*HAD'AKAR MARUBUTAN YOBE.* _2023_ _Daga marubuciya_. *Amina ma'aji (maman Khairat).* *ZAMAN TAKEWA* ```INA MAFITA``` Da sauri ta gama aikin ta agurguje saboda tanaso tawuce majalisan su, yaronta Mohammed duk kunu a bakin shi ko gyara mishi batayi ba "Mama kashi nakeji." "kaje kayi zarah ta wanke maka, in kun gama ga can abinci a kitchen Zarah ta d'iba muku yanzu zanje in dawo bazan d'adeba kunji? In Abban ku ya dawo kuce naje duba Mara lafiya ne." "Ummi yanzu yau ma fitan zakuyi? Kuje ku zauna kuta surutun da bashi da amfani ,duk namijin da ya wuce kuyi gulmanshi? Kuji tsoron Allah wallahi, malamin mu yace muddin zaka zauna a waje ba zaka fad'i alkairi ba toh kazauna a gidanka dan harshe masifa ne." "Kut! Yanzu Zarah ni kike gayawa wannan banzan maganan akan dan ina fita in rage lokaci? Toh kisani ko ubanki bai isa ya hanani fita ba ko ya takura mun , shegiya mai hali irin na ubanta! Ke wato ga y'ar islamiyya? Toh ki sani ko a ciki kike baki isa kiyimin wa'azi ba shegiya baki isa ba sai nafita,kinfi son na zauna takaicin ubanki ya kasheni wallahi wannan kuma kinyi k'adan." Ficewa Hauwa tayi tabar Zarah,Mohammed da Aliyu ta fice, tana Zuwa Maman Maimuna ce tayi magana "shegiya Hauwa wato tun d'azu nake ta gaya musu yanzun nan zamu ganki kin fitoh sai gakinan." Zama Hauwa tayi aka fara zance,wani mutum ne yazo wucewa da k'afa Hauwa tace"kai wannan mutum akwai tsayi ko ya matarshi takeyi jibgege dashi? Wannan in ya hau ruwan cikin ta ko motsi ma ba za tayi ba." "Ke dai bari kawai,mijin Maryam ne fa haka take fama dashi shi,sai iyayi bakiga ranan muna gaishe shi yaki amsawa ba dan rainin hankali,wai shi dole ga ustazi ko d'aga ido ya kallemu bayayi." "Hauwa tace "ni wa ya gaya mishi mijin wata yana gabana,bani da lokacin shi me zan samu ni wannan in dai mijina ne nashiga uku dan yadda yake dogo haka abun nashi yakeda tsayi." Aisha tace "kai Hauwa haramun ne fa ku dinga wannan, taya da auren ku za ku dinga kwatancen mijin wata gaskiya baku kyauta ba ,yanzu in matarshi ta ji kufa gashi muna mutunci,yadda kuke zagin mijin wata haka namu mazajen suma ake zagin su." Maman Maimuna tace "ni su zaga nawa mijin sankwoce dashi,sai gajarta,dan abun dai dai dani badai injishi har wuya ba kedai bari kawai." Dariya sukayi duk Wanda ya wuce a ranan sai anyi dashi,Maman Maimuna tana siyar da kayan tab'awa Hauwa tace "Maman Maimuna bani sandar ba'are na hamsin, Zarah zata kawomiki dan Allah" "Gaskiya bazan baki ba sai nayi sabo." "y'ar bura'uba ke ce matsiyaciya." Cover wayan ta tabud'e gudan dubu tad'auko "ki bani cenji kidauki kud'inki muza'a mayar talakoki banza kawai." "Oho dai bani haka" m?Maman Maimuna ta bata cenji d'ari takwas(800),a layi suka hauci ga almajirai da manyan mutane sai wucewa sukeyi a mota da kuma k'afa , basu watse ba sai kusan bayan la'asar shidin ma Hauwa tayi bak'ine daga cikin gari sunzo. "Sai anjiman ku" ta siyi cingam tana tafiya tana taunawa....✍ *Maman Khairat .*🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMAN TAKEWA* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ``Gajeren labari``` Daga marubuciya Amina ma,aji (maman khairat)📚✍ *HAD'AKAR MARUBUTAN YOBE* 2023 🅿️2️⃣ Hauwa suna zaune ne a wata anguwa da,ake kira DABO ALIYU acikin garin damaturu babban burnin jahar yobe. Daga shiganta da zarah tahad'u "ke waye yake kirana ?" inna ce tazo yanzo tund'azu tayi ,awa d'aya dazuwa abban kufa? yazo yafita ajiyar zuciya tayi a hankali tashiga parlour bakinta d'uke da sallama ,innace ta amsa samungu tayi ,tazauna "ina kwana inna " lafiya ya gantali shiru Hauwa tayi. "yanzu Hauwa abunda kikayi kenan taya za,ace mace batada aiki sai gantali meyasa kike haka yanzu kigani zarah itace ta d'aura muku girki ayya Hauwa ba,irin kune masu jefa iyalenku cikin garari ba kiji tsoron Allah wallahi yanzu akace mijin ki yadawo yafita nima naga lokacin fitarshi ina shigowa. Inna kiyi hak'uri duk ba haka bane kiyafemun dan Allah "gidan ne shiru ina fitane in rage lokaci shiyasa k'aniyar ki da rage lokaci yanzu ke ,kinfi k'arfin zama a gida sai kifita kuta gulma da cinye cinye Allah ya ganar dake wallahi duk ranan dakika kai Ibrahim bango dule yamiki kishiya. Haba inna meyakawo zancen kishiya kuma ,duk lokacin daya k'ara kaimun k'aranki zance yayi aure shine mafita kawai ,inna tatayi mata fad'a Sosai ran inna ya b'aci Sosai Bayan taraka inna tatafi dawowa gida tayi tagama abincin duk tazuba musu ,sukaci " zarah zanje in siyi kati a shagon maman maimuna "sai kindawo ummi,tun k'arfe bakwai da rabi7:30 tafita sukata hira har k'arfe tara da minti ashirin tadawo9:20 lokacin Ibrahim yadawo bai sametaba wanka yayi yasaka jallabiyar shi yazauna zarah takawo mishi abinci yaci yayi sallah isha,i . Sallama Hauwa tayi yayi kaman bai gantaba tanemi waje tazauna ,sannu da dawowa abban zarah yauwa " Hauwa ina kikaje da,daren nan ?meyasa bakida hankaline meke damun ki? zakibarmun yara sukad'ai kitafi majalisan Ku ,wallahi kinfara kaini bango aure ,zanyi kisani bazan tab'a zama dake kekad'ai ba kinajina "shikenan dan ka aureni sai in zauna inta yimaka gadi bazan fitaba sokake in zauna bak'in ciki yakasheni wallahi bazai,iyu ba kasani toh kayi auren mana akwai abunda zai dameni ne"kefa jahilace ballagaza Wanda taketare da duhun jahilci bansan bakida nutsuwa ba sai dana aureki. Nikake gayawa jahila,wallahi niba jahila bace kasani da kyau nikagayawa jahilako?eh angaya miki jahila nayi dana sanin auren ki wallahi banza Mara hankali,a ranan maganganu yagaya mata ,ko,a jikinta washe gari yana fita tana fita lokacin yaran suna d'aki. Monday Tunda Ibrahim yayi sallah bai koma bacci ba yata goge kayan makarantan yaranshi yagama ya had'a musu ruwan wanka sukayi wanka ya shiryasu har lokacin Hauwa tana bacci" ummi kitashi zamutafi meyasa sai katasheni ne? Kuje abun Ku ,mana karka k'ara tashina dule Mohammed yafice daga d'akin Ibrahim ne yashigo . "Ke Hauwa wace irin matane ke yanzu karfe takwas saura kina bacci motar yarannan haryazo zasu tafi" kai abban zarah yakake so nayi ne gaskiya,kana takuramun wallahi yaye ,abunda ta rufu dashi yayi wallahi sai kintashi ,ba,a son ranta tatashi ba "mezanyi maka? Kitashi ki kimtsa gidan nan dan Allah shikenan zanyi ,karki kuskura kifita Yau kinji yauwa matana . K'arfe tara yafice daga gidan zuciyan shi sai tsinkewa yakeyi yarasa dalili haka yaje office yazauna duk jikinshi a sanyaye yake,komeyasa haka aka ta,tambayan shi amma babu amsa ko kad'an.yana fita ko wanke wanke batayiba tafice daga gidan sai majalisa . Maman maimuna" yanzu fa muke shirin lek'aki sai gakinan munji shiru ,kubari sai dayafita nafutoh duk mazajen Su bamasu zama,a gida bane gara mijin maman maimuna shikam kullum yana gida. Aisha yadai kinyi shiru ,kibari kawai Yau duk jikina a sanyaye yake sai nakeganin kaman wani abu zaifaru "zaki farako ,Hauwa kenan nagaya miki abunda kedamu nane " kenima fa d'azu dana tashi haka naji zuciyata tsinkewa yakeyi hira sukatayi da gulman mutane dayawa har yaran suka dawo daga makaranta basu saniba Anty zarah yunwa nakeji kabari in nayi sallah sai in tafasa mana taliya muci toh toh inji aliyu alwala tayi tashiga parlour zatayi sallah ,a lokacin Mohammed yashiga kitchen ya kunna gas take wuta yataso wai zai hure wutar yakai fuskan shi kenan wuta yatashi a kitchen yakama jikin rigarshi tun yana ihu har ya kasa take wutar takama gidan ta silin takeci ,Aliyu ne yace Anty zarah inaji k'aurin wuta ka zauna kayi addu,a kai in kagama sallah bazaka dinga addu,a ba ganin wuta tayi tasama fita tayi a guje take wutar takama parlour ga badaman fita tanata kiran Mohammed Mohammed Mohammed kitchen ya k'one gaparlour a guje tayi hanyar kitchen wuta yakama kayanta sai ciwutar takeyi tanata kiran ummi ummi amma koji babu Wanda yayi haka wutar tak'onasu Mutane suntaru anata kashe wutar amma Hauwa batajiba sunata hira a majalisan su.....✍🏿 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMAN TAKEWA* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ```Gajeren labari``` Daga marubuciya Amina ma,aji (maman Khairat)📚✍ *HAD'AKAR MARUBUTAN YOBE* 2023 🅿️ 3️⃣ Mutane sai d'iban ruwa sukeyi motan kashe gobara aka kira wata matace tayi magana"ayya yaran sundawo kuwa? dannaga lokacin da,akazo d'aukan su ,wani shima yayi magana sundawo amma tun kusan k'arfe tara naga mamansu tafita nake ganin yaran ne sukadai motar kashe gobara ce tazo . Jin jiniya ne ya ankarar da su Hauwa kuyi shiru kaman jiniya nakeji "jiniya kuma? kemuda bakin mubazaki samu ,muyi shiruba,muci gaba an soya awara sunataci suna hira ,wani yaro ne yazo da gudu," maman zarah gobara gobara "a ina ?agidan ki wani tashi da sauri datayi yaron yace su zarah duk sun k'one dukansu " mekace yak'ara maimai tawa ko hijabi batà d'auka ba haka tafita hango gidanta tayi mutane sai kashe wutar sukeyi ,Hauwa sai kuka kaman mahaukaciya Wani mutum ya gigita mata mari "ballagazan uwa Wanda Allah yabaki yara bakisan yadda zaki ,kula dasuba kuka ,taketayi sosai sai rik'eta akeyi har aka kashe wutar dai dai lokacin da Ibrahim ya shigo layin dan ankirashi ,a waya yayi sauri yazo a d'ari yataho . Take da,akace yaran sun k'one yasuma a kadawo kanshi kowa banda tsinewa Hauwa bashida aiki mahaifinta ne yazo ,yayi mata duka awajen" Hauwa ban yafemiki ba dakikayi sanadiyar, rasa jikokina harguda uku bazan tab'a yafemiki ba badai gidanki baya zaunar dakeba sai gidan mutanen da karatun bai ishesu ba. Kinyiwa kanki dake kika k'one bazai tab'a damuna ba dakiyimun asarar jikoki duk mutanen gidan su Hauwa sunzo Harda inna mahaifiyarta duk sunzo ,an d'auko Mohammed a kitchen duk ya kone amma fuskan shi tafi k'onewa jikinshi babu in dazaka sa tsinke haka,a she tokane da k'ashi aka fitoh da gawarshi sai k'ashi a katara duk sun d'auko su zarah ne take numfashi kad'an k'adan aka fita dasu, Ibrahim anwuce dashi asibiti dan bashi taimakon gaggawa zarah ,itama asibiti aka wuce da,ita Hauwa duk tarikice tazama abun tausayi yara uku ,atare banda kuka babu abunda takeyi Aisha " kiyi hak'uri Hauwa haka Allah ya,aiko haka aka wuce da gawar Aliyu da Mohammed gidan su Hauwa dan a yimusu, sutura bayan antattara gawan nasu kowa daban daban aka nade gawansu k'afa daban hannu daban , aka hada awaje guda,ko ina daban daba da,wani abu bak'i aka rufesu Allah yamusu rahama yasa Aljanna ce makomarsu . Ibrahim sai da yayi awa ashirin da hudu kafun yafarka yafara ina zarah Mohammed Aliyu "bazan yafemiki ba Hauwa kincuceni kinrabani da yarana sune komai nawa Allah bazan yafemiki ba nasan sunje d'aura abunda zasuci ne .surutai yatayi sosai kaman mahaukaci dule sai anyi mishi allura yake samun bacci . Satinshi d'aya aka sallameshi kana ganin shi ,kasan baya cikin hankalin shi kullum yana asibiti wajen zarah shike kulawa da ita, watan tad'aya itama jiki yak'i dad'i kullum hannun ta yana rik'e dana Abbanta " Abba bani nasa wutan ba Mohammed shiyasa ina sallah wai zai d'aura abinci munsamu ummi batayiba"ina sallah nabarshi ,a tsakar gida, zan mutu Abba kayafemun zan mutu juya kanta tayi a she tafiyace Allah yajik'anku da rahama . A lokacin ko lura baiyiba sai cewa yake" beby zarah kinyi bacci kenan harzai gyara mata kwanciyar ashe tarasu yashiga tashin hankali gawan ,a ka d'auko akayi mata sutura ko,arba,in d'insu ba,ayi ba yasake Hauwa saki uku"yanzu nikasaka na fuskanci kowani irin hukunci ,agareka Ibrahim tundaga nan yahad'u da hawan jini kullum ba lafiya sai yana zaune yahau cewa zarah sannun ku da dawuwa dole aka kaishi asibitin mahaukata dan a gwada shi ,aga ko,akwai Marsala . Hauka tuburan yakeyi an d'aurashi akan magunguna yanata amfani da shi watanshi takwas a barno kafun yawarke k'arshe barin Damaturu yayi yakoma potiskum dan nanne garinsu d'an wata anguwa je jigawa, dan bazai iya zamaba .shekarar shi hudu ba mata kafun yayi aure Hauwa duk Wanda yafitoh neman auren ta in har a kagaya mishi sai yace yafasa tayi shekara takwas kafun wani dattijo ya aureta, shekarar su goma bata haihuba har yasaketa shima rayuwa kenan.... *A nan nakawo k'arshen labarin Hauwa darasin dake cikinta Allah yabamu ,ikon amfani dashi Tammat Tammat Tammat* Maman Khairat ce*ZAMAN TAKEWA* (Gajeren labari) Gaga marubuciya Amina ma,aji(maman Khairat)📖📚✍ *©️ HAD'AKAR MARUBUTAN JAHAR YOBE* 2023 🅿️4️⃣ *ZUWAIRA* "Zuwaira bana gayamiki Yau karkiyimun tuwo a gidan nan ba meyasa kebake jin magana?kayi hak',uri Baban sadeeq naga bamuda komai a gidan ne shiyasa na dafa tuwon bazan sakeba sai abunda kace. " kid'auke tuwan nan daganan ko,inyi jifa da kwanukan "Allah yahuci zuciyanka .karki kuskura muzauna inuwa d'aya dake nagayamiki toh Baban Sadeeq afuwan key d'in motarshi ya. d'auka yafice daga gidan bansan inda yajeba cen wajen k'arfe takwas yadawo yaje,ina kaje amsa yabata naje gunda ba tuwo sukeyi ba Alsudaniya naje *Alsudaniya* wajen da,aka tanadar dan abun cinye cinye da kayan mak'ulashi sallama yayi na amsa muda yara sunata kallo sannu da dawowa yauwa Babana Sadeeq neyayi magana fa,iza da yesmin suna zaune tashi sukayi daga parlour Zuwa nasu d'akin . Kiwuce kikawomun abunda zanzubawa su fa,iza ,ikon Allah!! nikuma da Sadeeq zanci kitchen tanufa takawo ,abunda zasuba,aciki gashi kimik'a a su fa,iza suci dan nasan ko abincin nan basuciba sai kita kashemu da ,tuwo memukayi miki ne. Tana hawaye ta,isa d'akin yaran nan " Mommy meyasa kike kukane?Babane ko !! kiyi hak'uri zaiwuce rungume yaran ta,tayi bata k'ara zuwa parlour ba tazauna harsuka gama cin abinci a damaturu suke dazama a wata anguwa dake hanyan maiduguri red bricks gaba da mega na NNPC layin da suke C138 anguwa ce dabaruwan kowa da kowa kullum a gida , suke basa fita ko,ina suna dawowa zasu zauna suyi karatu yaran ko assignment in an basu,kullum haka suke wajen shad'aya taje ta kwanta. amma bafa bacci takejiba rantane ya b'acci Yau itane Abbakar yakeyi mata haka? ,kaman ba auren soyayya sukayiba,abun yana bata mamaki,sosai. Ko b'angaren shi batajeba tayi baccin ta,a d'akinta da safe duk wani aiki tagama shi tad'auko wayarta zata shiga wani group taduba ko anturo mata sakon da,akace sai gobe tana hawa taga anrubuta maman Sadeeq gashinan tsalle tatayi saboda murna .ita kadai take,wuni in babu kowa a gidan zatayi bacci tatashi kafun tasake d'aura abinci. Har Baban Sadeeq yadawo shinkafa da miya tayi yaji ,kayan had'i sai qamshi yakeyi "Zuwaira zauna nibata abinci nakeyiba " Akwai matsala mai gidan yace yanason gidan shi yaronsa zaiyi aure k'wana kusa dan haka, kikira k'annen ki kutattare kayan ki,zamu k'aura "toh Baban Sadeeq Allah yasa hakan ne yafi zama mana Alkairi Amin . Cikin lokaci k'ankani suka gama had'a kayan ana kaiwa harsuka gama ,sunkoma *BENKALIYO*wata anguwa ce, duk a kan hanyar maidugurin yake nasune nakansu gyara kad'an ne ba,agama ba . Y'an layinsu sai shigowa sukeyi saboda asada zumunci daman gata da tsohon ciki dan tana watan haihuwarta ranan tana zaune sai gawata k'awarta Aisha " Qawata sannu da zuwa yauwa kinsha hanya "kawomun ruwa ishi nakeji sosai"kodai haihuwar ce yazo kibari kawai "nagaji da zama da Abbakar San bashida mutunci yanzu yafiye rashin mutunci ,meyafaru kedai bari zangaya miki kozaki samamin mafita komeye zanyi ,bari nakawo miki abun motsa baki ki d'an tab'a yauwa kinburge," gashi wow qawata kaman kinsan harda yunwa dan su mama tuwo sukayi nikuwa ba shiri nakeyi da tuwo a"narasa yadda ,akayi bakwason tuwo ,duk abunda Baban Sadeeq yakeyi mata duk tagaya mata"ki kwantar da hankalin ki zamuyi maganin shi kinada 5k Akwai Qwata zanje gun wani malami in karb'o miki wani abu kibashi yasha a shayi kingama duk yayuna, shisuke amfani dashi "zanyi Aisha koma meyene a zamanin nan yadda yan mata da zaurawa sukayi yawa, gara na mallakeshi na huta , Da, jaraaban shi da yamma zankawo miki sai kizuba mishi ko shayi ko ,abinci bakida matsala K'arfe shad'aya Aisha tafita daga gidan zuwaira gun malam tanufa dake anguwan bindigari tayi sa,a tasameshi " sannu malam yauwa Aisha kune tafe eh mune yagidan lafiya" daman malam nazo kataimaka ,wa Qawata wancen maganin da wasu na mallakan "bakida matsala za,a baki ko aikowa kikayi zamu baki baran tana keda kanki! Had'a mata magunguna da yawa yabata kikai mata, wannan kuma tasaka, a k'asan pillow konata konashi mungode, ko,gida bata wuceba takawo sak'on Zuwaira "Qawata harkin dawo kibari,akanki ba,abunda bazanyi ba tunda yanzu k'arfe hudu kitayani abincin kinji su biyu suka, shiga kitchen awa d'aya sungama komai sallama sukayi da Aisha sai najiki " shida saura k'waya 5:45 Baban Sadeeq yadawo yayi parking d'in motarshi yajidi ,kayan daya siyo ko sallama baiyiba yashigo" Baban Sadeeq yako sallama, bakayiba? "Zuwaira gidanki ko gidana? gidan Kane. " ke mutum yadawo baki karb'i kayan hannun shiba kikeyimun ,iyayi a dule ke mai wa,azi kitafi yobe mouse kiyi,amma nida gidana babu Wanda, ya,isa yayimun gadara,Allah huci zuciyan ka tartare kayan tayi gaba d'aya takai kitchen , abinci takawo yaci ,kafun yawuce masallaci su Sadeeq suna d'akin su ,suna wasa shekarar fa,iza 10 na yesmin takwas 8 na Sadeeq biyar5 suna son junan su,sai dai Sadeeq, irin halin mahaifin shi yagado,baya d'aukan raini k'wana uku dayin magani ,yafara aiki dan yarage masifa shiru yakeyi ,bayason hayaniya yazama kaman lusarin namiji ,Aisha,takira, "Qawata nagode gaskiya magani yafara aiki sosai ina godiya kice zank'ara bashi wani kud'in dan naji dad'in maganin bakida matsala Qawata. Kinfi haka a gareni a ranan Zuwaira tatashi da nak'uda gadan gadan asibitin maisandari sukaje sukayi sa,a Hadiza ce ke duty nadare ,awa biyu da kawota tahaihu tasamu yaron ta kekkewa dashi, shiryata ,akayi sukadawo gida y'an -uwa sai zuwa sukeyi aka cika gidan da,jama,a Ranan suna yazagayo aka sakawa yaro sunan Baban ta Mohammed shehu,ana kiranshi da fahad a,kayi hidima sosai Qawayen ta suncika d'akin gaba d'aya haka,taron suna yak'are ,tunda suka dawo anguwan yaran suka koyi rashin ji wai sai sunfita wasa tunba Sadeeq ba ga karnuka dayawa a layin haka Sadeeq zaita,wasa da kare ko,ajikinshi. Kullum charting Zuwaira tahad'u da Qawaye a wani group sai sudad'e sunata surutu ,har yaran sudawo daga makaranta basu samu komai ba dole in sundameta tatashi ta d'aura in tabar abu akan wuta sai ya k'oune zata tashi " Mommy kinga fa,iza ko takarb'e mun abuna "yesmin banace in kinganni da waya kidaina damuna ba! Kib'acemun daga nan yaronta fahad, harya yiwayo yafara rarrafe haka zaifita tsakar gida yata wasa,ita kuma tana fama da waya ahannunta .. ************akan mukubari ta d'aura ruwan wankan shi,yatafasa tazo tajuye a baho tashiga d'aki d'aukan sosan wankan shi wayarta ne yayi k'ara taduba Qawarta ne Wanda suka had'u a group sunata hira ta nanta da fahad,a waje ruwan yazubar ajikinshi ,take ya k'oune tundaga cikinshi har k'afofinshi ihu yayi ko jibatayi ba tanata hira daya k'ara na biyu kafun taji da gudu ta fice lokacin har fatan yatashi sai kuka yaketayi tarasa ,wani taimako zatayi mishi Kiran Baban shi tayi yazo " garin yaya "karkayi mun magana Mara amfani muwuce asibiti karb'an yaro akayi likitoti suka shiga dashi ciki,duk jikinshi ya sabule ko,ina har fuskan shi ruwan yatab'a wani likitane yafito " zamu rik'eshi na tsawon sati biyu muyi mishi aiki amma gabanshi kam sai a hankali dan koya girma in badai yasamu magunguna ba akwai matsala salati Baban Sadeeq yayi" Zuwaira garin yayi hakan yafaru? Kintsaya danna wayako? Gaskiya kincuceni wannan wani,irin abune"karufemun baki harkai ka,isa kayi magana,mamaki yatayi Wanda yanzu ko tsoron shi batayi dakuwa jikinta har karkarwa yakeyi,jinya sukatayi har,aka sallamesu yaro yakoma wani halitta daban ga duk tausayin shi ,sukeji .. Ko,a jikinta cigaba tayi da charting kodainawa batayiba,amma yanzu a d'aki suke da Baban Sadeeq yanason Sadeeq banda yanzu son yakoma, gun fahad,kullum sai Sadeeq yafita wasa baya dawowa da wuri sai an kira mangariba zaidawo jikinshi duk datti yana tawasa da kare sunata gudu kare yakama k'afanshi yaciza ya,kara kama gannunshi wani ihu dayayi take yagagara tafiya............✍ Maman Khairat ce🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ZAMAN TAKEWA 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 (Gajeren labari) Daga marubuciya Amina maaji(maman Khairat)📖📚✍🏿 *©️HAD'AKAR MARUBUTAN JAHAR YOBE 2023 🅿️5️⃣ Wani yaro ne ya ruga a guje maman sadeeq kare yaciji sadeeq wani sadeeq d'in aciki ?"na gidan nan ko hijabi bata d'auka ba tawuce waje ihu sadeeq yaketayi d'ayan motar tad'auka aguje tafice daga anguwan sai asibiti ihutakeyi kutai makamun kar yarona ya mutu gacen d'aya ya kwone k'arban yaron sukayi ,awa hudu, sukayi kafun suka fitoh da sauri tazo gunshi "malam nine Wanda nakawo yaro kare yacijeshi " ina mahaifin shi bayanan kikirashi yanzu yazo"taya kuka bar yaro yana wasa da kare har yacijeshi "ban saniba bansan kare yacijeshi ba ,wucewa yayi yabarta agun tana tsaye, sai hawaye duk tacika wajen da kuka. Kiran Abbakar tayi ringing d'aya ya d'auka ", mekuma yafaru da jarabarki "karene yaciji sadeeq " garin yaya kare yacijeshi? "banida amsar maganan ka sai kazo kashe wayar tayi . Minti arba,in sai gashinan " Zuwaira ,ina likitan gashinan mik'a mishi hannu yayi, suka gaisa sunana DR faisal ",taya kare yaciji yaron nan? ban saniba yanzu nazo banida labari " shikenan ga allurai guda shida duk sunada tsada ,a siyo ayi mishi dubu ,bakwai kowani d'aya ",ba matsala a siyo. gaskiya karya wuce Yau dan akwai matsala ,in yawuce yau" bari ,a rubuta maka ,Cikin asibitin ma,babu maganin duk wani babban shago yaje shiru babu ,dawowa yayi bai samuba, kira,akayi a taho da shi ,daga kano . *****K'wana akayi ba,a samuba anyi mishi wani,allura Wanda zai rage rad'adin amma shiru,kwana biyu kafun aka ,samu alluran ,akayi mishi , watan su d'aya babu wani Sauk'i sai yadinga abubuwa kaman nakare. DR faisal "yakamata a duba wannan Karen kardai mahaukaci ne dule, aka kira mafarauta suka kamashi ,aka kai Karen asibitin su gwaje gwaje ,akayi angano Karen yasamu tab'en hankali kowa yayi takaicin cizon addu,a ,akeyi Sosai amma abun sai a hankali, dole suka hak'ura sadeeq gurnani yakeyi Sosai. " Zuwaira kincuceni kin kasheni kinyi sanadiyar rasa yarana maza guda biyu kinnaka, samun su Allah ya,isa bazan yafe mikiba "nikake gayawa haka " angaya miki mezakiyi nasan charting kikeyi ,kikabar yaran nan yafice nace karkibar yaran nan sufita ,shiru wannan wace irin zaman takewa mukeyi. "Kayimun shiru ka,auroni dan kagayamun magana ko gadi kabani dazakata,yimun surutu ,d'auketa da mari yayi "Zuwaira kinyi kad'an banzama lusarin namiji dazaki juyaba ", duk abunda kikeyi ina kallon kine nazuba miki ,ido . Zanyi maganin ki banza kawai munguwa,Wanda bata d'auki aure da daraja ba, ficewa yayi daga gidan kiran Aisha tayi" Qawata akwai matsala yanzu Baban sadeeq yayimun tas "daman inaso in gayamiki wancen malamin yarasu jiya" rasuwa eh"kinsan koda rashin lafiya yakeyi magungunan shi k'aryewa yakeyi yanzu kuma yarasu"komai ya tsaya. Ikon Allah! Meye abun yi kenan ? Hak'uri zakiyi kawai kibari zansama miki wani,"kibari yanzu kare ya ciji sadeeq " zanzo in duba shi bana gari sai kindawo. Watan sadeeq biyu sai yadinga abu kaman nakare sai an rufeshi ,a d'aki kafun zai samu Sauk'i kowama yahuta . "Zuwaira daga na kalleki kaman ,in shak'eki nakeji dan haushi " yanzu ke duk abun nan dayafaru bazaki daina charting d'inba ,kiduba Cikin sadeeq yadda ya kumbura da hannun shi ya cenza kama ga yaron nan ya nakasa, hak'uri zakayi ba,a son raina hakan yafaruba "matsamun bakida amfani ,a gareni ko kad'an . Wani rana antashi da safe ,Cikin sadeeq ya kumbura yanata nishi, kafun su,isa asibiti rai yayi halinshi ,kuka Baban sadeeq yayi yanason sadeeq Sosai gaisuwa ,akeyi mishi Wanda suka San son dayake yiwa sadeeq, sai yaji yatsani anguwar gaba d'aya ma sadaka, akayi har kowa ya watse ko, kallon shi batayi tak'ara had'uwa da wasu shegun ,qawaye marasa hankali, wata uku tsakanin sadeeq fahad yarasu ,saura Yasmin da fa,iza, kullum takaici yakeyi yagaji da halin Zuwaira.....✍🏿 Maman Khairat ce🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ZAMAN TAKEWA 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 (Gajeren labari) Daga Marubuciya Amina maaji(maman Khairat)📚📖✍ *©️ HAD'AKAR MARUBUTAN JAHAR YOBE* 2023 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 🅿️6️⃣ *Zuwaira* Kullum rashin mutunci Zuwaira kemishi "nagaji da halinki banason ,in bude ,idona in kalleki ko kad'an ke munguwace " na yadda kadaina zagewa kana zagina kai meyasa baka yadda da k'addara ne ? Ban saniba bazan tab'a yadda da k'addaran ba tunda ke bakisan ,kibawa mutum hak'uri ba. "Meye hak'uri na zaibaka yanzu duk rashin mutuncin dakakeyi mun ,bai isheka ba dankaga nafara ramawa shine zaka ta ,tada jijiyan wuya kayi a banza kenan dan banida lokacin ka kokadan kaji da kyau . Fa,iza Mommy " Baba waiki zo "kice mishi bazan zoba kinji"Mommy Babane fa "shi Baban ubana ne ,inace ubanku ne", zanci miki mutunci Fa,iza kinajina ko wucewa tayi dan fad'an sak'on Mommyn nata" Baba wai bazata zoba injita shikenan barta zanfita sai kadawo . Yasmin nikuwa Mommy tanaban mamaki ,kiga yadda take walak'anta Baba "nima yana damuna zancewa Baba yayi aure kawai muma muhuta, babu ruwanmu ,da ita tunda hakane halinta gashi takashe mana sadeeq da fahad" karki k'ara fad'a k'wanan sune yak'are Allah ya jik'ansu . A k'wana, a tashi Abbakar yad'auki shawaran yaransa yafara neman, aure anyikuwa, sa,a andace yargidan babban malami ya aura ,suna zaman lafiya ko takan Zuwaira bayabi, wannan abu yana kwona ran Zuwaira yara duk sunkoma gun amarya Habiba kullum ,acen suke. Yana bacci yaji sauk'an ruwa ,a kanshi "Abbakar baka,isaba kayi kad'an kacimun mutunci kai ,asuwa "yanzu Zuwaira nikika jik'a kibiyoni har d'akina gun matana kinemi cimun mutunci " lalle yau ko, da zuciyana kike zaune ,in kuma akwai Wanda yake zugaki zanyi maganin ki,"Anty Zuwaira yazakiyi kishigomun d'aki ki jik'amun "anjik'a sai me, dan ubanki matsiyaciya banza mai kwaicen miji anyi asara. Kece babba makuwa dan ni an aureni dan so da k'auna bawai sai da, akasamu matsala ,aka aureni ba " a shema Anty Zuwaira gazawa kikayi bazanyi miki komai ba kinci darajan yaranki . Fitowa Abbakar yayi daga d'aki bayan ya sauya kaya "zoki wuce kifita nace kebada ma,ayi zaman lafiya da ke " wace irin macene ke mekike nufi zansab'a miki kifita nace Ikon Allah ! Bazan fitaba! Kaji da kyau tureta yayi yarufe k'ofa "kiyi hak'uri Habiba " bansan matanka jahila bace sai yanzu "banason kalman nan ko bakomai matata ce ,ta farko kuma auren soyayya mukayi ya Ta kyau tatamun Sosai yanzun uzuri zanyi mata, Duk masifar Zuwaira da bala,in ta yajure watarana tazuba barkwano acikin buta yayi tsarki dashi ,yata tsalle tana kallon shi ,da yafuskanci itane " Zuwaira nasake ki saki uku ki tattare komai naki kibarmun gida. Nikasaka eh ansakeki bakomai "kajira saka mako,babu ,abunda zai biyo baya sai Alkairi " ban yadda kitafimun da yara gidanku ba."wannan yaran naka masu irin halinka ,ina zanje dasu. Washe gari akazo aka d'ebe kayan Zuwaira babu ,abunda aka bari komai an d'iba ,gida yayi shiru babu masifa yara sai samun kulawa sukeyi ,a wajen Habiba. Watan Zuwaira uku ,a gida tahad'u da wasu qawaye masu zigata a dai dai ta ,tahau taje gidan ta ,ko sallama batayi ba ,fa,iza da Yasmin da Habiba suna zaune ,anata hira shigowarta suka gani ,tawatsa musu pertir , a jikinsu har fuskokin su ,kowa yahau ,ihu tafice daga gidan tahau a dai dai ta daman jiranta yakeyi . "Hajiya naga kinfitih da wuri? eh nafitoh na,ajiye sak'on ne basa gida ayya " dakinbawa makwabta karwani yashigo Habiba Kururuwa suketayi da neman taimako bakowa a gidan fuskansu tahau zogi ido yagagara bud'uwa sunsha Azaba Sosai almajiri ne yashigo yana bara yaji ihu yayi d'akin ya gansu a cikin wani, hali yayi waje da gudu"malam katai makamusu mutane a gidan nan fuskansu ta sab'ule kayi taimako dan Allah. Kafun meye mutane suncika a gidan aka cirosu ,suna fita d'akin yakama da wuta mutane sukayi, waje kafun kace meye gidan yacinye ,sukuma anyi asibiti dasu, babu Wanda, yakeda number Abbakar sai limamin anguwan . Kiranshi yayi"malam Abbakar kazo gida akwai matsala ko ,dadewa bai yiba ya,iso ganin gidanshi ,dayayi ya suma,awan shi biyu ya darfad'o "ina yarana da matana karsun kwoune nashiga uku, " basu kwouneba suna asibiti tashi yayi yanufi asibiti 'yayi mamaki dayaga fuskokin yaran duk sunkoma wani kala . Kururuwa, yakeyi akwai Wanda yayimun abun nan dule ,matsawa kusa da Habiba yayi "Abbakar nasan bazanyiba " waye yamuku haka?, Zuwaira ce "Zuwaira kuma eh ,itace gun fa,iza yayi ,itama tace Zuwaira ,duk yarikice a ranan yasmin ta rasu da Habiba ,dule ,aka kama Zuwaira akayi mata daurin rai da rai " tayi nadama Sosai nadamar da bashida amfani fa,iza ce tarage ita da Babanta sai dayayi shekara goma yayi aure shid'inma ba,a son ranshi yayiba bazaka,iya gane fa,iza ba in bakasan taba "kiyi hak'uri fa,iza haka Allah ya tsara zaki rayu ke kad'ai batare da y'an uwaba. Bazan yafewa Mommy ba " kiyafe mata Kinji mahaifiyar kice "tacuceni kuka takeyi Sosai dan takaici tanaka sata tacuceta . Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah ```a nan nakawo k'arshen labarin Zuwaira da Hauwa darasin dake cikin labarin Allah yabaku ,ikon amfani da shi Gaskiya mata mu gyara zaman auren, mu karmu biyewa sharrin shed'an dan zai kaimu ya baromu murage kishin da bashida amfani Qawaye sunataka rawan gani ,acikin zamanta kewar auren mu , yakamata mugane munje ibada ne ,ba shiririta ba mu,kula munga yadda rayuwar Zuwaira ya kasance da Hauwa Allah ya kyauta.......✍🏿 Maman Khairat ce ```