**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA BIYU 2 ✍️ PART A ✅♥️ Marubuci:- Najibullah Muhammad 🥷🥷 Typing/posting Najibullah Muhammad legends of the century ✍️🙏🥷 Kafin muci gaba da littafin mu akwai mutane da yawa da suke tambayata number ta. To ga ta... 08112778656 Email dina.. najibullahimuhammad405@gmail.com _________________________ Lokacin da Sarki Zurmatu da mukarrabansa suka baro filin GASAR JARUMTAKA suka nufi fada. Sai likitoci suka ciccibo Sadauki MARGIM suka wuce dashi dakin jinya don yi masa magani domin har yanzu jini na kwarara a wadannan manyan raunikan da Shugaban Dakarun yayi Masa. Da shigar su dakin jinya, sai suka debo kayan aiki suka tube Masa Riga don dinke Masa raunikan da ke jikinsa da Kuma gyara Masa karayar Kafafunsa. Kwatsam ba zato ba tsammani sai kawai aka ga Dakin ya kama girgiza kamar zai ruguje, sannan sai wata iska Mai tsananin karfin tsiya ta kutso cikin dakin. Saboda tsananin karfin iskar sai ta rinka daukar likitocin Dake Shirin yiwa MARGIM magani tana makasu a bango suna fadowa a matukar galaibace. Cikin kankanin lokaci duk suka gigice, suka dimauce saboda tsananin zafin kayen da iskar ke masu. Bayan kamar dakika Dari da Ashirin da faruwar hakan, sai iskar ta tsaya cak, Kuma dakin ya dena girgiza. Kwatsam sai aka ga wani Jan Hayaki ya nannade sadauki MARGIM sannan ya bace tare da shi. Koda ganin wannan Ala'mari sai gaba dayan likitocin suka rude, cikin tsananin razana shugaban likitocin ya ruga fadar Sarki Zurmatu domin sanar dashi wannan bakon Ala'mari. Ala'marin SARKI ZURMATU kuwa lokacin da ya Isa turakarsa sai ya tura aka kira Masa Waziri domin binciko Asalin wannan jarumin da ya fafata da Dakarun Sarki a filin Gasa. Cikin kankanin lokaci Waziri Mikilas ya zo turakar Sarki, bayan ya samu natsuwa sai Sarki Zurmatu ya dubi Waziri ya ce, ya Kai Waziri kayi sani cewa dalilin dayasa na kira ka shi ne, domin muyi bincike akan Asalin wannan bakon jarumi da ya fafata yaki a yau din nan. Ka sani cewa wannan jarumi yayi babbar bajintar da ba kowa zai iya yin kamarta ba, domin daga cikin jarumai dubu mawuyacin abu ne a samu biyar masu irin baiwarsa, don haka ya zama dole musan ko shi wanene kafin ya warke daga raunikan Daya samu a filin Gasa. Sarki Zurmatu yaci gaba da cewa, Waziri kayi sani cewa kimanin shekaru Ashirin da biyar da suka wuce, a lokacin da nake Neman haihuwa ruwa a jallo ban samu ba, bayan na Ziyarci bokaye Dari da saba'in da bakwai Amma ban dace ba, har na fara yanke Qauna da samun Magaji. Daga bisani ne naji labarin wani shahararren Boka a yankin Kasar BANBUS, Wanda ke rayuwa a bayan gari cikin kogon Dutsen BUKUL. Na samu labarin wannan shahararren Boka ne a wurin Bokan karshe da na ziyarta wato na cikon Dari bakwai da saba'in da bakwai, bayan Bokan yayi bincike sai yayi murmushi ya ce ya Kai wannan Sarki ka sani cewa duk duniyar Nan babu Wanda zai iya baka maganin matsalarka face mutum Daya, ba wani bane face Boka RAKUL na Kasar BANBUS. A halin yanxu duk duniya babu Bokan da ya kai shi karfin sihirin tsafi, domin shi ne Bokan da ya zagaye duniya Kaf! Ya tattara gaba dayan sirrikan tsafin da ke cikinta, sihiri Daya ne kacal ya rage Masa ya mallaka Wanda zai hada da nasa domin ya zama gagarabadau, da zaran ya mallaki wannan sihirin to bazai mutu ba sai ya cika shekaru dubu saba'in a duniya, Kuma tsawon wannan shekaru shi ne zai ci gaba da rike KAMBUN GASA NA SHUGABAN BOKAYEN DUNIYA. Wannan sihiri da Boka RAKUL yake nema ba komai bane face Yana son a tattaro mashi jinin gaba dayan dayan Sadaukan Duniya na jinsin bil'adama da ALJANU Wanda zai hadasu da wasu Alkaluman tsafi sannan ya shiga halwar tsafi ta kwana saba'in don tabbatar da wannan babban sihiri.. Bincike ya tabbatar da cewa indai Boka RAKUL ya cika wannan burin na shi to zai zamana cewa tamkar Yana mulkin duka duniya ne, domin komai zai zama sai da umarninsa yake aiki. A bisa wannan dalilin ne, Boka RAKUL ya dukufa binciken hanyar da zai cika wannan babban burin na shi, sai da yayi kwana Dari a cikin halwar tsafinsa Yana bincike ba ci ba Sha tsawon wannan lokaci, sannan daga bisani ya samu mafita. Mafitar kuwa ita ce, yayi bincike a madubinsa yaga cewa burinsa bazai taba cika ba, face yayi Amfani da Sarki Zurmatu saboda kasancewar a wannan lokacin duk duniya babu inda ya Kai Kasar BALLUS girma da yawan Dakaru da Kuma arziki. Saboda haka sai yayi Amfani da karfin sihirin tsafi ya juyar da mahaifar matar Sarki Zurmatu, ta yadda har abada bazata taba haihuwa ba har sai yazo gareshi Neman taimako daga Nan Shima sai ya kawo sharadinshi Wanda zai zamo sanadin cikar burinshi. Koda gama wannan bincike da Boka RAKUL yayi sai ya tuntsire da mahaukaciyar dariya har kwallar farin ciki na shatata akan kumatunsa saboda ya gano hanyar da zai cika burinsa. Ala'marin SARKI ZURMATU kuwa, bayan ya samu gamsassun bayanai akan Boka RAKUL da Kuma irin shahararsa, Sannan Kuma wannan Bokan ya tabbatar mashi da cewa Boka RAKUL ne kadai zai iya magance Masa matsalarsa. Nan take ya koma birninsa ya kama Shirin tunkarar birnin BANBUS don ziyartar Boka RAKUL. Bayan shafe tafiyar kwanaki arba'in bisa ingarman dawakai, sai Sarki Zurmatu ya iso kogon Dutsen BUKUL inda Boka RAKUL ya ke. Koda zuwansu bakin kofar Kogon, sai kawai suka ga gaba dayan Dajin da kogon yake ya gauraye da tsananin duhun da ko tafin hannun mutum Bai Isa ya gani ba, bayan kamar Dakika sittin da faruwar hakan sai sukaji an kece da mahaukaciyar dariya wadda Amsa kuwwar ta ya cika Dajin gaba Daya, zuwa can sai dariyar tayi shiru sannan ta ce, " lale marhabun da Gwarzo Kuma SADAUKIN SARAKUNA wato Sarki Zurmatu IBN Turmadu, kayi sani cewa na San duk abinda ke tafe Dake Kuma tabbas kazo inda za a share maka hawaye, don haka ka shigo cikin wannan kogon Kai kadai kabar dakarunka a wajen Kogon. Koda gama fadin hakan sai muryar ta dauke, sannan wani farin haske ya wanzu akan hanyar da za a bi aje inda Boka RAKUL yake, alhalin kuwa sauran Dakarun duk a cikin daji yake. Nan take Sarki Zurmatu yayi ta bin duk Inda wannan hasken yake, Yana tafiya Yana ganin abubuwan al'ajabi. Domin akan hanyar shigarsa kogon ne yayita ganin Kwarangwal din halittu iri-iri na kowace halitta gasu Nan birjik a sakale a jikin bango anyi masu wani irin nau'in rubuce-rubuce da harsuna mabambanta. Haka dai Sarki Zurmatu yayi ta tafiya har tsawon sa'a biyu Sannan ya iso wata Babbar fada Mai tsananin girma da fadi da kawatuwa.. Gaba dayan kayayyakin cikin fadar komai Sarrafa kanshi yake da kanshi. Hatta abinci da abin Sha, da zarar mutum ya zauna Kan kujera zasu kawo kansu da kansu a gaban mutum sannan su Rika zuwa dai-dai misali kusa da bakin mutum ya kama ci har ya koshi. Tabbas wannan wuri ya cika Aljannar duniya domin an tanadi komai da komai na Jin dadin rayuwar duniya. Sarki Zurmatu na cikin mamakin wannan kogon Dutsen ne ya hango wani mutum zaune akan iska sannan ya nannade Kafafunsa tamkar akan turba yake, Kuma ya rufe idanunsa Yana Karanta wasu abubuwan da ba a fahimta. A hankali tsohon ya cigaba da tahowa cikin iska har ya iso kusa da Sarki Zurmatu, sannan ya zauna daf da Sarki Yana Mai Yi Masa murmushi tamkar Wanda yaga Dan uwansa na jini. Har Sarki Zurmatu ya budi Baki da nufin magana sai Boka RAKUL ya dakatar da shi, Sannan ya ce ya Kai wannan Sarki ka kwantar da hankalinka na San duk abinda ke damunka ba sai kace komai ba. Domin ba wata matsala bace ke damunka face matsalar haihuwa, Kuma sai da ka Ziyarci bokaye Dari da saba'in da bakwai Amma baka dace ba, daga bisani ka hadu da Bokan da ya baka labarina wanda har ka zo nemana. Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL cikin tsananin mamaki ya ce tayaya duk Kasan da wannan Ala'mari alhalin akwai tazara mai yawa a tsakaninmu? Koda Jin haka sai Boka RAKUL ya bushe da dariya sannan ya ce, ka kwantar da hankalinka yakai wannan Sarki. Kayi sani cewa ni yanzu na taka wani matsayi da duk duniya babu Bokan da ya taka shi, don haka yanzun Nan zan nuna maka yadda Ala'marin ya kasance domin ka samu natsuwa. Gama fadin hakan keda wuya sai Boka RAKUL yayi da hannunsa na hagu izuwa ga bangon dakin da suke, take hoton birnin BALLUS ya bayyana. Nan take aka cigaba da Nuno hotunan irin matsalolin da suka rinka faruwa a dalilin rashin haihuwa har Sarki ya fara ziyartar Bokaye domin neman magani, aka ci gaba da nuna wuraren da Sarki yaje har izuwa Kan Boka na karshe, ana zuwa dai-dai Nan sai Boka RAKUL ya sake nuna bangon da hannun Hagu take hoton komai ya 6ace. Koda gama ganin haka sai Sarki Zurmatu ya Kara kamuwa da tsananin mamaki Kuma ya Kara tsinkewa da al'amarin Boka RAKUL ya tabbatar da cewa ya cika Hatsabibi. Boka RAKUL ya dubi Sarki Zurmatu yace yakai wannan Sarki Bukatar mai sauki ce, Amma mudin zaka yadda da sharudda guda biyu. Sharadi na farko shi ne, idan bukata ta biya da shekaru Ashirin zaka shirya GASAR JARUMTAKA a cikin birninka wadda zaka gayyato gaba dayan Sadaukan Duniya domin shiga wannan Gasa da za'ayi. Sannan sharadi na biyu shi ne, ya zama dole kaje Kasar RUM ka siyo wadansu Dakaru na musamman wadanda asalinsu sun kasance jinsin SAMUDAWA ne, wadannan Dakarun da zaka siyo da su ne zaka rinka Amfani wajen shirya GASAR JARUMTAKA da zaka shirya a tsakanin duk Jaruman da ka gayyato daga sassan duniya. Kayi sani cewa makaman da wadannan DAKARUN da zaka siyo suke Amfani da su, na Saka masu wani babban sihirin da duk mahalukin da aka yiwa rauni da su to bazai wuce kwana biyu a duniya ba zai mutu. Don haka inaso ya zamana cewa gaba dayan Jaruman Gasar da ka gayyato sun hallaka a sanadiyyar fafatawa da wadannan DAKARUN. Idan har ka yarda da wadannan sharudda to yanzu take zan biya maka bukatar ka. Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu ya kawo gwauron numfashi ya ajiye, daga bisani yace yakai wannan Boka mai abun mamaki kayi sani indai wannan zai sanyani cikar burina to na amince. Koda Jin wannan batu sai Boka RAKUL ya tuntsire da dariyar farin ciki, Sannan ya ce nayi maka alkawari a cikin kwana bakwai matarka zata samu ciki, sannan lallai zata haifi abinda ke cikinta lafiya Kuma abinda zata Haifa zayyi suna, daukaka, da tsawon Rai a duniya. Amma fa bayan wannan bazaka Kara haihuwa ba. Batare da Bata lokaci ba, Boka RAKUL yayi tsafi sai ga wani kullin magani ya bayyana a hannunsa, sannan ya mikawa Sarki Zurmatu ya ce, karbi wannan yakai SARKIN SARAKAI idan kaje gida a cikin dakin da kuke barci da matarka ka turara wannan a cikin dakin tare da ita, a ranar da kayi wannan aikin a ranar zata samu ciki. Don haka kuje na sallameku, sai bayan shekaru Ashirin zamu sake saduwa. Yana gama fadin hakan ya bace bat tamkar Bai gaba wanzuwa a wajen ba. Cikin tsananin farin ciki Sarki Zurmatu ya fito wajen Kogon, sannan ya tarar yanzu haske ya dawo ko'ina, suka hawo dawakansu suka dawo gida. A ranar da Sarki ya aikata abinda Boka RAKUL ya bashi, a ranar matarshi ta samu ciki kamar yadda ya fada.. Koda Sarki Zurmatu yazo Nan a jawabinsa sai kwalla ta cika masa idanu, sannan ya kara da cewa Ina tsoron kada wannan Jarumi ya samu nasara akan wadannan Dakarun batare da na cika sharadin Boka RAKUL ba. Idan kuwa haka ya faru to akwai gagarumar matsala, domin matsalar zata iya zama sanadiyyar tarwatsewar birnin Nan da duk wani abu Mai Rai na cikin birnin. Koda Sarki yazo Nan a zancensa, sai Waziri ya cika da tsananin mamaki, har Waziri ya budi Baki da niyyar cewa wani abu, sai kawai suka ga Shugaban likitocin da Sarki yasa su ceto rayuwar JARUMI MARGIM ya shiga turakar a firgice, Yana zuwa gaban Sarki ya zube ya kwashi gaisuwa Yana haki kamar ransa zai fita.. Nan take shugaban likitocin ya kwashe duk abinda ya faru a cikin dakin jinya a kokarin yiwa SADAUKI MARGIM magani ya fadawa Sarki. Koda Jin wannan batu sai Sarki da Waziri suka mimmike tsaye saboda tsananin razana da mamakin Jin wannan batu na shugaban likitoci, cikin fushi Sarki Zurmatu ya kwarara wani uban ihu Mai ban tsoro Wanda Amsa kuwwarsa ta cika fadar gaba Daya, kawai sai yayi nufin ya ruga izuwa dakin ganin da shi da Waziri domin su ganewa idanunsu sannan su San matakin da zasu dauka. Kwatsam ba zato ba tsammani sai kawai suka ga SHUGABAN BOKAYEN DUNIYA WATO BOKA RAKUL ya bayyana Tsulum a gabansu cikin wata irin mummunar shiga Kuma fuskarsa a murtuke, gaba dayan jikinsa Gurayen tsafi ne da Layun tsafi.... Kash! Laifin dadi karewa. Mu hadu a GASAR JARUMTAKA 2 B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma kayatacciyar HIKAYAR✍️✍️🙏 **GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA BIYU 2 ✍️ PART B ✅✅ Marubuci:- Najibullah Muhammad ✍️✍️✍️ Typing/posting Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷 Whatsapp No. 08112778656. CIGABAN LABARIN..... Lokacin da su Sarki Zurmatu suka ga BOKA RAKUL ya bayyana Tsulum a gabansu, sai suka Kara gigicewa musamman ma Sarki Zurmatu domin ya tabbatar da cewa lallai dalilin dayasa Boka RAKUL zuwa a wannan lokaci ba karamin Abu bane. Cikin tsananin damuwa Boka RAKUL ya dubi su Sarki Zurmatu ya ce tabbas akwai gagarumar matsala da take tunkaro mu wadda idan bamuyi dagaske wajen maganinta ba, to gaba dayanmu sai mun hallaka, hatta wannan birni naka sai ya zama tarihi cikin kankanin lokaci zai baje ya koma tamkar ba a taba yinsa ba. Cikin kaduwa Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL ya ce yakai wannan hatsabibin Boka, Maza ka sanar Dani abinda ke Shirin faruwa domin muyi gaggawar daukar mataki tun kafin dare yayi mana. Kafin wani daga cikinsu ya Kara cewa wani abu, tuni Boka RAKUL yayi nuni da hannunsa na hagu izuwa ga bangon dakin da suke, Nan take sai suka ga hoton dakin da aka shigar da SADAUKI MARGIM don yi masa magani, aka ci gaba da Nuno duk abubuwan da suka faru. Kamawa tun daga Kan lokacin da dakin ya fara girgiza da Kuma yadda kakkarfar iskar Nan tayi ta wurgi da sauran likitocin har zuwa Kan lokacin da wani Jan haske ya nannade sadauki MARGIM sannan ya bace da shi. Nan take Boka RAKUL ya Kara nuna wannan bangon da hannun Hagu take hoton komai ya bace. Sannan ya fuskance su Yana Mai cewa, ya Kai wannan Sarki kayi sani cewa bala'in da yake tunkaro min yafi karfin duk yanda kake tunani domin za'a iya asarar milyoyin rayuka a kokarin magance wannan matsalar. Koda Jin haka sai Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL ya ce, yakai wannan Boka na roke ka akan ka sanar abinda ke faruwa, domin a shirye nake na yaki koma wace irin matsala ce wadda take Shirin kawo mana barazana akan rayuwarmu, mulkinmu da Kuma mutuncinmu. Don haka ni yanzu Kai kawai nake Jira domin daukar mataki. Boka RAKUL yayi doguwar ajiyar zuciya gami da yake, ya ce " ya Kai wannan Sarki kayi sani cewa matsalar da ke tunkaro mu ita ce.. Akwai wani HATSABIBIN BOKA Dake nahiyar birnin SIN Wanda mukayi kunnen Doki dashi a bangaren ilimin tsafi, a bisa wannan dalili yayi bincike ya gano nufinmu akan Shirin mallakar duniya da duk abinda ke cikinta ta hanyar shirya GASAR JARUMTAKA, da Kuma Amfani da duk jinin Jaruman Gasar da aka kashe wajen kammaluwar bukatarmu. Koda ganin faruwar wannan Ala'mari Shima sai yayi alwashin Hana cikar burinmu, ya kudurce a ransa cewa lallai dole ne ya dakatar damu domin a rayuwarsa ya tsani ya kasance a karkashin mulkin wani ana bashi Umarni tamkar BAWA. Don haka Nan da Nan ya fara Shirin ceton duk jarumin da ya fafata a filin Gasa. Boka RAKUL ya ci gaba da cewa, ya Kai wannan Sarki kayi sani cewa kamar yadda na fada maka a shekarun baya cewa wadannan miyagun makaman da DAKARUNKA suke dasu sun kasance tsafaffu ta yadda duk Wanda aka Sara ko yiwa rauni da shi, to bazai Haura kwana biyu a duniya ba zai mutu. Duk Wanda ake so ya rayu bayan ya samu rauni da wannan makami to tabbas dole sai anje karkashin TEKUN ZALLUS dake bayan birnin SIN sannan an tsinko ciyawar KATUL an daka ta sannan an shafawa mutum a raunin da makamin yayi Masa kafin cikar kwanaki biyu, ana shafa Masa take zai warke tamkar wani abu bai taba samunsa ba, idan kuwa akayi jinkiri har zuwa kwana biyu to nan take zai mutu. Boka RAKUL ya ci gaba da cewa, daga Nan zuwa birnin SIN inda wannan Hatsabibin Boka yake, tafiya ce ta Kwanaki Dari da tamanin bisa ingarman dawakai kosassu masu lafiya. Yanzu haka wadansu Bakaken Aljanu ne BOKA GARGUS ya turo sukayi Masa wannan aikin. Wadannan sun kasance jibga-jibga Kuma manyan sadaukai marasa Imani daga jinsin ALJANU, domin Hatta a duniyar Aljanu sun fitini kowa an rasa yadda za'ayi dasu saboda tsananin zaluncinsu da Kuma karfin da suke dashi wamda ya wuce misali, a bisa wannan dalili ne BOKA GARGUS ya gayyato gaba dayan jinsin wadannan Bakaken Aljanun domin su rinka yi masa aiki, bisa yarjejeniyar a duk bayan wata guda zai rinka shayar dasu jinin bil'adama guda dubu, da Kuma dabbobi guda dubu saboda kasancewar jinin bil'adama da dabbobi ne abincinsu. Bugu da Kari wadannan Aljanun sun kasance masu tsananin karfin gudun tsiya tamkar kibiya, domin suna iya shafe sama da tafiyar wata guda a cikin sa'a guda kacal. Koda Boka RAKUL yazo Nan a zancensa sai hankalin Sarki Zurmatu ya Dunguzuma ainun sannan ya dubi Boka RAKUL ya ce, wai shin wace matsala zata biyo baya yayinda BOKA GARGUS ya ceto rayuwar JARUMI MARGIM kafin nan da cikar kwana biyu? Koda Jin wannan batu sai Boka RAKUL ya fashe da matsanancin kuka tamkar karamin Yaro, ya rinka tsalle yana faduwa Kasa kamar sabon mahaukaci, sai da su Sarki Zurmatu suka rirrikeshi sannan ya natsu. Daga Nan ya ce yakai wannan Sarki kayi sani cewa muddin muka bari Koda rayuwar mutum 1 ta tsira daga cikin jaruman Gasar to Kuma ba zamu Haura wata guda a duniya ba zamu mutu. Domin zamu rinka wayar gari ne sashen jikinmu Yana lalacewa Yana rubewa, a hankali- a hankali har tsutsotsi sun rinka fitowa a jikinmu suna cin Naman da ya zagwanye a jikinmu, da haka da haka mu rube gaba Daya kafin cikar kwanaki talatin, Kuma irin mutuwar da mukayi irinta gaba dayan mutanen birnin Nan zasuyi har kowa ya mutu. Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu Waziri Mikilas suka kamu da tsananin tsoro, saboda yanda rayuwarsu ta kasance a tsakanin tsaka-mai-wuya. Cikin tsananin damuwa kamar yayi kuka, Waziri Mikilas yace ya Sarkin Duniya, na rokeka akan muyi duk irin abinda zamu iya don rayuwarmu, Kasarmu da mulkinmu. Cikin tsananin damuwa Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL ya ce yanzu menene mafita akan wannan Ala'mari? Boka RAKUL yayi shiru daga bisani ya dubi Sarki Zurmatu ya ce, mafita guda Daya ce kacal. Shi ne dole ne mubi bayan wadannan Aljanun da suka sace Sadauki MARGIM kafin su samu nasarar kaiwa BOKA GARGUS shi har ya warkar dashi. Sarki Zurmatu ya Kara duban Boka RAKUL cikin damuwa yace, tayaya kake ganin zamu iya cimmasu kafin su Isa birnin SIN alhalin ka fada mana cewa duk duniya babu Aljanun da suka Kai su tsananin karfin gudu? Sannan Kuma tayaya zamu iya samun nasarar kwato jarumi margim har mu hallakashi daga hannunsu? Koda Jin wannan tambaya sai Boka RAKUL ya ce" hakane kamar yadda na fada maku cewa Aljanun da Boka GARGUS ya Aiko sukayi wannan aikin sun kasance masu tsananin karfin gudu tamkar kibiya, to kayi sani cewa har ila yau akwai wasu ALJANU na musamman wadanda suka kasance manyan IFIRITAI masu tsananin gudu tamkar na tauraruwa Mai wutsiya. Su dai wadannan Aljanu guda dubu ne, Kuma dukkansu sun kasance manya-manya kamar Tsauni. A tarihin rayuwarsu ba a taba samun aljanin da ya rigasu zuwa wurin da suka dosa ba, domin sau dubu saba'in suna lashe GASAR TSEREN GUDU da ake shiryawa a duk karshen shekara cikin fadar babban Sarkin Aljanu. Saboda tsananin karfin gudunsu a cikin kwana guda kacal suna iya yawace duniya Kaf! Wato su je karshen bangwayen duniya na bangaren gabas, Kudu, yamma da Arewa. Boka RAKUL ya ci gaba da cewa Ina Mai tabbatar maka da cewa, muddin muka bi bayansu tare da wadannan IFIRITAI to zamu iya cimmasu kafin su Isa birnin SIN da ragowar sa'a biyar. Koda Jin wannan batu sai hankalin su Sarki ya fara kwanciya, sannan Waziri Mikilas ya dubi Boka RAKUL ya ce, to yanxu tayaya zamu iya samun nasara a kansu yayinda muka riski wadannan Aljanun? Koda Jin wannan tambaya sai Boka RAKUL yayi shiru Yana tunani Mai zurfi, bayan tsawon lokaci Yana tunani daga can sai ya dago Kai ya Kalli Sarki Zurmatu da Waziri Mikilas sannan ya kyalkyale da dariya tamkar babu wata damuwa a ransa.. Bayan yayi Mai isarsa, ya dube su yace ku kwantar da hankalinku domin na gano mana babbar mafitar da zamu jefi tsuntsu biyu da Dutse Daya. Sarki Zurmatu ya ce fahimtar damu mafitar domin muji. Boka RAKUL yace mafitar ita ce, dole na Kasa Sarkin yakin ka ya tattaro mana gaba dayan JARUMAN GASAR JARUMTAKA su zo mu hadu mu hau Saman wadannan IFIRITAI domin muje dasu inda zamu yaki wadannan Aljanun. Da zarar mun riskesu sai muyiwa sauran jaruman Gasar bayanin cewa duk Wanda ya samu nasarar Kwato jarumi Margim daga hannunsu to shi ne ya lashe wannan Gasa. Kunga kenan burinmu zayyi saurin cika, domin nasan mawuyacin abu ne wani daga cikin jaruman Gasar ya tsira da rayuwarsa daga bala'in wadannan ALJANU. Koda Jin wannan tsantsar hikima da hangen nesa irin na Boka RAKUL sai dukkansu ukun suka bushe da mahaukaciyar dariya kamar bazasu dena ba, domin a zatonsu babu abinda zai hanasu samun nasara. Nan take Sarki Zurmatu yayi gagarumin Shirin yaki sannan ya fito ya wuce fada Waziri Mikilas da Boka RAKUL na take masa baya. Yana zama Kan KARAGARSA sai ya aika aka kira masa Sarkin yakinsa Mai suna DURKUL, wani gabjejen basamuden Kato ne Mai kirar manyan sadaukai majiya karfi. Koda Sarkin yaki DURKUL yazo gaban Sarki sai ya risina ya kwashi gaisuwa. Nan take Sarki Zurmatu ya fadawa Sarkin yaki duk irin abinda yake so akan Jaruman Gasa, cikin girmamawa Sarkin yaki yace angama ya shugabana Nan take Sarkin yaki yaje masaukin sauran jaruman Gasar sannan ya busa wani Kaho na musamman, Wanda da an busa shi to kowa daga cikin jaruman Gasar yasan cewa ana bukatar ganinsu cikin gaggawa. Nan da Nan kowanne daga cikinsu yayi gagarumin Shirin yaki sannan suka fito filin Gasar suka tsaitsaya suna jiran Umarni. Batare da Bata wani lokaci ba, Sarki Zurmatu yasa aka Tara gaba dayan mutanen birnin. Dama tuni SARKI FALWAN da YARIMA FAZAMAL da sauran zakakuran dakarunsu sunzo fadar Sarki Zurmatu cikin gagarumar shigar yaki. Bayan kowa ya halarci fadar, sai Sarki Zurmatu ya Mike ya fuskanci mutanen birnin gaba Daya sannan ya ce, " yaku jama'ar birnin BALLUS Mai albarka, kuyi sani cewa bayan fara Gasar Jarumtaka a yau din nan, wata Babbar matsala ta tunkaro mu, wadda indai bamuyi maganinta ba to tabbas sai kowa ya halakka a wannan birni.. A bisa wannan dalili ne muka shirya akan zuwa magance wannan matsalar, Sannan Kuma za'a cigaba da gudanar da Gasar Jarumtaka a can inda zamu tari abokan gaba, bayan mun gama da su sai mu dawo gida domin karasa Gasar da Kuma tabbatar da Alkawarinmu akan Wanda yayi nasara. Don haka yanzu take zamu tattara namu'i namu domin muje mu tari makiya don jinkirin kadan na nufin hallakarmu gaba Daya. Nan da Nan sai fadar ta kaure da hayaniya saboda Jin bayanin da Sarki yayi.. Nan da Nan kowa ya shiga cikin tsananin tashin hankali, domin wasu Nan take suka fara yin kuka. Koda ganin yadda mutanen suka firgice suke ta kace nace, sai Sarki Zurmatu ya daka masu tsawa, Nan take kowa yayi tsit tamkar daukewar ruwan sama. Kawai sai ya dube su a fusace ya ce bamu da isasshen lokacin batawa, kuyi hakuri kawai kuyi fatan Alheri, lallai mu ne da Nasara. Don haka a yanxu zan bar Amanar Kasa ta a hannun Waziri Mikilas domin yaci gaba da tafiyar da al'amarin Mulki kamar yadda aka Saba kafin mu dawo. Batare da wani Bata lokaci ba, Sarki Zurmatu da su Boka RAKUL da su Sarki FALWAN sukayi bankwana da sauran jama'a suka nufi babban filin Gasar Jarumtaka inda zasu hadu da Jaruman Gasa domin a dunguma a tafi. Da zuwansu filin Gasar sai suka iske Jaruman Gasar a tsaitsaye kimanin su dubu Dari cikin mummunar shigar yaki. Nan da Nan batare da Bata lokaci ba Boka RAKUL yayiwa Jaruman Gasar bayanin komai, sannan ya fiddo wani garin magani da cikin aljihunsa, sannan yayi tsafi garwashin wuta ya kama sannan ya barbada garin maganin a sama, kawai sai wani bakin Hayaki ya rinka tashi Yana taruwa a gefe guda, sai da hayakin ya shafe dakika Dari arba'in Yana tsiri a sararin samaniya sannan akaga ya rikide ya zama wasu manya-manyan halittu masu matukar girma har izuwa Kaso guda dubu, sannan kowannensu Yana da fuka-fukai guda Dari biyu da tamanin. Cikin girmamawa wadannan gungun Aljanun sukayi gaisuwa a wajen Boka RAKUL, sannan suka Ce me kake da bukata ya Bokan duniya? Nan take Boka RAKUL yace inaso ku dauke mu mu duka kubi bayan Aljanun da suka zo har fadar Sarki Zurmatu suka sace Sadauki MARGIM, lallai Ina so kuyi iyakar yinku domin mu riskesu kafin su Isa BIRNIN SIN. Koda Jin wannan batu sai shugaban IFIRITAN ya bushe da dariya, sannan ya ce Ashe ma bukatar ku Mai sauki ce, na rantse da KARAGAR SARKIN ALJANUN DUNIYA zamu iya riskasu a cikin abinda Bai wuce sa'a bakwai ba. Nan take suka kwashi gaba dayan Jaruman Gasar da su Sarki Zurmatu suka yi sama dasu a cikin tsananin gudun da yafi gaban kwatance. Wannan shi ne abinda ya faru a birnin BALLUS bayan su Sarki Zurmatu sunyi gagarumar shigar yaki sannan sun tafi domin riskar abokan gaba. ******. ***** ***** ***** A yamma da Kasar birnin SIN Kuma akwai wata kyakkyawar Kasa ta musulmai Mai suna NURUL HAYAT, Ita dai wannan Kasa na karkashin mulkin wani Sarki Adali Mai rikon addini da son zaman lafiya ana kiransa da suna MUSBAHU. SARKI MUSBAHU ya kasance tsoho dan shekaru casa'in da biyu, Amma Kuma har yanzu jikinsa Daram yake. SARKI MUSBAHU ya kasance Yana da wani da guda Daya tal a duniya mai suna USAMA. Usama shi kadai ne daa a wurin SARKI MUSBAHU Kuma ya kasance Gawurtaccen jarumi mai tsananin karfin damtse da Jarumtaka ta ban al'ajabi, domin shi kadai Yana iya yakar gari guda na Kafirai ya kashe na kashewa ya raunata na raunatawa, sannan kame matansu a matsayin bayi, ya kwashe dukiyarsu a matsayin ganima. A halin yanxu shekarun YARIMA USAMA 35 a duniya, Kuma a Kalla ya yaki kasashe guda tamanin ya Kafa tutar musulunci. Domin tun Yarima USAMA na Dan shekaru 15 a duniya yake fita Jihadi a duniya Kuma Yana samun nasara sosai akan Kafirai sbd kasancewarsa Jarumi na gaban kwatance. Hakika wannan halayya ta Yarima USAMA ba karamin farantawa mahaifinsa Rai take ba, domin bincike ya tabbatar da cewa tun SARKI MUSBAHU na Dan shekaru Ashirin a duniya yake yaki da kasashen Kafirai da matsafa, Yana musuluntar dasu, domin izuwa yanxu ya yaki kasashe sama da guda Dari bakwai Kuma duk ya samu nasara akansu. Tabbas SARKI MUSBAHU ya Sha gwagwarmaya da manyan Kafirai, Amma da karfin musulunci ba a taba kaishi Kasa a filin yaki ba. Babban burin Sarki MUSBAHU shi ne ya zamana cewa musulunci ya mamaye ko'ina da Ina a fadin duniya, a dena Bautar gumaka da ALJANU da komai Wanda ba Allah ba, ta hakane sukaci gaba da yaki suna Kafa Kalmar musulunci har sai da suka ci gaba dayan kasashen dake nahiyar su da yaki. To daman Yana daga cikin al'adar Kasar cewa duk Wanda zai hau KARAGAR MULKI ta Kasar, to dole ne ya shiga duniya domin JIHADI, Kuma bazai dawo ba har sai yayi nasarar musuluntar da kasashe a Kalla guda Dari biyar. A bisa wannan dalili ne yasa YARIMA USAMA ya fara shirye-shiryen fita JIHADI, Kuma a halin yanxu saura uku ya fita. Tun a wannan lokacin Banda farin ciki da murna babu abinda SARKI MUSBAHU da matarsa FADILA wato mahaifiyar USAMA sukeyi saboda ganin cewa dansu sauran kiris ya fita daukaka Kalmar Allah, domin sun San irin dimbin ladar da ke tattare da wannan JIHADI, Kai hatta sauran mutanen Kasar suna yin Taya YARIMA USAMA murna, sunaji a ransu cewa inama su ne zasu fita wannan JIHADIN. Haka dai rayuwa taci gaba da gudana har kwana ukun suka shude, washe gari tunda sassafe jama'ar gari sun taru makil a fada domin yiwa Yarima bankwana bisa wannan fita da zayyi. Sai da Yarima ya shafe sama da sa'a Daya da rabi Yana yin bankwana da mahaifiyarsa sannan ya samu ta sallameshi dakyar sbd tsananin sabo da shakuwa Dake tsakanin da da uwa. Batare da Bata wani lokaci ba, Yarima ya fito fada sukayi sallama da Mahaifinsa sannan suka yi sallama da sauran jama'ar gari, ya kama dokinsa dauke da jikkar guzurinsa da battar ruwansha ya hau ya tunkarin hanyar barin garin. Koda fitowarsa wajen birnin sai ya tunkari hanyar BIRNIN SIN Kai tsaye..... Wannan shi ne abinda ya faru a birnin NURUL HAYAT bayan YARIMA USAMA ya fito duniya yada kalmar Allah. ***** **** **** **** Ala'amarin wadannan gungun Aljanun na BOKA GARGUS kuwa, lokacin da suka sato Sadauki MARGIM sai suka kasance suna tsala matsanancin gudu a sararin samaniya, suka rinka gifta gajimare tamkar kibiyar da aka harba ta.. Sai da suka shafe sama da sa'a shida suna tsala gudu batare da wata matsala ba.. Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka hango wani bakin Hayaki ya turnuke a gabansu, Kuma ya cika hanyar daga sama har Kasa. Saboda tsananin yawan hayakin har tokarewa yake da sararin samaniya, Nan take wannan bakin Hayakin ya rikide ya zama wadannan gungun IFIRITAN masu dauke da su Sarki Zurmatu da sauran jaruman Gasa. Koda ganin haka sai gaba dayan Aljanun suka ja birki sannan suka sauko Kasa bisa turba, sai Suma su Sarki Zurmatu suka sauko daf da su. Kawai sai Boka RAKUL ya dubi wadannan Aljanun ya tuntsire da mahaukaciyar dariya wadda Amsa kuwwarta ta cika Dajin gaba daya, bayan yayi Mai isarsa sai ya dube su yace, " ya ku wadannan ALJANU tabbas Kun tafka babban kuskure da har kuke mafarkin rushe mana burinmu ta hanyar sato Sadauki MARGIM domin kaiwa SHUGABAN KU BOKA GARGUS. To kuyi sani cewa a yau zamu dandana maku azabar da tunda akayi duniya ba'a taba yiwa wani ba, domin babu dayanku da zayyi Rai. Koda Jin wannan batu daga bakin Boka RAKUL, sai wadannan Aljanun suka kyalkyale da dariya tamkar ana ruwan aradu, daga bisani sai shugaban bakaken aljanun ya nuna rundunarsu Boka RAKUL yace, yanzu ku a tunaninku iya ku kadai zaku iya kashe mu sannan ku kwace jarumi margim daga hannunmu? To kuyi sani cewa mun rantse da shugabanmu Koda yawanku ya ninka haka sau Dari ba zaku iya hanamu aiwatar da wannan aikin ba, don haka Muna masu shawartarku da ku kauce daga Kan hanyarmu domin mu cika aikin Dake gabanmu, idan ba haka ba Kuma dayanku bazai tsira daga kaifin takobinmu ba.. Koda Jin haka sai ran Boka RAKUL da na Sarki Zurmatu ya 6aci har ma zuciyarsu ta kama tafarfasa kamar zata kone, Nan take yace wa wadannan JARUMAN GASAR guda dubu Dari Maza ku afka masu Muga iyakar jarumtakarsu. Koda Jin wannan batu sai gaba dayan Jaruman Gasar Nan suka zare makaman su sannan suka ruga izuwa kan wadannan Bakaken Aljanun, Suma sai suka rugo garesu duk da cewa yawan Aljanun Bai wuce dubu tamanin ba.. Wohoho! Inda ace mutum na Nan lokacin da rundunoni biyu zasu hadu, da sai yayi tunani kamar tsakanin mutanen duniya da aljanun duniya ne za'a kafsa yaki saboda tsananin yawansu. Karar sawayen Jaruman Gasar da na Aljanun ya haddasa girgizar Kasa Mai tsanani, kururuwar mazaje ya haifar da dodewar dodon kunnuwan mutane Nan take wasu suka rinka kurumcewa. Yayinda wadannan rundunoni biyu suka hadu, Kaico! Bala'i ba'a sa masa Rana, Kuma tabbas idan kwana ya kare to dole ne sai anje, haka Kuma idan Kaji ance ga ki gudu, to sa gudu ne Bai zo ba.. Nan da Nan Aljanun Nan sukayiwa Jaruman Gasar Nan rubdugu da nufin su yagalgala su, sai dai kaga Aljani ya kawowa mutum caka da tsinin bakinsa, da zarar ya goce to duk abinda ya samu take yake kamawa da wuta ya kone kurmus Koda kuwa Dutse ne. Nan da Nan farmakin da aljanun suke kawowa Jaruman Gasar ya haddasa kamawar wuta a cikin Dajin gaba Daya, Amma har kawowa i'yanzu ko jarumin Gasa Daya Basu kashe ba. Domin Jaruman Gasar suna kaucewa duk harin da aljanun ke kawo masu. Sai da aka shafe dakika biyu cur ana fafatawa Amma ba Wanda ya samu nasarar komai, tabbas wadanda Jaruman Gasar sun kasance sadaukai na gaske, domin duk Wanda yaga irin harin da aljanun ke kawo masu Kuma suna kaucewa harin to dole ne ya ya jin-jina masu. Koda cikar biyu da rabi, sai shugaban bakaken aljanun yace kowa ya Dakata, Nan take kowa ya cak kawai sai ya dubi Jaruman Gasar yace " tabbas Kun tafka babban kuskure da har kuka yarda kuka sallama rayuwarku domin yakarmu, don haka idan Kun yi a wannan farmakin na farko bari Muga yadda zakuyi da na biyu.. Gama fadin hakan keda wuya sai aka ga shugaban bakaken aljanun Nan ya wangame bakinsa Yana Mai kyalkyala wata irin dariya ta musamman Mai hade da wata irin iska Mai matukar karfin tsiya.. Nan take sauran Aljanun suka rinka zama iska suka shigewa ta cikin bakinshi, yayinda iskar ta rinka surar Jaruman Gasar tana makasu a jikin bishiya, Nan da Nan iskar Nan ta galabaitar da sama da Jaruman Gasa dubu arba'in, a wannan lokacin tuni gaba dayan Aljanun sun gama shiga cikin jikinsa. Kawai sai ya tsuke bakinsa sannan ya takarkare ya kwarara wani uban ihu Mai tsananin Karar da har sai da bishiyoyi suka rinka karyewa suna faduwa Kasa, ruwan korama ya rinka fantsama, dabbobin daji suka rinka fadawa ramuwa suna mutuwa saboda tsananin razana, Kai hatta tawagar su Sarki Zurmatu sai da rabinsu suka rinka faduwa Kasa sumammu saboda tsananin razana, shi kanshi Sarki Zurmatu inba don Boka RAKUL ya tsafance inda suke ba, da tuni sun kurumce sbd tsananin Karar wannan aljanin.. Ba zato ba tsammani sai akaga wannan Aljanun sun rikide sun zama wani NARKEKEN ALJANI guda Daya Mai matukar girma da tsawo, saboda girmansa kamar kansa zai rinka tabo giza-gizai.. Nan da Nan wannan aljanin yayo Kan Jaruman Gasar ya rinka tamola dasu tamkar Yaro ya samu kwallo, Nan da nan ya rinka halba su sama suna shawagi tamkar karmami, kafin cikar dakika Dari da hamsin ya kashe sama da Jaruman Gasa guda dubu goma. Yayinda wannan jibgegen aljanin ya zage dantse wajen kashe jaruman Gasar, kawai sai yaji wani abu Mai tsananin gudu ya doke bayanshi, saboda tsananin dukan sai da yayi tafiyar taku goma sannan ya tsaya da kyar, Nan da Nan sai ya waigo don ganin Wanda yayi Masa wannan aika-aikar... WANENE YA DOKI BASAMUDEN ALJANIN NAN HAR YA KUSA FADUWA? WANE BANGARE ZAI SAMU NASARA A TSAKANIN SU SARKI ZURMATU DA KUMA ALJANUN BOKA GARGUS? SHIN A WANE MATSAYI RAYUWAR JARUMI MARGIM TA KE, ZAI RAYU KO KUWA HALLAKA ZAYYI? YA BATUN CIGABAN GASAR JARUMTAKA A BIRNIN BALLUS? WANENE ZAI ZAMA ZAKARA A CIKIN JARUMAN GASAR? Mu hadu a GASAR JARUMTAKA littafi na 3 don Jin cigaban wannan Kasaitaccen littafi Wanda ni Najibullah Muhammad nake kawo maku shi✅✅✍️🙏🙏🙏