HIRA DA MATATTU Jamila Umar Tanko: JUT Haqqin mallaka:Jamila Umar tanko Copyright: Jamila umar tanko HIRA DA MATATTU .....1 (True life story) Haqqin Mallaka: Jamila Umar Tanko Copyright: Jamila Umar Tanko Saudaukarwa: Na sadaukar da wannan littafin ga matan da suka yi jahadi wajen biyayyar aure ko su na raye ko sun rasu. Allah Ya duba yaransu ya raya su akan sunna. Gargadi: Baa yarda wani/wata ta juya labarin ban zuwa wata Shiga ba fim ko rubutu ba tare da izinin Marubuciyar ba. Sannan ban yarda a karanta shi a you tube channel, ba tare da izinina ba. [2/28, 5:26 PM] Jamila Umar Tanko: 1 Sharifah ta ci gaba da cewa "duk wanda ya san ni a duniya toh ya san ni tare da Shariqah dan kamar 'yan tagwaye mu ke. Mun shaqu sosai kamar yadda uwa take shakuwa da 'ya'yanta. Bayan son Allah (S.W.A) da ManzonSa (S.A.W) daman wannan baa hada su da kowa, sannan iyaye su daban ne. Duk duniya babu abinda na fi so irin yadda na ke son Shariqah, haka itama. Ita karamar kanwata ce ba ita take bi na ba ma, Bello ke bi na ita kuma take bin sa. Na riga ta yin aure da dadewa, amma a kullum tana gidana, idan ma bata zo ba ni zan je gida saboda ita, kasancewar mijina ba zaunin gari ba ne, yayi min lamuni idan baya nan zan iya tafiya gida in kwana. Kusan kullum tare muke kwana shinfidarmu daya, mu na raba dare mu na hira. Baiwar Allah ta fi ni hakuri da hangen nesa, ko da zan zazzage ta sai ta fada min gaskiya.Babu mai goyon bayana a duniya irin ta, komai girman matsalata tana tare da ni kuma ita kadai nake fadawa komai nawa. Ko kwalliya na yi idan Shariqah ba ta ce na yi kyau ba toh ba na yarda akan na yi kyau din. Na haifi 'yata Hamidah, na rantse da Allah bayan wahalar daukar ciki watanni tara da nakuda da shayarwa zuwa kwana arba'in ban san wahalar raino ba. Shariqah ce komai na game da kula da jaririya, duk wata kazantar jariri da zaryar zuwa asibiti ita ce. A lokacin ina tafiya jami'a wani lokaci ma ina gida a kwance ita ke faman rainon Hamidah. Har fada ake yi da ni ina cewa idan ba za ta yi ba a bar 'yar a wajen.Mutane su cika da mamaki. Ta yaya uwar da ta haifi 'yarta zata ce haka? Saboda na san ai ba za ta iya barin 'yar ba ne shiyasa nake cika baki. Watanni takwas kadai Halidah ta yi ta na shan nono, na yaye ta, na damqawa Shariqah suka kaura gidansu gaba daya. Hamidah ta tashi a tunaninta Shariqah ce mahaifiyarta, ta sanni amma ta dauka ziyara kawai nake kawo musu a matsayina na 'yar uwarsu. Hamidah ta sha laulayi na jinya kala-kala haka Shariqah ta ke wuni a layin asibiti tana jinyar ta. Samari da dama 'yan gayu sun sha ganinta a hanya su na so, daga sun matso suka ganta da 'ya har tana kiranta mummy sai su yi kwana a zatonsu matar aure ce. Qawayenta har tsiya suke yi mata cewa sai an yi kwalliya zaa fita unguwa kawai sai ta dauko musu 'ya tana bata musu tsari. ita kuwa sai ta ce idan zaa so ta dole a so ta da 'yarta. Ko tafiye-tafiye su ka yi qasashen waje da yake makarantar kudi ta yi kuma dukka qawayenta 'ya'yan masu hali ne ta kan fada musu ita bata son su siyo mata komai su siyowa 'yarta Hamidah. Ko ba ta fada ba ma sun san abinda zasu yi ya faranta mata rai shine su yiwa Hamdah sayayya. Daman gashi kamarmu daya ni da Shariqah dan haka Hamidah ta yi kama da ni sai ta yi kama da Shariqah. Aure ne kadai ya raba Shariqah da Hamidah. Na tabbatar da ta auri miji mai fahimta da daman da ita za ta tafi amma bata yi wannan sa'ar ba. Aka bar Hamidah a wajen mahaifiyarmu. Mahaifin Hamidah ba mutumin da ya san darajar gidansa ba ne, haka ba mai kula da haqqin iyalansa ba ne, shiyasa ma ya bar 'yarsa ake riqonta dan bai sauke nauyin da Allah Ya dora masa ba. Hakan ya fiye min alkhairi saboda idan na dauko ta na kawo ta gidana ma akan Hamidah kullum sai mun yi fada. Mutum ne da baya son zaman lafiya ko kadan, Idan ya na so ya bani haushi ko ya takale ni da fada toh sai ya hau azabtar da ita dan haka ne ma ta taso da tsoronsa kuma bata son ganinsa ma ko kadan. Bai sauke haqqina da Allah Ya dora masa na ciyarwa, sutura, asibiti, muhalli ba, dan haka bai hana ni fita neman kudina kowacce kasa ba. Dan mutuwar zuciya ma nawa yake so ya ci saboda zuciyarsa ta mutu. Mahaifiyata na tsaye tsayin daka akan matsalolina da na 'yata dan haka da jarina da na ta nake juyawa. Hakkinmu da ya tauye shine ya jawo masa koma baya, baya ganin daidai a dukka aiyukan da yake yi. Kullum ana korarsa daga aiki ya na wahalar neman wani aikin. Wannan kuma na bar shi da Allah, na ci gaba da kula da kaina da 'yata da taimakon Allah da taimakon mahaifiyata. Mu ka bar Hamidah a Karkashin kulawar mahaifiyata amma kuma a koda yaushe tana zuwa gidan Shariqah kasacewar gari daya ne kuma tazarar unguwannin babu nisa. Allah Ya bawa Shariqah haihuwa a jejjjere ba tsayawa. Allah Ya jarrabe ta da auren miji mai tsanani da kishiya da 'ya'yan kishiya mararsa kirki. Babban abinda ya kara kawo tangarda su na zaune su dukka a cakude a gida daya, bata jin dadin zama da su ko kadan. Shariqah mace ce mai hakuri, komai sai ta rufe bata fadar damuwawarta. Hamidah ce kadai ta san komai ita ce abokiyar shawararta amma sai ta ce ma ta kada ta fada min. Saboda sun san ina da zafi wasu lokutan bana son rainin hankali. Mahaifiyarmu mace ce mai son yara kuma a tsaye take akan matsalolin yaranta.Ko bayan rasuwar mahaifinmu ba mu ce wayyo Allah ba, saboda ba mu rasa komai ba. Mace ce mai kamar maza ta yi nata ta yi na wasu ma. Wahalar da Shariqah take sha a gidan miji bai nuna ba saboda ga ta a kusa da mahaifiyarta mai sonta mai taimakonta da dukiyarta da nuna ma ta so da kauna da bata shawarwari akan ta yi hakuri rayuwar aure ibada ce. Sai bayan da mu ka rasa Mamarmu sannan maraici dukka ya bayyana a jikin Shariqah. Bayan masifaffen kulle wanda ko islamiyya baa zuwa a gidansa, daman biki ko suna da gaisuwar mutuwa, dangi dukka sun sallama ta baya bari ta je a cikin Kano ma balle a wani gari. Dukka kayan dakinta masu kyau masu tsada na kasar waje, sai da suka kwankwatse, baya gyara balle ya canja musu kuma ke matar gidan da kudinki ba ki isa ki kawo masu gyara su shigo masa gida su gyara miki ba. Har da mugunta 'yayan waccan matar suke zuwa su lalata mata komai dan ita bata magana. Ta rame, ta yi baqi-qirin ta fita daga hayyacinta. Wataran kudin Pampers guda daya jal sai ta gagare ta balle na cerelec da zata bawa yaranta bata da shi, kuma shi babu wadannan a cikin lissafinsa. Yaranta sun tashi babu kuzari da yawa ma tana goyonsu sai da suka kamu da ciwon tamowa wato na rashin balance diet. Yara kanana sai dai su ci mai da yaji. Suturun da ta saba sakawa babu irinsu sai dai masu arha taron yuyuyu, man shafawa da sabulun da ta saba yin amfani da su a gidansu dukka babu. Kuma ya na da halin da zai yi fiye da hakan amma baya yi." *** *** *** Sharifah ta yi shiru ta yi tagumi dan tsananin takaici ta kasa kuka amma radadin da zuciyarta ke yi ya nuna a cikin idanuwanta. Sun yi jajawur, ranta a bace. Samha ta dafa hannunta tana jinjinawa alamar tana ba ta hakuri. Sharifah ta yi ajiyar zuciya ta ce "maganganun su na da yawa akan mutumin nan Adamu, ga shi sun haifi yara da yawa tare. Alfarmar yaran nan ta sa ba zan iya fadar rabin azabar da ya bawa Sharifah ba. Ko rabin-rabin abubuwan da suka faru ba zan iya fada ba. Wasu ma har yanzu ban sansu ba, an boye min baa so a fada min. Wasu kuwa ta kunshe a ranta ta tafi da kayanta ba zata iya fadawa kowa ba." Samha ta gyada kai ta ce "na fahimce ki kawata ki ci gaba da labarinki ki fada mana wanda zai iya faduwa. Na jinjinawa mata masu jahadin zaman aure irin su Shariqah. Aljanna na nan na jiran mata irinsu da su ka rayu cikin ukuba su ka yi biyayyar aure. Kamar Rabi'atul Badawiyya(RA) matan aljanna." Aliyu sai kabbara yake ya na jan gemu an tabo babin ustazai, ji yake dama ya hadu da wannan mijin na Shariqah ya yi masa nasiha. Anas kuwa babu abinda yake yi sai gyada kai yana tunano irin bautar da yake yiwa matarsa Binta, da irin 'yancin da ya bata na sakewa ta yi abinda take so, ta je inda take so amma bata gode masa daga ita har iyayenta.Ta na ta bin zugar qawaye da dangi. Ya ji dama Shariqar ya aura ta yi masa wannan biyayyar shi kuwa ya jiye mata dadi. Dan ya so Shariqah a rayuwarsa, ya so ya aure ta Allah bai kaddara ba. Kwatsam kawai ya ga katin daurin aurenta ba dan tana son mijin ba sai dan kadararrar aure da ta haihuwa. Wanda babu mahalukin da ya isa ya hana kaddarar bawa ta faru da shi. Wannan haka yake komai mukaddari ne kuma rubutacce ne. *** *** *** Sharifah ta ci gaba da cewa "Ko Shariqah tayi yunkurin fita daga gidan idan abin yayi ma ta yawa, mijin yana tsoratar da ita da cewa idan ta fita ma ina za ta je? Tunda bata da sauran gata iyayenta gaba daya sun rasu, danginta babu hadin kai, babu mai kula da ita. Kuma idan zata fita bata isa ta tafi da yaransa ba har da na goye, duk kotun da zasu je sai ya kwace su. Wannan rashin fahimtar ita take saka mata da yawa ci gaba da zama a ukuba a gidan mijin da yake gallaza musu har su rasa rayuwarsu. Ta kai ta kawo gidanta da suturarta da ta yaranta babu tsari gaba daya ba irin rayuwar da ta taso ba ce, ta fada wata rayuwar da ba ajinta ba ne, ba ta saba gani ba. Shariqah kyakykywar mace ta koma abar tausayi, baqiqirin ta rame babu maganar gayu ma. Aure bautar Allah babu wanda ya damu da ita a dangi, wasu lokutan ne ma idan na ganta na kan hau fada ina cewa akwai abinda take boyewa zan sami mijin in yi masa magana. Sai ta hana dan ya dora su akan kishiyarki na jin haushi dan na yi miki abu kaza dan haka ko marinsu yayi kokari suke su fito su na yaqe su na dariya kada kishiya ta gane an yi fada. Ya same su ya dinga cin karansa babu babbaka babu wanda yake yi masa magana. Bayan rashin wadatasu da kudi ga tsananin kulle, su ba zasu fita ba kuma baya so a zo. Takai ta kawo yana korar baqinsu, Idan bakuwa zata kwana sai dai a boye takalmana ta. Kishiyar na lallabawa ta fada masa akwai bakuwa a gidan Shariqah. Sai da tsakar dare misalin karfe goma sha biyu sai yayi sumame ya shiga ya ritsa su...." *** *** *** Sharifah ta yi shiru ta kasa ci gaba da magana saboda tsantsar radadin da take ji a cikin zuciyarta tamkar fami labarin yake yi ma ta, akan katon gyambon da yake fafare a cikin zuciyarta." Samha ta dafa kafadarta ta girgiza ta, ta ce "ki zubo da hawayen zai sa ki ji sanyi. Saboda Idanuwanki sun yi jajawur, zuciyarki ta na bugawa da sauri." Sharifah ta girgiza kai ta ce "haba Samha tun yaushe na wuce babin yin kuka akan bil'adama. Na yi rantsuwa da Ubangijin da Ya busa min numfashi ba zan sake yin kuka ba, sai dai in kai su kara wajen Allah wanda Shine gatana kuma gatan Shariqah, in roqe Shi ya nuna min hanyar da zan bulle wajen daukar mataki da fansa. Na shiga bala'an da ya fi karfin kuka, mutane sun ba ni mamaki kuma sun ci amanata wanda a baya ban taba sanin haka mutum yake ba sai yanzu." Samha ta fara tausayawa Sharifah tun bata gama jin labarinta ba. Ta tabbata Sharifah ta shiga bala'in da a dole ma kamanninta suka canja, ta rame ta yi baqiqirin tayi kuraje. Sharifah ta ci gaba da cewa "mijin Shariqah ya binciko bakuwar Shariqah, ya hada su su dukka ya ci musu mutunci. Shariqah na kuka bakuwar tana kuka ya ce ya yi rantsuwa ba zata kwana a gidansa ba. A cikin daren ya kore ta daga gidan, kuma 'yar uwarmu ce daga wani gari me nisa ta zo Kano yin sari. Ba ta san yadda zata bi ta je unguwar wasu 'yan uwan na mu ba. Yarinya budurwa ya kora a cikin dare dan qarfe goma sha biyu ta gota. Akwai karamar kanwar mu wacce muke uba daya mai suna Dinar, watarana ta zo hutu daga makaranta kwana itama aka ce sai dai a boye ta, har ta gama yin kwanakin da zata yi ba zai san tana ciki ba dan idan ya sani zai iya korar ta itama. Ba ta san shi ba sai dai ta dinga leqensa ta windo, tunda bata nan aka yi aurensu kuma bata zuwa gidan. Yaran Shariqah basu san danginta ba saboda baa kai su ziyara, toh uwar ma bata je ba balle yaranta. Dan haka basu san kowa ba sai wadanda suke iya daurewa da wulakancinsa su je gidanta. Asibiti ne kadai ya yarda ta je shima sai ya hada da tsine-tsine idan ta kuskure ta biya wani gidan. Wato ya san ta tara barka da gaishe-gaishen mutuwa bila adadin dan bakar mugunta shine baya so ta je ta sauke nauyi. Tunda ya fatattaki kawayenta da 'yan uwa ai zai fi samun damar da zai ci karansa babu babba akanta wannan ce manufarsa. Ta koma baiwarsa ba matarsa ba, ko generator zaa kunna sai idan yana gidan idan zai fita sai ya kashe, sai ya dawo zai kunna. Idan yayi tafiya kuwa idan zai yi wata guda ke matar gida ba ki isa ki kunna ba, ko da kina da kudin siyan man fetur. Daman ita uwar gidan 'yar wahala ce bata fito daga gidan dadi ba, ita Shariqah ce duk bata saba da wannan qangin ba. Akwai ranar da ta zuba mai a inji ta kunna. Ta kashe lafiya kalau amma dan annamimanci sai uwar gidan ta aiko danta ya yanke igiyar saboda idan ya dawo ya gan shi a lalace sai ace Shariqah ce ta kunna. Haka kuwa aka yi, ya zo ya tambaya aka gada masa Shariqah ce ta kunna, ya ci ma ta mutunci tas. Sunan kishiyar Talatuwa ita da 'yayanta suka dinga hada mata tughu kala-kala, a gaban Hamidah ake yin wasu abubuwan sai Shariqah ta ce kada Hamidah ta fada min . Abin ya kai har qawayenta da suka yi makaranta tare suka ga halin da take ciki ya kazanta. Hatta kujerunta na falo sun lalace idan baqo ya zauna akai sai ya zurmuka ciki sai an zakulo shi. Su ka hada meeting cewa anya kuwa na san halin da Shariqah take ciki kuwa? Amma aka yi shiru aka zuba masa ido? Su ka yi niyyar su zo su same ni. Daga baya me suka gani dai suka fasa zuwa dan su na ganin zaa ce sun shiga abinda da ba ruwansu tunda tana da dangi babu wanda ya taba yi masa magana, su yaya zaa yi su tsoma bakinsu? Wataran ledar pure water da za ta siya su sha ta gagare ta, bata da shi komai bai wadace taba. Idan ma asiri ya yi ya rufe mana baki toh asirinsa ya ci dan babu wanda ya iya yi masa magana. Ta yi hakurin jiran kudin hayar gidanta na gado dan ta gyara kujerunta amma da kudin suka zo sai ya karbe. Ya ce shi zai samo mai gyaran. Ta san halinsa ba zai taba bari maza su shigo su kwashi kujerun ba, har gara ta lallabashi shi din ya gyara sai ta bashi kudin. Mutumin nan ya karbe dukka kuma ya qi kawo masu gyaran. Mafarin da ta kamu da ciwon zuciya kenan." [2/28, 5:50 PM] Jamila Umar Tanko: 2 Ban san ma ta je asibiti an ce tana da ciwon zuciya ba, sai daga baya take fada min a waya. Dan a lokacin ba na zama a Kano, ina zama a Rivers ni da mijina. A lokacin Hamidah ta dawo wajena tunda babu inda za ta zauna kasancewar Mamarmu ta rasu. Na ji hankalina ya tashi matuqa na shiga damuwa ba 'yar kadan ba gami da tunanin me ya jawo ma ta kamuwa da ciwon zuciya da kananan shekarunta? Amma ban yi mamaki ba domin kowa ya dube ta ya san bata jin dadin gidan mijin..Sai a lokacin ne Hamidah ta ke fada min wasu daga cikin matsalolin da Shariqah take ciki. Da irin cin kashin da mijin da kishiya da 'yayan miji ke yi ma ta. Su yi ma ta rashin kunya kuma su daki 'ya'yanta." Sharifah ta juya ta dubi Hamidah wacce ke sharbar kuka ta ce " ki tashi ki shiga daki tunda ke zuciyarki ba ta iya jurewa idan ana labarin Shariqah." Hamidah ta ja kannenta suka shiga daki, masu wayon dai jikinsu ya yi sanyi sun ji an ambaci mahaifiyarsu, yayin da kananan suke wasansu basu kawo a ka ba ma. Allah sarki, Allah ba Ya barin wani dan wani ya ji dadi. *** *** *** Maman Samha ce take ta kiransu a waya hankalinta a tashe yake, ta kira lambobi kowannensu bai amsa ba. Ta shiga gagarumar damuwa dsn ta na zaton fatalwar ce ta tafi da su. Sai yanzu wayar Samha ta shiga girgiza, ta dauko da sauri ta duba taga 7 missed calls din Mama. Ta dubi Anas da Aliyu a gigice ta ce "Mama ce fa take ta kira ashe. Waye ya ce ma ta mun fita ne?" Anas ya tabbatar ma ta da cewa shine ya fadawa Samira, ko da ta Allah kan kasance aksnsu asan inda suka tafi . Kowannesu ya zaro wayarsa daga aljihu ya duba ashe ta kikkira su babu adadi. Anas ne ya zabura ya tashi da sauri ya ce "bari in sauka kasa in kira ta." Ya na sauka ya kira Mama ya fara yi ma ta bayani. Sharifah ta yi murmushin karfin hali ta ce " dole hankalin Mama fa ya tashi, kun zo gidan fatalwoyi ta ji shiru, ku ce ina gaishe ta kuma zan kawo ma ta ziyara." Sai su dukka suka kwashe da dariya har da Sharifah. Yayin da Samha da Aliyu kowannensu nauyinta ya kama su. Anas dai ya na ta faman yiwa Mama bayanin cewar ga su ga Sharifah da iyalanta mutane ne ba fatalwa ba, ta fayyace musu komai ashe duk rashin fahimta ne ya sa ake yi ma ta kallon fatalwa. Mama ta ji bayanansa banbarakwai zuciyarta ba ta yarda ba. Ta hau shi da fada ta ce "babu irin sigar da shu'umar yarainyar nan bata iya biyowa ba, dan ta yaudare ku, ta halakar da ku. In ga fatalwa da idanuwana har sau biyu. Daya da yamma a gidana daya a asibiti da tsakar dare a sigar gurguwa yanzu ka yi min musu ka ce ta gyaru ta dawo mutum. Ka fadawa Samha da Aliyu ku gaggauta barin gidan nan ko in yi muku baki." Anas ya zabura ya ce "Ah Mama me ya yi zafi haka? Allah Ya baki hakuri bari in kira su mu taho. Menene abin yi mana baki kuma? Tunda ba ki fahimta ba shi kenan ai." Anas ya ji nauyin yadda zai shiga ya fada musu wannan sako na Mama a gaban Sharifah, ga labari ya kwaranyo dadi. Anan ya tsaya ya tuttura musu text massages ta waya ya ce lallai-lallai su taso su tafi, ran Mama ya baci ta ce su taso." Kowannensu ya karanta sai suka hada ido su ka yi shiru, can da aka jima kadan sai Anas ya shigo ya sami waje ya zauna. Sharifah ta duba agogo ta ce "ya kamata ku tafi Mama na kira nima.kuma ina da ganawa da zan yi da Matar gwamna akan wasu harkoki. In sha Allah za mu hadu wataran ma karasa labarin." Daga dukkan alamu ta fahimci abinda Mama ta ce da sakonni da Anas ya turo mu su a waya. Sharifah ta raka su har kofar gida bakin get inda suka ajiye motarsu suka shiga su ka tafi. Kowannensu zuciyarsu cika da mamaki su na ganinsu kamar a mafarki, ga su tare da Sharifah da ake gudun famfalaqi idan an ganta, yau gata ga su har ta yi musu rakiya. Tabbas su na cike da mamaki gami da samun nutsuwa da kwanciyar hankali da Allah Ya sa suka gane ba fatalwa ba ce, sannan kuma dan cikin Samha mutum ne. Gidan Mama aka wuce kai tsaye aka same ta a farfajiyar get ta na ta kai kawo ta kasa zama a waje daya dan fargaba. Ta na ganinsu sai ta ji hankalinta ya kwanta bayan sun gaishe ta, aka dunguma zuwa cikin gida. Bayani suka yi mata tsaf akan tabbacin Sharifah mutum ce ga dalilan abubuwan da suka faru har ake zaton ba mutum ba ce. Wasu dalilan Mama ta aminta wasu ne basu kwanta ma ta ba, ita dai koma menene ayi baya-baya da Sharifah kawai. Samha da Aliyu suka sauke Anas a gidansa, kamar yadda suka dauko shi sannan suka wuce gidansu suma. Samha na shiga gida ta bugawa kawayenta su Nana Ahmad waya ta basu labarin Sharifah cewa mutum ce ba fatalwa ba ce. Ta fada musu dalilan da ya jawo suke tunanin ba mutum ba ce. Su ka tambaye ta ko ta bata labarin abubuwan da suka faru da rayuwarta ya jawo har kamanninta suka canja kuma menene maqasudin shariar ta a kotu? Samha ta tabbatar musu Sharifah ta shirya bata labarin rayuwarta bayan rabuwarsu sai kuma Mama ta kira su ta tubure ta ce su bar gidan. Amma za ta samu ta lallaba Mama ta bar ta su sake haduwa da Sharifah don jin ci gaban labarin. Sai dai ba ta sani ba ko sirri ne tsakaninta da ita, ko ita kadai ta fadawa ko kuma zata so kowa ya ji. Idan sirri ne toh ba za ta fada musu ba amma idan Sharifah ta amince kowa ya ji toh za ta sanar musu. Su Nana suka nemi da ta samo musu lokaci su hadu su dukka su je gidan Sharifah su ba ta hakuri akan gudun ta da suka yi, a lokacin da ta kawo musu ziyara gidajensu. Samha ta tabbatar musu cewa zata fada mata. Aliyu ya kula da matarsa ta dawo yadda take ada, ga hira da girken-girken da aka saba yi masa ana yi yanzu, bayan kwalliya da kalaman soyayya wanda dukka ya rasa su a baya. Sai ya ji dadi sosai kuma sai a lokacin ya sanarwa da 'yan gidansu labarin bayyanar cikin Samha. Dan duk tsawon lokacin nan bai fadawa kowa ba dan ana tunanin fatalwa ce ta yi ajiya. Amma yanzu komai yayi daidai dan haka ya daki kirji ya fada. *** *** *** Sharifah ce ke tukawa, ta tsaya sannan ta fito daga cikin wata tsaleliyar motar. Daidai lokacin Nana Ahmad da Maryam Alqali su ma sun fito daga cikin motar Nana. Sai kawai aka yi kicibus da su da Sharifah. Ko ba su fada ba ta gane sun razana. Maryam Alqali da yake 'yar karama ce sai ta labe a bayan Nana Ahmad ita ce barkekiya, Nana ta hau muzurai ita ba abin ta taka da gudu ba dan lokaci ya kure, su na daf da juna. Duk da an fada musu yanzu an tabbatar Sharifah mutum ce amma basu gama yarda ba. Sharifah ta dube su sai ta yi murmushi ta ce " Su Nana manyan mata." Ta wuce ta bar su anan a jikin mota su na makerketa. Nana ta fusata ta figo Maryam daga bayanta inda ta labe. Ta ce " munafukar Allah sai ki labe a bayana saboda ke 'yar karama ce, ni kadai ake kullata gashi nan ta ga baqina har da wani habaici take yi min. Muddin ka ga Fatalwa tana habaici akwai magana kenan nan gaba. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Shikenan na ga ta kaina." Maryam ta yi dariya ta ce "ance ba fatalwa ba ce ba fa mutum ce an tabbatar da hakan." Haushi ya sake rufe Nana ta ce " ai kin tabbatar da mutum din ce amma kika gudu kika buya a bayana. Ni da yake barkekiya ce babu in da zan labe ni ake gani ga shi nan ta kullace ni." Su ka hau kan bene ofishin lauyoyi, Nana ta zo wajen babban yayanta Bar. Inuwa Ahmad ta rako Maryam zasu tattauna akan wani case da Maryam Alqali take so ta shigar. Anan aka sake yin arangama da Sharifah tana zaune a reception itama tana jiran layi ya zo kanta za ta ga lauyanta Bar.Inuwa Ahmad yayan Nana Ahmad ba tare da kowannensu ya sani ba. Ashe waje daya su ka zo an sake cakuduwa. Nan ma suka yi turus suka ji kamar su koma amma ba hali saboda Sharifah ta tsare su da idanuwan nan na ta masha Allah manya-manya. Ga kujerun da za su iya zama dole sai a kusa da Sharifah ne. Da alama yana ganawa da wasu mutane a cikin ofishin, dan haka dole su jira. Kallon da Sharifah take yi mu su ya wuce na mutane dan ba ta ko qiftawa. Sun kasa gane dalilin wannan tsare su da idanuwan da ta ke yi. Maryam ta sake daka tsalle ta koma ta maqale a bayan Nana, dan tafi ta tsawo da qiba da fadi, Idan ta labe a bayanta baa hango ta ko kadan, takaici ya kara kama Nana. Ta shiga zulumin shin ta je su gaisa da Sharifah ko itama ta share ta su kalli juma kawai. Su na tsaye basu zauna ba duk da tayin da sakataren yake ta yi musu akan su zo su zauna amma suka ki zama. Su sun san dalilin da ya hana su zama, tsoron Sharifah ne. Ana cikin wannan hali ne sai mutanen cikin ofishin suka fito, Sharifah ta tashi ta shiga sannan su Nana suka samu damar zama. Nana da Maryam sai fada ake yi saboda labewar da take yi a bayanta, Nana ta ce ta daina yi ma ta haka. Maryam ta sha aradu muddin ta ga abin buya wallahi sai ta buya a bayanta kuwa. Sharifah ta dade a cikin ofishin Barista, su na ta tattaunawa da shi da alama case dinta babba ne. Ta fi awa guda sannan ta fito, har Nana ta shiga fargabar ko dai Sharifah ta bace tare da yayanta, ta ji kamar ta je ta leqa ta gani. [3/1, 12:30 PM] Jamila Umar Tanko: 3 Sharifah ta fito daga ofis bayan ta gama, ta same su a zaune, ta kalle su suka kalle ta sannan ta fita. Su Nana ba su ji dadin wannan abinda ya faru ba, ya kamata ace sun yi ma ta magana duk da itama ba ta yi mu su magana ba ai amma tana da dalili tunda sun dauke ta fatalwa zata ji tsoron ta yi mu su magana don kada su baje da gudu. Sai dai sun rasa abinda za su zaba shin ita ce ko fatalwa ce? Su ka shiga ofishin Barista da sauri bayan sun yi ma sa sallama, ko gaisawa basu yi ba Nana ta shiga jero masa tambayoyi. " Yaya ka san wannan matar ashe, wacce ta fita yanzu?" Ya ce "kwarai kuwa mun dade tare nine lauyanta duk da sai daga baya ta dawo wajena bayan ta gama shan wahala da wasu lauyoyin." Nana da Maryam su ka hada ido sannan suka sami waje suka zauna. Nanah ta sake cewa "Yaya ka ce kun dade tare ko?" Ya harare ta ya ce " ina ruwanki da mutanen da su ke aiki tare da ni ne? Menene matsalarki? Kin santa ne?" Nanah ta gyara zama ta ce "akan me ake yin shari'a da ita? Ita ta kai kara ko ita aka kai kara?" Wannan karon sai ya qi ba ta amsa, ransa ya baci har sai da fuskarsa ta nuna. Ya ce "ku fadi abinda yake tafe da ku kawai,babu ruwanki da case din wasu." Maryam ta gaishe shi sannan ta fara bayani. Shi kuma ya na sauraronta. Su na fitowa Samha suka kira a waya, su ka shaida ma ta sun hadu da Sharifah a ofishin lauya amma sun kasa yi ma ta magana kuma har ta gane su na jin tsorona har yanzu. Samha ta nuna bata ji dadi ba, basu kyauta ba. Sharifah a halin yanzu soyayya take bukata da kulawa, saboda ta rasa kusan kowa na ta, ta rasa komai. Duk da ba ta kammala ba ta labarinta ba amma alamu sun nuna haka, kowa ya guje ta saboda an ganta da wahalar yara. Game da shari'ar ce ma baa san ko da wa suke yi ba. Shin Shariqah take nemowa hakkinta ne bayan ta rasu ko wani zalumci aka yi ma ta daban? Nanah ta na dorawa Maryam laifi, Maryam na dorawa Nanah laifin cewa ita ce ta fara razana. Su ka yiwa Samha alqawari zasu sami lokaci su zo gidanta sai ta jagorance su zuwa gidan Sharifah su ba ta hakuri. *** ***. *** Samha na zaune sai ta ga kiran wayar Mamarta ya shigo wayarta, bayan ta amsa sun gaisa kamar yadda su ka saba. Kwatsam sai Mama ta ce " Samha! Yanzu na ji wa'azi a radio yadda kika san da mu ake, game da Sharifah. Malam ya ce babu fatalwa a duniya, babu wanda ya mutu ya taba dawowa duniya. Mun yiwa yarinyar nan mummunan zato." Samha ta ji dadi da jin kalaman da suka fito daga bakin Mama. Alhamdulullah. Mama ta dora da cewa "idan kin sami lokaci ko ki je gidanta ko ta zo gidanki ki saurare ta ki ji meye matsalarta in sha Allah za mu taimaka ma ta idan bai fi karfinmu ba. Mahaifiyarsu mutuniyar kirki ce bana manta alkhairan da su ka yi mana a lokacin aurenki. Lokacin da komai ya cabe min, ba mu da kudi su ne masu kudi babu abinda ba su dafa sun kawo gidan nan ba kowa ya ci ya sha ya koshi a taron biki. Bayan haka kuma kayan dakinkin ma su suka siya mana abubuwa da yawa." Samha ta gyada kai ta ce "kwarai kuwa Mama ban taba manta alkhairan bayin Allah nan ba. Mamarsu da su kansu, wallahi Mama ban taba mantawa da yiwa iyayen Sharifa addu'a ba har lokacin da ba ma tare, mun yi zumunci a baya sosai dan ba zan manta lokacin da Babansu yake zuwa mata visiting a sakandire ba, dukka kawayenta sai ya raba mana kudi da littattafai. In sha Allah zan sami lokaci in je gidanta, dan na san a yanzu dai ba zata zo gidana ba, dan tana da zuciya mun yi mata laifi akan abubuwan da mu ka yi zatonta da su. Ba ta ji dadi ba sam." Su na kashe waya sai Samha ta ji hawaye yana ta sirnano ma ta na tausayin Sharifah. Aliyu ya shigo ya iske ta na kuka, ya razana a tunaninsa ko mutuwa ma aka yi. Dakyar dai ta iya bashi labarin abinda ya faru tsakaninta da Mama, da labarin da su Nana suka ba ta cewa sun ga Sharifah a wajen lauya. Tabbas Sharifa tana buqatar kulawa, tana bukatar wani da zai tsaya a gefenta ya na karfafa ma ta guiwa ko da baa taimake ta da kudi ba. Tambayar da Aliyu ya yi ita ce "ina mijinta yake yanzu ko basa tare?" Samha ta ce "tare da kai fa ta ba mu labari, ba mu ji karshen labarin ba amma kamar da alama basa tare dan tana ta ambaton rashin kirkinsa. Ba ta taba jin dadin zama da shi ba." Aliyu ya tambaye ta "menene abin yi yanzu?" Ta ce su Nana sun ce zasu sami dama su zo ta jagorance su zuwa gida Sharifah dan su ba ta hakuri. Ba su saka rana ba dai amma zasu zo. Ya ce duk ranar da suka zo ya bata izini ta je koda ba ya gari. Samha ta ji dadi ta yi godiya sosai. Ta shiga tunano irin abincin da Sharifah ta fi so idan zasu je sai ta dafa ma ta ta kai ma ta. Dan ta san ita da yaran za su ji dadi a kalla zasu ga an kula su. *** *** *** Bayan wasu kwanaki ne qawayen Samha su ka hadu su dukka suka zo gidan Samha. Anan aka tayar da magana aka dinga hayani, maryam da Nana dai an basu laifi an ce ba su kyauta ba akan tsoronta da suke ji bayan sun tabbatar ba fatalwa ba ce yanzu. Samha ta na daga kicin ta na tsomo baki. Ta yi musu girke-girke kala-kala daman ita cikakkiyar chef ce har ma tana da makarantar da take koyar da girki. Ta na son girki kuma ta iya girki, tabbas ta sha karbar kambun yabo idan aka yi gasa ita ke cinyewa. Sunanta ya yadu ya bazu a fadin birnin Kano da ma arewa baki daya. Ashe da walakin goro a miya shiyasa dangin Aliyu su ka kasa yin nasara wajen tursasa shi akan ya rabu da ita ya auro wata. Ya qi fur ya ce shi sai Samha ita kadai. Allah sarki ya ce haihuwa ta Allah ce, tunda likita ya tabbatar mu su shi da ita dukka lafiyarsu kalau lokaci kawai suke jira. Ga shi kuwa lokaci ya zo, bai yi garaje ba, ya yarda da cewa baa yiwa Allah shishshigi, baa yi maSa tilas. Allahu akbar! Mai yadda Ya so a lokacin da Ya so. Su Nanah su ka ci su ka yi haniqan har da ma su daukarwa miji da yara a 'yar roba, saboda dadin abincin ba zasu taba iya dafa irinsu ba. Samha ta saba ganin hakan dan haka baya bata mamaki, dan duk wanda ya ci abincinta sai ya yi santi kuma sai ya so ya kaiwa masoyansa su ma su dandana. Amma fa ba dukka abincin ta kawo musu ba, ta ware na Sharifah daban ta adana a kicin. Abincin me yawa kuwa kasancewar ta ga su na da yawa, ga yara, ga Bello. Samha ba ta karbi lambar wayar Sharifah ba duk da ma alamu sun nuna ba ta riqe waya, sai wata karamar waya ce a hannu Hamidah. Amma dai za su yi shahada su je sun san ko ba ta gida yara na gida tunda akwai makaranta islamiyya da boko, ba za ta fita da su ba. A mota daya su ka dunguma suka tafi wato motar Nana ita ce babba. Su ka isa gidan Sharifah suka iske Bello ya fito zai shiga motar nan da su Nana su ka ga Sharifah a ciki a wajen barista, ashe motar Bello ce. Ya kalle su ya kawar da kansa gefe, kafin ma su sami waje su gyara tsayuwar motar, ya shige motarsa ya tafi, da alama har yanzu haushinsu yake ji musamman ma Samha. Su ka fito suka iske get din a rufe, sai su ka cika da fargabar ko babu kowa a gidan. Wadanda har yanzu zuciyoyinsu basu gama yarda da cewa ba gidan fatalwa ba ne, suka ji fargabar kwankwasawa yayin da wasunsu irin su Samha gaba gadi suka hau bugawa. Sai can da jimawa suka jiyo motsin tafiya, aka zo aka bude. Hamidah ce ta bayyana wannan karon idanuwanta sun yi jajawur, alamar ta sha kuka. Su Nanah su ka daka tsalle suka yi gefe, Samha ta harare su alamar su daina yin abinda suke yi haka. Samha ta rungume Hamidah ta na lallashi ta tambaye ta ko lafiya take kuka? Amsar ita ce "babu komai." Samha ta ci gaba da lallashinta akan ta fada ma ta abinda yake faruwa. Amma Hamidah ta dage ta ce ita babu komai. Samha ba ta yi mamakin kukan da Hamidah ke yi ba, saboda ta ji labarin shakuwarta da Shariqa dole har yanzu ta yi kukan rabuwarsu. Samha ta tambaya "Mamarku na cikin gida?" Hamidah ta gyada kai ta ce "Eh ta na sama." Samha ta kama hannun Hamidah su ka yi gaba tana ci gaba da ba ta hakuri da yi ma ta nasiha akan ta yi hakuri, kowanne mai rai mamaci ne. Mu dukka anan wataran za mu mutu mu tarar da su acan." Su Nana su na ta jan kafa su na tafe su na sanda yayin da zuciyoyinsu ke karkarwa. Har yanzu gidan tsoro yake basu duk da dai an gyara, ba irin yadda su ka gan shi rannan ba, ada dai ga duhun bishiya, ga na datti da kura amma yanzu fes da shi. Su ka hau sama cikin wani katafaren falo mai girman gaske kuma ya tsaru kamar a turai. Sai mamaki ya rufe su, ai basu taba zaton har da gyararren waje a gidan nan ba, sun zaci kwango ne kawai. Kowacce ta sami kujera ta zauna yayin da suka bawa Hamidah fulasan abincin da suka kawo mu su, ta karba gami da godiya sannan ta dora akan dining table, ta koma gefe ta tsaya. Sun tambaye ta ya fi a kirga shin ina Mamarta take dan ba su ganta a falo ba, sai Hamidah ta yi shiru ba ta ba su amsa ba. Ba su ankara ba muryar Sharifah su ka jiyo a daya daga cikin dakunan. Ta na magana cikin fushi da daga murya ta na cewa "ke 'yar uwata Shariqah ki koma ki kwanta. Na rantse da Ubangijin da Ya busa min numfashi kuma Ya raya ni nake yawo a doron kasa, kuma Shine Ubangijin da Ya dauke miki numfashi kina kwance a karkashin kasa, ba zan bari 'ya'yanki su wulaqanta ba. Ki koma ki kwanta, ki koma ki kwanta na ce , ki je ki huta abinki. Wannan yaqin na rayayyu ne ba na Matattu ba ne." Daga Samha har kawayenta su ka daka tsalle suka miqe tsaye, yayin da su ka bazama neman kofar da za ta sada su zuwa waje. Aka hau damben bude qofar da ta qi buduwa sai da kyar. Su ka falfala da gudu kai ka ce gudun famfalaqi suke yi, ba su tsaya a ko ina ba sai da suka gansu a farfajiyar kofar gida a bakin motarsu. Huci su ke musamman Nanah 'yar lukata. Ta na ta huci ta zaro mukullin motar daga cikin jakarta ta ce sai dai wata ta karba ta tuqa. Ta ci gaba da cewa "Samha ai na fada miki Sharifah ba cikakkiyar mutum ba ce, kika nece kika ce kin tabbatar mutum ce, ai gashi nan zaa kashe mu." Samha ta na ta nishi ta dafe kirji ta ce " Sharifah daman ta fada min, bayan ta yi rantsuwa da Ubangijin da ya halicce ta Ya halicci Shariqah ta ce tana magana da Shariqah fuska da fuska kamar yadda take magana da ni. Ta sake yin rantsuwa cewa Mamaci ya na sanin abinda yake faruwa a duniya kafin mu bil'adama mu sani. Ta ce idan malaman garin nan ko na duniya kaf zasu taru akanta su karyata ta ita fa ta fada ba za ta janye ba, cewa mamaci ya san abinda yake faruwa a duniya saboda ita ganau ce akan Sharqah ba labari aka ba ta ba." Maryam ta zabura ta dafe kirji ta ce "wato dai yanzu Shariqah na cikin dakin da Sharifah take magana, tare suke hira kenan? Ban taba ji ana HIRA DA MATATTU ba sai a yau. Mun shiga uku, innalilahi wa inna ilaihi rajuun.Wannan wacce irin Sharifah ce mu ka kwasowa kanmu?" Hamidah ce ta bayyana a bayansu har yanzu idanuwanta na cike da hawaye sun yi jajajur abin tsoro. Sai su ka razana su dukka, har wasu sun ruga da gudu baya mota sun sami mafaka. Hamidah ta sharce hawaye cikin sanyin murya ta ce "Mamana ta ce ku hawo sama, ta fito falo yanzu, ta na jiranku." Aka hau kalllon-kallo a junansu. Nanah ta yi karfin hali daga nesa ta ce "wacce Mamar ta ki daga ciki Sharifah ko Shariqah?" Maryam ta nisa ta ce "tab! ai ni kam sai dai a kai gawata cikin gidan nan kuma." Samha ta yi sauri ta katse su dan ba ta so su sake ganewa har yanzu a fatalwa aka dauke su. Ta ce " 'ya ta Hamidah ki fadawa Mamarki wani emergency kira aka yi mana zuwa asibiti. Ki ce ma ta za mu dawo a cikin satin nan in sha Allah. Ga abinci nan na dafa mu ku. Ku ci ke da kanananki. Su na ina ne ban gansu ba?" Hamida ta sharce hawaye ta ce " ba sa nan an sace su." Samha ta zabura ta dafe kirji ta ce "an sace su kamar yaya?" Muryar Bello su ka ji a bayansu ya dakawa Hamidah tsawa ya ce "ke Hamidah! shiga gida kuma ki saka sakata kada in kara ganin kafarki a waje." Jikinta na rawa ta shiga gida. Su ka juya su na kallonsa, ya na zaune a cikin motarsa yayin da ya wurgo musu wata uwar harara. Nan da nan kowacce ta hau laluben kofar shiga mota. Samha ce ke tuqawa dan Nana ta sha aradu ba za ta iya tuqi ba. Aka yi shiru babu wacce ta ke magana sai zulumi da tunani. Abin ya fi bawa Samha mamaki dan ada ta yarda Sharifah mutum ce dari bisa dari amma ta yaya take iya yin HIRA DA MATATTU? Su daman su Nana basu gama yarda Sharifah mutum ba ce dan haka ba su yi mamaki da yawa da ta fito a wata sabuwar sigar ba. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun kowacce ke kira. Samha tuqi take kamar za su tashi sama saboda zuciyarta tafasa take ta yi kawai, wannan labari ba za ta iya fadawa Mama ko Aliyu ba dan za ta iya saka babban kokonto a ransu bayan sun cire zargi a baya. Nanah ta yi ajiyar zuciya ta ce "Samha yanzu duk nacinki dai za ki rabu da Sharifah ko kuwa har yanzu za ki sake bata wata damar kuma? Ni dai na gama, na sallama ta, na hakura da kawancen nan, kawaye har sun yi min yawa dan na rasa ta ba komai, ni dai na yafe." Maryam ta zabura ta ce "ai ko ita kadai ce kawata a duniya na yafe ma ta wallahi, itama ta yafe min mu yi sallama." Rukayya ta yi ajiyar zuciya ta ce " daman ni da Sharifah ba shiri mu ke yi ba tun a jami'a, dan ta ga tana da kokari a jami'a ina cewa ta koya min karatu sai ta dinga yi min wani gani-gani. Daman can ma jinina da ita bai hadu ba, a dalilinku ne ma mu ke gaisawa." Halima ta girgiza kai ta ce "kai Rukayya ko a bayan idon mutum ne ka fadi gaskiya mana. Babu wanda zai yiwa Sharifa shaidar baqin hali wallahi, ga kyauta ba ta da mugunta. Kawai dai yanzu ta zama abar a gudu dan ba ta da kammannin mutane sak." Samha dai ba ta magana har suka isa gida suka fito suka shiga falonta aka zauna, aka yi jugum kamar gidan makoki. Samha ta zabura ta jawo wayarta ta kira Fanna ta saka ta a hand's free.Fanna na dauka ko gaisawa ba su ba. A gigice Samha ta ce "Fanna! dan girman Allah me kika sani akan matsalar da ke damun Sharifah. Ba ta fada miki wasu daga cikin matsalolinta ba?" Fanna ta yi dariya ta ce "ai kun yarda Sharifah fatalwa ce ta mutu ta dawo ko? Toh a je a hakan. Ban sani ba ko dan ni ma mun samu matsala iri daya da ita ne shiyasa ba na jin tsoronta. Dan nima na yi ciwo na mutu fa, mata da maza sun cika gida an fasa kukan mutuwata. Har an yi min wankan gawa, an saka min likkafani, maza sun kinkimi gawa za su fita da ni waje, zaa yi min salla a kai ni kabarina sai na farfado." Samha da kawayenta su ka daka tsalle har da Rukayya da take sallah suka fafara da gudu, suka yi waje. Anan Samha ta bar wayar a yashe, su na jiyo dariyar Fanna, ta na ta dariya babu kakkautawa, irin ta muguntar nan. Wannan karon yaren KANURI ta juye harshe take yi. Ta na ambaton sunanta da na Sharifah da na Shariqah. "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Me yake shirin faruwa kenan? Fanna ma fatalwa ce ashe shiyasa bata tsoron Sharifah, an ce ta zo ta raka mu gidan ta ki zuwa." Nana ce take magana har da hawaye. Su na ta kai kawo a farfajiyar gidan an rasa wacce ta iya shiga cikin falon. Su mayafansu ma suke so su dauko su tafi gidajensu. Kowacce na tunanin in da za ta kaura ta kwana ko mutanen da zata biya ta dauko a cikin danginsu su taya su kwana. Samha ta fi su dimaucewa ba ta so ta dawo gidan jiya na firgici da susucewa, kuma da alama dai sai ta dawo saboda duk yadda ta kai ga yiwa Sharifah kyakykywan zato abin ya ci tura. Da kyar suka samu suka yi jarumta suka shiga falon, ga waya nan a yashe a kasa. Da Samha ta duba 9 missed calls Fanna da 3missed calls din wata lamba wacce ta yi ma ta kama da ta Sharifah wacce ta taba kiranta da ita, ta gani. Samha ta sha aradu ba za ta amsa kiransu ba, ta ma kashe wayar gaba daya. Su Rukayya da aka yi sallah raka biyu baa idar ba aka runtuma da gudu ta ce za ta rama sallar a gida. Wasu ma sun manta take way din da suka yiwa miji anan saboda gigita, kowacce ta suri jaka da mayafi jiki na karkarwa ta fita. Daman dukkansu da motocinsu suka zo dan haka kowacce ta shiga ta ja ta tafi tana addu'a. Aka bar Samha ita kadai a gida tana muzurai, da sauki ma tunda Aliyu yana gari zai dawo komai dare, amma ta tabbatar zai neme ta a waya kafin ya iso, ga shi kuma ta kashe wayar. Ta hau kan abin sallah ta na lazumi amma fa dukka motsin da ta ji sai ta zabura ta waiwaya. Aliyu bai dawo gida da wuri ba sai bayan qarfe goma na dare ta wuce. Lokacin Samha ta gama zabura-zaburenta har ya zame ma ta jiki. Wani irin tsoro mai tsanani ne ke damunta. Amma ta kasa bawa Aliyu amsa a dukkannin tambayoyin da yake jero ma ta. Musamman akan dalilin da ya sa ta kashe wayarta. Amsar da ta bashi ba ta gamsar da shi ba na cewa babu caji. Sai ya kalli fitilar lantarki a kunne, ya jiyo ya dube ta. Ta lalubo wayar ta kunna sakonnin Fanna ne ya shigo har guda uku. Sako na farko ta ce "kin kira kina so ki ji labari kuma kin kashe waya." Sako na biyu ta ce " ki kunna waya mana." Sako na uku ta ce "in kina so in baki labarin matattu da fatalwa ki kira ni ki ji." Ta na karantawa sai ta zabura. Aliyu ya tsaya ya na kallonta. Can ya tambaya ya ce "kun sami zuwa gidan Sharifah kuwa? Me ya faru? Ko wata fatalwar kika gani ne na ga kin susuce?" Samha ta zazzare ido ta ce "fatalwa kuma? Ai an wuce wannan babin. Ba mu sami damar zuwa ba. Amma za mu saka wata ranar." Da ya ci gaba da yi ma ta kallon tuhuma sai ta yi gaggawar barin falon don kada ya gane ta. *** *** *** Bayan kwana biyu da rana misalin karfe biyu, Aliyu yayi tafiya, Samha na zaune ita kadai a falo ta na kallon talabijin. Sallama ta ji a bakin qofar falonta ba tare da ta ji an taba get ba, duk da ma dai get din a bude yake amma tana jin karar sa idan an taba. Muryar da ta ji ta daga ma ta hankali, ta yi kama da muryar Sharifah ko Shariqah ko Hamidah. Sai ta zabura ta miqe ta koma bayan kujerar lungu ta tsaya, ba tare da ta iya amsawa ba. Ta ga an bude labule an shigo sai ga Sharifah ta bayyana muraran, hannayenta dauke da manyan fulasanta na abincin da suka kai ma ta. Aka hau kallon-kallo a tsakaninsu sannan Samha ta tuna ashe bakuwarta ce, kuma sannu da zuwa da murmushi ake yiwa baqo. Samha ta washe baki ta yi murmushin karfin hali ta ce "yau Sharifah a gidana? Sannu da zuwa, ki zauna." Sharifah ta yi murmushi sannan ta sami kujera ta zauna. Yayin Samha ta shiga kicin hannunta na rawa ta dauko lemo da ruwa ta kawo ma ta. Sannan ta sami kujera daga nesa-nesa ta zauna. Kirjinta na faman dukan uku-uku. Bayan sun gaisa Sharifah ta ce "daga makabarta nake wallahi, na ce dai bari in biyo in ajiye miki fulasan nan in yi miki godiya." Samha ta dafe kirji ta maimaita "makabarta kuma? Me ake yi a makabarta? Waye ya rasu?" Sharifa ta shafa kai ta ce " na je ziyara ne. Na jewa Shariqata visiting. Kin san ana je musu visiting da guzurin addu'a ko?" Samha ta gyada kai cikin matsanancin tsoro ta ce "eh haka ne. Ina zuwa." Ta shiga daki ta dauko takarda da biro ta rubuta wasiyya. Ta ce "idan kun tsinci gawata ko an rasa ni na bace toh Sharifah ce, ta zo gidana ga mu mu na tare daga ni sai ita a gida." Kamar daga sama ta ji Sharifah ta kwalla ma ta kira, sai ta fito a gigice. Sharifah ta kalle ta ta yi dariya, ta ce "canza min tasha ina so in kalli wani horror fim a MBC 2, zasu maimaita yau. Jiya na fara kallo na yi bacci. Fim din Matattu ne, su na fitowa daga kabarurrukansu. Daga sun ciji masu rai sai su ma su zama su." Samha ta ji gabanta ya fadi da alama yau ta zo ta cije ta itama ta zama su. Hannunta na rawa ta dauko remote ta miqawa Sharifah yayin da ta yi wuqi-wuqi da ido, ta yi baya-baya ta zauna daga nesa da ita. Ana gama fim din da ake yi yanzu zaa fara wancan fim din na matattun da take so. Sharifah ta na ta yi ma ta hirar yadda abincin yayi dadi, sun sha santi. Har aka gangaro hirar su ta rannan akan rayuwarta. Samha ta fara sakin jiki akan babu yadda za ta yi dole ne ma ta sake. Samha ce ke tambayarta akan a ci gaba da labarin rannan amma da alama ma yau Sharifah ba ta son hirar. Samha ta ce "Su Nana sun ganki a wajen yayanta Barista kin je rannan sai suka ji tsoron yi miki magana saboda sun fi son su zo har gida su baki hakuri. Sun yi miki laifi ba dadi su baki hakuri akan hanya." Sharifah ta galla ma ta harara har sai da gaban Samha ya fadi. Sharifah ba ta bata amsa ba, ta ci gaba da kallon talabijin. Sai can ta ce "ai kun zo har gida kuma ku ka sake guduwa." Samha ta sunkuyar da kai ta kasa bada amsa. Sharifah ta kwashe da dariya har sai da Samha ta tsorata sannan ta ce " ku na bani mamaki, amma ba abin mamaki ba ne dan har yanzu ba ku san mutuwa ba ne ba ne, ba ku taba rasa wani makusancinku ba shiyasa har ku ke tsoron mutuwa da matattu." Samha ta gyada kai ta ce "har da wannan ma." Sharifah ta gyara zama ta ci gaba da cewa " Na tsaya a inda na ce a lokacin ina zama a kudu ni da mijina. A dalilin rashin lafiyar Shariqah na ji gara kawai in dawo kano in zauna a kusa da ita. Na kauro Kano na kama haya a kusa da unguwar da gidan Shariqah yake bai wuce naira hamsin a adaidaita sahu ba, na samowa Hamidah makaranta ta ci gaba." Samha ta ce maigidanki fa?" Sharifah ta tabe baki ta ce "a can na bar shi yana zuwa ina zuwa daman zamana da shi babu dadi na fi sha'awar mu rabu saboda daga ni har 'yarsa ba ma jin dadin zama da shi. Baya tsinana mana komai da albashinsa. Komai ni nake yi a gidan.Ya qi yin saki kuma baya kyautata min. So yake mu yi aure irin na 'yan duniya mu daki juna, mu zagi juna sannan mu fito titi mu tarawa kanmu mutane sai kuma mu koma gida mu bawa juna hakuri mu ci gaba da zama. Da na fahimci haka yake sai na ja masa layi ba na kula shi sam, abinda na sani shine aure bautar Allah ne aljannar mace tana karkashin tafin kafar mijinta, idan haka ne ba zan taba samun aljanna ba a irin wannan rayuwar ta mu ba." Samha ta gyada kai ta ce "wannan gaskiya ne, kin yi daidai." Sharifah ta ce "Dan haka na dinga baya-baya da shi dan kada ya illata mu. Na matso kusa da 'yar uwata dan na kula da ita kuma na taimaka ma ta sosai da kudina da kuma jikina da shawarata. Kwatsam wata dama ta samu ni da shi daman mun nemi tafiya turai Allah bai yi ba sai daga baya damar ta samu mu ka yi shawara mu kaura kawai. Na bar Hamidah a gidan da na kama haya na dauko wasu daga cikin dangina suka zauna da ita. Ina so ta gama sakandire sai in zo in tafi da ita kawai. Mu na can har mu ka shekara daman kamar yadda na fada miki a baya zamana da mijina a cakude a waje daya matsala ne, kullum fada. Abin ya zamanto har da cin amana kuma na gano shi ya fara son wata kawata acan, na gane abinda ke faruwa kawai na sallame shi mu ka rabu, na kama gaba na ya kama na sa gaban. Daga baya ma ya kasa zama ya dawo Nigeria ya ci gaba da lalacinsa. Ni ce daman me zafin neman na ci gaba da gina sana'a ta a can ni da wata kawata mai suna Fatima kt mu na zaune tare. Ina samun abin rufin asiri ina turowa gida ina taimakon 'yata da 'yan uwana musamman Shariqah. *** *** **** A satin da Shariqah za ta rasu na sami mai zuwa nan Turai na ce ta aiko min da gyararren wake da gyadar kunu. Kasancewar na san ba ta da kudi sai na turo ma ta da kudi na kashewarta da kuma wanda za ta sayi komai. Aka ce ita ta gyara min da hannunta, dan tayi-tayi da mai aikin ta yi ta qi mayar da hankali, dan haka sai ta yi da kanta. Ta rame sosai kasancewar ciwon ya na ta cinta. Na yi ta fama da ita akan ta turo min hotonta in gani amma ta qi, ashe ba ta so in ga yadda ta zama ne ta san hankalina zai tashi. A waya dai ga muryarta nan tangararai ashe jikin ba dadi. Koda yaushe muna hira a whatapp da sabuwar wayar da na turo ma ta, ta sare gaba daya ta ji a jikinta zata rasu. Muna hira na ce ma ta kwana biyu sai in ji zuciyata babu dadi, gabana ya na ta faduwa. Budar bakinta sai ta ce "ko ni ce zan mutu?" Na rasa amsar ma da zan ba ta yayin da hankalina ya sake tashi. Ana cikin wannan hali kwatsam Hamidah ta kira ni tana kuka ta ce min " Mama sai in ji na kasa bacci kirjina yana ta bugawa, zuciyata na tsinkewa." Nan ma na ji hankalina ya tashi matuka, na cewa Hamidah ta yawaita yin addu'a sosai da yawan alwalla da sadaka. Shariqah ta bani labari a waya ta ce ta kasance tana yawan yin barci mai nauyin gaske a koda yaushe, ba dare ba rana ba safe. Baccin da kowacce irin hayaniya ake yi ba ta ji, sannan kuma ayi ta tashinta ana girgiza ta dakyar take tashi. Ta tabbatar min wata duniya take tafiya, tana ganinta tana biye da wani mutum. Mutumin ya na hawa saman duwatsu, tana biye da shi. Sai ta waiwayo ta dubi bayanta sai ta ga 'ya'yanta guda biyar din nan dukka a warwatse wancan a wani lungu wancan a yashe a wani waje daban, sai ta zo ta na ta kokarin harhada su a waje daya amma sun ki haduwa. Sai ta hada wadannan sai ta sake hango wancan a can wani a wani waje, in ta dauko shi sai ta ga wancan a wani lungun. Tayi-tayi ta hada su a awaje daya ta kasa. Da ta fada min sai na yi shiru dan akwai tashin hankali babba a cikin labarin mafarkinta. Nima ina can ina yin nawa mafarkan, na ga daki guda ya kama da wuta, sai na fito a gigice da yara guda biyu a hannuna. Da na fada ma ta sai ta ce "ko dai mutuwa zan yi" Ban san ciwon ta ya kai haka ba, har nake ta kokarin ba ta kwarin guiwa, na ce ta fara yin business zan turo ma ta da kayan yara da takalma ta fara siyarwa. Ta amince nan da nan take ta murna. Akwai wani gidana karami da na taba siyar ma ta, ba ta fada min kai tsaye cewa mijinta ya qi kai ta asibiti ba amma ta ce min in karbi gidana in mayar ma ta da kudinta har ma ta yi mun ragin 500k hakan ya nuna a matse take da kudin. Ashe lafiyarta ta ke so ta tafi ta nemo. Na Amince har na tura ma ta wasu daga cikin kudin na fara biya. Hamidah ta dauke ta a hoto ba tare da ta sani ba ta turo min "innalilahi wa inna ilaihi rajuun." Ashe babu Shariqah, a kashi goma saura kashi uku, Shariqah ta kare ta rame sai kashi ga gayo tana yi. Karfin hali kawai take yi da take iya magana, ba ta daina aikin girki da yiwa miji wanki ba. Bayan kwanaki biyu Hamidah ta kira ni a gigice ta ce ga Muminta Shariqah babu lafiya, ta zo gidan ta same ta a yashe a kasa a falo, mijin ya fita bayan yaran sun je da gudu sun fada ma sa ba ta da lafiya, ya zo ya kai ta a asibiti. Ya ce baa fada masa da wuri ba, shi yanzu fita zai yi. Ko leqawa bai yi ya ga yanayin jikin ba. Bayan Hamidah ta wuni a makaranta ta je gidan sannan ta iske ta a cikin wannan hali. Daga ita sai yara kanana da mai aiki. Na cewa Hamidah ta samo adaidaita ta kai ta asibiti, yariyar nan karama ita ta saka ta a cikin adaidaita sahu su ka tafi. Kowanne asibiti baa karbe ta ba saboda babu gado kuma ba su da na'urar oxygen din da zaa saka ma ta saboda numfashi ya dawo sama-sama. Hamidah ta kira su Bello da sauran dangi aka hadu da su aka dinga fama. Mijin nan bai dauki waya ba har dare, babu irin kiran da baa yi ma sa ba ya qi dagawa. Karshe dai suka kai ta wani asibitin kudi, tunda babu gado ana gwamnati kasancewar a lokacin ana wani irin anobar zazzabi. Aka ce sai can da daddare mijin ya zo ya na ta yi ma ta tsawa. Wasu daga cikin dangi su ka hau kansa da fada sannan ya sassauta. Da kyar lokitoci su ka ceto rayuwarta, ta samu ta warware kadan, har muka yi magana a waya da ita.Bayan kwana biyu tana asibitin jiki ya sake rikicewa, na kira su a waya yadda na ji kowa a rikice na san Shariqah kuma babu. Na yi addu'a, na yiwa Allah SWA bakance, na yi sadaka, na saka dukkannin Malamai bayin Allah da na sani su sauke ma ta qur'ani akan Allah Ya jinkirta ma ta, Ya tashi kafadunta. Na yi tawasali da dukka kyawawan ayyukana da kaunar da nake yi wa Annabinmu dan gatan Allah Muhammadu Rasullulah (S.A.W)." Sharifah ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa yayin da hawaye ke zuba kamar an kunna famfo. Samha ma sharce hawaye take tayi ta yi dan yaqi tsagaitawa. Ta miqawa Sharifah tissue ba tare da ta iya magana ba. Sharifa ta karba ta goge ta face hanci, ta dago ta dubi Samha da jajayen idanuwanta Ta ce "Allah sarki Samha na zo na ba ta miki mood dinki, na tayar miki da hankali, na saka ki kuka." Samha ta ce "in ban tsaya na saurari labarinki ba ba zan taba yafewa kaina ba." Sharifah ta gyada kai ta ce "Na gode da kulawa sosai." Samha ta ce "ci gaba da labarin ina sauraro." Sharifah ta cije baki ta ci gaba da cewa " Wane mutum, babu gudu babu ja da baya idan lokaci ya yi, ko sakon daya Allah ba zai qara ma ka ba. Duk duniya babu mai iya hanawa, me afkuwa ta afku. Ba zan taba manta da yadda na ji baqin labarin nan ba. Shin mafarki nake yi zan farka ko da gaske ne? Haka nake shafa jikina dan in tabbatar. " Innalilahi wa inna ilaihi òrajuun." kawai na ke ambato. Kamar in yi fuffuke in diro Nigeria haka na ji. An sanar min ga Hamidah ta suma ga Bello ya dimauce. Babu abinda zan iya yi, nima ta kaina nake yi, ni kadai a kasar da ba tawa ba, sai ni sai kawaye da abokan arziki ne ke kewaye da ni su na bani hakuri. Na kasa kuka ma sai kirana ake ta yi a waya, daga ko ina a fadin Nigeria saboda ni na fi cancanta a yiwa jaje akan rasuwar Shariqah. Ban qi in kwashe dukkannin kudina da na mallaka a duniya dan in sayi sabon tikiti ba, in har zan samu tafiya a ranar.Mutumin kirki wani Alh. Musa ya yi min dukkan kokarin da zai yi, na hau kan return ticket dina ba tare da an kashe wasu kudi da yawa ba. Ta rasu cikin dare ta yi kwanan kaso da safe aka yi ma ta Jana'iza, ana sanar min da komai a waya. An fadi irin taron jama'a da suka sami halattar jama'izarta, ana yi ma ta kyakykywan zaton samun rahamar Ubangiji. Bayan ta cika da kalmar shahada kowa ya budi baki kyawawan halayanta ake ambato, fara'a, da kyauta, wasa da dariya, ta zauna kowa lafiya. Alhamdulullah ." Sharifah ta yi shiru zuciyarta na bugawa da gudu yayin da idanuwanta su ka ci gaba da zubar da hawaye masu zafi. Ta ci gaba da cewa "Wannan rana ta na daya daga cikin baqar ranar da ba zan mantawa ba. Baqaqirin kuwa, mai duhu gami da daci. Ban sami tafiya ba sai washe gari cikin dare, kowa a cikin Jigin nan sai da ya gane ina cikin bala'i. Na kasa tsayar da hawaye, komai ma na kasa ci ko sha. Ma'aikata masu kulawa su ka dinga zagayowa su na bani hakuri haka fasinjojin da suke zaune a kusa da ni su ka dinga lallashina. Hawayen ya na kwaranya da kansa ne ba tare da ina so ba. Radadi nake ji a can cikin zuciyata kamar ana gobara, na tabbatar na yi rashi a rayuwata, na sake samun qibi wanda ba zan taba dawowa daidai kamar da ba. Farin cikin rayuwata fiye da rabi ya tafi, babu dawowa sai dai maleji." Fuskar Samha ta jiqe sharkab da hawaye yayin da itama radadi da zugi ya mamaye zuciyarta. Ta dafa kafadar Sharifah ta na lallashi ba tare da san kalma daya tak da zata furta wacce zata kwantar ma ta da hankali ba. Sharifa ta sharce hawaye ta ci gaba da cewa "Na isa airport din Kano masu zuwa daukana su ka zo suka dauke ni, ban ma kira dangina ba dan na san su na cikin alhini, na fi son su gan ni kawai. Kwatsam dangina suka gan ni na diro, kowa ya ganni sai ya fashe da kuka amma fa ni na kasa yi. Yaranta na fara nema aka kawo min su, kanana da su abin tausayi. Allahu akbar! Na saka a raina kuma na furta a sarari "kun rasa uwa a zahiri amma ba ku zama marayu ba, tunda ina raye." A lokacin ban ma san ta bar wasiyya a fada min ba cewa kada in bar yaranta su rayu a wannan gidan ba." [3/1, 2:17 PM] Jamila Umar Tanko: 4 Ashe tashin hankali na gaba, na baya dukka wasa ne. Mu na gidanta aka yi zaman makoki aka gama kwana bakwai kowa ya watse. A ranar aka yi zaman farko da mijinta akan maganar yadda zaa yi da yaranta. Da ni da wasu daga cikin dangi, ga kuma babban yayanmu yaya Bellocity. A lokacin Adamu mijin Shariqah ya fara wasu kame-kame wanda baa gane in da ya nufa. Ya ce a bari ayi arba'in akwai wani tsarinsa da yake yi, aka bani hakuri aka ce mu zauna a gidan har a yi arba'in din. Mu na zaune a gidan ni da yayata daya da muke uba ya daya sai kuma kanwar mahaifiyarmu. Sai yarinyar da Shariqah take riqewa 'yar yayarmu ce mai suna Nidal mai kimanin shekaru goma sha uku, da ita yaran su ka saba sosai duk inda ta yi su na biye da ita. Su na zuwa makaranta su na dawowa. Sai kwatsam mu ka ji wata magana wai Adamu ya na so a bashi wannan karamar yarinyar da take rikewa wato Nidal zai aura. Yarinyar da take zaune a gidansa bai taba yin kara ya biya ma ta school fees ba, aka ce an sha koro ta daga makaranta idan Shariqah ba ta da kudi sai dai ta zauna a gida ta kusan cinye term amma ba zai biya ba. Da abu ya ci tura ma ta kasa Biyan private school sai kawai ta mayar da ita ta gwamnati Kuma me shekaru goma sha uku ce za ta reqe yara biyar? A lokacin ma babbar 'yar Shariqah ta na da shekaru tara, meye banbancinsu? Su dukka rainonsu ake yi. Dangi su ka yi masa caaa aka su ka ce ba zai yiwu ba, a ranar da ya furta kalmar nan a ranar aka zo har gidan suka dauke ta. Na kasa magana na zuba ido ina kallon true color sa, gaba daya kai na ya daure. Adamu fa da gaske yake ya kamu da son Nidal, har kama kafa ya je yana yi da iyayen yarinyar da kamanninta da sauran dangi, shi dai a bar shi ya aure ta, zata karasa karatun gidansa. Abin tambaya anan shine daman ya na son ta tun Shariqah na raye ne? Tabbas alamu sun nuna hakan, wato an tabbatar masa da cewa Shariqah za ta mutu har ya gama nasa plans din. Ikon Allah! Kaina fa ya daure ina kallonsu kawai. Shi dai dubararsa ita ce kada a fita da yaransa daga gidansa. Na dade da gane hakan, da ya fada min maganar Nidal, tambaya daya kawai na yi masa daga ita ban sake ba. "Shin me shekaru goma sha uku ce zata iya raino da tarbiyyar yara guda biyar?" Akwai wata yayarmu uba daya muke, bazawa ce, ta na da kirki sosai dan tunda aka yi rasuwar da ta zo ta dinga hidima da yaran nan, ita ce goyonsu, wankinsu, dafa abincinsu, wankansu, wasa da dariya da su. Nima hankalina ya kwanta da ta aure shi muddin an saka masa doka akan babu zalumci da tauye ma ta hakki kamar yadda ya yiwa Shariqah. Ba zaa sake zuba masa ido ayi shiru ya na yin abinda ya ga dama ba kuma. Saboda abinda na hanga na hango wannan hanyar shine kadai mafitar yaran dan muddin aka ce zaa fitar da yaran zaa sha rigima ba kadan ba. Ni kuma na rasa 'yar uwata na rasa dukkan wani farin cikina bana son wani tashin hankali kuma. Na ga alamar itama tana so sai aka yi shawarar cewar ya aure ta mana. Da aka fada masa sai nan da nan ya bata fuska ya ce shi sam babu tsarin auren bazawa a wajensa, haka ba zai iya auren babbar budurwa mai wayo ba. Sai dai 'yar shila wacce zai aura ya juya yadda yake so. Kuma alamu sun nuna ba dan 'ya'yan yake son yin auren ba kenan, bai damu da wacece za ta iya kula da su ba, kawai dan sha'awar kansa ne. Aka gama wannan sai ya gangaro maganar 'yar autarmu Dinar, 'yar kimanin shekaru goma sha takwas, wacce na ce miki a baya idan ta zo hutu gidansa sai dai a boye ta dan idan ya ganta korar ta zai yi. Ya ce itama a bashi zai aura, na ce masa ai gata ga shi ga kuma Mamarta. Anan na sami dama na fada masa dukka kuskurensa da yadda ya munanawa Shariqah. Ya firgita sosai dan ai ya zaci duk baa san musgunawar da yayi mata ba, tunda ya ji babu wanda ya taba tarar sa ya yi ma sa maganar. Da yake yana so a bashi kuma ya tabbatar ya aikata din, ai bai yi musu ba, sai ya shiga tuba gami da yin alqawarin zai gyara halinsa in sha Allah. Har dai aka cika kwana arba'in baa sami matsaya ba, da yawa daga cikin dangi sun nuna rashin amincewarsu ta yadda zaa sake daukar karamar yarinya a bawa mutumin da kowa ya san wahalar da ya bawa waccan. Hasali ma baqin ciki ne ya sa ta kamu da ciwon zuciya har ta rasu, babu wata kulawa da ya yi ma ta. Wannan abu a bude yake kowa ya tabbatar da hakan, an san halinsa an san halinda ake shiga a rayuwar gidansa. Wasu kuma su na ganin a bashi kawai saboda darajar yaran amma a ja masa kunne kuma shi ma da alama ya yi nadama. Yarinyar idan an yi ma ta maganar sai dai ta yi ta kuka ba ta amsawa. A zaman karshe wato ranar kwana arba'in Shariqah. Adamu ya so ace an gama magana an daura masa aure da Dinar kawai sai ta tare a dakin yayarta ba sai an kwashe yaran ba, amma abu ya ci tura dan baa tsayar da matsaya ba. Ransa ya baci sosai a lokacin da Bellocity ya tsura shi da tambayoyi ya ce "ka ce ba ka so a kwashe yara, mu kuma yanzu an yi kwana arba'in, zamu watse. Yaya kake so a yi da yaran? Ina za ka kaisu dan an ji kana hayaniya da uwar gidanka ta yi rantsuwa ta ce ba zata riqe su ba? Ko ta amince ma ai ba ita ce da alhakin riqon su ba, a addini dangin uwarsu ce. Sharifah ce ta fi cancanta ta karbe su, sai ta tafi da su. Wannan abu ya faru ne ba dan kowa ya na so ba. Sai Adamu ya fusata ya fada cikin fushi "shikenan a tafi da su." Ya tashi ya fice a fusace, ni na san kwarjinin Yaya Bellocity ne ya cika masa ido, dan mutum ne mai kwarjinin gaske, kai idan ka kalli fuskarsa ka san babu wasa. Ba ya so amma babu yadda Adamu zai yi muka kwashe kayan yaran, mu ka kulle kofar bangarenta, kowannenmu ya kama gabansa. Mu ka kauro gidan da su Hamidah suke zaune wato gidan da na kama haya wanda bashi da nisa da gidansa. A lokacin mutuwar ta dawowa kowa sabuwa fil, daga ni har yaranta da Hamidah. Haka muke lallabawa mu na rayuwa zuciya babu dadi. Na dauko Dinar daga hannun Mahaifiyarta don ta zo ta taya ni zama da kuma kula da yaran, sannan na samo mai aiki. Abinda ya fara damuna shine Adamu ya hana mu sakat, a koda yaushe safe da rana da yamma sai ya zo ganin yaransa. Sannan islamiyya ya ce bai yarda a saka su a ta kusa da mu ba, ya ce sai dai kullum Hamidah ta kaisu islamiyyar kofar gidansa kuma ta koma ta dauko su. Dan a zauna lafiya haka na takurawa Hamidah sai ta ajiye su sannan ta tafi ta su islamiyyar, sannan idan an tashi sai ta hau adaidaita ta dauko su. kullum sai baya magrib suke dawowa gida. Dokoki kala-kala dai mu na ta bi, bayan nan kuma ya ce duk asabar da lahadi a can gidansa zasu dinga yi, dan su dinga zuwa tahfiz tare da sauran yaransa.Nan ma na yi hakuri da hakan ake yin haka kullum. Bayan arba'in din Sharifah da sati biyu, kwatsam sai aka sanar da ni rasuwar babban yayanmu wato Yaya Bellosity ya rasu bayan yayi fama da gajeriyar jinyar kwana biyu." "nnalilahi wa inna ilaihi rajuun."Sharifah da Samha ne suka hada baki, suka fada a tare yayin da kowannensu ya yi shiru ya yi tagumi. Sharifah ta dago da jajayen idanuwanta ta ce "shine Bellon da nake sanar miki ya rasu na san baki san shi ba. A lokacin da muke yara har yayi aure, ya rasu ya bar mata uku da yara sama da ashirin shine babba a dakinmu. Shine mu ke ganinsa kamar uwa kuma shine uba, shine yake tsaya min akan komai nawa. Magana kuma ta kare Sharifah ta zamanto ba ta da iyaye bata da dangi, kusan dukkan masoyana sun tafi." Wannan karon Sharifah ta zubo da wasu hawaye masu zafin gaske yayin da tausayinta ya kama Samha matuqa. Samha ta sharce hawaye ta ce "sannu qawata ashe irin wannan tashin hankalin kika shiga amma baki taba nemana ba? Haba Sharifah ko dai ba zan amfane ki da komai ba amma mutum ai rahama ne, idan ina kusa da ke ai zan baki shawara, kuma in jajanta miki ai za ki ji dan sanyi " Sharifah ta sharce hawaye ta ce "na rantse da Allah ko motsi da kyar nake yi, ba na son yin magana ma, shiyasa bana riqe waya. Ba na bukatar taimakon kowanne bil'adama sai na Rabbul samawati. Ana cikin wannan hali na gigita da tashin hankali ga waccan ta Shariqah ga wannan ta Bello amma bawan Allah nan Adamu kullum yana cikin yi min kuri da barazanar zai kwashe yaransa. Dan ya ga na damu matuqa da son rikon yaran, kuma ina bin dokokinsa. Sai ya zamanto ma ya fara na nuna min, ai dole ma in bashi auren Dinar ko kuma ya kwashe yaran. Daga baya na fuskanci baya neman amincewar yarinyar dan ko ya zo bata kula shi ya san bata sonsa dan haka ni ce zan yi ma ta dole. Ko unguwa na fita sai ya fara bambamin fada yana kumfar baki wai na fita na bar yara zai kwashe su." Samha ta kama haba ta ce "ikon Allah sai kace shi yake aurenki. Kullen da ya saba yiwa Shariqah ne ya dawo kanki kuma?" Sharifah ta yi murmushin karfin hali ta ce " ke ma kya fada. Ni ko can asali ma ban taba sanin auren kulle ba, balle yanzu, ba mijina ba komai ba ya ce zai takura min. Da gadara yake tambaya sai ta, ya ce min yaya maganar aurensa da Dinar? Amsar da nake bashi ita ce ga ka ga ta nan ai, ku daidaita. Sai ya ce "ai ita yarinya ce ke za ki yi ma ta dole." Na ce "ba zan yi ma ta dole ba ko da kuwa ni na haife ta balle ban haife ta ba, dan yanzu an wuce yin auren dole." Samha ta ce " tab daman har yanzu akwai mutane irin wannan mutumin. Tun yaushe aka daina irin wannan rayuwar?" Sharifah ta ce "neman rigima ce kawai da nuna isa da izza. Irin wacce ya saba yiwa matansa, yana nuna musu mulki da sarauta shine abu ya dawo kaina. Da son takurawa mutane da neman fada. Ya nunawa kowa bai isa ba sai an bi abinda yake so kuma yana ganin kamar bani da kowa. Ashe ta karkashin kasa dangina da dama sun bashi goyon bayan ya yi min hakan. Da na gane inda ya nufa sai na cire tsoro da shakka, zuciyata ta dake. Da na ga ya fara bin dangina yana kama kafa da su sai na zuba ido. Anan aka sami mararsa kaunata da wasu masu kaunata. Aka sami wata da ta bashi labarin cewa anan qasan gidan da muke ma Dinar ta yi saurayi kuma ina sane amma na bar ta take kula. Ya zo a gigice kuma a fusace zai hau ni da fada wai ya ji labari Dinar ta yi saurayi kwanan nan kuma ina sane. Na taka masa burki na ce ka sani fa Dinar ba jaririya ba ce 'yar goye kuma tana da zabi, sannan ni ba zan yi ma ta dole ba kuma munafukar da ta fada maka haka ka je ka fada ma ta an yi din. Kuma wallahi a lokacin ban ma san komai akan maganar wani saurayi da Dinar ta yi ba, abinda na sani yaron yana da shago a kofar gidan da nake yana da kirki yana taimaka mana da aike da sauransu ko sunansa ban sani ba ma da farko. Daga na fita zan ga yana ta gaishe ni. Shine har su 'yan waje da suke wata unguwa har su ka san da labarin yaron aka je aka dinga juya magana. Nan fa ya fuska ya dinga zagayawa gidajen wasu daga cikin dangina aka barke da gulma kala-kala, ana zuga shi." Samha ta ce "ikon Allah yanzu a danginku har a sami mai bin bayan mutumin da ya azabtar da 'yar uwarsu? bayan duk abinda ya yiwa Shariqah? Kai amma zumunci ya lalace wallahi." Sharifah ta gyada kai ta ce "me kika ji ma ai abu na gaba kawata, za ki sha mamaki ace jininka ne yayi ma ka haka. Can kuma ga Shariqah ta kasa kwanciya a cikin kabarinta akan wannan dalilin." Sai Samha ta zazzare ido ta ji gabanta ya yanke ya fadi dan an dawo kan labarin matattu kuma." Cikin jimami Sharifah ta ci gaba da cewa "Ga ni na da ita na farko a bakin wata rijiya ne, na ganta ta na zaune ita kadai ta yi shiru ta sunkuyar da kai qasa idanuwanta a runtse. Na yi ma ta magana, ba ta dago ba. Na jijjiga ta ta runtse ido ta qi dagowa. Daga nan ta bace min da gani, na yi ta duba ta ban kara ganinta ba." Sai Samha ta dafe kirji ta ce " Ya salam! A bakin wacce rijiya kuma? Da safe ko da daddare?" Sharifah ta ce " gab da magrib. Daga nan na fara tunanin akwai abinda ake yi wanda ba ta so. Ina tare da yaranta zuciyata na quna na rasa karamar kanwata, na rasa babban yayana wanda nake ganin shine namijin da zai tsaya min a dukkannin lamurana. Rayuwa ta tsananta a lokacin ba na so in ga kowa ko in yi magana da kowa. Lokacin mutuwar tana tsaka da cin zuciyata na tana cin zuciyar Hamidah sosai kowa a cikinmu babu kuzari. Yaran Shariqa musamman masu wayon su na cikin alhini su kan shiga daki su kwanta akan kayanta su na kuka. Ina ta faman amsa tambayoyin kananan yaran, su na tambaya ta cewa Muminsu ta na asibiti amma me yasa har yanzu baa kai su sun duba ta ba. Ina iya kokarina wajen kawar musu da hankali. Ina ta shirya karya kala-kala wajen kwantar musu da hankali. Kowa da irin yanayin da ya fi so ya kasance idan ya shiga damuwa, wani ya fi son ya zauna yayi shiru, wani ya fi son yayi ta barci, wani ya fi son yayi ta kuka, wani kuma ya na son ya shiga cikin mutane, wani baya san ya ga kowa a kusa da shi. Nawa yanayin na fi son in zauna shiru a daki, bana so in yi magana, ba na so ayi min. Idan na kebe ni kadai a lokacin nake iya yin kuka ba tare da wani ya ganni ba. A daidai wannan lokacin da bana so in ga kowa in yi magana da kowa shi kuma mijin Shariqah ya kafa zarya a gidana yana kulafucin yaransa. Ya na ciyar da su yadda ya kamata abubuwan da bai basu a baya ba ma a yanzu yana kawowa, komai baja-baja amma bai dame mu ba. Babu mai iya ci, mai aikina ce da wasu kalilan daga cikin yaran ne ma ke iya ci. Dinar da Hamidah ba komai ne yake burge su ba sai sun zaba. Dokoki dai na takura barkatai alhali a lokacin bana son a takura min ko kadan abinda yake damuna shi yake damuna. Wannan dalilin ya sa ma na yanke alaqa da dukkannin kawayena ban sanar da su rasuwar ba ma dan bana so a dinga zuwa inda nake. Sauran kawayena wadanda na saba da su daga baya a harkar kasuwanci ko a gari su ma na guje su, babu wanda ya san a ina nake mo me nake ciki. Abinda zai ba ki mamaki zai daure muku kai shine na baro dukka abinda na mallaka na kasuwanci a hannun abokiyar kasuwancina Fatima kt. Ni ce karfin tsayawa har kasuwancin ya kafu, jarina ne ya fi yawa. Na rantse da Allah matar nan da yake bata tsoron Allah sai ta hada dukka ta cinye. Bayan ta fada min bakaken maganganu ta yi blocking dina a dukka wata kafa da zan same ta. Na sayi ticket zan je in hado kayana amma matsalar Corona ta ballo kai babu shiga babu fita. Haka aka soke tikitin ban Sami tafiya ba. Ashe bala'i ya na gaba, dukka wannan wasa ne. Ina zaune ina ci gaba da kula da yara su na zuwa makarantu islamiyya da boko ga kanwata ga mai aiki kowa yana iya kokarinsa. Ban San yadda ake raino ba dan ban iya shi ba ma, saboda nawa rainon Shariqah ce ta yi min. Yanzu Allah Ya juya lamuransa ni ce nake yi ma ta rainon. Daman haka aikin alkhairi yake idan ka yi abin alkhairi ko bayan ranka za ka tsince shi a gaba. Ga shi dai yadda ta yi min wahalar raino ba tare da ta yi tunanin zan biyata. Duk duniya banda yaran Shariqah babu wanda zan iya riqewa haka. Na salwantar da duk abinda nake da shi na yarda in rasa komai, na yarda in takure rayuwata in zauna waje daya dan kawai in kula da yaranta. Akan maganar auren Adamu da Dinar Allah shine shaidata na kira Dinar na zauna da ita na bata shawara akan ta nutsu ta yi tunani ta gani ko za ta iya yin wannan jahadin ta aure shi dan ta riqe yaran 'yar uwarta. Amsar da ta bani ita ce ta sa ban sake shiga maganar ba, ta ce dani ta rantse da Allah ko kwana daya ba za ta iya auren mutumin nan ba. Ta zayyano min wasu daga cikin mugayen halayensa wanda ta gani kuma wasu ta ji labarin wasu. Na ce ma ta amma ai ya ce ya tuba zai gyara halayansa, daga yanzu mace za ta sami 'yanci. Ta ce min "haba Aunty ko watanni uku baa yi ba fa da na je gidansa aka boye ni dan idan ya gan ni kora ta zai yi. Mutumin da ina matsayin kanwar matarsa uba daya amma bai san ni ba ban san shi ba, tsabar bai dauki danginta da muhimmanci ba." Na gasgata maganata, maganar kyautawa sam bai kyauta ba, amma yaya zaa yi tunda zuri'a ta hada, yara ba ba daya ba ba biyu ba har guda biyar. Ni kaina ina neman mafita ne dan ba zan iya zubar da yaran nan in tafi ba, in dai ba na sami takamaimai in da na tabbatar zaa kula da su ba ne. Idan kuwa babu dole in zauna da su, in hakura da komai nawa na rayuwa. Wannan shine ma abinda zai fiye min kwanciyar hankali tunda 90% na tabbatar bayan uwar da ta haife mu ni da Shariqah babu mai riqe yaran nan kwatankwacin uwarsu irina. Saboda haka ko da ace aurensa da Dinar ya tabbata ba zan ba ta yaran dukka ba sai dai in ba ta masu dan wayon su biyu zuwa uku kanan sai dai in riqe su. wala in zauna da su a kasar nan ko in tafi da su kasar da nake zama. Wanda na san halinsa ba zai yarda ba sai dai in an kai ruwa rana. Mu na cikin wannan hali maimakon dangina su shiga maganar a sasanta.A' a sai zuga da ake ta kai masa, gulma kala-kala, sai da aka bata a alqata da shi gaba daya. Wata rana ya zo ya same ni ya ce yana so akai masa yaran weekend su dukka har yar karamar da bata shiga makaranta ba. Na ce manyan dai su uku banda kananan ya ce su dukka yake so. Hamidah ta ji hankalinta bai kwanta ba ta ce da ni "Mama kada ki bayar da su dukka kada ya hana su fa." Na ce haba dai shima ba zai fara ba. Haka kuwa aka yi lahadi ta yi lokacin da ya kamata ya dawo da su yayi wato ranar lahadi da yamma saboda akwai makaranta ranar litinin. Wayarsa na ji ya kira ni ya tambaya ko ina gida? Na ce na fita amma ina hanya, idan yaran zai kawo su Hamidah na gida. Sai ya ce ba yaran ba ne magana ce da shi akan gado in hado musu takardun dukka gidajenta in bashi, yaransa kuma ya kwashe." Sharifah ta yi shiru saboda radadi da zugin da zuciyarta ke yi, yayin da Samha ta yi shiru ita ma zuciyarta ce ke tafasa, dan takaici da tausayin Sharifah. [3/3, 9:43 AM] Jamila Umar Tanko: 5 Samha ta ce "Sharifah na san ki a baya ki na da zafi bakya daukar raini. Yaya aka yi har mutumin nan ya sami dama yake taka ki yadda ya ke so?" Sharifah ta yi murmushi ta jingina a jikin kujera ta rufe ido kamar mai tunani har zuwa wasu 'yan lokuta sannan ta dago ta dubi Samha ta yi dariya. Ta ce " ba ke kadai ba ma ko 'yar da na haifa Hamidah ta yi min irin wannan tambayar. Samha wato na ga rayuwa, na tabbatar babu wanda ya Isa sai Allah, babu wani mai iko sai Allah. Dan Adam ba komai ba ne. Na qara yin imani, na koyi hakuri, na koyi tawakkali, ina so in gyara mu'amulata da Ubangijina, da kuma sauran jama'a. Me ya yi saura kuma a duniyata? Babu Mama, babu Baba, babu Yayana Bellocity, babu Shariqah. Na dogara ga Allah gaba daya na miqa maSa wuya, ina ganin kamar rayuwar matattu ta fi irin rayuwar da nake yi yanzu dadi. Na karkata gaba daya na fuskanci kabarina, kullum ina jiran isowar layi ya zo kaina. Samha me kika sani akan mutuwa? Me ki ka sani akan rayuwa? Me kika sani akan halayyar dan Adam? Ana ganin idanuwan iyayenki ba zaki taba gane masoyinki ba sai ranar da aka ce yau babu ran mahaifa za ki ga rashin kara da rashin kunya. Ko a sanin da kika yi min ada Samha, ba na neman fada ko kadan. Ina takatsantsan dan kada in shiga harkar wani in bata masa amma kuma bana so a shiga harkata a takura min. Idan na takura ne sai in fashe toh idan na fashe ba ta yin kyau. Ai Adamu bai kai rabin neman rigimar mijina ba amma da ya kaini karshe bai ji da dadi ba. Na kan bawa mutum dama mai yawa kafin in gaji. Ai yanzu na ke ba ki labarina da mijin Shariqah za ki ji yadda ta kaya. Sai ya tabbatar min ya kwashe yaran ba zai kawo min kuma dan rashin kunya ya kira ni yana yi min maganar gado. Bayan tun lokacin da aka yi sadakar arba'in ake ta bin kansa ya zo a zauna ya qi. Ashe shi niyyarsa babu rabon gado daman shine zai gada daga shi sai yaransa, idan ya auri Dinar sai ya dauki yaransa, ya karbe gado, sai ya yi gaba shikenan ya gama da shafinmu. Sai ya je ya ci gaba da mulkinka. Kuma daman dukka kara da bin dokar da nake yi akan kada ya kwashe yaran ne, yanzu kuma me yayi saura tunda ya kwashe? Na rikice ta inda na shiga ba ta nan nake fita ba, wani yanayi na shiga wanda ni da kaina ba yin kaina ba ne, har sai da Hamida da Dinar suka kwace wayar. Ina ganin bai taba jin maganganun da ya ji a ranar ba. Daga nan ya tabbatar ko ya sha giyar wake ba zai iya takowa ya zo gidana ba. Sai ya nemo Bello a waya. Sai ga kiran Bello ya na tambayata abinda ya faru sabanin abinda Adamu ya fada masa masa har ya shirya min wani sharri da karya karya kala kala. Daga nan fa fada ya fara a tsakanina da Adamu. Ya boye yara ba sa gidansa ba sa gidan iyayensa ya kai su ajiya. Ki duba fa ki gani wai yaran da suka rasa uwa yake yiwa wannan wulakancin alhali ga inda aka san darajar ake kaunarsa ya dauke su. Mu ka yi samame mu ka je gidansa babu yaran, wata 'yar uwata ta nemo lambar mahaifinsa saboda dattijo ne mun yi tunanin bai san rashin arzikin da dansa yake aikatawa ba. Amma sai kalamansa su ka nuna shine ma yake zuga shi akan ya kwato yaran. Tsohonsa ya yi rantsuwa su babu wanda ya isa ya riqe mu su yaransu, su ne masu alhakin rikewa. Ashe ma dai shine ya dora shi akan wannan karatun na ya sace yaran. Amsar da na bayar ita ce daga kaina kuwa za ku sauke wannan salon." Samha ta gyara zama ta ce "ikon Allah wannan wacce irin rayuwa ce? Daman ana yin haka?" Sharifah ta langwabar da kai ta ce " Wallahi Samha tunda daga ranar da aka kwashe yaran nan Shariqah ba ta sake kwanciya a labarinta ba, kuma ba ta barni na kwanta haqarqarina ba." Samha ta zazzare ido ta tambaya a gigice "Kamar yaya?" Sharifah ta sunkuyar da kai kasa kamar mai tunani, ta ce " duk in da na jefa kafata Shariqah sai ta jefa ta ta qafar. Bi na a baya kawai take take yi. Sai in juyo in tambaye ta Shariqah menene? Sai ta yi shiru ba ta magana. Babu safe, babu rana, babu dare, Sharqah na biye da ni. Sai daga baya na gane bin nan da take yi min ya na da alaqa da yaranta da aka kwashe ne fa, take so in karbo ma ta. Satin yaran nan uku cur baa san inda suke ba kuma ya qi fada. Haka itama ba ta taba yin fashin barina ba, koda yaushe ina ganinta. Ta biyo ni daga cikin gida mu ka fito kofar gida na shiga mota na zauna sai ta tsaya a bakin get, na ce ma ta ta zo mu tafi mana, sai ta tsaya ta qi ta shigo cikin motar. Ta san na gane abinda take so ta nusar da ni, wajen yaranta take so in je dan haka ba ta biyo ni ba." Kan Samha fa ya daure gaba daya, har hayaqi yake yi na rashin fahimta. Ta sosa goshi cikin in-line ta ce " Sharifah da tsaya pls me kike cewa ne akan Shariqah?" Sharifah ta yi murmushi ta ce "abinda kika ji ina fada shine dai abinda nake nufi. Ke dai ki biyo ni kawai ki ji karshen labari. Masana su ka bani shawara akan in kai shi qara wajen hukumar sulhu ta musulumci, su ne masu yin sulhu dan Allah da kuma fadar qur'ani. Da tambaya har na sami inda ofishinsu yake, na je na shigar da korafi. Nan da nan suka neme shi a waya, dakyar ya zo bayan ya gama kamun kafa da wani da ya sani a wajen. Amma maganar gaskiya kuma maganar cikin qur'ani baa canjawa. Aka ce ya dawo min da yara ni na fi cancanta na riqe su. Babbar matsalar da ta afku ita ce, a daren zaa fara kulle gari wato lock down, a lokacin Corona ne kuma a ranar zaa tashi da Azumi. Aka yi ta fama da shi akan ya dawo min da yaran dukka biyar din, saboda ana kan teburin sulhu ne ba kotu ba ce amma ya dage shi bai yarda ya kawo da su dukka ba sai dai ya dawo da kananan guda biyu. Kasancewar dare yayi zaa rufe gari aka tafi akan hakan amma bayan sati biyu zaa bude gari aka ce mu dawo. Yara biyu su na wajena, guda uku su na wajensa sai, ya fito da su daga inda ya boye su ya dawo da su gidansa. Anan ma na sake ganin Shariqah, ta ce min in zo in gani. Ina biye da ita har mu ka isa wani gida mai qofofi guda biyu. Ta bude qofar farko sai na ga haske sosai ga ranta guda biyu wadanda suke wajena kenan, su na ta bacci a cikin ni'ima. Sai ta bude qofa ta biyu sai na ga duhu na hango ragowar yaranta guda ukun da basa wajena, a cikin duhu da damuwa. Daga nan sai ta bace. Kin ga kenan ta na nuna min ga halin da wadancan suke ciki, kuma ta na so lallai-lallai su ma a dauko su kenan." Samha ta fada a bayyane " innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Sharifah wai me kike cewa ne?" Sharifah ta qura ma ta wasu jajayen idanuwanta da suka cika da kwalla ta ce "wai me kika ji ina fada ne? Abinda nake fada shine kike ji." Samha ta shafa jikinta don ta tabbatar ko tana raye. Eh tana raye tabbas dan ruhinta da gangar jikinta su na tare kawai dai ta na HIRA DA MATATTU ne. In har Sharifah mutum ce toh ba za ta dinga ganin matattu a fili haka ba, sai dai idan ita ma ta mutu din ne. Samha ta sadddakar asan ita kadai matattun nan su ka zaba suke bi suke so a dole sai ta ji labarinsu. Dan haka ya zama wajibi ta sallama ta zauna ta saurare su. Daga nan kuma ta san karshen zancen zasu tafi da ita ne kawai. Ta fara yiwa kanta addu'ar cikawa da imani, da fatan Allah Ya bawa iyalanta hakurin rashinka kawai. Amma ta fara gani kuma ta na jin abin da rayayyu ba sa ji, kuma ba sa gani. Sai kwalla ta cika ma ta ido ta fara ban kwana da rayuwa kuma. Sharifah ba ta damu ko bata ma kula da gumi da dimaucewar da Samha ta shiga ba, sai ta ci gaba da cewa "bayan sati biyu na koma hukumar sulhu aka ce bai zo ba kuma ya qi amsa kiran da ake ta yi masa a waya. Haka dai har sallah ta qarato, ana gobe sallah sai na kwashi yara biyun da suke wajena na aika masa da su. Don su yi sallah tare da 'yan uwansu, na kuma nuna masa cewar ni bani da niyyar raba shi da yaransa kuma shima bai isa ya raba ni da sauran ba. Ya cika da mamakina amma idan ya san wata ai bai san wata ba. Na shammace shi na dawo daukar guda biyun bayan sallah sai na hada guda hudu na tafi da su dan dayar ma tana ciki ne shiyasa ban hada da ita ba. Nima na kai su wani gida ajiya." Samha ta yi murmushin karfin hali ta ce "haba ni fa na san halinki kawata ba kya yafiya." Sharifah ta yi murmushi itama ta ce " bana son rigima amma ya siyo ta da kudinsa wallahi. Ya shigo gidana a gigice yana tsawa yana ihu ya na cewa in fito masa da yaransa. Ko kallo bai ishe ni ba, da shi da wata 'yar uwata suka buga.Ya ce wallahi ba zai yarda ba zai kai karata. Na ce masa bismillah. Sai na sami sammaci daga Hukumar Sulhu ta musulumci yana karata akan na je har gidansa na kwashe yara na boye. Tarihi ya maimaita kansa ashe babu dadi. Daman su ma su na nemansa ya qi zuwa, yanzu da ya ji wuya ya kawo kansa. Da ranar ta zo sai na je ana masa kira na tafi da yan uwana ya tafi da nasa. Aka fara magana irin ta sulhu, aka tabbatar masa sai an bi dangin uwa goma sha daya sannan aka ambaci mahaigiyarsa ba ma shi ba. Aka ce ya dawo da dayar ya bawa wata yar uwata ita ce babba nima in kawo yaran wajenta. Amma tun a ranar na fara gane wasu daga cikin dangina da na sami barka su na bayansa. A ranar wasu suka bayyana na gane basa tare da ni. Aka dinga kai kawo a Hukumar sulhu ta musulumci yayin da yake samun rakiyar wani wanda ba ma dan uwansa ba ne, shine aka wakilta ya tsaya masa dan kada in yi rinjaye akansa. Sunan dan zugar Idris ya dinga juya magana, sai an zo matsaya sai ya dawo baya har su ma hukumar suka gane shi, su ka tabbatar baya son ayi sulhu, dan basa shiri. Da aka tutsiye shi sai su ka gane bai san komai a addini ba ma amma yana ikirarin shima malami ne. Ashe da Adamu ya kwashe yaran gidansa aka kai su aka boye, su ka sami abin duniya, a sati ukun da yaran su ka yi a gidansa sai da aka azabtar da su da yunwa da kyara. Aka yards zaa bani yaran dukka amma dokokin da aka saka min su ne: zan tashi daga gidan da nake zaune in dawo gidan iyayenmu wanda shine gidan da na gada ni da Shariqah da Bello sannan duk karshen sati zai dinga kwasar yaran zuwa gidan sa jumaa zuwa lahadi da yamma. Ban yarda ba saboda babu tarbiyya ga yaran da suke da gida biyu. Anan dai aka daddanne ni aka in yi hakuri in yarda akan hakan dan an fi wata guda ana zarya. Na rasa dalilin da ya sa zaa tashe ni daga gidan da nake a kai ni wani gida alhali ba shi yake biya min hayar ba. Bello ya fi son hakan da wasu daga cikin dangi suka ce in yi hakuri, zaman hayar ma bai dace da ni ba daman saboda Allah ya rufa min asiri ai saukina ne. Na san halina ba zan iya zama a gidanmu ba kasancewar gini ne irin na da, komai ya kwararrabe. Na fitar da kudi mai yawa na fara gyaran saman gidan kusan komai sai da na fitar da shi na zuba na zamani. Mu ka tafi a haka, da na gama gyara na kaura can. Ya na aikowa duk karshen sati ana kai su. Amma sai ya shiga zuga su akan kada su yi min biyayya wato idan na gaji da halinsu sai dawo da su. Uba ne da hannunsa yake batawa yaransa tarbiyya innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Ya ce in sun shigo gidan kada su gaida kowa su sha kunu su wuce daki. Sannan ni bani da kirki ban tsinanawa uwarsu komai ba bana kaunarta. Ki duba ki ga wannan al'amari yana so ya wanke kansa alhali yaran sun san komai." Samha ta dafe haba ta ce " ikon Allah wannan wanne irin mutum ne kenan?" Sharifah ta ce "sai lokacin nima na gane haqiqanin halinsa na gaskiya. Dukka a dalilin haushin na qi yiwa Dinar auren dole. Ashe ma rigima baa fara ta ba sai a gaba. Ya na ta jin haushina akan nasarar da na yi akansa an bani yaran kuma babu yadda ya iya. Sai ya shiga ba su wulaqantaccen abincin da ya tabbatar ba zai ishe su ba kuma ba masu kyau ba. Dukkan abinda aka yanke masa ya ki bin doka. Ko kallonsa ban yi ba kuma ban koma na kai kararsa ba. Allah Ya dinga bude min ta wasu hanyoyi daban-daban ina ciyar da su. Bayan duk an yi haka ina zaune sai kawai na ga an kawo min sammaci daga wata kotu, anan birnin Kano mai nisan gaske daga unguwarmu wanda a ka'ida gidana da gidansa su na kusa da juna ya kamata ya kai kotun da tafi kusa da mu amma aka tafi wata unguwa da take karshen garin Kano. Sai na yi tafiyar fiye da awa guda kafin in kai. Ya na karata akan rabon gado, na rasa dalilin wannan karar, ga gado nan a hannunsa suke yana karbar kudin hayarsu. Gida daya ne mu ka yi hadaka da ita ni da Bello kuma a ciki muke zaune. Na nemi shawarar masana dan su bani shawara dan ba san kotu ba, ban taba zuwa kotu ba ko da rakiya ma. Da farko aka ce in dauki lauya nima, dan shari'ar yanzu in ba ka da lauya daman ka bar maganar samun nasara ma kawai. Sai daidaiku ne suke nasara. Na sami lauya na biya shi ya je kotu aka fara shari'a muka saurari dalilin karar. Wai ya na kara akan rzbon gado ya zayyano komai, har da wanda guda biyu ne kadai muke hadaka da ita . Sai kuma na ji an kinkimo wani gidana an saka a cikin lissafin. Gidan nan nawa da ne taba siyar ma ta sannan ta sake siyar min, cikon kudi kadai zan yi ma ta . Babu wanda bai san labarin ba har shi kansa ya san komai amma anan ya ce na ta ne. Mu ka mayar da martani akan ba haka abin yake ba. Abu kamar wasa sharia ta miqe ana ta zuwa kotu ba kakkautawa. Shi yana da kudin da yake ta biyan lauyansa ni ce yake so ya saka a wahala amma da yake Allah ba azzalumin bawanSa ba ne na dogara ga Allah. Hakan bai ishe shi ba sai su ka fara saye dukka lauyoyin da na dauka . Akwai lauyan da bai fada min ba zai yi ba sai ana gobe zaa je kotu sannan ya kira ni a waya ya ce ya janye. Yaransa su na ganin office din su ka ce sun taba zuwa da babansu. Wato ya siye su, lauyansa ke karbar lambarsu a kotu ya bi su ya siye su. Ana cikin wannan hali sai na sake jin kira daga wata kotu ta daban an kawo min sammaci, ita ma mai nisa ce sosai daga gidana. Ita kuma yana kara ta akan karbar yaransa." Samha ta dafe kirji ta ce " innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Sharifah irin rayuwar da kika shiga kenan? Amma hada zuria da irin su Adamu ya zama masifa wallahi." [3/5, 8:12 PM] Jamila Umar Tanko: 6 Sharifah ta tabe baki ta ce "mutumin da ya wulakanta matarsa tana raye kina ganin zai ji kunyar wulakanta ta ne bayan ta rasu? Ai duk abinda yayi min ba ni ya yiwa ba Shariqah ya yiwa....." Ba ta rufe bakinta ba wayarta ta dauki ruri sai ta dauko ta amsa, Fanna ce akan layi. Nan da nan sai Samha ta firgice dan a halin yanzu ta fi jin tsoron Fanna ma akan Sharifah. Sharifah ta ce "Fanna ga fim dinki ina kallo fa 'walking dead', a MBC 2 na tabbatar shi kike kallo kema ko dan na jiyo saurin?" Fanna ta ce "Ah ai ba zai wuce ni ba, ina son shi sosai." Samha ta ji kirjinta yana bugawa ta ce a ranta "me ya hada mata da son kallon fim din Matattu? In ba rami me ya kawo rami ?" Sharifah ta ci gaba da cewa "Fanna ya kike? Yaya yara? Meye kike so ki fada min rannan? Hamidah ta ce kina ta kira kin ce in kira zamu yi magana." Fanna ta fara magana, Samha ta na jiyo ta tana ta ambaton sunan Samha da Nana, sai ta tabbatar akan maganar rannan ce. Sharifah ta dago da sauri ta dubi Samha. Toh fah akwai magana kenan sai Samha ta ji hankalinta ya tashi da alama ta shiga tarkon fatalwoyi, shikenan Sharifah ta san har yanzu ban gama yarda da ita ba duk da labarin da ta ba ni. Wai ni wanne tsausayi ne ma ya kai ni yin qawance da Sharifah da Famna ne ma?" Samha ce ta fada a ranta. Sharifah ta qurawa Samha ido tana kallo yayin da take sauraron Fanna tana ta magana. "innalillahi wa inna ilaihi rajuun. Wanne tuggu kanuriyar nan take hada min ne?" Samha take karantowa a zuciyarta. Sharifah ta katse Fanna ta ce "ina tare da Samha ma yanzu haka, in kin amince zan saka ki a hand's free sai mu yi hirar tare." Fanna ta ce "ah ai na fi son haka ma daman, ina neman Samha dan ina ta kiranta a waya ma ba ta amsawa." Sharifah ta taso daga kujerar da take zaune ta zo kusa da Samha ta zauna yayin da ta bude muryar Fanna wacce take ta magana. Fanna ta ci gaba da cewa " Samha Ya kuke? Ina sauran kawayena su Nana?" Samha cikin tsoro da takura ta ce" lafiya kalau mu ke Alhamdulullah." Fanna ta ce "rannan mu na labari da ku sai kuma ku ka ajiye min waya babu sallama. Na dauka ku na neman ilimi ne akan rayuwar matattu." " Hmmm! Hmmm!!" Kawai Samha ke fadi ba tare da ta iya bada amsa ba. Fanna ta ci gaba da cewa "wai ni kam shin menene abin tsoro ne a fatalwa? Fatalwa mutum ne fa kamar ku, ya mutu ne kawai sai kuma ya tashi ya zo wajen kawayensa ko 'yan uwansa dan ayi zumunci. Har na ba ku misali da ni kaina na ce kamar ni din nan da na mutu kuma na tashi. Ko ba haka ba ne Sharifah? Kuma ke ma ai kin yi ciwo kika mutu kuma kika dawo ko?" Abinda ya daurewa Samha kai ya kara bata tsoro shine amsar da Sharifah ta bata. Sharifah ta gyada kai ta ce " Haka ne Fanna." Sai Samha ta zabura ta matsa daga kusa da Sharifah, ta ga ma dai gara ta tashi kacokan daga kusa da ita. Ta fara tunanin nemo mafaka dan dai wannan abu ya wuce tunaninta. Fanna ta ci gaba da cewa "shin ba ki bata labarin baqin karen da ya cije ki ba ne, har ya zama ajalinki ba ne?" Sharifah ta girgiza kai ta ce " ban bata wannan labarin ba dan na san kwakwalwarta ba zata taba ganewa ba Fanna. Mu kadai ne muke gane labarin juna." Samha ta fice daga falon ta isa farfajiyar gidan, sai ta fara tunanin ko ta fice ta shiga maqwabta duk da bata da gyale a jikinta, dan ba zata iya zama a kusa da ajalinta ba. Ba ta ankara ba ta ji an dafa bayanta, sai ta daka tsalle ta waiwayo a gigice. Sharifa ce dauke da mayafinta da mukullin mota da alama zata tafi. Wannan karon da Bello take magana a waya, ya na jiranta ne a gida zai fita da motar. Ba su sami damar yiwa juna magana ba, sai dai suka dagawa juna hannu, Sharifah ta fice da sauri. *** *** *** Samha ta dawo falonta ta zauna yayin da idanuwanta su ka dira akan wannan fim din me firgitarwa abin ba kyan gani, matattune hagar naman masu rai. Ta tashi da sauri ta kashe talabijin din ma gaba daya sannanta sami dan saukin hayaniyar, ta hada kai guiwoyinta biyu ta takure, ta na addu'a ta rasa abinda yake damunta. Ta na son zumuncinta da Sharifah ya dore amma ba za ta iya ci gaba da zaman zulumi irin wannan ba. Gaskiya tana ta sake bayyana duk da tana kawarwa gefe, amma abu ya ci tura. Sharifah ba mutane ba ne wasu halittu ne na daban. Maganar Fanna ce ta dinga dawowa cikin kanta da ta ta ce "shin ba ki bata labarin baqin karen da ya cije ki har ya zama ajalinki ba ne?" Sharifa kuma ta amsa da "eh haka ne ban bata labari ba." Meye hakan ke nufi?" Samha ta fara tunanin kawai ta yi irin yadda su Nana da Maryam su ka yankewa kansu shine sun hakura da kawance da Sharifah, ko da ita kadai kawarsu da ta rage a duniya. Samha ta ga hakan zai fiye ma ta alkhairi da kwanciyar hankali. Gara su yafewa juna dan duk iya yadda ta so Sharifah ta gyaru ta dawo daidai abu ya gagara, daga wannan sai a koma wancan. Samha ta sirnano da hawaye ta fada a bayyane "tunda uwata ta haife ni ban taba ganin masifa irin wannan ba." *** *** *** Bayan wssu kwanaki Aliyu ya dawo daga tafiya ya sami Samha a kwance ba ta jin dadin jikinta, Samira ta zo ta na taya ta zama. Amma a waya babu wanda ya fada ma sa cewar ba ta da lafiya wato dan kada hankalinsa ya tashi. Ya dinga fada musamman akan ba ta je asibiti an duba ta ba. Ko abinci bai zauna ya ci ba ya ce ta tashi su tafi asibiti. Sai da ya sami asibitin gyaneacology mai kyau da tsada sannan ya kai ta, aka bude file. Likita ta duba ta, ta duba abunda yake cikin cikin aka tabbatar lafiya kalau, amma an tabbatar mu su da cewa ba ta cin abinci kuma tana da damuwa da yawa da rashin bacci. Nan da nan Aliyu ya nemi da a ba ta "bed rest" Samha ba ta kaunar kalmar nan ta "Bed rest" dan daga 'bed rest' ta shiga bala'in da bata shirya ba. Ziyarar da Sharifah ta kai musu asibiti. Ta na addu'a wannan karon kada Allah Ya kawo ma ta Sharifah dubiya. Kwanakin Samha biyu a asibiti wannan karon kuwa ta mori bed rest dan ta huta sosai, ta yi bacci ta ci me kyau tana shan mai kyau. Bayan Mama babu wanda ya san tana asibiti balle 'yan dubiya su dame su. Samira ce ke zuwa gida ta taho musu abinci kala-kala ta kawo, Aliyu kuwa duk da ya zama busy amma kullum kafin ya fita aiki sai ya shigo, haka da daddare idan ya taso sai ya biyo ya duba ta kuma ya biya asibiti maqudan kudade. Ana dai cin kudi bana wasa ba amma dai ana ganin kulawa. Abin mamaki da rana misali qarfe goma sha biyu, Aliyu ya dade da tafiya, samira ta tafi gidan Samha dan ta dafa abinci, yayin da Mama kuma sun tafi yobe ita da Ana's gaisuwar mutuwa. Daman su ne kadai suka san tana asibiti,su kadai ne suke zuwa duba ta. Sai ta ji an yi sallama an murda qofa an shigo.Ta dauka ma'aikatan jinya ne wato (Nurses) amma ko su ne ai yanzun nan su ka fita. Me su ka manta, su ka dawo kuma? Wannan tunani na ta ba daidai ba ne wata mata ce ta shigo sanye da atamfa ruwan hoda da gyale shima ruwan hoda (pink color), ta na daga kai su ka hada ido da Sharifah. Yadda ka san bom ya fashe haka karar bugun zuciyar Samha ta kasance. "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" ta fada a bayane. Yayin da Sharifa ta taya ta suka karasa tare. Dan neman magana sai ta qi zama a kan kujerun da suke dakin ta zata zauna a gefen gadon kusa da Samha. Samha ta koma ta kwanta yayin da take numfashi sama-sama.Sharifah ta dauka duk a cikin ciwo ne, sai ta zabura ta riqe ta tana yi ma ta sannu. Ta dora da cewa "haba Samha kada ki dinga jefa kanki a cikin damuwa mana, alhali kina dauke da ciki na 'yan biyu ba ma guda daya ba." Samha ta sake gigicewa, ko ita kanta sai a daren jiya aka fada ma ta cewa tagwaye ne a cikinta. Ta ina Sharifah ta sani? Ita fa ba ciwo ba ne matsalarta, daman Sharifah ce matsalar. Ga matsalar da kanta ta zo har da karin wata babbar matsalar ma, ta kawo ma ta. Samha ta sirnano da hawaye ta na magana cikin sanyin murya ta ce "Sharifah! Ya kamata ki fada min gaskiya, maimakon ki bar ni ina ta wahala. Shin menene labarin karen da ya cije ki har ya zama shine ajalinki kika mutu kika dawo? Yaya ake kike sanin boyayyen al'amari? In har ke mutum ce ba za ki iya sanin ina nan ba. Waye ya sanar miki yara biyu ne a cikin cikina? Sharifah idan na mutu wallahi ke ce sila ba zan boye miki ba, ki na bani tsoro na kasa yarda da ke. Duk sanda na cirewa raina zargi akan ki sai ki aikata wani abu da kwakwalwata zata kasa dauka. Shin kin shiga wata kungiyar matsafa ne da kike iya bacewa ki ke ganin abinda baa fada miki ba?" Sharifah ta kwashe da dariya har kamar za ta shide. Samha ta sake sankarewa a kwace, ta yi saranda ta fitar da rai daga ci gaba da rayuwa. Sharifah ta jawo hannun Samha ta riqe, yayin da jikin Samha ya hau karkarwa. Sharifah ta ce "in har kowa bai yarda da ni ba, na san ke ce kadai a duniya za ki yarda da ni. Ba zan fada miki yadda na san kina nan ba amma lokaci zai fada miki, ba zan fada miki waye ya sanar da ni kina da cikin tagwaye ba amma mu na zaune za ki sani." Samha ta ce " na godewa Allah da Ya jarrabe ni da ciwo. Allah Ya bani mafita. Sharifah ta ce " za ki sauka lafiya ki haife kalau ma in sha Allah." Takaicin da ya sake addabar Samha shine har yanzu Sharifah ta kasa ganewa cewa itace ummul aba isin ciwonta. Idan ta fita daga rayuwata zata warke. Aka jima babu wanda yake magana, Samha dai ta saka hannu ta dafe goshi kamar mai ciwon kai yayin da hawaye ya yi ma ta qawanya daga ido zuwa bayan kunne. Sharifah ta tashi cimak ta linke gyalenta ta ajiye tare da jakarta a gefen kujera. Gami da cewa "an ce in zo in wuni tare da ke, in yi miki hira, in dauke miki kewa." Sai hankalin Samha ya tashi ta kalli Sharifah da gefen ido dan bata da kuzarin waiwayowa. Ta fada cikin sanyin jiki "waye ya ce ki zo ki zauna da ni? Ko dai kin zo ki tare ni ne, nima zan zama ku?" Sharifah ta ce "Mu su wa kenan? Ciwonki ai nawa ne Samha, dan haka ina nan har dare." Samha ta ce " na gode amma da kin tafi gida dan ki kula da yaran nan kanana." Sharifah ta yi dariya ta ce "Ah babu kowa a gidan sun tafi ziyara daga su har Hamidah sai gobe zasu dawo." Samha ta sake fashewa da kuka ba tare da Sharifah ta tabe dan ta juya baya tana ta salati tana fatan ta cika da imani. Wayarta ta dauko ta turawa Aliyu sako ta ce ya yafe ma ta da wuya ya dawo ya same ta da rai. Bai karanta ba sai da aka dade sannan ya kira a gigice. Tambayoyi yake ta jero ma ta ama ta kasa amsawa kasancewar Sharifah ta tsura ma ta idanuwa b ata ko qifatawa. Wa ta magana ya fada sai da Samha ta girgiza. Ya ce "saboda zaman kadaici ne ya sa na je gidan su Sharifah na fada ma ta baki da lafiya, ta zo ta taya ki zama ku wuni tunda Mama ba ta nan yau. Samira kuma in ta tafi sai an ganta dan kada a barki ke kadai babu dadi. Sannan kuma akwai wata tambaya da kika yi min akan Sharifah toh bani da amsar na san a cikin magagin bacci kika yi ta. Na tabbatar ba zai wuce labarin da Sharifah take ba ki ne, ba ku gama ba shine abin ya tsaya miki rai. Kika ce min baqin kare ne ya ciji Sharifah sai ta kwanta ciwo. Ni ba na so ki dinga saka abu a rai shiyasa nake so ta zo ta karasa baki labarin baqin karen." Haushin Aliyu ya rufe ta yayin da suka tsurawa juna ido ita da Sharifah. Duk da ma dai ta san Sharifah bata jin abinda yake cewa Samha ta kasa cewa komai. Wato Aliyu ne da hannunsa ya dauko ma ta ajalinta ya kawo ma ta. Ai shikenan zai ga karshen labarin baqin kare kuwa idan zuciyarta ta karasa fashewa, zai zo ya dauki gawa. Samha ta kashe waya ba tare da ta iya bashi amsa ba. Ya sake kira sai ta qi amsawa, da ya kira a karo na uku sai Sharifah ta dauka ta amsa Ta na dauka ta ce " Aliyu ina tare da ita kada ka damu, yau zamu sha labari da kawata. Ka ci gaba da aikinka ga ni ina kular maka da ita." Ya yi godiya ya yi ma ta sallama cikin jin dadi. "Tashi ki zauna in baki yogot ki sha, na ga ga kaji ma ga fruits. Da yake a gigice na taho ban tsaya na saya miki komai ba amma kada ki damu gobe zan kawo miki kwadon zogale, kin ji qawata." Samha ta qi tashi ta zauna, sai da Sharifah ta dame ta da magiya sannan ta tashi ta zauna. Sai ta ji tsoron da take tsananin ji na Sharifah ya ragu, tunda yanzu ta san wanda ya bawa Sharifah labarin tana asibiti da kuma tagwayen da suke cikinta. Tare suke shan kayan marmarin akan gado suke zaune, su na fuskantar juna Samha ta ga gara ma ta tsaya ta saurari labarin Sharifah akan ta mutu saboda zulumi. Samha ta kalli Sharifah da gefen ido cikin rashin fara'a ta ce " ki bani labarinki da na Fanna, Musamman yadda baqin kare ya cije ki." Sharifah ta yi murmushi ta ce "tabbas na yiwa mijinki alqawari yau zan zame miki radiyo mai jini za ki sha labari kuwa kala-kala, da na nan da na can ." " Can ina? Samha ta tambaya cikin rashin tsoro. Dan abin ya zame ma ta dole ma ta tsaya ta ji. Sharifah ta ce "duniyar rayayyu da duniyar matattu." Samha ta gyada kai ta ce " na shirya sauraro. " Ta na rufe bakinta Nana Anmad da Maryam Alqali ne suka murda kofa suka shigo hannayensu dauke da fulasan abinci. Da faraa suka shigo sai kawai aka yi ido hudu da Sharifah da Samha da su. Su Nana suka yi turus sula ja da baya su na zare idanuwa su kalli Sharifah su juya su kalli Samha. Nana ta zabura ta ce " A a ba wannan dakin muke nema ba." Sharifah ta ce "Nana nan ne mana ku shigo." Ta taso da sauri za ta tare su. Wani uban tsalle da wuntsulawa gami da zubar da fulasan hannu su su ka yi sannan su ka fafara da gudu. Sai Sharifah ta daga da fulasan daga qasa, Allah Ya sa basu bude abin ciki ya zube ba. Ta bude kofa da sauri ta leqa, babu su babu kamanninsu. Sharifah ta juyo ta kalli Samha cike da mamaki ta ce "kin san idanuwana ba sa gani sosai, kamar Nana Ahmad da Maryam na gani." Samha dan dariya har sai da ta kwanta, ta san abinda suka gani suka gudu. Samha ta fada a ranta "Su ne mana, amma nima na yi mamakin yadda ta gansu. Ban san wanda ya fada musu ba ma ina asibiti. Sharifah ba ta damu ba amma tabbas ta gane abinda ya sa suke gudu. Ta bude fulasan biyu sakwara ce a daya, dayan kuma miyar agushi ce ta sha kaji da kifi. Samha ta ce a zuba ma ta za ta ci sai Sharifah ta zubo musu tare. Samha har yanzu dariya ce take cin ta, amma sai ta dinga kunshe baki tana yi a ciki-ciki. Su na cikin cin abincin, wannan karon a kan kafet suka zauna suna ci. Kamar daga sama Sharifah ta ce "su Nana Ahmad da Maryam Alqali kenan. Manyan gari Hmmmmm. Na gane su fa tun ba yau ba." Samha ta na ta kawar da maganar dan bata so a yi amma Sharifah ta ci gaba da yi. Ta ce " basu san Sharifah ba ne ganinta kawai suke yi nesa-nesa amma nan gaba za su santa." Samha shiga gyara magana sai murmushi kawai Sharifah take yi. Sharifah ta ce "labarinmu mun tsaya a daidai in da na ce na amsa kira kotu ta biyu da ya kaini aka ce ana qarata ne akan in dawo masa da yara saboda ina da aure dan haka raino ya saraya a kaina. Ba ni da lauya ni kadai nake zirga-zurga daga wannan kotun zuwa waccan. Dukka dangina wasu 'yan mata ne guda biyu da muke uba daya su ne suke tare da ni, sauran kowa ya yi shiru har ta da Bello ya koma gefe ya zuba min ido, shi ya fi so in bar masa yaransa kawai ni kuma na ce ba zan taba bari ba. Cikar dangina da batsewarsu babu wanda ya kira Adamu ya ce masa bai kyauta ba akan wulaqancin da yake yi min ba, sai ma wasu sababbin informations da zai yaqe ni yake ta samu daga gare su. Ikon Allah kawai na tsaya ina kallo, na yi ta tunanin laifin da na taba aikatawa dangina na cancanci wannan hukuncin. Amma sai aka ce min wadaka da kudi yake yi musu, amma ban taba dauka cewa kudi zai sayi zumunci ba. Kuma ban taba sanin Adamu mai kudi ba ne dan na ga gidansa bai wadata ba ni ce ma nake yin aikinsa da bai sauke ba. Saboda a bi bayansa dan ya wulaqanta ni kudi yake ta rabo da kayan abinci da kayan dadi, har da ragunan sallah. Aka yi min wata irin Shari'a wacce ban gane ba zuwa biyu kacal mu ka yi, aka ji ta bakina sai kawai aka yanke hukunci aka ce an ba ni mako guda kacal in kwashi yara in mayar da su tsakar gidan ubansu. Lallai kuwa tunda na kima hijabi har qasa, gashi na kode na jejjeme ai dole su yi zaton bagidajiya ce. A take na bude baki a gaban kotu na ce ban yarda da wannan hukuncin ba, kuma ina neman kwafin Shariah zan daukaka kara." Wannan kalma tawa ce ta tabbatar musu da na san abinda nake yi ashe. Samha ta tafa hannu ta ce da kyau 'yar gidana na jinjina miki." Sharifah ta yi dariya ta ce "na rantse da ubangijin Musa da Haruna a lokacin na fara jin wani qarfi da rashin tsoro. Tabbas na ga mata a kotu su na ta wahala, ga rashin ilimi, ga rashin karfi, ga rashin wayewa kuma su na da gaskiya an danne musu haqqunansu amma basu da lauya basu da cikar kamalar da zasu iya tsawa su yi bayani. Abin tausayi, ya kamata idan akwai lauyoyi musamman lauyoyi mata da zasu dinga leqawa irin wadannan kotuna su na bibiya su taimakawa irin wadannan matan. Ina fitowa bakin kotu na hadu da mazigin nan da na fada miki a baya mai suna Idris, ya na murna sun yi galaba akaina. Na ce masa "ka gama murna amma ka sani babu kotun da ta isa ta raba ni da yaran nan. Ka je ka fadawa Adamu ni da shi sharia yanzu muka fara." Na fada da karfi cikin daga murya sai da kowa na cikin kotun ya waiwayo. Muryata radau har cikin kotu kowa yana ji. Bana tsoron kowa a lokacin banqi duniyar ta kife ba." Samha ta gyara zama ta ce "toh yaya aka yi kuma?" Sharifah ta ce "na shiga ofishin wani abokina lauya da yake babbar kotu wato high court a fusace na rufe shi da fada na ce ka na garin nan amma samun lauya daya da zai tsaya min ya gagara. Kai me kake yi da ba za ka tsaya min ba?" Ya ce "ni lauyan gwamnati ne ba zan iya tsaya miki ba amma ki kwantar da hankalin zan hada ki da wani lauya mai mutunci, malami ne, mai tsoron Allah shine na tabbatar idan ya ce zai yi zai yi, ba zai taba yarda su siye shi ba." Na yarda da maganarsa tunda ya ce tabbas shi mai tsoron Allah na san na gama dacewa. Ya kira shi a waya su ka yi magana sanan ya bani lambar wayarsa da addireshin ofishinsa wannan lauya shine Inuwa Ahmad. 'Yar uwata ce ma take ta kuka a lokacin, ni kuma na ce wallahi ba zan yi kuka ba, na daina bata lokacina in yi kuka akan mutumin da bai san darajar matar da ya aura da 'yayan cikinsa ba. Wallahi in raina zai salwanta a cikin yaqin nan, na yarda akan ina raye ina kallon yaran Shariqah su na wulaqanta. Dan shi ba irin uban nan da na san zai kula da yaransa ba ne, haka gidansa ba irin gidan da zaa kai yaro ba ne ya rayu, matar da bata kula da na ta yaran ba ma tayaya zata kula da yaran wata. Wacce ta tsana ma basu zauna lafiya ba. Ya na yi ne dan ya wulaqanta ni sai dai Allah bai wulaqanta ni babu mahalukin da zai iya wulaqanta ni. Ki hasko min maganar jifa irin na asiri, bana duba ba na zuwa a duba min amma Allah Ya na nuna min komai a mafarki, ka na taba ni zan ganka. Ko a suffarka ko a suffar wata dabba mai cutarwa amma a ko wanne hali ko da dakyar ne dai ina kubuta, baa samuna na. Ina da nacin addu'a da kuma tsarkakekkiyar zuciya. Ban cuci kowa ba Allah ba Zai bari a cutar da ni ba . Masu bani shawara su na bani shawara akan in bazama neman magani a wajen malamai, in tashi tsaye da addu'a akan in yi rinjaye akansa a Shari'a, bayan haka kuma kowa ya dube ni ya san ana jifana da asiri asiri a jikina Ba na kuraje amma a lokacin wasu kuraje suka feso min, ciwo kala-kala da kasala da bacin rai. Samha kin san ni nima na sanki, bin malamai da bokaye ba aikinmu ba ne. Ko da an takura ni na yarda na je to sau daya zan je kuma ba zan koma ba, sai in ga kamar na zubar da gaba daya imanina ne sai na yi sabuwar kalmar shahada. Abu daya na riqe shine in tashi cikin dare in roqi Ubangijin da Ya busa min numfashi, Ya raya ni, wanda raina ke hannuns Sa kuma idan na mutu gare Shi zan koma. Shi yake da wuta kuma yake da aljanna. Tunda kuwa na yi imani da haka na watsar da neman taimakon kowa, na daina bacci cikin dare, na dingi tashin dare ina rokonSa, Shine sarkin sardauna. Nayi imani da Shi, abu na farko sai na daina fargaba, na daina tsoron kowa. Duk wanda ya dogara ga Allah Shi kadai baya tsoron faduwa sai dai nasara a komai. Haka baya neman taimako daga wajen kowa sai Allah dan haka ya wuce wulaqanci. Baya gudun ko wani zai iya cutar da shi. Zai ji kamar duk duniya ya na daidai da kowa ko da kuwa bashi da ko Sisi ko wani mai karfi. Zai ji a ransa zai iya tunkarar kowanne irin bala'i da ake binsa da shi. Zai ji zuciyar ta washe babu haushin kowa. Baya tsoron talauci ko ya ce wani zai juya masa baya ya hana shi wani abu. Baya tantama ko kokonto akan abinda ya saka a gaba. Kawata na ga aya, na ga mu'ujuza da isa irin ta Ubangiji. Da na matso kusa da mahalaccina Allah da Shi nake magana cikin dare ke kya ce ina ganinSa a gabana tabbas Shi Yana kallona idaniyata bata ganinsa amma ruhins da zuciyata su na tare da shi 100%. Bayan na yi sallar nafilfili ina yi masa kirari da kyawawan sunayensu tsarkaka guda casa'in da tara, sai in yi tawasali da kyawawan aiyukan da na aikata daga ni sai shi, bayan na tuba kuma na yiwa masoyi salati SAW sai in yi magana da Ubangiji ke kya ce ina ganinSa, tabbas shi Ya na ganina amma zuciyata tana hasko shi. Buwayi gagara misali. Na ce "Ya ubangijin kai ka halicce ni, bani da kowa bani da komai sai kai kuma da kai kadai na dogara, kai ne ka ce mu roqe Ka, za ka amsa mana. Allah ka tsaya min da kanKa kada Ka bar ni da iyawata daidai da kiftawar ido dan ba zan iya ba." Samha ta ce : Allahu akbar! kawata na ji har tsikar jikina tana tashi. Tabbas ba kowa ya gane wannan sirrin ba. Dogara ga Allah Shi kadai babbar nasara ce." Sharifah ta ci gaba da cewa "Allah Ya nuna mu su Shine Allah kuma baYa mantawa da bawanSa a lokacin da bawa Ya tuna da mahalaccinSa, na rantse da Allah Samha mai Shari'ar farkon nan kacokan aka dauke shi daga alkalanci ba zai sake alqalanci ba ma a duniya. Shi kuma dayar kotun da ya ce zai kwace yara shine kika ganni a high court a sanadiyyarsa ne, yakardar da na cike ta kai can sama. Sannan ni da sabon lauyana mu ka fara shirye-shiryen daukaka kara. Nan fa ma su duba sharia suka dinga zaryar zuwa group-group kowa ya zo sai ya ce a bashi kwafin shari'ar Sharifah da Adamu ya gani. Daga nan ya tabbatar na maka karansa a can sama ne. Nan da nan aka dakatar da ni da lauyana daga ci gaba da yin Appeal, sai aka hada mu da wata kwanciyar lauya mai kare hakkin mata da kananan yara mai suna Bar.Aisatu. Ya ce ta shiga tsakiyarmu ta yi mana sulhu akan yaran, an fasa kwace su daga hannuna. Adamu ya sha takaici ya dinga bacin rai, sai da aka fi shekara baa gama sulhu ba. Dan an yi zama da yawa basa zuwa kuma ya daina ciyar da yaran ko kadan. Sai da ya shekara bai ga yaran da idanuwansa ba, ya daina nemansu. A wannan shekarar ni ce cinsu, ni ce shansu, suturarsu, ni ce school fees dinsu islamiyya da boko. Ni ma na rabu da shi ban neme shi akan taimakon komai ba. Ko Bello ba ya taimaka min da ko sisi haka a dangina babu wanda ya taba dauko kwayar taliya daya ya bani ya ce in ciyar da su. Amma fa ina zuwa gidajensu in ganin irin kayan alatu da Adamu yake kai musu kyaututtuka amma yaransa ya qi ciyar da su. Manufar ita ce idan na ji wuya zan mayar masa su da kaina. Amma ina? Ya manta ko su waye Sharifah da Shariqah ne? Ai yadda ba zan iya daukar Hamidah in 'yar da ita ba, ba zan taba iya daukar yaran Shariqah in zubar ba. Idan bara nake za mu yi tare mu ci abinci.Idan a titi nake kwana zamu kwana tare da su. A wannan lokacin rigimar nan hankalin Shariqah a tashe yake, kusan kullum sai ta zo min. Ina yawan ganinta wataran ta yi magana wataran ba ta yi amma tabbas ranta a bace yake, shari'ar nan da ake yi akan yaranta na damunta." Samha ta maimaita " ranta a bace yake kuma? Shariqah da kika ce." Sharifah ta yi murmushin qarfin hali ta ce "kwarai kuwa, ba za ki gane abinda nake nufi ba ne, sai nan gaba. Hmmm Samha! Sai a wannan karon ne na tabbatar Sharifah ba ta da dangi, daga sama ta fado saboda babu mutum daya daga cikin dangin uwata da na ubana da ya dauko kwayar taliya daya ko shinkafa kwano daya ya ce ki dafawa yara. Ba na so in zobe ladana amma na yiwa dangina bauta, da jikina da dukiyata. Amma sai su ka yi kamar ma basu taba sanin mu na shari'a ba saboda ya toshe bakinsu da abin duniya. Ko mun hadu babu wanda zai yi min maganar case dina da Adamu kuma ana hango shi a gidajensu ana zuwa ana fada min da duk abinda ya kai musu. Wai mutumin da bai wadata gidansa ba shine yake bin dangina ya dinke bakunansu da abin duniya, yana ta rabo kai kace dan takarar gwamna ne. Sun bani mamaki wannan abu ba zan taba mantawa da shi ba, shine na sake gasgatawa ka saki mutum ka kama Allah Shi kadai kawai saboda mutum mugun ice ne." Samha ta yi tagumi ta ce "kaina fa ya daure, innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Da ma kin tabo ni kawata sai ki ga bare ya taimake ka jininka bai taimake ba." Sharifah ta gyada kai ta ce "daman na dade da sanin haka, yawanci duk abinda na zama a rayuwa ta hanyar bare ne ba dai dangina ba. Amma na girgiza matuqa kawata, sai da aka zo babbar sallah lokacin da kowa yake yanka rago, wasu shanu wasu rakuma. Har ana gobe sallah ga ni da yara basu da aiki sai loqawa makwabta su na ganin raguna, su na dawowa da gudu su na bani labari. Mu a gidan babu ko kazar da zamu yanka kuma bani da kudi. A daidai wannan lokaci kuma mahaifinsu yana can yana raba raguna kuma ma rabon a gidajen dangina yake rabawa, kowa yayi kulas babu wanda ya fada min ko ya labari, balle ma su tare shi su ce ya kamata a a kaiwa Sharifah da yaranka." Sharifah ta yi shiru ta sunkuyar da kai kasa dan radadin da zuciyarta ke yi. Samha ta girgiza kai ta ce "an ci amanar zumunci. Wani irin zamani ya zo wai dan uwanka, jininka ne yake so ya ga ka tozarta. Yaya kika yi kuma?" Sharifah ta dago ta kalli Samha ta yi murmushi ta ce "kin manta ina da Allah? Wanda Ya rike Allah babu shi babu cewa na shiga uku. Na yi addua cikin dare na roqi Allah Ya rufa min asiri kuma Ya bani yadda zan yi Alfarmar yaran nan ya fitar da ni kunya. Na rantse da wanda Ya zabi Annabi Muhammad S.A.W Ya fifita darajarsa fiye da ta dukkannin halitta. Alert din dubu dari na tashi na gani, na wani tsohon bashin tikitin da na ce miki na biya zan koma turai in dauko kayana aka rufe ko ina saboda Corona. Kudin ya fi dubu dari uku na tambaya har na gaji dan shima an so a cinye min Allah Ya kwatar min wannan, ba dan komai ba sai dan Ya yi alqawari idan mu ka roqe Shi zai amsa mana." Samha ta yi kabbara ta riqe hannun Sharifah ta jijjiga ta ce "na baki kambun jarumta, haka na baki kambun wacce ta yi jahadi saboda zumunci. Allahu akbar duk kin shiga wannan tsanani ba dan jin dadin kanki, ba dan na 'yarki ba sai dan 'yaya 'yar uwarki saboda zumunci. Ba za ki wulaqanta ba in sha Allah. Nasara na tare da ke kawata." Sharifah ta gyada kai ta ce "na tashi da asuba na ga wannan kudi sai na yiwa Allah sujjada na yi maSa godiya banda Shi babu wanda Zai yi min haka. Bayan mun je sallar idi mun dawo gida, akwai wani bawan Allah da muke mutunci da shi tun Mamana ta na raye muka saba da shi, a Makka yake zama da. Shine ya zo da mota ya dauke mu ni da Hamidah mu ka tafi can hanyar Wudil kasuwannin kauye, lokacin raguna sun karya cikon kudi kadan na yi akan dubu farin nan na sami raguna guda biyu manya-manya. Mu ka zo muka yanka yara su na ta murna, mu ka yi layya kamar kowanne gida. Abinda ya bani mamaki har aka yi sallah aka gama bubu wanda daga cikin dangina ya aiko min da tsokar nama ko kwaya daya tal. Ashe da ban yi layya ba babu me bani nama. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun." Samha ta ce "ikon Allah. Amma na cika da mamaki. Tabbas ke din Jaruma ce dan ba kowacce mace ba ce zata iya daukar abinda kika dauka. Ke a maza ma ba kowanne namiji ba ne zai iya irin wannan tawakkalin ba. Kin rasa kowa daga cikin makusantanki, sannan kowa ya juya miki baya. Yaya sharia ta kasance? Sharifah ta yi dariya ta ce "sharia ta farko wato ta rabon gado an cire me sharia an kawo wani wannan shariar ai an ja ma ta layi sai ya bibiyi abinda aka yi a baya. Fiye da wata shida bai waiwaye mu ba ma. Ta biyu kuma da ya kai ni dan a kwace yara, ita wannan shari'a ai babu ita tunda an mayar da ita teburin sulhu, tare da wannan matar barista Aisata da na baki labari a baya, da aka ce ta yi mana sulhu. Mu na zuwa ni da lauyana shima da lauyansa amma fa sai mu yi zuwa uku su sai su ki zuwa dan ba haka suke so ba, su so suke a kwace yara a basu wanda ba zai yiwu ba kuma." Samha ta ce " sannu kawata shari'a har guda biyu, ya maka ki a kotuna daban-daban." Sharifah ta tabe baki ta ce "na fada miki waccan kotun da ya dauko gidana ya hada da na su ya ce dukka nata ne kuma an goyi da bayansa, har an saka ranar da zaa zartar da hukunci. Allah Ya yi ikonSa, kacokan aka dauke mai shariar aka kawo wani. Dan haka nasarorin da Adamu ya hango ya fara samu kacokan sun juye, kai a kasa kafafuwa a sama. Haka duk abinda ya kashe ya yi asararsu.Dangina da suka ci kudinsa babu abinda zasu iya taimakonsa da shi. Ko sun sha giyar wake dai babu wanda ya isa ya zo gabana ya zage ni balle ya fada min bakar magana akan riqon da nake yiwa 'yayan Shariqah. Tunda dai su sun manta duk wahalar da ya bawa 'yar uwarsu, a haka kuma su ke bude baki su ce su na kaunarta. Na yi addu'a Allah Ya tsare ni daga dariyar makiya da mahassada. Allah Ya rufa min asiri kada in tozarta kuma har yanzu a haka nake, babu tozarci kullum asirina a rufe yake. Hamidah da na haifa har ta gane tabbas Allah Ya na tare da ni a koda yaushe. Tun tana damuwa har ta daina idan na tashi bani da kudi sai ta shiga damuwa ta tafi makaranta jikinta a sanyaye amma wallahi tana dawowa sai ta bude wayata ta duba ko tantama babu zata ga kudi an turo min. Yanzu har abin ya zamar ma ta jiki, idan na ce bani da kudi sai kawai ta yi dariya ta ce "Mama ke 'yar baiwa ce, Allah ba ya hana ki." Samha akwai wani bashi da ya rikito min kudi ne mai yawa, cikin dare na tashi na yi sallah, na yi doguwar sujjada ina addu'a. Kawai ina idarwa sai na jawo wayata na duba. Wallahi Samha alert din dubu dari biyar na gani. Kafin ma in duba in ga daga ina kudin ya zo sai kawai na turawa wacce take bi na bashin kudi, sannan ma na bincika daga ina alert din ya zo." Su duka su ka yi kabbara a lokaci guda. Samha ta ce "dan Allah Sharifah ki bani sirrin addu'oin nan . Da gaske kike? Waye ya turo miki kudin?" Sharifah ta yi dariya ta ce "daman wasa ne ya tara mu anan? Wallahi daga CBN, kudin nan da ake rabawa na tallafin corona." Samha ta ce " kin bani satar amsa in sha Allah zan tattara lamurana waje daya in miqawa Ubangijina Allah. Wato ma mutum ya daina neman shawara ko fadawa wani matsalarka, dukka bata lokaci ne da tonar asiri.Gara kawai ka kalli gabas ka fadawa Allah." Sharifah ta ce "sosai Samha. Ga rashin lafiya dan a lokacin idan kin ganni ba za ki gane ni ba, kawai kuraje suka dinga feso min, idanuwana ciwo, wani lokaci har bana gani sosai. Idan ina tafiya sai in fara haki, har ana so a dora min ciwon zuciya. Sanda kika ganni ma me ai na ji sauki akan da. Addu'a kawai na tsaya ina ta yi, abinda na cewa Rabbil samawati shine Ya Allah zuciyata ba zata kamu da ciwo ba saboda a cike take da tsoronka da son matsayinka Annabi Muhammad S.A.W. dan haka zuciyata babu ciwo. Ya Allah kada ka kaddara zuciyar da ta cika da son Annabi ta kamu da ciwo. Ina zuwa gwaji zuciya babu ciwo Samha, alhali ada komai na alamun ciwon zuciya ya tabbata. Kai duk wanda ya ce babu Allah bai yarda da Allah ba, tabbas ya na cikin asara babba." Samha ta yi kabbara ta ce " gaskiya kin kama babbar madafa. Ina tare da ke 'yar uwa." [3/6, 5:15 PM] Jamila Umar Tanko: 7 Lokacin sallar azhar ta yi dan haka su ka katse labari, Sharifah ta shiga bandaki don dauro alwallah. Samira ce ta shigo a gigice har sai da Samha ta ji tsoro. Samira na ganin Samha sai ta yi ajiyar zuciya ta dafe kirji, har da wata kwallar farin ciki ce ta sirnano. Samha ta tambaya a gigice "lafiya? ina su Mama?" Samira ta ce " ba maganar Mama ba ne, ita yanzu ma mun yi waya sun isa lafiya. Kawayenki ne su Aunty Nana suka zo gidanki nemanki, na fada mu su ki na asibiti. Daidai lokacin na gama sakwara sai na basu su taho miki da ita dan an kira ni a BUK ance mu kai wani wani assignment da aka bamu. To ina can makaranta tare da kawayena mu na yi sai su ka hana ni sakat su na ta kira na a waya wai in kira Yaya Aliyu da 'yan uwa a je asibiti, sun baro ki kina cikin wani hali kina neman taimako. f Fatalwa ta saka ki a gaba bakya iya magana bakya iya daukar waya, kuma ba lallai ba ne ma likitocin su ganta ke kadai kike ganinta." Samha ta jawo Samira da sauri ta toshe ma ta baki ta yi magana cikin rada ta ce "yi a hankali Sharifah ce fa, tana cikin bandaki kada ta ji ki ba zata ji dadi ba. Allah Ya shirye su, su kuma. Babu wata fatalwa qawata ce kuma aminiyata." Samira ta yi tsaki ta na magana a hankali ta ce "daman Aunty Sharifah ce? su har yanzu ba zasu bar maganar fatalwar nan ba ne? Bayan an fayyace komai zance ya wuce. Wallahi sun hana ni karatu sai waya suke, Anti Nana har da kuka take yi min a waya." Samha ta ce "in ba ki gama Assignment dinki ba ki je ki gama kawai ki manta da su." Samira ta gyada kai ta ce "ba mu gama ba na Taso wallahi. Allah Ya sa ma da motarki na je da na sha wahalar neman abin hawa. Bari in koma da sauri." Ta fice da saurin, yayin da Samha ta jawo wayarta, missed calls dinsu ta gani ya fi ashirin da sakonni da na su da na Samira. Sakon Nana ne ta rubuta wai Samha ta fada musu gaskiya idan itama ta zama fatalwar ne su rabu da ita, dan sun ga alamu har akwai munafunci tunda in an yi shawarar rabuwa da Sharifah sai ta sake jajubo musu ita. Dariya ta kama ta ba mamaki ba, har sai da ta toshe baki, ta sha dariya ta gode Allah. Sannan ta ajiye wayar daidai lokacin Sharifah ta fito daga bandaki. Itama ta shiga don yin alwallah. Bayan sun idar da sallah ne Sharifah ta tambaya wacece ta shigo? Dan ta ji tana magana da wata? Samha ta yi murmushi ta ce "Samira ce ta zo ta dauki wani abu ta koma Makaranta." Ita fa Samha har yanzu a labarin Sharifah ba ta ji an sauka a in da take so a sauka ba. Alaqar Sharifah da baqin kare da ciwo da mutuwa, sannan kuma da labarin Fanna yadda ta mu. Samha dai sai tsokano labari take Sharifah tana zuqewa. Sharifah da Hamidah ne suka yi waya, Hamidah tana bata labarin cewa Mahaifinta ya kira ta a waya yana bata hakuri akan rashin kula ta da baya yi, ya san yayi kuskure zai gyara. Sannan kuma yana so ta tubure ta cewa mamarta ta dawo gidansa. Sharifah ta tabe baki ta yi murmushin karfin hali ta ce "Hmmm! Rabu da shi, idan ma mafarki yake yi to ya farka." Bayan sun kashe waya Samha ta gyara zama ta ce "watakila ya canja halinsa, ki yi hakuri mana ku koma." Wannan karon wata katuwar harara Samha ta amsa daga wajen Sharifah. Ta ce "kin san kuwa bayan rabuwata da shi aure sa nawa? Ya kai aure takwas yi, wata ma watanni uku kacal ta yi ta fita, wasu matan ma basu kai watanni ukun ba. Dan bashi da hali ko kadan. Ya zagi iyayenki,ya zage ki, ga cin mutunci, babu abinci, babu Biyan kudin haya, babu kula da yaranki, ke hatta kudin wutar lantarki in baki biya ba sai dai a yanke ba zai biya ba. Ga Hamidah nan zan iya rubuto abinda ya taba kashe ma ta tun daga ragon suna zuwa yanzu, ba ta ci dubu darinsa ba. Haba Samha ni kuma wacce irin asararriya ce da zan zauna da mai karancin addini? Wasu abubuwan ma ba zasu fadu ba saboda alfarmar aure da haihuwa. Danginsa su na kirana a ways su na roqo wai in dawo dan Auwal ba zai iya zama da kowa ba sai ni. Saboda ni kadai ce na iya yin zaman shekaru masu yawa da shi. Sun kuwa san wahalar da na sha da shi?" Samha ta bude baki ta dafa haba ta ce " wai! wai!! wai!! har abin na sa ya kai haka daman. Gaskiya wannan ba mijin zama ba ne. A haka kyakykywa da shi kamar wani gentle man." Sharifah ta ce "kyawun dan miciji ne, shiyasa nake so 'yan mata su gane su rabu da kyawun sura, su zabi hali, duk namijin da bashi da hali mai kyau kuma addini bai ratsa shi ba toh kada su sake su aure shi, koda yana zubar da naira dan za suyi nadama duniya da lahira.' Samha ta ce " gaskiya ne Allah Ya zaba miki wanda ya fi alkhairi kawata. Yanzu yaya kuke ciki da Adamu da maganar yara? Sanda mu ka zo na ga Hamidah tana kuka rannan, ta ce min an sace yaran ne. Ke kuma mu ka jiyo kina magana da Shariqah a daki. Me ya faru ne?." Sharifah ta kwashe da dariya ta ce "shine ku ka fice da gudu ko? Ai na san kun ji shine har yanzu su Nana suke ta guduna? Ba su da hankali." Samha ta ce " toh meye ya faru?" Sharifah ta ce "da aka fara zaman sulhu sai aka ce in bashi yaran ya gani saboda sun shekara bai gansu ba. Kin ga ai ba zan hana ba tunda an ce sulhu, ga lauyana ga lauyansa ga barista Aisatu ba zan kawo komai a raina ba ai ko? Kuma an yi Hutun makaranta a lokacin. Na rantse da Allah mutumin nan dan bashi da ta ido sai ya riqe yaran ya hana su, har sati biyar, ke har ya saka su ma a wata makarantar. Kamar mu na garin mahaukata inda babu doka. Ya manta a tsakiyar lauyoyi aka yi magana kuma an rubuta komai. Ya tafi ya sami lauyansa wai ya zo su je wajen Bar. Aisatu a canja magana, saboda shi ya dauka kowa ne a Nigeria ya yake karbar cin hanci. Ai kuwa ta yi masa fata-fata kuma ta tabbatar masa ya karya doka. Daman kuma lauyansa ya fada masa gaskiya babu in da zai je a goyi da bayansa, akan abin nan da ya yi. Su Shariqah ne suka shiga damuwa dan ta na zo min akai-akai, ranta a bace dan bata cika yin magana ba ma idan ta zo amma ina gane yanayinsa. Hamidah ce ma take ta kuka, shine a lokacin ku ka ji ina fadawa Shariqah gaskiya, cewa ta je ta kwanta wannan yakin na masu rai ne." Tsoro ya kama Samha gami da daurewar kai ta ce "Sharifah na kasa gane abinda kike fada idan kika ce Shariqah ta zo." Sharifah ta yi murmushi ta ce "ai na fada muku a baya, ni na gani da idanuwana mamaci yana sanin abinda yake faruwa a duniya." Samha ta ja wata doguwar ajiyar zuciya ta ce " kuma ya mutu mutuwar gaske, amma ake ganinsa?" Sharifah ta ce "ki dai mu je zuwa za ki ji komai. Ina zamana na ga an dawo da yaran, ban ce komai ba amma na fadawa lauyana duk abinda ya faru. Sai ya riqe Hamid dan yaron nan da nake yawo da shi wanda ya fi kowa sona a cikinsu, nima na fi shakuwa da shi. Sai ya riqe shi dan ya san abin zai taba min zuciya. Ya yi karya wai yaron bashi da lafiya, ashe har a makaranta ya saka shi." Samha ta ce "Adamu fa ya sami matsala, ya rasa yadda zai yi da ke ne yake wannan kame-kamen." Sharifah ta yi dariya ta ce "ya raina mata ne, bai dauki mace a komai ba sai ga shi ya takalo fada da mace ta hana shi bacci. Akwai mata ai kuma akwai mu na mata. Bayan nan aka dinga zamansulhu amma an kasa cimma matsaya. Bar.Aisatu har tausayi ta bani, tana ta kokarin yin sulhu amma abu ya ci tura. Ta na da abubuwa da yawa a gabanta, kullum a na layi a ofishinta, ga gidajen radiyo da dama su na yin hira da ita, haka take kashewa ta saurare mu amma mutumin nan ya dinga yi ma ta wasa da hankali. Bar.Aisatu ta dube ni ta yi shiru can ta ce " har misali nake yi da ke, kuma na fadawa mijina labarinki ya yi miki addua. Tunda nake sulhunta cases ban taba haduwa da wacce ta jajurce akan sai ta riqe yaran 'yar uwarta ba sai ke. Saboda idan dan wani abin duniya kike yi an zo lokacin da ko ciyar da su ma ya daina, amma baki gaji ba kullum na ki ake ci ma. Na sha ganin uwa da uba an rabu yana cewa ba zai riqe yaran ba ita ma tana cewa ba za ta riqe ba, sai mun shiga tsakani mun yi musu sulhu sai a raba yaran gida biyu kowanne a bashi. Amma ke gashi ba komai kike nema ba, a baki yaran 'yar uwarki ne kawai kike so ki riqe, tabbas na jinjina miki." Sai ta sirnano da hawa ta yi min addua." Samha ta langwabe kai ta ce "wallahi abinda nake ta tunani kenan a raina, nake cewa ko idan na mutu na bar yara nima anya Samira zata iya irin wannan jajurcewar kuwa ta riqe min yarana? Gaskiya ba kowacce 'yar uwa ba ce za ta yi maka haka bayan ka mutu ba. Allah Ya saka miki da alkhairi Sharifah, kin yi zumunci ba za ki taba wulaqanta ba kuma ba zaki yin kukan babu ba, har abada da yarda Allah." Sharifah ta ce "Amin . Allah Ya ara mana tsawon rai da lafiya da abinda lafiya za ta ci. Yara kuma Allah Ya sa masu albarka, Allah Ya raya su su zamanto sadakatul jariya ga uwarsu da mu ba ki daya. Bayan wannan tsohon alqalin da mu ka je da ke da na ce miki ya rasu daga baya, daman ai bashi kadai ba ne su ke handling case din ba, akwai wani dattijon arziki amma shi yana da zafin rai sosai. Ana gobe zamu koma zaman sulhu sai na koma wajensa na sanar ma sa maganar sulhu fa ta gagara. Daman shi bai yarda da maganar wani sulhu ba, ya fi so a daukaka kara a kawo mu su case din gabansu can babbar kotu. Ya ce babu maganar a raba hankalin yara su yi kwanaki anan su koma can gidan su yi kwanaki baya cikin tsarin raino. A daren ne na washe gari zamu koma wajen sulhu da tsakar dare ina kwance sai na ga Shariqah a kwance a kusa dani. Da qasusuwa a cikin bakinta, ta tauna ama ba ta zubar ba.Ta hada fululluka na kwanciya har guda biyar ta tokare kanta. Kin san duk wanda ya jera fulo da yawa ya kwanta ai kinga ai ba zai iya kwanciya ya yi balance ba, sai dai ace yana zaune ya tukaro kai da su.To a haka na ganta, cikin daki mai duhu-duhu da haske kadan, ga wundon dakin a bude wanwar. Ni kuma ina kwance a gefe bakina ya na ta addu'a amma ko yatsana na kasa dagawa. Ta cikin budadden wudon nan na ga mage ta shigo, ta zo daf da fuskata ta na kokarin ta yagushe ni, amma ta kasa ina ta tofa mata suratul Falak, nas, samad, hasbunallahu , da Auzubillahi minal shaidanur rajim.Tayi-tayi ta taba ni ta kasa, sai ta fita ta windo. Sai ga biri ya shigo shima haka zai taba ni ya kasa, ina ta addu'a, amma fa na sankare babu inda yake motsi a jikina sai bakina. Shima ya kasa taba ni, ya fita ta windo. Ya na fita sai kurwata ta dawo jikina. Na miqe zaune da sauri, na dinga tashin Shariqah dakyar ta farka. Na ce ta je ta zubar da qashin da yake bakinki ta, ta tashi ta je jikin windo ta tofar, na ce ta sake tofarwa da dukka sai ta zubar da su dukka. Sannan na ce ta zo ta gyara kwanciyarta ta kwanta.Ta zo ta sauke fululluka ta rage saura guda daya, irin yadda kowa yake kwanciya ta kalli gabas da bangaren dama ta kwanta. Da gari ya waye na cewa Hamidah da Bello yau sulhu zai zo karshe, Shariqah ta koma ta kwanta lafiya. Kin ga ban ma san a ranar mai duba shari'a ya je kotun yayi magana ba, a ranar zamu yi zaman sulhu a ofishin Bar.Aisatu muke zama da misalin karfe hudu aka ce, shi kuma da karfe uku ya shiga kotun. Shi kuma ya je da misalin karfe uku, lokacin ya rage saura awa daya mu fara zaman. Ya na shiga kotun ya sami kujera ya zauna, sai ya ce a bashi file din shariar Sharifah da Adamu. Ni da lauyana mu na can mu na ta jiransu a ofishin Bar. Aisatu. Daga baya itama ta karaso sai ta ke fada mana cewar su Adamu fa sun yi mata waya, wai Adamu ya ce azumi yake ba zai samu damar zuwa ba. Mu na cikin maganar ta nuna mana itama fa abubuwan gabanta take kashewa ta takura kanka sannan take iya zuwa ta zauna, amma kalli yadda suke wahalar da mu kullum. Ko bakinta bata rufe ba sai dai kawai mu ka ga Adamu da lauyansa sun shigo a gigice., bayan wayar da su ka yi su ka ce ba zasu sami damar zuwa ba. Daga dukka alamu mai sharia ne ya fafaro su ya ce lallai su zo a gama sulhun nan a yau, dan shima ya samu ya huta ina ta turo masa inspectors daban-daban ." Samha ta tsurawa Sharifah ido ta yi tagumi tana kallo Allah ne kadai ya san lissafin da zuciyarta take yi. Kanta ya daure tamau idan aka zo maganar matacce ya bayyana a duniya ana jira da shi.. Sharifah ta ci gaba da cewa "yaro bai san wuta ba sai taka, nan da na suka nutsu aka gama magana a ranar, abinda aka shekara ana jan magana. Nima ta roqe ni da in yi hakuri da wasu abubuwan ta san zan takura amma in sassauta in rabu da shi ya je dan kansa. Ya amince ya bar yaran a wajena su yi makarantar islamiyya da ta boko, amma zaa raba hutu gida biyu rabi a wajena rabi a wajensa. Sannan kuma za su dinga zuwa gidansa duk ranar juma'a su dawo gidana ranar lahadi.Daman tun farko akan wannan zuwa weekend ne da ban yarda ba ya sa ya kai ni kotu, saboda abinda nake yiwa yaran hange shine zasu rasa makarantar islamiyyarsu ta yamma a ranakun asabar da lahadi. Yanzun ma a hakan ake, yara su na asarar karatunsu an a ta wuce su. Amma kuma na yi ma sa uzuri dan bai san darajar karatun ba ne. Aka zayyano ma sa abinda zai dinga basu duk wata karshen wata n abinci, ya zauna ya na ta Jan magana ana ta musu da shi. Yara har guda biyar amma ko abincin yara biyu baya kawowa. Bayan rashin kyau da inganci na abincin amma ban damu ba, fatana Allah Ya kara min budi in kula da su, ya je dan kansa. Babu yadda ya iya da ni na fi karfinsa kuma na ci galaba akansa. Da shi da tawagarsa sun ji kunya kuma ya wahalar da kansa da dukiyarsa a banza bai sami yadda yake so ba. Alhamdulullah." Samha ta ce "tabbas kin gama magana. Harkar tsiya ce ace ka kasa ciyar da yaranka amma kana can kana burgewa a waje. Kada ya dauka ya ci banza, yaran su na kallon duk abinda yake yi ba zasu manta ba. Toh yaya maganar daya shariar da ya dauko gidanki ya ce na su ne?" Sharifah ta ce " ina zamana lauyana ya kira ni a waya ya ce ga Adamu da lauyana sun ce in zo a yi sulhu akan gidan nan nawa, ya yarda gidana ne ciko kawai zan yi ma ta. Sun yarda in basu cikon in riqe gidana. Na ce babu damuwa." Samha ta yi dariya ta ce " wato da dai ya dauka ke banza ce ya shirya miki wulaqanci. Ni kuwa ina bayin Allah nan su biyu da kika ce Babanku daya, su ne kadai suke tare da ke suke bin bayani?" Sharifah ta tabe baki ta ce "su ma ashe munafukai ne Samha. Hmmm! Har gara kowa ma da su, ashe har gara wadanda suka fito fili tun farko su ka nuna basa tare da ni. Su biyu uwarsu daya ubansu daya. Sun ga Allah Ya rufa min asiri fiye da su, a jikina suka jingine suke samu. Ba na so in tsawaita fadar abin kirkin da na yi mu su saboda dan Allah na yi zan zube ladana. Amma amfanin da na yi mu su ko Shariqah ba ta more yadda su ka more ni ba. Dayar da ba ta da aure, kacokan a gidana take zaune, ni ce komai na ta duk da tana aiki amma sai ta boye albashinta nawa kawai take ci. Kwanannan da baa dade ba, cikin dare Hamidah ta farka sai ta ji su a waya su na gulmata. Wai ashe bakin ciki su ke yi min duk tsawon wannan lokaci, musamman da na tafi turai ina samun kudi. Yanzu kuma murna suke yi na dawo ba ni da kudi ba ni da cikakkiyar lafiya, su na ta shewa fa su na cewa ta kare ma ta ai gashi nan ma bata da lafiya. Alhamdulullah. Sun godewa Allah zasu ga yadda zan yi kuwa. " "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Subhanallah. Uba daya fa kika ce. Shin me zumunci ya zama ne a wannan zamanin? Ashe wannan kiyayyar ta 'yan ubancin da ake fada da gaske ne?" Samha ta fada a gigice. Sharifah ta yi shiru zuwa wani lokaci ta ce "Addu'a nake ta yi a kwanakin kuwa, duk sanda na yi sujjada inaroqom Allah akan duk wanda baya zaune da ni da zuciya daya Allah Ya tona shi ya kuma cire shi daga cikin rayuwata. Ke kin ji gulmammaki da su ka dinga fitowa daga gidaje daban-daban? kuma wasu ma dangina ne na wajen uwa nan suke zuwa su na yin gulmar. Ashe ma sun dade su nayi tun mamarmu tana da rai suke yi mana wannan baqin cikin saboda Allah Ya rufa mana asiri. Mamana ta fi uwarsu rufin asiri, duk riqon da mu ke yi mu su shekara da shekaru ashe hassada na karkashin zuciyarsu basa kaunarka ko kadan. Gulma da kage da sharri ko bare ba zai fadi wani abin ba. Na tabbatar mu su duk na san abinda suka ce kuma na fada mu su dukka abinda aka fada min a gidajen da su ka je suka yi gulmar. Su ka dinga borin kunya, su na ta zage-zage, su ka amayo da kullutun hassadar da bakin cikin da ya dade yana addabarsu, yana ta cinsu, su ka fada da bkinsu kowa ya gane hassadar da suke yi min. Na ce kuma ta tashi ta bar min gidana ba zan kara iya zama da su ba dan za su kashe ni. Asiri ma su na yi min, wasu na gane wasu kuma ban gane ba amma ban taba nunawa na san ma su na yi ba. Samha wallahi ina sane na zuba musu ido tunda ita wacce mu ke zaune har malamin da ta je wajensa ta ce ayi min asiri ni da 'yata Hamidah ya zo ya fada min da bakinsa da azal ta ci shi, ya tona asiri ina ga kudinsa ne bata cika masa ba da ta ga aiki bai yi ba. Na ce mu su babu komai amma su ci gaba da taba ni haka asirinsu zai yi ta tonawa dan bani da hakkinsui. Akwai wadanda mu ke uba da yawansu basu da amfani a rayuwata, har almajirin gidana da me aikina da suke yi min aiki ina biyansu kudi amma wallahi sun fi yi min amfani akan su. Akwai wadanda na hada jini da su har gara ma bare dan basu taba yi min amfanin komai a rayuwata ba. Har jira ake aji wani bala'i ya same ka, su yi murna. Na san baka da ikon da za ka zabi wanda za ku fito daga ciki daya ba, da ana neman shawaraka ace ka zabi wadanda zaa hada ku, akwai 'yan uwana da yawa da zance kada a hada mu jini daya.Toh Allah ba Ya neman shawarar kowa Shi Ya san dalilin da Ya hada ku kuma ya ce a yi zumunci. Zumunci ya zama sai kana da kudi yanzu, idan baka da shi tun daga cikin gidanku za ka fara ganin wulaqanci. Shiyasa mutane mararsa tunani su ke fadawa neman yaki halal yaki haram. Toh maganar gaskiya ni ba zan fita neman haram dan a mutunta ni ba, gara a yanke zumunci da ni tunda ba na miqewa. Banda mutuwar zuciya ma ka zauna kullum.kana jiran a nemo a baka, ranar da mai baka bai bayar ba ka zage shi. Wannan wacce irin rayuwa ce haka? To kin ji karshen labarina da yadda Adamu ya yi min, da kuma dangina amma ba komai na yafe musu su dukka. Domin Allah Ya na son masu yafiya, idan ka yafe Shi ma sai Ya yafe maka. Dan mu dukka masu laifi ne, amma kada su dauka zan manta, ba zan taba mantawa da rashin adalcin da dangina suka yi min ba kowa ya koma gefe ya zuba ido a lokacin da nake tsananin bukatar kulawarsu." Samha ta kama hannun Sharifah ta riqe qam sannan ta sirnano da wani hawaye mai zafi. Ta ce "kin yi abinda Allah Ya ke so, kin zama mai yafiya kuma Allah Ya na tare da ke." Sharifah ma ta sharce hawaye ta ce "in sha Allah, ina fatan nima Allah Ya yafe min, wadanda na batawa nima su yafe min dan ba zance ni ba na batawa kowa rai ba. Amma abinda sani baa taba dan uwana a gaba in kyale wallahi sai in da karfina ya kare." Sharifah ta tashi ta tayar da sallar la'asar, sannan Samha ma ta tashi daman dukkansu da alwallarsu. Bayan sun idar da sallah sun dade su na addua, sannan su ka shafa. Samha ta kalli Sharifah ta yi murmushi ta ce "kawata yaushe kika zama malama ne? Na ji ki na ta ragargazo addua." Sharifah ta yi dariya ta ce "ai ni a ko ina nake ba na daina neman ilimi, acan kasar ma na shiga islamiyya haka anan ma na shiga ta ranar asabar da lahadi. Domin Allah Ya ce ka sanni kafin ka bauta min." Samha ta ce haka ne, da kyau kawata nima zan shiga islamiyya in sha Allah daman Aliyu yana ta fama da ni na qi mayar da hankali in shiga. idan Allah Ya sauke ni lafiya zan shiga. Ki qi ki bani labarin baqin kare dai." Sharifah ta kalle ta da gefen ido ta ce " ke wallahi kin cika naci kamar mayya. Subhanallah me kike so ki sani ne? Labarin baqin kare wannan ya faru ne tun mamana tana da rai, Hamidah tana karama. Na rantse da Allah Samha bani da makiyi ko maqiyiya a zuciyata, da zaa rutsa ni da bindiga ace sai na nuna makiyana wallahi ban san su ba dan ban kullaci kowa ba. Abinda na sani shine idan ka yi min nima zan yi maka a take, daga nan na manta. Toh amma tun ba na yarda har na fara yarda cewa ina da maqiya na boye a duniya, wadanda ba zan iya cewa gasu ba, kuma ban san dalilnsu na yi min wannan kiyayyar ba. Kamar yadda na fada miki ina da yawan yin mafarkai, za ki ga wani mafarkin tamkar bidiyo ake haska min ina ganin abinda yake faruwa a boye, ko kuma wanda yana daf da zai faruwa nan gaba. Sai na kasance mai nacin addu'a tunda na fara ganin wasu alamu a mafarkaina. Ina mafarkan kadangaru daman, da kuma karnuka, su na bi na da gudu zasu cije ni dakyar nake sha a cikin mafarkin basa damuna. Ko baa fada maka ba idan ka yi mafarki marar kyau za ka ji a jikinka ka tashi zuciyarka babu dadi. Har ya kai na fara tambayar masu ilimin fassarar mafarki aka tabbatar min kare da kandangare da miciji maqiya ne da aljanu. Ban kawo a ka ba kawai ina addu'a in kwanta. Tun ina ganin baqin kare a makabarta yana biye da ni, har rannan ya cije ni a mafarki kuma sai aka haska min kan karyar da ma ga ribbon kenan an nuna min karara mace ce ta cije ni. Wasa-wasa sai na kwanta ciwo, na kunbura suntum sai an kwantar sai an tayar. Dukka qasusuwan jikina ciwo su ke, ba dan kadan ba. Aka dinga yawo da ni gari gari asibitoci don neman magani ana ta gwaje-gwaje amma sakamako ya nuna bani da ciwon komai ko malaria babu. Likitan da ba bahaushe ba ya ce in je in nemi na gida amma na fi shi lafiya a dukka gwajin da ya yiwa kayan cikina da jinina bana dauke da kowacce irin cuta." Samha ta yi tagumi ta ce "ikon Allah Sharifah duk kika shiga wannan rayuwar amma ba ki taba fada min ba?" Sharifah ta ce "in fada miki in ce me? A lokacin mu na tare kuwa sai dai mu kan dade ba mu hadu ba. Ina kwance a national hospital Abuja mu ka tattara muka dawo Kano aka ci gaba da addu'a kawai. In takaice miki na kwanta cikin dare ciwo yana ta damuna. Radiyo a kunne sai na ji wa'azi malam ya fadi falalar karanta suratul qulhuwallahu ahad kafa dari, Karin ka yi barci. Sai na jawo carbi na karanta kafa dari na shafa sannan na roqi Allah Ya ba ni lafiya Ya yi min maganin ciwon nan. Sai na yi mafarkin Manzon Allah S.A.W ya bani ruwa na sha na shafa na rage dan kadan, sai na farka. Wallahi wallahi da na farka babu ciwo, Samha shikenan na warke har yau." Samha ta yi kabbara ta fashe da kuka ta rungume Sharifah. Ta ce " baiwar Allah Sharifah wallahi ina zaune da ke amma bana yi miki kallon mai ibada ko mai hakuri, ashe ki na da kyakykywar alaqa tsakaninki da mahaliccinki, shiyasa baa yankewa mutum hukunci kuma baa shiga tsakanin bawa da ubangijinSa" Sharifah ta yi murmushi ta ce "ba na taba bawa kowa wannan labarin dan mutane zasu dauka karya ma kake. kin kuwa san baa karya da mafarkin Annabi haramun ne. Mamana ce da wata kawata su ka dinga yadawa cewa Sharifah ta ga Manzon Allah a mafarki ya bata magani gashi ta warke. Kin san masoyanta ne sosai Mamana ta son Manzon Allah S.A.W Allah Ya sa ya cece mu baki daya. Na sha ganin irin wannan rubutun yana yawo a social media ban sani ba nawa mafarkin ne ko bayin Allah da yawa su na yin ciwo su ga Annabi Muhammad S.A.W ya basu magani ban sani ba. Amma tabbas nawa na gani kuma na warke Allah Ya kara mana son Manzon Allah S.A.W. Amma raina yana hannun Allah duk in da aka kai ga rashin kaunata da son ganin bayana idan Allah bai yarda ba dole su ganni su kyale ni." Samha ta ce "sosai kuwa haka ne. Fanna ta ce da kika yi ciwo kin mutu sai kuma dawo." Sharifah ta ce "an gama yi min kukan mutuwa tabbas, dan babu wanda zai ga jikina ya yi zaton zan rayu. Mutane kuka kawai suke yi idan suka ganni. Idan na kwanta sai in mafarkina in ganni a wata duniya dukka ko ina karnuka ne, ni na kuma duk jikina ya lauye na kasa tashi, wash mata sai su zagaye ni su na dariya. Ban sani ba aljanu ne ko matsafa ne ko kuwa mayu ne oho. Ni dai na dogara da Allah kuma Allah Ya warkar da ni ta hanya mai kyau. Idan ciwon nan daga Allah ne shikenan na ci jarabawa kuma na godewa Allah ban dorawa kowa ba kuma ba zargi kowa ba. Idan aljanu ne ko mutane su ma su je dan kansu. Yaya zasu yi da ni dan wanda ya halicci ni Ya na son ganina a raye basu da rai basu da mutuwa. Kuma in dai wani ne yayi min wannan dai ba zan taba yafewa ba, sai a lahira za mu tsaya a wajen hisabi." Samha ta ce "hakan ya nuna kin mutu sannan kika dawo kenan?" Sharifah ta harare ta ce "daman ana mutuwa a dawo? Ai rai daya ne idan ya tafi ya tafi kenan, in kin ga an mutu an dawo daman suma ne ba mutuwa ba. Toh ni ban suma ba amma an cire rai da ni. Wannan hausar Fanna ce ta yi miki sai ki yi ma ta uzuri tunda ba bahaushiya ba ce da ta ce na mutu na dawo. Amma ita a nata matsalar ta yi ciwo sai ta yi doguwar suma har an hada ta zaa kaita sai ta farfado. Wannan baya nufin ta mutu ta dawo ko ta yi fatalwa." Samha ta gyara zama ta na daukar ilimin da ba ta sani ba a baya. Ta ce "Shariqah doguwar suma ta yi kenan baa sani ba aka binne ta tunda tana dawowa duniya kuma ki yi hira fuska da fuska a bayyane." Sharifah ta yi shiru kamar mai tunani sau ta dauko wayarta tana daddannawa, ashe Bello ta kira a waya. Tambayarsa ta yi yana ina? Ya ce yana gida yana jin yunwa. Ta ce ya bari zata taho masa da abinci Samha fa jiran amsa take amma Sharifah ta qi maganar har ta fara hada kaya za ta tafi. Samha ta jawo hannunta ta zaunar ta ce " wallahi ba za ki tafi ba, sai kin bani labarin yadda kike yin "HIRA DA MATATTU ". Sharifah ta kwashe da dariya ta ce " hirata da Shariqah ta qarshe ita ce da ta kira ni a waya na hangota a zaune karkashin kasa, ni kuma ina zaune a cikin dakina anan ina duniya. Na ce Shariqah so mu ke mu ganki." Ta yi dariya ta ce "idan ku ka ganni ai guduwa za ku yi. Yanzu na zama ba irinku ba." Daga ranar ban sake ganinta ba sai lokacin da na fara ba ki wannan labarin, na ganta ta zo kofar gidana, na kamata na kai ta wani gida mai kyawun gaske da gado a wani daki mai haske. Na ce ta kwanta zan koma in kawo ma ta yaranta, sai ta ce a a kada in kawo ma ta su za ta dawo da kaita ta kwashe su amma ba yanzu ba." Sharifah ta miqe yayin da ta yafa mayafinta ta dauki jakar ta rataya. Samha ta tabbatar zata cutu in har Sharifah ta bace bata gama bata wannan amsar ba, abin zai yi ta damunta. Sai ta sake cafke mayafi Sharifah ta riqe gam ta ce "wallahi baki isa ba sai kin fada mun yadda matacce yake kira a waya daga cikin kabari har a yi hira da shi a waya." Aliyu ne ya shigo ya iske su ana kokawa, Samha ta damqe ta ita kuma ta na kokarin kufcewa Ya cika da mamaki amma sai ya ga su dukka dariya suke yi. Ya yi dariya ya ce "Lafiya kuwa? Lallai kun ci kun koshi har dambe ku ke?" Sharifah ta ce " matar nan taka yau ta karar min da dukka karfina wajen bata labarina, na gaji da magana, nace ma ta zan tafi shine wai zata hana ni." Samha ta ce " dan Allah Yah sheik ka saka sakata ba zata tafi ba sai ta bani amsa. Kai ne fa ka ce ta zo ta karasa bani labari, shine ta saka ni a rami ta qi fitar da ni, kuma idan ban ji amsar nan ba wallahi daina bacci zanyi sabo da tunani." Aliyu ya ji maganar hana bacci, sai ya danna mukulli ya datse da sauri. Ya ce " Sharifah ni ne fa na riqe ki, dan Allah ki koma ki zauna ki karasa bata labarin nan, ki ceto rayuwar 'yayanki tagwaye " Su dukka suka kwashe da dariya. Manyan ledoji cike da kayan marmari da lemuna na kwalaye hade da tsire da kaji masu yawan gaske ya ajiye a gabansu. Ya ce gashi nan ya kawo musu su yi ta ci. Yana so ya koma ofis amma ya ji dadin ganin Samha ta warware da taimakon Sharifah ya na roqomta da ta zauna har Samira ta dawo." Sharifah ta yarda ta koma ta zauna bayan Aliyu ya fita sai suka hau fada. Sharifah ta harari Samha ta ce " kin sami waje ne shine kike yi mana abinda kika ga dama dan kinga ana lallabaki." Samha ta yi ma ta gwalo ta ce "oho dai mijina ya baki amanata kuma kin karba." Samha ta bude nama jifgi ne guda ta ce Sharifah ta sa hannu su ci. Sharifah ta ce ta koshi amma a daukarwa Bello, ya na gida yana jin yunwa. Gida bi biyu Samha ta raba komai ta ba ta rabi. Samha ta kalli Sharifah ta ce " lalali ki na da zumunci da son 'yan uwa, Bello fa ba yaro ba ne amma kina ta shagwaba shi. Kuma kin ce ko shi bai taba taimakonki da taliya kwaya daya ba a lokacin da baban yara ya qi ciyar da su, amma ke har yanzu kina wahala da shi." Sharifa ta ce "haka ne amma babu komai. Haka zuciyata take bana iya hanawa. Bello ya na da kudi amma nawa yake ci kin ga ai hannun da yake sama ya fi wanda yake karba a wajen Allah.". Samha ta ce "bayan mun dauke ki fatalwa mu na gudunki sai gashi kin koma zama fes 'yar gayu, kin gyara gidanki da jikinki da yaran nan, da suturu masu kyau. Sharifah ta yi dariya ta ce "kaina na yiwa fada na cire damuwa da depression, na fara dawo da rayuwata kamar ta da dan na fuskanci kai za ka fara son kanka kafin wani ya so ka. Na dukufa da gyaran fatata da shan supplements da gyaran jiki da kunshi da turaren wuta. Na fitar da tsofaffin kayanmu na kyauta na siyo mana masu kyau. Na Samo almajirai suka yi sati su na kwashe bola da sharar tsakar gida. Ni da Bello mu ka hada kudi, dan aurensa ya kusa zai zauna a kasa. Shari'a ta kare kuma hankalina ya kwanta mutane masu guduna da masu surutu na lalace ta kare min sai daina murna, Sharifah ta tafi ta dawo." Samhabta ce " ina kika sami kudi?" Sharifah ta yi dariya ta ce "kin manta Ina da Allah?." Samha ta ce " Shine Ya ce mu tashi mu nema Zai taimake mu." Sharifah ta ce "rannan na ce miki zan yi meeting da matar gwamna, na fara samun kananan kwangiloli, ina samun 'yan kudi, wasu manyan ma sai nan gaba dan na samu an hada ni da oga kwata-kwata her excellencymun tattauna ta yi alqawura. Alhamdulullah mu na saka ran samun babban rabo. Har na bawa Bello kudin motata zai kawo min daga America, tunda harkarsa ce. Wannan motar da nake hawa ta sa ce." Samha ta ce " ina gaida ke, ga mace mai kamar maza. Allah Ya kara rufa miki asiri kawata, da mu baki daya." Sharifah ta ce " Amin." Samha ta ce " ba ki bani labarin yadda ake ganin matacce a yi hira da shi ba fa.Ranar da muka je gidanki ma kina magana da Shariqah a zahiri. Zuwa ta yi kenan?" Sharifah ta yi dariya ta ce "an kwashe yara an ki dawowa da su, na je har gidansa na iske basa nan ya boye su. Sai na dawo gida raina a bace na kwanta na yi bacci, shine na ga Shariqah a mafarki cike da damuwa. Motsin shigiwarku ne na farka shine ku ka ji ina yi ma ta wannan maganar, a mafarki na ganta na ba ta amsa a zahiri." Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce " kenan duka labarin da kika bani kika ce tana ta binki da wanda kika ce ta gyara kwanciya da maganar waya da ku ka yi, da kuma ganinki da ita na farko a bakin rijiya da magruba dukka a mafarki ne kenan?" Sharifah ta gyada kai ta ce " tabbas a mafarki nake ganin Shariqah kuma muke magana, har nake gane danuwarta " Samha ta d'ala ma ta duka a cinya ta ce " shine ki ke ta wahalar da ni da kwakwalwata? Na dauka a fili ma kike ganinta." Sharifah ta yi dariya ta ce " na yi miki haka ne dan na ga kin yarda akwai fatalwa a duniya ni kuma na san baa mutuwa a dawo " Samira ce ta shigo yayin da Sharifah ta miqe ta dauki babbar ledar, ta yi musu sallama ta tafi. Ba dan Samha ta na so ta tafi ta bar ta ba. Dan hirar ba ta ishe ta ba. Sharifah na isa gida ta ana kiran magrib, ta bawa Bello abinda ta kawo masa ta shiga ta yi sallah.Ta na idarwa, wayarta ta gani tana ta haske da alama sako ya shigo. Sako Samha ta rubuta ma ta kamar haka: "kawata ina tare da ke a dukka halinda kike ciki, ki dauke ni a matsayin 'yar uwarki jininki ina tare da ke duk halin wuya ko dadi. Ga kudi nan naira dubu dari biyu na turo miki ki yiwa yara soyayya ki kula da su. Sannan na yi miki alqawarin duk ribar da na samu a makarantata ta koyar da abinci zan dinga raba ta gida uku, Kashi daya zan dinga baki dan ki kara kula da yara. Na sami number ki da account number ki a wayarki a lokacin da kika shiga bandaki, dan na san idan na tambaye ki ba za ki bani ba. Ina yi miki addu'a Allah Ya taya ki riqe. Na gode Amiyarki Samha.Mahmud. Hawaye mai zafi gami da tausayin kanta da kanta ne ya far ma ta. Ta rantse da Allah a wannan zamanin da wuya ka sami mai sonka saboda Allah haka. Gashi dai kawata har ta fi 'yan uwanta,ta tausaya ma ta, ta yi ma ta kyautar bazata. Sharifah ta ba ta amsa da kalamai masu dadi ta nuna godiya da jin dadi. Haka ta tsaya tana kallon alert din dubu dari biyu a dunkule, abinda babu wanda ya taba yi ma ta haka a danginta bayan su na da masu kudin da zasu iya kyautar miliyan biyu ma ba tare da sun san sun yi ba yin ne ba zasu yi ba. Haka Sharifah ta ke jin saukar alert daga Samha lokaci-lokaci ba tare da ta saka rai ba, na kudi masu yawa kuma. Tabbas alkhairi baya faduwa a kasa, ta tuna sanda kudin motar zuwa makaranta da kudin handout yake gagarar Samha da Aliyu. Sharifah ce mai siya ma ta ko ta bata kudin mota ko ta dauko a motarta ta kai ta makaranta kuma ta biyo ta sauke ta idan sun tashi. Dan halak baya manta alkhairi ashe Samha ba ta manta ba itama. Allahu akbar! *** *** *** Wancan labarin ya rage tsakanin Samha da su Nana Ahmad ne, an hadu an haura an sauko an daidaita. Samha ta sha aradu duk mai daukar Sharifah fatalwa zasu bata idan Sharifah fatakwa ce itama su dauke ta fatalwa, duk daya suke sai dai su guje su, su biyu. Sharifah ba ta ce komai ba bata ma san an yi ba, sai dai ta ga Samha ta kawo su dukka gidanta, bayan sun gaisa ta ci gaba da sauraronsu, su ka gama bayani da bayar da hakuri. Ta ce ya wuce kuma ta gode. *** *** *** Kwanci tashi Allah Ya sauki Samha lafiya ta haife 'yan biyu su dukka mata, kyawawa kamar ubansu. An sha murna, abin mamaki aka saka mu su suna Sharifah da Shariqah. Da farko da aka fadawa Sharifah ba ta yarda ba, ta zaci wasa ne.Tabbas sun cika ma ta burinta da ta roqe ta a asibiti ta ce a sakawa baby sunan Shariqah, da suka zama tagwaye sai aka saka mu su har da sunanta. Sai yanzu ta sake yarda tabbas Samha aminiyar kwarai ce, haka da yardar Aliyu da ta mama. Dan Samha ta basu labarin Sharifah tas kuma ta ce dan Allah su dauke ta danginsu. Dan tana bukatar ja a jiki da soyayya da kulawa. Akwati guda Sharifah ta yiwa yaran cike da kaya har da 'yan kunnayen gwal, da alama kwangila nan mai karfi ta fara sauka. An hadu a sunan Samha da su Nana sai ga Sharifah da Fanna sun iso. Fanna ta cafke Nana gam ta riqe dan ta ga alamar tana dan jin tsoronta har yanzu. ta ce " ni ma fatalwa ce na zo mu tafi mu yi HIRA DA MATATTU a kabarina." Zo ka ga ihu a wajen Nanah, kowa ya kwashe da dariya har da kyakyatawa. Alhamdulullah! Karshe!! Madalla da alqalamin Jut. Mu hadu a sabon littafina mai suna LOKACIN DA NAKE RAYE. [3/6, 5:19 PM] Jamila Umar Tanko: Haqqin mallaka:Jamila Umar tanko Copyright: Jamila umar tanko Wannan littafi mai suna HIRa DA MATATTU na 2 na kudi ne. 300 ne kacal Zaa biya 0112240731 Gt bank Jamila umar tanko Idan an biya a turo shaidar biya ta wannan lambar: 08061225337 Na gode