawo na yi maka ba, kar ka wahala" "Ni jariri ne?" Ya yi maganar cikin haki. Idonta ya cika da hawaye ta ce "Ina jinka a jikina, fiye da jaririna" Ya yi murmushi ya ce "Rayuwata Husnah" yadda ta ga Abincin ma ya gagara ci, abin ya ƙara razana ta, ita dama kasa ci ta yi. Saboda ƙamshin ƙosan ma amai ya saka ta. Saboda ta ga yana so ne sosai ya sanya ta je ta sayo masa. Ta ba shi magungunansa ya sha, ya kwanta a kan katifa ta din ga danne hawayenta. Ta ɗaukko ƙatuwar bagco, ta fara kwashe kayansa na wardrobe, ta zuba a ciki, ta ɗebo nata kayan ta zuba. Ta ɗaga kai suka yi ido huɗu tana kwashe kayan,ya yi sauri ya lumshe idanunsa. Ta share hawayenta ta ce "Sayyid, bari na je na ƙaro bagco, wannan ba za ta isa mu kwashe kayanmu ba" "Ina zamu koma?" "Zan laluba mana, in sha Allah ba zai gagara ba". Cikin damuwa ya ce "Haƙƙina ne, ni yakamata na yi, ki yi haƙuri" "Shugaba, ba na son Irin wannan maganar da ka ke yi wallahi. Bari na je na dawo" ta ɗauki kuɗi ta fice. Ba ta zame ko ina ba, sai can gidan su.Ta sha mamaki ganin yadda gidan su ya ɗauki gyara, ko ina shar kamar ba gidan ba. Sai dai hakan ba shi ne a gaban ta ba, ta yi sallama ta shiga gidan. Cikin matsananciyar sa'a, ta tarar da Baba a gidan. Mama ma tana nan, su na ta hira a tsakar gida. Suka amsa mata sallama, Baba ya ce "Too Nana yau a gari? Ai na zata dangin uwa taki, ko Imrana sun tafi da ke?" Nana ta yi murmushi ta ce "Baba su kai ni ina? Ina wuni Baba." "Lafiya ƙalau" Ta kalli Mama ma ta gaishe ta, ta amsa cike da za zaƙuwar son jin abin da ya kawo Nana, ganin fuskarta ɗauke da alamun damuwa, duk da murmushin da take yi. Suwaiba ta fito daga ɗakinsu, jin muryar Nana, Nana ta kalle ta, ganin yadda wata jibgegiyar kaza baƙa ƙirin, da bataliyar 'ya'yanta aƙalla, sun kai ɗari, su ma baƙaƙe ƙirin, su na ta fitowa daga cikin ɗakin, su na biyo Suwaiba. "Suwaiba kina nan dama, ina Jamila?" Ta kalli Nana, ba ta ce mata komai ba, ta nufi banɗaki ta shiga, kajin nan suka bi ta ciki suma. Nana ta dawo da hankalinta kan Baba, sai dai ta kasa magana. Ya ce "Nana ya aka yi ne?" "Amm Baba dama, an sallame mu ne, daga gidan da Sayyid yake gadi" Baba ya waro ido, Mama ta ce "Ikon Allah, laifin me ku ka yi?" Nana ta yi shiru. Baba ya ce "Magana ake yi miki fa. Ta haɗiye wani yawu mai ɗaci ta ce "Ba mu yi laifin komai ba, ba shi da lafiya ne, ba ya iya aikin" Baba ya ce "Subhanallah, zazzaɓi ko zawo?" Kawai kuka ya zo wa Nana ta ce "Ciwon zuciya" Sai da Baba ya zabura, Mama ta ce "Too ciwon zuciya kuma? Ciwon zuciya ai na masu kuɗi ne, ina talaka ina ciwon zuciya?" Baba ya ce "To yanzu yaya aka yi?" "Baba na rasa yadda zan yi, yana kwance babu lafiya, allurar dubu ɗari biyu da hamsin za a din ga yi masa wata, ko a saka masa na'ura a zuciya ga shi kuma an sallame mu" Baba ya ce "Danƙari to ni Nana ina na ga wannan uban kuɗin har haka? Ina 'yan uwansa?" "Ba a san inda suke ba" ta yi maganar tana share hawayenta da gefen hijjabinta. Baba ya yi shiru sannan ya ce "Ina 'yan uwansa suke a Nijar ɗin?" "Baba ban sani ba, shi ma kansa bai san su ba" "A'a wane irin shirmen banza ne wannan? Tsawon wata shidan bai kai ki, kin gano 'yan uwansa ba?" Nana ta yi shiru, saboda takaicin da tambayar tasa ta bata. "To kin ga dai ɗakin Gaddafi, kayansa ne a ciki, kuma ya kulle abin sa, ya koma Ikko. Nan cikin gida kuma... Mama ta yi caraf ta ce "Ba zai ma yiwu ba, ya za a kawo mana gardi cikin gida, ga yara mata har da 'yan mata a cikin gida a ajiye, ba zai ma yiwu ba wallahi, ku nemi dai wata mafitar" Baba ya ce "To faɗi wace mafitar za a nema?" "A'a wannan kuma ku za ku nema, amma ba zai yiwu a kawo ƙato da ba muharraminmu ba, a yi mana jinya. Ciwon da ba warkewa ake yi ba, sai dai mutum ya gama wahala ya mutu, tun da dai babu kuɗin kula da shi." Wani irin kuka da dana sani, ya ƙwacewa Nana. Baba ya ce "Ya isa haka, yanzu ki koma can gidan, ki ɗan roƙe su, su ɗan ƙara muku lokaci, kafin a san abin yi" Nana ta yinƙura, Baba ya ci gaba da magana, har da gaya mata yadda za ta marairaicewa wanda suke yi wa aikin, da nuna musu tsagwaron talaucin da suke ciki, yadda za su ƙara ɗaga musu ƙafa. Tuni Nana ta daina gane abin da yake faɗa. Haka ta koma gidan, ba tare da samo mafita ba. A ƙofar ɗakinsu, ta tarar da shi yana zaune, tun daga shigowar ta, tana iya hango yadda yake haki. Ta ƙarasa da sauri, ta ajiye ledar hannunta ta ce "Sayyid ka gaji da jira na ko? Sannu ya jikin naka?" "Na samu sauƙi Alhamdillah" ta janyo ledar, ta fito da kankana fal, ta ce "Ka na son kankana, za ka iya sha?" Ya jinjina kai alamar eh. Ta din ga ɗauka tana saka masa a baki, Allah ya taimake ta, ya sha sosai. Sai dai gaba ɗaya ta rasa a ina yakamata ta ajiye tunaninta, duk lissafi ya ƙwace mata. Ummi ce ta faɗo mata a rai, amma ta kasa kiranta, saboda tana ganin Ummi mace ce, za ta iya ɗora mata ɗawainiya, amma kasancewar ba ta da wata mafita,ya sanya dole ta kira ta. "Hello Nana" "Na'am Ummi" "Ya na ji muryarki a sanyaye? Ko an gamu ne?" "A'a Ummi, an kore mu ne daga gidan da muke gadi" Ummi ta ware murya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, saboda me?" "Ba shi da lafiya ne? Ciwon zuciya yake fama, kuma gobe in Allah ya kaimu, aka bamu mu tashi, sabon mai gadi zai fara aiki. Na je na gaya wa Baba, amma ya ce na koma na ba wa masu gidan haƙuri su ƙara ɗaga mana ƙafa. Kuma sun yi mana ƙoƙari na san ba za su sake bamu dama ba". Ummi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yi haƙuri Nana, ki kwantar da hankalinki, ni da kin bi ta tawa ma, ba za ki gaya wa Baba ba, dan babu abin da zai yi miki. Yanzu za a samu kuɗi a hannun ki? A duba muku ko ɗaki ɗaya ne a nan unguwar, ku kama haya, kafin a samu yadda za a yi" Wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi ta ce "Eh, idan aka samu mai arha, zamu iya kamawa in sha Allah" "To shikenan, ki saurareni zuwa da safe in sha Allah, a daren nan zan bayar da cigiya, na san za a samu, mu nan Kurna ɗaki ba ya wahala" Cikin farin ciki ta ce "Allah ya saka da alkhairi Ummi, na gode sosai da sosai " ba ta tsaya katse wayar ba, cikin farin ciki ta koma ɗakin su da sauri ta ce "Sayyid, Ummi za ta saka a sama mana ɗaki, sai mu kama mu koma. Dama unguwar fuskar jama'a ce, zan iya fara sana'a ma na tara kuɗin allurar ka" Ya din ga bin ƙwayar idon Nana da kallo, cikin tausayawa da karaya. A saɓule ta ce "Ya na ga ba ka murna?" "Ina yi rayuwata, ina jin tausayinki ne, sab... "Za ka fara ko?" Ya girgiza kai alamar a'a. Haka ta tattare musu kayan su. Ƙarfe tara na dare, Ummi ta kira ta. Ta ɗaga cikin murna "Nana an samu gida na dubu ɗari da hamsin shekara, sai kuma ɗaki, amma shi wata shida dubu talatin, kuma da mutane a gidan" Nana ta ɗan yi shiru ta ce "A bamu na wata shidan tukuna, kar na ƙarar kuɗin hannuna. Kin ga zamu din ga komawa ganin likita, ga harkar abinci da magani, ko kuwa ya ki ka ce?" Ummi ta ce "Nima na yi tunanin hakan, turo kuɗin a cikin opay ɗina, na tura musu" "To Ummi, na gode sosai bari na turo miki" Nana jiki na rawa ta tura wa Ummi kuɗin, ta je ta samu Sayyid tana gaya masa. "Sannu Allah ya yi miki albarka " ya furta jiki a sanyaye. "Amin shugaba" "Ina jin yunwa" cikin murna ta ce "Za ka ci abinci? Na dafa maka? Me za ka ci?" "Ke ce ba ki ci abinci ba, nake jin yunwa" ta tura baki ta ce "Ba na jin yunwa, idan na ci amai zan yi" Ya sake cewa "Rashin lafiyata za ta ƙaru, ki ci kaɗan" "Dan Allah ka yi haƙuri. Kar ciwon nan ya ƙaru, na sha shayi ai idan na ci amai zan yi" ta tsallake shi ta kwanta. "Ki ci ko kaɗan ne" Cikin shagwaɓa ta ce "A'a na ƙoshi" "Allah ya sa wannan karon babyn ya zauna" "Amin, ya kuma baka lafiya ingantacciya" "Amin" Nana ta ce "Wallahi sai daɗi nake ji, da muka samu hayar ɗakin nan, ka ga ma zauna, na yi wata sana'ar ma, mu tara kuɗin yi maka allura". Ya kwanta a jikinta ya ce "Ba sai kin yi haka ba, ba na son duk wani abu da zai sanya ki sha wahala, gaba ɗaya ji nake na zame miki wani nauyi". "Ni ka daina faɗa ba na so." "Tom" "Rayuwata" "Na'am Shugaba Sayyid" "Ina mamakin inda su Habu suka tafi suka bar mu, na san ko ba komai da kin sami rangwamen wata ɗawainiyar, amma da yardar Allah idan na samu sauƙi, zan nemi abin... "Sai da safe" ta kaste shi. Ya ɗan yi murmushi ya ce "Ai na daina, kar ki yi fushi" Ta ce "Ai ba fushi ba, kuka ka ke son saka ni" "To na daina, kar ki yi fushi, kuma kar ki yi kuka, nima zan yi" yayi maganar yana yawo da hannunsa a jikinta. Sakin jiki Nana ta yi, saboda yadda ta yi kewarsa, sai dai a wannan karon ma, ya ji shi ba daidai ba, ya kasa komai. Yana jin yadda Nana ta yi bacci, amma shi bacci ya ƙauracewa idanunsa. Tunani daban-daban ya cunkushe masa zuciya. Ji yake da yana da gurin zuwa, da ya tafi ya bar ta, saboda wahalar da take ta yi da shi. Sai dai ko alama bai ji zai iya aikata hakan ba, kamar yadda yake faɗa, a cikin jikinsa yake jin ta. Ba zai iya matsawa ko ina daga gare ta ba. Ya kumna fitilar waya, ya haska ta ya kalli yadda take bacci cikin aminci, ba tare da damuwa ba. Fuskarta ta faɗa. Wani irin tausayinta yake ji, yadda yake ganin ya zame mata alaƙaƙai. Ya jima a zaune, kafin ya kwanta bacci. Shi ma sai da ya haɗa fululluka, ya tada bayansa da shi, kamar yadda likita ya nuna musu, sannan ya samu bacci ya ɗauke shi. Fitsari ya tashi Nana an fara kiraye-kirayen sallar Asuba, sai da ta fara dubawa, ta ga yana numfashi, sannan ta shiga banɗaki ta yi alwala. Ta fito ta ɗauki ruwa leda biyu ta shanye, wani irin daɗi ruwan ya yi mata, dama ga cikinta babu abinci, sai ta ji ta ƙoshi. Ta tayar da sallar Nafila, ta yi ruku'u, ta fara yinƙurin amai, ta hanci ta baki. Kakarinta ne ya tashe shi daga bacci, ya yinƙura ya bi bayan ta. A bakin ƙofa ya tsaya cikin tausayawa. Sannu kawai yake iya mata, abin duniya duk ya dame shi. Tare suka yi sallar asuba, ta kwanta saboda yadda jikinta duk ya saki. "Asmy" ya kira sunanta yana shafa bayanta. "Me za ki ci?" Ta girgiza masa kai alamar babu. "Mu je Asibiti to" "A'a Sayyid, zan ware in sha Allah, bari na yi bacci" Abin da yake bata mamaki, a kwanakin nan gaba ɗaya ta daina ganin Ƙaisar, ya daina zuwar mata, ko a bacci ko a zahiri. Ta ji daɗin baccin da ta yi, amma yanayin jikinta, babu daɗi zazzaɓi ne yake son kama ta. A hankali ta ji ana matsa tafukan hannayenta. Ta buɗe idonta, suka yi ido huɗu yana ta matsa mata hannu a hankali. "Sayyid ba ka da lafiya ka na wahalar da kan ka" "Ki zo ki ci Abinci, kin ga za ki ci ko?" Ya yi maganar yana nuna mata buredi, da soyayyen ƙwai da ya fita ya sayo mata. Ta yi zuru da ido tana kallonsa, har yanzu yana haki idan yana magana. Ya fara ƙoƙarin ɗago ta. Ta yinƙura ta tashi, ya zubo mata shayin da ya dafa. Ta kafa kai duk da zafin shayin nan, amma ya yi mata daɗi, ta buɗe maƙogwaro ta din ga sha. Ta cakali buredi da ƙwan kaɗan, shi ma dan kar ya ji babu daɗi, ta ci. Ta tashi ta ci gaba da tattare musu kayan su. Har cikin zuciyarsa yake jin zafin barin gidan da za su yi. Ɗan abin da ta ci, ko mintuna talatin ba a yi ba, shi ma sai da ta amayar. Cikin matsananciyar damuwa yake kallon Nana, idanunsa suka yi jawur, ƙirjinsa ɗauke da magana, amma ya gaza furta komai, sai zafi da raɗaɗi da zuciyarsa take yi. Ayshercool 08081012143 50 Ji suka yi an buɗe ƙofar gate, an yi sallama. Ya nufi bakin ƙofar su, ya leƙa ta taga, ya juyo ya kalli Nana ya ce "Yayarki ce" Ta waro ido ta ce "Wacce?" Ta taso tana leƙawa ta ga Ummi, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta. Ta ɗaga labule tana wani irin murmushi mai cike da nuna zallar farin ciki. Nana ta ce "Ƙaraso baƙuwar Safe" "To na koma ne?" "A'a ni na isa, shigo" Ummi na shiga, ta tarar da Sayyid, ya ɗora mayafin rawaninsa a kansa. Ummi ta ce "Sannu ina kwana" "Lafiya kalau Alhamdillah" "Ya jiki kuma, ta ce ba ka ji daɗi ba" "A'a na ji sauƙi Alhamdillah" "Allah ya ƙara afuwa" ya amsa da Amin. Ta mayar da idonta kan Nana ta ce "Dama zuwa na yi, na gani idan ba ki haɗa kaya ba, na taya ki, na biya mai 'yar ƙurƙura za su zo, tare da Nasiru a kwashe kayan. Ai dama Hajiyar da ki ke yi wa aiki ce, ta saya muku ko?" Nana jinjina mata kai. "To duk a kwashe su, na je na ga ɗakin, babu laifi, babba ne da banɗaki a ciki. Sai kuma akwai mutane biyu a gidan, duk masu aure ne." Nana ta ce "Ni dai tun da mun samu gurin zama, Alhamdillah Allah ya saka da alkhairi Ummi" Sayyid ya ce "Ma vie, bari na jira ku a waje" Ummi ta ce "Yi haƙuri. Na zo na takura muku ko?" Ya ce "A'a mun gode sosai da sosai da kulawa". Ya fita waje ya samu guri ya zauna. Ummi ta ce "Yau ma mijinki ya yi magana Nana" Nana ta yi dariya ta ce "Ai dama yana yi fa" "Gaskiya yana jin jiki Nana, na ji yana haki, ina 'yan uwan nasa ne?" Nana da kamar ta yi shiru, sai dai ta warware wa Ummi komai da komai, duk da ta ɓoye mata wasu abubuwan. Jiki a sanyaye Ummi take maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Nana Baba bai yi miki adalci ba, duk da mahaifinmu ne. Yanzu shikenan ba a san inda wannan 'yan uwan nasa suke ba, bayan taɓin hankali ba ma shi da asali, bai san daga ina yake ba?" "Ki yi a hankali kar ya ji, ba zai ji daɗi ba" ta yi maganar idonta na cika da hawaye. Ummi ta jinjina kai ta ce "Ki yi haƙuri Nana, komai tsanani akwai sauƙi in sha Allah, ki daina kuka" "Ummi ba kukan aurena da Sayyid nake yi ba, tausaya masa nake yi. Ga larura ban sani ba ma, ko guduwa suka yi suka bar shi. Amma dai na kasa yadda da hakan, da za su gudu su bar shi, da ba su tsaya masa zuwa yanzu ba. Tun da muka yi aure, musamman Habu shi ne yake ɗawainiya da mu. In sha Allah zan kula da shi, iya yi na" "Allah sarki Nana, kaf cikinmu babu mai ƙarfin tawakallinki da kuma haƙurin ki, Ubangiji Allah ya ƙarfafe ki, kar ki sare ba ki san a inda Allah zai ji ƙan ki ba. Idan ki ka lissafa yadda aurenku ya kasance, ke kin san akwai hikimar Ubangiji a cikin hakan, ki yi haƙuri." Ta yi murmushi ta ce "Ba wani abu in sha Allah, na gode sosai da sosai Ummi, da yadda ki ke ɗawainiya da ni, ba tare da kin gaza ba" "Matsa ko na mare ki, wace ɗawainiyar na yi miki?. Matsa ni" Nana ta matsa tana murmushi. Yana zaune yana tasbihi da yatsunsa, Siyama ta fito daga cikin gidansu, ta nufi gurin ajiye motoci, sam ba ta lura da shi ba, sai da ta fito da mota, ta gan shi a zaune, babu rawani sai mayafin da ya ɗora a kansa. Tun da suka yi ido huɗu, gabanta ya faɗi. Sai dai ta dake, ta ɗaukko wayar ta tana yi masa hoto, ba tare da ya sani ba. Ta ƙaraso da motar, ta fara horn, ko ɗaga kai bai yi ba, balle ta sanya ran zai buɗe mata gate ɗin. Kawai ta rufe motar ta tunkare shi. "Amm sannu, ina ta horn zan fita ne" ta yi maganar tana ƙara yaba kyawun da Allah ya yi masa. "Magana fa nake yi" Bai kalle ta ba, ya tashi ya nufi gate ɗin. Ummi ta ce "Nana wai me ki ke yi a jikin tagar nan?" Nana ba ta amsa mata ba, ta ɗora mayafi a kan rigarta ta fita. "Me yasa za ki saka shi buɗe gate, ina tunanin aikinmu da ku ya ƙare, tun da yau za mu bar gidan nan, kuma ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba." "Na kasa da ke ne? Tun da ba ku bar gidan ba, dole ya yi aiki, ko da aka ba ki kuɗi kin rage wani abu, saboda ba ku yi mana aiki ba?" "Ban rage ba kuma ba zan rage ba. A yau za mu bar gidan nan, idan ki ka ƙetare layi za ki sha mamaki." "Me za ki yi?" Ya nufo Nana, da jikinta ya fara tsuma ya ce "Ki yi haƙuri mu rabu lafiya" "Ka rabu da ni Sayyid" Murmushi ya yi,ya saka hannu ya riƙe Nana, da ranta gaba ɗaya ya ɓaci, har take tsuma. Ummi ta fito tana tambayar ko lafiya. Siyama ta ce "Ni kuma zan ga ƙaryar hauka da rashin hankali, ku zauna a ƙarƙshinmu, ku ci arzikinmu, kuma ki tsaya za ki yi mini rashin kunya?" Ummi ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri baiwar Allah, kin san zuciya. Ki yi haƙuri dan Allah ba ta kyauta ba" Nana tuni ta fita daga hayyacinta a hannun Sayyid, jikinta ya saki idanunta a lumshe sai hawaye da yake fita ta gefen idonta. Ummi ta tafi lallaɓa Siyama, Sayyid ya kai Nana ɗaki ya kwantar da ita. Jikinta ne ya fara karkarwa tamkar ana girgizata. Ummi ta dawo ɗakin, ta ga yadda ya rungume Nana a jikinsa, cikin damuwa take kallon Nana, tana mamakin dama haryanzu ba ta daina iskoki ba, ta ga wasu idan an yi musu aure abin yana lafawa, da ta ji Nana shiru bayan auren, ta ɗauka ta daina. Cikin damuwa ta ce masa "Dama tana yin haka haryanzu?" Ya ce "Ba kullum ba, sai ta yi fushi" Sosai Nana take kuka tana karkarwa dama Ummi matsoraciya ce, ko kafin ta yi aure, idan Nana tana yi tsoro take ji. Ya kai bakinsa kunnenta murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ki yi addu'a Husnah, ko ba za ta fito a bakinki ba, ki yi a zuciyar ki, ki daina kuka, ki yi haƙuri. Yi addu'a sosai ki daina kuka" A sama kamar cikin mafarki take jiyo muryarsa kawai, amma ba ta ganinsa, sai ita kaɗai a cikin sahara. Ta dage iya ƙarfinta tana Addu'a cikin ɗaga murya, amma a zahiri ba ta iya furtawa a kan harshenta, sai dai a cikin zuciyarta kawai. Tana zaune a cikin saharar, sai ga Yusra ta nufo ta. Nana ta yi shiru tana kallon ta. "Ƙawata" Nana ta ce "Yusra ko Haula?" "Haular dai. Ashe tashi za ku yi kuma?" "Eh, ina Yusra, ina fatan ba kya cutar da ita?" Ta yi murmushi ta ce "Bayan kin gaya mata abubuwan da za ta hana ni sukuni, zama take yi da alwala, ta daina tsorata ko na tsorata ta, hankalina ma dai ba a kanta yake ba sosai, ina can fafutukar neman soyayyar Ƙaisar" Nana ta yi shiru tana mamakin, yaya aka yi ita, ko ta yi alwalar ta yi addu'a, Ƙaisar ba ya fasa cutar da ita. "Da kin sani kin bar ni da matar nan, na ci gaba da wahalar da ita, yadda babarta za ta ƙara ɗanɗanar takaici, ba ta da mutunci shi yasa ma aka sakar mata 'yar ta" Nana ta ce "Ai ke ki ka saka a ka sakar mata 'yar, kuma Yusra ba bu wani abu da ta yi miki na laifi. Kuma ita kanta Hajiyar, tana da gaskiya mijina ba shi da lafiya ba ta yi ba dai-dai ba". "Ai shikenan, yanzu haka za ki tafi na daina jin ƙamshin girkinki mai daɗi" "Haula, dan Allah ko ke kin san waye Sayyid, daga ina kuma yake?" Haula ta waro ido ta ce "Taɓ, so ki ke dattijo ya kashe ni? Ko kuma ya azabtar da rayuwata. Yo bai bar ɗansa ba balle ni. Babu ruwana" Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah ki gaya mini, babu abin da zai yi miki " "A'a ba ruwana. Ai Ƙaisar ya gaya miki, shigen Asirin da aka yi wa Alhaji Fatuhu, aka yi wa mijinki, amma ke ni babu ruwana a wannan lamarin naku" Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Da gaske, abin da Ƙaisar ya nuna mini a mafarki ya faru? Alhaji Zailani ya yi wa Alhaji Fatuhu Asiri da ɗan Shukura?" "Sosai da gaske ne, ba ƙarya ya yi miki ba. Da zai ci gaba da buɗe miki ido, ki cigaba da ganin ɓarnar da bil'adama ku ke yi wa junanku, sai kin haukace. Alhaji Zailani yana gadon Asibitin, da aka ɗauke wa kishiyar Yusra ɗa" "Wace Yusran?" "Ƙawar ki mana, ita ce matar Sagir ta farko. Kin ga tafiyata kar na yi laifi, garin ɓare-ɓare na faɗi abin da za a hukunta ni" Nana ta zabura ta damƙi hannun Yusra da sauri, domin sake tambayar ta. Amma ta ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, ta buɗe idonta, ta kalli Sayyid, da ta riƙe masa hannu gam. Ta yinƙura ta tashi zaune, yanayin yadda ta ji jikinta, ta gane abin da ya faru. Ummi ta ce "Nana kin tashi? Ki wanke fuskar ki, masu ƙurƙurar sun kusa ƙarasowa.Ta tashi ta wanko fuskarta. Tana fitowa kuwa, masu motar suka ƙaraso. Aka kwashe kayan su Nana tsaf, sosai Nana take jin kewar barin ɗakin nasu. Ummi ta raka ta, suka shiga gurin Hajiy Halima, suka yi mata sallama. Tar Nana take jin hirar da suka yi da Haula a bacci, tana dawo mata kanta, ba tare da ta manta komai daga hirar ta su ba. Sai dai ta ƙi yarda zuciyarta ta gazagata komai a cikin maganganun Haula, ta dage wa zuciyarta da cewa shirmen mafarki ne, saboda tana yawan tunanin Yusra da take yi. Duk da tana jin kamar wani abu makamancin haka ya faru, wani abu mai kama da Alhaji Zailani ya yi wa Alhaji Fatuhu asiri, da kuma maganar jariri, amma ta kasa tuna komai. Ummi ta fita waje, domin tabattar da an shirya komai, a kan motar. Nana ta tarar da Sayyid a cikin ɗakin, yana ƙare wa ɗakin kallo. "Shugabana" ya waiwayo a hankali yana kallon ta. "An tafi samo abin hawa, za mu tafi, na ga ka zo ka tsaya a nan" "Nana" "Na'am Sayyid" "Ina kewar rayuwar da muka yi a ɗakin nan tare da ni da ke, ban san ya zan misalta miki ba. Ga ki dai a tare da ni, amma ina kewar ɗakin sosai. Sai na ji kamar ba zamu sake Rayuwa mai daɗin da muka yi a cikin sa ba" Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah, sai mun yi wadda ta fita komai da komai, da yardar Ubangijin talikai. Taho mu tafi" Da ƙyar ta riƙo hannunsa, suka fito idanunsa jawur. A adaidaita sahu suka tafi, da shi da ita da Ummi, sai dai ya ƙura wa gidan ido, tamkar ya ce a tsaya ya koma. Nana ta riƙo hannunsa cikin nata ta ce "Mu kyautatawa Allah zato, ina da yaƙinin rayuwar da zamu ci gaba, ta fi wadda ka ke kewa daɗi" "Ina fatan haka Rayuwata" Ummi ji ta yi tamkar ta yi tsuntsuwa, ta fita, ba ta san lokacin da Nana ta fitsare haka ba. Ta yi ta biye masa su na abu a gaban mutane, idan shi ba bahaushe ba ne, ai ita bahaushiya ce. Sun ɗan yi doguwar tafiya, daga Tudun yola, zuwa Kurna. Babban abin da ya soki zuciyar Sayyid, bai wuce ganin gidan akwai maza ba, duk da masu aure ne, amma har cikin zuciyarsa hakan bai yi masa tsari ba. Amma babu yadda ya iya, tun da ba shi da wata mafitar. Ɗakin nasu bai kai wanda suka baro girma ba. Cif ya ɗauke kayan su, sai dai babu sauran space ɗin kirki a ɗakin. Ga zafi saboda wata 'yar ƙaramar taga ce a ɗakin, kamar ɗakin tattabara. Abin takaicin bai wuce yadda yaran layin suka cika gidan ba, saboda ganin ana sauke kaya ana shiga da su cikin gidan. Sai da Ummi ta din ga korar yara, suka saka Sayyid a gaba da kallo, saboda ya yi shigar buzaye da rawani. Abin takaici har matan layin, wasu suka din ga leƙowa, masu son ganin ƙwal uwar daka kuwa, gidan suka din ga shigowa, da sunan sun zo gurin sauran matan da suke gidan, amma a zahiri, zuwa suka yi su ga suwaye kuma suka tare a gidan. Ummi tana tare da su Nana, har aka gama shirya ɗakin tsaf, duk da Nana su na da sauran kayan Abinci, amma ta yi waya aka kawo mata kayan abinci daga gidanta, ta girka wa Nana. Kasancewar Nana ba ita ta dafa ba, sai ta samu ta ci sosai. Sai da Ummi ta aiko musu da maganin sauro, saboda akwai sauro sosai da sosai a gidan, ga zafi, shi kuma ga yanayin ciwonsa ba ya son zafi yana buƙatar wadatacciyar iska. Haka Nana ta yi ta aikin fifita. Da safe Ummi ta sake aiko musu da Abin karyawa. Sai dai daga shi har ita, ba wani ci suka yi ba. Nana ta shirya ta ce "Sayyid, bari na je na yi musu sallama, mu gaisa da mutanen gidan" "To" "Yauwwa, kai ma zaka gaisa da mazajen su dan Allah, haka ake yi idan an je gurin, da ba a san mutum ba" kallon ta ya yi, ya maze kamar bai ji me ta ce ba, amma ta san ya ji ta sarai. Ta fita tsakar gidan, ta yi sa'a matan na tsagar gida, su na aikace-aikace. Nana ta ce "Sannu ina kwanan ku" Suka amsa mata cikin sakin fuska. Nana ta ce "Sunana Nana, ni ce muka tare a wannan ɗakin" "Allah sarki, sannu, ni sunana Barira, ga kuma Sajida, mai wancan ɗakin" Nana ta ce "Allah sarki, to ma sha Allah, Allah ya iya mana" sun so jan Nana da hira, amma ta tashi tsam ta koma ɗaki, gurin mijinta. **** "Alhajin Allah, aka ce ka tafi umara?" Alhaji Zailani ya ce "Ɗagawa na yi Alhaji Magaji, Madam ta tafi, saboda tafiyar ta yi karo da wani taro da za mu yi na shekara, shi yasa na ɗaga. Ashe kai ma na garin Abujan?" "Wallahi kuwa, na ma kwana biyu, ina neman wata kwangila ne. Ya jikin amininka kuwa, Fatuhu?" Alhaji Zailani ya yi wani irin makirin murmushi ya ce "Yana can ya kwanta dama" "Subhanallah, rasuwa ya yi?" "A'a na fa, yana nan a raye, amma rai ne kawai a jikinsa" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wallahi na yi mamakin yadda rayuwa ta yi wa mutumin nan tsutsun jaki lokaci guda, ga asarar dukiya, komai nasa an ƙwace an biya masa bashi. Kai Allah dai ya kyauta. Da tuni yanzu ya ja tawagar tafiyar umarar maulidin nan, da shi da 'yan uwa da abokan arziki" Alhaji Zailani ya ce "Sosai kam, faɗuwar wani ai tashin wani, yanzu waɗanda ya tare wa ƙofar arziki tun da ya gusa su ma za su ɗago" suka tafa su na wata irin ƙyaƙyacewa da dariya. ***** Jamila bakinta ya ƙi rufuwa, kasancewar a wannan karon a jirgi za su tafi babban birnin tarayya tare da Hajiya Sa'a. Hajiya Sa'a ta ce "Ai sai ranar da za mu je Dubai, ko Qatar ma, wannan ai ba wani abu bane ba sam. Sai kin gaji da hawa jirgi, muddin za ki ci gaba da bayar da haɗin kai" Jamila ta ce "Kai, wa ya ganni a Qatar" "Amm Jamila ina Nana kuwa?" "Tana gidanta, kwanaki ma na ji an ce ta yi ɓari" Hajiya Sa'a ta jinjina kai kawai. Daga airport aka zo da mota, aka ɗauke su aka tafi da su. Wani irin katafaren gida ne, da ko a irin finafinan Hausa da Jamila take gani, ba a taɓa hasko mai girma da kyansa ba. "Hajiya amma nan Hotel ne ko?" "A'a gida ne, a nan za mu yi taron shekara" "Ikon Allah, ai ganin gidan na yi ƙato guri-guri. To gidan waye?" "Gidan wani ne" Hajiya Sa'a ta bata amsa tana dariyar, ganin yadda gidan ya ƙayatar da Jamila. **** Kwanakin su Nana uku a gidan da suka koma, amma ita kanta, ba ta jin daɗin zaman gidan, duk da a gehtto area ta tashi ita ma, amma zaman gidan nan sam babu daɗi. Inda suka baro, sai ka wuni ba ka ji ƙwaƙwƙwaran sauti ba, sai na giftawar motoci. Amma gidan nan, musamman idan yamma ta yi, mata ne suke cika shi dam. A yi ta hayaniya, ana gulmace-gulmace, ga zantuttukan batsa da suke bajekolinsu a cikin gidan. A kafa dashi, a ci bashi, a yi gulmar wannan a yi ta mijin waccan. Hatta shimfiɗar aurensu ba su bar ta ba, bajekolin ta suke yi a wannan gidan. Yanzu ma yana kwance ya lumshe idanunsa, su na ta hayaniya su na musu, a kan kuɗin cefane. "Shugaba" ya ɗago idonsa ya kalle ta. "Sannu ya jikin?" Ya sake lumshe idanunsa ya ce "Na warke" Ta yi murmushi ta ce "Sayyid, na san ba ka jin daɗin zaman gidan nan, amma ka yi haƙuri in sha Allah, idan muka samu hali sai mu bar gidan nan" Ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar sauran jin daɗi, in dai ki na kusa da ni" ya yi maganar yana shafa fuskarta. "Sayyid" "Husnah" sai kuma ta yi shiru. "Faɗi mana" "Ba komai fa" "Shikenan zan shigo mafarkin ki, na ji" Ta ɗan yi dariya ta ce "Allah ne ya san dalilin da ya sanya ya haɗa mu, gaba ɗaya rayuwarmu wata iri, daban da ta sauran mutane, mu dai gamu nan" Ya yi murmushi ya ce "Shi yasa ba zan daina yi wa Allah godiya ba, da ya haɗa ni da ke. Rayuwa da ke wata afuwa ce a gare ni Rayuwata" ta ɗora hannunta a kan nasa tana murmushi. A hankali murmushin fuskarsa ya gushe, ya ce "Ba ni wayar nan, mu sake dubawa, ko wayar Habu za ta shiga" Nana ta ɗaukko wayar daga gefen ta, ta miƙa masa, ya karɓa ya danna lambar Habu, amma ta ƙara maimaita masa, wayar a kashe take. Ya sauke hannunsa cike da damuwa da fargaba. "Sayyid ka daina damuwa, in sha Allah su na cikin ƙoshin lafiya" "Asmy, rayuwa ba za ta tafi a haka ba. Akwai ɗawainiya da yawa. Ki yi haƙuri na san juriya da rashin son damuwata ya sanya, ki ke danne wa. Da nuna mini ba komai, amma na san ɗawainiyar nan ta yi miki yawa. Wallahi zuciyata na yi mini zafi, idan na ga ki na wahala" "Ni ba wahala nake yi ba" ta yi maganar tana tsuke baki. "Shikenan, na daina maganar" Jin wayar na vibrating, ya sanya suka kai hankalinsu kan wayar a tare. Amma sunan Adda Saude ne yake yawo, a kan screen ɗin wayar. Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Adda Saude ta amsa Nana ta ce "Adda ina wuni?" "Lafiya ƙalau Nana, ya ki ke ya mijin naki?" "Lafiya ƙalau, ina Adda Fati?" "Tana gidanta, ga Maijidda take son yin magana da ke" wata irin zabura Nana ta yi cikin murna ta ƙara nutsuwa. "Assalamu alaikum" "Mama" "Na'am Nana ya ki ke?" "Lafiya ƙalau, ya gida ya su Walida?" "Su na nan lafiya ƙalau Alhamdillah, ya mai gidan na ki?" "Lafiya kalau Mama" Sayyid ya ƙura wa Nana ido, yana ayyana abin da take ji a zuciyarta. Saboda fara'ar da ta mamaye fuskarta. "Ki na ji Nana, ina nan ina ƙoƙari, duk yadda zan yi zan zo Kano, na ganku in sha Allah, ki ƙara haƙuri, na san kin yi ki ƙara, ina nan tafe in sha Allah" "Kar ki damu Mama, ni jin muryar nan ta ki ma da na yi, na ji daɗi sosai. Kuma in sha Allah kafin ki zo, za mu riga ki zuwa da yardar Allah" "A'a ni ɗin dai zan zo na gan ku in sha Allah, ina fatan dai babu wata matsala?" "Babu matsalar komai Mama" "Yauwwa Nana, zan ci gaba da jaddada miki, ki riƙe Allah ki riƙe addu'a. Ki bi mijinki ku zauna lafiya. Ina fatan kin fafa sana'a Nana?" "A'a Mama, amma zan fara in sha Allah" "A'a Nana, kullum ki ce mini za ki fara, amma ba ki fara ba. Ina da buhun barkono, zan sayar na turo miki kuɗin, ki fara sayar da wani abin. Idan kuma barkonon ki ke so, na aiko miki Nana. Ni dai ban taɓa ganin mijin nan naki ba, amma yadda su Fati suka bani labari, da yadda nake jin muryarki, a duk lokacin da na kira waya, ina samun nutsuwa. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Amma ki yi sana'a, tun da mai ƙaramin ƙarfi ne, ki taimaka masa, kar ki sakar masa nauyi gaba ɗaya" "To in sha Allah Mama, amma dan Allah ki bar barkonon ki, zan yi sana'ar nan da yardar Allah, na rasa abin da zan fara sayarwa ne. Amma zan fara" "A'a zan sako miki buhu ɗaya a mota, ki gwada, kar ki zauna haka ba kya juya taro da sisi" "To Mama in sha Allah, na gode sosai da sosai " "Yauwwa, haryanzu ba ki da lambar Imrana ki turo mini" Nana ta ce "Ba ni da ita Mama" "To shikenan, ki gaida mijin naki" suka yi sallama, ta sauke wayar a hankali, ta yi shiru tana zancen zuci. Ta san da Mamanta su na tare da Baba, da ko ba za ta ɗauke mata ɗawainiyar da take ciki ba, za ta tausaya mata ta taya ta jajanta lamarin. Amma tun da ta je gida ta sanar da Baba halin da take ciki, ko ta waya bai kira ya tambayi ya suka ƙare ba, ya kuma mai jikin ba. Dama Mama ba a magana, mutanen da tun da ta yi aure, ba su taɓa taka gidan da take ba, yaushe za ta sanya ran su damu da halin da take ciki. Tana iya ƙoƙarinta, gurin rintse idanunta, daga aibun iyayenta, saboda kar zuciya ta ɗebe ta, ta afka cikin fushin Ubangiji, amma daga yadda Baba ya yi mata gurin aurenta, zuwa yanzu zuciyarta na ƙoƙarin bijirewa. "Ya ne?" Ta ji muryarsa. Firgigit, ta kalle shi ta ce "Babu komai. Mama na gaishe ka" "Ina amsawa, ina son na yi magan da ita, amma ina tsoron na karɓi wayar, maganar ta ɗauke" Nana ta ce "Haka ne, bari na fita da gas ɗina waje, na dafa mana taliya, ga kayan miya na aika yaran Ummi, sun sayo mini, ai za ka ci ko?" "Ke ma za ki ci ko?" Ta yi dariya ta ce "In sha Allah" Ta ɗauki kayan girkinta, ta fita kusa da ɗakinta, ta ɗora. Gaisawa kawai suka yi da matan gidan, ta nutsu a kan aikinta. Tana zaune mata na ta shiga suna fita, kowacce da abun da yake kawo ta. Da tana da isasshen guri, a ɗakinta, da babu abin da zai fito da ita waje yin girki, balle ta din ga kallon tumasancin da matan suke yi. Har da wadda daga ita sai hijjabi, da zani, babu riga babu brezia. Idan masu gidan suka dawo, haka suke tsallake mata su shiga ɗakunan su. Tun da Nana ta kammala girki, ta tattara komai nata ta shige ɗaki. Ta ji daɗin ganin yadda yau yake iya cin abinci, dan haka ita ma ta zage, duk da ba wani daɗi yake yi mata ba. Saboda rashin kamun kai na matan layin nan, sukan kai har goma da rabi, su na shiga su na fita a gidan tamkar bariki. Nana har ta fara murnar abincin da ta ci ya zauna, lokaci ɗaya ya taso sai da ta amayar da shi baki ɗaya. Tana fitowa daga banɗakin, ya ƙura mata ido, har ta ƙaraso ta kwanta a jikinsa, tana ɓata fuska. Ya ƙanƙame ta yana faɗin sannu. "Ɗan ka ya hana ni cin abinci, kuma yunwa nake ji" ta yi maganar hawaye na cika mata ido. "Yi haƙuri, sannu, to mu je Asibiti"ya yi maganar a jere. "A'a Sayyid, dole mu din ga tattala kuɗi yanzu. Yunwa nake ji sosai" ta yi maganar cikin shagwaɓa. "Me zan sayo miki?" "Ba komai" ji ta yi numfashinsa yana fita da sauri da sauri, a tsorace ta kalle shi ta ce "Sayyid jikin ne?" "A'a" ya furta a hankali. "Dan Allah ka yi haƙuri, da wasa nake yi maka, ai na san mata masu ciki, su na fuskantar irin haka, dan Allah ka kwantar da hankalinka. Ba na so mu zauna shiru, shi yasa na tsokane ka" "Tom" ya amsa a hankali. Kasancewar jikinta babu ƙwari, ya sanya ta kwanta da wuri, ganin shi ma ya samu bacci. A cikin bacci ta din ga jin wani irin rugugi, tamkar na hadari, ga shi ba lokacin damina ba ne. Ta buɗe idonta, ta ji wani irin huci, na fitowa daga gurin da yake kwance, ga wani irin nishi da kakari da yake yi, tamkar an yanka rago. Ayshercool 08081012143 51 Fitila ta laluba, ta ɗaukko ta haska shi, wata irin jijjiga yake yi, tamkar zai zauce, yana wata irin miƙa, yana nishi. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya faru? Me ya same ka?" Ta kai hannunta jikinsa, wani irin zafi ta ji yana fitowa daga jikinsa. Cikin zafin nama, ta cire rigar jikinta ta fara ƙoƙarin rungume shi. Amma ya hankaɗe ta, yana ci gaba da kakari. Ta sanya ƙarfi, da ƙyar ta shiga jikinsa ta ƙanƙame shi . "Zafi, ƙonewa nake yi, wuta Nana jikina ana ƙona ni" ya yi maganar haƙoransa na karo da juna, muryarsa na sarƙewa. "Sannu Sayyid, ka yi haƙuri ka daure, na san ka na shan wahala, kar mutanen gidan nan, su fuskanci halin da muke ciki ka yi haƙuri" Ta yi maganar cikin dauriya da dakiya, saboda yadda ita kanta zafin jikin nasa, ya sanya take jin, tamkar ta yi ihun, saboda tamkar ta rungume ƙarfen da aka ciro daga cikin wuta haka take ji. "Ahhh zafi!" Ya sake furtawa cikin mawuyacin hali. Ta kwantar da kansa a kafaɗarta, tana karanta masa abin da ya sauwwaƙa a kunnensa. "Ki cika ni, kar cikin nan ya kuma zubewa" "Babu abin da zai same shi" Ta saka bakin ta a kunnensa na dama, ta fara kiran salla. Ya yi wata irin miƙa, jikinsa ya sandare a haka. Ta koma kunnensa na hagu, ta fara iƙama, sai dai ta kakare, bayan shaƙar da ya yi wa wuyanta. Ya miƙe ya danne ta a kan katifar, ta kasa addu'a, ta fara kiciniyar ƙwacewa, cike da tsoron kar ta yi wani abu, da zai sanya mutanen gidan su ji, su zo su tarar da su a wannan yanayin. Gaba ɗaya ya rikiɗe mata, zuwa wannan tsohon cikin mummunar siffa, har dogon farin gemun sa, yana taɓa fuskarta, ga numfashinta tana jin zai bar gangar jikinta. A kan wani tsauni ta ganta, ta yinƙura da ƙyar, ta ja jikinta saboda azabar sanyin da take ji. Wuyanta sai raɗaɗi da zafin shaƙar da ya yi mata, ne yake damunta. Babu tsammani ta ga tsohon nan, a tsaye yana kallon ta. "A'uzubikalimatillahi tammat" ta furta tana ja da baya. Ya ɗan ja da baya, yana ci gaba da kallon ta. "Me na yi maka ne? Laifin me na yi maka da na cancanci haka?" "Ba ki yi mini laifin komai ba, hasali ma waɗanda suka yi mini laifin, ba sa Duniya amma ba zan taɓa hucewa ba, sai na hukunta su ta hanyar tarwatsa zuriyar su, da gadar da azaba da wahala ga duk wanda ya fito daga cikin zuriyar su. Na zaɓi na azabtar da ke fiye da kowa, saboda hakan ne zai sanya na ƙuntatawa Ƙaisar, da ya fifita bil'adam a kaina. Zan ci gaba da addabawa rayuwar ki, sai na sabauta ku a ƙarshe na sanya mijinki ya yi ajalinki. Ban taɓa alfahari da yi wa biladama wani aiki ba, kamar aikin da na yi a kan Buzun nan saboda a dalilinsa ya sake sada ni da abokan gaba na, kuma ba zan gushe ba sai na ɗauki mummunar fansar da sai na bar muku mummunan tabo a zuriyar ku" "To idan mu zuriyarmu sun yi maka laifi, shi kuma mijina me ya yi maka?" Ya tako ya ƙaraso gaban Nana ya durƙusa, ta din ga ƙoƙarin yin addu'a, amma ta kasa. Ya buɗe bakinsa, tana iya hango cikin bakinsa, yadda wani irin baƙin hayaƙi, ke ƙoƙarin fitowa daga bakin nasa, sai dai kan ya yi wani abu, ta ga ya ɓace. Ta motsa a hankali ta kalli Sayyid a can gefe, ya takure yana bacci. Ta matsa ku sa da shi, ta ji jikinsa ya saki babu zazzaɓin. Sai dai wani irin bacci yake yi,rabin idonsa a buɗe, ƙwayar idanunsa baƙar ta ɗauke sai farar. Ga alamar yana numfashi. Ta ɗauki bargo ta lulluɓe shi. Ta kunna karatun Alkur'ani a waya ta ajiye a gefe. Ta ja ta zauna ta yi shiru, abin duniya ya ishe ta, sai kuma ta koma tunani kamar yanzu ta yi rauni a ibada, shaiɗan ya yi galaba a kanta, kan cewar idan ta yi addu'a wahala ta fi tsananta a gare ta. Domin hatta addu'a kwanciya bacci, ranar da ba ta yi ba, sai ta kwanta ta tashi lafiya ƙalau, ba mafarkai babu ciwon ƙafa ko baya, ko ma jikin baki ɗaya. Azkar ma ba ko yaushe take iya yi safe da yamma ba. Ta yinƙura ta tashi, ta je ta ɗauro alwala, ta zo ta sake haska shi, ta ga bacci yake yi, ta nemi guri ta kwanta, ta ɗora hannunta a goshinsa, tana karanto addu'oin kwanciya bacci. ***** Jamila na miƙe a kan katafaren gadon, ga chips a gaban ta, ga kakkauran shayi, hannunta riƙe da zuƙeƙiyar wayarta. Abba ne ɗan gidan Hajiya Sa'a, yake yi mata magana ta what's app. "Ƙanwata, shi ne tun da ku ka sauka, ba ki neme ni ba ko?" "Ba haka ba ne, ba ni da data ne" "Kuma ba ki gaya mini ba, bari na saka miki. Ina Mummy?" "Ta fita" "Wai ina ku ka je ne a Abujan?" Jamila ta yi masa reply da "Ban san sunan gurin ba, wani gida ne dai mai kyau sosai" "Ok, to dan Allah ki kula da kan ki sosai da sosai, Allah ya bayar da nasarar abin da aka je nema, na ji ta ce taron kasuwanci ne ko?" "Wallahi dai ban sani ba tukuna" "Haka ta ce mini ni, ta tafi da ke ku ka bar ni a gida, ai shikenan" har za ta rufe data ta ga 10gb na data. Sai ta washe baki ta ce "Har 10gb na gode sosai da sosai" Abba ya ce "Babu godiya tsakanin, Yaya da ƙanwarsa, ki kwanta da wuri ki yi bacci. Ki yi addu'a kuma, sai da safe" "To yayana na gode sosai da sosai" suka yi sallama, ta rufe laste seen ɗin ta da online, ta tafi kallon videos a tiktok. Hajiya Amina ce ta shigo ɗakin, ta ce "Jamila ba ki yi bacci ba?" "Eh Mummy, kin dawo?" "Eh zan sake zuwa wani gurin ne, babu lallai na dawo da wuri, za mu yi meeting, ki yi kwanciyar ki" "To shikenan, sai kin dawo" "Yauwwa amma ba kya buƙatar wani abu, ko jin yunwa ko?" Ta ce "A'a a ƙoshe nake" "To sai na dawo" Hajiya Sa'a ta fice, ta rufe wa Jamila ƙofar. **** Nasiru tun ranar da ya je gidan Ummi, su Nana suka tashi, ya koma gida ya ba wa Baba labari. Baba ya ce "To shikenan ma, ta kwana gidan sauƙi, tun da sun samu mafita. Ni na san babu yadda za'a yi ma a kore su haka kurum, dan mijinta ba shi da lafiya akwai dai abin da suka aikata. "Dama wasu Buzaye abin yarda ne, kalli kayan da suka kawo mata fa, Allah ka dai ya san mugun abin da suke aikatawa, har aka kama su. Kai Nasiru to ya gidan da suka koma yake?" Cewar Mama cike da son jin ƙwaƙwaf. Nasiru na tauna rake ya ce "Normal dai gida ne, amma da wasu a gidan, wancan gidan da suka baro ya fi. Ɗakinsu ya fi kyau da girma, banɗakin har da famfo ga wuta, wannan kuwa gaskiya bai yi kyau ba" Ta sake cewa "Kuma da gaske mijin nata ba shi da lafiya?" Ya ɗaga kai ya ce "Kai, sosai yana daurewa ne kawai, idan ya yi magana haki yake yi fa, wannan karon na ga ya yi magana sosai. Da an yi abu sai ya ce mata Rayuwata, ki yi a hankali ki zauna ki huta" Sai ta sake zabura ta ce "Au rayuwata yake ce mata" "Kai Mama dan Allah ki rabu da ni, haba wannan tambayoyin kamar a kabari" "Kai a gidan uban wa ka san kabarin, sai ka yi saɓo tukuna" ya yi mata shiru, ya tashi ya ɗauki rakensa da yake sayarwa a ƙofar gida, da wuƙa ya fice. ***** Tun da garin Allah ya waye, Nana take tashin sa, amma ya ƙi tashi, irin wannan baccin da ta farka ta ga yana yi dai shi yake yi. Gaba ɗaya ta tsorata, ga dai numfashi yana yi, idan ta taɓa zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi jefi-jefi. Ta saka shi a gaba, ta ma rasa abin da ya kamata ta yi. Ummi takira ta a waya, ta tambaye ta babu matsala babu wani abu da take buƙata, ta ce mata eh. Har sha biyu na rana Nana ta rasa abin yi, ta kunna karatun Alƙur'ani a wayarta, ta ajiye masa sai dai bai fi mintuna talatin ba wayar ta ɗauke. Ji ta yi ana bubbuga ƙofar ɗakin nasu. Ta yinƙura ta tashi ta saka hijjabi, ta je ta buɗe. Sajida ta gani a tsaye, ta ɗan saki fuskarta su ka gaisa. Sajida ta ce "Mun ji shiru ne, ko ƙofa ba ku buɗe ba, shi ne na ce bari na ƙwanƙwasa ko lafiya?" Nana ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdillah, ba ma jin daɗi ne daga ni har shi, shi yasa ba mu fito ba, amma lafiya ƙalau muke" "Ok Allah sarki, ko dai amarya ce ne, haryanzu ba a gama cin amarci ba?" Ta yi maganar tana kallon Nana. Nana kawai ta yi murmushi, ta koma ɗakin, ta buɗe ƙofar ta saki labule. Dama ta gyara komai a ɗakin. Ta dafa shayi da habbatussauda, da citt, kanumfari, kimba, na'ana'a kamar yadda yake dafawa, ta zuba a flask ta rasa me za ta dafa, dan ba ta son cin komai. Tana nan zaune, sai ga 'yar gidan Ummi ta zo, Islam. Ta kawo wa Nana faten doya da wake, ya sha alayyahu. Ƙamshin attaruhun da ya daki hancin Nana, sai da ta haɗiye yawu. Ta ba wa yarinyar wayarta, ta miƙa mata caji. Ta ɗan zuba abincin tana ci, ta zuba masa ido, tana tunanin ko Asibiti za ta nemo mota su tafi, amma kuma sai ta tuna abin da ya yi jiya ba shi da alaƙa da ciwon Asibiti. Tana ta tunanin mene ne mafita, kuma ba ta son waɗannan maganannun matan, suk san halin da suke ciki ita da mijinta. Tana nan zaune tana bin sa da kallo, ta jiyo hirar Sajida da Barira, da wasu maƙwabta. Barira ta ce "Sajida, jiya da daddare, kin ji kamar ana nishi cikin dare?" Sajida ta ce "Wani irin nishi kuma? Ni ban ji ba" "Wallahi nishi, kamar ana kokowa kamar wani gurnani, ga Amiru ya yi bacci, na din ga jin tsoro na kasa bacci, na ce ko gamo na yi da aljanu" "Ba wasu aljanu, ba wani aljani da yake razana mutum, da wani sauti ko wani abu, duk ƙaryar banza ce" "Kai ni dai na tsorata, kuma daga nan haka na din ga jiyo sautin, wajen nan" ta yi maganar tana nuna ɗakin Nana. Sajida ta yi magana ƙasa-ƙasa, Nana ba ta ji me su ka ce, sai ji ta yi sun tuntsure da dariya. Ta yi ajiyar zuciya, ta fara tunanin ko dai wani gidan za su kama, ta san idan suka ci gaba da zama a gidan nan, asirin su na iya tonuwa, wanda ba za ta so hakan ba. Babu tsammani ta ga ya tashi zaune, ta tashi da sauri ta nufe shi cikin kulawa ta ce "Sannu Sayyid, ka tashi?" Shiru ya yi yana bin ta da kallo, tamkar ya ga wata baƙuwar halitta daban. "Sannu ya jikin naka?" Yanzun ma bai yi magana ba, ya ci gaba da bin ta da ido. Ta yi ta magana ya yi shiru, tamkar kurma. Can kuma ya tashi ya shiga banɗaki ya fito ya nemi guri ya zauna. "Sayyid, za ka yi sallolin da ba ka yi ba, Asuba da kuma Azahar, duk ba ka yi ba" ya yi mata shiru, ya kawar da kansa gefe. Ta tsiyayo ruwan shayi a kofi, ta zo gabansa da cokali ta zauna ta ce "To ɗan sha tea ɗin, sai ka ci abinci ka yi sallar" ya kawar da kansa ya yi mata shiru. Ta ƙara matsawa kusa da shi, kawai ya hamɓare kofin ruwan zafin ya kware mata, a wuyanta zuwa jikinta. Wata irin zabura ta yi, ta ja da baya tana tsuma, saboda yadda zafin ya ratsa fatarta. Ko kallon inda take bai yi ba, ya ja gefe ya ci gaba da huci. Ranta ya yi mummunan ɓaci, amma ta kalli fuskarsa, ta tabattar da yana hayyacinsa, babu yadda za a yi ya yi mata haka, dan haka ta yi shiru ba ta ce komai ba, ta tashi ta cire kayan, ta saka wasu. Haka suka wuni a ɗakin, bai yi salla ba, bai ci abinci ba, kuma bai yi magana ba. Ana yin sallar magariba, ya haura kan katifa ya kwanta. A jikin mudubi ta tsaya, tana haska ƙirjinta, yadda inda ruwan zafin ya zuba a ƙirjinta, ya ɗuri ruwa. Ta hasaka kan katifar, ta ga ya ci gaba da wannan baccin, mai rabin idonsa a buɗe, ta nemi guri a ƙasa lungun wardrobe ta kwanta. Sai dai yau ta kwanta cike da fargaba da kuma zullumin abin da zai faru, kar ta je ya sake shaƙe ta. Sam ta kasa bacci, da ta fara sai ta razana ta buɗe idonta, dama a kunne ta bar fitila ba ta kashe ta ba. **** Shukura ce tare da Sagir a zaune a cikin mota, ta zuba wa ƙofar gate ɗin Asibitin ido. Ya ce "Ya dai? Ki shiga ki fito ina nan ina jiran ki" "Wallahi haka kurum gabana yake faɗuwa, ko hanyar Asibitin nan ba na son na ni an faɗi sunan ta" "Shukura duk saboda da ɗan ki ya rasu, ban taɓa ganin mutum mara tawakkalli kamar ke ba" "Ba haka ba ne, wallahi yanzu ma ban da Mummy ta matsa, ba zan zo ba, bari na je na dawo" Sagir ya ce "Tom ki yi masa sannu, ni na zo na duba shi dama" ta jinjina kai ta fice daga motar. Tana shiga cikin Asibitin, ta din ga jin kamar a lokacin ne, za a yi mata aiki a cire ɗan cikinta, wata irin fargaba da yanayi mara daɗi ta din ga ji a jikinta. Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta, jiki babu ƙwari ta nufi ɗakin da Hajiya Amina ta kwatanta mata. Sai da ta yi knocking sannan ta tura ƙofar ta shiga. Fadila na zaune a gefen gadon kusa da Alhaji Fatuhu, ga cikinta ya yi wani irin girma, tamkar tana yinƙurawa ɗa zai faɗo. Sai dai gaban Shukura ya yi mummunar faɗuwa, ganin yadda Alhaji Fatuhu ya koma. Dogon mutum mai jiki, mai hasken fata, ya koma baƙi ƙirin ya yi wata irin mahaukaciyar rama, jikinsa tamkar fata kawai aka yafa wa ƙashi. Ta ji kanta ya sara, wani irin abu ya soki zuciyarta. Wani irin wari ɗakin yake yi, tamkar na mushe, ga shi dai babu ƙazanta a jikinsa, ga ɗakin a share a goge yana ƙamshin turaren wuta, amma ita warin mushe ta din ga ji, da ba ta san daga ina yake fitowa ba Fadila tana yi mata sannu da zuwa, amma ba ta kula ba, ta ƙarasa kan gadon, ta zaune. Yana daga zaune, ya kalle ta ya yi murmushi tamkar mai raɗa ya ce "Shukura" "Daddy, haka jikinka ya koma?" Ta yi maganar cikin matsanancin tashin hankali, da tuni hawaye ya wanke mata fuska. Ya ce "Alhamdillah, ai na ji sauƙi ko Maman Muhsin?" Fadila ta jinjina kai hawaye na zubo wa daga idonta ita ma. "An ce mini kin haihu ɗan ya rasu, ban zo na duba ki ba, na haɗu da wannan larurar" Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri ban zo na duba ka a kan lokaci ba. Ban zaci abin ya kai har haka ba" Ya yi murmushi yana jinjina kai, aka turo ƙofar ɗakin,gaba ɗaya suka waiwaya Doctor Sharif ne ya shigo, tare da wata nurse. Yana ganin Shukura ya yi murmushi ya ce "Hajjaju kwana da yawa, ni da na yi zaton zuwa yanzu ma, kin dawo mana awo? Ya gida ya mai gidan?" "Lafiya kalau" daga haka ta ja baki ta tsuke. Sai da ya sha jinin jikinsa, da irin amsawar da ta yi masa. Ya kalli Fadila ya ce "Uwar biyu, ya mai jikin?" Fadila ta ce "Alhamdillah mun gode Allah" "Ma sha Allah. Na ce ki je a duba ki, idan inducing ɗin ki za a yi, idan ma tiyata ya kamata a yi miki to. Amma kin ƙi" "Kar ki soma yarda, a kashe miki ɗa, gara ki je wani Asibitin" tsit suka yi baki ɗaya, suka waiwayo su na kallon ta. Jikinsa ne ya yi wani irin sanyi, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa. Cikin damuwa ya ce "A kashe mata ɗa kuma Shukura" "Nawa ba a hannunku ya rasu ba?" "Kuma ai ba kya ce za a kashe mata ɗa ba, nakin ma, Allah ne ya kawo ajalinsa" Shukura ta ce "Ba zan dai sake zuwa Asibitin nan na haihu ba. Daddy Allah ya ƙara afuwa. Maman Muhsin sai anjima Allah ya raba lafiya" Fadila ta ce "Amin, mun gode sosai da sosai Shukura, ki gaida gida. Mummy ma an ce ta tafi Umara ko?" "Eh wallahi. Allah ya raba lafiya" har Shukura ta fice, jikin Doctor Sharif tsuma yake yi, amma ya dake tare da ɓoye hakan. ***** Jamila na tsaka da bacci, ta ji ana tashin ta. Ta buɗe idonta ta ga Hajiya Sa'a a tsaye amma fitilar ɗakin a kashe. "Hajiya lafiya kuwa?" "Lafiya ƙalau, tashi ki saka wannan rigar mu tafi" Cikin mamaki ta ce "Ina?" "Ki saka sai mu je ki gani. Ki cire komai na jikinki ki saka ta" Bakinta fal tambayoyi, amma babu damar yi. A duhun ta karɓi rigar ta saka, kanta babu ko ɗan kwali, Hajiya Sa'a ta kama hannunta suka fice. Sun yi doguwar tafiya sosai, su na ratsa guri-guri, sai dai duk a cikin duhu ne. Jamila ba ta san ina suke bi ba, da kuma inda za su je ba. Aka buɗe musu wata ƙofa suka shiga, ta ja ta tsaya. Yanayin gurin babba ne yana da girma sosai. Sai dai da mutane a ciki, galibinsu maza ne. An kunna kyandira a gurin. A haka ta lura kayan jikinsu jajaye ne da baƙaƙe. Sun kewaye wata ƙatuwar tukunya a tsakiyar ɗakin, fuskokin su a rurrufe. Hajiya Sa'a ta ja ta suka samu guri suka zauna. Wani irin gurnani mutanen ɗakin suke yi, su na wasu irin maganganun da ba ta fahimtar abin da suke faɗa. Da alama ɗaya daga cikin su ne yake jagorantar abin da suke yi, mai kama da ibadar bautar wani abin. "Mun yi baƙuwa a gurin nan" cewar mutumin da yake zagaye tukunyar, yana faɗar abin da yake faɗa suna yi masa amshi. Hajiya Sa'a ta ce "Eh, baƙuwar mu ce, da na sanar da zuwan ta wannan bugiren" "Ita ce aka kasa samo jinin 'yar uwatta, uwar gijiyar uban duƙusa?" "Eh ita ce" "Mu na yi mata maraba da zuwa ƙungiya, za ta samu abin da take so. Idan duniya ce kun same ta kun gama. Babu wani abu da zai gagare ku. Can kuma wannan matsalar ku ce, ku neme ta ku rasa nan, ko ku nemi nan can kuma sai abin da hali ya yi. Mu na yi wa wanda ba su bayar da sadaukarwar su ta wannan shekarar ba, idan lokaci ya yi za su ga abin da ba su zata ba. Wanda suka riga su ka yi, mu na taya su murna da ƙara tabattar musu sun samu duniya, su taka wanda suka so, babu mai ganin bayansu, masu neman ɗaukaka za su samu, masu neman ilimi za su dace. Masu neman kuɗi sun samu, haka ma masu neman madafun iko. Mu na sake jaddada muku dokokin ƙungiyarmu, babu fita bayan an shiga. Babu tona asirin ƙungiya. Duk wanda ƙungiya ta buƙata za ka bayar, babu jayayya babu musu. Akasin haka jininka ya zama mallakin dodon ƙungiya". "Mun yarda, mun yi mubayi'a, mun bi dodon ƙungiya, mun bi sarkin ƙungiya, ranmu da jukkunanmu fansa ne a gare ku, muna son duniya, mu na son tabattuwar duniyarmu" suka haɗa baki su na maimaitawa. Jamila bin su kawai take yi da kallo, jin abin take yi tamkar a mafarki, kuma kamar wani film. Wani irin sauti mara daɗin ji ya karaɗe ilahirin gurin. Miƙewa mutanen suka yi, suka risuna tamkar za su yi sujuda. Su na ci gaba da karanto wasu irin abubuwa. Wani abu mai kama da guguwa, ya kashe kyanduran gurin. Ƙarar sautin abin, da surutun da suke yi ya karaɗe gurin, baka iya gane komai. Can bayan wani lokaci kuma, sai gurin ya yi tsit hasken kyanduran ya dawo. Suka ɓarke da wata irin shewa. Hasken ya haska gurin sosai da sosai, sai dai ba ta iya gane suwaye a gurin, kuma ta nemi Hajiya Sa'a ta rasa a gurin. Sai daga baya ta fahimci ashe akwai mata a gurin ba wai maza ne kawai ba. Aka din ga raba wani abu a cikin kofi, aka zo kanta a ka ba ta, ta karɓa ta sinsuna ta ji wani irin ƙarni mara daɗin ji ya daki hancin ta. Ta kawar da kanta yawu na taruwa a cikin bakinta. Ji ta yi an damƙi hannunta, an nufi wata ƙofa da ita. Tana ta ƙoƙarin gane waye, amma abu ya faskara ta kasa gane waye. Su na shiga ƙofar ta ga duhu ya ƙara gaurayewa, amma ta ji sanyin AC na ratsa ta. Ta ji an shaƙe mata wuya, an toshe mata hanci, ta fara kiciniyar ƙwacewa amma abu ya gagara, ta buɗe bakinta za ta yi numfashi ta ji an zuba mata wani abu, da ya fi ruwa kauri kaɗan, mara ɗanɗano. Tana gama haɗiyewa ta ji wannan ƙarnin ya mamaye mata hancinta da bakinta. Take ta yi yinƙuri ta fara amai, sai dai ba ta gama aman ba, ta ji jiri ya kwashe ta. **** Bangaren Nana kuwa, aka shiga kwana biyu, ba tare da ko ruwa Sayyid ya saka a cikin sa ba. Balle Abinci, ba wanka babu salla balle ya sha magungunan sa na matsalar zuciya. Ga shi kuma bai daina haki ba. Idanunsa sun yi jawur tamkar gauta. Laɓɓansa sun yi wata irin bushewa. Ga gashin nan butsu-butsu a hargitse babu gyara, ya koma mahaukaci sosai da sosai. Ga shi da ta tunkaro inda yake, ko ya hankaɗe ta, ko ya shaƙe ta. Ko kallonsa ta fiye yi, sai ya hau huci yana zabure-zabure tamkar zai kai mata duka. Ta yi iya ƙoƙarin ta, babu wanda yake shigar mata ɗaki. Ga laulayin ciki ya saka ta a gaba, ita kanta lallaɓawa kawai take yi. Ba ta yi da yawa ba a rana ta yi amai sau goma, tun cikin dare take farawa. Tun tana sha'awar ta ci wani abu har ta daina. Daga shayi sai ruwa, ko juice ɗin lemon tsami. Idan ta ga jikinta ya bushe ne, sai ta aika a sayo mata ruwan gishiri ta haɗa ta sha. Ga ranar da za su koma follow up, na Asibiti ya yi amma yana cikin wannan yanayin, a dole ta rabu da shi, ta ci gaba da addu'a. Sai dai yau gaba ɗaya Jamila ce take ta kaiwa tana komowa a ranta. Sannan ƙasan zuciyarta kuma haka kurum, take tunanin abin da ya sanya ta daina ganin Ƙaisar kwana biyu. "Allah ya sa dai lafiya" ta furta a fili, sai kuma ta yi saroro bayan wata zuciyar ta ce "Ina ruwan ki da lafiya ko ma babu, abin da ki ke neman maraba da shi?" Sayyid take kallo, zuciyarta na raya mata, ta matsa kusa da shi, ta jarraba yi masa karatu, amma tsoro ya kama ta, saboda gudun kar ya cutar da ita, ga ƙaramin ciki a jikinta, da take ta lallaɓawa tana fatan Allah ya bar mata. **** A hankali Jamila ta buɗe idonta, ta ganta a ɗakin da suka sauka da Hajiya Sa'a. Ta yinƙura za ta yaye bargon da take lulluɓe da shi, amma ta ji jikinta na yi mata wani irin ciwo mai tsanani. Ga wani irin raɗaɗi da azaba da ta ji a ƙasanta zuwa gurin bayan gidanta, tamkar an sanya abu mai kaifi an haɗe guraren biyu. Ta yaye bargon ta ganta a tsirara, jikinta duk an yi mata zane da jini, ta ɗaga ƙafarta ɗaya tana ƙoƙarin tashi zaune, amma ta ji ba za ta iya ba, saboda azabar raɗaɗi da zafin da take ji. "Wayyo Allah Mama, na shiga uku mene ne ya same ni haka? Nana, Suwaiba dan Allah ku taimake ni na shiga uku" Hajiya Sa'a ce ta shigo da sauri, tana faɗin "Daughter kin tashi?" "Mene ne ya same ni, me ya faru da ni?" "Yi shiru, ki kwantar da hankalinki, zan yi miki bayani. Amma ki daina wannan kukan. Taso mu je, ki yi wanka ki gasa jikin ki, ki karya tukuna. Cikin kuka ta ce "Ba na so, ki yi mini bayanin mene ne ya same ni? Ina ne nan? Me yasa nake jin wannan zafin, kuma me ye wannan rubutun a jikina?" Hajiya Sa'a ta ce "Ke ba na son hauka. A lokacin da Safiyya ta haɗa ni da ke. Nake kashe miki kuɗaɗe a banza zan yi miki ne, ba tare da na amfani komai a tattare da ke ba?  Kin gaza kawo mini jinin 'yar uwakki, kin ƙi shiga cikin harkar mata yadda nake so, kuma ga burinki na son abin Duniya, dan haka tallafawa burinki kawai na yi cicciɓa ki" Hawaye na kwarara daga idonta cikin sanyin murya ta ce "Yanzu me ya same ni?" "Taronmu na ƙungiya ki ka zo, kuma na nema miki sassauci ta hanyar ki bayar da budurcinki, ga sarki da kuma dodon ƙungiya maimakon a ce ki kawo jini tashin farko. Aljanin da ke da alhakin bamu kuɗaɗe,da jagorantar ƙungiyar, shi ne ya shiga jikin sarkin ƙungiya ya kwanta da ke, a matsayin barka da zuwa na ƙungiya kuma da sadaukarwar ki ta shekara!!! (Alhamdillah, da haka muka kawo ƙarshen book 1, sai mun haɗe a kashi na biyu). Ayshercool 08081012143