[10/05, 07:21] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA ƊAYA Tun da yamma ta yi, zuciyar Malam Hasan ta dare gida huɗu kwatankwacin kusurwar bangon Gabas, Yamma, Kudu da Arewa. Sakamakon kaɗuwa da mummunan tashin hankalin da ya baƙunci rayuwarsa da ta iyalinsa. Tafe yake jiki a saɓule tamkar kazar da aka jefa da wuƙa, haka ya ƙarasa kan layin gidansa hannuwa biyu suna dukan cinya. Hadari ne yake haɗuwa a garin, sassanyar iskar damuna mai saka annushuwa tana kaɗawa da ratsa jiki. Sai dai a ɓangaren Malam Hasan ba haka abin yake ba, domin wuyan rigarsa zuwa ƙirji, da gefen hammatarsa sun yi sharkaf da gumi. Har ya dafa langa-langar da ke tokare da ƙofar gidan nasa, sai kuma ya tsaya jim! Yana ƙura wa raunanniyar katangar gidan idanu tamkar yana son tantance kalar ƙasa da taɓon da aka gine dangar da su. "Allah Ka kawo mini mafita, Allah Ka fi ni sanin halin da nake ciki Ka hore mini kada na tozarta ba don ni ba; ba kuma don halina ba." Ya furta da wata irin raunanniyar murya, a hankali ya ɗaga ƙafarsa da ke sanye cikin matattun takalmansa da sun gama suɗewa ta ƙasa. Ya shiga cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, Rakiya ya hango zaune tana ba wa Fatihu abinci. Sai da ya ƙarasa gaban kwanon ya lura kwaɗon ƙanzo ne ta yi masa, wanda yake fari fat. Ba tare da ya samu sirkin ƙuli, magi da mai ba. Gishiri ne kawai Rakiya ta barbaɗa masa don ya ji daɗin ci a cikin bakinsa. "Sannu da zuwa Mai gida, Allah Ya sa dai an dace." Rakiya ta furta cike da damuwa, ajiyar zuciya Malam Hasan ya sauke yana sunkuyar da kai ƙasa ya ce. "Rakiya lamarin nan sai godiyar Allah, amma sisi da kika sani babu wacce na samu rance. Kowa na tambaya da irin uzurin da zai kawo mini, daga ƙarshe ma sai na lura wasu kuɗin ne ba za su ba ni ba." "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un, Ya Allah ka kawo mana ɗauki." Rakiya ta furta a sanyaye, zama Malam Hasan ya yi ya ce. "Amin Ya Rabbi." "Yanzu Malam ya za mu yi? Ka san fa Alhaji Bashari ba ya saɓa alƙawari, ba kuma ya ɗaga ƙafa. Wallahi tun da ya ce a yau sai mun bar masa gidansa, babu makawa sai ya zo ya ci mana mutumci." Rakiya ta sake maganar cikin damuwa, hannu ya zura a koɗaɗɗan aljihun da ke jikin koɗaɗɗiyar shaddarsa. Ya ciro garin kwaki da bai fi gwangwani biyu ba, sannan ya miƙa mata wani ɗan ƙullun suga ya ce. "Ga wannan jiƙa mana mu sha, kafin mu ga abin da Allah zai yi da mu." "To malam ko za ka kira shi a waya?" Shiru Malam Hasan ya yi da jin furucinta, sai ya zaro wasu 'yan canji a aljihunsa na gaba ya ce. "Wannan canjin da kika gani, wayar tawa na sayar wai ko Allah zai sa na samu rancan kuɗii na haɗa masa da su. Duka gabaɗaya ɗari takwas da hamsin na sayar da ita, tun da ta tsufa ta kwana biyu. Shi ne na sayo mana gari da suga, na ba wa Malam Idi biyan bashin da yake bi na. Yanzu kuɗin hannuna ko ɗari huɗu ba su kai ba, idan ya zo ya ji magiya da roƙon da zan yi masa shi kenan. Idan kuma bai haƙura ba, sai mu bar masa gidan." Yana gama magana aka fara kiran sallar Magriba, miƙewa ya yi ya ɗauro alwala sannan ya fita masallaci. Fatihu mai kimanin shekarae biyu ya miƙe ya dafa ta cikin gwarancinsa ya ce, "Umma a kala." Kwanon kwaɗon ƙanzon ta karɓa, ta tsiyayi garin kaɗan ta jiƙa masa sannan ta sake barbaɗa masa gishiri ta miƙa masa. Nan take ya hau ci, yana yi mata murmushi. Miƙewa ta yi ita ma ta jiƙa shi a kofi, ta yafici sugan ta zuba sannan ta fara sha a gaggauce saboda yunwa. Domin rabonta da abinci tun ɗumamen tuwon dawar da ta ci da safe. Sai da ta kammala shan garin sannan ta ɗauki buta domin ta ɗaura alwala, a daidai wannan lokacin Malam Hasan ya shiga bayan ya dawo daga masallaci. Ganinsa ya sa ta ajiye butar, ta ɗauki dogon kofin sulbarsa na shan ruwa ta juye masa ragowar garin kwakin da ya yi saura ta jiƙa masa. Karɓa ya yi ya fara cusa wa cikinsa, duk da ba wani daɗinsa yake ji ba duba da tarin damuwar da ta cunkushe kwanyarsa. Alwala Rakiya ta ɗaura sannan ta gabatar da sallar Magriba, sallamar da za ta yi daga sallah ta yi daidai da sallamar da aka fara rangaɗawa a tsakar gidan. Kuma kusan a daidai gaɓar hadarin da ke haɗuwa ya shiga bayar da walƙiya haɗe da yayyafi sama-sama. Hakan ya sa ta yi saurin fita ta ɗauki zanen goyo ta goya Fatihu, sannan ta koma daga ƙofar ɗakinta tana kallon abin da yake shirin faruwa. "Malam Hasan ya ake ciki?" Alhaji Bashari ya furta a ɗage, yana bin sa da wulaƙataccan kallo. A sanyaye Malam Hasan ya dire kofin garin da ko rabi bai sha ba ya ce, "Sannu da zuwa Alhaji..." "Riƙe sannunka, wannan ba shi ne abin da ya kawo ni ba, waɗannan kalaman idan na shiga gidana har gajiya nake da su. Ina maganarmu ta kwana? Da kuɗin ko babu?" Alhaji Bashari ya watsa masa tambayar yana ƙure shi da ido, cike da karaya da sarewa Malam Hasan ya ce. "Don girman Allah Alhaji ka yi haƙuri..." "Kai Zage, Ƙaribu da Goje ku shigo don Allah ba na son ɓata lokaci ruwa ya fara saukowa." Alhaji Bashari ya furta yana ɗaga murya, tun bai rufe baki ba matasan da ke ɗauke da siffar masu zuƙe-zuƙe suka shiga cikin gidan suna wuri-wuri da idanu. "Allah Ya taimaki mai gida, a sa kai ne?" Wanda aka kira da Zage ya furta yana cije gefen bakinsa, cikin isa Alhaji Bashari ya ce. "Ku fito masa da duk wani abu na cikin gidan nan ku dire a ƙofar gida. Ku gaggauta saboda kun ga yayyafi ya fara sauka, ba na son ya taɓa ni don mura yake saka ni." "An gama master, kai Ƙaribu sa ta sama." Goje ya furta da muryar maye yana surar tabarma da kwandon wanke-wanken da ke gefen ɗakin Rakiya. "Don Allah Alhaji ka rufa mana asiri kamar yadda Allah Ya rufa maka, don Allah ka ba ni iya yau kaɗai wallahi gobe gari yana wayewa za mu bar maka gidanka." Malam Hasan ya furta yana dafa ƙafarsa, da sauri Alhaji Bashari ya janye ƙafarsa kamar wanda kashi ya sauka a kanta. Cike da tsantsani ya ce, "Kada ka sake taɓa ni da wannan hannun naka Malam Hasan, ina fatan ka gane. Wallahi a yau babu abin da zai hana ni rufe gidan nan, zancan banza ma kenan. Mutane idan kuka samu gidan mutum kamar gadon iyayenku, dubi duk yadda kuka lalata mini gida. Ji gefen katangar nan yadda ta zube, kalli ƙofar banɗaki ita ma rawa take za ta faɗi. Ai wallahi ɗan baƙara na sake ba wa matsiyaci gida babu gaira babu dalili. Kai Ƙarubu, ku yi ku fito da kayan ɗakin mana." Alhaji Bashari ya furta cikin kumfar baki yana baza babbar rigarsa, a sanyaye Malam Hasan ya tashi. Don tun da yake a rayuwa kusan ba a taɓa gasa masa maganganun da suka ci zarafinsa kamar wannan ba. Ba tun ranar ya san Alhaji Bashari mutum ne mai wulaƙanci ba, amma bai taɓa tsammanin wulaƙancinsa ya kai haka ba. Rakiya da ke gefe goye da Fatihu ban da hawaye babu abin da take gogewa, suna nan tsaye carko-carko su Zage suka ciro yaƙunanniyar katifarta suka fita da ita. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fitar da komai na gidan, da yake dama ɗakin Rakiya ba wani kayan kirki ne da shi ba, saboda ba wasu kayan ɗaki gare ta ba. Daga katifa, tabarmu, Ghana Must go ta kayan sawarsu, labule, kwandon wanke-wanke da kujera 'yar tsugunno. Sheƙeƙe Alhaji Bashari ya dubi Malam Hasan ya ce, "Malam Hasan za ku iya fita, tun da a yanzu dai ni da kai babu kare bin damo. Kuma ba mu haɗa iri ba ballantana ka ce kana da gado a kaina." Malam Hasan da baƙincikin duniya ya mamaye shi ya dubu Rakiya ya ce, "Rakiya mu je, In Shaa Allah, ina da yaƙinin Allah ba zai tozarta mu ba." Kamar Rakiya tana jira sai kuwa ta fashe da kuka ta ce, "Abin da ka yi mana Allah Ya yi maka kai ma, In Shaa Allahu yadda ka wulaƙanta mu sai Allah Ya tozarta ka." "Dama ai tsiyar matsiyaci kenan, duk rufin asirin da na yi muku na ba ku mahalli kuke zaman haya ba ki gani. Ban da irinmu masu tausayi, waye zai ɗauki gida ya ba wa faƙirai faƙara'u alal lalurati gidan haya."Alhaji Bashari ya furta wa Rakiya. "Kada na sake jin bakinki Rakiya." Malam Hasan ya furta mata, harara ta wurga wa Alhaji Bashari sannan suka fita daga gidan. Malam Hasan yana fita Alhaji Bashari ya sa su Goje suka rufo ɗakunan guda biyu. Sannan suka fito waje ya datse ƙofar gidan da mukulli, a daidai wannan lokacin yayyafin da ake yi ya fara ƙarfi. A ɗan ruɗe murya tana rawa Rakiya ta ce. "Malam ina za mu saka kayan nan?" Damuwa ɗauke a fuskarsa ya ce, "Bari na ƙwanƙwasa gidan Malam Ado ko ya dawo." Tun ba ta yi magana ba Malam Hasan ya matsa gidan ya fara bugawa, ya ɗan jima a haka sannan aka buɗe masa. Ganin Malam Hasan ya sa shi ɗan tsuke ta ce. "Malam Hasan ne?" Malam Hasan ya gyaɗa kai ya ce, "Eh ni ne, Dama Wani taimako na zo ka yi mini." "Wallahi sisi ba ni da ita a yanzu Malam Hasan." Malam Ado ya furta yana zura hannuwa a aljihu yana kaɗawa, wani abu ne ya soki zuciyar Malam Hasan. A ransa ya raya wato shi duk wanda ya gan shi ya san neman rancan kuɗi ya zo kenan. "Ka san fa sha'anin damina dama sai godiyar Allah. Komai maleji ake yi da shi, ga kuma hidimar iyali." Kalaman Malam Ado suka dawo da shi hayyacinsa, ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Dama ba rancan kuɗi ba ne, kayana ne zan ajiye su idan babu damuwa zuwa nan da gobe ko jibi In Shaa Allah." Zuro kai Malam Ado ya yi yana bin kayan da kallo, sai ya ce. "To idan dai ba za su wuce jibin ba ai babu damuwa, ka san ni ma jibin nake son zubin kajin sallah." Malam Hasan ya saki murmushin yaƙe, don ba shi da mafita da ta wuce hakan ya ce. "In Shaa Allahu zuwa jibin ma zan kwashe su, na gode sosai." Amsa masa ya yi sannan ya wuce ya fara kwaso kayan kaɗan-kaɗan, har ya kwashe su gabaɗaya ya shiga da su wani ƙaramin ɗakin gidan Malam Ado. A gaggauce ya fito bayan ya gama kwashe kayan, ya ƙarasa wurin Rakiya ya ce. "Mu je." Murya na rawa ta ce, "Ina za mu je Malam?" Malam Hasan ya ce, "Gidan abokina Sale." Rakiya ba ta amsa ba, saboda a duk lokacin da ta buɗe ba ki hawaye ne yake shatata daga idanunta. Da ƙafa suke tafiya kasancewar suna da nisa sosai tsakaninsu da titi, sai da suka yi kusan rabin tafiyar ruwa kamar da baƙin ƙwarya ya tsuge, hakan ya sa Rakiya ta zare ɗankwalin kanta ta sake rufawa a saman hijabinta don Fatihu ya samu sauƙin dukan ruwan. 02/04/2000 Unguwar Na'ibawa, Kano. Alhaji Lawan mai goro zaune yake a ɗaya daga cikin kujerun da ke zagaye a falon, ƙatuwar television da DVD da ke kange a saman dubaidar ƙarfen ke fitar da amon hoton india mai motso na Mother India. Zaman saman kujerar ne ya gundure shi, don haka ya sauka ƙasa musamman da ya kasance lissafin kuɗi yake yi masu yawan gaske. Wayar gidan ce ta fara ƙara da ke kange a jikin bango, sai da ya ajiye kuɗin hannunsa sannan ya ɗauka. "Salamu Alaikum, Gambo dillali." Daga can ɓangaren aka amsa masa, "Wa alaikassalam, Alhaji Lawan na ji ka shiru fa, wai ko ka fasa ne mu sallama wa wani?" Cikin sauri Alhaji Lawan ya ce, "Haba Alhaji Gambo, ka san ba za a yi haka ba, yanzu haka jimillar kuɗi sun kammala. Irgasu nake yi sai na ƙaraso na kawo maka, amma ina fatan za a ba ni takardu da komai a yau?" Gambo dillali ya ce, "Takardu tun yaushe suke hannuna Alhaji, yanzu nan da yaushe za mu jira ka? Don mai gidan ɗazu ma sai da ya kira ni." "Nan da awa ɗaya In Shaa Allahu." Alhaji Lawan ya ba shi amsa sannan suka yi sallama, yana ajiye wayar Hajiya Tani ta shiga falon, zama ta yi a gefe ta zuba wa kuɗin idanu sai ta ce. "Alhaji kuɗi sun kammala kenan, ai muna nan da kai watarana sai ka ce na faɗa maka waɗannan da za ka saya sai ya fi wanda ka sayar daraja? Ka ga idan ka samu yadda kake so, har shaguna nan gaba sai ka fitar. Sayen ƙasa ai babu faɗuwa sai riba." Alhaji Lawan da yake cigaba da irga kuɗin gabansa ya ce, "Tani ta inda kike birge ni wallahi kina da dogon nazari da tunani, duk matar da za ta ba ka shawarar cigabanka ai ita ce matar zama. Wannan gonakin fa sai a yi gida da manyan shaguna biyar a ƙofar gida, kuma unguwar ba ƙaramar daraja gare ta ba. Karkarasa kuwa ai ba za ki haɗa ta da sashenmu ba, kuma duka gonakin duk girman filotai ukun miliyan ɗaya fa, don haka na sayar da gonata na haɗa don na saya watarana sai ki ji wani zancan ake ba wannan ba." Hajiya Tani ta jinjina kai ta ce, "Haka ne kam, Allah Ya sa albarka. Alhaji Lawan ya amsa da Amin, sannan ya cigaba da irga ragowar kuɗaɗen gabansa. Sai da ya kammala irga kuɗin tas, sannan ya zuba a wata ƙatuwar baƙar jakarsa. Ya dubi Hajiya Tani ya ce, "Ni zan ƙarasa 'yan dillalan, tun ɗazu na yi waya da Alhaji Nasiru shi ne wakilina. Na san ba shi da ɓata lokaci ƙila yana can." Hajiya Tani ta numfasa ta ce, "To shi kenan Alhaji, Allah Ya taimaka. Sai ka dawo." Jakar ya ɗauka ya fita gareji, ya saka a cikin mota. Sannan Fauwaz ɗansa mai shekara goma ya buɗe masa ƙofar ya fita da mota. Hausawa sabon titin 'yan dillalai da ke titin masallacin Murtala, unguwa ce da ke ɗaya daga cikin fitattun unguwanni da ke cikin ƙwaryar Kano. 'Yan dillalai, wani keɓantacce wuri ne da ke kan sabon titin. Wanda mafi yawa dillalai ne da ke hada-hada a wurin, wasunsu suna da wata sana'ar bayan ta dillanci. Yayin da wasu kuma suke zaune ba sa cas ko as, sai wannan dillancin kawai suka dogara da shi. Da yawansu ba samari ba ne, masu iyali ne wasu ma dattijai ne waɗanda suka ga jiya da yau a harkar dillanci. Gambo dillali ɗaya ne daga cikin manyan dillalan da ke rayuwa a wannan wurin, kusan su biyar suka yi haɗakar kama shagon da suke zama. Sai dai mafi yawa sun fi zama a bakin shagon, saboda bishiyoyin darbejiya da ke rufe da wurin don haka ƙofar shagon ta fi cikin shagon sanyi. Harabar 'yan dillalai tana da girma babu laifi, domin a kan gudanar da kasuwamci kala-kala. Akwai masu sayar da abinci, masu fura, kanikawa, shagon teloli, masu gashin balangu, masu gyaran inji da mashina da dai sauransu. Amma rinjayar da dillalai suka yi ya sa ake kiran wurin da 'yan dillalai. Daga masu zama a kan tabarmin harabar, wasu daga ciki ba su da aiki sai caca da bushe-bushen sigari, yayin da wasu daga ciki ko ƙamshinta ba sa son ji. Iya abin da ya kawo su shi suka saka a gaba, daga cikin dillalan da ke hada-hada akwai na gari masu yi domin Allah. Akwai kuma waɗanda suke cuta, ko su yi kaka-gida a kan fili, gona, kamfani, ko gida idan har ba a ba su abin da suka yanka na la'adarsu ba. Lokacin da Alhaji Lawan ya ƙarasa 'yan dillalai a can ya tarar da amininsa Alhaji Nasiru, ba su ɗauki lokaci mai tsayi ba suka shiga motar Alhaji Lawan suka ɗunguma zuwa unguwar Karkasara. Kasancewar a lokacin unguwar ba ta cika ba, ya sa take shiru sai ɗaiɗaikun manyan gidajen masu hannu da ƙunbar susa. Wasu katafaren gonaki ne, wanda yake farkon layin. Daga gabansa da bayansa fili ne fetal, an yi masa alama da an riga an saya ba na sayarwa ba ne. Gambo dillali shi ya sake dinga nuna masa gonakin, yana sake kwaɗaita masa darajar unguwar. Har yake fasalta masa zai iya gidan bene sama da ƙasa, mai ɗauke da kusan ɗakuna goma, har a samu babban garejin da zai iya ɗaukar mota biyu, Alhaji Lawan sai murmushi yake yi cike da annushuwa da farincikin a wannan ranar zai mallaki manyan gonaki kamar waɗannan. Suna tsaka da duddubawa, Alhaji Wali shi da wasu mutane biyu suka ƙaraso, sai da suka gaggaisa sannan Gambo dillali ya gabatar da shi. "Alhaji Lawan wannan shi ne Alhaji Wali, mamallakin waɗannan gonakin, a tare da shi akwai shaidun masu sayarwa." A karo na biyu Alhaji Lawan suka sake gaisawa, sannan ya fito da jakar kuɗi ya miƙa musu. Suka zauna suka fara lissafi tiryan-tiryan har suka kammala kuɗi ya cika cif, miliyan ɗaya. Takardun gonakin aka miƙa wa Alhaji Lawan ya saka hannu, Alhaji Nasiru shi ma ya yi sa hannu a wurin shaidar mai saya. Sai Alhaji Wali ya saka hannu da shaidunsa, suka yi addu'a da fatan alheri sannan Gambo dillali ya kawo gabaɗaya takardun ya miƙa masa suka tafi. Wayarsa ce ta fara ƙara, yana dubawa ya ga Hajiya Tani ce take kira. Da sallama ya ɗauka, bayan ta amsa masa ta ce. "Alhaji na ji ku shiru, na ce bari na ji ya ake ciki?" "AlhamduLillahi Tani, komai ya kammala. Mun gama ciniki har ya damƙa mini takardun ga su, sauran bayanin dai idan na dawo gida ma tattauna." Alhaji Lawan ya furta cike da farinciki. Amsa masa ta yi, sannan ta katse wayar. Shi da abokinsa Alhaji Nasir ne suka cigaba da duba unguwar suna tattaunawa, don shi ma Alhaji Nasir ya ci alwashin nemo kuɗi ya mallaki gona a Karkasaran koda ba ta yi girman da Alhaji Lawan ba. Sun kai kusan minti talatin suna dubawa, sannan suka nufi gida. Alhaji Lawan yana jaddada idan ya samu kuɗi zai ba wa leburori su zagaye masa shi. Su Gambo dillali sai da suka yi nisa da su Alhaji Lawan, sannan Alhaji Wali ya dubi Gambo ya ce. "Yautai mugun tsuntsu, ma sha miyarka sai ya yi dare. Kar dai ka ce mini hawan ƙawara ka yi wa mutumin nan?" Gambo dillali ya bushe da dariya, yana sake ƙanƙame jakar kuɗin a kafaɗarsa ya ce. "Idan fa ana cin baure, ba a tona cikinsa. Kai tun da na gara maka aiki ai kasan tatsuniyar gizo, ba za ta wuce ƙoƙi ba." "To wallahi dole ka ba ni kaso mai tsoka, don ka san an wuce lokacin aiki banza yanzu." Alhaji Wali ya furta haka suna bushewa da dariya. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [10/05, 08:08] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA BIYU RAKIYA Kasancewar hanyar fili gare ta fetal, ya sa suka gagara samun wurin da za su fake. Da yake babar hanya ce wacce take ɗauke da gwazazzaɓai sai ruwan saman ya fara taruwa a cikin ramuka har ba ka iya bambamce rami da kwata. Da sun yi taku ɗaya-biyu sai dai ka ji taɓal sun faɗa cikin ruwa, ganin hanyar tana sake malalewa da ruwan duba da yadda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya yake zuba. Ya sa Malam Hasan ya dubi Rakiya ya ce. "Rakiya ga gidan kallo can a gefen kwalbatin can mu tsaya a can." Rakiya ba ta iya amsa masa ba, saboda yadda Fatihu yake tsanyara kuka duk ya gigita ta. Gidan kallon duk da ya kasance da rumfa, amma haka feshin ruwan ya dinga jiƙa su. Suna nan tsaye, da takaici ya cika Rakiya sai kawai ta saka kuka. Malam Hasan sunkuyar da kansa ƙasa ya yi, yana jin kukan nata har cikin ɓargon jikinsa. A sanyaye ya riƙo hannunta ya shiga matsawa alamar rarrashi ba tare da ya iya tanka mata komai ba. Sai da ca ji kukanta mai isarta, sannan ta share hawayenta tana jin rabin baƙin cikin da ke cushe a ranta ya faɗa mata. Sun kusan tsaiwar minti ashirin, sannan ruwan ya fara tsagaitawa. Iskace take kaɗawa, sai walƙiyar da ake yi jifa-jifa. Shiru Malam Hassan ya yi, yana bin babbar hanyar da kallo, musamman yadda ya ga babbar hanyar ta shafe da ruwa. Kusan dama haka hanyarsu take, matuƙar damuna ta shigo haka suke fama da matsalar hanya. Wannan dalilin ne ma ya sa duk nisan hanyar masu abin hawa ba sa yarda su shiga, ko fasinja suka ɗauka sai dai su ajiye shi daga gefen titi. Rakiya ce ta gaji da tsaiwar, don haka ta sauko Fatihu daga bayanta tana ƙare ruwan rigar jikinsa. Ganin yana rawar ɗari ya sa ta yi saurin lulluɓa masa ɗankwalin da ta rufe shi duk da shi ma a jiƙe yake. Jigum-jigum suka yi kowannensu da abin da yake saƙa wa zuciyarsa, suna cikin haka har Malam Hassan ya lura da ruwan da ke tafiya a hanyar ya fara ja baya. Don haka ya dube ta ya ce. "Rakiya mu bar wurin haka, mu ƙarasa kada dare ya yi mana kin ga yanzun ma duhu ya yi." Malam Hasan ne ya fara tsoma ƙafarsa a ruwan, ita ma Rakiya ta biyo bayansa. Sai dai bisa tsautsayi ta ji ƙafarta ta taka wani abu mai kaifi, silar haka ya sa ta gurɗe ta kifa cikin ruwan. Fatihu da ke hannunta ya zame, ganin haka ya sa ta saki ƙara mai ƙarfi. A hargitse Malam Hasan ya shiga lalubensu ita da Fatihu, don ita kanta ji ta yi ruwa yana ƙoƙarin fisgarta. Fatihu kuwa sautin amonsa suka ji sau biyu, daga haka ba su ƙara jin amonsa ba. "Fatihu" Fatihu! Fatihu!" Rakiya ta furta a haukace tana rarrafe haɗe da laluben cikin ruwan, haka shi ma Malam Hasan ya shiga lalube yana kiran sunanta da na Fatihu. Riƙo hannun Rakiya ya yi, sai ya ji kamar su ma yana fisgarsu, cikin tashin hankali ya janyo ta suka koma saman dakalin gidan kallon. "Ka ƙyale ni na ɗauko Fatihu malam, na ji kamar kukansa don Allah ka bar ni kada ruwa ya tafi da shi." Rakiya ta furta a haukace cike da zallar tashin hankali, a ɗan tsawace Malam Hasan ya ce. "Me kike yi haka ne Rakiya? Ki dakata na duba shi mana, idan kika biyo ni sai ranki ya ɓaci." Yana gama faɗar haka ya sauka daga cikin rumfar ya shiga lalube da hannunsa yana kiran sunan Fatihu kasancewar babu haske a hannunsa. Sai da ya zura ƙafarsa a wani wuri, ya ji ruwa yana bin hanyar da rami a wurin. Wanda hakan ne ya sa ya ji gwiwarsa ta yi sanyi, lakar jikinsa ta mutu. Ƙwarin gwiwarsa ya tarwatse, jarumtarsa na neman rikiɗewa zuwa rauni. Cike da zafin nama ya cigaba da laluben a yunwace, jin ruwa yana niyyar jansa zuwa ramin ya sa shi yin baya cike da ɗacin zuciya. Cikin rumfar ya koma, Rakiya tana ganinsa ta miƙe zumbur ta ce. "Ina Fatihun?" Sunkuyar da kai ƙasa Malam Hasan ya yi ya ce. "Mu ɗauki dangana Rakiya, ina ji a jikina mun rasa Fatihu..." "A'a ba ka duba da kyau ba, ni zan nemo shi da kaina." Rakiya ta katse shi, sai ta miƙe cikin zafin nama tana ɗingisa ƙafarta saboda har lokacin wani irin zugi take yi mata. Sai dai firgicin da take ciki shi ya hana ta fahimtar yanayin da take ciki. "Kada ki fita Rakiya, Allah Ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya ƙaddara mana haka." Malam Hasan ya furta yana riƙo hannunta, duk yadda ta so fisgewa haka ya riƙe ta tsam a jikinsa. Cikin wani irin yanayi na kewa da shaƙuwa ta fashe da wani irin gunjin kuka, kukan da sauraronsa zai iya raunatar da zuciya har ya saka zubar hawaye. Kuka take tamkar ranta zai fita, dalilin haka ya sa duk dakiya da ƙarfin zuciyar Malam ya fara zubar ƙwalla. Sun ɗauki dogon lokaci a wannan yanayin, har suka ji wasu masallatan suna kiraye-kirayen sallar Isha'i. Tsirarun mutane ne suka fara wucewa, jin irin kukan da Rakiya take yi har lokacin ya sa wasu magidantan maza guda biyu da za su wuce, suka hasko wurinsu suna tambaya. "Malam ne yake faruwa? Lafiya?" Cike da ƙarfin hali Malam Hasan ya ce, "Lafiya ba ƙalau ba." Duk da hanyar ba ta da kyau, amma ta cikin ragowar ruwan da ya kwanta mutanen suka naɗe ƙafar wando suka ƙarasa, a karo na biyu suka sake wurga masa tambaya musamman yadda suka ga Rakiya tana kuka kamar ranta zai fita. "Ɗan mu ne tsautsayi ya faɗa masa..." Malam Hassan ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da su, lokaci ɗaya suka ɗauki salati cikin tashin hankali. Ɗaya daga ciki ya ce, "Wannan ba maganar da za a zauna a yi ta kuka ba ce, mu gayyato jama'a." Yana gama faɗar haka ya tafi da sauri yana yekuwa da shela, a hankali maza suka fara fitowa. Tsirrarun mata kuma suka dinga leƙowa da fitilu suna haske-haske, sai dai yawanci babu wani abu da suke iya gani duba da nisan da ke tsakaninsu da wurin da su Rakiya suke. Kafin wani lokaci maza sun taru sosai, wasu suka shiga ba wa Rakiya da Malam Hasan baki, yayin da wasu suka shiga haske-hasken wurare. Amma duk haske-hasken da suka yi na kusan tsawon awa biyu babu Fatihu sai iya ɗankwalin Rakiya ko zanen goyonsa ba a gani ba. Da ƙyar da suɗin goshi aka ba wa Rakiya baki ta daina kukan da take yi, wani mutum daga cikin mutanen ya ce su zo gidansa su kwana kafin zuwa wayewar gari a sake fitowa duba gawar Fatihu. Ɗaki guda aka ba wa Malam Hasan da Rakiya, sun lura matar gidan mace ce mai karamci ce. Sai da suka yi sallah sannan ta kai musu abinci, fir Malam Hasan ya kasa cin abinci. Amma sai ya shiga rarrashinta yana ba ta baki a kan ta ci, cikin zubar hawaye ta ce. "Malam kana tsammanin zan iya tauna ƙwayar hatsi a bakina, a ranar da na yi bankwana da Fatihu? Fatihu fa ya tafi ya bar ni shi kenan." Ta sake fashe wa da kuka, jikin Malam Hasan ya yi sanyi. Cike da lallashi ya ajiye abincin a gefe ya janyo ta jikinsa ya ce. "Ki yi haƙuri Rakiya, Allahn da ya ba mu Fatihu, Ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya ɗauke shi a daidai wannan gaɓar. Kada ki yi fushi da lamarin Ubangiji, domin ta yuwu mutuwar Fatihu a wannan gaɓar ta fi zame mana alkairi a rayuwarmu." Malam Hasan ya jima yana yi mata nasiha, Rakiya ta tsagaita da kukan sai hawayen da ke zuba daga idonta. Kusan kwanan zaune suka yi, sai gab da asuba bacci mai nauyi ya yi awon gaba da Rakiya. Koda aka kira sallar asuba bai tashe ba, sai da suka fita masallaci shi da mai gidan da suka kwana suka gabatar da sallah. Bayan sun dawo ya tashe ta ta yi sannan, a wannan lokacin masallatai suka shiga shelar abin da ya faru. Limanan ya ce idan gari ya yi haske a fita domin duba inda gawar Fatihu take. Bayan da Rakiya ta idar da sallah gari bai ƙarasa haske ba ta ce za ta je neman Fatihu, duk yadda Malam Hasan ya so hana ta fir ta ƙi hanuwa. Don haka mai gidan ya buɗe musu ƙofa suka fita gabaɗaya har shi, tun suna haske cikin caɓalɓalin da guntun ruwan saman ya kwanta har gari ya yi haske 'yan unguwa suka fito suka haɗu ana duba shi. Cikin hukuncin Ubangiji ba a tsinci gawar Fatihu a ko ina ba, sai a gefen wata ƙatuwar kwalbati. Shi ma dalilin da ya sa aka gan shi wani ƙaton dutse ne ya tokare shi, saboda girman kwatar maza uku ne suka shiga suka ɗauko shi fatar jikinsa duk ta kumbure da ruwa. A cikin buhu aka saka shi, jiki a sanyaye cike da karyewar zuciya suka miƙa wa Malam Hasan. Wani abu ya ji ya daki zuciyarsa, a daidai lokacin Rakiya ta ƙarasa ta ce. "Ya mutu ko Malam?" Shiru Malam Hasan ya yi, ganin buhun hannunsa yana ɗigar da ruwa ya sa ta yi saurin fisgewa tana duba ciki. Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki, sai kuma ta saki buhun ta fashe da wani irin gunjin kuka. Duka mutanen wurin shiru suka yi, saboda kowannensu zuciyarsa babu daɗi duba da irin mummunan yanayin da take ciki. Malam Hasan ya sunkuya ya fara rarrashinta, a daidai wannan lokacin 'yan jaridar gidan Radiyo suka ƙarasa domin rahoto ya je musu. Sai da ɗan jaridar ya gabatar musu da kansa ya kuma jajanta masa abin da ya faru sannan ya ɗora da cewa. "Malam Hasan muna son mu ji matsayinka, da kuma yadda wannan al'amarin ya kasance." Sai da Malam Hasan ya yi ta maza sannan ya faɗa masa abin da ya faru, da ya ji tambayoyin za su yi yawa ya dakatar da su. Haka kuma da suka buƙaci jin ta bakin Rakiya ya hana su, don ya lura tambayoyin ba ƙaramin tayar mata da hankali suke ba. Sai suka koma jin ta bakin mutanen unguwa, su ma suka sanar da su gwargwadon abin da suka sani. Jin dalilin da ya sa Malam Hasan ya fito daga gidansa, ya sa mutane suka kawi taro da sisi suka haɗa musu kuɗin mota. Domin sun buƙaci da a yi wa Fatihu sutura a nan ya ce zai ƙarasa garinsu a yi a can. Taxi suka tara tun daga titin har cikin ƙauyensu da ke garin Ɗanbatta. Sai da ya sallami mai Taxi, sannan suka ja ƙafa jiki a sanyaye suka shiga, Inna ba ƙaramin mamakin ganinsu da farar safiya ta yi ba. Malam Hasan ne ya gaishe ta ta amsa, Rakiya da fuskarta ta kumbura suntum sabod kuka ta ce. "Ina kwana Inna." A wulƙance Inna ta amsa sai ta ce, "Ciwon baki kike yi da ba za ki buɗe baki ki mini magana ba? Ina Fatihun yake? Ai kya miƙo mini jikana mu gaisa." Rakiya ta sunkuyar da kai ƙasa, lokaci ɗaya ta fashe da kuka. ALHAJI LAWAN Alhaji Lawan yana zuwa gida cike da murna HajiyaTani ta tare shi, sai da ta kawo masa ruwa ya sha sannan ta ce. "Alhaji sai kuma na ji ka ce an gama komai." Alhaji Lawan ya saki murmushi yana miƙa mata takardar ya ce. "Ga takardu ma sun zo hannu, sai ki adana mini su don kin fi ni iya ajiya." Hajiya Tani ta zaro takardun ta duba, bayanin fasalin gonakin ne da kusurwoyinsu ta fannin tsayi da faɗi. Sai bayanan masu saya da mai sayarwa, jinjina kai ta yi ta ce. "Kai amma fa kamar suna da girma sosai." Alhaji Lawan ya gyaɗa mata kai ya ce, "Girma ma ai ba a magana, so nake sai kayan da muka tura sun sauka mun ga abin alherin da muka samu na ga me ya dace na yi wa wurin. Zan dai gina mana ƙaton gida mu huta da yawon haya, sai ƙatuwar plaza da nake son yi wacce za a zuba shaguna." Cikin jin daɗi Hajiya Tanj ta ɗaga hannuwa sama ta ce, "Kai Allah mun gode maka, Alhaji Allah Ya kusa yanke mana haya." Alhaji Lawan ya saki murmushi ya ce. "In Shaa Allahu kuwa." Hajiya Tani tana shirin tashi Alhaji Lawan ya ce, "Ni kuwa ina yaran nan? Tun da na shigo ban ji motsinsu ba." Hajiya Tani ta ɗan gwasale baki ta ce, "Shi dai wancan gantallan ka san ai ba zaman gida yake ba Alhaji. Ita kuma Abida tun da na saka ta wanke-wanke don ba su fita ba, na yi mata faɗa take fushi a ɗaki." Sai kuma ta sake raunatar da murya cike alamun damuwa ta ce. "Yanzu Alhaji yaran nan ban isa da su ba kenan? Ko don ba ni ce na haife su ba ne oho?" Ransa Alhaji ya sake ɓaci, cike da damuwa ya ce. "Don Allah ki daina faɗar haka Tani, yaran nan tamkar 'ya'yanki suke kuma duk hukuncin da ya dace kina iya zartarwa a kansu." Tani ta rangwaɗa kai gefe ba tare da ta yi magana ba, Alhaji ya sake cewa. "Kira mini ita, idan ba ta yi aikin gida ba waye zai yi? Yara gabaɗaya so suke su sauya halayensu." Da sauri Tani ta miƙe ta fita, bayan wani lokaci suka dawo tare da Abida. A rakuɓe can gefe ta zauna musamman da ta lura da mummunan kallon da mahaifinta yake jifanta da shi. "Ba ki da mutumci ko Abida? Ina ganin kin fi ɗan'uwanki hankali ashe ya fara zuga ki? Me ya sa ba kya son yin aiki yadda ya kamata?" Alhaji ya furta yana tsare ta da idanu, muryarta tana rawa ta ce. "Ka yi haƙuri." Tana son ta ce masa ba ta da lafiya, tana jin tsoron bayan fitarsa kada Tani ta hukuntata. Don haka ta ja bakinta ta yi shiru, tana nan tsugunne ta ji ya ce. "Kin ci abinci?" Da sauri ta kalli Tani, sai kuma ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Eh" Sai ta ji ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa. "Idan aka ƙara kawo mini ƙararki wallahi sai na ɓata miki rai..." Maganarsa ta maƙale sakamakon sallamar da ya ji ta Fauwaz. "Fauwaz! Kai Fauwaz zo nan." Ya furta a ɗan fusace, ɗaga labulen Fauwaz ya yi bakinsa ɗauke da sallama sannan ya zauna. Fuskarsa a haɗae take tamau, don a duniya babu matar da ya tsana sama da Tani. Ko kaɗan jininsu bai haɗu ba, musamman da ya fahimci gashin ƙumar da take yi musu. "Daga ina kake? Kuma tun yaushe ka fita?" Alhaji Ya furta yana tsare shi da ido. "Ban daɗe da fita ba Abba..." "Ƙarya kake Fauwaz! Rabon da na gan ka tun safe, ko ka ɗauka ba na lura da kai." Tani ta furta a ɗan kausashe. Wani wulaƙantaccan kallo ya wurga mata, ya jima idonsa yana kanta har sai da ta ji ɗar a zuciyarta a kan irin kallon da yake yi mata. "Fauwaz ka kiyaye ni fa? Kana son ka koyi yawon banza da yara ko? Kai wanne irin yaro ne da kullum sai an kawo mini laifinka?" Fauwaz da takaici ya cika shi ya ce, "Wai Abba duk abin da aka faɗa maka sai ka dinga hawa kana zama, ka dinga bincike wallahi wani abin ƙarya..." "Ungo naka, gidanku na ce." Abba ya yi masa daƙuwa da hannu, Tani tana jin haka sai kawai ta fashe da kuka ta ce. "Ka ga irin abin da yaron nan yake yi mini ko Alhaji, yanzu tun yana yi mini a bayan idonka har ta kai yana ƙaryata ni a gabanka." Alhaji ya sake fusata, rai a ɓace ya ce. "Idan na sake jin makamanciyar maganar nan wallahi sai ranka ya ɓaci Fauwaz, sakarai marara hankali ka ba ta haƙuri." "Haƙuri?" Fauwaz ya furta cikin sigar tambaya yana kallon Tani, saboda Fauwaz irin yaran nan ne masu taurin kai. Musamman idan ya kasance a kan gaskiyarsa yake. "Ko ban isa in saka ka ba ne?" Abba ya furta murya a sama, Tani ta share guntuwar ƙwallar munafurci da ba ta gama sauka ba ta ce. "Alhaji yaron da yake ƙaryata ni shi zai ba ni haƙuri? Yanzu da Allah Ya ba ni haihu da ban haifi wanda ya fi shi ba." Alhaji ya saki ƙwafa sannan ya dubi Fauwaz ya ce, "Idan na sake magana wallahi sai ranka ya ɓaci." Kamar ba zai motsa bakinsa ba haka Fauwaz ya yi, sai bayan wasu sakanni sannan ya ce. "Yi haƙuri." Yadda ya yi maganar da ba su kasa kunne ba babu wanda zai ji, Tani ta haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ta amsa masa. "Tashi ka ba ni wuri sakarai." Alhaji ya furta masa, Fauwaz da Abida tare suka tashi suka fita. Suna fitowa Fauwaz ya riƙo hannun Abida ya ce. "Abida na gaji da zaman gidan nan." Muryarta tana rawa ta ce, "Ni ma na gaji yaya, tun da Umma ta mutu muke shan wahala." Ɗakinsu suka shiga, sai a lokacin ya ji jikinta da zafi zau. A ɗan gigice ya ce, "Ba ki da lafiya ne Abida?" Kai kawai ta gyaɗa masa, ya sake ce mata. "Kin faɗa wa Abba?" Ta girgiza kai ta ce. "Idan na faɗa masa Aunty dukana za ta yi, ɗazu ma ta dake ni saboda da safe na faɗa masa littafin makarantata ya cika." Fauwaz ya furzar da iska mai zafi cike da takaici ya ce. "Abida matar nan ba ta sonmu, ba ta son Abba kina ga ta saka shi ya sayar da filinmu." Muryarsa ta yi rauni, idanunsa suka ciko da ƙwalla musamman da ya tuna fafutukar da mahaifiyarsu ta yi ta sayi filin kafin ta rasu. Cike da yarinta Abida ta ce, "Allah zai saka mana, ai ita ma idan ta mutu sai mun sa Abba ya sayar da nata." Ganin yadda jikinta ya ƙara ɗaukar zafi, ya sa Fauwaz jiƙa tsumma yana saka mata a jiki, saboda tun tasowarsa haka ya ga mahaifiyarsu tana yi idan suna zazzaɓi mai zafi. Alhaji ya jima yana ba wa Tani haƙuri sannan ta sauka, daga haka ya tashi ya fice daga gidan. Tana ganin ya fita ta ciro waya ta latsa wata lamba, ba a jima ta ɗauka tana ƙasa da murya. "Ina fatan komai ya tafi daidai?" Daga can ɓangaren aka ba ta amsa da cewar. "Kada wani abu ya ɗaga miki hankali, kuɗi ga su a hannuna tun da ciniki ya riga da ya faɗa. Ragowar maganar idan mun haɗu ma tattauna." Sallama suka yi, Tani ta saki murmushin farinciki mai cike da tarin manufa sannan ta ce. "Alhaji Lawan kenan! Idan har ni Tani ina raye, daga yau ka fara irga asara ba riba ba." Sai ta sake sakin murmushi ta koma tana ƙare wa takardun gidan da ya damƙa mata ajiya kallo mai cike da tarin manufa. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [11/05, 16:08] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA UKU Fauwaz ya jima yana saka wa Abida ruwa a jikinta, har sai da ya ji zafin ya ragu sannan ya matse rigar ya shanya. Bacci ne ya ɗauke ta, don haka ya fita daga ɗakin yana tunanin yadda za a yi ya saya mata magani. Don har zuciya ta ayyana masa ya je ya samu mahaifinsu ya faɗa masa, amma da ya tuna irin makircin da Tani take ƙulla musu ba su cika kwashewa ta daɗi da shi ba, sai kawai ya haƙura. Ya yanke shawarar fita tsintar gwangwanaye kamar yadda ya ga abokinsa Musa yana yi. Kusan tun gabanin sallar Magriba da ya fita, ba shi ya dawo gida ba sai kusan tara saura na dare. Zuciyarsa a cunkushe take, sakamakon ya sha yawo sosai ya tsinci gwangwanaye da jarkoki, har ya sayar amma bai samu mai chemist ɗin layinsu ba. Sakamakon Peter mai chemist ya je garinsu kirsimeti, kuma shi kaɗai ne mai kemis ɗin da ke zagayen unguwarsu. Tani tana ɗaki ba ta ji shigarsa ba, Fauwaz yana shiga ɗakinsu ya samu Abida a zaune. Sai dai daɗin da ya ji da zazzaɓin jikinta ya sauka, tana ganinsa ta saki murmushi sai shi ma ya mayar mata da martanin murmushin. "Ya Fauwaz, idan na girma zan gina mana gida mu tafi mu bar su Abba a nan." Abida ta furta a hankali don kada Tani ta ji, zama ya yi a gefenta ya ce. "Ai ni ne babba, ni zan fara gina mana gida mu tafi, kuma har sababbin kayan wasa zan saya miki." Jin haka ya sa Abida ta saki murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana. "Fauwaz! Don Allah, koda wani yanayi da zai gifta wanda zai sauya maka rayuwarka, ka kula da ƙanwarka. Ku biyu Allah Ya azurta ni da su, ku haɗa kanku, ka ja ƙanwarka ka ji Fauwaz." Kalaman mahaifiyarsu ne ya dawo cikin kwanyarsa ana gobe za ta rasu, idanunsa suka ciko da ƙwalla. Gudun kada Abida ta fahimci damuwarsa ya sa shi saurin kawar da kansa. Suna nan zaune Tani ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ce. "Kai Fauwaz! Fito ka ɗebo mana ruwa." Shiru ya yi kamar bai ji ba, saboda gabaɗaya ya ɗora rushewar faruncikinsu a kanta. A karo na biyu ta sake yi masa magana, kai tsaye ya ce. "Yanzu dare ya yi." Ai kuwa kamar wacca ya kwara wa ruwan zafi a hassale ta ce. "To tun da ba za ka ɗebo ba, sai na bari idan ubanka ya dawo ya ɗebo mana." Wani irin ɗaci ya ji a ransa, cike da damuwa ya ce. "Ki daina zagin mahaifina." Za ta yi magana ta ji motsin shigowar Alhaji, yana ƙarasawa ya ce. "Me yake faruwa hayaniyar me nake ji?" Tani tana jin haka ta yi zaraf ta ce, "Wai don na ce Fauwaz ya ɗebo mana ruwa yake yi mini rashin mutumci. Ni dai ina jin Alhaji zan bari ka dinga yi masa magana da kanka, don ina gudun watarana na yi masa magana ya zage ni." Fauwaz da zuwansa bakin ƙofar kenan, ya bi Tani da kallon mamakin sharrin da ta yi masa. Tass! Alhaji ya ɗauke fuskar Fauwaz da mari har sai da ya bugu da jikin bango, da sauri Abida da ke gefe ta riƙe shi a tsorace da hukuncin da Abba ya zartar masa. Abba ya nuna shi da yatsa ya ce. "Daga yau idan aka sake yi maka magana ka musa sai ranka ya yi mummunan ɓaci. Ka yi maza ka wuce ka ɗauki bokiti ko na tattakaka, sakarai marar mutumci." Goge hawayensa Fauwaz ya yi, Abida ta ja hannunsa ta yi tsuru-tsuru saboda tsoro. Wani irin kallo suke yi wa mahaifinsu tamkar sun ga sabuwar hallita, domin gabaɗaya ya sauya kamar ba mahaifinsu mai sonsu da nuna musu kulawa ba. Fauwaz yana fita Tani da Alhaji suka rufa masa baya har lokacin bai daina faɗa ba. Fauwaz ba shi ya gama ɗiban ruwan ba sai kusan sha ɗaya saura don Tani har ta kwanta, a lokacin ne ya shiga kicin zai ɗebi abinci ya ci. Sai dai yanq zuwa ya ga sai burbuɗin shinkafa da ƙanzonta. Yadda cikinsa yake ƙugi ne ya kawar da ɓacin ransa, hawayen idonsa ya share sannan ya saka hannu ya kankaro ƙanzon ya zuba da mai ya zauna ya ci. Sai da ya ci ya wanke hannu sannan ya shiga ɗakinsu, a takure a can ƙarshen bango ya hango Abida a duƙunƙune tana rawar ɗari. Da sauri ya ƙarasa wurinta ya ɗago ta yana faɗin. "Abida! Sannu zazzaɓin ne?" Jikinta yana rawa ta gyaɗa masa kai, da sauri ya ƙarasa ya ɗauki rigar da ya shanya ya sake jiƙa ta ya shiga saka mata. "Sannu kin ji Abida, ɗazu na samo kuɗi don na sayo miki magani amma Peter ba ya nan." Fauwaz ya furta muryarsa tana rawa, ba ta iya amsa masa ba saboda yadda take jin jiki. Ya jima a haka har ya samu jikin nata ya rage zafi, yana nan zaune rungume da Abida ya ji bacci ya ɗauke ta. Ido ya zuba mata yana kuka, yana tuna rayuwarsu a lokacin da mahaifiyarsu tana raye. Yana cikin wannan yanayin har bacci ya yi awon gaba da shi. Wani irin kakari yake ji sama-sama a cikin baccinsa, jijjigar da jikinta yake yi ne ya farkar da shi daga wahalallan baccin da yake yi. Ɗakin baƙiƙƙirin yake, sakamakon fitilar da ke ɗakin kalanzir ɗin cikinta ya ƙare. Kiran sunanta ya shiga yi a hargitse yana jijjiga ta, sai ya ji jikinta zafi zau kamar wuta. A hargitse ya fita daga ɗakin kai tsaye ya nufi ƙofar ɗakin Tani, daga bakin ƙofa ya tsaya zai fara kiran mahaifinsu. Domin tarbiyyar da mahaifiyarsu ta yi musu kenan, babu wanda yake shiga ɗakinsu ita da mahaifinsu kai tsaye ba tare da an ba su izini ba. "Abba! Abba ka zo Abida wani abu take yi ba ta da lafiya." Fauwaz ya furta a ɗan ruɗe, daga can ɗakin mahaifinsu ya ce. "Kai waye nan?" Cikin sauri Fauwaz ya ce, "Ni ne Abba, Abida ba ta da lafiya wani abu take yi." Kamar wanda ya watsa wa ruwan zafi a hassale Abba ya ce, "To ni zan ba ta lafiyar ko yaya? Ko kuwa kawai don ka tashe mu ka katse mana bacci?" Yana daga waje ya ji muryar Tani tana cewa, "Ni ban san mene ne matsalar yaron nan ba. Wallahi da uwarsa tana raye cewa zan yi ita take kitsa masa duk wani abu da yake aikatawa. To ban da rashin lissafi yanzu idan ya faɗa maka me za ka yi mata? " "Shi ne abin da na gani, kai Fauwaz ka wuce ka tafi zuwa safiya sai a san abin yi." Abba ya furta daga cikin ɗakin, hawaye ne suka shiga sintiri a fuskar Fauwaz kamar an yi masa gorinsu. Har ya juya zai tafi ya ce, "Abba amma da Mama tana raye ba ka mana haka. Na san da tana nan haka ba za ta faru ba..." "To ka tafi maƙabarta ka dawo ita mana." Tani ta furta da wata irin murya, shi kuma Abba ya ce. "Lallai wuyanka ya isa yanka Fauwaz." "Ba irin abin da nake faɗa ba kenan, kai ma ka ga rashin kunyarsa ko?" Tani ta furta cike da zuga da son ƙara tunzura Abba, sai dai har Fauwaz ya fita daga ɗakin bai sake tanka musu ba. Duk da cikin dare ne hakan bai hana Abba ya cigaba da surfa faɗa ba, zuciyar Tani fes ta cigaba da ingiza shi yana hawa. Sai da ta tabbatar da ya gama cika fal da haushin Fauwaz sannan ta sake kwantar da murya ta ce. "Ni fa Alhaji ina son faɗar wata magana, amma sai ruwan tsoro ya mamaye ni." Tani ta sauya fuska cikin alamun damuwa, hasken ƙaramar fitilar touchlight ɗin da ke hannunsa ta sake bayyanar masa da zallar damuwar da fuskarta take ciki. "Faɗi mana Tani, ni a kan yaran nan tamkar mahaifiyarsu haka nake kallonki." Abba ya furta cikin damuwa, Tani ta gyara zama ta cigaba. "Ni fa sai nake ganin kamar ba iya abin da ya kawo Fauwaz ɗakin nan ba kenan." Cikin rashin fahimta Abba ya ce, "Ban fahimce ki ba Tani." Tani ta sake muskutawa kusa da shi sannan ta ce, "Ni fa ina zargin sata ce ta shigo da shi." "Sata!" Abba ya furta da wata irin murya mai cike da zallar tashin hankali, gaban Tani sai da ya faɗi da ganin mummunan yanayin da ya shiga. Har sai da ta fara tsammanin ko haƙonta a zai cim ma ruwa ba, sai kuma ta dake zuciyarta ta ce. "Ƙwarai kuwa, saboda ba rana ɗaya ba, ba kuma biyu ba da na taɓa ganin ya shigo mana ɗaki idan muna kwance. Don ko jiya sai da na nemi ɗari biyuna sama da ƙasa na rasa." Ganin zancan kamar yana shigarsa ya sa ta wara hannuwa tana taɓe baki ta ce. "Ka san an ce idan ba ka iya kama ɓarawo ba, sai shi ya kama ka. Ba na son na dinga yawan faɗa maka laifin yaron nan ka ga kamar ba na ƙaunarsa, ni kuma na ga ɗa ai na kowa ne..." "Haba Tani, amma me ya sa kika rufe mini magana mai girma kamar wannan?" Abba ya katse ta a ɗan hassale, cike da kissa ta ce. "Ka yi haƙuri Alhaji In Shaa Allahu ba za a sake ba." Furzar da iska mai zafi Abba ya yi, zuciyarsa tana zafi ya furta. "Yaushe Fauwaz ya zama haka? Sata? A cikin gidana? Ina ba zai yiwu ba." Tani ta dafa kafaɗarsa ta ce, "Ni kuwa idan har da gaske ka ba ni matsayin mahaifiyar Fauwaz, zan ba ka wata shawara wacce nake ganin ita ce mafita a gare mu gabaɗaya." Tana dire kalamanta Abba ya ce, "Faɗi kowacce iri ce Tani, domin mai sonka ai shi zai faɗa maka gaskiya. Wa ya sani ma ko yana yi a waje mutane suna nan suna ta kallona da abin." Abba ya ƙarasa maganar yana sakin ƙwafa, zuciyar Tani fari ƙal saboda farin ciki. Amma a fili sai ta marairaice murya ta ce, "Ni ina ganin abin da ya fi, tun da yaron nan nema yake ya janyo mana magana. Kuma muna iya bakin ƙoƙarinmu wurin kula da tarbiyyarsu, kawai ka kai shi almajiranci." Tani ta ƙarasa furucin tana satar kallon fuskar Abba. ƊANBATTA A yatsine Inna ta dubi Rakiya da ke gursheƙen kuka, Malam Hassan ya matsa kusa da ita cike da tausayi ya dafa kafaɗarta. "Yau kuma wani sabon kitifin kika ƙullo ba ki warware shi a ko ina ba sai nan a gabana? To ko laƙanin da bokanki ya ba ki kenan?" Inna ta furta cikin masifa, Malam Hassan ne ya yi ƙarfin halin cewa. "Inna Fatihu ne Allah ya yi masa rasuwa." Maganar Malam Hassan ta yi daidai da faɗuwar bokitin ƙullin kunun da ke hannun Inna. "Shi Fatihun ne ya rasu?" Inna ta furta a ruɗe, Malam Hassan ya gyaɗa kai idanunsa suka yi jajir kamar zai zubar da ƙwalla. Hakan ya sa Rakiya ta sake rushewa da kuka, tana sake jin soyayyar Fatihu a ranta. Hannu ya saka ta bayanta ya tallafo shi, Rakiya ta kunto Fatihu da ke bayanta. Malam Hasan yana sauke gawar Fatihu Inna ta zuba salati tana tafa hannu. Zuwaira da fitowarta daga banɗaki kenan ta ƙarasa tana tana faɗin. "Lafiya Inna?" Ganin su Malam Hasan ya sa ta datse kalamanta, ta zuba masa idanu tana kallonsa. "Ina fa lafiya Zuwaira, wai Fatihu ne ya mutu. Shi kenan hankalinta ya kwanta ai." Inna ta ƙarasa furucin muryarta tana rawa, da sauri Zuwaira ta dafe ƙirji tana ja da baya ta ce. "Fatihu ya rasu Inna? Yaya me ya faru da shi? In ce dai ba wata gubar Rakiya ta ɗura masa ba..." "Sai ma kin tambaya Zuwaira? Kamar ba ki san wace ce Rakiya ba." Inna ta yi saurin katse Zuwaira hawaye yana zuba sannan ta ɗora da cewar. "Shi kenan ɗan ɗaya-ɗayan da Allah Ya ba wa Hasan an halaka shi." "Inna don Allah ku tsaya ku saurari abin da ya faru, kada ku yanke hukunci kai tsaye." Malam Hasan ya furta cikin damuwa, a sheƙe Inna ta dube shi ta ce. "Hasan wai yaushe rawanin asirin da yarinyar nan ta yi maka zai warware?" "Don Allah Inna ki daina faɗar haka, Fatihu tsautsayi ne ya faɗa masa. Kuma tun fil azal Allah Ya ƙaddari shi ba mai tsawon kwana ba me..." Gabaɗaya duk abin da ya faru Malam Hasan ya kwashe ya sanar da su Inna. Yana rife baki Zuwaira ta wurga wa Rakiya kallon banza, sannan ta buga uban tsaki ta ce. "Inna don Allah ta yaya wacce ba ta san zafin haihuwa ba za ta riƙe ɗa dama? Wai ki ji Fatihu ya zame a ruwa kamar wani ɗan tayin kifi." A hassale Malam Hasan ya ce, "Kada na sake jin bakinki Zuwaira! Idan kika sake faɗar magana marar daɗi ranki zai yi mummunan ɓaci." Inna da zuciyarta ta gama zuwa wuya ta ce, "Ƙarya aka yi mata? Yanzu idan ɗan da ta ɗauki cikinsa ta sha wahalar laulayi ta yi naƙudarsa ne za ta sake shi a ruwa? Na ce za ta sake shi a ruwa?" Inna ta ƙarasa furucin tana zuba wa Malam Hasan idanu, sunkuyar da kai ƙasa ya yi zuciyarsa a dagule musamman da yake jin shasshekar kukan Rakiya har cikin ransa. Domin shi shaida ne a kan zallar soyayyar gaskiya da take yi masa. A yadda ya san halin Rakiya da kyawawan halayenta, ba zai yi tantama a kan mutuwar Fatihu ba koda ba ya wurin al'amarin ya faru. "Ai ta kashe uwarsa, tun da ta gama da uwar kin ga shi ma dole ta gama da shi yadda za ta kanainaye mini ɗa ba tare da wani ya raɓe shi ba." Inna ta furta cike da masifa, Zuwaira ta taɓe baki ta ce. "Inna ka yi magana cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa." "To ni na faɗa, idan ya ga dama ya yi mini duk abin da ya ga dama a kanta, dama ai ba yau ya saba nuna mini iyaka ta a kanta ba. Wanna baƙar annoba ni kam Allah Ya jarabce ni da ita, ga ki dai juya gaba da baya ba haihuwa kike ba amma kin kashe mai haihuwar shi ma ɗan da aka haifa ɗin kin hallaka shi." Wani irin sabon kuka mai cin zuciya Rakiya ta saki, sai kawai ta fice daga gidan tana jin tamkar zuciyarta za ta tarwatse saboda ɓacin rai. Da wanne za ta ji? Da rashin Fatihu da take jin sa tamkar ɗan da ya ratso ta jikinta ko kuwa da baƙaƙen maganganun ƙazafin da Inna take jifanta da shi? Duk da maganganun Inna ba baƙi ba ne a wurinta, amma na ranar sun fi dukan zuciyarta domin a lokacin ji take yi ko mahaifin Fatihu Malam Hasan ba zai kai ta jin raɗaɗin da take ji na mutuwarsa ba. Malam Hasan yana ganin Rakiya ta fita ya bi ta sauri yana kiran sunanta, hakan ya sa Inna ta yi saurin ɗagowa ta shiga ƙwala masa kira. "Hasan! Hasan! Ba za ka rabu da ita ba ka zo ina yi maka magana." Cike da zuga Zuwaira ta ce, "Ina zai zo zuciyarsa ta tafi Inna, ai wallahi sai kin yi da gaske a kan Yaya don ni wallahi ban taɓa tsammanin abin ya yi tsamari haka ba." Inna ta zuba hannuwa biyu a kumatu cike da jimami ta ce, "Zuwaira kin ga ya fifita waccan juyar a kan gawar ɗansa ko?" Zuwaira ta saka hannu ta ɗauki gawar Fatihu ta saka a wani ƙaramin ɗaki da suke ajiya shirge-shirgensu. Inna ta zauna a kan turmi zuciyarta tana ci gaba da tafasa, don a wannan karon ji take yi sai dai Hasan ya zaɓa ko Rakiya ko ita. Duk yadda Malam Hasan yake sauri sai da ya haɗa da sassarfa sannan ya cim ma Rakiya yana ƙwala mata kira. "Rakiya! Rakiya don Allah ki tsaya mana." Cike da ƙunan zuciya da ɓacin rai ta waigo tana faɗin. "Me zan tsaya na yi Baban Fatihu? Me zan zauna yi a wurin da ba a ƙauna..." Kukan da take dannewa ya ƙwace mata, wani abu ne ya soke shi a maƙoshi cike da lallashi ya ce. "Don girman Allah ki yi haƙuri Rakiya, ni da ke duka mun san halin Inna ba baƙo ba ne a wurinmu. Me zai sa ranki ya ɓaci tun da kin san halinta?" "Me ya sa raina ba zai ɓaci ba ko ni ba ɗan'adam ba ce ba ni da zuciya a ƙirjina? Me ya sa har yanzu Inna ta gagara fahimtar ni ba irin yadda take tsammani ba ce? Me ya sa ba ta iya ɗaga mini ƙafa a wannan gaɓar da zuciyata take cike da ɗacin rashin Fatihu ba. Kasan komai fa Baban Fatihu, ka san dai ba zan iya salwantar da rayuwar ɗanmu Fatihu ba..." Sai ta sake fashewa da kuka, a sanyaye ya matsa kusa da ita murya a tausashe ya ce. "Na san komai Rakiya, na san ba a kyauta miki ba. Kuma duk wanda kika ji an ba wa haƙuri an cuce shi ne, na tabbata watarana Inna za ta fahimce ki yadda ya kamata." "Zuwa yaushe kake tunanin Inna za ta ƙaunace ni? A shekara goma da aurenmu ba ta so ni ba sai daga baya?" Rakiya ta jefa masa tambayar cike da tausayin sabuwar rayuwar da za ta fara tare da Inna. Malam Hasan ya riƙo hannunta ya ce, "Don Allah ki zo mu je ciki, waɗannan maganganun za mu tattauna daga baya." Sai da Malam Hasan ya sake rarrasarta da kalamai masu taushi sannan suka koma cikin gidan. Lokacin da suka shiga Inna ta cika fam, suna zuwa gabanta cike da zafin rai ta ce. "Hasan! Hasan!! Hasan!!!" Gabansa yana faɗuwa ya ce, "Na'am Inna." "Sau nawa na kira ka?" Ya shafa kai a hankali ya ce, "Sau uku Inna." "To idan ni Kulu, ni na ɗauki cikinka na yi naƙuda na haife ka a yau sai ka saki wannan tsinanniyar yarinyar." Inna ta furta tana kafe shi da ido. Duk da a wannan lokacin ɓacin rai ya sa Rakiya tana son rabuwa da Malam Hasan, kalaman Inna ba ƙaramin tarwatsa nutsuwarta suka yi ba. "Hasan a yanzu daga Allah sai kai, ku kaɗai kuka zama gatan Rakiya. Don Allah duk rintsi kada ka salwantar da amanarta da na damƙa maka." Malam Hasan ya tuna kalaman mahaifin Rakiya waɗanda ya yi su yana gab da barin duniya. Nan take ƙwaƙwalwarsa ta sake tarayo masa da kalaman Inna, cikin girmamawa ya ce. "Don Allah Inna ki yi haƙuri, abin bai kai da haka..." Tass! Inna ɗauke fuskarsa da mari, ba Rakiya ba hatta Zuwaira sai da abin ya matuƙar ba ta mamaki. Inna ta nuna shi rai a ɓace ta ce. "Na riga da na gama magana, idan kuma ba za ka sake ta ba. Ka je ka ban yafe haƙƙina da ke kanka na mahaifiya ba." Cikin firgici Malam Hasan ya ɗago yana kallon Inna, ba ta tanka masa ba ta shige cikin ɗakin rai a ɓace. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [12/05, 17:48] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA HUƊU Da wani irin sanyin jiki Rakiya ta matsa kusa da shi, ta zuba masa ido tana karantar mummunan yanayin tashin hankalin da yake ciki ta ce. "Koda wasa kada ka yi ja-in-ja da mahaifiyarka. Tabbas ana sake mata, amma duk duniya babu mai maye maka gurbin mahaifiya. Ba tun yau Inna take gwada mini ƙiyayya ba, amma a wannan gaɓar ta zarce kowanne lokaci." Rakiya ta ja gefen hijabinta ta share hawayenta sannan ta cigaba. "Ban ga laifin Inna ba, domin kowacce uwa tana son ganin zuri'ar 'ya'yanta. Ni kuma kalar ƙaddara ta kenan ta rashin haihuwa, sai dai ba yin kaina ba ne..." Kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata, Malam Hasan zai yi magana ta katse shi da cewar. "Baban Fatihu ka bi mahaifiyarka, ni kuma zan tafi duk inda Allah Ya ƙaddara zamana zai ƙare a can." "Ba za ki tafi ko ina ba Rakiya." Malam Hasan ya furta cikin hargitsattsiyar murya mai cike da zallar ɓacin rai, sannan ya ɗora da cewar. "Koda ace ba ki kasance matata ba, haƙƙina ne na kula da ke matuƙar ba kya ƙarƙashin wani." Za ta sake magana ya riƙe hannunta da ƙarfi suka fita daga gidan, kai tsaye gidan Kawu Sani suka ƙarasa. A lokacin da suka shiga Kawu yana tsaye a bakin ƙofar ɗakinsa yana rufewa, kallo ɗaya za ka yi wa su Malam Hasan ka fahimci kwanciyar hankali ta bijirewa gangar jikinsu. "A'a, yau Hasanu ne da farar safiya haka?" Kawu Sani ya furta yana ɗan faɗaɗa fara'arsa. Murmushin yaƙe Malam Hasan ya saki ya ce, "Mune Kawu, barka da safiya." Kawu Sani ya amsa sannan suka gaisa da Rakiya wacce fuskarta ta yi jajir saboda kuka. Iya matarsa ce ta ƙarasa suka gaisa, tana shirin kai su ɗaki Malam Hasan ya ce. "Kawu dama ba zama muka zo yi ba, akwai maganar da take tafe da mu." Kawu Sani ya girgiza kai ya ce, "Hmmm Kulu ce ko?" Malam Hasan ya gyaɗa kai sannan ya kwashe duk abin da yake faruwa ya sanar da shi. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cikin faɗa-faɗa ya ce. "Indo wai yaushe Kulu za ta yi hankali ne? Wanne irin rashin hankali take son aikatawa haka? Yara sun rasa ɗansu ko gawarsa ba a binne ba take ƙoƙarin sake saka su a wani tashin hankalin." Iya da ke gefe ta furzar da iska mai zafi ta ce. "Wallahi a kullum lamarin Kulu yana sake ba ni mamaki, wai me ya sa wasu iyayen suka fi ƙuntatawa 'ya'yan da suke fi yi musu biyayya? Saboda Allah ina adalci a cikin hukuncin da ta yanke, rayuwa da mutuwa duk a wurin Allah suke, sai kace ba ta san ƙaddara ba." Kawu Sani ya girgiza kai ya dubi su Malam Hasan ya ce. "Ku wuce mu je gidan, wallahi idan Kulu ba ta yi wasa ba sai ranta ya yi mummunan ɓaci." A ɗan sanyaye Malam Hasan ya ce. "Amma Kawu don Allah kada ta..." "Kada ka damu na san yadda zan ɓullo mata." Kawu Sani ya katse shi, sannan suka wuce can wurin Inna. Lokacin da suka ƙarasa gidan a soro suka ci karo da Zuwaira, tana ganin Kawu Sani ta haɗe fuska murya ciki-ciki ta ce. "Sannu da zuwa Kawu..." "Wuce ciki mu je baƙar munafuka." Sum sum sum Zuwaira ta juya ta shige ciki, tun daga tsakar gida Kawu Sani ya fara ƙwala wa Inna kira. "Kulu! Ke Kulu ko sai na shigo ɗakin?" Inna ta fito fuskarta a cunkushe ta ce, "Ga ni Yaya." Kawu Sani ya janyo hannun Malam Hasan ya ce, "Maza zo ki tsine masa, na ce ki zo ki tsine masa sakarai wacce ba ta da hankali. Wato so kike ki sabauta yaron nan ko ki saka masa hawan jini ki tsugunnar da shi ko Kulu?" Inna ta sake haɗe fuska ta ce, "Yaya kai ne ba ka san abin da ya faru..." "Idan ba ki yi mini shiru ba sai na ci mutumcinki, wai Kulu yaushe za ki gane Allahn da ya busa miki numfashi, Shi ya dasa miki ƙwan da kika haihu ba tare da sisin kwabo ko wayo da dabararki ba? An ya Kulu kina son ki wanye lafiya kuwa?" Gabaɗaya shiru suka yi wurin ya yi tsit, Kawu Sani ya nuna Zuwaira da yatsa sannan ya ce. "Ke kuma daga yau, idan na sake jin kin faɗa wa Rakiya wata magana ke ko kallon banza kika yi mata wallahi tallahi sai na tattaka ki." Ya waiga wurin Inna ya ce. "Yanzu zan samu mai gari da Malam Liman a suturta yaron nan, zuwa nan da dare za mu zauna mu tattauna." Kawu Sani ya juya zai fita, har ya je bakin ƙofa ya waigo ya ce. "Idan kun ga dama bayan na fita ku cigaba da rashin mutumcin da kuka saba. Kai Hasan zo mu je." Ajiyar zuciya a fili Malam Hasan ya saki, jiki a sanyaye ya rufa wa Kawu baya suka fita. Bayan fitar Kawu daga Inna har Zuwaira babu wacce ta yi mata magana, ganin haka ya sa Rakiya ta ɗan samu ƙwarin gwiwar shiga ɗakin da gawar Fatihu take. Tana tsoma ƙafa cikin tsawa Inna ta ce. "Kada ki sake ko da wasa ki taɓa mini gawar jikana. Idan kin so kuma kin ga dama kina iya haihuwar naki, tun da ke dai kin zama ƙaddara wacce ba ta da zuciya." Shiru Rakiya ta yi sannan ta fito bakin bishiyar darbejiyar da ke tsakar gidan ta zauna. Tana nan zaune Zuwaira ta fita ta fara sanarwa da maƙota, cikin ƙanƙanin lokaci maƙota da abokan arzikin Inna da suka cika gidan. Sai dai a yadda Rakiya ta lura kowacce mace ta shigo da irin wulaƙantacan kallon da take jifanta da shi. Wanda hakan ne ya alamta mata ruwa ba ya tsami banza, don ta tabbata akwai maganar da Zuwaira ta sanar da su a kanta. "Don Allah ki dubi yarinyar nan kamar mutuniyar arziki, yanzu wa zai ce za ta iya aikata rashin imanin nan haka." Rakiya ta ji wata tsohuwa ta furta ƙasa-ƙasa, tana cikin nazarin kalaman tsohuwar ta sake jin wata ta ce. "Ke kuma Tatu kamar ba ki san karuwancin matan birni ba? Yoo shi ma Hasan ɗin ai an ce ba banza ta bar shi ba." Wata tsohuwa da ke kusa da Inna, wacce kana ganin yanayinsu za ka fahimci ita ce babbar aminiyar Inna ta karɓe zancen da cewar. "To Allah na tuba kya ce ita, ai ki ce ubanta tuni ya gama da Hasan. Abin da tun bai san kansa ba ake ba shi a ruwa da abinci yake ci me ya rage kuma? Ai wallahi matuƙar kika cigaba da zama Kulu za ki zaunau ganin idonki." Inna ta sake yin tsumu abin duniya yana sake damunta, cike da sanyin jiki ta ce. "Abuwa ya zama dole na ɗauki matakin da ya dace." "Atoh ke da ɗanki amma wata juyar banza ta fi ki iko da shi ina dalili." Abuwa ta amsa cike da taƙama tana jifan Rakiya da mugun kallo, don yadda take ɗaga murya da gayya take faɗa don Rakiya ta ji. Suna cikin tattaunawa Malam Hasan da wasu maza biyu suka yi sallama domin ɗaukar gawar Fatihu. Kai tsaye ƙaramin ɗakin da aka suturta shi suka shiga, lokacin da Malam Hasan ya rungumo Fatihu suka haɗa ido da Rakiya. Wani sabon kukan ta fashe da shi, duk yadda ta so tausar zuciyarta sai hakan ya gagara. "Yaya haka kawai nake jin kamar ba zan rayu da Fatihu ba, don Allah ga amanarsa nan, ki yi masa duk abin da mahaifiya za ta yi wa ɗanta. Domin na yarda da ke, kuma Fatihu ɗanki ne. Zan so ki tuna da wasiyar nan tawa a ranar da Fatihu ya zama magidanci, a ranar da za ki aurar da shi domin wannan ranar ita ce mafi mafarinciki ga kowacce mahaifiya." Kalaman bankwanan da mahaifiyar Fatihu ta yi mata a baya suka faɗo mata a rai, cikin wata irin murya da ba ta yi zaton kalaman za su fito ba ta ce. "Shi kenan ba zan ga auren Fatihu ba? Shi kenan yadda na rasa Hafsatu mahaifiyarsa shi ma na rasa shi? Na rasa Fatihu mai ɗebe mini kewa kenan Baban Fatihu?" "Ban yi zaton Ruƙayyar da na sani mai sanin hukunci da dokokin Ubangiji za ta cigaba da furta waɗannan kalaman ba. Na yi tsammanin ke ce mutum ta farko da za ta lallashe ni a kan babban rashin da muka yi." Malam Hasan ya furta mata haka a lokacin da ya ƙarasa gabanta da gawar a hannunsa. "Ruƙayya!" Ya kira sunanta da wata irin muryar mai taushi, wacce take bayyanar da zallar soyayya, kulawa da tausasawa. Ba ta iya amsa masa ba sai ido da ta zuba masa waɗanda suka kaɗa jajir tana hawaye, ya sake kwantar da murya ya cigaba. "Yana da kyau ki tuna, Ubangijin da Ya ba mu Fatihu yana iya ba mu ninkinsa a lokaci guda..." "Amma ba da wannan juyar ba." Furucin Inna ya katse shi, waigowa suka yi lokaci ɗaya suna kallon Inna. Matan gidan da suka shigo gaisuwa duk suka yi carko-carko, don tun lokacin da ya ƙarasa wurin Rakiya suka saki baki da hanci suna bin su da kallo. Wasu su ce ta mallake shi, wasu kuma su ce mahaifinta ne ya mallake mata zuciyarsa, shi ya sa yake mutuwar sonta ya gagara rabuwa da ita. "Hasan kai muke jira fa." Kawu Sani ya furta, ganin Inna ta yi tsaye a gabansu ya sa shi cewa. "Lafiya dai Hasan ko da wani abu?" Cikin sauri Hasan ya ce, "A'a babu komai mu je Kawu." Daga haka ya wuce suka fita da shi, sai dai har ya kai soro yana jin gunjin kukan da Rakiya take yi mai tsuma zuciya. Inna kuma ta koma ta zauna ƙawayenta suka cigaba da ƙus-ƙus suna zuga ta. Cikin lokaci ƙanƙani aka sallaci Fatihu aka kai shi makwancinsa, da yake rasuwar ƙaramin yaro ce daga mutanan ƙofar gida har matan cikin gidan ba su wani daɗe ba kowa ya watse sai tsirarun ƙawayen Inna da suke shirin ganin ƙwal uwar daka. BAYAN SALLAR ISHA'I Kawu Sani, Inna, Malam Hasan da Rakiya ne zaune a ɗakin Inna. Kusan kowannansu fuskarsa a haɗe take babu walwala, Kawu Sani ya dubi Malam Hasan ya ce. "Idan na fahimce ka Hasan, tun da har zaman can ya gagara za ka dawo nan gidanka wanda ka gada daga wurin mahaifinka?" Malam Hasan ya gyaɗa kai ya ce, "Kawu a can ɗin ne ba a samun cinikin faskaren sosai, dakon da nake haɗawa da shi yanzu sai a hankali, shi ya sa ma na yanke wannan shawarar ta mu dawo nan gida." Kawu Sani ya dubi Inna da ta cika fam ya ce, "Kulu kin ji abin da Hasan ya ce ko? Da ma kuma wannan gidan kin san gidansa ne da ya gada a wurin mahaifinsa. Don haka zai dawo tare da iyalinsa, idan na sake na ji wata magana marar daɗi daga gare ki wallahi ranki sai ya yi mummunan ɓaci." Sai da Inna ta furzar da iska mai zafi sannan ta ɗago ta ce, "Na ji duk abin da ka faɗa Yaya, amma kuma ni ma ina da sharaɗi." Dam! Ƙirjin Rakiya da na Malam Hasan ya buga kusan lokaci ɗaya, Kawu Sani ya dube ta yana karantar yanayinta ya ce. "Muna jin ki." "Ka yi haƙuri Yaya ba rashin kunya zan yi maka ba, amma dai Hasan ɗana ne. Kuma ni da kai ba ma samun kowacce irin matsala sai a sanadiyyar matarsa. Amma ƙiri-ƙiri an shanye..." "Kulu ba na san ƙananan maganganunki marasa lissafi." Kawu Sani ya katse ta a ɗan tsawace, wani abu ne ya sake tokare Inna. Ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce. "Sharaɗina mai sauƙi ne Yaya, don gaskiya ba zan zuba ido rayuwar Hasan ta ƙare babu 'ya'ya ba. Duk cikin 'yan'uwansa shi kaɗai ne bai samu wani cigaban ku zo mu gani ba, ga Gali nan tare suka yi aure 'yarsa Suwaiba mai shekara goma har samari sun fara tsayar da ita. Don haka na yanke shawarar a wannan karon sai ya auri Zuwaira." Da wani irin firgici Rakiya da Malam Hasan suka ɗago suna kallonta cike da zallar tashin hankali. GIDANSU FAUWAZ Jim Abba ya yi yana nazari, cike da gamsuwa da shawararta ya ɗago ya ce. "Maganarki a kan hanya take Tani, domin a makarantar allo ne kaɗai zai samu tarbiyyar da muke buƙata tun da ya riga da ya raina mu. Amma ban da lalacewa ta yaya yaro kamar Fauwaz da bai wuce shekara goma zuwa sha biyu ba har ya fara bin dare yana yi mana ɗauke-ɗauke." Tani ta saki ajiyar zuciyar farinciki, amma sai ta ɓoye jin daɗinta ta aro fuskar damuwa ta lulluɓawa fuskarta ta ce. "Shi ne tashin hankalin, amma idan aka kai shi makarantar allo zai koyi neman na kansa har ya iya tsayawa da ƙafarsa. Ka ga a can bai ɗauki na wani ba ballantana ya janyo mana magana, amma matuƙar muka cigaba da zama da shi a haka har 'yar uwarsa sai ya koyawa." Abba ya yi zaraf ya ce, "Wannan gaskiya ne Tani, wallahi shi ya sa nake ƙaunarki. Saboda kina da hangen nesa da sanin ya kamata." Tani ta saki murmushin jin daɗi, sannan ta cigaba da ɗora shi a kan shawarwarin da zuciyarta take saƙa mata wacce take gani ita ce hanya mai ɓille mata. Hawaye bibbiyu ne suka shiga sintiri a saman fuskar Fauwaz, a hankali ya ja ƙafa ya shiga wurin Abida da har lokacin take cikin mawuyacin hali. Ba shi da wata mafita, domin bai san kuma abin da zai yi mata ba. Don haka ya rungume ta ya fashe da kuka yana jin kewar mahaifiyarsa. Jikinta zafi ya ji shi zau kamar wuta, bakinta yana rawa cikin sanyin murya ya ce. "Yaya... mutuwa... zan yi." Girgiza kansa ya yi cikin kuka ya ce, "Ba za ki mutu ba Abida, da safe zan sai miki magani da kudun da na samo." Idanunta a lumshe suke don ko iya buɗe su ba ta yi, ta ɗago hannu tana laluben fuskarsa. Da sauri ya riƙo hannun ya ce, "Me kike so Abida?" "Ya... ya... ba na son na mutu na bar ka a wurin Aunty, yanzu Abba ya daina sonmu." Fauwaz ya kwantar da kansa a fuskarta ya ce, "Ba za ki mutu ba kin ji Abida, Abba kuma ba daina son mu ya yi ba Aunty ce take faɗa masa laifinmu. Shi kuma duk abin da ta faɗa sai ya yarda da shi. "Zan sha ruwa." Ta furta masa a galabaice, sai da ya kwantar da ita sannan ya miƙe da sauri ya ɗebo mata ruwa. Ta sha ruwan sosai, ragowar kuma ta ce ya shafa mata a jikinta don ta ji daɗi. Cikin hukuncin Ubangiji ya ji zafin jikin ya ragu da ya zuba mata ruwan, don haka yana zaune yana gyangyaɗi shi da ita bacci ya ɗauke su, ba shi ya farka ba sai da aka fara kiran sallar asuba. Lokacin da ya tashi idon Abida biyu, a wannan karon jikinta babu zafi sosai. Sai dai numfashinta da take fitarwa sama-sama, sai da ya yi mata sannu ta amsa a hankali sannan ya miƙe domin ya ɗauro alwala don ya tafi masallaci. Har ya je bakin ƙofa ta ɗaga masa hannu, don yadda numfashinta yake fita ya sa ta gagara furta sunansa da ƙarfi. "Yayy... yaya." Ta furta a sarƙe ganin har zai fita bai ganta ba, da sauri ya koma ya ce. "Ga ni Abida me kike so?" "Na yi mafarki... da Umma, ta ce... ka kusa daina wahala... da ni." Ta furta a wahalce, sai ta cigaba da cewa. "Ta... kuma ce na gaishe ka." Murmushi mai sauti Fauwaz ya saki cikin jin daɗi ya ce, "Allah da gaske Abida? Na ji daɗi sosai, ni kuma tun da Umma ta rasu sau biyu na taɓa mafarki da ita." Murmushi ta sakar masa, sai ya sake miƙewa zai tafi masallaci ta sake riƙo hannunsa. "Yaya ina son... na yi kuɗi... don mu koma wani gidan... Aunty ta daina ganinmu." "In Shaa Allahu idan na girma na samu kuɗi zan gina mana gida mu koma can." Ya furta mata kalaman har cikin zuciyarsa, sai a lokacin ya fita daga ɗakin ya je ya ɗaura alwala. Yana gama alwala ya ga mahaifinsa ya fito shi ma, babu wanda ya yi wa wani magana har suka fita. Suna hanyar masallaci Abba ya ce. "Ya jikin Abidan?" Kamar Fauwaz ba zai amsa ba, sai ya danne zuciyarsa ya ce. "Da sauƙi." Daga haka suka ƙarasa masallaci, sai da aka idar da sallah Fauwaz ya jima yana yi wa Abida addu'ar Allah Ya ba ta lafiya sannan ya fita. Kai tsaye wani ƙaramin asibiti ya nufa da ke Unguwa Uku da ƙafarsa, har lokacin da ragowar duhu a gari don haka yawancin babban titin Na'ibawa babu ƙananan motoci sosai sai manya. Kasancewar da ƙafa yake tafiya lokacin da ya ƙarasa Unguwa uku gari ya yi tangaran har rana ta fito, ƙaramin asibitin na kuɗi mai suna Farha Clinic ya shiga. A reception ya samu wata mata wacce da alama ba bahaushiya ba ce, sai da ya gaishe ta sannan ya miƙa mata kuɗin hannunsa gabaɗaya sannan ya ce. "Don Allah magani za ki ba wa ƙanwata, tana zazzaɓi sosai. Sannan mamana kafin ta mutu ta taɓa kai ta asibiti aka ce ƙodarta na ciwo ban sani ba ko ciwon ne ya tashi." Yadda yake maganar za ka fahimci kalaman daga zuciyarsa suke fitowa, sai dai da yake ba ta jin hausa sosai ya sa ta kira wani abokin aikinta wanda ya kasance bahaushe. Matashi ne siriri, fuskarsa a zagaye da baƙin gashi. Fari ne fat sai dai yana da ɗan ƙaton kai, sai da ya gama sauraronsa ya ce. "Ina mamanku ko babanku?" Muryarsa tana rawa ya ce, "Mamanmu ta rasu." "Babanku fa?" Ya sake jefa masa tambaya, ya lura da sauyin fuskarsa, sai ya kawar da tambayar da ya yi masa ya ce. "Likita don Allah ku ba ta magani tana jin jiki sosai, ko kuɗin ba su kai ba wallahi zan yi gwangwan na cika sauran." Tausayin Fauwaz ya kama shi, sai ya dafa kafaɗarsa ya ce. "Abokina nan asibiti ne, asibiti kuma ba sa bayar da magani kai tsaye har sai sun binciki marar lafiya, an yi masa gwaje-gwajen da ya dace sannan likita ya rubuta masa magani. Ka je gida ka samu wani babba ku kawo ta asibiti, idan likita ya duba ta sai ya ba ta maganin da ya dace ka ji." Tun bai dire kalamansa ba idanun Fauwaz suka ciko da ƙwalla, cikin damuwa ya gyaɗa kai don idan ya ce zai amsa masa kuka zai iya ƙwace masa. Ya karɓi kuɗin da ya ba su sannan ya juya ya tafi zuciyarsa cike da ƙuna, yana kuma fargabar halin da zai sake samun ta a ciki. A ƙasa ya ƙara komawa har Na'ibawa, har zai wuya 'yan lemo ya hango kemis ɗin Maman Junior tana ƙoƙarin rufewa don ya lura da alama abu ta ɗauka domin ba ta buɗewa da safe. "Maman Junior a ba ni magani." Ya furta yana miƙa mata kuɗin hannunsa, cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce. "Wone yiri magani?" "Ƙanwata ce take zazzaɓi, kuma kwanaki an ce ƙodarta tana ciwo." Zazzaɓin da ya ambata ta fi riƙewa, saboda yau da gobe da ake yawan sayen maganin zazzaɓi da sauran gama-garin cutuka a wurinta. Kemis ɗin ta buɗ ta shiga, sai ta haɗo masa maganin zazzaɓin maleria ta miƙa masa ragowar canjinsa. Gudu-gudu sauri-sauri a haka ya ƙarasa layinsu, tun daga farkon layin ya hango tsirarin yara a ƙofar gidansu. "Ikon Allah Ya wuce gaban komai, shekaran jiya fa Abida suna tare da Sumayya da ta gaishe ni ta ce min aikenta aka yi. Wai ita ce yau ta amsa kiran mahalicci, koico rayuwa tsakaninta da mahaifiyarta shekara guda kenan." Kalam maƙociyarsu da take shirin shiga gidansu suka daki kunnuwansa, waɗanda suka yi daidai da bugun zuciyarsa wacce take barazanar tarwatsewa. Share Pls Ummou Aslam Bint Adam 🌚 07062062624 [13/05, 18:20] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t SHAFI NA BIYAR A hargitse ya wurgar da ledar hannunsa jikinsa yana rawa ya ƙarasa ya riƙe hannun matar ya ce. "Umman Sumayya wace ce ta mutu?" Sototo ta yi tana kallonsa da mamaki, ganin haka ya sa shi girgiza hannunta yana ƙara tambayarta. Don haka ta ce. "Fauwaz wai kana nufin ba ka san Abida ta rasu ba? Ina ka je ne?" Bai jira ta dire kalamanta ba ya faɗa cikin gidan a guje, ita da ragowar matan da ke tsaye suka bi shi da kallon tausayi. Kai tsaye ɗakinsu ya shiga, sai dai yana shiga ya hango katifarsu da kayan da ya fita ya bar Abida da su a jikinta. Da wani irin sanyin jiki ya shiga, don har lokacin zuciyarsa wasu-wasin abin da kunnuwansa suka ji take yi. 'Abida ba ta mutu ba, ɗazu fa na fita na bar ta a wurin nan.' Zuciyarsa ta raya masa, amma sai ɗaya tsagin zuciyar tasa ya ankarar da shi. 'Idan ba ta mutu ba tana ina? Shin Umman Sumayya za ta yi maka ƙarya ne?' Cikin sauri ya fita daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Tani ya shiga. Daga can jikin bango ya hango Goggo Jamila ƙanwar mahaifinsu tana kuka, sai Tani da ke lungu tana sharɓar kuka waɗansu kitika-kitikan ƙawayenta suna rarrashinta, waɗanda sune suke sake ɗora Tani a duk turbar da take kai. "Kaico mutuwa! Yanzu shi kenan Abida ta tafi, yanzu ko kallon Fauwaz na yi dole hankalina ya dinga tashi. Yaran nan kullum suna tare, ta ina zai fara jure rashinta." Tani ta furta cikin kururuwa, ilahirin mutanen da ke ɗakin suka bi Fauwaz da kallon tausayi. Wani abu ne ya tokare masa maƙoshi, sai kuma ya ji wani irin sanyi tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa. Da ƙyar ya iya jan ƙafarsa ya fita daga ɗakin duk da ya ji Goggo Jamila tana ƙwala masa kira. Yana fita ƙofar gida ya ga Sumayya ƙawar Abida tana kuka, tana ganinsa kukanta ya ƙaru ta ce. "Yaya Fauwaz wai shi kenan ba zan sake ganin Abida ba? Shi kenan mun daina wasa da su 'yar gala-gala?" Motsa bakinsa ya shiga yi sai dai ya gagara furta koda kalma ɗaya, da sauri ya wuce ta ya nufi maƙabartar cikin sauri da yake a cikin unguwarsu take, yana fatan ya ga koda gawar Abida ce. Sai dai yana shiga ciki ya hango mutane suna fitowa, bai fasa tafiya ba har suka haɗu a hanya. Mahaifin Sumayya ne ya ce, "Fauwaz ina ka shiga tun ɗazu ana ta nemanka?" "Hmmm zai wuce ya tafi yawon banza, tun da shi ya saka a gaba. Me ka zo yi maƙabartar? Ai da ka yi zamanka a can ba sai ka zo ba." Abba ya furta yana yin gaba, ba tare da ya jira cewar Fauwaz ba. Yawancin mutane wuce shi suka yi, sai tsiraru da suke yi masa ta'aziya. Zannur abokinsa ne ya dafa shi ya ce, "Ka yi haƙuri Fauwaz, mu ƙarasa ka yi mata addu'a ba." "Me ya sa ne Zannur? Me ya sa rayuwa ta juya mini? Me ya sa duniyar ta yi mini zafi? Na rasa Umma a daidai gaɓar da ban zata ba, ga shi yanzu mutuwar Abida ta shammace ni. Me ya sa Abba ba zai fahimci halin da nake ciki..." Kuka mai tsuma zuciya ya ƙwace masa. "Saboda kowanne bawa akwai launin ƙaddarar da ke bibiyarsa, taka a haka ta zo maka. Ina fatan za ka yi addu'ar Allah sa haka ne mafi alheri. Yanzu mu je ka yi mata addu'a." Zannur ya furta yana jan hannunsa, cikin kuka Fauwaz ya ce. "Ina jin kamar ba zan iya zuwa na ga kabarin Abida ba." "Za ka iya, domin addu'arka tana da muhimmanci a gare ta." Da tausasawar Zannur Fauwaz ya ƙarasa gaban kabarin Abida, sai da ya ci kuka mai isarsa sannan ya kwarara mata addu'a. Tsakanin kabarin mahaifiyarsu da na Abida babu tazara sosai don haka ya ƙarasa ya yi wa mahaifiyarsu addu'a suka fito daga maƙabartar. Koda suka ƙarasa gida zaune ya yi a ƙofar gida, komai da kowa ya fita daga rayuwarsa. Domin ji ya yi rayuwar ta ishe shi, har fata yake yi ina ma ajalinsa ya riske shi domin ko kaɗan gani yake ba zai iya jure rashin Abida ba. Yana daga nesa yana hango mahaifinsa yana ta karɓar gaisuwar mutane. Yadda yake haba-haba wurin karɓar ta'aziyya ya sa shi tuna mahaifinsu na baya da ke bakin ƙoƙari wurin ganin ya kula da damuwarsu. Don a yanzu gani yake kamar an canza musu shi, haka aka cigaba da zaman makoki dangin mahaifinsa suna lallashinsa da ba shi baki. A cikin waɗannan kwanakin rayuwar ta yi masa sauƙi a fanin kyara, hantara da ƙalubalen da yake fuskanta a ɓangaren Tani da mahaifinsa. Sai dai ji yake da za a dawo masa da Abida da ya gwammaci ya cigaba da zama a cikin ƙuncin rayuwar da yake ciki. Wani babban abin da ya ɗaure masa kai da Tani yadda take haba-haba da shi, har idan aka gama girki take aikawa a kira shi, ta sa a ba shi nasa daban wai ya ci ya ƙoshi kada ya zauna da yunwa. Sai dai hakan ba ƙaramin sake hura wutar ƙiyayyarta ya yi a zuciyarsa ba, don haka a kodayaushe ta yi masa maganar abinci kalma ɗaya yake furta mata ya ƙoshi. Su kuwa dangin Abba ban da farinciki babu abin da suke yi, don Goggo Jamila cewa ta yi tabbas Fauwaz ba zai yi maraici ba. Ranar sadakar bakwai da safe, Abba yana zaune bayan da aka gama addu'ar bakwai kira ya shigo wayarsa. Saboda haniyar mutane sai da ya fita daga cikinsu ya koma bakin masallacin da ke kallo su, sannan ya ɗauka cikin sallama. Ba a iya amsa masa ba, sai jawaban tashin hankalin da aka rattabo masa. Tun bai gama wayar ba, ya zame hular kansa yana faɗin. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Shiru ya yi ya cigaba da sauraro har aka gama jawabin aka yanke kiran, daɓar ya zauna a kan dandamalin da ke gaban masallacin cikin firgici da tashin hankali ya ce. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Allahumma ajir ni fi musibati, wa aklifni khairan minha." Yana gama faɗar haka ya yanke jiki ya faɗi. KAWU SANI Murmushin takaici Kawu Sani ya saki, Inna ta sake tsuke fuska don a wannan karon ta ci alwashin dole Malam Hasan ya bi umarninta. "Ina ce wannan tsohuwar magana ce Kulu? Ba tun kafin Zuwaira ta yi auren farko aka yi maganar ba yaron nan ya ce ba ya yi mata son aure sai na 'yan'uwantaka?" Kawu Sani ya wurga mata tambaya, Inna ta cure baki wuri ɗaya ta ce. "Haka ne." Kawu ya ce, "To a yanzu ma babu ita..." "Don Allah ka yi.haƙuro Kawu, Baban Fatihu zai aure ta a wannan karon." Rakiya ta yi ƙarfin halin furta haka, wani irin kallo Malam Hasan ya wurga mata cikin wata irin murya ya ce, "Ni na furta miki haka Rakiya?" Rakiya ta girgiza kai sannan ta ce, "A wannan karon matuƙar ba ka auri Zuwaira ba ni ma na gama zaman aure da kai." A wannan karon shiru ɗakin ya yi, Kawu Sani ya numfasa ya ce. "Ka ji abin da matarka ta ce?" Gyaɗa kai Malam Hasan ya yi sannan ya ce, "Na amince zan aure ta." Rakiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci tana jin kishin mijinta, domin idan ta ce ba ta ji kishin kalamansa ba ta yaudari kanta. Amma ta san hakan shi ne kwanciyar hankalinsu gabaɗaya, don ba za ta taɓa manta tarzomar da suka sha a shekarun baya ba. "AlhamduLillah! Ma Shaa Allah, Allah Ya yi maka albarka Hasan. Ubangiji Ya haɗa kan iyalinka." Kawu Sani ya furta sannan ya mayar fa kallonsa wurin Inna ya ce. "Kada na ji ko na ga wata fitina ta ɓullo daga wurin Zuwaira, domin ke da ita duka bakinku ɗaya." Inna ta amsa masa zuciyarta fes don ta san ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba. Zuwaira tun da ta ji maganar aurenta da Malam Hasan ta shiga firirta da feleƙe, sai dai duk abin da take yi ko kaɗan Rakiya ba ta nuna mata alamar ta fahimce ta na. A cikin kwana biyun da suka yi tsangwamar da Inna take yi mata ta yi sauƙi, sai dai duk wanda ya zo gaisuwa sai ta ji wata mummunar magana daga gare shi wacce za ta sosa mata rai. Ana cikin haka har Malam Hasan ya koma ya kwaso musu kayansu, wanda ya tabbatar mata da Kawu Sani ne ya ba shi kuɗin ɗawainiyarsu. Ɗakunan da ke cikin gidan ciki da falo-falo ne guda biyu, sai falle-falle guda biyu. Ciki da falon ɗaya su Rakiya suka ɗauka, sai Inna ta haɗe kayanta a ciki da falo ɗaya ta ce idan an ɗaura aure Zuwaira ta ɗauki falle-falle guda biyu. Satinsu ɗaya da komawa Malam Hasan ya kama awakinsa da Inna take yi masa kiwo guda biyu ya sayar, sai suka rage saura tinkiya ɗaya da rago ɗaya. Da wani kaso daga cikin kuɗin ya biya sadakin Zuwaira, ragowar kuɗin kuma ya kafa jarin turare irin wanda ake yawo da shi a kwando ana sayarwa da kayan yari na cikin glass. Yadda Zuwaira take rawar kai abin ba ƙaramin ba wa Rakiya mamaki ya yi ba, saboda wasu kalaman da abin da take yi sam ba su dace a gaban Inna ba. Amma sai ta ga ita Inna ko a jikinta, a daren ranar Malam Hasan bai shiga gidan ba sai bayan sallar isha'i. Hannunsa ɗauke da kwandon turarensa, ɗakin Rakiya ya shiga ya same ta zukuɗum tana tunani. "Rakiya ba za ki daina tunanin nan ba? Ko kina son ki dinga ɗaga mini hankali idan na fita." Malam Hasan ya furta cikin damuwa, ganin haka ya sa ta saki murmushin yaƙe ta ce. "Tunaninka nake yi fa ba na Fatihu ba." Ya ɗan haɗe fuska cikin wasa ya ce, "Kina tunanin ɗanki dai." Ta saki murmushin yaƙe ta ce, "Har abada ba zan daina tunanin Fatihu ba." "Yanzu dai ba wannan ba, ga kayan da zan fara saidawa. Ki saka mini albarka da bakinki mai albarka." Ya furta yana miƙa mata kwandon turaren da glass ɗin yari, fara'arta ce ta faɗaɗa. Cikin jin daɗi ta shiga kwarara masa addu'a, sai da ya gama amsawa sannan ya ce. "Zuba mini abinci." Hararar wasa ta yi masa ta ce, "Kai da amarya take jiranka, ko ka manta ne?" Guntun tsaki ya saki, yana jin wani tsantsanin Zuwaira. "Ni fa na gaji da kara tun da ba ku san zuru ba, na ga alamar idan na yi shiru sai ta gama da kai tukunna." Suka ji an furta a tsakiyar kansu, a tare suka waiga suka ga Zuwaira riƙe da labule fuska a murtuke. "Mene ne haka Zuwaira?" Malam Hasan ya furta, kamar jira take yi ya dire ta ce. "Kwanana na biyo, tun da na ga ana ƙoƙarin cin amana ta. Don ma dai a banza abin yake wai an tsikari kakkausa, tun da ba iya ƙyanƙyashe ƙwan take ba..." Tass! Malam Hasan ya ɗauke fuskarta da mari, sannan ya nuna ta da yatsa rai a ɓace ya ce. "Idan ganganci ya sake biyo dake ta cikin ɗakin nan sai na tattaka ki." Da sauri Rakiya ta sha gabansa ta ce. "Haba Abban Fatihu, me kake yi haka?" Yana shirin ba ta amsa Zuwaira ta fita da sauri tana sakin kuka tamkar wacca aka ba wa saƙon mutuwa. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ka ga za ka janyo mini ko? Rakiya ta furta, Malam Hasan ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Kada ki damu don Allah, na sanki sarkin tsoro ce." "Hasan! Hasan! Za ka fito ne ko kuwa sai an ba ka izinin fitowar?" Inna ta furta cikin ɗaga murya, kusan lokaci ɗaya Rakiya da Malam Hasan suka dubi juna. Suna nan zaune suka ji an ɗaga labulen ɗakinsu. "To sake shi baƙar munafika, tun da ba kwananki ba ne sai ki ba shi dama ya yi gaba." Inna ta faɗa tana wurga wa Rakiya harara. "Ga ni zan fito yanzu." Malam Hasan ya furta, tun bai gama rufe baki ba Inna ta nuna masa hanya ta ce. "Fita mu je na ce maka, shashasha bawan mace." Babu yadda ya iya, haka ya bi bayan Inna jiki a saluɓe, don ba ya son ya sake wata maganar ya ja wa Rakiya wani sabon zagin ko baƙar magana. Tamkar raƙumi da akala haka ya bi bayan Inna har suka fita tsakar gida, ɗakin Rakiya ta nuna masa ta ce, "Maza ka shiga wurin amaryarka, idan ka ga dama kada ka taɓuka abin arziki. Sakarai kullum kana can wurin da babu ƙaruwa ballantana mamora." Jiki a sanyaye ya nufi ɗakin Rakiya bakinsa ɗauke da sallama ciki-ciki, yana shiga Rakiya ta yi farat ya tare shi cike da kissa da kisisina. Tsaye Malam Hasan ya yi yana kallon ikon Allah, don rashin kunyarta ba ƙaramin mamaki take ba shi ba. Ya san dama ba za a taɓa haɗa kunyar budurwa da ta bazawara ba, amma kuma ko kaɗan bai fuskanci haka daga wurin mahaifiyar Fatihu ba, domin ita ma a bazawara ya aure ta. "Barka da zuwa angona." Zuwaira ta furta tana dafa ƙirjinsa, mamaki ne ya sake mamaye shi da ya ga ta ware kamar ba ita ce ta fita tana zabga ihu daga ɗakin Rakiya ba. Bai amsa mata ba, sai gefen gado da ya zauna yana haɗe fuska. Ganinsa hannuwa suna dukan cinya ya sa ta wurga masa tambaya, kwata-kwata ya manta da sayen wani naman kazar amarci. Don wannan auren ya yi ne kawai da zummar ko Rakiya za ta samu salama a wurin Inna. Abincin da Inna ta girka Zuwaira ta miƙa masa, kamar ba zai karɓa ba sai kuma ya ci loma biyu ya ce ya ƙoshi. Zuwaira da kanta ta dinga jan Malam Hasan cikin kissa da kisisina har mai afkuwa ta afku a tsakaninsu. Don haka koda gari ya waye ko ƙofar ɗaki Zuwaira ƙin fitowa ta yi, wai ba ta jin daɗin jikinta don a dole ta nuna wa Rakiya wani abu ya gifta a tsakaninsu. Da safe koda Malam Hasan ya fito zai shiga ɗakin Rakiya fir Inna ta hana shi, a cewarta ba kwananta ba ne don haka ba ta da haƙƙi a kansa ranar. Yana ji yana gani ya tafi tallan turaren, don kwandon turarensa ma sai Inna ce ta ɗauko masa. Sannu a hankali zaman Rakiya da Zuwaira ya fara sauya salo duk da dama ba zaman daɗi suke yi ba. Sai Zuwaira ta ɓullo da duk ranar girkin Rakiya tun rana za ta fara kwanciya ta ce ba ta da lafiya, idan yamma ta yi sai ta haye gado ta rufa da bargo. A kan dole idan Malam Hasan ya dawo Inna take tilasta masa kwana a wurin Zuwaira. Saboda wani lokacin cewa take ana tsorata ta, ko ta ce motsi da giftawar mutum take gani. Tun yana ɗaukar abin kamar gaske har ya fara fahimtar makirci ne, damuwarsa ta ninku musamman da yake buƙace da matarsa Rakiya. Don a ƙalla ya kai sati uku ƙwarara bai kwana a ɗakin Rakiya ba, ko da rana bai isa ya shiga ɗakinta ba sai Inna ta fara yi musu masifa. Watarana Inna ta fita unguwa, yana zaune a bakin kasuwa ya ga wucewarta. Farinciki ne ya lulluɓe shi, don haka cikin sauri ya ɗauki kwandon turarensa ya wuce gida. Ya ci sa'a Zuwaira ba ta tsakar gida, don haka ya faɗa ɗakin Rakiya. A kwance ya same ta idanunta suna kan silin, da yake ta yi zurfi a duniyar tunani ko motsinsa ba ta ji ba. Sai da ya kira sunanta sannan ta kalle shi, da sauri ta miƙe tsaye kamar ta ga sabuwar hallita. Malam Hasan ya zuba mata idanu ganin lokaci ɗaya ta zabge duk ta rame, a hankali ya fara takawa wurinta Rakiya ta matsa da sauri ta faɗa jikinsa sai ta ji kuka ya ƙwace mata. Kukan da ta ɗauki kwanaki tana son zubar da hawayensa ba ta samu sukuni ba, tausayinta ya ji har cikin ransa. Ya saka hannu yana bubbuga bayanta, cikin so, ƙauna da tausaya ya ce. "Ki yi haƙuri farincikina." Sai da ta share hawayenta ta ce, "Ka fita kada Inna ta dawo." Bai iya amsa mata ba, sai janyo ta da ya yi ya sake riƙe ta tsam. Tana son ƙwace kanta amma ta kasa, ya sunkuya saitin fuskarta ya furta. "Na yi kewarki, kullum da tunaninki nake kwana nake tashi. Ban san ya zan ɓullo wa Inna ba." "Mu cigaba da haƙuri, watarana sai labari." Rakiya ta furta a sanyaye, don shi kansa ba ƙaramin tausayinsa take ba. Girgiza mata kai ya yi ya ɗago da fuskarta ya ce. "Ba zan iya ba Rakiya, saboda ina shiga haƙƙinki. Ya zama dole na nemar mana mafita."Ba ta amsa masa ba, ya cigaba da aika mata kalaman soyayya masu kassara jiki, a hankali yake aika mata da saƙon soyayya mai cike da kewarta. Rakiya mace ce da ta san kanta, don haka ta shiga mayar masa da martani. Kowannensu sai da ya nuna wa ɗan'uwansa ya yi matuƙar kewarsa, don yadda ta ga Malam Hasan ya birkice mata sai ka yi tsammanin babu mace a kusa da shi duk tsawon kwanakin da suka ɗauka. "Ka tashi ka gyara jikinka ka fita lokaci yana tafiya." Rakiya ta furta masa, ga mamakinta sai ji ta yi hawaye ya gangaro daga idonsa. "Me ya faru kuma?" Ta tambaye shi muryarta tana rawa, don ta fahimci dalilin hawayensa. "Ina sonki matata, ina ƙaunarki farincikina. Idan na fita yanzu ban san lokacin da zan sake jin ɗuminki ba, a cike nake da kewarki zuciyata ina jin kamar kada na matsa daga kusa da ke." Yadda yake magana ne ya kashe mata jiki, amma gudun kada a samu matsala ya sa ta shiga tausarsa. Suna nan maƙale da juna suka ji sallamar Inna, tamkar waɗanda suka ga mala'ikan ɗaukan rai haka suka firgice lokaci ɗaya kowannensu gabansa ya shiga faɗuwa. Tun shigowar Inna gidan ta hango takalmin Malam Hasan a ƙofar ɗakin Rakiya, don haka rai a ɓace ta ƙarasa ɗakin cikin masifa ta bankaɗa labulen ɗakin. Ta windon uwar ɗakin ta hango su da yake a gadon Rakiya a saitin windon yake. A kunyace su Rakiya suka ja zanen gado suka rufe jikinsu. Inna ta ja dogon tsaki cikin masifa ta ce. ."Ke dai wannan an yi jarabaiyar yarinya, yanzu don masifa da rana tsaka ma sai da kika yaudaro mini ɗa? Ki bar shi ya tafi nema amma kin kanainaye shi a ɗaki, wato kin samu dama na fita ko? To ka tashi ka fito ka je ka yi wanka ka fita nema, shashasha sai kace ba shi da wata matar don jarabar tsiya." Inna ta yi furucin da ƙarfi, jin Hasan ya amsa ciki-ciki ya sa ta ce. "Za ka fito ko sai na fito da kai da kaina?" A kunyace Malam Hasan ya zura wata doguwar rigarsa ya fito, ya nufi banɗaki yana jin ɗacin ɓacin rai a zuciyatsa. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [15/05, 18:55] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA SHIDA ABBAN FAUWAZ Da sauri mutanen da ke ƙofar gidan suka ƙarasa wurinsa suka shiga kiran sunansa, sai dai ganin ba ya numfashi ya sa aka yi gaggawar ɗaukarsa zuwa asibiti. Tun da Tani ta ji abin da ya faru ta saki sabon kuka da kururuwa, da farko abokan Abba cewa suka yi ta bari su je asibiti su ga yadda yanayin jikinsa zai kasance tukunna. Amma ganin yadda Tani ta ɗaga wa mutane hankali ya sa a kan tilas aka bar ta ta tafi asibiti. A lokacin da ta ƙarasa bacci yake yi ana ƙara masa ruwa, tana nan zaune bayan wani lokaci ya buɗe idonsa ya zuba wa fankar da ke wulwulawa ido kamar yana ƙidaya adadin gudun da take yi. "Sannu Abban Fauwaz!" Tani ta furta tana matsawa gabansa, a hankali ya dube ta cikin sanyayyar murya ya ce. "Tani ina cikin tashin hankali." Lumshe idonta ta yi cikin nuna damuwa ta ce, "Bari na fara kiran likita ya duba jikinka Alhaji. Saboda jininka ya hau, don haka suka ce idan ka farka a sanar da su." "Tani babu buƙatar kiran likitoci, don lalurar da ta afko mini babu likitan da ya isa magance mini ita." Abba ya furta da muryar damuwa, riƙo hannunsa Tani ta yi ta ce. "Komai ya yi tsanani maganinsa Allah." Abba ya jinjina kai sannan ya ce, "Wannan haka yake, amma abin da nake so ki fahimta. Irin wannan guguwar da ta taso mini, irinta ce wacce ake cewa gobara daga teku maganinta sai Allah." "Alhaji har yanzu riga kake ɗinka mini babu wuya, ban fahimci inda maganganunka suka sa gaba ba." Tani ta furta masa tana tsare shi da ido. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. "Kuɗin da na ara kwanaki, waɗanda na zuba a kayan da aka tafi da su kwatano da Ghana ne suka halaka." "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Ta furta a hargitse cike da tashin hankali ta ce, "Ban fahimci sun halaka ba Alhaji?" Abba ya furzar da iska mai zafi ya ce, "Kayanmu ne aka kama su, sakamakon an samu ƙwayoyin hodar iblis a cikin wasu daga cikinsu, Alhaji Ɗan gaske ya ce mu yi ta addu'a idan ba a nemi masu kayan ba domin hukunta su." "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Alhaji wannan wacce irin jarrabawa ce? Yanzu ya za ka yi da kuɗin wurin Alhaji Dikko?" Tani ta furta masa, jim ya yi yana nazari sai ya ɗago ya ce. "Wallahi ban sani ba Tani, ban san yadda za mu kwashe da shi ba." Zumbur! Ta ga ya miƙe, cikin sauri ta riƙo shi ta ce. "Yi a hankali Alhaji, ko a kira likitan ne?" Girgiza mata kai ya yi ya sauka a kan ƙafafuwansa sannan ya ce. "Gida zan tafi." Duk yadda Tani ta so hana shi fir ya ƙi amincewa, sai da ya fita harabar asibitin ya ci karo da abokansa waɗanda suka kawo shi asibitin. Bayan an gama biyan kuɗaɗen da aka kashe suka wuce gida. A washegarin abin da ya faru, sai da ta tabbatar da Abba ya fita, saboda tun a ranar Alhaji Dikko ya fara doka masa waya don ya ji makamar wurin da kuɗinsa za su ɓullo. Saboda ya ji labarin abin da ya faru da Abba a wurin mutane da dama. Abba ya tafi wurinsa ne domin ya ba shi haƙuri, ya kuma nemi alfarmar ya ɗaga masa ƙafa zuwa wani lokacin kaɗan. Uwar ɗaki Tani ta shiga ta ciro wata lamba a takarda, sai da ta kwafe lambar a wayar sannan ta latsa kiransa. Daga can ɓangaren ta ji an ce, "Kunama mugunyar ƙwaro, ga ki da harbi mai kai mutum ƙasa." Murmushin jin daɗi ta yi, kanta ta ji ya ƙara girma. Cike da isa ta ce, "Kuma ko a yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli ya ci gwagwgwaɓar riba." Shi da ita duka suka bushe da dariya. Yadda Tani ta shagala ne ta manta da Fauwaz yana cikin gidan, Fauwaz ya fito zai fita ya ji tana cewa. "Amma ya aka yi wannan tarkon namu ya kama shi yanzu? Ni fa na ɗauka sai tura ta kai bango. Ka san fa duka kuɗin da ya ranto na saka shi ya zuba a waɗannan kayan da yake shi mahaukaci ne." Daga can ɓangaren ya ce, "Ki ce ya ɓallo wa kansa ruwa. Yanzu kusan nawa ya ranto?" Shiru Tani ta yi tana nazari sannan ta ce, "A ƙalla za su kai miliyan uku, kuma daɗin da na ji maganin wurin malamin nan da ka karɓo mini bai karye a jikinsa ba." "Ke fa bala'i ce Tani, amma ki ɗan ɗaga masa ƙafa mana." Mutumin ya furta yana sakin murmushi, ita ma murmushin ta saki ta ce. "Wallahi tallahi ko Alhaji zai yi yawo tsirara ba zan rangwanta masa ba, don tun kafin yarinyar nan ta mutu tuni na yi masa farraƙu da su. Tsakaninsa da su sai tswangama, kuma duk abin da na faɗa ta zauna." "Sai da ke 'yar kunama." Ya furta cikin kanbabawa, jin haka ya sa ita ma ta amsa suka kwashe da dariya sai ta ce. "Lighter ka ƙara riƙe wuta fa, saboda daga wurin Alhaji Dikko kai tsaye tashar jirgin ruwa zai nufa." Amsa mata yi sannan ta ce za ta kira shi gada baya. Fauwaz da ke jin duk tattaunawar da Tani ta yi, duk sai ya ji tausayin mahaifinsu ya kama shi. Duk wani haushi da ƙullatar da ya yi masa ya saɓe, sai ya sake jin tsoron Tani ya sake mamaye shi. Duk yadda yake fasalta rashin imanin Tani sai ya ga ashe ta doke harsashensa. 'Yanzu ta ina zan fara nusar da Abba wace ce Tani?' Fauwaz ya raya a ransa, ganin ba shi da tsayayyar mafita ya sa shi barin wurin ya shiga ɗakinsa yana tunanin yadda zai ɓullo wa al'amarin. Tun daga wannan ranar kwanciyar hankali ta yi ƙaura a wurin Abba, ban da Tani da a zahiri take nuna masa tana cikin damuwa amma a baɗini ta fi kowa farinciki da al'amarin da ya same shi. Sai dai kuma ba ta so al'amarin ya faɗo a daidai wannan gaɓar ba, don tana gudun kada kwaɓarta ta yi ruwa tsululu asirinsu ya tonu. A ɓangaren Fauwaz ya samu sauƙin tsauwalawarta da ta Abba sosai, saboda kusan kullum mahaifin nasa ba ya zama a gida. Yau yana tashar jirgin ruwa yana fafutukar a saki kayansa, gobe yana ƙofar gidan Alhaji Dikko. Ita kuma Tani ya rasa abin da take ƙullawa kusan kullum da mahaifinsa ya fita take shurar takalminta ta fita. Ana cikin haka ne wani a cikin tashar jirgin ya ce zai yi masa hanyar da kayansa za su fito, amma sai ya biya kuɗi kusan dubu ɗari biyar. Jin haka ya sa Abba ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka ya dinga buga-buga tsakanin abokan kasuwacinsa na goro ya ranto kuɗi dubu ɗari biyar. Tun da Abba ya byar da kuɗin, mutumin yake yi masa yawo da hankali. Yau yace ba ya nan gobe ya ce an tura shi wani gari, daga ƙarshe ma har ya daina ɗaukar wayarsa. Ana cikin haka Alhaji Dikko ya tayar masa da ɓalli, don har hukuma ce ta shiga tsakaninsu. Don haka Tani ta shawarce shi da ya sayar da gonakin da ya saya idan ya so sai ya biya kuɗaɗen da suke kansa. Kai tsaye lambar Gambo dillali ya nema, amma sai ya ji ta a kashe ba ta shiga. Da yake a buƙace yake da kuɗi kai tsaye 'yan dillalai ya nufa yana nemansa. A nan mutanen wurin suka jaddada masa cewar ya bar garin, sakamakon dama can asali ba ɗan jihar Kano ba ne. Buƙatar da ke tafe da shi ya sanar da su, a nan Shamsu dillali ya shige masa gaba wurin tallata ƙaton gonakin nasa. Ko sati guda ba a rufa ba cikin hukuncin Ubangiji aka yi dace da samun mai saya, bayan da suka je aka duba gonakin suka yi ciniki ya ɗebo takardu ya miƙa masa. Da yake sun ga a buƙace yake da kuɗi bai wani ci riba da gonar ba, don kusan yadda ya saye su haka ya sayar da su. Yana karɓar kuɗin kai tsaye ya kai wa Alhaji Dikko ko gida bai koma ba, ya kuma nemi alfarmar ya ɗaga masa ƙafar sauran zuwa wani lokacin. Sai da suka yi rubutu a gaban wani ɗansanda kowa ya saka hannu sannan Abba ya wuce gida. Tun bayan fitarsa Tani ta cika fam da farinciki, a lokacin Fauwaz yana ɗebo ruwa yana zubawa a drump. A wani zuwa da ya yi zai juye ruwan ya ji muryarta can ƙasa tana cewa. "To yanzu me ya rage? Ai ƙarshen tuka-tuka tik, mun yi waya da shi ya sayar da gonar. A tsammaninsa sayar da wannan gonar shi ne rufin asirinsa, bai san ɗaya daga cikin manyan ƙofofin tashin hankalinsa ne suka buɗe ba." Amsa mata aka yi daga can ɓangaren sai ta cigaba, "Wai ka san waye Alhaji Dikko a kan kuɗi kuwa? Kai dai ka zuba ido ka sha kallo." Fauwaz ji ya yi zuciyarsa ba za ta iya ɗauka ba, don haka ya sauke bokitin kansa ya ƙarasa cikin ɗakin ya ce. "Ke wacce irin mace ce da ba ta tsoron Allah?" "Irin wacce mahaifinka yake muradin rayuwa da ita." Tani ta ba shi amsa tana tsare shi da ido, wata irin tsanarta ta sake mamaye shi. Ya dube ta ido cikin ido ya ce. "In Shaa Allahu yau zan sanar da Abba wace ce ke, da irin cutarwar da kike yi masa." Wata irin dariyar izgilanci ta saki ta ce. "Ai babban kuskuren da ka tafka a rayuwarka shi ne gangancin sauraron kalaman da nake yi yanzu. Waɗanda suka ingiza ƙeyarka har ka tsoma mini baki, kana tsammanin furucinka zai yi tasiri a wurin mahaifinka?" Ta wurga masa tambaya tana tsare shi da ido, shi ma ita yake kallo babu ƙiftawa. Yana jin kamar ya yi tsalle ya maƙure wuyanta, yana nan tsaye ya ji ta cigaba. "Da ace kalamanka suna da tasiri, da a daren da ƙanwarka za ta yi mushe sun ratsa jikin mahaifinka." Dum! Ya ji a tsakiyar kansa tamkar an buga masa guduma, ya runtse idonsa da sauri yana hasko fuskar Abida cikin mawuyacin hali. Tani ta nuna shi da yatsa cikin wata irin murya mai cike da zallar rashin imani ta ce. "Ka jira mummunan saƙon da zai iso gare ka..." Ba ta kai ga dire kalamanta ba, ta ji sallamar Abba ya shigo gidan. Haka ya sa ta saki murmushin ƙeta sannan ta rushe da kuka. ƊANBATTA Duk abin da yake faruwa Zuwaira tana daga ɗaki laɓe a jikin labule tana kallo. Farincii ne ya mamaye ta, don ita kanta ba ta san ya shigo ba sai hayaniyar Inna ce ta tashe ta. Sai da ta ga Malam Hasan ya shige banɗaki sannan ya fito tana yamutsa fuska, kan tabarmar da Inna ta shimfiɗa ta hau ta zauna. Cike da kissa da makirci ta ce. "Inna lafiya kike ta faɗa? Ni ma bacci ne ya kwashe ni da yake ba ni da lafiya, na kira Yaya kuma ya ce mini ya yi nesa da mu ya gangara sabon titi." Sakin baki Inna ta yi sannan ta ce, "Wato bayan cin amana har ƙarya Hasan ya koya kenan? Dole ya ce miki haka mana tun da yana liƙe a ɗakin baƙar munafukar nan." Zuwaira ta sake narke fuska ta ce, "Ai shi kenan, amma magani fa na ce ya kawo mini ɗazun." "To idan kika mutu ai ba asara ya yi ba, tun da ba 'yar gaban goshinsa ce babu lafiya ba. Bari ya fito zai zo ya same ni..." "A'a ki rabu da shi Inna, ni zan yi masa maganar. Idan kika masa zancan muna shiga ɗaki a kaina zai huce." Zuwaira ta tari numfashi Inna, Takaici ya sake rufe Inna ta ce. "Oh ni Kulu na haɗu da ƙaddara, wallahi da na san kalar asirin da uban yarinyar nan ya yi wa Hasan da tuni na ba wa almajiran soro sadaka sun ba yara zikiri an karya shi." Suna nan zaune Malam Hasan ya fito ya wuce ɗaki, a lokacin da ya shiga Rakiya tana duƙunƙune a cikin zanen gado tana kuka. Sosai ta ba shi tausayi, don har a ransa yana ji su suke cutar da ita a zamantakewar da suke yi. Sannan abin da Inna ta yi masa ba don mahaifiyarsa ba ce, da babu abin da zai hana shi ɗaukar mataki a kanta. Wanne irin abin ne yake damun Inna da za ta shigar masa ɗaki a lokacin da yake keɓewa da iyalinsa? Me ya sa duk cikin 'yan'uwansa babu wanda Inna take yi wa cin kashin da ake yi masa? Me ya sa ba zai samu farinciki ba? Waɗannan tambayoyin ya shiga jefa wa kansa. Shasshekar kukan Rakiya ne ta dawo da shi daga duniyar tunani, ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannunta. Da sauri ta fisge ta sake cusa kanta a tsakanin cinyoyinta. A yadda yake jin tausayin Rakiya, da ace zai iya rabuwa da ita da a take zai ba ta takardarta domin ta samu salamar rayuwa. 'Idan na sake ta ina za ta je? Da su wa za ta fara rayuwa? Shin na yi mata adalci idan na rabu da ita? Ko kuwa na riƙe amanar da mahaifinta ya damƙa mini?' Tambayoyin da ya dinga ƙissimawa a zuciyarsa kenan. 'Koda babu alaƙar aure a tsakaninku, kuma koda mahaifinta bai damƙa maka amanarta ba. Kai mai zame mata uwa da uba ne, domin mahaifinta ya yi maka gatan da iyaye suke yi wa 'ya'yansu. "Ba zai yiwu ba." Ya furta a fili cikin suɓutar baki ba tare da ya yi tsammanin zancan zai fito ba. Sake riƙo hannunta ya yi, tana niyyar ƙwacewa ya riƙe ta tsam a jikinsa. Ya kai bakinsa saitin kunnenta cikin tattausan lafazi ya ce. "Ba zan hana ki kuka ba, ki yi kukan idan har shi zai sanyaya abin da yake cikin zuciyarki." Kamar Rakiya tana jira, ta sake sakin sabon kukan da kana ji ka san daga ƙasan zuciyarta yake fitowa. Bubbuga bayanta ya shiga yi, har sai da ta ci kukanta mai isarta ya ce. "Ki yi haƙuri Rakiya, komai ya yi tsanani maganinsa Allah. In Shaa Allahu da jarina ya ƙara ƙwari za mu koma cikin gari, na sani ba a kyauta miki. Ana zalintarki kuma ana, shiga haƙƙinki, amma In Shaa Allahu zan yi bakin ƙoƙarin gyara wasu abubuwan koda ba a daina yi miki duka ba." Muryarta a dashe ta dube shi ta ce, "Ba na son ka yi abin da zai sa ka saɓa wa mahaifiyarka, ina son ka cigaba da yi mata biyayya. Kamar yadda ka faɗa ne watarana sai labari..." "Wai ba za ka yi ka fito daga ɗakin ba ne Hasan? Ka saka mace a gaba idan ba ka fita nema ba me za a ci?" Kalaman Inna suka katse maganarta, murya babu walwala Malam Hasan ya ce. "Yanzu zan fito." Daga haka ya shiga kintsa kansa sannan ya ɗauki kwandon turarensa ya fita. Bayan fitarsa sai da Rakiya ta sake shan sabon kukanta, ta ɗauki hijabi ta saka sannan ta fita banɗaki domin ta gyara jikinta. Tana fita kuwa Inna ta dasa zaginta Zuwaira ta shiga zuga ta, bayan ta fito har ta kusa shiga ɗaki Inna ta ce. "Ki sako kaya ki fito ga surfen gerona nan kwano uku yana jiranki." Cikin biyayya Rakiya ta amsa sannan ta shiga ɗaki. Kamar yadda ta amsa tana gamawa ta fita ta karɓi geron, tana surfawa Inna tana wanke ta da baƙaƙen maganganu. A wannan ranar Malam Hasan tun da ya shiga ɗakin Zuwaira ta sha jinin jikinta, amma sai ta nuna kamar ba ta fahimci yanayin da yake ciki ba. Don ko abincinta bai ci ba, dama kuma tun da ta tsiri rashin lafiyar ƙarya ta saka Inna ta sa shi kwana kullum a ɗakinta ya daina cin abincin kirki. Bai fi ya ci cokali ɗaya ya ce ya koshi, a wannan ranar da ta tambaye shi ko kula ta bai yi ba. Yana nan kwance ya ji ta ɗora hannu a jikinsa, cikin zafin zuciya ya fuske ta gefe. Da yake ya san halinta sarai, Zuwaira irin jarababbun matan nan ne da ba su da haƙuri. "Wai me ya sa kake yi mini haka ne, ko don ka ga na damu da kai? Kusan kullum kafin ka ba ni haƙƙina sai ka wulaƙanta ni." Zuwaira ta furta a narke cikin damuwa, tashi zaune Malam Hasan ya yi. Ya ji tsanarta ta sake mamaye shi. Da sauri ta ɗan ja baya, don ta yi tsammanin mari zai kai mata. Cikin tsana ya nuna ta ya ce. "Ke wacce irin mai son kanta ce? Ashe kin san halin da kike shiga amma kika sa nake danne haƙƙin Rakiya? Shin kina lissafin yau kwana nawa rabon da na kwana a ɗakinta? Kullum da kalar ciwon da kike tashi da shi, saboda kin san Inna ta tsaya miki ko? To bari ki ji, tun da abin na ki haka ne ni ma daga yau babu wani abu da zai sake shiga tsakanina da ke." Da sauri ta ɗago ta dube shi, ganin babu alamar wasa a fuskarsa ya ta miƙe ta ce. "Ai kuwa dole Inna ta ji, don wallahi ba zan yarda ba." Tana gama faɗa ta ɗaga labulen ɗakin, cikin ɓacin rai ya nuna ta da yatsa ya ce. "Wallahi tallahi kin ji na rantse miki, idan har kika sake kika fita daga ɗakin nan sai na sauke igiyar aurena uku da suke kanki. Sakarai wacce ba ta san sirrinta ba, ballantana na mijinta. Wai ganin ina yi wa Inna biyayya gani kike ba zan iya rabuwa da ke ba? Bari ki ji, daga yau za ku cigaba da raba kwana bibbiyun da kuke yi a baya. Idan kuma hakan bai yi miki ba sai na sauwaƙe miki, ƙarƙari na ɗauki matata na bar garin ba tare da kowa ya sake gani na ba." Yadda ta ga ransa ya ɓaci jikinsa har yana rawa ya sa ta shiga hankalinta, don ta san shi sarai yana da matuƙar haƙuri amma idan ransa ya ɓaci ba ya ji ba ya gani. Jiki a mace ta koma gefen gado ta kwanta, Malam Hasan ya miƙe ya zira doguwar rigarsa ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce ɗakin Rakiya. Tana gani ta gefen labule ya shiga ɗakin Rakiya, amma yadda take ƙaunar Malam Hasan ya sa ta ji ba ta shirya rabuwa da shi ba. Don haka ta koma ta kwanta tana hawaye, saboda wani irin zafin kishinsa da take ji. Tun daga wannan ranar Malam Hasan ya raba musu kwana, kuma koda Inna ta ga haka da ta fara faɗa Zuwaira da kanta ta shiga kare Malam Hasan da cewar ita ce su cigaba da kwanansu kamar yadda suke yi saboda ta samu lafiya. Hakan ya sa Rakiya ta samu 'yancin kwana da miji, sai dai wasu ƙalaubalen da ba a rasa ba waɗanda ta yi sabo da su har suka zamwemata jiki. An yi haka da wata biyu Zuwaira ta samu ciki, tun bayan da ta yi ɓatan wata ta fara tsiro da rashin lafiya duk da cikin mai sauƙi ta same shi. Inna tana ganin haka ta tasa ta a gaba suka tafi asibiti, sai ga shi gwaji na farko aka tabbatar da tana ɗauke da cikin wata ɗaya da sati ɗaya. Tun a asibitin Inna ta kira Malam Hasan ta sanar da shi, bayan da suka je gida a ranar wuni ta yi tana habaici da yarda wa Rakiya maganganu. Malam Hasan abu biyu ne ya haɗe masa, na farko yana farinciki da Allah ya sake azurta shi da rabo. Sai dai ya so a ce a jikin Rakiya ne, na biyu kuma yana fargabar sabon ƙalubalen da Rakiya za ta fara fuskanta daga wurin Inna. Don tun a ranar da aka tabbatar da cikin Inna ta kira Rakiya, ta kafa mata dokaki dangane da aikin cikin gidan. "Ke Rakiya ina ce dai kin lura arziki ya ƙwanƙwanso mana ƙofa, wacce ta kasance irin albarka ta buɗe masa." Shiru Rakiya ta yi, don ba ta fahimci kalaman Inna ba. "To ina nufin ciki Zuwaira gare ta, don haka ba kowanne aiki za ta dinga yi ba. Na faɗa miki ne domin idan kina da wani shiri ki ɗaura ɗamara, domin wannan cikin sai an haife shi lafiya kuma ya taka ƙafa shi ma ko ita ma sun hayayyafa. Domin mu gadon haihuwa ne ba juya ba." Rakiya ta ji wani abu ya soki zuciyarta, amma sai ta danne ta saki murmushi ta ce. "Ma Shaa Allah, wannan abin farinciki ne. Allah Ya buɗi ido lafiya." Inna ta yamutsa fuska tana taɓe baki ta ce, "Amin, idan ma bai kai zuci ba kanki. To ina son ki sani yanzu aikin gidan nan gabaɗaya ke za ki dinga yi, har zuwa lokacin da cikinta zai yi ƙwari." Zuwaira da ke gefen Inna tana cin ɗata tana yatsina ta yi zaraf ta ce, "Inna hatta girkin ma ta dinga haɗawa ranar kwanana." Rakiya ta ɗago suka haɗa ido, Zuwaira ta murguɗa baki ta cigaba da cin ɗatarta. Inna ta dubi Rakiya ta ce. "Kin ji dai abin da ta ce? Za ki dinga komai na gidan nan, idan cikin ya girma sai mu san abin yi." Muryar Rakiya a raunane ta amsa wa Inna, bayan Inna ta sallame ta ta wuce ɗakinta. Tana shiga ta zauna ta fara zubar da hawayen tausayin kanta. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [16/05, 18:10] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t SHAFI NA BAKWAI Sai da Rakiya ta ci kukanta mai isarta sannan ta ɗebi ruwan randarta ta ɗaura alwala a ɗakinta. Don tana gudun kada ta fita, su Inna su ga fuskarta su ɗauka maganar cikin ce ta saka ta kuka su yi mata mummunar fassara. Uwar ɗakinta ta shiga ta gabatar da sallah raka'a biyu. Ta roƙi Ubangiji da ya yaye mata damuwar da ke ƙunshe a zuciyarta, bayan ta gama addu'ar ta ji sanyi a ranta don ta ji kaso mafi yawa daga cikin damuwarta ta yaye. Rakiya ita ta cigaba da duk ayyukan cikin gidan, tun daga kan shara, wanke-wanke, wankin banɗaki da sharar turken awaki zuwa girki duk babu mai tallafa mata. Hatta abinci wani lokacin Inna cewa take ta zubo wa Zuwaira, ita dai Zuwaira sai dai idan girki ya zagayo kanta ta karɓi miji. Don ta lura a yanzu yana ba ta kulawa, kuma duk abin da ta ce tana so bakin gwargwado yana yi mata. Sai dai abu ɗaya ne ba ta jin daɗi yadda ta ga har lokacin bai fifita darajarta a kan ta Rakiya ba. Amma abin da yake damunsa bai wuce yadda ake yake cakuɗewa Rakiya ba, tun da ya lura a ɗan tsakanin nan har duhu ta yi duk da hasken fatar da take da shi. Da ya yi yunƙurin yi wa Inna magana sai Rakiya ta hana shi, saboda ta san ko ya yi maganar ba za ta sauya zane ba sai ma wani ƙalubalen da za ta sake fuskanta. Watarana Rakiya ta gama aikin gidan tas, har ta ɗora abincin rana da yake rana ta yi. Inna ta ɗebo mata kayan wankinta, ta ce ta wanke mata nan take. Ta gaji sosai, domin bayanta har ciwo yake mata. "Na ce Inna idan babu damuwa ko na bari zuwa gobe da sassafe sai na tashi da wankin?" Rakiya ta furta a ɗarare, Inna da har ta nufi ɗaki ta waigo ta ce. "Ai da uwarki ce ta ba ki wankin ba za ki faɗa mata haka ba ko?" Shiru Rakiya ta yi, Inna ta gama zazzage mata rashin mutumci ta yi gaba. Babu yadda ta iya, haka ta ja kujera ta zauna, ta haɗa ruwan wankin don ba za ta iya wankin a sunkuye ba. Tana cikin wankin Zuwaira ta fito da nata kayan, tana zuwa kan Rakiya ta watsa mata cike da izgilanci ta ce. "Ga nawa wankin nan, ciki ne ya hana ni iya taɓa ko rigar mama na wanke ballantawa kayan sawa." Da ido Rakiya ta bi kayan, saboda tsabar wulaƙanci har da wandunan pant da rigar mama waɗanda suka yi duƙun-duƙun saboda datti. Rakiya ta dube ta ta ce, "Ba zan yi miki wanki ba." Zuwaira baki ta buɗe cike da mamaki ta ce, "Au ni kike faɗa wa haka?" "Na faɗa miki Zuwaira, ko kin ɗauka tsoronki nake ji? Ko kuma kin yi zaton ni baiwarki ce?" Rakiya ta furta a hassale, Zuwaira ta saki dariyar izgilanci ta ce. "Mene ne marabarki da baiwar to? Ko kin ɗauka kina da sauran amfani wanda ya wuce ki ci ki yi kashi da aikin gida?" Rakiya ba ta kula ta ba ta cigaba da wanke kayan Inna, Zuwaira ta koma ta gabanta ta sake cewa. "Ki yi ki mayar da hankali ki wanke mini su tas, idan ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci. Banza juya marar mamora ballantana amfani." Furucin Zuwaira na ƙarshe ne suka daki zuciyar Rakiya, kamar ba za ta kula ta ba sai ta ɗago ta ce. "Da Ubangiji kike, domin Shi ne ya ba ki cikin, kuma na tabbata ni ma bai manta da ni ba." Cikin shewa irin ta izgilanci Zuwaira ta ce, "Ahayyee! Lallai fa sumumu-kasau an samu bakin magana, ai ke da haihuwa sai dai ki ga ana yi. Ko mugun halin bokan ubanki ya isa ya hana ki haihuwa...' "Kada ki sake zagin mahaifina!" Rakiya ta furta mata da wata irin murya gargaɗi, cikin raini Zuwaira ta ce. "Uban naki wata tsiyar ce da kike kumfar baki a kansa..." Tas! Rakiya ta sauke wa Zuwaira mari a fuska, zaro ido waje Zuwaira ta yi tana mamakin wacce ta mare ta. Don haka ta wage murya cikin kururuwa ta ce, "Ni kika mara?" "Na mare ki, ko yanzu kika yi gangancin sake zagin mahaifina sai na ninka miki wanda ya fi shi."Rakiya ta furta tana tsare ta da ido, Zuwaira ta tsorota da yadda ta ga ran Rakiya ya ɓaci. Amma don kada ta nuna mata ta ji tsoro ya sa ta dake ta sake cewa, "An zage ki, uban naki ba boka ba ne mashiriki? Ko ba shi ya mallake Yaya..." A wannan karon ma Rakiya ta sake sauke mata mari a fuska, ihu ta saki ta yi zaman 'yanbori a ƙasa ta ɓarke da kuka. Da sauri Inna ta fito tana tambayar abin da ya faru, Zuwaira ta dafe cikinta cikin kukan makirci ta ce. "Ina wai don na ce ta taimaka ta haɗa da kayana shi ne ta hau zagina, don na rama shi ne da hau cikina da duka." "Duka a ciki?" Inna ta tambaya a razane, Zuwaira ta gyaɗa kai tana sake murƙususu kamar wacce aka doka da gaske. "Amma ke dai an yi baƙar muguwa, yanzu saboda rashin imani yarinyar tana da ciki kika dake ta don ki kashe ta? Wallahi bari Hasan ya zo a yi wacce za a yi." "Gara ya zo ɗin, domin ni ma na gaji haka. Hasan ko ɗan autan zinare a cikin mazan aure ne na gaji da shi." Rakiya ta furta a zuciye, don a wannan gaɓar ta gama zuwa bango. Da mamaki Inna ta ce, "Ni kike faɗa wa haka?" "Duk abin da kika ɗauka Inna, na faɗa na gaji wallahi. Ai ba baiwa aka ajiye muku ba, wallahi duk abin da zai faru sai dai ya faru amma zaman gidan nan daga yau na gama shi." Rakiya tana gama maganar ta miƙe tsaye ta yarfe ruwan hannunta ta juya za ta shiga ɗaki. Da sauri Inna ta bi ta ta ce, "Au Allah rashin kunya za ki yi mini? Wankin ba za ki zo ki yi mini ba?" Rakiya ta juyo a hassale ta ce. "Ba zan wanke ba, ita 'yar gwal ɗin gabanki ta wanke miki. Ai da ni da ita duka 'ya'ya ne." Tana gama faɗa ta shige ɗaki tana jin zuciyarta tana tafasa. Sai da ta yi da gaske sannan ta taushi zuciyarta, don ji take kamar ta fita ta wanke Inna tas sannan ta koma ɗaki. Daga Zuwaira har Inna kasa magana suka yi, sai zuwa bayan wani lokaci Inna ta fara kumfar baki. Har aka yi sallar Isha'i kowannensu da abin da yake saƙa wa a zuciyarsa, Malam Hasan yana shigowa Inna ta fashe da kuka. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, sai da ya lallashe ta sannan ya fara tambayarta abin da ya faru. "Wallahi yau yarinyar nan Rakiya babu irin zagin da ba ta yi mini ba, daga kawai na ba ta wanki don Zuwaira ta kawo mata 'yan ƙwayayyaki ta ce ta matse mata ta hau ta da duka. Don na yi magana ta zage ni ta ce wankin ma ba za ta yi ba." Bayan Inna ta gama faɗa masa ƙarya da gaskiya ta haska masa tulun kayan wankinta, sai bokiti da ke gefe wanda ta fara wankewa. Ransa ne ya ɓaci, don haka bai tanka wa Inna ba ya nufi ɗakin Rakiya. Koda ya shiga a madadin ya ji ta bakinta sai kawai ya rufe ta da faɗa. "Rakiya me ya sa kika zagi Inna? Ko don kin ga ina bin bayanki ne? Kada ki manta fa mahaifiyata ce, zan iya sauya kowa da komai a duniyar nan ban da ita. Don kawai ta ce ki mata wanki, yanzu idan mahaifiyarki ce za ki ce ba za ki wanke mata ba?" Tun da ya fara faɗa ido ta kawo ta zuba masa, ranta ya sake ɓaci a kan wanda ya mamaye ta. Sai da ya gama faɗan har ya juya zai fita ta ce. "Hasan ba ni takarda ta na gaji." Da mamaki ya ce, "Hasan! Sunana kike kira kai tsaye?" "Na faɗa ka ba ni takardata na ce maka, don ina mai tabbatar maka da ko kai ne autan maza na gama zaman aure da kai. Na gaji, na gaji da cin kashin da ake yi mini duk don saoda laifin da ake ganin ni na ɗora wa kaina." Rakiya ta furta a hasaale, saboda idonta ya gama rufewa da zallar ɓacin rai. Malam Hasan ya saki dariyar yaƙe ya ce, "Ni da ke ai aurenmu mutu ka raba ne Rakiya." "Ai ba a aure dole ko? To ai kuwa yau ba zan ƙara kwana a gidan nan ba. Wallahi sai ka ba ni takarda ta, ka zauna da 'yar'uwarka wacce mahaifiyarka take son ku kasance tare." Tana gama faɗar haka ta shiga haɗa kayan sawarta, duk da a lokacin ita ma ba ta san inda za ta dosa ba, amma ji take yi gara ta bar gidan ko ta samu salama. Yadda ya ga Rakiya tana faɗar maganganu ya tabbatar da an gama ƙure haƙurinta, a shekarunsu goma da aure ba ta taɓa yin wannan fito na fito da shi kamar haka ba. A fusace ya fita daga ɗakin, bayan ya dawo ya same ta har ta saka hijabinta. Wata farar takarda ya miƙa mata, cikin wani irin yanayi ta dube shi ba tare da ta tanka masa ba. Duk yadda ta so rabuwa da Malam Hasan sai ta ji gwiwoyinta sun yi sanyi, ta dube shi muryarta tana rawa ta ce. "Sakina ka yi?" Bai amsa mata ba, ya ga ta ɗauki jakar kayanta za ta fita. Cikin sauri ya bi ta ya ce. "Wannan hukuncin ina ganin shi ne zai fiye mana alheri gabaɗaya, amma kafin nan ina son ki zo mu je gidan Kawu Sani ki kwana a can." "Babu ruwanka da inda zan kwana, idan na ga dama na kwana a titi ma damuwa ta ce." Rakiya ta furta tana fita, duk abin da yake faruwa Inna da Zuwaira suna tsakar gida suna ji. Saboda farinciki Zuwaira ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, Rakiya ta fita ko kallonsu ba ta yi ba ta fita daga gidan. Ganin haka ya sa Malam Hasan yana bi bayanta yana kiran sunanta, ta cigaba da tafiya ko waigensa ba ta yi ba. ABBAN FAUWAZ Abba yana ɗaga labulen ɗakin ya saki salati cike da mamaki ya ce. "Tani lafiya kike kuka? Ko wani abu ne ya faru?" Sai kuma ya waiga wurin Fauwaz da ya yi suman tsaye yana bin ta da kallon mamaki, Abba ya ce. "Kai Fauwaz me yake faruwa ne?" Fauwaz ya wara hannuwa a daƙile ya ce, "Abba kukan makirci take yi." Sototo Abba ya yi yana kallonsa, a ɗan faɗace ya ce. "Ka san me kake faɗa kuwa? Ko kuwa rashin mutuncin da tarbiyyar da kake yi ka gwada mata?" Kafin Fauwaz ya sake magana Tani ta ce. "Alhaji wallahi sai ka sake ni a yanzu ba sai an jima ba. Kamar ni ina matsayin matarka wai Fauwaz ya ɗaga hannu ya mare ni, saboda Allah ɗan da a haife da ace na haihu da wuri na haifi wanda ya fi shi ma." A razane Abba ya dubi Fauwaz ya sake mayar da kallonsa ga Tani ya ce, "Mari fa Tani?" "Au tantama kake Alhaji zan yi masa ƙarya ne? Ai shi ya sa na ce gara ka sake ni don wallahi ba zan iya zama gida ɗaya da wannan yaron ba." Tani tana rufe baki a fusace Abba ya rufe Fauwaz da mahaukacin duka. Ta ko ina yake kai masa duka, tun Fauwaz yana yunƙurin kare kansa har ya faɗi a ƙasa Abba bai daina dukansa ba. Sai da ya gaji don kansa, bayan ya ga Fauwaz yana fitar da numfashi da ƙyar sannan ya miƙe yana huci. Tani da daɗi ya gama mamaye ta, ta sake kwaɓe fuska ta ce. "Ni fa bayan wannan hukuncin dole ka san abin yi Alhaji, don yadda ka hukunta shi wallahi na san idan ya ji daɗin jikinsa sai ya yi mini abin da ya fi haka." Yarfe gumin fuskarsa Abba ya yi yana huci ya ce, "Gidan horo zan kai shi, kada wani abu ya dame ki don babu abin da zai raba ni da ke Tani. Ni da na rabu da ke gara na rabu da kowa a rayuwata." Sai a lokacin Tani ta saki murmushi ta ce. "Shi ya sa nake ƙaunarka Alhaji." Fauwaz da ke kwance cikin mummunan yanayi ya ce, "Abba... matar nan ba sonka take ba... wallahi..." Naushin da Abba ya kai masa a baki ne ya katse shi, bakinsa ya fashe jini ya fara zuba. Kafin wani lokaci tuni fuskar Fauwaz ta sauya gabaɗaya. A nan take Abba ya riƙo hannun Fauwaz cike da jin haushi, ya wurga shi ɗakinsa ya janyo ƙofa ya saka mukulli ya rufe. Sai da Tani ta haɗa masa ruwan wanka, wanda ya sha miyagun turarrukan da ta karɓa a wurin malamanta sannan Abba ya shiga ya yi wanka ya fito. Zaman da ya yi yana cin abinci a nan yake ba ta labarin cinikayyar da suka yi, da biyan bashin da ya yi. Sai kuma adadin ragowar kuɗaɗen da ake bin sa. Farinciki ne ya mamaye ta, har sai da fuskarta ta gagara ɓoye halin da zuciyarta take ciki. Don haka Abba ya ce. "Amma akwai wani albishir ko labari da kika samu ne Tani? Na lura kamar kina cikin farinciki." 'Dole na shiga farinciki haƙa ta, ta kusa cimma ruwa. Lokacin da zan kaɗa goge na ya zo.' Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Wani abu na tuno, amma ba yanzu zan sanar da kai ba sai ya tabbata In Shaa Allah." Shi ma murmushi ya saki ya ce, "Wato kina son ki ce za ki ba ni mamaki kenan?" "Tabbas za ka sha ruwan mamaki, don wataƙila tun da ka zo duniya ba a taɓa shayar da kai ruwan mamaki kamar wanda zan ba ka ba." Shiru ya yi ya zura mata ido, har sai da ta ji tsoron ko ya so fahimtar inda zancanta ya dosa. Sai kuma ta ga ya bagarar suka cigaba da hira, daga cikin hirar da suka tattauna har ta kai Fauwaz gidan horo. Bayan ya yi zaman gidan horo na wata biyu, daga nan za a ɗauke shi zuwa almajiranci. Kamar yadda Tani ta tsara masa haka Abba ya ɗauki Fauwaz ya kai shi gidan kangararru da ke titin Hajj Camp. Sai dai tun kafin a kai shi gidan horon suka fara da yi masa horon yunwa, don tun ranar da ya sa shi a ɗaki kullum sau ɗaya ake ba shi abinci da ruwa shi ma ba wani na kirki ba. A haka sai da ya shafe kwana biyar a cikin ɗakin, sai dai kafin Abba ya fita ya raka shi banɗaki ya yi uzurin da zai yi da ya gama ya mayar da shi cikin ɗaki ya kulle. Ana gobe za a kai shi gidan horon Abba ya shiga kai masa abinci, har ya juya zai fita a wahalce Fauwaz ya ce. "Abba na san abin da ba ka sani ba, don Allah ka ba ni dama na yi maka bayani. Ba na son ka yi danasani a lokacin da bayanina ba zai yi maka amfani ba." Dawowa Abba ya yi yana daga tsaye ya ce, "Ina jin ka, idan ka nemi yi mini shashanki ranka ya yi mugun ɓaci." Fauwaz ya ji daɗi sosai, duk da yunwa ta sa muryarsa ba ta fita amma ya yi ƙoƙarin mahaifinsa ya fahimce shi. "Abba akwai abin da Tani take shiryawa a kanka..." "Dakata Fauwaz!" Abba ya katse shi yana ɗaga masa hannu, domin duk wani abu da ya danganci kushe ko laifi matuƙar a kan Tani ne ba ya ji ba ya gani. "In dai a kan Tani ne mun dinga samun saɓani da kai kenan. Matuƙar ba za ka ɗauki Tani a matsayin mahaifiyarka ba, sai dai ni da kai mu kasance a mabambamtar inuwa." Daga haka Abba ya fita. Tun bayan da Fauwaz ya tafi gidan horo Abba da Tani suka cigaba da rayuwa, sai dai kusan malejin rayuwa suke yi domin al'amura da dama a ɓangaren kasuwanci sun tsaya masa cak. Sakamakon yana samun kuɗi yake kai wa Alhaji Dikko a rubuta su cigaba da lissafi. Suna cikin haka har Fauwaz ya shafe watanni biyu cif a gidan horo Abba ya ɗauko shi ya dawo da shi. Duk wanda ya san Fauwaz a baya, idan ya gan shi a wannan lokacin ba zai gane shi ba a tashin farko. Ya yi wani irin baƙi ya rame, kamar ba shi ba. Haka kuma wasu daga cikin ɗabi'unsa sun sauya sosai, duk da dama can ba mai magana ba ne. Amma a wannan lokacin sai rashin maganarsa ta ƙaru, ya koyi taurin kai fiye da yadda yake da shi a baya. Idan ya ce ba zai yi abu ba, duk horo ko hukuncin da za a yi masa ba su sa ya aikata ba. Haka kuma ya fita daga sabgar Tani, ita kanta a wannan lokacin har tsoron a bar su daga shi sai ita take yi a gida. Daga ƙarshe ma sai take kulle kanta a ɗaki idan Abba ya tafi kasuwa, duk wani abu da za ta buƙata saka shi a ɗaki take yi. Sai ta ga fitar Fauwaz sai ta fito da sauri ta rufe gidan sannan ta ɗora girki, idan ta gama sai ta buɗe gidan ta shige ɗakinta ta rufe. A haka suka cigaba da rayuwa har Abba ya ɗauke shi, ya kai shi garin Gombe almajiranci. Satin Fauwaz biyu da tafiya watarana da sassafe suna zaune aka ƙwanƙwasa ƙofar gidan, Abba ne ya fita yana zuwa ya ci karo da 'yansanda a ƙofar gidan. Gaisuwar mutumci suka yi, sannan ɗaya daga cikinsu ya ce. "Alhaji mun zo gayyatarka zuwa ofishinmu ne, sakamakon wata tuhuma da ake yi maka." Da mamaki Abba ya ce, "Tuhuma kuma?" Lokaci ɗaya suka gyaɗa masa kai, sai Abba ya ce. "To ku je In Shaa Allahu..." "Am sorry to say hakan ba zai yuwu ba, dole za mu tafi da kai ƙafarmu ƙafarka." Suka ba shi amsa kai tsaye fuska babu walwala. Jama'a za ku iya fara payment daga yau💃🏻 free pgs suna gab da ƙarewa. Naira 500 ne kacal ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [18/05, 18:15] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t SHAFI NA TAKWAS Abba ya yi mamakin jin furucinsu, don haka ya ce. "Amma don Allah ko zan san wanda ya turo ku wurina?" Wani baƙi daga cikinsu wanda ya kasance mai ƙaton ciki ya girgiza kai ya ce, "Babu buƙatar haka, idan mun je ofis za ka ji bayanin gayyatarka." Abba ya yi jim sannan ya ce. "To shi kenan, amma don Allah ku yi mini afuwa zan shiga na sanar da iyalina." A nan ba su musa masa ba, jikinsa a sanyaye ya shiga ya samu Tani a kan gado tana bacci. Tashin ta ya shiga yi a gaggauce, cikin magagin bacci ta ce. "Lafiya Alhaji." A gefen gadon ya zauna ya ce, "Ina fa lafiya Tani, ina cikin tashin hankali. 'Yansanda ne a ƙofar gida suka zo tafiya da ni." Firgigit ta wartsake idonta, cikin sauri ta ce. "Yan sanda kuma? Me ka yi musu? An ya ba ɓatan hanya suka yi ba?" Abba ya rausayar da kai ya ce, "Babu wani ɓatan hanya, tun da complete sunana suka ambata har da lambar wayata. Yanzu dai bari na je duk yadda ake ciki za ki ji daga baya." Miƙewa Tani ta yi ta biyo bayansa tana sallallami kamar abin ya dame ta da gaske. Sai da ya fita tana shigowa cikin gida ta tuntsire da dariyar ƙeta, sai da ta yi mai isarta sannan ta nufi ɗakinta ta doka sakata. Tun da su Abba suka ɗauki hanyar Bompai yake saƙa da warwara a cikin zuciyarsa, shi dai a iya saninsa lafiya ƙalau ya rabu da mutanen kasuwarsu ballantana ya ce wani abu ne ya haɗa shi da wani daga cikinsu har ya turo masa hukuma. Har Alhaji Dikko ne ya zo masa a rai, sai ya tuna kwana biyu kenan a tsakani da ya kai masa kuɗi kuma dama duk bayan kwana goma yake rage masa kuɗinsa koda babu yawa. Yana cikin wannan yanayin har suka ƙarasa Zone 1 hedikwata. Suna shiga bayan da Abba ya zauna aka shiga karanta masa ƙunshin tuhumar da ake ƙararsa a kai. "Shin ka san Alhaji Isa Kura?" Ɗan jim Abba ya yi yana nazari, don ji yake kamar ya san sunan kamar bai san shi ba. "Mutumin da kuka yi cinikayyar filaye da shi." Ɗansandan ya taƙaita masa dogon tunani, da sauri Abba ya ce. "Eh na san shi, wani abu ne ya faru?" Rubuta jawaban Abba ɗansandan ya yi sannan ya ce, "Shi ne ya yi ƙararka a kan ka zambace shi, ka ci amanarsa ka sayar masa da fili a kan fili." Dam! Ƙirjin Abba ya buga da ƙarfi, bakinsa yana rawa ya ce. "Gaskiya ba haka abin yake ba, yadda aka sayar mini da wurin nan ni ma haka na sayar masa da shi." Babu wanda ya tanka masa, ɗansandan da ke ɗaukar statement ɗinsa ya ga ya latsa waya ya kara a kunne. "Alhaji ka taho ne?" Amsa aka ba shi daga can ɓangaren sannan ya ce, "To sai ka shigo." Katsewa ya yi ya dubi Abba ya ce. "Wanda ya shigar da case ɗin ya shigo gidan nan, yanzu haka parking motarsa yake yi. Idan ya zo sai ka yi mana jawabi." Abba ya gyaɗa kansa yana ta'ajibin abin da ya faru. Suna nan zaune Alhaji Isah ya shiga fuska a haɗe sai muzurai yake yi. "Ofisa ya ake ciki?" Alhaji Isa ya furta yana kallonsu, ɗansandan ya janye file ɗin gabansa sannan ya dubi Abba ya sanar da Alhaji Isah. Rai aɓace Alhajin ya ce. "Malam kada ka raina mini hankali, a jiya na ɗebi ma'aikata da kayan aiki kawai na je na tarar da wani mutum ya yi gini har ginin ya kusa linta." "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Wallahi ban san yadda abin ya kasance ba..." "Ai kuwa za ka sani, don wallahi naira biyar tawa ba za ta yi ciwon kai ba." Alhajin Ya katse Abba, nan take suka shiga musayar kalamai. Shi Abba yana ƙoƙarin kare kansa, shi ma Alhaji yana nuna dagiya a kan haƙƙinsa. Har wayarsa Abba ya ciro yana neman layin Gambo dillali amma ta ƙi tafiya. Ganin hayaniya ta yi yawa ya sa ɗansandan cewa. "Yanzu ba abin tashin hankali ba ne, za mu yi duk cike-ciken da ya dace mu miƙa ku kotu. Idan ya so sai a yi bincike a tabbatar wa da mai gaskiya gaskiyarsa, wanda ba shi da gaskiya sai a hukunta shi." Da wannan suka tashi, a kan Abba ya saurari sammaci daga kotu. Koda Abba ya fita daga zonal kai tsaye wurin filin da ya sayarwa Alhajin ya nufa, sai dai yana zuwa ya yi turus ganin leburawa rututu suna ta aiki. Wasu suna kwaɓa ƙasa, wasu suna ɗiban bulo suna jerawa, yayin da wasu suke hawa tsani suna miƙa suminti. Ruwan mamaki ne ya wanke shi, don ya gasgata abin da ya gani ba gizo idonsa ke yi ba sai da ya tambayi ɗaya daga cikin leburorin. "Assalamu alaikum! Don Allah tambaya nake yi." Abba Ya furta yana mintsinin hannunsa don ya tabbatar da ba mafarki yake yi ba. "Wa alaikassakam, Allah Ya sa mun sani." Suka amsa masa suna zuba masa ido, sai da ya sake leƙen yadda ginin ya yi tsawo ya ce. "Don Allah waye mai wurin nan ina nufin wanda ya ba ku aikin ginin nan." "Amma bawan Allah ina ruwanka da mai ginin nan? Ko kai ma aikin kake son ka samu? To idan ma haka ne ya gama ɗiban ma'aikata" Abba ya girgiza masa kai, sai ɗaya daga ciki ya ce. "Mai wannan wurin ai ba bahaushe ba ne, kai ba ma ɗan ƙasar nan ba ne. Na wani ɗan china ne, idan kana jin kamfanin shinkafa na Girma rice to nasa ne." Abba yana jin haka jikinsa ya sake yin sanyi, don haka ya yi musu sallama ya wuce gida kansa yana masifar ciwo. Yana zuwa gida Tani ta shiga ɗakin ta ga lokaci ɗaya duk ya firgice ya fita hayyacinsa, zama ya yi ya zuba tagumi da hannuwa biyu. Ba ta yi tsammani ba ta ga hawaye bibbiyu suna fita daga idonsa. 'Hmmm wallahi tallahi hawaye ma yanzu ka fara shi.' Tani ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Alhaji wai me yaka faruwa ne, tun fa da ka fita na kasa zaune da tsaye." "Mene ne ma bai faru ba Tani? Komai ya rikice mini, masifa ta kowacce hanya sai faɗo mini take yi. Ya zan yi Tani? Mene ne mafita?" Nan take ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da ita, sai da ya goge hawayen idonsa sannan ya ɗora da cewa. "Na nemi layin Gambo dillali sama da ƙasa ba ya shiga, har wurin dillancinsu na je ko za a ba ni layin da zan same shi amma sun ce mini babu, yanzu haka sun ce matuƙar ban kawo Gambo dillali ba ni ne zan ɗauki asara tun da shi ya sayar mini. Kuma har abokinsa da suka zo tare na neme shi ban samu ba, ina cikin tashin hankali Tani." "Har yanzu ba ka shiga ba." Tani ta yi suɓutar baki ba tare da ta san zancan zai fita ba, da wani irin kallo ya dube ta. Cikin wayancewa ta ce. "Ƙwarai kuwa Alhaji, tun da ai za a iya samun abokinsa. Da ace babu abokin Gambon shi ne ka shiga tashin hankali." Tsaki ya saki bai tanka mata ba, suka yi shiru gabaɗaya kowannensu da abin da yake saƙa wa a cikin ransa. Daga wannan ranar Abba ya firgice ya lalace ya fita hayyacinsa don ko abincin kirki da bacci mai daɗi ba ya yi, duk inda zai buga neman Gambo dillali ya yi amma sama da ƙasa bai same shi ba. Yana cikin wannan gaɓar Alhaji Isah ya aika masa sammaci a kotu, kuma a wannan gaɓar ce Alhaji Dikko ya taso shi a gaba da zancan kuɗinsa don ya kwashe sama da sati biyu bai waiwayo shi ba. Saboda haka abin duniya goma da ashirin ya haɗe masa, ta ko ina fuskantar matsin lamba yake don ko kuɗin da zai ɗauki lauya ba shi da su. Sun fara zaman shari'arsa da Alhaji Isa ko wata guda ba a rufa ba, Alhaji Dikko ya aiko masa da na shi sammacin daga kotu. Cikin abin da bai wuce wata ɗaya ba Abba duk ya tsururuce, ƙanwarsa Goggo da ke ba ƙarfi gare ta ba kullum cikin yi masa addu'ar samun mafita take. Abu ɗaya ne ma ya ɓata mata rai da farko har ta ɗauki fushi da shi, maganar kai Fauwaz almajiranci da ba ta ji labari ba sai bayan da ya riga ya kai shi. Saboda da ta ji da wuri ita za ta ɗauke shi ya koma wurinta da zama, duk da har lokacin ba ta gane ainahin kalar Tani ba. Sai da ta ji jarrabawar da Abba ya shiga sannan ta sauke fushinta, har take zuwa wurinsa tana sake kwantar masa da hankali. A ranar da za su fara zaman shari'arsa da Alhaji Dikko, har ya shirya zai fita Tani ta biyo shi ta ce. "Ji mama Alhaji ina magana." "Tani sauri nake kada na makara." Abba ya ba ta amsa a gaggauce, da sauri ita ma ta sha gabansa tana cewa. "Ba daɗewa zan yi ba, da ka aiwatar ne za ka yi gaba malam." Jin yadda take yi masa magana cike da isa-isa ya sa shi kallonta, Tani ta turo ɗankwalinta gaba ta ce, "Takardar sakina za ka ba ni, don ni ba matar shan wahala ba ce." MALAM HASAN Ganin ta cigaba da tafiya sai ya sha gabanta da sauri ya ce. "Ba magana nake yi miki ba Rakiya, ki tsaya ki saurare ni." "Ba zan tsaya ba! Ka ƙyale ni na tafi tun da ba ni da sauran amfani a rayuwarka. Dama an faɗa mini tamkar baiwa haka nake, tun da babu wata mamora a gare ni saboda ni juya ce." Rakiya ta furta masa a fusace cikin ɗaga murya, waigawa ya yi ya ga babu mutane a ƙofar gidan nasu sai wani matashi guda ɗaya da ya zo wucewa. Malam Hasan ya sauke ajiyar zuciya, ya yi ƙasa da murya ya ce. "Don Allah ki daina ɗaga murya kada mutane su ji, ki zo ki wuce gidan Kawu yanzu a daren nan ina za ki je." "Zan tafi duk inda ya yi daidai da rayuwata, ka rabu da ni Hasan babu inda zan je." Rakiya tana gama maganar ta cigaba da tafiya, duk yadda Malam Hasan ya so ya dakatar da ita fir ta ƙi amincewa. Don haka ya riƙo hannunta da niyyar su koma, a haukace ta fizge hannunta cikin ƙaraji ta ce. "Ka rabu da ni, ba na son ganinka ba na ƙaunarka..." Tass! Ya tsinke ta da mari, cike da ƙunan zuciya ta riƙe kuncinta tana kallonsa hawaye yana zuba, ta ɗauki lokaci a haka cikin sassanyar murya ta ce. "Na gode da wannan tukwicin da ka yi mini, amma ka sani ko kashe ni za ka yi ba zan koma cikin ahalinka ba." Ta yi yunƙurin ƙwacewa ya janyo ta, ya saka hannuwa biyu ya matse ta a jikinsa. Sunkuyar da kai ya yi har sai da suka fara jin numfashin junansu, cikin muryar nadama ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri, a tsakanina da ke ba na son na ji kalman ƙiyayya da kike furta mini. Yanzu ki zo mu je ki gidan Kawu." Furzar da iska mai zafi ta yi ta girgiza masa kai ta ce. "Ba za ni ba, ka ƙyale ni babu inda zan je." Sai da Malam Hasan ya kai ruwa rana sannan ta amince ta bi shi suka wuce gidan Kawu Sani. Lokacin da suka ƙarasa Kawu Sani yana shirin rufe gida, yana ganinsu ya ce. "Hasan lafiya na ganku a daren nan? Hala Kulu ce ta sake yin wani rashin mutumcin?" Malam Hasan ya ɗan sosa kai ya ce, "Kawu maganar tana da ɗan tsayi, yanzu dai Rakiya za ta kwana a nan idan Allah Ya kaimu safiya zan dawo sai mu tattauna." Jinjina kai Kawu Sani ya yi ya ce, "Ikon Allah, Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan masifar." Suka amsa da Amin, Har Malam Hasan ya juya zai tafi Kawu ya ce. "Hasan idan ka san matsalar nan ta haɗa da su Kulu, to kana komawa ka ce gobe da sassafe ina son ganinsu ku dawo tare." Hasan ya amsa masa sannan ya tafi, bayan tafiyarsa Kawu da matarsa sun jima suna tausar Rakiya da ba ta baki, sannan suka bata makwamci ta kwanta. Malam Hasan yana komawa gida a inda ya bar su Inna a nan ya koma ya same su, Inna tana ganinsa ta taɓe baki ta ce. "To gantalalle, bayan ka sake ta uban me ka bi ta ka faɗa mata." Shiru Malam Hasan ya yi yana jin zuciyarsa babu daɗi, Inna ta ɗora da cewa. "Ai wallahi tun da har muka rabu da jaraba kun rabu kenan, na san halinka da nacin tsiya kana iya dawo da ita..." "Inna Kawu yana son ganinku gobe idan Allah Ya kaimu." Malam Hasan ya furta yana katse ta, riƙe baki Inna ta yi ta ce. "Ai ƙara ta kuka kai kenan ko? To Allah Ya kaimu ai duk wacca za a yi sai dai ayi ta ta ƙare. " Malam Hasan bai tanka mata ba ya miƙe ya shiga ɗaki, da yake Zuwaira ta san ba ta shuka abin arziki ba ko magana ba ta yi masa ba, saboda yadda ya hautsine musu tsoron tanka masa take ji. Washegari da sassafe su Inna suka dira a gidan Kawu, bayan an gaisa a nan ne ya nemi jin ba'asin abin da ya faru. Nan take Rakiya ta zayyane duk abin da ya faru, cike da jin haushi Kawu ya ɗauki hularsa ya jefa wa Zuwaira ya ce. "Yanzu Zuwaira rashin mutumcin naki har ya kai haka? Rakiyan ce za ta yi miki wanki har kike zaginta?" Inna da ta gama cika fam ta ce, "To amma ai ka ji ɗayan ɓangaren indai ba son kai za ka yi..." "Ke dallah rufe mini baki, kin girma ga yawan shekarun amma babu hankali." Kawu ya katse Inna, Rakiya ta saki murmushin takaici ta ce. "Kawu ni dai a wurina komai ya wuce, dama fata na ya ba ni takarda ta kuma AlhamduLillah ya sake ni jiya." Malam Hasan yana jin haka ya yi zaraf ya ce, "Ban saki matata ba Kawu, takardar da na ba ta jiya ba ta saki ba ce ta ban haƙuri ce." "Ni kuma gaskiya na gaji da zaman gidanka, domin mahaifiyarka da matarka sun mayar da ni baiwa ni ma kuma 'ya ce kamar kowa." Inna ta yi mamakin jin furucin Rakiya, nan Kawu da malam Hasan suka shiga ba ta haƙuri. Kafin Rakiya ta haƙura sai da ya tabbatar musu da cewar daga wannan ranar babu aikin Zuwaira da za ta sake ɗauka. Hatta wankn Inna ta daina idan ba ita ta yi niyya ba, yadda su Inna suka ga Rakiya ta fitsare idonta tana faɗar maganganu ya sa har suka ji shakkunta. Sai da Kawu ya yi musu faɗa da nasiha sannan suka wuce gida Rakiya sai harare-harare take tana shan kunu. Tun bayan da wannan al'amarin ya faru Rakiya ta samu 'yancin kai a cikin gidan, daga Inna har Zuwaira babu mai shiga sabgarta. Ita ma harkokinta take yi cikin kwanciyar hankali, kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci ta samu nutsuwa don har kiɓa ta yi. Ita kuma Zuwaira ta cigaba da feleƙe tana laulayin cikinta, yau ta tsiro da wannan gobe ta tsiro da wannan. Da gayya take kiran Malam Hasan idan yana ɗakin Rakiya ta ce masa wani abin take son ci, ko ta fito tsakar gida ta yi ta amaye-amayen ƙarya har sai Inna ta ƙwala masa kira ya fito. Daga ƙarshe ma sai ta tsiri cewa tana gane-gane a ɗakinta, don kada Malam Hasan ya zargi ƙarya take har da rana ko safiya haka take ihu ta ce ta ga giftawar mutum ko ta ce ta ji magana ko motsi a ɗakinta. Hakan bai taɓa damun Rakiya ba, don wani lokacin da kanta take saka shi ya tafi wurin Zuwairat ya kwana da ita idan makircin nata ya motsa. Da yake Inna tana sana'ar sayar da koko da kunu da safe, sai Rakiya ta fara sana'ar ƙosai da wainar gero kuma cikin hukuncin Ubangiji tas suke ƙarewa. Zuwaira tana ƙyalla ido da ta ga haka, sai ta tsiri aman ƙarya da safe ta ce warin suyar ƙosai da waina ne ba ta so. Shi kuma Malam Hasan ya ce ba zai dakatar da Rakiya ba, kuma da ta yi wa Inna ƙorafi sai ta ga ba ta ɗauki wani hukunci ba. Da ta ga makirci ba zai kai ta ba, sai ta zari bin gidajen malamai da bokaye. "Malam na yi yawo gidan malamai da dama, amma kusan duka kuɗina suke ci babu wata biyan buƙata a kan kishiyata. Don haka aka kwatanto mini wurinka, na ce zan gwada nan na gani." Zuwaira ta furta wa mutumin, wanda ya fi kama da riƙaƙƙen ɗan bori. Daga shi sai wani ganye a ƙugunsa, wuyansa, hannuwansa da tsintsiyar ƙafarsa duka sanye yake da wuri. Kansa cike yake da wani irin ƙazamin gashi marar tsafta, kallo ɗaya mai ƙyanƙyami zai yi masa ya ji zuciyarsa tana tashi musamman idan warin jikinsa ya daki hancin mutum. "Ni ba irin jabun malaman da kike zuwa wurinsu ba ne, kuma zan ci ki gyara ni ba malami ba ne. Ni boka ne taɓaɓɓe, ke ma kuma taɓaɓɓiya ce. Ki sa a ranki buƙatarki ta gama biya, saboda kin zo ne a kan kishiyarki. Me kike son ki yi mata, nakasa ta kike so ayi ko kuwa kashe ta zan yi. Domin ni ina kashewa, haukatawa kuma ina nakasawa amma da ikon Allah." Bokan ya furta mata yana zuba mitsitsin idanunsa a kanta, tsuru Zuwaira ta yi ta shiga zare ido jin bokan ya ninka ta rashin imani. Jiki yana rawa ta ce. "Ni kawai so nake.a datse alaƙarta da mijinmu, wallahi ba na son wani abu ya cigaba da shiga tsakaninsu. Amma ina son a ɓullo ta sigar da wani ba zai zarge ni ba, idan na ga wannan ya ci zan dawo ayi mini wani daban." "Idan na lura ke ƙaramar sheɗaniya ce, har yanzu da sauran imani a zuciyarki. Amma tun da kika zo wurina dole mu halaka gabaɗaya, zan yi miki yadda kike so kuma babu wanda zai zarge ki. Ungo riƙe wannan." Ya ƙarasa furucin yana miƙa mata wani garin magani da aka dama shi da ruwan sihiri a cikin farar leda. "Ki tabbatar wannan maganin ya taɓa jikinta, amfaninsa a kan mutum ɗaya ne. Indai ya taɓa mutum ɗaya kowaye, to ko ya sake taɓa wani ya riga da ya tashi daga aiki. Ki yaye don kada a samu matsala, idan kika shafa mata shi duk bayan magriba Aljani Furzum zai dinga saka ta nannauyan bacci, ba shi zai ƙyale ta ba sai gari ya waye. Kuma duk tashin da za a yi mata ba za ta tashi ba, garin maganin mun haɗa shi ne da ruwan wankan gawa da kuma iccan kabari." Hannun Zuwaira yana rawa ta miƙa hannu ta karɓa sannan ta ce. "Godiya nake boka Lado. Nawa ne abin da zan biya?" "Ba kuɗi za ki biya mu ba a zuwanki na farko, za ki kwanta tsirara akwai abin da baƙaƙen Aljanu za su ɗiba a jikinki. Amma kada ki ɗaga hankalinki, babu wanda zai cutar da ke." Ya furta mata yana ɗauko wani ja da baƙin ƙyalle, Zuwaira tana son musa masa tana jin tsoro. Don haka a ɗarare ta tuɓe kayan jikinta, cikin jikinta da ya fara fitowa bokon ya ƙura wa ido. Bayan ta kwanta ya rufa masa ƙyallayen hannunsa, sannan ya rufe idonsa yana kiran aljanu. Sun ɗan jima a haka sannan ya ce ta miƙe ta saka kayanta, daga wannan ranar kuma idan za ta zo kuɗi kawai za ta kawo masa su ma ba masu yawa ba. Zuciyar Zuwaira cike da farinciki ta nufi gida, sai bayan da ta shiga ɗakinta ta sake ciro ledar magani ta ƙare mata kallo ta tuntsire da dariyar ƙeta. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ajiye ta a gefe, ta shiga nazarin yadda za a yi ta kai maganin jikin Rakiya. Tun da na farko ita ba zama inuwa ɗaya suke yi ba, na biyu ba wata doguwar hira suke yi ba. Da ta yi tunanin ko ta takale ta da faɗa don ta shafa mata sai kuma ta tuna da boka ya ce maganin a jikin mutum ɗaya yake aiki. Kenan babu damar ta lakata ta shafa mata a jikinta. "Ko na bari idan dare ya yi sai na shiga ɗakinta na shammace ta?" Ta tambayi kanta, da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta. Tana nan zaune ta ji sallamar Malam Hasan, da yake ita ce da girki sai ba ta fita ba don ta san ɗakinta zai shigo. "Rakiya zo ki gyara wannan." Malam Hasan ya furta daga waje. Jin haka ya sa Zuwaira ta ce, "Bantan uba, ni da girkina amma a ba wa wata shegiya gyaran nama." Da sauri Zuwaira ta tashi, don duk a tsammaninta nama ne Malam Hasan ya kawo, bisa rashin sani ta take ledar maganin ta fasa ta. Maganin ya wanke yatsun ƙafarta, da yake a yunwace ta miƙe da masifa sam ba ta lura ba har ta fita tsakar gida. Littafin 500 ne ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta nan lambar 07062062624 idan littafin ya kammala zuwa doc 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [19/05, 17:24] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA TARA Zuwaira tana zuwa ba ta yi wata-wata ba, ta hankaɗa Rakiya da ke duƙe za ta ɗauki ledar da a Malam Hasan ya ajiye mata. Kasancewar Rakiya ba ta san da Zuwaira ba hakan ya sa da ta faɗi ta bugu a hannu sosai, daga ita har Malam Hasan sakin baki suka yi suna bin ta da kallon mamaki. Cike da masifa Zuwaira ta ce. "Saboda rashin adalci, ranar girkin nawa ka kawo nama za ka ce ta fito ta gyara. Dama ai ka sha cewa ta fi ni iya girki, wato shi ne za a nuna mini rashin adalci. To wallahi uban kuturu ma ya yi kaɗan ballantana na makaho." A wannan karon ma mamakin kalaman Zuwaira ne ya mamaye su, tana sunkuyawa za ta ɗauki leda ta ci karo da waken ƙosa da geron wainar Rakiya. Sororo ta yi jiki a saɓule ta ajiye, tana ɗagowa za ta juya ta tafi da sauri Malam Hasan ya fisgo ta ya ce. "Wai ke wacce irin jahilar mace ce? Me ya sa ko kaɗan ba ki san ciwon kanki ba? Yanzu me kika aikata haka? Ko kin ɗauka yadda kike abu da jahilci haka kowa ma yake yi?" Da farko shiru Zuwaira ta yi duk kunya ta kama ta, amma ganin Malam Hasan ya cigaba da yi mata faɗa ya sa ta fara borin kunya wai don kada Rakiya ta raina ta. "Eh na ji ɗin, duk abin da za ka ce sai dai ka faɗa. Ai da ba a yi mini rashin adalci ba zan magana ba, wa ya sani ma waken ko da kuɗinka ka sayo mata." Zuwaira ta furta tana wurga musu harara, don Malam Hasan ya ƙara tunzura ta sai ya ce. "To ai daɗin zama ne yake sa wa mace ta ce da miji baba, idan na sayo mata ai matata na ƙara wa jari ba wata ba." Zuwaira ta sake hassala, suna jin ta fara hargagi Malam Hasan ya miƙa wa Rakiya hannu ta riƙe ya ɗago ta. Don ya sake dagula wa Zuwaira lissafi ya rungume ta yana kaɗe mata ƙasar jikinta haɗe da yi mata sannu. Waken ya ɗauka da kansa ya kai mata har ƙofar ɗaki, sannan ya shimfiɗa tabarma a tsakar gidan ya ɗauko ƙaton kwandon turarensa don Allah Ya saka masa albarka jarinsa ya ninku. Dogon tsaki Zuwaira ta saki ta koma ɗakinta cike da takaici, sai da ta zauna idonta ya sauka a kan ƙafarta da take jin maiƙo. Ƙirjinta ne ya yi mummunan bugawa, har sai da ta dafe shi da hannunta tana jin tamkar zuciyarta za ta finciko ta fito sarari. Laluben ledar maganin ta fara yi ta hango ta a bakin ƙofa ledarsa ta fashe wanda ya tabbatar mata da take shi ta yi da ƙafarta. "Wayyo Allahna, na shiga ukuna." Zuwaira ta ƙwalla ihu tana ɗora hannu a ka, saboda zallar tashin hankali. A hargitse Malam Hasan ya shiga ɗakin da gudu, cikin damuwa ya shiga jera mata tambaya. "Lafiya me ya faru?" Rasa bakin magana ta yi, don ba ta san me za ta ce masa ba, cikin inda-inda ta ce. "Dama zame wa na yi na faɗi, sai nake jin ƙafata kamar ta gurɗe." Kallon tsaf ya yi mata, don duk wanda ya ƙare mata kallo zai ga ba ta yi irin zaman da za a ce mutum ya faɗi ba. Guntun tsaki Malam Hasan ya saki ya ce. "Amma kamar ba musulma ba Zuwaira, ai sunan Allah ya kamata ki kira ba ihu ba." Ita dai Zuwaira shiru ta yi tana kukan zuci, don hatta jikibta rawa yake saboda tashin hankali. "Ina ne wurin na yi miki addu'a." Malam Hasan ya tambaye ta yana zama a gefenta, ƙafar da ta taka maganin bokan ta nuna masa ta ce. "Duk ƙafar take yi mini ciwo, ka tofe mini ita." Gyaɗa kai Malam Hasan ya yi, sannan ya shiga karanta mata addu'o'in yana tofa mata. "Allah Ya sawaƙe, ki dinga kula." Ya furta mata cikin tattausan lafazi ganin duk ta yi laushi ta fita hayyacinta, wani tunani Zuwaira ta yi. Har ya je bakin ƙofa ta ce, "Ko na zo na je gidan Malam Bala mai kamu." Malam Hasan ya juyo ya ce, "Ke da kike fama ina za ki iya fita, ba gara na kira miki shi ba ya zo har gida. Amma ƙafar taki ta yi tsamari haka ne?" Zuwaira dama ta tambaye shi ne don ta samu ta fita daga gidan, ko ta je gidan bokan da ke can gaba da ƙauyensu ta sanar da shi ɗanyan aikin da ta aikata. Amma jin amsar Malam Hasan ya sa ta ce. "Ƙyale dai mu gani zuwa gobe, idan ban ji daɗin jikina ba ka kira shi." Malam Hasan bai kawo komai a ransa ba, ya sake yi mata sannu sannan ya fita. Bayan fitarsa wani sabon kukan ta dasa marar sauti, abin duniya ya haɗe mata don har ji take kamar rayuwarta ta zo ƙarshe. Tun da ta ga an yi sallar magriba zuciyarta ta cika da tsoro, da yake Malam Hasan bai sake fita ba har sai da ya lura da firgicin da take ciki. "Zuwaira wai akwai abin da yake damunki ne?" A firgice ta ɗago ta girgiza masa kai, ana kiran sallar isha'i Malam Hasan ya miƙe zai tafi masallaci da sauri ta riƙo shi ta ce. "Don Allah ka yi a gida." Da mamaki ya dube ta ya ce, "Sallar zan yi a gida Zuwaira? Wai ko wani abu ne yake faruwa ban sani ba na ga duk kin firgice." A wannan karon gyaɗa masa kai ta yi ta ce, "Eh wallahi tsoro nake ji, don Allah kada ka fita." Komawa ya yi ya zauna a gefen gado ya ce, "Ikon Allah, to shi kenan bari na ɗauro alwala sai mu yi jam'in tare." Da wannan maganar Zuwaira ta gamsu, Malam Hasan ya ajiye hularsa a kan gadon ya fita ɗauro alwala. Malam Hasan yana fita kamar wacce aka dasa wa allurar da ke saka bacci, lokaci ɗaya Zuwaira ta ji idanunta suna lumshewa. Duk yadda ta so dakatar da baccin ya gagare ta, nan take ta ɓingire nannuyan bacci ya yi awon gaba da ita. Koda Malam Hasan ya shigo murmushi ya yi ya matsa gabanta, ganin bacci take hankali kwance har da munshari sai ya ƙi tashinta. Ya ce zuwa jimawa kaɗan ya tashe ta, don tun da ta samu ciki idan ta fara bacci da an tashe ta da ciwon kai take tashi. Da yake shi ma ya gaji, kwanciya ya yi da niyyar kishingiɗa sai baccin ya yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai da asuba da ya ji motsin Zuwaira ta tashi. Da wani irin ciwon jiki Zuwaira ta wayi gari wanda ko kaɗan ba ta san dalilinsa ba, sai abin ya sake haɗe mata ga damuwar asirin boka Lado da ya faɗa kanta ga kuma ciwon jikin da ya addabe ta. Kuma ta gagara sanar da Inna domin ta san daga lokacin da Inna ta san ta fara zuwa gidan boka daga nan sun rana hanya. Saboda duk miyagun halin Inna ba ta yarda da bin malamai ko 'yan tsubbu ba. Hasali ma ko lura ta yi kana biye-biyen bokaye, daga lokacin ta kafa maka ƙahon tsana kenan duk ƙarfin alaƙar da ke tsakaninku. Ga shi Malam Hasan ya ƙi barin ta fita ko nan da can, don har ƙaryar ciwon ciki ta yi masa ya ce zai raka ta asibiti saboda faɗuwar da ta yi. Da ta ji haka har tsoro ta ji, a ranta ta raya ko dai ya fahimci halin da take ciki. Zuwaira haka ta shafe sama da kwana goma cikin wannan yanayin, duk bayan isha'i haka nannauyan bacci yake ɗaukarta. Malam Hasan ko kaɗan bai kawo komai a ransa ba, domin a tsammaninsa ciki ne yake saka ta yawan baccin da take yi. Musammam da ya tuna marigayya mahaifiyar Fatihu a lokacin da ta yi goyon cikinsa, da yake lafiya ƙalau suka zauna da Rakiya hatta girki wani lokacin ita take yi mata ranar girkinta, musamman idan ta ga tana bacci lokacin ɗora abinci ya wuce. A kwana na sha ɗaya ne Zuwaira ta tambaye shi zuwa kitso, bai hana ta ba don haka ta ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda farinciki. Ko wanka ba ta yi ba ta zura hijabi ta fita, kai tsaye ƙauyen Marke ta nufa, gudu-gudu sauri-sauri har ta ƙarasa bukkar boka Lado. A wannan ranar mata uku ta samu ita ce cikon ta huɗu, saboda yadda ta ƙagu har ji ta yi kamar ta shiga ba tare da an zo kanta ba. Da layi ya zo kanta tana shiga ko kyakkyawar gaisuwa ba ta yi masa ba, har ta buɗe baki za ta yi magana ya ɗaga mata hannu. "Ƙaiƙayi ya koma kan mashekiya ko?" Tun bai gama magana ba Tani ta hau gyaɗa kai, boka Lado ya cigaba da cewa. "Ki gode mini, ki kuma yi imani ni ne mai taimakon lamuranki da ba ki yi sati biyu cikin wannan yanayin ba." Jin ta yi shiru sai ya wara mata daƙwa-daƙwan idanunsa da suke jajir ya ce. "Ko ba ki yi imani da ni ba?" "Na yi imani da kai boka Lado, shi ya sa ma na dawo wurinka." Zuwaira ta furta murya tana rawa, boka Lado ya saki wata shashashar dariya wacce ta sake munana faffaɗar fuskarsa ya ce. "Tun da kika yi imani da ni kin gama taɓewa duniya da lahira, ni kuma dama da taɓaɓɓu nake mu'amala. Tashi ki saka ƙafarki a cikin ruwan can, idan kika yi haka komai ya warware daga jikinki. Da ace kin wuce makonni biyu, da za ki dawamma ne a haka." Da sauri Zuwaira ta miƙe ta isa gaban wani sihirtaccan ruwansa da ke cikin wata ƙatuwar jar ƙwarya. Ƙafar hagu ya ce ta fara sakawa, sai da ta tsame ta ta saka ta dama sannan ta koma ta zauna. "Me kike so a yi wa kishiyarki? Ko kin janye buƙatarki?" Ya wurga mata tambaya yana tsare ta da ido, furzar da iska mai zafi ta yi ta ce. "Boka ina son a hana ta nutsuwa, a raba ta da mijinmu. Sannan hatta sana'ar da take yi a dakusar da ita, sai dai kuma don Allah..." "Nan ya yi miki kama da wurin ambaton Allah?" Boka Lado ya katse ta a tsawace, sannan ya ɗora da cewa. "Idan kika sake ambaton sunan Allah sai na hallaka ki." Jiki yana rawa Zuwaira ta shiga gyaɗa kai ta ce, "Tuba nake, dama cewa zan yi kada ayi mata wanda za a ba ni ace na saka mata. Ina tsoron kada na sake samun matsala." Boka Lado bai tanka mata ba, ya ɗauko wani ruwa mai zarni a cikin wani ƙoƙon kai. Sai ya ɗauko wata yar tsana mai ɗan girma, wacce aka rubuce jikinta da jini. Ta ƙasan 'yar tsanar ya ɗauko ƙusa ya ɓula, sannan ya ɗura fitsarin a cikin 'yar tsanar. Abin da ya fi ba wa Zuwaira mamaki, yadda duk yawan fitsarin aka ɗurewa 'yar tsanar ba tare da ko kaɗan ya zubo ƙasa ba. Miƙa mata 'yar tsanar ya yi ya ce ta duba, duk iya dube-duben da ta yi ba ta ga fitsarin ba. Tana shirin yin magana ya katse ta. "Wannan da kike gani, tsafataccan fitsarin alade ne. Wannan 'yar tsanar da kika gani tana mazaunin kishiyarki ne, fitsarin da na ɗura mata yoyonsa za ta fara. Amma ina son ki sani, kishiyarki tana da ƙoƙarin riƙo da addini, sai dai kin san inda ta ba mu damar da za mu aiwatar da aikinmu a ƙwanciyar hankali?" Da sauri Zuwaira ta girgiza masa kai, Boka Lado ya cigaba da cewa. "Tana da ɗabi'ar zama kai babu ɗankwali, ba iya da rana ba har da daddare tana iya zama babu ɗankwali a kanta. Kuma idan ta zo kwanciya bacci ba ta damu da addu'a ba, mu kuma duk wani asiri mun fi gudanar da shi da dare. Ta wannan hanyar za mu yi amfani mu cimma manufarmu." Cike da ƙeta Zuwaira ta saki dariyar mugunta tana yi masa jinjina da hannu ta ce, "Aikinka yana kyau boka Lado." Wata matacciyar jaɓa ya ɗauko a cikin leda har ta fara wari, ya ɗauko 'yar tsanar ya saka wani zaren guru ya ɗaure sannan ya miƙa wa Zuwaira. A ɗan tsorace ta ja da baya, kallon da ya yi mata ya sa ta yi saurin miƙa hannu ta karɓa. Ya nuna wata tasa da ke kan wuta tana zaɓalɓala da jini a ciki ya ce ta saka tana ambatar sunan Rakiya. Haka Zuwaira ta matsa gaban wutar ta jefa su tana ambatar sunan kamar yadda ya ce ta yi, tana jefawa ya ya saki dariya ya ce. "Kin gama da wannan babin." Cike da farinciki Zuwaira ta kawo kuɗi ta ba shi, sannan ta yi masa godiya. Har ta miƙe za ta tafi ya ce. "A yau da daddare za mu gudanar da ƙarashen aikin a kanta, zuwa wayewar gari za ki ga abin da zai faru." "Godiya nake Boka Lado, haƙiƙa na yarda da hatsabibancinka." Daga haka Zuwaira ta fita zuciyarta fes ta wuce gida, kamar kuwa yadda Boka Lado ya ankarar da ita tana shiga ta samu Rakiya a zaune tana tsintar wake kanta babu ɗankwali. Zuwaira ta saki murmushin mugunta mai sauti har sai da Rakiya ta ɗago ta kalle ta. ABBAN FAUWAZ Mamaki kwance a saman fuskar Abba ya ce, "Tani kin san me kike faɗa kuwa?" Tani ta dube shi ido cikin ido ta ce. "Ƙwarai kuwa na sani, takardar saki na ce ka rubuta mini don ba zan iya cigaba da zama da matsiyaci ba." Matsawa gabanta ya yi, ya kamo hannunta ya shafa ya ce. "Tani kina ji na?" Da zafin nama ta fisge hannunta, cike da rashin mutumci ta ce. "Malam ka kama kanka! Ko kuma takaucin ya fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ne?" A fusace Abba ya ce, "Wai Tani kin san me kike faɗa? Ni mijinki kike faɗa wa haka?" "Wane ne mijin? Mijin irinka mijin banza da wofi, ƙasƙantacce matsiyaci..." Tass! Abba ya sakar mata mari a fuska, da sauri Tani ta riƙe kumatunta tana bin sa da kallo. A madadin ta ji zafin abin da ya yi mata sai ta saki murmushi ta ce. "Tun kafin yau na shirya jin marinka a fuskata, don kaine a makare. Abin da ba ka sani ba, tun ranar da na shigo gidanka nake shiri da tanadin abubuwa a kanka. Ruwanka ne ka nemi mafita, ruwanka ne ka tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi maka ƙafa." Daga haka Tani ta koma cikin ɗaki ta haye gado cike da rashin mutumci. Saboda mamakin kalaman Tani da ƙyar Abba ya iya jan ƙafarsa ya fita daga gidan, sai dai har ya isa kotun jikinsa a mace yake ga tarun damuwa da tashin hankali da suka zame masa abokan shawara. A wannan ranar da suka fara zaman shari'a aka gabatarwa da Abba tuhumar da ake ƙararsa a kanta, nan take ya amince da ƙunshin tuhumar. Bayan tattaunawa alƙalin ya cewa Abba da ya yi ƙoƙarin nema wa Alhah Dikko haƙƙinsa kafin wani zaman. Da haka zaman kotun ya watse, daga kotun Abba ya wuce gidan 'yar uwarsa Goggo. Kallo ɗaya ta yi masa ta ga duk ya sake fita hayyacinsa, sai da suka gaisa sannan ya sanar mata da abin da ya faru tsakaninsa da Tani. Murmushin takaici ta saki ta ce. "Yanzu ka ga maganar yaron nan tana hanya? Ka ga abin da Fauwaz yake son ankarar da kai, ka rufe ido kake ƙyamarsa." Shiru Abba ya yi, sai zuwa can ya ɗago cikin damuwa ya ce. "Wallahi tallahi ban taɓa tsammanin Tani za ta yi mini haka ba, Tani ta shammace ni ta ci amanata." Ya ƙarasa maganar kamar zai zubar da ƙwalla, Goggo ta jima tana ba shi baki sannan ya yi mata sallama. Da ɗan canjin da Goggo ta ba shi, ya tsaya ya sayi naman miya da zummar idan ya kai gida ko zai shawo kan Tani. Sai dai yana zuwa ya buɗe ƙofar ya ga gidan wayam, a haukace ya dinga duba ɗakunan yana kiran sunan Tani sai dai gabaɗaya kayan sawarta ya ga babu ta kwashe su. Daga kan Tv ya hangi wata farar takarda guda biyu, jikinsa yana rawa ya saka hannu ya ɗauka ya fara karantawa. _Har yanzu na san zuciyarka tana cike da wasu-wasi a kan kalaman da na furta maka, ina son ka sani. Ni Tani dama ina tare da kai ne domin biyan buƙatar kaina, a yanzu kuma na cimma manufa ta dole na wurgar da ƙwallon mangoro na huta da ƙuda. Ina tunasar da kai da ka sani, Tanin da ka sani a shekarun baya, ita ce dai wacce ka yi rayuwar aure da ita a yanzu. Girma da shekaru ba su isa su sauya Tani ba, idan Tani ta ce sai ta yi duk daren daɗewa sai ta zartar da shi. Zan sake sanar da kai, wallahi tallahi ko kana so ko ba ka so dole ka sake ni. Ka saurari haɗuwar da za mu yi a gaba._ Abba yana gama maganar ya ji gumi ya shiga keto masa, ɗayar takardar da ke gefe ya ɗauka sai dai tun kafin ya buɗe ta ya ga a ido ta fi wacce ya gama karantawa tsufa. Yana buɗe ta bayan ya ƙura mata ido ya ji gabansa ya yi mummunan bugawa, zanen rubutun da aka yi da baƙin biron da ke jikin takardar ya tuna masa da tarun al'amauran da suka faru a shekaru goma sha bakwai da suka wuce. Da sauri ya wurgar da takardar, sai ya ji tamkar ya riƙe ruwan dalma a hannunsa. Ya kifa kansa a sama cinyarsa yana faɗin. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Shiru ya yi yana jin zuciyarsa tana yi masa raɗaɗi, raɗaɗin da ya gagara tantance a mahallin da zai ajiye shi. Musammam da ya tuna shukar tsiyar da noma wa Tani a shekarun baya. Gobe za mu gama free pages ɗinmu🥳 jama'a yanzu ne za a fara naɗa GAMMON RAMA, kowa yasan za a sha tsami a cikinsa. Akwai tarin ƙalubale da darussan hannunka mai sanda, kada ku yi sanya domin yanzu ne za a fara wasan.👌🏻 500 ne ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan ya kammala zuwa document 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [20/05, 16:30] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA GOMA Abba ya jima a zaune cikin rashin daɗin yanayi, jikinsa a sanyaye ya miƙe ya shiga ɗakin su Fauwaz. Tsaye ya yi yana ƙarewa ɗakin kallo, abubuwa da dama suka shiga dawowa cikin kwanyarsa ciki har da mutuwar Abida. Sai a lokacin yake tuna irin kalaman da Tani take yi masa a kan 'ya'yansa, da irin shakulatan ɓangaro da ya yi a game da amanar da mahaifiyarsu ta ba shi kafin ta bar duniya. "Kaico Abidata, Allah Ya sabunta rahama a gare ki da mahaifiyarki." Ya furta a sanyaye, sai kuma Fauwaz ya faɗo masa, cikin nadama da danasani ya ce. "Yanzu ɗan cikina ne a almajiranci? Shin me ya faru da ni a wancan lokacin da na gagara gane gaskiyar da yaron nan yake son nusar da ni?" Amsar da ya gagara ba wa kansa kenan, shi kaɗai ya shiga surutan nadama a kan cuzgunawa su Fauwaz da suka dinga yi a baya shi da Tani. "Ya zama wajibi na je na dawo da shi gabana." Ya furta a sanyaye, sai kuma wani tunani ya faɗo masa don haka y furzar da iska mai zafi ya ce. "A ina zan samu kuɗin mota?" Saboda a wannan a gaɓar da yake hatta naira ɗari ta kansa wuya take yi masa, ganin rubuta wasiƙar jakin da yake yi ba za ta kai shi ba. Sai ya miƙe ya fito, ya shiga ɗakin kwanansu. A nan ma ɗakin ya shiga bi da kallo ganin Tani ta yashe komai nata, hularsa da ke yashe a ƙasa ya ɗauka ya saka. Tunanin zuwa gidan kawun Tani ne ya faɗo masa, don haka cike da ƙwarin gwiwa ya rufe gidan ya nufi shagon Nalami da ke bayan gidansa. Nalami yana ganinsa ya haɗe rai, Abba ya saki murmushi don ya san dalilinsa na sauya fuska. 'Tabbas rayuwa darasi ce, sautari idan kana da shi mutane kowa ƙaunarka yake. Amma da zarar wata jarrabawa ta afka maka a nan ne za ka fahimci wanda zai mu'amalance ka tsakani da Allah.' Abba ya raya a ransa, sannan ya yi sallama a shagon. A ɗan daƙile Nalami ya ce. "Wa alaikassalam." Abba ya ɗan yi jim sannan ya ce. "Don Allah Nalami kada a gaji da ni, yanzu ma aron ɗari biyu za ka ba ni, idan aka haɗa da waɗancan sun kama dubu ɗaya." Kamar Nalami yana jira ya yi zaraf ya ce, "A gaskiya Alhaji ba za ta samu ba, waɗancan ma yanzu nake shirin aika maka kuma sai ga ka." Nalami ya ƙarasa kalamansa yana ƙara tsuke fuska. "Alhaji kana da canjin ɗari takwas fa." "Alhaji ka biyo ni ɗari biyar jiya." "Kullum dai Alhaji ba ka gajiya, to an gode Allah amfana." "Gaskiya ne Alhaji, ni fa duk unguwar nan na fi jin daɗin cinikinka, saboda ko babu komai mutum zai ƙaru da 'yan canji." Abba ya tuna ire-iren kalaman Nalami a baya, a lokacin da kuɗi yake gara masa idan ya zo sayayya wurinsa. Don a wancan lokacin canji indai ba mai yawa sosai ba ne bar wa masu shago yake, musamman Nalami da ya fi kusa da gidansa. Amma shi ne a kan dubu ɗaya Nalami yake ɗaure wa fuska har yana nuna masa iyakarsa. 'Marar shi ba ya zuciya.' Abba ya sake raya wa a ransa, don haka ya ce. "Don Allah ka taimaka mini Nalami, zan yi ƙoƙari na haɗa maka kuɗin cikin ƙanƙanin lokaci." "A gaskiya wannan ne na ƙarshe indai ba ka kawo wani abin ba na gama ba ka rancen kuɗi." Nalami ya furta sannan ya zaro ɗari biyu ya miƙa masa a wulaƙance, idanun Abba ne suka ciko da ƙwalla. Ganin a kan ɗari biyu ana ƙoƙarin cin zarafinsa, ɗari biyun da yake ganin ba komai ba ce a wurinsa. Karɓa ya yi ya masa godiya ya tafi, a wancan lokacin da yake kuɗi suna da daraja. Ɗan achaɓa ya tara ya nufi unguwar Sheka gidan Kawun Tani. A lokacin da ya ƙarasa Dattijon yana zaune a kan bencinsa ƙofar gida, cikin girmamawa Abba ya russuna ya ce. "Barka da yamma Baba." Faɗaɗa fara'arsa Dattijon ya yi ya ce, "Barka dai, au Lawan ne da yammacin nan?" Abba ya ɗan sosa kai ya ce, "Eh ni ne Baba, ya mutanen gidan?" Baba ya nuna masa tabarmar da ke gefen bencin ya ce, "Ga wuri ka zauna mana, ya su Tani?" Abba har ya miƙe domin ya je ya zauna, sai ya ji gwiwarsa ta yi sanyi da tambayar da Baba ya yi masa. A saɓule ya zauna ya yi shiru ya faɗa tunanin wurin da Tani ta tafi, har sau biyu Baba ya yi masa magana bai ji ba. Sai da ya taɓa shi bayan Abba ya amsa Baba ya ce, "Lawan ko wani abu ne ya haɗa ka da Tani? Ina fatan dai lafiya ko?" Abba ya shafo gemunsa ya ce, "Eh to gaskiya ba lafiya ba Baba..." Duk abin da ya faru Abba ya kwashe ya ba wa Baba labari, sannan ya ɗora da cewa. "Shi ya sa na ce bari na zo nan, don na san duk garin nan babu wanda take da shi sama da kai. Da har zan je gidan abokin mahaifinta, sai na ga nan ne ya dace na zo tun da ka fi kusanci da ita." Gyaran murya Baba ya yi ya ce. "Eh kam tabbas haka ne, ni na fi kusanci da ita a kan Alhaji Harisu, tun da a lokacin da muka yi zaman Shagamu da mahaifinta Alhaji Harisu bai zo garin ba sai dab da mahaifinta zai rasu. Ni da shi bacci ne yake raba mu amininsa ne ƙud da ƙud." Da ɗam rashin fahimta Abba ya ce, "Baba kana nufin kai ba yayan mahaifinta ba ne?" "Yayan mahaifinta? Ita Tanin ce ta ce ni ne yayan mahaifinta?" Baba ya furta da sauri, Abba ya gyaɗa kai ya ce. "Eh haka ta ce mini bayan haɗuwarmu, shi kuma Alhaji Harisu abokin mahaifinta." "Tirƙashi! Lallai yarinyar nan makira ce, ashe haka ta iya yaudara? To wallahi yaro babu abin da na haɗa na jini da Tani, ni ban san ma yadda aka yi ta lalubo gidana ba. Ta zo da kukanta wai aurenta ya mutu ba ta da wurin zama, ganin irin zaman mutumcin da muka yi da mahaifinta ya sa na ba ta ɗaki. A lokacin har zance ta tafi dangin mahaifinta ko mahaifiyarta, to sai na ga kamar ba za ta ji daɗi ba tun da ta san da can ɗin ta taho wurina." Baba ya ƙarasa maganar yana sakin ƙwafa, sannan ya ɗora da cewa. "Ni ban san lokacin da Tani ta lalace haka ba, kodayake tun haɗuwarta da wani ɗan iskan yaro a shekarun baya duk ya lalatata. Allah dai ya kwashe masa albarka, duk ya gurɓata tunanin yarinyar nan." Shi dai Abba zuru ya yi kamar an jiƙa ɓera a buta, haka kawai jikinsa yake ba shi kamar shi ake kwashe wa albarka yana zaune. "To yanzu Baba a ina kake ganin zan iya ganinta?" Abba ya tambaye shi cike da damuwa, cikin sauri Baba ya wara hannuwa ya ce. "Allah masani Lawan, don wallahi ba na ce ba. Ka leƙa gidan Alhaji Harisu ƙila ko can ta nufa, ni kuwa dama ta gama zaman gidana don ba za ta haɗa mini masifa da kafirar ƙaryarta ina zaune ƙalau ba." A sanyaye Abba ya miƙe har zai saka takalminsa ya ɗan sunkuyo ya ce. "Amma Baba ya sunan yaron da ka ce ya cuce ta ya gurɓata mata tunani..." "Kai da ka zo neman matarka ina ruwanka da wani ƙato?" Baba ya katse shi a fusace sannan ya ɗora da cewa, "Wai me ya sa wasu mazan sun cika kishin masifa ne? Idan na faɗa maka sunan me za ka yi da shi bayan wannan zancan da nake yi maka ya doshi shekara goma sha biyar zuwa sama." Da sauri Abba ya zura takalminsa ya yi wa Baba sallama, don ya lura tun da ya faɗi ƙaryar da Tani ta yi masa ya hassala. Kai tsaye gidan Alhaji Harisu ya nufa, a lokacin har an fara kiran sallar Magriba. Sai da ya yi sallah sannan ya same shi ya sanar da shi abin da yake tafe da shi, sai dai shi kansa a nan ya tabbatar masa da Tani ba ta gidansa. Kuma ya ɗauki lokaci mai tsayi bai saka ta a idonsa ba. A saluɓe Abba ya baro gidan, ya shiga tunanin inda zai ga Tani saboda akwai muhimmiyar tattaunawar da yake son su yi. Lokacin da ya ƙarasa gida gani ya yi gidan ya zame masa kamar kango, saboda yadda damuwa ta cunkushe shi ko abincin da ya sayo ya kasa ci. Daga kan gado ya hango wata farar takardar, nan take gabansa ya faɗi. Domin a yanzu farar takarda ta fi komai ɗaga masa hankali, kamar wanda za a kama haka Abba ya miƙa hannu a hankali ya ɗauko takardar. Sai ya ga wani rubutun Tani ta ajiye masa. _Daga lokacin da ka karanta waccan wasiƙar, na tabbata zuciyarka a ɗokance take da san sanin wurin da nake rayuwa. Sai dai ka sani, za ka yi ta bulayi bara a kufai ne har zuwa lokacin da zan bayyana maka kaina. Kada ka ɗauka wannan takardar a tare da waccan na ajiye maka, a'a, na ajiye maka ita ne ɗazu bayan ka tafi gidan Baba nemana. Na barka lafiya._ Abba ya karanta wasiƙar babu adadi tamkar yana son gano wurin da Tani take a cikin takardar, a nan ya cigaba da zama har bacci ya yi awon gaba da shi. Daga wannan ranar sai rayuwa ta sake juye masa, al'amuransa suka cigaba da dagulewa. Duk shagunan da yake karɓar bashin kaya sun daina ba shi. Abokan kasuwansa kuwa tuni suka janye jikinsu daga gare shi, idan ya ce su ba shi aron kaya ya kasa ko zai ɗora na shi fir suke hanawa. A haka suka cigaba da zaman shari'a wani lokacin ma sai dai ya tafi kotun a ƙafa, wani zubin kuma ya nemi alfarmar a rage masa hanya a wurin masu ababen hawa. Sannu a hankali kwanaki suka cigaba da shuɗewa har aka kammala shari'ar su Abba, daga ƙarshe da ba a samu komai daga gare shi ba alƙali ya aika shi zaman gidan yari na shekara takwas babu zaɓin tara. Sakamakon an bi duk wasu ƙa'idojin da suka dace amma bai cika su ba, na farko an ce ya dinga biyan wani kaso lokaci-lokaci ya ce ba shi da hali. Alƙali ya ce ya sayar da wata kadararsa, ko a yi ƙiyasun kuɗinta ya mallaka wa mai fili ita. Amma gabaɗaya Abba ya nuna gazawarsa, Alhaji Dikko da Alhajin da ya sayi fili a wurin Abba suka lamunce da a tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari don ya yi musu zaman kuɗinsu. Don haka aka ingiza ƙeyar Abba da wasu tsirarun matasa, waɗanda su kuma aka same su da laifin fashi da makami. Babban abin da ya fi tsaye wa a zuciyar Abba shi ne Fauwaz, saboda a cikin kwanakin ya sha yin mafarkinsa cikin mummunan yanayi. Don haka yake ta neman yadda za a yi ya samu kuɗin motar da zai je ya ɗauko shi, sai dai haƙarsa ba ta cimma ruwa ba har aka kai shi gidan yari. Don haka ya sa a zuciyarsa duk ranar da Goggo ta kawo masa ziyara, zai ba ta adireshin garin da Fauwaz yake da sunan makarantar allon da ya kai shi. Ranar wata Alhamis ita ce ranar da aka kai Abba gidan yari, a ranar Asabar ɗin da ta zo yana zaune jigum cike da damuwa. Domin har da ya kwana biyu a gidan ya gagara sakin jikinsa yadda ya kamata, musamman da yake jin sa a takure da zaman wuri ɗaya. Mamaki abin yake ba shi da ya ga wasu sun sake kamar a gidajensu suke, ganin ana ta zuwa ziyarar mutane sai ya ji ina ma zai samu wannan gatan. 'Yanzu a duk duniya wa kake tsammanin zai kawo maka ziyara? Ko don wannan ai ka ga ranar Fauwaz.' Zuciyar Abba ta raya masa, bai yi tsammani ba ya ji hawaye ya ziraro masa. Sai kuma ya tuna da Goggo, ya san duk duniya Goggo yake da ita shaƙiƙiyar 'yar'uwa, kuma a yadda take ji da shi ya san za ta samu lokaci ta shigo masa. Yana cikin wannan yanayin wani ma'aikaci ya leƙo ɗakinsu ya ce, "Lawan Shu'aibu 2442." Da sauri Abba ya ɗago ya ce, "Ga ni." "Ka zo kana da baƙuwa." Ganduriban ya furta, wani irin sanyin farinciki ne ya lulluɓe shi. Jikinsa yana rawa ya bi bayansa, suna zuwa Abba ya yi turus sakamakon ganin wacca ya yi tozali da ita. Saboda tsananin mamaki har sai da ya murza idanunsa don ya tabbatar ba mafarki yake yi ba. GIDAN MALAM HASAN Suna haɗa ido Zuwaira ta yi tafi cike da izgilanci ta fara waƙoƙin habaici, Rakiya ba ta kula ta ba ta cigaba da tsintar wakenta. Saboda yadda Zuwaira take jin ɗokin ganin abin da zai faru har alla-alla take dare ya yi, ita kuwa Rakiya da ba ta san wainar da ake toyawa ba ta cigaba da sabgoginta zuciyarta fes cikin kwanciyar hankali. A daren ranar dama Malam Hasan a ɗakinta yake, tun bayan magriba ta yi kwalliyarta cikin riga da zani. Sai da aka yi sallar Isha'i sannan Malam Hasan ya shiga, da yake yawancin sai ya yi sallah yake shiga gida gabaɗaya. Sai da ya fara shiga ɗakin Zuwaira ya duba lafiyarta, da yake haka ƙa'idarsa take. Idan ba ya ɗakin mace to kafin ya shiga ɗakin mai kwana sai ya fara shiga ya duba lafiyarta sun ɗan taɓa hira ko ta minti biyar ce. Haka idan gari ya waye kafin ya fita sai ya leƙa ya ga yadda kika tashi. Tun da ya shiga ya lura da annurin da ke saman fuskar Zuwaira, har sai da ya gagara haƙuri ya ce. "Hala akwai wani albishir da kika ƙunshe mini a bakinki?" Kamar Zuwaira tana jira ta yi zaraf ta ce, "Ni kuwa nake da albishir Yaya." Murmushi ya saki ya ce, "Ina jin ki." "A'a gaskiya, sai Allah Ya kaimu zan sanar da kai tun da na tabbata shi ne babban albishir ɗin da za ka fara cin karo da shi." Zuwaira ta furta tana yin far da ido cike da kissa da jin daɗin ganin Malam Hasan ya sake mata yadda take so. Miƙewa ya yi ya ce, "To bari na wuce tun da ba za ki sanar da ni ba." Wani abu Zuwaira ta tuna ta yi saurin cewa, "Mafarki na yi fa wai na haifi tagwaye duka maza." Da sauri ta ga ya faɗaɗa fara'arsa ya ce. "Allah Ya tabbatar mana da alheri, ko ɗaya Ubangiji Ya ba mu masu albarka muna so." Nan take ta haɗe fuska ta ce, "Sai ka ce Allah Ya tabbatar mana ai, ko tagwayen ne ba ka so? Ko kuma don ba matar so ce da cikin ba?" "Zuwaira kina da matsala wallahi! Mene ne laifi a addu'ata? Ko kuwa kawai za mu ce Allah Ya tabbatar ko da ba mai albarka ba ne?" Shiru ta yi ta zumɓuri baki gaba, sai ta ga ya miƙe zai fita. Tunowa da al'amarin da zai faru da Rakiya ya sa dariya ta suɓuce mata sannan ta ce. "To sai da safe mu kwana lafiya." Mamaki ne ya kama Malam Hasan, don kusan tun da ya auro Zuwaira zai iya lissafa sau nawa ta yi masa sai da safe cikin tattausan lafazi, idan ba a ɗakinta yake da kwana ba. Amsa mata ya yi sannan ya fice ya nufi ɗakin Rakiya. Da sallama ya shiga ɗakinta, ya hango ta zaune a kan tabarma ta sha kwaliyya sai ƙamshi take yi. Hannuwa ya buɗe mata, tana daga zaune ta ɗan tura baki gaba tana ɗauke kanta gefe. Ya lura neman kaɗan take yi 'yan kishin su motsa, don haka ya kama kunnuwansa da hannuwansa ya ce. "Kaina bisa wuyana." "Ka koma can na yafe kwanan." Rakiya ta furta a shagwaɓe, waro ido waje ya yi cike da tsokana ya ce. "Idan kika sallama ni ina zan saka kaina? Ki yi wa Allah ki taimaki marayan Allah." Murmushi ta saki cikin zolaya ta ce, "Ai kana sani kake son yi wa marainiyar Allah riƙon sakainar kashi, kai da ga Inna nan a ina za ka kira kanka da maraya." Ƙarasawa ya yi ya zauna a kusa da ita, ya janyo ta jikinsa ya zuba mata ido cike da so ya ce. "Wai yaushe kika iya surutu haka?" Ta saka hannu ta riƙo fuskarsa kusa da tashi, har suna iya jin numfashin juna ta ce. "Ranar da ka fara iya haɗa ido da ni." Ta ƙarasa furucin tana kashe masa ido ɗaya, kamo ta zai yi ta miƙe da sauri tana dariya. Malam Hasan ya ce, "Yarinyar nan me kike nufi?" Sai da ta ɗauko tire ɗin abincinsa sannan ta ce, "Ka fi kowa sani ai ƙolona." Ita da shi gabaɗaya suka saka dariya, domin sun tuna lokacin da suka fara soyayya Malam Hasan yana matsayin Almajirin gidansu. Cikin farinciki suka ci abinci suna wasa da dariya, don a daren ranar sun faranta ran juna tamkar wasu sababbin amare. Tsaye take a wani ƙungurmin dajin da babu gida gaba da baya, sai manyan bishiyoyin kuka masu siffar ban tsoro. Lokaci ɗaya hadari ya haɗu, walƙiya ta dinga gilmawa ta ko'ina. Tana nan tsaye cikin firgici da tsoro ta ji bishiyoyin kukar suna takowa gabanta, waɗansu daga cikinsu suna ƙyaƙyata dariya marar daɗi sauraro. Daga saitin tsakiyar ƙafafuwanta ji ta yi ƙasa tana darewa, tana sauke idonta ta ga wani murgujejen maciji ya faso kai ta cikin ƙasa. Duk yadda ta so motsa ƙafarta domin ta gudun don ceton rayuwarta ta ji ta gagara, bakinta take son motsawa amma ko kaɗan ta kasa. Tana ji tana gani macijin ya sulalo kansa ta ƙarƙashinta. A daidai ƙasanta ta ji ya tura kansa, ya fesa mata wani ruwa mai tsananin zafi. Ta saki ƙara cike da azaba, tana kururuwar neman ɗauki. Ya jima a haka sannan ya zaro kansa, sai da ya matsa can gabanta sannan ya miƙe tsaye. Daga cikin macijin ta ga ya rikiɗe zuwa surar mace, ba ta ga fuskarta ba saboda ta ba ta baya kuma tana tafe tana ƙyaƙyata dariya. Firgigit! Rakiya ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi, motsawar da za ta yi ta ji ta sharkaf cikin ruwa. Warin da ya daki hancinta ne ya sa ta yi saurin bankaɗa zanin jikinta, tana cikin wannan yanayin ta ga Malam Hasan ya shigo ɗakin hannunsa riƙe da kaya yana sharce ruwan kansa wanda hakan ne ya tabbatar mata daga banɗaki yake. "Rakiya me yake faruwa ne? Ina ta shi na ga gadon ya ɓaci da ruwa, na yi tsammanin ko mafarki kika yi ruwan fitsari ne. Amma kuma sai na ji yana wari yanzu haka wanka na yi zan je masallaci." Wa Abban Fauwaz ya gani har ya gigice? Me ya aikatawa Tani a shekarun baya? Ya ya rayuwar Fauwaz za ta ƙarke bayan an rufe mahaifinsa a gidan yari? Shin zai dawo? Idan ya dawo wurin wa zai dosa? Kuma wacce irin savuwar rayuwa yake yi a can? Yaya makomar Gambo dillali? Ya ci bulus shi da Tani ko gaskiya za ta yi halinta? Tun a farkon labarin ba a ambaci dangin mahaifiyar su Fauwaz ba, shin tana da dangi ko ba ta da su? Idan tana da su a ina suke rayuwa? Da alama Zuwaira ta yi galaba a kan Rakiya, shin ya Rakiya za ta kaya ga tsangwamar Inna ga kuma sabuwar lalurar da ta same ta. Shin Rakiya z ata haihu kuwa ko kuwa ƙaddararta ce a haka? Idan aka cigaba da tafiya Inna za ta sauko ta ƙaunaci Rakiya, ko kuwa ƙiyayya ce ta har abada. Ina dangin mahaifi da mahaifiyar Rakiya da ba ta da kowa sai Malam Hasan? Yau idan Malam Hasan ya kwanta dama ina makomar Rakiya? Gabaɗaya waɗannan amsoshin suna cikin cigaban labarin nan.💃🏻🥳 AlhamduLillah mun kammala free pages ɗinmu, ga mai son cigaba zai biya 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624