[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. MABUƊI Idan aka ambaci kalmar 'Fuska' abin da yake fara zuwa zuciyoyi da dama, ita ce fuskar ɗan'adam da Allah Subhanahu Wata'ala Ya hallita masa. Wacce a cikinta Ya samar da rassa mabambamta, don a mafi yawancin lokuta ta hanyar ganin fuskar ne ake gane ɗan yanki kaza da kuma al'umma kaza. Idan muka dubi aure ta fuskar addinin Musulumci, za mu fahimci abu ne mai kyau. Domin koyi ne, ga sunnar Annabinmu Annabi Muhammad (S.A.W). Wanda hawa doron sunnar yana iya kai miliyoyin Al'umma zuwa ga turbar tudin tsira, wato Aljannar da kowanne cikakken ɗan'adam musulmi yake fatan rabauta da ita. Kuskurewa haka; ko wofantar da ƙa'idojin bin sunnar, suna iya kwasar al'umma zuwa ga wutar Jahannama. Wacce duk musulumin ƙwarai yake bakin ƙoƙari, wurin yin katangar ƙarfe/ tsari da ita. Kamar yadda muka sani, zamani rikiɗa yake tamkar hawainiya/wahainiya. Haka kowanne zamani da suffar da yake tafiya, tare da al'ummar da suke rayuwa a cikinsa. A wannan zamanin da ake tafiyar biri a yashi, mata da dama suna kallon aure da ta fuskoki daban-daban. Haka kuma wasu sukan kalli ƙarin aure, ko kawo abokiyar zama ta munanan fuskoki mabambamta. Musamman yadda iyayen gida suke ganin wayo ko dabararsu ce, ta sa aka auro su a matsayinsu na iyayen gida. Har wasu daga cikinsu suke cin duniyarsu da tsinken tsire, ta hanyar gasa wa amare gyaɗa a hannu. Ko kuma ɗanɗana wa maza kuɗarsu, domin hana su rawar gaban hantsi da amarensu. Saboda suna ganin sun zama tamkar ruwa a cikin gida ko kuma kujerun zama, da ko an ƙi ko an so dole a zauna da su. Ba tare da sun hangi me gobensu za ta haifar musu ba. To amma duk da yadda ake ganin iyayen gida suna wasan juyin waina da amare, lamarin bai sauya zani ba. Domin a ɓagaren amaren da suke ta cin alwashin mijin wata ne zaɓinsu, a guntun tunanin wasu daga ciki. Sukan yi tsammanin gazawa, gajiyawa da rashin so ne yake sa miji yake nemansu har ya aura a matsayin mata ta biyu, uku ko huɗu. Musamman da ya kasance maza da dama, sukan kwayewa iyayen gida baya tun a neman auren. Silar haka ne yake sa amare suke hangen kansu a bigiren cusguna uwargida, duk don su nuna musu miji ya daina yayinsu. Ko kuma sun daina ganinsu, a matsayin mata masu ƙirar da Allah (S.W.A) Ya hallata musu, domin su kasance sanyin idaniya a wurinsu. Ba tare da amaren suna tsalle ko yin ɗage ba, don su hangi yankan kunkurin Balan da suke yi wa rayuwarsu. SHAFI NA ƊAYA Gidan Yaya Salis cike yake da mata har da ƙananan yara, saboda yinin dannar ƙirjin da ake yi wa Aunty Murja. Tun da yamma ta ƙarato gabanta yake ta faɗuwa, don haka ta koma cikin 'yan uwanta da ke ɗakin gadonta. Musamman da giftawa ɗaya-biyu idan ta yi, daga tsakar gida zuwa falonta sai ta ji maganar da za ta sosa mata rai. Bilkisu zaune take a falon gidan ita da ragowar 'yan'uwanta, don yawanci cikin falon cike yake da su dangin miji. Kallon Hafsa ta yi ta ce. "Miƙo kuɗin na ki ankon, dama ai kin ce idan muka haɗu yau za ki ba ni. Kin san yanzu an daina kasuwanci da bashi, maza ki ba ni na ɗora lissafi." Murmushi Hafsa ta yi ta ce. "Aunty Bilkisu duk cinikin da kika yi ina laifi ma ki bar mini a ribar da kika samu." Harararta Bilkisu ta yi, za ta yi magana suka ga Aunty Murja ta fito ta shiga kicin. Salma ce ta ɗan zunguro Bilkisu, ta yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce. "Ni fa wallahi Aunty Murja tausayi take ba ni, duk da tana danne kishinta amma kin ga duk ta rame, ji fuskarta duk ta sauya kamar kuka ma ta yi." Taɓe baki Bilkisu ta yi ta ce, "Ni babu wani tausayi da ta ba ni, ai wallahi ba ƙaramin daɗi na ji ba. Ki duba fa ki ga yadda ta samu wuri a gidan nan, duk girman ɗakunan nan a ce daga ita sai 'yan 'ya'yanta uku. Duk ta bi ta kanainaye shi kullum sai uwar ƙiba yake yi, yanzu idan aka kawo amarya ai dole ta lanƙwashe ƙafafuwanta." Lokaci ɗaya suka saki shewa haɗe da tafawa. Hadiza da ke gefe, abokiyar wasan su Bilkisu ce ta ce. "Magana ta domin Allah fa babu macen da ba ta san sakewa a gidanta, sai dai idan ba ta samu yadda take so ba. Kishiya kuwa ai babu daɗi, ni wallahi Aunty Murja ma ba ƙaramin birge ni ta yi ba. Saboda ko babu koma ta kama kanta, babu abu ɗaya da za a ce ta yi a lokacin bikin nan." "Allah ko sakaran neman wurin zaman? To ni dai ina shafin amarya. Don jiya da na je lalle na biyo ta nan, danginta sun zo jere har taya su buga ƙusar labule na yi. Ke zanin gado ma ni na shinfiɗa, yoo hauka ake zan bi bayan matar wa ga wurin da ɗan'uwana zai ɓarje amarci." Bilkisu ta faɗa cikin isgilanci, sai kuma ta sake taɓe baki ta ce. "Wai kun ga yadda jiya ya tasa ta a gaba yake aikin lallashi, kai na sake yarda wallahi an shanye Yaya Salis har ƙafafuwansa. Wai duk yadda yake bautawa matar nan jiya har ji na yi yana yi mata alƙawarin sayen mota. Wallahi wannan auren da ya yi na san har da addu'arsu Baba, don yadda ta wanke hannu a kansa idan an ce zai kalli mace ma zan yi mamaki." Sadiya ta saki dariya ta ce, "Ni duk ba wannan ba, wallahi idonta kawai nake son gani idan an kawo amaryar. Yen yen yen yen abu kaɗan Abban Sajida, Allah Ya sa ya yi mata halin mazan ta gani ba dai ya yi auren..." Maganar Sadiya ce ta maƙale sakamakon ganin Aunty Murja ta fito daha kicin za ta wuce, duk da ta ji wasu daga cikin kalaman da suke tattaunawa sai ta yi kamar ba ta ji ba. Da za ta wuce ta sakar musu murmushi ta ce, "Sannunku da hutawa." Bilkisu ta yi zaraf ta ce, "Aunty Murja ai ke ce da sannu, kishiya ai ba sauƙi ba ce. Ni wallahi idan aka ce akwai ranar da Yaya zai yi miki kishiya ƙaryatawa zan yi, hmmm namiji rumbun ƙaya mai abin mamaki." Kafin Aunty Murja ta yi magana suka ji tsaiwar motocin 'yan kawo amarya a ƙofar gida. Guɗa aka fara saki ta ko'ina hakan ya tsananta bugawar zuciyar Aunty Murja. Idanunta suka ciko da ƙwalla, ba ta yi aune ba sai ji ta yi hawaye yana zuba. Bilkisu ce ta yi saurin sunne kai ƙasa tana dariyar ƙeta, da sauri Aunty Murja ta wuce ɗakinta jin kukan da take dannewa zai ƙwace mata. Su Sadiya ne suka miƙe da sauri suka nufi hanyar waje don tarbar amarya. Yadda Bilkisu ta zaƙe a lokacin za ka ɗauka ciki ɗaya suka fito da amaryar, don har wasu daga cikin dangin amaryar sun gane ta musamman waɗanda suka je jere. Yadda su Bilkisu suke haba-haba da amarya da danginta ya sa daɗi ya mamaye su, har suke ganin kamar sun fi sonta a kan Aunty Murja. Wasu daga ciki har suke tsegumin ko Aunty Murja ba ta da hali mai kyau, shi ya sa suke yin nan-nan da ita. Kusan duka 'yan uwan Yaya Salis sun watse tun bayan da aka kawo amarya, haka daga ɓangaren 'yan uwan uwargida Aunty Murja. Sai Bilkisu ce kawai ta rage, da yake ta ce mijinta Hafiz ne zai biyo ya ɗauke ta su tafi. Aunty Murja ba ƙaramin mamakin Bilkisu ta yi ba, a tsammaninta koda ya kasance yayanta ne zai yi auren, amma za ta iya yi mata kara ko don kada ta ji haushi. Amma abin da ya tsaye mata a rai Bilkisu ce har da fitar da atamfar anko, domin har wunin bikin Aunty Murja ta ce ba za ta yi ba, Bilki ta ce su za su yi idan ita ba za ta iya ba. Ganin irin rawar jikin da suke yi a kan amaryar ya sa ta sake janye jikinta da su. A lokacin da Hafiz ya zo ɗaukar Bilkisu a daidai lokacin Yaya Salisu ya shiga gidan, da gayya Bilksu ta raka shi sashen Murja don ta ga abin da zai faru. Tana tsaye a bakin ƙofa ta ga ya rungume Aunty Murja, daga shi har ita aka rasa wanda ya riga wani fara zubar da hawaye. "Ki yi hauri Ummu Sajida, kin san wane ne mijinki. Na san duk abin da zan faɗa a yanzu ba za ki yarda da ni ba, but trust me wallahi ban yi auren nan don na wulaƙanta ki ba. Har abada ke ta dabance a cikin raina, ke ta musamman ce 'yar Aljannata." Yaya Salis ya furta yana sakar mata fake a goshi, saboda Aunty Murja mace ce mai haƙurin gaske. Kuma har cikin zuciyarsa yake faɗar kalaman bakinsa, guntun tsaki Bilkisu ta saki ta nufi sashen amarya. Tana shiga ta ga ƙawayenta sun yi carko-carko, ta ji ɗaya daga ciki tana cewa. "Na'ima mu kam za mu wuce tun da angon har yanzu bai shigo ba, wai ba kin ce ya ce miki ya kusa ƙarasowa gidan ba?" Bilkisu ta taɓe baki ta ce. "Ina za ku gan shi yanzu? Yana can waccan uwar kusasun ta saka shi a ɗaki sai lailaye ta yake yana lallashinta. To Aunty Na'ima ni zan wuce, don na ga abin na yaya ba me ƙarewa ba ne, sai ya kawo ki gidana bayan kwana biyu." A ɗan kunyace Na'ima ta amsa, Bilkisu ta fita ta haye mashin ɗin Hafiz suka wuce gida. WASHEGARI Tun da gari ya waye Bilkisu ta lura da sauyin Hafiz, sai wani nannan yake yana haba-haba da ita. Sai da yaran suka tafi makaranta gabaɗaya sannan ya cewa Bilkisu. "Ummu Sayyid, don Allah magana nake so mu yi da ke ta fahimta. Kuma ki kwantar da hankalinki wannan ba wani abu ba ne, ni dai kin san ina sonki kuma ina matuƙar ƙaunarki Bilkisu." Gabanta ne ya faɗi, da sauri ta haɗe fuska ta ce. "Ka ga ni ba na son wannan kewaye-kewayen, duk me ya kawo waɗannan maganganun?" Murmushi ya yi ya ce. "Haka ne, to kin san komai da kika sani a rayuwa muƙaddari ne daga Ubangiji. Kuma kin san akwai abin da yake ƙaddara a cikin rayuwar mutum, ko ba ya so babu yadda zai yi da shi." Hafiz ya ɗan yi jim sai ya cigaba da cewa. "Dama tun kwanaki nake son sanar da ke, akwai wata yarinya da na yaba da hankalinta. Ko kaɗan ba ta da hayaniya, shi ya sa nake son aurenta. Don ba zan kawo wacce za ta tarwatsa mini gida ba..." "Dakata don Allah Hafiz, wannan wacce irin maganar banza kake faɗa mini? Yanzu dama akwai ranar da za ka munafurce ni? Ni za ka ƙara wa kishiya Hafiz?" Bilkisu ta furta cikin fusata. Hafiz ya sake kwantar da murya ya ce. "Wallahi na so sanar da ke tun rannan, sai kuma na ga za ku shiga bikin Yaya Salis don haka na bari sai an gama. To jiya bayan kin fita su Baba Ƙarami suka je kai kuɗin aurena wurin iyayen Amina." A wannan karon ma ɗagowa Hafiz ya yi yana satar kallonta sannan ya ce. "Wallahi ana zuwa, mahaifinta ya ce a ɗaura aure idan har da gaske nake yi. Idan ya so ko daga ba ya a yi duk bidi'o'in da ake yi na al'ada, wai saboda wasu samarin suna amfani da kai kuɗin aure don su ɓata ya..." "Kutumar..." Uban ashar ɗin da Bilkisu ta lailayo ta maka ya katse maganar Hafiza, nan take jikinta ya ɗauki karkarwa cikin tsananin zafin kishi ta cikumo wuyansa ta ce. "Wallahi duk shegiyar da ka aura sai ka sake ta, ni za ka wulaƙanta ka tozarta? Wallahi ko ka sake ta ko na kashe ka, kuma na kashe kaina yanzun nan." Bilkisu ta ƙarasa maganar tana fisgo sharɓeɓiyar wuƙa a kwandon wanke-wanke. GIDAN ALHAJI UMAR Hajiya Karima wayarta ta ɗauko ta latsa layin lambar mai gidanta, ba a ɗauki lokaci ba ta ji ya ɗauka. Don haka cike da ƙosawa ta ce, "Alhaji ko na wuce ɗaki ne? Tsawon minti goma sha biyar fa kenan da ka ce na fito kuma na ji ku shiru." "A'a ga mu nan zuwa." Daga can ɓangaren Alhaji Umar ya ba ta amsa. Tana nan zaune babu jimawa ta ji ya shigo falon baki ɗauke da sallama. Ɗago da kai ta yi ta amsa masa, ta hangi hannunsa a maƙale da na Shukura da take biye da shi. Zama ya yi a kujerar da ke kallonta, Shukura ta matsa jikinsa tana lafe kanta a gefen kafaɗarsa. A ɗan duburburce Alhaji Umar ya ce. "Wallahi... kin san akwai gajiyar biki. Duk ta gaji ne." Murmushi Hajiya Karima ta yi, duk da tana jin zafi a ranta amma sai ta danne ta ce, "Ai dama gajiya sai a hankali za ta warware." A hankali Shukra ta gyara mayafinta cikin dabara ta fara ƙarewa Hajiya Karima kallo. Hajiya Karima babbar mace ce da za ta kai shekara talatin da bakwai zuwa arba'in, ita da Alhaji Umar aure suka yi tun na saurayi da budurwa. Alhaji Umar zai yi shekara arba'in da bakwai zuwa hamsin, tun da suke tare da Hajiya Karima bai taɓa ƙara aure ba, sai a wannan lokacin da ya auro Shukura mai shekara goma sha takwas a duniya. Ta cikin mayafi Shukura ta yamutsa fuska a cikin ranta ta ce. 'Gaskiya baby ya yi haƙurin zama da wannan abar, don Allah dubi yadda duk naman fuskarta ya saki. Aba ta yi shirim da uwar ƙiɓa babu fasali.' Gyran muryar da Alhaji Umar ya yi ne ya katse gajeren tunanin da Shukura ta faɗa. "AlhamduLillah! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji (S.W.A), Hajiya ke da Shukura na haɗa ku a nan ne domin na yi muku 'yar nasiha. Gabaɗayanku matana ne, ke Hajiya ke ce babba. Idan kika kama girmanki za ku zauna lafiya babu rashin kunya ko tashin hankali, haka kema Shukura. Wannan uwargidana ce, ba ta da matsala da kowa tun zamana da ita. Ban auro ki don ki raina ta ba, haka ita ma daga ɓangarenta." Alhaji Umar ya furta cikin tausasan lafuza. Ya jima yana yi musu nasiha sannan kowa ya wuce ɗakinsa. Tun da Hajiya Karima ta shiga ɗaki ta ji zuciyarta duk babu daɗi, duk yadda ta kai ga danne kishinta sai da ta ji ƙwalla ta zubo mata. Saboda rana ta farko kenan, da suka raba makwamci da Alhaji tun tsawon shekara ashirin da biyar da aurensu. Alwala ta ɗauro ya fara gabatar da sallolin nafila, ta shiga kwararo addu'o'i sannan ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi. WASHEGARI Asubar fari ta ji ana buga mata ƙofa, a hankali ta yunƙura ta zage sakatar ɗakin. Alhaji ta gani sanye ta doguwar rigar, ta ɗan murza idanunta ta ce. "An kira sallar Asuba ko?" Murmushi Alhaji ya yi yana ɗan sosa kai ya ce, "A'a tukunna dai." Shiru ta yi tana jiran abin da ya kawo shi a lokacin, Alhaji ya sunne kai ƙasa ya ce. "Wallahi dama ashe gas ɗinta ne ba a haɗa mata ba. Shi ne na ce za ki ɗan ɗora mana ruwa." Ƙirjinta ne ya yi wani irin bugu da ƙarfi, nan take ta ji zuciyarta ta ɗauki tururi. Da wani irin kallon mamaki ta kalle shi, don ta yi tsammanin ko babu komai zai ji nauyin yi mata wannan maganar. Tun da kawaici mai sunan kawaici ta yi a lokacin shirye-shiryen aurensa. "Amm... dama... saboda ta ce ba za ta iya amfani da ruwan sanyi ba ne..." Alhaji Umar ya furta a rarrabe cikin jin nauyi, musamman da ya lura da irin kallon da take jefa masa. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA BIYU Haɗiye yawu mai ɗaci Hajiya Karima ta yi, ta shanye abin da yake ƙunshe a saman ƙirjinta ta ce. "Babu damuwa." Fitowa ta yi ta za ta nufi ƙofar kicin ɗinta jiki a sanyaye Alhaji Umar ya ce. "Na ce ko na zo na ɗora, na ga kamar na katse miki bacci." Kallon tsaf ta yi masa, kamar za ta yi shiru sai kuma ta ce. "Da ka san za ka iya ɗorawa kuma ka taso ni?" Shiru ya yi mata baice komai ba, Hajiya Karima ta ɗauki tukunya ta ɗora musu ruwan. Kan kujerar falo ta ga ya je ya zauna, har ta juya za ta shiga ɗaki daga can ɗakin Shukura ta ji an ce. "Babyyyyy!" A zabure ta ga Alhaji ya miƙe ya nufi ɗakin ta girgiza kai ta shige ɗakinta, tana tuna yadda ta ji ana cewa zama da kishiya sai an daure. Ashe dama haka matan da aka yi wa kishiya suke ji a cikin zuciyoyinsu? Ashe dama duk tsawon shekarun da ka ɗauka da miji idan ya yi aure sai ka ji zafi a ranka? Ashe gaskiya ne da ake cewa ba a tsufa da kishi haka ne? Ayarin tambayoyin da ta dinga jefa wa zuciyarta kenan, bayan ta shiga ɗaki. Sai da ta tabbatar da ruwan ya yi zafi sannan ta fito ta kashe gas ɗin ta koma ɗakinta, don ba ta son duk wani abu da zai kai kunnenta har ya ɓata mata rai. Alwala ta ɗauro saboda lokacin an fara kiran sallar Asuba, jin za a shiga masallaci ya sa ta nufi ɗakunan yaran gidan ta tashe su yin sallah. Da gari ya waye kamar kullum ita da Ruƙayya suka haɗa abin karyawa, bayan sun kammala ta zuba na su Shukura a cooler ta ajiye musu. Ita da yara kuma, suka baje a babban falo kamar yadda suka saba idan babu makaranta. Suna nan zaune suka ga Alhaji da Shukura sun ƙaraso ɗakin sai yatsina take yi, a ɗan kunyace yake son zame hannunsa daga cikin naya saboda ganin yaransa a wurin. Sake riƙe hannunsa ta yi gam, sai kawai ya wayance da cewa. "Mamana yau ko tayi babu? Amma dai ke kika yi girki don na ji gidan sai ƙamshi yake yi." "Ummm!" Ruƙayya ta furta a daƙile, saboda har lokacin ba ta daina fushin auren mahaifinsu ba. "Hajiya barka da safiya." Alhaji ya furta yana ƙoƙarin kawar da idonsa daga cikin nata, don haka kawai yake jin nauyinta. "Barka dai Daddyn yara ya kwanan amarya?" Alhaji ya washe baki ya ce, "AlhamduLillah." "Daddy ina kwana." Yaran suka haɗa baki suka gaida shi, amsa musu ya yi sai ya ce. "Ba ku gaida Auntynku ba." "Mazan ne kawai suka gaishe ta, amma Ruƙayya ko ƙurarta ba ta kalla ba." Zama Alhaji ya yi a ƙasa, ita ma Shukra ta zauna a kusa da shi tana ta yarfe hannu alamun ba ta jin daɗin jikinta. "Ina kwana." Shukra ta furta wa Hajiya tana sake yamutsa fuska, Hajiya ta luwa sarai da yanayin Shukra sai ta yi kamar ba ta gane ba ta ce. "Lafiya ƙalau, ya kwanan baƙunta." "AlhamduLillah." Shukra ta furta tana lafewa a jikin Alhaji. Miƙewa Ruƙayya ta yi za ta bar falon, mahaifiyarta ta ce. "Mami ɗauko abincin Auntynku a kicin." Wani baƙinciki ne ya mamaye ta, ta wurga mata harara karaf idonta ya haɗu wuri ɗaya da na Shukura. Wani siririn murmushi Shukura ta yi a cikin zuciyarta ta ce. 'Da alama yarinyar nan kin fi uwarki zafin kai, ai kuwa zan sauke miki shi don ni ba sa'ar yinki ba ce. Ubanki ne daidai da ni, da ni kike zancan.' Kamar mai ciwon haƙori haka Ruƙayya ta amsa da to, sannan ta wuce kicin ta ɗauko ta dire a gaban Shukura. "Shukura za ki ci ta zuba miki ne?" Alhaji Umar ya tambayi Shukura, girgiza masa kai ta yi cikin sangartacciyar murya ta ce. "Baby ta kai mana ɗaki, ni fa ko magana ba na so komai ciwo yake yi mini." Kunya ce ta kama Alhaji Umar, duk sai ya ji ya tsargu yana ganin kamar yaran duka sun fahimci abin da ya shiga tsakaninsa da ita. Haidar ne ya miƙe ya fita daga falon, sai ragowar 'yan'uwansa suka rufa masa baya. A zuciye Ruƙayya ta ɗauki cooler tana jin kamar ta kifa a kan Shukura, ta shiga ɗakinta ta dire mata ta fito. Tana dawowa ko zama ba ta yi ba ta wuce ɗakinta. Hajiya Karima sakato ta yi da baki tana kallon ikon Allah, saboda tashi ma da Shukura za ta yi sai da Alhaji ya taimaka mata. Tana ganin sun tafi ɗakin ta jinjina kai cikin mamaki ta ce. "Tirƙashi! Lallai akwai aiki." Ƙarasa cin abincin ta yi, ta ɗauki sauran na yaran da suka tashi ta rufe. Saboda ta san sun tashi ne ba don saun ƙoshi ba, sai don jin nauyin ganin mahaifinku da Shukura. Tun daga wannan ranar kullum Hajiya Karima ce take girki, idan kuma babu makaranta Ruƙayya ta taya ta. Tun a washegarin tariyar Shukura da dare ta cewa Alhaji za ta dinga girki ya dinga kai musu ɗaki suna ci a can, ya ji daɗi sosai sai ya sake jin Hajiya Karima ta mamaye zuciyarsa. Saboda tun da ya ɗauko maganar aure, har kawo lokacin babu wani abu da ta yi masa na hatsaniya ko ɓacin rai. Tsakaninta da Shukra sai gaisuwa, don tun washegari ta lura da wani irin kallon raini da take yi mata. Ita kuwa ta san ko Haidar da yake bin Ruƙayya ya girme ta, a ganinta abin kunya ne ta ce za ta nuna mata ta fahimci abin da take yi. A cikin waɗannan kwanakin na amarcin Daddyn su Ruƙayya da Shukura, kullum da kalar naman da ake sarrafawa a cikin gidan. Duk da dama can Daddy mutum ne mai ƙoƙari wurin farantawa iyalansa rai, sai dai kuma yadda yake ɓarin kuɗi wurin sayo kayan ƙwalam da maƙwalashe abin har mamaki yake ba wa Mommyn Ruƙayya. Ranar da Shukura ta cika kwana biyar da tarewa, a ranar Hajiya Karima ta fara fuskantar sauyin fuska daga wurinsa. Da farko sai ta yi tsammanin ko daga cikin abokan kasuwancinsa ne, suka yi waya wani ya ɓata masa rai. Saboda shiga ɗaya-biyu idan ya yi sai ta ji ya saki tsaki, ko kuma da ya ga abu sai ya fara faɗa. Ana gobe zai cika kwana bakwai a ɗakin Shukura bayan sallar Magriba, ya dawo daga masallaci ta ji yana ƙwala mata kira. A gaggauce ta shafa addu'ar da take yi ta fito ta ce. "Ga ni Alhaji." Cikin faɗa ya ce, "Wato kuɗin banza gare ni ko Karima? Saboda wulaƙanci na kawo dankalin nan ba za a shiga da shi store ba?" Da mamaki Hajiya Karima take kallonsa, don rabonta da jin ya kira ta da Karima har ta manta. Murya a sanyaye ta ce. "Ruƙayya ce ta ce a bari da safe za ta wanke store ɗin, saboda ya yi datti. Amma ka yi haƙuri Alhaji." Ƙwafa Daddy ya yi ya nufi ɗakin Shukura yana faɗin. "Ban da rashin sanin darajar abu, wasu matan ma nema suka amma ke an kawo kina wulaƙantawa." Sam ba ta ji daɗi ba, amma sai kawai ta haɗiye dumuwarta ta bar wurin. Ruƙayta tana dawowa, kallo ɗaya ta yi wa mahaifiyarta ta fahimci tana cikin ɓacin rai. Tambayar duniya ta yi mata a kan ta faɗa mata sai ta ƙi, don ta san Ruƙayya tana da riƙo. Kuma ta san dama ba ƙaunar Shukura take ba, sai kawai ta saka ta gyaran store ɗin a daren. Ranar Asabar ce ta kama ranar da Daddy zai koma ɗakin Hajiya Karima, tun da gari ya waye har zuwa dare Shukura take cika tana batsewa. Ganin yanayin da take ciki duk sai ya sake birkita shi, rungumo ta ya yi yana shaƙar ƙamshinta ya ce. "Yanayinki duk ya wargaza mini ƙwarin gwiwata Baby. Me yake damunki?" Kukan kissa ta fashe da shi tana sake shigewa jikinsa ta ce. "Habibi ina cike da fargabar kewarka, yanzu haka za ka bar ni cike da kewarka? Dama duk irin ƙaunar da ka ce kana yi mini kenan? Ni gaskiya ban gaji da jin ɗuminka ba, saboda kusancina da kai ya fi mini komai da kowa a duniyar nan." Ta ƙarasa maganar hawaye yana bin gefen idonta, sake matse ta ya yi a jikinsa tsam kamar wani zai ƙwace masa ita. Ya saka bakinsa a daidai kunnenta kamar mai raɗa ya ce. "Ni kaina zan bar ki ne ba don kin gundure ni ba, zan yi kewarki babyna. Amma ai ba wasu kwanaki ne masu yawa ba, kwana biyu ne kawai." Kamar ƙaramar yarinya sai ta hau shure-shure tana maƙe kafaɗa ta ce. "Ni dai wallahi ka nemo mana mafita, gaskiya ban gaji da kai ba." Ire-iren shagwaɓar da take yi masa ba ƙaramin narke zuciyarsa take yi ba, cikin so da ƙauna ya shafo fuskarta zai yi magana sai kawai ta haɗe bakinsu wuri ɗaya. A wannan lokacin haka Shukura ta dinga yaudararsa cikin kissa da kisisina, har ta birkita shi gabaɗaya. Sai da Daddy ya nemi tarawa da ita ta maƙale kafaɗa cikin shagwaɓa ta ce. "Kai da za ka tafi ka bar ni." A ɗan birkice Daddy ya ce, "Please ki bari, daga baya za mu yi maganar." Girgiza kai ta yi tana sake narkewa ta ce. "Ni a'a, sai dai idan za ka ƙara mini sati ɗaya." Ɗan jim Alhaji ya yi ya ce, "Idan na yi haka Mommyn Mami ba za ta ji daɗi ba." Da sauri cike da kishi Shukura ta ɗan ture shi ta ce, "Shi kenan, sai ka je can wurin nata ai." Marairaice murya Daddy ya yi saboda yadda ya yi nisan kiwo a buƙace da ita ya ce. "Haba baby don Allah kada ki yi mini haka." Turo baki gaba ta yi ta ce, "Kai ne da wani zance ai, kyauta za ka nema a wurinta? Ba sai ka sayo mana kwanan ba." Cikin sauri ya ce. "Yadda kika ce haka za a yi." Murmushi Shukura ta yi, ta janyo Alhaji ta sakar masa kiss sannan ta ce. "To ni dai ka je wurin nata sai ka dawo." Kamar mai jira sai kawai Daddy ya yi zaraf ya miƙe, ya zura doguwar rigarsa. Sai da ya ɗan daidaita kansa sannan ya fice ya nufi wurin Hajiya Karima. Shukura tana ganin ya fita ta saki dariyar ƙeta har da buga ƙafa, cike da isgilanci ta ce. "Tsoho ya ji haza saura hazihi." Sai kawai ta sake tuntsirewa da dariya. Kiran waya ne ya shigo wayarta, tana dubawa ta ga lambar ƙawarta Zuby ce. Da sauri ta ɗauka ta ce. "Wai haka kawai an san mutum amarci yake ci a dame shi da kira." Daga can ɓangaren Zubby ta saki shewa ta ce, "Ka ji shegiya ko har yaushe kika san daɗin mijin? Yarinyar nan kina lokaci fa. Tun rannan kike tashin kanmu da hotuna a status, idan mun yi comment kuma ba replay." Cike da shaƙiyanci Shukura ta ce, " Ku zauna kuna fama da ƙananan samari, ai wallahi auren mijin wata duniya ne. Zo ki ga mijin wata kuma uban wasu yadda yake ta biyayya tun da na zo, ke yanzu haka ma na aika shi ya sayo mini kwana a wurin waccan guzumar." Ihu Zubby ta saki ta ce, "Ke fa 'yar iska ce ba ki iya samun wuri ba." Shukura ta yi dariya ta ce, "To ina dalili, shekara da shekaru yana fama da tsohon... ke dai kin gane ba sai na faɗa ba. Yanzu kuma rana tsaka daga yin sati zai koma, ni wallahi na tsani matar nan don kwana biyun nan da na yi na fahimci yana sonta." Tsaki Zubby ta yi ta ce, "Ni fa daɗina da ke rashin hankali, to dama matarsa uwargidansa da suke tare sama da shekara ashirin zai daina sonta ne? Wallahi ki bi dai a hankali kada ki yi abin da za ta sa 'ya'yanta su ɓarar da ke." "Kutt ai kuwa da na ɓarar da ubansu ni ma, don wallahi da sai sun gwammace kiɗa da karatu." Shukara ta furta tana dariya, sannan suka yi sallama da Zubby ta kwanta tana jiran dawowar Alhaji. GIDAN HAFIZ Wani irin kukan kura Bilkisu ta yi ta nufi Hafiz da wuƙar gadan-gadan, da sauri ya yi baya amma tsautsayi ya sa ta same shi a tsintsiyar hannunsa. Wata irin azaba ya ji tana ratsa shi, nan take jini ya fara zuba. Ga mamakinsa sai gani ya yi ta sake ɗaga wuƙar za ta sauke masa, da sauri ya saka ɗayan hannunsa ya murɗe hannunta har sai da ya yi ƙara. Ta cakumi wuyansa tana kuka ta fara jijjiga shi tana faɗin. "Wallahi ba ka isa ka yi mini kishiya ba, tun da babu abu ɗaya da na rage ka da shi a cikin gidan nan." Bai kula ta ba, sai ma yarfe hannu da yake yi saboda azbabar da yake yi masa. Da gudu ya ga ta fita tsakar gida, haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta ba. Yana fita ya ga ta ɗauki galan ɗin man fetir ɗin da yake sayo man mashin ɗinsa. Cikin zafin nama ya hankaɗe galan ɗin, fetir ɗin ya zube a ƙasa. Za ta sake ɗauka ya tsinke ta da mari, rai a matuƙar ɓace ya nuna ta ya ce. "Idan ba ki da hankali wallahi zan nuna miki na fiki ɗanyan kai, saboda na ce miki na yi aure har kike neman illata ni ki illata kanki. Ke wacce irin mahaukaciya ce Bilkisu? Yanzu da ace da tsautsayi ya sa kin hallaka ni fa?" "Ni kake kira da mahaukaciya? Wallahi kuwa sai na nuna maka asalin haukana. Ba don saboda ka samu wata ne za ka yi mini haka ba? Wallahi sai na nuna maka asalin haukan da kake faɗa." Cikin kicin ta faɗa ta ɗauki ashana, tana zuwa ta ƙyasta a kan fetir ɗin da ya zube a ƙasa. Nan take wuta ta tashi, a tsorace yake bin Bilkisu da kallo saboda gani yake kamar wata aka canza masa ba ita ba. Ganin wutar tana ƙoƙarin laso wurin da mashin ɗinsa yake, ya sa shi ɗebo ruwa a bokiti ya kwara. Wayarsa ya ciro da sauri ya kira layin mahaifin Bilkisu ya sanar da shi abin da ya faru. Wayar Baba ya ce a bawa Bilkisu tana karɓa ta doka ta da ƙasa, da yake a ƙaramar wayarsa ya yi kiran kwaso batirin ya yi ya sake kunnawa. Layin mahaifin nata ya sake kira, yana ɗauka ya sanar da shi abin da ta aikata, a fusace mahaifinta ya ce ga shi nan zuwa ya katse wayar. Can gefe Hafiz ya koma ya zuba mata ido ganin yadda duk ta birkice, ta fita hayyacinta kamar sabuwar mahaukaciya saboda ko ɗankwali babu a kanta. Mamakinta yake yi sosai, musamman da ya tuna yadda ta yi uwa da makarɓiya wurin auren yayanta Yaya Salis. Don idan bai manta ba shi ya ba ta rancan kuɗi, ta saro atamfar ankon bikin da ta fitar take sayarwa tana ɗora ribarta. Yana nan tsaye ya tuna wata tattaunawa da suka yi shi da ita. "Abban Sayyid wallahi sai yanzu ne Yaya Salis zai yi aure, ka ga matar da zai auro kuwa? Yarinya doguwa ga gashi har baya, wallahi ba ka ga hanci ba har baka. Amma da kullum ya ƙare a kan Aunty Murja, ni a wata majiyar ma na ji an ce hatta kayan sallah shi yake yi wa ƙannenta." Murmushi Hafiz ya yi ya ce. "Shi dama ƙarin aure ai kamawa take yi, amma kuma ai na ji kina yabonta." Bilkisu ta taɓe baki ta ce. "A da kenan kafin Yaya ya faso gari, tun da ya yi kuɗi ba ka ga duk ta tattare komai ba. Makira ai wallahi gara ya ƙara auren ko ta shiga hankalinta." Jin jinin hannunsa yana cigaba da zuba, shi ya dawo da shi daga duniyar tunani. Wani ƙyalle ya janyo ya ɗaure hannunsa, ya cigaba da tsayiwa a wurin yana kallon kallo shi da Bilkisu. Bayan wani lokaci sallama ya ji a ƙofar gida, yana fita ya ga mahaifin Bilkisu ne da Yaya Salis. Iso ya yi musu cikin gida, tun daga tsakar gida suka tabbatar da abin da Hafiz ya faɗa musu. Suna zaune a falo Bilkisu ta shiga ɗakin tana sunkuyar da kai ƙasa kamar sabuwar maunafuka. Tana ƙoƙarin zama mahafinta ya tsinka mata mari, da sauri Hafiz ya matso gaba ya ce. "Don Allah Baba a yi haƙuri, abi a sannu don Allah." A zafafe Baba ya dubi Hafiz ya ce. "Ba na son sakarcin banza da wofi Hafizu, ita mahaukafiyar ina ce da za ta aikata ɗanyan aikin nan haka. Dubi yadda ta ji maka rauni a hannu." Shiru Hafiz ya yi, Baba ya shiga yi mata faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Daga ƙarshe ya ɗora da cewa. "Kuma ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, wallahi koda wasa na kuma jin kin aikata makamancin wannan haukar ni da ke ne. Idan kuma kika kuskura kika ƙure yaron nan har ya sake ki, wallahi sai kin fi jin daɗin zaman gidan yari a kan gidana. Allah Ya gafartawa mahaifiyarki, ke dai albasa ba ta yi halin ruwa ba. Lokacin da zan ƙara aure mahafiyarku ce ta tara mini kayan lefe, kuma har ta rasu ba ta taɓa aikata mini wani abin ɓacin rai saboda kishi ba. Shashasha sakarai marar tunani." Baba yana gama faɗa Yaya Salis ya ɗora, haka Bilkisu ta dinga share hawaye har suka gama suka tafi. Tun daga wannan ranar Bilkisu ba ta sake yinƙurin cutar da Hafiz ba, sai dai kala-kalan ruwan rashin mutumcin da take zabga masa. Don kusan a wannan lokacin ta daina girki da shi, tsakaninsa da ita sai ɓacin rai da baƙar magana. Idan ya zo neman haƙƙinsa wurinta haka za ta gasa masa maganganu ta juya masa baya. Ire-iren abubuwan da Bilkisu take yi bai tsaya iya kansa ba, har sai da ya shafi danginsa. Domin duk wanda ya je gidanta, matuƙar daga ɓangarensa ne ko karɓar kirki ba ta yi musu, ko ruwa ba ta ba su haka suke karkaɗe ƙafafuwansu su tafi. Gabaɗaya Bilkisu kallon munafukai take yi wa dangin Hafiz, don haka su ma suka janye jikinsu daga wurinta. Duk wani shige da fice da Bilkisu za ta yi don ta san yarinyar da Hafiz ya aura ta yi, sai dai har lokacin ba ta samu ba. Watarana da daddare, kimanin biyun dare. Ta jango wayar Hafiz, ganin password a jiki ya sa jikinta ya yi sanyi, wani tunani ne ya faɗo mata. Da sauri ta shiga gwada sunayen yaranta bai yi ba, sai ta gwada sunansa ta samu wayar ya buɗe. Whatsapp ɗinsa ta shiga, a nan ta fara cin karo da lambar Amina da irin zafafan kalaman soyayyar da suke yi wa junansu. Da farko ɗaukar lambar ta yi za ta kira ta zagi Amina, sai kuma wani tunani ya faɗo mata. Cikin sauri hannunta yana rawa ta rubuta. _Ni Hafiz Adam, na saki Amina saki ɗaya, na sake ta saki biyu na sake ta har saki uku. Sakamakon saɓanin da nake samu da matata saboda na aure ki, domin ba zan iya ɓata wa matata rai ba._ Bayan saƙon ya tafi sai ta goge saƙon daga kan wayar, sannan ta ajiye masa wayar a gefensa ta koma ta kwanta tana jin zuciyarta fes. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. https://chat.whatsapp.com/IAZVt2Pz4LvIcklCxSTHwo SHAFI NA UKU Lokacin da Hafiz ya tashi zai yi sallar asuba misscall ɗin Amina ya gani rubutu, yake ya ji masallaci sun shiga da sauri ya zura wayar a aljihu ya nufi masallacin saboda tuni ya yi alwala. Ana idar da sallah ya fito daga masallacin, ya ciro wayar a nan ya sake cin karo da wani kiran nata. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, hannu yana rawa ya ɗauki wayar yana faɗin. "Salamu alaikum, Amina." Kuka ya ji ta fashe da shi, hakan ya sake ɗaga hankalinsa. Jikinsa yana rawa ya sake cewa, "Amina me yake faruwa a gidan ne? Lafiya kike kuka?" Daga can ɓangaren Amina ta sauke ajiyar zuciya murya a dashe saboda kukan da ta sha ta ce. "Tambayata ma kake yi Hafiz? Tambaya kake yi me ya faru? Dama ka so cin mutumcina ne shi ya sa ka zo gidanmu neman aurena?" Da mamaki ya ɗago wayar yana bin lambar da kallo don sake tabbatar da wacce take magana, cikin rashin fahimtar zancanta ya ce. "Amina wai me kike faɗa ne? Kin san wa kika kira kuwa?" "Kana nufin na fara hauka ne Hafiz? Ko ka ɗauka ina shaye-shaye ne?" Ita ma ta faɗa a ɗan fusace. Shiru ya yi yana nazari, don ya san Amina sarai mace ce mai haƙuri. Tun da suke tare ba ta taɓa faɗa masa makamantan irin maganganun nan ba. Gwaron numfashi ya sauke cikin tausasa murya ya ce, "Don Allah Amina ki yi mini bayani ban san me yake faruwa ba." Wani takaicin ne ya sake rufe Amina, cikin gatse ta ce. "Kana nufin har ka manta sakin wulaƙancin da ka yi mini, saboda matarka ta fi ni a wurinka don kuna samun saɓani shi ne za ka sake ni? AlhamduLillah tun da har na fahimci matarka ta fi ƙarfinka, na gode ka aiko gidanmu a karɓar maka sadakinka." Daga haka Amina ta katse wayar. Wani irin gumi ne ya lulluɓe Hafiz, da sauri ya jingina da bango sakamakon jin da ya yi juwa tana yunƙurin taɗe ƙafafuwansa. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Ya furta a fili, sannan ya zura wayarsa a aljihu. Da sauri ya nufi gida, ya shiga kiciniyar fito da mashin ɗinsa waje. Yana rufe gidan ya hau mashin ɗinsa, kai tsaye ya wuce unguwarsu Amina. Yana zuwa ƙofar gidan ya ciro wayarsa ya yi mata kiran duniya ta ƙi ɗauka, ƙwanƙwasa ƙofar gidan ya fara yi a rikice. Don kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin damuwa. Mahaifinta ne ya buɗe ƙofar ya fito, cikin girmamawa Hafiz ya tsugunna ya gaida shi sai kuma ya yi shiru ya ma rasa ta ina zai fara yin magana. "Hafiz dama na so kiranka da kaina zuwa an jima. Amma na ji daɗi da Allah Ya kawo ka yanzu." Da sauri Hafiz ya ɗago ya ce. "Baba lafiya kuwa? Dama... dama na ji Amina tana ta wasu maganganu." Mamaki ne ya kama Baba, sai ya ce. "Shigo ɗakina, wannan ba maganar tsaiwa ba ce." Baba ya furta yana shiga ciki, kamar zakaran da ya bi ta mahauta haka Hafiz ya bi bayan Baba jiki a sanyaye. Yana nan zaune a ɗaki Amina da Baba suka yi sallama suka shiga, wayar Amina ya karɓa ya nuna masa ya ce. "Da asubar nan Amina ta nuna mini saƙon da ka turo mata cikin dare." Hafiz yana gama karanta saƙon ya ce. "Wallahi Baba ban san yadda aka yi ba, wallahi ba ni na rubuto mata wannan saƙon ba. Tun da ko a daren jiya lafiya ƙalau muka gama waya da ita." Hafiz ya yi jim, ya ɗago da sauri ya ce. "Sai dai idan matata ce, babu tantama wallahi sai dai idan ita ce Baba." Shiru Baba ya yi yana nazari, ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "To a gaskiya idan har haka ne sai ka tashi tsaye Hafiz, don ba na son duk wani abu da zai sa a dinga tashin hankali. Haka kuma wannan maganar ba za mu bar ta daga mu sai kai ba, dole ne ka kirawo manyanka a yi magana. Ita ma ya zama wajibi ka tsawatar mata, ka kuma kiyaye haƙoƙinta. Don za ka yi aure ba shi zai sa ka wulaƙanta matarka ba, ko ka dinga cin fuskarta kana cin zarafinta. Ka ji tsoron Allah Hafiz, wallahi idan ka cuci 'yar mutane Allah ba zai bar ka ba." Cikin girmamawa Hafiz ya russuna ya ce. "In Shaa Allahu Baba." Miƙewa Baba ya yi ya fita, har Amina za ta fita cikin sauri Hafiz ya ƙarasa ya riƙo ta. Rungumo ta ya yi jikinsa ya haɗa ta da bango ya ce. "Kina tunanin akwai ranar da zan iya rabuwa da ke ne?" A ɗan shagwaɓe Amina ta ce, "Na sani tun da tsoron matarka kake ji." Sunkuyawa ya yi ya sakarwa bakinta kiss ya ce, "Haka kike gani Meena, amma babu wani tsoro. Kin san duk macen da za a ƙara wa abokiyar zama dole a lallaɓa ta, musamman Bilkisu da take da kishi." Janye jikinta za ta yi ya sake matse ta ya ce. "Me ya sa kike guduna ne?" "To ni kada wani ya ganmu a haka." Ta ba shi amsa a sanyaye, zuba mata ido ya yi yana jin sonta na fisgarsa. Cikin wani irin yanayi ya ce, "Ai ba wamda zai shigo tun da kowa ya san ke matata ce, ba ki ga ma Baba ya ba mu wuri ba." Zaro ido ta yi tana rufe baki ta ce, "To wallahi ni tafiya zan yi, wato duk kallon haka suke yi mini?" Gyaɗa mata kai ya yi ya tallafo fuskarsa da hannu biyu ya ce, "Ina ƙaunarki Meena, na yi mamaki da har kika yarda zan iya rabuwa da ke." Tura baki gaba ya ta yi cikin jin nauyinsa, Hafiz lumshe ido ya ce. "In Shaa Allah nan da sati biyu za a kawo kaya, sai a yi wunin biki a wuce wurin don haƙurina ya fara ƙarewa." Sunkuyar da kai ƙasa ta yi cikin jin kunya, ya sunkuya saitin kunnenta ya yi mata raɗa a kunne. Da sauri ta ɗago tana rufe ido cikin jin kunya ta ce. "Allah Ya shirye ka, ni wallahi ba haka nake ba. Don Allah babu abin da ya dame ni." "Ai shi ya sa na ga ba kya hana ni idan ina..." Da sauri Amina ta saka hannu ta rufe masa baki, sai kuma ta ce. "Ka zo ka tafi ka bar Madam tun da farar safiya." Cikin kwaikwayon muryarta ya ce. "To duk ba ita ta ja komai ba." Dariya Amina ta yi ta ce, "Allah Ya shirya ka Hubby." Har ƙofar gida Amina ta raka shi tana jin soyayyar Hafiz a cikin ranta. Duk da ta ji zafin abin da Bilkisu ta yi, ta wani ɓangaren tana yi mata uzuri, saboda ba kowacce mace ce take danne zuciyarta ba idan za a yi mata kishiya. Hafiz yana zuwa gida ya samu Bilkisu tana yi wa yara shirin makaranta, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta. Haka shi ma bai kula ta ba ya zauna har yara suka gama cin abinci, ya ɗauke su ya kai su makaranta. Lokacin da ya koma tana kwance a kan gado, a gefenta ya zauna ya ce. "Bilkisu ki tashi za mu yi magana da ke." Ɗagowa ta yi ta kalle shi a sheƙe ta ce. "Faɗi maganarka ai kunne ne yake ji." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Bilkisu kin san ina sonki ina ƙaunarki, kuma kin san babu macen da zan kawo na bari ta raina ki, ko ta ci mutumcinki. Kin san ba zan ɗauki haka ba, duk abin da kike wa 'yan uwana ina sane, amma duk da haka ban bari ɗaya daga cikin ƙannena sun raina ki..." "Don Allah idan ba wata magana mai muhimmanci za ka faɗa mini ba ka ƙyale ni." Bilkisu ta faɗa rai a ɓace. Girgiza kai ya yi yana danne ɓacin ransa ya ce. "Muhimmancinta ne ya sa na same ki da maganar. Bilkisu yanzu ba ki ji kunyar saƙon da kika turawa Amina a matsayin ni ba ne? Ko kin ɗauka aure wasan yara ne da za ki yi wannan shirmen? Don Allah ki kama girmanki Bilkisu, ina respecting ɗinki a wurin Amina. Don haka ita ma ko da wasa, ba ta taɓa kawo maganar wargi a kanki ba, ina girmamaki fiye da yadda kike tsammani. Ki girmama kanki ta yadda ba za ki bada ƙofar da yarinyar nan za ta raina ki ba, ni idan kin yi mini zan iya shanyewa. Amma kin san ba lalle ne ita idan kin yi mata wani abin ta ɗaga miki ƙafa ba..." "To duk abin da za ka saka ta yi mana, wallahi duk shegiyar da ta kawo mini raini sai na yi mata dakan sakwara." Bilkisu ta faɗa tana tashi zaune. A ɗan zafafe Hafiz ya ce, "Kada ki sake zagar mini mata." Bilkisu ji ta yi kamar ya watsa mata ruwan zafi, don haka a zafefe ta ce. "Na zaga idan ka ga dama ka rama mata, 'yan iskan 'yan mata ba za su nemi mijinsu su aura ba sai mace ta raini mijinta su zo su aure suna tunƙahon mijinsu ne." Jin ba zai iya ɗaukar maganganun da Bilkisu take faɗa ba, ya sa shi ficewa daga ɗakin ya nufi ɗakin yaran ya kwanta a can. Kamar yadda Hafiz ya faɗa cikin ƙasa da sati biyu ya ƙarasa haɗa duk wani abu da ake buƙata na lefe, juma'a tana zuwa aka kai kaya gidansu Amina. A nan su kuma iyayenta suka tsayar da ranar juma'a mai zuwa, a matsayin ranar da za a yi wuni da kai amarya. Hafiz ya yi ƙoƙari sosai, akwati biyar ya yi mata daidai rufin asirinsa. Ya ba ta kuɗin kamu da gyaran jiki don shi ba shi da ra'ayin zuwa wurin kamu. Haka ita ma Bilkisu akwati guda ya cika mata da kaya, dangin atamfofi da lesuna da kayan shafe-shafe har da kayan bacci. Yaran kuma ya saya musu sababbin ƙananan kaya kala ɗaiɗai da shadda kala bibbiyu. A cikin satin Hafiz ya sa aka fitar da kujerun Bilkisu aka kai wurin kafinta ya gyara mata su, aka saka sababbin sosuna da sababbin yadi suka dawo kamar sababbi. Sai labulaye da ya saya mata masu yanayi da kujerunta duk don ya faranta mata. Sannan ya ba ta dubu hamsim ya ce ta yi duk wani gyara da za ta yi dangin kitso da ƙunshi. Ana saura kwana biyu Amina za ta tare ya kira masu fenti suka yi wa gidan fenti, sai dai jere ne ya hana 'yan uwan Amina su yi a ranar saboda yana tsoron kada Bilkisu ta aikata abin da za ta kunya shi a wurinsu. Ranar juma'a tun da sassafe 'yan uwan Amina suka je gidan Hafiz yin jere, kallo ɗaya suka yi wa Bilkisu suka fahimci zai yi wuya a yi zaman lafiya da ita a cikin gida. Don haka suka dinga kaffa-kaffa, gudun kada ta ce sun yi mata wani abin. Saboda sun ji sai faɗa take yi wa yara da habaici, kuma abu kaɗan yaro zai yi mata sai su ji ta rufe shi da duka. Kusan azahar suna ta aiki sai ga Fadila ƙanwar Hafiz, ta yi sallama cikin gidan hannunta ɗauke da ƙatuwar cooler. A ƙofar ɗakin Amina ta tsaya suka gaisa da masu jere, ta miƙa musu abincin ta yi musu bayanin kanta. Ta sake fita ta shigo da ruwa da manyan lemuka ta ajiye musu, sannan ta nufi ɗakin Bilkisu. Tun da Fadila ta shigo Bilkisu ta hango ta, ta cikin labule. Ta dubi ƙanwarta Hafsa ta ce. "Hmmm dangin miji ko baƙaƙen munafukai, dubi Fadila can ki ga. Wai ita aka aiko ta kawo musu abinci, saboda neman wurin zama. Wai yanzu duk yadda nake da su Fadila, haka za su yi mini su koma ɓangaren amarya." Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin ƙwafa. Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke ta ce, "To ya za ki yi ai sai haƙuri, kin san mijinki ne fa ɗan'uwansu. Kuma duk abin da yake so shi za su so, tun da ke dai bare ce a cikinsu." Shiru Bilkisu ta yi ta cigaba da girgiza ƙafa, suna nan zaune Fadila ta shiga ɗakin da murmushi bakinta ɗauke ta sallama. "Ina wuni Aunty Bilkisu." Fadila ta faɗa cikin girmamawa, tun daga ƙasa Bilkisu ta ɗebo Fadila da harara ta watsar a gwasale ta ce. "Lafiya." Shiru Fadila ta yi tana tsaye, don ba ta ga fuskar da za ta zauna ba. Bilkisu ta ce, "To ai sai ki koma can tun da wurinsu kika zo." "A'a abinci ne kawai na kawo musu." Fadila ta faɗa a sanyaye. Kamar Bilkisu tana jira ta ce. "Ai shi ne na ce ki koma can, tun da ni matar yayanki ce waccan ɗinma da za ki wurin matarsa ce." Fadila ba ta tanka wa Bilkisu ba ta fice daga ɗaki ta yi wa 'yan'uwan Amina sallama ta tafi. "Haba Aunty Bilkisu, ki dinga rage wani abin mana. Wai ba ki ga yadda Aunty Murja ta yi ba ne, kowacce mace fa tana jin kishi kawai iya taku ne." Hafsa ta furta, don ta lura idon yayarta ba ƙaramin rufewa ya yi ba. Cikin masifa ta ce . "Ita daban ni daban, malama kema idan ɓata mini rai za ki yi ki fice ki ba ni wuri." Hafsa ta yi shiru tana mamakin zafin ran 'yar uwarta. Koda 'yan uwan Amina suka gama jere ba duka suka tafi ba, sai aka bar mutum biyu a ɗakin da yayarta da kuma ƙanwar babanta. Suna gani Bilkisu shiga ɗaya-biyu idan ta yi sai ta yi musu habaici, ko ta saki tsaki tana harararsu. Sai da aka idar da sallar Magriba, sannan Hafiz ya aika aka ɗauko Amina zuwa gidansa. GIDAN ALHAJI UMAR Tun ranar da Shukura ta cika kwana shida a gidan Hajiya Karima ta yi ɗan jiƙe-jiƙenta, dangin abin da ya shafi tsimi da sauransu. Dama tun asali Hajiya Karima mace ce mai gyara sosai, tana da tsafta uwa-uba ba ta wasa wurin gyaran jikinta. Ta yi wannan haɗe-haɗen na musamman ne, saboda yadda ta lura da rawar jikin da Daddy yake yi a kan Shukura. Ba ta son ko kaɗan ya ga gazawarta, ko ta fuskaci wulaƙanci a wannan ɓangaren daga wurinsa. Saboda ta san duk son da namiji yake wa mace dole tana buƙatar gyara, kuma ko namiji bai fito ya bayyana ba idan bai samu yadda yake so ba za ta ga alama. Ko lokacin da Alhaji ya shiga ɗakinta, ta gama shan tsumin gumbar nonon raƙumi da ta sassaƙen ɓaure. Yana shiga ɗakin ta ƙare masa kallo duk sai ta gan shi a firgice, ƙarasawa ya yi gefen kujerar da take zaune ya sakar mata murmushi. Martanin murmushin ta mayar masa, ya riƙo hannunta ya ce. "Mommyn Mami kin ga yadda kika yi kyau kuwa?" Murmushi ta yi ta ce , "Wanne irin kyau kuma, kai da kake da amarya." Ta faɗi haka don ta ji me zai ce. "Kowa ai da irin nata kyawun."Ya furta mata yana murmushi. Shiru ta yi tana jin daɗi har a ranta, saboda ta ji an ce maza idan suka yi aure haushin iyayen gidansu suke ji. Amma ita sai ta ji yana yabonta, tana cikin tunani ta ji ya ce. "Dama zuwa na yi na nemi alfarma a wurinki." Ba ta kawo komai a kanta ba ce. "Alfarma kuma Daddyn Mami? Wacce iri kenan?" Gabansa yana faɗuwa, ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya dire a gabanta. Muryarsa tana rawa ya ce. "Amm... dama... so nake ki sayar mini da kwanaki bakwai." Dum! Ta ji kanta a saman kanta kamar an buga mata guduma, wani abu ne ya turniƙe mata ƙirji. Murya a ɗan sarƙe ta ce. "Ban... ban gane ba." Kunya ce ta kama shi, amma har cikin zuciyarsa yake jin ba zai iya ɓata wa Shukura rai ba, uwa-uba ba ya son yin nesa da gangar jikinta. A tattaro mayafin jarumta ya yafa wa kansa sannan ya ce. "Ina nufin ki sayar mini da kwana bakwai na ƙara a wurin Shukura." Ya ƙarasa maganar yana satar kallonta. Haɗe fuska ta yi tamau, rai a ɓace ta ce. "Ban amince ba Alhaji." Ransa ne ya fara ɓaci, don haka ya ɗauki kuɗin ya ɗora mata a cinya ya ce. "Shi ya sa na kawo miki dubu hamsin ga shi nan, kwana bakwai fa kawai zan ƙara haba Hajiya." Ya ƙarasa maganar a ɗan tsawace. Da mamaki take kallonsa ita ma, don ta sake ɓata masa rai sai ta ce. "Ka ɗauki kuɗinka ba na so, kuma kwana ban lamunce ba." Da sauri Alhaji ya ce, "Au haka kika ce? Ke wacce irin mace ce ne wai? Shekara nawa muna tare da ke kawai don na ce ki ƙara mini kwanaki za ki ɗaga wa kanki hankali? Yarinyar nan fa 'yar cikinki ce, don Allah ban da abin mata kishin me za ki zauna kina yi da ita?" Shiru Hajiya Karima ta yi har lokacin ba ta daina bin sa da kallo ba, zuciyarta ta fara wassafa mata abubuwa da dama. 'Kada ki yarda, idan kika amince masa wallahi daga ranar yarinyar nan za ta raina ki.' 'Ki yi haƙuri ki kyale shi ya yi kwanakin da yake so, 'ya'ya gare ki idan kika biye wa namiji ba kunya gare shi ba. Zai iya aikata abin da zai shafi tarbiyyar yaranki ko kuma ya sa su fahimci rashin jituwa a tsakaninku.' Shawarar ƙarshe da zuciyarta ta ba ta, ta ɗauka don haka ta ce. "Shi kenan babu damuwa, kwana bakwai ai kamar yau ne." Washe baki ta ga ya yi, ya matsa kusa da ita ya rungumo ta ya ce. "Yawwa ko ke fa Hajiya, idan kika kwantar da hankalinki Shukura ba baƙuwar zafi ba ce. Yanzu akwai abin da kika buƙata ne?" Girgiza masa kai ta yi a sanyaye ta ce. "Babu abin da muke buƙata." Miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, ya nufi ɗakin Shukura. A kwance ya same ta, ya rungumo ta ya ce. "Baby ta amince." Da sauri Shukura ta riƙe shi ta ce. "I love you Babyna." Fake ya sakar mata a goshi ya ce. "I love you too my baby." Ɗan lumshe ido ta yi ta ce, "To amma idan mun gama yau ina son shaƙatawa, almost six days kenan fa ina gida Baby." Shiru ya yi ya ce. "Don't worry baby, idan wannan ne an gama." Farr Shukura ta yi da ido sannn suka cigaba da hirar soyayya. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. https://chat.whatsapp.com/IAZVt2Pz4LvIcklCxSTHwo SHAFI NA HUƊU A daren ranar sai da Alhaji ya fita da Shukura, ba su suka dawo ba sai da dare ya tsala. Don gabaɗaya yaran gidan sun yi bacci sai Hajiya Karima ce ta ji motsin shigowarsu, shiru ta yi tana mamakin wai ita ce yau Alhaji ya sayi kwana a wurinta. Murmushin takaici ta yi tana jin hawaye mai ciwo yana zubo mata, ganin tunani zai yi mata yawa ya sa ta ɗauki carbi ta kwanta da shi tana lazumi har bacci ya yi awon gaba da ita. A washegarin ranar ma da yake Ruƙayya ba ta da lecture ta safe ita da Mommynta suka shiga kicin suka sarrafa abin karyawa. Kuma a ranar ne Hajiya ta ci alwashin yi wa Alhaji magana dangane da girki, tun da ta yi mata na kara wato girkin sati ɗaya. Tana son ta ji idan raba girki za su yi, ko kuma haɗewa za su yi. Su Shukura ba su fito ba sai kusan sha biyun rana, a lokacin yaran gidan duka sun tafi makaranta. Hajiya Karima tana zaune a falo tana kallo suka shiga, gaisawa suka yi da Alhaji sai washe baki yake yana haba-haba da ita. Shukura ba ta gaida ta ba, sai ita ce ta gaishe ta. A yatsine Shukura ta amsa mata, Hajiya ta yi kamar ba ta ga irin kallon rainin da take yi mata. Kwanciya Shukura ta yi a jikin Alhaji ta ce, "Baby yunwa nake ji." Jin haka ya sa a birkice Alhaji Ya ce. "Hajiya ina abincin ne?" Sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Yana kicin." Miƙewa ya yi da kansa ya shiga kicin ya ɗauko musu ya ajiye, har zai zuba musu Shukura ta maƙale kafaɗa ta ce. "Mu je can mana baby sai na fi sakewa." Kamar wanda ake ba wa umarni haka ya yi zumbur ya miƙe zai fita, cikin sauri Hajiya Karima ta ce. "Alhaji ina son magana da kai." Ɗan satar kallon Shukura ya yi sai ya koma ya zauna. Hajiya Karima ta ce. "Dama game da girki ne, na ce za a haɗa girki ne ko kowa zai yi nasa? Saboda ina son sani ne don Shukura ta karɓi girkint." Shiru ya yi yana son jin abin da Shukura za ta faɗa, don yana gudin ya ɗauki wani zaɓin ta ce bai yi mata ba, Hajiya kuma ta ga kamar zaɓin Shukura yake bi. "Tabɗi, gaskiya ba zan iya girkin haɗaka ba. Duka yaushe na zo da zan fara girka uwar tukunya, kowa dai ya yi nasa kawai shi ne magana." Shukura ta furta cike da tsiwa, jinjina kai Hajiya Karima ta yi tana jin zuciyarta na zafi. Kasa daurewa ta yi ta ce. "To ai kin san yana da tawagar kika aure shi haka." Kamar Shukura tana jira ta ce. "Eh saboda shi mijin mace huɗu ne, kuma don na aure shi ba shi zai sa na yi wa 'ya'ya bauta ba." Hajiya Karima za ta yi magana Alhaji ya ce. "Yanzu dai duk ba wannan ba, shi kenan kowacce ta yi girkinta ina ganin haka zai fi." Amsawa Hajiya Karima ta yi ta miƙe ta shiga ɗaki, taɓe baki Shukura ta yi ganin Alhaji zai bi Hajiya Karima ya sa ta riƙe hannunsa suka nufi ɗakinta. Alhaji Umar mai leda shi ne cikakken sunan Daddy, asalinsa mutumin Jigawa ne. Neman kuɗi ne ya kawo shi Kano, shi da Hajiya Karima auren saurayi da budurwa aka yi musu, mahaifinta da mahafinsa duka abokai ne. Don haka aka haɗa su aure a wancan lokacin, lokacin da aka yi aurensu Alhaji dako yake yi a kasuwar singa da ke Kano. Rashin wadataccan ƙarfi ya sa bai kawo Mommy a lokacin ba, har sai da ya ta haifi Ruƙayya (Mami). Da yake a lokacin ya ƙara samun cigaba ya zama yaron shago. Daddy mutum ne mai zuciyar nema, kuma a tsaye yake a kan iyalinsa daidai gwargwado. Ba za ka saka shi a cikin sahun hamshaƙan masu kuɗi ba, kuma ba zai shiga sahun talakawa ba. Shi mutum ne mai rufin asiri daidai misali, yana da dukiya mai yawa da kadarori. Hajiya Karima macece mai haƙuri da zurfin ciki, tun asali ba ta da hatsaniya. Zamanta da Alhaji ne ya sa a haka ake ganin ta yi baki, duk da wanda bai santa a baya ba zai dinga yi mata kallon marar son magana. Haihuwarta takwas da Alhaji Umar biyu sun rasu, sai guda shida da suke raye. Ruƙayya ita ce babba tana shekara shirin da huɗu, sai Haidar yake bin ta. Shi kuma tsiran shekara ɗaya ne tsakaninsu da yake kwanikar haihuwarsu ta yi. Sai Nabil, Nazir, Sadik da kuma Sulaiman ɗan autanta mai shekara goma. Lokacin da Alhaji ya yi aure bikin Ruƙayya saura wata biyu, don haka take ta Allah-Allah ta bar gidan ko ta rage ganin kayan takaici. Ita da Haidar gabaɗaya suna level 400 a makarantar Maitama Sule University da ke Kano, Nabil da Nazir kuma sun yi candy neman Admission suke yi. Sai Sadik da yake ƙaramar sakandire, shi kuma Sulaiman yana ajin ƙarshe na firamare ba. Tun da Alhaji ya raba girki kowa ya koma yin nasa, don haka wani lokacin sai a shafe wuni guda wani bai ga wani ba a cikinsu. A haka kwanaki suka dinga shuɗewa har Alhaji ya dawo ɗakin Mommy, yanayinsa babu yabo babu fallasa. Sai dai ta lura wuni Shukura ta yi tana shige da fice a gidan tana ɓace-ɓacen rai. Ita Hajiya abin har mamaki ya bata, saboda gani ta yi har idan kishi ne ai ita ya kamata ta nuna kishinta. Tun da ita ta shafe shekara da shekaru da shi suna tare. A daren ranar da Alhaji ya dawo ɗakin Mommy cikin dare suna kwance suka ji ihun Shukura, daga Daddy har Mommy rige-rigen fita suka yi don ganin abin da ya faru. A tsaye suka same ta daga ita sai wata yaloluwar rigar bacci, samarin gidan da su Ruƙayya ne su ma duk suka firfito. Ganin yanayin da take ciki ya sa su Haidar suka koma ɗaki, kallo ɗaya Ruƙayya ta yi mata ta saki tsaki har sai da Shukuran ta waigo suka haɗa ido, sannan Ruƙayya ta yi tafiyarya ɗaki. "Me ya faru kike ihu Shukura?" Daddy ya furta cikin kulawa. Kuka ta rushe da shi ta ce. "Ina kwance kawai na ji an shigo mini ɗaki, ban yi aune ba na ji an fara jan zanin jikina ƙasa." Cikin sauri Daddy ya ce. "Shigowa? Ɗakin naki aka shigo?" Gyaɗa kai ta yi tana cigaba da kuka, haskawa ya fara yi ya ga ko ina a rufe kamar yadda yake. Ya haske saman doguwar katangarsu bai ga alamar za a iya hawa ba, haka daga ƙofar da za ta sada ka da babban gate a datse take. Cikin mamaki Dadday ya ce. "Ko dai mafarki kika yi Shukura?" "Ni babu wani mafarki, bayan ana ji na yi ihu na ji an fito da gudu kuma ba fita aka yi ba a cikin gidan nan ne." Wani irin ɓacin rai ne ya dira a zuciyar Hajiya Karima, don ta fahimci sarai makirci ne da tuggu za ta yi wa yaranta. Rai a matuƙar ɓace ta ce, "Ke yarinya ki shiga hankalinki, wallahi kada ki kuskura ki saka yarana a cikin makircinki." "To ni me nace? Na ce 'ya'yanki ne suka shigo? To ko dama can haka yaran na ki suke?" Shukura ta yi maganar tana narkewa, a zafafe Hajiya Karima ɗago za ta yi magana Alhaji ya ce. "A'a Hajiya ki dai bari a gama jin bayaninta, da kike musawa Shukura yarinya ce da za ta yi ƙarya ne?" Jikin Hajiya Karima wani irin sanyi ya yi, ta zuba wa Alhaji ido cike da mamaki. GIDAN HAFIZ Sai da 'yan kawo amarya suka watse sannan Hafiz ya shiga gidan cikin shigar angoncinsa ta babbar riga. Ɗakin Bilkisu ya fara shiga, ya same ta a kwance a kan gado idanunta duk sun kumbura alamun ta ci kuka ta more. Duk sai ya ji tausayinta ya kama shi, zama ya yi a bakin gadon ya ce. "Ummu Sayyid." Ɗagowa ta yi ta dube shi, sai ta ga ya yi mata wani irin kyau. Nan take kishi ya mamaye ta, hawaye ya fara zuba daga idonta. Hannu ya saka ya goge mata, tana jin hannunsa ba ta hana shi ba. Cikin tausasawa ya ce, "Zo mu je falo." Girgiza masa kai ta yi ta ce. "Ba zan iya ba Abban Sayyid." "Don Allah ki daina kukan yana damuna." Ɗagowa ta yi ta zuba masa ido ta ce. "Yanzu fa wurin wata za ka tafi ko? Dama Hafiz za ka iya mu'amala da wata macen bayan ni..." "Don Allah ki daina wannan maganar Bilkisu, ki taso mu je please." A sanyaye ta zuro ƙafafuwanta ƙasa, ta ɗauki hijabi ta saka tana goge fuskarta. Ɗakin Amina ya shiga ita ma ta kira ta, Bilkisu tana ganinta gabanta ya shiga faɗuwa. Nasiha Hafz ya fara yi musu, jin ba za ta iya danne abin da yake cikin zuciyarta ba ya sa ta miƙe fuuuu ta shige ɗaki. Girgiza kai Hafiz ya yi, ya ce Amina ta koma ɗakinta, sannan ya shiga ɗaki wurin Bilkisu. Yana shiga ya hango ta ta cusa kanta cikin ƙafafuwanta, ƙarasawa ya yi gabanta sai kawai ta ɗago ta rumgume shi ta saki sabon kuka. Riƙe ta ya yi sosai, musamman yadda ya ji jikinta yana rawa. Murya a dashe ta ce. "Mutuwa zan yi." "Ki daina faɗin haka Bilkisu, ke fa musulma ce don Allah ki ɗauki wannan auren a matsayin ƙaddara."Hafiz ya furta cikin lallashi, sannan ya ajiye mata ledar kazarta da lemuka. Sallama ya yi mata har ya juya zai tafi ta ce. "Au da gaske wurinta za ka je?" Shi maganar ma dariya ta so ba shi, don ya lura wani abin da Bilkisu take yi kamar ba ta cikin hayyacinta. Ya waigo ya ce. "Eh." Sai hawaye ya cigaba da zuba daga idonta cikin kuka ta ce. "To ka je duk abin da ka yi mini, Allah ya yi maka Hafiz kuma ka zo ka ɗauki tsinanniyar kazarka ba na ci." Ta ƙarasa maganar tana yin jifa da ledar da ya ajiye. Hafiz bai kula ta ba ya wuce ɗakin Amina, sai da ya ba ta haƙurin jimawar da ya yi sannan suka shiga gabatar da abin da yake gabansu. Kamar wata wacce aljanu suka kama haka Bilkisu ta dinga ɓurumtu tana shige da fice a tsakar gida, kusan yadda ta ga rana haka ta ƙarasa ganin darenta. Da asubar fari ta ji Hafiz ya haɗa musu ruwan wanka ya kai banɗaki, jin haka ya sake ɗaga hankalin Bikisu. Da ƙyar ta lallashi kanta, ta samu ta gabatar sallar asuba. Tun asuba ta shiga ɗakin yaran ta dinga jibgarsu tana tashinsu sallah, abu kaɗan za su yi za ta fara zaginsu tana duka. Tsakar gida ta fita, ta cigaba da kwaramniya da kwanuka tana fafutukar ɗora abinci. Su dai yaran shiru suka yi, duk suka takure wuri ɗaya. Tsoron mahaifiyarsu duk ya kama su, sun san dai ranar asabar babu makaranta. Kuma sun ga sai shiri take yi tana musu masifar su yi su ci abinci kada su makara, tsoron kada ta dake su ya sa suka gagara faɗa mata. Don haka a ranar tun bakwai da rabi ta gama shirya su, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Amina ta shiga bugawa da wani irin ƙarfi. Tun da Hafiz ya yi sallar asuba bayan ya leƙa Bilkisu da yara, ya koma ɗakin Amina ya kwanta suka koma bacci. Suna tsaka da bacci suka ji bugun ƙofa a tsakar kansu, a hargitse ya fito daga shi sai gajeren wando yana faɗin. "Lafiya Bilkisu me ya faru ne?" Kallon yanayin da yake ciki ya sake turnuƙe ta, a fusace ta ce. "Ta ina za ka san abin da ya faru? Tun da ka saka mace a ɗaki kamar a kanta ka fara sanin mace." Ko kaɗan bai ji daɗin furucinta ba, saboda ko babu komai yaransa suna tsaye suna kallonsu. Rai a ɓace ya ce, "Wai me yake damunki ne Bilkisu? Wacce irin maganar banza kike yi haka a gaban yara ne?" "Ƙarya na yi? Ba macen ka saka a gaba ba? To duk jarabarka sai ka fito ka kai yara makaranta." Bilkisu ta faɗa cike da kishi. Waigawa ya yi ya hangi yaran duk sun yi zuru-zuru, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci a tsorace suke. Ga su sanye da uniform da kulolin abinci, girgiza kai ya yi a ransa ya ayyana tabbas Bilkisu ba ta cikin nutsuwarta. "Dama suna zuwa makaranta ranar asabar ne? Ko kin manta yau asabar?" Shiru Bilkisu ta yi cike da kunya, jin hayaniya ta yi yawa ya sa Amina ta ɗan turo ƙofar ta leƙo. Kanta babu ɗan kwali ta sha ƙananan kitso mai kyau, ta yafa zanin rufa a jikinta. "Ina kwana Aunty." Ta furta a sanyaye, wani mugun kallo Bilkisu ta wurga mata kamar tana jira ta ce. "Kada ki sake ce mini Aunty, ni ba yayarki ba ce. Me na haɗa da ke? Ai ƙanwata ba za ta taɓa auren mijina ba." Waigawa Hafiz ya yi ya ce. "Koma ciki." Babu musu Amina ta koma ciki, ya riƙe hannun Bilkisu ya kai ta ɗaki ya zaunar a kan kujera. Ƙasa ya yi da murya ya ce. "Haba Bilkisu, me ya sa duk maganar da nake yi miki ba kya ji ne? Don Allah ki kama girmanki, ba na son ki dinga abin da yarinyar nan za ta zo ta raina ki. Yanzu don Allah me kika yi haka? Kin fa san yau weekend, yaran nan ba sa zuwa makaranta." Idon Bilkisu ne ya ciko da ƙwalla ta ce, "To ai mantawa na yi." Hannu ya saka ya goge mata hawayen, zai miƙe ta sake cewa. "Yanzu shi kenan kuma ka daina sona." Shiru ya yi cike da damuwa, ya girgiza mata kai ya ce. "Idan ana mata ɗari ko fi, duk wacce zan auro ba zan daina sonki ba Bilkisu. Don Allah kada ki sa wannan a ranki, kin taɓa ganin namiji ya zauna da macen da ba ya sonta?" Girgiza masa kai ta yi ta ce. "To amma ai ga shi nan ka je ka kwanta da wata, shi kenan ta gama gane mini sirrinka." Murmushi ya yi don ya san kishi ne duk yake damunta, ya matsa kusa da ita ya ce. "Ke ce fa uwargida, ko kin manta ni da ke auren saurayi da budurwa muka yi? Duk wacce zan yi mu'amala da ita fa a bayanki ne, kuma da kike faɗin haka ita ma fa matata ce. Ba wurin macen banza na je ba, ko kin fi son na fara biye-biye a waje da na yi auren?" Girgiza kai ta yi, ya zauna ya cigaba da lallashin Bilkisu har sai da ya ga hankalinta ya ɗan kwanta sannan ya tafi ɗakin Amina. A wannan ranar Hafiz ya ɗauka Bilkisu za ta yi abincin safe da su, bayan da suka yi wanka ya fito ya tambaye ta kai tsaye ta ce ba ta girka da su ba, tun da ba ita ce da miji ba. Gudun tashin tarzoma ya sa shi fita ya sayo musu shayi a waje, saboda ba a haɗa gas ɗin Amina ba. Sai da suka karya sannan ya ɗauki silindarta ya tafi da ita ya ciko mata, a lokacin da ya dawo 'yan'uwan Amina sun zo da wasu tsirarin danginsa. Bilkisu kuwa tana ɗaki ko ƙurarsu ba ta bi ba, don gabaɗaya dangin Hafiz ya shafa musu kashin kaji. Yamma liƙis Hafiz ya kawo kayan miya ya ce Bilkisu ta gyara, a nan ma ta kafe kai da fata ta ce ba za ta yi girki ba. Idan kuwa ta sarrafa ba za ta ba shi da amaryarsa ba, babu yadda ya iya haka ya kai wa Amina. A lokacin da ya shiga ɗakin, zafi ya ji a jikinta na zazzaɓi saboda rashin ƙwarin jiki, tausayi ta ba shi sosai. Don haka ya rage kayan jikinsa ya gyara kayan miyar ya ba wa yara suka kai markaɗe, da kansa ya ɗora miyar ganin haka ya sa Amina ta miƙe cike da rashin ƙwarin jiki za ta taya shi ya ce ta je ta kwanta. Cikin lokaci ƙanƙani ya ƙarasa miyar, ya ce Bilkisu ta dafa taliya sai da ƙyar ya samu ta dafa ta miƙa musu. Tun daga wannan ranar Amina ta karɓi girkin rana da na dare, na safe ne kawai kowa yake yin na sa. Abin da Bilkisu ta tsira a cikin kwanakin amarcin Amina sai gari ya waye sai ta yi wa yaranta wanka da sassafe ta saka su, su shiga ɗaki wurin mahaifinsu. Wani lokacin ma idan suka shiga suna kwance a kan gado, haka Amina za ta sako hijabi ta janyo su falo. Babu wata dama da suke samu ta kulawa da juna da safe ko da rana, matuƙar yaran suna gida. Idan kuma yaran ba sa nan Bilkisu ta dinga yi musu habaici ta cewa Hafiz ya cika jaraba, ko ta ce ya auro makira mai karuwancin cikin gida. A haka suka cigaba da tafiya tun abin ba ya damun Amina har abin ya fara damunta, saboda akwai lokacin da rana Hafiz ya dawo suna ɗaki duk da sun tura ƙofa sai ji suka yi yara sun shigo ɗakin da suke kwance. "Lah Abba." Sayya mai kimanin shekara uku ta faɗa ganin mahaifinta yana mu'amala da Auntynsu. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍 ‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah! MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani! Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu: Gyaran gashi da kitson zamani Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai Kayan gyaran fata na gaske Lalle mai kyau da salo na zamani Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi Shirin amare da na musamman Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya. Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau. Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna. Tambaya/Booking: WhatsApp: 08062991549 Kira: 09016108092 / 08064532391 Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge. Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge SHAFI NA BIYAR A razane Amina ta ja bargo ta rufe jikinta, haka shi ma Hafiz cikin sauri ya janye jikinsa daga jikin Amina haɗe da rufe jiki. Ya haɗe fuska tamau cikin tsawa ya ce. "Fita daga nan." Ganin yadda mahaifinta ya birkice lokaci ɗaya ya sa ta fita da gudu tana kuka, miƙewa Hafiz ya yi yana suturce jikinsa. Bai yi aune ba sai ji ya yi Bilkisu ta banko ƙofar ta shigo cikin masifa tana faɗin. "Uwar me Sayyada ta yi miki kika dakar mini ita take kuka, baƙar munafuka kin san ba kya ƙaunarsu kika maƙale saboda kwantan da kika yi kika auri mahaifinsu." Ganin Amina ba ta falo ya sa Bilkisu ta faɗa ɗakin za ta yi magana ta ci karo da su suna gyara jikinsu, wani baƙinciki ne ya maƙure ta. Cikin zafin kishi ta ce. "Wannan wacce irin jaraba ce da rana tsaka salon ku ɓa ta mini tarbiyyar..." "Fita ki ba ni wuri ba na son rashin hankali." Hafiz ya katse ta a zafafe, yadda ya hautsine mata ya sa ta ja ƙafa ta fita don ta lura ransa a matuƙar ɓace yake. Amina da ke zaune a gefen gado kifa kanta ta yi ta fashe da kukan takaici, jiki a sanyaye ya ƙarasa ya rungumo ta ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri Amina." "Habibi na gaji, wallahi na gaji da abin da matarka take yi mini. Yanzu wanne irin abu ne a ce ni da ɗakina ba ni da sirri, ina kwance da mijina dubi yadda 'yarka ta zo ta same mu? Wanne irin kishi matarka take da shi, da har ta gwammace gara ta ɓata tarbiyyar yaranta? Wallahi matuƙar ba za ka ɗauki mataki ba ba zan cigaba da zama a haka ba." Amina ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye. Ya sani sarai Amina tana da haƙuri, don akwai abubuwa da dama da idan ya ga Bilkisu ta yi mata ya san idan ita ce ba za ta yarda ba. Cikin lallashi ya ce. "In Shaa Allahu haka ba zai sake faruwa ba, don Allah ki yi haƙuri babyna." Hawayenta ta share tana gyaɗa masa kai, bakinta ya sumbata. Ya janyo ta yana yi mata raɗa a kunne, turo baki gaba ta yi a shagwaɓe ta ce. "Ni a'a, ba yanzu ba." Marairaicewa ya yi kamar zai yi kuka ya ce. "Please, ai ba laifina ba ne da za a hukunta ni. Kuma kin san dai ba zan iya..." Sai kawai ya kashe mata ido ɗaya, ɗauke kai ta yi ta alamar fushin wasa ta ce. "Kuma hakan za ka haƙura ka bar wa dare, wai dama haka idonka yake a buɗe amma kafin aurenmu kullum sai ka yi ta sunne kai ƙasa." Dariya ya yi sosai ya ce. "To wancan lokacin da yanzu akwai bambamci ai, ni dai gaskiya ki san yadda za ki yi da ni." Hararar wasa ta yi masa, sannan suka cigaba da ba wa juna kulawa. A tsammanin Bilkisu tun da ta katse musu yanayin da suke ciki ta wargaza musu na wannan lokacin, ta ɗauka Hafiz zai fito ya same ta da maganar ta yadda za ta ja shi da faɗa har ya ɓata lokacin a wurinta. Jin shirunsu a ɗaki ya sake ɓata mata rai, don haka ta koma ɗaki ta cika fam da ɓacin rai. Tana nan zaune ta hangi Amina ta fito ta shiga banɗaki, tana wuce babu jimawa shi ma Hafiz ya rufa mata baya. Cikin suɓutar baki ta ce. "Kan babban bala'i, wato ni za a gwadawa bariki ido biyu da rana. Hafiz saboda ya wulaƙanta ni har wankan ma tare za su shiga?" Tana rufe baki sai hawaye ya fara zuba, don rabonta da shiga banɗaki tare da Hafiz tun Sayyid yana ƙarami. Tana nan zaune ta ga Amina ta fito, bayan wani lokaci shi ma Hafiz ya wuce ɗakin Amina. Sai da ya shirya cikin ƙananan kaya sannan ya fito hannunsa riƙe da wayar caza, ya ƙarasa ɗakin yaran da suke wasa. Hannun Sayyada ya kama duka biyun ya riƙe wuri ɗaya, ya shiga zabga mata wayar cajar a ƙafa da sauran jikinta. Nan take 'yan'uwanta duk suka takure wuri ɗaya cikin jin tsoro, don sun ɗauka yana gamawa zai koma kansu. Jin kukan Sayyada ya sa Bilkisu ta fito fuuu a fuskace ta kai hannu za ta janye ta. Da wata irin muryar ɓacin rai ya ce. "Idan kika taɓa mini 'ya ina dukanta wallahi sai kin tafi gidanku a yau." Janye hannunta Bilkisu ta yi, saboda duk abin ta tana matuƙar son Hafiz, koda wasa ba ta son wani abu da zai raba ta da shi. Kiran sauran yaran ya yi ya haɗa su wuri ɗaya, fuska a haɗe ya fara magana. "Daga yau sai yau duk wanda ya kuma shiga ɗakin mamanku ko ɗakin Aunty amarya, ba tare ya yi sallama ba sai na farfasawa mutum jiki. Sannan zan haɗa ku gabaɗaya, na kai can bolar bayan gari na watsar. Idan ya so nan gaba sai mamanku da Aunty amarya su haifo mini wasu yaran." A tsorace duk suka gyaɗa masa kai, cikin tsoratarwa ya buga musu tsawa da cewar. "Kun ji me nace ko? Kuma idan kuka yi sallama sai kun ji an amsa an ce ku shigo, idan ba haka ba wallahi dukan da zan yi wa mutum sai ya fi wannan." Baki yana rawa yaran suka amsa, ya ɗauko alawa ya damƙa wa kowa a hannu sannan ya lallashe su cikin nasiha ya tashi ya fita. Ɗakin Bilkisu ya shiga, saboda tun da ya yi mata magana ta yi zuciya ta fice ta tafi ɗaki. A zaune ya same ta ta haɗe fuska, shi ma fuskar ya sake haɗewa ya ce. "Bilikisu!" Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, ya dube ta ya cigaba da cewa. "Ba zan zura ido ki lalata mini tarbiyyar yara ba, saboda kishin rashin hankalin da kike yi, daga yau sai yau idan kika kuma tura mini yara ina ɗakin Amina ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba sai ranki ya ɓaci. Ni ba hana su shiga ɗakinta zan yi ba, amma ke ma ki san lokacin da za ki dinga tura su. Wai duk wannan abin da kike yi na mene ne? Ba dai don kana da na yi mu'amala da ita ba ne? To me ya yi saura yanzu? Na fahimci duk karar da nake yi miki da mutumtawar da nake yi miki ba kya gani. Bari ki ji, yadda kike matata haka Amina take a wurina duk matsayinku ɗaya, yadda kika san ni a matsayina na mijinki haka ita ma ta san ni. An faɗa miki kishi hauka ne? Ke wanne irin abu ne ba ki yi ba a lokacin da yayanki zai ƙara aure, ba ke ce amara ba har da ɗauko auko? Amma a kaf dangina wa ya taɓa zuwa gidan nan ya nuna miki yana farinciki da auren da zan yi, duk suna yi ne don su yi miki kara ba wai don ba sa so ba ne. Wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki, ina faɗa miki haka ne tun ba ki ƙure yarinyar nan ba. Idan kika buɗe mata ido nan gaba ba za ki ji daɗin zama da ita ba."Hafiz yana gama magana ya fice daga ɗakin rai a ɓace. Wannan faɗan da Hafiz ya yi wa Bilkisu da yaransa su Sayyada, shi ya sa Amina ta samu 'yanci sakata ta wala a ɗakinta. Don idan Hafiz yana nan, tana samun damar saka ƙananan kayanta masu jan hankali da rigunan bacci. Saɓanin a baya da take saka manyan kaya, gudun kada yaran su shiga su ga shigar da ba ta dace a jikinta ba. A ranar da Hafiz zai koma ɗakin Bilkisu tun safe take cikin annshuwa tana walwala. Hatta Amina da ba wata hirar suke yi ba, ta fahimci walwlarta. Tana zaune bayan la'asar ta ji sallamar Aunty Murja da Na'ima, duk da Amina ba ta sansu ba amma fuska a sake ta amsa sallamarsu tana yi musu sannu da zuwa. Fuska a sake su Aunty Murja suka amsa mata, suna cikin gaisawa Bilkisu ta leƙo a fusace ta ce. "To tsaiwar me kuke yi Aunty Murja ku shigo mana." Ƙarasawa suka yi ɗakinta, sai da suka gaisa Aunty Murja ta ce. "Oh ashe kuma haka abu ya faru Bilkisu, ni ai ina zaune rannan katsam Abban Sajida yake faɗa mini wai Hafiz zai yi aure. To daga baya kuma na ji an ce ba za ki yi wuni ba, don dama cewa na yi zan zo ƙafa da ƙafa. Da muka ji ba wuni sai kawai na cewa Auntyn yara ta bari ma zo daga baya." Taɓe baki Bilkisu ta yi ta ce. "Tsinanniya gata can ai, an kawo ta baƙar daga. Sai ta zo ta ci uwar da nake ci." Aunty Murja murmushi ta yi, ta tuna irin habaici da cin kashin da suka dinga yi mata. Sai kawai ta ce. "Allah Ya haɗa kanku, ya sa zuwanta alheri ne." "Haba Aunty Murja, kin taɓa ganin zuwan kishiya ya zama alheri?" Bilkisu ta faɗa cikin sauri, sunkuyar da kai Na'ima ta yi. Aunty Murja ko kaɗan ba ta ji daɗi ba saboda Na'ima tana wurin, don haka ta miƙe ta ce. "Mu bari mu wuce yawon namu da yawa, za mu leƙa barka matar yayan Auntyn yara ce ta haihu." Mamaki ne ya kama Bilkisu ganin yadda Aunty Murja ta ɗauki kishiya kamar wata ƙanwarta. Har soro ta raka su, Na'ima ce ta fara fita. Cikin sauri Bilkisu ta kamo hannun Aunty Murja ta ce. "Aunty Murja wai kishiya kike yi wa wannan haba-habar? Salon kina zaune ta zo ta raba ki da mijin? Ai wallahi ni da kishiya sai dai kallon banza." Murmushi Aunty Murja ta yi ta ce. "Ya danganta da irin kishiyar da kike da ita Bilkisu, ita kishiya kana karantar yanayin yadda ta zo ne. Idan ta zo da arziki ku yi shi, idan kuma da tsiya ne sai ki kama kanki. Ni ba abin da zan cewa Na'ima, saboda zuciya ɗaya take tare da ni da yarana. Yanzu haka zancan da nake yi miki Nimrah ta koma hannunta, kema ki karanci taki kada ki cuce ta. Ki zauna ke da ita zuciya ɗaya, sai ki ga zamanku ya yi daɗi." Ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke, tana jin magnar Aunty Murja kamar busar sarewa. Daga ɗan waje Na'ima ce ta leƙo ta ce. "Aunty kin san dai halin Abban Sajida, wallahi idan muka yi dare ke zan ɗorawa laifi. Ko kuma na kama hanya na yi gaba sai kin taho." A gaggauce Aunty Murja ta yi wa Bilkisu sallama tana dariya ta ce, "Wallahi ki ɗora mini laifi, ni ma sai na faɗa masa laifin jiya da na rufa miki asiri." Na'ima ta yi dariya suka tafi. Kwana biyu gidan Hafiz lafiya ƙalau ake zaune, saboda a ɗakin Bilkisu yake. Koda Hafiz ya koma ɗakinta, babu wani canji da ya nuna mata. Hasali ma duk don ya faranta mata, haka ya dinga santin girkinta da duk wani abu da ta yi masa. Shi kansa ya ji daɗi sosai ganin yadda ta watsar da komai, duk da ba wata doguwar mu'amala suke yi da Amina ba. Amma babu wani abin faɗa ko baƙar maganar da take haɗa su, haka daga ɓangaren Amina ta ji kewar Hafiz da zai bar ɗakinta. Amma hakan bai sa ta yi wata muguwar kissa ko ɓacin rai ba, hasali ma ta rungumi su Sayyada hannu bibbiyu. Don haka take jan su ɗaki su yi ta wasansu a cen. Tun a safiyar ranar da Hafiz zai koma ɗakin Amina Bilkisu take haɗe rai, da Magariba ta yi Amina tana gama girki bayan ta shiga wanka Bilkisu ta saci jiki ta shiga ɗakin Amina. Cikin sauri ta buɗe galan ɗin fetir ɗin da Hafiz yake sayan mai da shi, ta ɗebi kaɗan ta yaryaɗa a cikin kular abincin. Da sauri ta fito ta koma ɗaki zuciyarta fes, bayan wani lokaci ta ji ƙarar mashin ɗin Hafiz ya shigo cikin gidan. Dariya ta fara ƙyaƙyatawa har riƙe ciki, ta jikin labule ta hango Amina ta fito cikin tsaleliyar atamfa. Ta ƙafa ɗaurin ɗankwali ba ƙaramin kyau ya yi mata ba. Yana saukowa daga kan mashin Amina ta rungume shi, fake ta sakarwa kumtunsa. Ya saka hannu ya riƙo ƙungunta ya ce. "Wannan wankan zai sumar da ni." Murmushi ta yi tana fari da ido ta ce, "To ni kuma na yi yaya kenan?" "Sai ki farfaɗo da ni." Ya faɗa yana murmushi, ledar hannunsa ta riƙe suka shiga ɗaki. Yana shiga ɗakin, ya cire hula ya ajiye sannan ya fito ya shiga ɗakin Bilkisu. Gaisawa suka yi ya tambayi yaran, babu yabo babi fallasa ta ba shi amsa sannan ya fita. Yana fita ta sake sakin dariyar ƙeta, tana jiran sakamakon abin da ta aikata. GIDAN ALHAJI UMAR Jin abin da Ahaji ya faɗa ya sa Shukura ta sake kwaɓe baki ta ce. "Gaskiya ni dai tsoro nake ji baby, wallahi ba zan iya kwana a ɗakin nan ba kada a sake shigowa." Shiru Daddy ya yi, sai ya nufi ɗakin su Haidar ya ce. "Kai Haidar a cikinku akwai wanda ya fito waje ne?" Sun fahimci sarai inda maganarsa ta dosa, amma gudun ɓacin ransa ya sa suka ce masa a'a. Komawa ya yi wurin da ya bar su Shukura, ya dubi Hajiya Karima ya ce. "Ke ki je ɗaki Hajiya, zan zauna da ita zuwa nan da sallar asuba." Da ido Hajiya Karima ta bi shi, saboda ɓacin rai ko tanka masa ba ta yi ba ta nufi ɗaki zuciyarta tana suya. Cikin ɗaki Shukura ta shiga, Daddy ya rufe mata baya. Suna shiga ta shige jikinsa, tana runtse ido alamun tsoro take ji. Sannu a hankali yanayin salon zaman da suke yi ya sauya. Shukura ta shiga aika masa da saƙonni masu birkitarwa, ko kaɗan Daddy bai yi niyyar biye mata ba. Amma yanayin saƙon da take aika masa ya sa shi yi wa zuciyarsa biyayya, ya shiga mayar mata da martani. Jin Shukura tana ƙoƙarin kai shi matsayar da bai yi niyya ba, ya sa shi ɗagowa cikin wani irin yanayi ya ce. "Baby mu bari sai na dawo nan ko?" Cikin kissa Shukura ta fashe masa da kuka tana narkewa a jikinsa ta ce. "Amma ai ni ba haramun ba ce a wurinka, wai dama haka za ka dinga wulaƙanta ni ban sani ba." Yadda ta ƙarasa maganar tana haɗe jikinsa da nata ya sa jin wani abu yana fisgarsa a kanta, ya sunkuya ya laso hawayenta cike da so ya ce. "Ba na son kukanki baby." "To ni idan ba ka so ka daina hana ni." Ta furta tana sake aika hannunta cikin jikinsa. Cikin kissa da kisisina Shukura ta cigaba da sarrafa Alhaji har sai da suka biyawa juna buƙata, sai daga baya duk ya ji bai ji daɗi ba. Ko babu komai ya san wannan lokacin na Mommyn Mami ne. Shukura da gayya ta fita ta ɗora ruwa a tukunya, tamkar rana haka ta dinga buga tukunyar lokacin da za ta ɗebi ruwa. Sai da ta ɗora musu sannan ta koma ɗaki ta narke a jikin Daddy. Hajiya Karima tana shiga ɗaki ta haɗa kai da bango saboda damuwa, ba ta yi tsammani ba sai ji ta yi hawaye yana bin idonta. Babban abin da ya fi ɓata mata rai, yadda ake ƙoƙarin yi wa 'ya'yanta sharri amma ƙiri-ƙiri Alhaji ya turbuɗawa idanunsa toka ya bi bayan matarsa. "Dama akwai ranar da Daddyn Mami zai fifita mace a kan 'ya'yan da na haifa? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Ta furta domin ta samu zuciyarta ta yi sanyi. Kwanyarta ce ta tushe, zuciyarta duk babu daɗi. Don haka ta miƙe ta fita domin ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar nafila ko ta ji daɗi a ranta, tana fita ta nufi banɗaki don ta kama ruwa a nan ta ji motsin ruwa alamun ana wanka. Tana shirin komawa ɗaki ta ga Shukura ta fito, hannunta riƙe da na Daddy daga shi sai towel a ɗaure a ƙugunsa. Wani abu ne ta ji ya daki zuciyarta, sai ta yi kamar ba ta gansu ba. Ta shiga banɗaki ta kama ruwa sannan ta ɗauro alwala, ta nufi ɗakinta tana jin wani irin ɗaci a ranta. Shukura daɗi ta ji a zuciyarta, duk da ta ga Daddy duk ya birkice. Doguwar riga ya zura ya nufi ɗakin Mommy cike da sanyin jiki, a lokacin da ya je ta idar da raka'a ta biyu. Cike da borin kunya ya riƙo hannunta ya ce. "Ai ɗazu da kika ganmu ruwa na watsa saboda zafi, kin san garin kwana biyu..." "Ban tambaye ka ba Daddyn Mami. Ko wuta ka watsa wannan ba damuwata ba ce tun da kai da iyalinka ne, wannan sirrinku ne ba sai ka tona ba." Hajiya Karima ta katse shi cikin ɓacin rai, ganin yanayin da take ciki ya sa shi kama kansa. Ta sake tayar da sallah yana nan zaune duk jikinsa a sanyaye. Har gari ya waye Hajiya Karima ba ta ba wa Daddy fuska ba, shi ma ganin haka ya sa ya fara nan-nan da ita, bini-bini sai ya tambaye ta ko tana son wani abu. A kwana na biyun Hajiya Karima Shukura ba ta yi komai ba, lafiya ƙalau suka kwanta har Daddy ya koma ɗakinta. Sannu a hankali zamansu ya cigaba da tafiya, sai dai kusan kullum Mommy danne zuciyarta take yi. A ɓangare ɗaya kuma tana ƙara dannar Ruƙayya, don sautari ta sha cewa za ta tare da a kan wasu abubuwan da take yi a gidan ta mata magana. Amma sanin Shukura irin matan nan masu sharri ne ya sa take haƙurƙurtar da ita. Duk da an raba girki, amma wani lokacin Shukura tana sani sai ta ce wa Daddy ba ta yi girki ba na Hajiya Karima za ta ci. Haka zai je har ɗaki ya saka Ruƙayya ta zuba mata, kuma duk wannan abin da take yi Mommy ba ta taɓa tanka mata ba. Da ta lura da hakan ba zai kawo fitin ba, sai ta tsiri duk ranar girkinta za ta kira Daddy ta ce masa ba ta da lafiya, ko kuma ta ƙirƙiro wani abin da ba za ta yi girki ba. Idan ya ce zai taho mata da abinci sai ta ce masa ya kira Ruƙayya ya saka ta girka mata, tun Ruƙayya tana yin kara har haƙurinta ya fara ƙarewa. Ana cikin haka watarana Shukura ta yi wa Daddy waya, ta ce za ta yi baƙi kuma a ƙaryarta ta ce masa ba ta jin daɗi. Ruƙayya tana tsaka da typing ɗin assignment a laptop ɗinta, Daddy ya kira ta ya ce ya ta je ta karɓi ATM ɗin Shukura za ta yo cefane ta mata girkin baƙi. A ranar cike da ƙosawa ta ce. "Yanzu Daddy saboda Allah matar nan kullum lafiyarta ƙalau sai ta dinga ce maka ba ta lafiya, gaskiya Daddy ni na gaji." Daga can ɓangaren Daddy ya ce. "Mamana kina son na saɓa miki ko? Idan mahaifiyarki ce ta saka ki za ki faɗi haka? Daga yau idan na sake jin ta saka ki abu kin yi mata musu wallahi ranki zai ɓaci." Tana jin Daddy yana mata faɗa ta fara hawaye, ba don ta so ba ta je ta karɓa cike da raini Shukura ta faɗa mata duk abin da za a saya. Ana cikin wannan yanayin Shukura ta fara laulayi, sai ta fara tsiro musu da tsirfa kala-kala. Watana rana Daddy yana dawowa da yake a ɗakinta yake, sai kawai ta fashe da kuka. A rikice ya riƙo ta ya ce. "Me aka yi miki Shukura?" Shukura ta share hawayen idonta ta ce, "Waɗancan kajin da Hajiya ta zuba wallahi cutata suke yi, kullum sai na yi amai ya fi sau biyar saboda warin kashinsu har nan yake zuwa. Kuma idan ina aman ji nake kamar ɗan cikina zai zube, gaskiya ni dai ka saka ta fita da su wallahi." Hankalin Daddy ne ya tashi da jin furucinta, sai kuma ya yi shiru yana nazari saboda Mommyn Mami ta kusa shekara goma tana sana'ar kiwon kaji, kusan duk shekara sai ta zuba na sallah ƙarama, sallah babba da na maulidi. Kwantar da kai Daddy ya yi ya ce. "Ai na ga a bayan gida suke Shukura, kuma duka kajin yanzu ko wata ɗaya ba su yi ba. Ga shi kin ga da yawa ta zuba su, a ƙalla za su kai guda ɗari ko fi ma. Zan sayo miki turarurruka..." "Ka san dai ba na son ƙamshin turare tun da na samu ciki, wallahi ni dai idan ba za ta fita da su ba sai dai na bar maka gidanka ka sake ni. Dama ai ka fi sonta da ni, tun da ita ce uwar 'ya'yanka. Wa ya sani ma ko dama cikin jikin nawa ne ba ka so." A rikice Daddy ya ce. "Ba zan iya rabuwa da ke ba Shukura, bari na je na same ta." Daddy ya furta yana fita da sauri, Shukura ta faɗa kan gado tana sakin dariyar ƙeta. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. *ADVERT* Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍 ‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah! MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani! Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu: Gyaran gashi da kitson zamani Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai Kayan gyaran fata na gaske Lalle mai kyau da salo na zamani Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi Shirin amare da na musamman Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya. Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau. Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna. Tambaya/Booking: WhatsApp: 08062991549 Kira: 09016108092 / 08064532391 Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge. Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge SHAFI NA SHIDA A lokacin da Alhaji ya shiga ɗakin Mommy tana zaune tana waya, gani ya yi ta yi rubutu a cikin littafin da take lissafi da shi. "Eh rannan an kawo mini buhun dusa ashirin, wancan lissafin ai mun gama da shi. So nake a ƙaro mini buhu biyar, yanzu nawa zan ciko kuma?" Amsa aka ba ta daga can ɓangaren sannan ta ce. "To shi kenan, zan turo da kuɗin." Mommy ta ƙarasa maganar ta kashe wayar, jikin Alhaji ne ya yi sanyi. Duk sai ya ji fargaba ta cika shi, Hajiya tana ɗagowa ta sakar masa murmushi ta ce. "Daddyn Mami ka shigo ina waya, wallahi lissafi muke da Halliru mai kaji. Ina tunanin ma zan ƙaro guda ashirin fa, saboda Ɗan Fulani suya sport ya ce yana kamun guda tamanin." Murmushin yaƙe ya yi ya ce, "Eh haka ne, dama zuwa na yi mu yi wata magana a kansu." Amsa masa ta yi Alhaji ya zauna ya yi shiru, kallonsa ta yi ta ce. "Ina jinka Alhaji." Shiru ya sake yi gabansa yana faɗuwa ya ce, "To dama... game da kiwon kajin nan ne... to kin san Shukura ciki gare ta, shi ne..." "Shi ne me?" Mommy ta katse shi da sauri, saboda ta fahimci akwai abin da yake tafe da shi. Abba ya ce. "Wai warinsu yana damunta, har tana jin kamar za ta yi ɓari idan tana amai." Wani kallo Mommy ta yi masa, wanda hakan ne ya sa shi yin shiru da bakinsa. A ƙufule ta ce. "To yanzu me ta aiko ka a yi?" "Nake ganin tun da sun kwana biyu, me zai hana ki fitar da su ai za a samu masu saye. Ko ni ina da mutanen da za su saya, saboda kin san me laulayi. Idan ya so bayan ta haihu..." "Alhaji!" Hajiya ta kira shi sunansa cikin ɓacin rai, a sanyaye ya ɗago ya ce. "Ina jin ki." Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun da nake da kai, ba na ja'inja a kan maganar da ka faɗa. Amma ka sani a wannan karon ba zan amince da maganarka ba. Ka sani na kai shekara goma ina sana'ar kiwon kaji, tun ina kiwo da kaji biyar har Allah ya sa na ci gaba. Amma yanzu rana tsaka ka zo ka ce wai matarka ba ta son warin ka ji, kajin da suke can bayan gida sune warinsu har..." "Kina nufin ban isa da gidana ba kenan? Ko kina nufin kin fi ni iko da gidana?" Alhaji ya katse ta. Girgiza kai ta yi ta ce. "Ba haka nake nufi ba, amma wallahi a wannan karon sai dai ka yi haƙuri." Cikin zafin rai Alhaji ya ce. "To na dakatar da kiwon na ki ma gabaɗaya, saboda kawai na ce ki bari har zuwa lokacin da za ta haihu shi ne za ki faɗa mini magana." Baki sake Mommy take kallon Alhaji, ya miƙe ya nufi hanyar fita sannan ya waigo ya ce. "Zuwa nan da gobe akwai mutanen da za su yi miki maganar kajin, idan kuma ba haka ba ni da kaina zan sa a fitar da su." Har ya saka ƙafa zai fita Hajiya ta bi bayansa da sauri ta ce. "Ina mai tabbatar maka idan ka fitar mini da kaji wallahi-wallahi sai dai ka zauna da Shukura a gidah nan ba ni ba." Cak! Daddy ya tsaya, rai a ɓace ya waigo ya ce. "Wato kaji sun fi maganata kenan? Me kike nufi?" "Ina nufin zan bar gidanka?" Ita ma ta ba shi amsa kai tsaye. "Saboda kina baƙinciki da abin da za ta haifa? Yanzu dama akwai ranar da za ki ƙi jinina Karima? Saboda kawai na ce ki yi haƙuri zuwa wani lokaci za ki faɗi haka? Wato kin fi son ta yi ɓarin cikin kenan?" Ahaji Ya furta, Mommy da ranta ya gama ɓaci ta ce. "Idan duniya Shukura za ta haifa maka wallahi ba na baƙinciki ko ƙyashi, saboda na san na wuce ta har abada ni da 'ya'yana ne a gaba. Amma wallahi ba zan ɗauki kowanne irin cin kashi da yarinyar nan za ta yi mini ba." Kamar Alhaji zai yi magana sai kuma ya fice daga cikin ɗakin zuciyarsa tana suya. Can ɗakin Shukura ya shiga, tana ganinsa ta tashi zaune ta ce. "Ya ake ciki ne?" Dafe kansa ya yi ya ce, "Wallahi ta ƙi amincewa, ni na rasa yaushe Hajiya ta fara musu da ni." Shukura tana jin haka ta fashe da kuka, cikin tashin hankali ya riƙo ta ya ce. "Don Allah kada ki ɗaga hankalinki, wannan ba abin damuwa ba ne. Wallahi na yi bakin ƙoƙari don ta amince amma fir ta ƙi amincewa. Har tana ce mini za ta bar gidan nan idan aka fitar mata da kaji." Da sauri Shukura ta ɗago ta ce. "To sai me? Ba sai ka sake ta ba tun da ba za ta bi umarninka ba. Daɗin abin ai ba ita kaɗai ce matarka ba." Da wani irin sauri Alhaji ya fisge jikinsa daga jikin na Shukura, har sai da ta tsora ta. Rai a ɓace ya nuna ta ya ce. "Ko a mafarki kada ki sake tunanin zan iya rabuwa da Hajiya Karima, wannan matar da kike gani ita ce komai nawa. Kuma ban auro ki saboda na daina sonta ba, ina son matata domin ita ce rufin asirina. Duk wani mataki da kika ga na kai, wallahi ta silarta ce." Alhaji ya gama faɗa ya fita daga ɗakin a zuciye. GIDAN HAFIZ Bayan Hafiz ya watsa ruwa, zama ya yi daga shi sai kayan shan iska.A gefen Amina ya zauna, ya fara bin ta da wani irin kallo. Murmushi ta sakar masa, ya shafo fuskarta ya ce. "Na yi kewarki Meena." Cikin zolaya ta ce, "Ba wani nan ni ban ga alama ba." Matse ta yi a jikinsa tsam, ta saki 'yar ƙara kaɗan lokaci ɗaya suka saki dariya. Janye jikinta ta yi ta ce. "Akwai tea akwai drink wanne za ka fara sha?" Lumshe ido Hafiz ya yi ya ce. "Da ke zan fara mana." A ɗan shagwaɓe Amina ta ce. "Habibi ka fiye wasa fa." Sauka ya yi ƙasa, Amina ta zuba masa ruwan shayi a kofi, ta buɗe fulas za ta zuba masa abinci, daga bakin ƙofa suka ji Bilkisu ta zuro kwano cike da abinci ta ce. "Idan har kin yi haka don ki kashe ni ko ki kashe 'ya'yana, In Shaa Allahu sai dai ki gani a kanki. Saboda kin ɗebi naki abincin da na Abban Sayyid shi ne mu za ki hala ka mu, ai shi kenan Allah Yana kallo." Daga haka Bilkisu ta bar wurin. Kallon juna Hafiz da Amina suka yi, a sanyaye ta miƙa hannu ta ɗauko kwanon tana kallonsa, sai dai ko kaɗan ba ta ga komai ba. Abu ɗaya ta ji shi ne wari-warin fetir, Hafiz ya ɗauki abincin ya shinshina ya ce. "Me kuma ya kawo warin fetir a abinci?" A sanyaye Amina ta ce. "Wallahi ban san yadda aka yi ba. Lafiya ƙalau na yi girki na gama." Ajiye kwanon ta yi, ta fara zubawa Hafiz shi ma. Yana matso da plate ɗin gabansa ya ji warin fetir ya doki hancinsa, da sauri ya ɗago ya ce. "Amina wai me yake faruwa ne? Wannan wanne irin wulaƙanci ne za ki saka mana fetir a cikin abinci? Ina ce galan ɗin fetir daban na mai ma daban?" Idanun Amina suka ciko da ƙwalla, ta saka hannu ta share hawaye murya tana rawa ta ce. "Wallahi ban san komai ba, lafiya ƙalau na gama girki." "Ƙafa gare shi man ko hannu da zai zuba kansa? Shi kenan sai ki san yadda za ki yi da shi." Hafiz ya furta cikin fushi sannan ya zura doguwar rigarsa ya fice. Bilkisu da ke ɗaki murmushin ƙeta ta saki, ta ɗauko waya ta kira shi tana ji ya ɗauka ta ce. "Abban Sayyid yanzu ya zan yi da yara? Ga shi suna kukan yunwa." "Ki dafa musu taliya mana." Hafiz ya faɗa a ɗan faɗace. Kwantar da murya Bilkisu ta yi ta ce, "Ai ina tsoron ko man ne yake da fetir kada na sake saka musu a koma 'yar gidan jiya." Shiru Hafiz ya yi sannan ya ce. "Ki fara dubawa kafin ki zuba, idan kin dafa kuma ki zuba mini ni ma a cooler ina dawowa." Daɗi ne ya cika Bilkisu, ta amsa masa sannan ta kashe wayar. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA BAKWAI AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* *** Bilkisu drower kayanta ta buɗe, ta jima a tsaye tana nazarin waɗanda za ta ɗauka. Wata doguwar riga shara-shara ta ɗauko ta zura, ta shiga ɗakin yaran ta same su har sun fara bacci da yake an yi sallar Isha'i. Shimfiɗa ta yi musu ta ɗauko net ta saka musu, ta koma ɗaki sannan ta ɗauki ragowar taliyar da suka ci ita da yaran wacce ta zuba a cooler ta ajiye. Motsin Amina ta ji, don haka ta yi zaraf ta fito ta ɗauki buta ta yi kamar banɗaki za ta shiga. Amina ta gani ta fito da abincin ta saka a kicin, murmushin ƙeta Bilkisu ta yi ta shiga banɗaki bayan wani lokaci ta fito har za ta shiga ɗaki ta ja tsaki ta ce. "Aikin banza, haka kawai a jaza wa mutum ɗora girkin dare. Ai shi ma Abban Sayyid ɗin maganinsa kenan, kana tare da matarka cikin rufin asiri ka ci ba ka ci ba babu wanda ya sani. Amma haka kawai rana tsaka a ɗauko maka baƙar ƙaddara ta addabe ka, tun da nake a gidan nan 'ya'yana ba su taɓa kwanciya ba su ci abinci ba sai yanzu."Ta gama faɗar haka ta faɗa ɗaki. Amina da ke durƙushe tana juye abinci a tukunya ta share hawayen idonta, saboda ta yi tunanin duniya ba ta tuna a lokacin da ta zuba fetir a madadin mai a abinci ba. Kuma ko da ta gama girki ba ta ji warin komai ba, a sanyaye cikin damuwa ta koma ɗaki ta zauna. Waya ta ɗauka ta kira layin Hafiz ta ji bai ɗauka ba, abin duniya duk ya dame ta don bai taɓa yin fushi da ita irin haka ba. Bilkisu tana daga ɗaki wani tunani ne ya faɗo mata, da sauri ta ɗauki waya ta je bakin ƙofa yadda Amina za ta ji ta ce. "Hello Abban Sayyid, na ce ka haɗo mini da tsiren jiya da ka sayo mini. Amma dai yau kada a cika albasa, sai kuma su Sayyada yogot ɗin nan za ka taho musu da shi." Sai Bilkisu ta yi shiru kamar ana ba ta amsa sannan ta sake cewa. "A'a ba sai ka sayo mini kifi ba, kai dai ka sayo wanda za ka ci taliyar da shi." Ta sake yin shiru sai daga ƙarshe ta ce. "A'a ai abin da Amina ta yi maka bai kai ka ce za ka ƙauracewa kwanan ɗakinta ba. Ba a yi haka ba, gaskiya kada kasa ta ƙulla ce ni. Sai dai ka shigo kawai." Bilkisu ta lallaɓa ta koma kan kujera tana ƙunshe dariyar ƙeta, saboda ta san babu tantama Hafiz ba zai shigo ba sai da kifi. Ɗabi'arsa ce indai ta yi shinkafa ko taliya fara da mai to ba ya taɓa ci sai ya sayo kifi ya ci da shi, ita da yara kuma sai ya sayo musu balangu ko tsire. Amina tana daga ɗaki wani irin takaici ya lulluɓe ta, musamman da ta ji wai Hafiz yana faɗa wa Bilkis zai ƙauracewa kwanan ɗakinta. Kiransa ta gani, saboda haushi kawar da kai gefe ta yi ba ta ɗauka ba. Miƙewa ta yi ta shiga uwar ɗaki ta cire kwalliyar atamfar da ta yi, ta ɗauki wasu riga da wando marasa nauyi na bacci ta saka, sannan ta fita ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da sallah. Tana nan zaune ta ji sallamar Hafiz, mamaki bai gama kashe ta ba sai da ta ga Hafiz ya nufi ɗakin Bilkisu. Bai wani jima ba, ta ga ya ɗawo ɗakinta ya zauna, sai dai har lokacin fuskarsa a haɗe take. Kifin da ta ga ya fito da shi ya sake tabbatar mata da wayar da ta ji Bilkisu tana yi, Hafiz bai kalli ɓangaren da take ba ya ce. "Idan za ki ci ki sauko." Haushi ya kama ta da jin abin da ya faɗa, zuciya ce ta ciwo ta ta ce. "Na ƙoshi." Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta, bai tanka mata ba ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama ya tura mata ledar wani ƙunshin kifi gabanta ya ce. "Ga shi nan ki tashi ki ci." "Na ƙoshi ka cinye." Amina ta faɗa a karo na biyu, ransa ne ya ɓaci don ya san ba ta ci abinci ba. Cikin faɗa ya ce. "Wai saboda na yi miki faɗa shi ne za ki hau ɓata rai? Wani sabon hali za ki tsiro mini Amina? Kin san asarar yawan abincin da kika yi mini?" A ɗan zafafe ita ma ta ce. "To yanzu me nace maka? Kawai don na ce na ƙoshi sai ya zama abin faɗa? Idan ba da son ranka ka dawo za ka kwana a nan ba, ba sai ka koma can." "Me kike nufi Amina?" Ya jefa mata tambaya rai a ɓace. Shiru Amina ta yi, cikin hawaye ta miƙe ta shiga ɗaki tana kuka. Kukan da Amina ta yi shi ya sake harzuƙa Hafiz, don gani ya yi bai ga abin fushi da kuka ba saboda kawai ya nuna mata kuskurenta. Hafiz yana gama cin abinci kallo ya kunna, don ba ya son ya sabarwa kansa da zaman majalisa. Yana nan zaune har ya ji bacci don haka ya kashe ya shiga ɗaki, a lokacin da ya shiga Amina ta yi bacci. Rage kayan jikinsa ya yi sannan ya haye gado ya kwanta. Duk abin da ya faru tsakanin Amina da Hafiz, Bilkisu tana laɓe tana jin su. Daɗi ne ya cika ta, cikin farinciki ta koma ɗaki ta buɗe ledar kifin da Hafiz ya ajiya mata. Sai da ta cinye shi tas, sannan ta ɗauki ruwa ta sha ta haye gado ta kwanta hankali kwance. WASHEGARI Washegari koda Amina ta tashi yanayinta babu yabo babi fallasa, haka shi ma daga wurin Hafiz. Sai da ta zo yin wanke-wanke ta juye shinkafar a leda, saboda ko akuyoyi ba za su iya ci ba. Bilkisu ce ta sharo ɗakinta a lokacin tuni Hafiz ya jima da fita, da gayya ta sharo wata ƙatuwar takardar tsire wacce take sharkaf da mai, ƙuli da albasa. A yatsine ta sharo takardar da ta yi fakaka a saman makwashin shara ta ce. "Shi ma Abban Sayyada na faɗa masa ya cewa mai tsiren nan ya rage zabga mana albasa, amma kullum sai ya manta." Ta gefen ido Bilkisu ta kalli Amina da ke wanke-wanke, sai da ta je wucewa ta gabanta sannan ta saki takardar ta faɗi ƙasa da gayya don ta gani. Tsugunnawa Bilkisu ta yi ta share ta saka a shara, sannan ta wuce ɗaki tana murmushin mugunta. Wunin ranar haka Amina ta yi shi cikin damuwa, zuciya ta raya mata munafurcin da Hafiz zai tsiro mata. Har take ji a ranta da ya san ba zai yi musu adalci ba, da ba ta aure shi ba. A yammacin ranar sai da ta yi wanka sannan ta ɗora girki, bayan ta gama ta ɗebi nata ita da Hafiz sannan ta ba wa Bilkisu da yaranta. Kuma a wannan ranar lafiya ƙalau suka ci abinci, har Hafiz yana janta da hira saboda girkin da ta yi ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Hakan ne ya sanyaya zuciyar Amina har ta sauko daga fushin da take yi, ta so ta yi masa magana a kan rashin adalcin da ya fara yi amma sai ta ƙyale shi don kada ya ga kamar ta cika ƙorafi. Sannu a hankali rayuwar gidan Hafiz ta cigaba da tafiya, da daɗi babu daɗi haka suke rayuwa. Saboda kusan kullum da abin da Bilkisu take tsiro da shi, musamman idan Hafiz yana ɗakin Amina. Sautari idan yana ɗakin Amina sai dare ya yi za ta buga masa ƙofa ta ce ɗaya daga cikin yaran babu lafiya, ko kuma ta ce ya fito ya duba mata ɗakinta ta ji motsin wani abin. Tun Hafiz bai fahimta ba, yana biye mata. Har ya fahimci kamar da makirci a cikin lamarinta, saboda idan yana ɗakinta lafiya ƙalau suke kwanciya su yi bacci. Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri idan Hafiz yana ɗakinta sai ta fice ta koma cikin yaran ta kwanta, a ranar farko da ta yi da ya tambaye ta sai ta ce ita ta fi jin daɗin kwanciya a cikinsu. Da ya nemi kasancewa da ita nan ma sai ta ce ba ta buƙata, daga haka sai ta koma idan ya dawo ɗakinta sai dai ta zauna ta yi ta rusa kuka ko ta ce ya sake ta. Hakan ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ya yi ba, da ya tambaye ta sai ta ce masa idan yana ɗakinta ji take kamar ta kashe shi. Kuma sai jikinta ya ɗauki zafi kamar ana dafa namanta ko ana tsira mata allura. Wannan lamarin ne ya ɗaga hankalin Hafiz, ya shiga nema mata maganin aljanu a tsammaninsa ko su suka fara shafarta. Watarana da safe Hafiz yana shan shayi, ta fara shara, da gayya Bilkisu ta sharo ƙarƙashin kujera sai ga wata ƙatuwar laya ta fito. Da mamaki ta ɗauki layar ta ce. "Abban Sayyid kai ne ka ajiye ta." Yamutsa fuska ya yi ya ce "Ni kuwa me zai haɗa ni da laya Bilkisu? Miƙo mini na gani." Ƙin ɗauka ta yi ta janye gannu gefe ta ce. "Cab wallahi ba zan taɓa ba, haka kawai ban san ta mece ce ba zan taɓa ina zaune ƙalau." Miƙewa ya yi ya ƙarasa wurin ya yi bismillah ya ɗauka. Ya shiga warwarewa yana buɗewa sai ga wani busasshen ɗanyan nama, da ƙananan allurai a ciki. Wata takarda ya gani ya buɗe ta, a ciki ya ga an rubuta sunansa da na Bilkisu na farraƙu. Daga ƙasa kuma an saka sunansa da na Amina an yi rubutun mallaka." A firgice ya ɗago yana bin Bilkisu da kallon tausayi, sai a lokacin ya fahimci irin abin da ta ce masa tana ji a cikin jikinta. Kamar Bilkisu ba ta san da komai ba, ta matsa kusa da shi ta ce. "Me aka rubuta a ciki, ba ni mu gani." Naɗe takardar ya yi, don ba ya son ta gani ya cusa a aljihu ya ce. "Ƙarasa shararki babu damuwa." Haɗe fuska Bilkisu ta yi ta ce. "Kamar ya babu damuwa Abban Sayyid? Ya za a yi a ga laya a ɗakina kuma a ce ba zan gani ba, salon haka kawai a ce asiri na yi tun da dama yanzu ni ce mai lefi." Rasa abin da zai faɗa mata zai yi, sai kawai ya fice daga ɗakin ya shiga ɗakin Amina. A lokacin da ya shiga tana kwance, saboda a kwana biyun gabaɗaya ba ta jin daɗin jikinta. Kullum cikin tashin zuciya da kasala take, tana ganinsa ta tashi zaune a hankali. Cikin zafin rai Hafiz ya miƙa mata ya ce. "Mene ne wannan? Me kika aikata haka Amina?" Ita warin busasshen naman ma tayar mata da zuciya ya yi, ta ɗan yamutsa fuska ta ce. "Kamar ya ya? Mene ne wannan kuma" Takaici ne ya kama shi, rai a matuƙar ɓace ya shaƙo wuyanta yana jin kamar ya zabga mata mari ya ce. "Ina tambayarki mene ne wannan kina tambayata? Baƙar munafuka algunguma, ashe dama haka kike ban sani ba?" Hankali Amina ba ƙaramin tashi ya yi ba, duk sai ta birkice jikinta ya fara rawa saboda Hafiz bai taɓa birkice mata irin haka ba. GIDAN ALHAJI UMAR Alhaji yana fita Shukura ta yi shiru, don ba ƙaramin mamaki ya ba ta ba. Bata taɓa tsammanin har kawo wannan shekarun yana son Hajiya Karima haka ba, ta shi ta yi ta buɗe drowerta ta kwaso kayanta da duk wani abu da za ta buƙata ta saka a akwati. Tana shirin saka mayafi ya dawo ɗakin. Da mamaki yake bin ta da kallo, har lokacin fuska babu walwala ya ce. "Ina za ki?" Kuka Shukara ta saka, ta ce. "Wurin mahaifiyata zan tafi, gara na je can tun kai da matarka ba ku kashe ni ba. Idan na haife maka ɗanka sai ka je ka ɗauka ka kawo mata." Hankalin Alhaji ne ya tashi, cikin sauri ya riƙo hannunta ya ce. "Haba Sjukura, kawai saboda wannan maganar za ki yi fushi ki tafi gida? Tun da haka ne to zan kai ki ɗaya daga cikin gidajena na bayan gidan nan ki zauna. Haka ya yi miki?" Girgiza kai Shukura ta yi ta ce. "Salon idan ba ka gidana wani ya haura mini kafin ka zo duk abin da za a yi an gama ko? Wallahi ba zan iya zama a wani gidan ba. Ni kawai ka bar ni na tafi, idan ta fitar da kajin na dawo." Duk yadda Daddy ya so Shukura kar ta tafi fir ta ƙi amincewa, don haka ya ce zai kai ta ta yi kwana biyu idan ta ji daɗin jikinta sai ya dawo da ita. Hajiya Karima tana gani Shukura ta shirya ta fita, aka ɗauki ƙatuwar akwatinta aka fita da ita. Sai daga baya Alhaji yake ce mata ta je gida ta kwana biyu saboda ba ta jin daɗin jikinta. Bayan da Daddy ya tafi, Shukura tana shiga gida ta wassafa wa mahaifiyarta abin da ya faru. Bayan ta gama sauraronta ta ce. "Shukura abin da na fahimta ko za ki yi kissa fa dole sai mun haɗa da neman taimako. Don gaskiya na lura ba za mu cimma manufarmu ba, har sai mun kawar da hankalin mutumin nan. Saboda na lura ba ƙaramin so da shakkar tsohuwar guzumar nan yake yi ba, kin ga kuwa zama bai kama ni ba. Yadda ubanki ya mutu ya bar ni a talauci, na sha wahalar kula da ku tun kuna ƙanana ke da ƙannenki. Dole yanzu mu tara dukiya mu huta, tun da lokacin hutun ne ya zo." Shukura ta yi zaraf ta ce. "Ai Inna shi ya sa na kafe kai da fata na ce sai na zo gida, wallahi na tsani matar nan da 'ya'yanta. Komai za ki ji ya ce Hajiya, komai Mamana yadda kika san na shaƙe shigiyar yarinyar nan haka nake ji." Taɓe baki Innar Shukura ta yi ta ce. "Wannan ƙaramar alhaki ce, ki bari mu gama da ubanta na ta mai sauƙi ne." Ajiyar zuciya Shukura ta sauke ta ce. "Ai ita mun ma kusa rabuwa tun da aurenta bai fi wata guda ba yanzu, don ma saurayin ne ya ce a ƙara masa sati biyu saboda uzurin gabansa. Yanzu ya za a yi Inna?" Miƙa hannu Innarta ta yi ta ce. "Kawo kuɗi, ni kuma yanzu na bazama sha yanzu magani yanzu." Jaka Shukura ta zuge ta ɗebo kuɗi masu kauri ta miƙa mata. Nan take Innarta ta ɗauki mayafi ta fice ba ita ta dawo ba sai dare, don su Shukura har sun yi bacci suka ji motsinta. Sai da safe Inna ta fara yi wa Shukura bayani. "Wannan baƙar ledar da kika gani, a yadda ya ba ni a haka ya ce mu binne ta. Mai binnewar yana yi yana ambatar sunan Alhaji Umar, sai kuma wannan ruwan rubutu ne da za ki sha ki yi wanka da shi." Murmushi Shukura take yi tana gyaɗa kai, Inna ta sake ɗauko wata ledar ta ce. "Wannan kuma, sai a cikin gidansa za ki binne shi. Ki tabbatar wani bai gani ba, sai wannan ƙarshen zance sunansa." Inna ta ƙarasa maganar tana ɗauko wata ƙaramar ƙwalba mai ɗauke da wani baƙin abu a ciki ta ce. "Amma fa duk waɗannan abubuwan ba za su yi tasiri ba, har sai kin yi amfani da wannan. Za ki matsa shi a jikinki, ki tabbatar Alhaji ya yi amfani da ke yana jikinki. Idan kika yi shi sai ki yi sauran, daga nan magana ta ƙare." Murmushi Shukura ta yi ta ce. "Allah Ya bar mini ke Inna, gaskiya na ji daɗi. Ai wannan ma yau zan yi amfani da shi." Shukura ta furta tana adana su a jakarta. Hanif ƙanin Shukura ne ya zauna a gefenta ya ce. "Aunty tun kwanaki kika yi mini alƙwarin keke don Allah ki saya mini." Dafe kanta ta yi ta ce. "Na manta Hanif, amma zuwa an jima Siyama ta raka ka shagon Harisu sai ku tambayo mu ji nawa ne. Ita da Inna kuma dama alƙawarin waya na yi musu." Cikin jin daɗi Inna ta ce. "Ai haka nake ta son harkar arziki, yo ta ina zan zauna ganin kallon ruwa ƙwaɗo ya yi mini ƙafa." Lokaci ɗaya suka saka dariya. Sai da aka yi sallar magriba Shukura ta saka abin da Inna ta ba ta, da yake tun safe ta cewa Alhaji tana son ganinsa da daddare. Ana sallar Isha'i motarsa ta faka a ƙofar gidansu. Abaya ce a jikin Shukura, ta ciki kuma sai wasu figaggun kaya. Tana shiga ta zame abayar jikinta, kallonta ya yi yana murmushi ya ce. "Ki tausaya wa bawan Allah kada ki birki ta shi." Cikin shagwaɓa Shukura ta ce. "To ai idan na birkita shi sai na saita abina, tun da dama a lissafi yau kwana ne. Ni kuma kewarka na yi shi ya sa na kira ka dama, tun da babu mai kawar da damuwar sai kai." Ta ƙarasa maganar tana shiga jikinsa, cikin wani irin yanayi ya ce. To mu wuce gida kenan? Tun farko dama shi ya sa ban so kika taho ba. Kuma ni kaina a yau cike nake da kewarki, musamman da na tuna ba kya gidan." "Ka kama mana hotel don ni ba zan koma ba sai an kwana biyu." Ta ba shi amsa, da sauri Alhaji ya ce. "Hotel? Haba Shukura, da girmana da komai sai a ganmu ni da ke a hotel? Wasu fa mummunar fassara za su yi mana." Hawayen ƙarya ta fara yi ta ce. "To shi kenan, ai dama ba ka damu da ni ba. Tun da kana da wacce za ka nema a gida, ni kuma ko oho." Janyo ta ya yi jikinsa ya ce. "Ba haka ba ne Shukura, yanzu mu wuce kenan?" Gyaɗa masa kai ta yi, Alhaji ya saka wa motar key suka bar ƙofar gidan. Ummou Aslma Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA TAKWAS AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* *** Tafiya mai ɗan nisa suka yi daga unguwa uku, zuwa Arrayan hotel da ke titin Karkasara. Zuciyar Shukura ƙal saboda farinciki, a reception Daddy ya tsaya ya kama musu ɗaki. Suna shiga ɗakin Shukura ta faɗa jikinsa, cikin kissa ta ce. "Allah ka ga yadda nake ƙaunar wannan ruhin, Allah kada ka nuna mini ranar da zai juyawa soyayyata baya. Domin idan haka ta kasance, mutuwa zan yi." Riƙo hannunta ya yi suka zauna a bakin gado, ya zagayo da ita ta gabansa ya ce. "Ba na son na sake jin harshenki yana furta mini kalmar mutuwa, ina ƙaunarki Shukura ba zan iya jure rashinki ba." Murmushin gefen baki ta yi ta ce, "Amma ai ka fi ƙaunar matarka a kaina, kodayake duka-duka yaushe na shigo rayuwarka..." "Shiii! Idan ina tare da ke ba na ganin kowa a gabana, ke ce sarauniyata. Koda wasa, kada ki sa a ranki wannan fadar ba ta ki ba ce." Kiss ta sakar masa a baki, cikin salonsa ya shiga mayar mata da martani. Sai daga baya ya miƙe ya kira waya ya musu oder abinci, ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba aka kawo musu. Sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Alhaji ya ce ta raka shi su yi wanka. Har ta fara rage kayan jikinta, sai ta tuna da maganin da yake jikinta. Cike da kissa ta nuna masa ba sai sun yi ba, ta shiga ribatarsa har ta yi galaba a kansa. Tsoro ne ya kama Shukura ganin Alhaji ya ɓingire da bacci mai nauyi, girgiza shi ta fara yi a ɗan ruɗe amma ta ji shi shiru kamar gawa. A hargitse Shukura ta ɗauki wayarta ta shiga banɗaki, ƙasa ta yi da murya ta kira lambar Inna bayan ta ɗauka ta ce. "Inna da matsala fa." "Ba na fatanta kowacce iri ce, me yake faruwa?" Inna ta furta da sauri. A ƙagauce Shukura ta ce, "Inna bayan mun gama fa na ga jikinsa ya saki yana bacci, yanzu na yi masa tashin duniya ya ƙi."Murmushi Inna ta yi ta ce. "Kada wannan ya dame ki, ƙa'idar maganin ce haka. Yanzu ko zai farka zai kai ɗaya zuwa biyun dare, kada ki nuna masa damuwa ko tsoro idan ya nuna miki mamakin yin baccinsa." Sai a lokacin hankali Shukura ya kwanta don haka ta ce. "A nan za mu kwana kenan Inna?" "Ke ba na son sakarci, ba mijinki ba ne idan kun kwana sai me?" Wani tunani ne ya faɗo wa Shukura, cikin sauri ta ce. "Shi kenan sai goben Inna." Suna gama waya Shukura ta fice ta koma ta samu Alhaji yadda yake a kwance, zagayawa ta yi ta ɗauki wayoyinsa duka ta kashe. Sannan ta koma banɗaki ta gyara jikinta. Kamar yadda Inna ta faɗa Alhaji bai farka ba sai kusan ɗaya da rabi na dare, ita ma a lokacin Shukura ta yi bacci. Motsin da ta ji na Alhaji ne ya tashe ta, jikinsa ya ji duk ya yi masa tsami kamar an yi masa duka. Suna haɗa ido ya ji ƙaunar Shukura tana sake fisgarsa, banɗaki ya shiga bai jima ba ya fito ya sake janyo ta jikinsa. Sai bayan wani lokaci suka sake komawa banɗaki suka tsaftace jikinsu, sannan suka koma bacci. Washegari sai da gari ya yi haske suka tashi saboda makarar da suka yi, sai da suka yo sallah sannan suka sake kwanciya. Kunna wayarsa ya yi, yana kunnawa ko minti biyar bai yi ba ya ga kiran Hajiya Karima ya shigo. Guntun tsaki ya saki kamar zai ɗauka sai kuma ya saci kallon Shukura, wata irin shakkarta ya ji don haka ya sake kashe wayar gabaɗaya. Bacci suka koma, ba su suka tashi ba sai kusan sha biyu. Oder abinci ya fara yi musu, suna fitowa daga wanka aka kawo musu abinci. Cikin tsantsar soyayya Alhaji yake ciyar da su, yana jin kamar ya mayar da Shukura cikinsa. Don yadda yake jin soyayyarta tana fisgarsa ko lokacin farkon aurensu bai ji haka ba. Su Shukura ba su suka bar hotel ɗin ba sai kusan bayan la'asar, sai da suka biya ta Mubeen Store ya sayawa Inna kayan shayi da na abinci dangin, shinkafa, taliya makaroni, mai, maggi da sauransu. Sannan ya haɗa mata da kayan ƙwalam da maƙwalashe ya kai ta gida, da ƙyar Shukura ta bar shi ya tafi saboda yadda take narke masa tana zuba masa kissa. Daddy bai ƙarasa gida ba sai kusan sallar Magriba, a lokacin da ya shiga gidan sai ya samu Hajiya da yara duk sun yi jigum-jigum. Suna ganinsa daga ita har yaran suka ƙarasa wurinsa, cikin kuka Mami ta ce. "Daddy ina ka shiga tun jiya muna kiranka a kashe." A madadin ya amsa musu sai kawai ya janye Ruƙayya daga jikinsa, fuska a haɗe ya ce. "Ai gani na dawo yanzu." Sororo suka yi gabaɗaya suna bin sa da kallon mamaki, Hajiya Karima ta sakar musu murmushin yaƙe ta ce. "Ta yiwu akwai abin da yake damun Daddynku, bari na je na same shi a ɗaki." A sanyaye suka amsa mata, ta nufi ɗaki ita kanta tana jin zuciyarta babu daɗi. Lokacin da ta shiga ɗakin waya ta samu yana yi da Shukura, ya saki murmushi ya ce. "I miss too my baby." Yana sauke wayar Hajiya ta riƙo hannunsa ta ce, "Barka da zuwa ranka shi daɗe." "Barka!" Daddy ya amsa a daƙile, Mommy ta sake kawar da damuwar zuciyarta ta ce. "Daddyn yara tun jiya muke cikin tashin hankalin rashin ganinka, na kira waya ba adadi ba a ɗauka ba. Daga baya kuma da na kira na ji an yi rejecting, wallahi ka ganmu yau ko abincin kirki ba mu ci ba. Don har na kira Alhaji Gambo, muna shirin kai report." Cikin halin ko in kula Alhaji ya ce. "Kawai don ba a samu wayata ba sai a fara kira Alhaji Gambo ana jajena, a hotel na kwana tare da Shukura kuma ba na son hayaniya shi ya sa na kashe wayar." Wani abu ne ya daki zuciyar Hajiya Karima, amma sai ta danne ta ce. "To ai irin haka da sai ka faɗa mini, ka ga atleast mun san wurin da kake." A zafafe Alhaji ya waigo ya ce. "Don zan kwana da matata a wani wuri sai na faɗa miki? Haifata kika yi ko rainona kika yi?" A sanyaye Hajiya ta ce. "A'a." "To ki saurara mini haka, kin hana yarinya zama a gidan nan saboda baƙin kishinki, kenan babu dama na ɗauke ta mu keɓe a wani wurin idan ina da buƙatarta? Wai yaushe kika sauya ne Karima? Girmai-girmai da ke ki zauna kina kishi da 'yar cikinki? Me Shukura ta tsare miki ne a gidan nan? Wallahi idan ma baƙinciki kike yi da cikin jikinta, to In Shaa Allahu za ta haife shi lafiya." Alhaji Ya furta kalamansa rai a ɓace, kasa daurewa Hajiya ta yi ta ce. "Wai Alhaji me kake nufi ne? Saboda kawai na tambayi a inda ka kwana? To Allah Ya ba ka haƙuri, amma ka sani wallahi ko kaɗan ba na baƙinciki da abin da Shukura za ta haifa." "Idan ma kina yi sai dai mugun halinki ya faɗa kanki, sannan magana ta gaba da zan faɗa miki a kan wancan kiwon kajin da kike yi ne. Na gaji da ganin ana ɓa ta mini gida, kuma ba zan juri ɗaukar matar aurena ina yawon hotel da ita ba. Na ba ki daga yau zuwa gobe ki kwashe mini duk wani abu da ya danganci kiwon kaji, ko buhun dusa ɗaya ba na son sake gani." A hargitse Mommy ta dube shi ta ce. "Au ta nan kuma ka ɓullo, ai sai ya yanzu na gano inda maganarka ta dosa. Kaji ba yau na fara kiwo ba, kuma wata ba ta isa a saka na fitar da su ba. Idan ba haka ba sai na bar maka gidanka." Kamar Alhaji yana jira ya ce, "To ki tafi mana, idan haka kika zaɓa ai ƙofa a buɗe take ban riƙe ki ba." A razane Hajiya Karima ta zaro ido ta ce. "Ni kake cewa na tafi Alhaji?" "Ƙwarai kuwa, idan har haka kika zaɓa kina iya kwashe 'ya'yanki ku tafi." Yana gama maganar ya fita daga ɗakin. A sanyaye ta zauna a bakin gado, kawai sai ta fashe da kuka. Tana cikin wannan yanayin su Ruƙayya suka yi sallama cikin ɗakin hankali a tashe. Cikin damuwa Haidar ya ce. "Mommy wai lafiyar Daddy kuwa? Muna yi masa magana kin ga yadda ya hankaɗe Mami har ta faɗi ƙasa kuwa? Kuma bai tsaya ba ya fice daga gidan..." Maganarsa ce ta maƙale ganin mahaifiyarsu tana zubar da hawaye, da sauri suka ƙarasa cikin damuwa suka ce. "Mommy mai ya faru kike kuka? Ko Daddy ne?" Sai da Hajiya Karima ta share hawayenta sannan ta ce. "Daddynku yana buƙatar addu'arku Haidar, saboda jikina yana ba ni kamar ba ya cikin hayyacinsa. Yanzu haka kaji can ya ce a fita da su, ba ya buƙatar abin kiwo ɗaya a gidan nan." "A fita da su?" Suka tambaya kusan lokaci ɗaya, gyaɗa musu kai ta yi. Ruƙayya ta yi murmushin takaici ta ce. "Wallahi ba kowa ba ce sai annamimiyar yarinyar nan, hmmm amma a wannan karon ta yi ƙarya don uwarta. Wallahi ba za a fita da su ba." Waya Hajiya ta ɗauko ta ce, "Ku fita zan kira Alhaji Gambo." Damuwa lulluɓe a fuskarsu suka tashi suka fita, suna jin tsananin tsanar Shukura a ransu. Saboda tun da suka yi wayo, ba su taɓa ganin mahaifiyarsu tana kuka saboda ɓacin ran mahaifinsu ba. Alhaji Gambo aminin Daddy ne, garinsu ɗaya da shi. Kuma duk gwagwarmayar rayuwa kusan tare suka yi, kowa ya san sirrin kowa. Kuma duka su biyun suna ba wa junansu shawarwari, haka idan wata matsala ta iyali ce. Matar wannan tana iya kiran wannan ta yi masa ƙorafi domin a gyara. Hajiya Karima kiransa ta yi, bayan sun gaisa take sanar da shi duk abin da ya faru. Ko kaɗan bai ji daɗi ba, don dama tun da Alhaji ya ɗauko maganar auren Shukura, da ya bincika ya ji yanayin tarbiyyar gidansu Shukura sam auren bai kwanta masa ba. Don kafin a yi ya sha ba shi shawara, a kan ya haƙura da ita ya nemi wata. Haƙuri ya ba ta sosai, sannan ya ce ta bari zuwa dare zai zo gidan domin su tattauna gabaɗaya. Tun da suka gama Alhaji Gambo ya kira Daddy, ya ce masa zai shigo bayan sallar magriba. A yanayin muryar Daddy da ya ji sam kamar bai yi murna da zuwansa ba, ya yi mamaki matuƙa. Saboda koda a fushi yake bai cika nuna masa fushinsa ba. Bayan sallar Isha'i, Alhaji Gambo ne ya yi fakin a ƙofar gidan Daddy. Waya ya ciro ya kira shi ya sanar da shi, babu jimawa Daddy ya fita suka suka gaisa babu yabo babu fallasa sannan suka shiga. A falonsa na saukar baƙi suka zauna, Alhaji Gambo ya dube shi ya ce. "Wata magana ce fa tafe da ni, ɗazu Hajiya Karima ta kira ni. Amma kafin nan ka kira ta tukunna sai mu tatattauma gabaɗaya." Nan take Daddy ya haɗe fuska ya ce. "Dole sai ta zo? Duk abin da za mu faɗa mu yi mana." Shiru Alhaji Gambo ya yi, ya ɗan haɗe fuska ya ce. "Ka ga malam ka kira ta mu yi magana, ka san ni dai ba baƙon gidan nan ba ne. Idan ba za ka kira ta ba, zan leƙa na ce su Haidar su yi mata magana." Guntun tsaki Daddy ya yi ya fice, bayan wani lokaci sai ga shi sun dawo yana gaba Hajiya Karima tana biye da shi. Gaisawa suka fara yi, sannan Alhaji Gambo ya wassafa duk maganar da suka yi da ita, sannan ya ɗora da cewa. "A gaskiya ka ba ni mamaki Alhaji Umaru, yanzu kai ko wani ne ka ji zai yi wa iyalinsa haka ba za ka tsawatar masa ba?" "Dakata Gambo don Allah, wannan sabgar iyalina ce. Ban ce ka tsoma bakinka a ciki ba, wallahi sai ta fitar da kajin nan tun da Shukura ba ta son warinsu. Idan kuma rabuwarmu ta zaɓa, a yanzu sai na rubuta mata takardarta ta kama gabanta." Yana gama maganar ya wuce fuu har zai fita, sai ya sake waigowa ya ce. "Kuma daga yau babu kai babu sake shiga duk wata magana ta iyalina, kai ma idan har ka ce za ka bi wani ra'ayin ba na Shukura ba, a shirye nake da na datse duk wata alaƙa da ke tsakanina da kai." Daga haka ya saka kai ya fice. Daga Mommy har Alhaji Gambo jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, saboda ɓacin rai sai kawai ta fashe da kuka. GIDAN HAFIZ "Za ki buɗe baki ki yi mini magana, ko sai ranki ya ɓaci?" Hafiz ya buga wa Amina tsawa a zafafe, hawaye ta shiga yi baki yana rawa ta ce. "Wallahi... ban... san yadda aka yi ba, wallahi ban san komai game da wannan layar ba." Furzar da iska mai zafi Hafiz ya yi, zuciyarsa tana tafasa ya matsa kusa da ita kamar zai tsinka mata mari. Da sauri Amina ta ja da baya cikin matsanaacin tsoro, don ta gama saddaƙar da Hafiz hannu zai kai jikinta. Rai a ɓace ya nuna ta da yatsa ya ce. "Uwargidana, kuma uwar 'ya'ya ko hanyar gidan malamai ba ta sani ba, haka kawai ina zamana lafiya da matata za ki haukata mini ita. Shi ya sa kullum take yin abu kamar na mai shafar aljanu, ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni. Wallahi idan na sake ganin makamancin wannan shirmen sai ranki ya yi mugun ɓaci. Saboda mugun hali ki zo ki samu mace a ɗakinta kina ƙoƙarin illatata, ba zan juri ki zo ki hargitsa mini gida ba." Hafiz ya juya ya fita, kai tsaye kicin ya shiga ya ɗauko ashana ya fita da layar ya ƙona a waje. Duk abin da yake faruwa Bikisu tana daga ɗaki tana ji, zuciyarta fes don haka ta cigaba da harkokinta hankali kwance. Tun daga wannan ranar Bilkisu ta warware tas, ta daina duk wani makircin nesanta kanta da Hafiz. Wannan ya sake tabbatar wa da Hafiz zarginsa na Amina ce ta yi wa Bilkisu asiri, dalilin haka ya ƙara tsaurara tsattsamar alaƙa tsakaninsa da Amina. Suka koma irin zaman cin kunamar ƙadangare, don Amina wani haushin Hafiz take ji a kan abin da ya yi mata. Shi ma kuma haushinta yake ji, don haka ya koma kwanan falo. A kullum idan a ɗakinta yake zai ɗauko filo ya fito falo ya kwanta, saboda idan ya kwanta a kan gadon ma sai dai Amina ta juya masa baya. A wannan kwanakin Bilkisu sai nannan take da Hafiz kamar ta haɗiye shi, haka shi ma yake ba ta kulawa; saboda yadda ya ga ta saki jiki da shi saɓanin tun lokacin da ya auri Amina. Watarana Hafiz yana ɗakin Amina, har ya yi shirin zuwa kasuwa sai ya shiga ɗakin Bilkisu don ya yi mata sallama. Yana shiga bisa tsautsayi hannunta da manja ya kife masa a gaban riga, a kan dole ya shiga uwar ɗakinta ya cire kayan jikinsa ya ɗaura towel. Da yake Bilkisu ta ɗora ruwan wanka, sai ta ce bari ta juye masa ya sake yin wanka tun da duk jikinsa ya ɓaci. Sai da Bilkisu ta shiga uwar ɗaki ta ɗauro zani, sannan ta je ta juye masa ruwan a banɗaki. Hafiz ne ya shiga banɗaki cikin sauri, saboda ya yi rana bai fita da wuri ba. Bilkisu tana ganin haka ta yi zaraf ta fito tsakar gida, sai da ta je bakin ƙofar ɗakin Amina ta yi ƙasa da murya yadda Hafiz ba zai ji ba ta ce. "Ban da abin Abban Sayyid ka ce ba ka gajiya da ni saboda Allah, tun da dai ba kwanana ba ne ai sai ka bari sai ka dawo nan ɗin tun da ba guduwa zan yi ba. Ga shi haka kawai za ka saka ni jiƙa kaina ban shirya ba." Da ta tabbatar da Amina ta ji abin da ta faɗa, sai ta ce. "Koda yake bari na zo na taya ka, tun da shi ma sunna ne." Ta nufi ƙofar banɗakin tana gimtse dariyar mugunta, tana zuwa cikin sanɗa ta tsaya a ƙofar banɗakin. Saboda ta san ko kaɗan Hafiz ba zai bari ta shiga su yi wanka tare ba, tun da ba ranar girkinta ba ne. Tana jin motsin zai fito ta ce. "Idan ka gama Abban Sayyid ba ni bokitin ni ma zan yi wanka."Ajiye mata ya yi, sai ya wuce ya shiga ɗakin Amina ya sauya kaya ba tare da ya tanka mata ba. Tana ganin ya saka wasu kayan ya fita, ta shiga uwar ɗaki ta fashe da kuka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta share hawayenta, ta kwanta tana jin gabaɗaya zaman gidan ya ishe ta. Uwa-uba ga laulayin da take fama da shi, don a wannan lokacin ko abincin kirki ba ta ci. Bilkisu tana fitowa daga wanka ta shige ɗaki, sai da ta shirya tsaf sannan ta ɗauko wayarta ta kira Lami mai wanki. Tana ji an ɗauka ta yi ƙasa da murya ta ce. "Yawwa Lami na haɗa kayan wankin namu, ki aiko yaro ya zo ya ɗauka. Da nawa da na yara gabaɗaya set goma sha biyar ne, yawwa akwai kuma na Abban Sayyid za ki gansu daban. Su kuma sai ki ba wa Babansu Bala (Mijin Lami) ya wanke ya goge. Idan an gama sai a yi mini lissafi zan bayar da kuɗin." Amsa mata Lami ta yi sannan ta katse wayar, da sauri ta matsa bakin ƙofa. Sai ta latsa ainahin ringing ɗin wayarta ta ware volum, sai da ya yi na ɗan sakanni sannan ta kashe. Sai ta kai shi kunne a zuwan kiranta aka yi ta ce. "Hello Abban Sayyid, ka yi mantuwa ne?" Sai ta yi shiru kamar wacce ake yi wa magana ta sake cewa. "Kai Abban Sayyid yanzu bayan kuɗin makarantar yara da aka ƙara ga hidimar gida har da wanki? To shi kenan, bari na karɓo na wajen nata, Allah Ya ƙara buɗi Habibi." Sai ta yi ƙasa da murya kamar mai kukan gaske ta ce. "Haƙiƙa samun miji kamarka sai an tona Zauji, Allah Ya kula mini da kai." Daga haka sai Bilkisu ta ƙarasa ƙofar ɗakin Amina ta yi sallama, jin ta amsa sai ta ce. "Abban Sayyid ya ce ki haɗo kayansa na ɗakinki za a kai wanki." A sanyaye Amina ta amsa mata, sannan ta shiga ɗaki ta haɗo kayan wankin Hafiz ta kawo mata. Sai da ta karɓa ta ɗan yamutsa fuska ta ce. "Ni kam ko ba kya jin daɗi ne Auntyn yara? Na ga tun safe kina ɗaki." Murmushin yaƙe Amina ta yi ta ce. "Ba na jin daɗi ne shi ya sa." Bilkisu ta rausayar da kai alamun tausayi ta ce. "Ayya sannu, dama kin san fa sai an rabu ake jin daɗin jiki. Ni na yi mamaki ma, da Abban Sayyid yake fita ba tare da ya yi miki share-sharen ɗaki ba, don lokacin cikin Sayyid hatta moping sai ya yi mini yake fita." Wani zafi Amina ta ji a ranta, tana ayyana wato ita da yake ya daina sonta ko gyaran gado bai taɓa yi mata ba. Bilkisu ta saci kallon Amina a fakaice sannan ta ce. "Kodayake bari na dinga rage miki wasu ayyukan, ai ban san ba ki da lafiya ba." Tana faɗar haka ta fice, sannan ta ɗebo kayan wankinta ta fito da su tsakar gida ta ɗauki waya ta kara a kunne bayan wani lokaci ta ce. "Hello, Abban Sayyid." Shiru ta yi sai ta sake cewa. "Ashe Amina ba ta jin daɗi tun safe, na ce ko na karɓi kayanta a haɗa da namu a kai wankin? Tun da ka ga kayana da na su Sayyada ba su da yawa." A wannan karon ma shiru ta sake yi, sai bayan wani lokaci tace. "A'a don girman Allah ka yi haƙuri, ya za a yi ka ce ka rantse ba za a haɗa da nata ba. Don Allah kada ka yi haka ba za ta ji daɗi..." "Don Allah ki daina yi masa magiya Aunty, tun da bai yi niyya ba ai shi kenan. Wanki ai ba zai kashe ni ba." Amina ta furta cikin zafin zuciya, don a wannan karon ta gagara riƙe ɓacin ranta. Girgiza kai Bilkisu ta yi ta ce. "Haba ta ina za a yi haka, to ai kuwa nawa ma sai dai a bar shi gaskiya." Jim ta yi kamar mai sauraren abin da yake faɗa, sai ta ce. "To shi kenan, ka yi haƙuri zan bayar da su. Wai dama don kada ta ji babu daɗi ne ya sa na yi maganar, amma tun da maganar kayan na ta ya ɓata maka rai ka yi haƙuri." Bilkisu tana sauke wayar sai ga Habibu ɗan gidan Lami ya yi sallama, kayanta da na Hafiz ta haɗa ta ƙulle ta ɗaura masa a kansa. Amina tana shiga ɗaki, ta ɗauko hijabinta ta zura sannan ta rufe ƙofarta ta fice ko sallama ba ta yi wa Bilkisu ba. Tana jin zuciyarta na zafi, don yadda ta fita daga gidan ta ci alwashin ba za ta koma ba sai dai Hafiz ya kai mata takardar sakinta. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA TARA ALL NATURAL PRODUCT💃🏻 Tsumi Tsumin tighten Tsumin Sanyi Tsumin basir Tsumin 3in1 Kazar Amare yan mata. Kazar Amare zawarawa. Kazar Masu haihuwa. Kazar 3in1 Kazar uwargida ko amarya da suke son burge oga. Gumbar dabino. Gumbar kwakwa. Gumbar Madara. Garin dahuwar kaza. Garin dahuwar ciccibi. Garin dahuwar hanta. Garin dahuwar kwai. Garin dahuwar kifi. Garin hakin maye na sha da Madara ko nono. Ingantaccen tsumin maganin sanyi, wanda aka samo daga masunta masu kamun kifi,bayan maganin infection yana magance sanyin da aka sha a ruwa ko a tiles ko irin sanyin nan mai kumbura jikin mutum. Bugu da kari ana iya ba yara kanana masu fama da mura ko tari, haka akan dace idan yaro yana fitsarin kwance aka bashi in sha Allah yana dainawa. 09065730652 A tuntuɓi lambarmu. *** Bilkisu tana kwance a ɗaki ta ji fitar Amina, da sauri ta fito tsakar gida don ta sake tabbatar da zarginta. Ƙofarta ta gani a garƙame da kwaɗo, kuma ta san duk rashin daɗin zaman da suke yi da ita idan za ta fita sai ta yi mata sallama. Wannan ya sa ta sake tabbatar da zanginta na Amina yaji ta yi. Cikin tsananin farin ciki ta koma ɗaki ta haye kan gado, wayar Hafiz ta kira don ta bigi cikinsa tana jin ya ɗauka ta ce. "Yawwa na manta ban tamabaye ka ba, me za a dafa ne. Saboda na ga Auntyn yara ta yi bacci, kuma ka ga ba a tashe ta ba." Har cikin zuciyarsa ya ji daɗi, musamman da a kullum yake sake ganin sauƙin kan Bilkisu. Cike da farinciki ya ce. "Da ma kafin na fita na ga yanayin jikinta nata kamar ba ƙwari, ko doya da miya ma kika yi ta isa." Murmushi Bilkisu ta yi ta ce. "An gama ranka shi daɗe." Har ta kashe sai ta yi farat ta sake kira, yana ɗauka ta ce. "Na ce dama ɗazu na bayar da wankin kayanka da namu, ina jin zuwa gobe ma za kawo su." Ɗan jim Hafiz ya yi, kafin ya yi magana ta ce. "Dama bayan fitarka Yaya ya turo mini kuɗi, ka san ya sayar da gonarsa kwanaki." Sai a lokacin Hafiz ya ce. "Ma Shaa Allah, godiya nake Habibty." Lumshe ido ta yi, tana jin soyayyar Hafiz har cikin ranta. Sai da suka yi sallama a fili ta ce. "Haka kawai ina zaune ƙalau da mijina wata shegiya ta zo ta addabi rayuwata. 'Yan iska macizai da ba sa ramin kansu, don bala'i kowacce yarinya da ta yi kwantai sai dai ta ce mijin wata ne zaɓinta. In Shaa Allahu yadda kika fita kin fita kenan, ban da neman masifa da fitina ki je ki nemi naki mijin mana." Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin ƙwafa. AMINA Amina tana tafe a hanya tana hawaye, bakin titi ta ƙarasa ta tari adaidaita sahu ta wuce unguwarsu. Tuno halin mahaifinta da ta yi ya sa ta yi saurin daidaita fuskarta, don ta san idan har ya ji dalilin zuwanta gida sai ranta ya ɓaci. Don haka tana shiga gidan ta saki fuskarta kamar babu wani abu da yake damunta, sai bayan sun gama gaisawa mahaifiyarta ta ce. "Aminatu ke ce da ranar nan haka?" Gyaɗa kai Amina ta yi, ta ce. "Ai zuwa na yi na kwana biyu Umma, saboda ba na iya komai a gidan. Idan na warware sai na koma gida, don wallahi wani lokacin kamar zan faɗi saboda juwa." Shiru mahaifiyarta ta yi sai kuma ta ce. "Yanzu don ba ki da lafiya sai shi kuma Hafiz ɗin ya bar ki ki taho gida?" A ɗan duburburce Amina ta ce, "Na'am, eh shi ya ce na zo." Kallon tsaf mahaifiyarta ta yi mata ta fahimci tana cikin damuwa. Ganin irin kallon da take mata na tuhuma ya sa ta miƙe za ta fita, mahaifiyarta ta ce. "Amina me yake damunki?" Nan take idonta ya ciko da ƙwalla ta fara hawaye, sai da ta share hawayen ta ce. "Umma wai dama haka ake shan wahala? Wallahi ko ruwan shayi na sha ba ya zama." Ta faɗi haka, don a wannan lokacin ba ta son duk wani abu da zai sa a kira Hafiz gidansu har a yi musu sasanci. Ajiyar zuciya mahaifiyarta ta yi ta ce. "Ai dama tun da abu ya zo ga ma'iya sai Allah, marar kunya fita ki ba ni wuri." Amina ta yi murmushi, hira suka cigaba da yi da 'yan'uwanta. Duk sai ta ji damuwar da take ciki ta yaye, kuma wani abu da ya ba ta mamaki yadda ta zage ta ci abinci sosai saɓanin tana gida HAFIZ Sai bayan sallar Isha'i Hafiz ya dawo gida, bai yi mamakin rashin fitowar Amina ta tarbe shi ba. Saboda tun da suka yi faɗa ta daina zuwa taro shi idan ya shigo gidan. Kai tsaye ɗakin Amina ya ƙarasa yana zuwa ya yi turus, saboda ganin ƙwadon da ya yi. Bakin ƙofar Bilkisu ya ƙarasa, ta yi luf kamar wacce ta fara bacci. Sai da ya kira sunanta har sau uku sannan ta tashi tana murtsika ido, a yamutse ta ƙarasa bakin ƙofar ta ce. "Sannu da zuwa." "Yawwa sannu, ya yaran ya kike?" Hafiz ya tambaye ta, amsa masa ta yi ya sake cewa. "Ina Amina ta tafi? Na ga ƙofarta a rufe." Nan take ta sauya fuska cikin alamun mamaki ta ce, "Au wai dama ba ka san ta fita ba?" Ran Hafiz ya fara ɓaci, ganin haka ya sa Bilkis ta cigaba da cewa. "Ai ina jin ko azahar ba a yi ba ta fita, ni kuma dama ba ta yi mini sallama ba. Ka ga ba zan kawo ba ta fita babu izininka ba." Ƙwafa Hafiz ya yi ya ce. "Ya yi mata kyau." Daga haka sai ya wuce uwar ɗakinta, kaya ya sauya ya buƙaci da ta zubo masa abinci. Jikin Bilkisu har rawa yake ta fita cikin kwarkwasa ta haɗa masa kayan abinci ta dire a gabansa. Gani ta yi ya miƙe ya fita, ta yi jim tana nazari sai kuma ta taɓe baki. A can ƙofar gida wayar Amina Hafiz ya kira, har ta katse ba ta ɗauka ba. A hakan ya sake danne zuciyarsa ya sake kiranta, sai a lokacin ya ji ta ɗauka. "Da izinin wa kika fita daga gidana?" Hafiz ya wurga mata tambaya a fusace, cikin ɓacin rai Amina ta ce. "Da ka bi ni ta lallami ma, don ba zan dawo gidanka ba sai dai ka aiko mini takardata. Ka ga sai ka je can ka cigaba da rayuwa da 'yar gwal, tun da kai ba adalin namiji ba ne." A wannan karon zuciyar Hafiz har tafasa take yi, ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Haka kika zaɓa?" Cikin zafin zuciya da ganin Hafiz bai damu da tafiyarta gida ba ta ce. "Eh, ka kawo mini takardata ko na cigaba da samun farinciki a wurin iyayena. A wuni ɗaya da na yi a gidanmu, har na manta da duk wata cusgunawa da kake yi mini. Ka ga sai na yi rayuwa cikin salama da kwanciyar hankali." Hafiz bai tanka mata ba, ya saki ƙwafa haɗe da kashe wayar. Cikin gida ya shiga ya zauna a gaban a binci ya zura masa ido, Bilkisu ta lura da yanayin da yake ciki don haka ta ce. "Abban Sayyid ko wani abu ne yake damunka?" Girgiza mata kai ya yi, ya ɗauki cokali ɗaya na abinci ya saka a baki. Haka kawai ya ji abincin ya yi masa ɗaci, murya a dakushe ya ce. "Ɗauke na ƙoshi." Marairaice murya Bilkisu ta yi ta ce. "Abban Sayyid ko yanzu ban isa na ji damuwarka ba ne? Kyakkyawar fuskar da ke faranta mini zuciya ta alamta mini damuwa ta yi kwance male-male a samanta. Da za ka sanar da ni, wataƙila da sai na samu ƙwarin gwiwar faranta mata har ta manta wani kaso, daga cikin damuwar koda ba zan yaye maka duka ba." Shiru ta ga ya yi, alamar saƙon da take turawa ya fara ringajayar zuciyarsa. Ta matsa kusa fa shi har suna jin numfashin juna, saƙalo hannunsa ta yi cikin nata ta cigaba da cewa. "A da ban san kalar wannan fuskar a jikin surarka ba sadaukina, ba ka saba mini da fushinka ba. Don haka ne ma ganinka a cikin wannan yanayin ya fara azabtar da gangar jiki da ruhina. Don Allah koda za ka yi fushi, ka dinga tuna akwai hallitun da suke zagaye a ƙasan zuciyarka. Ka sani, ni na sani duk duniya idan ka cire su Inna. Nida Amina ne na biyu da ke ƙaunarka, haka kuma ni da ita ne muke durƙushe a ƙarƙashin inuwarka. Don Allah ka sassauta fushinka ko na ji daɗi a raina." Har cikin zuciyarsa yake jin soyayyar Bilikisu, saboda tana da baiwar iya tsara magana. Don haka ya ji kaso casa'in da damuwar da yake ciki ta tafi, ya janyo ta ya manna a ƙirjinsa ya ce. "Sautari idan na shiga wani yanayi, na kan ji ɗaci da tururi a cikin raina. Zuciyata ta kan dugunzuma, har wani lokacin na gagara sarrafa ta. Sai dai samunki a duniyata, yana gusar da dubban abubuwan da ke bazanar nakasta zuciyata. Ina matuƙar ƙaunarki Billyna, Allah Ya yi miki albarka." Cike da so Bilkisu ta sun baci gefen bakinsa ta ce. "Ka gama mini komai a duniya gwarzona." Ɗan sauya fuska ta yi cikin damuwa ta ce. "Amma ban sani ba ko ka samu layi Auntyn yara kuwa? Na kira ta bayan fitarka ba ta ɗauka ba." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Na kira ta, sai dai har yanzu ina mamaki sauyin halin Amina. A da zan iya bugar ƙirji a gaban duniya na yabi kyawun hali da ɗabi'arta, amma a yanzu ta fara ba ni tsoro. Ki ta ya ni da addu'a Allah Ya zaɓa mini abin da ya fi zama alheri." Wani sanyi ta ji a cikin ranta, ta lumshe ido cikin jimamin ƙarya ta ce. "Amin Ya Rabbi, ka san dama wani zubin sai zama ya yi zama ake gane halin mutum. To amma ina ta tafi?" "Gidansu ta tafi." Daga haka Hafiz ya miƙe ya nufi ɗakin yara. Haska su ya yi ɗaya bayan ɗaya, ya gansu suna bacci sannan ya koma ɗaki. Tun a wannan ranar Hafiz ya saka wa zuciyarsa ba zai je gidansu Amina don ya yi bikonta ba, tun da ba faɗa suka yi ba kuma ba wani laifi ya yi mata ba. Duk da yadda yake jin soyayyarta tana addabar zuciyarsa. Haka ita ma ta ci alwashin ba za ta dawo ba, duk da a kullum sai ta ji kewa da soyayyar mijinta. A wannan zaman da suke yi har suka shafe kwana goma a haka, ganin kwanaki suna tafiya ya sa mahaifiyar Amina ta matsa mata da maganar komawa. A ranar ne ta fito ta sanar da su dalilin zuwanta gida, daga mahaifinta har mahaifiyarta ransu ɓaci ya yi. Mahaifinta har ya kusa dukanta ya yi ummanta ta ce masa ya ƙyale ta, tun da ba ita kaɗai ba ce tana da juna biyu. A ranar Baba ya kira Hafiz ya ce yama son ganinsa da daddare, cikin girmamawa ya amsawa Baba. Hakan ne ya sa daga Kasuwa Hafiz ya wuce gidansu Amina. Cike da karramawa mahaifinta ya sa aka kai shi falon saukar baƙinsa, Amina ya sa aka kira masa tana shiga ta takure a gefe tana jifansa da harara. Baba ne ya fara jin ta bakin Hafiz, ya zayyane masa duk abin da ya sani. Sai dai bai faɗa masa ganin layar ɗakin Bilkisu ba, ita ma Amina cewa ya yi ta faɗi duk abin da yake yi mata. Sai kuwa ta zayyane duk maganganun da ta ji Bilkisu tana faɗa, da duk wasu makirce-makircenta. Baba yana gama jin haka ya saki murmushi, don ya fahimci koma. Hafiz ya dubi Baba ya ce. "Wallahi Baba ni ban san da duk waɗannan abubuwan da ta faɗa ba. Hasali ma a ranar da ta ce na kai wa su Bilkisu wanki, ita da kanta Bilkisun ta kira ni ta ce ta kai mana wanki maƙota za ta biya." "Hafiz na fahimci komai ba sai ka ɓata bakinka ba. Ke Amina shiga ki ɗebo kayanki." Baba Ya furta yana miƙewa, kamar za ta yi kuka ta ce. "Ni dai ba zan koma ba Baba..." "Kallon da Baba ya yi mata ne ya sa maganarta ta maƙale, don haka ta tura baki gaba tana hawaye ta shige cikin gida. Suna shiga Baba ya sanarwa da mahaifiyarta duk abin ya faru, sannan ya ɗora da cewa. "Amina Allah Ya haɗa ki da makirar kishiya ne, wacce ta fi ki wayo, kissa da makirci. Duk waɗannan abubuwaa da kika faɗa, ta yi ne domin ta tunzura ki. Tun wuri ki dawo cikin hankalinka, wallahi koda rana ɗaya ban taɓa jin Hafiz zai zalunce ki ba." Baba da Umma sun jima suna yi wa Amina nasiha, bayan Baba ya fita Umma ta sake nusar da ita yadda ake zama da kishiya. Daga ƙarshe ta ɗauki jakarta ta fito, ƙannenta suka yi mata rakiya har ƙofar gida. Cikin zumuɗi Hafiz ya ɗauki akwatinta ya saka a gaba, ta hau mashin suka wuce gida. Bilkisu tana gida ba ta san wainar da ake toyawa ba, don a ranar tun bayan isha'i ta yi wa yaran shimfiɗa suka kwanta. Ta sheƙa wanka cikin tsukakkun ƙananan kaya, wandon da ta saka da kaɗan ya sauka daga cinya. Sai rigar da ta saka mai yankakken hannu, ta yi haka ne don ta ja hankalin Hafiz saboda wani turaren humra da zumar mallaka da ta saya take son gwada amfaninsu. A lokacin da Hafiz ya shiga tana kicin, jin sallamarsa sa ta fito da sauri cikin kwarkwasa tana faɗin. "Oyoyo baby." Turus ta yi, ganin hannunsa ɗaya riƙe da akwati, ɗayan kuma yana riƙe da na Amina. GIDAN ALHAJI UMAR A sanyaye Alhaji Gambo ya dubi Hajiya Karima ya ce. "Ki yi haƙuri Hajiya, ni ina ganin abin da ya fi ki fitar da su ɗin. Saboda a matakin da ake kai daga ɓangarensa wallahi komai zai iya faruwa, saboda ki duba ki ga duk yadda nake da shi bai ji nauyin furta mini baƙaƙen maganganu ba." Cikin kuka Mommy ta ce. "Alhaji kada ka manta, tun muna tsohon gidan can fa nake kiwon nan! Yanzu duk haƙuri da kawar da kan da na yi lokacin aurensa, da sakayyar da Daddyn Mami zai yi mini kenan?" Ta yi maganar cikin kuka mai cin zuciya, ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Fiye da haka ma zai iya yi Hajiya. Ni da ke mun san da Umaru ba haka yake ba, jikina yana ba ni har da aikin sihiri a jikinsa. Amma idan aka yi haƙuri komai zai zama labari, yanzu idan na fita zan kira wasu abokaina da suke da suya sporta. In Shaa Allahu cikin su biyun za a samu wanda zai saye, idan aka sayar ba shi kenan ba tun da wannan ce matsalar." Hajiya Karima ta share hawaye sannan ta gyaɗa masa kai. Har ya miƙe sai kuma yace. "Don Allah ku ƙara haƙuri ke da yara, na san abin da ciwo sai an daure. Amma muna nan watarana za ki yi mamaki kamar ba a yi ba." Amsa masa ta yi sannan suka yi sallama. Koda Mommy ta koma cikin gida yaran ta samu duk sun yi carko-carko, faɗaɗa fara'a ta yi ta ce. "Mun gama magana da Alhaji Gambo ya ce zai haɗa ni da masu sayen kajin." Cikin takaici Ruƙayya ta ce. "Wato Daddy ya kafe dai sai kin sayar? Ai shi kenan, idan ma adalci ya yi Allah Yana kallo. Kuja sai Allah Ya saka..." Bige mata baki Mommy ta yi, rai a ɓace ta ce. "Idan na sake jin makamanciyar wannan maganar daga bakinki, wallahi sai ya yi jini. Shashasha sakarai, wani banzan hali za ki koya? Mahaifin naki kike faɗawa haka? Wallahi idan na sake ji zan ba ki mamaki. Tashi ki fice ki ba ni wuri." Mommy ta ƙarasa maganar a tsawace. Kusan lokaci ɗaya duka suka fita, Mommy ta zuba tagumi tana tunanin sabuwar rayuwar da suka faɗa ita da 'ya'yanta. A wannan ranar Daddy bai dawo gida da wuri ba, kuma ko da ta ba shi abinci kai tsaye ya ce mata ba ya ci. Tana gani ya ɗauki filo ya fice daga ɗakinta, haka Mommy ta kwana cikin takaici da ɓacin rai. Kwanan Shukura Biyu a gida ta tarkato ta dawo gidan, kuma a cikin kwanakin abokan Alhaji Gambo suka saye kaji da dusar wurin Mommy. Ga mamakinta, sai gani ta yi Daddy ya sa ana farfashe katafaren kejin kajin nata. Kamar za ta yi masa magana, sai kuma ta fasa gudun kada abin ya zame musu fitina. Tun dawowar Shukura ta lura da take-takenta, duk da dama can sun san da rashin mutumcinta. Amma a wannan lokacin ya ninka na baya, saboda kai tsaye take kiran Haidar ko Ruƙayya ta saka su aiki ko aike cikin gadara. Idan suka yi magana kuma ransu da na mahaifiyarsu ya ɓaci, saboda idan Daddy ya tashi faɗa yake yi mata ya ce ta hurewa yaranta kunne, tana son ɓata tarbiyyar da ya gina su a kai. A cikin lokaci ƙanƙani zaman gidan Daddy ya sauya salo, su Ruƙayya da suka saba zama su yi hira cikin wasa da dariya da mahaifinsu, a wannan lokacin duk tsoronsa suke ji. Da sun ji sallamarsa suke shiga taitayinsu, ita kanta Mommy wani lokacin gabanta har faɗuwa yake yi. Ta sha zuwa ta same shi don ta ji laifinta, amma ƙarshe sai dai ya rufe ta da faɗa. A cikin wannan zaman kai kuka ni tagumin da suke yi ne, Daddy ya karɓe mukullin store daga hannun Mommy ya koma hannun Shukura. Ranar da Mommy ta yi wa Daddy maganar haka ya gama ci mata mutumci, kuma da yake a ɗakinta yake cikin fushi ya tafi ɗakin Shukura ya kwana a can. A wannan lokacin Hajiya Karima har yayan Daddy ta samu da maganar, amma babban abin da ya ɗaga hankalinsu da kai tsaye ya ce a kan Shukura hatta shi ɗan'uwan nasa da suke ciki ɗaya zai iya rabuwa da shi. Haka Mommy ta cigaba da haƙuri, duk abin da suke so sai Shukura ta ga dama za ta ba su damar su ɗiba, don haka ta saka musu dokar shan shayi a sati sau biyu ragowar kwanaki sai kunu. Hatta abincin dafawa ita ta saka su yin tazarce daga rana zuwa dare, don haka Mommy ta same shi da maganar. "Daddyn Mami shin ka san abin da yake faruwa a gidan nan? Yanzu saboda Allah a ce kowanne irin abinci tazarce za mu yi masa." Fuska a haɗe Daddy ya ce. "Ai wallahi ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yanzu, yanzu ke Karima tsofai-tsofai ba ki san ya kamata ba? Yanzu a ce yarinya ƙarama ita za ta fi ki tattali da sanin ya kamata? Wallahi kin ba ni kunya." Duk yadda ta so shawo kan Daddy fir ya ƙi amincewa. Sai ya zamana idan tana son su sauya abinci, sai dai ta fitar da kuɗi a jikinta ta bayar su sayo abin da suke so, a haka suka cigaba da tafiya har bikin Ruƙayya ya rage saura kwana goma. Da farko Mommy ido ta kawo masa, saboda ta ga ko zancan kujera bai yi mata ba. Duk wani abu da uwa take yi wa 'ya na kicin babu abin da Mommy ba ta saya wa Ruƙayya ba, sai kayan gado ne kawai ya rage take jira daga gare shi. Ana saura kwana bakwai biki ta je har ɗakinsa ta same shi, fuska a sake ta fara yi masa maganar duk da lura da ɓata ran da yake yi. Sai da ya gama sauraronta sannan ya ce. "Kayan gado da duk wani abin buƙata kama daga kan abinci, garar amarya da komai da kika sani na buƙata na damƙa wa Shukura, ba sai kin wahalar da kanki ba za ta aiwatar da komai tun da ita kin ga ta zamani ce za ta fi ki sanin abin da ya dace." Hajiya Karima ji ta yi kamar ya watsa mata ruwan zafi, rai a ɓace ta ce. "Wallahi na gaji Alhaji, yanzu saboda wulaƙanci na haifi 'yar a cikina. Duk wata ragamar ɗawainiyar raino da tarbiyya na yi mata, rana tsaka ka ba wa wata bare kuɗin hidimar bikinta, wallahi ba zai yuwu ba. Ai kuwa wannan karon sai dai duk abin da zai faru ya faru." "Rashin mutumci za ki yi mini Karima?" "Wallahi duk abin da za ka faɗa sai dai ka faɗa, amma babu ƙatuwar da za ta yi mini wannan cin kashin." Ita ma Mommy ta katse shi a zafafe, Daddy ya miƙe a fusace ya ce. "Ba ni ne ubanta ba, wallahi idan kika saka tsiya auren ma sai na fasa shi." Cak Hajiya Karima ta tsaya, ta dube shi rai a ɓace ta ce. "Saboda mace za ka zubarwa da kanka mutumci, to wallahi bari ka ji idan har ka yi wannan abin kunyar. Wallahi zamana da kai ya zo ƙarshe, sai dai ka zauna da Shukura ba ni ba." Daddy ya matsa gabanta ya ce. "A yanzu ma kina iya tafiya ai ban riƙe ki ba." "Wallahi da zaman wulaƙancin da kake yi mini gara ka sawwaƙe mini, amma wallahi ka ji na ratse ba zan yarda ace kayan ɗakina da kuɗin hidimar biki yana hannun matarka ba." Hajiya Karima tana rufe baki Daddy ya ce. "Karima ba ki san na jima ina haƙurin zama da ke ba ko? To tun da haka ne ki je na sake ki saki ɗaya. Idan ya so sai ki yi rayuwar jin daɗi, 'ya dai ni na haife ta. Zan ga uban da zai ɗaura mata aure." Yana gama faɗa ya fice a fusace. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA GOMA ALL NATURAL PRODUCT💃🏻 Tsumi Tsumin tighten Tsumin Sanyi Tsumin basir Tsumin 3in1 Kazar Amare yan mata. Kazar Amare zawarawa. Kazar Masu haihuwa. Kazar 3in1 Kazar uwargida ko amarya da suke son burge oga. Gumbar dabino. Gumbar kwakwa. Gumbar Madara. Garin dahuwar kaza. Garin dahuwar ciccibi. Garin dahuwar hanta. Garin dahuwar kwai. Garin dahuwar kifi. Garin hakin maye na sha da Madara ko nono. Ingantaccen tsumin maganin sanyi, wanda aka samo daga masunta masu kamun kifi,bayan maganin infection yana magance sanyin da aka sha a ruwa ko a tiles ko irin sanyin nan mai kumbura jikin mutum. Bugu da kari ana iya ba yara kanana masu fama da mura ko tari, haka akan dace idan yaro yana fitsarin kwance aka bashi in sha Allah yana dainawa. Ta tuntuɓe mu a wannan lambar. 09065730652 *** Wani irin sanyi ƙafafuwan Mommy suka yi, kanta ta ji ya sara kamar an buga mata guduma. Da sauri ta tsugunna a ƙasa, saboda yadda ta ji juwa tana barazanar taɗe ƙafafuwanta zuwa ƙasa. Cikin ɗacin zuciya ta fashe da wani irin kuka, jin kukanta ya sa Ruƙayya ta shiga da gudu tana tambayarta. Yadda jikin mahaifiyarta yake rawa ne ya sa ta riƙe ta hankali a tashe ta ce. "Mommy lafiya me yake faruwa?" Har lokacin ba ta daina kuka ba, don haka ita ma Ruƙayya hawayen ya fara zubo mata. Sai da Mommy ta yi kuka mai isarta sannan ta ce. "Daddynku ne ya sake ni Ruƙayya." Da wani irin kallo Ruƙayya ta bi mahaifiyarsu, sai kuma ta zabura kamar zararriya ta miƙe tana ja da baya. "What are you trying to said Mommy? Don Allah kada ki maimaita mini wannan maganar, saki like how? Kina nufin Daddy ya sake ki, babu aurensa a kanki or what?" Cikin kuka Mommy ta ce, "Haka nake nufi Mami, tun farkon aurena da mahaifinku ko yaji ban taɓa yi ba. Amma because of that yarinyar har yau ni mahaifinku ya saka, Mami har yanzu ina ganin kamar mafarki nake yi." Ruƙayya tana shirin yin magana suka ji ƙarar taunar cingam ƙas ƙas ƙas, da sauri suka ɗago sai suka ci karo da Shukura a tsaye tana bin su da wulaƙantaccan kallo tana taunar cingma. "Ke! Zo ki karɓi takardar sakin uwarki ki kai mata, sai ku yi hanzarin tattare kayanku ku bar gidan nan. Don ba zan iya ganin wannan abar tana giftawa a gaban mijina ba, kin san zuciya ba ta da ƙashi. Kada shaiɗan ya gifta su fara wani irin zama da ita." Shukura ta furta cikin isa da izgilanci. Ran Mommy sake ɓaci ya yi, za ta yi magana Ruƙayya ta ƙarasa zuciyarta tana zafi. Cike da tsanar Shukura ta karɓi takardar ta fara kantawa. Babu ko tantama rubutun mahaifinsu ta gani, sai dai a wannan lokacin ta fi ganin laifin Daddy fiye da na Shukura, saboda da bai ba ta ba; ba za ta samu ƙwarin gwiwar zuwa wurinsu tana rashin mutumci ba. Shukura ta sake yamutsa fuska ta ce. "Yawwa, a gaggauta fita tun da ba gidan..." Marin da Ruƙayya ta zabga mata ne ya katse kalaman da take yi, cikin jin azaba ta dafe kumatunta. Kafin ta ɗago Ruƙayya ta sake ɗauke fuskarta da mari har sai da kanta ya bugu da bango. A razane Shukura ta ja da baya, ta saka hannuwa biyu ta dafe kumatunta cikin tsoro ta ce. "Ni kika mara Mami?" Cikin zafin zuciya Ruƙayya ta sake yin kanta gadan-gadan ta ce, "Na mare ki, wallahi idan kika sake furta kalma mara daɗi a kan mahaifiyata sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Annoba makira, In Shaa Allahu da sannu za ki girbi abin da kika shuka." Shukura ta sauke hannunta, ta nuna Ruƙayya da yatsa ta ce. "Wallahi za ki san kin kai hannunki saman kumatuna, na rantse da Allah sai na rama a kan wannan tsohuwar kilakin." Tana ganin Ruƙayya ta yo kanta, ta fita da gudu haɗe da fashewa da kuka. Lokacin da Shukura ta fita harabar gidan, Alhaji Umar ya shiga mota kenan zai fita. Tana zuwa jikin motar ta sake rushewa da kuka tana riƙe cikinta, da sauri Daddy ya fito jikinsa har rawa yake yi ya ce. "Me ya faru Shukura? Mene ne ya samu cikin naki?" Durƙushewa Shukura ta yi cikin kuka ta ce. "Kawai daga kai wa Hajiya takarda, shi kenan ita da Mami suka rufe ni da duka. Hajiya har tana dukan cikina, wai gara na rasa cikin kowa ya huta. Ni gaskiya ba zan cigaba da zaman gidan nan ba, wallahi ko dai su fice su bar ni ko kuma ni na fita bar su, don wallahi ba zan zauna su kashe ni ba." Cikin kumfar baki Daddy ya ce. "Ita Hajiyan saboda ba ta da hankali ta dake ki a ciki? Wato saboda na sake ta sai ita da Mami su huce a kanki ko? Bari na shiga gidan." Yana gama faɗar haka ya shige da sauri, har babbar rigarsa tana shirin kayar da shi. Shukura miƙewa ta yi tana sakin murmushin ƙeta, sannan ta rifa masa baya. Maigadi shiru ya yi cike da jimami, don duk da 'yan gidan ba shiga huruminsa suke yi ba amma ya fahimci zuwan Shukura bai kawo komai a gidan ba sai sharri. Lokacin da Shukura ta fita da faɗa Mommy ta tari Ruƙayya tana faɗin, "Ruƙayya kanki ɗaya kuwa? Kin san me kika aikata? So kike ki janyo wa kanki masifa kina zaune ƙalau?" Hawaye yana zuba daga idonta ta ce. "Mommy ba ki ji abin da take faɗa ba? Duk wannan maganganun sai na yi mata shiru, yanzu saboda Allah ban da Daddy ya ba ta fuska ta isa ta faɗa miki haka?" "Tun da mahaifiyarku ta ɗaure muku ai dole ku yi rashin mutumcin da kuka ga dama." Daddy ya furta a zafafe, cikin sauri Ruƙayya ta waiga ta ce. "Daddy ka ga..." Tas! Daddy ya ɗauke fuskarta da mari, kafin Ruƙayya ta yi motsi ya sake sauke mata wani. Rai a ɓace ya ce. "Don ba ki da mutumci matar tawa uwarki za ta saka ki daka? Ni za ku wulaƙanta saboda rashin tarbiyya." "Ai ba ita ba ce har da Hajiyan, kuma wallahi sai ka rama mini ko ni na rama." Shukura ta faɗa a shagwaɓe. Daga Mommy har Ruƙayya ɗagowa suka yi suna kallon Shukura, ta fakaici idon Daddy ta sakar musu gwalo sai kuma ta sake fashewa da kuka. "Ni ba zan rama miki ba, sai dai ki rama da kanki." Daddy ya faɗa yana matsawa gefe. Babu ko kunya Shukura ta matso da niyyar yi wa Mommy mari a fuska. Ruƙayya ce ta sha gaban Mommy, fuska a haɗe tana wurgawa Shukura mugun kallo. "Za ki matsa ta rama marin da uwarki ta yi mata ko sai ranki ya ɓaci?" Daddy ya buga wa Mami tsawa. Zuciya a ƙeƙashe ta ce. "Duk wani hukunci da za ta yi ta sauke shi a kaina, amma idan ta sake ta ɗora hannu a jikin mahaifiyata wallahi za ta gane kurenta." Cikin zafin zuciya Daddy ya sake marin Ruayya ya ce. "Haka Karima ta gurɓata tarbiyyarku ban sani ba? Ba za ki matsa ba sai na sumar da ke." "Ko za ka kashe ni Daddy ba zan bari wannan matsiyarciyar ta mari mahaifiyata ba." Ruƙayya ta faɗa zuciyarta a dake, don a yadda take ji a ranta komai za ta iya aikatawa a kan mahaifiyarta. Tana nan tsaye Daddy ya rufe ta da duka, amma taurin kai irin na Ruƙayya ya sa ta ƙi motsawa daga wurin. Kuka Mommy ta saka, ta janye Ruƙayya ta ce. "Ba sai ka illata mini yarinya ba, za mu tattara mu bar maka gidanka." Fisge Ruƙayya Daddy ya yi, a zuciye ya dubi Mommy kamar zai kai mata duka ya ce. "Kada ki sake shiga tsakanina da 'yata idan ina hukuntata. Idan ba haka ba wallahi ranki zai yi mummunan ɓaci." A daidai lokacin Haidar ya shiga, jin abin da ake tattaunawa ya sa ransa ɓaci. Shukura ta sake fasa wani sabon kukan ta ce. "Yanzu shi kenan sun daki banza da wofi ko? Wallahi ba zan sake kwana a gidan nan ba, kuma wallahi idan ban rama ba sai ka sake ni" Da sauri Daddy ya janyo Shukura jikinsa ya ce, "Babu inda za ki je, kuma mari kamar kin rama kin gama." Shukura da ke gaban Mommy ta ɗaga hannu ta zabga mata mari a fuska, ko sauke hannu ba ta yi ba Haidar ya ɗauke fuskarta da mari. A zafafe Daddy shi ma ya sauke wa Haidar mari sannan ya ce. "Ni za ka wulaƙanta ka tozarta Haidar? Ashe kai ma ba ka da mutumci?" Rai a ɓace Haidar ya ce, "Daddy ba ka ga abin da ta yi ba ne? Ni fa dama na jima ina tara yarinyar nan. Wallahi tuntuni darajarka take ci, da tuni na ɓarar da ita." A zafafe Daddy ya ce. "Za ka gane ba ka da hankali kuwa, idan hauka ne a kanka zan sa a sauke maka shi." Yana gama faɗa ya zaro waya ya nemo wata lamba, yana jin an ɗauka ya ce. "Hello officer, ina son ganinka yanzu. Please ka taho da yaranka." Daga haka ya katse wayar, da mamaki Mommy take kallonsa kamar za ta tanka masa sai kuma ta haƙura. Suna nan tsaye suka ga ya ja hannun Shukura yana lallashi suka fita. Daga Haidar har Ruƙayya rungume Mommy suka yi, Mommy da Mami sai kuka suke yi. Haidar ne ma yake iya lallashinsu, ba su ɗauki lokaci ba suka haɗa kaya a cikin akwatunansu. Gabaɗaya kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa. Suna gab da fitowa suka ji ƙarar motar 'yan sanda, babu jimawa suka ji muryar Daddy yana cewa. "Ku shigo ga yaron nan, ku zo ku tafi da shi. Ba shi tarbiyya ko kaɗan yaron nan, duk wanda ya zo belinsa kada a bada shi sai saka hannuna. Ku hora shi yadda ya kamata." Mommy da su Haidar suna tsaye, suka ga 'yansanda biyu sun shiga falon Mommy. Nan take suka saka masa hangoff a hannu, Daddy ya ba su umarnin su tafi da shi. Mommy tana kuka tana riƙe shi haka suka tasa ƙeyarsa suka tafi da shi, da ƙyar Ruƙayya ta lallashi Mami ta tsagaita da hawaye. Sannan suka ɗauki jakunkunansu suka fito harabar gidan. GIDAN HAFIZ Wani dogon tsaki Bilkisu ta saki cikin jin haushi ta ce. "Da ka san ba kai kaɗai ba ne ai da sai ka sanar da ni." Ajiye akwatin Amina ya yi ya rungumo ta jikinsa ya ce. "Kafin a fara faɗan ya kamata a yi mini oyoyo ɗin tukunna." Ajiyar zuciya Bilkisu take saukewa akai-akai, saboda yadda ta ji zuciyarta tana harbawa kamar ta faɗo daga ƙirjinta. Amina ta taɓe baki ta ce. "Sannu da gida Aunty." A sheke Bilkisu ta dube ta, ta ce. "Ke zan yi wa sannu, ni da nake gidan mijna sannun me za ki yi mini." Amina ta fahimci maganarta, don haka ta ce. "Ai da yake tare muke da Habibi, na san kuma kin sha aikin gida shi ya sa na miki sannu. Ga shi sai da na ce ya kira ki kafin mu ƙaraso amma ya ƙi." Bilkisu ji ta yi kamar an zuba mata borkon, Hafiz da ke tsaye mamaki ya kama shi, don shi dai ya san bai yi haka da Amina ba. Yana shirin yin magana Amina ta yi gaba tana faɗin. "Baby ka shigo mini da akwatin, kuma ni yau kwana za ka yi kana matsa mini ƙafa don ciwo take yi mini." Bilkisu jin haka ya sake hargitsa ta, rai a ɓace ta saki hannun Hafiz ta wuce ɗaki fuuuu kamar za ta tashi sama. Amina tana ganin haka ta saki murmushi, a ranta ta ayyana. 'Ashe dama matar nan sakarya ta mayar da ni, shi ne take kunna ni ban sani ba. Ai kuwa da ni take zancen.' Tana shiga ɗaki Hafiz ya shigar mata da akwatin, sannan ya fito ya nufi ɗakin Bilkisu. A kan kujera ya same ta, ya faɗaɗa fara'arsa ya ce. "Baby kin yi kyau sosai." A madadin ta ba shi amsa sai ta ce. "Wato Hafiz ni ka so tozartawa ko? Saboda za ka dawo da matarka shi ne ba za ka sanar da ni ba. Na gode, ai yanzu amfanina ya ƙare tun da ta dawo." Zama Hafiz ya yi a gefenta ya ce. "Haba Bilkisu, me ya sa za ki ce haka? Ina kasuwa mahaifinta ya kira ni, amma don Allah ki yi haƙurin rashin kiranki." Yana rufe baki sai kawai Bilkisu ta fashe da kuka, janyo ta jikinsa ya yi ya shiga lallashinta. Sai da ta tsagaita da hawayen sannan ya ce. "Ina abincina?" "Yana kicin." Ta ba shi amsa a daƙile. Har ya miƙe zai fita ya waigo ya ce. "Am dama tun da Amina ta dawo, a ɗakinta zan kwana yau." "To mene ne na faɗa mini Abban Sayyid, ai duk abin da ka yi ka isa ne. Da za ka dawo da ita ka faɗa mini? Sai don za ka je ka kwana a wurinta za ka yi mini 'yar murya, duk abin da mutum dai ya yi Allah Yana kallo." Murmushi kawai Hafiz ya yi ya fita, don ya fahimci rikici Bilkisu take ji, idan ya ce zai tanka mata sai ta mayar da abin ya zama babba. A ranar kwanan farinciki suka yi tsakanin Hafiz da Amina, duk wani tabon da take kallon Hafiz da shi ya goge. Kuma tun daga wannan lokacin Amina ta sauya taku, duk wani motsi da furucin Bilkisu tana ganewa. Don haka koda ta yi wani abin Amina ba ta nuna mata ta damu, wannan dalilin ne ya sa Amina ta cigaba da zaman aurenta cikin kwanciyar hankali. Sai laulayin cikin da yake danunta, shi ma a lokacin da ya shiga wata huɗu sai laulayi ya yi mata sauƙi sosai. Don babu abin da ba ta ci sai wanda ba a rasa ba, haka kuna ta ɓangaren ciwo zazzaɓin dare da yawan ciwon kan da take yi duk ta daina. Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri duk ranar da Hafiz yake ɗakinta, a ɓoye za ta aiki yaranta gidan wata ƙawarta Maman Siyama, da yake yaran Maman Siyama sun girmi su Sayyada sai su sayo mata Nama ko kifi a ɓoye. Sai ta yi girki da shi, ko kuma da safe ta sayo ƙwai tun da dare ta soya musu ita da yara. Haka wunin ranar Amina za ta yi ta cika tana batsewa, kuma sai abin ya haɗe mata ga saurin fushi irin na mai ciki ga kuma abin da Bilkisu take yi. A irin haka har faɗa suka taɓa yi da ita da Hafiz, ya yi mata rantsuwar duniya a kan ba shi yake saya wa Bilkisu ba ta ƙi yarda. Tun yana lallashinta har ya yi watsi da ita, sai watarana da ta jin sallamar yaro bayan ya shiga ɗakin Bilkisu har zai fita ta bi shi soro da sauri. Murmushi ta yi masa cikin bugar ciki ta ce. "Ni kam kifin da kake sayo wa Maman Sayyada yana da arha kuwa? Naman da kifin wanne ya fi sauƙi ne?" Yaron ya yi jim sannan ya ce. "Gaskiya kifin ya fi arha don Ummanmu ma shi take saya, amma na ga ita Maman su Sayyid ta fi son na sayo mata nama." Jinjijna kai ta yi ta ce. "To je ka, na gode ka ji." Ya amsa mata ya tafi. Ɗaki ta koma tana nazari, sai kuwa ta ɗauko waya ta kira Hafiz sai da ta ji ya ɗauka sannan ta fita tsakar gida ta ce. "Hello Habibi, ba na jinka ko network ne?" Bilkisu tana tsakar gida tana koyawa su Sayyada aikin makaranta, ta ji muryar Hafiz raɗau a kunnenta. Amina da ta tabbatar da Bilkisu ta ji, sai ta fakaici idonta ta katse kiran ta ce. "Yawwa dama na ce, don Allah idan za ka taho ka biya gidan Aunty Nana ka ba ta kuɗin naman kai ƙafa, don gobe farfesunsu nake so kuma ba na son na yi wahalar dafa su." Sai ta shige ɗaki ta ce. "Eh network ɗin ya dawo, to shi kenan Hubby Allah Ya bar mini kai." Amina ta leƙa ta windo ta ga Bilkisu ta yi kasaƙe har da sakin ƙwafa. Tun a daren ranar ta kira yayarta Aunty Nana ta tura mata kuɗi, ta ce da safe ta aika yara a sayo naman kai ta yi mata farfesu, idan ya so da rana idan Hafiz ba ya gida sai ta aiko a kawo mata. Kamar yadda suka tsara Amina tana zauna a tsakar gida washegari da rana, tana sai ga Usaina 'yar yayarta ta yi sallama. Da yake budurwa ce, kuma Amina ta kitsa mata komai tana shiga cikin ɗan ɗaga murya ta ce. "Aunty ga farfesun naman kan, wai Umma ta ce ga canjin dubu ɗaya da ɗari biyar na Yaya Hafiz." Amina ta karɓa ta buɗe, take ƙamshin ya mamaye gidan har ta ji yana shirin saka ta amai. Gani suka yi Bilkisu ta fito, Amina ta ɗan yamutsa fuska saboda dama can naman kai bai wani dame ta ba ta ce. "To ku kunci ne?" Yarinyar ta girgiza kai, sai ta ɗauko wata ƙaramar roba ta ɗauki ƙafa ɗaya ta ɗora a kai da romo ta ce a miƙa wa Bilkisu. Tun Usaina ba ta rife baki daga sallamar da ta yi wa Bilkisu ba, ta buga mata tsawa da cewar ba ta ci. Dariya Amina ta yi a ranta, ta dubi Usaina ta ce. "Ungo canjin nan nasa je ki kanti ki sayo mini multina guda biyu, don wannan naman kan ba lallai na iya cinye shi ba sai dai ki tafi da shi." Babu jimawa Usaina ta sayowa Amina, sai da suka shiga ɗaki sannan Amina ta yi ƙasa da murya ta ce. "Maza ki mayarwa da Aunty naman kan nan, don wallahi daurewa kawai nake yi ji nake kamar zan yi amai." Dariya Usaina ta yi, ta yi saurin fita daga gidan ba tare da Bilkisu ta ganta ba. Tun bayan zuwan Usaina Bilkisu ta cika fam tana jiran dawowar Hafiz, yana dawowa da daddare ko mashin ɗinsa bai gama ajiyewa ba fuuu Bilkisu ta je ta same shi a wurin ta ce. "Wallahi ka ji tsoron Allah Hafiz, don kuwa Allah sai ya tuhume ka a kan rashin adalcin da kake yi." Da mamaki ya dube ta ya ce. "Rashin adalcin me na yi miki?" Takaici ya sa Bilkisu ta fashe da kuka ta ce. "Yanzu don zalinci har naman kai za ka sa a dafowa Amina ni yarana muna zaune ko oho? Wallahi Allah ba zai barka ba, idan kuwa kana zalintata ban yafe maka ba." Rai a ɓace Hafiz ya ce. "Ni kike faɗa wa haka?" "An faɗa maka, mugu azzalumi. Wallahi ban yafe maka ba Hafiz." Har ya ɗaga hannu kamar zai mare ta sai ya sauke, bayan ya gyara mashin ɗinsa ya ce. "Amina! Amina!" Da sauri Amina ta ƙaraso ta ce. "Gani baby, ashe ka dawo." "Me yake faruwa? Na ji Bilkisu tana zancan naman kai?" Hafiza ya tambaya. Amina ta wara hannu ta ce. "Ranka shi daɗe itaa za ka tambaya, ba ita ta yi maka maganar naman ba." A ƙufule Bilkisu ta ce. "Ni za ku mayar mahaukaciya ko 'yar iska? Na ji kina waya kina cewa Hafiz ya biya ya kai kuɗin a saya miki naman kai, har a kawo ki kawo mini ɗazu shi ne za ki raina mini hankali?" Amina ta zaro ido tana tafa hannuwa haɗe da salati ta ce. "Aunty sharri za ki yi mini? Ni na ce Baby zai tura kuɗin naman kai?" Sai kawai Amina ta rushe da kuka. Ummou Asalam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA SHA ƊAYA KU ZO KU SAYI MUSULMAN KAYANMU💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Assalamu Alaikum Ina manyan mata yan gayu masu ji da kwalisa ... Ina masoyan jakankuna da mayafai da kuma sarƙoƙi? Ummee's Collection ta tanadar muku su kala kala acikin farashi mai sauki, lallai ku hanzarta kada a barku a baya. Domin mallakar naku sai ku tuntube mu anan What'sapp or call :- 08082350419 A ɗan rikice Hafiz ya riƙo Amina ya ce. "Haba Maman baby mene ne abin kuka kuma daga tambaya? Kin san fa na ce miki ba na son duk wani abu da zai dinga ɓata miki rai." Amina ta sake ƙaƙalo hawaye ya cigaba da zuba shaa, ta kwantar da kanta a jikin ƙirjinsa har tana sauke ajiyar zuciyar kamar wacce ta ci kuka ta more. Hakan ya sake damun Hafiz, a ɗan faɗace ya dubi Bilkisu ya ce. "Yanzu don Allah me kika yi haka Bilkisu? Ƙiri-ƙiri kin ɗaga wa yarinya hankali tana fama da kanta." Ran Bilkisu ya ƙara ɓaci, cikin kumfar baki ta ce. "Ni za ku yi wa makirci, munafuka ba ɗazu aka kawo miki ba har da ragowar canjinsa da kika sa aka sayo miki multina." A zafafe Hafiz ya nuna ta ya ce. "Kada ki sake ce mata munafuka, ban bari ta raina ki ba don haka son zuciyarki ba zai sa na bari ki wulaƙanta mini mata ba." Amina kamar tana jira ta sake fashewa da kuka ta ce. "Ka ji wani sharrin da za ta yi mini ko? Wai na sha multina Baby don Allah tun da na samu cikin nan ba sau ɗaya na sha ba? Ita ma ba amai ta saka ni ba." Hafiz ya gyaɗa mata kai sannan ya ce. "Bilkisu ba na son tashin hankali, kin san dai babu yadda za a yi na sayo abu a ɓoye na ba ta ban ba ku ba. Ki sama mini lafiya, kada ki sake ki sakawa matata hawan jini ki bar ni da wahala. Yarinyar nan ba huruminki take shiga ba, don haka ki kama kanki." Daga haka ya yi gaba yana riƙe da Amina har ya kai ta ɗaki. Bilkisu ta kusa minti biyu a tsaye tana hawaye, sai da ta gaji don kanta sannan ta wuce ɗaki ta zauna ta rafka tagumi. Nazari ta yi sosai, lokaci ɗaya ta miƙe tsaye zumbur tana kai kawo a ɗaki. "Wato yarinyar nan ni za ta yi wa bariki kenan?" Bilkisu ta furta cike da jinjina kai, ta koma ta zauna sannan ta sake cewa. "Ai kuwa kin yi da 'yar halak, idan kuwa haka ne yanzu muka fara wannan wasan." Ta ƙarasa furucinta tana sakin murmushi. Duk da Bilkisu ta gano makirci Amina ta yi mata, haka ta cigaba da cika tana batsewa. Da yake Hafiz shi ma a ƙule yake da ita, sai ya yi watsi da ita. Har sai da ta gaji don kanta sannan ta sauko. Tun daga wannan ranar Bilkisu sai ta ja baya da ƙulla makircin da take yi wa Amina, koda ta yi idan Aminan ita ma ta rama sai ta watsar da shi. Haka suka cigaba da tafiya har aka shiga watan azumi a lokacin cikin Amina ya shiga wata shida. Rimi-rimi suka ɗauki azumi kamar zamansu ya yi lafiya, sai da aka kai azumi na tara sannan Bilkisu ta kira Maman Siyama ta tura mata kuɗi. Da yake duk Azumi Yaya Salisu yana yi musu rabon kuɗi da atamfofi, don haka a ranar ta kira ta suka gama tsara duk yadda za su ita da Maman Siyama. Washegari sai da Hafiz ya tafi kasuwa, sannan wani ɗan matashi ya yi sallama a soron gidan. Bilkisu tana ji ta yi shiru kamar mai bacci, Amina ce ta amsa masa haɗe da tambayar waye. Daga can ɓangaren matashin ya ce. "Aike ne daga wurin mai gidan." Hijabinta ta ɗauka ta zura, sannan ta ƙarasa ta ce. "Kawo." Janye kayan ya yi ya ce. "Ai ya ce ba ke za a ba wa ba." Mamaki ne ya kama Amina, saboda ta san sautari idan Hafiz ya yi aike duk wacce ta fita za ta iya karɓa. A daidai lokacin Bilkisu ta ƙarasa tana ɗan murza fuska kamar mai bacci ta ce. "Au wai dama kai ya aiko? Yanzu na ji kiransa a waya ina bacci." Ɗan matashin ya ce. "Eh, ga shi wannan cewa ya yi na amfanin gida ne." Sai ya miƙa mata wata ƙaramar baƙar leda. Ya janyo wani ɗan ƙatan buhu, mai ɗauke da doya dankali har da kayan shayin su gwangwanayen madara. Da gayya Bilkisu ta ce. "To ai ya ce saƙon biyu ne, akwai na Babanmu." Matashin ya ce, "Eh ga shi nan, ya ce kun yi maganar zuwanki gida shan ruwa." Murmushi Bilkisu ta yi ta ce. "Kai yanzu Abban Sayyid duk shekara ba ya gajiya, to ɗan shigar mini da shi ciki don ya yi mini nauyi." Matashin kafin ya ɗauki buhun ya ce, "Yawwa ya ce ki duba drower kayansa, a cikin kuɗin da yake ba ki ajiya ki ɗauki dubu biyar ki ba wa Baba ya sa yi takalmi." Bilkisu ta wani narke kamar za ta yi kuka ta ce. "Har ban san me zan ce ba. Kai bari na kira shi a waya, maza shigar mini da kayan ciki." Wayar da ke hannunta ta latsa layin Hafiz, sai da ta tabbatar da Amina ta ji maganar Hafiz bayan ya ɗauka. Sai ta yi cikin gida tana faɗin. "Hello Aljannata." Katse wayar ta yi ta saka ta a aeroplane mood sannan ta cigaba da cewa. "Habibi ban san me zan ce maka ba, thanks you so much Zauji. Allah Ya bar mini kai har cikin aljanna." Tana gama faɗa ta sakarwa wayar kiss, sannan ta ajiye ta faɗa banɗaki ta yi wanka. Amina ta fi minti biyar a tsaye tana jin zuciyarta tana zafi, musamman da ta tuna yadda suka yi da shi a ranar da za a kai na azumi na takwas. Da ta ce ya ba ta kuɗi ta saya wa iyayenta kayan shan ruwa, ya ce mata ba shi da kuɗi. Hawaye ne ya zubo mata, don haka jiki a saɓule cike da tsangwamar kanta ta wuce ɗaki. Bilkisu ta saki murmushin ƙeta ta ce. "Kika ce ba kya ji yarinya, baƙinciki ma yanzu kika fara sha." A gurguje Bilkisu ta gama shiri tana fitowa, wani yaro ya shigo da sallama ya ce. "Wai nan ne gidansu Maman Sayyid?" Bilkisu ta saci kallon Amina da ke kwance a tsakar gida tana shan iska ta ce. "Eh nan ne, ya aka yi?" Yaron ya ce. "Wani mai adaidaita sahu a ƙofar gida ya ce a faɗa miki, wai mai ɗan sahun da Baban Sayyid ya turo zai kai ki unguwa ne." Amina tana zaune sai da ta tashi zaune, zuciyarta ta ji tana zafi. A hankali ta furta. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Bilkisu ta saki murmushi ta ce. "Ka ce masa tana zuwa." Tana faɗar haka ta yafa mayafinta, ta kinkimi buhun har ta je tsakiyar gida ta ce. "Auntyn yara ni zan wuce, ina jin ma ba sai kin yi abinci da yawa ba. Saboda har Abban Sayyid a gidanmu zai sha ruwa." Amina da baƙinciki ya gama cika ta ko amsawa ba ta yi ba. Bilkisu tana fita hawaye ya fara zubo mata, takurewa ta yi a gefe ta ci kukanta mai isarta. Sai zuwa can yamma ta ga kiran wayar Hafiz ya shigo mata, kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta taushi zuciyarta ta ɗauka don ta ji me zai ce mata. Sallama ya yi mata bayan ta amsa ya tambayi ƙarfin jikinta don ya ji muryarta ba kamar yadda ya fita ya bar ta ba. "Amina idan azumin nan yana ba ki wahala don Allah ki ajiye shi ki huta, ai Allah Ya ga halin da kike ciki daga baya sai ki rama. Saboda duk na ji muryarki wani iri, ko akwai abin da yake damunki?" Hafiz ya faɗa cike da kulawa, takaicin tambayarsa ta ji. Tana ganin kamar ma ya raina mata hankali ne, murya babu walwala ta ce. "Ba komai." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Dama kira na yi na faɗa miki, zan sha ruwa a gidansu Bilkisu, kin san mahaifinta duk shekara yana gayyarar surukai da 'yaransa shan ruwa a gidansa." "Hmmmm!" Kawai Amina ta ce, saboda tana buɗe baki za ta iya faɗa masa maganar marar daɗi. "Amina ko ba kya ji ne, cajin wayata zai mutu." Hafiz ya furta a gaggauce. A daƙile Amina ta ce. "Na ji." A sanyaye Hafiz ya ce. "Wallahi tun safe mantawa na yi ban sanar da ke ba. Amma ba daɗewa za mu yi ba, kuma su Sayyada suna nan za su ɗebe miki kewa." "Sai an jima aiki nake." Amina ta furta tana kashe wayar gabaɗaya. Hawaye ne ya zubo mata, cike da takaici ta ce. "Hmmm namiji munafiki, duk wani makirci namiji ya iya ƙulla shi. Wai ni zai mayar 'yar iska, saboda ya raina mini hankali." GIDAN ALHAJI UMAR Hajiya Karima suna zuwa harabar gidan motar Baba malam tana fakawa a ciki, da sauri ya fito daga cikin motar rai a ɓace ya ƙarasa wurinta ya ce. "Karimatu, abin da Mamana ta kira ni a waya ta sanar da ni haka ne?" Mommy ta goge ƙwallar idonta ta ce. "Haka ne yaya." Baba malam yayan Daddy ne, shi ne babba a cikinsu. Sun ɗauke shi tamkar mahaifinsu, don haka suke shakkarsa. Cikin ɓacin rai ya ce. "Ina Umarun yake?" Da hannu Mommy ta nuna masa cikin gidan, tun ba ta sauke hannu ƙasa ba ya wuce ciki yana ƙwala masa kira. "Kai Umaru! Umaru kana ina?" Daddy hannunsa riƙe da Shukura ya fito ta ce. "Ga ni." Tass! Baba malam ya ɗauke shi da mari har sai da hannunsa ya rabu da na Shukura, a tsorace ta ja da baya ganin abin da ya faru. Cikin fusata Baba malam ya nuna shi ya ce. "Ashe ba ka da hankali ban sani ba, ko ka fara shaye-shaye ne? Wato Umaru mu za ka tozarta ka wulaƙanta? Kana cikin hankalinta za ka saki Karima?" Ran Daddy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, a fusace ya dube shi ya ce. "Shi kenan ba ni da hurumun zartar da hukunci a kan iyalina? Yaya kai wa yake dakatar da kai a kan naka iyalin?" Baki sake Baba malam yake bin Daddy ya kallo, cikin mamaki ya ce. "Umaru ni kake faɗawa haka?" "Haifata ka yi da ba zan faɗa maka ba Yaya? Kowa fa ya ji da wutar gabansa. Karima matata ce kuma na sake ta, kawai shi ne har za ka zo ka gaban 'ya'yana ka kunyata ni ka mare ni." Wannan karon ba yayansa ba, hatta su Mommy tsoro lamarin Daddy ya ba su. Saboda sun san ko tari mahaifinsu ba ya yi, idan Baba malam yana yi masa faɗa. "Baby wai duk a kan wannan matar ake wannan abin, ai dama ni na jima da fahimtar danginka ba sa ƙaunata. Kuma tun da haka ne, ni ba zan iya cigaba da zama da kai ba..." "Ke rufa mana baki." Baba Malam ya katse kalaman Shukura, cikin ɓacin rai Daddy ya ce. "Yaya ina ba ka girmanka fa, amma wallahi kada ka sake yi wa matata tsawa. Haka kawai a dake ta a hana ta kuka, yarinyar nan sun zalince ta don kawai an ga ba ta da hatsaniya ne?" Jinjina kai Baba malam ya yi ya ce. "Ba laifinka ba ne Umaru, ke Karima ku wuce mu je can gidana." Daddy cikin halin ko inkuka ya ce. "Oho gara ku je, ba za ka birge ni ba sai ta gama idda ka aure ta." Daga Mommy har Baba Malam waigowa suka yi suna kallomsa, su Ruƙayya da ƙannenta ban da kuka babu abin da suke yi. Motar Baba malam suka shiga, rai a ɓace ya tuƙa su suka fice daga gidan zuciyarsa tana ƙuna. Suna zuwa gida ya sanarwa da matansa abin da ya faru, gabaɗaya jikinsu ne ya yi sanyi. Kuma nan take suka fahimci ba yin kan Daddy ba ne, don haka ya kira Mommy har ɗakinsa don ya ji takamaiman abin da ya faru. Sai da Mommy ta share hawayenta, sannan ta zayyane masa irin zaman doya da manjan da suke yi tsakaninta da Alhaji tun bayan tarewar Shukura. Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce. "Karimatu sai dai mu taya Umaru da addu'a, kuma zan saka masallatai da malamai su taya mu da yi masa addu'a. Domin tun furucinsa na farko da ya yi mini ɗazu na fahimci ba ya cikin hayyacinsa, ke shaida ce. Tun da kika da shi bai taɓa yi mini musu ba, ban taɓa faɗar magana shi da ragowar 'yan'uwanmu sun yi mini musu ba. Amma babu komai, In Shaa Allahu babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji. Yanzu za ku cigaba da zama a nan keda yara." Hajiya Karima ta numfasa ta ce. "Na gode sosai Yaya da karamcin da ka nuna mini, amma ka yi haƙuri na yake hukuncin zan koma gida." Girgiza kai ya yi ya ce. "Karima ashe har kawo wannan lokacin ba mu zama ɗaya ba kenan? To ai ko ba Umaru ba ne mijinki, ni me riƙe ki ne da yaranki idan kika duba zumuncin da ke tsakanin iyayenmu. Idan har na isa da ke, ban ba ki damar komawa gida ba. Kuma duk abin da kike buƙata ko yara, ki same ni kai tsaye ki tambaye ni." Godiya sosai Hajiya ta yi masa tana kuka, da suka gama magana sai ya ga ta jim kamar akwai abin da yake damunta. Cikin kulawa ya ce. "Ko akwai wani abu ne Karima?" "Yaya dama maganar Haidar ne, ina tsoron kada ya sa jami'an tsaro su azabtar da shi. Sai kuma maganar auren yarinyar nan da ya ce ba zai ɗaura mata aure ba." Mommy ta furta cikin damuwa. Murmushi ya yi ya ce, "Ki kwantar da hankalinki Karima, yanzu haka daga nan wurinsa zan tafi." Sai ya dafe kansa cikin damuwa ya ce. "Sai dai ban san wanne station aka kai shi ba." Mommy ta ɗan yi nazari ta ce, "Ina tunanin na Sharaɗa ne, saboda na ji ya kira DPO abokinsa." "D.P.O Ayagi kenan?" Baba malam ya tambaya. Gyaɗa masa kai Mommy ta yi. Baba Malam ya ce, "Ai ta zo gidan sauƙi, Indai Ayagi ne yayansa aminina ne zan yi masa magana In Shaa Allah." Sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Maganar auren Mamana kuwa kada wannan ya dame ki, da Umaru da babu Umaru za mu yi mata aure ta tare a ɗakin mijinta. Tun da muke ba a taɓa yin abin kunya a danginmu ba, don haka Umaru bai isa ya zubar mana da kima a wurin dangin saurayinta ba. Ki sa a ranki kamar an yi bikinta an gama idan muna da rai da lafiya." Cikin girmamawa Mommy ta ce. "An gode Yaya, Allah Ya ƙara girma da jinkiri mai amfani." Baba Malam ya yi murmushi ya ce. "Amin Ya Rabbi." Hajiya Karima tashi ta yi ta nufi ɗakin da aka ba ta, ɗakin akwai banɗaki da katuwar katifa a ciki. Ruƙayya kuma da ƙannenta Baba Malam ya ce su shiga cikin yaran gida su cigaba da mu'amalarsu. Da yake Baba Malam tsayayyan mutum ne, duka matansa biyun da yaransu kansu a haɗe yake. Hakan ne ya sa ko kaɗan Mommy ba ta fuskanci wani abu marar daɗi a gidan ba. Kamar yadda ya yi mata alƙawari, a ranar ya je ta taho da Haidar. Fuskarsa ta ɗan kumbura, saboda ya ce sun ɗan daddake shi. Sai da ya yi wanka da ruwan ɗumi sannan Baba malam ya kira family Doctor ɗinsu ya duba shi ya ba shi magani. Haka suka cigaba da rayuwa a gidan tun su Mommy suna ɗari-ɗari, har suka saki jikinsu ake komai da su. Sannu a hankali kwanaki suka dinga gangarawa har lokacin bikin Ruƙayya ya matso. Duk wata ɗawainiyar kayan abincin biki, gara da kayan ɗaki Baba Malam ne ya yi mata. Kuma da yake amaryarsa tana sana'ar gyaran jiki ita ta dinga yi wa Ruƙayya gyaran amare. Sai dai babban abin da yake damun Ruƙayya da Mommy, rashin bibiyarsu da Daddy bai yi ba duk tsawon kwananin da kusa kwashe. Lokacin da uwargidan Baba malam ta fahimci damuwarsu, zama ta yi da Mommy a ɗaki ta taushe ta. "Maman Mami, tabbas duk macen da take cikin irin yanayin da kike ciki dole za ta ji babu daɗi. Ace mijin da kake tare da shi sama da shekara ashirin, rana tsaka ya juya maka baya a kan wata ƙanƙanuwar yarinya. Amma abin da nake son ki sani komai ya yi zafi maganinsa Allah, idan Alhaji ya fahimci damuwarki zai ga kamar ba ya kyautata muku yadda ya dace. Don Allah ki cire komai a ranki Karima, ba na son ranar taron yarinyar nan da ya kasance miki ranar farinciki na tsinci damuwa a fuskarki. Kin ga ita kanta yarinyar idan tana ganin yanayinki ba za ta sake ba. In Shaa Allahu za a cigaba da roƙon Allah, idan ma wani abin ta yi masa ƙadarinta zai karye ki koma ɗakinki." Mama tana gama faɗa Mommy ta saki murmushin takaici ta ce. "Yaya duk maganganunki haka ne, kuma In Shaa Allahu zan kiyaye. Sai dai ba na jin zan sake zaman aure da abban su Mami." Shiru Mama ta yi ta ce, "Babu mai tilasta ki Karima, Allah Ya zaɓa mafi alheri. Mommy ta amsa da Amin. Ruƙayya ba wani event ta yi mai yawa ba, saboda dama can ba ta cika hayaniya ba. Henna day ta yi, sai kamu. Kuma duka a cikin harabar gidan Baba Malam aka yi decoration, aka kawo masu kiɗan ƙwarya suka sha biki. Ranar ɗaurin aure tun asuba Mommy da mutanen gidan suka shiga hidimar girke-girken abincin 'yan ɗaurin aure. Kallo ɗaya za ka yi wa Mommy ka fahimci tana cikin farinciki, danginta gabaɗaya a nan gidan suka sauka saboda ta sanar da su a gidan Baba Malam za a yi bikin. Sai dai babu wanda ta sanarwa da dalilin yin haka sai 'yan uwanta da suke ciki ɗaya, saboda kunyar faɗa take ji. A masallacin jikin gidan Baba malam da ke hotoro, yan'uwa da abokan arzikin da ya gayyata duka suka taru. Haka dangin saurayin Ruƙayya da abokansa suka yo zuga, mafi yawa sanye suke cikin fararen kaya. Baba malam da waliyin saurayin Ruƙayya ne a zaune har sun fara gabatar da ɗaurin aure, kamar wanda aka jefo daga sama haka Daddy ya faɗo cikin masallacin rai a ɓace ya ce. "Ban lamunce kowanne mutum ya ɗaura mini auren 'ya ba. Idan ba haka ba kuwa wallahi kowaye hukuma ce za ta raba mu." PROMO🔥🥳 PROMO🔥🥳 PROMO 🔥🥳 Mun kawo muku garaɓasa ne domin taya ku murnar bikin sallah💃🏻🥳 kowanne littafi mun zabge muku farashinsa. Shu'umar Masarauta 1&2 600 Baƙar Daula 300 Zaujatu Jinnul-Ashiq 300 An ya baiwa ce 200 Dubu Jikar Mai Carbi 200 Uwani 'YarƘashin Gwiwa 400 Gidan Likitoci cmplt 400 Naushin Wuta cmpt 400 Za ku tura ta wannan asusun na ƙasa. Aisha Adam 3090957579 Firstbank Sai shaidar biya ta wannan lambar. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA SHA BIYU KU ZO KU SAYI MUSULMAN KAYANMU💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Assalamu Alaikum Ina manyan mata yan gayu masu ji da kwalisa ... Ina masoyan jakankuna da mayafai da kuma sarƙoƙi? Ummee's Collection ta tanadar muku su kala kala acikin farashi mai sauki, lallai ku hanzarta kada a barku a baya. Domin mallakar naku sai ku tuntube mu anan What'sapp or call :- 08082350419 *** Ilahirin mutanen da ke cikin masallacin waigowa suka yi, suna kallon Daddy da babu ɗigon rahama a fuskarsa. Baba malam ji ya yi kamar ya tsaga ƙasa ya shige ciki saboda tsabar kunya, wani ƙanin mahaifin saurayin Ruƙayya ya dubi Baba Malam ya ce. "Alhaji lafiya? Me yake faruwa ne?" Daddy ya yi farat ce. "Ni mahaifinta ya kamata ku tambaya ba shi ba." Girgiza kai Baba Malam ya yi, ya dubi wasu securites ɗinsa ya yi musu magana, sai da ya matsa kusa da su ta yadda mutanen gefe ba za su ji ba ya ce. "Ku fita da shi, a kai shi ɗakin saukar baƙina." Babu ɓata lokaci suka tasa ƙeyar Daddy da ke masifa yana zage-zage. Baba malam ya dubi mutanen da ke zaune ya ce. "Don Allah ku yi haƙuri da ɓata lokacin da aka yi muku, wannan bawan Allahn da kuke gani ƙanina ne kuma mahaifin yarinyar nan. Sai dai kuma a kwanakin baya ne ya samu matsalar ƙwaƙwalwa. Ina mai sake ba ku haƙuri a karo na biyu." Cike da tausayawa mutanen cikin masallacin suka fara cewa. "Subhanallah, Allah Ya ba shi lafiya ai kuwa ga shi nan biri ya yi kama da mutum." Daga haka aka cigaba da ɗaurin aure, haka Baba malam da ragowar 'yan uwansa suka fara gaisawa ana ta yi musu Allah sanya alheri. Mommy tana cikin gida da 'yan biki, labari ya isar musu a kan abin da Daddy ya yi. Saboda takaici Mommy har da kukanta, sai da ta ji an ɗaura aure sannan hankalinta ya kwanta. Baba malam Allah-Allah ya dinga yi ya sallami mutane ya shiga cikin gida, kai tsaye ɗakin saukar baƙinsa ya shiga. Yana shiga 'yan'uwansa suka rufa masa baya, Baba Sani cikin damuwa ya ce. "Yaya don Allah ka yi haƙuri, kada wannan abin da ya faru ya sa ka saka shi a ranka ga shekaru sun ja." Girgiza kai Baba malam ya yi ya ce. "Kada ka damu Sani, yanzu haka Umaru yana cikin nan. Zan yi magana da shi, na ji mene ne matsalarsa." Yana gama faɗa ya saka mukulli ya buɗe ƙofar ya shiga, a zaune ya samu Daddy fuskarsa ta yi murtuk saboda ɓacin rai. Daddy yana ganinsa ya taso da sauri ya ce. "Yanzu abin da ka yi yaya ka kyauta mini kenan..." Bai rufe baki da Baba Malam ya ɗauke fuskarsa da mari, ya saka hannu ya sake taro fuskarsa da mari a karo na biyu. Can baya Daddy ya matsa yana bin Baba malam da kallo, cikin zafin zuciya ya zauna a kujera yana bin sa da mugun kallo. "Zo nan Umaru." Baba malam ya furta fuska a haɗe, babu musu Daddy ya zauna a ƙasa yana cin magani. Baba malam ya dubi ƙannensa da ke tsaitsaye ya ce duk su zauna, zama suka yi kowanne jiki a sanyaye sannan ya fara cewa. "Umaru me kake so ko kuma na ce me kake nufi game da mamana?" Shiru Daddy ya yi bai tanka ba, Baba malam ya cigaba da cewa. "Ban san shaiɗanin da yake kanka ba, amma ina mai tabbatar maka da duk wani abin da yake kanka sai na sauke maka shi. Ba ka da hankali da kake son biye wa mace don ka tozarta kanka, kuma ku wukaƙanta 'yarka da zuri'armu a idon duniya?" "Amma ai ba tun yau ba na ce na fasa auren." Cewar Daddy, Baba malam ya ce. "Saboda me?" Daddy cike da rashin jin nauyi ya ce, "Saboda cin mutumcin da ta yi wa Shukura ita da uwarta." Takaici ne ya rufe su gabaɗaya jin abin da ya faɗa. Baba malam ya ce. "Amma ka san wulaƙanci da cin zarfi ne ka ɗauki takardar saki ka ba wa Shukura ta kai wa Karima? Ko ka binciki abin da ta yi bayan ta kai mata takardar? Umaru wallahi ka tafka babban kuskuren da za ka yi nadamarsa nan ba da jimawa ba. Ka sani, wallahi har ka mutu ba za ka samu mace kamar Karimatu ba. Kuma aure ne na riga da na ɗaurawa mamana, idan ka ga dama ka kai ƙara ta har majalisar ɗinkin duniya. A shirye nake na fuskanci shari'a da kai." Motsa baki Daddy yake ƙasa-ƙasa yana ƙunƙuni kamar mai zagi ko magana, 'yan'uwansa da ke wurin su ma mamakinsa suke yi. Kamar zai tanka, sai kuma kawai ya miƙe ya fice daga ɗakin, har Baba Alasan zai yi masa magana Baba malam ya dakatar da shi. Sun jima suna tattaunawa sannan suka tsayar da matsayar sake miƙewa tsaye, domin su nemawa ɗan'uwansu magani a kan baƙon halin da yake ciki. Bayan sun gama tattaunawa da kansa ya sa aka kira Mommy har ɗaki, ya faɗa mata kalaman kwantar da hankali. Ya kuma ba ta haƙuri a kan abin da ya faru, sannan Mommy ta kwantar da hankalinta aka cigaba da hidimar biki. Yamma liƙis motar 'yan kai amarya suka yi fakin a ƙofar gidan Baba Malam, saboda ganin wannan farinciki Mommy har da kukanta a lokacin da za a tafi da Mami. Lokacin da suka rungume juna suna kuka cikin shasssheka Mami ta ce. "Mommy yanzu haka zan tafi ban yi sallama da Daddy ba? Mommy duk yadda Daddy ya ci alwashin kai ni ɗakin mijina Shukura ta rusa mana." Mommy ta share hawaye, ta riƙe ta tsam a jikinta ta ce. "Kada wannan ya rusa farincikinki Ruƙayya, mahaifinku yana buƙatar addu'a, domin hatta 'yan'uwansa ba su tsira daga sababbin halayen da ya tsinci kansa a ciki ba." Jinjina kai ta yi sannan suka yi sallama, yaya Mommy da Mama uwar gidan Baba malam ne suka riƙe ta har aka shigar da ita mota sannan suka tafi. Gidan Mami ya yi kyau sosai, haka mutane suka dinga yabawa. Ana jinjina yadda aka narka dukiya mai yawa a ciki, tun daga kan kayan kicin har zuwa kayan alatun more rayuwa. Tun ranar da Daddy ya bar gidan Baba Malam, bai sake waiwayowa ko ya kira shi a waya ba. Haka su ma suka duƙufa dai yin addu'a suna kai kuɗin sadaka masallatai, da makarantun islamiyyu da wuraren malamai a kan Allah ya warware matsalolin da suke tattare da Daddy. Cikin hukuncin Ubangiji watarana da daddare Daddy yana kwance, sai ji ya yi kamar an kwara masa ruwan ƙanƙara a kansa. Zumbur ya tashi zaune yana salati, Shukura da ke kwance ta ce. "Baby lafiya?" Cikin damuwa ya dafe kansa ya ce. "Wani mummunan mafarki na yi a kan Karima da yaran nan, wallahi na gansu a cikin mummunan yanayi." Gaban Shukura ne ya faɗi, amma sai ta dake ta ce. "To yanzu mene ne mahaɗinka da su da har za ka ɗaga wa kanka hankali." Da mamaki ya dubi Shukura ya ce. "Matar tawa kike faɗa mini haka a kanta da 'ya'yana, kin san me kike faɗa kuwa Shukura?" A wannan karon tsoron Shukura a fili ya bayyana, ta yi ƙarfin halin cewa. "Wace matar taka? Hajiya da ka daɗe da rabuwa ita, ai yanzu idan idda ce ma ta jima da gamawa yau wata nawa." A haukace ya dube ta ya ce. "Kin san me kike faɗa kuwa? Hajiya Kariman na saka?" "Ƙwarai kuwa, sai dai idan kai ne ba ka cikin hayyacinka, ko ka manta kai da bakinka ka ce mini ita da yaranta suna gidan Baba malam." Shukura ta yi maganar cikin gadara. Zumur ya miƙe ya zura doguwar rigarsa, sai kuma ya ɗauko wayar ya duba agogo ƙarfe biyu da rabi na dare. Lambar Baba malam ya lalubo ya latsa, har ta gama shiga ta yanke ba a ɗauka ba. A gaggauce ya sake kira, sai a wannan karon ya ji an ɗauka. Hankali a tashe ya ce. "Baba malam don Allah su Karima suna gidanka?" Cikin muryar bacci Baba malam ya ce, "Eh suna nan ya aka yi?" Ƙit Daddy ya kashe wayar, ya ɗauko mukullin motarsa da ke kan mudubi da sauri Shukura ta sha gabansa ta ce. "Wai ina za ka je da tsohon daren nan?" "Zan je na ɗauko iyalina." Daddy ya ba ta amsa. "Kutumar...! Saboda waccan tsohuwar kilakin za ka fita a tsohon daren nan? Ko ka manta yanzu babu aurenka a kanta? To ko kuma zaman dandi za ku fara..." Tass! Daddy ya wanke fuskarta da mari, cikin ɓacin rai ya ce. "Idan kika sake cewa matata tsohuwar kilaki wallahi sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Daga haka Daddy ya fice, ya nufi harabar gidan ya ɗauki mota ya fita. Hankali a tashe Shukura ta ɗauko waya ta latsa lambar Inna ta kira, daga can ɓangaren ta ji muryar mahaifiyarta cikin bacci ta ɗauka. Kuka da fashe da shi, hankali a tashe Inna ta ce. "Ke Shukura lafiya, ko jikin ne? Ina Alhajin yake?" "Inna aikin nan fa ina zargin ya karye." Shukura ta furta cikin kuka, Inna da ba ta fahimci komai ba ta ce. "Aikin me kuma?" "Asirin da muka yi wa Baby da Hajiya Karima mana, yanzu haka ya fice wai zai tafi dawo da ita gidan nan. Da na yi magana fa har da marina." Shukura ta ƙarasa maganar cikin kuka, nan take Inna ta wartsake ta ce. "Shukura an ya ba mafarki kika yi ba? Kin tabbatar da gaske ne?" "Wallahi ba mafarki ba ne Inna." "Ai kuwa mun shiga uku, wallahi zama bai ganmu ba. Bari zuwa safiya zan zo gidan." Inna ta faɗa cikin kwantar wa da Shukura hankali. A wannan lokacin haka ta zauna jigum, ta shiga tunanin nemawar kanta mafita. Don ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba. ALHAJI UMAR Daddy gudu yake yi tun iya ƙarfinsa kamar zai tashi sama, duk hanyar da ya bi idan jami'an tsaro suka tsayar da shi sai dai ya ce musu emergancy ne ya fito da shi ɗansa babu lafiya. Da an duba boot ɗinsa da cikin motar idan aka ga babu komai, sai a bar shi ya wuce. Yana zuwa ƙofar gidan Baba malam ya fara horn da ƙarfi, securities ne suka leƙo suka gan shi. Sai dai saboda tsaro ya sa ba su buɗe masa ba, ɗaya daga ciki ya nufi cikin gida yana ɗan bubbuga ƙofar. Da yake tun tashin Baba Malam da Daddy ya yi idonsa biyu, sai ya fito ya tambayi masu gadin. Yana jin an ce masa Daddy ne ya ce a buɗe masa gidan ya shiga, kamar wanda yake jira ana buɗewa Daddy ƙofa ya kunno hancin motarsa cikin gidan. Ko ƙarasa fakin bai yi ba ya fito ya nufi hanyar shiga cikin gidan, a bakin baranda ya samu Baba Malam a tsaye. Cikin tashin hankali ya ce. "Sannu da dare Baba malam, dama zuwa na yi na tafi da Karima." "Wace ce Karima?" Baba malam ya wurga masa tambaya fuska a haɗe. GIDAN HAFIZ Kamar yadda suka tsara Hafiz yana tashi daga kasuwa gidansu Bilkisu ya ƙarasa, mahaifinta dattijon arziki ne. Tarba mai kyau ya sa aka shirya musu kamar yadda ya saba duk shekara, sai da suka ci suka sha suka yi ƙat wurin sallar Isha'i sannan ya ɗauko Bilkisu suka taho gida. A lokacin da suka ƙarasa Amina tana zaune da su Sayyada a ɗakinta, yaran suna ta wasansu a junansu amma kallo ɗaya za ka yi wa Amina ka fahimci tana cikin damuwa. Saboda ɓacin rai ko da aka sha ruwa ba ta iya cin abincin kirki ba, ruwa kawai ta sha sai baƙin shayi. Tana zaune ta ji sallamarsu Hafiz, dariyar Bilkisu ta ji tana faɗin. "Haba kai kuwa Baby, ai dole kowaye ya ji daɗin abin da ka yi wa su Baba, Allah dai ya bar ƙauna a tsakaninmu." Zuciyar Hafiz ɗaya ya amsa da Amin, saboda shi ya yi tsammanin zuwansa shan ruwa gidan take nufi. Yaran suna jin muryar iyayensu suka fito a kuje suna yi musu oyoyo, rungume su Hafiz da Bilkisu suka yi. Sannan Hafiz ya ce. "Ina Auntynku ko tana cikin ɗaki." Sayyid ya gyaɗa kai ya ce. "Amma Aunty ba ta ci abinci ba, ruwa kawai ta sha." Da sauri Hafiz ya ce. "Kul, wa ya tambaye ka? Ba na son faɗar abin da ba a tambaye ka ba, koda wasa kada na sake ji." Daga haka ya ɗaga labulen ɗakin Amina ya shiga. Ita kuma Bilkisu ta ja hannun yaranta suka wuce ɗaki. "Maman baby barka da hutawa." Hafiz ya faɗa yana zama a gefenta, haɗe da ɗora hanunsa a kan cikinta. Ɗauke kanta gefe ta yi ta ce. "Barka." "Ko wani abu ne yake damunki?" Ya sake tambayarta. Girgiza masa kai ta yi, sai ya saki murmushi ya ce. "To a kawo mini abinci Gimbiya, kin san cewa na yi ba zan cika cikina ba sai na dawo gida na ci naki." "Ka kuwa yi wa kanka, don ni ban yi girki da ku ba. Tun da ka je gidan neman suna ai sai ka ci a can, sai dai kuma idan na sahur za ka jira." Amina ta yi maganar cikin fushi, da mamaki yake kallonta ya ce. "Ni kike faɗa wa haka Amina? Laifi ne don mahaifin Bilkisu ya gayyace ni shan ruwa? Kada ki manta koda ba Bilkisu nake aure ba, yana iya gayyatata tun da mahaifinta abokin mahaifina ne." "Ni wani abin na ce maka? Ko ka ji na yi maganar alaƙarka da ta mahaifinsu? Tun da dama ai da manufa a zuwan naka, wallahi duk abin da mutum yake yi Allah yana kallo." Amina ta ƙarasa maganar tana hawaye. Ransa ne ya fara ɓaci, amma ba ya san abin da zai kai ga ya biye mata don haka ya kwantar da murya ya ce. "Wai me ya sa kike yin haka Amina, ba fa yau mahaifin Bilkisu ya saba gayyatarmu ba. Don Allah kada wannan ya ɗaga miki hankali." A sheƙe Amina ta dube shi cike da takaici ta ce. "Wallahi bari ka ji Hafiz, Allah ɗaya za ka ce mini na yarda. Amma wallahi duk abin da kake faɗa sai dai na kalle ka, wai ni za ku yi wa bariki. Ai ita da yake matar so ce, kuma ana mutumta iyayenta ana daraja su ga shi nan ka narka iyayen kuɗi ka yi sayayya ka ba ta; ta kai gidansu. Ni kuwa da ke ba ka ɗauki iyayena da mutumci ba ko biyar ba ka ba ni ba, ai maganina kenan da na tambaye ka. Amma wallahi ka yi da 'yar halak, In Shaa Allahu tsinke na daina tambayarka." Tana gama faɗa ta fashe da kuka tana shigewa ɗaki. Da mamaki ya bi bayanta da kallo, shi kaɗai ya shiga nazari don gabaɗaya bai gane abin da take nufi ba. Jin kukanta yake har cikin ransa, har ya yi biris da ita sai ya ji ba zai daure ba, don haka ya shiga cikin ɗakin. Janyo ta ya yi jikinta ya ji zafi zau, cikin damuwa ya ce. "Haba Amina, ya ina yabonki sallah za ki kasa alwala. Don Allah me ya sa kike son ɗaga mini hankali muna zaune lafiya ni da ke." Amina ta goge hawayen idonta ta ce. "Dole ka ce zan ɗaga maka hankali mana Hafiz saboda ba ka ƙaunata, ai dama ba za ka ga rashin adalcin da kake yi ba. Dubi uban buhun kayan da ka turo wa Bilkisu ɗazu, ka ce ta kai gidansu na shan ruwa wai har da ɗan sahu ka turo a kai ta. Ni kuwa idan zan mutu da ciwo, idan za ni asibiti haka zan tafi na tari adaidaiata sahu a hanya." Tana gama faɗa ta ƙara rushewa da kuka. Shiru ya yi yana nazari, da sauri ya miƙe tsaye har zai fita ya dawo ya ce. "Ni aka ce na aiko da buhun kayan shan ruwa?" "Zan yi maka sharri ne? Wai Hafiz ni za ka mayar 'yar iska da ban san me nake yi ba?" Amina ta furta cikin fushi, jinjina kai ya yi ya ce. "Ta so mu je ina son yin magana da ku." Kamar Amina ba za ta miƙe ba, sai ta yunƙura ta tashi da ƙyar. Kai tsaye ɗakin Amina suka shiga, a lokacin ta gama yi wa yara shimfiɗa a ɗakinsu ta koma ɗakinta. Tana ganinsu a cikin ranta ta ce, 'Ai na san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya.' Amma a fili sai ta ce. "Abban Sayyid kune?" "Mune Bilkisu, zo ki zauna." Zama Bilkisu ta yi, Amina da fuskarta ta kumbura suntum saboda kuka ita ma ta zauna tana wurga musu mugun kallo. Hafiz ya dubi Amina ya ce, "Maimaita abin da kika faɗa mini." Tiryan-tiryan Amina ta sake faɗar abin da ta faɗa masa, ya ɗago ya dubi Bilkisu ya ce. "Bikisu ni da ke mun yi magana, a kan na aiko miki da kayan shan ruwa?" Bilkisu ta yamutsa fuska ta ce, "To dama ni na ce kai ka aiko ne, ke Amina hawainiyarki ta kiyayi rama ta. Sharri za ki yi mini ko haɗa ni faɗa za ki yi da mijina?" Kafin Amina ta yi magana Hafiz ya ce. "Ya isa haka." Waya ya zaro ya latsa lambar mahaifin Bilkisu, cikin girmamawa suka gaisa ya yi masa ban gajiya. Hafiz ya numfasa ya ce. "Baba don Allah wata tambaya gare ni, amma ba wani abu ba ne." Baba ya ce. "Yi tambayarka Hafizu." "Baba don Allah yau Amina ta kawo maka kayan shan ruwa ne?" Hafiz ya tambaya yana kallon yanayin Bilkisu da ta yi zuru-zuru. Baba ya ce. "Eh ta kawo mini kaya masu yawa, ta ce mini yayansu ne ya ba su kuɗi da kaya shi ne ta sayo ta kawo mini. Amma wani abu ne ya faru Hafizu?" Cikin girmamwa Hafiz ya ce, "A'a Baba, wata tattaunawa muke yi da ita ne. Na gode sosai Allah Yaa ƙara girma." Baba ya amsa sannan suka yi sallama. Da mamaki Hafiz da Amina suka dubi Bilkisu da ta yi tsumu, kamar an tsoma kaza a ruwa. Cikin gori Amina ta ce. "Amma dai wallahi kin ji kunya, girma ya faɗi raƙumi ya shanye ruwan 'yan tsaki. An girma dai ba a san an girma ba..." "Ya isa haka." Hafiz ya katse ta, sannan ta kira lambar Aunty Nana ya kai kunnsa. Sai da ya ji ta ɗauka sannan ya ce. "Aunty Nana da fatan ban katse miki bacci ba." Daga can ɓangaren Aunty Nana ta ce. "Ban kwanta ba Hafiz, an wuni lafiya ya iyali?" "AlhamduLillah, ya su Usaina?" "Duk lafiyarsu ƙalau, ina Amina da jiki?" Aunty Nana ta tambaya, sai da Hafiz ya amsa mata sannan ya ce. "Don girman Allah wata tambaya gare ni Aunty Nana." Jiki a sanyaye ta ce. "Wani abu ne ya faru Hafiz?" Hafiz ya ce, "Ba wani abu ba ne kawai tambaya ce da ni Aunty Nana." "Ina jinka Hafiza." Ta ba shi amsa. "Don Allah na taɓa zuwa na ba ki kuɗi, na ce ki yi wa Amina farfesun naman kai?" Hafiz ya furta yana kallon Amina. Ajiyar zuciyar Aunty Nana ya yi sannan ta ce. "Gaskiya ba ka taɓa ba, kwanaki dai Amina ta turo mini kuɗi ta ce a yi mata farfesu a kai mata..." Aunty Nana ta kwashe duk yadda suka yi ta faɗa masa. Godiya ya yi mata sannan ya katse wayar. Fuska a haɗe ya dube su ɗaya bayan ɗaya, ya nuna su da yatsa a haukace ya ce. "Wallahi duk wacce ta sake yi mini irin wannan makircin daga ranar zamana da ita ya ƙare, so kuka ku mayar da ni mahaukaci? Kun mayar da ni wani ɗan iska da za ku dinga raina mini hankali?" Ya furta a tsawace har sai da kowacce ta shiga taitayinta, don ba su taɓa ganin ya haukace musu haka ba. Ya miƙe tsaye jikinsa har rawa yake yi ya ce. "Duk faɗi-tashi da wahalar neman da nake yi ba a kanku nake yi ba? Amma za ku dinga caza mini kai, so kuke ku kashe ni da damuwa ku huta ko? Wallahi kun ji na rantse duk wacce na kuma samun ta yi irin wannan makircin sai ranta ya yi bala'in ɓaci. Makiran banza da wofi, an gaya muku yanzu ana irin wannam haukan kishin ne? Me kuka nema kuka rasa a wurina da za ku dinga raina mini hankali? Dama na yi wannan wayar ne domin na ƙure kowacce a cikinku, idan kun ga dama kada ku fasa. Na rantse da Allah daidaita nake da ku, sakarkarin banza da wofi." Hafiz yana gama maganar ya fice daga ɗakin rai a ɓace, daga Amina har Bilkisu kowacce shiru ta yi suka kasa magana. Jiki a sanyaye Amina ta miƙe ta koma ɗaki, tana zuwa ta ga kiran Aunty Nana ya shigo wayarta, sai da ta ɗauka sannan ta ji ta ce. "Amina lafiya mijinki ya kira ni yanzu yake tambayata? Kin san fa tun wancan lokacin na ce kada ki aikata abin da kika yi, wannan ba hanya ce mai ɓillewa ba kika dinga yi mini magiya." Cikin kuka Amina ta ce. "Wallahi Aunty ba halina ba ne, yau da gobe ta sa na ce bari na fara gwada abin da Maman Sayyid take yi. Amma In Shaa Allahu ba zan ƙara ba. Wallahi yau ba ki ga baƙaƙen maganganun da Hafiz ya faɗa mana ba." A ƙufule Aunty Nana ta ce, "Da kuka samu bai zazzage ku ba, wai me ya faru." Nan take Amina ta kwashe komai ta faɗa mata, cikin takaici ta ce. "Wa ya gaya miki idan kare yana haushi ana tanka masa? Ai Amina tun da kika gane halin kishiyarki sai ki ci maganin zama da ita. Ina hankali da tunani tare da tarbiyyar da kika samu? Wallahi da ace tana yi kina share ta yau da gobe dole ta gaji ta watsar, wallahi ki shiga hankalinki. Idan kila bari su Baba suka ji labarin makamancin abin da kika yi kin san sauran." Aunty Nana ta jima ta yi mata faɗa sannan suka yi sallama. Amina tana nan zaune tana jiran Hafiz ya shigo ta ba shi haƙuri, har bacci ya yi awon gaba da ita. Koda ta farka cikin dare ba ta gan shi ba, hankali a tashe ta ɗauko waya ta latsa lambarsa. Sai da ya ɗauka a ɗan rikice ta ce. "Habibi kana ina?" "Ina ruwanki da inda na je?" Ya bata amsa a takaice. "Don Allah kana ina?" "Ina ɗakin yara." Yana ba ta amsa ya katse wayar, hijabi ta saka ta fito ta shiga ɗakin su Sayyid. A can gefen yara ta hango shi a zaune ya rafka tagumi, cikin kwantar da murya ta ce. "Don Allah ka zo mu tafi ɗaki." Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya ɗago ya ce. "Kada ki wahalar da kanki Amina, ki bar ni a nan har sai na huce don kaina zan dawo. Idan kuma kika takura mini, wallahi idan na fice daga gidan nan ba za ku sake ganina ba." Duk yadda Amina ta kaɗa ta raya da Hafiz fir ya ƙi amincewa, haka ta haƙura ta koma ɗaki. Tun daga wannan ranar Hafiz ya koma ɗakin su Sayyid da kwana, a haka sai da ya shafe sati uku ba tare da ya koma ɗakin kowacce a cikinsu ba. Sai dai kowacce idan ranar girkinta ta zagayo, ta yi girki ta ajiye masa ya ci ya fita. Tun suna ganin abin Hafiz kamar wasa, har Amina ta samu Bilkisu ta ce su je su same shi su ba shi haƙuri. A lokacin Bilkisu taɓe baki ta yi ta ce. "Wallahi bai kai wannan matsayin ba, ke da za ki iya ba shi haƙuri kina iya zuwa don ni ba zan juri wulaƙanci ba. Duk haƙurin da muka ba shi a ranar da abin ya faru bai haƙura ba, tun da ba haifata ya yi ba ai sai dai mu dawwama a haka. Ba fa mu kaɗai muke da buƙata ba, shi ma ai taimakon kansa ne. Uwa-uba ma mace ai da jan aji aka santa, amma idan za ki je ga hanya nan." Ajiyar zuciya Amina ta yi ta ce. "To shi kenan, ai wai da gani na yi kamar ya dace mu je mu ba shi hauƙurin, amma bari mu gani a kwana biyu." Murmushin ƙeta Bilkisu ta yi a ranta, musamman da ta tuna ranar ita ce da girki. Daddare tun bayan Isha'i Bilkisu ta sheƙa wanka, ta yi gayunta cikin doguwar rigar atamfa. Ɗinkin ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, tun da Hafiz ya zauna cin abinci ta lura da satar kallonta da yake yi. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, sai da ta tabbatar da Amina ta yi bacci kusan sha ɗayan dare sannan ta sauya kayanta cikin wata figigiyar rigar bacci. Ɗakin su Sayyid ta shiga, ta hango Hafiz kwance a kan carpet yana kwance da kayan shan iska. A gefensa ta kwanta, cikin kissa mai jan hankali ta shige jikinsa. Ta kai bakinta saitin kunnensa ta ce. "Don Allah ka yafe mini Habibi, sonka zai kashe ni idan ka cigaba da azabtar da zuciyata. Ni kaɗai na san irin kewar da na yi duk tsawon waɗannan kwanakin." Ta ƙarasa maganar tana hura masa iska a kunne. Sannu a hankali yake jin saƙonta yana ratsa gaɓɓan jikinsa, don shi kansa ya san ba ƙaramin kewar matansa ya yi ba. Janye jikinsa ya shiga yi, don ba ya son nuna mata shi ma yana buƙace da su. Da sauri ta sake shigewa jikinsa cikin kukan kissa ta ce. "Ko za ka hukunta ni don Allah kada ka azabtar da ni ta wannan sigar, na saba da jikinka ba na son kana yin nesa da ni." Salonta ba ƙaramin rikita shi ya yi ba, a hankali ta fara yawo da hannunta a jikinsa. Tun yana jurewa har ya shiga mayar mata da martani, bakinta ta sake kai wa kunnensa ta ce. "Mu je ɗaki saboda yara." Bai musa mata ba, ya saƙalo ta suka wuce ɗaki sannan suka cigaba da farantawa juna rai. Bilkisu ta yi mamakin irin zafafan salon da Hafiz ya dinga yi mata, a nan ta fahimci ba ƙaramin kewarsu ya yi ba. Cikin dare suka wuce banɗaki suna riƙe da juna suka tsarkake jikinsu, a maƙale da juna suka koma bacci. Wurin gabannin asuba ta ji Hafiz ya sake kai hannunsa jikinta, cikin so da ƙauna suka sake farantawa junansu. A wannan karon ma tare suka shiga wanka, suna cikin banɗaki Amina ta fito za ta yi alwalar sallar asuba. Jin ana wanka ya sa ta dakata, don har cikin zuciyarta ba ta kawo komai ba. Tana nan tsaye Hafiz da Bilkisu suka fito suna riƙe da juna, Hafiz ya maƙale Bilkisu kamar wani zai ƙwace masa ita suka wuce ɗakin Bilkisu. Mun kusa kammala book 1 fa💃🏻 don haka masu son karanta book 2 su fara aiko da kuɗinsu, duk da masu himma tuni sun fara biya.💃🏻 Book 2 dai 500 ne idan ya zama document 800, za turo ta Acc. Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA SHA UKU Har suka shige ɗaki Amina ba ta daina bin su da kallon mamaki ba, jiki a sanyaye ta shige banɗaki tana sake jinjina girman makirci irin na Bilkisu. A haka ta ɗaura alwala, ta wuce ɗaki ta gabatar da sallar asuba. Lokacin da ta idar da sallah ta jima a zauna tana saƙa da warwara, don gabaɗaya kanta ya cushe. Sannan ba ta son ta yi abin da Bilkisu za ta ce ta kwaikwaye ta, tana nan zaune sai kawai ta dafe ciki da baya ta ƙwalla ƙara tana faɗin. "Wayyo Allah cikina." Hafiz yana daga ɗakin Bilkisu, da dawowarsa daga masallaci babu jimawa ya ƙaraso da sauri yana faɗin. "Amina! Lafiya, ko jikin ne?" "Wash cikina, wallahi ji nake kamar zan mutu." Ta furta tana satar kallonsa ta gefen ido, a hargitse ya sake tallafo ta ya ce. "Mutuwa Amina? Don Allah ba na so, ba na son ki dinga furta kalmar mutuwa hankalina tashi yake yi." Amina ta ja numfashi ta fesar tana yarfe hannu ta ce. "Wash! Hasbunallahu wa ni'imalwakil." A daidai lokacin Bilkisu ta ƙaraso ɗakin a yatsine ta ce. "Wai wanne irin ciwo ne da za a ce bai tashi ba sai yanzu da asuba." Ta yi maganar, saboda ta fahimci Amina ƙarya take yi. Don ta tabbata ganinsu tare da Hafiz ne ya sa ta yi yunƙurin yin ciwon ƙarya. A fusace Hafiz ya ɗago ya ce. "Haba Bilkisu, kina da imani kuwa? Ba ki ga halin da yarinyar nan take ciki ba?" Amina tana jin haka ta karyar da kai gefe ta ce, "Don Allah ka kai ni asibiti, ji nake ɗan cikina kamar zai birtso waje." A hargitse Hafiz ya ce, "Bari na yi wa maƙocina Habu magana, sai ya kai mu a adaidaita sahunsa." Yana gama maganar ya fice da sauri. Bilkisu ce ta riƙe ƙugu cikin tijara ta ce, "To munafuka algunguma, wallahi tun wuri gara ki ware. Don na san makircinki ne da munafurci ya sa kika yi ƙaryar ciwo." Amina ta dube ta tun daga sama har ƙasa sheƙeƙe, sannan ta miƙe tsaya ta yi taki biyu ta ce. "Ashe makiran suna da yawa, wai Bilkisu yaushe za ki sauya hali ne? Wallahi-wallahi zuciya ɗaya nake tare da ke, amma ƙarfi da yaji kin koya mini makirci da munafurci. Ƙiri-ƙiri na ce mu je mu ba wa Habibi haƙuri kika ce mini ba haka ba, ashe ni kika mayar 'yar iska. Tun da dai duk nasihar da ya yi mana ba za ki ɗauke ta ba, ni da ke mu zuba mu gani." "Ni kike cewa Bilkisu kai tsaye?" Bilkisu ta furta a ƙufule, Amina ta watsa mata harara ta ce. "Haifata kika yi da ba zan faɗi sunanki ba? Tun asali ina ba ki girma shi ya sa nake sakaya sunanki, amma tun da na lura ba zaman lafiyarmu kike so ba. Wallahi zan tafiyar da ke a yadda kika zo mini." Rai a ɓace Bikisu ta ce. "Sannu macijiya da ba ta ramin kanta, aikin kenan. Sai kun yi kwantai a gidajen iyayenku ku dinga aure mazajen wasu, ai wallahi na rantse da Allah sai kin yi nadamar auren mijina da kika yi. Saboda Hafiz nawa ne ni kaɗai, ƙaddarar da ta saka kika aure shi ita za ta sa na gasa miki aya a hannu." "Ai kuwa ni da ke sai dai mu gasawa juna, kuma dama can Hafiz ba mijinki ba ne ke kaɗai. Saboda Allah Ya ƙaddara masa auren mata har huɗu, ke ko yau zai kawo biyu ba zan ɗaga hankalina ba saboda na san kowacce mace da ƙaddararta. Kuma ki bar cika baki, saboda kema kina da 'ya'ya mata, idan Allah Ya ƙaddara musu auren masu mata za mu ga yadda za ki yi." Amina ta furta a fusace, Bilkisu ta yi saurin shan gabanta ta ce. "Mugun bakinki ya faɗa kanki, kin ɗauka yadda kika yi kwantai ta ƙare miki kika kasa samun mijinki sai na wata. Kin yi zaton kowa haka yake? Ai indai auren mijin wata ne baƙinciki da ƙuncin gidan miji yanzu kika fara gani." "Yanzu muka fara gani dai ni da ke, don babu abin da kika fi ni da shi wallahi. Duk tunƙahonki matsayinmu ɗaya, ke matarsa ce ni ma haka." Amina tun ba ta rufe bakiba Bilkisu ta ce. "Ƙarya kike wallahi, matsayina da na ki har abada ba zai zama ɗaya ba. Domin ni ce matarsa ta farko, ni na ɓare abina sabo kar a leda. Mahaifinsa da mahaifina aminaine, na san duk rintsi babu rabuwar aure tsakanina da shi. Ke kuwa gayyar tsiya arna a Idi, haka aka yayimo ki daga duniya aka kawo mana annoba gida. Ko yanzu zai iya rabuwa da ke, kuma ya zauna lafiya. Don ni da kika gani, na zama ƙadangaren bakin tulu ban fito ba sai da na shirya, na zama ƙasar saman kabari duk taƙamar mamaci sai na raɓe shi. Na zama kujerar zaman gida, ko an ƙi ko an so dole a zauna da ni." Bilkisu tana rufe baki Amina ta saki dariyar rainin hankali sannan ta ce, "Ai duk na banza ne, tun da kika kasa riƙe shi har ya fita waje ya nemo ni domin ya samu kwanciyar hankali. Da kin isa da isarki ai da kin dakatar da shi daga aurena, ba ki san sakaci na rashin gamsarwa da kulawarki ne ya sa shi auro ni..." A zuciye Bilkisu ta kai wa Amina mari, a daidai lokacin Hafiz ya kawo kai ganin haka ya sa shi shiga ɗakin da sauri ya ce. "Ke Bilkisu ba ki da hankali ne? Mace da ciki a jikinta kike marinta." "Na mara ɗin, ko za ka rama mata? Ni ka san irin magamganun da ta furta mini..." Tas! Ita ma Hafiz ya ɗauke fuskarta da mari. Amina da ke kwance a ƙasa ta saci kallon Bilkisu ta sakar mata gwalo, sai kawai ta fashe da kuka ta ce. "Wayyo Allah cikina za ta kashe ni." A hargitse Hafiz ya ɗago ta ya ce, "Sannu Amina, za ki iya tashi mu tafi ko na ɗauke ki." Kamar tana jira ta ce. "Jiri nake ji ba zan iya tashi ba, ga shi dukan da ta yi mini cikina ciwo yake mini." Hafiz ne ya ɗauki Amina cak zai fita cikin sauri Bilkisu ta tare ƙofar ta ce. "Wallahi babu inda za ka kai munafukar nan, kuma wallahi tun da ka mare ni sai na nuna muku ɗanyan kai." "Ki matsa na wuce Bilkisu kada ki ɓata mini rai." "Ba zan matsa ba." Bilkisu ta ba shi amsa kai tsaye, rai a ɓace ya sake cewa. "Ki matsa na wuce Bilkisu, wallahi idan kika bari raina ya ɓaci ba za ki ji da daɗi ba." "Wallahi sai dai ka yi duk abin da za ka yi amma ba za ku fita ba, saboda yau ranar girkina ce babu karuwancin da za ta nuna mini..." Bilkisu ba ta rife baki ba Hafiz ya hankaɗe ta ya wuce, daga can baya ta faɗi ƙasa warwasa don ba ƙaramij buguwa ta yi ba. Hafiz ya wuce da Amina ƙofar gida ya saka ta a Adaidaita sahu, sai da ya koma ya ɗauko katin asibitinta ya rufe ƙofar ɗakinta sannan ya fita suka wuce asibiti. Bilkisu ta jima a wurin tana kuka, sai da ƙyar ta yunƙura ta shiga ɗaki. Ta sauya kayan jikinta, sannan ta shirya yaranta ta tasa ƙeyarsu gidansu Hafiz. ALHAJI UMAR Da mamaki Daddy ya dubi Baba malam ya ce. "Yaya ina da Karima bayan wacce ka sani?" Fuska a tamke babu alamun wasa Baba Malam ya ce. "A da dai na sanka da Karima, amma a yanzu Karimar da na sani ba ka da hurimi da ita." "Don Allah Yaya idan wasa kake yi mini ka daina, wallahi tallahi hankalina a tashe yake. Ina son na ganta, saboda mummunan mafarkin da na yi a kansu." Daddy ya furta a hargitse. Kallon da Baba malam ya yi masa ne ya sa shi shiga hankalinsa. Ya nuna shi da yatsa ya ce. "Ni na yi kala da sa'anka ko wanda zai zauna yin wasa da kai? Kai Umaru! Kada ka raina mini hankali, Karima ba matarka ba ce. Ka koma can gidanka ka cigaba da zama da matarka, a yanzu haka tana gab da ɗaura aure. Idan kuma 'ya'yanka za ka karɓa, a yanzu zan shiga na taso maka su ka tasa ƙeyarsu a gaba ka tafi da su." Kafin Baba Malam ya gama magana tuni gumi ya wanke fuskar Daddy, hankali a tashe ya zube a gabansa ya ce. "Don girman Allah kada ka yi mini haka Yaya, wallahi ni ban saki Karima ba. Yaya ka yi mini rai, wallahi ji nake ba zan iya rayuwa idan babu ita ba." "Idan ka mutu kwananka ne ya ƙare Umaru, kada ka manta; a yanzu ba ni da uwa ba ni da uba. Don haka babu numfashin wani da zan rasa a yanzu, har ya ɗaga mini hankali. Ruwanka ne ka cigaba da rayuwa, ruwanka ne kuma ka zaɓi mutuwa. Amma ina me tabbatar maka, idan ka sake zuwa da maganar Karima gidan nan wallahi zan ba wa securities umarnin kada su bari ka sake shigowa." Baba malam yana gama magana ya shige ciki, da sauri Daddy ya bi bayansa sai dai kafin ya ƙarasa ya datse ƙofar. Daɓar! Daddy ya zauna a wurin yana jin duniyar gabaɗaya ta yi masa zafi. A nan barandar da Daddy ya zauna, yana nan zaune har aka kira sallar asuba, Daddy yana nan zaune Baba Malam ya fito zai tafi masallaci. A sanyaye Daddy ya ɗaura alwala ya bi shi suka wuce masallaci, sai dai kallon fuskar Baba malam da ya yi ya ji fargaba ta sake mamaye shi. A haka suka yi sallah suka dawo cikin gida, Baba malam yana gab da shiga cikin gida Daddy ya ce. "Don Allah yaya, don zatin Ubangiji ka..." "Umaru ba na son damuwa don Allah, yanzu haka kaina ciwo yake tun tashin da ka yi mini ina bacci. Ka je wurin matarka idan na yi nazari zan neme ka." Daga haka Baba malam ya wuce ya bar shi a tsaye. Kamar zai ɗora hannu a ka, haka Daddy ya wuce ya shiga mota ta nufi gida zuciyarsa a dagule. Lokacin da ya je gida gari har ya yi haske, a lokacin da ya shiga Shukura tana zaune a takure cikin damuwa. Tana ganinsa ta miƙe zumbur kamar marar gaskiya ta ce. "Baby ina fatan ka dawo lafiya?" "Eh." Kawai ya furta a taƙaice ya wuce ɗakinsa. Da sauri Shukura ta bi bayansa har ta shiga rai a ɓace ya ce. "Get out please, ba na buƙatar hayaniya." "Wai me kake nufi ne Alhaji? Ya za a yi a kan tsohuwar matarka ka dinga wulaƙanta ni. Wallahi ba zan ɗauka ba, idan ba za ka iya ba ka sallame ni sai ka dawo da ita." Shukura ta yi maganar cikin tsiwa, saboda sabon da ta yi. A fusace Daddy ya ɗago ya ce. "Idan haka kika zaɓa ki wuce gidanku, amma ki sani idan har bakinki ya sake furta magana marar daɗi a kan matata wallahi a bakin aurenki." A razane Shukura ta dube shi, jiki yana rawa ta ja ƙafa ta koma ɗaki. Sai da ta saka sakata sannan ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, a hankali ta janyo wayarta ta latsa lambar mahaifiyarta. Tana jin ta ɗauka cikin kuka ta ce. "Inna don Allah ki yi wani abu, wallahi da matsala." Daga can ɓangaren Inna ta ce. "Tun tasowa ta ban taɓa cin karo da matsala ba, don haka a yanzu ma ba zan ganta ba. Tun bayan sallar asuba na fito zuwa wurin malam, yanzu haka zan haɗa ki da shi a waya ki masa cikakken bayani." Bakin Shukura har rawa yake ta ce. "Ba shi Inna, maza ba shi don Allah." Tana faɗar haka ta miƙe ta shige banɗaki, don kada Daddy ya jiyo wayar da suke yi. Littafin kuɗi ne 500 idan ya kammala 800 ne. Za a turo a acc Aisha Adam 3090957579 First bank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624. Ummou Aslam Bint Adam🌚 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA SHA HUƊU Daga can ɓangaren Inna ce ta ba wa Malam waya, yana karɓa ya ce. "Yarinya faɗi buƙatarki." Kamar Shukura tana jira ta ce. "Malam duka aikin da ka yi mini a wancan karon ne ya lalace." "Yarinya aikinmu ba ya buƙatar garaje, ki yi mana bayani dalla-dalla ta yadda za mu san yadda aka haihu a ragaya." Malam ya faɗa a ɗan tsawace. Ta cikin wayar ta ji Inna tana faɗin. "Ke Shukura ki shiga nutsuwarki mana, ki yi masa bayani dalla-dalla yadda zai fahimta." Tsawa ta ji Malam ya buga wa Inna ya ce. "Tun kafin ki zo, muka san abin da yake tafe da ke. Kada ki sake cewa za a fahimtar da mu, domin mu masu sani ne. Kawai dai muna son ji daga gare ta ne, kin san waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi." Baki yana rawa ta ji Inna ta ce. "Tuba nake malam, a yi mini aikin gafara." Amsa mata ya yi, sannan ya sake yi wa Shukura magana. Tiryan-tiryan Shukura ta yi masa bayanin abin da ya faru, tun daga tashin Daddy daga bacci har zuwa dawowarsa. Sai da ya gama sauraronta sannan ya ce. "Haƙiƙa kishiyarki ta tashi tsaye ba da wasa ba, kuma wannan birkicewar da kika ga mijinku ya yi asiri ne ta yi masa." Shukura ta yi zaraf ta ce. "Ai wallahi na zargi matsiyaciyar nan." "To wannan ba damuwa ba ne, tun da kayanki suka tsinke a gindin kaba. Za a yi miki aiki iya aiki, amma fa sai kin zubar da kuɗi. Saboda aikin za mu yi da baƙaƙen aljanu, kuma su kansu za mu zubar musu da jini. Ragowar kayan aikin ma idan muka faɗa miki su, idan za ki shekara ɗari ba za ki same su ba." Ta ji malamin ya yi mata bayani. Cikin sauri ta ce. "A'a Malam, gara dai ka sayo da kanka. Ni kuɗi ba matsalata ba ne, nawa kake ganin za a bayar?" "Zan sanar da mahaifiyarki, domin ita ya kamata ta damƙa mini hannu da hannu." Amsa masa ta yi sannan suka yi sallama, sai bayan ta gama sannan ta fito ta koma kan gado ta kwanata. Tana jin damuwar da take ciki kusan kaso casa'in ta tafi, don haka ta samu bacci ya yi awon gaba da ita. ALHAJI UMAR Abin duniya ne ya haɗe wa Daddy, gabaɗaya komai ya fita daga rayuwarsa. Har ji yake yi, a kan Mommy matuƙar bai same ta ba zai iya rasa rayuwarsa. Babban abin da ya ɗaga masa hankali, har kawo wani lokaci mai tsayi Baba malam bai sake bi ta kansa ba. Idan kuma ya kira shi a waya ba ya ɗauka, haka ita ma layin Hajiya Karima ya kira babu adadi ta ƙi a ɗauka. Daga ƙarshe ma sai ya ji wayar ta daina shiga, da Momny ta ga ya ƙara sauya layuka yana kiranta da su, sai ta saka wayar a DND sannan ta samu lafiya da shi. Da Daddy ya ga ya bi duk wata kafa da zai samu Mommy bai samu ba, sai ya koma kiran ragowar 'yan'uwansa yana kai kukansa wurinsa. A ranar da ya kira yayansa Baba Yunusa ya gama zayyane masa damuwarsa, ba ƙaramin tausayinsa ya yi ba. Saboda ya san duk abin da ya yi a baya ba yin kansa ba ne. Cike da tausayin ɗan uwansa ya ce. "Umar wannan matsalar taka tana hannun Baba malam, saboda ni da 'yan'uwana ka san ba mu da hurumi a kan wannan maganar. Yanzu dai ka yi haƙuri, In Shaa Allahu zan gwada sa'ata na kira shi na ga ko zai saurare ni." Jiki a sanyaye Daddy ya taso daga gidan, bayan kwana biyu a tsakani Baba Yunusa ya kira shi ya ce Baba malam bai saurare shi ba. Tun Daddy yana ganin abin kamar wasa har aka sake shafe watanni a haka, duk wanda ya kira ya je wa da ƙorafin maganar Mommy sai dai ace masa ya bi ta wurin Baba malam. Wannan yanayin ya sake birkita shi, har zamansa da Shukura ya koma irin zaman doya da manja. Kwata-kwata ba ta ganinsa a gida idan ba dare ne ya yi ba, idan gari ya waye zai fice. Idan kuma ta matsa sai ya zauna a gida, ba shi da magana sai ta Mommy da iyalanta. Ga kaɗaici da ya dame ta, saboda gidan ya yi mata girma wani lokacin har tsorata kanta take yi. Musamman idan zuciya ta fara yi mata ayyane-ayyane, ga shi duk kuɗaɗen da suke kashewa a wurin malamai babu aikin da yake ci. A kan haka har faɗa suka taɓa yi da mahaifiyarta, saboda Shukura gani take kamar cinye mata kuɗi Inna take yi. Ita kuma Inna ganin bakin ƙoƙarinta take faɗi-tashi wurin bin malamai sai ya abin ya ɓata mata rai. Sai daga baya suka daidaita, ta cigaba da bata miyagin shawarwari amma babu wacce take mata amfani. Bayan kwana biyu da faruwar al'amuran, watarana da safe ciwon hawan jinin Daddy ya tashi. Hankali a tashe Shukura ta fita wurin mai gadi cikin kururuwa ta sanar da shi, da sauri ya shiga ɗakinta ya riƙo Daddy da ya fara fita daga hayyacinsa ya saka shi a mota. Da sauri Shukura ta shiga mazaunin direba ta tuƙa shi ta nufi asibiti da shi, cikin kulawa likitoci suka karɓi Daddy suka shiga ba shi agajin gaggawa. Sai da ta ga ya ɗan dawo hayyacinsa, sannan ta zame jiki ta fice daga ɗakin, ta latsa lambar Inna ta kira ta sanar da ita. Sai da ta gama sauraronta ta ce. "Wai Shukura me ya sa ba ki da wayo ne wani lokacin? Dama kin san haka jikinsa ya yi zafi shi ne ba ki sanar da ni ba? So kike mu gama ƙarar da gishirinmu a dahuwar ƙaho, ba tare da ya amfane mu da komai ba? Ko so kike mu yi wahalar hura wuta, zafin hayaƙi ya gama kashe mana idanuwa ba tare da mun sharɓi romon ƙahon da muke dafawa ba?" "To Inna ya kike so na yi? Ba fa ni na ɗora masa ciwon nan ba, duk ta sanadin tsohuwar matar nan yake neman kassara rayuwarsa. Wallahi ba na son na rasa Alhaji, saboda ba ƙaramin so nake yi masa ba." Shukura ta furta muryarta tana rawa. Dogon tsaki Inna ta ja sannan ta ce. "Wallahi kin ba ni mamaki Shukura, au ke da soyayyar gaskiya ce ta kai ki gidan? To ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni." Murya a sanyaye Shukura ta ce, "Ina jin ki Inna." "Har yanzu ba ki ci adadin kwanakin da na ɗebar miki a gidan Alhaji ba, duka-duka yaushe aka yi abin da mutuwa take ƙoƙarin hana mu rawar gaban hantsi? Ko fa haihuwar fari ba ki yi ba, idan ya mutu yanzu ribar me muka ci?" Inna ta furta cike da damuwa, kamar Shukura za ta yi kuka ta ce. "A'a Inna don Allah ki daina zancan mutuwa, ni dai tsakani da Allah nake son shi wallahi. Ina laifin abin da muke samu yanzu ma." "Shashasha! Ana nuna miki gabas kina cewa kudu ce. Yanzu dai abin da nake so da ke, ki shirya ki tafi gidan yayansa Baba malam ɗin, ki sanar da su rashin lafiyarsa. Sannan ki fashe da kuka ki nemi yafiyar Hajiyan da 'yan'uwansa, ni kuma duk abin da na zo asibitin na aikata a kanki kada ki tuhume ni. Duk a cikin plan ne, ke ko dawo da itan ne ki tsaya tsayin daka a dawo ita ai ribarmu ce." "Haba Inna, me kike faɗa haka? Gidan Baba malam fa? Kin san yadda suka tsane ni kuwa?" Murmushin manya Inna ta yi ta ce, "Yaro man kaza, kin san dai ba na ƙwaina ai sai da zakara. Kuma banza ba ta kai romo kasuwa. Tun da kika ji na faɗi haka ki bar ni mu tafi a haka, idan hagu ta ƙi ai sai mu koma dama. Tun da asirin ya ƙi ci, sai mu gwada kissa mu gani." Cikin damuwa Shukura ta ce, "Gaskiya Inna hankalina bai kwanta da wannan shirin ba, yanzu sai mu bari ya dawo da Hajiya ana zaune..." "Shukura kin san dai ba zan saka ki a hanyar da ba za ta ɓille mana ba. So nake mu dafa ta da ruwan jikinta, ta yadda za ta gwammace zamanta a waje saɓanin cikin gidan." Inna ta furta cike da kwantar da hankali. Murmushi mai sauti Shukura ta yi, sannan ta ce. "Allah Ya bar mini ke Innata." Inna ta amsa sannan suka yi sallama. Shukura tana shiga ta tarar har lokacin Daddy bacci yake, da yake allurar da suka yi masa mai ƙarfi ce. Kuma a wannan asibitin Daddy yake ganin likita, nurses ɗin ta samu ta ce musu za ta je gida ta dawo. Amsa mata suka yi, sai da suka kira wasu daga cikin ma'aikatansu suka zauna a wurin Daddy sannan ta wuce gidan Baba Malam. Shukura tana zuwa gidan Baba malam ta yi horn a bakin gate, mai gadi ne ya tambaye ta wurin wanda ta zo. Bayan ta sanar da shi, sai da ya ɗaga waya ya kira Baba malam ya sanar da shi sannan ya buɗe mata ta shiga. Duk da Baba malam ya ji ɗacin zuwan Shukura, amma ya bar ta ta shigo ne albarkacin tana auren ɗan'uwansa. Uwa-uba kuma ya sa an buɗe mata ne, don ya ji abin da yake tafe da ita. Shukura ta yi mamakin yadda mutanen gidan suke ta karrama ta, duk sai ta ji ta tsargu. Tana nan zaune Haidar ya shiga falon, wani mugun kallo ya wurga mata. Da sauri ta kawar da kanta gabanta yana faɗuwa, buɗe firji ya yi ya ɗauki ruwa ya yi gaba. Fitarsa babu jimawa Mommy ta shiga da niyyar cire wayarta a caji, kallon-kallo suka shiga yi wa junansu. Mama ba ta taɓa tsammanin Mommy za ta kula Shukura ba, amma sai ta ga ta saki murmushi ta ce. "Aunty yau baƙi ne a gidan namu?" Mama ta ce, "Eh wallahi, Shukura ce ta zo wurin Daddyn yara. Wai Daddyn Mami ne a asibitu ba shi da lafiya." Ɗan taɓe baki Mommy ta yi ta ce. "Oh dama fa haka ake ta fama, Allah Ya sawaƙe." Daga haka ta ɗauki waya ta nufi ɗakinta. Baba malam ne ya shiga cikin falon, Shukura tana ganinsa ta cigaba da share hawaye cikin shasshekar kuka. HAFIZ Su Hafiz suna zuwa asibiti likitoci suka shiga yi wa Amina tambayoyi tana ba su amsa, gwaje-gwaje suka yi mata suka tabbatar da cikinta lafiya ƙalau yake ba su ga wani abu da yake damunta ba. Sai kuma jininta da ya ɗan yi ƙasa kaɗan, abin da suka ce sun gani a jikin Amina kenan. Gudun kada Hafiz ya gano Amina, sai ta ce musu tana ɗan yawan ciwon kai. A nan suka sake ba su shawarwari a kan ta dinga samun bacci wadatacce, ta kuma dage da cin abubuwa da ke gina jiki. Suna fitowa daga asibitin ya ga kiran mahaifinsa, sai da suka shiga adaidaita sahu sannan ya ɗauka cikin girmamawa. Bayan sun gaisa Baba ya ce. "Hafiz kana ina ne?" Hafiz ya ce. "Baba yanzu na fito daga asibiti." "To idan ka gama ina son ganinka kai da Amina." Baba ya furta a gajarce, sannan ya katse wayar. Gaban Hafiz ne ya faɗi, don tun da ya ji haka ya san ba ya wuce Bilkisu ce ta kira ta faɗa masa wani abin. Ita kanta Amina sai da ta ji gabanta ya faɗi, da yake ba ta saba irin waɗannan ƙarairayin ba har gani take kamar idan suka je za a iya gano ciwon ƙarya take yi. Lokacin da suka ƙarasa gidansu Hafiz, su Sayyid suna tsakar gida suna wasa. Oyoyo suka yi masa, bayan da suka gaisa da mutanen gidan sannan suka wuce ɗakin Mahaifinsa. Tun da ya ga su Sayyada jikinsa ya ba shi Bilkisu tana gidan, sai da suka gaisa sannan Baba ya sa aka kira Bilkisu. Fuska a haɗe ta shiga ta nemi wuri ta zauna, Baba ya dubi Bilkisu ya ce. "Bilkisu maimaita mini abin da kika ce ya haɗa ku." Kamar tana jira, Bilkisu ta shiga wassafa jawabin abin da ya faru. Baba ya dubi Hafiz ya ce. "Shin abin da matarka ta faɗa haka ne?" Gyaɗa kai ya yi sannan ya cigaba da cewa. "Baba ni ban hankaɗe Bilkisu, saboda wata manufa ko don na wulaƙantata ba. Yanzu Baba saboda kwananta ne, sai ta ce ba zan kai Amina asibiti ba don ba ta da lafiya? Ita Bilkisun sau nawa idan kwanan Amina ne, za ta kira ni ta ce yaro ko ita ba lafiya amma haka nake fita na ba su kulawa." Ajiyar zuciya Baba ya yi ya ce. "A gaskiya Bilkisu ba ki kyauta ba, ko Hafiz ba ya nan ai ke mai kai 'yar'uwarki asibiti ne." Baba ya nuna Amina, sannan da sake kallon Bilkisu ya ce. "Ke Amina da Bilkisu na dawo gare ku, ku ji tsoron Allah a zamantakewarku. Ku sani duk wacce kuka cutar Allah ba zai bar ku ba, zan yabi Hafiz ba don yana ɗana ba. Amma ku sani yana ba kin ƙoƙarinsa a kanku, ku haɗa kanku ku rungumi mijinku ku zauna lafiya." Baba ya jima yana yi musu nasiha, har jikin Amina ya yi sanyi ta ji za ta watsar da duk wani zaman ƙarya da makirci da ta tsira. Ta saka wa ranta duk rintsi za ta cigaba da zaman haƙuri, da kyautatawa mijinta. Musamman da Baba ya nuna musu muhimmanci haƙuri da ladan da mace take samu ya yin ibadar aure. A kwanaki biyun da suka biyo baya, gidan Hafiz suna zaune lafiya ƙalau. Saboda Amina gabaɗaya ta zubar da makamanta, ta cigaba da zama da Bilkisu da zuciyarta ɗaya tsakaninta da Allah kamar yadda ta zo tun farko. Ita ma Bilkisu a haka nunawa ta yi kamar komai ya wuce, don haka ta dinga kwantar da kai har Hafiz ya gama sakin jiki gidansa ya zauna lafiya. Ana cikin haka kuma sai Bilkisu ta tsiro da wani sabon makircin, don har lokacin da cikin Amina ya tsufa ba ta cire rai da fitar da ita daga cikin gidan ba. Sabon layi Bilkisu ta saya ta saka a wayarta, idan Amina da Hafiz suna zaune sai ta tura mata saƙon soyayya. Idan ka ga irin saƙon za ka yi tsammanin saurayi ne ya turawa budurwrsa da yake tsananin so. Tun abin bai fara damun Amina ba, har watarana ta taɓa yin replay da cewar wrong number ne. Tun ana tura mata text har ta kai wani lokacin ana kiranta a waya, amma idan ta ɗauka sai ta ji an yi shiru. Tafi-tafi sai ya zamana idan ta ɗauka sai dai ta ji an ce ana sonta, ko an yi kewarta. Wani zubin har cewa ake yi an yi kewar ni'imarta. Tun da ta ji ire-iren miyagun kalaman, ba ta sake ɗauka ba. Kuma ba ta taɓa tunanin faɗa wa Hafiz ba. Ita kaɗai ta bar abin a cikin ranta, don ba ta ɗauka lamarin zai yi tsamari ba. Watarana da daddare Hafiz yana ɗakin Bilkisu yana cin abinci, sai ji ya yi ana ƙwanƙwasa ƙofa. Miƙewa ya yi ya fita ya buɗe ƙofar, wani almajiri ya yi gani da wata leda a hannu. Almajirin bayan ya gaishe shi ya ce. "Ai ko ni aka yi." "Kawo saƙon, waye ya turo ka?" Hafiz ya furta yana kai hannu zai karɓa, da sauri almajirin ya janye ya ce. "Mutumin ya ce kada na ba wa kowa sai Amina." Da mamaki Hafiz ya ce. "Wani ne ya turo ka? Wane ne shi?" Almajirin ya ce, "Eh wani ne a mota, ya ce na kawo mata." Zuciyar Hafiz ce ta fara tafasa, sai ya daure ya ƙwala wa Amina kira. Da ƙyar ta yunƙura ta taso, saboda yadda cikinta ya tsufa. Tana zuwa rai a ɓace Hafiz ya ce. "Ga aikenki nan sai ki karɓa." Da mamki Amina ta dubi Aljamirin ta ce, "Kai waye ya aiko? Daga ina kuma?" Almajirin ya waiga ya ce. "Wani ne a mota ya ce na kawo miki, ya ce a ce miki wanda ya ɗauko ki daga asibiti ne rannan. Wai ki kira shi idan kin ga wannan saƙon." Cikin mamaki Amina ta sake cewa. "Ni kuma? An ya nan aka ce ka kawo kuwa? Gaskiya ba nan ba ne." "Ni dai nan ya ce na shigo na kawo wa Amina." Almajirin ya faɗa, Amina za ta sake magana Hafiz ya ce. "Yana ina mutumin?" Almajirin ya ce, "Ai yana ba ni da ya ga na shigo ya tafi." Zuciyar Hafiz har ɗaci take yi ya kai hannu ya karɓi ledar ya ce. "Jeka kawai." Yaron ya juya ya fita, Hafiz ya buɗe ledar yana leƙawa. Farin hanki ya gani da turare, sai zoben azurfa da aka ƙawata mai ɗauke da alamun gift daha masoyi. Sai ya ga wani ɗan memo mai kyau, yana buɗe ciki ya ga an rubuta. ' _Ga ɗayar numberta nan, idan kin nemi waccan layin ba ki samu ba. Daga masoyinki da ke burin kasancewa da ke koda bayan kin haihu ne._' Nan take idanun Hafiz suka kaɗa jajir saboda tsananin kishi, kallon da ya wurga wa Amina ne ya sa cikinta ya karta. "Ina wayarki take?" Hafiz ya furta da wata irin murya, jikinta har rawa yake ta ce. "Ta...tat... tana ɗaki." Bai amsa mata ba ya wuce ɗakinta rai a ɓace. In Shaa Allahu gobe za mu gama book 1💃🏻👌🏻 Masu son karanta book 2 za su biya 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA SHA BIYAR BABA MALAM Da mamaki Baba malam ya dubi Shukura ya ce. "Lafiya dai na ga kina hawaye? Hajiya ko wani abin ne ya faru?" Ya tambaya yana kallon Mama da ke zaune a gefe, girgiza kai ta yi ta ce. "Babu abin da ya faru Alhaji, na ji dai ta ce Daddyn Mami yana asibiti babu lafiya. Ban sani ba ko jikin nasa ne, amma dai tun da ta shigo take hawaye." Baba malam zai yi magana Shukura cikin kuka ta ce. "Don Allah Yaya ku gafarce ni, ku yafe mini ku yafe wa Daddyn Mami. Wallahi yanzu haka yana can a asibiti rai a hannun Allah. Don Allah ka yafe mini Yaya, na san gabaɗaya kowa ya tsane ni saboda abin da ya faru." Jin rashin lafiyar Daddy ya sa gaban Baba malam ya faɗi, amma gudun kada ya nuna wa Shukura damuwarsa sai ya ce. "Tun daga haihuwar mutum dama ai ransa yana hannun Allah Shukura, Allah Ya ba shi lafiya. Batun tsana kuma da kika yi, duk cikinmu babu wanda ya tsane ki. Ƙarƙari dai abin da muka yi, mun dai tsani halinki ne." Shukura a cikin ranta ta ce, 'Ko ni ɗin kuka tsana kun yi ta banza, yanzu ma so nake na yi amfani da ku kafin buƙatata ta biya.' Amma a fili sai ta ce. "Dama na zo ne na nemi yafiyar Hajiyan Mami, wallahi na yi nadamar duk abubuwna da na aikata a baya. Don Allah Yaya ku yafe mana, wallahi sharrin shaiɗan da ruɗin ƙawaye ne." Shiru Baba malam ya yi ya ce, "Allah Ya yafe mana gabaɗaya, amma wannan ba magana ce da za a yi ta a taƙaitaccan lokaci ba. Muna buƙatar isasshen lokaci tukunna, idan ya so sai a tattauna abin da ya dace." Kamar mutuniyar kirki haka Shukura ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce. "Na gode Yaya, Allah Ya ƙara girma." Ganin ya yi shiru ta sake cewa. "Yaya don Allah ku taimaka ku leƙa a sibitin nan, Dadyn Mami yana jin jiki sosai." Karɓar adireshin asibitin ya yi, sannan ya ce ta wuce zai taho. Bayan tafiyar Shukura Mama ta dubi Baba malam ta ce, "Alhaji wallahi ban yarda da makirar yarinyar nan ba. Haka kawai nake ji a jikina ba da zuciya ɗaya ta yi wannan zuwan ba." Miƙewa tsaye Baba malam ya yi ya ce. "To ai kowa ya yi na gari kansa, idan ma da wata manufa ta zo Allah ya mayar mata da mugun nufinta kanta. Ki cewa su Mu'alim su shirya za mu je duba shi yanzu." Mama ta amsa masa sannan Baba malam ya wuce ciki don ya shirya. Sai da ya kira 'yan uwansa ya sanar da su, sannan ya fito shi da su Haidar da 'ya'yansa suka wuce asibiti. Kusan lokaci ɗaya motar Shukura da ta su Baba malam ta shiga harabar asibitin, saboda Shukura ta biya ta store ta yi musu sayayyar abubuwan da za a buƙata. Ganin ta taho hannuwanta ɗauke da manyan ledoji, ya sa Baba malam ya ce su Haidar da Mu'allim su karɓa, babu yadda Haidar zai yi don dai ya san ba shi da damar musawa. Amma da babu yadda za a yi ya karɓi kayan hannun Shukura, suna shiga reception suka hango Inna tana zaune jigum. Shukura tana ganinta har za ta mata magana, cikin zafin nama Inna ta tsinke da mari. Ɗgowar da za ta yi ta sake tsinke ta da mari, da sauri Baba malam ya matsa ya ce. "Subhanallah! Haba Hajiya ya da haka? Ba ki ga a yanayin da take ciki ba ne?" Inna ta fashe da kuka ta ce. "Alhaji ka bar ni na kashe yarinyar nan na huta da ta kaicin da ta ƙunsa mini, ashe dama kishiyarta Hajiya ba ta gidan? Sai ɗazu da ta kira ni take sanar da ni abin da ya faru. Wallahi Shukura ke dai ba ki da mutumci, albasa ba ta yi halin ruwa ba." Inna ta ƙarasa maganar tana sake kai wa Shukura duka, da sauri Shukura ta yi bayan Baba malama tana kuka saboda marin da Inna ta yi mata ba ƙaramin shigarta ya yi ba. Baba malam ne ya kare ta cikin lallashi ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri hajiya, idan ka ce za ka biye ta halin yara sai ka nakasa su a banza." Inna ta fyace majiya haɗe da rushewa da kuka sannan ta ce. "Alhaji yarinyar nan so take ta ɓata mini suna? Me ta aikata haka? Wallahi kin ci sa'a da Alhaji Ya ƙwace ki, amma wallahi idan ba ki saka Alhaji ya mayar da matarsa ba babu ni babu ke. Mara mutumci ina zaman-zamana za ki ja wa zuri'ata zagi, ke dai ba ki ji daɗin halinki ba." Inna ta furta tana sake kai wa Shukura duka. Da ƙyar Baba malam ya samu ya shawo kan Inna ta daina barazanar kai wa Shukura duka, haka a gaban kowa ta dinga jaddada idan Shukura ba tayi bakin ƙoƙari, ta saka Daddy ya mayar da Hajiya Karima ba za ta tsine mata. Wannan abin da ta yi ya sa mutane suka dinga yabonta, a ɓangare ɗaya suka dinga kallon Shukura a matsayin wacce take da uwa tagari amma ba ta yi koyi da ita ba. Lokacin da suka shiga ɗakin Daddy yana kwance ya ƙurawa saman silin ido, har suka ƙarasa wurin bai sani ba. Baba malam ne ya dafa hannunsa ya ce. "Sannu Umaru." A hargitse Daddy ya ɗago ya ce, "Yaya kai ne? Don Allah tare kuke da Karima?" Shukura da ke gefe ta ji wani abu ya daki zuciyarta, don ko mai irin sunan Mommy ba ta son ta ji an ambata. Baba malam ya ce, "Umaru ka nutsu don Allah, ba mu kaɗai ba ne a wurin nan. Ga yara ma sun zo duba ka." Sai a lokacin ya ɗago ya dubi su Haidar cike sa so. Su kansu ba ƙaramin kewar mahaifinsu suka yi ba, ganin ya rame sosai ya sa Haidar ya matsa kusa da shi jiki a sanyaye ya ce. "Sannu Daddy ya jikin?" Daddy da idonsa ya fara zubar da ƙwalla ya ce. "Haidar! Haidar ina Mommynku ko ba ta zo duba ni ba?" Gyaɗa masa kai Haidar ya yi ya ce. "Ta ce a duba ka, Mami ma ta ce gobe za ta zo duba ka." "Ai na warke Haidar, Yaya don Allah ka taimaka ka ce Karima ta dawo. Wallahi ban san lokacin da na sake ta ba, wallahi sharr..." Inna ta katse maganar Daddy sakamakon jifan Shukura da ta yi da takalmi ta ce. "Munafuka kin ji abin da mijinki yake faɗa ko? An ya Shukura zuciyar musulunci gare ki, wallahi tun wuri ki je ki nemi yafiyar mijinki, kuma ki bi duk yadda za ki yi ki sa ya dawo da matarsa idan ba haka ba wallahi kada ki sake takowa inda nake." Daddy har cikin ransa ya ji daɗin abin da Inna ta yi, Baba malam ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri haka, ba na jin daɗin furucin da kike mata." "Alhaji haushin yarinyar nan da nake ji, wallahi ji nake kamar na maƙure mata wuya ta mutu. Ace ki zo ki samu mace da mijinta sama da shekara ashirin, ki ƙulla makircin da za ki sa mijinta ya sake ta. Alhaji ta kyauta kenan?" Inna ta furta tana kumfar baki. Baba malam ya jinjina kai ya ce, "Ba ta kyauta ba, kin san ɗa ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba. Yanzu dai ki je gida ki huta Hajiya." Inna ta ƙarasa bakin gadon ta duba Daddy sannan ta yi musu sallama ta fita. Su Haidar ne suka fita waje, Shukura ta maƙure a bango ban da hawaye babu abin take yi. Daddy ya sauko daga gadon, ya russuna a gaban Baba malam ya ce. "Don girman Allah yaya ka taimaka ka dawo mini da Karima, wallahi tallahi ban san yadda aka yi na rabu da ita ba. Na yi rashinta a kusa da ni Yaya, don Allah ka tausaya mini." Daddy ya ƙarasa maganar yana hawaye, jikin Baba malam ne ya yi sanyi, zai yi magana Shukura ta matsa ita ma tana sake ƙwaƙulo hawayen munafurci ta ce. "Don Allah yaya ka taimaka mini, hankalina a tashe yake da jin furucin mahaifiyata a kaina. Don Allah yaya ka taimaka ka ba wa Mommyn su Mami haƙuri." Baba malam ne ya ce ta tashi ta zauna a kujera, saboda yanayin da take ciki tun da cikinta ya tsufa. Daga Daddy har Shukura zama suka yi dirshen suna ba shi haƙuri, sai da ya gama sauraronsu sannan ya ce. "Duk na ji maganganunku, to amma ku sani. Ba ni zan zauna da kai ba Umaru, Karima ce mai zama da kai, ita ta san irin zaman da ta yi da ku. Don haka sai da amincewar Karima sannan za a mayar muku da aurenku, idam ta yarda shi kenan idan kuma ba ta amince ba dole ku yi haƙuri." Bakin Daddy har rawa yake ya ce. "Zama ma ta amince In Shaa Allahu." "Allah Ya sa." Baba malam ya furta. A ranar Daddy ya matsa sai an sallame shi, sai da suka gwada shi suka ga jininsa ya ɗan daidaita sannan suka rubuta masa magunguna suka sallame shi. A daren ranar Daddy ya sheƙa wanka ya nufi gidan Baba malam da nufin ya samu ya shawo kanta. Tun da Baba malam ya ji zuwan Daddy ya sa aka aika kiran Mommy, sai da ta shiga wurinsa sannan ya ce. "Karima na san kin san duk abin da yake faruwa, a yanzu haka Umaru yana cikin gidan nan. Ya zo domin ya ba ki haƙuri a game da abin da ya faru, to ni yanzu a tsakiya nake. Ba zan goyi bayan Umaru ba don na tilasta miki ki komai gidansa, haka kuma idan kina son komawa ɗakinki ba zan hana ki ba. Umaru shi ne mijinki tun kuna saurayi da budurwa, ke kika san halinsa da irin zamantakewarku. Kada ki cuci kanki, idan kin ga za ki koma fani'ima, idan ba za ki koma ba shi kenan babu mai yi miki dole." Mommy ta jinjina kai sannan ta ce. "Haka ne Yaya, na gode sosai da wannan shawarar taka. Allah Ya ƙara girma." Baba Malam ya amsa mata sannan ya miƙe ya fita, tana nan zaune Daddy ya shiga bakinsa ɗauke da sallama. A kunyace ya zauna ya sunkuyar da kai ƙasa cike da damuwa ya ce, "Don Allah ki taimaka ki yafe mini Mommyn Mami, ni na san mai laifi ne don Allah ki yi haƙuri ki dawo domin mu rungumi yaranmu." Murmushin takaici Mommy ta yi ta ce. "Ai tuntuni na riga da na gama magana, Shukura ita ce matarka. Don haka ka je ka cigaba da zama da ita, ni kam na faɗa maka har abada na gama zaman aure da kai." Tana gama faɗar haka ta miƙe ta bar ɗakin, kamar ƙaramin yaro haka Daddy ya fashe da kuka. Yana cikin wannan yanayin Baba malam ya shiga, da mamaki yake kallonsa har sai da ya ɗan gimtse dariyarsa ya ce. "Umaru lafiya kuwa?" Daddy ya sharce hawaye ya ce. "Yaya Karima ta guje ni, wai ba za ta dawo gidana ba. Wallahi ba zan jya rayuwa babu ita ba." Sai ya sake fashewa da kuka, Baba malam ya saki murmushi ya ce. "To ai haƙuri za ka yi, yadda ka bi ka cunkusa mata kayan takaici a baya, haka za ka yi haƙuri ka yi ta lallashinta har ta sauko. Idan da rabon zama sai ka ga ta dawo maka, idan babu kuma sai dai ta auri wani." "Wallahi ba za ta auri wani mijin ba bayan ni, hauka ake yi matata Karima ta auri wani ƙaton. Wallahi kowaye sai na yi shari'a da shi." Daddy ya faɗa a ƙufule, Baba malam da ya lura kamar Daddy bai san maganganun da yake faɗa ba sai ya ce. "To shi kenan, yanzu ka je za mu yi magana da kai gobe." Da ƙyar ya lallaɓa Daddy ya tafi, bayan ya tafi Baba malam ya samu matansa ya dinga ba su labarin Daddy suna dariya, don Mommy ba ƙaramin birge shi ta yi ba. So yake ko za ta koma ta gara shi ya ji a jikinsa kafin ta koma. Cikin kwanaki biyu Daddy ya sake birkice musu, yadda ya ɗaga hankalinsa ba ƙaramin tausayi ya ba wa 'yan uwansa ba. Hakan ne ya sa suka same ta suka sake tausarta a kan ta yi haƙuri ta koma, a wani zuwa da Daddy ya yi ne ta ce masa ta amince. A lokaci har zuwa ya yi da sauri zai rungume ta, cikin sauri ta dakatar da shi da cewar. "Me kake shirin yi Daddyn Mami? Ko ka manta a yanzu ni ba matarka ba ce?" A ɗan kunyace Daddy ya sosa kai ya ce. "Ki yi haƙuri, wallahi na manta ne." Murmushi ta sakar masa, sai a lokacin ya sake ganin fara'arta tun barowarta gidansa. A washegarin ranar aka mayar wa Daddy da Mommy aurensu, su kansu su Haidar ba ƙaramin daɗi suka ji ba. Sai dai tariya ce Mama ta ce Mommy ba za ta koma a ranar ba har sai ta yi 'yan gyare-gyare. Satin da ya zagayo da na ɗaurin auren, a ranar Mommy ta koma. Abin da ya ba ta mamaki yadda ta ga Shukura tana ta haba-haba da ita, hatta abincin ranar ita ta girka ta kawo musu a ƙatuwar kula ita da yara. Murmushi Mommy ta yi ta ce. "Shukura kina fama da kanki har da wani girki? Sannu da ƙoƙari Allah Ya raba lafiya." Sunkuyar da kai Shukura ta yi ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri da abin da ya faru Mommy, wallahi sharrin shaiɗan ne." Mommy ta girgiza kai sannan ta ce. "Babu komai Shukura, Allah Ya yafe mana gabaɗaya." Daga haka Shukura ta miƙe ta fita, musamman yadda ta ga Daddy yana ta rawar jiki a kan Mommy sai zuciyarta ta hau suya. Tana shiga ɗaki ta datse ƙofa ta kira Inna tana hawaye ta ce. "Inna zuciyata za ta fashe, wallahi ba ki ga yadda yake rawar jiki a kanta ba." Daga can ɓangaren Inna ta yi murmushi ta ce, "Me ya sa wai kin fiye gajen haƙuri ne Shukura? Kada ki manta duk abin da nake yi a lisaafe yake. Ki duba ki ga yadda na sa suka yadda da ni, kowa gani yake ke ce ba ki yo halin kirkina ba. To yanzu ma so nake ki saki jikinki, ki nuna mata ke da ita duk ɗaya ne ta yadda za ki shiga jikinta. Sannan ina fatan duk abubuwan da na ce ki yi duk kin yi su? Kin san fa sune makamanmu na farko da za mu fara dasa bama-bamai a gidan." "Duk na kwaso su Inna, hatta ɗakinsa na shiga na ɗebi duk abin da kika ce. Ai bai san ina da mukullin ɗakin Hajiyan ba, na kai ɗakinta na saka don na san hankalinsu duka ba zai kawo komai a yanzu ba." Dariya Inna ta yi ta ce. "To ki rubuta ki ajiye, na rantse da Allah ba za a rufe sati guda ba, sai tarzoma ta tashi a gidan nan. Kuma ta cikin ruwan sanyi, za mu je har gida mu ci su da yaƙi." Shukura da Inna suka bushe da dariya lokaci ɗaya. GIDAN HAFIZ Jikin Amina yana rawa ta rufa masa baya, tana zuwa ta same shi a tsaye ya ɗauki wayarta yana dubawa. Gabanta ne ya shiga faɗuwa, yadda take jin jiri ya sa ta yi saurin zama a kan kujera. Ɓangaren kira ya duba, bai ga wani baƙon kira da ta yi ba sai wata lamba guda ɗaya. Yana dubawa ya ga a baya an kira ta ita ma ta kira, ɓangaren saƙo ya duba a nan ya ci karo da ire-iren saƙon da ake tura mata. Sai dai kuma bai ga ta mayar da martaninta ba, kansa ya ji ya sara masa. Idanunsa suka kaɗa jajir, jiki a sanyaye ya ajiye wayar. Ya mayar da kallonsa wurin Amina ya ce. "Amina da me na rage ki da shi a cikin gidan nan? Mene ne ba na gamsar da ke da har kika zaɓi cin amanata? Amina kina da aure da cikina kike soyayya da wani?" Jikin Amina ne ya shiga karkarwa, murya tana rawa ta ce. "Wallahi... ban... san komai ba Hafiz, na rantse da Allah ban san shi ba. Wallahi sharri ne..." "Uffan ba na son ji daga gare ki, munafuka maciya amana algunguma." Hafiz yana gama faɗa ya fita daga ɗakin, kai tsaye ya wuce ɗakin Bilkisu. Yana shiga ya zauna a kan kujera, ya zabga uban tagumi. Bai yi aune ba sai ji ya yi hawaye yana zuba, Bilkisu ta saci kallonsa sannan ta ce. "Abban Sayyid lafiya kuwa? Allah sa dai ba daga gida ba ne wani abu ya faru." Girgiza mata kai ya yi, muryarsa tana rawa ya ce. "Bilkisu me na rage ku da shi a cikin gidan nan? Mene ne nake tauye muku wanda ba na wadatar da ku da shi?" Bilkisu ta saki cokalin hannunta ta ce. "Wallahi babu komai Abban Sayyid, na rantse da Allah kafin a samu mijin nunawa kamar kai za a daɗe. Amma wani abu ne ya faru?" Girgiza mata kai ya yi ya ce, "Babu komai, wani abu ne kawai yake damuna." Shiru ta yi tana jin ɗaci a ranta, don ko kaɗan ba wannan hukuncin ta so ba. Suna nan zaune jigum-jigum, Amina ta shiga ɗakin cikin kuka ta ce. "Don Allah ka saurare ni Hafiz wallahi tallahi ban san komai a kai ba." "Amina kada ki sa na yanke hukuncin da ban yi niyya ba a kanki, ki fita ki ba ni wuri tun ranki bai ɓaci ba." Hafiz ya furta rai a ɓace. Ganin ya kuma harzuƙa ya sa ta ja ƙafa a sanyaye ta fita, da sauri Bilkisu ta ba ta ta ce. "Auntyn yara ni fa kun bar ni a cikin ruɗani, don Allah me yake faruwa." Amina ta fashe da kuka, sannan ta zayyane mata duk abin da ya faru. Da sauri Bilkisu ya ta shiga ɗaki wurin Hafiz ta ce, "Abban Sayyid don Allah..." "Bilkisu ba na son hayaniya don Allah." Hafiz ya dakatar da ita a fusace. Tun daga wannan ranar Hafiz da Amina suka shiga wani irin zama marar daɗi, tun yana fushi da Bilkisu a kan maganar da ta so yi masa har ya sauko. Sai dai kuma tsakaninsa da Amina ko gaisuwarta ba ya amsawa, idan ya kwana a ɗakinta ma sai dai ya ɗauki fulo ya fito falo. Idan yana ɗakin Bilkisu kuwa, haka za ta dinga jiyo hira da shewarsu. Kusan kullum Amina a cikin kuka take, sai dai lokaci-lokaci Bikisu tana zama ta yi ta tausarta tana ba ta baki a kan zamanta da Hafiz. Ana cikin haka, har watarana Amina ta tashi da ciwon naƙuɗa, a lokacin da ciwon ya tashi Hafiz ba ya nan. Don haka Bilkisu ce ta yi uwa da makarɓiya ta kai ta asibiti, sai da suka je ta kira Hafiz ta sanar da shi ta kuma kira 'yan'uwan Amina. Duk kusan lokaci ɗaya suka ƙaraso, da zuwansu babu jimawa nurses suka fito suka sanar da ta haifi jaririnta namiji. Har a ransa Hafiz ya ji daɗi, kuma ya nuna farincikinsa. Haka dangin Amina sai farinciki suke yi, ban Bilkisu da take sakin murmushin yaƙe. Don ji ta yi gabaɗaya ranta ya ɓaci, saboda ba ta taɓa tsanmanin Amina za ta haifi namiji ba. Bayan da aka gama gyara Amina da jaririnta ne aka ba su damar shiga, jaririnta ƙato tubarkallah. Kuma kallo ɗaya za ka yi masa ka ga tsananin kamar da yake yi da mahaifinsa, don haka Bilkisu kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta tana jin wani abu ya tokare ƙirjinta. Sai washegari aka sallami Amina, kuma a nan danginta suka ce za su tafi da ita gida ta yi wanka a can. Hafiz bai hana ba, don har a ransa dama ba ya jin zai iya cigaba da zama da ita. Ita kanta Bilkisu ba ƙaramin daɗi ta ji ba, don ta ci alwashin cimma manufarta kafin Amina ta yi arba'in. Hafiz ya haɗa mata kayan barka masu yawa gwargwadon ikonsa, bayan ya kai mata ita ma Bilkisu ta sayi atamfa da kayan jarirai kala biyu ta kai mata. Dangin Amina sun saki jiki da Bilkisu sosai, saboda yadda Amina take ba su labarin daddaɗan zaman da suke yi, musamman yadda suka ga ta yi hidima da Amina a lokacin haihuwarta. Ranar suna Hafiz ya raɗa wa jariri suna Muhammad, sai dai har kawo wannan lokacin babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsa da Amina. Ita ma kuma sai ta yi kamar ta sanarwa da 'yan uwanta sai ta haƙura, don gani take za su iya shawo kan matsalar daga baya. Tun safe gidan su Amina ya cika maƙil da dangi, 'yan'uwa da abokan arziki. Zuwa azahar aka cigaba da shagalin suna, mutane har maƙota saboda yadda aka cika. Haka Bilkisu ma da maƙotanta suka yi zuga cikin adaidaita sahu biyu suka je suna, daga ɓangaren 'yan uwan Hafiz ma duk sun yi kara sun kuma haɗa sha tara ta arziki. Wata baƙar mata ce a shekaru za ta yi arba'in, sanye da ƙaton hijabi ta shiga cikin gidan sunan. Tun daga soron gidan da fara faram-faram tare da haba-haba da mutane, aka dinga gaisawa da ita cikin karamci da mutumta juna. Har ɗaki ta shiga suka gaisa da Amina, ta shiga yi mata barka tana ta yaba kyawun da Amina ta yi. Amina ba ta san matar ba, sai ta yi tsammanin ko a abokan arzikin da iyaye ko 'yan'uwa suke mu'amala da ita ce. Suna nan zaune ƙawayen mahaifiyarta na makaranta suka shigo su da yawansu, gefe ta matsa suka shigo aka gaisa. Ta miƙa musu jaririn aka cigaba da hira, bayan ɗan wani lokaci Amina ce ta shiga banɗaki don ta gyara jikinta. A nan suka miƙe suka yi sallama suka fito tsakar gida, matar suka miƙawa jaririn. Don a tsammaninsu 'yar'uwar su Amina ce, kafin su gama rurumar saka takalmi cikin sauri matar ta saɓa jaririn abaya. Ta goya shi ta saki jihabin jikinta, tana ganin sun yi hanyar waje ita ma ta zura takalminta ta fice daga gidan. Sai da ta ƙarasa can titi, sannan ta samu mai mashin ɗin da suke tare. Da sauri ta haye suka bar unguwar, sai da suka yi nisa sosai. Sannan ta zaro wayarta ta kira layin Bilkisu ta sanar da ita unguwar da ta dosa. Shin mene ne dalilin Bilkisu da ta sa aka sace ɗan Amina? Kuma ina za a kai shi, me za a yi masa? Ya ya Amina za ta yi? Kuma wa zai wanke ta a wurin Hafiz idan wannan maganar ta fita? Idan Hafiz ya ji an ɗauke ɗansa wanne mataki zai ɗauka? Kada ku manta maza ba su da uzuri a kam yara ko kaɗan. Mene ne harsashenku game da ƙullin da Shukura ta ajiye? Shin za ta yi galaba a kan Mommy ko yaya? Shukura ta kwantar da kanta a wurin Mommy da dangin Alhaji, shin ita da Inna haƙarsu za ta cimma ruwa ko a wannan karon ba za ta yi galaba ba? To jama'a waɗannan amsoshin suna cikin littafi na biyu.🥱 ALHAMDULILLAH a nan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya, mai son cigaba zai biya ta wancan asusun. Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 [04/02, 14:12] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. TSOKACI: Labarin ya faru a gaske, sai kwaskwarima da na yi masa. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA ƊAYA Gumi ne yake keto mata ta ko ina, saboda yanayin tsananin zafin garin da ake busawa. Sai dai zafin da take ji bai kai rabin wanda yake ɗamfare a birnin zuciyarta ba, duba da zafi, zugi da raɗaɗin da ke kwance kane-kane a cikin ranta. Wanda a kullum cigaban da yake samu, shi yake kuma dakusar da ƙwarin gwiwarta. "Fauziya! Ke Fauziya, ki fito ki rufe mana gida. Kin san dai gidan matan aure ne, za ki bar mu a yashe salon wani ƙaton ya faɗo mana." Kiran mafarautar da A'ilo take yi mata, ya katse igiyar tunanin da ta zabarto ta ba tare da ta sani ba. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tsakar gida, tana shirin magana A'ilo ta sake katse ta. "Allah dai ya kusan raba yari da ɓarawo, don masifa a ce kullum sai ka kwanta a ishe ka da bige-bigen ƙofa. Haƙƙi dai na zaman maƙotaka, wallahi ana shiga haƙƙinmu. Baban Walid ya shigo tun ɗazu ki je ki rufe mana ƙofa. Idan mijin naki ya dawo, ki riƙe hannunsa ki kai shi har ɗaki. Don wallahi idan ƙaton mashayi ya sake faɗo mini ɗaki sai mun sheme shi." Ko kaɗan ba ta ji zafin maganganun A'ilo ba, domin kusan duk maganganunta a hanya suke. Don haka ta gagara furta koda kalma ɗaya, ta ƙarasa soron mai cike da duhu ta haska da 'yar ƙaramar wayarta ta rufe ƙofar. Sai da ta haska yaranta da ke kwance a ƙofar ɗaki, ta gyara musu kwanciya sannan ta koma ciki. Domin zafin da ake yi ne ya sa ta yi musu shimfiɗa a waje, kamar yadda ragowar matan gidan kowacce take yi wa 'ya'yanta shinfiɗa a ƙofar ɗaki. Idan dare ya tsala gari ya ɗan saki, sai kowacce ta mayar da yaranta ɗaki. A hankali ta zauna, bayan ta kashe fitilar wayarta ta latsa lambar mijinta Kabir. Sai dai tashin farko aka tabbatar mata wayar a kashe take, ta mayar da kallonta wurin agogon wayar ya nuna mata ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare. Gyangyaɗi take yi daga zauna, don haka ta kishingiɗa da gefen gadon. Don kada ta kwanta nannauyan bacci ya ɗauke ta, daga baya Kabir ya zo ya yi ta bugun ƙofa da ƙarfi yana ja mata zagi a wurin matan gida. Da yake baccin yana kanta, nan taka ya yi awon gaba da ita. "Wayyo Allah ƙafata! Mami ƙafata cinnaka ya cije ni." Kururwar Fatima ta katse mata daddaɗan baccin da ya yi awon gaba da ita, a gigice ta fita tsakar gidan ta shiga kiciniyar haskewa da hasken fitilar wayarta. Inun Fatima ya cika gidan, saboda azabar harbin kunamar da yake ratsa ta. "Mene ne Fatima? Me ya samu ƙafar ki?" Fauziya ta shiga jera mata tambayoyi tana haska ƙafar tata. Ba ta ga komai ba, sai dai wurin da Fatima ta riƙe ya yi wani irin ja. Da hannu ta janye ta gefe, sai kuwa ta ci karo da wata ƙatuwar baƙar kunama za ta gangara wurin da Na'ima take kwance. Da sauri ta suri wani takalmi da yake gefenta ta buga mata, nan take kunamar ta mutu. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, sai ta rasa taimakon da ake yi na gaggawa idan kunama ta harbi mutum. Ga Fatima da ke sakin kuka kamar za ta shiɗe, duk ta gama gigita ta. Hijabinta ta ɗauko, ta ɗauki Fatima mai kimanin shekara uku ta goya. Wani irin nauyi ta ji, saboda tsohon cikin jikinta da kuma goyon Fatima da ta yi. Kan mudubi ta fara dubawa saboda a nan take ajiyar kuɗi, amma ita kanta ba ta da tabbacin za ta samu kuɗi masu yawa. Naira ɗari biyu taci karo da ita, da sauri ta ɗauka ta fita tsakar gida, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Lawisa tana yin sallama. "Salamu alaikum. Lawisa! Lawisa." Cikin bacci Lawisa ta amsa mata, Fauziya ta gyaya goyon Fatima ta ce. "Don Allah ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Zan leƙa na miƙa Fatima kemis, kunama ce ta harbe ta." "Subhanallah kunama fa? To bari na dubo miki, amma dai ba za a samu dubu ɗaya ba." Lawisa ta furta tana daga ɗaki. Fauziya tana nan tsaye, Lawisa ta ɗaga labule ta miƙe mata kuɗin hannunta, "Fauziya wallahi ɗari da hamsin kawai aka samu ga ta." Fauziya ta karɓa tana faɗin. "Don Allah zan tura ƙofar gida idan na fita, koda na dawo idan an rufe Lawisa. An ce ba a son barin harbin kunama da sai na bari zuwa safiya." Lawisa ta furta, "Shi kenan sai kin dawo, Allah dai ya tsare mu. Wallahi shi ya sa kullum na kwantar da su Siyama hankalina yana wurinsu, wannan zafi Allah Ya sa mu ga wucewarsa lafiya." Fauziya ta amsa sannan fita. Kemis ɗin da ke bayan layinsu ta zagaya, tun ba ta ƙarasa ba ta hango shagon a rufe. Ta kalli yagulallun canjin hannunta ɗari. 'Bayan kemis ɗin Bala ina zan kai Fatima?'' Fauziya ta raya a ranta, sai wani tunani ya faɗo mata. Da sauri ta sake ɗaga waya ta kira lambar Kabir, amma har lokacin a kashe take. Don haka ta yanke shawarar zuwa shagonsu, don ta fi tunanin ba shi da caji ne ya sa wayarsa take kashe. Bakin titi ta nufa, a lokacin babu mutane sosai sai tsirari da suke kai-komo. Zuciyarta a cunkushe take tafiya, saboda kukan da Fatima take rairawa ga ciwon ƙafafuwa da bayanta suke yi. Ta ɗan jima a bakin titi babu adaidaita sahu, har ta yanke shawarar fara tafiya da ƙafa. Saboda shagon su Kabir ana iya zuwa da ƙafa, sai dai akwai 'yar tafiya sosai. Tana tafe tana saƙa da warwara a cikin ranta, ga shi duk lallashin da take yi wa Fatima ta ƙi yin shiru. Wani mai adaidaita sahu ta hango, da sauri shiga ɗaga masa hannu. Har ya wuce ta, ganin goyon da yake bayanta ya sa ya dawo. "Baiwar Allah wannan yarinyar da take kuka daga ina?" Mai ɗan sahun ya tirke ta da tambaya, yana wurga mata kallon tuhuma. "Yata ce, shagon Babanta zan je kunama ce ta harbe ta zan kai ta kemis." Fauziya ta furta a gajiya, kallon da yake yi mata na rashin yarda ya sa ta ɗan waiga ta ce. "Fatima ki faɗa masa me ya samu ƙafarki." Fatima ta sake sakin ihu cikin kuka ta ce, "Cinnaka mai allura ne ya harbe ni, wayyo Mami ƙafata. Don Allah ki cire mini allurar cinnaka." Sai da mutumin ya haska Fatima, sannan ya ga zallar kamar da suke yi da mahaifiyarta. Ya ce Fauziya ta shiga, bayan ta zauna ya wuce da su. Ba su yi wata tafiya mai mugun nisa ba suka ƙarasa, ta miƙa wa mai adaidaita sahu ɗari biyun don ya ɗauki kuɗinsa. Ya ce mata ta je kawai, bayan ta yi masa godiya ta nufi layin da shagon ɗinkin su Kabir yake. Tana gab da ƙarasawa shagon, ta ga wani ya fito daga ciki da mukulli yana shirin rifewa. "Assalamu alaikum." Fauziya ta yi masa sallama, mutumin ya amsa mata yana saka mukullin ƙofar. "Don Allah Kabir fa?" Kallon tsaf ya yi mata, yanayinta ya ga ba ta yi kama da masu karɓar ɗinki ba. Kuma koda ɗinkin za ta karɓa, tana mace har sha biyu saura yana ganin dare ya yi. "Hajiya lafiya?" Fauziya ta dafa bango a gajiye ta ce, "Matarsa ce." Sai a lokacin mutumin ya ɗan faɗaɗa fara'arsa. "Ah Allah sarki, ai ban gane ki ba. Wallahi Kabir ya fita tun bayan sallar isha'i, ni kaɗai na rage a shagon ni ma yanzu zan tashi." Wani abu ya tsaya a zuciyar Fauziya, amma don kar ya fahimci wani abu sai ta saki fuska ta ce, "To shi kenan na gode." Kamar ta karɓi aron kuɗi a wurin mutumin, sai kuma ta haƙura. Don ba ta san duk wani abu da zai taɓa mutumci, da martabar Kabir. Kemis ɗin da ta hango a farkon shigowarta layin ta nufa, ta sake zaro ƙaramar wayarta ta latsa lambar Kabir ko Allah zai sa ta shiga. Bugun farko ta ji an ɗauka, don haka ta yi saurin faɗin. "Hello." Ita ma sai ta ji an ce hello da muryar mace, amma sai ta yi tunanin ko network ne ya maimaita abin da ta faɗa. "Abban Na'ima kana jina?" Daga can ɓangaren ta ji an ja dogon tsaki an kashe. Dam! Gabanta ya yi wani mummunan bugawa, wanda ya sa juya ta fara zabarin ƙafafuwanta har take yunƙurin wurgar da ita. Da sauri ta sake latsa lambar amma sai ta ji ta a kashe, haka kawai ta ji zuciyarta tana yi mata wasu-wasin ko kuskuren lamba ta kira. Kamar wacce take bitar hadda, haka ta fara karanta lambar Kabir a fili tana saka wa a cikin wayarta. Ta sake latsa lambar ta kira saboda ta fita daga kokonton da take yi, amma sai ta ga duk lamba ɗaya ce da wacce ta kira da farko. Wani irin abu ta ji ya tokare mata maƙoshi da ƙirji, ta haɗiyi yawu mai ɗaci har ta ƙarasa shagon mai Kemis ɗin da yake ƙoƙarin rufewa. Da sauri ta ƙarasa ƙofar shagon tana faɗin. "Don Allah ka taimaka ka duba yarinyata kafin ka rufe, wallahi kunama ce ta harbe ta." Tausayinta ne ya kama shi, ya zare kwaɗon ƙofar ya koma ciki. Saboda tsabar gajiya, da ƙyar ta iya sauko Fatima ta miƙa masa. Bayanin abin da ya faru ta yi masa, sannan ya yi wa Fatima allurai. Ya ɗebo magunguna ya yi mata bayanin yadda za a ta dinga ba ta, jiki a sanyaye Fauziya ta ce. "To nawa ne kuɗin?" Sai da ya sake duba magungunan ya ce, "Hajiya gabaɗaya kuɗinki dubu huɗu da ɗari biyar." Kirjin Fauziya ya buga, ta dubi wayarta da ko dubu huɗu ba za a saye ta ba ta ce. "Don girman Allah ka yi mini wata alfarma, don Allah ka yi mini haƙuri zuwa gobe da safe. Yanzu haka shagon mahaifinta na zo ba ya nan, wallahi ɗari biyu ce kawai a hannuna." Cike da takaici yake wurga mata wani kallo, ya furta. "Haba Hajiya, yanzu ni kin yi mini adalci kenan? Tun farko ai da sai ki ce mini ba ki da kuɗi, ni ma fa ba shagona ba ne. Yanzu idan Oga ya zo me zan ce masa? Kin san dai gari ba gaskiya, magana ta Allah ba zan iya ba ki kayan dubu huɗu da wani abu ki tafi da su ba." Wayar hannunta ta miƙa masa ta ce, "Na san ban kyauta ba, amma don Allah ka yi haƙuri. Ga wayata ka riƙe, zuwa gobe In Shaa Allahu zan kawo maka cikon kuɗin..." "A'a gaskiya, ba zan karɓi wayarki ba. Zan dai karɓi magungunan, ki je gobe da safen sai ki kawo kuɗin. Idan ma ba ki dawo ba, ni a aljihuna na biya kuɗin allurar da na yi mata." Mai kemis ɗin ya katse ta yana kwashe magungunansa, sannan ya miƙe mata wayarta ya ƙoƙarin fitowa daga ciki. Duk yadda Fauziya ta kai ga roƙonsa fir ya ƙi amincewa, saboda ya jaddada mata shi ma ba shagonsa ba ne. Idan aka samu matsala a aljihunsa yake ciko. A wannan karon ma haka ta dinga tafiya a ƙafa, sai dai wannan lokacin har ta ƙarasa gida ba ta samu adaidaita sahu ba. Sai tsirarun motocin gida da suke kai kawo a titi. Ta ci sa'a kamar yadda ta janyo ƙofar haka ta same ta, ta yi mamaki sosai da har sha biyu da kusan rabi amma Kabir bai dawo ba. Ba yau Kabir ya saba kai dare da sunan yana shago ba, amma bai taɓa haure sha biyun da rabi na dare a waje ba. Wannan ne ya sake tabbatar mata da zarginta. "An ya Kabir ɗina zai iya zuwa wurin wata mace a tsohon daren nan?" Ta furta tana sake tuna muryar wacce ta ɗauki wayar. "Kabir ɗina babu macen da take gabansa." Fauziya ta faɗa tana girgiza kanta. Da haka ta miƙe ta sake yi wa su Na'ima shimfiɗa a tsakar ɗaki, ta kwantar da su don ta samu Fatima ta tsagaita da kukan. Bugun ƙofarsa ta ji, ta ji wani ɓacin rai ya lulluɓe ta. Kamar ba za ta tashi ba, tuna gidan ba su kaɗai ba ne ya sa ta yunƙura ta fita ta buɗe masa. Saboda haushinsa da take ji, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce ciki. Suna shiga ɗaki ta ɗebo kayan abincinsa ta ajiye ba tare da ta tanka masa ba. "Ummu banat lafiya kuwa? Na ga kamar ba yadda na saba ganinki ba." Kamar tana jira a ƙule ta ce, "Ta ya za ga gan ni dama? Bayan kana can wurin 'yanmatanka, yanzu Abban Na'ima cin mutumcin da wulaƙancin har ya kai ka tafi wurin wata har na kira ka ba ta waya." Idanunta suka ciko da hawaye tana jin wani maƙaƙi a cikin zuciyarta. "Ai duk wulaƙancin da za ka yi mini ban cancanci haka daga gare ka ba, amma babu komai akwai Allah." Ta ƙarasa maganar cikin shasshekar kuka. "Innalillah wa inna'ilaihir raji'un! Yanzu ni kike zargi Fauziya? Ni Kabir ɗinki kike zargi da yawon gidan 'yanmata? Yanzu ko wani ne ya jefe ni da waɗannan kalaman, ashe ba za ki iya wanke ni ta hanyar shaidata ba?" Shiru Fauziya ta yi tana mamakin kalamansa, tana kallon rainin hankalin da yake shirin yi mata. Ita kanta da wani ne ya sanar da ita abin da ta ji a lokacin, ba za ta taɓa yarda ba. "Kana nufin wacce ta yi mini tsaki ɗazu ba ka santa ba? Ko kana nufin ba wayarka ba ce? Don Allah Abban Na'ima kada ka mayar da ni wacce ba ta san me take yi ba." Kabir ya sake marairaice murya ya ce, "Haba Fauziya, mene ne nawa ba ki sani ba? Kina tsammanin akwai wata mace da zan ɓata lokacina a kanta? Wallahi abin da kike faɗa ban san shi ba. Haba Fauzeena, yau fa da farinciki na ƙaraso gida saboda 'yan canjin da na samo." Ya yi maganar yana sakin murmushi ya cigaba da cewa. "Wallahi yau aiki ne ya sha mini kai, mun jima ba mu yi ɗinki irin na yau ba." Girgiza kai Fauziya ta yi tana jin ɗaci a ranta, a ɓangare ɗaya tsoron Kabir ya fara kama ta saboda ita da Kabir ba sa ɓoyewa junansu komai. "Abban Na'ima yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki? Yaushe ka fara yi mini ƙarya?" Ƙirjin Kabir ya buga da ƙarfi yana shirin yin magana ta katse shi. "Ko minti talatin ban yi da baro shagonku ba, kuma an tabbatar mini da tun bayan sallar Isha'i ka bar shagon. Ashe kullum ninke ni kake yi? Ina nan yashe da baki ban sani ba." "To ai fitar da na yi daga shagon gidan Alhaji Musa na je, kaya na kai wa iyalinsa kin san duk cikin shagonmu ya fi yarda da ƙwarewa ta. To lokacin da na je ƙofar gidan na kira wayarsa a kashe. Da na ce a yi mini sallama da shi, sai yaran gidan suka ce yana ganawa da wasu abokan kasuwancinsa, sai dai da na jira su kammala. Ganin zaman ya yi yawa ya sa na bayar da wayata aka jona mini caji a gidan, lokacin da Alhaji ya sallame ni har na kusa zuwa gida, na tuna na bar wayata a gidan shi ya sa na koma na karɓo." Kabir ya janyo ledojin da ya shiga da su ya ce. "Ki dubi wannan sayayyar da na yi, duk da kuɗin da Alhaji ya biya ni ne. Wannan shinkafar kwano ɗaya ce, ga taliya da makaroni guda bibbiyu sai wake kwata da na ƙaro mana." Ya sake buɗe ɗayar ledar ya ce. "Wanna kuma fulawa ce kwano ɗaya, ga sabulun wanka da omo dama na ji kin ce za ki yi wanki. Sai biskit da alawar yara." Sai ya sakar mata murmushi ya miƙa mata wata ledar ya ce, "Ga shi har tsire na sayo mana mu da yara, kin ga da safe sai mu sha da shayi tun da har madara na sayo." Har a ranta ta ji daɗi, domin duk halin Kabir mutum ne da ya tsayu a kan ciyar da iyalinsa. Shi ba mai ƙarfi ba ne, amma indai a ɓangaren ciyarwa ne ko wani mai kuɗin ba zai nuna masa komai ba. Amma haka kawai ta ji zuciyarta ba ta aminta da abin da ya faɗa mata ba, duk da ta ji kaso mafi yawa na daga damuwarta ta yaye. "Ina jin a cikin gidan Alhaji ne aka ɗauki wayar da kika kira, amma kin san babu wata mace da zan ɓa ta lokacina a kanta. Haba Fauzeen KB, har kya kawo wani abu ki sa a ranki don Allah?" Jin sunan da ya faɗa mata ya sa ta saki murmushi, nan take ta aminta da shi. Ganin ya shawo kanta sai ya miƙe ya sauya kaya, ya zura jallabiyarsa ya ɗauki ƙatuwar butar da ke cike da ruwa ya ce. "Bari na watsa ruwa wannan zafin ya yi yawa." Har zai fita ta katse shi. "Yau fa kunama ce ta harbi Fatima a ƙafa." Da sauri ya juyo ya ce, "Garin ya ya?" Ya ƙarasa tambayar yana duba ƙafar da Fauziya ta haska masa. A nan ta sanar da shi duk yadda suka yi da mai Kemis, ya ɗan yi jim ya ce. "Wallahi ciki da waje dubu ashirin ne suka rage mini, nake son na adana ta na samu cikon dubu goma sha biyar na haɗa. Domin na sayi ƙofar da za a saka mana a ginin can. Ko ba mu samu ta ɗakuna ba sai mu yi haƙuri zuwa wani lokaci." Sai ya ɗan yi jim ya ce, "Amma daga wurinki babu wani abu da za a samu?" "Wallahi babu Abban Na'ima, sai dai zuwa gobe Dillaliya za ta zo mu ji nawa za ta yi wa firjin nan kuɗi, ni babban tashin hankalina wa'adin kwanakin nan da suke ƙaratowa. Tun da yau saura wata guda cif, kuma na tabbata Alhaji Mudi ba zai taɓa ɗaga mana ƙafa ba. Da ya zo ya yi mana korar kare gara na sayar da firjin, a yi abin da ba ya rage mu koma. Tun da ba wutar nepa muke samu ba, ka ga yafi ajiyar da ake yi da shi." Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce, "Allah zai kawo mana ɗauki, amma gaskiya ba na son ki sayar da firjinki Fauziya. Ki bari dai mu ga yadda Allah zai yi da mu, idan muka koma can wataƙila a dinga samun wuta sai ki yi sana'a da shi." Fauziya ta gurgiza kai, "Kai fa ka ce mana ya ce ranar da notice ɗinmu ya ƙare duk wanda bai tashi ba zai fitar masa da kayansa titi, tun da har muna da abin da za a ɗaga a sayar ɗin ya fi zaman wulaƙanci Abban Na'ima. Na gaji da gidan nan, na gaji da zaman takurar da nake yi ni da 'ya'yana a ciki." Fauziya ta ƙarasa maganar tana jin ɗaci a ranta. "To shi kenan Fauzina, amma dai aro zan karɓa idan Allah Ya hore na ba ki kuɗinki ko jari kya ja." Daga haka ya saka kai ya fice, ta bi bayansa da hararar wasa ta ce. "Ko ba aro ba? Lallai Abban Na'ima." Da yake hanyar banɗakin, da hanyar fita duka kusan hanya ɗaya ce. Da sauri Kabir ya yi soron gidan, ya latsa lambar Surry don tun bayan da ya baro wurinta ya saka wayar a blacklist ta yadda ko ta kira shi ba za ta yi ringing ba idan ba shi ya duba ya gani ba. Murya ciki-ciki ya ji ta ɗauka tana faɗin. "Na gode Kb har ni za ka yi blocking saboda ka koma gida, ai na gwada kiranka da wani layin na ji ya shiga." Kabir ya yi ƙasa da murya ya ce, "Kin san bala'in da kika kusa ɓallo mini kuwa? Wai Sury dama bayan kin shiga gida da wayata matata ta kira kin ɗauka? Gaskiya ban ji daɗi ba kada ki sake yi mini haka." Ganin ran Kabir ya ɓaci sai ta kwantar da murya cikin kissa ta shiga ba shi haƙuri, da yake duk ba a nutsuwarsa yake ba sai ta fahimci haka. "My Kb wai lafiya na ji muryarka haka? Kamar a tsorace kake?" Kabir sai da ya ɗan leƙa don kar ataho bai ji ba ya ce, "Ke ina soron gidanmu fa, yanzu haka wankan da kika jaza mini zan yi shi ne na raɓe a soro. Kin ga yanzu dai sai da safe, kada ta ji ni shiru ta biyo bayana." Har zai kashe ta shagwaɓe murya ta ce, "Baby don Allah kada ka fasa zuwa kai ni ganin ginin da kake yi mini, ka san yadda na gama ba wa ƙawayena labarin gidan kuwa? Gaskiya dole na yi bidiyo na nuna musu." Kabir ya saki murmushi ya ce, "Haba love, ai tun da na yi miki alƙawari kin san ba zan saɓa miki ba, yanzu dai ki yi bacci da tunanina..." Motsin da ya ji a bayansa ya sa shi saurin waigawa, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi sakamakon tozalin da ya yi da Fauziya. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [07/02, 10:10] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BIYU Irin kallon da take wurga masa, ya shi saurin sauke wayar daga kunne gabansa yana faɗuwa. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, tana bin sa da kallon tuhuma. Duk da ba ta ji wayar da yake yi ba, amma tana da tabbacin da mace yake yin wayar. "Abban Na'ima wankan kenan?" Fauziya ta furta murya babu walwala. Kallo ɗaya za ka yi wa Kabir ka fahimci ba shi da gaskiya, a ɗan diririce ya ce. "Wallahi wata amarya ce ta dame ni da kira, wai gobe ɗaurin aure ban gama mata ɗinki ba." A wannan karon ita kanta Fauziya ba ta aminta da shi ba, duk da a cikin duhu ne amma hasken fitilar wayar ta fallasa sirrin zuciyarsa. "Abban Na'ima!" Ta furta kamar za ta yi kuka, saboda sauye-sauyen halayensa a kullum ƙara ba ta tsoro suke yi. "Abban Na'ima, yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki?" Kabir da har lokacin ƙirjinsa yake bugawa, ya ɗago wayar da yake har lokacin bai kashe ba ya ce. "Ga ta ai ban kashe ba, kina iya yi mata magana Fauziya." Kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta karɓi wayar. Saboda ta fahimci kamar akwai abin da yake ɓoye mata. "Hello!" Fauziya ta furta cikin sanyin murya, daga can ɓangaren Sury ta amsa. "Uwar gida sarautar mata!" Kusan lokaci ɗaya zuciyoyin Kabir da na Fauziya suka buga da wani irin ƙarfi. "Ban da abinki uwar gida, Oga ai ba na ki ba ne ke kaɗai." Maganar Sury ta katse su, nan take jikin Kabir ya ɗauki karkarwa saboda ya yi tsammanin Sury za ta rufa masa asiri. Fauziya tana shirin yin magana Sury ta cigaba da magana. "Idan kika riƙe Oga ke kaɗai mu costomers ina muka kama? Kin ga gobe ɗaurin aurena, a haka ma sai magiya nake kada ya jirga ni, shi ya sa na kasa haƙuri na kira yanzu na yi masa tuni." A fili Fauziya ta sauka ajiyar zuciya ta ce, "Shi kenan, Allah Ya sanya alheri." Sury ta amsa da Amin, sannan ta katse wayar. Butar ya ɗauka ya wuce banɗaki, ita kuma Fauziya ta wuce ɗaki duk sai ta ji ba ta ji daɗin abin da ta yi masa ba. Fauziya tana da kishi sosai a kan Kabir, sau tari sai ta yi wani abin sai kuma ta ji ba ta kyauta ba. "Allah ka rage mini raɗaɗi da zafin kishin bawan Allahn nan, ina tsoron kada zuciya ta sa na fara zargin mijina." Ta furta a raunane. Washegari tun da gari ya waye, Fauziya ta fito ƙofar ɗaki ta fara haɗa musu kayan karin safe. Da yake kowacce abin girkinta yana ƙofar ɗakinta, kasancewar babu kitchen a gidan. Gidan da su Fauziya suke zaune, gidan haya ne mai ɗauke da ɗaukunan mata biyar. Kowacce daga mai yara biyu sai zuwa uku, kuma dukkansu ɗakunansu falle ɗai-ɗai ne sai banɗaki ƙwaya ɗaya da suke amfani da shi. Dalilin da ya sa su A'ilo suka kafa wa Fazuiya ƙahon zuƙa saboda, duk cikinsu mijinta ya fi nasu rufin asiri. Domin ta fi su yawan sauyin tukunya, don Kabir idan da 'yan kuɗi a hannunsa haka zai sayo musu nama ko kifi ko ba can mai yawa ba ta sarrafa. Kuma indai Fauziya ta yi sauyin girki duka sai ta zuba a 'yan robobi ta aika masu, saboda fita haƙƙin maƙotaka. Duk cikin gida Lawisa ce kawai ta su ta zo ɗaya, ba ta yi mata irin cin kashin da su A'ilo suke yi mata. Don haka Fauziya da Lawisa suka haɗa kai, su kuma su A'ilo suma su uku suka haɗe kansu. Da yake ita Lawisa ba ta da haƙuri, sai ya zama suna shakkarta don suna yi mata kan kara take yi musu na itace. Saɓanin Fauziya da ta kasance mace ce mai sanyi, tsananin haƙuri da kawaici. Duk abin da za su yi mata ko su yi wa yaranta, sai dai ta yi shiru idan kuma yara aka yi wa sai dai ta zaunar da su a ɗaki. Babu damar yaranta su fita wasa tsakar gida, sai yaran su A'ilo su doke su da yake kusan duk sun girme su. Ita kuma Fauziya ƙiris suke jira ta yi wani kuskuren, ko ta taɓa kayan wani daga cikinsu sai su hau ta da faɗa. Don haka gidan suke zaune kara zube babu haɗin kai, hatta shara kowacce sai dai ta share iya ƙofar ɗakinta. Banɗaki ma kuwa sai dai kowacce idan mijinta zai yi wanka, ta ɗauki buta ta je ta wanke masa. Shara ce kawai idan ta cika suke haɗawa, idan ta cika wannan ce za ta biya idan wani karon ta sake cika sai wata ma ta bayar da kuɗi a kwashe. Maman Sabir tun da ta fito tsakar gida take leƙen abin da Fauziya take dafawa, ana cikin haka Kabir ya fita ya sayo musu ƙwai guda huɗu. Nan take gidan ya cika da ƙamshin suyar ƙwai, baƙinciki da hassada suka ƙara cika zuciyoyin su. Bayan ta gama sai da ta gutsiri kaɗan-kaɗan ta saka a leda kowacce ta miƙa mata, sannan suka shige ɗaki ita da iyalanta suka karya. Da yake ranar Lahadi ce babu makarantar boko ya sa bayan sun gama ta yi wa yaranta wanka. Kabir ya ɗauki Fatima ya mayar da ita kemis, ya karɓo mata magunguna sannan ya wuce shagonsu na ɗinki. Su Fatima ne suka fita tsakar gida wasa, abin ka da yaro duk kyarar da yaran su A'ilo suke yi musu da sun ga suna wasa haka za su je su shiga cikinsu. Zaman su a wurin babu wuya kenan sai Nabila ta fisge abin wasanta a hannun Na'ima ta ce, "Umma ta ce na daina wasa da ku, babanku ɗan shaye-shaye ne." Duk da ba su san me kalmar take nufi ba, amma tun da suka ji suna yawan faɗa musu cikin tsangwama sai suka ƙyamace ta, Na'ima ta ɓa ta fuska ta ce. "Ba dai babanmu ba, sai dai babanku. Abi yana siyo mana alewa da biskit, ba ɗan shaye-shaye ba ne." Duk cikinsu Sabir yayan Nabila ya girme su, don kusan shekararsa goma. Ya fi su wayo don haka ya ce, "Ke mu babanmu ba ya shaye-shaye, Ummanmu ta ce mu daina wasa da ku kada mu zama 'yan'iska. Wai babanku har shiga ɗakin matan aure yake yi."Yaron ya ƙarasa magana yana dariyar tsokana. Abin sai ya yi wa su Na'ima ciwo, don haka suka shiga mayar da martani abin har ya zame musu faɗa. Suna cikin kokawa su Nabila suka tararwa Na'ima da duka, da ta ji zafi ita kuma sai ta ciji Hafsa a hannu. Nan take iyayensu suka fito, dama kamar jira suke yi. Cikin masifa Maman Sabir ta fisge Fatima tana ƙwalawa Fauziya kira, Fauziya da ke ɗaki ta yi saurin fitowa tana shirin yin magana Maman Sabir ta katse ta. "Wallahi wannan shi ne na farko na ƙarshe, ko da wasa idan Fatima ta sake cizar mini 'ya'ya sai na ɗauki hannunta na tura musu a baki sun rama. Ƙarya aka yi uban na su ba mashayi ba ne? Na ga rannan da ya yi mankas ɗakin A'ilo ya faɗa." Fauziya ta yi shiru ta rasa bakin magana, Lawisa ta ɗaga labule tana faɗin. "Haba ku kuwa kamar ba ku san faɗan yara ba har za ku shiga? Wallahi indai yara ne kuna zaune za su ba ku kunya..." A zafafe Abu ta katse ta. "Sai ki bari idan an ciji naki 'ya'yan sai ki faɗi haka, za ki fito ki yi wa mutane gwalangwaso. Don sun ce ubansu ɗan maye ne shi ne za ta cije su. Shekaran jiya waccan, ina ce butata ya ɗauka ya yi mini wurgi da ita ta fashe." Lawisa za ta sake magana Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta girgiza mata kai sannan ta ce. "Don Allah ku yi haƙuri, In Shaa Allahu ba za su sake cizonsu ba." Kusan lokaci ɗaya suka taɓe baki, Fauziya ta yi wa su Na'ima magana suka wuce ɗaki. Jiki a sanyaye ita ma ta wuce ɗaki, tana jin su A'ilo suna ci gaba da yadda mata magana da habaici haɗe da yin dariya. "Mami wai mene ne shaye-shaye? Me ya sa kullum su Sabir suke ce mana Abi yana shaye-shaye?" Tambayar Na'ima ta katse dogon tunanin da Fauziya ta faɗa. Ras! Ta ji gabanta ya faɗi, da sauri ta kamo hannunta fuska ɗauke da alamun tsoro ta ce. "Kul Na'ima yara ba sa faɗan irin wannan maganar kin ji! Babu kyau kada na sake jin kun faɗi haka." Lokaci ɗaya suka gyaɗa mata kai, sai Hidaya ta ce. "Mami to ki faɗa wa su Hafsa su daina faɗa kada Allah Ya ƙona su a wuta." Fazuiya ta yi murmushi ta ce, "Su ma mamansu za ta faɗa mu, sannan don Allah Hidaya ku daina zuwa cikinsu kuna wasa. Ba ga kayan wasanku nan ba, ku dinga zama a ɗaki kuna yi kun ji." Lokaci ɗaya suka amsa mata, tana nan zaune ta ji sallamar Sadiya facalarta. Daga wurin da take zaune ta amsa mata, Sadiya ta shiga tana faɗin. "Uwar huɗu, wai har yanzu ba za ki kotse ba ne?" Fauziya ta miƙa mata fulo ta ce, "Zauna uwar 'yan sa ido, ni kaina kullum jiranta nake yi." Sai da suka gaisa Fauziya ta ce, "Ina zuwa haka da tsakar rana?" Sadiya ta yi dogon tsaki tana kallon su Na'ima da ke wasa ta ce, "Ai tun da akwai radiyo mai jini dole na gyara zancan. Wallahi Fauziya komai ya yi mini zafi, kin san dai halin wancananka. Yau haka ya ƙare mini zagin cin mutumci, saboda kawai na ce ya biya ni kuɗaɗen da nake bin sa bashi. Ke dai shaida ce kin san ba yau ya fara zagin iyayena ba, ni ma yau na gaji na rama. Ke faɗa har sai da ya kaimu tsakara gida, shi ne fa o'o (Inna) ta shigarwa ɗanta suka yi mini zagin ƙare dangi. Abin da ya sake ɓata mini rai kwanana uku kenan ina zazzaɓi, kullum nace ya ban kuɗin magani sai ya ce mini yake ba shi da kuɗi. Amma ina duba wayarsa a chart ɗin da suke da budurwarsa, na ga ya tura mata dubu shida kuɗin ɗinki wai bikin yayarta ake yi." Sadiya ta furzar da iska mai zafi, tana tuna ɗacin abin da mijinta ya yi mata ta cigaba. "Kin san fa shi indai a kan 'yanmata ne duk arzikinsa a nan yake tafiya, ni kuwa ina gida ko oho wani lokacin na omon wanki ma gagarata yake yi." Fauziya ta girgiza kai cikin damuwa ta ce, "Ke ma Sadiya tun tuni kin san halinsa, da kin sani ba ki biye masa ba kun yi ba daɗi a gaban yara ba. Ita kuwa dama kin san yaranta ba sa laifi, kwanaki fa a gabanta ya mare ki amma sai cewa ta yi ai ɓata masa rai kika yi." Kamar Sadiya za ta yi kuka ta ce, "Idan ban biye masa ba Fauziya ya zan yi? Kina ga fa haka zai tsallake ya bar mu indai akwai tsaba babu ruwansa da kuɗin kayan mahaɗi, duk ni nake fafutukarsu. Ga shegen kule-kulen mata har da na hauka, don wallahi da kuɗin da yake kashe musu ba gara mu ya kashe mana ba." "Eh to haka ne, lamarin ne sai haƙuri kawai. Ni dai ta nan fanin sai dai na ɗaga hannu na gode wa Allah, domin gaskiya babu macen da ta sha gaban Kb da har zai tsaya ɓa ta lokaci a kanta..." Murmushin da Sadiya ta yi ya katse furucin Fauziya. "Ban ga laifinki ba, da kika faɗi haka. Domin ruwan da ya dake ka shi ne ruwa. Amma ni dai a wannan gaɓar da zamantakewata da Ali, ta koma irin da zaman cin kunamar ƙadangare. Na rantse da Allah ko me aka ce mini ya yi ba zan musa ba, ki bar cin alwashin namiji saboda ko yaya basa rasa 'yanmatansu ke dai ki ga rijalu kawai." Fauziya ta yi dariya ta ce, "A'a Sadiya, dole na bigi ƙirji wallahi ko a gaban mutanen duniya Kb ɗaya a cikin dubu, ya zamo mini tamkar zara a cikin taurari. Ni shaida ce wallahi-wallahi tun daga ranar da ya muka fara soyayya, har kawo yanzu babu macen da yake kulawa." Sadiya ta miƙe tana gyara hijabinta ta ce, "To ni bari na zo na wuce, ko ba komai mun ɗan tattauna na rage zafin da nake ciki. Kada na daɗe uwar masu gida ta fahimci na fita, na ƙara wani laifin." Har soro Fauziya ta raka ta, Sadiya ta yi ƙasa da murya ta ce. "Wai mutanen gidanku har yanzu zaman naku sai a hankali ne? Na ga da na yi sallama A'ilo ba ta amsa mini ba." Fauziya ta furta, "Hmmm ke dai bari, wallahi shi ya sa zaman gidan duk ya gundure ni." Fauziya da Sadiya sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Sai da ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta, shi ma Nazir ya tafi kasuwa. Sannan ta shige uwar ɗaki, ta buɗe drower kayanta. Daga can ƙasa ta zura hannu ta ciro 'yar ƙarama wayarta, ta koma gefen gado ta zauna sannan ta kunna ta. Ba a ɗauki lokaci ba wayar ta kunnu, nan take ta latsa wata lamba ta kira, daga can ɓangara aka ɗauka. "Barka da safiya sarauniyata!" Maimuna ta saki murmushi cike da kissa ta ce, "Barka dai jarumin jarumai." "Wai sai yanzu ya matsa ya ba mu wuri ne? Wallahi tun safe nake jin ƙishirwar muryarki." Jafar ya furta cike da sha'awa. "Hmmm to ya za a yi? Ka san abin ka da mai iyali ko ya fita ai dole sai na sallami yara." Jafar ya yi murmushi ya ce, "Me zan samu? Don wallahi yau kwana biyu kenan, na kasa kataɓus da waccan sakaryar." Dariya sosai Maimuna ta yi ta ce, "Wallahi babu ruwana, kai da Maman Nana." Jafar ya sake kwantar da murya cikin wani irin yanayi ya ce. "Moon!" Yadda ta ji ya ambaci sunanta ya sa har sai da ta ji tsikar jikinta tana tashi, ta janyo filo ta rungume cikin wata irin murya ta amsa. "Na'am Abban Nana!" Ajiyar zuciyarsa ta ji har a fili, ya sake narke murya ya ce. "Ba na son ki dinga kirana da wannan sunan, tun da ita ma waccen haka take faɗa. Don Allah ki saka mini sunan da zai dinga faranta mini rai." Maimuna ta lumshe ido, ta ɗan shagwaɓe murya ta ce. "Baby ya yi?" Shi ma sai ya yi irin muryarta ya ce, "To ya zan yi? A dinga faɗa mini hakan, amma dai har yanzu kin ƙi ki ba ni dama na nuna miki zallar soyayyar da nake yi miki a cikin zuciyata." Jafar ya sake kwantar da murya cike da shauƙi, kamar wanda yake waya da matarsa ya ce. "Moon! A gaskiya Naziru ba ƙaramin dace da sa'a ya yi ba. Wallahi da ace ke na fara gani kafin Sumayya, da babu abin da zai hana ban aure ki ba. Don Allah ki ba ni dama koda sau ɗaya na nuna miki salon tawa kulawar." Wani farinciki ne ya lulluɓe Maimuna, tabbas ko bai faɗa mata ba. Ta sha ji a bakin Maman Nana, cewar Jafar gwani ne a fagen kulawa da soyayya. Don da bakinta take ba ta labarin Jafar irin maza nan ne masu buɗaɗɗan ido, don cewa ta yi wani lokacin wayewarsa har tsoro take ba ta. A duk lokacin da Maman Nana take ba wa Maimuna labarin mijinta, sai dai ta yi ta sha'awa tana jin ina ma ita ce ta yi dacen samun miji wayayye mai rifin asiri kamar ita. Kafin daga baya kuma su tsunduma kogin soyayyar da suka yi nisan kiwo ba tare da sun ankare ba. "Moon! Ba ki ce komai ba." Jafar ya katse mata tunani, Maimuna ta yi murmushi sannan ta ce. "Ina tsoron kada Maman Nana ta gano mu, ka ga a cikin unguwa ɗaya muka." "Haba My Moon, ai dama ko don magulmata ba za mu haɗu a unguwa ba. Wallahi ko hotel zan iya kama mana..." Cikin razani Maimuna ta ce, "Hotel!" Kafin Jafar ya yi magana daga can falo ta ji motsi, da sauri ta katse wayar ta zare batirinta. Jikinta har karkarwa yake, ta tura wayar cikin drowerta. Tana waigowa ta ga Naziru yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirjinsa. "Maimuna da wa kike magana?" Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi, cikin firgici bakinta yana rawa ta ce. "Ni... ni... kuma?" Fuska ta ga ya ƙara haɗewa, bai tanka mata ba sai gyaɗa mata kai da ya yi. Kabir yana fita daga gida tun bai ƙarasa titi ba, ya kira Sury. Cikin muryarta mai fisgar hankalinsa ta ce, "Matsoracina! Wato sai yanzu ka samu damar fita daga gida?" Kabir ya saki murmushi ya ce, "Kin gan ki ko?" Sury ta ɗan haɗe fuska kamar tana gabansa ta ce, "Kb ni fa jiya abin da ya faru ka sa na fara jin tsoron ko yadarata kake yi. Ka duba fa ka gani tambaya ɗaya matarka ta yi maka amma duk ka birkice, yanzu a haka za mu yi auren har ka kai ni gidan da kake gini?" Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Haba baby, me ya sa kike kawo wasu-wasi a cikin soyayyarmu ne? Kin san dai ina sonki ina ƙaunarki. Ko soyayyar da na nuna miki jiya ya ci ki fahimci irin soyayyar da nake yi miki. Ki ajiye maganar aure, wannan wani lissafi nake yi a kansa kin san ke ba kalar zaman gidan haya ba ce." Sury ji ta yi kanta ya sake girma, ta lumshe ido cike da jin soyayyar Kabir tana sake nuƙurƙusarta. Domin Kabir irin mazan nan da suka iya nuna zallar soyayya, duk cikin samarin da ta yi babu wanda take yi wa mutuwar so kamar Kabir. Sun jima suna hira sannan suka yi sallama, suka tsayar da magana a zuwa bayan la'asar zai kai Sury gidan da yake gini ta gani. Har zai saka wayar a aljihu sai ya ha wata lambar ta shigo, guntun tsaki ya saki kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka. Yana ɗauka ya ji ta fashe masa da kuka, shiru ya yi yana jin kukanta har cikin jikinsa. "Kukan na mene ne?" Kabir ya furta cikin tattausan lafazi. "Na gagara jure rashinka ne, na gagara jure horon da ke raunatar da zuciyata. Kabir! Ka san na saba da hutawa a lambun ƙaunarka, sai da ka bari zuciyata ta yi nisan kiwo a ƙaunarka sannan kake ƙoƙarin fincike ta da ƙarfin tsiya. Me ya sa kake azabtar da ni Kabir?" Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Hafsa kenan! A kullum haka kike faɗa a fatar baki, amma kin gagara nuna mini zallar soyayyar da kike faɗa. Hotuna biyu kawai na ce ki ɗauka ki turo mini, amma kin ƙi yarda ko ba ki yarda da ni ba ne?" Jim Hafsat ta yi tana nazari zuwa can ta ce, "Shi kenan, zuwa dare zan turo maka matuƙar za ka sauka daga dokin zuciyar da ka hau." Kabir ya cije baki yana murmushin samun nasara ya ce, "Haba ko ke fa Hafsyna, da sai nake ganin kamar ni nake wahalar da kaina a kanki." Hafsa ta ce, "Hmmm ba za ka gane halin da nake ciki ba, yanzu dai yaushe za ka zo." Shiru ya yi yana nazari, don Sury ta kwaɗaitar da shi irin salon tata soyayyar. Kuma ko babu komai ya san idan ya kai ta kangon da yake gini, zai iya samun fiye da abin da ta yi masa a soron gidansu a daren jiya. Don haka ya ce, "Ammm yau dai gaskiya ɗinki ya yi mini yawa, saboda akwai kayan amaren da ban kammala ba. Bayan haka ma, Oga yana raba mana ɗinki saboda gobe za a tafi da su Abuja. Ina jin sai zuwa gobe za ki gan ni." Hafsa ta narke murya ta ce, "Wallahi na yi kewarka, kwana ukun da ka daina ɗaukar wayata ji nake kamar mun shekara ɗari uku." Kabir ya yi murmushi sannan suka cigaba da hira, bayan sun gama ya wuce shago. Bayin Allah wasa farin girki kenan, me kuka fahimta a game da rayuwar Kabir? Kabir yana da 'yanmata amma ya aka yi Fauziya ba ta sani ba? Kuma me kuke tunanin ya sa ta ba shi yarda 100% a kan babu budurwar da yake kulawa. Ga dai Maimuna tana soyayya da mijin maƙociyarta, shin wacce amsa za ta ba wa mijinta Naziru? Sai na ji daga gare ku.😄 Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [07/02, 20:00] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA UKU Tun da yamma ta kawo kai Sury ta fara doka wa Kabir kira, saboda zumuɗi tun bayan azahar ta gama shiryawa. Kasancewar akwai ɗinkunan da Ogansu ya tara na 'yan wunin biki ya sa shi tsayar da ragowar yaran shagon ya raba musu ɗinkunan domin su yi saurin gamawa. Wannan dalilin ne ya sa da Sury ta kira shi ya sanar da ita, ta ɗaga mata ƙafa ko zuwa gobe ne. Ko kaɗan ba ta ji daɗi ba don haka ta nuna masa ɓacin ranta. "Kb shi ya sa nake tsoron soyayyarmu, wallahi sai na ga kamar yaudarata kake yi. Na kai kwana nawa ina son ka kai ni na gano ginin nan, amma yanzu ka zo kana tsara ni." Kabir ya miƙe ya fita zuwa ƙofar shagon ya ce, "Kin gane Sury, wallahi da gaske nake yi miki. Amma tun da haka ne ki ba ni zuwa nan da bayan sallar magriba, duk yadda zan yi na san yadda zan ɓullowa Oga koda ban gama aikina ba." Sury ta ɗan yi jim sannan ta ce, "Amma ka san bayan magriba Yaya Umar ba ya barinmu fita, sai dai na san dabarar da zan yi masa." Kabir ya yi saurin faɗin, "Yawwa Suryna, kamar ba mace ba. Don Allah ki shawo mana kansa ba za ku daɗe ba, muna gama gani za mu wuce." Sai a lokacin Sury ta ji daɗi, ganin ya lallaɓa ta ya sa shi yim sallama da ita ya koma cikin shagon. Ɗinkin kusan mutum uku ne a gabansa, don haka ya ci gaba da ɗinkin cikin sauri don ba ya son abin da zai sake ɓata ranta. Girgiza kai Maimuna ta yi, don har cikin ranta gani take kamar Nazir ya ji kalaman da suke tattaunawa. Amma gudun ta yi saurin bada kai bori ya hau, ya sa ta ce. "Gaskiya sai dai idan kunnenka ne." Shiru ya yi yana kallonta kamar mai nazari, har sai da ta sake tsarguwa. Domin a lokacin da ya shiga ji ya yi kamar waya take duk da bai ji abin da take faɗa ba, amma da yake ya ga wayarta tun a falo sai ya basar. Yana shirin yin magana ta ce, "Ko dai waƙar da ka ji ina yi ce?" Cikin halin ko inkula ya ce, "Wataƙila! Ina wayarki take?" Ya tambaye ta don Nazir mutum ne mai bin diddigi da tsanani a kan iyalinsa. "Tana falo!" Ta ba shi amsa a taƙaice. Falo ya koma ya ɗauki wayarta, sai da ya yi shige-shige sannan ya saki muryarsa ya ce. "Wallahi mantuwa na yi, na manta hulunan mutane ɗauko mini suna drowerta." Sai a lokacin hankalin Maimuna ya kwanta, ta shiga ciki ta buɗe drowersa ta ɗebo masa hulunan ta ba shi sannan ya sake fice. Ajiyar zuciya ta sauke a fili, sannan ta furta. "Dole na sauya taku, tun da mutumin nan yana key da yake buɗe ƙofa. Ya zama dole na yi takatsantsan, idan ba haka ba a samu matsala." Gate ɗin ta sake komawa ta saka sakata a gidan, sannan ta koma ta zaro ɓoyayyiyar wayarta. Mayar da batirin ta yi bayan ta kunnata ta sake kiran Jafar. "Hello!" Ta furta cikin kashe murya. Daga can ɓangaren Jafar ya ɗauka murya can ƙasa, sai kuma ta ji muryar Abdul yana kuka. "Wai kana nufin ba ja fita kasuwa ba? Na ji kamar muryar Abdul ko?" Murmushi Jafar ya yi ya sake jan bargo ya ƙudundune, wani shauƙi yana fisgarsa a kan Maimuna ya ce. "Ya za a yi na iya fita? Bayan ina lulluɓe da bargon bege da kewarki. Don Allah Moon ki nemar mana mafita mana, ki tausaya mini wallahi muryarki ba ƙaramin gigita nutsuwata take yi ba." Shiru Maimuna ta yi, tana nazarin hanyar da za ta ɓullo musu domin ita kanta ta kwaɗaitu da ta ga irin soyayya da Maman Nana take faɗa mata. "Ka san dai halin Nazir mutum ne mai shegen kishi, ga shi da zargi da bin diddigin duk abin da nake yi. Kana ga hatta unguwa ba ya iya barina na je, shi yake kai ni duk inda za ni. Wallahi kaina ya kulle ban san ya zan yi ba." Nazir ya kwaɓe murya ya ce, "Wallahi ni sai na ga kamar ma ba kya jin irin soyayyar da nake yi miki. An ya kin san yadda zuciyata ta kamu da mutuwar sonki kuwa..." Salatin da Maman Nana ta saki ya sa Jafar ya yi sauri ɗagowa, nan take gabansa ya faɗi. Maman Nana da kishi ya gama tirniƙe ta ta ce, "Na gode Abban Nana, yanzu wulaƙanci da tozarcin naka ya kai har ka haye mini kan gado ka kira wata shegiya kuna waya da ita? Yanzu ka yi mini adalci kenan? Ashe duk alƙawarurrukan da kake ɗaukar mini na ƙarya ne." Sai kuwa ta fashe da kuka. Hamdala ya yi a ransa da ya fahimci Sumayya ba ta gane da wacce yake waya ba. "Don Allah ki yi haƙuri My love, wallahi duk wani abu da kika ji na faɗa wa yarinyar nan a fatar ba ki ce. Wata yarinya ce ta nace mini, ni kuma ba na son yi mata rashin mutumci kin san wulaƙanci babu kyau shi ya sa nake soj mu rabu lafiya." Wani irin mugun kallo tajw jifansa da shi, rai a ɓace ta ce. "Idan kai ba za ka iya yi mata rashinn mutumci ba hi zan iya, ka kira mini ita in zazzage ta ko wacece." Kamar gaske Jafar ya ɗago wayar ya kira ta amma sai suka ji a kashe, ya saki murmushi a cikin ransa. Ya rungumo Maman Nana ya ce, "Kin ji wayar a kashe take, amma riƙe ki yi blocking ɗinta da kanki. Dama ni ban taɓa kiranta ba, ita take kirana amma tun da an yi haka babu ni babu ita. Munafuka haka kawai za ta haɗa ni faɗa da iyalina ian zaman lafiya da ita." Har a ranta ta ji daɗi, don haka ma ta ɗan saki fuskarta. Ta karɓi wayar ta saka ta a blacklist, sannan ta ce. "Abban Nana wallahi wannan ita ce ta farko ta ƙarshe, kada ka mata kwanaki ma haka na yi yaƙi da kai a kan Fati wacce ka ce wai ƙanwar abokinka ce. Wa ya sani ba ko ita ce wannan, wai yanzu duk irin kulawar da nake ba ka amma sai ka kula 'yanmata." Maman Nana ta ƙarasa maganar cikin ɗacin rai. "Don Allah ki daina dawo da bara bana, waccan ta wuce kuma wannan ma In Shaa Allahu ta wuce ba zan sake ba." Ruwan wanka ta juye masa ta dawo ta ce, "Lokacin fitarka yana tafiya ga ruwan wanka can na juye maka." Yanayin da yake ciki na tunanin Maimuna ya sa shi janyo hannunta ya ce, "Wai kwana biyu ba ki da lafiya na ga ko gayyatata ba kya yi!" Murmushi ta yi masa ta ce, "Ai na ga ba ka dawowa da wuri ga gajiya shi ya sa." Da yake ta kwantar da Abdul ya yi bacci, sai bayan da komai ya gifta a tsakaninsu sannan suka faɗa toilet lokaci ɗaya. A gurguje ya shirya ya tafi kasuwa ganin har sha biyu saura, Maman Nana ta cigaba da aiki cikin sauri tana alla-alla ta gana ta leƙa gidan Maimuna. Tun lokacin da Maman Nana ta fara magana, Maimuna ta yi shiru tana sauraronsu. Lokacin da ta ji Jafar ya ce zai kira layin Maman Nana ta zage ta, sai ta yi sauri ta kashe wayar gabaɗaya. Haka kawai ta ji wani irin kishi ya rufe, ta shiga hango irin rarrashin da Jafar zai mata. Domin Maman Nana ta sha ba wa Maimuna labarin idan Jafar ya yi mata laifi matuƙar shi nw ba shi da gaskiya har kusan tsugunna mata yake yi. Sai da Jafar ya shiga mota yana driving sannan ya kira Maimuna amma sai ya ji ta a kashe, guntun tsaki ya saki ya ajiyw wayar sannan ya cigaba da driving. Sai da ya cikin shagonsu sannan yana duba wayarsa ya ga misscall ɗinta. Hannunsa har rawa yake ya kira ta ya ce, "Wallahi Sumayya ta yi bala'in ba ni haushi, ina tsaka da jin muryarki ta zo ta yi mini tsaye a ka." Ya yi maganar yana sakin tsaki. "Hmmm bayan da ka gama ba ta haƙuri kenan, ai na san yadda kalw bala'in jin tsoronta." Jafar ya saki dariya ya ce, "Kamar wani matsoraci, idan muka haɗu ai za ki gane ni jarumin gaske ne " Maimuna ta yi murmushi za ta yi magana ya katse ta. "Yanzu dai ba wannan ba, na lura haɗuwa za ta yi mana wahala. Amma me zai hana na saya miki babbar waya sai mu dinga chatting da ita, na fito na dinga ganinki ina jin daɗi ko na samu nutsuwa." Shiru Maimuna ta yi ta ce, "Kana ganin ba za a samu matsala ba?" "Matsalar me Moon? Ai kin ga wannan layin da muke waya babu wanda ya sanki da shi, kuma ke ba kowa za ki yi wa magana ba sai ni. Ba sai mu dinga magana ba." 'Maimuna me kike shirin aikatawa ne? Wai ko kin manta kina da aure?' Wata zuciyar ta raya mata a rai, sai ta ji sam zuciyarta ta mata babu daɗi. "A gaskiya sai na yi nazari, sai an jima zan dafa wa yara abinci." Jin sauyin muryarta ya sa shi saurin faɗin, "Lafiya My Moon, ko kina da wata damuwar ne? Turon lambar asusunki sai na turo miki dubu ashirin ko kati ki saka." Da sauri Maimuna ta ce, "Dubu ashirin fa?" Jafar ya yi murmushi ganin kamar tarkonsa ya kama ta ya ce, "My moon, na rantse da Allah, zan iya ɓatar da ko nawa ne a kan samun farincikinki. Idan ba za su ishe ki ba, ki faɗa mini sai na ƙara miki." Bugun ƙofar da Maimuna ta ji ana yi mata ya sa ta ce, "Ana buga ƙofa, zan turo maka account number." Daga haka ta katse, tana zuwa gate da ta buɗe ta ga Maman Nana ta shigo da alama ranta a ɓace yake. Kabir yana idar da sallar magriba, bai tsayana ko ina ba sai ƙofar gidansu Sury. Waya ya zaro ya kira ta, tana ɗauka ya ji muryarta a can ƙasa taha faɗin. "Mu gaɗu a bayan layinmu ta ɓangaren hannunka na dama, idan ka zagaya ka same ni a bakin layin ƙarshe." Kabir yana jin haka ya amsa mata sannan ya katse wayar, kwatancan da ta yi masa ya bi. Yana zuwa ya daidai wurin ya shiga waige-waige, daga bayansa ya ji ta ce. "Bai gane matarsa ba." Da sauri ya waigo, cikin mamaki yake bin sa da kallo. "Wai baby ke ce?" Sury ta saki murmushi ta ce, "To ya za a yi, ai idah hagu ra ƙi sai a koma dama. Ƙarya na yi zan je dubiya, shi ya sa na ɓoye niƙab ina zuwa bayan layi na saka. Yanzu dai mu yi sauri kada a ga na daɗe." Kabir ya kanne mata ido ɗaya ya ce, "To shi kenan amaryar Kb, amma daga jiya zuwa yau na yi kewarki." Bakin titi suka ƙarasa ya tsayar musu adaidaita sahu, shi kansa ya ji daɗin yadda Surayya ta ɓatar da kamanni. Domin har a cikin ransa yaja fargabar wani ya gan shi, kuma a yanzu kowayw ya gansu yana iya ce masa ƙanwarsa ce. Tafiyar kusan minti ashirin suka yi, da yake sabuwar unguwa ce gidajen tsilli-tsilli haka suke. Tun daga farkon layin Kabir ya ce mata. "Ki jira a nan zan je na buɗe ƙofa na shiga, bayaj wani lokaci zan taɓo ki a waya sai ki biyo bayana. Kin san mutane da munafinci, ba za a rasa 'yan tsurku ba. Kina miƙe layin nan da zan bi idan kika yi kwana gida na farko za ki ga ba fulasta ƙofarsa ta langa-langa ce." Sury ta amsa masa shi kuma ya yi gaba. Lokacin da Kabir ya shiga layin gidan babu kowa a waje, don haka jikinsa har rawa yake ya latsa lambar Surayya ya ce mata ta ƙaraso. Yana nan tsaye ta ƙarasa ciki, kunna fitilar wayarta ta yi saboda duhu ta shiga haske cikin gidan. Ciki da falo ne guda ɗaya, sai fallan ɗaki da banɗaki a ciki. A gefe banɗaki ne da kitchen sai ɗan ƙaramin tsakar gida. Kusan an gama komai, sai daɓe, fulasta, fenti, ƙofafi da winduna su suka yi saura. Farinciki ya sa Sury ta rungume shi tsam, tana faɗin. "Gaskiya gida ya yi masoyina, amma kana ganin wannan ƙarashen zai iya kai wata nawa baba gama ba?" Tun da ta rungume shi ya ji duk yanayin jikinsa ya canza, jikinsa a mace ya shiga yawo da hannunsa a jiki sa. Da wata irin murya ya ce, "Kin san samun namu lokaci-lokaci ne, amma dai ina fatan har aurenmy ba zai haure shekara ba." Ganin saƙon da take aika masa ya fara tasiri a jikinsa ya sa Sury ta cigaba shi ma yana mayar mata da martani. Dogon hijabin jikinta ya zame mata, dama Surayya kafin ta fito sai da ta faki idon mahaifiyarta ta zuro dogon wando da ƙaramar riga a ciki sannan ta zura zumbulelen hijabinta har ƙasa. Duk zuwan da Kabir yake yi wurin Sury wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, bayan rungume-rungume da shafe-shafen da suke yi wa juna. Don haka da ya ji Sury za ta zo ganin gidansa ya ci alwashin saninta a wannan ranar, yana tsaka da yawo da hannunta ya ci karo da abin da bai yi tsammani ba. "Mene ne wannan?" Kabir ya faɗa ransa a ɗan ɓace. "Gabannin magriba period ɗina ya zo!" Ta furta masa, don dama ta ƙi faɗa masa ne saboda kada ya fasa kawo ta. Domin ta san matuƙar suka zo gidan ta san sai ya nemi koda taɓa wannan ɓangaren ne. Cikin wata irin murya ya raɗa mata a kunne, "Yanzu ya za ki yi da ni?" Murmushi ta sakar masa ta ce, "Dabarun mu na mata mana, ko ba ka san idan macen aure tana wannan halin akwai dabarin da take yi ba." Ya sani sarai, domin Fauziya duk a halin da take ciki tana ƙoƙarin faranta masa. Amma shi sam ba haka ya so ba, ita ma Sury ta fahimci haka amma ta basar. Babu kunya Surayya ta shiga sarrafa shi, tamkar yadda macen aure take yi wa mijinta. Suna cikin wannan yanayin kiran Fauziya ya shigo cikin wayarsa, kamar ba zai ɗauka ba tuna matsalar da aka samu a daren jiya da ta je shagonsu aka ce ya fita da wuri ya sa ya ɗauka don ya ji abin da ya faru. "Hello!" Daga can ɓangaren Fauziya ta ce, "Abi barka da yamma!" Ya ɗan yi gyaran murya don ka da ta fahimci sauyinsa ya ce, "Barka dai Ummu Banat, ya jikin?" Ta amsa masa tana wurga masa tambaya. "Amma ba ka shago ko? Na ji ban ji ƙarar ɗinki ba?" Duk da ya san zai yi wuya Fauziya ta gane a inda yake, amma sai da ya ji gabansa ya faɗi. Ya janye jikinsa daga jikin Surayya yana faɗin, "Na'am eh na je karɓo wa oga kayan ɗinki ne, ina zuwa an zo kaina." Daga haka ya katse, tun da ya fara waya Surayya take wurga masa harara tana shirin yin magana ya ce. "Ayi mini afuwa." Juyar da kai gefe ta yi cikin fushi, ya shiga lallashinta sannan Surayya ta cigaba da sarrafa shi. Sai da suka ɗauki lokaci a haka sannan Kabir ya samu nutsuwa, da yake gidan akwai rijiya sai kawai ya ja ruwa da gugura ya yi wanka da ita sannan suka fito daga gida. A yi haƙuri da error ban yi editing ba🫠 Ummou Aslam Bint Adam🌚 +2347062062624 [09/02, 20:22] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA HUƊU Fauziya tana gama waya da Kabir ta tashi da sauri ta faɗa banɗaki ta sheƙa wanka, bayan ta fito ta ciro wata doguwar riga ta saka. Jikin rigar roba ce, ba ta da tsayi har ƙasa. Daga iya gwiwarta ta tsaya, ta ɗauko kum ta fara gyara gashinta. Fauziya irin dogayen matan nan ne, sai dai tana da ɗan kauri. Tana da ƙira sosai sai dai ba fara bace tas, tana dai da haske da kuma yalwar gashi. Faka gashinta ta yi jelar ta sauka har gadon bayanta, ta ɗebi turarruka masu ɗaɗin ƙamshi ta feshe jikinta da su. A gaban mudubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, su Na'ima sai zagaye ta suke yi suna cewa ta yi kyau. Ita kanta ta san ta yi kyau, don haka take ta ɗokin Kabir ya dawo ya ga kwalliyarta. Dafa tsohon cikin jikinta ta yi ta saki murmushi, domin ta san Kabir mutum ne mai san ƙananan kaya. Jin kiran sallar Isha'i ya sa ta saka zumbulelen hijabinta har ƙasa, ta tasa su Na'ima suka gudanar da sallar Isha'i. Bayan sun idar sai da ta yi wa yaran tilawar Alƙur'ani, sannan ta zuba musu abinci suka ci. Da suka gama suka ɗan yi wasa sannan ta yi musu shimfiɗa a tsakar ɗaki, don ta ci alwashin duk zafi ta daina fitar da su waje. Kabir da Sury tare suka tafi har unguwar su Surayya. Ita ta sauka ta wuce gida, shi kuma ya wuce shagonsu. A lokacin da ya koma Ogansu ba ya nan, don haka shi ma bai zauna ba ya fice daga shagon. A madadin ya wuce gida yana fitowa sai kiran abokinsa Abbati ya shigo masa. "Ya Abbati kana iya?" Kabir ya furta bayan ya ɗauki wayar, daga can ɓangaren cikin muryar maye Abbati ya ce, "Ga mu a majalisa, kai fa muke jira kwana biyu nan ba ma gane maka sai wani eh yane kake yi wa mutane." "Don Allah mijina ka daina wannan shaye-shayen, a yanzu matsayinka na uba ne. Idan za ka yi sara, ka dinga lura da bakin gatari kana wasa shi. A yanzu da muke rayuwa, kamata ya yi ka duƙufa a neman ciyar da mu halali ba shaye-shaye ba. Allah Ya yi mana arzikin 'ya'ya mata, ina gudun kada watarana idan suka girma a dinga goranta musu. Ka yi mini alƙawarin ba za ka sake shan komai ba Kbna." Kabir ya tuna kalaman da Fauziya ta yi masa, bayan ya dawo hayyacinsa a ranar da ya faɗa ɗakin A'ilo yana cikin maye. Murya a can ƙasa ya ce. "Ku sha kawai Abbati, Fauziya ba ta san shaye-shayen da nake yi." "Ɗan abin rage zafin shi ne za ka ce Fauziya ba ta so? Kai yanzu kana namiji mace ce za ta zauna tana yi maka ƙabali da ba'adi? Haba bros kada ka bayar da maza mana, don Allah ka taho muna jiranka." Daga haka Abbati ya kashe, har zuciya ta ce masa ya yi tafiyarsa gida, sai kuma wata ta ce ya je ya sha ko kaɗan ce. Saboda shi kansa kwana biyun da ya yi bai sha ba, har jin sa yake yi wani iri. Don haka daga nan bakin ƙofar shagon ɗinkinsu ya wuce bayan wata makarantar firamare, wacce iren-irensa suka laɓewa a lungunta suke shaye-shaye. Kabir yana zama T-boy ya miƙa masa wata 'yar roba haɗe da da wata baƙar leda, nan take Kabir ya fara shaƙa yana ɗaɗɗakar ruwan robar kafin wani lokaci tuni ya yi wa kansa caji. Jin shiru har ƙarfe goma da rabi Kabir bai shigo ya sa Fauziya ta ɗauki wayarta ta latsa lambarsa. Sai dai wayar ta ƙari ringing har ta katse bai ɗauka ba, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi. Zuciya ta shiga raya mata ko dai Kabir yana wurin shaye-shayen da ta hana shi, girgiza kanta ta yi cike da ƙwarin gwiwa ta ce. "In Shaa Allah a wannan karon ba zai sake ba..." Maganarta ce ta katse sakamakon jin mummunan bugun ƙofar da ake yi, wanda ya gigitata saboda tsoro, firgici da tashin hankali. "Fauziyataaaaaa! Fauzeeeee, zooo ga ni na zo." Kalaman Kabir cikin maye suka doka sallama cikin dodon kunnenta, ba yau ta saba jin haka daga gare shi ba. Amma a wannan ranar sai ta ji wani irin ɗaci, ɓacin rai da baƙinciki ya mamaye ta. Ta kalli su Na'ima da ke kwance a ƙasa, haka kawai ta ji tausayinsu a ya kamata. Hawaye ne bibbiyu suka fara zuba daga kwarmin idonta, tana nan zaune ta sake jin ya buga ƙofar da ƙarfi yana cewa. "Don Allah... kar ki min faɗa... ni babu abin da na shaaaa..." Sanin halin mutanen gidansu ya sa ta yunƙura da ƙyar ta fita, inuwa ta gani a bakin ƙofar Maman Sabir da alama a tsaye take tana leƙen ganin abin da zai faru. "Ni fa... ba na shan... komai, Fauziyaaaaaa ko kin sha kin bugu ne... kika yi bacci... ki zo ki buɗeeee." Ta sake jin muryarsa a daidai lokacin da ta tura ƙofar gidan, tana buɗewa ya faɗo jikinta da yake ya saki jikinsa a kan ƙofar. Hannu ta saka ta kare cikinta, tana shaƙar ƙamshinsa ta ji yana wani irin warin hayaƙi. "Fauzinaaaa." Ya furta yana shafa fuskarta, takaici ne ya gama maƙure ta. Ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta dube shi tana jin kamar ta rufe shi da duka, a wannan ranar ji ta yi da ace su kaɗai ne a gidan tana buɗe masa za ta bar shi a wurin. Idan ya ga dama ya shiga ko ya kwana a nan, amma gudun kada ya shiga ɗakin matan aure ya sa ta kamo shi. Suna tafe yana layi tana dafa bango, tana shiga tsakar gida ta hangi A'ilo da Maman Sabir suna magana ƙasa-ƙasa. Duk da ba ta ji me suka faɗa ba, amma jikinta ya ba ta maganarta da Kabir suke yi. Ta girgiza kanta cike da tausayin irin rayuwar da take ciki, sannan suka shiga ɗaki. Suna ganin Fauziya ta shiga ɗaki suka saki shewa haɗe da tafi A'ilo ta ce. "Ke dai Maman Sabir a kullum maraɗinki ba ya kunya, wato yau kuma da haka kika shigo. Sabon salo kiran salla da usur, ai gara haka da ki faɗa ɗakin da ba na ki ba." Maman Sabir da tuni ta fahimci zancan ta ce, "Ke kuwa ai dukan da kuka yi mini ban ji da daɗi ba. Abin dariyar ma, baban Sabir tunkur yake zama bai yi bacci ba yana jirana." Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya. Lawisa da take ɗaki take jin su kamar ba za ta tamka musu ba, sai kuma ta yi zaraf ta leƙo ya ce. "Sai ki yi takatsantsan kuwa, domin babu ruwan Ubangiji. Ba abin mamaki ba ne ki ga Sabir ya gado ki. Ni ina fata da roƙon Ubangiji, tun da har fatan da kike yi wa kanki kenan Ubangiji Ya sa Sabir ya gaji abin da kike yi wa izigili." Tana faɗar haka ta koma ɗaki. "Wallahi sai dai ki gani a kanki, aniyarki ta biki mai mugun baki." Maman Sabir ta furta cike da tsoro. Fauziya suna shiga ɗaki, bayan ta saka shi ya tsallake su Na'ima da ke kwance sai kuwa ta sake shi rai a ɓaci. Daga gefen gadon ya faɗi, kansa ya bugu da katakon gado. Cikin azaba ya runtse ido yana shafa wurin, takaici ya sa Fauziya ta zauna a gefen gadon sai kawai ta fashe da kuka. Sai da Maimuna ta tura ƙofar ta rufe sannan ta waigo tana bin bayan Maman Nana da harara, ganin za ta waigo ya sa ta saki fuska cikin wayancewa ta ce. "Uwar gida kuma amarya a gidan Baban Nana, ke kaɗai ki sha kurumki daga ke babu ƙari." Maman Nana ta saki guntun tsaki ta zauna a kan kujera, sai kuma Maimuna ta sha jinin jikinta duk da Jafar ya tabbatar mata da ba ta gane da wacce yake wayar ba. Amma sai ta ce, "Uwar Nana ko dai kin samo wa Abdul abokin wasa ne? Na gan ki duk a sanyaye." Maman Nana ta zaunar da Abdul da bai wuce shekara ɗaya ba ta ce, "Ni da wannan ne ai da sauƙi, sai na saka shi ya ɗauko mini mai aiki ta dinga komai kamar lokacin da na yi cikinsa." Cikin bugar ciki Maimuna ta ce, "To! Me yake damunki?" "Wallahi ban tabbatar namiji munafiki maci amana ba ne ba sai yau, wai har ni Abban Nana zai munfurta?" A razane Maimuna ta dube ta, tana shirin yin magana ta cigaba. "Wai har ni zai dinga yin waya da budurwa a ɗaki? Tsabar wulaƙanci ya saka ni aiki, ina can ina haƙilo ko yaro ya ƙi riƙe mini ashe soyayya zai sha. Wallahi ta ci sa'a ban same ta a waya ba, da sai na ƙare wa kaf danginta zagin rashin mutumci. Sai da na raini mijina yanzu kuma 'yan'iskan mata za su fara kawo mini hari, wallahi duk yarinyar da ta yi gangancin auren mijina sai na lahantata." Ras! Ƙirjin Maimuna ya buga, don ta san halin Maman Nana akwai ta da baƙin kishi. Amma duk baƙin kishinta ba ta ji ko ɗar ɗin za ta iya rabuwa da Jafar ba. Dalilin haka ya sa ta dafa ta ta ce. "Gaskiya ni Abban Nana ma ya ba ni mamaki, saboda Allah duka shekararku nawa da zai dinga wani kule-kulen 'yan'mata?" Maman Nana ta wara hannu tana taɓe baki alamun kema dai taya ni gani, don Maminuna ta sake zuga ta sai ta ce. "To ai ko ni me shekara goma da aure Nazir ba shi da budurwa, ina laifin ma ya bari ku shekara ko sha biyar ne kin ga lokacin ke da yaranki kun samu jindadin da kuka samu bakin gwargwado. Amma kina zaman zamanki a kwaso miki gayyar tsiya, gara dai tun wuri ki san abin yi." Ai kuwa nan take Maman Nana ta sake cika, rai a ɓace ta ce. "Ai wallahi bari ya dawo, dama ai na faɗa masa sai ya kira mini budurwar idan ba haka ba zai ga ɓacin raina." Wani irin farinciki ya mamaye zuciyar Maimuna, saboda a yanzu babu abin da yake damunta sama da ta ji Maman Nana ta ce suna cikin daɗi ita da Jafar. Ta sake taɓe baki ta ce, "To ni ban da ma abin namiji, mace har mace kamar ki me zai yi da wata kuma. Dirin nan bakin gwargwado kina da shi, gashin nan kina da na zaman falo. Ke dai a fuska ba za ce miki mummuna ba, to don Allah me namiji yake so da ba ki da shi." Maman Nana ta yi caraf ta ce, "Jaraba fa irin ta namiji, ki duba ki ga irin magungunan da ke ɗurawa cikina Maman Dija, ke kanki shaida ce saboda Abban Nana na fara shafe-shafen man bilicin, tun da na lura yana leƙe-leƙen fararen 'yanmata." 'Ba dai leƙe ba, sai da faɗawa. Jafar ai ya yi nisan kiwo a kan alkyabbar mata.' Maimuna ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "A toh ga shi kina ƙoƙari a turaka ma na ji kin ce ba kya sanya, to wai da ba kin ce har zauce miki yake ba?" Maman Nana ta yi ƙwafa ta ce, "Yaushe rabo? Ni yanzu rabona ma da shi ai mun kusa sati, Abban Nana da yake da jaraba wai shi ne har yake sha mini ƙamshi jiya. Ƙiri-ƙiri mutumin nan ya ce mini ba shi da lafiya..." "Sati fa Maman Nana? Ke kuwa kina me? A gaskiya ki dawo nutsuwarki, ni fa ba don kar na faɗa ki ji haushi ba da na ce wani abu." A zabure Maman Nana ta dafa Maimuna ta ce, "Faɗi mana, ni da ke ai kin san ba ma haka." "Astagafirullah ba wai zargi nake ba, sai na ga ko dai budurwar tashi ce ta ɗauke masa hankali? Kin san fa 'yan'matan yanzu wallahi idonsu a buɗe yake, ba abin da ba sa yi wa sauraye ke kina can yashe a baki suna harkarsu." "Bantan uba! Ai kuwa sai yanzu kika kamo mini bakin zaren." Maman Nana ta furta jikinta yana karkarwa, sannan ta cigaba. "Ai kuwa zan saka ido a kansa, wallahi idan na gano wani abu a tsakaninsu sai an maimaita yaƙin dunuya na biyu." Maimuna ta cigaba da zuga ta, sai ta gama yi mata famfo sannan ta yi mata sallama ta tafi. Tana fita Maimuna ta saki shewa, cike da ƙeta ta ce. "Sakarya wawiya marar lissafi, in dai ni ce wallahi baƙinciki yanzu kika fara ƙunsa. Sai na raba ki da jin daɗin, da kike hura wa 'yan unguwa hanci kina faɗar ke mowar miji ce." Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [11/02, 14:13] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BIYAR Maman Nana ta fita babu jimawa yaran Maimuna suka dawo daga makaranta, hankalinta yana kan wayarta saboda so take Jafar yaa turo mata kuɗin ta goge alert ɗin. Sai da su Asiya suka ci abinci suka wuce Islamiya sannan Maimuna ta sake lalubar wayarta. Kamar ya san wayar tana hannunta nan take ta ga alert na dubu ashirin, wani irin tsalle ta buga tana riƙe baki. Jikinta har rawa yake ta shiga ɗaki ta ɗauko ƙaramar wayarta ta saka batirin ta kunnata, a gaggauce ta shiga kiransa sai dai bai ɗauka ba don dama ta san ba lallai ya ɗauka ba sai dai ya kira ta. "Baby yanzu na ga kulin ya shigo." Maimuna ta furta muryarta har rawa take yi, jin sautin murmushin da yake yi har cikin zuciyarta ta yi. Ta ya ce, "Yanzu saboda dubu ashirin kika kira? Haba my Moon, don Allah kada ki sake yi mini haka." Maimuna ta saki murmushi, tana shirin magana ta ji ya shagwaɓe murya ya ce. "Ni fa na gagar haƙuri gaskiya, na biya ta kasuwar waya na saya miki sabuwar babbar waya wacce za mu dinga ganin hotuna da bidiyon juna." Maimuna ta ji daɗi sosai, amma tana tsoron kada asirinta ya tonu Nazir ya gano ta. "To ya za a yi ta zo hannuna? Kuma ni ina jin tsoron kada Nazir..." "Idan muna magana ba na son ki dinga ce mini kina tsoron Naziru, wai wanne irin zama yake yi da ke da kike mugun jin tsoronsa." Jafar katse ta cikin sauri, shiru Maimuna ta yi sai ya cigaba da cewa. "A gaskiya alamu sun nuna ba kya jin daɗin zama da shi, a haka ka gan shi kamat na gari yana sunkuyar da kai ƙasa. Amma ya zo a jiye kyakkyawar mace, yana azabtar da ita." Sai kuma Jafar ya ɗan kwantar da murya ya ce. "Haba my Moon, ki duba irin kulle da takunkumin da yake yi miki? Wai a haka kika iya zama da shi har tsawon shekara goma? A gaskiya an ci amanar kyau wallahi." Jin maganganun Jafar sai suka soso mata mikin da yake ɗamfare cikin zuciyarta, kalamasa suka yamutsa zuciyarta tana jin ɗacin yaudarar da Naziri ya yi mata a shakarun baya. "Hmmm ai Nazir ya dasa mini mikin da zai jima a zuciyata bai goge ba, lokaci kawai nake jira my baby." "Kada ki jira lokaci Moon, kamata ya yi lokaci ya jira ki. Saboda yara uku rak ba za su hana ki rawar gaban hantsi ba. Wai ma kina kallon kanki a mudubi kuwa?" Tambayar da Jafar ya yi mata ya sa Maimuna ta yi saurin matsawa gaban mudubinta tana ƙarewa kanta kallo. "Ni fa tun ranar da na fara ganinki na san Allah Ya zuba halitta, kuma wallahi duk wanda ya ganki ba zai cw kin taɓa haihuwa ba. Ba kamar waccan kasaran da ta yi shaɓar da jiki ba, dubi ƙirjinta ba kyan gani duk ya saki ya tamushe kamar an tsoma leda a ruwa." Dariya Maimuna ta shiga ƙyaƙyatawa har da riƙe ciki, sai da ta yi mai isarta ta ce. "An ya ba faɗa kake ba Baby, ka san fa babu laifi ƙawar tawa tana mayar da hankali wurin gyara." Jafar Ya saki tsaki ya ce, "Hmm ke dai a yi sha'ani kawai, yanzu dai wayarki zan ba wa Maman Nana ta kawo miki gobe..." Tun bai gama magana ba ta katse shi, "Maman Nana fa? Ka san me kake faɗa kuwa Jafar?" Dariya ya yi a fili ya ce, "Saboda zan ba wa maman Nana waya ta kawo miki har shi ne ya sa kike kiran sunanan gatsal? Zan ba ta ta kawo miki kamar yadda na faɗa, zan ce mata mijinki ne ya ba hi sautin waya daga kasuwa. Sai na ce ya miƙo miki, amma sai na kintaci lokacin da Naziru ba ya gida don kada a samu matsala. Idan kuma na samu wata mafitar shi kenan, ko kina da wata shawarar?" Kamar Jafar yana ganinta ta girgiza kai ta ce, "A'a babu." Sun ɗan ɗauki lokaci suna waya sannan sula yi sallama cile da kewar juna. Fauziya tana nan zaune a gefen gado tana hawaye ta fara jin sautin munaharinsa, wanda hakan ne yake tabbatar mata da tuni bacci ya yi awon gaba da shi. Haska shi ta yi da wayar hannunta, tana ƙare masa kallo. Ta kawar da kai gefe cikin sanyin murya ta ce. "Ya Allah Ya Ubangiji ba don ni ba, ba don halina ba. Allah ka shirya mini mijina." A inda yake ta bar shi, ita kuma ta haye gado ta kwanta zuciyarta a cunkushe ɓacin rai, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da asuba ta yi cikin bacci ta ji Kabir yana tashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune. Sai ta ga ya yi mata kalar tausayi ya zauna a gefenta, ya saka hannunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta. "Don Allah ki yi haƙuru Fauzina!" Kabir ya furzo kalamansa ƙasa-ƙasa. "Zuwa yanzu ya ci avw na haddace waɗannan kalaman naka, ka sake ni Abban Na'ima zan yi sallah. Ta ba shi amsa rai a ɓace, Kabir ya riƙo ta a jikinsa tsam ya ce. "Wallahi ba laifina ba ne, su Abbati ne suka ingiza ni amma In Shaa Allahu wannan ne ƙarshe." "Ashe idan su Abbati suka ce ka shiga wuta sai ka bi su ko? A yanzu babu wata magana da za ka faɗa mini na yarda da kai a kan shaye-shaye. Su Abbati sun isa su yi maka dole idan kai ma ba ka so ba." Kabir ya yi shiru har sai da Fauziya ta gama sannan ya shiga lallaahinta. Alwala ya fita ya yi, ya wuce masallaci. Bayan ya dawo cike da daɗin baki ya ce. "Ni kuwa ya maganar Dillaliya? Allah Ya sa ta taya kayan da mutumci." Da yake a lokacin Fauziya ta ɗan sauko ta ce, "Ta taya shi dubu saba'in har ta bada rabin kuɗin." Fauziya ta miƙe ta buɗe drower kayanta, jakar ratayarwa ta ɗauko ta zura hannu ta zaro kuɗin ciki ta miƙa masa. "Ragowar ta ce sai bayan kwana uku, an jima idan gari ya waye ta ce za ta zo da wanda zai ɗauka." Kabir ya janye hannunsa daga kuɗin ya ce, "A'a ki ajiye a wurinki ko jari sai ki ja da su" Girgiza kanta ta yi ta ce, "A'a ka cika ka sayi wani abin na aikin gidan can, ka an rage. Idan ta kawo cikon kuɗin, kafin nan kai ma ka samu wasu sai ka haɗa da na wurinka kafin dai ranar tashinmu an rage abin da za a rage." Fauziya ta ɗan kalli ɗakinsu da shinfiɗar su Na'ima cikin damuwa ta ce. "Na gaji da zaman da muke yi ɗaki ɗaya Abban Na'ima. Yaranmu sun fara wayo kwana da su a ɗaki ɗaya zai iya haifarwa tarbiyyarsu da matsala." Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Haba ne Fauzina, amma kuɗaɗen da kike ba ni a ginin nan ina gudun wani abu a nan gaba." Yanayin yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya ya sa jikinta ya yi sanyi, ta dube shi a sanyaye ta ce. "Me kake gudu Abban Na'ima?" "Ina gudun kada watarana abin abu ya haɗo mu ki yi mini gori, sannan tarin kuɗaɗen da kika ba ni lissafinsu nake yi. Idan Allah Ya buɗa mana nan gaba zan biya ki kuɗinki." Maganar Kabir ba ƙaramin ɓa ta ranta ya yi ba, domin duk abin da take yi wa Kabir tana yin sa tsakani da Allah ne domin a ganinta rufin asirinsa tamkar rufin asirinta ne. A irin kalubalen rayuwar da ta fuskanta a kaf faɗin duniya gifa biyu ne ya zame mata gata kuma madogararta. Daga gidan mahaifinta sai gidan mijinta, gidan mijin da take fatan sai dai mutuwa ta ɓamɓare ta daga ginin turɓayarsa. Gidan mahaifinta kuwa a yanzu ba ta fata ko burun kawo wata ƙaddara da za ta kwashe ta daga gidan mijinta kuma aljannar duniyarta zuwa ƙangin bauta wato gidan mahaifinta. Amma sai ta ji Kabir yana faɗar kamalan da take jin tamkar bai ba ta matsayin da ta ba shi a cikin zuciyarta ba. Don haka a ɗan ƙufule ta ce. "Shi kenan tun da kai abin da ka ɗauka kenan sai ka lissafa abin da nake bin ka, tun da ai da na ba ka cewa na yi na ba ka aro." Murmushi ya yi don ya fahimci ta ji haushi, sai ya gyara zama ya ce. "Tuba na ke uwargida kuma amarya a gidan Kb babban tela. Haba Fauzin Kb fushin na mene ne?" Fauziya ta ɗan kwaɓe murya a shagwaɓe ta ce, "To ai kai ne da wata irin magana." Hira suka yi ɓarke da ita har gari ya ƙaraaa wayewa, gabanin Kabir zai fita ta ce masa za ta je gida ta gaida mahaifinsa. Amma sai ta fara biyawa ta wurin Inna ta gaida. Fita ya yi ya sayo mata ɗan omo, sabulu da magi ƙulli bibbiyu. Ƙulli ɗaya ya ce ta miƙa wa mahaifiyarsa, ƙulli ɗaya kuma ta kai wa mahaifinta. Godiya ta zuba masa sosai, ta sake ba wa Kabir wani matsayi a zuciyarta. Domin kusan duk ranar fa za ta je gaida mahaifinta sai ya sayo wani abim ya ce ta kai masa, har turare sayo mata yake ya ce ta kai masa. Kyautatawar da yake wa mahaifinta ya sa Kabir ya sake samun fada a zuciyarta da zuciyar mahaifinta har ma da matan babanta. Don ba ta taɓa zuwa gida haka, idan ya saya wa mahaifinta abu. Ita kuma da ɗan canjin hannunta na kuɗin kitso ko gyaran tsumma da take yi sai da saya wa matan babanta ɗan magi ko tsintsiya. Wani lokacin kuma ƙannenta take sayawa alewa ta tafi musu da shi, haka idan za ta leƙa gidan mahaifiyarsa Inna ko bai ba ta komai ba da kuɗinta take ɗan saya mata omo da ɗan abin da ba a rasa ba. Shirya su Na'ima ta yi tsaf cikin ankon atamfa dogayen riguna, sannan ita ma ta shirya cikin doguwar rigar abaya ta ɗora babban mayafi ta yane kanta. Lokacin da za ta fita Lawisa kawai ta yi wa sallama, saboda magana bai daɗi ba ta taɓa haɗa ta da su A'ilo. Koda ita ta yi musu mai daɗi, sai sun san yadda suka yi suka mayar mata da martanin baƙar magana. Duk wanda ya ga Fauziya da 'yan'matanta uku sai sun birge shi, saboda kusan gabaɗaya tazararsu babu yawa. Daga gidan su Fauziya zuwa gidan Inna babu nisa sosai, don a adaidaita sahu bai fi naira ɗari ba. Idan mutun bai sa ƙyuya ba ma zai iya zuwa da ƙafa. A lokacin da Fauziya ta yi sallama a gidan Inna Sadiya tana tsakar gida tana wanki, Inna kuma tana zaune tana ɗaurin tsintsiya. Sadiya ce ta faɗaɗa fara'arta ta ce, "Yanzu uwar biyu ba ki rufe fita ba sai kin haife mana ɗa a titi?" Murmushi Fauziya ta yi mata, ta ƙarasa gaban ta tsugunna ta ce. "Barka da hutawa Inna." Inna ta ɗan taɓe baki ta ce, "Wane hutu Fauziya ana fama da rayuwa." Fauziya ta sake yin murmushi saboda idan da sabo ta saba da halin Inna domin irin matan nan ne da ba su da godiyar Allah. Saboda bakin ƙoƙari 'ya'yanta suna kyautata mata, amma duk lokacin da suka haɗu sai ta yi jajen tana cikin wani hali. A cikin yaran Inna mijin Sadiya da Kabir ne marasa ƙarfi sosai, don haka ta fi ji da matan 'yan uwan Kabir. Kuma a haka ma tana nannan da Fauziya saboda kyautatawa da take yi mata, amma Sadiya da yaranta da suke zaune a gida ɗaya kullum cikin tsangwama da kyara suke. Su Na'ima suka zube ƙasa suka gaida Inna, Inna ta ɗan taɓe baki ta ce. "Ai dama ku ba na ganinku sai idan uwarku za ta zo, ko ban isa a turo mini ku ba ne oho." Sadiya da Fauziya suka haɗa ido suka saki murmushi, Inna ta sake leƙen hannun Fauziya ta ga ba ta ga komai ba sai kuwa ta sake cewa. "Kabirun ma kusan sati guda kenan ban gan shi ba, tun ranar da ya kawo mini garin tuwo da taliya. To dai nan ɗin da ba kwa son zuwa, nan ne dai gidanku tun da ubanku ma a nan ya tashi. Kuma ni na haifi Kabiru babu yadda kuka isa ku yi da ni." Shiru su Na'ima suka yi, saboda dama babban dalilim da ya sa ba sa son zuwa wurin Inna yawan faɗanta. Sau tari Fauziya za ta shirya su musamman ranar Juma'a ta cw su zo su gaida Inna amma suna zuwa ko zaman minti talatain ba sa yi suke tafiya. Wani lokacin ne ma suke zama su yi wasa da yaran Sadiya. "Ke Salim ku zo ku ɗauki tsintsiyoyin nan, ke kuma Zainabu ga mafitai ki ɗauka. Yau idan kika sake ki yar munnda kuɗi wallahi sai ubanki ya biya ni kuɗina." Inna ta furta wa 'ya'yan Sadiya tana tura musu farantan da aka jera tsintsiya da mahutan. Sadiya ko kaɗan ba ta jin daɗin tallan da Inna take ɗora mu, don dai babu yadda za ta yi ne amma ba ta son tallar musamman ga Zainab da ta kasance 'ya mace. "Inna ga wannan a yi wanki da shi babu yawa." Fauziya ta zaro ledar daga kan cinyarta. Ina sai da ta ɗora wa su Salim farantin tsintsiya sannan ta waiga wurin Fauziya riƙe da baki ta ce, "Oh ke dai Fauziya ba kya gajiya, to an gode madalla. Ai kuwa kin ce na sha wanki, dama kayan sawata duka sun ƙare sai masu datti. Ai ka ga masu abin kirki, amma wasu kuya ko ƙullin gishiri ba su san su ba ni ba. Ke dai Allah Ya yi miki albarka, wannan ciki da kike ɗauke da shi Allah ya sauke ki lafiya ya sa ki haifo wa Kabiru magaji." Fauziya ba ta amsa ba, suna nan zaune suka ɗan taɓa hira. Fauziya tana son su keɓe da Sadiya amma tana tsoron fassarar da Inna za ta yi musu. Sun ɗan jima suna hira Inna ta ce, "To yanzu ni dai ragowar Taliya ɗaya gare ni ballantana na dafa mana abinci, ko da wuri za ku wuce ne Fauziya." Girgiza kai Fauziya ta yi tana mamakin rayuwar Inna, Fauziya ta miƙe ta ce. "Yanzu za mu wuce Inna, dana zan je gaida Baba ne na ce bari na zo na gaishe ki." Nan take kuwa Inna ta hau washe baki ta ce, "To shi kenan ku gaida gida, shi kuma Kabiru ki ce masa ina son ganinsa." Fauziya ta amsa sannan ta nufi hanyar fita, da sauri Sadiya ta bi ta tana faɗin. "Wai har za ku tafi, bari mu fita tare dama zan miƙa wa Mariya kayan wankin da na yi mata." Da biyu Sadiya ta bi Fauziya suka fita, suna fita Fauziya ta ce. "Wai dama har yanzu su Salim ba su daina tallar muhucin nan ba?" Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai na kusa barin gidan nan Fauziya, wallahi na gaji haƙurina ya kusa ƙarewa." "Idan kin tafi yaran kuma fa Sadiya?" Cikin halin ko'inkula ta ce, "Allah zai raya su, wasu ma suna tasowa babu iyayen kuma su yi rayuwa kamar kowa." Fauziya ta tsaya tana bin Sadiya da kallo, duk ta lalace saboda rashin kwanciyar hankali. "Don Allah ki daina wannan maganar, addu'a za ki cigaba da yi har Allah Ya hore muku ku bar wa Inna gidanta. Kin san zama wuri ɗaya dama yana kawo haka, ki cigaba da addu'a sai ki ga watarana sai labari." "Hmmm ba za ki gane ba Fauziya, ni na san takaici da baƙincikin da nake ci a gidan." Cikin ƙarfafa gwiwa Fauziya ta ce, "Babu abim da ya fi ƙarfin addu'a." Fauziya da Sadiya sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama, Fauziya ta wuce ta tari adaidaita sahu suka wuce gidan mahaifinta.A tsakar gida ta samu mahaifinta yana ta bambamin faɗa a kan 'yan nefa sun zo karɓar kuɗin wuta. Har ƙasa ta tsugunna ta gaida shi, sannan ta miƙa masa saƙonsa, nan take Baba ya shiga washe baki yana saka mata albarka. Ɗakin Inna Sakina ta shiga da yake a nan ɗakin aka raini Fauziya, bayan sun gaisa ta fara bin ƙannenta da alawoyi tana danƙa musu. Su Nai'ima kuwa dana tun a tsakar gida suka fara wasa da ƙannen mahaifiyarsu. Kabir yana fita daga gida kai tsaye wurin masu sayar da ƙofa ya nufa, ƙofofin ba ƙaramin tsada ya ji sun yi masa ba. Ya cika da ragowar kuɗin wurinsa ya sayi guda ƙofofin guda uku, ƙofar farko ta ƙofar gida. Sai ɗakin da yake a tsakar gida, da kuma ƙofar falon gidan. Daga nan wurin can gidan nasa ya nufa, ya kira masu saka ƙofofi suka fara aiki. Ba su suka gama ba sai yamma liƙi, gabanin zai fito daga gidan kiran Hafsa ya shigo masa, zama ya yi a bakim dandamalin rijiyar sannan ya ɗauka. "Gimbiyar mata!" Ya furta cike da kashe murya, daga can ɓangaren Hafsa ta ce. "An ya kana jin abin da nake ji kuwa?" Kabir ya sake kwantar da murya ya ce, "Haba Hafsyna, don Allah ki daina faɗin haka." Hafsa ta ce, "Ka duba whatsapp ɗinka na turo maka da hotuna." Jikin Kabir har rawa yake ya katse wayar, sannan ya yi saurin buɗe datarsa. Yana shiga whatsapp ya fara cin karo da saƙonninta, buɗe hotunan ya yi ya ga ta ɗauko masa hoton ƙirjinta da ƙasanta kamar yadda ya buƙata. Cikin wani irin yanayi ya sake kiranta, a kunyace Hafsa ta ɗauka sai ta ji duk muryarsa ta sauya. "Baby kin yi kyau sosai, amma don Allah ki yo mini bidiyo mana." Hafsa da duk ta ji nauyinsa ua kama ta ta ce, "Baby gaskiya ka yi haƙuri, wallahi wannan ma da ƙyar na iya turo maka." "Guda ɗai-ɗai fa kawai za ki yi mini, kuma kin san ai aurenki zan yi ko ba ki yarda ba?" Shiru ya ji Hafsa ta yi, ya ɗora da cewa. "Akwai kuɗin da nake saka ran za su shigo mini nan da kwana uku. In Shaa Allah a satin naa za a kawo kuɗin aurenmu." Daɗi ya lulluɓe Hafsa, jikin yana rawa ta ce. "Zan turo maka amma don Allah kana gani ka goge." Cikin sauri Kabir ya ce, "Wallahi ina gani zan goge." Kashe wayar Hafsa ta yi ta shige ɗakinta ta yi masa bidiyo ta tura masa. Kabir yana ganin bidiyon a ruɗe ya shiga yi mata replay da kalaman batsa, tun tana jin nauyinsa har ta fara biye shi. Yamma liƙis Fauziya ta koma gida ta ɗora musu girki, a wannan karom ma ana yin magrina ta kira Kabir ta sake tuna masa maganar da suka yi game da alƙawarin da ya ɗaukar mata ba zai sake shan komai ba. Sannan ya ce ta yi tsala masa kwalliyar domin a cike yake da kewarta. Zuciyar Fauziya fes ta tsala wanka cikin wata doguwar riga marar nauyu, ta raba gashinta gida biyu kamar wata 'yar baby ba ƙaramin kyau ta yi ba. Suna nan zaune ita da yara kimanin ƙarfe tara suka ji sallamarsa. Kusan lokaci ɗaya ita da yaran suka rungume shi har ita suna faɗin. "Abi oyoyo." Rungume su ya yi gabaɗaya, sai Fauziya ta saci kallon yadda suke nishaɗi ita da yaran saboda dawowarsa da wuri kuma a cikin nutsuwarsa, sai ta ji ƙwalla tana shirin zubo mata. Ɗaya bayan ɗaya ya tsugunna yana sumbatar yaran a goshi, sai ya ɗago ya dube ta suka haɗa ido. Rungumo ta ya yi jikinsa yana kashe mata ido ɗaya, irin kallon da take bin sa da shi ya sa shi hura mata iska a fuska. "Wannan kwalliyar zan biya tukwicinta an jima." Ya furta matana hankali, ta sakar masa murmushi ta ce. "Na fa tsufa da yawa." Kafaɗa ya maƙale mata cikin kwaikwayon muryarta ya ce, "Ni ban yarda ba." Duk da yaran ba su fahimci me suka tattaunawa ba, jin yadda mahaifinsu ya maƙale murya ya sa suka fata ɗariya. Hula, agogo da wayarsa ya ajiye a gefen gado ya ɗauki bokiti ua zuba ruwa ya tayi yin wanka. Kabir ya manya shaf da abin da Hafsa ta turo masa bai goge ba har ya iya ajiye wayarsa, kuma ya bar hotunan ne saboda udan ya keɓe ya dinga kalla yana jindaɗi. Fatima ce ta ɗauki wayar ta shi, da yake wani lokacin idan yana gida ya kan kunna musu game ko cartoon su kalla. Shige-shige suka fara yi masa har suka shiga cikin gallery ɗinsa, Na'ima tana ta zura kanta ta danna ɗaya daga cikin bidiyon da Hafsa ta tura masa. Fauziya da ke tsugunne tana jera masa kayan abin ci ta ji muryar mace raɗau a kunnenta tana faɗin. "Baby kana gani, wannan bidiyon..." A giguice Fauziya ta fisge wayar daga hannunsu jikinta yana karkarwa, sakamakon ji irin bayanin batsar da buduwar take yi. Domin a bidiyon hafsa tana yi masa tana bayanin komai dalla-dalla. "Lah Mami mene ne wannan?" Na'ima da ta fi su wayo ta tambaya, sai da Fauziya ta saita nutsuwarta ta ce, "Bidiyin wata marar lafiya ne da take neman taimako, za a haɗa mata kuɗi a yi mata magani. Na sha faɗa muku idan mutum ya ajiye abu sai an tambaye shi ake taɓawa ko?" Gabaɗaya suka gyaɗa mata kai, Fauziya fa take jin wani abu yana taso mata a ƙirji ta yi ƙarfin halin faɗin. "To daga yau, ko da wasa ka da na sake na ƙara ganin ku taɓa wa mutum wayarsa. Idan ba haka ba ranku zai ɓaci." Su Fatima suka amsa mata. Ear pices ta ɗauko ta saka a kunne, ta shiga bidiyan ta kunna shi. Jikinta ya ɗauki karkarwa gabanta yana wani irin bugu da ƙarfi, lokaci ɗaya hawaye ya wanke fuskarta domin bidiyon ya matuƙar ƙazanta. Da sauri ta shiga whatsapp ɗinsa, ta ga yawanci masu saƙon duk maza ne don haka take mamaki a inda Kabir ya samu wannan bidiyom. Har za ta fita ta ga an saka costomer Hafsa lace bubu, tana shiga ta karo da emojin heart ta turowa Kabir. Can sama ta haura ta fara cin karo da saƴonnin batsar da suka tattauna, a nan ta gado wannan bidiyon na Hafsa ne tun da ga muryar ta nan ta kunna voice ɗinta ta ji." Jikinta yana rawa ta kifa wayar, sai ta jingina da bango tana jim wata irin tsanar Kabir ta mamaye ta. Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [11/02, 19:29] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHIDA Tun tana zubar da hawayen zuci don kada yaranta da ke zaune su fahimci halin da take ciki har ta gagara sarrafa zuciyarta saboda wani irin zafi da ɗacin da take yi mata. Hawaye taka sosai tana shassheka tamkar za ta shiɗe, saboda wani irin kakkarwa da jikinta yake yi ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri-sauri. Ganin halin da mahaifiyarsu take ciki ya sa suka ƙarasa wurinta suna tambayarsu, ba ta iya tanka musu ba sai ma wani irin kallo da ta dinga bin su da shi kamar ta ga sababbin hallita. A ranta ta ayyana ƙila yarinyar da suke musayar munanan kalamai da Kabir ko kaɗan iyayenta ba su san abin da take aikatawa ba. Sai kawai ta rungumo su jikinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, ganin haka ya sa su Fatima su ma suka rairai kukan su ma. Duk da ya san ba hali ko ɗabi'ar Fauziya ba ne binciken wayarsa, haka kawai yana wanka da ya tuna ya bar wayar a kan gado ya ji gabansa ya faɗi. Nan take ya yi sauri ya kwakkwara ruwa ya fito, don ba ya so Fauziya ta fahimci irin alaƙar da ke tsakaninsa da su Hafsee. Kamar wanda aka kifa haka Kabir ya faɗa cikin ɗakin har yana tuntume, Fauziya ta ɗago tana kallonsa ta ƙura masa ido. Ganin yanayin da ya same ta ita da yaran da kuma mummunan kallon da take wurga masa, ya sa ƙirjinsa ya buga da wani irin ƙarfi. Da gudu yaran suka tafi wurinsa cikin haɗin baki suka ce, "Abi Mami ce take kuka." Yanayin yadda ya ga hankalin yaran ya tashi ya sa ya kalli wurin da ya ajiye wayarsa, rashin ganinta a wurin ya sa shi tabbatar da tabbas mai afkuwa ta riga da ta afku. Ya san duk irin saɓanin da za sh samu da Fauziya ba ta iya zubar da hawayenta a gaban yaran, duk abin da za su yi ko wata tattaunawa ce sai ta bari sun tafi makaranta ko kuma idan sun yi bacci amma gudun kada ya bada kai bori ya hau sai ya yi kamar bai san dalilin ɓacin ranta ba ya ce. "Ummu banat lafiya kike hawaye a gaban yara?" Tamabayar da ya wurga mata ta ji ta yi tamkar ya zuba mata ruwan dalma, ta dube shi cike da mamakin wai ita Kabir zai raina wa hankali. Murmushin takaici ta saki sannan ta miƙa masa wayar ta ce, "Ungo wayarka, cikina ne yake ciwo." Ya san ta faɗi haka ne saboda gudun yaran su fahimci shi ya yi mata wani abin, Na'ima ta ɗauko kwalmar maganin tarinsu ta miƙa mata ta ce. "Ammi riƙe ki sha magani ba na son na ga kika kuka!" Ƙuri ta yi wa yarinyar tana kallo, murya a dashe ta ce. "Wannan maganin yara ne Na'ima, cikin nawa ya sarara idan na tashi zan ɗauko maganina a cikin jaka." "Amma za ki daina kuka?" Na'ima ta sake wurga mata tambaya, gyaɗa mata kai Fauziya ta yi. Dai kuma ta ƙarasa gaban Kabir ta ce, "Abu ni dai ka kai Ammi asibiti, ba na son ta dinga kuka ni ma zan yi." Ta ƙarasa maganar tana janyo hannunsa. Tamkar wanda aka liƙewa ƙafa da super glue, haka ya ji ƙafarsa ta manne ta ƙasa wata irin shakkar Fauziya ta kama shi. "Ko... ko... za mu... wuce asibiti..." Ya furta bakinsa yana rawa, sai dai tun bai fire kalamansa ba Fauziya ta wurga masa mugun kallon fa ya sa shi haɗiye kalamansa. "Ai jikin mamanku da sauƙi Na'ima, ba sai mun je asibiti ba. Yanzu dai bari na yi muku shinfiɗa kun ga gobe kuna da school." Tana gee har lokacin idonta yana kan Kabir, da take yi masa kallo kamar tana som gano wani ɓoyayyan abu daga jikinsa. Shafa jikinta take yi don ta tabbatar ba mafarki take yi ba, ta saka hannu ta mintsini cinyarta jin zafin ya ratsa wurin ya sa ta tabbatar da zahiri ne. Tana kallo Kabir ya kashe wayar gabaɗaya, jikinsa gar rawa yake ya ɗebo kayan shimfiɗa ya yi wa yaran. Yana gama shimfiɗar ta ga ya ɗauki wayarsa ya fice daga ɗakin alamar fita ma zai yi daga gidan gabaɗaya. Tun da ya fice Fauziya take saƙa da warwarar hukuncin da za ta yanke, ban da kai wa da kawowa babu agim da take yi. Hat yanzu zuciyarta rawa take yi a kan ko dai idanu da kunnuwanta ba su jiyo mata daidai ba. Babban abin da ya sake ɓata mata rai, yadda ta ga ya ɗauki wayar ya fice daga gidan wato duk ma abin da za ta yi ta je ta ƙarata. Ta jima tana ƙoƙarin dakatar da hawayen idonta, amma ta kowanne ɓangare ya gagara ba ta haɗin kai. Shinshina jikinta ta fara yi tana son gano ta inda ta gaza, ta ɗaga rigarta tana kallon mamanta ko za ta ga hango aibun na jikinta. Domin Allah ya yi mata baiwa duk da haihuwarta uku ga ta huɗu za ta yi amma mamanta bai lalace, ballantana ta ce ko nata ne suka zube har yake hangen na wasu. Kuma idan ma lalacewa suka yi a tsawom shekaru bakwai da aurensu bai ci ace ya ɓoye mata ba. Har gara ya faɗa mata domin ta san matakin gyaran da za ta ɗauka. Ta matsa gaban madubi tana bin kanta da kallo, sai dai har ta gaji da tsaiwa ba ta gano makusar da za ta sa Kabir ya dinga musayar munanan kalamau da hotuna da 'yanmata. Gajiya ta yi da tsaiwar ta zauna a gefen gado, sai ta shiga tausayin kanta da 'ya'ya matan da ta haifa. "Wannan wacce irin rayuwa, aai yaushe zan sanu kwanciyar hankali? Sai yaushe zan samu nutsuwa kamar kowa? Sai yaushe..." Wani sabon kukan ya sake ƙwace mata, a wannan ranar da take jin kamar zuciyarta za ta yi fiffike ta ɓullo daga ƙirjinta, ba ta shayi ko kunyar bayyana kukanta a sarari domin gurin ɗabi'u da halayen Kabir ba a ranar suka fara yi mata ba. Kamar kuwa Fauziya ta sani, su Ai'lo da ke ɗaki duk sun kasa kunne suna son gano dalilin kukan nata. Don sun san fa wuri ya dawo gida ba a buge ba, ballantana su ce takaicin rashin dawowarsa ne ya saka ta kuka. Lawisa da ke ɗaki har sun kwanta ita da mijinta ta gagara haƙuri, ta fito zuwa ƙofar ɗakin Fauziya. "Maman Na'ima! Maman Na'ima ke jaɗai ce zan iya shigowa?" Fauziya da muryarta ta gana dacewa ta ce, "Shigo ni ɗaya ce." Tana shiga ɗakin ta ɗan ƙasa fa murya ta ce, "Me yake faruwa MamAn Na'ima? Tun ɗazu nake jiyo kukanki lafita kuwa?" Ta san Lawisa tana ƙaunarta tana ba ta kulawa, amma wannan wani gingimemen sirrin mijinta ne da ba za ta iya furta mata ba. "Mahaifiyata na tuna Lawisa, mahaifiyata cw ta faɗo mini. Akwai abubuwa da dama da nake ganin iyaye mata suna yi wa 'ya'yansu Lawisa na rasa wannan gatan. Ban san wa zan raɓa na ji danshi da sanyin mahaifiyata." Jikin Lawisa ya yi sanyi, da jin kalaman Fauziya. Domin ta taɓa ba ta tsakure kaɗan daga cikin labarinta, da irin baƙar wahalar da ta sha a hannun matan babanta. Sai ta yi tsammanin ko wani abin suka yi mata bayan ta je gidan, don haka ta dafa kafaɗarta ta ce. "Ba kuka za ki yi mata ba Mamam Na'ima, addu'a ya dace ki yi mata. Ki yi haƙuri watarana sai labaru."Fauziya ta gyaɗa kai sannan ta yi mata godiya Lawisa ta koma ɗakinta. Tana nan zaune kimanin sha biyu da rabi na dare Kabir ya shiga gidan, a ɗarare ya zauna ya san Fauziya sarai da zafin kishi. Duk sai ya ji haushin kansa da tun yana gama gani bai goge ba. A tsammaninsa Fauziya za ta kula shi amma ga mamakinsa sai ga ko ƙurarsa ba ta kalla ba. "Fauziya don Allah..." "Ba na buƙatar jin komai daga gare ka." Ta furta a kausashe tana ɗaga masa hannu. Shiru ya yi ya kasa cewa uffan, Fauziya ta miƙa ta koma gefen yaranta ta kwanta ta shiga nazari da lissafin takaicin da mummunan ganin da ta yi. Bayan Maman Nana ta koma gida haka ta sake cika fam, don tana aiki amma zuciya tana raya mata abubuwa da dama har aka yi sallar Magriba Jafar ya dawo. Yana zura ƙafarsa cikin gidan ya bi ta da wani kallon cike da ƙyama, ya saki guntun tsaki sannan ya wuce ɗaki. Yanayin fuskar Maman Nana ce ta sa ya tuna abin da ya faru kafin ya fita, don haka shi ma ya yi watsi da ita. Kaskon turaren wuta ta ɗauka har za ta fita Jafar ya ƙwala mata kira, fuska a haɗe ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ce. "Ga ni." Sabuwar wayar ya ɗauko gal a cikin kqalinta ko buɗewa ba a yi ba, ya miƙa matasa sai kuwa ta saki fukarta ta hau washw baki don ta yi tsammanin ita ya sayo wa sabuwar waya. "Idan kin fita ki miƙa wa Maman Asiya, idan Naziru ya dawo ta ba shi saƙon sa da ya ce a taho masa da shi." Murnar Maman Nana ta koma ciki, nan take ta haɗe rai don kusan sati uku kenan ba ta da waya tun da Abdul ya jefa mata wayarta a ruwa. Ta yi nacin Ya sayo mata waya kullun da zancan da zai ɓullo mata. Gidan Maimuna ta ƙwanƙwasa da yake Maimunan ta san da maganar wayar da sauri ta je ta buɗe ƙofar, tana ganin Maman Nana ta ji wani farimciki ya lulluɓe ta. Wayar hannunta ta miƙe mata, sannan ta ce. " A ɗan sammun gawayi zan yi turaren wuta." Maimuna ta ce, "Wannan wayar kuma fa?" "Baban Nana ne ya ce ki ajiye wa Abban Asiya." Kamar Maimuna ba ta san kwanan zancen ba, ta saki fuska cikin murna ta ce. "Allah Ya sa Abban Asiya suprise zai yi mini, don bai yi mini zancen za a taho masa da waya ba." Maimuna ta saka cokali tana ɗiba gawayi ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Wai har yanzu ba ki gama girki ba Maman Asiya? Kai gaskiya masu girkin gawayi kuna ƙoƙari ina zan iya wannan jidalin?" Wani takaici ya maƙaure zuciyar Maimuna, ta bi bayan Maman Nana da harara a ranta ta ce. 'Ni za ki yi wa iskanci kenan? To wallahi daga wannan karon kema kin daina aiki da gas ɗin, ba dai ni za ki yi wa iskanci ba? Za ki ga muna ƙoƙari ganin idonki.' Maman Nana tana gama ɗiban wutar ta yi wa Maimuna sallama ta fice, a ta cikin riga Maimuna ta sakaya ledar wayar ta shige uwar ɗaki ta ita. Kayan sakawarta ta ɗaga daga can ƙasa ta tura wayar, ta ciro ƙaramar har za ta saka layi ta kira shi sai ta mayar saboda ta fi son sai zuwa jimawa idan ta sallami yaranta sun yi bacci ta kira shi su sha hira kamar yadda suka saba daddare kafin Nazir ya dawo. Tun da dama can shi Nazirba mutum ne mai dawowa gida da wuri ba, idan ma ya dawo ɗin mafi yawa lokaci hankalinsa yana kan wayarsa bai cika ba ta lokacinsa ba. Hatta su Asiya sai da suka lura da farincikin da take ciki, amma sai ta nuna musu ba komai. Da yake a ƙage take da ta ji muryarsa, ana idar da sallar Isha'i ta yi musu shimfiɗa. Sai da ta tabbatar da bacci ya kwashe su sannan ta shige ɗakinta ta ciro ƙaramar wayar da suke waya ta kira shi. A ɓangaren Jafar kuwa tun bayan da ya lura da haɗe ran da Maman Nana take yi, shi ma sai ya yi watsin iska da ita. Hakan kuwa ya sake ɓata mata rai, don haka ta ci alwashin za ta gasa masa a ya a hannun ta cikin ruwan sanyi. Yana gama cin abinci ya fice daa gidan, ya tafi can nesa da layinsu wurim da ya saba waya da Maimuna ya zauna. Ya jima yana dakon flashing ɗinta har sai da ya fara cire rai, sai ransa ya ɓaci da ya ayyana ko dai Naziru ne ya dawo shi ya sa ba ta smau damar kiransa ba. Yana nan zaune ya ji flashing ɗinta, a fili ya saki ajiyar zuciya. Hannunsa har rawa yake ya latsa layin nata, tana ɗaga wa ya ji ta fashe masa da wani irin kukan kissa. Wani abu ya ji yana zarga masa wanda ya kashe masa ilahirin jijiyoyin jikinsa. Sai da ya yi ƙarfim hali sannan ya iya fisgar maganar bakinsa. "Wannan shagwaɓar taba gigita ni my Moon, idan ba kya son hana ni bacci a ɗan daga ta da kukan nan haka." Daga can ɓangaren Maimuna ta sake yin wata shasshekw wace ta sake birkita shi, murya can ƙasa kamar wacce take waya da mijinta ta ce, "Ina kukan farinciki ne my J. Haƙiƙa ka faranta mini rai domɗn wannam wayar ba ƙaramin tsada gare ta ba." Murmushi ya yi mata ya ce, "Ko nawa zan iya ɓatar mini Moon, fata da burina kawai ki mallaka mini kanki." "Idan hat ni ce kamar ka samu J, kada ma ka sake wasu-wasi a kan soyayya ta." Har Jafar zai yi magana Maimuna ta katae shi a shagwaɓe. "Ɗazu matarka ta ci mutumcina bayan ta zo ɗiban gawayi, a gaskiya raina ya ɓaci domin an daɗe ba a ci zarafi kamar na yau ba. Duk da ba cikin faɗa ta yi mini magaanar ba, amma a wasan dare ta ƙare mini cin mutumci. Har takw yi mini ƙafafa a kan ita amfani take yi da gas." Sai kuwa Maimuna ta rushe da kuka, kukanta yake ji har cikin ransa. Don ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cikin rarrashi ya ce, "Ya isa haka baby Moon. Wallahi tun ranar da na fara ganinki ba ki kalar amfani da gawayi ba. In Shaa Allaha na san yadda za a yi na saya muki gas ki daina amfani da gawayi. Ita kuma ki bar ni da ita na rantse miki da Allah daga gobe ta daina amfani da gas gabaɗaya. A yanzu ma don dai dare ya yi, da a daren nan zan siyo masa kurfoti da buhun gawayi." Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [13/02, 21:16] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BAKWAI UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Wani irin farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Maimuna, saboda dama ba a ranar Maman Nana ta saba zuwa tana yi mata fariya, tana baje mata jin daɗin da Jafar yake yi mata ba. Wani abin ma sai ta lura kamar da gayya Maman Nanan take yi, saboda mijinta duk ya fi ragowar mazajen layin rufin asiri. Wannan ne dalilin da ya sa Maimuna ta ci alwashin sai ta tarwatsa farincikinta, tun da ita ba ta samu kwatankwacin abin da Maman Nana take samu a wurin miji ba. "Na ji kin yi shiru ko hukuncin da na ɗauka bai yi miki ba?" Jafar ya furta jin Maimuna ta yi shiru, Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Hakan ya yi Baby J, to amma ta ya ya zan mallaki gas ɗin? Ni dai ba sana'a nake yi ba ballantana na cewa mutumin nan saya na yi." "Wannan mai sauƙi ne Moon, zan san yadda zan ɓullowa lamarin." Hirar soyayya suka cigaba da yi tamkar ma'auratan da suke nesa da juna, kowanne yana cike da kewa da begen ɗan uwansa. Suna gab da yin sallama Jafar ya ce, "Wayar nan da na aiko ba ta buƙatar caji, na saka mata caji ɗazu. Abin da ya rage kawai don Allah ki ɗaukar mini hotunanki." Maimuna ta ce, "Sai zuwa gobe idan Nazir ya fita, amma ka ɓoye su ta yadda matarka ko wani ba zai gani ba." Murmushi Jafar ya yi ya ce, "Kada ki damu akwai folder da nake ɓoye hotuna, a nan zan ɓoye naki." Yana faɗin haka daga gefensa ya ji Nazir ya yi masa sallama yana daga kan mashin, duk da ya san Nazir ba zai taɓa fahimtar da wacce yake magana ba. Amma sai da gabansa ya faɗi, ya cire wayar daga kunnensa ya ce. "Ale Nazir barka da shigowa." Nazir ya ɗan rage gudun mashin ɗinsa ya ce, "Barka dai Alhaji Jafar, ka na nan a bayan fage kana waya ko? Ai sai na aika na faɗa mata." Nazir ya yi furucin cikin barkwanci. "Tuba nake kada ka sa a rufe mini ƙofa." Jafar ya furta yana kama kunnensa, dariya Nazir ya yi ya wuce gida. Ganin ya tafi ya sa Jafar ya ja dogon tsaki yana mayar da wayar kunne ya ce, "Ina tsaka da farinciki wannan mutumin zai datse mini, don Allah Moon ki rage ba shi kula a turaka. Wallahi haka kawai kishinsa yake nuƙurƙusata." Maimuna da ita kanta haushin Nazir ya kama ta ce, "Ai yau duk bala'insa babu ma abin da zai haɗa mu, dama na kwana biyu ina juya masa baya." Kamar ba za su rabu ba haka suka yi sallama. Maimuna tana gama wayar ta yi saurin mayar da ita wurin da take, ta yi sauri ta haye gado ta kwanta ta rufe ido. A kan kunnenta Nazir ya shiga gidan, ya ɗan jima a falo sannan ya tashi ya shiga ɗakin. "Maimuna! Maimuna!" Ya furta yana bubbuga filonta, yamutsa fuska ta fara yi tana miƙa kamar wacce ta jima tana bacci. "Sannu da zuwa." Ta furta masa tana sakin hammar ƙarya. "Yawwa sannu ya gida?". A hankali ta zuro ƙafafuwan ƙasa, ta jinginta kanta da fuskar gadon ta ce. "Lafiya ƙalau." Ya yi mamakin a 'yan kwanakin nan da Maimuna ba ta yi masa ƙorafi, domin kusan kullum idan ya dawo gida sai ta yi masa ƙorafi a kan kai wa daren da yake yi a waje. Miƙewa ta yi ta fito falo, Nazir ya rufa mata baya. Kayan abincinsa ta ɗebo ta ajiye masa har ta miƙe za ta koma ɗaki ya riƙo hannunta. "Maimuna kwana biyu na ga duk kin sauya, me yake damunki ne?" Fuska babu walwala ta ce, "Me ka gani?" "Na ga kwana biyu kamar ba ki damu da ni ba, kuma ni dai na san ba wani abu na yi miki ba." Nazir ya furta a sanyaye. "A'a babu abin da yake damuna kawai dai baccin da na tashi ne!" "Ba haka ba ne Maimuna, a 'yan kwanakin nan ko ƙarfe nawa na dare zan kai ba za ki kira ni ba, idan na dawo kuma ba za ki tambaye ni dalilin kai wa daren da na yi ba. A yanzu ko zan kwana ina chatting uffan ba za ki ce mini ba, ni sai na ga kamar haushina kike ji." "A'a ni babu wani haushinka da nake ji, ai kowa rayuwar da ya ga dama ita yake yi. Tun da na lura kulawar da nake ba ka ce ta sa kake yi mini wasu abubuwan, don haka na bar wahalar da kaina." Maimuna ta sake yin maganar tana shirin tafiya. "Zauna mana, yau fa hira nake son mu yi. To yanzu dai ki yi haƙuri, ga biskit da chocolate nan na taho muku da shi ke da yara." Ta fahimci sarai hirar da yake nufi, domin dama ba ta cika amfani a wurin Nazir ba sai yana buƙatarta. Sau tari idan hakan ta taso babu wata kulawa da nuna soyayya haka kawai zai afka mata, ta kawar da kai gefe ta ce. "Ai kuwa sai dai ka yi haƙuri zuwa gobe kaina matsanancin ciwo yake, shi ya sa ma na sha magani na kwanta ɗazu." Tana gama maganar ta janye hannunta ta wuce ɗaki, kamar sakarai haka yake bin Maimuna da kallon mamaki. Ya san dai Maimuna ba shiga gidan kowa take ba, ballanta ya ce maƙota ne suke zuga ta. Kuma ya santa da ƙorafi matuƙar ya ɓata mata rai ko bai san laifin ba za ta fito ta sanar da shi. Da sauri ya tashi ya bi ta ɗakin a lokacin har ta ja bargo ta rufa, ransa ya sake ɓaci amma sai ya saita nutsuwarsa ya ce. "Magana nake yi miki fa Maimuna kika shigo ɗaki." Tana daga kwance ta ɗago ta ce, "Ni ma ai amsa na ba ka Abban Asiya." Ƙwafa ya yi ya juya ya fita, ya zauna ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama uzurinsa sannan ya shiga ɗakin ya kwanta a gefenta, juyi yake shi kaɗai yana mamakin sauyin halinta. Don haka ya so danne buƙatarsa amma sai ya gagara, hannu ya kai ta janyo ta kamar tana jira ta ture shi tana faɗin. "Haba Abban Asiya, wai me kake yi haka na ce maka ban da lafiya fa." "Kin sauya Maimuna, Me ya sa kike son horar da ni ne? Yau rabona da ke kwana nawa, rannan kin ce mini zazzaɓi kike. Shekaran jiya kin ce ciwon baya, yanzu kuma kin ce mini kanki yana ciwo. Idan kina ganin ba za ki iya ba ni haƙƙina ba sai na ƙara aure." Nazir ya furta cike da barazana saboda ya san Maimuna tana da kishi, amma cikin halin ko in kula ya ji Maimuna ta ɗago ta ce. "Sai me don ka yi aure Naziru? A kaina za ta zauna? Ko ni zan ciyar da ita, ruwanka ne ka ƙara aure kuma ruwnaka ne ka bari na samu lafiya. Idan kuma ƙarin auren ka ga shi ya fi maka mafita wallahi ni ko a gefen takalmina." Tsoro ne ya kama shi saboda ya ji an ce idan mace ba ta ba ka kulawa, ba ta nuna kishi a kanka kawai zama take yi da kai ba don soyayya ba. Da a ce a shekarun ba ya ne ba zai yi mamakin jin haka daga gare ta ba, amma yanzu da shekarun aurensu suka tura ya lura duk ta zubar da makamanta. "Au haka kika ce?" Nazir ya faɗa a zafafe. "Eh haka na faɗa, tun da kishiya ba a kaina aka fara ba." Tana gama faɗa ta sake gyara kwanciyarta. Cike da kewar Maimuna Jafar ya nufi gida, a lokacin da ya shiga ƙarfe goma sha ɗaya da rabi. A zaune tunkur ya samu Maman Nana da alama jiransa take yi, ya shiga ɗakin kamar bai ganta ya fara rage kayan jikinsa. "Abban Nana wato fitar da ka yi gidan su budurwarka ka tafi ko?" Bai waiwayo wurinta ba ya ce, "In ji wa?" "Sai an faɗa mini?" "To tunaninki bai harsaso miki daidai ba." Shi ma ya faɗa fuska a haɗe. Hakan kuwa ya sake harzuƙa ta, rai a ɓace ta ce. "Wai Abban Nana me kake nufi ne? Ka bi ka sauya mini lokaci ɗaya na rasa gane kanka, da idan ka shigo gidan bayan sallar Isha'i ba ka sake fita sai washegari. Amma yanzu kana gama cin abinci sai ka fice ba za ka dawo ba sai dare, na gaji fa wallahi na gaji da irin cin kashin da kake yi mini." "To idan ba za ki iya ba sai ki nemawar kanki mafita." Ta riski miyagun kalamansa a cikin kunnuwanta, ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Cike da tsoro ta dube shi amma sai ta nuna masa ba ta fahimci abin da yake nufi ba ta ce. "Me kake nufi?" "Ina nufin idan ba za ki iya zama da ni da ki kama gabanki." Wani irin dum! Ta ji kamar an kwaɗa mata guduma, da sauri ta runtse idonta ta buɗe su a kansa. Ta taka gabansa muryarta tana rawa ta ce, "Abin da za ka ce mini kenan Abban Nana? Dama ka gaji da ni ban sani ba?" "Ko ban gaji da ke ba wulaƙancin da kika tarko ne ba zan ɗauka ba, na lura samu ma yana saka mace ta yi iskancin abin da take so. Amma babu damuwa tun da irin zaman da kike so mu yi shi kenan." Shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta, ta shiga nazari daga safiyar ranar zuwa dawowarsa ko za ta iya tuna laifin da ta yi masa amma ba ta iya tunawa ba. "Don Allah ka faɗa mini laifin da na yi maka Abban Nana?" Bai tanka mata ba ya saki tsaki ya ɗauki fulo ya koma kan kujera ya kwanta. Abin duniya ne ya haɗe wa Maman Nana, sai ta ji ya fara ba ta tsoro domin lamarin nasa ƙara yin gaba yake yi. Don haka ta shiga alla-alla gari ya waye ta leƙa gidan Maimuna ko ta ba ta shawarwarin abin da za ta yi. Washegari Tun da Jafar ya yi sallar Asuba bai koma ba, gari yana yin haske ya shiga cikin kitchen ya ɗauke tukunyar cilinder gas ya fice da ita. Da yake Maman Nana ba ta tashi da wuri ba, saboda a daren bacci bai ɗauke ta da wuri ba ko kaɗan ba ta san wainar da ake toyawa ba. Sai da ta ji alamun buɗe gate ta tashi ta fito, a tsammaninta Jafar fita ya yi kasuwa. Banɗaki ta shiga bayan ta fito ta shiga kitchen za ta shirya wa su Nana abin breakfast da na makatanta. Amma sai ta ga wayam babu clinder, ba ta kawo komai a kanta ba; sai ta yi tsammanin ko ƙaro musu gas zai yi saboda idan ya ga ya kusa ƙarewa yana ɗauka ya ƙaro mata. Tana daga ƙofar kitchen ta hango shi yana kokawar shigowa da ƙaton buhun gawayi, sai da ya ƙarasa ya jingine shi sannan ya sake fita gate ya sauke mirgino buhu na biyu. Maman Nana tana tsaye ya gama dire buhunnan gawayin har guda biyar, sannan ya ɗauko kurfoti ya dire a gabanta. Fuska a haɗe ya ce, "Daga yau ga abin da za ki dinga girki da shi, gas ya sake tsada ba zan iya sayensa ba. Cilnder ma na sayar wa mai shagon da nake sako mana gas, sai a ci gaba da malejin rayuwa tun da komai tsada yake sake yi." Jafar yana gama faɗar haka ya shige ɗaki. Kabir kwance ya yi a kan gado, yana jin haushin kansa a kan abin da ya aikata. Fushin Fauziya ya fi komai ɗaga masa hankali, don Fauziya mace ce mai haƙuri da sauƙin kai. Amma idan ta yi fushi ba ta iya zuciya ba, juye-juye ya fara yi yana hangen ta da take kwance idonta biyu tana hawaye. A hankali ya tashi zaune ya tsugunna a gefenta murya a sanyaye ya ce. "Fauziya! Don Allah ki tashi mu yi magana, ba na son ki saka kanki a cikin wani hali saboda yanayin da kike ciki." Ɗagowa ta yi ta dube shi, tana jin sautin muryar martanin batsar da yake mayarwa da Hafse a cikin kunnuwanta. Zuciyarta ta shiga zafi, wani abu ya tokare ƙirjinta. A hankali ta fara jin mararta tana tsira mata, ta cije bakinsa tana girgiza kai. "Don Allah ki yafe mini..." "Idan ka sake yi mini magana zan fice daga gidan nan na ba ka wuri." Ta katse shi da wani irin sauti, kamar sabon munafiki haka Kabir ya ja jiki yana sunne kai ƙasa ya koma kan gadon ya zauna. A cikin wannan daren daga shi har Fauziya bacci rabi da rabi suka yi, sai bayan Asuba ta samu bacci mai hauyi ya yi awon gaba da ita. Tun da Kabir ya tashi bai koma ba, saboda ya san ya yi wa Fauziya laifi a hankali ya dinga aiki don kada ya tashe ta. Shi ya dafa wa yara abinci, ya shirya su suka tafi makaranta. Sannan ya shiga ɗakin ya share mata, kwanukan wanke-wanken kuma ya ajiye a bakin rariya zai wanke mata. Lawisa tana sanye da hijabi tana girki a bakin ƙofarta ta hango shi ya tsugunna zai yi wanke-wanke, miƙewa ta yi ta ƙarasa wurin ta ce, "Baban Na'ima ka bari zan wanke mata, ko jikin Maman Na'iman ne." Kabiru ya ɗan sosa kai ya ce, "Eh ta tashi ba ta jin daɗi ne, shi ne ta ɗan kwanta zan rage mata aikin." "Subhanallah! Allah Ya raba lafiya, bari na ƙarasa girki sai na haɗa na wanke da nawa." Godiya ya yi mata sannan ya koma ɗakin, tun da ya shiga yana son ya tambaye ta abin da za zai girka musu da rana yana shakkar tashinta da ɓacin ranta. Tukunyarta ya buɗe ya ga akwai sauran miya, sai kawai ya ɗora taliya ya dafa musu. Kafin Fauziya ta tashi tuni Kabir ya gama komai, hatta turaren wutar da take sakawa ya saka musu. Ya shiga ɗakin ya same ta a bakin gado a zaune ta tashi, fuskarta ta sauya sosai daga jiya zuwa yau duk ta rame. "Ga ruwan wanka zan sirka miki sai ki yi wanka." Kabir ya furta yana satar kallonta, ko kallonsa ba ta yi ba har ya sake maimaita mata. "Don Allah ka matsa daga gabana Kabir." Da sauri ya fice daga ɗakin, ya shiga banɗaki ya yi wanka. A inda ya bar ta a nan ya same ta, bayan ya shirya ya tambaye ta abin da take buƙata a wannan karon ma banza ta yi da shi. Don haka ya zaro dubu ɗaya ya ajiye mata, bayan ya fita ta bi bayansa da kallon tsana. Miƙewa ta yi ta ɗauki wata 'yar babbar leda ta ɗebo kaya a drowerta, sai da ta yi wanka ta ɗauki kular abincin su ta zuba, sannan ta saka wata doguwar rigar atamfa ko man kirki ba ta shafa ba. Bakin ƙofar Lawisa ta ƙarasa ta ce. "Lawisa ga abincin yaran nan da kayan makarantarsu, idan sun dawo don Allah su wuce makaranta." Lawisa ta karɓa tana faɗin, "Ai na leƙa kina bacci, wai ko abar ce ta zo." Fauziya ta girgiza mata kai ta ce, "Ga wannan mukullin kuma koda babansu zai dawo." Da mamaki Lawisa ta bi Fauziya da kallo, don ba ta taɓa tafiya unguwa ta ajiye mukulli ta ce a ba wa Kabir ba, amma sai ta haɗiye abin a ranta don tun daren jiya ta fahimci akwai abin da yake damunta saɓanin maganar da ta faɗa mata. Sallama Fauziya ta yi mata ta fice daga gidan, tana fatan wannan fitar da ta yi daga cikinbaƙin gida ya zame mata ita ce fita ta ƙarshe da za ta yi masa. +2347062062624 [14/02, 17:27] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA TAKWAS UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Kabir tun da ya fita daga gidan ba a nutsuwarsa yake ba, kwata-kwata ya rasa me yake yi masa daɗi. Zuciyarsa ce ta shiga wassafa masa laifin abin da ya aikata, har yake jin kamar ya rabu da su Hafsee ya rungumi matarsa ita kaɗai. Ɗaya tsagin na zuciyarsa kuma, ya shiga kwaɗaita masa haɗe da harsaso masa surorin jikin Surayya da Hafsat. Nan take ya ji sam ba zai iya rabuwa da su ba, koda a ce bai auri su duka ba. To tabbas dole zai auri ɗaya, domin zuciyarsa ta jima tana kaɗayin dandalar ni'imar da Allah ya yassare musu. Rashin walwala da sukunun da yake ciki, ya sa mutanen cikin shagon suka lura da shi. Har suke tambaayarsa ko ba shi da lafiya, saboda Kabir mutum ne mai faram-faram yana da sakin fuska sosai. Ganin ya gagara gudanar da aikin da yake yi, yamma liƙs ya yi wa Ogansu sallama ya ce zai koma gida saboda ba ya jin daɗin jikinsa. Lokacin da ya tunkaro gida, kamar ya kira Fauziya a waya ya tambaye ta ko akwai abin da take buƙata ya sayo mata. Sai kawaa ya haƙura, saboda ko sunanta ya tuna gabansa faɗuwa yake yi. Lokacin da ya ƙarasa gida kusan shida saura, su Na'ima suna jin sallamarsa suka fito daga ɗakin Lawisa da sauri suka rungume shi. Mukulli ta ba wa Fatima ta ce ta kai masa. Kabir turus ya yi a bakin ƙofar ganinta rufe da kwaɗo, kamar yaran sun san tambayar da take cikin zuciyarsa Hidaya ta ce. "Mami ta je unguwa!" Gabansa ne ya faɗi, ƙafafuwansa har rawa suke yi saboda tashin hankali. Da ƙyar ya iya saita nutsuwarsa hannunsa yana karkarwa ya buɗe ƙofar ɗakin suka shiga, yana shiga ɗakin ya fara kiran layin Fauziya sai dai tashin farko ya ji an ce masa a kashe take. Kamar zai yi hauka, haka ya fara zagaye ɗakin da sauri-sauri. Wani tunani ya faɗo masa cikin sauri ya sake riƙo hannun yaran, ya kai su ƙofar ɗakin Lawisa ya ce su shiga zai je ya dawo. Rufe ɗakin ya yi ya sake ba wa Lawisa mukullin sannan ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama. "Ina Fauziya ta tafi? Ko dai ta tafi gidansu ne? Fauziya ba ta taɓa yin yaji ba, ko ƙarata ta kai gidansu? Yanzu haka za su dinga yi mini kallon mutumin banza? Kai Fauziya ba za ta yi mini haka ba, ina da tabbacin ba za ta bankaɗa labulen sirrina ba." Haka Kabir ya dinga tafiya yana surutai kamar sabon taɓin hankali, domin kafin ya ƙarasa bakin titi gani ya yi hanyar ta ƙara yi masa nisa. A gurguje ya tari adaidaita sahu ya nufi uguwarsu Fauziya, yana zuwa ya samu mahaifinta a ƙofar gida yana sallar magriba. A hargitse ya zube a gabansa yana faɗin, "Baba barka da yamma." "Baba ya yi masa kallon tsaf ganin ƙafafuwansa duk sun yi butu-butu, da mamaki ya ce. "Barka dai Kabiru, kai ne da doshin magriba haka? Ya Fauziya da yaran?" Turus! Kabir ya yi ya ɗan sosa kansa, gabansa ya cigaba da faɗuwa saboda fargaba. Amma gudun kada Baba ya gano shi sai ya ce, "Duk lafiyarsu ƙalau, dama wucewa zan yi na ce bari na biyo mu gaisa." Baba ya saki murmushi ya ce, "To Ma Shaa Allahu, ai jiya mun ga abin alheri. Allah dai ya raya zuri'a." Jiki a sanyaye Kabir ya amsa sannan ya cewa Baba zai wuce. Haka Kabir ya cigaba da tafiya yana kiran layin Fauziya har lokacin a kashe, gidan ƙawarta Jamila ya je suka gaisa. Ita ma ta wurga masa tambayar Fauziya, don ta yi mamakin ganinsa a ƙofar gidanta. Saboda rabon shi da gidanta, tun tana amarya da suka zo mata shi da Fauziya kusan shekara biyar kenan. "Kabir ko ƙawar tawa ce ta haihu?" Jamila ta jefe masa tambaya tana gyara mayafinta. "Amm dama na ɗauka ta ƙaraso nan ne, da yake ta fita ɗazu ta ce mini idan ba ta yi yamma ba za ta biyo ta nan. To mukullin yana hannunta, kuma akwai ɗinki wata Mai jego da aka zo karɓa daga nesa, ga ɗakin ta rufe shi. Na kuma kira wayarta a kashe." Ita ma Kabir ya zabga mata ƙarya, Jamila ta ce. "Ai kuwa ba ta biyo ba, ina jin ko kun yi saɓani a hanya tun da magriba ta yi." Amsa mata Kabir ya yi suka yi sallama. Tunanin duniya ya shiga yi a kan inda zai je ya lalubo Fauziya, saboda tun da suke duk faɗan da za su yi ba ta taɓa yi masa irin haka ba. Wayarsa ce ya ji ta fara ƙara, da sauri ya ciro ta a tsammaninsa ita ce sai ya ci karo da lambar Surayya. Guntun tsaki ya saki ya ƙi ɗauka, amma sai ta cigaba da kira. A ƙufule Kabir ya ɗauka yana faɗin, "Wai Surayya me ya sa kin fiye naci ne? Idan kika ga ban ɗauka ba ai kin san ina uzuri." Daga can ɓangaren Surayya ta kwantar da murya ta ce. "Haba sweet..." "Babu wani sweet, Surayya ba na cikin nutsuwata yanzu haka duniyar ta yi mini zafi." "Me yake damunka baby? Ko za ka zo na rage maka damuwa?" Kamad Kabir ya buɗe baki ya faɗa mata abin da ya faru, sai kuma ya tuna idan ya yi haka kamar ya rusa soyayarsa ne, idan Surayya ta ji labarin hotunan tsiraicin da hafsa ta tura wa Fauziya ne ya sa ta fita daga gidan. "Wannan ba damuwarki ba ce, family issuesne." Daga haka ya katse wayar, sai ya sake lalubar layin Fauziya amma a kashe. Gida ya ƙarasa ya laɓe a soro, don kada mutanen gidan su fahimci akwai matsala tsakaninsa da ita. Ganin har lokacin ba ta dawo ba ya sa Kabir ya nufi gidan Inna domin ya sanar da ita halin da ake ciki, a lokacin da ya shiga gidan har an fara kiraye-kirayen sallar Isha'i. Yana shiga ɗakin Inna ya nemi wuri ya zauna haɗe da haɗa kai da gwiwa. Inna da ta gama alwala ta shiga ɗakin ta ce. "Kabiru nake gani da daren nan?" Kabiru ya share ƙwallar idonsa ya ce, "Inna ni ne." "To ashe Fauziyan ta isar maka da saƙona, amma ba ka samu zuwa ba sai yau. Yau kuma me ka kawo mini, saboda dama garin tuwona ya ƙare." Inna tana yin gama magana ta ji Kabir yana shasshekar kuka, a ɗan kaikaice ta leƙa fuskarsa ta ce. "Wai kuka kake yi Kabiru? A cikin yaranka wata ce ta mutu?" Kabir ya girgiza mata kai, Inna ta sake cewa. "To Fauziyan ce ta mutu?" A nan ma ya sake girgiza mata kai. "To uban me ya sa ka kuka tun a farkon daren nan? Ni dai na san rabon da na ga kukanka tun ranar da mahaifinku ya mutu." "Inna gida na koma na ga Fauziya ba ta nan, na je gidansu da niyyar tambayarsu sai mahaifinta ya tambaye ni ya take, kin ga kenan ba ta je can ba. Ga shi dama ba ta tambaye ni ba, ban san inda ta tafi ba." Kabir ya ƙarasa maganar yana zubar da ƙwallah. Wani takaici ne ya maƙure ziciyar Inna, ta dube shi a wulaƙance tana sakin dogon tsaki ta ce. "Mttssswww amma dai Kabiru ka yi asara wallahi, yanzu a kan mace kake zubar da ƙwalla? Ashe abin da ake faɗa gaskiya ne, yarinyar nan ta gama wanke hannu a kanka." Inna ta koma bakin gado ta zauna ta cigaba da cewa, "Yo wai ma Fauziyar yarinya ce? Da za ta fice har ka dinga neman saboda ta ka ganɗma lalacewa" Cikin damuwa Kabir ya ce, "Wallahi Inna ni ne da laifi, ni na ɓa ta mata rai, duk macen da ta ga abin da na yi fiye da haka ma za ta iya aikatawa." "To ai sai ka yi ta yi tun da wahala ta aure ka, yanzu kuma a ina ta bar yaran?" Kabir ya ce, "Suna ɗakin matar gidanmu." "Amma wannan yarinya an yi baƙar munafika, haka kawai ina zaune ƙalau ta ɗaga mini hankali. Sai ka fita ka kai cigiyarta gidan radiyo, tun da lalacewarka ta kai haka." Daga haka ta saka hijabinta ta tayar da sallah. Kabir da ya lura zamansa a wurin Inna ba mafita zai kawo masa ba, sai ya miƙe ya fice. Kasancewar Sadiya ta ji duk abin da yake faɗa, sai ta tsayar da Kabir tana tambayarsa. A nan ya zayyane mata duk abin da ya faru, duk da bai fito ya faɗa mata laifin da ya aikata ba. Shiru ta yi tana nazari, amma har cikin ranta take ji Kabir ne bai kyautawa Fauziya ba, domin ta san tana da haƙurin gaske. Saboda damuwa Kabir haka ya dinga takawa a ƙafa, yana tafe yana jimamin halin da take ciki da tsohon ciki a wannan lokacin. A haka har ya ƙarasa gida. Tun lokacin da Fauziya ta tashi daga bacci ta ji mararta da bayanta suna ciwo, don haka ta yanke shawarar zuwa asibiti. A ranta tana fatan koda haihuwar ce ta zo mata, tana fatan ta kasance silar tafiyarta lahira. Duk haihuwa ukun da ta yi Kabir ne yake kai ta asibiti, daga baya kuma sai ya kira matar mahaifinta ya sanar da ita idan sun je. Amma da yake zuciyarta a cunkushe take da haushin Kabir, ya sa ta ɗauki duk wani kaya da za a buƙata a asibiti. Ta ƙi sanar da Lawisa ne, saboda ta san idan suka tafi ita da Lawisa asibiti babu a inda su Na'ima za su zauna ballantana su ci abinci. Sai da ta fara biyawa ta gidan Dillaliya ta roƙe ta, da ta ba wani abin daga cikin cikon kuɗin firji, bayan ta karɓi kuɗin ta fice daga gidan. Fauziya ba ta damu da kallon da mutane suke yi mata ba, tana tafe tana hawaye haka ta dinga tafiyar ƙafa domin ya taimaka mata wurin samun saurin naƙuda. Ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu adaidaita sahu ya kai ta asibiti, a lokacin da ta je asibiti ana duba ta aka ga tana 5cm. Wayarta ta ciro ta fara kiran ƙanwarta da suke uba ɗaya ba ta same ta ba, ta kira ta matar babanta ita ma a kashe. Na'ima ba ita ta haihu ba sai bayan sallar magriba, ta haifo jaririyar 'yarta mace kyakkayawa mai kama sak da Kabir. Ido ta ƙurawa jaririyar tana kallo, saboda tsananin kamar da suke yi da mahaifinta. Wani irin takaici ya kamata sai kawai ta fashe da gunjin kuka, Midwife ɗin da ke gefe ta dafa ta ta ce. "Maman baby kukan kuma na mene ne? Ai farinciki ya kamata ki yi, tun da Allah Ya raba ku lafiya." Murmunshin yaƙe Fauziya ta yi, sannan ta ciro wayarta ta sake kiran lambar ƙanwarta Shukura. A wannan karon ta ci sa'a an ɗauka, a nan ta sanar da ita asibitin da take. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba Shukura ta ƙarasa asibitin, bayan an gama duba ta da jaririyarta aka sallame ta suka wuce gida. Lokacin da Fauziya ta yi sallama da gudu yaranta suka fito daga ɗakin Lawisa suna faɗin. "Mami oyoyo." Turus! Lawisa ta yi ganin Shukra tana rungume da jaririyar Fauziya, tsalle Lawisa ta buga ta ƙarasa gabanta ta ce. "Wai dama matar nan abin da kika fita kenan? A gaskiya kin shammace ni Maman Na'ima, shi ma kuma Abban Na'ima abin ka da namiji bai ce mini haihuwa kika fita ba. Barka-barka uwar 'yan'mata, In Shaa Allahu matar gwamna kika haifo mana." Fauziya ta saki murmushi, tana shirin shiga ɗaki su A'ilo suka fito suka yi mata barka sama-sama kowacce tana yamutsa fuska. Sai da Shukura ta yi mata ɗan abin da ba a rasa ba, sannan ta wuce gida. Kafin wani lokaci tuni Lawisa ta ɗora mata ruwan wanka, sai da ta surka mata sannan ta karɓi jaririyar ita kuma Fauziya ta shiga wanka. Bayan Fauziya ta gama Lawisa ta haɗa mata ruwan shayi ruwan bunu. Karamcin da Lawisa ta yi mata ya sa ta dinga zabga mata godiya, har sai da Lawisan ta nuna ɓacin ranta. Sai da ta yi wa su Na'ima shimfiɗa, ta tambayi Fauziya ko akwai abin da za a yi mata ta ce a'a, sannan Lawisa ta yi mata sallama ta tafi ɗakinta. Lokacin da Kabir ya shiga gidan hango ɗakin ta ya yi a kunne da fitila, wanda hakan ne ya ba shi tabbacin ta dawo gidan. Ƙafarsa har harɗewa take saboda sauri, a haka ya faɗa ɗakin. A zaune ya same ta jingine da gado, yanayin fuskarta babu yabo babu fallasa. A fili Kabir ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, saboda farinciki kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha. Fauziya yi ta yi kamar ba ta gan shi ba, sai dai kallo ɗayan da ta yi masa ta fahimci duk ya fita a kamanninsa. Ƙafafuwansa sun yi futu-futu kamar wanda aka tuno daga rami, a gefenta ya zaune murya a raunane ya ce. "Fauziya!" Ido ta zuba masa tana kallo sai dai ba ta amsa masa ba, ya riƙo hannunta a sanyaye ya ce. "Hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba da na dawo na ga ba kya gidan nan, don girman Allah ki yi haƙuri ki saurare ni. Na san na yi kuskure amma don Allah ki yafe mini." Ajiyar zuciya Fauziya ta sauke tana janye hannunta daga cikin nasa ta ce, "Da a ce ban yafe maka ba, da fitar da na yi ba zan sake tsoma ƙafata a cikin gidan nan ba." Lumshe ido ya yi cikin farinciki ya ce, "Wallahi wannan yarinyar da kika ga maganarmu ban jima da haɗuwa da ita ba, kuma kin san akwai shaiɗanun mata da suke jan hankali maza. Wannan ne nan farko da ƙarshe, In Shaa Allahu haka ba za ta sake faruwa ba..." "Wannan ba damuwa ta ba ce Kabiru! Amma ka sani, ka zabtare kaso casa'in da tara na daga cikin yarda, ƙauna da amincin da na damƙa maka. Ka shayar da ni ruwan mamaki Kabir, mamakin da har zuwa numfashina na ƙarshe ba zan daina yin sa ba. A kullum ina son ka dinga tunawa, kai ma uba ne. Uban 'ya'ya matan da kake yunƙurin ɓa ta tarbiyyar 'yar mutane." Shiru Kabir ya yi yana jin kalamanta suna ratsa shi, ko babu komai ya ji daɗi da ta furzo abin da yake cikin zuciyarta. Ya sake marairaicewa ya ce, "Duk abin da kika faɗa haka ne, In Shaa Allahu zan kiyaye. Amma don Allah ki daina fushi da ni, wallahi fushinki shi ne abin da ya fi komai ɗaga mini hankali." Kabir ya faɗa yana jiran amsarta, kukan jaririya ya ji a bayanta. Fauziya ta juya ta ɗauko ta tana yunƙurin ba ta mama, wani irin abu ne ya tsarga masa kamar wanda aka yi wa shocking. Da wata irin murya cike da ruɗewa ya ce, "Wai dama kin haihu Fauzina?" Fauzina da ta ji ya faɗa ya sa kalmar ta ƙara ba ta mata rai, ta tuno boyis ɗin da ta saurara wanda ya yi wa Hafsa da ta ji yana cewa, duk duniya bai taɓa yi wa kowacce mace soyayyar da yake yi mata ba. Ganin ba ta za ta ba shi amsa ba, ya sa shi saurin karɓar jaririyar ya rungume a ƙirjinsa. Kamar mutum-mutumi haka Maman Nana ta daskare a tsaye tana kallon Jafar har ya shige ɗaki, ita abin ma mamaki ya ba ta. Domin tun da suka yi aure ba ta taɓa amfani da gawayi ba, duk da a shekarun baya ƙarfin Jafar bai kai na yanzu ba. Rufa masa baya ta yi cikin ɗakin, yana ganin haka ya sake haɗe fuska. "Abban Nana wai me yake faruwa? Me ya sa kake son cusguna mini? Me na yi maka duk ka canza kake ƙaƙalo abin da za ka cusguna mini?" Maman Nana ta yi maganar muryarta tana rawa. "Me kuma na yi miki?" "Amma clinder fa ka ɗauke mini ka kawo buhunhunan gawayi ka ajiye mini." Sai da ya ɗaura towel ɗin wankansa sannan ya ce. "Su waɗanda suke amfani da gawayin mutuwa suka yi? Ko kuma taɓo ya yi musu a goshi? Am sorry to say na ga ke gidanku ma da itace suka amfani." Saukar kalaman Jafar a kunnenta ji ta yi tamkar an buga mata guduma. Maman Nana ta haɗiyi wani irin abu mai ɗaci a zuciyarta, idonta ya ciko da ƙwalla. "Gori za ka yi mini Abban Nana? Ko dai ka daina ƙaunata ne? Wane ne yake zuga ka a kan iyalinka ne?" Jafar ya matsi toothpaste kamar ba zai tanka mata ba, sai da ya je bakin ƙofa ya waiga ya ce. "Babu ɗaya daga ciki, kawai ke kika yi zargin haka. Yanzun ba ni da ƙarfin saka gas ne..." "Wallahi kana da shi Jafar, sai dai idan wani ne yake zuga ka kuma wallahi ba zan yi amfani da gawayi ba." Maman Nana ta furta cikin kuka, jin hayaniyarsu ya sa Abdul ya rarrafa ya riƙe ƙafarta ya saka kuka shi ma. Ɗaukarsa ta yi tana hawaye ta ji ya ce, "Ke dai Sumayya wallahi ba matar rufin asiri ba ce, ban da haka saboda na kawo miki gawayi, za ki yi mini hayaniya har maƙota su ji." Wani irin sak Maman Nana ta yi, tana jin wata irin juwa tana yunƙurin taɗe ƙafafuwanta. Hawaye ya shiga kwarara daga kwarmin idonta, cikin ƙunan zuciya da sarewa ta ce. "Yau ni kake kira da ba matar rufin asiri ba Jafar?" Cikin halin ko inkula Jafar ya ce. "Mata nawa ne a nan unguwar suka amfani da gawayi? Su sun yi wa mazajensu irin abin da kika yi mini? Idan kina son rufin asirina ba hannu bibbiyu za ki karɓa ki sarrafa ba, mata ku dai halinku sai Allah. Da kun samu sake a gidan miji sai ku manta halin da kuke ciki a gidanku." Baƙaƙen maganganun Jafar suka sake baƙanta ranta, zama ta yi a wurin ta ci kuka ta more saboda ɗacin da zuciyarta take ciki. Tana nan zaune har Jafar ya fito daga banɗaki, sai da ya gama shiryawa sannan ya ce mata. "Idan kin gama ki miƙa su Nana makaranta ni ina da uzuri da wuri zan fita." Yana gama maganar ya fice. Kamar ta ga sabuwar hallita haka ta bi bayan Jafar da kallo, zuciyarta ce ta shiga yi mata saƙa da warwara. Sai ta fita ta fara yunƙurin kunna kurfitin, amma ta ƙona ashana ta fi goma ba ta kama ba. Sannan ta ɗauki wata ledar pure water ta kunna da ita A nan ta samu wutar da kunnu, da yake tana da ruwan tea fulas sai ɗumame kawai ta yi, bayan ta sauke ta ɗora doyar su Nana ta makaranta. Saboda rashin sabo Maman Nana ba ta gana suyar doya ba sai kusan ƙarfe tara na safe, da yake bayan su Nana sun gama breakfast shirya su ta yi ta miƙa su. Sai daga ba ya ta kai musu abin break, da ta koma ta ɗora abincin rana. Wuni ɗaya da ta yi gidan gabaɗaya ya ɓaci da toka, hannuwanta sun yi baƙi da gawayi. Sai kusan azahar ta gama girki sannan ta gyara gidan. Ranta ya ɓaci sosai da ta ga cikin faratanta duk baƙin gawayi, gyara gidan ta yi bayan ta gama ta faɗa wanka. Sai da ta yi wa Abdul wanka sannan ta shiga gidan Maimuna, a harabar gate ɗin ta same ta sanye da hijabi ta ce. "Sai ina kuma uwar Asiya?" Maimuna ta gyara saka hijabin ta ce, "Wallahi almajirina ne bai zo ba, ga lokaci ya ƙure yara sun kusa dawowa kuma gawayina ya ƙare." Maman Nana ta saki tsaki ta ce, "Hmmm wai kin san ni ma yau Abban Nana buhunnan gawayi ya dire mini? Wallahi namiji ɗan kunama ne. Kin ga cin zarafin da ya yi mini yau a kan na ce ba zan yi girki da gawayi ba?" Maimuna har cikin zuciyarta ta ji wani irin daɗi, a cikin zuciyarta ta raya. 'Ƙaryar banza ashe ke marar kunyar ƙarya ce?' Amma a fili sai Maimuna ta ce, "Ikon Allah, ni kam lamarin Abban Nana kullum ƙara gaba yake, wai ni ko dai neman aure ya fara ne? Maman Nana sai fa kin tashi tsaye, ba na son dai ki yi mini wata fassarar da sai na ce gaskiya sai kin haɗa da neman taimako." Maman Nana ta yi shiru tana juya kalaman Maimuna a ranta. Ummou Aslam Bint Adam🌚 +2347062062624 [17/02, 19:53] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA TARA UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Ganin kamar tarkonta ya kama Maman Nana ya sa ta saki murmushin gefen baki, ta ɗan taɓo ta da tuni ta dulmiya kogin tunani. "Na ga kin yi shiru Maman Nana, amma fa kada ki yi mini mummunar fahimta. Lamarin ne nake ganin kamar ba banza aka bar shi ba, tun da ke da bakinki kike cewa a duniya Abban Nana ba ya son abin da zai sa ki wahala ko ya ƙuntata miki. Kwanaki na ji kin ce har girki yake taya ki da rainon yara, shi ya sa na ce ko za ki haɗa da neman taimako." Maman Nana ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan girgiza kai, don ko kaɗan ba ta da ra'ayin zuwa wurin malaman a kan duk wani abu da ya sha mata kai. "Kai an ya kuwa Maman Asiya? Gaskiya ba zan iya ba, saboda malaman nan idan ka fara zuwa wurinsu sun fara kunto maka matsaloli kenan. Bari dai mu gani zuwa nan gaba." Maman Nana ta ƙarasa maganar tana dafa ƙofar, ba haa Maimuna ta so ba. Don haka ta taɓe baki a fakaice ta ce, "To ai shi kenan, Allah Ya yi mana magani. Kin san akwai malamai akwai kuma muna malamai." Maman Nana ba ta tanka mata ba, suka fito ita da Maimuna. A madadin Maman Nana ta koma gida sai ta shiga gidan ɗayar maƙociyarsu da ke ɓarin hannun hagu, buga ƙofar ta yi babu jimawa Maman Sudais ta buɗe mata. Daga bakin ƙofa Maman Nana ta tsaya ta ce, "Maman Sudais kwana biyu." Maman Sudais da ba ta cika shiga shirgin maƙotan ba ta taɓe baki ta ce, "Lafiya ƙalau, daga ina haka?" "Gidan Maman Asiya na leƙa." Maman Nana ta furta, nan take Maman Sudais ta haɗe rai sannan ta ce. "Aminan juna kenan, ki gaishe ta idan kun sake haɗuwa." Maman Sudais ta faɗa cike da ƙagauta, ganin haka ya sa Maman Nana ta fita ta wuce gida. Maman Sudais ba ta da shige-shigen maƙota, idan har ta shiga gida to sai dai idan abin jaja ko murna ne ya kai ta. Ba wai dom mijinta ya hana ta ba, sai don tuntuni haka tsari da ra'ayinta yake. Koda cefane ta fita sai dai ta sayi abin da za ta saya, idan sun haɗu da maƙotan a bakin hanya sai su gaisa. Har gara idan ta ga an ɗauki kwanaki tana iya leƙawa a tsaitsaye su gaisa ta koma gida, dalilin da ya sa ba su cika ga maciji da Maimuna ba tun watarana da Maman Sudais ta kama Maimuna da ƙanwar mijinta suna gulmarta, da yake ko kaɗan dangin mahaifin Baban Sudais ba sa son ta. Yau da gobe shigar da take yi gidan Maimuna ya sa suka yi sabo har da ƙanwar mijinta, a ranar da za ta kama su bayan ƙanwar mijin tata ta fito da niyyar tafiya gida, sun yi sallama tun da jimawa sai ta faɗa gidan Maimuna. Ashe ita take ƙara hura wuta tsakanin Maman Sudais da dangin mijinta, duk wani sirrinta take kwashe take faɗa musu. Dalilin da yake da a kullin suke ƙara kafa nata ƙahon zuƙa, Maman Sudais ta fito sayen ashana ta ga Salma ta fito daga gidan Maimuna tana faɗin. "Ai wallahi daga yau yaya ya daina saya wa mahaifinta maganin hawan jinin, gara da kika faɗa mini. Ina zuwa wallahi kamar Umma ta ji labari..." Maganarta ta maƙale sakamakon ido huɗu da suka yi da Maman Sudais, murmushin takaici ta sakar mata ta ce. "Maimuna kenan, na ba ki yarda da aminci ashe cin dunduniyata kike? Idan kuwa ni ce yadda Annabi ya bar duniya na bar ki kenan." Cike da borin kunya Maimuna ta ce, "To zancenki ake yi da za ki faɗa wa mutane magana? Idan kin bar ni Baban Asiya ne ya bar ni ko me? Ai dama ba zamanki nake yi ba." A ranar haka suka rabu baram-baram dutse a hannun riga, tun daga wannan ranar idan ba abin jaje ko gaisuwa ba ne babu abin da yake haɗa su da Maimuna. Gaisuwar ma sai da Abban Sudais ya takura mata da yake ta sanar da shi komai, kuma shi mutum ne mai fahimta ya ce ta kiyaye zamanta da maƙota. Don haka take takatsantsan da gabaɗayansu, tsakaninta da su sai hirar duniya ko ta yara. Kuma tun daga lokacin ta rage ba su fuska, shi ya sa yawanci suka daina shigar mata sai Maman Nana da take leƙa mata sama-sama. Sai da Maimuna ta sayo gawayi bayan ta ɗora girki, ta sake shiga ɗaki ta ɗauko sabuwar wayarta da Jafar ya aiko mata, dama tun bayan fitar Nazir ta ciro ta haɗe da saita komai ta yi masa Salam ta whatsapp. Saboda farinciki kamar Jafad zau taka rawa haka suka ɓa ta lokaci suna musayar kalaman soyayya, domin a ranar Maimuna ba ta yi aiki gida da wuri ba. Don haka a yanzun ma da ta koma ta kira shi voice call ta whatsapp da yake ta ga yana online, yana ɗauka suka dasa daga inda suka tsaya. Daga ƙarshe ya ce ta ɗauki hotuna masu kyau ta tura masa. Wannan ne ya sanyaya mata jiki, kuma tsoro ya kamata. Har ta shiga wasu-wasin kada ta zo tsautsayi ya ratsa Maman Nana ta gani, duk da ta ji ya ce mata zai ɓoye amma haja kawai ta ji tana tsoron tura hoton. A ɓangaren ɗaya kuma ta ji kamar ba ta kyauta masa ba, domin shi ya zuba maƙudan kuɗinsa ya saya mata wayar saboda haka. Jin ta shiru ba ta tura masa ba ya sa shi kiranta a waya ya sake tunasar da ita, sai da Jafar ya yi da gaske sannan ra iya tura masa tana sake jadadda masa da ya san yadda zai yi ya adana hoton ta yadda kwaɓarsu ba za ta taɓa yin ruwa tsululu ba. Nazir irin bauɗaɗɗun mazan nan ne, kuma yana ɗaya daga cikin mazan da ba su damu da ba wa mace haƙuri ko lallaɓa ta ba idan ta yu fushi ko idan sun yi mata laifi. Idan har Maimuna ta ga ya ɗan sakar mata fuska to a ranar yana buƙatar kusantarta ne. Abin da ya fi ci wa Maimuna tuwo a ƙwarya bai wuce rashin ba ta kulawa ba, idan Nazir ya dawo gida ba shi da abokiyar hira sai wayarsa. Koda hira Maimuna ta zauna tana yi masa sai dai ya dinga ba ta amsa sama-sama, amma kaso casa'in cikin ɗari (90%) hankalinsa yana kan wayarsa. Da yake Maimuna tana da ɗan surutu ta dinga yi masa mita kenan, tana nuna ɓacin ranta. Hakan ne ya sa wani lokacin Nazir ba ya dawowa gida da wuri, sai ya gama uzurorinsa a waje. Ya kasance mutum mai takura, bin diddigi da rashin yarda. Don hatta maƙota ba ya barin Maimuna shiga, su ma kuma a ɓoye suke shigo mata bai sani ba. Duk inda Maimuna za ta je shi zai kai ta, kuma bai cika kai ta da rana ba har sai ya dawo daga kasuwa. Kuma idan ya kai ta duk taron da ake yi sai dai ya jira ta a ƙofar gida agama ya tafi da ita. Maimuna tun tana zama ta ci kuka bayan aurensu har abin ya zame mata jiki, kuma sannu a hankali Nazir ya aurensa ya sure mata har take jin Allah Ya kawo sanadin da za su rabu wala mutuwa ko sakin aure. Sakamakon halinsu da ya yi hannun riga da ita, tun da har babbar waya ya hana ta riƙewa a cewarsa duk wani abu da zai buɗe idonta ba zai lamunra ba. Tun da ai sai mace ta yi mu'amala da mutane ake ba ta munanan shawarwari, ko a zuge ta ta sauya halaye. Idan kuwa aka ɗora mace a doron da ya ɗora Maimuna, a ganinsa hakan ne zai daidaita mace ta zama kamila tun da idonta bai buɗe ba. Tarihin Maimuna Maimuna 'yar asalin garin Dutse ce da ke jigawa, mahaifi da mahaifiyarta duk 'yan can ne. Kuma su biyar ne a wurin iyayensu, yayanta Sadik shi ne babba sai ita take binsa ƙannenta mata uku suke biye da ita. Maimuna ta yi karatunta na addini daidai gwargwado, ha boko kuma ta tsaya a secondary. Domin mahaifinsu mai sauƙin ra'ayi ne, idan yarinya ta samu miji zai aurar da ita ra'ayin mijinta ne ta cigaba ko ya hana ta. Idan ba ta samu miji ba kuma ta cigaba da karatu, kuma hakan ce ta faru da Maimuna. Tun tasowar Maimuna 'yar gayu ce mai sosai, tana son ƙwalisa. Uwa-uba tana da wayewa, don ƙawayen da take hulɗa da su duk masu buɗaɗɗan ido ne. Maimuna tun tasowarta take da tsari, don ra'ayinta ne auren namiji mai kuɗi da iya soyayya. Kuɗin ma bai cika tasiri a ranta ba matuƙar namiji zai ba ta kulawa da soyayya koda mai rufin asiri ne za ta iya zama da shi. Dalilin haka ya sa ta gama tsara rayuwar da za ta gudanar a gidan aurenta, ita da mijinta. Tarihin Nazir Nazir haifaffan garin Kano ne, sai dai mahaifi da mahaifiyarsa asalinsu 'yan garin Katsina ne. Neman kuɗi ne ya kawo mahaifinsa garin Kano, a nan duk aka haife su shi da ƙannensa. Mahaifinsa yana da mata biyu da 'ya'ya takwas, ƙannensa da suke uwa ɗaya guda uku ne duka maza. Sai waɗanda suke uba ɗaya su shida kasancewar shi ne babba a wurin mahaifinsa. Nazir kasuwancin hulunan maza yake a kasuwar kwari, shagonsa babba ne kuma yana da rufin asiri bakin gwargwado. Nazir ya haɗu da Maimuna ne a wurin dinner wani abokinsa da suka yi a garin jigawa, da yake tana daga cikin manyan ƙawayen amarya. Tun da Nazir ya ganta ya maƙale mata har aka tashi daga taron, amma kafin su a watse sai da suka yi musayar lamba sannan ya kai ta har ƙofar gidansu ya sauke ta. Ko kaɗan Nazir bai kwanta a ran Maimuna ba, don tun daga yanayinsa bai yi mata kalar irin mijin da take burin zama da shi ba. Shi kansa Nazir ya fahimci haka, don ko kiran wayarta ya yi wani lokacin ba ta ɗauka. Da ya yi bincike a kanta, sai aka yi masa bayanin halinta tsaf da yanayin waɗaanda take mu'amala da su. Hakan ne ya sa Nazir ya lulluɓe kura da fatar akuya, sai da ya tabbatar da da ya siffantu da irin mijin da Maimuna take muradi sannan ya koma mata tsamo-tsamo. Tun Maimuna tana share shi har ya fara karkato da hankalinta kansa, don tuni ya saye zuciyarta ta hanyar ƙyale-ƙyale da kayan ƙawa. Ya shiga shayar da ita romon zallar soyayya tana sharɓa, har sai da ta dinga gina musu irin rayuwar da za su gudanar a gaba. Hakan ya sa Nazir ya bijirowa Maaimuna da maganar turo magabatansa, kafin ta amince da ta suka yi yarjejeniya a kan bayan sun yi aure za ta cigaba da karatu. Don tana da burin yin aiki a gaba, tashin farko Nazir ya amince mata. Hakan ya sa aka tsayar musu da lokacin aure, da lokacin ya ƙarato Nazir ya yu mata bajimta ta hanyar kama manyan kuma ƙayatattun wuraren taro na alfarma. Matsalar farko da Maimuna ta fara fuskata a ɓangaren ƙawayenta ne, domin ko wata ba su yi ba da aka tashi bikin wata ƙawarsu ya ce ba za ta je ba. Lamarin da ya kai su ga yin faɗa, saboda Samira aminiyar Maimuna ce ta yi mata ƙoƙari a sha'anin bikinta. Wannan faɗan har sai da ya kai su gaban iyaye, a nan kuma kowa ya ba wa Maimuna rashin gaskiya da cewar mijinta yana da damar da zai hana ta zuwa bikin kowacce ƙawa, kuma mahaifinta ya jadadda mata idan har ta kashe aurenta ba tare da wani dalili ba sai dai ta nemi wani wurin ba gidansa ba. Wannan ikon da Nazir ya samu ya sa kai tsaye ya yanke alaƙar Maimuna da ƙawayenta, tun suna yin kara suna zuwa wurinta har kowa ya janye jikinsa saboda ba zuwa wurinsu take yi ba. Hatta garinsu sai ta shafe lokaci mai tsayi.ba ta je ba, idan sun tashi tafiya kuma shi zai kai ta ya zauna a ƙofar gida idan yamma ta yi ya ɗauko ta su dawo gida. Sannu a hankali Nazir ya dinga bijirowa Maimuna da ɓoyayyun halayensa, tun daga wani faɗa da suka yi ya karɓe babbar wayarta ya ba ta ƙarama. Sannan makarantar da suka yi yarjejeniya ya ce ba za ta cigaba da karatu ba, da ta kai ƙararsa gida kuma sai iyayenta suka nuna mata tun da aure gaba yake da komai gara ta zauna ta yi ibadar zaman aure. Da zaman aurensu ya yi zama ne Maimuna ta fahimci kuɗin da yake mata facaka da su ba su kai haka ba, don a farko kallon mai kuɗi take yi masa sai daga baya ta gane duk munfurtarta y yi. Tun daga wannan lokacin Nazir ya sire wa Maimuna, tana dai zaune da shi ne saboda biyayyar mahaifinta. Da zaman haka ya ishe ta sai ta nuna wa Nazir tana buƙatar yin kasuwanci, amma fir ya ƙi ba ta dama. Wata irin ƙaunar Fauziya ce ta lulluɓe Kabir, yana daga tsaye ya zauna a gefenta ya haɗe ta ita da jaririyar ya rungume su cike da so da ƙauna. Ƙwace kanta Fauziya ta shiga yi, ya riƙe ta tsam sai suka saki ajiyar zuciya kusan lokaci ɗaya. "Don Allah ki bar ni na ji ɗuminku!" Kabir ya furta cikin shauƙi, fa sauri Fauziya ta fisge zuciya tana ɗaci ta ce. "Ni a wa da za ka ji ɗumina? Ka bari ka je wurin Hafsa ai tana da abubuwan da ba ni da su." Kabur sam bai ji daɗi ba, ya marairaice murya ya ce. "Duk fa wasu kalamai da kika ji ina na fatar baki ne, babu abin da ya taɓa haɗa ni da ita. Ni ko gidansu ma ban sani ba." Fauziya ba ta tanka masa ba, ta taɓe baki tana bin sa da harara. Tun daga wannan ranar Kabir ya shiga nannan da Fauziya, ita kuma har lokacin ba ta ba shi fuska. Ya yi mata ɗinki kala uku masu kyau, sai jaririya da saya mata rigunan kanti kala uku. Su Na'ima kuma suja tashi da atamfa ɗaiɗai, ba ta yi wani taro ba. Tsirarun mutanen da ba a rasa ba, ta yi kyau sosai kamar ka sace. Kabir da ya shiga gidan ya ganta sai ya shiga rawar ƙafa, ganin kada mutane su fahimci ba sa shiri ya sa ta saki jiki 'yan uwa suka shiga ɗaukarsu hoto. A wannan lokacin Kabir bai samu damar yanka wa jaririya hakika ba, sai haƙuri da ya ba wa Fauziya da yake ta san yanayin samunsa ya sa ba ta damu ba. Sannu a hankali Kabir yake ta shawo kan Fauziya har ta saki jiki da shi suka dawo kamar da, amma kafin nan sai da ta tasa shi a gabanta ya kira Hafsa ya ci mata mutumci don a ganinta duk budurwar da za ta tura wa namiji tsiraicinta ba matar aure ba ce. Saboda kafin ta sa ya kira shi sai da ta tambaye shi idan auren Hafsat zai yi ya ce a'a, don haka ta hura masa wutar sai sun rabu idab ba haka va ta bar masa gidan ya zauna da ita. Wannan shi nw dalilin rabuwar Kabir da Hafsa, saboda duk rashin zuciyar mace sai ta ji haushin irin wulaƙancin da ya yi mata. Don Kabir yadda ya dinga cin zarafinta nuna wa ya yi kamar dama can Hafsan ce ta maƙale masa, a yadda ta fahimta ma nuna wa yake ba su da dpguwar alaƙa ita da shi. Ranar da Kabir ya je ƙofar gidansu ba ƙaramin cin mutumci ta yi masa ba, duk yadda ya kai ga son lallashinta ko kaɗan bai shige ta ba. Saboda a ganinta Kabir ba mijin aure ba ne tun da bai isa da matarsa ba, domin ya bayyana a fili ba zai iya adalci ba. Ranar Juma'ar da suka wayi gari ita ta yi daidai da saura kwana biyu rak su tashi, don tun ranar Laraba Lawisa ta tashi suka kama haya a unguwar rimin kebe. Ranar Juma'ar kuma ita ma A'ilo ta tashi, sai su Maman Sabir da suka haɗa kayansu su ma washegari Asabar za su tashi. "Abban Na'ima ban gane maka ba, har yanzu fa ba ka ce mini komai game tashinmu ba. Ka san halin mutumin nan ba sho da mutumci, mutanen gidan nan duk sun fara tashi. Saboda gudun tozarci fa na sayar da firjinmu domin mu samu mu ƙarasa abin da ba a rasa ba." Fauziya ta yi maganar zuciya babu daɗi tana ƙoƙarim danne ɓacin ranta. Saboda tun da kwanakin tashinsu ya ƙarato, ta ga wata alama daga wurin Kabir. Kuma idan ta yi masa naganar ko dai ya bagarar, ko kuma ya fara faɗan ta cika gajen haƙuri. Haɗe rai Kabir ya yi ya miƙe yana shirin fita ya ce, "Eh haka ne, amma duk tsiya ai ba za mu rasa wurin zama ba." Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai dama ba ina nufin za mu rasa wurin zama bane ina maganar ginin can ne. Ko a rana ɗaya za mu kwashe? Amma ko rana ɗaya za mu kwashe sai dai ko zuwa gobe, tun da jibi na tabbata sai ya zo da masu fitar da kaya." "Wai me ya sa kin fiye mita da takura ne Fauziya? Mtsww Allah Ya sawaƙe da wannan halin naki, ai ki kammala haɗa kaya gobe za mu koma gidan Inna kafin na ƙarasa." Kabir yana gama magana ya fice daga gidan. A yi haƙuri da errors kwana biyu kuma ban zauna ba ne, shi ya sa ban yi typing ba. Ummou Aslam Bint Adam🌚 +2347062062624 [18/02, 18:45] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA GOMA UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Kamar wacce ta ci karo da sabuwar hallita haka ta bi bayan Kabir da kallo, nan take ta cigaba da nanata kalaman da ya faɗa mata kamar mai yin hadda. Ba ta yi aune ba ta ji murfin idonta ya buɗe, hawaye ya shiga kwarara kamar idaniyar ruwa mai gudana. Duk yadda ta yi hoɓɓasar dakatar da shi sai abin ya gagara, maƙogaronta ya shiga ɗaci tana jin wani abu ya tokare mata ƙirji. Nan take ta ji ƙirjinta ya hau ciwo, don tun daga mummunan ganin da ta yi a wayar Kabir da ranta ya ɓaci sai da ta ji wani abu ya tokare mata ƙirji, sai bayan wani lokaci kuma ta ji ya lafa mata. Don bala'in da yake cikin zaman gidan Inna ba abu ne mai sauƙi ba, duba da irin abubuwan da take gani tana yi wa Sadiya. Da kuma wanda ita kanta Sadiyan take faɗa mata, wani tunani ne ya faɗo mata don haka ta yi saurin janyo wayarta ta latsa layin Kabir. Sai fa ta kusa katse wa ya ɗauka yana faɗin. "Ina hanya." Tana jin yana shirin kashewa ta ce, "Magana nake son mu yi Abban Na'ima." Kamar ba zai amsa mata ba, sai kuma a daƙile ya ce. "Ina jin ki." Gaban Fauziya ya shiga faɗuwa, tana fargabar irin fassarar da zai yi wa kalamanta. Jin shiru ya sa Kabir ya ce, "Kin san ba ki da abin faɗa kika kira ni?" Maganar da ya yi ba ƙaramin bugun zuciya ta saka ta ba, ta yi ƙarfin halin faɗin. "Abban Na'ima don Allah ka kama mini haya!" "Saboda me?" Ya wurga mata tambaya a gaggauce. "Haka kawai, ina ganin kamar za mu fi sakewa. Na ga gidan Inna kamar babu ɗaki, ga kuma yara." Guntun tsaki ya yi ya ce, "Duk ɗakunan gidan Innar ne za ki ce babu? Ko dai zama da mahaifiyar tawa ne ba kya so?" Kamar Fauziya za ta yi kuka ta ce, "A'a na ga ɗakin da ya rage ba kowa shirgi suke ajiyewa." Ajiyar zuciya Kabir ya sauke ya ce, "Na sa yara sun gyara ɗazu, idan Allah Ya kai mu da sassafe akwai mai motar da na yi wa magana zai zo ɗaukar kaya." Murya tana rawa ta ce, "Ko na kira dillaliya ta sayi keken ɗinkin nan nawa? Idan ya so kafin jibi sai mu nemi ɗaki." A hassale Kabir ya ce, "Wai me kike nufi Fauziya? Mahaifiyar tawa ce ba kya ƙaunar zama da ita? Ko kin manta ita ta ɗauki cikina wata tara ta haife? Saboda raini har ni kike cewa za ki kamawa haya, a kan ki zauna da mahaifiyata?" Nan take ta rikice, don ta san dama ba lalle ya fahimci irin abin da take gudu ba. Tuni hawaye ya wanke fuskarta, tana shirin magana ta ji Kabir ya katse a fusace. Kuka Fauziya take yi wanda take jin ɗacinsa yana fitowa daga ƙasan maƙoshinta, tsakar gidansu ta ƙura wa ido tana hangen ɗakin Lawisa. Tana ji a ranta yadda zuciyarta take zafi, da ace Lawisa tana nan ita ce mutum ta farko da za ta fara faɗawa halin da take ciki ko ta ji sanyi. Duk da wannan ba ɗabi'arta ba ce, amma tana jin idan ba ta sanar da wani ba zuciyarta za ta iya bugawa. Tashi ta yi ta fara kai wa da kawowa domin neman mafita, amma gabaɗaya kanta ya cushe. Tunanin tafiya gidan mahaifinta ta yi, a nan ma ta ga sam ba mafita ba ce domin mahaifinta ba zai taɓa goya mata baya ba. Da wannan tunanin Fauziya ta wuni har sai da zazzaɓi ya rufe ta, haka daren ranar ya zo mata cikin ƙunci. Da Kabir ya dawo ta ga yana fushi ba ta tanka masa ba, da ta miƙa masa abinci kuma ya ce ba ya ci. Ita ma da yake a cike take da haushinsa, ba ta sake bi ta kansa ba ta kwanta. A daren ranar kwana ta yi tana miyagun mafarkai a kan zamanta da Inna har gari ya waye. Tun da farar safiya mai motar da Kabir ya yi wa magana suka yi sallama, ya fara fitar musu da kaya. Fauziya tana haɗa kaya tana hawaye, Na'ima da Fatima tun da suka ji mahaifiyarsu ta ce gidan Inna za su koma duka walwalarsu ta dusashe, amma da yake Hidaya ba ta san dawan garin ba haka ta dinga tsalle tana murna. Sai da aka gama kwashe kayan tsaf sannan ta leƙa ta yi wa Maman Sabir sallama, da neman yafiyar juna. Tun da suka doshi layin ƙirjinta yake bugawa, tana fargaba irin zaman da za su gudanar a cikin gidan. Tsayuwarsu a ƙofar gidan, ya yi daidai da tsala ihun da Salim yake yi. Jiki a sanyaye Fauziya ta tsoma ƙafarta cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama. Inna ta hango a zaune ta maƙure Salim a ƙasan ƙafafuwanta tana tsala masa dorina yana sakin ihu, sai da ta gaji don kanta sannan ta ce. "Don ƙaniyarka gobe ma ka sake zubar mini da kuɗin tsintsiya, wallahi dukan da zan yi maka sai ya ninka wannan." Sai a lokacin ta ɗago ta dubi Fauziya ta ce, "Baƙin safe ashe kun ƙaraso, ga ɗaki can sai ku fara jera kaya." A ɗarare Fauziya ta gaishe ta, su Na'ima da dukan Salim ya tsorata su ya sa duka suka riƙe zanin mahaifiyarsu a tsorace suna leƙen Inna. "Ku kuma leƙen me kuke yi mini kamar ba ku sanni ba? Ku dama uwarku ba ta koya muku gaida mutane ba ko? Kai shi ya sa 'ya'yan Mudam suke birge ni, uwar su Zaliha akwai tarbiyyar. Ai kuwa ga yaranta nan gwanin birgewa, duka tarbiyyarta suka gado." Ita dai Fauziya ba ta kula ta ba, ta wuce ɗakin da aka nuna mata. A bakin ƙofa ta tsaya tana ƙarewa ɗakin kallo, ɗan ƙanƙani ne ko gadonta ta haɗa ba zai zauna a ciki ba. Ballantana a kai ga saka keken ɗinki, kwanuka, manyan robobi da akwatunan kayan yara. Sadiya ce ta ƙarasa wurin fuskarta cike da jimami ta ce, "Fauziya kun ƙaraso?" A madadin Fauziya ta amsa mata sai kawai ta fara zubar da ƙwalla, a tsorace Sadiya take waigen wurin Inna tana girgiza mata kai. Ita ma girgiza kan ta fara yi cike da tausayin kanta da 'ya'yanta. Da ƙyar ta ja ƙafa ta faɗa cikin ɗakin. Sadiya ce ta rufa mata baya ta yi ƙasa da murya ta ce, "Fauziya ba ta son tun daga zuwanki Inna ta fahimci ba kya son zaman gidan nan. Don Allah ki yi haƙuri ki mayar da komai ba komai ba, ni ban ma san yadda aka yi kuka gagara tarewa a gidanku ba. Allah na tuba indai aka yi rufi ko a ya yake ai gidanka ne, sannu a hankali sai a ƙarasa." Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce. "Sadiya!" Ɗagowa Sadiya ta yi jin yadda Fauziya ta kira sunanta, Fauziya ta share hawaye mai ɗaci ta cigaba da cewa. "Kabir ɗin da na sani a baya kamar ba shi ba ne yanzu ba, Kabir ya sauya mini Sadiya. Ina tsoron kada wani abu ya biyo bayan tariyarmu, domin a yanzu ban cika gane gabansa da bayansa ba." A fili Sadiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Tabɗijam! Lallai da alama tura ta kai bango Fauziya, tun da har yau ke kika fito kika faɗi aibun Kabir, tabbas an kusa zuwa daidai gaɓar da nake son a zo." Sadiya ta kamo hannun Fauziya ta ce, "Shi ya sa ba tun yau ba, nake nuna miki ba a ɗaukar yarda ɗari bisa ɗari a damƙa wa ɗa namiji. Ki zauna da shi saffa-saffa, ta yadda idan ya yi watsin iska da ke abin ba zai ɗaɗa ki da ƙasa ba. A duk lokacin da na ga kin nuna wauta, sau tari ina son na ankarar da ke amma ina gudun ki ga kamar ina son haɗa ki da mijinki. Ko kuma ki ga ina kushe shi, don haka na kawo na mujiya na zuba miki." Fauziya ta share ƙwallar idonta ta ce, "Haka ne Sadiya, amma don Allah kada ki ga laifina. Idan kika cire mahaifina Kabir shi ne mutum na farko da na shaƙu da shi, na kuma damƙa wa ragamar rayuwata." Sadiya za ta yi magana daga can waje suka ji Inna ta ce, "Ke Sadiya me kike yi a ɗakin Fauziya tun ɗazu ne? Ko munafurcina za ki kai mata, ga tuwo can kin bar shi yana kamawa sai ki je ki kwashe mana." Jiki yana rawa Sadiya ta amsa mata, sannan ta kalli Fauziya ta ce, "Sai na sake shigowa bari na je kada na ja miki karantsana a wurinta." Daga haka ta fice. Shiru Fauziya ta yi tana ayyana ita ma kenan irin wannan rayuwar za ta fara. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fara jan kayan tana lodewa a gefe, sai ta ɗauko katifata ta shifiɗa. Ragowar wurin da ya rage bai fi kwanciyar babba mutum ɗaya ba, keken ɗinkinta, mangal ɗin girki da abin zuba ruwanta ba su samu wuri ba sai a ƙofar ɗaki ta ajiye su. Sannan ta ɗora musu abinci, bayan ta gama ta zuba wa yaranta sannan ta zuba kaɗan a roba. Ita kuma Inna ta saka mata a plate ta rufe, Sadiya ta miƙa wa na robar sai kuma ta ba wa Inna nata. A yatsine Inna ta dubi farantin har Fauziya za ta miƙe Inna ta ce, "Au ashe fa ke ba ki san tsarin gidan nan ba ko?" Fauziya ta gyaɗa kai. Inna ta saki murfin ya faɗi ƙasa a wulaƙance ta ce, "Abincin rana a gidan nan haɗa shi ake a yi girka gabaɗaya, girkin safe da na dare ne kowa yake yin nasa. Sannan daga yau kada ki sake zuba mini abinci a ciki shatalallan faranti, saboda mu a lokacinmu kwanon uwar miji daban ake yi mata don haka ki kiyaye wannan ma ai wulaƙanci ne." A sanyaye Fauziya ta amsa mata, ta koma ɗakinta. Tana shiga ta ga Zainabu, 'yar wurin Sadiya ta cika hannu da ƙatuwar lomar abincin su Na'ima ta tura a baki, tana ganin Fauziya ta sake kwasar ƙatuwar loma ta fita a guje tana dariya. Hidaya da Fatima suka saka kuka suna faɗin, "Ta cinye mana abinci, Mami tun ɗazu take kwashe mana abinci." Shiru Fauziya ta yi sai ta ji duk zuciyarta babu daɗi, buɗe tukunya ta yi ta ɗebo daga cikin wacca ta rage za ta ci ta zuba musu. Ta zauna gefen katifa ta janyo tukunyar ta fara ci a ciki, tana nan zaune ta ga Zainbu da ƙaninta Faisal ɗan shekara ɗaya da rabi suka dinga leƙensu sai su tafi da gudu. Tun daga wannan ranar, zaman Maman Nana da Jafar ya koma irin zaman doya da manja. Sakamakon rashin kyakkayawar alaƙar da take shiga tsakaninsu. Kuma har kullum zaman nasu ƙara tsamari yake, don Jafar ya jima da ƙaurace mata. Idan dare ya yi sai dai ya ɗauki filo ya tafi falo ya kwanta, gari yana wayewa kuma ko breakfast ba ya yi yake fita. Idan ta ce abu ya ƙare sai dai ya ba ta kuɗi ta sayo kaɗan, saɓanin a baya da komai idan ya tashi dire mata yake yi mai yawa. Wani abu da Jafar ya tsiro mata da shi sai suna zaune ya ɗauki waya ya yi ta latsawa yana sakin murmushi, ita kuma da ta yi magana kamar jira yake sai ya rufe ta da faɗa. Watarana tana suna zaune da safe, da yake ranar ba ta ga alamar zai fita da wuri ba. Waya ta ga ya latsa yana kai wa kunnensa, tsam ya tashi ya wuce uwar ɗaki sai ta ji ya kashe murya yana faɗin. "Barka da hutawa My Moon." Ƙirjin Maman Nana ya buga da ƙarfi, don a yanayin maganar da ta ga yanayi ta fahimci da mace yake waya. Ta jinjina kai tana sauke ajiyar zuciya ta ce. "Wato duk wannan cin kashin da yake yi mini saboda mace ya yi mini fana? Ai kuwa ba zan lamunci ya dinga yi mini waya a ɗaki ba." Tuni zuciya ta ɗebe ta, ita ma ta faɗa cikin ɗakin a daidai lokacin ta ji ya ce. "Wallahi tallahi Moon babu wata 'ya mace nake jin kewa da muradinta a yanzu, ganin hotunanki kaɗai suna iya hargitsa ni har na gagara gane kaina." Tsaye Maman Nana ta yi hawaye ya gama wanke idonta, baki yana rawa ta ce. "Abban... Nana... ashe a kan wata 'yar iskar kake wulaƙanta ni?" Ɗago kansa ya yi ya kalle ta, ga mamakinta sai ta ga ya ɗauke kansa gefe ya cigaba da cewa. "Na rasa abin da zan yi miki don ki yarda da abin da nake faɗa, kin san Allah ke ta daban ce a cikin mata..." Shiru Maman Nana ta yi tana ƙura masa ido cike da hawaye, har gani take kamar ba Jafar ɗinta ba. Domin a baya Jafar ba ƙaramin shakkarta yake yi ba, amma a yau wai shi yake yabon wata a gabanta. A haukace ta fisge wayar ta yi wurgi da ita, cikin matsanancin kishi haɗe da ƙaraji ta ce. "Jafar ni za ka mayar mahaukaciya? Da wacce 'yar iskar kake waya a ɗakina..." Maganarta ce ta katse sakamakon wani gigitaccan mari da ya sakar mata, idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai. Ya dube ta a hargitse ya ce, "Kada ki sake ce mata 'yar iska, idan kuma ba haka ba wallahi sai na ɗauki mummunan mataki a kanki." Wani irin sanyi jikin Maman Nana ya yi, sai kuma tsoro ya kama ta. Har take ganin kamar Jafar ba a hayyacinsa yake ba, ta sake matsawa gabansa ta riƙo rigarsa tana jijjiga shi, a ganinta ko hakan zai sa ya dawo hayyacinsa. Hawaye yana zuba ta ce, "Kana cikin hayyacinka kuwa Jafar? Ni kake mari saboda na cewa wata 'yar iska?" Kamar yana jira ya yi saurin faɗin, "Na mare ki Sumayya, wallahi idan kika kuma faɗar mummunar kalma a kanta sai na yi miki abin da ya fi haka." Maman Nana ta ji kamar ya watsa mata ruwan zafi, zuciya a ƙeƙashe ta ce. "Na faɗa 'yar iska karuwa don Allah ka kashe ni a wurin nan." Kamar wancan karon haka ya sake tsinke ta da mari, sai dai a wannan karon tagwayen mari Maman Nana ta samu. Wayarsa ya ɗauka, da yake dama ya yi wanka sai kawai ya shiga ɗaki ya saka kayansa ya fice daga gidan. A wurin Maman Nana ta durƙushe tana kuka kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta sannan ta sauya kaya. Ta ɗauki Abdul da yake bacci ta goya shi ta fito daga gidan, duk wanda ya ganta kallo ɗaya zai yi mata ya fahimci ba ta cikin nutsuwarta. Gidan Maimuna ta shiga ta same ta zaune a falo, Maimuna tana jin shigarta ta saki murmushin ƙeta saboda duk abin da suka yi a kan kunnenta, tunda wayar ba mutuwa ta yi ba a lokacin da ta yi wurgi da wayar Jafar. Amma a fili tana ganin Maman Nana ta dafe ƙirji ta ce, "Lafiya kuwa Maman Nana? Me ya samu fuskarki ta kumbure haka?" Da yake har lokacin da ɗacin abin a ranta, sai Maman Nana ta rushe da kuka mai cin zuciya. 'Na rantse da Allah kuka ma yanzu kika fara, mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura." Maimuna ta faɗa a ranta, amma a fili cikin ruɗewa ta ce. "Maman Nana ki yi magana don Allah, kin ɗaga mini hankali. Daga gida ne aka kira ki wani abu ya faru, ko Abban Nana ne?" Maman Nana ta girgiza kai, Sai Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "To mene ne? Don Allah ki yi mini magana, wannan kukan da gani dai ba na lafiya ba ne." "Wai yau ni Jafar ya mara saboda wata maman Asiya, Jafar ya zama wani iri wallahi asiri aka yi masa, don Jafar ɗina ba ya cikin hayyacinsa." Maman Nana ta yi maganar cikin kuka. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Kada ki ce mini tun yarinyar da muka yi magana da ke kwanaki? Ai kin ga sakacinki Maman Nana, tun wancan karon na ce ki ɗauki mataki amma kika tsaya sanya. Yanzu ai ga shi kina gani ƙarfi da yaji yarinya ƙarama ta shanye shi." Cikin ƙaguwa da neman mafita ta ce, "Yanzu mene ne abin yi Maman Asiya?" Shiru Maimuna ta yi kamar mai yin nazari, sai ta ɗago da sauri ta ce. "Gidanku sun san abin da ya faru?" Girgiza kai Maman Nana ta yi, sai Maimuna ta ce. "Yanzu abin da za ki yi kai tsaye ki wuce gida, ki sanar da iyayenki a san halin da ake ciki. Saboda wallahi matuƙar ba a ɗauki mataki ba abin ƙara gaba zai yi, kin san aka ce idan namiji ya ji daɗin dukanka ya samu wuri kenan. Kar ma ki faɗa masa za ki tafi, ki bari sai dai ya dawo kawai ya ga ba kya nan. Idan aka yi muku sulhu daga baya sai ku daidaita ki dawo, amma ina mai tabbatar miki da sai kin tashi tsaye." Shawarar Maimuna ba ƙaramin kwanciya ta yi a zuciyar Maman Nana ba, haka ta dinga ba ta shawarwari daga ƙarshe suka yi sallama ta fita. Da yake makarantar su Nana a bakin titi take, sai ta da ɗebi kayansu sannan ta wuce ta makarantar ta ɗauke su suka wuce gidansu da ke unguwa uku. Tun bayan da Maman Nana ta yi wa Maimuna sallama da ta ji fitarta daga gida, ta kira Jafar ta kwashe ƙarya da makirci ta faɗa masa. Don har cewa ta yi Maman Nana tana ta zaginsa kuma ta ce ta tafi gidansu kenan, domin ta gama zaman aure da shi. Maganar da ta fi tsaye masa a rai da Maimuna ta ce wai Maman Nana tana kuka tana cewa, ta yi dana sanin haɗa zuri'a da shi, domin shi ba miji kuma uba nagari ba ne. Da irin waɗannan miyagun huɗubar, Maimuna ta samu yin galaba a kan Jafar. Har shi ma ya hau dokin zuciya da cewar ba zai taɓa nemanta ba, kuma ba zai je biko ba tun da ba shi ya ce ta tafi ba. Ya kuma ci alwashin ko a ranar ta nemi takardar saki, a shirye yake da ya miƙa mata kayarta. A ranar tun yamma ya dawo gida saboda ya san Maman Nana ba ta nan, kuma har cikin zuciyarsa da zai samu yadda yake so kuma da babu 'yan gulma tsaf zai ce Maimuna ta zagayo su sha soyayya. Amma da yake ya san akwai matan maƙota da suke kai kawo, sai ya haƙura da buƙatarsa. Ya shiga ɗaki ya rage kayan jikinsa sannan ya jira Maimuna a waya, ya ce ta kunna data za su yi magana. Ita ma da yake ta gama girki ta kuma sheƙa wankan ƙananan kaya, sai wayar ta shi ta zo mata a daidai. Ta whatsapp ya kira ta video call, ta ɗauka a kunyace tana sunne kai ƙasa. "Wai wai wai, wannan wankan duk ni aka yi wa? A gaskiya baby za ki hargitsa ni." Sai kuma Jafar ya shagwaɓe murya ya ce, "Don Allah idan babu damuwa ki zagayo mana Moon. Wallahi babu wanda zai gane, domin a cike nake da ƙishirwarki."Maimuna ta yi shiru tana nazari, domin ita kanta wannan lokacin ta jima tana buri da fata. Tun da dare ya yi bayan ta kwantar da yaran ta yi shiru tana ƙare musu kallo, Na'ima da Fatima ne ta yi musu shimfiɗa daga ƙasan katifa. Hidaya da Humaira kuma ta yi musu shimfiɗa a kan katifa, tana nan zaune Kabir ya shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa ta yi ta mayar da kanta gefe, saboda haka kawai haushin Kabir take ji. Shi kansa shiru ya yi ganin yanayin kwanciyar da suka yi, sai kuma jikinsa ya yi sanyi tausayinsu ya kama shi. Kayan abincinsa ta ajiye a gabansa, ba tare da ta ce masa uffan ba. Shi kansa ya fahimci fushi take da shi, sai ya ɗan saki fuska ya ce. "Haba Fauzina yanzu wannan fuskar da kika haɗe duk saboda za ki zauna da mahaifiyata ne, zaman nan fa ba na dindindin ba ne. Don Allah ki daina ɓata ranki ba na so." Fauziya da dama ciki take da shi ta ce. "Ni ba ina fushi da zaman da zan yi tare da mahaifiyarka ba ne Abban Na'ima, domin Inna tamkar mahaifiyata haka na ɗauke ta. Kawai yanayin zaman ne bai yi mini ba, dubi a inda yaran nan suka kwanta. A gaskiya sam babu tsari wallahi, don girman Allah ka bari mu koma gidannmu idan ya so ko a hankali sai ka ƙarasa." Kabir ya ɗan yi jim ya ce, "Ummu banat kin san dai muna da maƙiya, waɗanda suke son ganin cigabanmu, wallahi ba na son na koma a ga gidana ko fulasta babu. Kin san idan aka ce shago ba naka ba ne sai haƙuri, Oga ba wata kyakkaywar sallama yake mana ba. Kin ga Allah Ya taimaki Sani da yake shi kekensa ya kai shagon, shi yake cin gashin kansa. Sai dai ɗan kuɗin da yake bayarwa duk shekara, wanda Oga yake cikawa ya biya kuɗin shago. Ni ma kin ga da ina da keken kaina rufin asirin da zan samu sai ya fi haka." Shiru Fauziya ta yi, ta kallo keken ɗinkinta da ke waje. Ta tuna ba wani ɗinki take samu ba, mafi yawa sai ɗan gyare-gyare da mata suke kawo mata. A yadda take jinta kamar kwance cikin ƙaya, babban burinta bai wuce ta ga sun tashi daga wannan gidan ba. Don haka ba ta yi dogon tunani da nazari ba ta ce. "Indai hakan zai sa ka yi ka ƙarasa mana, ga kekena nan ka ɗauka Abban Nana. Babban fatana Ubangiji ya rufa mana asiri." Tana gama magana Kabir ya rungumo ta jikinsa, sai ya shiga sakar mata kiss a duk ilahirin jikinta. Cikin wata irin murya ya ce, "I love you my Fauzee." Fauziya ta saki murmushi ta ce, "I love you too Abi." Gani ta yi Kabir yana yunƙurin wuce gona da iri, don haka ta janye shi daga jikinta ta ce, "Ga abincinka fa." Kafaɗa ya maƙale mata yana bin ta da wani irin kallo ya ce. "Idan da ke abinci da komai ba ne." Tana shirin sake yin magana Kabir ya janyo ta jikinsa, ya shiga yawo da hannuwansa a cikin jikinta. "Wallahi kunya nake ji, magana ta Allah ba zan iya wani abu a cikin ɗakin nan ba. Don gani nake kamar Inna tana jin duk abin da muke yi, tun da kaga ɗakinmu a jikin ɗakinta yake. Kuma ka dubi kusancin kwaniya da muka yi da yaran nan." Kabir ya zame hannun rigarta ƙasa, ya ɗora kanta a saman cinyarsa cikin wata irin murya ya ce. "Babu abin da za ta ji, don haka kada ma ki..." "Kabiru! Kai Kabiru ashe kana ciki?" Maganar Inna da bakaɗa labulen ɗakin da ta yi ne ya sa maganar da Kabir yake yi ta maƙale, cikin tsananin jin kunya Fauziya ta tashi tana jan rigarta sama. Inna ta saki baki haɗe da riƙe baki ta ce. "Dole na ji ku shiru a ɗaki mana, ku dai wallahi an yi jarababbun yara. Don masifa tun a farkon dare? Ko tara fa ba ta yi ba, shi ne za ki saka yaro a ɗaki ki ƙadandane kamar alkaki." Shi kansa kunya Kabir ya ji, ya ɗan sosa kai ya ce. "Amma Inna ai da kin yi sallama kafin ki shigo." "Ba zan yi ba, na ce ba zan yi shashashan banza da wofi. Ina ganin jarabar su Sadiya da duk asuba za ka ji su suna karafniya da ruwa kamar kifaye, ashe nasu shafar mai ne tun da ga ku; ku tun garin bai nausa ba. To idan ka gama shinshine-shinshinen sai ka zo ka same ni a ɗaki." Inna ta ƙarasa maganar tana sakin tsaki sannan ta wuce ɗakinta. Bayin Allah na kusa kammala free pages, masu son littafin za su biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [19/02, 17:43] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHA ƊAYA GIDAN INNA Wani irin ɓacin rai ne ya lulluɓe zuciyar Fauziya, rai a ɓace ta miƙe tsaye tana ɓalle maɓallin rigarta. Shi kansa Kabir bai ji daɗi ba, cikin tausasa harshe ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri Fauziya." Fuska babu walwala ta ce, "Babu damuwa." Ya ɗan leƙa fuskarta ya ga har lokacin babu alamar fara'a, duk sai ya ji babu baɗi. "Kin san iyaye wani abin sai ana haƙuri da su." Ya furta a sanyaye. "To ni me na ce Kabir? Ka je idan ka gama sai ka ci abincin." Fauziya ta furta bayan ta zura doguwar rigar bacci, can gefen katifa ta koma ta kwanta. Kamar Kabir zai yi mata magaba sai kuma ya fasa ya nufi ɗakin Inna. A bakin gado ya samu Inna da alama ta gama cika, ya zauna a ƙasa ya ce. "Gani Inna." "Kai ma ashe sakarai ne Kabiru ban sani ba? Don Allah kai ba ka ji kunyar kanka ba, a ce tun farkon dare ka naniƙe 'yar mutane a ɗaki? Kai Allah dai ya sawaƙe da wannan jaraba ta 'yan zamani." Shiru Kabir ya yi, sai ya ji kunya duk ta kama shi. Inna ta taɓe baki ta ce, "To dama kuɗinka na wurina nake son na ranta, idan ba amfani za ka yi da su ba. Na ji an ce barkono ya sauko a ƙauye zan saro na dinga ƙulla wa yaran nan." Da sauri Kabir ya ɗago ya ce, "A'a Inna, dama na ce ki adana mini su ne saboda ban samu ciko ba. Amma zaman da muka yi da Fauziya, yanzu ta ba ni keken ɗinkinta, idan na sayar da shi sai na haɗa kuɗin suka cike dubu ɗari. Idan ya so sai a tura su Yaya su kai kuɗin, don Allah Inna kada ki taɓa ko sisi, wallahi yayan yarinyar nan ne ya ba ni sati biyu. Idan ban tura ba zai iya aura mata wani." Inna ta wara hannu ta ce, "Ai ka ga matar rufin asiri, wallahi da Sadiya ce sisi ba za ta ba shi ba. To idan an kai kuɗin auren wai a ina za ka saka ta, ban da abin ka ai da bari ka yi ka kammala gidanka tukunna. Ka ga lokacin hidima ta yi maka sauki, don ma kai Allah Ya haɗa ƙashin arzikinka da na matarka" Tagumi Kabir ya zuba da hannuwa biyu ya ce, "Wallahi ni ma haka na so Inna, to yayanta ya matsa ne. Haka ta kira ni tana kuka wai zai aura mata wani ɗan uwansu idan ba ta fitar da miji ba." A gwasale Inna ta ce, "To dama mene ne ribar yawan zancen idan ba aure za a yi ba? Ai gara a yi wacce za a yi a wuce wurin." Kabir ya tashi daga wurin da yake zaune, ya hau kan gado gefen Inna ya riƙo hannunta, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce. "Amma wata alfarma nake nema a wurinki Inna, don girman Allah ki cewa su Yaya kada su faɗa wa matansu. Don ina gudun kada Fauziya ta ji labari, da so samu ne ma har sai bikin ya matso tukunna." "Idan ta ji uwarka ce da za ta hana ka aure? Ko kuma ƙanwar uwarka ce ita?" Kabir ya miƙe tsaye cikin tsoron kada Fauziya ta ji ya ce, "Don Allah Inna ki yi shiru kada ta ji, kin san fa yadda aka yi wurin sayen filin gidan can da kuma ginin. Wallahi idan ta sani tana iya cewa Surayya ba za ta zauna a gidan ba, tun da haɗa su nake son yi.." "Mtsswww." Inna ta ja dogon tsaki ta cigaba da cewa, "Amma dai wallahi an yi lusarin namiji, shashasha da bai san ciwon kansa ba. Saboda ta sayar da firjinta ta ba ka ka sayi ƙofofi, sai ta hana ka yin aure? Wai me ya sa kake son zama sakarai hotiho ne Kabiru? Kai ne fa miji ba ita ba, wai dama haka ka lalace a wurin yarinyar nan ban sani ba?" Kabir ya saka hannu yana kare bakinsa alamar Inna ta yi shiru, ya sake kwantar da murya ya ce. "Ba fa kuɗin firji nake nufi ba, wannan ai na ƙarshe-ƙarshe ne da ta ba ni. Kin manta na ce miki kuɗin gadon wurin mahaifiyarta ne, ta ba ni muka haɗa da kuɗin wurina muka sayi filin, to a ginin ma akwai kuɗaɗen da ta ara mini sai daga baya ne ta ba ni na firji." Jin kalaman Kabir ya sa Inna ta taɓe baki ta ce, "To sai me? Kai dai an riga da an shanye ka wallahi." Kabir da ya lura Inna ta ɗauki zafi kuma tana iya tsula wa kwaɓarsa ruwa, sai ya shiga rarrashinta. Sannan ya nuna mata da ta gargaɗi 'yan'uwansa a kan maganar auren, har ya samu ya shawo kanta. A lokacin da ya koma ɗaki Fauziya tuni ta yi bacci saboda gajiyar aikin da ta sha, cikin sanɗa ya sake jan ƙafa ya fice daga ɗakin sai ya nufi hanyar fita. A bayan layinsu ya tsaya ya zaro wayarsa ya latsa lambar Surayya, bugu ɗaya wayar ta yi ya ji ta ɗauka muryarta da alamun bacci. "Baaabyyy." Jin yanayin muryarta ya sa jin wani irin yanayi, ya kwantar da murya yana raɓewa a jikin bango ya ce. "Baby wannan muryar tana azabtar da ni." Surry ta saki murmushin ƙeta ta ce, "Kamar yadda taka take hargitsa ni ba." "Albishirinki zumata." Cikin sauri Suryy ta ce, "Goro My." "In Shaa Allahu a satin nan su Yaya za su kawo kuɗin aurena gidanku." Farinciki kwance a saman harshenta ta ce, "Don Allah da gaske?" "Zan yi miki wasa ne?" Kamar tana gabansa ta girgiza masa kai, Kabir ya cigaba da cewa. "Ina tunanin har da rana za a saka, kafin nan da shekara guda In Shaa Allahu na gama haɗa lefe." Surry ta sake kanne murya ta ce, "Na ji daɗi sosai sadaukina, ina ƙaunarka masoyi." Shi ma Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Na yi kewar komai naki." "Surayya da komai mallakinka ce Kbna." Wata sabuwar soyayyarta ce ta sake mamaye shi, ya gyara tsayuwarsa haɗe da sakarwa wayar kiss kamar yana tare da Surayyan. Sun jima suna musayar daɗaɗan kalamai, sai da dare yayi sosai sannan suka yi sallama Kabir ya koma gida. Yanayin da Surayya ta jefa shi a ciki ne ya sa bayan ya gama cin abinci, ya lallaɓe jikin Fauziya domin ya rage zafi. Duk da ya so a ce Surayya ce a maƙale a gefensa, amma a haka ya samu da ƙyar Fauziya ta ba shi haɗin kai. Domin gani take ko yaya suka yi motsi Inna za ta iya gane halin da suke ciki. Washegari tun da farar safiya ta fara jiyo hayaniyar Sadiya da mijinta, tun suna yin faɗan da cacar baki a cikin ɗaki har suka fito tsakar gida. Kamar Fauziya ta danne kada ta fita, sai ta ji kamar dukanta Sadiya Yaya Nura yake yi. "Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, Allah sai ya saka mana." "Kada ki yafe mana, ai wallahi na yi nadamar aurenki." Cikin kuka ta ji Sadiya ta ce, "Ni zan faɗi haka don wallahi na gama zama da kai har abada." Da sauri ta fita tsakar gidan tana faɗin, "Subhanallah me yake faruwa haka?" Wurin Sadiya ta ƙarasa da ke yashe a ƙasa tana kuka, a daidai lokacin Yaya Nura ya fito yana faɗin. "Ki tarkata komatsanki ki koma can baƙin garinku, na ƙarashe ragowar igiyar aurenki a kaina. Na saki, yau zan yi bacci da saleɓa." Sadiya ta fisge hannunta daga jikin Fauziya ta ce, "Sai me? Ai wallahi da wannan ƙaddararran auren na ka gara na ƙarasa rayuwata a haka." A wannan lokacin Kabir ya fito daga banɗaki ya ce, "Haba Yaya, a gaskiya abin da ka yi sam bai dace ba. Aunty Sadiya ba ta cancanci haka daga wurinka ba, ga duka ga saki abin ya yi yawa." "Ɓarauniyar za ka ce na cigaba da zama da ita? Me ake da mace ɓarauniya ana zaune ƙalau, ni wallahi da na san haka zuri'arsu take ta ɓarayi; wallahi da ban auro ta ba. Haka kawai ta zo ta gurɓata mini zuri'a da mugun hali." Inna da tun farko take ɗaki tana sauraronsu, sai a lokacin ta leƙo ta ce. "Ai wallahi ya yi mini daidai, saboda Allah Sadiya duk ta raina yaron nan. Miji wasa ne? Abin ya kai har da sata, yara gasu nan su uku ne Allah ya raya su." Mamaki ne ƙarara ya lulluɓe Fauziya, don son zuciyar Inna a bayyane yake ƙarara. Duk wanda ya ga Sadiya ya ga halin da take ciki ya san ba ta jin daɗin gidan aure. Cikin tsantsar tsana Sadiya ta miƙe ta isa gaban Inna zuciya tana suya ta ce, "Ai dama 'ya'yanki ba sa laifi, amma ki sani ki bar ganin 'ya'ya maza duk gare ki. In Shaa Allahu sai kin ga sakayyar son zuciyar da kika nuna mini, shi kuma yadda ya azabtar da ni da yunwa haƙƙinmu ba zai bar shi ba. Sata kuma da ake iƙirari ko gaban malamai na je hukuncin sata ba zai hau kaina ba. Saboda abinci ya hana mu, ni kuma na shiga rumbunsa na ɗiba zan girka mana shi ne ya rufe ni da duka. Allah Ya ba ni wanda ya fi ka, domin kai ba mijin aure ba ne." Yaya Nura ya saki dariyar izgilanci ya ce, "Kina fama da gajartar ne za ki samu wanda ya fi ni, ai ni ma tsautsayi ne ya taɗe ƙafafuwana har na faɗo kanki. Ki tashi ki fice mana daga gida, kuma kada ki sake ki ɗaukar mini 'ya'ya." Tuni hawaye ya wanke Fuskar Fauziya ta ce, "Sadiya wai mene ne haka kuke yi a gaban yara ne?" Ta kalli yaran Sadiya da su Na'ima da suka yi carko-carko, wasu daga cikinsu suna hawaye. "Waɗannan mutanen da kika gani ƙarshen butulaye ne, ba su san karamci da hallaci ba Fauziya. Hakan shi ya fi mini alheri In Shaa Allahu." Sadiya tana gama magana ta miƙe ta shiga ɗaki, kayan jikinta ta sauya. Ta ɗauko wata ƙatuwar jakarta ta loda kayanta a ciki, hijabinta ta saka ta fice daga gidan. Maƙota ta dinga bi tana karɓar kuɗaɗen waukau da take bi, sannan ta ƙarasa titi ta taro Mai adaidaita sahu har ƙofar gida. Kusan a inda ta bar Fauziya a nan ta koma ta same ta, suna ganinta gabaɗaya suka yi kanta cikin sanyin jiki. Ɗaki ta shiga ta jango ƙatuwar jakartata, Salim da Zainabu suka ƙarasa suka rungume ta suna kuka. "Don Allah kada ki tafi Umma." "Umma idan kika tafi Inna dukanmu za ta yi." Suka furta cikin kuka, hawayen da Fauziya take riƙewa ne ya fara zuba. Ta saka hannu ta toshe bakinta tana kuka, Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci hawaye masu zafi suka shiga tsiyaya daga idanunta. Cikin tausasa lafazi ta riƙo hannunsu ta ce, "Zan dinga zuwa ina ganinku lokaci-lokaci, Allah Ya yi muku albarka Zainabu." "A'a mu dai ki tafi da mu." Zainabu ta faɗa tana hawaye. Da sauri Yaya Nura ya ƙarasa a fusace ya fisge hannunsu yana faɗin, "Duk wanda na ƙara jin muryarsa sai na taka wuyan yaro." Fauziya ta ƙarasa cikin kuka ta ce, "Don Allah ka bari ta yi sallama da 'ya'yanta cikin salama, wannan hawayen da ka ga suna fitarwa har abada ba za su manta da shi ba." "Da ta san tana ƙaunar yaran take ƙin yin haƙurin zaman gidan ubansu." Sadiya ta dube shi cike da tsana ta ce, "Kada ki damu Fauziya, ni uwa ce na tabbata duk daren daɗewa za su nemo ni. Hakan da ya yi ba shi zai sa su kankare ni a matsayina na mahaifiyarsu ba, ba don na san halin mugun halin gidan nan ba. Da sai na damƙa miki amanar 'ya'yana, amma na san wacece ke Fauziya da kyakkyawar zuciyarki. Ina fatan Allah ya sada mu da alheri. Fauziya ta rungume Sadiya tana hawaye, a hankali ta janye jikinta tana jan jaka har ƙofar gida. Ganin haka ya sa su Salim suka saki matsanancin kuka suna ƙwala mata kira. Sadiya ba ta waigo ba sai ma hawaye da take zubarwa, jakar ta saka a cikin adaidaita sahun. Har ta zauna a ciki tana jin ihun Zainabu da take ƙwala mata kira tana ihu, sai kawai ta kifa kanta a kan cinyoyinta ta saki gunjin kuka mai cin zuciya. GIDANSU MAIMUNA Shirun da Maimuna ta yi ya sa Jafar ya ce, "Kin yi shiru My Moon." Maimuna ta ce, "Gaskiya tsoro nake ji, kada tsautsayi ya sa Nazir ya dawo bai same ni a gida ba. Ka san akwai matsala tun da ba barina fita yake ba, ni dai ina ganin mu cigaba da yin video call hakan zai fi." Ba don ya so ba ya narke mata ya ce. "To ya na iya baby? Amma dai gaskiya ki rage mini kayan jikinki, na fi son na ganki sosai bari ni ma ki ga." Jafar yana gama maganar ya jingine wayar a gefe, ya zame ragowar ƙananan kayansa. Ita ma Maimuna babu kunya, ta zame rigar jikinta. Ya rage daga ita sai rigar mama, can saman gadonta ta haye sannan ta ɗauki wayar ta ce. "Baby ka gama kuwa." Ido suka haɗa ta cikin wayar, Jafar ya ji wani irin abu ya tsarga masa. Bakinsa yana rawa saboda shauƙi ya ce, "Mooooonnn." Yanayin yadda ya kira sunanta ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido, sai ta buɗe su tana ƙura wa faffaɗan ƙirjinsa mai cike da yalwataccan gashi da kallo. 'Haƙiƙa dole Maman Nana ta dinga ɓarin zancan a kanka, tabbas! Jafar ba irin ragowar sauran mazaje ba ne.' Maimuna ta raya a ranta, tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Baby wai dama haka Allah ya zuba miki sura? A gaskiya Nazir ba ƙaramin dace ya yi ba." Maimuna ta shagwaɓe murya ta ce, "Nazir ne ya yi dace ko Maman Nana? Allah Ya sani ba zan ɓoye maka ba Baby J. Wallahi za a daɗe ba a samu ingarman namiji kamarka ba." Kalaman Maimuna suka sake kashe masa jiki, ya kwantar da murya cikin shauƙi ya ce. "Ina ma yanzu haka a tare muke, da na shayar da ke romon soyayyar da ba ki taɓa sharɓa ba. Ina kewarki Moon, ina ƙaunarki komai ina ji a kanki Habibtee." Maimuna ta saki murmushin jan hankali, suna cikin haka Jafar ya nemi Maimuna da ta cire rigar da ta rage mata, kamar ba za ta iya ba sai sheɗan ya sake ingiza ta. A hankali ta cire komai na jikinta, suka shiga musayar munanan kalaman batsa. Suna nuna wa junansu duka sassan jikinsu, Daga Jafar har Maimuna ba ƙaramin gigicewa suka yi da ganin surar junan ba. A haka har Jafar ya yi galaba a kanta, ta amsa masa gayyatar da ya dinga yi mata magiya. Maimuna ta amsa masa da cewar za ta shiga wurinsa washegari idan Nazir ya tafi kasuwa, tun da yaranta suna makaranta. Ya so ta shiga a ranar amma ta nuna masa yamma ta yi, yaranta za su iya dawowa daga makaranta. Daga ƙarshe suka yi sallama cike da kewar juna. MAMAN NANA Tun bayan da ta fita daga gida take tafe tana hawayen baƙinciki, ta biya ta makarantar su Nana ta ɗauke su suka wuce gidansu, yaran sai tambayarta suke yi ta ce musu ba ta da lafiya. Lokacin da ta je gida mahaifinta ya fita kasuwa, ta sanar wa mahafiyarta duk abin da ya faru. Ko kaɗan ba su ji daɗin abin da Jafar ya yi ba, amma ita ma sun yi mata faɗa sosai kuma suka ba ta rashin gaskiya. Daddare bayan mahaifinta ya dawo, mahaifiyarta take sanar da shi abinda ya faru. Kiran Maman Nana ya yi, ta tunkari ɗakin gabanta yana faɗuwa. "Amma ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yau Sumayya, an faɗa miki miji wasa ne da za ki cakumi wuyansa a kan yana waya da budurwa." Mahaifinta ya rufe ta da faɗa bayan ta zauna. "Baba marina ya yi fa a kan na ce mata 'yar iska, kuma don wulaƙanci a ɗakina yake waya da ita." Mahaifinta ya girgiza kai ya ce, "Idan ya yi waya a ɗakinki Sumayya, tambarin wayar ne zai fito a goshinki? Tun da kin faɗa da baki bai ji ba me ya sa ba za ki bar masa ɗakin ba? Kin san maza kowa da irin halinsa ai, wani har ya gama neman aurensa mace ba za ta sani ba. Wani kuma a gabanta zai yi komai, to yanzu da kika yi hakan me ya rage shi?" Maman Nana ta saka kuka, Baba ta nuna ta da yatsa ya ce. "Daga yau kada na sake jin kin aikata wannan ɗanyan aikin Summaya, idan kin ji yana wayarsa ki bar masa ɗakin ko ki kama aikin gabanki. Kuma ko da wasa kada na sake jin ki kira budurwarsa da 'yar iska, ke ba a auren aka aure ki? Namiji ai mijin mace huɗu ne, bayan ita ma yana ikon neman guda biyu ya aura." Cikin shasshekar kuka ta ce, "Baba ba za ka gane ba, Jafar duk ya canza mini kamar ba shi ba. Yanzu fa ko abinci bai cika ci ba, ga shi gas ɗin da nake aiki ya ɗauke sai buhun gawayi ya dire mini. Da na yi masa magana har gori ya yi mini, wai su Umma ma da itace suke amfani." "Ƙarya ya yi? Ai ba ƙarya ba ne, ko ɗazu ma da shi kika ga na yi girki ai. Yaran yanzu ba ku ajiye komai ba sai baƙin kishin tsiya." Mahaifiyarta ta yi maganar cikin faɗa. "Tun da har yana ciyar da ke yana tufatar da ke, duk abin da ya kawo miki matuƙar ba guba ba ne sai ki karɓa, da hannu bibbiyu ki yi godiya ki sarrafa shi. Haba Sumayyan Baba ina ganin ki kamar mai wayo ashe ba haka ba ne, don Allah ki kiyaye gaba. Shi kuma zan kira shi ya zo na yi masa faɗa don a sharuɗɗan aure babu dukan mace a ciki." Baba ya ƙarasa maganar cikin tattausan lafazi, sai ya ciro wayarsa ya latsa lambar Jafar ya ji ta a kashe. Ya mayar da kallonsa wurin Sumayya ya ce. "Na kira mijinki wayarsa a kashe, yanzu dai dare ya yi babu damar ki tafi. Amma idan Allah Ya kai mu gobe da safe, ki shirya yaranki ki koma ɗakinki za mu yi magana da Jafarun." Maman Nana ta gyaɗa masa kai, Mahaifi da mahaifiyarta sun jima suna yi mata nasiha sannan ta tashi ta koma ɗaki. In Shaa Allah gobe za mu gama free pages, masu son littafin za su biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Idan kun ba ni haɗin kai zan yi ƙoƙari na kammala shi kafin Azumi🥹 idan kuma na ga kun wankacalar da ni, sai na bari zuwa bayan Sallah idan muna da yawancin kwana.🥸 Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [20/02, 19:45] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHA BIYU GIDANSU MAIMUNA Ganin irin miyagun ɗabi'un da Maimuna ta ɓullo wa Nazir, ya sa shi tattara ta gabaɗaya ya yi watsi da ita. Dama can ba ya dawowa gida da wuri, don haka ko da ya kai dare idan ya ci abinci hakan ba ya hana shi ya sake fita. Har mamakin Maimuna yake, saboda gabaɗaya halayenta sun sauya. Maimunan da ya sani a baya ko kara ya ajiye ba ta isa ta ƙetare ba, duk da taurin zuciya irin nata sai da ta kai ta kawo ya sa ta yi laushi, ta yadda ko musu ba ta isa ta yi masa ba. Amma a yanzu Maimuna ta yi masa rainin da ko ƙannensa ba su yi masa ba, ya hana ta shiga mutane ya hana ta hulɗa da maƙota. Ya hana ta riƙe babbar waya, ya hana ta shige cikin danginta sosai. Ya hana ta cigaba da karatu duk don kada ta saba da shiga jama mata su zuga masa ita. Amma sai ga shi a rana tsaka tana shuka masa rashin mutumci son ranta, don a yanzu ba ta shakkun idan ya faɗi magana ta mayar masa. Dalilin haka ne ya sa ya tsiri zuwa majalisar gaban gidansa, da yake wasu maƙonsu suna zama shi ma ya bi sahunsu. A ɓangaren Maimuna kuwa hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, saboda tana jin fitarsa take yin zaraf ta ɗauko wayarta ta kunna data su fara shan soyayya ita da Jafar. Maimuna bayan whatsapp har sabon Acc na facebook ta buɗe, amma ba da sunanta na ainahi ba sai kawai ta rubuta 'Matar Mai Rabo' ta cigaba da fantamawa tana harkokin gabanta. Zaman Nazir a majalisar kenan, ya samu maƙocinsa Adam yana nuna wa ɗayan maƙocin wani rubutu da ya ga an yi posting ya ce. "Ni ban san me matan aure suka ɗauki aure ba, bini-bini za ka ga rubutu ace wai a bata shawara ga halin da take ciki. Don Allah dubi wannan, wai mijinta ya hana ta cigaba da karatu bayan an yi yarjejeniya a ba ta shawara." Lawan ya saki tsaki ya ce, "Sakarcin fa, ai mata wasu a cikinsu mahaukata ne. Na tabbata a nan wasu za su zuge ta har ta kashe auren." Haruna ya ce, "A'a ba lalle ba, ka san wasu matan suna jin nauyin tambayar 'yan'uwansu neman mafita. Sai suka zaɓi a ɓoye sunansu tun da ba wani ne zai gane su ba." "Kai wannan fa ba magana ba ce, shi ya sa tun matata tana budurwa na ce mata ban yarda da wannan hawa soshiyal midiyar ba." Adam ya faɗa cikin ɓacin rai. Jin haka ya sa Nazir ya yi zaraf ya ce, "Ai wallahi tun farko shi ya sa na datse duk wata alaƙa da za ta sa a hurewa iyalina kunne, ba sai ta fita ko tana hawa soshiyal midiyar kanta zai sake wayewa ba? Don lalacewa kwanaki haka na ji ana maganar wata matar aure tana soyayya da wani matashi. Shi ma kuma a onlayin ɗin suka haɗu." Haruna ya yi dariya ya ce, "Wallahi ina faɗa muku mace fa kariyar Ubangiji ce, wallahi duk kaffa-kaffarka idan mace ta so ninke ka a baibai wallahi ba za ka taɓa ganewa ba. Kai tsanani fa ba shi ne ba, ka yi ƙoƙari iya iyawarka a kan kula da iyalinka. Kada ka saki gidanka sakaka, kuma kada ka tsananta. Sauran sai ka bar wa Allah, shi zai tsare maka su." Ya ƙarasa maganar yana miƙewa, sai sauran ma suka miƙe. Nazir ya kaɗe rigarsa ya ce. "Ai wallahi wannan zance ne, kai dai kawai kowa ya ji da gidansa. Amma ka saki mace take walwalawa ai ka riga da ka daɓa wa kanka wuƙa, musamman ma ace ka bar ta tana aiki ko sana'a kuɗi yana juya mata. To kuwa sai abin da ka gani, don matan auren yanzu wallahi mafi yawa sun gama lalacewa." "A'a gaskiya Alhaji Nazir, waɗannan zantukanma bai kamata mu dinga danganta su da iyalanmu ba, Allah Ya nesanta mana su da dukkan wani abin ƙi." Adam ya furta, sannan suka yi wa junansu sallama. Gida Nazir ya nufa sai kuma tunanin Maimuna ya faɗo masa, don haƙurinsa yana gab da ƙarewa. Tun da ta yi watsi da shi, a duk lokacin da ya neme ta sai kawo masa wani uzurin. Maimuna tana kwance ta ji motsin shigowar Nazir, da sauri ta ɗauki wayar ta ɓoye ta koma ta kwanta. Haka kawai ya ji kamar ba bacci take yi ba, don haka ya zauna agefenta yana bubbuga hannunta. "Maimuna! Maimuna." A yatsine ta tashi tana faɗin, "Ya aka yi?" Mamaita kalaman ya yi yana jin ɓacin rai, ya ɗan haɗe fuska ya ce. "Ki tashi mu yi magana." "Ni bacci nake yi sai da safe ma yi maganar." A ɗan tsawace ya ce, "Ki tashi na ce, yanzu nake son mu yi maganar." A hankali ta tashi yana sakin guntun tsaki. "Me ya sa kike ƙaurace mini, me ya sa duka kika canza kin raina niMaimu kada ki bari ki kai ni bango." Murmushi ta saki cikin halin ko inkula ta ce, "Wane kalar ɓacin ranka ne bn sani ba Nazir? Ai sai dai ka faɗa wa wata macen idan ka sake aure." Idanunsa suka kaɗa jawur saboda ɓacin rai, ya matso kusa da ita ya damƙi hannunta yana faɗin. "Uban waye yake zuga ki da yake hure miki kunne har kika raina ni?" Ido cikin ido ta kalle shi ta ce, "Sai ka fara sanar da ni wanda ya zuga ka har ka tauye ni, ka kuma dakushe burikana saboda zalinci ka ƙuntata mini ta hanyar tsauwalawa. Sannan ni kuma na sanar da kai wanda ya zuga ni." Shiru ya yi yana kallonta kamar a ranar ya taɓa ganinta, cikin rashin damuwa ta ce. "Idan kuma ba ka da abin magana sai na yi kwanciyata." "Ni kike faɗa wa haka Maimuna." Nazir ya tambaye ta a zafafe, sai kuwa ta mayar masa da martani cikin sauri kamar tana jira. "Na faɗa maka Nazir, na fa jima ina tara ka a zuciyata. Wlalahi-wallahi daraja ɗaya kake ci a wurin, wato mahaifina. Da ace mahaifina ba ya raye, wallahi da na jima da datse alaƙar auratayyata da kai." Tas! Ta ji ya sauke mata mari a fuska, zuciyarsa tana suya ya nuna ta da yatse. "Duk rashin mutumcin da kike tunƙaho da shi, wallahi daidai nake na sauke miki su. Kin san wane ne ni sarai, ba zan ɗauki wannan iskancin ba." Maimuna ta dafe kumatu tana bin sa da kallon tsana, har zai fita ta ce. "Allah Ya isa ban yafe maka ba, kuma wallahi indai ni ce ba zan taɓa komawa yadda nake a baya ba." Nazir bai kula ta ba ya fita, kai tsaye cikin store ɗin ta ya shiga. Ya ɗauko wani ƙaramin mukulli ya rufe shi, sannan ya ɗauke ƙaramar wayar Maimuna da ke falo ya koma ɗakin. Duk abin da yake yi tana jin sa, don ba sabon abu ba ne idan sun yi faɗa ya rife store ɗinta na kayan abinci. Sai dai kullum idan zai fita ya ɗebo mata wanda za ta dafa. Fulo ta ga ya ɗauka ya tafi falo, ta taɓe baki tana nuna ko a jikinta. Don ta sake ɓa ta masa rai sai ta furta. "Ko a jikina, wai an tsikari kakkaura." Ta gyara kwanciyarta, tana ayyana irin abin da za ta yi wa Nazir don ta huce takaicin marin da ya yi mata. GIDAN INNA Tun bayan fitar Sadiya gidan Inna ya kacame da iface-ifacen kukan yaranta, Inna ban da kyara da hantararsu ba abin da take yi. Fauziya ce ta janyo su ta rarrashe su, da ƙyar Zainabu ta ta yi shiru. Zazzaɓi ne ya rufe Fauziya, saboda duk cikin matan 'yan'uwan Kabiru Sadiya ce ta hannun damanta, suna ba wa junansu shawara musamman da ya kasance Sadiya ba ta da kowa a garin. Sai su rufe su binne ba tare da wani ya ji labari ba, domin dama Kabir da Yaya Nura sune masu ƙaramin ƙarfi. Gudun raini ne ya sa su Fauziya suka kama kansu, don haka ma ya sa matan su Yaya Tasi'u ko gidansu ba sa zuwa. Abincin kari Fauziya ta haɗa gabaɗaya har yaran Sadiya, bayan ta gama ta zuba wa yaran. Suka fara ci, sai dai ta lura har lokacin sun gagara sakin jikinsu. Kabir kafin ya tafi sai da ya kira Mai adaidaita sahu ya fita da keken ɗinkin Fauziya, kai tsaye shagonsu ya wuce da shi. Ya yi sa'a Ogansu yana nan, yana ganinsa ya washe baki ya ce. "Allah Ya taimaki Oga" Oga ya faɗaɗa fara'arsa ya ce, "Kb namu." Janyo keken ɗinki ya fara yi har ya samu ya shigar da shi cikin shagon, sai ya ce, "Oga ya ka ga keken? Ay na faɗa maka sabo ne bai ji jiki ba." Tasowa ya yi daga mazauninsa ya sake leƙa keken ya ce, "Gaskiya ne kuma na ga butterfly ne. A ajiye shi a gefe, zan sa a yi masa service sai ku cigaba da amfani da shi." Kabir ya matsar da keken ciki, sai kuma ya saki murmushi ya ce. "To Oga cittar fa?" "Idan za ka tafi an jima ka yi mini magana, zan ba ka rabin, rabin kuɗin kuma sai zuwa nan da rana ita uku." Ba haka Kabir ya so ba, ya so ace duka kuɗin ya samu. Amma duk da haka ya san idan ya karɓi kuɗin, za su cika a haɗa a kai gidansu Surayya. Tun daga wannan ranar zaman Fauziya da Inna ya fara ɗaukan sabon salo, sai dai Fauziya tana bakin ƙoƙarinta don ganin wani abu bai haɗo su ba. Duk safiya idan ta yi abinci tana bakin ƙoƙarinta, don ta ga ta ba wa su Zainabu abinci ko yaya ne duk da ciyarwarsu ta koma hannun Inna kacokam. Kwana biyu da tafiyar Sadiya, har gida Yaya Tas'u ya zo ya ƙarewa Yaya Nura faɗa a kan sakin da ya yi wa Sadiya. Don wani lokacin idan suka yi faɗa tana zuwa ta kai ƙararsa wurinsa, shi kuma sai ya je ya yi masa faɗa. Idan aka yi haka sai Sadiya ta samu sassaucin rashin mutumcinsa, bayan kwana biyu kuma ya ɗora daga inda ya tsaya. Duk aikin da Sadiya take yi wa Inno sannu a hankali ya dinga dawowa kan Fauziya, lokaci ɗaya ta yi wani irin duhu ga rashin hutu daga wannan sai wannan. Murmurewar jegon da ta yi duk sai ta zuge, a ɓangare ɗaya ga tunanin halin da gininsu yake ciki. Saboda halayen Kabir sun dawo mata sababbi, don tana yi masa magana yake rufe ta da faɗa. Idan Inna ta jiyo sai ta ƙarasa bakin ƙofa ita ma ta cigaba da tofa albarkacin bakinta. Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta lura da take-taken Inna tana son fara ɗora wa su Na'ima talla ba. Duk da ba ta fito ta faɗa ba, amma ta lura da yanayin shaguɓen da take yi. Hakan ne ya sa ta shiga takura wa Kabir a kan ya saka su a makaranta, amma sai dai ya ce mata ba shi da kuɗi. Kuma ta rasa wurin da yake zuwa, a kullum ya dawo gida da wuri haka zai buga wankan ƙananan kaya ko manya ya fice daga gidan. Wani lokacin ma sai ta yi bacci yake dawowa, saboda gajiya ta sa ana yin sallar Isha'i take yin bacci. Watarana suna zaune bayan magriba yana tsaka da shiri ta ce. "Abban Na'ima!" "Ina jin ki." Ya amsa mata yana saka belt ɗin wandonsa. "Wai kasuwar ɗinkin ce yanzu ba a samu ko yaya? Zaman yaran nan babu makaranta baya zai mayar da su, don Allah ko Islamiya ce ka saka su." Sai da ya ƙarasa komai sannan ya ce, "Islamiyyar ma ai ba kyauta ake zuwa ba, ki bari idan na samu kuɗi zan saka su. Kin san dai yadda abubuwa suke ƙara tsada." Saboda takaici ba ta tanka masa ba, ya gama shiryawa yana fesa turare, a daidai lokacin wayarsa ta kawo haske da yake a silent take. Da sauri ya ɗauke wayar ya saka a aljihu har zai fita Fauziya ta ce, "Abban Na'ima ni fa ban gane wannan shige da ficen nan da kake yi ba. Ina za ka je ne da daren nan?" "Haifata kika yi da za ki tsare ni da tambaya, ina ruwanki da wurin da za ni? Kin san dai yanzu na daina shaye-shaye ballanta ki kafa mini zargi." Sai kawai ya saka kai ya fice daga ɗakin, shiru Fauziya ta yi tana nazari. "Tabbas ruwa ba ya tsami banza, wallahi akwai abin da Abban Na'ima yake ƙullawa." Ta faɗa a sanyaye, tana jin nadamar ba shi kekenta. Saboda ta san da ko da kuɗin gyaran da take yi ne za ta iya samu ta biya musu kuɗin makaranta, a nan take tunani ya faɗo mata a kan ta fara yin wankau tun da yanzu Sadiya ba ta nan. Sai kuma ta ga sam ba za ta iya wankau ba, don wani lokacin ko wankin yaranta ta yi wuni take bayanta yana ciwo. Sai kuma dabara ta faɗo mata a kan ta fara yin kitso, da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta a kan idan gari ya waye za ta shiga maƙota duk ta faɗa musu. Kabir yana fita daga gidan ya ciro wayarsa ya latsa lambar Surayya yana faɗin, "Na fito fa baby." Surayya ta akashe murya ta ce, "Tun ɗazu fa nake ciki da muradin son ganinka gwarzona." Amsa mata ya yi sannan ya kashe wayar. Adaidaita sahu ya tara kai tsaye ya wuce unguwarsu Surry, waya ya ciro ya kira ta sannan ta fito. Kamar kullum idan za su yi zance a soron gidan suke yi, hakan ce ta sa yanzu ma ta shimfiɗa musu dadduma a soro. Rungumo Surayya ya yi, ita kuma ta kamo bakinsa ta fara sakar masa kiss. Nan take Kabir ya fara birkice mata, ya shiga kai hannunsa cikin sassan jikinta. Jingina suka yi da bango, ita ma Surry ta fara sarrafa shi da hannunta tamkar ƙwararriyar matar aure. "Baby na gaji fa!" Kabir ya furta cikin wani irin yanayi. "Kamar yau ne fa, ba yanzu saura wata goma ba. Ni fa ba don 'yan gidanmu ba, da ko ba lefe tsaf za a sha biki. Don tun lokacin da aka tsayar da rana na so a saka wata shida." Janye kansa ya yi daga cikin ƙirjinta ya ɗago yana kai hannunsa ciki jikinta sannan ya ce, "Amma kafin lokacin me ya sa ba za ki ɗan dinga rage mini zafi ba dear?" Surry don ta zolaye shi sai ta ce, "Ba kana da mata ba, ya kake abu kamar wanda bai taɓa aure ba." "Mtswww." Ta ji Kabir ya ja dogon tsaki sannan ya ce, "Ana maganar matan da suka cika cikakkun mata, kina sako mini zancan waccan abar. Don Allah ki taimaka mu dinga zuwa gidan can kina yi mini dabaru." Wani irin daɗi Surry ta ji, saboda ta jima da fahimtar matarsa ba komai ba ce a wurinsa. Ta sake maƙale shi ta ce. "Shi kenan my love, zan yi ƙoƙari na dinga yi wa su Yaya dabarar fita, kasan tun da aka saka ranarmu yake saka mini ido sosai." Sake haɗe bakinsu Kabir ya yi sai da suka ji alamar motsin za a fito, da sauri ya sake ta yana sauke numfashi, Surry ta wayance da cewa. "Hasko nan mu ga ko can azurfar taka ta yi." Wayarsa ya zaro ya fara haska mata, kamar masu neman azurfar gaske. Suna cikin haka Yaya Umar ya yi musu sallama ya fita daga gidan. Ya so sake yamutsa Surry ta nuna masa ya yi haƙuri za ta dinga zuwa can gidan, saboda tana tsoron kada yayanta ya sake dawowa ya kama su. Cike da kewar Surry Kabir ya fito daga soron gidan, yana fitowa babu jimawa ya zaro wayarsa. Misscall ɗin Farha ya gani har sau uku, ya latsa layin nata yana karawa a kunne ya ce. "Ina fatan sarauniya ba ta yi fushi da ni da." "Idan na yi ma ai ka saba kanainaye zuciyata har ta yi maka afuwa." Farha ta furta cikin shagwaɓa. Murmushi ya yi yana jinjina baiwar da yake da ita. Kabir irin mazan nan ne masu iya tsara zance da kanainaye zuciyar 'yanmata. Ya ƙwarai sosai wurin iya yaudara da kife mace, kuma yana ɗaya daga cikin maza masu kule-kule da ƙoƙarin dandanlar arzikin jikin budurwa. "To yanzu dai ayi mini afuwa cajina ya ƙare, zan kira ki da asuba. Ina fatan za ki yi bacci da ni a zuciyarki." Kafin su yi sallama sai da suka yi musayar kalaman soyayya sannan ya katse. Lokacin da ya ƙarasa gida tuni Fauziya ta yi bacci, don haka ya ɗauki buta ya faɗa banɗaki ya tsarkake jikinsa sannan ya koma ɗaki. Sannu a hankali haka rayuwa ta cigaba da tafiya watanni suna shuɗewa, Fauziya ta fara kitso babu laifi tana samun ɗan kuɗin kashewa. Da kanta ta saka yaran a wata makaranta da ake yi boko da Islamiyya, sai dai duk da hakan ba su tsira ba sai da Inna ta fara ɗora musu tallar barkono ranar Alhamis da Juma'a. Tun Fauziya tana kara har ta gagara haƙuri ta yi wa Inna magana, a lokacin faɗa ta rife ta da shi amma da shi ma Kabir ya nuna yaransa ba za su yi talla ba sai ta kawo ido ta saka masa. Fauziya da karanbami har magana ta yi a kan su Salim, a nan ne Inna ta ce daga Kabir har ita ba su isa ba matuƙar ba mahaifinsu ne ya hana ba. Wannan dalilin ne ya ja wa Fauziya da yaranta baƙin jini a wurin Inna, ko fita suka yi tsakar gida wasa ta dinga zaginsu tana hantarasu wani lokacin har da duka. Daga ɓangaren Kabir shi ma zamansa da ita tuni ya sauya salo, don babu abin da za ta yi masa haka kawai zai ɗauki fushi da ita. Ko kuma magana kaɗan za ta yi masa sai ya rufe ta da faɗa, daga haka ma sai ya ƙaurace mata. Domin a zaman da suke yi sun tafi kusan wata biyu ba tare da wani abu ya gifta a tsakaninsu ba. Ana cikin haka watarana Kabir ya dawo da daddare a lokacin sha ɗaya saura, a zaune ya samu Fauziya ta yi shiru tana nazari. Tsakin da ya ja ne ya sa ta ɗago tana kallonsa, karaf idonta ya sauka a kan damɓareren jambakin da ke gaban rigarsa har zuwa leɓensa. Ta haɗiyi wani irin yawun takaici, amma ba ta tanka masa. Kamar yadda ta yi tsammani, buta ta ga ya ɗauka ya tafi banɗaki. Ba tun ranar ba, dama ta lura da shi kusan kullum idan ya dawo ya yi wanka ya fita, to bayan ya sake dawowa daga yawonsa sai ta ji ya ɗebi ruwa yana wanka. Ya tafi banɗaki ba jimawa ta ji kira ya shigo wayarsa, a kan windo ta hango wayar jikinta har rawa yake ta saka hannu ta ɗauka. Wannan ce rana ta farko da zuciya ta ingizata a kan ta ɗauki wayarsa, ƙirjinta yana bugu ta ɗauki kiran da ta ga an ributa 'Sec wf' Ɗauka ta yi sai ta yi shiru daga can ɓangaren ta ji an ce. "Baby don Allah idan za ka yi wanka ka turo mini hoton lovely ɗina, ni ma na turo maka ina wanka ka duba whatsapp ɗinka." Da sauri Fauziya ta katse, ta ci sa'a wayar babu key tana duba whtaspp ta ga sakon lambar da aka kira. Ƙazantaccan hotun surorin jikin Surry ne, sai ta yi sama a nan ta ci karo da hotunan al'aurar Kabir ya tura mata hotuna. Sai kuma wasu hotuna da ta gansu rungume da juna hannun Kabir yana saman ƙirjin Surry. A yadda ta gani babu riga a jikinsa, ta ga kuma ita ma Surayyan ko ɗankwali babu a kanta. Amma sai ta lura wurin da suke kamar ba gida ba ne. "Innalilla wa Inna ilahir raji'un." Fauziya ta furta tana jin kanta yana sarawa, idabunta suka fara ganin dishi-dashi. Ɗakin da take ciki ta ga ya fara juya mata. GIDANSU MAIMUNA Saboda fushin da Nazir yake yi da Maimuna ya sa koda gari ya waye bai bi ta kanta ba, wanka kawai ya yi ya ɗebo shinkafa kofi huɗu ya tsiyayo mai wata 'yar roba ya ajiye mata sannan ya fice kasuwa. Maimuna tana kallonsa duk abin da yake yi har ya fita, da yake a lokacin tuni yaranta sun tafi makaranta, wanka ita ma ta shiga ta tsala a banɗaki. Bayan ta fito ta zaro wayarta ta ga misscall ɗin Jafar, goge hannunta ta yi za ta kira ta ga wani kiran ya sake shigowa. Tana ɗauka cikin zumuɗi ya ce. "Baby ke fa nake jira." Murmushi Maimuna ta yi ta ce, "Na gama komai kayana zan saka." Katse kiran ya yi. Maimuna ta jima a gaban drower kayanta, sai ta ɗauko wasu figaggun ƙananan kaya ta saka, ta zaro zumbulelen hijabinta ta zura. Ƙaramar wayarta ta gani Nazir ya mantata a falo, don ta tabbatar da ya yi nisa da gida sai ta kira shi. Har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka. "Ina jinki." "Na ga ka ajiye mana shinkafa, har dare ko iya rana." Ta furta tana sauraron yanayin wurin da yake. Daga cikin wayar ta ji alamar yana cikin kasuwa, don ta ji ana tambayarsa hula lamba ashirin (Size 20). "Har dare za ku dafa." Ya ba ta amsa a zafafe yana katse wayar. Tsalle ta buga sannan ta ɗauko mukulli ta rufe gidanta, kamar yadda Jafar ya ce zai bar mata gidan a buɗe haka ta same shi. Duk da ta san Maman Nana ba ta nan, haka kawai ta ji gabanta yana faɗuwa. Tana shiga ciki ta hango shi daga shi sai gajeren wando, da sauri ya ƙarasa ya rungume ta yana zame hijabin jikinta. Wata irin kunyarsa Maimuna ta ji ta sunne kanta ƙasa, shi kuwa ya shiga laluben jikinta kamar waɗanda suka jima da sanin juna. A kan gadon Maman Nana suka yada zango, Jafar ya shiga rage mata kayan jikinta har ya raba ta da su gabaɗaya, ya shiga gwaɗa mata zafaffiyar soyayya. Abin da ya birge ta, ya kuma ba ta mamaki yadda ta ga Jafar ba ƙyamar komai na jikinta. Abin da Nazir bai taɓa yi mata ba, don shi ko kiss bai damu da ya yi wa mace ba. Sai da Maimuna da Jafar suka gigita juna sannan komai ya wakana a tsakaninsu, cike da so ya rungumo ta a jikinsa ya ce. "Don Allah ki cigaba da ni haɗin kai zumata." Gyaɗa masa kai ta yi har lokacin hannun Jafar yana cikin jikinta. Bayan gari ya waye sai da Maman Nana suka ci abinci sannan ta yi musu wanka, ta nufo hanyar gidanta. Mahaifinta ya yi mata nasiha sosai, ya sake tabbatar mata da zai kira Jafar ya yi masa faɗa. Da yake ita ma tana da mukulli a hannunta, tana zuwa bakin gate ta saka key ta buɗe jamlock ɗin. Ta yi mamaki da ta ga motarsa a gida har lokacin, amma sai ta yi tsammanin ko lalacewa ta yi bai fita da ita. Don haka ba ta yi wata-wata ba ta nausa kanta ciki, tun daga tsakar gida ta fara jiyo sautin dariya da wasannin da suke yi a cikin banɗaki da ruwa suna wanka. AlhamduLIllah a nan ƙarshen free pages ya ƙare, ba sai na tsaya bayanin irin cakwakiyar da za a riska a gaba ba. Mai son cigaba zai biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 In Shaa Allah Jibi Asabar zan cigaba da posting a paid group Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [04/12/2024, 14:28] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA ƊAYA Jar mota ƙirar golf ce take tafiya a hankali, saboda tsufa da lodin magunguna tare ɗima-ɗiman manyan sifikun da suka yi mata nauyi. Ta baya boot ɗin motar a buɗe yake waɗansu matasan samari ne a zaune, hannuwansu riƙe da jarkokin magunguna suna ɗagawa. Tayoyi da gefen motar duk sun yi butu-butu, saboda ƙura da jar ƙasa. Mai maganin gargajiyar yana daga cikin motar, ya sake ƙara volum ɗin recording ɗin tallan magungun da yake yi. "Alhaji ko Hajiya idan har matsalarku sanyi ne ku zo ga babansa. Ni fa ba na rantsuwa a kan magungunana saboda sadidan ne, amma idan har kuka sha maganina bai yi muku aiki ba ku dawo na ba ku kuɗinku. Ina mai fama da sanyin ƙashi, sanyin mara da ciwon baya ku zo ga waraka ta zo muku har gida. Alhaji kai ne ake ganinka kullum cikin babbar riga, ana yi maka kallon cikakken namiji amma a baɗini kana jin kunya to ka zo mu saka labule don Allah." Mai maganin ya rage volum ɗin recording ɗin, sai ya zuro kansa ta window ganin ya ƙaraso wurin da jama'a suke zirga-zirga ya ce. "Al'ummar Annabi ina magidancin da yake son huce takaicin sanyin nan da muke ciki? Amma ɗan kanoma ya yi masa mugun kamu. Don Allah kada ya ji kunya, ya zo ya samu mai warakar sanyi matsalarsa ta kau da ikon Allah. Cutar rana, kumburin ciki, zafin bayan gida, basir da cutar sanyi duk ni ne likitan da ke magance su." Baba Inu da ke kishingiɗe a kan benci ya tashi zaune, ya ɗan ƙanƙance ido yana ƙarewa motar da mai motar kallo, saboda masu magungunan ba baƙinsa ba ne, don yana iya tantance duka masu magungunan gargajiyar da suke shigowa garinsu. Musamman yadda suke haba-haba da shi, duba da yadda ya zame musu babban costomer. "Kai mai magani, zo nan." Baba Inu ya kira shi yana yafito shi da hannu. Da sauri mai maganin ya gyara paking ɗin motar yana kaikaitata a daidai ƙofar gidan. "Babana da Innata ga ɗan baiwar masu magani ya sauka, mai warkar da matsalar sanyi ya zo kada a yi wasa." Mai maganin ya sake furtawa a loudspeakersa. Ƙuri Baba Inu ya yi masa ya ce. "Abokina amma dai kai baƙo ne a garin nan ko?" Mai maganin ya gyaɗa kai ya ce, "Yanzu ma wucewa na zo yi, duk mai matsalar sanyi ya zo muna bayar da taimako don Allah. Idan ya sake na tafi ba zan sake dawowa ba sai baɗi." "Miƙo mini wancan maganin na jarka, nawa ne kuɗinsa?" Baba Inu ya tambaya, yana nuna wata zungureriyar jarka da ke cike da jiƙaƙƙun itatuwa a ciki. Jarka biyu mai maganin ya miƙa masa yana faɗin. "Wannan da kake gani darr kenan, Mai gida ba kowa nake sayarwa ba sai mai sa'a. Ko kana shan kunya a wurin iyalinka, don Allah ka ɗaga roba ka sha rabi ka shiga wurin uwargida ka dawo ka ba ni bayani." Baba Inu bai jira cewarsa ba ya ɓalle murfin robar, ya ɗaga ta sama sai da ya ga maganin ya ƙare sannan ya wurgar da jarkar. Mai maganin ya zaro ido waje ya ce, "Master amma ka kwana a wannan layin ko?" Horn ɗin da Baba Ibrahim ya yi ne ya katse Baba Inu da yake shirin bayar da amsa. "Abokina ja motarka gefe ga masu iko da gidan sun ƙaraso." Mai maganin ya ja motarsa gaba, a daidai lokacin Baba Ibrahim ya ƙarasa da ta shi motar ya yi parking sannan ya fito daga ciki. Tun lokacin da mai maganin ya ƙarasa gaban Baba Inu ya shawo kwanar layinsu, a kan idonsa Baba Inu ya ɗaga ya shanye. Da sallama ya ƙarasa wurinsa haɗe da faɗin. "Yaya barka da hutawa." Baba Inu ya ɗan kalle shi a sheƙe ya ce. "Bokan turai yau kuma lafiya na ga ka dawo da wuri?" Baba Ibrahim ya ce, "Lafiya ƙalau Yaya." Ganin Baba Ibrahim ya tsaya ba tare da ya yi magana ba ya sa Baba Inu ya ce, "Iro ya aka yi? Ka saka ni a gaba ko kai ma a miƙo maka maganin ne?" Da sauri Baba Ibrahim ya ce, "Allah ya kiyashe ni, ni kam." Baba Inu ya dube shi a gwasale ya ce, "Yo dama ina abin yake maye ya ci jariri, mai mace ɗaya har ya bugi ƙirji ya saka kansa a sahun mazaje. Ai maza kam suna inda suke." Baba Ibrahim ya girgiza kai ya ce. "Yanzu Yaya hanyar da ka ɗauko wa kanka mai ɓillewa ce? Saboda Allah a ce kai kullum cikin shaye-shaye da jiƙe-jiƙen magunguna kake kala-kala. Kullum masu magani sai dai su dinga layi a ƙofar gidan nan, mutanen garin har sun fara gane ka? Magungunan fa yawanci waɗanda kake sha babu wata ƙa'ida kai tsaye kake hankaɗa wa cikinka, kuma mafi yawa masu haɗa magungunan nan da ka suke yi ba su da ilimin abin. Ko mu da muke likitocin asibiti, babu yadda za a yi mu ɗauki magani mu ba ka ba tare da mun duba ka ba." Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya cigaba da cewa. "Yaya da ace kuɗaɗen nan da kake kashewa a sayen magungunan tara su kake, da ko nauyin karatun yara ka rage da su. Amma ka bar yara haka, hatta makarantar allo ba duka ne suke zuwa ba. Kuma saboda Allah ga shi nan, kullum wasu ƙananan ƙwayayan ake sake ƙyanƙyashe maka." Baba Inu ya ɗago fuska a haɗe ya ce, "Ka gama ubana? Idan ba ka gama ba na yi shiru ka cigaba." Baba Ibrahim ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Na gama." "To shige ciki ka ba ni wuri, ashe shi ya sa ka kwaso fuska kamar akwatin zaɓe ka zo ka tsaya mini a ka. Wallahi Iro ka fara ba ni tsoro, da ace kana da iko na tabbata da sai ka yi duk yadda za ka yi domin ka turmushe mini ƙwaiƙwayen haihuwa. Amma ka don kanka, na lura baƙinciki da hassadar ne fal ranka. Allah bai hore maka irin ƙwaiƙwayen haihuwa masu yawa da albarka kamar ni ba." Bab Ibrahim a fusace ya ce, "Wallahi gaskiya ka faɗa, yadda kake sakin jiki kai da matan da kake aura kana saki da ina da iko sai na farke ka na ƙone maka su kowa ya huta. Tun da haihuwar kawai ka sani ba ka san jidalinsu ba." A ɗan tsorace Baba Inu ya dafe ƙirji, yana bin Baba Ibrahim da wani irin kallo ya ce. "Kai dai Iro an yi mai mugun hali, mugun bakinka ya faɗa kanka. Sai ja je ka yi ta fama da 'ya'ya huɗu, ni kam haihuwa yanzu na fara tun da ban san mai jin ƙaina ba." Ganin Baba Inu bai ɗauki zugar Baba Ibrahim ba ya sa Mai maganin ya zuro kai ya ce. "Ai mai gida shi ya sa a kullum idan za mu fito, muke addu'ar neman tsari miyagu irinsu masu hana a yiwa bayin Allah ciniki." Takaici ya sa Baba Ibrahim ya shige cikin gida ba tare da ya tanka musu ba. Saboda halin yayan nasa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba. Baba Iro yana shirin yin magana daga soron gidan ya ji, gijif! Kwacakwar! Alamar ana jan kaya a buhu. Baba Saleh ne ya fito da ƙaton buhun magungunansa, ganin motar mai magani a ƙofar gidan ya sa ya murtuke fuska yana harare-harare cikin habaici ya fara waƙa. Komai baƙin cikin tsololon ƙato. Wallahi sai dai ya yi ƙototo. Na zama kainuwa a wannan loto. Ƙaryar mai baƙinciki ya ga bayana, har masu ƙin sayan maganina. Yana gama faɗar haka ya fizgo ƙaton buhunsa da yake ja da ƙyar, sai ga shi bisa tsautsayi ya fiszo da ƙafar bencin da Baba Inu yake kai. Bencin ya yi gaba shi kuma Baba Inu ya hantsila ta baya ji kake darr ya yi zaman 'yan bori a ƙasa. Kamar bai san da shi a wurin ba Baba Saleh ya saki buhun hannunsa yana rafka salati sannan ya ce. "Wai Yaya dama kana nan ƙofar gida? Ikon Allah sannu!" Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin riƙo hannun Baba Inu, da sauri ya bige hannunsa rai a ɓace ya ce. "Wallahi duk baƙincikin mutum bai isa ya ga bayana ni Inusa don uban mutum! Haka zan daɗe na yi ƙarko shekaru irin na dabino, sai na ga bayan maƙiyana. Kai mai magani, ungo dubu biyar ka yi mini haɗin komai da ruwanka." Baba Inu bai yi niyyar sayen maganin dubu biyar ba, amma don ya ɓa ta wa Baba Saleh rai ya yi haka. Baba Saleh ya buga tsaki yana wurgawa mai maganin harara, ya nufi wata tsohuwar motarsa da yake tallan magungunansa, ya buɗe ya tura buhun maganin da ke cike da jarkokin magani sannan ya rufe. Inna ce ta fito daga gida a fusace hannunta riƙe da Laraba, ta dubi Baba Inu bayan sun yi sallama da mai maganin ta ce. "Inu na gaji da cin kashin da ake yi mini a cikin garin nan." Da mamaki Baba Inu ya dube ta ya ce, "Me aka yi miki Inno?" "Ba ni aka yi ba Laraba aka yi wa, kuma duk wanda ya yi wa Laraba ni ya yi wa. Mai gari ne yake son ganina da ita, wai Laraba ta tare Ɗahe ɗan gidan Sa'a mai ragadada ta cinye masa. Saboda Allah ina Laraba za ta kai ragadada cikin ɗan bokiti ban da son zuciya?" Jin haka ya sa Laraba ta juya gefe a fakaice ta sake suɗe hannunta da ya yi shanana da miyar ragadada. Baba Inu ya zuba mata ido ya ce, "Wallahi duk abin da aka ce mini wannan hatsabibiyar yarinyar ta yi ba zan musa ba, shi ya sa tun da satin nan ya kama nake jiran shigowar Uwar marayi garin nan. Wallahi babu abin da zai hana Laraba zuwa birni, ta je can ta yi aikatau ko na huta da takaicinta. Ni duk cikin 'ya'yana babu sai siffar 'ya'yan aljanu irinta." Wani irin haushin Baba Inu ya kama Inno, sai kawai ta ja hannunta suka wuce wurin mai gari. Tun daga nesa da aka hango Inno tafe da Laraba ƙananan maganganu suka fara tashi a fadar mai gari. Sanƙira ne ya yi magana sannan kowa ya yi shiru. Da sallama Inno ta zauna a kan tabarmar fuska a haɗe ta ce. "Allah Ya taimake ka, na ji wai kana nemanmu ni da Laraba!" Mai gari da tun da Laraba ta zauna yake bin ta da mugun kallo ya ce, "Wai ne ma Inno?" Ya mayar da kallonsa wurin Laraba ya ce. "Ke Laraba waye wannan?" Laraba ta yi kicin-kicin da fuska tana duban Ɗahe kamar ba ta gane shi ba ta ce, "Ban san shi ba, amma na ga yana yi mini kama da 'ya'yan Baraka mai hancin salansa." Haushi ya sake cika Mai gari ganin irin rainin hankalin da Laraba ta yi masa. Ya sake nuna Huwaila wacce ta kai ƙarar Laraba, a kan ta jefa mata bokiti da guga a cikin rijiya. Laraba ta sake ƙanƙance ido ta ce. "Wannan kam Lado ƙeya ne!" Sai kuma Laraba ta washe baki ta ce, "Lado ƙeya dama ka dawo daga Legas?" Haushi ne ya lulluɓe mai gari, mutanen wurin wasu suka fara dariya yayin da wasu kuma haushin Laraba ya cika su, don kusan duka mutanen garin babu wanda ba shi da tabon ɓacin ranta. Tsam mai gari ya taso ya zo gaban Laraba, a tunaninta tambayarta zai yi sai ji ta yi ya zabga mata gigitaccan mari, har sai da ta ga waɗansu taurari sun gilma mata. A razane Laraba ta dafe kunci saboda marin ba ƙaramin zafi ya yi mata, amma sai ta basar don ba ta san ta kunyata kanta a gaban mutanen garin. Ta sake basarwa ta sake ba shi irin amsar da ta ba shi da farko. A wannan karon ma haushi ya sa Mai gari ya sake ɗauke fuskarta da mari, abinka da farar fata lokaci ɗaya fuskarta ta yi jajir. Ganin haka ya sa ran Inno ya ɓaci ta dube shi a fusace ta ce. "Wallahi Sama'ila ka kiyaye ni, jikata fa ba jaka ba ce..." "Ai dama duk wani iskanci da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata, wallahi mai gari sisina ba zai yi ciwon kai ba sai an biya ni ragadadata. Har kayan miya da mahaɗi kusan dubu biyar na kashe." Sa'a mai ragadada ta faɗa a ƙufule. Cikin tsoratarwa da burgagi Mai magari ya miƙe tsaye yana buɗa kafaɗu ya ce, "Inno tun da haka kika ce, bari na aika ku birni wurin hukuma ta yanke mata hukunci. Kin ga idan aiƙali ya ji irin tuhume-tuhumen da ake yi mata ƙila ma ya aikata gidan yari." Jin haka ya kaɗa hantar cikin Inno, hankali a tashe ta zungoro Laraba ta ce. "Ke Laraba ki yi magana." Laraba ta yi wa Mai gari ƙuri tana yi masa kallon ba ka daki banza ba, har sai da cikinsa ya kaɗa amma sai ya basar ya ce. "Laraba kin tare Ɗahe kin cinye masa ragadada kin tula masa ƙasa a ciki, ita kuma Huwaila kin jefa mata guga da bokita a rijiya yanzu da kin jefa ta ciki me za ki ce?" Laraba ta wurga wa Huwaila harara ta ce, "Kai Lado ƙeya tun da ka dawo garin nan yaushe muka haɗu da kai!" Huwaila ta fashe da kuka cike da takaici ta ce, "Mai gari kana ji tana mayar da ni Lado, yanzu Laraba ta rasa da wa za ta haɗa ni sai Lado ƙeya?" Mai gari ya kalli Sanƙira yace ya tsinko masa itacen dalbejiya ya zuge masa ganyenta. Jikin Sanƙira har rawa yake ya haye bishiyar da ke gefensu, ya fisgo manyan reshe ya zuge ya miƙa wa mai gari. Kafiya da taurin kan Laraba ya sa ko gezau ba ta yi ba, duk da gabanta sai faɗuwa yake yi. Rai a ɓace Mai gari ya shiga rafta mata ta ko ina, mutanen wurin suka marmatsa don kar a same su. Tun Laraba tana daurewa har dauriyarta ta ƙare ta fashe da kuka tana mutsu-mutsu. Inno ban da kuka da kururwar neman taimako babu abin da take yi. Yaran da suke zagaye da su ne suka fara tafi suna tsalle da waƙa, saboda tun da suke ba su taɓa ganin abin da ya saka Laraba kuka ba. Laraba mai kuka ye ye. Ga majina da yawu ahayye. Gobe ma ta ƙara ye ye. Ku zo mu yi mata ɓarɓaɗan tusa a tsakar ka. Idan suka kai baitin waƙar sai su ƙarasa su dunguro kan Laraba da ke shasshekar kuka. Mai gari sai da ya gaji don kansa sannan ya koma kujerarsa cike da son nuna birgewa ya ce. "Duk wanda ya sake aikata makamancin abin da Laraba ta yi, hukuncin da za mu yi masa kenan. Ina Inno take?" Cike da jin haushi a daƙile Inno ta ce, "Ga ni." "Za ki biya Huwaila da Sa'a kuɗin ɓarnar da Laraba ta yi musu." Inno ta yi tsagal ta ce. "Ai kuwa ba za ta saɓu ba, ya za a yi a daki yarinya sannan kuma na biya." Mai gari zai yi magana suka ga Laraba ta miƙe zumbur! Kamar wacce aka yi wa allurar doki. Don irin zaburar da ta yi ba ƙaramin tsoro ta ba shi ba, ba shi kaɗai ba, hatta ragowar mutanen wurin sai da suka ja da baya. Idanunta sun yi jawur saboda kuka, ta dube su ɗaya bayan ɗaya abinka da mai manyan idanu sai suka sake fito. Ta fara takawa a hankali wurin saitin fuskokinsu, ta cigaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya kamar wacce take haddace kamanni da sunayensu. Da ta je kan mai gari sai ta matsa dab da shi ta gwalalo masa ido waje har sai da ta ja baya, sannan ta cigaba da kallon mutanen gefensa Tana zuwa ƙarshe, sai kawai suka ga ta ɗiba a guje ta fice daga cikin fili ta nausa daji, hankali a tashe Inno ta rufa mata baya tana faɗin. "Laraba! Ke Laraba ina za ki je?" Tun ba a je ko ina ba Laraba ta yi wa Inno nisa, ganin Inno za ta tafi ya sa Mai gari ya ce. "Inno wai ni za ku yi wa dirama? Ke da Laraba wa ya ba ku ikon tashi daga wurin nan. Wallahi ba don ina duba darajar marigayi Baffa babba ba, da ke da jikarki tuni na kore ku daga garin nan." Mai gari yana rufe baki, suka hango Laraba ta tunkaro wurinsu a guje, hannuwanta ɗauke da wasu tafka-tafkan reshen bishiya. Ba ta yi wata-wata ba ta shiga tafka musu kan mai uwa da wabi a haukace tana wani irin ƙaraji. Lokaci ɗaya wurin ya hautsine, Mai gari saboda tashin hankali da rarrafe ya dinga tafiya, domin da farko da ya saka gudu sai da ya yi adungure sau uku babbar rigarsa tana taɗe shi. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [04/12/2024, 15:03] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA BIYU Kamar wata fusatacciyar zakanya, haka Laraba ta cigaba da yin kan mutane tana fatka musu itacen da yake hannunta. Ban da wani irin gurnani babu abin da take yi, Inno da ke raɓe a can gefe jikinta ya shiga karkarwa saboda tsoro da tashin hankali. Don tun da take da Laraba ba ta taɓa ganin ta yi irin haka ba, Sanƙira ta hango maƙale a gefen bishiya. Ta yi wani irin zullo haɗe da ƙaraji ta tunkari wurinsa, kamar sabon marayan da ba shi da mafita. Haka Sanƙiran ya saki wani marayan kuka zai fita da gudu, Laraba ta tuna yadda Sanƙira ya dinga zuge ganyen bishiyar yana wurga mata harara sai kawai ya ɗaga hannu ta tafka masa itace a baya. Sanƙira ya gantsare cikin azaba ya ce, "Wayyo Mai gari bayana wash! Wallahi wannan ba dukan bil'adama ba ne." Mai gari da babbar riga ta sarkafe shi yana rarrafe yana dungurawa ya ce, "Wallahi na ajiya sarautar na damƙa maka yanzu kai ne mai garin." Laraba ta saki murmushin ƙeta ta riƙo babbar rigar Sanƙira ta baya, suna gudu tana tafka masa ice a baya. Ganin Larabar tana neman kai shi ƙasa, ya sa Sanƙira ya yi wani ƙaraji ya dara gaban rigarsa gida biyu, da yake dama rigar ta kwana biyu nan take ta rabe biyu. Sanƙira ya zuba a guje ya bar Laraba da babbar riga a hannu, filin wurin ya sake cakamewa da ƙurar ƙasar da take tashi. Mai gari ya hango Laraba tana tunkaro shi, cikin tashin hankali ya zuba kabbara kamar wanda yake filin jihadi. A wannan karon Allah Ya ba shi sa'a ya samu da ya miƙe bai sake faɗuwa ba, gudun kada babbar za ta sake ba shi matsala ya sa ya tuɓe ta ya wurgar. Ya taƙarƙare ya fita da gudu, takalmansa da hularsa sai tsalle suke yi suna tashi sama. Laraba ta so ƙyale shi amma da ta tuna irin marin da ya zazzabga mata sai ita ma ta rufa masa baya da gudu. A lokacin da Mai gari ya ƙarasa gida, Salame matarsa ta rako Inna mahaifiyarta da ta zo duba ta sakamakon rashin lafiyar da ta yi. Suna nan a soro ya shiga a guje, cikin neman maɓoya ya fisgi hijabin jikin Inna ya yi gaba da ita. Cikin tashin hankali Inna ta fara ihu tana kiciniyar ƙwace kanta, don Mai gari janta yake da gudu ga kanta ya cukwikwiye mata a cikin hijabi. Ragowar mutanen gidan suna jin ihu daga waje, da suka ga a yadda mai gidansu ya shiga yara da manya sai kowa ya nemi maɓoya. Laraba ce ta yi tsaye tana wani gurnani, ta ga tsakar gidan kowa ya fashe sai wani ɗan ƙaramin yaro da bai fi shekara biyu da rabi zaune a kan fo. Irin kallon da Laraba take yi masa tana gwalo ido, ga zungureren itacen da ya gani ya sa yaron ya miƙe a zabure yana ihu ya shige ɗakin mahaifiyarta. Tun da Mai gari ya fisgi hijabin Inna, ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a uwar ɗakin Salame a can ƙarƙashim gadon ƙarfenta. Ya shiga sauke numfashi da ƙyar yana muzurai, hannunsa ya kai wurin wandonsa ya ji ya yi sharkaf. Jiki yana karkarwa ya zura kansa cikin hijabin Inna ya ce. "Salame ina jin fa gudawa na yi, wallahi har yanzu ji nake abu yana tsiyaya a jikina kamar an kunna fanfo." Inna da kunya, haushi da baƙincikin Mai gari suka cika ta murya a dakushe ta ce. "Ai kana da hannu ko?Sai ka yi ƙoƙari ka kashe fanfon." A razane Mai gari ya ɗago, sai a lokacin idanunsa suka sauka a kan fuskar sirikarsa. Ya fito daga ƙarƙashin gadon a guje, yana zuro kai ya ga Laraba ta ƙwalla wata irin ƙara ta yanke jiki ta faɗi. Daga Mai gari har ragowar mutanen garin da suke leƙowa tsaye suka yi suna kallonta, aka rasa wanda zai tunkare ta ballantana ya yi yunƙurin tashinta. Laraba ta ɗan jima a haka sai kuma ta fara buɗe idonta a hankali tana salati, tashi ta yi zaune tana kalle-kalle kamar mai neman wani abu ta ce, "Kai, waye ya kawo ni nan?" Shiru gabaɗaya suka yi mata, ta tunkari wurin mai gari a ɗan razane ta ce. "Mai gari me nake yi a nan?" Baki yana rawa Mai gari ya ce, "Ni ma tambayar da nake son yi miki kenan, amma yanzu ki fara zuwa gida tukunna." Laraba ta saki murmushi a fakaici ganin yadda duk ya birkice, sannan ta fito ta nufi hanyar gida. Kamar sun ga sabuwar hallita haka mutane suka dinga bin Laraba da kallo, ita kuwa ta maze tana tafe tana hura hanci tana buɗa kafaɗa har ta je gida. Baba Inu yana shiga gida kai tsaye ɓangarensa ya nufa, tun daga bakin ƙofa ya tsaya ya yi gyaran murya yana haɗe fuska, lokaci ɗaya yaran suka fara shiga taitayinsu. Iyayensu kuma suka shiga tsawatarwa 'yan ƙananun da ba su yi wayo ba. Larai ce da girki ranar, a tsakiyar gida ta ajiye tukunyar abincin rana sai ƙanana da manyan kwanuka birjik a gabanta. Waɗansu ƙananan yara ne kusan su huɗu waɗanda ba su wuce shekara ɗaya zuwa da rabi ba, biyunsu riƙe suke da kwanuka suna kukan yunwa suna kama zanin Larai. "Gaskiya Indo ba kwa kyauta mini, da wanne zan ji? Da aikin abinci ko da waɗannan yaran. Ke Kulu zo ki janye mini su don ubanki!" Ta ƙarasa maganar a fusace ta fisge kwanukan hannun yaran. Baba Inu ne ya ƙarewa tukunyar kallo, ya matsa gabanta a kausashe ya ce. "Ke Larai satar mini abinci kika yi? Kika ƙara a kan wanda na ɗebar muku, da na ga kin rafka wannan rafkekiyar tukunyar?" Jiki yana rawa Larai ta buɗe tukunyar ta ce. "Mai gida tukunyar girkin ce ta ɓule shi ya sa na ɗora wannan." Leƙa tukunyar ya yi ya hango abinci a can ƙasan tukunyar sannan ya sauke ajiyar zuciya ya wuce ɗakinsa. Mukulli ya saka ya buɗe, ya ɗauko wata 'yar madaidaiciyar tukunya ya miƙa mata yana daga tsaye ya ce. "Maza ɗumama mini miyar nan." Da sauri Larai ta karɓa ta ɗora a kan murhun, Baba Inu ya koma kan benci ya kasa ya tsare yana ganin yadda take rabon abinci. Kowanne kwano idan ta ɗauko bai fi ta yafita ludayi ɗaya da rabi ba, saboda idan da sabo sun saba a kullum abincin ba isarsu yake yi ba. "Mai gida a zuba maka kana marmarinsa?" Larai ta tambaya tana gyara goyon Fure da ke bayanta. "A'a ku ci kawai!" Baba Inu ya furta a daƙile. Larai ta ɗebi ragowar wanda ta rage masa cikin murna ta shiga ƙara wa kwanonta. "Ke Larai wallahi son zuciyarki yawa gare shi, ba za ta saɓu ba wallahi sai kin ƙara wa kowa." Hansatu ta yi caraf ta yi maganar ganin abin da Larai take yi. Babu yadda ta iya ganin Baba Inu yana wurin ya sa ta shiga ƙarawa kowanne kwano bai fi cokali ɗaiɗai ba. Bayan ta gama ta ce kowa ya ɗauka, a guje yara da 'yan matasan cikinsu suka ɗauka da sauri, wasu tun a tsaye suka fara zuba loma duk da abincin yana ƙona su. Ƙamshin ɗumamen miyar ne ya fara dukan hancinsu, Larai ta sauke har za ta kai masa ɗaki Baba Inu ya ce ta kawo gaban bencinsa ta ajiye. Abu da ke da tsohon ciki wani irin ƙwaɗayi ya taso mata. Kwanon abincinta ta ɗauka ya ƙarasa wurinsa cikin marairaicewa ta ce. "Don Allah mai gida ko man miyar ne, ka taimaka ka yafa mini na ci ko na samu sauƙin abin da nake ji. Wallahi ƙwaɗayi ne ya addabe ni." Wani banzan kallo Baba Inu ya yi mata ya ce. "Cewa aka yi idan ba ci ba za ki mutu?" Abu ta yi saurin girgiza masa kai, Baba Inu ya sake haɗe fuska ya ce. "To yanzu baƙincikin wanda zan ci kike yi? Idan kuma ba na cin mai maiƙon, ta ya ya zan iya samun ƙwarin jikin nemo muku abincin da kuke ci." Abu ta haɗiyi yawu tana kallon farantin da Baba Inu ya zuba miyar da ƙirjin kaza, sai da ya rufe tukunyar ya miƙa wa Larai ta mayar masa ɗaki sannan ya ce, "Wallahi ba don cikin jikinki ba, da idan ba ki matsa daga kaina ba sai na sheme ki. Dubi yadda kike ɗebo mini fuska kamar an matse lemon tsami." Abu babu yadda ta iya, haka ta ja jiki a sanyaye ta koma ƙofar ɗakinta ta zauna. Ƙaton biredi ya ɗauko ya gutsira sannan ya mayar ya saka kwaɗo ya rufe ɗakin nasa. Kan bencin ya koma ya fara yagar biredin yana dangwalar miyar da ita, daga yaran da suke wurin har iyayensu ban da haɗiyar yawu babu abin da suke yi. Wani ɗan ƙaramin kwanon sha ya buɗe kusan cike yake da nono, ya zura hannu a aljihu ya zaro wani ƙullin maganin ƙarin kuzari da ya saya a daren ranar. Ragowar ƙullin ya kunce ya zuba ya jujjuya ya ajiye shi a gefe, ya ci gaba da yagar kazar yana dangwalar biredi da miya. Baba Saleh sai da ya gama loda duka magungunansa a cikin mota sannan ya koma gida, domin ya yi wa Ɗan Bishir sallamar tafiya yawon tallar magani. Yana shiga sashensa, ya samu ɗan bishir yana tsanyara ihu kamar wanda ake ƙwaƙwalewa idanu. Wani irin bugu ƙirjinsa ya yi, kamar wanda ya yi tozali da gawar mahaifiyarsa. A hargitse ya janyo Ɗan Bishir ya rungume yana jin zuciyarsa tana zafi ya ce. "Ɗan bishiririna, waye ya taɓa ka? Me aka yi maka?" Ɗan Bishir ya sake narkewa yana wani tale baki irin na shagwaɓaɓɓun yaran da aka sangarta ya ce. "Innaaaaaa! Inna ce ta dungure mini kai. Wayyo Allah kaina." Jikin Baba Saleh har karkarwa yake, saboda a duk duniya idan da abin da yake ɗaga masa hankali ganin kukan Ɗan Bishir. Ya nuna Uwale idanu cike da masifa ya ce. "Sau nawa zan ce ki daina zalintar yaron nan Uwale? Ke wacce irin uwa ce kamar ba ke kika haife shi ba tsabar rashin imani, wallahi ba don kin ci darajar ke kika haife shi ba yau sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Ran Uwale ya gama ɓaci ta nuna masa randar ruwan da suke sha ta ce. "Wallahi Mai gida wannan abin da kake yi ba soyayya ba ce, ɓata tarbiyyarsa kake yi. Dubi fa randar ruwan shan mu ya ɗauki omo da mai ya zuba mini, don na dungure masa kai kake yi mini wannan tijarar? To wallahi na gaji, na gaji da wannan abin da kake yi mini. Kai kuma don ubanka ko yau ka sake yi mini irin wannan ɓarnar sai na dungure ka." Uwale ta ƙarasa maganar tana sakarwa Ɗan Bishir ƙozo a ka. Wata irin gantsarewa ya yi yana canyara ihu tamkar wanda aka caka wa wuƙa, a fusace Baba Saleh ya kai wa randar duka ta bada tus! Ruwanta ya mamale a tsakar ɗakin, cikin ƙaraji ya ce. "Ba dai a kan randa za ki illata mini Ɗan Bishir ba? To wallahi idan ba ki da gaske ba, yadda na ragargaje randar nan kema sai na ragargaza ki." Baba Saleh ya yi furcin yana sunkutar Ɗan Bishir da zai yi shekara shida a tsaye, ya ɗauke shi yana shafa bayansa zuwa kansa yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki. Ya rungume shi a ƙirji cike da so, ya waiga yana wurga wa Uwale mugun kallo. Har lokacin Ɗan Bishiri bai daina tale baki yana kuka a shagwaɓe ba, Baba Saleh ya kalle shi har lokacin zuciyarsa zafi take ya ce. "Me kake so ka ci Ɗan Bishirina." Ɗan Bishir ya wale baki yana duban mahaifiyarsa tana mata harara sannan ya ce. "Namaaaa!" Baba Saleh ya sauke shi ya ce, "Don nama banza Ɗan Bishir, bari na je na yanko maka na zabi ko kaji." "Na zabiiiiiiiiii." Ɗan Bishir ya faɗa a sangarce. Harara ya wurga wa Uwale sannan ya fice daga sashensu, yana zuwa ƙofar gida ya yi turus ganin abokinsa Sani yana ba wa yaro sakon a kira shi. "Ga ni na zo a daidai ya aka yi?" Sani ya ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa, sannan ya sauke idonsa a kan jakar wanzaman da ke rataye a kafaɗar Baba Saleh. "Karenka ya kai tsaiko ko Sale? Wai har ni za a kira na cire beli na yi wa jaririya aski, amma sai na ji labarin ka yi mini shigar ɓurtu alhalin ka sani ni ɗan gado ne a harkar wanzanci ba ɗan ka-ta-haye kamar kai ba?" Baba Sale ya saki tsaki cikin halin ko-in-kula ya ce. "To mene ne marabar dambe da faɗa? Don kana ɗan gado ka koya mini harkar wanzanci, na zo ni kuma Allah Ya saka mini nasibi duka costomers ɗinka sun dawo wurina wani avu ne? Wai ma da kake wannan abin, kai da kake jin ka ɗan gado da ni ta-ka-haye ba duka wanzamai za a ce mana ba? Kai matsa ka ba ni wuri Ɗan Bishiri ya aike ni, don aikensa ya fi mini wannan sokiburutsun banzan da kake yi mini." Baba Sale ya gegara ya wuce shi, ya nufi wurin Sadau mai nama. Bayan fitar Baba Saleh cikin takaici Uwale ta ɗauko zani ta shiga tsane ruwan tana matsewa. Mugun kallon da take jifan Ɗan Bishir da shi ya sa ya yi saurin ficewa daga ɗakin. Kai tsaye sashen Baba Inu ya nufa don tun da ya ji shiru ya san abinci suke ci. Ɗan Bishir irin kwaɗayayyun yaran nan ne da duk abin da suka ga ni, za su ce suna ci koda a hannun babba ne. Sangartar da Baba Sale ya yi masa ce ta sa ya koyi wannan mummunar ɗabi'ar. A lokacin da ya shiga sashen Baba Inu da bencinsa ya fara cin karo, ya hangi Baba Inu a can ƙofar ɗakinsa yana rabawa yaransa waɗansu ƙananun alewa. ragowar naman kazar da ya gani ya saka hannu ya ɗauka, ya kai ba ki ya fara zuge tsokarta yana lumshe ido. Sai da ya gama cinyewa tas, sannan ya ɗauki kindirmon nonon da Baba Inu ya zuba magani ya ɗaga kansa ya ɗaɗɗaka, a shagwaɓe ya wurgar da kwanon ƙasa bayan ya shanye ya ɗauki ƙashin kazar ya fara tauna. Ƙarar jefar da kwanon ce ta ja hankalin Baba Inu, da yara da suke gabansa. Ganin abin da Ɗan Bishir ya yi ya sa Baba Sale ya ƙarasa wurinsa rai a ɓace ya kai masa duka a baya. Ɗan Bishir ya tale baki a shagwaɓe ya saka kuka yana yi wa Baba Inu daƙuwa haɗe da faɗin. "Uwakaaaa!" Zuciyar Baba Inu ce ta fara tafasa, ya saka hannu zai dake shi da sauri Ɗan Bishir ya fita da gudu yana faɗin. "Allah Ya isa." Zucya tana tafasa Baba Inu ya rufa masa baya, suna zuwa mararrabar hanyar da take haɗa kowa da ke cikin gidan ya samu nasarar cafko shi, bai yi wata-wata ba ya tsinke shi da mari. A daidai lokacin Baba Sale ya ƙarasa wurin, ganin abin da aka yi wa Ɗan bishir ya sa shi wata irin zabura a haukace ya yi kukan kura ya tunkari wurin da suke tsaye. Share pls 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [05/12/2024, 19:57] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA UKU Jikin Baba Sale har karkarwa yake yi, ya ƙarasa wurinsu ya suri Ɗan Bishir da ya gantsare yana wani irin ihu da kuka, rungume shi ya yi tsam a ƙirjinsa ya shiga lailaya masa baya yana sasshafa shi. Lamo Ɗan Bishir ya yi yana sauke ajiyar zuciya don dukan da Baba Inu ya yi masa ba ƙaramin shigarsa ya yi ba, Baba Inu ya dube su rai a ɓace ya ce. "Idan ubanka bai koya maka tarbiyya ba, ni idan ka shigo gonata ladaftar da kai zan yi. Shashashan banza da wuri, yaro ya duk ya bi ya sangarce kamar tasowar gidan gwauro." Ran Baba Sale ne ya sake ɓaci, saboda dama ba ya ƙyale shi ba ne. Yana jiran ya gama lallashin Ɗan Bishir ne kafin ya dawo kansa. A hankali ya dire Ɗan Bishir, ya sunkiya ya yi masa raɗa a kunne. "Tsaya a nan zan rama maka ka ji Ɗan Bishiririna!" Ɗan Bishir ya kwaɓe baki a shagwaɓe ya ce. "Da ƙarfi za ka rama mini." Baba Sale ya gyaɗa masa kai, sannan ya tunkari Baba Inu da ya juya baya yana shirin shiga sashensa. Wani irin kukan kura ya yi haɗe da sufa sai ya yi tsalle ya ɗafe masa wuya, maƙure shi ya yi sosai ya shiga kai masa duka yana harbo shi da ƙafarsa. Jin irin shaƙar da Baba Sale ya yi masa ya sa Baba Inu ya zuciya ya wulwulo shi ya damfara shi da ƙasa, a galabaice Baba Sale ya yarfe hannu yana dafe ƙugu ya ce, "Wayyo Allah Uwale ki zo ya karya ni." Ihun da Baba Sale ya saki ne ya janyo hankulan mutanen gidan, ba a ɗauki lokaci ba mutane suka cika wurin kowa ya yi carko-carko. "Subhanallah me yake faruwa Sale?" Baba Ibrahim ya tambaya a razane, don irin ihun da Baba Sale ya yi za ka ɗauka farke masa ciki ake yi. Yana daga kwance ya ɗaga hannu yana fitar da numfashi da ƙyar ya ce, "Yaya Inu ne yake ƙoƙarin datse rayuwata da ta Ɗan Bishir, don Allah ku nesanta mu da shi kada ya hallaka mu." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke, Baba Inu ya yi kicin-kicin ya haɗe rai yana hura hancin yin galaba a kan Baba Sale. "Don Allah Yaya me kuke yi haka kamar ƙananan yara? Kai ne babba fa, ko me Sale ya yi maka ba sai ka rabu da shi ba ko ka yi masa faɗa. Amma yanzu ina daɗi a ce yara suna ganin irin wannan abin da kuke yi? Ta ina yara za su haɗa kansu?" Baba Ibrahim ya rufe su da faɗa, saboda lamarin gidan nasu a kullum ƙara taɓarɓarewa yake yi. Baba Inu ya dube shi a sheƙe ya ce, "Kai Iro, dube ni da kyau ka kalli ƙwayar idona." Baba Inu ya yi maganar yana ware dara-daran idanunsa da girma ya sa suka fara shigewa, sannan ya ɗora da cewa. "Wane ne wannan?" Ya tambayi Baba Ibrahim yana nuna Ɗan Bishir. "Ɗan Bishir ne!" Baba Ibrahim ya ba shi amsa. "Yanzu Iro ko Sale ya isa ya zage ni ballanta wannan yaron mai zubin buhun bagco!" Duka mutanen wurin suka girgiza kai cike da son ƙara ingiza Baba Inusa, saboda kowa ya san rashin kunyar Ɗan Bishir don haka yake da baƙin jini a wurinsu. Nan take Baba Inu ya ba su labarin abin da ya faru, da abin da Baba Sale ya yi masa. A razane Baba Sale ya miƙe jiki yana karkarwa, ya nufi hanyar sashensa da gudu ganin Ɗan Bishir ya yi hanyar, ya rarumo shi ya riƙo shi sai kawai ya ɓarke da kuka. Kallonsa suka tsaya yi suna mamakin kukan da yake yi, ya tako wurinsu a guje yana saɓule burmemiyar doguwar rigar Ɗan Bishir ya ce. "Jama'a ku taimaka mini Ɗan Bishir ya sha maganin ƙarin kuzari, wayyo Allah yaya don Allah ka kawo mini ɗauki." Ya ƙarasa maganar yana miƙa wa Baba Ibrahim shi sannan ya ɗora da cewa. "Don Allah ka yi masa wani abu yaya kai ne likita, Allah Ya sa ba ajali ne yake kiransa ba ban da haka ina Ɗan Bishiri ina shan maganin kuzari?" Yana gama maganar ya sake ɓarkewa da kuka. "Ka ga Sale kada ka ɓata wa kanka lokaci, idan har kana son rayuwarsa ka ba ni wani abin ni kuma zan ba ka lambar mai maganin sai ka nemi makarin maganin a wurinsa. Bokan turai ta ina ya san abin da aka haɗa?" Baba Inu ya yi maganar yana sakin murmushin ƙeta. Baba Sale ya yi zaman 'yan bori a wurin ya ce, "A kan Ɗan Bishir zan iya sadaukar da komai da na mallaka, Yaya nawa zan ba ka don Allah ka ba ni lambarsa." Baba Inu ya ɗauke kai gefe cikin basarwa ya ce. "Dubu ashirin!" A firgice Baba Sale ya ce, "Ashirin fa Yaya?" Baba Inu ya yi gaba abinsa cikin halin ko-in-kula ya ce. "Kada ka biya matsalarka ce, ni ko yanzu na mutu akwai masu yi mini addu'a da yawa." Jin haka ya sake ɗaga hankalin Baba Sale, ya janyo ƙafarsa yana ba shi haƙuri, babu yadda ya iya haka ya shiga cikin gida ya ɗauko dubu ashirin ya damƙa masa. Sannan Baba Inu ya karanto masa lambar mai maganin, jikin Baba Sale har rawa yake ya yi masa bayanin abin da ya faru. Mai maganin ya tabbatar masa da babu abin da zai faru da shi, sai dai ya ja hankalinsu a kan su dinga lura sosai saboda kar gaba a samu matsala. Ɗaya bayan ɗaya suka fara watsewa, Baba Inu ya koma sashensa zuciyarsa fes don shi wannan abin da ya faru ya zame masa alkairi. Yana nan zaune ya ji sallamar Malam Jibrin, jin haka ya sa ya dubi su Abu a kausashe ya ce. "Ke Abu da fatan kun haɗa wa yaran nan kayansu ko? Ga sallamar Malam Jibrin can na ji, bari na je mu gaisa." Tun da Baba Inu ya fara magana ta haɗe fuska, saboda Allah Ya sani ba za ta iya bayar da yaranta a kai su makarantar allo ba. Yana zuwa ƙofar gida ya samu Malam Jibrin, daga gefe wata ƙatuwar motar Bus ya gani kusan rabin motar cike take da yara waɗanda za a kai makaratar allo. Bayan sun gaisa Malam Jibrin ya ce. "Malam Inu ina fatan an gama kintsa yaran? Saboda direban motar sauri yake akwai sauƙon da ake jira zai bayar a hanya." Yaya Inu ya faɗaɗa fara'arsa yana jin kamar za a sauke masa wani gingimemen nauyi daga kansa ya ce. Malam Jibrin ba ka da matsala yanzu za su fito, amma fa an samu ƙarin yara uku." Shiru Malam Jibrin ya yi ya ce, "Yaran kuwa ba su yi yawa Malam Inu? A baya fa yara shida ka ce za a tafi da su. Idan mun yi gaba akwai 'ya'yan Malam Sallau guda biyu da za mu ɗauka." Duk da yana jin zafin fitar kuɗin amma sanin sauƙi zai ƙara samu ya sa ya zaro dubu uku ya miƙa wa Malam Jibrin ya ce, "A ƙara da wannan Malam Jibrin, ka sha ruwa a hanya, ka san yaran ne duk kansu ɗaya. Da su Barau masu shekara huɗu zuwa biyar ne zan bari amma su ma ai sun tasa, Allah na tuba abu da girman ɗan mutum babu wuya." Malam Jibrin ya kalmashe dubu ukun saka a aljihu yana murmushi ya ce, "Yo shekara huɗu mene ne ba za su iya yi wa kansu ba? Ai duka sun tasa, kuma Allah ai shi yake raya bawa ba mutum ba." A daidai wannan lokacin Malam Isiya ya ƙarasa da ɗansa Musbahu mai kimanin shekara goma sha biyu, hannunsa riƙe da ƙaton buhu wanda ya haɗa masa ƙanzo, garin kwaki, sabulu da omon wanki. Bayan sun gaisa da Malam Isiya, ya kawo 'yan kuɗi ya ba shi. Malam Jibrin ya ce, "Malam Isiya ya na ganka da ƙaton buhu bayan jakar hannunsa, akwai yaran da za mu ƙara a motar fa." Malam Isiya ya yi murmushi ya ce, "Kayan abincinsa ne a ciki, ai ba ka da damuwa Malam Jibrin zan biya kuɗin kujera biyu, don tare za mu tafi. Saboda na je na ga mkarantar da za a kai Musbahu, mu gaisa da malamin kafin daga baya lokaci zuwa lokaci na dinga zuwa ina gano shi ina kai masa kayan abinci." Malam Jibrin ya kalli Musbahu ya ce, "Lallai Musbahu kai ɗan gata ne, abin da iyaye da dama ba sa yi kenan! Kai ma Malam Isiya Allah Ya sa da gaske kake." Malam Isiya ya ce, "Me ka ɗauke ni Malam Jibrin? Ai yayansa Ɗahiru da ke garin Kaduna yana karatu, duk bayan wata biyar nake zuwa wurinsa, domin na ga halin da yake ciki kuma na kai masa kayan abinci da 'yan kuɗaɗen sayen abin buƙata. Kawai kuma saboda ka kai yaro makarantar allo sai ka manta da shafinsa? Yara fa amana ce da Ubangiji Ya damƙa mana kuma ranar Lahira sai ya tambaye mu a kan kiwon da ya ba mu." Malam Jibrin ya jinjina kai, Yaya Inu yana jin haka ya zame ya shige gida yana faɗin zai haɗo kan yaran su tafi. Saboda sho ko ɓarin gyaɗa babu wanda zai ba wa a cikinsu, abin da yake ciyar da su ma Allah amfana. Yana shiga tsakar gida ya ci karo da su Basiru kowanne ɗauke da ƙaton buhu a kansa, iyayensu ne suka ɗauko ƙanzo da garin kwakin da suka tanadar musu. "Ku yi sauri ku shirya su Barau, Idi da Iro ƙarami, su ma da su za a tafi." Sororo suka yi jiki a sanyaye Larai ta ce, "Don Allah malama..." "Wallahi sai an tafi da su, tun da na rantse babu kaffara. Idan sun zauna yaran uwar me za su yi musu? Kun fi son yara su zauna babu ilimi mutanen gari su dinga zagina." Sanin halinsa na kafiya ya su Larai suka shiga shirya ƙananan yaran kowacce tana share hawaye, ban da Abu da ta ja ta tsaya ta ki motsawa. "Ke ba ki ji abin da na faɗa ba ne?" Yaya Inu ya faɗa yana haɗe rai. "A gaskiya Malam ba zan iya bayar da Bukar da malami a tafi da su ba, dududu shekarar Bukar nawa? Ko biyar da rabi bai rufa ba. Shi kuma malami shekara huɗu, idan sun je wa zai kula da su ya ba su abinci?" Abu ta faɗa tana ƙanƙame Malami. Ran Yaya Inu ne ya ɓaci, suka shiga ja'inja yana jan Malami tana ja, daga ƙarshe ya ɗauke fuskarta da mari sannan ya fisgi hannunsu suna ihu da kuka Abu tana yi ya nufi hanyar fita. Da gudu Abu ta bi shi duk da tsohon cikin jikinta, ya waigo a fusace ya ce. "Wallahi Abu idan har kika tako zuwa soron gidan nan a bakin aurenki tun da ba ki da hankali." Abu ta yi turus, tana jin wani irin ɗaci a ranta. "Iyataaaa!" Malami ya faɗa cikin kururuwa, da gudu Abu ta rufa masa baya har ƙofar gida yana zuwa ya damƙawa Malam Jibrin su, ya fisge su kamar kaji ya watsa a cikin mota. A zafafa Yaya Inu ya koma cikin gidan Abu ta bi shi tana kuka, ya waigo a zafafe ya ce. "Daga nan ki wuce gidan ubanki, na warware ragowar igiyar kanki." Daga haka ya shige cikin gida. Ɗaya bayan ɗaya 'yan masu wayon suka fara fita cike da ɗoki, musamman da suka leƙa suka hango motar da take jiransu a ƙofar gida. Su Barau da yake ƙanana ne suka dinga kuka suna tirjewa iyayensu ma suna kuka. Jin kuka da ihu tare da hargagin Yaya Inu ya sa rogawar mutanen gidan suka fito suka yi carko-carko, Inno ce ta tambayi abin da ya faru a nan Yaya Inu ya sanar da su. Takaici ne ya kama Baba Ibrahim rai a ɓace ya ce. "Yaya wai saboda Allah wacce irin rayuwa kake yi haka? Yanzu don Allah kamar su Barau za ka kai birni makarantar allo? An ya kana tunanin goben yaran nan?" Yaya Inu yaji kamar Baba Ibrahim ya zuba masa ruwan zafi, rai a ɓace ya mayar masa da martani. "Kai Iro kada ka faɗa mini maganar banza da wofi, ba ɗazu ka gama faɗa mini magana a kan rashin iliminsu ba. Kai za ka faɗa mini na hango gobensu, akwai shege ɗaya a cikin gidan nan da yake ciyar mini da su? Tun da ni na samu kaina a gobena ai shi kenan! Daga yau ma kada wani ƙaton banza ya sake shiga hurumin iyalina." Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana fisgar Idi da ko wando babu a jikinsa ya yi waje da shi. Su Larai suka durƙushe a wurin suna sakin kuka. Suna nan tsaye suka ji tashin motar, hakan ya sake ɗaga hankalansu, a daidai lokacin Yaya Inu ya dawo yana muzurai yana harare-harare. Bayan Sallar Isha'i Zaune yake a matsakaicin ɗakin da aka ware masa, daga gabansa wani ƙaton fulas ne cike da farfesun kaji. Sai da ya zuge tsokar cinyar kazar hannunsa, sannan ya ɗaga ƙaramar wayarsa ya danna wata lamba. Bugu ɗaya ta yi ya ji an ɗauka, ya yi ƙasa da murya ya ce. "Barka da hutawa 'Yar gwal!" Malam mai Yasin ya furta yana kurɓar romon naman, amsa masa ta yi sannan ta ce. "Ni fa na gaji wallahi..." Da sauri ya katse ta. "Haba 'Yar gwal, na faɗa miki kwantan ɓauna na yi wa mutanen gidan nan, har na samu na aure tsohuwar nan. Ni na san Inno ba za ta ba ni matsala ba sai dai 'ya'yanta, amma ina aure ta magana ta ƙare. Tatsarta zan ta yi har na tara mana kuɗin da za mu hole, kada ki ji muryata ƙasa-ƙasa har yanzu nuna musu nake ba ni da lafiya." Daga can ɓangaren 'Yar gwal ta saki dariya ta ce. "Shege Malam Gambo wallahi ko shaiɗan bai kai ka shaiɗanci ba." Malam mai Yasin ya saki dariyar shakiyanci, suka cigaba da hira sannan suka yi sallama. Ya kai kusan awa guda a zaune a bakin gadon yana yi mata firfita, saboda ko kaɗan ba ya son abin da zai dagula lissafinta. A hankali Rahina ta buɗe idanunta ta sauke su a kan mai gidanta Labaran, murmushi ya sakar mata ganin za ta tashi ya sa ya ɗago ta zaune sannan ya rungume ta sakar mata kiss a goshi. "Barka da tashi masoyiya!" Labaran ya furta cike da so yana jin kamar zai lashe Rahina. Fari ta yi masa da ido ta ce, "Wai tun da na kwanta kana zaune masoyi?" "Ina zan matsa daga wurinki ƙaunata. Yanzu dai bari na sirka miki ruwa ki yi wanka. Ya ƙarasa maganar ya fita daga ɗakin." Rahina ta bi bayansa da kallon soyayya tana jin tamkar ita kaɗai ta yi dacen miji a duniya. Tana nan zaune ya dawo ya riƙo ta, ganin za ta tuɓe kaya ya saka hannu ya fara rage mata. Rahina ta ɗaura zani ta yafa ɗan kwali a kanta, Labaran ya riƙe mata hannu ɗayan hannun nasa yana riƙe da kwandon wanka suka nufi hanyar banɗaki. Sai da ya ga ta shiga banɗakin, sannan ya koma domin ya zuba mata abincin da za ta ci idan ta fito. Rahina irin matannan ne masu tsayi da ƙiba, shi kuma Labaran ɗan tsamurmuri ne ko tsayin kirki ba shi da shi. Yadda yake son Rahina da kishinta ji yake zai iya aikata komai a kanta. Malam mai Yasin yana daga zaune a ɗakinsa ta labule ya hango wucewar Rahina, ya jima ransa yana biyawa da ita don haka bayan tafiyar Labaran ya yi zaraf, bayan ya ji ta fara sheƙa ruwa ya nufi banɗakin cikin sanɗa. A hankali ya tura ƙofar banɗakin, da yake dare ne sai Rahina ta yi tsammanin ko Labaran ne ya shiga domin ya tayata wankan. Malam mai Yasin yana shiga da sauri ya wara hannuwansa ya dadumo ta, cike da so da ƙauna Rahina ta ce. "Wallahi ba don kada na saka son zuciya ba, da sai na ce duk duniya babu matar da ta kai ni sa'ar miji masoyi." Malam mai Yasin don kar ya yi magana ta ji muryarsa sai kawai ya ce, "Ummmmm!" Ya cigaba daduma hannunsa a jikinsa. Rahina tana shafo fuskarsa ta ji gemunsa da gashin bakinsa sun yi mata ƙababa, a razane ta ja da baya da ta ce. "Wayyooo Allah! Masoyi ka zo kwarto a banɗakin nan." Da gudu Malam mai Yasin ya fice daga banɗakin ya faɗa ɗakinsa, Labaran da ke ɗaki jin ihun Rahina ya sa ya zaro wani kafcecen almakashi irin na aikin gona ya tafi da shi. Yana zuwa banɗakin ya shiga jera mata tambayoyi, ba ta tanka masa ba sai ji ya yi ta fashe da kuka. Ganin ba shi da wata mafitar ya sa shi ma ya rushe da kuka har da majina, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce. "Kwarto ne ya shigo mini banɗaki, kuma tas ya gama lalube ni." Wani abu ne ya soki ƙirjin Labaran tsananin soyayya da kishinta ya rufe shi. "Sai da na laluba gemu da gashin bakinsa, na gane ba kai ba ne tun ba ka da shi." Rahina na ƙara faɗin haka ta sakin kuka. Jikin Labaran ne ya shiga karkarwa zuciyarsa tana zafi, cikin huci ya ce. "Na tabbata Ado ne! A cikin gidan nan shi ne tuzuru sako zaninki ki tafi ɗaki, wallahi yau sai na guntule shi da almashin hannun nan nawa. Nan gaba sai na ga da me zai nemi yin kwartoncin." Labaran yana gama magana ya fita a guje yana wani irin ihu kamar wanda zai tunkari maƙiya a filin yaƙi. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [10/12/2024, 16:47] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA HUƊU Kasancewar yaya Ado dawowarsa daga wurin aiki kenan, ya sa ya shiga rage kayan jikinsa domin ya watsa ruwa ya gabatar da sallar Isha'i. Yana daga cikin ɗakinsa ya fara jiyo ihun Labaran, ya girgiza kansa cike da takaici, yana jin haushin yadda gidansu ya zama tamkar gidan haya saboda yadda zuciyar kowa take a kusa. Ihun da Labaran yake kurmawa ne ya janyo hankulan mutane wasu suka fito, wasu kuma suka tsaya suna leƙensa daga window. Yayin da wasu kuma suka rifa masa baya, domin su ga irin wainar da zai toya. Sashen Yaya Ado ya shiga, ya tsaya daga bakin ƙofa yana sauke numfashi cike da zafin rai. Yaya Ado ne ya leƙo da kansa daga shi zai gajeren wando, ya haɗe fuska ganin Yaya Ado da ragowar mutanen gidan a sashen ba tare da sun nemi izininsa ba. Saboda yaya Ado mutum ne mai tsattsauran ra'ayi, kuma yana da ƙa'idoji don haka suke cewa karatun boko ya mayar da shi mai aƙidar yahudawa. "Me ya sa ka shigo mini ba tare da izinina ba?" Yaya Ado ya tambaya fuska a haɗe, Labaran ya ji kamar ya watsa masa ruwan zafi mai haɗe da attaruhi, saboda ganinsa da ya yi da gajeren wando kaɗai ya sake harzuƙa shi, musamman da ya tuna Rahina ta ce kwarton yana ta shafe ta a banɗaki. A hankali Labaran ya fara takawa jikinsa har karkarwa yake, hannunsa riƙe da ƙaton almashi. Ganin haka ya sake ɓata ran Yaya Ado, saboda a duniya ya tsani wani ya raɓo ɗakinsa saboda muhimman takardunsa da ba ya son wani ya taɓa masa. A harzuƙe ya tunkari Labaran ya ce. "Kai Labaran ba magana nake yi maka ba?" Mutanen wurin carko-carko suka yi cikin mamaki suna kallon Labaran, cikin shammata Labaran ya yi kukan kura ya yi kan yaya Ado yana ɗaga almashin sama, kamar yadda sojoji suke yi a filim yaƙi ya ce. "Zuwa na yi na halaka ƙasurgumin fasiƙi da wannan almakashin." Yana gama magana ya kai hannu yana ƙoƙarin fisgar gajeren wandon Yaya Ado. Nan take suka shiga kiciniya, Yaya Ado yana ƙoƙarin kare kansa shi kuma Labaran ƙarfi da yaji yake ihu da kururuwar sai ya guntule shi. Ganin haka ya ɓata ran yaya Ado, ya fusata ya ɗaga Labaran ya damfara shi da ƙasa. Labaran bai daddara ba ya sake miƙewa duk da ya ji zafin buguwar ya ce. "Wallahi yau ko kashe ni za ka yi sai dai mu kashe juna, ko banza na san zan mutu a fagen shahadar kare mutumcin matata." Yana rufe baki sai kawai ya saka hannu ya zugo gajeren wandon ƙasa. Matan da suke wurin suka saki ihu suna fita waje a guje, yayin da Baba Ibrahim da Baba Sale suka yi kansu Labaran da gudu ganin da gaske yana shirin aikata abin da yake faɗa. Fitar Hansatu ya yi daidai da parking ɗin motar Fadil, da gudu da ƙarasa wurinsa cikin kururuwa ta ce. "Likita don Allah ku taimako wallahi kisa za a yi, Ado ne da Labaran." Cikin izza ya sauke baƙin gilashin idonsa, ya zuge gilas ɗin motar cikin golden voice ɗinsa ya ce. "Lafiya?" Ya tambaya saboda bai ji abin da ta faɗa ba, sakamakon gilashin motar da ke rufe. "Ado da Labaran ne za su kashe kansu har da makami, don Allah ku zo ku kawo ɗauki." Hansatu ta sake maimaitawa a hargitse, ganin yanayin da take ciki na firgici ya sake tabbatar masa da abin da take faɗ. Ya saka hannu ya dafe goshinsa cikin takaici, saboda a kullum danasanin sakancewar zamansa a wannan gidan gandun yake yi. Bai tanka mata ba, ya ajiye lapcoat ɗinsa ya buɗe murfin motar ya fito. Ƙamshin turarensa ya bugi hancin Hansatu, ita dai haka kawai rayuwar Fadil take birge ta don haka ma ta ci alwashin aura masa Badariyya, idan ta ƙara zama budurwa tun da dama namiji ai mijin mace huɗu ne. Kuma matar Fadil ko kaɗan ba za ta nuna wa Badariyya komai ba, sai kyau da iyayin da take taƙama da ita likita ce. "Suna ina?" Fadil ya katse mata tunanin da take yi. Da hannu ta nuna masa mangaren Yaya Ado. Da sauri Fadil ya shiga, a daidai lokacin Malam mai Yasin da Inno su ma suka ƙarasa. A lokacin yaya Ado ya samu nasarar ƙara ɗaga Labaran ya buga da ƙasa, hakan ne ya sake ɗaga hankalin Inno sai ta fashe da kuka, da ƙyar aka samu aka riƙe Labaran, shi ma yaya Ado aka riƙe shi kowannensu sai sauke ajiyar zuciya yake yi. Malam ya kwantar da murya kamar bai san abin da ya faru ba, ya shiga tambayarsu abin da ya haɗa su. Rai a ɓace yaya Ado ya ce. "Kun san dai a cikin gidan nan ba sabgar kowa nake shiga ba, saboda ba na ɗaukar raini ba zan ɗauki cin zarafi ba. Yanzu saboda Allah shekara nawa na ba wa Labara? ko Sale da yake bi na, ya isa ya zo ya yi mini iskancin daLaraban ya yi mini ballanta shi ƙanina na biyu? Wallahi ko da wasa ka sake kwatanta mini abin da ka yi sai na ba ka mamaki sakarai bawan mace." Daga haka yaya Ado ya fisge hannunsa ya shige ɗakinsa. Tun ba su ji ta bakin Labaran ba suka fara ba shi laifi a zuciyarsu, saboda kowa ya san yaya Ado shi kaɗai yake gudanar da rayuwarsa bai cika shiga shirgin kowa ba bayan gaisuwa. Don haka ma ake zargi da raɗe-raɗin ko aljana ce ta aure shi, tun da ga ƙannensa nan har biyu sun daɗe da aure amma shi shiru. "Kafin ku ji abin da ya faru don Allah zan tambaye ka Likita!" Labaran ya yi maganar yana kallon Fadil. Gyaɗa masa kai ya yi alamar yana sauraronsa Labaran ya ce. "Idan yanzu na saka almashin nan na guntule yaya Ado, akai wani dashe da za a yi masa a likitance?" Takaici da kunya suka hana Fadil yin magana, kamar dai ba zai magana ba sai kuma daƙile ya ce. "A'a" Labaran ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana jin kishin Rahina yana nukurkusarsa ya ce, "Yaya Ado ne ya shiga banɗaki ya lalube mini masoyiya tana wanka, saboda ya ga dare ya yi kuma wallahi idan duk garin nan gatansa ne sai na gama da shafinsa." Labaran yana gama faɗar haka ya shamace su ya fisge ya faɗa ɗakin Yaya Ado cikin ƙaraji yana faɗin. "Gafara ga maza nan bisa kanka." Ganin haka ya sa su ma ragowar mazan da ke tsaye suka rufe masa gaya. Da ƙyar suka samu suka sake yage Labaran, sai da aka kai ruwa rana sannan aka ba wa Labaran haƙuri ya haƙura. Dalilin da ya sa Labaran ya haƙura, saboda Baba Inu da Baba Ibrahim sun tabbatar da yaya Ado a kan idonsu ya shiga sashensa, kuma suna tsaye Labaran ya zo yana cewa an shiga banɗakin da Rahina take wanka. "To kuwa idan haka ne akwai kwarto a cikin gidan nan, kuma ni da ma daga cikin ilimin da Allah Ya ba ni akwai na gane kwartaye. Kuma ni dama tuna zuwa ban yarda Ado zai aikata hakan ba. Za mu zuba aiki cikin ɗan ilimin da Allah Ya ba mu, Allah Ya sa mu dace." Malama mai Yasin ya yi maganar da wata irin murya, kamar irin waliyan bayin Allahn nan. Gabaɗaya suka amsa masa sannan kowa ya watse. Washegari Tun da asuba bayan da Inno ta tashi Laraba yin Sallar Asuba, ta tabbatar mata da ba za ta je makaranta ba, saboda irin cin zarafin da Mai gari ya yi mata a gaban mutane da yaran gari. Don haka har kimanin ƙarfe tara na safe tana kwace a kan gado tana bacci, daga ita sai rigar atamfa da ɗan kanfai a jikinta. Zanin ya zame ya faɗi gefen gado, yayin da ɗankwalinta ya faɗo ƙasa. Sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin Inno, Inno tana ganinsa ta haɗe rai fara mita sama-sama. "Haka kawai a dinga tayar mini da zaune tsaye, ina dalili a ce duk bayan kwana uku sai an auna jinin mutum. Ni dai tun farko Burema ya cuce ni da ya sayo abin nan ya ce ka dinga auna jinina." Fadil ya zaune a gefenta bayan ya gaishe ta ya ce. "Ba ni hannunki!" Inno ta watsa masa harara ta ce, "Kai Boka ni fa na gaji da wannan ɗaurin hannun. Kaf zuri'armu babu mai ciwon hawan jini, sai da ubanka ya ƙaƙaba mini." Fadil ya sake haɗe fuska ya ce. "Inno sauri nake fa." Ya ƙarasa maganar yana riƙo hanunta, Inno ba don ta so ba Fadil ya gama gwada mata hannu. Kasancewar ta taɓa fama da ciwon hawan jini, yana shirin fita ya hango Laraba a kan gado tana sharar bacci. "Yarinyar can me ya hana ta zuwa makaranta?" Inno ta ɓata fuska don ta san yanzu sai ya tilasta mata zuwa. "Tun asuba ta ce mini jikinta yana ciwo ba za ta je ba, ka san jiya zanen zabuwa Mai gari ya yi mata. Ni ma kuma da ma ko ba ta faɗa ba, ba zan bari ta je makaranta da ɗanyan jiki ba." Fadila bai tankawa Inno ba ya ƙarasa ya buɗe firjinta, ya ɗauko ruwa mai sanyi ya ƙarasa ya kwara a kan Labara. A hargitse ta tashi cikin masifa ta ce. "Uban waye ya zuba mini..." Maganarta ce ta maƙale ganin Fadila tsaye a kanta, ya naɗe hannuwa a ƙirji fuska babu walwala. Ta shiga murtsuka fuska tana kawar da kanta fege. "Tashi ki yi shirin makaranta. Labara ta tura baki ta ce. "Ni ba za ni makaranta yara su raina ni ba!" "Idan na sake magana wallahi sai na karya ki biyu!" Fadil ya faɗa a tsawace. Jiki yana rawa Laraba ta tashi ya janyo kayanta a cikin drower, waɗanda suka cukukuɗe kamar an ƙwato daga bakin kura. Uwar ɗaki ta shiga ta sako kayanta duk sun yi ɗauɗa, wandonta kuwa saboda rashin guga duk ya tattare ta baya da kaɗan ya fi gwiwarta. "Ni fa yunwa nake ji!" Laraba ta faɗa cikin ƙunƙuni. "Ba dole mutum ya ji yunwa ba ƙarfe tara na safe, a gaskiya Boka kada ka tura Laraba makatanta ba ta ci abinci ba..." "Wuce mu je!" Fadil ya katse Inno. Labara har da hawayenta ta ɗauko jakarta wacce ta kasance ta ɗinki buhu ta rataya. A tsammaninta ita kaɗai za ta tafi, sai ta ga Fadil ya bi ta tana gaba yana biye da ita a baya. Laraba tana zuwa ƙofar ajinsu ta ja ta tsaya ganin Fadil ba shi da niyyar tafiya. Ɗagowa ta yi za ta yi magana, kallon da ya wurga mata ya sa ta shige cikin ajin jiki a sanyaye. "Ke daga ina kike?" Malam Sule ya wurga mata tambaya. Laraba tana shirin yin magana Fadila ya yi sallama a ƙofar ajinsu. Malam Sule ya ƙarasa ya miƙa masa hannu suka gaisa. "Ga yarinyar nan na kawo, don Allah malam a saka ido a kanta ba ta son zuwa makaranta. Kuma duk ranar da ta makara ko ba ta zo ba, matuƙar babbu wani ƙwaƙƙwaran dalili a hukuntata." Fadil ya faɗa. Malam Sule ya washe baki ya ce. "In Shaa Allahu Alhaji za a yi yadda kace." Fadil ya yi masa godiya, sannan ya shiga ofishin Headmaster ya sake jaddada masa maganar da suka yi da Malam Sule, Headmaster ya ji daɗi sosai domin yana son ya ga iyayen da suka tsaya a kan kula da shige da ficen yaransu. Daga ƙarshe Fadil ya yi masa godiya, sannan ya wuce gida a gurguje saboda ya kusa makara. Malam sule dama abin nema ne ya samu, saboda yana daga cikin malaman da suke hora ɗalibai. Yana shiga ya dubi Laraba ya ce ta je gaban allo ta tsaya, sannan ya ce mata idan ya gama biya musu darasi sai ta karanta masa abin da ya rubuta. Laraba ta wurga masa harara a fakaice, ta koma ta tsaya ta haɗa rai domin ko kaɗan ba ta san raini. Tana daga tsaye wasu daga cikin 'yan ajin suka dinga yi mata gwalo, wasu kuma suna tsokanar dukan da aka yi mata. Malam Sule subject ɗin English language yake ɗaukarsu. Kuma a ranar Comprehension ya yi musu, sai ya rubuta musu short story mai taken 'Tortise and the goat' kasancewar duk cikin ajin babu mai textbook. Sai da ya karanta da turanci sannan ya fassara musu da hausa, ya dubi Laraba da tun da aka fara karatun hankalinta yana kan ƙofa, tana kallon dukan makarar da ake yi wa sauran ɗalibai. Don ko bayanin da ya yi da hausa ba ta gama saurare. Malam Sule ya haɗe rai ya ce. "Maza biya mana, ki fara yi da turanci sai ki fassara." Shiru laraba ta yi tana bin allon da kallon, don ta tabbata da allon yana magana ƙila zai iya baya mata kansa saɓanin ita da babu abin da ta gane sai baƙaƙen a b c d, su ma idan da za a saka mata wuƙa a wuya ko guda goma ba za ta iya karantawa ba. Laraba ba ta yi tsammani ba ta ji ya zuba mata bulala a baya, don haka ta taƙarƙare ta fara yi masa wani irin yare wanda ita kansa ba ta san me yake nufi ba. Duk yadda Malam sule ya kai ga mazewa sai da ya kawar da kai ya saki murmushi, sannan ya ce ta fassara da hausa. A nan ma Laraba babu tsiyar da ta tsinana, sai sokiburutsu da ta dinga yi masa. 'Yan ajinsu kuwa suka shiga ƙyaƙyata dariya suna yi mata ihu, Laraba ta ƙulu sosai don haka ta yi kukan kura ta faɗa kan Suwaiba ta rufe ta da duka, don ta fi jin haushinta dama saboda har gwalo take mata tana raɗawa na kusa da ita abin da za su faɗa. Da sauri Malam Sule ya fisgo Laraba saboda ya yi mata maganar duniya ta ƙi ji, ya shiga dukanta da zafafe. Zuciya ta kuma ciwo Laraba ta sake cukumo Suwaiba, tana kai mata naushi a baki har sai da ya fashe. Malam Sule mari ya zabga kata, sai a lokacin Laraba ta ja da baya ta dube shi a haukace cikin ɓacin rai ta ce. "Kai malam kada ka sake dukana, wai ba kai ne ɗan gidan Bala mai satar agwagwa ba ko an faɗa maka ba mu sani ba." Wani abu ne ya caki zuciyar Malam Sule, saboda bai taɓa tunanin za ta yi masa wannan bankaɗar ba. Cikin borin kunya ya rufe ta da duka, sai da ya zane Laraba sannan ya riƙe hannunta ya dinga bin ajujuwa da ita, yana saka kowanne prefect ya yi mata bulala biyar kuma 'yan aji su yi mata ihu. Ranar zuciyar Laraba ta gama dagulewa, don haka ta ci alwashin ko sama da ƙasa ce zaata haɗe ba za ta ƙara zuwa makarantar ba. Kuma sai ta hukunta iyaye da 'ya'yan da suka ci zarafin, shi kuma Malam Sule ta ci alwashin sai ya yabawa aya zaƙinta a wurinta. Duk irin zaman doya da manjar da suke yi tsakanin matan Yaya Inu, sai da suka ji jikinsu ya yi sanyi a kan sakin da ya yi wa Abu. Duk da ba baƙon abu ba ne a wurinsu amma irin son da suka san Yaya Inu yana yi mata ne ya ba su tsoro domin ba su taɓa tsammani ba. Hansatu ta fi kowa shiga damuwa saboda duk matan da Yaya Inu yake saki, idan suna da yara ƙarƙashin kulawarta suke komawa, kasamcewar ita ce uwargida a wannan lokacin. Sun jima suna janjantawa da suka ji motsinsa sai kowacce ta shiga aikin gabanta. A yanzu Indo ita ce matar Yaya Inu ta uku, ita ce take bin Larai. A ƙalla ta kai shekara huɗu a gidansa, 'ya'yanta uku duka maza. Babban ɗanta Uzairu bai fi shekara uku da watanni ba, sai mai bin sa Ya'u mai shekara ɗaya da rabi. Sai kuma jaririn da take goyo mai wata shida Hannafi. A washegarin ranar da aka saki Abu akwai bikin da matar yayan Indo ta gayyace ta, a wani ƙaramin gari da ke gaban garinsu. Tun safe Indo ta katsa wanka ta ɗauko galleliyar atamfarta yadi ta saka, ta yi wa su Larai sallama tana jin kamar za ta je wata sabuwar duniya. Larai a ranta take jin dama ita ce take da 'yan uwa a birni, da suke biki har ake gayyatarta da ko babu komai ta samu abin yi wa su Hansatu gori. A gidan kamun bikin da Indo ta je ne, ta tarar da wata mata da aka ɗauko Hajiya Zanni mai gyaran aure tana yin lecture ma'aurata. Matar irin masu safarar magungunan mata daga Kano zuwa Saudiyya ne, ita take koyar da su kissa da dabarun jan hankalin miji wanda zai mallake zuciyar miji. Saboda yadda take yin lacture cikin batsa ya sa mata sai shewa suke, mafi yawa daga ciki suka ƙuduri niyyar yi wa mazajensu daga ciki har da Indo, da take ganin kamar ta mallake Yaya Inu ta gama. Daga ƙarshe Hajiya Zanni mai gyaran aure ta ɗebo magunguna ta fara tallatawa. Jikin Indo yana rawa ta zaro ɗan canjin jakarta ta sayi wani magani mai suna, kin yi wa kishiya fintinkau da idonka idona. Cike ɗoki Indo ta tafi gida, koda ta je gida haka ta dinga kallon su Larai a sheƙe tana yi musu kallon tausayi, mai tafe da izgilin na yi muki nisa don a yanzu sai yadda na yi da mai gida. Daɗin sai ya haɗe mata biyu sakamakon ita ce da girki ranar, tun kafin magriba Indo ta gama komai. Ta caɓa wanka, ta ɗauko wani turarenta na Binta sudan, ta bulbule jikinta da shi kamar yadda ta ji Hajiya Zanni ta ce namiji yana son ƙamshi. Indo har ƙaguwa ta yi a idar da sallar Isha'i Yaya Inu ya shigo gida, sai ga shi a ranar ya yi jinkirin shigowa don har kusan goma saura. Haka ta zauna a gefen gado har ta fara gyangyaɗi, sannan ta ji shigowarsa. Da sauri ta ɗauko Hannafi ta kai shi gefen Uzairu ta kwantar da shi, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce ba a zuwa turaka da yara suna takurawa uwargida da mai gida. Turarenta na Binta sudan haɗe da jan miski ta ɗauko ta sake bulbulawa, ta janyo wani fakeken gajeren wandonta a drower shi ma ta shafe shi da jan miski. Ta nufi ɗakin Yaya Inu hannunta ɗauke da tiren abinci, dama daga ita sai ɗaurin ƙirji wanda hakan duk yana cikin lecture Hajiya Zanni. Tana shiga ta ajiye masa abincin a gefe sai kuma ta ja ta tsaya a wurin, Yaya Inu ya ɗago fitilarsa ya haske ta yana shirin yi mata magana sai ya ga Indo ta saki zanin jikinta ya faɗi ƙasa. Saboda duk huɗubar da Hajiya Zanni ta yi musu ta haddace ta kanta. Da mamaki Yaya Inu yake bin Indo da ke tsaye tumɓur sai ɗan kanfai, da wata sakakkiyar rigar mama a jikinta wacce suk ta zuge ta saki kamar gugar jan ruwa saboda yawan sakawa. "Ke Indo lafiyarki kuwa?" Yaya Inu tambaya a tsorace. Indo ta ji daɗi har ranta, don ta ji Hajiya Zanni ta ce akwai wani shauƙi da miji yake shiga idan an yi masa haka. Indo ta fara harba ƙafa tana wani juyi ita a dole rawar India za ta yi a gabansa, Yaya Inu zai sake magana Indo ta wurga masa wannan burgujejen gajeren wandon da ta ɗauko, wanda ta jiƙe shi sharkaf da turaren miski da Binta sudan. Gajeren wandon ya sauka a saman fuskar Yaya Inu, ya yi sakatoto yana bin ta da kallon mamaki. Indo ta yi wani tsalle tana harba ƙafa haɗe da fisge rigar maman jikinta, kusan lokaci ɗaya ta kifar da kwanon miyar abincin Yaya Inu. Kuma a daidai lokacin rigar maman ta faɗa saman wuyan Yaya Inu da ya gama kai wa wuya. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [10/12/2024, 19:47] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA BIYAR Ko kaɗan Indo ba ta damu da ganin ɓarnar da ta yi masa ba, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce duk cikin sirrikan da ta ba su babu na yarwa indai a ɓangaren mallaka da saye zuciyar miji ne. Don haka ta yi wata girgiza ta cake a wuri ɗaya, ta fara miƙa masa hannu ɗaya irin yadda jaruman india suke yi, idan za su miƙa wa masoyinsu hannu domin su yi rawa. Ta miƙe ƙafa gaba da zummar ta yi tsalle ta dira a gaban Yaya Inu, ta yadda za ta ɗago shi ta manna a jikinta kamar yadda Hajiya Zinni ta kwatanta musu, bisa tsautsayi ƙafarta ta harɗo labulen ɗakin ya faɗo a kanta. Kukan Hannafi ta fara ji sama-sama da alama ya tashi daga bacci, amma sai ta basar ta tunkari Yaya Inu da zuciya ta gama cika shi. Don yadda yake ji ransa ya ɓaci kamar ya tashi ya shaƙe Indo, saboda wannan sabon iskancin da take ƙoƙarin kawo masa. A gabansa ta tsaya tana wani rangaji, iska ta fara kaɗo cikin ɗakin saboda sanyin da ake busawa. Burgujejen gajeren wandonta ya fara kaɗo fuskar Yaya Inu, Indo ta yi masa wani far da idanu ta ƙanƙance murya ta ce. "Taso mu yi rawa lantarkin zuciyata..." Kalaman Indo suka katse sakamakon fisgowar da Yaya Inu ya yi mata, ta faɗi ƙasa daɓas! Gwiwoyinta suka bugu da ƙasa. A tsammanin Indo shauƙin da Hajiya Zanni ta ce maza suna shiga ne ya fara kama Yaya Inu, don haka ta shanye zafin da ta ji ta sake wurƙila idanu da sunan fari tana wani banƙarewa kamar kazar mayu ta ce. "Na jima ina alla-alla kwanakin girkina su dawo, saboda na shayar da kai romon soyayya..." Takaici ya sake lulluɓe Yaya Inu, ya ɗaga hannu ya yi wa Indo mahangurɓa a fuska. Wani irin mummunan yanayi ya ratsa ta, don haka a gigice ta miƙe da niyyar ceton kanta. Yaya Inu ya shatalo ta da ƙafarsa ta faɗa kan miyar kukar da ta zubar. A fusace ya ɗaga hannu ya zabga mata mari cikin fusata ya ce. "Wannan iskancin a gidan uban wa kika koyo shi? Wallahi ko kukar bulukiya ce a kanki sai na sauke miki ita." Indo ta fashe da kuka tana jan jiki gefe ta ce, "Yanzu mai gida duk abin da na yi maka ban birge ka ba, saboda Allah duk wannan kissa da kisisinar..." "Au to, sai yanzu na gano! Wato saken da kika samu na zuwa cikin gari, shi ne kika haɗu da siraran karuwai suka koya miki wannan karuwancin ko? To ba a gidana ba, tun wuri ki watsar da abin da yake kanki idan ba haka ba ki ƙara gaba." Shiru Indo ta yi tana share hawaye. Daga can bakin ƙofa Hansatu da Larai suka ƙaraso suna tambayar abin da ya faru saboda sun ji ihun Indo, Yaya Inu bai tanka musu ba saboda har lokacin haushin Indo yake ji. Ita ma Indo ban da hawaye babu abin da take yi, don haka kowacce ta ƙunshe dariyarta cike da ƙeta suka koma ɗaki. Saboda dama haushin Indo suke ji, a kan shan ƙamshi da kallon wulaƙancin da ta dinga yi musu. A kunyace Indo ta tashi za ta fita Yaya Inu ya ce, "Kuma tun wuri ki gyara mini ɗaki tas, kika ɗebo siraran cinyoyi kamar tsinke ashana. Yo ni akwai wani iya shege da wata figaggiya za ta yi mini?" Takaici ya sake cika Indo, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zare rigar mamanta da ke saƙale a wuyansa. Ta ɗauki zaninta ta ɗaura sannan ta shiga kiciniyar gyaran ɗakin, a cikin ranta ta shiga tsine wa Hajiya Zanni da miyagun shawarwarin da ta ba ta. Washegari Tun kusan kimanin ƙarfe huɗun asuba ya farka yake sharɓa kuka, tun yana yin na zuciya har ya dawo yin na sarari. Sautin sasshekar kukan da Baba Sale yake yi ne ya farkar da Uwale daga baccin da take. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa, da sauri ta zaro ƙaramar wayarta a ƙarƙashin filo ta haske ɓangaren da Ɗan Bishir yake bacc. Ganin yana bacci cikin kwanciyar hankali ya sa, ta dubi Baba Sale ta ce. "Me yake faruwa mai gida?" A maimakon Baba Sale ya ba ta amsa sai ya sake kallon wurin Ɗan Bishir ya fashe da kuka. Jikinta ne ya yi sanyi don rabonta da ganin kukansa, tun wata rashin lafiya da Ɗan Bishir ya yi kusan shekara ɗaya da rabi kenan. "Mai gida don Allah ka cire ni a cikin duhu, wallahi hankalina duk a tashe yake." Uwale ta furta jikinta yana rawa, don ta ayyana abubuwa da dama a cikin ranta. Baba Sale ne ya faɗa jikinta kamar wani sabon maraya, ya ja majina cikin kuka ya ce. "Kamar kin manta yau ne za a yi wa Ɗan Bishir shayi! Yau ne fa wa'adin kwanakin da za a yi masa kaciya ya cika." Baba Sale ya yi maganar yana share ƙwalla, haɗe da shigewa jikin Uwale kamar wani ƙaramin yaro. Ya ɗago murya a dashe saboda kukan da ya ci ya ce. "Uwale hankalina a tashe yake, wallahi duk wani abu da zai taɓa lafiyar Ɗan Bishir ba na son shi..." Kuka ya sake cin ƙarfinsa, takaici ya mamaye Uwale amma gudun kada su fara raba hali tun da asuba ya sa ta ce. "To ya za a yi, ai dama kowa da haka ya fara. Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah na ji har an shiga masallaci." A hankali Baba Sale ya fita yana jan majina, ya ɗauro alwala ya wuce masallaci. A lokacin da ya ƙarasa masallaci a raka'ar ƙarshe ake, bayan an idar ya tashi ya ciko raka'a ɗaya sannan ya yi sallama. Baba Sale hannu ya ɗaga ya fara zazzago addu'a, mutane ba su yi tsammani ba sai ji suka yi ya fashe. Sororo mutanen wurin suka yi, Yaya Ado har zai fita ya koma ya zauna. Duka mutane suka yi carko-carko suna kallonsa, Malam Rabe ne ya yi ƙarfin halin zuwa kusa da shi ya ce. "Sale me yake faruwa ne?" Baba Sale ya sharce majina ya fara wata shassheka kamar wanda uwarsa ta mutu ya ce, "Ina buƙatar addu'arku. Domin kowa ya san ɗana ɗaya ne a duniya wato Ɗan Bishir! Kuma ina fatan ya haifa mini jikoki ashirin da huɗu sai dai kash..." Kuka ya sake cin ƙarfinsa. Gaban su Baba Labaran ya faɗi, don duk wanda ya ci karo da irin kukan da Baba Sale yake yi za ka ɗauka mutuwa aka yi masa. Cikin haɗin baki hankali a tashe duka mutanen cikin masallacin suka ce. "Sai dai me?" Baba Sale ya rungumo hannun Yaya Inu ya shiga goge fuskarsa da shi ya ce. "Ku yi mini fatan a yi a gama wa Ɗan Bishir shayi, an jima Bala wanzan zai zo ya yi masa don ni ba zan iya ba. Ba ni da ƙarfin zuciyar ta guntule Ɗan Bishir." Jin haka ya sa takaici ya mamaye su, a zafafe Yaya Inu ya fisge hannunsa ya ce. "Kai dai ka zama gantalalle ɗan wahala. Yanzu shayin da za a yi wa Ɗan Bishir ne kake wannan iskancin, kai Allah Ya tsine iskanci da magoya bayansa. Shi ya sa ka sakar mana murya kamar an kunna generator kana ihu, Allah wadaran naka ya lalace." Daga haka Yaya Inu ya fice daga masallacin rai a ɓace. Ɗaya bayan ɗaya haka mutane suka watse kowa yana mita, Baba Sale ya koma gida ya sake saka Ɗan Bishir a gaba yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki. Tun da Ɗan Bishir ya tashi daga bacci Baba Sale ya ɗauke shi ya rungume, hatta abinci a baki ya dinga ba shi. Kimanin ƙarfe tara na safe Bala wanzan da yaransa suka ƙarasa ƙofar gidan, Uwale ce ta iya ɗaukar Ɗan Bishir ta miƙa masa. Domin Baba Sale uwar ɗaki ya shige ya haɗa kai da ƙarfen gado yana kuka. Saboda shekara ta uku kenan ana cewa za a yi masa shayi yana ɗagawa saboda soyayyar da yake yi masa. Yana nan zaune Inno ta aika kiransa, da ƙyar ya iya fita ya nufi sashenta fuskarsa ta kumbura saboda kukan da ya sharɓa. 'Yan'uwansa ya gani gabaɗaya a zaune, ya yi mamki matuƙa don haka ya zauna a gefe yana kallonsu. Inno ta dube su ɗaya bayan ɗaya, sai kuma ta saki wani murmushi zuciyarta fes ta ce. "Dalilin da ya sa na tara ku a wurin nan ba komai ba ne, illa na sanar da ku wani abin alheri kuma abin farinciki da ya tunkaro mu. Kuma na tabbata za ku ji daɗinsa, domin cigaba ne da zai iya kai ni aljanna da ku bakiɗaya." Fuskarsu ɗauke da fara'a gabaɗaya suka furta. "Ma Shaa Allah, gaskiya wannan abin farinciki ne Inno. Allah Ya sa mu dace." Inno ta sake washe baki fuskarta wasai kamar gonar auduga ta ce. "Amin Ya Rabbi." "Amma Inno wanne abin farinciki ne haka?" Baba Labaran ya tambaya. Inno ta rangwaɗa kai gefe ta ce, "Dama zan sanar da ku mun gama daidaitawa da Malam, don haka ma na ce zan sanar da ku a ɗaura mana aure ranar Juma'a mai zuwa." Sororo gabaɗaya suka suna kallonta cikin mamaki Baba Ibrahim ya ce. "Inno aure fa kika ce?" Inno ta haɗe rai ta ce, "Eh sunnar Annabi!" Ajiyar zuciya Yaya Inu ya yi ya ce, "Yanzu Inno tuntuni ba ki yi aure ba sai yanzu? Saboda Allah tun da ƙarancin shekarunki bayan da Baffa babba ya rasu ba ki yi ba sai yanzu da girma ya cim miki? Gaskiya Inno ki yi tunani." Inno ta yi wa Yaya Inu kallon sheƙeƙe ta ce, "Ka karanta mini aya ko hadisin da Allah Ya haramta wa tsohuwa aure! Yanzu Inusa sunnar Annabi kake ƙoƙarin daƙilewa?" Yaya Inu ya yi shiru don zuciya ta gama zuwar masa wuya. Saboda dama tun farko jininsa bai haɗu da Malam mai Yasin ba. "Yanzu Inno da za ki ce za ki auri mutumin nan mu da ba mu san asali da tushensa ba, babu wanda muka sani na shi fa. Abu ɗaya ne fa ya haɗa mu da shi taimakon da muka yi masa a airport, sanadin kamen da aka yi masa wanda har yau babu wanda muka sani a cikin danginsa. Gaskiya ko za ki aure shi sai mun san wani daga cikin danginsa." Baba Ibrahim ya yi maganar fuska a haɗe. "Wallahi kai ka ma yarda ta aure shi, na rantse da Allah yadda na tsani ƙyamusasshen tsohon can idan ban sheme shi ba Allah Ya tsine mini!" Yaya Inu ya faɗa jikinsa yana karkarwa. Inno ta yi karaf ta ce. "To wallahi ku shaida duk wanda na ji ko kallon banza ya yi wa Malam sai na ɗaga masa mamunana. Kuma dama na faɗa muku ne saboda na fita haƙƙinku na 'ya'ya atoh, don kada ku ji muna kashewa da binnewa ni da shi a ɗaki ku fara yi mana ɗan zargi. Duk da dai dama na faɗa masa auren ɗauko buta za mu yi." Inno ta sake kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta cigaba. "To ku ban da abinku ace yau uwarku ta mutu da aure a kanta ba ya fi daraja a wurinku ba? Allah na tuba duk haƙurin da na yi da ubanku tsawon shekaru bai wadatar ba? Wallahi da shi ne ma ba zai ɗauki shekarun da na ɗauka bai yi aure ba, a toh a yanzu na samu wanda zai ba ni walwala da kulawa gwargwadon farincikina. Da ku ɗaura mini aure da kar ku ɗaura duk ɗaya, saboda yanzu zan tafi wurin Malam Liman ya zama waliyina shi kuma Malam Ladan ya yi wa Malam walicci ashafa mana fatiha." Shiru ta ji sun yi ba tare da sun tanka mata ba, ta kalle su rai a ɓace ta ce duka su fice mata daga ɗaki. Nan take duk suka fice, Baba Ibrahim zai fita ya waigo ya ce. "Idan Allah Ya kai mu zan ɗauki jininki da na Malam ɗin sai na yo muku gwajin da ake yi kafin aure." Haɓa Inno ta riƙe ta ce. "Kai Iro ka fita a idona na rufe, uban me zan yi da wani gwaji ni da zan yi auren ɗauko buta." Baba Ibrahim ya fita don ya lura Inno a fusace take, sai dai ya ci alwashin zai shawo kanta ya yi musu gwajin koda ba za ta haƙura da auren ba. Malam mai Yasin da yake raɓe abayan katanga yana jin duk abin da suke faɗa ya saki murmushi a fili ya ce. "Ashe na kusa ɓarje amarci tun da na tsinci dami a kala. Na ci mai kyau na sha mai kyau, nan gaba kuma na kwashi ganima son raina." Ya ɗaga kansa yana kallon tanƙamemen gidan gandun ya ce. "In Shaa Allahu har wannan gidan sai na mallaka, da ni kuke zancan dan ubanku." Yana jin motsin tafiya ya yi sauri ya faɗa ɗakinsa ya saki labule. Tun da Laraba ta dawo gida ta ci alwashin idan sama da ƙasa ce za ta haɗe ba za ta sake zuwa makaranta ba. Kuma ko da gari ya waye, sai ta yi shirin makaranta kamar wacce za ta je da gaske, amma sai ta nufi cikin gari ta shiga yawace-yawacenta. Ta jima tana tunanin hanyar da za ta ɓullo wa Mai garu da su Malam Sule, a kan cin zarafin da suka yi mata amma har lokacin ba ta samu mafita ba. Sai da ta daidaici lokacin tashi ya yi sannan ta kamo hanya ta fallo da gudu, a bisa tsautsayi za ta tsallaka wata hanya shi kuma wani matashi ya shawo kwana da motarsa ya ɗan make ta. Laraba tana ganin haka ta sake bajewa a ƙasa tana numfarfashi, a gigice matashin ya fito daga motar jikinsa sanye da uniform ɗin NYSC. Laraba ta ƙyallere ido a kaikaice bayan ta hango fitowarsa ta sake runtse ido tana ihu. "Wayyo Allah! Ƙafata da kaina za su ɓalle. Wayyo Allah." Ganin yadda matashin ya gigice ya sa Laraba ta sake narkewa. "I'am very sorry dear!" Ya furta a gigice yana ɗago ƙafar Laraba da ya ga ta dafa ta. Laraba ta yi shiru tana bin zara-zaran dogayen yatsun hannunsa, don dama ba ta fahimci abin da ya ce ba. "Lets go to hospital..." "Wayyooooo jama'a ya karya ni." Furucin Laraba ya sake katse shi. "Ki yi haƙuri please mu je hospital, a ga me ya faru da ke." Kallon da Laraba take wurga masa da dara-daran idanunta ya sa tsoro ya kama shi, a ransa yake raya ko dai aljana ya bige? Yana nan tsugunne ya ji ta bushe da dariya. Ta sake zaro masa ido ta ce. "Kai an gaya maka gadon gidanmu suna zuwa asibiti? Mu za ka nuna wa boko?" Cikin Mahmud ya kaɗa, gabansa yana faɗuwa ya ce. "Ku yi haƙuri me kuke so." Laraba ba ta tanka masa ba, ta nuna masa wata katuwar bishiyar kuka da ke gefe. Ganin haka ya sa shi zaro ido, sai kuma ta nuna masa hanyar fadar Mai gari. Shiru ya yi don bai gane abin da take nufi ba, ta ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa ta ga bai yi kama da ɗan garinsu ko maƙotan garinsu ba ta ce. "Mu gadon gidanmu ba a iya biyansu da kuɗi ko kadara, idan har aka cutar da su. Sai dai a tambaye su abin da suke muradi a yi musu." Bakinsa yana rawa ya ce. "Don Allah faɗi abin da kike so ko mene ne zan yi miki." Laraba ta ja ƙafa da rarrafe ta ce, "Matso kaji don kada aljani Karbu ya ji ka." Yadda Mahmud ya matso da sauri kamar zai faɗo kanta ya sa dariya ta kusa ƙwace mata. Ta maze a ta fara yi masa raɗa a kunne, da sauri ya zaro mata ido. Laraba ta gyaɗa masa kai sannan ta ce. "Wallahi idan ba ka aikata son raina ba sai na saka aljani batoyi ya babbake ka, kuma na sa ya bi har gidan iyayenka ya ƙone su ƙurmus. Sannan ya haɗa maka baƙin sharri a garin nan, gara tun wuri ka tafi zan biyo ka ta cikin iska duk abin da za ka yi ina ganinka. Idan ka faɗa ba daidai ba na hukunta ka ba." Kamar Mahmud zai yi kuka ya nufi hanyar fadar Mai gari da Laraba ta kwatanta masa, su Mai gari tun daga nesa suka fara hango shi don haka suka zuba masa idanu suna kallo. Mahmud yana zuwa ya taka har tsakiyar shimfiɗar Mai gari ya fara bin su da kallo kamar yadda Laraba ta tsara masa, yana yi yana waige don kar ya yi ba daidai ba ta sa a ƙone shi. Gabaɗaya a tsorace suke don sun yi tsammanin soja ne, Sanƙira ne ya yi ƙarfin hali ya ce. "Samari daga ina haka? Wa ya ba ku izinin taka shimfiɗar ranka shi daɗe..." Sanƙira bai gama magana ba, Mahmud ya ɗauke fuskarsa da mari. Saboda tsoro har ji ya yi marin yana yi masa yaji-yaji a fuska. Lokaci ɗaya suka shiga taitayinsu, cikin Mai gari ya shiga kaɗawa gumi yana keto masa. Malam Bukar ya yunƙura zai tashi ya tafi, Mahmud ya buga masa tsawa. "Ni da kuka ganni ba mutum ba ne, na zo muku da wannan surar ne domin ku bil'adama ne. Idan na kwashe ku na tafi da ku a can ne za ku yaba wa aya zaƙinta. An turo ni ne daga hukumar kare haƙƙin aljanu, domin na zo na bi diddigin cin zarafin da aka yi wa 'yar cikinmu wato aljanun da ke jikin Laraba." Mahmud yana gama faɗar haka mutane wurin suka shiga rige-rigen gudu, Mai gari tsalle ya yi ya haye bayan Sanƙira kamar wani ɗan biri. Saboda tashin hankali Sanƙira bai yi wata-wata ba ya damfara Mai gari a ƙasa, ya naɗe babar rigarsa ya take ƙafarsa ya bar wurin a guje. Mai gari yana shirin guduwa, taku ɗaya Mahmud ya yi ya cafko rigarsa. Duk yadda ya so ya ƙwacewa ya kasa, ga shi yawancin mutanen wurin sun gudu sun bar shi. Sai kawai ya taƙarƙare ya fashe da marayan kuka, ta ƙasa kuma gudawa ta ƙwace masa tana zuba. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [11/12/2024, 20:07] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA SHIDA Wani irin ƙyanƙyami ne ya kama Mahmud jin yadda Mai gari yake ta sakin gudawa babu ƙaƙƙautawa, ya ɗan waiga bayansa cike da tsoro don su kansu da ace ba a tsorace suke ba, da sai sun fahimci tsoron da yake kwance a saman fuskar Mahmud. Mai gari hawaye da majina da suka gama wanke masa fuska ya dubi Mahmud ya ce. "Da wanne suna zan kira ka ranka shi daɗe, kuma cikin jinsinku ana iya kiranku da wannan sunan? Ka dubi Allah, ka dubi Muhammadur Rasulillahi ka yi mini rai ka yafe mini." Mahmud ya tsuke fuska ya ce. "Kada ka sake yi mini magiya, domin ni ma umarni na karɓa daga sama, a madadin hukumar kare jinsin aljanu ta ƙasa, sun wakilto ni na zo na tafi da kai da taƙadiran mutanenka zuwa fadar majalisar ɗinkin duniya ta aljanu. Amma tun da sun gudu da kai za mu tafi." Jin haka ya sake ɗaga hankalin mai gari sai kawai ya sake fashewa da kuka, don ba shi da wata mafita da ta wuce haka. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya shiga yi wa Mahmud magiya, Mahmud ya tuna yadda suka yi da Laraba ya dube shi ya ce. "Za mu yi maka afuwa amma da sharaɗi, sharaɗin kuwa za ka ɗebo zabin gidanka guda huɗu ka yanka su a kan waccan bishiyar." Mahmuda ya nuna masa wata bishiyar tunfafiya, Sanƙira da ke laɓe a bayan katanga ya zaro idanu duk da ba da shi ake ba. Mai gari ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya ya ce. "Zabin banza ranka shi daɗe, wallahi ko rago ka ce yanka shi zan yi." Ganin zai yi gaba Mahmud ya ce, "Ba mu gama ba ai, shi wannan jinin da zai sauka a kan bishiyar tunfafiya shi zai goge laifin da ka yi a ofishin shugaban ƙungiyarmu. Saboda ka san haka nan ma aljanu zubar da jini suke yi, gangar jikin kuma ka taho mini da buhu zan kai a kwankwantsa namansu, a madadin naman jikinka da za a yi kwatsa-kwatsa da shi." Mai gari ya shiga gyaɗa kai kamar na ƙadangare. Ya ƙalla wa Sanƙira kira ya ba shi umarnin da ya je gida ya ɗebo zabi guda huɗu. Sanƙira ya yi wuf ya sake ɓuya, don haka aka rasa wanda zai kawo wa Mai gari zabin da zai fanshi kansa sai Sahabi ne ya yi ta maza ya je gidan ya ɗebo. Kamar yadda Mahmud ya ba shi umarni, haka Mai gari ya ƙarasa bakin bishiyar tumfafiyar ya fara yanka zabbin ɗaya bayan ɗaya har ya yanke su duka. Bayan Mahmud ya karɓi zabbin ya cewa Mai gari. "Abu na ƙarshe da zan faɗa maka shi ne, ka kiyaye ɓacin ran Laraba. Wallahi tun wuri ka haɗa mutanen garin nan su nemi yafiyarta." Mahmud ya sake daidaita baƙin gilashin idonsa ya cigaba. "Idan ba haka ba sai mun tsotse romon kanka, kuma daga yau duk abin da kuka ga Laraba ta yi to ba yin kanta ba ne. Duk wanda ya yi gangancin sake taɓa ta zai mutu nan take, ko kuma mu ɗauke shi mu yi ta azabtar da shi." Mahmud ya gama magana ya juya kansa a ƙasa ya cigaba da tafiya, Mai gari yana ganin haka ya fice a guje ya nufi gida ƙafar wandonsa ta yi sharkaf da gudawa. Ga mamakin Mahmud yana zuwa ya tarar Laraba ba ta nan, a tsorace ya ajiye ɗan buhun zabbin ya yi sauri ya faɗa motarsa ya fisge ta da gudu ya bar cikin dajin. Tun da Laraba ta hango shi ya tunkaro ta, take ƙyaƙyata dariya tana da saman bishiyar dalbejiya har Mahmud ya ja motarsa ya yi gaba. Dirowa ta yi ta buɗe buhun tana dariya har da riƙe ciki, sai kuma ta yi shiru tana tunanin yadda za ta yi da zabi har guda huɗu. Mai daban-daban ne ya faɗo mata a rai, wani mai nama da yake can tsallaken ƙauyensu, wanda ya jima da cewa yana sonta. Da sauri ta suri buhun kamar marar gaskiya ta shiga bi ta cikin gonaki ya har ta isa wurinsa. "Larabayyo 'yar Larabatuwa! Yanzu Laraba sai ki dinga guduna, saboda Allah mene ne aibuna?" Mai daban-daban ya furta mata cike da so. Laraba ta maze ta ce, "Mai daban-daban ka san shi so makaho ne, to kwanaki shi ya lulluɓe mini idanu a kan wani mutumi amma yanzu ba ya gabana kai nake so!" Wani irin daɗi ya mamaye shi don haka ya ce. "Kai amma na ji daɗi Laraba, wallahi yau da ƙyar zan iya yin bacci yanzu faɗi duk abin da kike so a wurin nan a yanka miki." Laraba ta yatsina fuska ta ce, "Eh wancan balangun za ta yanko mini ko yanka sha biyar ne, amma kafin nan ga zabin Inno nan ta ce a kawo ka gyara ka gasa mata." Jikin mai daban-daban har karkarwa yake, ya fara yankawa Laraba nama. Ya kalli wani yaronsa ya buga masa tsawa a kan ya karɓi buhun hannun Laraba ya je ya gyara su. Bayan ya miƙa wa Laraba balangun ta ce. "Na gode sosai masoyina mai daban-daban, yanzu waɗannan zabin idan ka gama gasa su ka ajiye da daddare zan zo na karɓa." Mai daban-daban ya amsa mata yana washe baki. Laraba har ta yi gaba ta waiga ta sake jan kunnensa, a kan kada ya aika zabin gidansu za ta dawo ta karɓa da kanta. Mahmud bai yi tafiya mai nisa ba, isa bakin wani babban symbol ɗin sabulun wanka da ke gefen titi. Ya ciro waya ya kira abokinsa Muddasir, wanda suka yi da shi za su haɗu a adaidai wurin da ya kwatanto masa. Bugu biyu wayar ta yi ya ɗauka. Daga can ɓangaren ya ce. "Ga ni nan ina hango ka na kusa ƙarasowa!" Daga haka Muddasir ya katse. Cikin ƙasa da minti ɗaya mai adaidaita sahu ya sauke shi. Sai da Mudassir ya biya shi kuɗinsa ya ƙarasa wurin motar Mahmud ya ce, "Mutumina ashe ka gane kwatancen!" Cike da damuwa Mahmud ya ce, "Allah ka yi mana tsari da ƙauye, yanzu saboda Allah a nan za mu yi service?" Mudassir ya yi murmushi yana zama a sit ɗin gaba ya ce. "Kai kukan daɗi kake yi, da muka samu aka canza mana school zuwa ta garin Gangaren dutse? Da ace an bar mu a garin Rafin gurgu fa? Yanzu ba ga su Haidar can ba suna fama." Mahmud ya saki guntun tsaki ya ce, "Yanzu ina za mu bi mu ƙarasa garin Gangaren dutsen?" Mudassir ya nuna masa hanyar shiga garinsu Laraba, gabansa ne ya faɗi amma sai ya basar don ba ya san ya sanar da Mudassir abin da ya faru da shi ya yi masa dariya. Ganin sun tunkari hanyar garinsu Laraba ya sa Mahmud ya ce, "Wai ina ne garin? Mun kusa zuwa ko da saura. Mudassir ya ce, "Mun kusa zuwa, da ka miƙe za mu bi ta kan doguwar hanyar can har ƙofar gidan mai gari, ka san dole sai mun gabatar da kanmu a wurinsa tun da zama ne ya kawo mu. A hargitse Mahmud ya taka burki cikinsa yana kaɗawa, Mai garin da ya gama sakawa zawo a wando ne za su je wurinsa su gabatar da kanku? "Lafiya Mahmud?" Mahmud da gumi ya gama rufe shi kamar zai yi kuka ya ce. "Wallahi ba lau ba Mudassir." Ya ƙarasa maganar yana yin parking ɗin motar a gefen hanya, sai kawai ya kifa kansa a kan sitiyarin motar. Cike da shauƙi Mai Yasin yake kallon Inno jin amsar da ta ba shi, dangane da sanar da iyalanta a kan maganar aurensu. farinciki fal zuciyarsa ya ce. "Allah mai haɗa jinin mumini da mumini, Allah kaɗai ya san alkairin da yake ɓoye da silar haɗuwarmu a Saudiyya. Haka kawai na ji kin sake kwanta mini Inno, a gaskiya marigayi ya dace da mace." Inno ta saki murmushin jin daɗi kanta a ƙasa, ita dai nutsuwar Malam da daɗaɗan kalamansa waɗand ta rasa a baya suna birge ta. Har a cikin zuciyarta tana jin ina ma tun tana budurwa, Allah Ya aiko mata shi cikin rayuwarta, da babu yadda za a yi ta yi rayuwa da tsohon mijinta da ko kaɗan bai iya soyayya da tarairaiyar mace ba. Mai Yasin ya saci kallonta da gefen ido ya ce. "Innota ko ba kya jin daɗin yabon da nake yi miki? Ko da za ki ji babu daɗi sai dai ki ji, amma Allah Ya sani ƙaunarki ta jima da ɗamfaruwa a cikin zuciyata." Inno ta ɗago ta dube shi ta ce. "Haba Malam, ai duk macen da ta yi dace da kai a matsayi mace ta more a gidan duniya da Lahira." 'An zo wurin, dama nan nake ta jiran mu ƙaraso.' Malam ya raya a cikin ransa, yana murmushi mai ɗauke da manufa a ransa. Ya ƙanƙance murya cikin yaudara da karuwanci ya ce. "Wallahi tun da na wayi gari jikin nan yake son dawo mini Inno, ga bakina salam babu daɗi kamar yawun mage. Nace ko zan samu koda kaza ko naman kasuwa?" Inno ta sauke ajiyar zuciya, tana mamakin yadda Mai Yasin ba ya gajiya da murƙushe cinyoyin kaza, amma da ta tuna a kullum ya ci kazar ya kuma sharɓi romonta ƙara samun lafiya yake sai ta ce. "To Malam ka ga dai yaran nan ɗazu kusan baram-baram muka rabu da su dutse a hannun riga, kuma dama mai ƙoƙarin sayo maka Iro ne. Yanzu dai ban san cikinsu wa zan tunkara ba, tun da kazar jiya ma shi ya taho da ita." Mai Yasin yana gama jin haka sai kawai ya fashe da kuka, ya fara jan magina yana matsar ƙwallah. Sororo Inno ta yi jiki a sanyaye ta ce. "Lafiya malam?" Mai Yasin ya ja majina ya ce, "Kaico rashin haihuwa, kaicona Allah ka cigaba da ba ni dangana. Da 'ya'yan da na haifa ne ai duk tsiya za su kawo mini duk kuwa yadda muka yi da su, yanzu kamar dai garken wannan yaron Inu har sai na tambaye shi idan na yi niyyar ɗiban kaji ko zabi? Amma tun da ban haifa ba dole na yi haƙuri da rayuwa." Shiru Inno ta yi tana nazari don ta san mammaƙo irin na Yaya Inu, amma don ta kawar da damuwar Malam sai ta ce. "Daga yau kada ka sake faɗin yaran nan ba kai ka haife su ba, kai tamkar mahaifinsu ne kuma duk abin da kake muradi, ka yi kanka tsaye ko ka tambaye ni idan kana jin nauyi." Malam ya hau gyaɗa mata kai, Inno ta miƙe tsaye har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce. "Kaji kake so ko zabi?" Malam ya sake narkewa a katifa yana sakin murya a dole shi marar lafiya ya ce, "Idan da so samu ne a samo matasan samarin zakaru masu jini a jika, tun da ai muma a wannan satin ne tariyarmu!" Inno ta saka mayafin ta rufe fuska ta fice tana dariya, tana fita Mai Yasin ya buga tsalle a kan katifa yana rawar oya shake body. Kai tsaye sashen Yaya Inu Inno ta nufa, a lokacin da ta je ba ya nan sai matansa. Cikin girmamawa suka gaishe ta, bayan ta amsa ta ce su buɗe mata garken awaki da shanunsa. Kusan lokaci ɗaya suka kalli juna, Larai ta yi ƙarfin halin faɗin. "Inno amma bai ce za ki zo ɗaukar..." Cikin tsawa Inno ta katse ta. "Dama ban ce miki na faɗa masa ba, Malam ne ya ce mini yana sha'awar matasan samarin zakaru ni kuma na zo zan bincika masa, idan ya zo ki sanar da shi abin da na sanar da ku." Daga haka Inno ta nufi garken ta hankaɗa ƙofar zagayen da ƙafarta. Safare da Dubu 'ya'yan Yaya Inu ne suka taya Inno ɗiban zakarun guda uku ta fice da su, ta yi wa Malam magana da kansa ya fito zuwa bakin rariya ya yanka su. Inno ta ɗora ruwa ta shiga gyaran kaji, sai ga shi babu jimawa ƙamshin farfesun kaji ya cika gidan, ta zuba a babban food flask wanda ta saba zuba wa Malam ta kai masa. Ta ɗebi ɗan madaidaici ta ragewa Laraba a kai, ƙafa da wuya a cikin tukunya. Cikin sauri Yaya Inu yake tafe, hannunsa riƙe da baƙar leda wacce take cike da sababbin magunguna da ya taho da su daga bakin kasuwa. Saurin da yake yi La'asar ta ƙarato, ga shi mai maganin sanyin da ya saya ya sanar da shi ba a wuce ƙarfe huɗu na yamma ba tare da an dafa an sha shi ba, saboda ƙa'idarsa kenan. Shi kuma a ranar yake son yin amfani da shi kuma ba ya fatan lokaci ya ƙure, shawo kwanar da zai yi ne ya ci karo da Hajara tsohuwar matarsa wacce ya ji labarin mijin da take aure ya mutu. Dama tun da ya saki Abu zuciyarsa ta shiga wasu-wasi a kan ya dawo da ita. "Ranki shi daɗe, yau Hajara ce a gari?" Yaya Inu ya faɗa yana washe baki, Hajara ya ɗan yatsina fuska ta ce. "Eh ni ce sai aka yi yaya Inusa?" Yaya Inu ya fara gyara zaman hularsa ta tashi ka fiya naci, ya saka hannu yana gyara wuyan rigarsa yana murmushi ya ce. "Hajarata tun rannan nake ta so na zo mu gaisa, saboda kin san lamarin duniya komai ɗan haƙuri ne. Wallahi na so na zo na yi miki gaisuwa ma amma Allah bai nufa ba, na ce ƙila ma rabona ne ya yi gaba da marigayi." Hajara ta ƙanƙance ido cikin masifa ta ce. "Rabon me? Allah Ya tsare ni da komawa gidanka Inusa, ai ni babbar godiyar da na yi wa Allah da ya sa ban haihu da kai ba. Da zaman yunwa zan ji ko da rashin sutura, kai yanzu ba ka ga yadda na koma ba?" Yaya Inu ya yi shiru yana bin ta da kallo cike da so, don ta yi shar fatarta har ƙyalli take. Dama ya ji labari an ce a gidan tsohon mijinta ta haɓɓaka uwar gida. "Ai yanzu wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa na wuce ajinka wallahi Inusa, su dai waɗancan wahalallun matan naka sai su yi ta zama kafin layin saki ya biyo ta kansu." Tana gama maganar ta yi gaba, ran Yaya Inu ya ɓaci ga rashin samun haɗin kanta da na baƙaƙen maganganun da ta faɗa masa. Ya bi ta da sauri ya ce. "Banza 'yar wahala an faɗa miki ba zan samu wacce ta fi ki ba, ki zuba ki gani nan da kwanaki kaɗan zan ɓarzo wacce ta fi ki komai." Hajara ba ta kula shi ba ta yi gaba, shi ma Yaya Inu ya ƙarasa gida rai a ɓace. Tun daga bakin ƙofa ya fara yin ball da kwanika saboda yadda yake a fusace. Hakan ya sa su Larai suka sake shiga taitayinsu, yadda ya ga sun yi tsuru-tsuru ne ya sa ya fahimci abin da ya faru. "Lafiya kuka yi wani zumu-zumu da idanu kamar an shaƙe zakaru?" Indo da har lokacin haushinsa take ji, saboda abin da ya yi mata dariya ta kusa ƙwace mata amma sai ta danne ta ce. "Zakaru kam ai ba shaƙa kaɗai suka sha ba, karo suka yi da wuƙa yanzu ma sun wuce birnin tumbi." Yaya Inu ya haɗe fuska ya ce, "Abokin wasanki na zama Indo?" Indo ta fara tafiya irinta ta kai kajiyo, sannan ta sanar da shi abin da Inno ta yi. Jikinsa ne ya shiga karkarwa saboda duk duniya babu abin da yake saurin ɗaga hankalinsa irin a taɓa garkensa. Da sauri ya nufi sashen Inno ya same ta a ɗaki ya ce, "Inno na ji wani zance a kan garkena." Jin haka ya sa Mai Yasin da ya ke zaune a ɗakin Inno ya tauna wani ƙashi wanda ya ja hankali Yaya Inu, wani ƙululun baƙinciki ya tokare maƙoshinsa, ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana sauraron Inno. "Ubanku ne yake marmarin matasan samarin zakaru, shi ne na lalubo 'yan matsakaita uku na yanka masa." Yaya Inu ya fara huci ya ce, "Amma Inno ko za ki ɗiba ai sai ki sanar da ni." Mai Yasin ya yi farat ya ce, "Kai Inusa kana neman albarka kuwa? Saboda mahaifiyarka ta ɗebi zakaru uku ka zo za ka yi mana tijara, kai yaro ka shiga hankalinka ka nemi albarkar uwa." Haushi ya sa yaya Inu ya tunkari Malam yana jin kamar ya murɗe masa wuya, da sauri Inno ta sha gabansa ta ce. "Ni ka dake ni Inusa ka ji! Ka dake ji na ce." Shiru Yaya Inu ya yi saboda yadda zuciya ta ciyo shi, sai kawai ya fice daga ɗakin. Malam ya jima yana zuga Inno ai kuwa ta cika ta yi fam, daga haka ya koma ɗakinsa ya zura doguwar riga ya tafi banɗaki zai yi wanka. Yaya Inu yana daga harabar gidansa ya hango shi, ganin Malam ya shiga wanka ya sa shi faɗawa ɗakinsa da sauri ya ɗauko wani ƙullin yajinsa, ya zura wata doguwar dorina a aljihu ya nufi banɗakin da Malam ya shiga. Sai da ya laɓe ya ji malam ya saɓa sabulu a fuska sannan ya banka banɗakin ya watsa masa yaji a fuska, Malam yana shirin yin magana saboda yadda ya ji an banko ƙofar banɗakin ya ji an zuba masa abu a fuska. Da sauri ya buɗe ido zafin sabulu da na yaji ya haɗe masa a ido lokaci ɗaya, cikin zafin zuciya Yaya Inu ya shiga zabga masa dorina ta ko ina. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [14/12/2024, 19:51] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA BAKWAI Tun da mahaifiyarsa ta kawo shi duniya bai taɓa jin azaba irin wacce yake ji ba, a tsammaninsa aljanu ne suke yi masa wannan izayar don haka Malam ya shiga karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa. Ban da kuka babu abin da yake yi, a zuciye Yaya Inu ya ce masa. "Wallahi koda wasa idan ka sake cewa za ka ci kaza ko zakaru a gidan nan, sai na yi maka abin da ya fi haka. Munafikin Allah dama ba ka san haushinka nake ji ba, ubanmu ya kwanta dama sama da shekara ashirin Inno ba ta taɓa marmarin aure ba sai a kanka. In sake jin ka saka ta, ta taɓa awakina wallahi sai na lahira ya fi ka jin daɗi." Daga haka Yaya Inu ya fice daga banɗakin kai tsaye ya wuce ɗakinsa ya sauya kayan jikinsa. Kai tsaye garken awakinsa ya shiga, wani sabon takaici ya mamaye masa zuciya musamman da ya tuna danƙwala-danƙwalan zakarun da Inno ta saka aka yanka. Tun da ya fara magana cikin gargaɗi Malam ya fahimci Yaya Inu ne, sai da ya ji ya fita daga ɓanɗakin ya yi ƙoƙarin buɗe idonsa ya ji wata azaba ta ratsa shi. Ruwa ya laluba ya shiga kwarawa, ai kuwa ya ji kamar yana zuba wa jikinsa ruwan zafi saboda raɗaɗin da yake ratsa shi. Malam bai wata-wara ba ya fito a guje yana ihu da neman taimako haɗe da faɗin. "Jama'a taimako, wani marar imanin zai hallaka ni. Jama'a ba kwa ji na ne ku kawo mini ɗauki." Ihun da Malam yake yi ne ya ja hankulan mutane yara da manya, sai dai manyan da sun yi arba da shi suke komawa a guje. Labaran da Rahina ne suka shigo ba tare da sun san abin da ya faru ba, Rahina da Malam suka yi gware tana yin arba da shi ta kurma ihu suka shige sashensu ita da Labaran a guje. Ɓaɓatun da Malam yake yi ne ya sa Inno ta fito a tsorace ta ce. "Malam lafiya kuwa?" Turus Inno ta yi ta zuba hannuwa a ƙirji cikin tashin hankali, shi kuma Malam jin muryar Inno ya sa ya tunkare ta da gudu yana faɗin. "Inno ki taimaka mini idanuwana za su makance, Innota jikina azaba yake yi mini kamar ana babbake ni." Inno ta zuba kabbara ta fita da gudu tana faɗin. "Malam ka yi mini aikin gafara wannan aikin ba nawa ba ne." Malam Ya rufa mata baya har sashenta yana faɗin. "Inno a gidan nan ke kaɗai ce kike ƙaunata, ki taimaka mini ki ce iyalina ta gobe." Inno ta banka ɗaki da yake sashenta shiru yake babu kowa, sai hakan ya sake ɗaga hankalinta ga Malam ya biyo ta a gigice. Ta danna sakatar ɗakin ta ce, "Ka gafarce ni wannan aikin na maza 'yan uwanka ne." Duk bugun da Malam ya yi Inno ba ta buɗe masa ba. Ana cikin haka Baba Ado ya shiga ya same shi, ko kaɗan bai ji daɗi ba domin tun a ƙofar gida aka fara ba shi labari. Towel ya miƙa masa murya a daƙile ya ce. "Ka suturce jikinka." A fusace Malam ya yi warci towel ɗin ya yi wurgi da shi ya ce, "Suturar banza da wofi, kai idan za ka taimaka mini ka ba matsa daga gabana, domin ni kaɗai na san bala'in da nake ciki." Tsaki Yaya Ado ya yi ya ce, "Wallahi idan ba ka ɗaura towel ɗin nan ba, zan tafi na bar ka. Darajar tsufanka na gani shi ya sa na zo taimaka maka, idan ba haka ba wallahi da sai dai ka yi ta zama a haka." Sanin halin nunkufurcin Yaya Ado ya sa da sauri ya fara lalubar towel ɗin ya ɗauka ya ɗaura a ƙugunsa, kamar ƙaramin yaro haka ya zaunar da shi ya shiga wanke masa fuska da ruwa da sabuli. Zafin ciwukan da dorinar ta ji masa ya sa ya dinga ihu kamar yaro ƙarami, a haka har Yaya Ado ya gama wanke masa sai dai har lokacin wani irin raɗaɗi yake ji. Har ɗaki Yaya Ado ya raka shi ya haye katifa yana rawar ɗari, nan take zazzaɓi ya rufe shi. Tun lokacin da Bala wanzan ya gama yi wa Ɗan Bishir kaciya ya shiga kiran layin Baba Sale, sai da ya yi ta maza ya ɗauka a nan yake sanar da shi an gana yi masa kaciyar. Jiki a sanyaye ya fita ƙofar gida, yana yin ido huɗu da Ɗan Bishir ya ji wasu zafafan hawaye sun zubo masa. Da ƙyar ya miƙa hannu ya karɓe shi, har zai shiga gida abokinsa Sani wanzan ya zo wucewa. Ya kalli Baba Saleh sai kawai ya tuntsire da wata irin dariya, wacce shi kaɗai ya san manufar yin ta. Haka kawai gaban Baba Sale ya faɗi, amma sai kawai maze ya wurga masa harara ya shige gida. Ɗan Bushir ban da yage baki yana kuka babu abin da yake yi. Yana zuwa ya kwantar da shi a kan gado, ya sa gefen rigarsa ya share hawayen ya ce. "Ɗan Bishiririna! Ɗan Bishiri ka yi haƙuri ban kyauta maka ba ko? Yanzu me kake so na sayo maka?" Ɗan Bishir ya kalli gabas da yamma, ya kalli mahaifiyarsa da ke gefe a zaune kalli mahaifinsa. Sai ya sake ɓarke baki ya saki kuka. Ƙirjin Baba Sale ya buga da ƙarfi ya jikinsa yana rawa, ya rungume Ɗan Bishir ya dubi Uwale fuska shaɓe-shaɓe ya ce. "Uwale tsoro nake ji, wallahi ina cikin tashin hankali." Uwale ta sauke ajiyar zuciya, saboda ta san za a yi haka ko ma fiye da haka. "Me ya faru mai gida?" Baba Sale ya ja gefen ɗan kwalinta ya share hawaye ya ce. "Ina tsoron ko dai an guntule Ɗan Bishir gabaɗaya, Uwale kada fa Bala wanzan ya nakashe mini ɗan ɗaya-ɗayana..." Kuka ya ci ƙarfinsa. "Yanzu mai gida duk yaran da ka dinga yi wa shayi, iyayensu ba su ce za ka nakasa musu 'ya'ya ba sai da abin ya zo kanka? Kamar ba ka san yadda Bala yake da ƙware a harkar wanzanci ba? Kar ka manta shi fa ɗan gado ne." A hassale Baba Sale ya ce. "Kowa ai nasa ya sani, ni gudan jinina kuma magajina na sani don haka a kansa zan yi magana..." Ita ma Uwale ta katse shi. "To ai ɗa na kowa ne, shi ya sa ɗa da dukiya ba a yi musu mugunta. Kuma hausawa suka ka ƙi naka duniya ta so shi, ka kuma so naka duniya ta ƙi shi. Wallahi wannan zazzafar soyayyar da kake yi wa Ɗan Bishir ba za ta kai ka ba. Don ba zan ɓoye maka ba a cikin gidan kowa haushinsa yake ji, ko kaɗan ba shi da farin jini a wurin yara da manya." Wani irin kallo ya shiga wurga mata, yana jin a ransa yadda ta caɓa wa Ɗan Bishir baƙaƙen maganganu da ace ba a yi masa kaciya ba, babu abin da zai hana bai kora ta gidansu ba. To don dai ya san idan ta tafi babu mai jinyarsa. "Baaabaaaa!" Ɗan Bishir ya furta a shagwaɓe, da sauri Baba Sale ya amsa masa sai ya ce. "Zan ci abincin Rahina, daɗi gare shi. Ni ba zan ci komai ba sai abinci ko shayinta." Zumbur Baba Sale ya miƙe ya ce, "Ai kuwa yanzu zan karɓo maka, zauna Ɗan Bishiririna ga ni nan zuwa." Ya ƙarasa maganar yana zuwa bakin ƙofa, ya waigo yana jifan Uwale da harara ya ce. "Shi Ɗan Bishir dai ya zama kabewar kan kabari baƙincikin mai taushe, duk wani mahassadi sai dai ya gan shi ya ƙyale." Daga haka ya fice daga ɗakin. Kai tsaye sashen Labaran ya wuce, daga bakin ƙofa ya tsaya yana sallama. A lokacin Rahina ta tsakar gida a zaune tana shan iska, Labaran yana wanka a ta bayan kitchen ɗinsu don ya ce kafin ya samu kuɗin da zai rufa musu banɗakin sashensu, a nan za su dinga wanka saboda abin da ya faru da Rahina. "Wa alaikassalam." Rahina ta amsa sallamar tana yunƙurin miƙewa domin ta saka hijabinta, daga can gefe ta ji Labaran ya ce. "Kada ki sake ki ƙara magana." Shiru ta yi saboda ta san zafin kishinsa, shi kuma Baba Sale jin an amsa ya saki murya ya ce. "Amarya mai daɗin tuwo da miya, angon na ki yana ciki?" Wannan yabon da Labaran ya ji ana yi wa Rahina ya sake ɓata ransa, don haka ya zura gajeren wandonsa ko kunfar jinsa bai wanke ba ya fita fururu ƙofar gida. "Lafiya Labaran me yake faruwa?" Baba Sale ya furta fuska ɗauke da mamaki. Labaran ya yarfe kumfar fuskarsa ya ce, "Ita ta kawo haka! Ka san dai abin da ka aikata haramci ne ko? Ka zo ƙofar gida ka zage muryarka kana magana iyalina tana sauraronka, ba ka tsammanin ta ji muryarka ta yi mata daɗi?" Ran Baba Sale ne ya ɓaci, amma da ya tuna Ɗan Bishir ya zo nemarwa abinci sai ya wayance. "Labaran kenan, yanzu dai duk ba wannan ba. Wallahi Ɗan Bishir ne yake son cin abincin Rahina, saboda zaƙin girkinta kasan na daban ne." Tun Baba Sale bai gama magana ba Labaran ya hau huci, rai a ɓace ya ce. "Allah Ya isa, wallahi ba zan yafe maka ba, da wannan yabon. Yanzu saboda Allah abincin Rahina ne wani zindiƙin sankacecen ƙato yake yabawa haka?" Zuciya ta fara ciwo Baba Sale ya ce, "Kai Labaran kada ka faɗa mini maganar banza da wofi, ban da aska da tasha jinin Ɗan Bishir ka isa na tako wurinka neman abinci ne? Ka faɗa mini ko nawa ne zan biya ka, ka sayar mini abincin nata." Labaran ya buga tsalle kamar mai shirin tashi sama, saboda yadda kishi ya tirniƙe shi ya ce. "Ba askar kaciya ba Allah Ya sa abba-tuwa ce a kansa, wallahi ba zai ci abincin Rahina ba. Yanzu ni kake kallo ka ce na sayar maka da abincin Rahina? Ko kasan sayar maka da abincin nan daidai yake da na sayar maka da wani tsagi na daga baiwar da Allah ya ba ta?" Haush ya sake mamaye Baba Sale sai kawai ya zuciya zai faɗa gidan, da sauri Labaran ya suri wani ƙaton itace. Ganin haka ya sa Baba Sale ya fice, shi kuma ya rufa masa baya yana faɗin. "Jama'a ku tare ga baƙin kwarto mai lasisi nan." Baba Sale yana faɗawa cikin gida ya danno ƙofar ya saka sakata, Labaran ya yi bugun duniya bai buɗe masa ba. Ganin yadda Mahmud ya yi zuru yana nazari ya sa Mudassir ya taɓo shi ya ce. "Wai me yake faruwa ne?" Mahmud ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi Mudassir na haɗu da wani iftila'i a cikin wannan ƙauyen, ina cikin damuwa kuwa matuƙar Mai gari ya gano ni." Mudassir ya bi shi da kallon mamaki don a iya saninsa da Mahmud, wannan ne zuwansa garin na farko, saboda har yana kan hanya shi ya dinga yi masa kwatance. A tsorace Mahmud ya kwashe duk abin da ya faru tsakaninsa da Laraba ya ba shi labari, tun bai rufe baki ba Mudassir ya dinga sheƙa masa dariyar ƙeta. Haushi ne ya kama shi, ya dube shi rai a ɓace ya ce. "Ka ma mayar da ni ɗan iska wato ga mahaukaci ko?" Cikin dariya Mudassir ya girgiza masa kai ya ce, "Wallahi a garin wannan tsoron naka watarana sai ka halaka kanka. Yanzu kai Mahmud aljanu ne za su kai ka su baro? An ma kuwa aljanar gaske ce? Ace aljanu su nemi ya yanka musu zabi su tafi da su? Gaskiya akwai ayar tambaya." Jiki a sanyaye Mahmud ya ce. "Wallahi a wannan dajin ba na jin za a samu bil'adama a cikinsa, kai ganin idona na fahimci ba mutum ba ce. Yanzu tun da ka ce dole mu gabatar da kanmu wurin mai gari sai dai ka wakilce mu." "Kai ka san yadda mutanen ƙauye suka ɗauki mai gari kuwa? Ai dole sai mun haɗu mun gabatar da kanmu ya san da zamanmu a garinsa, wallahi yadda ka ci ubansa shi ma haka zai ci na ka idan ya gano ka." Mudassir ya furta yana gimtse dariyarsa. Wata dabara ce ta faɗo wa Mahmud ya saki murmushi a fili ya ce. "Mu je gidan da ka ce za mu sauka, na san yadda zan yi da su." Mudassir ya shiga kwatanta masa hanyar, suka sauya akalar hanyar zuwa wani ɗan madaidaicin gida mai ɗaki biyu wanda babu kowa a cikinsa. Mudassir ne ya ɗauko mukulli ya buɗe musu ƙofar suka shiga da kayansu, a kan wani ɗan ƙanƙanin gas da Mahmud ya taho musu da shi suka ɗora ruwan wanka. Sai da suka yi wanka suka sha ruwan tea da Mudassir ya dafa musu, sannan ya ce su shirya zuwa wurin mai gari. Mahmud shadda ya saka fara ƙal, ya ɗauko hula ya saka. Sai kuma ya saka face mask a fuskarsa idonsa yana sanye da glass. Mudassir kuwa ya saka ƙananan kaya sun yi kyau sosai, duk hanyar da suka bi sai abi su da kallo ana ganin 'yan birni sun shigo garin. Lokacin da suka ƙarasa ƙofar gidan mai gari shiru suka ji shi kamar babu mutane, a ƙofar gidan suka tsaya duk da Mahmud ya rufe fuskarsa amma gabansa faɗuwa yake kada Mai gari ya gano shi. "Salamu alaikum!" Mudassir ya yi sallama yana zura kai soron mai gari. Shiru suka ji ba a amsa ba, da yake ɗakin Mai gari a soro yake yana jin duk abin da suke faɗa. "Na yi mamaki da na ji ba a amsa sallamar ba, ɗazu fa da na zo a kan idona ya shiga gida." Mahmud ya furta a hankali, shi kuma Mai gari jin haka ya sa cikinsa ya sake kaɗawa, don ya yi tunanin hukumar kare haƙƙin aljanun ce ta sake turo wakilanta. Yana daga cikin ɗakinsa gumi ya shiga keto masa, wani ɗan matsakaicin matashi da ya zo wucewa ganin su Mahmud a tsaye ya ce. "Wai Mai gari kuke nema?" Mudassir ya gyaɗa masa kai, don yaron ya yi musu magana da biyu ne saboda ya birge abokansa da ke can labe suna kallonsu. Ko babu komai dai ya san ya yi wa 'yan birni magana. "Idan kuka yi magana bai amsa ba, yana nan cikin ɗakinsa ku ƙwanƙwasa masa." Yaron ya furta yana niyyar wucewa, Mudassir ya ce masa. "Don Allah zo ka shiga ka yi mana sallama da shi, ka ce baƙi ne suka zo akwai muhimmiyar maganar da suke son tattaunawa da shi." Gaban Mai gari ya sake faɗuwa, nan take jikinsa ya shiga karkarwa. Jin furucin saurayin da kuma baƙin da suke ƙofar gidan, ya sa shi sake firgicewa musamman da ya kallo ƙauren ɗakinsa ya karye ba shi da damar rufewa duk abin da zai faru sai dai ya faru da shi. Doguwar rigar shaddar jikinsa ya cire, ya zame dogon wandonsa daga shi sai gajeren wando. Don haka ya wala ƙafafuwa ya saita bakin ƙofa, cikin shirin ko-ta-kwama. Don ya ci alwashin sai dai ya fice a guje amma ba zai zaune hukumar kare haƙƙin aljanun ta sake hukunta shi. Musamman da ya san idan suka ritsa shi a ɗakin babu mai ƙwatarsa sai Allah.. Cikin murna yaron ya shiga soron gidan Mai gari yana sallama, ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin zai yi magana sai ji ya yi Mai gari ya fito a guje ya baje shi a ƙasa. Ya tattakura ya fita da gudu, a daidai lokacin, yaron ya fasa ihu saboda zafin buguwar da ya yi. Su kuma su Mudassir ganin yanayin da Mai gari ya fita a guje su ma sai suka rufa masa baya suna gudu, don a tsammaninsu wani abin ne ya koro shi daga cikin gidan. Saboda yadda Mahmud ya fi tsorata shi ne yake biye da Mai gari, hularsa da glass ɗinsa sai da suka yi kusa tsalle uku sannan suka faɗi a ƙasa. Abin da ya sake ɗaga hankalin mai gari, yadda ya ga duk waigen da ya yi sai ya ga su Mahmud suna biyo shi a baya. Don haka ya tattakura ya ce. "Jama'a ku kawo mini ɗauki, hukumar kare haƙƙin wancan jinsin za su halake ni." A madadin a samu wasu su fahimci maganar Mai gari, sai dai duk majalisar da suka wuce su ma sai su rufa musu baya saboda tun da suke ba su taɓa ganin Mai gari da gajeren wando yana gudu ba. Sai da Inno ta bari jikin Malam ya sarara masa da zafi, sannan ta sake aikawa ɗaya bayan ɗaya ta kira iyalanta. Tun da suka shiga ɗakin suka fahimci ran Inno ya gama ɓaci, Malam kallo ɗaya ya yi wa Yaya Inu ya ji gabansa ya faɗi, don haka ya sauke kansa ƙasa. "Gabaɗaya na tara ku ne domin na yi muku godiya a kan cin mutumcin da kuka yi mini. Ba malam kuka wulaƙanta ba, ni kuka wulaƙanta. Idan har saboda na ce za mu yi aure da Malam ne kuka yi haka mu zuba ni da ku, a yau ba sai gobe ba zan yi wa Malam Liman magana bayan sallar Magriba a ɗaura mana aure." Gabaɗaya shiru suka yi Baba Ibrahim ya ya ce, "Har ga Allah Inno ni ban san abin da ya faru ba, hasali ma ba na gidan a lokacin da abin ya faru." "Dama ni ban ce kai ba ne Iro, jikina yana ba ni Inusa ne saboda na yanka zakarunsa na dafawa malam." Malam da ya tuna gargaɗin Yaya Inu ya yi sauri ya ce, "A'a Inno ba na jin Inu zai aikata mini haka." Inno ta sake ba wa Malam haƙuri, ta kuma ba su umarnin da su ba shi haƙuri tare da biyan kuɗin sadaki dubu hamsin. Babu yadda suka iya haka suka ba shi haƙuri sannan suka fice. Suna fita Inno ta aika aka kira mata Malam Liman, bayan sun gaisa ta kawo kuɗi ta damƙa masa na sadaki. Ta yi masa bayanin duk abin da ya faru, Malam Liman ya yi mata Allah sanya alheri sannan ya tafi. Bayan sallar Magriba kuma aka ɗaura auren Inno da Mai Yasin a kan sadaki naira dubu hamsin. Lokaci ɗaya gari ya ɗauka a kan maganar auren Inno, baƙinciki ya mamaye su Baba Ibrahim. "Magana ta gaskiya hankalina bai kwanta da wannan mutumin ba, na ɗauka maganar auren nan za ta kwana biyu har na yi musu gwajin jini saboda muhimmancinsa. Gaskiya duk kun jagula al'amarin nan." Baba Ibrahim ya furta cike da takaici. "Uwar me gwajin zai yi ne da ka addabe mu da zan can nasara, da tun can da ake yin aure babu gwajin me ya faru da mutanen baya? Ko shi Baffa lokacin da zai auri Inno an yi musu gwajin ne? Kai ni ba wannan ne agabana ba, fargabata kada tsohon nan ya sake gangancin taɓo garkena." Yaya Inu ya faɗa. Baba Ado ya tuntsire da dariyar ƙeta ya ce, "To garkenka kuma ai sai dai kar a kuma, ba ka ji labarin Inno ta sa an fita da matashin ragonka ba? Ɗazu nan fa aka wuce musu da shi wai Ali mai tsire ne ya gasa musu..." Tun bai gama magana ba Yaya Inu ya shaƙo wuyansa jikinsa yana rawa ya ce. "In ji uban wa?" Baba Ado ya zame hannunsa yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya, jikin Yaya Inu ne ya sake sanyi don ya san Ado da miskilanci idan ka ga dariyarsa to wata ƙetar ya samu. Bai iya tankawa 'yan'uwansa ba ya faɗa cikin gidan da sauri, kai tsaye ɗakin Malam ya nufa don a can yake jin muryarsu sama-sama. Kamar wanda aka jefe haka ya faɗa ɗakin, Yaya Inu ya yi turus ganin wani shimfiɗeɗen gasasshen nama a gaban su Inno suna reɗa da wuƙa. Ta ci sabuwar atamfa sai murmushi take, Malam da bai san naman ragon Baba Inu suke ci ba, ya sake yanko wata shimfiɗeɗiyar tsoka cikin gadara ya tura a baki. Yaya Inu da ya rasa mafita sai kawai ya zauna a bakin ƙofar ya fashe da kuka, Sai a lokacin Inno ta lura da shi. Ta washe baki ta ce, "Kai Ɗan Inuna, a duniya me za ka yi wa kuka tun da kana faranta ran iyaye. Wai dama haka ragon nan ya kiwatu, ni fa lokacin da ka ce mini an taya shi dubu hamsin na yi mamaki. Ashe-ashe rabon mu sharɓi ganimarsa a daren tariya ta da babanku ne." 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [17/12/2024, 19:46] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA TAKWAS Duk maganar da Inno take yi babu ɗaya da Baba Inu yake ganewa, saboda wata irin juwa da ya ji tana ɗibansa. Hankali a tashe Mai Yasin ya furzar da naman bakinsa, gabansa yana bugawa ya dubi Inno ya ce. "Inno kina nufin wannan ragon da aka gaso mana muke ci ragon Inusa ne?" Cike da son birgewa Inno ta saki murmushi ta ce, "Ragon Inusa ne, ai sau biyar ana taya shi yana ƙin sayar da shi, mutumin ƙarshe da ya zo ko sati uku ba a yi ba dubu saba'in ya taya shi." Inno ta kalli wurin Yaya Inu da har lokacin kuka yake yi kamar wanda mahaifiyarsa ta mutu, ta kalli Mai Yasin da ya gama firgicewa ta ce. "Na jima ban ci gashin nama da ya yi daɗi kamar wannan ba, ai wallahi Inusa Allah ne kaɗai zai biya shi saboda ko lokacin da na sa aka fita da ragon ba ya gidan..." Kukan da Mai Yasin ya saki ne ya katse furucin da Inno take yi, hankali a tashe ta dube shi haɗe da faɗin. "Malam lafiya kuwa?" Mai Yasin ya girgiza mata kai cikin kuka ya ce, "Babu komai Inno, kawai ina taya Inusa jimamin rashin ragon da ya yi. Gaskiya Inno ba ki kyauta masa ba, me ya sa ba ki nemi jin ta bakinsa ba kafin a yanka." Mai Yasin yana gama faɗar haka ya sake ɓarkewa da kuka. Sororo Inno ta yi jin abin da ya faɗa, saboda yadda ta san shi da son nama ba ta taɓa tsammanin zai faɗi haka ba. "Malam ai saboda wancan karon na ga ya ji haushin zakarun da aka yanka masa shi ya sa na ɗauki rago, yanzu da a zo duk bayan kwana biyu muna yanka zakaru ba gara mu yi mai gabaɗaya ba." Mai Yasin yana haɗa ido da Yaya Inu ya ga ya yi masa wani mugun kallo, mai ɗauke da manufar za mu haɗu da kai, sai kawai ya cusa kansa cikin cinyoyi kamar ƙaramin yaro ya sake ɓarkewa da kuka. Shiru Inno ta yi ta rasa bakin magana, kukan Yaya Inu da na Mai Yasin ya cika ɗakin. Jiki a sanyaye Yaya Inu ya miƙe yana dafa bango, don ji ya yi wata hajijiya tana yunƙurin taɗe masa ƙafarsa. A daddafe ya fice daga sashen su Inno ya wuce sashensa, su Baba Ibrahim suna wurin da ya bar su amma saboda halin da ya shiga ya sa har ya wuce bai tanka musu ba. Zazzafan zazzaɓi ne ya rufe shi don haka ya shige ɗakinsa ya ja bargo ya rufa, domin kusan a ƙasa da shekara goma sha biyar wannan ce asara mafi muni da ya tafka. Bayan Yaya Inu ya wuce sashensa, Baba Ibrahim ne ya shiga sashen Inno ya yi sallama daga tsakar gida, Inno ce kawai ta amsa masa ya yi gyaran murya sannan ya ce. "Inno dama wata 'yar magana gare ni idan babu damuwa." Daga can ɓangaren Inno ta ce, "Na taso ko za ka shigo ciki?" Baba Ibrahim ya ji daɗi yadda ya ji muryar Inno wasai, don haka yake fatan Allah Ya sa ta ba shi haɗin kai a game da buƙatar da zai je musu da ita. Ya matsa bakin ƙofar sannan ya ce. "A'a zan shigo ma, da yake maganar da ku duka za mu tattauna." Sai da Inno ta amsa masa sannan ya shiga cikin ɗakin ya zauna daga gefe, ganin har lokacin Mai Yasin bai daina kuka ba ya sa mamaki ya kama Baba Ibrahim don haka ya ce. "Inno lafiya? Me ya samu Malam?" Inno ta ɗan canza fuska ta ce. "Wai fa don ya ji na ce ragon Inusa na saka aka gasa mana, shi ne yake taya shi kukan jimami!" Baba Ibrahim ya yi ƙuri yana kallon Malam, saboda haka kawai ya ji bai yarda da hujjar yin kukansa ba. "Inno magana ta gaskiya ba a kyauta wa Yaya Inu ba, ina laifin ma ki sa a ɗebi kaji amma a ce rago guda ai kuma ya yi muku yawa." Baba Ibrahim ya furta, don ya san fiye da jinya ma ɗan'uwan nasa yana iya yi saboda soyayyarsa da abin duniya. "Mu ajiye wannan zancen a gefe Iro, yanzu me yake tafe da kai." Baba Ibrahim ya yi jim sannan ya ce. "AlhamduLillah! Haƙiƙa ina godiya ga Allah (S W.A) da Ya sa haɗuwarmu da kai Malam da zamo mana alheri. Tun da aka ce harka ta auratayya ta shiga tsakani, to kuwa ta wuce komai. Amma wani hanzari gare ni ba gudu ba Inno da kuma Malam!" Baba Ibrahim ya ɗago ya ɗan dube su sannan ya cigaba da cewa. "Dama maganar gwajin jinin da na yi rannan ita ce na zo zan sake maimaitawa. Don Allah ina son ka fahimce ni Malam, ba ina son a yi wannan gwajin don wata manufa ta ko saboda ba mu yarda da kai ba ne. A'a ina son a yi muku wannan gwajin ne saboda a tantance lafiyarka da ita Inno, saboda kada a cutar da ɗaya daga cikinku ko kuma gudun samun wata matsalar da ba ma fata a nan gaba." Tun da Baba Ibrahim ya fara magana Mai Yasin ya haɗe rai, Inno ta dube shi sheƙeƙe ta ce. "Kai Iro fita daga idona na rufe, yadda yahudanci ya ratsa ka so kake ni ma ka ribace ni ko? Wallahi tun ranar da na ji kana yi wa Inusa faɗa, a kan yawan haihuwa na fara zargin ka karɓo kwangilar yahudawa. Kai Iro ka ji tsoron Allah, yanzu lokacin da na auri ubanka akwai wani tsirfar gwajin jini kafin aure ne? Ni za ka haramtawa sunnar Annabi ina zaune ƙalau?" Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa, don dama ya san za a rina an saci zanin mahaukaciya. Shi kuwa Malam zuciyarsa fes, duk da ya san lafiyarsa ƙalau amma shi kansa bai yarda da sabuwar al'adar da ta shigo ta gwajin jini kafin aure ba. "Wallahi Inno ba ni da wata alaƙa da Yahudawa kamar yadda kuke zargi, shi wannan gwajin jinin yana bayyana rukunin jinin da kika ɗauke da shi. Gwari-gwari bari na yi miki bayani, nau'in rukunin lafiyar jini na gado shi ake kira da Genotype. To kamar yadda muka sani Inno kowanne ɗan'adanm da Allah Ya hallita, yana tare da wasu ƙwayoyin halitta da suke gudana a jikinsa, kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake yi. Misali idan iyaye suna da nau'in jini mai kyau sai su haifi yara lafiyayyu, idan kuma aka samu akasin haka sai a haifi yara masu ɗauke da matsalar amosanin jini wacce aka fi sani da sikila. Bayan wannan gwajin akwai kuma wanda yake bayyana cututtuka da dama kamar: Ciwon hanta, hawan jini, cutar damuwa (Depression) sai uwa-uba cutar ƙanjamau (HIV/AIDS) da ragowar cututtukan da ban lissafa ba. A gwaje-gwajen da ake yi kafin aure akwai cutukan da idan aka same su, ake haƙura da auren. Akwai kuma wanda ake yin auren sai a bayar da shawarwari." Baba Ibrahim ya faɗa cikin tattausan lafazi. "Innalillahi wa 'inna'ilahi raji'un! Yanzu Iro ni ko Malam a cikinmu wa kake yi wa fatan ƙanjamu? Mu za ka mayar 'yan iska, masu yawon kwararo? Idan na ce kana ƙoƙarin raba sunnar Annabi ka ce ba haka ba. Yanzu tun da ubanku ya rasu akwai ƙaton da ya sake taɓa mini hannu? Ta shi ka fice mini tun raina bai ɓaci ba." Inno ta faɗa a zafafe tana nuna masa hanyar fita. "Don Allah Inno ki fahimce ni, ba ina nufin zarginku nake yi ba. Ita cuta mai karya garkuwar jiki, ai ba sai an sadu tsakanin mace da namiji ake samunta ba, ana iya ɗaukarta ta hanyoyi da dama kamar amfani da reza ɗaya, burushin wanke baki, kibiya wacce mata suke kitso, kilifa ta masu aski, askar wanzamai, wuƙa, abin yankan farce, allura ta asibiti da allurar ɗinki. Duk ana iya ɗauka da su matuƙar dai jinin mai ɗauke ita zai taɓa abubuwan da na lissafa, wanda ba shi da ita idan ya yi amfani da su to tabbas zai iya kamuwa shi ma. Inno hanyoyin suna da dama fa, kuma gwajin jini na genotype yana bayyana rukunin jinin da ya dace su haɗu wurin aure da waɗanda ba su dace ba. Kin ga mai rukunin jinin AS ba zai yiwu ya auri mai irin nasa na AS ba, haka zalika mai jinin SS ba zai auri mai SS ko mai AS ba saboda gudun kada su haifi yaran da za su zo da lalurar sikila, su yaran su wahala haka su ma iyayen su wahala wurin ɗawainiya." Kallon da Inna take jifansa da shi ya sa ya tsahirta sannan ya ce, "Inno na ga kamar ba ki gama fahimtar bayanina ba. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, kuma daga gwajin ake samun genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda uku kamar haka: AA, AS da SS. AA sune masu cikakkiyar ƙwayar halitta, AS kuma su ake cewa carrier, akwai ɗan rauni a cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukun sune SS masu ɗauke da amosanin jini wato sikila. Saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar ya kai maƙura. Shi ya sa muke yawan jan hankulan mutane, da su tabbatar da sun yi gwaji jini tun kafin soyayya ta yi ƙarfi. Muke kuma hankaltar da muhimman abubauwan da ya kamata a lura kafin aure, idan an duba genotype din sune kamar haka: Rukunin farko yana nufin mijin, ba biyun kuma yana nufin matar, sakamakon kuwa irin yayan da za a samu ne. 1. AA +AA = AA, AA, AA, AA (Za a samar da 'ya'ya masu cikakkiyar lafiya.) 2. AA + AS = AA, AS, AA, AS, (Shi ma aure ne mai kyau, kuma babu matsala a lafiyar 'ya'yan da za a haifa, amma bai kai na saman ba.) 3. AA + SS = AS, AS, AS, AS, (Shi ma wannan auren ana iya yin sa, duk da akwai 'yar matsala kaɗan a kan 'ya'yan da za a haifa. Za su zama AS ne duka, ma'ana carriers) 4. AS + AS = AA, AS, AS, SS, (Akwai matsala, domin za a samu ɗa ko 'ya mai cutar sikila) 5. AS + SS = AS, SS, SS, SS (Akwai matsala sosai domin kusan kaso tamanin 80% na 'ya'ya za su zama masu cutar sikila) 6. SS + SS = SS, SS, SS, SS, (Akwai matsala mai muni, domin dukkan 'ya'yan da iyayen sikila ne, za su ƙare cikin tsanani da wahalar rashin lafiya..." A zafafe Mai Yasin ya katse shi, "Kai Iro ka kiyaye ni, kai yanzu mu za ka zaunar kana nusar da mu gaibu? Waye masanin gobe idan ba Ubangiji ba? Yanzu zurfin da ka yi a yahudancin har ya kai ka fara ja da hukuncin Ubangiji, kana yi masa shisshigi a kan halitar bayinsa? Wane ne kai ban da gajiyayye wanda fushin Allah kaɗai zai iya tarwatsawa, wallahi ka dawo cikin hayyacinka, don ba abin mamaki ba ne yanzu Ubangiji ya mayar da kai ragon sallah. Sakarai dube ka a ido kamar mutumin kirki, amma dai kai an yi zindiƙin bayahuɗe." Inno da takaici ya gama cika ta, ta nuna masa hanya rai a ɓace ra ce. "Fice mini daga ɗaki Iro! "Don Allah Inno..." "Na ce ka fita ko!" Ta katse shi a zafafe. "Shashasha, kai ni dai kam ban san ƙaddarar da ta saka na yarje maka ka yi karatun nasara ba tun asali, idan abin da ka faɗa haka ne me ya sa ku duk ban haife ku a nakashe ba?" Inno ta faɗa cike da masifa, babu yadda ya iya haka Baba Ibrahim ya fita jiki a sanyaye don ba haka ya so ba. Ko kaɗan auren Inno da Malam bai ɗaɗa Laraba da ƙasa ba, saboda mutuminta ne tun zuwansa gidan yake faran-faran da ita. A cewarsa 'ya'ya da jikiokin Inno tamkar nasa haka ya ɗauke su, dalili kenan da ya sa ya sake mamaye zuciyar Inno tun bai furta mata kalmar so ba. Laraba ganin Inno ta tafi ɗakin Mai Yasin ya sa ta yi zaraf ta ɗauki hijabinta ta nufi wurin mai daban-daban, a lokacin da ta je ya gama gashe mata zabin sun yi jar suya gwanin birgewa. Laraba ta basar kamar gaske ta ce masa. "Mai daban-daban Inno ta ce na tambaye ka, nawa ne kuɗin aikin naman sai a biya ka." Mai daban-daban ya washe baki cikin jin daɗin ganin Laraba tana sakar masa fuska ya ce. "Haba Laraba, yanzu saboda ni na fi kowa rashin kara sai na karɓi kuɗin Inno don na yi mata aikin zabi, ai a kanki Laraba babu abin da ba zan iya sadaukar miki ba." Laraba ta fakaice shi ta ɗan taɓe fuska sannan ta ce. "Ashe haka kake sona ban sani ba Mai daban-daban?" Mai daban-daban ya miƙa mata ledar da ya zuba zabin a ciki ya ce, "Tun farko dama ai ke ce kika ƙi ba ni haɗin kai Laraba, amma bakina ai ba zai iya furta irin soyayyar da nake yi miki ba." Laraba ta yi masa murmushi sannan ta tafi gida, sai dai fargaba ce fal a ranta tana tunanin me za ta ce wa Inno, idan ta tambaye ta a inda ta samo nama mai yawa haka. Tun da ta doshi kwanar layinsu ta ga wani matashin saurayi yana biye da ita, ita mamaki ma abin ya ba ta don idan aka cire Mai daban-daban babu namijin da ya taɓa cewa yana sonta, saboda duka mutanen garin kallon marar hankali suke yi mata. "Yan mata, don Allah ki tsaya ina da magana da ke." Matashin ya furta yana shan gabanta, Laraba ta ɗan haɗe fuska kamar ba ta fahimci me yake son faɗa mata ba ta ce. "Malam lafiya kuwa?" Sai da ya gyara gaban rigarsa ya saki murmushi sannan ya ce. "Tun ɗazu da kika wuce na ji kin kwanta mini a zuciyata, to na ga bai da ce na tsayar da ke a can ba shi ya sa na biyo ki zan ga gidanku." Laraba ta ɗan maƙale murya ta ce, "To gaskiya ni dai ina da masoya da yawa, amma ka san dai an ce mace allurar cikin ruwa ce. Kuma yanzu aike na aka yi, sai dai idan na kai aiken ka tsaya na fito." A fili ta lura da yadda matashin ya ɗan tsora ta jin ta ce tana da masoya, amma da ya ga ta ba shi dama sai ya sauke ajiyar zuciya. Laraba zuciyarta ƙal, don ita ma so take ta gwada yadda ta ga su Bushira yayyanta da suke uba ɗaya suke yi kafin su yi aure ko ta ji abin da ake ji. A ƙofar gida matashin ya tsaya Laraba tana shiga cikin gida ta zura da gudu ta nufi sashen Inno, har a ranta tana fargabar kada ya gudu kafin ta shiga ta fito. A uwar ɗakin ta ajiye ledar ta sake zurowa da gudu ta koma, sai da ta je soro sannan ta tsaya ta ɗan daidaita nutsuwarta tana mayar da numfashi. "Ɗan samari na dawo!" Laraba ta furta tana wani kanne ido. Martanin murmushi ya mayar mata ya ce, "Barkanki da dawowa sarauniyata, ni dai sunana Habu kuma ba a ƙauyen nan nake ba. Na zo ne daga maƙotan garin nan, ban sani ba ko kin san gidan Malam Lado mai itace?" Laraba ta yi murmushi ta ce. "Wallahi na gane shi, sam-sam ba shi da mutumci. Sau ɗaya na taɓa tsinkar masa mangwaro ya kai ƙarata har gaban mai gari, kawai dai na raga masa ne saboda na ga ƙafa ɗaya gare shi." Habu ya saka hanu ya rufe bakinsa ya ce, "Yayan mahaifina ne fa!" Cikin halin ko'in kula Laraba ta ce, "Ita gaskiya ai dama ɗaci gare ta." Shiru ya yi yana tsoron kada ya sake wata maganar ta ce ta fasa son shi, don ya lura kamar ba ta rufa-rufa. Don haka ya basar ya ce. "Na tambayi sunanki an ce sunanki Laraba, amma Laraba ai ba sunan ainahi ba ne." Laraba ta yi fuskar tausayi ta ce, "Sunana Aminatu, sunan mahaifiyata na ci kasan tana haihuwata ta mutu. Ana kirana da Laraba ne saboda ranar Laraba aka haife ni, ga kuma sunan Innata da na ci." Cike da tausayawa ya yi wa mahaifiyarta addu'a, sannan suka ci gaba da hira duk da mafi yawan hirar da Laraba take yi masa shirme da shirirta ne, amma haka kawai ya ji tana birge shi. Tun da ya shawo kwanar layin hasken fitilar motarsa ta haske su Laraba da ke tsaye a ƙofar gida, suna hira ita da Habu tana ta sheƙa dariya. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cike da ɓacin rai ya ja dogon tsaki har sai da matarsa Nabila da ke gefe ta kalle shi ta ce. "Baby lafiya?" Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Nothing!" Shiru suka yi har suka ƙarasa ƙofar gidan, sai da ya fita ya buɗe gate ya koma cikin motar ya shiga da ita cikin harabar gidan, sannan ya yi hanyar fita a zafafe. Saboda ya lura koda Laraba ta gan shi babu wani tsoro ko shakku a tattare da ita. "Baby ina za ka je kuma?" Nabila ta furta, don ta lura da sauyinsa. "Get inside, i am coming back righ now." Bai jira cewarta ba ya fice. Shiru ta yi tana nazari, haka kawai ta ji ƙirjinta ya buga da wani tunani ya faɗo mata. Cikin sauri ta ce. "No! It can't be happen!" Ta buɗe motar ta ɗauko lapcoat ɗinta da jaka ta rataya sannan ta shige sashensu. "Shiga gida!" Dr Fadil ya furta wa Laraba a tsawace, ta wani kwaɓe fuska ganin zai yarfa ta a gaban saurayi ta ce, "Zance fa nake yi Ya Fadil." Ɗan zaro ido waje ya yi jin abin da Laraba ta faɗa masa babu ko shakku. "Idan na sake magana ranki zai ɓaci." Laraba ta fara hawaye rai a ɓace ta ce, "Wallahi Ya Fadil ka fiye shiga haƙƙina, kai lokacin da kake soyewarka wa ye ya hana..." Marin da ya sauke mata ne ya sa ta katse ragowar kalamanta, gefen bakinta ya fashe ganin irin ƙasƙancin da ya yi mata ya sa ta fashe da kuka tana faɗawa cikin gida da gudu. "Haba Malam wannan wane irin abu ne haka? Mene ne aibu a maganganun da ta yi da za ka mare ta..." A fusace Dr Fadil ya ɗauke Habu da mari, ya nuna shi da yatse cike da masifa ya ce. "Dama ku ne irin 'yan iskan samarin da suke hurewa ƙananan yara kunne ko? Idan na sake ganinka a ƙofar gidan nan, sai na karairayaka na watsar a ƙasa." Daga haka Fadil ya shige gida ya bar Habu riƙe da kunci, ƙwafa ya yi ya ja ƙafafuwansa ya bar ƙofar gidan, a ransa yana jin idan sama da ƙasa za ta haɗe ba zai daina zuwa wurinta ba saboda soyayyarta ta yi masa mummunan kamu. A harabar gidan Laraba ta yi zaman 'yan bori ta fasa ihu, kamar wacce ake ƙwaƙwalewa idanu. Mutane suka shiga fitowa daga ɓangare-ɓangare ciki har da su Inno, takaici ne ya cika Fadil ya yi tsaye ya harɗe hannuwa a ƙirji yana kallonta. "Ke Laraba lafiya kike ihu da daren nan kamar wacce ta taka 'ya'yan shaiɗanu?" Inno ta faɗa a ruɗe. Laraba ta sharce majina da ɗan kwalinta fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce. "Ba Ya Fadil ba ne ya koro ni ina zance da saurayina, haka kawai ya dinga falla mini mari duk ya zubar mini da aji a gabansa." Inno ta yi kicin-kicin ta haɗe rai ta ce. "Kai Boka ka fita idona na rufe, Larabar ce ba ta isa zance ko mene ne nufinka? Ina ce saba'ar watannan ta cika shekara goma sha biyar? Ga Lantan nan sa'arta ce haihuwa biyu za ta yi a ɗakin miji." "Wallahi idan na sake ganin Laraba a ƙofar guda sai na ci mutumcinta, dama duk iskancin da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata Inno. Ni da ita za mu ga mai taurin kai." Dr Fadil ya furta a zafafe yana barin wurin, a daidai lokacin Nabila ta ƙarasa tana jin abin da yake faruwa. Inno tana shirin yin magana suka ji wani sabon kukan daga ƙofar shigowa. Salame 'yar gidan Larai ce ta ƙarasa cikin kuka, kowannesu fuska ɗauke da mamaki suka wurga mata tambaya. "Lafiya Salame?" Sai da ta share hawaye sannan ta ce, "Jamilu ne ya sake ni." Kusan lokaci ɗaya suka ɗauki salati, cikin kumfar baki Yaya Inu ya ce. "Uban me kika yi masa da zai sake ki a daren nan ga tsohon ciki a jikinki." Salame ta ja majina ta ce, "Saboda ya sayo shayi ruwan bunu da awara zai sha, ni kuma na ji sha'awarsu na ɗauki ƙwaya biyu da shayin na sha. Shi ne kawai ya sake ni." Ta ƙarasa maganar cikin kuka, takaici ya mamaye mutanen da suke tsaye. Yaya Inu a ƙufule ya ce. "Shayin banza da wofi da har zai sake ki a kansa, wannan ai rashin hankali ne. Bai ga halin da kike ciki ba ne?" Larai da ke tsaye ta saki murmushin takaici ta ce. "Dama gwano ai ba ya taɓa jin warin jikinsa, yanzu mai gida har kana da bakin magana don an sako maka 'yarka, kuma a kan dalilin da bai taka kara ya karya ba? Ai na sha faɗa maka, wannan auri sakin da kake yi ba zai haifar mana da samun ɗa mai ido ba, domin kai ma uba ne kuma duk abin da ka yi wa 'yar wani sai an yi wa ta ka. Idan ba ka manta ba fa, Raliya a kan ƙosai ka sake ta. Mariya kuma a kan man shanu, ga Abu kuma a kan kai yara almajiranci. Ni ma da kake zaune da ni saboda na zama kujera ce, duk tarkacen yaran da ake tafiya a bar maka ni nake riƙe su. Ka ga yanzu kai ma kana da zaurawa uku kenan a gida, wannan kaɗai ya isa ya zame maka izina..." A fusace ya katse ta. "Larai ni za ki yi wa rashin mutumci a gaban mutane?" Baba Ibrahim ya ce, "A duk maganganun Larai babu cin mutumci, sai zallar gaskiyar da har yau ka gagara gane ta Yaya Inu, ya kamata ka dawo cikin hayyacinka. Aure-auren da kake yi ya yi yawa wallahi, yanzu ko wuƙa aka saka mini ba zan iya lissafa adadin mata nawa ka aura ba. Ka gyara zamantakewarka da iyalinka, sai ka ga Allah Ya daidaita lamuranka. Duk da dama aure da mutuwa yana wurinsa, amma ka sani akwai jarabtar da Allah yake yi wa bawa a kan abin da yake aikatawa." Mai Yasin da ke gefe ya zuba wa Salame da kuka idanu yana lashe baki, saboda fara ce tas kamar Yaya Inu sai dai 'yar ƙibar mahaifiyarta da ta ɗauko. 'Yanzu wannan danƙwaleliyar aka saki, ai kuwa wannan mijin nata an yi sakarai.' Malam ya furta a cikin ransa. "To tsohon munafuki, ai babu kuɗin kowa a cikin auren da nake yi, kuma babu ƙaton da yake ciyar mini da su idan sun dawo gida. Ke shige gida muje." Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana tasa ƙeyar Salame shi ma ya shige ciki, daga haka kowa ya watse. CIKIN DARE Tun da Mai Yasin ya ci karo da Salame ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka kawai ya ji wani abu yana fisgarsa a kanta. Duk da tana yanayin kama da Laraba amma ta fi Labara zama cikakkiyar mace 'yar duma-duma kamar yadda yake muradi, Inno da ke gefensa ta miƙe za ta yi masa sallama ta ce. "To Malam ni zan wuce ɗaki ko akwai abin da kake buƙata a yanzu?" Wani munin Inno ya gani saboda yadda Salame ta mamaye zuciyarsa, haushinta ya kama shi don haka ya ɗan yi tsaki a hankali ya ce. "Babu komai za ki iya tafiya!" Inno ta yi mamakin yanayin furucin da ya yi mata, ganin haka ya sa Mai Yasin ya wayance da cewa. "Raina ne duk a ɓace wallahi, a ce ka saki mace da tsohon ciki wannan ai hauka ne." A fili Inno ta saki ajiyar zuciya cikin jin daɗi, don yadda Mai Yasin yake nuna wa zuri'arta kulawa abin yana burge ta. "Lamarin babu daɗi dai sam malam, ni bari na wuce sai da safe." Mai Yasin ya amsa mata yana alla-alla ta fice, shi kaɗai ya dinga zarya a ɗaki yana tunanin yadda zai ɓullowa halin da yake ciki. Wata dabara ce ta faɗo masa ya saki murmushi mai sauti, kamar wanda aka yi wa dole haka Mai Yasin ya zauna tunkur har ƙarfe biyun dare ta cika. Daga shi sai gajeren wando ya zare sakatar ƙofa ya nufi sashen Yaya Inu, wannan ne zuwansa na farko sashen don haka cikin sanɗa ya kama gajeriyar katangar ya dira. Sakatar ƙofar ya zare ya bar ƙofar a buɗe saboda koda rana ta ƙwace masa ba zai sha wahalar guduwa ba. Da yake da ɗan hasken farin wata, cikin sanɗa ya dinga bin ɗakuna yana leƙe, sai dai idan ya zura kai ba ya iya hango komai ta ciki. A haka har ya nufi ɗakin da Yaya Inu yake kwance ya shiga, domin jikinsa ya ba shi a nan Salame take a kwance. Tun dag bakin ƙofa Mai Yasin ya kwanta ya fara jan jiki a hankali, don kada a ji motsinsa a haka har ya haye kan katifar da Yaya Inu yake kwance. Cikin bacci Yaya Inu ya ji ana shafa masa jiki, da ɗan magagin bacci ya ce. "Hansatu ce!" Jin muryar Yaya Inu ya sa ƙirjin Mai Yasin ya buga da ƙarfi, amma don kar ya yi saurin gano shi sai ya ce. "Ummm." Tsaki Yaya Inu ya yi ya ce, "Ke dai kin cika jabara Hansatu, don masifa na ce miki zazzaɓi ne a jikina amma saboda ƙalata sai kin zo kin tsotse ragowar ruwan jikina." Mai Yasin ya yi shiru ya cigaba da kai hannun yana laluben Yaya Inu, shiru Yaya Inu ya yi yana mamakin yadda Hansatu ta iya irin waɗannan abubuwan don bai taɓa jin haka daga gare ta ba. Don haka sai abin ya birge shi duk da yana jin zazzaɓin jikinsa, ya shiga mayarwa da Mai Yasin martani yana faɗin. "Ke dai Hansatu wannan jarabar Allah Ya yaye miki, duk halin da mutum yake ciki ba za ki..." Maganar Yaya Inu ta maƙale, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi jin ya shafo gashin baki da gemu buzu-buzu, sai kuma ya kai hannu ya shafo kai ya ji wayam babu gashi sai ma wani sulɓi da ya ji kan yana yi kamar bayan sulba. Mai Yasin kusan mutuwar tsaye ya yi, Yaya Inu ya yi kukan kura ya ce. "Ƙundun uba, jama'a kwarto a ɗakina zai haike mini." A yi mini afuwa da rashin update kwana biyu, na shiga rububi amma yanzu na dawo free. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [01/01, 17:08] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA TARA A madadin Mai Yasin ya saki Yaya Inu ya yi ta kansa, sai ma ya sake ƙanƙame shi ta baya ya maƙale murya cikin ƙarfin hali ya ce. "Haba Mai gida me kake son mayar da ni?" Sororo Yaya Inu ya yi jin abin da Mai Yasin ya faɗa, sai ya fara zargin ko dai shi ne bai shafo daidai ba, ko kuma hannuwansa ne suke yi masa gizo. Don haka ya sake lalubo Mai Yasin ya ji ƙasunbarsa ta masa ƙabe-ƙabe, ya shafa gefen cinyarsa ya ji gajeren wando. A zafafe cikin zafin nama, ya kai masa naushi a fuska yana faɗin, "Mai gidan ubanka, ɗan iskan kwarto. Jama'a a kawo ɗauki." Ganin da gaske asirin Mai Yasin yana shirin tonuwa, ya sa shi fita a guje; shi ma Yaya Inu ya rufa masa baya. Sai da suka je tsakar gida Yaya Inu ya fisgo gajeren wandon Mai yasin, saboda babu riga a jikinsa idan ba haka ya yi ba zai iya kama shi har ya cim masa ba. Ganin dumu-dumu ya shiga hannu sai Mai Yasin ya zage iya ƙarfinsa ya barke wandon ya rabe biyu, ya fita a guje saboda tashin hankali a tsammaninsa sashen Inno ya nufa. Ba tare da ya ankara ba, ya haye katangar sashen Labaran ya dira. Cikin ɗakin ya faɗa a guje jikinsa har karkarwa yake yi, yana jin sa a kan katifa ya ja bargo ya rufa gumi yana keto masa. Labaran ne ya fito daga zagayen wurin da suke tsugunno, sai da ya ajiye butar a ƙofar ɗaki sannan ya shiga ya buɗe randa ya sha ruwa, ya ƙarasa gefen gadon Rahinatu. Murmushi ya saki a fili ganin mutum ya gangaro wurin kwanciyarsa, a tsammaninsa Rahinatu ce. Cike da shauƙin soyayya ya furta. "Rahinatuwa kenan! Bari na gyara ki da kaina, don kada na katse miki bacci mai daɗi." Ya ƙarasa maganar cikin tattausan lafazi mai haɗe da soyayya, sannan ya saka hannu ya gyara hannun Mai Yasin da gumi ya gama wanke shi, ya yi mamaki sosai da ya ji hannun kamar ba na Rahina ba saboda ita mace ce mai ƙiba sosai. Da yake ɗakin babu haske sai ya bar abin a ransa ya raɓa ta gefe ya kwanta, sauke hannunsa da zai yi a gefen Rahinatu ya ji ana karkarwa ga gumi ya jiƙe shi. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, a sanyaye ya ce. "Rahinatu lafiya kuwa? Me yake damunki na ji kamar kina rawar ɗari " Daga can gaban Mai Yasin, Rahina ta ɗago tana ɗan yanutsa fuska ta ce, "Baby lafiya kake magana da tsohon daren nan?" Da sauri Labaran ya zaro ido waje, saboda Mai Yasin a tsakiyarsu yake. Labaran shiru ya yi ya sake saɗaɗa hannu ta cikin bargo ya shafo ƙafar Mai Yasin ya ji, don ya tabbatar da ba aljani ne ya jawo masa hari ba. Saboda a fitar da ya yi fitsari a tsammaninsa indai ba aljani ba, babu wanda zai shigo masa ba tare da ya ji ƙarar buɗe ƙofa. Ƙafar Mai yasin ya shafo ya ji 'yan yatsu irin na shi saɓanin kofato da ya yi tsammani, sai ya kai hannu ya shafo kansa. Mai Yasin ya maƙale murya ya ce, "Masoyi kada ka yarda da ita ni ce ainihin matarka." Ware ido Rahinatu ta yi don sai a lokacin ta lura da mutum a kusa da ita, jin furucin Mai Yasin ya sa Labaran ya shafo ƙasunbarsa, ya lalubo ƙirjinsa sai ya ji shi wayam. "Kai la'ananne sai na kashe ka, garsamemen ƙato a gefen Rahinatuna! weeeeeeeeee huuuuuuu." Labaran ya furta a haukace haɗe da yin gurnanin da ya razana Mai Yasin, hakan ya sa ya bankaɗe bargo ya fita da gudu Labaran ya rufa masa baya. Cikin shammata Mai Yasin ya juyo ya yi masa mahangurɓa a fuska, cikin tsananin jin azaba ya zube a wurin. Rahinatu ta fito tana ihu da kururuwa, a haka Mai Yasin ya samu ya cire sakata ya fice. Ya fita kenan Yaya Inu ya sako kai cikin sashen Labaran, ya shiga wuri-wuri hannunsa ɗauke da barandami da kokara. A haukace Labaran ya fisge daga hannun Rahinatu ya cakumi wuyan Yaya Inu yana faɗin, "Wallahi yau ko ni ko kai a gidan nan, tun da ka nemi gwada mini kwartanci." Yana faɗin haka ya kai wa Yaya Inu naushi a baki, jin zafin haka ya sa Yaya Inu ya watsar da kokarar hannunsa ya falla wa Labaran mari, nan take suka shiga kiciniya Rahinatu ban da ihu babu abin da take yi. Kafin wani lokaci tuni iyalan Yaya Inu sun cika sashen Labaran, da ƙyar aka raba su kowannensu yana mayar da numfashi. "Kai Labaran idan ka bari na riƙe ka wallahi sai na sumar da kai, shashasha wanda bai san ciwon kansa ba." Yaya Inu ya yi furucin yana buga tsalle, kamar zai ƙwace daga hannun su Bashar. Labaran ya ji wani takaici ya lulluɓe shi, don gani yake Yaya Inu ya gama cin tuwo a kansa, saboda maganar da yake yi masa kamar an dake shi ne kuma aka hana shi kuka. Ya zabura a hassale ya ce. "Ka dai yi asara Inusa, ka ajiye riɗa-riɗan mata amma kana bibiyar matan wasu, wallahi idan gabaɗaya mutanen garin nan gatanka ne, sai na ɗauki haƙƙin iyalina da ka shiga har cikin turakar sunna kake ƙoƙarin aikata fasadi." Shiru kowa ya yi, cike da mamaki Hansatu ta ce. "Kai Labaran kana nufin bayan sashenmu kai ma an shigo maka? Yanzu fa ihun Mai gida ne ya taso mu." Yaya Inu ya ɗago gajeren wandon Mai Yasin ya ce, "Wannan shi ne abin da na samu daga jikin kwarton, kuma wallahi sai na kai wa Mai gobe da nisa ya saka shi a bala'in da bai taɓa zato ba." Sai a lokacin jikin Labaran ya yi sanyi, kunyar yayansa ta kama shi, suna shirin watsewa suka jiyo ihun Inno a ɓangarenta. Kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka bi sashenta sai dai ƙofar a rufe suka same ta, Yaya Inu ne ya kama katangar ya dire sannan ya buɗe wa ragowar ƙofa. A tsaye suka samu Inno butar hannunta ta tuntsire a bakin ƙofa ruwan cikinta ya zube, Inno tana ganin su Yaya Inu ta riƙe su jiki yana rawa ta ce. "Inusa wani ya shigo gidan nan, don yanzu haka na fita fitsari na ga giftawarsa da gudu. Babban tashin hankalin ma, gamo na yi domin zir ɗinsa haka yake ko bante babu." Ba su saurari jin ta bakin Inno ba suka fita da gudu suna haske-haske, Mai Yasin ya yi tsumu-tsumu a ɗaki yana saka kayansa, ya yi lakur a kan katifa yana mayar da numfashi. Sai da suka yi binciken duniya amma ba su gan shi ba, suna cikin haka Mai Yasin ya fito yana tambayarsu kamar bai san abin da ya faruba. Labaran ne ya yi masa bayani, bayan ya gama Yaya Inu ya ce. "Ai na yi mai wuyar tun da na samu tufafinsa, zan sa Mai gobe da nisa ya yi mini aiki mai zafi a kansa. Dama abin da yake buƙata takalmi ko wani abu da aka samu daga jikin ɓarawo ko kwarto, wallahi daga wannan karon ba zai sake haurewa gidan wani ba." Jin haka ya sa cikin Mai Yasin ya kaɗa, wani zazzafan gumi ya yanko masa. Ya ƙarasa gaban Yaya Inu ya riƙo hannunsa da ke karkarwa ya ce, "A'a Inusa ka bar mini komai a hannuna, ka san dai kamar yadda na faɗa muku zafin aikina ne ya sa ake kira na da Mai Yasin. To ni zan..." Kallon da Yaya Inu ya shiga wurga masa ne ya sa shi katse kalamansa, don yadda ya ga yana kallonsa har sai da ya sa shi tsarguwa. "Ka bar mini komai a hannuna, ni na san irin shige da ficen da nake yi a wurin malamai, don haka zan ji da shi." Jiki a sanyaye kamar zakaran da ya shuri wuƙa, Mai Yasin ya ja jiki gefe. Yaya Inu ya fice yana muzurai, babu jimawa kowa ya watse. Ganin duk irin gudun da Mai gari yake fallawa su Mahmud ba su daina bin sa ba, ya sa shi ɓarkewa da kuka yana gudu yana waigensu. Ba shi ya tsaya ba sai da ya ƙarasa tukubar tsiren Mai daban-daban, yana shiga rumfar a guje ya yi bayan su Haladu da ke zaune a kan benci. Zumbur! Suka miƙe, cikin damuwa Sallau ya ce. "Subhanallah! Ranka shi daɗe lafiya kuwa? Me yake faruwa daga kai sai gajeren wando?" Kafin Mai gari ya bayar da amsa su Mahmud suka ƙarasa cikin runfar, ganinsu ya sa bakin Mai gari ya shiga karkarwa hannu yana rawa ya nuna su ya ce. "Su... ne, wallahi ba... mutane ba ne. Ku taimaka..." Bai ƙarasa maganar ba ya yanke jiki ya faɗi, cikin su Mahmud ya sake kaɗawa don Mudassir tuni ya fara hawaye, ya dubi Mahmud ya ce. "Mahmud ka janyo mana masifa muna zaune ƙalau." Sai ya sake ɓarkewa da kuka, hawayen da Mahmud yake riƙewa ne ya ɓalle haɗe da wanke fuskarsa lokaci ɗaya. Sun juya za su fita da sauri Mai daban-daban ya danƙo wuyan rigarsu yana faɗin. "Billahillazi la'ilaha'illahuwa sai kun tsallaka mai gari, kai babu wanda fa zai bar wurin har sai mai gari ya dawo hayyacinsa." Su Mahmud suka yi tsilli-tsilli ƙirjinsu yana bugawa. "Wallahi a ɗaure su har sai ranka shi daɗe ya dawo hayyacinsa, idan ba haka ba sai sun tsallaka shi, dubi idon munafuka sun yi kama da baƙaƙen mayu. Wai ma ku su waye a garin nan!" Daga ƙarshe Sallau ya wurga musu tambaya. Daga Mahmud har Mudassir aka rasa mai magana, ba su yi aune ba Mai daban-daban ya fiszo wata ƙatuwar igiyar da yake ɗaure damin itace, shi da Haladu suka shiga ɗaure Mahmud da Mudassir. "Wallahi mu baƙi ne kuma ɗalibai, don Allah ku kunce mu. Wallahi ba mu yi gadon maita ba." Madassir ya faɗa murya tana rawa. Babu wanda ya kula shi, sai da suka ɗaure su tsaf sannan suka shiga yayyafa wa Mai gari ruwa. "Wallahi matuƙar ranka shi daɗe ya mutu gabaɗaya sai mun ƙone ku." Mai daban-daban ya furta, ganin sun gama juye ruwan buta guda a kan Mai gari ba tare da ya motsa ba. Mahmud da Mudassir kusan lokaci ɗaya suka kallo wutar tukubar naman Mai daban-daban, kamar haɗin baki sai kawai suka ɓarke da kuka; bayan zuciya ta gama raya musu Mai gari zai iya mutuwa tun da sun ga bai motsa ba. Dukan ƙirjin Mai gari aka fara yi ana shafa masa ruwa a fuska, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya. Ya buɗe idanunsa a hankali yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya. "Su waye ku? Mu ne ko kuma su ɗin ne?" Mai gari ya faɗa yana raba idanu kamar ƙosan sadaka. "Allah Ya taimake ka Mai daban-daban ne, sannu ya jikin naka?" Mai daban-daban ya furta yana tallafo Mai gari. Tashi ya yi zaune ya sake kallonsu, sai a lokacin komai ya shiga dawo masa. "Mai daban-daban ni kaɗai kuka gani, ko kun ga wani jinsin bayan ni?" Mai gari ya tambaya a firgice. "Allah Ya taimake ka kai kaɗai ka fara shigowa, sai kuma waɗancen matasan." Ya faɗa yana nuna masa su Mahmud, da fuskarsu ta kumbure suntum saboda kuka. A zabure Mai gari ya miƙe jikinsa yana rawa, gudun kada ya sake fita da gudu ya sa su Haladu suka dafe kafaɗunsa. A madadin Mai gari ya yi musu bayani sai ya fashe da kuka, yana cusa kansa a cikin jinkinsu. Cikin tashin hankali ya ce. "Wallahi ba mutane ba ne, aljanun Laraba ne daga hukumar kare haƙƙin aljanu ta faɗin duniya." A razane suka dubi su Mahmud, Mai daban-daban ya bugi ƙirjinsa sannan ya zaro wani kwalli a aljihu ya saka a idonsa. Ya kalli su Mahmud na wani lokaci ya ce. "Waɗannan yaran mutane ne, domin babu wani aljani da ya isa ya yi mini kurari. Sa'a kuka ci na ji an ambaci sunan Laraba da tuni na sheƙa kurwarku ƙiyama." Mahmud ya ƙanƙame Muddasir ƙirjinsa yana bugawa. "Kai uban me ya kai ku razana Mai gari." Ya wurga musu tambaya yana zare ido. "Dama wannan ne..." Da sauri Mahmud ya katse Mudassir da yake son tona masa asiri, ya kwashe abin da ya faru tsakaninsu da Mai gari na aiken yaro da suka yi, don a yi musu sallama da shi su gabatar da kansu a wurinsa. Kunyar duniya ta lulluɓe Mai gari musamman da ya gan shi a yashe da gajeren wando, ya dubi Haladu cikin tsare gida da borin kunya ya ce. "Kai Haladu, a suturta mu ba ma son raini. Muna buƙatar babbar rigarku, wane irin iskanci ne za a gan mu a haka; kuma a ƙyale mu tsirara ana ƙare wa surarmu kallo?" Haladu ya gimtse dariyarsa, ganin yadda Mai gari yake cijewa yana haɗe rai, ya ciro babbar rigarsa ya miƙa masa. Mai gari ya dubi Mai daban-daban ya ce. "Ku kuma sai mun buƙaci hula za a ba mu saboda rashin girmama na gaba?" Tun bai gama magana ba, ya ciro hular kansa ya miƙa masa. Bayan ya saka ya dubi Sallau cikin kurari ya ce. "Ba tun yau ba, muka lura kuna da jiji da kai. Idan ba ku kwaɓo takalmanku ba, za mu yanke muku hukuncin noman gonar bayan gidanmu." Da sauri Sallau, ya sunkuya ya ce. "Tuba nake ranka shi daɗe." Daga haka ya miƙa masa takalmansa. Mai gari ya dubi su Mahmud yana baza babbar riga ya ce. "A kunce su yanzu, kuma su same mu a ƙofar fada idan Allah Ya kaimu." Daga haka ya yi gaba, har ya fara tafiya borin kunya ya sa sake juyowa ya ce. "Kai Haladu za a bi bayanmu ana yi mana kirari, ko sai mun tura ku birni gidan yari!" Da sauri Haladu ya koma gefen Mai gari, yana tafe a gefensa yana yi masa kirari. Shi kuma yana tafe cikin ƙasaita kamar ba zai tata ƙasa ba. Mai daban-daban ya kunce su Mahmud, suka fito daga runfar jiki a sanyaye kamar marayun zakaru, suka nufi hanyar gidan da suka sauka. Washegari A hankali yake bubbuga ƙofar sashen Inno, kusan minti ɗaya yana tsaye ba tare da an buɗe ba. Inno ce ta ƙarasa tana faɗin, "Waye haka zai ɓalle mini ƙofa? Saboda Allah mutum bai gina mini ba, da farar safiya ya nemi karya mini ita..." Ba ta ƙarasa maganar ba ta cire sakatar, ganin Fadil a tsaye ya sa Inno ta ɗan ƙanƙance ido ta kalle shi tana faɗin. "Wane ne haka kamar Iro?" Fadil ya saki murmushi don ya fahimci Inno rikici take ji, shi kuma ba zai biye mata ba. "Eh shi ne." Ya ba ta amsa yana gegarewa ta gefe ya wuce ciki. "Kai boka ni fa na gaji da ganinka a sashena, ita waccen figigiyar matar taka ban isa ta zo ta gaishe ni ba kenan? Kullum sai dai ka ɗebo doro ka shigo mini gida." Fadil bai tanka mata har ya shiga ya zauna, kasancewar ranar weekend ce ta sa koda da ya ga Laraba tana bacci bai tanka wa Inno ba. "Ina kwana Inno?" Ya furta mata. "Lafiya ƙalau boka ya mugun halin matarka? Don ni dai ba zan ce ga abin da ta yi mini na laifi ba, amma wallahi yadda take kwaɓe fuska kamar kunu kullum babu fara'a, ya sa nake mata kallon mai mugun hali." Ido ya zuba mata yana kallo, ya saki murmushin gefen baki saboda idan ba ka san halin Inno ba, sai ta ɓa ta maka rai a banza. "Inno wata magana na ji, a gaskiya ba zan lamunci ki yi zaman aure da mutumin da ba a tantance jininsa ba." Tun da ya fara magana take kallonsa a gwasale, sai da ya gama ta ce. "Ubanka Iro ma haka ya gan ni ya ƙyale ni, wallahi bokan turai ka shiga taitayinka tun ban yi maka iyaka da ɓangarena ba." Hannu ya saka a aljihu ya ɗebo wasu kuɗi masu kauri ya miƙa mata. Ino ta karɓa tana zuba kabbara. "Allahu akbar kabiran, wato boka ni fa inda kake burge ni kenan. Akwai ka da kyauta har ka fi uwarka miƙa hannu, dama ba zan saka Iro ba don babu abin da ubanka yake ba ni." Dariya sosai Fadil ya yi, musamman da ya kalli gwangwanayen madarar da ke kan firjinta, ya tuna gorin da Inno ta yi masa ta ce mahaifinsa ne ya kai mata. Yana shirin yin magana ta ce. "Ka ga idon nan, tun jiya yake yi mini rawa. Ni dama na san ko dai kuɗi zan samu ko kuma baƙi zan yi." Haɓa ya riƙe yana kallon Inno ya ce. "Kenan saboda fatar idonki tana rawa sai ki samu kuɗi ko ki yi baƙi? Inno me ya sa har yanzu ba za ki watsar da camfe-camfen nan ba? A kimiyance fa ba haka abin yake ba, babu dalili da zai sa don fatar idonki tana rawa ki samu kuɗi duk camfi ne. Kuma dama duk abin da ka camfa shi, za ka ga yana tabbata kamar yadda tsafi yake gaskiyar mai shi." Inno ta yi kicin-kicin da fuska ta ce, "Kana nufin ƙarya nake kenan? To ba ubanka Iro ba, ko yayan uban Inusa bai isa ya karyata ni ba, ku da komai na ku sai kun sako iyayi da tsurfar ƙaryace-ƙaryacan yahudawa." Fadil ya ɗan girgiza kai ya ce, "Allah da gaske Inno duk camfi ne, a kimiyance fa wasu dalilai ne suke haddasa haka. Har ka ji tsokar jikin mutum, ko wani sashe na jikinsa yana rawa wato (twitching) a kimiyance mu ce nervous ticks. Dehydration, wato bushewar jiki da ƙarancin ruwa a jikin mutum yana haifar da haka. Akwai yawan shan abubuwa masu ɗauke da caffiene , wasu a ɓangare ci ko sha zuwa yawaita shan magunguna hana zugi barkatai, ba tare da shawarar likita ba. Musamman magungunan da za ki ji ana kira da ciwo goma, ko ciwo takwas. Haka idan sinadarin ƙara ƙarfin ƙashi wato vitamin D, da vitamin E na rage dattin jiki zuwa calcium suka yi ƙaranci, duk zai iya janyo wani sashe na jiki ya dinga rawa. Akwai kuma rawar hannu, da za ka ji haka kawai hannunki yana rawa. (Neurological disorder) Ana iya gadon rawar hannu, kamar idan iyaye da kakannin suna yi. Shi ma kuma, akwai wanda wani dalili yake saka haka." Inno ta shiga tafa hannu a tsorace ta ce, "Wallahi ni dai a kaf zuri'ar dangin uwata da ubana babu maye ko mayya. Don haka babu ta inda Iro zai gaji maita, ballantana ya haifo maye sai dai ko a can dangin uwarka. Ni kake cewa ban da bitamin a jikina boka? An ya a makarantar da ka yi karatun likitancin nan, ba su sayar maka da maita ba?" Yadda ya ga Inno ta tsorata ne, ya tabbatar masa da gaske take faɗar maganganun har cikin zuciyarta. Ya saka hannu ya dafe kai ya ce. "Haba Inno don Allah ki fahimce ni, ni fa ba haka nake nufi ba. Ina yi miki bayanin abin da yake kawo motsin wani sashe na jiki ne, kamar yadda kika ce fatar idonki tana rawa." Shiru ta yi tana kallonsa a gwasale, ganin haka ya sa Fadil ya cigaba. "Inno har yawan rashin hutu ko wadataccan bacci yana haifar da haka, haka fargaba ko damuwa duk suna cikin abin da yake janyowa. A ɓangare ɗaya, yawan zuƙar taba da shan giya duk yana daga cikin abubuwan, da za su iya saka wani sashe na jiki ya dinga motsi, kamar ki ji hannu, ido ko tsokar cinya tana motsi. Idan kina son gujewa haka, sai dai ki kiyaye waɗannan abubuwan da na lissafa, yawaita shan ruwa, samun hutu da bacci da yawan cin kayan marmari. Masu zuƙar taba kuma, muna ba su shawarar guje wa zuƙar taba da shan giya, haɗe da takatsantsan wurin shan magunguna masu ɗauke da caffeine. Idan kuma matsalar ta ta'azzara sai mutum ya wuce asibiti, domin ya ga likita." A fusace Inno ta wawauro muhuci ya raɗa wa Fadil ta ce, "Fice ka ba ni wuri, mutumin banza da wofi. Yanzu ni kake zama ka cewa ina shan giya, giya fa boka..." Sai kawai Inno ta ɓarke da kuka, Fadil ya fice yana shafa kafaɗa don dukan ba ƙaramin shigarsa ya yi ba. Tun daga ɗaki su Hansatu, suka fara jin yadda Yaya Inu yake wurgo ƙullin kaya da kwanukansu tsakar gida. Kusan lokaci ɗaya Hansatu da su Indo suka yi carko-carko, a ƙofar ɗakin suna kallonsa. "Mai gida Lafiya wai? Dubu yadda kake jefo mana kaya tsakar gida." Hansatu ta faɗa tana tattarawa kayan wankinta. A daidai lokacin Yaya Inu ya sake wurgo wata tukunya da farantin Indo suka fashe lokaci ɗaya. Ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi, ta kwashe cikin masifa ta ce." Malam mene ne haka muna magana ka yi shiru?" Yaya Inu ya tako yana kallonsu a wulaƙance haɗe da yamutsa fuska kamar ya ga kashi, ya dafa ƙofar ɗakin ya yi bake-bake ya ce. "Gabaɗayanku ku kwashe mini wannan tarkacen haukan, saboda gobe za a ɗaura mini aure. Kuma a yanzu ne na san zan yi aure, zan auri farincikina mai faranta mini rai. Wacce ta san mutumci da ƙimar aure, tun a yanzu ta fara shagwaɓa ni tana lailaya ni. Wallahi idan ta zo duk wacce ta koya mata ƙazanta da mugun hali sai na ci mutumcinta. Saboda a kullum idan na kalli ku fuskokinku kama kuke yi mini da sumammun birirrika." Da sauri Hansatu ta saka hannu ta rufe bakinta saboda mamaki da ɓacin rai. "Mai gida cin zarafin naka har ya kai ka kira mu da birrai?" Hansatu ta faɗa a zafafe. Indo tana shirin yin magana, suka ji muryar Abu ta shigo gidan tana faɗin. "Yawwa Goggo, mun zo a daidai ma ga shi nan yana gida." Ɓata rai Yaya Inu ya yi yana ƙanƙance ido ya ce, "Bayan na warware igiyar aurena da ke, uwar me ya kawo ki gidana da farar safiya Abu?" Abu ba ta tanka masa ba, tana zuwa ta ɗaga hijabi ta miƙa masa jaririya. Ba Yaya Inu ba, hatta su Indo zaro ido waje suka yi suna kallon yanayin kalar jaririyar. "Ke mene ne wannan? Kuma waye uban wannan abin?" Yaya Inu ya furta yana janye jiki cike da ƙyanƙyami. "Kai ne ubanta, kuma a haka ta zo duniya." Ganin kamar Yaya Inu ba zai karɓa ba, ya sa ta dire masa jaririyar a ƙasa. Kwana biyu na yi nisan zango, bayan na ɗanyi rashin lafiya sai kuma muka shiga biki. Na gode sosai da kulawarku, Allah Ya bar zumunci. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [01/01, 19:10] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA GOMA A zabure Yaya Inu, ya buga tsalle ya dira a gaban Abu da Goggonta da suke shirin fita. Goggo ta haɗe rai ta ce, "Kai Inusa, ka ba mu hanya mu wuce. Ciki ne dai Allah Ya raba ta da shi lafiya, don haka muka kawo maka abarka." Yaya Inu saka hannuwa biyu, ya yi bake-bake a bakin ƙofar ya ce, "Ku je ina? Don Allah Goggo kada ki shiga gonata, saboda akwai ragowar mutumcinki a idona." Ya waiga wurin Abu ya ce. "Wallahi tun muna mu biyu, ki gaggauta ɗauke wancen abin daga cikin gidan nan!" Abu tana shirin magana Indo ta saki shewa har da guɗa tana buga cinya. "Ahayye! Allah na gode maka, ai dama Allah ba azzalumin bawa ba ne sai bawan da ya zalinci kansa. Yau ga shi muna ji muna gani, satar kwana da karya dokar Ubangiji ta bayyana a fili mun gani." Indo ta ƙarasa maganar tana sakin dariyar izgilanci. Hansatu ma dariyar take yi ta isa gaban Yaya Inu tana kallonsa a watse ta ce, "Yanzu don Allah mai gida ba ka ji kunyar abin da kuka haifo ba? Ke yanzu Abu ba ki ji kunyar iyayenki da sauran danginku ba? Tirƙashi! Yau ake yin ta a gidan nan, abin da muke hange a nesa ya zo kusa da mu. Yanzu mai gida jarabar taka har ta kai ka dinga kusantar Abu tana jinin al'ada?" Yaya Inu da ya gama zuwa wuya a zafafe ya ce, "A gidan uwar wa kika ga na kusance ta tana jini? Ko kin ɗauka ban san hukuncin addini ba." Su Indo suka kwashe da dariya kusan lokaci ɗaya, Hansatu ta kalli wurin da jaririyar take kwance tana mutsu-mutsu ta ce. "Ga shaida can mun gani, ko ba zabiya ta haifa maka ba. Ai an yi walƙiya mun ganku, duk munafuncin da kuke yi ashe Allah zai tona muku asiri ba ku sani ba. Ba ni kaɗai ba, kowa ya san sai an kusanci mace tana jinin al'ada ake haihuwar zabiya." Abin duniya goma da ashirin ya haɗe wa Yaya Inu, ya haɗiyi yawu mai ɗaci kamar zai yi kuka ya ce. "Billahillazi la'ilaha'ilahuwa ban taɓa aikata wannan ɗanyan aikin ba. Ni fa shi ya sa nake tantama, magana ta Allah a ce duk dangina babu zabiya sai yanzu zan haife ta. Wallahi tun ban kai ku wurin hukuma ba, Abu ki ɗauke yarinyar nan ki kai ta wurin ubanta. Da ma ni da ke babu kare bin damo." Hankalin Abu ya tashi, saboda babu abin da yake ɗaga mata hankali irin ta yi ido biyu da ɗansanda. Duk da tana da gaskiya, amma haka gumi ya shiga karyo mata, ta ƙarasa ta ɗauki jaririyar cikin ƙarfin hali da barazana ta ce. "Au haka ka ce ko? To kafin ka kai mu wurin hukuma, ni da kai na zan fara kai ƙararka. Ka san dai ko lokacin 'yan matancin na kai ne mutumin da nake kulawa. Don haka babu wani uban yarinyar nan, idan ba kai ba. Ai na sha faɗa maka ka daina satar kwana kana kirana turakarka amma sai ka ce ba haka ba. Ka dinga koɗa ni kana ce mini matar so, ni kuma ina jin daɗi domin na ɓa ta ran su Indo nake biye maka. Sai yanzu za ka ce ba ka san zancen ba, za ka yi bayani a gaban ƙuliya." Tana gama faɗar haka ta yi waje fuu! A fusace. Hansatu ta gyaran ɗaurin ɗan kwalinta, irin ɗaurin ture ka ga tsiya ta ce. "Kai yau Allah na gode maka da ka nuna mini wannan rana. Ayyiriri! Shagali wan dina. Ai gara da ta tafi da 'yarta don wallahi ba zan riƙe gayyar tsinuwa ba, yarinya an same ta a tsine ta rayu a ciki cikin tsinuwa sannan a ce za a dire mana ita. Haka kawai muna zaune a kawo mana annoba cikin zuri'a ta kwashe mana albarkatun cikin gida." Daga haka ta wuce cikin ɗakinta, su Indo ma haka. Yaya Inu jiki a sanyaye ya nufi ɗakinsa yana nazarin baƙin cikin da Zainab ta dasa masa. A ɓangare ɗaya yana fargabar abin da zai je ya dawo, saboda shi dai ya san bai taɓa kusantar mace tana jini ba, satar kwana dai kam ya san yana yi babu adadi musamman idan mace ta ɓata masa rai. Don ya rama abin da ta yu masa sai ya kira wata macen da ba girkinta ba, musamman Abu ta kwana a ɗakin. Babban tashin hankalinsa, ya yi mata barazana da hukuma kamar yanda ya san tana tsoron 'yansanda amma ya lura ko a jikinta. Zaune yake ya yi shiru yana kallon Ɗan Bishir da jijiyoyin jikinsa suka gama yin laushi, ya ja riga ya share hawayensa. Yana jin ina ma yana da ikon dawo da ciwon shalelensa kansa, da tuni ya dawo da shi. "Mai gida zaman nan naka fa ba zai kai mu ba, a ce yanzu tun da aka yi wa yaron nan shayi ba za ka fita kasuwa ba. Ita zara fa ba ta barin dami, don Allah ka tashi ga magungunanka can na haɗa maka su." Baba Sale ya ja majina ya ce, "Haka ne Uwale, amma gani nake idan na fita kamar wani abu zai faru da shi. Ban taɓa ganin kaciyar da ta lalace haka ba, ki duba fa ki ga yadda take yin ruwa. Yaron nan duk kuzarinsa ga shi nan ba shi da kataɓus." Ita kanta Uwale ƙarfin hali take yi, don tana nuna rauninta ta san abin da mijin na ta zai yi sai ya fi haka, don haka ta shanye hawayen idonta ta ce. "Haka ne, amma ko ka zauna ɗin ma abin da Allah Ya ƙaddara shi zai faru. Shi kuma idan mun ga ba ta daina ruwa ba, sai mu sake kiran wanzan mu yi masa bayani. Tun da maganin wurinka ma bai sa ta ƙame ba." A sanyaye Baba Sale ya miƙe ya shiga ɗaki, ya ɗauko wani ƙaton buhu da ke cike da magunguna. Ya ƙarasa gaban Ɗan Bishir ya ce, "Ɗan Bishiriri ni zan fita nema." Ɗan Bishiri da ya yi lugub, saboda yadda yake jin jiki ya kalle shi da shanyayyun idanunsa ba tare da ya amsa masa ba. Da ƙyar Baba Sale ya iya ɗaga ƙafarsa ya fita Uwale tana biye da shi. Suna fita Fadil yana fitowa bayan sun gaisa ya wuce ya shiga motarsa da ke gefensu. "Au Mai gida na manta ba ka bayar da maganin Shamsiyya ba, kada sai ka tafi ta aiko." Uwale ta furta. Buhun ya buɗe ya ɗebo wasu matsakaitan magunguna a cikin jarkoki guda huɗu, sannan ya ɗauko wata ƙaramar roba mai ɗauke da man shafawa na magani ya miƙa mata. Ya ɗago jarkokin guda biyu, ya nuna mata wurin da aka yi bayanin maganin a jikin takardar. "Wannan ki ce mata sai ta ci abinci za ta sha, maganin sanyin mara ne. Kuma sau biyu ake sha safe da yamma, duk lokacin da za ta sha murfi biyu za ta sha saboda yana da ƙarfi sosai." Ya sake ɗauko ragowar roba biyun da yake ba iri ɗaya da waɗancan ba ne ya ce. "Wannan kuma idan ta tashi biyu za ta raba shi, ta sha rabin roba yau gobe ta sha rabi. Shi kuma wannan man zafi ne, na ciwon bayan da ta ce tana yi ne. Za ta dinga shafa shi a bayanta safe, rana da dare. Amfaninsa iya baya ne. Kar ta ji ƙafa ko gwiwa tana yi mata ciwo ta shafa, ba zai yi mata aiki ba. Duka dai bayanan maganin suna jiki, na san kin fahimta abin da ba ta gane ba sai a bari na dawo, saboda ba na son na ba wa mutum magani ya sha ba daidai ba a samu matsala." Duk bayanin da Baba Sale yake yi Fadil yana cikin mota yana jin sa, ba ƙaramin birge shi ya yi ba. Don haka ya fito ya ƙarasa wurinsa cike murmushi ya ce. "Am Baba Sale na ji duk bayanin da kake yi mata, kuma AlhamduLillah ka birge ni matuƙa. Saboda yadda na ji kana bayanin magungunanka daki-daki cikin ƙa'ida, ta yanda ba zai haifar wa mutane matsala ba." A sheƙe Baba Sale ya dubi Fadil ya ce. "Kai yaro da me ka ɗauki masu magungunan gargajiya? Jahilai ka ɗauke mu ko yaya? Ka ɗebo tsila-tsilan ƙafafuwanka kamar ƙwailayen lawashi za ka yi mini iyayi." Kunnuwansa Fadil ya riƙe ya ce, "Allah Ya huci zuciyarka ba haka nake nufi ba, ka yi abin da ya dace ne shi ya sa na yabe ka. Saɓanin wasu masu magungunan da suke sayar da magani babu dosage, mutum ya sha yadda ransa ya so babu ƙa'ida." Baba Sale ya taɓe baki ya ce, "Da ka ɗauka maganin asibiti ne kaɗai yake da galihu? Masu magungunan ai wasu suna suka tara, kamar yadda a cikin likitocin akwai muna likita. Kai dube ni nan. Sana'ata ba irin ta sauran masu magani ba ce. A yanzu ma idan na samun jari, babban wuri zan buɗe na huta da gararanba a titi. Sai na sake inganta su, don ina da burin har jami'an lafiya zan zuba tun da ni dai ka san summun bukumin ne, zo na kashe ka da turanci ban sani ba ballantana na san harkar gwaje-gwaje." Fadil ya saki murmushi, ya yaba masa sosai da sabon tsarin inganta maganin da ya ɗauko, har zai tafi ya waigo ya ce. "Na ji Daddy ya ce an yi wa yaron nan shayi ya jikinsa?" Jin tambayar Fadil ta sa hawaye ya zubo masa, ya saka hannun rigarsa ya share. Mamaki ne ya kama Fadil yana shirin magana Baba Sale ya ce. "Ɗan Bishir dai ga shi can rai a hannun Allah, daga kaciya jikin yaro sai fitar da ruwa yake duk ya jagalgale abin ba kyan gani. Na saka masa magani a banza, haka wanzan da ya yi masa kaciyar ya aiko masa da magani amma sai ta fara kamewa sai ta koma 'yar gidan jiya." Ya ƙarasa maganar yana fashewa da kuka. "Subhanalla, kuma ka kai shi asibiti?" Kamar Baba Sale yana jira ya ce, "Kaciyar zan kai asibiti don lalacewa? Wai me ya sa a kullum, sai ka nemi wulaƙanta mana sana'ar wanzanci ne?" Fadil ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni fa ba da wata manufa na faɗa ba, yanzu mu je na ga yanayin jikin na sa." Babu musu Baba Sale ya yi gaba Uwale da Fadil suna biye da shi. Suna zuwa suka samu Ɗan Bishir a yashe a ƙasa, kudaje sun yi yamama a kan jikinsa. Da sauri Fadil ya ƙarasa ya fara karkaɗe masa, ya ɗago a ɗan zafafe ya ce. "Garin yaya kuka bari jikin yaron nan ya yi haka? Saboda Allah dubi yadda ƙudaje suka bin sa ko su ba su isa su saka masa wata cuta a jiki ba." Mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, jin kalaman Fadil ya sa Baba Sale ya saki wani wawan kuka har sa da ya tsorata Uwale da Fadil. Ya riƙo hannun Fadil jikinsa yana rawa ya ce. "Boka wallahi ban san yadda aka yi ba, don Allah yanzu mene ne abin yi?" Jim Fadil ya yi sannan ya ce, "Mafita kawai a ɗauke shi zuwa asibiti shi ya fi fa'ida. Don haka a yanzu muke bayar da shawara idan za a yi kaciya a san wuraren da ya dace a kai yara, ba zan kushe ta wanzamai ba. Domin tun daga shekarun baya zuwa kusan ɗan shekara ashirin da yake a yanzu, kusan yawancin duka kaciyar gida aka yi musu. Amma a inda gizo yake saƙar, rashin kula da tsaftace kayan aikin yin ta zuwa kula da ita bayan an yi wa yara, sune manyan ƙalubalen." "Wai boka da kake ta ƙafafa a kan shayin, asibiti shin tana da bambamci da ta gida ne? Duk dai ba abu ɗaya ake yi ba?" Uwale ta tambaya, don ta fara jin haushin yadda Fadil yake fifita aikinsa a kan sana'ar mijinta. Fadil ya cigaba da karkaɗe wa Ɗan Bishir ƙuda ya ce. "Gaskiya akwai bambamce-bambamce da dama. Kamar yadda muka sani shayi wacce a kimiyance ake kira (Circumcision) wata ƙaramar tiyata ce da ake cire fatar loba (Foreskin) wacce take zazzagowa ta rufe kan al'aurar namiji(Glans). Kaciya tana da dalilin da ya sa ake yin ta, daga ɓangaren addini zuwa al'ada. Mafi yawancin ƙasashen da suka ci gaba, suna yin shayi ne a rana ta farko da aka haifi jariri. Wasu ƙabilun kuma suna yi bayan suna ko idan an yaye yaro. To amma kin ga a irin yankin ƙabilunmu, yawanci ana yi wa yara daga shekara uku zuwa bakwai. Sannan rashin yin ta babbar barazana ga lafiya ne. Kamar yadda shayi ke da dalili akwai amafanin da take da shi, musamman a ɓangaren lafiya. Domin yin ta yana bayar da kariya daga saurin ɗaukar cutar infection, saboda cututtuka suna iya ɓoyewa a ciki idan ba a cire fatar ba. Tana bayar da kariya daga kamuwa da penile cancer, a ɓangaren mata kuma zai rage musu kamuwa da cervical cencer, har ma da matsalar saurin kamuwa da ciwon (Balanitis) kumburin saman al'aurar namiji. Da ma sauran cututtukan da ban lissafa ba." Jikin Uwale ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Baba Sale ya zube a ƙasa kamar wanda aka zare wa laka ya ce. "Yanzu boka duk wannan bayanan a kimiyance ka karance shi? Shi Ɗan Bishir wannan ruwan da take yi na me ne ne?" Ganin yadda Baba Sale ya ɗaga hankalinsa, ya sa Fadil ya tsugunna a gabansa ya ce. "Ka kwantar da hankalinka Baba Sale, wannan ba komai ba ne In Shaa Allah za a kamo bakin zaren matuƙar aka je asibiti. Rashin kula da tsaftar wurin ya sa infection ya shiga, har ya haifar da zubar wannan ruwan da kake gani. Idan har aka je asibiti za su duba shi, su yi abin da ya dace su ba shi magunguna. Ni ma don dai ina da uzuri, da zan iya yi masa treatment. Amma ba zai yuwu, a bar yaro haka har tsawon lokacin da zan dawo ba. Sannan yana da kyau a kula da tsaftar raunin, kada a bari ƙudaje da wasu ƙwarin su dinga hawa jikinsa; saboda za su iya fesa masa ƙwayoyin cutar da ido ba zai iya gani ba. Rashin kulawa da tsafta, haɗe da takatsantsan zai iya haifar da kamuwar cutuka, har ya haifar da fiye da wannan da muke gani wanda ba ma fatan hakan." "Uwale maza ɗauki Ɗan Bishir mu tafi asibiti, wallahi ni babban tashin hankalina kada ma abin ya guntule ya faɗo ƙasa." Baba Sale ya faɗa cikin hawaye. Fadil ya jima yana ba su shawarwari da ƙwarin gwiwa sosai, sannan suka fito suka shiga mota ya sauke su a asibiti shi kuma ya tafi uzurinsa. Motar Fadil ta fita babu jimawa Mai adaidaita sahu ya sauke Baba Ɗanladi, hannunsa ɗaya riƙe da matarsa ɗayan hannun kuma riƙe da akwati. Sai da ta sauka sannan ya ɗauko musu akwatinan su ya ajiye a gefe. Kuɗi ya zaro ya biya mai adaidaita sahun, ya kamo hannunta yana shirin shiga gida Uzee gaye ya ƙarasa wurin bakinsa a washe kamar gonar auduga ya ce. "Oyoyo jirgin ceto, Oga murfi namu na gargajiya, uban gidan kowanne mai cin mushe. Duk wanda kwaɓarsa ta yi ruwa ya zo a ɗaure masa, ka suturta kuma ka rufa asirin gayu. Ina wanda ya samu 'yar shila ya bige aka samu matsala? In wanda bargon suturarsa yake son yayewa? Ya zo ga mai lulluɓe masa har ya yi bacci. Oga murfi wannan 'yar shilar ita ma zuwa ta yi a kifar da madafun ikonta ne?" Tun da Uzee guye ya fara maganar kan Baba Ɗanladi ya ƙara girma, ya faɗaɗa fara'arsa ya ce. "A dai dinga iya baki Uzee saboda tsaro ba don tsoro ba. Wannan da kake gani ba costomer ba ce, matar da na auro ce." Murmushi ta yi tana jifan Uzee da wani karuwan kallo, wanda kallo ɗaya kawai ya yi mata ya fahimci ita ma 'yar hannu ce. Uzee ya yi ƙasa da murya ya ce. "Wallahi Oga murfi ka zo a daidai, domin yanzu haka akwai wata yarinya da rana ta ƙwace mini. A taƙaice dai cikinta wata biyu kenan, don Allah ka rufa mini asiri kamar yadda ka saba ka ɓarar da shi." Baba Ɗanladi da irin su Uzee suke kira da Oga murfi ya ce. "Ka ga zuwana kenan, ko cikin gida ban shiga ba. Koda zan dawo bakin aiki sai zuwa nan da sati guda, domin shi kansa chemist ɗin yana buƙatar gyara." Uzee gaye ya yi masa godiya, sannan Baba Ɗanladi ya shige cikin gida hannunsa maƙale da na matarsa da yake jin ta kamar tsoka ɗaya a miya. Tun daga harbar gidan mutanen cikin gidan suka shiga yi masa barka da zuwa, sai dai kusan kowa bakinsa ƙunshe yake da magana kasancewar ganin Baba Ɗanladi rungume da wata mace mai zubin 'yan duniya. Amma da yake ba su ga fuska ba, sai kowa ya tsuke bakinsa. "Lale marhabun wa nake gani haka da hantsin nan?" Inno ta faɗa tana washe fuska, turus ta yi ganin Ɗanladi sarƙafe da mace a gefe. Inno ta ƙanƙance ido tana ƙare mata kallo ganin gashin doki ya yi mata yaro-yaro a fuska. "Ɗanladi daga ina ka samo wannan abin?" Inno ta tambaya tana miƙe wa tsaye rai a ɓace. Ɗanladi ya saki murmushin soyayya, ya shafo fuskar matarsa cikin so ya ce. "Inno wannan ita ce matar da na auro ai, so nake sai mun zauna na gabatar miki da ita." Inno ta fara bin ta da kallo, tun daga ƙafa har zuwa tsakiyar kanta. "Baby ina buƙatar hutu ka san na gaji. Mu je ɗaki ka yi mini tausa." Ta furta tana shafa jikin Ɗanladi. Inno salati ta saki tana tafa hannu ta ce. "Yanzu Ɗanladi, ƙaddarar da ka kwaso mana kenan wannan mai zubin alakwankwan ɗin?" Ɗanladi ya sunkuya ya sumbaci matarsa ya ɗago ya cewa Inno, "Wallahi Inno kamar kin sani wannan ita ce ƙaddarata. Jin ta nake har birnin zuciyata. Beb wannan ita ce Mom ɗina, you know i told you Dad ɗina ya jima da mutuwa." Ta ɗago tana taunar cingam ta ce, "Am so sorry Mom, ya kike?" Inno ta saki baki da hanci tana kallon ikon Allah. Jin maganganu a tsakar gida ya sa Mai yasin ya leƙo yana faɗin. "Inno ke da waye ha..." Maganarsa ce ta maƙale, sakamakon haɗa ido da suka yi, lokaci ɗaya wani irin tari ya turnuƙe shi. Daga can ɓangarenta ita ma ido ta zaro, amma sai ta daidaita nutsuwarta ta basar kamar ba ta san Mai yasin don kada su gano su. 'Me ne ne alaƙar wannan yaron da 'yar gwal? Ko dai aurensa ta yi ban sani ba, lallai kuwa dara ta ci gida idan har haka ne.' Mai Yasin ya raya a ransa. Ɗanladi ya zaro mukulli a aljihu, ya buɗe ɗakinsa ya fara jan akwatinansu ya shigar musu da su ciki. 'Yar gwal a wurin ta fara rage kayan jikinta, ta zame mayafinta ta wurga a kan igiya. Ta zamo hular gashin dokin kanta za ta wurga igiya a daidai lokacin Yaya Inu ya shigo cikin gidan, a bisa tsautsayi ta jefa masa a fuska. Warin gashin ya daki hancinsa, a tsantsance ya wurgar da shi gefe rai a ɓace yake kallonta, cikin tsawa ya ce. "Ke! Wace ce ke?" Daga cikin ɗaki Ɗanladi ya ce, "A'a Yaya Inu, kada ka sake ka sake yi wa 'yar gwal tsawa don ba zan lamunta ba." Da mamaki Yaya Inu yake ƙare mata kallo ya furta. "Za ki fice daga gidan nan ko sai na sumar da ke? Kai Ɗanladi, a gidan uwar wa ka samo wannan abar mai zubin surar Fir'auna?" 'Yar gwal ta bi Yaya Inu da kallo a ranta ta raya. 'Ni za ka yi wa barazana? Ai kuwa za ka ga aikin 'yan bariki. Sai na nuna maka sheɗan ne uban gidana ba Fir'auna ba.'' Yaya Inu yana shirin sake magana, 'Yar gwal ta yi wata wawar sufa ya ɗane shi. Na kusa kammala free page In Shaa Allah, ma su son cigaba za su fara payment daga yanzu. 500 Aisha Adam 3090957579 Firstbank evidance ta wannan no ba 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [04/01, 13:36] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA SHA ƊAYA "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ke! Wane irin iskanci kike yi haka? Ba za ki cika ni ba, sai na saɓa miki." Yaya Inu ya yi kalamansa yana kokawa da 'Yar gwal amma fir ta ƙi sakinsa, ta ƙadandane shi sosai kamar mayen ƙarfe. "Ke yarinya, ba ki da mutumci ashe ban sani ba, ba za ki sakar mini yaro ba." Inno ma ta yi maganar tana ƙarasawa wurinsu. Mai Yasin ya gimtse dariyar ƙetarsa, saboda dama a ciki yake da Yaya Inu. Kuma ya san fiye da haka ma 'Yar gwal za ta iya aikatawa. Ganin da gaske 'Yar gwal ba za ta sake shi ba, ya sa ya tattare iya ƙarfinsa da niyyar ya warɓo ta ƙasa, sai ta maƙale shi ƙam a madadin 'Yar gwal ta faɗo sai wata wawiyar tusa ce ta ƙwacewa Yaya Inu. "Subhanallahi! Inusa mene ne haka da sakin tusa?" Mai Yasin ya furta, sannan ya ce. "Ke yarinya kanki ɗaya kuwa? Kamar muna ƙasar kafirai za ki ƙadandane mutumin da ba muharraminki ba." 'Yar gwal ta ɗago tana bin sa da wani irin kallo, sai kawai suka ji ta saki jiki ta faɗi yaraf a ƙasa. Sai a lokacin Yaya Inu ya ja gefe yana kaɗe riga, ya cigaba da wurga mata kallon tsana kamar zai mata duka. "Sannu babyna, ko jikin ne ya dawo?" Furucin Baba Ɗanladi kenan. 'Yar gwal ta fara jera atishawa, Ɗanladi ya ɗago ya dubi Yaya Inu ya ce. "Shi ya sa tun farko na ce babu ruwanka da ita, saboda ni na san aljanun jikinta ba sa nisa da ita. Ina zaman zamana za ka rikita mini mata babu gaira babu dalili." Ɗanladi ya ƙarasa maganar yana ɗaukar 'Yar gwal ya shige ɗaki da ita. Inno ta shiga share hawaye ta ce. "Inusa yaushe ɗan'uwanka ya yi lalacewar haka? Wai Inusa saboda ya mayar da mu ba komai ba a wurinsa, har shi zai je wani wuri ya aurar da kan shi. Inusa ba za ku yi wani abu a kai ba?" Yaya Inu da ya gama cika da mamaki ganin ƙiri-ƙiri 'Yar gwal ta raina musu hankali ya ce. "Inno kin fi kowa sanin wane ne Ɗanladi, tun da rayuwar da ya ga ta fiye masa ba sai ya yi ba." Daga cikin ɗakin Ɗanladi ya ce. "Inno yanzu auren da na yi ne ba za ki saka mini albarka ba? A da kuna yi mini ƙage, kuna cewa ina lalubar yaran mutane a chemist ɗina. Amma yanzu kuma na yi auren ma ba za ku sarara mini ba? Sunnar Annabin ce kuke ƙyashi na raya?" 'Haƙiƙa na lura duk balaja'un Inusa ashe shi shafar mai ne a kan wannan. Tirƙashi, wannan Ɗanladin ai ya gama tashin kaina.' Mai Yasin ya raya a ransa. Yaya Inu ya kamo hannun Inno ya furta. "Mu je Inno, idan kika biye ta wannan yaron ranki ne zai yi ta ɓaci a banza. Yanzu mu je ciki ni ba wannan ce damuwata ba, wani tashin hankali ne yake tafe da ni da na garara samun nutsuwa." Inno ba ta musa ba, ta bi bayan Yaya Inu suka shiga ɗaki. "Inno ɗazu Abu ta zo, ta kawo mini jaririyar da ta haifa..." "Amma dai wannan yarinya an yi marar mutumci, yanzu ita saboda rashin hankali daga haihuwar yarinyar za ta ɗauko ta kawo maka? A kanta aka fara mutuwar aure?" Inno ta katse shi tun bai ƙarasa magana ba. "Don Allah Inno ki bari na dire maganata." Inno ta yi fakare tana jiran ya gama magana ta ɗora daga inda ta tsaya. "An samu matsala domin yarinyar zabiya ce. Ni kuma gaskiya ina zargin ba 'yata ba ce, saboda kowa shaida ne ban taɓa haihuwar zabiya ba." A razane Inno ta ja da ba ya tun bai gama magana ba, ta fara dubansa da wani kallo sannan ta ce. "Kada ka raina mana hankali Inusa, batun ka ce 'ya ba ta ka bace ai bai taso ba. Saboda kowa ya san ta yadda ake samun zabiya, sai da ka je ka gama saɓon Allah sannan za ka same ni kana yi mini 'yar murya? Me zan iya yi maka a yanzu? Bayan Allah ya yi ikonsa, ai sai dai ka ɗauki na Annabawa. Ka je can kai da Zainabun ku yi ta istigifari kuna tuba ga Allah." Inno ta yi maganar tana miƙewa, har za ta shige uwar ɗakinta ta waigo ta ce. "Yawwa dama daga yanzu kada ka sake ka shigo mini. Saboda kada zunubin da kuka kwaso Allah Ya jarabce ni da shi." Tana gama maganar ta shige ciki. Kamar Yaya Inu zai ɗora hannu a ka, haka ya fice daga sashen Inno abin duniya ya haɗe masa. Yamma ce sakaliya, sanyin la'asar tuni ya riga da ya sauko. Fadar Mai gari cike take da mutane ana zaune ana zaman fada. Mafi yawan mutanen da suke zaune gulma ce ta kawo su, a kan abin da ya faru da Mai gari. Shi ma da yake ya fahimci haka sai ya tsuke fuska, ya dubi su Mahmud da suke takure kamar zakarun da aka tsamo daga ruwa ya ce. "A madadinmu da na talakawan yankinmu muna yi muku barka da zuwa. Muna buƙatar ɗayan bayan ɗaya, ku gabatar da kanku a gaban mutane. Mudassir ne ya ɗan muskuta zai yi magana, Mai gari ya yi wa Mahmud ƙuri da ido ya ce. "Kai yaro, kamar na san fuskar nan taka?" Cikin Mahmud ya karta, amma sai ya yi ta maza ya ce. "A'a ranka shi daɗe, sai dai idan mai kama da ni ka sani. " Jin Mai gari ya yi shiru ya sa Mudassir ya furta, "Ni dai sunana Mudassir Najib, ɗaya daga cikin ɗaliban da aka turo daga babbar Jami'a yin bautar ƙasa (NYSC)." A fili Mai gari ya faɗaɗa fara'arsa yana jinjina kai, saboda ya ji ya ce bautar ƙasa suka zo don haka sai ya ci banza. Har ya fara lissafa kansa, a sahun mahajjatan da za su sauke farali a bana. Duba da irin aikin gonar da ya ayyana zai jibga wa su Mudassir. Shi ma Mahmud ya gabatar da kansa, sannan Mai gari ya fara baza babbar yana haɗe rai ya ce. "Tun da har Gwamnati ta aiko ku garin nan, na tabbata babbar Masarauta ƙasar nan ta san irin gudunmawar da nake bayarwa a ƙasata. A don haka, ya zame muku wajibi ku zage damtse ku yi mini noma yadda ya kamata." Mai gari ya zaro ido waje cike sa barazana ya sake dubansu ya ce. "Ku dube ni nan, bautar ƙasa ba wasa ba ce yara ina fatan kun gane. Domin shinkafar da kuke miƙe ƙafa kuke ci, ita ma sai da aka gama bauta mata sannan ta bauta muku a cikinku. "Ammm amma ina ganin kamar ba ka fahimce mu ranka shi daɗe. Service muka zo fa, ga wannan takardar za ka iya karantawa." Mahmud ya ƙarasa maganar yana miƙa masa takardar. Gaban Mai gari ya faɗi, da ya ga ya miƙa masa wata zungureriyar takarda mai cike da rubutun turanci. Sai da ya fakaice su ya sharce gumin fuskarsa, sannan ya riƙe takardar yana ɗan matse idanu ya fara karantawa. "Assalamu Alaikum. Ni Mai girma gwamna, na aiko waɗannan jajirtattu kuma haziƙan ɗaliban nan, domin su zo garin nan su taya Mai gari aikin gona wanda muke kira da bautar ƙasa. Kuma a don haka, muke jan kunnensu domin su jajirce wurin yin aiki tuƙuru. Idan ba haka ba, za mu zartar musu da mummunan hukunci." Mai gari ya ɗago yana muzurai, daga can ƙasa ya ga wani rubutu da lambar waya har da saka hannu, sai ya ce. "Ga lambar wayata nan ni mai girma gwamna, duk wani ƙorafi da kuke da shi kai tsaye za ku iya tuntuɓa ta. Kuma duk wanda ya yi ba daidai ba a cikinsu, muna bayar da umarnin Mai gari ya saɓa masa. Idan da hali ma ya ci tararsa." Tun da ya fara jawabin Mahmud da Mudassir, suka yi zuru suna kallonsa cike da mamaki. Mutanen da ke wurin suka ɗauki sowa cikin kambaba Mai gari suka ce. "Allah Ya ja zamaninka mai martaba. Haƙiƙa gado ba karanbani ba, duk wanda ya san gidanku ya san mane ne mulki." Mai gari ya fara zuba doro yana kalle-kalle cikin izza. Hambali da yake gefe cikin tsananin jin kunya ya ce. "Allah Ya taimake ka, idan na fahimce su fa kamar ba haka suke nufi ba. Duk da dai ni ma ba karatu na yi mai zurfi ba, iya ka ta diploma. Idan aka ce an tura ɗalibi NYSC wato bautar ƙasa, ana nufin ya hidimtawa ƙasa ta hanyar bunƙasata da ciyar da ita gaba. Kuma kamar wani ƙarin horo ne, da ɗalibai suke sake gogewa; domin su zama shugabanni ko al'ummar da za a yi alfahari da su a gobe. Amma a gafarce ni ranka shi daɗe, idan na faɗi ba daidai ba." Tun bai gama magana ba Mai gari ya fusata. Rai a ɓace ya nuna Shazali ya ce. "A kanannaɗe shi a hukunta shi, mu zai kawowa raini a gaban fada? Shazali, yaron nan yana nufin fada ba ta san me take yi ba ne?" "Allah Ya taimake ka, abin da bawan Allahn nan ya faɗa fa haka ne. Ba aikin gona muka zo ba, kamar yadda ka faɗa..." Da sauri Mai gari ya katse Mahmud. "Kai yaro ka iya bakinka. Shin ya bari mun gama fesar da maganganun bakinmu ne? Ko numfashinmu ya tara? Abin da muke shirin faɗa kenan ya yi mana katsalandan, don haka dole a hukunta shi." Kallon tsaf Mahmud ya yi masa, yana jinjina ƙarfinsa. Bayan Mai gari ya sallame su, suna tafe a hanya ya ce. "Na lura da Mai garin nan tsaf, ashe duk burgagin banza yake yi. Ba abin da ya sani wallahi, kawai su yake naɗewa." Mudassir ya yi murmushi ya ce, "Ai kuwa sai dai su ya naɗe su, don idan ya shiga tawa gonar sai na yi masa naɗin da ya fi na huhun goro." Gabaɗaya suka saka dariya. Baba Sale shi da Uwale ba su suka dawo daga asibiti ba sai yamma liƙis, saboda bayan likita ya gwada Ɗan Bishir sai da aka ba shi gwaje-gwaje. Bayan sakamakon ya fito aka yi masa dressing, sannan aka rubuta musu magungunan. Duk soyayyar da Baba Sale yake yi masa haka ya danne shi da ana wanke masa, saboda likita ya tabbatar masa da matuƙar bai samu kyakkyawar kulawa ba komai zai iya faruwa, tun da har wurin ya fara ruwa yana ɗan wari. Likitan ya gargaɗe su sosai, wurin kula da tsaftar sabon gyambo koda ba na kaciya ba ne, sannan ya ce bayan kwana uku su koma a sake duba jikin nasa. Bayan sun koma gida, ko zama bai yi ba ya nufi gidan Bala wanzan. A ƙofar gida ya tsaya ya ce a yi masa sallama da shi, yana nan tsaye yaron ya dawo tare da wani ɗan matashin saurayi. "Kai Tasi'u, ina mahaifinka yake?" Baba Sale ya furta fuska babu walwala. Matashin da ba zai wuce shekara goma sha uku ba, ya rausayar da murya cike da neman tausasawa ya ce. "An tafi da Baba ofishin 'yan sanda ɗazu." Da sauri Baba Sale ya ce, "Ofishin 'yansanda fa? Me ya yi aka kai shi can?" "Ban san takamaiman abin da ya yi ba, amma an ce wai Idi Naira ya yi wa aska, kuma wai ana zargin yana da cutar ƙanjamau!" "La'ilaha'illa'illahu Muhammadur Rasulillahi, Sallallahu alaihi wasallam. Ɗan Tasi me kunnuwana suke zuƙo mini? Kada ka ce mini Ɗan Bishiriri ya kamu, wayyo Allah Tasi riƙe ni da ƙarfi duhu nake gani." Baba Sale ya yi maganar yana jin wata irin hajijiya tana yin ɗiban karan mahaukaciya da shi. Da sauri Tasi'u ya riƙe shi yana kiran sunansa da ƙarfi, "Baban Ɗan Bishir lafiya." A hankali Baba Sale ya ɗago duk da ba ya gane abin da Tasi'u yake faɗa sosai ya ce, "Tasi'u maza kai ni ofishin 'yansandan." Kamar sabon ɗan maye haka suka tafi Tasi'u yana riƙe da shi, don har suka ƙarasa wani irin layi yake yi idanunsa suna yi masa gizo. Su Baba Sale suna zuwa, suka samu Bala Wanzan a tsaye yana bayani. "Wallahi tallahi yallaɓai ban taɓa sanin Idi Naira yana da cutar abar nan ba, ni ko sunanta ba na son faɗa. Kuma babban tashin hankalina yaran da na yi wa shayi, a ranar da wannan tsautsayin ya afku. Domin su ne masu tasowa ba su mori ƙuruciya ba..." Wata irin ƙara suka ji gijiiiiiif Baba Sale ya faɗa ta saman kanta, saboda tun a bayanin farko da ya ji Bala wanzan yana yi, ya ji ƙafafuwansa ba za su iya ɗaukarsa ba. Kalaman Bala na ƙarshe suka sa ya ga wani baƙin duhu ta lulluɓe idonsa, numfashinsa ya ɗauke. "Subhnallah! Waye wannan? Lafiya?" Wani kurtun ɗansanda ya ƙarasa kansa yana tambaya. Tasi'u ne ya yi musu bayanin abin da ya faru tsakaninsa da Baba Sale, har zuwansu cikin station ɗin. Ruwa aka ɗebo aka zuba masa, a hankali ya farfaɗo yana daga kwance yake kallon mutane ɗaiɗai. Ya yunƙura a hankali ya zauna sai a lokacin komai ya shiga dawo masa. "Yallaɓai Ɗan Bishir, kun bincika mini Ɗan Bishiriri." Wani Sergent da ya fahimci Baba Sale, ya dubi Bala Wanzan ya ce, "Kai Wanzan ka yi wa yaron wannan mutumin kaciya ne?" Da yake a lokacin an mayar da Bala cikin cell, yana daga ciki ya ce. "Eh na yi masa yallaɓ..." Tun Bala bai gama magana ba Baba Sale ya sake sumewa a wurin, haka suka sake zuba masa ruwa ya sake farfaɗowa. Sai dai su kansu abin da ya fi ɗaga hankalinsu, yadda Baba Sale yana farfaɗowa zai sake suma. Har sun lura ko ya farfaɗo ba ya zama cikin hayyacinsa. Don haka suka tattarashi hankali a tashe suka yi asibiti da shi, sai bayan sun je suka saka Tasi'u ya yi musu rakiya har gida aka sanar da Uwale da su Baba Ibrahim halin da ake ciki. Tun da suka fito daga asibitin yake zabga sauri, cikin sassarfa ta rufa masa baya ganin ya fara yi mata nisa ya sa ta fara ƙwala masa kira. "Masoyi! Masoyi don Allah ka jira ni saurin me kake yi kamar za ka tashi sama." "Ya muke da jirgin sama? Na ce ya muke da shi?" Baba Labaran ya furta a zafafe. Sororo ta yi tana kallonsa don har tsoro-tsoro ta ji, ganin yana yi mata faɗan da ba ta saba gani a tattare da shi ba. Hasali ma ba ta ga abin faɗa a maganarta ba. "Asibiti na uku kenan a yau muna zuwa suna yi miki gwaji, amma duk maganarsu ɗaya kamar haɗin baki. To magana ta gaskiya na fi son mace a haihuwar fari, saboda magaji nake nema. Haka kawai duka asibitocin sun ce mace suka gani. Wallahi da sake an ba wa mai kaza kai." Da mamaki ta dube shi ta ce. "Da sake fa ka ce Masoyi? Shin butulci za ka yi wa uabangiji ne? Mutane nawa ne suke neman haihuwar ba su samu ba, mace ko namiji mai albarka ya kamata ka roƙa." Maimakon ya ba ta amsa sai kawai ya saki tsaki ya yi gaba yana faɗin. "Kanki ake ji, ni na gama faɗar ra'ayina." Daskarewa Rahinatu ta yi, ta ɗora hannunta a kan ƙaramin cikin jikinta da bai fi wata uku da satika ba. Cikin sanyin murya ta ce. "Dama duk soyayyar da mutumin nan yake yi mini ta fatar baki ce? Haƙiƙa Labaran ya cika butulu." Daga haka ta fara takawa a hankali, ta rufa masa baya tana jin zuciyarta na suya. Damuwa haɗe da tarin ayarin tunaninnika ne suka cunkushe masa kwanya, saboda Indo da su Hansatu sun nemi mayar da shi kamar mahaukaci. Don da sun kalle shi sai kowacce ta gimtse fuska, yana bada baya sai su kwashe da dariya. Rumfar Tsalha mai kayan miya nufa, yana zuwa ya yi sallama amma babu wanda ya amsa masa. Kamar haɗin baki, lokaci ɗaya mutanen cikin rumfar suka watse . Turus Yaya Inu ya yi, yana shirin magana ya ji Tsalha ya ce, "A gaskiya malam Inusa ka dakata da zuwa cikin rumfata, saboda ka da ka kawashe mini albarkar cinikayyata. Ba zan ɓoye maka Inusa ka san dai ni abokinka ne, maganar haihuwar zabiyar nan fa ya karaɗe ciki da wajen garin nan don haka ka yi hattara." Daga haka Malam Tsalha ya koma kujera ya zauna yana haɗe rai, don kada Yaya Inu ya samu fuskar zama. Kamar zakaran da aka tsamo daga cikin ruwa haka Yaya Inu ya fito ya nufi hanyar gida, tunanin Zuly matashin kai ce ta faɗo masa. Ya saki murmushi ya nufi ƙofar gidansu. Ƙaramar wayarsa ya ciro ya kira ta, ba a ɗauki lokaci ba ta fito tana taunar cingam. "Haskena ashe kaine da yamma haka?" Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Takanas na shiryo na zo na ganki domin na huce takaicin zuciyata, saboda ke kaɗai ce hasken da ke yaye duhun da ke ɗanfare a ciki." Sai da ta hura kwai da cingam ta ce, "Wani zance nake ji yana tashi, wai an haifar maka zabiya 'yan gidanmu har sun fara bala'i. Ni kuwa na ce duk bala'insu ba zabiya ba, ko rabi mutum rabi aljan aka haifa maka babu wanda ya isa ya han ni aurenka." Farinciki ya sa ta Yaya Inu ya zaro rafa kuɗi har dubu goma ya miƙa mata. "Ki sha lemo da wannan, masoyiyata kuma hasken zuciyar Inusa." Alewa ta buɗe ta wurga a baki ta tsotsa, sannan ta zaro ta miƙa masa cike da kissa. Cikin so da ƙauna Yaya Inu ya karɓi alewar, ya jefa a baki ya yi mata sallama. Yana gab da shiga gida ya hango wani mai magani, yana tafe da wata ƙatuwar Mp3 da wani faffaɗan kwando mai ɗauke da magungunan maza a ciki. "Ina mai matsalar kuzari? Ina namijin da ya rako maza? To ya hanzarta ya zo ga adamalmala. Maganina rabo ne, maganina sa'a ce. Alhaji sai mai tsananin rabo ne zai dace na ba shi, ina mazan da basir ya jima da yi musu illa? Alhaji ba ka nisan zango wurin tuƙa sitiyarin mota? Don Allah ka zo, ga mai adamalmala ya dawo. Idan na bar garin nan ba zan dawo ba, maza kaɗai nake ba wa magungunana domin na fi kishinsu a kan mata. Alhaji ko Malam kada ka ji kunyar karɓa, indai matsalarka a ɓangare iyali ne ta kau. Sabon aure za ka yi ne? Ko kuwa ka rasa gane kan matanka ne? To maza gangaro ka karɓa sadakar ƙalilance, ni dai ba na rowa domin burina na kankaro mutumci a wurin maigida." Yaya Inu ya tsaya a jikin bishiya ya yafito shi da hannu, Mai maganin ya ƙarasa wurinsa adaidai lokacin Na Balaraba ya ƙarasa ta wurin zai wuce. "Kai wa nake gani kamar Gambo, ko idanuna ne?" Cewar Gambo. Mai maganin ya ɗago yana kallon Na Balaraba da sauri ya ce, "Kai! Wa nake gani kamar Na Balaraba? Dama rai kan ga rai?" Yaya Inu ya washe baki, "Na Balaraba ka san shi ne?" Na Balaraba ya furta, "Na san shi farin sani, yanzu ne dai zumunci ya zama yanda ya zama, shekara biyar zuwa shida rabona da shi." Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Ka ce faɗuwa ta yi daidai da zama, dama kiransa na yi zan sayi magani." Mutumin tun da ya yi tsaye yake ƙarewa Yaya Inu kallo, har sai da gabansa ya faɗi. Amma jin Na Balaraba ya ce ya san shi ya sa ya saki jikinsa. "Haba ba ka da damuwa Inusa, ka sayi maganinka wannan da kake gani ba na shakku a kansa." Yaya Inu ya nuna wani magani ya ce yana son saya, Mai maganin ya yi zaraf ya ce. "A'a mai gida bari na ba ka wannan, ai wannan shi ne gagara-badau an buga da kai an barka." Ya ƙarasa maganar yana miƙa masa wata roba ƙarama ya ɗora da cewa. "Yanzu kana komawa gida tun da magariba ta ƙarato ka shafa shi, sai bayan minti talatin ka wanke da ruwan ɗumi. Ka zuba wa sarautar Allah ido za ka ba ni labari idan na sake dawowa." Jiki yana rawa Yaya Inu ya zaro kuɗi ya biya. Bayan Mai maganin ya tafi Baba Ado da yake gefe ya ce masa. "Yanzu Allah Yaya, ba za ka raba kanka da gabzawa kanka waɗannan magungunan barkatai ba? Haka kawai maganin kare da doki kowa na ka ne, ba ka duba inganci ko ka je wurin masu magungunan gargajiya waɗanda suka san kansu ka saya..." A sheƙe Yaya Inu ya katse shi. "Kai dakata kada ka yi mini rashin kunya, tuzurun banza da wofi. Wai har da su kaza a cin danƙo? Kai da ko arzikin auren ba ka samu ba, shi ne har za ka zauna kana yi mini fi'ili? Tun da kai 'yan mata aljanu sun gama tsuƙe jijiyoyin jikinka, ai sai ka bar masu raya sunnar Annabi su yi. Da uwar kuɗina nake saya babu wani ƙato da yake saya mini, don haka kada ka sake shiga hurumina." Yaya Inu yana gama magana ya shige gida a fusace. Yana zuwa ɗakinsa bayan ya huta ya shafa man kamar yadda Mai maganin ya faɗa masa, bayan kamar minti biyar da shafa man ya ji wani irin zafi yana ratsa shi. A ɓangare ɗaya kuma ya fara jin kamar ana tsoma wurin a ruwan zafi, ba shiri ya tashi ya rage dogon wandon jikinsa. Ya ɗauki muhuci yake firfita, jin azabar ta yi yawa ya sa yaYaya Inu ya faɗa banɗaki a guje har yana ɓari da kwanuka. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, bayan ya shafo jikinsa ya ji tamkar ba na shi ba. Yaya Inu yana kai kallonsa, ganin sauyin hallitarsa ya sa wani wawan kuka ya kwace masa. Saura na ji wani ya yi wa Yaya Inu dariya.😂 Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [05/01, 19:31] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA SHA BIYU Indo tana daga bakin murhu ta fara jiyo numfarfashin Yaya Inu da shasshekar kukansa, da farko ba ta yi tsammanin shi ba ne. Saboda hayaniyar yaran da ke kai-kawo a cikin gidan, sai da ta kasa kunne sosai sannan ta fahimci kukan babba ne. Mamaki ne ya kama ta, don su Hansatu gabaɗaya suna nan ballantana ta ce wata daga cikinsu ce. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar banɗakin tana zuwa ta ji yana faɗin. "Kaico wannan wanne irin tsinanna magani da mai maganin ne? Ai kuwa ni da magani irin wannan har abada." Sai ya sake ɓarkewa da kuka. Ƙirjin Indo ya buga da ƙarfi, ta ɗan buga ƙofar banɗakin ta ce. "Mai gida lafiya kuwa? Me yake faruwa?" Daga can cikin banɗakin Yaya Inu ya ja majina ya ce, "Shigo ciki Indo." "Cikin banɗaki fa Mai gida?" Ta tambaya da mamaki. Yaya Inu bai sake tanka mata ba saboda yadda abin duniya ya dame shi, tambayar Indo ma haushi ta ba shi, don haka ya ja baki ya tsuke. Jin Yaya Inu ya yi mata shiru, ya sa Indo ta faɗa banɗakin gabanta yana faɗuwa musamman da ta tuna bai taɓa yin haka ba, kada ko wani abin ne ya same shi a ɓanɗakin ba ta sani ba. "Mai gida lafiya kake kuka a banɗaki?" Indo ta yi maganar bayan ta samu Yaya Inu har lokacin a tsugunne. "Indo na haɗu da wani iftila'i, wallahi ina cikin tashin hankali komai ya canza mini, al'amarin ya munana." Muryar Yaya Inu kaɗai da ta ji ce ta tabbatar mata da tabbas babu lafiya, ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Me ya faru dai yanzu?" Yaya Inu ya zauna a kan wani ɗan dandamali da suke zama su yi wanka, ya dubi Indo da shanyayyun idanunsa da suka yi mitsi-mitsi saboda kukan da ya sha ya ce. "Ku je ku kori yara ɗaki, ki kira mini su Hansatu ku mayar da ni ɗakina. Saboda su kansu jijiyoyin ƙafafuwana sun yi sanyi, ji nake kamar da na wani aka zuba mini ba nawa ba." Jin haka ya sake ɗaga hankalin Indo, ta ja ƙafafuwa jiki a sanyaye ta samu Hansatu da ke ɗinkin mahuci ta furta. "Mai gida fa babu lafiya Hansatu." Da yake har lokacin Hansatu cike take da haushin Yaya Inu, kai tsaye ta ce. "Allah Ya sawaƙe, kowa ma fama yaka da rashin lafiya." "Wannan fa ba irin rashin lafiyar yau da gobe ba ce, don ya ce a tura yara ɗaki mu je mu ɗauke shi mu mayar da shi ɗakinsa." Furucin Indo ya sa Hansatu zaro ido, a razane ta ce. "Shi Mai gidan za mu ɗauka mu kai ɗaki? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Da sauri Hansatu ta miƙe, kowacce ta shiga ƙoƙarin tura yaranta ɗaki. Kafin wani lokaci tuni yaran sun shige ciki, Hansatu ce a kan gaba sauran suna biye da ita. A inda Indo ta bar Yaya Inu, a can suka koma suka same shi. Yana zaune ya haɗa kai da gwiwa. Abin da ya sake ɗaga hankalin matan nasa, ganin hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa yana ambaliya. "Mai gida! Wai me yake faruwa haka?" Hansatu ta jefa masa tambaya a rikice, Yaya Inu da muryarsa ta shaƙe can ciki ya ce. "Ku yi tara-tara ku kai ni ɗaki. " Da yake Yaya Inu ba mutum ne mai ƙiba ba, ya sa su ukun suka haɗu suka ɗaga shii suka yi ɗaki da shi suka kwantar a katifa. Zani suka janyo suka rufe masa jikinsa, suka yi carko-carko kowacce tana saƙa da warwara a cikin ranta. "Ɗazu gabanin zan shigo gida na haɗu da wani matsiyacin mai magani, bayan na saya ya ce mini na shafawa ne. Ina shafawa kun ga abin da ya faru!" Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana bankaɗe zanin rufar da suka rufa masa, wannan karon hankalinsa ya fi tashi don ya lura da ci bayan da yake ta samu a jikinsa. "Innalillahi! Malam mene ne haka a tsotse kamar hanjin ligidi? Wannan wane irin magani ne haka ka shafa?" Hansatu ta faɗa a ruɗe. Indo ta jinjina kai ta ce, "Gaskiya wannan abin akwai ayar tambaya, amma babu lambar waya a jiki da sai ka kira shi." Yaya Inu ya yi zaraf ya ciro robar maganin, cikin sa'a ya ci karo da lambar mai maganin. Yana kira bugu biyu ta yi ya ɗauka, nan take ya zayyane masa duk abin da ya faru. Daga can ɓangaren ya ce. "Allah sarki Mai gida, na manta ai tun farko ban yi maka wannan bayanin ba. Amma kada ka damu wannan ba komai ba ne, dama a rana ta farko dole za ka fuskanci haka. Amma zuwa gobe war haka komai zai dawo daidai." Yaya Inu da kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu har sai na kai gobe war haka? Yanzu fa ƙarfe takwas na dare, haka zan yi ta zama a zuƙe?" "Wannan ba wani abu ba ne, idan har maganin ya game duk jikinka, muna nan da kai sai ka nemo ni ka kawo mini kwastoma saboda kyawunsa." Kalaman mai maganin kenan da suka ɗan ƙara wa Yaya Inu ƙwarin giwa. Larai da ke riƙe da haɓa ta jinjina kai ta ce, "Magana ta gaskiya Mai gida lamarin nan fa ya ba ni mamaki, ba yau ka fara amfani da irin wannan maganin ba fa. Wallahi akwai dai magana, ka tuhumi tsakaninka da Ubangiji gaskiya." Yaya Inu ya zaburo ya ce, "Ke Larai me kike nufi?" Larai ta murguɗe baki gefe ta yi ƙasa da murya ta ce, "A'a toh, ga dai abu ya bayyana nan tun da har ka haifo zabiya. Ƙila fushin da Allah Yake yi da kai ne ya jarabce ka ta wurin, ba sai a ga ta saɓon Allah ba. Tun da Ubangiji da kansa Ya yi hani da kusantar mace tana cikin jini..." "Na rantse da Allah zancanki yana hanya Larai, kai duniya jama'a akwai darussa a rayuwar nan fa." Indo ta furta tana jinjina buwayar Ubangiji. Kalaman su Larai ba ƙaramin ɗaga hankalin Yaya Inu ya yi ba, yana daga kwance ya tashi zaune ƙirjinsa yana bugawa ya ce. "Na rantse da girman Allah ban taɓa aikatawa ba, Allah ne shaidata. Na shiga uku Hansatu ku taimaka mini, wallahi ina cikin wani yanayi." Larai ta yi hanyar waje ta ce, "Wallahi Mai gida ni kam a yanzu ma tsoron taɓa ka nake yi, kada na je ni ma wata hallitar tawa ta tsotse." Daga haka ta yi ficewarta. Kuka Yaya Inu yake iya ƙarfinsa, ya janyo zanin Hansatu yana ɗago mata hannu. Ba ƙaramin tausayi ya ba ta ba, saboda duk abin da zai saka Yaya Inu kuka ba ƙaramin tashin hankali ba ne. A sanyaye Hansatu ta zauna ta ce, "Mai gida! Yanzu mene ne abin yi?" Yaya Inu ya wara mata hannu alamar ba shi da mafita ya furta, "Sai abin da kika ce Hansatu." Indo ta gimtse dariya ta yi ficewarta, don ita ma a wani ɓangaren ya fara ba ta tsoro. "A'a kai ne mai faɗa aji ai, tun da kai rana ta ƙwacewa. Laifi dai ka riga da ka aikata, kawai dai ka yi ta isgifari. Sannan sai mu zuba wa sarautar Allah ido, zuwa washegari kamar yadda Mai maganin ya faɗa." Wata sabuwar soyayyar Hansatu ta mamaye shi, ya riƙo hannunta ya ce. "Hansatu dama haka kike sona, ke kaɗai ce ba ki guje ni ba a cikinsu." Hansatu ta yi wa Yaya Inu ƙuri da ido, tana tuna soyayyarsu tun ta saurayi da budurwa. Sannan ta tuna irin cin kashin da yake yi musu, musamman na ranar ta ce. "Ai wannan kalaman da kake faɗa na fatar baki ne ranka shi daɗe, mu da ka ce fuskokinmu kamar na sumammun birarrika? A'a za ka yi aure ai, ni ma abin da ya sa ka ga na tsaya a kanka, ina duba darajar da ka ba ni a cikin matanka da ba ka taɓa sakina ba. Tun da ni ma ka mutumta ni a matsayina na uwar gida." Shiru Yaya Inu ya yi kunya ta lulluɓe shi, Hansatu ta cigaba ɗebe masa kewa sai da ta fara jin bacci sannan ta wuce ɗakinta. Dai-dai da abincin dare Yaya Inu da ƙyar ya iya ci, haka ya kwana cikin tunani da bacci mara daɗi yana miyagun mafarkai kala-kala. Lokacin da su Uwale suka samu labarin abin da ya faru ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, abin sai ya haɗe mata goma da ashirin ga halin da Ɗan Bishir yake ciki, da zargin da ake yi ya kwashi cuta mai karya garkuwar jiki ga kuma halin da mijinta yake ciki. Da yake dawowar Baba Ibrahim kenan daga wurin aiki, ko gidan bai shiga ba ya ce wa Uwale ta koma shi zai je ya ji abin da yake faruwa. Kai tsaye ƙaramin asibitin gwamnati ƙauyen nasu ya wuce, a can ya samu Baba Sale ana yi masa ƙarin ruwa . Da yake an yi masa allurar bacci sai ya zauna a gefensa yana jiran tashinsa. Kusan zaman awa guda Baba Ibrahim ya yi, sannan Baba Sale ya buɗe idonsa. "Sannu Sale, ya jikin naka?" Baba Sale ya tashi zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi, ya dubi Baba Ibrahim murya tana rawa ya ce. "Yaya ka ji abin da ya faru ko?" Ya gyaɗa masa kai ya ce, "Sale ina son ka saurare ni da kyau don Allah. Na farko dai kai musulmi ne, ka yarda da ƙaddara mai kyau da akasinta. Sannan ka san Ubangiji ne ya ba ka Ɗan Bishir, a lokacin da ba ka yi tsammani ba. Don haka kenan ko a yau Allah Ya yi niyyar ɗauke abinsa zai iya. To me zai sa ka kashe kanka a banza da wofi, ko ka janyo wa kanka ciwo ya kwantar da kai. Lokacin da na zo likitoci sun tabbatar mini ko a asibitin nan ka yi suma ya fi bakwai, don Allah ka kwantar da hankalinka. Yanzu ina son daga nan zan wuce na je na samu Bala Wanzan, da shi Idi Naira na ji yadda aka haihu a ragaya. Idan na ji ta bakinsu sai mu wuce asibiti ɗungurungum a yi haihuwa da hanji, amma babu yadda za a yi a dinga faɗar cuta da fatar baki ba tare da an tabbatar ba." Da sauri Baba Sale ya riƙo hannunsa ya furta. "Yaya zan bi ka, gara a yi komai a kan idona." Baba Ibrahim ya sake haɗai rai ya ce, "Idan ka san za ka yi mini hayaniya ko ka je kana sume-sume gara ka yi zamanka a nan." Cikin sauri Baba Sale ya girgiza kai, Baba Ibrahim ya yi wa lokitocin bayani sannan ya biya su kuɗin ruwa da alluran da ake yi masa; suka wuce Police station. Bayan sun gaisa Baba Ibrahim ya gabatar da kansa sannan ya ɗora da cewa. "Yallaɓai zuwa na yi domin na ji kan zancen abin da ya faru, idan da yuwuwar zuwa asibiti a yanzu sai mu wuce gabaɗaya." Sergent ɗin da ke tsaye ya buɗe wani file ya zaro takarda ya ce, "Alhaji wani mutum mai suna Malam Shehu mai doya shi ya kawo ƙarar Bala wanzan, yana tuhumarsa da cin zarafinsa bayan ya je ƙofar gidansa. Sannan laifin da Bala ya yi har da zagin ɗaya daga cikin ma'aikatanmu, abin da kuma ya sake dagula case ɗin zargin cutar HIV da ake yi wa Alhaji Idi Naira. Yanzu haka shi ma Idi ya kawo Malam Shehu wurinmu, a kan zargin yana ɓa ta masa suna da wannan cutar." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu za mu iya ganin Bala Wanzan ɗin?" "Gaskiya sai dai zuwa gobe idan Allah Ya kai mu." Ɗansandan ya furta. Babu yadda suka iya haka suka wuce gida, sai dai kaso talatin a cikin ɗari na damuwar Baba Sale ta ragu, saboda ya ji an ce Alhaji Idi Naira ya yi ƙarar Malam Shehu zai ɓata masa suna. Mai Yasin tun da ya saka 'Yar gwal a idonsa soyayyarta ta dawo masa sabuwa fil a ransa, haka a ɓangare ɗaya kishinta ya mamaye shi, yana jin tsanar Ɗanladi a ransa don dai kawai yana shakkarsa ne. Yana daga ɗakinsa ya hango ta, ta nufi banɗaki da buta a hannu shi ma ya yi zaraf ya ɗauki buta ya rufa mata baya. Tana shiga banɗaki za ta turo ƙofa ta ji mutum yana ƙoƙarin turowa, suna haɗa ido ta saki murmushi irin na 'yan bariki ta ce. "Mai Yasin namu, ashe a wannan lungun ka lafe?" Mai Yasin ya riƙo hannunta ya ce, "Ga ni kuwa kin gani, wai dama 'Yar gwal za ki iya auren wani namijin ba ni ba?" 'Lallai wannan gafalallan tsohon naka wasa ne.' Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Ka da ka sake kallona a matsayin matar aure, saboda wannan auren nawa shi da babu duk ɗaya. 'Yar gwal ta auri Ɗanladi ne domin ta yi masa tatsar mai, idan ta kwashe albarkar aljihunsa sai ta ƙara gaba." "Sai da ke 'Yar kunama!" Mai Yasin ya yi maganar yana dariya, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce. "Yanzu ni ya za ki yi da ni?" "A'a ka ji da tsohuwar da ka samu, idan fa muka bari suka san alaƙarmu na rantse da Allah ni da kai sai dai mu yi biyu-babu. Kawai mu cigaba da sabgarmu, kowa ya wawuri abin da ya wawura ko a fakaice ma dinga haɗuwa." Guntun tsaki Mai Yasin ya ja, ya ce. "Wa yake ta wata tsohuwa? Ƙila dai a rashinki yau na waiwayi haƙƙina a wurinta." 'Yar gwal ta saki dariya, sannan ta ce ya yi maza ya tafi don kada wani ya gansu. Bayan 'Yar gwal ta koma a tsakar gida ta ci karo da Laraba tana 'yar carafke, tana shiga ta ɗebo wankin rigunan mama da ɗan kamfai ta wurga mata a fuska. Tsaminsu haɗe da warin man bilicin ɗin da 'Yar gwal take shafawa ya bigi Laraba, ta ture su tana yamutsa fuska. "Ke! Wanke mini su yanzu, ina son su fita sosai." Da mamki Laraba take kallon ta. "Ko ba za ki wanke ba? Kika zubo mini ido irin na marasa tarbiyya kina kallo." Laraba ta tashi ta ɗaga wani wargajejen ɗan kamfai, sai kawai ta tuntsire da dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta tsugunna, ta janyo wata warɓeɓiyar rigar mama ta ɗago ta ta sake kwanciya tana dariya. "Don uwarki dariya ma za ki yi mini? Wato ni za ki mayar 'yar iska?" Laraba ta tsagaita da dariya tana ɗan tsuke fuska ta furta. "Kambu... Kada ki sake zagin uwata tana ƙasa, ki zagi kowa nawa ban ta uwata wallahi. Ehe, ba dole mutum ya yi dariya ba wannan ai ya isa na yi hijabi da shi." "Rashin kunya za ki yi mini?" 'Yar gwal ta ƙarasa gaban Laraba a fusace. Laraba ta juya mata baya tana ɗago ɗankwalinta gaba ta ce. "Faɗa wa ƙeya ɗankwali ya ba ki amsa 'yan mata." Laraba tana juyowa 'Yar gwal ta wanke ta da mari, a hargitse Laraba ta ɗago za ta yi magana Ɗanladi ya ƙarasa yana faɗin. "Kin yi mini daidai sanyin zuciyata, wato har yanzu kina nan da iskancinki ko Laraba? Maza wuce ki kwashe su ki wanke kada ranki ya ɓaci." Idon Laraba ya yi ja saboda ɓacin rai, ta harari 'Yar gwal a hankali ta ce. "Allah Ya isa ban yafe..." Tun ba ta gama magana ba, kamar haɗin baki Ɗanladi da 'Yar gwal suka make bakinta, nan take bakin ya fashe amma a dole ta kwashe kayan, ta fara wanki saboda yadda Ɗanladi ya ciro belt zai zane ta da shi. Sai da ta yi wa kayan ruwa kusan huɗu kowanne 'Yar gwal tana cewa bai wanku ba, sai a na biyar sannan suka bar Laraba ta fara shanya a lokacin har an fara kiran sallar isha'i. Jin shirun Laraba ya yi yawa ya sa Inno ta fito daga sashenta, tana zuwa harabar ta ci karo da ita tana shanyar kaya su Ɗanladi suna tsaye a kanta. "Laraba me kike yi haka da daren nan?" Murya tana rawa Laraba ta ce, "Wanki." Inno ta ƙanƙance ido ta ce, "Mene ne wannan kamar ɗan diras? Ke wuce ciki mu je." Da sauri Laraba ta saki na hannunta ta wuce ciki, Inno ta dubi Ɗanladi rai a ɓace ta ce. "Ba baiwa aka sayo muku ba, tun da ba ka da mutumci haka matarka ma ba ta gaji arziki ba wallahi ba za ku mori Laraba. Mun kwana a gida ɗaya, amma ban da mutumci da za ku zo ku gaishe ni." Inno ta wuce sashenta a zafafe. Ran Laraba ya ɓaci sosai, ita kanta ta san a banza ma tana dafa mutum da ruwan jikinsa har ya nuna, ballantana sun taɓo ta da kansu. Don haka ta ci alwashin yadda suka azabtar da ita sai ta rama. Tun da dare ya fara yi Laraba ta fara zarya, tana saka da warwarar abin da za ta aikata, tana wucewa ta ga 'Yar gwal a ƙofar ɗaki tana dama kunun gyaɗa. Da sauri ta faɗa ɗakin Inno, a can drower madubi ta buɗe ta ciro wani maganin hawan jinin Inno, mai saka bacci ta ɓallo guda takwas. A ƙa'ida Inno ɗaya take sha a wuni guda, kuma a hakan ma bacci yake saka ta sosai. Bayan jininta ya sauka ne aka sauya mata wani, don haka ta daina shansa. A cikin ƙaramar farar leda ta zuba su ta ɗebi ruwa kaɗan ta zuba, sai da ya narke sannan ta fita cikin sa'a kuwa ta ga 'Yar gwal ta shiga ɗaki. Da sauri ta matse maganin a cikin jug ɗin kunun, ta juya cikin sauri ta bar wurin. Tana laɓe a bakin ƙofar Inno tana leƙe ta ƙofa, ta ji lokacin da 'Yar gwal ta ɗauka ta shiga ɗaki. Zuciyar Laraba ƙal da haye katifa ta kwanta, tana shirya irin muguntar da za ta yi musu. A fili ta saki dariya, Inno ta wurga mata harara sannan ta ɗauki furar Mai Yasin ta nufi ɗakinsa. Saboda Laraba ta taki mugunta haka ta zauna tunkur, har kusan ƙarfe ɗayan dare. Sai da ta fito cikin sanɗa zuwa ƙofar ɗakin Mai Yasin, ta kasa kunne ta ji munsharin Inno da Mai yasin sannan ta saɗaɗa ta fice daga sashensu ta isa ɗakin Ɗanladi. A yadda ta fahimta sun jima da yin bacci, don lokacin da ta ɗaga labulen ɗakin a ƙasa ta gansu sun ɓingire suna bacci, 'Yar gwal tana jingine da bango da kofin kunnu a hannunta. Sai da Laraba ta saka ɗankwali ta rufe fuskarta, sannan ta ɗauki sauran kunun ta juye mata a fuskar. Wani tunani ne ya faɗo mata ta fita da sauri, ta ɗauko jarkar ruwa irin ta 'yan-ga-ruwa ta tuttule musu ruwan gabaɗaya a ɗakin. Ta janyo galan ɗin man gyaɗarsu ta sheƙa a ƙafafuwan 'Yar gwala da Ɗanladi, ta kai jarkar man ta saƙala mata a hannu. A hankali ta lalallaɓa ta ja ƙafar Ɗabladi sai ta ji ya tafi yaraf, daga shi da ma sai gajeren wando da singlet. Ta ɗauko ƙaton omonsu ta zazzage masa a jiki zuwa fuska, har ta je za ta fita ta hango belt ɗinsa da sauri ta ɗauka ta fara zabga musu ɗaya bayan ɗaya. Sai da ta ga sun fara motsi sannan ta fice daga ɗakin da sauri, ta nufi ɗakin Inno. Tana zuwa ta shige bargo ta kwanta tana dariyar ƙeta, babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita. Mai Yasin tun da ya sha fura suna hira da Inno ya ga bacci ya ɗauke ta, bai tashe ba don shi ma ba son tafiyarta ɗakinta yake ba. Yana gama shan furar babu jimawa shi ma bacci ya ɗauke shi, ba shi ya farka ba sai kusan uku saura na dare. Inno cikin bacci ta fara jin alamun ana lalubar mamanta, da yake bacci ya sha kanta cikin magagi ta ce. "Laraba wani wulaƙanci ne kike ji da shi haka?" Shiru Mai Yasin ya yi ya ci gaba da sabgar gabansa, Inno ta gyara kwanciyarta jin har lokacin ba a daina lalubarta ba, kuma har lokacin idonta a rufe yake da sauran bacci a kanta ta furta. "Laraba zan ci mutumcinki fa." Mai Yasin ya kashe murya, shi a dole yana son lallamar Inno don kar ta ba shi matsala ya ce, "Wannan Ɗanlami ne ba Laraba Innota." Firgigit Inno ta yi ta ware idonta, a rikice ta ce. "Malam mene ne haka?" Mai Yasin ya kashe mata ido ɗaya ya ce, "Haba Innoniyata, kamar wata 'yar sha uku duk kin firgice. Sharuɗɗan aure ne fa nake son cikawa." Inno tana shirin ture Mai Yasin ya murɗe 'yan hannuwanta, ta yi mamaki matuƙa yadda ta ji ta kasa kataɓus. Don ba ta taɓa tsammanin yana da ƙwari haka ba, Inno babu yadda ta iya haka ta zubawa sarautar Allah ido. Tun tana tsine wa Mai Yasin a zuciyarta har ta fito fili, don shi da ita sun yi yarjejeniyar auren ɗauko mini buta suka yi. In Shaa Allahu wannan shi ne shafi na biyun ƙarshe, gobe zan gama free pages. Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA SHA UKU Inno har gari ya waye ban da hawaye babu abin da take yi, da ta kalli Mai Yasin ban da kallon tsana babu abin da yake wurga masa. Shi kuma Mai Yasin ban da juyi a katifa babu abin da yake yi, saboda wani bacci da ya samu mai cike da kwanciyar hankali. Jin shasshekar kukan Inno ce ta farkar da shi, ya ɗago cike da shauƙi ya ce. "Innota! Haba Innota, me ya sa kike son ɗaga mini hankali da farar safiya haka? Maimakon ki zo na ninke ki a bargo, mu cigaba da baccin cikar fariciki amma sai ki ɓa ta ranki a banza. Ko me na yi miki ai soyayya ce, haba Innaniyota!" Inno ta share hawaye, a hankali Mai Yasin ya dinga fasa mata kai yana yabonta tare da nuna mata zallar soyayya. Saboda ya lura da abin da Inno ta fi so, ya kuma fi saurin sace zuciyarta da shi. Nan take ta saki jikinta, sannan ta miƙe za ta fita da sauri ya ce. "Inno me za ki fita ki yi, kina fama da kanki?" Inno ta jingina da jikin ƙofa ta ce, "Abin kari zan haɗa mana..." "Allah Ya sawaƙe ki fita ki haɗa kayan abinci, da kanki kina fama da ɗanyan jiki." Murmushi Inno ta saki har cikin ranta ta ji daɗin kulawar da yake ba ta. "Bari ki ga na je wurin Sule mai shayi, na kaso mana dubu biyar ɗin nan." Da sauri Inno ta ce, "Malam dubu biyar fa?" Cike da son nuna burga Malam Ya ce, "Dubu biyar ɗin banza, ni duk yawan kuɗi ba kin fiye mini su ba Innota." Kan Inno ya ƙara girma, za ta fara magana wayar ta ta fara ringing. Malam ne ya miƙa mata, sai da ta ɗauka ta kai kunnenta sannan ta gane muryar aminiyarta ce, kasancewar sabuwar wayar da Fadil ya sauya mata, ba a iya saving da shaidar mota ko jirgi da a baya ake yi mata. "Assalamu Alaikum, Hajiya Goggo barka da safiya." Daga can ɓangaren Goggo ta ce, "Wa alaikissalam, barka dai amarsu. Inno ga mu nan a tasha yanzu motarmu za ta taso." Cike da farinciki Inno ta ce, "Kai amma dai gaskiya kin yi mini bazata, Allah Ya kawo mini ke lafiya." Goggo ta amsa da Amin sannan ta furta, "To agaida mana angonmu kafin mu zo, don na ji muryarki ta sauya amarci ya karɓe ki tsohuwar nan." Inno da Goggo suka saki dariya lokaci ɗaya, daga haka suka yi sallama. Ba tun yau ba Mai Yasin yake jin labarin Goggo a wurin Inno, a lokacin aurensu ma ta so zuwa wani jikanta ya rasu don haka ta ɗaga zuwan sai daga ba ya. Tun bayan fitar Laraba sama-sama suka dinga yunƙurin buɗe idonsu, amma fatar idanunsu ta yi wani irin nauyi don haka suka gagara buɗewa. Sai dai wasu abubuwan da suka faru gani suke yi kamar a cikin mafarki ne. Ɗanladi da 'Yar gwal ba su suka farka ba, sai kusan ƙarfe tara na safe. Ɗanladi ne ya fara farkawa ya ji jikinsa duk ya yi tsami, a hankali ya buɗe idonsa ya ci karo da ɗakin ya yi jaga-jaga. Ransa ne ya ɓaci da ya ci karo da mai ya yi luntsum a tsakar ɗakin, ga jarkar man a hannun 'Yar gwal ta yi share-share a ƙasa tana munshari. A fusace ya ƙarasa wurin da take yashe, ya tsinka mata mari wanda ya sa ta miƙe tsaye a gigice. "Tsabar iskanci dama ba ki daina shaye-shayen da na hana ki ba? Dubi irin rashin mutumcin da kika yi mana?" Da mamaki 'Yar gwal take bin jikinta da ɗakin da kallo, ta dafe kumatu ta ce. "Ni ka mara?" A harzuƙe Ɗanlami ya ce, "An mare ki ko za ki rama? Da yake har lokacin maganin bai gama sakin ta, ta yi luuu da idanu ta furta. "Wallahi ba ka mari banza ba sai na rama." "Ashe kuwa zan yi miki ɓarin makauniya, tsabar rashin mutumci in saka sama da dubu goma sha na sayi jarkar mai ki rubar a ƙasa. Wallahi yau sai kin gane ke ƙaramar ƙwaya kike sha." A zabure 'Yar gwal ta miƙe tsaye tana kaɗa ƙugu ta ce, "Ƙwayar ma ai mataki-mataki ce, billahillazi sai na nuna maka ko a gidan giya akwai babba. Kai ba wani shege fa." Daga haka ta cakumi wuyan Ɗanladi, ganin haka ya sake ɓa ta ransa don haka ya shiga kai mata duka ita ma tana ramawa. Kasancewar ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba, ya sa 'Yar gwal ta fara laushi. Wannan ya sa, ta ɗauki wani burugali a bayan ƙofa ta ranƙwala masa a goshi, nan take goshinsa ya yi wani tsororo ya kumbure suntum. Azaba ta sa Ɗanladi ya kai mata naushi a ba ki, sai ga bakin 'Yar gwal ya fashe har haƙorinta ɗaya na gaba ya faɗo. Kafin wani lokaci tuni bakin ya kumbure sai sheƙi yake yi. Sai da suka jigatu don kansu sannan suka faɗi gefe, ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba. 'Yar gwal ta fara tattara kayanta tana kuka, hakan ya sa jikin Ɗanladi ya yi sanyi. Ya tsugunna a gefenta cikin tattausan lafazi ya furta. "Me kike yi haka 'Yar gwal?" Ba ta tanka masa ba, ta cika akwatinta, ta fizgi mayafi ko wanke fuskarta ba ta yi ba saboda ɓacin rai za ta fita. Da sauri ya janyo ta, ta faɗo jikinsa ya ce. "Haba 'Yar gwal, don Allah ki yi haƙuri kin san dai ba zan iya rabuwa da ke ba. Wallahi ɓacin ran abin da kika yi mini ne ya sa haka, ke ma kin san ba ki kyauta ba." Har a ranta ta ji daɗi saboda ita ma dama ba ta yi niyyar tafiyar ba, ta yi hakan ne don ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Ta janye hannunsa fuska a haɗe ta ce, "To ai gara na ba ka wuri tun da hakan shi ya fiye maka, da ka dinga tuhuma ta a kan abin da ba ni da masaniya." Shiru ya yi yana nazari, don shi ma a iya saninsa dai 'Yar gwal ta daɗe ba ta shaye-shaye, kuma ko ta bugu ba ta irin wannan ɓarnar. "Yar gwal jiya bayan mun sha kunu me ya faru?" Ba ta ba shi amsa ba, ta taɓe baki. Wani irin tsoro ya kama shi, don ya ga jikinsa da na 'Yar gwal duk sun yi ruɗu-ruɗu. "An ya ɗakin nan babu aljanu kuwa?" Ya yi tambayar cikinsa yana kaɗawa, 'Yar gwal ta ce, "Ah to gidanku ne dai, ka fi kowa sanin yadda yake ai." Ɗaladi ya jima yana rarrashin 'Yar gwal, daga ƙarshe dai ta haƙura. Shi da kansa ya shiga gyaran ɗakin, don 'Yar gwal cewa ta yi ba za ta taɓa komai ba. Washegari tun da farar safiya Zuly matashin kai ta dokowa Yaya Inu waya, cike da kissa take yi masa kalaman tausasawa domin tana son sake karɓar kuɗi a wurinsa. Yaya Inu duk damuwar da yake ciki lokaci ɗaya ta yaye, ya miƙe a hankali ya saka wata jallabiyyarsa ya fice. Ƙofar gidansu Zuly ya ƙarasa, ya kai mata dubu goma sha biyar kamar yadda ta buƙata. Ta kashe masa ido ta ce, "Yanzu fa nan da awa biyu zuwa uku na zama taka. A gaskiya duk macen da ta yi sa'ar samunka ta yi dacen miji." Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Waɗannan kalaman na ki suna sake birkita ni Zulyta. Yanzu dai bari na wuce gida na sallami waɗancan mutanen, na fara shirin tafiya ɗaurin aure." Zuly ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Tun yanzu baby?" Yaya Inu cikin tausasa lafazi ya ce, "Sai yadda kika ce." Zuly ta yi wani far da ido ta ce. "Ni na isa, Allah Ya taimake ka aje ayi yadda ya dace. Don na fi son mijina ya zama adali." Yaya Inu sai da ya yi da gaske sannan ya tafi daga wurin Zuly, yana tafiya ta wuce gidan Hajiya zuma mai magungunan mata. Ta kai mata dubu biyar cikon kuɗin magungunan da take bin ta. Saboda ba ƙaramin haɗi ta yi mata ba, don ta ci alwashin kafin ta fito daga gidan Yaya Inu sai ta tatike shi tsaf, domin ba da niyyar zama ta je ba. Don haka ta je aka saka mata inplan, don ma kada ta ɗauki ciki. Tun da hantsi ya yi suka ga shiru Mai gari bai fito ba, Azeema ce ta shiga ɗakin saboda dama girkinta ne. A zaune ta samu Mai gari ya haɗa kai da gwiwa yana hawaye, hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Jiki a sanyaye ta zauna kusa da shi ta ce, "Ranka shi daɗe lafiya? Me yake faruwa da kai a farar safiyar nan kake kuka?" Mai gari ya ja majina yana sharce hawaye, ya saka hannu ya dafe saitin zuciyarsa da yake bugawa da sauri ya ce. "Azeem ina cikin wani yanayi mara musaltuwa, zuciyata tana cike da muradin da ban san lissafin da mutane za su lissafa a kaina ba." Azeema ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun shekaran jiya na fara lura da sauyinka ranka shi daɗe, amma na yi maka tambayar duniya ka ce mini babu komai. Mene ne a zuciyarka da yake damunka?" Kai tsaye Mai gari ya ce, "So ne, so ne yake nuƙurƙusar zuciyata kuma ban san a lokacin da ya yi mini kamun kazar kuku ba. Yanzu haka na takure kaina a ɗakina ne, saboda kada na fita fada zuciyata ta fisge ta zuwa gidansu." "Wace ce ita?" Ta wurga masa tambaya. "Laraba ce Azeema, wallahi zuciyata har wani tartsatsi take a kanta." A razane Azeema ta ce, "Laraba tsidigu dai? Eh lallai dole ka ce jarabta. Ranka shi daɗe ko dai mafarki kika yi, ka rasa wacce za ka so sai waccan sheɗaniya hatsabibiyar yarinyar Lara..." Ba ta gama magana ba, Mai gari ya gwaɓe mata ba ki ya fashe. "Kada ki sake danga ta mini Laraba da shaiɗanu, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Tsoro ne ya kama Azeema, jikinta a sanyaye ta fice daga ɗakin domin ba ta tantama akwai ciwon da ya samu mijin nasu. Kamar yadda suka tsayar da magana, a washegari Baba Ibrahim da Baba Sale har da Ɗan Bishir suka sake komawa police station. "Alhaji na yi mamaki ƙwarai da na ji an ce case ɗin naka ne? Me ya yi zafi haka?" Baba Ibrahim ya tambayi Alhaji Idi Naira. Alhaji ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Wani zance ne ya fara yawo a cikin garin nan, wai ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki Dr, ni kuma a iya sanina ba ni da ita. Da na bi diddigin maganar, sai aka ce an samo zancen daga wurin Malam Shehu, don haka na kawo shi ƙara. Sai bayan na zo na ci karo da Bala wanzan a nan , ni kuma ba zan laminta ba har sai an bi mini haƙƙina. Daga nan ma kotu nake son a tura mu." Malam Shehu ya yi fiƙi-fiƙi cike da tsoro ya ce. "Wallahi tallahi ni ma ba ni na faɗa, jita-jita na ji ana yi kuma sai aka yi sara a kan gaɓa. Ni kuma ina ganin kamar Bala wanzan ya sani, amma ya munafurce ni." Bala wanzan ya zaburo yana faɗin, "Amma ai kai ka kawo hukuma har gida suka tafi da ni, ka ce na yi maka aski wai kai ma kana zargin ka kamu." Jin hayaniya tana neman kacamewa wani Sergent ya buga musu tsawa yana faɗin. "Ba ma son hayaniya, kai Bala tun da kai aka fara kawowa ka yi musu bayani." "Ni dai tun da nake ban taɓa yi wa Alhaji Idi Naira aski ba sai wannan karon, ya kira ni har gidansa na yi masa aski da gyaran fuska. To bayan na fito daga gidansa, sai na wuce gidajen iyayen yara da dama na yi wa 'ya'yansu kaciya, wasu ma har aski na yi wa iyayensu. Sai kuma jarirai biyu da na cirewa hakin wuya. Bayan kwana biyu, sai na fara jin surutun wai Alhaji Idi Naira yana ɗauke da cutar ƙanjamu. Kwatsam! Ina zaune sai ga jami'an tsaro su zo da Malam Shehu, su ka tattaro ni suka yi awon gaba da ni." Sergent ɗin ya gama rubuta jawabin Bala wanzan, sannan ya dubi Idi Naira. Idi Naira ya shiga wurga wa Malam Shehu harara ya ce. "Yallaɓai wannan mutumin ya ci mutumcina, ta hanyar yi mini ƙazafin da ban ji ba ban gani ba. Kawai saboda kwanaki na yi fama da rashin lafiyar farankama, shi ne aka fara yawo da ni wai ina da ciwon ƙanjamau. Har wasu suna cewa ƙurajenta sun fito mini." Ƙuri Baba Sale ya yi wa Alhaji Idi Naira yana kallo, saboda irin ramammun mutanen nan. Idi Naira ya ɗora da cewar. "Dr kai ne likita, saboda Allah ina haɗin cutar farankama da ƙanjamau? Ko saboda kullum sun ga ina lalacewa kamar ɗibana ake yi? Ni lafiyata ƙalau, masifar uwar gida da amaryata ne suka saka ni a gaba." Sai a lokacin Baba Ibrahim ya numfasa jin musu da hatsaniya ta fara kacamewa ya ce. "A'a gaskiya babu haɗi ma tsakanin cutar ƙanjamau (HIV) da cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX). Tun da ita cutar ƙanjamau wato HIV (Human Immunodeficiency virus), cuta ce da take karya garkuwa da kariyar jikin ɗan'adam. Ta yadda za ta ba wa ƙwayoyin cututtuka damar shiga jikin salin-alin, ba tare da wata kariya ba. Alamomin cuta mai karya garkuwar jiki sun haɗa da: Ɓarkewar zawo, yawaitar kaluluwa, matsanancin zazzaɓin da ya ƙi jin magani har zuwa lokaci mai tsawo, ciwon maƙoshi, yawaitar fitowar ƙuraje babu dalili, gumin dare koda lokacin sanyi ne, ramewa da rashin cin abinci, tashin zuciya da amai sai tari mai ɗaukar lokaci ba tare da ya ji magani ba." Cikin Alhaji Idi Naira ya kaɗa sosai, saboda yana jin kusan kaso mai yawa na alamomin da ya ji Baba Ibrahim ya lissafa. "To amma wani hanzari ba gudu ba, koda mutum ya ji irin alamomin da na lissafa ba zai ce kai tsaye yana da cutar ba, har sai ya je asibiti an gwada shi kuma an tabbatar." Jin furucin Baba Ibrahim ya sa Alhaji Idi Naira ya sauke ajiyar zuciya, Bala Ibrahim ya cigaba. "Amma ita cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX), ƙwayoyin virus na varicella-zoster ce take haifar da ita, cutar tana iya kama yara da manya. Kuma ana iya ɗaukarta ta hanyar shaƙar numfashin mai ɗauke da ita, cin abinci, makwanci ko wasanni tare.Tana saka ciwon ciki, zazzaɓi mai zafi, firgita, jajayen ƙuraje masu ɗurar ruwa, da matsanancin ƙaiƙayi. Mafita ɗaya ce a kiyaye haɗa mai cutar da wanda ba shi da ita, yin gaggawar zuwa asibiti domin bada agajin gaggawa. Killace mai fama da ita, da karɓar rigakafi." Baba Ibrahim ya dubi Idi Naira ya furta, "Ka ga kenan babu alaƙa tsakanin cutar ƙanjamau da farankama Alhaji, amma duk ba wannan ba, yanzu ku tashi sai mu wuce asibiti gabaɗaya a yi muku gwajinta domin kowa ya fita daga zargin." Cikin Alhaji Idi Naira ya ɗuri ruwa saboda shi kansa ba shi da tabbacin rashin cutar, sakamakon idan ya tafi Lagos har ya dawo da matan banza yake mu'amala. Ya haɗe fuska tamau ya ce. "Dakata Dr, babu inda zan je ni lafiyata ƙalau." Ganin borin kunyar da Idi Naira yake yi ya sa kowa ya aminta da tabbas biri ya yi kama da mutum, domin rashin gaskiya ya bayyana ɓaro-ɓaro a fuskar Alhaji Idi Naira. Yaya Inu yana komawa gida daga wurin Zuly matashin kai ya samu Hansatu da Larai sun riƙo Salame ranga-ranga za su tafi da ita asibiti. "Subhanallah! Hansatu lafiya?" Yaya Inu ya furta a razane. "Wallahi Mai gida jikin ne ya rikice ina jin haihuwar ce ta zo." "Allah Ya ba ta lafiya, yanzu ina za ku kai ta?" Kai tsaye hansatu a ce. "Asibiti, saboda jikin ya ba ni tsoro." A gwasale Yaya Inu ya ce, "Yanzu haihuwar ce har sai kun yayime ta zuwa asibiti? A can ɗin rage mata zafin ciwon za su yi?" Haushi ya sa Hansatu ta yi gaba ba tare da ta kula shi ba. Shi ma daɗi ya ji saboda ya san ƙarshen zance a ce ya kawo wani abin. Fadil ne ya ɗauke su a motarsa ya wuce da su asibitin ƙwararru na Malam Aminu Kano (AKTH). Kasancewar a can yake aiki, kai tsaye ɗakin haihuwa aka wuce da ita domin a duba ta. A gwaje-gwajen likitocin ne suka tabbatar da ba ciki ba ne, sai dai ba sa ganin komai a cikin nata. Hankali a tashe Hansatu ta kira Yaya Inu, a lokacin ya ci babbar rigarsa zai tafi ɗaurin aurensa. "Mai gida akwai damuwa ciki dai na jikin Salame ashe ba ɗa ba ne." "Mene ne idan ba ɗa ba? Hansatu kada ku janyo mini masifa a farar safiyar nan. Ni fa ba na son damuwa, yanzu haka ɗaurin aurena da Zuly zan tafi." Baƙin ciki ya sa ƙwalla ta zubo wa Hansatu a ƙufule ta ce, "Yanzu abin da za ka ce mini kenan? Mai gida kana nufin Zuly ta fi 'yarka Salame?" "Hansatu kada ki ɓata mini rai, kin san dai jiya a yadda na kwana. Auran nan da za a ɗaura ne kawai yake ba ni ƙwarin gwiwa, har kika ga ina walwala. Ke bari na wuce kada ki ɓa ta mini lokaci, saboda matashin kai ta ce mini waliyinta wutar ciki gare shi zai iya tafiya idan na makara." Daga haka Yaya Inu ya katse, ya tura waya a aljihu ya rufe ɗakinsa sannan ya fice. Yana kai kansa zai fita a ƙofar gida ya ci karo da Mai gari shi da su Sanƙira, cike da girmamawa mai gari ya russuna ya ce. "Barka da fitowa!" Hannuwa biyu Yaya Inu ya kai ya fara shafa idonsa, a ransa yana ayyana ko dai gizo idonsa ya yi yake nuna masa Mai gari ne yake tsugunna masa. "Ranka ya daɗe ya haka kuma?" Mai gari ya russuna ya ce, "Duk girmanka ne ai, ga wannan a rage da abincin yara." Sanƙira shi da Muzammil, suka shiga kiciniyar sauke buhunhunan kayan abincin daga cikin kura sannan suka tafi. Mai gari har zai juya da sauri Yaya Inu ya tsayar da shi. "Ranka shi daɗe ni fa ka saka ni a duhu, waɗannan ɗin na mene ne?" Mai gari ya shafa kai ya ce, "A da dai ban yi niyyar sanar da kai yanzu ba, amma na ga kana neman ƙarin bayani ne Baba. Magana ta gaskiya Allah Ya jarabce ni da son Laraba, kuma aurenta nake son yi." Yaya Inu ya bayyana mamakinsa a fili, saboda duk cikin yaransa babu mai baƙin jini da samari ba sa kulawa kamar Laraba. Amma ganin irin rawar ƙafar da Mai gari yake yi masa, da tarin arzikin da zai samu ya sa ya ce. "Idan ma yanzu a shirye kake, ka wuce mu je masallaci domin yanzu haka ni ma ɗaura mini aure za a yi!" Cike da shauƙi Mai gari ya ce, "A yi haka kuwa?" Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Me ya rage Mai gari? Ni ma ai an sauƙaƙa mini wannan bidi'ar wunin bikin, da mata za su zo su yi ta cinye abinci." Godiya sosai Mai gari ya yi, ya ce zai je ya sauya kayansa sannan ya ƙarasa. Hakan kuwa aka yi, Mai gari yana zuwa masallaci ana gama ɗaurin auren Yaya Inu da Zuly matashin kai. Yana zama ya miƙa wa Malam Liman sadaki ya zama waliyinsa, aka ɗaura aurensa da Laraba a kan sadaki naira dubu ɗari. Fitar Yaya Inu daga gida babu jimawa Goggo ta ƙarasa, almajirai ne suka shiga da ƙullin kayanta. Inno tana hango ta, ta ƙarasa wurinta cikin farinciki ta rungume ta tana faɗin. "Lale marhabun yau ga mutanen Jibiya." Goggo ta saki murmushi ta ce, "Ga mu Allah Ya kawo mu, wai ina Laraba ban ji motsinta ba?" "Idan kika bibiya ta fita ta ɗauko mini magana, yarinya yadda kika san rainon ifiritu." Goggo ta saka dariya cike da zolaya ta ce, "Ni kam wai Inno hala yaron ciki gare ki? Irin wannan ƙyalli da kike yi haka." Inno ta saki guntun tsaki ta furta, "Wuce mu je ku gaisa da Malam, kafin mu shiga ki fara zuba mini labari." Tun shigar Goggo gidan da Mai Yasin ya ji muryarta, ƙirjinsa ne ya yi wata irin bugawa da ƙarfi. Haka kawai ya ji gabansa yana faɗuwa, jin muryar matar da ko a duniyar mafarki ba zai manta da ita ba. Da sallama ɗauke a bakin Inno suka shiga ɗakin, Mai Yasin yana ɗaga ido karaf ya sauka a kan Goggo da ta daskare a wurin. "Malam Jafaru! Dama tsawon shekaru a nan ka laƙe bayan ka halake mini dukiyar marayu? Allah na gode maka, tabbas addu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza. Azzalumi maha'inci, ka ci amanata kuma ka tafi ka bar ni da ƙallagaggen aurenka a kaina." Mai gari ya jima bai yi farincikin da yake ciki a wannan ranar ba, saboda mallakar Laraba da ya yi ji yake kamar ya mallaka faraincikin duniyarsa gabaɗaya. Yaya Inu ne ya sanar da shi tariyar Laraba, za ta kama sati mai zuwa saboda 'yan saye-sayen kayan ɗaki da za a yi mata. Bayan sallar Isha'i Zuly matashin kai da wasu fanɗararrun ƙawayenta biyar, suka yi mata rakiya zuwa ɗakin miji. Dama da rana ma tare da ita aka yi jere, don haka da za a kai ta suna tafe suna hira. Zaune take a ɗakin ta, tana jiran shigowar Yaya Inu hayaniyar yaran ta cika mata kunne. Cike da izza ta fita tsakar gidan a gadarance ta ce. "Ku waɗanne irin dabbobi ne, ku da yaranku da za ki dinga tunɓele da dare?" Indo da dama zuciyarta take cike da kishi fal ta ce, "Yadda muka zama dabbobi, sannu a hankali ke ma za ki zama dabbar, har ki haifo balami a ciki gaba da yin tamɓelen da shi." A daidai lokacin Yay inu ya shigo, yana shigowa duka yaran suka nustu suna yi masa sannu da zuwa, ko ƙurarsu bai kalla ba ya wuce wurin Zuly ya kamo hannu ta suka wuce ɗakinsa. Sabuwar hira suka dasa suna ƙyalƙayala dariya, zuciyar Indo kamar za ta buga, tun tana tsakar gida tana jin hirarrakinsu har dare ya yi ta shige ɗaki ta kwanta. Ganin Yaya Inu ya ja filo da abin rufa ya sa Zuly matashin kai ta ce, "Yaya haka ne masoyi? Ban gane ba an yi gabas da kare." Ƙirjin Yaya Inu ya buga amma sai ya basar ya ce, "Na gaji ne kin san fa yau na sha baƙi." Zuly ta ɗan tsuke fuska ta ce, "A'a ai kuwa haka za ka yi haƙuri ka tashi, don ni in saluɓe namiji ba abu ne mai wuya a wurina ba." Tsoro da kunyar Zuly ya mamaye shi, saboda tun da yake aure bai taɓa auro fitsararsiyar mace irinta ba. A ɓangare ɗaya kuma bai san me zai ce mata ba, hasali ma wata irin kunyarta yake ji. Yana cikin nazari, ya ga Zuly ta miƙe tsaye tana warware ɗankwalin kanta ta ce. "Na ka wasa ne Malam Inusa, ai ni ba na sanya. Ba ka ji ma laƙabin sunana ba matashim kai? Bari ma ka gani." Zuly ta ƙarasa maganar tana fisgo siraran ƙafafuwan Yaya Inu. Ya auren Yaya Inu da matashin kai zai kasance? Shin Yaya Inu yana warkewa ko ya tafi kenan? Wacce badaƙalar za a yi a gidan Mai gari da Laraba? Shin za ta so Maigari ko shi yake wahalarsa? Ina matsayin auren Inno da Mai Yasin? Yaya Mai Yasin zai yi tun da asirinsa ya tonu? Zai zauna da Goggo da Inno ko yaya? Mene ne a cikin Salame idan ba ɗa ba? Ya matsayin gwajin da za a yi wa su Ɗan Bishir? Yar gwal da Ɗanladi zaman su zai ɗore? Duka waɗannan tambayoyin da ma waɗansu, amsarsu tana cikin cigaban littafin GIDAN LIKITOCI. AlhamduLillah, a nan na kawo ƙarshen free pages ga me son ci gaba za ta biya ta 500 Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚