👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ *BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM* Da sunan ALLAH mai rahama mai jin ƙai. Ya Allah ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'umma, ka kuɓutar da hannu na daga rubuta abinda zai cutar da wani na da ni kai na. ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @watpadd Sultywrites22 STEP 1 PAGE _______1 & 2 Tsananin zafin ranar daya tsananta ne yasa ta sake duba wayarta a karo na ba adadi, daidai lokacin da agogon ya nuna ƙarfe 1:30pm, sautin ƙaraurawar tashin dalibai data jiyo ne ya sata sauke zazzafar ajiyar zuciya. Matashiyar budurwa ce mai matsaƙaitan shekaru, kyakkyawar gaske, olive skin colour ne da ita me matuqar ɗaukan ido, fuskarta ta kasance oval shaped, ga wasu deep eyes dake gare ta masu matuqar haske yayin da eyeballs ɗin suka kasance masu dan tsini domin ba flat suke ba gabaɗaya, tana da yalwar gashi wannda hakan ya gaza ɓoyuwa saboda wasu kwantattun gashi da suka zagaye goshinta har zuwa gefen kunnuwanta, haka zalika gashin girarta da na idanunta kamar Wadda tayi fixing, tana da hanci dan daidai tare da ƙaramin baki me launin light brown. Kaɗan kaɗan take buga wayar hannunta a Kan lips ɗin ta tana kallon yaran dake rububin fitowa daga makarantar, wata kyakyawar yarinya ce da baza ta wuce shekaru 7-8 years ba ta fito tana kalle kalle. "Shazeen". ta ƙwalawa yarinyar Kira Wanda hakan yasa ta juyowa da sauri zuwa saitin da taji kiran, kwasowa tayi a guje tana zuwa ta faɗa jikinta cikin jin daɗi ta ce, "Aunty Hushaima yau kinzo da wuri". "Eh, Amma na sha dukan rana ai, maƙaryaciya kawai, kika cemin yanzu 1pm Ake tashin Ku? Yaya baya zuwa ɗaukanki har sai kowa ya watse yake zuwa?". "Whl ALLAH Aunty Hushaima 1pm ne, yau ma assembly ɗin da aka sakeyi yanzu ne ya sa ba a tashemu kan lokaci ba, kuma ma munyi practical na tie and die ne, kinga ba". Ta ƙarashe Tana nuna Mata hannuwanta da gaban rigarta da sukayi staining. Riqo tsintsiyar hannunta tayi suka fara tafiya tana faɗin, "Kun sha tie and die Kam, sai muje gida ki zauna ki wanke kayan tas". "Aunty Hushaima ki siyamin aipo ki gani, whl tas zan fidda su, na fiki iya wanki ai". Ta faɗa tana ɗan cilla ƙafa irin yadda yara keyi idan wani Abu ya musu daɗi. "Ai bakin ki ne aipo ɗi......" Maganar ta ce ta tsaya sakamakon caɓin da ya wanke su gabaɗaya har fuskarta, ba shiri ta saki hannun Shazeen tare da dage hannayen ta sama tana kallon white palazzo ɗin ta da gabaɗaya ya ɓaci. "Kam burauban can". Ta faɗa cikin ɓacin rai tare da ɗagowa idanunta suka sauka Kan wasu shegun motoci guda biyar baƙaƙe sidik kirar mercedes benz GLE class, dukkan su a rufe suke da tinted glass hakan yasa ba'a iya ganin na cikin sai dai na ciki yaga na waje, kana ganin motocin kasan ba na qananun mutane bane. Ganin yadda sukayi wucewar su yasa ranta ƙara ɓaci cikin zafin nama ta sunkuya ta wawuri wani qaton dutse ta seta motar dake ƙarshe bata ƙarasa barin layin ba ta wurga mata sai ji kake tass glass ɗin baya ya tarwatse, dama abunka da ya sha rana, salati mutanen dake wurin suka fara yi yayin da wasu suka dafe bakunan su cike da tsantsar fargabar abinda zai je ya dawo da kuma mamakin ƙarfin hali irin nata. Wani dattijo da ya riqo hannu wasu yara biyu dake sanye da uniform ɗin makaranta irin na jikin Shazeen ɗin ya ce , "Ke kuwa jikata me ya kaiki taɓo irin wa'anna mutanen, da yawa yawan su basu san darajar ɗan Adam ba, yanzu haka kika bibiya ɗan wani babban ne, su na jin kansu da girma kamar su suka shimfida ƙasar sai sa suke yin yadda suka ga dama, su taka Wanda suka so a lokacin da suka so kuma su zauna lpy". Cikin qunar rai ta ce, "To ai Baba daɗin ta ƙasar ta ALLAH ce ba mallakin wani ba bare yayi iko da ita, kuma mulki da arziki ai duk na ALLAH ne shi ke bada wa ga wanda yaga dama haka kuma jarrabawa ce ga duk wanda ya bawa, Kuma yana iya karɓe kayan sa a duk lokacin da yake so, kuma duniya bata da tabbas tunda rigar aro ce k........." Maganarta ta katse sakamakon motocin da sukayi parking a daidai saitin su, cikin rawar jiki dattijon nan yaja hannun yaran suka bar wurin. Ita kuwa ba tare da wani fargaba ba ta nufi wurin su tana ƙara haɗe girar sama data kasa, wasu garadan mutane ne suka fito kallo ɗaya zaka musu ka shaida excort ne saboda shigar dake jikin su ta baqaqen kaya, fuskar nan kuwa in ka kalla sau ɗaya baza ka so sake kallo ba. Ɗaya daga cikin su ne ya matso inda take tare da fidda hannu ya zabge ta da marin da sai da tayi taga taga kamar zata faɗi tayi saurin dafe motar, hannunta akan kuncinta, wasu stars ne kawai ke kai kawo daga idanunta zuwa cikin kanta. "Ke dabbar ina ce? Kinsan nawa ne glass ɗin motar da kika fasa? to ko duk dangin Ku aka haɗa baza a samu rabin kuɗin ba...." kasa ƙarasawa yayi saboda saukar marin bazatan da yaji, da mamaki ya ɗaga kai yana kallon yadda take huci, juyawa yayi ya kalli ɗaya abokin aikin nasa take sauran suka firfito suka zagaye su. Ba tare da ta dubi ko da ɗaya daga cikin su ba ta ce, "kai ɗin banza kai ɗin wofi, kana me gadi dakai har zaka ɗaga hannu ka mare ni sannan in tsaya kallon ka, ba'ayi wannan halittar ba Whl ". Shi dai har lokacin bai fita daga shock ɗin marin ba tunani ma yake itan ce ta mare shi ko kuwa dai wani ne, dan ya kasa yadda cewa akwai mace mai ƙarfin halin da zata iya kallon sa sannan har ta ɗaga hannu ta wanke shi da mari kamar haka, ballantana wannan yarinyar da dukkanta bata ƙarasa ko ƙirjin sa ba. Gyaran muryar da akayi ne yasa duk suka ɗago suna kallon direction ɗin da sautin ya fito, wani kyakkyawan matashi ne tsaye kana kallon sa kasan ALLAH yayi halitta, duk da kuwa duk gulmar ka baka isa cewa ga kamannin sa ba saboda fuskarsa dake rufe, sanye yake da white kaftan ɗinkin monogram da yayi fitting ɗinsa sosai, kansa sanye da p cap black haka idanunsa suna cikin wani sunshade da ya cinye kusan rabin fuskar sa, daga kan hancin sa kuwa zuwa bakinsa noes mask ne wanda hakan ya ɓoye kamannin sa sai abin da ba'a rasa ba, ƙafarsa tana sanye cikin white prada wetlook loafers. "Aram! Meke faruwa?". Ya tambaya da wata irin nutsatstsiya kuma kamilalliyar murya. Cike da ɓacin rai da har lokacin ya kasa ɓacewa akan fuskarta ta ce, "Kai har ka tambayi meke faruwa, au touu da alama kai ne shugaban azzaluma...." Haɗiye sauran maganar tayi dalilin wata mahangurba da ɗaya daga cikin excort ɗin ya kai mata, cikin kaushin murya ya ce, " Ke ki iya bakinki, kinsan kuwa waye a gabanki ?". Tana ɗagowa taga jinin da ya biyo hannunta, tsuke bakinta tayi tare da tattareshi ta tofa akan white loafers ɗin nasa. Runtse ido yayi tare da ɗauke ta da wasu gigitattun maruka da sukafi wanda Aram ya mata dan har sai da ta Kai ga zubewa a ƙasa, ƙoƙarin hana idanunta tara ruwa tayi tare da furta, "ALLAH ya isa ban yafe ba"........ A harzuƙe securities ɗin sukayi kanta, saurin ɗaga musu hannu yayi hakan yasa duk suka qame a inda suke suna huci kamar wasu mayunwatun zakuna, ɗayan ya ce, "kee boss kike wa ALLAH ya isa". "An masa ALLAH ya isan, mugaye , azzalumai, macuta masu matashin Kai da hakkin mutane". "Boss......" Girgiza masa kai yayi hakan yasa wanda ya soma Maganar haɗiye wani yawu mai ɗaci, dan ba haka yaso ba, so yayi boss ya basu dama yau suci uban shegiyar yarinyar nan suga ƙarshen tsaurin idon nata. Kallon Sama da ƙasa ya Mata na seconds kafin ya maida kallon sa Kan yaran nasa dake ta faman zazzare ido suna sauke numfashi cike da ɓacin rai, ɗan girgiza kansa yayi tare da sakin wani sirritaccen murmushi wanda shi kaɗai ya san ma'anar sa, cikin normal Muryar sa mai sanyi da saukar da nutsuwa ga mai sauraro ya ce, "Ku je da ita ta biya kuɗin glass ɗin data fasa, sannan a tabbatar min da waye ya sata". Da sauri ta ce, "Tsaya Malam waye Kai a faɗin ƙasar Nifaz? Miye inkiyar ka da in anji za'a shaida ka, me Ka ajje me Ka bawa wani ajiya da har zaka fara tunanin turo ni akayi wurin ka? Me kake taƙama dashi? Wannan kayan wutar? to bara kaji ko a kwalar riga ta dan ka sa a tafi dani, muje har birnin sin, amma ni ma Whl sai an biyani kayan mu da aka ɓata da cabi yauwa". Ta ƙarashe tana tankwashe ƙafa daga zaune da take akan ƙasa. "Meye kayan naki da aka bata". Ya tambaya still idanun sa a kanta ta cikin munafukin shade ɗin nasa. Juyawa tayi tare da kwala kiran Shazeen dake rakabe bayan poll wire, a tsorace ta taho. Janyota tayi tare da nuna masa kayanta sannan ta nuna wandonta da goshinta, "Ina fatan kana gani dai da kyau. Ko mu ba mutane bane ? ko kuma bamu da Yanci, to whl nima ba zan yadda ba ". Ba tare da yayi magana ba ya juya zai koma mota, tsalle tayi ta dire gaban sa, "Kai shugaban azzalumai, Whl ko ku kun haƙura ni bazan haƙura ba, dole ne a biyani hakkin kayana da aka ɓata, ko nai ta ja maku ALLAH ya isa har duniya ta naɗe kuma whl ALLAH ya isa guba aya ce me hana kwanciyar kabari". "Ku janye min ita daga nan ". ya faɗa Yana keɓewa ya wuce ta gefenta gudun kar ta ƙara tunzira shi, dan in banda self control irin nasa da ba abinda zai hana ya bar su Aram suci ubanta, saboda yadda tayi masifar ɓata masa rai, saidai ba zaiyi hakan ba saboda wani dalili, Marin da ya mata ma baisan lokacin da yayi shi bane saboda shi mutum ne me tsananin kyankyami. Ganin yadda suka nufo ta gadan gadan yasa ta yi kwafa ta wuce tare da ɗaga murya ta ce, " Whl bana yafi ya kuma s......" Haɗiye sauran maganar tayi tare da jan hannun Shazeen da niyyar tafiya taji an wurgo Mata Abu a fuska, bundle din 1k ne ya sauko Kan hannunta, juyawa ta yi ta bisu da kallo har sun shiga motocin su sun fara tafiya. Kuɗin ta ɗauka tare da jujjuya su sai kuma taja kwafa ta zura su a jaka . Abun hawa ta tsare musu suka hau ba tare data damu da ta kaɗe ƙasar jikinta ba. "Madam ina zamu ne?". Mai tuk tuk ɗin ya tambaya bayan sun fara tafiya. "Kwanar chiriku".......... "Gsky Hajiya ba can nayi ba"....... Sai da ta watsa masa harara sannan ta ce, "Au dama ba Sana'a Ka fito yi ba, ko akwai iya wuraren daka ware kake yin Sana'ar taka?". "Kinga ni fa da zaki hau baki ce min ga inda zaki ba, dan haka yanzu ki sauka kawai ki tari wani abun hawan ni ba can nayi ba". "Kai kama isa, uban kuturu yayi kaɗan whl yadda Ka ɗauko mu sai Ka kai mu ko na tara ma jama'a". "Ke ni zaki nunawa jan wuya, whl sai na farfarɗe ki, baki sanni bane a ƙasan gada nake kwana in gaya Miki". Ya faɗa yana zaro wata ƴar ƙaramar wuqa daga kugunsa. "Kallo nan"........ ta faɗa tana ɗage masa gefen rigarta itama wanda hakan ya bayyana wata zungureriyar wuqa dake soke a gefen wandon nata. "Baza ka buɗe min ido ba cikakkiyar yar ƙasar Nifaz nake, ina yawo da ita ne saboda kariya daga irin Ku, dan haka kar kace zaka nuna min duniya, dan ko da nazo cikin ta idanuwa na a buɗe nazo, gwara Ka wuce mu tafi salin Alin karatun yan yankan kai, in ba haka ba na gwada ma nawa tashancin whl". Girgiza kai yayi tare da Jan kwafa ya maida tasa wuqar, ya bawa machine ɗin wuta suka wuce ba tare da ya sake cewa uffan ba, dan yasan lalle yau ya ɗauko yar hau daidaishi, kwatance ta dinga masa har suka ƙarasa Kan layin sannan ta ce ya tsaya, sauka sukayi ta zaro ɗari biyar a jakarta ta bashi, bata tsaya sauraren me zaice ba ta ja hannun Shazeen suka wuce, unguwa ce irin ta talakawa dan babbar mota ma in ta shiga sai ta maqale amma duk da haka layin tsab yake ba kamar irin sauran unguwanni na talakawa ba Wanda warin kwatami ma da bola sun ishe Ka. Ƙofar wani madaidaicin gida suka tsaya tana kokarin ciro makullin Shazeen ta ce, "Aunty Hushaima gidan a buɗe yake".......... Ta ƙarashe tana tura ƙofar ta shiga tana rangaɗa sallama, bin bayanta tayi suka shige. A ɗan ƙaramin tsakar gidan ta tarar da wani saurayi durƙushe yana wanki, kallon tulin kayan su da ya ɗaibo tayi kafin ta ce, " Sahnish kayan nan basu ma yawa ba, ai da jira na kayi na dawo sai muyi tare". Ɗagowa yayi Yana goge fuskarsa da omo ya fantsama, sosai yake tsananin kama da su biyun. "Whl kawai na dawo ne naga ba abinda nakeyi to dama akwai yar ɗari uku da na samo, shi ne fa na ɗauki ɗari da hamsin na siyo omon nan, nace bari na wanke kayan dan dama tin shekaran jiya naga sun taru. Amma lpy na ganku kamar wanda sukayi wasan ƙasa? Ke kuma me ya sameki a fuska?". Ba tare data bashi amsa ba ta zaro kuɗin da mutanan da bata san ko su waye bane suka bata, firfita ta shigayi dasu tana ɗan wani ƙasaitaccen murmushi. Saurin ɗauraye hannun sa yayi ya nufo inda take tsaye. "Hushaima ina kika Sa....samu kuɗi masu yawa irin wanna?". Ya ƙarashe yana Mata kallo me cike da tarin tambayoyi. Gyalen dake wuyanta ta cire ta ɗaura Kan igiya sannan ta wuce yar inuwar dake kofar dakin su ta zauna tare da faɗin, "karaso mana, kayi tsaye a wurin kamar wani bafade". Cikin sanyin jiki ya ƙaraso ya zauna a gabanta tare da zuba Mata ido. Labarin abinda ya faru ta bashi sai da ta gama, ya ce, "Me ya kaiki Hushaima, baki san ko su waye su ba, yanzu idan kuma suka cutar dake fa ina kike so in sa kai na, ya kike so ayi da Shazeen". Ya karashe cikin tashin hankali. "Dadi na dakai raguwar zuciya kuma a matsayin ka na namiji, whl Ka daina tsoro Sahnish, kuma ni ban ma san zasu bani kuɗi ba, kawai dai nasan na musu ɓarna dan gsky raina yayi masifar ɓaci ne, kuma ina neman hanyar da zan fidda Kai na saisa kawai na tsiri wanna borin kunyar". "Dubi fuskar ki fa Hushaima, ji yadda lebenki ya kumbura". Ya ƙarashe yana kai hannu kan kumatunta da shatin yatsu yake nan shimfiɗe a fuskarta ta. Kwafa taja tare da shafa kumatun nata ta ce, "Ai Whl sai na rama Sahnish ka rubuta ka ajje ka kuma zuba ido ka gani komin daren dadewa, ni ni ni dai har za'a wawwanke da maruka har uku"........... Ta ƙarashe tana me girgiza kanta ta sake jan Ƙwafa. Sahnish da ya saki baki yana kallon ta ne ya ce, "Da kika samu suka barki basu tafi dake ba shi ne kika samu damar fadin sai kin rama ko, wai da ALLAH Hushaima yaushe zaki barmu mu zauna lpy ne? Ina rabaki da kalmar saikin rama ɗin nan, ba fa komai bane ake nasarar rama shi, a wani wurin hakuri da yafiya sune j........." Shiru yayi sanadiyar kallon da take wurga masa. Sautin "hmmm" ya fidda ba tare da ya ƙarasa maganar da ya faro ba. "Kaga yanzu dai duk ba wanna ba kasan muna da buqatar kudin nan, dan ka san jibi ne ranar da Malam Ado ya bamu mu bashi kudin hayar sa ko mu bashi gidansa, dama abinda muka hada bai wuce dubu talatin ba kaga sai a bar wancan yaso a cire dubu sittin din a nan a bashi ko ya kace?". "Eh hakan yayi saura dubu arbain kenan ". "Akwai kudin makarantar Shazeen da za'a fitar dubu goma sha biyar, dama abun na rai na dan na san nan da sati biyu zasu fara magana akai su ma". "Saura ashirin da biyar". "Toh sai a siya kayan Abinci na dubu goma, kai ma Ka dau goma ni na dau biyar, wancan talatin din kuma baza mu taba ta ba yanzu saboda bamu san matsalar da Ka iya taso wa ba wanda zamu buqaci kuɗin". Kallonta yake cikin wani yanayi me wuyar fassarawa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Gsky Hushaima bazan karɓi komai daga kuɗin nan ba ke da Shazeen kunfi kowa buqatar sa dan haka Ku riqe kawai ". "Me sa zakace haka Sahnish, duk abinda ya shafe mu ne ai, in babu kuma ai kai ma me nemowa Ka kawo ne". "Eh ni ya Zama dole na Nemo na kawo maku saboda ni ne namiji, ina kunyar ranar da zan fita na dawo ban samo komai ba bayan kuma nasan kuna da buqata, dan haka ki barsu kawai dan ALLAH kar kice ah ah". "Shikenan tashi kaje Kayi mana cefane ko shi ɗin ma baza Ka iya karbar kudin ba na soke kaya na?"..........Murmushi yayi dan ko ba a fada ba yasan taji haushi ne. "Me dame zaa siyo?". Taɓe baki tayi sannan ta ce, "taliya ce da kayan miya ita zata fi sauqin bararrakawa a yanzu dai, sai Ka samowa Shazeen ko cornflakes ne dan nasan baza ta iya jira na gama ba". Ta ƙarashe tana miqa masa kuɗin. Karɓa yayi sannan ya tashi ya zura takalmin sa ya fita, ita kuma ta fara kwala kiran Shazeen. "Shazeen Shazeen wai me kikeyi a dakin nan ne? karfa ki cinye min caji kinsan ba kaiwa zanyi ba tunda wanna yayan naki ya sake musu baki sun gille wayar wutar ai shikenan sai kowa ya zauna". ------------------------√ "Kamal in mun ƙarasa motar mu kaɗai ce zata shiga ciki, su Aram su jira mu a waje ba dadewa zamuyi ba"........Ya faɗa da sanyayyar Muryar sa. Kallo na na dawo dashi gareshi, a yanzu ya cire p cap, sunshades da kuma noes mask din. kyakyawa ne ajin ƙarshe dan irin caramel skin ɗin nan ne dashi mai kama ido sai wani fidda annurin haske yake, bashi da saje amma gemun nan da gashin bakin sun sha gyara sun wani kwanta gwanin sha'awa, yana da dogon hanci tare da madaidaicin lips da suka kasance pink, idanun sa irin sleepy eyes ɗin nan ne masu saukarwa da mutum kasala, dole ma in Ka kalle Shi Ka ƙara saboda shi ɗin ƙarshe ne. "Okay boss an gama". Shi ne abinda kamal ya furta tare da dannawa su Aram ɗin kira. Tafiyar minti goma ce ta ƙarasa dasu inda zasu kamar yadda ya faɗa motar su ce kawai ta shige cikin gidan bayan an bude musu gate ɗin, bayan kamal yayi parking ya fito da gudu ya buɗe masa kofa sannan ya wuce booth ya dauko wani sabon loafers black, ciro shi yayi daga kwalin sa sannan ya zare ledar tare da cire soso ɗin dake ciki, ya wuce ya zura masa shi a foot space. Takalmin ya sanya sannan a hankali ya ziro kafarsa guda, komawa yayi ya jingina da headrest ɗin tare da lumshe idanun sa tsawon seconds ya bude su sannan ya yunqura ya ziro ɗaya ƙafar tare da dukkan jikinsa, compound ɗin gidan ya bi da kallo kafin ya doshi hanyar da zata sadashi da cikin gidan, door bell ya danna sannan ya zube hannuwan sa cikin aljihun rigar sa. Kusan minti biyu aka ɗauka kafin a buɗe ƙofar, wata budurwa ce tsaye sanye da vest da legging wanda ya tsaya iya guiwarta kanta ya sha kitso da gashin doki da ya sauka har kan mazaunanta, fara ce amma irin farin nan da aka hada da na kanti. Bashi hanya tayi tana faɗin, " Wai wai wai , Ya Amjad da gaske kai ne yau a gidan mu". Saida ya karasa cikin falon ya zauna sannan ya ce, "Ni ne mana khadeejatou, ykk?". Ɗan ɓata fuska tayi, "Haba ya Amjad Kai dai har yanzu khadeejatou nan sai kace a ƙauye, zamani fa yanzu ya canza, ina laifin deeyyah". Taɓe baki yayi da faɗin, "Khadeejah ai shi ne suna, ko baki san sunan matar Annabi Muhammad ta farko bane Nana Khadeejah macen data fara Musulunta ta kuma yi imani da Annabi Muhammad tun farkon bayyanar wahayi, why zaku dinga bata sunayen ku da sunan wani zamani bayan ga sunaye masu asali, sai kunje garin canje canje kun sanyawa kanku sunan aljanu, ni ba wannan ba sauri nake ina mommy?". Tura baki tayi gaba tare da faɗin, "Yanzu ta hau sama bari na faɗa Mata"....... Ta ƙarashe tana wucewa da sauri har tana haɗawa da dan gudu dan zuwa sanar da mommy. Jingina yayi da headrest ɗin tare da ɗan ɗage kansa sama yana kallon pop ɗin, a ahankali ya shafo fuskar sa tun daga goshi har zuwa wuyansa tare da furzar da wani zazzafan numfashi sannan ya ɗago, bin komai na falon ya fara yi da kallo kamar mai haddace su kafin ya zaro wayar sa kirar iPhone 17 white in colour ya fara latsawa, minti biyar tsakani ya fara jiyo motsin saukowar su, bai daina abinda yake ba har saida ya tabbatar da bayyanuwar su cikin falon sannan ya dago Yana kallon su, dattijuwar macece da akalla zata yi shekaru 56 - 57 a duniya, Amma yadda ta suturta jikinta da kayan ƙawa da kyale kyale zai sa ka dauka she's in her early 40s, Khadeejah biye da ita. "Barka da fitowa mommy". "Haaa'aa Kaga yaron ummun sa, gabaɗaya ta hana Ka zuminci da mu ko sai ita da danginta kawai?". "Ko daya mommy whl ba haka bane, abubuwan ne sai a hankali". Ya faɗa yana saukar da kansa ƙasa. "Kai ba aiki ba, Kai ba iyali ba miye abubuwan da zai hana ka zumunci bayan kuma gari ɗaya muke, kai ko koyi da yan uwan ka baka yi duk wani taro su na kokarin halarta amma kai Ka ware Kan Ka daban ko?". Ta ƙarashe tana zama ta ɗora da faɗin, "deeyyah kawo masa ruwa". " Afuwan mommy in sha allah za'a gyara". Ya faɗa still kansa na kallon ƙasa. "To ai shikenan, ya gidan ?". "Lpy kalau alhamdulillah". "Ya su ummun ta Ka da su hajiya zunaira, ya kuma jikin yayan?"......... Shuru yayi na wasu daqiqai kafin ya ce, "dukkan su lpy, jikin dada da dama alhamdulillah". " ALLAH ya kawo masa karshen wahalar nan shi ma Whl, in sha allah ni ma zan shigo na ga jikin nasa. Ya batun aure kuma Amjad? Ko shi ma an yafe shi? To Kaga idan ma har na waje suna tsoron abinda kaje yazo ne, mu sai mu shiga qauye mu bincika a dangi, mu ai dole haka zamu rufa asiri tunda hannun Ka baya taɓa rubewa Ka yanke Ka yar, dan nasan a dai bare ba wanda zai dauki ƴa' ya baka. Wai ma Amjad wani tsautsayin ya kaika jefa kanka a matsala irin wannan ne kana zaman ka lafiya ba abinda ka nema ka rasa". Dan siririn murmushi yayi kwata kwata baza ka iya cewa ga yanayin da yake ciki ba. "Mommy a yanzu bani da bakin magana domin duk abinda zan faɗa mutane zasu ga kamar ina ƙoƙarin kare kai na ne amma lokaci alkali kuma shi zai bayyana gsky ko akasin ta". Zuba masa ido tayi tana son gano yanayin da ya ke ciki amma ta ƙasa, hakan yasa ta ɗan yamutsa fuska da faɗin, "Kayi hakuri fa in maganar tawa ta ɓata ma rai, Amma gsky ce ni dole na faɗa ma a matsayina na ƙanwar mahaifin ka dan bazan jin tsoron idonka ba. Sai sa ake so mutum ya kasance nagari mai aikata ayyukan kwarai ba wai amfani da fuska biyu ba saboda akwai ranar qin dillaci, kuma masu iya magana na cewa rana ɗaya ta barawo rana ɗaya tak ta me kaya, In wani yayi rawa an bashi kudi in wani yayi duka zaici, zaren ba kalar yadin bane sai kaga Kai ALLAH yayi using dinka as example, shiyasa ake so a dinga sara ana duban bakin gatari. Ni whl banji dadin abin nan ba sam sam Amjad banso kayi wasa da damar da mahaifin ka ya baka ba". Tun da ta fara magana ya janyo wayar sa yana ɗan latsawa duk da kuwa kana kallo kasan ba wani abun kirki yakeyi a ciki ba, har sai da ta ƙare maganganun nata masu kama da shagube sannan ya miqe yana gyara rigarsa daidai lokacin da deeyyah ta dawo falon riqe da tray data shiryo refreshments a ciki. "Nagode Mommy, ni zan wuce". "Haba Amjad har zaka wuce kuma, yaushe ma Ka shigo ko minti talatin fa bakayi ba sannan kace zaka tafi, ka kusa shekara biyu fa rabon Ka da gidan nan". "Haka ne mommy Amma yanzun ina sauri ne , in sha ALLAH in an kwana biyu zan dinga zagayowa". "To shikenan Amma ga ruwa yar uwarka ta kawo ma ai ko shi ka tsaya ka sha"..........dan shafa kansa yayi tare da ɗan kaɗashi kaɗan ya ce, "in na sake zuwa zan sha in sha ALLAH". " To ba damuwa ka gaida mutanan gidan". Ƙasa ƙasa ya ce, "zasu ji". Tare da sa Kai ya fice. Juyawa deeyyah tayi wurin mommy kana ta ce, "Mommy meya faru ? na ga kaman ba haka ya shigo ba" . "Ke da kika iya lura da wannan hargitsatsen ma kenan, shi da ba gane farin cikin sa ko akasin sa ake ba, dama a haka ya shigo ai. Tashi ki je shirya ki zo na aikeki ki karbo Min saqo wurin deedy". "Mommy Amma ya Amj....." "Keee zaki tashi ki bani wuri ko zaki tsaya min kinibibi". Mommy ta katseta a tsawace dan tasan nacin deeyyah ɗin. Sai da ta sake kallon ƙofar falon nasu sannan ta tashi tana tura baki ta bar falon. Mommy kuwa deeyyah na barin falon wata number da akayi saving da Hajiya zunaira ta dannawa kira, sai da ta kusan tsinkewa aka amsa. "Hello Hajiya zunaira!". "Naam ƙawata, mun wuni Lpy". Faɗin Hajiya zunaira........."Lpy kalau ya mirrah?" "Whl tana nan lpy, ina Deeyyah tah?"..........."Tana nan lpy yanzun ma ta hau sama. Yanzu fa shegen yaron nan ya tashi daga nan"......... Shiru Hajiya Zunaira tayi kafin ta ce, " wani yaro kenan?". "Matsala ta dake bakya harbo jirgin da wuri wannan yaron kishiyar taki mana Nadeera"..........."Auho Amjad wai?" "Shi dai, kinsan ai ada kilibabbar uwar tashi ta hanashi zuwa sai da ranar nan muka hadu a gidan yaya Maheera sunan yarinyar wurin ta data haihu baki samu zuwa ba, ai kuwa na mata tas shi ne yau ta turo shi". "Hmmm ai hajiya Fareeha karki taɓa ganin laifin yaran nan dan ba ruwan su duk wani iya shege uwar ke daura su akai, sai sa ni kinga yaqi na da baqar algunguma nake yi ba abinda ya sha min kai da ya'yan ta ". "To ai kuma kina nunawa ya'yan soyayya ai baza taji zafin duk abinda zaki mata ba". "Hajiya Fareeha kenan". Hajiya zunaira ta faɗa tare da yin wata yar bazawarar dariya. "Tsaya nan kallon ruwa ƙwaɗo ya Miki ƙafa, ki cigaba da dariya". Mommy ta faɗa. "To ni yanzu me ya rage min hajiya Fareeha, ɗan nata ma da suka dauki burin duniya suka ɗaura masa ita da Alhajin gashi nan ya ɓata rawar sa da tsalle, uban ma duka daya ya kwantar dashi to sai mai kuma? ya'yan nawa dai su ne yanzu akan komai to miye kuma zai tada min hankali ni yanzu ALLAH na tuba". "Shegiyar gari Ke fa kin dafe ƙasa saisa kika koma gefe kika yi shuru abinki ko. Ai bake kaɗai abun nan ya wa dadi ba har dani, ashe dai yaro Musa ne a fuska firauna a zuci, ai yanzu kafin ya fita saida na tabbatar ya shaqa da zafi dan ma dai kinsan yaron wani irin juyayye ne kwata kwata ba'a taba karantar facial expressions ɗin sa". Ta ƙarashe tana kwashewa da dariya. " Kuma whl yaron yana da biyayya Hajiya Fareeha kawai dai kinsan in an budewa yaro ido da kuɗi sai kiga ta kowacce hanya neman su zaiyi ba tare da yayi tunanin me zai faru gaba ba". " Kaji Hajiya zunaira da wata magana da ALLAH, yanzu har zakiyi zancen kudi a cikin zurriyar Hashim Darwin, ai ke kinsan yaya ba ƴaƴan sa ba hatta jikokin jikokin sa ba zasuyi talauci ba, su dai kawai dama can basu gaji arziki ba, yaya ya kwaso mana jaraba ya kwaso mana jinin tsiya". Dariya Hajiya zunaira tayi da faɗin, "Baki da dama ƙawata ya kamata ki samu ki shigo fa". "Yanzun nan nake maganar Whl, in sha ALLAH zan samu na shigo mu sha hira dai"........."To shikenan zan zuba ido saura ki jirgani". "Habaa ke kuwa ai kinsan Bama haka, in sha ALLAHU kafin alhaji ya dawo daga tafiyar nan zanzo mu wuni ". "To shikenan Allah ya kawoki lpy". Daga haka sukayi sallama, tashi Mommy tayi tana kiran masu aiki da suzo su kwashe refreshments ɗin da deeyyah ta bari a wurin sannan ta wuce saman itama. SHIN WAYE AMJAD? MIYE DALILIN MOMMY NA JIFANSA DA IRIN WANNA ZAZZAFAN KALAMAN? MEYSA YAYI TUNANIN AIKO HUSHAIMA AKAYI? WACECE HUSHAIMA, SAHNISH DA KUMA SHAZEEN? SANNAN INA IYAYEN SU SUKE? MIYE DALILIN DA YASA SUKE RAYUWA SU KADAI? KU CIGABA DA BI NA DOMIN MU SAMO AMSOSHIN WANNA TAMBAYOYI TARE. NOTE: THIS IS A WORK OF FICTION , NAMES, CHARACTERS, EVENTS AND OTHER ELEMENTS ARE THE PRODUCT OF THE AUTHOR'S IMAGINATION, ANY RESEMBLANCE TO ACTUAL PERSONS LIVING OR ACTUAL EVENT IS PURELY COINCIDENT. NO PART OF THIS BOOK MAY BE REPRODUCED OR SHARED, INCLUDING ON YOUTUBE WITHOUT THE AUTHOR'S PERMISSION. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd Sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 3 Fitowa yayi cikin tafiyar sa me cike da kwarjini da kuma nutsuwa kansa a ƙasa wanda hakan ya hanani gane yanayin da ya ke ciki. Tun kafin ya ƙaraso kamal ya bude masa ƙofar motar, yana zuwa ya shige, shi Kuma ya rufe ya koma mazaunin driver yaja suka fice, sauran motocin na ganin fitowar su suka rufa musu baya. A karo na biyar wayar sa take ta faman tsuwwar neman Agaji dauka yayi da niyyar kasheta gabaɗaya idonsa ya sauka akan sunan dake yawo kan screen din, " My Ninie". tare da wani maroon heart emoji da Kuma emojin padlock da key. Ganin Kiran na kokarin tsinkewa ya sashi amsawa tare da Kai wayar kunnen sa idanun sa kan titi yana kallon hanya. " Amour dama kana kusa nake ta Kiran ka baka dagawa ". Saida ya lumshe idanun sa da a yanzu suka dan sirka da red saɓanin lokacin da suka shiga gidan mommy da suke a washe kamar madara. "Ina hanya ne Ninie". Ya faɗa a sanyaye. "To kuma kana hanya ai ba Kai kake driving din ba, amour ko dai ina takura ma ne". Ta ƙarashe kamar zata fashe da kuka. Yanayin yadda tayi maganar ya sashi furzar da zazzafan numfashi tare da faɗin, "I'm sorry Ninie". Shuru tayi kafin ta ce, "I'm the one who's supposed to tell you that". "Why?". Ya tambaya. "Shirme na ya sa ina ta ma surutai ba tare dana tsaya na tantance yanayin ka ba, meke faruwa ne amour, waya bata ma rai?". "Nayrah!"......... "Naam rabin ran Nayrah". "Nayrah!"..........."Naam Habiby nah". "Nayrah!".......... Ya sake fada a karo na uku. Dariya tayi tare da faɗin, " Whl Yadda kake Kiran sunan nan sai naji kamar na bayyana a gaban ka amour, na kalla cikin idanun ka domin na gano abinda ya bata ma gwarzo na rai dan na ɗauki mataki ba tare da bata lokaci ba". "Ji ki, sai kace iyawa zakiyi". Cike da confidence ta ce, "Zan iya mana, a kanka ai ko aljani ne ina iya faɗa dashi talkless of mutum da ina ganin sa yana gani na". Wani killer smirk yayi Mai sauti har saida jerarrrun fararren hakoransa na gefen dama suka bayyana, Wanda ni kai na saida zuciyata ta buga da wanna tsadadden murmushin saboda kyawun da ya masa. " Abinda ni ke nufi shi ne zaki iya gane me ya ɓatamun rai idan kin kalla cikin idanun nawa ne?".......... Dan shuru tayi can kuma ta ce , "to ai Kai ɗin ne ma duk hasashen mutum sai ka maida shi karya ko da na canka ma zakace ba haka bane". "Ai bakya canka daidai din ne". Ya sake faɗa cikin taushin murya. "Dama kullum haka kake musawa ai, Amma kasan dai ina ganewa daga Muryar ka ko". "Ehen shi ma saboda kinsan kina sani surutu ne ai, saisa in bakiji na Buɗe baki sosai ba kike iya fahimta". "Naji amma with time kuma zan baka mamaki". "Ya kamata ki bani mamakin nan da wuri, dan Gsky bazan auri matar da bata iya fuskantar yanayin da nake ciki ba har sai na buɗi baki na faɗa mata". Ya faɗa cikin sigar tsokana. "To dama wa yace ma nima zan iya auran mutum mai wuyar sha'ani irinka, dama maneji zanyi kawai". "Kyaji dashi dai, kinga dan saurayi kin rikice a kansa. Bari In na koma gida zan kiraki". Dariya tayi kana ta ce, "To, ALLAH ya kaika gida lpy, ALLAH ya karemin kai, ka kula min da kanka kaɗan". "Ameennn ya Allah, and zan kula Miki da kai na da yawa ma". Ya faɗa yana ɗan murmushi. Ajje wayar tayi bayan ya kashe tare da janyo pillow ta rungume tana murmushi ɗaga kan da zatayi idon ta ya sauka kan mahaifiyarta dake tsaye ta zuba mata ido, "laa mumu yaushe ki..kika shigo". Ta tambaya cikin yanayin dake nuna alamar rashin gaskiya a tattare da ita. "Nayrah da wa kikayi waya?". Mumu ta tambaya ba alamun wasa a tattare da ita. Sake rikicewa tayi duk da kokarin saita kanta da take saboda sanin halin mahaifiyarta ta, "Mumu ba kowa fa, ba waya nake ba". Ta faɗa duk da tasan kallon da taga tana mata da wuya ace bata ji ta ba. "Tambayar ki nake da wa kikayi waya?". Ta maimaita tambayar a kausashe. "Amm, dama dama Amla ce, Kuma ma network ya hana naji ta ma sosai". "Baki da gaskiya Nayrah, wato har yanzu baki rabu da wanna annobar ba ko? Kin dage sai kin janyo mana bala'in da daga mu har dangin mu za'a shafe tarihin mu ko?". Idanunta ne suka ciko da kwalla ta ce, "mumu Dan ALLAH ki daina cewa haka, whl Amjad ba annoba bane, shin mumu kin ganshi da idanun ki ko kin tabbatar da abinda akace ya aikata, mumu dan ALLAH ki sauqo haka, ya kamata ace ko da kowa zai yarda ke da daddy zaku kasance mutane na farko bayan iyayen sa da zaku ƙaryata ku Kuma kareshi a wurin al'umma, mumu ki tuna alherin Amjad a gare mu bakiɗaya mana, mutumin kirki ne shi whl na rantse miki"........Ta ƙarashe kwallar dake maqale a idanunta na gangarowa. "Ba shakka, to sannu uwata ahh nace sannu uwata, ko shi bai mana gori ba sai ke uwar iya Mai dogon baki, ke dai kinsan ko da can ubanki ai ba talaka bane, tunda sai da ya riqe muqamin Deputy governor ya kuma riqe muqamin house of rep jarrabawa ce kawai ta rayuwa ta bada ƙofar da har shi Amjad ɗin ya taimaka mana. Ina so na Kara tabbatar Miki bake ba auran wanna yaron dan baza ki janyo mana abun kunya cikin zurriya ba, gwara tun wuri ki nesanta kanki dashi tun kafin mahaifin ki ya samu labarin cewa har yanzu kuna tare, dan ba hannun na a ciki wawiya wadda bata san ciwon kanta ba"........ Ta faɗa sannan ta juya ta fice a dakin. Kuka Mai sauti Nayrah ta fashe dashi bayan fitar mahaifiyarta ta tare da kifa kanta cikin pillow ta cigaba da raira shi kamar danshi aka aikota. -----------------√ "Yauwa tun da dai har ba ku da gado a gidan Nan to ku tashi ku barmin gida na, na baku yau zuwa gobe." Cikin tausasa harshe Sahnish ya ce, "haba malam ado ina dai cewa kuɗin haya ne matsalar, Kuma ga kuɗin ka nan an baka to kuma miye na tashin hankalin". Cikin daga murya ya ce, "Bana buqatar kuɗin hayar ku dan sayar da gidana zanyi, in kuma Kuna da kudin biya ne to sai ku fito dashi ". Cikin gajiya Sahnish da tun dazu shi ke ta faman bawa malam ado baki ya juyo ya kalli Hushaima dakewa Shazeen kalaba ya ce , "Hushaima ki sa baki mana, kina jin fa abinda yake cewa". Ba tare data kalle su ba ta ce, " Har nawa ne kuɗin gidan naka". "Miliyan uku ne Kuma nasan kaf dangin ku basu da miliyan uku, in ma Kuna da dangin kenan ". "Kai malam ado ya fa ishe ka, tun dazu kake ta faɗawa mutane maganganu, ana lallabaka kana wani boƙarewa wanna gidan naka ma har wani gida ne, ai baya daga cikin Sahun gidaje". Faɗar Hushaima daga inda take zaune. "A haka dai a haka ya muku alfarma kuka samu matsugunni har kuka rufawa junan naku asiri, ke kinsan ko banza na muku rana, dan lokacin da kuke gallafiri a titi, ba dan ni ɗin ba ai da ba Mai baku gida ku kaɗai a wanna lokacin". Miqewa tayi daga zaunen da take ta ƙarasa wurin su, karɓe kuɗin tayi daga hannun Sahnish ta zura a aljihun doguwar rigar dake jikinta sannan ta ce, "kai ado kake ko wa, in ga uban da ya isa yazo ya fitar damu gidan nan daga yau zuwa gobe, dan ma kaga ana lallabaka to bari na ma da Yaren daka fi ganewa". "Um um Hushaima, ki tsaya mu bi abun Nan a hankali fa". "An fasa binsa a hankali, yayi duk uban da yaga zai iya". "Haka kikace ?". Malam ado ya faɗa a fusace. "Eh Haka nace ko zanji duka ne"......... Ta faɗa tana zare masa idanu tare da ƙara taku ɗaya zuwa gabansa. "Au to ni dukan nawa zakiyi kenan kike fiffiqa "...........Sahnish ne ya shige tsakiya tare da faɗin, "Dan Allah ku bar wannan abun, malam ado muje waje muyi magana, kayi hakuri". "In dukan ne ma zaka gaza dakuwa ne, Amma ni kayi kaɗan na ɗaura hannu na a wanna ƙazamin jikin naka saidai nasa a lallasa min Kai, in kaga dama Kar kayi hakurin gida Kuma baza a tashi ba in ga isasshen daya isa ya fitar damu". Cikin hayyaqowa ya ce, "in ban tozartaki na kunyata ki a bainan nasi ba kice ni ba ado danga nake ba"..........Biyo su tayi dan lokacin har sun Kai soron kofar gidan dalilin Sahnish daya ke binsa Yana turashi tare da kalaman ban hakuri. Itama daga murya tayi wurin faɗin, "Kai da ka san su kenan ni nan da kake ganina bana gudun wani abun kunya tijararriyar Kai na ce, bana gudu bare tsoron wani tozarci, ka dade bakayi ba, shege ka fasa". "Haba Dan ALLAH Hushaima wai miye hakan ne , na samu na turashi waje Kuma kin sake biyo mu sai kun tara mana mutane". "Kai dallah banza rufemin baki, au Kai yanzu har gudun a tara mutane kake, rigima wa ta kashe , sai me dan an tara mutanen ko akwai ɗan iskan da ke ciyar da mu ko ya shayar damu ko Kuma shi zaman da muke a gidan sa kyauta yake mana? Tambayar ka nake a fadin unguwar nan in zaka kwana da yunwa ka tashi da ita akwai Wanda zai kankaro ƙanzo yace ai gidan nan basu ci ba ko Sahnish ya kwana da yunwa?". "Whl ki daina irin hakan ba kyau ke macece"......... Yana kaiwa nan ya juya ya fita tare da gabzo kofar ya barta sake da baki, "ahhhh lalle Sahnish ka girma"......... Ɗaga kanta tayi sama tare da sanya hannunta tana gwada tsayinta, "well is allowed, zaka dawo gidan ka sameni ne dan jar qaniya". Ta faɗa tana me juyawa ta koma ciki. "Aunty Hushaima kizo ki karasa min kitson ni kam". Faɗin Shazeen dake zaune rabin kai da kitso rabi babu. "Daure kan haka Shazeen da daddare na karasa Miki".........Ta ƙarashe tana zagaye tsakar gidan hannunta ɗaya ta dunƙule tana nausawa cikin ɗaya tafin hannun. Can Kuma ta wuce daki bata jima ba ta fito dauke da mayafin ta kallon Shazeen dake danne danne a wayarta tayi kafin ta ce, " zan fita Shazeen Amma ba zan dade ba, ga wayar nan zan barmiki kiyi game". "To, amma karki daɗe ". Shazeen ta faɗa ba tare da damuwa ba da alama dama ta riga ta saba da zaman gidan ita kaɗai, yayinda ita Kuma Hushaima ta nufi soron gidan tana faɗin," kizo ki kulle, Kar Kuma ki bude sai kinji muryar dayan mu". Ko da ta fita bakin titi ta nufa ta tsayar da abun hawa. "Hajiya Ina zuwa?". Mai tuk tuk din ya tambaya. Shuru tayi tana taunar lips dinta kafin ta ce, "wurin dillalai".........."Wurin dillalai Kuma hajiya wace unguwa kenan?" Cikin masifa ta ce, " Wace unguwa zan faɗa ma? Kai duk gararambar da kake a titi baka san in da dillalai suke zama ba ne kake sake min tambaya, nace ma ka Kai ni majalisar dillalai, in ka sani Bismillah in Kuma baka sani ba wuce ga hanyar nan har darus Salam". "ALLAH ya huci zuciyar ki, hau muje". Sai da ta galla masa harara Sannan ta shiga yaja suka wuce. Tafiyar minti bakwai sukayi ya tsaya gaban wata rumfa tare da faɗin, "yauwa munzo, a wanna rumfar ba irin dilallan da Babu". Kallon yanayin wurin tayi kasancewar yamma ce yasa da yawan dattijai da kuma matasa masu zaman kashe wando sun fito shan iska majalisa wanda hakan ya haifar da yawaitar hada hadar masu kasuwanci a wurin daga kan masu pure water, gyada, rake da sauransu. Sauka tayi tare da zaro Naira ɗari ta miqa masa, karɓa yayi ya jefa a ma'adanar kuɗin kasuwancin sa sannan ya karawa machine ɗinsa wuta. Wurin ta karasa tare da yin sallama, mutane huɗu ne zaune a runfar sai cikon na biyar dake zuzzuba musu shayi a kananun cups suka amsa. "Da Allah tambaya nake?" "Allah yasa mun sani " daya daga cikin su ya amsa. "Da Allah dillalin gidaje irin na haya nake nema". Washe baki yayi da faɗin, "kinzo gidan, Nan da kika gan mu duk dillalai ne Amma kowa da irin gidajen da yake dillanci, gidan haya kike so, wani irin hajiya". "Ƙarami kamar me daki biyu da bayi, sai madafa". "Apartment ko zaman mutum daya?" "Zaman mutum daya ". "An gama ki bani number ki, duk abinda ake ciki sai na kiraki na sanar dake ko?". "Ba damuwa Amma na bar tawa wayar a gida saidai na baka tawa sai ka kirani ya so sai nayi saving taka". "To shikenan, ga wayar saka a ciki"......... Karɓar wayar tasa kirar baby Nokia tayi tare da loda number ta a ciki ta yi flashing sannan ta miqa masa, ta musu sallama ta baro wurin, da ƙafa ta tako har zuwa gida, lokacin data shiga gida har an Kira sallar magriba, alwala sukayi itada Shazeen sukayi sallah, bayan sun idar Shazeen ta dauko littafanta ta fara yin homework din da aka basu a makaranta, ita kuma Hushaima ta tashi ta wuce kitchen domin sama musu abinda zasuci. A haka Sahnish ya shigo da sallama hannunsa ɗaya riqe da leda gefen dardumar ya zauna tare da ajje ledar a gefen sa ya ce, " Shazeen karatu ake haka ne ?". "Homework nakeyi yaya , sannu da zuwa". "Yauwa Shazeen". Ya faɗa yana Kallon Hushaima data fito daga kitchen dauke da hancin su tumatir da tattasai data ciccire ta wuce bola ta zubar. " Yameer na waje yace yayi ta Kiran wayarki ɗazu bata shiga". "Kaje kace masa bana Nan". "Kayya Hushaima Wai miyesa kike son yiwa mutane wulakanci ne, ke wai bakya so kiyi aure ne, kinfi so mu dauwama daga wanna gidan hayar zuwa wanna ana mana wulakanci, kinga in kinyi aure ai zaki tafi da Shazeen abubuwa da yawa zasu ragar mana daga nan zamu san inda rayuwar mu ta dosa, Amma yanzu fa kwata kwata bamu da alqibla kawai dai muna rayuwa ne kamar wasu sakakkun shanu". Daga inda take ta girgiza kai tare da faɗin, "Sahnish"..........Sai Kuma tayi shuru tare da yin ɗan murmushin fatar baki ta ce, "Zanso hakan Amma bamu da wannan gatan, wa kake tunanin zai auri yarinyar da suke zaman kansu, ka riga ka san irin aladar mutanan mu baza su taɓa aurawa ya'yansu yarinyar da basu kama wani nata ba, ba iyaye ba dangi, Dan haka Kar mu yaudari kan mu Sahnish, muyi kokarin ganin kawai mun gina kan mu, duk Wanda kaga yazo wuri na na koreshi to na ga da gaske yake ne kuma kai ma ka sani". Tagumi Sahnish yayi kawai yayinda ita Kuma ta nufi waje saboda kwankwasa kofar da ake. Tana buɗe kofar ta tarar dashi tsaye kan dakalin gidan, Yana ganin ta ya ce, "kina ban wahala Hushaima, na fa kusan minti talatin kofar gidan Nan". "Ayyah sannu ya kake ?". "Lpy kalau, to ki saki fuskar mana, ko dai Sahnish ne ya fito dake ba shiri ko kuma dai ni ɗin ne ba'a shirya gani ba".......... Ya ƙarashe yana karkace kai kamar wani Maraya, dan gyara tsayuwar ta tayi tana daga cikin soron gidan dan kafarta ko takalmi babu gwara ma kanta akwai dankwali. Murmushin da bai kai zuci ba tayi tare da faɗin, "Ni kawai mamakin ganin ka nake". "Miye Abun mamakin? Dama munyi dake na dai na zuwa ne? kece ma fa kika min laifi". "Yameer kenan abinda na gaya ma ba laifi bane gaskiya ce wadda ni da Kai duk mun San ta, to meysa zamu bari mu yaudari kan mu, na riga na fada ma ni bani da lokacin soyayya saboda ko na bata ruwa bazan girbi amfanon ba". "To ni Kuma ya za'ayi da zuciya ta". Ɗauke kai tayo daga kallonsa kafin ta ce, " Ka bata hakuri ka Kuma nisanceni hakan shi ma zai taimaka ma". "Ni ban taba ganin yarinyar da take cewa a nisanceta ba sai ke Hushaima, wai meysa ? Ni fa da arziki nake son ki kuma ba wasa ya kawo ni ba, a gobe in kin amince min zan turo iyayena a nema min auranki". Sautin "hmmmm". Ta ja tare da kaɗa kanta kadan ta ce........... 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______4 Sautin "hmmmm". Ta ja tare da kaɗa kanta kadan ta ce, "Bansan meysa kake da son ai ta maimaita abu ɗaya ba yameer, Dan ALLAH mu hakura kawai, nagode da soyayyar ka gareni Ina roqon ALLAH ya baka Wadda ta fini, Ina Maka fatan alheri, dan ALLAH karka ƙara zuwa in da nake"........ Tana kaiwa nan ta juya ta shige tare da rufo kofar gidan harda saka sakata. "Hushaima! Hushaima! Ki tsaya kiji Dan ALLAH". Shuru yayi ganin da gaske fa baza ta saurare shi ba, komawa yayi ya jingina jikin motar sa tsawon wasu minutes kafin ya shiga ya tada ta ya bata wuta ya bar layin zuciyar sa a cinkushe, dan ALLAH ya gani yana matuƙar son Hushaima. Ita kuwa Hushaima ba alamun wani damuwa a tattare da ita ta koma ciki, samun Sahnish da Shazeen tayi suna faman yanka kankana. "To iyayen ciye ciye kun yi sallah tukunna kuka zauna yanke yanke?" Sahnish ne ya ce, "Eh ai kinsan dake mu ɗin rainon Pope leo ne"....... Shazeen ce ta ce, " yanzu fa muka idar Aunty Hushaima". A fusace ta ce, "Whl Sahnish ka fita ido na, Kai na tambaya ne Dan iya, dama ɗazu Ina cike dakai ". Ba tare da ya dago ba ya ce, "to Kuma ba sai ki rage ni ba. Yameer din ya tafi ne?"........... Ya ƙarashe Yana ɗagowa, wucewa tayi ta dau buta kana ta ce, "Eh." Bai sake cewa komai ba ya maida kansa suka cigaba da abinda sukeyi shi da Shazeen ɗin, har Hushaima ta dauro alwala tazo zata tada sallah. turo mata tray ɗin yayi da faɗin, "Duba yanka Hajiya ba irin naki ba me kamar haƙorin giwa". Tsaki taja da faɗin, "Kai ka sani Kuma in ka tashi ka duba min girkin dake kan wuta"........ Ta ƙarashe tana kabbara sallar Isha da aka Kira tun shigowar Sahnish ɗin. "Zo muje mu Duba girkin kafin ta idar" ..........Ya faɗa yana ɗaukan slice ɗin kankanar da suka yanka guda ɗaya ya sa a baki sannan ya miqe, tashi Shazeen tayi itama dan dama ita tun suna yankawa ta shanye kusan rabi, kitchen ɗin ta bishi suka shiga. Ita kuwa Hushaima ko da ta idar hijabin ta cire tare da komawa ta kwanta akan dardumar tana kallon sararin samaniya da wata ya haska zagaye da taurari masu haske, kaɗan kaɗan iska ke kaɗawa, sosai tayi nisa cikin duniyar tunani har bata san tsawon lokacin data ɗauka ba sai muryar Shazeen dake mata ihu a kunne ne ta dawo da ita hankalinta, da mamaki ta bisu da kallo ganin har dafadukar macaroni ɗin data hada ta dahu har sun zubo shi. Kallon Sahnish tayi taga shi ma ita yake kallo, maida kanta tayi kan Shazeen da faɗin, "Wai har kun gama?". "Akwai wani zahirin da kike nema bayan wanda ke gabanki"........ Sahnish ya faɗa cikin sigar tsokana, harara ta watsa masa shi Kuma yayi dariya kana ya ce, "sako hannu kiga Kar yayi sanyi ". Bismillah sukayi dukkan su tare da sa hannu suka fara cin abincin a tare cikin mazubi ɗaya kamar yadda suka saba, Sai da suka gama Sahnish ya dauka tray ya wuce dashi kitchen ita Kuma Shazeen ta dauko tsintsiya ta fara kokarin tattare wurin, ganin haka yasa Hushaima nade dardumar tare da hijab ɗin sannan ta dauki tray kankanar tayi ɗaki. Saida suka gama tsaftace gidan suka wanke kayayyakin da sukayi amfani dashi sannan Sahnish yabi bayan Hushaima inda ya bar Shazeen bakin rariya tana wanke hannayenta da kafafunta. Shiga yayi tare da neman wuri ya zauna bakin yagalgalalliyar katifar tasu irin ta yam makaranta duk ta gama siɗewa. Kayan data gama linkewa ta haɗa ta ajje tare da dawowa kusa dashi ta zauna tana tambayar. " Ya akayi Sahnish? Ina ka baro Shazeen din Kuma". "Kai ke kina da matsala Shazeen gida a rufe zata fita ta sama ne. Ina kudin hayar Malam Ado ?". "Me zakayi dashi?". Ta tambaya tana me tsareshi da fisgaggun idanun nan nata masu matukar rikitarwa. "Mun daidaita dashi ne dama, yace gobe zaizo ya karɓa"........Shuru tayi can kuma ta ce, "Dan hau, ni da ai har na bazama na sa a nemo mana gida mu tashi mu bar masa tsiyar sa". "Yadda gida je ke wahala har kina tunanin zamu samu gida a dan wanna tsakanin ne, ki bari dai kawai tunda na lallabashi zai karɓa na yanzun, kafin lokacin wani biyan yayi sai mu haɗa kuɗi mu nemi wani gidan mu tashi, ba shikenan ba an rabu lpy ba". "Zancen banza ma kenan, zan tashi a gidan nasa sannan mu rabu lpy, ai whl duk wulakancin da ya mana sai na rama sai na ci masa uwa na huce haushi na".........."Hushaimaaaaa"...... Shuru yayi saboda Shazeen data shigo, canza zancen yayi da faɗin, "ban kankanar na ibi tawa na wuce daki". Tray ta jawo masa. "Miqomin cup din can Shazeen"....... Ya faɗa Yana nuna mata cup ɗin dake gefen Hushaima dan yasan yanzu yana cewa Hushaima miqo min wata sabuwar paragraph ɗin zata bude. Kankanar ya ɗiba bayan Shazeen ta miqo masa cup ɗin sannan ya miqe da faɗin, " Sai da safen ku"........"Allah ya tashe mu lpy". Hushaiman ta amsa. "Yaya sai da safe"........." Sai da safe Shazeen." Ya amsa yana ficewa daga ɗakin. ----------------√ Amjad kuwa daga gidan mommy gidan sa suka wuce, ba shi ya fito ba sai karfe 8:30pm, yana sanye da wasu lightwears, ash comfy long pant da tee na Lululemon brand sai baza kamshi yake kamar wani ango. Shi da Kamal kaɗai suka fita, ya hana sauran binsu. Gaban wani ratsatstsen gida suka tsaya iya gate ɗin gidan kaɗai Abun kallo ne bare aje ga girman gidan da ya kasance kamar wata unguwar guda, wasu irin murtuka murtukan sojoji ne da ba kasafai ake ganin su ba sai a filin yaqi kowannen su riqe da manyan bindigu ba alamun Imani a tare dasu, ballatana Kuma daga ganin su ba musulmai bane, kansu ya sha sankwal sai kyalli yake cikin hasken fitilun da suka haske ilahirin gidan daga ciki har waje. Bayan an Bude musu gate ɗin suka shiga wata miqaqqiyar tafiya suka sake yi ko Ina ka kalla sojojin nan ne sai fama zazzare idanuwa suke. Tun daga farkon shigowar ka zaka hango wani tsararren gini da baza ka taba kawowa a kasar nan kake ba, saboda yadda plan din gidan ya fito dakyau, bangare uku ne ɗaya gefen dama, ɗaya gefen hagu sai ɗayan dake tsakiya Amma Kuma a haɗe suke, saidai Kuma kowa yana da kofar shiga bangaren sa daga waje ba tare da ya bi ta bangaren ɗaya ba, haka Kuma in sunso zasu iya zuwa bangaren ɗayansu ba tare da sun fito waje ba. Parking lot ɗin dake shaqe da wasu irin jibga jibgan motoci masu numfashi suka nufa, kafin ma kamal ya fito wani soja har ya buɗe masa kofar yana masa barka da zuwa, ba yabo ba fallasa ya amsa masa, kamar yadda fuskarsa take a ko da yaushe ita ba'a ɗaure ba ita Kuma ba a sake ba. Ƙarasowa sauran ma sukayi suna ta miqa masa gaisuwa, Sai da duk ya amsa musu sannan ya ce, "Fatan ba wata matsala?". " No sir ba wani matsala"...... Ɗaya daga cikin su ya amsa. Dan daga kansa yayi alamar yayi, sannan ya juya ya wuce su Kuma suka rufa masa baya har gaban building ɗin, ƙofar dake right hand side ɗin sa ya nufa Wadda itama masu tsaron ta daban suke, nan ma gaisheshi suka shigayi ya amsa sannan ya wuce ciki shi ɗaya Yan rakiyar tasa Kuma suka juya domin komawa bakin aikin su. Ciki ciki yayi sallama dan yasan ba lalle ya samun wani a falon ba, hakan ce kuwa ta kasance dan ba kowa sai wani makeken television Mai kamar cinema dake ta faman aiki shi kaɗai an rage volume gabaɗaya, qaton falo ne da ya cinye set din kujeru uku, faɗar kyawun falon nan sai wanda ya gani amma zan baku dama ku kiyasta shi a kwakwalwar ku kawai. Wata hanya yabi data sake fitar dashi wani falon da yafi Wanda ya baro haduwa saidai bai kaishi girma ba. Saida ya wuce faluka huɗu sannan ya bayyana gaban wata kayatacciyar staircase, hawa yayi saman, nan ma bakowa sai ma'aikata dake ta Kai kawo domin tabbatar da tsabtar muhallin, a bakin wata kayatacciyar ƙofa ya tsaya tare da yin knocking kusan minti biyu ƙofar ta buɗe da kanta, sa Kai yayi ciki da sallama, wani shiryayyen bedroom ne da yaji kayan alatun more rayuwa, gaban gadon ya ƙarasa inda na hango wata kyakyawar dattijuwa zaune tare da wata yarinya da baza ta wuce 13 years ba, ita yarinyar na zaune a ƙasa kan Italian rug ɗin dake shimfiɗe a ɗakin ta miqe kafafunta ta tisa litattafai gaba, ita Kuma matar tana zaune a saman idanunta sanye da farin medicated glass da ya karawa fuskarta kyau gabanta laptop ce take yan latse latse a Kai, shigowar sa ya sasu ɗagowa gabaɗaya, wani sassanyan murmushi ne ya wanzu a fuskar dattijuwar lokacin da Amjad din ya ƙaraso gefen ta ya zauna. Hannu ta Kai ta shafa kumatun sa, " Babban mutum! yau Ina ka shiga tun safe ban ganka ba? Ka fita baka shigo ba". "Kai Anah sai kace wani yaro, Kuma ma na shigo baki tashi ba ai saisa nace karsu Adla su tasheki". "Good evening Uncle"........Dafa kan yarinyar yayi da fadin, "Evening baby girl, karatu ake tayi ne haka". Anah ce ta ce, "To tashi kije wajen Adla ku ƙarasa karatun tare in da akwai inda baki gane ba ta nuna Miki"...........Da "to". ta amsa sannan ta tattare litattafan ta fita. Juyowa tayi gabaɗaya wurin sa da faɗin, " First of all kaci abinci tukunna?".........." Banci ba Anah, kuma ina shigowa naji wata yunwa whl"........Ya karashe yana karyar da kai gefe. "Ja'iri, to baka san hanyar dinning ɗin bane ko kuma zuwa kayi ka faɗamin na tashi naje na ɗaibo ma".........."Ayyah Anah ni ne fa". "Kai ɗin, ka ga dama ina neman ka amma tunda yunwa kakeji tashi ka fara zuwa ka ci abincin sai ka dawo muyi Maganar". "Gsky Anah sai dai a kawo nan whl, na gaji da yawa ne yau". Bata sake cewa komai ba ta danna wani abu a gefen gadonta, ba'a rufa minti biyu ba akayi knocking, remote ɗin da ke gefen ta ta dauka ta danna ƙofar ta buɗe wata maid ce ta bayyana sanye da uniform black and white, cikin harshen turanci ta ce, "Gani mah". "Ki kawowa babban mutum abinci"...... " Okay mah". Ta amsa tana ɗan duƙawa sannan ta juya ta fita. "Naje gidan mommy dazu".......Ya faɗa bayan fitar maid ɗin. "Mommyn, Mommy". Ta maimaita kamar bata gane ba. "Mommy Fareeha maman khadeejah"..........."Ohhkkk Allah sarki to ko kai fa Amjad, ka same su lpy?"......... Ɗan taɓe baki kana ya ce, "Hmmm, da sauki dai". "Nasan komai Amjad, kuma daman nasan a yanzu sai mun kai zuciya nesa, ada can ma ya aka ƙare ballantana yanzu da suka samu abun faɗa, Amma ka cigaba da hakuri komai me wucewa ne, in sha ALLAH, ALLAH zai toni asirin duk wanda suka ma wanna sharrin, muna nan muna kaiwa ALLAH Kukan mu kuma ALLAH baya bacci". Dan shuru yayi kafin ya ce, "Anah meysa baza a barsu da halinsu ba, kamar yadda kika ce kawai mu barwa ALLAH komai shi yasan daidai Amma karmu roqi ALLAH ya toni asirin su". Wani irin kallo ta watsa masa Wanda ya sashi sunkuyar da kansa ƙasa. " Amjad k......." Kiran dayan shigo system ɗin ne ya hanata karasawa , video call ne daga wata number da akayi savings da Afia, miqa hannu yayi ya amsa kiran. Wata kyakyawar macece ta bayyana a screen ɗin tana zaune dauke da wani baby boy da bazai haura 2 years ba akan cinyarta, "heiiii babbabb....." Shi ne abinda yaron ya faɗa cikin gwarancinsa yana ɗago musu hannu. "Hello my love". Amjad ɗin ya amsa shi ma yanawa screen din wani irin tausassan kallo. Murmushi Afia tayi wanda ya bayyana tsananin kamar ta da Anah, ta ce, " kai gauron uncle ya kamata kayi aure mu tarkatoma ya'yan Ka mu kawo ma, duk sun bi sun addabi mutan........" Kafin ta karasa maganar wasu yara su biyu suka yo kanta ɗaya ta kai ɗaya kuma ta gabanta kamar zasu shige cikin wayar, sai fama ihun Kiran Uncle Amjad, Uncle Amjad suke. "To tunda bani aka Kira aji ba, Bari na kashe laptop ɗi na sai Ku neme shi ta wurinsa"....... Da sauri Afia ta ce, " Afwan Anah, ni kinga ba ruwana ai, ni uwata na Kira naji muryarta". "Umm masu uwa manya, kefa an riga an daɗe da yayeki, ki daina wani Abu kamar wata auta". Amjad ya fada Yana harara ta. "Oho dai dadin ta Kai ma ba autan bane ai ranka ya dade". "Ni kuwa ai kinsan ba ya ni, tunda Ku kuna da yauwa ni kuwa ni ɗaya ne". "Kaji goɗoɗo dakai uban su wane kakan su wance ko kunya bakaji. Anah ALLAH ki dinga wa yaron nan faɗa ". "Whl ki fita ido na Afy ni zaki haɗa da uwata, yanzu sai na Kira mijinki na faɗa masa dan halin da kika koyo, naji in yana da sa hannu a ciki"..........."Anah kina jinsa ko, Yana mantawa cewa ni yayar sa ce". "Ku dai Kuka sani, kai Mai gidan haka zamuyi dakai wato ko nema na ma bakayi to m......" Knocking ɗin da akayi ya tsayar da ita ɗagowa tayi tana kallon kofar da har Amjad ya ɗauki remote ɗin ya buɗe, maids ne su biyu suka shigo niqi niqi da warmers suka jera a kasa sannan suka fita. Sauka yayi ya zuba abincin ya fara ci, idan Afia ta tsokano shi kuma ya rama har ya gama sannan ya dauki gorar ruwa . "Anah ALLAH ku daina bashi abinci, in yayi zuciya yayi aure". Hannu ɗaya ya kai kan Laptop ɗin ɗayan kuma ya sanya gorar ruwa a ɗan karamin bakinsa yana sha, ganin yana shirin rufe laptop ɗin yasa Anah bige hannun da faɗin, "Meye hakan kuma?"......Saida ya cire gorar ruwan sannan ya ce, "to Anah bakya ganin tsokanata take ne". "Au tsokanar ka ma nake, tsakani da ALLAH haka kawai ka dinga zuwa kana cinye musu abinci, Anah har yanzu yana nan da cin nan kamar gara ko". Baice komai ba ya koma ya zauna yana cigaba da shan ruwan kaɗan kaɗan amma idonsa akan screen ɗin. "Kinga Afia ki bar mutumin nan in ba so kike yayi gaba da laptop ɗin ba". "Anah ki korashi kawai yazo ya wani samu gaba muna magana, yauwa Anah ina su Esham da Adla ɗazu na kira Adla ban samu wayar ta ba". Amjad daya miqe riqe da gorar ruwan sa ya ce, "An dai ji kunya. Anah dama fa kira tayi tace Miki ta kira Adla taji muryar ƴarta bata samu ba shi ne ta lalubo ki a rashin option". Kafin Afia tace wani abu Anah ta ce, "To ina ruwanka". "Ni kunga tafiya ta ma"....... Ya faɗa yana nufar kofar, Anah ta tsayar dashi ta hanyar kiransa, "ina zaka kuma bayan nace ma ina son magana dakai"........."To Anah ai naga kamar yanzun waya kike". "Nop tsaya". Ta faɗa tana maida kanta ga screen din laptop din ta ce, "Afia bari zan kiraki back ɗan ban 10 minutes". "To". Ta ce yayin da Anah kuma ta kashe kiran tare da ture laptop ɗin daga gabanta ma gabaɗaya. Dawowa yayi ya zauna shi ma yana fuskantar ta. "Amjad! Miye matakin daka dauka akan wannan abun ko kuma miye matakin da kake kokarin dauka?". "Anah ni fa ban aikata abinda suke fada ba, dan ALLAH ki kwantar da hankalin ki mana". "Hankali na bazai taɓa kwanciya ba a cikin wannan halin da ake ciki Amjad, kuma sanin baka aikata ɗin ba ne yasa nake tunanin me zai hana ka shigar da ƙarar gidan radio da kuma televsion ɗin da suka wallafa wannan labaran ba, sannan su fito da wanda ya basu wannan labaran bogi da naso nayi Magana da Juraysh sai naga ya kamata na fara tuntubar ka". Shiru yayi yana wani tunani kafin ya ce, " Anah a yanzu bamu da damar yin hakan saboda hukuma ta shigo cikin lamarin, yanzu gabaɗaya idon duniya ya dawo kai na da duk wani motsina, Al'umma gabaɗaya sun zubawa ƙasar Nifaz ido ne domin ganin iya gudun ruwan su, muna wani motsi zai zama qarin matsala, gwara mu bari su gama binciken a lokacin da suka tabbatar bani da laifi, mu kuma lokacin sai mu ɗaukaka namu ƙarar". "Kai ɗin ba me laifi bane Amjad". Riqo hannuwanta yayi duka biyun cikin nasa yana hango tsananin damuwa dake cikin ƙwayar idonta ya ce, " Ban aikata ba Anah, kuma addu'ar ki itace kaɗai zata iya fiddani a halin da nake ciki ba wai damuwar ki ba, Anah ni kai na tafiya kawai nake amma a yanzu rashin lpyr Dada ma tafi komai ɗaga min hankali, ke kaɗai nake gani na danji karfi a jiki na". Girgiza kanta tayi da faɗin, "ALLAH zai bayyana Gsky , kuma in sha ALLAH duk wanda ke son ganin bayan ka ba zai yi nasara ba saidai kai kaga bayan sa, kuma ALLAH sai ya wulakanta rayuwar sa". "Ah ah Anah, Ni Bana son ganin bayan kowa ina so kawai ki roqa min ALLAH da ya kareni yasa nafi karfin duk wani mugu ya kuma bani nasara da Sa'a. Anah dukda an halatta wa wanda aka zalunta ya yi addu'a kan azzalumin daidai gwargwadon zaluncin, amma an fi so ayi haƙuri, a yafe kuma a nemi shiriya ga azzaluman, domin samun lada a wurin ALLAH. Saboda kamar yadda addu'ar alkhairi take dawowa haka mummuna". Murmushi tayi tana kallon sa cike da so da ƙauna kafin ta ce, "Nagode da tunatar wa Amjad , ALLAH ya ma Albarka, ALLAH ya tsareka daga duk wani sharri ya baka sa'ar rayuwa". "Ameen Anah tah ko ke fa, to yanzu ina iya tafiya? Dan inaso naje naga jikin Dada ne". "Saura abu daya, batun yarinyar nan da iyayen ta". "Anah wannan ai kotu ce zatayi aikin ta, kuma barrister Nazar zaiji da komai, karki damu in sha ALLAH ba wata matsala". "Sauri kake kaje kaga Dadan ka ko? Sai sa kake ta yanke min zance". Yar dariya yayi yana shafa kansa tare da tashi ya ce, "barin je Anah". "To, a fito lpy". Ta faɗa tana binsa da kallo mai cike da ƙauna da kuma tausayin ɗan nata na miji kwara ɗaya. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______5 & 6 Ko da ya fita ta cikin sashen nasu ya shiga bangaren mahaifin nasa. Kallo ne ya Koma sama domin komai na wanna bangaren linkin wancan ne ko ma nace yafi wancan. Sojoji ne tsaitsaye ta kowani angle na kofar sashen yadda ko sauro ne yayi ƙwaƙwaran kuka sai sun ji. wucewa yayi ciki inda ya tarar da wani mutum zaune yana waya, kallo daya zaka masa Ka tabbatar da ɗan uwansa ne saboda kammani na jini dan basa wani kama a yanayin halitta, yana ganin sa ya kashe wayar da fadin, " Dama kana garin nan Amjad?". Fuskar sa ba yabo ba fallasa ya ce, "Kai za'a tambaya ai Awais, an kusa sati biyu bamu hadu ba". "Eh tou, abubuwan ne da yawa muyi nan muyi can, Gashi ka ga kai yanzu baka komai duk nauyin ya dawo kan mu, shi kuma Julaybin Abubuwa sun masa yawa, so mu ne dai tsaye Kan komai ni da Nuhail, yanzu ma cewa nayi bari na shigo naga jikin Dada, da ranar ba samun dama ake ba". Murmushin gefen Baki yayi tare da wucewa yana fadin, "haka ne ALLAH ya taimaka "....... Ɗakin mahaifin sa ya nufa tare da tura ƙofar ya shiga da sallama. Wani dattijo mai kamala ne ya amsa yana ɗaurawa da, "Barka da zuwa yallabai". Jingina yayi jikin kofar tare da fadin, "Baba Sufi baza ka daina kirana da yallabai ɗin nan ba , Ni fa kamar ɗan ka ne"........... Ya fada hankalin sa kan wani wuri, kallona na Kai Kan inda yafi bada hankalin nasa, wani dattijo na hango kwance Kan wani ƙayataccen gado idon sa akan Amjad ɗin dake tsaye. Takowa ya shigayi cikin sanyin jiki zuwa gaban gadon , yayin da wanda ya kira da Baba Sufi kuma ya miqe daga zaune da yake a bakin gadon yana ɗan murmushi ya ce, "Bari na dan zagaya, kafin ka fito"........Ya ƙarashe yana ficewa daga dakin. Gaban gadon ya durkusa tare da dago hannun dattijon ya sanya cikin nasa ya Kai bakin sa ya bashi peck sannan ya ce, " Barka da Daren my hero." Murmushi ya masa tare da lumshe idonsa ya buɗe wanda hakan ya sake bani mamaki shin baya magana ne. "Dada na, yau baka ganni ba ko? Na fita tun sassafe ne sai yanzu na shigo"..........Kallon da mahaifin nasa yake masa me alamun tambaya ne ya sashi faɗin, "Naje yin wani Abu mai muhimmanci ne, sannan na ma je Wurin mommy Fareeha, kuma tace in gaishe Mata da Kai itama zata zo in sha ALLAH. Yau na gaji sosai Dada kai na har ciwo yake .........." Haka ya cigaba da bashi labarai yana masa hira amma duk wanna Abun ba umm bare um um, saidai in abu ya masa yayi murmushi in tambaya ce ya lumshe idanun sa ya bude, babu magana sannan ba inda ke motsi a jikin sa . Bashi ya bar ɗakin ba saida yayi bacci sannan ya gyara masa kwanciyar ya fita. A falon ya samu Baba Sufi zaune shi kaɗai riqe da kofin shayi. "Baba Sufi kuma shi ne ka gudo nan kayi zaman ka". "Ai cewa nayi bari na barku ku gana"........." Ina Awais?".........Amjad din ya tambaya yana bin falon da kallon. "Ai ko dana fito ma ban sameshi anan ba Gsky, Maybe ya tafi ne ko kuma ya shiga wurin Hajiya"....... Ɗan shiru yayi kafin ya ce, " Shikenan Baba Sufi bari naje, sai da safe". "To Allah ya tashemu lpy, Nima ina jira ne in Hajiyar ta shigo sai naje na kwanta". "Ai ya ma yi bacci fa"..........Amjad ɗin ya faɗa yana zura hannun sa ɗaya a aljihu, ya nufi hanyar barin falon. Ɗakin sa ya wuce tare da zaro wayar sa ya kira Nayrah, tana ɗagawa ya ce , "Niniyous ykk"..........Ɓata rai tayi kamar yana gabanta ta ce, "Sai yanzu ne ka tuna Dani ko". "Ke dai ba'a rasaki da ƙorafi, yanzu ne na samu zama ai". "To naji, me kakeyi yanzu"..........Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce, "Me zanyi ninie, yanzu na shigo ɗaki na kwanta"........Jin tayi shiru ya sashi faɗin, "Tunanin me kike?". "Tunanin ka "..........."Ni kuma? Me nayi da na hana zuciyar Ninie hutu ta shiga tunani na?"......... Ya faɗa yana juyawa ya kwanta akan cikinsa saɓanin da da yake reran, pillow ya janyo ya daura kansa akai tare da ɗaura wayar saman kunnen sa . "Mumu ce ke fushi dani"..........cike da ƴar damuwa ya ce, "Saboda ni ne ko?".........Ɗaga masa kai tayi kamar yana gabanta kana ta ce, "ɗazu ne ta ji muna waya, shi ne take ta fada, Amour na rasa taya zanyi na shawo kan mumu ta fahimtar da dad game da sharrin da akai maka, gabaɗaya taƙi yarda da duk wani abun da zan faɗa mata, nayi iyaka koƙarina amma kullum ma kamar ƙara tunzirasu ake".........Ta ƙarashe cikin yanayin dake nuna tana jin ɗacin maganar da take furtawa. "Hakan ba laifi bane Ninie, domin abinda mumu da dad sukayi shi ne abinda kowani iyaye nagari zasuyi akan ƴar su, kuma suna sonki ne saisa suka kasa fahimtar duk wani bayanin da zaki musu a kai na". "Bann... Bangane ba Amour me kake nufi?". "Ke yarinya ce baza ki fahimta ba, Abinda nake so dake kar muyi gaggawa domin gaggawa daga shaiɗan ne jinkiri kuma alheri ne. Kiyi haƙuri ki sa musu ido kiga abinda zasuyi". Unexpectedly yaji ta fashe masa da kuka, cikin kukan take faɗin, "Amour kai ma yanzu ka goyi bayan a rabamu kenan? Shikenan dama nasan ni kaɗai nake faman zubin adashin da ba ranar ɗauka. Na riga na san ba so na kake ba, kawai dai ina takura ma ne. Sai ka wani dinga dauka na a banza a banza, an gaya ma in na rabu da kai mutuwa zanyi ne, kai ɗin banza ai da bansan ka ba nake rayuwa, dan haka yanzu ma in na rabu dakai ba abinda zai far...u".........ta ƙarashe Maganar a rarrabe saboda kukan da yaci ƙarfin ta, kashe wayar tayi tare da yin wurgi da ita. Haɗe kai da guiwa tayi ta shiga raira kukanta bilhaqqi da gaskiya dan tana matuqar son Amjad, shi ne first love ɗin ta Kuma da shi take fatan ƙare soyayyar ta. A bangaren Amjad kuwa kafin yayi yunqurin cewa komai ta katse kiran. Dafe goshinsa yayi da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana riqe da wayar sa, sam baiji zafin Maganar ta ba takaicin sa kukan da takeyi, yasan irin yadda suke ƙaunar Junan su shi da Nayrah domin ba dan Abubuwan da suka faru ba da kuma wanda ke kan faruwa a yanzu to da ba zai wuce wata biyu ba auran su saboda har baiko an musu, to amma ya zaiyi? Zaije ne ya nunawa iyayen ta ƙarfi ko kuwa zai iya canza abubuwan dake faruwa dashi ? Hakurin dai shi ya kamata suyi har komai ya daidaita saidai ita ta kasa fahimtar hakan, gani take kamar bai damu ba saboda shi mutum me zurfin ciki, da wuya ya fito ya faɗi damuwa ko yanayin da yake ciki, wannan yasa Nayrah ke ganin laifin sa. Tashi yayi riqe da wayar sa ya zura mule slippers din sa ya fice daga dakin. __________sosai ta sha kukanta har ta godewa ALLAH sannan ta tashi da niyyar shiga toilet ta wanke fuskarta kawai taji an turo ƙofar ɗakinta an shigo, saurin waigowa tayi kasancewar ba wadataccen haske a ɗakin yasa a tsorace ta ce, "Nashwa?"..........Shiru taji sai ma locking ƙofar da akayi a tsorace ta bude baki da niyyar yin ihu. "Shiiiiiii"..........Ya faɗa yana ɗaura yatsansa akan lips ɗinsa alamar tayi shiru. A tsorace taja baya tana binsa da wani irin kallon tuhuma saboda matsowar da yayi yasa ta gane shi ne, cikin rawar murya ta soma tambayar sa, "Amour y..ya ya akayi ka shigo gidan nan? Taya ma ka wuto duka kofofin gidan nan har ka hawo sama ka shigo ɗaki na bayan ko ina a kulle yake? Na shiga uku! ALLAH yasa ba wanda ya ganka"......... Gabaɗaya a hargitse take jero masa tambayoyin kamar wadda taci kai. Harɗe hannuwan sa yayi a ƙirji yana jifanta da wani irin narkakken kallo mai cike da tsantsar ƙauna, ya buɗi baki da faɗin, "A kanki ba irin kasadar da bazan iya ɗauka ba Ninie, ko da kuwa sanadin hakan zan rasa rayuwata ne. Ki nutsu muyi Magana".............. girgiza masa kai ta shigayi tare da faɗin, "Bazan iya ba, I'm afraid ina tsoro Amour wani zai iya zuwa ya gan ka".........Ta ƙarashe ko ina na jikinta na rawa. Fisgota yayi tare da riqo kafaɗunta da hannayen sa idanuwan su cikin na juna sai dai ita kallon firgici take masa, sake kwantar da murya yayi wurin faɗin, "Ina son ki ninie, duk duniya ALLAH ne kaɗai zai iya rabamu saboda dama shi ya haɗamu, ita soyayya a zuciya take ba wai a baki ba, domin daɗin baki in yayi yawa ƙarya da yaudara ne ke shigowa ciki. Ina son ki ninie, ki yarda dani, ki kuma yarda da cewa ina tare dake duk rintsi saidai idan kece kika gujeni"...........a hankali jikinta yake saki, maganganun sa suna ratsa ta, nutsuwar ta tana dawowa Ajiyar zuciya ta sauke tare da zamewa daga riqon da ya mata ta koma ta jingina jikin bangon ɗakin tana kallon sa. "Ka tafi to, ina tsoron kar wani ya ganka a sake samun matsala". "Kin fiya tsoro da yawa, in ma an ganni ai kece sila, in dai zaki kashemin waya kina kuka to kuwa a duk inda kike a kuma kowani lokaci zaki iya gani n........" Kafin ya ƙarasa sukaji Knocking, da sauri ta matso wurinsa tana yarfa hannu da faɗin, "Shikenan kaga abinda nake gaya maka ko, yanzu ya kake so nayi"..........shiru yayi idonsa akan Ƙofar ya ce, "Wa kike tsammani a wannan lokacin?". "Wace irin tambaya ce wannan amour, mutanan gidan mu ne mana, kuma kasan in suka ganka kashi na ya bushe".........ta faɗa cikin raɗa, wucewa yayi bakin gadon ya zauna tare da faɗin, "jeki ki duba". Ƙara rikicewa tayi sai ta nufi ƙofa ta dawo wurin sa, gashi har lokacin Knocking akeyi. "Ki nutsu kije ki duba". Ya sake faɗa a dake. Daurewa tayi ta nufi ƙofar ta buɗe tana waiwayen sa, ido huɗu tayi da Mumu dake tsaye tana binta da kallon tuhuma kafin ta ce, "Yau kuma wani munafurcin ne yasa kika kulle ƙofar?"..........Dan Susa kanta tayi, cikin alamu na rashin Gsky ta ce, "Am dam..a dama naji tsoro ne saisa na rufe". "Ban hanya na wuce"........... Mumu ta faɗa tana kokarin sa kai cikin ɗakin, da sauri ta tare da faɗin, "Mumu dan ALLAH karki shiga ɗakin a hargitse yake gyara nake duk na fito da kayan ".......... Ta ƙarashe tanawa Amjad alama da hannu da ya tashi ya shige toilet. "Zaki ban wuri ko sai na gaura Miki Mari, uwar me kike boyewa cikin ɗakin"......... Mumu ta ƙarasa tana ture ta tare da shigewa ɗakin. Wani irin tsuma jikinta ya ɗauka, ta kasa ko da ƙwaƙwaran motsi ballantana ta juya jira kawai take taji me zai biyo baya. Bin ɗakin Mumu tayi da kallo Kafin ta ce, "Me kike shiryawa ?"..........Yadda taji Mumu tayi tambayar ya sata ɗan juyowa, waro idanun ta tayi gabaɗaya ganin ba Amjad ba alamar sa a ɗakin, wurga ido ta shigayi ko zata ga inda ya ɓoye ta ma manta da Mumu dake binta da kallo har sai da ta ce, "Whl ki kiyayeni, idan na gano akwai abinda kike ɓoyewa sai naci ubanki a gidan nan, ki wuce mu tafi Nashwa bata jin dadi kije ki kwana a ɗakinta". "Ni me zan ɓoye Mumu, dan ALLAH ki yarda dani mana".........juyawa tayi ta fita tana faɗin, "Ni dai na gaya miki, kuma karki ɓatan lokaci ina jiran ki a ɗakin nata, ina so in je in kwanta". Wata gauron ajiyar zuciya ta sauke bayan fitar Mumu, bincika ɗakin ta shigayi lungu da sako har toilet amma bata ganshi ba, tsayawa tayi tana tunanin ina ya shiga to, tsuwwar da wayarta ta fara yasa ta nufeta tana zuwa taga shi ne cikin sauri ta ɗauka kafin tace wani abu ya riga ta da faɗin, "Karki wahalar da kanki wurin bincike na, ni na riga na tafi, ki wuce ki tafi kinsan Mumu na jiran ki, Kuma ki kula ki kuma rage tsoro dan zaki tonawa kanki asiri ne kawai". "To wai yaushe ka fita? Ta ina ma ka bi?"........ Ta tambaya cike da tsantsar mamaki. Ba tare da yabi takan tambayar ba ya ce, "good night, have a sweet dreams of me"..........Yana kaiwa nan ya kashe ya barta saqalo riqe da waya. ---------------------√ Sai da ta Kintsa komai na gidan sannan ta shiga wanka dan tuni Sahnish ya tafi kai Shazeen makaranta, ko da ta fito shiryawa tayi ta dauki Jakarta ta fita tare da kulle gida ta saka maqullin a jaka. Abun hawa ta tara sannan ta shaida masa inda zai Kaita. A gaban wani ratsatstsen wuri da a saman aka rubuta STARLIGHT BEAUTY CO. Suka tsaya, sallamar me tuktuk ɗin tayi sannan ta shiga wurin. Babban wurin ne da ya gaji da haɗuwa, kallo ɗaya zaka masa kasan wuri ne na masu hannu da shuni, ba abinda ba'a yi a wurin kama daga kan su saloon, spa, pedicure, manicure, henna da sauransu. A reception ta tsaya suka gaisa da receptionist ɗin sannan ta ce, "Mai wajen fa?"..........Dan kallon tuhuma matar ta mata kafin ta ce, "baiwar ALLAH lpy dai?". Ƙasa ƙasa ta watsa mata wani kallo sannan ta ce, "lpyr ce ta kawo haka, gyaran jiki zata min, ni amarya ce Amma bana son aikin yara kuma bana son wasa saisa nafi buqatar nayi magana baki da baki da ita"......... Sai da receptionist ɗin ta sake ƙare mata kallo sannan ta ce, " Bata zama yau, Amma kinyi sa'a yanzu nayi waya da ita tana hanya, kina iya zama ki jira ƙarasowar ta". "Eh to, ALLAH yasa karta daɗe dan ina da uzuri"........ Ta ƙarashe tana wucewa ɗaya daga cikin kujerun dake reception ɗin ta zauna tare da ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya kamar wata shegiya, bin wurin ta shigayi da kallo tare da jinjinawa samun wuri irin na masu kuɗi, kawai mutum yazo ya biya dubunnen kuɗaɗe dan kawai a yanke masa farce ko kuma a wanke masa ƙafa. Bata daɗe da zama ba wata babbar mata ta shigo. "Barka da zuwa Hajiya"........ Receptionist ɗin ta faɗa tana fitowa daga wurin da take wanda wani gajeren gini da akayi ya kewaye tare da barin wurin shiga da fita kamar kofa, an yi plan din abun ne kaman zagayayyen table tare da sanya kujera daga cikin cycle ɗin saidai shi ba table bane hasali ma da gini ne aka manna masa tiles. "Yauwa jumayma, ya kokari?" .........Ta faɗa cikin sakin fuska. "Lpy kalau Hajiya"..........."To masha ALLAH"........ Ta faɗa tana wucewa ciki, jumayma ta rufa mata baya. Bata jima ba ta dawo hannunta dauke da tumbler da kwalin exotic, stool ta janyo ta ɗaura akai tare da faɗin, "Ga lemo Ki sha, na faɗa mata, ki ɗan jira kaɗan". "Ba damuwa"............Ta faɗa cikin tsare gida kamar wata uwar masu gida, sannan ta ƙara da fadin, "AC Nan naku baya aiki sosai fa". "Bari a Kara ".......... Jumayma ta faɗa, har hannunta na rawa wurin ɗaukan remote ɗin ta kara mata, sannan ta koma wurin zamanta ta zauna. Ko kallon tumbler ɗin batayi ba bare lemon, gabaɗaya hankalin ta ma naga TV dake manne a bango tana aiki inda ake nuno labarin wani shahararren wanda ake zargi da laifin safarar mutane zuwa ƙasashen waje, mai labaran ta ƙara da , "Wanda ake zargi da wannan laifi ba kowa bane face Amjad Hashim Darwin, wanda a yanzu duniya gabaɗaya ta zubawa ƙasar nifaz ido ne domin ganin hukuncin da zata ɗauka. Kamar yadda kuka sani shi ɗin ya kasance hatsabibi mai aiki da fuska biyu, ya dau tsawon lokaci yana aikata wannan laifi ba tare da an farga ba. Ruhotanni sun sake bayyana cewa a dukkan record na laifukan da ake samu dangane da laifin safarar mutane shi ne number 1 suspect, Amma kuma ba'a kamashi dumu dumu ba sai dai har yanzu jami'an mu suna iya bakin kokarin su wurin bincike. Yanzu zamu bawa Mutanen mu damar fadar ra'ayoyin su dangane da wannan case ɗin daya rikita ƙasa gabaɗaya akan Number waya kamar haka 091.........." Tana ƙarashewa kira ya shigo, " Hello salamu alaikum". "Wa alaikum salam".........." Da wa muke tare?" Mai gabatar da labaran ta tambaya. "Kuna tare da Alfah Zuhair, daga babban birnin Nifaz". "To Malam Alfah mai zaka iya faɗa game da wannan case ɗin ?"..........."A gsky muna kira ga gomnati data ɗau tsautsauran mataki akan wannan mai laifi ba tare data duba matsayin da mahaifin sa yake dashi ba a ƙasa da kuma duniya bakiɗaya, domin a halin yanzu al'ummah sun shirya tsaf domin ɗaukan doka da hannunsu idan har suka ga gomnati zatayi musu wasa da hankali kamar yadda aka saba banbanta doka a tsakanin talaka da Mai kuɗi, saboda jama'ar gari sun alaqanta wannan jan Lokacin da ake tayi da sunan binciken domin a janye hankalin su daga kan case di......." "Ranki ya dade, Hajiya ta ce ki shiga"........ Maganar Jumayma ta katsewa Hushaima kallon labaran da take. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta miqe tare da ɗaukan kwalin exotic ɗinta ta wuce ciki. Saida ta tsaya ta jefa kwalin lemo a jaka tana fadin da ganin wannan mai zubin munafukan kasan zatayi baqin hali, ALLAH dai ya ɗaura ni akan oganniyarta ta. Ni kuwa nace ke dai komai akayi ba'a fita a wurin ki Hushaima. A wani karamin falo ta samu hajiyar zaune, tana ɗaura ido a kanta dariya taso subuce mata ganin fuskar matar kamar kwarya ta sha bille ta ko Ina, sam a shigowar ta bata lura ba ko dan ita tana daga side na kofar shigowar ne. Fisgewa tayi abun ta sannan gaishe ta. Amsawa tayi ba yabo ba fallasa sannan ta ɗaura da fadin, "Sorry na barka kina ta jira, na tsaya wani lissafi ne". " Bakomai hajiya, dama dai wani dan taimako nazo nema wurinki". "Taimako Kuma?"......... Ta tambaya tana Ƙare mata kallo ganin batayi kama da mabaraciya ba balle tace bara take katse mata tunanin tayi ta hanyar faɗin, " So nake ki taimaka ki ɗaukeni aiki anan wurin dan ALLAH, ni din bazawara ce miji na ya mutu ya barmi da marainiya, hajiya ga matsin gari na rasa in da zan sa kai na". Shuru matar tayi kafin ta ce, " Toh baiwar ALLAH ba wai naqi bane amma a qa'ida bama ɗaukan mutum haka daga sama b......" Kafin ta ƙarasa Hushaima ta riqo hannayen ta kamar zata fashe da kuka ta ce, "Hajiya ki taimake ni Dan ALLAH, duk wanda ya taimaki wani ALLAH zai taimake shi, Hajiya tunda har ALLAH ya baki dama da kuma halin yin taimakon Wannan ma soyayya ce da rahama ta musamman, idan kuma har kayi amfani da wannan damar da aka baka don taimakawa, to kai ma zaka samu sakamako mai kyau na lada a wajen ALLAH". Shiru hajiyar tayi tana tunani kafin ta ce, "Shikenan ka tashi kaje reception wurin Jumayma ka cike form, ba damuwa in sha ALLAH. ALLAH zai kawo mafita"..........Ta Ƙarashe tana bin Hushaima da kallon tausayawa ganin da ƙarancin shekarunta ɗawainiya irin wanna ta hau kanta. Ni kuwa nace an kai wata sharaton. " In ka cike, ko zuwa gobe ma zaka iya farawa. ya so in kazo sai muyi maganar albashi".......Godia ta fara mata kamar zata ari baki har saida ta tsaida ita da fadin, "karka damu ai duk yiwa Kai ne"........Sai da ta sake mata godia sannan ta fito cike da farin ciki. Reception ɗin ta dawo, samun Jumayma tayi tana waya kuma ga dukkan alamu hajiyar ce ta kira take sanar mata. Ja gefe tayi ta tsaya har saida ta gama sannan ta ce, "Hajiya tace nazo wurin ki na karɓa Form"........ba tare data kalle ta ba, a wulaƙance ta ce, "Na ji".......Saɓanin ɗazu da ta tarɓe ta da rawar jiki. Drawer dake wurin ta bude tare da zaro Form ɗin ta ɗaura mata pen ta tura mata gabanta , ta koma ta zauna tana sake haɗe girar sama data ƙasa kamar a kanta Hushaiman zatayi aikin. Zubawa paper ido Hushaima tayi kamar mai irgen rubutun, jin shirun yayi yawa yasa Jumayma kallon ta da fadin, "Ya dai?".........." Kinga kamar fa an samu kuskure a rubutun nan." Wani kallon rainin wayo tai mata kafin ta taso ta janyo paper da faɗin, " kinga Malama cewa akayi ki rubuta sunan ki, number wayar ki, Adreshin ki, email address, NIN number, Acc number, sunan guarantor din ki, number wayar sa da Adreshin sa. Ai ba wani dogon turanci bane ballantana har ki nemo wani kuskure a ciki".......... Ta ƙarashe tana sake tura mata paper gabanta. Bata ce komai ba taja biron ta ɗaura kan paper saidai ta ƙasa rubuta komai, sai sake bin rubutun take ɗaya bayan ɗaya, can kuma dai ta ɗago da faɗin, "zan iya tafiya da ita gida gobe in zanzo sai na taho da ita?". "Zaki iya miss"....... Jumayma ta fada cikin izgilanci tana dariya. Bata bi ta kan dariyar da Jumayma ɗin ke yi ba ta dauki paper tayi waje, duk da kuwa tasan me takewa dariyar. Da Ƙafa ta shiga takawa saboda akwai ƙarancin abin hawa na haya a unguwar kasancewar layi ne na masu kuɗi. Saida ta tsaya ta musu cefane sosai wanda zai ɗan musu kwana biyu sannan ta tari abun hawa ta wuce gida cikin farin cikin samu aikin yi. Wuraren Sha biyu ta tashi ta shiga kitchen domin ɗora musu sanwa, Sahnish ne ya shigo jikin sa duk jini, ga hannun sa a ɗaure da rigar sa da ya cire ya daure hannun da ita. Fitowa tayi daga kitchen din tana faɗin, "Albishir........." Maganar ce ta maqale mata sakamakon ganin sa haka a ruɗe ta shiga jero masa tambayoyi. " Meya faru da kai Sahnish? Meya sameka? Hadari kayi?". Wucewa yayi bakin Ƙofar ɗakin su ya zauna dakyar ba tare da ya kalleta ba ya ce, "Ba komai bane fa ɗan ciwo ne naji kawai".......... girgiza masa kai tayi da faɗin, "Baka saba min ƙarya ba, dan haka in kayi dole in gane, taya zaka ce ba komai, ka kalli kanka kuwa "..........."Nace Miki bakomai kawai"..........Ya faɗa still kansa a ƙasa. Baya baya ta fara kafin ta ce, "Whl idan baka fadamin ba sai naje har garejin naku naji abinda ya faru, in na dawo kuma sai naci qaniyar ka billahillazi. Ya zaka fita lpy ka dawo min haka ga hannunka a daure sannan ina tambayar ka kace min bakomai, Ni zaka maida sauna, ko ka manta na rigaka zuwa duniyar ne". Ɗan kallon ta yayi kafin cikin ƙarfin hali ya ce, "ki min alqawari ko na gaya Miki baza kiyi komai ba". A tsawace ta ce , "Dan ALLAH Ni ka fadamin ka daina min kwana kwana kana bata min lokaci".............Shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba can Kuma ya ce, "Su karafiya ne". "Suka ma me?" Ta tambaya cikin zaquwa. "Duk wanna abinda kika gani"......... Ya bata amsa cikin fargaba. "Me ka musu?"..........." Me kuwa zan musu ai kinsan ba abinda zai haɗani dasu, faɗan ki ne ya shafeni sunce wai sun daki kuɗinsu". Wata ashariya ta lalubo ta kwantsama sannan ta ce, "In kuwa haka ne lalle sun Kawo karshen iskancin su da kansu, wa yace musu ana irin haka Dani, whl in duk duniyar nan gatan su ne sai zaman unguwar nan ya gagare su, dabar ma in ance musu ga hanya baza suyi ba". Kafin yayi magana ta zari gyalen ta dake kan igiya tayi waje yana kiranta Amma ko juyowa batayi ba, Cikin karfin hali ya fara kokarin tashi ya bita amma jikin sa ya masa nauyi hakan ya sashi dafe Kai yayi shuru kawai cikin tsananin tashin hankalin abinda Hushaiman zataje tayi. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______7 & 8 Zaune suke gabaɗayan su a dinning suna breakfast dad, Mumu, Nayrah da kuma kannen ta uku Nashwa, da majeed sai kuma Nashmi. "Nashwa ya jikin naki?".......Dad ya tambaya yana kai Mug bakin sa. "Naji sauƙi dad Alhamdulillah".........." Masha ALLAH, ALLAH ya ƙara sauƙi, amma in kinji zazzaɓin ya dawo kuje asibiti". "In sha ALLAH dad"..........kallon Mumu yayi da faɗin, "to Hajiya Latifa ni zan fita ba wata Matsala ko?"......... tissue ta ɗauka ta goge bakin ta sannan ta ce, " Akwai abu ɗaya, batun Farshad gata nan ka faɗa mata da bakin ka saboda ni ta raina ni, ban isa nayi magana ɗaya ba saita maida min goma". Rufe Nayrah da faɗa dad yayi kamar zai haɗiye ta ɗanya har abin yaso ban mamaki, cikin zafin rai ya ce, " kin san dai abinda ya faru dangane da wancan baragurbin da kika kawo mana dalilin jajiɓe jajiɓan ku na tsiya, sannan na riga na muku iyaka ke da shi kuma batun baikon ma yanzu babu shi na warware. Akwai yaron Aboki na Farshad, kuma na riga nayi magana da mahaifin sa na kuma bashi auranki saboda bana ma so aja Lokaci, zaizo ku gaisa sauran naji wani abu marar daɗi sai na mugun saɓa Miki whl". Cikin rawar murya ta ce, "Haba dad, haba dad dan ALLAH karku yiwa Amjad haka, shi ɗin bai cancanci hakan daga gare ku ba, dad nasan kai ɗin babban mutum ne kuma ka riqe muqamai da yawa, amma ka tuna halaccin Amjad a gareka ba wai ina ma gori bane, kawai ina ma tuni da baya ne, a lokacin da dukkanin abokan naka suka gujeka suka daina yi da kai saboda kawai ka samu raunin arziki ba tare da sun duba kai ɗin waye bane ada, amma shi fa ? Yana tare da mu . Dad zuciya me halacci bata manta alheri dan ALLAH dad karka rufe idanun ka ". Mumu ce ta amshe da, "A lokacin ai bamu san ainahin ɗayar fuskar tasa ba, waya sani ma ko dan ya gan mu da yara ne yayi cinikin su ya bamu kuɗin idan ya samu sarari ya yi gaba dasu, ko kuma ke da shegen rawar kanki in ya samu dama ya ɓata Miki rayuwa ya cucemu. Kin shiga zuciyar sa kinga niyyar sa ne a lokacin da ya taimake mu? ba'a isa ayi magana ba sai kice a dinga tuna alherin sa". "Ko ɗaya Mumu Amjad zuciya ɗaya ya taimake mu, kuma nayi mamakin yadda zantukan mutane suka samu wurin zama a zuciyar ku, whl Mumu! dad!, in kuka tsananta akan Amjad zakuji kunya, Ni nasan waye shi kuma nasan bazai taɓa aikata wa'annan abubuwan ba, kawai dai mutane ne suke son masa ƙazafi saboda shi ɗin sananne ne, ko kuma masu son yin amfani dashi su ɓatawa mahaifin sa suna, amma Gsky zatayi halinta nan bada jimawa ba". "Ke Nayrah saurara duk wannan maganganun naki bashi zai wanke shi daga zargin laifu......." "Kaji ko dad kai ma zargi kace".......... Ta katse shi, tashi yayi bata ankara ba ya wanke ta da mari sannan a dake ya ce. "Keee dakata min haka kinji ko, dan mun baki damar magana ba shi yake nufin zaki dinga ja in ja damu ba, har kina ikirarin zamuji kunya, akan wani banza can da baki haɗa dangi dashi ba kike fatan iyayanki suji kunya tsabar baqar zuciya, to bari kiji ko ya aikata ko bai aikata a yanzu bamu iya bashi auran ki saboda sunan sa ya riga ya ɓace a idon duniya, in kuma ɗan taimakon da ya mana ne ada a yanzu zan iya linka masa na maida masa, kuɗin ma da bamu san na halal ne ko haram ba, wawiyar banza wawiyar wofi". Bataji zafin Marin da dad ya mata ba sai zafin maganganun da yake jifan Amjad dasu. Cikin dacin rai ta ce, "Dad sai dai kuyi hakuri ban taba qin wani abu da kuke so ba Amma in dai kuka hanani auran Amjad to whl bazan auri kowa ba, saidai ku kai gawata"......... Tana kaiwa nan ta miqe ta bar dinning ɗin da gudu tana fashewa da kuka. "Sai dai kuwa ki mutu shashashar banza shashashar wofi, dan kin mutu zan damu ne". Dad ya faɗa cikin tsananin fushin da ya sake ɗauremin kai. "Ka gani ko Alhaji, kana dai gani, yarinyar nan nema take tafi ƙarfin mu anya yaron nan ba asiri ya mata ba, yarinya lokaci daya ta birkice ".........….. Mumu ta faɗa tana tana nuna hanyar da Nayrah tabi da hannu. A hankali Nashwa ta ture plate ɗin abincin dake gabanta ta miqe tabi bayan Nayrah ɗin. Majeed ma miqewa yayi tare da faɗin, "Nashmi tashi mu wuce school kar muyi late, dad mu zamu wuce". "Ku sauka lpy".........Ya faɗa har lokacin sauke numfashi yake da zafi zafi alamun akwai abinda ke cin ransa. Ba tare da Mumu ta lura da yanayin sa ba ta ce, "Alhaji yaran nan duk sun zama munafukai fa, ka duba duk sun tashi sun bar abincin saboda kawai an yiwa wannan me shegen taurin kan faɗa"..........."To laifin waye?"........ Ya tambaya a kausashe. "ban gane laifin waye ba?"............itama ta maida masa tambayar tana zuba masa ido, kallon ta yayi na tsawon seconds kafin ya sauke ajiyar zuciya da faɗin, "laifi na ne. Bari naje sai na dawo".........kwafa taja ta bishi da kallo har ya fice sannan ta tashi ta bar dinning ɗin itama. ____________Nayrah na shiga ɗaki gaban mirror ta wuce ta tsaya tana kallon kanta yayin da hawaye ke zarya akan kumatun ta, ta dau tsawon 3 minutes kafin ta share hawayenta ta nufi inda wayar ta take ta ɗauka tare da dannawa Amjad kira, har tayi ringing ta katse bai ɗaga ba , sake kira tayi a karo na biyu saida ta kusan katsewa ya ɗaga, a lokacin fitowar sa kenan daga wanka yaga wayarsa na ta haske alamar shiga da fitar kira, dauka yayi tare da picking call ɗin yasa a handsfree sannan ya matsa gaban mirror ya ɗaura wayar. "Ya Niniyous ɗi na ta tashi?"........ Ya faɗa yana goge gashin kansa da ƙaramin farin towel ɗin dake rataye a wuyansa. "Amour kana ina?"........... Ta tambaya in a serious tone. Tsayawa yayi da abinda yake saboda yanayin yadda yaji Muryar ta, sa hannu yayi ya ɗauki wayar da faɗin, "Meke faruwa?"........ Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce, "Da matsala Amour, Dad yace wai ya warware baikon mu sannan ya bada ni ga ɗan abokin sa wai Farshad". A maimakon ta ji alamun damuwa a tattare dashi kamar yadda ita take ciki tunda wanna abun ya faru, sai taji saɓanin hakan dariya taji ya kwashe da ita, dariya yake cike da jan hankali wanda in kana sauraron sa baza ka so ya daina ba, haka in kana gabansa ne baza ka gaji da kallon sa ba, saboda yadda dariyar ta masa kyau da kuma salon da yake yin ta. Shiru tayi tana sauraron sa har ya tsagaita sannan ya ce, "To yanzu miye abun tashin hankali Ninie, ke fa Matsala ta dake kina da saurin rikicewa abu kaɗan ke firgita ki, ina kika taɓa ganin an warware baiko haka, in kin manta in tuna Miki harta sadakin ki fa na bayar kawai fatiha ce ba'a shafa ba, sannan daga sama ace Miki an warware baiko kuma ki tashi hankalin ki". " Ka fahimceni Amour kar ka dauki abun nan wasa, whl su mumu sun watsar da duk wannan"...........ajje wayar yayi yana daukan Gris dior body creme ya ce, "Ki kwantar min da hankalin nan naki Niniyous, zanyi wani Abu a Kai Karki damu kinji "...........Shuru tayi dan hankalin ta ya rabu ne gida biyu kuma. "Baki yarda dani bane tawan?"......... Ya faɗa cikin wata irin murya me saukar da kasala. "I tr..ust you "............Ta amsa tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya. "Sai da dai kikayi kuka ko? To na dai na cewa karkiyi kuka duk lokacin ma da kikaji kina sha'awar yin sa ki kirani nazo da bucket na tari kayana". "Dama ai Baka damu ba, tunda abar tsokana nake zama a wurin a a maimakon ka lallashe ni".........dariya ya kyalkyale da ita kafin ya ce, "Kina da katoton aiki a gabanki kuwa, ni dake wa zai lallashi wani?". Murmushi kawai tayi da faɗin, "ALLAH ya yafe ma amour".........." Ameen tare da Niniyous". Haka suka cigaba da hira yana shiryawa har ya gama sannan suka sallama ya dauki abubuwan da zai buqata ya fita . Dinning ya fara zuwa yayi breakfast sannan ya wuce sama, a falon farko ya same su ita da Adla, ƙarasawa yayi ciki ya zauna tare da gaishe da Anah , shi kuma Adla ta gaishe shi. Amsawa yayi tare faɗin, " ke yau baza ki makaranta bane?"..........."bani da lectures yau yaya"........ Jinjina kansa yayi sannan ya ce, "Anah ni zan fita, dama nace barin hawo naga ko kin fito". "To yanzu da sassafen nan ina zaka Babban mutum"....... ɗan shafa fuskar sa yayi kana ya ce, " Anah na riga na saba da fitar, in na zauna gidan takura zanyi, amma ba nisa zanyi ba". "Ba wai bana son ka fita bane, hankalina ne baya kwanciya in Ka fita har sai naga ka dawo". "Karki damu Anah zan biya na ɗauki su Aram ai, ba abinda zai faru in sha ALLAH". "Shikenan amma ka kula da kanka, ALLAH kuma ya kare min kai ya maka Albarka ya kuma baka Sa'a"..........."Anah Ni fa ?"....... Adla ta faɗa tana bata fuska. Miqewa yayi tare da dungure mata kai, "Uwar gasa, Anah ni na wuce".......Ya faɗa yana daukan hanyar barin falon. "To ALLAH ya dawo da kai lpy "........ Anah ta sake faɗa. Saida ya biya ya duba Dada sannan ya fita in da ya tarar da kamal yana jiransa. "Ina kwana boss"......... "Ka tashi lpy?". Ya tambaya yana shiga motar da kamal ɗin ya bude masa. "Alhamdulillah". Kamal ya amsa yana rufe masa ƙofar sannan ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar yaja suka fice. Gidan sa suka nufa, suna shiga su Aram suka zagaye motar tasa fitowa yayi yana amsa gaisuwar kowanne su sannan ya wuce ciki ɗaya daga cikin su ne yabi bayan sa sai da suka shiga falon can ciki sannan ya tsaya ba tare daya juyo ba ya ce, "Philip da wani abu ne?". Da sauri Philip da dama jira yake a bashi umarnin magana ya ce, "Yes boss, wata gagarumar nasara ce domin mun samu request daga SHADOW yana so mu masa aiki ne, duk wasu sauran details na tura ma "..........Amjad da tun lokacin da aka ambaci SHADOW ya juyo cikin wani irin slow move, murmushi yayi yana tafa hannu kana ya ce, " Weldon Weldon Philip, lalle wannan ɗin nasara ce a gare mu, yanzu zan duba komai, kaje zan neme ka in na gama"..........."Okay Boss". Philip ya faɗa yana dan rusunawa alamar girmamawa sannan ya juya ya fita. Ɗakin ya wuce gaban wani ƙayataccen curtain da ya ƙarasa dakin kyau ya tsaya, zaro wayarsa yayi tare da yin wani danne danne sannan ya ɗago ya yaye curtain ɗin, wata computer ce ta fara magana a jikin bangon ga wata danger dake kawowa da ɗaukewa, hannunsa ya ɗaura akan danger take computerta gabaɗaya ta kawo wata greenlight tare da shatin yatsun hannunsa saida ta gama scanning din tafin hannun nasa da fingers print sannan wata kofar sirri ta buɗe ta jikin bangon, wani madaidaicin ɗaki ne ya bayyana baza ka taba cewa rana bace dan dim light ne kawai a ciki, yana shiga kofar ta rufe kamar ba a tsaga ƙofa a wurin ba, gaban wani tsararren table ya nufa da kafa yaja kujerar ya zauna, tare da danna wani abu a wayarsa wuta ya kawo a socket socket ɗin, wayan ya sake latsawa take Ac ɗin dake ɗakin suka Kunnu su ma, wayar system ɗin dake kan table ɗin ya jona jikin socket, still hankalinsa akan wayarsa har system ɗin ya gama budewa sannan ya ɗaura wayar gefen system ɗin a kan table, ya gyara zama tare da maida hankalin sa akai gabaɗaya ya fara wani aiki, sai da ya ɗau good two hours sannan ya kashe komai ya tashi yana miqe hannuwansa da suka tara jini. Wayarsa ya ɗauka ya kashe AC da wutar ɗakin sannan ya buɗe ƙofar ya fita. Gaban gadonsa ya nufa yana zuwa ya faɗa akan gadon tare da janyo pillow ya ɗaura kansa akai ya lumshe idanunsa amma ba bacci yake ba saboda ƙafarsa da yake dan jujjuyawa kaɗan kaɗan, ya ɗau tsawon lokaci a hakan dan har sai da akayi kiran sallar azahar sannan ya tashi yayi sallah. Fitowa yayi ya wuce dinning, ɗinbin mamaki ne ya kamani ganin yadda dinning ɗin ke shaqe da manyan warmers, komai cikin tsari. Plate ya dauka da spoon ya ɗaibi abinda zai iya ci sannan ya tsiyayi juice ya koma ya zauna. Yana kai spoon bakinsa wayar sa ta fara haske ba tare da ya daina cin abincin da yake ba ya yi picking call ɗin daga ɗaya bangaren akace, " Whl kai ba ƙaramin Kwaro bane Amjad, ka iya ƙera mota me tafiya da kanta sannan ka bar mutum da faman wahalar tuqi". Murmushi yayi me sauti sannan ya ce, "To ai shi ne wahalalle shi wanda yake ganin shi ne matuƙin". "Baka da kyau Sam Sam Whl, Mu kan mu tsoro kake bamu"..........lemo ya kurɓa da faɗin, "Habaaa ranka ya dade ai banda ku". "Kai dai a bar zancen, na gama karanta saqon ka har na ma reply amma nace sai na kiraka, dan haka kaga sai anjima mayi magana".......bai ce komai ba har ya kashe wayar. Ajje wayar yayi sannan ya cigaba da cin abincin sa har wani kaɗa ƙafa yake . Yana gamawa ya koma parlour tare da kiran Philip. "Have a seat "......... ya faɗa a lokacin da Philip ya karaso. Zama yayi kamar yadda ya bashi umarni yayin da shi kuma hankalin sa na ga wayar dake hannun sa can kuma ya ce, "Philip who do you think you can take with you to former deputy governor house Alhaji nu'uman?".........Shuru Philip yayi kafin ya ce, " I think Nazbeer". Dan girgiza kansa yayi da faɗin, "No you are not going with Nazbeer I have got something else for him"........."But boss, what's the issue?" Shiru yayi kamar ba zai yi magana ba yana cigaba da latsa wayar sa ya ce, "check your phone, I sent everything to you, Jan kunne ne kawai. Ina da Abubuwa da yawa a gaba na zan shiga ciki, fatan ba wata matsala ?".........."Then Danny will go with me, if that's the case". Dan matsa yatsan hannun sa yayi har sai da yayi ƙara sannan ya ce, "Be careful, Ku San takun ku, karku bani matsala". "Yes boss!" "Alryt you can go".......... Ya faɗa yana kallon wani wuri kamar me tunani, har Philip ya tashi zai fice ya kira shi, "Philip!" "Yes boss"...........Philip ya faɗa yana tsayawa tare da juyowa yana fuskantar sa. " Call Baba Sufi and ask him to call Awaais and the rest. Tell him to tell them dada's seriously sick, he's looking for me but he couldn't reach me, and send doctor kinal. Then make sure you cut our resident's network after they arrive, and take care of the rest of the matters. karka bani matsala ka san dai komai, I've repeated myself"..........Yana gama faɗin haka ya tashi ya wuce ciki. Bashi ya fito ba saida akayi sallar laasar, sanye yake da wani crazy blue jean da ash shirt, kafarsa sanye da sneakers na kamfanin Louis Vuitton, haka fuskarsa ya sanya wani makeken sunshades tare da noes mask sannan ya kawo wata arniyar P cap ya sanya tare da juya gaban ya koma ta bayan . Tafiya yake cikin nutsuwa har ya fito compound ɗin gidan, nan su Aram dake zazzaune suka taso suna masa Barka da fitowa, hannu kawai ya ɗaga musu ya nufi mota, da sauri suka bude masa ƙofar ya shige, kamal ya shiga mazaunin driver. Janye wa sukayi gefe dan sun san tunda bai neme su ba baya buqatar su a fitar tasa. A hankali Kamal yayi reverse tare da juya kan motar ya harba ta kan titi ba tare da yasan in da zasu ba, saida sukaje kan roundabout sannan ya ce , "Airport muka nufa"............"okay boss"......... Kamal ya Amsa. --------------------√ Ba tare da wani tsoro ko fargaba ba a tare da ita ta dumfari majalisar su karafiya inda ta hango su suna ta yan zuqe zuqen su. Tana zuwa ta fisge wiwin dake maqale a gefen kunnen jagwa tana ci da wuta, wurgarwa tayi a kasa tare da tula mata ƙasa da kafa ta mirtsiketa sannan ta ɗago tana huci a fusace ta ce, " Wani ƙaramin tataccen ɗan iska ne a cikin ku ya daki Sahnish?"............ Ta ƙarashe tana wani mutsitsike ido. Kana kallon ta kasan bata san wani abu wai shi tsoro ba. "Hahaha". Suka kwashe da wata irin dariya irin ta basawa kafin ɗaya daga cikin su wanda ke sake naɗa musu rizla ya ce, "Dukkan mu ne amma ni na jagoranci tawagar, ya akwai Magana ne?". "Maganganu ma, ashe ƙaryar iskanci kuke, ina cewa ni kuke bi kuɗi, to ku tare ni mana tunda dani ta haɗoku bada shi ba, meysa zaku sanya shi cikin faɗan da ba nasa ba, to whl zaku san kunyi da yar halak sai na baku mamaki". "Keeee bar nan kafin na Miki ɓalli ɓalli anan wurin billahillazi ".......... Karafiya ya faɗa yana miqewa riqe da wuqa a hannun sa sai langi yake shi kaɗai kamar igiyar shanya. "In naki fa ko zaka matsar Dani ne".........Ta faɗa tana juya masa manyan idanuwan nan nata masu rikitarwa. Yunkorowa yayi da faɗin, "kwarankwatsa zan bazar dake a wurin nan in bi ta Kan ruwan cikin ki in wuce". Gyara tsayuwa tayi da faɗin, " In Ka fasa Ka raina iyayen da suka haifeka banza wawa ragowar hayaki, kuma na rantse sai kunsan dani kuke wasan, kun sanni sarai ai kunsan hali na"......... Wata zaftareriyar wuqa jagwa ya ɗauko a can gefen su tare da sara ta akan ƙasa ya ce, "ware!".......... girgiza kanta tayi da faɗin, "ALLAH ya ragewa Aya zaqin ta ba'a shirye na fito ba, amma da kai kaii dai whl baka isa ɗaga min wuqa ba, amma ku jira juyowa ta"..........Ta ƙarashe tana nuna su da yatsa sannan ta juya ta bar wurin . "Yihuuu wa yace damu bamu ba muma muce dashi bashi ba, har akwai mai ɗaga mana yatsa a garin nan bamu gille hannun ba gabaɗaya"..........Ya ƙarashe cike da kuri. Ɗaya abokin nasu ne ya taso shi ma kamar zai kifa ya dafa kirjin jagwa ɗin da faɗin, "kwanta kwanta naman kaji, a huce haka"......... ƙoƙarin wucewa ya fara yana faɗin, "ka barni in je in qaddamar Mata zandam, mu da mukeyin gaba da gaba da maza a dawa ma bare wannan ƙaramar kwaron". "Huce haka, barta zamuyi maganin ta kai kasan ko yanzu mun zabure ta, dan ba ƙaramar illa mukayiwa wancan yaron ba, dan haka rabu da ita in kere na yawo zabo na yawo........" Ya ƙarashe yana jan fito. Ƙwafa jagwa kana ya ce, "Amma ba dan ka hanani binta ba ko, da sai an kasa gane kamannin ta"......... Ya ƙarashe yana komawa gefen karafiya ya zauna tare da zarar kara ɗaya ya bata wuta. Hushaima kuwa daga wurin su karafiya ba gida ta koma ba wani wuri ta nufa, sai da tayi tafiya ta tsawon minti talatin da kafarta dukda uban ranar da akeyi amma sam bataji Saboda murɗaddiyar zuciya irinta ta. Tana zuwa ta faɗa wani uncompleted building kamar wadda aka jefo, mamaki ne ya kume ni ganin wasu irin riƙaƙƙun yan daba na gaske masu ji da tashen tsageranci da tashanci, tana zuwa ta wuce ta tsakiyar su ta ɗale kan wani bulo ta zauna tana goge gumin fuskarta da bakin gyalenta. Sai da ta ɗau tsawon minti goma a ciki sannan ta fito ta wuce gida. Tana shiga Sahnish dake kwance yana dakon jiranta, ya fara kokarin miqewa, da sauri ta ƙarasa ta taimaka masa ya zauna, cikin damuwa da kuma takaici ta ce, " Tashi Ka daure muje asibiti ". Wani yawu me zafi ya haɗiye saboda ciwon da maqogoron sa ke masa kafin ya ce, "Baza muje asibiti ba chemist ma yayi". "Sahnish raunin dake jikin Ka yafi ƙarfin chemist, Ka daure Ka tashi mu tafi kaji".........ta sake faɗa tana kallon sa cike da tausayawa. "Asibiti yanzu in munje ma zaman jiran layi zamuyi, zaifi kyautuwa muje chemist ɗin dai ". "Kai daina min musu Sahnish muna Ƙara ɓata lokaci ne ni inada abunyi, Ka tashi muje mu dawo kuma ai ba asibitin gomnati zamuje ba". Waro idanunsa yayi kana ya buɗe baki zaiyi magana ta ce, "kar fa ka ƙara ce min komai, a tafashe nake bana so na sauke haushi na a kanka".........Bai sake yunqurin cewa komai ba ya fara ƙoƙarin miqewa ta taimaka masa ya miqe, a haka suka fito, a soron ƙofar gidan ta barshi taje ta ɗauko abun hawa, sannan suka taimaka masa ita da me tuk tuk ɗin ya shiga suka tafi. Kamar yadda ta fada private hospital suka nufa, da taimakon me tuk tuk suka shigar dashi ciki sannan ta sallameshi ya tafi, file taje ta Buɗe masa sannan aka musu iso zuwa ɗakin likitan, bayan ya duba shi ya rubuta masa magunguna da allurar tetanus, sannan akayi dressing raunikan, aka ɗaura kashin hannun nasa da ya goce. Kallon ta likitan yayi bayan an gama ya ce, "Hatsari ya samu ne ?". "Yan iskan unguwa ne kawai"........Ta bashi amsa dukkan hankalin ta na Kan duk wani motsi na Sahnish ɗin. "Ashsha haka suke whl duk sunbi sun addabi mutane, ka yi magana su bi dare su datsaka kamar rake, ALLAH dai ya kare gaba. Amma saisa ake so mutum ya guji abinda zai haɗashi dasu dan in suka bugun nan cinnaku ne basu san na gida ba, kallo wannan laifi yake zama a wurin su. "An gama ne Dr zamu iya tafiya?"........Ta tambaya dan yanda takeji zuciyarta na Ƙara hauhawa a duk kallon da zatayiwa Sahnish ɗin, shi kansa Dr ɗin maganganunsa ƙara ɓata mata rai suke, kamar ta rufe shi da duka. "Eh zaku iya tafiya, Amma zaki dinga kawo Shi ana dressing raunikan, ga wanna in kin fita pharmacy saiki biya kuɗin ki karbi magungunan". Karɓar takardar tayi sannan ta ƙarasa ta taimaka masa ya tashi suka fito. A reception ta zaunar dashi sannan ta wuce pharmacy tayi payment, ta fita ta Nemo tuk tuk ta dawo ta taimaka masa suka fita, tsayawa sukayi suka dauki Shazeen daga makaranta sannan suka wuce gida gabaɗaya. Ko da suka isa gida ɗaki ta kaishi ya kwanta domin ya samu yayi bacci ya huta. Kitchen ta shiga ta ƙarasa abincin data fara kafin shigowar Sahnish sannan ta zubawa Shazeen ta gyara gidan, dan ita ko yunwar ma bataji abinda ya dame ta ma ya ishe ta, ga yan kuɗaɗen da suka rage musu ba yawa, ga kuma jinyar Sahnish, aikin data samu kuma ba wai daga zuwa za'a fara biyanta ba dole sai tayi aiki zuwa ƙarshen wata. Wunin ranar sukuku tayi Shi har dare saida Sahnish ya tashi ne ma ta ga jikin nasa sannan ta samu ta sawa cikin ta wani abu shi ma dan Sahnish ɗin ya dame ta ne. Yana zaune shi da shazeen a ɗakin sa Hushaima ta shigo, wuri ta nema ta zauna tare da faɗin , "Shazeen zo ki cikemin takardar nan".........Ta ƙarashe tana miqa mata Form ɗin data taho dashi tare da pen. "Takardar miye wannan ɗin ?".......... Sahnish ya tambaya yana binta da kallo. "Form ne na aikin da na samu a wani wurin saloon starlight beauty co., To da sukace gobe ma nazo na fara amma kuma tunda naga baka da lpy zan bari ka ɗan ji sauqi tukunna ". Cikin farin ciki ya ce, "Kai alhamdulillah ALLAH abun godia. Kina ji baza ki fasa zuwa gobe ba, kije aikin ki dan bana so azo a samu matsala daga farawa kuma suzo su canza shawara. Kinsan a yanzu aikin yana da matukar muhimmanci a yanayin da muke ciki". Bata bashi amsa ba har sai da ta gama faɗawa Shazeen abubuwan da zata cike dasu sannan ta ce, "to wai taya ma zan tafi na Barka kai kaɗai a gida alhalin baka jin daɗi. Zan je ɗai na kai musu Form ɗin sai na faɗa musu uzuri na yaso ko jibi in jikin naka ya sake yin kwari sai na fara zuwa". "Wai jikina yayi kwari sai kace wani jariri, dan ALLAH ki bar wanna zancen kawai da safe ki shirya ki tafi". "ALLAH ya kai mu, Shazeen miqo min ledar magungunan sa da pure water can na bashi mu tashi muje mu kwanta dare yayi kema Karki kasa tashi makaranta ".........tashi Shazeen tayi ta ɗauko ruwan da magungunan ta bata. Sai da Hushaima ta tabbatar ya sha magungunan sa sannan suka masa saida safe suka fita. Washe gari da sassafe ta tashi kamar yadda ta saba ta gama duk abinda zatayi ta shirya Shazeen, suka yi kalaci a tare sannan suka fita gabaɗayansu suka kullo gidan. Sai da suka fara sauke Shazeen a makaranta sannan suka wuce asibiti aka masa dressing ciwukan, bayan sun fito Sahnish ya ce, "Mu biya a saukeki sai a wuce dani gida"........."Ah ah muje dai naga ka shiga gidan sai ni a juyo dani". "Ke fa kullum kike maidani kamar wani Yaro, sannan kuma kizo kina faɗan cewa in zama jajirtacce"..........."To ai baka nunamin kai ɗin jajirtaccen bane ballantana na sake ma ragamar komai". "To ai ke kika hanani zama jajirtaccen"........ Shiru ta masa shi kuma ya cewa mai tuk tuk ɗin ya kaisu starlight beauty co. Basu ƙara magana ba har mai tuktuk ya faka ƙofar wurin Sahnish ya ce, "To sauka kije ALLAH ya bada Sa'a, amma tsaya wa zai ɗauko Shazeen a makaranta"........ Dan jim tayi kafin ta ce, "zan cigaba da daukota zuwa lokacin da zakaji sauki sai Ka karba". "To islamiyyar fa?"............"Eh to wannan dai gsky saidai ka kira malamin nasu ka sanar masa uzurinka saboda kaga bazai yiwu na bar wurin aikin har so biyu ba". "Shikenan to ba damuwa zan kirashi. Sai kin dawo"........ɗaga masa hannu tayi tana faɗin, "ka kula da kanka ". Sannan ta juya ta shige, shi kuma ya bawa mai tuktuk ɗin umarnin tafiya. Yau ma Jumayma ta tarar sai cleaners dake ta aikin tsaftace wurin, "barkan ki"........Hushaima ta faɗa tana zaro Form ɗin a jaka ta tura mata gabanta. Kallon tara saura kwata jumayma tai Mata sannan ta ɗauke Kai, taɓe baki Hushaima tayi sannan ta wuce ta nemi wuri ta zauna. Shuru shuru har 10 sai sauran ma'aikatan dake ta shigowa, tashi tayi ta koma wurinta tare da faɗin, "sannu"........."Yauwa"........ ta amsa tana yatsina kamar taga kashi. "Hajiya fa?"........."Bata zo ba"..........."Jiya bata Miki bayani bane ".........."Wani irin bayani?" ........."Na ɓangaren da zan dinga aikin mana". Sake ƙyabe fuska tayi sannan ta ce, " ki koma ki zauna sai ta shigo".........Bata sake cewa komai ba dan bata so a ja zancen da zai Kai matsayin da matar nan zata Kai ta bango dan tsab zata iya kwaɓe musu tun ba'a yi nisa ba. Kusan minti talatin ta ƙara sannan ta kirata. Kamar baza taje ba saboda a wulaƙance tayi kiran amma ta taushi zuciyarta ta tashi ta ƙarasa wurin nata. "Muje a nuna Miki aikin da zaki dingayi"..........Binta tayi a baya suka shige ciki, suna shiga ta ce, "Bunayna ga sabuwar ma'aikaciya nan ku nuna mata yadda aikin yake".........Da " to". Bunayna ta amsa sannan Jumayma ta juya ta fita. "Bismillah ƙaraso".......Bunaynan ta faɗa tana Murmushi, dan ita sam bata da matsala haka ma sauran abokan aikin nata, hakan yasa Hushaima bata samu wata matsala ba wurin koyon abubuwan da suke nuna mata. Zuwa rana suka fara attending customers, sosai wurin ke cika da manyan hajiyoyi da ya'yansu, hakan yasa ta zage suke ta jibgar aiki kamar jakai, har zuwa lokacin da hajiya ta iso nan tasa aka kirata bayan sun gaisa ta ce, "Ina fatan dai ka gane komai ai?"........" Eh hajiya ai ba wahala ma aikin". "To yayi kyau , akwai kayan aiki in ka tashi yau zasu baka, shi Ake sawa, sannan albashin ka dubu Arba'in monthly, cox ni kaga ma bani da buqatar Ƙarin maaikata kawai dai dan na tausaya Maka ne". "Ba damuwa hajiya a hakan ma nagode, saidai ina da ɗan uzuri anjima zanje ɗauko yarinya a makaranta, dama qanina ne zai dinga ɗauko ta to kuma baijin dadi yanzun"........."Ba damuwa, amma Karta shiga lokacin aiki da yawa". "In sha allah ".......... Ta faɗa tana tashi ta koma wurin aikin su, wurin jakarta ta nufa ta sanya wayar ta a ciki sannan ta koma ta cigaba da aikin da takeyi kafin hajiya ta kirata ta bari ta fita. "Kam burauban can, Ni za'a yashe, to whl ko sama da ƙasa zata haɗu bazan yadda ba sai an fito min da dukiya ta". Da mamaki duk ma'aikatan dake wurin suka kalli juna da faɗin , " Ai kuwa hajiya wurin nan wani abu bai taɓa ɓata ba bare kuma sata ki dai duba ko kin barshi a mota, amma tabbas ba wanda zai dauka Miki wani abu a nan". Wata budurwa ce ta ce," To wai me aka sace Mata ne ma?" "Kudaɗe na gabaɗaya babu sannan akwai zobe da bangles ɗina na gold da na cire nasa a jaka yanzu saboda zaa yanke min farce, amma yanzu na duba babu su ba alamar su, ƙafa ne dasu da zasu fita da kansu in ba ɗauka akayi ba". ɗaya daga cikin ma'aikatan ce taje ta sanar da hajiya abinda ke faruwa tana zuwa matar ta ce, " Gwara da ALLAH ya kawoki, sata suka min kuma whl tun muna shaida juna kisa yaranki su fitomin da abubuwana". "Ya hakuri Hajiya mu bi a sannu, kaya basa ɓata anan wurin amma bincike bai bar komai ba"....... Ta ƙarashe tana kallon su tare da tambayar, "iya Ku kenan ko akwai Wadda ta fita kafin nazo?". "Iya mu kenan sai wanna yarinyar data fita ta dawo, sai kuma ma'aikaciyar dataje ta sanar Miki yanzu"......... Ta karashe tana nuna Hushaima da kuma Elijah . "Ita wannan ba wani wuri taje ba sabuwar ma'aikaciya ce ma ni nasa aka kirata Amma tunda abun yazo da haka bari ayi caje kawai, barin kira Jumayma "......... Ta faɗa tana dialing contact din Jumayma, sunkuyar da Kai Hushaima tayi tana cigaba da abinda take. Jumayma ce tazo ta caje kowa, saida ta gama ta ce............... 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______9 & 10 Jumayma ce tazo ta caje kowa, saida ta gama ta ce, "Hajiya baa samu komai a jikin su ba". "Kowa ya miqo jakunkunan su ki zazzage anan"......... Hajiya ta sake faɗa. Ba musu kowa ya jeho jakar sa aka fara zazzagewa ana zuwa kan jakar wannan budurwa data tambayi me aka sata sai ga bangles da zobe sun faɗo, salati duk ma'aikatan suka sa banda Jumayma data so a jakar Hushaima aka samu. Karɓa matar tayi sannan ta ce, "Akwai kuɗaɗen Ku sake dubawa ".........sake zazzagewa akayi Amma ba'a samu komai ba. "Billahillazi tunda aka samu wa annan a jakar ta, to kuɗin nan yana wurin ta dan wuri ɗaya na sa su". Rantsuwa ta fara ita bata san ya akayi wa'annan kayan suka shiga jakarta ba Amma ba wanda ya saurareta sai hajiya data tambayi matar, "kuɗin naki har nawa ne?". "Zasu Kai dubu ɗari da saba'in, kuma whl naira ta baza tayi ciwon Kai ba dan ni da Ka min sata gwara Ka tambayeni na baka, dan haka ta fito min da kuɗi na ko na haɗata da Wanda zasu karɓar min"......... Ta karashe cikin daga murya . Hushaima na gama aikin tsifar da takeyiwa wata mata ta ƙarasa ta dauki jakarta tare da gyalen ta sannan ta ce , " Hajiya zanje na dawo". "To adawo lpy, Amma karki Daɗe fa na faɗa miki". "Toh"........ Tace, tana ɗagowa idanunta ya shige cikin na wanna budurwar, kallon Kar ta san Kar sukawa juna kafin Hushaima ta juya ta fice. Abinda ya faru kuwa shine a lokacin da Hushaima ta dawo daga kiran Hajiya idonta ya sauka kan budurwar nan dake zura mata wani abu a jaka ba tare da kowa ya lura ba, tsayawa tayi saida ta jira ta gama sakawa sannan ta shigo ɗauke Kai tayi kamar bata gani ba ta dauki jakar ta zura wayarta sannan ta koma bakin aikinta, saida ta fuskanci hankali baya kanta sannan ta ɗauki jakar ta buɗe kamar zata ɗauki wani abu, kuɗade ta gani tare da bangles da zobe tsananin mamaki ne ya kamata, bata tsaya dogon tunani ba kawai ta ɗebe kuɗaɗen ta ɗaga pillow kujerar da suke ajje kayayyakin su ta saka, sannan ta ɗauke bangles ɗin da zoben ta wuce kamar zata jefa abu a dustbin ta zura su jakar wanna budurwar, ta wuce ta koma kan aikinta da mamakin wannan budurwa na meysa tayi sata? Dan tana da tabbacin ba rashin kuɗi bane saboda tasan kafin ta shigo ma maybe saida ta biya kusan kuɗin data sata din. Kuma meysa bata zaɓi jakar kowa ba sai ta ta? WANNAN KENAN. Tuk tuk ta tsare ta hau lokacin data fita titi, ta faɗa masa inda zai kaita, kuɗaɗen ta ɗauko ta haɗa su wuri guda ta sa a jaka dan da a aljihunta ta zuba su, " tsuntsu daga Sama gashashe"....... Ta faɗa tana murmshi tare da ɗage kafaɗunta sama alamar i don't care. Ko da ta ɗauko Shazeen tsayawa sukayi a hanya ta musu takeaway ita da Sahnish sannan ta bata ta shigar musu da shi gidan, Dan ita daga tuk tuk ɗin ta juya bata tsaya ko ina ba sai police station....... TO JAMAA ME HUSHAIMA TAJE YI POLICE STATION KUMA? -------------------√ "Hello julaybin"........"Awais kana ina?". "Yanzu na ke shiga family house, ina ta neman wayarka ana ce min line busy, ance jikin dada ne ba daɗi, shi kuma wannan Baba Sufi ɗin yanata neman wancan matsiyacin yaron, kasan abinda ake ciki, in ya same Shi a waya har ya rigamu zuwa za'a iya samun matsala, saisa ma na hanzarta isowa". "Nima gani daf da gidan, ALLAH yasa ina kusa da gidan, Ka kirawo nuhail kuwa?". "Yes inajin ma yana ciki, dan tun dazu yace min ya shigo shi ma". "Shikenan kaje Ku tsaya kan komai kafin na iso, kasan shi Nuhail ya fiya sanyi sai a gama damu bai sani ba". "Baka da damuwa Julaybin"........ Da haka sukayi sallama sannan suka tsinke Kiran daidai lokacin da drivern Awais din yayi parking ƙofar shiga part ɗin dada, Buɗe masa akayi ya fito da sauri ya wuce ciki sai faman baza babbar riga yake, a falon cikin ya tarar da Nuhail tsaye shi da Hajiya zunaira mahaifiyarsu. " Hajiya ya na ganku anan kuma? Kai Nuhail ba cewa nayi komai za'ayi karka bar wurin ba, ya zaka dawo Waje ka tsaya". "Cewa tayi a bata wuri tayi aikin ta fa, to ya kake so nayi da ita".........Tsaki Yaja zai wuce ciki Dr kinal ta fito, Nuhail ne ya nufo ta yana tambayar, "Ya jikin nasa Dr?". Tana ƙoƙarin basu amsa Julaybin ya shigo shi ma sai hayya hayya babbar rigarsa takeyi. "ya na ganku a tsaitsaye meke faruwa"........ Ya faɗa yana binsu da kallo. "Amm Ku kwantar da hankalin Ku, muna Kan aiki ne, yanzu nayi wa abokin aiki na Dr Hazeem waya zai kawo min wasu kayan aiki, Amma muna san Ku kasance a kusa gsky incase ko zaa buqace Ku". "To Dr ko za'a biku dashi hospital ɗin kawai in a gidan abun zai bada wahala"........ faɗin Awais. "Nop a gidan sai anfi gajarta masa wahala gsky, in sha ALLAH zamu shawo Kan matsalar yanzun ma saboda akwai allurar da ya kamata nai masa to ban taho da ita bane". "To ba damuwa kuyi aikin naku"....... Nuhail ya faɗa yana cire hular kansa. __________A guje ta faɗa falon kamar an jeho ta tana faman kiran Anah, "Anah! Anah! ". "Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun, haba Adla irin wanna Kiran har kinsa gabana ya fadi whl, meke faruwa?". "Anah jikin Dada ne ba daɗi, wai ana ta neman ya Amjad kuma ba'a samun sa, yanzun naga duk su ya julaybin sun iso". "Subahanallahi tun yaushe?"...... Anah ta tambaya tana tashi daga kishingiɗen da take. "Yanzun nan! An kira likitoci ma suna kansa har yanzu, kuma su hajiya ma duk suna can bangare". "Shi ne mu kuma sai yanzu muke ji? Ni dazu ai lafiya na barshi, wuce muje"........ Ta faɗa cikin tashin hankali tana tashi ta wuce gaba. Ta hanyar da zata sadata da bangaren ba tare da sun bi ta compound ɗin ba. A zaune suka samu hajiya zunaira yayin da su Julaybin ke tsaye suna ta Kai kawo kamar gaske, shigowar su Anah yasa su ɗagowa su duka, Awais ne ya dakatar da Adla dake ƙoƙarin shiga ɗakin, " ke da ALLAH dakata nan, ko duk Baki gan mu tsaye bane, Doctors ne a ciki suke aikin su, kika taho kina neman kutsa kai". A ɗarare ta ce, "Ya Awais please inaso na shiga naga jikin dada ne dan ALLAH". "To uwar kinibibi ke kaɗai ya haifa ne, baga Mirrah can ba a bangaren hajiya, ai ko daga can kika zauna kika masa addu'a ta wadatar ba sai kun zo Kuna ƙara tayarwa da mutane hankali ba. koma can ki zauna"........ Julaybin ya faɗa. Anah ce ta ce, "Hajiya zunaira saboda ALLAH muna gida daya jikin Alhaji ba daɗi a kasa sanar mana". Wayar da Hajiya zunaira ke latsawa hankali kwance kamar ba abinda ke faruwa ta ajje da faɗin, "Ha'a yau naga ikon ALLAH, ƴaƴana suka kirani suka sanar min ke ina naki ɗan? ina cewa shi aka fara nema ba'a samu ba, saisa dadin Ka haifa da yawa kenan saboda baka san waye me jin ƙanƙa a cikin su ba, kuma in ɗaya bai tsaya ma ba saura zasu tsaya ma, yanzu ba ga sauran ƴaƴan nasa zagaye dashi ba, shi kuma Wanda ya fifita ɗin ya zubar dashi kamar baisan darajar sa ba"....... Jin martanin da Hajiya zunaira ta mayar yasa Anah jan bakinta tayi shuru, ba wai dan bataji zafin maganar ba, sai dan ta san in ta tanka mata hakan zai iya haifar da mummunar bacin rai a tsakanin su bayan kuma a yanzu ba hakan bane yafi cancanta dasu. Gwada layin Amjad ta cigaba da yi amma baya shiga bama network gabaɗaya a Kan wayarta ta. "Wai Awais ya akayi ba network ne a part ɗin nan tun dazu nake gwada Kiran wanan Dr ɗin har yanzu bai ƙaraso ba".........Julaybin ya faɗa yana ɗan jijjiga wayar sa. "Whl ni ma na gwada baya tafiya inajin daga MTN din ne"....... Awais ɗin ya bashi amsa shi ma yana faman hawa da sauƙan jirgi (wato flightmode) Sun daɗe tsaye kafin Dr Hazeem ya iso, Haƙuri ya basu tare da shigewa ciki da sauri, kusan mintuna bakwai suka fito tare shi da Dr kinal ɗin, tashi Anah tayi ta nufe su dan jin yadda Ake ciki. " Ku kwantar da hankalin Ku, jikin da sauƙi dan har ya samu bacci ma, ba kuma wata matsala, kuna iya ma zuwa Ku ganshi"........ Ta faɗa tana nuna musu Hanyar ɗakin da hannu. Ajiyar zuciya Anah ta sauke yayin da Awais ya bi bayan Dr kinal da Dr Hazeem zuwa waje shi kuma Julaybin ya wuce gaban hajiyar su, yayin da Nuhail, Anah da Adla suka shige ɗakin Dada. Bayan su Dr kinal sun tafi Awais na ƙoƙarin juyawa ciki, Kira ya shigo masa, ɗagawa yayi Yana faɗin, "Badar ya Ake ciki ne?". "Ranka ya daɗe Amjad ya tashi zuwa Belgium yanzu". "Whatttt?"........ Ya faɗa cikin karaji da tashin hankali, "How taya?". ___________Dukan hannun kujerar da yake kai yayi da faɗin, "Taya zaku bar hakan ta faru, kun kuwa San me hakan ke nufi, in har kun tabbatar da tashi Amjad Hashim Darwin to tabbas plan ɗin mu na daf da rushewa, abinda muke gudu yana shirin faruwa, abinda muka binne yana shirin bayyana". " Shakka babu maganar Ka abun dubawa ce Alhaji Abid".......... Ɗaya daga cikin mutanan dake zaune a ɗakin ya faɗa sannan ya ɗaura da. "Dan kamar mun yiwa Kura sarƙa ne ta warware, kasan kuwa Kan mu zata nufo". "To ai abinda ya ban mamaki Alhaji hammoud shi ne, taya duk idon da muka baza a garin nan ace har yaron nan ya shirya tafiya bamu samu labari ba saida ya tashi anya kuwa, anya kaiiiiiiiiii da sake, abun nan da mutukar ɗaure kai yake gsky". ------------------------√ Bata jima a cikin police station ɗin ba ta fito ta shiga tuk tuk ɗin data ajje yana jiranta, suka wuce ya maidata wurin aikin nasu, bata samu kowa ba sai su Elijah. Bunayna ce ta ce, "Hushaima kinyi missing bayan tafiyar ki ba ƙaramin rikici aka sha ba"........ Elijah ta ce, "ai tana nan aka fara". "Amma bata nan ai lokacin da matar tace zata kira police in bata biyata ba daƙyar Hajiya ta bata haƙuri, amma yarinyar nan tayi mirsisi tace bata ɗauka ba wala ALLAH kuma kunyar fito dashi tayi, daƙyar dai nake gaya Miki aka samu tayi wa matar nan transfer ɗin kuɗin sannan aka rabu lpy". Hushaima ta ce, "Ta dai biya ɗin kenan?". Wata abokiyar aikin su itama me suna irepa ta ce, "To abun mamaki har tana kuɗin me zaisa tayi sata tunda gashi har tana da kuɗin da ta iya biyanta a Acc ɗin ta". "Nima dai abun ya ɗaure min kai gsky"....... Bunayna ta faɗa. Itadai Hushaima bata ƙara cewa komai ba ta nemi wuri ta zauna tare da faɗin, "ALLAH ya kyauta"........Haka suka cigaba da attending customers har zuwa lokacin tashin su wato karfe Shida. Tare suka fito dasu Bunayna, sallama suka yiwa Jumayma a lokacin da suka ƙaraso reception ɗin, ita kuwa ko kallon ɓangaren da take ma take batayi ba dan kwata kwata jinin su bai haɗu ba. saida suka fito titi sannan suka rabu kowacce ta tsari abun hawa ta wuce gida. Ko da Hushaima ta isa gida, a nan tsakar gidan ta same su, Sahnish na kwance akan tabarmar da suka shimfiɗa ya tada kansa da pillow da ya ɗauko daga ɗaki hannunsa marar ciwo riqe da wayarsa yana scrolling, Shazeen kuma na gefensa tana zane zane jin sallamar ta yasa ta taso da gudu ta rungume ta tana faɗin oyoyo oyoyo. Riqeta tayi tana ɗan murmushi ta ce, "To ai zaki kada ni kuma, mu zube ƙasa gabaɗaya ".........ta ƙarashe tana riqo hannunta suka ƙarasa wurin Sahnish, zama tayi tana faɗin, "Sahnish ya jikin naka?". "Na ji sauki fa, ya wurin aikin naku ?". "Ahh aiki ba laifi fa, dan daga zuwa saida nayi gamdakatar......" Tsayawa tayi tare da kallon Shazeen sannan ta ce, "Ungo shigar min da gyalen na ciki, ga wayata ma ki haɗa ki kai min ɗakin ki zauna ki jirani yanzu zan shigo kar kuma kimin danne danne a ciki"........ Ta ƙarashe tana miqa mata gyalen da wayar. "To"........ Ta faɗa tana tashi ta tattare takardunta sannan ta karɓi Kayan ta wuce. Tashi zaune Sahnish yayi da faɗin, "Inajin ki wani irin gamdakatar kikayi? Ba dai kinyi sabon kamu ba". Harara ta watsa masa sannan tasa hannu a jakarta ta fito da Kuɗaɗen ta ajje a gabansa tana faɗin, " kalla nan". Ɗauka yayi Ya jujjuyasu sannan ya maida ya ajje yana kallon ta ya ce, "To ina jinki, ya akayi?". Labarin abinda ya faru ta bashi kaf, shiru yayi harta gama sannan ya ce, "Sata fa kenan Hushaima".........."AHH sata!, to ni nayi satar?". "Amma meysa baki maida gabaɗaya ba, kika maida abun hannun kika ɓoye kuɗin". "Dana zama wawuya ma, ni fa taso qalawa Sharrin satar ALLAH ya ceceni, sannan kuma kace na maida duka, wato ta tafi ma a banza kenan. Amma yanzu da nayi hakan ai gashi an sa ta biya a aljihun ta kaga in da daɗi gobe ma ta ƙara. Ni kuma banyi sata ba, satar min akayi aka bani dan haka ni bani da laifi". Buɗe baki yayi zaiyi magana ta ce, "karka ƙara ce min komai. kasha maganin Ka?". " Eh".......Ya faɗa yana komawa ya kwanta ita kuma ta tashi ta shige ɗakin su. Wuraren takwas na dare ta fito tsakar gidan tana sanɗa kamar ɓarauniya ganin Sahnish baya nan yasa ta riqo Shazeen sukayi soro, tsayawa tayi sannan ta dan rage tsawon ta tare da riqo kafadun shazeen ɗin ta ce, "kinaji, idan yaya ya nemeni kice kai na ke ciwo na sha magani na kwanta. yanzu zan dawo ba zan daɗe ba ki kulle ƙofar ki koma ciki wayata tana ɗaki ki ɗauka kiyi game kafin na dawo kinji"........ Ɗaga Mata Kai tayi alamar toh. "Yauwa Shazeezee ta, zan kawo Miki bobo in zan dawo"......... ta faɗa tana buɗe Ƙofar ta fita, sai da ta tabbatar Shazeen ta rufe gidan sannan ta ɗaga wata yar baby Nokia ta Kira wata number bayan an ɗaga ta ce, "Saga kunje ne?". "Yanzu muka fito, kina ganin flashing ɗina to kawai komai ya kammala, mun gama namu". "Nagode saga sai na jika"......... Ta faɗa tana kashe wayar ta fara tafiya har ta fita daga Kan layin abun hawa ta tsara sannan ta faɗa masa in da zai kaita. A ƙofar police station ɗin nan ya ajje ta, sauka tayi ta shige ba jimawa ta fito tare da ƴan sanda mutum uku, ganin ta nufi motar Yan sandan yasa mai tuk tuk sauqowa yana faɗin, "Hajiya ya zaki tafi kuma baki bani kuɗi na ba"........ Kallon Sama da katsa ta masa kafin ta ce, " kamar ya ban baka kuɗin ka ba, salon cutar da Kuka koyo Kenan kuma". "Ahh ke kinga tsaya a ƙofar police station muke whl kika min gargar ina iya shigar da karar ki". "Kar Ka fasa shigarwar Dan ALLAH, ko ina za'aje ina da gaskiya ta tunda ban shiga ciki ba saida na baka kuɗin ka"........ Ɗaya daga cikin police ɗin ne ya ce, "ku tsaya wai meke faruwa?". "Ranka ya daɗe na ɗauko ta na kawo ta nan ne, muna tsayawa ta fice ta shige ciki ba tare data bani kuɗi na ba, na ɗauka jiran ta zanyi saita fito, yanzu kuma ta fito tana neman raina min hankali". "Ƙarya yake ranka ya daɗe sharri kawai yake son yi min saboda yace min sai ɗari biyar nace ban yadda ba ɗari uku zan bayar shi ne yanzu yake son ya juya zancen". "Kai miye shaidarka na cewa bata baka ba?". "Amma dai ranka ya daɗe kasan da ta bani bazan tsaya ba saboda Kan aiki na nake". "To ke miye shaidar kin bashi". "Ni nasan na bashi dari uku ƴan dari dari sabbi, kuma a duba in da suke ajje kuɗi a cikin tuktuk ɗin tasu in karya nayi"......... Ƙwafa me tuktuk ɗin yaja tare da faɗin, "Ni bani da sabbin kuɗi ma a kudaɗe na gabaɗaya amma bari za'a ƙure ƙarya".......... Sargeant ne ya ce, "Muje in gani sai in tabbatar"....... tsayar dasu tayi da faɗin, "harda ni za'aje, dan whl bazan yarda ya qala min sharri a banza ba". " Corpor Hambali Ku shiga mota bari na kashe wanna case ɗin tukunna"........Ya faɗa Yana sasu a gaba zuwa wurin tuk tuk ɗin . "Ni zaki cuta ko to bari a kure ƙaryar me ƙarya, kikayi wasa sai kin shiga cell ba dai taƙamar ki 419 ba". "Ayya in baka iya kama ɓarawo ba shi sai ya kama Ka, Ka sani a cell kace ko? to ni in har ta tabbata sharri kamin sai na sa an rufe Ka, azzalumi kawai". "Kai! Kai! kusan a gaban wa kuke. Bude Ka duba mu gani"......... Buɗewa yayi ya ɗauko kuɗaɗen da yayi ciniki gabaɗaya ranar sai ga sabbin yan ɗari ɗari guda uku da sauri ta ce, "Ka gani ko ranka ya daɗe, bana faɗa ma ba to nima Whl bazan yadda ba ni zai ɓatawa suna ya biyo ni yana min tijara a bainan nasi"........ Shi dai Mai tuk tuk sakin baki yayi kawai Yana kallon ta saboda tsananin mamaki da ya kusa halakashi a tsaye, shi dai yasan bata bashi kuɗi ba, kuma tunda ya dauke ta bai ɗauki kowa ba sannan wannan sabbin kuɗin ba kuɗin kasuwanci bane hasalima a aljihun sa suke ya akayi suka koma cikin abun da suke tara kuɗi a tuk tuk ɗin, tirkashi Anya kuwa mutum na dauko? Yayiwa kansa tambayar da bashi da amsar ta. Waya sargeant yayi saiga wani dan sandan ya fito, "Constable ka shiga dashi ciki a shigar da tuk tuk ɗin tasa ma sai mun dawo tukunna, saboda sauri muke yanzu akwai aikin dake gaban mu". "Ranka ya dade ya za'a min haka kuma ? Ni ne fa me gaskiya"........ Harara ta galla masa sannan ta juya ta wuce zuwa motar yan sandan ta buɗe ta shige, sargeant ya shiga shi ma suka wuce, yayinda aka shige da me tuk tuk da tuk tuk ɗin sa zuwa cikin station ɗin. Sai da suka biya headquarter din Drugs law enforcement agency suka dau jami'an su mutum biyu sannan suka wuce, A hanya taga flashin ɗin saga hakan yasa ta ce, "ranka ya daɗe mu ɗan ƙara sauri Kar su bar wurin fa". "Ke dai ba kinyi naki ba, ai shikenan yanzu kuma ki barmu muyi namu aikin. Da ace akwai irin Ku a cikin al'umma da bata gari basuyi yawa ba"........ Jami'in da suka ɗauko ya faɗa. Murmushi tayi kawai bata Ƙara cewa komai ba har suka shiga layin , "Yallabai Ku tsaya na sauka saboda Kar su gane fuskata". Sargeant ne ya ce, "Eh ai dama ba tare zamu ƙarasa ba, amma kinsan akwai case ɗinki da me tuk tuk ɗin can, saidai ki biyomu a motar hayar". " To ranka ya daɗe zan biyo bayan ku in sha ALLAH"........ Daga haka suka sauketa sannan suka wuce majalisar su karafiya daga ɗan nesa suka faka motar sannan jami'an nan biyu suka sauka su sargeant kuma suka tsaya kan hanyar. Suna zaune suna yan bushe bushen su karafiya ya ce, "Jagwa wai ina mutumin naka yayi ne, dan ina ga ni zan nausa nayi yar wawura dan nayi tass ko na cloud babu"........... Zandam ne ya ɓuɗe baki zaiyi magana aka kaiwa kugunsa cafka, "innalillahi wa inna iiii... Ilaih......" Marin da aka wanka masa ya hanashi karasawa, "Zaku wuce mu tafi ko zaku tsaya mana gardama" . "Ahh ranka ya daɗe tsaya kaji, whl tlh ba komai bane yar jigaret ɗin nan ce kawai muke busawa". "Ehn zakuje can ku bada bayani ai". "Qaluuuuuuuuu innalillahi wa inna ilaihir rajuun jagwa hattara, hattara dai"..........Karafiya ya faɗa yana raba ido. "Kuna yunqurin guduwa ina tasar ƙafafunku aiki"........ Jami'in ya faɗa yana fiddo da bindingar dake bayan wandon sa. Haka suka tisa keyar su karafiya zuwa mota, tana tsaye taga wucewar su, tsayawa tayi neman abun hawa, saida tayi mintuna kusan ashirin sannan ta samu mai tuk tuk ɗin da ya ɗauketa ta faɗa masa inda zai Kaita. Ko da ta ƙarasa su Sargeant basu dawo ba da alama suna headquarter ne, haka ta zauna suna ta aikawa junan su da saqon harara itada me tuk tuk , basu jimaba su Sargeant suka shigo, basu umarnin biyoshi office yayi sannan ya shige. Office ɗin nasa suka bishi, wurin zama ya nuna musu baya ya zauna. Nan ya buqaci su sake masa cikakken bayani, amma a maimakon hakan sai suka kacame da cacar baki ganin suna kokarin tara masa mutane a office ya sashi faɗin, "Ku dakata nan ba tasha bane ko gidan karuwai, nan police station ne kuma kuna gaban hukuma ne". "Ranka ya dade sharri fa ya min whl sai ya biyani tara"..........kafin sargeant yace komai me tuk tuk ya ce, " Ai ke dama daga ganin ki kinyi zubin yan damfara". "Ahhhh kwarai ba shakka, to bari kaji nama fasa sai anje kotu, an bi min hakki na". Har wurin 11pm ana rikici tsakanin Hushaima da me tuktuk, a lalle ta tubure sai ta shigar da ƙara kotu, daƙyar dai Sargeant ya tausheta ta karbi ɗan kuɗin da me tuk tuk ya haƙura ya bayar matsayin tarar sannan ya samu ya sullube ya bar station ɗin. Abinda ya faru shi ne lokacin da Hushaima ta ga me tuk tuk ɗin nan wani makaho ya sauke, a gabanta makahon ya zaro dubu ɗaya ya bashi, laluba aljihunsa yayi kafin ya buɗe wurin ajiyar kuɗin su na cikin tuk tuk ɗin ya zaro Naira hamsin ya bashi, karɓa yayi a lokacin tare da cewa yaro ɗari da hamsin ka ɗauka kenan? Ba fa nisa daga inda ka ɗauko ni. Shi kuma yace iya abinda zai iya kenan, in ba nisa ka tako da ƙafarka mana. Makahon bai sake cewa komai ba ya juya yana dogara sandar da faɗin ALLAH ya kyauta. A lokacin ne ita kuma ta isa gaban tuktuk ɗin tare da faɗa masa inda zai Kaita nan yace ya shiga suje. Ya faɗa yana ɗan sunkuyawa duba wani abu a ƙasa a lokacin ne kuma canjin nan na ɗari uku suka zubo daga aljihun sa ba tare da ya lura ba ya fita domin goge glass din tuk tuk ɗin nasa, a lokacin ne ita kuma ta ɗauka ta saka masa a cikin ma'ajiyar kuɗaɗen. To kunji yadda akayi dai, fatan kuma kun fahimci dalilin Hushaima na saka me tuk tuk a tsaka me wuyar nan. WANNAN KENAN. Gyara zama sargeant yayi bayan fitar me tuk tuk sannan ya ce, "Am da farko dai muna ƙara Godia da gudunmawa da kuma haɗin kan da kika bamu, domin yaran nan ba ƙaramin criminals bane saboda an same su da ƙwayoyi masu hatsarin gaske saboda binciken da akayi ya nuna ƙwayoyi ne masu saurin juya ƙwaƙwalwar dan Adam su sashi yayi abinda baiyi niyya ba, kinga kuma ba dan mun kamasu ba yanzu zasu iya cigaba da sayarwa matasa, su kuma suna saya suna sha suna aikata abinda bai dace ba, wanda hakan shi ke ƙara daƙushe mana tunanin matasan mu masu tasowa wanda ya kamata ace yanzu su ne ake damawa dasu a gomnati da sauransu. Mun gode kuma qasa na qara alfahari da samun irin ki". Dan sunkuyar da kanta tayi tana ɗan murmushi kafin ta ce, "bakomai ranka ya dade sai dai......" Jin tayi shiru ya sashi faɗin, "Go ahead faɗi maganar ki ba damuwa". "Ranka ya dade!, Kuna ƙoƙarin kama masu sha da sayarwa amma kuma kun taɓa tunanin a ina suke samu ? Su waye suke basu ? Minene dalilin da yasa ake raba musu irin wa annan ƙwayoyin? Saboda a yadda ka faɗa ɗin kaga kenan ƙwayoyi ne masu tsada ya za'ayi yan jagaliyar unguwa su dinga amfani dasu ".........shiru sargeant yayi kafin ya ce, "Muna iya bakin ƙoƙarin mu Hushaima, abun ne yake nema yafi ƙarfin mu, saboda yawan irin wa'annan case ɗin da ake yawan samu na kama matasa da kayan shaye shaye, da kuma case ɗin dabar nan da yayi yawa ga masu kwacen waya su ma, lamarin ƙasar Nifaz saidai addu'a kawai". Numfashi ta sauke sannan ta dago da faɗin, "ALLAH yayi jagora ranka ya daɗe ni zan wuce"......... miqewa yayi ya ce, "Muje na taka Miki". Tare suka fito har bakin kanta sannan ta musu sallama zata wuce ya tsayar da ita da faɗin, "Anya zaki samu abun hawa yanzu kuwa dare yayi sosai fa". "Ba damuwa ranka ya dade me tuktuk ɗin da nazo dashi ɗazu yana waje ai". "To shikenan, ALLAH ya tsare"........."Ameen". Ta faɗa tana ficewa. A kofar station ɗin ta tarar da ɗayan me tuk tuk ɗin zaune yana gyangyadi yana ganin fitowar ta ya miqe yana faɗin, "Haba hajiya ya zaki zo ki shanyani a waje cikin sauron nan, ni da nasan irin dadewar da zakiyi ai da kin sallameni kawai na wuce". "Kaga muje kawai da ALLAH"......... Shigewa yayi yana mata mita, bata ce dashi komai ba har suka ƙarasa in da zai ajjeta dubu ɗaya da ɗari biyar ta zaro ta bashi, tana ƙoƙarin tafiya ya tsaida ita. "Bangane ba hajiya ya dubu ɗaya da ɗari biyar kuma, ko dan zaman jiran da nayi ai ba kya bani dubu ɗaya ba". "Au da ALLAH fa, yanzu a hakan ban ma adalci ba kenan na baka dubu ɗaya harda wata ɗari biyar sannan kuma ka tsaya kana ce min wai bai ma ba"........ Girgiza kanta tayi da faɗin, "To kawo ɗari biyar ɗin sai na baka dubu ɗaya"........kare mata kallo yayi duk da cikin duhu ne sai hasken wata daya hasko su kaɗan . "ki dauko dubu ɗayan tukunna". Tsaki Taja da faɗin, "kai karka ɓatamin lokaci bacci nakeji, nama iya abinda zan yi wannan ɗin ma ka godewa ALLAH dan shi ya tsaga da rabon ka".........Ta ƙarashe tana ƙoƙarin barin wurin, hannu ya kai zai warci jakarta ta aikuwa ta daddage ta zabga masa mari. " Durun uwa (Ni kuwa nace salatin arna)". Ya faɗa yana dafe kuncin sa, saidai Kafin ya ɗago ba ita ba dalilin ta, raba ido ya shigayi akan layin da yake ba kowa shiru bakajin komai sai haushin karnukan ƴan vigilant. Ɗaga murya yayi da faɗin, "kuma ALLAH ya isa" . Ya ƙarashe yana komawa cikin tuk tuk ɗin sa da sauri faɗi yake, " Gwara na cikawa rigata tun da saura na, dan da alama yarinyar nan irin yaran nan ne da ake haɗa baki dasu a kawo ka lungu a bigeka a rabaka da machine ɗin ma". Amfani tayi da spare key ɗin da take dashi ta buɗe gidan ta shiga, sannan ta maida ta rufe a hankali, ciki sanɗa ta shiga tsakar gidan ganin ba kowa tayi saurin faɗawa ɗaki, da Shazeen ta fara cin Karo a ƙasa tana bacci ga wayarta a gaban ta. Wayar ta ɗauka ta kunna flashlight sannan ta ɗauki Shazeen ɗin ta maidata Kan katifar tasu. Rage kayan jikinta tayi ta ɗaura zani ta ɗauko ƙwandon soso da sabulun su ta fita zuwa bayi dan watsa ruwa. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______11 12am daidai agogon birnin ƙasar Nifaz ya buga, garin yayi shuru sosai saboda ruwan da aka ɗauka tsawon awanni sama da biyar anayi, ko ina ya dau sanyi sosai, rahamar ALLAH ta sauka sanyin da talaka da mai kudi duk zai isa garesu, sanyin da baza Ka biya ko Sisi ba kafin Ka sameshi, shin wanna kaɗai bai isa mu dauwwama muna godewa ALLAH da niimarsa gare mu ba. A bangare guda kuma wasu suna nan su na amfani da wanna yanayin ta hanyar morar sa akan gurbatacciyar hanya. MYSTIC HIDEAWAY shi ne sunan dake manne jikin tangamemen gate ɗin, wasu murɗaɗɗun garada ne majiya ƙarfi tsaye a kofar gate ɗin suna zazzare idanu, kana ganin tsarin wurin kasan club ne irin na ƴa'ƴan manya masu hannu da shuni, wani VIP underground room ne da ba kowa ake bawa hayar sa ba sai wane ɗan wane a cikin masu kuɗin ma. Wasu manyan mutane ne zazzaune a wasu kujeru da suke zagaye da wani ƙaramin table dake gabansu, kwalaban lemo ne da giya kala kala ga tumblers kowanne ɗauke da ƙanƙara a ciki, ɗakin ya ɗau sanyi sosai har raɓa raɓa yake dan dukda sanyin gari hakan bai hana su ƙarawa da na'urar sanyaya ɗaki ba wato AC, sai dai wurin akwai ƙarancin haske sosai haka zalika duk dukan kiɗan dake tashi a maka makan speakers ɗin dake sama su fa a wannan underground ɗin basa wani jinsa sosai. Kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar da wani abu me muhimmancin suke tattaunawa. Ɗaya daga cikin su ne ya ce, " Ni fa a ganina an kashe maciji ne ba'a sare kansa ba, dan wai mun durƙushe yaron can a idon duniya ba hakan na nufin mun durƙushe ahalin sa bane fa, kuna gani ma kamar wata dama muka bawa wa'annan ƴan uwan nasa tunda gashi har ɗaya daga cikin su ya fara kokarin kafa kansa. kuma kunsan sunan Hashim Darwin ba zai kankaru a jikin su ba. Nisawa ɗayan yayi kafin ya ce. "Wato ba wai na tari numfashin ka bane Hajj zawaad, Amma ba wai fa mun dusashe taurarin yaron nan bane kawai saboda kar su goga damu a fagen kasuwanci ah ah, Hasali ma dai mun jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya a bangaren sir Ahuoyzah yana kallon hakan a matsayin damar sa ta samun more customers tunda an kashe kasuwar Hashim Darwin sannan kuma zai samu damar karɓar end of the year award na higher export percentage, Amma mu kuma ta fuskar mu, munyi hakan ne saboda sirrin mu dake hannu mahaifin sa, wanda a ganin mu kusancin sa da Amjad ɗin yasa muke tunanin yasan komai game damu kuma a kowani lokaci zasu iya tona mana asiri a idon duniya, tunda kunga ai already kafin mu bi ta kan yaron sai da muka kwantar da uban ko?". "Maganar ka haka take Alhaji Abid, Amma yanzu to miye Abun yi?". Wanda aka Kira da alhaji Abid ne ya ce, "Abinyi anan shi ne yanzu ba wurin wanna yaron ya kamata mu maida hankalin mu ba, saboda kunga ko tafiyar da yayi ta sirri ce bare ace mutane zasuyi ca wurin zurfafa bincike infact banda mu ma inajin ba wanda ya san yayi tafiyar". "Amma dai kasan sir Ahuoyzah bazai kasa sani ba, saboda ko da ya samu aiki ba fa ya ɗauke idanunsa bane akai". Faɗin Alhaji Huzaif. "Dan ya sani ai duniya bata sani ba, akace ma shi ma munafukar tafiya yayi ai, dan haka ba abinda ya taɓa shirin mu, kawai mu ƙara sa masa ido shi kuma batun sir Ahuoyzah sai mu maida hankali kan su julaybin ɗin domin su ne yanzu suke son shigowa gaban sa". "To Kai Hajj zawaad ba kace aminin shi Awais yake ko wa mutumin ka bane Kuna having good time?". "Sosai ma !"........Hajj zawaad ya amsa. "To Kabi ta wajansa mana ka samo duk wani information na Agenda ɗinsu". "Baku da damuwa, komai zai tafi yadda akeso"...........Hajj zawaad ya amsa sannan Alhaji hammoud ya karɓa da faɗin, "kaiiiiii an sha gwagwarmaya fa, wai ma waye farko ya bada shawarar a yaɗa cewa yaron nan Human trafficker ne". Wata muguwar dariya Alhaji Abid yayi da faɗin, "kaga mugun nan".......Ya ƙarashe yana nuna Hajj zawaad. Girgiza kai Hajj zawaad yayi yana kai tumbler da ya zuba stute cranberry juice a ciki ya ce, "To ai ji nayi ana ta kai kawon yadda za'ayi da shi Amjad ɗin da ubansa, ana neman hanyar da za'a kassara su bayan ga hanyoyi mafi sauki shi ne kawai na kawo shawara". "Baka da kyau mutumi na"........ Alhaji Abid ya faɗa yana miqawa Hajj zawaad hannu suka tafa. "To yanzu ya maganar exporting crude oil ɗin? kunyi magana da sir Ahuoyzah din ne?"....... Hajj zawaad ya tambaya. Alhaji Hammoud ne ya ce, "Eh munyi magana da safe, nayi masa bayanin customers ɗin namu dake ƙasa, yace zai Bamu AP sai mu haɗu dashi mu tattauna gabaɗaya, kunga daga nan ma sai mu shigar masa da bayanan su Julaybin ɗin ko?". "Hakan yayi. Kai ina John ya ƙaro mana ice cube ɗin nan mana"........ Alhaji Hammoud ya faɗa yana kurɓe ragowar wine ɗin dake cikin tumbler ɗin sa. Wani Wanda tunda suka fara magana baice komai ba sai kurɓe kurɓen sa da yake ne ya ce, "Kuna ta magana Amma baku duba cewa akwai inda burin mu bai Kai ba"........Alhaji huzaif ya ce, " Na me fa?" Gyara zama yayi da faɗin, " Mun fito mun shaidawa duniya Amjad na ɗaya daga cikin manyan masu safarar mutane na ƙasa da ƙasa sannan duk kasashe sun ɗauka, an ɗarsa zargi a zuciyoyin al'umma Sannan an haddasa cece kuce, munbi ta ƙarƙashin ƙasa mun sanya ana ta bincike akan sa, ƙasashe sun zuba ido suga iya gudun ruwan ƙasar Nifaz saboda Abu ne da muka bayyana na matsayin ƙasa da ƙasa, kuma har ƙasar Belgium ta fito tayi ikirarin in ƙasar Nifaz bata kammala bincikenta tayi abinda ya dace ba to su a basu shi suyi masa hukuncin da ya dace, Saboda su ma sun samu sunan sa a sawun Farko. Abu na farko mu a iya ƙasar Nifaz shirin mu ya tsaya, ya akayi ƙasar Belgium ta samu sunan sa a sahun farko na masu laifukan safarar mutane da akeyi a ƙasarta? Abu na biyu meysa bakuyi tunanin yadda akayi ya samu visa ba a wannan lokacin? Abu na uku ya akayi ya fita daga ƙasar Nifaz?"......... Ya ƙarashe yana komawa yayi relaxing jikin kujerar da yake zaune. Shuru ɗakin yayi ba kajin komai sai sautin numfashin su dan ba ƙaramin dukan zuciyoyin su zancen Alhaji Malayin yayi ba. Can dai Alhaji Abid yayi ƙarfin halin faɗin, "kana nufin anyi sara kan gaɓa kenan?"..........da sauri Hajj zawaad ya ce, "Tabbas nima abinda na fara tunani kenan, in na fahimta mu ɗin kawai mun fitowa da duniya abinda ke ɓoye ne, mun kuma yaye musu duhun dake zagaye dasu, tunda gashi sanadin abinda mukayi yasa suka ƙara faɗaɗa bincike har suka tono Abinda ke ɓoye ". Shi dai Alhaji Malayin bai sake cewa komai ba sai su Hajj zawaad ɗin ne suke sake tattauna Maganar. _____________Daga nesa suka ajje motar sannan suka fito suka shiga takawa da kafar su, suna sanye da wata qatuwar baƙar jacket da bakin wando, sun rufa hular jacket ɗin a kansu, suna zuwa securityn ya bude musu ƙofar gate ɗin suka shige, kallon gabas da yamma sukayi kafin ɗayan ya kaiwa securityn bugu take ya zube kasa wanwar kamar wanda ba rai a tattare dashi, kulle gidan ɗayan yayi sannan suka kalli juna tare da yin wata alama da ido, nufar building ɗin sukayi suna zuwa suka fara buga ƙofar da ƙarfi kamar zasu sauketa ƙasa. Bugun kofar da ake ya farkar dasu daga bacci, a tsorace Mumu ta ce, "Alhaji kaji abinda naji kuwa?"......... Cikin rawar jiki ya shiga maimaita innalillahi wa inna ilaihir raju'un, "Mun shiga uku Hajiya Latifa, wa yake mana irin wannan bugun tsakar daren nan, tashi maza kije ki tashi yaran nan ki haɗasu daki ɗaya ki kulle"......... Ya faɗa Yana tashi da sauri ya warci wayar sa domin Kiran yan sanda saidai ba service kan wayar ko kaɗan. Har takai bakin ƙofar fita ya ce, " Hajiya Latifa ina wayar ki, yi sauri da ALLAH miqomin". "Ka ɗauka gata can "........ Ta faɗa cikin rawar murya tana buɗe Ƙofar ɗakin ta fice. Bugun Ƙofar farko a kunnen ta ya sauka wanda hakan ya sanya ta yin wani juyi sai gata a ƙasa cikin tashi hankali ta fara neman switch ɗin light, hanyar ƙofa ta nufa sai Kuma ta dawo a guje ta ɗauki wayarta, har ta ɗaura hannunta kan handle ɗin ƙofar sai idonta ya sauka kan screen ɗin wayarta da ya kawo haske, dafe kirjinta tayi tare da sauke wani naunauyan numfashi, cikin sanda ta bude ƙofar ta fita da sauri ta sauka downstairs, da lalube ta gano ƙofar falon a hankali ta ɓude sannan tayi sauri ta faɗa kitchen ta kulle. Ko da suka shigo maida ƙofar Philip yayi ya rufe yayin da Danny kuma ya kunna hasken falon amma har zuwa lokacin ba'a iya ganin fuskar su saboda hular jacket ɗin data rufe kusan rabin fuskar. A ƙofar ɗakin suka haɗu tana kokarin dawowa yana kokarin fitowa, ko Ina na jikinta kerma yake ta ce, "Alhaji banga Nayrah ba, babu kowa a dakin ma". "Kamar ya bakiga Nayrah ba ? Ina take to? Ina su nashwan?". Zuwa lokacin hawaye ya fara zuba a idanunta, ta ce, " Duk suna Nan Amma ba Nayrah in..........." Maganar da sukaji a ƙasa ana basu umarnin saukowa ne ya sanya su kallon juna yayin da mumu ta ɗaura hannuwanta a baki a ƙoƙarin ta na tare Kukan da ya taho mata. Dad ne yayi ƙarfin halin jan Ƙafa ya nufi downstairs ɗin Yana tafiya kamar me tsoron ƙasa, bin bayansa mumu tayi tana riqo rigarsa, a haka suka sauko falon ƙasa, suna kokarin zama a ƙasa Danny ya ce, " Have a seat"........ tare da nuna musu kan kujerar, cikin rawar jiki suka Ɗaura jikinsu, har lokacin mumu maqale take da dad. Janye hulunan sukayi baya wanda hakan ya bayyana fuskokin nasu. Philip ne ya ce, "Bamu zo da niyyar cutar daku ba hasali ma saqo ne daga Boss"......... Kallon kallo akayi tsakanin mumu da dad kafin dad yayi ƙarfin halin furta, "saqo Kuma ? Wani irin saqo ne haka? Daga Ina Kuma?". "Daga Boss"......... Shuru yayi Yana juya sunan a bakin sa kafin a ƙarshe kamar wanda aka matsa ya ce, " AMJAD HASHIM DARWIN"......... Zabura dad yayi ya miqe da faɗin, "Okay ashe armed robbers ma a karkashin sa suke, shi gashi tijararre shi ne zai aiko mun barayi tsakiyar dare cikin gidana tsabar wulakanci saboda shi bai gaji arziki ba ko......." "Alhaji ka bari"......... Mumu da har lokacin a tsorace take ta faɗa. Bige hannunta yayi ya cigaba da faɗin, "ke rabu dani in yi magana, ba uban da nake tsoro kinji, in banda rashin gsky da duniya ma ta shedeshi da ita, ya aiko mutanan arziki mana ko yayi aiken ido na gani ko Kuma shi yazo da kansa, ohhh ashe fa shi yanzu gudun ceton rai yake ko, to ka koma ka faɗa masa in ya isa yazo da kansa Ina jiran sa, ƴata Kuma ko zata tsufa a gida bana bashi auran ta yauwa". A fusace Danny ya ɗaga hannu kamar zai kaiwa dad mari, saurin riqo hannun Philip yayi tare da saukeshi yana girgizawa Danny Kai sannan ya ce, " Bamu da lokacin da zamu ɓata anan, saqon da ya bamu shi ne Kar kayi gangancin saka wani a matsala ta hanyar jingina shi da madam Nayrah domin hakan zai I........." Tarar numfashin sa dad yayi, "iyaka yace zai sa a ɓatar dashi ko? to Kar ya fasa ya'ta sai na aurar da ita ga mutumin kirki wanda nakeso, ni za'ayi wa barazanar banza da wofi". "With due respect sir ina baka shawara daka janye wannan zancen naka, dan babu halittar data isa Boss yayi takara da ita". "Duk uban daya fasa......"..... Mumu ce ta toshe masa baki. "Dan ALLAH alhaji kabar abun haka". Cikin ɗaga murya ya ce, "bazan bari ba whl bazan bari ba, yar tana matsayin ya'ta ace za'a min iko da ita, wato ma fin ƙarfi zai nuna min, Kai ku fice min a gida ko na haɗaku da hukuma dama neman Ku suke ido rufe, yanzu zasu ɗaure ku daga Ku har shi tantirin shugaban naku har igiya tayi saura, shi ma ai baifi ƙarfin hukumar ba kuma tana nan tana jiran sa". Murmushi Philip yayi tare da bubbuga bayan Danny sannan ya juya ya fice Yana maida hular kansa, shi ma Danny ya rufa masa baya. "Da Kar Ku fita mana, ƙaryar banza ƙarya wofi". Nayrah ce ta fito daga kitchen hawaye jage jage a fuskarta ɗan tunda taji abinda ke faruwa tsakanin su dad da su Philip hankalin ta ya tashi ta shiga kiran sa amma bata shiga, sam bata san cewa matakin da ya ce zai ɗauka kenan ba, kuma tashin ta kenan daga bacci a firgice taga text ɗinsa cewa ta buɗe Ƙofa saisa batayi wani tunani ba ta buɗe, ashe ƴan daba ya turo musu yanzu in da sun yiwa dad wani abu fa?. A gaban dad ta durƙushe kafin tayi magana ya rigata da faɗin, "Au to dama kina ciki kenan, tsohuwar munafuka wato baki rabu da mutumin nan ba ko? in ba haka ba taya zai san Maganar da nayi dake har ya turomin ɓarayi cikin gidana da tsakar dare , keee wato bakyaji ko, ni wai me kuke nema dani ne da kuke neman janyo min magana ku tozarta ni cikin alumma". "Dad dan ALLAH kayi haƙuri da ab........." Bai bari ta ƙarasa ba ya ce, "Ke ALLAH ina iya ɗaukeki da Mari idan baki kauce kin ban wuri ba, aure kuma dake da Farshad babu fashi ko zaki mutu na shaida Miki".........ganin dad ya hau dokin zuciya ba kuma zai saurare ta ba ya sa ta tashi ta wuce sama tana zubar da hawayen rashin madafa. Meysa Amjad zai yanke hukunci ba tare da ya nemi shawarar ta ba, gashi yanzu komai ya sake tabalɓalewa. "Haba Alhaji Dan ALLAH mu bi komai a sannu, kayi hakuri, ka zauna in kawo ma ruwa ka sha sai muyi magana". "Bani shan ruwan, ba abinda zan sha kema ai da haɗin bakin ki, kina sane da duk abinda yarki takeyi kika boye, burin ku dama ni ku hana rayuwata zaman lpy da kwanciyar hankali. To karki yi kuka dani in ya'yan ki suka salwanta". "Haba Alhaji Ka dinga min adalci mana , Ka tuna da ni na baka shawarar aurar da Nayrah ga Farshad, duk saboda miye? Ba saboda mu tsira daga sharrin yaron nan bane". Cikin fushi ya sake cewa, "Amma kina sane ai tana tare dashi har yanzu".........."Alhaji! "........ Ta kira sunan sa cikin wani salo, juyowa yayi ya zuba mata ido na ɗan seconds sai kuma ya dauke kai . "Zauna!". Ta faɗa cikin salon bada umarni. Zaman yayi ba tare da ya kalle ta ba, ita kuma ta tashi ta je kitchen ta ɗauko masa ruwan ta miqa masa ba musu ya ƙarba ya sha sannan ta ce, "Tashi mu tafi sama muyi magana a nutse"........ Ba musu ya tashi ya wuce tabi bayansa. ------------------------√ Washe gari ranta fes ta tashi, saida suka gama komai kamar yadda suka Saba ita da Shazeen sannan ta tashi Sahnish shi ma ya shirya, tare sukayi kalaci sannan suka fice gabaɗayan su, Shazeen suka fara saukewa a makaranta sannan suka wuce asibiti domin ayi wa Sahnish dressing ciwukan sa, daga nan suka wuce ta sauka wurin aikin ta sannan shi Kuma aka wuce dashi gida. Lokacin ɗaukan Shazeen nayi taje ta daukota ta maidata gida sannan ta koma wurin aiki sai lokacin tashin su. Yau ma tare suka fito kamar jiya dan su bunayna basu da matsala sam gasu da saurin sabo. Yau ma kamar jiya a bakin titi suka rabo kowa ta wuce gida, ita dai Hushaima kasuwa ta wuce duk da gajiyar dake tattare da ita ga wani bacci da take ji dan daren jiya bata samu bacci da wuri ba, haka dai ta daure ta shiga. Shigar ta kenan wayarta ta fara ringing ɗauko ta tayi a jaka, ganin Sahnish yasa tayi saurin ɗauka tana faɗin, "Sahnish lpy kuke?". "Kash, in anyi magana kuma kice ke jaruma ce gashi yanzu daga waya har kin tsorata, to Me kike tunani?". Tsaki taja, "Mtwee kana da matsala, miye ne ni?"........."Munga kin dade ne." "Na shiga kasuwa ne akwai abinda Nike son siya"..........."To muma a siyo damu". "Tunda ka ban ajiya ba"........ ta faɗa tare da kashe wayar ta maida jaka, daga bayan ta taji ance.......... 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______12 & 13 Daga bayan ta taji ance, "sannu ƙaramar ɓarauniya"..........Juyawa tayi idonta ya shige cikin na yarinyar nan da tayi sata a starlight beauty co. sannan ta nemi ta ɗaura mata, Saida ta ƙare mata kallo sannan ta ce, "Yauwa sannu babbar barauniya".........."Ina kudi na ?"........ Yarinyar ta tambaya. "Dama kin bani ajiya ne?"............ Itama Hushaiman ta maida mata tambayar tana binta da wani kallon banza. "Kuɗin da kika sata jiya, suna Ina?". "Haa ikon ALLAH, au da kika sata kin bani ne kince na ajje Miki?". "Amma dai kinsan ba naki bane meysa kika ɗauka, meysa baki maida su jakar tawa tare da Abun hannun da zoben ba, kika sani ramakon kuɗin da banci ba". Wani gafalallen murmushi Hushaima tayi tare da faɗin, "Ke kina da kuɗi makamancin wancan ɗin kikayi sata". "Amma dai kinsan ko kogi baiki daɗi ba, kuma abinda na sata ɗin da nayi a Sa'a ai kinga yafi abinda nake dashi ɗin, kawai ki ragemin zafi mu raba asara". "Zancen banza ma kenan, kinga ni shawarar da zan baki shi ne ki nemi Abun yi domin sata ba sana'a bace dan sai wani ya ajje kin gani zaki ɗauka, in Bai ajje ba Kuma rayuwar ki tana cikin gararin babu, Dan haka ki maida hankalin ki tun da sauran mutuncin ki kafin a samu wasu su ankare dake su Miki dukan da baza ki moru ba"........ Tana kaiwa Nan ta juya da niyyar Ƙara gaba yarinyar nan ta riqo kafaɗarta tare da juyo da ita da ƙarfi tana faɗin, "Whl baki Isa ba ɓarauniyar banza ke har kina da bakin bawa wani shawara, ko kema ba satar kikayi bane?". Hushaima na juyowa ta buge hannun da ƙarfi tare da nuna ta da yatsa ta ce, "kinga karki ɓatamin rai whl zan iya janyo miki Abun kunyar da har ki mutu baza ki manta ba, sannan ni ban taɓa sata ba, kyauta ce kika ɗauka kika ban tunda ke kika sakamin a jaka Kuma kika biya a asusun ki. Sannan Kuma gargadi na ƙarshe ko a titi kika ganni kika nuna kin sanni sai kin gwammace mutuwar ki kafin wanna ranar, banza Mai matacciyar zuciya, ki rufawa kanki asiri ki wuce ki bar kasuwar Nan tun kafin masu kaya su fara nemanki"............Ta Ƙarashe tana wucewarta ta bar yarinyar tsaye sake da baki cike da mamakin yadda akayi Hushaiman ta san tayi sata a kasuwar, jijjiga Kai tayi cike da borin kunya ta ce, "Zaki San sata gidan barawo rance ce"........... Ta ƙarashe tana saka hannu cikin hijab ɗin ta ta gyara zaman jakar dake kugunta Wadda take cike da hakkin mutane data sanfe. Ita kuwa Hushaima tana gama sayan abinda zata saya ta tari abun hawa ta wuce gida, tama manta da batun wata ɓarauniya. Ganin me tuktuk ɗin na ƙoƙarin ɗaukan wata hanya daban ya sata faɗin, "Miqewa fa zamuyi"............ "Eh hajiya ai na sani zan biya ne na karɓi saqo sai mu wuce". "Kaga Malam tunda mun kusa kawai mu ƙarasa ka saukeni sai ka wuce".........Hushaima ta faɗa. "To Hajiya ai nan gaban mu ne zan karɓi saqon duk kan hanyar ne "............wata wadda Hushaima ta tarar a cikin tuk tuk ɗin ta ce, "Ni mun ma iso, sauke Ni anan" ..............."Gsky bazan tsaya ba ai ba nan mukayi dake ba". "Kamar ya baza ka tsaya ba tace ma ta iso haa"........ Hushaima ta faɗa a fusace. "Whl ko me zakuyi bazan tsaya ba sai na kaiku in da zaku".......... hankali tashe matar ta ce, "Malam nace ma na iso ka tsaya na sauka ko na ma ihun ɓarawo Whl" . "Whl bazan tsaya ba"............ screwdriver Hushaima ta kafa masa gefen wuya da faɗin, " ko ka tsaida mashin ɗin nan ko na burma ma ita whl"........... Gefe guda kuwa matar nan leqowa tayi tana ihun faɗin ɓarawo jama'a ɓarawo ku taimaka. Jin haka ya sashi ƙara gudun mashin ɗinsa ɗan yasan yana tsayawa in mutane suka rafke shi sai sun halaka shi saisa kawai ya gommaci in ma caka masa Hushaiman zatayi saidai ta caka masa. Wani irin bugu Hushaima ta daddage ta kai masa a gefen wuya, rawa kan tuk tuk ɗin ya fara masa a hannu saboda a bazata yaji bugun, take jijiyar muqamikin sa ta riqe yayinda gudun tuk tuk ɗin ya sassauta, kafin ya gama dawowa hayyacin sa Hushaima ta kudunduni kayanta tayi tsalle ta dira a waje ganin haka yasa ɗaya matar ma bin bayanta. Nan mutane suka rufarwa tuktuk ɗin saidai ko da sukayi nasarar isa gareta me tuk tuk ɗin ya suma, ita kuwa Hushaima ba tare data damu da yan raunikan data ji ba ta tsari wani me tuk tuk ɗin ta wuce gida tana godewa ALLAH da ya taimake su. Tana shiga ta samu Sahnish tsaye a tsakar gidan yanayin fuskar sa ne ya shaida Mata kamar yana cikin damuwa, ƙarasa shigowa tayi kallon furkarsa ta ce, "Sahnish lpy meke faruwa?" "Meysa kike da taurin Kai ne Hushaima? Meysa duk abinda kika sa kanki sai kin yi ? Meysa in kina Abu bakya tunanin abinda zaije yazo"...........Cikin Rashin gane Kan zancen sa ta ce, "me.. me kuma ya faru?" "Meysa zakiwa su karafiya shu ne idan kuma suka gane da sa hannun ki ciki fa? Whl baza su barmu ba kuma kin sani ". "Shu ne kuma? Ni ? To ina ruwana dasu, ni ai tun ranar da suka ma wannan dukan naje mukayi cacar baki ko kallon inda suke zama ban sake yi ba, to uban wa ma yace ni na musu Shu ne?". "Ba uban daya gayamin Sarkin masifa, kawai naje shagon Juma ne zan saya katin waya, sai naji wani yana faɗin wai hukumar yaqi da miyagun kwayoyi ta ƙasa ta kama su karafiya, kotu ma ake shirin kaisu saboda an same su da kwayoyi masu hatsari". "Eh shikenan kuma sai zuciyar Ka tace ma ni nasa a kama su ko, saboda nice kullum cikin rigima ko Sahnish? Wai meysa Baka kyautata min zato ne? kullum a cikin zargi na kake nayi kaza nayi kaza". A sanyaye ya ce, " kiyi hakuri, yadda kika fita ranar da qudurin fansa yasa nayi zaton haka".........bata ce masa komai ba ta ajje jakarta tana kokarin cire gyalenta suka ji ana kwankwasa ƙofar gida, kallon ta yayi da faɗin, " waye ne?". Wucewa tayi ciki tana Kiran Shazeen ta ce, "Ina cewa tare dakai muke tsaye, kaje Ka duba mana". Juyawa yayi ya fita zuwa ƙofar gidan dan ganin waye ita kuma ta shige ɗakin su. Yana fita ya tarar da wasu maza biyu tsaye sai wata makociyar su. "Lpy dai?".......... Ya tambaya yana binsu da kallo. Matar ta ce, "Gashi nan tun ɗazu ya Kafa min a ƙofar gida yana neman haɗani rigima da mijina, wai sai na fito masa da Hushaima nace masa ba nan bane yaqi yarda, to kai kaga gidan nata karka ƙara dawowa ƙofar gida na". Kallon sa Sahnish yayi da faɗin, "To lpy dai?"..........."Eh lpy ba lau ba nayi mata kayan ɗaki ne sai ta bani rabin kuɗin tace zata cikamin rabin daga baya na bata kayan, to kusan sati kenan dana haɗota da yara na suka kawo Mata kayan, dake Babbar mota bata shigowa sai suka ajje daga bakin layi ita kuma tasa aka ɗauko mata kayan aka shigo dashi nan layin, to naji shiru kuma bana samun layin ta shi ne na ɗauko yaron da suka zo tare ya nuna min gidan wannan matar, ita kuma tace ba nan bane". "Kayan ɗaki ? Kuma anan gidan? Sannan kace Hushaima?"........... Ya tambaya cike da mamaki. "Eh, kaga ka shiga ka kirata kawai"..........Jijjga kansa yayi da faɗin, "kwantar da hankalin ka, zan kirama ita mana"...........Ya faɗa yana juyawa ya wuce ciki har lokacin mamaki yake. "Hushaima!, Hushaima!". "Wai Sahnish lpy kake ta ƙwalamin Kira haka, wanka fa nake son shiga".........Ta ƙarashe tana leqowa. "Eh wasu mutane ne suka zo neman ki, suna ƙofar gida "..........."Wasu mutane kuma? To uwar me zan musu?". "Ah waqa a bakin me ita ai tafi daɗi, ki leqa dai ki gansu tukunna". "Kai dallah in zaka faɗamin su waye ka faɗamin bana ciki da iskanci". "Ya hakuri bani na kar zomon ba, wai wani kafinta ne da ya haɗa Miki kayan ɗaki, kika karɓi kaya kuma kika gudu baki cika masa kuɗi ba".........ya ƙarashe yana dariya ƙasa ƙasa. "Kai kaga inda aka shigo da kayan ɗaki a gidan nan ne?"...........ƴarfa hannu yayi da faɗin, "To ni na san muku ne, yanzu dai kije ki sallamesu". Ƙwafa taja ta nufi ƙofar gidan, tana fitowa matar ta ce, "Gsky zan gaya Miki karki Ƙara taro rigima ki turomin gidana wannan ai sai ki kashe min aure"........... Matar ta faɗa cikin ɓacin rai. Saqale Hushaima tayi baki buɗe tana kallon ta kafin cikin ɓacin rai ta ce, "Ke da ALLAH malama dakata ni na nuna masa gidan ki ne, ke kinsan ba gudun rigima nake ba bare kice tsoron hakan yasa na turoshi gidan ki. Ki kama kanki Bana shiga harkar kowa a unguwar nan duk kuma wanda ya shiga tawa to whl rashin mutuncin da zan keta masa ko karai bazai shishina ba , Kai kuma uwar wa kayi wa kayan ɗaki?"......... Ta ƙarashe tana zaro masu rikitattun idanun ta. Duk wanda ya kalle ta a wannan lokacin yasan tabbas ba karamar yar rigima bace ba kuma tsoro a tattare da ita daidai da misqala zarratin. "Dan ALLAH kiyi hakuri"...........Ya faɗa yana juyawa wurin matar ya ce, "Ni fa ba wannan bace wadda nake nema". "Kai malam karfa ka rainamin hankali, wannan dai itace Hushaima kaɗai a unguwar nan". "Hushaima ne sunan ta amma ba wannan bace"......... Carpenter ya faɗa, Hushaima data maidasu TV ta buɗe baki zatayi magana dan tuni ta gano wata ce kawai ta damfare shi a layin ta kuma yi amfani da sunan ta, Kuma duk yadda akayi ta mata farin sani ne, bata kai ga yin Magana ba ta hango wata matashiyar budurwar na fitowa daga wata arniyar BMW i5 sedan, tana sanye da wasu shegun English wears riga da wando, fuskarta manne da wani makeken glass, kyakyawa ce sosai gashi kallo ɗaya zaka mata ka hango class a tare da ita daga yanayin takunta ma. Da wani irin kallo tabi mutanan dake ƙofar gidan kamar taga wasu sabbin halittu daga wata duniyar kafin ta maida kallon ta ga Hushaima data ɗan saki fuskar ta duk da ba wai murmushi take ba. "Mutan new york saukar yaushe? Bismillah shiga daga ciki mana Ina zuwa". "Ke dai bari tun last week na dawo ban faɗa Miki bane saboda dama surprise nake son miki"......... Ta ƙarashe tana sake kallon mutanan sannan ta shige ciki tana faɗin, "Saikin shigo". Ita kuwa Hushaima baquwarta ta na ida shigewa ta fara tijare mutanan nan tare da yin jam'u ga dukkan mutanan unguwar ta musu tas sannan ta ce ALLAH yasa wata ta sake amfani da sunan ta whl sai taci mata uwa, duk ta tara mutane a ƙofar gida daga karshe ta ce, "ku Kuma ku daibi kafuran ƙafafunku ku bace min daga ƙofar gida tun kafin rai na ya ida bacewa"...........sumi sumi suka wuce, da kallo ta bisu kafin ta ce, "Munafukan mutane da ana ruwa suna irgawa tsabar sa ido, ALLAH yasa wani me tsautsayin ya sake daibo kafa yazo ƙofar gidan Nan"..........Ta Ƙarashe tana juyawa ta shige tare da gabzo ƙofar. A tsaye ta samu baquwarta ta tana danna waya, ɗaki ta wuce ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa tana faɗin , "Ya hakuri Amla na barki a tsaye kina jira". Sai da ta zauna sannan ta kalli Hushaiman data zauna ita ma, ta ce, " ƙawata meke faruwa Wai?". "Mtwee barni kawai, mutanan unguwar Nan ne suke neman su tsokano ni, kinsan mutane baka shiga harkar su ma nema suke su taqale ka, wai wata ce akayiwa kayan ɗaki bata cika kuɗin ba ta gudu Kuma Wai sunan ta Hushaima shi ne suka kawo carpenter nan".........."Yanzu ya kukayi dasu?" "Ai kema kin sani, na saita musu hanya mana, to ni akwai wata sabuwar buɗewar ido da za'a nuna min ne". Dariya Amla tayi da faɗin, "ƙawata kenan baki da dama, nayi missing dinki sosai whl". "Ki bari kawai, ai Ina ganin videos ɗin ku a yanar gizo, naga kin sake karɓo mana lambar yabo, ALLAH ya sanya alheri". Murmushi tayi me ƙayatar wa kafin ta ce, "Ameen ƙawata, Ina su Shazeen ne naji gidan shuru ko tana makaranta?". "Duk suna Nan, Shazeen!, Shazeen!". "Naam".......... Ta amsa tana fitowa daga ɗakin ganin Amla yasa ta taho da gudu ta faɗa kanta tana dariya, itama rungume ta tayi daga zaunen da take tana murmushi ta ce, "Sweetheart ykk ya scul ?". "Lpy kalau aunty Amla, kullum Ina tambayar Aunty Hushaima Ina kika tafi, tace min kin tafi New york, har mafarkin ki nayi jiya". Kallon Hushaima tayi tana murmushi ta ce, "kinji ko, ni Anya bazan daina ƙawancen nan dake ba, oh sweetheart nima kullum sai na tambayeki, yayar nan taki ce baƙin hali ya mata yawa, taƙi haɗamu mu gaisa". "Can ta matse muku kuma, sai ki ɗaga ta ai kije ki faɗawa Sahnish ga Amla ta zo ya fito su gaisa". "Dama Sahnish Yana Nan?"........."Yana ciki, saidai in wani Abun yakeyi"..........Tashi Shazeen tayi ta wuce ɗakin Sahnish domin sanar masa saqon Hushaiman. Gyara zama Amla tayi tare da zaro wani form a jakarta ta ce, " Nayi wani karambani, Amma karɓi dai ki gani".......... Karɓa Hushaima tayi ta zubawa takardar ido sai Kuma ta ɗago tana kallon Amlan da yanayin neman Ƙarin bayani. "Form ɗin neco ne da aka fara siyarwa shi ne na siya Miki, kinga in results ɗin ya fito sai a samu wata higher institution ki jo na". Da wani irin yanayi take kallon Amlan har tagama maganar sannan ta furzar da zazzafar iska, "Amla naji dadin karamcin ki a gareni, Amma da kinyi shawara dani baza ki siya ba domin ni inaga asarar kuɗin ki kawai kikayi, dan bazan iya zama na rubuta komai ba". "To in baza ki iya ba, ba sai asa a rubuta miki ba, ai ba abinda zai gagara". Sunkuyar da kanta tayi kamar me jin kunyar abinda zatace, kafin ta buɗi baki ta ce, "Amla taya zan nuna shaidar gama secondry sannan na kasa kare Kai na".......Da fuskar tambaya Amla take kallon ta saidai kafin tayi magana su Sahnish suka iso. "Ahh yau kuce manyan baki ne a gidan namu". Yar dariya tayi da faɗin, " Kaji Sahnish Kuma da wani batu, ni ai ba baquwa bace, ya kake ya gidan?". "Ni dai karki canza min zance ba haka nake nufi ba, Alhamdulillah kin iso lpy?".........."Lpy kalau alhamdulillah, meya same ka? ciwo kaji ne ?" Hushaima ce ta karɓa maganar da faɗin, "Me machine ne ya bugeshi"..........."Subahanallah, ALLAH ya kare gaba, sannu Sahnish". "Yauwa amla nagode, Bari na koma daga ciki kafin Ku gama". "Ah ah, kaga bama jimawa zanyi ba, tunda na dawo ban fita ba sai yau shi ne nace Nan zan fara zuwa". Murmushi yayi da faɗin, "Mun gode sosai, ALLAH ya bar zuminci".........Tashi Hushaima tayi ta shiga ɗaki ta ɗauko dan kwalin ta suka fita raka Amla ɗin gabadayan su, tana ƙarawa Hushaima bayani Kan maganar neco ɗin da Kuma amfanin ilimin, anan Sahnish yaji, sosai ya nuna jin dadin sa tare da mata godia. Har wurin motar ta suka rakota, buɗe bayan motar tayi ta ɗauko wasu shopping bags guda biyu masu kyau ta miqawa Shazeen ɗaya sannan ta miqawa Hushaima ɗaya da faɗin, "Tsarabar New York ce, ba yawa gashi Nan ke da Sahnish"......... "irin wanna dawainiya haka Amla, mun saki wahala da yawa ai". "Kinga madam ba fa Dan ke na kawo ba, kawai dai dan karki sawa na kannen na ido ne saisa kawai na Dan Kara dake". Sahnish ne ya amshe da. "Kinga Amla rabu da wanna baki ne da ita kamar aku"........ Duka ta Kai masa ya kauce Yana dariya, juyawa tayi wurin Shazeen da faɗin, "Shazeen kiyi wa aunty Amla Godia". "Ina ruwanki, tun kafin ki faɗa tayi ai Madam"......... one side smile ta saki wanda ya sake fito da kyanta saboda ba ko yaushe takeyin murmushin ba saisa in tayi yake mata kyau. "Muna ƙara Godia Amla, ALLAH ya saka da khairan". "To Ameen"........ Amla ta amsa tana shiga mota, daga nan sukayi sallama tare da dan matsawa gefe shi kuma Sahnish ya shiga duba mata hanya da zatayi reverse ta fita daga layin. Saida ta fita a layin sannan suka juya gida. A tsakar gidan suka zube nan kan tabarmar suna duba kayan. Sahnish riga da wando ne masu kyau da turare sai Hushaima data sako mata dogayen riguna uku, ɗaya armless sai long sleeve ɗin da take tafe da ita a ciki, biyun kuma jacket suke tafe dashi wanda ta tsaya iya ciki, sai turare da veil ƙarami. Na Shazeen kuma English wears ne masu kyau na yara daidai shekarun ta tare da hair oils da ribbons sai su chocolates. Ita dai Hushaima tattare nata tayi ta wuce ɗaki ta ajje tare da form ɗin da Amlan ta bar Mata su cike zata dawo ta karɓa, sannan ta cire kayanta ta ɗaura zani ta fita ta shige wanka. Har ta fito su Shazeen na tsakar gidan, sai gwada kayan take, tana ganin Hushaiman tayi saurin matsawa tana faɗin, "Aunty Hushaima kinga yadda kayan suka min kyau"........ Cikin Jin dadi ta ce, "Naga kayanki Shazeen, Kaya sunyi kyau sosai, ALLAH yasa a kashe lpy, mun godewa aunty Amla".......Tsallen murna tayi ta koma wajen Sahnish ita kuma ta shige ɗaki dan shiryawa, wata yaloluwar doguwar riga ta material marar nauyi ta saka tare da jan robar wandon data ke daure gashinta da ita, fatabarakar Rahman shi ne abinda baki na ya iya furtawa ganin yalwar gashin Kan Hushaima Wanda dama tun daga fuska zaka shaida akwaishi Amma baza Ka taba tunanin zai Kai haka ba, dogo ne sosai dan ya kusan wuce kugunta gashi da tsantsi saidai bashi da cika can can kuma ba baƙi bane, light brown ne. Masarci ta dauka ta taje sannan ta daure shi in a sleek bun style. Juyawa tayi da niyyar fita Shazeen ta shigo da jakar kayan ta ɗaya hannun kuma ledan sweets ɗin ne, karɓar jakar kayan tayi ta ajje sannan ta karɓa na sweet ɗin ma ta eba mata kaɗan daga ciki ta bata sannan ta boye sauran ta juya ta fice. Yana zaune a inda Shazeen ɗin ta barshi, zama tayi kusa dashi sannan ta kira sunan sa , "Sahnish!"........... Ɗagowa yayi yana kallon ta ba tare da ya amsa ba. "Kai za'a cikewa form ɗin nan bani ba". "Kamar ya bangane ba?" .........Ya faɗa yana bata dukkan hankalin sa. "Kai zaa zanawa bani ba, Kai zakafi buqatar ta"........ Dan shuru yayi kafin ya ce, "Dani dake fa duk Abu ɗaya ne, kinfi kowa sanin abinda baza ki iya ba to ni ko tunanin somawa ba zanyi ba, ni inaga kawai mu faɗawa Amla gsky". "Ban gane a faɗawa Amla gsky ba, kana so ka kunyata mu ma kenan, nace mata iya jss muka tsaya sannan yanzu kuma muce mata bamu taba zaman aji ba ko me ?".......... Ta ƙarashe tana wurga masa wani kallon cikin ido, shi ma kallon nata yake, tsawon two minutes suka ɗauka kafin ya ɗauke kansa da faɗin, "Shikenan duk abinda kika yanke, amma ki tuna shi dai karatu ba abu bane dake ɓoyuwa ina gudun ranar da Amla zata gane muna mata ƙarya, saboda ta ɗauke mu kamar yan uwa". Dan shiru tayi tana tunani kafin ta ce, "A tsawon lokacin da mukayi duk bata taɓa fahimta ba sai yanzu, kai dai ka bari ɗin a zana makan kawai"......... Bai sake cewa komai ba ya tattare kayan sa ya wuce ɗaki, ita kuwa gyara zama tayi tare da nutsawa cikin duniyar tunanin rayuwar su. -------------------------√ Tsaye yake kunnen sa maqale da waya, kallo ɗaya zaka masa Ka tabbatar da ba'a cikin dukkan nutsuwar sa yake wayar ba. "So nake kawai Ka binciko min ta yadda akayi har ya samu visa ya fita wata ƙasar, kuma ma ya akayi ba wanda ya sani bayan kuma a yanzu bashi da ikon ƙetara ko da iyakar ƙasa ne bare kuma ya yi tafiya wata ƙasar a jirgi".........Daga daya bangaren akace. "Oga Awais duk iya binciken da zanyi nayi shi a dai bangare na amma babu wata shaida data bayyana mana cewa Amjad ya fita daga ƙasar Nifaz, domin ɗazu na aika yarana airport ɗin su min bincike kwata kwata bama sunan sa a list ɗin mutanan da suka tashi daga birnin Nifaz a ranar da kuma satin nan gabaɗaya". "Amma an tabbatar min ya shiga WorldLink international airport a shekaran jiyan da yamma"......... Awais ɗin ya faɗa cikin yanayin dake nuna a qage yake da samun bayanan da yake so. "Tabbas ya shiga airport Amma saidai wani abun yaje yi, dan gaskiya bincike na ba kuskure a ciki".........takaici yasa ya ƙasa bashi amsa sai kawai ya Kashe wayar tare da dafe Kai cikin takaici ya furta, "Oh sh**t yaron nan Yana son wargaza mana lissafi fa".........Wata number ya sake dialing ana ɗagawa ya ce, "Akwai wani labari ne ta wajen Ka?". "Akwai matsala dai, dan ni whl kai na yana barazanar rabewa biyu, idan fa harta tabbata Amjad ya fita alkadarin mu ya karye, burikan mu sun watse, sannan sirrikan mu na barazanar bayyana, gashi ina ta neman number Julaybin bana samun sa na kirawo Atiq yace min shi tun safe ya fita, na kira Bisma kuma ta shaida min julaybin din ya dade da fita, nayi tunanin har kaina ya kama ciwo". "Tsaka mai wuyar da kake ciki Nima ina cikin ta Nuhail ko nace muna cikin ta domin duk mu ukun nan shirin mu ne silar tarwatsewar farin cikin sa, aikin mu ne yayi sanadiyyar watsewar alqiblar rayuwar sa tare da sanyashi a tsaka me wuyar da yake ciki a yanzu, shin ya kake tunanin makomar mu wurin al'umma da kuma dada da zan iya cewa sanadiyyar abinda mukayi ne baqin ciki ya kwantar dashi saboda kasan yadda yake ƙulafuncin shegen Amjad ɗin nan". "Haqiqa muna cikin tashin hankali ba wai, amma yanzu miye mafita?". "Mafitar mu ɗaya ce shi ne muyi fatan Kar zancen tafiyar da aka faɗa ya fita wurin Al umma, ALLAH kuma ya rufa masa asiri ba'a samu wani dan media ya masa hoto ba a airport ɗin"..........."Kuma Awais da gasken yayi tafiyar?"........Nuhail ya tambaya. "Ba zan iya ce ma komai ba Nuhail, bangare biyu sun tabbatar min da Amjad yayi tafiya bangare uku kuma sun tabbatar da babu jerin sunan sa a wa anda suka tashi ma". "To yanzu a wace matsayar zamu tsaya, Nima bangare na na saka a bincika mi........" Bai ƙarasa maganar ba ƙira ya shigo, "To gama shi nan ana kirana". "Karka kashe ɗaga nima inaso inji".......... Picking Nuhail ɗin yayi da faɗin, "kawule ya Ake ciki?". "Ranka ya dade daga farkon titin airport ɗin zuwa cikin sa gabaɗaya ɗauɗauku 15 ne, a kowacce kuma result ɗaya ne an shiga dashi airport ɗin daidai karfe 4:40pm a mota kirar range rover silver colour tinted glass, saidai an samu ɗaukewar wasu daga cikin cameras ɗin daga shigar sa wa'anda sune suka wargaza mana lissafi a yanzu, kasancewar baza mu iya tantance ya shige cikin filin tashin jirgin bane ko kuma bai Shiga ba, saidai an auna nauyin tayar motar da suka shiga nauyin ya ragu akan yadda ta shiga hakan ya tabbatar da ya sauka daga motar kenan"......... Duka nuhail ya kaiwa bango cikin qunar rai ya ce, " Duk yadda za'ayi Ku gano cewa ya tashin ne ko kuma bai tashi ba ko nawa ne zamu biya kasan kuɗi ba matsalar mu bane". "Haka ne yallabai Amma kasan dokar daka ce akan aikin, so munayin sa ne ta sirri idan har zamuyi da zafi zafi to tabbas zance zai iya fita"......... Awais ne ya tare maganar da faɗin, "kaga Kubi a hankali Ku dai kawai Ku gano mana ya fita ko kuma yana cikin birnin Nifaz ne har yanzu"..........."Shikenan ranka ya dade zamuyi iya kokarin mu". "Zan tura ma na mai yanzu"........... Nuhail ya faɗa, shi kuma ya shiga zuba masa godia, katse kiran yayi, yayinda Awais ya ce, " Nuhail kana ganin baza mu gwada Kiran Amjad ɗin ba ". "Mu kirashi mu masa uwar me, zamu bada Kan mu ne kawai, kuma hakan zaisa yayi zargin wani Abu tunda ba saba kiran sa mukayi ba, kasan shi da brain". "Shikenan, Bari muga abinda hali zaiyi, in na gama abinda nike anjima maybe zan shiga gida wurin hajiya ". "In Ka fito daga gida Ka kirani sai mu haɗu a can".......... Da haka sukayi sallama tare da katse wayar. TO FA, MY PEOPLE NI KAINA ABUN NAN YA FARA ƊAURE MIN KAI FA🤔 TO WAI SHIN TSAKANIN SU AWAIS DA SU HAJJ ZAWAAD SU WAYE KE DA ALHAKIN DUSASHE TAURARIN AMJAD? GASHI DAI KOWANNE BANGARE SUNA IKIRARIN DA SA HANNUN SU A CIKI? TUKUNNA MA MIYE MATSAYAR DA SUKE SAN CIMMA A KANSA? MEYSA SU DUKA SUKE FARAUTAR ABU ƊAYA? WANI IRIN SIRRI NE KE LULLUBE DA AMJAD DIN? SHIN SU HAJJ ZAWAAD SUN SAN CEWA SUNA FARAUTAR ABU ƊAYA DASU AWAIS NE ? TO WAI AMJAD YA BAR ƘASAR DA GASKE KO KUMA DAI AKWAI WANI ABUN DA YA FARU DA MU BAMU SANI BA?🤔 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ ___________________________________ @whatpadd pen_of_simplicity STEP 1 PAGE _______14 & 15 Tana zaune duk abun duniya ya isheta tun ranar dasu Philip suka zo gidan da daddare take neman layin sa bata samu, ga dad da mumu sun hura Mata wuta da zancen Farshad ɗin da suke son haɗa su aure, tayi nitso cikin tunani taji wayar ta na ringing, ɗagowa tayi tabi wayar da harara dan tasan bazai wuce jarababben Farshad ɗin da ya takurawa rayuwar ta ba, ɗauke kanta tayi ba alamar zata dauki wayar har kiran ya tsinke wani ya sake shigowa. A fusace ta warto wayar da niyyar ɗagawa ta gaggaya masa magana koma me zai faru ya daɗe bai faru ba amma ganin number da batayi zato ba ya sata zubawa screen ɗin wayar Ido, code number ɗin ƙasar denmark ce ɓaro ɓaro kafin tayi yunqurin ɗagawa Kiran ya katse wani ya sake shigowa, ɗagawa tayi ba tare da tayi magana ba, nutsatstsiyar muryar nan tasa ce ta daki kunnen ta, "In ba Nayrah ba waye Amjad zai wa Kira har uku bai yi picking ba". Take ta manta da fushin da take dashi a shagwabe ta ce, " Amour....." Sai kuma ta fashe da kuka. "Kin ga abinda bana so ko, in Kukan zakiyi Bari na kashe sai kin gama"........Da sauri ta haɗiye Kukan nata tana faɗin, " kayi hakuri Dan ALLAH karka kashe". "To naji, faɗa min yanzu waya ɓata miki rai har yayi sanadiyyar zubar tsadaddun hawayen nan".......... Sake shagwaɓewa tayi kamar yarinyar goye cikin wata irin baby voice ta ce, "ba kai bane" ..............Saurin tashi yayi daga kishingiɗen da yake a wani makeken gado da zai iya cin mutum shida ko bakwai, ba wani tarkace a ɗakin sosai amma ɗakin ya tsaru iya tsaruwa, daga left side dinsa glass ne a maimakon wall zaka iya hango komai da kowa dake waje, amma shi kuma na waje bazai iya ganin ka ba, opposite da bed din kuwa wata TV ce manne kamar wata wallpaper dan kwata kwata bata da kaurin normal TV, sai kuma sofa guda biyu da karamin table a tsakiya, a right side ɗinsa kuma wardrobe ne haɗe da dressing mirror ɗinsa. "Me nayi?"............ Itace tambayar da ya Mata Yana miqewa ya taka zuwa gaban glass ɗin yana kallon mutanan dake harkokin su a ƙasa hakan yasa na gane cewa shi a upstairs yake. "Ka tsokano mana aiki fa, tun ranar daka turo yaranka ɗin nan nake neman wayarka bana samu gashi ko a online bana ganin ka" . "Yanzun me ya faru?"..........."Dad ya ƙara ɗaukan zafi dakai domin aiken da kayi ba abinda ya magance sai ma ƙara taɓalɓala komai da yayi, da kayi shawara dani da baza kayi irin wannan aiken ba, Meysa ma kai baka zo da kanka ba ko kuma kayi magana da uncles ɗinka su samu dad da Maganar". "Ninie!, I know what I'm doing fa, kuma kinsan a yanzu s......." Shiru ya danyi sai kuma ya canza zancen da faɗin, "ba zai yiwu na zo gidan ku a halin da ake ciki ba, amma kiyi hakuri". "To yanzu me muke ciki, dan ni Whl wannan Farshad ɗin ya takura min ALLAH na gani". "Kamar ya?"...........Ya tambaya yana gyara tsayuwar sa. "Yazo gida ban saurare shi ba, shi ne yake takuramin a waya"..........dan lumshe idanun sa yayi tsawon mintuna dan har ta ɗauka ya sauka daga kan layin ma sai taji ya ce, "Bakomai!, Ni dai kawai abinda nake so dake shi ne ki daina tada hankalin ki, saboda in kika tada hankalin ki ni kuma bazan samu nutsuwar yin abinda ya kamata ba kinji am Mata na". Murmushi tayi tana jin wani sanyi a ranta ta ce, "Shi ne kayi tafiya baka faɗamin ba, sannan kuma ka rufe duk wata hanyar da zan same ka dan kawai ka tada min da hankali ko"..........kwantar da murya yayi har lokacin kuma idanun sa a lumshe suke ya ce, " Ba haka bane Ninie, wayar ce ta samu Matsala ban kuma samu time na maida hankali na saya wata ba". Cike da shiririta ta ce, "Ai baka damu dani bane saisa, da ace ka damu da jin murya ta ai da a lokacin zaka saya wata".......... murmushi yayi me sauti da faɗin, "kullum ƙorafin ki iri ɗaya, ya kamata ki caza style ko kuma ki bani gari na koya Miki sabo"............."Denmark ka tafi ko? Naga code number ɗin can". A ɓoye ya sauke ajiyar zuciya kafin yayi Magana ta riga shi da faɗin, "Kar fa kayi tunanin zan faɗawa wani". "To Ni yanzu kinji nace ki faɗa ko Karki faɗa ne"............"Nasan ai tafiyar sirri kayi so baza kaso wani yaji ba". Shiru yayi yana mamakinta duk da ba abun mamaki bane dan yasan duk wanda yasan yayi tafiya a wannan halin yasan tafiyar sirri ce saboda already bashi da ikon fita ko ina a yanzu har sai an gama bincike, saidai kuma gefe ɗaya dariyar zallar ƙuruciyarta yake data ƙasa wani further thinking akan tafiyar, sai kawai ya basar da faɗin, "kaga wife material me riqe sirrin mijin ta, i know you will make a good wife". Dariya tayi me sauti wanda ya sake sanyashi murmusawa shi ma tare da faɗin, "ko kunya "........... Daga haka suka cigaba da hira yana sake tabbatar mata da ita ɗin tasa ce kuma ba mai rabasu sai ALLAH. Sun daɗe suna wayar kafin suyi sallama, juyawa yayi da niyyar ajje wayar akan bed ya wuce bathroom dan tashin sa kenan daga bacci ya kirata, text message ne ya shigo wayar tasa, dakatawa yayi tare da buɗewa, Address ne tare da time, Saida ya gama dubawa sannan ya rufe ya cilla wayar Kan gadon ya wuce bathroom ɗin. Tsawon minti 30 ya ɗauka kafin ya fito waist ɗinsa ɗaure da milk towel, caramel skin ɗin nan tasa sai wani glowing take ruwa na darewa kamar wani jikin kifi, gaban mirror ya tsaya Yana goge jikinsa, kusan minti goma sha biyar ya ɗauka yana shafe shafe kafin ya miqe ya Ƙarasa ya bude wardrobe ɗin ya ɗauko kayan da zaisa Wanda suke cikin ledansu alamun sabbi ne, Kan gadon ya cillasu su ma sannan ya rufe sip ɗin ya bi bayan su. Wata oversized t shirt ce white me karamin hannu tare da wani sky blue ripped jeans, safa ya saka tare da white canvas ya ɗauko white nautilus watch din sa na Company patek Philippe ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa sannan ya ɗauki wayarsa da keyn ɗakin ya fita. Sanyi ake tafkawa na bugawa a jarida dan kankara ce kawai take zuba ta ko wani angle, sai dai duk yawanci mutanen dake Kai kawo kananun Kaya ne a jikinsu hakan ya nuna sun saba da irin wannan yanayin garin, da ƙafarsa ya dinga takawa ba tare da ya tsaida abun hawa ba sai da yayi tafiyar kusan 15 minutes sannan ya tsaya a wani cafe shop, coffee da cookies kawai yayi order, ba jimawa aka kawo masa. Kaɗan kaɗan yake kurɓa kamar baya so yana kalle kallen yadda kowa ke harkar gaban sa can kuma ya jawo wayar sa ya shiga contact kamar zaiyi dialing contact ɗin Anah sai kuma ya fasa, WhatsApp ya shiga ya danna mata Kira saida ta kusan tsinkewa ta ɗauka, "Assalamu alaikum Anah". "Wa alaikum salam, Amjad ya kake?"...........Ta faɗa Muryarta a dake, take yasha jinin jikin sa jin yadda ta ambaci sunan sa kai tsaye da kuma yanayin Muryarta da yaji. Kwantar da murya yayi dan yasan laifin sa amma sai ya waske da faɗin, "Anah meke faruwa? Lpy dai?" ............."Bakomai. Me kaji?". "Anah Dan ALLAH"..........Shuru tayi, ya sake cewa, "kiyi hakuri to in na Miki laifi a rashin sani". "Ina ka shiga tsawon kwanakin nan ana ta neman ka, na kira su Aram sun shaida min rabon ka da gidan wurin kwana huɗu, haka mahaifin ka jikin sa ya motsa akai ta neman ka ba'a samu, tukunna ma ina kaje? Kana sane da cewa satin nan za'a shiga kotu da mutanan can"..........."Anah wanna shi ne kaɗai damuwar ki?". "Babban mutum bana so Ka ƙara shiga matsala, wadda kake ciki ma ina roqon ALLAH ya kawo mana mafita, duk da nasan baza ka aikata duk wa'annan abubuwan ba, amma na rasa Mesa hankali na ya ƙasa kwanciya, mutane sun sakoka gaba babban Mutum". Cikin son ƙarafafa ta yayi murmushi da faɗin, "Anah ɗanki fa jarumi ne in sha ALLAH ba abinda zai faru ki kwantar da hankalin ki, sannan kuma batun wannan kotun fa babu ita".........."Ya zakace babu ita". "Ba zan iya ce dake komai ba Anah amma dai nace Miki baza a zauna kotu a satin nan ba, sannan kuma batun In da nake na danyi wata ƴar tafiya ne amma ba nisa nayi ba, ai kinsan a yanzu bani da ikon barin ƙasa so naje KM ne nan da kwana biyu zan dawo, na takura ne da yawa Saisa na danje na sha iska". "Ah ah babban mutum karka yi sake, ka kula sosai tunda kaga har sun tunkari kotu da Batun ai kasan sun shirya hujjojin su ko da na ƙaryar ne saboda in basu da su abun zai dawo kansu ne, kotu ai ba wurin wasan yara bace. Bana goyon bayan ka gana da alkalin ko ka nuna sanayya ko dukiya, kawai dai inaso a bayyana gaskiya su kuma ko su waye ke da hannu a ciki a toni asirin su dan nasan tabbas sayansu akayi". "To Anah duk abinda kikace za'ayi, amma Anah meysa bazan auri yarinyar ba kawai, a gani na hakan shi zai rufe ƙofar duk wani cece kucen mutane". "Whattttttt Baka da hankali ne Amjad, me kake faɗa haka, karuwar da akayi haya ita da iyayen ta suka maka sharri ita kake so Ka aura anya baka fara shaye shaye ba kuwa". Dariya ya fashe da ita. "Sorry Anah da wasa nake fa, yi hakuri maida wukar"........... Ajiyar zuciya ta sauke Amma dukda haka hankalin ta bai kwanta ba, kafin tace wani Abu ya tare ta da faɗin, "Anah zamuyi magana anjima ki cewa Dada na ina gaishe shi, anjima zan Kira video call ki hadamu". "Allah ya kaimu, Ka Kula da kanka"............ Ta faɗa a hankali. Ko da ya kashe wayar tunanin maganar tasa ta shiga yi, tasan halin danta ciki da bai tunda har yayi wannan maganar to akwai wani abu a ƙasa, Ni kuwa nace Anah kin dai san wasu halayen sauran kuma baza aji mutuwar sarki a bakina ba. Wata number da akayi saving da Juraish ta kira, Anah ɗagawa ta ce, "Hello Juraish.........." ----------------------√ Sauri take ta zabgawa kasancewar yau sun makara shiyasa a maimakon su tsaya girka wani abu kawai ta fita siyo musu kosai, saidai me tana shiga gidan ta samesu sunyi cirko cirko, Sahnish ne tsaye da wasu manyan mutane su uku suna magana, ƙarasa shigowa tayi da sallama tana binsu da kallo kafin ta maida kallon ta ga Sahnish ɗin tare da tambayar, "Sahnish lpy dai? meke faruwa?". "Wai Malam Ado ne ya saida gidan nan, su kuma suna buqatar mu tashi daga yau zuwa gobe dan ya daɗe da saida musu duk zaman da muke ma a cikin notis (Notice) ɗin da suka bayar ne". Maida dubanta tayi Kan mutanen kana ta ce, "Malam baku san cewa ya karɓi kuɗin hayar mu bane?". Ɗaya daga cikin su ne ya ce, " Wannan mu ba damuwar mu bace tsakanin Ku ne dashi, mu abinda muka sani mun saya gida ya kuma karɓi kuɗin mu da shedu da komai, dan har munzo munga gidan ma yace da akwai mutane a ciki amma mu baku notice zuwa lokacin da kuɗin hayar ku zai ƙare, yanzu kuma lokaci yayi munga shiru, Alfarmar da zamu iya muku kawai daga yanzu ne zuwa dare, gobe da sassafe zamu zo karɓar makullin gidan mu".........Ba tace komai ba sai jijjiga Kai da take . Sahnish ne ya ce, "bakomai to, ALLAH ya Kai mu". "Ameen"............ suka amsa sannan suka juya suka fice. Miqawa Shazeen dake ɗaura igiyar takalmin ta ledar kosan tayi sannan ta ce. "Sahnish ina takardar da malam ado ya baka Lokaci da ka bashi kudin hayar?"..........."Tana ɗaki". "Dauko mun ita kayi sauri kuma"........."Me zakiyi da ita?". A fusace ta ce "Nace kaje ka ɗauko min Ka tsaya tambaya ta me zan yi da ita to haɗiye ta zanyi ko ma cinna mata wuta kaji". Bai Ƙara magana ba ya shiga ɗakin sa ya ɗauko mata, karɓa tayi ta wuce ɗakin su ta ɗauko handbag ɗinta ta nufi soron gidan tana faɗin, "Ga ƙosan nan wurin Shazeen in ta gama Ka miqata makaranta".........Kasa cewa komai yayi har ta fice. Bata tsaya ko ina ba sai gidan Malam ado, dutse ta ɗauka ta shiga buga ƙofar dashi, wata budurwar yarinya ce ta fito tana faɗin, "waye ne da sassafen nan ".........."Ubanki yana nan ?" Ta Tambaya a fusace. Kallon Sama da ƙasa ta Mata sannan ta ce, "Malama lpy?". "Yana nan ko baya nan?".........Ta sake maida Mata tambayar. "In yana nan uwarki zaki masa "........ Wani matsiyacin tsaki Taja sannan ta ce, "Eh ita zan masa, sallamo min Shi". Shuru tayi tana kallon ta, Hushaima na shirin sake magana ta juya ta shige cikin gidan, ba Jimawa suka fito yana gaba tana bayansa, yanayin tozali da Hushaima ya sha mur da fadin, "ke lpy zaki zo ki damu mutane da sassafe ". "Kai Asararren tsoho, macuci saurara kaji zuwa nayi Ka dawo mana da kuɗin hayar mu daka karɓa tunda Ka saida gidan". Wata matsiyaciyar dariya ya kwashe da ita. "Yarinya bari kiji ai ni kuɗi baya shigowa hannu na ya fita, kuma qanin ki ne ya tilasta min na karɓa, dan haka da ALLAH bar kofar gidan nan Kar nasa yarana su miki shegen duka". Murmushin gefen Baki tayi tare da juya kanta ta ce, " Ina cewa Ka dai karɓa kuɗin hayar?". "Na karba kuma naci banza, ba ubanda kika isa kiyi".........."Haka kace?" "Nace na Kara cewa ma kuwa "........... Ya ƙarashe Yana sake gyara tsayuwa, gyada kanta tayi sannan ta juya ta fara tafiya tana jinsa yana ta faman kuri cewa yaci banza tare da aibata su amma ko juyowa batayi ba ballatana ta san yanayi. Tana shan kwanar layin taji ana kwala mata Kira daga bayan ta, "baiwar ALLAH baiwar ALLAH"......... Tsayawa tayi tare da juyowa tana kallon mutumin dake Kiran nata dattijo ne amma irin wanda bariki tayi aman su ɗin nan ne dan kallo ɗaya zaka masa kasan ɗan tasha ne cikakke kuma an buga duniyanci, asuwakin dake bakin sa ya cire tare da tsiyayar ruwa a butar dake riqe a hannun sa ya kuskure bakin sannan ya ce, " Da farko ni sunana Junaidu amma anfi sani na da ilerika, matasa kuma na kirana da Baba ilerika, Dama cewa zanyi meya haɗaki da Malam ado ne tun daga farkon layi nake jin yadda yake ɗaga miki murya". Saida ta gama Ƙare masa kallo tsab sannan ta ce, "Muna haya ne a gidan sa, ya karɓi kuɗin mu kuma ashe ya daɗe da saida gidan har ma notis ɗin da masu gidan suka bayar ya ƙare, sunzo sun bamu iya yau kawai gobe zasu zo su karɓa makullin gidan su, kuma nazo nace ya dawo mana da kuɗin mu yace yaci banza". " Tirkashi, indai Malam ado ne zaiyi fiye da haka, cikakken ɗan 419 ne ai, yanzu wani mataki kika dauka?".........."Ka sanshi ne?" "Farin sani ma kuwa, abokina ne ada kafin tamu ta hadomu muka raba gari, yanzu ke ya zakiyi kin samu gidan ne". "Ai bazan yadda ba ƙara zan kaishi ko zan tashi sai ya biyani kuɗi na". "Yauwa yar albarka hakan shi ne daidai ni zan ma yi Miki shaida in kina so". "Nagode".......... ta faɗa tana cigaba da tafiya , saurin shan gaban ta yayi, "Ya zaki tafi bamu gama magana ba ai, akwai ɗakin haya idan kina buqata a cikin gida na ne ba a wani wuri ba". Ɗan Jim tayi kafin ta ce, "Bani kaɗai bace mu uku ne saidai idan zaka iya samo min gida me ɗaki biyu". Washe Baki yayi da faɗin , "Ai indai baza ki damu ba a gidan nawa ma zaki samu ɗaki biyu kuma babu takura, kowani ɗaki dubu 35 ne harda bayi a ciki". Shuru tayi kafin ta ce, " Zanyi shawara da qanina tukunna". "To ba laifi, bani lambar telephone dinki"........Karanto masa tayi ya saka sannan ya kirata tayi saving nasa. "To zan saurari kiranki ba"........ Gyada masa Kai tayi alamar to sannan ta koma gida. A Buɗe ta samu Ƙofar gidan tana sa kai Amla na ƙoƙarin fitowa hakan yasa sukayi Karo, baya kowaccen su ta ja, "Haa basu tafi makarantar bane ko kuma ya dawo?"............"Su waye kuma ?" Amla ta tambaya tana kallon ta. "Su Sahnish mana". "To ai Nima nayi mamakin ganin gidan a buɗe na ɗauka kuna ciki na shiga kuma naga ba kowa, dama na fito ne zani wani wuri na biyo na karɓi form ɗin nan, Amma meke faruwa na ganki kamar a birkice". "Bakomai whl ina sauri ne kawai muje na baki Kar na ɓata miki lokaci "...........Ciki suka koma ta shiga ta dauko Mata form ɗin ta dawo, riqo hannunta tayi cikin nata kana tace, "Amla ke kin wuce ƙawa a wurina kin zama yar uwa, ina godia ga dukkan alheran ki garemu bakiɗaya, Dan ALLAH ki cike takardar nan da sunan Sahnish, ina fatan hakan be ɓata Miki rai ba". Shuru Amla tayi tana kallon ta kafin tayi Murmushi da faɗin, "Ko ɗaya whl raina bai ɓaci ba sai ma jin dadi da nayi, kawai takaicin na da ban karɓo guda biyu ba bansan haka bane ai". "ALLAH ne bai qaddara Miki asara ba Amla, Dan ni abinda ya shafi karatun ne gabaɗaya bana so domin bashi da amfani a wuri na". Buɗe baki Amla tayi zatayi magana tayi saurin girgiza Mata Kai , "Dan ALLAH Kar muyi haka dake, bana son ki tambayeni abinda bani da amsar sa, kiyi hakuri". "Shikenan Hushaima tunda hakan kike so, wani surname da other name zan sa tunda naga ko waiwayar Form ɗin ma bakuyi ba". "Duk abinda kika sa".........." Ina nufi sunan mahaifi da kaka fa?". Amla ta sake tambaya tana kallon ta, Shuru Hushaima tayi tana kallon wani gefe can kuma ta ce, "SAHNISH HUSHAIMA SHAZEEN". Cikin rashin fahimta Amla ta ce, "Bangane Sahnish Hushaima Shazeen ba, sunan uba da kaka fa nace Miki ko kin kurmance ne"........... Ta ƙarashe tana aika mata da hararar wasa. Ba tare data kalle ta ba ta ce, "Bashi da sunan da ya wuce wannan, in kuma wani daban kike nema to saidai fa a hakura"........Tana kaiwa nan ta shige ɗaki ba tare data bari sun haɗa ido ba. Saqale Amla tayi da takarda a hannu tana maimaita sunayen da Hushaiman ta fada Mata kamar me hadda har Sahnish ya shigo kamar wanda aka koro turus yayi ganin Amla, ƙaƙalo murmushin dole yayi da faɗin, "Amla ina kwana?" "Ina kwanan mu Sahnish".......... Ta faɗa tana ɗan kawar da mamakin dake kan fuskarta. "Ta dawo ne?" "Eh ta dawo, gwara ma da ALLAH ya kawoka zancen form ɗin nan ne tace a cike ma shi to Amma bansan sunan da zanyi amfani dashi ba wurin baba da Kaka". "Kai Hushaima akwai kafiya har Yanzun dai ta kafe sai ni ɗin kenan"......... Ya Ƙarashe Yana nufar ɗakin nata saidai kafin ya Kai ga shiga Amla ta dakatar dashi, "karka damu Sahnish hakan ba damuwa bane Kai dai fadamin sunan kawai, ina so in tafi saboda ina da wani uzuri ne". "SAHNISH HUSHAIMA SHAZEEN". "Kuma?"..........Ta faɗa cikin daurewa Kai, kallon ta yayi da tambayar, "Wani Abun ne?". Saurin girgiza kai tayi, "Ah ah ba komai bari naje ɗin, kace Mata na tafi sai munyi waya"........ Ta Kai Ƙarshe tana nufar ƙofar gidan. Binta yayi da kallo ko zai gano dalilin canzawar yanayin fuskar ta amma ya gagara, can kuma ya taɓe baki tare da dage kafaɗun sa ya shige ɗakin Hushaiman Yana Kiran sunan ta. A tsaye ya sameta ta bawa ƙofar baya tana jin shigowar sa ta juyo tare da faɗin, " yauwa ungo, ga wannan kuma"........ta miqa masa takardar da ya bata ta shaidar biyan kuɗin hayar tare da dubu ɗaya. "Kaje Ka bayar a maka irin wanna rubutun, a wajen kudin asa dubu ɗari maimakon sittin ɗin nan"........."Me zaayi wai?" "Da hausa fa nake ma magana"........."Eh naji ai me sa zaayi hakan." "Zaka sani daga baya, sannan mun samu wasu ɗakunan haya guda biyu Amma ba gida guda bane, to nacewa mutumin sai nayi shawara tukunna". "In dai ke baza ki takura ba sai a kama ɗin, ni bani da matsala, saboda kinga bamu da lokaci daga yanzu zuwa dare ne, Amma kuma kinsan bamu da kuɗi isasshe a hannun mu ko?". "Kai dai yanzu kayi sauri kaje a maka irin rubutun yanzu Ka kawo min ina jiran Ka".........a aljihu ya saka sannan ya juya ya fita . 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______16 & 17 "Barka da rana Anah". "Yauwa juraish, yakeka ya gidan?"..........." Lpy kalau Alhamdulillah Anah ya jikin Dada?". "Da sauki Alhamdulillah, da ALLAH tambaya nakeso na ma"............Sake nutsuwa yayi tare da bata dukkan hankalinsa ya ce, "To Anah ALLAH yasa na sani". "Baka da wani labari game da abinda dan uwanka yake shiryawa kuwa?"............ Dan gajeren Murmushi yayi kafin ya ce, "Anah Whl Amjad ko ruhin dake jikinsa bai isa yace ga next target ɗin sa ba balle ni, nasani duk a family ni da shi munfi kusa amma ni ma Akwai limit ɗi na dan kwata kwata bai bani irin damar da zan shiga jikinsa ba ballatana nasan duk wani moves nasa, infact ni a fahimta ta mutum ne shi da a zuciyar sa kawai yake ayyanah Abu sai dai ya aiwatar dashi, bashi da alqibla ko ada bare a yanzu da abubuwa suka tabalbale sosai, kwata kwata bashi da abokin shawara. Amma me ya faru ne?". Zazzafan numfashi ta furzar kafin ta ce, " Batun yarinyar nan ne da iyayen ta, ɗazu nayi waya dashi ina faɗa masa zancen shiga kotun nan kasan ya tafi KM to shi ne yake ce min wai baza ayi zaman kotu a satin nan ba, ni abun ya ɗaure min Kai". Dan shuru yayi kafin, "Gsky bani da wani labari game da wanna"............"To da ALLAH inaso Ka sa a min bincike akan hakan". "Shikenan Anah, in sha ALLAH za'ayi". "Nagode juraysh ALLAH yayi albarka, Ka gaida min da Aunty batoola". "Zataji in sha ALLAH".........Daga haka suka yanke wayar. Kallon Adla da suka shigo ita da Esham tayi, ganin su cikin shiri ya sata faɗin, "ina zuwa haka?". "Zamu Ɗan je shopping ne daga nan zamu biya gidan Durrah tun shekaran jiya take cewa tana son gani na". "Shikenan kuje karku daɗe Ku Kula, amma wa zai kaiku?". Dan shuru tayi kafin ta ce, "Ni zan ja mu mana Anah........" "Kanki yana rawa ko Adla, ki wuce kuje amma su dabee su rakaku". "To "......... tace sannan suka Mata sallama suka fita. -----------------------√ Wurin Juma me kanti yaje, shago ne dake gaban layin su kaɗan yawanci ma duk abubuwan da zasu saya a wurin sa suke saye, Dalilin da yasa kuwa ya kai masa shi ne juma yayi karatu har matakin HND dan sau da yawa su kanyi hirar da Sahnish ɗin Saisa ma yanzu baiyi tunanin kowa ba saishi. Ganin da mutane a shagon ya sashi ɗan tsayawa har saida ya gama sallamar kowa sannan ya ce, "Malam juma dan ALLAH so nake Ka taimaka kayi min irin wanna rubutun". "Tooh Malam Sahnish wani irin rubutu ne da zai gagare Ka ni kuma na iya"..........Dariya kawai Sahnish yayi ya miqa masa, saida ya duba sannan ya ɗago tare da faɗin, "yanzu komai irin wanna za'ayi?". "Eh kawai kuɗin zaka Ƙara nan dubu ɗari zaka sa "............Shuru Malam juma yayi kafin ya ɗauko biro da takarda ya fara rubutun, miqa masa yayi bayan ya gama . "Kai amma nagode sosai Malam juma ". "Bakomai Sahnish fatana dai ALLAH yasa ba rigima bane". "Kai ma kasan bazan saka a rigima ba ai, bari naje, ina sauri ne"............Ya Kai ƙarshe yana sa Kai ya fice daga shagon, gida ya koma inda ya sameta a tsakar gidan tana jiran sa, tana ganin sa ta ce, " Juya muje". Kallon mamaki ya bita dashi kafin ya ce , "ina kuma?". "Okay so kake in barka Ka zauna Ka huta ni kuma ina titi ina neman yadda zanyi ko? tsakanin ni da Kai wa ya kamata yayi wanna abun da nakeyi? amma Kai Ka zama macen ni na zama namijin ko" .............. Yadda ta hayyaƙo take masifa yasa Sahnish ce wa , "ALLAH ya Baki hakuri muje"........ Saboda sanin halin yadda ya ganta a tunzure ɗin nan tana hayaqi kaɗan take jira ta kama da wuta. Tare suka fita suka kulle gidan, Shi dai binta yake kawai kamar wani yaronta, Sahnish irin mazan nan ne masu sanyi sosai kafin kaga zafin sa a daɗe. Abun hawa ta tsare musu tare da faɗin inda zai kaita, a ƙofar police station ya sauke su, tana sauka ta ciro kuɗin sa ta bashi ko tsayawa ciniki batayi ba ta wuce ciki . Da corpor Hambali suka fara haɗuwa cikin wasa da dariya suka gaisa shi dai Sahnish Yana rakuɓe a bayanta kamar wani marayan ɗan tsako, kallon ikon ALLAH kawai yake dan shi ko hanyar police station ɗin ma bai sani ba bare kuma cikinta. "Amm Sergeant Ubayd fa ?" "Kai anya Sergent Ubayd ya shigo yau kuwa, amma lpy dai ko?". Gyara tsayuwa tayi da faɗin, "Ai idan aka ga gemun kaza, an ga ranta. Ba lpy ba, wani ne muke haya a gidansa............." Zayyane masa komai tayi ta rufe da fadin, "ya kuma ce duk abinda zanyi nayi kuɗi ya cinye". "Kai Kai ashsha wanna mutum bai kyauta ba, yanzu ina receipt na shaidar kun bashi kuɗi ko wani shaida na zahiri ma'ana mutum". "Ga dai takardar da yake bamu nan, kuma ga qani na nan shi ya bashi kuɗin da hannun sa"......... Ta Ƙarashe tana miqa masa. Karɓa yayi Yana faɗin, "Eh ga takarda Kam, Amma kuma ɗan uwanki bai isa yayi shaidar ki ba, ba wani a wurin lokacin da aka bashi kuɗin, dan wannan ma takarda ce kawai ba receipt ba".......kai tsaye ta ce, "Ita dai wannan takardar ita yake bamu tun asali ma, sannan kuma akwai wani abokin sa ma da suka zo tare a lokacin da zai ƙarɓi kuɗin"............ Ta faɗa without second thought. "Yanzu dai me kike so ? Saboda akwai hurumin da yake namu akwai kuma Wanda dole saidai rent tribunal". "Ni kawai ya dawo mana da kuɗin mu, mu kama wani mu basu gidan su tunda su sunce da safe suke son makullin, kuma baza su iya Ƙara notice ba saboda sun daɗe da biya ". "Shikenan, yanzu kinsan inda zamu samu shi abokin nasa ?". "Inama da number sa ai sai a kirashi yazo". "Okay ki kirashi, bismillah ga waje Ku zauna".......... Ya faɗa yana nuna musu bencin dake ciki. Wucewa tayi ta zauna shi dai Sahnish yana daga Bakin Kantar a tsaye . Kira ɗaya tayiwa Baba ilerika ya ɗaga, " Hello". "Yauwa hello"..........."Ina magana ne da Baba ilerika?" . Ta tambaya domin tabbatarwa. "Ni ne mana hajiya, harkun yanke shawarar ne?". "Kazo police station ta gangare Kan batun Malam ado"........... Bai ma Bari ta ƙarasa ba ya ce, " Au to to, ta tashi kenan, to gani nan zuwa yanzu kuwa"............Kashe wayar tayi sannan ta shaida musu Yana zuwa, ba'a dade ba kuwa sai gashi Mai tuk tuk ya sauke shi, shigowa yayi Yana washe baki kamar gonar auduga kaucewa Sahnish yayi ya bashi hanya. "Assalaaaaamu alaikum"............. Ya rangaɗa wata sallama kamar yan kawo amarya sun kawota gidanta. "Wa alaikum salam"............ Corpor Hambali ya amsa . "Barkan Ku dai, ya aikin?".........Tasowa Hushaima tayi da faɗin, " yauwa gashi nan ma ya karaso". "Kai ne abokin Wanda suke haya a gidan sa ?". "Eh ni ne yallabai amma ALLAH yasa dai ba kuɗin wani ya sake ci ba aka kulle shi, dan ni whl na gaji da zuwa bailin Malam ado a rayuwata gsky ranka ya dade, ku kaishi kotu kawai nifa aminin sa ne ba uwa ko uba muka haɗa ba, ai ni da nasan ma wata rigimar ya tsokano ba zanzo ba". "Bata gaya ma dalilin kiran naka bane?"..........." Ah ah ranka ya daɗe kawai tace nazo police station ta gangare Kan Maganar malam ado, to Bansan wannan maganar bace ai". Daga Hushaima, Sahnish harsu corpor kowa da mamakin da yake. Hushaima mamakin ta bai wuce na yadda Baba ilerika ya ƙware wurin iya shirya makirci ba, shi kuma Sahnish mamakin sa na shirin da Baba ilerika da Hushaima sukayi ne domin shi tunanin sa Hushaima ta shiryawa Baba ilerika wanna abun, su kuma Yan sanda mamakin su na Malam ado ne kenan dama an shaide shi ɗan rigima ne kuma ya saba taro rikici tunda gashi har aminin sa yace ya gaji da zuwa bailin sa. Katseshi Corpor hambali yayi da faɗin, "kanaji duk ba wannan bane "...........Abinda Hushaima ta faɗa masa ya kwashe ya zayyane masa sannan ya karashe da tambayar, "hakane?" "Kwarai da aniya ranka ya daɗe a gabana suka bashi kuɗi akayi rubutu ya basu takarda ". "Shikenan yanzu Kai zakazo muje azo dashi ke kuma Hushaima Ku zauna Ku jiramu dasu corpor babba, wanna ai kince qanin ki ne ko?"........."Eh ranka ya dade". "Kuma kikace shi ya bada kuɗin da hannun sa?" Ya sake tambaya. "Eh ". ta amsa . "To zamuje tare dashi mu taho da shi Malam ado ɗin yanzu "............. Ya faɗa Yana wuce wa wani office Jim kaɗan ya fito suka tafi, Shi da Baba ilerika da Sahnish sai kuma wani dan sandan da yake sanye da fararen kaya, ya tukasu a motar police ɗin suka tafi. Ko da sukaje gidan Malam Ado basu sameshi ba ganin zasu ɓata lokaci suka bar sallahu sun juyo zasu taho Kenan sai gashi, tsayawa yayi ganin motar yan sanda a ƙofar gidan sa, "Officer lpy?". "Lpy ce ta kawo mu zamu je dakai ofishin mu ne ka ɗan amsa mana wasu tambayoyi". "Ah ah officer kaga ni ba wani amsar dana sani bare har a tambayeni, meye ma zai haɗani da bayanin da zai kaini har offishin ku". "Karka damu ba jimawa zakayi ba yanzu zaka dawo". "Ni Wai m......" Maganar sa ce ta maqale sakamakon idon sa da ya sauka akan Sahnish da baba ilerika. "Au thooo kune, to Kai Kuma a wa?"......... Ya faɗa Yana nuna baba ilerika da hannu. "Kaga malam ba hayaniya muka zo yi ba, kazo muje kana bata mana lokaci".......... Ƙwafa yaja ya shige suka tisashi a gaba har mota saida ya shiga sannan suma suka akaja suka wuce . Har suka ƙarasa banda jan kwafa Babu abinda malam ado yake, bayan anyi parking suka firfito suka shige ciki, anan kan bencin dake bayan kantar suka zazzauna Corpor hambali ya koro jawabi sannan ya ida da tambayar, " Haka akayi?" "Hakane Amma su suka matsa sai na karɓa, na riga na faɗa musu saida gida na zanyi su tashi suka nace kamar da kuɗin ubansu na gina gidan". "To ai da sai ka bar mana kuɗin mu nemi wani ko, kuma saika karɓe? sannan ai baka ce mana a notis muke zaune ba cewa kayi zaka saida". "Wancan shi yaga dama ya baku amma ni kuma dole na karɓa kuɗin kwanakin da kuka ƙara, yoo in banda ma cuta irin ta yahudu taya mutum zai saya gida ace sai an bada wani notis ai duk kwanan da mutum zai ƙara karɓi kuɗi kawai. Ku wai baku ma da dangi ne ko daga sama kuka faɗo in ma baku da iyaye......." Tare shi tayi da faɗin, "Um um malam Ado kaga karkayi kuskuren shiga hurumin da ba naka ba, bar ganin ka haka whl Ina iya fidda hannu na sharara ma mari billahillazi"........... Ta ƙarashe tana miqewa daga zaunen da take. "Ni zaki mara ? Ranka ya dade Kuna dai ji ". "Kai zan mara ɗin, kafi ƙarfin a mare kan ne tsohon banza kawai"..........Sahnish ne ya riqo hannunta yayin da corpor ya ce, "Kunga duk ku tsaya sulhu ne ya zaunar damu anan ba wai tashin hankali ba, Kai malam ado yanzu sun ce ka biyasu kuɗin su, su tashi su bawa masu gida gidan su gobe da safe". "Ai kuwa bani da ko asin da zan iya biya saidai su nemi wani wuri su fake in na haɗa kuɗin na basu, Kuma ma ai sai ayi lissafin kwanakin da sukayi a gidan dan ni ban yarda da wani notis ba yauwa". Cikin ɗaga murya Hushaima ta ce, "ka ma Isa, ka Isa? whl tlh billahillazi huwar rahmanu baka motsawa ko Ina in baka fito da kuɗin nan ba, kuma Naira biyar bata ciwon kai a ciki tasss zaka dawo dasu yadda aka baka, notis kuma wannan ba da mu zakayi ba, hukumar data Shar'an ta notis ɗin zakaje ka ƙalubalanta ". "To sai ki ɗauki Babu tunda ana haifo abinda Babu shi". "Ranka ya daɗe nazo nan ne saboda a ƙwatar mana hakkin mu dan haka ku sashi ya fitomin da kuɗi na dubu ɗari cifff ko Naira ɗari ce bata cika ba whl ba ina zaije". Wata bahaguwar juyowa malam Ado yayi, "dubu me banji sosai ba, dan sake faɗa?". "Ka jini Sarai ai, bani Kuma Kara maimaitawa". "Wa kika bawa dubu ɗarin tukunna, ai ni ainahi ma abinda kike biyan gidan dubu sittin ne". "Eh Amma wanna shekarar ai da muka samu matsala kace sai an Ƙara ma muka Ƙara ma Kuma yanzu zaka ce baka san zance ba". Corpor hambali ne ya ce, " A jikin takardar shaidar biyan dubu ɗari ne ga Kuma abokinka da suka bayar a gaɓansa, " Malam nawa ta bashi?"........... Ya ƙarashe yana duban Baba ilerika. "Dubu ɗari ta bashi sannan ta bani la'adar dubu goma". "To Kai kaji". "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, dama nasan za'a rina tunda aka dauyko wanna tsohon najadun tsohon ala tsi alatsitsi ala tsine". "Ka dinga sa minjaye malam ado tsoffin najadu dai, Kai ma ai ba tsohon arzikin bane, wace miyar ce ba'a sha dakai ba". "Kai Kai ka kiyayeni fa yasin Ina iya sauke ma hakwaran da suka rage ma a duniya". "Shege ka fasa"........... Baba ilerika ya faɗa yana murmushin mugunta. Tsawa Corpor ya musu ganin baza su saurara ta lumana ba. "kukace faɗa zaku mana anan Ina iya saka ku a cell na rufe whl. Kai kuma ka biyata kuɗin ta kawai a wuce wurin". "Nifa Ranka ya daɗe nace ma kuɗin nan bani dasu, a caje ni in karya nayi". "Ranka ya daɗe nafa riga nayi rantsuwa".......... Hushaima ta faɗa tana wani ƙanƙance firgitattun idanun nan nata sannan ta waro su lokaci guda wanda hakan ya ƙara mata wani sirritaccen kyawu. "Ai ko aradu kika haɗiya saikin saurara whl t.....".......... Kafin ya Kai zancen da yake son faɗa kawai yaga tayi caraf ta zare wayarsa dake gaban aljihun rigar sa . "Kam bura uba"......... Ya faɗa Yana miqewa . "Ku saurara mana haba". "Ranka ya daɗe zamuje wurin saida waya da wani anan wajen, in mun saida zan ɗauki kuɗi na abinda yayi ragowa na bayar a kawo masa"..........ta faɗa saboda tasan ko banza wayar tasa tafi ƙarfin dubu ɗari. "Ki fa bani waya ta, Ranka ya daɗe Ina akeyin haka?". "Wanna shi ne abinda zamu iyayi in kana da kuɗin ta ka bata in Kuma babu aje a saida a kawo ma ragowar ". "Naji ta bani wayata zan biya". "Au ashe dai ta tabbata cutar daka saba yiwa mutane kake so ka gwada a kansu"............"Ba ruwanka dani ilerika, karka kuskura ka shiga sabgata na gayama"...........Malam Ado ya faɗa a fusace. "Ya isa haka, Kai ka gama naka kana iya tafiya ma"..........Corpor ya faɗa yana nuna Baba ilerika. "To ranka ya dade nagode"......... Baba ilerika ya faɗa Yana tashi ya fita. "Ina kudin yake yanzu?".........."Saidai muje ATM ko wurin me pos a zara amma fa ni dubu sittin na sani". "Bafa batun dubun sittin malam kuɗin su dubu ɗari ne ga dukkan shaidu sun shaida in Kuma kace dubu sittin ne Kai ka kawo taka shaidar".........Shuru yayi tare da jijjiga kansa yaja Ƙwafa, "Shikenan muje bakomai". Haka suka fita gabaɗayansu harda Corpor Hambali sukaje ya cira dubu ɗarin ya miqa musu sannan ta bashi wayar sa ya tafi. Dubu goma ta fitar a ciki ta ce, " Ranka ya daɗe ga wanna Kai ma ka Sha ruwa". Ita kuwa Hushaima ba komai ya sata ƙara dubu arba'in ɗin nan ba akai saidan cin mutuncin da Malam ado ya dinga musu tare da nuna ita ɗin bata isa yin komai ba, da kuma rashin sanar dasu ya sayar da gida da baiyi ba kuma ya karɓi kuɗin su. WANNAN KENAN. "Ai dama kin barshi, wanna ai aikin mu ne , kuma kina daga cikin wadda hukuma ke alfahri da ita duk abinda zakiyi bakya daukan doka a hannun ki"......... Ya Kai ƙarshe yana tura dubu goman sa a aljihu. "To Ranka ya dade nagode sosai".........."Zaku wuce ne ko Kuma a rage muku hanya". "Ah ah karka damu zamu samu abun hawa ".......... Daga haka sukayi sallama sannan suka bar wurin ita da Sahnish, "Sahnish inaga mu wuce ɗauko Shazeen kawai nasan kafin mu ƙarasa Sha biyu tayi, bana son su fara sallah a rufe hanya". "Duk wanna Abun da ake yanzu ki samu ki saya wani abu kici tun safe ko ruwan shayi baki kurɓa ba fa". "Kai kake ta wani ruwan shayi Sahnish idan ka ce zaka zauna Kuma zaka nuna sanyin jiki whl wulakanta zakayi a rayuwa, saboda ita rayuwa kamar caca ce babbar riba tana zuwa da babbar kasada ne iya ribarka iya kasadar ka, ko zaka mutu kayi kokarin ganin baka wulakanta ba Ina Ƙara jaddada ma, baka buqatar wani ya tsaya ma domin kare mutuncin kanka. "............ Shi dai Sahnish Bai Ƙara cewa komai ba sai maganganun ta dake Kai kawo a cikin kansa da Kuma tunanin yadda suke rayuwa tsawon lokacin da Hushaima takai tana sacrificing abubuwa da dama saboda shi da Shazeen. Har suka tare tuktuk suka hau tunane tunanen da yake kenan. Basu sallami me tuktuk ɗin ba dan already an tashi su Shazeen ɗin lokacin da suka ƙarasa makarantar dan haka ɗaukota kawai Hushaima ta sauka tayi suka juyo. Sai a lokacin ta ɗauko wayarta ta Kira Ilerika bayan ya ɗaga ta ce, "A ina zamu haɗu ne ALLAH yasa bakayi nisa ba?"..........."Eh yanzu dai na fito zan fita". "To in ba damuwa ka jiramu kan titin yellow chain". "To ba matsala hanya ta ce ai"........Daga haka sukayi sallama. Suna sauka a bakin titin kuwa ta hango shi tsaye Yana busa sigarin sa, "Riqe hannun Shazeen ku wuce gida Sahnish, bari naje na ji yadda za'a yi". "Ah ah mu dai jiraki anan ɗin Amma ki kula daga ganin mutumin can tsohon Dan duniya ne Kuma kinsan yan bariki basu da amana ". Wani silent smile tayi da fadin, "Kai ma kayi wanna tunanin Sahnish bare kuma ni". "To ni din me kika maidani?"............Bata bashi amsa ba ta wuce , ganin ta yasa ya fara ƙoƙarin kashewa ta katseshi, "Karka takura kanka baba ilerika ni bani da matsala ai. Zancen ɗakunan hayar daka faɗamin ne yasa na neme ka"..........Washe baki yayi, "tou tou Ina sauraren ki kuɗin sun samu kenan? yanzu zuwa zamuyi kiga ɗakunan ko Yaya?"........... Ya tambaya a jere. "Ah ah ba sai naje ba ai nasan baza ka tallata min Abun banza ba, yanzu zaka ban lambar Acc ɗin ka sai a tura ma kuɗin". "Too Amma da cash ne da sai yafi sauki fa"........"ai bani da cash ɗin ne amma kana bani za'a tura ma yanzu". "To ba damuwa "...........Ya faɗa soke sigarin tasa a gefen baki ya sanya hannu ya ɗauko wayar tasa ya tura mata. Duba wayarta da tayi ƙara alamar shigowar saqo tayi tare da faɗin, "In an tura zan kiraka in faɗa ma". "To in kin tura ɗin a ina zamu haɗu na baki makullin". "Ah ah kaje ka sa a share a wanke, in an gama saika Kira ka fadamin kawai, yanzu ga wanna".......... Ta ƙarashe tana zaro kuɗi daga jakarta ta miqa masa, karɓa yayi tare da karkacewa aka wani ɗage kai sama ana irgawa. "Goma cirr"..........."Ka Sha ruwa da ita". "Yiii huuuu sai da ni, au ya hakuri na shaafa, godia nake irin albarka, kina turowa za'aje a fara aiki". "Ba damuwa sai ka jini "............ta faɗa tana juya dan komawa inda su Sahnish ke jiranta. "Me ya faru ?"........... Sahnish ya tambaya tana kallon yanayin fuskarta da ya canza Lokaci guda. "Bakomai, ungo wanna kaje wurin me pos ka bashi ya turawa mutumin can kuɗin hayarsa ka karbo takardar shaidar turin"............ Ta ƙarashe tana miqa masa kuɗin hayar ɗakunan data ware tun a tuktuk. "Yanzu maimakon ki bashi kawai ga kuɗin a hannun ki, kuma sai anyi wata wahalar zuwa wurin me pos"..........wani kallo tai masa kafin ta ce, "Kaga irin wayon naka da in anyi magana kake faɗa ko, kawai sai naje na bashi kuɗi bani da wata shaida? ai mu dashi yanzu kar ta san Kar ne ko daga abinda ya faru a police station ma". "To shi kuma Kuɗin da naga kin bashi fa ?"........."Wanda zai Sha ruwa"..........."Meysa to?". "Zai mana amfani"........ta faɗa tana maida wayarta jaka bayan ta tura masa Acc number ɗin Baba ilerika taja hannun Shazeen suka wuce shi Kuma ya wuce shagon Juma don zuwa turawa Baba ilerika kuɗin hayar. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______18 & 19 Ƙarfe biyu daidai ya tashi daga gaban system ɗin sa, daga shi sai short nicker, zuge curtain ɗin yayi glass wall din ya Bayyana wanda hakan ya bashi daman ƙarewa ko Ina kallo garin yayi shuru sosai baka jin motsin komai sai ƙaran kukan wolf daga nesa kaɗan kaɗan, maida curtain ɗin yayi ya rufe tare da yin miqa ya koma gaban system ɗin ya kashe, sannan ya wuce gaban wardrobe ɗin ya ɗauko kayan da zaisa, tsabar yauqi irin nasa saida yaja 30 minutes kafin ya gama shiryawa cikin Biker jeans dark brown tare da t shirt dark brown sannan ya ɗaura light brown trench coat, ƙafarsa sanye da Boot shi ma dark brown. wucewa yayi zuwa wurin bedside drawer ya buɗe ya zaro wata ƙaramar bottle kamar ta Syrup, buɗewa yayi tare da ɗage kansa ya kurɓe shi duka sannan ya cilla kwalbar cikin dust Bin, Jim yayi a tsaye na tsawon 4 minutes sannan ya wuce kan gadon ya ɗauki neck gaiter ya sa sannan ya daura fedoras a kansa, bug ya ɗauka ya maqala a kunnuwansa, wani file dake kan mirrorn sa ya wuce ya ɗauka ya sanya cikin trench coat din sannan ya fita ya kullo ƙofar ya sanya key a aljihun sa. Tafiya yake yana waiwaye wanda hakan yasa kallo ɗaya zaka masa kasan bashi da gaskiya, wata kwana ya yanka wadda tayi daidai da connecting ɗin bug ɗin kunnen nasa, dafe kunnen yayi yana sauraran maganar da ake masa ta ciki, duk kwana da zai shiga in yazo sai a faɗa masa, yana zuwa kan wani layi muryar dake fita ta ciki ta fara rawa, sake dafe kunnen yayi saidai baikai ga jin komai ba ya yi disconnecting gabaɗaya. "Sh**t "........... Ya furta yana datse haƙwaransa tare da jujjuyawa yana bin layin da kallo, shuru yayi na wasu second sai Kuma ya ɗaga Kai ya kalli wani gida duk da a duhu ne amma yana iya hango mutanen dake tsaye suna shanya a balcony ɗin kasancewar ba ƙofa sai stairs kawai shi ma kamar na kasa ce, matakalar ya bi har ya hau wurin su, yana shirin yin magana, ɗayan cikin su ya garo bucket gabansa wanda ya gangara har ƙasan stairs ɗin ta other side, wurin yabi da kallo juyowar da zaiyi ba mutanan, da sauri yabi stairs ɗin yana kalle kalle, haka ya cigaba da tafiya ba tare da yasan inda hanyar zata kaishi ba amma kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar ba wata damuwa a tare dashi saboda tafiya yake cike da nutsuwa kamar ko yaushe. A gaban wasu mutanen ya bayyana su huɗu ne kan kujera suna shan shisha, ɗaya daga cikin su ne ya taso yana faɗin. " Sai yanzu kake zuwa?". Saida ya kalla sauran ukun da suke harkar gaban su kafin ya ce, "Duba agogon hannun ka"............"3am ne yanzu".........Ya amsa . "Shi ne time ɗin da aka bani. Waye wanda zan gani?"........... Ya tambaya yana kare masa kallo cikin dan hasken dake wurin. Juyawa yayi wurin sauran da faɗin, "Jam ga baqon fa ya ƙaraso".......... Tashi jam yayi yana faɗin, " Ina zuwa". Shigewa yayi gaba sannan wanda ya fara tarar Amjad yabi bayansa, shi ma Amjad ɗin ya rufa musu baya, gaban wata ƙatuwar ƙofa suka tsaya makulli Jam ya ciro daga aljihun sa tare da buɗe ƙaton ƙwadon dake jikin ƙofar, wani babban falo ne ya bayyana a gabansu tafiya suka cigaba dayi har sai da suka ƙure ƙarshen falon, hannunsa ya ɗaura akai tare da faɗin, "Gamu munzo!"........wata murya ce da basu san daga inda ta fito ba ta ce, "Na ganku ai". Tiles ɗin dake gabansu ne ya fara buɗewa slowly, wasu stairs zuwa ƙasa ne ya bayyana a gaban su. ( aiki ja, Mamaki ne ya sake kasheni, saboda daga waje in kaga gidan baza ka taɓa tunanin zai dauki wanna Wuraren ba, dan kallo ɗaya zakayi masa kace in akayi wata iska me ƙarfi tsab zatayi gaba da gidan). Shiga yayi suka bishi a baya suna gama shiga tiles ɗin ya koma ya rufe wani shiryayyen falo ne cike da mata da maza kamar wani ƙaramin club, wani slow music ne ke tashi speakers kawai kakeji suna dukan kiɗa, wasu na rawa, wasu na zaune kujerun dake cikin falon suna hira haɗe da ciye ciye, wasu Kuma suna yan kurɓe kurɓen su, hayaqi ne kawai ke tashi sai ka zata wani abun ake babbakawa. Dakatar dasu wani mutum yayi, baka ganin komai nasa sai idanunsa kawai Kai kace irin ninja ɗin nan ne. Wanda ya fara tarar Amjad ne ya ce, "Wurin BB LALO"........... baice komai ba ya wuce can ciki wurin wata doguwar kujera wanda wani mutum ke zaune ya ware hannuwansa kan headrest ɗin kujerar, ƙafarsa ɗaya Kan ɗaya, hannun sa riqe da tumbler na wine, gefen sa wata mace ce sanye da yar ƙaramar riga da wando Wanda dasu da babu duk ɗaya, ta ɗaya gefen ya matsa tare da raɗa masa wani abu a kunne, da hannu ya masa alama da yaje ya shigo dasu. Zuwa yayi ya faɗa musu su ƙaraso sannan ya shige gaba suka bi bayansa zuwa wurin BB LALOn, Sai da ya Ƙare masa kallo sannan ya masa nuni da wurin zama da hannu, tare da duban matar dake gefensa tun kafin ma yayi magana ta miqe tabar wurin, zama Amjad yayi, yayinda BB LALO ya buɗi baki cikin murya irin ta uban daba ya ce, "AMJAD HASHIM DARWIN?"..........gyada masa Kai yayi alamar eh. Bubbuga dantsen hannunsa yayi sannan ya ce, "buɗe!"......... janye dogon hannun trench coat ɗin tasa yayi bai ƙarasa ba yaji wani irin radaɗi a dantsen hannun nasa kafin ya gama dawowa nutsuwar sa har jam ya zare abun dake hannun sa me kama da syringe, da ido BB LALO yayi masu alamar suna iya tafiya, juyawa yayi ya bar wurin da sauri yayinda shi Kuma mutumin da ya fara taryan Amjad ɗin ya gyara tsayuwa da alama bai gane me BB LALO ya faɗa da ido ba. Gyara zama BB LALOn yayi da faɗin, "Ina P I file din ka?"........... Zaro file ɗin Amjad yayi a cikin rigarsa ya miqa masa, mutumin nan da ya masu iso ne ya ƙarɓa sannan ya miqa masa, duddubawa yayi sannan ya ɗaga Kai ya kalli mutumin da sauri ya bar wurin, bai fi two minutes ba ya dawo da faɗin, "Gashi sir".......... Da Kai ya masa alamar ya miqawa Amjad ɗin. Karɓar files ɗin guda biyu Amjad yayi tare da buɗe na farkon, saida ya gama karantawa sannan ya ɗago ya kalleshi da faɗin, "Kai ne shadow din k........." Bai rufe bakinsa ba yaji harbin bindiga da baisan daga inda ya fito ba, da wani slow move ya Kai kallon sa gefensa inda mutumin nan da ya tarye shi yake tsaya Amma sai ya ganshi zube a kujerar dake gefensa goshin sa na fidda jini alamar shi aka harba, kafin ya gama tantance meke faruwa ya tsinci murya BB LALO in da yake faɗin, "Wannan shi ne hatsarin dake tattare da Shadow, an ma uzuri saboda wanna shi ne zai kasance aikin ka na farko dashi, kuma information da ya samu a kanka yasa ya buqaci yin aiki tare dakai, saboda shi yafi son aiki da wanted criminals irin ka, dan haka Ka kiyaye. Shi ɗin daban yake, inuwa ce da ganin ta sai a haske shi kuma duhu ke lulluɓe dashi, aiki dashi abu ne me matukar hatsari akwai rules a file ɗin dake hannunka, ka karanta sannan kayi signing, Kuma ka sani baka da samar canza ra'ayi tunda har ka zo nan to rayuwa ko mutuwa shine kawai zabin da kake dashi". Wani shaiɗanin murmushi Amjad yayi Wanda ya sanyashi rikiɗewa ya saje dasu. "Ni da kake gani, zaɓi tsakanin rayuwa da mutuwa bashi bane a gabana, saboda dama ban fito ba saida na shirya tunda kaga har duniya ta shiga rudani a kaina Kuma still ina rayuwana yadda nakeso to ka tabbatar da ni ɗin zaɓi na ba ɗayan biyu bane, zuciyata ta kan kirkiri zaɓi sama da uku, ba buqatar nayi ma dogon bayani dan shi Wanda zanyi wa aiki ya riga da ya san waye ni"..........ya ƙarashe Yana zaro pen a aljihun sa yayi signing. "Gebriel karɓi Ka haɗa da wannan Ka tabbatar sun isa wurin oga domin sanyasu a record". Karɓa Gabriel yayi tare da haɗa files ɗin wuri guda. " Ka Kira azo a dauke min gawar nan".......... Faɗin BB LALO Yana sipping wine ɗinsa hankali kwance. "Okay!"............Gabriel ya Amsa tare da barin wajen. Gyaran murya yayi yana sake relaxing cikin kujerar ya ce, " A wanna file ɗin dake hannunka akwai paper work na iya adadin mutanen da ake buqata daga wajen ka sannan akwai wani specified person da ake buqata shi ma, akwai sunansa, address da kuma duk wani info ɗin sa a ciki". "To batun payment fa? Dan ni farashi na per person ne ba wai grouping nake ba". Girgiza masa kai BB LALO yayi kafin ya ce, "Ba'a tsadance kuɗi dashi dan shi duk wa'anda ke aiki dashi price ɗaya ke garesu, a yanzu za'a baka rabi in aiki ya kammala zaa cika ma." Ɗan shuru Amjad yayi kafin ya ce, "Inajin kamar ban yadda dakai ba, Anya ba gadar zare aka shiryamin da sunan shadow ba, in ba haka ba ai shi zai ban aiki tsakanin ni da shi ba wai dakai ba" ...........Amjad ya faɗa yanayin sa na ɗan sauyawa haka zalika bugun zuciyar sa Amma a fuska baza ka taɓa iya cewa ga halin da yake ciki ba, Dan masu iya magana nacewa labarin zuciya a tambayi fuska Amma a wurin Amjad ba haka bane duk abunka baza ka iya karantar abinda ke zuciyar sa ba daga yanayin fuskarsa. Wata irin dariya irin ta basawa BB LALO yayi kafin ya ce, "In dai akan shadow ne kar kayi tunanin ganinsa ko haɗuwa dashi har iya tsawon lokacin da zakayi aiki dashi, shin zaka iya yadda in nace ma tsawon shekaru ashirin Ina aiki tare dashi Amma ban taɓa ganin sa ido da ido ba"........... Ɗan dakatawa yayi tare da ɗaukan kwalbar wine ɗin dake gabansa akan table ɗin da ya raba tsakiyarsu tsakanin sa da Amjad ɗin, sake tuttulawa yayi a tumbler ɗin sannan ya cigaba, "Zaifi kyautuwa idan ka kawar da duk wani tunani dake kwakwalwar ka, ka maida hankali Kan aikin dake gabanka ba wai batun ganin Shadow ko wani abu ba. Akwai deadline na aikinsa yana nan a cikin file ɗin dan haka Ka Kula ka Kuma kiyaye dokar sa".......... Ya Ƙarashe yana ɗaukan wayar sa ya tura wani saqo, wani Ninja ɗin ne yazo sanye yake da kaya irin na Gabriel hannun sa ɗauke da wata babbar suitcase, da ido ya masa alamar ya bashi. A gaban Amjad ya ajje sannan ya juya ya bar wurin. "Wanna shi ne rabin kuɗin aikin ka, kana iya tafiya".........Bai sake cewa komai ba ya ɗauki suitcase ɗin ya tashi. Kunsan meysa suka harbe wanna mutumin dukda shi ɗin ya kasance Yana aiki a karkashin su ne, to saboda ya kuskure wurin fahimtar alamar da BB LALO yayi musu da ido, haka suke basu da sani ko sabo, kuskure kaɗan kayi a bakin Ranka. _____________Shi kuwa Amjad Masaukin sa ya koma, bayan yayi locking ɗakin ya Ƙarasa bakin gadon tare da ɗaura suitcase ɗin akai ya buɗe shi, tozali yayi da bundles na wasu miqaqqun pounds masu uban yawa, dan zai iya cewa daga bank sai cikin suitcase ɗin nan saboda yadda suke wani daukan ido"...........wani light smile ya saki tare da lumshe idanun sa ya buɗe, ɗaukan suitcase ɗin yayi ya adana sannan ya faɗa bathroom. _____________"Anah wato maganar gsky mutanan nan sun gudu, ni daman tun farko nasan basu da gaskiya shirya musu komai akayi". "Hasbunallahu wani imal wakil, to Juraysh meysa baza a nemo su ba, in aka barsu sunci banza kenan sun ɓatawa yaro na suna Kuma sun gudu". "Ai Anah ko mu bamu nemo su ba hukuma zata nemo su, inaga mu bar musu komai kawai dan dole za'a nemo su, in Kuma ba'ayi hakan ba mu sai mu dau mataki". "Shikenan, amma gsky raina yayi matuƙar ɓaci whl wanna ai rainin wayo ne ma, wai dan ALLAH me mutane suke so da yaron nan ne? Me ya tare musu a rayuwa? Kowa bashi da buri da ya wuce su ɓata shi, ka duba fa sanadiyyar haka Alhaji ya kwanta ba baki ba ƙafa ba hannu wanna wani irin tashin hankali ne". Cikin jimami Juraysh ya ce, "Anah duk wani Wanda ke nasara a kan komai kamar Amjad dama dole yayi maqiya a boye ai harma da filin, shi ɗin fa guguwa ce da in ya taso dole kowa yayi ƙasa da kansa, ALLAH ne kaɗai yasan iya adadin mutanan da Ƙurar Amjad ta shigarwa ido". "ALLAH ya fisu, cigaban sa Kuma da basa so in Sha ALLAH saidai zuciyar su ta buga, ni gashi ma tunda ya tafi KM ɗin nan ban cika samunsa a waya ba". "Kai Anah bafa yau Amjad ya saba tafiye tafiyen nan ba, Kuma kinsan dama duk lokacin da yayi tafiya to ayi sallama da samunsa a waya ". "Amma Kuma yanzu ai a cikin ƙasa yake Bai kamata ace ana rashin samun sa ba kamar da da yake fita abroad. Me ma yaje yi to shi da yanzu ba wani aiki yakeyi ba, ba gwara ya zauna a gida ba Nima Ina ganin sa hankali na ai sai yafi kwanciya". "Amma Anah abun zai masa yawa idan akace za'a takurashi sosai, sai ya zama rana zafi inuwa quna, kawai dai mu cigaba da addu'a har ALLAH ya bayyana gsky ". Sallamar Nuhail ta katse musu zancen nasu, Juraysh ne ya amsa, bayan ya ƙaraso ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan ya zauna yana faɗin, "Anah barka da rana". "Barka Nuhail ashe ka shigo, ya gida ya yaran?". "Duk sunan nan lpy, ai ƙawar taki ma saida na mata wayo na fito dan in dai taji nan zanzo an dinga rigima da ita kenan saita biyoni". "Allah sarki, Kai Kuma baka son kawo su ba". "Ba haka bane Anah, Ina cewa zan taho da ita su ma sauran zasu ce sai sunzo ni kuwa bazan iya yawo dasu duka ba saisa sai nace su bari sai maman tasu zatazo saisu biyota". "Allah sarki, ALLAH ya albarkace su gabaɗaya ". "Ameen ya ALLAH!, ya wurin Amjad kuwa, kwana biyu bana ganin sa kuma bana samun wayar sa, dama akwai wata maganar da zamuyi ne?". "Eh tou nima gsky ba kasafai nake samunsa ba tunda yayi tafiyar nan". Ta tabbata dai yayi tafiyar kenan ya faɗa a zuciyar sa, ba tare da yasan zancen zucin da yake ya fito fili ba. "Naam magana kake ne".........Anah ta tambaya. Da sauri ya ce, "Ah ah bakomai cewa nayi mu bamu ma san yayi tafiyar ba ina yaje ne?". "Khor maksar"..........Juraysh ya bashi amsa a daƙile Yana hararar sa ta ƙasan ido. "Au ashe ma Yana ƙasar ai na ɗauka ko ya samu fita ne dukda har yanzu bamuji abinda ƙasashen suka yanke ba a Kan sa, kuma gashi abun yana son shafar yanayin aikin mu dan a yanzu babu zancen fitar da Kaya daga refinery's ɗin Dada haka kuma kasuwar ƙasashe masu shigowa HD aurum mining yanzu sunja baya, ga batun case ɗin sa da yarinyar nan Kuma naji an fara raɗe raɗin wai an batar da yarinyar da iyayen ta". Kallon Anah Juraysh yayi kafin ya ce , "kamar ya? an batar dasu ko Kuma sun gudu saboda basu da gaskiya". "Ei to ni dai abinda naji kenan cewa an batar dasu "..........."A Ina kaji?". "Zancen duniya ai baya ɓuya malam Juraysh, ni dama abinda yasa nake neman sa mu tattauna kenan saboda wanna Abun qimar gidan mu ce gabaɗaya, batar da yarinyar da iyayen ta bashi bane solution kamata yayi a zauna ayi maslaha". "Kai cema akayi shi ya ɓatar dasu kenan?"............ Juraysh ya tambaya yana tsare shi da ido. "Haka mutane suke cewa, Wai saboda gudun tonuwar asirin sa". "To kai mutane ne? Kai ai ɗan uwansa ne, kai me iya ƙaryata wa ne ma ba wai kazo kana cigaba da yayatawa ba". "To yanzu wani wuri naje nayi zancen ne? Ina cewa anan wurin daga ni sai Kai sai Anah, waye bare a cikin mu Anah da take mahaifiyar sa ko Kuma Kai da kake cousin ɗin sa". "Whl ku canza hali, Sam wanna bashi bane abinda ya kamata ku dingayi matsayin ku na yayyun sa, abinda ya shafe shi ai ya shafe ku ne duka". "Ya isa haka juraysh"......... Anah ta faɗa tana ƙoƙarin tausar zuciyarta dake zafi. "Ka dai yi min gurguwar fahimta ne kawai Juraysh Amma ba damuwa, Anah ni zan koma".......... ya karashe Yana miqewa ya musu sallama ya fita. Waya Anah ta ɗauka. "Anah me zakiyi?".......... Juraysh ya katseta. "Juraysh so nake naji ko da gaske da sa hannun sa a ɓatan yarinyar da iyayen ta, hankali na gabaɗaya ya kasa kwanciya, zuciyata ta rasa sukuni". Girgiza kansa yayi da faɗin, "Haba Anah Kar ya zama kema ana influencing ɗinki mana, Anah idan har Amjad zaisa a batar dasu kenan bashi da gaskiya kuma ya aikata laifin da ake zargin nasa dashi"........... Shuru tayi ya sake faɗin, "kiyi tunani sosai fa Anah, ni whl ko wa'annan Yan uwan nasa ba wai na yarda dasu bane, ki duba fa yadda yake Ƙara wani sussunkuyar dakai, shi fa munafiki baya zuciya duk abinda zaka masa zai shanye ne". Shuru Anah tayi tana tunanin maganganun Juraysh ɗin Kuma da alama suna tasiri a tattare da ita. _____________Zaune suke a wani madaidaicin falo su biyu ne sanye da ƙananun kaya polo t shirt da sweet pant irin na sport, t shirt ɗin ta bayyana ƙwaryar tumbin nan nasu ras dashi. "Dalilin da yasa na buqaci ganin ka Alhaji Huzaif daga ni sai Kai ba tare da ko su Abid sun sani ba shi ne nasa an ɗauke yarinyar nan da iyayen ta"............Saurin kallon sa Alhaji Huzaif yayi kafin ya ce, " Mai sa zakasa a ɗauke su, yanzu in kotu ta zauna aka nemi ganin su fa, ai sai mutane suce dama ƙazafi suka masa". "Eh ai gudun tonuwar asirin sa ne yasa ya ɓatar dasu"......... Kallon sa yake cike da Neman Ƙarin bayani. "Saboda a wannan zaman zasu bayyana shaidun da kotu ta buqata mana sunan sa zai ida baci ". Shuru Alhaji Huzaif yayi kafin ya ce, "To naji, amma ai tare ake komai dasu Alhaji Abid mesa yau Kuma kace mu haɗu mu kaɗai daga ni sai Kai?". Gyara zama yayi da faɗin, "Abinda ya tara mu anan daban ne, bana so mu bawa Ahuoyzah haɗin Kai ya samu wanna karɓuwa a majalisar man fetir ta duniya, domin fa mu yan kallo zamu dawo". "Ehhhh Kuma haka ne, amma Kuma ai zai biyamu sannan yanzu in mun masa haka miye namu"......... Ɗaura ƙafarsa yayi ɗaya kan ɗaya yana murmushi ya ce, "Zamu barwa Ramphant Juwaira filin domin shi ya dace ya samu wanna karramawar ta wanna shekarar". "Canza hanya zamuyi dasu kenan?"....... Alhaji Huzaif ya tambaya yana gyara zama . "Ko ɗaya muna daga nan ɗin zamuyi komai Amma bana so su Hammoud su sani, na janyo ka ne saboda Kai ma ka samu alheri a tare dashi, saboda shi babu wanda yafi mu shiga gabansa kuma kasan bai taɓa samun ko da star ɗaya ba so yana cikin ɗokin samu, zai sakar mana ragamar komai ne". Cikin jin dadi Alhaji Huzaif ya ce, "Dama ai munafukai ne, ni dama tun can na lura sun ɗaukemu kamar wasu yaran su, Kuma mu zamu bisu ta ƙarƙashin ƙasa saidai su gansu kasat wanwar"...........Dariya sukayi tare da tafawa Hajj zawaad ya ce, "kanka na ja Mutumi na". "Amma fa wani hanzari ba gudu ba".........."Ehh wanne kenan?". "Batun yaran HD". "Ina sane da su barsu, dama nake basu kawai suyi nasu tunda yara ne kuma kasan ai su basu san Kan harkar ba, wancan yaron ne ya sani yanzu kuma sun tsige shi gefe, so ba abinda zasu samu wahalar banza zasuyi karshe zasu bace a kasuwar duniya gabaɗaya". Girgiza Kai Alhaji Huzaif yayi Yana Dariya ya ce, "Baka da daɗi Hajj Zawaad". _____________Tsaye yake a ɗakin mahaifin nasu Yana Kai da kawowa waya ce maqale a kunnen sa yana faɗin, "Awais karka min wasa mana kai ma da nake gani me ƙwaƙwalwa, kasan Amjad yana da basira sosai, yana iya bincikosu in ka ajje su a kusa, san samu a fitar dasu daga ƙasar gabaɗaya, ni fa duk wanna shirun da yayi akan komai hankali na bai kwanta saboda na tabbatar akwai abinda yake shiryawa ta ƙarƙashin ƙasa". Daga ɗaya bangaren Awais ya ce, "Julaybin fitar da wa'annan mutanan ba ƙaramin aiki bane a yanzu kai ma ka sani al'ummah sun san fuskar su hakan kamar tonuwar asirin mu ne ai". Shuru yayi can Kuma ya ce, "ka shirya su ka sasu a mota su tsallake iyaka mana a baɗɗa musu kammani kawai"..........Awais zai sake magana ya ce, "ka ga karka kuskura ka sake kirana in ba wanna labarin zaka bani ba"...........Yana kaiwa nan ya katse Kiran yana sauke naunauyan numfashi tare da duban mahaifin nasu dake binsa da kallo idanunsa taf da hawaye. Dariya yayi cike da rashin Imani ya ce, "Ohhh I'm so sorry daada an taba na gaban goshi ko? Whl karka ga laifin mu shi yake shiga gaban mu. Amma kasan wani Abu Dada na ɗauka ma alqawarin tozarta Amjad a gaban idonka da idon duniya sai ya wulakantu irin ƙasƙantacciyar wulakantar da Kare ma bazai shinshina ba, sai mu gani ko soyayyar da kake masa zata iya ceton sa"...........Ya ƙarashe da sautin dake bayyana tsananin wutar gabar dake zuciyar sa sannan ya juya ya fice a fusace. _____________shigowa masaukin nasa yayi wanda baisan wa ya kama ba ma daga airport kawai aka bashi Address card da key ko fuskar wanda ya bashi bai gani ba. Zubewa yayi kan gadon Yana sauke numfashi dawowar sa kenan daga yawon zaga garin da ya fita, sosai yake sake jin son yin aiki tare da Shadow dan daga gani kamar yadda yake hasashe akwai riba a tare dashi, to amma tsarin su fa, ta ya zaiyiwa Wanda bai sani ba aiki, ya daɗe Yana lissafe lissafe kafin ya tashi ya rage kayan jikinsa ya janyo system ɗin sa, jadawalin aikin dake gabansa ya shiga tare da dudduba abinda ya kamata, saboda so yake ya koma gida a satin nan dan can ma akwai abubuwan dake gabansa. Saida ya gama duk wasu abubuwa masu mahinmanci sannan ya kashe komai ya wuce bathroom ya watsa ruwa ya fito ya fada gado don gobe da yamma zai bar kasar Denmark . TO JAMA'A NASAN KUN DASA AYOYIN TAMBAYA A WANNA PAGE ƊIN, TO NIMA DAI HAKAN TAKE A WURI NA ALQALAMI NA NE KAWAI ZAI BAYYANA MANA AMSOSHIN MU. -------------------------√ Tun bayan lokacin da ya kira ya shaida Mata kuɗi ya shiga bai ƙara kira ba saida akayi sallar la'asar sannan kiransa ya shigo wayarta, tsame hannunta tayi daga cikin ruwan da suke ƙarasa wanke kayayyakinsu tare da karɓar wayar da Shazeen ta kawo Mata, amsawa tayi inda ta tsinkayo Muryar sa na faɗin, " Hello". "Hello Baba ilerika ya ake ciki?"............." yauwa hajiya gashi na ɗauko motar ɗaukan kayan ki turomin addreshin gidan". "kaga ba fa wani wuri bane da nisa titin da muka haɗu dazu, wannan dai layin da ya shiga ciki, kuna shigowa ma Ka kirani zan fito saboda ba lalle motar ta iya ƙarasowa ƙofar gida ba". "To tou shikenan"............Ya faɗa tare da kashewa, Shazeen ta miqawa wayar, "Ungo riqe in ya Kira ki faɗamin bari na fito da kayan, Kai kuma Sahnish kayi Ka haɗa ƙwanukan nan gasunan zuwa da motar ɗaukan kayan"...........Ta ƙarashe tana wucewa ɗaki ta fara fito da kayansu kasancewar ba wasu kayan kirki bane yasa kafin su ƙaraso duk ta firfito dasu suna shigowa bakin layin ya kirata, dankwalin Shazen dake kan igiya ta zara ta rufa a kanta sannan ta zira slippers ɗinta ta fita. Na gaya muku wani abu? Hushaima sam bata damu da ta wani suturta jiki ba a cikin unguwa Saisa yawanci yan unguwar suke mata kallon karuwa yar iska, ita kawai duk abinda zuciyarta ya raya mata to fa bata tsayawa wani tunani kai tsaye takeyin sa ba ruwanta da kowa kawai rayuwarta take kamar ita kaɗaice a cikin duniyar, tana kuma sane da kallon da yan unguwar suke mata, amma sam hakan bai dameta ba, ba kuma ta damu da gyara tunanin kowa ba tunda har ita ta san kanta. WANNAN KENAN. A nan farkon layin ta hango su hakan yasa ta Ƙarasa tana faɗin, "Anan kuka tsaya ashe, dama na faɗama ai, motar baza ta samu shiga ciki ba, saidai muje dasu su kwaso kayan ". "Layin naku ne sai hakuri amma ba damuwa, Kai sauko muje a ɗauko kayan"........ Ya fada Yana wucewa gaba, suna zuwa ta shige gidan, ganin sun tsaya ya sata faɗin, " Ku shigo Ku fita dasu mana ". "Kuje Ku kwaso, Bari na jiraku anan"............Ya Ƙarashe Yana matsawa jikin wani kango dake opposite da gidan ya kunna lalitar sa yana ja Yana kallon su suna kwaso kayan har suka gama sannan ya kashe ya koma ƙofar gidan inda Hushaima ta fito. "Zaku tafi da Sahnish sai yaga gidan, nawa ne kuɗin motar?". "5k ne, nama ɗauka tare zamu tafi ai gabaɗaya". "Ah ah karka damu zamu shirya sai mu taho anjima in sha ALLAH, ga wanna 4k ne anjima zan baka ɗayar in kana dashi Ka ranta min ". "Ba damuwa hajiya sai kun karaso, muje ko?"...........ya faɗa Yana kallon Sahnish da ya fito Yana dandabe ruwan dake hannunsa a bayan wandon sa. "Bari muje ".......... Sahnish ɗin ya faɗa yana wucewa. "Tom sai kun dawo"..........Faɗar Hushaima tana me gyara tsayuwa, daga nan bakin Ƙofar take hango su har saida suka shiga motar suka tafi sannan ta koma ciki . Lokacin da Sahnish ya dawo zaune ya samesu sun gama shiryawa, gefen su ya zauna yana faɗin, " Wai ALLAH gamu gare ka". "Menene kuma?"..........ta tambaya tun kafin ya kai ga zaman. Ɗan tsayawa yayi tare da kallonta sannan ya gyara zaman sa yana girgiza kai ya ce, " To ai kya bari na zauna Azagwai. Wai ni dama Hushaima mutumin nan bai kaiki kinga gidan ba kika zuba masa kudi har wurin 70k". Juyowa tayi gabaɗaya gareshi tare da ragewa manyan idanuwan ta girma ta ce. "Me ya faru? karka cemin tarihi ya maimaita kansa?". Murmushi yayi me kama dana ƙarfin hali ya ce, "Amma kinyi kuskure babba d........." 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______20 Murmushi yayi me kama dana ƙarfin hali ya ce, "Amma kinyi kuskure babba da baki fara zuwa kinga gidan ba, dan whl zancen da nake Miki ni dai bazan iya cewa dake komai ba saidai kin gani da idonki kawai ". "Kai dallah Ka min bayani Yadda zan gane mana Ka dinga wani shige da fice". "Ayya kwantar da hankalin ki, gida dai akwai shi, ɗakuna ma akwaisu amma sauran labarin sai idanun ki sun gane Miki"...........Tsaki taja ta tashi ta bar wurin saboda takaicin sa. Saida sukayi sallar magriba sannan suka fito, kulle gidan sukayi suka taka zuwa titi suka tsare abun hawa suka hau. Saida suka tsaya gidan Malam ado dan bashi ɗan makullin. A fusace ya karɓi makullin yana binta da harara har ta koma tuk tuk ɗin suka wuce. Kwa na ce kawai ta raba gidan Malam Ado da gidan baba ilerika, tun daga farkon layin Hushaima take bin irin mutanan dake wurin da kallo, layin babba ne dan yana da faɗo, ba takura kuma, ba wuta amma hakan bai hana mutanen unguwar harkar gabansu ba, wasu da fitilar wayarsu wasu da touchlight hakan ya rage ƙarfin duhun dake unguwar, mutane ne ta ko ina kamar yanzu gari ya waye amma fa kallo ɗaya zaka musu saidai kace ALLAH ya shirya kawai. A ƙofar wani gida Sahnish ya umarci Mai tuk tuk ɗin da ya tsaya, shi ya fara sauka sannan ya ce, "ku fito mun iso".........saukowa sukayi sannan suka sallami me tuktuk ɗi , dakalin kofar gidan tabi da kallo inda a can ƙarshe wasu yam Mata suke zaune suna buga whot babu mai ko dankwali a cikin su. "Har kun iso kenan ?"........ Maganar Baba ilerika da basu lura dashi ba ta dawo dasu daga duniyar kalle kallen da suka tafi. "ALLAH yayi mun karaso baba!"...........Hushaima ta faɗa. "To bismillah Ku shigo mana".......... Ya faɗi yana wucewa gaba. A baya suka bishi soro suka fara ratsawa, ɗakuna ne birjik a ciki yayinda wasu matasan samari ke zazzaune kana ganin su kaga yan zauna gari banza, da ƙafa Baba ilerika ya shuri ƙafarsu ya wuce yana faɗin, "Ana nan ana ƙarawa suminti dumi ko. Gafaran Ku dai"..........ya ƙarashe Yana doka kyauren da ya raba soron da cikin gidan. Ina bama wanda yaji dan wata danbarwa suka tarar a cikin gidan anayi, wasu dattawa ne suke faɗa, ɗayan a ɗan karkace yake alamun yana da lalurar shanyewar ɓarin jiki, ɗayan kuma lpy Lau yake shi ke ma riqe da kwalar rigar marar lpy yana faɗin, "Whl kayi wasa ina iya cillaka cikin rijiyar nan, kana fama da ƙafa ɗaya hannu ɗaya zaka addabi mutane da bala'i a cikin gida". Dunƙule hannunsa me lpy yayi yana wani zabura shi ala zai kai duka gashi sai haki yake yana faɗin, "Jefani kaga whl saidai mu nitse tare, ni zakawa iskanci da buraubanci Adamu". "Kai Kai ni kake zagi"............Kaca kaca kokawa ta ɓalle, dawo da kallon ta tayi Kan mutanan da suke tsakar gidan wasu suna ƙofar ɗakunan su wasu kuma sunyi shimfida ƙarƙashin manyan bishiyun mangwaro dake tsakar gidan. Gyaran murya Baba ilerika yayi tare da ƙarawa muryarsa ƙaudi, ya shiga faɗin, "Tohh ya ahlul fituntunu ina muku sallama tare da yawun bakin sabbin baƙin da mukayi, wanda dazu kukaga an shigo da kayan su, to yanzu sun samu ƙarasowa, Kar naji Kar na gani kun dai san Halina yauwa. hajiya bismillah"......... Ya ƙarashe Yana nunawa Hushaima hanya, har ƙofar ɗakunan ya kaisu. Hushaima ta leqa ɗakunan nasu dake maqota da juna sannan ta ɗauki na farkon me haɗe da toilet itada Shazeen. Daga nan sukayi sallama da Baba ilerika ya juya ya fita su kuma suka shiga Kimtsa dakunan. Saida ta kimtsa ko ina ta musu shimfida sannan ta bar Shazeen data fara bacci ta fita tare da jawo Mata ƙofar ta rufo, kamar yadda suka shiga haka ta fito ta samesu saidai yanzu ba faɗa ake ba kawai suna zazzaune ne suna hira, gidan gabaɗaya ƙaurin hayaqin kayan bushe bushe yake, ga wasu mutanan da bata gansu bama a lokacin shigowar su, yanzu taga sun ƙaru hakan ya tabbatar Mata da cewa lalle sun shigo gidan yawa, kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta ta wuce ɗakin Sahnish, Yana zaune Yana linke kayan sa ta shigo, ɗagowa yayi da faɗin, "Yanzu nake son zuwa wurinku ma". "Maganin sauro zaka tashi Ka siyo mana".......... Ta faɗa tana zama gefen katifar tasa da ko zani bata dashi, marabar ta da suminti kaɗan ne. "Ku shiga net mana ko baki ɗaura ba". "Kana mantawa da cewa Shazeen bata zama cikin net ko". "Oh na manta whl, Amma yanzu dare fa yayi kuma ni bansan kan unguwar nan ba ki Kira tsohon can mana ". "Kai dai kawai kace kaga Yan daba sun firgitaka baza ka iya fita ba kawai". Yar dariya yayi kana ya ce, "Su ɗin ai abun tsoro ne kuma duk me hankali dole yayi gudu da ransa, mutanen da gabaɗaya kansu a juye yake, hanyar lafiya ai a bita da shekara". "Yanzu dai a takaice baza Ka fita ɗin ba". Dan susa kansa yayi da faɗin, "Ni fa nama gaji bacci nakeji whl ". "To yama kyau saida safe".......... Ta faɗa tana miqewa ta fice, bin bayanta yayi da kallo kawai Yana mamakin yadda ALLAH ya bawa Hushaima taurin zuciya da rashin tsoro wanda yayi imani ko a cikin mazan ba kowa ke da irin jarumtar ta ba. Tana fita bata tsaya ko ina ba sai ƙofar gida nan ta tarar da wata sabuwar tashar da aka kafa a ƙofar gidan, gefe guda motocin masu kuɗi ne sunyi layi yan mata sai kai kawo suke, gefe guda kuma kungi kungi ne kowa da clique ɗinsa ga wani kida dake tashi irin na yan tasha, yadda kasan kasuwa akeci. Ƙare musu kallo tayi can idonta ya sauka kan wani container tare da hango wannan marar lpyr da ɗazu suka tarar ana faɗa dashi zaune a ciki, da alama container tasa ce . Sauka tayi daga kan dakalin ƙofar gidan ta tsallaka wurinsa. "Salamu alaika". Kallon sama da ƙasa yai mata ba tare da ya amsa sallamar ba ya ce, " Wacce zaa baki excel ko bensin ko rotmans".......... Hararar ƙasan ido ta aika masa tare da tabe baki ta ce, "Burkutu nake so kana da ita?". Dariya yayi, "Ashe hajiyar babban Kai ce babu saidai ki Ƙara gaba". "Kaga Malam maganin sauro na igiya zaka bani in da akwai".......... Tashi yayi Yana jan ƙafa ya ɗauko yana faɗin, "Akwai mana " . Karɓa tayi tare da ɗauko naira ɗari ta miqa masa ta juya zata tafi ya tsaida ita. "Tsaya mana ga canjin ki". "Barshi kawai "........... Ta faɗa tana ƙarasa barin wurin zuciyar ta cike da mamakin wanna bawan da ƙafa ɗaya a duniya ɗaya a lahira Amma maimakon ya koma ga ALLAH ya nemi lahirar sa, ya ƙare a saida sigari da goro. ------------------------√ Wani tsararren falo ne da ya gaji da haɗuwa, bashi da girma sosai haka zalika babu wasu tarkace da yawa a cikin sa. Wata kyakyawar matashiyar budurwa na hango zaune riqe da waya ta kurawa hoton wani kyakyawan saurayi ido, kyakyawa ce ajin ƙarshe in nace kyakyawa ina nufin pure beauty, ba wani kayan kirki take sanye dashi ba domin wani guntun custard colour mini skirt ne, sai yar ficiciyar riga data tsaya iya cibiyar ta itama custard colour ta ɗaura wata jacket da tsayin ta zai kai har guiwa grey colour, ta tattare curly golden brown hair ɗinta ta daure in a ponytail style, ƙafarta sanye da high heel René caovilla da igiyoyinsa suka kusan kai guiwarta su ma. Wata Mata ce ta shigo kallo ɗaya zaka mata kasan ko zata girmewa ta zaunen ba zaifi da shekaru biyu zuwa uku ba, saidai ita fara ce sosai irin farin turawan nan mai kauu ɗin nan kamar takarda, gashinta orange colour Amma ita ba curly bane straight ne itama irin style ɗin wancan ɗin tayi saidai ita ta tufke shi ya sauka har kusan ƙarshen bayanta, sanye take da irin leather skintight ɗin nan black yabi fatar jikinta kamar wanda aka liqa, sai wata halter neck blouse milk da tabi jikinta itama, kunnen ta maqale da bud, ƙafarta Kuma sanye da wani high heel me masifar tsini na Company Versace Kai zaka ce in an taka karyewa zaiyi, cikin harshen turanci me fita da European accent ɗin su ta ce , "Kia you still haven't gotten ready yet, you know we are the ones to pick the boss up from the airport"...... Saidai har ta ƙaraso ta zauna kusa da ita bata sani ba tayi nisa a wata duniyar bata jin Kira, warce wayar tayi tare da yiwa screen ɗin kallo ɗaya ta fice a gallery, ta rufe wayar ta bata tana da girgiza kanta kaɗan ta ce, "Reeslan still? common get up let's go"........... Ta ƙarashe tana tashi ta nufi ƙofar fita tana faɗin, "The boss's flight will land in the next 30 minutes".........Kamar wadda aka tsikara haka ta mike jikinta har ƙyarma yake tabi bayanta tana haɗawa da dan gudu ta ce, "Ashley wait for me please". Wata orange Lamborghini suka shiga Ashley ce ta shiga mazaunin driver ita kuma kia ta shiga passenger seat, da wani irin gudu ta ɗauki hanya, cikin salo da kwarewa take murza steering kamar me juya spoon a pot. Ko da suka ƙarasa airport ɗin basu fito ba, a cikin mota suka zauna, kusan 7 minutes sai gashi ya fito kamar ba Amjad ɗin mu ba, dan saida na kalla na sake kalla dan tabbatar wa, ya sha wani shegen aski da ya mugun fito da kyawun fuskar sa, sanye yake da ash suit da tayi mugun karɓar body structure ɗin sa, idonsa manne da wani munafikin black sunshade, fuskar nan baza ka taɓa karantar yanayin da yake ciki ba, hannunsa ɗaya riqe da wani suitcase. Wasu sojoji ne sun kai wurin su bakwai suka nufo wurin sa, tsayawa yayi jim yana bin kaf ilahirin airport ɗin da kallo kamar me shirin aiwatar da wani abu, a maimakon ya miqo da tafiya akan right side ɗin da yake sai ya yanke yabi left side ɗin sa. Su Ashley da suka firfito daga motar lokacin da suka hango fitowar sa, suka kalli juna Ashley ta ce, "Where's he?"........... Ta ƙarashe tana waige waige amma ko me kama dashi bata hango ba, ita kuma kia gaban bonnet ɗin ta koma tare da ɗage ƙafarta ɗaya ta ɗan lankwasata ta jingina da motar tare da harɗe hannuwanta a kirji saidai ita ƙasa kawai take kallo. Ashley data gama dube dubenta ta juyo da niyyar zuwa wurin kia wayarta tayi ƙara, dakatawa tayi da tafiya tare da sanya hannunta a aljihun wandon ta dauko wayar ba tare data duba sunan me kiran ba ta ce, "Hello Ace!"........bansan me akace ba daga ɗayan bangaren ta ce, "Okay!".......... Tare da kashe wayar. "Kia!!!"..........Ta kira ta da dan karfi tare da nufar motar tana faɗin, "let's go, let's go!"...........Bata bawa kia damar tambayar ta ba saboda kunna motar da tayi ta na bata wuta, da sauri kia ta faɗa motar ko gama rufewa batayi ba Ashley Taja motar da mugun gudu suka bar airport ɗin, sai a lokacin kia ta kalleta da faɗin, "Meke faruwa?" "An dan samu matsala, Ace yace muje zasu zo daga baya". "Boss fa ake magana?"............Kia ta sake tambaya tana kallonta. Hankalinta na bisa titi ta sake cewa, "Suna tare".......... Daga Nan duk shuru sukayi har suka koma gida. Suna shiga kia ta wuce daki ita kuma Ash ta zauna anan falon tare da kunna TV, ta bawa masu aikin umarnin kawo Mata kayan taɓawa, time to time take duba agogon dake manne a bango har 12am ta buga, tashi tayi tana hamma ta bi bayan kia da tuni tayi bacci, ruwa ta shiga ta watsa sannan ta fito ta sanya PJ's ta kwanta. My people nasan kuna cike da tunanin ko ƙasar Nifaz ne nan to ba ita bace, zaku san wace ƙasa ce nan gaba kaɗan. Misalin 3:00am Kia ta buɗe ido saboda Knocking ƙofar ɗakinsu da akeyi dan dama sam ita bata da nauyin bacci, "who's that?" ..........."you guys should wake up and come out, we are waiting for you in the living room"........... Muryar wani namiji ya daki kunnenta, sai da ta makawa ƙofar harara kamar yana gabanta sannan ta ce, "Mu na zuwa, tun kafin ka fasa mana kunne da bugu"...........Ta ƙarashe tana jan tsaki sannan ta tashi zaune tare da fara tashin Ashley, buɗe ido tayi tare da tambayar, "what?"..........." Get up, they are waiting for us in the living room". Tana kaiwa nan ta tashi ta fita, tashi itama Ashley tayi tana mirtsika idanunta tabi bayanta, tare suka shiga falon inda wasu maza biyu suke zaune Amjad cikon na Uku, ɗaya kana kallon sa kaga Italian kyakkyawa ne aji karshe, sai kuma dayan da in baifi Amjad fari ba to zasu zo ɗaya, kallo ɗaya zaka masa kasan akwai class. Duk ɗagowa sukayi suna kallon su Kia da suka shigo, saida suka ƙaraso suka zauna sannan suka farawa Amjad sannu da zuwa. "Thanks"....... Kawai ya ce sannan ya gyara zama da faɗin, "let focus on what brings us here, Ace explain to them yanayin yadda aikin yake". Dan zakuɗowa Ace yayi sannan ya fara musu bayani dallah dallah banda Amjad daya gama kwashe komai a brain box ɗinsa tun daga Denmark, Har Ace ya gama bayanin sa ya rabawa kowa aikin da zaiyi. Ashley ce ta ce, " What about akil?"........ Ido Amjad ya zuba mata yayin da su kuma suka zuba masa suna jiran jin me zaice, tsawon mintuna biyu suna a haka can ya Miqe yana gyara rigarsa ya ce, "Widad will tell you everything"......yana Kai nan ya sa kai ya fice daga falon wanda yayi daidai da karar shigowar saqo a wayar widad ɗin. Minti talatin suka ƙara a falon sannan suka tashi kowa ya nufi makwancinsa dukda kuwa lokacin 4:30am na dare kenan. Misalin karfe 6pm na agogon ƙasar, tsaitsaye suke dukkaninsu a airport ɗin, Amjad na sanye da thaki colour jeans da black t shirt sai black p cap daya dora ya Janyota ta rufe rabin fuskarsa da take tsuke kamar kullum hannayen sa zube cikin aljihun wandon, gefen sa widad ne shi kuma sanye yake da combat jeans army green da sage colour t shirt. Amjad ne ya fara magana ba tare da ya kalle su ba. "Ya kamata mu maida hankali muyi masa aiki fiye da na kowa saboda mu ma mu sami yadda mukeso, especially ke Kiara kina ban matsala a tafiyata ya kamata kisan wannan aikin daban yake da sauran, kuma ni kinsan a hal.........." Bai karasa ba aka fara Kiran pasinjoji masu tashi, dunƙule hannuwansu sukayi su ukun Amjad, Widad da Ace suka nausa da junansu Amjad ya sake cewa ku kula, sannan suka wuce. Saida suka ga shigewar su Sannan suka koma mota suna jiran jin tashin jirgin su sannan su bar airport ɗin. Bayan an kammala duk wani Abu da ya kamata suka shige cikin jirgin, baza Ka taɓa kallon su kace tare suke ba yadda kowa ya sha murr, ana saura 2 minutes jirgi ya tashi aka fara sanar da cewa an tsaida tashin jirgi saboda samun sanarwa da akayi cewa Akwai criminals a ciki da ake zargin cewa sun shiga da miyagun kwayoyi. Kallon kallo akayi tsakanin Amjad da widad kafin kowannen su ya ɗauke kai, jami'ai ne suka fara shigowa suna bincike tare da karbar passport ɗin kowanne suna dubawa, tashi Amjad yayi ya wuce cikin toilet ɗin jirgin, hakan yasa Widad shi ma tashi da sauri sai............ 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______21 & 22 Kallon kallo akayi tsakanin Amjad da Widad kafin kowannen su ya ɗauke kai, jami'ai ne suka fara shigowa suna bincike tare da karɓar passport ɗin kowanne suna dubawa, tashi Amjad yayi ya wuce cikin toilet ɗin jirgin, hakan yasa Widad shi ma tashi da sauri sai wani jami'i ya sha gabansa da faɗin, "Your passport?"............ Komawa yayi ya zauna tare da miqa masa passport ɗin, karɓa yayi yana dubawa yana kallon sa har ya gama sannan ya miqa masa, tare da sanya portable millimeter wave scanner yayi searching ɗinsa sannan yayi gaba. Amjad kuwa yana zuwa toilet din ya shige ko kula ma'aikaciyar dake tsaida shi baiyi ba ya shige ya rufo, buga masa ta farayi Amma shuru ba alamun zai buɗe, zuwa lokacin jama'ai uku ne a wurin, kallon su tayi da faɗin, "Make an emergency call"..........daidai lokacin Amjad ya buɗe ya fito yana gyara belt ɗin wandon sa. "Hands up"............ ta faɗa tana nuna shi da pistol ɗin ta, ko alamar yaji bai nuna ba sai da ya gama gyara zaman wandon sa. "Search him "...........Ta sake faɗa tana kallon wasu jami'an mutum biyu. Bai motsa ba haka Kuma bai ɗago ba har suka gama caje shi tare da miqa Mata passport ɗinsa da wasu ID'S ɗin da suka samu a jikinsa, karɓa tayi ta duba da sauri jikinta ya fara rawa, ba tare daya ɗago ɗin ba ya saki wani killer smirk da shi kaɗai yasan ma'anar sa, ita kuwa faɗi take, " I'm very sorry sir, we misunderstood you da ALLAH kayi hakuri akan aikin mu muke ne"....... Baice komai ba ila hannu da ya miqa mata, da sauri ta saka miqa masa abubuwansa, karɓa yayi yana sake janyo P cap ɗin sa ya har wurin. Komawa yayi wurin zaman sa ya zauna ba tare da ya kalli inda Widad yake ba Wanda shi ma a lokacin ya zauna ko daga Ina yake Kuma oho. Daga nan aka fara sanar da cewa an bawa jirgin izinin tashi saboda an kama masu laifin. A bangaren su Ace kuwa sunji sanarwar da akayi hakan yasa hankalin su yayi masifar tashi sai Kai kawo suke, kiara ta ce, " I need to go inside....." "To do whattt?". Ace ya amsa yana baza hannu cikin gashin kansa cikin yanayi na rashin nutsuwa. "You know there's gonna be a problem if we don't do something, so let's go do something about it"............. ta amsa masa a zafafe tana wucewa, cikin zafin nama ya fisgo hannunta tana kokarin faɗuwa ya sanya mata ƙafa ta tsaya cak jijjiga mata Kai yayi da faɗin, "kinsan waye boss sannan kinsan waye Widad har meysa zaki tashi hankalin ki". "But A......" "Shiii, mu tafi kawai"............. Girgiza masa Kai tayi ta buɗi baki kamar zatayi magana sai Kuma tayi shuru, sanarwa suka faraji cewa jirgi zai tashi a tare suka sauke wata ajiyar zuciya, ɗagowar da zasuyi suka hango Kia na fitowa daga cikin airport ɗin tana tura wani Abu cikin aljihun jacket ɗin dake jikinta taku take kamar ba mace ba, tana zuwa ta wuce su ta shige mota tare da ja ta bar airport ɗin gabaɗaya dan dama da mota biyu suka zo Ace da Amjad da widad, sai kiara da Ashley. "Ni ka hanani amma Kuma gashi ita taje tayi abinda ya kamata"........Rasa me zaice da ita Ace yayi saboda bai san ya akayi ma ya tsaya riqe Ashley ba a maimakon kiara da duk suka san halinta in ta furta Abu to fa sai tayi gata da brain, she's very smart saidai in bataga dama ba Wanda hakan ne yasa Amjad ke warning ɗinta da Kar ta bashi matsala. Tare Ace da Ashley suka shiga mota ya jasu suka wuce gida su ma. Tafiyar 6 hours 30 minutes sukayi a sama kafin su sauka a babban birnin Nifaz, ko kallon juna basuyi ba kasancewar Widad shi ma haifaffen ƙasar Nifaz ne. Amjad kuwa yana fitowa ya tarar da kamal yazo ɗaukan sa shiga yayi tare da faɗin, " Livy Street".......... Hakan yasan Kamal gane ainahin gidan sa suka dosa. --------------------√ Kamar yadda ta saba Kiran sallar farko akan kunnen ta akayi dan daman batayi wani baccin kirki ba saboda duk da maganin sauron data sa abun yaci tura kasancewar yanayi na damuns sauraye sun yawaita, kusan kwana tayi tanawa Shazeen firfita. Miqewa tayi ta wuce toilet ɗin nasu dake cikin ɗakin ta ɗauko buta ta fito tsakar gidan, Duhu ne dan haka tayi amfani da hasken wayar ta wurin haskawa ta daibo ruwa a rijiyar data gani a tsakar gidan daga can gefe ta zuba a butar sannan ta ɗauka ta wuce, tana kokarin komawa ɗakin nasu Sahnish na fitowa daga nasa ɗakin, miqa yayi tare da faɗin, "Har kin tashi ashe? na ɗauka zaki makara ai saboda gwajabniyar jiya". "Wace gwajabniya kuwa, kaji ka kamar jiya muka fara".......... Ta fads tana shigewa ɗakin. "Yanzu dai na jiraki kenan ki miqomin butar?"........... Tsayawa tayi da faɗin, "Ba toilet a ɗakin ka ne?". "Ahh lalle jiya a ruɗe kika shigo gidan nan, Saida fa kika shiga kika duba kowani ɗaki duk a lokacin baki lura ba toilet ba". "Ina fa na lura, ka shigo to in na gama sai na baka". "Barni in sha iska kinji ɗakin nan kamar kurkuku Yasin, ke dai in kin gama miqomin ai naga ma ga toilet nan a waje". Wucewa tayi ta barshi, Saida ta ɗauro alwalar ta dawo ta tashi Shazeen taje tayi itama da ragowar ruwan data rage mata, sannan taje ta ɗauko butar ta leqo ta miqa masa ta koma, hijaban su ta ɗauko musu ta shimfiɗa darduma suka tada raka'atanil fajr sannan suka ɗan zauna har aka Kira sallah sukayi, suna gama azkar Shazeen ta koma bacci ita Kuma ta tashi ta fita, samu tayi rabin mutanen gidan duk sun firfito masu ɗiban ruwa sun bi layi dan guga ɗaya ce haka zalika da yawa daga ɗakunan basu da toilet sai wanna na waje guda ɗaya, ɗakin Sahnish ta wuce inda ta tarar dashi zaune kan Abun sallar da ya idar da sallah zama tayi da faɗin , "Sahnish dole fa mu nemi stove kaga dai ba zai yiwu na kunnawa mutane gawayi a ɗaki ba a zo a samu akasi na babbakawa mutane guda". "Nima tun jiya nayi wanna tunanin amma Kuma kina da kuɗin ne a hannun ki ?". "Babu whl dan abinda ke hannu na baifi na ɗan Abun da zamuci ba a hakan ma inaga ba zai Kai mu wata ba, har Ina tunanin ko zan tambayi wani abu daga cikin albashi na, sannan Kuma ga batun canzawa Shazeen makaranta". "Canjin makaranta Kuma ?".......... Ya tambaya yana jifanta da kallon mamaki. "Eh suna Ƙare zango nan kuwa tunda dama zangon karshe suke zasuyi canjin aji, zan nema mata wata me haɗe da islamiyya kawai Wadda in ta tafi tun safe sai 6pm ko 5 ". "Meysa to?" "Ni da Kai ba yara bane munsan daidai da ba daidai ba amma ita fa? zaman gidan nan zaiyi matukar tasiri akan tarbiyyar ta ya Kuma gurɓata tunanin ta". Ajiyar zuciya Sahnish ya sauke da faɗin, " ALLAH ya kawo yadda za'ayi, nima yau zan fita lalube na ALLAH yasa na dace". "Amma kasan Kai zaka ɗauko ta daga makaranta ko, Kuma in ka ɗauko ta karka fita ku zauna a ɗaki sai lokacin islamiyyar su yayi ku fita tare". "Aiki sabo kenan". "Haka zaka daure, ni bari kaga naje na shirya ban ma san inda zan samu ruwan ba naga sunyi layi kamar masu karɓar sadaka gwara nasan nayi tun wuri "........... Ta ƙarashe tana tashi ta fice, layin data gani yanzu yafi na ɗazu dan haka tayi saurin shiga ɗaki ta ɗauko bucket ɗin su tazo ta sa a layi sannan ta koma kan wani benci tana kallon masu Kai kawo daga masu ɗaura kirji sai masu vest Kuma harda matan aure wai, wani mutum ne ya fito daga wani ɗaki hannu maqale a kirji sai wani gatsina yake, "Rama ke rama kina Ina ne fatan dai kin samun bokiti na dai, Dan nace Miki yau sammako zanyi zamuyi tafiya da Alhaji". Rama dake ebo ruwa ta ce, "Da ALLAH Shamsy karka dameni ni, ladanka na samu ma da zan ebo ma ɗin". Sake noke hanci yayi da faɗin, "To yar masu gida, kema kinsan ko banza da bazata kike rawa, in kika min rashin ta ido kuwa ki gani a ƙwaryar ki".......... Ya ƙarashe yana murguda baki tare da dafe hanci sama. Ita dai Hushaima dariya take a zuciyarta amma a zahiri wani ɗan guntun murmushi me siririn sauti tayi tare da tafa hannu a zuciyar ta ta ce yau Kuma ga inda rayuwa ta juyo daku Hushaima. "Wace shegiyar ƙafar ke mun dariya ne anan, ni whl ƙaramin aiki na ne in kwaɓe mu daku da kowace shegiyar karuwar da takejin ita balagaggiya ce, ba abinda ya Sha min Kai , to in banda ma iskanci taya mutum yana magana ana masa dariya dan dai anga mutum bai shiga harkar kowa ba". Taɓe baki Hushaima tayi tare da duba wayar ta ganin suna neman yin late especially Shazeen me makaranta gashi su kuma sun tsaya kace nace basu iba ruwan ba basu bar wasu sun ɗiba ba, tashi tayi ta ɗauki bucket ɗinta ta matsa gaban rijiyar ta ajje, gugar da wata mata ta danne da ƙafa ta janye tare da ƙoƙarin zurawa cikin rijiyar, wata irin danka taji ta bayanta tana juyowa sukayi ido hudu da wata budurwa kana ganin ta kaga tatacciyar Yar duniya. "Ke wani kikafi ne anan wurin da baza ki iya jira layi yazo Kanki bane saboda ke gaki shafaffiya da Mai, to baki isa ba kauce ki ban wuri". "kiyi hakuri uzuri ne dani ba wani me yawa zan iba ba ". Dukan kafaɗar ta tayi cike da tashen iskanci dake fisgar dusar kwakwalwarta ta ce, "ke baza ki iba ba har sai na ɗiba yaso su sokayen in sunga dama su hakura su zuba Miki ido ki ɗiba".......... ta ƙarashe tana matsar da ita ta warci gugar ta jefa a rijiyar. Girgiza Kai Hushaima tayi tare da ja baya ta bata wurin, "Duduwa kawomin kapilas ɗin nan na Ƙara dashi". "Ke kin ma isa"........ Wadda take Kan layi ta faɗa tana watsa Mata wani kallon banza. "Wani irin na isa ni da gidan uba na, ke zan tambaya ma kina yar kale"..........Ta faɗa tana riqe kugu. "Ke da ALLAH dakata uban naki ai ba kyauta muke zaune a gidan nasa ba, zaman kuɗin mu muke yauwa". "Ke kowa layi yazo kansa sai ya iba iya adadin abinda ya ke so, Dan haka baki isa hana ni iban ruwan nan ba whl"........Hayaniya ce ta barke a tsakanin su kamar zasu bawa hammata iska kowa na mayar da martani cikin zafi. "Tou Tou ALLAH yayi dare gari ya waye tsoffin guzmaye an tashi za'a fara halin da aka Saba "......... Da mamaki Hushaima ke kallon Baba ilerika da ya shigo ashe ba'a gidan ya kwana ba dan baiyi kama da wanda ya kwana gida ba, yana hangota tsaye ya ƙaraso yana faɗin, " Hajiya kece nan tsaye, ba dai hanaki ɗiban ruwan sukayi ba". Ba yabo ba fallasa ta ce, "Layi ne baizo Kai na ba ai, mun tashi lpy?". Wani ashar ya lailayo tare da faɗin, "Duk Ku gyara ku bawa hajiya wuri ta ɗiba"....... A tare sukace bamu gane ba ita hajiyar wankakkiya ce data fi kowa kenan". Warce gugar yayi Yana faɗin, "Ke ban wuri dan uwar ki, bana son tumasanci ". "Amma dai Abun da kake yi kasan ba daidai bane ko"........... Yarinyar da ya warci gugar a hannunta ta faɗa tana harararsa ƙasa ƙasa, fasa zura gugar yayi tare da ɗaga ta da nufin buga mata da gudu ta bar wurin. "Na dauka kin girma ai, to ko uwarki bata isa in tsaya ta tsaya Ina magana tana ce min ba haka ba dukda nasan duk wani iskanci uwayen ku ke koya muku, to whl ku shiga hankalin ku dani a gidan nan kafin na shata muku tsagwaron rashin mutuncin da yafi naku, ƙananun yan iska kawai". "Bari na ɗiba ruwan Baba ilerika"........... Hushaima ta faɗa a ƙoƙarin ta na karɓar gugar ganin Baba ilerikan ya buɗe wata sabuwar chapter magana. "Bari na ɗaibo Miki mana".........Ya faɗa Yana katse masifar da yakeyi ya ja ƙwafa ya zura gugar. Cikin jin daɗi Hushaima tayi masa godia tare da komawa gefe ta tsaya, Nan fa yan ƙananun maganganu da habaice habaice suka fara tashi dan dai ba yadda zasuyi da Baba ilerika ne saboda tijirarsa tafi ta kowa a gidan mutum ɗaya yake tsoro shi ma wato babbar yar sa wadda ta kasance uwar dakin duk wata me bakin uwa ita Kuma ba cika zama tayi a gidan ba sai tayi wata nawa bata leqo ba gidan ba. Saida ya cika Mata ruwan a bokitin taf sannan ya ɗauka Yana faɗin, " Muje a Kai Miki, Ina aka taɓa tarbar bako haka, banda ma mutanan gidan nan da ba mutunci suka sani ba"......... Ita Hushaima ma nauyin abun ta fara ji ganin sa babba Wanda zai iya haifar Wadda ta fita ma amma shi ko a jikinsa da alama ya saba irin wanna fadancin, a ƙofar ɗakinta tace ya ajje mata zata ƙarasa dashi sannan ta sake masa godia ta ɗauka ta shige. A gurguje tayi Wankan ta tashi Shazeen ta shiga , kaya tasa ta fita ta kaiwa Sahnish kuɗin da zai siyo musu waina da kunu, sannan ta Koma ɗaki ta ƙarasa shiryawa. Tana cikin maqalawa Shazeen igiyar takalmi Sahnish ɗin ya shigo ya miqa Mata ledar sannan ya zauna yana faɗin, " wai me ya faru naga duk inda na gifta a gidan nan daga masu nuna ni da hannu sai masu yi da baki sai kace wanda yayi wani abun kunya". Sai da ta juye wainar a kwanu sannan ta ce , "Kai yanzu miye abun faɗa ma, in kana da damuwa da hakan zuwa zakayi Ka samu duk Wanda ya nuna Ka ɗin ya nuna ma abun nunawa a jikin Ka"..........Ta faɗa hakan dukda kuwa tasan ko za'a sa masa wuqa a wuya bazai iya ɗin ba. Hararar ta yayi tare da dauke Kai bai Ƙara cewa komai ba harta turo masa nasa cup ɗin gabansa tare da ajje Kwanun wainar a tsakiya ta miqawa Shazeen nata cup ɗin kunun ita Kuma ta riqe nata da ɗayan hannun tana fadin, " Shazeen shaf shaf (sharp) fa Kar mu makara". A gurguje suka gama sannan ta ɗauki Jakarta suka fito gabaɗaya, kulle ɗakin tayi ta miqawa Sahnish makullin, "Gashi nan Ka Kula saura kazo Ka cemin ya ɓata". "Ba zance ba, a dawo lpy"..........."Sai mun dawo yaya". Shazeen ta faɗa tana ɗaga masa hannu. " To Shazeey a dawo lpy, ayi karatu sosai". Tunda suka fito bata ɗaga ido ta kalla kowa ba harta fice a gidan dukda kuskus ɗin dake sauka cikin kunnenta. A kofar gidan ta tarar da wata sabuwar kasuwa kowa da abun da ya kasa me awara, me kosai, me waina , me dankali, me kunu, me shayi kowa na Kai kawon sayan abinda zai karya, jijjiga kanta tayi kawai taja hannun Shazeen suka wuce bakin titi, kasancewar babban titi ne yasa basuyi wahalar samun abun hawa ba, saida ta Kai Shazeen makaranta sannan ta wuce wurin aikin nasu. Tana shiga da Jumayma ta fara cin Karo, ko nuna ta ganta batayi ba ta fara ƙoƙarin wucewa, tsayar da ita jumayma tayi, "Hey wait tsaya Nan".......... Ja tayi ta tsaya fuskar nan ba sauki Amma bata ce komai ba. "Jiya me ya hanaki zuwa? sannan kuma baki yi report ba". "Kece me wurin ko ke zanwa refot din?". "Amma ni ke da alhakin supervising ɗin Ku ai tare da sanin ya performance ɗin ku yake, Amma ke daga farawa kin fara skipping Kuma a haka in wata ya cika ba'a baki salary ɗinki daidai ba kice an miki rashin adalci". Dukda bata fahimci English words ɗin ba amma a jimlar da sukazo yasa ta ɗan fahimci wani abun. Dan haka ta gyara tsayuwa da faɗin, "Ashe kin samu qarin matsayi bayan gadin masu shige da fice da aka baki, to in kina da hannun jari a wurin nan karki barni na wuce sa'o'i 3 kinji, ɗaya biyu uku "........... Ta ƙarashe tana irgawa da yatsunta. "In kuwa har sa'a uku ta wuce ina nan wajen to kin cika banza marar abun yi me gadi". Tana gama faɗa ta wucewar ta ciki ta bar Jumayma baki Buɗe. "Ni kika fadawa haka ? lalle talaka bai san samun wuri ba, ni kuwa nace har tulu yayi dariyar tukunya bayan duka ƙasa ne. "To Bari hajiyar tazo zakuwa kisan ni ba banza bace, jaka me kwakwalwar kifi bata gane komai sai iskanci".......... Ita dai Hushaima ko juyowa batayi ba tayi shigewar ta. Lokacin da hajiya tazo da baƙi suka shigo hakan yasa Jumayma bata samu damar Mata magana ba har saida suka tafi sannan ta samu shiga office ɗin nata, saidai me tana shiga ta samu Hushaima ciki suna magana, turus taja ta tsaya yanayin ta na nuna rashin jin dadin ganinsu ɗin a haka. "Yauwa gwara da ALLAH ya kawo ka Jumayma, ƙaraso".........Hajiya ta faɗa. Cikin sanyi jikin da bata San yadda akayi ya lullube ta ba ta ƙaraso tana harara Hushaima ta nemi wuri ta zauna. "Jumayma meke faruwa ne tsakanin ke da Hushaima?". "Me tace Miki hajiya?". "To ai ke na tambaya ko, tunda ita naji nata?......... Abinda ya faru da safe ta faɗa Mata tare da maganganun da Hushaima ta faɗa Mata sannan ta ɗora da, "Hajiya tunda ta fara aiki haka takeyi min, Kuma ko ba komai duk ma'aikatan wurin nan suna bani girmana, Amma ita sai tai ta wani jijji da Kai kamar wata yar sarki". "Ya isa to, ke Hushaima kinji haka ne?". "Ko kusa ba haka bane ranki ya daɗe, abinda dai da na gaya Miki Shi ne daidai, don ni tunda na fara aiki wurin nan Jumayma bata so na kamar na tare mata wani Abun, ƙarshe ma cewa tayi taci alwashin sai tasa kin koreni, hajiya bansan abinda zai faru ba a gaba gwara tunda mutunci na kawai na hakura na bar wurin nan, na nema a wani wurin tunda abun ba zai yiwu ba". "Baza ayi haka ba Hushaima, ka kwantar da hankalin ka ai ni ke da wurin ko, ba Jumayma bane ke da ikon korarka dan haka karka damu, kai kuma Jumayma dan ALLAH Kar naji Kar na gani, Bana son irin wa annan ƙananun zancen masu Kai kawo. Ba sanin juna kukayi ba ba komai ba anan fa kuke haɗuwa kawai daga an tashi Kuma shikenan, Kuma in ma Hushaima ya bar aiki anan miye ribarka Jumayma, wani ai baya tarewa wani Abun da ALLAH ya bashi. Da ALLAH Kar na ƙara jin Abu makamancin haka". "In sha ALLAH Hajiya". Jumayma ta faɗa Amma a zuciyar ta kuwa wani haushin Hushaima take ƙara ji. "Haka nake son ji, kuna iya tafiya, Jumayma kai kuma ka kawomin lissafin nan"........ Da "To"......ta amsa sannan ta tashi ta fita, gyara zama Hushaima tayi da faɗin, "Ranki ya daɗe dama ina da wata yar magana ne?". "To inajin ka"......... Hajiya ta faɗa tana bawa Hushaiman duka hankalin ta. "So nake a bani wani Abu daga cikin albashi na a karshen wata sai a Zara"...... Shuru hajiya tayi kafin ta ce, " Gsky there's no way da zan iya Baka wani Abu daga albashin ka, saboda kai sabuwar ma'aikaciya ne ko albashin farko baka fara karɓa ba, ka dai yi hakuri ko ka nemi rance wani waje in watan yayi saika biyasu". "Shikenan Nagode Hajiya ba damuwa"....... Daga haka ta miqe ta fita ta koma bakin aikin ta . 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______23 & 24 Haka rayuwa ta cigaba da miqawa yau da dadi gobe babu, da buga buga suke cigaba da gungurawa Amma duk da haka sun rufawa kansu asiri, haka zalika ta bangaren Baba ilerika sosai yake mutunta su tare da nuna musu kulawa tun mutanen gidan na kuskus akan cewa saboda yaga yar budurwa kyakyawa ne har suka fito fili suna faɗin ai karuwar sa ce dama saisa ya fitar da ya'yansa ya basu ɗakunan. Mu ɗan waiwaya baya abinda baku sani ba shi ne lokaci da Baba ilerika yace wa Hushaima akwai ɗakunan haya, ya'yan sa ne a ciki ya fitar dasu ya maida mazan ɗakin soron ƙofar gida, matan kuma ya ce su koma su raɓe ɗakin yan uwansu, a faɗin sa basu da amfani tunda basa kawo masa komai dan haka in sukayi wasa duk sai yayi waje dasu ya zuba yan haya a gidan dukda yanzu ma rabin ɗakunan yan haya ne a ciki. Yau ta kasance lahadi su Hushaima basu da aiki, Shazeen kuma da Sahnish zai fita ya wuce ya kaita tahfeez da suke zuwa tun 10am sai 5pm a duk ranakun weekend. Zaman ɗakin ne ya isheta taji gwara ta fito ta sha iska duk da kuwa bata san zaman tsakar gidan, saboda har yanzu bata shiga sabgar kowa harkarta tsakanin ta da Baba ilerika ne sauran mutanan gidan kuwa saidai in ta kama, dan tunda ta karanci duk ba wanda ke kallon kan ɗan uwansa da gashi taja mutuncin ta. Sanye take da ɗaya daga cikin rigunan da Amla ta kawo masu tsaraba, miqewa tayi tana neman Abinda zata rufe gashin kanta wanda na lura shi kaɗai Hushaima ta damu data suturta a duk inda take zakaga kanta a ɗaure da dankwali, ganin zata wahala yasa ta zari dankwalin atampa kawai ta kafa daurin ture sannan ta dau wayarta ta fita. Kusan yau duk kowa na gida ga kuma alamar hadari dake haɗowa wanda yasa zafi ya yawaita, yawanci kowa na waje yana shan iska ƙarƙashin manyan bishiyun mangwaron dake cikin gidan, wanda suka yiwa kusan rabin filin tsakar gidan rumfa, kowa da abinda yakeyi wasu kuma zaune suke kawai suna gulmar junan su. Fitowar Hushaima yasa ido ya dawo kanta aka fara kuskus ɗinta, bata kalli kowa ba ta Ƙarasa Kan wani table data gani an ɗaura qullin kayan wanki akai, ture kayan tayi gefe ta zauna tare da ɗaura kafa ɗaya Kan ɗaya, ta buɗe game a wayarta tanayi amma kusan duk hirar da suke tana ji , kunnen ta ne ya ɗauko Mata maganar da wata da Ake Kira da Sa'a super keyi da ƙawarta Wadda tafi tunanin ba a gidan take ba, saboda ita har yanzu tsabar yawan mutanan gidan baza ta iya ware su ba, faɗi take, "Kee kowa ya iya takunsa ustazi ne, amma wanna da kike ganinta akuya ce me fatar kura, karuwar Baba ilerika ce ai har kawalcinta yake yana haɗata da wasu manyan alhazawa a waje yaga yar kyakyawa, ke ai kinsan Baba ilerika baya zubin adashin da ya san ba ranar ɗauka ". Cikin bacin rai ta ɗago da Niyyar maida martani idanunta ya sauka cikin na wani kyakyawan matashin saurayi da ya fito daga wani ɗaki, yana sanye da t shirt me ƙaramin hannu sea blue da Ash wando, fari ne amma ba irin kau ɗin nan ba, fatar jikin sa a murje take kamar ta wani ɗan jariri, lips ɗin bakin sa pink dasu sunyi shar suna shining kamar ya shafa lipgloss suna zagaye da sirrin gashin Baki, hancin sa ɗan karami haka idanun sa irin Magnetic eyes ɗin nan ne masu kyawun kallo, baya tara gashi amma Wanda ke kansa a kwance yake baki siɗik ga laushi, kunnensa ɗaya maqale da earpiece. Kallonta yake shi ma kamar yaga wata sabuwar halitta, ganin ido na ƙoƙarin dawowa kansa ya sashi basarwa yana ɗan kashe idanun saboda ranar data hasko ƙofar ɗakin nasa, sai da yabi gabaɗaya mutanan dake tsakar gidan da kallo sannan ya Ƙarasa fitowa, A tsaye yake dan duk inda ake buqatar namiji wanna gayen ya Kai, ga six packs din sa da shatinsu ya fito dar ta cikin t shirt ɗin saboda fitting ɗin gymnastics body ɗinsa da tayi. A bangaren Hushaima kuwa ganin ya dauke kansa yasa itama sauke nata ƙasa da mamakin wannan kyakyawar halittar data gani a yanzu a kuma cikin gidan da kwata kwata bai Mata kama da irin mutanan dake rayuwa a ciki ba, take ta manta da martanin da taso yiwa Sa'a super, jama'a duk fa wanna kyawun da Hushaima ta rude a Kai baikai rabin kyawun ta ba. " May I sit"........... Ta juyo wata murya, ɗagowar da zatayi kawai ta ganshi tsaye a kanta ba tare data san lokacin da ya ƙaraso ba, sai dai kuma ko da ta kalle shi bai mata kama da shi yayi maganar ba. "Stop looking at me before I poke your eyes out"............ Sai a lokacin ta tabbatar da eh lalle shi ɗin ne yayi magana, voice ɗin sa is so deep gata very clear sannan gata da low sound dan ko ita badan idanunta na kansa ba taga motsawar ɗan bakin nasa da baza tace shi yayi maganar ba, amma kuma duk wannan abun a banza tunda bata san me yace ba hakan yasa ta sake ɗauke kanta kawai. "Ya jey zaka zauna ne ta tashi ko Kuma na kawo ma wani Abun zaman ?"............ Baheelah yarinyar kawu Adamu ta faɗa tana tasowa cikin salon dake nuna neman shiga take. Ko kallon ta baiyi ba ya sanya farar ƙafarsa dake sanye cikin slippers ya ture kayan wankin dake gefen Hushaima qasa sannan ya zauna, matsawa Hushaima tayi can karshen bencin, har yasa hannu zai ɗauko wayar sa a aljihu ya tsaya ɗagowa yayi yana kallon space ɗin data bada a tsakanin su fuskarsa dauke da dimbin mamakin da ya gaza ɓoyuwa ya ce, "Are you in this house ? "............ Ya tambaya idonsa a kanta, kallon sa kawai ta tsaya yi kamar wata doluwa dan kwata kwata bata fuskanci abinda yake faɗa ba. " A gidan Nan kike?"........... Ya sake tambaya da wannan daddadar muryar tasa . "Eh". Hushaima ta amsa. "Sabuwan zuwa?".............Ya sake tambaya, Kai kawai ta gyada masa alamar eh, still idon sa a kanta ya sake faɗin, " Bana son kallo". "Ikon ALLAH, to Kai da wani idon kake kallona har kasan Ina kallon ka?"........... Tayi karfin halin faɗa duk da yadda takejin zuciyarta na rawa har lokacin. Ɗauke kansa yayi ya Ƙarasa zaro wayar tasa, taɓe baki Hushaima tayi tare da tashi da niyyar komawa ɗaki Baheelah ta ce, "Duk iya firirita dai da kissa irin ta kilaki saidai ta canza sheqa dan ba kowani tsuntsu bane me jan gashi yauw........." Ai bata karasa ba taji wani abu dummm akan fuskarta daga kan hancinta zuwa bakinta, da mamaki take kallon Hushaima dake binta da wani fusataccen kallon, dan duk gidan Baheelah na daga cikin tatattun marassa kunya gata da zubin garada wanda hakan yasa wasu daga ciki suke shakkar ta. "Whl ki kiyayi ƙetara iyaka ta, bana tsallaka iyakar kowa a gidan nan, ba wai Kuma dan duk wani munafurcin da kukeyi baya dawowa kunne na bane, dan duk wata taqala da ake nemana da ita Ina sane da takun kowani kare da ƙarya kawai banga Sa'an yi na bane a cikin ku saisa, amma daga yanzu zan saukar da kai na daidai da matsayin naku inci kusun uwar duk shegiyar data sake shiga gonata. Banza jakar maza an gaya Miki kowa ire iren ku ne ballagazazzu" . Ai take duk aka miqe saboda yadda Hushaima ta rikiɗe musu lokaci guda, yan surutai ne suka fara tashi wasu na bayan Baheelah wasu kuma na cewa Hushaima ta burgesu, harda masu cewa gaba da gabanta yau an samu wadda ta kwaɗe Baheelah, sai masu cewa dama bar raina mutum shuru shuru in aka ƙuresu basu da daɗi. Duk wanna abun da ake yi Jey kamar baya wurin dan ko nuna yaji ma baiyi ba, tunda ya zaro wayar sa bai sake ɗaga ido ya kalli wani ba ballatana ya nuna yasan abinda ake yi. A tunzure Baheelah ta ɗaga hannu da niyyar kaiwa Hushaima duka saidai kafin hannunta ya sauka a jikin Hushaima ta danqe shi tare da maida shi baya da ƙarfi har saida yayi Ƙara ta kuwa raka mata shi da wani wawan Mari ji kake tasss kamar tartsatsin wuta, da yawa yawan manyan da suke wurin sai da suka dafe kumatun su haɗe da saka sallallami amma babu wanda yayi ko da gigin tunkarar inda suke. "Whl kika sake yunkuri Kai hannu jiki na sai na illataki, shashasha Dabba kawai"............Ta faɗa a zuciye tana hankaɗata ta juya zata wuce ɗakinta, wani irin ihu Baheelah ta kurma ta fara dira tana sama da ƙasa, da sauri wata babbar mata ta fito daga bayi tana faɗin, "Na shiga uku meya samu Baheelah? ku Kira min Adamu".......... Ta ƙarashe tana nufar wurinta, da sauri wata budurwa ta riqeta tana faɗin, "A'a dakata umma Ina zaki? tana cikin wanna halin ai kawai a leqa waje a Kira su wulu suzo su ɗaure ta tukunna, mutanan ne suka tashi kuma kinsan hadarin dake tattare da aljanun Baheelah, ranar haka ta kusa Kai Fandi lahira".........kafin ta ida magana ma har samarin gidan sun shigo duduwa data kirasu tana biye dasu. Igiyar shanya Jimbo ya figo tare da nufar inda Baheelah take tana faman bige bige, rirriketa sukayi suna kokarin zargayeta, wani ihu ta sake kurmawa tare da yin wata girgiza saiga su Jimbo sun watse kamar wasu fari, kuka umma ta fasa yayin da Baheelah ta tashi a guje zata nufi rijiya. "Ku rike min ita dan ALLAH, ku taimake ni, na shiga Uku".......... Tashi su Jimbo sukayi daƙyar suka sake riqota amma duka ɗaya ta sake musu suka sake bajewa, ai bagimba daga inda yake kwance ya fara rarrafe yana neman hanyar fita dan saida akayi wata Hajijiya dashi kafin ya samu isa kan ƙasa. Runtse idanu Hushaima tayi take ko ina na jikinta ya ɗau ƙerma harta lips dinta, wani irin numfashi taja tare da dunƙule hannuwanta ta juyo a wani irin fisge ta nufi wurin Baheelahn, wasu irin gittattun Mari guda biyu ta sauke mata. A hankali Jey ya ɗago tare da sauke idanunsa a kansu saboda yadda yaji ƙaran saukan dukan kamar ba mutum aka daka ba, wani wawan wawura Baheelah ta kaiwa wuyan Hushaima tare da haɗata da bango ta makure. ihu wasunsu suka sa yayinda wasu suke dariya harda tsalle suna tafi. Su Umman ne sukayi waje da gudu dan zuwa neman masu kawo masu ɗauki Kar ayi kisan Kai. Shi kuwa Jey gyara zama yayi yana kallon su kamar ya samu cinema. " Ni zaka shaqe "............ Hushaima ta faɗa tana kallon cikin idon Baheelah da ya rikiɗe. Ai a ɗari suka watse kowa yaja baya, wasu na faɗin whl itama aljanun ne da ita wanna faɗan ba na mutane bane. Rufe idanu Hushaima tayi tare da sa hannu ɗaya a wuyanta sai gashi duk ƙarfin da Baheelah ta sa babu shi ta banɓare hannun daga wuyanta, ba tare data buɗe idanun ba ta haɗo yatsun Baheelah na hannu guda biyu manuna har saida sukayi Ƙara ji kake gugurus, mahaifiyar Baheelah in banda ihun kuka ba abinda takeyi gashi duk wanda ya shigo yaga abinda ke faruwa baya iya tunkarar su, ga gida ya cika maƙil da jama'a harda maƙota fadi ake a Kira malamai Kar su kashe kansu, buɗe idon da Hushaima zatayi gabaɗaya kwayar idanun sun koma blue ba fari ko kaɗan, yanke jiki Baheelah tayi ta faɗi ita Kuma Hushaima ta tsallake ta ta wuce dakinta ai da gudu aka dinga kaucewa ana bata wuri. Tana shiga ta kullo ƙofar ta nemi wuri ta kwanta anan ƙasa kan siminti tana haki kamar wadda tayi tseren gudu. A tare baba ilerika da kawu Adamu suka ƙaraso dan dama shi kawu garba yana bakin container sa kuma duk abinda ke faruwa yana da labari Kuma yana ganin shige da ficen da akeyi a gidan nasu, Amma yace ba abinda zai shigar dashi gidan nan haka kawai, maybe ma aljanun Baheelahn ne suka jefar da shi a banɗaki suka kawo masa shanyewar ɓarin jiki, dan haka bai ajje ɗa ba bai ajje jika ba a cikin gidan in sun ga dama su kashe kansu ma ba abinda ya sha mai kai. Ganin har lokacin Baheelah bata farfaɗo ba yasa kawu Adamu miqewa yana faɗin, " Dole ma wanna Annobar su bar gidan nan, haka kawai za'a kashemin ƴa". "Saboda Kai ka kawo su ? ko zaman ka suke? Ko kuma kana da gado a gidan"....... faɗin baba ilerika yanawa kawu Adamun wani matsiyacin kallo. "Amma dai kasan da taimako na aka tashi ginin gidan nan ko, tunda ba kuɗinka kaɗai bane a ciki". "To sai ka faɗamin in filin naka ne ?"........... Nan fa rikici ya balle tsakanin kawu Adamu da baba ilerika shi yana cewa saisu Hushaima sun bar gidan shi Kuma Yana cewa bai isa ba haka suka wuni abu ɗaya ranar. Shi kuwa Jey zaman son sake ganin Hushaima yayi dan shi bai gama yadda ita ɗin ma ruwa ɗaya bace gabaɗaya, Amma har ya sha zamansa ya gaji bata sake fitowa ba, haka ya hakura ya tashi ya fita da tunanin ko aljanun sun ɗauke ta ne data shige datkin, Ni kuwa nace Jey ka raba kanka dan Hushaima dan whl in ta danqe ka mu dai bamu iya kwatoka hannunta yauwa . ----------------------√ Tunda Amjad ya sauka a Nifaz bai buɗe wayoyin sa ba tsawon kwana biyu saboda ƙoƙarin sa na daidaita abubuwan dake gabansa haka zalika ba wanda yasan ya dawo sai su Philip. Yau yake shirin tarkatawa ya koma can gida wurin su Anah, Misalin 6:30pm idar da sallar sa kenan ya jawo system ɗinsa da niyyar tura wani saqo, sanye yake da royal blue ɗin fitted jallabiya da tayi masifar karɓar sa, ji yayi an turo ƙofar falon nasa, sanin ba Mai shigo masa wannan falon nasa na ciki kai tsaye in ba Philip ba shi ma Kuma sai ya tsaya ya nemi izini ta hanyar Knocking, ɗagowa yayi da niyyar ganin waye idon sa ya sauka a kanta . "Nayrah!"........... Ya faɗa da mamaki saboda ko da wasa Bai taba kawo zuwan ta gidan sa ba a irin wannan lokacin, ya akayi tasan ya dawo? Waya fada mata ? Meya kawota? Wani irin faduwa gabansa yayi amma ya yi ta maza. Tsaye take idanun ta yayi ja sosai alamun taci kuka har ta godewa ALLAH, Adire gown ce a jikinta duk tayi squeezing kamar wadda aka ƙwato daga bakin kura, wani Kukan ta sake fashewa dashi tare da tahowa da gudu, ganin haka yasa ya miqe tsaye tana zuwa ta faɗa jikinsa cikin muryar kuka ta shiga faɗin, "Na sha gaya ma kana ɗaukan Abun nan da wasa, to gobe za'a ɗauramin aure da farshad, Amjad in na rasaka Bansan in da zan sa kai na ba, bazan iya rayuwar aure da kowa ba in ba Kai ba. Naga gabaɗaya kai baka damu ba, tun kafin wanna abun ya faru nake faɗa ma ka tsaida ranar auren nan kaki sai sawa kake ana ƙara jan lokaci, wai ya kake so nayi da rai na ne ? Ina tabbatar ma da in aka ɗaura auren nan rayuwata tazo ƙarshe Amour"...........Ta ƙarashe tana fashewa da wani sabon kuka Mai taba zuciyar mai sauraro tare da sanya masa invitation card ɗin cikin hannunsa. Zameta yayi daga jikinsa lokaci ɗaya idanunsa sa ya canza kala saboda ɓacin rai, ba tare da yabi ta kan invitation card ɗin dake hannun nasa ba, cikin wani kakkausan sauti da bata taɓa tunanin yana da irin sa ba ya ce, "Amma ban taba tunanin baki da hankali ba sai yau Ninie, kinsan abinda kikayi kuwa ? Kinsan me zuwan ki zai haifar min? Kinsan me zai biyo baya yanzu ? Innalillahi wa inna ilaihir rajuun".......... Dafe kansa yayi zuciyar sa na luguden duka, shi kadai yasan saqe saqen dake zuwa cikin kansa, cillar da katin yayi wanda har lokacin bai samu arziƙin kallo daga Amjad ɗin ba. " Tashi ki fita"..........ya faɗa a dake. Ba shiri ta haɗiye kukanta tare da ɗagowa tana kallon sa cikin ɗinbin firgici, ta buɗe baki da niyyar magana ya tare ta, "kiyi maza ki bar gidan nan nace Miki ko bakyaji ne?". Gyaɗa kanta tayi tare da faɗin. "Na sani dama, kai ɗin kanka kawai ka sani, zan tafi tunda ni nazo in da kake, amma karka ƙara nema na, Karka ƙara kusanto rayuwata nima na barka kamar yadda kake buqata ɗin, Zan karɓi ƙaddarar data zo m........." kasa ƙarasawa tayi ta juya a guje ta fice daga falon. Jagwab ya koma ya zauna hannuwansa dafe da kansa, tunane tunane kawai yake can Kuma ya miqe da sauri kamar wanda ya tuna wani abu ya warci system ɗin ya wuce ɗaki yana me kasheta gabaɗaya ya ɗaura a kan gadon a lokacin da ya shiga dakin, sannan ya wuce ya ɗauki wayoyin sa ya kunna, kiran wata number da akayi saving da Nazbeer yayi, ana ɗagawa bai saurari gaisuwar da Nazbeer ɗin yake masa ba ya ce, " Kayi maza ka bi motar data fita daga gidan nan yanzu". "Boss ai ta ɗan jima da fita, kuma a yadda ta fita ɗin nan kamar fa ta qure gudun motar ne ". Cikin ɗaga muryar da bai saba ba ya ce, "Ka bita nace, Kuma ka hanzarta, titin sea Stone zakabi har zuwa mrovo rock, yanzu yanzu karka ɓata lokaci". "Okay boss"............ Ya faɗa tare da kashewa ya kira wata number ana ɗagawa ya ce, "Jack ya ake ciki kun same shi ne?". "No boss, an samu matsala domin yanzu nan muka baro ƙofar gidan an kawo gawar yaron ". "Whattttt!"...........Ya fada da ƙarfi Wanda har hakan yasa jijiyoyin kansa Sarawa kasancewar hayaniya ba dabi'ar sa bace yafi gane abu simple. "Yes boss ance wai kashe shi akayi Amma ba'a san dame ba saboda ba yanka bane ko harbi sannan ba accident bane kuma ance ɗazun ya fita da yamma, yanzu Kuma aka kirasu an tsinci gawarsa a gefen titi tare da motarsa ". "Innalillahi wa........." Bai ƙarasa ba kiran Nazbeer ya shigo hakan ya sashi katse wayar Jack ya ɗaga ta Nazbeer ɗin. "Boss motar data fita yanzu fa gata nan akan mararrabar mrovo rock tayi accident, ɗaya motar da sukayi accident ɗin ma ta tashi da wuta, yanzu haka an Kira Ambulance". Wani irin rugugi yaji a cikin kansa ba shiri ya laluba bakin gado ya zauna yana karanto duk addu'ar da tazo bakinsa ganin komai yana neman ƙwace masa, daƙyar ya iya daidaita kansa sannan ya samu faɗin, " Ka bisu ka san hospital ɗin da zasu, sannan ka sanar dani zanzo yanzu ". "Boss........"....... Saurin Tarar sa yayi, "I must come Nazbeer, dole naje koma me zai faru"..........Ya ƙarashe yana me kashe wayar, wani siririn gumi ne ke zirarowa ta gefen goshin sa na dama daƙyar ya samu ya miqe, key ɗin mota ya ɗauka ya fita . Kamal na ganin sa ya taso, tsaidashi yayi ta hanyar ɗaga masa hannu ya wuce wurin motar ya shiga ya tada ya fita dan already securities sun buɗe masa gate ɗin. Mathew ɗaya daga cikin body guard ɗin sa ne cikin gurbatacciyar hausar sa ya ce, "Kamal bai kamata mu barta ta tafi ita kade ba, yanayin sa akwai damuwa". "Yes Mathew, inaga mu bishi a baya ". "Lets be fast, Aram let's follow the boss "..........Ya faɗa Yana yafito Aram ɗin suka shiga motar da Kamal ɗin ya fito da ita daga parking space suka bar gidan. A hanya Nazbeer ya kirashi tare da shaida masa hospital ɗin da aka Kaita, bai tsaya jin ƙarashen zancen ba ya kashe tare da Ƙara gudun motar. Kusan a tare suka ƙarasa hospital ɗin dasu kamal dukda gudun da yayi dan suma ba ƙaramin taka mota sukayi ba, tare suka shige amma shi bai lura dasu ba saboda tashin hankalin da yake ciki, duk inda ya wuce sai an bishi da kallo harda masu nuna shi saboda yau ba zance sanya p cap ko nose mask ya ma manta dasu, A kofar emergency ya tarar da Nazbeer ɗin. "Ina take?". "Sun shige ciki da ita" ............Wayar sa ce ta fara ringing, kallon screen ɗin yayi dake wayar na hannun sa ne, da mamaki ya dago Yana kallon Nazbeer, "kace motar data fita tayi accident?". "Eh boss yanzu haka suna ciki tare da yarinyar ". "You are a big liar Nazbeer, sure I will fire you".........Jikin Nazbeer ɗin ne ya fara rawa ya shiga rantse rantse kan maganar daya faɗa gsky ce, Bai saurare shi ba yai picking call ɗin yana faɗin, "Hello My ninie............... 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______25 & 26 "You are a big liar Nazbeer, sure I will fire you".......Jikin Nazbeer ɗin ne ya fara rawa ya shiga rantse rantse kan maganar daya faɗa gsky ce, Bai saurare shi ba yai picking call ɗin yana faɗin, "hello My Ninie........" "Salamu alaikum".......... Muryar wani namiji ta doki dodon kunnen sa . " Wa alaikum Salam, Ina m......"...........Katseshi akayi ta hanyar faɗin, "Amjad?". "Yeah"..........Ya amsa cikin ƙarfin hali tare da fargabar jin abinda zai biyo baya. "Da ALLAH muna san ganin ka yanzu a general hospital, saboda me wayar tayi hatsari Kuma ta bamu number ka ta buqaci a kira mata kai ". "Tana Ina yanzu ?"..........."Sai kazo dai". "Ina kofar emergency ɗin "..........Ya bashi amsa. "Okay bari nazo na shigo dakai"............ Mutumin ya faɗa tare da kashe wayar , kallon Nazbeer da yayi tsuru tsuru yayi sai Kuma ya ɗauke Kai ba tare da yace komai ba. Fitowan da wani Dr yayi ya sanya jami'an tsaron da suka zo tare da ambulance ɗin tasowa suna tambayar, "Ya ake ciki Dr?". " Da sauki muna kan aiki ne".......... Ya ƙarashe Yana kallon Amjad da mamaki ya ce, "Ranka ya dade dama Kai ne"............Kai ya ɗaga masa kawai alamar eh. Nasan Kuna cike da mamakin yadda ake girmama Amjad a ko Ina ko? To bashi kaɗai ba dukkan ya'yan Hashim Darwin girman da ake basu daban ne a faɗin duniya ba ma a ƙasar Nifaz kaɗai ba, Amma kuma girmamawar da ake bawa Amjad tafi ta sauran saboda Alhaji Hashim yafi nuna shi a idon duniya, kowa kuma ya shaida cewa ya fi kusanci dashi, Dan akwai inda in su Awais suka shiga ba a san fuskarsu ba matsayin ya'yan Hashim Darwin, Amma Amjad ko yaro ƙaramin ya san sunansa da kuma fuskarsa. "Bismillah muje"........... Dr ya faɗa yana komawa ciki, bin bayansa Amjad yayi suka wuce ciki har zuwa ɗakin da Nayrah ɗin take, tun daga bakin Ƙofar da ya hango ta yaji jijiyoyin jikinsa sun mimmiqe, Nayrah ɗinsa ce ta dawo haka a ƙasa da hour ɗaya, lalle ALLAH me yadda ya so da bawan sa ne, daidai da taku ɗaya in ALLAH bai nufa ba baza kayi shi ba whl. Cikin dakiya ya Ƙarasa gaban gadon, idanunta biyu sai binsa take da wani irin kallo me taɓa zuciya hawaye ne ya cika idanun nata, da sauri ya girgiza mata Kai tare da riqo hannunta ba tare da ya ma sani ba, ya ce "Ninie......!" Tare shi tayi da muryar dake nuna mai ita na cikin tsananin yanayi na rashin lpy ta ce, "Amour ashe zakazo gareni, Amour please let me die with my dream come true........" Shuru tayi tare da jan numfashi daƙyar ta ce, "I want to be your wife even if it means it's the last thing I do in this world, Amour wlh duk abinda na faɗa ƙarya ne ba daga zuciyata yake ba, ji nake kamar mutuw........." Saurin rufe mata baki yayi yana mai girgiza mata Kai, Wanda hakan yasa ta lumshe idanun ta har hakan ya bawa hawayen da ya taru a kwarmin idanun nata damar sauqowa. Dariyar ƙarfin hali yayi dan kana kallo kasan iya fatar baki ta tsaya saboda yadda idanunsa suka sauya, jijiyoyin kansa sun fito sunyi rada rada. " Nayrah!"...........Slowly ta buɗe idanunta ta sauke a kansa . "Kin amince da aure na a duk yadda nake da Kuma yadda zaki sameni a gaba?"........... lumshe idanunta tayi ta buɗe alamar eh. "Kin shirya fuskantar duk qalubalen dake tattare da kasancewa tare dani?"............ Nan ma da confidence ɗinta ta ɗaga masa Kai. "Zaki iya zama dani ko da kuwa baki sameni a yadda kike tunani ba?". "Zan iya kasancewa dakai a duk yadda kake Amour, ko da duk duniya kuwa zasu juya ma baya ni Ina tare dakai har iya karshen rayuwata"............ta faɗa dakyar muryanta na seizing, wasu doctors ne suka iso wurin gadon tare da Dr ɗin farko wanda ya shigo dashi, matsawa Amjad ɗin yayi ya basu wuri amma still hannunta na cikin nasa, examining ɗinta sukayi kafin su janyo cylinder oxygen suka saita suka maqala mata saboda ganin numfashinta yana sake yin qasa. Idanunta a Kansa hannun ta cikin nasa har Drs' ɗin suka gama abinda yankamata sannan suka matsa gadon dake gaba. Wani zazzafan numfashi ya furzar kafin ya ce, "Ninie na miki alqawarin gobe za'a ɗauramin aure dake in sha ALLAH, I'm ready na fuskanci kowacce irin matsala ce in dai hakan zai faranta Miki".......... murmushin karfin hali ta masa yayinda shi kuma ya sanya hannu ya goge mata hawayen dake gefe da gefen idanunta ya juya da niyyar fita, Mumu da Dad ne suka sawo kai a rikice, ganin Amjad a wurin ya sake hassala Dad. "Touu ai sai kace min Kai ne ummal kabaisin ɗin da ke son kashemin ya', Wai bama nace Maka karka Ƙara zuwa inda ya'ta take ba. Okay Bama wannan ba wato bayan ta shaida ma gobe za'a ɗaura mata aure shi ne kabi ta ƙarƙashin ƙasa ka sa aka kashe yaron mutane ko? Kana tunanin baza a gano ka bane?"...........Kallon dad yake kawai kamar ya samu wani TV yayinda ita Kuma Nayrah idonta yana kansa ne, addu'ar ta ALLAH yasa Kar Amjad ya buɗi baki yace wani Abu, dan tasan tabbas ba dan Dad bane da babu wanda ya isa ya matso inda yake ballatana har ya tsaya gaban sa ya gaya masa magana haka ba taunawa. Saida yayi namijin ƙoƙari wurin saita kansa, ba tare da yabi ta kan Maganar Dad ɗin ba ya ce, "Dad Ina roqon alfarma wurinka, Ina so gobe a ɗauramin aure da Nayrah". "Wanna alfarma kake nema ko Kuma sanar dani kakeyi ubana, to bana aurawa ya'ta wanted criminal Kuma dan iska me lalata ya'yan mutane, Abu na karshe shi ne ka fita harkar ya'ta na shaida ma na ƙara"........... Sauke ido ƙasa Amjad yayi zuciyar sa na wani irin ƙuna kamar zata kama da wuta, ɗagowa yayi da niyyar maida masa wanna martanin idon sa ya sauka cikin na Nayrah dake kuka Marar sauti, ga majinyata duk hankalinsu ya dawo kan su da sauri ya juya ya fita yana taku cikin butsuwa kamar ba abinda ya dameshi. "Duk inda zakaje hukuma saita kamoka, In kuna ji da kuɗi da matsayi shi ma ubansa wani ne ai kuma bazai Barka ba". "Alhaji ka rage murya Dan ALLAH, ka fara duba halin da yarka take ciki mana haba". " Rabu dani kinji, ku in aka biya taku baza ku kwaci yancin kanku ba"........... Dr ne ya dawo wurin su yana fadin, "Haba ranka ya daɗe kai fa babba ne hakan bai kamata ba, ko ba komai ai ka bari in kunje gida ku tattauna saboda nan ɗin wuri ne na jinya a dinga ɗan rage murya". Shuru Dad yayi tare da jan kwafa. _____________Ko da ya fita wurin motar sa ya wuce su Kamal zasu bishi yace ba tafiya zaiyi ba su jira anan. Wayar sa ya dauko yayi wasu yan latse latse sannan ya kashe, idon sa akan harabar asibitin, ba'a fi 2 minutes ba wayar ta fara ringing, ɗagawa yayi da tambayar, "Kaga saqon?"............ Bansan me akace a ɗaya bangaren ba ya sake faɗin, "Ina son nan da hour uku a gama komai"......... Shuru yayi Yana sauraran me maganar can Kuma ya ce, "Eh ka faɗa mata, zuwa anjima ma ai zan shiga wurin nasu"............Shuru ya sake yi kafin ya ce, "in kaje ka kirani zan haɗasu"...........daga haka ya kashe wayar tare da juyawa da niyyar komawa ciki yaga giftawar mutum ta bayan motar tasa, tsayawa yayi jim kamar me tunani ganin kamar laɓe aka masa, can Kuma ya ɗaga ƙafa ya wuce cikin asibitin. -------------------------√ Bayan ta kai Shazen waje tayi fitsari suka koma cikin asibitin, dube dube ta fara amma bata hango Sahnish ba, wucewa tayi wurin da ta bar Sahnish ɗin zaune inda ta ga wani mutum a maimakon sa, "Salamu alaikum bawan ALLAH da ALLAH ko kaga inda saurayin dake zaune a wurin nan yayi?"........... "Kamar yabi bayan ku ai". Mutumin ya faɗa yana miqewa ya wuce ciki. "Okay" .......... Ta faɗa tare da juyawa da sauri, Dad dake tsaye a daf dasu yana waya sai surfa ruwan masifa yake ko shi da waye oho ya juyo tare da bin bayan Hushaima da kallo yana me kashe kiran ya zura wayar a aljihu. Waje ta nufa kamar wadda hankalin ta baya jikinta, saboda bata san inda Sahnish ya tafi Neman su ba, ga shi bashi da lpy Kuma, ko lura batayi ba da Amjad ta bigi kafaɗar sa zata wuce juyowa tayi shima ya ɗago, kallo ɗaya ya mata ya wucewar sa kamar ba abinda ya faru, ganin ya wuce yasa itama jan hannun Shazeen sukayi waje da sauri, a nan ta samu Sahnish ɗin tsaye yana kalle kalle da alama neman ta inda zasu fito yake. "Har ka tsorata ni whl Kai da baka da lpy Kuma ka fito nan ka tsaya bayan na barka a ciki, ko so kake sauron asibitin ya sake tara ma gajiya". "To ai naga daga cewa bari ki rakata fitsari kinje kun zauna, ni Kuma na gaji da zaman ne whl tun 4 fa muke nan". "To ya za'ayi Sahnish babu ce tasa, muje kawai Ina ledar magungunan"?". "Gasu a hannu na"........... Ya faɗa yana ɗaga mata su, Har sun fara tafiya taja ta tsaya kamar wadda tayi mantuwa tare da juyawa da sauri ta sake kallon ƙofar shiga asibitin saboda fuskar Amjad ɗin da tayi flashing a ƙwaƙwalwarta sai taga ya mata kama da wani wanda ta sani amma kuma ta kasa tuna a ina. "Lpy?". Sahnish ya tambaya shima yana bin inda take kallo ɗin . Girgiza Kai tayi alamar ba komai taja hannun Shazeen sukayi gaba, ba wanda ya ƙara cewa komai har suka tari Abun hawa suka hau, shi dai Sahnish binta kawai yake dan yasan duk kuɗin hannun su ya Kare. A kofar gidan ya sauke su, sauka sukayi Hushaima ta ce, " Barin shiga in ɗauko ma kudin".......... Da " To". ya amsa sannan suka wuce ciki. " A ina zamu ɗauko kudin?". "Kaga ka wuce ka kwanta kawai karka Ƙara tambayata inda zan samo, ka barni da zafin da kaina keyi Dan ALLAH". " ALLAH ya baki hakuri , Saida safe ".......... Ya faɗa yana wucewa ɗakin sa, itama ta wuce nasu ta rufo ƙofarta kamar bata ajje me tuktuk a waje ba . Mai tuk tuk kuwa Jin shuru ya sashi kutsawa cikin gidan, "Gafaran ku dai". Ya faɗa saboda ganin yanayin mutanan gidan yasan irin wannan sallamar ce daidai dasu dake shi ma ɗin ɗan kwalta ne. "Ya akayi ne malam zaka shigowa mutane gida kai tsaye?"............Yar Charas ta faɗa tana aika masa da saqon harara ganin kayan dake jikinsa da kuma takalmin ƙafarsa. " Eh wata mata nake jira, tace na jirata ta kawomin kuɗi na kuma naji shuru". "Kaga ƙofar ɗakin ta can, matsa daga can dan ALLAH Karka gurɓata mana iskar muhalli"............. Faɗin Shamsy dan daudu dake zaune tsakiyar yam matan gidan yana kwalliya kamar wata mace. Me tuktuk bai ce dashi komai ba ya wuce zuwa ƙofar ɗakin Hushaima da suka nuna masa tare da ƙwanƙwasawa . "Malam ka saki jiki ka buga sosai, yanzu saita iya manna ma hauka tace bacci take".......... Wata dattijuwa dake barar gyada ta faɗa. Jin bugu kamar zaya ɓalle mata ƙofar ɗaka ya sata tattare sauran kuɗaɗen su data haɗa ta ɗaga ƙasan katifa ta sa sannan ta tashi ta fito tana shan mur ta ce, " Ya akayi?". "Bangane ya akayi ba, kuɗi na malama"..........Ya Ƙarashe yana miqa mata hannu. "Ka bani ajiya ne da zaka zo karba"..........Ta faɗa tana watsa masa wani wulakantaccen kallo. "Ke da ALLAH karki nemi raina min hankali mana, ki fito min da kuɗi na kawai ". Wani dan iskan murmushin gefen baki tayi tana wani abu da haƙori qiii qiii ta ce, " Ai kudi ya ciwu, da hannu na kuma bana baka kuɗi, to wai ma tsaya su wanda kakewa aikin a banza kake musu ne da har kake miqe jijiyoyin wuya akan kuɗin da bai wuce dubu ɗaya ba". "Ahhh kamar yaya? Ke bar ganin fa kina taƙama da bariki nima ita ta raine ni whl zan zabga Miki rashin mutunci ban kuɗina dan durun uwarki" ......... Ya faɗa a fusace. Kallon sa tayi cikin ido sannan ta ɗaga kai ta dubi mutanan dake tsakar gidan cikin ɗaga murya ta ce, "ku rufe ƙofofin gidan nan kuzo kuyi aikin ALLAH". Dan ja baya yayi da faɗin, "Kamar ya a rufe ƙofar gida, me kike nufi ne?". "kamar ya a rufe Miki ƙofa, ki Bashi kuɗinsa in zaki bashi ya wuce kawai".......... Aunty Barma ta faɗa tana watsa mata kallon ƙasan ido. Ba tare da tabi ta kan maganar aunty Barma ba ta ce, "Tun ban tona ma asiri ba kaja tsumman ƙafafuwanka ka fice a gidan nan dan whl Ni dai nafi karfin duk wani me sharri da qulunboto"..........Ƙwafa yaja ba tare da wani tunani ba ya ce, "Zanje amma kuma zan dawo, kuma saikin bada kuɗin nan, dan baza ki cinye min kuɗi ba kuma ki ce zaki nunamin isa da gadara"........... Ya faɗa yana juyawa ya fice, girgiza kanta kawai tayi tana binsa da wani irin kallo da ita kaɗai tasan ma'anar sa kafin ta juya ta shige ɗaki zuciyarta cike da saƙe saƙe. Nan fa aka juye hirar zuwa kan Hushaima dan dama duk gidan haushin ta suke ji in ka cire baba ilerika, kawu garba da Kuma Jey da dama shi Babu ruwan sa da sabgar kowa. Ba'a rufa minti talatin ba sai ga me tuk tuk ɗin nan ya dawo da gangin yan daba kamar wanda zasu je fada da wasu group ɗin, wai nan duk mutum ɗaya aka ɗaibowa, kana ganin su kasan ba'a cikin nutsuwar su suke ba, duk sunsha sunyi makil, kowannen su daga me sanda sai me adda sai haɗa hanya suke kamar igiyar Lipton. Da gudu mutanan gidan dake waje suka shigo ciki, suma na cikin basu tsaya tambayar ba'asi ba suka ara ana kare sai ɗaki har suna gware da juna , Jey da ya kawo Kai da niyyar leqowa yaga meke faruwa jin Ife Ife da kuma ƙarar guje guje amma tozali da yayi da gangin yan daban da suka danno Kai ya sashi komawa da baya, kafin kace me tsakar gidan kamar an share shi, daga masu leqe ta window sai ta ramin ƙofa. Ba ƙaramin tashi hankalin Sahnish ya tsinci kansa a ciki ba ganin abinda ke shirin faruwa, buɗe ƙofa yayi ya fito tare da tare me tuk tuk ɗin nan ya shiga bashi haƙuri, "Malam dan ALLAH kayi hakuri, whl za'a biyaka kuɗin ka, kuɗin ne babu a hannun mu amma ko wani abu ne za'a Saida a biyaka ". "Shi ne?"......... Ɗaya daga cikin yan daban dake karkace kamar bishiyar kuka ya tambaya yana kallon Sahnish. "Bashi bane ƙanwar sa ce, itace fitsararriyar........" Bai gama magana ba Hushaima ta buɗe ƙofa ta fito tana hamma, "Uban waye yake son hana mutane bacci cikin daren nan....... Au ashe Kai ne, su ne masu karɓa ma kuɗin kenan?"..........Ta faɗa tana nuna su da yatsun hannun ta biyu, ta riqe kugu tana musu kallon tara saura kwata. "Hushaima da ALLAH ki koma ciki, wai miye haka kikeyi ne, kaga malam muje na samo kuɗin ka na baka". A tsawace ta ce, "Kai da ALLAH dakata Ina zakaje kake wani firirita, tukunna ma uban wa ya baka damar fitowa daga ɗakin". "Gsky Hushaima abinda kike bakya kyatawa ki basu hakuri m........" Bai karasa magana ba ta dallah masa wani mari, "Yaushe har kayi wayon da kasan me duniya take ciki da har zaka faɗamin abinda ya kamata inyi. Kai na dawo kanka, ka rantse dai bakasan rayuwarka ko? Kuma a dole dole sai kun amfana da jini na". "Ahhhh kai ba wata whl"...........Ɗaya daga ciki su ya faɗa yana daga addar sa ya kai mata sara, wani irin cafa tayi wa addar, runtse ido Sahnish yayi saboda yasan dole ta gifce hannu. Warto Addar tasa tayi tare da gyara mata riqo ta ce , "Haka ake riqe Adda malamai ashe dabar taku ma baku shirya ba kuka shigo, kallon kallo sukayi. Da addar ta nunasu tana faɗin, "Whl duk wanda baibar ƙofar ɗakin nan ba da wanna addar zan zubda jinin sa". Baya baya ɗayan yayi yana shaqar wani abu a hanci rabinsa a duniyar mu rabin sa a duniyar bacci ya ce, "Karfa gwada mataaaa...kwarewar mu"......... Gorar dake hannun Wanda aka Kira da Karfa ya ɗaga da niyyar buga mata Sahnish yayi saurin shiga tsakiya suka kuwa sauke masa ita a gadon baya, wani irin ihu ya fasa Wanda ya tunzira Hushaima ji kake shafff ta tafi da naman hannun Wanda ya bugawa Sahnish gorar, ganin haka yasa suma suka rufar mata, rufe ido tayi tare da fara wasa da Addar hannunta ta kan me uwa da wabi cikin ƙasa da minti biyar ta zubar dasu gabaɗaya a ƙasa sai jini kake gani kawai yana tsartuwa . Da jan ƙafa kowannen su ya kwashi jiki ya fice, mai tuktuk ne na ƙarshe yana kokarin fita ta haɗa masa wani harbi da ƙafarta sai gashi ya koma ya zube, gabansa ta Ƙarasa tare da faɗin, " Su wa kakewa aiki kai kuma?"..........jikinsa ne ya ɗau rawa ya shiga roqon ta kan tayi hakuri ta barshi ya tafi. "Ai ka riga ka makara, na baka dama kayi wasa da ita, dan haka ko ka faɗamin su wa kakewa aiki ko ka faɗawa hukuma, tukunna ma fara fito da abubuwan dake jikinka"........... Ta faɗa hannunta ɗaya riqe da kugu ta kafa bakin Addar a ƙasa, tabbas duk wanda ya kalla Hushaima a wannan lokacin sai ta bashi tsoro saboda yadda ta rikiɗe a lokaci guda . Sai a lokacin Jey ya dawo duniyar mu kifta idanun sa yake kamar wanda yayi ƙarya girgiza kansa yayi tare da ƙarfin halin fitowa dan duk mutanan gidan sun qame a inda suke, ƙarasawa yayi wurinsu tare da taimakawa Sahnish ya miqe kallon Hushaima da har lokacin bata motsa ba ta tisa mai tuktuk a gaba, ya ce, "Ya fa ji ciwo". Ba tare data dauke idonta akan me tuktuk ba a fusace ta ce, " Ya mutu ma kowa ya huta, nagaji nace masa ya koma ɗaki yaqi, ba ruwan sa a wannan abun yaqi ji duk abinda ya sameshi shi ya juyo ba abinda ya shefe ni". Da mamaki yace, "Eh?" . Saboda ganin ai duk abinda tayi saboda dukan da ya same sa ne amma take cewa ya mutu kowa ya huta. "Eh din"......... Ta amsa still ba sassauci a tare da ita. Baba ilerika ne ya shigo da sauri har yana ƙoƙarin kifawa ,jinin dake wurin yabi da kallo kafin ya maida kallon sa kan addar dake kafe a ƙasa da Kuma hannunta dake zubar da jini, ga me tuktuk jikinsa sai faman kerma yake daga inda yake tsugunne. "Subahanallahi Hushaima me ya faru? Ina Majalisa aka kirani anga gangin baqin yan daba sun shigo gidan Nan". Kanta a sama take kallon sa, a daƙile ta ce, "To da kazo me zaka iya yi, loma ɗaya zasuyi dakai ko birbidi baza su bari ba".........maida Kallonta tayi kan me tuktuk, "Kai Karka ɓatamin lokaci ka fito da abinda ke jikinsa ko na raba kanka da gangar jikinka na rage mugun iri"..........Ta faɗa tana ɗaga Addar ta ɗaurata gefen wuyansa, da sauri Jey ya saki Sahnish ya matsa gabanta tare da sanya hannu ya fisge Addar daga hannunta, a fusace ta ɗago idonta ya sauka cikin na Jey sai kuma tayi da nata tana haɗiyar wani yawu. "Kai fito da abinda ke jikinka"..........Shi ma ya faɗa kamar yadda yaji tans faɗa ɗin. "Ni na gaya muku bakomai a jikina, Dan ALLAH ku barni in tafi ".......... Wani kallon banza ya watsa masa kafin ya zaro wayarsa ya kira yan sanda, yana kashe kiran ya matsa ya sanya hannu a aljihun me tuktuk ɗin ya shiga caje shi, da sauri ya zaro hannun, mai ya tuna kuma sai ya maida tare da ɗauko wata leda cikin hanzari ya kunce ta in da tozali da wani farin kyalle, wani irin tashi tsikar jikinsa keyi tun ma kafin yaga abinda ke ciki saboda yadda kyallen ke jiqe da jini, yana budewa idonsa ya sauka kan kwayar idanu da kuma harshen Mutum, Runtse idanunsa yayi da ƙarfi yayin da Hushaima kuwa ta nufi mutumin nan gadan gadan cikin wani irin fusata, ba tare da ya buɗe ido ba ya sanya hannunsa ɗaya ya riqo tsintsiyar nata hannun. Salatin Baba ilerika yasa mutanan gidan suka fara leqowa har suka fito gabaɗaya ai suna gama sanin Meke faruwa suka rufarwa me tuktuk ɗin nan, duk ƙoƙarin Jey na ganin ya kwace shi ya ƙasa ga Hushaima da take neman kwacewa daga riqon ɗaya mata ga Sahnish kuma a zube a ƙasa. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaji jiniyar yan sanda, suna shigowa sukayi kan me tuktuk da mutanan gidan sukawa raga raga kamar kura taga nama, miqawa dan sanda ɗaya wannan kyallen jey yayi sannan ya sake musu bayanin abinda ya faru daga nan suka ɗauki me tuktuk sukayi waje dashi, sakin hannunta Jey yayi yabi bayan yan sandan, ita kuwa Hushaima ko kallon inda Sahnish yake batayi ba ta wuce ɗakinta tare da gabzo ƙofar. Bai fi minti huɗu ba ya dawo cikin gidan inda ya samu mutanan gidan ana ta maida zance, wurin Sahnish ya wuce direct yana faɗin, "Baba ka taimaka min mu kai yaron nan asibiti Dan inaga kamar sun ji masa ciwo a shoulder ɗinsa " . Baba ilerika da hankalinsa bai yi wurin Sahnish ba sam, ya nufo wurin da hanzari yana faɗin, "Subahanallahi Sahnish, ashsha ashe Kai tsautsayin ya faɗawa kuma, taimaka masa muje, kai rayuwar nan ta zama Abun tsoro"........... Da taimakon baba ilerika Jey ya kai Sahnish asibitin kusa dasu, ALLAH ya taƙaita babu karaya kawai buguwa ne, nan suka basu magungunan suka masa allurar pain reliever Sannan suka taho, a hanya Jey ya ce, "i think itama taji ciwo a hannu ku ƙarasa kawai, ni zan tsaya chemist na taho da Nurse da zaiyi treating hannun nata". "To ba damuwa Jawaad ALLAH yayi albarka kaji, ai kayi taimako whl ba kaɗan ba". "Ka kula dashi baba bari naje"...........Ya faɗa Yana wucewa ya barsu. Ko da ta shige ɗaki wuri ta nema ta zauna tare da zubawa hannayen ta ido, ji take kamar ba lpy take ba, kamar akwai abinda ke juya rayuwarta, komai na neman rikita mata tunani, wani abun bata sanin tayi sai bayan ta gama. Cikin wanna yanayin taji knocking a hankali ta ce, "Waye?"..........Mai makon ya amsa sai kawai ya shigo ciki, gyara zaman ta tayi tana kallon sa dan bata taɓa zaton gani sa ba, daga ƙofar ɗakin ya tsaya tare da karewa ɗakin kallo a ƙasa da second 60, idonsa ya tsayar a kanta kamar wanda aka tilasta ya ce, "Na zo da Nurse zai Miki dressing hannun ki fito waje". Kallon hannun tayi har lokacin yana fitar da jini kaɗan kaɗan ga wasu har sun daskare, miqewa tayi dankwalin kanta ya zame sunkuyawa tayi da niyyar ɗauka gashin kanta ya kunce, warwarewa ya dingayi daga daurewar data masa in a sleek bun style har ya baje a gadon bayanta gabaɗaya, harta ɗauki gyalen Kuma ta fasa ta ɗauko hijab ta zura, har tazo zata fice sai ta ɗan ɗago da niyyar satar kallon sa ganin bai motsa ba, karaf idonta ya shige cikin nasa, kallon ta yake kawai irin kallon nan me cike da tarin tambayoyi da sauri ta ƙarasa ficewa, ya rufa mata baya yana tunanin yanayin gashin kanta da ya gani sai kace aljana. Tana fita ta samu baba ilerika da wani me lab coat zaune sai first aid box a gabansa Wanda tafi tunanin shine nurse ɗin da Jey ya faɗa mata, kujerar tsugunno data gani ta ja ta zauna tare da miqa masa hannun. "Sannu Hushaima ALLAH ya tsare gaba".........Baba ilerika ya faɗa. Akan labban ta ta amsa da Ameen Dan gabaɗaya bata jin ƙarfin jikinta . Spirit ya dangwalo a audugar ya fara goga mata. " Sorry"......... Ɗagowa tayi ta kalle shi tsaye yake a wurin kanta hannayen sa zube a aljihu dukda fuskarsa a hade take ta nuna alamun tausayawa, murmushi ta masa kawai ba tare da tace komai ba. Har aka gama aka naɗe hannun da bandage bata motsa ba, miqewa tayi bayan an gama ta ce, "Nagode baba ALLAH ya Kara girma".........Juyawa tayi bangaren sa inda idanunsa ke yawo a kanta kamar me nazari, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke Kai a zuciyar ta kuwa faɗi take shi sai yace baya son kallo shi Kuma yaita ƙarewa mutane kallo, "Nagode". Ta faɗa cikin sanyin murya . "Kije ki duba shi"............ Shine abinda ya faɗa yana nufar hanyar fita daga gidan tare da nurse ɗin, bayan sa ta bi da kallo tanajin wani abu na taso mata a rai kafin ta juya ta kalla ƙofar ɗakin Sahnish ɗin a hankali taja ƙafarta zuwa ɗakin. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 27 Yana shiga dad ya nuna masa hanya da hannu yana faɗin, "Na faɗa na Ƙara maimaitawa ba kai ba ya' ta, karka kuskura Ka je inda take, in ba haka ba whl sai na wulakanta Ka saidai ni ma Ka sa a kashe ni"........... Mathew da ya fusata ne ya boqaro, tare shi Amjad yayi ta hanyar ɗaura hannunsa a ƙirjin Mathew ɗin ya maida shi baya, sunkuyar da Kai Mathew yayi zuciyar sa na tafarfasa ya ce, "Sorry Boss". Idonsa akan dad ya ce, "kaci albarkacin ƴarka daga lokacin da ka sanyo ƙafarka cikin asibitin nan zuwa yanzu, zan tafi ba kuma zaka sake gani na a inda kake ba har sai ka neme ni da kanka". "ALLAH shi sitira na neme Ka, me zanyi dakai me zaka min, in kuma gori kake son min ne sai Ka zauna Ka lissafa abinda ka min a baya in biyaka, kai kasan waye ni ada ai ba matsiyaci bane gaba da baya, ALLAH ne ya qaddara min hakan har Ka samu damar taimaka min ɗin, kuma wannan tsohon baikon babu shi na warware shi ko da Farshad ɗin ya mutu kuwa"............ Girgiza Kai Amjad yayi tare da yin one step backward sannan ya juya ya fita, su Kamal suka rufa masa baya banda Mathew da saida ya sake komawa wurin dad ya nuna shi da yatsa yana huci kamar zakin daya fito farauta, kwafa yaja sannan ya juya yabi bayansu. " To ko duka na zakayi ne, kaji Dan iska qaton banza".......... Ya faɗa shi ma tare da jan kwafar sannan ya juya ya koma ɗakin da yasa aka canzawa Nayrah ɗin. Ko da suka fita gidan su ya nufa, Kamal na yin parking aka buɗe masa, da sassafar ya fito wanda ba halinsa bane Ada dan Amjad komai nasa a hankali yakeyi cikin nutsuwa, saisa in kana sauri to karka neme shi dan shi acewar sa duk abinda aka sa gaggawa za'ayi dana sani ne daga baya. Ko lura da Julaybin da kuma Alhaji fuad bin talib tsohon abokin kasuwancin Dadan su baiyi ba yayi shigewar sa ciki, kallon Julaybin alhaji fuad yayi cikin harshen turanci ya ce, "Wannan ba Amjad bane?"........ Murmushi Julaybin yayi Yana gyara tsayuwa ya ce, "Shi ne, ai kasan duk wanda ya sai rariya yasan zata zubda ruwa, tun bayan tonuwar asirin sa haka yake kullum cikin tashin hankali da firgici da kuma tsoron abinda zai biyo baya".......... Jijjiga kai Alhaji Fuad yayi tare da furta. " ALLAH ya kyauta"........ Yana sake kallon inda Amjad ɗin yabi sannan ya wuce Julaybin ɗin na take masa baya zuwa mota. A falo ya samu Anah da jikokin ta sai Durrah da Adla dake dinning masu aiki na serving ɗinsu, gaisheshi da yaran suka farayi yasa duk hankalin su ya dawo kansa, kusa da mahaifiyar tasa ya zauna. "Yanzu na gama waya da Hunaiz, ina ƙoƙarin kiranka sai gaka kuma ". "Eh Anah"............Ya faɗa fuskar sa ba annuri ko kaɗan . "Ya min bayanin komai amma nace yayi magana da mahaifin sa, su suje saboda kasan bangaren Dadan Ku baza su taɓa shiga ba ko dan wanna laifin da aka qaqaba maka, saidai ko yayyin naka ai kayi magana dasu ko?". "Bana buqatar su anan bangaren". "To wai ma me yayi zafi ne haka naga dai tsawon lokacin da aka yi baikon nan, ni nake binka ma kana cewa ba yanzu ba, sannan yau kuma kwatsam kace gobe kake so a ɗaura aure ba shiri ba komai ana tsaka da wannan tashin hankalin ". Saida yaja numfashi sannan ya ce, "Anah ban taɓa faɗa Miki abinda ke tsakanina da mahaifin Nayrah bane, tun bayan faruwar abun nan saboda bana so hankalin ki ya tashi dad ɗin Nayrah Y.........." Duk abinda ya faru daga lokacin da aka bayyanawa duniya cewa yayiwa wata ƙaramar yarinya fyade zuwa faɗin da ake cewa yana da hannu a cikin masu safarar Mutane ƙasashen duniya, har zuwa yanzu da suka rabu a asibiti. "Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun ²" .............Shi ne abinda Anah ke maimaitawa, "To yanzu miye abinyi kenan? Su Akram ɗin wurin wa zasu je bayan uban yarinya yace bazai baka ba". "Gidan kakanninta zasuje su samu uncles ɗinta". "Kana tunanin su zasu iya aurar da yar ɗan uwansu ba tare da izinin sa bane?". Gyada kansa yayi alamar eh sannan ya ce, "Abinda na sani kawai a gobe za'a ɗauramin aure da ita bayan an sauko daga masallaci". "ALLAH ya kawo ma sauki a lamarinka Babban mutum, amma naso Juraysh ka ɗaura akan Maganar, ko ba komai ai shi ne gaba da Hunaiz abinda zai yi Hunaiz bazai iya ba, kuma shine kuke haɗa kai dashi". Kafin yace wani abu su Durrah suka shigo falon da niyyar tsokanar sa amma ganin yanayinsu su duka yasa jikinsu yayi sanyi, zama sukayi durrah ta ce, "Anah meke faruwa na ganku haka? Akwai matsala ne?"......... Zazzafan numfashi Anah ta furzar sannan ta zayyane musu halin da ake ciki, cikin qunar rai Adla ta ce, "Whl ya Amjad karka yafewa duk wanda ke da sa hannu a wanna qazafin da aka maka, kasa a binciko ma su sannan ka tozartasu a idon duniya". Durrah ta amsa da, "Tabbas an cutar damu Anah dan ba karamin giɓi aka mana ba ta hanyar ɓatawa Amjad suna, saboda an san dukda kasancewar shine ɗa namiji ƙarami a cikin gidan, shi ne ke tsaye a gidan nan, shi ke jagorantar abinda manyan suka ƙasa saisa aka shirya masa haka". Dagowa yayi yana bin kowaccensu da kallo kamar wanda baya gane abinda suke faɗa. Anah ce ta ce, "Zato zunubi Durrah a yanzu baza mu ɗaurawa kowa ba, Ni kawai fatana ya wanku a idon al'umma, so nake zargin da ake masa ya kauce, batun a nemo wanda sukayi a tozarta su duk bai taso ba, Mun barwa ALLAH tunda ALLAH baya bacci Kuma sai ya saka masa"........Miqewa yayi yana duba agogon hannunsa ya nufi hanyar fita, Durrah ce ta ce, "Ina zaka Kuma ?". "Ina zuwa"............Ya faɗa tare da ficewa cikin sauri. Dawo da dubanta tayi wurin Anah da faɗin, "Anah fuskar Amjad bata cika bayyana halin da zuciyar sa take ciki ba amma yau ta nuna, tabbas ba batun yarinyar nan bane kaɗai, akwai wani Abun da ya ɓoye mana"..........Shuru Anah tayi itama ta lula duniyar tunani can Kuma ta ce, "Kar dare ya muku durrah ya kamata ku wuce gida". "Ah ah Anah bazan iya tafiya na barku a wanna halin ba, Dama kuma daddyn su Arzan ɗin ma baya nan, kawai zan sanar dashi a waya zan kwana anan zuwa gobe muga abinda ALLAH zaiyi"...........Anah bata Ƙara cewa komai ba sai tashi da tayi ta wuce ɗakin ta. Yana fitowa kamal dasu Mathew suka taso a ɗarare amma ganin baice komai ba ya bawa kamal ƙarfin guiwar shiga driving seat dan already an budewa Amjad ɗin har ya shige, su kuma Aram da Mathew suka shige ɗayar mota suka rufa musu baya, saida suka hau hanya ya ce, " Asibiti zamu koma"...........ya ƙarashe yana sake duba agogon hannun sa. Da "to". Kamal ya amsa masa. Lokacin da suka isa ɗakin da Nayrah ɗin take yan sanda suka samu guda biyu tsaitsaye ƙofar ɗakin, girgiza Kai kawai Amjad yayi tare da zuwa ya wuce ta gabansu ya ratsa ta tsakiyar su ya shige ciki ba tare da ya ko ɗaga ido ya kalle su ba, su Kuma su Kamal sukaja suka tsaya daga nan waje. Kallon juna yan sandan sukayi ɗayan ya ce, "Kai Awsaf cewa fa yayi Kar mu bar wani namiji ya shiga in ba likita ba. ko Kuma a Kira matar sa ta tantance mutumin".......... Hararar sa Awsaf yayi da faɗin, "To Kai me yasa da yazo shiga ɗin baka hana shi ba sai nine me tsautsayi a ka". "To ai Kai naga baka yi magana ba".......... Tsaki yaja ya ɗauke kansa da faɗin, "In ya fito kana iya tsaidashi ka tambaya waya bashi izinin shiga ko kuma ka bishi ciki ai baka makara ba". "Ai saidai in mu bishi tare". "Kai da wa ?"........... Awsaf ya tambaya yana masa irin kallon nan na baka da wayo. "Ni da Kai mana". "Kaga da ALLAH Sargeant ƙarami kayi min shuru kaji". Shi kuwa Amjad ko da ya shiga ɗakin bai samu kowa ba domin Mumu tana toilet sai Nayrah dake kwance tana bacci, gaban gadon ya matsa daidai lokaci wayar sa ta fara haske alamar shigowar kira, sake kallon Nayrah ɗin yayi ya kalla me Kiran wayar, lips ɗinsa na ƙasa ya kamo ya dan ciza sai Kuma ya juya da niyyar fita yaji an riqo hannun sa, juyowa yayi dan ganin waye idanun sa suka gauraya da nata, kallon sa take da sirkakkun idanunta, hannun sa dake cikin nata ya kalla sannan ya maida kallon sa kanta kokarin cire oxygen ɗin ta fara ya riqe hannun, kwacewa tayi ta cire, ciki dasasshiyar muryarta na marassa lpy ta ce, " Meke faruwa?". Kamar bazai faɗa mata ba sai Kuma yace, "wata waya zaki amsa"...........Da ido ta masa alamar to......."Zaki iya?" ...........Ya sake tambaya yana kallon ta, nan ma da ido ta amsa masa da eh. Amsa Kiran wayar dake ta shigowa yayi tare da maqala mata a kunne, amsa sallamar da akayi a cikin wayar tayi sannan ta yi shuru can Kuma ta ce, " Da sauki iyani"...........Banji me aka ce a ɗayan bangaren ba ta ce, "Ameen nagode Iyani"..........Shuru tayi tana sauraron abinda Iyanin ke faɗa a ɗaya bangaren, a hankali ta ɗaga ido ta dubi Amjad ɗin da Shi ma ita yake kallo, "Eh iyani haka ne Kuma na amince"........Shuru tayi can Kuma ta ce, "to". Zare wayar yayi sannan ya maida mata oxygen ɗin da sauri ganin tana jan numfashi da kyar. " zan tafi sai gobe in sha ALLAH zan dawo, ALLAH ya baki lpy My Ninie ALLAH ya tashi kafaɗun ki".......... Sansanyan murmushi ta masa tare da ɗan daga masa kai, shi kuma ya juya ya fita da sauri . " A sauka lpy".......... Sargeant ƙarami ya faɗa yayinda Sargeant Awsaf ya Maka masa harara. Shi kuwa bai ma san sunayi ba yayi gaba abinsa su Kamal suka rufa masa baya. Ko da mumu ta fito bin ɗakin tayi da kallo saboda tsarabar kamshin turaren sa da ya bari a ɗakin, kallon inda Nayrah take tayi taga bacci take, zuwa tayi ta buɗe ƙofar ɗakin tare da kallo su Sargeant ta ce, " Akwai Wanda ya shigo ne?"......... Da sauri Sargeant ƙarami ya ce, "Kai ah ah, ai ko aljani bai shiga ɗakin nan ba bare mutum". Tsaki Sargeant Awsaf yayi da faɗin, "Ba Wanda ya shiga ma'am". Komawa tayi tana tunani ko ta window ne iska ya ɗauko kamshin wani turaren. ____________A bangaren Julaybin kuwa bayan ya raka Alhaji Fuad ya tafi, bangaren mahaifin nasu ya koma cikin farin cikin yana zuwa ya samu su Nuhail a inda ya barsu zama yayi, Awais da ya kasa hakuri ya ce, "Ya ake ciki ta faɗa ne?". "Kai bari, wancan yaron naga ya shigo a fusace, tunda nake ban taba ganin fuskarsa a irin yanayin dana ganta yau ba". Nuhail ya ce, "To me ya faru haka".......... Awais ya cafe da, " koma me ya faru ba ƙaramin abu bane gsky".......... Julaybin ya sake cewa, "ko ma dai miye nayi matukar jin dadi dan da ya tsaya wurin Alhaji Fuad da an samu matsala dan kasan bansan ya dawo ba saisa da ya min batun zaizo duba jikin Dada ban hana shi ba, to ashe munafikin yana nan". "To yanzu ya kukayi dashi?"........... Nuhail ya tambaya cikin zumuɗi. "Yace ba damuwa zai neme mu ". "To batun HD AURUM MINING ɗin fa?".......... Nuhail ya sake tambaya. "Kana da son dawo da magana baya ai kasan Babu ita a yanzu dama Dada Amjad kawai ya ɗaura akai to shi Kuma yanzu gabaɗaya ƙasashe sun rushe Alaqa da duk wani abu da zai sanya suyi mu'amala dashi, so kaga babu batun ta koma sunyi kayan sai dai a karyar dasu a banza a cikin qasar Nifaz". Awais ya ce, "kasan ko a labarai yanzu an daina sakota Amma ba wanna ba kasan yadda irin aikin nan yake, kana da kuɗi isassu a wajen ka dai ko?"...........Ya faɗa yana kallon Julaybin ɗin. "Eh to da a tunani na so nake nayi exporting wasu crude oil yaso sai na canza account ɗin da zasu sa daga na dada zuwa nawa, amma ina tantance mutumin da zamuyi harkar dashi ne ba tare da yaron can ya sani ba". "Hakan yayi ka fidda da dan yawa dan nima Ina bukatar ɗan wasu personal kuɗaɗe gsky"........... Awais ya faɗa yana gyara zama. Nuhail ya ce, "kamar ka shiga raina Awais, kawai ka fidda duk Wanda suke a ƙasa yaso in an tura kuɗi sai ka ɗauka abinda zaiyi a harkokin buɗe ma'aikatun namu sauran sai kowa ya ɗan riqe a hannu ko ya kukace?". "Ba damuwa, Amma a sirrance zamuyi saboda In yaron can yayi magana mu tuhume shi kan hakan kun gane plan ɗin ai?". Faɗin Julaybin. "Hakan ma yayi"........... Nuhail ya faɗa, da haka suka rufe zancen suka shiga wata hirar. WAYE HASHIM DARWIN? Hashim Darwin cikakken hamshakin Mai kuɗi ne da duniya gabaɗaya take ji dashi, Yana da ma'adanai na tono gold da Kuma sauran precious stones wanda ba kowa ya san dasu ba sai masu masa aikin Wa'anda suka kasance amintattun sa, abinda kawai duniya ta sani yana da ma'aikatar dake sarrafa gold, diamond da sauran precious stones din da duk duniya a HD AURUM MINING (Hashim Darwin aurum mining) kawai ake samun irin su, nan ne fa duniya ta masa ca kowa burin sa ya kulla alaqa dashi ya Kuma samu irin gold da diamond ɗin HD, tare da bashi offer ɗin zuwa ya kafa brand a ƙasashen su, Amma yaqi yace yafi son yan ƙasar sa su amfana wanda hakan ya janyowa ƙasar farin jini a idon duniya, a hankali ya mallaki rijiyoyin man fetur yana refining ɗin sa tare da fitarwa ƙasashe mabanbanta. Yana da mata biyu matar sa ta farko Hajiya Zunaira ƴaƴanta Huɗu Julaybin shine na farko sai Nuhail mai bin sa sannan Awais sai Kuma autarsu Mirrah. Duk kan su sunyi aure har da yayansu Mirrah ce kawai take karatu. Sai Kuma ya'yan amarya wato Anah, lokacin da ya auro Anah mahaifiyarsa da danginsa basa sonta kwata kwata dan daƙyar ma suka bari akayi auran abunka da rabo dan da cewa sukayi ba zaa yiwa Hajiya Zunaira kishiya ba. Anah ma ya'yanta huɗu Afiya itace babba sai Durrah sai Amjad sannan Auta Adla . Alhaji Hashim mutum ne dake son ya'yansa a jikinsa Amma Hajiya Zunaira ta janye ya'yanta ta ɗaura su akan cewa su gina nasu karsu bi mahaifin su su tayashi ya kafa kansa alhalin suna da yan uba, komai ya tara tare zasu raba, hakan yasa yanaji yana gani ya'yan hajiya Zunaira suka gagare shi dole ya haƙura ya bar mata su ya kuma ja bakinsa yayi shuru ya zuba musu ido, har zuwa lokacin da Anah ta haifi Amjad, Alhaji Hashim ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗaura masa ko bacci a jikinsa Amjad yakeyi hakan yasa ya taso kamar wani abokin sa, a lokacin da Amjad ya girma ya mallaki hankalin kansa sai mahaifin nasa ya ɗaura shi akan komai nasa dan ko abokan kasuwancin sa da yawa sun ɗauka Amjad ne kaɗai ɗansa namiji dan shi suka sani. Ba wani sirri tsakanin sa da mahaifin sa dan basa boyewa junan su komai harta mahaqar golds ɗin sa da ba kowa ya sani ba Amjad ya sani. Lokacin da su Julaybin suka buɗi ido suka kuma farga da yadda Amjad ke tsaye akan komai na dukiyar mahaifin su ga kusancin dake tsakanin su, a lokacin ne wutar ƙiyayyar sa ta huru a zuciyar su, nan suka fara Neman hanyar da zasu matsar dashi su dusashe taurarin sa sannan su ɓata shi a idon duniya, har suka nemo wasu mutane suka biyasu suka fito suka shaidawa duniya cewa Amjad ya yaudari yarsu ya mata fyaɗe, ɗan iska ne bashi da aiki sai lalata qananan yara, harda shigar da ƙara a kotu, basu barshi haka ba suka bi ta ƙarƙashin ƙasa inda aka fara raɗe raɗin cewa Amjad ɗin na safarar mutane ƙasashen duniya, wanda hakan ya sanya jinin mahaifin su ya hau sosai har ya yanke jiki ya faɗi inda ya kamu da cutar locked in syndrome wadda aka fi sani da paralysis . WANNA KENAN. Alaqar dake tsakanin su da Ahuoyzah kuma Kan batun kasuwanci ne, shi Ahuoyzah yana da nasa matatar man fetur ɗin Amma kwata kwata baiyi sunan da HD refinery tayi ba, haka yasa suka shirya poisoning din Alhaji Hashim ta hanyar haɗa baki da na kusa dashi domin a sanya masa gubar dake ƙone jini ya mutu, ALLAH bai basu Sa'a ba, sai suka sa aka laqabawa Amjad sharrin fyade da Kuma kasancewar sa ɗaya daga masu masu safarar mutane, domin Ahuoyzah ya samu Inganta nasa refinery ɗin a idon duniya ya maye gurbin HD refinery, su Hajj zawaad Kuma duk yaran sa ne . WANNAN KENAN. Ramphant juwaira sabon Dan kasuwa ne me tasowa, dan a yanzu ne ya kafa tasa refinery ɗin shima Kuma yakeson gogawa cikin wa'annan manyan a lokaci guda. Akwai number yabo da kasashe ke bawa duk ma'aikatun man fetur ɗin da suka fi kowa fitar da mai a duk ƙarshen shekara, shine tsakanin Ahuoyzah da Ramphant yanzu suke takarar karɓar wanna number yabo dan yanzu Babu HD refinery a lissafi . TO KUNJI YADDA ABUN YAKE, SHIN WAYE ZAI KARƁI WANNA NUMBER YABO TSAKANIN WA'ANNAN BIYU? KUMA MA WAI A CIKIN SU WAYE YA AIKATAWA ALHAJI HASHIM DA ƊANSA WANNA AIKIN ? KO KUMA DUKKAN SU NE? IN DUKKAN SU NE YA AKAYI TUNANIN SU YAZO ƊAYA NA ABUNDA ZASUYI ? 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd STEP 1 PAGE _______28 & 29 Ko da ta shiga ɗakin Sahnish ɗin bacci ta sameshi yanayi saboda harda maganin bacci suka bashi dan ya samu hutu, fitowa tayi ta jawo masa ƙofar sannan ta koma ɗakinta. Ranar bata samu wani baccin kirki ba kawai dai tana kwance ne ita ba ido biyu ba ita ba bacci ba, hakura tayi ta tashi ta zauna tare da dauko wayarta ta duba lokaci 3:03am, maida wayar tayi ta ajje tare da tashi ta fito mutum ta gani tsaye a bakin rijiya Yana ɗiban ruwa daga shi sai shortnicker wanda hakan ya bayyana murdaddun tsokar jikinsa wanda ke shafe da gargasar lallausan bakin gashi, shagala tayi da kallon sa saboda akwai wuta a lokacin har bata san lokacin da ya gama ɗiban ruwan ba ya ɗauka ya wuce ɗakinsa, da kallo ta bishi dan sarai tasan ya ganta ɗauke Kai kawai yayi, ajiyar zuciya ta sauke tare da wucewa zuwa ɗakin Sahnish da har lokacin yake bacci dan haka ta ɗauki bokitin sa dake gefe a ɗakin taje ta dibo masa ruwa ta dawo ta ajje masa sannan ta koma ɗakin su ta ɗauki nasu ta ɗaibo rabi saboda ciwon dake hannunta idan ta ciccika baza ta iya ɗauka ba. Komawa tayi ta zauna har aka Kira sallah ta tashi taje ta ɗauro alwala, ta tashi Shazeen ma taje tayi. Raka'atanil fajr suka farayi sannan suka tada sallah, tashi tayi ta fita bayan sun idar ta bar Shazeen na azkar ɗin safe, ɗakin Sahnish ta koma har lokacin bacci yake ƙarasawa tayi tare da fara tashin sa, "Sahnish! Sahnish!!"......... Wani irin fargaba tare da tsoro ne ya dirar mata ganin ko motsi baiyi ba, hakan ya sa ta daddage ta Kai Mai duka a dantsen hannun sa tare da Kiran sunan sa da dan karfi. Bude ido yayi yana kwaɓe fuska alamar zafi ya ce, "Me na Miki da sassafen nan zaki fara duka na?"......... Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi kana ta ce, "Tashi Ka makara har an idar da sallah". Tashi yayi zaune ai da sauri ya saki yar Ƙara, "Wayyooo ALLAH"............saurin riqeshi tayi tana faɗin, " sannu har yanzu kafadar ce?"...........Daga Mata Kai yayi alamar eh. Cikin tausayawa ta ce, "Sannu, zaka iya tashi ko in samo ma botiki kayi alwalar anan basai kaje waje ba eh?".......... "To ". Ya ce kawai tare da jingina da bangon ɗakin. Tashi tayi ta fita tana waiwayen sa harda cin tuntube bata dade ba ta dawo da wani ɓantararren bokiti da buta, a tsaye ta same shi yana ƙoƙarin fitowa. "Ana Kai da na tafi ɗauko ma kuma Ina zaka". "Zan Kama ruwa ne, zan iya ai karki damu".........." Muje to ". Ta faɗa tana taimaka masa suka fita daga ɗakin , tana tsaye a tsakar gidan har ya gama abinda zaiyi suka koma ɗakin nasa yayi sallar sannan ya koma ya kwanta, sannu ta dinga jera masa har ya koma bacci kamar ba ita bace jiya take cewa gwara ya mutu kowa ya huta. Tashi tayi ta fita, ta rasa me zatayi zuciyar ta gabaɗaya a cinkushe take, haka duniyar ma juya Mata take dan abin da zasu karya ma in tayi wasa sai ya gagare su, Dan kuɗin da take jalalawa bai kai ya kawo ba Shazeen ta fara zazzabi sukayi jigilar allura daga nan Sahnish shi ma ya amsa shikenan dan ragowar kuydin shi ma yabi ruwa sai abinda ba'a rasa ba yan canjin da basu fi dubu daya da ɗari biyu ba, gashi har yanzu wata baiyi ba bare ta karɓa albashin ta. Ɗaki ta koma ta zauna tare da zubawa Shazeen ido wadda ta koma bacci akan abun sallah, a zahiri Shazeen ɗin take kallo Amma a baɗini hankalin ta yayi wani wurin, har saida rana ta fara fitowa sannan ta tashi Shazeen dan tayi Wanka tayi shirin makaranta saboda ita yau batajin zata fita aiki kawai zata kira hajiya ta sanar da ita baza ta samu zuwa ba. Tana nan zaune har Shazeen ta shiga wanka ta fito ta sanya Kaya anan ne tasan dole fa saita tashi ta samowa mata abinda zata karya. Hijabinta ta ɗauka tana faɗin, "Zanje na samo miki abinda zaki karya, zaki zauna nan ko zaki tafi ɗakin yaya?"........."Zanje ɗakin yaya ". Shazeen ɗin ta faɗa. "To muje".......... Hushaima ta faɗa tana fita daga ɗakin Shazeen ɗin tabi bayanta, saida taga ta shiga ɗakin nasa sannan ta juya ta fita waje da mamakin jin yau gidan nasu yayi tsit kamar an sauya mutanan ciki, duk wanna karaniyar da hayya hayya ɗin nan babu ita, wurin jamcy me abincin yan gayu ta nufa a nan Yar kasuwar dake ƙofar gidan nasu. Jamcy ɗaya daga cikin masu hayar gidan ne dake sana'ar siyar da abinci a kofar gidan, ta yi da safe tayi da yamma kuma kullum a wurin ta Hushaima ke siya musu abun Kari haka abincin dare dan tunda sukazo basa girki. " Sannu Jamcy". Washe baki Jamcy tayi da faɗin, "Hajiya Hushaima har an fito kenan?". "Eh whl, Danwake zaki bamu". "To take away nawa ? Sannan me kwai ko marar kwai?". "Marar kwai, take away biyu"........... Da saurin ta ta amsa da to sannan ta hau zubawa, ta gama ta miqa Mata . "Amma Jamcy yanzu babu kuɗi a hannuna in na fito anjima zuwa dare zan baki"...........Ta faɗi haka ne saboda bata son taba kuɗin hannunta duk rintsi bata yarda ta bar hannunta ba komai tunda har tasan ba wani suka ajje da zasuje ya basu ba in wani abu emergency ya taso, dama jiya da ba dan abinda ya faru ba ta ƙudindi ne su ne ta bawa me tuktuk nasa ta maqale ragowar dan ko shi Sahnish ɗin baisan ta rage wannan ƴan kuɗin ba. "A'a Hushaima kinga Kar muyi haka dake, in kina da kuɗi ki biya ki tafi, in baki dashi ki ajje min kayana akwai masu saya ". Ta faɗa dan tasan irin su Hushaima idan kayi bashi dasu kun dinga rigima kenan, ballatana ita da take ganin rigimarta ta girmi ta kowa ba kuma zata iya ja da ita ba. Shuru Hushaima tayi can Kuma ta ce, " Shikenan naji, yanzu abinda za'ayi bari in na shiga ciki sai na ɗauko miki kuɗin, yanzu na bar Shazeen ciki tana jira kuma makaranta zata kar ta makara". Miqewa Jamcy tayi cikin rashin mutunci ta ce, "In kin isa na zama titi mota ta dinga bi ta kaina, Nima fa bar gani na haka duk wani salon tantiranci na sanshi dan haka in kinga kin bar nan to kin ajje min kayana ko kuma kin bani kuɗi na, ina ruwana da wata Shazeen , Shazeen ɗin banza Shazeen din wof........" Bata ƙarasa ba taji wani Abu me dumi a bakinta ɗagowa tayi tana kallon Hushaima dake tsaye tana huci ta ƙanƙace birkitattun idanun nan nata ta da lpy lau ma rikita mutum suke bare kuma zuciyar ta motso. Tofar da abun daya taru a bakinta tayi sai ganin jini tayi guda guda tare da hakori guda ɗaya . "A duk Ranar da wanna ƙazamin bakin naki ya sake furta wani abu marar kyau Kan Shazeen to dukkan wa'annan jerin hakwaran naki saina wargaza su wawiya kawai" .............Ta Ƙarashe tana wurga mata ledar ɗan waken a fuska ta juya ta bar wurin ranta a bace. A soro ta haɗu da Baba ilerika da alama yau a gida ya kwana, ya sha sabuwar shadda sai kyalli take harda kafa hula aka wani karkaceta gefe, tafiya yake yana wani cilla ƙafa irin duniya daɗi ɗin nan tare da raira yar wakar sa ta mamman shata, fura me nonooo gyadar da sai in ka sauka cikin daji........" Ganin Hushaima ta shigo rai bace ko ganin gabanta batayi ya sashi kaucewa ya bata hanya ta wuce, "tou ALLAH yayi dare gari ya waye, yau kuma wani me Iftila'in safen ne ya taɓo wanna ruwa biyun?"............ leqa cikin gidan yayi kamar zai bita sai kuma ya fasa, "Kai gwara dai nayi tafiya ta kawai, bari ma kaga kashe wayar nan zanyi Kar ma a neme ni dan yau nisan zango zanyi "......... Ya faɗa Yana zaro wayar tasa ya kashe bai gama maidata aljihu ba yaji sautin wani ihu a kunnen sa. A lokacin da Jamcy ta gama gane me ya faru da ita wani irin ihu ta zunduma ta Ƙara kurma wani, tsirarrun mutanen gidan nasu da suka maida layin ƙaramar kasuwa suka yo kanta da gudu dukda yau ko rabinsu Babu a wajen. Da yawa sunga ganin abinda ya faru wasu Kuma basu lura ba, da sauri Baba ilerika ya fito ganin jamaa zagaye da Jamcy ya sashi ƙarasawa da sauri Yana tambayar, "Meya faru?"........ Ɗaya daga cikin yayansa ne me suna Bagimba ya ce, "ita da wanna yar hau ɗin daka kwaso mana ce". "Ashsha ashsha subahanallahi meya faru haka? Me ya hada su?". " A gsky Baba ilerika Ka kawo mana bala'i da masifa a cikin gidan nan, shikenan yanzu kuma an fara daga waje, wasa wasa abun ya fara dawowa cikin gida, to whl ko ka sa su bar gidan ko mu mu barshi, Ina dalilin wanna Abu". Faɗin lady Cyama. Yar charas ta ce, "Ni fa duk kallon su nake yadda suke tsayawa take musu illa, ai whl dani ta taɓo Bala'in mu bazai ƙare ba saidai mu tona rami mu binne Kan mu, ita ɗin banza in aljanu take ji dashi Ni bishiyar kuka ma a kai na ta ƙarƙace". "Yanzu kun tsaya kuna ta magana ku taimaka Ku kamata a kaita chemist mana ko bakwa ganin har yanzu bakinta jini yake ne".......... haka dai aka kwashi Jamcy aka wuce chemist da ita, Wanda suke da abun sayarwa kuma a wurin suka koma bakin kasuwancin su suna maida zancen yadda akayi. Ita kuwa Hushaima ko da ta koma ciki, ɗakinsu ta shiga ta ɗauko ragowar kuɗin ta nufi ɗakin Sahnish, a zaune ta same su shi da Shazeen dan sakin fuskarta tayi dan kar Sahnish ɗin ya fahimci wani abu ta ce, "Saida kika tasheshi ko Shazeen?". "Dama baccin nawa baiyi nisa ba naji shigowar ta".........." To tashi muje na miqaki makaranta karki makara, nan basu fara komai ba, ko ƙosai na siya Miki a hanya".......... Tashi Shazeen tayi ta yiwa Sahnish sallama suka fito, ɗakinsu ta shiga ta ɗauko jakarta sannan Hushaima ta kulle ɗakin, wayarta ce tayi ƙara, Ɗan tsayawa tayi ganin Amla ke Kiran, picking tayi ta maqala a kunne, "Hello Amla?". "Hello bestie kina gida ?". "Eh Amma zan Kai Shazeen makaranta yanzu na dawo". "Okay thom gani nan zuwa ki turomin address ɗin naku, Sahnish Yana nan ai?". "Eh yana nan baya ma jin daɗi ne ". "Subahanallahi ALLAH ya bashi lpy, turomin ɗin kawai sai nazo"......... Da "To". Ta amsa sannan sukayi sallama ta kashe, ajiyar zuciya ta sauke tare da kama hannun Shazeen ɗin sukayi waje. Saida ta tsaya ta siyawa Shazeen da Sahnish ƙosai a leda daban daban sannan ta tsare musu abun hawa suka wuce, Saida taga shigar Shazeen ɗin cikin makaranta sannan tace da me tuktuk ɗin ya juya da ita, daga hanya tace ya ajjeta sanin in tace ya maidata inda ya ɗauko su kuɗin zaiyi yawa. Da ƙafarta ta taka har gida tana shiga ta wuce ɗakin Sahnish, Yana kwance Amma ba bacci yake ba kamar dai me tunanin wani abu, ajje masa ledar tayi a gabansa da faɗin, "Ɗauki kaci ka samu ka sha magani". Kallon ta yayi da faɗin, "ke kuma fa?". "Naci".........Ta amsa ba tare data kalle shi ba. Bai sake cewa komai ba, ita Kuma ta juya ta fita ɗakinta ta koma ta share ta kimtsa komai a muhallin sa, Kira ne ya sake shigowa wayarta ta, da sauri ta ɗauka da faɗin, "Hello Amla!". "Gani a kan layin kizo ki shigo dani". Da "To". ta amsa sannan ta tashi ta fito gaba da gidan kaɗan ta hango wata mota mai huci duk da ba motar da Amlan tazo rannan bace Amma ta san dama Amla bata hawan mota ya wuce wata ɗaya bata sauya wata ba, Dan haka ta nufi wurin, tun kafin ta ƙaraso Amla ta buɗe motar ta fito tana wani yauqi kana ganinta kaga model, sanye take da farin jeans da riga doguwa data kai mata har qauri tana da yanka daga both side tun daga kan faffaɗan waist ɗinta har ƙasa red colour, sai wani dan ƙaramin veil data yafa Wanda ya zame daga kanta ya koma kan kafaɗarta, gashin nan daya sha kuɗi sai ɗaukan ido yake, ga ƙafarta tasha wani arnen heels. Rungume juna sukayi Hushaima ta ce, "Yanzu nake shirin kiranki in ji ALLAH yasa ba kwantaccen nawa kika kasa ganewa ba, Kar naje na ɓatar da yar mutane azo a naɗeni". Ɗan dukan kafaɗarta tayi tana dariya ta ce, "ke kin fiya Neman Magana, yanzu mu ƙarasa ciki dai, ya jikin Sahnish ɗin". " Da sauki fa "........... Ta faɗa tana wucewa suka ƙarasa ciki, da wani irin kallo Amla ta dinga bin gidan da mutanan cikin sa dan bata saba ganin irin wanna rayuwar ba, saboda ita banda dalilin Hushaima Amla duk mu'amalarta da masu hannu da shuni takeyi. A ɗakin Sahnish ta musu masauki, yana zaune yaga shigowar su, ledar pure water da ya Sha magani ya ajje gefe yana faɗin, "Amla kece tafe?"........." Ni ce Sahnish, ya kake? ya jikin?". " Da sauki Alhamdulillah"...........Ita kuwa Hushaima ɗan kwalin kanta ta cire tare da zama tana faɗin , "Sahnish kasha magungunan naka?" "Na sha yanzu, ga wanna ragowar na kasa cinyewa whl "........... Ya faɗa yana nuna Mata ƙosan da ya rage mata, dan yasan bata ci ba kawai ta faɗa ne. Janyo ledar tayi tana faɗin, "Ai baka ci komai ba akwai abinda kake ji ne?". "Babu komai whl kawai baki na ne ba dadi". "Zazzabin nan ne ko?".............Amla ta tambaya tana bin ɗakin da kallo. "Shi ne whl, Shazeen ce ta fara sannan ta miqamin"........... Sahnish ɗin ya yi saurin tarar zancen gudun Kar Hushaima ta faɗa zancen abinda ya faru jiya da daddare, dan shi Sahnish mutum ne me shegen son sirri. "Gsky Hushaima banajin daɗin abinda kike min".......... Faɗar Amla. Gyara zama tayi tana buɗe ledar ƙosan ta ɗauka ta fara ci da faɗin, "Me nayi kuma ni da kullum a cikin laifi nake a wurin ki". "Shin wai miye laifi a ciki dan kina da bukatar Abu kin tambaye ni ne". "In ina da bukata kikace, ni kuma alhamdulillah". "Shikenan ya Miki kyau Hushaima nagode, yanzu dukkan Ku anan ɗakin kuke?". "Dakin Sahnish ne nan, ni da Shazeen kuma ɗakin dake farkon wanna". "Zan sake yiwa Mommy magana, gsky yaso ko kafin a samu wani gidan ne sai Ku dawo wurin mu". Dakatawa tayi da cin ƙosan da take ta ce, "Amla dan ALLAH karki matsawa mommy lalle saita amince mun zo mun zauna a gidan Ku, mu bar maganar nan dan ALLAH in dai har ba kina so ta gane har yanzu muna tare ba ki shiga matsala kuma". Shuru Amla tayi can kuma ta ce, "shikenan Amma dai......." Dan shuru tayi can Kuma ta ce, "Dama abinda ya kawoni Kan batun thumb print ɗin su Sahnish ne da za'ayi yau shine na zo muje, kuma Naga bashi da lpy, ya za'ayi kenan?". "Zai iya mana, in lokaci ya wuce kuma ai zamu saki asara, Abu dai na dan lokaci Sahnish tashi kaje ka watsa ruwa ka shirya, bari ma na Kai ma ruwan". "To ai kema sai ki shirya mu tafi taren".......... Kamar zatace ah ah sai kuma dai tace to tare da tashi ta fita da ledar ƙosan, bata jima ba ta dawo ta dauki bokitin ruwan data ɗaibo masa dazu ta Kai toilet ɗin tsakar gidan, ta dawo, tashi yayi ya dauki kayan wankan ya fita ita kuma ta ce, "Muje daki na, na shirya kafin shi ma ya gama" . Tashi Amla tayi tabi bayanta suka wuce ɗakin su. "Ke kuma me ya sameki a hannu"....... Amla da sai a lokacin ta lura da hannun Hushaima da take ta boɓɓoyewa dan kar Amlan ta gani. "Ki bari fa yanke wa nayi da ƙarfen ƙofa jiya da daddare"........kamo hannun tayi tana dubawa ta ce, "Amma fa ta yanke ki sosai, kinyi allurar TT?". Zame hannun tayi tana faɗin, "Ina da ita ban dade da yi ba ai". Ta ƙarashe tana rage kayan jikinta ta wuce bathroom ɗin. A gurguje tayi wanka ta shirya sannan ta ɗauki gyalenta da wayarta suka fito ta kulle ɗakin ta jefa makullin a aljihun doguwar rigar atampar dake jikinta, ta wuce ɗakin Sahnish domin sanar dashi suna jiransa. Basu jima ba suka fito tare shi ma ya shirya, ita ta kulle masa ɗakin sannan ta miqa masa makullin suka jero zuwa waje, yayinda mutanan gidan suka bisu da ido ganin Amla a tare dasu dan basu taɓa Tunanin suna da wani dan uwa ko abokin arziki me kuɗi ba. Suna Kai wa soron ƙofar gida yan sanda na shigowa tare da Jamcy dasu lady cyama, "Yauwa gata nan ita ce".......... Jamcy ta faɗa tana nuna Hushaima da hannu. Wani irin kallo Amla ta yiwa Hushaima kafin ta ce........... ----------------------√ Amjad ko da ya bar asibitin gidan sa ya koma a can ya samu Hunaiz zaune cikin mota yana jiransa. Bayan Kamal yayi parking ya fito ya buɗe masa shi ma ya fito, direct wurin Motar Hunaiz ɗin ya nufa, Yana zuwa ya ɗaura hannunsa kan murfin motar dake buɗe, kyakyawan matashin saurayi ne zaune yana latse latse a waya, ɗaya hannunsa Kuma riqe da can ɗin coke da yake sipping kaɗan kaɗan, ɗagowa yayi jin kamar tsayuwar mutum a Kansa, ganin Amjad tsaye ya sashi sakin dan murmushi da faɗin, " Yaushe ka shigo ne, tun ɗazu nazo akace baka ƙaraso ba sai kawai nace barin jira, har na fara tunanin ko ka wuce can gida wurin su Anah". Dan girgiza kansa da ke masa ciwo kaɗan yayi da faɗin, "Nop, muje ciki".......... Ya ƙarashe tare da sakin ƙofar ya juya ya wuce ciki, sake gyara zama yayi yana cigaba da abinda yake kamar bai san cewa Amjad ɗin na jiransa ba, har saida kiran sa ya shigo wayar, dan bata fuska yayi alamar irin an katse masa wani abu me muhimmanci da yake yi, kashe wayar yayi ya fito yana tafiya cike da ji da kai irin na samari masu tasowa yan 24-25, Yana shiga ya same shi a falon farko yana zaune ya zubawa ƙofar shigowa ido alamar shi yake jira. Zama yayi da faɗin, "Sorry na ɗan tsaya duba wani abu ne"........bai bi ta kan zancen sa ba ya ce, "komai ya kammala ne?". Gyaɗa masa kai yayi alamun tabbatar wa kana ya ce, "Yes ni dai na gama nawa, duk abinda kace shi nayi, sai kuma muce ALLAH ya nuna mana goben lpy". "Nagode bros, ALLAH ya saka da alheri"........ Murmushi ya ɗanyi sannan ya ce, "Juraysh ya Kira ni yana tambayata wai me ke faruwa ko sunyi magana da Anah ne ko yaya ne, Ni ban fahimce shi sosai ba, sai nace masa ina tare da abokai na i will call him back, saboda tunda naji yana tambaya nasan maybe bakuyi waya bane". "Yea, bamuyi ba, Amma zan kirashi anjima in Sha ALLAH". "To shikenan ni bara na wuce". "Alryt sai mun haɗu goben"........ya faɗa Yana miqewa sukayi sallama da Hunaiz ɗin ya wuce, shi ma ɗaki ya wuce, kusan kaman 30 minutes ya sake fitowa ya zauna, daidai lokacin Nazbeer yayi sallama ya shigo, wuri ya nema a ƙasa ya zauna da faɗin, "Gani boss ". "Ina bayanin da nace Ka samo?". "Boss kamar yadda na gaya ma ne wancan motar ta qone ƙurmus, Amma duk binciken da akayi ya nuna babu mutum a ciki lokacin data tashi da wutar". A hankali ya fitar da numfashi kafin ya ce, "Ya speed ɗin su yake a lokacin da sukayi accident ɗin? Sannan kuma daga bugawar tasu motar ta kama da wuta ko kuma an dau lokaci?". Gyara zama Nazbeer yayi kana ya ce, "Ita wancan motar ta ƙure gudun ta dan kamar da gangan ta tunkaro motar data fita gidan nan, sannan kuma anja kamar seconds 100 kafin motar ta kama da wuta"......... Shuru yayi tare da daga kansa sama tsawon wasu mintuna kamar me wani lissafi, can ya ce, " Shikenan, jeka Ka turomin jack". "Okay boss"........... Ya faɗa tare da tashi ya fita, shima tashi yayi ya shiga ɗaki ya ɗauko ƙaramar system ɗinsa ya dawo ya zauna, kaɗan kaɗan yake danna keyboard ɗin kamar me tsoron wani abu, cikin wanna yanayin jack ya shigo, bai ɗago ba saida ya gama shigar da abinda yake sannan ya dago, wasu takardu jack ya miqa masa, karɓa yayi ya fara dubawa tare da Kai hannunsa goshi a hankali yake buga goshin nasa da yatsansa manuniya yana sake bin rubutun kafin ya rufe ya dago yana kallon Jack daya nutsu cikin shirin amsa ko wace irin tambaya. " Jack, are you sure no one knows what we discussed and what you were gonna do?”. "No one boss, infact ban ma tafi da motar gidan Nan ba, sai na ari ta wani aboki na"........ Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon wayarsa dake haske ya ce, " you can go, I will call you later"........" Okay boss "...........Ya fada tare da tashi ya fita, ɗaukan wayar sa da system ɗin sa yayi ya wuce ciki tare da locking ƙofar sannan ya rage light ɗin ɗakin, sannan ya ɗaga wayar, daga daya bangaren Kamar wanda aka sawa bindiga a kai Widad ya ce, " Wai meysa baza a taɓa ma kira ɗaya ka ansa bane, ka san uzurin da ya sa na Kira kan ne".........Shuru yayi kawai dan shi bai iya ja in ja ba a rayuwar sa, ko kuma ya tsaya yiwa mutum explaining reason dan Ka fahimce Shi. "Ina jinka". Ya faɗa tare da yin shuru yayinda shi ma widad ɗin yayi shuru daga ɗayan bangaren, Neman wuri yayi ya zauna dan yasan halin Widad, Saida ya gama dibidibitun sa sannan ya masa bayanin dalilin kiran. "Ka nemi wayar Ash ko Ace, zasu faɗa ma dan ni tunda na dawo ma banbi ta kan aikin nasa ba, dan nan ma na tarar da wani a gaba na"........takaici yasa Widad kashe wayar ba tare da yace komai ba ganin kayan haushin da Amjad ɗin yake neman cusa masa, ace damar da suka daɗe suna nema yanzu ta samu Kuma ya tsaya yana musu wasa da hankali. Shi kuwa Amjad ba komai ya sashi faɗawa Widad haka ba sai sanin cewa in yace shi zai masa bayani Widad ya dinga masa iskanci kenan, haka Kuma in ya haɗashi da kiara yasa kumammu biyu ya haɗa dan Kiara tafi Widad iskanci, gwara gwara ma Ace duk da shi matsalarsa rashin ɗaukan Abu serious kafin ya bawa abu mahimmanci sai ya dinga tsokane tsokane kenan, ita Kuma Ash matsalarta da widad wanna miskilancin nasa da take ɗaukan hakan kamar girman Kai, Amma dai gwara wa'annan biyu suna iyawa dashi. Ɗakin sirrinsa ya wuce Kai tsaye, bashi ya fito ba sai wuraren 2:30am sannan ya fito ya wuce kitchen ya haɗa coffee ya dawo falon ya zauna tare da Kunna TV, Yana sha yana kallo har sai da ya shanye sannan ya tashi ya wuce ɗaki, wanka yayi sannan ya sauya Kaya ya sake fitowa cikin shirin fita, zuwa lokacin karfe wurin 3 da wani Abu. Shi fa Amjad ba ruwan sa da dare saidai idan bashi da abun da zaiyi ne, amma in dai yana da Abubuwa a gabansa to shi lokacin ne ma ranar sa, dan yafi jin dadin aiki da daddare ma fiye da rana. Ni kuwa nace aikin dare ai na maras gaskiya ne in dai ba tsayuwar dare zakayi ba. Shi kaɗai ya fita dan ko Kamal bai ɗauka ba, sai 6am ya dawo gidan, ɗakinsa ya wuce baifi 10 minutes ba ya sake fitowa, yanzu tare dasu Kamal da Aram suka fita, main house ɗin su suka nufa. Ana buɗe masa kofar motar ya fice bai tsaya ko Ina ba sai ɗakin sa, ya shige yayi kwanciyar sa sai 9am ya fito ya sake ɗaukan wanka cikin tattausan yard Marar nauyi milk colour ya daura black p cap ɗinsa data zame masa dole, hannunsa sanye da wani diamond watch, kafarsa kuma sanye da wani Italian slip on sandal brown. Anah dake tsaye tana magana da masu aiki hango shi yasa ta sallamesu, ƙarasowa yayi yana faɗin, " Good morning Anah".........." Babban mutum dama a gida Ka kwana". Gyada Mata Kai yayi alamar eh sannan ya ce, "Yanzu ma sauri nake fita zanyi". "Ai kuwa ba inda zaka sai kayi break, dan jiya na tabbatar baka samu damar cin komai ba, ga idanun ka ma sun nuna baka samu bacci ba". Shafa fuskar sa yayi da faɗin, "Zanci fa in na fita Anah whl ina sauri ne".......... kallon sa kawai ta tsaya yi wanda haka ya sashi sunkuyar da kansa ƙasa, mamaki take yau Amjad ne ake cewa ya tsaya yaci abinci yana cewa sauri yake in ya fita zaici, sai kawai ta riqo hannun sa ta wuce dinning dashi, yana ɓata fuska yana komai haka ta sashi a gaba saida ya taba kayan karin duk da baici sosai ba dan daga jiya da magriba zuwa yanzu kwata kwata baya sha'awar komai, haka ya samu ya silale ya fita. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______30 & 31 "Ranka ya dade meke faruwa?". Amla ta tambaya tana binsu da kallo. "In munje can zaki ji, ke wuce muje". Dan sandan ya faɗa yana nuna wa Hushaima hanya da hannu, ni kuwa nace um um yallabai bi a sannu. "Dan ALLAH ranka ya dade me tayi?". Sahnish ya faɗa yana riqo hannun Hushaima. "Faɗa sukayi da wanna ta fidda mata hakori, dan haka dole sai muje can". "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un". Sahnish ya fada yana kallon Hushaima data ɗauke Kai kamar bata san anayi ba . "Ranka ya dade in ba damuwa ina so mu ɗan keɓe da ɗaya daga cikin ku muyi magana". Amla ta fada. Da sauri Jamcy da kumburarren bakinta ta ce, "Ranka ya daɗe ni fa ba zan yadda ba, duk ma wani abu da za'ayi sai anje can station yww". "Ke wai waya gaya Miki Ina tsoron station ko yan sandan naki da kika ebo, ni wanna ba baƙon wuri bane a wuri na, na saba dashi dan haka bana tsoron zuwa". Hushaima ta faɗa tana watsa wa Jamcy wata banzar harara. "Wai dan ALLAH baza kiyi shuru bane Hushaima, ranka ya daɗe muje daga wajen two minute please". Ɗan sandan nan na farko ne ya bita suka fita, saida suka kwashe kusan minti biyar su Hushaima na tsaye sai harare hararen juna suke har ɗan sandan ya dawo Amla biye dashi, kallon su Hushaima ɗin tayi da fadin, "ku muje Kar muyi late ko" . "Ke baiwar ALLAH kuje Ina, ranka ya dade ban gane suje ba". "Barsu suje, bashir jira mu a waje bari muyi magana, ke ma baiwar ALLAH ɗan jira mu "............Ya faɗa yana kallon ɗaya ɗan sandan da lady cyama, fita sukayi kamar yadda ya buqata, Dan already su Hushaima har sun fice. Sai da suka hau hanya Amla ta ce, "Yanzu fisabilillahi Hushaima baza ki daina abinda kikeyi ba".........Sahnish dake back seat ne ya cafe da faɗin, "Whl Amla kamar kinsan abinda ke raina amma ban isa nayi magana ba sai ta taso min da faɗa Wai na zama soko, ni ba namiji bane waye waye "..........." Hmmm, ALLAH ya kyauta". Kawai Amla ta faɗa daga nan suka yi shuru dama Hushaima bata ce dasu ci kanku ba tunda suka shiga motar. A cikin wata babbar makaranta tayi parking sannan ta buɗe ƙofa tana faɗin, "Muje ko". Buɗewa sukayi gabaɗayan su suka fito, da kallo suka dinga bin makarantar har suka isa wani ƙayataccen office. "Welcome Miss Amla ". Wata mata da akan table ɗin nata naga wani tag name da aka rubuta Mrs Jenny a ƙasa Kuma aka rubuta PC wato principal, cikin karramawa ta tare su, bayan sun gaisa ta ce. "Have a seat". Ta faɗa tana kallon su Sahnish ganin kujerar data nuna musu yasa suka gane me take nufi, zama sukayi Mrs Jenny ta ce, "is he the one, Miss Amla?". Ta faɗa tana nuna Sahnish. "Yes he's"........." Alright to amma zai ɗan jira saboda suna da ɗan yawa". "Gsky Mrs. Jenny, we're in a hurry, and he's not even feeling well. Can you do us a favor and let them go ahead with it now?".......... Ɗan shuru Mrs Jenny tayi kafin ta ɗauki waya ta kirawo wani Mr Anis, Ba'a jima ba ya shigo, nuna Sahnish tayi da hannu tare da faɗin, " Kuje dashi yayi thumb print nasa yanzu suna sauri zasu tafi bai jin daɗi ne".........." Okay ma'am ". Mr Anis ya amsa sannan yace, "let's go". Da sauri Amila ta ce, "Sahnish kuje ayi ma". Miqewa yayi suka fita tare da Mr Anis su Kuma suka jirasu anan, basu daɗe ba ya dawo har anyi an gama, sallama sukayi wa Mrs. Jenny sannan suka fita. Amla ce ta kalla agogon hannun ta da faɗin, "Wayyo na shiga uku". Saurin kallon ta sukayi Hushaima ta ce, "lpy dai? me ya faru?" . "Whl daddy ne ya bani saqo na kai wani wuri so na ɗauka zamu gama da wuri kafin lokacin gashi yanzu har time ɗin da ya bani na ƙoƙarin shigewa, dan ALLAH ku ɗan min hakuri muje na kai aikar sai na kaiku gida". "Kash Whl Amla wani lokaci kina da ban haushi, to miye a ciki Kuma, har sai kin wani ce muyi haƙuri ai da kin faɗa ma saqon zaki fara kai wa, yanzu muje mazaa kar mu ƙara ɓata lokaci"...... Da sauri suka ƙarasa wurin motar suka shiga Amla ta tada aka buɗe musu gate suka fice. Sunyi tafiyar kamar minti talatin kafin su tsaya gaban wani qaton gida kamar dai guest House haka gidan ya tsaru kamar a turai. Horn sukayi a gate ɗin security ne ya leqo tare da ƙarasawa ta side ɗin Amla. "Daga Ina?". Ya tambaya yana ƙare musu kallo. "Na kawowa me gidan naku saqo ne"..........Sai da ya sake Ƙare musu kallo sannan ya ce, "Ya san da zuwanku?". "Ban sani ba, amma kace masa daga alhaji Zawaad"...........Juyawa yayi ya koma ciki ba daɗewa sai gashi ya dawo, buɗe musu gate ɗin yayi suka shiga, a makeken parking lot ɗin da zai iyacin sama da mota 20. Parking Amla tayi tana kallon yanayin gidan wanda daga can gefe aka fasalta shi kamar wani Chambers, buɗe dashboard storage ɗin motar tayi ta ɗauko wani file tare da faɗin, "Hushaima muje ki rakani, Sahnish kai sai ka dawo nan driving seat ka zauna Ka jiramu ko".......... Da "to". Ya amsa sannan suka buɗe ƙofa suka fice suna sake ƙarewa tsarin gidan kallo especially Hushaima data zama wata yar ƙauye a wurin, dan gsky tsarin gidan ya haɗu matuqa gashi dai gida ne amma kuma gefe guda an ware an fitar da ɓangaren office office. Gaban building ɗin ofisoshin suka tsaya, wurin wani mutum dake tsaye sanye da uniform, Amla ta ce, " Am ko zaka yi mana jagora zuwa wurin me gidan"..........."Me gidan ai ya daɗe ba lpy sai ɗansa Oga Amjad dake zuwa shi ma ba kullum ba, amma dai yanzu kunyi Sa'a yana ciki". "To Dan ALLAH yi mana iso, saqo na kawo masa". "Muje to" .......... Ya faɗa Yana wucewa ciki. "Ni Kam Amla je ki fito kawai, wurin nan ya min kyau Ina so na ɗan zagaya kafin ki fito". Ta faɗa tana bin wurin da kallo cike da shaawa dan har cikin zuciyarta wurin ya burgeta. "Ah ah in baza ki shiga ba to ki koma mota, ai ba haka mukayi dake ba, haka kawai kije ki ɓacemin in zo tafiya in rasa inda kike". Amla ta faɗa dan tasan halin Hushaima kar taje ta kwaso mata magana Saisa ta faɗi haka. "To naji shikenan, barni na koma ɗin".........Ta faɗa tana juyawa ta nufi motar, girgiza kai Amla tayi tabi bayan security ɗin nan. Saida taga shigewarta sannan ta juyo cikin shauqi take bin flowers ɗin da kallo wasu ta shafa, wasu ta cira, wayarta ta ciro ta shiga Snapchat ta fara ɗaukan hoto har bata san lokacin data tsinci kanta a cikin wani ƙayataccen garden ba, sake gyara wayarta tayi tana cigaba da ɗaukan pics ɗin, wasu ƙananun karnuka ta hango irin na turawan nan da zaku ga suna tafiya gashin jikinsu na jan ƙasa, ɗan komawa tayi da baya ta laɓe ba wai dan tana tsoron karnukan ba sai dan tana gudun su ganta suyi haushin nan nasu, dan ba abinda ke saurin hargitsa mata lissafi irin Kukan Ƙare, daga inda take laɓe ta cigaba da ɗaukan hotonan view ɗin harda karnukan, kwata Kwata bata lura da mutum a wurin ba. Amjad dake tsaye yana waya tunda ta shigo tana ɗauke ɗauken hoto yake kallonta ta ƙasan ido, juyowa yayi dakyau daidai lokacin da ta laɓe a jikin ginin saboda hango karnukan da tayi amma sai yaga still ɗaukar sa hoton take, hannayenta da gefen fuskarta ya zubawa ido tare da faɗin, "Ina sane da komai Hanash, Kai dai ka cigaba da aikin ka kawai, sannan ka tabbatar duk wani shige da ficen da za'ayi a sirrance ake yin sa, Kar kowa ya sani, tunda already an gama shirya komai, so ba wata matsala for now sauran maganganun zamuyi anjima, I'm going to attend to something now"..........Yana kai wa nan ya kashe wayar ba tare da ya saurari amsar na cikin wayar ba, ya nufi inda Hushaima take, ɗaya daga cikin karnukan ne ya fara haushi yana tsalle tare da bin ƙafar Amjad ɗin yana wasa, ai da wani irin sauri Hushaima ta bar wurin. Dakatawa yayi da tafiya tare da lumshe idanun sa ya buɗe, fasa bin wurin yayi ya juya ya shige ta ƙofar baya. Ko da ta fita daga garden ɗin direct inda su Amla suka shiga ta nufa tana haki tsabar rikicewar da tayi har wani duru duru take gani dafe bangon tayi tana sauke numfashi. "Are you alright?"......... Ɗagowa tayi ta ga wata mata tsaye tana kallon ta. "Da ALLAH ko kinga ƙawata data shigo yanzu Ina tabi?".......... Kallon rashin fahimta matar take mata dan batajin hausa, wani saurayi ne da ya fito daga wani office yana tsaye gaban wasu print server yana printing ya ce, "I think she's with the Oga Amjad guest, excort her, she's in that office".......... Saurayin ya faɗa yana ƙarewa Hushaima kallon tsaf, dan baza ka taba kallon ta kace irin yaran nan ne dako wuqa ƙasa musu a kai baza su iya ko da rubuta sunan su bane, saboda Hushaima ta samu wayewa sosai karatun ne sai a hankali, amma dai zamuji komai nan gaba. "Okay let's go". Matar ta faɗa tana nuna mata hanya tare da shigewa gaba, bin bayanta tayi har zuwa wani madaidaicin office, ba tarkace sosai a cikin sa, table ne kawai da main chair sai guest chair guda ɗaya wadda Amla ke zaune tana ganin ta tayi saurin miqewa tana tambayar, "Me ya shigo dake kuma, ke da kikace kin fasa shigows?" . "So you are together, right?"......... Matar ta tambaya. "Yes". Amla ta amsa, bata sake cewa komai ba ta juya ta fita tare da ja musu ƙofar. Gaban table ɗin ta Ƙarasa tana cire gyalenta ta hau firfita da hannunta. "Wai me ya faru ne?".......... Amla ta tambaya tana binta da kallon tuhuma. "Kare". Ta bata amsa har lokacin wata juya juya take ji. "Mtweee wai Kare ke kin fiya tsoro whl, ni duk na ɗauka wani abun ne ma, ina Sahnish ɗin?"........."yana mota mana". Ta faɗa tana zagayawa ta zauna kan main chair dake office ɗin tanajin kamar zata kifa. Bata fi two minutes da zama ba aka buɗe ƙofa, shigowa yayi Philip biye dashi, da sauri Amla ta miqe saboda kwarjinin sa da ya cika office ɗin, "ina kwana?".......... Ta faɗa a ɗarare, Kai kawai ya ɗaga mata alamar lpy. Philip ne ya nufi wurin Hushaima da sauri cikin faɗa ya fara faɗin, "Come on, get up, who gave you the right to sit in the boss’s chair". "Hushaima tashi mana, ko bakiga mai wurin yazo bane ". Amla ta faɗa da sauri. Ɗagowa tayi ta kalla Amla sannan ta kalla Philip dake tsaye kamar zai Kai mata duka a fusace ta miqe tare da wurga kujerar baya da ƙafarta cikin fushi ta ce, "kujerar banza kujerar wofi, akan kujera zaku kamawa mutane ihu a ka, kujerar lu'u lu'u ce ko ta zinare aikin banza aikin wofi".........ɗaga hannu Philip yayi zai kai maketa Amjad ya girgiza masa Kai alamar Kar yayi sannan ya zagaye su dan isa ga kujerar tasa, saidai bai gama wucewa ba Hushaima ta tsirtar da yawu tare da jan tsaki. "Hushaimaaaa me haka? lpyr ki kuwa? Zo ki fita to, tafi ki jirani a can". "Dama zan fita ai ko baki faɗa ba Kuma kema karki sake kice zaki ɗaga min murya yauwa"........ Philip ne yayi saurin shan gabanta da faɗin, " You can’t go anywhere, you disrespected the boss, you have to go, bend and tell him sorry before you leave". "Dan ALLAH je ki bashi hakuri to". "Whl ba'a haifi uban da zanje in bawa hakuri ba, gwara tun wuri ma ku cire wannan tunanin a ranku". "Hey, you know who the boss is and his dad here?". Cikin ɗaga murya kamar zata kai masa duka ta ce, "kaci durun uwarka da turancin, in ka Isa ka faɗa da hausa mana kagani". Ɗagowa Philip yayi ya kalli inda Amjad ke zaune kan kujerar sa hankalinsa kwance kamar baisan meke wakana ba, kamar yasan Philip ɗin shi yake kallo, sai ya ɗago shi ma, da hannu ya masa alamar ya bata hanya ta wuce kawai. Matsawa yayi Yana faɗin, "kinyi Sa'a whl amma da sai kinyi bayani ƙaramar marar kunya kawai"......... Juyawa tayi ta fice da sauri, komawa Amla tayi ta zauna tana satar kallonsa cike da mamakin wani abu data barwa kanta sani, haƙuri ta fara bashi ya katseta. "Go ahead and say what brought you here, I have things to attend"......... Ajiyar zuciya ta sauke a sirrance kafin ta miqa masa File dtin da faɗin, "Daddy na ne yace na kawo ma wannan". Karɓa yayi da faɗin, "Alryt, you can go". "Thank you". ta faɗa tare da tashi ta sake satar kallonsa suka haɗa ido da sauri ta juya ta fice. Takarda ya yaga a gefe yayi dan rubuta akai ya miqawa Philip tare da yi masa thumb, "Good job". "Thank you boss". ya faɗa tare da duba takardar sai Kuma ya juya ya fita . ______________A mota ta tarar da Hushaima sai ruwan masifa take kamar zata kama da wuta, shiga tayi da faɗin, "Gsky Hushaima baki kyauta ba ko kaɗan, kawai ki tofawa mutum yawu sannan kija masa tsaki, kinsan waye shi kuwa? Kuma ma tun farko ai da baki zauna a kujerar ba, ko kuma da kika jisu sai ki tashi ki bashi wurinsa, ALLAH ma ya taimakeki whl da yace a barki ki tafi dan nikam bani da ƙarfin fitar dake anan". "Wai meke faruwa?".......... Sahnish ya tambaya dan shi bai gane Kan masifar Hushaiman ba, shi dai kawai yana jin ta ne. Faɗa masa abinda ya faru Amla tayi bata ƙarasa rufe bakinta ba Hushaima ta ce, "In zaki maidani in da kika ɗaukoni ki maidani, in Kuma baza ki maidani ba in san inda rana ta min". Girgiza Kai Amla tayi tana cilla hancin motar ta Kan titi dan already ta saba da zafin zuciyar nan ta Hushaima. Wayarta ta ɗauka tana driving ta lalubo wata number da akayi saving da ride or die tayi dialing, Saida ta kusa katsewa akayi picking, "Hello Amla!"......... Handsfree ta danna hankalinta akan titi ta ce, "Nashwa ykk?" "Lpy kalau alhamdulillah". "Ina Nayrah ɗin?"........."Muna asibiti whl jiya ta samu accident." "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, wani asibitin ne Nashwa"........ta tambaya a rikice cikin tashin hankali. "General hospital, A&E section ". "Ina kusa da Asibitin bari na ƙaraso Nashwa ".......... Ta ƙarashe tana kashewa sannan ta ɗago da niyyar magana ta tsinci idanun Hushaima a kanta tana jifanta da wani kallon tuhuma, hankalinta ta maida titi da faɗin, "Besty ina friend ɗin nan tawa Nayrah da nake baki labari, to itace tayi accident, bari muje mu duba ta sai na kaiku gida ko". Hushaima da har lokacin idonta ke kan Amla, a dake ta ce, "Ba zani ba, sauke ni a nan".........."haba Besty dubiya fa akace, ai ko dan ladan da zaki samu kya je".......... Faɗin Amlan, saidai kafin ta rufe bakinta Sahnish daga bayan mota ya karɓe da faɗin, "ki sauke mu daga nan ɗin kawai Amla". Da mamaki Amla ta kalli Hushaima da yanayin ta yafi na ɗazu tsanani sannan ta kallo Sahnish ta mirror wanda shi ma daga kallon data masa ta fuskanci kamar mood ɗin sa ya canza, to meke faruwa? Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsar ta, sai kawai ta ce, "Shikenan muje na kaiku gidan sai na dawo". Ba wanda ya ƙara magana a cikinsu sai Amla dake mamakin sauyawar Sahnish ɗin dan a iya tsawon lokacin da suka kasance tare baza ta iya cewa ga lokacin da taga wani yanayi na daban a kan fuskar Sahnish ɗin ba, to me ya sauya shi lokaci guda? Ni kuwa nace ummm inji me ciwon hakori. Kowa da abinda yake tunani har suka ƙarasa gidan, tana tsayawa Hushaima ta Buɗe mota ta fice tayi shigewarta ciki ba tare da ta ko waiwaye su ba, Sahnish na ƙoƙarin fita shi ma Amla data ƙasa haƙuri ta ce, "Sahnish wai meke faruwa? Naga kai ma kamar yanayin ka ya sauya wanda kuma ba haka na shigo motar na sameka ba?"........... Dan jijjiga kansa yayi tare da faɗin, "Bakomai Amla, kai na ne ya sara whl, ina so ne dama naje na sake shan magani na huta "........... cikin gamsuwa da bayanin nasa ta ce, "Ayyah, ALLAH sarki, sannu kaji ALLAH ya baka lpy, dama sai a hankali zaka warware ". Ta ƙarashe tare da sanya hannu a jakarta ta ɗauko kuɗi masu yawa ba tare data irga ba ta miqa masa. Dukda yasan suna da buqatar kuɗin saida yayi shakkar karɓa a yanzu saboda wani dalili nasu shi da Hushaiman, maganar Amla ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi. "Ka karɓa mana Sahnish ba yawa". "Da kin barshi Amla, Kar mu ɗaura Miki nauyi da yawa ". "Bakomai Sahnish, Dan ALLAH Ka karɓa, Ni da ku ai duk ɗaya ne "........... Ba yadda ya iya dan yana matuƙar jin nauyin Amla ko dan ɗawainiyar da take dasu, haka ya karɓa ya sa a aljihu dan bazai tunkare ta da kuɗin yanzu ba saita huce sai ya nuna Mata. Sallama ya mata sannan ya shige ciki shi ma. Lokacin data shiga gidan bata ko kalli kowa ba ta shige ɗakinsu, kan yaloluwar katifar tasu ta zube tana jin kanta na wani irin Fisga ga zuciyarta dake tafarfasa, sunan ALLAH ta fara ambato kaɗan kaɗan ta fara jin nutsuwarta na dawo mata, abinda ya faru tsakanin ta dasu Amjad ne ya shiga dawo mata daki daki a ƙwaƙwalwarta kamar wadda aka tsikara ta zaune, "Shi ne, tabbas shi ne ko da a wancan lokacin ban ga fuskar sa sosai ba, amma ku ma suma Boss suka kira shi dashi".........Shiru tayi tana recalling scent na perfume nasa, na lokacin da suka fara haɗuwa da na yau. Hushaima akwai matuqar wayo take ta gane shi ne, tun daga kan yatsun hannunsa da Saida suka kwanta a kumatunta zuwa yanayin jikinsa, turaren sa tare da sunan da suke kiransa dashi. Dan baza ta kwanta da muryar sa ba tunda a yau baiyi Magana ba ballatana kuma fuskarsa wadda baza ta iya cewa ga kamanninta ba a haɗuwar su ta farko sai yau. "waye shi?"........... Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsar ta, wayarta ta ɗauka ta hau neman layin Amla amma bata ɗaga ba, cillar da wayar tayi tare da miqewa tsaye tana faɗin, "wataƙila wannan itace damar da zan samu ta ɗaukan fansa". Readers in baku manta ba ai Hushaima ta ɗau ƙudirin ramuwar abinda Amjad ɗin ya mata a ranar da suka fara haɗuwa to yanzu fa an tada tsohon giɓi ko ya zata kaya oho. Shuru tayi tana ɗan buga hannunta cikin na juna, wayarta da tayi ƙara ce ta dawo da ita duniyar mu da sauri ta matsa ta ɗauka ganin Amla. "Hello Ƙawata ".......... Cikin jin dadin jin muryarta haka alamun ta sauko Amla ta ce, "Besty w......" Tarar ta tayi da faɗin, "Waye wannan wanda mukaje wurin sa ɗazun?"......... Shuru Amila tayi kafin ta ce, "lpy dai?" "Lpy ni dai, dan ALLAH ki bani amsa ". "Amjad Hashim Darwin shi ne sunan sa mahaifin sa shine mamallakin HD AURUM MINING da Kuma HD REFINERY ai baza ki ƙasa sanin sa ba saboda sannane ne gidajen television na gida dana ketare duk suna yawan nuna su shi da mahaifin sa, saisa nayi mamakin abinda kikayi masa saboda Babban mutum ne". "Amla abinda na tambayeki daban amsar da kika bani daban, cewa nayi waye shi ba waye mahaifin sa ba". "To Besty ni abinda na sani ai shi na fada Miki k........." Bata ƙarasa ba Hushaima ta kashe wayar tana jan siririn tsaki. komawa tayi ta zauna ta shiga tunane tunane, a haka Sahnish ya shigo ya sameta ta zuba wa wuri guda ido, shigowar sa ya sata ɗagowa ta zuba masa ido har ya ƙaraso ya zauna gefenta tare da faɗin, "Anya ba su ba ne?"........... ɗaga masa kai tayi sannan ta ce, "Ba wai Sahnish su ne, ni lokacin da Amla take bani labarin ta ban taɓa kawowa su bane sai yau da naji muryar ɗayar". "Yaushe suka dawo garin nan da zama to"..........Shiru tayi ba tare data bashi amsa ba, hakan yasa shi ma yaja bakinsa, kowanne da abun da yake tunani can kuma Hushaima ta miqe ta ɗauki gyalen ta da waya tana faɗin, "Ni zan fita, in Barka a ɗakin ne ko ya?".......... Ganin yanayin ta ba yadda yayi tunani ba ya sashi zaro Kuɗin dake aljihun sa ya miqa mata, "Gashi nan Amla ce ta bayar". 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______32 Karɓa tayi ta irga dubu hamsin ne, talatin ta ɗauka ta miqa masa ashirin sannan ta juya da niyyar fita, kallon kuɗin yayi kafin ya ce, "Hushaima tsaya, wanna ai yamin yawa ke ce fa dawainiya take kanki, ki Ƙara ragewa"..........juyowa tayi ta kalle shi, "Wai kana nufin ni zan cigaba da wanna Kai kawon ne, dole fa Kai ma ka miqe ka san abunyi, zaman hakan ba zai ma ba, ya kamata ace komin ƙanƙantar sa kana samowa, dan yanzu hatta Shazeen in za'a saya mata wani abu saidai a haɗa in ba haka ba ta haƙura"............. Ta ƙarashe cikin faɗa tare da juyawa ta fice dan tasan in ba haka tawa Sahnish ba bazai taɓa miqewa ya tsaya da ƙafarsa ba yadda take so, gashi dai akwai zafin nema amma abu kaɗan sai ya hanashi neman, abu kaɗan ke rikita shi, yayi ayyukan ƙarfi da yawa amma daga ɗan abinda bai kai ya kawo ba sai ya ce shi ba zai koma ba ya bar wannan aikin, haka kwanaki ya samu aiki wurin mechanics amma daga su karafiya suka ritsa shi shikenan ya tsorata ya bar aikin, yayi aikin wanki da guga a wani gida shi ma ba'ayi nisa ba ya zube rashin lpy wai pneumonia ya kamashi, yayi aikin sayar da ruwa na jarka amma kwata kwata ya ƙasa iyawa da gwagwarmayar dan yana tsaye sai abokan aikinsa suzo su cike kurar ruwansu suyi gaba yana kallo bayan kuma shi ne akan layi. Ita Kuma ba wai ta gaza bane ah ah, kawai dai tana so ya zama me juriya, saboda yau da gobe ba abinda ta bari, gatan da zata masa shi ne ta nuna masa yadda zai dogara da kansa ba wai sai da ita ba. ______________ita kuwa Amla tana zuwa asibiti Nashwa ta fito ta mata jagora zuwa ciki, bayan ta gaisa dasu Mumu ta ƙarasa kujerar dake gefen gadon Nayrah ɗin da Mumu ta nuna mata ta zauna, "Sannu dear, ashe haka ya faru".......... Ta faɗa tana kallon Nayrah ɗin cike da tausayawa halin da taganta a ciki. Cikin ƙarfin hali Nayrah ɗin ta ce, "Haka ALLAH ya qaddaro Amla sai dai muce ALLAH ya kiyaye gaba yasa hakan shi yafi alheri"..........." Alheri kuma? A irin wannan iftila'in?". Amla ta tambaya tana kallonta da mamaki. Murmushi tayi wanda bai kai zuci ba tana ɗauke Kallonta daga kan Amlan. "ALLAH ya baki lpy ya tsare gaba".........." Ameen ya rabbi". Ta amsa. "Kinsan da kiran me na Miki Nashwa ta sanar dani wannan abun da ya faru, saurayin ki fa na gano"............" A ina ?". Ta tambaya tana kallonta. "Daddy ne ya aikeni na kai wa wani saqo, to ashe ni ban sani ba shi ne wanda zan bawa saqon, shi ne fa na kira na miki tsegumi"........ Satar kallon inda su Mumu suke tayi ganin hankalin su baya kansu ya sata faɗin, "Amla Ki rage murya dan ALLAH"........ ɗan kallon tuhuma Amla ta mata kafin ta ce, "Ya dai? Any problem?". "Bari kawai Amla ke dai ki tayani da addu'a"........... Ta ƙarashe tana gyara kwanciyar ta saboda hankalinta da ya koma kan Amjad ɗin, shiru sukayi can kuma Amla ta ce, "Da tare zamuzo da besty na, to sai su.........." Saurin canza zancen tayi da faɗin, "To qanin ta ba lpy saisa, amma tana miki sannu". Cikin jin daɗi Nayrah ɗin tayi Murmushi da faɗin, "Ni dai ALLAH ya nuna min ranar da zanga besty ɗin nan da aka hanani zama da zancen ta, gashi hotonta ma rowar sa akemin". "Ke bari bestyn tawa ce sai ni, kwata ƙwata bata yadda da hoto amma zance mata ke kike so ko kuma duk ranar da naje na haɗaku a video call "...........haka suka cigaba da hira sama sama kafin Amla ta musu sallama ta tafi. ---------------------√ Sai da ya gama duba takardar sannan ya maidata cikin file ɗin ya ɗauka ya fita, main office dinsa ya koma tare da Kiran Nazbeer a waya, ba'a ɗau lokaci ba ya shigo, "Ungo Nazbeer ka maidawa Alhaji zawaad wanna file ɗin nasa sannan ka sanar masa cewa duk abinda su Julaybin sukeyi da sani na tare muke aiwatar da komai, dan haka kar ya wani damu kansa".............. "Okay boss". Nazbeer ya faɗa yana ɗan risinawa ya karɓa file ɗin. Bai ce komai ba ya ɗauki abinda zai buqata ya yi waje inda ya samu su Kamal suna jiran sa, shiga yayi Kamal ya rufe sannan shi ma ya shiga yaja suka fice zuwa Masallaci dan har lokacin sallar juma'a ya kusa. Bayan an sauko daga masallaci suka nufi wani wuri, a gaban wani tangamemen gida suka tsaya, Horn sukayi me gadi ya buɗe suka shiga anan ya hango Juraysh da Hunaiz sai daddyn su Juraysh ɗin da Kuma uncle ɗinsa ɗaya wato brother Anah tare da wasu manyan mutane su uku. Yana fitowa juraysh ya baro wurin su ya nufoshi yana Murmushi ya miqa masa hannu yana faɗin, " Da ai cewa nayi ba zan zo ba tunda abin haka ne, har zaka nemi Hunaiz ka sashi aiki bayan ga ni"...........Hunnunsu cikin na juna suna musabaha ya ce, "kai fa oga ne, tunani na ko kana da wani aiki me muhimmanci a gabanka ne, nasan Kuma in dai na faɗa ma zaka iya katsewa kace zaka yi nawa aikin, kuma naga ga Hunaiz da ba abinda yake yi". "To naji Amma ai ko kira kayi ka sanar dani, ba dan Anah ba ai da saidai naji labari"........... Shafa gemun sa yayi kadan da faɗin, "Bari kawai Juraysh kasan yadda abubuwan suke". "Haka dai kullum baza ka taɓa canzawa ba, yanzu ma gashi saida ka makara, dan har an ɗaura, zuwan da kayi ma ka same mu tafiya zamuyi, dan haka sai munci tarar ka"............Ya ƙarashe cikin sigar zolaya. Smirking yayi da faɗin, "I know yallabai a mun afuwa, muje na gaisa dasu a gurguje, hospital zan wuce wurin amarya ta"........... Dukan wasa Juraysh ya kai masa a baya yana faɗin, "Ummm kaji sabon ango to ai Ka bari ta warware ko"..........."Mtweee kai whl ka fiya wasan banza". Haka suka jero tare zuwa wurin mutanan, har ƙasa Amjad ya durƙusa ya gaishe su, Juraysh ya ce, "Wannan cousin brother ɗin mu ne". "Masha ALLAH"............Ɗaya daga cikin mutanan ya faɗa yayinda ɗayan ya ce, "Wait wai wanna ba Amjad bane ?".......... Brothern Anah ne ya ce, "Shi ne mana ".......... Kallon juna sukayi kafin ya sake cewa, "ALLAH sarki, Amjad dama ana ganin ka ido da ido, na dauka sai a BBC dasu CNN?". Dan murmushi yayi kawai Juraysh yayi saurin faɗin, "Daddy barin rakashi yace zai gaisa da mutanan gidan"...........Ya faɗa saboda gudin aja zancen wata maganar ta ɓullo kuma. Daddyn nasu ne ya ce, " To mu dai mun wuce, in Kun fito kwa samemu gidan Anah taku, Hunaiz kai sai ka jirasu ku taho tare ko".......... Hunaiz da ya ƙarasa suka gaisa da Amjad ne ya amsa da, "To Daddy". A ciki ma Juraysh ne yayi introducing ɗin sa a matsayin cousin ɗin sa da yazo gaishe su, a tsatsaye suka gaisa da matan sannan suka fito daidai lokacin Dad ɗinsu Nayrah ya kawo Kai a fusace ko ganin gabansa ba yayi da alama dai labari yaje masa. Ja baya Amjad yayi dan bashi hanyar wucewa kallon kallo sukayi na kusan minti biyu kowa da tasa ma'anar kallon kafin Amjad ɗin ya keɓe ya fice ba tare da ya ce dashi komai ba haka Juraysh ma yabi bayansa suka fice, cikin tsokana Juraysh ya ce, " Ga sirikin naka fa, naga sai muzurai yake da alama za'a tada gidan nan gwara muyi mu bar wurin nan tun Kafin bomb din ya tashi damu"........... daidai lokacin da Hunaiz ya ƙaraso wurin su dan dama shi a waje ya jirasu, Amjad ne ya ce, "Nagode dude's, ALLAH ya bar zuminci, ina ga ba wuri ɗaya zamuyi ba dan zanje hospital ne kamar yadda na faɗa ma, ku Kuma naga kamar su Uncle na jiran ku ko" ..........ya faɗa yana ɗan susa girarsa. "To ai harda Kai suke nufi".......... faɗar Juraysh ɗin. Duba agogon hannun sa yayi tare da girgiza Kai ya ce, " Bazan samu komawa gida yanzu ba, duk abinda ake ciki muyi waya da kai ko Hunaiz". Rakashi sukayi har mota sannan suka koma wurin tasu motar, Saida suka ga fitar su sannan suka shiga cikin wadda suka zo Hunaiz ya ja suka fice. ______________Dad yana shiga ya tarar da mahaifiyar sa zaune tana rabawa jikokin ta alawowin ɗaurin aure da aka shigo dasu. "Iyani! Iyani me wanna tsinannnan yaron yazo yi gidan nan ?"........... Ɗaure fuska tayi da faɗin, " Wa kenan?" . "Wanna yaron Amjad mana". "Au, Yan uwan sa ya rako mana, ko bakasan yan uwa suke da sirikin naka bane ". " Ba rako yan uwansa yayi ba shi ne sirikin nasa"........... Yayyun dad dake shigowa falon suka faɗa, ƙarasowa sukayi suka nemi wuri suka zauna. "Whatttt Yaya Adam, kasan kuwa me kuke faɗa, Amjad Hashim Darwin shi ne siriki na?". "Kwarai"......... Yaya Adam ya Amsa da alamun tabbatar wa. "To whl ba wanda ya isa dole a warware auran Nan, tukunna wa ma yace a daurawa ya'ta aure ba izini na, bayan ina takawa a doron duniya ban mutu ba". "Ita Yar taka ai da amincewar ta dan saida mukayi baki da baki da ita ta kuma tabbatar mana da ta amince. Domin jiya muna zaune yaron nan ya aiko ɗan uwansa ya same mu ya shaida mana tsawon shekara ɗaya da wani abu da yi musu baiko, yanzu Kuma ya buqaci a sanya ranar ɗaura aure kace baka amince ba, kai akwai wanda zaka aurawa ƴarka. Yara kuma suna san junan su tunda har yarinya na ɗaukan ƙafa ta bishi har inda yake, saidai dake shi ɗin ɗan albarka ne baiyi Amfani da hakan wurin cutar da ita ba, sai ma nema da yayi ta faɗa masa inda zai samu wasu daga cikin yan uwa domin ya kai abin wurin su, ita kuma ta masa kwatancen nan gidan"........... Yaya Najib ya ɗaura da, "Mu Kuma baza mu sake zubama ido kai da matarka ku sake irin rashin albarkar da tasa kayi a baya ba ". A fusace dad ya ce, "Nifa ba gwanin ta aka min ba yauwa Kuma aure sai an raba shi ko Kuma na shigar da Ƙara, wai ko baku san waye yaron nan bane, yaron da ƙasashen duniya suke bincike a Kansa wanted ne fa, bayan haka Kuma matan banza yake nema ko baku da labarin iyayen yarinyar da suka shigar da Ƙarar sa bane, okay dake ba ɗaya daga cikin ya'yan ku bane ko ". Iyani ce ta ce, "Wai dakata Nu'uman ada daka ɗauki yarka kayi mata baiko dashi ba ka yi bincike kasan waye shi bane? Ina cewa ko Neman mu baka yi ba tsakanin Kai da dangin matarka ku kayi abunku ko? Okay saboda a lokacin kana cikin inuwar arzikin sa, ni dama nace bana Ƙara shiga cikin harkar ka ko ta iyalin ka wanna ma da kaga na karɓa su Najib ne suka dinga bani baki, ba fata nake ma ba Nu'uman amma abinda ka aikata Ka biyewa son zuciyar Matar ka whl wanna hakkin bazai taɓa barin ka ba".......... Bai tsaya yaji karashin zancen Iyani ba ya juya ya fita ba tare da ya Kara cewa komai ba, asibitin ya koma dan yana da tabbacin can Amjad ya nufa. Bayan fitar sa iyani ta kalli su yaya Najib kana ta ce, "Maganar da yake faɗa gsky ce Najib?"........... Saida ya sauke numfashi sannan ya ce, "Haka ne Iyani, dan a yanzu ma maganar da ake ance duk ma'aikatun su na gold da refineries ɗinsu ƙasashe sun dakata da mu'amala dasu, shi kansa yaron ance wai an tsayar da passport ɗinsa daga ƙetara ƙasa na wani lokaci dan har yanzu ana Kan bincike ne ". "Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun, to batun neman matan da yake fa? Shi ma da gaske ne?". "Shi ma dai haka mutane suke faɗa amma baza muce gashi ba tunda bamu gani ba da idanun mu ba, Sunce wai ya yaudari wata yarinya ya lalata mata rayuwa har sanadiyyar hakan ta samu Matsala a ƙwaƙwalwa, yanzu haka dai ance suna gaban kotu, ance wai dan iyayen yarinyar basu da ƙarfi ne saisa har yanzu Ake jan shari'ar yau gobe yau gobe"...........Yaya Adam ne ya dakatar dashi ta hanyar faɗin, "Dakata Najib duk wanna bayanan da kake idarwa a gaban Ka akayi ne?"............." Yaya Adam bakaji abinda nace bane, bamu gani da idanun mu ba, ba kuma mu shaida ba amma ina faɗa mata abinda mutane suke faɗa da kuma abinda duniya ta shaida bama cikin ƙasar Nifaz ba kawai, kuma Kai ma kana gani kuma kana karantawa a news". "Najib mutum kamar Amjad dole zaiyi tarin maqiya na ɓoye Da na fili, dan gsky Ni kam har yanzu zuciyata ta ƙasa aminta da wa'annan shaci faɗin da ake yayatawa"........... Juyawa yayi wurin Iyani da faɗin, "Iyani ni sanin da nayi wa yaron nan, yaron kirki ne dan duk cikin iyalan alhaji Hashim, ance yafi ji dashi saboda hankalin sa da nutsuwar sa kawai dai akwai wani Abu a ƙasa". Ajiyar zuciya iyani ta sauke da faɗin, "To ya akayi kuka yarda akayi auran bayan kunsan haka abun yake, danni kwata kwata ban sani ba kawai kun shigo min da yaro ne cewa shi yake neman auran Nayrah mahaifin ta kuma yaqi har yarinya ta fara binsa gida". Yaya Adam ya ce, "Haka ne Iyani daga jiya zuwa yau da safe Kai har lokacin da aka ɗaura auren mu kan mu bamu san ba yaron da yazo jiya bane mijin domin ko a wajen suna ma da suka ce Amjad Hashim bamu kawo komai ba saboda mun ɗauka ko sunan ne yazo ɗaya tunda su anasu sunan akwai Darwin a ƙarshe saidai zuwan sa yanzun shi ya bayyana mana cewa bashi bane, dan a gaban mu shi mahaifin yaron da yazo jiya ya kirashi da Hunaiz, yanzu ma kawai na rasa yadda zan cewa shi Nu'uman ɗin ne saisa na shirya masa cewa shi Amjad ɗin ne ya aiko ɗan uwansa, Amma a zahiri yaron da yazo jiya a matsayin zuwan kansa yayi ya rufemu". "To duk ba haka ba ita yarinyar wa take so ne?"........... Iyani ta tambaya. Yaya Najib ya ce, "Amjad, dan saida na zayyane mata duk abinda ya fada min ta tabbatar min haka ne, sannan na sake ce Mata da izinin ki Amjad yazo neman a ɗaura muku aure tace eh, kin amince tace eh". "Kenan akwai wani Abu tunda har bai bayyana kansa ba sai bayan an ɗaura auran, in kuwa haka ne ya kamata Ku bisu asibitin domin Ku tabbatar da gaskiya"............. Faɗar Iyani dan hankalin ta ya kasa kwanciya wannan yaro ya musu shiga shiga ba zurfi, yaya Adam ne ya kalli yaya Najib da faɗin, "Nima tunanin da nake kenan inaga muje mu ji Kar ya zama mune marassa gsky, tunda kaga bamu ma sanar masa ba saida aka ɗaura muka ce yazo ya ƙarɓa sadakin ƴar sa "............ Iyani ta cafe da faɗin, "Ai ba laifi kukayi ba dan shi Nu'uman ba sanin ciwon ɗa yayi ba bai damu tabi shi ba ya gudu da ita indai wanna matar na ƙarƙashin sa ba abinda ya dameshi duk ta gama mallake shi". Miqewa yaya Adam yayi yana faɗin, "Bari muje muji abinda ake ciki iyani". "To sai kun dawo ALLAH yasa muji alheri, amm Nafi'u ya tafi ko? ". Yaya Najib ya ce, "Eh bayan an ɗaura aure ya wuce, yace yana da wani uzuri ne, har yake cewa mey sa ma ba'a ɗaura auren a masallaci ba bayan anyi Sallah. Kuma ma dai Ni whl sai yanzu abun ya dawo min Mey sa sukace lalle sai a gida". "Kaga da ALLAH Najib wuce muje, kai akwai ka da son ayi gaba ayi baya, iyani mu mun wuce". "ALLAH ya tsare hanya, ku gaishe min da yaran. ina Amfani aure irin wanna, Nu'uman dai baiyi dacen mata ba sam........" Haka suka fita suka barta tana Mita ita kaɗai. Lokacin da Amjad ya isa asibitin Mumu ya samu sai ƙannen Nayrah ɗin, ba laifi jikin da sauki dan tun asuba aka cire oxygen ɗin tana dai kwance hannunta maqale da drip, tura ƙofar yayi ya shiga da sallama bayan yayi knocking sau ɗaya, duk miqewa sukayi banda Nayrah dake kwance sai pale eyes ɗinta data zuba masa tana kallonsa cike da tsantsar so da ƙauna, gaisheshi su Nashwa sukayi ya amsa musu a sake sannan ya gaishe da Mumu, fuska a ɗaure ta amsa sannan ta ɗaura da faɗin, "Me ya kawo Ka bayan kasan kashedin da Alhaji ya ma". "Wurin matata nazo "...........Ya faɗa kai tsaye ba tare da wata shakka ba. Kallon Nayrah dake kwance tayi sannan ta kalli Amjad ɗin, "Wace matar taka ? Kai wai ko Ka fara haɗawa da kurɓe kurɓe ne"........... Ni kuwa nace Mumu Anya bakwa wuce gona da iri kuwa ke da Dad. Bai ɗaga ido ya kalle ta ba haka zalika bai bata amsa ba sai wayar sa da ya zaro daga aljihu ya buɗe yayi playing wani video ya miqawa Nayrah kasancewar volume a ƙure yake yasa Mumu ta gama jin komai, video ne na ɗaurin auren sa da Nayrah ɗin harda sadakin da aka biya da silillikan gold's masu nauyi na companyn HD AURUM MINING. Video na ƙarewa mumu ta buɗi Baki da niyyar magana Dad ya banko ƙofar kamar zai balle ta Wanda har saida Mumun da kanta ta zabura, ita kuwa Nayrah wani sassanyar murmushi tayi tare da gyara kwanciyar ta dan a yanzu bata da wata sauran fargaba kuma jinta take kawai she's safe, ni kuwa nace Anya kuwa Nayrah? To bari dai mu gani. "Kai sakar min ya'ta tunda bani na aura ma ita ba kuma banga uban da ya isa ya ɗaurawa ya'ta aure ba ina raye"............." Amma ai kai ka Bani auran nata ko?"............ Amjad ya bashi amsa Yana ɗago kansa tare da zare p cap din da ke kan nasa. "Ko da na Baka ai lokacin bansan waye kai ba, yanzu kuma da duniya ta fito da ɓoyayyen halin da kake ɓoyewa nace na warware, kuma na fasa" . "Bai warwaru ba, bai kuma fasu ba "........... Amjad ya bashi amsa Kai tsaye . "To Baka isa ba kuma zanga in duk duniyar nan akwai wanda ya isa ya zo ya ɗaukar min ya, ko ya cilastani kan abinda banyi niyya ba". Dan gajeren murmushi yayi da faɗin, "Dad a yanzu fa ina tsaye ne a gabanka matsayin sirikin Ka kuma miji ga yarka wanda yafi Ka iko da ita "............ Ɗaga hannu Dad yayi da niyyar kai masa Mari me ya tuna kuma yayi saurin sauke hannun yana jan kwafa, murmushi Amjad ɗin ya sakeyi tare da girgiza kansa ya ce, "Dad bana bukatar yin doguwar jayayya dakai Amma abinda nake so Ka sani wani yana cin albarkacin wani, Haka zalika duk da zaki ya kasance shugaba a dawa yasan damisa na iya fito na fito dashi , shuru shuru ba tsoro bane iya taku ne, Andddd silence is not weakness it's power"........... Yana kaiwa Nan ya juya ya kalla Nayrah sannan yayi waje. "Ke kinajin dai abinda kika janyo min ko, a gabanki ya tsaya ya kalla idanun mahaifin ki ya gaya min magana, to shikenan mu zuba mu gani "............ Ya faɗa yana juyawa zai bishi mumu ta ce, "A'a Alhaji karka bishi ya isa haka, inaga lokaci yayi da zamu zubda makaman yaqi tunda bakin alqalami ya riga ya bushe kasan dai ba fin ƙarfin yaron nan mukayi ba, da Kai da duk wanda kake tunanin yana bayanka whl in da ya ga dama zai iya batar daku a doron ƙasa dan haka yanzu ka bari mubi Abun nan a sannu a samu ya sakar mana Yar mu kawai ba tare da wani tashin hankali ba, Kuma ba kowa zaka kama ba Yan uwan ka ne tunda su suka daura auren s ........" Maganarta ta yanke a lokacin da aka buɗe kofar ɗakin. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______33 & 34 Maganarta ta yanke a lokacin da aka buɗe ƙofar ɗakin ne. Shi kuwa Amjad yana fita ya haɗu dasu yaya Adam na shigowa, Yaya Najib ne ya tsaida shi tare da faɗin, "Yauwa Amjad gwara da ALLAH ya haɗamu, dama muna neman ka Kuma ko bamu sameka anan ba daman zamu sa a kiraka". "ALLAH yasa ba damuwa bace". Ya faɗa cikin ƙoƙarin sa na saita muryar sa gudun bayyana ɓacin ransa. "Amjad so muke ka faɗa mana gsky shin Kai ne Mijin Nayrah da gaske ko kuwa yaya abin yake ne?"............" Ni ne". Ya amsa musu kai tsaye. Kallon yaya Adam yaya Najib yayi kafin ya ce, "To kuma meysa zaka ɓoye kaƙi bayyana kanka har saida aka ɗaura auran, kuma me sa ka turo dan uwanka matsayin shi ne mijin". Ɗan gyara tsayuwar sa yayi da faɗin, " In da ace ni ne da kai na nazo a jiyan da a yanzu ba'a ɗaura auren ba, saboda ku ma bana yanke zaton irin abinda mahaifin ta yayi shi zakuyi, amma da na tura Hunaiz a matsayin ni ne, gashi a yanzu ai an ɗaura auren ". Yaya Najib ya ce, "Amma daka bayyana mana kanka da sai yafi ai, saboda aure ba'a yin sa da ɓoye ɓoye, Kuma bincike a aure ai ba laifi bane". "A yanzu ma Kuna iyayin binciken ai Uncle, dan amsar da zaku samu kafin auran da yanzun duk ɗaya ce Kuma nasan kun santa". "To wai hakan ne ko Kuma ah ah magana ne ta mutane?"...........Faɗin yaya Adam ɗin cike da tararrabin wannan lamari. Hannayen sa ya zube cikin aljihu tare da ɗan girgiza kansa ya ce, "Lokaci alkali, Mai laifi Yana iya cewa bashi bane dan Kare kansa, haka Kuma ko da marar laifi ne cewa zaiyi ba haka bane, ba wai zai amsa da gaskiya bane saidai yace bashi bane, domin tabbatar da ni ɗin ne wanda ƴar ku ta aminta dashi kuna iya ƙarasawa ciki"............Yana kaiwa nan ya raba ta tsakiyar su ya wuce Yana Ƙara jawo p cap ɗinsa yadda zata rufe fuskar tasa da kyau, Kamal da yaja gefe ganin yana magana dasu yaya Adam yayi saurin rufa masa baya. Barin faɗa muku wani abu ada ba abinda Amjad ya tsana irin P cap amma tunda wanna maganar ta fito sai ya zaman ko Ina yaje mutane na nuna shi da baki wasu da hannu a ɓoye ko a fili, kowa da irin abinda yake faɗa a Kansa, hakan yasa ya qulla abota da ita saboda ɗauke idanu a Kansa. WANNAN KENAN. "Me ka fahimta a zancen nan nasa Najib?"............ Hannu yaya Najib ya watsa alamar ALLAH masani, sannan ya fara tafiya ganin haka yasa yaya Adam rufa masa baya, sai da suka tsaya sukayi tambaya aka nuna musu ɗakin da Nayrah ɗin ke jinya. A buɗe suka samu Ƙofar ɗakin dan haka suka sa Kai kawai tare da yin sallama, duk cikin su rasa me amsawa akayi sai su Nashwa da suka amsa tare da gaishesu. "To bayan wancan cutar da kuka mana sai da kuka sake biyo baya kuyi mana wata kuma? Dan daga ganin ku ba alheri bane ya kawo ku"......... Faɗar Mumu cikin ɗaga murya. "Eh eh me ya kawo ku nan, Kuma me kuka biyoni ku min?".............Dad ya faɗa yana muzurai. Yaya Najib ne ya ce, "Kabi a sannu Nu'uman duniya wanda bai zo bama jiransa take ballatana mu da muke cikin ta, mu dama mun daɗe da barin ka da matarka da Kuma iyawar ka dan haka yanzu ba wurin ku muka zo ba. Sai ku jira har sai lokacin da muka zo dan ku sai kuyi abinda ke ranku".......... Yunkurawa Nayrah tayi da niyyar zama yaya Adam ya tare ta ta hanyar faɗin, "koma ki kwanta Nayrah, ALLAH ya baki lpy ya tsare gaba"............. Komawa tayi ta kwanta tana amsawa da Ameen, yaya Adam ya sake cewa, "Nayrah shin kinsan Wanda kika amincewa jiya a waya cewa a ɗaura muku aure?"............ "Eh Uncle Adam na sani". "Waye?"............ Yaya Adam ya sake tambaya. "Amjad Hashim Darwin". "Au da sanin ki ma kenan munafuka kina gadon asibitin kina shirya wata ƙulleleniyar". Faɗin Dad a fusace . Yaya Adam ya ce, "To alhamdulillah Nayrah mu zamu koma, ALLAH ya baki lpy dama abinda mukazo mu tabbatar kenan saboda yadda abun yazo yasa muka shiga shakku, Amma tunda da sanin ki da Kuma amincewar ki ALLAH ya bada zaman lpy ya kauda fitina a tsakanin ku" . "Ameen Uncle Adam nagode sosai. Uncle Najib nagode a gaida min iyani ".......... "Zataji in sha ALLAH ". yaya Najib ya faɗa daga nan suka juya sukayi waje ba tare da sun sake kallan ko inda su Mumu suke ba, a fusace dad ya ce, "Banga amfanin zaman ki ba latifa, dama duk abinda yake faruwa dani har mutane ke jin haushi na kece sila".......... Da mamaki Mumu ta ce, "Alhaji ni?". Tare da nuna kanta da yatsa. "Kwarai kuwa kece nan, gabaɗaya kin hana rayuwata zaman lpy, haba da ALLAH wanna wani irin abu ne "........... Ya faɗa yana juyawa ya fice cikin ɓacin rai shi ma. Cike da fargaba Mumu ta ja kujera ta zauna tana bin bayan Dad da kallo cike da son gasgata abinda Dad ɗin ya faɗa. "Mumu kiyi hakuri dan ALLAH".......... faɗin Nayrah idanunta na cikowa da kwalla. "Whl idan kika ƙaramin magana Nayrah sai na rufe ki da duka, ba a gadon asibiti ba ko a makara kike ba abinda zai hanani cin ubanki yau"............. Wani abu me ɗaci Nayrah ta haɗiye tare da juyar da kallon ta wani wuri, tashi su Nashwa sukayi suka fice daga ɗakin dan karma suyi wani dan kuskure faɗan ya dawo kansu, tunda suka ga ta gadon asibiti ma ba'a barta ba ballatana su da ƙafafunsu. ----------------------√ Shuru Sahnish yayi bayan ta fita Yana tunanin maganar ta can kuma ya maida kuɗin aljihun wandon sa ya ɗauki ɗan makullin ɗakin data bar masa ya fice ya kulle mata ɗakin ya wuce nasa. Tana fita bakin titi ta nufa tare da tsayawa ba tare da tasan inda zata ba kawai dai taji gidan na Mata zafi ne ita kuma ta riga ta kira hajiya tace Mata baza ta samu damar zuwa aiki ba ballatana yanzu ta shirya ta tafi. Mai tuktuk ne ya tsaya a gabanta tare da faɗin, "Hajiya tafiya me?".........."Eh". Ta faɗa ba tare data duba ko waye ciki ba ta hau . "Ina kikayi hajiya?" "Duk inda Ka nufa ".......... Ɗagowar da zatayi idonta ya shiga cikin nasa kamar kullum yau ma ƙananun Kaya ne a jikinsa da sukayi matuƙar amsar sa, hannun sa riqe da wayar sa idonsa a kanta ganin ta juyo gareshi ya sashi ɗauke idanunsa tare da faɗin, "ki daina kallo na"............. Kwata kwata baisan meysa ba a duk lokacin da Hushaima ta zuba masa ido sai ya dinga jin jikinsa na amsa wa gabaɗaya, tun ranar da ya fara ganin ta a gidan, saboda Hushaima ALLAH ya bata ƙarfin ido Wanda ko yaya ta zuba ma su sai kaji su har cikin ɓargon Ka . A nata bangaren kuwa ɗauke kanta tayi tana mamakin yadda akayi har yake kamata tana kallon sa, dan ita kwata kwata kallo ba dabi'ar ta bace dan ko a hanya zaku haɗu to fa zaka iya zuwa ta gabanta Ka wuce bata sani ba don gabanta kawai take kallo, Amma sai gashi takan samun kanta da yiwa Jey dogon kallo. Maganar Mai tuktuk ya dawo da ita daga duniyar data tafi, "Hajiya nace ni fa Crimson bites na nufa, nan zan sauke bawan ALLAH nan"............" Ba damuwa nima sauke ni a can ɗin"............. Kallon ta yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juyar da kansa yana kallon titi. Suna hawa wani titi kawai wasu yan zauna gari banza suka kama tuktuk ɗin suka ɗale ba alamar imani a tare dasu suka zaro wuqaqe tare da faɗin, "Wayar Ku ko ranku?".......... Me tuktuk cikin rawar jiki ya ɗauko yar rakani kashin sa ya miqa musu, shi kuwa Jey dama ba musu ya ce, " Dan ALLAH to ku tsaya na cire SIM ɗi na". Hushaima kuwa kallon su tayi ta watsar, "ke ina wayarki"........... Ɗayan ya faɗa da buɗaɗɗiyar muryarsa. Fuska a haɗe ba alamar tsoro ta ce, "Na barta a gida mana, da irin ku a gari mutum zai dinga yawo da waya ne, ai saidai in binmu zakuyi sai na ɗauko na baku tunda ina tsoron ku". Ta faɗa tana watsa musu Hararar ƙasan ido. "Haba baiwar ALLAH ke kuwa bakya San rayuwar ki ne, me akayi akayi waya, wayar banza Dan ALLAH ki basu". Me tuktuk ya faɗa jikinsa na rawa. A faɗace ta ce, "Sai kazo Ka ɗauko musu ai, in kuma rai na a hannun su yake to karsu barni na Ƙara minti ɗaya, tana kaiwa nan ta sauka daga tuktuk ɗin tare da faɗin, " Waye me karɓar wayar a cikin ku ". Kunna babur ɗin me tuktuk yayi Yana faɗin, " Ni Kam tafiya zanyi whl kije can Ku ƙarata, maybe ma tare suke ".......... Saurin dakatar dashi Jey yayi da faɗin, "Haba mana Malam sai kace ba musulmi ba, ai bai kamata a barta anan ba, kuma ku daina ɗaurawa mutane abinda baku da cikakken sani a kansa"............ Yana kaiwa nan shima ya dira daga tuktuk ɗin daidai lokacin da Hushaima ta juya tana magana dasu da alama tsiwar nan tata ta ƙarfin hali take musu, ɗaya daga cikin su ne ya daga wuqar zai burma Mata a wuya, kallon titin Jey yayi kwata kwata irin titin nan ne da babu mutane sosai da sauri ya nufesu domin taimaka mata saidai kafin ya ƙarasa kawai yaga tayi wata irin juyowa kamar walkiya sai gani yayi sunja da baya suna layi kafin lokaci guda su zube a ƙasa. Wani irin birki yaja tare da saurin toshe hancin sa da hannun saboda ganin abinda Hushaima tayi amfani dashi, hoda ce wadda ake amfani da ita wurin bugar da mutum tare da sanyawa ya tafi bacci ko dogon suma. Sunkuyawa tayi tasa hannu ta zaro wayar Jey da ta me tuktuk ɗin ta nufo wurinsa, tana ƙarasowa ta zira masa wayar a aljihun gaban rigar sa sannan tayi wajen tuktuk ɗin. Jey da ya daskare a wajen yabi bayanta da kallo kafin ya juya ya bita shi ma cike da ɗinbin mamaki tare da tunanin wacece wannan yarinyar wai. Yana shiga me tuktuk da ya danqi wayarsa ya bawa machine ɗin wuta suka bar wurin, dan shi ma akan idon sa akayi komai saida suka fito idon mutane ya ce, " ke kuwa baiwar ALLAH me ya haɗaki da irin wanna hodar?". "Saboda tsaro mana, ko kai yanzu baka ga amfanin ta bane, yanzu fa rayuwar ta zama iya ruwa fidda kai, in ka iya allon ka ka wanke". "Amma fa hakan na da hatsari Hajiya, dan kaman kina bawa mutane ƙarfin guiwa ne cewa su ɗauki makamai da kuma doka a hannun su". "Au sai yanzu ka sani, baka san cewa doka ta bawa dan ƙasa damar amfani da ƙarfin da ya dace ba don kare kansa ko dukiyarsa daga wasu masu hari. Ballantana kuma a yanzu da bamu da tsaro. To saman ma a gurɓace take ballantana yan ƙasa, in har da sama a gyare take to fa dole yan ƙasa ma zasu zama gyararru. Yanzu ire iren mutanan can kana hanasu abinda suka nema zasu sokeka kamar raqumi kuma sun soke banza ba abinda za a musu, to wa ke da asara? Yan uwanka ne da abokan arziki, dan haka in ka samu kanka a irin wannan halin kayi iya naka ƙoƙarin ka fara tsira da rayuwar ka tukunna sai ka sako jami'an". Shi dai Jey kallon ta kawai yake yama kasa cewa komai sai tunane tunane ne ke kawowa ƙwaƙwalwar sa farmaki, dukda tanajin idanunsa na yawo a jikinta bata ko nuna ta sani ba bare ta kalla inda yake ba. A ƙofar gate din Crimson bites Mai tuktuk ɗin ya sauke su, juyawa tayi zata tafi ya ce, " Hajiya kudin fa ?".......... Da hannu ta nuna Jey da har lokacin bai sauko ba ta ce, " Zai biyaka ". "Bangane zan biya ba kin bani ajiyar kuɗi ne?". Ya tambaya kai tsaye. "Eh?".......... Me tuktuk ɗin ya tambaya yana juyowa ɗan shi bai ji abinda Jey ɗin ya faɗa ba kawai dai yaji sautin Magana ƙasa ƙasa. "Na baka mana, ai ba nawa kaɗai bama har da naka da zaka biya duk na haɗa na baka ". "Ikon Allah". Me tuktuk ya faɗa Yana kallon Hushaima da mamakin yadda akayi taji maganar da ko shi da yake kusa dashi baiji ba bare ita da take da dan tazara dasu dan ita tana daga wajen tuktuk ɗin ne. Jey bai Ƙara cewa komai ba yasa hannu a aljihu ya ɗaukowa mai tuktuk ɗin iya nasa kuɗin, Dan da yayi niyyar biya mata amma yanzu ya fasa, sai dai me dubu biyu ya ci Karo dasu wanda baisan ya akayi suka zo jikin sa ba, da mugun mamaki ya ɗago suka haɗa ido harara ta watsa masa tare da yin gaba ta shige wurin . "Malam za dai ka biya kuɗin ko dan kaga ta tafi". "Nawa ne ?"........... Ya tambaya daƙer dan ji yake kamar ya zura a guje anya yarinyar nan mutum ce kuwa . "Ɗari takwas"............ Ya bashi amsa, A maimakon ya bashi dubu ɗayar ya canza ya bashi ɗari biyu sai ya haɗa duka dubu biyun ya bashi, sannan ya sauka da sauri yabi bayan ta ba tare da ya kula me tuktuk ɗin dake ce masa dubu biyu fa ya bashi. Samun ta yayi har ta nemi wuri ta zauna a wani table dake can ƙarshe, saurin tsayawa yayi tare da saita nutsuwar sa sannan ya cigaba da tafiya, sai da yazo table ɗin da take zaune yaja kujera ya zauna, "Ya akayi kuɗin ki yazo jiki na?". Shine tambayar da ya fara mata . "Kuɗin wa'ancan yan hau ɗin ne, harajin wayar ku da suka so awon gaba da ita ne na karɓa muku". "Ya akayi kika samu wancan hodar ?"........... Ya sake ɗaura mata wata tambayar. "Bai shafe ka ba ". Ta faɗa tana bin wurin da kallo. "Wacece ke?"............ Ɗagowa tayi tare da ɗaura dukkan hannayen ta kan table ɗin ta tokare habar ta dashi sannan ta zuba masa eyes ɗin ta, ɗauke kansa yayi dan bayaso ya sake ce mata ta dai na kallon sa, taji haushi ta fasa bashi Amsa, ɗan gajeren murmushi tayi sannan ta koma ta jingina da bangon kujerar tana me janye idanunta a kansa ta ce, "Zan gaya ma wacece ni da sharadin ni ma zaka gaya min wanene Amjad Hashim Darwin"............ Da wani irin sauri ya ɗago da faɗin, "Me... M.. me kikace ?". -----------------------√ Tsaye yake gaban wardrobe ɗinsa yana ciro PJ's ɗin da zai sanya wayarsa dake kan bedside drawer ta fara ƙara, matsawa yayi ya ɗauka ganin sunan dake yawo akan screen ɗin ya sashi saurin picking tare da faɗin, "Barka da dare sir"........... daga ɗaya bangaren akace, "Yauwa barkan ka dai Rear admiral Juraysh, ya aikin?".........cike da girmamawa ya ce, "Aiki da godia Alhamdulillah ". "To Masha ALLAH, dama na kira ne na sanar ma kaya na zasu shigo yau da daddare kamar yadda aka saba, da tun ɗazu naso sanar ma to ina dan wani aiki ne, ka sanar da mutanan ku dake iyakar ruwan, banaso a samu Matsala da ALLAH ". "In sha ALLAH baza a samu ba sir, yanzu nan zan sanar dasu "..........."To Shikenan Juraysh, Nagode sai ka jini". "You are welcome sir"............ Ya faɗa cike da jin daɗin da muryarsa ta gaza ɓoyewa. Yana katse kiran Juraysh ya lalubo wata number ya danna mata kira ana ɗagawa ya ce, "Na gama da wancan matsalar, yanzu kawai idan kaya sun iso dama kasan yadda mukeyi ai, Saidai wa'annan fa daban suke da wa'ancan dan sun gayamin akwai excessive nitrates and nitrites, ko yaya akayi amfani dashi amfani da wannan takin amfanin gona zai yi tsiro yayi kyau amma daga baya kaɗan komai zai lalace, in kuwa an samu wanda suka tsira to fa in al'umma sukaci wannan kayan gonar zasu illatu. Sannan Ku tabbatar kaso casa'in na kasuwannin taki an musu juye da wannan sabon takin, ku basu shi a farashi me sauƙi ƙasa da farashin da su suke saro nasu sannan kuyi amfani da dabarun ku wurin zayyana musu irin kyawun shi wannan takin. And batun su Alhaji Abid su ma, akwai kayan da muke basu a ciki a cire a basu". "ALLAH ya taimaki HE, A daɗe anayi sai gaskiya"......... wani ƙayataccen murmushi Alhajin birnin yayi tare da faɗin, "Ba damuwa ka sanar dasu Abid ɗin dai da ALLAH". "Yanzu kuwa ranka ya daɗe, na Barka lpy"......... bai ce komai ba sai girgiza kansa da yayi kamar na cikin wayar na gabansa sannan ya tsinke kiran, ya danyi wasu latse latse kafin ya rufe wayar, ya miqa hannu kan stool ɗin dake gabansa ya dauki tumbler dake ɗauke da sassanyar grapes juice har raɓa take. _______________shi kuwa Juraysh cike da farin ciki ya shiga neman number mutanan su dake iyakar ruwan da kayan HE suka saba shigowa dan sanar dasu saboda kar a samu matsala. "Hello jibrin"..........."ranka ya daɗe Barka da dare". "Barka Jibrin ya aikin?"............."Da godia ranka ya daɗe". "To madallah, ammm akwai kayan da zasu shigo anjima da tsakiyar dare ka sanar da abokan aikin ka banaso a tsaya wani bincike ku barsu su wuce kawai". "To ranka ya daɗe yadda kace haka za'ayi in sha ALLAH".......... "Nagode sai ka ji Ni". Daga haka sukayi sallama ya kashe wayar. Tashi yayi ya sauya kayan Sannan ya nufi hanyar fita daga ɗakin wayarsa da ya ajje bakin gado tayi ƙara alamar shigowar saqo, fasa fitar yayi ya koma ya ɗauka, dubawar da zai yi yaga wani nannauyar alert ne, wata yar ƙarar jin daɗi yayi dan kuɗin da HE ya tura masa a yanzu yafi na ko yaushe, bai yi ƙasa a guiwa ba shi ma ya kira jibrin yace ya turo masa acc number ɗinsa zai saka masa wani abu su sha ruwa shi da abokan aikinsa. Daga nan ya zura wayar a aljihu ya fita cike da wani energy da naunauyan alert da irin wannan ne kawai ke bada shi. -----------------------√ "Kasan tun ɗazu naso mu haɗu, to naje wuri sir Ramphant ne kuma na tarar yana da baqi ban ma samu ganin sa ba".......... Faɗin Hajj zawaad. "Meke faruwa ne ? Ni tunda na shigo Naga kamar baka cikin nutsuwar Ka".......... Faɗin Alhaji Huzaif. Zama Hajj zawaad yayi sannan ya ce, "Bari kawai Alhaji Huzaif wa'annan yaran Alhaji Hashim ɗin ne suke ƙoƙarin fitar da crude oil me ɗinbin yawa domin suyi amfani da kuɗin wurin kammala gyare gyaren sabuwar ma'aikatar su ". Cikin Rashin fahimta Alhaji Huzaif ya ce, "To miye aibun hakan?" . "Matsalata dakai rashin saurin fahimta, shin ko Ka manta yaqin mu akan miye ne? ai fitarwar da zasuyi a yanzu kaɗai zai iya Kai percentage ɗin da dole mu haƙure musu lambar yabon nan, kasan su ma ɓarayin kansu ne ballatana yanzu sun samu dama kawai yadda suke so sukeyi". "Kaiiiii inaaaaa hakan ma bamai yiwuwa bane ai, to yanzu me kayi akai?"............" Shi ne abinda nake faɗa ma Ka kasa fahimta ai, ni abinda nayi na aikawa dashi Amjad ɗin bayanin komai saboda nasan bashi da masaniya akai ko zaiyi wani Abu amma shegen sai yace yasan komai ai da sanin sa, saboda shi bazai iya cigaba da running din komai kai tsaye bane a yanzu saisa ya miqawa brothers ɗin sa ". "To wai ba ance an daina karɓar ko sayan komai daga garesu bane ma?". "Haka dai wasu suke faɗa".........." Bangane haka wasu suke faɗa ba?". Girgiza Kai Hajj Zawaad yayi tare da faɗin, "Mu dukkan mu haka muke zato Amma kuma sir Ramphant juwaira ya tabbatar min da ba hakan bane domin suna fitarwa kawai dai an daina zuwa a karɓa ne a wurin su, shi ma ya sanar min batun cewa su Julaybin ɗin na shirin fitar da wani gwagwaban crude oil ɗin". "Kenan wasa da hankalin mu ake ?". "Ko kuma muke wasa da hankalin mu da Kan mu ba, kasan iya adadin kuɗin da Ahuoyzah ya zubar kuwa, duk a Kan ɓacin sunan yaron nan In har suka tashi a banza ai inajin sai ya kwanta ciwo, kasan yan jaridu da gidajen television nawa aka saya kuwa ko dake Kai lokacin baka cikin mu sai sa baza ka sani ba". "To yanzu me ake ciki?"........... Kafin Hajj Zawaad yace komai wayansa tayi Ƙara duba wa yayi tare da faɗin, "kaga Yan halak yanzu nake shirin Kiran su". "Waye ne?"........... Alhaji Huzaif ya tambaya. "Alhaji Abid ne " ............ Ya faɗa yana amsa wa tare da sanya wayar a handsfreee. "Hajj zawaad ya akayi kana ina ne?". Faɗin Alhaji Abid Muryar sa wasai wasai, ɗaga Kai Hajj zawaad yayi suka kalli juna shi da Alhaji Huzaif sannan ya ce, "Ina gidan gona, ta samu ne naji muryar Ka normal". "Ai Ka bari abubuwan farin ciki sai faruwa suke, labarai biyu ne amma dai bari na fara da wannan ɗin, kasan burin mu na daf da cika kuwa?".........."Kai da ALLAH fa, shaqa min mana?". Hajj zawaad ya faɗa cike da zumudi. "Yau Allah yayi fa, mutanan ne suka aiko azo a naɗe yaron can Amjad dama nace muku ai bincike sukeyi suna haɗa bayanai, to fa shi yanzu tasa ta ƙare dan saidai ya ƙare rayuwar sa a babban kurkukun ƙasa, kuma daɗin daɗawa gashi gobe za'a shiga koto nan ma ga yarinya da iyayenta babu. Shi kuwa kaga yau dashi da duk wani masoyan sa basu ba bacci"........... Ya ƙarashe yana gaggaba dariya, dariyar shima Hajj zawaad yayi ransa fess yayinda Alhaji Huzaif ya ɗan murmusa dan bayaso Alhaji Abid yasan suna tare da Hajj zawaad. "To yanzu zyaa wallafa ne ko kuwa?". Hajj Zawaad ya tambaya. "Waya Gaya ma , ai sai an gama da kotu gobe idan an naɗe shi anyi gaba, sai kuma mu sanar wa duniya da namu labarin ". "Kai Amma naji dadin wanna batu naka alhaji Abid gobe sai mu haɗu da wuri ko saboda a Ƙara tattaunawa". "Eh zanyi magana da Sir Ahuoyzah ma abinda yace dani zan turawa kowanne ku saqo yanzu ma ina kashewa Alhaji Huzaif zan Kira". "To kace labarai biyu ne........" Kafin ya ida Alhaji Abid ɗin ya riga shi da faɗin, "Anjima cikin dare kayan mu zasu sauka fa "............"Kayi magana dashi ne?". "Shi wa?"......... Alhaji Abid ya tambaya. "Ka fa san wanda nake nufi"........Dariya Alhaji Abid yayi kafin ya ce, "Tun ɗazu fa, yace dai na saurari kiransa, idan an kai inda aka saba kai wa zai kirani". "To amma Alhaji Abid wani hanzari ba gudu ba, dukkan mu munsan kuɗin kwayoyin nan sunfi haka, amma sai a wani ce mu rabasu a mafi ƙanƙantar farashi baka ganin anan ma baza mu haɗa wata yar camama ba". "Ah ah Hajj zawaad, mutamin nan fa ido ne dashi a ko ina, kuma kaga biyanmu yake da kuɗaɗe masu nauyi, inaga kamar in munasan ribatuwa dashi to kawai mu masa yadda yake so, shi ma ya mana yadda muke so, kowa ya zauna lpy". "Wai shi miye ribarsu da yake zubda wannan miliyoyin kuɗin ba tare da samun wata riba ba sai ma faɗuwa?"......... shuru Alhaji Abid yayi can kuma ya ce, "ALLAH masani, amma su ai ba mahaukata bane da zasuyi abun da babu riba". "Zaiyi ko zasu yi?"........... Hajj zawaad ya sake tambaya. "Hajj zawaad bari na amsa wata waya da ALLAH "......... Alhaji Abid ya faɗa ba tare da yabi ta kan tambayar Hajj zawaad ɗin ba. Sallama sukayi ya kashe, sautin hmmm Hajj zawaad ya fitar sannan suka cigaba da magana da Alhaji Huzaif. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______35 & 36 Lokacin da labari ya zo wa Anah tana ɗaki wurin Dada tana bashi abinci, Kiran Adla ya shigo wayarta ajje bowl ɗin macaroni salad ɗin dake hannunta tayi tare da ɗaukan wayar tayi picking call ɗin, kuka adla ta fashe mata dashi, cikin Muryar kukan take faɗin, "Anah dan ALLAH kiyi sauri ki zo"............. Sosai gaban Anah yayi wani irin faɗuwa Amma ta daure saboda Dada bata so ta yi wani abu da zaisa ya zargi wani abu, dama gashi tun ɗazu yake mata kallon tambayar ina Amjad tace dashi yana lpy yayi tafiya ne Saboda bataso ta tada masa hankali wurin faɗin irin kaikawon da Amjad ɗin yake kan yi Yanzun, amma duk da haka bata ga alamar ya yarda da abinda ta faɗa masa hundred percent ɗin ba. "Shikenan Ina zuwa"........... Duk da idanun Dadan da takeji a kanta bata nuna ta sani ba sai kawai ta ɗauki bowl din da niyyar cigaba da feeding ɗinsa amma sai ya datse bakinsa alamar ya isheshi, kallon sa tayi da faɗin, " ka Ƙara mana ai bakaci sosai ba". Da ido ya mata alamar a'a ya ƙoshi, tashi tayi ta ɗauko ruwa ta bashi sannan ta goge masa bakin sa, ta kunna masa TV Dan ta rage masa kewa, "Bari na shiga ciki na dawo yanzu"........... Da ido ya amsa da to sannan ta ɗauki bowl ɗin ta fice, duk taku ɗaya da zatayi daidai yake da ƙaruwar bugun zuciyarta, masu aiki ta bawa bowl ɗin sannan ta wuce samanta, tana shiga falon Adla dake waya tana kuka ta saki wayar ta nufo ta da gudu tare da faɗawa jikinta. Riqe ta tayi ta shiga tambayar, "Adla meke faruwa ne meya faru kike kuka?".........." Anah ya Amjad ya Amjad...." Shi ne abinda take ta maimaitawa. Ture ta Anah tayi cikin dauriya ta ce, "ke dallah in zakiyi magana kiyi kinji ko, me ya samu Amjad ɗin? Yana Ina ?". "Anah sojoji aka turo su tafi da ya Amjad kan zargin da ake masa wai an gama bincike za'aje a tsare shi kafin a yanke masa hukuncin "............ Wata hajijiya ce ta ɗauki Anah har saida Adla ta riketa tana faman Kiran sunan ta, da gudu esham taje ta ɗauko ruwa me sanyi. Da taimakon su ta zauna, sannan Esham ta miqa mata bottle ɗin ruwan tana mata sannu amma sai ta ture alamar batason ruwan. "innalillahi wa inna ilaihir raju'un"............ Shine abinda bakinta ke iya furtawa, sai hawaye sharr. "Yana Ina ne yanzu Adla ? Sun tafi dashi ne? Sun sameshi?".......... Duk a jere take jerowa Adla wa'annan tambayoyin Muryar ta na rawa. "Bansani ba Anah, ai baya gida, inata neman wayan sa bana samu, ya Awais ne ya shigo yana neman ki dan ya sanar Miki abinda ke faruwa a waje amma bai same ki ba, nace masa kina wurin Dada shine ya fadamin wai an baza sojoji ana neman ya Amjad wa......" " Ya isa haka Adla barni haka, nemo min wayar Juraysh". Wayar ta ɗauko ta fara kiran number juraysh, Kira ɗaya ya ɗaga, cike da barkwanci ya ce , "Hello Adeedyn Anah, Amaryar Ya Jurays....... ".......... Katseshi tayi daga wasan barkwancin da ya fara kamar yadda suka saba ta ce." Ya juraysh kana Ina dan ALLAH". Jin yanayin muryar ta ya sashi miqewa ba shiri kamar tana gaban sa ya ce, "Adla lpy? Meke faruwa?"........... Anah ce ta karɓi wayar, "Juraysh hukuma na neman ɗan uwanka ido rufe yanzu, wai zasu tafi dashi wurinsu". "Anah karki ce min Amjad, su waye suka zo Kuma?". "Sojojin gomnati mana, wai sun kammala bincike". "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Anah kin gani ko na faɗawa Amjad mu ɗau mataki tun lokacin amma yaqi yace gsky zatayi halinta, Anah in har da gaske anzo tafiya dashi kenan zargin da akewa Amjad tabbatacce ne ya kasance ɗaya daga cikin international human traffickers, saboda hukuma baza ta aiko a tafi da mutum ba ba tare da tayi ƙwaƙwaran bincike ba".........Wani hawayen baƙin ciki ne ya sake zubowa anah Dan ta rasa amsar da zata bawa Juraysh ɗin, ya akayi Amjad ɗinta ya kasance ɗaya daga cikin su? ita ta yarda da Amjad bazai taɓa aikata hakan ba, haka zalika ta yadda bazai yiwu hukuma ta ɗau mataki akan abinda batayi ƙwaƙwaran bincike ba, Wai meke faruwa ne? Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsa sai kawai ta sake rushewa da kuka tare da faɗin, "Sake gwada kiransa mu gani "............ Adla da ta cire wayar daga kunnen Anah ta kashe kiran Juraysh ta shiga neman number Amjad ɗin. _______________Zaune yake shi da philip gabaɗaya Hankalin sa yana kan Philip ɗin, yana sauraren abinda yake faɗa masa cikin nutsuwa, sanye yake da 3 quarter da vest smooth caramel skin ɗinsa sai sheqi yake. Philip ne ya ce, "Boss a yanzu haka maganar da nake ma ya canza musu asibiti zuwa city clinic"............ Murmushi yayi da faɗin, "Manta dashi yanzu ba tashi nake ba, ya batun mutanan kuwa kasan so nake kafin lokacin da ya eba mana mu gama nasa aikin?" . "Nayi magana da su danny ai sunce an haɗa 70%". "Kiramun shi ".......... Ya faɗa yana cigaba da danna normal system ɗinsa, bayan Danny ya ɗaga Philip ya miqo masa wayar, "Hello Danny". Da sauri danny ya nutsu jin muryar Amjad a maimakon Philip, "Good evening Boss". "How about the people?"........." An haɗa 70 percent out of 100 na mutanan da ka buqata Boss". "Have you contacted Ace or Ash or kia?" "Yes Boss, munyi magana"........... Shuru yayi can Kuma ya ce, "kunsan ba aikin mutum ɗaya bane a gabanmu ya kamata ku hanzarta mu gama da wannan"........." Noted Boss". "Wait danny how about widad?". Ya tsayar dashi daga ƙoƙarin kashe wayar da yake. "I haven't heard from him yet Boss, you know how he's, sometimes he doesn’t even pick up the call"..........."Don't mind him. Just make sure you check how it's going with him". Daga Nan ya miqawa Philip wayar tare da cigaba da Abinda yake yi. Bayan philip ya kashe ne ya gyara zama da faɗin," Boss daman"............. Dakatawa yayi tare da faɗin, "uhmmm what's it?"........... "batun su Oga Julaybin"........." Inaji go ahead". " Accountant ya kirani ya shaida min cewa kuɗaden da suke Zara ya wuce misali, har ya kai yanzu kuɗin da ya kamata ya shiga account ɗin Alhaji nasu yake shiga"........... Ture system ɗin yayi tare da faɗin, "Abinda duk ma'aikatan can suka kasa fahimta shi ne no matter how much they collect, Dada’s wealth won’t end, they just grab what they can and leave the rest. I told Baba Hakim to tell them that Aurum mining’s low‑key now, business stopped. But regarding the refinery, it’s almost that time of year. Since they can get the countries to collect crude oil from them it’s pure profit for us all, as our export percentage would goes up. Kai wai ko daga yadda yaran Ahuoyzah suke son nayi wani abu na tsaida su bai isa shaida ma so suke kawai su zama sune a farko ba wannan year ɗin". Murmushi Philip yayi yanajin ina ma shi ne da brain din Boss ɗin nasa, in dai wayo ne duk ta inda ka biyo Amjad ya san ta ina zai ɓullo ma. "Boss yanzu sai batun yarinyar"........... Ɗan ƙurawa wani wuri ido yayi alamar tunani kafin ya ce, " Which girl?" ............ Buɗe waya Philip yayi tare da nuno masa hoton Hushaima tsaye a ƙofar gida sanye da wata yaloluwar riga marar nauyi, ta ɗaure kanta da dankwalin Atampa fuskar nan a haɗe tana hararar wani wuri, gefen ta kuma group ne na maza da matan gidan nasu zaune suna poker kamar yadda suka saba duk dare. Ya ɗan dauki lokaci yana kallon hoton kafin ya ɗauke kansa ya mayar kan Philip cike da neman Ƙarin bayani amma bai ce komai ba. "Boss a du bayanan dana haɗa a kanta an tabbatar da su uku suke rayuwa ita da kannen ta biyu, mace da namiji, domin har gidan wanda suka fara haya a wurinsa an kaini yace shi ya fara basu gida a garin nan dan a lokacin kowa ya hana su gida ganin dukkansu ba wasu manya bane, sai shi ne ya basu gida haya amma ba wanda ya san daga inda suka zo ko Ina iyayen su, a dukkan bayanan dana samu Kuma ita ke ɗaukan nauyin kanta da Kuma na yan uwan nata, tayi aiki daban daban amma Kuma duk inda ta fara aiki bata daɗewa suke korarta saboda zafin Kai irin nata, an tabbatar min bata da tsoro domin ba ta shakkar kowa da komi, sannan daka zagi ƙannen nan nata biyu gwara ka zagi iyayenta, an shaida min ƙaramar kanwar tasu ce kawai take karatu domin su ko bindiga zaka sa musu a ka baza su iya faɗa ma ɗauko wancan ba da harshen turanci, nayi iyakar bakin kokari na ko zan samu wani bayani na inda suka fito ko iyayen su amma ban samu ba, saidai tana da ƙawa guda ɗaya, yarinyar alhaji zawaad ce ma, ance sun daɗe tare amma kamar ita mahaifiyar yarinyar bata san alaqar su saboda talakawa ne kuma basu da asali". Numfashi ya furzar tare da furta, "Miye alaqar ta da Alhaji zawaad da Kuma Mahaifin Nayrah?" "Gsky a bincike na basu da wata alaqa, shi dai Alhaji zawaad mahaifin ƙawar ta ne".........Girgiza kansa yayi da faɗin, "Baka taɓa min binciken abu sau biyu ba, amma a wanna zan baka umarnin yin second round, domin duk wannan info ɗin da ka bani wrong ne". Yana kai wa nan ya maida kallon sa kan kofar da ake knocking tare da ba da izinin shigowa, Aram ne ya shigo tare da durƙusaqa cikin girmamawa ya ce, "Boss kayi baqi fa a waje". Duba agogon dake manne a bango yayi kafin ya ce, " Baƙi Kuma? Philip akwai Wanda yace zaizo ne?"......... Aram ne ya amsa shi da faɗin, "Boss inaga ko akwai matsala ne domin sojoji ne". Shuru yayi yana tunani can Kuma ya miqe ya ɗauki system ɗin ya wuce ɗaki yana faɗin, "kaji dasu Philip ina zuwa"......... Yana isa ɗakin ya hango wayarsa dake kan gado tana haske alamar shigowar kira, ƙarasawa yayi ya ɗauka inda yaga sunan Juraysh yana yawo akan screen ɗin, zama yayi bakin gadon tare da faɗin, " Juraysh ya ake ciki ne?". "Amjad kana Ina ? Hankalin Anah ya tashi saboda an sanar dasu cewa ana Neman ka, an aiko a tafi dakai bisa laifin da ake zargin ka akai"............ Sake gyara zama yayi tare da ɗaga ido yana kallon kansa a mirror dake facing ɗinsa, baka isa gano halin da yake ciki ba a wannan lokacin sai dai in zuciyar sa zaka buɗe ka shige, a hankali ya shafo gemunsa sannan ya ce, "Juraysh ga Anah ga Kuma Dada, da ALLAH ka kula dasu sosai". "Me kenan Amjad, kana nufin da gaske kana aikata hakan? da gaske kai me safarar mutane ne? Ka samu a duhu Amjad ?". Ya tambaya a rikice. "Ba zan iya ce dakai komai ba Juraysh"......... Cikin ɗaga muryar da kanaji kasan tashin hankali ne ya jawo ta ya ce, "kamar ya baza ka iya ce min komai ba kasan kuwa abinda ke faruwa, me sa ko ma ka aikata baza kayi ƙoƙarin Kare kanka ba. Anah fa Kai kaɗai take dashi ya kake tunanin zataji, ga dada ma dake kwance kasan sanadin ka yake kwance, wai wannan wani irin abu ne?". Kansa ya ɗage sama still wayar na maqale a kunnen sa ya ce, "Juraysh Ina so ka shaidawa su Anah cewar bana gari nayi tafiya dan haka ta kwantar da hankalin ta, zan dawo in komai ya lafa, ni kuma i know what to do". " Ka gudu fa Kenan?"................ ---------------------√ Ɗagowa tayi tare da ɗaura dukkan hannayen ta kan table ɗin ta tokare habar ta dashi tare da zuba masa eyes dinta, ɗauke kansa yayi dan bayaso ya sake ce mata ta dai na kallon sa, taji haushi ta fasa bashi Amsa, ɗan gajeren murmushi tayi sannan ta koma ta jingina da bangon kujerar idonta na kallan wani wuri ta ce, "Zan gaya ma wacece ni da sharadin ni ma zaka gaya min wanene Amjad Hashim Darwin"............ Da wani irin sauri ya ɗago da faɗin, "Me... M.. me kikace ?". "Amjad Hashim Darwin"........... Ta nanata kai tsaye tana kallonsa. Ni kuwa nace eh kwarai to bari muga yadda za'a buga wasan nan, shi yana can yasa a masa bincike a kanki ko miye dalilinsa oho? Ke kuma kina nan da taki qudurin fansar, to mu saidai muce ALLAH ya bawa me rabo Sa'a. "Meysa kike son sanin sa ?"............ Yarfa hannuwa tayi tare da faɗin, " Burgeni yake, na kamu da son sa, ina so naje gareshi domin na bayyana masa soyayya ta amma bansan taya zan fara ba, saisa nake son sanin waye shi "............ A boye ya sauke wata gauruwar ajiyar zuciya tare da jan karamin tsaki, ciki ciki kamar me koyon magana ya ce, "Taya zaki fara son wanda baki sani ba? Tukunna ma a ina kika haɗu dashi da har kika fara sonsa".......... kai tsaye ta ce, "A TV".......... kafin yace wani abu waitress ta iso wurinsu tare da tambayar su abinda za'a kawo musu, Jey ne ya bata umarnin kawo musu fried stir spaghetti da shredded chicken sai ruwa da lemo. Shuru shuru kamar ba zai sake magana ba, kowa da abinda yake tunani can ya ce, "Mahaifin sa Hashim Darwin sanannane ne, domin refinery da Kuma company na aurum mining dinsa na ɗaya daga cikin companies da ƙasashe ke ji dasu, shi ne ɗan auta a maza Kuma shi kaɗai ne namiji a wurin mahaifiyar sa"............ "yana da yan uba kenan?". Ta sake watsa masa wata tambayar. Shuru Jey yayi kamar bai ji ta ba. Jin bai bata amsa ba ya sata girgiza kai tare da faɗin, " kenan dai shi bashi da wani labari sai na mahaifin sa?"........... Juyowa yayi yana mata kallon rashin fahimta kafin ya ce , "Ban fahimta ba?" . "Kai ne mutum na biyu daka ban wanna amsar duk tambayar da nakeyi ba ita ake ban amsar ba, duk wanda nacewa waye shi sai ya fara bani tarihin mahaifin sa, hakan ya nuna min shi ɗin ba kowa bane face banza, soko, da bashi da ginin kansa sai wanda aka masa ashe duk wannan abun fanko ne kwalin ne kawai me kyau amma ciki ba komai, gwara da ALLAH yasa na sani tun yanzu kaga zan taƙaitawa kai na wahala dan ni nafison mutumin da ya ginu da kansa ba wai wanda aka gina wa ba ".......... ta ƙarashe tana jan fatar lips ɗin ta na kasa ta kama cirewa, sakwato Jey yayi sake da baki yana kallon ta maganganun ta na kai kawo a kwakwalwar sa. Kawo musu abincin da yayi order shi ya dawo dashi nutsuwar sa, abinci ne plate biyu sai lemo da ruwa da yace kowa ɗai ɗaya. "ke kawo min leda ".......... Hushaima ta faɗa tana kallon waitress ɗin . "Okay ma let me check". "Menene ?"........... Ta tambaya tana mata wani kallon banzar bazara. " Cewa tayi bari ta duba, ni karki tara mun mutane".......... Jey ya yi saurin faɗa rai a haɗe dan shi dama tun ranar farko ya gane Hushaima fa kan ba komai sai bala'i da tsiwa fal ciki. Hararar ta watsa masa da faɗin, "Sai akace ma banji bane, ai naji tace zata duba ɗin "............ Tsaki yaja tare da miqewa ya bar wurin, kallon sa tayi sannan ta kalli wayar sa dake wajen hakan na nuna ba tafiya yayi ba kenan . Bai ɗaɗe ba ya dawo dan kusan a tare suka dawo shi da waitress ɗin da Hushaima ta aika ta kawo mata leda, zama yayi tare da ɗaukan mocktail Juice din ya fara sipping a hankali. Ita kuwa Hushaima ledar ta karɓa tare da fara ƙoƙarin juye abincin a ciki ta tsinto maganar Jey, "What a messy, ke wai miye haka, ke bakyajin kunya ne ?"............ Ya faɗa Yana jin kamar ya mangareta tsabar takaicin dake cinsa, shi ya ma rasa dalilin da yasa bai raba tafiya da ita ba ko dan baisan ɗanyan kan nata ya wuce yadda yake tunani bane. "Kunya? Kai ka Santa "............ Ta faɗa tana ƙarasa juye abunta sannan ta ɗaure ta miqe . Cikin ɗinbin mamaki ya bita da kallo ganin tana ƙoƙarin tafiya yayi saurin tsaidata da faɗin, "Zauna please".......... Ko kallon sa batayi ba bare yasa ran zata tsaya da sauri ya ɗauki wayar sa ya bita, saurin shan gabanta yayi cikin ɓacin rai ya ce , "Wai wacece ke da ina miki magana zaki min banza". Ita ma nuna masa hannu tayi da faɗin, "Kai waye da zaka ban umarni in bi, to ni ba Wanda ya isa ya ban umarni in bi in dai ba radin Kai na ba, matsa ka ban hanya na wuce "........... Ta faɗa tana yanke shi tayi wucewar ta, baki sake ya bita da kallo sai Kuma ya nuna kansa da faɗin, " Me? Oh no ".......... Ya faɗa tare da ficewa daga wurin shi ma. Hushaima tana fita ta samu Abun hawa dan haka ta tsare shi tare da faɗa masa inda zai Kaita. Shi ma ko da ya fito bai bi ta kanta ba ya tsallaka titin wurin wasu masu container yaja ya tsaya ya zubawa titi ido, ni kuwa nace to ko dai neman wanda zai huce a kansa yake. Ita kuwa Hushaima me tuktuk na direta ta bashi kuɗin sa ya bata canji ta shige ciki, faɗan nasu na gado ta samu sunayi a gidan sai ife ife suke sun tara mutane fal, batabi ta kan kowa ba ta wuce ɗakin Sahnish in da ta sameshi zaune yana kallon wani indian Film a wayarsa me suna Eagle, "Kai ina ɗan makullin daki na"........... daga jin yadda tayi magana bai nemi ƙarin bayani ba ya ɗauko makullin ya bata, fita tayi ta koma ɗakinta. Ba ita ta fito ba saida lokacin ɗaukan Shazeen yayi daga makaranta taje ta ɗaukota ta dawo, abincin data ɗaibo shi ta zuba mata taci, tana cikin ci ne Sahnish ya shigo, abincin yabi da kallo dan yasan ba a saida irinsa a layin amma sai bai tambaya ba kawai ya nemi wuri ya zauna tare da faɗin, " kina nan kuwa aka sha rigima da kawu adamu da baba ilerika?". "Na shigo na same su sunayi ɗazu ai, me ya haɗasu?" . "Kawu adamu ne yaje ya kwaso mutane wai azo a raba gida a bawa kowa hakkinsa shi Kuma baba ilerika ya dire yace baiga uban da zai raba masa gida ba tunda fili nasa ne kawu Adamu kawai taimakon kuɗin gini ya kawo suka haɗa, dan haka ba mahaifin su bane ya bar gidan bare yaje ya ɗauko mutane yace a raba gado "...........Tsaki taja tare da faɗin, "Aikin kenan me ka tara me aka barma, kaci abincin ne kai?". "Naci, ke ina kika samo wanna?"......... Ya ƙarashe Yana nuna abincin dake gabansu . "Jawaad ne mukaje wani wurin abinci shine ya siya ". "Jawaad? Waye hakan"..........." Mtweee Kai kana da matsala, Jey nake nufi to". "Auuu dama sunan sa jawaad?". Yayi tambayar tsakanin sa da ALLAH dan shi bai taɓa sanin sunan sa jawaad ba, yasan dai ana ce masa Jey. "To Wai shi Kuma ɗan waye ne na ga dai shi ba ɗan su baba ilerika bane Kuma baiyi kama da matsiyaci ba ballatana nace talauci ne ya kawo shi haya wanna gafalallen gidan, dan ko suturun da yake sawa sun isa biyan kuɗin ɗakuna a gidan nan bama daki ɗaya ba". "Wai bautar ƙasa yazo yi a garin nan". "Shi ne Kuma duk ya rasa gidan da zai zauna sai wanna, duk gidajen haya da irin afatmen (Apartment) ɗin dake cikin garin nan ". "To Sahnish kana iya zuwa ka tambaya in baka yarda ba, ni dai abinda naji kenan". Hushaima ta faɗa yayinda a zuciyar ta kuwa wani tunanin ne ya hauro. Bari muji a Ina Hushaima ta samu wanna hodar ? In baku manta ba lokacin da su karafiya suka jiwa Sahnish ciwo bayan taje ta gaggaya musu magana ai taje wani kango wurin wasu yan daban to anan ne ta karɓi wanna hodar saboda tsaro, dan tayi tunanin ko su karafiya zasu biyo mata ta bayan gida. Kuu ma kunsan ta ya aka kama su karafiya da wa'annan mugayen kwayoyin bayan ku ma su ko haɗa ido da irin wannan ɗin basu taɓa yi ba, to da sa hannun wa'annan yan daban ne saboda tasan sun taɓa samun matsala a junansu, amma dake duk sallamammu ne sai suka sake dinkewa, to ashe ta ciki na ciki ne da taje ta nemi su sanya mutanan su su ramawa Sahnish sai suka bata wannan shawarar ta zuwa wurin yan sanda sannan suka shirya mata yadda za'a kame su karafiya cikin ruwan sanyi, to da wannan shawarar tayi amfani, kunji yadda akayi . Kar fa kuyi mamakin yadda akayi ta san irin wa'annan manyan yan daban, whl Hushaima duk wasu yan iska dake birnin Nifaz ta sani, yarinya ce fitinanniya fiye da yadda kuke tunani. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______37 & 38 " Ka gudu fa Kenan?" . "Kamar haka"............. Yana kaiwa nan ya kashe tare da rufe sim ɗin gabaɗaya ya tashi ya zura jallabiya ya fita. Wasu Manyan manyan sojoji mutum shida ya tarar zaune a falon yana fitowa duk suka miqe suna masa Barka da fitowa, shi ma amsa musu yayi cikin natsuwa, wanda hakan yasa na Ƙara murza ido na dan tunani na bangani da kyau ba, takardar dake nannade a hannun ɗaya daga cikin sojojin ya miqa masa, karɓa yayi ya warware ya duba, sai da ya gama karantawa sannan ya ɗago da faɗin, " Wait for me a bit ". Juyawa yayi ya koma ciki, bayan kamar minti talatin ya fito sanye da maroon suit yayinda ƴar cikin ta kasance white, sosai yayi kyau matuƙa hannunsa riqe da wrist watch ɗin sa yana ɗaurawa, Philip ya yafito da hannu, da sauri ya iso ba tare da ya bar abinda yake ba ya ce , "Philip ka kula da komai kafin na dawo, akwai wani meeting na gaggawa da zan halarta yanzun, duk wasu sauran abubuwa in na dawo ka gabatarmin dasu"............ Yana Kai nan ya fara tafiya duk suka rufa masa baya . Daga gidan sa basu tsaya ko Ina ba sai wani babban secure conference hall dake cikin headquarter ɗin tasu, sunayin parking jibga jibgan sojojin dake tsaitsaye suka buɗe masa ƙofar ya fito, cikin takun nan nasa na nutsuwa ya nufi cikin conference hall ɗin, tare da jagorancin sojoji uku da Kuma wasu ukun dake take masa baya, already dama shi ake jira dan haka yana tsayawa ƙofar tayi scanning ɗinsa sannan ta buɗe ya shige, su Kuma sojojin sukaja suka tsaya daga waje saboda taro ne na manyan mutane. Qaton ɗakin taro ne da ya matuƙar tsaruwa gwanin birgewa sai tashin sanyi da kamshi yake wanda ya haɗu da room fresheners da Kuma turarukan manyan mutanen dake zaune a wurin, gashi daga kallon wurin zaka tabbatar akwai tsaro sosai, babban round table ne a tsakiya sai kujerun da suka masa qawanya, kowani kujera da Mic a gabanta tare da tag na suna da kuma rank ɗin mutum. Direct gaban kujerar da ba kowa ya nufa wadda aka rubuta Agent Amjad Hashim a jikin tag ɗin dake kan table ɗin saitin empty kujerar. Zama yayi sannan ya danyi gyaran murya, yayi sallama kafin ya fara da gaisuwa da Kuma ban haƙuri na ɓata lokutan da yayi. Wani babban mutum ne da a jikin tag ɗin sa naga an rubuta CDS, shi ya amsa da faɗin, " Ba damuwa, in akayi la'akari da rashin sanar ma da ba'ayi ba, sai mutane kawai da muka tura ma. To dama dai dalilin wannan zaman namu na gaggawa ya ta'allaqa ne kan batun wannan gawurtaccen mai safarar mutanan da mukaji shiru tun bayan daka dawo ka shaida mana yadda kukayi da kuma abinda kake shiryawa, baka sake cewa damu komai ba?". Ɗan sunkuyar da kansa yayi tare da gyara mic ɗin dake gabansa ya ce, "Sir abinda yasa ban sake cewa daku komai ba, muna kan aiki ne, ba wai kai tsaye mukeson kamashi ba, Muna son mu san me ake yi da mutanan? Ina ake kaisu ? Sannan su waye suke sashi? Dan wanna ta'asar bata mutum ɗaya bace, in kukayi duba matsalar tafi shafar nahiyar mu in particular ƙasar Nifaz da ake kan fuskantar barazanar satar mutane. In da mata ne kawai sai a iya tunanin wani abu daban, amma haɗawa ake gabaɗaya harda maza, abu ne me sauƙi mu gano mutanan dake yin wannan aikin, amma fa in an kamasu gobe ma wasu za'a shigo dasu kuma zasu ɗora daga inda wa'ancan ɗin suka tsaya ". Shuru ɗakin taron ya ɗauka na tsawon wani lokaci kafin IGP ya ce, "Munji dukkan bayanan ka Agent Amjad, kuma mun gamsu amma fa ka sani Al'umma yanzu gabaɗaya sun zuba mana ido kan ganin matakin da za'a ɗauka a kanka, mu dukkan mu mun haɗu munyi tunani kan abinda kayi wanda a lokacin daka aikata baka nemi shawarar kowa ba kayi gaban kanka sai daga baya kuma ka sanar mana, a tunani na hanyar da kabi tayi tsanani da yawa gsky. Taya zaka fara bayyanawa duniya Kanka matsayin international human trafficker dan kawai saboda wani mutum ɗaya, wanda nasan in kayi amfani da baiwar kwakwalwar da ALLAH ya baka zaka iya kama shi ba tare da ka sanya kanka a wannan tsananin ba"............ Saida ya tabbatar da IGP ya Ƙare maganar sa sannan cikin nutsatsiyar muryar sa me cike da confidence da Kuma calmness ya ce, " Amm Sir Al'ameen duk yadda kuke tunanin Shadow Whl ya wuce nan, idan da banyi amfani da sawa an yada wanna zancen ba, bazai nemi aiki dani ba, kuma a farko nayi tunanin idan zanyi aiki dashi zan ganshi ne face to face saidai Abun ba haka yake ba, domin duk cikin masu yin aikin dashi ma ba fa wanda ya taɓa ganin sa kawai aiki suke masa, mutum ne da ya dade yana cin dudduniyar ƙasashen duniya. A binciken da nayi a duk shekara yana sawa ana bashi mutane sama da dubu uku Kuma daga ƙasashe mabanbanta, hakan ya nuna yana da mutane a ko ina kenan ? A wace duniyar yake da har yake tara irin wanna mutanen Kuma gomnatin ƙasar bata ankare dashi ba? Taya ma ake shiga da mutane ba tare da an sani ba ? Har yanzu muna kan nemo wannan amsar ne, sannan matsalata yanzu ai da mutanen gari ne ba da hukuma ko gwamanti ƙasashe ba, dan already ai kunsan daga Babbar headquarter ta Brussel an aikawa kowace gomnatin ƙasa da takarda cewa akan aiki nake, kuma kowacce ƙasa ta sa hannu ta amince mana". NSA ne ya ce, "Amma Agent Amjad kasan ba Kai bane mutum na farko da ya fara aiki akan shadow ba ko?". "Yes Sir na sani, manya na da yawa sun sadaukar da rayuwar su wurin farautar shadow amma har sukayi nasu suka gama basu samu ba sai dai ni Kuma..........." Dakatawa yayi tare da sa hannu a aljihun suit ɗin sa ya ɗauko wani card me ɗauke da stamp ɗin kasashe da dama tare da sa hannun sa a kasa ya ɗaura kan table ɗin sannan ya ce, "Wannan shine alqawarin dana ɗauka wa qasashen da abun nan ya shafa cewa zan kawo ƙarshen shadow da duk wani wanda ke bayansa, Kuma ni ne zan miqashi ga hukuma domin a yanke masa hukunci "............ Girgiza Kai NSA yayi tare da faɗin, "Baza ka iya ba Amjad"............." Zan iya sir". Ya amsa yana wani guntun Murmushi cike da confidence. "Shikenan amma batun jama'ar mu ya za'ayi dasu kenan "............IGP ya sake faɗa. "Ni daku da Kuma duk wasu jami'ai na ƙasa da na ketare knows who I am, so dan al'umma inaga a cigaba da jan hankalin su wurin faɗin cewa ana cigaba da bincike kamar yadda sauran ƙasashen ma ke faɗar nasu, har zuwa lokacin da zan gama aiki na". "In kuwa haka ne, dole a ƙara ma matakan tsaro saboda hukumar JISD ma ta buqaci hakan ɗan a duk cikin team ɗin naku sunan ka ke yawo". "I'm sorry sir Amma bana bukatar abinda zai janyo hankalin mutane Kai na". Director general na NIA ne ya ce, "Zasu kasance tare da Kai a matsayin ana tsaron ka ne dan Kar ka gudu, are you akay with that?". "Thank you sir"........... Shi ne abinda ya faɗa wanda hakan ya nuna musu ya amince. To wai yanzu kun gane IDs ɗin miye wa'annan securities ɗin jirgin suka samu a jikin Amjad da har ta dinga bashi hakuri, to special ID ɗin sa ne da hukumar JISD ta basu a lokacin da suka fara mission kan shadow, tare da ainahin ID ɗinsa na jami'in tsaron farin kaya. Sannan in baku manta ba a lokacin da su Hajj zawaad ke tattaunawa ai sun ambaci ƙasar Belgium ma ta buqaci a bata Amjad ta yanke masa hukunci idan har ƙasar Nifaz sun kasa saboda itama ta samu sunansa a cikin jerin masu laifi na ƙasarta to duk a cikin tsarin aikin su ne, dan acan babbar headquarter ɗin tasu take. Sannan abu na ƙarshe lokacin da aka sanar da wanzuwar criminals a cikin jirgin da zai tashi daga Belgium zuwa ƙasar Nifaz da gaske ne akwai criminals ɗin a ciki kuma duk an kasa ganosu sai widad, shi ya ganosu ya kuma kamasu ya miqawa securities na airport ɗin, a lokacin kuma kiara ta ƙaraso wurin daga nan ya mika mata sauran aikin ya koma cikin jirgin, ita kuma ta sanar da jami'an dake da alhaki a wannan bangaren. WANNAN KENAN. Minister of communication ya sake amsawa da, "About the matter of rape, are you also accountable for the circular?".......... Shuru yayi dan bazai iya bayyana sirrin gidan su ba sai kawai ya ce, "No I'm not"............. Kallon director general of NIA minister of communication yayi tare da faɗin, " DG i think ya kamata ayi bincike akan wannan abun, cox people are taking it serious Kar saboda abinda ya faru yasa maqiya su samu damar yada tasu manufar anyhow, dama abun na zuciyata dan bamu samu zama bane saisa ma ban taso da zancen ba". Ɗan jijjiga kansa yayi kafin ya ce, " Zan sanya ayi bincike akan hakan"........... shi dai Amjad baice komai ba dan yasan bashi da ikon hanasu amma kuma ba hakan yaso ba . Minister of justice ya ce, "Gobe ne zasu tsaya a kotun ai dan ɗazu nayi waya da judge C. John". "To ka shaida masa ya tabbatar ya tsaya kan case ɗin, ya kuma yi abinda ya dace". Daga haka suka sake tattaunawa kafin su fito gabaɗayan su, aka bashi sojoji mutum takwas matsayin Wanda zasu kasance tare dashi har zuwa lokacin da komai zai kammala. JISD wato joint intelligence and security division tawagar bincike ce ta haɗin guiwa, tawaga ce da hukumomin tsaro na ƙasa da ƙasa ke amfani da ita musamman idan manyan laifuka suka shafi ƙasashe da dama a lokaci guda, kamar dai laifin safarar mutane na ƙasa ƙasa da ake tuhumar shi wannan Shadow da ba'asan ko waye shi ba. Saida suka tantance jami'ai masu ƙwaƙwalwa matuka tare da ƙwazo kan aikin su da jajircewa, in dai bincike ne daga nesa in ka taho kawai tsirara suke kallon ka saboda tsabar iya aiki irin nasu. Amjad ba wanda yasan yana daga cikin su a duk family ɗinsa sai mutum ɗaya wanda bazan faɗa muku shi a yanzu ba sai nan gaba, zakuji kuma ku ga komai da kanku. Philip, Danny, jack da Nazbeer dukkansu jami'an sirri ne dake ƙarƙashin Amjad ɗin. Philip kam ma Amjad shi ne sanadiyyar sa na zama jami'in sirri. Duk ƙarshen shekara Hukumar tasu na haɗa ayyukan dake gabansu sannan su rarrabawa jami'an su, kasancewar su jami'an JISD ba inda aikin su baya kai su in dai abinda ya shafi arewacin Atlantic slice ne. Ba aikin da yake ɗaukan su sama da wata biyu amma gabatar da aiki akan shadow ya ruguje wanna Fariya tasu domin da yawa daga jami'an su sun buga sun ƙaɗa amma babu wani labari kan shadow bare Kuma su yi nasara, sai dai a taron da sukayi na wannan ƙarshen shekara, Amjad ya zabi aiki akan shadow, a take Kuma Widad ma ya amsa cike da ƙarsashi, nan Ashley ma tace zata shiga cikinsu, take Kiara ma ta daga hannu, haka Ace da Kuma Akil. Nasan zakuyi mamaki idan kukaji waye Akil, to ba kowa bane face mutumin dasu BB LALO suka kashe gaban Amjad, sun turashi cikin su BB LALO da niyyar ya samo musu wani bayanai saidai fa duk tunanin su ya kunce dan duk wanda yake tare da SHADOW to fa takunsa daban yake. Ganin ba wani motsi ta bangaren Akil yasa Amjad shirya wannan plan nasa, sai gashi kuma tun farko farkon tafiya Akil ya rasa rayuwarsa akan hanyar binciken SHADOW. Hmmmm a tunanin ku su Amjad zasu iya binciko shadow kuwa? Kuna ganin gabaɗayan su zasuyi nasara a tare? Ko kuma dai za'a sake rasa wasu rayukan? To muje zuwa dai. Ba karamin dadi hukumar tasu taji ba dan haka ta sake ƙarfafa musu guiwa tare da basu tabbacin duk wani taimakon da suke buqata a shirye take ta basu, sannan ta naɗa Amjad matsayin team commander na wannan tawagar. Widad da Amjad kwata kwata basa shiri ada akwai zazzafar gaba a tsakanin su wadda ta juye ta koma gasa a fagen aiki, Kwata kwata widad baya son Amjad ya fi shi kwazo da ƙoƙari, shi kuwa Amjad a lokacin duk abinda yasa a gaba sai yayi nasara gashi da kwarjini da farin jini a cikin jama'a, kaɗan kaɗan widad ya fara ɓata masa aiki tun baya fahimta har ya gano cewa Widad ke ɓata masa aiki, a lokacin ne zazzafar gasar ta fara a tsakanin su, in aka basu aiki saidai kowannen su ya rasa su barwa na ƙasa dasu, sosai Widad ya sake dagewa amma duk da haka fa Amjad na gabansa ya kuma canza sabon salo da Widad ya rasa ta yaya zai ɓullo masa, tuni Amjad ɗin ya sake shan gabansa amma duk da hakan bai yarda ya gaza ba sai ma salo da ya canza shi ma, Akwai wata jarrabawar qarin girma da suka shiga, sosai Widad ya shiga tashin hankali a lokacin da yaga questions ɗin dan har sauran sun gama sun fara fita, kawai yaga an sauke masa paper tare da zare tasa ko da ya ɗago bai ga kowa ba amma yana dubawa yaga an gama tsarge masa komai, cikin farin ciki ya je ya miqa tasa ya koma inda suke zama bayan sun gama har sai result ɗin ya fito, sai wani buɗawa yake, shi dai Amjad bai ɗaga ido ya kalle kowa daga cikinsu ba, har aka zo sanar musu da result, Amjad da widad kunnen mage sukayi domin score nasu ɗaya amma a haka Widad yake faɗin rage masa akayi, a cikin wanna set nasu su hamsin ne amma su goma sha biyar ne suka wuce. Daga nan aka musu qarin girma suka cigaba da aiki, saidai kuma a yanzu Widad yana ƙoƙari sosai har ya zaman yanzu aikin sa shi ke zuwa na farko kafin na Amjad, shi kansa mamaki abun yake bashi har ya dasa ayar tambaya akan hakan, sai kawai ya shiga bincike, akwai wani aiki da aka basu na bincike akan expired magungunan da ake shigowa dasu amma sai a sauya musu kwali a dinga sayarwa mutane, ko da suka haɗa report suka kai sai aka yaɓawa Amjad matuƙa. Da mamaki Amjad ɗin ya ɗago dan yasan abinda yayi sai idonsa ya sauka cikin na Widad dake masa murmushi, baice komai ba ya ɗauke Kai . Sai da suka fito widad ya sameshi tare da masa godia dan ya gano cewa lalle Amjad ba irin mutanan da yake tunani bane, duk zazzafar gasar da suka dinga tafkawa ashe wai saboda ya sanya Widad ɗin ya jajirce ne, kuma shi ya sanyawa Widad answer na questions ɗin da aka basu lokacin jarabawar qarin girma, shi yake qin yin aiki ya barwa Widad, ba ƙaramin nadamar abubuwan da ya dinga wa Amjad ɗin yayi ba a lokacin daya gano wanna abubuwan. Dan ya tabbatar ko me ya zama da taimakon Amjad . Wannan shi ne silar ɗinkewar su, suka zama kamar wasu yan uwa, su kansu hukumar tasu ba karamin daɗi sukaji ba saboda ganin haɗin kan masu kwazo biyu, kamar yadda Amjad ya tabbatar sunan widad ya shiga cikin jerin masu ƙwazo, haka yasa shima widad ya saukar da Kai ya ke koyon wasu abubuwan bilhakki da gaskiya a wurin Amjad ɗin, dama shi Amjad bashi da matsala, sosai suke matuƙar ƙaunan Junan su dukda basa bayyanawa, dan Widad ba dai miskilanci ba ga jin kai da yanga kamar wata mace, amma duk da haka Amjad ya iya zama da kayansa, suyi faɗa su shirya, duk da faɗan baya wuce kan iya shegen Widad din da in ya motsa yake ƙular da Amjad ɗin. WANNA KENAN. Game da Syrup da Amjad ya sha lokacin da zai je wurin su BB LALO wanda wasu suke tambayar shin yana shaye shaye ne ? Ko ɗaya Amjad jami'i ne da ya san illar da shaye shaye ke yi a ƙwaƙwalwa kuma yake yaqar ta'amali da hakan, abinda ya sha ba komai bane face biotin liquid, shi ɗin maganin dake causing inaccurate interpretation a blood test result Wanda shi ne abinda su BB LALO sukayi wato su basa tantance mutum ta fuska ko murya saboda sunsan akwai ta bogi dan haka suke ɗaukan sample na jinin mutum, shi kuma Amjad shi ne yayi amfani da biotin dan kauda Bara. Cikin tsananin tashin hankali Juraysh ya miqe bayan ya gama waya da Amjad ɗin saboda shi bai taɓa tunanin abin zaiyi worst haka ba, amma kuma abinda zuciyar sa ta ƙasa aminta dashi shi ne Amjad criminal ne, duk da in har wannan abu ya tabbata na cewa hukuma na nemansa to fa dolensa ya yarda amma how comes, dan makullin mota ya zara ya fito cikin sauri, mahaifiyar su da suke kira da Aunty ya tarar tana yiwa ƙannensa magana kan suje su kwanta dare yayi, ganin fitowar sa a birkice kamar bai gansu ba yasa ta kiran sunan sa , "Kai!". Ta faɗa Kasancewar Juraysh ɗan fari yasa bata iya kiran sunan sa kai tsaye saidai tace kai ko kuma yaro. Dakatawa yayi tare da juyowa ganinsu ya sashi faɗin, "Ahh Aunty baku kwanta ba?".........."ina zaka ka fito kana ta zabga uban sauri haka?"......... ɗan shafa goshinsa yayi tare da faɗin, "zanje wurin Anah ne". "Anah? Lpy dai ?"........... Ta tambaya tana ƙureshi da ido, ɗauke kansa yayi tare da faɗin, "Amjad ne ya barmin saƙo a gidan shi ne nakeso in je in karɓa". "Kuma shi saqon ba'a iya bari a karɓeshi da safe , dare fa yayi yanzu, inaji ma 11 ta gota, kuma kasan yadda gari yake"..........."karki damu Aunty yanzun zan karɓo na dawo". "Shikenan, a dawo lpy, Karka daɗe". _______________Tsaye suke dukkansu su ukun a parking lot suna tattaunawa kan Batun Amjad da suke da tabbacin zuwa yanzu an yi gaba dashi dan sun kira ɗaya daga cikin yaran Amjad ɗin ya shaida musu sunzo sun tafi dashi, tunda dama Awais din ne ya faɗa musu inda zasu sameshi. Awais ne ya ce , "Yanzu duk ba wanna ba tunda har anyi gaba dashi ina ga kawai a dawo da yarinyar nan da iyayen ta suce su kawai sun yafe"............ Julaybin da ya tafi wani tunani ya ce, "Kai Baka da hankali Awais wani lokacin sai Ka dinga abu kamar Ka manta hukuma ba wurin wasan yaro bane, ai kawai a boyesu in komai ya lafa a Kara musu wuta su bar kasar domin ni banason wani jeka ka dawo"........... Kafin Awais ya bashi amsa motar juraysh ta shigo ciki, dariya Nuhail yayi da faɗin, " kaga Hamana ba zama tunda an naɗe firauna".......... Dariya shi ma awais ya kwashe da ita suka tafa, shi dai Julaybin bai ce komai ba sai bin motar juraysh ɗin da yayi da kallo . Juraysh kuwa hana fitowa ya wuce ciki ba tare da ya nuna ya gansu ba a zuciyar sa faɗi yake dole yayi wani abu dan shi whl bai yadda da duk wannan Abubuwan da ake faɗa ba, especially yanzu da ya shigo yadda yaga farin ciki fuskar su Nuhail ya tabbatar masa akwai wani Abu. TO GA DAI SU AWAIS GA KUMA SU HAJJ ZAWAAD KOWA NA TUNANIN AIKIN SU NE YAYI NASARA BAYAN KUMA DUKKANSU ZAN IYA CEWA TAFIYA SUKE AKAN GADAR DA SHI UBAN GAYYAR NE YA SHIMFIDA DA KANSA. TAYA SUKE TAFIYA AKAN GADAR SA BA TARE DA SUN SANI BA ? KO YA WASAN ZAI KASANCE ? WAYE DAGA CIKIN YARAN AMJAD YAKE CIN DUNDUNIYAR SA? MUJE ZUWA DOMIN SAMO AMSOSHIN NAN TARE DAKU. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______39 Misalin ƙarfe 2 na dare fitsari ya tashe ta, leqawa bayin tayi taga ba ruwa hakan ya sata ɗaukan buta ta dauki wayarta ta kunna Flash light ta fita, tsakar gidan duhu ƙirin dan ba wuta, mutum ta hango tsaye ya ɗage Kansa sama, ƙurawa dan bakinsa ido tayi hakan ya sata fahimtar Magana yake, yana sanye da sweet pant black sai white vest, dukkan hannuwan sa riqe da waist ɗinsa, haske shi tayi da fitilar wayarta ta amma bai juyo ba, ba tare da wani ɗar ba ta nufeshi tana zuwa ta sake haske fuskar sa, ajiyar zuciya ta sauke ganin Jey ne. "Ashe ma Kai ne, har nace ko wani barawon ne ya shigo mana"............ Ido kawai ya zuba mata ba tare da yace komai ba sai dan bakinsa dake tauna chew gum kaɗan kaɗan cike da salo, juyawa tayi da nufin zuwa ta ɗaibo ruwan taji an figo ta, wani irin juyi yayi da ita tare da shigewa bayan wata ballalliyar kofar da aka jingine jikin bango, kallon sa take cikin ido dan gabaɗayanta rungume take a jikinsa, da hannu ɗaya yake riqe da ita dayan kuma ya saka ya rufe bakinta da hancinta, idonsa cikin nata yake mata alama da kar tayi wani yunquri. Kawu Adamu ne ya fito da ƙatuwar sanda yana faɗin, "kaii su waye Anan? Yanzu kuma an fara biyo dare za'a mana ɗan hali saboda anji na saya machine, to whl ba ɓarowa ba ko aljani bai isa in ajje ya ɗauka ba in kuma da Wanda ya isa ya fito muyi gaba da gaba"............. Ya faɗa Yana daga sandar sa, Umma delu ce ta biyo bayansa tana faɗin, " Haba Malam wai miye haka? ta ya zaka fito tsakar dare Ka tara mana mutane, waye zai wani bi dare ya hana kansa bacci akan wata roba robar Ka".............. Nan fa ya juyo kanta, "To to yar hassada, ke Delu ki fita ido na, to ita dai roba robar da kike rainawa ita da yawa suke nema basu samu ba dan haka ki barni na yi takiya ". "Wani karamin ɗan iska ko yar iskar ce ta hana mu bacci tsakar dare, ɗan baccin da bawa zaiyi ma ya kwantar da haƙarƙarin sa sai azo a dinga firgita shi, ni whl bana son irin haka".......... Faɗar Shamsy yana fitowa daga ɗakinsa kansa sanye da under skirt. Kallon banza kawu adamu ya masa tare da faɗin, "Harda su kaza a cin danƙo, Kai Ka Bari sai ƙashin Ka yayi kwari Ka zama namiji sai kazo kayi magana "..........."Ahayye cas, yo ni me zai haɗani da kwarin ƙashi ina mace me rauni, amma fa in ka kawo min ba gishiri whl sai in iya kwaɓewa mu daku a fidda raini, kai yanzu na tsaya ka tsaya ai sai a zaɓeni ba'a zaɓe ka ba, ahhh yoo saboda ALLAH fa"............ Ya ƙarashe yana wani lankwashe Kai, takaici ne ya kawo kawu Adamu wuya, tsaki ya buga tare da jan sandar sa ya koma ɗaki umma Delu ta rufa masa baya. "Wuuu yaji tsoro".......... Shamsy ya faɗa yana ɗaura hannunsa a baki kamar me guɗa, sannan ya juya ya koma ɗakinsa. Sai a lokacin suka saki numfashi a tare dan zakuyi mamaki in nace muku tsawon lokacin nan Jey da Hushaima basu shaqi ko fitar da numfashi ba, Wanda hakan ya sake sawa Jey shakkun Hushaima saboda ba kowa bane zai iya ɗauke numfashi na tsawon wanna mintunan ba Ka ganshi daram. Fitowa sukayi yana riqe da tsintsiyar hannun ta gam, ganin yana ƙoƙarin nufar ɗakinsa da ita yasa ta faɗin, "Malam ina zamu ne ni Ka sakeni".............." Shut up". Ya faɗa a ɗan zafafe yana ɗaura yatsansa akan ɗan bakinsa alamar ta rufe masa baki. "Anki ayi shattaf ɗin whl Ka sake ni ko na tara ma jama'a".......... bai saurare ta ba bai kuma tsaya ba har saida suka shige ɗakin nasa, wurgata ciki yayi tare da rufe ƙofar ya kunna solar touchlight ɗin dake ɗakin take ɗakin ya dau haske rauuuu. Dukda a zafafe ya wurgata cikin ɗakin bata yarda ta faɗi ba, tsaye take tana kallon sa don ganin iya gudun ruwan sa. Wata karamar kujerar roba dake gaban wani table ya nuna Mata tare da faɗin, "zauna"........... ba musu ta zauna, laptop din sa dake buɗe ya rufe tare da tattare duk wasu tarkace sannan ya zauna bakin table ɗin kana ya ce, "Ina so in tambaye ki a karo na biyu, wacece ke?" Dariya tayi cike da gaɓunta ta ce. "Ikon ALLAH yau ni ake tambaya wacece ni, gsky daɗi na da gobe saurin zuwa, ban taɓa tunanin wanna ranar zatazo kwana kusa ba ai"........... Shi dai Jey kallon ta yake ko kiftawa babu, gyara zama tayi tare da gyara murya ta fara magana, "Da farko suna naaa Hushaima Sahnish Shazeen, sannan ni mutum ce kamar Ka ina aiki a Starlight beauty Co. kuma nayi aiki a wurare daban daban, nayi cleaner a wata ma'aikata, nayi aikin gyaran su zobo a wani kamfani, nayi aikin raino a wani gida, nayi aikin girka abinci a otel(hotel), haka a wata moll (Mall) ma ina ɗan zagaya musu wurin ko da wasu zasu zo su nemi a zaɓa musu irin su man gashi ko na jiki masu kyau, daga ƙarshe kuma yanzu ina aiki a wajen gyaran jiki da sauransu"......... Kallon yadda take magana cike da confidence da kuma bakin gskyr ta da ya hango cikin idonta yayi, Amma duk da haka sai ya ce, " In kin gama shirya tatsuniyar taki saiki faɗamin ta asalin". "Me sa to zan ma karya, tukunna ma in kasan bazan faɗa gsky bane me sa Ka tambaye ni, to kaje Ka tambaya kowa wacece Hushaima tunda ni ba Ka yarda da abinda na faɗa ma ba, Ni bana ƙarya kuma bana munafurci". "Ai nasan hanyar tambayar kuma zan iya sanin waccece ke ba tare da naji daga gareki ba, kawai na zaɓi na tambaye kin ne. Ki fadamin wace ke, daga ina kuke? Su waye mahaifanku?"............ Cikin wata irin fusatar data bashi tsoro ta miqe tana faɗin, "Shin baza a iya sanin mutum dan kansa ba sai an jingina shi da wani, dole dole sai kana da iyaye ko kuma sai ansan matsayin iyayen Ka tukunna za'a ce Kai wani ne, tukunna ma miye haɗi na da kai "........... Cikin wanna munafukar muryar tasa ya ce, "lower your voice madam, karki tarawa kanki jama'a". "Whl karka ƙaramin magana, kuma bazan rage muryar ba Kai kana tunanin akwai Wanda nakejin kunya ne, wai ko dan an same ni a ɗakin ka zanji wani abu ne, ban ajje uban kowa da zaice na jawo masa abun kunya ko abun magana ba dan haka ban damu da duk wasu maganganu ba, mu kaɗai muke rayuwar mu kuma mu kaɗai zamu rayu bamu buqatar kowa da komai ko kuma sauya tunanin kowa a kan mu, duk ma yadda kuka ɗauka hakan ne"........... tana kai wa nan ta nufi kofa a fusace, saurin shan gabanta yayi. Cikin wani irin fushi ta ce, "Whl in baka kauce Ka ban hanya ba sai na sharara ma Mari"........... Zaro ido yayi cike da ɗinbin mamaki kafin ya haɗiye wani yawu daƙyar ya ce , "Okay naji but zauna na yarda da abinda kikace kawai tsokanar ki nake, ke ɗin wata ce kuma jajirtacciya da bakya buqatar bango domin jingina bakya buqatar dakalin dafawa, haka kuma bakya buqatar taki domin tsirowa, irin Ku abun so ne da alfahri a ko ina, ke din wata ce Hushaima plz have a seat". Ya ƙarashe da wani irin sauti yana nuna mata wurin data tashi, ɗagowa tayi ta zuba masa idanunta da suka rikiɗe zuwa ja a lokaci guda, ɗan ja baya yayi tare da harɗe hannuwansa a ƙirji yana jifanta da wani irin kallo, "Bazan iya zama ba ina son kaɗaicewa a yanzun, ka bani hanya"........... Ba musu ya matsa Mata ta wuce, neman wuri yayi ya zauna zuciyar sa fal da tunani iri iri. Ko da ta dibi ruwan daga rijiya direct a kanta ta shiga watsawa saida tayi wurin sau uku ko sanyin ruwan bataji sannan ta sake ɗaibo wani ta zuba a butar dake wurge anan ta wuce ɗaki, fitsarin ta shiga tayi sannan ta dawo ta sauya kayanta dake ɗigar ruwa ta kwanta tana sauke numfashi. Ranar kusan makara tayi sallah dan har saida Sahnish ya shigo, sosai ya sha mamaki ganin Ƙofar ɗakin su a buɗe. Dan ta saba in dai lokacin sallah yayi saita shiga ta tabbatar ya tashi saisa da bai ganta ba ya biyo sawu, tana kwance ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba amma ta kasa tashi. Hannunta Sahnish ya shiga bubbugawa yana Kiran sunan ta saidai har Shazeen ta buɗe ido ta tashi ita bata motsa ba, a firgice ya Kira sunan ta da ɗan ƙarfi, wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke tare da buɗe idanun ta da har yanzu basu washe ba . "Hushaima lpy? Ko baki da lpy ne?" "Sahnish har kun tashi mie?"......... Ta faɗa tana tashi zaune. "Har ma anyi Sallah ai, nayi mamaki da banji yau kin shigo wuri na ba kamar yadda kika saba saisa ma na shigo na duba".......... da sauri ta miqe tana faɗin, "Miyesa baka tasheni da wuri ba, ni ai kafin ayi Sallah nake shiga na dubaka". A gurguje taje tayi alwala ta dawo Shazeen ma data buɗe ido ta shiga tayi, shi dai da kallo ya bisu har sukazo suka tada sallar suka idar, sai lokacin ya ce, "Hushaima meya faru dake ?" . "Meka gani?".......... Ta tambaya ba tare data kalleshi ba. "Fuskarki ta nuna kamar akwai damuwa". "Na danyi ciwon Kai ne amma na sha paracitamol (paracetamol)". "Dama na sani za'ayi haka, ko in ɗauko miki ragowar maganin maleria nan ki Sha?"........... Tashi tayi ta cire hijab ɗin ta wuce toilet ta ɗauko bucket a toilet tana faɗin, "Ni fa naji sauki ba abinda zan sha kaji". Daga haka tayi waje samu tayi already mutanan gidan sun hau layi dan yau ta makara, Bonbon dake sawun farko cikin makirci ta ce, "Aunty Hushaima zo ki ɗiba mana ni bari na dawo kan layin naki"..........." Kar na takura Miki bonbon ban sani ba ko uzurinki yafi nawa, karki damu zan jira ". "Ah ah gsky". Ta faɗa tana barin in da take tazo ta ɗauki bokitin Hushaima ta sa akan layin ta sannan ta ɗauke nata ta dawo dashi layin Hushaiman, godia ta mata sannan ta koma kan layin nata. Tsaki Jamcy taja tare da faɗin, "Shiga sharaf ba shanu, a dai rage shishigi". "In ba tsoro ba mutum ya ambaci suna mana tarihi ya maimaita kansa yanzu sai na sake rage yawan hakoran mutum"........... Dariya duk suka kwashe da ita wadda ta Ƙara tunzira Jamcy amma batace komai ba sai kwafa da taja dan har yanzu tana jinyar bakinta ne. Haka Hushaima ta ɗiba ruwan ta wuce ba tare da tace da su ci kanka ba, bata samu Sahnish a ɗakin ba sai Shazeen dake ƙarasa assignment ɗinta dan haka ta shigewarta wanka Saboda yau zata aiki. -----------------√ Cikin kuka take faɗin, "Dad Dan ALLAH ka ban wayata, mumu ki sa baki mana" . Zaburowa mumu tayi da faɗin, "Ni sai dai in sa miki duka wawiyar banza wawiyar wofi ". "Mumu Amma naga ai mijina ne Kuma ........" Dad ne ya tare da faɗin, " To tattabara sarkin aure, tun wuri ina shaida Miki ki cire zancen auran nan a ranki dan sunan sa warwararrre, tukunna ma a prison zakuyi zaman auren ne? mutumin dake hannun hukuma a yanzu"............ Wani sabon kukan Nayrah ta fashe dashi, a lokacin ne Kuma doctor ya shigo ɗan kallon su yayi tare da yin sallama ya ƙarasa shigowa, amsawa sukayi dad ya masa ya aiki, sake dudduba jikin Nayrah ɗin yayi kafin ya ce, "Ranka ya daɗe in baza ka damu ba ku ɗan bamu waje ina so nayi magana da ita". "Ba dai wata matsala ko Dr?"........... Mumu ta tambaya. Girgiza mata Kai yayi kana ya ce, "Nop babu, kawai Ina so na mata wasu yan tambayoyi ne". Ba musu suka juya suka fita Saida suka rufe ƙofar doctor ya ce, "Sorry to interfere but wanna biological parents dinki ne?".......... Nayrah da har lokacin kuka take me cin rai na jin cewa an kama Amjad ɗin ta, ɗaga masa Kai kawai tayi alamar eh. Ɗan shuru yayi kafin ya ce, " Ya kamata ki rage Kukan nan ko ki daina shi gabaɗaya for your health, a yanzu hutu kike buqata ba wai ki dinga tafasa jinin ki ba ".........." Dr ka aramin wayar ka Dan ALLAH ". Ta faɗa da dasasshiyar muryarta. "Me zakiyi da ita?" ............ "An kwace tawa ne Kuma inaso na kira mijina"........." So you are married?". Dr ya tambaya da mamaki. Sake gyada masa Kai tayi alamar eh, dan shuru yayi can Kuma ya zaro wayar ya cire password sannan ya bata. Hannun ta har rawa yake wurin karɓa da sauri ta loda number Amjad a wayar sannan ta kira saidai baya shiga haka taita gwadawa amma amsar ɗaya ce wayar a kashe, dan dole ta haƙura ta bawa Dr wayar tare da komawa ta kwanta. Bai ce mata komai ba ya ɗauki kayan aikin sa yayi waje anan ya samu Dad Mumu ta sashi gaba tana ta masa zazzage zazzage, "Emm inaga ba damuwa zaku iya tafiya, ya kamata a barta ta huta dan tana buqatar sa Kuma bama san ana hayaniya sosai"........... Ya faɗa saboda ganin zaman nasu ba abinda yake haifar wa sai ƙarin tashin hankali wa marar lpyn. Mumu ce ta ce, "Dr ai ni nake kwana a wajen ta"........... Girgiza mata Kai yayi, "Hajiya ko bakya nan mu nan hospital ɗin muna da kwararrun ma'aikata dake kula da majinyata, ba laifi idan kunje kun dawo da safe "........... Dad ya ce, "Shikenan ba damuwa duk abinda ake ciki in da wani abu ka kirani ka faɗamin"..........."karka damu Alhaji, ba wata matsala in sha ALLAH ". Daga haka suka shiga yiwa Nayrah ɗin sallama hankalin su kwance cewa an kama Amjad basu da wata sauran fargaba. Ko da suka shiga samun ta sukayi kwance ta bawa ƙofar baya, Mumu ta ce, " Inajin ma tayi bacci ai muje kawai". Juyawa sukayi Dad a gaba Mumu a bayansa kamar wata uwar sa suka fice tare da jawo mata ƙofa, duk tana jinsu amma taƙi motsawa. Juraysh kuwa daƙyar ya lallaba Anah sannan ya baro gidan Misalin 12:30am. Shi kuwa Amjad suna dawowa gidan nasa, ɗakin sirrin sa ya shige ya Kira su Ash conference call, tattaunawa suke Kan aikin da suke na shadow Amjad ya ce, "Widad a wurin Ka ne fa har yanzu ba wani labari, har yanzu baka samo mutumin da suka bada detail a Kansa ba ne?". Shuru yayi har saida Amjad ya ɗan buga hannun sa a goshi dan ya sallama widad shiririta kawai yakeyi dan yasan halinsa wani sa'in, ya tsinto yar muryar nan tasa kamar ɓarawon da aka ritsa, " Na samo komai, kawai Ku gama naku aikin sai Ku min magana"......... Cikin rashin yarda Amjad ya sake faɗin, "In da akwai wani taimako da kake buqata Ka faɗa tun wuri?" . "Babu"........... Ya faɗa daga nan suka cigaba da tattaunawa shi dai widad sai in ta kama yake sanya baki amma yana sauraran su, Ace ya ce, "But widad what's special game da mutumin?". Shuru sukaji suna dubawa suka ga ya sauka daga Kan layi, Amjad ya ce, "Don't worry dukda akwai abubuwa a gabana zan bibiyi abun".......... Daga haka sukayi sallama kowa ya kashe. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______40 & 41 Washe gari da wurwuri ya tashi ya shirya dan dama baiyi wani baccin kirki ba, sanye yake da milk silver dust yard ɗinkin yayi fitting ɗin jikinsa sai tashin kamshi yake, ga gemun nan da gashin baki ya sha gyara sai ɗaukan ido yake, haka gashin kansa ma duk ya kwanta luf kamar na ɗan jariri nan kuwa tsabar kuɗin da yake ci wurin gyara ne, kunnen sa kamar ko da yaushe maqale da wani ɗan white bud. Yana fitowa ya tarar da Philip yana jiran sa gaishe shi yayi sannan ya ce, "Boss your breakfast is ready"............ Dan akwai cooks maza dake wa yaran gidan abinci in kuma yana nan gidan ne sai su masa nasa daban, zaku sha ɗinbin mamaki in nace zan fada muku yawan mutanen da suke aiki ƙarƙashin Amjad kuma duk shi ke ɗauke da duk wata dawainiyar su ba ruwansa da banbancin Addini, saisa suke jin akan sa zasu iya bada rayuwar su, saidai kuma a yanzu an samu zakka wato dan qunar bakin waken dake sanar dasu Awais duk motsin Amjad ɗin. Ɗan kallon saitin dinning ɗin yayi kafin ya ce, "Anya zan iya cin wani abu kuwa Philip, kasan aikin dake gaban na kuwa but let me just have a tea, jiya ka sanar da Wali (ɗaya daga cikin cook ɗin) batun ƙaruwar sojojin da muka samu?". "Eh boss tun a jiyan ai, yanzu ma inajin sun gama yin breakfast ɗinsu". "Okay ". Daga nan bai Ƙara magana ba suka nufi dinning ɗin Philip yaja masa kujera ya zauna ya yi serving ɗinsa black tea da snacks sannan ya koma falo ya zauna jiran sa har ya gama ya fito, tashi yayi ya bi bayansa sukayi waje suna magana ƙasa ƙasa, tasowa su Aram sukayi lokacin da suka ga fitowar sa bayan sun gaisa ya ce, "Daga yanzu Ku zauna a gida kawai idan da wani aiki zan muku magana, amma yanzu ga wa'anda zamu fara fita tare na wani lokaci ". Cikin Rashin jin dadi su Aram suka amsa da to dan sun riga sun saba da kasancewa dashi in dai yana ƙasar. " Muje kamal". Ya faɗa yana wucewa, da sauri ɗaya daga cikin sojojin ya wuce da niyyar buɗe masa, Philip yayi saurin yi masa magana ƙasa ƙasa, waskewa yayi yaja ya tsaya jikin motar shi kuma ya buɗe masa ya shige sannan kamal ya shiga driver seat, ɗaya daga cikin sojojin ya shiga passenger front seat sauran kuma suka shiga sauran motocin su tare da sa motar sa a tsakiya suka fice daga gidan Philip kuma ya juya ya koma ciki. Direct asibitin da aka canzawa Nayrah suka nufa, sosai aka dinga kaucewa ana basu waje saboda kallonsu kawai zai sanya ka saki fitsari a wando, already yasa anyi magana da Dr ɗin daman tun dare dan haka office ɗinsa suka tambaya aka nuna musu. Wasu mutane dake zaune a reception na hospital din, ɗaya ya ce, " Wai wancan ba Amjad din nan bane?"........... ɗayan ya amsa da, " Shi ne mana, baka ga har wasu jami'ai na masamman masu take masa baya aka bashi ba"..........."to wai har yanzu ba'a gama binciken bane?"............. "Kash kana da maida zance baya, to wai dama ba da haka ake so a raina mana hankali bane, su dama ai tunda manya ne ba'a musu hukunci kawai za'a ɗauke mana hankali ne daga nan a samu fitar dashi daga ƙasar sai an manta da batun sannan a dawo dashi, nawa akayi irin haka, kai yanzu fa in kana da connection kayi duk abinda kake so kawai".........." To in dai hakane ai akwai alkalin Alkalai, shi zai sakawa rayukan da aka salwantar"..........." Barsu kawai da halin su Rabiu, je ka duba mana result din test din ya fito ne ?". __________Suna shiga likitan ya miqe cikin girmamawa ya ce, "barka da zuwa ranka ya dade".......... Hannu ya miqa masa sukayi musabaha sannan ya ce, " Ina ne room din ?"............. Da sauri Dr ya ce, "Ahhh to muje kawai in nuna muku mana". Ya ƙarashe yana zagayowa ya fito daga gaban table ɗin nasa ya nufi ƙofa cikin hanzari, ilahirin jikinsa rawa yake saboda wa'annan firgitattun sojojin da bai taɓa zaton akwai irinsu a ƙasar Nifaz ba, binsa sukayi zuwa ɗakin da Nayrah ɗin take, tana zaune akan kujera hannun ta riqe da mug ɗin tea da Nashwa ta zuba mata, sai wata cleaner dake canza bedsheet. Sallama Dr yayi ya shiga sai wani soja sannan Amjad da kamal dake bayansa sauran kuma sukaja suka tsaya a bakin Ƙofar. Nayrah ta Kai spoon ɗin tea bakinta bata san lokacin da tayi masa wata wawiyar kurɓa ba saboda ɗagowar da tayi idanunta ya sauka kan Amjad, tari ta fara ba ƙaƙƙautawa da sauri Nashwa ta karɓi mug ɗin ganin yadda hannunta yake rawa sannan ta shiga jera mata sannu. Ɗagowa ta sakeyi a lokacin da tarin ya lafa tun daga kan kafarsa dake sanye da kyakkyawan brown loafers har zuwa kan kyakyawar fuskar sa dake fitar da wani sirrin kyau . "Ina kwana ya Amjad"........... Nashwa ta faɗa tana tashi daga gefen kujerar. " kin tashi lpy?". Ya maida mata da tambaya a maimakon amsa gaisuwar, ɗan ɗago Kai yayi ya kalli Kamal, da sauri Kamal ya juya wurin su Dr tare da faɗin, "In ba damuwa mu ɗan je daga waje Dr".......... Ba musu Dr ya fita yana faɗin a fito lpy, Nashwa ma gyalenta ta ɗauka ta fita, cleaner kuwa dama tunda suka shigo Dr ya korata, dukkansu ficewa sukayi suka ja musu ƙofa ya rage daga shi sai ita, gefen ta ya Ƙarasa ya zauna tare da riqo hannayenta gabaɗaya cikin nasa ya Kai baki yayi kissing yana murmushi, sai lokacin ta dawo nutsuwar ta cikin rawar murya ta ce , "Amour Kai ne gabana"........... Gyada mata Kai yayi alamar eh, kuka ta fashe dashi tare da faɗawa jikinsa, riqota yayi yana shafa bayanta a hankali yace, "Stop crying I'm here okay ?".......... Cikin kuka ta ce, " Amour bansan meysa Mumu da Dad canza ba gabaɗaya sun daina so na, haka jiya suka kwace min waya, sannan suka canza min asibiti duk dan su nisanta ni da kai, kuma su kace wai anzo an tafi dakai saidai in prison zan bika mu zauna "............." Ya isa Ninie, ai na riga na faɗa miki in har kin shirya aure na to sai kin shirya ɗaukan duk wani qalubale kika ce kin amince, wannan shi ne abinda na guje miki tun a baya Ninie ba wai ina jan lokacin auran mu bane haka kawai ina da dalilin yin haka saidai a lokacin ke kuma kin kasa ganewa, ba ƙarya su dad sukayi ba wanna sojojin da kika gani an sasu ne su dinga tsaro na, har sai sun kammala bincike saboda suna gudun a neme ni a rasa, amma ki kwantar da hankalin ki".......... Wani sabon Kukan ta sake fashewa dashi. Tausa murya yayi da faɗin, "Ninie kin fa san baki da lpy ko ? shi ne kike nema ki ƙarawa kanki damuwa ni ma Kuma ki samun, meysa baza ki kwantar min da hankali bane ninie, meysa bazai zama in nazo wurin ki na samu sauƙi ba, ya kamata ace ki zama jaruma"........... Ɗagowa tayi daga kirjinsa tare da goge hawayen fuskarta tayi murmushin da bai Kai zuci ba, sai faman gyada masa Kai take amma ta ƙasa cewa komai, tashi yayi ya ɗauko gorar ruwa ya dawo ya zauna tare da buɗewa ya sanya mata a baki, ba musu ta buɗe bakin ta fara sha ba wai dan tanajin ishirwar ba sai dan wanna shi ne na farko da zai shayar da ita wani abu da hannunsa. Ta shagala a kallonsa har Saida ruwan ya kwareta. "Ufff sorry". Ya fada yana hura mata iskar bakinsa a fuskar ta tare da ɗan bubbuga bayanta a hankali, gyada masa kai tayi alamar she's Okay sannan ya rufe gorar ya ajje ya jawo kanta ya kwantar a kan shoulder ɗinsa, wayar sa ya ɗauka ya Kira kamal yana ɗagawa, ya ce, "Kamal turomin Dr ɗin". Ba'a fi 3 minutes ba Dr ya shigo, ba tare da ya motsa ba ya ce, " Ya jikin nata?". "Ai ba wani internal injury ranka ya dade sai dai bruises ɗin da muke treating"........... Gyada kansa yayi sannan ya ce, "kaje ka rubuta min sallama sannan ka rubuto duk wasu abubuwan da zata buqata, ka Kuma sama mana nurse ɗin da zata kula da ita a gida, Kar a wuce 15 minutes"............ Yana kaiwa nan ya miqe tare da kamo hannu Nayrah ɗin data bi shi da kallon rashin fahimta, ƙoƙarin tashi tayi da taimakon sa, Dr ya ce, " Ai ranka ya daɗe yanzu ba zai yiwu ta taka ƙafar sosai ba saidai ko a kawo wheel chai........." Kasa ƙarasawa yayi saboda wani kallo da Amjad ɗin ya watsa masa tare da rankwafowa ya ɗauke ta kamar wata yar baby, waje ya nufa da ita a haka, su Kamal na ganin sa suka rufa masa baya, ɗan dakatawa yayi sannan ya ce, "kaje ka taho da wancan sister ɗinta ta "............ Ya ƙarashe yana cigaba da tafiya, a cikin motar da yazo ya sanyata sannan ya rufe ya zagaya shi ma ya shiga, ita dai Nayrah da kallo kawai take binsa har Kamal ya ƙaraso shi da Nashwa, rage glass ɗin bangaren sa yayi tare da faɗin, "Ita ta shiga gaba shi Kuma Masood(ɗayan sojan) ya koma wancan motar tare da su Joseph, akwai nurse ma da Dr zai bada ta shiga wadancan motocin tare dasu"..........." Okay boss"......... Kamal ya amsa tare da buɗewa Nashwa gidan gaba ta shiga sannan ya koma wajensu Joseph. Bayan an gama komai suka dawo tare da Dr ɗin motar da su Amjad ke ciki. "Zaka ga saqo"........ Shi ne kawai abinda ya faɗa sannan ya rufe glass ɗin, Dr kuwa sai godia yake wa Kamal kamar shi ya masa albishir ɗin ko kuma shi zai bashi kyautar, buɗe mota kamal yayi kawai ya shige mazaunin sa na driver. Nashwa ce ta ce, "Nayrah baba jamilu fa yana nan yana jira"........... Ɗan murza yatsu Amjad yayi kafin ya ce, "Da ALLAH Kamal yi sauri kaje ka sallame shi kace ya tafi gida kawai, karka daɗe". Ya faɗa a qage yana duba agogon hannunsa, da sauri Kamal ya sake fita yaje ya sallami drivern sannan ya dawo suka tafi. "Bluevielle". Ya faɗa a takaice . "Okay boss ". Kamal ya amsa. A bakin gate ɗin wata haɗaɗɗiyar Estate suka tsaya, Saida akayi searching ɗin motocin nasu sannan suka shige. Estate ne na bugawa a jarida ya haɗu iya haɗuwa, an ƙawata shi da wasu irin shuke shuke ta ko ina. Gidaje ne a jere amma kowani gida zagaye yake da wasu dogayen bishiyu sai yar hanyar shiga da suka bari, manufa babu katangar data yanka wa mutum iyakar yankin gidan sa, sai dai bishiya kawai, estate ɗin tsit ba hayaniya sai kukan tsuntsaye da suka kafu a bishiyoyin. Gaban ɗaya daga cikin su Kamal yayi parking sannan ya fito ya buɗewa Amjad ɗin da har sojoji sun zagaye motar tasu, Saida ya fito sannan ya miqawa Nayrah hannu ta kama tana ƙoƙarin ɗaura ƙafarta kan ƙasa yayi sama da ita, cikin gidan ya wuce ba tare da ya kalli kowa ba. Kallon Nashwa da tayi tsuru tsuru Kamal yayi sannan ya ce, " ki shiga mana, ke ma nurse ku shiga tare, ai kin ɗauko jakar magungunan ko?". "Yes sir"........... Nurse ɗin ta amsa sannan tabi bayan Nashwa suka shige . Bai direta a ko Ina ba sai cikin wani ƙayataccen bedroom da ya gaji da haɗuwa, a bakin gadon ya ɗaura ta sannan ya ɗan rankwafo kamar me raɗa ya ce, "Zanje wani wuri yanzu in dawo, maybe anjima ki ganni amma in baki ganni ba karki damu zansa a kawo maki waya da Kuma duk abinda zaki buqata ga Nashwa ga kuma nurse nan okay?".......... Riqo hannun sa tayi tare da faɗin, "Ina zaka tafi Kuma? sannan nan ɗin ina ne ?". "In har baki na so a kame mijin ki bane to dole sai na tafi yanzu, nan kuma shi ne gidan ki kece matar gidan".......... Ya karashe yana mata wani sassanyar murmushi cike da bata kwarin guiwa. Idanun ta ne suka ciko da hawaye, ba tare data saki hannun nasa ba ta shiga jero masa addu'o'in tsari da kariya, Saida ta gama sannan yayi hugging ɗinta cike da zallar soyayyar ta dake neman sauya masa tunani, After his parent ba ya jin akwai wanda yake so sama da Nayrah saboda ita ɗin abar so ce a gareshi, ta bashi dukkan soyayya da yarda ta kuma riqe masa alqawari. After some minutes yayi breaking hug ɗin yana kallon cikin idonta da gashin idon e jiqe da hawaye sai wani far far take dasu wanda haka ya kara Mata kyau, one side smiling yayi tare da kamo fuskarta ya manna mata wani light kiss da ya sata kallonsa ba shiri saboda yadda taji abun unexpected, da sauri ya miqe ya nufi ƙofar fita yanajin kamar ya fasa tafiyar, saidai bashi da wannan damar a yanzu Wanda shi ne dalilin da ya hanashi yin aure tun a wancan lokacin saboda manyan ayyukan dake jiransa sam bayaso ya shiga hakkin ta, saidai kuma wannan nasa tsarin da tunanin ne ga tsarin da ALLAH ya masa dan haka bashi da ikon canza hakan. A falo ya tarar da Nashwa tare da nurse ɗin nan sunyi tsumu tsumu kamar shege a rabon gado. " Ina wayar ki?". Ya tambaya yana tsareta da ido, ba musu ta miqa masa, karɓa yayi ya zura a aljihu sannan ya ce, "Zansa a kawo maki wata da Kuma duk abinda zaku buqata, Akwai me gyaran gidan a waje idan kuna da buqatar wani abu kafin su Aram su ƙaraso"........... Da "to". Ta amsa sannan tayi masa fatan dawowa lpy, ta wuce ɗakin da taga ya fito dan tafi tabbacin Nayrah na ciki. Jama'a kuna ganin Dad ba zai tada bomb ba kuwa idan labari yaje masa? Ga Amjad da ƙarfin hali ka ɗauki matar ka amma tsabar neman magana harɗa ƙarawa da sister ta. Eh kwarai akwai ɗan ƙaramin yaqi kuwa dan Amjad yazo da bidi'a. ---------------------√ A cikin wasu yan lokuta shaquwa me ƙarfi ta shiga tsakanin Hushaima da Jey, Dan yanzu kwata kwata jinsa suke kamar wani baban yayan su, tun ranar da abin nan ya faru Jey ya karance alqiblar Hushaima ya kuma ke binta yadda take so ɗin, a bangaren masifar ta kuwa ba abinda ya sauya sai ma gaba da abun yake sake yi, dan duk wanda ya tabo ta ko waye gatansa sai yaji a jikin sa, sai tai ma shegen duka ba abinda ya dame ta, bata shakka kuma bata tsoro wanna abun shi ya sanya Jey Ƙara janta a jiki saboda wata manufa tasa da ya barwa kansa sani, yanzu sun samu saukin rayuwa dan wani abun shi yake musu. Tun mutanan gidan na adawa da ita har ya zama kowa tsoron ta yake Kuma binta suke duk abinda take so shi akeyi kamar ita ce me gidan, rigimar da ada ake yi a gidan yanzu kaso 70% ya ragu saboda tsoron Hushaima, yanzu duk wasu yan tasha tsoron gidan su Baba ilerika ake. Sahnish kuwa dubu ashirin ɗin nan data bashi yaje wurin masu turare suka hada masa yazo yake siyarwa Kuma ba laifi yana samu sosai, ganin haka yasa Jey ya ƙara masa jari. Ita Kuma uwar gayyar tana aikin ta a Starlight beauty Co. akan batun Amjad kuwa bata hakura ba tana nan akan bakarta ɗan Hushaima akwai naci ga kafiya da taurin Kai, Saidai duk wani Binciken ta kan Amjad amsa ɗaya ake bata na ƙarfin dukiya da matsayi na mahaifin sa, sai Kuma laifukan sa da ake faɗa, saidai ita duk ba wannan take son ji ba, kwata kwata bata yarda da abinda ake faɗa mata ba gashi tana neman hanyar da zatayi ramuwar da ta ɗau alwashi ba tare data shiga matsala ba, duk da tasan inda yake da kuma inda zata sameshi amma tasan bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane, dan haka ta cigaba da faɗaɗa tunanin ta kafin ta waiwaye shi. Sahnish ne tsaye a shagon juma shi da Shazeen sanye da uniform da alama daga makaranta ya ɗauko ta, jira yake juman ya gama sallamar wanda suke a kan layi, wani ne ya ce, "Malam juma tun dazu fa nake tsaye kazo ka auna min shinkafar mana"..........."ya hakuri malam Audi bari nazo, irin wacce za'a baka royal ko tomato rice ?". "Babu irin ta mu ta gida ne?"............ Mutumin ya tambaya. "Gsky yanzu bamu cika ɗauko ta gida ba, babu ma su da yawa a kasuwa, kuma mutane ma sunfi sayan wa annan ɗin".........."Kai bawa bai san ina zai sanya kansa a ƙasar nan ba wato mutanan nan ƙarfi da yaji nema suke su raba mu da abincin mu na gida domin su tasu kasuwar ta buɗe "............. Wani mutum da ya gama sayayya yana duba canjin sa da malam juma ya bashi ya ce, "Ai ka bari kawai Malam, in baka dashi kuma saidai ka mutu, tunda gashi dai wasa wasa zuwa gona da kiwo fa yanzu yana nema ya koma tarihi, saidai a shigo mana da komai amma mu baza mu iya fitar da namu ba, saboda kawai an raina mana wayo". Shi dai malam Audi ce wa yayi, "ALLAH ya kyauta, Malam juma zuba min royal din shakaɗeka guda".......... Dan baya so maganar tayi nisa saboda yanzu abu kaɗan zaka furta, za'a cafke ka dan baka san da wa kake tare ba wasu ma jami'an sirri ne suke basaja. Sunkuyawa juma yayi yana ɗaibowa Malam audi shinkafar ya amsa da, "To in Banda abinka malam waye zai fita kiwo a kashe shi a banza, ba saisa kaga dabbobin sun ƙara tsada ba, haka zalika nomar yanzu kana cikin gona saidai kaji an zagayeku da bindigu in baka da tsawon kwana daga nan kai taka ta ƙare, dole hakan dai za'a dinga lallaba rayuwar"............ Ya ƙarashe yana miqawa Malam Audi ledar ya bashi kuɗin ya miqa masa canji ya fita. "Malam Sahnish me za'a baka?"............" Sabulun wanka zaka bani da omo". Ɗaukowa yayi ya miqa masa shi kuma ya bashi kuɗin ya ɗauki kayansa ya masa sallama ya fito yana tariyo hirar su Juma me shago, duk da dai shi ma yana da abin faɗar amma ya zabi yayi shiru ɗin. ______________ A kofar Starlight beauty Co. ɗin ya umarci me tuk tuk ɗin da ya tsaya sannan ya sauka tare da faɗin, "Dan jirani yanzu zan fito". Ya ƙarashe yana nufar ƙofar gate ɗin wurin ya tsaya tare da Kiran number Hushaima amma bata yi picking ba, ɗan tsaki yaja ya maida wayar sannan ya nufi ciki yana turawa gate ɗin ya buɗe, da ido yabi compound din kafin ya wuce ciki, yana shiga reception din Jumayma dake haɗa kayanta ta ɗago tana dubansa, dan already sun riga sun tashi, "Malam lpy dai?"............"kalau, wuri na yazo kina da matsala da hakan ne?". Hushaima data fito daga ciki ta faɗa tana watsawa Jumayma harara, Jey baice komai ba ya juya ya fice, Jumayma Kuma taja tsaki, bin bayansa tayi tana faɗin, "tsaka ma da tayi ALLAH ya tsine mata, ba dai yadda zakiyi dani". A cikin tuk tuk ɗin ta sameshi, tana zuwa ta shige ba tare data dube shi ba, shi Kuma ya bawa me tuk tuk ɗin umarnin tafiya, kallon ta yake har saida ta juyo suka haɗa ido harararta yayi kafin yayi magana ta ce, "Dai na kallo na ni ma".........."Me zan kalla anan?"..........."Kai kafi kowa sani ai"............yar dariya yayi tare da ɗauke Kansa ba tare da ya sake cewa da ita komai ba, hakan yasa ta buga tagumi tare da zuba masa ido kawai, a duk lokacin da Jey yayi dariya har kumatun sa suka lotsa sai ta samu kanta cikin yanayin data kasa fassara shi, yana jinta yayi banza da ita suna zuwa kusa da layin su yace me tuktuk ɗin ya tsaya sannan ya sauka. "Ya dai?"........... Hushaima ta tambaya. "Zan siya wani abu ne ku ƙarasa ka sauke ta"..........."Nima zan sauka anan ". Ta faɗa tana saukowa kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya bashi kuɗin ya yi gaba, da sauri tabi bayansa suka cigaba da tafiya can kuma ta ce, "Ni kuwa Jey Ina da tambaya?". Kallon ta yayi ya ɗauke Kai baice komai ba . "Yau dai ka daure ka amsa min tambayar nan kullun na tambaye ka game da yan uwanka ko garin ku sai ka ƙi bani amsa meysa baka so na sani, ko baka yarda dani ba ne"..........." Me sa ba zanso ki sani ba, ai kin cancanci ki sani ko ?". Ya ƙarashe cikin sigar tambaya me ɗauke da rainin wayo, bata bashi amsa ba dan taji haushin yadda yayi maganar sai kawai ta cigaba da tafiyar ta, tama yi gaba abunta, dan takaitaccen murmushi yayi tare da tsallakawa kan wani dakali in da wani shirgegen mutum ke zaune kan bencin dake kan dakalin ya zubawa hanya ido. Jin baya binta yasa ta juyo ganin inda ya nufa ya sa ta dan tsaya Tare da ƙuresu da ido. Miqa masa hannun mutumin yayi bayan ya miqe a lokacin da ya ƙaraso yana washe baki, zama gefen bencin Jey yayi ba tare daya miqa masa hannun ba ya bige da faɗin, "Na danji ciwo ne saisa "........ Dan shi mutum ne me tsananin kyankyami ga mutumin kuma rigar jikin sa ma har tashi take, komawa yayi ya zauna tare da faɗin, "Alhaji kazo lpy?".........."lpy kalau Alhamdulillah, batun aikin nan da mukayi magana ya samu in sha ALLAH gobe zanzo muje su ganka su ma interview sai ka fara aikin". Godia ya fara zuba masa kamar zai sunkuya, "No bakomai karka damu". Ya faɗa yana ɗauko kuɗi daga aljihunsa ya miqa masa, da sauri ya sa hannu zai amsa kamar walkiya yaga an warce kuɗin ............. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd SultyWrites22 STEP 1 PAGE _______42 Godia ya fara zuba masa kamar zai sunkuya, "No bakomai karka damu"............ Ya faɗa yana ɗauko kuɗi daga aljihunsa ya miqa masa, da sauri ya sa hannu zai amsa kamar walkiya yaga an warce kuɗin, ɗagowa yayi tare da kallon Hushaima da fuskarta ke ɗaure tamau kamar an aiko mata da azarailu, zaiyi magana ta miqawa mutumin da faɗin, "Nima barin samu wannan ladan "........... Kallon ido cikin ido sukeyi ita dashi, irin kallon kar ta san kar ɗin nan. Sosai ta Ƙara haɗe girar sama data ƙasa tare da faɗin. "Karɓa mana, ni da shi ai duk ɗaya ne yayana ne"............ Yaqe mutumin ya fara, "Ahh Ranki ya daɗe, kina iya ajje min, whl nauyin ki nake ji ne"............" In zaka karɓa ka karɓa". Ta sake faɗa a dake. "Ke wai meye hakan"........... Jey ya faɗa a fusace dan ransa ya fara ɓaci ganin aika aikar da Hushaiman ke kokarin yi, Itama a tsawace ta ce, "ka tashi ka bar nan wajen ".......... Miqewa yayi a zabure tare da riqo tsintsiyar hannun ta da niyyar janta su bar wurin saidai ko gezau batayi ba wanda hakan ya bashi mamaki, wani irin kallo ta wurga masa sannan ta juya wurin mutumin ta ajje masa kuɗin a gefe, ta juya dan kanta ta bar wurin . "Ya hakuri jiddu yarinyar ce batajin magana ko kaɗan".........." Ba damuwa Alhaji sai goben Amma dan ALLAH gobe karka zo da ita"..........." In Sha ALLAH yanzu ma hanya ce ta biyo da mu tare da ni kaɗai zanzo ai"............" To ba matsala a gaida gida, ALLAH ya Ƙara girma"............ Da "Ameen". Ya amsa sannan ya bi bayan Hushaima. A kan kwanar layin su ya same ta tsaye tana ganin sa ta rufe shi da faɗa kamar uwar sa, shuru yayi kawai ya zuba mata ido karta tara masa idon mutane dan Sahnish ya faɗa masa idan ta hau tana masifar nan ba'a mata magana dan tana iyayin komai. Saida ta gama cikin ƙoƙarin danne bacin ransa ya ce, "Meysa kika hana na bashi kuɗi? Kin sanshi ne? Meye tsakanin ki dashi?"........... Tsaki taja sannan ta ce, "Kanka na rawa whl, to ka sani da na bari ka bashi kuɗin nan da hannunka da baka Ƙara 24 hours a duniya "........... Tana kaiwa nan tayi wucewar ta, zaro ido yayi da jin kalaman ta. Kamar wanda aka sassaqa haka ya ƙame a wurin yana nanata maganganun ta me take nufi ? Wata tambaya ce ta dawo masa, "Shin miye dalilin da yasa aka bada sunan sa ? Juyawa yayi ya kalli hanyar da suka baro sannan ya kalla kan layin nasu da sauri yabi bayan Hushaima, yana zuwa ɗakin sa ya shige ya fara haɗa duk wasu important abubuwan sa, jin Kiran sallar magriba ya sashi zuwa yayi alwala sannan ya wuce masallaci, bai shigo gidan ba sai goma na dare, ɗakin sa ya wuce tare da kulle ko ina ya rage haske sannan ya qule can ƙuryar ɗakin ya Kira waya kusan two missed call ba'a ɗaga ba, tsaki yaja tare da datse hakoransa cikin jin zafin Kiran da yayi ba'ayi picking ba, yunkurawa yayi da niyyar tashi Kira ya shigo wayar, kalla yayi ya ɗauke Kai tare da komawa ya zauna saida akayi missed call huɗu ana biyar ya ɗaga, da ga ɗayan bangaren akace, "Sorry widad ka Kira, wayan baya kusa dani ne ". "Nima naga kiranka na fara wani aiki ne".......... Ya faɗa cike da iya shege, Murmushi Amjad yayi daga ɗayan bangaren ya ce, "Ya akayi to ?" . "Na gama komai sai Abu ɗaya"............sai da Amjad ya nisa kafin ya ce, "Inajin ka"........... "batun samo dalilin da yasa aka bada sunan sa".......... katsesa yayi da faɗin, " ALLAH yasa Ka samo dalilin dan hakan zai taimaka mana akan aiki sosai". Girgiza kansa yayi kamar yana gabansa kafin ya gyara zama yana faɗin, "Ban samu ba amma zan ma rubuto ma wani text yanzu"..........." Wani text Kuma widad bayan gashi muna waya, let be serious plz". "Game da case ɗin ne fa shi ma, in Ka duba ba sai ka kirani ba"........... Daga haka ya kashe wayar ya shiga rubuta masa message ɗin bayan ya gama ya tura masa, ya kashe wayar sannan ya tashi ya fita, ɗakin Hushaima ya nufa, a buɗe ya sameshi sai hayaniya ce ke tashi daga ciki, ita dasu bonbon ne suke ludo su biyar ne sai ihu suke idan ɗaya taci, bayyanar sa yasa sukayi tsit kamar ruwa ya cinye su, yar charas tayi ƙarfin halin faɗin, "Ya Jey sannu da zuwa ".......... hannu kawai ya ɗaga musu tare da faɗin, "ku dan jira a waje". Ba musu suka tashi suka fita, turmi ya ɗauko ya zauna yana dan sake fuskar sa ya ce, "Yau kuma ina kika kai Shazeen?". "Tana ɗakin Sahnish ai, can na korata"..........."shi ne Kuma ba'a neme ni ba?"............" To Kai ba gashi ka kawo kanka ba"..........." Ummm dogaron ki Kenan saisa kika qi zuwa ko saboda kinsan dole zan biyo baya". Satar kallon sa tayi ta ƙasan ido sai dai ta makaro dan ya ganta, murmushi yayi da faɗin, "Ɗago ki kalla da kyau yadda ko a mafarki baza ki manta kamar ba"............" Ina Abun yake ?". Dariya yayi kamar bashi ba sannan ya ce, "kin rama 1/1, yauwa wata tambaya zan Miki Please, ɗazu meysa kika hana na bawa mutumin nan kuɗi da hannu na?". Wani wuri ta ƙurawa ido kafin ta ce, "Meye haɗin ka dashi kai ?"............" Kawai muna mutunci ne sosai, so Ina ɗan taimaka masa kinsan yanayin rayuwa kuma dai ana tare tunda duk maqota muke"............"To Ka nisance shi da Kuma duk abinda zai sanya kayi hannu dashi". Ta ƙarashe tana juyo da kallonta kansa. "Meysa kika ce haka? Yana da wata illa ne?" ............" Babba ma kuwa ". "To ki faɗamin mana saboda na kiyaye"............" Abinda zan iya faɗa ma kawai kayi nesa dashi ". Shuru yayi cikin ɗaurewar Kai, sha'anin Hushaima na ɗaya daga cikin abinda ke bashi ciwon Kai a yan kwanakin nan, can Kuma ya ce, "Hushaima zan sake Miki wasu yan tambayoyi, ba Kuma zan Miki hakan bane dan ranki ya ɓaci ki gayamin gsky dan ALLAH, Hushaima wacece ke Ina nufi background dinki? Miye asalin ki? Ina iyayen ki? Meysa kuke rayuwa haka shin ba dangi in ma ba iyaye?"........... Ya karashe a ɗarare saboda yasan halin birkitacciyar saidai da mamakin sa sai yaga tayi ɗan Murmushi da faɗin, "Shegu ne"............"shegu Kuma? ". Dariya ya kwashe da ita saboda yadda ta fadi kalmar, sosai yayi dariya kafin ya ce, "Please be serious mana". Kallon data watsa masa ya sashi faɗin, " Sorry Amma ki bar batun wasa, kuma bakyau, be kamata ki sheganta kanki da kanki ba".........." Baka yarda ba ko, to da gaske nake ma bamu da iyaye haka muka buɗi ido muka tsinci kan mu a duniyar mu"............"kenan ku ba Yan uwan juna bane?" "Tsakanina da Sahnish shekara ɗaya ne "........." Kamar ya bangane ba?"............" Mu bar zancen nan Jey zuciya na ya fara ɓaci, Dan ALLAH ". Numfashi ya fitar Yana sake kallon ta yayin da ta ɗauke Kai daga garesa. Shuru yayi yana kallonta shi kaɗai yasan saƙe saƙen da yake, sun daɗe zaune a haka kafin ya zaro kuɗi daga aljihun sa masu yawa ya miqa Mata, "Ga wanna Hushaima nasan zaki buqace su".......... yanayin yadda yayi Maganar yasa ta ɗan waiwayo suka haɗa ido, a sanyaye tayi ƙasa da nata tare da karɓa ta ce, "Mun gode sosai Jey, ALLAH ya Kara arziki"........... Da "Ameen". Ya amsa sannan ya miqe da niyyar fita har yaje bakin kofa ya juyo suka sake haɗa ido, kusan second 60 sannan ya juya ya fita, ɗakin Sahnish ya nufa, shi ma bai wani daɗe ba ya bashi kudi sannan ya masa saida safe ya koma ɗakin sa. Yadda Jey bai rintsa ba haka Hushaima kowa da abinda yake yi, shi Jey aikin gaban sa yake haɗawa ita kuma Hushaima tunanika ne suka Mata yawa. A Kan kunnen Jey Hushaima ta fito ɗiban ruwa da asuba, Miqewa yayi tare da ɗaukan jakar sa ya saɓa a baya, a jikin window ya tsaya yana kallon ta harta gama ɗiban ruwan, har ta juya zata wuce sai kuma ta juyo tana kallon ƙofar ɗakin nasa, kaucewa yayi daga jikin window har sai da yaga ta shige sannan ya buɗe ƙofar a hankali ya fito ya nufi soron ƙofar gidan yana tafiya a hankali kamar wani ɓarawo har ya Ƙarasa ya buɗe kofar ya fice sannan ya maida ya rufe. -----------------------√ Lokacin da driver yaje wa Mumu da batun wani yazo ya tafi dasu Nashwa harda sojoji, kwashe shi tayi da mari ba tare data duba dattijantakar sa ba, "Kai baka da hankali ne, akan idon Ka aka tafi da ya'yan nawa Ka kasa Kira Ka sanar min ko Ka sanarwa alhaji, shi ne Ka kwaso ƙafa yanzu kazo kake faɗamin dan baka data ido, to whl Ka jira Ka gani sai ka yiwa yan sanda bayani "............. Jiki na rawa Baba jamilu ya durƙusa Yana bawa Mumu haƙuri, Amma kwata kwata bata saurare shi ba sai ma ɗaga waya da tayi ta kira yan sanda ta sanar musu abinda Ake ciki, sannan ta cigaba da zazzaga masa har saida yan sandan suka ƙaraso, "Officer gashi nan, Ku tafi dashi har sai ya faɗa muku inda ya'ya'na suke, Dashi aka haɗa baki aka ɗauke su, yanzu zamu biyo baya in alhaji ya dawo"............"karki damu ranki ya daɗe, zamuje dashi muyi bincike kafin ku iso". "Shikenan Nagode, sai mun ƙaraso"........... Haka aka tisa ƙeyar Baba jamilu aka wuce dashi, Sai a lokaci ta Kira Dad wanda yaje sadakar bakwai na Farshad, tana sanar masa hankali tashe yace gashi nan zuwa, bai ɗau lokaci ba ya karaso har yana cin tuntuɓe a ƙofar shigowa garin sauri, "Garin ya haka ta faru hajiya Latifa?"..........." To Alhaji ni ai bana wajen dama na aika Nashwa da breakfast ne sai nasa Malam jamilu ya kaita a zuwan in Ka dawo daga wurin sadakar sai muje, to shi ne kuma yanzu Malam jamilun ya dawo yana sanar min wai wasu mutane da sojoji sunje sun tafi da Nayrah da Nashwa, to na Kira yan sanda sun tafi dashi nace sai munzo tukunna"............."Dauko ɗauko gyalen ki maza, mu fara zuwa asibitin tukunna "......... Ya faɗa yana juyawa ya ficewa da sauri, itama Mumu wucewa tayi ɗaki ta ɗauko gyalenta ta fito suka wuce Hospital ɗin. Suna shiga office ɗin Dr suka nufa, riqo wuyan rigarsa Dad yayi a fusace ya ce, "Kai tsohon munafuki ina ya'ya'na suke?"..........." Haba Alhaji menene hakan, Ka sake ni mana wanna ba halin manya bane fa ".......... Dr ya faɗa ba wani alamun damuwa a tare dashi, wato abinda ya kamata mutane su gane in ana ganin mutuncin ka Karka yadda ka ɓata wannan kallon a idon mutanan dake mutuntaka, ku dai duba girman Dad da kuma muqaman da ya riqe, amma kace nace ɗin da sukeyi yau da gobe a cikin asibitin ya zubar musu da mutunci. "Idan na kaika lahira acan saika faɗi halin manyan mutanen, nace ina ya'ya'na suke? wato dama daku ake haɗa baki ana ɗauke ya'yan mutane ko, okay bayan jariran da kuke ɓatarwa yanzu kuma kun koma kan manya ko". " To Ka sake in ma bayani mana".........." Baza a sake Ka ba"......... Dad ya faɗa kamar zai Kai masa duka, Mumu ce ta ce, "Ya hakuri Alhaji barshi muji me zai faɗa". Sakin sa dad yayi ba ɗan yaso ba sai dan baya iyawa Mumu musu. " Ina ya'yan mu suke ?". Mumu ta tambaya. Gyara zaman rigar sa yayi da faɗin, " Mijinta yazo ya tafi da ita mana". Kallon Dad Mumu tayi shima ya kalle ta . " Wani mijin nata, mijin da yake garƙame hannun hukuma ".......... Dad ya faɗa ba tare da tunanin yanzu duk abinda ya shafi Amjad ya shafe su bane tunda yana auren yar'su. "Alhaji Amjad Hashim Darwin, Ka tambayi kowa a asibitin nan Shi yazo da kansa ya tafi dasu "............." Okay kenan Kai ma yaron sa ne, to sai Ka nuna min inda ya'ya'na suke don ubanka ".......... Dad ya faɗa yana kaiwa Dr naushi, nan fa faɗa ya kaure daƙyar securities suka banɓare Dad sukayi waje dashi, a fusace Mumu ta ce, "Ka jirayi sammaci, zaka amsa Kiran kotu dan sai munyi kararka".......... Murmushi Dr yayi da faɗin, "Ba damuwa hajiya a kowani lokaci a shirye nake in sha ALLAH". Kwafa Mumu taja sannan tabi bayan mutanan da suka lallaɓa dad sukayi waje dashi. Kaii Jama'a Dad dan bala'i ne. ________________Haka take a bangaren su Awais labarin da ya iske su shi ya gusar da farin cikin da suka kwana dashi. Kira Nuhail ya samu inda ake shaida masa cewa lalle fa an saki Amjad ya koma gida .........." Ban gane an saki Amjad ba, kasan me kake fada kuwa?"..........." Ranka ya dade ban Kira Ka ba saida na samu tabbacin abinda nake faɗa, an sake sa tun a jiyan da daddaren amma an haɗashi da jami'ai su tsare shi har sai an tabbatar da zargin da ake masa ". Ajiyar zuciya Nuhail ya sauke kafin ya ce, "Har Ka firgita zuciya ta Raska, yanzu ya mutanan nan kuna dai tsare dasu har yanzu ko?"..........." Ai ranka ya daɗe ba wasa suna nan an killace su"..........." To ba damuwa in da wata matsalar Ka sanar dani, yanzu zan ɗan amsa wata wayar". Bai Jira amsar Raska ba ya kashe tare da Kiran Awais dan yasan Julaybin mutum ne me uzururruka ba kasafai Ake kiransa a waya a same shi ba ko da kuwa maganar urgently ne. Bayan Awais ya ɗaga Nuhail bai saurari gaisuwar da yake masa na ya tashi lpy ba ya ce, "Awais Ka Sami labarin an sako wancan tsinannan?".......... Ba tare da wata damuwa ba Awais ya ce, "Ban samu labari ba, Amma me ya faru?".........." Ya zakace mun me ya faru, Kai nama ji kamar Baka damu ba"..........." To nuhail ai dama kasan baza su rike shi ba akan laifin da bai aikata ba in dai har sunyi binciken gsky, ni fa dama a jiya kwana nayi da tunani in dai har aka riqe Amjad, to whl da gaske yana aikatawa kawai faɗuwa ce tazo daidai da zama, ba wai qagen da muka masa bane, saisa ma abun ya dameni Amma yanzu faɗa min ɗin nan da kayi yasa nasan to lalle akan kaiɗin mu yake tafiya, Dan haka muje next sai menene kuma?". Shuru Nuhail yayi yana digesting ɗin maganar Awais dan kwata kwata shi tunanin sa bai ma Kai nan ba, jin Awais yana hello hello ne ya sashi faɗin, "Amma fa Awais kanka na ja kasan kwata kwata ni banyi wanna tunanin ba in fact nama mance da cewa wai mu muka ƙirƙira kawai na tafi a zuwan cewa ya aika ne"............"hahahaha". Awais yayi wata dariya me cike da Alfahri kana ya ce, "To yanzu ya Ake ciki?". " Eh sun sake shi ɗin Amma wai sun haɗa shi da jami'ai, wai dan Kada ya gudu har sai an tabbatar da hakane ko ba haka ba"..........."To yanzu duk ba wanna ba kayi magana da Julaybin, ya sukayi da mutumin ya kamata ace munyi komai da zafin nama kafin a gama bincike a gano gsky ya kamata ace zuwa wanna lokacin ma'aikatar mu ta tsaya da ƙafarta sannan mu rushe batun Duk wani Abu na Dada a duniya sai muga miye dogaron nasa, tunda dama kaga already batun AURUM COMPANY sun tsaya saboda babu kasuwa, kaga dai komai na Dada ya fara tashi aiki sai mu kuma sunan mu ya fara yawo a iska yana zaga duniya, shi kuma kaga ko da ma an wanke shi ba kowa bane fa zai yarda dashi daga nan komai zai sake tsaya masa cak". "Wato in na tuna wanna Abu yana bani nishadi Awais, yanzu in na gama da gida zanje na sameshi dan kasan shi ba'a cika samun sa a waya ba "..........."To hakan yayi karkayi sanyi Nima zuwa anjima in rana ta fito zan leqa gidan wurin su hajiya na jiyo meke tafiya a can".......... Da haka sukayi sallama sannan kowa ya kashe. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd SultyWrites22 STEP 1 PAGE _______43 & 44 Washe gari kamar yadda suka saba bayan ta gama dafa musu jallof ɗin spaghetti a yar ƙaraman stove ɗin da Jey ya siya musu, ta zubawa Sahnish da Shazeen sannan ta zubawa Jey nasa ta fita dan kai masa, gaisawa sukayi da mutanan gidan data samu a filin tsakar gidan nasu sannan ta Ƙarasa ƙofar ɗakin Jey ɗin, saidai da mamakin ta ƙofar a rufe, ɗan bubbugawa tayi amma shuru Aunty Barma dake wanke wanke bakin rijiya ta ce , "Tity anya kuwa yau Jawaad na nan, dan tunda na fito yau ƙofar nan a rufe na ganta "............. Ɗan shuru tayi tana kallon ƙofar kafin ta ce, "Aunty Barma Anya kuwa? ko dai bacci ne ya ɗauke shi har ya makara"........... Ta ƙarashe tana sake doka ƙofar da karfi, buɗewa ƙofar tayi wanda yayi sanadiyyar hantsilawar ta cikin ɗakin saboda ta saki jiki sosai, kwanun data zubo abincin ya zube mata a jiki, saidai ko takan zafin ƙonuwar da tayi batabi ba saboda tashin hankalin data tsinci kanta a ciki na lura da babu Jey babu kayan sa, ƙarasa shiga tayi ta fara daddage tarkacen da ya bari, ganin da gaske fa babu shi babu alamar sa bare kayansa ya sata fita da gudu tana Kiran sunan mama Atine wato matar Baba ilerika ta farko, fitowa mama Atine tayi daga ɗaki sanye da Kaya daban daban, riga daban zani daban an kai shi har ƙirji, dankwalin nan a gaban goshi take faɗin, "Tity meke faruwa irin wanna Kira da fara kainar safiya?"......... Riqo kafaɗunta tayi a ɗan rikice ta shiga tambayar, "Ina Baba ilerika"............"Ashsha, zancen banza, yoooo wanna kuma da yawo kamar yaci ƙafar kare, ai kema kinsan ba kullum yake kwana gida ba tunda raba mana kwanan yake da yan tasha, Hala wani kuɗin ya cinye miki ?"............. Ɗan dafe kanta tayi ba tare data bawa mama Atine amsa ba ta yi waje tana warware ɗan kwalin kanta, dan sanye take da doguwar rigar material ɗinkin A shape da ya kama surar jikinta, kasancewar bata da rama ta ko ina a cike take. Tafiya take sauri sauri gudu gudu bata tsaya ko ina ba sai shagon hayar da Baba ilerika ya kama a sirrance yake zuwa ya kwana idan kwanan gidan ya ishe shi ko kuma matan nasa sun hura masa wuta, tana zuwa ta shiga bubbugawa, wata ce ta buɗe kana ganin ta kaga fitsararriyar kilaki, kallon sama da ƙasa tawa Hushaima kafin ma tayi magana Hushaiman ta rigata da faɗin , "ina yake?"..........Gatsinawa tayi a ɗage ta ce, "Ina yake, kamar ya ina yake? Shi wa?".........Tsaki Hushaima taja dan a yanzu bata da lokacin wanna hayaniyar sai kawai ta ce, "Baba ilerika"........... Leqowa yayi daga shi sai vest da dogon wando na atampa Yana faɗin, "Waye da sassafen nan blacky ?"......... Idon sa ne ya sauka akan Hushaima dan jim yayi alamar baiso zuwan nata ba ko kuma yanayin data samesu ne oho, kallon blacky dake bin Hushaima da harara yayi kafin ya ce, "koma ciki Blacky ina zuwa"............ Zatayi magana ya ce, "Shige mana haa". Wucewa tayi ciki shi kuma ya dawo da kallon sa Kan Hushaima cikin borin kunya ya shiga faɗin, "Hushaima me ya kawo ki nan? in kina nema na ai zaki iya Kiran wayata, kuma ma kinga kwata na faɗa shine wannan matar ta taimaka min na wanke rigar tawa, ina jira ta bushe ne in taho gidan. Tukunna ma wa ya kwatanta miki wurin nan har yace miki ina nan? ". Ya ƙarashe yana ɗan shafa bayan wuyansa. Dan sosai yake kunyar Hushaima, yana jin nauyin ta tun a farkon haɗuwar su saboda yadda take bashi girma, ko ya'yan sa baya kunyar su ganshi da mace dan sun ma saba saboda shi da su ɗin kar ta san kar ne. Ba tare da tabi takan zantukan sa ba ta ce, "Baba shin ko Jey ya faɗa ma zai tafi ne"......... Shuru yayi kafin ya ce, "Baya nan ne?" . "Baya nan ya ma kwashe kayansa gabaɗaya sai ɗan makullin ɗakin da ya bari a ciki". "Eh to lokacin ƙarewar kuɗin hayar sa dai baiyi ba Maybe kuma ya canza shawara ne, Amma to da wani Abu ne ko akwai wani Abun ki a wurin sa ne?"........... Shuru Hushaima tayi ta rasa me zatace dan ita sai yanzu ma irin rikicewar da tayi ya dawo Mata. "To kin kirashi ne a waya?". Maganar Baba ilerika ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi. Tabb to ita tama tuna da wata Abu wai waya . "Bai dai sanar da Kai ba Kenan?". "Ina fa ai ni rabo na dashi tun ranar da na ganshi shi da Sahnish can majalisar su Amiru me shayi da daddare". "Amma Baba, ya kamata ace fa kana bincike kafin ka bawa mutane wurin zama a gidan ka, domin a irin hakan tabbas wata rana zaka bawa wani ɗan ta'addan mafaka ba tare da ka sani ba". "Eh to, za'a kiyaye na gaba kam, to amma shi Jey ɗin wani abun ya aikata ne?". "Bakomai kawai dai na gaya ma saboda gaba, tunda kaga yanzu ma sai tashi akayi aka tarar babu shi, to haka in wani azzalumin ne sai ya gama aika aikarsa ya gudu ya Barka a wahala".......... Ta ƙarashe tare da juyawa ta bar wurin da ɗan sauri sauri, kawai tunani yadda rayuwar su ta kasance tare da shi take. A da in akace zata shaqu da wani har ta tsinci kanta a irin wannan yanayin dan kawai ya barta saita ƙaryata saidai kuma gashi hakan ya faru a lokacin da bata taɓa tunani ba, "Jawaad". Ta faɗa a hankali tana cigaba da tafiya, maganganun su na jiya da daddare suka shiga dawo mata, a haka har ta Ƙarasa gida, ba tare data bi ta Kan kowa ba ta wuce ɗakinta, bata tarar dasu Sahnish ba kuma tasan bazai wuce ya tafi Kai Shazeen makaranta ba. Wayarta ta ɗauka ta gwada kiran layin Jey ɗin saidai baya tafiya, murmushi tayi me ciwo, bata taɓa sanin irin ginin da yayi a zuciyar ta ba sai yanzu da suka tashi babu shi, ɗage kanta tayi sama tana tunanin rashin adalcin da zuciyarta ta mata, wanna dalilin ne yasa take taka tsantsan da zuciyarta a kan kowani ɗa namiji da ya nemi ya raɓe ta saboda bata son shaquwarsu ta zame mata rauni saidai kash Jawaad ya shammace ta. Ta jima cikin ɗakin zaune har Sahnish ya dawo ya sameta a haka, neman wuri yayi ya zauna yana faɗin. "Hushaima ina kikaje ne? daga fita Kai abinci kuma na jiki shuru, na fita na tambaya akace ai kin fita, sai nace Kar Shazeen ta makara bari kawai na kaita na dawo kafin nan kin dawo dan nasan ba nisa kikayi ba". "Sahnish Jawaad ya tafi"..........."To ai zai dawo tunda kinsan wani lokacin yana fita da wuri "........... Girgiza Kai tayi tare da faɗin, "Ina nufin ya tafi, tafiyar da bana tunanin zamu sake haɗuwa". Shuru yayi Yana kallon cikin idanun yayar tasa me cike da longing wanda yasa jikinsa yayi sanyi. "Kunyi sallama kenan, har ya gama NYSC ɗin?"........... Kallon wasu sec ta yiwa Sahnish ɗin kafin ta ɗauke kanta, sautin hmmmm ta fitar tana ɗan tsuke bakinta idonta akan wayarta ta ce, "Kawai yayi wasa da hankalin mu ne gabaɗaya Amma bana tunanin NYSC yake, aiki dai yazo yi". Ta ƙarashe tana dago idanunta da suka ƙara haske har wani sheqi suke ta zubawa Sahnish su. "Wani irin aiki kuma?"............. "Baza Ka taɓa fahimta ba Sahnish dan haka bar zancen kawai. Ya bani wasu kuɗi jiya yace na ajje zasu min amfani wai ashe shi sallama ce yakeyi a dunƙule ". "Nima ya bani wasu "............ Gyada masa Kai tayi tana haɗiye wani abu da ya tsaya Mata daƙyar ta ce, "Ka tafi wurin Sana'ar ka kawai, nima aiki zan wuce"............ Ta na Kai nan ta miqe ragowar abincin nata dake cikin tukunya ta kwashe ta zuba a container ta rufe ta saka a jakarta a zuwan in taje aiki taci, ta ɗauki waya da abubuwan buqatarta ta, miqewa Sahnish yayi shima suka fice tare, a dawo lpy ya Mata sannan ya wuce ɗakinsa dan ya shirya ya fita. Ko da taje aikin yau komai tayi Jey ne ke yawo a ranta har aka tashi, Sahnish ta Kira taji ya ɗauko Shazeen dan already an canza mata makaranta yanzu tun safe in ta tafi sai 5:30 suke tashi, nan ya shaida Mata gasu a hanya ma zasu shiga gida, hakan ya sa ta tsari abun hawa domin wucewa gidan itama. Hanyar da sukabi jiya ta bi a ƙofar gidan wanna mutumin ta tsaya tare da ƙwanƙwasawa, wata yarinya ce ta fito suna haɗa ido da Hushaima ta zuba a guje ta koma cikin gidan tana Kiran umma, ƙofar shiga gidan Hushaima tabi da kallo sai ga wata babbar Mata ta fito ɗan nesa da Hushaima ta tsaya tare da faɗin, " Baiwar ALLAH lpy? Daga ina?". "Lpy kalau dama wurin Mai gidan aka aiko ni ko yana nan?"........... Da sauri Matar ta ce, "Dan girman ALLAH kiyi hakuri m.........." Tarar ta tayi da faɗin, "Dama wasu kuɗi ne yayana ya bayar yace na kawo masa ".......... Ajiyar zuciya matar ta sauke amma daga ganin ta a tsorace take. "Tun da safe ya fita ai, yaje wata ma'aikata ne za'a masa interview to har yanzu kuma bai dawo ba"............" Tun karfe nawa ya fita ne?". "Tun bakwai ne bama ta Ƙarasa cika ba gsky"............."Kuma bakuyi waya ba?"..........." Ai bashi da waya whl".......... ajiyar zuciya ta sauke da faɗin, "To ba damuwa in ya dawo zan dawo ". Ta ƙarashe tare da juyawa ta bar ƙofar gidan dan ta samu amsar tambayar ta. -----------------------√ Yau kimanin kwana biyar kenan tunda ya Kai su Nayrah gidan nan, bai sake bi ta kansu ba amma yana bibiyar komai dake tafiya, ya kuma aika musu dasu Aram suna Kula dasu da kuma yi musu duk abinda suke da buqata. Shigowa yayi cikin wani tangamemen office me matuƙar kyawu, bayansa wasu mutane ne suma sanye da suit black and white su huɗu sai cikon na biyar amma shi ya cire rigar suit ɗin sai white shirt ɗin kawai ya bari, kyakyawa ne dan colour skin ɗin sa colour ce me matuqar ɗaukan hankali wato shiny light brown, Yana da manyan idanu tare da hanci madaidaici, bakinsa light pink sai maiqo yake kamar ya shafa lipgloss, gashin kansa da yasha gyara me matuqar laushi kana gani kasan jinsin Hausa Fulani ne. Riqe yake da wasu files suna tafiya yanawa Amjad ɗin bayani, wanda yayi kamar hankalinsa baya kan mutumin amma kuma shi yake saurare har suka ƙarasa gaban table ɗin dake office ɗin, tsayawa yayi tare da zage zip ɗin rigar ledar da ya shigo da ita wadda ta rufe ko ina na jikin sa sai kansa kawai, ɗaya daga cikin wa'ancan huɗun ne ya sunkuya ya janye masa ita daga ƙafarsa sannan suka ja gefe suka tsaya, karbar files ɗin hannun mutumin yayi ya bubbuɗe ya duba sannan ya ce, "Hanash kamar yadda Ka saba tafiyar da komai ka cigaba a haka kawai, bana ma so wani yasan na shigo office ballantana kuma batun fitar da kaya, already tunda har anyi magana dasu da kuma adadin da zamu basu to made up the percentage ɗin da muke buqata as usual every year, yanzu ƙasashe uku ne damu a ƙasa kowanne zamu basu 30.33 million barrels kai ne a tsaye a kan komai, so sai ka Kula"............ Ya Ƙarashe yana zaro pen daga gaban aljihun sa ya buɗe murfin da bakin sa idanun sa akan paper yayi signing in da ake da buqatar signing ɗinsa sannan ya buga stamp ya miqa masa. Murmushi Hanash yayi yana kallon sa ya ce, "Ba abinda zai gagara ai ranka ya dade .........." Kasa ƙarasawa yayi saboda harara da Amjad ɗin ya aika masa, "In baza Ka iya Kiran sunan ba Ka barshi". Shafa kansa yayi da faɗin, "Sorry sir ". Juyawa yayi ya nufi hanyar barin office ɗin ba tare da yace komai ba, da ɗan gudu gudu Hanash ya bishi yana faɗin, "Wait bros tsaya kaji mana". Dakatawa yayi da tafiya har ya karaso, kallon fuskar Amjad ɗin yayi tare da ɗan yin dariya, sake hararar sa Amjad yayi, "Zaka Faɗi abinda ke bakin Ka ne ko nayi tafiya ta". Amjad da Hanash kusan abokan wasa ne dan tare suka taso saboda mahaifin Hanash shi ne babban abokin sirrin Dada duk wani sirri na Dada ya sani kuma duk wani harkar kasuwancin dada mahaifin hanash shi ke Ƙara bashi shawarwari da kuma abubuwan daya kamata. Sunyi zama na amana, Dada shi ya dau nauyin karatun Hanash har ya gama sannan ya buqaci mahaifin sa da ya shigo dashi cikin aikin kamar yadda shi ma a lokacin ya shigo da Amjad, sai ya zamana tasu tazo daya har zuwa lokacin da mahaifin Hanash ya faɗi ya mutu, ba ƙaramin jimama mutuwar mahaifin Hanash Dada yayi ba kafin daga baya ya sanya Hanash ya maye gurbi mahaifin nasa shi kuma Amjad ya maye nasa gurbin, saidai ya dinga taimaka musu da wasu abubuwan idan bukatar hakan ta taso har zuwa lokacin da wannan abun ya faru shi ma ya kwanta. WANNAN KENAN. "Ai kai ne kaƙi tsayawa kaji, tunda kayi aure sai wani sha min kamshi kake ni ma fa zanyi auren nan yauwa"..........." Ta tabbata dai baza Ka faɗa abinda zaka faɗa ɗin ba kenan sai kayi halin naka". "Tsaya zan faɗa". Ya faɗa Yana nutsuwa sannan ya ce, "Da gaske nima na kusa aure". Tsaki Amjad yaja zai cigaba da tafiya, Hanash ya ce, "Batun su ya Julaybin, ya za'ayi dasu idan sunzo karɓa kasan last week sun min magana tare da fadin akwai mutumin da zasu bawa 10 million barrels a shirya musu"............"Ka basu mugani in zai wuce"............ Da alamun rashin fahimta ya Ƙarasa wurin sa yana faɗin, "Ban gane ba kamar ya kenan?". " A shirya musun kamar yadda suka buqata amma ni na ce ma ba abinda zai motsa daga nan, wancan kuma Dama mun gama maganar da kai, dan haka muje ka rakani na wuce ina da wurin zuwa". "I trust you sir". Hanash ya faɗa tare da Sara masa yana dariya. " ALLAH ya shiryeka Hanash ya kawo lokacin da zaka girma"......... Fadar Amjad Yana shigewa. "Eh mana ai dole zakace ALLAH ya kawo lokacin da zan girma tunda kai ka shige daga ciki kasan da........." Shuru yayi yana dariya saboda wani kallo me kama da harara da Amjad ɗin ke masa. " Ka cigaba da sakin baki dai, da mutane a bayanka sunajin wannan shirmen naka zasu rainaka dan su bani bane daka saba yiwa iya shege".......... ɗan satar kallon sauran ma'aikatan dake bayansu Hanash ɗin ya yi kafin ya ce, "Basuji ba ai". Murmushi yayi tare da ɗan jijjiga kansa ba tare da ya sake cewa komai ba har suka fito zuwa gaban wani private jet ɗin dake fake a wani makeken fili a jikinsa an rubuta HASHIM DARWIN, daga nan sukayi sallama da Hanash ɗin ta hanyar hugging juna sannan ya miqawa sauran ma'aikatan nasu hannu ya juya ya shige jirgin yana gyara zaman suit ɗin sa, Saida suka ga tashin su suna ɗaga musu hannu sannan suka juya ciki. A cikin wani filin da yafi wancan girma private jet ɗin ya sauka, fili ne babba gaba da baya sai wani tangamemen gini na Factory, wani irin dogon gini ne me matuƙar kyau da ɗaukan hankali, anan ya tarar dasu Kamal suna jiransa, yana saukowa suka rufa masa baya zuwa cikin ma'aikatar, nan fa kallo ya koma sama dan faɗar tsaruwar cikin ma ɓata baki ne, noes mask ya sanya sannan suka wuce ciki shi da wasu ma'aikatan da suka fito tarbarsa saida suka fara shiga wurin wasu engines wanda ke narkar da dunqulallun gold da kuma wanda ke yankawa tare da fitar da shape na irin sample ɗin da ake buqata, sai da ya gama zagayawa sannan suka fito, sun danyi tafiya kafin su isa wani bangare shi kuma duk glass ne zagaye da wurin ba bango na bulo ko ɗaya, sample ne na golds ɗin su na HD AURUM MINING iri iri a cikin glass cube suna juyawa da kansu sai ɗaukan ido suke, gaba kaɗan kuma bangaren diamonds ne da wasu irin precious gems masu matuƙar kyau, wurin ta ko ina ka juya kana ganin fuskarka saboda glasses ɗin dake ɗaukan ido ga wani irin sanyi da kamshi na musamman dake tashi, sai da ya gama duba komai sannan suka fita, wani bangaren suka sake nufa ko nace store domin danyen golds ne da diamond da kuma sauran precious gems amma ba gyararru bane, dan a duddunƙule suke ba ayi shaping dinsu ba, nan ma sun daɗe suna zagaye kafin su fita daga wanna bangaren su wuce bangaren ofisoshi, nan ma office ɗin sa dake Ma'aikatar ya nufa sannan yace a kawo masa duk wasu bayanai, bayan ya gama dubawa ya kalli Baba Hakim, dattijo Mai riqon Amana da gaskiya shi ya tsaya tsayin daka wurin ganin baiyi wasa da amanar da Dada ya danqa masa ba tun lokacin da suka fara wanna harkar lokacin da jajayen sawayen su. "Amm Baba Hakim a duk wa'annan record ɗin dana duba Aurellon sultanate sun fi karɓar diamond fiye da kowani customer na mu kuma naga kamar masarauta ce, me sukeyi dashi? Suna kasuwancin sa ne?"........... Murmushi Baba Hakim yayi irin nasu na manya kafin ya ce, "Ai Amjad Aurellon sultanate su ne customer namu na farko tun lokacin da mahaifin Ka ya kafa wannan masana'antar, baka cika zuwa bane kafi neman a turama komai ta waya saisa ba lalle Ka san irin wa'annan abubuwan ba tunda abu ne da za'a rubuto, amma a yanzu da komai yake a gabanka ai gashi Ka gani, ba kasuwancin sa suke yi ba gini sukeyi dashi"........... Da mugun mamaki Amjad ya ce, "Gini kuma Baba Hakim?"............" Kwarai kuwa Amjad, ita wanna masarautar ai babu ta biyunta a duniya a dai ƙarfi, qawa da kuma mulki, suna da ƙarfin arziƙin da duk wata masarauta ta duniya bata isa tsayawa gaba da gaba da su ba, su ke nada duk wani sarki haka kuma suna d............" Ganin dogon tarihin da Baba Hakim yake son daukowa yasa Amjad yin dan Murmushi cikin son tsagaita maganar ya ce, "Baba gsky zanzo har gida Ka ban wanna labarin, Amma yanzu mu koma kan aikin dake gaban mu, naga kamar akwai mutane da yawa da suka biya ba'a basu kaya ba ". "Eh ai kasan kaikace ba kamar da ba da za'a basu direct, hanya ɗaya ce damu ta sirrin daka buqata, saisa muka fi son a haɗa gabaɗaya yaso a aika musu a lokaci guda, hakan ma ba ƙaramar wahala yake bamu ba wurin lissafi". Nisawa Amjad yayi kafin ya ce, "Na ɗan lokaci ne ai baba a Ƙara hakuri damu dai".........." Haka ne muna ta addu'a Amjad, ALLAH ya bayyana gsky ya kuma toni asirin su"............ Miqewa Amjad yayi da faɗin, "Ni inaga zan wuce saboda hanya". "To ba damuwa muje na raka Ka, in sha ALLAH nima da aiki ya ɗan ragar min zan shigo na duba jikin alhaji Hashim ɗin "............" ALLAH ya kaimu ". Ya faɗa suna fita har wurin motocin dake pake ta bayan Factory ɗin Baba Hakim ya rakashi, sai da yaga tafiyar su sannan ya koma. Ƙarfe biyar daidai suka iso, a wani irin gajiye yake jinsa, dan tun 6am suka fito amma ko ba komai ya rage wani aiki, direct Bluevielle ya basu umarnin zuwa dan tun ɗazu yake ganin Kiran Nayrah kuma yasan ƙorafin da zata masa kenan. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd Sultywrites22 STEP 1 PAGE _______45 & 46 Tsaye take a ƙofar gidan misalin 11pm tana kallon mutanan gidan nasu da su lokacin ne ranar su ta fara, sun ƙure kiɗa akan layin, masu rawa nayi, masu ƙarawa sama hazo nayi, masu fira nayin tasu masu zance da samari nayi, masu cinikin abinci nayi, masu poker nayi kowa dai da abinda yakeyi, in banda hayaniya ba abinda ke tashi yadda kasan tasha ko kasuwa. Bata cika fitowa a irin wanna lokacin ba saboda baccin ta ma take kwanciya tayi, amma gabaɗaya yanzu zaman ɗakin zafi yake mata, tunani daban daban ne suke kawowa ƙwaƙwalwarta farmaki a duk lokacin data kaɗaice ga Jey da har lokacin tana jinsa a ƙasan zuciyarta, dan yanzu ma har ta kwanta bacci ta ƙasa, shi ne ta tashi ta fito domin ta samu sukunin abinda ya dameta. Sanye take da Palazzo peach colour sai armless T shirt milk mai matuƙar taushi, kanta yane da wani yalolon ƙaramin gyale, gefen ta kuwa Mahrazu ne abokin su Wulu sai wani ƙoƙobarewa yake yana magana shi a dole nigga, ita kuwa sam ma hankalinta baya kansa kamar ma bata san da wanzuwar mutum a wurin ba ta tafi wani tunanin daban. Wani irin taku sukaji kamar za'a girgije ƙasa, ga wata ƙura data taso kai kace girgizar ƙasa za'ayi, kafin kace me mutane sun fara gudun ceton rai, sai ihu wasu na faɗin ya'juj wa ma'juj ne suka bayyana, wasu na faɗin zaizayar ƙasa za'ayi, tsabar bala'i wasu ta cikin murhu suka dinga bi wasu ta cikin Kwanun Mai, wanda suka bugu sukayi maƙil kuwa ƙwata suka shige, gabaɗaya wurin ya hargitse karo kawai kake ganin anayi duk wanda ya faɗi kuwa ta kan ruwan cikinsa ake bi. Ita dai Hushaima kaucewa kawai tayi ta bawa masu gudu hanya dan Kar ayi gaba da ita, amma ita ko a jikinta ba ma alamar wani tashin hankali a tattare da ita dan sai taga abinda ya ture rawanin buzu, komawa tayi ta jingina da wata ƙaramar katanga dake jikin dakalin nasu wadda tayi kamar makari. Raba ido ta shiga yi daga gabas zuwa yamma, wasu ingarman giwaye ne suka sawo Kai kan layin suna tafiya suna ihu tare da dage dogon bakin nan nasu sama, sai da suka zo daidai saitin ta suka tsaya, kallo Hushaima ta Kai kan mutanan dake kan Giwayen maza ne sanye da wasu irin kaya kamar na fata dukkan su fuskar su ba alamun imani a tattare dasu, wuyansu sarkafe da sword tare da archery, dawo da kallon ta tayi kan Giwar da take sahun farko wadda ta banbanta da wa'ancan tun daga kan ado, wani irin faɗuwa gaban ta yayi wanda bata taɓa jin irin sa ba har saida ta motsa daga jinginar da tayi, daidai lokacin matashiyar budurwar ta juyo bangaren Hushaiman idonta ya sauka akanta, sanye take da dogon wando da riga marar hannu na Cashmere goat, rigar ta sauka har Kan cinyoyinta amma a yanke take daga both side haka ma ta gaba, kanta ba ko dankwali sai long brown curly hair ɗinta da ta ɗan kama rabi a tsakiya sauran duk ya sauko kan kyakyawar fuskarta, ƙafarta Kuma sanye da wani boot me kyau, dirƙo wa tayi ƙasa still idanunta akan Hushaima ta tako zuwa gabanta tana binta da wani irin kallo me wuyar fassarawa, ita ma Hushaima baki buɗe take kallon ta ganin irin fuskarta a jikin wanna budurwar, a tare suka Kai kallo jikin su wanda shi kaɗai ne kawai ya banbanta su shi ma ba wani da yawa ba, kawai dai Hushaima zata ɗan fi wancan cika ne da kaɗan, Amma bacin hakan komai nasu iri ɗaya, kalar skin ɗin su, doguwar fuskar su, wannan kwayar idanun tasu masu rikita marassa gsky kai harda masu gskyr ma, sirancin karar hancin su, dan brown lips ɗin su duk irin ɗaya. Da hannu yarinyar take nuna Hushaima kamar tana so tayi magana sai Kuma ta juya da sauri ta kama giwar ta ɗale kamar wata tsuntsuwa, su ma sauran mutanen da suka sauko ganin ta sauko suka koma tare da motsa giwayen nasu suka fara tafiya kaɗan kaɗan har suka bar layin, ita dai Hushaima ta ƙasa yarda da abinda idon ta ya gane mata shin ko dai ta zautu ne? Dafe kanta tayi da dukkan hannayenta saboda yadda yayi wani irin masifar sarawa, Nishin da taji ne ya sata sauke hannun data riqe kan nata dashi, a Hankali ta juyo tare da fira ƙafarta ta bi inda take jin nishin tana zuwa taga kamar mutum raɓe, Bismillah tayi tare da Kai hannu ta ɗan tabo shi, ɗagowa yayi wanda hakan ya tabbatar mata da mutum ne kamar yadda tayi tunani. Fari ne tass kamar ka taɓa jini ya fito, yana da dogon hanci kamar an zana da biro, haka dark red lips ɗin sa wanɗanda ke zagaye da wani kwantaccen baƙin saje tare da tsararren gashin baki da ya ƙara ƙawata fuskar tasa, kallonta yake da grey piercing eyes ɗin sa da suke nan kamar ya sanya musu kwalli amma in ka lura da kyau zaka san natural ne ba wai kwallin bane, haka gashin girarsa dana idanunsa kamar zasuyi magana, uwa uba gashin kansa da ya wani baje har fuskar sa kasancewar sa me tsayi da laushi haɗi da santsi. Ɗan ja baya Hushaima tayi tana sake ƙare masa kallo dan bata taɓa zaton ganin irin wanna halittar anan wurin ba, ganin sa dafe da kafaɗar sa ga jini da ya bata yellow t shirt ɗin jikinsa ya sa cikin tausayawa ta ce, "Sannu kaji ciwo ne ?"............ Sai dai a maimakon ya bata amsa sai ya dafa bangon ya miqe, still hannunsa dafe da kafaɗar tasa dake zubda jini. Ganin sai ya kalli hanya ya kalleta kamar me son tantance wani abu ya sata faɗin, " Muje cikin gida a samu Abinda za'a sawa ciwon naka, kana zubda jini sosai". Ƙura mata ido yayi kawai ko kiftawa ba yayi kamar wanda yaga wata sabuwar halitta. " Ni ba cutar dakai zanyi ba in ma tunanin haka kake, gidan mu zamuje a sa ma magani".......... Ta ƙarashe tana nuna masa kanta tare da shi sannan ta nuna mashi gidan su ma'ana ta masa maganar kurame. Nan ma bai yi magana ba sai wucewa da yayi ya nufi gidan nasu data nuna, da sauri tabi bayansa tare da saurin shigewa gaba suka shige cikin gidan da yake tarwai kamar anyi yasa ko motsin kirki bakaji, ɗakinta ta wuce dashi tare da faɗin, " zauna barin je in samu Toshi (tissue)"............ Ta faɗa tana masa alama da hannu na abinda zata samo a goge jinin, Da kallo yabi ɗakin yana yatsina fuska ba tare da ya zauna ba ya wani tsirtar da yawu ya juya ya fice, baki buɗe Hushaima ta bishi da kallo har ya fice kafin ta juya ta kalli inda ya zubar da yawu sannan ta bishi wajen, a tsakar gidan ta same shi sai raba ido yake kamar wanda yaga wasu sababbin abubuwa. Ɗakin Sahnish ta nufa tare da bubbuga masa ƙofar, Ƙara ƙanƙame Shazeen Sahnish yayi tare da fara karanto duk Addu'ar da tazo bakin sa, Jin shuru ya sata faɗin, "Sahnish in kana ji na ka zo ka buɗe min"......... Ai da wani mahaukacin sauri ya miqe tare da zuwa ya buɗe mata ƙofar ba tare daya saurari wani abu da zata faɗa ba ya jawo ta ciki yana kokarin maida sakata ta bige hannun sa da faɗin, "Kai bana son shashanci me hakan, zo muje da ALLAH "............." Ina ?"........... Ya tambaya kamar bai yadda dai ita ba. Jan hannun sa tayi suka yo waje, ai idon sa na sauka a kan sa yayi wani u turn ya dawo bayanta Yana faɗin, " innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahamanir Rahim". Ɗagowa yayi yana binsu da kallo, tsaki Hushaima taja tare da faɗin, " Je ka ɗaibo masa ruwa ya wanke ciwon "..........." Au Wai dama kema kina ganin sa?". Sahnish yayi tambayar tsakanin sa da ALLAH, dan shi whl ya ɗauka gamo yayi. "Bana san iskanci Sahnish zan saɓa ma whl, mutum ne kamar ka ɗan kauye kawai". (Jamaa kuji Hushaima fa sai kace itama bata ruɗe ɗin ba). A ɗan tsorace ya wuce yana keɓe keɓe, nufar inda yake Hushaima tayi tana zuwa ta ce, " Cire rigar ka wanke wurin"........... Ta faɗa tana nuna masa abinda zaiyi dan ita tafi tunanin yana da larurar magana ne, amma a mamakinta sai taga ba musu ya zare rigar wanda hakan ya bayyana murɗaɗɗen jikinsa da yake nan fari tas ga wasu kwantattun gashi masu laushi dake kwance a kirjinsa sun biyo layi ta tsakiyar cikinsa har zuwa cibiyarsa, ɗauke idanunta tayi zuciyarta na skipping beat ta maida kallonta wurin kafaɗar tasa inda shatin yankan ya ke nan rafkeke ga jini har lokacin zuba yake sosai ta jinjina ƙarfin halin wanna bawan dan yankan ya shiga sosai, "Sahnish bashi ruwan in ka ebo bari na ɗauko hijab naje wurin Dr misbah na kirashi"..........." Ah ah ke dai ki tsaya anan ɗin ni  bari naje na zo dashi sai na fiki sauri ai "........... Ya faɗa yana sakin gugar ya fice da sauri dan whl ba zai yarda ta barshi da wanna aljanin ba dan shi har yanzu ya ƙasa yarda mutum ne, zuwa tayi ta ƙarasa ɗaibo ruwan ta kawo gabansa tare da faɗin, "Gashi Ka wanke wurin kafin Dr yazo"........... Ɗauke Kai yayi kamar bai gane abinda take nufi ba"........."To Ka wanke hannun Ka".......... Ta sake faɗa tana nuna masa. Da wani irin daddadan sauti me kama da busar sarewa a hankali cikin natsuwa, da Arabic accent ɗin sa ya ce, "Bani so"........ Zuba masa idanunta kawai tayi cike da mamaki kenan dama yana magana, cikin son sake sauraran melodious voice ɗin sa ta ce, "Baka son me?"..........ɗauke kansa yayi ma kamar bai san da mutum a wurin ba, numfashi ta furzar kawai tare da riqe waist dinta da hannayen ta can kuma ta sunkuya ta ɗauka rigar tasa daya jefar ta karkaɗe tare da wanke gefe guda sannan ta ɗan jiƙa ta nufo shi da niyyar goge jinin dake binsa, warce rigar yayi tare da wurga Mata a fuska a fusace ya ce, "Stop this shit". Haushi taji sosai, daga tana son taimaka masa a shi ne zai dinga wasu abubuwa kamar wata baiwar sa a fusace itama ta nuna masa hanya da faɗin, "Fitar mana daga gida to, kaje can in ma kasheka zasuyi su kashe Ka, yanzu haka Kai Ka tsokano su ma da bala'in ka". Jama'a har kura tace da kare maye, yau Hushaima ke kiran wani da ɗan bala'i, eh to lalle abun ya yi tsamari. Amma ina ko nuna yasan tanayi baiyi ba haka ta cigaba da bambamin faɗa kamar zata kama da wuta, faɗi take kawai yazo ya fice musu a gida, idonsa a kanta kuma yana jinta amma ko motsi baiyi ba har su Sahnish suka shigo shida Dr misbah . Saida ta harare shi sannan ta ce, "Sannu da zuwa Dr"........."yauwa Hushaima yaki ke". "Lpy kalau? Ga wanda zaka duba nan yanka ne ya samu a wurin kafaɗa ". Matsowa Dr misbah yayi a ɗarare dan har ga Allah shi ma tsoron tunkarar sa yake saboda wani irin kwarjini da ya masa. Kallon sa da ya dawo dashi kan Dr misbah yasa ba shiri yaja birki, hannu ya miqa masa alamar ya bashi first aid box ɗin, kallon hannayen nasa Dr Misbah yayi ganin ba komai sai first aid box ɗin da yake riqe dashi ya sashi miqa masa hannun sa na rawa ya koma can baya ya tsaya. Zuba masa ido sukayi su duka ukun, tsugunnawa yayi tare da Buɗe first aid box ɗin ya dauko cotton da spirit ya dangwala ya fara goge wurin yana ɗan bata fuska har ya goge wurin tass ya sake ɗauko antiseptic ya sanya a wurin, sannan ya ɗauko surgical needle da suture thread ya sanya ya fara ɗinke wurin kamar ba jikinsa yake ɗinkewa ba cike da kwarewa da kuma nutsuwa har ya gama, sterile gauze pad ya sanya sannan ya manna medical tape, ba tare da ya maida kayan da yayi amfani dasu mazaunin su ba ya ture first aid box ɗin da ƙafa. Ajiyar zuciya Hushaima ta sauke tare da ƙarasawa ta haɗa abubuwan ta maida ta rufe sannan ta miqawa Dr misbah da faɗin, "ina zuwa"......... Ɗakinta ta shiga ta ɗauko dubu ɗaya ta miqa masa da sauri ya karɓa yayi godia ya fice yana waiwayen su. Juyawa tayi ta kalli Sahnish sannan ta maida kallon ta kansa da faɗin, "zaka tashi Ka shiga ɗakin ne ko yaya?"........  Ko kallon ta baiyi ba ballantana ya nuna yaji maganar ta, juyawa tayi wurin Sahnish da faɗin, "Shiga Ka kwanta Sahnish saida safe Ka turomin Shazeen ma tazo ta kwanta". Tana gama faɗa ta wuce ɗakin ta, da sauri Sahnish ma ya wuce ɗakin sa suka barshi anan. Samu yayi Shazeen tayi bacci dan haka bai tasheta ba kawai ya ɗauko ta . A tsaye ya samu Hushaima hannunta ɗaya akan waist ɗinta kamar me tunanin wani abu, kwantar da Shazeen yayi sannan ya wuce wurin Hushaiman tare da jawota daga bakin Ƙofar ya ce, "Hushaima me ya faru wai? Ina kikaje ɗazu da ake cikin wanna tashin hankalin? Waye wancan kuma?". Duk a lokaci guda yake jero mata wanna tambayoyin. "Wani abun mamaki Sahnish wata halitta na gani sak kamar ni, abun ya ɗaure min kai ya sanya ni a ruɗu, dama ana samun irin haka? dan ni nasan ana samun masu kama ɗaya amma wannan kamar ta wuce kama sai naga kamar ni ce "............."A Ina wau?". Sahnish ya tambaya yana binta da kallon tuhuma. "Yanzu mana, abinda kaji anawa gudu wasu mutane ne akan giwaye suka shigo Kan layin Kuma ga dukkan alama wancan mutumin suka biyo, Kuma su suka ji masa wannan ciwon, Amma whl yarinyar sak ni ce". Shuru tayi tare da dafe kanta da hannu ɗaya sai kuma ta ce, "Sahnish ina son sake ganinta, amma bansan a wace duniyar zan ganta ba, ina so kai ma ka ganta domin ka gani ko muna kama ko kuma ni ce na zauce sahnishhhhhh". Ta ƙarashe tana runtse idanunta, ita tasan abinda ta gani amma kuma wani sashin na zuciyarta yafi bata kamar ba daidai take ba. Shiru Sahnish yayi dan shi yafi yadda da gamo Hushaima tayi. Hushaima na ƙoƙarin sake magana sai ganin mutum sukayi ya faɗo ɗakin, saurin matsawa Sahnish yayi ya bashi wuri, da ƙafa ya dinga ɗaɗɗage shimfiɗar dake ɗakin kamar me neman wani abu ganin haka yasa rai ɓace Hushaima ta ce, "Kai malam da ALLAH dakata nan fa ba gidan ku bane, in kaga zaka iya zama ka zauna in baza Ka iya ba ga hanya nan wuce ka tafi inda kafi wayo, ni taimakon ka kawai nayi ba hakkin ka bane a kai na, kuma mu abinda ALLAH ya bamu kenan"............ Da wani irin voice da saida yasa Sahnish riqo hannun ƙofar yana jiran ƙet ya zura waje ya ce, "Mind your tongue, baki da Matsayin da kowacce irin magana tazo bakin ki zaki faɗamin. Akan wannan ƙazamin ban ɗakin da ko in da dokuna na ke kwana yafi shi"........ Zaro idanunta waje tayi tare da ƙare masa kallon tsab sannan ta ce, "Ɗakin nawa ne ma banɗaki, to whl summa tlh sai ka fita ka tafi gidan ku, ai ka iya yin laifi ka biyo jikin gatangar mutane kana mannewa kamar kadangare, meysa su ka kasa tsayawa ka gaya musu maganganun s........."....... Wata irin juyowa yayi wadda saida tasa Hushaiman ta matsawa baya, gabanta na ɗan faɗuwa, da hannu ya nuna ta alamar warning sannan ya ce, "Ki shiga hankalin ki in ba haka ba zaki fuskanci hukunci da tsawon rayuwarki zaki ƙareta a dana sani, zan miki uzuri yanzu saboda bakisan waye ni ba amma......" Ya ƙarashe yana watsa musu wani kallo da ya ƙarashe faɗar abunda bakinsa bai faɗa ba, sannan ya ɗora da faɗin, "Fita a nan wurin kafin nayi fatali dake". "Jar buuuu........." Toshe mata baki Sahnish yayi sannan ya fara janta dan yasan ko za'a kasheta baza tayi shuru ba shi Kuma ya tsorata da furucin wannan aljanin ganin da iya gaskiyar sa yayi maganar amma dukda haka Hushaima sai da ta ƙarashe faɗar abinda ta soma, daƙyar Sahnish ya turata waje, a fusace ta ce, " Whl sai ya fito mun daga ɗaki, ai ba ɗakin ubansa bane".......... "Dan ALLAH kiyi hakuri Hushaima, baki san waye shi ba. Ki tuna in fa wani abu ya sameki da ni da Shazeen ne zamu shiga matsala, ke kaɗai mu ke da, wanna mutumin daga ganin sa wani babba ne Kuma zai iya aikata abinda ya faɗa ɗin nan, dan haka ki barshi ba dai ɗaki bane kizo mu koma nawa mu zauna zuwa safe ai dole zaisan in da rana tai masa". "Sai ka wuce ai ka je ka ɗauko mun yarinya, dan bansan mugun Alkaba'in dake tare dashi ba, saboda whl in na shiga Ina iya Ƙwada mai mar........" kafin ta rufe bakinta ma Sahnish ya faɗa ɗakin duk da dukan da kirjin sa yake yi, ko kallon in da yake baiyi ba ya sake ɗauko Shazeen ya fito . Ranar kusan duk gidan kwanan ido biyu sukayi dan ba wanda ya rintsa, da asuba bayan sunyi sallah ta tashi ta fita, ƙwanƙwasawa mutanan gidan ƙofa ta dingayi dan duk sun ƙasa fitowa, a hankali suka fara leqowa kowa ya ganta sai ya fito da sauri yana tambayar abinda ke faruwa tace musu ba komai kawai suyi abinda ke gabansu sannan ta wuce ɗakin su, a tsaye ta sameshi yana danna wayarsa goldstriker iPhone 3Gs supreme, kansa a ɗan sunkuye Wanda hakan ya bawa gashin kan nasa damar zubowa ya rufe fuskar sa, bokitin data shigo ɗauka ta ɗauka ta fita ba tare da tace dashi komai ba taje ta ɗaibo ruwa, suna tsaye a tsakar gidan suna maida zance harda su baba ilerika dasu kawu adamu kawai suka ga wasu murtika murtikan mutane sun shigo sanye suke da wasu irin kaya, bujen wando da riga red and dark brown sai wata hula Mai kamar ship dake a saman red hair ɗinsu, su biyar suka shigo sai zare ido suke su nufi wannan ɗakin su nufi wancan duk sun fito da kowa sai a ƙarshe suka nufi ɗakin Hushaima ita dai tana tsaye a wajen rijiya hannunta ɗaya akan kugunta ɗaya riqe da guga tana kallon ikon ALLAH, mutum biyu ne suka shiga ɗakin ba jimawa suka fito tare da bawa kowa umarnin yayi ƙasa, da sauri duk suka zube kan guiwowin su Banda Hushaima data harde hannuwanta a kirji............. ----------------------√ A falo ya samesu itada Nashwa dan tuni an sallami nurse tunda Nayrah ɗin ta warke, cikin sakin fuska ya amsa gaisuwar da Nashwa ke masa tare da kallon Nayrah dake ta kumbure kumbure tun shigowar sa ita a lalle tayi fushi, baice mata komai ba ya wuce . "Ya Amjad". Nashwa ta Kira sunan sa, dakatawa yayi tare da juyowa yana sauraren ta, "Yah Amjad daman Ina so naje gida ne in ba damuwa"........ A ɗarare tayi maganar kanta a ƙasa saboda bata san amsar da zai bata ba, dan tun ranar ya aiko musu da sabbin wayoyi amma fa duk Numbers ɗin yan gidan baya aiki bama ya shiga gabaɗaya. Ba alamun damuwa ya ce, "Ai baki fadamin ba Nashwa, ki bari in na fito sai muje na kaiki da Kai na".......... Cikin Jin daɗi ta ce, "Nagode sosai ya Amjad, a fito lpy"......... Wucewa yayi ciki, yayin da cikin fushi Nayrah ta tashi tabi bayan sa, yana cikin rage kayan sa yaji shigowar ta dakatawa yayi da unbuttoning ɗin rigar ya juyo tare da buɗe mata hannu alamar ta taho, turo baki tayi tare da juya masa baya, "Ninie rigima". Ya faɗa yana takawa har inda take ya yi hugging dinta ta baya tare da zuro kansa ta wuyanta. Kuka ta fashe masa dashi tare da juyowa ta fara tureshi, faɗi take, "Ni ma whl nashwa zan bi na fasa zaman dakai, tunda gadin gida Ka ajjeni inyi". Dariya yayi wadda ta mance rabon da taga yayi irinta kana ya ce, "Haba yarinya ai ƙarya kike whl, zama daram Matar Amjad"......... Wani kukan shagwaɓar ta sake fashewa dashi, hannun ta yaja zuwa bakin gadon ya zaunar da ita sannan ya zauna, In a serious tone ya ce, "Miye matsalar ne Ninie, bana son ganinki cikin damuwa hakan yana ɗaga min hankali, a baya Ina cewa batun auren mu ne, yanzu kuma an yishi an wuce wurin, dama na fada Miki auren bashi bane wahala a wuri na........" Shuru yayi yayin da ta ƙarasa masa da faɗin, "Zaman auren ne matsalar ko ? To shikenan ai laifi na ne". "Ninie Please ki fahimce ni mana, kinsan yanayin ayyukan dake gabana a yanzu kuwa, ina da abubuwan dake buqatar lokaci na Amma duk da haka Ninie dole zan raba Kai na biyu saboda na Miki abinda kike so ki daina tada hankalin ki dan ALLAH ". Ya ƙarashe yana jin kamar zai sa ihu, tafin hannuwansu ya haɗa tare da zura yatsunsa tsakiyar nata yana matsawa a hankali. kallon sa tayi taga yadda ya cakuɗe fuska yana kallon ta kamar wani baby, goge fuskar tayi sannan ta ce, "Wani irin aiki ne kakeyi a yanzun, bayan duk wani aiki ka tsayar da yin sa". Ta sakaya da hakan dan baza ta iya faɗa masa kai tsaye cewa an tsayar dasu kowani aiki ba. Dan girgiza kansa yayi kaɗan kafin ya ce, "In har Ninie ta yarda da mijinta to karta ƙara tuhumar sa kan aikin sa, in lokaci yayi da kai na zan sanar Miki"......... Wani kallo ta jefa masa kafin ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ka samu labarin su Mumu kuwa? Saboda mu dik mun ƙasa samunsu a waya, nasan yanzu haka hankalin dad ya tashi sosai ".......... Murmushi yayi da faɗin, "Yes dan har ma ya aika sammaci gida cewa na sace masa yayansa biyu". Dafe kirjinta tayi da faɗin, "Again, Amour Dan ALLAH kayi hakuri da abubuwan dasu Dad suke ma, duk a dalilina ne dad ke wulakanta ka haka amma Kai kasan da ba haka suke ba, su Mumu suna son ka sosai "..........."Na sani Ninie saisa nake musu uzuri ai, na fahimci halin da suke ciki Kuma anjima zamuje mu Kai Nashwa gida  tare, daga nan zamuje gida wurin su Anah". Ya ƙarashe yana sakinta ya nufi hanyar toilet sai Kuma ya tsaya tare da juyowa ya ce, "faɗa abinda ke bakin ki?" Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce, "Da gaske da sa hannun ka a mutuwar farshad?"......... Haɗe girar sama data ƙasa yayi kafin ya ce, "Eh............ 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd SultyWrites22 STEP 1 PAGE _______ 47 & 48 "Da gaske da sa hannun ka a mutuwar farshad?" ............ Haɗe girar sama data ƙasa yayi kafin ya ce, "Eh". Da baya baya ta tafi tare da faɗawa kan gadon, runtse idanunta tayi da ƙarfi saboda yadda zuciyarta tayi wani irin hantsilowa kamar zata faso ƙirjinta ta fito, ko ina na jikint ƙerma yake, kenan saboda ita yasa aka kashe Farshad, kenan saboda ta faɗa masa su dad sun dage sai ta auri Farshad shiyasa yayi tunanin kashe shi ne mafita. Maganar sa ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula tare da buɗe idanunta da sauri. "Haka Dad ɗinki ya ce, amma ni bansan komai ba, son samu suyi bincike ba wai maqalawa Wanda ransu ke so ba".......... Daga haka ya juya ya wuce toilet ya barta nan zaune tana binsa da kallo kamar wata doluwa. _______________Dad ne zaune shi da Mumu suna magana faɗi yake, " Ai duk abinda ya samu ya'yana sai yayi bayani gaban hukuma saboda a gaban kowa ya fita dasu ". "To wai Kai Alhaji duk binciken da akayi ba'a samo inda suke ba ko shi ɗin in da yake?"..........." To ke da kin ɗauka ƙaramin hatsabibi ne yaron nan ina gaya Miki kina ƙi, ni fa dama tun farko dan kun nuna k..........." Maganar sa ta katse sakamakon shigowar Nashwa da Nayrah ɗin, da sauri duk suka miqe yayinda Nashwa ta tafi da gudu ta rungume Dad tana faɗin, " I missed you dad".......... ita Kuwa Nayrah tsayawa tayi ta kasa gaba ta kasa baya saboda tsoron tarbar da su Mumu zasu Mata kasancewar tasan suna fishi da ita ne ko daren ranar da suka baro asibitin, tunaninta ya katse ne a lokacin da Mumu ta riqo ta tana faɗin, "Nayrah Nashwa ALLAH Alhamdulillah, ya akayi kuka zo nan ? A ina aka boye Ku ? Ba dai abinda ya same Ku ko?"......... Ta faɗa tana tattaba jikin Nayrah ɗin kamar me neman wani abu . Komawa sukayi suka zauna, Dad ya ce, "Nashwa ALLAH yasa ba kwace muku wayoyi akayi ba, saboda kwata kwata ba'a samun ku?".......... ƙiftawa Nashwa ido Nayrah tayi hakan ya sata faɗin, "Dad wayoyin ne suka sami matsala tawa ta fashe ta Nayrah kuma ta faɗa ruwa sai yau ya Amjad ya kawo mana wasu, kuma muna lpy ba abinda ya same mu muna gidan Nayrah ɗin ne". "Gidan Nayrah ?"........... Mumu ta maimaita tana wurgawa Nayrah ɗin wani kallon da ya sata sunkuyar da Kanta ƙasa. " ALLAH sarki Nayrah ban taɓa ganin Amarya marar galihu irin ki ba, kice haka aka kwashe Ku kamar awaki aka je aka zubaku a gida ko"............ Dad ne ya amsa da faɗin, " Duk fa abinda zaki faɗa a yanzu ihu ne bayan hari hajiya Lateefa, ni dai tunda suna lpy ai shikenan". Da mamaki Mumu ta ce, "Shikenan kamar ya? kana nufin Ka hakura Ka yarda ta cigaba da zama dashi kenan ?"........ Shuru Dad yayi yana kallon Nayrah data sunkuyar da Kanta tana wasa da yatsun hannuwanta".........." Ki barta tunda haka ta zaba taje ALLAH ya bada Sa'a". Mumu zata sake magana Amjad ya shigo da sallama, wuri ya nema gefen Nayrah ya zauna sannan ya gaishe da Dad ya juya zai gaishe da Mumu ta tareshi da faɗin, " Riqe gaisuwar Ka bama buqata, wato mu zaka nunawa iko ko? Ka ɗauke mana ya'ya tsawon sati wato ka zuba mana ido kaga iya gudun ruwan mu ko? to yayi muma yanzu zamu nuna ma ƙarfin namu ikon, Nayrah idan har kika sake kika bishi ban y........." Dad ne ya tare ta da faɗin, "karki fara hajiya Lateefa, karki kuskura kiyiwa ya'ta baki ina cewa ita tace taji ta gani, to mu barta mana ai munyi namu ko, ke tashi ki fita ki barmin gida"............ Miqewa Amjad yayi da faɗin, "Muje"........... Jiki a sanyaye ta miqe, wani murmushin takaici Dad yayi tare da ɗauke Kai ya dubi Nashwa da jikinta duk yayi sanyi tana kallon yar uwarta ta , "Ke tashi ki wuce ciki". Dad ɗin ya faɗa cikin ɓacin rai. Gaban Mumu Nayrah ta ƙaraso tare da zubewa Kan guiwowinta saidai kafin tace wani Abu taji saukar wasu tagwayen maruka Kan kuncinta, da sauri Amjad yayi waje dan bazai iya daurewa ba ganin ana dukanta a inda bazai iya rama mata ba, wasu zafafan hawaye ne suka sauko Mata, ɗago Kai tayi tana kallon Mumu cikin rawar murya ta ce, "Mumu na hakura na yafe auran whl na hakura Dan ALLAH kiyi hakuri "............" Ba fa zaki haƙura ba ki tashi ki bishi ai kin makaro, da lokacin kafin kije gidan sa kikace Kin haƙura zan yarda Amma yanzu whl Baki isa ba, tashi ki fita". Dad ya faɗa a fusace yana miqewa kamar zai kai mata duka, da gudu ta tashi tayi waje, tashi Mumu tayi da faɗin, "Wai Alhaji meke damunka ne? ya kake neman jefa min ƴa' a rami ne, ya ina ƙoƙarin shawo Kan lamarin gidana kana wargaza min, in kuma yayi amfani da wanna damar ya saida min ya' fa "............" Ke kaɗai kika haife ta ne?". Dad ya tambaya sharply. "Alhaji!."......." Lateefa". A tsorace Mumu taja baya tana bin Dad da wani kallo me kama da tsoro tsoro. Kaɗai rigarsa yayi ya wuce sama ya bar Mumu sake da Baki, abinda ya daɗe bai faru ba tsawon shekaru kenan, Meke shirin faruwa da ni ne? Ta wa kanta tambayar da bata da amsar ta. -----------------------√ "Ke baza ki durƙusa bane?"........... Wani me ƙiran adawan farko ya faɗa yana zarewa Hushaima ido. Ba tare da wani alamar firgici a tare da ita ba ta ce, "Kan wani dalilin zan durƙusa kenan?" ..........." Ke ba fa a mana rashin kunya ko gardama, Maleekh ne zai fito kuma dole ki durƙusa dan shi ɗin shugaba ne a gareki da duk wasu al ummar dake yankin nan da kuma wasu yanki na duniya". Buɗe baki tayi cikin salon rainin wayo ta ce," Au da ALLAH fa? Shugaban ƙasa ne ko uban gida na ne ko kuma miji na ne shi da zai shugabance ni?". "Shi din yarima ne mai jiran gado na AURELLON SULTANATE".......... take duk mutanan dake tsakar gidan suka sha jinin jikin su tare da yin ƙasa da kansu ko numfashin kirki daƙyar sukeyi, wani irin tsit gidan yayi kai kace mutuwa ce ta gifta. Shuru tayi dan tabbas ta taɓajin tarihin wanna masarautar a wurin Amla, a yadda ta faɗa Mata masarautar tafi kujerar shuwagabanni da yawa iko da ƙasarsu. Dawowa tayi daga gajeren tunanin data tafi amma bata jin akwai wata halittar da zata iya durƙusawa dan kawai ya wuce cabbb ta ma zama banza kenan "............." baza ki bi umarnin da ake baƙi bane sai fushin Maleekh ya hau kanki?".............." Whl sai dai ku kasheni Amma in dai sai na durƙusa sannan zai wuce to saidai yayi tsami a ɗakin". Ɗaga wata murɗaɗɗiyar dorina dake hannun sa yayi ya zabga mata ya sake ɗagawa zai Ƙara mata Sahnish yayi saurin shiga tsakiya wani ihu ya sa tare da buga tsalle ya zube a wurin saboda dorinar da mutumin ya sauke mai sai da ya jiyo ƙamshin lahira, cikin wani irin yanayi na fita hayyaci ta dyago tare da fizge dorinar, da hannu ya kai mata duka, ta tare lokaci guda idanunta suka sauya launi, da sauri Sahnish ya rarrafa gaban Maleekh kamar yadda suka ambata, wanda a lokacin ya fito daga ɗakin ya sanya wata sabuwar riga, take iskar gidan ta sauya zuwa ƙamshin turaren sa na bolt lightning. Ƙafarsa Sahnish ya riqo ya shiga roqon sa, "Dan ALLAH ka taimaka Kar su ji mata ciwo, Dan ALLAH Kai ɗin babba ne Kuma shugaba ne ga Al'umma, bai kamata ka bari aci zalin Al'ummar ka a gabanka ka ba, ka taimake mu dan ALLAH, ko dan ƙanwar mu Bamu da kowa sai ita Dan girman ALLAH karsu kasheta ka taimake mu". Ya ƙarashe yana nuna Shazeen dake kuka sosai tana kokarin zuwa wurin Hushaima ɗaya mugun ya riqeta. Sai dai duk wannan magiyar da Sahnish yakeyi ko ɗagowa Maleekh bai yi ba ballantana ya san yanayi, tunda ya zube hannayen sa a aljihu kansa a ƙasa gashin kansa dake baje ya zubo ya rufe fuskar sa. Tashi Sahnish yayi dakyar saboda jikinsa dake masa wani irin azababben radaɗi tun da ya samu rabonsa, rarrafawa yayi ya riqe ƙafar wanda ke dukan Hushaiman yana bashi haƙuri, wata irin harbi ya kai masa da ƙafar sai ganin Sahnish sukayi ya wani tashi kamar tsuntsu bai sauka a ko ina ba sai ƙofar soro, amma duk da haka yana sauka ya sake miqewa ya nufi wurin sauran saidai ba wanda ya kalleshi ballantana ya tanka masa, saida mutumin nan ya tarawa Hushaima gajiya iya iyawarsa, ita kuwa har lokacin a tsaye take ƙiƙam bata da niyyar sunkuyawa, dan tun tana ƙoƙarin faɗa ta ƙwaci kanta har ta haƙura ta tsaya kawai . A lokacin da ya dago kusan da yawa daga cikin mutanan gidan dake satar kallonsa ta ƙasan ido, ba dan a tsare suke ba da sai sun ara ana Kare saboda tozali da wannan kyakyawar halittar da sukayi, sosai kyawun sa tsorata su. " Ya Isa gaɗɗo".......... Ya faɗa da daddaɗar muryar nan tasa, sannan ya fara tafiya da sauri sauri cike da ƙarsashi da kuma takun jarunta kamar wani saɗauki ya nufi hanyar fita daga gidan, da sauri duk suka rufa masa baya saidai taku daya biyu sukayi gaɗɗo ya zube a wurin. Rufowa kansa sukayi suna tambayar sa lpy, wani irin ihu ya ƙwalla da sai da gabaɗaya unguwar ta amsa faɗi ya ke, "Kuyi hakuri dan ALLAH Kar ku tabani".......... Da Mamaki mutanen gidan suke kallon sa ciki har da Maleekh daya dakata da tafiyar ya juyo yana kallon gaɗɗon dake zube a ƙasa yana ja da baya da baya yana faɗin karsu taɓashi. Zamewa tayi a wurin tana ƙanƙame jikinta tare da faɗin, "Sahnish ruwa, ruwa".......... Da sauri ya matso wurinta yana kiran sunan ta. " Ka zuba min ruwa a jiki na, Sahnish kayi sauri zan mutu"......... Ta faɗa jikinta na wani irin kakkarwa, ai baisan lokacin daya ɗauki wani bokitin dake cike da ruwa ba ya juye mata a jiki wata irin doguwar ajiyar zuciya ta ja take haƙoran ta suka fara haɗuwa da juna kamar wadda masassara ta kama . Hannu suka Kai da niyyar riqo gaɗɗo Amma Ina wani ihun ya sake kurmawa tare da tashi zaiyi waje a guje da sauri sauran yan uwan nasa suka riqeshi. " Karku sake shi ku kaishi mota"........... Maleekh ya faɗa a dake sannan ya juya ya fice. Daƙyar aka kakkama gaɗɗo aka fitar dashi zuwa mota sai fisge fisge yake. Da sauri su Baba ilerika sukayi kan Hushaima data dora kanta kan kafaɗar Sahnish sai ajiyar zuciya take saukewa. Baba ilerika ne ya ce, "Sahnish ka samu kuje ciki ta canza kaya bari na samo mota a Kaita asibiti"............" Ga mashin ɗi na ma"......... Kawu adamu ya faɗa, tsaki Baba ilerika yaja tare da juyawa ya nufi hanyar waje. "Kaji ko kaji ba, kyakk wato yanzu hassada fa ba sai na waje ba Ɗan uwanka ma tsab wani lokacin zaiji kamar ya hadiye ka saboda ka shigar masa ido". "Haba adamu, ya a na alhinin wani abu Kuma zaka taso da wata Maganar". Faɗin mama Atine. "Ke da ALLAH rufemin baki, ai dake mijin ki ne dole zaki bi bayan sa, dama duk tare kuke ƙullawa to whl nasha tabara na sha Yasin duk abunku saida ku ganni ku banni". "Kaiii Alhaji na ina yinka, sai sa kake burgeni, daɗi na da gobe saurin zuwa, haka zasu ganmu ayye haka zasu barmu ayye da gani da barmu daidai da fura da damu daidai.........." Umma delu ta faɗa tana tafi, a zuciye mama Atine ta kaiwa kafaɗar Umma delu duka da faɗin, "Ke delu karki ce zaki samun baki a magana ta, whl tsab zaki haɗiye harshen ki a wurin nan"......... Buge hannun Umma delu tayi tare da faɗin, "ke Atine bar ganin ki himmm, ƙashi ɗaya ne dani whl"..........." To ko za'a gwada ne". Mama Atine ta faɗa tana ja da baya tare da gyara daurin zaninta da kullum yake kan kirji. "A'a ku tsaya, wai meysa kuke haka ne? Ku yi ta abu gaban ya'yan ku ko kunya bakwa ji". Kandala Amaryar baba ilerika ta faɗa tana shiga tsakiyar su. "Bani waje ki gani kandala, idan ba gyarawa Atine zama nayi a gidan nan ba baza ta daina min gani gani ba".......... Daƙyar da siɗin goshi aka raba mama Atine da umma Delu. Shi kuwa Sahnish tuni ya taimakawa Hushaima ta tashi suka shiga ɗaki ya ɗauko mata kayan da zata canza sannan ya fito ya bata wuri ta sauya. Saida ta gama ya koma ɗakin ya taimaka mata suka fito daidai lokacin Baba ilerika ya shigo da saurin sa ko bi takan su Mama Atine baiyi ba yace da Sahnish su fito. Da ragowar kuɗin da Jey ya basu sukayi amfani a asibitin yayinda Baba ilerika yayi uwa yayi makarɓiya ya tsaya akan komai saboda Sahnish na tare da Hushaiman hatta magungunan da aka basu shi yaje ya siyo ya dawo sannan suka nufo gida. Sai da Hushaima tayi kwana biyu tana jinyar jikin ta kafin ta warware ta cigaba da harkokin ta. ----------------------√ AURELLON SULTANATE💎 AURELLON SULTANATE wata babbar masarauta ce me girman gari guda domin duk abinda za'a samu a gari to akwaishi a ciki kama daga Kan population na mutane wanda dama suke haɗuwa su zama gari to su ne matakin farko na kafa Aurellon sultanate, domin kuwa mutanen cikinta yawa ne dasu, kuma duk yaren su ɗaya al'adun su daya in kaga wanda ba nasu ba to daga cikin bayi, hadimai, fadawa ko kuma dakarun su ne. Akwai makaranta, jami'a, asibitoci, court, police station, barrack na sojoji, fuel station, gidan television nasu, masana'antun su, ɗakin karatu na musamman (Library), Hotel, Shopping Malls, Airport, da dai sauran su, they are very creativity domin yan baiwa ne su, suna ƙirƙirar abubuwa da dama su fitar dashi ƙasashe, duk mutanan dake cikin Aurellon basa fita wajen ta yin aiki, a cikin masarautar su sukeyi, saidai su fita waje dan ra'ayin kan su amma ba dan neman wani abu da basu dashi a masarautar su ba, duk wasu abubuwan more rayuwa sun tanadarwa kansu in nace komai ina nufi komai. Suna da kwararrun masu busa sarewa da kuma gwanintar murza linzamin dawakai. Sultan Abdulbasit Abdulaziz wato Sarkin garin ya kasance dattijo me adalci ga al'ummar sa, mutum ne mai kuma sauƙin Kai da son zaman lpy, yana da mata uku, Sheikha Barrah itace matar sa ta farko tana da ya'ya takwas duk mata, biyar sunyi aure sai uku ne a gabanta. Sai Sheikha Balqis tana da hudu mata ɗaya namiji, biyu sunyi aure saura yan mata biyu da namiji ɗaya. Sai Amarya wato Sheikha Mahra tana da shida huɗu mata biyu maza, ɗaya ce kawai tayi aure. Ginin Aurellon sultanate ya fita daban a tarihin qawatattun gine ginen duniya, domin gini ne da aka narka dukiya akayi shi ba algus, wasu irin dogayen gini ne da sukayi matuƙar tsaruwa saboda haɗuwar su, kusan duk wani abun qawa da aka qawata ginin dashi diamond ne, ta yadda ko ba wuta hasken wannan diamond ɗin da kuma glasses ɗin nan kaɗai ya isheka ballatana ba'a dauke musu ko na second ɗaya. A bangaren ƙarfin iko kuwa tana da ƙarfin iko fiye da tunanin me karatu, domin kuwa mulkin su absolute monarchy ne duk sarkin da za'a naɗa sai aurellon ta duba cancantar shi take Naɗashi kuma karkuyi tunanin su take zuwa ah ah, sarkin da za'a naɗa ɗin ne zasu zo Aurellon tare da mutanan sa, idan ta Naɗashi sunayin shagalin bikin tayashi murna sannan su haɗashi da yan rakiya har zuwa masarautar tasa, tana da ƙarfin ikon dakatar da shugaban ƙasa da zarar ta samu labarin wani batanci da yakewa al'ummar sa, duk duniya shakkar tinkarar ta suke, suna da tsaro sosai tare da dokoki da kuma qa'idoji ba wanda ya isa shiga cikinta kai tsaye haka zalika fita. ______________Wani ƙayataccen falo ne da yaji kayan qawa da more rayuwa, zagaye yake da wasu royal cushions set uku sai TV da kuma na'urorin sanyaya ɗaki , banda sassanyan ƙamshi me kwantar da zuciya tare da sanyi AC ba abinda ke tashi, wani kyakyawan dattijo na hango zaune kan kujera ya ɗaura ƙafarsa kan wani tumtum me laushi, fari ne tas ga dogon hanci kana ganinsa kaga irin larabawan asalin nan, Sanye yake da farar saudi thobe, lallausan gashin nan ya koma grey saboda furfurar data fito akan Black silky hair ɗin nasa, zai iya kaiwa shekaru 67 a duniya. Hannun sa riqe da wani ƙaramin mug Mai masifar kyau sai walwali yake, kallo na nakai gaban sa inda wata kyakkyawar mata da zatayi shekaru 45 zuwa 46 a duniya amma ba zaka taɓa zaton takai wannan shekarun ba dan in Ka kalleta zakayi tunanin baza ta haura 30yrs ba saboda kyawun jikinta da ya haɗu da jin dadi, sanye take da Mukhuwar kalar red and peach wuyanta da hannayenta kuwa duk ta ƙawata su da wasu danƙararrun gold na HD AURUM MINING, sai walwali take. Cikin harshen larabci dattijon ya ce, "Mahra kin cika son wahalar da kanki da yawa, da kin bar Khadiman sun yayyanka ai"........... Kallo na Kai kan abinda take yi, grapes ne da apple take yankawa a cikin wata ƙaramar bowl. "Zan iya barin su suyi komai Sultan amma ba zan bari khadimai suyi hidimar mijina ba"........ Wani dan gajeren Murmushi yayi cike da izzar mulki ba tare da ya sake cewa komai ba, saidai yanayin fuskarsa ta nuna yaji dadin maganarta, wannan dalilin yasa duk cikin matan sa Mahra ta fita daban, saboda duk abinda ya shafe shi bata barwa khadimai ko bayi ita takeyi da kanta, shiyasa matsayinta yake na daban a wurin sa, har hakan yasa abokan zaman ta suke ganin kamar yana fifita ta tane akan su saboda itace mahaifiyar sarakee me jiran gado. "Ya jikin Rouslan kuwa?".......... Sai da ta miqa masa bowl ɗin sannan ta gyara zamanta kusa dashi tare da faɗin, "Dama Ina ta so nayi ma maganar Sultan, Ni wai meysa ba za'a fitar da Rouslan waje ba, na rasa gane kan wannan rashin lpy tasa, daga wannan Dr yace ciwon zuciya sai wannan yace migraine sai wanna yace kaza gabaɗayansu sun kasa gano ainahin abinda ke damunsa". Kafin Sultan yace wani abu wata budurwar yarinya da baza ta wuce 17 years ba ta shigo da gudu kamar zata kifa. "Haba Albee ya zaki shigo haka k........" Bata rufe bakin ta ba wani dogari ya shigo da sauri shi ma yana sanye da uniform dinsu red and dark brown, a murɗe yake kamar wani dan wrestling, zan iya ce muku duk dogaran Aurellon sultanate ba wanda zaka kalla sau ɗaya ka so sake kalla, zubewa yayi kan guiwowinsa kansa a ƙasa ya ce. " Tuba nake Sultan a mun afuwa, gimbiya Albeena ce tazo zata shigo na buqaci ta tsaya na nema mata izini tukunna amma bata saurare ni ba ta shigo, amma idan nayi laifi ai mun aikin gafara".......... Ya ƙarashe yana mai sake yin ƙasa da kansa. " Zaka iya tafiya"........... Sheikha Mahra ta faɗa. "ALLAH ya ƙarawa Sheikha lpy "......... Ya faɗa cikin tsantsar girmamawa tare da tashi ya fita ya jawo musu ƙofar. Rarrafawa tayi wurin mahaifin nata tana da faɗin, "Abbu Ya Reeslan...... "........ Numfashi da take saukewa da sauri sauri ya hanata ƙarasawa sai ƙofa da take nunawa, "Reeslan yana Ina?"......... Sheikha Mahra ta tambaya. Kuka Albeena ta fashe dashi tare da faɗin , "Ummu an kashe su". Zakuɗowa ummu tayi daga cikin kujerar tare da faɗin, "Wace irin maganar banza ce wanna Albeena kanki ɗaya kuwa?"............ "Ummu an Kira wayoyin ku ba'a samu ba, yanzu aka sanar da an Kai musu hari Kuma ba wanda ya tsira duk sun mutu". "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, innalillahi wa inna ilaihir raju'un"......... Ummu da Abbu suka shiga maimaitawa a tare, miqewa Abbu yayi amma sai tsayuwar ta gagare shi saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga dukda yadda yake ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin nasa saboda Ummu, komawa yayi ya zauna yana kallon yadda falon ke juya masa. "Ummu tawaam miqomin wayata a ɗakina yanzu". Cikin ƙarfin hali Ummu ta miqe ta wuce ciki. Bata jima ba ta dawo da wayoyi biyu a hannun ta, "Sayyid Iffan ne yake ta Kira fa Sultan".........." Kawo mu gani". Ya faɗa a Nutse kamar ba abinda ya dameshi, karɓar wayar da ta bashi yayi tare da answering call ɗin, bai tsaya bi ta kan gaisuwar Sayyid Iffan ɗin ba ya ce, "Iffan a wani hali Maleekh yake?"........... Shuru sayyid Iffan yayi cikin jimamin labarin da zai sanar da sarkin nasu. Shi ɗin ya kasance minister labarai ne na nan masarautar tasu, duk wani labarin da ya shafi masarautar tasu to kafin kowa ya samu labari shi yake fara samu sannan ya isar da Labarin cikin masarautar. Sanin cewa Sultan baya maimaita Magana sau biyu yasa shi daurewa ya ce, "A yanzu duk mutanan da Maleekh ya fita dasu an kashesu sai dokunan su kawai aka bari, amma shi babu wata masaniya akan halin da yake ciki dan ba'a ganshi ba".......... Allah sarki dattijo Mai tawakkali duk da girgizar da zuciyar sa tayi bai bari hakan ya bayyana a muryar sa ba, ya ce, "Iffan ka yiwa Babil magana a tabbatar an binciko halin da Maleekh yake nan da 1 hour". ( Babil shi ne minister bincike na masarautar, dan su fa basa haɗawa mutum ɗaya aiki biyu saboda aikin masarautar su girma ne dashi) . "An gama Sultan ". Sayyid Iffan ya faɗa cike da girmamawa, kashe wayar Sultan yayi tare da kallon Ummu wadda kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da kukan zuci take, "Ummu tawaam karki damu, in Sha ALLAH ba abinda zai sami Reeslan, dan ni banji a jikina ya mutu ba in sha ALLAH yana raye kuma zai dawo gida cikin ƙoshin lafiya, dan haka kuje kawai ki kula da Rouslan, Kar ku bari labarin nan yaje masa har sai mun samu kira daga Babil "......... Da, "Okay". Ummu ta amsa a sanyaye tare da juyawa ta koma cikin ɗakin, jim kaɗan ta fito sanye da wata zazzafar alkyabba red me golden stones sai ɗaukan ido take. Tashi Albeena da har lokacin kuka take marar sauti tabi bayan mahaifiyarta ta, sai da suka wuce wani corridor sannan suka isa gaban wani transparent elevator suka shiga ya sauqo dasu qasa. A wani qaton falo da yafi na saman haɗuwa da qawatuwa suka ɓulla, bayi suka tarar tare da khadiman dake bangaren Sultan ɗin suna ta kai kawo, suna ganinsu duk suka zube suna mata Barka da fitowa haɗe da kirari irin wanda akewa matan sarakee, ɗaga musu hannu tayi kawai ta wuce Albee biye da ita, su ma duk rufa mata baya sukayi kamar yadda al'adan gidan take na raka duk wata gimbiya da zata shigo bangaren, haka suka dinga wuce tafka tafka falukan har suka fito zuwa shahararren compound ɗin gidan da ya gaji da haɗuwa, ta ko ina fitulu rau kamar rana. Wata mercedes maybach series S ce Pake a ƙofar fitowar da alama dama su ake jira, dogaran dake tsaitsaye ne suka buɗe musu both side na ƙofar motar, Ummu ta shiga Albee kuma ta zagaya ta ɗaya side ɗin. A hankali motar ta fita daga ɓangaren na Sultan ta kewayo ta left side ɗin da a sama aka rubuta , S. MAHRA da manyan harrufa wato Sheikha Mahra da wasu irin sea blue gems. Tsayawa motar tayi yayinda dogaren dake gaba suka fito da zafa suka buɗe musu, suna fitowa dogaren dake bangaren suka tattaso suna jero musu kirari, Ummu batabi ta kan kowa ba ta shige Albee biye da ita kamar jela. Nasan zakuyi tunanin shin babu hanyar shiga part ɗin ummu ne daga na Abbu? To akwai a taƙaice zaka iya zuwa kowani part na Matan Sultan ta cikin bangaren sa, dan bangaren nasa shi ne a tsakiyar nasu, saidai fa akwai yar tafiya, to wannan tafiyar ce Ummu baza ta iyayi ba a yanzu saboda zuciyarta data mata nauyi a dalilin tashin hankalin da take ciki, dan a lokacin da zata shigo bangaren ba ta gaba ta shigo ba ta cikin part ɗin nata ta isa. Suna shiga falon farko suka hadu da Reeslan da ya fito, sanye yake da kananan kaya maroon ɗin t shirt da baƙin wando, wanda suka Ƙara haska farar fatarsa, gashin Kan nan kuwa ya raba shi biyu ya ɗaure na saman a tsakiya da band na ƙasan kuma ya zubar dashi akan dokin wuyansa. Riqo hannun sa ummu tayi da faɗin, "Ina zaka kuma Rouhi?".......... Sake kallon sa nayi da kyau cike da ɗimbin mamakin sunan data ambata, yoo ai ni na dauka Reeslan ɗin ne ya samu isowa sai da na ƙura ido sosai na lura wannan bai Kai Ruslan ɗin murdewan jiki sosai ba, Amma bacin haka komai nasu irin daya ne hatta da kallon su ɗin nan me isa har zuciyar bawa, to a hakan ma fa wai nayi ƙwaƙwa ne dan na samo abinda ya banbanta su. "Ummu da gaske Habiby ya mutu? da gaske ba'a ganshi ba, ba'asan in da yake ba?".......... Duk da a cikin tsantsar tashin hankali yake amma magana yake cike da nutsuwa da kuma aji irin na ya'yan da jinin sarauta ke gudu a tsoka da jijiyoyinsu. Bata bashi amsa ba ta ja hannun sa suka wuce ciki. Suna shiga ɗakinta ta nufi wurin two seater sofa dake ciki ta zaunar dashi sannan ta zauna gefen sa wanda hakan yasa tsananin kamannin ta dashi ya bayyana a yanzu da suka jera, cikin tausasawa ta ce, "Kwantar da hankalin ka Rouhi, Habibyn ka yana lpy in Sha ALLAH, karka tada hankalin ka"........... Dan girgiza kansa yayi tare da faɗin, "Ummu ɗazun fa da yamma yace min yau so yake ya fita wajen gari ya sha iska tare da dokin sa Hirtik nazo muje nace masa ah ah ni bana jin fita yau yaje kawai, saboda bana jin ƙarfin jiki na nasan in ya sani zai tashi hankalin sa ne. Whl Ummu nayi dana sanin rashin binsa da maybe a Kai na hakan zai faru ba shi ba......"............ Katseshi tayi da faɗin, " Haba Rouhi kayi shuru mana haka, ai kowani bawa da tasa qaddarar, ko dan Kuna tare sai ace bari a goge qaddarar Reeslan a rubutuwa dan uwan tagwaicin sa Rouslan? Abinda nake so dakai karka sa damuwa a ranka Dan ALLAH, Abbunku yasa a bincika duk inda yake nan da 1 hour, Kuma kasan ƙasa da haka zamu samu labari dan haka Ka kwantar da hankalin ka kaji. Ka ma ci abinci tukunna?".......... Ta faɗa cikin sigar lallashi da Kuma tausayawa ɗan nata saboda shaƙuwar dake tsakanin sa da ɗan uwan nasa. Reeslan da Rouslan identical twins ne da basu da banbanci a komai dan ko mahaifan su ba a kowani lokaci suke iya banbance su ba, Dan ma dai Rislan yana da zafi sosai gashi mafaɗaci ba'a taɓa yin doguwar magana dashi a wanye lafiya in anja da nisa ma yana iya rufeka da duka. WANNAN KENAN. "Sai Habiby ya dawo zamuci".......... Zazzafan numfashi Ummu ta furzar ba tare data iya sake cewa komai ba sai waya data ɗauka tayi kira ana dagaywa ta ce, "Ziyada ke da su waye?". A ɗan sanyaye ziyada ta ce, "Ni da su Albeena ne, sai su Nuaymin da suka shigo ɗazu"..........." Turomin su Nuaymin ɗin ɗaki na yanzu"........ Dan shiru tayi jin Ummu na shirin kashewa ya sata faɗin."Ummu ya ake ciki batun ya Reeslan?"......... "Albeena bata gaya miki bane?". "Tace wai Abbu yasa a bincika ba?".........."Eh turo min yaran kawai"..........Ta yanke maganar saboda yadda Rouslan ya kafeta da ido. Ba'a jima ba sai ga wasu yara sun shigo su uku babbar bata fi 10 years ba sai mai bin ta da bazai haura 8 years ba, sai kuma wani yaro da baifi 5 ba sai ta karshen da itama bata fi 4 ba. Suna hango Rouslan suka nufo wurin sa, Nuaymin ya ce, "Khali (uncle) Ina jigsaw puzzle ɗin nan da ɗazu kace mu ajje idan khali Reeslan ya dawo zamuyi wasa dashi to linda ta batar da sauran sai guda biyu ta bari". "Khali whl karya yake min shi da Nuaymah ne suka watsa abinsu, Ummu ALLAH kicewa Nuaymin ya fita ido na yaran nan ya rainani, kullum sai ya ce nayi ƙarya". Faɗar babbar cikin nasu da aka Kira da Linda . Murmushin ƙarfin hali Ummu tayi tare da biyewa yaran dan dama tace suzo ne saboda Kar su bar Rouslan ɗin yayi tunani sosai, kusan 30 minutes wayar Rouslan ɗin tayi Ƙara zarota yayi daga aljihu ai yana ganin me Kiran ya miqe tsaye da sauri. "Menene ? Waye?". Ummu ta tambaya a jere, inaaa bai tsaya bata amsa ba yayi answering call ɗin tare da faɗin, "Habiby where are you?"......... Miqewa itama Ummu tayi tana kallon sa da jiran amsar da zai faɗa. "Zamuzo yanzu mu taho dakai".........." No karku zo yanzu ku bari sai da safe I'm safe here, har sai safiyan kun iso". "Ah ah Habiby ka bari muzo yanzu ka faɗa mana location ɗin da kake"............" Me sa kake da gardama Rouh nace ku bari sai da safe mana ". Ya faɗa cikin faɗa faɗa, miqawa Ummu wayar Rouslan yayi saidai itama duk yadda tayi dashi yaqi faɗar inda yake kawai dai yace musu yana lpy da safe suzo su ɗaukeshi anjima zai tura musu location ɗin. Ko da suka gama wayar Ummu Sultan ta kira ta sanar masa, Kiran sa yayi shi ma sukayi magana daga nan ya kira Ummu yace karsu damu su barshi sai da safen kawai, dole ba yadda suka iya da taurin kan Reeslan haka suka haƙura. Ranar kwana sukayi suna waya da Rouslan ɗin wanda yaqi yarda ya koma ɗakin sa yace tunda Reeslan baya nan a ɗakin ummu zai kwana, itama daren bata samu kwanciya ba kwana tayi tana nafilfili har zuwa sallar asuba, sai Lokacin Rouslan ya tashi ya fita, ɗakinsu yaje yayi shirin masallaci ya fita ana idarwa kuma ya dawo ɗakin Ummu still, saidai bai jima da shingiɗa akan sofar ba bacci ya ɗauke shi ba tare da ya shirya masa ba dan a nufin sa zai huta ne zuwa wayewar gari sai su tafi ɗauko Habiby tare. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 49 & 50 Sai wurin rana su Reeslan suka iso Aurellon sultanate, a gaban wani tangamemen gate me masifar girma suka tsaya, dan idan da mutane ne zasu buɗeshi to fa sai an samu gardawa sama da talatin tukunna su iya motsa shi saboda faɗi da kuma tsayinsa, a samansa an rubuta WELCOME TO AURELLON SULTANATE da wasu irin glitters gems masu walwali. Automatic gate dan haka sai da ya gama screening motar tasu sannan ya buɗe da kansa suka shige ciki, wasu jibga jibgan securities ne tsaitsaye suna ta Kai da kawowa dukkansu sanye da uniform ɗin su red and dark brown. Sai da suka sake tafiya me ɗan nisa sannan suka isa second gate shi ma tsayawa sukayi yayinda wata computer ta fara magana cikin harshen larabci tana musu welcome. Shi kuwa gogan naku sai tsaki yake bugawa, dan da ace mutane ne ke jinkirtawa kafin su buɗe gate ɗin nan da tabbas babu abinda zai hanashi sauka ya haɗa kansu da gate ɗin saboda ba abinda ya tsana a rayuwarsa biyun jira. Sai da ta gama yan surutanta gate ɗin ya buɗe suka shige, hanya suka miqa kamar zasu bar gari, sosai sukayi tafiya kafin su isa gaban wani ƙaton round me kaman water fall sai fidda wani glitters sea blue waters yake gwanin sha'awa, roundabout ɗin ya raba hanya huɗu ne ta west, east, north da south, sai da suka zagayo sannan suka ɗauki hanyar da tayi north ɗin. Bari kuji wani abun burgewa game da Aurellon sultanate, suna da matuqar tsafta fiye da yadda kuke zato dan tunda muka shigo banga ƙasa ko ƙura a cikin wannan masarauta ba, domin bayan shimfiɗadɗiyar kwaltar dake kan hanyar ko ina ka ɗaga ido ka kalla wani irin shinfiɗaɗɗen block ne kawai yake ɗaukan ido. Part ɗin Sultan suka nufa tun kafin sun ƙarasa suka dinga sakin horn dan sun san halin Reeslan, ai kuwa suna shigewa tun kafin motocin su tsaya wasu suka diro tare da kama murfin motar da yake ciki suka buɗe immediately motar na tsayawa saboda gudun Kar suyi laifi. Cike da sassarfa da kuma izza ya fito daga motar, take duk suka zube suna zuba masa kirari amma ko kallon su bai yi ba ya shige, Dan dama shi sun riga sun sani bayan Matan Abbu duk wanda zai shiga sai an masa iso amma fa banda Reeslan dan tsoron sa da kwarjinin sa ma bazai barsu su ɗaga Ido su dubeshi ba ballantana har suce ya jira a nema masa izinin shiga dan tsaf zai haɗa ma mutum jini da majina, kansa a sama yake baya ɗaukan wargi ko daidai da misalai zarratin, whl kuskure kaɗan zakayi sai ka gwammace kiɗa da kalangu. A falon farko ya tarar da yan uwan sa da Ummu sai Abbu da ya fito da Niyyar zuwa fada domin janaizar mutanan da aka kashe wanda suka fita tare da Reeslan ɗin jiya amma jin cewa su Reeslan ɗin su na hanya ya sashi tsahirtawa. Da sauri su Albeenah suka nufeshi cike da farin cikin ganin sa sukayi hugging ɗinsa suna masa barka da dawowa lpy, hugging ɗinsu yayi back one by one sannan ya wuce wurin mahaifin sa ya yi hugging ɗinsa shi ma, ɗan bubbuga bayan sa Sultan yayi sannan ya ce, "Alhamdulillah tunda Ka iso lpy dama ku nake jira, ni yanzu zanje fada domin na samu janaizar mutanan mu da aka kashe, amma zuwa dare kazo ina son ganinka ".........."To Abbu ALLAH ya tsare ". Ya faɗa Yana komawa kusa da Ummu dake murmushin Farin ciki a zuciyarta kuwa ƙara godia takewa ALLAH da ya tsiratar Mata da gudan jinin ta. Duk ALLAH ya tsare sauran yaran sukawa Abbu, ya amsa musu yana sa kai ya fice, fadawan sa suka rufa masa baya zuwa mota inda zai shiga su wuce fadar. Kirjin sa ta ɗan daka cikin so da ƙauna ta ce, "Bakaji Ibny meysa zaka fita, duk cikin masarautar nan bai isheka zagaye da dokin ba?".......... Dafe wurin kafaɗar tasa yayi kusa da inda Ummu ta daka, a hankali ya furta, "Ouchhh Ummu zafi"........ Kallon sa tayi cikin kulawa ta ce, "Menene kuma? Bana son zolaya fa".........." Ummu I'm hurt here na samu rauni". Ai take duk suka rikice suka shiga tambayar sa me ya faru dashi? me ya same shi? Sai dai a maimakon ya basu amsa sai cewa yayi , "Ummu ina Rouh? Ban ganshi anan ba?"........... Huyam ce ta ce, " Yana room ɗin Ummu yana bacci bai ma san an tafi ɗaukoka ba, da tare dashi za'a tafi, but ya Reeslan me ya same Ka ? A ina kaji ciwon?".......... Bai bata amsa ba ya juya da sauri yayi waje, bin bayan sa Ummu ma tayi tana faɗin, "Ki kiramun Dr Abyan yazo part ɗi na yanzu ya sake duba min shi". Da sauri kuyanginta suka rufa mata baya. Ko da Ummu ta fita Reeslan har ya karɓi key mota ya fice daga part ɗin, dan dama shi dole take kamawa a tuqashi, yafi son yayi tuqin sa da kansa yadda zai ƙurewa motar gudu son ransa. Ganin haka ya sa Itama ta shiga nata motar da aka buɗe mata sauran kuyangin suka shiga sauran motocin biyu da suka zo a ciki, suka bi bayansa. Yana shiga ɗakin Ummu ya wuce da ɗan gudu gudu wanda hakan ya ban mamaki ganin magajin kujerar Aurellon na gudu. To saura kuma wasu suce na fiya sa ido. Yana shiga ya nufi wurin sofar tare da durƙusawa wurin kan Rouslan ɗin ya sanya hannu ya maida masa gashin kansa baya sannan ya ja hancinsa da faɗin, "Rouh! Rouhi I'm back, I missed you, wake up"........ A hankali yake jin sautin muryar ɗan uwan nasa kamar a mafarki wanda yasa ya fara buɗe idanuwan nasa masu cike da bacci a hankali har ya sauke su a kansa, zabura yayi ya miqe lokacin da ya gama tantance Reeslan ɗin ne a gaban sa, riqo shi yayi yana faɗin, "Habiby yaushe Kuka dawo, shi ne Ummu bata tasheni ba anje ɗauko Ka dani"............ " Easy Rouhi, ba gani na dawo ba, tashi mu tafi ɗakin mu".......... Girgiza masa Kai yayi da faɗin, "Habibyy you are not okay, please tell me me ya sameka sunyi ma wani abu ne?". Ya tambaya cikin damuwa. Bazai iya boyewa Rouslan komai ba dan haka ya cire rigar sa tare da nuna masa inda aka yanke shi sannan ya ce, "Ka gani yanka ne but I escaped it, ya ma fara warkewa". Ɓata fuska yayi da faɗin, "Habibyy Please Ka daina fita ba tare da ƙwaƙwaran tsaro ba, ya kamata ace munje hospital an sake duba wurin fa"......... Riqo masa hannuwa yayi da faɗin, "Ni ma fa likita ne Rouhi ko ka manta ne? And nayi duk abinda ya kamata so karka damu, tashi muje ɗaki nayi wanka kai ma kayi dan nasan bakayi ba". Ba musu ya miqe suka fito in da suka haɗu da Ummu na shigowa, idonta ne ya sauka akan ɗinkin dake shinfide a faffaɗan ƙirjin nasa ta wurin kafaɗa, hankalin ta ne yayi mummunar tashi duk ta rikice saboda ba ƙaramin yanka bane, dakyar suka kwantar Mata da hankali sannan suka samu suka wuce . --------------------√ Tafiya takeyi da ƙafa, tasowarta kenan daga wurin aiki bata samu abun hawa da wuri ba shi ne take dan tattakawa gaba kaɗan ko zata samu, cincirundon mutane ta hango sun cika a bakin wani layi, ɗan rage tafiya tayi saboda yanzu duniyar ta zama abinda ta zama karta je bata son taron miye ba, Hakan yasa ta ƙarasa wurin wasu mutane dake zaune bakin wani shago suna shan rake, sallama ta musu suka amsa sannan ta ce, "Da ALLAH meke faruwa a can ?"......... Ɗaya daga cikin su ne ya ce, "Yaron Alhaji Hashim Darwin ne yake rabon kuɗi wai, mu Kuma duk hakan ba birgemu zaiyi ba yauwa, tunda duk anyi walkiya mun gan su a rana".......... Ɗayan ya amsa da faɗin, "To wa ma ya sani ko kuɗin tsafi ne kana karɓa ka ɓace, wai ba qanin su bane ake zargi da safarar mutane, to wa ya sani ma ko tare sukeyi suke neman su rainawa mutane hankali su nunawa duniya ba ruwansu". "To ai su wa'annan fa yanzu ne ma suke wani mutumta mutane da suka ga zata kwaɓe musu gabaɗaya, Amma ada duk cikin su ba me mutunci gwara ma Amjad ɗin to ashe shi ma ladabin ɗan kunama ne da haka suke saye zuciyar mutane suna kwashe su, mu kuma dake yunwa ta kashe mu ana watsa mana tsaba sai mu bi su". Ita dai Hushaima sallama ta musu bayan ta gama jin zancen nasu sannan ta cigaba da tafiyar ta cikin nutsuwa, gajiya tayi ta tsaya tana duba abun hawa tare da zaro wayarta ta fara ƙoƙarin kiran Sahnish saboda kar suga shiru hankalin su ya tashi. Bayan Awais ya gama sallamar mutanan ya juya da Niyyar yi wa yaran sa magana idon sa ya sauka kan Hushaima, Ƙura mata ido yayi a daidai lokacin data samu Abun hawa kenan. "Zubairu ku shigo mota, ina so mu bi wancan mai tuktuk ɗin".......... Ba ɓata lokaci zubairu ya sanar da sauran suka shige ɗaya motar shi kuma ya buɗe wadda Awais yake ciki ya shiga mazaunin driver ya tada suka bi me tuktuk ɗin da Hushaima take ciki har suka ƙarasa gidan ta sauka ta biya me tuktuk ɗin ta shige ciki. Ɗan nesa da gidan suka tsaya, Awais ya ce, " Zubairu fita ka min bincike akan yarinyar can data sauka a tuktuk ɗin can ta shige gida yanzu, shin matar aure ce ko kuwa dai irin tamu ce"......... "To ranka ya dade". Zubairu ya faɗa tare da buɗe motar ya fita ba tare da ya kashe ta ba. Wata yarinya ya tarar wurin kawu garba sai musayar maganganu suke irin nasu na yan duniya, sallama ya musu suka juyo suna kallon sa, Yarinyar ce ta ce, "Malam ya akayi ne?" "Da ALLAH tambaya nake"........... "To tambaya kuma mu ba gidan Radio ba "......... Kawu garba ne ya karɓe da faɗin, "ALLAH yasa mun sani". "Yauwa dattijo da ALLAH nasan kunga wata yarinya da me tuktuk ya sauke yanzu ta shige gidan can da ALLAH tambaya nake a kanta?"......... Kallon Yarinyar kawu Garba yayi da tambayar, "Akwai Wadda ta shiga gida ne yanzu?"........ Ɗan mere baki tayi da faɗin, " Ba Wadda ta shiga in ba tity ba (sun sawa Hushaima sunan tity ne saboda ƙarfin zuciya irin ta ta, rashin tsoro sannan in tace zata yi abu to ko sama zata haɗe da ƙasa sai tayi, TITAN shi ne asalin sunan suka yanke suke cewa tity, yana nufin Huge, powerful and unstoppable). Ita kuwa ba matar aure bace shegiyar kanta ce, in ma miji ta samu suke shirin aure har ya turo ka masa tambaya a kanta, to whl ka bashi shawara dan yarinyace me zaman kanta gata yar bala'i, yan sanda, yan daba, yan doka Kai har aljanu da shaidanu ma tsoronta suke ji, dan haka tun wuri ka naɗe malaman kafafunka ka Ƙara gaba".......... "Shikenan to Nagode ". Zubairu ya faɗa tare da barin wurin ya juya ya koma inda sukayi parking motocin su, yana shiga ya zayyane wa Awais abinda yarinyar can ta shaida masa kan Hushaima. Wani ƙayataccen murmushi yayi da faɗin, " To kai zubairu me kake jira, ai kasan irin su muke so, maza je ka ka sallamo min ita, dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe ".......... " Angama ranka ya dade". Zubairu ya Amsa tare da sake fitowa daga motar ya wuce ƙofar gidan, ƙwanƙwasawa ya shigayi tare da buga sallama. "Wai waye ne ya ke damun mutane da bugun ƙofa da magribar Nan?". Gboy yaran baba ilerika ya faɗa yana fitowa daga ɗaya daga cikin ɗakin dake soron, ganin zubairu ya sashi faɗin, "To ya akayi ne?". "Sannu, da ALLAH wata yarinya Tity nake so ka min sallama da ita". "Kkaiii gidan nan ba'a yiwa kowa iso sai dai ka shiga ka isar wa kanka, Amma kafin nan zaka bada kuɗin ƙofa". Ya faɗa da Muryar dake nuna kamar a make yake. Hannu ya miqa masa alamar ya bashi kuɗin ƙofar, ba musu Zubairu ya zaro kuɗi daga aljihun sa masu yawa ya miqa masa, kawu adamu ne ya sawo Kai zai shige gidan ganin kuɗin da ake miqawa Gboy ya sashi yin caraf ya warce yana faɗin, " Wanna rabo na ne dama Ina bin ubanka bashin dubu goma ".........." Ahh kaii jagus ya haka ne, wancan ai abinda ya haɗaka da tsoho na ne, Kuma ehh can ku haɗe Amma ka bani kuɗi na, dan baka san ƴar buga bugar da nayi na same shi ba". "Tsaya nan Kai tayi kaji, ɗan wahala"......... Kawu adamu ya faɗa Yana wucewar sa ciki ba tare daya kalli inda zubairu yake ba, bayan kawu adamu zubairu yabi domin shiga gidan ai da sauri Gboy ya shiga gabansa tare da bubbuɗe hannu ya ce, "Kai malam ya ne, ina kake neman shiga ai baka ban kuɗin ba"........." Kamar ya ban baka kuɗi ba, ina cewa a hannu ka wancan tsohon ya warce ba a hannu na ba". "Kai kwarankwatsa dubu baka wucewa in baka bani kuɗin nan ba, Kai karka rainamin wayo fa ina iya ma balli balli na bajeka kamar banda alqur'an".......... Tsayawa zubairu yayi kamar ya koma amma yasan can ma ran Awais ne zai baci idan yaji akan kuɗi ya dawo dan haka ya sake zaro wasu kuɗin ba tare da ya sake magana ba ya damƙa masa sannan ya wuce cikin. Ko da ya tsinci kansa a cikin gidan rasa inda zai dosa yayi sai kawai ya tsaya wurin su mama Atine tare da faɗin, "Da ALLAH Tity fa?"......... Ƙofar ɗakin ta mama Atine ta nuna masa da hannu tana cigaba da bare gyadar ta. " Nagode". Ya faɗa tare da wucewa in da ta nuna masa, a zuciyar sa kuwa mamakin abinda uban gidan nasa ya gani a tattare da yarinyar dake irin wanna gida yake, shi da ke sa a kawo masa classic bebs kalar wacece yake so, daga kowani gari, yan mata masu aji yan kwalliya, amma shi ne kuma yau ya ƙare a local gidan karuwai irin wanna, dan shi kwata kwata zubairu a gidan karuwai ya ɗauki gidan su baba ilerika, dan yanayin sa da ya gani baiyi tunanin akwai matar aure ɗaya dake rayuwa a ciki ba. Kwankwasa ƙofar ɗakin nata yayi, Hushaima data ɗaura zani tana kokarin shiga wanka taji bugun kofar ɗakin nata, dakatawa tayi da faɗin, " waye ne?"............" Ni ne, kinyi baƙo ne"........ Zubairu ya faɗa . Ɗan shuru tayi kafin can kuma ta ɗauko hijab tasa ta nufi kofar ta buɗe, Ƙare masa kallo tayi tare da faɗin, "Ya akayi? Daga Ina?". "Ba sai kinsan daga Ina ba customer ne zaki iya fitowa yana waje yana jiranki"......... Dan jim tayi kafin ta ce, " Okay jira ina zuwa". Ta faɗa tare da komawa ciki, a gurguje ta maida kayanta data cire sannan ta fito, tsaye ta sameshi yana jiranta, ganin fitowar ta ya sa shi shigewa gaba ita kuma ta rufa masa baya. A gaban motar suka tsaya, Zubairu ya buɗe mata ƙofar baya, kama ƙofar tayi ta riqe ba tare data shiga ba, "To ki shigo mana, inaga ai sai yafi ko?".......... Faɗin Awais da ya zuro kansa, kallonsa tayi na wasu seconds kafin ta zura jikinta ciki ta zauna amma ƙafafunta duka a waje suke kamar yadda ƙofar motar take a buɗe, kamar zai sake magana sai kuma yayi shiru, can kuma ya ce. " Sai kuma ki min ƙwalele ki wuce, haka akeyi ? Ummm yam mata". Idonta a kansa ta ce, "Ai bansan ka taya bane Alaji"........... Dariya yayi irin ta Alhazawan birni kuma gogaggun yan duniya sannan ya ce, " To Kar na ɓata miki lokaci da yawa ga wanna card ɗi na ne, in kin shiga ki Kirani sai nayi saving taki number ko".......... Juya idanunta tayi tare da faɗin, " Sai dai wayar tawa ce sai na kai gyara dan yanzu shiga ta ina ƙoƙarin shiga wanka ta faɗa ruwa". "Ahh to karki damu ai kinga yaro na zubairu ko, zan aiko shi ya kawo Miki waya anjima kinji, wannan ai ba wani abu bane"....... Godia ta masa sannan ta fita daga motar, ta wuce ciki, shi kuma Zubairu da yake maqale jikin katanga kamar ƙadangare yana jira su gama, ganin ta fito ya sashi ƙarasawa ya buɗe motar ya shiga, ya tada suka bar layin. Da daddare kuwa suna zaune a ɗaki dukkansu suna hira, zubairu ya ƙwankwasa ƙofar ɗakin nata, tashi tayi ta buɗe ba tare data tambayi waye ba saboda tasan Wanda take expecting, shi din ne kuwa miqa mata ledar dake hannun sa yayi da faɗin, "Gashi inji alhaji yace idan kin haɗa Yana jiran kiranki"........" Okay ka mashi godia dan ALLAH"........ " Ba damuwa". Zubairu ya faɗa tare da barin ƙofar ɗakin, ita Kuma ta koma ciki tare da cillawa Sahnish kwalin wayar, ɗauka yayi ya buɗe da mamaki a fuskar sa ya ce, "Hushaima sabuwar waya nake gani Ina kika samu haka?". "Wani alhaji ne ya saya min fa ".........."kice duka ɗaya kika wanko shi tass, wannan wayar ai me tsada ce, iPhone 17pro fa kinsan kuɗinta kuwa. Hmmm amma dai ki kula, a tsaya dai a iya wanke wanken dan nasan wannan fagen kam kin haddace shi amma kar a wuce gona da iri".......... Batace komai ba sai ɗaukan tsohuwar ta ciro sim ɗin ta miqa masa da faɗin, " Haɗata a kirashi yanzu". ---------------------√ Duk da baiyi niyyar fita ba a lokacin saboda so yake anjima yaje gida yaga su Anah da jikin Dada amma halin da Nayrah ɗin take ciki a yan kwana biyun na damuwar abinda ya faru tsakanin ta da mahaifan ta ya sashi fito da ita night date. Zaune suke a wurin daga ita sai shi, wuri ne da ba kowa yake zuwa ba akasari manyan masu kuɗi ne ke zuwa su huta saboda waje ne me saurin comforting soul, atmosphere ɗin wurin is so relaxing, akwai sport center, akwai bangaren wurin cin abinci akwai cinema da sauran su, a yanzu ma fitowar su kenan daga wurin sport ɗin suka zauna aka kawo musu refreshments suna sha suna hira cikin nishaɗi. A waje Kuma wata shegiyar mota ce ta sako kai zata shige ciki, Amma sai aka tsareta tare da faɗin anyi reserving wurin gabaɗaya har sai Wanda ke ciki ya fito, sauke glass ɗin motar yayi tare da yafito Kamal dake tsaye can gefe jikin motocin nasu, da sauri Kamal ya taho ganin Awais ne me Kiran, yana ƙarasowa ba tare da Awais ya amsa gaisuwar sa ba ya ce, "Waye a cikin Nan?"........ Ɗan shafa Kai Kamal yayi kafin ya ce, " Boss ne da madam". Shuru yayi can Kuma ya ce "Kaje kace su buɗe min ƙofa, yayan wanda yake ciki ne"....... Ba musu Kamal ya wuce wurin securities da kuma sojojin nasu dan yasan halin Awais yanzu sai yaci mutuncin sa, ko da ya faɗa musu saida suka Kira Amjad suka sanar masa, murmushi yayi kawai tare da faɗin ba damuwa su barshi ya shigo. Buɗe masa akayi ya wuce can nesa ya yi parking cikin dan duhuwa, sannan ya juyo wurin yarinyar dake zaune a gefensa tare da faɗin, "Karki fito, mun fasa zaman a nan ɗin ma, bari kawai na je na gana dashi sai nazo mu tafi, qani na ne". "Okay". Da sauri na juyo jin muryar Hushaima, da gasken kuwa itace hakimce a passenger front seat na motar Awais. Buɗe ƙofar yayi ya fita, a hankali itama ta buɗe ta fito ta bi bayan sa dan sai taje taga qanin nasa da saboda yana ciki aka hanasu shiga sai kace wani shugaban ƙasa. Wajen ba haske sosai hakan yasa Awais bai san tana binsa a baya ba har suka kusa isa inda su Amjad suke, tasowa Amjad yayi wanda hakan yasa Hushaima saurin shigewa lungun dake hannun damanta, wurin Amjad yabi da kallo sannan ya miqawa Awais ɗin hannu yana faɗin, "Yau Kai kaɗai ka fito kenan?". Miqa masa hannun Shima Awais yayi suka gaisa ya amsa da, " Na gaji da yawo da driver ko wani escort ne, Kuma kasan Ina da damar na zagayawa ba tare da takura ba "......... ya faɗa cikin sigar shaguɓe. Murmushi yayi da faɗin, " Haka ne ". Ya ƙarashe yana satar kallon lungun da Hushaima ta shige Sannan ya ce, "ƙarasa ku gaisa da Nayrah bari nasa a kawo ma wani abu".......... Kamar zaice ah ah sai Kuma ya wuce table ɗin da Nayrah ɗin take . Ta kawo Kai da niyyar komawa mota dan taji abinda suka faɗa saboda saisa tayi ƙoƙarin barin wurin kafin ya zagayo ya ganta saidai ina ta makaro tana kawo kai shi Kuma yazo shigewa kallon kallo sukayi irin na cikin ido ɗin nan kowa da abinda ke cikin zuciya da kuma kwakwalwar sa............... *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 NE KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 51 & 52 Ta kawo Kai da niyyar komawa mota dan taji abinda suka faɗa Saisa tayi ƙoƙarin barin wurin kafin ya zagayo ya ganta saidai ina ta makaro tana kawo kai shi Kuma yazo shigewa kallon kallo sukayi irin na cikin ido ɗin nan kowa da abinda ke cikin zuciya da kwakwalwar sa, da sauri sauri ta wuce wurin motar tasu, bin bayanta yayi da kallo na wasu yan seconds sannan ya juya ya wuce ciki ya masa order refreshments ɗin da ya faɗa sannan ya koma inda ya bar su yana faɗin, "Amma Awais yau fitar nan ta musamman ce ko? Danni nayi zaton ko kai da hajiyar taka ne".......... ta ƙasan ido Awais ya maka masa Harara sannan ya ce, " Nothing special fa, kawai na ɗan fito na zagaya ne, yanzu ma tafiya zanyi banaso dare yayi min sosai". "Ko dai bakaso ta gaji da jiranka"............ Amjad ya faɗa yana ɗan Smirking tare da tsare shi da ido yana sipping mocktail drink ɗinsa da ya ɗauka akan table ɗin hankali kwance ya wani karkace kai yana binsa da wani kallon ƙasa ƙasa. Cikin alamun rashin gsky Awais da ya miqe ya ce, "Wa.... Wacece kuma, nace ma Ni kaɗai na fito k........." Saurin tareshi Amjad ɗin yayi da faɗin, "Calm down, Ni fa Hajiya nake nufi, kar ta gaji da jiranka baka koma gida da wuri ba ta kulle ma ƙofa". Ya ƙarashe cikin sigar zolaya yana wani tsuke baki tare da yiwa drink ɗin wata yar iskar zuqa. Kame kame Awais ya fara saboda yaso ya kwafsa, "To... to ai kai ne baka taɓa yi wa mutum magana kai tsaye "......... taɓe baki Amjad ɗin yayi daidai lokacin waiter ɗin ya ƙaraso. " To ai ka tsaya ka sha wani abu ko?"............ "Na sha in naje gida". Awais ɗin ya amsa yana barin wurin ba tare da ya ƙara kallon in da suke ba, da hannu Amjad ya yiwa waiter alamar yaje kawai, sake sipping mocktail drink ɗin yayi da dan dama a bakinsa sannan ya juya wurin Nayrah data tafi wata duniyar saboda maganganun da Awais ya faɗa mata a dunƙule wanda ta kasa warware su, straw ɗin da Amjad ya tsokala mata a kumatu ne ya dawo da ita duniyar mu, Ajiyar zuciya ta sauke tare da dawo da kallonta wurinsa. Bakinta ya nufa da straw ɗin hakan yasa ta ɗan buɗe ya shige, ɗayan bakin straw ɗin ya sanya a cikin nasa bakin sannan ya Fara transferring ɗin juice ɗin da ya guntsa zuwa bakinta through straw ɗin......... _______________Shi kuwa Awais yana shiga Mota ya samu Hushaima zaune tana game tayi baya da kujerar ta harɗe kafafunta ta ɗaura kan dashboard ɗin kamar motar ubanta. "Sorry na barki ke ɗaya ALLAH yasa zafi bai damar min ke ba?".......... Wani irin juya kwayar idanuwanta tayi sannan ta musu masauki a kansa kafin ta ce, "Eh kam ya takura min matuqa......." Take ya shiga bata haƙuri amma sai ta katseshi da faɗin, "Sa'a ɗaya yaci kawai dan baka kusa dani ne amma ko a kan tukubar tsire zan zauna in dai kana kusa dani to fa ba zanji komai ba face sassanyar iska me kaɗawa cike da begen ka".......... Wani irin murmushin jin daɗi Awais ya saki ba tare da ya shirya masa ba sannan ya tada motar yayi horn aka buɗe musu suka fice daga wurin. Sai wurin 12am Awais ya yi parking a bakin layin nasu saboda yana sauri ya koma gida dan in dai ba ƙaryar tafiya yayiwa matar sa ba baya kai wa kamar wannan lokacin a waje amma gashi yau Hushaima ta riqeshi har zuwa wannan lokacin ga kuma matar tasa tana ta kira ya kasa ɗagawa. Ɗan karkatowa yayi wurinta tare da faɗin, "To kwalisata sai yaushe kenan? ".......... Shuru tayi tana rolling wa'annan firgitattun idanun nata kamar me tunani, can kuma ta tsayar dasu wuri ɗaya ta kalleshi tare da faɗin, "Duk lokacin da kaji kana buqatar gani na, ni ɗin a ko yaushe a shirye nake da amsa kiranka"......... cikin jin daɗin kalaman ta ya ce, " To baki da matsala sai munyi waya kawai, ga wanna".......... Ya faɗa Yana miqa mata bundle biyu na 1k, karɓa tayi ta sanya a jaka sannan ta ce, "ALLAH ya Karo wanin su, Amma da ALLAH in tambaye ka mana".........."Eh to da inaga idan tambayar ba wai dole yanzu kike son amsar ta ba mu bari sai gobe mana, ko kuma muyi waya in naje gida". Ɗan girgiza kanta tayi da faɗin, "Alaji kana tsoron matar ka ne?". Saurin gyara zama yayi yana faɗin, "Wane ita, ita ɗin banza, Inajin ki ALLAH yasa na sani ". Ɗan taɓe baki tayi a sace sannan ta ce, "Wanna qanin naka ya kuke dashi ?". "Step brother na ne, shi ne autan mu a maza, Wani abun ne?"........... ɗan girgiza kanta tayi kana ta ce, " Bakomai kawai dai ina daga mota naga wani kallo ne da yake ma kamar dai......" Shuru tayi kuma yayin da Awais ya danyi wani gajeren murmushi sannan ya ce, "Ai baza ki gaza jin suna sa ba, Shi ne ake zargi da safarar mutane a ƙasashe da dama".......... wani iri tayi da fuska kamar wadda ta sha wani abu me ɗaci sai kuma ta yi saurin sakin fuskar tana wani tunani a ranta saboda ko da ace sunan kaka suka haɗa zaiji kunyar faɗar haka a waje amma sai taga har kamar Alfahri yake ma da faɗar. Jama'a wani abu dake birgeni game da Hushaima akwai zurfin tunani, a cikin seconds sittin kacal zata warware komai ta cilla shi ma'aunin sa, wato Baiwar ƙwaƙwalwa ba wai sai me ilimi ba kaɗai, wanda bai taɓa zaman aji ba ma sai kaga ALLAH ya bashi. Irin su Hushaima ne in suka samu masu tsaya musu sai kaga sun zama wasu kuma abun Alfahri a cikin al'umma da kuma duniya gabaɗaya. Katse tunanin nata tayi da faɗin, "Ohh ohkk Tabbas naji labarin, ance har yayi wa wata yarinya fyade ma suka Kai kotu yanzu haka ya ɓatar dasu ba'a san in da yarinyar da iyayenta suke ba"........... Da sauri ya ce, "Haka ne, gashi yana neman bata mana sunan gida, ko wanna sojojin da da kika gani hukuma ce ta sanya su dinga tsaronsa har sai an gama tattara bincike sannan suyi ram dashi a yanke masa hukunci daidai dashi". Zubawa Awais ido tayi har ya gama ɓatancin sa akan Amjad ɗin sannan ya ce, "To kwalisata idan har ita kenan tambayar ina iya tafiya?". Ya ƙarashe da sigar neman umarni. Gira ɗaya ta ɗage tare da kafaɗunta biyun sannan ta ce, "Me zai hana, Sai da safe, ALLAH ya tashemu lpy"......... ta ƙarashe tare da buɗe ƙofar motar ta fita tana ɗago masa hannu har yayi reverse ya bar layin sannan ta wuce gida tunanika fal ranta. Tana zuwa ta shige Dan dama ba'a rufe gidan da wuri. A ƙofar ɗakinta ta samu Sahnish tsaye sai faman danna waya yake a gaggauce da alama ita yake nema, yana ganin ta ya taho da sauri yana faɗin, "Hushaima daga Ina kika fito?". Tsayawa tayi tare da faɗin, "Sahnish ban gane daga Ina na fito ba tsaro na kake ko me?". "Haba Hushaima Kar zaman gidan nan ya rinjayi tunanin ki mana, ni nasan ba haka kike ba Amma wanna shi ne Karo na biyu da kike ƙoƙarin ɓoye Min wani Abu, Ranar Lahadi haka kika fita tun rana sai karfe tara na dare kika dawo, na tambaye ki, kikace min abokiyar aikin ki ce ta haihu, Hushaima! Na fa sanki fiye da yadda na san kai na ba abokiyar aiki ba ko ita me wurin taku ce ta haihu ba zuwa zakiyi ba amma na bar maganar ta wuce, yau kuma tun da akayi sallar magriba kikaci kwalliya Kika fita sai yanzu kike dawowa, ina kike zuwa?". "Na shiga uku ni Hushaima, to Sahnish kamani ka daka sai na fada ma kaji"..........Ta Ƙarashe tana wucewa ta buɗe ɗakinta ta shige ta bar Sahnish ɗin baki sake, cike da damuwa ya juya ya wuce ɗakin sa ya ɗauko Shazeen ya dawo mata da ita ɗakinta ya juya ya fice tana masa magana ma ko juyowa baiyi ba. Shi kuwa Amjad Bayan tafiyar su Awais da kamar 30 minutes ya ce da Nayrah ta tashi su wuce ya Kai ta gida akwai inda zashi, tashi tayi tana ɗan kumbura fuska jin cewa zai Kaita gida ya barta shi kuma ya sake fita maybe ma ba a gidan zai kwana ba kamar yadda yai musu lokacin da ya kawo su ita dasu Nashwa. Har suka je gida tana kumbure kumbure ko da aka buɗe mata ƙofar mota ma qin fita tayi ta juyo tana kallon sa ganin kamar hankalinsa ma yayi wani wuri ya sa ta riqo hannun sa tare da ɗan leqo fuskar sa, dawo da kallonsa yayi kanta tare da yi mata ɗan murmushi ya shafo gefen fuskarta da faɗin, " Ya akayi ne Madam ?"......... Zumɓuro ɗan bakinta tayi kafin ta ce, " Me ke damun ka ? Na lura tunda ya Awais ya tafi mood ɗin ka ya sauya". "Bakomai kawai dai zanyi missing ɗin ki ne, bana so nayi nesa dake ko na minti ɗaya my Ninie, ina buqatar Jin motsinki a kusa dani a ko da yaushe"......... Ya karashe yana jan fluffy kumatun ta. Ajiyar zuciya ta sauke maganganunsa na ratsa jikinta, a shagwabe ta ce, "To to ka fasa fitar mana, ka bari sai da safe, ni tsoro ma nake ji".......... Yana ƙoƙarin magana wayar sa tayi Ƙara alamar shigowar saqo, dubawa yayi yaga Philip ne hakan ya sashi faɗin, "Akwai aikin da dole a daren nan zan kammalashi, amma in na gama zaki ganni ko nan da jibi ne". "What next tomorrow fa ?". Ta faɗa a rikice. Cike da tabbatar wa ya amsa da. "Yes"....... A zuciyar sa kuwa yana matukar tausaya musu shi da ita, a matsayin su na sabbin aure da ko 1 month basu cika ba, ace basu samu damar kasancewa da juna ba ko da na tsawon sati biyu ne, saurin kawar da tunanin yayi saboda Kar hakan ya kawo masa nakaso a ayyukan sa sannan ya sake cewa, "Shiga gida sai na wuce, kinga an fara nema na". Bata ƙara ce masa komai ba ta sauka jiki a sanyaye, zagayowa tayi ta ɓangaren sa cikin dauriya ta kamo fuskar sa da hannuwanta duka biyun tana kallon cikin idon sa ta ce, " ALLAH ya Kare min Kai gaban ka da bayan ka, ya ma katanga daga duk wasu masu sharri". Ta ƙarashe tana me manna masa peck a both cheeks ɗin sa sannan ta juya ta shige ba tare data tsaya jiran amsar sa ba, da wani irin kasalallen murmushi ya bita har ta shige sannan ya basu umarnin tafiya. Direct family house ɗin su suka nufa, ko da aka Buɗe masa ƙofa bai fita ba saida ya gama waya da Philip sannan ya ziro da ƙafar sa ɗaya waje cikin nutsuwa ɗayar ma ta biyo baya sannan ya fito gabaɗayansa ya nufi Ƙofar part ɗin mahaifiyar sa, bayan ma'aikatan sun buɗe masa ya wuce ciki. A falo ya same ta tsaye tana duba agogo tana ganin shigowar sa ta sauke ajiyar zuciya dan dama saboda ya sanar Mata zai zo yau ɗin ne yasa ta ki kwanciya tun ɗazu dan tasan Amjad baya Alƙawari ya karya komin matsi in dai ya faɗa to ko yaya sai ya kwantanta shi. "Ya hakuri Dan ALLAH Anah na barki kina ta jira whl bansan zan Kai dare haka ba sai sa na faɗa miki gashi kuma kin hana kanki bacci kina jira na ". Murmushi tayi tana kallon Ɗan nata cike da so da ƙauna ta ce, "Yanzu ma na fito daga ɗaki ai, na manta ban faɗawa masu girkin nan abun da zasu girka da breakfast bane, Ya surukar tawa?" .........Ta faɗa tana ƙarasawa cikin falo ta zauna a ɗaya daga cikin expensive cushion ɗin dake falon, a gefen ta ya zauna tare da ɗaura kansa Kan kafaɗarta yana kallon fuskarta. "Um um Kai fa yanzu ba yaro bane karkazo Ka kassara min kafaɗu, kaje can kayiwa matar taka, ni yanzu na yaye ka, ace mutum sai san jiki da shagwaɓa kamar wani yaro ( ni kuwa nace ummu mu faɗa Miki waye Amjad a waje ko mu bari duniya ta sanar Miki). "Anahhhh please mana". Ya faɗa a shagwabe. "To naji gyara zaman ka muyi magana ".......... Ɗan zakuɗawa yayi amma bai tashi ba, pillow ta ɗauka ta buga masa aka tana faɗin, "Zauna daidai nace ma, haba cikin daren ma sai ka sani surutu"....... Tashi yayi gabaɗaya tare da sauka ƙasa ya tankwashe ƙafafuwan sa a gabanta Yana kallon ta, wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Anah ALLAH ya gani tana mutuwar son Amjad duk cikin ya'yan ta, ko dan Shi kaɗaine namiji. "Anah !"........... Ya Kiran sunan ta a tausashe ganin ta lula wata duniya . "Anah meysa kike sa damuwa sosai a ranki na faɗa miki in sha ALLAH babu abinda zai faru sai alheri, Amma in ina ganinki cikin damuwa to ni ma fa ba zan sami nutsuwa ba". "Dole na damu Amjad, bazan ɓoye ma ba kullum da Kai nake kwana a rai nake tashi, abin nan yana tsoratani matuka baka da laifi amma meysa za'a dinga jan wani bincike, an takuraka da yauwa Amjad baka da sakewa kamar na da, baka da sakewa a cikin Al ummar ƙasarka, kuma ance baka isa fita wata ƙasar ba, kana cikin gidan Ka ana tsaron Ka a ƙofar gida, wanna wace irin rayuwa ce". "Anah na Miki alqawari tunda bani da laifi duk daran daɗewa gaskiya zatayi halin ta, kuma ke kinsan da ace ina da laifi da tuni yanzu ba wanna zancen ake ba tunda magana ake ta duniya gabaɗaya kuma kinsan basa bincika abu sau biyu saboda cigaban su in ma mu nan suna ta jeka ka dawo ".......... Da wa'annan kamalan yayi amfani ya samu ya kwantar Mata da hankali sannan ya ce , "kotu fa ta sanya neman mutanan nan, saboda an zauna babu su ba wani tsayaye nasu, dama kuma can su ba lauya bane dasu". "Kasan ni ma lokacin nan saida nasa Juraysh ya min bincike a kansu amma ba wani labari game dasu an ce su gudu, to Amma Kai ya akayi kasan sun gudu tun a lokacin daka faɗamin, Anya Amjad baka san wani Abu a Kai ba kuwa?"........ Yar dariya yayi da faɗin, "Anah gsky kin fiya rigima kema yanzu har juraysh kika sa bincike, fisabilillahi me ya haɗa sojan ruwa da bincike, ko da ke barin yi shiru, amma dai ya akayi kuma bai binciko sun ba"............. "Kai Bana son wasan banza wai ni kakar Ka ce da zaka sani gaba da tsokana". Haɗa hannuwansa yayi wuri ɗaya alamar ban haƙuri sannan ya ce, "Ya hakuri Anah ta ba tsokanar ki nake ba, kawai dai ina mamaki na yadda kike sanya juraysh a aikin da yake nasa da wanda yake ba nasa ba. Amma Anah meysa kike tunanin ko inada masaniya a Kai, Anah whl ni ba ruwana kawai dai ina predicting abu ne tun kafin ya faru, nasan basu da hujjar da zasu bayar dama burin su su yaɗawa duniya ne to kuma sun yaɗa, kuma sunsan kotu zata Hukunta mutanen ne idan har ta kama su da laifin ƙarya da ƙazafi, whl Anah marar gaskiya ko a ruwa gumi yake ni nasan tabbas hakan ce zata faru kuma gashi hakan ne ya faru"........... Ita dai Anah kallon sa kawai take har ya gama bayanin sa sannan ta ce, "Ka dage da addu'a Amjad, ta ko ina Ka haɗa makiya da bansan me Ka tare musu a duniya ba, dan in a san ransu ne basu kaunar su buɗi ido su ga kana takawa a doron ƙasa. Abu na biyu Ka Kula da matar Ka Nayrah, dan ita ɗin amanar Ka ce, ban samu na kebance dakai ba ranar da Kuka zo amma inaso na faɗa ma duk rintsi duk wuya ka Kula da yarinyar nan, tayi ma halacci kuma itace irin matar da kowani namiji zai yiwa kansa fatan samu, a lokacin da kowa ke kyarar Ka ita kuma a lokacin ta nuna ma ƙauna, ta zaɓe Ka Wanda har hakan ya zama silar da iyayenta suka juya Mata baya, a yanzu Kai ne kaɗai hope ɗin ta, ina Mai Ƙara jaddada ma Ka Kula da ita"......... Muryar sa ce ta Ƙara yin sanyi akan ainahin yadda take, tunani ya shiga yi na yadda zai ainahin raba kansa biyu, yana cikin wanna tunanin maganarta ta dawo dashi, "Ka tashi kaje kaga dare yayi kuma Ka barta ita kaɗai, da ka sani ma ai ka bari sai da safe kazo ". ALLAH sarki Anah ita ta ɗauka gida zai koma, to bari dai na kame baki na kar Agent Amjad yaji ni. "To Anah Amma zan shiga naga Dada Dan inaso mu dan tattauna"..........Ya faɗa while a zuciyar sa kuwa cewa yake dole Ku min uzuri Anah. Ita kuwa Anah mamakin Amjad ɗin take yadda baya taɓa gajiya da tattaunawa da mahaifin nasa wanda shi tsakanin sa dashi ji ne kawai da ido, Amma sai ta ce, " Toh ALLAH ya tsare Ka gaida Nayrah ɗin in kaje". Ta faɗa tana miqewa, tashi yayi shi ma sai da ya rakata har ɗaki sannan ya Mata saida safe ya fito. ---------------------√ AURELLON SULTANATE💎 Cike makekiyar fadar take da duk wasu masu matsayi a masarautar tun daga Kan Mai martaba Sultan zuwa Kan hakiman North da south east da west wanda suka kasance ƙanne a wurinsa zuwa kan sauran yan uwan nasa, sai kuma su wazir, imam wato limamin fada, sai khaleep Wanda ya kasance kamar sarkin musulmin masarautar gabaɗaya, sai Amirul bahr wato kwamandan ruwa, sai Qadi Mai jagorantar shari'a a cikin masarautar, sannan Hajib Mai tsaron kofa kenan shi ne babban jami'in Sultan me kuma kula da shige da ficen mutane da kuma tsare tsaren fada, sai wali wato mai Kula da yankin masarautar, sai aminul Darb shi ku ma mai kula da dukiyar masarauta da muhimman hanyoyi na kasuwanci, sai katib wato sakatare kuma marubucin masarauta shi ke da alhakin rubuce rubuce na hukuma, wasiku da kuma dokoki da Adana bayanan gomnati, sannan Amirul jaysh wato commandan sojoji na masarautar, sai sheikhal balad shi ke da alhakin Samar da tsaro na gida da bin dokokin masarauta da kuma Kula da tsaftar masarautar, da dai sauran su dan idan nace zan tsaya lissafo dukka mutanan fadar nan to fa zamu shafe Babi biyu ba'a gama ba saboda suna da yawa sosai. Wazir ne yayi gyaran murya tare da gyara mic ɗin dake maqale a rigarsa domin sautin maganar sa ya isa ga dukkan mutanan fadar cikin harshen larabci ya fara magana, " Assalatu wassalamu ala Nabiyyul Kareem, Assalamu alaikum ya ayyuhal mu'minin, ina muku barka da halattar wanna taro na gaggawa da aka kira, kamar yadda Kuka sani a yan kwanakin da suka wuce Maleekh Reeslan ya fita da mutanan sa domin shaqatawa, sai kuma aka Kai masa farmakin bazata Wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu daga cikin mutanan mu".......... Dakatawa yayi kaɗan sannan ya cigaba, "To kamar yadda Kuka sani ne babu wanda zai mana hakan face mutanan SWORD OF FIRE KINGDOM, kuma hakan ce ta tabbata gashi nan kuji daga bakin waziril bahas (ministan bincike)". Gyara zama Babil yayi tare da buɗe takardun dake gaban sa sannan ya soma magana kamar haka. "kamar yadda muka tsaya tsayin daka muka tabbatar munyi sahinhin bincike tabbas mutanan sword of fire ne suka kai wa su Maleekh hari, kuma ba kowa bane ya jagoranci wannan harin bazatar face li'iliti Anoosha, domin ko da suka kashe mutanen mu saida sukabi sahun Maleekh ɗin domin su far masa shi ma, ALLAH Bai basu sa'a sun gan shi ba"..........Waziri ne ya ƙarɓa da faɗin, "Tabbas ya kamata ace abinda suka aikata bai tafi a banza ba, domin hakan na nufin har yanzu Queen Hirut fa tana Kan bakar ta ne, kuma tunda suka fara bi ta Kan Maleekh to tabbas gobe Sultan zasu hara". Take Yan surutai suka fara tashi cikin fadar, Gyaran murya Sultan yayi take fadar ta ɗau dumi kowa yayi tsit ana sauraren sa. Magana ya fara kamar haka, "Ni inaga a aika musu da wasiqa ta neman qarin bayani, dalili da kuma tuba, haɗe da neman gafara daga su zuwa wanna masarauta"............ " ALLAH ya taimaki Sultan ya Ƙara lpy, maganar Ka bata da ta biyu amma ni a tawa shawarar wanna harin da gangan suka Kai Shi, kuma wanna bashi bane na farko amma duk muna ɗaga musu ƙafa, nan gaba bamu san abinda zasu aikata gare mu ba ya Sultan, inaga kawai mu ma mu rama dan su san shuru shuru fa ba tsoro bane "......... Yana Kai nan yayi shuru. Qadi ne ya karɓi zancen da faɗin, " Wazir ni inaga abinda Sultan ya faɗa shi ya kamata a aikata, a fara aika masu da wasiqar tukunna raddin su shi zai bamu amsar hukuncin da zamu dauka ".......... Da wanna kowa yayi na'am sannan aka rufe taro da addu'a, kowa ya tashi ya koma kan aikinsa sai mutanan fada dake zama tare da Sultan. Fitowa Reeslan da Rouslan sukayi daga cikin fadar suna sanye da Kaya iri ɗaya haka gashin kansu da ya sha gyara sai ɗaukan ido yake ɗaure a bayan ƙeyar su sun saki jelar ta sauka har gadon bayansu. Rouslan ne ya ce, "Yanzu gashi Ka taso mu munfito idan Abbu ya neme mu fa?"......... Ya faɗa grey piercing eyes ɗin sa akan Reeslan ɗin. Taɓe Baki Reeslan yayi da faɗin, " Sai Ka koma ka zauna ai tunda ba riqe ka nayi ba, amma ni dai bazan iya wanna zaman jimamin ba, zuciyata zata iya tsayawa, ni yanzu ma Zanje naga Hirtik ne in zaka muje in baza Ka ba ka wuce muje in kaika gida". Ya ƙarashe idonsa na yawo akan wani bafade da yake kallon su ta ƙasan ido, da sauri ya kauda kansa ganin Reeslan ya tsaida idanunsa akansa saidai ya makara. "Kai zo"......... Ya fada sharply. Cikin faɗuwar gaban abinda zai faru Rouslan ya ce, " Kai da wa kuma ........." Saboda yadda yaji muryarsa ta sauya a lokaci guda. Saidai kafin ya rufe bakinsa ma Reeslan ya wuce wurin wanna bafaden da jikinsa ya fara ƙerma cikin faɗa faɗa ya ce, "Ƙasa"............ rikicewar da yayi yasa bai ma san Reeslan ɗin ya ƙaraso gabansa ba har sai da ya tsinkayo Maganar sa, jiki na rawa ya durƙusa tare da buɗe baki da niyyar bashi hakuri ya buga masa guiwar ƙafarsa a haɓa, ji kake gab hakwaransa sun haɗu da juna, Bai bari ya gama dawowa hayyacin sa ba ya kifa masa wani wawan mari, da sauri Rouslan da ya iso wurinsu ya riqe hannun kana ya ce, " Kayi hakuri mana Habiby, muje Please" .........." Rabu dani Rouh, kallon bakin mu yake muna magana saboda ya ji abinda zamu faɗa yayi munafurci to duk kar nake kallon ku". "Dan ALLAH Habiby ya isa, Muje kawai"..........."Whl bai isa ba, Ka bari in fidda masa hakora tukunna".......... Da yawan fadawan fadar suna kallo amma basu da damar ko ɗaga ido saboda kowa yasan tashin hankalin Reeslan. Akeem da yazo shiga fadar ya tarar da Reeslan na bala'i Rouslan na tausarsa ya sashi fitowa da sauri ya nufo wurin su, "Khali Rouslan meke faruwa ne?". Dawo da kallonsa yayi kan Akeem ɗin yana huci ya ce, "Ina ruwan Ka ne? Kai kuma sakeni tunda ba mahaukaci bane ni".......... Ya ƙarashe yana fisgewa daga riqon da Rouslan ya masa, tausa murya Akeem yayi kana ya ce, "ALLAH ya baka haƙuri khalee, dama wai dan naga ranka a ɓace ne shi ne na tambaya "..........Tsaki yaja kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya wuce inda motar su take. Ɗauke ido Rouslan yayi daga kansa bayan ya wuce tare da ɗan buga goshinsa kaɗan da hannu saboda kansa da ya ji ya wani mugun Sara masa, cikin ƙarfin hali ya ce, "Ƙar ka damu Akeem, wani abu ne ya ɓata masa rai, je ka kayi uzurin da ya kawo ka, bari na ƙarasa". "In sha ALLAH ni ma anjima zan shigo wurin ummu ai"........." Ba damuwa sai kazo"...... Rouslan ɗin ya faɗa ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake ba. Yana shiga motar Reeslan ya fisge ta kamar zai tashi sama. "Kar kace ban gaya ma ba amma kaga wannan shegen yaron Akeem daga shi har kakarsa ina tausayawa ranar da zan waiwayo su".......... Kallon sa Rouslan kawai yake kafin ya ce, "Kaiiiiii Habiby! Kakarsa fa uwa take a garemu saboda matar mahaifin mu ce, ka daina faɗar haka".......... Wani sharp look ya wurga masa na seconds kafin ya ɗauke kansa ya maida kan titi ba tare da ya sake cewa komai ba, shi kuma Rouslan ɗin ya cigaba da faɗin, "Bai kamata ace kana irin haka ba habiby, kai kenan ba wanda ya tsallake zagi ko zargi a wurinka kowa munafuki ne kowa ɗan iska ne, Ni gsky bana jin daɗin haka kuma Akeem ɗin nan, ɗan ka ne tunda ɗan babbar yayar ka ne".......... Ɗan jijjiga kansa yayi kafin ya ce, " Kaga Rouh, baka san komai ba kayi shiru kawai"............ " Ba wani abinda ban sani ba duk abinda ka sani na sanshi". Iska ya furzar daga bakinsa yana ɗan bugar kan steering motar ya ce, "Akwai ranar qin dillanci, Ranar da kowa zai san SIRRIN ƁOYE. Komai yana da rana ko da yake tana da jinkiri"............ Zuba masa idanu kawai yayi, yayinda shi kuwa ya maida hankali kan tuqinsa hankali kwance kamar bashi yayi maganar ba, jan bakinsa Rouslan yayi ya tsuke ganin maganganun na neman fin ƙarfin tunanin sa, sai kawai ya jingina kansa dake masa ciwo jikin headrest har suka ƙarasa gida. Sauka Rouslan yayi Lokacin da aka buɗe masu ƙofar tare da leqowa ta window ya ce, "Take care of yourself, Karka daɗe". Bai jira amsar sa ba ya yi saurin juyawa ya wuce saboda wani sarawa da kansa yayi ba kuma ya son Reeslan ɗin ya gane saboda zai iya fasa zuwa ganin farin cikin sa wato Hirtik. Da kallo yabi Rouslan ɗin har ya kusa shigewa part ɗin kawai ya buɗe motar ya fito, taku ɗaya biyu yayi ya cin masa dan Reeslan ba dai zafin nama ba, tsayawa Rouslan yayi tare da faɗin, "A'a ka fasa tafiyar ne ?". Bai bashi amsa ba sai shigewa ciki da yayi hakan yasa shi ma ya rufa masa baya cikin dauriya yake faɗin, "Magana fa nake ma"........... Ganin yadda hankalin hadimai ya dawo kansu inda suka fara zubewa suna miqa musu gaisuwa yasa Rouslan yin shuru tare da ɗaga musu hannu ya cigaba da bin Reeslan da ko arziƙin kallo basu samu daga wurin sa ba. A falo na biyu suka tarar da su Albeena da kuma su Hibba, step sisters ɗinsu. Sannu da zuwa suka musu, Rouslan ya amsa musu sama sama saboda ciwon kan dake damunsa, Albeena baki abun magana cikin zumuɗi ta ce, "Yauwa ya Reesla........" Bai barta ta ƙarasa ba ya katsa Mata wata tsawa, "Ke karki dameni kinji"........ ba ita kaɗai ba dukkan su saida suka sha jinin jikinsu. "Kai kuma wuce muje Ka huta"......... ya faɗa calmly kamar bashi yayi tsawa yanzu ba, duk da Rouslan ɗin bai faɗa masa ya gane cewa baya jin daɗi saboda duk motsin Rouslan, Reeslan na sane dashi haka shi ma Reeslan ɗin duk motsin Rouslan yana sane dashi ba dan karkuce wani abu ba da sai na iya cewa daidai da bugun zuciya ɗayansu in ta sauya suna ji a jikinsu. 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 53 Ko da ya wuce bangaren Dada, a ƙofar falon sa na ciki ya tsaya tare da yin knocking, daga ciki Hajiya Zunaira ta ce, " Waye ne cikin daren nan?"........... Ba tare da ya bata amsa ba ya sake knocking, "Waye wai?" ........... Ta sake tambaya still baiyi magana ba kuma bashi da niyyar yi ɗin sai ma agogon hannun sa da yake ta dubawa alamar a qage yake. Tasowa tayi ta leqa ta peephole, kasancewar falon ba haske sosai yasa bata gane shi bane dan ya sunkuyar da kansa ne yana duba wayarsa, a ɗan fusace ta buɗe ƙofar tana faɗin, " Wai wannan wani irin iska........" Maganarta ta katse saboda idonta da ya sauka akan Amjad da ya ƙarasa tura ƙofar baya ya shigo cikin wani low deep voice ya ce. "I'm ". Matsawa tayi baya kana ta ce, "Amjad kai ne kuma inata magana kayi shuru"........."Ni ne hajiya ai banason na ɗaga murya ne ban sani ba ko Dada yayi bacci ba daɗi a tashe Shi". "Haba Kai kuwa ko yayi bacci ai zaiyi farin ciki ga duk Wanda ya tashehi ya ganka, yau kusan kwana biyu kenan fa bai saka a ido ba, gsky Amjad ya kamata ace kana daurewa kana leqowa kullum duk da yanzu kayi aure ka ware kanka, amma Ka san mahaifin Ka fa ba Wanda ya fi shaquwa dashi kamarka, kaga ɗazu da aka gwada jininsa ya hau sosai whl". Cikin yar damuwa ya ce, "Amma Anah bata faɗamin ba"............."Eh to ai ba lalle ta gaya ma ba maybe bata so ta tada ma hankali ne, ko kuma itama ɗin bata sani ba tunda ba leqowa take ba idan mugun halin ya motsa. Wai saboda kwana na ne sai tace baza ta shigo ba, Yo mutumin ma da bashi da lpy har wani kwana za'a raba"........... Ta gefen ido ya kalle ta sarai yasan Hajiya zunaira na yar tsama da mahaifiyar su amma fa su duk ɗaya ne a wurin ta, dan bata nuna masu banbanci tsakanin su da su Julaybin ɗin data Haifa kawai dai ita matsalarta ta kishin da takeyi da mahaifiyar su ne, kuma a wurin ta hakan bai shafi yaran ba. Saidai tana sane da zazzafar ƙiyayyar dake tsakanin su Julaybin ɗin da su Amma ta nuna ita ba ruwan ta ba kuma abinda ya shafe ta bane, faɗa ne na yan uwa ita miye nata dan haka Ko su Julaybin ɗin zasu kashe su binne a gabanta baza ta ce musu ci Kanku ba kawai dai ita baza tace suyi ba ko su bari duk yadda sukayi can ta matse musu, haka kuma da ace shi kansa Amjad ɗin zaizo gabanta yayi zancen cewa su Julaybin ɗin sun masa kaza ko sai ya rama ko yace shi ma zai aikata musu wani abun, to fa ba zata ce masa kanzil ba in ya iya allon sa ya wanke. "Yanzu dai hajiya ki dubamin ko bacci yake" ............. "Haba Amjad Kai da mahaifin Ka ai ba mai ma iyaka dashi kaje Ka duba in idon sa biyu to, Dan ni tun dazu ina nan ina wani Abu ne ban shiga ɗakin ba da zan fito dai na barshi yana bacci"......... A Nutse ya ce, " To Hajiya in yana buqatar wani abu fa kinga ai ba yadda zaiyi ya Kira wani yace ya masa ko, ke kuma kina nan ai baki sani ba"......... Dan buga tsakiyar kanta tayi da hannu tana juyawa ta wuce cikin falon tana faɗin, " Abin ne ai da gajiya Amjad kuma ragon azanci nayi da ban tsaida Sufi ba tunda dama shi yake zama kusa dashi "..........Takaicin da ya kamashi shi ya hanashi magana, abinda Anah sa baza ta taɓa yi ba kenan, bata taɓa nuna gajiyawa da Dadan su ba tunda abun nan ya faru, dan haka baice komai ba ya wuce ɗakin, a hankali ya tura ƙofar ya shiga ɗakin so quiet bakajin komai sai ƙarar na'urar sanyaya ɗaki Wadda ta gauraya da room freshener take bada wani cool sanyi, a hankali ya taka zuwa gaban gadon sai a lokacin ya lura idon mahaifin nasa biyu zama yayi gefen sa fuskar sa na wanzar da wani murmushi Wanda ya fito daga can cikin zuciyar sa, dan Amjad bayan Anah ba wanda yake so sama da mahaifin sa saboda shi ne first friend ɗinsa a duniya, riqo hannun sa yayi cikin nasa kana ya ce, " Dada kaci abinci kuwa?"........ Da ido ya amsa masa da eh. "kanajin ƙishi?"......... Ya sake tambaya, nan ma da idon ya masa alamar ah ah . "To akwai abinda kake buqata?"......... alama ya masa da babu, numfashi ya sauke a hankali sannan ya ce, " Dada sirikar Ka na gaishe Ka, kuma Dada kasan me? na siyo ma ostrich daga US, suna nan ina maka kiwon su a gida na, amma akwai wani me faɗa a cikin su ni dai da nace kawai zan bayar dashi, sai yai ta bin Ninie da gudu ita kuma tsoron su take tayi ta ihu, rannan ina wanka Dada naji ihun ta na ɗauka wani Abu ne ya faru kawai ina fitowa na gansu har tsakiyar ɗaki ta dale Kan gado tana ta zunduma ihu".......... Dariya Dada yayi har saida hakwaran sa suka bayyana, Murmushi yayi shi ma cikin jin dadi ya sake damqe hannun Dadan cikin nasa ya ce, "Dada akwai wani abu da nake so Ka min addu'a akai ALLAH yasa nayi nasara".......... Da ido ya masa alamar zaiyi nasara kuma yana masa addu'a. Miqewa yayi tare da rungume Dada daga kwancen da yake yayi kissing ɗin hannunsu dake cikin na juna ya ce, " Zan tafi Dada bana so Ka dinga damuwa dan baka ganni ba akwai abubuwan da suka sakoni gaba da yawa Amma inaso Ka dinga Ji a ranka ina lpy matukar Kana min addu'a. Yanzu dai na kunna ma TV ko zakayi bacci?"......... Alama ya masa da zaiyi bacci dan dama yana cikin baccin yayi mafarkin Amjad ɗin shine farkawar da yayi, yanzu kuma da ya ganshi hankalin sa ya kwanta. Gyara masa kwanciya Amjad yayi sannan ya rage masa gudun AC ya juya ya fita zaune ya samu hajiya Zunaira ta kishingiɗa ta harde tana goga screen ɗin waya tana kora lemu alamar bata da wata damuwa, sallama ya Mata tace ya gaishe da Nayrah sannan ya fice. Yana fita direct gidan sa da su Philip suke ya nufa, Yana shiga ya tarar dasu Ashely gabaɗayansu wanda isowarsu kenan a Daren, bayan sun gaggaisa Ace ya ce, "Tun ɗazu muke jiranka ka shanya mu kana can kana tsinkar fure".......... Murmushin da bai yi niyya bane ya ƙwace masa ya ɗago yana kallon Philip dan yasan shi ya sanar musu, sunkuyar da kai Philip yayi yana ɗan shafa kai. Maganar Ace ta katse shi, cikin serious tone ya ce, "To yanzu dai kasan bamu da time ɗin da zamu ɓata, ya kamata ace munyi komai mun gama"............ Ƙarasawa yayi ya zauna yana ɗan satar kallon Widad ko nace Jey da ya hakimce sai wani taunar chewgum yake kamar mace, "Ya Ake ciki ? Fatan komai ya kammala?"........... Ashley ta ce , "Yes mutanen da suka buqata duk sun kammala, so yanzu miye next?"........... "Amm abinda za'ayi Next shi ne zamu tuntuɓe su, su faɗa mana inda za'a Kai mutanan da inda zamu karɓa cikon kuɗin anan ne zamu kafa musu tarkon farko"......... Sauqe ƙafar da ya ɗaura Kan ɗayar Widad yayi tare da faɗin, "Bafa tarko muke neman kafa musu ba, saboda Kai kasan da tarko ne da wancan mutumin BB LALO shi zamu kama, to amma ko mun kamashi bashi da wani info da zai bamu akan Shadow saboda shi ma bai san waye shi ba, abinda ya kamata shi ne tunda yanzu mun tsallake first step, bincike zamuyi na ganin taya Ake shigar da mutane garin ba tare da sanin gomnatin su ba, waye kuma wanda ya ke isar dasu ga shadow ɗin". Dukkansu sun bashi full attention nasu suna sauraron sa har ya gama sannan Kiara ta ce, "Yes binciken da ya kamata muyi kenan, yaso idan muka haɗa musu tarko da mutanan dake wurin mu, sai mu kama Wanda dama munsan bamu da haufi zai jagorance mu zuwa wurin shadow ɗin"........... Nisawa Amjad yayi yana me aminta da shawarar su dan yasan clique ɗin nasa duk zaqaƙurai ne kuma akwai sharp brain saisa baya da haufi a kan kowannen su, sai kawai ya ce, "Ina so kowa daga cikin mu yayi nasa binciken ya kuma samo wa'annan amsoshin within 24 hours"...........Tashi duk sukayi suka masu sallama wuce ɗakin su da already Philip ya nuna musu masaukin da aka gyara musu a cikin gidan, Dan kamar yadda kuka sani Ace da Ashely ba yan ƙasar bane aiki ne yake haɗasu, Ashley mutumiyar UK ce yayinda Ace kuma ya kasance mutumin Italy, Kiara kuwa tafiyar awanni ma a mota zata iya kaita garin su kawai dai tana bakin aiki ne. Falon ya rage daga Philip dake tsaye sai Widad da Amjad da duk suka tafi kurman tunani, can Amjad ya ɗago ya kalli Philip tare da tambayar. "Akwai wani abun ne?" . "Eh Boss batun yaron nan da aka kashe kamar yadda kace muyi bincike, wanda suka kasheshi suna da hannu a hatsarin da Madam ta samu, Amma ga file na bayanan da muka tattara". Ya fada Yana miqa masa, karɓa yayi ya duba sai da ya gama ya saki wani one side smiling da yafi kama dana takaici, ɗan jijjiga kansa yayi tare da biting lips ɗinsa sannan ya rufe file ɗin ya ajje gefen sa. "Sai me kuma?". Ya sake tambaya ba tare da ya bar wata alama ta halin da yake ciki ba akan fuskarsa. "Sai batun yarinyar nan Boss, ban samu wani bayani Kan ahalin ta ba domin duk wani bayani da za'aban saidai a bani akan su ukun, unfortunately babu info akan abinda ya shafi dangi ko mahaifanta, sannan kuma bata da haɗi da mahaifin madam haka kuma su Hajj zawaad kawai friend ɗin yar sa ce sai dai........." Ɗan shuru yayi yana murza maganar da zai faɗa a bakin sa, ƙureshi da idon da Amjad ɗin yayi ne ya sashi furta, " Sai dai akwai boyayyar alaqa tsakanin ta da Oga Awais"......... Slowly ya maida kansa jikin headrest ɗin tare da rufe idanun sa na wasu minutes hannun sa ya Kai fuskarsa ya shafa sannan ya Buɗe idanun, tunanin sa kenan yarinyar karuwa ce tunda shi kaɗai yasan waye Awais da kuma wanna boyayyar halayyar tasa ta neman Mata wadda yakeyi a boye to Amma.......... katse tunanin yayi tare da kallon Philip tin kafin yayi magana ya juya ya fice dawo da kallonsa yayi Kan Jey da hankalinsa ke kan wayar dake hannun sa ga ɗan bakin nan dake motsi cikin salo me jan hankali, takaici ne ya sake kumeshi dukda ƙoƙarin kauda kansa da yake sai da ya yi magana. "Haba mana widad ". Ɗagowa yayi Yana yin kwai da chew gum ɗin dake bakin sa cikin wani salo ya riqe Kwan da gefen baki kana ya ce. "Ya ne?". "Please Ka daina wanna abun mana ba daɗi, Kai ta chin chew gum sai kace karuwa "..........Ya faɗa Yana kallon Jey ɗin a yatsine kamar yaga wani abun kyankyami saboda a duniya in akwai abinda Amjad ya tsana bai wuce yaga anacin chew gum ba. Hannuwan sa biyu ya ɗaga tare da faɗin, "Is okay, yanzu akwai sauran wani Abu ne?"...........Sai da ya maka masa harara kafin ya ce, "Baka samu wani haske Kan mutumin naka ba ?".......... Yar nutsuwa yayi cikin wanna maqalalliyar murya tasa Mai kama da an masa dole ya ce, " Babu wani abu special a tare dashi saiii da........" Abinda ya faru na ranar da Hushaima ta hanashi karɓar kuɗi a hannun sa ne ya dawo masa to amma ya zaice da Amjad, taya zai sako Hushaima a aikin nasu bayan babu wanna tsarin infact sai ma Amjad ɗin ya raina shi yace zuwa yayi yana kula mata . "Sai dai me?" Amjad ɗin ya tambaya. "Zan sake bincikawa"..........." Shikenan ba damuwa, zaka tafi ne ko anan zaka kwana?"........ Girgiza kansa yayi alamar ah ah tare da miqewa ya ce, "zanzo da safe in sha ALLAH".........." ALLAH ya kaimu ". Amjad ya faɗa shi ma yana tarkata file ɗin ya ɗauka ya wuce ɗakinsa. ------------------√ Ko da ta tashi yau bata bi ta Kan Sahnish ba ta dai shiga da asuba kamar yadda ta saba ta tarar dashi yana sallah, tun daga nan bata sake bi ta kansa ba saida suka gama shirin su da Shazeen suka fito sannan ta wuce dan miqa masa abun Karin sa, saidai da mamakin ta ƙofar ɗakin nasa a rufe, Meenakshi ce ta ce, "Ai Sahnish ya kusa minti ashirin da barin gidan nan"......... takaici ya sata faɗin, "To yawa kansa bari na nemi almajiri na bashi"....... Da sauri Meenakshi ta ce, "Wani almajiri in dai ku bakwa da buqata kawoshi nan"......... Dama ba wani Abu bane Heinz beans ne da bread Wanda Awais ya Mata shopping ɗin su jiya sai tea data dafa ta haɗa masu dashi, miqa Mata tayi tare da faɗin, "In kin gama ki barmin kwanun a wurinki in na dawo zan karɓa". Daga haka taja hannun Shazeen suka fice. A makaranta ta ajjeta kamar yadda suka saba sannan ta wuce wurin aikin ta. Wuraren 11:30 am Awais ya kirata ɗauka tayi tana sakin murya bayan sun gaisa ya ce, "ki na gida ne?".......... "A'a ina wurin aiki". Ta bashi amsa Kai tsaye. Ɗan shuru yayi kafin ya ce , " wurin aikin da nisa ne? Ina ne? ".......... Yayi tambayar a haɗe, faɗa masa tayi ya ce, "To ai ina kusa da layin ma, ki fito ina son ganin Ki, ina layin da yake kallon inda kika tari abun hawa kusan magriba ranar da muka fara haɗuwa to layin zaki shigo ki ɗanyi tafiya kaɗan zaki ga motata pake, saboda nan ɗin kamar unguwata ce inada mutane sosai a wurin"......... Ba tare da wani tunani ba ta ce, "Okey, gani Nan".......... Ta faɗa kana ta kashe ta zaro powder dake jakarta ta sake shafawa, ta sake murza oil perfume a gaggauce ta maida kayan jaka ta fito, ta leqa domin ta sanarwa Hajiya zataje ta karɓo saqo ta dawo ta tarar bata nan reception ta wuce tare da faɗin, "Am Jumayma zan fita nan bakin layi na karɓo saqo ba nisa zan ba, na leqa na sanarwa hajiya kuma na tarar bata nan". A wulakance Jumayma ta ce, "Baki da ikon fita sai tazo ki tambayeta da kanki tunda ai bani na ɗauke ki aiki ba"........." Dake kurkuku na shigo? To sai na fita kuma na riga na sanar Miki tunda kince bake kika ɗaukeni aiki ba kinga Baki da ikon hana ni fita ai"......... Tana kai wa nan ta sa Kai tayi waje, kwafa Jumayma taja sannan ta cigaba da ayyukan ta tana shirya abinda zata faɗawa Hajiya idan ta riga Hushaima shigowa. A inda ya faɗa mata anan ta same shi wurin ba kowa saboda sabuwar unguwa ce yanzu ake gine gine a layin, buɗe Mata ƙofar baya yayi ta ɗayan side ɗin, tana zuwa ba ɓata lokaci ta shige tare da rufewa, fita zubairu yayi ya bar musu motar a kunne saboda AC wani gini ya shige saboda Kar ma mutane suzo wucewa su ganshi su fara cika duk da ba Awais ɗin suka gani ba amma sun san duk inda Awais yake to fa Zubairu yana nan, gashi kuma ya riga ya ɓata mutanan da raba musu kuɗi a duk lokacin da ya shigo. Wani Mayen kallo yake binta dashi har saida ta gaishe shi sau biyu baiji ba, haɗa yatsunta tayi a saitin fuskarsa suka bada sauti sai lokacin ya dawo nutsuwar sa, murmushi yayi da faɗin, "Gsky ke din me kyau ce Hushaima".........." Na Saba jin wannan ai Alaaaji na".......... Wani ƙayataccen murmushi ya saki saboda yadda zuciyar sa take wani yarr yarr a duk lokacin data kirashi da Alajin ta ɗin nan, gashi yadda take furtawa da wani irin salo. "A gsky naji daɗin yadda kikayi saurin bani matsayi a zuciyar ki".......... Wani farr tayi da idanuwan nan nata masu rikita bawa tare da faɗin, "Ko nayi gaggawa ne ?"......... Harda datse harshe wurin saurin amsa ta da, "Ina ina naji dai daɗin wanna matsayin a wurin kyakyawa, zinariya, ɗawisuya kamar ki, ".........." Kai Alaaaji wai sai kace yau Ka fara ganin me kyau, Ku ai kun saba Hulɗa da turawa, labarawa, Indiyawa to kuma wani kyau ne zai ruɗe Ku". "Kyau kyau ne Amma kyan Hushaima daban yake, zan so na mallaki wanna kyakyawar halittar cikin gida na ni kaɗai in dinga kalla ina jin daɗi"......... Ɗagowa tayi ta zuba masa idanuwan nan nata tana kallon cikin kwayar idonsa direct har cikin zuciyar sa wanda hakan yasa shi faɗin, "Kiyi hakuri ƙwalisata ki daina min irin wanna kallon dan baki san ya nake ji bane a duk lokacin da kika zubamin wa'annan idanuwan naki masu haske gabana har faɗuwa yake, a dinga tausaya min mana"......... ya ƙarashe yana ɗan kwantar da kai gefe, murmushi ta ɗanyi tare da ɗauke kanta ta rasa meysa mutane basa so ta ringa kallon su wanna shi ne Karo na ba adadi da ake faɗa mata haka, ba ga Matan ba ba ga Mazan ba ta rasa miye aibun idanunta. Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce, "Alaji muje Kai tsaye Kan abinda yasa Ka nemi mu haɗu bayan kuma jiya da daddare muka rabu, dan banyi tsammanin kiran ka ba a irin wannan lokacin". "To yanzu laifi ne dan na buqaci ganin masoyiya? Kuma dai ba wannan ba Magana ta gsky son ki nake Kuma ina so ne muyi aure, dan haka ki Bani dama na zanta da mahaifin ki"......... Kai tsaye ta ce, "Ban shirya aure ba". Wani ɓoyayyen murmushi ya saki dan dama ya san komai gami da ita kawai latsi ne irin nasu na yan duniya dan haka ya ce, "To yanzu ya kike so Ayi?"........."Duk yadda kace". Ta bashi amsa kai tsaye idanunta akan window tana bin layin da kallo. "Zaki iya amsa gayyata ta zuwa guest house ɗina yau da daddare?". "Yayi wuri da yawa dan har yanzu ba wai na gama sanin Ka bane gabaɗaya, dan ku sanannu ne ba hakan ke nuna baku da ɓoyayyen hali ba, na sani ma ko kana yankan Kai ne Ka kaini gidanka Ka ciremin ido ko wani sassa na jiki na ka kaiwa dodon tsafin ku"........ Dariya wawan yayi sosai saboda yadda tayi Magana tsakanin ta da ALLAH amma shi sai ta bashi dariya, dan haka ya ce, "Dama kina tsoro ?". "Ahh Alaji rayuwar nan fa ɗaya ce, kuma daga ita sai mutuwa, sannan ba'a mutuwa a dawo, tsoro akwai inda yake da kyau akwai inda bashi da kyau, kamar yadda Ka faɗa hasashen Ka gsky ne bani da tsoro, amma a inda nasan zan iya kare kai na, ba wai kawai dan na yarda da kai na bazan yi waiwaye ba in ina tafiya". Jinjina Kai yayi a lokacin data gama maganar sannan ya ce, "Amma meysa kika ce haka ?"......... kai tsaye ta ce, "Baka sauraren labarai ne, ai yanzu abinda ke faruwa kenan saboda da kunga shukar da babu Mai ita sai Ku ta Mata ban ruwa daga ta girma Ku fisge ta tun daga jijiyar". "Hmmm!, a gsky bana daga cikin su Hushaima, dan ni duk kuɗaɗe na na halal ne ". " Ba damuwa, zamuyi waya zuwa dare, zan koma bakin aiki na".......... Idon sa a kanta ya ce, "Aiki fa ba naki bane kwalisa, kamata yayi ace kina gida kina hutawa saidai kawai ki dinga jin alert, ke ai ba kalar wahala bace, ni duk abinda kike so zan baki kuma zan miki daga kan naira miliyan ɗai ɗai ɗai har ɗari ba matsala ta bace in dai zan samu haɗin kai daga gare ki". Girgiza masa Kai tayi cikin halin ko in kula da jin maqudan kuɗaɗen da ya ambata ta ce, "Ba haka nake ba, aiki na shi ne dahir ɗi na, Kai naka na ɗan lokaci ne, daga Ka samu abinda kake so zaka ɗage a lokacin wa kake so na Nemo ya bani, ni bana matsawa komai zanyi amfani da nawa idan Ƙari ya samu in Ƙara, tunda ko teku bata ƙin ƙari amma dogaro da abun wani ba na Hushaima bane".......... Tana Kai nan ta fara ƙoƙarin fita, kuɗi ya zaro masu yawa ya sauke Mata Kan cinyarta, ɗauka kawai tayi ta zura a jaka ta fice ba tare data sake ce dashi uffan ba. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥              _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐                *SULTYWRITES*                          A-K-A                [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._    @wattpadd sultywrites22            STEP 1 PAGE _______54 & 55 Da Harara Jumayma ta bita a lokacin da ta shigo, wata yar budurwa ce ta fito daga manicure section baza ta haura 16 years ba, waya ce maqale a kunnenta sai sauri take, kallo ɗaya zaka mata ka san daga gidan Naira ta fito tun daga kan yanayin shigar ta zuwa takun da take, ba tare data lura da Hushaima dake tahowa ba suka mangaji juna, kafin Hushaiman ta gama tantance yarinyar data mangajeta taji saukar wani mari a kumatun ta kamar daga sama, a fusace yarinyar ta fara masifa, " Ke wace irin jaka ce dabba da bata ganin gabanta, kin shigo kina wani kalle kalle zaki goga min wannan ƙazamin jikin naki me warin talauci, are you insane nace are you insane ? Stop looking at me with those bastard eyes of yours, wawiya kawai". Wani irin tafasa Hushaima take kamar zata kama da wuta tunda take a duniya ba wanda ya taɓa yi mata cin mutuncin da wannan yarinyar da ko Sahnish ya girme ta tayi ba. Ai bata san lokacin da hannunta yakai kan kwalbar wani hair oil dake Kan kanta ɗin reception ɗin ba sai ji kake tartsatsa ta rotsawa yarinyar nan a tsakiyar kai, wani irin ihu yarinyar ta kurma tare da zubewa ƙasa tana juyi hannayenta riqe da kanta, take jini ya fara malala dan kwalbar saida ta fashe a irin dukan da Hushaima ta Mata da ita, amma duk da haka bata haƙura ba sunkuyawa tayi kan yarinyar tare da faɗin, "Idan wannan shi ne tarbiyyar da aka baki, kuma kin saba yiwa mutane suna kyale ki saboda kina yar masu kuɗi, to ni baza ki min na kyale ba wannan iya marin fuska ne na rama amma ki kwana da sani duk maganganun da kika faɗa whl sai kinyi danasanin yin su, sai kin durqusa gaba na kina roqo n........" Kafaɗar ta da aka riqo ne ya katse ta, ba tare data san waye bane tana ɗagowa ta sauke mata mari. Riqe baki duk ma'aikatan da ihun yarinyar ya fito dasu sukayi ciki harda Hajiya data ɗaura hannunta aka dan tasan Hushaima ta jiqa mata aiki, ita kaɗai tasan wacece Hajiya sulaimiyya da ƴarta Huda amma gashi Hushaima ta fasawa yar kai kuma ta mari uwar. Ai hajiya sulaimiyya batabi ta kan marin ba tsabar gigicewa da tayi, kan ƴar ta ta nufa tana kiran sunan ta ganin kamar ta suma ga jini na zuba kamar an yanka ƙaramar dabba. Juyawa Hushaima tayi tana ƙoƙarin fita Hajiya sulaimiyya ta ce, "Karku barta ta fita, Ku taimaka ku kama min yarinya ta mu Kaita asibiti karta mutu, na shiga uku na"......... Ta faɗa cikin tsantsar tashin hankali. Su Jumayma ne suka taimaka aka kai Huda Mota sannan suka dawo ciki suka haɗa kofa suka kulle. Ita kuwa Hushaima tunda taji furucin hajiya Sulaimiyya dama bata wahalar da kanta ba ta koma ta zauna tana huci wai yau itace wannan banzar figaggiyar yarinyar zata mara, to ai ko a namijin ma sai ya jira whl, Amjad ne kawai mutumin da ya ƙetara iyakar ta bata ɗau mataki a lokacin ba, amma zuciyarta ta hanata sukuni ta sanya take ta kai kawo ta ɓata lokacin ta da energy ɗin ta akan sa dan kawai ta samu hanyar ɗaukan fansa. Ƙwafa taja kawai, tana kallo suka ciccibeta sukayi waje, suka dawo suka tsare ƙofa, cikin tashin hankali Hajiya ta dawo ciki bayan su Hajiya sulaimaniya sun tafi, a rikice yake faɗin, "Hushaima ashe haka kake, da tana ɗaukan ka mutumiyar kirki me hankali, gaskiyan hausawa da suka ce tsintacciyar mage bata mage, amma nasan da kisan waye ne wannan matar da kika mara kika kuma fasawa ƴar ta kai da baka aikata ba, dan zata iya rufe wurin nan a cikin hour guda idan taga dama kuma whl ka shirya dan ta kira hukuma ni kuma ba ruwana".  Wato yadda kukasan da dutse take dan idan bangon reception ɗin nan ya amsa to Hushaima ma tayi magana, ko ma ɗaga kai batayi ba ta kalle ta tunda ta zubawa wani wuri ido ko kiftawa batayi sai kaɗa ƙafa take kamar goɗiya. Haka Hajiya ta gama bambaminta taja gefe ta tsaya dan tasan idan har ta sake Hushaima ta bar wurin nan to kashin ta ya bushe wurin hajiya Sulaimiyya, dan ita zata rufe a matsayin Hushaiman har sai ta fito da ita alhalin ita yanzu ko lahira za'a Kaita batasan daga ina Hushaiman take ba. Suna a tsaitsayen kamar sojojin haya har polisawan suka ƙaraso, ba musu Hushaima ta tashi ta bi su suka fita, saidai ganin inda suke neman sata ya sa taja baya da faɗin, "Whl bazan hau bayan mota ba"......... Katsa Mata tsawa ɗaya daga cikin su yayi da faɗin, "Kina me laifi har kina da zabin inda zaki shiga, common get in jare". "Whl ba zan shiga nan ba kuma ai laifi bani kaɗai bace me laifi ita ta fara nema na da bala'i"........ Ɗan sandan ne ya kalli Wadda ta kasance mace a cikin su kana ya ce, "Monica get her in"........... Da sauri Wadda aka Kira da Monica ta riqo keyar Hushaima da nufin ta turata ciki aikuwa ta make hannunta da faɗin, "karki Ƙara taɓani karkiga kina yar doka whl sai na iya tsinka miki mari". "Ohh really so are you threatening me ? Lalle baki san hukuma ba, ni zaki mara?"..........Tsaki Hushaima ta ja tare da tura mata keya ta ce, "ko titin ƙarshen duniya zamu muje ni dai kawai ba zan shiga baya ba Yauwa"........ Kan bindiga ɗaya dan sanda ya kafa mata da faɗin, "Zaki shiga ko sai na tarwatsa ƙwaƙwalwar ki anan"......... Kallon sama da ƙasa tai masa kafin ta ce, "Dan ALLAH karka fasa, dani da ku marabar mu uniform ne kawai dan yadda kuka saida ranku kunawa ƙasa aiki, nima haka na saida raina nakewa rayuwata aiki dan haka karka fasa harbawa, ga me fili ga me doki, ka harba mu gani in hukunci bai hau kanka ba kai ma". Duk yadda aka Kaɗa aka raya Hushaima ta kafa ta tsare baza ta shiga baya ba, anyi ta barazanar anyi ta ƙarfin amma daga inda ta tsaya bata motsa ba, haka dole suka haƙura ta shiga cikin motar sannan suka wuce da ita. ---------------------√            SWORD OF FIRE KINGDOM 🔥 Masarauta ce ta jajirtattun Mata domin Kai tsaye zamu iyacewa feminist kingdom ce, Saboda Matan su suna da power da freedom fiye da mazan, domin su suna ɗaukan mazan su ne matsayin bayin su, kwata kwata maza basu da yan'ci a wannan masarautar suna rayuwa ne Matsayin bayi kuma ƙasƙantattu. Su ɗin sun kasance masu bautar rana ne, kuma a tsarin mulkin sarautar su ƙani ko ƙanwar sarauniya bazai iya gadar mulki ba dole sai dai ɗan wanna me mulkin, gashi duk masu mulkin sunfi haifar mata hakan yasa su suke ta hawa da sauka akan wanna kujera. Sun ƙware sosai a fannin Archery, art da agriculture, sannan sun iya sword fighting sosai dan training me ƙarfi akewa kowani yaro ko yarinyar da ya taso a masarautar tun suna ƙanana sai sa duk ƙanƙantar yaro zakaga yana wasa da sword kamar me. Suna da arziki sosai amma fa basu ko taɓo ƙafar Aurellon ba amma kuma saboda ƙarfin zuciya irin tasu a haka suke ja da Aurellon ɗin. A bangaren tsarin gini kuwa qaton castle ne matuƙar girma da kyau, a cikinsa akwai ƙofofi da bangarori da dama dan har palace ɗin a cikinsa yake, haka ta bayan castle ɗin ma wasu parts parts ne da aka ware na ma'aikatan masarautar maza. Abinda ya jawo rikici tsakanin su da Aurellon ba komai bane face yankin su da Aurellon ta kafa masarautar ta akai domin ainahin mahaifin Queen Alitash 1 wato Nujum Samrah shi ya zauna a wannan yanki da iyalansa mafarauci ne sosai, saidai dare ɗaya aka tashi aka samu gawarsu shi da matar sa, ƙanwarsa da kuma mahaifinsa, sai ƴar'su guda daya da ba'a ganta ba, bayan wucewar wanna al'amari ne aka kafa Aurellon, sai kuma aka samu labarin bayyanar Yar tasu mai suna Alitash saidai ko da ta dawo tayi ƙoƙarin amsar yankin mahaifin nata amma hakan ya gagara, wannan dalili yasa ta tafi ta kafa ta ta masarautar itama tun ba'a farga ba har sunan masarautar ta ta ya fara yaɗuwa a wannan lokacin ne ta fara qalubalantar Aurellon, wannan shine asalin rikicin su da har yanzu yaqi ƙarewa duk wani jinin Queen Alitash da ya hau ɗorawa yake daga inda aka tsaya.  WANNAN KENAN!. Wani sassaqaqqen dutse ne da aka sassaqa a suffar mutane zaune akan wata sassaqaqqiyar kujera dake ƙofar wani kogon dutse riqe da wata sanda da suke kira da sandar doka sai wani qaton zobe da suke kira da zoben adalci. Babban fili ne a ta gabansa wanda ke cike da duk mutanan dake rayuwa a masarautar ciki harda Queen Hirut, dukkanin su sanye suke da fararen kaya qal idanunsu duk a rufe, kowannensu riqe da wani kasko da suke jefa wasu itatuwa a ciki hayaqi na tashi. Wata wadda ga dukkan alamu itace malamar tasu tana tsaye gaban wannan sassaqaqqen gunkin riqe da nata kaskon idanunta a rufe, gefenta kuma wani mutum ne durƙushe gaban wannan dutse, baqin ƙirin dashi gashi dan siriri kamar aljani, matar ce ta fara magana. " Ya kurangina, ya hasken duniya, ya babban Alkali ka bayyana mana adalci a yau, kamar yadda kake bayyana kowane lungu da sako na ƙasa (Astagfirullah)".......... tana yi tana baza hayaqin da hannunta, haka ta cigaba da yan surkullen su cikin harshen amharians, tsawon lokaci suna a haka har sai da rana ta daidaita a sararin samaniya sannan duk suka buɗe idanuwansu. Tashi wannan mutumin yayi ya ɗauki wani qoqo dake cike da wani ruwa a gefensa itama matar ajje nata kaskon tayi ta ɗauki qoqon dake gefenta sannan suka matsa wurin su Queen shi da ita,  ɗaya bayan ɗaya suka fara binsu suna yayyafa musu wannan ruwan har suka gama sannan duk suka durƙusawa kurangina, daga nan kuma suka tafi raka Queen Hirut faɗarta sannan kowa ya tafi yin ayyukan gabansa. Wannan shi ne bautar da sukeyi a kowacce safiya idan rana zata fito haka in zata faɗi zasu fito ne su tsaitsaya a gaban kurangina suna wasu surkullen su har sai rana ta faɗi. _________Qaton yanki ne dake ƙarshen iyakar masarautar wanda aka ware domin yin noma kawai. Ɗaya daga cikin mutanan dake yin kunya ne ya taɓo ɗan uwansa yana nuna masa dawakan da suka tsaya daga bakin iyakar masarautar tasu. A daidai lokacin ɗaya daga cikin mutanan dake kan dokin ya ɗaga wani abun busa me matuƙar kyau da kyalli ya kai bakinsa tare da jan wata doguwar busa tsawon seconds 120 ba tare da yaja numfashi ba, kusan duk wanda ke cikin masarautar ba wanda bai saki abinda yakeyi ba domin hakan alama ce dake nuna anyi baqi daga Aurellon ko kuma sun kawo saqo. Sakin abinda sukeyi sukayi tare da nufar wurin mutanan dake kan dawakan, kafin ma suyi magana suka miqa musu takardar da suka zo da ita tare da juya akalar dawakan su suka tashi Ƙura sannan suka rufa a guje suka bar wurin. Kallon Ɗan uwan nasa yayi da fadin, "Dawit wanna fa inaga saqon Queen Hirut ne".......... "Kuma kaga ya kamata muyi gaggawar isar dashi gareta dan bamu san me ya ƙunsa ba tunda daga Aurellon ne"........ Ya ƙarashe yana kallon tambarin eagle dake jikin takardar domin tambarin eagle shi ne alamar Aurellon a duk faɗin duniya . "Muje muyi sauri in mun dawo ma ƙarasa"....... Dawit ya faɗa yana cilla fartanyar sa a inda yake haqa kunyar sannan suka tafi da gudu dan isar wa da sarauniya saqon ta. Ko da suka ƙarasa wani dogari ne ya tare su tun kafin suyi magana ya ce, "Ina saqon?"........ Miqa masa sukayi ya juya ya shige cikin fadar ba tare da yace dasu komai ba. Wow zo kuga qawa ta ainahin gargajiya da zamani domin fadar Queen Hirut ba wai an ƙawata ta bane da iyakacin abubuwan zamani ah ah harda na gargajiya, kama daga kan zane zanen dake bangon zuwa kan furnitures da sauransu.  Kaso 60 na mutanan fadar mata ne kaso 40 ne kawai suka kasance maza, ta kowani Angle kuwa dogare ne riqe da sword sai kyalli yake. Daga mazan har matan Babu Wanda zaka iya cewa ga kyallin hakoransa a waje gwara su mazan gasu nan ga kamar su ne, suna zaune a ƙasa kamar wasu almajira alamar ba jin dadin yanayin suke ba kawai dai a rashin zabi ne suke nan. Ga kuma wasu murtika murtikan Siberian tigers dake ta shawagin su cikin fadar kamar a daji. A tsakiyar fadar wanna dogarin ya zube tare da fara zubawa Queen dake hakimce kan wata iriyar ƙayatacciya kujera dake a saman stage ɗin fadar, both sides ɗin ta ma Siberian tigers ɗin ne kwance sai lashe baki suke suna bin kowa da kallo. Tana sanye da cersei gold dress saidai ita tata an ƙerata ne da fatar dawisu, kanta ba komai sai silky golden yellow hair ɗin ta da ya zubo kan kafaɗunta ta ɗaura wata crown hat akai, ba fara bace can haka zalika ba baƙa bace za'a iya kiran skin dinta da golden yellow, ga dogon hanci kamar su suka zana kayansu haka dan bakin nan tsit kamar cokali ba zai shiga ba ga idanuwa tubarkalla, dattijuwa ce dan zata iya kai shekaru 52 - 53 haka, amma kyawun jiki da kuma daular mulki da arziki ya sanya sai kayi tunanin baza ta fi 40 ba. Bayan ya gama mata kirari ya ce, "Saqo ne daga Aurellon"......... Ɗaya daga cikin mazan dake zaune ne, wani dattijo ya yunqura ya karɓa takardar sannan yace da dogarin yana iya tafiya, Saida yayi godia sannan ya tashi ya fita. Wata matashiyar budurwa ce hakimce a wata ƙayatacciyar kujera da zan iya cewa daga ta Queen Hirut sai tata a kyawu, baza ta haura shekaru 28 ba a duniya, kalar skin ɗinta irin na Queen, tana sanye da Medieval Dress me Corset Belt da Wide Sleeves red and gold. "Me kake jira ne Abal (baba) karanta mana".........Ta faɗi hakan a tsaurare ba wani alamun tausasawa ga mahaifin nata . Gyara zama yayi sannan ya warware Scrolls paper ɗin dake nannade. Da turanci suka rubuta letter ɗin saboda sun san su basajin yaren su na Arabic. " From his majesty sultan Abdulbasit Abdul Aziz. AURELLON SULTANATE. To honourable council of sword of fire kingdom, the Queen Hirut." "We have received irrefutable reports that your daughter Anoosha and her agent conspired to murder crown prince Reeslan Maleekh, our heir and that the prince personal guard was brutally slaughtered in the act. Such treachery strikes at the very heart of our dynasty and cannot be tolerated. So you are here by warned to surrender all conspirators involved in the plot within ten days and offer a formal apology and suitable reparation for the loss of the prince's protectors failure to comply will compel us to take all necessary measures to avenge our blood and protect our succession and the peace between our realms will be irrevocably broken. We pray this matter can be resolved without further bloodshed and await your swift response." " SULTAN ABDULBASIT ABDULAZIZ, the king of Aurellon sultanate"......... Sai stamp ɗin eagle da suka buga a kan sunan. A fusace yarinyar ta miqe cikin yaren amharians ta ce, "What!!!!! Inati kinaji fa, kamar ma barazana suke mana, a yaushe ma akayi hakan, Ina ita Anooshan take ma? Kawai dan sunga kwana biyu mun saurara musu, bafa zasu mamaye mana wuri ba sannan ace za'a ɗinga nuna mana iko kuma. Inati ya kamata mu nuna musu har yanzu fa muna nan ba abinda ya sauya"........ Take aka fara bata baki ana mata kirari Matsayin ta na babbar Ya' a wurin Queen Hirut Kuma magajiyar Crown ɗin sword of fire kingdom, kasancewar Queen Hirut ya'yanta biyu ne kawai a duniya Azal itace babba sai Anoosha. "Kai Azeeb maza ɗauko kayan rubutu ka maida musu raddi". Cikin wata ƙasaitacciyar murya dake nuna Mai ita yana ji da iko da Kuma izzar mulki Queen Hirut ta ce, "Za'a tura musu amma ba yanzu ba, domin yanzu in aka tura musu sunyi nasara a kan mu kenan in har dama sunyi hakan dan su tabomu ne,  Amma shurun mu shi zai fi firgita su ya Kuma sasu a cikin fargabar rashin sanin menene shirin mu, Dan haka zamu tsahirta da maida musu raddi har zuwa kwana biyu ba dai kwana goma suka ce sun bayar ba to barsu"......... Jijjiga Kai Azal tayi alamar ta gamsu da maganar mahaifiyarta ta sannan ta juya ta nufi hanyar barin fadar saboda ranta ya baci sosai baza ta iya cigaba da zama ba, dan a ganinta hakan rainin hankali ne da zubda qima a wurin su, Siberian tiger ɗin ta guda ɗaya ta rufa mata baya suka fice daga fadar. ----------------------√                 WIDAD (JEY) A Daren nan yana fita Bai tsaya ko Ina ba sai gida sau ɗaya yayi horn wani security ya leqo ganin motar sa yasa ya wangale masa gate ɗin, da hannu ɗaya ya murza steering motar ya shige ciki gabaɗaya tukin ma yanayin sa ne a kasalance kamar bayaso, dan kamar yadda yake motsa steering wheel ɗin da hannu ɗaya haka ma da kafa ɗaya yake amfani wurin break da clutch dan ɗayar ma tuni ya naɗeta akan seat. Saida yayi parking jikin jerin jibga jibgan motocin dake parking lot ɗin sannan ya buɗe motar ya fito a hankali, gyara zaman rigar dake jikinsa yayi sannan ya doshi building ɗin gidan nasu cikin takun nan nasa na yanga. Key ya zaro a aljihun sa ya buɗe ƙofar ya shige, duhu ne ya mamaye ganinsa dan duk an kashe wutar falon alamun mutanen gidan sun kwanta. Amfani yayi da hasken screen ɗin wayarsa don ganin hanya, direct upstairs ya nufa, tun daga kan stairs yake jin kukanta hakan ya sashi ƙara ɗan sauri, yana zuwa ƙofar ɗakin ba tare da yayi knocking ba yasa hannu ya murda handle ɗin ƙofar ya shiga. Wata budurwar yarinya na hango zaune bakin gadon kwata kwata baza ta wuce 17 years ba tana sanye da silky pj's silver colour, hawaye ne ke zuba akan fuskarta tasa wata baby da baza ta wuce shekaru uku ba a duniya, kuka yarinyar take shaɓe shaɓe da hawaye, kyakyawar gaske ce dan kallo ɗaya zaka mata ka hango tsananin kamannin ta da Widad har ma ta ɗarashi a kyau dan ita farace sosai kumatun ta har wani ja ja yake. Tana ganinsa ta fara miqa masa hannu tana Kiran baba tare da ƙoƙarin sauka, ƙarasawa yayi yasa hannu ɗaya ya ɗauketa ya sabata a kafaɗar sa tare da kallon budurwar ya ce, "Me haka Najmah, dama in tana kuka haka kike sata gaba kina kallo, baza ki iya lallashin ta bane ko bakisan in Kukan ya mata yawa zai iya sata ciwon ciki ba, ina ma wancan lalatacciyar take?"........ Magana yake a fusace cikin faɗa Amma muryar sa sam ba hayaniya ko kaɗan. "Ni ya Jey na rasa ya zan mata ne ina ɗaki ina bacci na jiyo kukan ta, shi ne nazo na dubata kuma tun ɗazu nake lallashinta taqiyin shiru".........."To meysa baza ki tafi da ita ɗakin ku ba". "Ya Jey kasan halin ya Azhar, yanzu sai tace munzo mun hanata bacci da hayaniya".......... "Okay good yayi kyau"..........Ya faɗa tare da juyawa ya fita, ƙasa ya sauka inda ɗakin sa yake, ko da ya duba har ta koma bacci dan haka ya shinfiɗe ta saman gadon sa sannan ya rage kayan jikinsa ya shige wanka. Bai jima ba ya fito kugunsa daure da towel Ash colour sai wani ƙarami dake hannun sa yana goge wuyansa dashi, da alama wanka yayi. Gaban mirror ya nufa ya ɗanyi shafa sama sama sannan ya wuce ya zaro PJ's ɗin da zaisa. Sai da ya gama shiryawa sannan ya haye kan gadon tare da ɗauko wayarsa ya shiga dubawa saboda tsawon lokaci bai samu wannan damar ba kasancewar in yana kan aiki ajje duk wani personal abu nasa yake, WhatsApp ya fara shiga messages ne rututu, wata number da akayi saving da emojin heartbreak ya tsurawa ido kafin can kuma ya buɗe message ɗin, video ne aka Turo masa hakan ya sashi rage volume saboda kar ƙaran ya tashi yarinyar sannan yayi playing, lokacin da ya gama kallo gabaɗaya yanayin sa ya sauya tsananin ɓacin rai ya bayyana a fuskarsa in banda huci ba abinda yakeyi, cilla wayar yayi gefe tare da ɗaga kansa sama, Adam apple ɗin sa sai sama da ƙasa yake, wani Murmushin takaici yayi kafin ya dawo da kallonsa kan babyn dake kwance a gefensa a hankali yakai hannu kan lallausan gashin babyn yana shafawa, Ji yake inama zai iya dawo da hannun agogo baya, inama ina ma, ganin tunanin sa zai karkata wani wurin ya sashi tashi ya fice parlour tare da zama ya kunna TV duk dan ya ɗaukewa kansa wancan tunanin dan yasan ko yace zaiyi bacci ma bazai taɓa iyawa ba a wannan yanayin. -------------------------√                  AMJAD Kwata kwata ranar bai samu bacci ba yadda yaga dare haka yaga rana, black tea kawai yake dirkawa cikin sa yana murzar aiki, sai da yayi sallar Asuba sannan ya Kira Nayrah, sun yi kusan minti talatin suna waya kafin sukayi sallama ya ɗan kwanta domin ya rintsa. _____________A bangaren su Alhaji Abid kuwa haɗuwa sukayi domin sake tattaunawa bisa jagorancin Hajj zawaad da Alhaji Huzaif. Hajj Zawaad ya ce, "Kunsan meysa na nemi mu haɗu mu sake tattaunawa kafin isowar mutumin nan nasu Awais, inaso mu danyi wani cuwa cuwa ne domin muma mu ɗan fita da kaurin mu"........ Alhaji Malayin ya ce, "Kamar ya kenan Hajj Zawaad?". "Kunga ai cewa yayi mu ce dasu za'a cire musu 30%, to ni abinda na gani mai zai hana mu ce wa mutumin za'a ɗauke masa 25% mu Kuma 5% ɗin sai mu rabeshi a tsakanin mu, kunga ai mun ƙaru ko ya kukace?"........... Alhaji Hammoud yayi saurin faɗin, "Maganar ka haka take Hajj Zawaad nima nayi wanna tunanin Kai ko 20% muka ce an cire masa amincewa zaiyi wa yaqi sauqi saboda kunga whl sir Ahuoyzah yana samun abinda yake so, to mu fa ya zubda mu kenan tunda dama amfanin mu Kenan, shekara nawa muke aiki a ƙarƙashin sa bacin albashin mu me muke samu, mutumin nan fa ko wayar mu baya ɗagawa direct ballatana ya saurari wata matsala ta mu". Alhaji Huzaif ya ce, " Tabbas maganar ku haka take kawai ayi hakan tunda a tsakanin mu ne, mu kashe mu binne Kar kowa yaji ko ya kace Alhaji Abid?". "Ai ni duk yadda kukace to fa daidai ne kawai ayi sha'ani".......... Haɗa ido Hajj zawaad da Alhaji Huzaif sukayi wani makirin murmushin nasara Hajj zawaad yayi tare da gyara zama aka wani ɗage ƙafa ɗaya aka ɗaura kan kujera tare da faɗin, "Ni fa Kun sani ne ? har na fara tunanin shiga siyasa da zarar komai ya tafi yadda nake so takarar minister man fetur zan fito kawai ayi me gabaɗayan". Dariya Alhaji Abid ya kwashe da ita tare da faɗin, "Kai Ka rufawa kanka asiri, in dai baso kake ka zama ministan yan kurkuku ba, Dan whl kana shiga siyasa sunan duk wasu asirin mu ya tonu ne, kaiiiii Hmmm siyasa fa ? Lalle ma Hajj Zawaad me ya shiga kanka da yawa haka ko dai kai ma kabi layi ne". "Kai ai kaji Baka faɗan alkhairi Alhaji Abid, amma fa da gskyr ka dan abu na farko ma da za'a fara tonowa shi ne batun harqallar ƙwayoyin nan"......... "Ah to ina baka kana ki". "Ah ah to ai in hakane Wanda yake shigo dasu har yake raba mana ai shi za'a fara kamawa"........ da sauri Alhaji Abid ya ce, "ka.. ka sanshi ne?"........ "Ina zan sanshi bayan duk kabi ka kididdibe shi gani kake zamu kwace ma hanya ". "Ahh haba Hajj Zawaad ai duk mun zama ɗaya ai ba wannan a tsakanin mu, Ka gane shi ɗin ne baya so mutane da yawa su san fuskarsa saboda shi ɗin babba ne, hakan zai iya jawo masa matsala, jiya ma yace min akwai wani babban contract da za'a kawo zai kuma sanya sunan mu a ciki". Alhaji Malayin ya ce, "kaiiiiii mutumina harka sai faɗawa take ". Ya ƙarashe yana bawa Alhaji Abid ɗin hannu suka tafa cikin jin daɗi. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥              _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐                *SULTYWRITES*                          A-K-A                [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._    @wattpadd sultywrites22            STEP 1 PAGE _______56 & 57 ____________zaune suke dukkan su a falon mahaifiyar su hajiya Zunaira suna fira cikin nishaɗi, Mirrah ce ta shigo bayanta maids ɗin gidan ne ɗauke da warmers. A kan Chinese rug ɗin suka yada zango, saida suka fara shimfiɗa leather mat sannan suka shirya warmers ɗin dasu plate akai suka juya suka fita. Kallon Hajiya Zunaira dake hakimce kan kujera ta wani zaquɗo glasses ɗin rashin mutunci kan hanci Kuma tana kallo ta samansa a maimakon ta cikin sa, wayarta take latsawa hankali kwance. "Hajiya ni zan shiga bangaren Anah akwai wani assignment da ban gane bane zanje muyi da Adlah".......... Ba tare data kalle ta ba ta ce, "Sai kin dawo". Cikin faɗa Julaybin ya ce, "Ba inda zaki dawo ki zauna, ke kenan baki da wurin zuwa sai wurin Adlah sai kace ƙanwar uwar ki ce ita. Ke jakar inace da kanki baya ɗaukan abinda aka koya Miki a class, Okay sai su Adlah ne kaɗai masu kwakwalen ɗaukan karatu ko? Ku Kuma dake taku kwakwalwar ta kifi ce?"......... Dariya Nuhail yayi da faɗin, "Julaybin ka rabu da yarinyar nan Dan ALLAH taje duk inda zata in ma cikin Anah zata koma ta sake haifota ya rage nata, ai ita ba yarinyar goye bace da za'a ce har yanzu sai an haska mata hanya". "Baza ka gane ba Nuhail abun akwai haushi ne. Duk gamu mun haɗu anan ta zauna ayi hira da ita a'a ita baza ta zauna tayi nishaɗi cikin yan uwanta ba sai wurin ƴar uba ko? to jeki, kifi ruwa gudu"......... A sanyaye Mirrah ta wuce ta zauna kusa Hajiya Zunaira tana faɗin, "Ya hakuri Yaya na tuba bansan Ranka zai ɓaci ba".......... Tsaki yaja Awais ya ce, " Ku da kuka iya magana ma kenan ai ni in Mirrah tayi wani abun ji nake kamar na kamata na nada mata na jaki ko zata dawo nutsuwarta". "Kaiiii ka maida hankalin ka kaji ko, ƴar tawa zaka naɗawa na jaki, a gaba na ma kake faɗa?".......... Hajiya Zunaira ta faɗa tana ajje wayarta a gefe. " To Hajiya yarinyar ce da Abun haushi Ke kuma Bakya tsawatar mata". "Ku tsawatar muku nakeyi? kaji yaro, kaga ka barmin Ya' tayi rayuwarta yadda take so, kowa da irin rayuwar da ya zaɓawa kansa Kuma kowa yana da ƴancin yin abinda yaga dama". Julaybin ya ce, " To ai shikenan yanzu dai duk ba wanna ba, ga abinci ya sauka ya kamata Ku sauqo mu zauna muci, ke Mirrah matso ki zuzzuba mana"......... Sauqowa Mirrahn tayi ta fara serving ɗin su. " A tray ɗaya zaki zuba"....... Nuhail ya faɗa, haka kuwa tayi ta haɗa su gabaɗaya a tray ɗaya tana ƙoƙarin zuba nata ya sake faɗin, "Kema tare zamuci, Hajiya ce kinsan bata zaman ƙasa dan haka zuba mata nata ita"........ Da "To". Ta amsa sannan ta zubawa Hajiya Zunaira nata a plate daban ta tashi ta ɗauko stool ta ɗora mata akai, ta sake dawowa ta zuba mata sanyayyar watermelon and pawpaw juice ɗin da ya sha sanyi har raɓa yake ta suke mata a gefe sannan su ma ta zuzuba musu ta zauna suka faraci. Ba wanda yayi Magana har suka gama sannan ta kirawo masu aikin suka kwashe suka gyara wurin kamar ba'a ci abinci ba. Julaybin ne ya nisa da faɗin, "Hajiya akwai wasu kuɗaɗe masu ɗan nauyi da zasu shigo ko kina da buqatar wani abu?"........... Ba tare data damu da jin ta ina ko Kuma ta yaya kuɗin zasu shigo ba ta ce, "Ai kasan bamu da buqatar komai a gidan nan ". "To ke fa?"......... Ya tambaya yana kallon Mirrah. "Nima ba komai Yaya waya ne Kuma jiya aka kawomin 17pro sabuwa, haka mota ma last month Ya Amjad ya sa aka kawo mana sabbi ni da Adlah so babu abinda nake buqata". Taɓe baki yayi saboda sunan Amjad data ambata sannan ya ce, "To shikenan dama shine abinda muka ce bari muzo mu tambaye ku, tunda ba abinda kuke da buqata zamu shiga mu tambayi Anah itama ko da akwai abinda suke buqata a matsayin mu na manya Kar azo ana ƙananun maganganu ko ba haka ba?". "Yadda ya muku "............ Hajiya Zunaira ta basu amsa dismissively tana kurɓar juice ɗinta . Tashi sukayi suka musu sallama suka fice suna maida zancen yadda zasu kasa kuɗin da bai shigo hannunsu ba. A falo suka samu Anah tana kamawa Esham gashinta, ɗagowa tayi tana kallon su cikin wani yanayi dan basu cika haɗuwa su shigo Mata a haka ba indai ba wani abun bane marar daɗi ya faru, Amma dukda haka saita aro jarumta tayi murmushi da faɗin, "Bismillah Julaybin Ku ne tafe"........ Saida sukayi masauki Kan tsadaddun cushions ɗin sannan Nuhail ya ce, "Mu ne Anah, mun sameku lpy?".......... Gaishe su Esham tayi suka amsa Awais ya ɗaura da cewa, "Ya wurin mamanki kuwa ? Su suna can kuma ba'a ganin su, dukda nasan batayi niyyar zuwan bane kawai"........ Anah ce ta amsa da, " Nuhail ai zaman aure take dole sai mijinta ya yarda, kuma already ai duk karshen shekara suna zuwa Hutu hakan ma ai yafi, Amma ta dinga yawo daga wanna ƙasar zuwa wanna ni kaina hankali na bazai kwanta ba"........."Eh duk da haka, ai ko dan rashin lpyr Dada, tunda sukazo sau ɗaya fa bata sake zuwa ba". "To Nuhail da zuwan Afia da rashin sa ai duk ɗaya ne, dan zaifi amfani ma in ta zauna a inda take tana masa addu'a kawai, kaga ko da sukazo farkon rashin lpyr wurin watan ta biyu amma me hakan ya ƙara?".........Taɓe baki Julaybin yayi kana ya ce, "Anah dama abinda ya kawo mu munzo muji ko kina da buqatar wani Abu ne saboda kinga yanzu duk wasu abubuwan Dada a hannun mu yake, so ya kamata ace mun bincika muji ko da abinda kuke buqata saboda mu sauke nauyi ko ba haka ba?"......... Murmushi Anah tayi duk da a zuciyarta tasan ba wai tsakani da ALLAH sukazo tambayar ta ɗin ba sunzo ne saboda su nuna Mata yanzu fa ba ɗan ta a kan duk wani abu na Dadan. Bata nuna musu komai ba ta ce, "Duk abinda zamu buqata to kafin mu buqace Shi Amjad yayi Shi dan haka bama buqatar komai, ALLAH ya bada Sa'a". Awais ya ce, "To ai ganin halin da yake ciki yasa muka ce Kar a ɗaura masa nauyi da yawa, in har da wani abu sai ki faɗa ayi ko ba haka ba Julaybin?".......... Girgiza Kai tayi tare da faɗin, "Ko da ace Amjad baya tsaye yanzu a kan duk wani abu na mahaifin sa ba hakan na nufi in yana buqatar kuɗi bazai iya zara bane, daku dashi ai duk ɗaya ne, kuna da iko shi ma yana da iko kawai dai a yanzun Ku ke tafiyar da abun ne sai sa"......... Ta ƙarashe tana murmushi Wanda hakan ba ƙaramin qona ransu yayi ba, Nuhail ya ce, "Well tafiyarwar ma ai da shi yakeyi Amma yazo ya bata rawarsa da tsalle, ni na rasa me muka rasa na dukiya da Amjad zai janyo mana zagi da cin mutunci irin wanna, ai abun da takaici ace qanin Ka na jini wai shi ke safarar mutane, ɗa ga Hashim Darwin fa wadda duk duniya ake yi dashi. Anah abinda baki sani ba fa duk hour ɗaya yawan adadin kuɗaɗen dake shiga Acc na Dada ba'a san yawan su ba amma a haka saboda rashin godiyar ALLAH Amjad ya jefa kansa a wahala, abun kunya whl".......... Miqewa Anah tayi da faɗin, "To Julaybin in kun gama ku gaida gida, ni zan shiga na shirya akwai inda zani ne"........ Tana faɗin haka ta wuce ciki Esham ma ta rufa mata baya. Kallon Nuhail Awais ya yi da faɗin, "Kaga ni ko ba'a isa a faɗi aibun wannan ɗan gwal ɗin ba a gabanta". "Muje kawai"......... Julaybin ya faɗa Yana miqewa tare da gyara zaman hannun babbar rigar sa suka yi waje. ---------------------√ Hushaima kuwa suna zuwa police station DPO ya bada umarni a wurgata cell sai anji halin da Huda take ciki a hospital tukunna. Su kuwa su Hajiya Sulaimiyya sai yamma sukazo itada Hajiya Yakura, iso aka musu zuwa office ɗin DPO, nan Hajiya sulaimiyya ta sake kora masa jawabi sannan aka ɗau statement ɗin su saboda Hajiya sulaimiyyar tace baza ta yarda ba sai anje kotu, bayan an gama komai ta cika DPO da kuɗaɗe masu nauyi sannan ta ƙara jaddada masa ko uban waye yazo kar a bada bailing Hushaima, daga cikin cell sai gaban Alkali. Sanin matsayin ta yasa DPO ya amince without second thought, gashi kuma an cika shi da yan canji. READERS A TUNANIN KU WACECE WANNAN HAJIYA SULAIMIYYA ƊIN ? Shi kuwa Sahnish dama lokacin ɗauko Shazeen daga makaranta na cika yaje ya ɗauko ta suka tsaya ya saya mata abinda zata ci suka wuce gida. Ko da suka koma gidan a rufe suka samu ɗakin Hushaiman, bai wani damu ba dan yasan wani lokacin suna riga ta dawowa dan haka yace Shazeen ta wuce ɗakin sa shi kuma yaja benci kusa da Barde dake zaune yana ta faman lissafe lissafe shi da Uday na kuɗin da zasu rarraba wa mutanen su wanda zasu fita rally tare kamar yadda su ma aka neme su aka ɗaura su akai dan su kasance ƴan daban siyasa. Shi ma zaman sa yayi yana lissafin turarukan sa da wanda suka ƙare da wanda zai ƙara siyowa da kuma ribar sa, saidai har ya gama Hushaima bata shigo ba hakan yasa ya tashi ya wuce ɗaki ya rage kayansa ya ɗauko bokiti ya fito ya ɗibi ruwa ya shiga wanka, ko da ya fito ya koma ɗakin ya shirya ƙofar gida ya fita sai dai shuru shuru har akayi kiran sallar magriba ya koma cikin gidan yayi ya sake fitowa ya zauna, har lokacin sallar isha yayi ya sake tashi yaje yayi ya dawo ba Hushaima ba labarin ta, tun yana ɗaukan abun wasa har ya haqura ya tashi. Cikin gidan ya koma ya wuce ɗakin sa, wayarsa dake hannun Shazeen ya karɓa ya shiga contact ya lalubo number Hushaima yayi dialing dan da yaqi kira ne saboda fushin da yake da ita, missed call ɗaya, missed call biyu, missed call uku ba'a ɗaga ba duk da hankalin sa ya fi bashi yau ma wannan saurayin nata ne ya ɗauke ta daga wurin aiki amma Kuma yasan duk inda take bata qin ɗaukan wayar sa, saboda a duk inda take hankalin ta yana kansu indai zata ga wayar sa zata ɗauka taji lpy yake kira, wannan tunanin da yazo masa ya sanya hankalin sa tashi, juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya tare da faɗin, "Shazeen saka hijab ɗin ki mu fita"......... Ɗaukan hijab ɗin nata na makaranta tayi ta saka dan dama kayan makarantar ne a jikinta har lokacin saboda duk kayanta na ɗakin Hushaima ne kuma key na wajenta. Riqe hannunta yayi suka fita bai tsaya ko ina ba sai wurin aikin su Hushaima dukda yasan a irin wannan lokacin ba lalle ne ya samu kowa ba, hakan ne kuwa ya kasance dan a kulle ya samu wurin sai wani mutum tsaye da touchlight ɗin sa yana ta haske haske, ƙarasawa yayi wurin sa tare da masa sallama, amsawa yayi yana me haske su da touchlight ɗin. Hannu Sahnish yasa ya kare fuskar sa da faɗin, "Malam ka haske mana ido kuma ai"..........."Eh to ai dole na haska saboda tsaro rayuwar ta yanzu ba gaskiya ne, Daga ina haka?". Gyara tsayuwar sa yayi kafin ya ce, "Da ALLAH nazo tambayar yar uwata dake aiki ne anan, munga lokacin tashi yayi kuma bata dawo gida ba shi ne nazo tambaya naji ko lpy"..........."To ai yaran dake aiki anan da yawa waccece daga ciki?".........."Bansan ko kasan sunan ta ba, Hushaima!". "Au tooooo, wata yar fisgagga masifaffiya zakace, ai wata yar masu kuɗi ta fasawa kai ɗazu da rana, to shi ne matar ta kira police suka rakice ta can dai haka sukayi gabas maso yamma ban dai san wani station ɗin aka wuce da ita ba". "Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun³"........ shi ne abinda Sahnish yake ta nanatawa kafin yayi ƙarfin halin faɗin, " Da ALLAH Malam ko kasan station ɗin da suka je?"..........." Kaga nifa gadi kawai nake musu, saidai na baka lambar Hajiyar me wurin sai ka kirata kaji dan nasan ita baza ta kasa sani ba".......... Da sauri ya ce, "To Nagode, bani lambar"...........Ya ƙarashe yana zaro wayar da sauri hannun sa har rawa yake wurin loda number da me gadin ke faɗa masa cikin wayar. Ita kuwa Hushaima ƴan sandan nan sunyi juyin duniya ta basu number wani nata su kira taqi, su dama dan su kira ne su faɗa musu halin da ake ciki ne ko suna da halin ɗaukar lawyer, sannan a samu wanda zai dinga kawo Mata ruwa da abinci har lokacin da za'a shiga kotu, amma Hushaima ko kallon su ma batayi ba ta bawa banza ajiyar su, da suka gaji suka fadawa DPO yace su barta da kanta zata bada in taji wuya, saurayen cell kaɗai in aka barta dasu sun isheta. Sahnish na kiran Hajiya yakura ta shaida masa police station ɗin da Hushaiman take, ba ɓata lokaci yaja hannun Shazeen suka nufi police station ɗin, bayan sun shiga yayiwa yan sandan dake kan kanta ɗin sallama suka amsa, " Yauwa sannu"......... Wani daga cikin ɗan sandan dake rubuce rubuce bakin kantar ya faɗa yana bin Sahnish ɗin da kallo ganin yadda yayi wani iri kamar marar gaskiya saboda rashin sabo da irin wuraren, dan shi duk abin tashin hankali baya son sa, ganin uniform din ƴan sanda ma ko soja firgita shi yake ni kuwa nace lalle Hushaima tayi gsky, anya Sahnish ba maza ya rako duniya ba kuwa. Daurewa yayi da faɗin, "Amm da ALLAH ranka ya daɗe tambaya nake ko nan aka kawo wata da sukayi faɗa a wani salon sunan ta Hushaima Sahnish Shazeen ". "Nan ne!, Ya akayi ?".........." Qanin ta ne ni mun ji shuru ne har lokacin tashin su yayi bamu ganta ba, shi ne mukaje muka tambaya aka faɗa mana abin da ya faru da kuma inda aka kawo ta"......... Juyawa ɗan sandan yayi wurin sauran ya ce, "Constable Buhari DPO na nan kuwa?"......... Ɗan shiru Constable Buhari yayi kafin ya ce, "Anya kuwa saidai na duba banajin yana nan gsky". "To da ALLAH je ka duba in yana nan kace masa ɗan uwar yarinyar nan ne da ke da case dasu Hajiya sulaimiyya"..........Tashi Constable yayi ya wuce ciki can sai gashi ya dawo yana faɗin, "Ya tashi saidai ya dawo gobe". "To kaji baya nan saidai ka dawo gobe kamar ƙarfe goma haka". "Yanzu officer ba za'a iya bamu bailing ta ba kenan?"........ Dariya yayi yana kallon Sahnish ɗin kafin ya ce, "Kai yaro baili fa kace? ai bama a fara wannan zancen ba tunda ba'a san halin da yarinyar data fasawa kai take ciki ba, dan har yanzu ance bata farfaɗo ba, kuma ma in zan Baka shawara tun wuri ka fara neman lawyer dan iyayen yarinyar sun buqaci a turasu kotu kuma har an ɗau statement dinsu ma zaa aika so batun baili duk babu shi a yanzu". Wani irin faɗuwa gaban Sahnish yayi, cikin rawar murya ya shiga roqon su amma ko dubansa basuyi ba ƙarshe ma sai cewa ɗayan yayi, "To kai haka ma ake zuwa baili kamar zakaje karɓar sadakar kunu"......... Cikin rashin fahimta Sahnish ya ce, "Bangane ba ranka ya daɗe"..........." Shikenan tunda baka gane ba juya ka koma inda ka fito, ka dawo goben". "To officer dan ALLAH ka min alfarma na ganta mana"........ Kallon baka da hankali suka masa kafin ya ce, "Kai baza ka ganta ba ka wuce ka bamu waje ka cika mu da surutu".......... Cikin rawar ƙafa Sahnish yaja hannun Shazeen sukayi waje hankalin sa in yayi million ya tashi, wurin wa zai nufa wa ya sani da zai masa alfarma, sun kusa minti talatin tsaye a bakin police station ɗin kafin ya yanke shawarar kiran baba ilerika. Ɗaga waya yayi ya kira shi........ Baba ilerika ne kishingiɗe a majalisar tasu shi da abokan sa sai tafka muhawara suke akan lamarin siyasar ƙasar Nifaz ɗin, Wani me suna Jarwai ya ce, " Kai ni fa Malam lawan ba zan taɓa yarda cewa ba izinin gomnati a duk wa'annan abubuwan dake faruwa ba, kai ai bani ba ma duk me hankali yasan da wata a ƙasa kawai so ake mu saki sana'ar mu, mu dogara da abubuwan da ake shigo mana dasu daga waje a Matsayin cigaba daga nan kuma mu koma ƙaraƙashin ikon su ya zama su zasu ɗinga juyamu yadda suke so, saboda bamu da ikon sarrafa komai daga ƙasarmu"............ Malam lawan ya ce, "Yanzu miye laifi dan an kawo abubuwan cigaba mun karɓa, ku bakwa ganin ƙasashen da basa ƙarɓar abubuwan cigaba ya suke? Ai basa gaba". "Ai kuwa sunfi zaman lafiya Malam lawan, shin ka taɓa jin labarin irin wa'annan gurbattatun abubuwan dake faruwa a irin wa'annan ƙasashen? Ai babu. Saboda ta hanyar da ake shigo mana da abubuwan da ake cewa na ƙaruwa ne ta nan ake shigo mana dana cutuwa ma, Kaga ka yarda kawai jarwai ya fika gsky a wannan Maganar, taya ma to za'a ce mu saki kiwo mu saki noma za'a dinga shigo mana da komai ba sai mun wahala ba, in kuma munaso muyi da kan mu za'a shigo mana da Artificial intelligence ɗin da zasu sauqaqa mana kayi tunani fa". Jarwai ya ce, "Ai qasimu ba dan komai bane kawai dan su rabamu da sana'o'in mu ne, kuma ba zai yiwu ba dan tunda suka fara motsa wannan Maganar to akwai shirin da sukeyi dan haka whl kowa ya nemi sana'ar hannun da ba wata shegiyar gunkin ko engine da za'a sawa battery ace zai iya yi, wannan shi ne kawai abinda zai cecemu". Shi dai Baba ilerika yana daga kishingiɗen sa yana goga ashuwakin sa yana kallon masu wucewa ba tare da yace dasu uffan ba, wayar sa ce ta Fara ƙara, zarota yayi daga aljihun gaban rigar sa ganin Sahnish ya sashi yin picking tare da karawa a kunne. "Helo Sahnish ya akayi ne?". "Baba akwai matsala whl".......... Yadda yaji Muryar Sahnish ɗin ya sashi tashi daga kishingiɗen da yake yana faɗin, "Subahanallahi ALLAH ka raba mana hanya da matsala, meke faruwa?". "Baba Hushaima ce suka samu matsala da wata a wurin aikin su har ta fasa mata kai, to yanzu sun kawo ta police station nazo nayi duk iya bakin ƙoƙarina sun hana ma a ganta ". "Tooo abinda ya faru kenan, yanzu kai kana ina ? Kuma wani police station ne?". "Ni muna ƙofar police station ɗin yanzu......." Nan ya kwatanta masa police station ɗin. "To ku jirani anan bari na ƙaraso, kaik jama'a daga wannan sai wannan Hushaimaaa"....... Ya ƙarashe yana kashe wayar tare da miqewa ya kalli sauran abokan nasa da suke ta faman tabka muhawara sannan ya ce, "To Jarwai mu wata yar camama ta taso, za kuma mu ƙara gaba"....... Dariya Jarwai yayi kafin ya ce, "Shege ilerika bakaso a zauna lpy in dai akwai ci a rigimar"......... Miqewa tsaye yayi yana karkaɗe rigar sa ya ce, "Ahhh to kuwa kaga laifi na ne duk inda ci yake kuma ai kowa yana so "......... "To ko nazo na raka ka ne". Faɗin Malam lawan. "Makaho ne ni ko kuturu da bazan iya kai kaina ko ina ba har sai na nemi ɗan jagora, ko kuwa ah ah jariri ne ni da sai an ɗaukeni?"......... Girgiza Kai Malam lawan yayi yana Dariya ya ce, "kaga ni fa wasa nake mutumi na, jeka ka dawo". Qasimu ya ce, "Kaga ilerika jeka abunka rabu da su, kar ma su ɓata ma lokaci harkar ta wuce ka". -------------------------√              AURELLON SULTANATE💎 Ziyada ce ta shigo falon da Ummu ke zaune tare da hadiman ta, kowa da aikin da yake wasu kuma suna zaune a gabanta suna mata hira, wasu suna matsa mata ƙafafu, wata tana haɗa mata tea, suna ganin shigowar ziyadan suka fara risinawa suna mata Barka da shigowa duk da a zaune suke. Cikin takun da ke nuna eh ita ɗin jinin sarauta ce kuma sarautar ma ta Aurellon ta ƙaraso, wuri ta nema ta zauna ba tare da tayi magana ba, ganin yanayin fuskarta yasa Ummu faɗin, "Ku tashi kuje kawai sai na neme ku"............" A tashi lpy sarauniyar sarauniyoyi, ALLAH ya ƙara miki lpy"....... Suka haɗa baki wurin faɗa suna miqewa. Wadda take haɗa tea ce ta ce, "Ranki ya daɗe za'a miqo tea ɗin ne ko naje?"......... Hannu kawai ta miqa mata alamar ta bata, duqawa tayi kan guiwowin ta sannan ta miqa mata ɗan ƙaramin mug ɗin na gold dake haɗe da wani ɗan ficicin teaspoon da kuma saucer da aka ɗaurashi akai. Tana karɓa Khadimar ta juya ta bar wurin. "Meke faruwa ne ziyada?"....... Ummu ta tambaya tana kurbar tea ɗin dake hannun ta . Kafin ziyada tayi magana Reeslan ya shigo yana gyara zaman band ɗin kansa, sanye yake da wata Black Polo t shirt data fito da kyakkyawar surar jikinsa ta cikakken ɗa namiji sai caramel colour skinny jeans da ya sa, baiyi masauki ko ina ba sai gefen Ummu, ɗan tsukakken bakinsa ya kai bakin mug ɗin dake hannun Ummun ya kurɓi tean, sai kuma ya gyara zamansa tare da sanya dukkan hannayen sa biyu ya karɓe mug din da saucer yana faɗin, "Ummu saidai fa kisa a kawo miki wani, waye ne ya haɗa a cikin khadiman naki?"........... Sakin baki Ummu tayi tana kallon sa kafin ta kai hannu ta riqe kunnen sa ta murɗe, ɗan ɓata fuska yayi amma bai ce komai ba, dungure masa kai tayi tare da faɗin. " Ka nutsu ɗan ALLAH Reeslan, ka ajje duk wani rashin ji a gefe, ka sani kai ne fa magajin kujerar Aurellon, ni kwata kwata na rasa ya zanyi dakai whl". "A'a Ummu ni fa nace saidai Habiby ya ƙarɓa ko shi ko Sahel dan gaskiya ni bazan iya wata sarauta ba, dan ALLAH ki daina faɗar hakan ma Ummu yana bata min rai whl"........ Ya faɗa yana tsuke fuska kamar bai taɓa sanin wani abu Murmushi ba a duniya. Ajiyar zuciya Ummu ta sauke tana kallon ɗan nata da a ko da yaushe su kayi ƙoƙarin kwatanta shi da sarautar tasu sai ya nuna bacin rai da fushi ko da kuwa Sultan da kansa ne zai masa maganar. "Tohm shikenan naji yanzu daga ina kake?"........ Ba tare da ya kalleta ba alamar ransa ya ɓace da maganar data masa ya ce, "Naje Horse ranch na duba Hirtik ba lpy, sai na biya fada wurin su Abbu ". "To ka tashi kaje wurin Rouslan domin bayajin daɗi inajin tun fitar ka yake ta amai sai da aka kira Abyan ma yazo ya duba shi, amma Imam ya aiko da ruwan addu'a, kai ma in kaje Ka ganshi kazo ka karɓi naka kasha "..........Tunda ta ambaci Rouslan bashi da lpy ya juyo da mugun sauri, "Ummu bansani ba ai meysa ba'a kirani ba, how za'a kira wani Abyan bayan gani, wai meysa ake min haka ne, shikenan mutum baya kuskure ne, ko shi Abyan ɗin baifi ƙarfin kuskure ba. Ba dan alqawarin da nayi wa Rouhi ba whl da sai na koma kan aiki na saidai duk abinda zai faru ya faru"......... Kafin Ummu tace wani abu ziyada ta ce, "Yah Reeslan ka tarar da abinda ke faruwa da kaje fada".......... Ɗan kallon ta yayi hankalin sa akan Ummu da ita kuma ta juya wurin Ziyada tare da tambayar ta, " Meke faruwa ne ziyada? Tun ɗazu na lura da magana a bakin ki kuma kinzo kin zauna kinyi shuru". "Ummu Ammu yassar ne akace ya yanke jiki ya faɗi yanzu a fada ". "Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun me ya sameshi haka?" . Reeslan da ya tashi domin zuwa wurin Rouslan ya ce, "Sai dai haƙuri Ummu, amma Ammu yassar ba zaiyi ba, shi ma mutuwa zaiyi".......... Dafe ƙirji Ummu tayi idanunta na cikowa da hawaye cikin rawar murya ta ce, "Reeslannnn! Innalillahi wa Inna ilaihir raju'un, Reeslan bana hanaka irin wannan maganganun ba meysa bakajin maganata? Meysa Reeslan so kake sai zuciyata ta buga ko?"..........Ta ƙarashe cikin Muryar dake bayyana tsananin tashin hankalin da take ciki, wannan shine karo na uku da irin haka ta faru kuma in Reeslan ya ambaci mutuwa mutum zai yi, to fa mutuwar yake amma Ummu bata taɓa yarda wani ya sani ba ciki harda mai martaba, sai addu'a kawai data dukufa dayi saboda bata so a canfa mata ɗa. Ita kuwa Ziyada da bata san abinda ke faruwa ba sai cewa tayi, "yah Reeslan me Ammu ya ma da zaka masa fatan mutuwa?"......... Wucewa kawai yayi ba tare da ya bawa ɗayansu amsa ba , Ummu ce ta ce, "Ziyada karki sake naji wannan maganar a bakin wani, yadda akayi ta a nan a barta a nan whl ko da wasa naji ta sai ranki ya ɓaci".........Tana kaiwa nan ta miqe ta bar falon zuciyar ta cike da fargabar abinda zai biyo baya. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______58 Reeslan na shigowa ɗakin su ya tarar da jakadiya dake zaune kan shag rug ɗin ɗakin nasu tana tsiyayawa Rouslan ruwan addu'ar da Ummu tace tazo ta bashi wanda Imam ya aiko, Wani irin ɓaci yaji ransa bai san lokacin da ya katsa mata wata tsawa ba, da faɗin, "Me kikeyi Anan, tashi ki fita kafin na saɓa miki kamanni"......... Take jikin jakadiya ya ɗau rawa har cup ɗin hannun ta na suɓucewa ya faɗi. " ALLAH ya huci zuciyar Maleekh dama Sheikha ce ta buqaci nazo na bashi "..........Ta ƙarashe tana tashi zata fita, ciki ya ƙarasa in da take tsugunne tare da ball da kyakkyawan Jug ɗin yana faɗin, "Su wannan uban wa kika barwa ? tattare tsiyarki ki fita da ita "..........." Habiby p......." "Kaiiiiii Shut".......... Ya faɗa yana ɗaura yatsan sa kan ɗan mitsitsin lips ɗin nasa. Harara Rouslan ɗin ya watsa masa ta gefen ido yadda shi kaɗai kawai zai gani sannan ya ɗauke kansa, Wucewa jakadiya tayi jikinta na ɓari ta shiga tattare kayan dan Jug ɗin tuni ya tarwatse ruwan addu'ar ya zube, haka ta tsitsince sannan ta nufi ƙofar fita. "Kuma ki turo wadda zata gyara ɗakin nan"........ Ya faɗa Yana matsawa wurin two seater sofa ɗin da Rouslan ke zaune a kai. Zama yayi yana huci kamar wani tafasasshen ruwan zafi. Sai a lokacin Rouslan ya sake cewa, "Haba Habiby ruwan Addu'a ne fa Imam ya aiko kazo ka zubar, ayoyin ALLAH ne fa"........ Wani kallo ya watsa masa Amma baice komai ba shi kuma ya cigaba da faɗin, "Kuma jakadiya ko ba komai tayi ya'ya damu, ka tuna tun bamu fi shekaru huɗu ba a duniya take tare da mu, ya kamata ace kayi limiting actions ɗinka toward her". Hannunsa ya kai goshin Rouslan ɗin yana faɗin, "Me kake ji yanzu? Ummu tace min bakaji daɗi ba bayan fita ta?".......... Ɗan sauke numfashi yayi dan maganar da yake ma ƙarfin hali ne shi kaɗai yasan me yakeji a jikinsa wani irin turirin zafin zazzaɓi ne kawai ke fita. "Shi Abyan ɗin da yazo ya baka magani ko kuma kawai iyayi yazo yayi ma? Meysa ma tukunna baka kirani ba har ka bari suka kira wani Abyan"........ Ya faɗa wannan karon a tausashe da kuma kulawa . Lumshe idanun sa yayi ya buɗe kana ya ce, " Ya min Allurai dai, ga sauran can ma ya bari ya ce in kazo sai ka duba yaso ka cigaba da yi min. Kuma banaso ne na tashi hankalin ka a inda kake saisa ban kiraka ba"........ Jijjiga kai Reeslan ɗin yayi tare da tashi ya wuce gaban gadon nasu, bedsheets ɗin dake kai ya cire gabaɗaya sannan ya wuce ya ɗauko wani sabo ya dawo ya shimfiɗa ya canza pillow case ya gyara gadon tsaf tsaf, sannan ya dawo ya kamo hannun Rouslan ɗin kamar wani yaro, miqewa yayi ya bishi har zuwa bakin gadon, nuna mashi kan gadon yayi da faɗin, "Kwanta ka huta". "Ina zaka ?".......... Rouslan ɗin ya tambaya yana kallon sa. "Ba inda zani wanka ma zan shiga, nima in na fito kwanciyar zanyi na huta ai"........... Rouslan bai Ƙara cewa komai ba ya hau ya kwanta, wata na'ura Reeslan ɗin ya kunna ita kuma iyakarta zagayen gadon kawai zata sanyaya, in kuma sanyi ne zata baka dumi kamar dai Ac amma Ac in Ka kunna duka ɗakin zata game ita kuma wannan iyaka gadon ne kawai. Saida ya seta ta sannan ya sauke wasu ƙayatattun transparent curtain dake zagaye da gadon. Daidai lokacin akayi Knocking, "Waye ?"..........Ya tambaya a daƙile. "Khadimah Jamila ce jakadiya tace nazo na gyara ɗakin"......... Saida yaja tsaki sannan ya Ƙarasa ya buɗe ya koma tsakiyar ɗakin ya tsaya tare da riqe waist ɗinsa da hannayen sa, "ki nannade rug ɗin ki fita dashi ki canzo wani karki ɓatamun lokaci kiyi sauri"......... Duk wannan maganar yana yin tane cikin faɗa faɗa a qage irin wanda ya ke jira ayi kuskure kaɗan ya kaiwa mutum duka. Duk da nauyin rug ɗin haka ta nannaɗe shi sannan ta shiga ƙoƙarin ja amma duk da haka bai ga ƙoƙarin ta ba ya ce, "Da ALLAH ki sa ƙarfi kiyi maza ki fice dashi, ki zo kiyi abun dake gabanki, kina abu sai kace wanda ake rainon ku da yunwa"......... Bata ce komai ba sai saka dukkan ƙarfinta da tayi ta ja shi waje sannan ta kira wata khadimar tace ta janye wannan ta sa a ɗauko wani a store yanzu yanzu, Kasancewar sun san aikin Reeslan ɗin yanzu yanzu ne shi bai san wani abu wai sai anjima ba yasa cikin hanzari ta kira wata ta tayata ɗauke wannan ɗin. Dawowa ɗakin khadima Jamila tayi tana haki ta tattare Wurin sannan tayi mopping, lokacin aka shigo da wani sabon rug ɗin tare suka haɗu ita da wadda ta kawo suka shimfiɗa sannan suka zube a gabansa tare da faɗin, "Ko da akwai abinda za'a yi wa maleekh?".......... Tsaki yaja da faɗin, "Dama ku biyu na kira ne ?".......... Da sauri wadda ta kawo rug ɗin ta tashi zata fita har ta kai ƙofa ya ce, "keehhhhh"......... Datse hakwaran sa yayi tare da kallon gadon da Rouslan ke kai yana bacci, cikin ƙoƙarin yin ƙasa da Muryar sa ya ce, "Nace ki fita ne ko kuwa na sallame ki ne? ba tambaya na muku ba? "......... Jikinsu ne ya ɗau rawa a tare suka ce, "ALLAH ya huci zuciyar Maleekh ". "Ku bace min da gani kafin nayi pieces da miskinan ƙasusuwan ku"........ Ai kafin ya ƙarasa sunyi waje tare da rufo ƙofar, kwafa yaja sannan ya wuce wurin bedside drawer ya jawo burner ɗin sa ya jona ya wuce ya ɗauko turaren wutar su, dan shi takanas yake zuwa ya kwaso na Ummu daga an haɗa mata sabbi, kaɗan ya zuba dan already ɗakin nasu ya riga ya kama da kamshi dan ko pillown su ka ɗauka in Ka ajje to kai ma kamshin ya kama jikin ka kenan. Bathroom ya wuce domin watsa ruwa ya zo ya kwanta ya huta. ------------------√ Ranar ko da ya tashi bai fita ko falo ba daga ɗakin sirrinsa sai normal ɗakinsa, gyaran ɗakin ma yana ciki akayi, haka abinci a ɗakin yaci sama sama saboda hankalin sa na kan aikin da yake, ko su Ace bai haɗu dasu ba sai Philip da ya sanya ya dubasu ya Kuma tambaye su ko da akwai abinda suke da buqata. Ba abinda yake sai bincike a kan shadow tun 11am yake Abu ɗaya har 3pm Amma ba wani labari domin Shadow Yana da mutane a kowani ƙasa Wanda suke masa safarar mutane, Saidai Kuma a duk binciken sa mutanen nasa ko wuqa zaka sa musu a wuya su faɗa ma inda za'a samu shadow to fa Saidai ka datsa musu wuqar nan bama inda yake ba hatta kamannin sa basu sani ba fari ne? Baqi ne? ah ah yellow ne baza su iya faɗa ba kamar dai yadda BB LALO ya faɗa masa, tashi yayi daga gaban table ɗin yanajin kamar kansa zai kama da wuta, tunda ya fara aiki Matsayin jami'in sirri Ba'a taɓa bashi aiki yayi failing ba hakan yasa ko da aka danqa masa aiki kan Shadow baiji ko ɗar ba dan gani yake kamar ƙaramin aiki ne, tun da ya tashi ko wanka baiyi ba daga shi sai short nicker yake ta dirzar wannan uban aikin. Kai kawo ya shigayi a ɗakin sirrin nasa yana tunane tunane har baisan iya tsawon lokacin da ya ɗauka ba sai jin Kiran sallar la'asar yayi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fice zuwa master room ɗin nasa, toilet ya wuce ya ɗauro alwala ya fito, jallabiya ya zira kawai ya tada sallah. Yana idarwa ya miqe ya koma ɗakin sirrin ya sake dasa sabon zama gaban system ɗin ya ɗaura daga inda ya tsaya, Amma still ba wani labari kawai dai matsayar da ya tsaya itace dole wa'anda zasu ɗauki mutanan da zasu basu zasu kaisu inda ake tara mutanan, Kuma dole ne shadow ya kasance a kusa dasu koma ta Ina yake. Da haka ya yanke nasa hukuncin kawai zasu Kira suce musu sun gama aiki su faɗa musu inda zasu Kai musu mutanan, numfashi ya furzar tare da kashe system ɗin da duk wasu abubuwan da ya kunna lokacin da ya shigo sannan ya fita daga ɗakin ya koma master room. Miqa yayi tare da langwashe hannayen sa baya suka bada sauti ƙas ƙas haka wuyan sa ma, direct bathroom ya wuce tsawon 30 minutes yayi a ciki sannan ya fito lokacin anata kiraye kirayen sallar magrib, wata jallabiyar ya ɗauko ya sanya ya tada sallah, yana idarwa ya cire ya wuce gaban mirror can ma sai da ya ɓata kusan minti ashirin ba dai sai na fada ba kunsan mutumin naku da sluggishness ya fiya lakwai lakwai tu. Tashi yayi ya wuce gaban sip ɗin nasa ya ciro kaya maras nauyi, wani army green cargo shorts da black armless t shirt Mai laushi kamar auduga ya feshe jikinsa da turaren sa me kamshi. Saida ya gama duk abinda zaiyi ciki harda sallar isha Sannan ya fito daga ɗakin. Haka take a wurin su Kiara tunda suka tashi sukayi wanka suka fita sukayi breakfast Kiara ta koma ɗakin da suka sauka ita da Ash, ta fara aikin binciken Shadow, Ash kuwa Philip tasa ya zagaya da ita gidan ta ɗanyi kalle kalle sannan ta koma ɗaki ta samu Kiara ta tasa system ɗin ta a gaba, itama wucewa tayi ta ɗauko ta ta ta jona a caji tana faɗin, "Kin samu wani info ne Kia?".......... Ba tare data ɗago ba ta ce, "Ash kinsan abinda ke ban mamaki a duk ƙasar da yasa a samo masa mutane to a bakin border wanna ƙasar ake ajje masa wa'anna mutanen". Cikin alamun rashin fahimta Ash ta ce, "kamar ya kenan ? Ban fahimta ba ?". Ɗagowa kiaran tayi tare da cire hular dake kanta ta wulla kan gado Sannan ta ce, " Hakan na nufin bashi da takaimemiyar ƙasa, su kawai yaran nasa aikin su su kawo masa mutanen bakin border daga nan Kuma su juya suyi tafiyar su". "Kenan akwai mutanan sa a bakin kowace border?"........." Yes that's the fact, to Amma yanzu ta Ina kike ganin zamu soma kamashi ?". Ash na kunna system ɗinta ta ce, "ki daina Abu kamar ba jami'ar bincike ba idan dama taqi sai Abi hagu, zamuyi amfani da na'urar tracker ne kawai". "Yes yes Ash kin kawo idea, dole idan da tracker a jikin mutanan mu, duk inda sukaje zamu san takunsu da Kuma motsinsu har mu sameshi". Wata bazawarar dariya Ash tayi hankalinta akan system ɗin ta da take caccaka da zara zaran yatsun hannunta kamar wata typewriter ta ce, "Wai kina tunanin dan munyi amfani da tracker shikenan zamu samu inda shadow yake?" ............"What do you mean? Kin sake sani a duhu?". Kiara ta tambaya tana sake haɗe rai. "Kinga shikenan daga na haske ki da fitila kema naki shadow zai bayyana".........."Stop joking Ash it's not time for that". "What I mean shi ne in munyi amfani da tracker zamu San inda ake Kai mutanan, sannan zamu San me akeyi dasu sai muje mu ebe su, dole hakan zai girgiza shi Kuma duk inda yake zai motsa wannan shi ne target ɗin mu, motsin sa muke so daga inda yake kawai, Amma fa karkiyi depending kan magana ta do your own investigation, that's just my own idea and perception"........... Ta faɗa tana cigaba da aikin ta, Shuru kiara tayi tana kallonta tsawon 2 minutes kafin tayi focusing back Kan nata aikin, suna a haka ne Ace ya shigo tare da musu excuse Ash ce ta ɗago tana kallon sa, bakin gadon ya zauna tare da ɗaura tasa system ɗin a gefen gadon Yana kallon su, Dan suna opposite ne dashi a kan wasu kujeru guda biyu da wani table a tsakiya, Ba tare da Kiara ta ɗago ba ta ce, "Ace how far ?". Dan watsa hannayen sa yayi tare yana ɗan taɓe baki ya ce, "Not too far, daga nayi gaba sai nayi baya, sai sa kawai na taho nan, dan Philip yace har yanzu Amjad ɗin Bai fito ba". "To muma hakan take, Amma fa Ash ta kawo wata idea......." Nan ta faɗa masa yadda sukayi da Ash ɗin. "Yes wannan idea ce me kyau, Amma Kuma inaga me zai hana mu datsi duk wayoyin Yaran nasa domin musan ta ya suke waya ? Shi yake Kiran su da kansa ko kuwa dai ya abun yake? Mutane nawa ne suke Kiran su? Sannan daga wace ƙasa aka fi Kiran wayoyin ?". Kallon Kiara da hankalin ta gabaɗaya yana kan system ɗin ta tayi kana ta ce, "Ace ma fa ya kawo idea shi ma, Dan daga inda aka fi kiran wayar nan zamufi focusing akai". Ace ne ya sake cewa, " But baza mu yanke hukunci ba har sai Amjad ya fito, Amma kunyi waya da widad ne?".......... Wani dogon tsaki Kiara taja tare da faɗin, " Wanna Ɗan wulakancin bame Kiran sa saidai Amjad ɗin dake iya haƙuri dashi, dan ni bazan Kira mutum mu tsaya breathe competition ba, sai kace baisan aikin sa ba"......... Ash kuwa taɓe baki tayi ba tare da tace komai ba, Ace ya ce, " Ni fa na rasa wannan Yar tsamar da ke tsakanin ku da Widad, especially ma ke kia ko dai ko dai?"......... Ya ƙarashe cikin salon zolaya. Wata banzar harara Kia ta wurga masa da manyan idanuwan nan nata. "To kunga ko tun da na shigo bata ɗago ba sai da nayi Maganar sa"......... Ya sake faɗa yana dariya. Ashley ta ce, "God forbid, me Kia zatayi da wani Widad ai sai a rasa waye mijin waye matar".........." To ni dai bari kuga na kirashi dan inajin dukkan ku kun kyasa ne saisa kuke ta cece ku ce a kansa"........... Ya faɗa yana ɗage musu gira ɗaya. A kufule Kiara ta ce, "Kuma a rasa wanda za'a kyasa sai widad, me yake dashi da zaija hankalin".......... Ashley ta ce , "Ke da kike kallon shi ma har kika lura bashi da abun jan hankalin, ni ai ko kallo ma bai isheni ba"..........wani irin kallo Kiara ta watsa mata kafin ta ce, "Me kike nufi?"..........Shi dai Ace dariya yake kawai dan ya san ya haɗasu kwafso. Har tayi ringing ta gama Jey bai yi picking ba, Kiara kuwa kamar ita ta Kira, rai a ɓace ta ce, "Dan ALLAH ka rabu da mutumin nan Ace, yanzu gani zaiyi kamar baza mu iya komai ba in ba shi shiyasa zai tsaya yiwa mutane yanga"........ Girgiza Kai kawai Ace yayi tare da ɗaukan system ɗin sa ya ce, "Ummm bari kuga na koma inda na fito sai anjiman ku". Shi kuwa Jey lokacin da Ace ma ya Kira bacci yake sharba Abun sa, dan bai samu yin bacci ba saida yayi sallar Asuba shiyasa bashi ya tashi ba sai 12:00pm, wanka ya shiga ya fito sannan ya shirya cikin white jeans da royal blue shirt ya fito, dinning ya nufa ba komai akan dinning ɗin dan tuni sun manta da yin breakfast har an gyara wurin, a madadin ya Kira masu aikin sai ya gwammace ya wuce kitchen ɗin da kansa, Yana shiga ya tarar da maids ɗin na faman aikin girka abincin rana, suna ganin sa suka fara gaishe shi, amsa ɗaya ya basu wato, "lpy". Sannan ya buɗe fridge ya ɗauka natural madarar shanu da ake kawo masu jarka guda duk bayan sati biyu zuwa uku daga ƙauyen mahaifin su, tsiyaya yayi a Tumbler sannan yayi waje, a dinning ya zauna tare da zaro wayar sa nan yaga missed call ɗin Ace Amma bai maida Kiran ba, ya cigaba da scrolling ɗin wayar yana kurɓar madarar har ya gama sannan ya tashi ya bar tumbler ɗin a wurin. Sama ya wuce ɗakin mahaifiyar sa saboda yadda yaji gidan nasu shuru yasan Azhar tana wurin aiki, kasancewar ta babbar yar jarida a BBC, Najmah kuwa yasan tana makaranta itada Bushra. Kamar yadda yayi tunani kuwa hakan ne zaune ya sameta a ɗaki tana waya, wuri ya nema ya zauna har ta gama sannan ta kalle shi tana ƙara faɗaɗa fara'ar fuskarta ta ce, "Jawaad ka tashi". A hankali ya ce, "Na tashi Ammie jiya na dawo late kunyi bacci". "Eh kwarai Kam Najmah ta gaya min, dan lokacin Da muka tashi nake tambayar ta Bushra tace ai a wurin ka ta kwana, shine nace ta je ta ɗauko ta tazo su shirya su tafi makaranta, ya aikin naka Ina fatan ba wata matsala". "In Sha ALLAH Babu Ammie saidai ki tayamu da addu'a Dan muna kan wani aiki ne me wahala sosai". "Karka kirashi me wahala Jawaad domin duk yadda ka ɗauki Abu haka zai zo ma, in ka ɗauke shi da zafi to fa a tafashe zai zo ma haka in ka ɗaukeshi da sanyi to fa a kankara zai zo ma. Kawai abinda zakayi shi ne ka sanya a ranka zaka iya, ka sani Kai ɗin fa jinin soja ne sojan ma kamar mahaifin ka brigadier general Aleeyou barkidɗo, Wanda ya bada ransa wa ƙasar sa Wanda ya sayar da rayuwar sa akan ya bari a cigaba da yaɗa ɓarna, Wanda ya zaɓi mutuwa akan ya take gaskiya kuma ya bari a cutar da Al'ummar sa, Wanda ya zaɓi yin fito na fito da duk me shirin kawo tashin hankali da tarzoma a ƙasarsa, inaso past life ɗin mahaifin ka ta zama inspiration ɗin ka". Girgiza kansa yayi Yana sake Jin wata ƙwarin guiwa na shigar sa sannan ya ce, "in Sha ALLAH Ammie na gode da tunasar wa ". "To ko Kai fa, Amma dai da gani baka samu breakfast ba, Dan nasan an kwashe komai na ɗauka kafin ka tashi zasu gama lunch ai". "Ammie Ina so na samowa Bushra nanny saboda kinga Azhar ba zama take ba saboda yanayin aikin ta, Najmah Kuma tayi ƙanƙanta ace an bar ragamar rainon Bushra a hannunta sannan ga makaranta"..........Ya shigo da wata maganar a maimakon Wadda ammie tayi masa. Shi fa haka yake ba komai yake amsa shi ba kuma karku ce akwai Wanda yake zaɓa yakewa haka a'a general ne, dan shi ko magana idan tayi tsawo to baya bi ta kanta haka ko a chat in dai zaka masa VN to fa bazai buɗe ba Amma typing komin yawansa zai karance Maka ne kasa da mintuna bakwai ko biyar, ba fa dan karamin note ba, a'a irin wanda zakaga read more ashirin ko sama . Shuru Ammie tayi can Kuma ta ce, " A maimakon Nanny me sa baza ka samo mata uwa ba Jawaad ya kamata Ka haƙura ka manta da abinda ya faru a baya, yau tsawon shekaru kusan uku kenan tun yarinyar nan batafi awa ɗaya a duniya ba. Ka haƙura da ita tunda har kaga tsawon lokacin nan bata waiwayeku ba ya kamata ace ko wani irin so kake mata ka haƙura ka aika mata da takardar ta, ka manta da ita ka auro wata da zata maye ma gurbinta ka fara sabuwar rayuwa". Sai da ya gama sauraran ta sannan ya ce, "Ammie ina so in gaya Miki dama wancan mutumin Amb. mudassir ya mun magana kan Azhar ya kuma ce ita tace ya tuntuɓe ni, ya nemi mu basu rana zasu zo tambaya so nace ya saurareni, ya kike gani?"..........Wani irin kallo take jifan sa dashi kafin ta ce, "Jawaad baza ka taɓa canzawa ba ko? Kai dai duk lokacin da za'ayi gabas Kai yamma zakayi lokacin da za'ayi yamma Kai Kuma gabas zakayi, naji batun Azhar Amma ya Ina ma wata maganar kana kawo min wata". A hankali ya sauke numfashe tare da faɗin, "Ammie ba wai naqi sakin matar can bane saboda ina fatan wata rana na dawo da ita, a'a haka kuma ba wai naqi aure bane dan wani abu sai dan kar na huce haushi na akan Wadda bataji ba bata gani ba dan har yanzu ban huce daga abinda mahaifiyar Bushra tayi ba"........ Ya faɗa mahaifiyar Bushra ne dan shi ko sunan ta baya son ji, har godewa ALLAH yake da Bushra ta ɗauko komai nasa sai farin ne kawai na mahaifiyar, matar data zaɓi ruɗin duniya sama da ƴar ta, matar da taso zubda gudan jinin ta tun kafin yazo duniya saboda wani buri nata na banza, matar da ta guji ƴarta tun kafin taji duminta bare tasan abinda ta haifa dan shi ya tabbatar in dai ba'a bakin nurses ba mahaifiyar Bushra bata san me ta haifa ba, tunda ko ganin ta batayi ba tace a miqa masa abinda yake nasa saboda ma karta ganta ta shiga ranta. Murmushin takaici yayi saboda abubuwan da ya shiga dawo masa a kwakwalwar sa kamar yanzu Abun ke faruwa. "Shikenan naji, Kuma nasan komai me wucewa ne wataran Kai da kanka zaka kawo min Wadda kake so, Amma abinda zance ma shi ne ba sai ka kawo wata nanny ba Bushra zata dawo ƙarƙashin kulawata in Sha ALLAH dama kuma ai ba'a hannun Najmah kaɗai take ba, Dan haka karka damu ka tsaida hankalin ka wuri ɗaya kawai your baby is safe"......... Cikin gamsuwa ya gyaɗa mata Kai sannan ya miqe da faɗin, "Zanje nayi sallah"..........."To shikenan sai ka fito, ka fa fito kayi lunch". "In sha ALLAH ". Ya faɗa yana barin ɗakin. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______59 SWORD OF FIRE KINGDOM🔥 Ƙaton prison ne daga can karshen yankin masarautar, prison ɗin zagaye yake da manya manyan katti ko riga ta kasa sakuwa a jikinsu sai sword da kuma Archery da suka rataya a wuyansu da kafaɗa in banda muzurai ba abinda suke. Ƙofar wani cell aka buɗe, wani kyakyawan matashin saurayi ne ya fito daga ciki, kallo ɗaya zaka masa kasan baya farin cikin fitowar sa daga jail ɗin, ba kuma alamun nadamar abinda ya aikata aka kawo shi wurin a tattare dashi. Honey skin tone ne dashi wanda hakan yasa na fuskanci duk yawanci kalar mutanan masarautar haka suke sai wasunsu da suka kasance dark brown, yana da broad chest, well built body, sharp eyes, pointed noes, sensible ears and strong arms. Ahmad Haisha'an kenan yaro ne matashi da bazai haura 28 - 30 years ba a duniya, shi ɗin ɗane ɗaya tilo ga amintacciyar baiwar Queen Hirut mai suna Muru wadda a duk duniya ba abinda ta tsana sama da Haisha'an, duk da tana mahaifiyar sa ba komai tsakanin su sai kyara da tsangwama. Tun yana ƙarami Queen Hirut tasa aka kashe Mahaifin sa saboda kawai sun gano shi ɗin musulmi ne kuma baya bin Addinin su na bautar rana, ya taso cikin kaɗaici, shi kaɗai yake rayuwar sa sai abokin sa guda ɗaya Omaine, shi ma ɗa ne ga wani bawa a masarautar. Haisha'an ya qullaci abinda akawa mahaifinsa saisa ya tsani Queen Hirut fiye da komai a rayuwarsa sa, sosai yake takun saqa da ita da kuma mulkin nata, baya shakkar ya tsaya gabanta ya faɗa mata magana kowacce iri ce tun bai kai haka ba, wanda hakan yasa rabin rayuwar sa a prison yayi. Mahaifinsa a ɓoye ya shiga musulunci kuma a ɓoye yake aiwatar da addinin amma shi Haisha'an a bayyane yake aiwatar da addinin dan dama shi tunda ya taso a cikin Musulunci ya taso saboda ko da aka haife shi sai da mahaifin sa ya yi masa Adhan a kunnen sa a ɓoye, haka kuma ko da ya fara wayo yayi ƙoƙarin ganin ya koya masa duk wani abun da ya shafi Musulunci har zuwa lokacin da aka gano aka kashe shi a lokacin ne kuma Haisha'an ya ɗaura ɗamara ya cigaba da neman ilimin Addini sosai kafin ya fito fili ya nunawa mutanen nasu shi ma musulmi ne kamar mahaifinsa nasa, sai dai abun Mamaki Queen Hirut ta kasa sawa a kashe shi kamar yadda akawa mahaifinsa sai dai tasa a kaishi prison a bashi horo sannan ta fakewa mutanen ta da cewa Haisha'an yana da amfani a masarautar ko dan aikin da yake yi tuquru, saboda in ya tashi aiki kamar bai san ciwon kan sa ba, aikin da mutum goma zasuyi zai iya haɗawa a lokaci ɗaya, Amma a baɗini ba hakan bane, ko ma miye zamuji a gaba. WANNAN KENAN. Bin Custody Officer ɗin yayi zuwa office ɗin su suka bashi kayayyakin sa ya canza ya ɗauki na ɗauka ya juya ya fita ba tare da yace dasu komai ba, a bakin qatuwar Ƙofar gate ɗin prison ɗin ya tarar da Omaine tsaye yana ganin sa ya taho da sauri cikin farin ciki ya rungume shi tare da faɗin, "Alhamdulillah ɗan uwa, ina tayamu murna a wannan karon ma, kasan da naji shiru har na fara tunanin ko na gota lissafi ba yau bane"....... Ya ƙarashe yana ɗagowa tare da bin Haisha'an ɗin da kallo, hannu Haisha'an ya kai kan kafaɗar Omaine ɗin ya ɗan bubbuga sai kuma ya ɗage kansa sama yana bin ko ina da kallo ganin canje canjen da aka sake samu, murya can ƙasan maqoshi ya ce, " Har yanzu matar nan bata mutu ba?"....... Da sauri Omaine ya rufe masa baki tare da riqo hannun sa ya fara ƙoƙarin jansa saidai ko motsi bai yi ba kamar wanda aka sassaqa ganin haka yasa Omaine ɗin faɗin, "Ka taimaka mu bar ƙofar prison ɗin nan Haisha'an, ka rufa mana asiri in dai ba so kake ka sake komawa ba".......... ɗage kafaɗunsa yayi cikin halin ko in kula ya ce, "Can yafi daɗi ai Omaine, saboda ƴancin da zaka samu a can babu shi anan". Matsowa yayi kusa dashi tare da yin ƙasa da murya kamar me raɗa ya ce, "Dan ALLAH ka bar wannan zancen Haisha'an, ba ta yadda mutum zai ji dadi ya kuma samu nutsuwa yana garkame"..........Ta gefen ido ya kalli Omaine ɗin da duka dukansa a iya kafaɗar Haisha'an ɗin ya tsaya. "Kai yanzu da kake saken wani daɗi kakeji? Wace nutsuwa kake da ita? a yau ƙaramin kuskure kana iya yi ko iyayen ka ko wani mafi soyuwa a gareka ba ɓata lokaci ya baqunci lahira, Matar da babu imani a ranta, matar da ta maida ran mutum kamar ran kaza bayan ALLAH shi ne kaɗai me rayawa kuma shi ne me kashewa, amma kuma su suce su ne masu kashewa a lokacin da suke so? Ni da kai maza ne kuma mun san girman da ALLAH ya bamu, ya bamu matsayi na masu kulawa da shugabanni (Qawwamai) a kan iyalansu da al'ummarsu tare da jagoranci a gare su, amma ka duba yadda rayuwar mu ta kasance a Matsayin bayin su wanda basu da daraja a idanunsu". Shi dai Omaine bai bi ta kan zancen ba duk da yasan Haisha'an ɗin yana kan gsky, amma yasan yana amsa masa to fa zai tayi ne har ALLAH ya kawo wanda zai tseguntawa Hirut yanzu azo a samu matsala, gashi shi ko zuwa akayi aka ce mata ya faɗi kaza to indai ya faɗa ɗin a gabanta zai maimaita, dan haka Omaine ya ce, "Yanzu ina muka nufa?". "Zanje nayi wanka first sai mu zagaya bayan gari"......... "To abinci fa?". Omaine ɗin ya sake tambaya. Kallon gefen ido yayi masa suna cigaba da tafiya, kamar ba zai ce komai ba dan an dau kusan minti uku kafin ya ce, "Ai a wancan gidan sai na fara cin abinci na qoshi sannan a rarrabawa saura, tunda babu shegiyar da zata mulkeni saboda ni ne sarkin su a ciki"...........Ya faɗa cikin halin ko in kula shi kuwa Omaine jan bakin sa yaja ya zuge ganin Haisha'an ɗin kamar ma ƙara ƙeƙashewa zuciyar sa take. Ɓangaren da ya kasance na ya'yan bayi suka nufa tare da wucewa ɗakin su Omaine ya buɗe suka suka shige. Kan gadon Omaine ya faɗa, shi Kuma Haisha'an ya wuce toilet ɗin bai jima ba ya fito ya bude sip ɗin da kayan sa ke ciki komai yana nan tsaf kamar yadda ya tafi ya barsu, kuma yasan aikin Omaine ne, a gurguje ya shirya saboda lokacin sallar la'asar da ya lura yayi, gaban gadon ya ƙarasa in da Omaine ke kwance ƙafafun sa a ƙasa. "Omaine! Omaine "........ Ya faɗa yana ɗan bugar ƙafar sa, buɗe ido Omaine da ya fara bacci yayi daƙyar tare da faɗin, "Har ka fito ne?". "Eh, Kaje kayi Alwala lokacin Sallah yayi "........ Nasan zakuce shin Omaine musulmi ne? Eh Omaine ya musulunta dashi da wasu daga cikin mutanan masarautar ta dalilin Haisha'an, sai dai su a ɓoye suke komai. Tashi Omaine ɗin yayi ya wuce toilet dan zuwa ya ɗauro Alwala, da wani irin kallon me kama da na tausayi Haisha'an ya bishi, dan daga ganin yadda yake baccin ma kasan irin na wanda yasha aikin nan tuquru ya gaji ne, katse tunanin nasa yayi ta hanyar wucewa ya shimfiɗa musu Abun sallar sannan ya tsaya jiran Omaine ɗin ya fito sannan yaja su Sallar bayan sun idar Omaine ya ce, "To ni dai a gaskiya zan wuce naje na karɓa abinci, Dan kasan fa in dai ka sake aka gama rabo baka je ba to fa Saidai ka jira na dare". Gyada masa kai yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma ya ce, "In ka gama ka same ni a can"........ Da " To". Omaine ya amsa sannan ya tashi ya fita, Shi ma Haisha'an ɗin tashi yayi ya dauka sword ɗinsa da Archery ya rataya sannan ya saka takalmin sa ya fita. Tun daga nesa ya hango wata jar Ƙura data rufe hanya sai wani ƙara ke tashi daga can iyakar garin, ba tare da wani tsoro ba ya doshi wurin yana matsowa sautin kofatun dawakai na Ƙara ƙarfi a kunnuwan sa har yazo daf da iyakar yankin nasu sannan ya tsaya, suma suna zuwa basu ƙetara ba suka dakata a hankali Ƙurar ya fara raguwa, kallo ɗaya ya musu yasan daga Ina ne, ɗaya daga cikin su ne ya ɗaga abun busar sa zai busa kawai yaga kamar an yi sama da abun busar, da sauri ya ɗago idonsa ya sauka kan Haisha'an ɗin da ya sauke Arrow and bow ɗin sa ƙasa alamar shi ya harbi abun busar ya faɗi, kafin suce komai ya ɗaga murya yadda zasu iyajin sa tare da faɗin, " Sarauniya bata nan tayi tafiya, Dan haka in saqo ne Kuna iya bani domin na isar dashi wurin Crown princess".......... Kallon juna sukayi tare da danyin magana a junan su sannan ɗaya daga cikin su ya matso gaba kaɗan da dokin sa tare da ɗan kwantowa ya miqowa Haisha'an ɗin takardar dake hannun sa, shi ma takowa yayi Amma be ketara ba daga nan ɗin ya miqa hannu ya ƙarɓa shi Kuma mutumin ya juya akalar dokinsa sauran suka rufa masa baya . Ɗaga takardar yayi ya kalla tambarin eagle dake jiki, rigar sa ya ɗage ta baya ya zira ta sannan ya juyo daidai isowar Azal tana sanye da skinny leather jeans tare da wata armless riga ta fata data kai mata har guiwarta, ƙafarta sanye da boot sai Daenerys's dress data ɗaura akan kayan nata tare da sanya hular rigar da akayiwa bakinta ado da gashin farar wolf. Deanerys dress wata riga ce me kamar alkyabba amma bata da kaurin alkyabba tana da ɗan maballi daga wuya. Tafiya take cikin gadara da nuna isa gefen ta Siberian tiger ta ce me suna Simba bayan ta Kuma bataliyar yan rakiyar ta ne, a gaban Haisha'an ta tsaya suna kallon cikin idanun juna wanda ba abinda ke fita daga cikin idanun kowannen su sai tsantsar tsana wa junan su, dawo da kallon ta tayi kan hannun sa ɗaya dake riqe da Arrow, Bayan sa ta kalla inda har lokacin akwai sauran ƙurar da bata gama washewa ba, bin wurin tayi da ido kamar me nazari kafin ta dawo da kallon ta kansa da Kai ta nuna masa bayan sa sannan cikin gadara ta ce, " Kai meke faruwa anan?"......... Juyawa yayi ya kalli bayan nasa kana cikin rainin wayo ya ce, " A Ina ?"......... Wani kallon banza ta masa kafin ta ɗaga sword din ta Wanda yake daban dana kowa a kyawu da ƙarfi, Dan daga Sandar Queen Hirut sai sword ɗin ta saboda su komai nasu daban ne dan an riga an gama dafa shi da siddabaru. A kan wuyan sa ta Ɗaura sword ɗin tana wasa dashi kafin ta nufi fuskar sa, a kan kumatun sa ta tsaya tare da juya fuskar sa tana taku a hankali har ta Juya Haisha'an ya koma yana facing iyakar garin nasu ita kuma tana tsaye gefensa, Kan kafadar sa ta sauke sword ɗin nata kafin ta ce, "Can nake nufi". "Lion ne da Bengel tigers suka yi rikici "......... Ya faɗa idonsa akan yatsun ƙafar sa da yake motsawa a hankali. Ɗan shuru tayi can Kuma ta janye sword ɗin nata ta juya ta fara tafiya mutanan nata suka rufa mata baya. Bai juyo ba sai da ya tabbatar sun bar wurin sannan shi ma ya waiwayo, right side ɗin sa ya nufa, yayi tafiya me ɗan nisa kafin ya isa kan wani qaton dutse me matuƙar tsayi da faɗi dan kusan shi ya zagaye rabi garin ta bangaren gabas kuma a ƙarƙashin sa ne kurangina yake sassaqaqqen gunkin su Queen Hirut, zama yayi a kan dutsen yana kallon view ɗin masarautar tasu kafin ya sanya hannu a bayansa ya zaro takardar ya buɗe. Lokacin da ya gama karantawa ɗaga takardar yayi ya rabata gida biyu sannan ya sake rabata huɗu, kuci kuci yayi da ita kafin ya turata bakin sa ya taune, tsaki yaja yana faɗin, "Ku Kuma in kunji shuru ku ɗau matakin da ya muku. ALLAH yasa ma aurellon ɗin ta yiwa garin tashi ɗaya kowa ya huta........" Bai ida rufe bakin sa ba yaga yar Aiken fada ta fito da masu mata rakiya akan giwayen su sunyi hanyar fita daga yankin nasu, da kallo ya bisu kafin ya sake jan tsaki ya ce, " Yan wahala kawai"............ " Su wa?". Juyowa yayi wurin Omaine da ya ƙaraso ya nemi wuri kusa dashi ya zauna, "Ina zasu ne?"......... Ya tambaya yana dawo da kallon sa gabaɗaya kan omaine. "Ina tunanin zasu tafi maida takardar raddi ne wa Aurellon"..........."Dama sun aiko da wata takardar kenan?". "Sun Kara aiko wata ne?".......... Shi ma omaine ɗin ya maida masa tambayar yana kallon sa, ɗauke kansa yayi da faɗin, "Ita kuwa waccan matar dake rawar jiki ko da yaushe tana kan gaba wurin assasa wuta wata rana sai ta faɗo ta karye, munafukai kawai, wata cocumber da ita kamar wadda aka dire"......... Dariya sosai Omaine ya shiga yi shi kuwa Haisha'an ko murmushi baiyi ba kamar ma bashi yayi maganar ba sai arrow ɗin da ya zaro ya shiga zane zane akan dutsen kamar me haɗa wani abu. "Amma whl Haisha'an baka da kirki, yanzu me matar can tayi ita fa kawai yar aike ce". Ba tare da ya daina abinda yake ba ya ce, "Ai ban ma fara rashin kirki ba whl, yanzu ba mai Ƙara kulle ni dama can ba wai ikon ta ko ƙarfin mulkin ta bane yasa take sawa a rufeni, dan da na ga dama ko hour ashirin da huɗu ba zanyi ba zan fito, to yanzu ba zan ƙara komawa ba na fito kenan, amma ɗaya bayan ɗaya zanci uban duk wanda ya sake ya shiga harkata, itama wanna me zubin shansherar tara ta nake, duk lokacin da ta kai ni bango sai na shayar da su ruwan mamaki ". "Kaga Haisha'an Ina rabaka da li'iliti Azal, kasan yadda kaji sunan ta Azal to whl idan kuka haɗa hanya, Azal zata zame Maka a rayuwa. Ni dai kawai kayi hakuri Ka ɗauke idonka daga kan lamuran masarautar nan". "Inah bata neme ni ba ko?". Ya tambaya, sunkuyar da Kai Omaine yayi saboda baisan abinda zai faɗa masa ba game da tambayar da ya masa na cewa ko mahaifiyar sa ta neme shi. "Shikenan ba sai kamin ƙarya ba Omaine na samu amsa ta, bakomai tashi muje ni in ganta". Kamar omaine zai ce Kar yaje sai Kuma yayi shuru saboda yasan ko sunje ma wulakanta su zatayi taita faɗar maganganu marassa daɗi akan Haisha'an ɗin kamar ba ita ta haifeshi ba, Amma ba yadda zaiyi bai isa ya nunawa Haisha'an ɗin baya san zuwa wurin mahaifiyar tasa ba dan yasan hakan zai iya sawa su samu matsala a abotar su. Dan Haisha'an duk da mahaifiyar sa bata son sa shi yana son ta, duk da ta tsaneshi shi yana kaunar ta, duk da ta wofanta da rayuwar sa shi Kuma tana zuciyar sa, akanta zai iya samun matsala da kowa. -----------------------√ Sahnish na nan tsaye shi da Shazeen har baba Ilerika ya iso. "Suna Ina?". Ya tambaya. "Suna ciki"......... Sahnish ɗin ya amsa masa, kallon cikin police station ɗin yayi kafin ya ce, " Akwai yan kuɗaɗe a wurin ka ne?"......... Da sauri ya laluma aljihun sa gabaɗaya kuɗin kasuwancin na sa ya ɗauko dubu sha biyar ne ya miqa masa, karɓa yayi sannan ya ce, "Biyoni muje"........ sai da ya tsaya ya zuge biyar ya canza musu aljihu ba tare dasu Sahnish ɗin sun lura ba sannan ya shige. " Salamu alaikum"....... Baba ilerika ya faɗa lokacin da ya shiga. "Wa alaikum Salam"......... Suka amsa suna binsu da kallo idonsu na sauka kan Sahnish suka haɗe rai, Constable Junaid ya ce, "Kai wai ba munce Kaje bane sai gobe ". Baba ilerika ne ya amshe da faɗin, "Ai tare muke officer, dashi da Wadda kuka tsare ɗin ai duk ya'ya na ne, a taimaka mana mu ganta Dan ALLAH officer, ya min bayanin komai Kuma in Sha ALLAH da safen zamu zo muga DPO amma yanzun muna so mu ganta"............"Ka ga baba na riga na faɗa masa ba zai yiwu ku ganta ba sai an sanar da DPO". "Shikenan ba damuwa, amma officer Ina son ganin ka ya za'ayi ne ?".......... Kallon abokan aikin nasa yayi kafin ya ce, " Muje daga waje"..........ya ƙarashe yana fitowa daga bayan kantar suka fita waje tare da baba ilerika, kuɗin ya zaro daga aljihunsa a dunƙule, yana faɗin, " Ranka ya daɗe ga wannan ka sa kati, ɗan minti biyar ma yayi yawa"........ Ɗan basarwa yayi da faɗin, "Ahh ahh ka barshi kawai, muje tunda minti biyar kace". "A'a baza ayi haka ba Ranka ya daɗe ka karɓa ɗin dai ba yawa".......... Ya faɗa Yana zura masa a aljihu, washe baki yayi kana ya ce, " Ai baba shi yaron naka ne duk bai yi wanna bayanin ba, yazo ya dage sai ya ganta mu Kuma kasan dole mu bi dokar DPO ". "Karka damu officer kasan Yara, abinda yasa ma aka samu matsala bai Kirani bane da wuri"........Ya faɗa Yana bin bayan Constable suka wuce ciki, jan rigar Sahnish yayi da faɗin, " Muje "....... Binsa sukayi inda ya nuna musu wani table da faɗin su zauna bari ya fito da ita. Hushaima kuwa tana tsaye cikin cell ɗin banda sauro ba abinda ke garzar ta ga wurin gabaɗaya daga ta zauna sai kuɗin cizo ya fara gallara mata gashi ba ruwa ba abinci, Amma tsabar zuciya ko yunwar bata ji kawai tunanin ta yadda zata rama wanna cin mutuncin da yarinyar ta mata, ko tunanin tana raye ko ta mutu batayi ba. Kai jamaa ni kaina zuciyar Hushaima ta fara bani tsoro fa, maganar Constable ta ji Yana faɗin, "Ke fito ga Yan uwanki sunzo ganin ki, minti biyar kuke dashi"......... Batace komai ba ta fito ya wuce gaba tabi bayansa, da gudu Shazeen ta nufi wurin ta tare da rungume ƙafafunta tana faɗin, "Aunty Hushaima Ina kika tafi kika barmu yau mun Sha wahalar neman ki ni da yaya"......... Murmushin yaqe tayi tana riqo hannun Shazeen ɗin tare da kallon Sahnish da ya karaso wajen su. " Hushaima ya akayi hakan ta faru?"......... ɗauke kanta tayi tana kallon wani wuri kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta shiga bashi labarin abinda ya faru a taƙaice, kafin ta dawo da kallonta kansa. "Whl summa tallahi na rantse da Ubangijin sammai da ƙassai Sahnish yarinyar nan sai tayi nadamar rayuwarta, tunda ta sake ta ƙetara iyaka ta sai tasan ni daban nake da sauran mutane, sai na rama ramuwa mafi muni, sai na sata kukan da sai hawayen ta ya qafe"........... Ta yi Maganar cikin qunar zuciya. Da wani irin yanayi Sahnish yake kallon ta shi ya san wacece Hushaima bata rantse bama aka ɓata mata saita rama ballantana wannan da tayi rantsuwa me girma haka, sai kawai ya rasa abun cewa sai kallon ta da yake kamar wata hoto, Baba ilerika da yazo wurin ne ya ce, "kiyi hakuri Hushaima". Wani one side smiling tayi tare da juyawa wurin Baba ilerika ta ce, "Baka san abinda aka min bane baba ilerika, amma bakomai ina ɗan sandan nan, Sahnish kaje ya baka jakata ka ɗau makullin ɗaki na saboda Shazeen ko zata ɗauki kayanta saboda na makaranta....... kaga wani abu zai shiga kunnen Ka"........Ta ƙarashe tana ɗan matsawa ta kama kunnen kamar zata cire masa wani abu a hankali ta ce, "Akwai kuɗi a jakar ku ɗauka ko zaku buqaci wani abu"........ Kwata kwata Baba ilerika bai ankare magana Hushaima ta wa Sahnish ɗin ba . Constable ne ya zo yana faɗin, "Lokaci fa yayi"........." Eh ai yanzu zasu wuce"........ Hushaima ta faɗa tana gyarawa Shazeen hijab ɗin ta ta kalli Sahnish da faɗin, "Ka kula da kanka kuma ka kula da Shazeen". "Hushaima yanzu anan zamu barki a gaskiya bazan iya tafiya ba saidai a haɗamu a cell ɗin duka".......... Sahnish Ya faɗa Muryar sa na karyewa. A dake ta ce, "Kai kallo nan karka sake kace zaka min kuka, namiji kake ko baka sani ba ne, ka nuna min haka ta hanyar ƙoƙari na fita anan wurin, dan shi ne kaɗai ƙaunar da zaka nuna min ba wai ka tsaya zaka min kuka ba". "Wai tun yaushe kike nan Hushaima?".......Baba ilerika ya tambaya. "Tun wuraren 12pm ne"........ Ta bashi amsa sharply. "Kaii abu baiyi daɗi ba sam, yanzu tun wannan lokacin kike nan ba ruwa ba abinci". "Zanje na siyo mata wani abu yanzu".......... Sahnish ya faɗa tare da duban Constable ya ce, " tace ka bani jakarta in ɗauki dan makulli a ciki ". "To Shazeen ga yaya duk abinda kike so ki fada masa ni yau bazan kwana tare da ku ba kinji".........."Ni gaskiya bazan bi yaya ba aunty Hushaima kizo mu tafi tare dake"........ Ta ƙarashe tana jan hannun Hushaiman alamar tazo su tafi. "Wuce wuce muje"......... Constable ya faɗa yana tisa ƙeyarta, bata ƙara cewa komai ba sai kallon Sahnish da tayi sannan ta juya ta wuce . *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 60 & 61 Ɗauke kai Sahnish yayi yana hana raunin zuciyar sa bayyana saboda maganganun Hushaima. Suna tafiya da Constable zai maidata cell ta ce , "Akwai kuɗi a jaka ta ka ja qanin nawa gefe ka bashi su duka kace ya baka wani abu a ciki".......... Take constable ya sake fuska harda faɗin, "Ba matsala in da akwai abinda kike buqata ma ki faɗa sai a kawo".......... Bata ce dashi komai ba ta yi shigewar ta. Komawa yayi wurin su tare da kiran Sahnish ɗin wani office, binsa yayi suka shiga ya ɗauko jakar tare da sa hannu ya ɗauko kuɗaɗen kusan dubu dari uku ya bashi tare da ɗan makullin sannan ya ce, "Tace ka bani wani abu a ciki"......... Ba musu Sahnish ya zaro dubu talatin ya bashi, hararar Sahnish ɗin yayi kafin ya ce, "To jeka dama shi ne abinda tace a baka ai"........ Saka kuɗin Sahnish yayi a aljihu sannan ya juya ya fita wurin su baba ilerika tare da faɗin suzo su tafi. Sai da suka fito ya ce, "Baba mun gode sosai da kulawar ka ALLAH ya saka da alheri". "Bakomai Sahnish yanzu ina zaka ne?"......... Faɗar Baba ilerika a daidai lokacin da suka fito daga station ɗin, tirjewa Shazeen tayi tare da fasa kuka tana nuna ƙofar station ɗin da hannunta. Sahnish da shi ma yake jin kamar ya fashe da kukan ya daure ya ce, "Shazeen yanzu zamu dawo mu tafi da ita ai, ki daina kukan kizo mu tafi "........."Ni yaya ka barni anan wurin aunty Hushaima kaje ka dawo"........."Ah ah Shazeen nan wajen akwai karnuka masu cizo, kizo dai muje mu dawo"......... Sai dai Firr Shazeen taki tafiya a lalle sai dai a barta a wurin Hushaima ko kuma a fito da ita su tafi. "Kaga Sahnish kana ƙara ɓata lokaci kuma kaga dare yayi kar ka rasa abinda zaka siyawa Hushaima ɗin, azo kuma ta kwana bataci komai ba ka ɗauki yarinyar nan mu wuce kawai"........ Shawarar baba ilerika Sahnish ya ɗauka ya sunkuya ya ɗauki Shazeen tana tirjewa tana ihu suka wuce. "Baba a ina kake tunanin zamu samu abinda za'a siyawa Hushaiman ". "Ai Sahnish inaga yanzu saidai ka siya mata abun kanti kawai dan whl yanzu baza ka samu kowa ba sha biyu fa saura".........."To me za'a siya mata a kantin?". "Ka siya mata ko kifin gwangwani da biredi ma "..........." To". Sahnish yace sannan suka cigaba da tafiya har suka samu wani kanti suka siya mata harda ruwa da maganin sauro sannan suka koma suka bawa Constable Junaid ya kai mata. Abun hawa Baba ilerika ya tsaida musu sannan ya ce, "Sahnish kana da yar dubu uku haka ?".......... Saida ya shiga tuk tuk ɗin ɗauke da Shazeen da ta sha kuka ta gaji harta fara bacci baiwar ALLAH. Ya ce, "Ba gida zaka bane Baba?". "Ah ah dama Kai na tsarewa abun hawan saboda ga yarinya a hannun ka karka wahala".......... Hannu Sahnish ya saka a aljihu ya zaro dubu biyar ya bashi, karɓa yayi tare da faɗin, "Ah tou madallah godia nake Sahnish, in kun ƙarasa zan kiraka naji kunje lpy". "To". Sahnish yace sannan ya bawa me tuktuk ɗin umarnin tafiya. Ko da suka ƙarasa gida ɗakin Hushaima ya buɗe suka shiga ya kwantar da Shazeen sannan ya zauna gefenta dan shi kam kwata kwata ba ma ya jin baccin, tashin hankali yayiwa zuciyar sa qawanya tunani kawai yake yadda za'ayi ya fito da Hushaima, wanna wace irin baqar Rana ce? ko da wasa bai taba zaton akwai ranar da Hushaima zatayi kwanan cell ba, yana cikin wannan yanayi kiran Baba ilerika ya shigo Wayarsa kamar yadda ya faɗa kira yayi yaji sun isa gida lpy sannan ya kashe. Shi dai Sahnish yadda yaga dare haka yaga rana da safe ya tashi Shazeen ta yi shirin makaranta ya samo mata abinda zata karya dan shi bayajin akwai abinda zai iya sawa cikin sa bayan Hushaima na can kulle bataci komai ba. Yana miqa Shazeen makaranta ya wuce police station ɗin duk da sunce sai 10am DPO zai shigo hakan bai hanashi zuwa da wuri ba, tsayawa yayi ya saya musu kunu da ƙosai sannan ya wuce ciki, samu yayi su Constable na shirin shifting wasu zasu shigo, nan ya sanar da Constable Junaid yana son yaga Hushaima Sannan ya bata abun kari, ba musu Constable ya buqaci ya ɗanɗana duk abinda ya kawo kamar yadda doka ta tanada sannan ya shiga ya kirawo masa ita. Fitowa tayi idanunta sun ɗan tasa ga alamun rashin bacci a tattare da ita, kwana ɗaya duk tayi wata firi firi da ita kamar kazar mayu Amma Kuma kallo ɗaya zaka mata kasan bata karaya ba Kuma babu nadama ko dana sani a zuciyarta sai ma wutar ɗaukan fansa dake sake ruruwa, cikin ƙoƙarin ɓoye damuwa ta ce, "Sahnish Kun kwana lpy?". "Hmmm da sauki dai, dan ni dai kasa rintsawa nayi kawai tunani na a wani hali kike a wanna wurin". "Karka damu Sahnish Kai dai kawai kayi min ƙoƙari na samu fita daga nan ɗin saboda a fahimta ta yarinyar iyayen ta nada ƙarfi Kuma kasan yanayin ƙasar Nifaz a gurbace take da cin hanci dole zamu fuskanci barazana. Ina Shazeen ta tafi makaranta ko?". "Ta tafi, ga wanna Abun karyawa ne na taho Miki dashi "........ Kallon sa tayi da faɗin, " kai ma ai baka karya ba"....... ɗan shafa Kai yayi kafin ya ce, " Na karya mana". Karɓa tayi tana faɗin, "Haba Sahnish na sanka fa dan haka Ka samu wani abu kaci kafin DPO ɗin ya shigo, kaga ba dama bare na zauna anan muci wanna tare". "Shikenan zan fita in samu wani Abun Amma ba zanyi nisa ba Ina nan ɗin har yazo, ALLAH yasa Abubuwan suzo da sauqi"......... Da haka suka rabu Constable ya maidata cell shi Kuma ya fita Neman abinda zaici. Ƙarfe goma dai dai DPO ya shigo kamar yadda suka faɗa, yayinda goman tayiwa Baba ilerika a ƙofar police station ɗin. Bayan Sahnish ya gaishe da DPO ɗin ya tashi da niyyar binsa, wani Sargeant ya dakatar dashi da faɗin ya tsaya tukunna sai DPO ya shiga office ya zauna, komawa yayi ya zauna a daidai lokacin kuma baba ilerika ya shigo. Bayan sun gaisa da Yan sandan ya ce, "Sahnish ashe Kai kana nan ma tun ɗazu nake gwada wayar ka bata shiga ai". "Ba caji ne baba, Ina kwana ".........." Lpy kalau, to ya ake ciki ya shigo ne?"..........Ya ƙarashe Yana zama kan benci gefen Sahnish ɗin. Kafin Sahnish ya bashi amsa Sargeant ɗin nan ya fito tare da fadin suna iya shiga wurin DPOn. Tashi sukayi suka bi bayan sa har office na DPO, gaishe shi suka yi ya nuna musu wurin zama sannan ya bawa Sargeant umarnin tafiya. "Ranka ya daɗe mune yan uwan Hushaima"........ Baba ilerika ya faɗa. "Okayy kunji abinda ya faru ko?" . "Munji Ranka ya daɗe Amma muna neman alfarmar a bamu bailing ta yaso duk abinda za'ayi ma sai ayi daga baya"........... Baba ilerika ya sake amsa masa. Girgiza Kai DPO yayi da faɗin, "Baza mu iya baku bailing ta ba a halin yanzu domin batun fa da ake yanzu yarinyar da abinda ya haɗosu tana ICU ne ba'a sa halin da take ciki ba. Kuma ma kamar yadda kuka ji mahaifan wanna yarinya sun buqaci a turaku kotu domin a bi musu hakkin ƴar su". "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Ranka ya daɗe baza mu iya ganin ka ba a sasanta". "Baba wanna ba batu bane na sasantawa mu aiki muke don Kare hakkin Al'umma, ƴarka me laifi ce domin attempting kisan Kai tayi". "Ranka ya daɗe whl tsautsayi ne Hushaima ko Dabba baza ta iya kashewa ba bare mutum"......... Faɗin Sahnish cikin matsanan cin tashin hankali. "Yaro wanna ba magana ta bace ni dama abinda yasa na neme ku saboda mu faɗa muku ne ku shirya in da hali ku ɗauka mata lawyer "........... "Yanzu baza a iyayin komai akai ba kenan ranka ya daɗe?". "Baafa za a iyayin komai ba na gaya ma, in Kun gama Kuna iya tafiya"......... Dpo ya faɗa Yana buɗe wasu file file dake gaban sa alamun ya gama magana. Duk yadda Sahnish da Baba ilerika suke tunanin Abun ya wuce nan sunyi iya bakin ƙoƙarin su Amma DPO ya ma ƙi sauraren su wanna Abun ba ƙaramin ɗagawa Sahnish hankali yayi ba. Yana cikin tunanin mafita a ƙofar police station ɗin Amla ta faɗo masa a rai aron wayar baba ilerika ya ƙarɓa ya saka number Amlan dan ya haddace ta tun da daɗewa. Saida ya mata missed call biyu sannan ta ɗaga Amma batayi magana ba, " Hello Amla". "Sahnish!". Ta faɗa dan ta gane muryar sa. "Naam Amla Ina kwana?"......... "Mun tashi lpy Sahnish? Ya Shazeen da Besty?"......... Wani zazzafan numfashi ya furzar sannan ya ce, "Akan bestyn taki ne ma dalilin Kiran, jiya Hushaima a cell ta kwana sun samu dan matsala da wata yarinya a inda take aiki harta fasa mata Kai da kwalba to har yanzu yarinyar bata farfaɗo ba gashi ance iyayen ta sun buqaci a turasu kotu, amma kuma an hanamu bailing ta duk iya ƙoƙarin da zanyi nayi amma ba wani alamun nasara saisa na nemeki". "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, haba Sahnish ya ma za'ayi ka barta ta kwana a cell Dan girman ALLAH, meysa baka Kira ni ba tun a Daren"........ Faɗa sosai Amla take kafin daga ƙarshe ta ce, "yanzu a wani police station ɗin kuke"........."Ta nan wurin Alolo barrack". "Shikenan gani Nan zuwa"........ Ta faɗa tare da kashe wayar. Bari mu ɗanji alaqar dake tsakanin Hushaima da Amla. Hushaima da Amla sun yi kusan shekaru biyu da sanin juna ta sanadiyyar faɗa da Hushaima ta shigarwa Amla a wani restaurant lokacin ita Hushaiman tana aiki a wurin matsayin waitress, tazo kawowa Amla abinda tayi order ne ta tarar suna faɗa da wata yarinya in da ta fuskanci ita yarinyar ce tayiwa Amla rashin kunya ai kuwa taci uban yarinyar ta lakada mata shegen duka, sosai Amla taji daɗin hakan har take maidawa Hushaiman abinda ya faru a ƙarshe ma ta karɓi number ta, dan Hushaima akwai shiga rai in taso, akayi Sa'a kuma itama Amlan tana da son jama'a ba kuma ta da ƙyamar talaka. Bata San komai game da Hushaima ba bayan ƙannen ta biyu sai ko zaman kansu da suke, ko da ta tambayeta game da iyayen su sai taga Hushaiman ta canza mata fuska wanna ya sanya bata Ƙara bi takan maganar ba dan ma karsu samu matsala kamar yadda itama Hushaima ɗin bata taɓa tambayar ta wani abu da ya shafi rayuwar ta ba saidai in ita ta faɗa mata. Wani abu gami da Hushaima yadda bata so a tambayeta wani abu dangane da rayuwar ta haka baza ta tambayi wani ba saidai in ganin damansa ya faɗa da kansa, bata son sanin sirrin kowa in dai ita zata riqe nata. A bangaren mahaifiyar Amla kuwa lokacin data san da alaqar ƴarta dasu Hushaima ba ɓata lokaci tayi mata iyaka da su, Dan ita Macace da bata san talaka Kuma bata da mutunci ko daidai da kwayar zarra bare da taji labari su Hushaiman zaman kansu suke kuma talakawa ne, saidai duk da haka ita Amla bata fasa muamala da su Hushaiman a ɓoye ba domin tana jin su kamar yan uwanta na jini ko dan ta taso ita kaɗai ce a wurin mahaifan ne. Amla ya' ɗaya ce tilo ga Alhaji zawaad Wanda duk wani buri nasu sun tattara sun ɗaura kan ta, sai dai ita tun tasowar ta bata da wani buri da ya wuce ta zama runaway model kuma ALLAH ya cika mata burinta dan yanzu ba qasar da bata zuwa fashion modeling, mahaifanta kuwa sun mara mata baya 100 percent dan duk abinda take so duk muninsa to su ma suna so. WANNAN KENAN. -----------------------√ AURELLON SULTANATE 💎 Ko da ummu ta koma ɗaki tasan baza ta samu me Martaba a yanzu ba dan haka ta Kira wazirin fada yana ɗagawa ya fara mata kirari, bata ce komai ba har ya gama sannan ta ce, " Wazir meke faruwa a fada?". "ALLAH ya Kara Miki lpy, Sheikh yassar ne ya yanke jiki ya faɗi, yanzu haka an tafi dashi asibiti". "Me ya sameshi toh?"..........."Haka kawai Ranki ya daɗe, dan lpy lau ya shigo daga yankin sa na west yazo kawowa Sultan gaisuwa, an ma daɗe zaune ana hira dashi kawai akaga ya bingira, kusan zan iya cewa irin abinda ya faru dasu marigaya Sheikh Sameer"......... A cikin zuciyarta ta shiga maimaita kalmar innalillahi wa Inna ilaihir raju'un kafin tayi ƙarfin halin faɗin, "Shikenan Wazir Nagode". "Hutawar ki lpy Giwar Sultan".......... Ajje wayar tayi kawai tare da dafe kanta tunanin ta yafi karkata kan Anya kuwa Reeslan baisan wani abu ba ko Kuma dasa hannun sa, saurin kauda wanna tunanin tayi kafin ta ɗauki waya ta Kira Imam Maher . "Assalamu alaikum sheikha" .......... "Wa alaikum Salam warahamatullah Imam". "Mun wuni lpy sheikha, ya jikin Maleekh ?"..........." Alhamdulillah imam, da ALLAH ina son ganin ka anjima in Kun tashi daga fada". "To sheikha in yanzu ma kikace sai na Taho ai". "Sai anjiman dai"........... Ta faɗa tare da ajje wayar a gefen ta. Jakadiya ce tayi sallama sannan ta shigo dan duk cikin khadimai ba Wanda ke shigowa har uwar ɗakan Ummu Kai tsaye sai jakadiya saboda yadda ummu ta yarda da ita ta Kuma maida ita abokiyar shawarar ta saboda gaskiya da riqon amanar jakadiyan. A ƙasa jakadiya ta zauna tare da faɗin, "ALLAH taimaki sheikha, ALLAH ya Ƙara lpy da girma ya Kare mana ke". "Jakadiya ya ake ciki, kin bashi ruwan addu'ar?".......... Shuru jakadiya tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa kwata kwata bata so ta ce da Ummu ga abinda Reeslan ɗin yayi saboda karta haɗashi da mahaifiyar sa Amma Kuma to me zatace mata dan baza ta iya yiwa ummu ƙarya ba, Dan haka ta katse shurun da faɗin, "Reeslan Maleekh ya buqaci a barshi ya huta sai anjima a bashi, a takaice dai bai sha ba yanzun". Girgiza Kai ummu tayi da faɗin, "Kai Kai Kai lamarin Reeslan sai ALLAH, ina ruwan shan ruwan addu'a da hutu, tukunna ma shi zai sha ko Rouslan, kaiiii allahumma ka shirya min yaron nan"........ ta ƙarashe Maganar cikin tsantsar damuwa. "Sheikha ko akwai wata matsala ne?"........ Ajiyar zuciya ummu ta sauke tare da faɗin, "Jakadiya wata musiba ke shirin tunkaro mu wadda nake ga idan nayi shuru Abun zai cigaba da faɗaɗa ne har yayi girman da baza mu iya tarewa ba". "Subahanallahi ranki ya daɗe wani Abun ne ya faru?". "Reeslan ne .........." Nan ummu ta kwashe abinda ke faruwa ta faɗa mata, cikin jimami da kuma damuwa jakadiya ta ce, "Ranki ya daɗe bana son ki sa damuwar abun nan a zuciyar ki, inason ki tuna Maleekh fa likita ne Kuma duk mutanan nan da suke faɗuwa a gabansa ne, kinga kuwa zai iya gane wani abu game dasu, misali ko sun samu bugun zuciya na farar ɗaya wanda zai yi wuya ace sun tashi kinga kuwa hakan ba zai zama laifi ba". Girgiza Kai ummu tayi da faɗin, "Jakadiya ba likitan da ya isa yace wannan mutumin mutuwa zaiyi bazai tashi ba sannan kuma ya mutu, ni na fara zargin ko dai Reeslan na da kambun baka ne bamu taɓa sani ba". "To Kuma Ranki ya daɗe ke fa yanzu kikace ba Wanda ya isa yace mutum zai mutu kuma ya mutu, haka ma in kanbum bakan ne ai ba'a iya haka zai tsaya ba, ranki ya daɗe Karki manta fa a hannu na su Maleekh suka tashi idan har da suna da irin wannan Matsalar ni zan fara sani. Kawai abinda nakeso ki kwantar da hankalin ki, ki cire duk wani zargi a ranki mu bar hakan a matsayin lokacin su ne yayi kawai". "Toh Jakadiya ba'a qin ta mutum, Amma nayi waya da imam anjima zaizo inason mu tattauna kan wanna batun". "Ranki ya daɗe tattauna wannan batu da Imam kamar fitar da zancen nan ne, kuma kinsan kina da magauta zagaye dake hakan zai kawo tsirko da tsegumi, kuma ALLAH ya taimake ki nasan ko Sultan zaiso wannan maganar ta kasance sirri, saboda Tsakanin Reeslan Maleekh da Rouslan Maleekh dole a cikin su ne ɗaya zai gaji kujerar nan idan Maganar nan ta fita hakan zai zama barazana ne a garesu"........... Shuru Ummu tayi tana nazarin maganganun Jakadiya wanda suke kan hanyar gaskiya, lalle shawara tana da daɗi, kallon jakadiya tayi da faɗin, "Nagode da shawara jakadiya, kina iya tafiya". Tashi jakadiya tayi da faɗin, "ki huta lpy Sheikha"........... Da Kai kawai ta amsa mata ita Kuma ta juya ta fita. _______________kai Sahel me haka nake gani?".......... Wata dattijuwar mata da zata Kai shekaru 57 ta faɗa cikin firgici da tashin hankali, tana sanye da kayan da kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da dukiya da mulki sunbi jininta, kyakyawar gaske ce saidai ita ba fara bace tarr ɗin nan, sheikha Balqis kenan mata ta biyu wurin Mai martaba. Cikin yanayin maye ya ce, "Um... ummie me ya shi sh shigo dake Nan ne wai, k...ke ke bakya zama wuri ɗaya..aa"..........Ya ƙarashe Yana warfa hannu alamun meysa, baiyi aune ba yaji saukar mari. "Ni zaka tonawa asiri Sahel, duk faɗi tashin da nake a kanka ka rantse sai ka bani kunya ko? Tukunna a gidan uwar wa ka kwaso wannan kayan shaye shayen? Sahel Ni zaka sa a bala'i Sahel?"....... kuka ta fashe dashi saboda takaici da kuma baqin ciki, ita kaɗai ta san ya takeji a zuciyarta. Sosai ta tsaya a kan Sahel don son ya fito a nutsatstse kuma kamili saboda ganin ya'yan Ummu sun ɗauko hanyar da ba zai yiwu a basu mulki ba kasancewar shi Rouslan kullum cikin laulayi yake, shi kuma Reeslan kamar a fiffisge yake ba cikakkiyar nutsuwa a tare dashi wani sa'in, hakan yasa ta dage ganin ita nata ya fito a kamili mai hankali da nutsuwa tunda su uku ne maza in har yan biyun Ummu basu samu ba to shi za'a bawa amma gashi duka ɗaya yana neman watsa mata ƙasa a ido. Dadin dadawa kayan shaye shayen da ta gani a tattare dashi wanda hakan ba ƙaramin laifi bane a Masarautar tasu dan sam ba'a shigo da wani abu da ya danganci maye, duk kuma wanda aka samu da wannan laifin hukuncin shekaru ashirin ne a prison tare da horo me tsanani wannan yasa hankalin ta Daɗa tashi. "Ki... K.. kiyi hakuri to za za a gyara ".......... Girgiza kanta tayi hawaye na cigaba da sauka akan fuskarta, a zuciye ta shiga bincika ɗakin saidai abinda ta gani ya sa a tsorace ta ja baya tare da dafe bango saboda wata Hajijiya data ɗibeta, ƙwayoyin maye ne da Syrup harda cocaine ta tarar a cikin kayansa, ba inda baya rawa a jikinta shi kuwa inaa tuni ma ya tafi bacci, yadda zuciyarta ke bugawa yasa ta rasa addu'ar da zata karanta, sai da tayi kusan minti biyu kafin ta samu bakin karanto Allahumma ajirni fi musibati. Kusan minti uku ta ƙara kafin tayi ƙarfin halin zuwa tasa Hannu ta fara kwashe kwayoyin ta nufi toilet ta zuba tayi flushing, Syrups ɗin ma ta juye ta bisu da ruwa, kwalaben ne dai ta rasa ya zatayi dasu sai ta zubasu a dustbin ta sanya hannu ta ciro ledar ta ƙulle ta Ajje su bayan ƙofar toilet ɗin. Zufar dake goshinta ta share sannan ta ƙarasa gaban washing basin ta wanke fuskarta da hannuwanta ta fito, alkyabbarta ta ɗauka ta sanya sannan ta fita tare da kulle ɗakin ta waje ta sashin ta, tana fitowa khadiman da suke mata rakiya suka rufa mata baya har suka dawo ainahin bangaren nata. "Ki turomin khadima Shafeeqa"......... ta faɗa kamar ba ita ba saboda tayi ƙoƙarin ganin damuwarta bata bayyana ba. Tana shiga ɗakinta ta cire alkyabbarta ta ta nemi wuri kan sofa ɗin dake ciki ta zauna tana sauke numfashi, ba'a fi minti biyu ba khadima Shafeeqa tayi sallama ta shigo tare da zubewa a gabanta ta shiga jero mata kirari, ita kuwa bata ma san tanayi ba tayi zurfi a tunanin da take, sai can ta farga, juyowa tayi ta kalle ta sai kuma ta ɗauke kai tare da faɗin, "Dr Ashir zaki kiramin yanzu, don banajin daɗi ina buqatar yazo ya gwada BP na".........."Subahanallah, an gama ranki ya daɗe yanzu za'a kira shi , ALLAH ya ƙara lpy ALLAH ya ƙara miki nisan kwana"......... ɗaga mata kai kawai take harta gama ta tashi zata fita sai kuma ta ce, "Dawo Shafeeqa".......... cikin hanzari ta dawo ta zauna. "Menene a bakin ki?".........Ɗan susa kai khadima Shafeeqa ta fara kafin ta ce, "Ranki ya daɗe dama... Dama mun samu labari ne cewa an Kai Sheikh yassar Asibiti ranga ranga ba yadda yake, ban sani ba ko kin samu labari".......... Dukda Halin da take ciki sai da ta saki wani shu'umin murmushi kafin ta ce , "kina iya tafiya". "Hutawarki lpy gimbiyar Aurellon"........ Ta faɗa tare da juyawa ta fice. Wayarta ta ɗauka bayan fitar khadimarta ta tare da dannawa wata number Kira ana ɗagawa ta ce, "Abubuwa na tafiya yadda ake so kenan?"........ Daga ɗaya bangaren akace, kwarai Me gadon zinari domin Shi ma ana zaune aka ga ya ɓingira. Murmushi Marar sauti tayi sannan ta ce, "in Sha ALLAH Sahel shi ne zai mulki aurellon sai dai fa wani hanzari ba gudu ba".......... Shuru tayi yayinda na cikin wayar ya ce, "ALLAH yasa ba wata matsalar bace Sheikha"......... Sai da ta nisa kafin ta ce, "Ba abinda nake ɓoye ma, Sahel yana son sanyani a tashin hankali bansan ta ya ya samu........." Duk abinda ya faru da abubuwan data gani a ɗakin Sahel ɗin ta kwashe ta faɗa masa sannan ta ɗora da faɗin, "Yanzu bansan yadda za'ayi a fita da kwalaben nan ba. Abun da yafi ɗaure min Kai shi ne a ina ya samu irin wa'annan kayan bayan irin tsaron dake Aurellon tun daga kan jami'an mu zuwa na'urorin su ? Abun yayi matuqar ɗaure min Kai tare da ban tsoro fa".......... Cikin son ya kwantar mata da hankali ya ce, "Zanyi wannan binciken ta ƙarƙashin ƙasa, sannan kuma batun kwalabe karki damu nasan yadda za'ayi zan aiko da amintattun yara na akwai yadda za'ayi su fita dasu ba tare da an sani ba". "Nagode Kwarai da gaske, saidai wani hanzari ba gudu ba, ina tsoro abinda zai biyo baya tunda Sahel ya fara da haka".......... "Karki damu Sheikha ba abinda zai gagara zan je wurin malamin nan a bashi sunan Sahel ɗin ya masa aikin da za a mantar dashi duk wani abun shaye shaye"........ Cikin farin cikin Sheikha Balqis ta ce, "kai amma Nagode kwarai da gaske, in kai min haka ka gama mun komai in sha ALLAH muna gama waya zaka ga saqo"..........."Ai ni ne da Godia Sheikha, burin mu kawai Sahel ya hau kujerar Aurellon "........ Cikin jin daɗi ta ce, "in sha ALLAH. Sai na jika"......... Ta katse maganar saboda Knocking da ake yi, bada izinin shigowa tayi inda khadima Shafeeqa ta shigo tare da sanar da ita Dr ya ƙaraso yana falo. ____________A wannan lokacin yan Aiken Queen Hirut suka ƙarasowa, Arrow and bow ɗaya daga cikinsu ta saita tare da harbawa daidai saitin wata Bell, wadda ta kaɗa sau uku ƙaran ta ya gauraye kusan rabin Aurellon, ita wannan Bell ɗin ita ke sanar da isowar su, takanas saboda su aka maqala ta, saboda ada idan suka zo saidai suyi ta musu ruwan Arrow a cikin masarautar har sai an gani an shaida isowarsu wanda hakan ke cutar da wasu da dama dan wani lokacin ya kan samu wasu mutanan, wasu su raunata wasu su mutu. Wazir ya ce, "ALLAH ya taimaki Sultan kamar fa wa'ancan mutanan ne suka kawo saqo"......... Girgiza Kai Sultan yayi alamar yaji, juyawa wazir yayi wurin jagoran masu aike da Kuma karɓa ya ce, "Mutallab a aika maza a ƙarɓo saqon yanzu". "Annnnn gama wazirin aurellon"........Ya faɗa Yana tashi sannan ya risina alamar girmamawa ga Sultan kana ya juya ya fita domin isar da saqo zuwa ga mutanan nasa cewa aje a ƙarɓo. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 *NOT EDITED* PAGE _______ 62 & 63 Saida yayi sallar magriba sannan ya shirya ya fita, Direct gidan Amjad ya nufa. Kamar ko da yaushe Philip ne ya taryeshi sannan ya masa iso zuwa falon da suke haɗuwa, ba kowa ciki sai Ace dake dan danna waya ɗagowa yayi Yana kallon su har suka ƙaraso ciki Jey ya miqa masa hannu suka gaisa shi Kuma Philip ya wuce Dan sanar da zuwan Jey ɗin wa Boss ɗin sa. "To ka saki fuskar mana irin wannan muzurai da kake sai kace zakayi karo da ɓauna"....... Ace ya faɗa cikin salon zolaya. Kallon sa yayi ya ɗauke kai, "In ma wata ce ta haɗama zafi to ka qone a can".......... Hararar sa Jey yayi amma bai ce komai ba, kuma daman yasan ba zaice ɗin ba haka ya cigaba da tsokanar sa har sai da ya sashi Magana, "Dan ALLAH ka barni in sha iska, kai bakinka baya ciwo ne?"........."Shaqe ka nayi ne ? Bakina kuma ai ina brush me zaisa yayi ciwo"......... Ƙwafa Jey ya ja tare da zaro wayar sa ya share Ace ɗin. Ɗan serious yaci kafin ya ce, "Ɗazu na kiraka bakai picking ba dama inaso naji ya labari ta wajen ka"........ Ba tare da ya kalle sa ba ya ce, "Me kake sauri ka bari su ƙaraso mana ko Kuma in na faɗa ma Kai zaka isar musu ne ni nayi tafiyata?" ......... Ace bai Ƙara cewa komai ba yaja bakin sa yayi shuru tare da cigaba da daddana Wayarsa. Suna nan zaune har su kiara suka shigo kamar kullum Kiara na sanye da dogon wando da top Mai hannu ɗaya long sleeve, curly brown hair ɗin nan nata zube a gadon bayanta daga tsakiyar kan ta kame shi da pin, ita Kuma Ash tana sanye da white denim mini skirt da black top Wadda daƙer ta rufe cibiyarta, ƙafar Nan tasha high heel kamar zai karye, sai system ɗin ta data riqo, "Excuse".......... Suka faɗa tare da Neman wuri suka zauna , Ace da ba ya rabuwa da tsokana ya ce, "Wannan kwalliyar wa akayi wa?"......... ɗagowa sukayi suna kallonsa, da ido ya musu alama da Jey dake zaune hankalin sa akan Wayarsa yana mata dannar wulaqanci kamar bayaso, Ash ce ta ce, "Da ba ma wanka ne?"......... ita kuwa Kiara wata muguwar harara ta watsa masa ta ɗauke kai. Bai daddara ba ya sake cewa, "Wanka yayi kyau kuma na yaba"........ ya Ƙarashe yana ɗagawa Ash gira ɗaya tare da sakar Mata wani italian killer smirk. Ɗauke kanta tayi kawai dan tasan in ta biyewa Ace zasu tayi ne. Ƙasa ƙasa suke sake tattaunawa kan case ɗin ita da kiara har su Amjad da Philip suka bayyana a falon, miqawa Jey hannu yayi sukayi musabaha sannan ya miqawa Ace ma wanda kasancewar sa cikin su Shi ma ya fara sabawa da hakan, su Ash suka gaishe shi ya amsa sannan ya zauna shi Kuma Philip ya tsaya daga gefen hannun kujerar da yake zaune. "To ya ake ciki? Meye sakamakon da kuke tafe dashi?"..........Ya faɗa yana kallon su. Kiara ce ta motsa da faɗin, "Ni a nawa binciken da nayi shi ne duk mutanan da ake bawa shadow babu cikakken wajen da ake kaisu kawai boarder garin ake kaisu a ajje........." Bayani ta musu kamar yadda tawa Ash da safe sannan Ash ta ɗaura da faɗin, "Ni inaga muyi amfani da trackers da na'urar ɗaukan sauti a jikin mutanan da zamu bashi saboda mu bibiyi inda ake kaisu da Kuma abinda yakeyi dasu, kaga zamu samu hint sosai"........... Ace ya ce, "Amma kuna ganin hakan ba zai bamu matsala ba kuwa?"......... Amjad ne ya amsa masa da. "Kai miye naka binciken ya baka toh?". "Kamar yadda ka sani ne, ba wani haske da zamu iya samu akan Shadow domin tunda kaga kowani ƙasa sunyi bulayin nemen sa sun kasa kasan ba ƙaramin hatsabibi bane, abinda yake ɗaure min kai shi ne shi fa baya karɓar tsoffi sannan baya karɓar yara ƙananu, matasa yake karɓa sannan kuma baya bada fifiko a tsakanin maza da mata, ma'ana wai yace mata sufi yawa a mutanan da za'a bashi ko kuma maza Sufi yawa. Amma ni inaga kawai mu tattara bayanan representative ɗinsa na kowacce ƙasa sanan mu datsi bayanan wayoyin su ciki harda BB lalo, ƙasar da aka fi samun Kira nan zamu fi maida hankali akai". Girgiza Kai Amjad yayi tare da faɗin, "ko Kuma ƙasar da ba'a fiya Kira daga can ba ko?"........ Ash ta ce, "Meysa kace haka?". "Ohh Wai kina tunanin duk abinda zaija attention zai kasance a ciki ne, ai duk inda kikaga komai baya tafiya sosai to nan zamu fi bincikawa. Widad bakace komai ba?"..........Ya ƙarashe yana maida kallon sa kan Jey da yayi relaxing yana binsu da ido, sauke ƙafarsa dake kan ɗayar yayi kafin ya ce, "Kai banji naka bayanin binciken ba da Kuma abinda ka yanke". "Ohh common widad be serious mana, magana ake ta aiki fa in dai har kayi binciken nan let us know what you found out".......... Ɗage kafaɗun sa yayi tare da faɗin, "Well shawarwarin ku sunyi Kuma hakan ya kamata a fara bi Amma idan wanna plan ɗin baiyi ba, Na samo plan B idea". Cikin zaquwa Amjad ya ce, "Go ahead miye plan B ɗin?".......... Ɗan shuru yayi Yana binsu da kallo kafin ya maida kansa ƙasa . Qasa qasa Kiara taja tsaki, cikin yanayin dake nuna ranta ya fara ɓaci ta ce, "Bamu da lokaci Widad ba Wai hira ake ba ko Kuma an nemi wani labari da zaka jawa mutane aji"........... Ɗagowa yayi ya zubawa Kiara ido na tsawon wani lokaci har saida Amjad ɗin ya gaji ya ce, " Kai muke sauraro fa?"......... Hakan ne ya dawo dashi hayyacin sa waskewa yayi da faɗin, "Akwai wata yarinya........" A fusace kiara ta sake cewa, "Me ya haɗamu da yarinya mu da muke kan aiki Kuma?"........ Ace ya ce, "To kin tsaya kinji me zaice ne ballantana ki hau dokin zuciya"........ kallon sa Ash tayi dan tasan da biyu yayi Maganar, wink ya mata yana wata yar munafukar dariya. Jey ne ya cigaba da faɗin, "Akwai wata yarinya a ƙasar Bangkok da nayi bincike ya' ce ga shadow "........... Kusan duk haɗa baki sukayi wurin faɗin , "Yar Shadowww"......... Cikin mamaki Banda Amjad da baice komai ba kawai kallon Jey yake yana nadar bayanai tun ma kafin Jey ɗin ya Ƙarasa magana. "Yes ya' ce ga shadow sai dai tun tana ƙarama ya ɗauketa daga gabansa ya haɗata da wani wanda zai dinga kula da ita ya Kaita can ƙasar tare da nunawa mutane cewa ƴar sa ce". "Shin ita tasan waye uban nata na gaskiya?"....... Ash ta tambaya cikin kullewar Kai. Girgiza kansa yayi da faɗin, "Wannan shi ne iya abinda na samu, ta San Shadow ne mahaifin ta bata sani ba bani da masaniya akan hakan, miye dalilin da ya sa ya ɗauke ta daga gabansa ya Kaita can ban sani ba, kawai abinda na sani shi ne tunda ta shigo bata taɓa barin ƙasar Thailand ba kunga kenan hakan na nufin tabbas shadow yana zuwa ganin ta a sirrance saidai taya? Yaushe? Kuma a Ina? Ban sani ba". Ajiyar zuciya Amjad ya sauke sosai ransa yayi sanyi Kuma yaji hankalin sa ya ɗan kwanta at least suna da second option, wanna shi ne dalilin da yasa yake haƙuri da halayyar Jey saboda kwakwalwar sa na masifar ja. "Ina so ka tura min duk bayanan da ka samu akan ta"........ Juyawa yayi wurin Philip da faɗin, "Kaje ayi duk abinda ya dace a sanya tracker a cikin jikin su da Kuma na'urar ɗaukan sauti da sauransu, ayi connecting ɗin komai yadda ya kamata karka bari a samu matsala, sannan a gama komai daga yanzu zuwa safiya, your time start now". "Yes boss".........Ya faɗa tare da juyawa zai tafi ya dakatar dashi, "Idan an gama ka kawo mana mutumin da Widad ya kawo". "Yess boss".........Ya sake amsawa sannan ya juya ya fita da sassarfa. System ɗinsa da ya shigo da ita ya ɗauko ya kunna tare da janyo stool ɗin dake gefen kujerar sa ya ɗaura akai yadda kowannen su zai gani sannan ya ce, "Za'a Kira BB LALO a shaida masa aiki ya kammala Ina za'a Kai yaran"........ Nan duk suka amince a kirashi ɗin. Kiran sa yayi wannan PA ɗin nasa daya harɓe Akil ya ɗauka nan ya sanar masa shi ne Kuma yana son magana ne da BB LALO, cewa yayi su riqe waya zai Kai masa, bayan ya Kai masa Amjad ya ce, "Good evening sir"........."Evening ya akayi?" "Dama aikin nan ne an kammala Ina za'a kaisu, sannan a Ina zamu ɗauki cikon kuɗin mu"........... Murmushi BB lalo yayi me sauti kafin ya ce, "Ka saurareni Ina zuwa?"..........Ya faɗa tare da kashe Kiran. Da sauri ya juyawa Ash system ɗin tare da faɗin, " Tabbas Kiran waya zaiyi yi sauri ki mana kutse cikin layin nasa"......... Da sauri Ash ta sauko ƙasa gaban system ɗin cikin kwarewa ta fara sarrafa laptop ɗin, cikin second 100 tayi hacking na wayar BB lalo duk da kuwa matakan tsaro masu karfi dake kan wayar tasa amma haka Ash tayi tambari dasu. Kamar yadda Amjad yayi hasashe hakan ne waya yake yi da wani mutum. "Henry ka shaidawa Oga yaran nan Amjad fa har ya kammala aikin sa dan haka suna buqatar a basu location da zasu Kai mutanan da Kuma cikon kuɗin su". "BB LALO wanna yaron daga gani kwararre ne gsky, wato ana binciken sa amma yana cigaba da shuka tsiyarsa lalle za'aje dashi. Kasan Wanda muka bawa aiki tun kafin yaron nan har yanzu basu kammala ba, tabbas nasan shugaba zaiyi farin ciki, abinda za'a yi su kaisu kusa da iyakar ƙasar Nifaz ɗin, kamar yadda aka saba in sunje zasu tarar da kuɗin su a can, zamuyi magana da shugaba abinda ake ciki game dasu zan sanar ma". "Aiit thank you Henry".......... Da haka sukayi sallama cikin sauri Amjad ya ce, "Maza samo mana bayanin wanna mutumin waye shi? Ga dukkan alamu ya na magana da Shadow kai tsaye, ki datsi layin sa shi ma"......... Cikin zafin nama Ash ta fara aikin da Amjad ɗin ya sata gabaɗayansu hankalin su ya dawo kan Ash ciki harda Jey da ya ɗan zakuɗo yana kallo shi ma, kusan mintuna 10 kafin ta juyo ta kalle su a sanyaye ta ce, "Boss baza mu iya datsar number ta sa ba, ga dai number mun ɗauka Amma nayi nayi ba zan iya hacking wayan nasa ba saboda Akwai matakan tsaro masu tsauri sosai akai, sannan ba wani bayani a Kansa kawai dai abinda muka samu shi ne yana Bangkok a yanzu haka"......... Ɗagowa Amjad yayi ya kalli Jey da Shi ma ɗin shi yake kallo kafin ya ce, "Tabbas wanna shi ne mutumin dake riqe da yar tasa"......... Ace ya amsa da, "Ba wai a maganarka, shi ne ma". Dafe Kai Amjad yayi saboda takaicin rashin samun bayani a Kansa da basu yi ba. Yana cikin wanna tunanin Kira ya shigo daga BB LALO bayan ya ɗaga ya shaida masa abinda wancan mutumin ya faɗa kamar yadda sukaji. "Okay sir nan da zuwa safiya zasu isa"........ Amjad ya bawa BB LALO amsa . " Alright ". Ya faɗa tare da kashewa . "Ya kamata mubi bayan Philip domin ganin komai ya kammala da wuri Kuma ba'a samu matsala ba"....... Ash da jikinta yayi sanyi kan case ɗin ta ce, "ka manta baka Kira Sir Richard ka faɗa masa abinda ake ciki ba. Miqewa yayi tare da faɗin, " kuzo muje wayar na ciki"......... ya ƙarashe yana wucewa a sanyaye saboda gabaɗaya kansa ciwo yake masa, baya so a samu matsala ne ko kaɗan saisa hankalin sa ya tashi. Jey ne ya tashi yabi bayansa sannan Kiara tabi bayan Jey, Ash ma miqewa tayi saidai kafin tayi wani taku Ace ya janyo rigarta ta baya, Kasancewar takalmin ƙafarta me tsini yasa tayi baya kamar zata faɗi, riqo waist ɗinta yayi da hannu ɗaya tare da faɗin, "Haka akeyi kuma zaki tashi baki jirani ba"........."Meysa zan jira ka to?". Ta Tambaya tana binsa da wani irin kallo, ɗage kafaɗar sa yayi tare da faɗin, "Saboda ki samu karsashin tafiya ba tsoro"......... kafin ta gama gane me yake nufi yaja hannunta sun nufi ciki. ------------------------√ SWORD OF FIRE KINGDOM 🔥 Lokacin da Omaine da Haisha'an suka shiga gaishe da mahaifiyar sa sun same ta ne cikin shiga ta alfarma kamar ba baiwar ba, durƙusawa sukayi suka gaishe ta, a wulakance ta ce, "Har ka fito kenan". "ALLAH yayi Inah"..........Ya faɗa cikin tausasa murya. "To ni dai ba abinda zan ce ma sai jiki magayi in Kuma baka gaji da zaman can bane, to ka cigaba da nuna iyawa Kai ba komin komai ba dillalin kashi"......... Kansa a kasa ya ce, "in Sha ALLAH zan kiyaye Inah". Wani banzan kallo ta masa kafin ta ɗauke kai ta ce, "Ya rage naka, kar ma ka kiyaye ɗin. Ka je ka gaida Queen Hirut?".......... Shuru yayi dan a duniya ba abinda ya tsana sama da jin sunanta, ya tsani abinda zai haɗashi da ita. Inah ta sake cewa, " To tun kafin taji labarin an sakeka bakaje ka gaishe ta ba ka zo ka shafa min kashin kaji ka ɗauki tsumman kafafuwan ka ka tafi, ka kuma dinga tunawa kai ba koman kowa bane face dan bawa da baiwa". "To Inah"........Ya amsa da to ɗin ba Dan ya so ba sai dan bazai iya mata musu ba, kuma ba zai iya ja in ja da ita ba". "Ku tashi ku bace min da gani".......... Tashi sukayi a sanyaye suka fito, Omaine ya kalleshi, shi dai ba abun yace dashi Kar yaje ba yasan baya kaucewa maganar Inah Kuma yasan in yaje palace ma wani aikin zai ɓaro Yana cikin wanna tunanin yaji maganar Haisha'an ɗin, "Omaine ka jirani anan bari naje na dawo yanzu mu shiga kasuwa muga ko da abinda zamu kama"......... Girgiza Kai Omaine yayi da faɗin, "Bazan barka Kai kaɗai ba Haisha'an duk inda zaka Ina tare dakai".......... "Omaine bana so kowa ya shiga matsala ta dalili na". "Then saika kiyaye matsalar"......... Bai Ƙara cewa komai ba sai hular sa Mai kama da tashi ka fiya naci da ya zaro ya sanya akan lallausan golden hair ɗin sa wanda duk da ba wani samun gyara yake ba amma a kwance yake ya zuba masa ta ko ina kamar wani kwando, na gaban nan ya sauka har kusan kan girar sa, da ya ɗaura farar hular saita haska shi sosai sun yi tafiya kafin su iso main ƙofar castle ɗin, shiga sukayi sannan suka ɗauki hanyar palace suna zuwa masu tsaron ƙofar suka dakatar dasu ta hanyar tura su baya ɗayan ya ce, "Kai Ina zuwa?"........... Omaine ya amsa da, "Zamuje gaida Queen ne". "Ku tsaya a sanar mata"........Ya faɗa tare da shigewa ciki, can yazo yace su shiga. Takalman su suka cire sannan suka shige. Daga tsayen da yake ya ɗan rusuna da faɗin, "Barkan ki da rana Queen" ......... Yayinda omaine ya yi flat a ƙasa kamar yadda gaisuwar fadar take. A fusace assistant din Queen wato Chief Benish ta ce, "Kai matsiyaci ɗan baiwa jikan bayi durƙusa tun kafin fushin sarauniya ya hau kan ka"........ Juyawa yayi ya kalle ta a dake ya ce, "Fushin sarauniya ba fushin ALLAH bane Babu inda akace idan zamu gaishe da wani bawa mu kwanta masa kamar zamuyi sujjada, ALLAH kaɗai akewa sujjada". "Javed ku saukar dashi ƙasa"......... Chief Benish ta faɗa tana miqewa cikin fushi, wasu gardawa dake cikin palace ɗin ne suka nufo inda yake tare da rirriqe shi suka shiga kokawar sai sun kaishi ƙasa, su uku shi ɗaya Amma sun gagara kai shi ƙasan kamar yadda aka basu umarni iyakar sa kawai ya sauka kan guiwowin sa yana fuskantar Queen Hirut da ita ma shi take kallo. "Ni dai bazan gaji da faɗa Miki gaskiya ba ke da mutanan ki, hanyar da kuke bi ba Mai bullewa bace, Ina muku da'awa ne saboda Ina mu ku kwadayin samun rahamar ALLAH inason ku ɗanɗani ni'imar dake cikin addinin gaskiya, addinin ALLAH, abinda kuke bautawa itama baiwar ALLAH ce, Kuma ba ita ta halicce ku ba. Abu na ƙarshe shi ne ki sani ko kin sa an kaini prison in dai ba sawa kikayi a kasheni ba dole wata rana zan fito Kuma in na fito haka zan cigaba da faɗaɗa ayar ALLAH, Ni kuma nasan ke baki isa ki min abinda ALLAH bai min ba, in har kwana na bai ƙare ba baki isa ki kasheni ba ..........." Bai ƙarasa ba wa'annan gardawan suka haɗa masa wani duka sai jini, hannun yasa ya dangwalo jinin sai kuma ya kalli Queen Hirut da in ranta yayi dubu ya ɓaci sai huci take daga zaunen, Cheif Benish ce ta ce, "Javed a kai shi guardroom a bashi horo me tsanani"......... Haƙuri Omaine ya fara basu cikin rawar jiki tare da faɗin, "Haisha'an ka basu haƙuri mana, ranki ya daɗe ki gafarce mu ki masa afuwa".......... Amma ina taurin kai irin na Haisha'an ko motsa bakinsa baiyi ba haka suka ja suka fice dashi Omaine ya bisu yana roƙar su amma ko kallon sa basuyi ba ƙarshe ma ball ɗaya daga cikin su yayi dashi. Guardroom wani ɗakin duhu ne a ƙarƙashin ƙasa da suke horar da masu laifi, ɗakin ko hannun ka baka iya gani gashi ba iska sosai sai zafin masifa, da yawan mutane in aka kaisu can basa fitowa da ƙafarsu saidai gawarsu hakan yasa hankalin Omaine mugun tashi, baiji bugun da suka masa ba ya sake tashi ya bisu yana sake roqon su idanun sa shaɓe shaɓe da hawaye, masu tsaron wajen suka sa su fitar musu da omaine sannan suka haɗu suka tura Haisha'an ciki. Da gudu Omaine ya juya dan zuwa wurin Inah domin ya sanar da ita, dan yasan ita kaɗaice zata iya ceton Haisha'an, a ƙofar bangaren su ya tarar dasu suna kokarin fitowa itada wasu daga cikin bayin, zubewa yayi gabanta tare da faɗin , "Inah dan ALLAH ki taimaki rayuwar Haisha'an Queen Hirut ta sa a kaishi Guardroom, Please Inah"........ Ya ƙarashe hawaye na zubo masa . "Kamar yadda ka faɗa Queen Hirut ni kaina ta isa ta zartar da hukunci a kai na ballantana kuma ɗa na, and dama na gaya masa ai tunda har baiji ba shikenan shi ya jiwo in ya mutu ma bani da asara taurin kan sa ya ja masa"......... Tana kaiwa nan ta yi gaba, sake shan gaban su yayi yana riqo ƙafafunta, mari ta zubga masa sannan ta sake cewa, "Kai idan ka sake motsawa daga inda kake da niyyar bi na, na rantse da kurangina (Astagfirullah) sai na sa an maka abinda bakayi zato ba"......... Daga haka ta fisge ƙafarta ta wuce. A can kuwa ko da suka shige da Haisha'an guardroom sarƙa suka sanya masa a kugu kowa ya ja ɗaya sannan suka shiga zabga masa wasu irin dorina na fatar kada, baya gani balle yasan ta inda dukan yake fitowa har ya kare kansa dan haka yayi surrender kawai, tun yana daurewa har ya kai ƙasa ga ba iska sosai, ga duka ta ko ina. Sosai ya fara fita hayyacin sa, jijiyoyin jikin sa suka fara saki. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 64 & 65 Ko da Amla tazo tare suka koma wurin DPO da Sahnish dan Baba ilerika ya wuce yin wani uzurin da yaji Abun yafi ƙarfin sa, bayanin da DPO yayiwa su Sahnish ɗin shi ya sakewa Amla, saidai Amla tayi ƙoƙarin aiki da dukiya Amma fa sam DPO yaqi sauraran ta dan haka suna fitowa ta nemi ganin Hushaima, bayan an fito da Hushaima suka kalli juna, dafa kafaɗar ta Amla tayi da faɗin, "Hushaima ashe tsautsayin da ya faru kenan?"......... Ɗan gajeren Murmushin gefen baki tayi da faɗin, "Ba tsautsayi bane tsayawa kai da kare mutunci ne"......... Jan hannun ta Amla ta ɗanyi da faɗin, "Haba ya ana ƙoƙarin kashe wata wutar kina ƙoƙarin kunna wata, karki Ƙara faɗar haka, na samu DPO Amma yaqi ma saurare na dan haka yanzu zamuje wurin CP Kuma zamu ɗauki lawyer Amma ki cire zancen wata tsayawa kai or whatsoever ɗin Nan ko da an tambayeki kice tsautsayi ne ba dagangan kikayi ba........" Kafin ta rufe bakinta Hushaima ta ce, "Saboda me zanyi ƙarya bayan ita ta ɗauki wani kuturun hannunta ta mare ni sannan ta gaggaya min maganganu. Mari fa ? ke kinga yarinyar ne wai ni ni zata kalli tsabagen idona ta dallawa mari, whl ko kaɗan banyi nadama ba Kuma wasan Bai tsaya iya nan ba, ni za'a wulakanta a jefa a cell ko?".......... Kwafa taja tare da yin murmushin da ita ta barwa kanta sanin ma'anar sa. "Wai ke Hushaima me hakan fisabilillahi, ya sai ana gabas kina yamma wanna yarinyar ki sani ba ƴar kananan mutane ba.......".........."ALLAH yasa uban ta ne shugaban ƙasa Amma whl bazan canza kalamai na ba, in sunga dama su ɗaureni har igiya tayi saura". Sahnish da yayi tagumi yana kallon su ya ce, "kin ganta nan dai Amla ni har na rasa ya zanyi whl". "Kaga in zaka san yadda zakayi ka fitar dani daga nan wurin to, in Kuma baza ka iya ba ka sanar min nayi iya nawa". Cikin ɓacin rai Amla ta ce, "To Wai ba fitar dake ɗin ake so ayi ba Amma kin kasa sauraron abinda ake faɗa miki, wai yaya ne Hushaima Anya ba wani abu kika sha ba kuwa. And kinsan yadda zakiyi ki fitar da kanki ne kika bari kika kwana anan ɗin?"...........Tana kaiwa nan ta juya ta kalli Sahnish da faɗin, "Ka sameni a mota"....... Ta ƙarashe tana barin wurin, tashi Sahnish ɗin yayi sannan ya ce, "Dan ALLAH Hushaima ki sassauta wanna nuqufarcin naki wanna zafin ran ba zai kaiki ko Ina ba ki barmu mu rayu cikin salama muji da Abu ɗaya mana ". Wani banzan kallo ta watsa masa kafin ta ce, "Kai saurara min kaji ko, karka ce zaka min wasu surutai, dukda nasan ni ba kowa bace bazan karɓi raini da wulakanci a wurin kowa ba, ban shiga harkar kowa ba Amma duk wanda ya shiga tawa whl banqi mu Kai daga nan har kotun qoli ba". "Allah ya kyauta "........ Shi ne abinda Sahnish ya sake faɗa tare da juyawa yabi bayan Amla . Daga nan state police headquarter suka nufa inda Amla tayi amfani da matsayin mahaifin ta domin su samu ganin commissioner ɗin da wuri, bayan an musu iso suka gaishe shi. "Have a seat ku zauna mana ga guri".........Ya faɗa cikin fara'a yana nuna musu wurin zama. "Thank you sir "........ Amla ta faɗa tare da zama tanawa Sahnish alamar ya zauna shi ma. "Fita ma zanyi ai naji ance daughter alhaji Zawaad ne nace to bari na tsaya na saurareki, ya wurin mahaifin naki kwana biyu ma bamuyi waya ba". "Yana Nan lpy sir, yana gaishe ka ma abubuwa ne suka dan masa yauwa saisa "........."Ah to ba damuwa Ina amsawa, akwai wani matsala ne?" . "Eh sir dama ........" Abinda ya faru ta fada masa, take ya fara faɗa, "Shi Wakili (DPO) wato abinda yakeyi kenan, how za'ace baza a bada bailing yarinya ba kisan Kai tayi ko me? bari na kirashi naji dama aikin da ya keyi kenan"......... Ya Ƙarashe yana ɗaukan wayarsa ya Kira DPO tare da rufe shi da faɗa. Saida ya gama sannan DPO ya masa bayani. "Shikenan bari zanyi magana dasu"........... CP ya fada a sanyaye sannan ya ajje wayar yana kallon Amla da Sahnish tare da zaro hanky ɗin dake gaban rigarsa ya goge fuskar sa da gumi ya fara karyo masa, Nisawa yayi kafin ya ce, " A gsky Amla case ɗin nan babba ne domin ance har yanzu yarinya na coma sannan Kuma........." Ɗan shuru yayi kafin ya cigaba, "Unfortunately ba zan iyayin komai akai ba, saboda yarinyar da aka raunata ɗin ya' ce ga Alhaji Awais Hashim masu HD REFINERIES da kuma AURUM MINING, Kuma kinsan fitattu ne shugaban ƙasa ma ba ya musu wahalar gani. Abinda zance da ku kawai shi ne kuje ku ɗauki kwararrun lawyers sannan ku tsaya da addu'a dan gsky a fahimta ta nema suke su maida abun babba, kuma suna amfani da connection ne"......... Take jikin Sahnish ya ɗau rawa dan da a tsaye yake ba abinda zai hanashi yanke jiki ya faɗi duk da baisan mutumin da aka ambata ba Amma yasa wanna HD ɗin da CP ya ambata dan ana yawan ambaton ta gidanjen TV da radio, wata juya juya ya fara gani ai baisan lokacin da ya sauko daga kan kujerar ba, "Ranka ya daɗe Dan girman ALLAH ka taimaka min whl ita kaɗai nake da ita a duniyar Na........". "Kaga Sahnish tashi muje"......... Amla ta katseshi saboda tasan ba abinda magiyar zata amfana. Cikin mutuwar jiki ta miqe domin ta Ƙare musu gabaɗaya saidai suje su sake shawara Amma case da babban mutum kamar Alhaji Awais bata hango nasara ba. Gashi ba yadda zatayi ta sanarwa mahaifin ta ko zai iyayin wani abu akai, dan idan mahaifiyar ta taji zatayi mummunan Saɓa mata saboda yadda ta tsani su Hushaiman . "Shikenan sir mu zamu wuce mungode sosai"..........."You are welcome ki gaidamin Alhaji da kyau da ALLAH". "Zaiji in Sha ALLAH"......... Ta faɗa tana fita, Sahnish ya rufa mata baya. Ko da suka shiga mota kuka Sahnish ya fashe mata dashi wiwi kamar wani ƙaramin yaro, kasa ce masa komai tayi dan bata da wata kalma da zatayi amfani da ita wurin tausarsa saboda itama abun ya fara ɗaga mata hankali, har suka koma police station ɗin, sannan ta kalleshi da faɗin, "Sahnish nasan halin da kake ciki Amma kayi hakuri ka sawa zuciyarka dauriya, zan ajje ka anan ne saboda inaso naje gida nayi tunanin mafita, in Sha ALLAH Hushaima zata fita ka kwantar da hankalinka". Goge fuskar sa yayi ba dan ya yadda ba sai dan kawai ya jita ne dan maganar CP ta cire masa hope a zuciyar sa. "Mun gode sosai Amla, ALLAH ya kaiki gida lpy"........... Ya faɗa Yana buɗe ƙofar motar, har ya fita Amla ta ƙasa cewa komai saboda tsananin tausayin su da taji ya cikata, da haka taja motar ta bar wurin. Shi Kuma Sahnish kan kwalbatin dake opposite da police station ɗin ya nema wuri ya zauna. Wuni yayi cur a wurin dan ya shiga ya nemi ganin Hushaima suka hanashi Wai ba'a zirga zirga haka ya haƙura ya miqa musu abincin da ya siyo mata ya koma ya zauna har lokacin ɗauko Shazeen yayi yaje ya ɗaukota, itama magana ɗaya ce a bakinta wato Ina aunty Hushaima, rasa amsar da zai bata yayi Dan haka yace bata dawo ba. Abinci ya tsaya ya siya mata sannan suka koma ƙofar police station ɗin suka kafa sabon zama har dare ya kai mata Abinci sannan suka wuce gida . Washe gari ma daƙer da siɗin goshi ya samu ganin ta nan ya shaida mata abinda su CP suka ce. Fuskarta cike da dimbin mamaki ta maimaita, "Alhaji Awais, yanzu wanna yarinyar da na fasawa Kai yarinyar Alhaji Awais ce?" . "Kin sanshi ne ?"........... Sahnish ya tambaya yana kallon ta, batace masa komai ba illa murmushin data saki kawai, sai miqewa da tayi da faɗin, "Sahnish Kaje kawai karka damu"........... "Bangane ba Ina zaki kuma kinsan da ya akayi na samu suka barni na ganki ne?". "Kaje kawai Sahnish nace ma karka damu "....... Tana kaiwa nan ta wuce ta koma cell ɗin da kanta, shi kansa Sargeant da kallon mamaki ya bita dan shi bai taɓa ganin yarinya irin wanna ba . Haka Sahnish ya tashi ya koma wurin da ya zauna jiya ya zubawa titi ido. Kwanan Hushaima shida a police station duk wani Kai kawo da Amla dasu Sahnish zasuyi sunyi Amma babu wata alamun nasara, dan haka Amla ta nema mata wani kwararren lawyer da zai tsaya mata dan gobe ne zaman kotun. Da Misalin 3:06pm na ranar lahadi Hushaima na hango tare da barrister zaune yana mata tambayoyi game da case ɗin nasu, a waje Kuma Amla ce da Sahnish, Shazeen sai Baba ilerika tsaye suna jiran su. DPO ne ya fito take su Sargeant suka shiga sara masa kwata kwata bai lura dasu Sahnish ba saboda kamar a rikice ya fito. "Amm Sargeant Sunusi, maza Kaje ka fito da yarinyar nan da suke case da su Alhaji Awais ayi gaggawar sallamar ta yanzu yanzu ta bar station ɗin nan karta Ƙara minti biyar a ciki, sannan zancen kotu kace mata babu shi an janye"..........." Yes sir". Sargeant sunusi ya faɗa tare da sara masa shi Kuma ya juya ya koma Office ɗin sa. Kallon kallo aka shigayi tsakanin su Baba ilerika, Sahnish ne ya ce, "Amla naji daidai kuwa? an sallami Hushaima fa Kuma an janye Ƙara?". Itama Amla cikin ɗaurewar Kai ta ce, "Abinda naji kenan nima to Amma........, Wait bari naje wurin DPO ɗin"......... ta faɗa tana wucewa yayin da Sargeant Sunusi Kuma ya fito dasu Hushaima da barrister tare da wucewa ya ɗauko mata kayayyakin ta ya bata jiki na rawa saboda cika umarnin DPO. A ciki kuwa Amla tana shiga ta samu DPO yana waya, "Yes sir ai an sallame su ma tuntuni".......... Shuru yayi can Kuma ya ce , "Okay sir godia nake".......... Kashewa yayi tare da kallon Amla ya ce, "Ah Ah dama kina Nan?". "Eh DPO naji ka fito kace mu tafi sannan Kuma an Kori Ƙara shine nazo naji cikakken bayani". "Ba wani cikakken bayani da zaki samu Amla abinda na sani kawai muma umarni aka bamu daga sama kan mu saketa dan haka kuje kawai, case closed". " Shikenan ranka ya daɗe mun gode ".........Daga haka ta juya ta fita. A compound ta tarar dasu, remote ɗin motarta ta matsa motar ta buɗe ba tare data tsaya ba ta ce, "Ku shigo muje". -------------------------√ AURELLON SULTANATE 💎 Ko da Mutallab ya aika da Yaran sa karɓo saqon Queen Hirut daga bakin gate ɗin su suka tsaya, Wata mata ce ta sauko daga kan giwar ta miqa musu sannan ta juya ta koma ta kama giwar ta ɗale suka juya suka bar wurin, sai lokacin suma masu karɓar suka juya ciki. Mutallab suka kaiwa shi Kuma ya koma fada yana zuwa ya zauna a tsakiyar fadar tare da faɗin, "An karbo saqon ya Sultan"......... Wazir ne ya ce, "Karanta a fili muji". Karbar Mic ɗin da wani bafade ya bashi yayi ya maqala a gaban rigarsa sannan ya warware takardar ya fara karantawa kamar haka . From: The Honorable Queen Hirut the queen of sword of fire kingdom. To : His Majesty King sultan abdulbasit Abdul Aziz Theron of the aurellon sultanate. "Your accusations are as outrageous as they are unfounded. The sword of fire kingdom has neither the interest nor the need to conspire against your fragile dynasty. Crown Prince Rislan, while tragic, is no fault of ours, and we will not be scapegoated for the shortcomings of your own court’s security. Your demand for conspirators is laughable and As for your request for reparations, we suggest you direct your grievances inward, for the incompetence of your own kingdom is not our financial responsibility. Should you persist in these baseless accusations or threaten the peace with your bluster, know that the sword of fire kingdom will not hesitate to defend its honor and sovereignty. We advise you to temper your paranoia and reconsider your position, lest you find yourself embroiled in a conflict you are ill-prepared to win. _Signed_ The Honorable queen of the sword of fire kingdom. Sai stamp ɗinsu da aka buga me hoton wuta sai sword guda biyu da sukayi crossing a tsakiyar ta. Duk shuru mutanan fadar sukayi ana jiran jin hukuncin da Sultan zai yanke. Gyaran murya yayi tare da faɗin, "Suna sukan masarauta Kai tsaye, sannan sun nuna a shirye suke Dan haka ramuwa ta tabbata a kansu, saboda haka na bada izinin a tura mutane domin ɗaukan fansa. Iya adadin mutanen da suka kashe mana kawai za'a kashe". Da sauri Badram ( sarkin yaqi) ya miqe tare da faɗin, "Angama ya Sultan"......... Ya faɗa yana me jinjina masa da hannu tare da sauke kansa ƙasa kaɗan sannan ya juya ya fice daga fadar dan zuwa shirya mutanan da zasuje sword of fire kingdom. Babu wanda wanna hukunci na me martaba bai wa daɗi ba saboda wannan cin kashi nasu Queen Hirut akwai rainin wayo a ciki. _______________Sheikha Barrah ce tsaye a ƙuryar ɗakin ta tana cizon yatsa, gabanta wata kyakkyawar yarinya ce da baza ta wuce 19 years ba tana sanye da wata golden dress me matuqar kyau da ɗaukan hankali, siririn mayafin data yafa ya zame ya koma kan wuyanta hakan ya bawa lallausan baqin gashinta na larabawan asali bayyana kasancewar ribbon ɗin data sa ya cire yana jefe a bayanta, gashin kuwa baqi sidik dashi ya kai har ƙarshen bayanta dan har taɓa ƙasa yake daga durqushen da take. Dukda sanyin Ac dake ɗakin ita gumi take ga hawayen da ya gama wanke fuskarta, cikin shesheqar kuka take magana Muryarta harta dashe. "Maama dan girman ALLAH ki barni na tafi, ki amince nayi nesa da masarautar nan, nayi nesa da kowa maama ki taimaki rayuwata, zuciyata zata iya bugawa idan na cigaba da zama".......... Ganin mahaifiyarta ta batace komai ba har lokacin yasa ta matso ta sake riqo ƙafafunta cikin raunin murya ta ce, "Maama ki qaddara bansan komai ba, na rantse Miki ko zan mutu bazan fidda sirrin ki ba domin ke uwata ce, kawai inason nayi nesa daku ne saboda.........." Shiru tayi saboda kukan da yaci ƙarfin ta, wani irin yawu Maama ta haɗiya kwat kafin ta ce, "Tashi ki je sai na nemeki". Ba yadda zatayi domin ta san in har ta sake ran mahaifiyarta ta yafi haka ɓaci to fa komai zai iya biyo baya. Share hawayen ta tayi kafin ta ja gyalenta ta rufa akanta ta tashi ta fita tana layi kamar wadda ta bugu saboda kukan da ta sha ya mata over. Sulham kenan autar uwargida Sheikha Barrah, a maimakon ta fuskanci soyayya da tarairaya na kasancewarta auta sai take fuskantar kyara, tsangwama da hantara a wurin mahaifiyarta ta, gata da farin jini kowa son ta yake amma banda mahaifiyarta domin in a gaban yan uwan ta ne ko mahaifinta Sultan tsantsar soyayya da tausasawa ne tsakaninta da mahaifiyarta ta amma yayin da bata ganin idonsu to fa a nan ne zata shiga cusguna mata, tun da ta taso a haka take ba tare da tasan laifin data aikatawa mahaifiyarta ta ba. WANNAN KENAN. A ɗan tsorace ta bi bayanta da kallo har ta fice ta rufo ƙofar, sai a lokacin ta saki ajiyar zuciya tare da ƙarasawa gaban mirror ta ɗauki wayarta ta sanya wata number tayi dialing, saidai har ta katse ba'a ɗaga ba, bata haƙura ba ta sake kira, saida tayi missed call uku ana huɗun aka ɗaga, a hasale ta ce, "Wai ina ka Ajje waya inata neman ka? To ka sani akwai gagarumar matsala, kwan nan yana ƙoƙarin zame mini baragurbin da zai iya hanani rayuwa lpy wanda a ƙarshe in nayi wasa zai iya zama silar ajali na". "Subahanallahi me kike shirin gayamin ne ya Sheikha ?".......... Saida ta Ƙara taku biyu sannan ta ce, "Shi dai wanna kwan da muka taɓa killacewa da hope ɗin mu kyankyashe abin cikin sa to shi ne kafin mu farga ya zama baragurbi, kuma an samu ƙaramar ƙofa ta ɓule, lalle kuma idan mukayi sake ta zama babba to tabbas warin sa zai iya bugar hancin kowa, wanda hakan ba ƙaramar matsala zai jawo ba kai Ka sani".......... Ajiyar zuciya aka sauqe daga ɗaya bangaren kafin ya ce, "Yanzu me ye kike ganin abun yi?".........."Zan zuba masa kasa". Da sauri ya ce, "Kul Sheikha karki soma zuba wa baragurbin nan ƙasa, ba shi bane masalaha domin hakan zai janyo zargin dalilin da wanna kwan ya fito baragurbi". Shuru tayi yayin da ya cigaba da faɗin, "Ki bani lokaci zan san abunyi, Amma karki bari ruwan ya tsiyaye gabaɗaya. Saboda yanzu muna cikin wani tashin hankali ne da alhinin rashin Sheikha Yassar saisa kikaga kin min missed calls ban ansa ba ina cikin mutane ne". Cikin wani sabon tashin hankalin da ya gaza ɓoyuwa akan fuskarta ta ce, "Kace Sheikh yassar ya mutu?". "Kin dai san ba zan Miki ƙarya ba ko, na ma ɗauka kin samu labari ai shiyasa kike kirana, domin ko karɓo gawar ba'ayi ba yanzu daga asibiti, dan baifi mintuna ba da rasuwar"......... Sauke wayar tayi daga kunnen ta ba tare data kashe ba, "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un yassar ya mutu hakan na nufin ba wani shaqiqin me martaba kenan da zai iya gadar sa face ɗaya daga cikin yayansa ukun Nan. Inaa tunda har ni dana kasance mace ta farko ban bawa Sultan magaji ba to suma ba mai gada a cikin ya'yan su whl"..........Ta ƙarashe tana wucewa ta buɗe sip ta ɗauko ƙayatacciyar alkyabbarta sannan ta kira khadimarta ta sanar mata zasu fita a shirya mata mota zuwa bangaren Anjani (Mahaifiyar su Sultan). Gyara fuskarta tayi sannan ta sanya Alkyabbarta ta zura takalminta ta fita, mutum huɗu khadimai ta samu suna jiran ta tana fitowa suka fara mata kirari ba tare data saurare su ba ta wuce suka rufa mata baya suna cigaba da mata kirarin har waje inda aka shirya mata mota uku, ta tsakiyar aka buɗe mata ta shige saura khadiman suka shiga sauran motoci biyun, a hankali motocin suka fice daga part ɗin. Tafiyar minti goma ya kaisu bangaren Anjani dake cike da jama'a alamar mutuwar Sheikh yassar ɗin ta fara zagaya masarautar, ta ko Ina ka kalla dogaran su ne tare da khadimai suke ta Kai kawo. _____________Ita kuwa ummu lokacin da labarin mutuwar yassar ya risketa kuka ta fashe dashi sosai na tausayin kanta, Albeena ce ta shigo ɗakin ganin ummu na kuka yasa ta ƙarasa jiki a sanyaye ta zauna wurin ƙafarta tana kallon ta ba tare da tace komai ba, tissue ummu taja ta goge fuskarta tare da faɗin, "Albee tashi kije ki Duba min in su Rouslan basu Kai ga fita ba ki turomin su"......... da "To". ta amsa sannan ta tashi ta fita dan zuwa aikar ummu. Tana zuwa ƙofar ɗakin suna fitowa cikin shiga iri ɗaya fitted white Thobe da royal Arab ghutra da suka ɗaura a kansu. Ɗan rikicewa Albeena tayi ta zuba musu ido saboda ta ƙasa banbance Rouslan da Reeslan ɗin. "Kee miye kika wani zuba mana ido, Me ma ya kawoki nan?" .......... Sai lokacin ta gane Reeslan ɗin, tunda dama shi masifar sa ce take sa a gane shi, ɗan ja baya tayi a tsorace ta ce, "Ummu ce tace a kira ku dama". "To tafi mana ko sai kin samu gaba ne uwar mu"......... Da sauri sauri gudu gudu ta juya ta bar wurin, Rouslan ne ya kalleshi da faɗin, "Bakyau fa, duk kabi ka firgita yara kasa sai tsoron ka suke ji". "Rabu dasu, na munafurci ne ai jiya ina jinsu suna gulmata itada ƙawayenta kawai dai dan Ina sauri ne da sai na zane musu uwar jiki"......... Rouslan bai sake bi ta kan zancen ba sai cewa da yayi, "Ba fa tashi sama zamuyi ba". "To tsaya kana lakwai lakwai tu kasan dai in Akazo sallar gawar, Abbu bai gan mu ba ransa zai ɓace"........... Ɗan sauri Rouslan ɗin ya Ƙara Amma duk da haka ya kasa kamo Reeslan Saboda shi takun jinin saraki yakeyi cike da nuna isa da mulki shi kuma Ruslan takun zakuna yakeyi cike da ƙarsashi da kuma zafin nama. A haka suka ƙarasa ɗakin Ummu, knocking sukayi sannan suka jira ta basu izinin shiga. Bakinsu ɗauke da sallama suka sa kai. "Ummu barka da rana "......... Rouslan ya faɗa yana zama . "Wurin janaizar zaku?"......... ta tambaya tana kallon Reeslan da yayi ƙasa da Kai kamar yasan shi take kallo. Rouslan ya amsa da , "Eh ummu, whl Ummu jikina yayi sanyi da mutuwar Ammu, mutumin kirki ni whl Abbu nake tausayawa nasan sai yaji mutuwar fiye da kowa saboda duk cikin yan uwan da suke uwa ɗaya uba ɗaya su biyu suka rage maza". "Ya za'ayi Rouslan, ɗai ɗaya mukazo Kuma ɗai ɗaya zamu koma sai dai muce ALLAH yasa mu cika da kyau da Imani wanda suka rigamu Kuma ALLAH yaji ƙansu". "Ummu kuka kikayi ne sosai haka".......... Reeslan da ya saci kallon Ummu ya faɗa da mamaki dan yasan Ummu akwai dakiya da ƙarfin zuciya. Shi ma Rouslan Saida Reeslan ya faɗa ya lura da idanun ta da suka ɗan tasa yana jiran jin amsar da zata bawa Reeslan ɗin . "Reeslan! Ka faɗamin gsky dan ALLAH meke faruwa dakai?".......... Kallon juna sukayi shi da Rouslan kafin Rouslan ɗin ya ce, " Ummu lpy Lau yake me kika gani?"......... "Kai rufe min baki Kai na tambaya ne?".......... Sunkuyar da Kai Rouslan yayi yana satar kallon Reeslan ɗin Wanda yayi shuru sai murza yatsun hannuwansa yake. " Kai nake tambaya ka min shuru?". Ɗagowa yayi kamar zaiyi magana sai Kuma ya sake juyawa ya kalli Rouslan, tashi yayi da sauri ya fita, shi ma Rouslan ɗin tashi yayi ya mara masa baya suka bar Ummu sake da baki cikin ɗaurewar kai. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ ___________________________________ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 66 & 67 Ɗakin sirrinsa suka shige gabaɗayansu ya kukkuna komai sannan ya ɗauko Sectra tiger ɗinsu da suke communicating da headquarter ɗinsu dake can Brussel ɗin ta ciki, yayi connecting da VPN ɗinsu wato virtual private network, sannan ya danna kiran kai tsaye. Bayan sir Richard ya ɗaga Amjad ya saita muryarsa da faɗin. "Hello good evening sir".......... " Evening Agent Amjad, how are you?". "Good sir, dama na kiraka ne Kan batun aikin da muke yi akan Shadow.........." Kwashe komai yayi ya faɗa masa duk yadda ake ciki. Cike da ƙarfin guiwa Sir Richard ya ce, "Banajin duk wani aiki da za'a danqa shi a hannun ka Agent Amjad, Dan haka kayi ko ma miye, kawai dai in kuna da buqatar taimakon mu to akoda yaushe kuyi gaggawar sanar damu, dan haka all the best". "Thank you sir".........Ya faɗa a sanyaye, tabbas dole su dage wurin ganin sun gano mutumin nan. Sir Richard na kashe waya ya kalle su da faɗin, "Bamu da time, muje kawai"....... Ya ƙarashe yana fita suka biyoshi a baya shi kuma yayi latse latsen sa ƙofar ta rufe. Motar sa Jey ya shiga, shi ma Amjad ya shiga tasa shi da Ace, Kiara da ashley suka shiga mota ɗaya tare da Nazbeer da yace yayi driving ɗinsu, sauran masu tsaron da aka bawa Amjad ɗin suka shiga sauran motocin sannan suka fice daga gidan suka nufi state headquarter ɗin tasu da aka killace mutanan acan, suna zuwa suka samu Philip da sauran jami'ai suna ta aikin. A wani babban ɗaki me kama da office suka yada zango sannan ya ce da Philip da ya taryosu. "Philip kawo mutumin da Jey ya kawo, i can't wait kuzo saisa muka biyo sawu".........."Okay boss"....... Philip ya faɗa tare da juyawa ya fita, wayar Kiara ce tayi Ƙara hakan yasa ta ɗaga Kai taga duk sun zubo mata ido sai ta kashe kiran, sake Kira akayi ganin tana ƙoƙarin sake kashewa yasa Amjad faɗin, "Pick your call mana"......... Tashi tayi da faɗin, "Excuse please". Ta ƙarashe tana fita daga office ɗin, ƙasa ƙasa Ace ya ce da Ashley, "Kufa me da hankali ba soyayya mukazo yi ba"........"To ina ruwanka?"....... ta faɗa tana Hararar sa. "ALLAH yasa wani ya kiraki kiga yadda za'ayi"....... zata ƙara magana Philip ya shigo da mutumin sai raba ido yake, Tsakiyar office ɗin suka durƙusar dashi, daga shi sai three quarter, wasu yan na'urori Philip ya miqawa Amjad da faɗin, " Wa'annan sun kammala, sune Wanda za'a dinga jin motsin su wanna Kuma a system za'a sanya dan a dinga ganin inda suka nufa". "Yanzu wanna an saka masa tracker da soundtrack ɗin?".......... Ace ya tambaya. Kafin Philip ya bada amsa Amjad ya ce, "Yes ". " How?"........."Ohh Ace karka ban kunya mana kaifa kwararren jami'i ne "......... Shuru Ace yayi ya zubawa mutumin ido can Kuma ya ce, "Yes yes gasu nan a fatar kansa"......... Ya faɗa Yana nuna kan mutumin dake nan tankwal kamar ba'a taɓa halittar gashi a fatar kan ba dan har wani kyalli take, sai dai komin Ƙura idonka baka isa kace akwai wani abu a gun ba bayan halittar kan mutum saisu da suka haddace sa ido. "Jey ɗauki system ɗin nan ka je ka yi connecting a waje tare da Bluetooth ɗin, sannan ka sanarmin results in komai yayi"........ Amjad ya faɗa Yana maqala kunne ɗaya sannan ya miqa masa system ɗin dake gaban sa, karɓa Jey yayi ya fita, can kan motar sa yaje ya ɗaura system ɗin tare da sanya wani abu kamar memory sannan ya maqala ɗayan abun a kunnensa me kamar Bluetooth, sai ga su Amjad sun bayyana a cikin system ɗin tar haka Kuma yana jin muryoyin su da abinda suke faɗa dan haka ya ce, "komai yayi"......... Murmushin jin daɗi Amjad yayi kafin ya kalli Philip ya ce, "Aiki yayi kyau, ka kawo mana sauran na'urorin, ya kamata each and everyone of us ya samu na'urar sauraron sauti da kuma ta GPS da video feed, sannan in Kun gama a cikin daren ku shirya ku nufi iyakar ƙasar nan karku bari aga fuskar ku kaji ko". "Yes boss"....... Philip ya amsa, miqewa Ace yayi da nufin ƙarasawa gaban table ɗin Amjad saidai taku ɗaya yayi ya riqe kansa kafin su ankara sai ganin sa sukayi a ƙasa . " Ace!, ace!"...... Ash ta fara Kiran sunan sa, da hanzari duk sukayi kansa ita da Philip shi ma Amjad tasowa yayi yana faɗin, "Ace ya baka da lpy ne?"........ Tari ya fara tare da qaqarin amai kamar zai fitar da abinda ke cikinsa Amma ko yawu baya fita a bakin nasa, a hankali idanun sa ke juyewa bakin na barin cikin su, jijjiga shi Amjad ya farayi Yana Kiran sunan sa, dip sukaji yayi da sauri ya ce, "Philip get the cars, kiramun Widad" .......... Kafin ya rufe bakinsa Jey ya shigo, da sauri ya ƙaraso wurin su ganin abinda ke faruwa, yayinda Philip ya fita domin ya sanar da su Kamal su matso da mota. Da taimakon su akasa Ace dake sanqame kamar gawa a mota. "Philip kayi handling sauran abubuwan karka fasa komai Kuma ka tabbatar komai ya tafi daidai kar a samu matsala".......... Ya faɗa yana zagayawa ya shiga motar da akasa Ace ɗin a ciki yayinda Jey ya shiga gaba ya bar motar sa a can, su Ash Kuma suka shiga motar da suka zo a ciki dan already ta samu Kiara ne a zaune ciki tana waya Kuma da alama da gida take wayar saidai kamar a tsorace take wayar. Da mahaukacin gudu motocin suka fita daga harabar State headquarter ɗin. -----------------√ SWORD OF FIRE KINGDOM 🔥 Jin shurun yayi yawa yasa masu gadin shiga guardroom ɗin tare da amfani da touch light ɗin su me haske sosai, a nan suka gansu yashe a ƙasa kamar gawa ga Haisha'an zaune ya kunce daga sarkar da suka masa, duk ya jigata sosai dan jikinsa ko ina jini ne, basu bi ta kansa ba suka shiga ciccibar waɗanda suka shigo dashi a rikice suka fita dasu, tsabar rikicewa ko rufe guardroom ɗin ba suyi ba, tashi yayi tare da goge jinin dake sauqa gefen idon sa zuwa gefen bakin sa, rarrafawa yayi ya fita daƙyar, Yana fitowa ya zube a bakin wurin yana fitar da numfashin wahala. Omaine dake ta Kai kawo a ƙofar wurin kamar zai yi ihu Ba abinda yake in banda addu'a a zuciyar sa na ALLAH ya kuɓutar da Haisha'an. Gani yayi masu gadin sunzo sun wuce da wanna fadawan akan kafaɗar su, da gudu ya shige wurin, nan ya hango Haisha'an ɗin zube a ƙasa rigar jikinsa duk ta farfashe ga jini dake zuba ta inda suka jijji masa ciwo, "Haisha'an!, Haisha'an! "........ Ɗagowa yayi ya kalleshi garara sai Kuma ya maida idon sa ya rufe, kama shi yayi da kyar ya miqar dashi tare da ratayo da hannunsa ɗaya a kafaɗar sa suka fara tafiya zuwa ɓangaren su. Suna shiga ɗakin su ya zube a bakin ƙofar, da hanzari Omaine ya wuce toilet ya samo ruwan ɗumi da towel ya dawo inda Haisha'an ɗin yake zube kamar kayan wanki, yagargiyar rigar ya zare masa sannan ya shiga goge masa jikin nasa, dukda irin tsananin azabar dake ratsa kwakwalwar sa baiko motsa ba har Omaine ya gama da bayan ya mirgina shi ya fara goge masa kan kirjin sa zuwa ciki idanun sa fall da hawaye sai sannu da yake ta faman jera masa, Dan yasan akwai azaba kawai dauriya yake, haka ya gama sannan ya maida komai toilet ɗin ya zo ya taimaka ya ɗaurashi kan tsohon gadon nasu. Duk shekara Queen Hirut take canza kayayyakin masarautar Amma banda bangaren mazan, wa'annan su saidai a basu kuncen da aka fidda daga bangaren Matan. Buɗe idanunsa da suka ɗan tasa yayi ya kalli omaine ɗin da ya miqe da faɗin, "Zanje na samo ma magani ba zan daɗe ba yanzu zan dawo"....... Yana kaiwa nan ya juya ya fice da sauri. Har ya fara bacci lokacin da omaine ya shigo hannunsa riqe da wani dan qoqo, wurin sa ya nufa ya hau kan gadon sannan ya fara shafa masa wani koren magani dake cikin qoqon, yatsina fuska yayi amma bai ce komi ba. "Sorry ɗan uwa in Sha ALLAH zai daina zafi"........ Haka ya dinga bi yana shafa masa a duk inda yaji ciwo har ya gama shafe masa a fuska, kirji da ciki sannan ya ce, "Taimaka ka zauna in shafa ma a bayan"....... Ba musu ya tashi ya zauna yana yatsina fuska alamar jikin ya masa tsami sosai, cikin tausayawa omaine ya sake cewa, "Sannu. Dan ALLAH Bros, ka haƙura ka bar mutanen nan da abinda suka zaɓawa kansu, kowa ai kabarin sa daban ba dole bane saisun yarda da gaskiyar da kake ƙoƙarin fahimtar dasu". A Ɗan jigace ya ce, "Ba fa ina so su yarda bane Omaine wannan ya rage nasu amma Ni dai gsky ce bazan fasa faɗarta ba, Ka sani tunda har suka kashe mahaifi na saboda kawai yana addinin Musulunci a ɓoye to whl Ni ba zan ɓoye ba kuma Bazan fasa faɗa mata Gsky ba da ita da mutanan nata, kuma a gaban kowa zanyi sallah zanyi azumi in tana da iko a hannun ta Nima ta kasheni"......... Ɗan shiru yayi kafin ya cigaba, "Ka sani Omaine a duk randa Queen Hirut tasan da yawa daga cikin mazan masarautar ta sun musulunta ciki harda mijin ta toh fa kisan gilla zata musu kamar yadda suka wa mahaifi na, shin a haka kake so mu cigaba da rayuwa? to ba zai yiwu ba ". Shuru omaine yayi cikin jimami dan yasan tabbas abinda Haisha'an ɗin ya faɗa gsky ne, dan sun karɓi shahada a wurin Haisha'an a ɓoye ne kuma duk ranar da Queen Hirut ta sani lalle yasan kashe su zatayi. Shuru yayi yana cigaba da tunani har ya gama shafa masa a bayan sannan ya ce, "Haisha'an kasan miye tunani na?"........ Girgiza masa Kai yayi alamar a'a sai ka fada. "Ka ajje batun yin gaba da gaba da Queen Hirut har sai munyi yawan da zamu qalubalance ta, kasan sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi"........ Shuru Haisha'an yayi baice komai ba, ganin haka yasa Omaine tashi ya wuce bathroom dan wanke hannunsa. ____________A bangaren Queen Hirut kuwa ta aika ne a Kira Muru akan Haisha'an, lokacin da Muru ta iso palace sallamar duk mazan sukayi sannan suka rufe ƙofa kamar yadda sukeyi in zasuyi wata magana a tsakanin su. A kujerun dake wurin Muru da sauran bayi suka zauna, dan su bayin su mata basa zama a ƙasa cox ana daraja su sosai. Sunkuyar da Kai tayi alamar girmamawa sannan ta ce, "Gani ya shugaba ta". "Muru!"....... Queen Hirut ta Kira sunan ta a kausashe. "Abun bauta ya sanyaya zuciyar shugaba ta"....... Muru ta faɗa still kanta na kallon ƙasa. "Ɗanki ya kasance babban me laifi a masarautar Nan, ba Kuma dan wani dalili ba da yanzu baya takawa a wanna doron duniyar tamu". "Tuba nake shugabata, haqiqa ni bani da ja kan duk abinda kika yanke akan Haisha'an ko da kuwa za'a yanke masa hukuncin kisa ne saboda lalle Haisha'an ya keta doka dole jinin sa ya halatta wa Abun bauta domin ya aikata saɓo ". Murmushin Jin daɗi Queen Hirut tayi saboda bata taɓa yanke hukunci ko Kuma tayi shirin aiwatar da wani abu kan Haisha'an ba Muru ta bata hakuri kan kartayi Wanda ita Kuma take ganin hakan matsayin tsantsar girmamawa da Muru ke mata. "Masarauta tana alfahri dake Muru dan haka kije bangare na ki jirani"......... Cikin jin daɗi Muru ta ce, " Ina godia shugaba ta"........ Miqewa tayi sauran bayin ma da suka zo tare suka miqe tare da risinawa alamar girmamawa ga Queen sannan suka rufawa Muru baya, suna fita wani bafade ya shigo, daga bakin Ƙofar ya zube, Mrs Ruthy kanwar Queen ce ta ce, " Kana iya shigowa Kibrom". Tashi yayi sannan ya ƙaraso tsakiyar palace ɗin da faɗin, "Abun bauta ya sanya miki albarka, an samu su Hailu a guardroom cikin fitar hayyaci bayan sun shiga tare da Haisha'an dan bashi horo, a yanzu haka suna cikin wani mawuyacin hali"......... Chief Benish ta ce, "Ina shi Haisha'an ɗin?" "Mun barshi a ciki baya motsi"........ Girgiza Kai tayi tare da kallon Queen Hirut sannan ta ce, "Kibrom Kaje kaji dasu". Miqewa yayi da fadin, "An gama legna". (mekakelegna, wato chief minister). Tashi yayi tare da sake durƙusawa alamar girmamawa ga Queen sannan ya juya ya fita. -----------------√ Anan wajen Amla tayi sallama da barrister sannan ta nufi inda su Hushaima suke tsaye ta buɗe musu motar ta hanyar danna remote ɗin dake hannunta tare da faɗin, "Ku shiga mana"........ Ita da Hushaima da Shazeen suka shiga gaba, baba ilerika da Sahnish suka shiga baya, Saida suka dau hanya ta ce, "Amma Hushaima kin Kira wani ne?". Itama Hushaiman da take cikin qullewar Kai ta ce, "Whl ban Kira kowa ba Amla, da nasan da Wanda zan Kira ya fidda ni a nan wurin ai da bazan Kai wanna kwanakin a ciki ba". Sahnish ya ce, "Amma fa Abun ya ɗaure min Kai, Kuma duk wanda yasa a saki Hushaima to lalle sama yake da su wannan Awais ɗin, kiga fa yadda DPO ya fito a rikice ko ganin gabansa ba yayi". "Gsky ba ƙaramin mutum bane Kam, saboda nima da na nemi ya min ƙarin bayani cewa yayi kawai daga sama ne, to daga sama aljanu ne?"....... Amla ta faɗa, baba ilerika ya amsa da, " koma dai minene ai sai mu godewa ALLAH tunda har ya fito da ita lpy". Amla ta ce , "haka ne baba, ALLAH dai ya tsare gaba Kuma Hushaima Dan ALLAH ki kiyaye ki dinga tausar wannan zuciyar taki, kinga dai wahalar da muka Sha ba Dan ALLAH ya taimake mu ya yanke mana wahalar ba da har yanzu muna ciki. Sahnish ka dinga bawa yayar nan taka ruwan buta tana sha ko ALLAH zai sa wannan zafin zuciyarta ta ya ragu". "In Sha ALLAH"........ Ta faɗa fuskarta na kallon titi, shi dai Sahnish uhummm kawai yace dan ya san Hushaima ba ruwan buta ba ko butar aka guggutsira aka bata in zuciyar nan ta motsa sai tarihi ya maimaita kansa. "To nifa inaga in kin samu wuri zaku sauke ni a nan dan ba gida na nufa ba"........ Faɗar Baba ilerika. "Baba za'a shiga majalisa kenan"....... Hushaima ta faɗa tana ɗan sassauta fuskarta. "To Hushaima abunki da me iyali ai saida buga buga, zama wuri ɗaya ai na Wanda ya Tara ne"......... Ya faɗa daidai lokacin da Amla tayi parking gefen titi ya buɗe Ƙofar ya fita. Ita kuwa Hushaima girgiza kanta kawai tayi da jin maganar baba ilerika, to mutumin da baya ciyar da gidan sa baya shayar dasu baya tufatantar dasu wani nauyi ne a kansa, juyawa tayi da faɗin, "Sahnish in akwai kuɗi a wurinka bani". Ragowar kuɗin dake jikinsa duka ya zaro tare da irgawa ya miqa mata su yana faɗin "Dubu huɗu ne suka rage dama". "To Sahnish ALLAH ya kaiku gida lpy"....... Baba ilerika da ya leqo ta window ya faɗa. "Baba ga wanna kayi kuɗin mota"....... Amla ce ta ce, " kinga riqe dubu huɗun zakuyi wani abu dashi, ungo miqa masa wanna"....... Ta ƙarashe tana miqa mata dubu goma. Karɓa tayi ta miqa masa. " Kai Hushaima harda wata wahalar Kuma?". "Bakomai baba, mun gode da karamci sosai, ALLAH ya saka da alheri". "Ni ne da godia ai Hushaima. Hajiya Nagode fa ALLAH ya tsare hanya"........ Ya faɗa yana ɗaga musu hannu tare da zaro karar sigarin sa da lighter ya kunna sannan ya tsallaka titin ya ɗauki hanya da Ƙafa. Amla ta ce, "Ni whl a farko kallon mutumin banza nake masa Amma ganin yadda yake ta Kai kawo tare da Sahnish sai naji ya burgeni whl". "Amla ai ko mutumin banza ma yana da ranar sa, bar ganin mutum haka kace bashi da amfani whl kowa da irin amfaninsa da Kuma ranar sa"....... Faɗar Hushaima. Sahnish ya amsa da, "Gsky dai baba ilerika ya mana rana, ko da ace bashi da Abun taimakon mu ya mana Kara Kuma ya kasance a tare damu da Kuma shawarwari". Amla ta ce, "Nima na gani whl, Amma dai daga gani har yanzu baiyi retire ba"........ Ta ƙarashe tana Yar dariya. Dariya Sahnish yayi shi ma yayin da Hushaima ta ce, "Baba ilerika ai sai shi, ALLAH dai ya shiryeshi". Haka suka cigaba da hira har suka ƙarasa gida, parking tayi a ƙofar gidan, fita Sahnish yayi tare da mata sallama , Hushaima ma buɗewa tayi Shazeen ta fita tana ƙoƙarin fita itama Amla ta tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta, "Hushaima"......... tsayawa tayi daga ƙoƙarin sanya ƙafarta a waje da take ta juyo tana kallonta. "Hushaima nayi wani tunani ne, ya kamata ki zama cikin shiri, domin ko ma waye yasa aka fito dake to zaizo gareki ko kuma saqonsa, saboda ya sanki".......... Tayi Maganar idonta akan layin. "Ya San ni?"...... Hushaima ta Tambaya da ɗinbin mamaki. Dawo da kallonta kan Hushaiman tayi tare da faɗin, "Tabbas ya sanki, saboda haka kawai daga sama ba zai taimaki mutumin da bai sani ba. Ni dai na faɗa Miki ki zama cikin shiri saboda bamusan da wacce zaizo Miki ba".......... Hushaima data shiga ruɗin tunani ta girgiza mata kai sannan ta juya ta fita ba tare data sake cewa komai ba. A ƙofar gidan ta tarar da Sahnish da Shazeen tsaye suna jiranta, wucewa tayi kawai ba tare data ce musu komai ba, Sahnish dake riqe da hannun Shazeen ya rufa mata baya yana faɗin, "Duk sallamar ce awa guda". Tun daga soro sukeji ife ife har suka ƙarasa ciki, tsayawa sukayi suna kallon yadda Yarinyar baba ilerika da yarinyar kawu adamu ke dokuwa a filin tsakar gidan, gefe Kuma iyayen su ne ke ta musayar baki suma kamar zasu kaiwa juna hannu, ga lady cyama data saki sauti a MP ɗin ta suna cashewa dasu yar charas. Juyowa Hushaima tayi ta kalli Sahnish kafin ta ƙarasa da sallama, Amma ina ba wanda ya lura dasu ma bare yaji sallamar ta, itama dai kawai tayi ne Amma tasan ba ji zasuyi ba. Wucewa ɗakinta tayi Sahnish ya buɗe mata ɗakin ta shige sannan suka bi bayanta shi da Shazeen, tsab suka samu ɗakin dan kullum sai Sahnish ya gyara kafin ya fita. Tsayawa tayi tare da faɗin , "Sahnish yanzu ruwa zakaje ka samo min nayi wanka, dan whl ni kaina kyankyamin kaina nake kusan sati guda ba wanka ".......... Wucewa yayi ya ɗauki bokitin dake ƙofar toilet sannan ya fita yana faɗin, "Yanzu kuwa". Wayarta ta ɗauka a jaka tare da dubawa, sosai ta cika da mamakin ganin ba missed call na Alhaji Awais ko ɗaya, shuru tayi tana tunanin ko dai ya gano itace ta jiwa yarinyar sa ciwo, katse tunaninta tayi tare da rufo ƙofar saboda hayaniya ta wuce ƙuryar ɗakin sannan ta danna masa kira sai dai har ta katse bai ɗaga ba, ba ƙaramin fargaba ta shiga ba da rashin ɗagawar tasa, shiru tayi tana bubbuga wayar akan lips ɗinta, cikin rawar jiki ta sake kiran number tasa har tazo katse wa ya daga. "Hello Hushaima"......... Ɗan shiru tayi saboda jin yanayin Muryar sa kamar ransa a ɓace yake. Tausasa Muryarta tayi da faɗin, "Alaji na kana Lpy?"............"Ina Lpy kwalisata ykk, kwana biyu"..........."Alaji lpy kuwa naji Muryar ka wani iri?". Tayi tambaye a ɗarare. Cikin sautin dake bayyana fushin sa ya ce, "ki bari Hushaima wai wata yar iska can da ba kowan kowa ba kawai ma'aikaciya a wurin saloon ne ko whatsoever ma wai ta fasawa yarinya ta kai sannan ta ɗauki matsiyacin hannunta ta mari matata, imagine kamar ni a ƙasar nan ai min wannan cin mutuncin". "Subahanallahi Alaji abinda ya faru kenan? an kama yarinyar amma?".......... Ta tambaya dan jin amsar da zaice . "Ina ranar da muka rabu to ai ranar abun ya faru, tun a ranar aka kulle shegiya, na ci alwashin tozarta yarinyar nan in kuma ga gatanta a ƙasar nan dan gobe za'a shiga kotu daga can in Sa a wulla min shegiya gidan yari amma sai dai me........" Shiru yayi yana huci alamar abun yana masa ciwo. "Kai alhamdulillah gsky Alaji gwara ka nuna mata waye kai a ƙasar nan, to in banda ma tsaurin ido irin na talaka ai ko makaho yasan bakin rijiya ba wurin wasan sa bane, ko daga kallon yar ka ma ai tasan ba tsarar ta bace amma har tayi mata irin wannan lahanin sannan ta mari Hajiya". "To ai Baki sani ba"..........Ya tare ta. "Wai ɗazu kawai na samu labari an sallame ta ba tare da izini na ba, wai na tambayi dalili amma saidai ace min inyi hakuri daga sama ne, duk wanda nasan zan kira kan batun nan na kira amma amsar ɗaya suke bani sannan anqi faɗamin daga saman waye, wai ni za'a tozarta a garin nan ". "To yanzu kai Alaji hukuncin me ka yanke?".........."Whl whl whl Hushaima jinin Hudaibiyya ba zai zuba a banza ba sai tasan cewa tsakanin sama da ƙasa akwai tazara ko uban waye ya tsaya mata kuwa sai na tozarta ta sai nayi watagigi da rayuwar ta"........... Shuru tayi can kuma ta ce, "Alaji baka tunani turota akayi?". Dif Awais yayi ya ɗauke wuta domin sai da ta faɗa wannan tunanin yazo kansa kenan anyi amfani da ita ne don cin ma wani abu yanzu kuma da suka samu abinda sukeso suka bi ta ƙarƙashin ƙasa suka sa aka sake ta, jijjiga kansa yayi cike da gamsuwa da tunanin da yayi ya ce, "Kinsan kwata kwata banyi wannan tunanin ba, kai gsky kina da brain My ƙwalisa"........ Lumshe idanunta tayi ta buɗe tana sakin wani shu'umin smirk ta ce, "Alaji ina so Ka barmin komai a hannu na, na maka alqawari sai na gurfanar ma da ita a gabanka, da kaina zan kawo ma ita".......... Dukda yana cikin yanayin ɓacin rai hakan bai hana shi darawa ba saboda maganarta ta da yaji kamar tatsuniya, da har ya fara wani tunani daban sai kuma yaji ta shigo da wannan shirmen, dariya yayi sannan ya ce, "Kaji ki da wata magana dan ALLAH, ke da baki santa ba ta ina zaki iya nemo ta. Ni fa sai da kikayi maganar nan ƙwaƙwalwata ta kawo wuta saboda yarinyar da akace yar matsiyata ce gaba da baya bazawara kuma me ya'ya marayu kaiii akwai wani abu. Amma yanzu ke bakisan fuskar ta ba, baki san inda take ba sannan kice zaki kawo min ita?". Wani silent smile ta sake saki tare da yin one step forward ta ce, " Alaji sanin talaka ai sai talaka, in dai har ka yarda dani da kuma alqawarin da na ma ni kuma sai na kawo ma ita cikin ruwan sanyi, kuma zan so duk wannan alwashin daka ɗauka ka aiwatar dashi a gabana. Amma inaso kafin nan ka sa a fara bincika ma ko turo ta akayi kuma ka sa ido a mutanan dake kusa dakai ".......... Ɗan shiru yayi yana sauraran ta da kuma tunanin Maganarta na ƙarshe, ba dan ya gama yarda da batun kawo yarinyar ba gabaɗaya amma dai yaji ɗan sanyi sanyi, dan haka ya ce, "Shikenan ƙwalisata zanyi duk yadda kikace, kuma na bar Miki komai amma fa in kika Saɓa alqawari kuma........." "Hmm Alaji kenan karkayi mamaki in nace ma wanna shine alqawari na uku da na taɓayi a duniya, saboda bana ɗauka alqawarin da zan karya, na yanzu shi ne na uku kuma sai na tabbatar na cika ma shi saidai kai ka fasa abinda ka faɗi". "I like your confidence, kina burgeni matuka whl, kinsan wannan rikicin ne ya hannani kiranki tun ranar, ke ma kuma sai yau kika tuna Dani". "ALLAH Sarki Alaji, yau na fito daga asibiti fa kwana na shida acan bansan inda kai na yake ba, zazzaɓi nayi me zafi"........ A ɗan dame ya ce "Subahanallahi ya jikin naki ?". Sake langwaɓewa tayi da faɗin, "Da sauki Alaji amma fa naji jiki ba ƙarya".........Ta ƙarashe tana kallon Sahnish da ya shigo da bokitin ruwan ya kai mata a ƙofar toilet ya Ajje saboda Shazeen dake cikin bayin, sannan ya dawo bakin katifarta ya zauna yana kallon Hushaiman dake tsaye tana waya. "Zanzo anjima in sha ALLAH, ALLAH ya ƙara sauki kinji sannu, da ba dan wannan abubuwan da suka shige min kai ba ai da ko asibitin ne sai nazo, to bansani ba"........ Ya mata ƙarya dan Alhaji Awais duk wani iya shegensa a ɓoye yake kamar yadda kukaji Amjad ya faɗa shi kaɗai yasan wannan ɓoyayyen halin nasa dan ko su Nuhail da Julaybin basu sani ba ballantana kuma iyalinsa daga shi sai direban sa Zubairu wanda shi ne idon sa a harkar. "Bakomai Alaji Nagode sosai, sai kazo ɗin". "Ba komai ki huta yanzu sai na shigo zuwa anjiman in sha ALLAH ". TO FA JAMAA GA DAI HUSHAIMA TA DAU ALQAWARIN KAWO WA ALHAJI AWAIS WADDA TA FASAWA YAR SA KAI BAYAN KUMA TA SAN ITA CE , SANNAN TA CE YA SANYA A MASA BINCIKE SHIN KO TURO TA AKAYI KUMA YA SANYA IDO AKAN MUTANAN DAKE KUSA DASHI, SHIN BAKWA GANIN TA FAƊI HAKA NE DAN TA KAWAR MASA DA HANKALI WANI WURI? KO KUMA TAYI HAKAN NE ITAMA DAN CIN MA WANI NUFI NATA? TO WAI SHIN YA KUKE GANIN ZA'A ƘARE? ZATA KAI MASA KANTA NE KO KUMA YA ABIN ZAI KAYA ? WANI ALQAWARURRUKA NE GUDA UKU DA TACE A TSAWON RAYUWAR TA SU KAƊAI TA TAƁA ƊAUKA? YA BATUN ALWASHIN FANSA DA TACE SAI TA ƊAUKA AKAN HUDA WATO YARINYAR ALHAJI AWAIS? WAYE YA SA AKA SAKI HUSHAIMA? MIYE DALILINSA NA SAWA A SAKE TA? SHIN YA SANTA NE DA GASKE KAMAR YADDA AMLA TA FAƊA ? WAI SHIN SU WAYE SU MA? INA IYAYEN SU? INAGA TAMBAYOYIN ZASU MUKU YAWA BARI DAI NA BARKU HAKA MU HAƊU A STEP 2, KARKU BARI A BAKU LABARI. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥              _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐                *SULTYWRITES*                          A-K-A                [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22            STEP 1 PAGE _______ 68 & 69            AURELLON SULTANATE💎 Rouslan bai tarar da Reeslan ba sai a mota, shiga yayi kawai dan already an buɗe masa, baice da Reeslan komai ba shima baice dashi komai ba a haka motocin suka fice daga ɓangaren na su. Ɗan juyowa Rouslan yayi da niyyar satar kallon Reeslan daidai lokacin shi ma ya kallo Rouslan ɗin, kallon juna sukayi na tsawon second sittin kafin su sake ɗauke kansu still basu ce da junansu komai ba, can kuma a hankali kamar mai tsoron wani ya jisu Rouslan ya ce, "Meysa baka sanarwa Ummu ba?"......... Kallon sa Reeslan ɗin yayi kafin ya ce, "Kai meysa baka faɗa mata ba". "I can't! "........ Ya faɗa muryarsa ɗauke da damuwa. "Abun da kake tunani ba shi Ummu take nufi ba Rouh, saboda akwai abinda ke faruwa d........" Shuru yayi tare da maida kansa kan glass ɗin window yana kamo lips ɗin sa na ƙasa. Juyowa Rouslan yayi gabaɗaya ɓangaren Reeslan cikin wani irin yanayi ya ce, "Akwai wasu abubuwan da suka fi wa'annan kenan ?"........ Juyowa Reeslan yayi kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru tare da sake juyawa yana kallon cikin masarautar tasu ta windown . Rouslan Bai sake cewa komai ba sai ma lumawa da yayi cikin wata duniyar tunanin . Kamar wanda aka tsikara cikin faɗa ya ce, " Kai wai baza ka taka motar nan bane kana tuqa mota kamar wanda ke tuqa jaki"......... Ba sai na faɗa ba kunsan waye zai faɗi haka Reeslan Maleekh ne naku na gargajiya. "Afuwan Maleekh, ALLAH ya huci zuciyar ka"......... Driver ya faɗa yana ƙara take motar a guje. Ƙwafa yaja baice komai ba har suka ƙarasa masallacin fada in da ya cika jingim da mutane bako masakar tsinke duk inda ka wulga mutane nen su ne, wai a lokacin ma ba'a fito da gawar yassar ɗin ba kenan. Can na hango Sultan kana kallon sa kasan yaji mutuwar ƙanin nasa . Fadawan da suka rako su Rouslan ne suka shige gaba tare da fara tutture mutane suna faɗin, "Gyara gyara magada kujera aurellon zasu wuce, takawar ku lpy yayan sarki jikan sarki sarauta aurellon dole"......... Basu tsaya ko ina ba sai wurin mahaifin su Sultan, rungume shi sukayi wannan ta left wannan ta right ba sai na faɗa ba kunsan yadda gaisuwar larabawa take. Dan bubbuga bayan su yayi a hankali tsawon seconds kafin su ɗago da faɗin, " ALLAH yajikan Ammu, ALLAH ya bamu hakurin rashi yasa Mala'ikun Rahma su karɓi bakwancin sa". A hankali Sultan ya motsa labbansa tare da amsawa da ameen, daga haka suka koma gefen sa suka tsaya suna jira a fito da gawar. ______________Tun da ya fito hadimai suke zubewa suna kwasar gaisuwa a wurin sa ko lura da ummie dake zaune a falon tare da masu mata hidima baiyi ba ya nufi waje yana wani buɗawa kamar wani nigga. "Sahel!"...........Ummie ta kira sunan sa. Tsayawa yayi tare da juyowa sai kuma ya fara takowa zuwa inda take yana faɗin, "Ummie kina nan ashe ban lura ba ai, na fito ina sauri naje wurin rasuwar nan kar ki zo kina faɗa kuma"........Ya ƙarashe yana faɗawa cikin luntsumammun cushion ɗin dake cikin makeken falon. Kallon khadiman nata tayi ba tare da tayi magana ba duk suka miqe suka bar wurin, dawo da kallon ta tayi kansa yana sanye da wani arnen crazy jean sage colour tare da wata oversized t shirt dark blue, ƙafarsa sanye da wani white canvas, haka wuyansa wasu dogayen sarqoqi ne kunnen sa ɗaya maqale da ɗan ƙaramin ɗan kunne me masifar kyau da tsada. " Yanzu Sahel a haka zaka fita? a haka zaka je gaban mahaifin ka da al ummar gari? a haka zaka je wurin da akayi rasuwa? Ba fa club bane ko joint ba kuma cikin abokai zaka ba. Kawun ka ne fa ya rasu, haba dan ALLAH wai kullum sai ka sani magana ne?". Kallon jikinsa yayi da faɗin, "Ummie miye aibun kayan nan fisabilillahi, ko kinsan dollars nawa na ɓatar wurin sayen su kuwa?". "Kai da ALLAH tafi can sha sha sha da baisan inda ke masa ciwo ba, ka tashi kaje ka canzo wannan kanbaltun kayan kamar ɗan bori ka kuma cire wa'annan sarqoqin banzan, kayi shiga ta mutunci kazo ka wuce"............  Miqewa yayi yana faɗin, "Gaskiya ni zan koma in da na fito wannan ai takura ne, ace mutum bazai sake yayi abinda yake so ba, to in banyi a gidan mahaifina ba a ina ake so nayi". "La ilaha illallahu, oh ni balqis ALLAH nagode ma wannan yaro ya zanyi dashi ne, duk inda nayi sai yayi wani wurin"........... Ta faɗa cikin damuwa, tana nan zaune yazo ya fice har lokacin qunquni yake, ya dai sauyo kayan amma kuma still ƙana nan kaya ne saidai wannan da ɗan mutuncin su. Ganin driver ya nufi bangaren Sultan ya sashi faɗin, "Bashshar ina muke zuwa ne ina cewa wajen rasuwar zamu je". "Eh ranka ya daɗe ai a bangaren mai martaba ake zaman matan kuma a gidan marigayi suke". "Okey"...........Ya faɗa yana zaro wayar sa ya shiga lallatsawa har suka ƙarasa, buɗe masa ƙofa akayi bayan sunyi parking amma sai da yaja kusan minti ishirin yana waya da wata budurwa sa mai suna Tina, Sannan ya sako ƙafafunsa waje ya fito, nan fadawa suka rufe shi suna masa kirari masu masa gaisuwa nayi, bundle ɗin 1k ya zaro a wata jaka dake rataye a ƙugunsa ya ɓalle wrappers ɗin tare da watsa kuɗin sama take suka shiga kokawar ɗiba, wata ya sake ballewa ya watsa saida yayi haka kusan sau huɗu sannan ya dauki hanyar shiga duk da kuwa a wajen ma akwai mutane sosai dake zama. Yana shiga ya hango mahaifin nasa zaune kan wata one seater royal cushion daga gefen damarsa Rouslan ne da Reeslan zaune suna taya shi karɓar gaisuwa sai kuma su Ammu Fayzan wanda suke uba ɗaya da mai martaba da kuma su wazir da sauran hakimai, da kuma duk wasu masu matsayi a masarautar su ne cike a wannan falon, ƙarasawa yayi ta tsakiyar su ba tare da ya cire takalmin sa ba ballantana yayi sallama sai hannu kawai da ya ke ɗaga musu har ya Ƙarasa wuri su Sultan, gefen su Rouslan ya zauna tare da miqa musu hannu sannan ya ce , " Abbu ya qarin hakuri, a mun afuwa ban samu ƙarasowa da wuri ba whl, ashe Ammu ya wuce to ALLAH yasa anje a Sa'a"............ Sunkuyar da Kai su wazir sukayi yayin da Reeslan ya juyo ya zuba masa ido kawai, kallon Reeslan ɗin Rouslan yayi suka haɗa ido ya sunkuyar da kansa . Wazir ne ya ɗan matsa kusa da Sultan da kallo ɗaya zaka masa kasan ransa a ɓace yake tun bayan shigowar Sahel ɗin, magana suka ɗanyi da wazir kafin ya tashi ya zo inda suke zaune ya kamo hannun Sahel ɗin da faɗin, " Muje nayi magana dakai". Miqewa yayi yana faɗin, "To Abbu Ni daga can zan wuce ALLAH ya kara hakuri"......... Ya faɗa tare da bin wazir suka wuce ɗaya falon da ba mutane. Gyaran murya wazir yayi da faɗin, "Sahel! Ran mai martaba ya yi masifar ɓaci da abinda kayi a matsayin ka na ɗansa, wannan shigar ba da ita ya dace a ganka ba a daidai wannan lokacin, sannan a lokacin da ake cikin alhinin mutuwa bai kamata kazo ka tada hayaniya ta hanyar watsa kuɗi ba, wannan ya saɓa dokar Masarauta domin watsa kuɗi Kamar almubazzaranci ne shi kuma almubazzari ALLAH da kansa ya faɗa a cikin Alqur'anin sa me girma innal mubazzarina kanu ikwanash shayaɗeen, in sadaka kayi niyya ka bayar hannu da hannu a mutunce sannan magan........"........... Katse wazir yayi da faɗin, "Ah Ah baba wazir Kar muyi haka dakai, ba wani dogon turanci kawai fito kace Abbu baya buqata ta a kusa da shi, dama can yafi son su Maleekh a wurin sa saisa su baya ganin laifin su"............ Yana kaiwa nan ya juya ya fita ya bar Wazir sake da baki. Hotel ɗin da ya kasance na sauqar baki ne a cikin masarautar nan Sahel ya buqaci a wuce dashi sannan ya ɗaga waya ya kira wata number, ana ɗaga wa yace, "Hello Captain".........  Cike da girmamawa wanda ya kira da Captain ya ce, "Da girman kujerar ka yarima ƙarami"..........." Am kaga a shirya min tafiya yau zuwa Paris". "An gama yarima Ƙarami amma saidai shirye shiryen zasu iya kai mu zuwa ƙarfe 12 am".........."Ba matsala da an gama ka kira ni". "In ALLAH ya yarda ranka ya daɗe karka samu damuwa"........ Bai tare da ya bashi amsa ba ya kashe wayar yana ciza baki. Suna Ƙarasawa hotel ɗin da baza ka taɓa tunanin wai a cikin masarautar yake ba saboda girman sa dan zai iya kai wa hawa ishirin ko sama, anan duk wani sarki ko shugaban ƙasa da ya kawo ziyara masarautar yake sauka, a samansa an rubuta "AURELLON GUEST IN" da wasu army green stones masu ɗaukan ido, karku manta komai na aurellon daga gold sai diamond sai kuma sauran precious stones. Fadawan nasa na ƙoƙarin binsa domin rakiya ya dakatar dasu da faɗin, " kuje kawai kamar 11pm kwa dawo"......... Ya faɗa tare da shigewa da sauri securities ɗin suka fara zubewa suna miqa masa gaisuwa, hannu kawai yake ɗaga musu har ya Ƙarasa reception ya karɓi key ɗin ɗaya daga cikin vip rooms sannan ya wuce wurin elevator. Su Rouslan kuwa ranar basu motsa ko ina ba sai dare bayan anyi sallar Isha tare dasu a masallacin fada suka musu sallama suka wuce. Sai da suka shiga mota Reeslan ya ce, "Rouh kaji abinda naji kuwa ɗazu?"........."A ina?". Rouslan ɗin ya tambaya ba tare da ya kalleshi ba. Murya can ciki ya ce, "Warin wine naji a jikin Sahel".........Wani irin side look Rouslan ya bashi kafin cike da dimbin mamaki da ya gaza ɓoyuwa a muryarsa ya ce, "Warin me?"......... Shi ma ba tare da ya kalleshi ba ya ce, "Wine, kuma ba wai tabbas itace".......... Rouslan baya buqatar ya musawa Reeslan Saboda yasan duk abinda zai faɗa gsky ne , da ɗan alamun mamaki ya ce, "But taya aka samu wine a Aurellon?".......... Girgiza masa kai kawai Reeslan ɗin yayi Amma baice komai ba, shi ma bai sake ce masa komai ba sai Nazarin yadda akayi Sahel ya samu wine a cikin masarautar tasu. A gajiye suka ƙarasa gida dan haka ko ɓangaren Ummu basu shiga ba suka shige nasu, zubewa Rouslan yayi kan gadon yana faɗin, "Wash whl nagaji yau mun zaunu ba ƙarya, Habiby massage please"......... Ya ƙarashe a shagwaɓe, harara Reeslan ɗin ya watsa masa yana rage kayan jikinsa ya ce, " kai dama ai baka da wuyar gajiyar, Dan abu kaɗan ka gaj........" Bai ƙarasa maganar dake bakin sa ba wata guguwa mai ƙarfi ta doko windows ɗin ɗakin har saida suka girgiza, zaune Rouslan ya tashi yana kallon windows ɗin kafin ya ce, "Dama akwai hadari a garin nan ne da muka shigo?". Reeslan bai bashi amsa ba illa wurin window da ya nufa, fitulun ɗakin ne suka fara rawa hakan yasa Rouslan tashi da sauri ya Ƙarasa wurin Reeslan da ya ɗaga curtain ɗin ɗaya daga cikin windows ɗin, a tare suka kalli juna cikin firgici lokaci guda kuma Reeslan ya fara huci Kamar wani kumurcin zaki shi kuma Rouslan ya riqo damtsen hannun Reeslan ɗin yana jin wata irin juya na ɗibansa. ______________11:30pm daidai Sahel ya fito daga hotel ɗin, ya sake wanka ya sauya kayan sa, nan ya samu fadawan sa na jiran sa kamar yadda ya faɗa musu, shiga yayi sannan suka ɗauki hanyar airport ɗin dake cikin masarautar, nasan zuwa yanzu kun waye da irin girman da Aurellon sultanate take dashi. Suna daf da shiga airport wasu mutane suka sha gabansu hakan ya sasu tsayawa ba shiri, dukkansu fuskokin su a rufe ne idanun su kawai kake gani , ƙofar motar da Sahel yake ciki suka buɗe tare da faɗin, "Fito "......... Da mamaki ya kalle su ɗan yasan basu taɓa fuskantar barazanar yan fashi ko yan ta'adda cikin masarautar tasu ba saboda tsaron da suke dashi. Fadawan ne suka fito gabaɗaya zasu rufar musu ai kuwa suka fito da bindigu tare da faɗin, "kuna motsawa sai mun harbeku, kuyi ƙasa, kai kuma ka fito"............ ɗaya daga cikinsu ne ya harzuqa ganin mutanen da basu kai su power ba suna ƙoƙarin kawo musu wargi, take murɗaɗɗun tsokokin dake kirjinsa suka fara motsawa, cikin rashin tsoro ya dunfaro su saidai kafin ya ƙaraso sun sakar masa bullet a ƙafa, take sauran suka sauka kan guiwowin su cikin firgici, shi kuwa Sahel ganin abinda ke faruwa ai bai ƙara minti guda ba ya sauko, mutum biyu suka sashi gaba zuwa wata mota sauran Kuma suna tsare da fadawan har saida wa'ancan suka shiga suka tada motar sannan suka bar wurin da gudu suka wuce motar tasu suka ɗale tare da tashinta suka bar wurin, suma fadawan basu tsaya ba suka sabi ɗan uwan nasu da aka harba suka sanyashi cikin mota suka rufa musu baya, saidai ko ƙurar motar su basu tarar ba. TOH FA SU WAYE SUKA ƊAUKE SAHEL KUMA? ME ROUSLAN DA REESLAN SUKA GANI HAKA? MEYE DALILIN TSANAR DA MAAMA TA YIWA SULHAM? WAYE WANDA SUKAYI WAYA? MIYE TSAKANIN SU? MU HAƊE A STEP 2 DOMIN SAMO DUKKA AMSOSHIN NAN. ------------------------√ Suna ƙarasawa asibiti Amjad bai jira an gama tsayawa ba ya buɗe ƙofar motar yayi cikin hospital ɗin, Bai jima ba ya dawo tare da wani Dr da nurses sai gadon tura marassa lpy. Nan aka ɗaura Ace akai sannan aka wuce dashi ciki, dukkansu rufa musu baya sukayi harda jami'an tsaron da aka bawa Amjad ɗin, a ƙofar ɗakin suka tsatsaya, Jey ya ce, "Wai me ya faru dashi ne?".......... Ash ce ta amsa masa da , "Tashi yayi kawai sai muka ga ya dafe kansa kafin kace wani abu ya faɗi" .......... Kiara na ƙoƙarin magana Dr ya fito. "Dr ya ake ciki?"......... Ash ta riga tambaya. "I'm sorry ko da kuka zo dashi ma ya riga ya rasu"........... Amjad ƙasa ko da motsi yayi shi dai kawai ya zubawa bakin Dr ido ne, Ace ɗin da yanzu suke tare, yanzu suka gama magana sannan daga Faɗuwa ace ya rasu, gabaɗaya ya ɗauke wuta Amma a fuskar sa baza ka iya gane halin da yake ciki ba. Jey ne ya ce, "Kai Dr ka san aikin ka da kyau kuwa?"..........."Sai haƙuri Amma ya riga da ya rasu ranka ya daɗe". "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un"........... Jey ya faɗa yana cafkar gashin kansa da matukar ƙarfi . "Dr what was the cause of his death?"........... Kiara ta faɗa a ruɗe. Girgiza Kai Dr yayi tare da faɗin, "We don't find any reason komai na jikin sa lpy ƙalau, kawai kwanan sa ne ya ƙare". "No Dr ba yadda za'ayi mutum ya mutu ba dalili, ko dai baku da abubuwan gwaje gwaje yadda ya kamata ne?"............ Ash ta sake tambaya, abunka da ba musulma ba su a nasu sanin mutum baya mutuwa haka kawai dole sai da sanadi. Daƙyar Amjad ya jawo magana daga ƙirjin sa dan tabbas yaji zafin mutuwar Akil amma Kuma ta Ace tafi tsaya masa a rai, "Dr ku shirya gawar, Ash kuyi duk cike ciken da ya kamata ku karɓo gawar".......... Yana faɗa ya matsa wurin Jey tare da dan bubbuga kafaɗar sa alamar ban haƙuri, ɗagowa Jey yayi idanuwan sa sunyi jajir kusan duk da basu kasance yan ƙasa ɗaya ba a wuri ɗaya aka basu horo kuma anan suka fara aiki kafin kowa ya koma aiki ƙarkashin hukumar ƙasarsa amma duk wani aiki na haɗin guiwa irin wannan tare suke yi. Ace abokin faɗansa ne dan akwai shi da son tsokana da wasanni, shi Kuma Jey baya san damuwa da surutu sai dai shi kuma Ace indai yana wuri to fa sai ya hana Jey sakat. Girgiza masa Kai Amjad yayi tare da jan hannun sa sukayi waje jami'an tsaron suka rufa musu baya, a jikin motar su suka tsaya Jey ne ya ce, "Amjad na fara sarewa akan case ɗin nan, tun tafiya batayi nisa ba mun rasa mutum biyu, Anya kuwa kana ganin zamuyi nasara?". "Haba Widad, meysa zaka nuna gazawa meysa zaka alaqanta mutuwar Akil da Ace da wanna case ɗin da muke "............Girgizawa Amjad Kai yayi da faɗin, "Ka tuna lokacin da aka harbi Akil kai da kanka ka shaida mana sunce wanna shi ne hatsarin dake tattare da neman sanin Shadow". "To Widad yanzu wani ne ya harbi Ace ko Kuma munje binciken Shadow ne Ace ya mutu? Ka ajje wanan maganganun gefe, ka sani in mun jajirce mun samo shadow lada zamu samu ka tuna dubban rayukan al'umman da suka salwanta a hannun sa, kayi tunani ta wace hanyar ran su yake fita a jikin su, wace irin azaba ake gana musu?"......... Dakatawa yayi tare da jan zazzafan numfashi ya ce, "Ka kira ka sanar dasu sir Richard, nasan zasu buqaci a tura musu gawar can Kai sai ka bi su saboda su Kiara mata ne bai kamata ace su zata je ba, and moreover Ashley ma kasan dole zan buqace ta saboda baza ayi wasa da wannan damar ba"......... Gyada masa Kai Jey yayi kawai, a lokacin kuma su Ash suka fito da gawar tare da wasu nurses, bayan motar Amjad da yasa aka ciccire kujerun aka saka gawar. Har suka gama komai suna shirin tafiya Amjad ya lura da Jey dake tsaye kawai yana binsu da ido . Komawa yayi wurin sa a sanyaye ya ce, "Widad muje !".......... Binsa yayi a baya suka wuce. Gida Amjad ɗin da suka baro suka nufa tun daga hanya Jey ya Kira ya sanar da sir Richard, take aka bada izinin kai gawar tasa Saboda su Kuma a can su sir Richard ɗin zasu Kira familyn sa su sanar dasu dan su je can ɗin su haɗu. Cikin minti goma Sha biyar aka gama musu komai na tafiya Kuma sunyi Sa'a a daren da misalin 4am akwai jirgin da zai tashi zuwa Belgium ɗin dan haka suka sake juyawa suka ɗauki hanyar airport ɗin gabaɗayan su, Nan ma saida aka gama duk wasu cike cike Dan ma dai duk inda suka nuna ID ɗinsu ba'a tsaurarawa, tuni aka wuce da gawar Ace, Jey ya kira mahaifiyar sa ya sanar mata saboda bai samu ya koma gida ba ta bishi da addu'a. Side hug ya bawa Amjad sannan ya ɗagawa su Ash hannu ya wuce da ɗan sauri saboda har an fara sanarwa jirgi ya kusan tashi. Jan hannun Ash dake share hawaye kiara tayi suka bar wurin, shi ma Amjad bin bayansu yayi kansa a ƙasa baza ka taɓa iya gane yanayin da yake ciki ba, Ace ya shigo ƙasar Nifaz da ƙafarsa yau an fita da gawarsa kamar yadda Akil ya shiga Denmark da ƙafarsa aka fitar da gawarsa, maganar Widad ta ɗazu ce ta dawo masa cikin kansa, saurin kawar da zancen yayi yana ƙarfafa kansa ya shiga motar da aka buɗe masa suka wuce gidan nasa.  Suna shiga wayar Philip na shigo masa inda yake faɗa masa sun ɗau hanya da mutanan. Tunda suka koma ba wanda ya rintsa a cikin su har gari ya waye, wanka kawai sukayi suka Sha tea Ash ta fita wurin Nazbeer da Philip ya bawa na'urorin ya kawo masu ta koma ciki wurin Amjad ta bashi. Ɗai ɗaya ya basu itada Kiara shi ma ya ɗau ɗaya, ƙurawa biyun dake hannun sa ido yayi wanda suka kasance ɗaya na Widad daya na Ace, zubasu yayi a aljihu tare da miqewa kan resting chair ɗin dake bedroom ɗin nasa. Baisan iya tsayin lokacin da ya ɗauka a haka ba yaji knocking, kallon ƙofar yayi tare da faɗin, " come in "........ Kiara ce ta shigo tare da faɗin, "Boss Philip ya Kira yace Yana ta Kiran wayarka baka picking, nan da 20 minutes zasu ƙarasa Dan haka mu kasance a ankare"........... Ido kawai  ya zuba mata harta gama ma bai sani ba ya tafi wani tunanin daban har Saida ta ce , "Boss should I go". "Kiara Kevin!".......... Ya Kira full name ɗin ta. Da mamaki Kiara ta ce, "Yess boss"......... Dan kwata kwata baza ta iya irga lokutan da Amjad ɗin ya kirata da full name ɗin ta ba. "Ku ɗauko systems ɗinku ke da Ash ku sameni a Survey room"........... "Okay". Ta faɗa tare da juyawa ta fita tana waiwayen sa. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin data rufe ƙofar sannan ya tashi ya ɗauko wayar sa missed calls ne da messages da yawa bai bi ta kansu ba ya ɗauki na'urorin ya nufi wurin curtain ɗin, ɗan janyeshi yayi a sanyaye sannan yayi ƴan latse latsen sa, ya sanya palm ɗin nasa tayi scanning ƙofan ya buɗe, kunna wutar ɗakin yayi ya jona computer ya sanya na'urar da Philip ya aiko ya saita komai, yana cikin haka ya hango shigowar su Ash ta ƙaramar cctv camera ɗin dake jikin curtain, ɗaukan Wayarsa yayi ya tura wa kiara saqo, suna ƙarasawa wayanta dake hannunta yayi ƙara alamar shigowar saqo, code ɗin da zasuyi amfani da ita ya Turo mata, sanya code ɗin tayi Ƙofar ya buɗe suka shiga, kujera suka ja suka zauna jiran Kiran Philip, basu fi 8 minutes ba ya Kira Ash tare da sanar mata yanzu zasu ajje su. "Okey"...........Ta faɗa tana typing a system ɗinta dake kan cinyarta sai ga su dajin da suke ya bayyana dake shi ma Philip ɗin ya sanya irin na'urar da suka sanyawa mutanen saboda tsaro. Hakan ce a wurin Kiara da Amjad ma, suna ganin lokacin da su Philip suka ɗauki wasu manyan jakankuna na kuɗaɗen da aka ajje musu sannan suka shiga wata mota suka bar container da mutanan suke ciki anan. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* 👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑 🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥 _A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._ ⭐MALLAKIN⭐ *SULTYWRITES* A-K-A [YOUNG WRITER]✍️ ___________________________________ *STARS TALENT WRITERS*. _Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._ @wattpadd sultywrites22 STEP 1 PAGE _______ 70 Kuɗaɗen suka ɗauka tare da shigewa ɗayar motar ciki harda driver container, suka juya suka bar iyakar. Kusan 10 minutes aka buɗe container wasu mutane ne su biyu duk fuskokin su a rufe ba abinda ake iya gani sai ƙwayar idanunsu, Mutum ɗaya suka fitar daga container suka sanyashi gaban motar sannan suka ja suka Miki hanyar da tabi left side nasu suna tafiya akan dogon layin, dan su basu ƙetara iyakar ba su kuma basu cikin ƙasar Nifaz, sun dai raba hanya, a haka sukayi tafiya me ɗan nisa sannan sukayi parking, wasu mutanan ne masu irin shigarsu suka zagaye container. Sauqowa sukayi tare da buɗe mutanan suka firfito dasu sannan suka tisa su a gaba . Sake nutsuwa su Ash sukayi tare da danne Na'urar sauraron sauti dake kunnuwansu yadda zasuji maganganunsu dakyau, sunyi tafiya me ɗan nisa da ƙafa dan har sun shiga desert kafin su ja su tsaya ɗaya daga cikin mutanan ya ce, "Ai inaga munzo ko?". Ɗayan ya amsa da, "Yes zamu iya tafiya, mun gama namu aikin"......... Juyawa sukayi suka fara tafiya, sake nutsuwa su Amjad suka yi ko ƙwaƙwaran motsi basa yi sai dai me, kafin ƙiftawar ido komai yayi disconnecting daga kan GPS, video feed da kuma sound ɗin, da sauri Amjad ya tura kujerar sa baya tare da tashi ya matsa wurin su Ash saidai su ma hakan take a wurin su. "Ya akayi haka?"......... Ya tambaya ƙirjin sa na dukan tara tara. Ashley ta ce, "Ko dai sun gano ne?"......... Kiara ta amshe da, "Akwai matsala fa, dan mun rasa su" . Dunqule hannu yayi ya nausa a iska tare da saurin ɗaukan wayar sa yayi Kira a headquarter ɗin su ta ƙasar Nifaz ya bada sanarwar a aika musu da sojoji kan iyaka a kuma rufe boarders ɗin ƙasar gabaɗaya, yana gama faɗa bai tsaya sauraron answer ba ya kashe ya kira Juraysh, ringing take amma ba'a ɗaga ba jijjiga wayar ya shiga yi yanajin kamar ya tashi sama. Da sauri kuma ya danna wayar ya kashe lokacin da Juraysh ɗin ya amsa saboda kwata kwata ya manta cewa a gida basu san waye shi ba, juya akalar kiran yayi zuwa headquarter ɗin tasu ya sake shaida musu a tsayar da duk wasu kaya da zasu fita ta ruwa daga ƙasar Nifaz ɗin sannan ya kashe Kiran ya wuce ya ɗauko sectra tiger smartphone ɗin sa ya kunna yayi connecting da VPN ɗinsu, kira yayi zuwa headquarter ɗinsu ta Brussels amma bai samu Sir Richard ba ance suna meeting, Sir Johnson dake kan layi Amjad ya shaidawa halin da ake ciki saboda yana so su ma su zama a ankare a kuma shaidawa duk sauran countries da abun ya shafa domin su baza jami'an su. Cire na'urar sauraron sauti dake kunnensa yayi ya wurgar cikin takaici da baƙin ciki ya sake komawa kan computer ɗin ya cigaba da ƙoƙari ko zaiyi connecting amma ba abinda ya samu, ba tare da ya ɗago ba ya ce, "Ash Kira Philip kice babu wani second option da za'a yi trying?".........." Okay"....... Ta faɗa tana me dannawa Philip kira saidai amsar da ya basu itace Babu, dake a handsfree tasa yaji komai kafin yace wani abu sectra tiger smartphone ɗin sa ya fara Ƙara ɗagawa yayi ganin daga Brussels ɗin ne, cikin faɗa sir Richard ya ce, " Agent Amjad ya akayi haka ta faru ? Yanzu ake sanarmin saqonka, meke faruwa?". "Sir an samu matsala ne, mun rasa mutanen Kuma plan ɗin mu ya rushe ". "Whatttt Kun rasa mutanen fa kace, Amjad ya zakayi wasa da rayukan jama'a, ai anyi dakai cewa zakayi amfani dasu ne wurin kama me laifi ba wai ka salwantar da su ba ". "I'm sorry sir but dole ne mu rasa wasu rayukan domin ceto wasu, Ina buqatar a nema min izinin shiga Bangkok yau domin aiwatar da wani bincike, shi ne kawai second option ɗin da nake dashi sir kuma in sha ALLAH bazan bari wannan damar ta kauce min ba". Kashewa Sir Richard yayi ba tare da ya bashi amsa ba, yayin da shi kuma ya juya zai fita Ash ta ce, "But Amj........" Tarar numfashinta yayi da cewa, "But what Ash, we don't have a choice , we have to go for the plan B and I have to do it myself, idan wani abu ya samu mutanan nan, zan ɗaura alhakin su a kaina ne cox I was the one that brought up this idea dole ne duk yadda za'ayi na je Bangkok domin ganin nayi Amfani da plan B ɗin nan, just pray for me. In kun fito ku ja curtain ɗin sannan ku sanar dani ta waya saboda na rufe ɗakin. Sannan kuma zaku cigaba da zama a gidan nan kuji da sauran binciken da ya kamata ga Philip sannan ga Widad nasan zuwa gobe shi ma zai dawo ku cigaba da aikin tare ni Kuma zanje can naga yadda za'ayi, in sha ALLAH za'a dace, kuma zamu dinga communicating duk abinda ake ciki har na dawo".......... Yana kaiwa Nan ya juya ya fita yana sanya wayarsa a silent saboda Juraysh dake dawo da kiran da ya masa ɗazu, gidan gabaɗaya ya bari ya nufi Bluevielle wurin Nayrah. KAKA TSARA KAKA, MY PEOPLE HMMM TO NIMA NA RASA ABUN CEWA, GA FA AMJAD YA SHIGA TSAKA ME WUYA, TO WAI MA YA AKAYI AKA RASA MUTANAN? KO DAI SUN GANE SHIRIN DAKE JIKIN MUTANAN NE? IN SUN GANE WANE IRIN MATAKI SHADOW ZAI ƊAUKA AKAN AMJAD? YA KUKE GANIN AMJAD ZAIYI DA NAYRAH? ZAI SANAR MATA WAYE SHI NE KO YA YA? GASHI KUMA YA SHIRYA TAFIYA BANGKOK DOMIN HAƊUWA DA YARINYAR SHADOW ME KUKE TUNANIN ZAI FARU? SHIN DA GASKE YA' CE GA SHADOW ƊIN? ZAIYI NASARA KUWA? SHIN DA GASKE ACE YA RASA RAYUWAR SA NE AKAN CASE ƊIN SHADOW?. DUK WANNAN AMSOSHIN NAKU ZAKU SAME SU NE A STEP 2, KU DAI KARKU BARI A BAKU LABARI DOMIN BAMA A FARA WASAN BA. _______________Zaune suke su duka a ƙayataccen falon baqi na gidan Julaybin ɗin gabansu abubuwan motsa baki ne iri iri a gabansu. Nuhail ne ya ce, "Mr kanar ya kaga yanayin ƙasar tamu?" Cikin gurbatacciyar turancin sa me haɗe da Indian accent ya ce, "Whl ƙasar ku akwai kyau sosai, mutane naku akwai karamci". "To Masha ALLAH, batun business na crude oil da zamuyi dakai wanda kazo a Kansa, already munyi magana dakai ka buqaci kanaso kazo, mu da munso daga can ma idan muka gama komai sai a aika ma kamar yadda ake yi amma kace sai ka zo da kanka, to Alhamdulillah yau gaka a ƙasar mu, ya maganar tamu?"........ Shuru Mr kanar yayi kafin ya ce, "A gaskiya farashin ku ya min tsada" . " Kamar ya ya ma tsada bayan kuma mun gama magana dakai kan wancan farashin, ka sani muna da mutanen da zamu bawa amma muka keɓance muka baka"......... Faɗar Julaybin. "Gsky Mr Julaybin wannan shine gskyr magana ku sake shawara".......... Nuhail ne ya ce, "Mu ba wata shawara da zamuyi kai dai zamu bawa lokaci kayi shawara, kasan dai yadda akeyi da refinery ɗin mu a kasuwar duniya". "Shikenan to, zan sake dubawa"......... Mr Kanar ya faɗa yana tashi ya musu sallama ya fita. Awais ya ce, " Kuji da ALLAH mutum kamar daƙuwa an taimake shi yana neman ya nunawa mutane iya shege, wa ma ya shige masa gaba ya zo ƙasar? shi ma fa riba zai samu ai mai gidansa zai sayarwa". "Rabu dashi in ma zugashi ake zai dawo ne".......... Julaybin ya amsa ba tare da damuwa ba dan yasan duk inda Mr Kanar ɗin yaje sai ya dawo. ________________"Hajiya Akwai matsala domin maganar da nake miki kotu ta kamo mutanan nan kuma whl kinsan in sukaji Matsi komai zai iya faruwa". "To yanzu miye abunyi? Kuma ina shi sani yake?". "Sani ai tuntuni ya gudu saboda yasan zaki neme shi, an tabbatar min kwanan sa huɗu kenan ba'a ganshi ba". "Ya kamata ka samo mana mafita domin in asirin mu ya tonu whl mun shiga uku, ga tsinuwar jama'a da zamusha..........." Katse ta yayi da faɗin, "zaki sha dai, ni ai ba wanda ya san da hannu na a ciki ballantana ya san fuskata, kuma abinda baki sani ba har Farshad yaron ƙasim datti da aka kashe suna tunanin da sa hannun Amjad, ni ne nan ba wani ba haka zalika hatsarin motar da Nayrah tayi Ni na shiryashi kuma ban so ta fita da ranta ba dan so nayi ta mutu a wannan accident ɗin, saidai duk wannan abun ba wanda yasan dashi saboda na iya taku na"........... Cikin tsantsar damuwa ta ce, "Amma shi ne ka barni na zira jikina har haka "......... Dariya ya kwashe da ita kafin ya ce, "Da kinsan baki shirya ba kika fito, ai ba zancen kare wani a wannan harkar, karki manta sharri fa kika fito ƙullawa ba alheri ba sannan kiyi tunanin wani ya taimaka miki dan ya hango zakiyi tuntube ? Inaaaa ai ba wannan bayanin". Ajiyar zuciya ta sauke cike da fargaba da kuma tunanin abinda kaje yazo ta ce, " To naji amma dan ALLAH duk yadda za'a yi, kayi kar asiri na ya tonu whl zan tozarta fiye da tunaninka, ni ko ma kashe su ne ayi kawai in dai asiri na zai rufu". "Ba fa zai yiwu a kashe su ba domin suna hannun hukuma " . "Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun".........Ta faɗa tana zubewa a cikin kujera gabaɗaya duniyar Hajijiya take mata............. A bangaren su Hajj zawaad kuwa tuni ya gama da Mr kanar saidai yaqi yadda ya barsu su keɓe da Sir juwaira, komai za'ayi yana tsakiya. Sir Ahuoyzah kuwa ce masa yayi Mr Kanar yaqi sauraron sa ma wanda hakan ya sa ya tashi hankalin sa sosai ya shiga neman mafita ido rufe. ANA WATA GA WATA, SHI KUMA WAYE WANNAN DA YACE SHI YA KASHE FARSHAD SHI KUMA YA SHIRYA ACCIDENT ƊIN DA NAYRAH TAYI? SANNAN KUMA WACECE WANNAN HAJIYAR DA SUKE AIKATA KOMAI TARE? YA ZA'A ƘARE TSAKANIN AWAIS DA MR KANAR? ME ZAI FARU IDAN SIR AHUOYZAH YA GANE HAJJ ZAWAAD YACI AMANAR SA?. WATO MY PPLE HARGITSIN DAKE CIKIN STEP 2 MA BAZAI KWATANTU BA . -----------------------√ SWORD OF FIRE KINGDOM 🔥 Zaune suke a makeken falon nasu da aka shafe rabin sa da wani irin painting na tigers. "Azal ina so ki je England ki kaiwa queen Elisa ziyara, tunda Anoosha bata nan da sai kuje tare"........ Azal ce ta ce, " Inati ni fa abinda na lura gabaɗaya Anoosha bata son abubuwan sarautar nan ne saisa ma bata son zama tare damu, saboda tasan in dai tana masarautar nan dolen ta ne zaki saka ta ciki a Matsayin ta na little princess". Murmushin ƙasaita Queen Hirut hirut tayi kafin ta ce, "Rabu da ita zan yiwa Sharutta magana a kanta ko tana so ko bata so dole ta zauna ta dinga kama Miki wasu abubuwan, saboda daga ke sai ita abun bauta ya bani, Azal ko ruhi na ya tashi zuwa sama ku tsaya sosai da ƙafarku kuma karku sare har sai kun ƙarɓo ƴancin mu ta hanyar ƙwatar yankin mu dake Aurellon". "Baza mu taɓa saduda ba Inati kuma itama Anoosha zan neme ta da kai na saboda mu kaiwa Queen Elisa ziyara tare saboda tafi jin daɗin abun". Jinjina kai Queen Hirut tayi kafin ta ce, "Ina alfahari dake Azal abun bauta ya sanya miki albarka". "Mesgalehu (thank you)".......Azal ta faɗa tare da miqewa sannan ta ce, "Zan zagaya gari inati domin naga meke wakana"......... Jinjina mata kai tayi alamar to, daga haka ta juya ta fita tare da Simba da duk inda ta sa Kafa yana biye da ita. Tana fita daga falon fadawanta na musamman suka rufa mata baya, giwa guda ɗaya ce a ƙofar bangaren Queen Hirut ɗin dan haka ita kaɗai ta kama ta ɗale su kuma suka bita a ƙafa, haka suka dinga zagaya masarautar tasu har suka zagayo ta wurin Dutsen Kurangina, sauka tayi daga kan giwar taje ta tsugunna gabansa tayi yan surkullensu sannan ta miqe ta baro wurin, zagayawa tayi ta fara tattakawa kan dutsen har ta hau can qololuwa tana kallon masarautar tasu kafin ta juya bayanta, zubawa wurin ido tayi can kuma ta juya ta yafito ɗaya daga masu take mata baya tare da tambayar, "Meke faruwa a can ?"....... Sunkuyar da Kai yayi kafin ya ce, "Haisha'an ne da mutanan sa".......... Wani mari ta tsinka masa da bayan hannu kafin ta ce, "Uban waye shi da har zaka wani ce min Haisha'an ne da mutanan sa, shi kansa ba komin komai bane da har zai ajje wasu a ƙarƙashin sa, tukunna ma waya bashi izinin fita daga masarautar saboda ai can ba yankin mu bane?"......... Yana dafe da kumatun sa ya ce, "A gafarce ni li'iliti, na tuba"......... Tsaki taja tana hararar inda su Haisha'an ɗin suke kafin ta fara gangarawa don isa garesu. Haisha'an yana zaune ne daga shi sai dogon wando saboda har lokacin ciwukan jikinsa basu gama warkewa ba, gefen sa omaine ne da kuma wasu daga cikin bayin masarautar da zasu kai su goma, sun kunna wuta da ƙirare suna jin ɗumi hannayen su ɗauke da Alqur'ani me girma, daga can gefe kuma wasu mutum biyar ne zaune suna hira haɗe da zane zane akan lallausan farin yashin dake wurin sai dai kuma suna sauraren karatun nasu amma da alama su ɗin har yanzu basu karɓi musulunci ba. Omaine da ya fara hango ta a razane ya ce, "Haisha'an bayan ka li'iliti Azal ce fa take tahowa"........ Juyawa yayi dan tabbatarwa yana ganin ta ya miqe yana faɗin, "Duk ku ɓoye fuskokin ku baza ta gane ku ba tunda ba uniform bane a jikinku"........ Ya faɗi haka yana tashi ya ƙarasa Wurin ta, ja tayi ta tsaya irin tsayuwar rashin mutuncin nan a gadarance ta wani bubbuga ƙafa, gashin ta da iska take kaɗawa yana ta dawowa kan fuskarta, janye gashin tayi daga kan fuskarta ta tare da ƙare masa kallo a ƙasƙance ta ce , "Kai waya baka ikon tara mutane anan, tukunna ma uwar me kukeyi da ku ka tsallake cikin masarauta kuka wuto nan? Da izinin wa kuka fito?". "Sarki baya buqatar izini domin shiga faɗarsa, saboda nan ɗin nima fada tace"......... Ya faɗa yana sake ɗaure fuska dukda dama fuskar tasa shi ko da yaushe kamar an aiko masa da saqon mutuwa. "Whatttt, waye kai? da har zaka sanyawa tosasshiyar ƙwaƙwalwar ka tunanin mallakar wata fada, ko fadar aljanu baka da matsayin mallaka ballatana ta mutane, matsiyaci bawa ɗan baiwa jikan bayi....."....... Ai kafin ta ƙarasa ya kaiwa maqoshin ta wani irin damƙa gabaɗaya ya fita hayyacin sa ya wani irin juyewa, "Wace ke da zaki shigo yankina kice zaki ɗaga min murya har ma ki zage ni, yau sai na kasheki, sai na kasheki naga uban da ya tsaya Miki, in kasheki in kashe banza dabba marar amfani". Ya ƙarashe yana huci. Qaqari li'iliti Azal ta fara tare da ƙoƙarin ƙwace kanta ta hanyar Amfani da ƙarfin tsafin da suke dashi a jikinsu saboda irin haka amma ina ta ƙasa saboda riqo ne ya mata bana wasa ba, idanun ta duk sun firfito. Masu tsaron ta kuma dukkansu suna daga kan dutsen suna kallo dan basu da izinin gangarawa wannan wurin saboda iya kan dutsen nan iyanan ne iyakar masarautar su, kuma tsallaka shi zai zama taka dokar Masarauta ne, shahada ɗaya daga cikin su yayi zai sauka saidai taku ɗaya yayi Haisha'an ya wurga masa wani kallo ai ba shiri ya juya har yana kokarin suɓutowa . Cikin shaƙaƙƙiiyar Muryarta dake neman daukewa ta ce, "Sim...Simba"....... wani tsalle Simba yayi ya dira har saida kura ya tashi a wurin tare da yin wani ƙara me sauti ya shiga zagaye su amma ya kasa matsawa kusa da Haisha'an ɗin da ya ɗau alwashin barwa Queen Hirut saqo akan ƴar ta Azal........... TO FA MEKE FARUWA KUMA? GA FA HAISHA'AN YANA ƘOƘARIN KASHE UWAR MASU GIDA THE GREAT PRINCESS OF SWORD OF FIRE KINGDOM. ME HAISHA'AN KE TAƘAMA DA SHI NE WAI? IYAKAR DA MASARAUTA TA HANA ƘETARAWA SHI YA ƘETARA HAR YANA IKIRARIN FADAR SA CE , LALLE AKWAI TASHIN HANKALI. ANYA BASHI BANE SHADOW KUWA🤔 TO BA RUWANA KAR AJE A SANARWA AGENT AMJAD NACE KU DAI MU HAƊE A STEP 2 ---------------------√ Dariya yake irin tasu ta manya kafin ya ce, "Ai ranka ya daɗe yanzu rabi da ƙwatan mutanen dake ƙasar Nifaz Hankalin su kaɗan ne daga mata har maza saboda ƙwayoyin da muka shigo musu dashi sunyi matuqar tasiri dan maganar da nake ma yanzu duk inda muka kaɗasu nan zasubi, babu wasu masu nutsuwar da wai in wani abu ya faru zasuyi zurfin tunani domin gano dalilin assasa shi instead ma sai kaga sun maida hankali kan wani abun da bashi da muhimmanci, kaga ɗalibai suna sha a matsayin maganin da zai sauqaqa musu karatu ta hanyar ɗauke musu gajiya da hana su bacci, ma'aikata ma haka, matasa masu zaman banza tare da yan matan dake cikin damuwa, a ganinsu hanya ce da zata sauqaqa musu basu san kuma mune suke sauqaqawa ba". Girgiza kai babban mutumin dake zaune yayi kafin ya ce, "Munsa hannu a project ɗin nan na farin da za'a kawo domin a bi gonaki a sake su dan haka suna hanya ya kamata ku shirya da mutanan ku yadda abubuwan zai wakana akwai Budget me ƙarfi da za'a rarraba dan wannan ba irin wancan bane, saboda a yayin da duk amfanin gonakin su ya lalace dole ne zasu haqura su rungumi abincin waje da muhimmanci, dama kuma kaga noma da kiwo na ɗaya daga cikin abinda zai yi wahalar kawarwa amma yanzu da zarar an kawar dasu sauran abubuwan zasu zo da sauki". "Yaushe kayan zasu iso ?"......... ɗayan ya tambaya. "Nan ba da jimawa ba dama suna jira ne amfanin gona ya gama tsiro wa, amma nasan zasu sake neman mu, so zamu zama cikin tsammanin su". WANNAN SHI NE ANA WATA GA WATA, SU WAYE WA'ANNAN? DAGA INA SUKE ƘARƁAR WANNAN UMARNIN ? MEYE GOAL ƊIN SU NA YIN HAKAN? WANNAN AIKI NASU ZAI YIWU KO BA ZAI YIWU BA ? IN BAI YIWU BA WAYE ZAI DAKATAR DASU? DAGA INA ZAI FITO? MY PEOPLE HMMM CAKWAKIYAR TANA STEP 2, DAN ZAKU SHA RUWAN MAMAKI, TUNANIN KU ZAI JUYA FROM LEFT TO RIGHT, ABUBUWAN DA BAKUYI ZATO BA ZASU FARU, ZUKATA ZASU RAUNANA, AKWAI DISAPPOINTMENT SOSAI AMMA KUMA ZAKU NISHADANTU ZAKU MA KU ILMANTU KU DAI KU KASANCE TARE DANI. *TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.* SAI MUN HAƊU A STEP 2. INA ROQON ALLAH YA SADAMU DA ALHERIN DAKE CIKIN WANNAN WATA NA RAMADANA, YA BAMU IKON AZUMTARSA GABADAYA. RAMADAN KAREEM.