💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 01* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ _Ba kowanne lokaci qaddara ke baka zabi ba......ba kowanne lokaci qaddara ke alamta maka abinda zaya faru dakai a rayuwa ba_ _Wasu sabbin fuskokin cikin rayuwarmu sukan zame mana MAFITA kuma TUDUN MUN TSIRA ba tare da ko alamar hakan zata iya faruwa tsakaninmu dasu ba_ _Akwai manufa me yawa cikin barin ZUCIYA da abinda ke cikin ZUCIYAR a lullube......ta inda karin maganar bahaushe ya fadi a daidai da ZUCIYA SIRRIN ME ITA_ _Shi SO yakan afku a dukkan yanayin da yaga dama.....yaso.....ya kuma daidai dashi.....CIKIN TSANANI ko cikin DADI........AN SHIRYA MASA KO KUMA AKASIN HAKANNE_ _LU'U LU'UNTA DABAN YAKE DA SAURAN.......TABA DAB DA SANIN HAKA WATA QATUWAR QADDARA TA AFKO RAYUWARTA......wadda tayi silar mantar da ita wacece AKHNAN SULTANE MUHAMMAD HAMMUD_ _SHI DINNE JAGORANTA.....KUMA GARKUWARTA NA HAR ABADA_ *_SHEIKH MUHAMMAD HAISAM MOTII ABBA JIFAR_* *_Boyayyar alaqa ce tsakanin masarautar OROMO ETHIOPIA da masarautar AGADEZ NIJER_* *_Muje zuwa da sunan Allah me rahama me jin qai_* *FALAAK* Har ya kammala karatun ya tashi daga gurin tana jin a jikinta kamar yana gurin,kamar shine zaune a gurin ba gurbin daya tashi ba. Sassanyar ajiyar zuciya ta saki tana sake rungume litattafanta a qirji. Iya qamshinsa kawai wani abune da take yini ta kuma kwana dashi. Batasan me yake gudana a zuciyarta ba,bata kuma tantance abinda takeji ba,amma a jikinta tana jin akwai wani abu baqo tattare da ita,akwai wani abu da bata taba jinsa akan kowa ba. Badee'a ta rigata yin gaba tini,haka kawai taji zaman gurin bai isheta ba,shi yasa tace badee'a ta tafi. Ta miqe a nutse da nufin komawa kan kujerun da aka tanada don zama a gurin,saidai dab da zata gifta idanunta suka kai kan wayarshi. Gabanta yadan fadi kadan,da alama mantata yayi. Komawa tayi da baya ta tsugunna ta dauki wayar tana juyata a hannu. Wata irin waya ce me daukan hankali da kyau a idanu,takai hancinta a hankali ta sansana,ni'imtaccen qamshin nan nasa yakai mata har cikin kwanyarta. Murmushi ne ya qwace mata,qamshin na daya daga cikin abinda yake kasheta tattare dashi,duk wani turare nata ta rainashi a yanxun,ta kuma kasa jinsa kamar nasa. Wani abu ne ya d'arsu a ranta,saita juya fuskar wayar da sauri,tayi double click saman fuskar wayar don bataga wani madanni ko daya a jikinta ba. Haske ya bayyana saman fuskar wayar,saita fara qoqarin budeta. Ga mamakinta ba wani password akai,kai tsaye ta nufi bangaren kira,ta zuba numbers dinta ta kuma danna kira. Cikin qasa da second kiran ya shiga,wayarta dake hannunta ta fara tsuwwa,ta kalli wayar tata tana sakin murmushi. Ta samu nasarar mallakar number dinsa,wanda ita kanta batasan me zatayi da ita ba,kawai dai taji a ranta kamar hakan ya kamata tayi. Wani bugawa taji zuciyarta tayi saboda qaruwar qamshinsa a gurin. Da sauri ta daga kanta,shine a tsaye yana fuskantarta,da tazarar taku a tsakaninsu wanda bai hanata ganin wannan sassanyan kyan ba,wannan kyawawan labban dake da daukan hankali,da idanun nan dake dauke da wani maganadisun kwarjini. Hannunta ta boye a bayanta qirjinta yana bugawa da wani irin tsoro. Kada dai ace ya ganta?,idan yayi tsammanin bincike take masa a waya fa?. A nutse ya daga hannunsa yana miqa mata gami da kauda idanunsa daga kanta,ta fahimci me yake nufi,saita taka a hankali zuwa gabansa wani irin tsoro na gilmawa cikin idanunta. Irin tsoron da yake gani saman fuskar noory,irin tsoron fuskar Aanani ko Aareef idan sun masa laifi. Rusunawa tayi ta miqa masa wayar tasa,ya karba yana qoqarin sakata a aljihun jubah dinsa,kafin ya sake miqa mata daya hannun nasa yana tsareta da kaifafan idanun nan nasa. Ji tayi kaman dukka duniya ta mata nauyi,idanunsa suna da nauyin da ba kowa ke jure kallonsu ba,batasan meye a cikinsu ba,amma sunsha bamban dana mutane dubbanni data sani. So take ta boye wayar tata idan zaiyuwu,so take ta kaita inda bazai iya ganinta ba,to amma bazai yuwu ba,wayarta yake buqata daga yaren da idanunsa suka gaya mata,haka nan ta sake matsawa ta miqa masa wayar tata. A nutse ya karba fuskar nan a dinke kamar wanda baisan ma'anar kalmar dariya ba kaf rayuwarsa,abinda ya sake ruda falaak kenan. Duk daurewarsa bata taba ganinsa cikin irin wannan yanayin ba irin yau. Can qasan zuciyarsa kuwa murmushi ne fal wanda baka isa kace hakan bane saman fuskar sa. Sanda yake goge number dinsa da take yunqurin saving murmushi ne ya sake taso masa daga can qasan zuciyarsa,ta wani jera alphabet da baisan wanne suna zata bashi ba. Yanayinta yana masa kama sosai dana noory dinsa.......wani lokacin kuma saamee,har qasan ransa baiji dadi ba data fara jin wani abu a kansa,bai shiryama hakan ba,hasalima kallo daya yake mata da noory saboda kamanceceniyar yanayinsu da halayyarsu,duk da zata iya bawa noory din shekara daya ko biyu. Akwai tsoro wasu lokutan akwai sakalci a wasu al'amuran nasu,so amma zaisan duk yadda zaiyi don ya cire mata wannan matsalar. Tayi yarinta da yawa tayi handling issue na fadawa soyayyar da ba zaka sameta ba,ba zaka zamu result me kyau ba,saidai duk da qarancin shekarunta yana jin tayi qoqari sosai data iya boye abinda yake ranta bata bayyana ba. Iya contact dinshi kawai ya goge,bai shiga ko ina ba don ba wannan buqatar bace tasa ya karbi wayar ba,hasalima shi din mutum ne bame yawan zurfafa bincike ba,indai ba lamarin yana buqatar hakan ba. "Karbi" Ya fada da harshen farasanci dataji accent din ya fita da wani irin launi me dadi. A tsorace ta tako ta kuma qaraso gabansa. "Idan har kinaso mu fara samun sabani na farko dake to ki bari na lura kina wasa da karatu,binciken abinda ya shafi sirri ne na mutum kaman waya haramunne.......lokacin ki na karatu wadannan shekarun ne,idan suka wuce miki ba lallai ki iya yinsu,ki ribacesu ki kuma maida hankali a kansa sama da komai.......idan naga sabanin haka.....na iya bulala,ko sultane bazan fadiwa ba....zan zaneki ne da kyau". Ya fada yana miqa mata wayar. A nutse ya juya yana barin gurin,sai ta kasa daina kallonsa da takunsa na qasaita da ginshira. Komawa tayi da baya ta zauna tana tariyo maganganunsa. Me yake nufi?,ba komai ta gane a ciki ba. Kunya ta saukar mata sanda zuciyarta ta raya mata "Akwai wani abu daya gano ko ya fahimta" Sai ta dora hannunta tana rufe bakinta,sai kuma murmushi ya subuce mata. Maganansa na qarshe,wai zai zaneta.......qanwa yake kallonta kenan?. Idanunta ta juya tana jin dadi can qasan ranta,itakam koda matsayin qanwa dinma kawai ya bata hakan ya isheta,ta miqe tana jin wani irin nishadi a ranta ta soma takawa zuwa hanyar da zata sadata da sassansu. *AKHNAN* A hankali ta bude idanunta da takejin sun mata nauyi sun kuma yi mata wani irin babu dadi,kaman an watsa mata tsakuwa a cikinsu. Lumshesu ta sakeyi sannan ta kuma budewa still tana tariyo awannin da suka wuce,saidai kuma sautin karatun qur'anin da take iya jiyowa ya saka mata wata irin nutsuwa data karkatar da hankalinta daga tuna komai zuwa ga sauraren karatun. Wata irin murya me cike da softness da calmness,wani qira'a da idan zata iya tunawa a shekarun baya da suka wuce.......sanda morsa safiyya take shishshshigi cikin rayuwarta take kunna mata irinta sak da sautin da yake can qasa a duk sanda ta kwanta zatayi bacci. Koda ta kwanta ba karatun idan ta farka komai dare zata samu karatun yanayi ta cikin wata bedside lamp dinta dake hade da speaker din da ba lallai ka iya ganewa a jiki take ba. Duka duka batafi shekaru goma sha biyu ba a sannan,amma duk sanda ta farka ta samu karatun yana yi sai tasa hannu ta kashe gami da jan tsaki. Tana jin kawai ana disturbing peace din mutum ne da kuma baccinsa. Daga qarshe kuka ta dinga yiwa mammina,har sai da aka daina kunnawa,wanda batasan ya akayi mammina ta cika mata wannan muradin nata ba,tadai shaida mata tana shafa sumarta a ranar. "Daga yau bame sake damun baccin princess......an daina kunna miki,kiyi baccinki yadda kikaga dama". Ayau,a wannan asubahin da alfijir yake ketowa karatun ke isketa,sai takejin nutsuwa tana dawo mata a hankali. Ta miqe ta zauna a nutse,sannan ta zuro santala santala qafafunta sama,ta saka hannunta tana zare led fask mask din fuskarta,wadda takan sanya ta lullube fuskarta gaba daya,tana kuma blinking red light da yake taimakawa wajen maintaining na kyan fuska da sakin sinadarin collagen dake dawwamar da quruciya. Gefe ta ajiye machine din,don ba wani abu nata da tasan inda ake adanashi. Duk abinda ta cire kota ajiye akwai me daukeshi,a alkinta mata shi zuwa sanda zata tashi nemansa. Wannan hidimar tata bata taba qarewa ko tsaiwa ba,tun daga sanda aka haifeta har kawo yau da take a matsayin cikakkiyar mutum. Hannu tasa tana daure gashin kanta me tsaho da sulbi,sannan ta sake saka hannun tana maida maballan pyjamas dinta daya cire garin kwanciya,tasa qafa ta jawo flip-flops dinta dake gefan gadon fari tas kalar pyjamas din jikinta ta zura ta miqe a hankali sautin karatun yana sake shigarta. Lokacin sallar asuba ya kubce mata da kusan mintuna talatin zuwa da biyar,kuma tasan hakan baya rasa nasaba da baccin kirki data rasa a jiya ba. Toilet dinta ta tura ta shiga,komai yana nan intact yana jiranta,wani yanayi me daukan hankali da iska me kyau dake fidda sassanyan qamshin kayan kula da bayi. Gurin toothbrush dinta ta duba,sai ta lura ba'a saka mata toothpaste ba. Yamutsa fuska tayi,ta bude a kasalance ta dauko,ta kuma karashi kusa da wani abu dake maqale a bango,matso kansa toothpaste din yayi saman brush din,ta taka tana matsawa gaban sink din dake da wani irin ado kamar na duwatsun da akan samo qarqashin ruwa,ta kunna tap ta soma wanke bakinta,idanunta kan fuskarta,maganganun su aisa da suka raba dare jiya a dakinta suna dawo mata. Wanka take fara yi a irin wannan lokacin,amma bata qaunar ko kadan lokacin sallah ya qwace mata,uwa uba kuma jikinta tana jin kaman dan zazzabi keson sauko mata,sai tayi alwalar kawai ta dauko qaramin towel na tsane jiki ta fito. Still har yanxu daddadan sautin yana ci gaba da ratsowa dakinta,ta ajiye towel din hannunta,ta qarasa inda duk dare birra ke ajiye mata daya daga cikin lafiyayyun after dress dinta na sallah,biyu take ajiye mata kullum,ta zabi color din da ya kwanta mata,sai ta dauki farar ciki dake fidda wani irin kwantaccen qamshi ta dora saman pyjamas dinta. Qamshin rigar ta shaqa sosai a hancinta,qamshi ne da takeso sosai "Baikai wannan qamshin ba" Wata murya daga can qasan zuciyarta ta furta. Qaramin tsaki taja,tasan wanne qamshin ne,qamshin mutumin hippodrome da tuni ta bashi wannan sunan,da kuma qamshin wancan sheikh din da har yanzu take tantama a kansa. Taya za'ayi mutum irinsa daba abinda ya sani sai litattafan Arabic ya samu qamshin da ita kanta batasan adadin nawa ta kashe saboda samar da irinsa ba?. Saman abun salla ta qarasa dake wata corner dab da glass door din da zata fiddaka kyakkyawan balcony dinta dake maqotaka da sassan kusa da ita,ta zabi ayita a nan saboda tasan sashen ba kowa,ba kuma lallai a zauna nan din ba bare kai kawon mutane ya dameta koya hanata sakewa. "Sallallahu alaihi wasallam" Ta fada a hankali sanda ta kammala sallar take kuma zaune saman abun sallarta daidai sanda ya karanta ayar. "MUHAMMADUR RASULULLAH". Ita kanta batasan me ya zaunar da ita ba,take kuma ci gaba da sauraren karatun da take sake jin kusancinsa sosai da inda take zaune. Idanu ta zubawa curtains din da suke rufe glass door din,wadanda ke dagawa a hankali,sai taji sha'awar shiga balcony din,wanda takan dauki kwanaki ba tare data shiga ba,ta miqe a nutse tana taka qafafunta saman lallausan carpet din dake a gurin,ta isa gaban qofar ta murda lock din ta soma qoqarin budewa. Batasha wuyan budewa ba,duk da tayi mamakin hakan,don duk sanda zata shiga bude mata akeyi,bata taba budeta da kanta ba. Wata irin iska me dadi gami da kusantowar karatun fiye da dazun suka risketa,ta lumshe idanuwanta tana takawa zuwa gaba sosai idanunta akan sashen da karon farko ta hangin qyallin haske a cikinsa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 02* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ____________________________ "Yaushe aka tare?,waye a ciki haka?" Ta tambayi kanta tana zuba idanu cikin balcony din sashen dake fuskantarta. Ba wani alamu na motsin kowa,saidai shatin alamun mutum da take dan iya hangowa ta glass door din da aka dan yaye labulenta kadan,amma bayaga haka ko kalar kayan jikinsa bata iya gani. Ci gaba tayi da kallon gurin sautin yana ci gaba da ratsata. Wani irin karatu me cike da hikima gwaninta da fasahar harshe,wani!irin karatu data jima bataji karatu me dado haka da yaja hankalinta. Hasalima ba zata iya tuna sanda ta tsaya mintuna masu dan dama har haka tana sauraren karatun qur'ani ba,tun daga wancan ranar da take kwana dashi ta kuma nuna bata buqata aka kuma dakatar. Duk sanda iska zata dan daga labulen sai ta sanya idanunta a tsakani ko zata gane mutumin dake dakin,amma har zuwa sanda yakai qarshen sura,karatun kuma ya tsaya cak,hasken cikin dakin ya sake raguwa bata gano komai ba. Samun kanta tayi da jan tsaki,tana jin ranta yana baci. Tsanar data yiwa mutanen irin Hakeem tana sake ninkuwa. Shine ko kuma tace sune sila,banda haka ta tabbatar babu ta yadda sultane zai sanya wani a daura da ita ba tare data sani ba. Juyawa tayi tana komawa ciki,sai a sannan ma taga ta bata lokuta ashe masu yawa,batasan ma me yakai damuwarta na lallai sai taga wanda ke karatu ba,ta qarasa shigewa tana zuge curtains dinta ta fada saman gadonta cikin salon kwanciyar rub da ciki tana jin yadda kanta yake qara sarawa. Tana ji na'aurar gefan gadonta tana gaya mata ana neman izinin yin magana da ita amma tayi banxa da ita,har sai data dameta ta dauka zummar dannawa wanda ya dameta kakkaifan warning,sai kuma taji muryar birra cikin qanqan da kai. "Ayimin afuwa,tuba nake,daga kitchen ne suke neman alfarma,ki fadi abinda za'a yi a matsayin abincin karinki na yau,jiya basu samu daman dauka daga gareki ba". Qaramin tsaki ta sake ja,wanne irin abinci ne zai iya kaiwa cikinta yau?,ita kadai tasan me takeji,ya kuma takeji. A duk sanda ta tuna sultane ya gama ganawa da iyayen Hakeem sai taji ta tsani kowa ta tsani komai. "Kada su dafa komai,su wuce sassansu,ke kadai buhaina da bushira na bawa izinin zama a sassana" Ta fadi tana kife na'aurar gami da juyar da kanta gefe cikin zurfafa tunanin mataki na gaba daya kamata ta dauka don dakatar da sultane. A nutse ya zare idanunsa daga inda yake zaune yake hangota. Tun daga tsaiwarta har barinta gurin duka yana ganinta fes. Yana da kaifin gani kamar yadda yake da kaifin ji,duk dagawar da labulen zaiyi yana iya hangenta ta tsakiyarsa,hakanan duk karatun da yake yi yana yine ba tare da alqur'ani a hannunsa ba. Qafarsa daya aza daya saman daya ya sauke yana fidda siririn numfashi. Basai an gaya masa ba......ya hangi tarin girman kai me yawa a tattare da ita......a tattare da komai nata,dabi'a mafi muni wadda ita tayi silar barin shaidan jerin sahun mala'iku zuwa ga qasqantacce wulaqantacce kuma la'anannen Allah. Basa jituwa da duk inda wannan dabi'ar take,ko kuwa yaya kake dashi. ★Batasan ya akayi ba,sai tsintar kanta tayi da dogon baccin da bata tashi ashi ba sai misalin qarfe biyu saura na rana. Zuwa lokacin ta fara jin yadda hanjin cikinta yake yamutsewa guri daya,duk da rashin kyakkyawar mu'amalarta da cin abunci,amma tasan dole a yau kam taji yunwa. Dan abinda take zama ta sanya a cikinta da sunan abinci a qalla kwanaki biyu kyawawan rabonta data zauna ta cishi. Pyjama din jikinta ta zare,ta kuma daurawa fatarta me sheqi da daukan ido towel tayi daurin qirji dashi,abinda ya bawa dirarren jikinta me wani irin shape dake bala'in daukan hankalin maza daman fitowa. Ko ba'a gaya maka ba,kalan fatarta daban yake ko cikin 'ya'yan gata,ko cikin masu arziqi da wayewa gami da sarauta idan ta shiga kallonta akeyi. Tasan darajar jikinta,tana iya kashe masa ko nawa ne don ta gyara kanta ta fita a MACE sak,wannan ya sanya duk inda ta shiga take zama abar kallo. Yau ba wanda ta nema,ita ta hada ruwan wankanta da kanta,ta kuma tsaya cikin shower ta wanke gashinta tsaf da kalolin mayukan wanke kai,ta kuma dawo gaban mirror ta busar dashi tayi oiling duka da kanta,ta fesheshi da hair mist,wanda kafin ta kammala ta gaji tubus kaman wadda tayi wani gagarumin aiki. Ba aikinta bane,abinda kawai yake aikinta wanke jikinta ta kuma shafa mai,amma kula da gashinta,suturan data cire dama wanda zata saka,gyaran faratanta da qafafunta dukka ba wanda tasan ya akeyinsa. Yau ma da kanta ta shiga closet dinta ta duba wata English gown ta wani lite material,butter colors me adon manyan flowers sky blue me haske sosai. Daga sama daidai qirjinta ce,daga qasa kuma ta bude sosai don umbrella shape ce. Euro dari biyu da hamsin ta siya rigan,wani zuwa da sukayi UK,kimanin naira dubu dari biyu da casa'in,bata taba sakata sai yau don ta shige cikin tarin tulin suturunta da bata taba amfani dasu ba. Hannunta duka duka iyakarsa dantsen hannunta. Tayi wani irin sassanyan kyau,duk da fuskarta ba alamun walwala ko digo,kawai sanya kunne take tana jira taji ta inda sultane zai kirata,ko shi ko mammina. Saka kunne take taji ta ina labarin aurenta zai bulla?,auren da takeji cikin ranta koda gawarta ba zata bari wani Hakeem can ya mallaka ba. Wasu irin flip-flops da gown din tazo dashi ta zurawa lallausar qafarta,su dinma laushi ne dasu sosai,ta tsaya gaban dressing mirror ta jawo jewelry organizer dinta ta ciro qaramar barima data dace da kayan ta soma maqalawa kunnenta. DAWISU shine sunan da wani lokaci mammina kan kalleta ta kirata dashi. Allah ya zuba mata son tsafta da ado,tana da wani irin son kwalliya da zai wahala koda cikin gida take a zaune irin haka zaka sameta da madaidaicin adon daya dace da yanayin,wanda baiyi sama da yawa ba ba kuma zaka kalleta ka kasa ganin nau'in adon jikinta ba. Ta sauke hannunta kenan daga kunnenta wayar da kusan ko yaushe a silent take ta soma haske,sai takai idanunta kai tana karanta sunan mammina dake yawo. Gwiwarta taji gaba daya tayi sanyi,don batasan me mammina zata gaya mata ba,don haka taja kujera ta zauna tana daga kiran. Da siririyar muryar nan tayi sallama,mammina ta amsa mata tana fadin. "Wai lafiyarki?,tun jiya akacemin kin kwanta da wuri,yau kuma na bibiyi sassanki sunce baki sauko ba,kince ma kada a dafa komai......to me kika ce daga jiya zuwa yau din?" Sai data sauke numfashi ta lumshe idanunta tana budesu. "Bana sha'awar komai mammina.....ba abinci nake buqata ba a yanzu". Shuru mammina ta danyi tana saurarenta,abinda ya bawa Akhnan daman sake tambaya. "Ya ake ciki mammina.....sai nakeji kamar lokaci na yana qurewa". Kaman mammina din ba zatayi magana ba,sai kuma ta magantu a sanyaye. "Sun fara da kawo dukiyar aure......raqumma hamsin da gold". Wani irin faduwa gabanta yayi,muryarta tayi sanyi sosai. " Mammina......da ranki?,kina raye zan rasa samun wani muradina?". "Ba zaki rasa ba biftu.....sultane yayi wata irin kafewa da saukeshi sai anbi a hankali,ba babban dalili ne zai sakashi sauka,ko janyewa daga bangaren hakeem takai tsaye,tunda har ya karbi dukiyar aurensu,dole sai munbi a hankali......wannan karon koda ta kama mu sanya morsa safiyya cikin lallashinsa......zan duqa mata zan kuma saukar da kaina na roqa miki haka". "Indai alfarma ta bangarenta ce mammina banaso......" Ta fada a zafafe da tarin qiyayyar da ko sunanta bata qaunar ji. "Biftu!" Mammina ta kira Akhnan da wani irin yanayi daya sanyata dole tayi shuru. "Ki sauka ki nema wani abun kici,idan kin gama kizo ki sameni,akwai shawaran da zamuyi". "Okay" Kawai ta fadi tana sauke wayar gami da katseta. Cikin izzar nan tata take saukowa daga stairs din. Duka gidan shuru ba motsin kowa,kuma tasan hakan baya rasa nasaba da umarnin data bayar. Ba komai saman dining kamar yadda ta buqata,bata damu ba,don dama bata jin zata iya cin komai,saita juya tana shiga kitchen da kanta,abinda ta shafe a qalla shekara biyar zuwa bakwai rabonta da yi. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Komai yana killace a kuma tsaftace cikin tsari da sanin makamar aiki. Tea kawai take da buqatar sha,amma batasan yadda zata hada ba,don haka tasan ya zame mata dole ta kira wani cikinsu birra ya hada mata,saita daga wayarta tayi kiran da duka duka na sakanni ne ta kuma yanke kiran kai tsaye ba tare data jira an daga ba. Cikin qasa da minti biyar birra ta shigo kitchen din. Duk saita rude ganin Akhnan din tsaye cikin kitchen din. Ta qaraso da matuqar girmamawa ta rusuna tana fadin. "Allah ya taimakeki me kike buqata?,dadai kin koma kin zauna,kome kike buqata saina kira cook din ta hada miki". Hannu tadan daga mata. " Basai kin kirasu ba......hadamin tea kawai". "An gama" Ta furta tana yin gaba da hanzari. Cikin mintuna ta kammala hada mata,sannan kuma ta wuce mata dashi saman dining,ta taka a hankali ta bita a baya,ta zauna sosai birran na qoqarin saka saka mata kyakkyawan yadin da ake shimfida mata saman jikinta. Hannu ta daga mata kawai,sai birran ta maida hankalinta gurin raba mata tea din gida biyu yadda zai mata dadin sha. Rusunawa tayi bayan ta gama tana ja da baya. "Akwai wani abu?". Kai ta girgiza mata. "Kina iya tafiya" Ta amsa mata tana daukan cup din tea din takai bakinta. Wani taste da qamshi daban taji ya mata a baki,saidai taste din bawai ya canza bane sosai,don haka sai ta aza daga bakinta wanda yake da alaqa da rashin jin dadin da zuciyarta take ciki. "Alhamdulillah" Ya furta a nutse sanda ya kammala shiryawa cikin kaftan pyjamas da ya dace da amam din kanshi daya zauna masa sosai ire iren na malaman qasar Indonesia. Sak irin shigar mazan da Indonesia,saidai kaman yadda ya saba a wasu lokutan yakan zagayo da jelar amam din kanshi ya lullube hancinsa zuwa habarsa,ba zaka iya ganin komai ba banda kyawawan zagayayyun idanunsa da kuma cikakkiyar girarshi. Yau din ya wareta ne kawai do nufin kewayawa cikin gidan. Ya sanarwa da me wada,kuma yace ya zabi duk wanda yakeso ya tayashi tattakin cikin gidan,kai tsaye kuma yace MAHER don shine zai dace sosai da tsarin aikinsa,tunda kusan maher din yasan gurare da yawa na cikin gidan. A nutse ya sauko,ya sani zuwa yanzu Maher bai iso gidan ba,sai ya tako a nutse yana ratsa parlor din nasa,daidai sanda muryar jibrilla hadimin da aka sake bashi yayi magana wanda baima lura dashi ba yana goge dining area. "Ranka ya dade......me martaba ya aiko da saqo a baka idan ka sauko" Ya fadi yana duban wata farar takarda a hannunsa. Baice komai ba ya miqawa jibrilla hannu,shi kuma ya tako a hankali yana rusunawa gami da miqa masa takardar. A nutse yaci gaba da takawa a hankali,sannan ya bude takardar yana dubawa. Minti daya kacal ya gama karantawa,sai ya nannadeta yana azata saman conceal mirror din dake daura da gurin. Buqatar ganinsa yakeyi a kebantaccen library dinsa. Haka kawai yake ganin girman dattijon,yayin da a wasu lokuta kuma yake kallonsa kamar motii dinsa ta bangaren wasu dabi'u nasa da sukayi kamanceceniya. Ya riga yasan kusan map na gidan gaba daya,yasan location na gurare da yawa cikin gidan. Bai taba nuna hakan ba,saboda sirranta aikinsa da kuma sirranta matsayinsa,don haka ko a yanzun daya fito a nutse,sai daya tambayi me wada direction din library din sannan ya wuce kanshi tsaye. Sosai hanyar da zata sadaka da library din keda wani irin yanayi me daukan hankali. Guri ne dake da tarin bishiyu da suka qarawa gurin qarancin haske suka kuma sanyashi ya zama da wata irin weather ta musamman data dace da daminar dake sanyo kai da jiran umarnin rabbu don soma zubar da ruwa ga doron duniya. Sosai yanayin gurin yayi masa,yaci gaba da takawa a hankali yana sake karanta gurin,har zuwa sanda ya isa makekiyar qofar library din. Tun daga bakin qofar zakasan cewa lallai an tsara gurin sosai da wani irin yanayi da zai baka nutsuwar yin karatu zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 03* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ Hadimai hudu ne ke kula da bakin qofar,wasu irin tsayyayun mutane da yanayin jikinsu kawai zai gaya maka alamun qarfi me yawa a tattare dasu,suna tsaye kyam,tahowarsa kuma ya sanya biyu daga cikinsu matsawa suka buda masa qofar suna rusunar da kawunansu qasa gami da buda masa hanya sosai. Cikin nutsuwar shin nan yayi sallama a nutse cikin tsarrarren library din. Tun a ranar farko da bincikensa ya fada ga library din yaga tsarinta ya masa,zai kuma dace da yanayin nutsatstsen karatu. "Wa'alaikumussalam warahmatullah" Sultane dake zaune saman daya daga cikin lafiyayyun tausasan kujerun zama da aka zuba a gurin ya amsa,fuskarsa yana gauraya da murmushi. "Maraba da sheikh muhammad" Sultane ya sake fadi yana gyara zamansa sosai,ya dubi nannie dake zaune daura dashi. Ta jima cikin library din suna tattaunawa da sultane din,wanda duka akan abinda ya shafi auren akhnan ne. Tun daga wancan ranar daya gaya mata kada ta sake tuntubar akhnan din,sai bata sake neman nata ba,bata kuma sake magana akan komai ba. Ta sani tunda har sultane yayi magana akai akwai wani dalilin nasa. Mahaifinta ne,ya fita sanin d'iyarshi,tasan tabbas akwai dalilin da ya sanya yace kada ta sake bari maganan ya shiga tsakaninta da alkhnan. "Ga yaro na Fatimatou" Sultane ya furta yana murmushi gami da miqa hannuwa haisam dake takowa gurin. Murmushi nannie ta saki tana duban haisam din. Ba ranar da zama zai hadata da sultane bai bata labarin haisam ba,mamaki take kullum na yadda ya shiga ranshi haka farat daya,to amma itama a yau nata mamakin ya ragu duba daya data masa. Akwai wani irin cikakken nutsuwa da kamun kai tattare da shi,uwa uba tana hangen kwarjini me yawa a tare dashi da wani irin haske da ita kanta batasan na meye ba. "Ba shakka,yau naga muhammad haisam" Ta fadi tana girgiza kai har yanzu idanunta a kansa sanda yake zama daura sultane din. Cikin girmamawa suka gaisa da sultane,ya juya akalar gaisuwar tasa ga nannie wadda shekarunta suka kusa na nanay dinsa. Cikin kulawa sa wata qaunar haisam din ta amsa masa. Godiya ta masa me yawa game da kula da karatunsu falaak da kuma amincewa ya zama mashawarci ga sultane din,sannan ta miqe. "Bari na bawa uba da d'ansa guri ko?" Tayi maganan tan dariya gami da gyara lullubinta. Murmushi sultane yayi,yakanji kamar duk wani matsala na rashin samun magajin d'a namiji ta yaye masa a duk sanda ya tuna da haisam,a duk sanda haisam yake gefansa. "A fito lafiya" Ta sake fadi tana rusunawa sultane din cikin nuna girmamawar data saba gareshi tun daga quruciya kawo yanzu. "Allah yasa" Ya amsa mata shima cikin kulawa. Shuru gurin ya danyi bayan ficewar nannie,sai ya gyara zamansa sultane din yana matso da farantin dake cike da kayan marmari gaban haisam din. "Allah yasa ba ayyukanka na katse maka ba......baka kwana da sanin zan nemeka ba ka tashi da hakan" Kai ya girgiza a nutse,fuskarsa adan sake ba yadda ta saba kasancewa ba. "Ba wani damuwa a cikin hakan". "Bismillah mana" Sultane ya fada yana masa nuni da fruit din. Baice masa komai ba,ya miqa hannu ya dauki fruit din,ya riqe a hannunsa ba tare da yaci ba. Ya lura kaman akwai maganar da sultane din yakeso yayi dashi,amma kuma kamar tana masa nauyin fadi,wannan ya sanyashi ya gyara zamansa kadan yana fadin. "Ina fatan ba wani matsala ko damuwa bace?". Murmushi ya kuma saki yana girgiza kai. "Ko daya......shawara ce nake da buqatarta" Sai ya miqe ya zauna sosai. "Gami da bayi maza da mata dake cikin gidan nan.......akwai hade haden auren da nake buqata nayi.....inason shawara kan zamansu a cikin gidan,dukkaninsu sun balaga sunkai munzali,morsa safiyya tana aiwatar da wannan tsarin ga hadiman bangarenta". Kai haisam ya jinjina,kima da darajar sultane tana qaruwa a idanunsa. Gefe guda matar daya ambata din,ya yabawa girman hasashenta da hankalinta. Mace kamar ita har tayi wannan tunanin,ta kuma dinga aiwatarwa da dukka qwarin gwiwarta da qoqarinta?. Sunan nata sai ya maida tunaninsa baya,kamar dai itace wadda ta sanya oustaze Ousmane kawoshi a madadinsa......sannan kamar itace mace ta biyu a gurin sultane din indai bai manta ba,indai kuma lissafinsa ya bashi daidai. Tunaninsa da fatansa dukka masu kyau ne,yana da tsananin hangen nasa da kuma qoqarin kare haqqin musulunci,sai ya maida apple din inda ya daukota ya hade tafukan hannunsa guri guda. "Akwai tarin kuskure da sabawa addini akan ajiye bayi ko hadimai ko 'yan aiki maza da mata cikin gida ba tare da aurar dasu ba ko kuma duba buqatunsu na dan adam ba.......akwai tarin tuhumar cikar nagartar dukkan wanda ya aikata wannan....." Kai sosai sultane ya girgiza cikin gamsuwa. "Abu mafi kyau shine......a basu dama kowa ya zabi wanda yakeso,a kuma aurar dasu kaman yadda musulunci ya tanada" "In sha Allah" Sultane ya fadi yana jinjina kai,zuciyarsa girman haisam da qaunarsa suna sake samun gurin zama. Yana yiwa mutanensa da yawa kwarjini,kwarjinin da ya sanya malaman dake tare dashi ba kowanne lokaci suke bashi shawarar da zata dace da shinda ya kamata ayi ba. Yafi buqatar jin gaskiya a bakunansu fiye da su gaya masa abinda rai da zuciyarsa sukeson ji,amma ba kasafai suke iyayin hakan ba,saidai ya hango wannan qualities din tattare da haisam din. Shuru ya sake wanzuwa a tsakani,har yanzu haisam yana ganin akwai wani magana ta daban da sultane yakeso yayi cikin idanu da bakinsa......sai ya sauke idanunsa yana maidawa ga littattafan dake gefansa cikin nazarin wadanne iri ne. ★A hankali ta hadiye tea na qarshe data kurba,ta kuma dire cup din saman table din tana jin yadda wata kasala da mutuwar jiki take saukar mata lokaci guda. Idonta ta lumshe sannan ta budesu lokaci guda,a hankali ta dafa table din ta miqe ta fara sauka daga gurin tana jin yadda kasalar take bin jikinta. Ta alaqanta hakan da yunwar data tarawa cikinta na kwana da kwanaki,yanzun kuma ruwan zafin da tasha ne qila yake sauka a jikinta yana sake mata gabobinta. Wayar hannunta ta daga tana duban lokaci,bata manta ba mammina nason ganinta,kuma kiran mammina din abune me matuqar muhimmanci a gareta. Tana buqatar taje,don tana neman duk wani hanya da dabara da zai sanya sultane ya janye daga qudurinsa,banda haka a yanayin kasalar da takeji ba abinda take buqata irin ta koma samanta ta kwanta ta huta,ta kuma qara bacci,ta tabbatar awa daya zuwa biyu zata tashi fresh. Saman takeso ta koma,amma sai taji ba zata iya hawa stairs din ba,don haka ta matsa na'urar dake kusa da ita,ba jimawa birra ta qaraso a gaggauce. "Zan fita gurin mammina.......shiga ki samomin abu mafi kusa dake da zan lullube kaina" Ta qarasa maganan a kasalance. Cikin girmamawa ta amsa ta kuma haura saman da azama,ba jimawa ta sauko da wata Riga. Gabanta a hude yake,tana zubi da alkyabba don hade take da hular da zaka saye kanka dama fuskarta gaba daya,tana da dogon hannu bata da nauyi kwata kwata,saidai ita tsahonta gaba dayanshi bai qarasa har qasa ba. Baya kawai ta juyawa birra din,ita kuma ta qaraso cikin girmamawa da kulawa ta zira mata,akhnan din ta sanya hannu ta rufa hular a kanta sannna ta fara tattaki don ficewa daga sassan. "Zan iya yi miki rakiya?" Birra ya fada tana sadda kanta qasa,kai kawai akhnan din ta kada mata alamun bata buqata sannan taci gaba da takawa tana ficewa. Iska sosai ta zuqa sanda ta fara takawa a farfajiyar da zata zame mata kamar ragin hanya,yadda zata bulle sassan mammina ta hanyar mahadar data hada library din sultane da kuma shiyyar mammina din. Tanason hanyar,saboda tafiya a hanyar yana tuna mata abubuwa masu yawan gaske,tafiya a hanyar yana tuna mata rayuwarta a France,lokacin karatunta da wasu lokuta takejin kewar da takan sanyata siyan ticket ta koma qasan tasha iska na satittika sannan ta dawo. Hanya ce da ba wani zirga zirgar mutane,duk wanda ka gani a area din amitacce ne,sannan kuma akwai abinda ya kaishi ta gurin. Library din sultane ne kawai a gurin,sai dakunan ajiyar kayayyaki na musamman na sultane mammina da morsa safiyya,sai akayi masa gurin hutawa kebantaccce,da kuma hanyoyin da zasu iya sadashi da hanyar da zata bulla dashi sassan kowacce cikin matan nasa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) A hankali take takawa da salon tafiyar nan tana me matuqar jan hankali,saidai a yau din tafiyar ta kasance da wani irin yauqi saboda kasalar dake ci gaba da saukar mata,har tana jin kamar qafafunta ma sundan fara nauyi,hakanan wayar hannunta taji dama ta barta a sassanta bata fito da ita ba. Ba kowa kuma ta gurin ballantana ta bashi wayar ya maida mata,hakanan dai tayi ta maza taci gaba da riqon wayar a hannunta tana kuma ratsa guri.. "Idan ba damuwa ina iya tafiya?" Haisam ya buqata yana duban sultane cikin girmamawa,ganin bai sake cewa komai ba,ga kuma saqon da abdii ya aiko masa kan maher yana jiransa. Murmushi ya saki yana jinjina kai. "Kana iya tafiyarka muhammad,ina fatan kuma ba zaka gajiya ba a duk sanda na sake kiranka". "In sha Allah" Ya amsa masa a nutse sannan ya miqe,cikin girmamawa sultane shima ya miqe,a jikinsa yakejin haisam din abun girmamawa ne. "Na gode qwarai da gaske da sadaukarmin da lokacinka da kayi" Sultane ya fadi. Sosai haisam yakejin godiyar sultane din tayi girma a gareshi,saidai kuma baice komai ba ya fara takawa sultane din yana masa tattaki har bakin library din. A nutse yasa hannu ya sauke yankin daya lullube bakinsa zuwa hancinsa yana sheqar iska sosai yana aikata hunhunsa gami da ci gaba da takwa da qasaitaccen takun nan nashi. Har yanzu idanunsa na hango masa magana kwance a idanun sultane......to wacce magana ce?,wacce damuwa ce haka data masa nauyin daya gaza fadi. Bai kammala aje zaren wannan tunanin ba yaji kamar an wafci hankalinsa da kalaman. "Bakka kana bane eenyuuf hin hayyaminaa........Sanduuqa sana irraa fagaachuu hin dagatinaa........Sun lubbuu kee balaaf saaxiluu dagachuu.....Ajaja Mammina ti" Wata irin jarumta yayi gurin riqe kansa,y kuma kame hankalinsa da nutsuwarsa da barin waiwayawa zuwa ga inda maganar take fitowa. Dukkan wani reaction da zaiyi zai nuna cewa eh yaji yaren oromo......yaji kuma wani abu da yaja hankalinsa,wanda baya fatan hakan ya faru. Yarensa sirrinsa ne......reaction dinsa akan komai makaminsa ne. Yaren oromo cikakke yakeji......da wasu nauyayan saqo daga bakin bayin nan guda biyu. Dayan ya fahimci fuskarsa TAMIM na farko daya fara gani maqale jikin window din sultane......saidai bai samu nasarar ganin fuskar mutum na biyu ba,don ya bada baya yana kuma bada umarni da zafi zafi da alaman bacin rai akan bude gurin daya fahimci wani store dinne. "Kada kabar kowa ya sake bude gurinnan......kada ka manta,kayi qoqarin nesanta kanka da akwatinnan.......manta hakan yana daidai da sanya rayuwarka cikin hatsari......umarnin mammina ne wannan" Ya maimaita maganganun cikin kansa yana kuma sake tisasu yadda zasu zauna a gurbin da yake buqatar su zauna din,har yanzu kuma idanunsa suna kallon qasa,saidai idanun hankali dana zuciyarsa suna tare dasu sanda ya sanya hannu yana rufe gurin suka kuma taka suna barin gurin da sautin magana qasa qasa da baya iya jin abinda suke fadi. Lallai bai shakka gidan sarautar agadez itace TA DAYA da zarginsu zai fada a kai......kuma itace ta farko daya kamata hankalinsu ya koma kai. A yau yaji yaren oromo gaba daya da irin karin harshen da yake tabbatar masa OROMIA ne koma waye yayi wannan maganan,dashi din dame sauraronsa. Cikin mamaki ta damqe hannuwanta da taji yatsunta sun fara rawa kamar wadanda aka kama ake sarqesu cikin na juna,tadan sunkuyar da kanta tana duban yadda yatsun nata sukaci gaba da motsawa da hanzari hanzari. Mamaki ya kamata tana jin yadda idanunta suka soma mata nauyi,kamar sunkuyar da kan nata data yine bai musu daidai ba suke yunqurin fadowa daga gurbinsu zuwa qasa,wannan ya sanya daga kanta da sauri,a wannan karon kuma ba inda idanun nata suka sauka sai a kanshi. Bibbiyu bibbiyu idanunta suke gani kafin su fara nuna mata blurry (dishi dishi). Amma duk da hakan idanunta basu gaza sauka sosai kuma fes cikin fuskarsa ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 04* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ Zagayen idanunsa take ta qoqarin tsaida idanunta tare da kwatantasu da wadannan idanuwan.....wannan idanun da suka zame mata barazana a hippodrome......wadannan idanun da suka zama barazana ga zaman lafiyar baccinta.......wadannan idanun da babu wani dare da zai mamaye sararin subhana......ta kwanta da zummar bacci ba tare da sun farmaki baccin nata ba. Wannan qamshin.......wannan turaren shine abu na biyu daya dinga tasowa tun daga tazarar dake tsakaninsu yana yin kyakkyawar ajiya cikin hancinta. Kaman zata shide saboda yadda takejin qofofin iskarta suna rufewa suna raguwa daya bayan daya,amma hakan bai hanata shaqo qamshin da kyau ba,abinda ya sake dawo mata da hoton hippodrome cikin idanuwanta kenan fes. Nutsuwarsa dake bayyane muraran saman fuskarsa,da takunsa dake cike da wata ajiyayyar qasaita ne taji yana qona zuciyarta dake wani irin matsewa a qirjinta,kamar ana saka hannu ana barazanar takureta guri daya. A yau gangar jikinta dama zuciyarta gaba daya suna sake bata tabbacin shine.......daidai sanda yake ci gaba da takowa cikin kame ganinsa da kuma shagala da al'amuran da suka shafeshi kadai,da zare kai daga cikin al'amuran da basu kasance damuwarsa bane. Wani irin sanyi taji yana ratsa kowanne sashe na jikinta,amma taqi baiwa hakan hankalinta,tafi tattara hankalinta a kansa. Har yanzu bai dago idanunsa ko sau daya ba ballantana ya kalleta,har yanxu bai dubi sashen da take ba ballanta ta samu nasarar aika masa da saqon data binne cikin idanunta. Wani irin ninkuwa gudun zuciyarta yayi,abinda ya fara barazanar daukewar numfashinta sanda haisam din yake dab da ita,abinda ya bata daman sake kallon qwayoyin idanunsa......irin kallon da ake kira na tsaf da tsaf......kallon daya tabbatar mata SHINE ABOKIN KARAWARTA NA WANCAN RANA. KAMANCECENIYAR nada yawa.......hujjojin data tara a kansa sunyi yawan da za'a iya kauce musu,ta lumshe idanunta sanda numfashinta yake yunqurin toshe hanyar da zata samu iskar da zata kaiwa hunhunta.......taji kaman iska ta dauketa tana shirin cilli da ita wani guri na daban,abinda ya tilastata dauke idanunta daga kanshi tana riqe wuyanta da daya hannun,daya hannun kuma ta miqashi da zummar dafa bango,saidai ko kusa da bango batakai ba bare ta samu tallafinsa,sai tayi baya kaman fefan takarda tana shirin zubewa warwas a qasa. Duk da cewa numfashinta kadan ya ragewa qirjinta amma hakan bai hanata ganin bayyanarsa a gabanta. Kamar walqiyar data gifta cikin sararin samaniya da wani irin hanzari da yanayin gushewar hankalin da take ciki bai hanata fahimtarsa ba ya sanya hannunsa ya tare bayanta,abinda ya hanata kaiwa qasa kenan. Numfashi ta sake zuqa da wani irin qarfin daya sabbabawa qirjinta dagawa. Fata take ta samu koda qarin mintuna ne da zata tabbatarwa kanta shine yake tallafe da ita......shine yake riqe da ita,kamar dai a wancan lokacin..... .a wannan filin.......a wannan yanayin da thunder yaso kayar da ita,tana ganin gurin yana ninka duhu a idanunta da ainihin duhun data sanshi dashi,amma still fuskar nan......idanuwan nan masu wani irin kaifi sun juye mata......ranar da lokacin duka a yanzu suna dawo mata kamar yanzu abun ya faru. Hancinta na sheqar qamshinsa fiye da ko yaushe,fiye da yadda ta saba jinsa......da wani irin kusanci,da wani irin taushi,kamar dukka duniya ta tattaru a iya gurinne. Bakinta da zuciyarta na dauke da maganganu......na dauke da abubuwa da yawan gaske da zataso fada.......zataso tayi abubuwa da yawa a gurin,amma tana jin kamar duniyarta tana qarewa,kamar numfashinta na qarshe take zuqa. Qirjinta na qara matsewa da yadda ta tabbatar cikin hannuwansa take a yanxu haka,kuma batajin zata iyayin komai akan hakan "Toi encore toi?......pourqoui toujours toi? (Kai?.....kaine kuma dai......me yasa ko yaushe sai kai?" Ta motsa labbanta tana maganan a hankali muryarta tana kakkaryewa....ganinta na qoqarin dusashewa amma tana qoqarin tsaidashi. Janye idanun nasa yayi da sauri daga kan labbanta yana lumshesu gami da furta "Hasbunallahu wani'imal wakeel" Saboda sosai wani irin abu yayi tasiri cikin jikinsa......tsigar jikinsa yayi mummunar zubawar da banda namijin qoqarin da yayi ba abinda zai hanashi saketa a gurin. Mamakin qarfin halinta yakeyi,yasan akan me take magana,tunda already shi din ya riga yasan wacece........amma a wannan yanayin da take......a abinda yake iya hasashe?. Sake maida dubansa kanta yayi karo na biyu,dabara tana qwace masa na abinda ya kamata yayi. Idanunsa ya sake sauka saman lips dinta,saidai abinda ya gani a karo na biyu ya dakeshi sosai. A dazu a kuma dukka ganinta da yayi a rayuwarshi idan bai manta ba pink lips ne da ita......amma a yanzun lips din canzawa suke suna komawa wani color na daban. Wannana abun daya gani ya sanyashi matsawa da fuskarsa dab da tata zuciyarsa na bugawa a hankali saboda irin kusancin da suka samu me yawan gaske. Idanunta ta lumshe abubuwa biyu suna kutsawa cikin rayuwarta da takejin kamar tana kan gargara,na farko gaurayar numfashinsu guri guda da suka fara musayarsa wanda duk numfashin da take zuqarsa da qyar dinnan yana cakuda da wannan qamshin dai natacce......na biyu kuma wani abune taji ya taso a qirjinta zuwa maqogoronta ya kuma ga mafitar numfashinta na qarshe. "Subhanal malikul quddus" Ya fadi da hanzari saboda kai hancinsa da yayi daidai lips dinta. "Qaseera" Sunan ya doka a tsakiyar kanshi farat daya. Baya manta komai......kaman yadda baya manta dukkan wani training daya samu a yayin horon aikinsa. Dukka wani training nasa yazo ne cakude da personal baiwan da Allah ya bashi. Qwayar idanunta ya sake kalla,a hankali suna sauya launi zuwa kalar yellow daya sake tabbatar masa qaseera tasha. "How comes?" Ya tambayi kansa da kansa idanunsa still a kanta yana jin wani irin yanayi yana ratsashi. Laluben sunanta ya soma yi cikin kansa,don ya zame dole yayi keeping maimaita sunanta don ya samu yadan riqeta conscious. "Akhnaaan" Ya furta sunan da wani irin sauti da zai gaya maka akwai banbancin yare a tsakaninsu. Idanunta da suka lumshe,ruwan hawaye kuma na azaba ya soma jiqa zara zaran eyelashes dinta ta bude a hankali,ya kalli tsakiyar idanunta yana ganin yadda blue pupil dinta ya nutse cikin sclera(farin dake cikin idanu) wanda suka canza zuwa yellow din. Har tsakiyar kanta taji kiran,duk da yadda take kokawa da numfashinta. Da hanzari ya dagata cak wani abu yana dukan qirjinta ya soma takawa da ita ganin dafara kadan saman labbanta da suka koma purple shar. ★"Alhamdulillah". Morsa safiyya ta furta sanda motocinta sukayi parking a muhallin adana motoci na sassanta. Tana shirin daga idanunta taji an bude mata bangaren da take zaune,koda ta daga idanu sai taga Armelle ce wadda ta sadda kanta qasa ta kuma ja da baya riqe da murfin motar. "Armelle......ina kyautata zaton ke kika koyawa falaak shegen son kada nayi nisa.....duka duka fa ko awa daya banyi ba,ba'a kammala karbar lefen bama na taho......" Ga mamakinta gyada kai kawai armelle tayi,sai ta zubawa armelle idanu.......tana hangen wani baqon yanayi a tattare da ita,amma batayi gaggawar tambaya ba,har zuwa sanda ta sako qafafunta waje. A mamakance take bin dukka fuskokinsu da kallo,kusan kowa ta kalla a cikinsu sai taga ba wani sauran kuzari ko fara'a a tattare dashi. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Armelle?......me yake faruwa yau?....tun daga farkon gate nake ganin gidan ba kamar yadda na fita na barshi ba" . A nutse armelle ta saukar da kanta qasa,tana jin wani irin nauyi. Ta yaya matar data sadaukar da dukiyarta girma da matsayin da Allah ya bata domin inganta rayuwarsu da qoqarin sakasu farinciki?,ta yaya ita din zata zama mutum ta farko da zata zo mata da mummunan labarin da tayi imani ba wani labari mafi muni a gurinta da zai biyo bayansa. Sautin murya da kukan falaak shine ya fanshi armelle,abinda ya sanya armelle janyewa baya a hankali,ya kuma saka morsa safiyya waiwaya zuwa ga inda takejin sautin kuka yana fita. Falaak ce......cikin gudu gudu sauri sauri,abinda ya tsinka jinin morsa safiyya kena,ya sanyata mata tarin fargabar data hanata motsawa,har falaak ta qaraso ta kuma zube a jikinta tana rungume morsa safiyya da kyau tana sakin wani sabon kukan daya ratsa har tsakiyar tsokar zuciyar morsa safiyya din. Shafa gadon bayan falaak kawai takeyi,ta gaza tambayarta komai saboda tsoron abinda zataji. Kukan da falaak takeyi kuka ne me tsananin nauyi da ko wanda ke nesa ya jishi yasan yana fita ne direct ne daga ainihin cikin zuciyarta. "Momma.......yaa biftu tasha guba......tasha guba momma.......tana can batasan inda hankalinta yake ba" Falaak ta qarasa fada tana fashewa da sabon kuka. Wani irin dokawa qirjin morsa safiyya yayi da wani kalar tashin hankali. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.......innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta maimaita sau kusan hudu tana qoqarin tattara hankalinta da a yanzu tasan tafi buqatarsa sama da komai. A hankali ta sanya hannu ta zare falaak daga jikinta,sai ta miqa hannun ta damqi tsintsiyar hannun falaak. "Tana ina?". "Sassanta......amma mammina tasa an hana kowa shiga.......daga ita sai bappi ne a ciki" Falaak din ta fadi cikin jin ciwon yadda taso shiga din,amma mammina ta leqo tana gaya mata kukanta zai tta'azzara yanayin da akhnan take ciki,so ta tsaya a baya ta mata addu'a. Ko gane sauran bayanan falaak morsa batayi ba,tasan kawai tace dasu armelle "Ku wuce bakin ayyukanku" Taci gaba da jan hannun falaak suna takawa zuwa shiyyar da zata sadata da sassan akhnan din. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 05* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ________________________________ Shuru kawai parlor din ya dauka,kai kace babu wani sauran me rai dake raye a cikin sa. Cikin wani irin salubabben yanayi sultane ke tsaye gaban akhnan,cikin wani yanayi dashi kansa bazai iya fassarashi ba. Tsahon mintuna kafin ya tsugunna gabanta a hankali,inda take kwance kawai,banbancinta da gawa qalilanne. Hannunsa ya sanya ta qasan duvet din da take lullube dashi ya kamo hannunta,wani irin sanyi tafukan hannun nata sukayi,a hankali ya furta. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". A nutse haisam dake tsaye gefe daya ya daga idanunsa ya zube akan sultane din,dukkan jikinsa yana jin ya masa wani iri. Tun wanzuwarsu a gurin har zuwa kwantar da ita da akayi da bata taimakon farko da yayi gudun kada illar gubar tayi barnar da ba zata gyaru ba,bai sake daga idanunsa ya kalleta ba ko sau daya. Kwata kwata tsaiwarsa a gurin ma ta zame masa kamar lalura ne kawai saboda shigowar me martaba a sanda yake qoqarin fita,shigowar da sultane din kuma yayi,wani yanayi yake ciki da yake buqatar wani a kusa,wanin da zai riqe koda hannunsa ne yaji sassautin abinda yakeji. Yanayin sultane din kadai ya gama bayyanawa haisam rudun da yake ciki,saidai zallar jarumta irin ta basaraken mutum,irin jarumtar dake nasa jinin kenan shima,irin jarumtar kuma da aka sani cikin jinin dukka wanda yake da jibi da SARAUTA. "Muhammad" Sultane ya kirashi muryarsa da tayi laushi can qasa,kansa kawai haisam ya daga yana duban sultane din,saidai kafin yace komai muryar mammina cikin wani irin yanayi ta tunkarosu,sai kuma gata ta iso. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.......ya Allah.......ya Allah ka taimakemu.....ka rufa mana asiri.....kar ka bari wani abu ya samu yarinyar nan" Tayi maganan sanda take wucewa kai tsaye zuwa ga inda akhnan ke kwance numfashinta yana fita da wani irin yanayi da ba haka ya saba fita ba. Gaba daya ta rungumeta cikin jikinta,wani irin kuka me tafe da hawaye ya qwace mata. "Me yasa zaki aikata haka?,me yasa zaki illata kanki akhnan?.....ashe dama baki haqura ba?,dama baki janye kalamanki ba?,dama da gaske kike sai kin sha din........Allah ka taimakamin.......d'iyata ya Allah" Ta qarashe fadi tana sakin wani sabon kukan. A hankali ya lumshe idanunsa sai kuma ya budesu,ya motsa a hankali yana gyara hannun rigarsa. Yana da nufin fita ne daga sassan gaba daya,don dama dole ke tsaye dashi a gurin,shi ya gama nashi part din,ya gama iya abinda zai iya. Bayason kallon drama din matar nan,kanshi shuru yafi buqata,hayaniyarta kuma ya karanci me yawa ce,da gaske damunsa zatayi. "Muhammad........ba wani qarin taimakon da zaka mata?,likita baya kusa........amma yana hanyan isowa" Sultane ya fada cikin wata muguwar karaya yana dauke idanunsa daga kan mammina,kalamanta kuma suna huda qirjinsa,karayar data sanya tausayin sultane din saukar masa lokaci guda. Lallai koda ba'a gaya maka ba zaka fahimci tsantsar soyayyar da sultane yakewa akhnan......sosai haisam ya gama fahimtar irin girman wannan qauna da soyayyar....wadda a ransa yakejin indai har yana son yarinyar har haka,to lallai ba qaramin qoqari yayi ba gurin horata ta hanyar aura mata wanda babban muradinta shine ya janye aura mata shi din. "Akwai........za'a iya bata injection na Atropine" Ya furta a hankali,duk da yana jin kamar bai dace ya buda sirrinsa ba ko yaya ne. Ga duk wanda ya qware a aikin binciken sirri a qasarsu,suna da horo na musamman wajen irin wadannan abubuwa saboda shirin kota kwana da kuma yiwuwar faruwar irin wadannan abubuwa kan daya daga cikinsu ko su kansu,sirrinsu ne da ba wanda ya sani,amma a yanzun da yake kallon tsakiyar idanun sultane din dake jirkice da tarin rudani da abubuwa iri daban daban......yanajin kamar wajibinsa ne ya taimaka.......kwanyarsa kuma na bankado masa daya daga cikin ayoyin qur'ani dake fadin DUK WANDA YA RAYA RAI QWAYA DAYA TAMKAR YA RAYA MUTANE GABA DAYA NE kamar yadda farkon ayar ke fadin idan ka kashe rai daya kaman ka kashe al'umma gaba daya ne. Cikin wani irin gaggawa da zafi sultane ya saki umarnin nemo ruwan allurar ko a ina yake cikin qasa da mintuna goma. *MORSA* Dukka hankalinta dama tunaninta baya tattare da ita sam sam. Kawai dai tana d'aga qafarta tana kuma saukewa ne bisa tabbacin ba zata fadi ba,saboda ko ina na cikin gidan wani shimfidadden terrazzo ne me matuqar kyau da daukan hankali. Kukan falaak kawai ke yawo cikin qirjinta da kunnuwanta,yadda falaak ke kuka yana sake tabata gami da sake motsa wani tashin hankalin a tare da ita. Wai akhnan ta sha guba?......guba dai?,ko daya hankalinta da zuciyarta basu dauka ba basu kuma nutsu ba. Tana tunkaro sassan akhnan din duk wani hadimi dake tsaron gurin wanda mammina ta sanya ya soma buda mata hanya ba tare da tace komai ba,taci gaba da kutsawa falaak na riqe a hannunta. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Shine abinda bakin mammina ke maimaitawa tana riqe da akhnan cikin jikinta. Ko ina ina jikin mammina rawa yake,wani irin tashin hakali yana bayyana kansa saman fuskarta,hatta da hailalan da take ambatawa bakinta rawa kawai yakeyi. A nutse da irin nutsuwar da ba kasafai take barin gangar jikinsa ba ya taka zuwa ga box din da yasa aka shigo masa dashi yanzun na allurar daya buqata din. Kunnuwansa suna kan sautukan mammina da bakinta ya kasa daina maimaita hailalan da takeyi duk da yadda yakeso ya raba kanshi da hayaniyar matar,a daidai lokacin da sultane ke tsaye saman kansu idanunsa akan akhnan din cikin wani irin yanayi me wuyar fassara,ya kasa matsawa,abinda ke yawo cikin kansa kawai shine zantukan mammaina data furta dazu "Kenan dama ita ta shirya poisoning din kanta?" Tambayar da yaketa maimaitawa kansa ita kenan. Tun dazun ya gaza sake cewa komai,yanayinsa wani yanayi me wahalar fassara da kai tsaye ba zaka iya karantar abinda yake ranshi ba. Tas haisam ya zuqe ruwan allurar da nutsuwa,a daidai sanda gaba daya hankalin mammina ke kanshi. Qatotuwar ayar tambaya ta ajiye "Me ya hada malami da iya allura?.....meye hadinsa duka duka da harkar lafiya?" Ta fadi tana nazartarshi da wani irin yanayi da ba lallai ka fahimta ba. Yana fidda iskar data shiga cikin syringe din sallamar morsa safiyya da muryarta ke shaking ta wanzu a falon,abinda ya janye hankalinsu su duka kenan,banda haisam da yaci gaba da abinda yake a qoqarinsa na bata allurar ya kuma fice daga gurin don bawa iyalin daman ci gaba da abinda ya shafesu. "Sheik muhammad" Falaak dake maqale a bayan morsa safiyya ta fadi da sautin da morsa dince kawai ta jishi,saita dan dubi sashen da falaak din ke kalla kafin ta zare idanunta daga kansa. A karon farko data kalleshi cikin yanayinta da ba na nutsuwa ba,ta hangi tarin kamala da kuma nutsuwa a tattare dashi. Wani kallo mammina din ke bin morsa safiyya dashi,saidai kallo ne dake qudundune tsakanin duffan daba kowa zai masa fahimta ta kai tsaye ba. Kai tsaye morsa safiyya ta isa gabansu idanunta akan akhnan dake jikin mammina. Idanunta suna bude,amma ba alamar tana iya gani ne ko gane kowa......ba kuma alamar tana tare dasu a duniyarsu,ba kuma alamar tana fahimtar abinda ke gudana a dakin. "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Abinda morsa safiyya ta maimaita kena har sau uku tana qoqari kada ta rasa nutsuwarta a tare da ita. Hannunta ta miqa a hankali ta aza saman qirjin akhnan. Yanayin bugun zuciyarta da fitar numfashinta sai ya tuna mata WATA RANA WANI YANAYI makamancin wannan......a sanda SAFEENA mahaifiya ga akhnan ke kwance a qirjinta kamar a haka,a sanda a hankali tana furta kalmar shahada har harshenta ya karye,ruhinta kuma ya fita daga gangar jikinta. Jarumtarta ce taji ta karye,hawaye suka taru sosai a idanunta. Mammina dake karance da ita wani boyayyen murmushi ya subuce mata,sai ta saitashi ta kuma dulmiyashi cikin tsakanin kwataccen baqincikin dake saman fuskarta,da wata raunannan murya tace "Momma safiyya......kinga kalar ibtila'in daya samemu?,wallahi ban taba tunanin biftu zata aikata abinda ta furta ba....." Ta qarashe maganan hawaye na gangarowa daga idanunta. A nutse morsa safiyya ta daga idanunta tana azasu saman fuskar mammina. Kafeta tayi da idanun tana mamakin jin kalaman daga bakinta. Dama akhnan din tayi wannan iqirarinne.......dama ta furta hakan?,amma ita ta sani bata shaidawa ITA KO SULTANE ba?,koda bata gaya mata ba me yasa bata gayawa sultane ba?. "Jinin safeena bazai aikata wannan ta'addancin ba ga wani bama bare kanshi" Bakin morsa safiyya ya motsa a hankali ta furta maganan tana duban mammina kai tsaye. Ta fada ne ba tare da tasan ma ya fita daga bakinta zuwa zuciyarta ba. Ta fada ne saboda tana jin hakanne har tsakiyar ranta,ta kuma fada ne saboda kowanne sashe na jikinta yana gaya mata bai yarda da faruwan hakan ba. "Bismillah muhammad" Sultane ya fadi yana yiwa haisam izinin yiwa akhnan allura. Zare idonta mammina din tayi daga kan morsa tana azawa kan haisam. Shi takeso ta yiwa maganar......shi kuma takeso ta dakatar,amma sai ya mata wani irin mugun kwarjinin da taji ba zata iya magana dashi ba,don haka ta maida idanunta kan sultane. "Biftu tana cikin mafi hatsarin yanayi........kalleta sultane,ta yaya wanda bai qware ba a aikin lafiya zai mata allurar da dukkaninmu bamu da tabbaci akan ita ta dace ayi mata?" Ta fada tana nuna tsananin hargitsewarta. "Ni na aminta da muhammad.......na kuma aminta da dukkan komai da duj wani bayanai da zasu fito ta bangarensa" Sultane ya fadi da dukka qwarin gwiwarsa yana duban mammina. "QALUBALENA......SHINE QALUBALENA.....NOTED" ta furta qasan ranta. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Kusan baima ji abinda mammina ke fada ba,don tayi maganan ne qasa qasa a sanda wayarsa shi kuma ta dauki hankalinsa saboda jerin gwanon kira da yake gani daga abdii da maher. Riqe allurar yayi a hannunsa,sai ya waiwayo yana daga qafansa,idanunsa suka saukan kan falaak,abinda ya sanyata yunqurin dauke idanun nata da sauri gabanta yana wani irin mahaukacin faduwa. Bata taba zaton zai ganta ba,tunda ta zauna a gurin ya janye hankalinta gaba daya,duk rudewar da take ciki hakan bai hanata ganin tsantsar kyan da shigar tayi masa ba. Ya sake shammatarta da wani mamakin na ganin cawa shine zaiwa yaa biftu allura.......dame dame ya iya?.....dame dame ya sani har haka?" Take tambayar kanta. Bai barta ta gama janye idanun nata ba ya riqe kallonta da kyau cikin idanunsa yana mata sign din ta fiddo masa hannuwan akhnan. A hankali ta miqe,ta kuma tsugunna gaban akhnan din ta miqa hannu zata zaro hannunta. "Tsaya" Mammina ta fada tana yunqurin yin aikin da falaak din ta taso tayi. Wani irin zafi da bacin rai ne ya sake sauka saman zuciyar safiyya,sai ta saka hannunta gaba daya tana janye akhnan zuwa ga nata jikin,ta kuma kamo hannun falaak ta dora kan na akhnan sannan ta miqe a hankali don bawa haisam space yadda zai mata alluran a sake. Ta sani zamansu a gurin zai sanya ya matse da yawa,daga yawan zancansa da falaak ke mata ta sake samun tabbacin mutum ne shi da bai fiya son cakudayya da mata ba,matsawan zai bashi peace. Miqe dogon hannun akhnan din falaak tayi wanda ke dauke da lafiyayyar fara tas din fatarta me daukan idanu. Fatar da ake kashe ma wani maqudan kasafin kudi duk shekara don ta kasance cikin lafiya da kulawa. A nutse ya qaraso gurin,yakai idanunsa ga hannun,sai ya janye kallonsa da sauri can qasan ransa yana furta. "Astgafirullah......astgafirullah" A yau cikin awanni qalilan yana jin yawan zanubansa a saman kansa. Yana baqinciki da ranar da zata bullo ya zamana yana da wani rubutaccen sabo da yayi,yana kunyar Allah akan haka,yana kunyar ayyukansa na sati suje da wannan rubutaccen sabon a cikinsu. Alama ya sakewa falaak kan ta juya masa iya tsintsiyar hannunta kawai. Ta fahimceshi,iya zaman karatunsu,don haka ta jawo duvet ta kuma lullube hannun akhnan din,ta bar masa inda ya buqata. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE06* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _______________________________ A nutse ya sunkuya ya kuma fara sanya qarfen allurar cikin fatarta yana kallon yadda take shiga a hankali. Idanunta ta juya a hankali sanda tsinin allurar ya caketa tana dagasu zuwa sama inda take iya hangen blurry face dinsa. Yanayin buguwar poison din a jikinta ya sanya take ganin fuskarsa kaman dab da tata......yake kuma sake maida fuskarsa zuwa ga wancan ranar wadda ke lullube da yadin rawanin daya zagaye habarsa dashi. Allurar na shiga tana jin ganinta yana sake daidaita,yanar data rufe ganin nata tana wankewa tana qarawa ganinta qarfi,wannan ya sanya kafin ya gama mata allurar wadda ake turata zuwa jikinta a hankali a hankali ganinta ya dawo tar.......ya kuma bata daman ganin fuskarsa sosai da clear view. Zare allurar yayi,falaak ta sanya hannuwanta dukka biyun ta amsa ta taka zuwa ga dustbin ta sanyata a ciki,wani abu yana motsawa sosai a qirjinta game da haisam. Kusancinsu a yau,yanayin yadda yayi allurar cike da qwarewa da takatsantsan. Ita din dalibar lafiya ce,amma daga yadda yake allurar ta tabbatar akwai qwarewa me tarin yawa a cikin aikinsa. "Zan wuce" Ya fadiwa sultane a taqaice cikin girmamawa. Kai sultane ya jinjina,ya fahimci baya buqatar ci gaba da zama a cikin su,amma yayi masa dukkan abinda ya kamata yayi,ya katse uzurorinsa da dama saboda matsalan iyalinshi......duk da cewa inda haisam zaici gaba da wanzuwa a tare dasu zaiso hakan,to amma kuma bai kamata ya qure kawaicinsa da yakanarsa ba,don haka yace "Na gode qwarai sheikh muhammad......na gode" "Allah ya bata lafiya" Ya furta a tausashe da yanayin daya sanya morsa safiyya sake ganin kimarsa,su ukun kuma sultane morsa safiyya da falaak suka amsa da ameen. Yana takawa don ficewa mammina ta aza idanunta a kansa. Akwai tarin abubuwa da yawa......akwai tarin damarmaki da take dasu ta samesu a yanzun......akwai hanyoyi da suka bude mata da zata iya bata tsakaninsa da sultane......a gabansa takeson yin haka,amma batasan wanne irin kwarjini gareshi ba da ta kasa tsaidashi bare ta fadi Koda abu guda daya a akanshi da zai jefa koda kokwanto da wasiwasi a zuciyar sultane. Sai daya kammala ficewa tas sannan ta maido hankalinta dakin,yanayin takunsa daban yake da takun data saba gani......akwai wani abu me girma da nauyi a cikin character dinsa. Numfashi ya sauke sau uku a jere don ya samu yayi calming kanshi. Abubuwa da yawa......abubuwa da yawa idanunsa da kwanyarsa gaba daya suke hange. Wayarsa ya sake fiddawa,sai ya samu miscall din su abdii ya qaru,wannan karon harda na omar,ga na maher daya tabbatar yana dai ci gaba da jiransa ne. Duka bai kirasu ba,don bayason dogon magana ko dogon bayani,omari kawai zaifi fahimtarsa kaman yadda aka saba,don haka shi din ya kira kai tsaye. Bugu daya ya daga da cikakkiyar sallama,haisam ya amsa masa can qasan maqoshinsa. "Kazo ka dauke yaron nan abdii,ya sakani a gaba da tashin hankali,wai yayita kiranka baka daga ba,maher ma kuma yacemin ya kasa samunka,gashinan zaune kaman zai fashemin da kuka?". "Ka cewa maher na daga fitan sai gobe......ka gayawa abdii ina lafiya,amma yau kam duka bana buqatar shashancin nan nasa........please ka karbi mota gurin salana kazo ka daukeni". "Yanzu?" Ido ya lumshe yana girgiza kai. "No.....zanyi wanka ne" "Amma maher yacemin ka shirya har ka fito kuma". "Eh.....wani dalili ya sanyani komawar". Ya furta very calm,yana fatan shima omari din kada yaja maganan da tsaho. " Xan shigo palace kenan da motar?". "Idan tunaninka ya kwance omar zaka iyayin hakan" Ya amsa masa a gajarce kawai yana kashe wayar,sannan ya sanyata a aljihunsa yana ci gaba da komawa sashensa na cikin gidan. "Astagfirullah" Yaketa maimaitawa sanda yake fidda kayan jikinsa,kayan da bai taba tunanin akwai wani abu da zai sanyashi dawowa nan kurkusa ya canzasu ba. Ruwa me matuqar dumi yana sauka saman kansa idanunsa na runtse yana tambayar kansa. "Why?,me yasa ko yaushe sai ita?" Ya tambayi kansa yana jin wani abu yana bin sassaj jikinsa da ya sanya jikinsa wani mugun mutuwa tubus. Zai iya rantsuwa da Allah hannunsa bai taba kaiwa jikin kowacce d'iya mace ba. Yana bala'in kame jinsa ganinsa dama hannuwansa harda qafafunsa daga dukkan wani abu irin wannan. Amma me yasa ta zama mace ta farko da gangar jikinsu keta haduwa haka?,ba daya ba ba biyu ba?,kusan sau uku kenan,kuma dukka ta dalilin wani abu?. Zuciyarsa tana yin sanyi idan ya tuna komai bai faru bane akan son rai ko son zuciyarsa,ya faru ne kan akasi kawai irin na dan adam. A gurguje ya shirya,don akwai maganganun da yakeso yayi da omar masu muhimmanci. Ya taka a nutse tun daga sassansa har zuwa ficewarsa daga gidan,yana takawa a nutsensa har zuwa inda suka saba tsaida mota su jirashi. Tun daga nesa da omar ya hangoshi ya bude masa gaban motar kusa dashi,don yadda haisam din ya bashi command ya sanya baima sa salana ya tuqoshi ba,kawai sai ya karbi motar. Tab ne a gabansa wanda yake video call shi da maleek da naseeb. Naseeb din suna guri daya da maleek ne saboda ziyara daya kai masa. Duk da yadda aiki ya banbamta musu guraren rayuwa,amma hakan baya hanasu kaiwa juna ziyara lokaci bayan lokaci. Kowa a cikinsu yana iya ziyartar dan uwansa a duk inda yake,kafin lokacin da suke haduwa ta lokaci guda dukkaninsu yayi. Da tattausar muryarsa yayi sallama yana sako gangar jikinsa cikin motar,sam hankalinsa baya kan tab din,baima lura da ita ba,yayin da idanun maleek da naseeb da sukayi shuru suna son surprising nasa yake kansa cikin murmushin nan dake cike da soyayyar juna. Hannu ya bawa omari sukayi musabaha kafin ya zame hannun yana azashi saman qirjinsa,sai kuma ya sake zame hannun yana neman madannin da zai bashi daman kwantar da kujerar yadda zai samu daman yin relaxing sosai. Tsaiwa kawai yayi yana kallon screen din,yayin da naseeb ya saki dariya sosai,maleek na tayashi ta hanyar murmushi kasancewar shima din ba ma'abocin yin dariya bane kaman dai haisam din. "Mr lowering gaze......wai meye hakan?" Maleek ya tambaya da yanayin sarauta cikin jininsa shima kamar dai haisam din. Kai kawai haisam ya girgiza murmushi yana qwace masa,omari ya shammaceshi,hakanan wannan karon yaji kunya ta yadda aikin gaba daya ya shagaltar dashi daga barin nemansu. "Wanne irin aiki ne ya shagaltar dakai haka?.....na dauka wata me rabon muka samu data dauke mana hankalin sheikh dinmu?" Maleek ya sake fadi yana murmushi. "Ka sani ko ya samu nasarar kammala aikinsa da kuma gwagwgwabar kyautar princess of agadez?" Naseeb ya fada yana dariyar tsokana. Tsokana dabi'ar naseeb ce,har sun riga sun saba da haka,amma wannan karon maganansa ta yiwa haisam girma tare da maido masa mode da dabi'u dukka na akhnan daya sani,da sauri ya furta. "A'uzubillah......a'uzubillah" Gami da miqa hannu ya kashe gaba daya karatun qur'anin dake tashi can qasa ta speakers din motar. Harara ya fara watsawa omari........ya tabbatar akwai wata magana da suka fara dasu naseeb din,sai omar din ya fuske gami da mazewa yaqi yarda ya kalleshi,duk da yadda yakejin nauyin idanuwansa kamar kullum "Don Allah......na roqeka wannan maganan ya fita a bakinka naseeb koda wasa kake......ban shirya wasa da zazzafar wuta ba" Ya qarashe maganan yana hade tafukan hannayensa biyun guri guda alamun roqo. Dukkansu dariya ya qwace musu,maleek ya jinjina kai sannan yace. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Me kake tsoro obbo?......There's no woman on earth you can't deal with". Kansa ya jinjina a hankali yana kadashi. Ya lumshe idonsa a nutse sannan ya bude yana motsa labbansa da yanayin daya tabbatar musu akwai gajiya a tattare dashi,walau ta jiki kota tunani. "I want peace always.......am not interested in drama". Maganansa ya sanya omari da naseeb sakin qaramar dariya,yayin da maleek yayi murmushi. Kasantuwarsu daga gidan sarauta dukkansu shida haisam......hakan ya sanya akwai kamanceceniya na wasu dabi'u a tsakaninsu,don haka duk cikinsu bakwai din yafi kowa fahimtar haisam,saidai yafi haisam din mu'amala da 'yammata duk da cewa tsaftatacciyar mu'amala ce da yake sanya ran zaben matar aure a cikinsu. Kai ya gyada yana duban haisam din "Kaima kasan ka taro match......tunda ka kayar da ita a gasa cikin yankinta". Kansa ya juya kadan,sai yanzu yanayin kallon da take masa ya dawo masa. Ya sani,ya kuma fahimta tanason fahimtar cewa shine abokin takararta ne,duk wani motsi da acting nata ya nuna masa hakan,saidai shi kuma sam bazai taba bata wannan damar ta gano komai ba. Ba drama ko wasa bane ya kawoshi yankinsu,ya kuma kawoshi masarautarsu,yazo ne kawai ya kammala wani aiki ya fice ya koma zuwa qasarsu. Aiki ne da zai tabbatar da zaman lafiyan iyayensa......zaman lafiyar qasarsa......da kuma zaman lafiyar yankinsa da qabilarsa. Akan wadannan abubuwan daya lissafa ba shakka zai iya sadaukar da komai,shi yasa yakeji a cikin jikinsa da jininsa......ya shirya tunkarar komai don cimma nasara,musamman a yanzun da yake ganin wasu kebantattu kuma baqi sabbin abubuwa suna gilmawa ta gabanshi. Hira sukai sosai irin ta abokai shaqiqai da suka saba da juna,hirar har takai sai da aka tabo su mutallab,dukkansu suka hadu cikin video call din cikin yanayi na kewar juna,duk da haisam din kusan yayi relaxing ne cikin kujerar,sai daya biyu kawai yake jefa bakinsa yayi murmushi a wuce gurin. Sun saba da irin dabi'ar nan tasa,musamman a lokutan da bayason dogon magana,suma kuma sun iya tafi da 'yan miskilancinsa. *AGADEZ PALACE* Dukkaninsu hankalinsu idanunsu dama numfashinsu dukka sun tsaidashi ne akan doctor hadizatu data kasance qwararriyar likitar dake aiki cikin masarautar,qarqashin babban clinic na masarautar da yake aiki don duba marasa lafiya na cikin gida da ciwukansu basuyi girma da yawa ba. A hankali ta zare allurar da kafin ta kammalata ta jiqe da gumi,allurar da tayi ta cikin cannula cikin takatsantsan da nutsuwa. "Alhamdulillah" Ta fada tana goge fuskarta da handkerchief tana kuma kallon yadda gumi ya fara jiqa goshin akhnan. Falaak ce ta sanya tattausan handkerchief din da aka kawo cikin tarkacen da aka ajiye a gurin ta soma share mata goshinta,yayin da aisa ta dauki remote tana dan qara qarfin Ac din dakin. "Anyi nasara gubar ta fara sakinta in sha Allah,ga alamu nan.......amma tabbas lallai duk wanda ya kawo idea din mata allurar farko ba qaramin sanin abinda yakeyi yayi ba......allurar ta taimaka qwarai wajen saurin saukar da tasirin allurar da akayi mata yanzu.......sannna ta dakatar da harbuwar gubar zuwa sassan da idan ta tabasu to xai wahala a samu rai da rayuwa,kamar hanta qoda hunhu da kuma zuciya" Sosai wani irin kima da qaunar haisam ta sake samun kyakkyawan gurbi a zuciyar sultane. Da gaske muhammad din ya zama wani sashe me muhimmanci a tattare dashi raywarsa dama ta iyalinsa. Baya tunanin inda bai wanzu a gurin ba akhnan zata kai wannan labarin da akeyi a yanzu......lallai yana sanya rai yana kuma kyautata zaton ubangiji ya laluba cikin tulin tarin ayyukansa ya aiko masa dashi ne kawai. "Zata iya bacci har na awa kusan uku ko hudu,kada a tasheta,a barta ta huta sosai......idan ta farka kada ace mata komai,ku jira abinda zata soma cewa,sai a sanar dani da zarar ta farka,so samu gurin ya zama so quite" Kai morsa ke jinjinawa tana kuma fahimtar bayanan doctor hadizatu sosai. "Ina ganin ya kamata abarta hakanan ta huta......." "Aisa........falaak.......shehnaz.......ku zauna tare da 'yar uwarku,ku bata duk kulawar data dace har zuwa sanda zata farka". Morsa safiyya ta furta da wata kalar izza da take bayyana kanta da kanta a tattare da ita,tayi kuma maganar tata kanta tsaye ba tare data dubi koda shiyyar da mammina ke tsaye ba,wadda ke shirin tsara yadda za'ayi ta yadda zai dace da plan dinta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 07* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ "Hakan yayi.....don Allah.....wannan din ba qaramin abu bane da wasa ko shashanci zai shigo ciki,ku kula da ita da kyau,duk wani motsi da zai zamana kuna buqatar wani kuna iya kira" Nannie da tunda tazo ta samu guri ta zauna,gwiwarta tayi wani irin sanyi da bata taba jin tayi makamancinsa ba. Hankali cikin kuma wani irin salo me kama da gilmawar walqiya ta shanye duk wani mamaki da bacin rai daya saukar mata na katsalandan wa umarninta da kuma hambarar da iyakokin da take qoqarin shatawa. "Gaskiya ne.....don a wannan yanayin dole ku sake ninka kulawarku a kanta......kada sakacin da mukayi a baya ya sake maimaituwa......kada kuyi nesa da ita don Allah koda na sakanni ne" Mammina din ta fada tana sanya gefan tattausan mayafinta tana dauke hawayen daya gangaro mata. A nutse morsa safiyya ta waiwayo ta kuma aje mata wani irin kallo kafin ta dauke kai. Har yanzu zuciyarta bata aminta ba bata kuma tsaya guri daya ba......amma kuma wani sashen na zuciyarta na gaya mata. "Inda mammina ce.....inda mammina nada plan na kashe akhnan da bata kawo war haka a raye ba,bata kasheta a sanda take da cikakken dama a kanta ba sai yanzu data mallaki hankalin kanta?. Kusan dukkansu morsa safiyya mammina nannie da kuma sultane suke fitowa daga bangaren akhnan din. Ba wani a cikinsu da yake da kuzarin yin magana a cikinsu,duk kuwa da cewa kowa magana ne fal bakinsa. "Ina gayyatarku zaman cin abinci gobe da daddare" Abinda sultane kawai ya fada kenan,abinda kuma yake gaya musu a yau bashi da muradin ganin kowa,sai yayi gaba yana ci gaba da takawa don isa farfajiyar da zata sadashi da hadimansa daya tabbatar suna nan tsaye suna jiransa a inda ya dakatar dasu. Morsa safiyya ce ta soma yin gaba ba tare data waiwayo ko tace da kowa komai ba. Nannie ta bita da kallo kafin ta maido dubanta kan mammina. "Har yanzu na kasa aminta da cewa biftu ce da kanta ta dauki guba tasha saboda qiyayyar auren wani?". Kaman dazun,hawaye masu yawa ta tsane da gefen mayafinta daya kasance cotton. "Ni kaina Nannie banda an gaya min dama a jiya da magabatan hakeem suka iso da dukiyar aure ta fadi saita sha gubar,a gaban aisa da shehnaz da sauran hadimanta,wanda duka sai dana bisu daya bayan daya na tabbatar ta fada din......to amma kuskuren da nayi shine dana dauka abun shirme ne kawai,bawai tana fada bane da gaske.......ashe da gasken take,don Allah ku yafemin Nannie.......ki bawa me martaba haquri,a yau a karon farko yarda da tabbaci da ya bani akan d'iyarsa.....a karon farko na kasa.......na gaza,nayi sakacin barin magana irin wannan har taso tayi sanadin d'iyarsa tilo" Ta qarasa fada tana kama dukkan hannuwan Nannie ta riqe cikin nata tana sakin kuka me qaramin sauti. Sosai abun ya taba Nannie,bata taba ganin soyayya irinta mammina da akhnan nan,saita riqe hannun mammina din sosai itama. "Haba zaituna?......meye haka kikeyi?,kin manta matsayinki cikin gidan nan kuwa?,idan wani cikin hadimai yazo wucewa fa?". "Na cancanci inyi wannan kukan Nannie,ku barni nayi ko zan daina jin kasawata akan akhnan" "Baki kasa ba zaituna......shekara nawa take qarqashin kulawarki?,daidai da mummunan zazzabi bata taba yinsa ba,duk mutumin da zai kwashi wannan shekarun.....dondai kwana daya faruwar abinda baida ikon tsaida faruwarsa bai kamata a tuhumeshi ko ya zama abun tuhuma ba akai". Ta fada da sigar lallashi. "Allah yasa morsa safiyya ta fahimci hakan.....Allah yasa ta gane haka" Ya fada muryarta tana rawa. "Zata fahimta muddin ita din ba butulu bace" Nannie ta amsa da dukkan confidence dinta. Murmushi ta saki sirrintacce a sanda suka juyawa juna baya. Nannie tayi hanyar da zata sadata da sassanta,itama kuma ta juya son isa ga nata sassan. ~ "Idan har tasan tayi iqirarin shan wani abu da zai iya cutar da lafiyarta......idan har tasan halinta na shekara da shekaru a matsayinya na wadda ta raineta.....idan har ya kasance ta kauda kai daga dukkan wannan ba tare data shaidawa kowa ba koda barazana ne ayi don dakatar da afkuwar abun.......lallai akwai babbar ayar tambaya a ciki.......akwai wani shiryayyen mission da nake iya sansanowa......" Omari yayi maganan yana qanqance idanunsa ciki,yana jin kuma wani abu yana jan hankalinsa sosai akan maganar. "Omar" Haisam ya kira sunansa da alamun gajiya cikin muryarsa. "Ba wannan maganan nakeso ka maida tunaninka akai ba......duk abinda mukaji......ko muka gani haka zamu barshi a yadda muka sameshi.......ba saboda wannan matsalar muka shigo masarautarsu ba.......ba qididdigar alaqar dake tsakanin junansu mukazo tantancewa ba......abinda ya kawomu kawai shine neman gujajjen me lafin da yaso bata mana alaqar diplomatic na qasashenmu........let's prioritize the mission" Ya furta da seriousness dinsa. A nutse omari ya daga kai ya dubeshi. Ba tun yau ba,ya sani cewa mutum ne bame yawan shiga sharafin wasu ba,amma kuma hakan ba yana nufin bashi da tausayi ko taimako ba...... Yana da wata irin zuciya me taushi,duk da cewa wasu lokutan yana da kafiya da kuma zafin rai akan abinda yake gaskiyarshi kenan,amma a nan bai dauka zai wofantar da al'amarin da a yanzun da kanshi ya gama zube masa lissafin yadda hasashensa yake iya hangen komai ba. "Amma.......what about your....." "Ban hada maka zancansu dana aikinmu ba don ya zamana zamu sakashi lallai lallai cikin ayyukanmu ba......na hada maka ne don ka fahimta,ka kuma gane hasashena yayi daidai na sanya matar ta zama cikin sahun mutane na gaba gaba da zamu tsananta sanya idanu a kanta ita da duk wanda ya rab'eta?.......that's it" Idanu suka zubawa juna shida omari din,kafin omari ya janye nasa kallon bayan wasu sakanni. "Amma ka sani.......ko akwai wani dalili da Allah ya aikomu a irin wannan lokacin cikin gidan?......ba lallai ya zamana dalilin kawai shine ceto martabar Ethiopia kadai ba........." "Da kuma ceto rayuwar halitta mafi soyuwa a gareni MOTII.....kammaluwar aikin nan shine zai bani guarantee na safety din motii,bama motii kadai ba.....harda nanay dama duk wanda ya kwana ya tashi cikin aba jifar palace" Ya qarashe maganan da wani irin yanayi a muryarsa da idanunsa. "Bazan hanaka ba taimako ba idan ka shirya yi......amma dole ya zamana bayan aikinmu ne bawai a ciki ko a gaban aikinmu ba........take heed.........akwai wasu mutane cikin masarautar da zargina ya soma sauka a kansu......akwai wasu mutane da bansan yawan adadinsu ba a masarautar da nake da tabbacin suna da alaqa me qarfi da oromo.......bansan su nawa bane,amma mutum biyu daga ciki masu suna iri DAYA sune suspect dina na farko. Tabbas akwai alaqa tsakaninsu da matar......saidai bansan iya zurfin alaqar da adadinta ba......sannan su nawa ne masu jin yaren?,tana cikin masu jin yaren ko wata qabila ce ita daban cikin Ethiopia bawai oromo ba?,akwak.kebantaccen dakin dakin daya zama na musamman kuma mallakarta ita daya,ta yaya zamu kai ga cikinsa?.......ta yaya hakan zai taimakemu zuwa ga inda ainihin me laifinmu yake?,.....wadannan sune abubuwan da zamuyi aiki akai yanzu.........salawi da beeno dukkaninsu zasu tattaro su dawo daga garuruwan da aka turasu,zasu kama haya cikin daya daga cikin gidajen dake daura da masarautar.......sannan kaima......" Sai kuma ya dakata kadan. "Nima zan antayo cikin gidan?" Kai ya girgiza a nutse. "Bana tunanin zaka hau wannan position din,saboda tunaninka da daidaiton da nake da buqata a gareka kaman yayi low,baikai adadin da nake buqata ba". Qaramin dariya omari ya saki,ya sani haisam ya fadi hakane saboda ya shigo da batun akhnan da case din cikin gidan cikin aikinsu. "A duk sanda ka shirya kawoni kusa da kai ina maraba" Ya furta yana miqa hannu gami da tashin motar. Dubansa yayi kaman zai tambayeshi sai kuma ya fasa,omari din ya fahimci haka,yasan kuma tunda yayi hakan miskilancinsa bazai bari ne ya tambaya din ba,sai ya buda baki a nutse. "Zan kaika wani guri......ina sanyan ran zaka samu kalar yanayin da kake buqata" Be amsa masa ba,saidai ya jawo system dinsa da yasa omari din ya fito masa da ita,ya azata saman cinyarsa ya kunnata sannna ya fara shigar da bayanan da yake da buqata. Ganin haka sai omari din ya maida karatunsa yana sanyashi a matsakaicin sautin da bazai dameshi ba. ★★★ Idanunta ta sake maidawa ta lumshe gami da jinginar da kanta da fuskar gadon da take kai. Kusan dukkan wanda ya shigo tsakanin Nannie.....mammina......aisa...shehnaz.....harma da falaak maganganunsu dukka akan abu guda daya suke maimaitawa. Abu guda dayan da itadai batasan dashi ba,batasan kuma da zamansa,batasan ma yaushe ya faru ba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Abu daya ta sani tasan kuma ta furta,ZATA SHA GUBA wanda bayan janyeta da shehnaz da aisa sukayi zuwa daki maganganunsu sun sanya wannan kalamin ya zagwanye daga zuciyarta tas ya fice,taji kuma bata da wani sauran marmari ko niyyar aikata komai,ta kuma kwanta ranta ba komai face zallar zugi radadi da fatan janyewar sultane daga dukkan qudurinsa da yasha alwashi akai......ta kuma kwana ne da zazzabin data dinga jinsa sosai cikin jikinta,baya ga haka ba wani abu data wayi gari dashi a ranta a ranar. Abu na biyu birra.....birra na cikin amintattunta da tayi imanin koda zabin a kashe akhnan ko a kashe birra dinne.......yarinyar zata zabi mutuwarta akan wani abu da zai taba lafiyar akhnan din. Uwa uba kuma ma shine,a gabanta birra ta gama hada komai suka fita a tare. Ba wai tana wani guri bane na daban aka hada mata tea din,da normal ruwan da ta saba amfani dashi cikin gidanne,to amma yaya akayi aka samu wani abu ya shiga har cikin tea din dabai dauki tsahon lokaci ba daga hadashi har zuwa shanyeshi?. Wani irin daurewa kwanyarta kawai take sakeyi da wani dogon tunanin da bata hangi hanyar da zata samu tarin tambayoyin dake sarqafe da ita ba,uwa uba ba wanda ya tsaya ya saurari komai daga bakinta,sai tarin fada da nuna mata kuskurenta da kowa yake qoqarin yi. Abinda yafi daga mata hankali rashin ganin koda gilmawar sultane tun jiya kawo yau din,ba kuma wanda ya mata maganarsa ko yace komai a kansa. Abu irin wannan idan har zai sameta ta tabbatar sultane zai iya zama mutum na farko da zai kasance tare da ita bayan mammina.........idan bai zama na farko ba saboda tsananin kulawa da damuwa da al'amuranta da mammina takeyi to lallai babu abinda zai hanashi kasancewa na uku. Itama batayi yunqurin kare kanta ba ko kadan,saboda batasan ma idan ta bude bakinta me zata ce ba?. Da wannan kalar tunanin birra ta nemi izinin shigowa dakin,ta kuma murda handle din ta turo qofar da sallama ta shigo. Idanunta ta ware a hankali tana dubanta,a nazarin farko ta karanci zallar tashin hankali da rudanin dake kwance saman fuskar yarinyar. Ko digo a ranta bataji akwai wani mugun nufi da zai fito daga bangaren birra din ba,muryarta can qasa tace. "Ranki ya dade......lokacin wankanki yayi.....zan shiga na hada ruwan wankan,nace ko zaki kasance tare dani a yayin hada ruwan?" Ta tambaya jikinta yana rawa da zaka iya hanga idan ka zuba mata idanu. Zare dubanta akhnan tayi daga dubanta,muryarta can qasa ta bata umarni nakai tsaye. "Shiga ki hada" Kawai tace da ita. Ba musu ko saba umarni tsakaninsu daga gurin uwar gijiyarsu,hakan yana daidai da aikata laifi me girma,don haka ta taka tana wucewa shiyyar da bandakin yake. Bata jima ba ta fito dauke da bathrobe me azabar laushu fara qal da takalman wanka,wanda kusan duk bayan kwanaki ake sauya mata su,kuma idan aka fiddasu ba'a dawowa dasu sun gama aiki kenan. Tsugunnawa tayi ta ajiye mata takalman,ta ajiye rigar a gefanta sannan ta taka a hankali ta nufi wani sashen na daban inda facial care products dinta suke da tame using wasu kafin ta shiga wanka wasu bayan ta figo ta dauko box dinsu gaba daya don sauqaqe mata tashi zuwa inda ta saba zama tayi amfani dasu. Saidai tana takowa ta mata alama da hannu ta juya ta maidasu. Da taimakon birra din ta shirya cikin wasu sauqaqan English wears riga da skirt. Sai fuskarta tayi wani fayau,ramar da tayi tsakanin jiya da yau ta fito sosai kamar wadda ta shekara tana ciwo. Skin cream perfume dinga ta matsa tana shafawa a hannunta. Idanunta suka sauka daidai inda yayi mata allurar a jiya wanda ya bada wani dan siririn tabo kaman an diga baqin lalle a gurin saboda zafin allurar. Yatsanta takai ta shafa gurin,tana son tunawa,yayin da tunawar tazo mata da wani irin mummunan faduwar gaba. Stool din dake bayanta ta koma ta zauna akai tana tuna komai..... zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 08* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _____________________________ "Shine......shine" Abinda zuciyarta ta maimaita mata har sau biyu,a cikin jikinta ma still tana jin shine. "Comment est-ce possible?(yaya hakan zai kasance?)" Ta tambayi kanta tana juya abun. A hankali kuma sai wani tunanuka suka soma cushe kan nata,ta gaza daidaita tunanin ya zauna da kyau a kanta har ya gamsar da ita. Ta yaya malamin da baisan komai ba sai karantarwa zai samu irin wannan experience din na sarrafa dawakai?......har ace ya tsere mata?,ya kere iyawarta ita da aka haifeta cikin sarauta tsahon dukka rayuwarta?. Yaushe ya mallaki wayewa?,yaushe ya mallaki qwarewa da sanin makamar sarrafa halittu masu yawan sarrafawa irin dawakai?. Kai ta girgiza a hankali,ba wani abu daya bata gamsuwa akan abun,illa abu biyu rak da tabbas suke sanyata takejin KAMAE SHINE. qamshinsa da kuma wadannan idanun da batasan wani ido a duniya da takejin wani na daban a kansa ba. Miqewa tayi tana yanke tunanin,saboda samun tabbacin da tayi tana dab da zaluqo ko waye. Tasan tamim zaiyi dukkan abinda zaiyi don tabbatar da wannan,tana jin ya kamata ta aje hankalinta akan wannna na wani lokaci,ta fara fuskantar yadda zata yakice Hakeem daga rayuwarta kwata kwata. "Mammina ta iso......tana dakunan qasa,tana so tayi magana dake" Birra ta fadi kanta a qasa,har yanzu taqi hada idanu da akhnan. Kai kawai ta daga,ta sanya hannu tana daukan wani dan qaramin scarf ta dora saman kanta bawai don kwalliya ba,amma sai ya zame mata tamkar ado ya sake qawata fuskar nan take dake da wani irin sirrintaccen kyau. Cikin mutuwa da rashin qwari jiki take saukowa. A dazun tana kwance mammina ta shigo,bata bude idanu sunyi magana baki da baki ba,amma kunnuwanta na iya sauraren fadan da taji tana yi harta gama ta fice. Ko a yanzun tana tsaye ne kawai cikin falon da ba kowa daga ita sai mammina. Wani yanayi take hanga saman fuskar mammina da bata taba ganin irinsa ba. "Ways kika aika ya siyo miki gubar da kika durawa kanki?" Ta tambayeta a kausashe,da kuma wani bayyanannen fushi da ya raunata zuciyar akhnan din karon farko. "Kema mammina......kema kin yarda ni da kaina nasha guba?" Ta motsa labbanta tana fadi da wani yanayin karaya daya tara ruwan hawaye cikin qwayar idanunta duk da basukai ga zubowa ba. Rauninta ya bayyana sosai,raunin da ba wanda ya sanshi ko ya taba ganinsa,daga ita sai sultane,sai kuma morsa safiyya data kasance ta ukunsu. "Bansha komai ba mammina......ki yarda dani,banda tea da nasha a lokacin,dana kammala kuma nayi nufin amsa kiran da kikayimin.....a hanya abun ya faru dani". Ta sani,wannan itace amsar da zata bata idan ta matsa,saidai kuma bata shirya amsar wadannan bayanan ba.....bata kuma shirya bata ko qofa guda daya da zata fidda bayanan zuwa ga wani ba ko kuma wani guri ba......don wannan shine makaminta......sassauqar hanyar kuma da zata sadata zuwa ga cikar burinta MATAKIN FARKO. Dubanta takeyi ba wani sassauci a tattare da ita. "Yaushe kika fara yanke hukuncin shirya qaryawa mamanki biftu?.......kin manta da iqirarin da kikayi da kanki?,kin manta cewa keda bakinki kika ce sai kinsha?......okay.....yanzu kina son qaryatawa kenan?,kinason nunawa duniya da abokan adawar mahaifinki cewa sultane ya gaza bawa gudar d'iyarsa kariya?......idan ya gaza bawa gidansa cikakken kariya da tsaro hakan yana nufin baya iya mulkar jama'arsa al'ummarsa da talakawansa yadda ya dace,tunda har aka iya keta dukkan wani shinge da tsaro aka zuba gubawa gudar diyarsa......hakan yana nuna shi gajiyayye ne kasasheshe ne da bazai iya tabuka komai ba.......to kiji da kyau......muddin hakan ta faru KEMA KIN RASA TAKI DARAJAR.....duniya zataci gaba da kallon mahaifinki ne a matsayin uba me rauni maras alfanu. Tsaye kawai tayi tana duban mammina......yadda a yau din mamminan ta gaza fahimtarta,yadda ta gaza mata uzuri......ta gaza fahimtarta. Mammina tafi kowa saninta a duniya,tafi kowa fahimtar halayenta,tafi kowa sanin abinda zata aikata da wanda ba zata aikata ba. Tafi kowa sanin qarya sam bata burgeta,qarya bata bata sha'awa......qaryar kuma tana cikin jerin sahun abu na qarshe da bata iya aikatawa a rayuwarta. Tafi ganewa ta tunkari tsanani ko sauqi da dukkan gaskiyarta,tafi ganewa bayyanar da zahirin abinda yake rai da zuciyarta a madadin yin qaryar. "Koma me kika aikata bazai canza sunanki daga sunan DIYATA ba,kuma hakan bazai karyamin gwiwa ba,bazai kuma hanani tsaiwa don samar miki da masalar rayuwarki da abinda rai da zuciyarki suke muradi ba". Mammina tayi maganan a sanda take qofar qarshe na fita daga falon. Hanyar data wuce akhnan take bi da kallo. Koda mammina bata fita ba,bata da wani sauran energy da zatayi mata wani bayani,ta gama bayaninta tana ji har ranta yarda da ita ko takurawa wani ya aminta da ita bai zama dole ba. Wani shu'umin murmushi ne yake fita saman fuskarta,tana kuma takawa zuwa qaramar fadar sultane daya shirya zama dasu a wannan lokacin cike da cikakken qwarin gwiwar lallai zata fito da nasararta. Taji dadi qwarai da yadda maganganunta suka dakushe yunqurin akhnan na bayyana gaskiyarta. A yanzun ba gaskiyar akhnan take da buqata ba.........shurunta shi tafi buqata,shirunta shine tsani na farko kuma hanya mafi sauqi da zata sadata da muradanta. Tun daga qofar farko ta samu sanarwar yana tattaunawa ne da wazirinsa alhaji ahmadu sallau,da alama kuma ba dashi kadai yake ganawa ba,don haka ta zagaya ta wani daki na musamman dake liqe da gurin wanda aka tanadeshi don zaman jiran sultane din irin haka. Duk bayan daqiqa saita duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta,tana sane ta rage wasu daqiqu masu yawa daga lokacin da sultane yace zasuyi zaman,saboda tsarinta da plan dinta yafi tafiya a daidai,sai kuma tazo ta cimmasa da baqi. Qaramin tsaki taja sanda takejin fitar baqin sultane,ta miqe a hankali ta buda qofar da zata sadata da ainihin falon faadar tana sanya qafafunta da zummar jiransa. Ko yaya ne tana lissafin akwai mintunan da zasu bata daman kebancewa dashi kafin zuwan kowa,saidai kuma tana zama sallamar morsa safiyya wadda suke takowa tare da sultane ta yanke mata dukkan wani hanzari da takeyi. Fes momma ta ganta,amma saita dauke idanunta daga kanta tana tattara hankalinta ga sultane cikin sakin sassanyan murmushin da tayishi ne saboda jifan tsuntsu biyu da dutse daya. Cak wani abu yayi mata tsaye a qirji,daidai sanda idanunta ke sauka akan morsa safiyya din,da alama wata magana sukeyi da sultane din da batasan meye suke tattaunawa ba. Iska sosai ta furzar daga bakinta tana qoqarin daidaita numfashinta da kuma sanyaya zuciyarta da takejin ta matse sosai a qirjinta,sannan tattaro dukkan wani yanayi da zai iya baka cewar cikin nutsuwarta da walwalarta take ta dora saman fuskarta. "Marhaba......barka da shigowa zaki gwarzon mazaje" Ta furta da wannan salon na girmamawa tana miqewa tsaye,sanda morsa safiyya ke qoqarin kwashe masa pillows din saman kujerar da zai zauna a kai,abinda ya sake dasa wani kakkaifan mashi saman zuciyarsa sanda morsa safiyya ke neman gurin zama daura dashi ta zauna da wannan nutsuwar da basarwar tata. Yanayi da nature dinta guda daya dake taba mammina kenan......tana da fada......tana da zafin zuciya,amma tana da wata kalar kamewa da idan bataso ba ko fuskarka ba zata kalla ba bare tasan da wanzuwarka a wajen. Wani lokaci wannan dabi'artata......wannan halin nata yana ma mammina kwarjini sosai. "Barkanki giwar agadez" Ya fadi da yanayin da yasa mammina alfahari sosai,duk da fuskarsa bata nuna ainihin abinda bakinsa ya fada. "Ina fatan ka yini cikin aminci da qoshin lafiya?" "Alhamdulillah.....kema ina miki fatan hakan" Anzo gurin da takeso,tambayar kuma tazo mata daidai,saita rusunar da idanunta cikin wani yanayi. "Ba wannan nutsuwar sam a tare dani......banajin wani aminci ko kwanciyar hankali,tun daga sanda na fahimci akhnan tasha guba dalilin auren dole" Ta furta da wata irin rusunanniyar murya. Shuru sultane din yayi yana dubanta,kamar yadda morsa safiyya ta dakata da komai,ta kuma zuba idanunta akan mammina din. "Ban zaci abun zaikai har haka ba......ban dauka da gaske take zata sha ba me martaba......." "Wannan hujjar kika riqe kika qi shaidawa kowa iqirarinta?......" Muryar morsa safiyya da dukka qoqaromta na hadiye abinda yake ranta ya kasa cimma gaci. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Yadda tayi tambayar da wani irin yanayi cikin muryarta.......yadda sautin ya fita yaja hankalin sultane da mammina,harma da nanay dake sanyo kai gurin ba tare da kowa ya ankara da shigowarta ba. Kai tsaye,kuma ido cikin ido morsa safiyya ke duban mammina. "Indai har da gaske ne iqirarin da kikeyi.....ke kika raini biftu.....kinsan kowanne hali da dabi'a nata.....kinsan komai da zata iya aikatawa dama wanda ba zata iya aikatawa ba.......indai har da gaske ne kina jinta kamar diyar data kwanta a mahaifarki watanni tara kika haifeta,koda baki gayawa kowa ba.....koda kowa bai sani ba,mahaifinta......sanadinta,kuma jigonta yana da haqqin yasan iqirarin diyarshi......indai ba akwai manufa shiri ko wani tanadi ba cikin shurun......bai cancanci ayi shuru ga dukka iqirarin da d'iyar dake da kafiya da taurin kai irin AKHNAN ba". Idanun morsa safiyya da kallonta kawai a kanta ya gaya mata akwai babbara barazana......akwai abubuwa masu tarin yawan daya kamata tayi garkuwa dasu kafin wani abu ya girgiza gaskiyar dake lullube da ayyukanta a zahiri. "Me kike cewa safiyya?.....me kike shirim cewa?" Ta fadi tana son gano bakin zaren komai ta dora ga aikinta na gaba. "Bance komai ba,ban kuma shirya fadin komai ba......saidai tarin qalubalantata a gareki na rashin shaidawa mahaifin biftu iqirarinta har sai dame afkuwa ta afku......nayi imanin inda kinsan ZAFIN HAIHUWA inda kinsan DARAJAR 'YA'YA ba zaki aikata haka ba" . Maganan ta daketa da zafin data saba dukanta,saidai kuma da wurwuri ta gano ta kuma fahimci akwai wani d'anannen tarko cikin maganan morsa safiyya,da biyu a yau ta maimaita maganan gaba sultane,gaban nanay da ta lura ita daya ta ankara da tsaiwarta daga qofa. Duk da cewa tarko ne maganar tata,amma ta hango tarin mafita a cikin tarkon......ta hango hanyar bullewarta. "Ya isa safiyya" Sultane ya fada da sigar dakatar da momma safiyya,amma saita murmusa don har yanzu batakai gaci ba. "Ka barni na gaya mata,zan gaya mata abinda yake shine.......illar bada tarbiyya ga macen da batasan ciwon haihuwa b........" "Ya isheni haka safiyya!.....ya isheni!!!" Mammina ta magantu cikin wani irin fushi tana miqewa tsaye. Irin wannan fushin morsa safiyya ke fata da burin gani a tattare da ita......irin wannan fushin da take fata ya kaita ga yakice akhnan ta barta zuwa gareta......ta barta zuwa ga ainihin UWAr data cancanci rayuwarta........ta barta da AHALINTA na haqiqa........ta barta taju GARDIN soyayya da 'YAN UWANTAKA daga ahalinta na asali.......ahalinta na tsatso. "Ki jima kina jifana da miyagun kalamai saboda haihuwa......kin dade kina fadamin dukka maganan da yazo bakinki akan akhnan......." "Baki kyauta ba safiyya.......ba halinki bane,bai kuma kamata a yanzu ace kinyi ba,bai dace ki rama alkhairi da sharri ba" Muryar nanay dake bayyanar da zallar bacin rai ta iso gurin Nanay din tana takowa zuwa ciki gami da gaza jure ci gaba da tsaiwa daga bakin qofar don kada ta shigo ta yanke maganar da yakeyi da iyalin nasa. Amma ganin maganganu suna neman juyewa zuwa zafafan musayar yawu daka iya bada sakamako maras kyau taga ya dace ta qaraso ta kamawa d'an uwanta wannan rigimar da take hange cewa ta yau din ta dabance......ta yau din me girma ce. Da sassarfa mammina ta taka tana cimma Nanay. Idanunta cike fal da hawaye ta kama hannunta. "Don Allah ki gaya mata.......ki kuma tambayeta sai yaushe zata ga alkhairi na?.......sai yaushe zan zama MACEN ALKHAIRI a idanunta. Me takeso,me take buqata nayi bayan wanda nayi da zai gamsar da ita?" Mammina ta fada hawayen da ya tarar mata yana saukowa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 09* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ "Tsahon shekaru ashirin da suka yita shudewa kawo yau.....ko meye ya kamata morsa safiyya ki fahimceshi......ko menene ya kamata ki yafeshi" Murmushi me dauke da wani nannuyan ciwo morsa safiyya ta saki. Tana hangen wani kwantaccen hali dabi'a zubi da tsari na musamman daga kowanne motsin mammina din. Abubuwan suna sake kwance mata kai,amma alqawari ne ta yiwa kanta,bakin rai bakin fama......ba zata taba sassautawa muradan mammina ba......ba zata taba rusuna musu ba......ba zata taba sauke mata kai ba......ba zata taba bari ta mulketa ba......ba kuma zata daina adawa da kowanne tsari da shiri nata ba muddin bata saki kurwa da rayuwar akhnan ba. "Akwai wani lulluben duhu dake nannade cikin wasu irin yankuna masu tsananin duhun daya kusa fin duhun da suke boye dashi......ba zaku fahimci komai ba......wani yare ne da baya buqatar harshe ko motsi na labba ballantana akai ga fitar sauti.........abu daya data tambayeni kan me zatamin na yaba.....abu dayannan shine KI 'YANTA RAYUWAR AKHNAN.....KI RABU DA ITA DA DUK ABINDA YA SHAFETA". Sosai kalmarta ta farko tayi duka me sauti a qirjin mammina.......bada hankali ga kalmar kuma na nufin d'arsuwar alamu masu tarin yawa ga zukata da kuma ayyuka,don haka ya zabi yin duk wani tattaki nata da fidda salon iya kauda hankalinta akan jimla ta biyu,don haka ta saki hannun Nanay a hankali,wani murmushi yana subuce mata maras armashi,tayi taku uku tana sake kusanta kanta da inda morsa safiyya ke zaune. "Wannan shine cikar burinki......shine cikar burin da har ki mutu ba zaki sameshi ba muddin ba kyakkyawar niyya da nufi bane a zuciyarki......HAR ABADA bazan wulaqanta akhnan ta hanyar banzatar da ita da rayuwarta ba kaman yadda kike fata,jinin sultane yafi qarfin wulaqanci ko kuma tozarci na har abada a hannun zaituna.......idan baki da labarin soyayya KOMA KI TAMBAYA cikin hamshaqiyar qasar data tara isassun mata irin ZAITUNA.......Zan sadaukar da farincikina saboda farincikin akhnan.....zan iya yaqi da kowa don akhnan ta samu 'yancin da yayi daidai da rayuwarta........kamar yadda a yanzu nake tsugunnawa saman qafofina nake roqarka ka janye auren hakeem akan akhnan......ko don ka ceto rayuwar da qwaya daya tal da ita kadai SAFEENA ta iya baka" Mammins tayi maganan tana sulalewa saman gwiwarta gaban sultane. SAFEENA dukkan rauninsa ce......safeena dukkan qwarin gwiwarsa ce a sanda yake raye. Sa'insarsu gaban should wani abune daya jima irin haka bata sake faruwa ba a gabansa. Kamar kowacce ta mance da wanzuwarsa a gurin,kamar kowacce ta mance da hukuncin aikata haka a gabansa?. "Zan dauki alhakin komai......amma bazan iya jurar rasa biftu ba.......ta fara da shan guba.....dukkanmu gaba bamu da tabbacin abinda zai faru da rayuwarta". Wani irin masifaffen tashin hankali ne morsa safiyya taji yana yanko mata. Idan ana lissafin ANNOBA tana ganin cewa mammina tafi gaban a kirata da sunan ko a sanyata a sahun......tafi qarfin sunan ANNOBA saidai wata halitta daban da tasha banban da yanayi da tunanin dan adam. Soke auren akhnan da hakeem hakan yana nufin dawowar kowanne lissafi baya?. Hakan yana nufin maida kowanne lissafi izuwa farkonsa?,tarin gwagwarmaya tarin dauki ba dadin da akayi dukka sun koma farkon lissafi?. Akwai wani tunani......akwai wani target akwai kuma wani ajiyayyen abu kuma boyayye a bayan kowanne faruwar al'amari. "Soke auren hakeem da akhnan da zakayi shine babban kuskuren da zaka aikata sultane...." Morsa safiyya ta fadi tana girgiza kanta gami da qoqarin boye dukkan tsoron dake cin ransa. Da wata irin fusata mammina ta waiwayo tana duban morsa safiyya. "Wannan shine kalar maqaryaciyar soyayyar da kike iqirarin kina yi mata?......kar ya soke auren?.......yau tasha gube gobe tasha ruwan batir?......burinki kawai tayi aure?,tabar gabanki bayan ba saman kanki take rayuwa ba?,me ta tsare miki?.....tayi aure kowanne yanayi ma zata shiga ba damuwarki bane?,saboda BAKE KIKA HAIFETA BA?,SABODA BA FALAAK BACE?" "ZAITUNA!......kul dinki.....kul bakinki ya sake....." Maganan da morsa safiyya ta fara da wani irin zafi daya sanyata miqewa tana nuna mammina da yatsa maganan ya katse saboda tsawar da sultane ya sakar musu. Ba wadda bataji ta koma hayyacinta ba,don baquwar halayya ce ga sultane din. Yana da wani irin girma da yake bawa kowaccensu saboda kowacce akwai wani ajiyayyen dalili da yasa take da girma da daraja a idanunsa. "Idan har wanzuwata a guri bata hanaku aibata kawunanku ba.....meye zai sanya ku fasa?" Yayi tambayar da harshen da yasa kowacce jinin daya fara tafarfasa a jikinta ya fara sanyaya. Ganinta da jinta taji kaman ya makance na wucin gadi,yau ita ake duban cikin idanunta ake cewa jinin safeenarta BA ITA TA HAIFETA BA?. Wata bare can?,wata cikakkiyar abokiyar adawar da dukka tsahon rayuwarsu basu data biyunta?,tabbas.....idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zatayi ba.....inda safeena tana raye a yau,zataji ciwo sama da ciwon da ita takeji yanzu cikin qirjinta,saidai wannan ciwon.....wannan radadin ta haramtawa mammina ganinsa.....ba zata taba bari ta fahimceshi ba. "A shirye nake na dauki mummunan mataki akan kowaccenku......muddin kasancewata a guri ba zata zama sitiyarin control dinku ba!" Ya sake fadi wani fushi me kaifi yana gilmawa ta cikin idanunsa yana nuna yatsansa dan manuni. "Kayi mana afuwa" Nannie ta furta ita kanta a yau tana jin banbanci tsakanin yanayin sultane na yau dana kullum. Shuru ne ya ratsa dakin,tamkar ba ragowar wani abu me numfashi a cikin dakin. Numfasawa sultane yayi,yana qoqarin daidaita kanshi da ragewa kansa damuwar da yakeji tana tasiri kadan kadan cikin zuciyarsa. Yana jin qwarin gwiwar hukunta akhnan.......yana jin takai lokacin da zata fuskanci fushinsa dama hukuncinsa,yana jin wani tasiri na maganganun morsa safiyya a ransa,yana ganin wasu daga cikin gaskiyarta,koda ta kasance me taurin kai,koda ta kasance me kafiya,koda ta kasance me tsaurarawa da yawa. "Dole ne na janye auren akhnan da hakeem.......tunda wadanda keda alhakin karbar auren sun janye suma". Tsahon rayuwarta zata iya cewa,ta jima bataji wani labari daya saukar da wata irin farinciki me girman gaske cikin zuciyarta ba.......ta jima bataji abinda yazo mata a bazata irin wannan a wadannan shekarun ba. Murmushi ko dariya take buqatar tayi a irin yanayin don furzar da yanayin da zuciyarta ke ciki,amma saita rikide da nuna alhini dama tsoro baro baro saman fuskarta. Yadda morsa safiyya ke dubansa da wani irin dimaucewa,haka mammina ke kallon sultane da yanayin daya kebanta da zuciyarta kadai. Wani irin zafi zuciyarta ke mata,tana so ta riqe bakinta,tana so tayi shuru kada ta tanka,amma tana jin idan tayi haka,idan har sai ta jira sultane yace wani abu da kanshi zuciyarta zata fashe,zuciyarta ba zata iya dauka ba. "Amma.......ba nadama?......ba kuskure cikin faruwar?......" "Sun janye saboda labari yaje musu.......'yar da d'ansu ke burin kawowa cikin ahalinsu da ake zaton mace ta gari ce......yarinya nutsatsiya me biyayya ga maganar magabatanta abun ba haka bane..........a dazu na aika an maida musu da dukiyar aurensu da komai da komai nasu cikin mutuntawa kamar yadda suka kawo......" Shuru gurin ya sake dauka,kafin a hankali nannie ta magantu. "Koda basu janye ba,koda basu fasa ba ni a nawa hasashen janyewar shi yafi alkhairi.......a duk sanda irin haka ta sake faruwa,ba wanda yake da tabbacin abinda zai ci gaba da faruwa,koma meye......ko yaya yanayin yakai ga hasala ko baci akhnan diyarmu ce,kuma lallai muna qaunar rayuwarta sama da yadda zamu qaunaci rayuwar kowa" . Ji tayi bata da wani sauran zama a gurin,ji tayi bata da sauran abinda zata zauna tayi a gurin,tana jin idan taci gaba da zama abubuwa sake kwabewa zasuyi,idan har tace zataci gaba da zama abubuwa zasu lalace ne. Ba zata iya shuru ba,ba kuma zata iya ci gaba da saka idanu tana kallon komai yana tafiya a yadda yake a yanzu ba. Da nannie da sultane akwai wani abu daya gifta ta cikin idanunsu da batasan sai yaushe zai bude ko ya yaye ba. Bata sani ba......shin cikin qullin mammina ne data sha ALWASHI?,ko kuma tsananin soyayyar akhnan ce take jawo wasu abubuwan?. "Ayimin afuwa......na barku lafiya" Abinda morsa safiyya ta fadi kenan tana miqewa a hankali tana jin kamar bata ganin gabanta sosai ta fara takawa tana fara fita a dakin. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Da kallo nannie ta bita,zatayi magana sultane ya daga mata hannu kawai alamun ta barta. Ya sani,zataji tsananin rashin jin dadi,ya sani zata zargeshi a zuciyarta,ya sani,zataga zallar rashin adalcinsa......to amma inda ta haqurqurtar da wannan zuciyartata me yawan fushi,me saurin fusata da zata fahimci komai bai canza ba. "Janye auren hakeem bai canza komai ba!" Ya fada da yanayin daya dawo da hankulansu mammina kanshi. "Eh......kwanan watan dana sanya na auren akhnan bazai canza ba......hakanan duk wani shiri da nayi akan bikinta ban canza komai ba......komai yana nan akan tsarinsa.......watanni biyu masu zuwa tabbas diyata akhnan zata zama MATAR AURE......" Maganan saita dan saka rudani a zukatansu,musamman zuciyar mammina dake cike da babban buri da kuma shirin da take fata ya fado yayi daidai da wannan lokacin. "Ki gayawa 'yarki.....daga sultane of agadez......Muhammad hammud.......taci nasarar janye maganae auren hakeem a kanta......amma ba abinda zai canza wa'adinta na zama matar aure,watanni biyun aurenta.......sune watannin da take dashi na kawo duk wanda takeso........don nayi alqawari......ni ba mutumin banza bane,qafar wani d'a da zummar son ganinta ya aureta ta yanke daga zuwa gidan nan indai a kanta ne.......watanni biyu kacal take dasu ta kawo wanda takeso ta aura.......ku rubuta ku ajiye......daga yau zuwa biyar ga watan sama,a ranar juma'a,muddin bata kawo wanda takeso ta aura ba......ni.muhammad hammud zan daura mata aure da duk wanda naga dama. Ba kuma lallai ya zama kalar mijin da takeso ba......ba kuma lallai tasan waye ba wataqila har sai ta shiga dakin aurenta......aure na dindindin.......auren da saidai a fidda gawarta daga gidansa" Ya fada da wani irin sauti daya tabbatarwa nannie da mammina ba wani sassauci ko sauyi a maganarsa. Ba qaramar juriya tayi ba data iya shimfida tashin hankali saman fuskarta ba. Sunan ALMAZ kawai ke mata yawo saman harshe da kwanya,saidai ba yanzu ba.......ba da sauri haka ba......ba'a wannan taqin ba.......akwai ragowar taku biyu zuwa uku daya kamata tayi. "Amma sultane......ta yaya mace kaman akhnan.......mace me tarin martaba da mutunci za'a buqaci ta fidda mijin aure a wannan tsukakken lokacin,shi baka tsoron ya zamana tayi zaben tumun dare?". " Zaituna" Ya furta da tarin nutsuwar nan tasa da yau take cakude da bacin rai. "Daga rana irin ta yau....bana son wata magana data shafi akhnan akan aure a sake tasomin da ita,abu daya nake jira ta sanarmin ta samu miji shikenan". Qasa tayi da kanta,wani irin farinciki yana shawagi da zagayawa da ita a duniyarta. "Allah ya huci zuciyarka,tuba nake" Abinda ta furta kenan kanta a qasa ba tare da sun hada ido ba. ♣️:~ Juyawa tayi ta sake juyawa ita daya cikin dakin tana jin kamar wani kida ko sauti na musamman ake busa mata. Irin wannan yanayin yanayi ne da yafi dacewa ka rabashi da wani mutum na musamman daga gefenka,to amma ita din bata gama aminta da dukkan kowa ba ballantana ta saki jiki yasan dukkanin fuskokin data mallaka. Tana da tarin girma da alfarma,banda haka tabbas ya cancanci tayi wannan juyinne a sararin da zata shaqi iska da kyau. BURINTA MAFARKINTA da kuma MURADINTA na shekara da shekaru a yau yana dab da cika. Ta yarda a karan kanta cewa ita din WUTA ce......wata irin WUTA me tsananin had'ari duhu da kuma baqin HARSHE dake iya nakasta rayuwar duk wanda ya rab'eta. Wannan lokacin ta jima tana jira,cikin tarin mafarkan IDO BIYU da tashayi a zaune cikin duniyarta. Wannan lokacin data lashi takobin ajiyewa kaf familyn DIORY MUMMUNAN TARIHI da zaita bibiyarsu har qarshen rayuwarsu. Wannan lokacin da tasha alwashin sanya SAFEENA kuka da hawayenta.......tasha alwashin sanyata cikin tarin NADAMA DA DANASANI koda kuwa qasa ta lullube idanunta.....koda kuwa tana kwance cikin kushewarta.......wannan lokacin wani lokaci ne daya girmimi a kirashi da DAUKAN FANSA......lokaci ne na ajiyewa ahalin gaba daya MUMMUNAN TARIHI. Z'a haife 'ya'yan da ba za'a taba alfahari da samunsu ba.....'ya'yan da zasu zamewa tarihi BARAZANA.....'ya'yan da za'a ce zaman uwarsu JUYA shine mafi Alkhairi sama da haihuwarsu. 'Ya'yan da muddin suna raye a duniya.....muddin sun wanzu a doron duniya.....to a kowacce rana da qwayar idanuwa zasu sauka a kansu......baqinciki ne zaici gaba da hallaka zukata da yawa d'aya bayan d'aya har zuwa ranar da tarihi rayuwa da tsahon zamani zai shafe babinsu gaba daya. ALMAZ da AKHNAN dukkaninsu cikin tarko suke......cikin tarkon da babu me iya fahimta,koda kuwa TAMIM ne......koda kuwa YALWA ce......koda sauran boyayyun ma'aikatanta ne......wannan din wani sirri ne dake tsakanin zuciyarta zuwa qirjinta kawai. (Tofa.....me karatu?,wanne irin qudunannen sirri ne wannan?.......Allah yasa ko yaya mammina ta buda mana zuciyarta ko zamu iya fahimtar me take qullawa haka tsakanin almaz da akhnan). zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 10* ____________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ Batayi wani gaggawar zuwa ga akhnan ba,sai misalin qarfe sha daya na dare. Tanason tabar mata dukkan daren ya qare a tunani da neman mafita,mafitar data tabbatar bata da ita......neman mafitar kuma shine zai danganata da zuwa inda take.....zuwan nata kuma shine abu na qarshe da take fata da burin kasancewarsa. Qasaitattun kayan baccin alfarma masu taushi da kyau ta saka a jikinta,sannan ta dora doguwar riga yalwatacciya akai,don tana saka ran daga nan ta biya ta sassan me martaba ta sake kashe awanni don sake dasa abubuwa da take buqatar sanyawa da ajiyewa cikin zuciyar sultane,ajiyar da zata mata amfani wata rana. Daga ita sai yalwa kawai suka fita,suna ratsawa cikin gidan da sawaye suka dauke saboda kutsowar dare,sai gilmawar hadimai da fitarsa a sannan ya zama dole,da kuma masu bada tsaro na sashe sashe dama gidan gaba daya. Sanye yake da Moroccon jallabiyya da aka saqata da wani silk yadi me sulbi da wani irin daukan idanu,yayin da qafarsa ke sanye da wani lallausan halfshoe daya dace sosai da yanayin rigar. A daren hula ce kawai saman kanshi kalar rigar,wanda yawan larabawa ke amfani da ita. Wani irin dare ne daya cika da hasken watan da zai gaya ma mutum wata ya fara nisa,abinda yake sake zaburar dashi kan aikin kenan,ya kuma hanashi kwanciya a daren. Target biyu yake dashi,wanda ya tabbatar yana buqatar kulawa da takatsantsan. Samun matsayin D'A a wajen sultane ba yana nufin zaiyi komai bane gaba gadi.......dole komai ya zamana akan tsari kulawa da kuma takatsantsan. Tsakanin jiya da shekaran jiya....bayan shudewar kowacce daqiqa tunaninsa yana sauka akan banguls din hannuwanta.......abun adon da yake da tabbaci cikin kaso saba'in cewa qirar qasar ETHIOPIA ne.......abun hannu me daraja da tsada kwatankwacin wanda suka taso suka gani nanay tana amfani dasu a yawancin lokuta. Abun ado ne da yawan matan sarauta da attajirai na qasan Ethiopia a wasu shekaru a baya suke amfani dashi......to amma aikinsa aiki ne dake tafe da yaqini da samun tabbaci gudun samun kuskure. Dole yana buqatar wannan abun hannun......dole yana da buqatar sa a hannunsa don turawa ayi masa bincike tare da bashi tabbacin wanda hasashensa ya yawaita a kai ne?. Dakin ajiye ajiye na gidan......wani guri na biyu da shima yake cikin lissafinsa......amma kafin isa gareshi yana buqatar sanin abubuwa da yawa. Canzawar motsi zirga zirga da kai kawo na gidan daga daqiqa zuwa daqiqa.......yaya kowanne qofa window da sashe na gidan yake kasancewa daga kowacce daqiqa zuwa wata daqiqar......wannan shine abinda ya fito dashi,yana kuma tafiya ne da cikakken nutsuwar nan tasa,can qasan zuciyarsa kuma suratul rahman yake karantawa ba tare da sauti ba,sai motsawar tausasan lips dinsa da motsawar Adams Apple dinsa lokaci zuwa lokaci. Idanunsa ya dauke daga windows din da yake qoqarin kiyaye adadinsu da kuma wadanda kake iya hangen haske a cikinsu da wadanda ma duhu ke lullube dasu,alamun dake nuna akwai guraren da masu rayuwa a ciki sukayi bacci a daidai wannan lokacin. Alamun takun da yaji shi ya sanya ya sake sassauta yanayin tafiyarsa,haruffan dake cikin surar suna sauka a zuciyarsa gami da wata irin nutsuwa,ma'anoni da girman ubangiji dake bayyana cikin ta yana jin kamar suna sauka a ruhinsa da kuma zuciyarsa kai tsaye......a daidai wannan lokacin idanunsa suka sauka a kanta sanda take takowa cike da wani kalar karsashi. Duba na nutusuwa yayi mata kafin a hankali ya zare idonsa daga kanta yana maidawa ga inda yake sauke sawayenshi. Qasan zuciyarsa yana sake jin abu me qarfi yana dasuwa a ranshi. Ita dimma kamar wancan mutumin,akwai dan wani abu daya jirkita yanayin zubinta dana al'ummar agadez......akwai wani tasiri na daban cikin yanayinta da babu shi jikin agadasawan yankin,duk kuwa da yadda shigarta yanayinta damu'amalarta suke maidata ba'abzina ta sosai.......amma yanayin da kamannin da yadda a komai nata al'adar abzinawa ke shiga tayi kane kane ya soma d'arsa wani qaqqarfan zargi a ransa. Dare daya tal ya kwashe yana bincika tarihi yanayi da al'adun kowacce qabila dake cikin qasar da yankin na nijer,a wannan daren guda daya bacci bai ziyarci idanunsa ba ko sau daya. Yasha coffee har baisan iyaka ba,amma kuma bai damu da rashin baccinsa ba,don ya tattara dukkan abinda yakeso,ya kuma san duk abinda yakeso ya sani,wannan ya sanya daga wannan kallon yaji cewa tabbas akwai wani abu daba daidai ba. Bata ankara dashi ba,har sai da tazarar data rage tsakaninsu ta kasance bame yawa bace. Yalwa ce ambaci sunanta a hankali,yanayin kiran kadai ya gaya mata akwai wani abu,don haka kai tsaye gabanta ta kalla bawai sashen yalwa ba. Wata irin bugawa zuciyarta tayi,amma sai tayi gaggawar zuqar iska sosai tana daidaita kanta,kafin a hankali ta sauke numfashin tana gayawa kanta da kanta wani abu. Sarrafa kansa yake qoqarin yi don yanayinsa ya dace da yadda zaiyi magana da ita. A yanayin kallonta ya tabbatar akwai abubuwa da yawa game da ita. Yadda take kallon kowa da yadda take hada nutsuwarta a duk sanda taga wani baqon abu da bata saba gani ko mu'amalanta ba. Wani yanayi da yake bayyana a tattare da wasu mutane da suke dauke da baqin abubuwa a cikin halayyarsu da dabi'arsu. "Barka wannan lokaci" Ya furta a nutse yana qoqarin daidaita matsayinsa da yanayinsa da yadda ya fahimci tana mu'amala da hadimanta. Murmushi ta kawo ta aza saman fuskarta,ta kawo wata irin sakewa ta sake shimfidawa a sama sannan ta amsa masa. "Barka kade sheikh muhammad........ina fatan ba wani matsala bace ta fito dakai cikin irin wannan lokacin?". Kai ya jinjina yana daukar wasu abubuwa cikin kalamanta yana turasu wani sashe na zuciyarsa tare da shirya amsar da zaya bata duka cikin qasa da second biyar. "Ba wata matsala.......ina buqatar iska me kyau ne kawai" Ya amsa mata a taqaice ba tare daya kalli idanunta ba. Kai ta jinjina a hankali,burinta da muradinta shine ya kalleta,tana son karanto wasu abubuwa cikin idanunsa. "Amma ai da kasanar......yanzun kai din kamar d'a kake a wajenmu.......sai a hadaka da wanda zai maka jagora gudun shiga shiyyar da bai dace da girmanka da matsayinka ba". Murmushin qasan zuciya y saki wanda ko labbansa bai motsa ba bare ka gani,ya sake aikewa da kalamanta wani sashe na zuciyarsa,sannan ya motsa kadan alamun yana nufin wucewa. "Bazai zama damuwa ba.......ba wani zurfi ko nisa tattakin zaiyi ba......duka duka na awa daya ne......a fito lafiya" Ya fada da salon girmamawa yana ci gaba da wucewa a hankali. Bin bayansa tayi da kallo komai na tunaninta yana warwarewa lokaci guda. "Tabdijan" Ta furta a sanda yake bacewa ganinsu tana aza idanunta akan fuskar yalwa. "Ya wuce a sanda bani na bashi umarnin hakan ba,bai kuma nemi izinin wucewa ba.....bai kuma dakata da tafiyarsa ba a sanda ya ganni.....hakanan ba wani alamun kwarjini da nakewa kowa a cikin muryarsa.......yana bani amsa ne da wani irin qwarin gwiwa da tsaiwa a muryarsa.........lallai akwai wani abu.......akwai wani abu daban cikin JININSA.....ko ya kasance irin abinda ke cikin jinin SARAUTA ko kuma halittarsa zuciyarsa da ruhinsa masu tsananin qwari ne......yalwa" Ta kira sunanta tana ci gaba da takawa a nutse. "Allah ya baki nasara" Ta amsa da girmamawa. "Kinga dukkan abinda na fada?" "Qwarai da gaske......abu daya ne kawai dana gani,baya kallon mutane" "Yana da addini da kuma sanin addini.....maza irinsa suna da wannna dabi'ar.......bawai tsananin girmamawa bace a gareni.........inason insan wayeshi?......idan har sakamakon yazomin mutum ne yadda muke zatonsa ordinary kaman kowa.......to lallai ina buqatar sa cikin tafiyata........ina buqatarsa a gefe na.......". "Sheikh haisam din?" Yalwa ta tambaya cike da tantama. Qaramar dariya ce ta kubcewa mammina.......tana jin wani nishadi yana ratsata. "Da kamar wuya ko?......abune me sauqi yalwa.......KUDI ba sune masu maida abinda bazai yiwuwa ba ya yiwu......kudi sune masu juya kowanne mutum zuwa yanayi da siffar da kake buqatar ganinsa a kanta. Idan kana buqatar mallakar wani abu......ko wani mutum idan ka gutsira masa IKO cikin ikon da kake dashi komai ma zai sallama maka......malamai a wannan lokacin sunfi kowa son zuciya da mutuwar zuciya......mallakar wannan malamin shine abu mafi sauqi da nake hange zanyi......inaso daga yau dukkanin motsinsa ya zama abun bibiya......inason daga wannan lokacin duk inda zai saka qafarsa.....duk inda zai sauketa ya zamana abun kiyayewa......bacci ne kadai idan zai kwanta na yarda ma rataye da aikin yaje ya huta a sannan.....na bawa tamim wannan aikin......amma inaso wannan ya sake zama wani aikin na daban ba tare da kowa ya sani ba". Yatsansa yakai kunnensa ya taba a hankali,wani tattausan murmushi ya subuce wanda ya tsaya saman labbansa. "Tamim" Ya maimaita sunan a hankali yana motsa labbansa. Ya fahimci akwai tarin abubuwa tattare da mutum biyun nan da suke sharing suna GUDA DAYA,sai ya jinjina kansa cikin wata irin nutsuwa "Kwanciyata bacci?.....shine zai zama lokacin faduwarki.........lokutan kwanciyata bacci.....sune zasu zama lokutan kwanciyar dukka wata sa'arki......zanyita bacci kala daban daban,daga nan har zuwa kwanakin dana fahimci WACE KE?. INA KIKA SAKA GABA?....kin shiga cikin lissafi na...." Ya fada qasan zuciyarsa da wata irin nutsuwa. Bai taba tunanin na'urar daya wurgar a gurin zata kawo masa amfani da wani bayanai daya shafeshi shi karan kansa ba......bai taba tunanin na'aurar zata zama me amfani me girma har haka ba. Hanyar dake gefan hagunsa ya kalla,yaji kuma a cikin ransa itace hanyar data dace ya shiga ba tare daya damu da komawa daukan na'urar ba. Bata da wani girma da wani zai gane meye,tafi kama da ba'awon gyada sak da sak,yasan ba jimawa wani zai taketa shikenan amfaninta ya qare a wajensa. Har qasan ransa yakejin matar tamkar tana da alaqa da duk wani bahagon al'amari da masarautar ta taba fuskanta,duk da bai sani ba.......amma motsinta na baya dana yanzu yana gaya mata tana daya daga cikin QALUBALEN SULTANE.....tana daya daga cikin MATSALOLINSA TABBAS!. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Yanaso yana mugun sha'awar ayyukansa subi takan mutane irinta......sa'arsa daya bai shigo agadez don ceto masarautar agadez ba......bai shigo agadez don bawa sultane ko iyalinsa ko mulkinsa kariya ba......ya shigo agadez ne kawai saboda QASARSA.....ya shigo agadez ne don ya kare rayuwar MAHAIFINSA.....hakanan ya shigo agadez ne don ya zaqulo boyayyen mai laifin nan ya damqawa qasarsu shi!. Iya wannan kawai zai iya sanyata ta tsira muddin bata zama cikin wadanda yake tuhuma ba......daga sanda ta sadashi da abinda yake muradin farauta ta fita daga AGENDA dinsa. Tunda buhaina ta gaya mata an shiga tattaunawa tsakanin sultane mammina da nannie ta kasa cikakken sukuni. Kowanne irin zama ne ta tabbatar yana da alaqa da ita.....koda ba don ita aka zauna ba ta sani issue dinta yana abu na gaba gaba da za'a tattauna akai. Yau da kanta ta shirya shirin baccinta,don bata dade da sallamar birra ba,wadda suka jima yarinyar na mata kuka da rantsuwar bata xuba mata komai cikin tea dinta ba. Bata da wani kokwanto akan birra ko kadan,yadda ta yarda da ita haka ta yarda da kanta,to amma tana ji a jikinta tabbas akwai wani abu,akwai abinda ya faru......bai kamata kuma tabar komai yaci gaba da tafiya a haka ba. Tafi karkata dukkan amincinta akan tamim......to amma a yanzun tamim din yana kan wa'adin ragowar kwanaki biyu na aikin data bashi,tana jin zata jirashi don sake bashi wani aiki na bincika mata me ya farun,wannan ya sanya ta hana a taba duk wani ruwa da kwanuka na bangarenta,har zuwa sanda tamim din zai dawo. Sanda birra data dawo take shaida mata mammina ta shigo tana buqatar ganawa da ita. Bata kammala jin abinda birra ke fadi ba ta soma yunqurin sauka daga gadon. Net din dake zagaye da gadon ma wanda take controlling nashi da remote gani tayi yau baya saurin zugewa don ya bata hanya,saita sanya hannu ta yayeshi gefe tana saukowa. Bata ko tsaya neman flip-flops dinta ba ta soma taka tattausan tafin qafanta kan carpet din tana qoqarin cusa gashinta me tsaho da sulbi cikin bonnet da take mahadin kayan jikinta. Yadda take saukowa daga stairs din a gaggauce ya sake sanya mammina cilla plan dinta da qara masa wani adadi. Ido ta lumshe tana sake budesu akan akhnan din,wani irin kishi yana ci mata zuciya. Har tana jin kamar wani ciwo ciwo na dunqulewar da zuciyarta tayi guri daya. Wani irin sassanyan kyau yarinyar ke dashi,kyan data tabbata banda wasu dalilai ba abinda zai sanya akhnan ta rufa shekaru goma ba tare da an aureta ba zuwa ga ahali mafi daraja da sukafi na mahaifinta. Ita kanta akhnan tana mata kyau,saidai kyan yana tsaye mata a rai da wani irin ciwo saboda tuna daga inda ta samo ASALIN KYAN nata. Daga gurin safeena ne......wannan kyan nata da tayi imani yana daya daga cikin abinda ya sanya ta rasa wannan martabar.......ta rasa wannan darajar.......ta kuma rasa wannan MATSAYIN da TAMBARIN na MATAR FARI a gurin sultane. Bayan kyan ya mata wannan sanadin......wannan KYAN HALIN da a wajenta ba komai bane face zallar kissa da kisisina ya sake zame mata silar qara rasashi a KARO NA BIYU,ya sake cillata can nesa da matsayin zamowa MATA TA BIYU ga sultane din. Ware idanunta tayi akan akhnan sanda take kusa isowa da inda take. Tuna baya kadan da tayi ya sake rura wata sabuwar wutar a zuciyarta. Ta zubawa akhnan idanu,tana tuna fuskar safeena da wani lokaci zaka ganta shimfide akan fuskar akhnan din. Sau da dama tana mamakin kanta na yadda ta tsaya bin akhnan ta wannan doguwar hanyar. Tana ganin imaninta da yawa idan ta tuna shekarun data dauka kawai tana dakon ta dauki FANSA akan abinda tana iya aiwatar dashi cikin kwana uku kacal. To amma zuciyarta tasha gaya mata cewa. "Daukar fansa yafi ciwo a sanda aka manta......yafi ciwo a sanda aka saki jiki.....yafi ciwo a sanda zamani da shekaru suka cilla......a sanda akayi imanin komai bazai canza ba......komai bazai kuma faru ba" Ta yadda da wannan magana ta zuciyarta.......kuma itace take mata jagoranci a dukka tsahon shekarun nan kawo yanzu. Safeena zallar muguwa ce.....muguwar da bata da kamanceceniya,salon muguntar da batajin idan zata dawo duniya ta mutu sau dubu hakan zai sassauta abinda takeji a kanta kota yafe mata,a sanda ta tabbatar rabuwa tazo tsakaninta da sultane......a sannan ma bata barta ba,bata bar sultane ba,saida tayi abinda ya sake jawo mata asarar matsayinta,ya kuma kusa sake jawo mata rasa sultane din rashi na har abada,ta yaya zata manta da dukka wadannan abubuwa?,ta yaya zata yafe cikin sauqi?,don dai ita ta kawo wawanci duniya?. Yadda taga akhnan na kallonta ya sanyata sakin sassanyan murmushi "Ina tunanin irin halin da zan shiga yanzu iwarhaka inda na rasaki......biftu......kina taba tunanin inda muradinki ya cika masarautar agadez gawa biyu zasu sallata?" Kai ta kada tana duban mammina. Batasan me yasa a wannan lokacin mammina ta gaza yarda ba ita ta aikatawa kanta haka ba?. Ta lura da irin kallon da akhnan din ke mata,don haka ta nuna gefanta dab da ita. "Zauna a nan" Bata musanta ba ta zauna din,mammina ta zuba mata ido tana tattara nutsuwarta a kanta. "Munci sa'a,munci kuma nasara.......sultane ya janye maganan hakeem a kanki......labarin abinda ya faru ya isa kunnensu,don haka sun janye,nasara taki ce". Manyan idanun nan da sukan rusuna wani lokaci kamar name jin bacci ta ware gaba daya. Labarin yazo mata a bazatar da bata taba kawota nan kusa ba,ta rasa me zata yiwa mammina?,kawai saita shige jikinta gaba daya tana mata wani wawar runguma. Wacce irin qauna ce haka mammina ke mata?,anya yadda mammina ke sonta ko mahaifiyarta idan ta dawo duniya zata qaunaceta irin haka kuwa?. "Bansan me zance miki ba,bansan wanne kalar godiya zanyi miki ba" Akhnan ta fada idanunta suna cika da hawaye,tana jin kamar an warware mata wani qaton dauri da aka yiwa rayuwarta gaba daya. Rungumar data matan tana mata kamanceceniya da sanya buhun qarfe na wuta a jikinta,amma hakan bai hanata shafa bayan akhnan din ba,kafin ta janyeta a jikinta a nutse da tausasawa tana cewa. "Da abu guda daya tal zaki biyani". Tsaida idanunta akhnan tayi kan fuskar mammina tana kallonta. "Sultane yayi rantsuwa ba abinda zai fasa ko ya hana daura miki aure nan da watanni biyu masu zuwa.......amma da zabin kanki da zaki kawo........saboda haka karki bani kunya......yadda na tsaya akan al'amarin nan har aka fasashi......inaso ke kuma cikin qasa da wata biyun ki fidda miji ki kaiwa sultane kaman yadda ya buqata". Idanunta ta sake warewa a karo na biyu tana duban mammina a hargitse. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 11* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ Bata ko tsaya neman flip-flops dinta ba ta soma taka tattausan tafin qafanta kan carpet din tana qoqarin cusa gashinta me tsaho da sulbi cikin bonnet da take mahadin kayan jikinta. Yadda take saukowa daga stairs din a gaggauce ya sake sanya mammina cilla plan dinta da qara masa wani adadi. Ido ta lumshe tana sake budesu akan akhnan din,wani irin kishi yana ci mata zuciya. Har tana jin kamar wani ciwo ciwo na dunqulewar da zuciyarta tayi guri daya. Wani irin sassanyan kyau yarinyar ke dashi,kyan data tabbata banda wasu dalilai ba abinda zai sanya akhnan ta rufa shekaru goma ba tare da an aureta ba zuwa ga ahali mafi daraja da sukafi na mahaifinta. Ita kanta akhnan tana mata kyau,saidai kyan yana tsaye mata a rai da wani irin ciwo saboda tuna daga inda ta samo ASALIN KYAN nata. Daga gurin safeena ne......wannan kyan nata da tayi imani yana daya daga cikin abinda ya sanya ta rasa wannan martabar.......ta rasa wannan darajar.......ta kuma rasa wannan MATSAYIN da TAMBARIN na MATAR FARI a gurin sultane. Bayan kyan ya mata wannan sanadin......wannan KYAN HALIN da a wajenta ba komai bane face zallar kissa da kisisina ya sake zame mata silar qara rasashi a KARO NA BIYU,ya sake cillata can nesa da matsayin zamowa MATA TA BIYU ga sultane din. Ware idanunta tayi akan akhnan sanda take kusa isowa da inda take. Tuna baya kadan da tayi ya sake rura wata sabuwar wutar a zuciyarta. Ta zubawa akhnan idanu,tana tuna fuskar safeena da wani lokaci zaka ganta shimfide akan fuskar akhnan din. Sau da dama tana mamakin kanta na yadda ta tsaya bin akhnan ta wannan doguwar hanyar. Tana ganin imaninta da yawa idan ta tuna shekarun data dauka kawai tana dakon ta dauki FANSA akan abinda tana iya aiwatar dashi cikin kwana uku kacal. To amma zuciyarta tasha gaya mata cewa. "Daukar fansa yafi ciwo a sanda aka manta......yafi ciwo a sanda aka saki jiki.....yafi ciwo a sanda zamani da shekaru suka cilla......a sanda akayi imanin komai bazai canza ba......komai bazai kuma faru ba" Ta yadda da wannan magana ta zuciyarta.......kuma itace take mata jagoranci a dukka tsahon shekarun nan kawo yanzu. Safeena zallar muguwa ce.....muguwar da bata da kamanceceniya,salon muguntar da batajin idan zata dawo duniya ta mutu sau dubu hakan zai sassauta abinda takeji a kanta kota yafe mata,a sanda ta tabbatar rabuwa tazo tsakaninta da sultane......a sannan ma bata barta ba,bata bar sultane ba,saida tayi abinda ya sake jawo mata asarar matsayinta,ya kuma kusa sake jawo mata rasa sultane din rashi na har abada,ta yaya zata manta da dukka wadannan abubuwa?,ta yaya zata yafe cikin sauqi?,don dai ita ta kawo wawanci duniya?. Yadda taga akhnan na kallonta ya sanyata sakin sassanyan murmushi "Ina tunanin irin halin da zan shiga yanzu iwarhaka inda na rasaki......biftu......kina taba tunanin inda muradinki ya cika masarautar agadez gawa biyu zasu sallata?" Kai ta kada tana duban mammina. Batasan me yasa a wannan lokacin mammina ta gaza yarda ba ita ta aikatawa kanta haka ba?. Ta lura da irin kallon da akhnan din ke mata,don haka ta nuna gefanta dab da ita. "Zauna a nan" Bata musanta ba ta zauna din,mammina ta zuba mata ido tana tattara nutsuwarta a kanta. "Munci sa'a,munci kuma nasara.......sultane ya janye maganan hakeem a kanki......labarin abinda ya faru ya isa kunnensu,don haka sun janye,nasara taki ce". Manyan idanun nan da sukan rusuna wani lokaci kamar name jin bacci ta ware gaba daya. Labarin yazo mata a bazatar da bata taba kawota nan kusa ba,ta rasa me zata yiwa mammina?,kawai saita shige jikinta gaba daya tana mata wani wawar runguma. Wacce irin qauna ce haka mammina ke mata?,anya yadda mammina ke sonta ko mahaifiyarta idan ta dawo duniya zata qaunaceta irin haka kuwa?. "Bansan me zance miki ba,bansan wanne kalar godiya zanyi miki ba" Akhnan ta fada idanunta suna cika da hawaye,tana jin kamar an warware mata wani qaton dauri da aka yiwa rayuwarta gaba daya. Rungumar data matan tana mata kamanceceniya da sanya buhun qarfe na wuta a jikinta,amma hakan bai hanata shafa bayan akhnan din ba,kafin ta janyeta a jikinta a nutse da tausasawa tana cewa. "Da abu guda daya tal zaki biyani". Tsaida idanunta akhnan tayi kan fuskar mammina tana kallonta. "Sultane yayi rantsuwa ba abinda zai fasa ko ya hana daura miki aure nan da watanni biyu masu zuwa.......amma da zabin kanki da zaki kawo........saboda haka karki bani kunya......yadda na tsaya akan al'amarin nan har aka fasashi......inaso ke kuma cikin qasa da wata biyun ki fidda miji ki kaiwa sultane kaman yadda ya buqata". Idanunta ta sake warewa a karo na biyu tana duban mammina a hargitse. Wani sabon tashin hankalin takeji yana saukar mata yana maye gurbin nutsuwa da walwalar data samu na sakannin baya da suka wuce. Wanne irin daurin talala ne wannan?......wanne irin d'aurin goro sultane yake mata?,wanne irin bahagon hukunci ne?,wanda banbamcinsa da hukuncin baya daya janye kadanne?. "Mammina....." Ta kira sunanta labbanta suna rawa kadan,idanunta a kanta wani kalan tashin hankali yana sauko mata. Tsareta mammina tayi da idanu.......irin abinda takeson gani shine a kwance saman fuskar akhnan din. Irin yanayin nan take buqatar gani,kuma ta ganshi,wannan shine abinda yake sake tabbatar mata da qarfi da kuma kaifin nasararta. "....banaso kice komai biftu.....muddin abinda zaki fada din bai dace da hukuncin sultane ba" Ta qarasa maganan tana girgiza mata kai. Itama kai take girgizawa tana duban mammina din. "Mammina.....meye bambancin wannan hukuncin da wanda sultane ya janye?,.......ina zan samo miji cikin watanni biyu?.......ya manta wace akhnan?......khadeeja muhammad hammud?......ya manta cewa rayuwar wani d'a namiji bata cancanci ta gauraya da rayuwata ba?.....ya manta cewa ba musaye nakeso ba?......ba dakatarwa kadai nake buqata ba?.......nesantawa nakeso.......ya nesanta rayuwata daga rayuwar kowanne d'a namiji". (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Kai mammina ke girgizawa tana dubanta. "A yanzu.....a kuma qadamin da sultane yake kai komai zai iya faruwa......wannan ra'ayin naki dole ki saukeshi.......wannan tsarin naki dole ki warwareshi......dole ki fuskanta kibi dukkan abinda yake tsarin sultane.......mun fara kaiwa wata gaba dashi......gab'ar dana fuskanci sai munyi da gaske zamu b'ulle......sai da takatsantsan zamu sha a hannunsa,saboda tunaninsa a yanxu ba nashi bane shi kadai.....ba shi kad'ai yake tunaninsa ba". "Amma mammina........me yasa?....." "Ya isa akhnan" Mammina ta furta a hankali tana canza yanayin fuskarta,sai kuma ta miqe tsam tana zame jikinta. "Bazan yarda naci gaba da baqinjini ba......bazan bari aci gaba da yimin mummunan kallo ba......aci gaba da fassara tarin alkhairaina zuwa wani abu na daban ba.......kiji kiyi tunani da kyau.....amma karki manta......ko da zabinki ko babu zabinki kina iya zama rabon me rabo,kamar yadda sultane ya tsara hakan......yanzu dukka ragowar aikin yana hannunki......na gama nawa aikin" Mammina ta fadi a nutse sanda takai dab da qofar fita daga parlor din. Bata motsa ba.....batayi kuma yunqurin fita ta bita kota dakatar da ita,don a karan kanta takeji duk wata kafa ta tunaninta ta toshe ta kuma tsaya mata cak. Lallai tana buqatar nisan tunani da kuma nisan nazari......lallai tana buqatar kebancewa,tana kuma buqatar qure duk wani nisan tunani da zatayi akan MEYE MAFITARTA?. ★Idan tace zata iya wassafa adadin abinda takeji a jiki da zuciyarta tasan tabbas tayi qarya. Wani irin yanayi ne dake d'auke da wani irin tsukewa qunci da tashin hankalin da batasan ta ina zata bullo masa ba. Abu guda daya ta sani shine.......ba zata taba bari zaituna taga rauninta ba,ba zata taba qyaleta ta fahimci tayi rauni tattare da ita ba. Iya boye yanayin da zaituna ke jefata a ciki wani kalar tashin hankali ne da ta tabbatar qarfin jarumtar dake yawo a jininta ne kawai yake tallafarta ta wannan bangaren. *_"BA'A QWACEMIN ABINDA YAKE NAWA NE NA ZUBA IDO NA QYALE,BA'A SHIGA GONATA BA TARE DA NA DAUKI FANSA BA......BAN IYA KAWAICI KO HAQURI BA......DUK WANDA YA SHAYAR DANI MADACI SAI NA SHAYAR DASHI GUBA.......DUK WANDA YA DANDAMIN ZAFI SAINA D'AN D'ANA MASA RADAD'I MAFI CIWO KODA YANA KWANCE CIKIN KUSHEWARSA......SHEKARU KO DADEWAR ZAMANI BASA HANANI KO SU MANTAR DANI AIWATAR DA FANSATA_* Maganganu ne da suka zauna mata daram a cikin kwanyarta......cikin daren farkonta data soma kwana cikin masarautar agadez......ta kuma zama MATA mallakar sultane Muhammad. Daren da ta fara sanya zaituna a idanunta madadin sultane......daren da kowanne ango shike marabtar amaryarsa....a daren zaituna ce ta marabceta........bayan ta sanyata ta dole ta amsa sunan AMARYA......duniya dukka sun kalleta da wannan sunan a madadin GIRMA DA MATSAYI na uwar gida da take dashi a qa'idance. RABOn falaak ta tabbatar shi yayi rantsuwar daya tilastata a wannan daren ta tare a masarautar da sunan matar SULTANE. Banda wannan rantsatsen rabon......tako ta ina....ta kowacce fuska bata ga ta inda zata iya kutsen shigowa ba. Har yau har kwanan gobe zaituna bata daina qoqarin binne sunan falaak......ta daina amsa sunan 'YA ga sultane ba......tana d'aga daraja tare da sunan akhnan BAWAI DON TANA SON HAKAN BA.....SAI DON FIR QARFINTA DA WATA SALON QADDARA TAYI. Taba qofar da akayi shine abinda yaja hankalinta kadan,ta waiwaya tana ajiye ajiyar zuciya,idanunta ya sauka akan falaak. Kamar ko yaushe,cikin suturar data suturce jikinta ko ina,rungume da daya daga cikin litattafanta na makaranta. Dubanta ta maida ga fuskar falaak din,kullum qara wani cika take da nutsuwa da haske. Tun daga sanda malamin ya shigo rayuwarsu taketa noticing canje canje sosai daga falaak din,saidai akwai wata fargaba kadan qasan zuciyarta dake sake fadada a ranta duk sanda ta kalli yadda falaak din take sake canzawa daga dabi'u zuwa halayenta. Bataso falaak din tayi SON MASO WANI......batason falaak din ita kuma qaddararta da jarrabawarta tazo ta wannan fannin....... Kacokam ta canza course dinta na makaranta ta koma bangaren addini,wanda ada ba wannan ne zabinta ba. "Momma.......nannie ca takeson magana dake" Ta fada tana duban idanun momma din. Kai ta gyada mata a hankali tana dauke dubanta daga falaak din,saidai maganan da falaak din ta qara yi ya dakatar da ita daga qoqarin daukan mayafinta da takeyi. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 12* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________ "Momma.......nace idan ba damuwa.....me zai hana a dinga aikawa da sheikh haisam abinci?" Waiwayowa tayi tana duban falaak din. "Shi yace yana buqata?" Kai ta girgiza a hankali. "Aah.....hasalima naga me wada da daya daga cikin masu girkin sultane yakai masa shi......sannan lokaci lokaci tare sukanci abinci da sultane din.....kawai dai naga ya dace ne,kuma kaman girmamawa ce a matsayinsa na baqo na muhimmanci a wajenmu" . Idanu ta dan zubawa falaak din,tanaso tace mata aah......to amma tana ganin kamar barinta zai iya zama wata hanya ta alkhairi a nan gaba. Ta aminta da nutsuwarta,dari bisa dari ba zata aikata abinda bai dace ba.....kaman yadda takeji akan sheikh haisam.......ta jima bataji wata irin nutsuwa me tarin yawa da tasiri akan wani dan adam.ba bayan shi. "Ba kullum ba falaak.....lokaci lokaci". "Kamar juma'a juma'a?" Ta tamba morsa safiyya cikin wani irin yanayi na zumudi. "Ba laifi" Ta amsa mata tana kewayeta ta fice,zuciyarta kuma na sake bata tabbacin abinda take zargi. Lallai akwai wani al'amarin cikin zuciyar falaak din,saidai bata sani ba,ita kanta ta fahimci hakan ko bata fahimta ba?. Koma meye zata kasance jajiryacciyar uwa da zata saita d'iyarta,ba kuma zata bari tayi wani abu da zai zubda kimarta da martabarta ba dama martabar gidansu gaba daya. Da sallama cikin nutsuwa ta qarasa tana zama gefan nanny din. Ta amsa mata itama tana duban morsa din. "Me yasa ana tsaka da magana zaki tafi safiyya?" Nanny ta fada tana duban morsa safiyya. Bata iya cewa komai da ita ba,don batasan me zatace matan ba. Bataso kuma ta buda baki abinda bai kamata ba ya fita a bakinta. Nanny tana da wani irin kima a idanunta......ba kuma zata iya manta qauna da kulawar data bata ba......bama ita din ba.....SAFEENA wanda qaunar data yiwa safeena ce ta gutsirar mata kadan daga cikin ta. "Banyi tunanin haka daga gareki ba safiyya.......na sanki.....mutum ce ke me rama halasci da halasci.....mutum ce ke me tsananin girmamawa da kyautatawa........amma kuma karon farko kina nema ki manta ki take dukkan alkhairan da mammina tayi miki?......kinsan ciwon da gorin haihuwa yake dashi kuwa?". Ta fadi maganan tana duban morsa safiyya. Idanunta ta lumshe sannan ta girgiza kanta a nutse,still bata iya cewa komai din ba,wannan ya bawa nanny daman ci gaba da magana. "Akwai ciwo.....akwai kuma zafi me yawa safiyya....ko bare wanda baki sanshi ba ban zaci zaki iya masa haka ba ballantana matar data dauki jininki FIYE DA KANTA.....Duk duniya ta shaida haka......ta mata riqon da ko kanta akace ta riqe iya abinda zatayi kenan,saidai wasu kusakurai 'yan kadan da basu kai ayi mata hukunci dasu ko ko a qyamaceta saboda su ba......da kuma rufewar idanuwa da soyayya kan iya jawowa kan ko waye ma". Wani abu me tauri morsa safiyya ya hadiye da ya wuce ta maqogoronta da qyar. Tana hange tana hasashe tana kuma ji a jikinta kamar akwai wani gagarumin yaqi dake tunkarota a gaba.......tana jin kamar akwai wani gagarumin abu da zai iya faruwa a gaba......wanda batajin tana da qwarin gwiwa ko qwanjin tallafarsa da iya nata qarfin. Sake Imani takeyi,tana kuma sake gasgatawa gami da nutsewa cikin mamaki,da gaske MAMMINA TA ILLATA KOWA A GIDAN......MAMMINA TA YIWA TUNANIN KOWA ILLA......bata ji a jikinta shirunta na shekara da shekaru yana nufin komai daidai yake tafiya cikin masarautar........nuna kishinta tsakanin ita da ita da kwantaccen salon da ba wanda zai fahimta kawai bata tunanin ya GAMSAR da zuciyar zaituna.......ya kuma bata irin nutsuwar da takeso,ko kuma ya cike wannan ramin....wannan zuciyar da kuma wannan rurutacciyar wutar fansar data gani kwnace cikin idanunta tun a ranarta ta farko. Murmushi ta saki a hankali,cike da wata nutsuwa da zata sanyaka kayi tunanin har zuciyarta abinda ke wakana kenan. "Ko kadan......ban qyamaceta......ban toxartata ba,ban kuma hukuntata ba......koda karen daya rayu tare da safeena yafi qarfin wulaqanci a gurina.......kawai abu daya na sani......bana bari a wafce abinda yake haqqina ne a gudarmin dashi xuwa muhallin da komai zai iya kasancewa.......bana kuma iya zuba idanu haqqin JINI ya toxarta......bana kuma iya tozarta alqawura mafi girma da aka dauka a lokacin da ruhi ke bankwana da gangar jikin data kasance mafakarsa ta shekara da shekaru,yake kuma bankwana da iskar data kasance mahadinsa tsahon wanzuwarsa a duniya........zaituna zataci gaba da kasancewa UWA ga akhnan kamar yadda ta tsara hakan ya kasance.......amma hakan bawai yana nufin na koma baya bane ya shige na kuma saje da 'yan kallo da wadanda suka saki ragamar sarrafuwar tunaninsu a hannun wani........taci gaba da amfana da wannan damar......taci gaba da zama UWA ga akhnan......saidai kuma akwai guguwar da idan ta taso a nan gaba kadan......ba wasu hannuwa da zasu iya tareta.....na gode sosai da karamcinki nanny....ke din 'yar uwace ta gari ga d'an uwanta.....xan qoqarin yiwa zuciyata saiti amma a sanda ya kamata". Ta sani....nanny din ta sani,akwai zaurance kalmomi masu harshen damo masu damar gaske cikin maganganun morsa safiyya.......saidai saninsu fahimtarsu ko warwaresu basu take buqata ba....salaama take buqata da wanzajjen zaman lafiya don dorewar shugabancin da mulkin sultane cikin nutsuwa da kwanciyar rai. ♣️★Wannan nazarin......da wannan nutsuwar da take buqata sune suka kwashe mata darare biyu cif ba tare data iya sarrafa tunaninta ta fidda maslaha guda daya a cikinsu game da hukuncin sultane ba. Tana jin kamar kota ina a daure take.........bata sakeji daga mammina ba......bata kuma sake yo aike daga sashenta zuwa nata ba.....sai takejin komai kamar baya tafiya daidai,saita fara jin kamar ta rasa wani bango da zata jingina dashi......ba jimawa kuma ta fahimci mammina itace qarfinta......itace jigonta......itace qashin bayanta. A hankali ta sake tabbatarwa tana buqatar mammina a kowanne hali......tana buqatar shawararta......ita daya ce tayi imanin zata samar mata da mafita. Da wannan tunanin a wannan daren ta shiga wanka,ta kuma wanke kanta da hair gel dinta ma qamshin strawberry. Maimakon ta busar dashi da tarin nau'ikan drayers din da take dasu kusan kala goma.....kawai sai taji a daren iska take buqata me kyau data fuskanci ita ke kadawa ta hanyar buda curtains din windows din dakin,iskar kuma dake tashi da wani dadaddan yanayi na qamshin qasa daga farkon damina. Tanason yanayin,amma kuma tana tsoron damina......tana tsoro ruwan sama ya tabata da yawa,ta sani iska irin wannan tana bata wani irin nishadi,tana kuma rage mata nauyin zuciya sosai.....don haka sai kawai ta shirya kanta cikin wata cotton night gown fara qal,wadda tsananin haskenta yake kashe idanu. Har qasa take,ta kuma suturce jikinta sosai,hakanan hannunta yakai har gwiwar hannu,saita dauki comb kawai bayan ya fesa turare ta kuma shafe tsadajjiyar fatar nan tata da designer cream dinta na dindindin. Kyawawan idanunsa ya sake zubewa dukkaninsu saman screen din system din dake gabansa. Wanda ya dauki a qalla awa daya zaune cikin balcony din yana qoqarin zana abun hannun nata exactly kamar yadda ya ganshi. Baya son koda qwarzane daya daya gani a jikinsa ya canza idan aka tashi qerashi,tun daga adon dake jiki da kuma nau'in color dinsa girma da fadinsa yanaso ya kasance daidai da yadda ya ganshi. Qaro hasken system din yayi,abinda ya sanya ya qara masa yawa a ido,dole ya sanya hannu qasan foldable table din daya dora system din,ya zaro farin glass din da yakanyi using lokaci lokaci idan hasken na'ura ya fara damunsa,ko buqatar sakashi ya tashi a wasu lokuta,musamman da eye glasses din ya kasance na musamman,don yana iya connecting nashi da wayarsa yayi receiving call ba tare da kowa ya gane waya yakeyi ba. Idanun nasa ya janye yana lumshesu guri daya ganin komai ya zanu kaman yadda yakeso,relaxing bayansa yayi jikin kujerar yana jin yadda gajiya ke saukar masa saboda dadewar da yayi a zaune din. A hankali ya furxar da sassanyan iska daga bakinsa,a lokuta da yawa irin wadannan idan ya gaji,karatun qur'ani ne kawai ke bawa zuciyarsa dama gangar jikinsa wani irin hutu da nutsuwa,don haka a hankali yayi bismillah,cikin muryar nan tasa me zurfi dake kamanceceniya data sheikh afif muhammad taj ya soma karatu da sassauqar murya cikin surar da yafi so cikin suroron qur'ani. A hankali take takowa zuwa farfajiyar veranda din saman nata,tana sanya hannunta tana warware gashin nata da suke sarqafe da juna. Sautin karatun da taji irinsa kwanaki ya fara sauka cikin kunnuwanta a hankali,saita ci gaba da takawa tana jin yadda karatun ke shigarta a hankali da wani irin yanayi. Shuru tayi tana ci gaba da wara gashinta cikin wata irin mutuwar jiki data saukar mata daga shigowarta gurin,wadda bata shigo da ita ba,ta tabbatar daga fara sauraron karatun dake mata wani irin mugun dadi ne yanayi ya fara ratsa gabbanta. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "What a beautiful sound" Ta furta can qasan ranta da qaramin turancinta da yaren faransanci ya rinjayeshi,saita taka a hankali zuwa saman daya daga cikin kujerun hutawa na alfarma dake wajen,zaman nata kuma a wajen sai ya sake kusanto mata da sautin sosai kusa da ita. A nutse take sauraron karatun,kamar bata qaunar wani harafi ko daya ya subuce mata. A hankali zuciyarta ke wani irin sanyi,kamar bacewar walqiya ta dinga ji tunanikan dake cunkushe a kanta suna bajewa. Nutsuwa da daidaito yana samuwa cikin dukkanin tunaninta da zuciyarta. Ta nutsu sosai ta kuma shagalta wajen sauraron sautin karatun tare da mamakin daga inda sautin yake fitowa. Daidai lokacin yakai qarshen surar ya kuma yanke karatun a hankali kamar daukewar ruwan sama,abinda ya sanyata daga kanta da sauri kaman me neman wani abu nata daya bace mata. A nutse ya ware idanunsa,ya miqe ya zauna sosai jin sautin alamun shigowar saqo ta system din nasa,abinda ya bashi tabbacin duba saqonshi na zanen bracelet din daya tura ga SHAKUR shakur din yayi,sai ya zauna sosai yana maida idanunsa ga system din,saidai kuma idanunsa fadawa sukayi side line na system din nasa dake daukar masa duk wani motsi dake gaban ginin hagu da kuma damansa. Yanayin motsin daya gani daga gaban veranda din nasa ya sanya jan arrow din ya dora saman camera ta farko ya budashi sosai,take ta bayyana tsaye cikin veranda din nata. Sassalkan gashinta da bai kammala bushewa ba ya kwanta sosai daga gaban goshinta kafadunta zuwa bayanta. Rigar ta zauna a jikinta sosai,saita maidata kamar wata 'yar tsanar roba da aka zauna aka yiwa kyakkyawan qira da zabin halitta me daukan hankali. Juyawa tayi zuwa baya sannan ta sake juyawa zuwa gaba,abinda ya bashi tabbacin akwai abinda take nema kenan. A hankali ya zame idanunsa daga saman system din ba tare daya motsa komai nasa ba banda idanun ya maidashi kan ainihin veranda din nata direct. Cikin wani nutsuwa idanunsa suka sauka a kanta,sanda ta sanya hannunta tana tattare tulin gashinta tana daureshi tsakiyar kanta,waiko hakan zai bata daman sake jin sautin da qilan zai mata jagorar da zata fahimci daga inda karatun yake fitowa. "Subhanallah" Ya fadi a hankali yana zare idanunsa daga kanta gami da saukesu saman keyboard na system dinsa yana sauraren wani bugu qwaya daya tal da zuciyarsa tayi daya aika jini me gudu da yawa zuwa sassan jikinsa gaba daya. Shuru yayi yana sauraren kowanne motsi da amsawar da jikinsa yayi gami da yanayin bugun zuciyarsa,can qasan ranshi ayar nan da Allah madaukakin sarki ya saukar zuwa ga muminai maza da mata kan runtse gani tana masa yawo akai(lowering gaze). Numfashi yaja sosai yana saukeshi,yana kuma qara imani da gasgatawa cewa babu kuskure cikin dukka umarnin da Allah ya bayar. Akwai fitina me yawa cikin KALLO kawai......shi yasa Alla sw t yayi qoqarin datse fitintinu ta hanyar kallo da dama wajen umartar bayinsa su runtse ganinsu. Numfashin ya sake saukewa a karo na biyu........wani baqon yanayi ne da bai taba jinsa ba akan kallon kowacce diya mace......duk da kasancewarsa ma'abocin kame ganinsa daga kallon dukkan abinda yake ba halalinsa ba.....amma wani lokaci yanayin aiki ko tafiya yakan hadashi da matan da ba musulmai ba da suke shigar data sabawa shari'a,amma bai taba jin komai game dasu akan wannan ba. "Dole ka sake nisantarta" Zuciyarsa ke gaya masa tana kuma tariyo masa yadda arashi ya dinga hadasu shi da ita da irin kusancin daya kusa zame masa alaqaqai kowanne kwanciya baccinsa. Kauda idanunsa ya sakeyi daga kan camera din,yana miqa hannu cikin qwarewa yayi cancel front camera din dake kawo masa hoton gaban balcony dinnata ba tare daya kalli system din ba. Sai daya samu wannan tabbacin sannan ya maida dubansa kai yana ci gaba da aikin ba tare daya sake maida idanu ko hankalinsa a kanta ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 14* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ Ba wani naqasu ko kasawa da saamee ke dashi......ta cika macen da za'a sota da dukkan quality dinta,to amma hakanan baisan me yasa yakejin a ransa bata hau mizani ba. Ya jima yana bincikar kansa me yasa yakejin kamar saamee ta rasa wani abu?.....me yasa yakejin kamar akwai wani hali dabi'a da yake nema da saamee ta rasa?. Ya dade yana tambayar kansa indai har saamee nada wani dabi'a ko halayya data rasa.....wacece?.....wacece zatayi?,wacece kuma zata cika?. Amsar daya ce har yau BAI SANI BA.....BAISAN ME TA RASA BA.....BESAN KUMA ME TAKE NEMA BA. Abu daya daya sani wanda baisan ko yana da alaqa da ganin gazawar saamee ba bawai don ta gaza din ba?..... Mutum ne da komai yafison ya mallakeshi da JARUMTARSA......komai yafison yayi YAQI kansa bawai ya sameshi daga kwance ba. Jininsa na GWAGWARMAYA NE......yana ganin komai akayi yaqi a kansa yafi zama da kima da daraja.....anfi kuma riqeshi da dukkan qarfi.......har abada kuma idan zaka kalli wannan abun zakafi tuna kanka da sunan JARUMI bawai LUSARIN NAMIJI BA. Idanunsa da suka shanye ya daga a hankali,daidai sanda yaga gilmawar inuwa ta bayan labulen dake tsakanin parlor din Bedroom din nasa. Kamar gilmawar walqiya komai ya bace,ya zubawa gurin idanu a hankali kafin kuma wani miskilin murmushi ya subuce masa. "Wannan shine iya zurfinka?......wannan shine iya qwarewar taka?" Ya furta can qasan ransa yana gyada kansa da cikakkiyar nutsuwa sannan ya miqe yana takawa a nutse yana nufar parlor din. Baiyi zaton komai zaizo da sauqi har haka ba.....bai dauka kuma zatayi zaben lusarin me binkice irin wannan ba. Amma ta wani gefen sai ya mata uzuri,tabbas ya sani,inda tasan girman had'arin da yake dashi......dan sanya idanu na gaske zata nemo ta hadashi dashi ba wannan qaramin halittar ba........amma ko meye shi ya masa daidai......zaiyi wasa da hankalinta yadda ya kamata. *AKHNAN* Komai batace musu ba,illa kunnuwanta kawai data basu tana sauraren mitarsu a kanta sanda birra ke miqa mata kayanta tana shiryawa da kanta. Tanaso komai zasuyi cikin daren nan da mammina suyishi a qare.......mafita take nema,ba kuma mafita irin wannan da sultane ya bata ba. Mafitar da zata fita gaba daya daga cikin sharuddan sultane,taci gaba da rayuwarta kamar yadda take a baya. Duk kusan mita da qorafinsu akan ta koma sahel couture ne. Jinsu kawai takeyi.....yadda takeji da kamfanin.....yadda kamfanin yake qunshe da wani irin tasiri a rayuwar qasar niger gaba daya,da yadda aikinta tuquru yakai kamfanin wani tudu da bata taba tsammani ba ko a mafarki abun ya bata tsoro. Daidai da sultane abun ya daure masa kai.......ya kuma sake daga darajar akhnan a zuciyarsa da idanunsa. Wasu irin tarin nasara da ninkuwa da komai na kamfanin yayi wanda ba wanda a cikinsu ya taba hango masa nasara irin haka a kurkusa. Sahel couture wata kyauta ce ta ba zata da sultane ya taba mata a rayuwa. Ruhin dukiyarsa gaba daya,kuma sirrin dukiyarsa,ba zatan data girgiza mutane da yawan gaske,ta sake kuma haska girman matsayinta a zuciyar sultane din,wanda hakan ya sanyata alfahari me yawan gaske. A wannan lokutan bata taba tunani ko kawowa ba akwai wani abu me suna DAMUWA da yake da tasirin nesanta da Niamey ma gaba daya bare sahel couture din kansa ba. A nutse ta karbi bakin mayafin da birra ke riqe dashi,ta kuma soma Rolling saman sumarnan tata me sulbi da data kwanta luf saboda yadda birra ta gyarata sosai ta matse mata ita cikin siririn band da bazai takurawa darenta ba. "Ba wani tunani nawa da yake daidai a yanzu.....ba wani sauran qwarin gwiwar data ragemin da zata ban damar jagorantar sahel couture yanzu.....mammina tasan da hakan,ta kuma gaya miki ke kikafi cancanta kici gaba da jagorantarsa......bansan me kike jira ba" Tayi maganar a nutse da tasirin izzarta cikin fitar kowanne lafazi daga labbanta. "Kinsan wani abu?" Shehnaz ta fada tana qarewa akhnan kallo,wadda tayi wani irin sassanyan kyau,kai ba zakace nan da wanni zata kwanta ba,saika dauka ta shirya ne don fita wani guri daban a wajen gidan. Akhnan bata amsa ba,sai aisa data dubi shehnaz alamun ita suke saurare. "Ke kika maida komai me zafi akhnan.......amma inda zaki sassauta zuciyarki......wallahi na hango miki wani kyakkyawan zabi....zabin da nake da yaqinin zaki samu nutsuwar da baki taba hange ko tunani ba......sheikh haisam akhnan......." Wata irin wawiyar juyowa akhnan din tayi......sannan ta zubewa shehnaz idanun nan nata dake da surkin kwarjini irin na d'iyoyin da sarauta ta game jininsu. "Koma meye kikeson fada abu mafi alkhairi ki barshi a bakinki.......idan kuma har shaye shaye kika fara shehnaz daga yau ba zaki sake marmarin kusantar irin abinda kika sha ba ballantana ya suranta miki qazamin tunani irin wannan har abada.........ba wani namiji daidai dani a yanzu a duniyar nan......bansan ko gaba ba,koda qaddara ta sanya na amsa sunan MATAR AURE.....to koma waye wannan mijin....." Sai bata qarasa ba ta girgiza kai da wani irin yanayi daya tabbatar musu da tarin abubuwan dake binne cikin zuciyarta,take ganin baki yayi kadan ya furtasu daidai. "Zanje naga mammina" Iya abinda ta fada musu kenan ta soma takawa tana fita a dakin. Cikin qasaita da jinta cikin cikakken tsaro take takawa a filin da zai kaita kai tsaye zuwa sassan mammina din. Wata irin iska ce me ratsa jiki take kadawa gami da kai kawo daga kowanne kusurwoyin duniya.......idanunta ta zare daga duban qasaitattun katangun dake zagaye dasu,wadanda iya kallonsu kawai na sake sanya mata jin izza da qasaita. Tabbas.....lallai inda za'a tasheta a wata rayuwa ta daban,a kuma bata zabi,babu shakka zata yita zabar kasancewarta cikin ahalin SARAUTA. Iya ginin da masarautar agadez ta mallaka da wani irin tsari da aka zamanantar dashi tayi imanin zai wahala a samu tsarin masarauta tasu kaf Africa. Sararin samaniya ta maida dubanta,duk da cewa duhun dare mamaye saman gaba daya,hakana bai hana hasken farin wata nuna hadarin dake lullube a saman ba,hadarin da ya jima yana haduwa,kuma a yau kamar yana nuna ya tumbatsa da yawa,nan da wasu mintuna ko awanni yana iya hade jikinsa dukka tsaf,ya kuma jirayi umarnin sarkin sarakuna wajen shayar da al'ummar agadez dama na nijer gaba daya ruwan farko. Iskar ta mata dadi qwarai.....kamar yadda yanayin ya mata dadi.......saidai hakan bai hana kalaman shehnaz yin suya sosai a qirjinta ba. Iya fitar furucin daga bakin shehnaz sai takejin kamar ta qasqanta......kamar neman kai ake da ita......yanzun har araharta takai haka?......me yasa sultane yakeson lallai sai ya zabtare dukkan wani girma nata da darajarta ya watsar?,har wadanda kimarsu da martabarsu batakai ba suyi tsammanin sunkai tsaikon da zasu kusanci iyakokinta?. Ba wani taku da zatayi ba'a zube a qasa bisa saman gwiwoyi ba cikjn gaisuwar ban girma,wanda ko daya bata amsa ba sai birra dake amsa mata. Wannan din dabi'arta ce......kaman yadda yake girmanta ne......baka isa tana takawa a farfajiyar guri ba kaima naka qafafun suci gaba da takawa ba,zaka jira har sai sanda ta bada baya ko tabar gurin. Girman da dukkan al'ummar masarautar ke bata banbancinsa kadanne dana sultane,kowa fata yake......qoqari yake ya kyautata mata da dukkan girmamawa saboda farincikin sultane. Tun daga qofar mammina ta farko masu tsaron qofar ke janyewa gami da sauke idanunsu qasa tare da kaucewa kallon akhnan din da yake kasancewa zunubi ne ga kowanne d'a namiji cikin masarautar muddin ba ita ta lamunce maka hakan ba. *MAMMINA* Zare wayar dake kunnenta tayi a nutse tana duban bakin qofar inda yalwa ke durqushe ta yadda bata iya hangota. "Ina neman izinin yin bayani idan an lamuncemin haka" Ta fada da wani yanayi da ya gayawa mammina akwai labari a bakin yalwa din. "An baki" Ta fada tana gintse wayar gami da ajiyeta. "Gimbiya akhnan na dab da shigowa sassannan". Shiru mammina tayi......kafin wani shu'umin murmushi ya subuce mata. Tun kwanaki data diba mata a ranta basu cika ba sai gashi akhnan din ta gaza jurewa ta nemota?. Lallai ba shakka ta wannan fannin tayi tinjimin aiki da ya kamata ta yabawa kanta da kanta. Tayi aikin daya zame mata makami mafi muni a idanu da zuciyar morsa safiyya......ta yadda bata yadda za'ayi morsa safiyya ta iya karbe akhnan daga hannunta......har gaban abada,koda itace tace akhnan din ta koma hannun morsa safiyya din,ta juya akalar girma da biyayya shawari da matsayin uwa data bata. "Banaso kai tsaye a barta ta iskeni......banaso ta samu ganina kai tsaye cikin sauqi kaman yadda yake a baya". Ta fada fuskarta na sake fadada da fara'a. "An gama" Yalwa ta fada tana miqewa da hanzari da kuma sassarfa tana sauka qasa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Sanda tazo matakalar qarshe akhnan na shigowa. Ita daya ce,ta baro birra a baya,don birra din tazo iyakacin shingen da ba wanda ya isa ya d'arashi cikin bayi ko hadimai. Qasa yalwa tayi da kanta,duk da yadda zuciyarta ke bugun uku uku amma idar da abinda ran uwar gijiyarta keso ta kuma tsara tamkar bauta yake a wajenta. "Allah ya taimaki hasken agadez......Allah ya baki yawan rai da nisan kwana......kamar giwa ta samu kwanciya nake zato......ko za'ayi haquri a koma zuwa gobe?". Cak akhnan ta tsaya daga daga qafarta da tayi zuwa stairs na farko sannan ta waiwayo ta zubewa yalwa idanunta. "Kinsan dawa kike magana?" Ta furta cikin izzar data kada hantar yalwa. "Kinsan me kike cewa?......." "Tuba nake ranki ya dade,ayimin aikin rai" Ta fada muryarta da labbanta dukka suna rawa saboda tsananin tsoron akhnan din daya shigeta. Kamar ba zata sake cewa komai ba......amma saita jinjina kai ta juya taci gaba da takawa. "Koda wasa karki sha'awar xaki sake maimaitawa" "Na tuba in sha Allahu" Ta amsa mata tana jin gwiwoyinta kamar ba zasu dauketa ba. Duk taku daya da takeyi ranta yan sake suya,yaushe tayi arahar da kamar yalwa wai itace zata mata iso?,iso fa akan mammina......mamminarta na da bau irinta kaf rayuwarta. Kaman yadda batayi sallama ba bayan ta canko dakin da mammina din zaune,sai kawai ta jingina da qofar dakin tana harde hannuwanta a qirjinta,fuskarta shimfide d wani nannuyan yanayi. Taji shigowartata,amma ba lokacin nuna batasan ta shigo din ba. Tana so ta sake shuka wannan qagautar a zuciyarta......tanaso komai ya kasance cikin shimfidadden tsarin da idan ta hau ha zancan sauka.....shakku ko kokwanto. Tanaso komai ya kasance daidai ta yadda zata iya fito na fito da dukkan wanda yace zai kawo naqasu ko gyara a tsarin.....tanaso akhnan da kanta da kuma hannuwanta tayi mata yaqin da ita ya cancanci ta yishi ba tare da ita din ta daga koda yatsarta ba. Tasan tunda ta shigo ta tsaya ba zatayi magana ba,ba kuma zatace komai ba,don haka ta waiwayo kamar me shirin daukar wani abu,saita zube idanunta a kanta. Fuskarta shimfide da alamun mamaki take dubanta. "Biftu......yaushe kika shigo?". Kai ta girgiza a hankali,tana iya hangen taruwar ruwan hawaye saman qwayar idanunta dake da wani sheqi kaman an diga mai a cikinta,idanun da idan ka kallesu zaka dauka tun asali hawayen ne a ciki,saidai yanayin halittarsu kenan. Tashi tayi daga jinginar da tayi ta tsaya da qafafunta tana duban mammina din. "Ni nazo.....nazo mammina,tunda ana dab da shiga tsakaninmu" Ta qarasa maganan tana jin duk wani rauni nata yana dawowa sabo,muryarta na karyewa,alamu suna gaya mata kuka zai iya qwace mata daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Kai mammina ta girgiza,ta miqe a nutse ta soma takowa zuwa inda take. Hannayenta ta riqe a tausashe,ta kuma sanya idanunta cikin na akhnan ta fara magana. "Bazanci gaba da kusanta kaina da gurin da zan zama abar zargi ba......ko meye zanyi cikin rayuwarki na alkhairi biftu cikin zargi nake gurin morsa safiyya da ire ir.......". zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 15* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ____________________________ "To tayita zargin mana......uwata ce?.....ko ta haifeni ne?....mahaifiya daya ce mutum keyi a duniya,sauran saidai su zama uwaye kawai......tawa mahaifiyar kuma ta rasu.....ke na zaba.....ke kika cancani ki maye gurbinta,harma gurbin da yafi nata din,don kece kikayiwa rayuwata komai da dukkan kulawa garkuwa da kuma gata". Idanunta mammina ta lumshe tana budesu lokaci guda. Wani abu me dadi taji yana rantsa kwanyarta yana sake sanyaya mata zuciya. Iya wannan aikin kawai da tayi yana sake gaya mata ita din JARUMA ce.....me jumurin jiran shekaru dubunnai domin wanzar da fansa a inda ya dace. "Sultane fa biftu?....kin shirya fiddani kunya?". Hannuwanta ta zame daga cikin na mammina,ta soma takawa tana zarcewa cikin dakin gami da barin mammina a tsaye a nan tana fuskantar qofa. " Na shirya fiddaki mammina.....saboda ke daya TAK!......saboda in saka miki farinciki da sadaukarwar da kika dade kinamin......amma ban shirya samar da mafita ni daya ba.......kin barni nayi aikin da bazan iya yinsa ni kadai ba......kin sani idan ba mammina ba akhnan?" Takai qarshen zancanta da sigar tambaya tana kuma waiwayowa gami da duban mammina duk da cewa har yanzu mammina din tana tsaye ne tana fuskantar qofa ta bawa cikin dakin baya. Dole murmushi ya subucewa mammina din. Ta sake yarda tabbas taci galaba tako ina ta wannan fannin......ta mallaki halitta mafi soyuwa a zakutan ahalin guda biyu.....halitta mafi soyuwa qirjin macen da data kasance MAQIYIYA ta biyu wadda ta maye muhalli da gurbin maqiyiyarta ta farko. Ta sani......akhnan ba zata iya wani motsi ba cikin rayuwarta.....akhnan ba zata iya yanke kowannw hukunci ba cikin rayuwarta......akhnan bata da wani zabi cikin rayuwarta face abinda ta shirya ta kuma dorata a kai.....a haka ta raineta......a haka ta girmar da ita don ta dace da irin wannan yanayin da wannan lokacin da suke ciki A YANZU!. Sai data tabbatar ta maida yanayin fuskarta yadda ya kamata ta kasance sannan ta waiwayo tana takawa da salon tata qasaitar gami da dawowa cikin dakin. Dukkanin hannuwanta akhnan ta riqe tana mammina din da wani irin rauni da tsaf zaya karya zuciyarta banda zuciyar tayi wani irin nisa da koda alamun kira bataji ballantana sautinsa. "Na baki wuqa da nama mammina......ki yanke duk abinda kike ganin ya dace.......ki zabarmin mijin aure......indai hakan shine burinki.......na tabbatar bazan cutu ba......ba kuma zaki zabamin wanda zai cutar da dukkan burika da mafarkaina ba". Hannu mammina ta sake zamewa tana kada kai gami da rabe akhnan din zata wuceta. "Sultane ya zaba miki mazaje masu yawan gaske akhnan,dukkaninsu baki karba ba,shin wacece mammina da zata aikata hakan?.....morsa safiyya ita yafi kamata ki bawa wann....." "Mamminaaaaa......" Ta kira sunanta da wani hargitsatsen yanayi. Da gaske har cikin jini da tsokarta bata qaunar shiga ko rab'ar matar cikin dukkanin lamuranta. Kiran sunanta kawai a inda take tsaye yana sanyata tana jin kamar komai nata zai tabarbare ne. "Da sultane da morsan dukkaninsu ke na zaba a cikin su.....zakimin wannan alfarmar ko bazan samu ba?" Ta fadi kanta tsaye sarautarta tana motsawa. Sosai wani abu yake sake kwanciya cikin ran mammina........tana jin dadin yadda komai yake wanzuwa......amma a wannan taqin bata shirya amsa komai ba.......tanason komai ya zamana wankakke ne daga zargi,don haka ta girgiza mata kai kanta tsaye,fuskarta na nuna lamu alamu na bacin rai. "Baza yi ba biftu a wannan karon". Cak ta qame a wajen,kwanyarta na cika da tarin mamaki. Tana duban mammina dinne amma tana ganin kamar ba mammina dinta ba?. Me jiran kokenta a kullum don ta share mata hawaye?. Me zaman jiran jin matsalarta ta kaudar mata da ita?. Wadannan mutanen dake kai kawo a ranta zuciyarta na sake tabbatar mata da sunyi nasara,su suka shiga tsakaninta da mammina dinta. "Shikenan......zanje nayi duk abinda naga dama......rayuwata ce" Ta fada kawai a taqaice sannan ta juya da wani irin fusata tana laluben qofa. Shuru tayi tana rufe idanunta,ta kuma zurfafa gami da aika kaifin jinta can nesa. "Daya....biyu.....uku....." Taci gaba da irga takun akhnan,gami da hasashen saukarta daga stairs din zuwa qasa. Bata bude idanunta ba,bata kuma dakata da lissafa takun ba har sai da ta lissafa taku talatin da biyar cif......abinda yayi daidai da isarta dab da sassan nanny sannan ta juyo da sassarfa ta mara mata baya,so samu ta hada da kiran sunanta.......amma abune da zai zama wani irin cikin birnin iko da mulkinta,don haka sassarfar kawai ta hada da ita,tana da tabbacin zata cimmata a daidai inda lissafinta ya tsaya. Kusan duk inda zata gifta duk da darene kauce mata hanya suke,sannan su sadda kansu cikin girmamawa da ganin yadda giwar sultane din ke tafiya da salon sassarfa. Sai da idanunta suka fara hangota sannan ta fara kiran sunanta,kiran daya isa kunnen akhnan din,ya kuma sanyata tsaiwa cak duk kuwa da cewa so samu ta wuce ba tare data tsaya sauraren kira mammina din ba. Dab da zata isketa nanny ke fitowa daga nata sassan,da alama ziyarar data saba fita a daidai wannan lokacin zataje,saita dakata tana duban akhnan,kafin ta maida dubanta ga mammina dake qarasowa gurin d wani irin sauri daya fita daga al'adar tafiyarta. Kafin mammina ta iso tuni nanny ta sallami dukkan hadiman dake tare da ita,ta kuma sanyasu su tsaida wucewar kowa ta gurin har sai sun bar gurin,ta maida dubanta ga akhnan. Ita takeso ta fara tambaya.....amma ta tabbatar a yanayinta ba zatace komai da ita ba koda zasu shekara a gurin,don haka ta maida dubanta ga mammina. "Lafiya zaituna d'iyarki take?". Kai mammina ta juya cike da zallae alhini tana duban nanny. A hankali ta sake sanya qafarta gaba tana barin gurin,b wanda ya sake tsaidata tsakaninsu sai kallo da suka bita dashi,kafin mammina ta tattara idanunta akan nanny "Rigimar biftu na neman zautani nanny......ban sani ba ko ke zaki iya fahimtar da ita?" Kai nanny ta girgiza tana duban akhnan data fara nesa kadan dasu kafin ta sake kallon mammina. "Duk wani abu da kika kasa fahimtar da biftu bana tunanin akwai wanda zai iya......bana tsammanin akwai me ita sarrafata". " So take lallai lallai ta azamin nema mata mijin auren daya dace da ita.....ki duba wannan girman al'amarin nanny,indai ba baqinjini takeson qaramin ba?" Mammina ta fada da wata kwantacciyar murya dake nuna karaya sosai cikin sautinta. Murmushi nanny ta saki tana dafa kafadar mammina. "Indai don wannan ne.....banga wani aibu a ciki ba,idan ana lissafin wanda yafi kowa sanin ciwo da zafin haihuwar biftu idan aka cire safeena kece ta daya......hakan da tayi ya nuna ita din d'iyace 'yar gaske da tasan girman halacci......maza kiyi hakan indai shine zai daidaita tsakaninki da d'iyarki". Idanu mammina ta zubawa nanny,a saman fuskarta shakka kokwanto da rauni suna yawo,can qasan zuciyarta kuma wani shimfidadden farinciki ne zallah gami da taya kanta da kanta murnar samuwa da kuma tabbatuwar nasararta. Nanny ta fahimci kamar maganan bata gama zaunawa mammina ba,don haka ta motsa tana yiwa shema'u hadimarta alama da hannu ta qaraso. "Kibu biftu,ki shaida mata ta dawo zuwa ga sassan mammina.....injini". " Zan sameta nanny......ta dauki zafi,rabu da ita" Mammina ta fadi tana soma takawa tana bin gwadaben da akhnan ta wucesun. Da kallo nanny ta bisu,murmushi yana fita a fuskarta. Bata taba ganin qauna irin ta mammina da akhnan nan ba....qaunar da zata iya rantsewa koda tsakanin wasu 'ya'yan da iyayensu na asali da suka haifesu babu ita. Batasan adadin abubuwan data saqawa zuciyarta ba zata aiwatar daga daren yau zuwa gobe ba. Ta riga ta zartarwa kanta a goben zata bar agadez zuwa Niamey,kuma ba zata sake lamuncewa kowa ya ganta ba. Koda sultane dinne,koda ita mammina din ce. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Dafa kafadarta da taji anyi shi ya tsaidata. Tasan mutum daya ce tak ta isa tayi hakan a gareta,don haka tana waiwayo ta fada jikinta ta rungumeta tana sakin kuka. "La....la....la,wanne irin abun kunya kike shirin bari?,hawayen sarauniyar agadez haka a fili a araha?" Mammina ta fada tana goge mata fuskarta dake kwance saman kafadarta. Wani qwarin gwiwa taji yana hauro mata kamar yadda ta saba ji.......tabbas mammina itace qwarin gwiwarta. Duk wani pattern da take rayuwa akai tsarin mammina ne. Ta nuna darajar matsayin da Allah ya bata,ta nuna mata girman da take dashi......ta karantar da ita cewa ITA TA MUSAMMAN CE.....tana da banbanci da sauran yara......tana da banbanci da sauran duk wani halitta dake rayuwa cikin masarautar. Wannan motsa mata izzar tata da tayi ya sanya ta hadiye kukanta,ta kuma bi mammina wadda ke riqe da hannunta tana takawa da ita zuwa wani kebantaccen guri dake da tarin kima a gurin mammina dama duk mutumin da zata gana dashi a gurin. Hannayensa zube cikin aljihun wandonsa yana nazartar gurin cike da tarin mamaki. Yana da kusan dukkan map na gidan amma bai taba lura da wanzuwar gurin ba. A yanzun da yake nazartar gurin da idanunsa da zaka dauka a rufe suke.....yana iya hangen yadda gurin zai iya linking nasa da wancan kebantaccen dakin ajiyar da ya zama guri na biyu da yake buri da muradin shiga ya duba wasu abubuwa da jikinsa ya jima yana bashi akwai bayanan da zai iya buqata cikin gurin. Lokutan da agogo ke bashi yakeso yayi amfani dasu a tsakanin lokutan,ya tabbatar yana cikin lokutan da dan bibiyarsa ba lallai ya sake kasancewa dashi ba har zuwa awa daya a gaba. Zai iya ci gaba da kasancewa dashi daga awa dayar har zuwa awannin biyun da zai samu tabbacin ya kwanta......daga nan kuma zai dora aikinsa ne bayan ya tabbatar asubahi tayi,wadannan sune hasashen jadawalin lokutan daya tabbatar zaiyi amfani dasu gurin bibiyarsa. Bazai dawo nan kusa ba saboda yayi motsin da ya fuskanci yaja hankalinsa har ya miqe ya maida qofarsa ya rufe A ZATONSA baisan cewa TARKO bane kawai haisam din ya D'ANA MASA don tabbatar da cewa sun fara aiki da umarninta?. Motsin sawayen da yaji ya sanyashi sake nutsuwa da kyau......muryarta kuma ta zama abu na farko daya fara shiga kunnensa. "Kin taba ganin inda uwa ta iya qyale yarinyarta tasha wahala?.....kin taba ganin inda d'iya tayi fushi da uwarta?". Ya haddace muryarta da kyau,sautinta yana da banbamci da sauran sautukan da yake ji cikin masarautar,duk da yadda yake qure qoqarinta gurin daidaita harshenta dana kowa su saje a ma'auni guda daya......ma'aunin da sai kana da qwaqwalwa da fikira irin tasa zaka iya sansani banbance banbance a tsakanin abinda aka gauraya guri daya. Ta ganshi a ranar nan,a yanzun kuma bazai zama lokacin daya dace ta sake ganinsa ba,don bai shirya ajiye zargi ko kokwanto a kansa a zuciyar kowa ba,don haka ya taka a hankali ya shiga tsakanin bishiyar dogayen yaro masu tsahon gaske guda biyu dake gurin. Wayarsa ya zaro a hankali jin alamun shigowar saqo,ya rage hasken sosai yana duba saqon daya shigo masa. Bobbo muhammad dawud ne,ya sani akwai tattaunawa da zasuyi,duk da ta chart ne ta kebantacciyar manhajar da sukanyi musayar tattaunawa,amma bai dauka zai nemeshi haka da wuri ba. Tsaiwarsa ya gyara yana maida hankalinsa kan wayarsa,ya soma maida messages din bobbo din,duk da ba hakan yaso ba,yaso yana daki a nutse,amma idan yace zaya jira kaucewar kowa baisan yawan tsahon lokacin da zai dauka ba. "Zauna a nan ki saurareni da kyau" Mammina ta fada tanawa akhnan nuni da daya daga cikin kujerun dake ajiye a gurin. A nutse ta qarasa ta zauna,sannan mammina din ta taka itama zuwa kujerar dake daura da ita. Dukkanin hannuwan akhnan ta kama ta aza saman cinyarta,ta sanya idanunta sosai cikin nata. "Inaso ki saurareni sosai da kunnen basira......inaso ki bani duk wani hankali naki da kike dashi" Kai ta gyada a hankali,batajin akwai wani sauran abu da mammina zata buqata daga gareta ta kasa yi mata shi. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 16* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________ "Kisa a ranki ni din tamkar mahaifiya nake a gurinki ba UWA ba.......ba wani tsanani da zaizo da zan iya juya miki baya.....to amma dole wataran kaza take taka d'anta badon bata sonshi ba.....aah,saidai kawai ta bashi wata tarbiyya.....idan nace a komai na rayuwarki zanci gaba da zaqewa.....zanci gaba da kasancewa a gaba gaba hakan zai iya zame mana matsala......" Takai qarshen maganar tana sauke numfashi. "Duk wank hukunci naki da zabi naki ina tare dashi biftu......duk wani kalan abu da zai saka rayuwarki a nishadi ina tare dashi biftu.......zakiyi aure kamar yadda sultane yake da buqata.....zaki aure amma zaki auri mijin da zai zamana qarqashin juyawarki umarninki da kuma haninki......zaki auri mijin da kece zaki shirya ki kuma tsara kalar rayuwar da kike buri da mafarki......mijin da bai isa ya sakaki ko ya hanaki ba,zai kasance qarqashin sarrafawarki". Idanu akhnan ta lumshe tana sake budesu lokaci guda hade da wani irin lafiyayyen murmushi. Lallai ba shakka duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi.......duk wanda ya girmeka ya girmeka har abada. Abadan duk duniya bata da wani masoyi daya d'ara mammina.....a wannan gabar har cikin tsakiyar zuciyarta da ruhinta tana jin cewa koda sultane SAI YA JIRA a soyayyar mammina a gareta......ta sake gasgata cewa idan ba MAMMINA babu ita AKHNAN.....tabbas ba zata taba kai labari ba idan ba mammina na gefanta ba. To wai me yasa tun baya ita batayi irin wannan tunanin ba?......namijin da zai zama miji a idanun sultane kawai amma cikakken HOTO a idanunta da bazai hanata aiwatar da komai da ta tsara cikin kundin rayuwarta ba?. "Kina jina?" Muryar mammina ta dawo da ita daga tunanin data fara nisan zango a cikinsa. Kai ta gyada mata tana sauke blue eyes dinta da rashin wadataccen haske ya sake sanyawa ya zama wani me qyalli da daukan idanu. Sama ta daga kanta mammina din,saboda digar yayyafi da taji cikin jikinta gami da haskawar walqiya,alamu ke nuna ruwan saman farko zai sauka kenan da yardar me duka yau a qasar agadez. Idanunta ta mayar kan akhnan,wadda yayyafin ruwan bai sanyata ta qifta idonta daga kan mammina ba. "Ki nemo mijin ki kawo......zan tsaya don tabbatuwar dukka wadannan sharud......" "Mammina manaaaa......" Ta furta da wani sassanyan yanayinta daya fusgi hankalinsa daga inda yake tsaye,inda hankalinsa yayi nisa sa maganganunsu ya tura dukka hankalinsa da nutsuwarsa zuwa ga bobbo muhammad dawud. Kyawawan idanunsa ya daga yana kallon gabanshi,duk da bai iya ganin komai sai alamunsu a mazaunin dake gaba kadan dashi. Tafin hannunsa ya sanya yana goge yayyafin ruwan daya sauka saman screen din wayar nasa yana kuma qoqarin hanashi ci gaba da sarrafa wayar saboda yadda yake dan qara yawa. Baisan me yasa sautin nata ya fusgi hankalinsa ba.......sai ya sanya tafin hannun nasa yana yiwa wayar rumfa da xummar rage saukan ruwan saman screen din,saidai a wannan karon kunnuwansa sun gaza kaucewa daga tsintar maganganunsu. "Da gaske nake mammina......na baki wuqa da nama......ki kawo duk wanda kikaga ya miki.......fatana na rayu cikin 'yanci,irin 'yancin da kowacce mace maras igiyar aure a kanta zata rayu dashi......ban taba sha'awar soyayya ko tarayya da kowanne namiji ba.....don har yanzu bana zaton an halicci irin ajina daya dace da MARTABATA". Har cikin jinin dake harbawa a jikinsa yakejin zancansu bai shefeshi ba,burinsa su matsa shima ya wuce ciki kafin ruwan yakai ga bata masa waya ko katse muhimmiyar maganar da yakeyi da bobbo......amma a wannan gurbin baisan sanda yaja wani siririn tsaki ba. Haka kawai yakejin wani bacin rai kadan kadan yana tasiri a ransa. Banda girman kan dake dawainiya da ita yana tunanin akwai tasirin jahilci. Wacce irin uwar goyo ya rabauta da ita wadda ke goyon bayan duk wani shirin shirme nata maras ma'ana?. "Zai kasance ni na zaboshi......amma ki koyawa kanki nunawa duniya cewa shine zabinki......idan hakan bata faru ba,bana tunanin zan sake zama cikin matsalolinki irin wannan har abada". Kai ta girgiza sanda ruwan ya fara damunta saboda yanayin saukarsa daya qara yawa. "Komai zai kasance kamar yadda kika buqata mammina ta......na gode da kasancewarki cikin rayuwata" Ta furta sanda suka miqe a tare,ta kuma matsa tana rungume mammina din sosai da tarin soyayyarta danqare cikin zuciyarta. A hankali mammina din ta zareta daga jikinta tana sakar mata murmushi. "Nan da kwana uku kawai zan gabatar miki da duk wanda nake ganin zaibi umarninki ne kawai". " Ba buqatar hakan......koda zamu qare zamanmu ban ganshi ba bana buqata mammina.......buqatata daya na amintar da sultane.....na fita daga fushinsa" "Idan har kikayi hakan kowa ma zai iya fahimtar komai" Amsar data bawa akhnan kenan ta soma takawa don barin gurin duba da yadda ruwan yayi qarfi lokaci daya. Idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda bishiyar ta gaza rufe saukar ruwan duka cikin kansa,duk da ta tare wani kaso da bai taka kara ya karya ba. Maganganunsu na qarshe ne suka maimaita kansu cikin kansa,yayin da zuciyarsa ta yunquro da wani qaqqarfan yunquri tana gaya masa. "Not your business haisam......not your business". Kansa ya gyada a hankali,har cikin zuciyarsa yana jin hakane,zuciyarsa gasiya ta gaya masa,wani sashen kuma na zuciyar tasa tana cike da wani irin yaqini da zargi me qarfi akan MAMMINA. Yanajin tana sake cika dukkann wasu sharuddan zargi da zato me qarfin gaske a tattare da ita......yana jin a duniya a yanzu itace bakin zaren ZATONSU ta farko.......a jikinsa yake jin akwai wani abu binne. Sultane ne kawai ya gilma cikin tunaninsa da idanunsa......yana ji da dukkanin yaqininsa akwai wani abu da ba daidai ba......amma kuma yana gayawa zuciyarsa da kansa cewa ba huruminsa bane......BINCIKE YA KAWOSHU AGADEZ.....aiki yazo yi kawai ya koma,aikin da yake sanya rai yake kuma jin cewa kwanakinsa qalilan suka rage. Ya rage baccinsa......ya hana kansa jin dadi walwala da tafiye tafiyen da yakanyi don kawai sake gane girman buwayar Allah saboda aikin kadai. Ya kasa samun nutsuwa na tsahon shekaru....baccinsa yakan yanke idan ya tuna koda kowanne lokaci rayuwar MOTII zata iya fuskantar barazana. Barazanar dake gabansa.......aikin dake gabansa yafi gaban wannan abun da yake gani a yanzu.....bayajin kuma yana da sauran abunyi akai.....abu daya ne yasa hankalinsa yake kaiwa gurin,jikinsa yana bashi matar itace zata zame musu tsani na samun wani abu ko yaya ne game da AJANI AHMED. Sauka ruwan yake da wani irin yanayi daya tayar da qamshin qasa. Sassanyar iska dake kadawa da walqiya me tsananin haske tsakanin zubar ruwan da iskar. A haka yake takawa cikin cikakkiyar nutsuwarsa,kamar ba ruwan sama ke sauka saman kanshi ba. Abu daya kawai yayi.......zare kewayayyar hular dake saman kansa,ya riqeta a hannunsa,wannan ya bawa ruwan damar sake kwantar da sumar dake kansa me yawa da kuma sulbi. Ruwan farko kenan da ake sanya ran ya kasance tafe da tarin albarka,yaci gaba da takawa yana furta ALLAHUMMA SAYYIBAN NAFI'AN da kyawawan jajayen labbansa masu sulbi. Yanayin ya tuna masa ne da jimma........tana da wani irin dadi a yanayin damina irin haka. Kyawawan shukoki da tsirrai,guraren da zaka kebe kanka cikin nutsuwa wanda yake sanyashi nishadi a yawancin lokuta. Akwai guraren na musamman daya warewa kansa cikin masarauta,wanda shi daya yake rayuwa ya kuma kebe kansa a gurin idan yaso. Gurine da ba kowa ma ya taba samun daman shigarsa ba cikin masarautar. Bai manta randa omar ya taba samunsa a daya daga cikin gurin. Sosai ya daga kai yana shaqar iskar me dadin dake kadawa a gurin,wani irin tattausan qamshi daya wanzu a gurin sakamakon yawaitar kyawawan furanni. "Gurin nan sam bai dace dakai ba......gurin nan yafi kyau da zaman masoya......ko ma'aurata.....za'a mori soyayya sosai ta gurin nan" Ya fada da dukkan gaskiyarshi. A sannan harara ya watsawa omar,yana ganin damuwarsu kawai dukka bata wuce soyayya?,amma sannu a hankali sai tunanin ya fara zauna masa.....dole ya janye shiga gurin gudun faruwar karkatar hankalinsa daga mission dinsa zuwa wani tsari da bai shirya masa ba a sannan. _AKHNAN_ Duk da warwarar matsalar tazo mata da wani gundumemen sharadin da bata taba tsammanin zai gindaya cikin rayuwarta ba,amma hakan bai hanata jin sassauci a zuciyarta ba yayin da take takawa zuwa hanyar da zata sadata da sassanta. Ba wani tsoro yau tattare da ita saboda tare da birra suke takawa zuwa sassan nata,duk da tsoron ruwan sama sa take dashi wanda ya samo asali tun daga yarinta. Kamar yadda bataso ya daketa ba tare da wani qwaqqwaran dalili ba......tun zazzabi daya taba saka mata sau daya......hakanan bata son saukarsa saboda tsananin tsoron tsawa da take dashi,amma a yau din yadda zuciyarta ta fara taurarewa da yanayin dake fuskantota,sai ta baiwa ruwan daman sauka a kanta haka kai tsaye,saidai yadda taga yana qara yawa ya sanya tadan qara saurin tafiyarta,tana kuma dakatar da birra dake qoqarin lulluba mata wata qaramar lema. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Hannu kawai ta miqa mata ta karbi sabon cherry din da aka ciro mata,wanda ya zame mata al'ada shan fruit kowanne dare bawai abinci ba. "Zan kwanta da wuri idan na shiga......kina iya tafiya" Ta sallameta don tasan akwai buhaina da bushira da yau zasu kasance a sassannata. Birran na qoqarin mata bayanin basa kusa a yau din amma tuni tayi gaba zuwa sassan nata. Ruwan na sauka da wani irin nau'in sanyi,sanyin daya ratsa fata da tsokarta,ya kuma taba zuciyarta a hankali kuma yana sauke mata maganan da suka soma yi dazu da safe da tamim. "Kiyimin afuwa.....na gaza gano komai a kansa.....dukka iya bincike na,saidai ban dawo haka a banza ba,na samo launin fatarsa......qwayar idanunsa.......da tsahonsa.....launin gashinsa......sannan an bani tabbacin dan qasar Ethiopia ne yankin jimma......" Yayi maganan yana buda mata envelope din dake qunshe da komai a ciki. Tsarin zubin halittarsa dake rubuce daki daki ta dinga kalla. Giant ne........launin fatarsa bata cika haske da yawa ba,saidai sam ba baqi bane.......idanunsa na da nau'in shape din almond......farin me haske sosai,baqinciki me duhu......fadin qirjinsa dana kafadunsa duka yana nuna halittar namijin daya kasance giant sosai.....me qirar qarfi kamar yadda ta shaida hakan daga riqon da yayi mata. Ta maida komai ta rufe tana kwantantawa da mutumin dake a mazaunin malami me karantaswa cikin masarautar mahaifinta. Akwai tarin kamaceceniya sosai a wadannan bayanan da abinda take iya gani tattare dashi......saidai har yanzu wadannan bayanan basu bata cikakkiyar gamsuwa da hujja me qarfi ba......amma ta rasa abinda yasa zuciyarta dari bisa dari taqi aminta da cewa bashi bane. Duk bata hangen wani qwarewa ko sanin rayuwa ga malamin addini da har zaisan yadda ake sarrafa doki haka da tarin hikima da kuma ilimin sanin sarrafa dabbobi,ta tabbatar ko waye zai aikata hakan dole akwai wani D'IGO na SARAUTA cikin jininsa.....koda ba ahalinta bane amma tabbas yana da alaqa da ita komai qanqantarsa. Takan bata lokuta masu yawa tana nazarin......indai har shine yanzu c Kai tsaye ta durfafi qofar sassan nata,saidai kuma ta samu a rufe take,da alama kuma me kula da wajen baya kusa. Sai a sannan ta tuna kusan ta sallami kowa sanda zata fita din. Tana da wani hali me kyau guda daya,a duk sanda bata buqatar komai takan sallami hadimanta na kusa dana nesa don suje su kwanta suma su huta,ba kasafai take barin kowa yayita tsaiwa akan hidimarta awa ashirin da hudu ba. Wani siririn tsaki taja,gabanta yana wani irin faduwa saboda yadda rugugin hadari ya fara tasowa,wanda ta tabbatar zai wahala yazo ya wuce walqiya bata biyo baya ba. Tsaiwan zai zama bata lokacine a wajenta,sai ta yanke bi ta qofa ta biyu ta sassanta dake dogon balcony din daya hada sashenta da sashen dake maqotaka da nata. Guri ne da takan dauki kwanaki bata bishi ba,musamman da yake ma ba mazauniyar agadez bace......saidai kuma idan tana buqatar kadaici,ko bata buqatar kowa ya ganta takan bi ta nan ta fice abinta zuwa dukka sassan da takeso. *HAISAM* Tun sanda ya fito da niyyar komawa ta qofar bayan ya fito. Tun sanda ya gama karantar duk wani lungu da saqo na sassan da kewayensa yasan da qofar,amma bai taba bi ta nan ba. Ba komai yake motsi ko wani action a kansa ba.....bayason yawaitar motsinsa akan abubuwa da yawa su jawo hankulan jama'a a kansa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 17* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _____________________________ Akwai abubuwan da yasan dasu,amma yayi kamar baisan da wanzuwarsu ba.....akwai abubuwan da ya sansu amma yanayi kamar baisan komai akai ba ko bai fahimta ba. Yau din ya shirya bi ta nan ne don yasan inane mahadar da ta hada nan shiyyar da kuma sashen da qofar ke a ajiye. Har cikin jikinsa yau din yakejin sanyi da saukar ruwan. Yanason damina sosai,yana cikin sahun yanayiyyikan da yafi so a dukka wasu yanayi da muke dashi cikin rayuwarmu,saidai kuma damina da sanyi sukan zama wani yanayi dake farautar nutsuwar gangar jikinsa gaba daya. Suna sauke masa wani irin feeling me matuqar nauyin gaske,don haka sau tari killace kansa yakan qara yawa ne a duk sanda aka samu mamakon ruwan saman daya sanyaya gari....ko kuma yawaitar sanyi sosai cikin dare zuwa safiya. Dukkaninsu da sassarfa suke tako stairs din dake kallon juna,wanda zata sadaka da gajeriyar veranda data hade fuskokin balcony dinsu da zai sada kowanne da ainihin sassansa ta baya. Yadda bata kula da shi ba tana kokawa da dankwalinta da ya nace saiya sauka daga kanta saboda santsin jiqaqqen gashinta.......daya hannun kuma tana rungume da Cherry's dinta da mistake kadan zatayi su zube......idan kuwa har suka zube ta tabbatar zai zama ba rabonta bane,don ba komai yake taba qasa ba tacishi ba,dare kuma yayi da ba yadda za'a sake shiga garden din a debo mata wani. Saidai duk da yadda takai ga takatsantsan da sauri idanunta sun rufe,kuma cike suke da tsoron da har ta iso dab dashi a sanda hankalinsa shima ke kan keys din hannunsa yana duba wanda yake na qofar. Bangazar juna sukayi,kuma a take cherry din da yake tattali ya watse daya daya a gurin. "Subhanallah" Ya furta da deep voice dinnan nasa dake cike da sound na nutsuwa a cikinta yana yin taku biyu baya,kamar yadda itama taja baya da sauri cikin matsanancin tsoro,bugun zuciyarta ya sake ninkuwa ta ware manyan idanunta sosai a cikin sassauqan hasken da bame yawa ba,tana jin wani irin yanayi yana shigarta a hankali saboda shaqar wannan qamshin da tayi. Wannan qamshin dai da har yanzu ta gaza gane waye ainihin mamallakinsa?.....wannan malamin dake a gabanta yanzu?......ko abokin tserenta ne daga hippodrome?. Wannan qamshin dai daya tsaye mata a kwanya......ya yiwa kansa kyakkyawan gurin zama tsakanin tunaninta zuciyarta dama kafofin hancinta. Dukka idanunta ta ware ta zuba masa,duk da cewa bata iya ganinsa tarwai,amma tana iya ganin yadda sumarsa me santsi ta kwanta sosai har saman goshinsa ta kuma sauka sosai a qeyarsa. Walqiyar data gilma me tsananin haske ita ta bata daman hango wadannan idanun.......wadannan idanun dai da suka hanata sukuni.....wadannan idanun dai dake sake bata qaimi cikin kowanne taqi da taku nason cimma mamallakinsa ta masa hukunci me tsauri.....wadannan idanun da ba abinda take hanga a cikinsu face kallon raini da qanqanci da suke mata,tun daga wancan ranar har zuwa yanzun da walqiyar shima ta bashi daman ganinta sosai,amma a nutse taga ya janye idanunsa daga dubanta kamar yaga wani abu mafi muni ko qyama. Yanayin kallon daya jefa mata,ya kuma dauke idanunsa hankali kwance kaman baiga barnar da yayi mata ba ya tunzura zuciyarta sosai. Ba wani d'a namiji daya isa ya tsaya gabanta kamar haka koda baiyi mata barna irin haka ba,ballantana shi daya watsar da cherry din da bata taba daukar wani abu daga takun daya haura goma ba sai yau. "Kamar dai baka gani......kamar dai makaho ne kai?" Ta fada cikin hasala tana laluben maganganun da zata fada masu zafi. Tun daga wancan ranar da taga yadda sultane ke nan nan dashi wani kakkaifan haushi da tsana sauka sauka a ranta game dashi,daga sanda ta fahimci da gaske sultane ya bashi matsayin da nata ne ita kadai ta sake jin bata da sauran ABOKIN ADAWA da yayi saura duk duniya saishi. Da gaske tana da kishin a dauki son da ake mata ko kalar kulawar da ake mata a bawa wani. Tsarinta ne haka,ta taso ta tarar komai nata ne.....komai ita daya akewa......ita kadai ake saurara......so ba zata juri hada komai da kowa ba.....koda kuwa falaak ce......bata lamunta ta tsaya matsayi d'aya daidai dana falaak din. Tana ganin sam bai cancanci matsayin da sultane ya bashi ba......malami fa?,me karantarwa?.....me sultane zaici dashi?,me sultane zai qaru dashi?,banda shi din da zai sake zamewa sultane din kayan nauyi?. Tana tunanin zaya daga kai yayi mata kallo na biyu ne.....wanda yake fatan hakan ta kasance ko don ta samu hanya ta biyu da zata sake fadin magana me zafi,wataqila ta rage haushin dakw zuciyarta,amma ga mamakinta bai ko yi niyyar karkatar da kallonsa a kanta ba......tamkar ba wani halitta me rai dake tsaye a wajen,sai ya tsugunna a nutse yasa hannunsa yana tattare cherry din guri daya. Ta fahimci so yake ya tattare mata ya bata abinta ba tare da komai ya sake cewa ba......a yanzun ba wannan take buqata ba.......ko yaya tanaso ta gaya masa magana me zafi da zata damu ransa,don haka sai taja siririn tsaki. "Koda ka tattarasu........kimata ta wuce naci abinda ya watse haka a qasa" Cak ya dakata daga tattarawar da yakeyi,ya sanya tafin hannunsa saman gwiwarsa ya miqe cikin tarin nutsuwarsa ba tare da ya daga kai ya dubi inda take tsaye ba. A nutse ya fara takawa yana nufar balcony dinsa. Tarin mamaki ya kusa daskarar da ita. Wanne irin mutum ne shi?,dame yake taqama?,ya manta qarqashin alfarmar mahaifinta yake rayuwa?,ya manta wace ita?,matsayinta?,da girman ikon fada aji da take dashi da bazai mata yadda dukka sauran hadimai ke treating dinta ba?. Inda daya daga cikin mutanen dake rayuwa cikin gidanne,wadanda suke qarqashin ikonsu da kulawarsu kamar yadda yake shi din a yanzu ya aika mata haka,lallai da yanzu yana durqushe cikin feshin ruwan yana hurwar ta yafe masa,amma sai gashi shi cikin nutsuwa ma yake barin gurin. Wannan fusatacciyar zuciyartata ke gaya mata. "Waye shi da zai aikata mata hakan kuma ya wuce lafiya salin alin?" Wannan fusatar ita ta sanyata takawa d'af d'af,ta kuma sha gabansa sanda yake shirin dora qafansa saman step din da zai shiga balcony dinsa. Da dukkanin blue eyes dinta take kallonsa da wani irin kwantaccen fushi. Tana son bashi assignment da har ya gama rayuwarsa cikin gidan bazai gama dashi ba.......idan har girman kai yakeji tanason ta yage wannan rigar girman kan. Ba jiya ko shekaran jiya ba......ta hangi wani tasiri na izza tattare da dabi'arsa,wanda take ganin baikai ace akwai wannan cikin jininsa ba,a matsayinsa na malamin da baisan komai ba sai karantarwa. Qasqantar da kai ne kawai ya kamaceshi ga masu mulki da sarauta irinsu,bawai nuna izzar da sam bai mallaketa ba,baibi hanyarta ba,baima san ina muhallinta da zai ajiyeta cikin qualities dinsa yake ba. Tsakiyar idanunta yake kalla da kyau,duk da qarancin hasken dake wajen amma bai hanashi gano zallar girman kai da tsiwar dake dawainiya da ita ba. Walqiyar da aka sakeyi mai madaidaicin haske ita ta sake haska masa fuskarta sosai. Kwantacciyar sumarta data sauka har gadon bayanta da kuma kafadunta ta bayyana sosai saman zagayayyar fuskarta dake da wani irin sirrintaccen kyau me wani irin sanyi. Mayafin dake saman kan nata ya koma rabi saboda santsin gashin da kuma yadda iska ke kadashi kadan kadan. Idanunsa ya zare daga kanta da wani irin mutuwar dukka gabbansa yana maida dubansa gefe daya. Tsaiwarta a gurin wani abu ne da zai iya masa tasirin da baya buqata,dukan da ruwa ya yiwa jikinta ya sanya doguwar rigar silk material din mannewa a jikinta sosai,ta kuma fidda shape na gurare da yawa a jikinta,shin ita bata ganin hakane?. Yaji tambayar tazo kansa. Idanunsa ya lumshe sannan ya budesu,yana jin yadda feshin ruwa ke sauka saman fuskar tasa,yana kuma jin yadda taci gaba da qananun mitoci wanda ya cakuda da sautin ruwan dake sauka saman roofing din veranda din. Siririyar muryar dake da wani irin taushi......taushin da bai hana bayyanar tsiwarta qarara ta cikin maganganunta ba. Dare ne......wanda saukar ruwan sama kan iya hana kowanne mutum dake nesa dasu qarar kowanne sauti komai girman sautin. Tana tsaye gaba kadan dashi da tazarar da bame yawa ba......duk wanda ya gansu a haka a irin wannan lokacin a kuma irin yanayin da ita take ciki ba shakka ba abinda bazai iya ayyanawa ba a ransa. Baya son ya sake aza idanunsa a kanta,don ya tabbatar duk yadda zaiyi don ya kaucewa kallon guraren da bai halatta ya gani din ba abune me wahalan gaske,don kusan rabin sumarta a bude yake. "Zaki iya matsawa kiban guri na wuce princess?" Ya fada calmly ba tare daya waiwayo ko ya aza idanunsa a kanta ba,saidai kuma can qasan ransa fushinsa ne yake motsawa kadan kadan,wanda bayason yayi wani motsi da zai tasirantu a kanta. Fushinsa na yadda ta tsare masa hanyar shiga sassansa,duk da akwai sauran space da zai iya wucewa din,saidai yayi qanqantar da zai wahala ya wuce lafiya ba tare da sun gogi jikin juna ba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Ranta ya sake baci,ta sake zubawa gefan fuskarsa da kwantaccen qasumbarsa me tsari ta sake kwanciya saboda jiqewa da tayi idanu. Abinda take magana akai daban?,abinda yake fadi daban?,damuwarsa kawai ya wuce?.....tana magana dashi yana dauke idanu zuwa wani sashen na daban?. Ko waye ko kuma meye sultane ya daukeshi wannan karon sai ta sanya an hukunta matashi,irin hukuncin da nan gaba bazai sake mararin koda hada hanya da ita ba. Daidai sanda ta bude qaramin bakinta daidai lokacin wata irin walqiya me kashe idanu da wata irin tsawa gauraye ta karade sararin samaniya. Idanunsa ya lumshe yana motsa labbansa a hankali da addu'ar tsawa da ma'aiki ya koyar "Alhamdulillahil lazi yusabbihur ra'adi bi hamdihi.....walmala'ikatu min kifatih". A hankali ya bude idanunsa suka kuma sauka a kanta. Tana tsugunne a qasa ta cure guri daya. Ko ina na jikinta rawa yake,wanda yake bayyanar da tsananij tsoro a tattare da ita me yawan gaske. Idonsa ya sake daukewa ya maida gefe,sai ya qara sautinsa yana maimaita addu'ar a fili daidai da yadda zata iya ji. Duk da muradinsa shine ya wuceta abinsa kafin bacin ransa yakai ga bayyana......amma fuskar sultane yake iya hanga a gurin......kebantattun maganganunsa da sukayi......maganganun da suka tilasta masa aminta da alfarmar da sultane ya nema a tare dashi bai ko iya musa masa ba. "Ko yaya idan akhnan na cikin hadari.....nakanji wani abu a jikina,nauye nauye sunyimin yawa.......bazata samu kulawata yadda ya kamata ba,don Allah ko yaya koda sau daya ka zama me kula da lamarin daya shafeta daidai yadda zaka iya,ba don kowa ba saidon GIRMAN ZATIN ALLAH" Sautukan dake dawo masa kenan a yanzu.....yana kuma sake ji da ganin yadda dan qaramin amincin dake tsakaninsa da sultane keson takurashi. A tsanake ya juya a hankali yana nufar sashen qofar balcony din nata bayan wasu sakanni. Maqullansa ya zaro,cikin hikima irinta qwarrarun jami'ai da suka goge ta fannin aikin tsaro binciken sirri dana qwaqwafi ya bude qofar. Takowa yayi a nutse yana dawowa nashi qofar,tsugunnawarta ya bashi space sosai da ya samu ya wuce a tsanake,ya isa qofar balcony din nasa ya zura key ya bude qofar ya turata sanna ya sanya qafarsa a hankali bakinsa dauke da addu'ar shiga gida. Da sauri ta daga kanta sannan ta waiwaya zuwa bayanta,daidai sanda yake maida qofarsa ya kulle abinsa. Zumbur ta miqe tana waiwayen hagunta da damanta. A yanzun ba kowa a gurin,a yanzun ita daya ce sai ruwan saman dake sauka,wani tsoro ya sake mamayarta,ba shiri ta fara tattakawa da sassarfa tana nufar qofartata wanda ta sameta a bude,da hanzari ta shige sannan ta maidata ta rufe tana maida numfashi a jejjere kamar wadda tayi tseren gudu. Sai data kusa kashe a qalla mintuna goma sannan numfashinta ya daidaita,ta saka hannu ta zare yalolon mayafinta daya jiqe ta yar a gefe,ya kuma sauka daidai kwandon Cherry dinta dake dauke da Cherry din. Wani tsaki taja baqinciki yana taso mata. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 18* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________ Yadda yayi matan yafi zubda Cherry din bata mata rai,ita zaya bari a gurin da ko izinin tafiya bata bashi ba?.....wai yana Manta wacece ita?......baiga yadda kowa ke treating nata ba da kulawa da kuma respect?.........matsayinta yake mantawa ko kuwa?.....lallai dole ta sanyashi yayi dana sanin aikinsa a kanta....dole ta sakashi ya koyi yadda zai girmamata......ko wanne matsayi kuwa sultane ya bashi dole ya gane akwai banbamci tsakanin d'an gida da yaron gida. Inda wani abun ya sameta a inda ya barta ma kenan baida asara shi?. To waye ya bude qofar balcony din?,don tayi imanin ba wani a kusa ballantana ta dauka shine ya bude,saita dora tafin hannunta saman kanta tana jin gaba daya lissafinta yana dagulewa. Ta saba da a girmamata cikin kome da zata buqata........ta saba ta bada umarni nakai tsaye abi........ta saba tayi kome da takeso bame iya daga kai ya kalli qwayar idanunta ballantana yace tayi ba daidai ba......a yau din sai takejin kamar an mata babban wulaqancin da duk duniya ba abinda yake sama da wannan,sai kawai ta juya tana shigewa ciki cikin wani irin fusataccen yanayi. Duk sunan hadimar da yazo bakinta shi take kira da qarfi,wani irin gini ne da ruwan da akeyi a waje sam idan kana ciki ba zaka sani ba saidai ko idan ka kalli windows ko glass doors din da aka qawata wasu bangwayen dasu,wannan ya bawa duk wadanda ke kusa da nan damar jin muryar uwar gijiyar tasu,suka kuma bar dukkan abinda sukeso kowacce ta taso don amsa kiranta. Kamar kowanne mutum da ya kwana ya tashi cikin agadez qasa sukayi da kawunansu kamar yadda suke tsugunne a gabanta. "Uban waye yace ku tafi ku kwanta ba tare dana shigo ba?" Tayi tambayar data bawa kowa mamaki a cikinsu,kasancewar sunsan tsarikanta. A lokuta irin wannan bata buqatar a dameta,bata buqatar kuma kowacce irin hayaniya a kusa da ita,kowa yasan wannan,kowa ya haddace wannan,don haka kusan tafiya kowa yake zuwa makwancinsa. Maimakon ta dauki shurunsa a matsayin girmamawa,don babu me iya bata amsa a cikinsu,sai kuma hakan ya tunzarata da wani irin kalar bacin rai. Fada sosai ta dinga yi,kalar fadan daya sake bawa kowa mamaki a cikinsu......kalar fadan da ko sanda tasha guba bata yishi ba. "Ranki ya dade...." Birra dake da wannan qarfin halin ta matso dab da ita ta fada da yanayin da yaja hankalinta kadan. "Kayanki a jiqe suke,sanyi yanata shigarki.....kiyi haquri ki canza kaya sai kizo kiyi mana duk kalar hukuncin daya dace". Maganan birra kenan data sauketa,ta juya tana haurawa zuwa sama a zafafe ba tare data sake bi takan kowa ba,tana isa kuma ta wuce dakin data zaba kwana a ciki ta murza key,don ko birran bata buqatar ta kusantota a sannan. Da d'aya da d'aya ya rage hasken fitilun dakin yana jin zuciyarsa wani iri ba dadi. Fushi ke motsa masa amma yanata maimaita a'uzubillahi minashshaidanir rajeem don ya sani saukowar fushi daga shaidanne. Yana saisaita room heater ko zai samu sanyin jikinsa ya ragu ya fahimci omari yana nemansa,sai ya qarasa ya dauki na'urar ya azata saman table hade da wayarsa da damshi kadan ya tabata,ya sakata a hands free yana yana qoqarin balle links din hannun rigarsa don zare rigar daga jikinsa,ruwan da ya tabashin ya sanya wani lallausan qamshi na tashi a jikinsa na unique perfume dinsa. "Barka da dare captain sheikh" Omari ya fada da salon tsokanar da wani lokaci yakanji sha'awar tsokanarsa da ita. "Yauwa" Ya amsa masa can qasan maqoshinsa,adams apple dinsa yana motsawa daga sama zuwa qasa,daya daga cikin alamun fushinsa kenan. Dan shuru omar yayi,yana jin sauyi tattare da haisam din,saidai kuma ya sani,shi din wani kalar introvert person ne,ko a yanzun daya dauka wayarsa yana kyautata zaton haisam din yana tsammanin maganar aiki ce,baisan wasu awanni zai nema a bashi ba. "Ya palace din?" Ya tambaya a taqaice kada sakannin daya ware na amsashi ya qare. "Fine" Kawai yace yana zare rigar samanshi,fara qal din cotton singlet dinsa tana bayyana wadda ta lafe a jikinsa,ta kuma fidda qirar ginannen jikinsa da faffadan qirjinsa dake cike da lallausar gargasa. "Awa ashirin da hudu nakeso a bani aro" Omar ya fada "Zuwa ina?" Ya tambayeshi yana duqawa zuwa ga fuskar wayar ranshi yana jin yana sake jagulewa. "Zinder kawai zanje....." "No..." Ya fada kai tsaye yana katseshi. "Baka tambayeni abinda zanje nayi ba" "Ba buqatar hakan" Ya sake amsashi a taqaice. "Just 24hrs fa?" "I said nooooo!....." Ya fadi a zafafe da wannan zuzzurfar muryar tasa. Shuru ne ya ratsa tsakaninsa da omar din,lumshe idanunsa omari yayi yana ji a ransa akwai abinda ya taba zuciyarsa a yau din. Ya sani haisam din yana da fahimta yana kuma da sauqin hali.....saidai idan ya tashi baudewa ko bacin rai yana da tsananin taurin kai da kafiya. Ba ma'abocin fada bane.....don yafi ganewa shuru a yawancin lokutan da ransa ya baci maimakon magana ko nunawa a aikace......dole yasan akwai abinda ya taba ranshi daya sakashi replying masa maganansa a haka. Wayar kawai omari ya sauke a kunnensa sanda yaji alamun ya gintse wayar,qaramin murmushi yayi ya ajeta gefe,ya jawo daya wayar tasa yaci gaba da amfani da ita,da cikakken tabbacin haisam din zai sake nemansa. Silent ya maida wayar da kuma na'urar tasa,ya sanya dukka yatsunsa goma cikin jiqaqqiyar sumarsa yana jin yadda ransa yake sake dagulewa. Kome meye ya zama dole ya gaggauta matse kwanakin aikinsa yabar masarautar. A dazun banda tasirin sabo da aikinsa da yayi,saura kadan wannan jinin na SARAUTA dake motsawa cikin jininsa ya sanyashi yin wani abu da yasan dole zai d'arsa zargin WAYESHI a zuciyar yarinyar. "She's stubborn......" Ya fada yana motsa fresh lips dinsa da suka sake wani irin kyau da daukan hankali. Numfashi sosai yaja ya kuma fesar,ya lumshe idonsa yana budesu sanda yake nufar hanyar bathroom. Me yasa?......me yasa?,tambayar da yaketa maimaitawa kansa da kansa kenan,ba tare da yasan akan ainihin meye yake tambayar ba. Yana da hadari a karan kansa ya sani......aikinsa ya dauke hankalinsa daga kan komai da kuma qoqarin bin umarnin Allah da yake cewa. "Ka gayawa muminai maza mu runtse ganinsu su kuma kiyaye farjinansu" Me yasa take qoqarin shiga kowanne runtse ganinsa?....kame kansa da idanunsa?. "Me yasa kake damuwa bayan a baya baya damunka?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar sanda ruwan daya saisaita ta hanyar shower me tsananin dumi ya soma sauka tsakiyar kansa. "Zaka kai lokacin da duk wani guje guje bazai maka ba saidai aure......kana da lafiya......cikakkiyar lafiyar da ba kowa keda irinta ba......kaga kuwa aure ya zama wajibi....dole a kanka.......ka gama duk ayyukanka na watanni ko shekarun daka tsara....wallahi dole sai aure.....shi kadai ne ya dace dakai". Daga daga cikin maganganun amjad kenan a wani yammaci da suka shirya picnic cikin gari jimma iya su yasu. Baice da khadeem komai ba,shi da Amjad dake goyon bayansa,ya bishi ne da idanu kawai. Bakasafai ya fiya magana me tsaho da khadeem ba,don ta fannin magana ba zaka taba kadashi ba,don baya gajiya da ita......shi kuma daya daga cikin abubuwan dake masa wahala kenan,musu ko maimaita magana,yafi ganewa zama shuru don yafi bashi nutsuwa da nazartar abubuwa a yanayin da suka dace. Wannan ya sanya maleek wani lokacin yakan kirashi da mr introvert bayan mr lowering gaze da suka bashi. Murmushi kadan yakanyi,bai hana kowa kiranshi da sunan da yayi masa ba a tsakaninsu su shidan,don kusan alaqa ce da aka ginata tun kafin a gama mallakar hankalin kai. Duk wani magana da bayani da sukeyi akan aure ya sani.......ya karanta komai,yana da tarin ilimi akan aure da ma'amalolinsa wanda su sam basusan yana dashi ba.......ya tara ilimi akan fannnin aure da mu'amalar miji da mata masu tarin yawa cikin litattafan manya manyan malaman addini masana asalin ilimin zamantakewa wanda basu da adadi. Ya karanci zamantakewa a gidaje masu yawa......gidajen sahabbai gidan annabi S A W kanshi baisan adadin littatafan daya dubasu ba.....bugu da qari ya fisu sanin aure ya wajabta a wuyansa.......don idan akwai inda yake da rauni to ta wannan fannin ne.....shi yasa ya lazamci azumi ya kuma lazumci kame idanunsa da nesanta kansa daga dukkan wata mu'amala data shafi 'ya'ya mata.....to amma yanaso ya yishi ne a sanda ya samu gamsuwar zai iya doguwar rayuwar da BABU SAKI tsakaninsa da duk macen da zai aura din. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Yanason ya zabi macen da yakejin komai nata yayi masa,macen da hankalinsa bazai sake kaiwa kan kowacce 'ya mace ba bayan ita.......yanason kuma komai ya kasance a right time da zai spending rayuwarshi da ita cikin tarin nutsuwar da zataji a ranta gidanta na aljanna......mijinta na aljanna ne aka gaggauto mata dashi duniya.....ba a irin wannan lokacin da ta kowanne bangare tunaninsa yake a jagule da rashin samun gamsuwa da tsaro rai lafiya da rayuwar motii ba. A gaggauce ya shirya kansa cikin wata long sleeve riga ne nauyi da zata bashi kalar dumin da yakeso,sannan ya sanya wandonta da yake mahadin rigar. Yana gaban mirror yana sake kwantar da sumarsa tunanin abinda ya faru dazu ya sake dawo masa. Dauke idonsa yayi daga mirror din yana jan tsaki jin yadda tsigar jikinsa ta zuba. Bata da kunya ko kadan.......shi din kuma mutum ne me mutuntawa da baya shiri da masu wannan dabi'ar,wannan ya sanya ya tsaya tsayin daka akan ANANI sanda ta fara irin wannan dabi'un,sai daya tabbatar ya saitata yadda ya dace. Da kanshi ya hadawa kansa coffee,yana jin sassan ya masa shuru. Dole tasa ya sanya abdii ya koma personal gidansa,don kwanakin kadan kadan ya tsara zai dinga yi yana komawa ainihin gidansu,harsai sanda yaga abdii din ya dauki saiti da salon da yakeso,ya kiyaye duk abinda yace ya kiyaye din. Hannun hagunsa ya soke cikin aljihun wandon nasa,na damansa kuma yana sipping coffee din kadan kadan. Shan tea da coffee wata halittacciyar halitta ce a jinin duk wani dan Ethiopia,musamman jimma oromia dake noman coffee din gaba daya. Cup din ya dire bayan ya shanye,omari yana fado masa,sai a yanzun yaji kamar baiwa omar din daidai ba. Aboki ne kuma dan uwa shaqiqi a gareshi,saidai wasu lokutan dole yanayin aiki ya sanya ya mu'amalanceshi irin mu'amalar uban gida da yaronsa.....don komai a rayuwa yana buqatar saiti. Na'urar ya dauka ya kunna,ya kuma tura masa permission letter gajeriya ya tura masa. Sanda saqon ya sameshi murmushi ya saki,dama ya sani......indai haisam ne zai dawo. Dabi'unsa masu ban sha'awa ne qwarai da burgewa,saiya maida masa amsa cikin girmamawa a matsayinsa na ogansa bawai abokinsa ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 19* ★★★Dare makwantar mugu inji hausawa......tabbas haka yake,a irin wannan daya daga cikin wadannan dararen da suka kasance da busawar sanyi sakamakon saukar ruwan saman da aka samu a daren jiya,hakan sai ya zamanto sanadin daukewar sawayen mutane da wuri daga waje zuwa gidajensu dama dakunan baccinsu. A tsakiyar wannan daren mammina ke ratsa cikin unguwar. Daga gefanta TA FISU ce......tafisun da sunanta yayi daidai da aikinta dama alfanunta a gurin mammina. Tafusun ta kasance wani bangare me girma da muhimmanci tattare da mammina wanda yawancin mutane basu san da hakan ba basu kuma fahimci haka ba. Duk da kasancewar ta fisu me girman matsayi a sassan mammina din......amma dukkan wani aiki da motsi nata yana nuna zallar rashin jituwa da rashin samun fada da fuska tattare da mammina din. Yana da wahala ka samesu sun kebe.....kamar yadda yake da wahala kaji ta ambaci sunanta idan har wani muhimmin abu ya taso mata. Hasalima saita kasance me yawan tafiye tafiye.....don kusan cikin gidan kowa ya sani cewa tana tafiya wasu qasashen sarin kayan kasuwancinta,tazo dasu gidan ta siyar tas ta sake komawa ta saro wasu ba tare da takurawa ko saka takunkumi daga wajen mammina din ba. Daga nesa can suka baro mutum biyun da suka zamo amintattunta na gaske gaske,wadanda ta sanya suka musu tattaki cikin shigar da ba zaka gane daga ina suka fito ba. Tayi hakanne saboda daren daya soma yi,daren yayi nisan da fitar zata iya zame musu qalubale,duk da cikakken yaqinin amincin da yankin nasu yake dashi. *HAISAM* Sanye yake da long sleeve hoodie shirt a jikinsa baqa wadda ta dace da yanyin sanyin da yake busawa a gari ta kuma dace da skinny jeans din jikinsa. Saman kansa baseball cap ne wanda ya lullubeta da hular dake maqale da rigar jikinsa. Boots ne a qafafunsa masu tsananin daukan idanu,duk kuwa da duhun daren da kuma kalarsu da suka kasance baqaqe. Dukka hannunsa zube yake a aljihun wandonsa saboda sanyin da yake kadasu,idan ka ganshi a lokacin ba zaka taba dauka shine sheikh haisam ba. Dressing dinsa baqo ne da sam ba kasafai ya fiya yinsa ba,amma yana tsananin fidda wani irin sirrin kyau tattare dashi gami da bayyanar da zallar quruciyar dake yawo cikin jinin jikinsa. Sosai wannan tsahon nasa ya fito,tsahon da dole ka kirashi da GIANT kai tsaye a iya kallon farko kawai,tsahon ya dace da yanayin cikar jikinsa da kuma murjewarsa,wanda kai tsaye wasu lokutan zaka iya kiransa gabjeje saboda yawan motsa jiki da qarafuna da injina masu nauyi da yake yawaita yi. Ko a yanzun daya kasance wani irin dare me yawan shuru,cikin nutsuwar nan data zame masa dabi'a yake takawa abinda,kai bakace ya dauki duhun dare ko nisansa a bakin komai ba. Ba wani tsoro ko firgici a tattare dashi,daga fuskarsa har zuwa zuciyarsa,zuciyarsa dake motsawa can qasan qirjinsa tana kuma maimaita ayoyin qur'ani da maimaitasu din ya zama wata dabi'a ta ruhi da zuciyarsa a duk sanda ya samu kansa cikin shuru da kadaicewa kaman haka,ayoyin shafi na biyun qarshe na cikin suratu al_imran,wanda ke bayani akan halittar sammai da qassai da kuma jujjuyawar dare da yini,tsarkake girman ubangiji kan yadda ya halitta ya kuma tsara komai. Bayan haddar qur'ani gaba dayansa da Allah ya azurtashi dashi......akwai tafsirinsa daya kammala tun yana da shekaru goma sha takwas a duniya zuwa sha tara,don haka a duk sanda yake karantashi yana jin kamar yarensa yake magana dashi saboda fahimtar fassara da ma'anar kowacce aya,don haka ko a yanzun da yake karanta ayoyin yana sake girmama zatin Allah daya halicci dare,daren kuma ya zama mahutar kowanne bawa.....mahutar kowacce irin halitta. Shuru yakan mamayi ko ina,zirga zirga tana taqaita a bisa dole,jikkuna suna kusantar makwancinsu zuwa ga bacci,baccin da yake tamkar dan uwan mutuwa saboda karbar ruhin kowa da Allah yakeyi. Yana dawo da ruhi da rayukan wadanda yaso suci gaba da rayuwa,ya kuna riqe ruhikan wadanda kwanakinsu suka qare a duniya. (Fahimtar ma'anar qur'ani a sanda kake karantashi abune me wani irin gard'i da ba zaka fahimta ba sai in kana gane ma'anoni da fassarar ayar,kuyi qoqari yaranku su fahimci hakan,zai taimakawa hankulansu imaninsu da tarbiyyarsu,hakanan BACCI abune daya kamata a kiyaye ladubban yinsa,akwai addu'o'in da sukazo na bacci kala kala,a cikinsu kuma akwai wadanda suke dauke da addu'ar neman gafarar Allah idan daga wannan baccin rai yayi halinsa,shi yasa akeso kafin ka kwanta ka cika da aiki me kyau,kamar nafila ko karatun qur'ani istigfari da sauransu,da yawa cikin novel nasan muna qoqarin saka nafila yayi sannan ya kwanta ko shafa'i da wuturi,duka muna qoqarin nuna muku kafin ya kwanta ko ta kwanta wani aiki me kyau tayi,do bakasan zaka tashi ba ko ba zaka tashi ba,Allah ya bamu cikawa da kyau da imani). K'irjinsa cike yake da jiran sakamakon abun hannun da ya tura a qera masa,a yanzun tunaninsa yayi nisa zuwa ga yadda zai fidda asalin abun hannun daga ma'ajiyarsa zuwa gurinsa don gudanar da binciken da zai zame masa mabudi na farko kuma tsani na farko da zai fara takawa zuwa ga inda mai laifinsu yake. Zuwa yanzu ya gama karantar tsari da yanayin unguwar gaba daya,kusan ya gama da komai daya shafeta cikin dararen da yake fita. Ya gama sanin manyan mutanen dake rayuwa a cikinta,adadinsu sunayensu dama ayyukansu. Idonsa ya sake daukewa daga sararin samaniyar da yau sam ba alamun hadari sai taurari data bar musu,yana sauke dubansa a gabansa,daidai sanda ya sake ganin gilmawar mata biyu. Mata biyu kamar wancan karon,kamar wancan lokacin,da irin suturar daya gani a wancan lokacin,saidai banbancin kawai a yanxun ba wata mota daura dasu,da qafafunsu suke shiga layin. Da wani irin hanzari ya jawo baseball cap dinsa da hoodie dinsa ya rufe fuskarsa da kyau,da wani irin kuzari kuma ya nufi layin da yaga sun shiga din cikin kula da takatsantsan da motsinsa. Sanda ya isa babu su ba alamarsu,ya qarasa a hankali qasan wata matashiyar bishiya data bada rassa ba masu yawa ba,wadda aka dasata daga farkon layin,ya jingina sosai da ita yana sake sajewa a jikinta. Da dukka wannan fikirar da basirar yake bin gidajen dake jere cikin layin da kallo cikin nutsatsen nazari. Layi ne da yake jerin sahun layikan da suke dauke da manyan mutane sosai fiye da kowanne layi......layi ne kuma da yafi kowanne qarancin zirga zirga na jama'a koda kuwa da rana ne. Ci gaba yayi da kallon gidajen,kowacce qofa a rufe take,ba wata qofa guda dake a bude,abinda yaso cakuda hankalinsa kenan ya kuma so kauda tunaninsa ya gaza sanyawa kowanne gida a ciki wata ayar tambaya. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Kai ya girgiza a hankali,ko kadan bazai yarda da kwanyarsa a lokacin ba,lokaci ne daya kamata tayi aikinta yadda ya dace. Ganin gilmawar wasu mata sanye da uniform na gidan sultan of agadez......a dare irin wannan daya zama doka ce ta hana shiga da fita cikin lokaci irin wanna har sai safiya tayi. Da wani salo da yanayi na tafiyar da batayi daidai da tafiyar da ake yinta bisa qwarin gwiwa gaskiya da rashin tsoro ba. Yayi nisa......akwai tazarar da zai zamana zai wahala ace kusanci ne ya kawosu unguwar.....ko cudanyar maqotaka,unguwanni ne dake maqotaka ada juna,saidai kuma mabanbanta ne. Da cikakken kuzarinsa ya miqe daga jikin bishiyar,ya kuma tsaya qyam da qafafunsa yana sake zube hannuwansa a aljihun wandonsa sosai yana sake zube idanunsa akan gine ginen. Iska sosai ya zuqa yakai hunhunsa sannan ya furzo da ita daidai sanda lissafinsa yazo kan gida na shida. Idanunsa cak ya tsaida akan gidan yana qare masa nazari. Kowanne gida dake layin yana da sassauqan fenti da bai tsufa ba bai kumayi sabunta da yawa ba,amma shi wannan gidan sabon fenti gareshi. Kowanne gida akwai sassauqan haske dake nunawa kadan,alamun wani girin fitilunsa a kashe suke,wani gurin kuma a kunne,amma wannan gidan dundum yake,ba wani alamun haske komai sirantarsa a tattare dashi. Akwai mazubin shara gaban kowanne gida don inganta layin,amma daya lura sosai babu mazubin sharar a gaban wannan gidan...... Sake zagayawa yayi da idonsa sauran gidajen kafin ya sake maida dubansa gaban gidan. Daga alamunsa daga waje yana da yalwa da wadatar da za'a iya shigar da mota cikinsa kamar sauran dukkanin gidajen unguwar da layin,amma motar tana fake a waje ita daya qwallin qwal...... So samu ya qarasa jikin motar,ya duba wadanne lambobi ne a jiki,duk da motar daya taba gani anbi diddigin lambobin jiki,saidai duk zurfin binciken da sukayi basu samo komai a kanta ba,hasalima plate numbers din isn't valid a region na agadez dama nijer gaba daya. Saidai kuma a tsari irin na aikinsa yasan hakan zai iya zama da hadari......takawa koda d'ani guda ne daya inda yake tsayen zuwa gaba,komai zai iya faruwa,wanda inda sabon ma'aikaci ne shi ko maras gogewa yasan abinda zaiyi kenan,saidai a aiki irin nasu......akwai wasu damarmaki da kana ji kana gani zaka barsu hakanan su wuce su subuce maka saboda wani dalilin da yafi wannan qarfi da amfani. Sake bin layin yayi da kallo,akwai dan kiosk qwara biyu tal,wanda a binciken layukan da yayi na wancan lokacin dukkaninsu suna saida qananun abubuwan da shiga kasuwa zai zamewa mazauna unguwar wahala. Sai ya janye manyan idanunsa da suka rusuna kadan,ya saka yatsansa cikin kunensa,take wani red light yayi blinking na wasu sakanni sannan aka fara magana. "Ina buqatar beeno yanzun nan,a bunu street,banaso ya haura mintuna biyar don ina hanyar barin layin.......gida ne number ta shida.......ya zama shine target din" Ya qarasa fada yana kuma gimtse kiran kai tsaye. Ya samu iya abinda yake buqata a nan din,yanaso yayi gaba kafin wadanda suka wuce din su dawo ko zai samu nasarar sake samun wani abun da zai bashi haske daga hanya har zuwa cikin gidan sarautar,sai ya maida hannayensa zuwa ga aljihun wandonsa ya soma takawa a nutse da kuma lura yana barin gurin. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 20* *MAMMINA* Tun daga farfajiya ta biyu take iya jiyo sautin almaz cikin hargagin data tabbatar tashin hankali akeyi dashi. Idonta ta lumshe kafin ta budeshi cikin bacin rai gami da jan qaramin tsaki. "Kamar muryar yaron nan nakeji" Mammina ta fadi don samun tabbaci. "Shine......ba shakka shine" Ta fisu ta fada tana jinjina kai. Shuru ya biyo baya,tamkar mammina din ba zata ce komai ba kafin ta sake magantuwa. "Banda target ne cikin rayuwarsa gaba daya......banda wata shiryayyar qaddararsa ce data ahalinsa ke tunkararsa wadda ba makawa saita samesu......tabbas da na canza yaron nan". Wani murmushi ta fisu ta saki "Dabi'unsa zaki canza bawai shi din zaki canza ba,aikinmu na yanzu shine mu canzashi zuwa yadda mukeso din,mu canzashi zuwa kalar mijin burin AKHNAN.....abun harinmu shine ya mamayi rayuwarta ta soshi fiye da yadda takeson SULTANE dole muyi sadaukarwa me yawa akan hakan don tabbatuwar wannan MANUFAR don samun zuri'a daga garesu cikin sauri kaman yadda buri da mafarkinki suke......ki barni dashi" Tafisu ta fadi suna buda qofar da zata sadasu da ainihin gidan,don tuni sunsan da zuwanta,anbar komai kuma ta yadda zata samu daman shiga ciki ba tare da kowa ya fito ko yazo ya bude mata ba. "Na rantse idan baka bani ba......zan kubce muku irin kubcewar da ba zaku taba samoni ba!!!" Ya fadi da wata tsawatacciyar muryar data sanya wata mummunar faduwar gaba saukarwa mammina......muryar ta cilla can qololuwar cikin tunaninta,ta lalubo wani sauti da yayi sak da sak da wannan sauti da muryar da almaz. "Akwai wani dan tasirin kamanceceniya a sanda yake magana cikin fushi?" Ta yiwa kanta tambayar data saka zufa tsatstsafowa a goshinta. "Tafisu.....banaso ya sake magana cikin fushi.....banaso na sakejin yanayin sautinsa yana fita cikin fushi" "Na fahimta" Tafisu ta fada tana jinjina kai wani kalan murmushi na fita saman fuskarta. Wannan murmushin wani kalar abune da a wasu lokutan yake bawa mammina mamaki. Duk yadda takai ga iya wasan kwaikwayo cinye firgici da damuwa.....maye gurbin tsananin tashin hankali da sassanyan murmushi tafisu ta fita iya buga wasa ta wannan bangaren. "Amma kuwa da ka yiwa kanka da kanka asarar tulin arziqi......tulin jin dadi maras yankewa da yake jiranka....." Muryar tafisu ta ratsa hargagin almaz da wani irin murmushi.e taushi saman fuskarta tana dubansa. A fusace ya waiwayo,suka zubawa juna ido shi da tafisu suna yiwa juna kallon kallo har sai daya janye dubansa yana furzar da iska daga bakinsa,wannan ya bawa tafisun daman isa gabansa. Zamewa tayi cikin salo na sarauta ta durqushe a gabansa cikin tsananin girmamawa tamkar tana gaban sultane "Ranka ya dade....... Kai da kake shirin zama suruki ga qasaitaccen sarkin africa irin sultane?.....kai da kake shirin mallakar da jagorantar gurin da yafi ko ina kawo maqudan kudade kaf dukiyar surukinka?......kai da kake shirin zama mutum me qololuwar martaba?....ina kai ina wadannan tarkacen a yanxun?......" Idanu ya zubawa tafisu yana jin wani abu me kama da girma girma yana sauka saman zuciyarsa.......tasirin girman ya soma danne tasirin fushinsa,yana saukar da wani sassauci a dukka zafin da zuciyarsa da jikinsa ma ya dauka. Ta fahimci hakan tafisu,bama ita kadai ba hatta da mammina din,saita dan dago a hankali. "Inda zaka nutsu ka kwantar da hankalinka......ka bamu aron nutsuwarka da kamalarka na wani dan lokaci......gaba kadan daki guda zaka mallaka na dukka kalar kayan da kake kwadayin sha kakejin labarinsu kuma baka taba samunsa ba......ko daga wacce qasa yake kuma ko daga wanne yanki ake kawoshi sarrafashi ko nomashi......amma fa lallai sai kayi haquri na wani dan taqaitaccen lokaci". Idanunsa ya dauke,yana jin wani girma yana saukar masa. Karon farko da cikin dabi'arsa yakeso da buqatar wannan girmamawar da bai taba samunta ba,a yanzun sai tazo masa da wani irin yanayi da yaji kome akeso yayi zaiyi,indai zaici gaba da samun wannan girmamawar,don haka ya koma ya zauna dabas saman daya daga cikin tsadaddun sofas din dake masa dadin kwanciya sosai tun xuwansa gidan. A sace ta kalli mammina,mammina din ta jinjina kai cikin tsananin mamakin yadda tafisu ta iya sarrafa komai cikin qasa da mintuna biyu kacal. Almaz din dake da wahalar sha'ani,tsananin taurin kai da rashin jin magana,kafiya da tsaiwa cak akan abinda yasa kanshi amma ta iya cinsa da yaqi haka da sauri?. Qarasowa tayi ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa tana dubansa. Yayi fresh yayi kyau a kwanakin kamar yadda ta buqaci ganinsa haka,saita dauke idanunta ta maida kan tamim dake tsaye,wanda tunda suka shigo bai sake cewa komai ba. "Kana iya komawa masarauta,yau a ciki zaka kwana,akwai yiwuwar sultane ya nemeka da safe koda asubahi" Kai ya jinjina yana rusunawa cikin girmamawa,sannan ya juya yana nufar hanyar fita zuciyarsa tana matsewa guri guda. Shuru dakin ya dauka na wasu sakanni,kafin ta fisu ta matso tana ciro wata jaka daga qugunta. Wareta tayi ta fito da wasu takardu da kudade ta zubesu saman table din data jawo zuwa tsakiyarsu. "Muna maka murna......zaka samu 'yanci fiye da yadda tsuntsun dake shawagi a sararin samaniya ke samu". Kalmar 'yancin da tafisu ta ambata itace taja hankalinsa har ya dago da kansa da a dazu suke kallon sama. Yanci itace kalmar da yafi buqatar ji,yasha gwada yin nisa da rayuwarsa dama duk mutanen da ya sani don yayi rayuwar tasa a yadda yakeso cikin sakewa.......amma baya nisan zango yake sake tsintar kansa cikin wadannan mutanen dai da yake tunanin ya yiwa nisa. Duk inda ya motsa rayuwarsa kamar ana monitoring dinta ne.......rayuwar sa tana zagaye ne da wadanda keda iko a kansa wanda ba kasafai ya fiya banbancesu ba.....kamar yadda yake rayuwar ba tare da sanin hagunsa ko damansa ba,daidai da rashin daidai dinsa ba.......saidai ba abinda ya gane daga qarshe illa KUDI. Ya fahimci sune suke da ikon sarrafawa mutum komai yadda yakeso.......ya fahimci sune suke da qarfin ikon sawa ayi koda ba'aso,a kuma bari koda ba'aso ba,don haka har ransa yakejin ya karbi tayin wannan aikin don kaiwa ga buqatarsa,wannan ya sanya ya miqe ya zauna sosai yana duban bayanan da tafisu ta soma masa kan takardun da adadin abinda zai iya zama nasa. Murmushi kawai yakeyi yana jin mafarkansa suna budewa zuwa reality. Aikin duka ya masa wani irin sauqi,don tako ina ribarsa yake hangowa ba wata faduwa a ciki. Matsalarsa da damuwarsa qwaya daya ce.......kayan mayensa da suka zame masa jini da tsoka.......kayan mayensa da baisan yadda zai sarrafa kansa ya haqura dasu na watannin da suke fadi ba. Amma dukka yana hangen ba laifinsa a ciki,dasu aka ciyar dashu aka shayar dashi kuma aka tufatar dashi tun haihuwarsa. Tunda ya fara wayo,tunda ya fara sanin me ake kira da DUNIYA da RAYUWA sune ababen karin kumallonsa.....abokan rayuwarsa safiyarsa zuwa darensa gaba daya. Wuninnika da darare masu yawa suna zuwa su shude ba tare daya sani ba,ba tare da yasan me ya faru a cikinsu ba,ba kuma tare da yasan kwanakin sati nawa ya shafe a bugensa ba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Ci sha da sutura dukka ba matsalarsa bane.... Duk da tun tasowarsa baya aikin komai.....bai iya aikin komai ba.....ban taba shiga makaranta ba,bai taba riqe biro ko fensir ba sai sanda ya cika shekara ashirin cif.....aka masa mummunar tarkiyar da baisan dalilinta ba,baisan kuma daga ina abun yazo ba aka koya masa rubuta sunansa da sauran abubuwan da zaka tsammaci karatu yayi.....daga nan ya koma rayuwarsa ta baya,amma bai taba rasa lafiyayyen abinci da sutura ba. Kaman yadda dakinsa yasha banban da dakin kowanne d'an gata,saidai baisan cikakkiyar ma'anar rayuwarsa ba. Suturunsa masu kyau da tsada da cimarsa ya sanya wasu suke kallonshi a ne girman kai. Girman kan da baisan ma ma'anarsa ba. Kawai dai ya sani yana da tsananin zafin zuciya,ba ruwansa da kowa don bayason raini ko maganan banza,yanzun nan ya yima mutum dukan mutuwa ba komai bane a wajensa,kuma ba wata hukuma dake iya kamashi,wanda Shima baisan me yasa hakan take faruwa ba. *HAISAM* Daga nesa dashi cikin duhuwar yake iya hasashen wani kalar motsi a tsakanin wasu shukoki da aka qawata street din dasu,idanunsa ya qanqance kadan yana kaifafa ganinsa gami da rage hanzarin tafiyarsa,cikin qwarewa kuma yake sake kusantar inda yake iya hasashen motsin,saidai kadan ya rage ya isa kunnuwansa suka dauko masa motsin wani sauti daga bayansa wanda kwanyarsa ta bashi akwai 'yar qanqanuwar tazara a tsakaninsu. Da hanzari idanunsa suka bashi gurin tsaiwa daya dace,hakan yayi ya saje da duhun gurin yana duban agogon dake d'aure a hannunsa yana irga taku da daqiqun da suke shudewa har zuwa sanda yaji an wuce ta gabansa. Idanunsa ya aza sosai yana bin bayan wanda ya wuce din da kallo yana lissafa fadin kafadunsa zubin tafiyarsa da komai take kuma kwanyarsa ta harba masa BABBAN TAMIM ne. "Asitti maal hojjechaa jirtu?" Tataccen yaren oromo ya sauka a kunnensa da salon tambayar ME KUKEYI A NAN? tamkar yana cikin qasar Ethiopia yanki oromo. Hannun nasa ya sauke da wani irin hanzari. Sautin babban tamim ne......hakan yana nufin shima YAREN OROMO NE?. "Dhiifama,nuti Madame eegduu(muna neman afuwa,uwargida muka rako)" Muryar wani ta bayar da amsa,wanda take ya daidaitata da muryar tamim qarami. "Tsaiwarku a nan kuskure ne,kuma hadari ne,don lokaci ne na hana zirga zirga ga kowanne mazaunin cikin fada.......idan lokacin dawowarta yayi kowacce hanya zata kasance mata a bude.....muje ciki zan saita hakan" Tamim ya fadi sannan kuma takunsu ya dadu alamun dukkaninsu suna komawa ne ciki. Wani irin mamaki ya hanashi motsawa daga gurin har zuwa shudewar wasu mintuna daya tabbatar ba za'a samu wanzuwar kowa a gurin ba,koda me jira da bibiya ne sannan ya ciro jikinsa daga gurin yana takawa a nutse yana nufar katafaren ginin masarautar dake gabansa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE PAGE 21* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ____________________________ Kenan ba mutum daya ba kawai.....ba kuma mutum biyu ba,akwai qarin wasu mutanen dake jin da amfani da yaren oromo?. Yana takawa a nutse amma yanason tantance waye asalin TAMIM cikin mamallaka sunan guda biyu?. Suna ne baqo da ba kasafai aka fiya sakashi ba cikin qabilar oromo......tabbas dole akwai mamallakin sunan na asali.....akwai wanda kuma ba asalin sunansa bane. Cikin kulawa ya zagaya ta shiyyar da yakan koma cikin gidan. Ya tarar da HILAL tsaye bakin qofar cikin shiga ta masu tsaron qofar kamar yadda suka saba tsaiwa da kuma sanya suturarsu,ya dage masa qarfen tsaron da akan rufe qofar cikin matuqar girmamawa yana bashi hanya. Hannunsa kadan ya motsa alamun yabawa hilal da jinjina yana wucewa cikin gidan. Kansa tsaye ya wuce sashensa yana qoqarin jingine tunanin don bibiyar beno akan aikin daya turashi. Agogo ya kalla,zuwa sannan ya tabbatar beno yana dab da isa gurin indai ya isa akan daidai lokacin da ya tsara masa,don haka ya qara sauri yana murza key ya buda sassan yana shiga yana motsa labbansa da sallama. Saman kujera ya hangeshi,abdii ne kwance rigingine,ya kife wani littafi saman qirjinsa da alamu suka nuna yana tsaka da karantawa bacci ya daukeshi. Can qasan ranshi yayi murmushi wanda sam bai nuna ba koda saman labbansa,ya taka a hankali ya zare littafin yana ajiyewa gefe. Ko yaushe abdii yana maida kansa yaro saboda shi. Koda yaushe abdii baida zuciya indai a kansa na,baya fushi sam,ko me zai gaya masa don yayi nesa dashi kaman yadda ya buqata baya yarda da hakan,baisan wanne irin qauna haka yake masa ba. To amma a irin wannan yanayin da al'amura suka fara bayyana kansu sam bayason abdii din ya cika kusanci dashi. Gefan qafafunsa ya tsaya ya miqa hannunsa kadan ya tabashi,sai ya bude idanunsa kuwa da sauri. "Ka koma ciki ka kwanta" Yace masa kawai yana haurawa sama idanunsa kan agogo yana ci gaba da lissafa lokaci. Kayan jikinsa ya zare bayan ya samu signal na beno,ya kuma musanyasu da wasu farare qal din pyjamas masu dogon hannu da tsananin taushi. Wani irin kyau yayi duk kuwa da cewa ba tufafi bane na ado,sassalkar sumarsa ta kwanta luf saman kansa ta kuma dan hargitse kadan garin sanya pyjama din jikinsa,sai ya qara fita ya duba ma'ajiyar coffee dinsu,ya sameta cike da zazzafan coffee. Yana da sauqin kai a abubuwa da dama,da kansa ya zuba cikin wata qawatacciyar tea pot. Sosai balcony din ke masa dadi,wannan ya sanya ya taka zuwa ciki dauke da tea tray din,ya kuma dora saman wani stool dake da wata zagayayyar sofa me taushin gaske. *AKHNAN* Tafukan hannayenta duka biyun ta shafa saman lallausar fuskarta data haska cikin rolling din dake saman kanta,wanda ta yishi da mayafin after dress din jikinta data sanya saboda sallar isha'i da tayi yau a makare. Duka yau din bata iya tsinana abun arziqi ba,tun bayan da sukayi magana da mammina akan gobe zata gabatarwa da sultane mijin data zaba. Zataje ita daya,ba zata mata rakiya ba wannan karon,fuskarta kuma ba zata bayyana ba,don magana ce tsakanin uba da d'iyarsa. Tana jin nauyin sultane har cikin jininta na yadda zata iya kallonsa ta gaya masa ga mijin da ita take so ta aura,ga kalar zabinta. Mijin da ko sau daya taqi yarda taga koda hotonsa. Maida idanunta tayi ga aisa dake kwance rub da ciki sama gadonta,yau haka kawai tayo qaura ta taho dakinta kwana. Ta taho da dukka ayyukan sahel couture tace a nan zatayi,wai ko hakan zaisa hankalin akhnan ya koma ga kamfanin. Tun dazu take aikin tana kuma mita. "Komai na enterprise ya tabarbare.......komai baya tafiya akan tsari da doka,kina wasa sa shugabancinki,komai yana shirin lalacewa,iya abinda zamu iya riqawa nida shehnaz munyi......mammina ta kasa aiwatar da komai akai,ban sani ba,tsananin yardar data bawa mutanen ne ko kuwa?" Aisa ta fada da gasken gaske tana hango downfall na kamfanin. Tana gano yadda wani taqi kadan ya rage kamfanin yakai qasa warwas,ta soma jin kishin wahalar da sukasha a kamfanin,ta soma jin ANYA BA ZATA KARBA ba kamar yadda mammina ta fada?. "Ta rayuwar me sahel couture din ake yanzu haka........idan sahel ta fadi dasa hannunki a ciki......mammina tace ki karba saboda tasan a yanzu banda energy din komai amma kin wofantar......ki daina complaining min komai aisa" Ta furta tana miqewa daga saman abun sallar. Iska me kyau takeso ta shaqa sama da wadda ke cikin dakin ko zatayi tunani me kyau,saita ware rolling din,saidai bata sauke dankwalin duka a kanta ba,ta doshi qofar da zata sadata da private bedroom balcony dinnata. Da kallo tabi akhnan,ba wani abu da yake daidai a yanzun a tare da ita da gaske ne........tana jin kawai zata karba......zatayi accepting,ba tare da TUNANIN KOMAI BA ta soma rubuta doguwar wasiqa me dauke da sharhin karbar office din akhnan din a madadinta wadda za'a sanar da kowanne department. A hankali take takawa a cikinta tana zuqar fresh air din da kyau tana aikewa hunhunta,ta kama dankwalin da kyau cikin jikinta tana curewa guri daya saboda sassanyar iskar dake kadawa wadda keda dan qarfi kadan kadan. Gaba ta matsa jikin qarfen da ya yiwa gurin qawanya ta sanya hannunta ta dafeshi tana duban qasan stairs din daya kasance wata farfajiya dake bayan gidanta da takan zauna lokaci lokaci. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Iska ta fitar sirirya daga bakinta,tana dan ji a jikinta kamar ba ita kadai bace tsaye a gurin,saidai ta sani,ba wani mahaluqi daya isa ya tsaya a inda take tsaye a lokaci irin wannan idan ba aisa ko shehnaz ba,wanda dukkansu ba daya daga ciki. Ido ta lumshe sannan ta budesu tana jin wata kewa tana ratsata,a wasu watannin baya da suka shude,ba wani abu da yake bata nishadi irin wannan lokaci. Tana jin dadin tsaiwa a wajen,tana jin dadin irin iskar da gurin yake bayarwa,tana kuma sake samun cikakken nishadin da tunda ta tashi a rayuwarta nishadin kawai ta sani,batasan wani abu waishi baqinciki qunci ko bacin rai ba,sai a wadannan kwanakin,sai a wadannan lokacin da aka hana rayuwarta da tunaninta sakat akan 'YA'YA MAZA!. Yunqurin shigarsu rayuwarta kawai yana neman gigita mata rayuwa,ina ga ance yau gasu cikin rayuwartata?.......da dukkan qarfin ikon da zasu mallaketa su kuma sarrafata?.....ita ta dade da fahimtar sam BA ALKHAIRI ciki wannan halittar a rayuwar mace me gata da 'yanci irinta. Siririn tsaki taja tana dauke idanunta daga qasa tana dawo dashi sama saboda wannan kalar qamshin da take jiyoshi kamar nesa kadan da ita. Kai tsaye kuma idanun nata suka sauka a kansa,sanda yake tsaye gaban nasa qarfen balcony din,ya maida hankalinsa sosai ga wayar hannaunsa yana dannata da wani irin sauri kamar me wasa da abun wasan yara saboda tsananin haddade mazauni da muhallin kowanne keyboard dake fuskar wayar. Beeno yake maidawa amsa da sauri gudun faruwar kowanne kuskurd,ya fadi masa kada ya sake yayi magana dashi saidai ta hanyar tura saqo,yaci gaba da zama a gurin kuma har zuwa sanda zasu tabbatar ba fita ko motsin wani,sannan yanaso ya yiwa gurin alama......gobe akwai na'urar da yakeso su sanya a gurin. Tsaiwa yayi cak bayan ya tabbatar saqon yaje,sai kiran omar ya shigo masa,abinda ya sanyashi daga kansa daga kallon wayar ya karata a kunnensa wannan. Shuru yayi manyan fararen idanunsa suna dan juyawa kadan,kafin a nutse ya motsa kyawawan labbansa da dumin coffee din daya fara sha ya sake sanyasu suka zama masu laushu,color dinsu kuma ya fita sosai "Yes...." Ya amsa maganan omari da wani irin calmness da haka kawai yakejin jikinsa yana mutuwa. "No omari......" Ya sake amsawa yana lumshe idanunsa da mamakin baqon yanayin dake shiga jikinsa lokaci daya. "Continue observing......don't act yet.....I'II handle it" Ya fadi yana gyada kansa a nutse. Zare wayar yayi daga kunnensa,hankalinsa yana kan device din dake maqale a kunnen nasa wanda yake monitoring motsin beeno da kyau. "Reduce the noises beeno,motsinka ya danyi yawa" Ya fadi a hankali a nutse yana jj kaman shine a gurin yana sake matsawa gaban balcony din hankali da idanunsa suna kan wayarsa. A hankali ya zare dubansa daga kan wayar yana daga idanunsa a sanda yake sanyata a aljihun wandon jikinsa.......kai tsaye idanun nasa suka zarce kanta,sanda take tsaye cikin wani haushi da bacin rai dake tsirowa daga qasan ranta. Tana sanye da fararen kaya yana sanye dasu......ashe bayan jubah da jallabiyyar da yake sanyawa har yana da zabin sauya kaya cikin dare haka don ya samu sakewa cikin masarautar da take mallakin ubanta?.......tana tattaki saman farfajiyar data kasance tata ita daya a matsayinta na 'YA GUDA kuma mallakin sultane muhammad hammud......shima ya samu irin wannan chance din a matsayinsa na BAGIDAJEN malamin da ba abinda ya sani sai zallar litattafai larabci da yaren da qila na uwa ne.......sai hausarsa da yake yinta da qyar wadda sam bata mata dadin saurare. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 22* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ Ta mallaki sashe guda......shima sultane ya mallaka masa sashen daya kasance cikin sassan masu girman daraja cikin gidan. An bashi masu tsaronshi......an wadata shi da dukkan abinda aka wadatata dashi.....to wai shinma mens bambancinta da wannann BAQON kuma DAN CI RANI wanda ya shigo cin arziqin mahaifinta?. "Morsa safiyya ce sila" Sashen Zuciyarta dake cike da tsanarta ya gaya mata kai tsaye. Ta gamsu sama da dari bisa dari ba,duk wata matsala daga matar yake,duk wani hanya da zata tozarta gami da qasqantar da matsayinta itace a gaba gaba......waishin TA YAYA ZATASO WANNAN MATAR?.....HAR GABAB ABADA!. Kai tsaye idanunsa suka gauraya guri daya,wanda kafin yakai ga hakan idanunsa suka soma sauka ga sassalkan gashinta da iska ke wasa dashi tana watsashi daga hagun fuskarta zuwa dama. Bata kwanciya da kowanne nau'in ribbon saboda takura,wannan ya bawa iska daman kada gashin nata duk yadda taga dama bayan ta zame dankwalin nata daga kanta zuwa kafadar hagunta ba tare data sani bama saboda tsabar yawan tunani da bacin ran dake cunkushe fal qasan zuciyarta. Sosai ta kafeshi da dukka kallonta.....wadannan idanun ababen zargi ne a gurinta.....wadannan idanun da take da muradin musu zuzzurfan kallo,wanda ta tabbatar idan tayi hakan tsaf zata iya ganewa da fahimta.....SHINE NA HIPPODROME?. "SHINE" Wasu lokuta zuciyarta ke gaya mata. Ta tabbatar qaqqarfan haushi da tsanarsa da takej bayan rashin jituwa na cikin jini da jijiya da takeji akan dukka gidadawan malamai irinsa......wanda basu da wani arziqi daya wuce na zama su karantar da takarda.....akwai wani kwantaccen abu na daban kuma daya qara assasa hakan. A yau tana jin zata zurfafa kallon wadannan idanun da batasan me ya banbantasu da sauran idanu ba .......duk da kaifin da takeji yana shigarta.....duk da kaifin da takeji kamar suna dashi,shigen kaifin da takanji cikin idanun sultane wasu lokutan da suke hanata duban sultane din kai tsaye a yawancin lokuta. Duk da 'yar qaramar tazarar dake tsakaninsu amma hakan bai hanashi hangen tsananin IZZA da GIRMAN KAI gami da TSIWA me qarfin gaske cikin idanunta ba,ya barta ne taci gaba da duban qwayar idanunsa kaman yadda ya fahimci muradinta kenan......kamar yadda ya fahimci tanaso ta karantashi ne ta idanun da yayi imanin koda shekara guda zasuyi tsaye a gurin ba zata iya karantar duk abinda takeson ta karanta daga gareshi ba......sai idan shi yaso......sai idan shi yaga dama ya buda mata hakan. Duk wani motsinta na binciken abokin tseren wasanta yana da masaniya akai.....zuwan tamim na qarshe....wanda shi ya yarje su bashi gwajin tsahon da komai nasa. Yayi hakanne saboda yana son tantance zurfin kwanyarsu,yana son gane zurfin tunaninsu da tsinkayensu,amma sai yaji duka ya rainsu da wannan gwajin ya kasa kaisu inda ya kamata ace sunkai. Har gwara ita yana mata kallon mace me rauni ta kowanne fanni,amma ga tamim fa?,da yake cikakken namiji daya zama amintacce a wasu kebantattun ayyuka na musamman cikin gidan?. Damqe qarfen tayi da kyau tana qwararawa kanta gwiwar ci gaba da kallon tsakiyar qwayar idanunsa a sanda taji wani abu me haske yana ratsa cikin idanunta,yana soke duk wani confidence nata.......a sanda take hangen kallon da yake mata da bai nuna komai ko wani yanayi na ita din ta masa kwarjini ba kaman yadda ta saba yiwa kowa da zai kalli idanunta haka kai tsaye a gurare daban daban,wani irin calmness duba yake mata don qure qarfin gwiwar da takeji tana dashi. Da wani irin mugun sauri kamar numfashinta yana shirin qwacewa daga hunhunta ta kauda fuskarta gefe tana sauke wani kalan numfashi me tsananin nauyi. Sai ya janye idanunsa shima daga kanta yana sake fiddo wayarsa a nutse abinsa saboda duba mintunan da beeno ya shefe ba tare da ya sake jin motsinsa ba kwata kwata. "Me yasa na kasa?" Ta tambayi kanta. "Me yasa yake kasancewa a duk inda bana buqatarsa?" Ta sake tambayar kanta a wannan karon baqinciki da bacin ran yadda ta gaza ci gaha da dubansa yana mamaye Zuciyarta. Bata samu sakamakon komai ba,sai rikicewa da kokwanton SHINE?....BASHI BANE da Zuciyarta ta sake afkwa a ciki. Sake matse qarfen tayi da hannunta tana sake jin baqinciki da sabuwar tsanarsa tana ratsata. Ta kasa Karantarsa ta cikin idanunsa,ta kasa gano komai.....me yasa?. "Are you on the line?" Ya tambayi beeno muryarsa can qasa. "Yes obbo.......inajin ba zamu qara minti takwas ba a gun.....naji kaman akwai alamun koda kowanne lokaci za'a iya fitowa" Kai ya jinjina. "Good.....use silent device kayi snapping min pictures na wadanda suka fito......shut the flash and sound" "Yes sir" Ya fada cike da girmamawa. Katse wayar yayi,daidai sanda yaji muryartannan da yawancin lokuta tana zuwa kunnensa ne da sautin tsiwa tana fadin. "Masarautar mu tana da doka......tana kuma da qa'idojin da bai kamata a dinga yawo barkatai a cikinta ba a dukka lokacin da mutum yaga dama......wasu suna da buqatar sirri sosai......da janye sanya idanu a kansu". Shuru yayi yana dubanta duba na kai tsaye. Yana hasashen inda a jimma ne......inda a Ethiopia ne lallai sai wannan attitude din nata na tsiwa ya sauya. shirunsa ya haifar mata da kokwanton daya tilasta mata waiwayo ta dubeshi,sai ta sake kawar da kai. "Har yanzu baka haddace dokokin rayuwa cikin masarautar agadez ba.........idan kanason tsira da idanunka lafiya ka guji kallon gimbiya akhnan haka kanka tsaye babu ko martabawa da girmamawa bare rusunawa". Baisan wani siririn murmushi ya kubce masa ba,yayi qasa da idanun nasa bawai don cika umarninta ba.....aah....saidai yadda namakinta ya sake cikashi. Tana rayuwa a wannan 'yar qanqanuwar duniyar tata ba tare da tasan cewa duniya ta cika da manyan masarautu ba......duniya ta cika da manyan sarakuna dake da tsananin girma qarfi da tasirin da inda a zamanin yaqe yaqe ne loma guda zasuyi da masarautar tata da abinda ke cikinta. Wani sashe na fadar aba jifar ya tuna......wanda ba kowa a ciki.....wanda yake yashe cike da kayan alatu na alfarma da ake sauyawa duk shekara......amma ba kowan da zai zauna a ciki duk tsaruwa sa tsadar abubuwan daya qunsa.....muhallin da ya kusa girman sassanta da wanda yake ciki da wanda iyayenta mata biyu dukka suke ciki. "Wanda ke buqatar sirri da wanda ke cikin nutsuwa.....mutanen da qirjinsu bai nauyaya sa zuzzurfan tunani da tsoron rushewar gobensu ba.....a irin wannan lokacin suna cikin dakunansu kwance suna bacci cikin cikakkiyar nutsuwa" Yayi maganan da wani irin salo da harshe da ya sake sanyata kallonsa a sace a karo na biyu. Kansa ya daga shi kuma yana duban taurarin dake sararin samaniya,ya rage duban nasa kadan yana sake motsa kyawawan labban nan. "Duk wanda shimfidarsa ta gagareshi......tabbas damuwa da neman mafita dole ya watsoshi waje". Wani iri shock taji ya kamata,wata irin tsarguwa ta saukar mata. Damuwa da rashin mafita?.....anya baisan komai ba?,baisan abinda yake faruwa dama wanda zaya faru gobe ba?. Wani irin fargabar rasa izzarta da girmanta ya sanyata lumshe idanunta sannan ta budesu. Zaya zame mata babbar barazana da abun kunya indai har sultane ya gama sanar dashi komai. Bataso bata kuma barin abinda zai taba izzarta sam,bata bada qofar gano lagonta,don haka ta sake maida dubanta kanshi cikin wani irin fushi,dai dai sanda yakai cup din coffee dinsa bakinsa hankali kwance idanunsa cikin cup din yana duban abinda ya rage bai shanye ba. "Ka sake da yawa cikin masarautar nan" Ta furta tana jinjina kai bacin ranta yana bayyana muraran saman fuskarta. Baikai ga sauke cup din ba wata iska me qarfi ta taso ta yaye dankwalin kanta gaba daya,bata kuma direshi ko ina ba saikan fuskarsa ta lullube idanunsa harma da cup din coffee din da yake sha. Tsaiwa yayi cak da hadiyar coffee din,lallausan qamshin dake jikin dankwalin ya soma shigewa hancinsa sosai. A hankali ya saka hannunsa guda daya ya yaye dankwalin,riqeshi yayi a hannunsa yana dubansa kafin ya maida idonsa kanta. Duba yayi mata irin na dazu,normal duba ne amma sai takejin kamar wannan kallon da yayi mata yasha banban da wanda yayi mata dazu. Wani irin nauyi taji yana cikata,sai take jinta kamar tana tsaye a tsakiyar waje ne dake da tarin al'umma ba tare da cikakken kallabi ko hijabi ba,duk da yalwatacciyar after dress din dake jikinta wanda a qasanta wasu lausasan riga da wando na bacci ne kalan farare suma. "Subhanallah" Ya fada a hankali yana zare idonsa a kanta,gashinta wuyanta dama saman qirjinta dukka sun bayyana,duk da yadda take hade jikinta guri guda dashi baisan meye ma'anar hakan da takeyi ba. Jira take ya cillo mata dankwalin amma tana jin girman kai da izzar tambayarsa,saita ci gaba da hade jikinta guri daya kawai fushi yana sake mata tasiri da tunzura Zuciyarta. Takowa ya sakeyi a nutse zuwa gaban qarfen balcony din,zura dankwalin ya soma yi ta cikin qarafunan. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Bama wanzuwa a gurbin da ba'a gayyacemu ba......kaman yadda bamu aminta da fita cikin dare ba idan ba damuwa ce sila ba......" "Wannan ba abinda ya shafeka bane" Ta fada da hanzari saboda zuwa yanzu tana jin kamar yasan komai daya shafeta,kamar yasan dalilin fitowarta,ita kuma ba abinda tafi tsana a duniya irin kasan weakness dinta. Cak ya tsaya bayan ya kammala dauren mayafin daidai sanda ta fadi ba damuwar tasa bane,sai ya daga shanyayyun idanunsa da zuwa yanzu suka sake janyewa ya zube mata su. "Na sani" Ya fadi kansa tsaye,sannan ya juya da wata irin nutsuwa ya kwashe tray dinsa da wayarsa yana takawa cikin ginshirar nan tasa yana wucewa. Da idanu ta rakashi har zuwa sanda ya maida qofarsa ya kulle ya zuge labulensa. Maida kallonta tayi ga dankwalinta,yadda iska ke wasan kura dashi jikin qarfen balcony dinsa. Wani irin takaici da baqinciki suka cika Zuciyarta. Dankwalinta ne daure jikin qarfe kaman wata tsintacciyar mage?,koda bawon ayabar da taci ta jefar abar girmamawa ce cikin masarauta......koda kwalin data gama shan abu abun girmamawa ne gurin daukeshi daga gurin,yau ga suturarta tana yawo tsakanin iska da qarfe?. Juyawa tayi da wani irin sauri tana komawa cikin bedroom din nata,yanayin shigartata ya janyo hankalin aisa ta miqe daga kwanciyar rub da cikin ta ta zauna sosai. "Waye shi?,me ya dauki kansa?.......qasqantaccen malamin da baisan komai ba bai iya komai ba sai koyarwa.......sultane ya bashi dama d qofar da zai iya maida min magana!" Ta fadi cikin hargagi muryarta na shaking. Idanu aisa ta zuba mata,ta fahimci inda maganan ta dosa.....ta kuma gano komai "Akhnan......calme toise mana.....sultane ya fiki sanin dukkan abinda ya dace...." "Don Allah tsaya mana aisa.....me yasa ba'a ajiyeshi sassan baqi ba?.me yasa sultane zai kawoshi kusa dani ya dinga takuramin?....ko ya dinga rainani yana ganin matsayinmu daya?,sultane ya dauki matsayin d'ansa ya bashi......wannan banyi magana ba.......ya dauki muhallin da iyalinsa da 'ya'yansa kawai suka cancanta,shima bance komai ba........yanzun kuma anzo gurin da bazan lamunta ba......bazan dauki qasqantar da matsayina ba". "Biftu mana!" Aisa ta fadi tana mamakin yadda akhnan ta zafafi lamarin da yawa,duk da bata gama sanin ainihin meye ya faru a yanzu ba,amma don takun saqa tsakaninta da kowanne malamin addini tasan ya qara qulluwa ne bayan hakeem da akayi niyyan bata,a yanzu tasan sai abinda yaci gaba,don kamar hakan ya qara matsa mata qaimi ne. "Biftu" Aisa ta sake kiranta da nutsuwa. Wannan karon idanunta da suka juye da bacin rai ta zubawa aisa din,tana jin kamar zata dameta da qabli da ba'adi,zata kuma hanata aiwatar da abinda ta qudura. "Guy dinnan ina miki rantsuwa da Allah ba ordinary mutum bane..... Ki tsaya ki fahimta da kyau.....ba ordinary sheikh bane......" "......eh,na sani na kuma gani,sau biyu yana niyyar rungumata da sunan taimako,kuma a gobe basai jibi ba zan gayawa sultane komai,ya nisantani dashi,ya kuma karbi matsayin dansa daya bashi don bai cancanta ba". Baki aisa ta rufe tana dubanta. "Akhnan......ki dauki komai da sanyi fa?......kada kizo ki fola masa" Motsa bakinta tayi da zummar sakin ashar wa aisa,amma kasancewar bata saba ba saita kasa fita. "Na rantse da Allah gwara na auri tantirin mashayi dan iska mara galihu"(fata na gari lamiri inji bahaushe,yana da kyau ka dinga iya harshensa ka iya yiwa kanka fata me kyau). Dukka idanunta aisa ta fidda waje,mamakin akhnan yana mamayeta,wanne irin tsana ta yiwa sheikh haisam?.....mutumin da iya tsahon rayuwarta a duniyarta cikin nutsatsen nazarinta bata taba ganin NAMIJI daya tattara dukkan abinda takeso ba kamarsa.....bama ita ba.......tunda taji shehnaz na fada tabbas ba wata d'iya mace da zata aza idanu a kansa taji baiyi mata ba. Wani irin dabi'u ke tare dashi da kowacce rana take sanyasu zama ita da shehnaz suna tattauna banbancinsa da sauran masu karantarwa. "Na aika ko zai dinga daukana karatu weekend kawai idan munzo daga Niamey amma yace a bani haquri,ranakun hutunsa ne,bayaso kuma tsarinsa ya karye.....kansa tsaye ba ruwansa da matsayina cikin gidan nan ko abinda zan dinga biya,me wada ma yace sam bai ganeni ba" Shehnaz ta fada tana murmushi. Dariya kadan aisa tayi. "Toke da aikin zakiji koda karatun" Kafada shehnaz ta daga. "Dukka.....tunda weekends kawai naso karatun ya zama,naji falaak harda Aafereen na bala'in son karatunsa,da alama yana da hikimar zance da iya koyarwa,amma kuma kinsan me?" Kai aisa ta girgiza. "Babban dalilin kawai muryarsa nakeso na dinga ji,wani irin qamshi ne dashi bansan da kalar wanne turare yake amfani ba" "Nima naji shehnaz.......turaren kadai da zan samu ko nawane zan siyeshi" A lokacin shigowar akhnan ya katse musu hirar. Tana daga zaune tana jin yadda akhnan din ta birkice tana ta fada ita daya,tana kuma daukan kayayyakinta da suke nuna lallai yau kam ba zata kwana a dakin ba,saita koma kawai tayi kwance tana kallonta. Da qyar take iya hada kayan da daukarsu ma,saboda tsabar sabo da tayi duk wata hidimarta yi mata ita akeyi,ta rufe idonta tana jin qarar rufe qofar da tayi. Numfashi ta sauke tana sake shiga mamaki. Me ya zafafa akhnan ya zafafa fushinta akan mutumin data tabbatar baya da lokacin kowa?. A ganinta yanzu lokaci ne daya kamata ace ta damu da aurenta dake tunkarota......da matsalolin sahel couture,bawai ta damu da mutumin data tabbatar bai damu da zamanta da ayyukanta ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 23* _________________________ *Assalamu alaikum warahmatullah* *_Ina me farincikin sanar daku in sha Allah gobe zan saki hotunan tsala tsalan takalmanmu da suka iso kai tsaye daga qasar sin wato CHINA_* *_Takalman yara maza da wasu nau'ikan unisex DAKI BARI_* *_MUNA MUKU ALQAWARIN AMINCI DA QUALITY IN SHA ALLAH_* *_ZAKU IYA JOINING GROUP DINMU TA WANNAN LINK DIN_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX *KO MAGANA DANI KAI TSAYE TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER WAYAR* 08187255862 *SIYAN NA GARI....MAIDA KUDI GIDA*🙌🏽🙌🏽🙌🏽🙌🏽 ____________________________ A nutse ya zauna saman sofas din parlor din yana maida hankalinsa gaba daya akan beeno daya tabbatar masa da fitowar mutanen cikin sakanni masu zuwa. Duka da Akhnan da dukka matsalarta dama abinda ya faru ya tattara yayi cilli dasu,don yanajin wannan aikin dake gabansa a yanzu yafi shirmenta amfani. *MAMMINA* A nutse nutsuwar dake da alaqa da takatsantsan suke fitowa daga cikin gidan. Hannunta ta sanya ta jawo lullubin dake saman kanta wadda sutura ce ta ayaana da a yanzu ta maidata mallakinta,ta rufe fuskarta ruf tamkar amaryar dake shiga gidan miji ranar farko. Shuru ya wanzu a tsakaninsu ita da tafisu,har zuwa sanda mammina din ta magantu. "Meye hasashenki akan lamarin nan ta fisu?". Wani murmushi ta saki,tana duban hanyar da suke wucewa sosai. "Idan har an samu hadin kan almaz......indai har yayi kaman yadda muka tsara,lallai komai zai tafi a daidai.....nasara ce kawai zataci gaba da wanzuwa......wannan kuma shine xai baki damar maida hankalinki ga ETHIOPIA". Kai ta jinjina a nutse itama tana duban hanyar,tsahon wasu sakanni sannan tace. "Haka kawai jikina da zuciyata ke yawan rayamin akwai abinda ke tafiya ba daidai ba a wancan qasar...... Kamar akwai wani gibi akwai wani abu daya kauce daga muhalli da gurbin daya kamata ya kasance akai,duk kuwa da cewa kowanne bangare sun tabbatar min da cewa komai lafiya". "Idan har kin samu wanna tabbacin kin kuma gamsu,to lallai komai din lafiya ne,idan kuma har zuwa wani lokaci zuciyarki kikaji baki gamsun ba......to ki gasgata zuciyarki......ki zurfafa bincike,har sai kin gano abinda ya haifar da wannan jin da kikeyi a zuciyarki......ko kuma har sai kin samu gamsuwa d'ari bisa d'ari" Kai take sake jinjinawa cike da jin gamsuwa da dukka maganganun tafisu. Sunan ako wacce rana tana jin ua dace da ita......sunan tafisu sai takejin kamar don ita kadai aka samar dashi,don kusan tafi duka sauran hadiman amfani ga mammina. "Amma....." Ta fada mammina din tana dan dakatawa. "Na cika da mamakin yadda kika sarrafa almaz haka cikin sauqi tafisu?" Murmushi me dan qaramin sauti ta sauke,shudewar wasu daqiqu sannan tace. "Kina manta cewa wannan jinin fa dake yawo a jiki ba qarya bane.....gado ba qarya bane.....ba kuma karambani ba.......komai lalacewar wannan tsatson sai wani abu yayi tasiri tattare dashi da zai tuna masa asalo da tushe.......makullan juya tunanin almaz......sarrafa almaz yadda kikeso shine......ki mu'amala dashi da karramawa......ki nuna kowa dake tare dashi ya girmamashi" Kai take jinjinawa,da gasken gaske taji dadin wannan shawarar ta tafisu. "Kinci kyautar sulalla na gold tafisu guda hamsin". "Godiya nake" Ta fadi tana rusunawa mammina din. *BEENO* Idanunsa na a kafe akan matan dake takawa cikin unguwar da ko gilmawar kare babu. "Mata biyu ne.....saidai dukkansu fuskokinsu a rufe suke,koda zanyi hotonsu bana tunanin obbo zaka ga fuskokin nasu" "Listen beeno" Haisam da ya dafe dukka hannuwansa saman dining table ya fada,sannan ya miqa hannun nasa yana gyara Bluetooth din kunnensa. "Snap a pic.....quick" Ya furta da wani deep sound me cike da umarni. Hotuna uku ya dauka,duk da cikinsu ba wanda fuskokinsu suka fito,saidai yana shirin matsawa baya don boyewa ganinsu busassun ganyaye suka motsa kadan,abinda ya sanya mammina kama hannun tafisu gami da tsaidata cak. "Motsi kamar nakeji". Muryar ta sauka a kunnen beeno,abinda ya sakashi danna wani abu a gefen kunensa daya bawa haisam sign na DANGER. "Ya muntaqeem.......ya hayyul qayyumu" Haisam ya fadi yana furzar da iska daga bakinsa. "Keep calm beeno......kar kayi wani misbehaving......hold your breath for 30 second.....har sai sun wuce" Ya fada yana damqe hannunsa,yana jin kamar ya bayyana a gurin. Horon riqe numfashi abune me wahala koda a cikinsu ne.......amma ya aminta da beeno din,yana jin kamar zai iya......zaiyi succeeding. "Banji wani baqon motsi ba.......banji wani baqon qamshi ba,inda akwai wani a nan dole iskar gurin ta sauyamin" Tafisu ta fada yana girgiza kai gami da ci gaba da sake watsa dubanta a kowanne sashe. Kai mammina ta jinjina a hankali. "Na yarda dake......amma jikina yana bani haka har yanzu" Ta fada tana ci gaba da tafiya a hankali cikin takatsantsan fiye da yadda suka fara tahowa a dazu. "Koda ba komai.....jin irin wannan yanayin a tattare dani bai fiya bani aminci ba......zan dage qafa har zuwa sanda almaz zai gana da me martaba" "Hakan ba laifi bane" Tafisu ta fada tana bata qwarin gwiwa. Qarar sakin numfashin beeno ya tabbatar masa komai ya tafi normal. "Good job......kada ka motsa daga gurin sai bayan minti talati......ka isa gida lafiya" Haisam ya furta yana katse na'urar. Wata kujera ya jawo ya zauna sasai akai,ya jawo personal system dinsa ya jona device din ya kunnata yayi connecting. Kai tsaye ya wuce fannin tura hotuna,yayi clicking duka hotunan uku da beeno ya tura masa ya soma nazarinsu. Nazari ne irin na qwaqwaqwafi da qwararrun jami'ai na binciken sirri ke yi a kan kowanne abu daya fado hannunsu da sunan bincike. Dukkaninsu ba wadda ya samu nasarar ganin fuskarta kaman yadda beeno ya gaya masa,saidai kaya dai kaman wancan ranar.....kamar wancan lokaci. Tufafi ne na masu muqami sosai cikin masarautar agadez din.....manyan muqamai da sun kusa mata hamsin daga manyan sassan gidan uku. Iska ya furzar,yana jin lokaci yayi da zai sanya idanu yasan bayanan kowacce mace dake ta'ammali da uniform din,matsayinta da kuma iyakacin hurumin da take dashi a gidan. Yana shirin rufe hotunan sai ya fasa,ya koma hoto na biyu yayi zooming nasa sosai. Hoton tafisu ne a farko,don haka shi ya fara zuqowa. Hannunta ya fito sanda take gyara itama lullubin kanta don sirranta fuskarta. Akwai wani abun hannu na duwatsu da suka zama ado wa tsintsiyar hannunta. Iya gurin kawai ya yanke ya fiddashi hoto me zaman kansa. Dukka hotunan yayi marking sannan yayi forwarding nasu zuwa ga wani sabon adreshin,da rubutu taqaitacce da yaren Oromo a qasa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Ina buqatar bayanan tsaho da hasashen qiba na kowacce mata.......wannan hannun inason bayanai da binciken qwaqwafin me shi.......a fidda asalin halittar da me shi zata iya kasancewa dashi. Yana kammalawa ya tura,sai ya maida bayansa ya jinginar da makarin kujerar yayi relaxing sosai yana jin yadda a yau gajiya take bin sassan jikinsa. Maher yayi kadan,yana buqatar kota yaya ya zuba ma'aikatansa Shima cikin gidan.......yana aqalla kowacce qofa ya zamana akwai mutuminsu koda mutum daya daya ne......tabbas zaiga sultane a gobe duk da bai shiryawa hakan ba,zaisan kuma yadda zai shigo da tsarin cikin sauqi. Hannun rigarsa ya nannade ya kuma wuce zuwa toilet ya daura alwala,ya dawo ya shimfida lallausan abun sallarsa ya tayar da sallah a nutse. Sallar dare wani makaminsa ne ne qarfi da girman gaske tsakaninsa da ubangijinsa.......wani qarfinsa ne walwalar matsalarsa sannan kuma jagoransa a duk sanda ya sanya wani al'amari a gaba dama rayuwarsa ta yau da gobe. Koda ya idar ya jima saman abun sallar yana karanta wasu addu'o'i,tsantsar dangantaka me qarfin gaske yake ji tsakaninsa da ubangijinsa a irin wannan lokacin. Gari yayi shuru,ko ina yayi duhu ciki harda dakinsa da yake zaune a yanzu haka,don yana jin dadin kebancewar da zaiyi da ubangijinsa ta zamana cikin sassauqan haske da ba can can zaka gane abinda ke dan nesa da kai ba. Shafa addu'arsa sai ya zamana kamar maqullin budewar duk wata dabara tasa. Qaramin murmushi ya subuce masa yana sake imani da yaqinin cewa,tabbas idan ka roqi Allah kana da nufi me kyau,to tabbas ne zaya amsa maka addu'arka a kusa ko a nesa,sai ya miqe tsam yana kunna bedside lamp da yakeji haskenta kadai ya isheshi. Komai ya bude sosai cikin kansa........kai tsaye ya jawo wayarsa da har ya riga ta kasheta ya soma da kiran maher. Bugu biyu kawai maher din ya daga,muryarsa da sanyi sosai da alama bacci nason fara daukarsa. "Ka matsa daga qofa na?" "Aah......lokaci baqai qarasa ba" "Akwai buqatar koda lokaci yayi kada ka matsa din.......akwai qaramin hari da zai faru yanzu cikin gidan,kada ka aiwatar da komai banda abu biyu,basu hanyar shiga da basu hanyar fita cikin mintuna goma kadai.......ba wanda za'a cutar ba wanda za'a illata......kawai akwai hankulan da nakeso a tabasu da shiyyar da nakeso a bawa qarfi....." "Done obbo" Ya fada cikin tsananin girmamawa da biyayya. "A bayan ka basu qofa sun fice ina buqatar basajar da zata bayyana cewa kaika fatattakesu daga shiyyar zaituna da suka nufaci zuwa......koda qaramin rauni ne ka samar dashi a jikinka......zan kula da wannan". "An gama obbo" "Ka fahimta?" Ya tambayeshi don gudun samun sabani. Kai ya jinjina "Sama da yadda kakeso na fahimta" Ya amsa masa da qarfin gwiwa. "Ka fara shiryawa,amma na'urarka ta kunne ta zama active to keep in touch" "Yes obbo" Sai duka suka gintse kiran,sannan ya maida akalar kiran ga omari. "A cire beeno a ciki......he done the best a wannin da suka wuce,a bashi relaxation hours" Ya bayar da umarni wa omari. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 24* ________________________ *Assalamu alaikum warahmatullah* *_Ina me farincikin sanar daku in sha Allah gobe zan saki hotunan tsala tsalan takalmanmu da suka iso kai tsaye daga qasar sin wato CHINA_* *_Takalman yara maza da wasu nau'ikan unisex DAKI BARI_* *_MUNA MUKU ALQAWARIN AMINCI DA QUALITY IN SHA ALLAH_* *_ZAKU IYA JOINING GROUP DINMU TA WANNAN LINK DIN_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX *KO MAGANA DANI KAI TSAYE TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER WAYAR* 08187255862 *SIYAN NA GARI....MAIDA KUDI GIDA*🙌🏽🙌🏽🙌🏽🙌🏽 ____________________________ *_WASHEGARI_* Cikin wani kyakkyawan kurta pyjamas yake da akayi da sassauqan yadi navy blue a idanu,sadai asalin zare da audugar da aka saqa kayan masu tsadar gaske ne. Simple dinki akayi mata wanda ya fidda kyansa da kuma haibarsa,kamar yadda color din kayan ya fidda moderate hasken da fatarsa ke dashi me ban sha'awa. Da alama cikin shirin fita yake,saboda gefansa agogo ne da farin rawanin da ya nadu ya zauna sosai saman gewayayyar hular da yakan sanya me wani irin yanayi me daukan hankali,rawanin da yawan mutane ko ince malaman Indonesia Malaysia ke amfani dashi. Tsaye yake riqe da takardun guda biyu a hannunsa,tsaiwar data fidda siffa da zubinsa na GIANT GUY dake sa wani irin cikakkiyar suffa da kamala me janye hankali da idanu. Takardar farko dake dauke da gwajin komai dangane da hoton matan jiya bata dauki hankalinsa ba kamar wannan ta biyu,wadda ke dauke da qerarren abun hannun daya gani daga hannun mammina......da kuma bayanan da bincike ya bayar akan abun hannun. Abun hannu ne me dad'ad'd'en tarihi tabbas,wanda a yanzu ba kowanne gida ake samunsa ba cikin oromian region,sai gidajen sarakuna da manyan attajirai,wanda Shima yasan da hakan,amma abinda yafi janye hankalinsa shine an samu tabbacin akwai me irin abun hannun cikin iyalin gidan AJANI da ita daya ta taba mallakar irinsa,saidai kuma an samu bacewar abun hannun ba'a san kuma inda za'a ganshi ba bare a zurfafa bincike a kansa. Danyan gwal ne aka dunqule aka sarafashi a haka,wanda gidan mahmud ajani shine gida na farko da aka taba ganinsu da irinsa,wannan ya sanya nasu ya banbanta da irin na kowa. Takardar ya maida ya ajiye kafin Shima ya zauna a gefanta yana fidda siririyar iska daga bakinsa. Yana jin wani qarfin gwiwa da yaqinij qarfafa zarginsa akan mammina. Meye hadinta da qasar Ethiopia?........meye hadinta da abun hannun daya kasance shaida ce kuma alama ce ta attajiran qasarsa?......ya akayi ta samu abinda ya kasance yana da alaqa me qarfi da zuri'ar AJANI AHAMED?. Yatsunsa ya cusa cikin gashin kansa,ko yaushe abubuwa sake gabatowa suke gabansa da zafinsu,ta kowanne bangare ta kowanne sashe da qulli da dabaibayi komai yake zuwa masa.......amma zuwa yanzu ya samu cikakken hujjar da zai sanya idanu......cikakken hujjar da zai fara bibiyar al'amuranta da tsananin qarfi. Faruwar komai a jiya kawai yasan wani babban mabudi ya samu,wata babbar hanya da komai zaizo masa da sauqi.....dole ya dauko asalin abun hannun daga can cikin dakinta zuwa hannunsa don ya aike dashi a sake duba masa tabbacin SHI DINNE?. System dinsa ya jawo,yayi wasu rubuce rubuce sannan yayi saving ya maidata ya ajiye,ya miqe a nutse yana daukan Amama dinsa ya qarasa gaban madubi. Yaji dadin nemansa da sultane yayi a yau din,don dama yasan dole hakan tana iya faruwa......zaya nemeshin ko don abinda ya faru a jiya cikin wasu sassa na gidan. Wannan kjma shine target dinsa,zai ganshi ne a sanda shi sultane din da kansa ya nema zuwa gurinsa,ya kwana jiya yana addu'a samun sassauqar hanyar shigar da buqatarsa,ya kuma samu dukkan wani dama,komai ya tafi daidai,komai kuma ya tafi har fiye da yadda ya tsara. Ya dora amaama din saman kansa,jelar da kanyi reto daga gefan kafadar damansa ya zagaye habarsa har zuwa saman hancinsa da ita yadda ya saba yi a yawancin lokuta,wannan ya santa dogon hancinnan da kyawawan labbansan masu daukan hankali. A nutse yake saukowa zuwa qasa,inda ya samu cook dinsa ya kammala breakfast tsaf cikin tsafta da tsari. Yau din shi daya ya kwana cikin sassan,don abdii ma cikin plan din jiya bai kwana cikin gidan ba. Cikin matuqar girmamawa ya rusuna yana gaidashi gami da yi masa barka da fitowa. Kai ya gyada masa,sannan a nutse ya shaida masa a kwashe komai,zaiga sultane ne,baisan kuma ko qarfe nawa zai shigo ba. A nutse yake karantar yanayin sauyawar masarautar daga jiyan zuwa yau,yanayi ne da zai tabbatar maka akwai wani alhini daya faru. Gefan sassan mammina da morsa safiyya akwai qarin adadin masu bada tsaro Sosai fiye da ko yaushe......saidai na gefan mammina din har yaso ya dara na morsa safiyya. Idanunsa ya janye yana lumshesu,wani qaramin murmushi dake boye qasan mayafin amaama dinsa ya qwace masa. Haka mutane ire irenta suke,basa qaunar mutuwa ko wani abu da zai kawo barazana ga rayuwarsu......iya wannan motsin nata kawai ya sake dasa zargi me qarfi game da ita a ransa. Cikin girmamawa da martabawa sultane ya miqe da kansa don tarbarsa kamar yadda ya saba. Yana ganin girma da martabar dattijon basaraken da yakeji a jikinsa akwai abubuwa da yawa da suke boye daga saninsa. Akwai abubuwa masu yawa daya kamata ya sani smma baisan dasu ba,akwai al'amuran da suka yiwa saninsa b'atan dabo da badda bami. Cikin girmamawa daidai da yadda zaiwa motii ya bashi hannu sukayi musaba,murmushi kwance saman fuskar sultane,yana jin wannan feeling din wannan yanayin na tamkar yana tare da dan cikinsa daya rasa shekarun baya AHMAD. "Bismillah" Sultane ya fadi yana nunawa haisam daya daga cikun kujerun dake kewaye da gurin,wanda dab dasu wata kyakkyawar table mat ce me girma da aka soma zube royal warmers da spoons na cin abincin sultane din. Kafin su fara tattauna komai akayi sallama daga bakin qofar parlor din. Falaak ce sanye da baqar doguwar riga yalwatacciya sosai,ta kuma lullube kanta zuwa kafadunta da baqin mayafi mahadin doguwar rigar. Duk da kasancewarta me dan duhun fata amma shigar tayi mata kyau sosai,ta kuma fidda sanyin halin da take dashi. A kansa idanunta suka fara sauka,gabanta ya fadi da wani irin kwarjini me yawan gaske da taji yayi mata. Dan kwanakin da suka tafi hutu kawai na tsakiyar lokacin karatu sai taji kaman ta jima sosai bata ganshi ba. Ta nema dukkan wani dalili da zaya sa ta ganshin amma kuma babu,yau dinma ba zata ne,bata sanya ran zata ganshi ba,amma hakan sai ya mata dadi sosai. Cikin tsanaki da nutsuwa take shigowa cikin parlor din,kanta a qasa tana jin wani irin nauyi fargaba da kuma faduwan gaba yana saukar mata. "Ta kasa zaune ta kasa tsaye.....kada a rabata da dan tsohon babanta ko?" Sultane ya fadi cikin murmushi da salo na tsokana daya alamtawa haisam akwai sakewa sosai tsakaninsa da ita,da kuma kalar qauna da jituwar data banbamta dana 'yar uwarta. Murmushi kawai ta saki,bata tsaya biyewa sultane yadda ta saba ba,ta qarasa gaban haisam ta tsugunna tana gaidashi. Cikin girma ya amsa mata,abinda ya yiwa sultane dadi,saboda yanayin ya masa kama da yadda babban yaaya yake daukan girma wa qannensa. "Abincin ya iso,a nan zan zuba maka bappi?,ko saman table?" Tayi tambayar idanunta akan sultane,amma duka hankalinta yana kan haisam da kacokam idanunsa akan wayarsa suke yana karbar wasu bayanai daga maher na abinda ya faru daren jiya. "Aah zuba mana a nan,ga yayanki nan ma tare zamu karya dashi" Miqewa tayi a tsanake,duk da yadda takejin qafafuwa da hannayenta suna dan rawa,saboda har yanzu kwarjininsa dukanta yakeyi,abinda ya danja hankalin sultane kadan kenan a kanta,yaci gaba kuma da noticing yadda ta zagaya rukunin kujerun dake gabansu inda table mat din yake tana zuba abincin kamar ba nutsuwa sosai a tattare da ita yadda ya santa. "Muhammad" Sultane ya kira haisam bayan ya maida dubansa kansa. Qaramin murmushi dake dauke da girmamawa ya saki,yana ajiye wayarsa gefansa. "Ya mukaji da alhinin abinda ya faru damu a jiya?" Haisam ya fadi cikin girmamawa da son ya fara dora tattaunawarsu a gurbi da muhallin da zai sanyo buqatarsa. "Mun godewa Allah.....ba wanda ya rasa rai ko yayi rauni me yawa,sai hadimi guda daya da akace shine ya bawa sassan zaituna kariya......ba'a samu rayuwarshi ba sai dazu da safen bayan qarfe takwas saura" Kai haisam ya jinjina,ko sultane bai dora komai ba yasan akan maher yake magana. Maher din yayi aiki me kyau har fiye da yadda ya zata,kuma komai ya tafi daidai da harshi kansa ya gamsu da acting din da yayi. Wannan dalilin ya sanya shi da kansa yake saluting kalar team din da yayi raising da kanshi cikin national intelligence security service. Team ne da babu rago.....babu malalaci a ciki,kalar team din da sai aiki na musamman ake fita dasu KAMAR KUMBO KAMAR KATANTA.....da gaske yadda shugaba ya kasance haka dole mabiyansa zasu kasance,yadda SHEIKH MUHAMMAD HAISAM yake jajirtacce......haka kowanne namiji dake qarqashinsa yake tashi da kalar wannan jajircewar....da kalar wannan qwarin gwiwar....da kuma kalar wannan jarumtar tabbatacciya daga ZUCIYA DA QWANJINSU. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Duk da inaji a jikina lamarin ba wani babba bane......amma zaituna ta tashi hankalinta da yawa......tun jiya har yau qoqarin fahimtar da ita nakeyi ako ina ana iya samun irin wannan yanayin amma bata fahimta din ba.....tadai nunamin damuwarta ba tata bace karan kanta,damuwarta kan mutanenmu ne,jama'ar da muke mulka wadanda suka cancanci samun zaman lafiya da tsaro me kyau qarqashin shugabancinmu". Idanunsa ya lumshe a hankali yana jinjina kanshi sannan ya sake budesu akan fuskar sultane. Jinjina kansa bawai na gamsuwa da bayanai da sultane ya bashi ba......ba na gamsuwa da abinda mammina ta fada bane......na gamsuwa da cewa lallai matar ta iya buga wasanta yadda ya dace.....lallai ta iya amfani da kowacce kalar dama da zata gifta ta gabanta ne. "Na fahimci akwai gaskiya cikin kalamanta,don ita daya ce damuwarta ta zama gaba da abinda zai sameta ita a karan kanta.......wannan ya sanyani tunanin irin tsaron da zamu qara cikin gidan nan don kaucewa faruwar irin abinda ya faru a jiya ko wanda yafi haka a gaba". Komai sai haisam yaga yazo masa da wani irin sauqi da bai taba zata ba,duk da zai wahala ya kafu saman abun sallah ya yiwa Allah naci da neman dafawarsa akan wani abu kuma hakan bata tabbata ba. "Gaskiya ne,haqqin kowanne shugaba ne ya kula da rayuka da lafiyar mutanensa......don kuwa Allah SWT zai tambayeshi ranar qiyama game da kowacce rai qwaya daya data yaya ta rayu qarqashin mulki da ikonsa" Kai sultane yake jinjinawa kawai,zamansa da haisam yana sake tuna masa girman nauyin dake kansa,wanda koda iya wannan kadai ya rabauta ya isheshi,ballantana kuma zuciya da ruhinsa cike suke da dorewar alaqar tafi haka. Gyara zamansa sosai sultane yayi yana tattara hankalinsa ga haisam "Yanzu me kake ganin za'ayi?,wacce hanya da shawarwari zamu bi?" Ya tambayi haisam yana so yaji ta bakinsa. *Mammina* Ko qiftawa idanunta basu sakeyi ba tun daga lokacin da kunnenta ya jiyo mata babban motsi qararraki da ifce ifce. Daga sanda yalwa ta shaida mata kamar an kawo farmaki cikin masarautar kuma tunda ta sauka daga saman gadonta bata sake hawa kanshi ba. Ba zatace bata zauna......ta zauna amma yayin da take tahiyar sallah,amma banda hakan,har yanzu da agogo ke nuna sha daya ta gota ba wani data aiwatar na dukka al'adun data saba yi daga safiya zuwa wannan lokacin. Farmaki ne da aka kawo cikin gidan,farmakin da za'a iya cewa idan ya qazanta kai tsaye ya shafi kowa.......to amma cikin jininta da jikinta takejin kamar an kawo farmakinne kai tsaye saboda ita.......tamkar itace abun hari takai tsaye da aka nufata. Hankalinta ya tashi qwarai sanda ta kalli maher da yayi kaca kaca da jini......abinda ya sake tabata,ya kuma saka mata shakka kokwanto da rashin nutsuwa me tarin yawa. Da tafisu ta fara ganawa,don a ranar ba wanda ya smau ganinta cikin hadimanta,don ko wanka ma bata samu damar yi ba don tana jin a yanzu bata wannan take ba. Bata bari matsala ko yaya ta gilma mata,don ta riga ta canfa.....kowacce matsala daga qarama take farawa kafin ta zarce zuwa babba. "A jiya naji a jikina akwai wani a sanda muka fito daga ganin almaz.......bayan na zargi wani abu kuma saiga wani baqon lamarin da nake zargin ba daga can ya biyo diddigi da sawunmu ba?" Ta furta tana duban tafisu. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 25* Kai ta girgiza a hankali tana duban mammina. "Inda akwai wani mahaluqi tabbas zan iya jin dumin numfashinta daga tazarar dake tsakaninmu......ba numfashin wani dan adam ta gurin sam sam......bana tunanin akwai wani daya wanzu a gurin" Kai mammina ta girgiza cikin rashin gamsuwa da bayanan tafisu. "Lallai akwai wani baqon abu......akwai wani abu daban dake wanzuwa a muhallin da ba nashi ba.....a muhallin da ada babu shi a gurin" "Akwai shigowar baqi ne masarauta?......ina cewa kin datse duk wata hanya da qofa da zata bawa baqo daman shigowa ko zama cikin masarauta?". Kai ta gyadawa tafisu,amma gefe guda tana zurfafa tunaninta. "Ba wani sabon baqo da aka sake samu........saidai akwai baqon da yashigo tun kafin wannan lokacin..????" Ta qarasa maganar kamar tana yiwa kanta tambaya ko tuhuma game da haisam. "Tafisu........maza kiramin bulama" Ta fada a dan rikice. Sama da qasa tafisu ta girgiza kanta alamun girmamawa sannan ta tashi zuwa hanyar fita. Fitar tafisu tana jin kamar ta jawota ita da bulama din ta tsincesu a gabanta. Ta manta shaf ta bada aikin bibiyar mutumin,ashe tana da tarin hangen nasa har haka ita kanta bata sani ba?. Samun kanta tayi cike da fatan ta samu wani abu da zaya bata haske game dashi,wasu bayanai da zasu iya haska mata shi......ba shakka idan har haka ta kasance YA SHIGA UKUN DA BABU FITOWA. Abubuwa da yawa ta dinga hadawa game dashi cikin kanta. Bata taba samun halittar da take ganin kwarjininta sama dashi ba,hakanan kuma zuciyarta da ruhinta sam sun gaza jin aminci game dashi.....gefe daya tana jin wani qaqqarfan rashin jituwa dangane dashi dake zabalbala daga jininta a kansa. Duk wani baqo daya samu gindin zama ya karbu hannu bibbiyu itace ta karbeshi.....dalili......bata abu a banza......bata aikata aikin da bazata samu yabo ko kwarzantawa ba daga bakin sultane mazauna gidan dama talakawan AGADEZ. Ta buda hannuwanta bibbiyu tana karbar baqi da 'yan gari dama dukka wanda rayuwa ta raunatashi......wannan yaja mata soyayayya farinjini da qauna me tarin yawa daga garesu.....don haka sai taji kamar FADUWA ce ace mutum kamar haisam din daya samu karbuwa a gun sultane da wani yanayi da har yau yake bata mamaki ace kuma SAFIYYA ce silar shigowarsa masarautar ba ita ba. Da farko ta dauka iya wannan kawai shine dalilin da ya sanya ta fara jin rashin jituwa a kansa,sai daga bisani ta fahimci KWARJINI yake mata......yana da tasirin IZZA cikin jininsa,wanda ta saba kowanne malami ma da yake cikin masarautar neman gindin zama yake a gurinta don ya samu karbuwa daga sultane......amma shi wannan koda sau daya bai nemi ganawa da ita ba.....hasalima kamar baida labarin komai a kanta.....,kamar kuma baida labarin irin TASIRI da qarfin IZZAR da take da ita cikin gidan gaba daya. Kwarjininsa da take yawaita gani ya sake dasa mata qatuwar ayar tambaya......yadda yake iya girgiza tsarinta da idanunsa kadai ya sanya takeson sanin komai a kansa,don tana jin kamar ba ordinary mutum bane. Tunaninta ya yanke sanda tafisu ke shigowa ciki bulama na bayanta. Ya qaraso jikinsa na rawa ya zube a gabanta yana kwasar gaisuwa. "Ina labari......wanne abune na daban daka samu ganowa cikin aikin dana baka?" Ta fada tana watsa hannuwanta kamar wadda ke jiran ya bata wani abu. "Allah ya baki tsahon rai......ko a yanzu a bakin aikin nake kika sanya aka nemoni.......bana taba daga masa qafa tun daga safiya har zuwa sanda dare zai shigo......to amma komai da kike zato a kansa ba haka bane.......ba kasafai yake fita ba don baisan kowa a garinnan ba.......yafi zama yayi karatu shi kadai cikin dakin litattafansa. Abu daya ne da zan iya cewa na gani shine,kawai zuzzurfar alaqa ta aminci tsakaninsa da sultane da tsahon shekaru ban taba ganin wanda ya bawa aminci irin haka ba,yana kebewa dashi,daga shi saishi......yana kuma iya bashi ragama r yanke wasu hukunce hukunce da suka shafi lamuran masarauta,harma yana iya cin abinci tare dashi kamar dan cikinsa.....kamar dai yanzun,suna tare da zummar cin abincin safe shi dashi da gimbiya falaak,darensa duka bacci yakeyi,koda sallar dare a farkon dare na fahimci us fiya yinta,yana kwanciya bacci da wuri bai fiya wanzuwa ido biyu ba har zuwa asuba.....na biyu kamar yana da zurfi da kaifin tunani dana hangen nesa......akwai motsi da yawa da yayi wanda ya sanyani a zargin yana ganina koma ya ganni,to amma sai daga baya na fahimci bai fahimci ina biye dashi din ba kamar yadda na zata......yana tsarguwa ne da hakan". "Indai zai tsargu da ana bibiyarsa kuwa tabbas akwai wani QULLI cikin zuciyarsa.... Wanda ke rayuwa sak baya raya wani zaya bishi.....koda an bishi ma yasan ba wani abu da za'a tsinkayo bare a bankadashi,ka sake kusantarsa kadan......ka kula da takunka da kyau......bana buqatar samun wani akasi ko wani abu na ba daidai ba" Tayi maganar da kakkausan gargadi cikin idanunta. Qasa ya zube kansa yana maimaita mata shima. "Ba zaki samu wani akasi ba ko sau daya na Miki wannan alqawarin" Ya amsa kanshi a qasa "Kana iya tafiya,an sallameka" Tafisu ta bawa bulama umarni,ya yunqura yunqurawar data bayyana tsaho da fadinsa,ya fice a gurin da sassarfa don zuwa ya dora daga inda aikinsa ya tsaya. "Duk da a daidai wannan lokacin nake sanya ran akhnan zataje gabatar da almaz wa sultane......ina buqatar shiga gurin" Ta furta a fili tana jin buqatuwar zuwa gurin sultane din don komai ya wanzu a idanunta. "An gama" Tafisu ta fadi tana miqewa don bawa mammina daman shirya kanta. "Ki nema tamim ki shaida masa.......nan da minti ashirin zan fito,zan kuma ganshi kafin na wuce gurin sultane". "An gama" Ta sake fada tana rusuna mata sannan ta juya tana ficewa. Cikin mintuna ashirin da biyu ta shirya tsaf,cikin madaukakin adon dake bayyanar da kalar cikar kamalar izzarta da kuma amsa sunan GIWAR SULTANE. Sunan dake matuqar yi mata dadi,sunan data tabbatar a duk sanda safiyya zata jishi yana haifar da wata susa sai qwarzane cikin zuciyarta. "Tamim yana dakin baya yana jiranki" Tafisu ta gaya mata sanda ta fito cikin qasaitarta,da zubin taku da yanayin da baka isa ka tsinciki damuwa da firgicin da zuciyarta ke ciki ba tun daga daren jiya zuwa yau din ba. Ita daya ta isa shiyyar,ta samu tamim din a tsaye,sanye d wadannan kayan dake sake nuna irin girman jikinsa da kuma dacewa da muqamin BAUTA. Ginannen jikin da ka iya razana me shirin kawo wargi. Bayyanarta ya sanya tamim lanqwasa gwiwarsa ya kuma zube a kansu yana miqa gaisuwa,tamkar yadda dabi'arsa take a duk sanda yake gaban mammina ko gaba wani daga cikin ahalin sultane din. "Tamim!" Ta kira sunansa da sautin daya tabbatar masa magana ce me tsananin muhimmanci a tattare da ita. "Ki dade kiyi qarko" Ya amsa mata yana daga kuben takobin dake rataye a qirjinsa. "Me yake faruwa a Ethiopia?" Ta masa tambayar Kai tsaye,tambayar data sanya shuru ya ratsa a gurin na wucin gadi,kafin tamim ya amsata. "Komai yana nan kamar yadda yake.....komai yayi bacci,wasu abubuwan sun sume kuma suna dab da mutuwa......ba wani tashin qura ko razanannen motsi da zai farkar ko rayar da wadannan abubuwan" Kai ta girgiza tana duban tsakiyar qwayar idanunsa. "Banajin gamsuwar haka a jikina......inaso a sake bincika min......idan nace a bincikamin bawai bincike na kwana daya zuwa sati daya ba.......a'ah,bincike na iya adadin kwanakin da komai zai fita da anihin amsarsa.........bana buqatar amsa da gaggawa,sakamako me kyau nake buqata.......sakamakon da shine zai zame mana jagora zuwa tayar da tsohon aiki ayi masa kwaskwarima zuwa sabo......na gaji da wanzuwa akan wasu turbobi da suke tsikarina suna tauyeni.......ina buqatar a kammala shirin komai a kuma kawo qarshen komai,koda kowa da komai zai mutu" Kansa ya kafe a qasa cikin tsananin biyayya. "An gama" Ya fadi yana cake takobinsa a qasa,ya dogara da ita sannna ya miqe. *akhnan* Ta gama shiryawa cikin wani yadi me sauqi dake bayyana asalin qabila da yarenta na cikakkiyar buzuwa gaba da baya,shigar da take sanya ran zata sanyaya zuciyar sultane ya kuma kalli magana da zataje dashi da sassaqan harshe. Tana fatan yadda yake qaunar ganin safeena cikin irin wannan suturar,a yau ya dubeta da idanun da basu da maraba da irin duban da zaiwa safeena din,cikin soyayya qauna da martabawa. Ba mammina a gefanta......amma ta samu qwarin gwiwa me yawa daga gareta. Ta yita kallon kanta da kanta a madubi,tayita kallon fuskarta a madubin tana juya yadda zata fuskanci sultane yau.....da zabin daya jima yana mata tana wofantarwa.......ta ture nasa muradin.....ta tunkude zabubbukansa har goma sha hudu.....ta kuma zo da nata zabin. Amma tana ji a ranta akwai daidai me yawa cikin nata zabin data yiwa rayuwarta.....bawai tayi bane don ta watsawa sultane qasa a idanu.....bata yi bane don tozartashi ba.....ba kuma tayi bane don ta nuna masa bai isa ba......tayi ne saboda tattalin kanta da rayuwarta da a nan gaba take da tabbacin zai fuskanci haka duk daren dadewa. Baya taja a hankali jikinta na fidda sassauyan qamshin turaren kabbasa na kamfanin INCENSE BY KABODAUGHTER daya mamaye ilahirin suturun sawarta,wanda ba wani cikakken motsi da zatayi sai sirrin wannan sirrintaccen qamshin ya fita. (Tasted and trusted,duk wani turaren wuta da khumras da zaku gani cikin novel dinnan ingantattu ne dana tabbatar da iyawarsu d qwarewarsu fiye da yadda kuke zata +2348032119803). Birra kawai ke take mata baya,suna tafiya a nutse har zuwa sanda daya daga cikin wayoyinta dake hannun birra suka dauki tsuwwa. Cikin girmamawa ta matso dab da bayanta da zummar mata bayani,bata barta tace komai ba ba tare data waiwayo ba ta daga mata hannu "Ko waye ki daga ki sanar dashi bazan iya daga kira ba a yanzun" Komawa tayi da baya,neesha ce ta kuma shaida mata abinda akhnan din tace. Batace da birra komai ba sai da suka kawo gabar da iya matsayin birra kenan kuma dole ta koma. "Ki sake kiranta ki gaya mata,duk wani damuwan office tayi maganan da aisa,idan bata sameta ba shehnaz". Sannan taci gaba da takawa a nutse kamar wadda ke irga adadin takun da zata iyayi. Da lallausar muryar nan tata dake da wani irin value da tsada gami da wahalar ji a kunnuwan maza da yawa tayi sallama,sallamar da bata bada wani sauti me yawa ko qarfi ba,amma ta bawa dukkan wanda ke cikin parlor din damar jin siririyar sallamar,ciki harda sultane dake zaune saman wani tattausan kilishi na daban yana fuskantar falaak da kuma haisam dake zaune saman wani kilishin na daban,gabansa shiryayye butar shayi ta wani nau'in qasa da tab'o da aka sarrafa me tsananin riqe zafi saboda gidan sarauta irin wannan. Tea set ne da sultane ke ji dashi sosai,wanda ita daya a duniya ya iya mallakawa irinsa saboda girma da zurfin soyayyar dake tsakaninsu. Ya tanqwashe qafarsa cikin nutsuwa,har kana iya hangen lallausar socks din qafarsa,duka hannuwansa biyu riqe da wayarsa yana sarrafata,don ba kasafai ya fiya son aza hankalinsa akan abinda bai shafeshi ba. Magana ce tsakanin 'ya da mahaifinta,changing course falaak din ke sonyi kai tsaye zuwa bangaren qur'anic science. Cikin sanyin murya take bawa sultane hujjojinta,saidai can qasan muryarta shi ya dago wani abu da sultane din bai hanga ba. Saidai baice komai ba,don yana ji a ransa na huruminsa bane.....bai shafeshi ba. Hasalima ba komai yakeson sultane yaci gaba da sanyashi a ciki ba......don zamansa temporary ne,baya son sultane din yayi mugun sabon da rashinsa a kusa zai iya zame masa matsala da kuma damuwa. A karon farko idanunta suka fara sauka a kanshi sanda sultane da falaak duka suke daga kansu zuwa gareta,saidai shi din labbansa ne kadai suka motsa alamun ya amsa sallamar,amma koda gashin idonsa bai motsa ba da nufin daga kanshi har ya sauke dubansa a kanta. Wani irin abu taji ya saukar mata,zuciyar ta taji tana quntacewa guri guda tana matsewa a qirjinta. Banda sultane ya riga daya ganta.....banda irin wannan ranar yafi dacewa suyi magana da sultane su qare don ta samu daman komaqa Niamey a cikin wannan satin ba shakka da ba abinda zai hanata komawa da baya saboda ganinsa da tayi a wajen "Me yasa ko yaushe?.....ko yaushe nake buqatar 'yancina?,ko yaushe nake buqatar magana da mahaifina shi din yake kasancewa a gurin?......me yasa na rasa 'yancinnan......wannan matsayin na kebancewa daga ni sai sultane tun daga sanda ya wanzu a masarauta?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar tana jin wani irin bacin rai yana sauka matar gami da gusar da dan guntun freshness din data samu na samun bulalliyar mafita. Da wannan kallon dake cike da kulawa......da wannan kallon dake dauke da qaunar datasha banbam data sauran 'ya'yan da ya haifa......qaunar da a wannan karon yake qoqarin yaqi da ita yake dubanta. Da rusunannun idanunta ta qaraso tana yiwa kanta muhallin zama daura da falaak. Numfashinta take qoqarin daidaituwa,tana jin yadda dakin gaba daya ya gauraye da wannan qamshin dai. Wannan qamshin da har yanzu ta rasa makamancinsa......qamshin nan daya zame mata tamkar jarrabi tun daga hippodrome kawo yau......qamshin da har yanzu ta rasa waye ainihin mamallakinsa?......wanne irin turare ne wannan me kassara gabobi?. "Barka da safiya yaa biftu" Falaak ta gaidata cikin girmamawa qauna da kulawa irin ta 'yan uwantaka. Motsa labbanta tayi da qyar tana maidawa falaak. "Barkanki.......barka da safiya bappi" Ta furta tana rusunar da idanunta da kanta don nuna girmamawa ga sultane din. "Barkanki kadai khadeejatu". Ya kirata da asalin sunanta,sunan da ya sauka sosai saman zuciyar haisam ya kuma maimaitashi cikin qirjinsa har sau biyu 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 26* Sunan wani suna ne da yake da tarin daraja martaba da kima a idanunsa,sunan NANAY dinsa......halittar 'ya mace ta farko daya soma so da qauna a rayuwarsa,yake kuma qauna har yanzu,yake martaba dukkan wanda yake da irin sunan bama ita kanta din ba. Dauke idanunsa sultane yayi daga kan akhnan din data koma wani cool,yana karantar duk wani yanayi nata da motsinta,yana kuma ankare da yadda bata gaida haisam din. "To kaji muhammad......ita kuma qanwar naka canjin course din da takeso tayi kenan" Sultane ya fada da murmushi saman fuskarsa yana duban haisam cikin tarin kulawa da kuma kwadayin shigar haisam din kowanne al'amari daya shafi iyalinsa. Ya fuskanci har yanzu haisam din bai shiga lamarin iyalinsa da zurfi yadda yakeso ya shiga ba. Yanaso ya saje dasu ya dinke dasu sosai,ya zama ba wani banbamci ko kadan a tsakaninsu. Wani miskilin murmushi daya kashe zuciyar falaak ya kuma sanya gabanta tsananta faduwa ya saki,ya tashi ya gyara zamansa sosai yana duban sultane. "Ana iya bata dama a ganina.......abinda ta buqata bai sabawa ra'ayinka da burinka ba......bai kuma sabawa addini da al'adarta......ubangiji zai sanya albarka sosai a ciki". "Gaskiya ne" Sultane ya fadi cikin tsananin gamsuwa yana gyada kanshi. Daga qasan ransa yana jin kamar akwai wani saqo da yakeson isarwa ne me matuqar muhimmanci. Iska ta zuqa sosai cikin kiyayewa da fitar numfashinta,ta qanqance idanunta kadan tana jin saukar maganarsa cikin tsakiyar zuciyarta,tana jin maganarsa kai tsaye tana tunkarota da wani irin yanayi me qarfin gaske. A hankali zuciyarta ta fara maimaita mata DAKE YAKE,maganan ta soma takura zuciyarta tana son tilasta mata jin muzanci,muzancin da alfaharinta da izzarta suka hana ya mamayeta. "Zan baka mamaki......zan kuma kunyataka gaban sultane tabbas.......sai sultane yasan kaine namiji na farko daka fara hada jiki da diyar da yafi qauna duk duniya har sau uku!" Ta dire alwashin cikin zuciyarta tana jin qwarin gwiwar kiran sunan sultane din. "Bappi......" Ta kirashi tana sunkuyar da kanta "Khadeejatu" Ya amsa mata kai tsaye. "Zan iya samun mintuna biyar?". Idanu sultane ya dan zuba mata sannan ya waiwaya ga falaak. "Tashi kije mamana......zamu qarasa maganan". Gyada kai falaak tayi,sannan cikin girmamawa ta rusuna "A fito lafiya" Tace da sultane da kuma haisam da hankalinsa yayi nisa wajen bin CCTV camera din dake sassansa wanda yayi linking nata da wayar hannunsa. Wani motsi yake gani very suspicious ta daukan da yaja hankalinsa sosai. Numfashi ta sauke me nauyi,me yasa sultane ya gaza fahimtarta?,ba falaak take buqatar ya sallama ba......ba falaak take nufi ta matsa daga gurin ba,shine bata son gani a tsakaninsu.......shine bata qaunar wanzuwarsa a gurin.....tanason lokutan babanta ita kadai ne,tanaso ta kebe da mahaifinta ita kadai ba tare dashi a gurin ba. Tana ganin ya cancanci ya sallameshi......ya kamata ya fahimci akwai SIRRI cikin rayuwarta da wani bare bai kamata yaji ba.......magana ce data shafi rayuwarta da sirrinta,BATA SHAFI WANNAN SHEIKH DIN BA DAN GIRMAN KAI irin girman kan da take ganin yana batawa kansa lokaci ne.....irin girman kan da take gani bai kamata ya dorawa kansa shi ba a matsayinsa na ba kowan kowa ba,a matsayinsa na wanda baisan komai ba,baisan me rayuwa ke ciki ba. Tayi imanin koda cikin gida koda cikin fada tace zata zagaya dashi wasu guraren sai qauyancinsa da rashin wayewarsa sun bayyana muraran. Shurun da tayi batace komai ba ya sanya sultane dauke dubansa a kanta,ba tare daya buqaci tayi magana ba ya aza kan haisam. "Umra nake buqatar zuwa d'ana.......wannan lokacin na dauki lokaci me tsaho banje ba,ina buqatar zuwa gurinnan" Sultane ya fadi yana duban haisam. Daidai sanda ya gama gane gilmawar wanda ya gani,ya kuma tsaida daukan a daidai inuwarsa,ya daga manyan fararen idanunsa yana duban sultane cikin girmamawa. Kai ya jinjinawa sultane din,ya sani koda sultane bai fadi ba,sultane din yana buqatar yawan zuwa gurin don ajiye buqatunsa.......ya kuma yarda ya aminta shi din me yawan zuwa gurinne......wataqila shi yasa gagarumar gobarar dake ci cikin gidansa ta qarqashin qasa ubangiji ya hanata tayi tasirin da zata qona gidan qurmus ta kuma hadiye hardashi. Masarautar qunshe take da manyan al'amuran da idanun sultane basa iya gani.......tana dauke da manyan sirrika da manyan qullikan da haisam yakeji a jikinsa sun haura wadanda idanunsa suke gani. Inda shigowa rayuwarsu shine manufarsa.......inda ace shigowa rayuwarsu shine abinda target dinsa da farko,ya tabbatar akwai sirrikan da zai tonasu masu azaban doyi da rashin kyan gani. To amma tashi masarautar itace a gaba........tasa masarautar itace ta fiddoshi daga ainihin nashi izzar nashi sarautar da nashi qafin ikon dana mulki,ta maidashi wani malami dake zaune qasan alfarmar wasu cikin yanayi na karantarwa kadai. "Idan zai yuwu wannan karon inaso mu tafi tare,don inaso nayi kalan umrar da ban taba yi ba tare dakai d'ana,inason sanin gurare masu muhimmanci da zan gudanar da addu'o'in dake tari tari a zuciyata,ban sani ba ko zuwan qarshe zanyi,qila shi yasa Allah ya jefoka cikin rayuwata". Sultane ya fadi still murmushin nan baibar saman fuskarsa ba. Wani irin abune ya harba cikin qirjinta tana jin iskar da take shaqa wadda tun dazu ke gauraye da turarensa tana matse mata. Tun daga ranar data mallaki hankalin kanta itace take riga kowa sanin plan din sultane,tun daga sanda tasan meye ma'anar umara da aikin hajji ita sultane yake fara gayawa Lokacin da yakeson zuwa,su zauna kuma su tsara lokacin tafiyar.......ta dauki hutu daga company ta rakashi suje su dawo........yau duka wannan malamin ya samu nasarar ture dukka wadannan muqamai nata da sauri haka?.......anya baiyi amfani da asirin da taji da yawansu suna dashi ba wajen mallakar sarakuna ko juya akalar tunaninsu ba?. Dole ta zame cikin dabara ta zauna sosai,tana ji har cikin jininta yadda yau sultane ya maidata wata baquwa daban a gabansa,ya jawo bare......wanda babu dangin iya ko na baba a tsakaninsu yake fadimasa abinda ita ya kamata ita ya cancanta ta fara ji daga bakinsa. Baima maida hankali ga batun da tazo dashi ba......hankalinsa dukka yana kai wannan malamin da ayanzu jikinta ya fara bata akwai abinda ya yiwa sultane na janye hankali. "Na tsaneka......na tsaneka,tabbas saina nisantaka da mahafina......mahaifina nawa ne ni kadai.....sirrakansa da komai nasa......nan din layikana ne da babu me tsallakeminsu na zuba masa ido" Tayi maganganun qasan ranta tana hadiyar yawu da qyar saboda wani abu daya tsaye mata a wuya. Sallamarta da muryarta data fita fes da wani irin confidence shine abinda ya dakatar da maganan da sultane yayi niyyar fada ya waiwaya yana amsa sallamar tata,kamar yadda haisam da bai waiwaya ba ko motsawa daga zamansa ba ya motsa labbansa yana amsa sallamar muryarsa can qasa da sautin da bazaka jishi ba. Shine mutum na farko da idanunta suka fara sauka a kansa,ta zube idanunta fes a kansa,zuciyarta na wani irin motsawa. Tana jin inama zata ita sanin zahirinsa da badininsa da iya kallonsa kawai da takeyi a yanzu?. "KUSANCI" Abinda zuciyarta ta fara ayyana mata a kanshi kenan,tana qoqarin sarrafa kalmar ya daga fararen idanunsa a nutse,abinda ya harba wani irin faduwar gaba a sassan zuciyarta ya sanya janye idanunta da sauri a kansa,saidai hakan bai hanashi fahimtar kallon qurillar data zube masa ba wanda tuni ya jishi a jikinsa tun daga shigowarta gurin. "Zan iya tafiya idan hakan ya zamana ba damuwa a tattare da sultane?" Haisam din ya fadi qasa qasa cikin girmamawa. Kai sultane ya girgiza yana murmushi. "Akwai sauran maganganun da bamu kammala ba ai,baka gayamin yuwuwar tafiyar tamu ba ko dagata zuwa wani lokaci?". Sultane yayi.maganan daidai qarasowar mammina. Sake dauke idonta tayi daga kansa daga kallon qurillar data sake shiga a kansa akaro na biyu. Zamewa tayi cikin tsananin biyayyar nan da ba abinda ya sauyata tun daga wadancan shekarun xuwa yanzu ta soma gaidashi da salon gaisuwar da koda cikin bacci yake yasan ZAITUNA CE. Ta laqanci wani irin tarin girmamawa da sirrikan sake lulawa cikin zuciyarsa da samum matuqar girmamawa fiye da kowanne dan adam,saidai har yanzu wannan abun ya gaza canza MATSAYIN SAFEENA a rayuwarsa,abu daya daya fahimci mammina ta jima tana son samu kenan MATSAYIN SAFEENA daga bisani kuma ya karanci ta watsar da wannan ta shiga fafutukar gina nata matsayin,wanda ya ginu din kuwa da wani irin girma da kima. "Daya biyu uku hudu" Can qasan zuciyarsa yake lissafa adadin tsahonta sanda ta miqe daga gaban sultane tana laluben muhallin daya dace da zamanta,gurbin da zai bata daman ganin komai daidai da lissafi da hasashenta. Da wani irin yanayi yake iya hangenta,wanda zaka rantse da Allah bai damu da kowa ba sai wayarsa dake hannunsa,saidai bayan ta gaba idanunsa ta gefen hagu da dama na idanunsa ya samu wani irin horo da yake iya monitoring motsi da reaction na komai da kowa. Tsaf lissafinsa ya tuqe ga adadin tsahon mace ta biyu cif da cif.....daidai sanda take zama saman kujerar cikin wata nau'in izza dake cakude da taqama idanunta a kansa tana fadada fara'arta da zummar fara dasa harsashin farko a kansa na fara bashi kulawa ta musamman don shiga cikin komarta cikin sauqi. "Barka da warhaka sheikh muhammad" Tunda ta shigo ta karanci akwai abinda xai iya faruwa masu shige shige da wannan......akwai wani abu daya tsinto cikin muryarta da yake gaya masa confidence din data aro,wataqila don ta cimma wani abu ne.....ko don ta nuna cikin harin jiya ba abinda ya tsoratata ko kadan......saidai yafi karkata ga cimma wata buqatar.....don tun daga daren jiya zuwa safiyar yau ya samu labarin nasarar dasa kakkaifan tsoro da sukayi cikin zuciyarta. Da kalar girmamawar data bashi ya amsa mata gaisuwarta,sai taji wani iri,don bada wannan salon bada wannan harshen taso ya fara karbarta ba a karon farko ba a gaban sultane. "Khadeejatu baki gama shiryawa yin maganan bane?" Sultane ya furta yana duba agogon hannunsa. Numfashi ta sake ja kamar zata zuqe dukka isar da tayi saura a gurin,ta daga kai a sace tana duban mammina. Taji a jikinta sanda mammina ta shigo mamminan zata saita komai......zata sanya sultane ya tashi wannnan malamin daga gabanta......daga cikin shirgin daya shafesu.....cikin al'amuran da suke kebantattu garesu. "Muhammad haidam D'ANA ne......dan sultane muhammad hammud agg abba ne daya cancanci komai.....yake da ruwa da tsaki da dukkan komai" Kai tsaye sultane yayi maganan data daure musu kai gabadayansu..basusan daga inda maganar ya samo asali ba,basusan daga inda maganan ya dauko ba. Ido ta samu ta hada da mammina ko akwai wani taimako?,saidai idanu ta juya mata abinda ya alamtawa akhnan ba wani sauran abinda ya rage banda ta fasa maganar a gaban wannan malamin. Nazarinsa ya janye daga kan matar yana ganin yadda tayi amfani da idanunta ta sarrafa tunanin akhnan din,sarrafawar da lafazin mahaifinta ya gaza yinsa wanda ke dauke da sautin gargadi da wani tasiri kadan na bacin rai a cikinsa. "Done" Ya fada can qasan ransa,abinda yake buqata ya tattara a kanta kaso saba'in cikin dari ya kammala,iya wannan kason kawai ya isheshi ya afka cikin bin diddigin kowanne motsinta har zuwa sanda zai san alqarta da mutanen da suke farauta. "Bappi......na fitar da mijin auren kamar yadda ka buqata". 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 27* Tsit parlor din yayi,wani irin shuru ya ratsashi kamar ba sauran halitta a cikinsa data rage. Zukatan mutane biyu suka shiga nazarin kalmomin da suka fita a bakin akhnan din. D'aya bayan daya haisam ke fasa kalaman bakinta.......bawai don bada hankali akan masa'alar da bata shafeshi ba,don shiga nazari a kalamai daga bakunan mutanen da bai gamsu da maganganunsu ba ya zame masa dabi'a. Introvert person ne na gasken gaske. Wanda shurunsa yakan zama nazari ne......kauda dubansa yakan kasance hakaltar dan adam. Yanayin kaman bai gani ba kuma ya gani,zaka dauka ya manta amma yana hankalce......yana ajjiye da komai. Ba komai ke burgeshi ba kaman yadda ba komai ke bata ransa ba,ko yaya yake akwai alamu na rashin gaskiya a tattare dakai yana iya fahimtar hakan,omari yakance. "Me laifi kamar wani qamshi daban yake maka cikin hancinka?" Murmushi kawai yake baiwa omari amsa dashi,shi kansa a lokuta da dama mamakin kansa yakeyi. Sake janye nazarinsa a kanta yayi ya maida kan mammina da tayi qasa da kanta. Iya nutsuwar da yanayinta ya nuna kadai ya tabbatar masa tasan komai......iya yadda tayi shuru kawai ya tabbatar masa akwai wani abun a bayan shurunta. Me yasa sultane bazai fahimta ba wai?. Ya samu kansa da tambayar kansa da kansa. SULTANE BA IRIN KAI BANE......MUTANE DA YAWA BA IRINKA BANE. Amsar da zuciyarsa ta bashi kenan ta kuma tilastawa kanta da kanta yin relaxing. "Kula da al'amuranta da suka shafi bincikenka shine priority dinka.....shine dolenka,dole komai ka barshi a inda ka ganshi,dole komai ka barshi a yadda yake indai bai taba bincikenka ba....hakanne kawai zai baka nutsuwa da tafiyar da aikinka kadai cikin tsari da yanayin daya dace" Ya fadawa kansa da kansa,sai ya samu kansa da zare duk wani yanayi da aikinsa daya soma hawa kan ruhinsa da zuciyarsa. Zuciyar sultane taci gaba da harba jini a hankali,yana jin sauran buri da fatansa yana kwaranyewa. Mafarkin da yasha shafe darare yana yi......addu'o'in da yafi tunanin rashin alkhairi da rashin dacewar abun ubangiji ya kalla wataqila ya dakatar da amsar addu'arsa. Sai da yayi gyaran murya "Ma sha Allah......Allah yasa albarka,na tayaki murna.....amma kuma.....sanda kika shigo banga kin gaida WALIYYIN naki ba" Ya furta maganan yana tsare akhnan da ido. Idanunta ta daga da sauri abubuwa biyu suna dukanta. Yadda SULTANE yayi accepting maganan cikin sauri?,cikin sauqi?,ba tare da kalar kowacce tambaya ba?,ba tare da kalar kowanne challenge ba. Maganan WALIYYI ita tayi Mata tsaye a rai,tana son banbance ma'anar waliyyin da ya furta,amma kwanyarta ta kasa wani cikakken aiki a wadannan mintunan,sai tayi qasa da kanta tana jin muzanci yana bin sassan jikinta da jininta gaba daya. Muzancin da bata taba jin kalarsa ba tana jin yadda kalaman sultane ke raunata duk wata izza tata daya kamata ya zama na farko wajen dagata tana fadin. "Barkanka da safiya". Da fari kamar baiji maganan nata ba,don ba a nan hankalinsa da lissafin abubuwa masu muhimmanci a wajensa yake ba,amma sai zuciyarsa ta harbo masa muryartata,abinda ya jinkirta amsawarsa kadan kafin yace "Barka". Kai sultane ya jinjina,yayin da yanayin amsawar tasa ta sake danqara wani irin zafi saman zuciyarta,zuciyar daketa kokawar gano WALIYYINKI da sultane ya fadi,saidai kuma bai barta tayi nisan zango a tunani ba ya gajarta mata komai ta hanyar fadin. "Juma'a......juma'a me zuwa ba wannan da muke ciki ba za'a daura aurenki da mijin da kika gabatarmin din......in sha Allah sheikh haisam zai wakilceni zai zama madaurin aurenki!". A razane ta dago kai......ba kuma ita daya ba,hatta da mammina maganan ya razanata. Bata razana bane don daura auren akhnan da aka zabge masa kwanakin wata ba......ta razana ne saboda GIRMAN MATSAYIN da sultane ya dauka ya baiwa malamin. A iya saninta.....dauren auren d'iyar sarauta.....diya me cikakken gata,wadda izzarta darajarta da martabarta ya kerewa dukkanin diyoyin gidan sarautun da nijer ke dashi......waliccin aurenta wani abune me tsananin tsada da kowa ke yunwar a bashi,da kowa ke fatan sultane ya zabeshi.....wani abune da zai zama GIRMA da martabawa me tarin yawa da ba zata shafe ba cikin babin tarihin rayuwar dukkan wanda aka bawa......wanne irin GIRMA da MATSAYI ne yaron ya taka haka a zuciyar sultane cikin qaramin lokaci ba tare data ankare da haka ba?.......sai a yau ta sake yadda ta kuma tabbatar da gaske ne sultane YA D'IYANTAR DASHI......da gaske ne da sultane yace YA MAIDASHI D'ANSA da gaske yana nufin abinda ya fada din......iya yau kawai ta tabbatar mata da haka. Amma kuma tana raye?.....ta yaya zata bari haka ta faru?.....ta yaya zata bari haka ta kasance?. Ta kasa haifawa sultane MAGAJI kamar yadda ta hana kowacce d'iya mace haifa masa magaji sai magajiya qwalli biyu da take jinsu kamar wutar dake cin naman jikinta a kowacce safiya idan ta kallesu. BAI KAMATA TAYI SAKACIN DA WANI ZAI HAURO ta saman kanta ba......ya rusa duk wani matsayi kusanci da martaba da tayi shekaru tana tattalinsu ba.....bai kamata ta bari wani ya fado tsakiyar wannan kakkauren zaren data debi shekaru tana saqashi ba ya tsinkashi. Waninma da har yanxu xuciya da gangar jikinta ke alamta mata DANGER a duk wani kallo da zata aza idanunta a kanshi ba. "Bappi......bayan dukka wanzuwar su kawu mammani dake raye?". Akhnan ta samu kanta da furta tambayar tana duban sultane da wani irin sanyin mamaki daya daketa. Kai tsaye yake duban idanunta shima,sannan ya jinjina kai. "Bakisan MATSAYIN D'A a wasu guraben ya haura na DAN UWA BA?......Bakisan kuma matsayin D'A wajen yin waliccin auren qanwarsa ya zarta na kawunnanta ba?" Maganar tasa ta fito da wani nauyi me yawa daya sanyata maida kanta qasa kawai. Banda tauri da kafiya gami da tsaiwa da zuciyarta ke dashi.......banda tattalinnan da takewa GIRMA da IZZARTA ba abinda zai hanata fashewa da kuka a yanzun nan. "Amma ranka ya dade......Allah ya taimakeka.......bai kamata kafin ka yanke rana da komai ka tsaya gana da yaron ba?......kasan wayeshi da asalinsa?" Tayi maganar da sanyin murya da sanyin zuciya,sanyin daya sanya haisam tattarasu dukka ya aza saman ma'auni daya. "Ba buqatar hakan......indai ta iya gabatarmin dashi......ta sani ya dace da dukka wani tsarinta ne......ku shirya komai,zata zama matar aure nan da kwanaki goma masu zuwa.....kaji abinda na fada muhammad?" Ya maida dubansa da tambayarsa kan haisam da yayi kaman baya wajen. "Indai wannan din umarni ne daga gareka zan cikashi in sha Allah" "Umarni ne haisam.....umarni ne muhammad" Ya furta cikin nuna girman umarnin nasa da gasken gaske. "Ranka ya dade......ba kuskure kuwa?,.......ya kamata a duba.....muna neman alfarma,aure ba wasa bane.....diyarka mafi daraja zaka miqa......." "Zaituna ya isa haka......na rufe wannan babin har abada,na rufe matsalan akhnan akan aure har abada......bana son wani ko wata su sake tayar da ita......yin hakan zai iya sawa mutum ko waye ya fusakanci mummunan hukunci daga wajena kai tsaye kuma" Runtse idanunta tayi tana jin kamar jiri na shirin kayar da ita daga zaunen da take. Ta gaji da zama a gurin,tanaso ta shaqi wata iskar daban bayan wannan,tana jin kamar wannan iskar ta gurbace da yawa,don haka ta miqe cikin girmamawa. "Na gode bappi......" Ta iya hada kalmomin da qyar "Madalla" Ya amsa mata a taqaice yana kauda idonsa daga dubanta,wani abu yana cakar zuciyarsa. "Tafiyar zata yuwu?" Sultane ya sake tambayarsa,tambayar data aza masa wani tarin nauyi ta kuma sake jan hankalin mammina cike da mamakim wacce tafiya sultane din zaiyi wadda ita bata da labarinta?. Tafiya da sultane wani abune da zaya bata tsarin aikinsa gaba daya......dukkan wani plan nasa na kammal aikinsa cikin wata daya zuwa wata daya da rabi yana jin zai iya samun naqasu ko koma baya. Amma kuma ta yaya zai fito ya gayawa sultane haka kanshi tsaye?. "Na fahimceka muhammad......kada ka damu,zamu wuce da babban limamina......zan iya barin kulawar masarauta a hannunka?,sati biyu kacal da jagorancin wazeer hamza?". Wani nauyin ya sakeji sultane ya aza masa,amana komai qanqantarta tana masa nauyin gaske,baya qaunar dukkan wata amana da za'a bashi ace ya riqeta,idan kuwa har aka bashin yana qoqarin cikata da dukkan iyawarsa......da duk wani qarfi nasa daidai da yadda yasan yana da abun fada gaban Allah. To amma a yanzun idan yace zai riqe wannan amanar......yayi imani a jininsa yana jin SARAUTARSA zata iya motsawa......zata iya bayyana kanta da kanta daga lungun da yaje ya ajeta......zata danne matsayin da yaketa qoqarin daidaita kansa a yanzu......zata iya murqushe siffarsa ta MALAM ZALLAH ayanzun ta fito da siffar da har yabar agadez bazai yarda a sanshi a cikin ta ba wato SARAUTA. To amma bai kamata ya wofantar da komai da sultane yazo masa dashi ba,don haka ya motsa kadan. "Zanyi iya abinda dama da iko suka bani,bani da alaqa da mulki ko sarauta irin naku.....bansan ya komai zai tafi ba" Maganarsa ta harba wani abu saman zuciyar mammina daya tilasta murmushi fita saman fuskarta. DAMA ce wannan din da idan tayi amfani da ita da kyau zata zame mata silar samun abubuwa masu yawan gaske. "Na yarda dakai,na kuma aminta dakai,nasan zakayi iyakacin iyawarka da dukka qoqarinka.....Allah yayi maka albarka,ya sakawa uwayen da suka kawoka duniya da alkhairi....." "Ameen" Ya amsa yana lumshen idanunsa,addu'a da ya yiwa motii da nanay yana jin sun biyashi a komai. Abinda ya kawota ya kammala,ta samu kuma sama da abinda take buqatar samu,don haka ta miqe tsam cikin girmamawa. "Ina neman izinin zuwa babban asibiti......zan duba maras lafiyanmu da hari ya ritsa dashi a jiya,da sauran majinyata dake asibitin" Sirrintaccen murmushi ne ya kubuce daga can qasan zuciyar haisam "Good job maher" Ya furta can qasan ransa. Shi ya buqaci maher da ya buqaci ganinta.....kuma kafin zuwanta an gama tsara yadda komai zai kasance. Yana buqatar fitarta daga masarautar koda na awa daya ne.....wannan space din yake buqata don isa ga abun hannun nan.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 28* Murmushi kadan sultane yayi,duk da cewa baya cikin yanayin. Wani kyakkyawan dabi'arsa da haisam yayi noticing shine,yana da son farantawa iyalinsa da sauraren ra'ayinsu,dabi'ar da tayi kamanceceniya sosai data motii dinsa. Qoqarin shiga sahun mazan da manzan Allah yace sune mafi alkhairi a duniya...wato mazan da suka kasance mafi alkhairi ga iyalansu,wadanda suka samu shaida me kyau game da iyalansu kenan. Dabi'un mammina da yawa suna burge SULTANE.....cikin su harda yadda ta zama me sakakken hannu da nuna damuwa ga mutanenta tsananin damuwa. Morsa safiyya hakan take itama,saidai nata da banbanci,tana duba abinda ya cancanta a yiwa hakanne,wanda bai cancanta ba tana dauke idanunta daga kai. Ba komai take bari a bayyana ba na alkhairinta.....sabanin mammina da takan bayyana motsinta na alkhairi komai qanqantarsa,takance tana yin hakanne saboda sauran masu sukuni suyi koyi da ita,su taimaki wanda baidashi....wanda ya gaza dame nema,hakan kuma sai sultane yaji shima hujja ce. "Allah ya bashi lafiya shida sauran majinyata,masarauta zata ganshi in sha Allah". "Giwa na godiya" Ta amsa cikin tsananin ladabi sannna ta juya tana takawa a nutse ta fice. *HAISAM* Jikinsa yaji yana mutuwa a hankali sanda yake baro sassan SULTANE. Akwai mintuna ashirin kafin lokacin sallar azahar. Sosai yaji gilmawar mutum daga bayansa,gilmawar da baka isa ka gane an wuce din ba idan ba irin mindset dinsa kake dashi ba,saidai shi yaga inuwar,yaga kuma wucewar ta inuwar gabansa,saidai yanayi zubi siffa da tsarin wanda yake kyautata zaton ya wuce din bai masa kama da suffa da zubin bulama ba........sai ya dauko qididdigar jikkunan TAMIM guda biyu. A tamim qarami lissafinsa ya tsaya,yadan maida tunaninsa baya kadan akansa kafin ya samu guri ya ajiye nazari a kansa zuwa lokacin da zai zama free,don yanzu akwai abinda yakejin yafi masa komai muhimmanci da ya aiwatar dashi. Daga saba'in xuwa saba'in da biyar yaji ya sake matsar da matakin mammina. Ta shirya komai kuma ya faru kaman yadda taso shine abinda zuciyarsa ke faffasa masa shi. Tafi kowa sanin halin sultane,tafi kowa kuma karantarsa.....idan ranshi ya baci akan abu baya doguwar magana a kansa......tayi nasara,saidai tata nasarar shi ta zame masa wani.mabudin aikinsa. A yau dinnan yakeso ya fara dasa masa tarakuna har guda biyu......don haka ya wuce Kai tsaye zuwa ga sassansa yana sanar da yaron gidansa qasa da mintina ashirin yana buqatar dukkan wasu masu alhakin kula da tsaron gidan dama wanda ke kula da kowanne sashe na gidan,hadimi da hadima,babba ko yaro,mace ko namiji a babban filin dake ajiye a bayan ginin masarautar daya tabbatar zai daukesu gaba daya,ya kuma aikewa da omari saqon karta kwana da dukkan tsarikan da yake ganin zai amfani dasu. Dukkanin nazarinta da nutsuwarta ta hada guri daya,tana kuma sake zurfafa tunaninta gaba daya akan komai daya faru tsakanin jiya da yau din. Tana jin wani iri da qyashin yadda sultane ke shirin miqa ragamar komai a hannunsa,a hankali kaman yana raunana power din kowa.......kamar yana son fara juya ra'ayin sultane da fara sarrafa tunanin sultane din. Kamar ya fara aiki da wani abu me qarfi da batasan meye ba wajen sarrafa sultane din da tunaninsa gaba daya. Riqon qwarya wa fada da kuma damqa waliccin auren akhnan a hannunsa?. Wani siririn murmushi ya qwace mata,ta gyada kanta a hankali. Tana jin kamar lokaci ne wannan na samun cikakkiyar damar da zata sake wani abun fashewar,abun fashewar da take kyautata yaqini da zaton zai iya tashi harda shi,ya kuma zame masa mummunan bala'in da zaiyita binsa har qarshen rayuwarsa. Can qasan zuciyarta kuma zafi takeji,zafi takeji sosai na yadda sultane ya yanke hukuncin damqa ragamar masarauta da auren akhnan a hannunsa. Da farko ta tashi a yau da zummar ta jashi a jiki don sarrafashi kaman yadda take sarrafa kusan duk wani me fada aji cikin masarautar.......to amma tana kokwanton yiwuwar hakan,don wani abu take hange tattare dashi da yasha banbam da wanda take gani gurin sauran mutane. Juyawa tunaninta yayi ga Maher......ta jima tana ganin matashin cikin gidan,tana kuma da haske a kansa kan baida matsala da kowa. Irinsa take so,irinsa ne kuma kewaye da ita,wadanda sukan iya sadaukar da rayukansu da rayuwarsu saboda ita,ba shakka ya cancanci ta duba wani gurbi ko muhalli kusa da ita tayi masa mazauni. *HAISAM* Cikin qanqanin lokaci ya kammale dukkan wasu masu tsaro na gidan. Hadimai ne bayi ne da sauran ma'aikata da masarautar ta qunsa,ya kuma yiwa taken laqabi da taren wayar da kai. Qofofi hudu yasa aka fitar na shiga gurin taron. Uku na shigar mata,biyu na shigar maza. Kowacce qofa kafin ka shiga sai ka sanya sunansa saman takardar dake ajiye a bakin qofa a hannun manyan hadimai na gidan,ciki kuwa harda tamim babba da qarami da kuma bulama. Yana sane ya basu wannan aikin na tsaiwa kan kowa ya rubuta sunansa,hakan shine zai riqe masa su a gurin,ba wata dama ko hanya da musayen aiki ko matsawarsu a gurin har sai an kusa tashi a taron. Duk wani hadimi da hadima dake tsaron sassan mammina an tsara rukunin zamansu a can ciki,yadda fita daga dakin taron zai zame musu long process,baya ga haka ya kasance doka ta zama dakin taron har zuwa sanda za'a kammala taron. Shi da kansa yaso ya jagoranci shiga sassan mammina,saidai yana da wani irin fikira da tsananin hangen nesa. Bacewarsa a gurin zai iya zama babbar ayar tambaya ga duk wanda yasan wani plan daya shafeshi komai qanqantarsa. Duk da bai sani ba,amma yana jin a hankali wani abu me kama da ana ci gaba da babiyar kowanne motsi da daga qafa tasa. Cikin hikima qwarewa da sanin makamar aiki yake hada ayyuka biyu. Aikin farko shine monitoring na shigar abdii sassan mammina,tun daga qofar farko da zaka taras ta shiga sassanta har zuwa gurin da suka nufaci zuwa. Camera ne qarama da ya sanya abdii maqalewa daga gaban rigarsa,ta yadda zai dinga ganin komai tamkar tare suke shiga gurin dashi. Bai taba tunani ko kawowa a ransa zai bawa abdii wannan aikin ba. Amma yadda yaron ya tsaya a gabansa da wani irin confidence yaji a ransa bari ya gwada. Ya dafa kafadarsa bayan ya gama shirya abdii din da yanayin shigar da yakeso ya shiga gurin. "Wannan ba muhallin wasa bane abdii,wannan din wani gagarumin aiki ne mafi hatsari da zakayi......faduwa ko nasarar dukka ni zatafi shafa kai tsaye......rayuwar motii rayuwar nanay rayuwar oromia gaba daya". Da wani kalan murmushin nutsuwar da bai taba gani ba saman fuskar abdii din yake kallonsa. "Obbo......nayi maka alqawari.....zan cikashi,zan kuma baka mamaki" Abinda yace da haisam kawai kenan. Musayar kallo suka yiwa junansu na wasu daqiqu,haisam din ya dan daki kafadar abdii sannan ya ya juya a nutse yana ficewa. Kamar a yanzun da suke gurin,ya rarraba aikin zuwa ga mutane daban daban,duk da basu da yawa,amma yana saka ran qaro wasu cikin mutanensu uku da suka rage suna rayuwa cikin agadez din tun kafin isowarsa qasar. Beeno da salawi suna cikin hadiman,sun saje sosai dasu suna karantar reaction din kowa. Bayason bayyana fuskar dukkanin mutanensu,saboda hakan zai zama wani hadari ne na daban,kuma zai zama wata hanya ta rashin security. Omari yana tare dashi amma ta bayan fage,yana tayashi monitoring motsin abdii da ya soma nisa cikin sassan mammina din. Zuzzurfan muryar nan tasa dake dauke da wani irin amo ya sanya duk wani dake gurin nutsuwa da tattarar hankalinsu guri guda a kansa. Kusan ba wanda a gurin baisan sheikh muhammad haisam ba,musamman hadimai mazan dake cikin gidan,wanda dukkaninsu sun samu sanarwar nad'ashi a matsayin D'A,sanarwar da ta zauna cikin kwanyar kowanne hadimi na gidan take kuma aiki tamkar sauran dokoki cikin gidan. Har cikin jinin tamim yakejin wani abu yana tsarga masa game da yanayin muryar haisam din,wani irin yanayi da ya saukar masa da wata mummunar kasala a dukka gabobinsa. Yana jin wani abu daban tattare dashi,yana jin wani yanayi na daban a muryarsa......kamanninsa dama tsaiwarsa gaba daya. A nutse ya koma da baya bayan kammala jawabansa ya bawa ME WADA guri. Shine kusan dukkanin shugaban hadimai maza dake gidan,wanda haisam ya zauna dashi na mintuna goma sha biyar kafin su shigo nan din,ya kuma bashi tsarin abubuwan da zai gabatar musu. Akwai sabbabin dokoki da tsare tsare daya shirya gabatarwa daga sanda sultane ya tashi zuwa umra. Sai a yanzu yake jin kamar wata dama ya samu da zai bude wuta akan aikinsa ba tare da tunanin sultane zai hango komai daga gareshi ba. Sabbin dokoki ne da zasu zama wajibi akan kowa dake rayuwa cikin gidan,yanaso kuma ya gabatarwa da sultane su ya sanya hannu a jimlace su zama TABBATACCIYAR DOKA da zai rarrabata tsakanin dukkan hadimai da bayi na gidan. "Be fast abdii" Haisam ya furta qasa qasa yana duban tsakiyar tafin hannunsa da na'urar ke maqale,wanda zaka dauka tasbihi yakeja. "Na kusa qarasawa ainihin muhallin da take kebancewa" Ya fada cikin qwarewa da takatsantsan da dukka motsinsa,duk da taswirar hannunsa da haisam ya tsarata tsaf tana nuna masa kowacce hanya daya kamata kayi. Qofar glass din ya zuge gefe daya,ya kuma shiga a hankali. Tafkeken parlor dinta daya zama na musamman ne ya soma bayyana,wanda yake dauke da wani irin nau'in ado da yaja hankalin haisam din. "Obbo......oromian....." "Dakata!" Haisam ya tsaida abdii. "Ba wani hatsari?" Abdii ya tambaya saboda tsayuwar data zama ta ba zata. "Turn to your left side" Ya bashi umarni yanason ganin wani abu da yaga gilmawarsa. Yadda haisam din ya fadi masa hakan yayi,take tafkeken frame din dake dauke da wani nature drawing ya bayyana. Sosai haisam ya zubawa frame din idanu,wasu abubuwa suna dawo masa akai. Wasu shekaru can baya da wasu memories da suka ja hankalinsa sosai. "Ka dauki hoton frame din ka turamin......kafin ka shiga ciki.......kaje ka duban dining table na sassa......idan baka samu komai ba a nan ka qarasa store da yake manne da babban kitchen dinsu". "An gama obbo" Abdii ya fadi yana ciro wayarsa yayi snapping frame din sannan ya soma laluben bangaren dining. Ba jimawa ya sameshi,tun bai qarasa ba ya hangeshe sheqi da kwanukan abinci na alfarma da suka janye hankalinsa. A yanayinsa kamar anci abinci ba jimawa a wajen. "Inason ganin kwanukan da kyau.....da abincin dake cikin kowanne......ka hanzarta,don kowanne lokaci hankalinta yana iya karkatowa gida" Haisam ya fada yana duban agogon dake harbawa saman device din. "Ko da zatazo ta ritsani,ba shakka sai na yiwa obbo wannan sadaukarwar,koda wannan shine abu na qarshe da zan aiwatar cikin rayuwa ta" Abdii ya furta da wani irin confidence da ya sanya haisam sakin sassanyan murmushin da baiyi niyya ba. "Obbo....." "Stay silent abdii.....just be quick......you know idan ta sameka a nan you finished" "Obbo......English dina baiyi qarfi ba ka sani...." "Abdii" Ya kirashi da zuzzurfan muryarsan nan me kauri cikin sigar jan hankali. Ya sani sarai halin abdii,komai sai ya sanyo wasa a ciki,idan kuma baiyi da gaske ba lallai lokaci zai iya qwace musu.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 29* Daya bayan daya abdii ke musu hotuna,bakinsa cike fal da zance d kuma mamaki. Komai na abincin kamar suna cikin yankin jimma.....komai kamar suna sassan qabilar oromo.........hatta da shayin. Kai tsaye haisam yaci gaba da guiding nasa,yana yi yana kasa hankalinsa biyu omari yana riqa masa,har zuwa lokacin daya isa ga bedroom dinta da bincike ya nuna masa tafi zama a cikinsa,saboda gwaji da awon yawan saukar numfashi a dakin da yayi daga bayan gine gine gidan. "Finally obbo......from where i should start?". Ya tambaya cike da jiran umarni. *MAMMINA* "Idan ka qarasa villah street ka tsaya a nan" Mammina ta bawa driver din nata umarni nakai tsaye bayan fitowarsu daga duba Maher da aka bata tabbacin sallamarsa a yau din. Sosai Maher ya cika da mamakin ganin zuwanta ita daya qwallin qwal,ba wani tarin motocin dake take mata baya a duk sanda zatayi fita irin wannan.....ba wani hadimi ko me tsaronta kamar yadda ta saba fita irin wannan?,wannan yabar masa ayar tambayar da tana fita ya aikewa haisam da hasashensa da kuma abinda ya gudana tsakaninsu. Villa street din wani guri ne daya zam emata wata mahada......wata mahada me tarin sirri,zuzzurfan sirrin da ba wani hankali ko tunani a nan kusa da ya taba tsinkayoshi. Rufaffe kuma adanannen sirrin da duk tsananin kusancinka da ita bata lamuncewa kowa saninsa ba. Wayarta ta fiddo,ta kuma soma shigar da wasu lambobi da ko da wasa bata taba ajiyarsu cikin wayar ba,iyakacin zamansu cikin kanta,da zarar kuma ta sakasu a wayar ta gama duka amfanin da zatayi dasu take sharesu. Tana shirin danna dan maballin kira kira ya shigo wayarta,ta tsaya cak ta zubawa kiran ido tana kallonsa. Siririn tsaki taja,akhnan ce.....a irin lokaci irin wannan bata qauna ko fatan abinda zai katse mata dukka shirinta,to amma a yanzun tana buqatar yarinyar a kusa......tana buqatar nuna mata tausaya sama da yadda ta saba a baya,don haka ta yanke nata uzurin ta daga kiran. Iya daga kiran mammina din kawai ya sanyata sakin wata nannauyar ajiyar zuciya. Ta kowanne bango ji take rayuwar ta matseta,komai kuma baya tafi mata daidai. Wani muzanci takeji har cikin jininta.......wani fusataccen yanayi takeji da dukkan abinda sultane yayi mata a gaban malamin. "Mammina.......ina buqatarki......ina buqatarki a kusa dani" Sirrintaccen murmushi ne ya subuce mata saman labbanta. Yadda dukka rayuwarta numfashinta da kowanne kalar motsi nata ta dogara da ita yana burge mammina din.......yana mata dadi idan ta tuna yadda ta sanya dukkanin motsinta ta ta'allaqa da ita. "Na sani akhnan.....karki wani damu......fitar gaggawa ce ta sameni,naje duba mara lafiyan daya raunata ta sanadinmu......ina kan hanyar dawowa nan da awa daya". "Okay" Ta amsawa mammina din da wani irin yanayi. Wani boyayyen rauni ne da ita daya ita zaituna take iya ganeshi..... Murmushi ta sake saki,a hankali dai wannan taurin kan......wannan kafiyar.....wannan zafin kan yana juyewa zuwa wani irin rauni da laushi. "Muje zuwa.....sakamako ne wannan zuwa gareku gaba daya ahalin diory hamani". Ta furta a sarari qasa qasa. Lambobin ta sake zubawa ta kuma kira,dab da zata katse wata kakkausar murya mara dadin amo ta amsa da "Alo" "Ina bakin iyaka" Ta fada a taqaice,ba tare kuma da an amsa mata ba aka kashe kiran,sai itama bata damu ba,don tasan hakan wani tsari ne dadadde da suka jima akai. A nan duk wata mota data daukota take sauketa,ta kuma juya ta koma ta tsaya a duk nisan inda aka umarceta......sannan wata motar daban ta dauketa ta qarasa da ita zuwa SANSANIN SIRRINTA!. Tana maida wayarta jakarta wani irin mummunar faduwar gaba da batasan daga inda ta yanko ba lullubeta. Har cikin kunnuwanta takejin sautin bugawar da zuciyarta tayi,saita maida idanunta ta runtse. Tsahon sakanni talatin ta dauka tana qoqarin saita kanta da wani irin tashin hankali. Wani yanayi da ba kasafai yake alamta mata komai yana nan a daidai ba......wani yanayi da a cikin kaso dari kaso sittin idan ta jishi akwai wata matsala ko damuwa da batasan da ita ba a bayan fage. "Juya mu koma" Ta bawa driver dinta umarni kai tsaye. Haka kawai takejin hankalinta yayi gida,haka kawai takejin kamar akwai abinda ta manta,kamar abinda ya kamata ta dauka bata dauka ba,kamar akwai abinda ta bari ba'a muhallin da ya kamata ta barshi ba. Cikin cika umarninta ya karya kan motar yana fadawa hannun dake daura dasu yana qarawa motan sauri kamar yadda ta buqata. Wayarta ta sake cirowa,tana tuna cewa taga tarin missed calls din yalwa. Da gaggawa ta maida kiran tana tsammanin dagawa daga bugu daya kaman yadda ta saba,saidai har ta gama ruri ba'a dauka ba. Abun ya bata mamaki qwarai,don ba wanda yake da zarrar da zata kirashi a kiran farko ba tare daya daga mata waya ba,don ba kasafai suke kiran hadimi ko bawa ba,saidai susa daya daga cikin hadimansu su kira musu duk wanda suke da muradin magana dashi,wannan shine cikakkiyar izzarsu....qasaitarsu da kuma sarautarsu. A kira na biyar data yiwa yalwa sai taji kamar ta rufe idanunta ta bude ta ganta a gida "To waye zata kira?" Ta tambayi kanta da kanta,kafin tunanin tafisu ya fado mata. Saida na'ura ta gaya mata ba zata iya sadata da tafisu ba sannann ta tuna,yau tunda asussuba tafisun ta wuce zuwa fataucin data saba yi duk bayan wani zango don kadar da hankalin me hankali a kanta. "Ina buqatar nan da mintuna goma mu isa gida" Kawai ta fada cikin umarni nakai tsaye "An gama ranki ya dade" Driver din ya amsa mata yana qarawa motar gudu kaman yadda ta umarta. "DONE!" Shine abinda abdii ya fada da muryar nan tasa da akan komai ma saita alamta wasa a cikinta. "Tamam" Haisam din ya furta wanda kalman ya aike da saqon zuwa kunnuwan omari beeno da salawi. Damqe komai yayi cikin tafin hannunsa,sannan a nutse ya kira sunan salawi. "Daga hannun hagunka,ka matsa kadan a sanda aka fara bada damar fita.....da yawansu ba zasu fita ba......saidai na tabbatar akwai masu fita a cikinsu bayan fitata......ka gayawa beeno wannan aikinsa ne qidddigesu.. Akwai wayoyin dukkan wanda ke amfani da waya a ciki da aka zube......inason ka bincike min wayar da aka fi samun adadin kira......kiran daya kasance number daya ce......ina buqatar safarar dukka bayanan cikin wayar zuwa ga email dina......banason aikinka ya haura minti uku kacal" "An gama" Ya amsa masa kamar yadda suka horu da karbar umarni kai tsaye ba tare da musu ba. Kunnuwansa suna iya jiye masa yadda gurin ya hautsine da yabo kan horaswa da aka basu cikin awa daya kacal da basu san da ita ba......tarin ilimin daya fadakar dasu abubuwa masu tarin yawa,da tarin godiyar da bai iya bambance muryoyin dake maganan saboda sanarwar da me wada ya bayar kan tsibin envelope din da aka zube masu dauke da kudaden da yace wata qungiya ce tace a raba musu kyauta. Kudade ne masu kauri ya sanya aka shirya masa su cikin qasa da awa daya kafin xama taron,ya fiddasu ne cikin asusunsa na rabon tallafi ga marayu da iyayen marayu da ake gudanarwa qarqashin kulawa haadeem cousin dinsa. Bai tsaya iya Ethiopia kadai ba,tallafi ne daya shafi kowacce qasa cikin qasashen africa......wannan karon ya sanya aka karkato dashi nijer din. Yanaso ya fara iske abdii,amma kuma lokacin sallah ya riskeshi,sallar kuma tana cikin abu na farko da dukka kalar tsananin daya shiga baya wasa da lokacin ta,baya kuma bari ta kufce masa,don haka ya wuce masallaci kai tsaye kawai. *MAMMINA* Banda tarin izzar da takeji da babu abinda zai hanata sauka daga motar kafin isowar hadimanta,saidai duk da yadda hankalin ta ke son samun qarin bayanin sauyin data gani tun daga babbar katangar da zata sadaka da ainihin cikin ginin masarautar mamaki yake mamayarta. "Me yake faruwa?.....ina kika ajiye wayarki?" Ta jefawa yalwa tambayar cikin dakewa ba tare data bari yalwar ta fahimci dan rudanin dake kai kawo saman fuskarta ba "Taro muka shiga....." "Wanne iri kenan?" "Na wayar dakai.......sheikh haisam ya shirya shi.....zan miki bayanin komai.....muje daga ciki" Ta fada tana riqe mata handbag dinta da kyau,tabi kuma sahun hadimanta dake take mata baya a hankali har zuwa cikin sassan nata. Dukkaninsu suna da iyakarsu,suna da iyakar da yalwa kadai ke iya qetareta,don haka suka ja tunda daga wannan iyakar,suka barta ita da yalwa suna wucewa ga parlor na gaba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Banason maimaita tambaya ta....." Mammina ta fada daidai sanda take tsaiwa tsakiyar parlor din ba tare data dubi yalwa ba. "Taro ne aka shirya na awa daya kawai" Saita soma siffanta mata yadda komai ya gudana har zuwa tashinsu. "Ina kyautata zaton yana neman suna ne wajen sultane......yana neman matsayi ne kawai a wajensa.......yanaso ya sallama masa ne dari bisa dari!" "Tir da kalar tunani irin naki wasu lokutan da basu da wani amfani!!!" Mammina ta dakawa yalwa tsawa tana tsaidata cikin tsananin rudani. "Allah ya huci zuciyarki" Yalwa ta fada tana yin qasa da kanta cikin fargaba da taraddadin shiga gona ko hurumin daba nata ba,wanda tasan hakan baida alaqa da komai sai sanya kanta a uku da bala'in da batasan wanne nau'i bane. Wani irin rudadden yanayi ke yawo cikin kwanyarta,a wannan lokacin tafisu kadai take buqata,wadda ta tabbatar ita da ita ne kawai tunaninsu zai iya zuwa daya. Yadda yalwa ta gaya mata yadda komai ya faru ta aje qatuwar ayar tambaya akan komai.....saidai batasan akan ainihin meye take tuhumar ba.....meye kuma bata yarda dashi ba?......kawai tana jin akwai wani abu shiryayye.......akwai wani abu daba daidai ba har cikin ruhi da zuciyarta. Ba kasafai tafiya gasgata abubuwa ba koda abubuwan da suka kasance na gasken ne ba jabu ba......takan dauki lokaci tana sanya idanu da jarraba komai kafin ta miqa wuya da hannu ta karbeshi a yadda kowa yake kallonsa. "Akwai wanda bai halasci taron ba cikin masu hidima a gidannan?" "Kowa da kowa ne" Ta amsa mata a qasqance. Ta jijjiga da qarfi,tanason qulla zaren tunanin akan wacce manufa aka shirya hakan,saidai kuma ba abinda kwanyarta ke mata kai kawo akai sai irin hasashen yalwa dai sak. "Yana neman yabo......yana neman gurbin zama......yanason ya siya soyayyar al'ummar gidan,ta kowacce fuska takara yakeyi da matsayinki". Duk da jerin gwanon wadannan tunanikan amma sai taji yaqi dacewa da abinda ke mata zirga zirga......ta gaza aminta da kalar wannan harsashen sam. "Dashi aka gudanar da taron?" Ta sake tambayar yalwa. "Shi yayi dukkan jawabai". " Kota daqiqa daya baibar gurin ba?". "Ban gani ba Allah ya taimakeki,dashi aka fara dashi aka kammala". Shuru ya sake ratsa gurin,kafin wata ajiyar zuciya ta subuce mata. Tana jin bai kamata ta daga hankalinta akan malamin da tasan bai mallaki komai da zai iya challenge nata ba......bashi da wata power......baida wani iko na komai,face tarin litattafan da ta sanadin,ta albarkacinsu yake samu yake sha. A yanzun akwai abubuwa da yawa daya kamata ta girmama ta fadada sanya hankalinta akai. Saidai shi dinma.....akwai dalilai da yawa da suke sanyata take gaza dauke hankalinta a kanshi. Tana iya cewa shine mutum na farko banda IBRAHEEM da taji yana mata kwarjini irin haka,mutum na farko da dukka yanayinsa yake mata kama da wani BASARAKE da IZZA ke kewayewa cikin jininsa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 30* A kansa ta fara ganin mutumin da tana zaune saman kujera shima yana zaune. A kansa ta fara ganin mutumin dake iya duban qwayar idanunta yayi magana da ita a tsanake. A kansa ta fara ganin mutumin da sam batayi masa wani kwarjini ba ko daya......tarin jaran gwanon wadannan abubuwa suke sanya mata wani yanayi na daban a kansa. Bawai a kansa malamai suka saba baquntar gidan ba,amma kowa yana rayuwa ne a qarqashin ikonta,gwargwadon yadda takeso ya rayu bisa tasarrufinta. "Ki nema tamim duk inda yake kice ina buqatar ganinsa a yanzu". "In sha Allahu.....ki huta lafiya,da fatan za'a gafarceni" Yalwa ta fada ta yunqura ta miqe tana ficewa. Da idanu tabi yalwa din har sanda ta bacewa ganinta. Ta sauke hannayenta data rungume qirjinta dashi tana jan siririn tsaki. Ta tsani yadda takejin wani fargaba da razani suna ratsata......ba halinta bane batason kuma dabi'ar ta soma keta jininta. Tana da tarin abubuwa da takeso ta aiwatar,wadanda suke buqatar JARUMTA da RASHIN TSORO,abubuwa masu yawan da raguwar zuciya ba zata aikatasu ba. Tsam ta miqe ta isa ga freezer din dake ajiye tana aikinta,ta bude da kanta ta zaro ruwa me sanyi sosai. Tana neman abinda zai sanya kanta ya huce......tana neman abinda zai sanyaya mata tunaninta ko kwanyarta zata dawo aiki da kyau. Tana dora gorar saman freezer din sanarwar isowar tamim ya marabceta. "Zan fito yanzu......bulama ya jirayi tafiyarsa tukunna" Ta fada tana komawa mazauninta na dazu. Alkyabbar data shigo da ita ta sake maidawa,ta kuma maida yanayinta cikin izzarnan da bata yarda ta gushe daga gareta,ta fara saukowa cikin takun isa da nutsuwar da bata jin takai mata har cikin zuciya. Har qasa yakai gwiwoyinsa kamar yadda ya saba,bai kuma gyara ba har sai data samu guri ta zauna. "Ya ake cikin cikin qasar can?" Ta tambayeshi a izzance. Zamansa ya gyara sosai kanshi a qasa. "Na sanya dukkanin wasu matakai da zasu zurfafa bincike,kuma sun dauki adadin wasu kwanaki akan zasu bani cikakken bayanin dana buqata.....kwanakin ba zasu haura goma sha hudu ba......" "Suyi qoqari kada su dara sama da haka.....ko nawa suke buqata za'a biyasu......bayanai kadai nake buqata,sautin motsin kowanne me rai.....kowanne dan adam da ya shiga cikin da'irar buqatunmu......ban dauke kowa ba,yaro ko babba,mace ko namiji.....shugaba da mabiyi!" "Yadda kikeso hakan za'ayi Allah ya qara miki nisan kwana" Tamim ya furta da yaren oromo da yakanyi amfani dashi kadai idan suka kebe irin haka......a muhallin daya tabbatar ba wani mahaluqi da zai iya jinsu. "Wanne sakaci ke shirin faruwa cikin gidannan qarqashin jagorancinka!" Mammina tayi magana a gaba ta biyu cike da kausasawa me yawan gaske. Qasa yayi sosai da kansa cikin neman afuwa daya sabawa kanshi kafin yakai ga jin wanne kalar laifi gareshi?. "Akwai dama wani me zartarwa da tsara wani abu cikin gidannan ba tare dana sani ba?.....ba kuma tare dana sahale ba?,har kuma ku mara masa baya?" Tayi tambayar tana jin wani sabon bacin ran yana motsa mata sama dan dazu. "Tuba muke giwa.....tuba muke uwarmu maganin kuka mu......taron yazo ne a bazata......lokacin da kika fita a gidan,ba damar neman izini ko sanarmiki......sannan duban matsayinsa a gurin sultane daya sahale masa aiwatar da komai,sultane ya shaida mana umarninsa daidai yake da nashi,haka girmamashi daidai yake daka girmamashi.....shi din d'a ne a gurinsa halak malak......" "Ya isheni haka tamim!" Ta fada tana daga masa hannu. "Kuskure na farko da zaku fara yi kenan,ku yadda ku daidaita matsayina da nashi......saidai nan gaba kadan zan cire masa wannan girman daka zuciyar dukkan wanda yake ganinsa da girman!" Ta fadi cikin cin alwashi. Wannan alwashin nata ne,ba wani daya isa yayi mata shiga hanci da qudundune ta qyaleshi!.....ko wayeshi!. "Kada ka yarda irin haka ta sake maimaituwa......duk qanqantar zartarwa ina buqatar ta fara wucewa ta gaba na" "An gama" "Akwai wani abu ne daya haifar da rashin aminci ko wani motsi da ba'a amince masa ba?". Shuru tamim yayi,kafin ya girgiza kai a hankali. "Banga komai ba......saidai wannan kwarjinin nasa daya cika gurin gaba......" "Tamim.......akwai wani me kwarjini ne sama da nawa?" "Babu" Ya amsa mata cikin qanqan da murya "Yaushe idanunka suka fara ganin hakan?" "Ayimin aikin gafara" Ya fada yana rusunawa,abinda ya haifar da shuru kenan. "Zaka iya wucewa,ka tuntubi bulama ko akwai wani sabuwar alama ko sabuwar masaniya?". Ta fadi tana jin ranta yayi jagulewar da bazata iya ganin bulama bama. "An gama Allah ya baki nasara" Ya fada yana miqewa,ya sake kai gaisuwar ban girma sannan ya juya yana fita. Iska ta fesar,tana son ta riski akhnan don auna gwargwadon matsayar tunaninta,tanason kuma ta samu layin tafisu,don tana son shirya komai na auren akhnan ta fanni biyu. Bangaren akhnan din da almaz da takeso kowanne motsi ya tafi da babban motsin da zai ajiye alamun GIRMA cikin dukiyar aure shigarsa da cikar kamalar da zata masa jagorancin samun KARBUWA a zukatan kowa da kowa. *MORSA SAFIYYA* A nutse ta amsa sallamar nanny tana ajiye carbin dake hannunta a gefanta saman lallausan kujerar da take zaune a kai. Daya daga cikin palukanta na alfarma dake sassanta,wanda ke dauke da wani irin sassanya kuma nutsatstsen yanayi. Iya nutsuwa da tsarin sassanta kawai zai gaya maka adadin tata nutsuwar data wanzu har saman fuskarta,duk da tarin ciwuka da firgici tsoro da take boyewa cikin fitowar kowacce rana zuwa faduwarta,amma qarfin riqonta da addu'a ya sanya nutsuwa takan mamaye dukkan wani fargaba da tsoronta. Cikin girmamawa ta marabci nanny kaman yadda suka saba. Ta zauna suna maganar su Aeera data samu daga falon farko sun gwagwgwafe ana musu lalle. "Haka kawai don rigima falaak ta tashi kira da neman a kira mata me jan lalle.......wai sun karanta cewa sunnah ce me qarfi......tanaso lallai tayi koyi da abinda annabi ya umarci mata su dinga yi". Kai nanny ta gyada tana murmushi. "Sosai sheikh yake da qoqari.......ban taba ganin matashin da nutsuwa tayi masa hijabi ba irin malamin nan nasu,ko yanzu bamu dade da gama maganarshi da babansa ba sultane" Ta fada tana murmushi,murmushin daya sanya morsa itama sakin nata murmushin. "Komai na falaak ya canza,nutsuwarta ta sake yawa,abubuwa da dama sun sauya tattare da ita,duk wansa ya sameshi a matsayin d'a ko suruki dole yayi alfahari da hakan". Morsa safiyya ta fadi tana sakin murmushi,har cikin zuciyarta tana jin dadin sauyin falaak din. Hakan yana sake tabbatar mata da girman tasirantuwa da mutanen kirki da mutanen arziqi. Daidai nan hadiman morsa safiyya suka gama cika gaban nanny da kayan ciye ciye sannan suka janye. "Ai dama sun jira......basuyi wannan lallen ba,bata hannuwansu zasuyi,su dake da biki a nan kusa" Nanny ta fada tana murmushi. Maganan ya danja hankalin morsa safiyya,ta daga idaunta tana duban nanny din ba tare data tambaya komai ba. "Daga qarshe dai akhnan ta fidda miji.......in sha Allah kuma sultane ya sanya daurin aurenta sati na sama". Nanny ta fadi alamun farinciki yana wanzuwa saman fuskarta. Wani irin duba na mamaki morsa safiyya takebin nanny dashi,maganar tayi mata mugun zuwa a bazata. Idanunsu ya hadu guri daya,abubuwa da yawa nanny din ta fuskanta tattare da morsa din. "Ta fidda miji?,a yaushe?,a 'yan tsukakkun kwanakin nan?,kuma har ta iya gabatarwa sultane?" Tayi tambayar dukka ga nanny wata irin shakka tana ratsata. Kai nanny ta gyada "Nima nayi mamakin juyewa da sauyawar ra'ayinta haka cikin qanqanin lokaci......saidai shi Allah ba yadda baya iya sauya al'amuransa a yanayin da yaso,a kuma lokacin da yaso" Shuru morsa safiyya tayi,tana jin wuta tana dauke mata. Kowanne sashe na jikinta yana gaya mata wannan ba ra'ayin biftu bane......ba ra'ayin akhnan bane. Fuskar mammina ta gilma ta cikin idanuwanta,ta lumshe idanuwanta a hankali ba tare data iya furta komai ba. Cikin kunnenta ake mata busa da kamar kalaman. "Tayi nasara a kanki" Wani sashen na zuciyarta kuma yana kokawa da hakan......yana kuma qaryata abinda takeji daga qasan ranta. "Safiyya" Nanny ta kira sunanta tana karantar yanayinta. Bata amsa ba illa bude idanunta da tayi tana duban nanny. "Na roqeki don Allah......karki zargi komai,kada kisa komai cikin qasan ranki,komai Allah yana shiryashi ne daidai da tsarinsa,ki bita da fatan alkhairi da dukka gudunmawar da zaki iya bata don samun ingantaccen aure me dorewa......sultane kansa ya rufe maganar,yace dukkan wanda zai dawo masa da hannun agogo baya zai iya fuskantar fushi da kuma bacin rai......banason ranki ya baci safiyya.....banason wani abu mara dadi.ya gilma tsakaninki da sultane dalilin kishi". Idanu ta zubawa nanny shuru yana dan ratsa gurin,sai kuma ta saki wani siririn murmushi. "Kishi?" Morsa safiyya ta maimaita kalmar,saita jinjina kanta a hankali "Koda nace miki toh.....koda nace miki ba komai to tabbas kema kin sani qarya nakeyi. Na rasa idanuwa irin nawa cikin agadez da zasu dinga ganin kalar abinda ni nake gani......na rasa hankula da zuciyoyi irin nawa SAK!. Akwai tarin duffai daya kamata ace sun yaye.....ban sani ba,ko lokacin yayewarsu ne baiyi ba?,amma a cikin jikina zuciyata da gangar jikina suna bani lokacin yana dab da yi......koda bani da abinda zan yiwa khadeeja......amma akwai kyakkyawar alaqa tsakanina da ubangijina.......akwai sauran fili me yawan gaske da zan gurfana gaban ubangijina,ya kuma saurareni da dukkan rahamarsa da jin qansa,komai tarin buqatu da qorafe qorafe na.......bazan iya hana kowa aikata komai akan akhnan ba......amma kuma nima ban manta ba......addu'a tana sauya qaddara mara kyau izuwa me kyau......addu'a tana sauya tarin qaddarori...." Takai qarshen maganar tana jinjina kanta cike da tarin yaqini da tabbaci da wani irin gamsuwa da takeji har cikin qasan ranta da zuciyarta. *MAMMINA* sai data gama shiryawa tsaf cikin wani silk material na hareer me tsadan gaske sannan ta koma saman stool ta zauna tana sake gwada kiran tafisu. Ajiyar zuciya me sanyi ta sauke sanda tafisun ke mata sallama cikin qasqantar da murya. "Daga yanzu......zaki tafiya ta qarshe wadda ta haura zagayen agadez.......zaki kasance a kurkusa kuma a duk sanda ba buqaceki". "Duk yadda kikeso shine abinda zai faru.....duk yadda kikeso kuma haka za'a yishi.....fansar lokacina raina da lafiyata a gareki". Wani qasaitaccen murmushi ta saki,tana jin ta gama samun dukkan wata dama ta duniya......an gama hore mata sarrafa dukkan wani mutum dake kewaye da ita,burika qwaya biyu kadai sune abinda suis rage mata cikarsu. "Yayi kyau......inaso a gobe ki kasance cikin masarauta.......ina buqatar kowanne shiri ya fara gudana na bayyanar almaz a matsayin surukin masarauta.......sannan ina buqatar kowanne shiri ya zama a tsare,irin shirin da akewa bikin kowacce d'iya ta gata. Inaso a shirya dukiyar aure mai gigita hankali da tunani,inaso a gabatar da gaisuwar aure kalar wadda ba'a taba gani ba......inaso girma da izza su nuna kansu,inaso a siyawa almaz mutunci martaba da kwarjinin da ba'a taba ganinsa tattare da dukkan wanda ya taba zuwa neman auren akhnan ba.......komai inaso ya wanzu bayan tafiyar me martaba umara kafin kuma dawowarshi". 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 31* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ "An gama......ki qaddara komai ya wanzu kamar hakan". Kai mammina ta jinjina cikin izza sannan ta katse wayar. Idanunta ta maida saman fuskarta tana sake sakin wani murmushin,a nutse takai hannunta saman fuskarta tana shafawa,wani murmushin yana sake yanke mata. Tana matuqar kula da kanta da fatarta gami da jikinta gaba daya,wannan ya sanya zai wahala ka iya qididdige shekarunta kai tsaye. Dukkanin duniyarta a yau wani dadi take mata,komai ya hau saiti,komai kuma yana tafiya a hannunta yadda takeso. DAUKAN FANSA yana mata matuqar dadin da yake wanzar da zuciyarta cikin wani irin nishadi da aminci........ballantana fansa irin wannan,fansar da take da tabbacin ba'a taba wani abu a tarihin rayuwarta da take buqatar fansa a kansa ba irin FANSAR SAFEENA. A nutse ta miqe,ta dora alkyabba mara nauyi saman rigar jikinta daidai sanda idanunta ya sauka akan jewelry organizer dinta. Haka kawai ta samu kanta da zubawa gurin idanu tana jin sauyin bugun zuciyarta,shakka da kuma kokwanto suna ratsata a hankali,taji kamar wani abu yana fincikar hankalinta a kansa,sai ta miqa hannu ta danna wani madanni,take ya bude ya kuma ware dukka fadinsa dake dauke da sassa sassa. Akan abun hannun idanunta suka fara sauka,kallon daya saukar mata da wasu yani mabanbamta da har sai daya kaita ga miqa hannu ta daukeshi tana juyashi cikin hannunta. Abune me matuqar tsada da daraja a gurinta,bawai kuma don daga gurin wanda ya fito ba tun asalinsa,sannan bawai don tsadar da yake dashi ba kasancewarsa d'anyan narkakken gold ba......aah,saidai kasancewarsa me dauki da wani tarihi me nauyi a gurinta. Iska taja me yawa a hunhunta,zuciyarta na jin qin aminta da zamansa a gurin haka kawai,zamansa a wajen takejin baiyi mata ba a daidai wannan lokacin da take da tarin zarge zarge da ayoyin tambayoyi akan kusan kowa da kowa ma,sai ta taka kawai a hankali tana wucewa zuwa ainihin kebantaccen closet dinta,ta wuce kai tsaye ga ajiyayyen safe dinta,ta jawoshi ta saka abun a ciki ta rufe tana jin ya samu amintaccen gurin zama sama da dressing table dinta,sannan ta fara takawa tana ficewa a daga walk-in closet din. Dab da zata fita a gurin jikinta ya saukar mata da wani irin yanayi. Saita tsaya cak,ta waiwaya tana sake qarewa gurin kallo. Mintuna aqalla uku ta shafe a haka tana duban gurin. Batasan me yasa takeji a jikinta kamar akwai wani abu daya taba gun,kamar akwai wani daya kusanci gurin?,amma ko daya bataga wani abu daya sauya gurin ba,daidai da qananun alamomi data sanya da ba wanda zai gane alama ce ajiyayya da zata iya fahimtar da ita an taba mata wani abun,an shiga gonarta ko an wuce iyakarta,dukka suna nan a muhallinsu,ba ko daya daya fadi ko ya canza yanayi. Siririn tsaki ta saki,ta juya tana qarasa ficewa,cikin ranta da kanta tana tuhumar kanta da kanta. Me yasa haka kawai,a sanda take buqatar nutsuwa irin wannan tunanin da shakka suke saukar mata?. Bayan tayi imanin ba mutum ba,ko aljani zai masa matuqar wahalar tsallake dukka matakan tsaron data sanyawa sassanta ya isa ga wannan closet din,kome girman tsafi asiri ko siddabarun da yake taqama dashi. "Nutsuwa kike buqata zaituna" Ta gayawa kanta da kanta,sai taja iskar ta kuma fesar a waje,abinda ya bata qanqanuwar nutsuwar da take da buqata. Da dukkan izzarta take takawa d'ai d'ai cikin gidan,tari bayi da hadimai suna darewa suna bata hanya gami da miqa gaisuwa,gaisuwar da hadimanta ne ke amsata,saidai takan bisu da murmushi kadan kadan don tabbatar da yabon KIRKI da sukeyi mata. Duk da Kai tsaye hankalinta yana ga isa sassan akhnan,amma kuma hakan bai hanata ganin wasu tsirarun sauye sauye ba a farfajiyar gidan,abinda yadan janye hankalinta kadan,amma ta cillashi sashen qwaqwalwarta na abubuwan da zata nazarta a nan gaba. Ba wanda ya dakatar da ita daga wucewa kai tsaye zuwa ga main bedroom na akhnan din,yayin da hadimanta suka yiwa kansu matsaya a waiting room suna jiran dawowar uwargijiyar tasu. *HAISAM* Yana tsaye ne tsakiyar beeno omari salawi da abdii,hannunsa zube cikin aljihun jubah dinsa bayan ya zare rawanin kansa ya ajiyeshi gefe tun bayan shigowarsu gurin. Idanunsa dukka ya zuba ga qunshin abun hannun dake gabansa,yana sauraren bayanin qarshe da omari yakeyi har zuwa sanda ya kammala. "Tamam" Ya fadi a nutse yana fidda hannayensa daga aljihun jubah din nasa,sannan ya fara tattaki a nutse yana samun daya daga cikin kujerun dake kewaye da parlor din ya zauna. "Beeno da salaana.......inason ku shirya shiga sahun masu tsaron qofofin sultane palace.......omari zaka fita a qasar nan yau da abun hannun nan.........inaso ka damqashi kai tsaye ga buba......kafin sannan ina buqatar nanay ta ganshi iya na mintina biyar kacal". Ya qarasa maganan yana fiddo takardar da abdii ya hado masa da ita wadda ya sameta yashe cikin kwandon shara na dakin. Warwareta yayi da kyau yana duba takardar,shuru ya sake ratsa dakin,kafin a hankali wani murmushi mara zurfi ya kubce masa. "Oromia handwriting.......definitely matar nan 'yar qasarmu ce......yarenmu ce.....kuma qabilarmu ce......." "Amma obbo me zai hana ka bari ta fahimci kasan yaren?,ka kuma iya yaren?,hakan zai baka damar ganin reaction na fuskarta,reaction dinta kuma shine zai bayyana gaskiyarta ko akasin haka". Baisan ya miqa hannu ya ranqwashi saman kan abdii ba saboda takaici. "Sai kayi abun arziqi saika dawo kayi na tsiya,na rasa a wanne mataki ko gurbi ya kamata na ajjiyeka......har yanzu banaji a raina zan baka gurbi a national intelligence......bansan ko matsayin me goge goge da shara ba" Ya fada yana zubewa abdii idanun nan nasa masu tsananin kwarjini girma kyau da haske. Dariya suka dan saki,dukkaninsu suna hangen wautar abdii a wasu lokutan,amma Kai tsaye idan kace yayi gadon baiwar fikira da basira bakayi kuskure ba. "Bakasa yare sirri bane?......a duk sanda ka tsinci kanka cikin yaren da basusan ka iyashi ba.....karka kuskura ka nuna musu ka iya wannan yaren,hakan zai baka information da security wanda qwarewarka a aiki bazai baka ba.......a cikinku akwai wanda yasan na fara jin yaren mutanen agadez?,buzaye?" Sak dukkaninsu sukayi,cike da tsananin mamakinsa. Komai nasa na musamman ne yadda ya kasance na musamman,yana sanya aikinsa gaba da komai,yana sanya aikinsa sama da komai,yana iya koyar komai saboda aikinsa,kamar yadda yake iya barin komai din saboda aikinsa. Murmushi ya saki a nutse ganin yadda mamaki ya bayyana saman fuskarsu. "Wanne irin aljananci ne wannan?" Omari ya fadi kai tsaye,wanda ba wanda zai iya fadin hakan dama idan ba omari din ba. Kai ya jinjina masa a nutse,sannna ya miqe yana maida cloak robe dinsa kafin ya amsa masa. "Ka sanya tunaninka gaba da komai kafin ka fara gwada aikata komai......har yanzu inajin ban kammala cika ba,tunda ji kawai nakeyi ban iya maidawa" Ya furta maganan yana soke takardar cikin aljihunsa. "Sanda zaka fara maidawar ma dukkaninmu bamu da labarin indai kaine.....zamu wayi gari kawai muji kana yarawa ne" Omari ya fadi cikin tuhuma,yanayin daya sanya haisam kauda kai da guntun murmushin nan saman fuskarsa,ya aza idanunsa akan salawi. "A darennan nakeso takardun sabbin dokoki su isa hannun me wada......zuwa safiya nakeso ta game masarautar gaba daya....na riga na samu sahalewar sultane,zasu fara aiki ne nan take,kuma kowa zai hau kan saitin aikinsa a goben.......inaso ku maida hankulanku jikinku,kusa a ranku sati hudu kawai ya rage mana mubar qasar nan,kwana talatin kawai muke dashi don kammala aikinmu" Ya qarasa maganar da wannan seriousness din nasa dake qara musu qaimi. Tare suka fita da omari a daya daga cikin motocinsa da salaana yake jansu,suka kuma ajiyeshi a sabon gurin da yake sauka a yanzu,don akwai abinda yake buqatar zuwa gida ya kebe kansa ya duba a nutse. *MAMMINA* Idanu ta zubawa dakin tana dubanshi ganin yadda yake a hargitse kafin ta maida dubanta kan fuskar akhnan dake tsaye tana danne danne a wayarta. Shimfidadden yanayin dake nuna kwantaccen fushi ne can qasan zuciyarta da ya bayyana sosai har saman fuskarta. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Cikin girmamawa birra ta amsa sallamar mammina din,ta ajiye bathset din data dauko da zummar sakawa cikin luggage tana zubewa qasa don kai gaisuwa ga giwar sultane din. A taqaice ta amsawa birra,sannan ta dora da tambayar. "Shirin meye kukeyi haka?". Qasa tayi da kanta,kafin ta bata amsa akhnan da tayi cilli da wayarta saman gado ta amsa. " Nasa an siyamin ticket yanzu......Niamey nakeso na koma a yau......inajin komai ai ya kammala ko?,duk wani me lissafi ya cika lissafinsa a kaina" Tayi maganar dake nuna zallar fushinta cikin kalamanta. Kadan gaban mammina taji ya fadi,don maganarta a wannan lokacin sai taji kamar da ita akhnan din take. Ta gefe daya fargabar bacin tsarinta ne ya saukar mata,bata shirya komawar akhnan Niamey yanzu ba......don komawarta Niamey yana daidai da komawarta bakin aikinta ne,wanda sam a yanzu ba wannan tsarin. Tana buqatar space koda na sati uku ne zuwa hudu......sanda aisa ta soma nisa cikin riqon qwaryar da take saka ran zata farashi cikin satin nan. Ta jima tana zurfafa hasashenta akan aisa......tana da wani quduri na daban a kanta,akwai kuma wani tunani da zuzzurfan hange da tayi a kanta. Tuni birra ta fice don basu guri da kuma cika umarnin kaucewa daga dukkan ganawar da mammina zatayi da akhnan,wannan ya bawa mammina damar qarasawa cikin dakin tana kama hannun akhnan ta zaunar da ita. "Me yasa wasu lokuta bakya tunani.....bakya kuma zurfafa hasashenki?" Mammina tayi maganan alamun fushi kadan yana bayyana a sautin muryarta. "Har yanzu zuciyar sultane a tunzure take,kinaso kici gaba da abinda zaki tunzura zuciyarsa maimakon yin abinda zaki amintar dashi?" Mammina ta sake fadi wannan karon tana sassautowa da muryarta. "Me ya rage mammina?.....me ya rage kuma?......wannan qaunar wannan kulawar sultane dukka ya tuntsirar da ita......tun daga sanda ya yaye dukka wani hijabin sirri dake tsakanina dashi gaban bagidajen malamin can.....tun daga sanda ya nunawa wancan bagidajen malamin da baisan komai ba illa allo da tawwada sirrina,ya dauki matsayina ya bashi,ya kusanta kansa dashi fiye da yadda yake kusanta kansa dani.....ya maye gurbina dana malamin can,daga qarshe ya dauki ragamar daurin aurena ya damqa a hannun mutumin da baida asali,tsintacciyar magen da bamusan daga wanne datti da daudar ya fito ba!" Tayi maganar da fushi sosai cikin idanunta fuskarta dama muryarta,don rawa muryar tata takeyi kaman yadda idanunta suke tara ruwan hawayen da zasu iya sauka kowanne lokaci. Sosai mammina ta nutsu,ta kuma zuba mata ido tana karantar yadda abun yayi mata zafi. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 32* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ "Naji zafi fiye da wannan zafin da kikaji sanda safeena ta qwace min sultane a hannuna.....sultane din da ba shine abu na farko data fara qwata a hannuna ba......naji zafi fiye da wannan zafin da kikaji sanda na samu labarin haihuwarki......naji zafi sama da wannan a sanda nake iya kallon safeena a matsayin matar sultane a sanda nake gefe cikin tarin baqinciki da qunci kuma ba abinda zan iya aikatawa a sannan......ina kanjin zafi a duk sanda na daga ido na kalleki a matsayin DIYA ga sultane,ba kuma nina haifeki ba.....inakan jin zafi a duk sanda na tsinceku keda sultane kuna sirrin da ba wanda yake iya bayyanawa saike kadai. Ya kamata ne na barki kiji wannan zafin.......ya kamata na qyaleki,amma kuma zan tayaki mu tunkudeshi saboda tanadin dana miki a gaba. Kin cancani kiji zafi sama da wannan zafin da kikeji a yanzu,kin cancani hukuncin da yafi wannan tsanani keda zuri'ar diory hamani gaba daya. Idanunta ta janye tana maida hankalinta ga akhnan da tsananin kafiyarta da taurin kanta ya taimaka mata taketa qoqarin maida hawayen daya rantse sai ya zubo. "Wani lokaci ina raina wayonki biftu,bakisan ba kowanne lokaci bane akecin nasara da aiwatar da komai cikin zafi ba?. A wasu lokutan saika kwanta an tattakaka anbi ta kanka kafin nasara take zuwar maka......kin sani,bazanbar komai ya tafi a haka ba,amma ya zama dole a yanzu ki siffantu da siffar macen dake shirin zama AMARYA da mijin daya zama ZABINTA" Tayi maganan tana sake zube mata duba na tsanaki. "Kamar yaya?" Akhnan din ta tambayi mammina kai tsaye,tana kuma fatan bawai zata sanyata yin duk abubuwan al'ada da sukeyi ga amare ba har zuwa ranar aurensu. "Da farko dole zan gargadi sheikh haisam don yasan iya matsayin da yake tunanin ya taka kada ya rudeshi......na biyu zaki gana da angonki almaz......." "Babu buqatar hakan mammina......bana buqatar ganinsa,ya zauna a inda yake,na zauna a inda nake". " Zaki ganshi biftu dole.....dole zaki ganshi,ko kinaso duniya ta karanci cewa almaz zabina ne ba zabinki ba?" Ta fadi da 'yar fusata a muryarta,fusatar data sanya akhnan maida hankalinta jikinta. "Na soma gajiya da musunki biftu......na fara tunanin nan gaba kadan zaki daina yarda duk wata shawarata" Ta fada cikin bacin rai tana gwada miqewa,saidai akhnan din ta kamota abinda ya sake maidata ya zaunar da ita kenan. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Kiyi haquri" Taji muryar akhnan din ta fita da wani irin sanyi. Wani farinciki ya saukar mata,don kuwa wannan kalmar wata kalma ca da bata tunanin ko sultane yana yawan jinta a bakin akhnan din. Kalma ce da tafi kowacce kalma wuyar furtawa a bakinta baya ga kalmar INA SONKA/KI. Muryarta ta sasasauta,saidai har yanzu bata saki fuskarta ba. "Aure zakiyi a idanun duniya irin auren da kowacce yarinya 'yar gata takeyi,aure zakiyi da dole idan kinaso ya saje da auren gaske sai anyi dukkan wani abu da aka saba gani......indai kinaso a barki da sa'ido dabin qwaqwqwafi......a barki kiyi rayuwarki kalar wadda kika tsara kike muradi.......koma lalacewar auren 'yar sultane a zuciyarki sunansa dai BIKIN AURE,dole a komai baki akwai GIRMA a komai naki akwai MARTABA a komai naki akwai DARAJA akwai MULKI. Koda bikin binne gawa ne dole naki yasha banbam dana kowa. Biki nakeso muyi da zaya bar tarihin da bazai gogu ba,biki nakeso ayi irin wanda ba'a taba yin kwatankwacinsa ba tunda aka kafa qasar agadez......biki nakeso ayi da labarinsa zai zagaye nahiyar africa gaba daya......bikin da za'a jima ana labarinsa.......bikin da bazai goge a bakuna da zukatan al'umma ba komai tsahon zamani". Saita dakata tana gwargwada adadin yadda maganan ya shigi akhnan din. Numfashi take saukewa a hankali,tana jin wannan girman izzar da martabar suna saukar mata. Izzar da tuntuni ina ta qara qarfinta cikin jininta da dukka fitar numfashinta. Wadannan kyawawan blue eyes din nata ta daga tana duban mammina dasu,tana jin dukka yarda da aminci da abinda ta gaya mata. "Me ya kamata ayi?" Murmushi mammina ta sake,tana gyara zamanta cikin jin dadi tana dubanta. *HAISAM* zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 33* MACE TA GARI aljannar duniyar namiji ce,tasan wannan,shi yasa koda yaushe bata gajiya da yiwa yaranta maza da mata addu'ar dacewa da aboka rayuwa,shi yasa kuma kullum hankalinta yake karkata kan saamee. Tana ganin tasan komai kan haisam,tana ganin kamar zata iya jure komai,yanayinsa attitude nasa da komai ma,to amma sai bata bari zuciyarta tayi mata zabi ba,ta barwa Allah yayi wannan zabin da duk wadda ya dace a sanda ya dace koda saamee dince. *NOTE~Qalubale gareki uwa,kinga tun a zamanin nan,samun miji na gari,da mace ta gari yana wahala,ina ga zamanin 'ya'yanki?,tun yanzu da basu da hankali ya dace ki tsaya musu da wannan addu'ar,suma ki koya musu yinta tun basusan tsadar abinda suke roqa a gurin Allah ba. Bayan miji na gari da zai sauke mata kowanne haqqi da Allah ya dora masa,ki roqa mata personally mijin da zaiyi tarayya da ita cikin damuwarta,walwalarta da baqincikinta,samunta da rashinta,wanda Allah zai jarabceshi da tsaftatacciyar soyayyarta,soyayyar da zata sanya ya zama ABOKIN RAYUWA na gaske,MIJIBANCIN na gaske,ba wanda zai sauke iya haqqoqinsa din kawai ba kuma shikenan,can cikin rayuwarta tana jinta empty......tana jin loneliness,Alla ya datar mana dasu.* "Ina buqatar qarin sani akan iyalin ajani" Ya furta da yaren oromo. Shuru ya ratsa tsakaninsu sannan nanay ta gyara zamanta. "Matansa biyu ne......duk da ana rad'e rad'in ya auri wata matar a boye,wanda ba kowa ne ya santa ba,sa'annan ma ba'a kai ga tarewa ba ajalinsa ya riskeshi,so ba wanda zaice ga fuskarta ko gata,saidai wataqila cikin makusantan abokansa na qut da qut. Shahararren dan kasuwa ne na duka duniya gaba daya,harqallar kasuwancinsa tafi tsakanin sarakuna na qasashe da attajirai,don yana kawo duk wasu kaya na alfarma da zai sanya gidan sarauta ya amsa sunanshi. Matarsa ta farko yaranta biyar,hudu mata namiji guda daya ka sanshi basai na gaya maka ba,tunda shike tsaye tsahon shekarun bayan daya mallaki hankalinsa don binciko wadanda sukayi kisan gilla wa mahaifinsa. Matarsa ta biyu kuma wadda ya aureta ne shekara guda kafin a kasheshi bata haihu dashi ba kwata kwata......." "Meye sunanta?" Haisam ya samu kansa da katse nanay,don binciken kusan yana jin dole zai biyo ta kanta itama. "Zeenatu.......zeenatu sunanta,mahaifinta ba wani sananne bane,don baida sana'ar data wuce saida nau'ikan gahwa a qaramin shagon unguwa,saidai tana da kyau daya sanya take da tarin manema,wannan akace shine dalilin daya hanata zaman aure,don tana aure take fitowa,a qalla sai data auri maza biyar ajani ne na shida. Duk da kowa yasan ajani bai mata ba,bata kuma sonshi,amma haka ta aureshi,wannan dalilin ya sanya bayan an kasheshi uwargidansa da yaranta mata don sannan namijin bai wani girma ba tunda shine qarami sukace basu yarda da ita ba. Anyita tafka shari'a dasu,amma daga bisani kotu ta wanketa,don bata da hannu ko masaniya. Andai samu shatin hannu da sauran abubuwa kan wanda yayi kisan,saidai duk irin nema da bincike na jami'ai sun gaza samoshi". "Kina da masaniyar inda zan iya ganinta ita zeenatu din?". Kai nanay ta girgiza. "Ba wanda zaice maka ga inda zeenatu take,don ana rade radin ma ta bata,shekara da shekaru ko gilmawarta ba'a sake gani ba cikin qasar nan,wasu ma na zargin uwar gidanta ki dangin ajani daketa zargin qiyayya tasa ta kashe musu dan uwa sune suka batar da ita" . Shuru haisam yayi,yana kuma juya labarin cikin kansa. Haka kawai dan adam bazai bata ba kaman kudi.......ace rana tsaka an nemeshi an rasa?. Dan adam dinma mace me cikakken hankali wadda ta samu kaso na gado me yawa ace ta bace?. "Amma meye haka me nauyi na ajani dake hannun motii da aka yita attempting kai masa hari?" Ajiyar zuciya me nauyi nanay ta sauke. "A rabon gadon da aka yi ba'a taba komai na taskokin ajani ba guda biyu,mahaifinku shine amintaccensa guda daya,kuma shi daya yasan inda za'a samesu da yadda za'a sarrafa danyar dukiyar dake ciki,kama daga gold da Diamond,wasu tarin abubuwa masu darajar gaske,maganan da sukayi ta qarshe da ajani,kaman yasan ana fakon kasheshi,ya gaya masa muddin yaga ya mutu to kasheshi akayi,wadanann sirrikan dukiyar kuma yanaso ya masa alqawari bazai bayyanasu ba......zai adanasu saboda iyalinsa da d'ansa,har sai sanda komai ya bayyana kan wa da ya kasheshi,idan har ba haka ba,idan har ya damqa dukiyar ga iyalinsa,to tabbas za'a qarar dasu ne daga doron duniya,za'a yita binsu ana kashesu daya bayan daya saboda wannan dukiyar......a daren munyi magana da motii hankalinsa a tashe,ya bawa ajani shawarar ya qara yawan masu tsaronsa,ya kuna nema hukumar tsaro ta shiga cikin sahun masu bashi kariya,amma sai ya yiwa motii murmushi kawai "Idan ajali yazo ba wata kariya da zata iya kareka......saidai fatan cikawa da imani" A safiyar ranar ne zuwa azahar kuma labarin kisan gillar da akayi masa a gidan gonarsa ya karade qasar nan dama maqwaftan qasashe" Nanay ta dakata tana tuna girman tashin hankalin da qasar ta fuskanta a lokacin,saboda ajani Ahmed kamar amintacce ne daga wata qasar da Ethiopia ta maida dan qasarta halak malak saboda alfanu na kudaden shiga da take samu ta sanadin kasuwancinsa. Shuru haisam din yayi shima,kafin ya sake daga kanshi yana dubanta. "Sanda aka fara kaiwa motii farmakin farko......zenatu tana Ethiopia?". Kai Nanay ta girgiza. " Takai shekara biyu ko uku a sannan bata nan". Lumshe idanunsa yayi,wani dan qaramin murmushi yana subuce masa,tunaninsa yana hada wasu abubuwa kafin ya bude idonsa. "Inaji a jikina zeenatu tana raye......inaji kuma a jikina akwai mafakar data samu take shirya abubuwa wa qasarmu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa" Yayi furucin da nutsuwarsa. "Me kake cewa muhammad?" Nanay ta tambaya da mamaki. "Ba komai nanay,kici gaba da yimin addu'a,amma inaso na sanya motii alfahari me yawa dani,zan kare masa qasarsa da rayukan al'ummarsa in sha Allah" Kai ta gyada a hankali. "Allah ya baka nasara,ya doraka akan kowa da komai". "Ameen nanay" Dan shuru tayi sai kuma tace. "Kana kiran saamee koda bayan lokaci ne kuwa kuna gaisawa?". Idanu yadan zubawa Nanay kadan yana karantarta kafin yace. " Wani abu ya faru ne?" Kai nanay ta girgiza,tana jin sai yaushe hankalinsa zaikai kai ne?. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Kawai naga ta damu da rashin wanzuwarka a gida,harma fiye da 'yan uwanka" Dan qaramin murmushi ya sauke "Idan haka kike buqata nanay zan dinga kira in sha Allah". Kai ta girgiza itama tana murmushi. "Banda matsawa kai,a duk sanda dama ta bayar da hakan,kaji kuma zaka iya kiran" "Na gode" Ya fada da girmamawa da kuma tarin qauna. "Omari zaizo,zai kawo miki wani saqo ki duba ko zaki iya tuna wani abu akai" Kai ta jinjina a nutse "Allahumma bareek" Ta fada tana dafa kanta wanda hakan yana nufin tanajin kamar ta dafa kan haisam dinne direct,kansa ya qansqantar yana amsa mata,tamkar yadda yakeyi a gabanta. Ko bayan gama wayar tasu wayarshi ya dauka yana bude hotunan da yasa abdii ya tura masa. Da kwanukan abincin ya fara,komai da komai irin na yaren oromo,best dishes da Oromian people suke dashi,komai kamar a qasar. Ajiyar zuciya ya saki yana sake jin lallai AKWAI WATA A QASA,sannan ya koma ga hoton frame din da abdii din dai ya turo masa. A idanun me kallonsa,da kuma idanun wadanda suka dauki shekaru suna rayuwa tare da ita. Tura hoton yayi cikin sirrintacciyar system dinsa,sannan ya aikashi zuwa ga sashen bincike na can qasar yayi dan gajeran bayani a qasan hoton. ★★Tsaye take cikin qawataccen lambun nata da takan wanzu a cikine a duk sanda take cikin nishadi da walwala.irin wannan. Yanayin yana taimaka mata qwarai,yana sake inganta mata nishadinta. Tun bayan da sultane ya fita zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na agadez,zama kadan tayi taga mabuqata sannan ta kebe kanta cikin qasaitaccen lambun nata. Tun tsakanin jiya zuwa yau din bata bawa kanta sukuni ba,shirye shirye kawai takeyi na irin uwar dukiyar da za'a narkar wajen tsarawa akhnan din komai na aure a zahiri,yayin da a badini aikin ya zame mata biyu,shirya almaz da kuma shirya dukiyar auren da take sanya ran za'a gabatar da ita bayan almaz yazo sun gana da akhnan kamar yadda al'ada ta tanadar. Lefen auren da za'a kawo da kuma yadda bikin zai kasance,wanda ta tsara gudanar da komai bayan daurin aure gudun wanzuwa ko gilmawar wata matsala,kuma ta tsara komai ya kasance a haka ne don kashe bakin tsanya. Duk da wadannan damarmakin data samu tana jin wani susa cikin ranta idan ta tuna yadda sultane yake sake jaddadawa haisam kula da nauye nauyen da yake ganin da haisam din kawai suka dace,saidai wani sashe na zuciyarta yana bata tabbacin bai isa ya hana faruwar komai ba,bai kuma isa ya sanya komai ya faru ba. Ta gani sun kebe da sultane a gurin,sunyi maganganun da har yanzu suke gilmamata da tsananin kwadayin son jin meye da meye sultane ya gayawa haisam din a kebe?. A yanzun da take gurin,tana waya da amintacciyarta ne dake mata siyayya da order na duka wasu kayan qyale qyalen alfarma na buqatar rayuwa,daidai lokacin data hangi tahowar yalwa da sassarfa hannunta dauke da wata takarda fara. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 34* Idanunta akan yalwa,amma hankalinta yana kan wayar da takeyi,saidai zuwan yalwan bai hanata yin wayarta ba,har zuwa sanda ta kammala wayar da cewa. "Ki lissafa dukka adadin da kudin ya kama,zan tura miki,a tsara komai yadda ya dace,yadda kuma zai qayatar". "An gama ranki ya dade" Ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta yanke wayar tana jiyeta saman doguwar takardar daje gabanta data sanya sabeera tayi list din komai. "Ya ake ciki?" Ta tambayi yalwa tana dubanta a tsanake. Kasa magana yalwa din tayi,sai miqa mata doguwar takardar tayi tana komawa mazauninta ta zauna. Kamar ba zata karba ba,sai ta sanya hannu a qasaice ta karba,ta bude takardar tana dubawa cikin tattara hankalinta guri daya. saidai tun batayi nisa ba hankalin nata ya dagu sosai,ta tsuke girarta tana duban jerin sabbin dokokin masarautar AGADEZ. Tarin mamaki ne ya soma yankowa yana lullubeta,wasu irin tsare tsare da dokokin da tunda aka kafa masarautar bata taba ganin shigensu ba. A fusace ta dangwarar da takardar,ta daga idanunta cikin wani irin yanayi na fusata tana duban yalwa. "Uban waye ya zartar da sabbin dokoki da hukunce hukunce irin wannan,ba masaniyata?,ba yarjewata?,ba kuma neman ta baki na kaman yadda aka saba?". Qasa yalwa tayi da kanta,tana iya hango kwantaccen fushi saman fuskar mammina din,wani irin wutar fushi data jima bataga kamarta ba. "Allah ya huci zuciyarki,ya baki yawan rai.....sheikh muhammad haisam ne" Yalwa ta fadi cikin kwantar da murya. Madaukakin mamaki da kuma fargaba ne suka hadu gaba daya suka cakude mata,tayi ciki ciki da idanunta tana duban yalwa da wani irin tsini da kaifi cikin idanunta. "Sheikh muhammad haisam?" Ta maimaita sunan kamar yau ne rana ta farko data taba jin sunan. Kai ta girgiza sosai "Qwarai kuwa.... Don dama a taron da aka gabatar jiya an bada sanarwar samun sabbin dokoki cikin gidan nan saboda yanayi na tsaro,da kuma qarin sabbin masu tsaron cikin gida da kuma kowacce qofa" . Wani irin zazzafan gumi taji yana karyo mata tashin farko. Kokwanto da kuma zargi me girma yana samun sabon mazauni a ranta game dashi. Ta yaya zai halicci wani tarnaqi a daidai sanda take ganin akwai space me girma da komai zai faru ya qare kafin dawowar sultane?. Sati biyun da sultane zai fara yi a france,da wata daya da zaiyi a madeena tana ganin sun isa ta aiwatar da komai. Tana sanya ran a sanda zaya dawo ma ya samu akhnan din da tsarabar jikansa. Wanne irin mutum ne shi da hankalinsa zaikai ga shiryawa da tsara abubuwa irin wadannan a daidai wannan lokacin?. Hannu ta sanya ta sake dauko takardar tana sake dubata daga farkonta zuwa qarshe,saidai still ta kasa samun nutsuwa jira takai ga rubutun qarshe dake qasan takardar,saboda tunaninta dake yamutsewa. Jikin kowacce doka akwai qalubale me tarin yawa.......a jikin kowacce doka akwai tasgaro da matsaloli da zasu iya cin karo da kowanne muradi nata. "Me kike tsoro?,me kuma kike jira da zaki zauna yaro qarami irin wannan ya fara wasa da hankalinki?.......WAYESHI?". Tambayar da tayi mata tsaiwar mashi kenan cikin tsakiyar zuciyarta,yayin da zuciyarta ta kasu sassa daban daban akan haisam. Tun daga sanda ta fara ganinsa zuwa yau takeji wani abu na daban a kansa wanda bata taba jin irinsa akan kowanne mutum ba........wani yanayi hali da dabi'u take hanga tattare dashi da suka sha banban dana kowacce baqo dake zaune yana rayuwa cikin gidan......me yasa lokaci daya wani baqo zata dinga jinsa na daban cikin gidan?,me yasa zai samu wani irin power da koda wadanda suka shekara ashirin basu da ita?. "Ki tura saqona izuwa sashensa......a shaida masa kome yakeyi yazo inason ganinsa!.....sannan a nemomin tamim..... Amma zan ganshi ne bayan na gama ganawa da wancan yaron" "An gama.....cikar muradanki sune farincikinmu" Ta fada tana miqewa da dukka karsashinta don cika umarninta. "Yalwa" Ta kirata a qasaice ba tare data kalleta ba,saita amsa mata a ladabce. "Raina yana tsananin bace,banason in zauna jira,don banaso yazo ya ruskeni a sanda zuciyata ta fara sassauta......sa'annan daga yau zuwa wayewar garin gobe.....kowa dake cikin gidannan inaso yaji a jikinsa,yasan kuma MIJIN GIMBIYA AKHNAN zaizo don ganawa da ita,inaso ayi gagarumin shirin da ba'a taba yiwa mazajen baya ba a kanta" "An gama......an aiwatar kamar yadda kika ce ranki ya dade" Saita juya da sassarfa tana barin shiyyar. Idanunta ta runtse tana jin zafi a ranta,zuciyarta na cika da d'ar d'ar......gabanta na wani irin bahaguwar faduwa a duk sanda zuciyarta ta raya mata. KADA KOWANNE GIRMAN IKO YA KOMA HANNUNSA. Duk da bata fita cikin mutane ba taba kebance a nan ita kadai,amma wani irin kunya ce take saukar mata. Tana ji kamar ma kowa ya soma fahimtar abubuwa sun fara fita daga ikonta. Abubuwa da yawa cikin tsukin nan suna fara barin da'irarta......saboda wani malami da baisan kan duniya ba ballanta girma da qarfin iko na gidan sarauta ba?. Da qyar ta yiwa kanta saiti ta koma ta zauna tana jiran isowarsa,bataso yazo ya same ta a tsaye ballantana har ya fahimci daga mata hankali lamarin yayi,ta fesar da iska daga bakinta tana duban hanyar cike da qaguwa. _____Tun daga nesa kana iya hangen yadda farar jubah din jikinsa ta zame masa wani irin ado me daukan hankali,hular daya sanya saman kansa ga rufe tsakiyar kanne kawai saboda laushi da santsin sumarsa. Qafarsa daya kan daya ya dorata,hannunsa dauke da littafin fataawan nisaaa yana dubawa a hankali. Zaman ya masa dadi,duk da cewa ya zauna dinne don yayi charge din kansa da shurunsa. Ba kasafai ya fiya son hayaniya ba,yana ji tana hawan masa kaine a yawancin lokuta. Ko a yanzu abdii na zaune a gefansa,kuma tun dazun abdii din ke satar kallonsa. Yasan magana ce a bakinsa,amma shurunsa da tsumewarsa suka sanya abdii jan baki yayi gum. Duka duka bai rufe awa daya da kammala zama tsakaninsa da wazirin sultane ba,wanda a yanzu yake a mazaunin mataimakinsa cikin fadar. Ya fahimci akwai abubuwa masu yawa,ya kuma karanci matsaloli ne masu yawa lullube da masarautar sama da katangun da masarautar ke dasu. A nutse ya qaraso cikin girmamawa. Yaron gidansa da aka sake bashi saddam ya qaraso cikin girmamawa yana rusunawa. "Barka da warhaka" Saddam din ya furta yana rusunawa cikin girmamawa tamkar zaikai har qasa,saidai bai qarasa kaiwa qasan ba saboda tuni haisam din ya hanasu yi masa haka. A nutse ya sauke qafarsa daya qasa yana rufe littafin hannunsa,gami da sanya yatsa daya a tsakiya. Da kai ya amsawa sadam yana lumshe idanu gami da budesu,can cikin kansa yana jin hayaniya ta soma masa yawa. Yana shawarar qarshen satin ya wuce personal gidansa koda kwana daya ne yayi,ya gaji da yadda kwanyarsa take tattaro dukka matsalolin masarautar tana shirin dora masa,duk da yadda yake qoqarin barranta kansa da dukkan wata damuwa da ba ta aikinsa ba. "Sarkin gida ne ya iso da saqon kira daga giwa mammina.......tana buqatar ganinka yanzu yanzu" Kadan ya zubawa saddam idanu,yayin da abdii ya saki abinda yakeyi ya zubawa saddam din idanu shima. Har cikin rai da zuciyarsa yana mamakin yadda suke ma haisam din karan tsaye,yadda suke isar masa da umarni?,amma wani lokaci idan ya tuna HAR YANZU BASUSAN WAYESHI BA sai yaji zuciyarsa ta sassauta,ba kuma hakan yana hanashi jin haushi ba gami da jin kamar ya sanar musu waye haisam din da suke rayuwa dashi?,saidai koda yaushe idanun haisam din dama kallonsa a kansa na gargadi ne da tuna masa doka da qa'idar da yake kai. Wani lokaci yakan cilla tunaninsa baya,yakan tuna irin girma da nauyin matsayin haisam din cikin Ethiopia,amma gashi yau cikin qasar agadez ya zabi yayi rayuwa a matsayin wani gama garin malami ba tare da kowa yasan nasa girman matsayin ba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Idanunsa ya sauke daga kan fuskar sadam yana dan sakin boyayyen murmushi. Hasashensa da dukka zarge zargensa sun tabbata,tarko ne ya d'ana kuma ya kamata,wannan kiran ko wani motsi daga gareta yake jira gashi kuma ta motsa din,iya haka kawai ya bashi tabbaci. Saidai kuma tazo a gabar da 'yan miskilancin nasa suka motsa,real version dinsa na introvert ya soma aikinsa a jikinsa,don haka ya maida bayansa jikin kujera yayi relax yana amsa masa. "Naji,na kuma karbi kiranta,zan kuma isketa,amma ba yanzu yanzu ba,akwai qananun abubuwa da nakeso na kammala". Cikin matsanancin mamaki da kuma tsoro sadam ya daga kansa yana duban haisam din. Karon farko!.....a karon farko giwa ta kira wani yana sanar mata bazai samu daman amsa kiranta ba har sai a sanda shi hakan yayi masa?. Harara kawai abdii yake zabgawa sadam ganin yadda ya qame a gurin,da alama amsar haisam din ke tabashi,inda yasan girman wanda ke a gaban nasa wannan sai yafi girgiza hankalinsa akan amsar da aka bawa uwar dakin gidan gaba daya. Shurun da haisam yaji ya sanya ya zare littafin daga fuskarsa ya zube idanunsa akan sadam yana kuma tambayar lafiya?,da idanunsa kawai ba tare da ya buda bakinsa ba. Wani abu me tauri sadam ya hadiye maimakon tuni da yakeso ya yiwa haisam akan wace giwa? Da kuma irin girman matsayinta a agadez dama nijer gaba daya. Wani mugun kwarjini haisam din yayi masa,har kwarjinin dake cikin idanunsa suka danne girman mamaki da kuma girman matsayin zaituna dake gilmawa cikin zuciyarsa,sai ya miqe a hankali yana juyawa,cikin ransa dauke da zulumin yadda zaya isar da saqon ga sarkin gida daya tabbatar zai gayawa yalwa ne ba tare da shi ya kasance mai laifi ba. "Obbo" Abdii ya kira sunan haisam a hankali. "Ya akayi?" Kawai yace dashi ba tare daya dauke idanunsa daga kan littafin ba. "Baikai lokacin da zasusan naka matsayin ba da kuma waye kai?" Shuru haisam din yayi,har abdii ya fidda ran amsawarsa,sai kuma ya zame littafin yana duban abdii da dukka idanun nan nasa masu tsananin kwarjini. "Banzo nan na zauna na rayu dasu don nuna musu girman matsayina koni waye ba......nazo ne don cimma nasara.....nasarata nake nema bawai jaddada matsayi ba". Shuru abdii yayi,yana duban sanda haisam din ya miqe yana ajiye littafin " Ka shiga dashi ciki......lokacin sallah saura mintuna kadan,kayi alwala zamu wuce masallaci,sannan ka shaidawa salaana,gobe da dare yazo ya daukeni a hanya.....zanje gida" Dan dubansa kadan abdii yayi sanda yake tattare litattafan,daga yadda yayi maganar kamar ya gaji da komai ma,sai ya amsa masa yana dauke sauran takardun ya fara wucewa ciki. Parlor din farko ta dawo ta zauna,muhallin da hadimanta suka fiya kai kawo a cikinsa. Tanaso a yau ta sauke masa wani kaso mafi girma cikin izza da girman da yake tunani ya samu,tanason ta rage masa kaifin abinda yakeji a kansa idan ma har wannan ya soma tasiri a kansa. Ta zabi tayi hakanne gaban hadimanta mata don yafijin kunya,yasan kuma shi din ba kowan kowa bane,ba kuma komai bane. Wayarta ta ajiye gefe tana duban yalwa sanda take shigowa Parlour din,daidai sanda hadimanta uku ke aikin shirya mata gabanta da kayan marmari dana motsa baki duk da bata buqaci hakan ba,amma ta maida musu shi al'ada saboda nuna cikar izzarta. "Ina fata kin sanar dashi saqona.....don bani da lokacin zaman jira,ina da abubuwan yi da yawa a gabana" Ta fada cikin zaquwa da son isowar tasa,saidai tana qoqarin binne hakan da izzarta. "Kiyimin aikin gafara,amma yace bazai samu isowa yanzu ba......akwai qananun abubuwa da yakeso ya kammala". Ba hadiman dake kai kawo da masu shirya mata kayan maqulashe a gabanta kadai bane suka kadu da maganan ba......hatta da wadanda ke nesa kadan da gurin saida hakan ya nuna jikkuna da fuskokinsu,don daya daga cikinsu saida apple din da take qoqarin yankawa ta subuce a hannunta. Mammina tabi apple din dake gangarawa gefe da kallo tamkar tana kallon faduwarta da kuma gangarewar mutuncinta da tsiyayewarsa a idanun duk wani wanda ke qasanta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 35* Mammina tabi apple din dake gangarawa gefe da kallo tamkar tana kallon faduwarta da kuma gangarewar mutuncinta da tsiyayewarsa a idanun duk wani wanda ke qasanta. Ta tabbatar apple din ta fadi ne bawai don abun yazo bane a al'adance yadda aka saba......ta tsinkayi dalilin faruwar hakan da kallon data yiwa idanun kowaccensu. Wani irin abu me ciwo yana sukar mata zuciya ta maida dubanta ga fuskar yalwa. "Hukunci ya shafeki.......ta yadda nan gaba zaki san yadda zaki dinga isar da saqonnin magana kunnuwan zaituna.....dole ki koyi ladabin isar da saqo yalwa.......ki tashi ki nemi tamim kice ya tabbatar ya kawomin sheikh gaba nan da mintuna talatin.......a gaya masa bijirewa kirana bazai haifar masa da d'a me ido ba,bijirewa kirana kuma yana daidai da qarewar kwanakin zamansa cikin masarautar nan". Gaba daya jikin yalwa kama rawa yayi,tsananin tashin hankali yana saukar mata,abinda taketa tsoro kenan,wannan ya sanya ta dauki kusan mintuna goma tana juya da sigar da zata isar mata da saqon,don amsarsa ta gigitata fiye da yadda zaitunan ta gigita. Dole ta tashi,don bata bata damar yin magana ba,idan kuwa har ta sake tayi tayi imanin qaruwar laifi da kuma hukunci ne a kanta,saita juya ta sauka tana fita a gurin da sassarfa. A nutse ya kammala alwalarsa,ya kuma yi taku biyu yana bari muhallin da aka gewaye a farfajiyar tasa saboda alwala irin haka. Tattausan handkerchief ya zaro daga aljihunsa yana rage lemar hannuwansa dake dauke da gargasa,wanda hannun jubah din jikinsa yana tattare ne har saman gwiwar hannunsa dab da dantsensa. Ba alamun takun takalma saboda gurin shimfide yake da lafiyayyar grass carpet.......amma cikin jikinsa yakejin kamar akwai wanda idanunsa ke kansa,kamar akwai wanda ke tahowa nan inda yake. A nutse ya cira idanunsa yana duban shiyyar da yakejin motsin takun na tunkarosa,sai ya zube idanun nasa gaba daya akan tamim dake takowa da wani irin karsashi da cikakken kuzarin dake nuna da dukka lafiyarsa yake isowa gareshi. Tun daga saman kansa zuwa qafafunsa wani irin abu me qarfin gaske ya ratsashi,wanda ya fito kai tsaye daga idanun haisam zuwa nashi idanun. Samun qafafunsa yayi da yin laushi,kuzarin daya shigo dashi gurin da zummar tasa haisam din a gaba har zuwa gaban mammina sai ya nemeshi ya rasa. Sai haisam din ya zare idanun nasa cikin nutsuwar nan tasa yana sake hannun rigarsa a hankali. Ya karanci komai dake cikin idanunsa,ya kuma karanci da yanayin da ya tunkaroshi,saidai ya sani.....koda wanda yafi tamim hadari ne.....koda wanda yafi tamim jin power ne ba abinda zai iyayi a kansa. (Akwai addu'o'in da muddin suka ratsa jikinka ba wani abu dake karyaka sai qarfin ikon Allah.....tsananin ambaton Allah yana bada wannan kariyar,ba sihiri bane,ba kuma tsafi bane). "Barka da yammaci" Tamim ya samu bakinsa da furtawa "Kana lafiya?" Kawai ya amsa masa gaisuwar da tambaya "Lafiya qalau alhamdulillah......" Sai ya danyi shuru sannan ya tattara dukka jarumtarsa. "Saqo ne daga uwar gida giwa......tace na shaida maka,mafi girman kuskuren da zaka aikata a rayuwarka shine ka bijirewa kiranta........yin hakan daidai yake da kawo qarshen zamanka cikin gidan nan dama yankin agadez gaba daya.......ta umarceni dana shaida maka cewa,kayi gaggawar amsa kiranta,ka ajiye dukkan abinda kakeyi ka sameta a inda ta buqata cikin mintunan da basu haura biyar ba". Yakai qarshen zancan yana zubawa haisam idanu don ganin iya adadin tasirin da maganar tayi masa. Saidai baiga komai tattare da haisam din ba,baiga sauyin nutsuwa ko kadan a tare dashi ba,hasalima wani tattausan murmushi yaga ya saki,sannan a nutse ya daga idanun nan dakewa tamim wani irin tasiri ya dubeshi. "Ka shaida mata ka gayamin,kuma naji......zan amsa kiranta idan na kammala uzurin gabana kaman yadda na fadi da farko" Abinda ya fadiwa tamim kenan a nutse,sannan ya fara zura takalmansa a dogayen fararen qafafunsa ya soma takawa a nutse yana barin gurin. Da kallo kawai tamim ya bishi yana jin wani irin madaukakin mamaki yana ratsashi. A karon farko,a kuma tarihin mammina......a tarihin rayuwarta kaf cikin agadez an samu wanda ya tsaya ja in ja da umarnin mammina giwar agadez. Har wani irin tashi tsigar jikin tamim takeyi,don yana auna irin girman hukuncin da mammina din zata sanya ayi masa. Yana hangen irin baqar azaba da baqin hukuncin da zai fuskanta daga gurinta,yana tausayin yadda daukakar da sultane yayi masa ya rudeshi.....shi kansa a yanzun da yake takawa don isarwa da mammina saqon abinda ya fada cike yake da fargabar yadda zata karbi bayanin. "Fadi abinda ya gaya maka kai tsaye,ban kuma lamunce ko boye ko ka sauya koda harafi daya cikin zantukansa ba" Ta fada tana jin jikinta yana tsuma saboda tsananin mamaki da bacin ran daya shayar da ita. Ajiyar zuciyar samun sassauci tamim ya saki. Wannan damar data bashin sai ya zamana kamar sassauci a tare dashi,don haka bai boye din ba,ya fadi ya kuma dora da fadin. "Ya cancanci ya fuskanci kalar hukuncin da wani a yankin nan da gidan nan bai taba ganin irinsa ba......saboda me sha'awar gwada koda irin hakan ya kiyaye" Tamim din ya fadi zuciyarsa cike da hassada da kishin haisam. Guraben da ya samu a gurin sultane da morsa.....gurabe ne da matsayin daya jima ya shafe lokaci me tsaho yana nemansu bai samu ba. Wasu matsayine da suka kasance qarshen mafarkinsa a kowacce rana,amma rana tsaka an samu wanda ya samu wannan gurbin a taqaitaccen lokacin da idan aka kwatanta da nasa shekarun daya kwashe daidai suke da qiftawar idanu. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Shi yake da ikon zabar lokacin amsa kiran masarauta?" "Tabbas.....yace zaizo idan ya samu sararin hakan bayan kammala uzurorinsa". Kai take sake jinjinawa cike da wani tarin mamakin. "Zaizo a wani lokaci?,idan ya samu sarari" Ta sake maimaita maganar cikin jin wani abu yana girgiza girmanta. Kai ta jijjiga da qarfi sannan ta,waiwaya ga tamin "Tashi kaje.......ka qarasa aikinka......inaso almaz a gobe ya fito a cikakken mutum......inaso almaz a gobe ya fito da fitar da yanayin da zai sace zuciyar akhnan lokaci daya,banaso mu rasa wannan damar......." Ta fadi tana kauda tattauna zancan haisam a tsakaninta da tamim,duk da ita daya ce tasan abinda takeji,amma batason abinda zai dauke hankalin tamim daga shirin zuwan almaz a gobe. Kai tamim din ya girgiza a hankali,yana jin zallae rashin adalcin da ake shirin gwada masa. Ya kwantanta buda abinda ke cikin baki da zuciyarsa,amma a duk sanda ya zauna gaban zaituna da zummar fadin irin tukuicin da yake buqata daga hannunta na bautar shekara da shekaru sai yaji ya kasa,sai yaji ya gaza.......amma a yanzun da ake shirin sanya almaz gaba dashi......ake shirin sanya almaz gaban buqatarsa,sai yakejin kamar wani abune da zuciyarsa ba zata iya jura ba. A nutse yayi sallarsa ya gama,ya kuma yi addu'o'insa,wanda yana shafasu kira ya shigo wayarsa. Baikai ga ciro wayar ba,wadda ba ringing take bayarwa ba ba kuma vibration ba,wata alama ce da shi daya yake gane shigowar kira ya fahimci waye yake kiran. Sanda ya daga wayar muma qaramin murmushi ya subuce masa. Maleek ne,sai ya taba na'urar kunnensa ya maida wayar aljihunsa ya miqe yana yiwa maleek cikakkiyar sallama,baya amsa waya a masallaci saboda girmama muhallin da kuma girmama wanda ake bautawa a gurin. Yana amsa wayar a nutse yana bin hanyar da zata sadashi da sassan mammina. Ya shirya tunkararta ne dama bayan yayi sallah,bai shirya zuwa gareta ba a kiranta na farko. Hankalinsa yana ga yanayin yadda gidan ya fara daukan saiti da sabbin dokokin da tuni suka karade gidan,suka kuma ratsa kowanne bangare na gidan,suka isa hannun kowanne hadimi bawa da wanda keda alhakin tsaro na gidan. Duk inda ya gilma ko ya taka qafarsa gaisuwar girmamawa ce take biyo baya,saboda kowa na cikin gidan yana qoqarin ganin ya cika umarni da burin sultane na daukar haisam tamkar dan cikinsa. ____kyakkyawar fuskarta shimfide take da wani irin yanayi dake cike da miskilanci,rashin walwala da kuma takurar da takeji tun daga zuciyarta harma da ilahirin rayuwarta gaba daya. Saidai duk da hakan ba zaka rasa hangen wannan sassanyan kyan a tattare da ita ba sanda take saukowa daga cikin motar data kasance mallakinta,bayan ta raka aisa ta tashi zuwa Niamey ta filin sauka da tashin jiragen sama dake agadez din. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 36* Kamar kowanne lokaci hadimanta guda biyar din dukka suka kasance tare da ita cikin hidimarta,birra na cire sauran diguwar rigarta data rage a cikin mota,buhaina na gyara mata lullubin matsakaicin mayafin dake jikinta,bushira na qoqarin rufe murfin motar,yayin da barratu ke clearing mata hanya. Wani abu guda da a kullum yasa take sake jin jinin sarauta da izza cikin kanta da jikinta,yake kuma qara mata nishadi da jin dadin irin tsatson data fito. Saidai a yau din wannan zuciyar tasha banban da ko yaushe,wannan walwalar da nishadin da take samu can qasan zuciyarta a yanzun babu shi ko kadan a tare da ita,zuciyar cike take da rudani,tana jinta a quntace tamkar wanda aka sanya a wani saqo daban aka killaceta. Shehnaz na daga bayanta tana amsa wayar jamaal a nutse,ba wani daga murya ko hayaniya,wannan zai sanya daqyar ka iya jin abinda take fada. A yanayi irin wannan baushin shehnaz da aisa ke kamata. Sunayi kaman basusan ciwo da dadin rayuwarsu ba?. Namiji ne kawai halittar da zai iya daga hankalin mace,ya sanyata cikin tsananin damuwar da zata iya qare rayuwarta a ciki,amma a hakan dukka sun runtse idanunsu daga ganin kowanne aibu nasu?. Misali me sauqi a kanta,bata shimfida hannayenta ta karbi kowanne namiji ba......bata marabci kowanne d'a namiji cikin rayuwarta ba.....amma duk da hakan gigita rayuwarta suke shirin yi?. Ranar gobe tana lissafata cikin mafiya munin ranaku a rayuwarta da bata taba zuwa mata ba. Wata rana da bata taba lissafinta cikin kwanakinta ba na duniya kaf,koda kuwa zatazo bata lissafa zuwanta a nan kurkusa har haka,ta yaya zata manta da MORSA SAFIYYA cikin rayuwarta ne?. Wani nauyi takeji a qirjinta sosai idan ta tuna qalubale ne yake tunkarota ta kowacce fuska. Mammina ce kawai qarfinta......banda tana da mammina bata da tabbacin ina rayuwa zata kaita. Wani siririn iska ta fitar daga bakinta.......ba abunda ke sanyata cikin jin qasqanci idan ta tuna waliccin aurenta a hannun waye ya rataya a yanzu?...... MALAMI......BAQON MALAMI.......TSINTACCIYAR MAGE!. Duk da irin tarin darajar da take dashi......tarin dangi da ahalin da zasu iya aurar da ita?......amma sultane ya zabi horar da ita ta hanyar damqa waliccinta a hannun wanda ko cikakken asali bayi dashi?. Idanunta ta daga a hankali sanda tunaninta ya kawo wannan gabar don yanke hukuncin sassanta zata nufa ko zata shiga daya daga cikin guraren dake bats relief cikin gidan a duk sanda ta shiga rudani irin wannan?. A daidai lokacin ne kuma idanunta suka sauka a kansa,wanda da saukar nata idanun shima ya daga manyan fararen idanunsa suka sauka saman fuskarta dake da wani irin kwantaccen kyau......kyan daya bayyana tarwai cikin dan qaramin hasken ranar daya haske farfajiyar ya kuma nuna ainihin kalar qwayar idanunta. Idanunsa ya zare a hankali sannan tattausan murmushi ya kubce masa wanda labbansa da suka motsa ne kawai suka bayyana murmushi yayi saboda maganan da maleek ya gaya masa ta cikin wayar. Idanunta ta janye itama da wani irin hanzari tana jin wata irin faduwar gaba data saukar mata. Wani irin kwantaccen kwarjini da wata ajiyayyar izza ta hanga tattare dashi,abubuwan biyu suka ciccibi tunaninta suna jefashi wani sashe na daban dake cike da zallar mamakin "MALAMI DA IZZA?....MALAMI DA KWARJINI?" Ta tambayi kanta da kanta wani abu yana mata tsaye qasan ranta. Me yasa a kowacce siffa data kebanta dasu?,a kowacce siffa da tafi dacewa dasu?,a kowacce siffa data kasance mallakinsu ce sai ya cusa kansa yayi tarayya dasu?. Meye hadinsa da wannan izzar?,meye hadinsa da wannan kwarjinin da yake nunawa saman fuskarsa?. Abu mafi qona mata rai shine......ta lura a duk sanda idanunsu zasu hadu guri daya faduwar gaba itace abu na farko dake fara ziyartarta......a duk sanda zasu hada idanu da ita shine yake fara janye idanunsa kafin ita. Baisan ma zunubi bane kallonta haka kai tsaye ido cikin ido?. Koma meye sultane ne ya janyo mata,ya bashi dama da yawa,damar kuma har takai ya bashi wuqa da naman zartarwa cikin rayuwarta. Yadda ta lumshe idanunta haka ta dauke numfashinta a sanda yake shirin giftata. Zuwa yanzu tana tsoron shaqar wannan qamshin.....qamshin da ta soma zargin akwai wani sihiri a cikinsa. Ba wani rana.....ba wani lokaci da zata shaqi wannan qamshin bai maqale mata a hanci da tunaninta ba a yinin ranar gaba daya. Kowanne qamshi a duniya yana da asali da kuma inda aka samoshi,amma wannan mayen qamshin ya rasa asali da dukka wani bin diddigi da tayi masa. "Barka da warhaka sheikh" Ta tsinci muryar shehnaz a bayanta tana gaidashi cikin tarin girmamawa. "Barkanki" Amsar daya bata kenan yana maida wayar maleek kunnensa yana ci gaba da takawa. Idanunta akhnan ta qanqance tana jin wani abu me nauyi yana sauka qasan zuciyarta. Wani irin bacin rai sabo ya soma tasiri cikin ranta tana kuma iya sauraren yadda shehnaz ta qaro sauri tana qoqarin jera kafadarta da tata. "Me yasa kike qoqarin zubda girma da kimarki shehnaz?.....me yasa kike qoqarin nunawa duniya ke din ba kowan kowa bace?" Dubanta shehnaz takeyi cikin zallar mamaki. "Kamar yaya biftu?" Ta tamabaya maganan tana warwarewa shehnaz kai. A nutse ta waiwayo tana ajewa shehnaz wani kallo kafin ta dauke kanta,a hankali cikin izzarnan ta fara magana. "'Yar asali kike.....jinin sarauta cikakka daga agadez.....me yasa zaki zubda kanki akan wancan tsintacciyar magen da ba wanda yasan asalinshi?,ke ya kamata ya fara gaidawa......yakai har qasa gurin matuqar baki girma,amma kuma baiyi hakan ba saboda sultane ya bashi dukkan wata dama,tsananin girman kai yana sanyashi jin cewa wai shin wani ne......bayan ba kowa bane face wulaqantaccen......" "Biftu mana!" Shehnaz ta fada tana duban akhnan da mamaki,yadda take maganan da wani birkitaccen fushi. "Kina manta darajar da Allah ya yiwa malamai ne?" Hannu akhnan ta dagawa shehnaz ba tare data waiwayo ta kalleta ba,idanunta na bayyanar da zallar bacin ranta "Bana buqatar naji komai.......ya isheni" Ta fadi har cikin zuciyarta tana jin takai geji,a yanzun bata buqatar maganan kowa akan komai. Ta Jima shehnaz tana dubanta kafin ta dauke idanunta a hankali ta maida gabanta. Mamakin yadda kullum akhnan ke qara birkicewa yana kamata,tuna maganganun da sukayi da aisa kafin ta wuce ne kadai ya hanata cewa komai,saitaci gaba da lissafe lissafenta a ranta,tana kuma nema mata shiriya gurin ubangiji. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) A nutse ya zare device din daga kunnensa bayan ya yiwa maleek sallama,dab da zai shiga sassan mammina ya hada sabon connection da omari ya maida device din kunnensa a nutse yana sake takawa zuwa ciki. Wani abune ya gilma cikin idanunsa daya tilasta masa sanya yatsansa babban da manuni yadan shafi idanunsa yana furta "Subhanallah". Budesu yayi a hankali hoton yana dawowa cikin idanunsa. Baby face dinnan nata dake cike da wani irin yanayi dake nuna zallar gajiyarta rauninta da kasawarta,saidai alamu na tsananin taurin kai kafiya da kuma qi fadi irin nata yasa takejin ita din tsayya ce da ba rauni ko gajiya a tattare da ita,wanda kai tsaye a kuma kallon farko yake iya hangen dukka wadannan abubuwan a tattare da ita. Abu guda daya da yayi masa tsaye a qirji......yadda take kewaye tsakiyar wata da'ira me fadin gaske.......yadda ake wasa da rayuwarta ake juya wannan kafaffen ra'ayin nata daga hagu zuwa dama ba tare da ita tasan hakan ba.......ba tare data fuskanci hakan ba. A nasa idanun wani abune me sassauqan fahimta da ganewa......to amma ya sani a karan kansa,shi dabanne.....shi kuma na dabanne da yake iya hangen komai daga nesa tarwai kamar yayewar hijabi. Bayaso ya shiga wasan daba nashi ba......amma tabbas wasan zai bada ma'ana inda ace shine abinda ya shigo dashi agadez.......an taki bahaguwar sa'ar da baya kallon kowanne aiki sai nasa aikin.....wannan ya sanya wasan zai zame masa abun kallo yana daga zaune a inda yake. Yana raina izzarta......yana raina tsaiwarta da kafiyarta.....yana kuma raina mulki da sarautar da takeji tana yawo a jikinta. Ya sake raina jaririyar kwanyarta......data bari ake gara rayuwarta tamkar ball a hannun qananun yara tsakiyar fillin qwallo. Baizi agadez don kowa ba sai don MAI LAIFIN DA SUKE FARAUTA......BAIZO AGADEZ BA SAI DON QASARSA ETHIOPIA......BAIZO AGADEZ BA SAI DON MOTII DA NANAY DA AL'UMMARSA......baiga dalilin da zai sauka daga wadannan matakai da tsanin nasa ba. Saidai duk da haka,duk da tarin wannan raunin......duk da tarin wannan siffofin,yana hangen wani YAQINI da JAJIRCEWA ta cikin dukka motsi da yanayinta. Da gaske ne ita din bata karbar FADUWA da gaske ne TSAYAYYA CE akan dukka quduri da burinta,saidai yanaji a jikinsa da sannu komai zai canza.....da sannu qilan za'a cimmata a rushe komai.....wataqila a sannan ya jima a jimma Ethiopia,har ma ya mance da wata qasa daya taba wanzuwa wato niger. Kai tsaye suka dinga buda masa hanyoyi har zuwa inda zai riskar mammina. A kowanne taku akwai hadimi guda daya da zai masa jagora zuwa inda take mataki mataki. Tsarin sashenta daban yake,banbamcin da ya bayyana qarara da kowanne sashe na gidan. A zahiri karon farko kenan da ya taba bayyana cikin sassan,saidai a badini kuwa sashen ba baqonsa bane,saidai ya wawantar da kansa yadda ya kamata don yayi kama da mutumin da karon farko daya taba tsintar kansa a gurin. A kowanne motsi da kuma kowanne taku yana hankalce da yadda ba wata doka data soma aiki a sassan mammina din. Kowanne shiyya na gidan ya samu cikakken rahoton fara wanzuwar dokar da fara aiki da ita,ciki kuwa harda shiyyar sultane duk da bayanan,da sashen morsa safiyya. Yayi marking hakan da alama ta biyu da zaiyi nazari a kanta,yana sake maida hankalinsa da inda hadimar ke masa iso tana janyewa baya,da alamu iya tata iyakar kenan. Tun daga nesa kafin ya qaraso ta tattara dukka nutsuwarta,ta kuma bude dukkan basirarta dake mata jagora zuwa fahimtar zurfin tunanin dan adam a sanda taso karantarsa. "Wa'alaikumussalam......bismillah" Abinda tace da haisam kenan a sanda ya qaraso farfajiyar da take zaune. A nutse ya taka yana isa gaban wata kujera qwaya daya data fita daban da sauran,yayi bismillah a hankali yana zama,saita daga kanta tana duban yalwa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 37* "A marabceshi kamar kowa.....a kuma wadatashi da dukkan abun ci da abun sha" Ta furta da cikakkiyar izzar dake nuna girma da nisan inda ta dauki kanta da kuma kalar matsayin data bashi. Idanunta ta daga a hankali,tana iya karantar zallar nutsuwar dake kwance saman fuskarsa,ba wani tsoro ko fargabar kasancewarsa a gabanta,duk da yadda takewa tarin mutane kwarjinin da ko cikakken zama a gabanta ba kowa ke iya yinsa. Wani adanannen kwarjini da tasa aka mata tattalinsa daga kowanne jini dake harbawa a jikinta. "Sheikh haisam.....tuntuni na aika a kiramin kai......ba'a sanar maka bane?" Tayi tambayar da manufa tayin titsiye da kuma son ganin adadin girma da kwarjinin data yiwa idanunsa da zuciyarsa. Kai ya gyada a nutse bayan ta ajiye tambayarta harma ta huta ta hanyar shaqar sabon numfashi,yana jin kamar nashi jinin OROMIA din yana shirin motsa masa,jinin ABA JIFAR amma yasa wani abu me nauyi ya danneshi yana daidaita yanayinsa da lokacin. "Eh an sanar dani" Ya amsa mata a taqaice. Yadda ya amsa mata kai tsaye ba wani kwana kwana ko neman boye laifinsa ya tabata sosai,abinda bata taba gani ba,bata kuma saba gani ba,sai ta jinjina kai. "An sanar dakai.....amma ka bata wasu mintuna da suka kusa tasamma jimillar awa guda cif,na kiraka ka wofantar da kiran?" Ta fadi da zafi zafi wannan karon a muryarta. Kamar dazun,sai daya shaqi nutsatstsiyar iska sannan ya sake motsa labbansa. "Akwai banbamci tsakanin wofantarwa da zuwa a makare......ba kowanne kira bane amsashi akan lokacin da aka yishi yake nuna girmamawa ba......manufar daya ce wanda aka kira ya amsa......gani na amsa a lokacin da yafi dacewa......idan kuma ba damuwa,kamar shiga cikin maganar kai tsaye zaifi,saboda mu ceci lokaci ni dake gaba daya" Yayi maganar kansa tsaye yana zube idanunsa cikin nata. Kafeshi takeso tayi da idanunta,amma ta rasa wannan qwarin gwiwar,saita janye dubanta a kansa,zuciyar taqi yarda da kwarjini yayi mata,saidai tafi alaqanta hakan da fushin da takeji a kansa. Bata jin zata sakar masa wanna gabar da sauri haka ba tare data saukar masa da warning ba saboda gaba "Cikin masarautar nan.....cikarta da batsewarta.......yana zama wajibi akan dukkan wanda na kirashi ya amsa kirana a sanda na buqata". Kansa ya juya a hankali,ya fahimci maganan rashin xuwa kiranta a sanda taso ta mata zafi sosai,hakan shi kuma yayi masa. "A tawa al'adar da yaren.....girmamawa sifface ta dattako.....ga duk wanda ya amsa kiranka ya girmama koda baizo a sanda ka buqata ba" Ya amsa mata yana sassauta harshensa. Bayaso nan da nan tayi fusatar da zata rudar da hankalin omari daga fuskantar abinda haisam din yakeso ya fuskanta. Maganar tasa ya daketa ta kuma taso da wani tsohon al'ada da wata tsohuwar karin magana daga asalin nata yaran,ta kuma motsa idanunta kamar zata waiwaya gareshi ta kalleshi don tabbatar da abinda ya fada,amma koda ta tuna da nata mission din saita kauda hakan. Saidai hakan da tayi bai hanashi daukan haske ba. "Ka zartar da wasu sabbi kuma baqin dokoki ba tare da neman ta bakina ko ganawa dani ba.....shin waye ya baka wannan izinin?". Murmushi ne dan siriri ya qwace masa,saidai ya tsaya iya labbansa,duk da hakan kuma bai hana tsarguwar mammina ba da rayawa a ranta kamar murmushin taga yayi ba,saidai bai bata dukkan dama ta gane hakan ba. Ya kamata tambayar ta bashi mamaki,amma kuma yadda ya tsammaci tuhume tuhumenta zasu iso haka suka sameshi. "Ba kowa". "Ba kowa?" Ta tambaya a mamakance,tana jin ta samu gaba da zata soke kowacce doka hankali kwance. "Eh.....ba kowa,saidai bayan na gama rubuta dukkan dokokin,na gabatarwa da sultane,inda hankalinki a nutse yake da zaki iya ganin stamp da sanya hannun sultane qasan kowacce doka" Ya fada da wani irin calmness yana sake tattara nazarinsa a kanta. Wani shocked taji sosai har cikin jininta,jin da sanya hannun sultane aka wanzar da komai,ba tare da kuma sultane ya kirata yaji ta bakinta ba yadda suka saba sanya kowacce sabuwar doka a tare. "Na tabbatar daukuwa da hankalin sultane yayi ne kan wannan tafiyar ya hanashi nemana......amma hakan bawai yana nufin kana da qarfin ikon zartar da doka kai kadai ba". Kansa ya sake juyawa a hankali,cikin Tarin nutsuwa idanunsa tsakiyar nata yace. "Sanya hannun sultane ya wadatar........dokar bata an qirqireta bane saboda ke,an qirqireta ne saboda masarauta.....shi yasa ya zamana ba wani laifi don an kafata ko an zartar da ita bada saninki ba.....dukkanin dokar an yita ne saboda tsaron masarauta" "Tsaro ga masarauta ko kuma neman ikon sarrafa komai da kowa?" Murmushi ya sakeyi kadan,na wannan karon yafi na dazu bayyana. "Ikon sarrafa komai wannan siffar Allah ce mahalicci shi kadai.....ni dake da sultane duk bamu da hurumi a kanta". Maganar tasa sai taji kaman yana qoqarin tube mata rawanin ikonta ne,don haka cikin qanqance idanu tace masa. " Kasan wacece ni kuwa?". "Kowa nasan wayeshi.....kowa kuma nasan wa yake qoqarin zamantowa ko kasancewa kamar shi". Wani irin abu taji ya sauka yana sarar gabban jikinta. Wani irin gumi taji yana qoqarin tsatstsafo mata,saidai tasan barin hakan ya faru,barinsa ya karanci hakan babban kuskure ne a tare da ita,don zuwa yanzu cikin jikinta takejin BA HAKA KAWAI YA SHIGO AGADEZ BA....BA HAKA KAWAI YA SHIGO MASARAUTA BA.....BA GAMA GARIN MALAMI BANE. "Amma kasan cewa masarautarmu a zaune take lafiya kafin shigowarka cikinta?" Ta sake fadi yanayinta yana nuna fara daukan zafi. "Zaman lafiya ba shine shuru ba......wani lokaci shuru yana boye abubuwa masu nauyin gaske....cikin rashin sa'a saika dauka lafiya ce ta kurmantar da komai din" Ya amsa mata da wani irin nutsuwa a tattare dashi. A karo na biyu ta sake jin kamar dutse ya dauka ya jefeta dashi cikin tsakiyar kanta. "Waye shi?" Ta samu kanta da tambayar kanta da kanta,zuciyarta da tunaninta suna neman zamewa. Zuciyarta ke mata wani irin tsalle,tana kuma cikata da shakku a kansa,sannan tana son jefa mata rudanin da bata shirya ko tunanin fuskantarsa ba a daidai lokacin. "Akwai wani da kake zargi?....ko akwai wani abun zargi cikin masarautar damu muka gaza hangoshi sai kai?". Tayi tambayar cikin zafi,tambayar data sanya ita da kanta wuta dauke mata,don bata tsara ta fidda masa zafinta har haka akan komai ba. Shuru ya ratsa dakin,haisam kallonta da wani irin duba da takejin kamar yana toxartata ne ko kuma qoqarin karantar dukkan wani plan nata. "Zai iya yiwuwa......amna zartarwa a yanzu ba na daya daga cikinmu bane....saidai ki taimaka wajen tabbatuwar amincin amanonin rayukan dake tsakanin hannunki da na sultane.....saini yanzu da aka sakani a ciki zuwa lokacin da zan miqa muku amanarku" Yakai qarshe yana miqewa a nutse,yana kuma jin yakai gejin maganganunsa,yana sake ji a ranshi tako ta ina matar ta tabbatar ABAR ZARGI TA FARKO!. Yadda take takawa a nutse yake tabbatar mata fita zaiyi,hakan kuma yana nuna zai tafi ne koda bada izininta ba,koda batace ba,koda kuma bata gama fadin abinda ke ranta ba,wanda tana da tambayoyin da amsarsa ce kadai zata gamsar dashi. "Kabi a hankali sheikh haisam......masarauta tana iya hadiye baqi ba tare da ganin koda burbushin da za'a bi diddiginsu ba......karka manta gidan nan nawa ne,kada kayi abinda zai sanya da kanka ka fahimci KAI DIN BA KOWAN KOWA BANE" Wani faffadan murmushi sama dana dazu ya kubce masa,ya sakeshi a nutse ba kuma tare daya waiwayo ba. Ya yadda kalaman baki sune abu na farko dake fara fada maka WAYE WANE?. Ya aminta su din wasu maqullaine da a yanzu suka bude masa wata qatuwar qofa da zai sake zurfi a bincikensa "Gida mallakin sultane ne.....ina tsaiwa daidai iyakokin da zasu amintar dashi ne shi kadai.......isata kuwa....." Ya fada yana waiwayowa a nutse. "Lokaci yana tafe da zai baki amsarta......na isa? Ko akasin haka?" Ya fada yana tsaiwa daga nan gami da bata space,saidai bata iya cewa komai ba,wannan ya bashi daman juyawa yana ficewa,saidai duk da hakan bai hanashi jin furucinta na qarshe ba. "Zan tabbatar da cewa na nunawa duniya kai din ba kowan kowa bane.....zan nunawa duniya baka isa a komai ba face zallar malami me cin takarda allo da tawwada". A nutse ya zare Device din daga Kunennensa don ya fara jiyo karadin omari. "Ina mamakin yadda yariman jimma yake iya dauke wadannan kalaman.....don Allah ko sau daya kayi abinda zatasan your not an ordinary man" . Goshinsa kawai yake murzawa a hankali yana qoqarin calming kansa. Idan ya biyewa zancansu omari shirme zasuyi kawai a agadez,su kuma bata lokaci a banza cikin agadez din,su komawa Ethiopia a empty zero hands. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) ____**Hannu ta miqa tana sake jawo takardar tana fidda wani huci daga bakinta zuciyarta tana jin kamar zata fasa qirjinta ta fito. A karon farko a rayuwarta ta d'an d'ani yadda dacin jayayya da qasqantar da isa take ga wanda yakejin ya isa yakai ta kowanne fanni. Idanunta ta maida saman dokokin tana sake bitarsu tun daga farko,tana so kuma ta dire kan sanya hannun sultane din da yayi iqirari akai. _daga wannan daren,bayi da hadimai ba'a lamunce musu zirga zirga tsakanin sassa ba daga bayan sallar isha,har sai da rubutaccen izini_ _Dukkan masu ziyara zuwa cikin kowanne sashe zasu rubuta sunayensu asalinsu yare da qasarsu,da dalili na ziyarar kaman yadda tantancewa zata hau kan kowanne hadimi da bawa dake rayuwa cikin MASARAUTA daga gobe_ _an haramta kowanne ganawa da bayi a kebantattun dakuna ko gurare_ Kasa qarasa karantawa tayi,saboda tsananin bugu da qirjinta yakeyi. Tanajin kowacce doka qwaya daya tana kiran sunan ZAITUNA ne kai tsaye,saita zarce da idanunta kan sa hannun sultane. Sa hannu ne da tafi kowa sanin girma da qarfinsa. Sa hannu ne daya kasance na daban wanda muddin sultane yayi irinsa saman takarda to kowacce magana ce komai qarfinta ta zama TABBACIYAR da babu sauyi a cikinta!!!. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 38* "Yalwa!" Ta kira sunanta kai tsaye a yau din da kanta. "Ki nemomin tamim yanzu.....ki gaya masa kada yazomin da tsohon labari,sabuwar magana nake son ji" . Umarnin daya qara yawan rawar jikin yalwa da son cikashi,wataqila wannan ya shafe hukuncin da take zaman jiran fuskanta kan aikenta na dazun. ★ "akwai boyayyu kuma nannadun al'amura masu girma da yawa cikin masarautar nan......haisam,akwai wani abu daban dake cikinta bayan abinda muke nema.....akwai wani abu na daban dake faruwa bayan bincikenmu......girman abinda ke cikin masarautar nan yafi qarfin princess akhnan kawai....yafi qarfin rikicin cikin aurenta kadai......inaji a jikina haisam.....matar nan tana hadarin gaske,me yasa ba zaka taimaki sultane ba?." Omari dake zaune suna fuskantar juna shida haisam ya furta damuwa zaune fal saman fuskarsa. Wani irin kallo haisam yayi masa yana qoqarin daidaita kansa tsakanin idanun omari din. "Kasan me kake fada kuwa omari?" Ya masa tambayar calmly,saidai idanunsa na nuna girman abinda yake fadi din. "I know haisam.....na sani" Ya fadi kai tsaye yana duban idanun haisam,yanason ya fahimci da gaske yana jin interest na fadada bincikensu da bin diddigin cikin gidan. Kallon kallo ne ya wanzu a tsakaninsu na wasu sakanni kafin haisam ya zare idanunsa. Da gaske ya karanci tunanin omari,kuma da gaske yake fadin abinda yake fada din,ba wasa sam a ciki. "I wasn't cross boarders to save the palace" Ya furta da wani irin accent dake nuna tasirin yaren oromo cikin harshensa,yayi maganar ne kuma yana dauke dubansa daga kan omari,yana maida dubansa ga cup din gabansa da omari ya zuba masa coffee. Idanu sosai omari ya zubawa haisam din,a karon farko yana mamakin sauyawar dabi'ar haisam din. Baida kutsa kai kan sha'anin mutane.....amma yana damuwa kan mutumin da duk yaga zai cutu muddin yana da ikon taimaka masa. Me yasa a yau a yanzu yake kauda kai daga taimakawa akhnan da mahaifinta?. "Amma......me yaci gaba da shigo da issue dinta cikin maganamu inde haka ne?" Omari ya jefa masa tambayar. Sau daya tak ya daga ido ya kalli omar,sannan ya dauki mug din coffee dinsa ya shanye,kana ya miqe a nutse yana zube hannayensa cikin aljihun trouser din jikinsa,ya taka a hankali zuwa bakin qarfen balcony din. "Saboda tana kanannade da wadda nake zargi....dole a wasu lokutan maganan case dinta ya dinga ratsowa cikin aikinmu" Ya amsawa omari a nutse can qasan zuciyarsa kuma yanason canko dalilin da yasa omar ya masa wannan tambayar. Ya sani dukkansu ba wanda ke magana ko tambayar da bata da fa'ida ma'ana ko dalili......ko akwai wani dabi'a ko halayya ta daban da yake nunawa kan abinda ya shafi case din?. Bai iya gano komai ba,bayaso kuma ya waiwaya ya kalli omar kada ya dauka akwai wani abu daban da yake rayawa a ransa. Kaman yasan kuwa kallonshi omar din yake,kaman kuwa yasan neman reaction qwaya daya omari yake daga gareshi. Ya jima yana raya wani abu a ransa game da haisam din. Bai taba masa wani dogon zance daya shafi akhnan ba.....amma ya dade da sanin wata dabi'a kebantacciya daga haisam din,dabi'ar da baya jin ko haisam din yasan yana da ita,dabi'ar da yasan itace SILA SANADI da saamee da MENELIK suka kasa samun matsugunni a zuciyarsa,duk kuwa da cewa suna da kowanne irin quality da ake buqata na zahiri daga gurin d'iya mace. "Amma kasan sultane ya amince da kai?....." ".....wannan ne ma ya bani dalili na qauracewa iyakokinsa da shiga al'amuran da suka kebanci iyalinsa.......ina da kishi me yawa da nauyi,yadda bazan bari a kusanci iyalina ba daidai da d'ani ko taku guda ba.....hakanan bazan kusanci iyalin kowa da zarafinsu ba sai akan wanda gaskiya take buqatar tayi adalcinta a kansa" Ya qarashe maganar yana waiwayowa idanunsa cikin na omari. Wani kallon kallon suka sake yiwa juna,sai kawai omari ya jinjina kansa a hankali sannan ya sauke idanunsa yana cewa. "Nan da kwanaki uku maleek zai kawo maka ziyara,ba kuma iya gidanka kawai ba,har cikin masarauta yake sha'awar shigowa" "Allah ya kaimu" Ya fadi kawai cikin nutsuwar rai. Dukkanin aminan nan bashi da haufi a kansu,sunsan boyayyen aikinsa da ko cikin ahalinsa ba kowa bane ya sani,tsananin amincin dake tsananinsu ya sanya sukasan kowanne doka da strategy na aikin,don haka bai shakkan haduwa da kowannensu a kowanne lokaci a kuma kowanne irin yanayi,bare maleek da abubuwansu da yawa yazo daya,saidai ta wani fannin sukance maleek ya fishi sauqin sabo da jama'a,duk da shi dinma SARAUTA na yawo a jininsa. *MAMMINA* Abinda takeji a ranta a lokacin wani irin yanayi ne da tun zamanin SAFEENA bata qara jin irinsa ba. Wani irin qanqanci takeji har a cikin jininta,wani irin tozarci da ya sanya takeji wani irin zafi saman fuskarta kaman an watsa mata borkono. Kafin tamim ya iso tafisu ta rigashi isowa,tayi dukkan me yuwuwa ta kwantar da hankalin mammina amma hakan bai samu ba. "Wai me kike tsoro game da malamin dake rayuwa qarqashin alfarmarku?" Kai ta jijjiga sosai tana gote da hannayenta. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Ba malami bane gama gari......ba irin malamin da kika saba gani bane.....wannan idan na runtse idanuna ZAKI nake gani a gabana tafisu.....idan na kulle kunne na TSAWA nakeji tana fita a bakinsa maimakon magana irin ta kowanne dan adam.....shi ba irin kowa bane tafisu......tabbas akwai wani abu na daban a tare dashi". Shuru tafisun tayi,tana son gwargwaje magangun mammina cikin ma'aunin nazari da lissafinta,amma sai sallamar tamim ta yanke mata wannan hanzarin. "Me ake ciki game da labarin Ethiopia?" Ta tambayeshi kai tsaye. Bai zauna ba,don bata bashi wannan damar ba yayi qasa da kansa ya soma magana cikin girmamawa. "Sun gaya min,akwa alamu gwada biyu da suka gwada akwa wani shinge daya motsa daga muhallinsa.....alamu ne ba'a samu tabbaci ba" "Su maida kai akan wannan alamun!.......su bani tabbaci a nan kusa!!" Ta furta atsawace tana jin wani abu yana motsawa daga qasan zuciyarta,tamkar an fusgi zuciyartata an kuma jijjigata. "An gama ranki ya dade......amma ki sani.....kallon kallo yana da hadari a wadansu lokutan,sai gwani shike iya satar kallo ya kuma fusgi abinda ganin ya bashi a sanda na kewayensa basu ankare da haka ba" Shuru ya ratsa tana fahimtar saqon da tamim ke aike mata da karkataccen harshe,saidai a yanzu zuciyarta bata aminta da shawarar tamim ba. "Tafiyar hawainiyarmu bata kawomin alfanun komai ba bayaga MAFAKA,mafakar fa wani lokaci nake Allah wadai da ita...,hanzari nake buqatar gwadawa wannan karon,koda bayani ya motsa wasu sassa da zasu farka daga dogon baccin da suke......akwai wani taku na musamman.......dama ya kamaya susan KIFI NA GANINKA ME JAR KOMA!" Tayi maganan a wannan karon tana jin itama ta shirya ta kowanne bangare!!!. _Uhmmmm.....me karatu,tafiyar fa zazzafa ce......abubuwa da yawa na shirin qulluwa agaba ba'a bigiren da aka shirya qulluwarsu ba,FADUWA DA NASARA......YIWUWAR FARA AFKUWAR SABON WASA TSAKANIN MAMMINA DA HAISAM......SHIN WASAN WAYE ZAIWA DADI?......WAZAI AFKA CIKI?.....KU BIYONI MUJE......._ zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 39* *AKHNAN* Idanu kawai takebin mammina dashi,wanda ta zauna tana bude kyautan da suka kusa cinye kaso daya cikin uku na dakin hutawar nata daya bayan daya kowanne tana ajiyeshi a gefe bayan ta bude. "Ba zaki takura ba da rayuwa dashi.....nasanshi nasan mamanshi tsahon shekaru,bayason takura wannan shi ya hanashi aure tuntuni,yana neman matar da zatayi rayuwarta ne kawai ba tare data dameshi ba.....zaki samu dukkan wata izza daga sunan family dinsu kawai....zaki samu kalar sakakkiyar rayuwar da kikeso......kalli a iya yau kawai kyautukan alfarmar daya sauke miki" Mammina ta fadi tana ci gaba da bude kyautukan,wanda kusan kowanne box dake gurin tasan meye a ciki,amma yadda take nuna zumudinta zaka dauka karon farko data fara ganin kayan alatu na rayuwa irin haka. Baki kadan akhnan din ta tabe,don sam bataji wata burgewa tattare da almaz ko daya a ranta ba. Eh ta karanci abinda mammina ta fada a kansa,da gaske bayason damuwa,ganinsa na farko ta tabbatar da hakan,ta sauke numfashi kadan tana sake tabe baki tare da tuna awannin baya da suka wuce. Cikin qasaita dake cakude da fargaba ta yiwa kanta matsugunni saman daya daga cikin lafiyayyun kujerun da aka qawata gurin dasu. Wani irin ado da wani irin yanayi da tunda take ganawa da dukka mazajen da siltane yake mata ba'a taba tsara gurin irin haka ba. Juyawa birra tayi da nufin fita daga gurin ta basu sarari,saidai a nutse da salon kalar umarnin data saba basu ta tsaida birran,sai birra din ta koma gefe daga bayanta ta tsaya tana sauke kanta a qasa. Da dukka manyan kyawawan idanunta ta qure mutumin da kallo,wanda ke sanye da wata qawatacciyar alkyabba,bayan takalmin da aka yiwa wani irin qawataccen ado daya zame ya ajiyeshi a gefansa. Kansa yana duqe a qasa,wanda bazai bata dama da ikon gane fuskarsa da kyau ba,saidai mamaki ya soma ratsata a hankali na rashin tantance bacci yake ko gyangadi?,don sam bataga alamun waya a hannunsa ba ballantana tayi tunanin waya yake dannawa. Izzarta ta hanata magana,a haka suka shafe a qalla mintina biyar kafin ya motsa a hankali yana daga kansa gami da jinginar da bayansa a kujera. Idanunsa ne ya soma sauka akan fuskarta,kaman yadda nata idanun suka sauka a kanshi,kallon kallo kuma ya sarqafe tsakaninsu na wasu sakanni kafin ta fara janye idanunta mamaki yana sauka a hankali saman zuciyarta. "Shin me mammina ta gani tattare dashi data hangi dacewarsu?" Tambayar data soma yawo kenan saman kanta,wadda ta tilasta mata maida idanunta a karo na biyu kansa. Still shima ita yake kallo,saidai a wannan karon yayi qoqarin sakin murmushin daya dan fidda kyansa ya kuma haska wani abu cikin idanunta. Sake zare dubanta tayi daga kansa tana rasa kowanne feelings a kansa. Soyayya dai dama tasan bata da lokacinta,bama kuma batunta akeyi ba,saidai wannan tarin baqincikin da bacin rai da tsananin tunzura da takeji a zuciyarta a duk sanda wani namiji ya tsaya a gabanta da sunan neman aure a yanzun bata jin ko guda daya..... Me yasa dukka sharuddan data tsara gindaya masa?.....me yasa duk wani doka data tsara shimfida masa don yasan cewa bawai zai amsa sunan mijinta da gasken gaske ba suke sulalewa?. "Na sani.....kada ki wani damu......zaki rayu yadda kikaga dama.....kaman yadda zan rayu yadda naga dama" Ya furta da wani izza ciki muryarsa da yadan ja hankalinta sosai ta sake daga kai tana dubansa. Wannan karon tsakiyar idanunsa kawai ta kalla kai tsaye,sai takeji a ranta kamar ta taba ganinsa a wani guri kafin nan,kamar ta taba saninsa kafin yanzu,saidai dukka tunaninta ya gutsire a sanda yayi wani motsi nan take tarin hadiman data fahimci tare dashi suke suka fara shigowa gurin,shi kuma ya miqe tsam yana takawa da wani kamata irin yanayi data kasa tantance ne meye.....izza ce?.....ko nasa yanayinne a haka?. Ko sanda zata dawo daga tunaninta tuni sun kammala jere takin kyaututukan data dinga binsu kawai da kallo ba tare da tasan ainihin meye da meye a ciki ba sun kuma juya suna take masa baya. Bataji kalmar DACEWA ko BURGEWA tattare dashi ba.....saidai sam bata damu ba,don dama ba auren wadannan dukka zatayi ba. "Gobe in sha Allahu zasu gabatar da sadakinsu" Mammina ta fadi tana tattara hankalinta akan akhnan bayan ta gaji da bude kyaututukan. Sanin dukka abinda ke ciki ne ya gajiyar da ita,tanaso kuma tayi saving lokacinta. Sosai akhnan din ta tsuke idanunta tana duban mammina. Abu na farki daya fara zuwa mata kai shine SHIEKH HAISAM shine zai yanke adadin dukiyar da za'a bayar shi kuma ya basu ita?. Idanunta ta dauke daga kan mammina,wani sabon bacin ran yana shimfida saman fuskarta. A hankali da wani irin coolness ta motsa labbanta. "Me yasa saishi mammina?.....me yasa sultane zaiyimin haka?" Ta tambaya tana sake maido dubanta ga mammina. "Wannan izzar.....wannan kimar,wannan dangantakar kwanann nan zata fara zama tarihi cikin agadez.....kwanan nan qyamata da ala wadai zata maye gurbin komai" Wannan shine abinda yake yawo saman zuciyar mammina din,saidai kuma a fili murmushi ta saki. Har a ranta takejin matsalolin da take dasu guda biyu ne......tana kan hanyar kauda daya ta fuskanci dayar.......saboda haka dukkan wani uzuri da akhnan zata bayar tana daukarshi a matsayin wani bata lokaci ne kawai. "Iya wannan lokaci,iya yanzu ne kawai yake da dama a kanki biftu,ki kwantar da hankalinki,daga wannan lokaci na miki alqawarin bazai sake shiga gonarki ba.....zan nesantashi da dukka iyakokinki,keda igiyar aure ma zata baki dukkan wata power?,kin manta wannan igiyar auren zata dawo da dukka wata kyakkyawar alaqa da dangantaka tsakaninki da sultane?,duk wani kusanci da kika rasa zaya dawo miki,meye abun damuwa?,ba abinda ya rage miki sai ki nutsu komai ya tafi daidai da hankulan masu nazari" Kai ta girgiza a hankali,hakan taketa qoqarin yi,amma sai takejin abun kamar yayi mata wahala. "Niamy nakeso na koma mammina" Ta furta da wani irin sarewa,tana jin komai bayayi mata daidai. Murmushin dake kwantar da zuciya ta saki tana maida hankalinta a kanta. "Gaggawar me kike?,zaki zauna a shiryaki kaman kowacce amarya me gata,ko randa aka daura aure ne zaki iya wucewa niamy keda mijinki,wanda hakan shi zai sake bawa sultane nutsuwa da aminci a kanki......" Kai ta girgiza a hankali,a yanzu ba abinda take buqata irin ta samu 'yancinta,ta kuma koma rayuwarta kamar yadda take a baya,mara tarin matsaloli,rayuwa me cike da 'yanci da zartarswa akan dukkan abinda takeso. "Sahel couture......ya miki nisan da bazai dawo hannunki kamar yadda yake a baya ba.....har gaban abada......zan tabbatar ya sake zamewa daga hannunki ta hannun amintacciyar taki" Ta furta qasan ranta tana sakin murmushi a bayyane,murmushin da akhnan ke kallonsa a matsayin wata hanya guda daya da mammina ke amfani da ita don samar mata da nutsuwa. ★A nutse suke takawa cikin farfajiyar kebantattun sassan haisam din da sultane ya mallaka masa,zuwa doguwar veranda da zata sadashi da qofar da zasu isa kai tsaye ga sassan nasa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Yarima haisam tare da yarima maleek,wanda dukkaninsu suka narke cikin masarautar agadez da wani irin yanayi da bazai baka daman fahimtar sarautar dake jinin kowannensu ba. Saidai kuma kowannensun akwai wani irin kwantaccen kwarjini a tattare dashi,irin kwarjinin da jinin sarauta yake gaadarwa kowanne ahali nashi. Dukkaninsu suna sanye ne da fararen tufafin da aka saqasu daga lallausar auduga me darajar gaske,saidai ba kowa bane zai fahimci hakan,saboda sassuqar sutura ce a jikin kowannensu. Maleek yana sanye da kurta pyjamas ne riga da wando,saman kansa kuwa Indonesian cap ce sassauqa data dace da suturar jikinsa,yayin da haisam ke sanye da jallabiyya fara sol me wani irin sulbi data dace da zatin tsahonsa da kyakkyawar fatarsa ta asalin qabilar oromia da suka sabawa ainihin kalarsu ta hanyar yin haske kadan daga ainihin skin color dinsu. Komai na adon zaren jikin rigar fari ne qal,hakanan hiram din daya yiwa wani irin nadi na asalin samarin larabawa shima fari ne sol daya fidda kyan fuskarsa da dogon hancinsa dake zauna sosai saman fuskarsa ya sake bayyana tsananin kwarjinin idanunsa guda biyu. Half shoe ne a qafarsa shi dinma fari ne sol,lallausa kuma sassauqan da zai wahala ka fahimci yana yanayi da takalmin basarake. Da azahar maleek ya sauka,ya kuma soma sanyawa an saukeshi a personal gidansa dake wajen masarautar,ya fara zuwa suka gana sannan suka tattauna akan yadda zai baqunceshi cikin masarautar,saboda tsarin shiga da fitar baqi daya sauya yanzu,dole ana buqatar bayanansa da kuma asalin yarensa wanda tuni haisam ya shirya kowanne bayani da zai bayar. Dab da magariba maleek ya shigo gidan,daidai lokacin da haisam din ya kammala ganawa da dattawan da sukazo karbar auren akhnan a hannunsa kaman yadda sultane ya buqata. Sunzo da tarin sadakin da ya sanyashi mamaki......ba kuma mamakin yawan sadakin ba.....saidai ya riski wani yanayi daya sanyashi zuzzurfan tunanin da har yanzu bai gama sakinsa ba. Hannun wanda ya miqo sadakin shine abu na farko daya fara kalla......daga yanayin hannun.....yanayi na ainihin zubin halitta,bai hangi wani alamu da ake iya ganewa daga qafa zuwa hannu dake tabbatar da nasaba ba,wanda wani ilimi ne da ba kowa yake dashi ba. Abu na biyu yaga gilmawar almaz......fuska da kamanninsa suka dinga masa yawo a ido,saidai yawan busy din da yayi a yau din ya cunkushe masa duk wani haske da zai iya tuna masa INA YASAN ALMAZ?........A INA YA TABA GANIN FUSKARSA?. Ya yita maimaita ma'anar sunan dama sunan cikin kansa. Almaz yana nufin DIAMOND (lu'u lu'u cikin yaren oromo). Kai ya jinjina a hankali,yana jin dukkan gamsuwar cewa zaituna ita ta fiddawa akhnan miji kamar yadda a ranar data gabatar da hakan ya zargi an shirya mata komai ne,an kuma karanta mata komai,nata zartarwa ba tare da wani sauran zabi daya rage mata ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 40* "Albarkar auren itace abinda mukafi buqata,ba tarin sadaki ba,iya wannan adadin sune abinda muka yanke muku" Ya fadi cike da dattako yana sake karantar yanayin kowannensu. Cikin qasa da minti daya kacal ya karanci kallon kallon da sukewa junansu. Kamar wani kallo ne na rashin tabbas......kallo ne na rashin sukuni da rashin sakewa da hukuncin daya zartar din. Bai sake basu daman magana ta biyu ba ya miqe wazeer kuma ya dafa masa baya cikin gamsuwa da abinda haisam din yayi. Ya shaidawa sultane komai,wani irin farinciki ya ratsa sultane din yana aje numfashi a hankali. Gefe daya kuma yana baqincikin subucewar wani abu me daraja daga cikin ahalinsa.....wani abu da yayi tsananin sanya rai a kansa "Komai kaga ya dace ka zartar muhammad.....wuqa da nama duka suna hannunka" Abinda ya amsashi dashi kenan a taqaice. Ko yanzun da suke tattaki zuwa sassan nasa don maleek ya fara kewar coffee yana so yasha kafin ya wuce masaukinsa dake personal gidan haisam din tunani ne fal kansa. Fuskar mutumin da aka bashi tabbaci shine wanda aka karbawa auren ya gaza barin idanu da tunaninsa. Bawai yana mamaki bane.....ba kuma yana raina matsayi dacewa ko cancanta ba,duk akwai abubuwa masu tarin yawa daya kamata ya tsaya tsakanin kotunan sultane ya amsasu inda yana da hurumi akan abinda ya shafi rayuwarta......saidai aah......yana jin kamar akwai wani abu da yakeso ya sani......yana jin kamar akwai wani al'amari dake da alaqa da bincikensa. "Karon farko da omar ya zauna gidan sarauta zama me dan tsaho kamar haka......shi yasa komai yake sake burgeshi,kasan kowacce rana sai ya bani labarin agadez?.....wannna yaja ra'ayina zuwa ga agadez din" Maleek ya fada yana murmushi yana kuma jin yanayin qasar da garin duka ya masa. Kadan haisam ya jingine tunanin dake ransa,ya danja fasali kadan sannna ya magantu. "Kamar ba aiki ne me girma a gabanmu ba.....ka yawaita maimaita masa ko zaifi fahimtar abinda nake nufi......kowanne gidan sarauta lullube yake da tarin abubuwa da idanu basa iya ganinsa......rayuwa ko tsoma kai a cikinsa sai jajirtaccen namiji". Kai maleek ya kada,don ya fahimci maganan haisam sama ma da yadda yakeso ya fahimta din. "Gimbiya akhnan" Maleek ya fada a hankali da qaramin murmushi,sannan ya dan juya kadan yana kallon haisam. "Ko kasan ina da labarinta kadan kadan,bada wata masaniya me yawa can can ba tun kafin omari ya fara gayamin komai akan abinda ya shafeta?" Maleek yayi maganan yana maida dubansa gabansa. "Akwai nazzirou dan qasar nan ne,yankin diffa,amma yana rayuwa a agadez....." "Na karbi sadakinta dazun.....daurin aurenta rana ita yau,idan kana sha'awar zama daya daga cikin shaidun daurin aurenta kana iya kaiwa har rana ita yau a agadez" Haisam ya Fadi da yanayin daya bayyanawa hakeem sam sam baya da wani interest akan hirarta ma. Murmushi me dan sauti maleek ya sauke. "Wannan bayani haka da wurwuri?" "Saboda bana buqatar dogon hira akan sha'aninta......inajin kamar shigarta cikin bincikena tana sake dagulamin shine kawai tare da shiga qofofin da bai kamata ta tsaya a nan ba". "Dalili?" Maleek ya buqata still yana boye murmushin sa bai kuma kalli haisam ba ya bada dukkan hankalisa ne kawai a kansa. "Wanzuwarta akan wasu hanyoyi da qofofi sune silar bata lokaci na da dadewata cikin wannan masarautar da 'ya'yan cikinta ke rayuwa cikin dimuwa da rashin sanin birnannun sirrikan dake shirin binne musu rayuwa da ransu......ciki harda tata rayuwar data dauketa da wani irin kima da tsananin girman da batasan cewa batakai can ba" Ya sauke maganan da wani irin zafi kadan cikin muryarsa,saidai can qasan ransa yana jin wani mutuwar jiki yana sauka masa. "Kasan da haka captain......me zai hana kayi ceton daka saba?" Maleek ya tambaya kai tsaye yana duban haisam gami da rage saurin tafiyarsa kadan. Duk da cewa dare ne amma hakan bai hana maleek ganin yadda haisam ya waiwayo yana zuba manyan fararen idanunsa ba,kafin ya janyesu a hankali. Yan miskilancin suka biyo baya,sai daga bisani daya tuna maleek ne sannan ya motsa bakinsa a nutse. "Ban gaji da kare mutuncina da martabata ba........inda ace namiji ne.......zan iya qundunbalar aikata hakan........ta yadda koda ya qalubalanceni ina iya zage qwanjina na nuna masa munin abinda yacemin.......amma d'iya mace?......" Sai ya tsaya bai dakata ba yana girgiza kansa. "Diya mace irinta......data yiwa kanta ado da qawa da rashin iya magana......data yiwa kanta ado da qawa da tarin rashin kunya,nakanji a raina inama ace ta fito daga jini da tsatson oromia....." Sai yayi shuru bai qarasa ba. Duk da bai qarasa din ba maleek ya fahimci me yake nufi. Tabbas qabilarsu qabila ce da girmama manya ya zama daya daga cikin dokokinsu,ya zama wani abu da ake rainon kowanne d'a nata,tun daga haihuwa har zuwa girma. "Akwai wasu dabi'u da qualities a tare da ita.......akwai wasu halaye da ba zaka sake samun irinsu sak ga kowacce mace ba a nan kusa.....qila sai bayan shekaru masu yawan da qila zuwa sannan furfura ta gama zama abar ado a kanka da fuskarka" Maleek yayi maganar kai tsaye tana kuma sauka saman zuciyar haisam. A hankali ya soma maido maganan daga farkonta zuwa baya,yana qoqarin mata mazauni me kyau.......saidai isowarsu dab da gurin,da kuma hango omar da yayi tsaye a gurin da nashi cup din gahwar ya sanya ya maida maganan da yakeson maidawa malee din. Ya tabbatar idan omar yaji maganan bazai qare ba......ba kuma zai mutu ba,amma indai ta maleek ne shi kadai zai wahala ya sake tayar da maganar,saidai ko bayan wani lokaci ba wannan ba. Hand shaking suka bawa junansu da wani irin yanayin musabaha da Huggin da zai nuna maka tsantsar qauna dake tsakaninsu. "Ka shiga kasha ka fito mu wuce.....akwai hira me tsaho yau kam" Omari ya fadi yana dan duban haisam kafin ya maida hankalinsa ga agogonsa. Baiko kalleshi ba haisam din,don har yanzu kwanyarsa cike take da tarin tunaninnika. A nutse maleek ya wuce ya barsu a nan,shuru ya ratsa gurin na wasu daqiqu,omar na sipping coffee dinsa,haisam kuma yana tsaye da wannan tsaho da murjewar jikin dake nuna asalin halittarsa ta GIANT MAN. *AKHNAN* Batasan adadin hadimai nawa ta sanya su kula mata da shigowar haisam ba tun daga sanda adadin abinda ya karba a matsayin sadakinta ya isa kunnuwanta. Batasan adadin sau nawa ta tsaya gaban mirror tana sake qarewa kanta da kanta kallo ba. Ta sanya hannu ta baje lallausar sumar nan tata me daukan hankali ta ainihin buzuwa kuma ba'abzina. Wanne irin muni ko lalacewa ya hango a jikinta......wanne irin naqasu ko kasawa ke tattare da ita da zai karbi mafi qasqancin sadaki da sunan sadakinta?. Sadakin da koda manyan hadiman da suka jima cikin gidan.....manyan hadiman da sarauta takewa ALFARMA su shiga rigarta sunfi qarfin wannan sadakin ballanta ita AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD diyar SULTANE guda. Haifaffiyar diyar da har yanzu ba'a samu wata yarinya data kamo rabin qafarta a daraja da kuma gata ba kaf masarautun da qasar niger keda ita. Yarinyar da izzarta da cikar gatanta ya sanya take ganin bata da SA'A cikin yaran sarakuna ballanta har ta qulla aminci ko qawance da daya daga cikinsu. Kai ta girgiza a zafafe tana jin wani sashe na qwaqwalwarta na tafasa da wani irin matsanancin bacin rai. SULTANE NE SILA......ta yaya zai hada mu'amalarsa da bagidajen da baisan komai ba face tarin litatttafai da tawwada?. Me yasa duk gatanta.....duk shahara da family din mahaifiyarta sukayi idanma bata da gefan uba ya gaza wakilta mutum daya da zai zama jagora wajen aurar da ita?. Sai wannan mutumin da takejin TSANARSA ta fita daban data sauran dukkan malaman data sani. Wannan mutumin da takejin yafi dukkan sauran malaman da suka rayua fadar baqar aniya da baqin sihiri. Dukkan malamai na baya da suka rayu cikin masarautar girmamata suke.......mutuntata suke da tsananin mutuntata ra'ayinta.....bata da wata hujja ta tsanarsu face tsana data musu tun ta asali.....amma kuma wannan fa?.....shi kuma fa?. Ya karbe ya kuma ture dukkan wani matsayi da take gani da kusanci tana dashi. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Tana jin wata fusata da ba zata barta ta fara magana da mammina ba......tanajin ya mata nisa ta tsaya shawara da mammina. Shi ya aikata,shi ya kamata ya fara ganin fushinta. Ya dace zuwa yanzu yasan iya matsayinsa.......ya kamata ya fahimci ya zurfafa da yawa,ya kamata ta farkar dashi idan ya soma shaqar iskar 'yanci da yawa harta bugar dashi ya manta matsayinsa......ya kamata old version na AKHNAN BIFTU ya motsa. Cikin jikinta da jininta gaba daya takejin kunya.....kunya me lullube da wani irin tarin baqinciki na yadda ya zartar mata da hukunci cikin rayuwarta,bayan shi din ba kowan kowa bane a rayuwarta,shi din bai darajar da hannayensa ma zasu taba sadakinta ba.....amma dukka sultane ya tattara wannan damar.....wannan kimar.....wannan martabar ya damqa masa. Shigowar birra ya sanyata daukan siririn band ta tattare gashinta me tsaho da sulbi ta daureshi,birra ta matso cikin girmamawa da zummar mata shiri na musamman,ga zatonta baqi gareta masu muhimmanci cikin daren,ko wata muhimmiyar fita. "Kaya kawai zaki bani na canza,cikin gida zan shiga" Ta fada tana qoqarin karbar kayan da tuni birra ta cika umarninta ta ciro mata su. "Ki tabbatar da lafiyar hanya,sannan a dubamin kowanne sashe na gidannan a gayamin inda wancan malamin yake a yanzu haka". Tayi maganan tana fara zame hannayen rigar baccinta da har tayi shirin kwanciya labarin sadakin daya fara yawo cikin gidan ya hanata kwanciyar. Dan damm kadan birra tayi,tana tuna sabuwar dokar hana zirga zirga daga wannan sassan zuwa wancan sashen da lokacinta yake dan da fara aiki kamar kowanne dare daya zama zartaccen hukunci cikin masarautar. Tana kyautata zaton jwar dakin nata ta manta?,duk da bata da tabbacin tana da masaniyar fara aikin dokar. Dole ta shaida mata,don gudun karya dokar kamar yadda akayi gargadi me zafi akan kowa. "Allah ya taya miki sirrin farincikin sultane......akwai doka da aka sanya na hana zirga zirga daga goma na dare a masarauta gaba daya". Cak ta daga fararen idanunta dake dauke da blue din qwayar idanu daga tsakiya tana zube dubanta akan birra,kallon dayayiwa birra nauyi,kwarjinta daya cakude da tsananin bacin rai yana tasowa. "Doka?......waye gwanin sanya doka a sanda sultane baya nan?,sa'annan har yake da qarfin ikon tilasta kowa yin biyayya ciki harda ku da kuke qarqashin umarni da kulawarmu?" Sake yin qasa da kanta birra tayi sosai sannan a ladabce tace. "Sheikh haisam" Ta fadi a hankali. Tunani kwanyarta ta cilla,amma bata wahal da ita da dogon nema ba ta canko mata wanda birra din ke nufi,saboda shi kadaine yake amfani da laqabin sheikh a jikin sunansa. Wani sabon bacin rai taji yana sauko mata,ta ware idanunta sosai tana duban birra da kyau. "Birra......hala kin manta a gaban wa kike da kike iya sanar mata akwai wata doka bata sultane ba da zata bi?" Tayi maganar da maqurar bacin rai da kuma mamakin yadda komai yake sarrafuwa ta hannunsa. "Tuba nake ranki ya dade,kiyimin rai" Idanunta kawai ta maida ta lumshe tana jin yadda adadin farashin tsanarsa ke ninkuwa a ranta,kafin daga bisani taja iska me nauyi "Kada na bude ido na ganki a nan,ki kuma aiwatar da umarni na......doka koda ta sultane ce a yau nasa qafa na taketa,ballanta ta tsintacciyar mage". Sosai kalaman suka yiwa birra girma,bata kuma sake tsaiwa cewa komai ba ta fice da sassarfa,don ya zame mata dole cika umarnin uwargijiyarta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 40* "Albarkar auren itace abinda mukafi buqata,ba tarin sadaki ba,iya wannan adadin sune abinda muka yanke muku" Ya fadi cike da dattako yana sake karantar yanayin kowannensu. Cikin qasa da minti daya kacal ya karanci kallon kallon da sukewa junansu. Kamar wani kallo ne na rashin tabbas......kallo ne na rashin sukuni da rashin sakewa da hukuncin daya zartar din. Bai sake basu daman magana ta biyu ba ya miqe wazeer kuma ya dafa masa baya cikin gamsuwa da abinda haisam din yayi. Ya shaidawa sultane komai,wani irin farinciki ya ratsa sultane din yana aje numfashi a hankali. Gefe daya kuma yana baqincikin subucewar wani abu me daraja daga cikin ahalinsa.....wani abu da yayi tsananin sanya rai a kansa "Komai kaga ya dace ka zartar muhammad.....wuqa da nama duka suna hannunka" Abinda ya amsashi dashi kenan a taqaice. Ko yanzun da suke tattaki zuwa sassan nasa don maleek ya fara kewar coffee yana so yasha kafin ya wuce masaukinsa dake personal gidan haisam din tunani ne fal kansa. Fuskar mutumin da aka bashi tabbaci shine wanda aka karbawa auren ya gaza barin idanu da tunaninsa. Bawai yana mamaki bane.....ba kuma yana raina matsayi dacewa ko cancanta ba,duk akwai abubuwa masu tarin yawa daya kamata ya tsaya tsakanin kotunan sultane ya amsasu inda yana da hurumi akan abinda ya shafi rayuwarta......saidai aah......yana jin kamar akwai wani abu da yakeso ya sani......yana jin kamar akwai wani al'amari dake da alaqa da bincikensa. "Karon farko da omar ya zauna gidan sarauta zama me dan tsaho kamar haka......shi yasa komai yake sake burgeshi,kasan kowacce rana sai ya bani labarin agadez?.....wannna yaja ra'ayina zuwa ga agadez din" Maleek ya fada yana murmushi yana kuma jin yanayin qasar da garin duka ya masa. Kadan haisam ya jingine tunanin dake ransa,ya danja fasali kadan sannna ya magantu. "Kamar ba aiki ne me girma a gabanmu ba.....ka yawaita maimaita masa ko zaifi fahimtar abinda nake nufi......kowanne gidan sarauta lullube yake da tarin abubuwa da idanu basa iya ganinsa......rayuwa ko tsoma kai a cikinsa sai jajirtaccen namiji". Kai maleek ya kada,don ya fahimci maganan haisam sama ma da yadda yakeso ya fahimta din. "Gimbiya akhnan" Maleek ya fada a hankali da qaramin murmushi,sannan ya dan juya kadan yana kallon haisam. "Ko kasan ina da labarinta kadan kadan,bada wata masaniya me yawa can can ba tun kafin omari ya fara gayamin komai akan abinda ya shafeta?" Maleek yayi maganan yana maida dubansa gabansa. "Akwai nazzirou dan qasar nan ne,yankin diffa,amma yana rayuwa a agadez....." "Na karbi sadakinta dazun.....daurin aurenta rana ita yau,idan kana sha'awar zama daya daga cikin shaidun daurin aurenta kana iya kaiwa har rana ita yau a agadez" Haisam ya Fadi da yanayin daya bayyanawa hakeem sam sam baya da wani interest akan hirarta ma. Murmushi me dan sauti maleek ya sauke. "Wannan bayani haka da wurwuri?" "Saboda bana buqatar dogon hira akan sha'aninta......inajin kamar shigarta cikin bincikena tana sake dagulamin shine kawai tare da shiga qofofin da bai kamata ta tsaya a nan ba". "Dalili?" Maleek ya buqata still yana boye murmushin sa bai kuma kalli haisam ba ya bada dukkan hankalisa ne kawai a kansa. "Wanzuwarta akan wasu hanyoyi da qofofi sune silar bata lokaci na da dadewata cikin wannan masarautar da 'ya'yan cikinta ke rayuwa cikin dimuwa da rashin sanin birnannun sirrikan dake shirin binne musu rayuwa da ransu......ciki harda tata rayuwar data dauketa da wani irin kima da tsananin girman da batasan cewa batakai can ba" Ya sauke maganan da wani irin zafi kadan cikin muryarsa,saidai can qasan ransa yana jin wani mutuwar jiki yana sauka masa. "Kasan da haka captain......me zai hana kayi ceton daka saba?" Maleek ya tambaya kai tsaye yana duban haisam gami da rage saurin tafiyarsa kadan. Duk da cewa dare ne amma hakan bai hana maleek ganin yadda haisam ya waiwayo yana zuba manyan fararen idanunsa ba,kafin ya janyesu a hankali. Yan miskilancin suka biyo baya,sai daga bisani daya tuna maleek ne sannan ya motsa bakinsa a nutse. "Ban gaji da kare mutuncina da martabata ba........inda ace namiji ne.......zan iya qundunbalar aikata hakan........ta yadda koda ya qalubalanceni ina iya zage qwanjina na nuna masa munin abinda yacemin.......amma d'iya mace?......" Sai ya tsaya bai dakata ba yana girgiza kansa. "Diya mace irinta......data yiwa kanta ado da qawa da rashin iya magana......data yiwa kanta ado da qawa da tarin rashin kunya,nakanji a raina inama ace ta fito daga jini da tsatson oromia....." Sai yayi shuru bai qarasa ba. Duk da bai qarasa din ba maleek ya fahimci me yake nufi. Tabbas qabilarsu qabila ce da girmama manya ya zama daya daga cikin dokokinsu,ya zama wani abu da ake rainon kowanne d'a nata,tun daga haihuwa har zuwa girma. "Akwai wasu dabi'u da qualities a tare da ita.......akwai wasu halaye da ba zaka sake samun irinsu sak ga kowacce mace ba a nan kusa.....qila sai bayan shekaru masu yawan da qila zuwa sannan furfura ta gama zama abar ado a kanka da fuskarka" Maleek yayi maganar kai tsaye tana kuma sauka saman zuciyar haisam. A hankali ya soma maido maganan daga farkonta zuwa baya,yana qoqarin mata mazauni me kyau.......saidai isowarsu dab da gurin,da kuma hango omar da yayi tsaye a gurin da nashi cup din gahwar ya sanya ya maida maganan da yakeson maidawa malee din. Ya tabbatar idan omar yaji maganan bazai qare ba......ba kuma zai mutu ba,amma indai ta maleek ne shi kadai zai wahala ya sake tayar da maganar,saidai ko bayan wani lokaci ba wannan ba. Hand shaking suka bawa junansu da wani irin yanayin musabaha da Huggin da zai nuna maka tsantsar qauna dake tsakaninsu. "Ka shiga kasha ka fito mu wuce.....akwai hira me tsaho yau kam" Omari ya fadi yana dan duban haisam kafin ya maida hankalinsa ga agogonsa. Baiko kalleshi ba haisam din,don har yanzu kwanyarsa cike take da tarin tunaninnika. A nutse maleek ya wuce ya barsu a nan,shuru ya ratsa gurin na wasu daqiqu,omar na sipping coffee dinsa,haisam kuma yana tsaye da wannan tsaho da murjewar jikin dake nuna asalin halittarsa ta GIANT MAN. *AKHNAN* Batasan adadin hadimai nawa ta sanya su kula mata da shigowar haisam ba tun daga sanda adadin abinda ya karba a matsayin sadakinta ya isa kunnuwanta. Batasan adadin sau nawa ta tsaya gaban mirror tana sake qarewa kanta da kanta kallo ba. Ta sanya hannu ta baje lallausar sumar nan tata me daukan hankali ta ainihin buzuwa kuma ba'abzina. Wanne irin muni ko lalacewa ya hango a jikinta......wanne irin naqasu ko kasawa ke tattare da ita da zai karbi mafi qasqancin sadaki da sunan sadakinta?. Sadakin da koda manyan hadiman da suka jima cikin gidan.....manyan hadiman da sarauta takewa ALFARMA su shiga rigarta sunfi qarfin wannan sadakin ballanta ita AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD diyar SULTANE guda. Haifaffiyar diyar da har yanzu ba'a samu wata yarinya data kamo rabin qafarta a daraja da kuma gata ba kaf masarautun da qasar niger keda ita. Yarinyar da izzarta da cikar gatanta ya sanya take ganin bata da SA'A cikin yaran sarakuna ballanta har ta qulla aminci ko qawance da daya daga cikinsu. Kai ta girgiza a zafafe tana jin wani sashe na qwaqwalwarta na tafasa da wani irin matsanancin bacin rai. SULTANE NE SILA......ta yaya zai hada mu'amalarsa da bagidajen da baisan komai ba face tarin litatttafai da tawwada?. Me yasa duk gatanta.....duk shahara da family din mahaifiyarta sukayi idanma bata da gefan uba ya gaza wakilta mutum daya da zai zama jagora wajen aurar da ita?. Sai wannan mutumin da takejin TSANARSA ta fita daban data sauran dukkan malaman data sani. Wannan mutumin da takejin yafi dukkan sauran malaman da suka rayua fadar baqar aniya da baqin sihiri. Dukkan malamai na baya da suka rayu cikin masarautar girmamata suke.......mutuntata suke da tsananin mutuntata ra'ayinta.....bata da wata hujja ta tsanarsu face tsana data musu tun ta asali.....amma kuma wannan fa?.....shi kuma fa?. Ya karbe ya kuma ture dukkan wani matsayi da take gani da kusanci tana dashi. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Tana jin wata fusata da ba zata barta ta fara magana da mammina ba......tanajin ya mata nisa ta tsaya shawara da mammina. Shi ya aikata,shi ya kamata ya fara ganin fushinta. Ya dace zuwa yanzu yasan iya matsayinsa.......ya kamata ya fahimci ya zurfafa da yawa,ya kamata ta farkar dashi idan ya soma shaqar iskar 'yanci da yawa harta bugar dashi ya manta matsayinsa......ya kamata old version na AKHNAN BIFTU ya motsa. Cikin jikinta da jininta gaba daya takejin kunya.....kunya me lullube da wani irin tarin baqinciki na yadda ya zartar mata da hukunci cikin rayuwarta,bayan shi din ba kowan kowa bane a rayuwarta,shi din bai darajar da hannayensa ma zasu taba sadakinta ba.....amma dukka sultane ya tattara wannan damar.....wannan kimar.....wannan martabar ya damqa masa. Shigowar birra ya sanyata daukan siririn band ta tattare gashinta me tsaho da sulbi ta daureshi,birra ta matso cikin girmamawa da zummar mata shiri na musamman,ga zatonta baqi gareta masu muhimmanci cikin daren,ko wata muhimmiyar fita. "Kaya kawai zaki bani na canza,cikin gida zan shiga" Ta fada tana qoqarin karbar kayan da tuni birra ta cika umarninta ta ciro mata su. "Ki tabbatar da lafiyar hanya,sannan a dubamin kowanne sashe na gidannan a gayamin inda wancan malamin yake a yanzu haka". Tayi maganan tana fara zame hannayen rigar baccinta da har tayi shirin kwanciya labarin sadakin daya fara yawo cikin gidan ya hanata kwanciyar. Dan damm kadan birra tayi,tana tuna sabuwar dokar hana zirga zirga daga wannan sassan zuwa wancan sashen da lokacinta yake dan da fara aiki kamar kowanne dare daya zama zartaccen hukunci cikin masarautar. Tana kyautata zaton jwar dakin nata ta manta?,duk da bata da tabbacin tana da masaniyar fara aikin dokar. Dole ta shaida mata,don gudun karya dokar kamar yadda akayi gargadi me zafi akan kowa. "Allah ya taya miki sirrin farincikin sultane......akwai doka da aka sanya na hana zirga zirga daga goma na dare a masarauta gaba daya". Cak ta daga fararen idanunta dake dauke da blue din qwayar idanu daga tsakiya tana zube dubanta akan birra,kallon dayayiwa birra nauyi,kwarjinta daya cakude da tsananin bacin rai yana tasowa. "Doka?......waye gwanin sanya doka a sanda sultane baya nan?,sa'annan har yake da qarfin ikon tilasta kowa yin biyayya ciki harda ku da kuke qarqashin umarni da kulawarmu?" Sake yin qasa da kanta birra tayi sosai sannan a ladabce tace. "Sheikh haisam" Ta fadi a hankali. Tunani kwanyarta ta cilla,amma bata wahal da ita da dogon nema ba ta canko mata wanda birra din ke nufi,saboda shi kadaine yake amfani da laqabin sheikh a jikin sunansa. Wani sabon bacin rai taji yana sauko mata,ta ware idanunta sosai tana duban birra da kyau. "Birra......hala kin manta a gaban wa kike da kike iya sanar mata akwai wata doka bata sultane ba da zata bi?" Tayi maganar da maqurar bacin rai da kuma mamakin yadda komai yake sarrafuwa ta hannunsa. "Tuba nake ranki ya dade,kiyimin rai" Idanunta kawai ta maida ta lumshe tana jin yadda adadin farashin tsanarsa ke ninkuwa a ranta,kafin daga bisani taja iska me nauyi "Kada na bude ido na ganki a nan,ki kuma aiwatar da umarni na......doka koda ta sultane ce a yau nasa qafa na taketa,ballanta ta tsintacciyar mage". Sosai kalaman suka yiwa birra girma,bata kuma sake tsaiwa cewa komai ba ta fice da sassarfa,don ya zame mata dole cika umarnin uwargijiyarta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 41* Sassauqar rigar buba ce data zauna mata das a jiki,duk da bada fadi ta gefe da gefe amma ta tsakiya ta zauna daidai fadin qirjinta da kuma shafaffen cikin ta. Wani irin yadine me taushi daya kasance daya daga cikin suturun da asalin buzaye kan sanya a jikinsu,sai mayafin da baida cikakken kauri data dora saman kanta da zummar suturce sumarta,ta zurawa sambala sambalan qafafunta takalmin tana jan wani irin tsaki kamar zata cire harshenta. Da wani irin qasaita take saukowa daga stairs din,kowanne motsinta kowacce gaba ta jikinta tana fidda lallausan qamshin incense by kabodaughter,duk cewa bata qara wani turaen ba a yanzu,amma yadda qamshin ya kama suturarta haka ma jikinta ya sanya ko yaya ta motsa ko ta gifta sai wani irin sassanyan qamshin ya fitini hancinka. Birra buhaina da bushira dukkaninsu suna tsugunne suna dakon fitowarta,don haka sai kowacce ta miqe suna saita kansu gami da fara take mata baya cikin girmamawa da bada kariya ta musamman ga amanar sultane dake hannunsu. ★Shirunne yaci gaba da gudana a gurin da wani irin yanayi na kadawar iska dake nuni da tasowar hadari da kuma yiwuwar zubar ruwa daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Tun yammacin ranar hadarin yake qugi yake kuma hada kansa,so a yanzun ba abun mamaki bane don ya soma zubda ni'imar daya qunso a cikinsa. "Me ka fahimta game da yanayin nanay akan wannan abun hannun?" Haisam ya tambayi omari kai tsaye,don yanason gwada nasa kaifin hasashen ba tare daya buda masa bayanan daya samu daga gurin nanay ba. Bayanan da suka tunzurashi kuma ya saka wani sabon binciken bin qwaqwaq afi da diddigin yadda akayi ZEENATU amaryar ajani tayi baton dabo. Rana ta qarshe da aka ganta a Ethiopian da gurin da aka ganta na qarshe. Tare da matsawa da kunna kowanne abu da zai tayar da qurar lullubin tsohon aiki tsohon bayani,tayar da duk wani ma'aikaci daya ajiye aiki a wancan shekarun,duk wani ma'aikaci na shige da fice daya ajiye aiki shekaru goma baya da suka wuce har zuwa yanzun. A jikinsa yakeji da gasken gaske komai yana kan turbar bayyana da warware kansa. Zarginsa yana sake tabbatuwa da qarfafa akan mammina da kowanne irin wucewa second. Bayanai yana iya samunsu yanzu na abinda ke gudana cikin gidan,saidai ya sake tabbatarwa TSANANIN WAYO gareta,wanda hakan yake sake sanyashi damqe tasa damarar da kyau. Ta canza duk wani takunta,saidai a wannan sauyin akwai wasu qofofin data bari a bude da suke iya kai ganinsa ga wani sabon babin zargin. Sake jaddada tsaro da tsari dama qofofin dakin ajiyarta dake cikin gidan,wanda ba wani daki da aka tasamma wannan aikin sai nata. Yaga zallar rashin wayonta a nan,hakan kuma ya zama NUNA KAI da motsi dake tabbatar da tsarguwa da rashin yarda,motsinta ya haifar mata da kuskure,KUSKUREN da ya qara jan hankalin haisam zuwa ga isa ga ma'ajiyar. Ya tabbatar akwai tarin SIRRIKA ajiye a ciki,girman sirrikanne kuma ya sanya hankali da nutsuwar mammina suka kasa samun sukuni da tunanin abubuwan dake binne a ciki. "Ina tunani gani da hasashen nanay tasan komai akan abun hannun,don reaction dinta ya nuna hakan" Omari ya fada yana tattara hankalinsa akan haisam. Shuru ya sakeyi yana jinjina kansa a hankali,sai ya ajiye nannauyan ajiyar zuciya. A hankali ya motsa bakinsa cike da tarin nutsuwar nan data zame masa jiki. "Jikina yana gayamin......akwai wata alaqa tsakanin zaituna da zeenatu,qaqqarfar alaqa" Ya fadi can qasan yana qanqance idanunsa saboda sabon gilmawar wani motsi me qarfi da yaji,motsin daya tabbatar omar baikai ga jinsa ba,bayaso kuma yaji din don a yau yana son sake aikewa da mammina ne wani babban GARGAD'I da yakeso ya ganshi baro baro saman fuskarta da ayyukanta. Kai omari ya gyada shima yana gamsuwa da zancan. "Idan hakan ta kasance fa?". Shuru yayi sannan wani irin lallausar murmushi ya kubce masa lokacin da idanunsa suka sake dauko masa inuwar bulama dake qoqarin kusanto inda suke.....saidai kar yake hangen inuwar bulama da irga kowanne motsi nasa. " Zan shayar da kowa mamaki" Ya bada amsar don isar da saqo ga bulama da motsinsa,da kuma isar da saqon amsa ga omari. Tun daga nesa kadan dasu ta sauke idanunta a kan mutum biyun dake tsaye gaban qarfen,tana tsammanin kasa tantance malamin tsakanin mutum biyun,saidai a sanda idanunta suka sauka kan mutum na biyu daga qasan zuciyarta taji tana gaya mata SHINE. Idanunta ta qanqance tana ci gaba da duban bayansa tana jin kamar tayi taku guda ta isa gabansa maimakon taku kusan goma sha biyar da suka rage tazarar dake tsakaninsu "Kafi gaban bada mamaki.....saidai kace al'ajabi,ina tsoronka sometimes" Omari ya fadi yana kurbe coffee dinsa. Maganan ya sanya haisam murmushi kawai,ya maida dubansa ga gabansa sosai yana hangen yadda iska ke wasa da ganyen bishiyoyin daketa rangaji a gabansu tare da ci gaba da karantar sauyawar kowanne motsi na bulama da yake iya qiddigeshi cikin kansa da yanayin lissafin ma'abota kakkaifar qwaqwalwa dake aiki da intelligence na security. Baiyi niyyar sake cewa komai ba......sai kuma sabon takun da yaji a bayansa ya sake waftar wani kaso na hankalinsa,saidai hakan bai iya janye nazarinsa akan bulama ba dake sake kusantosu cikin irin hikimar da yake zaton yana da ita,kamar yadda takun bai sanyashi ya juya bayansa ba kamar yadda omari yayi. "Subhanal malikul quddus" Omari ya furta qasa qasa yana tabo haisam,still idanunsa suna kan akhnan da nata duban yake tsaye akan haisam kawai,haisam din da bai ko motsa ba bare ya waiwayo gareta. "Haisam......princess din agadez ce da kanta" Omari ya furta a karon farko daya soma ganinta ido da ido kuma kai tsaye haka. Wani irin mamaki ke saukowa yana lullube omari,da gaske ne yadda ake radi radin kyawunta,yadda ake wassafata har bai kai yadda take a fili ba,ganinta a fili ya zarta yadda ake maganarta,tabbacin da gaske ba kowa bane ya taba tozali da ita. "Idan har tazo nan ne saboda ni.....ka barta ta qaraso,banaso kaci gaba da damuwa da isowartata" Abinda yace da omari kenan still na abinda ya sauya daga tsaiwarsa a gurin hankalinsa na rarrabuwa gida uku yana kuma qoqarin kula da kowanne sashe. Wani bacin rai me nauyin gaske ya soma narke mata yana ratsa kowanne lungu da sashe na zuciyarta. Ta tabbatar tayi imanin yaji takun tafiyarta,kamar yadda ta fahimci akwai wani a gefansa dake tsaye tare dashi da yaji alamun tahowarta,amma yanayin tsaiwarsa bai canza ba ballanta yakai ga waiwayo inda take. Me ya dauki kansa?,me yakejin kansa?,wannan kadai yana sake tabbatar mata ya shirya yin hakanne don ya wulaqanta ya toxartata ya qasqanta matsayinta a duniya,a yau kuma taci alwashin saita maida wannan martanin a kansa,saita sanya yaji fiye da zafin da ita taji. Tazara kadan ta rage a tsakaninsu,ta tsaya cak tana goye hannayenta a qirji gami da sake zuba masa idanu ta baya tana sake zurfafa kallonta a kansa. Taku hudu omari yayi yana basu space,space din dabai nesantashi da ji da ganin abinda ke faruwa ba. Yaji tsaiwarta a bayansa,saidai yanajin kamar kusancin dake tsakaninsu yayi yawa,amma duk da hakan bai juya ba sai bayan wasu sakanni da suke sake tabbatarwa da akhnan shi din MA'ABOCIN GIRMAN KAI NE. Bataga alamun zai juyo ba....bataga alamun yasan da wanzuwarta a gurin ba,haqurinta kuma ragagge ne da ba zata iya jiran reaction dinsa ba,duk da tarin izzar da take cinta sai ta sake goye hannunta sosai a qirjinta,cike da izza,cike da jin isa ta motsa labbanta,tattausar muyar nan da bacin rai ya yiwa murfi ta soma yawo cikin iskar dake kadawa tana isar da saqonta ga kunnuwansa. "Wannan itace hanyar da malamai suke bi don qasqantar da daraja kima da martabar 'ya mace.......da bautar da ita cikin aure da sunan addini da kuma musulunci da irin son zuciya da qarairayinsu!" Sosai sautin maganarta ya zauna masa cikin kai da zuciya da wani irin dumi da yaji yana mamayar zuciyar tasa. Numfashi yaja ya aika har cikin hunhunsa yana kiran sunan Allah can qasan zuciyarsa da neman taimako kada shaidan ya rinjayeshi,sai ya saki qarfen da yake dafe dashi ya waiwayo a nutse idanunsa suna sauka a kanta. Guri daya idanunsu suka sarqe,ya sake zare dubansa daga kan fuskarta data bayyana tarwai ta siririyar walqiyar dake haskawa kadan kadan wadda bata dauke da sautin komai,wannan shi zai baka damar ganin yadda iska ke wasa da mayafin saman kanta,da sassalkan wani siririn gashinta me santsi daya ratso ta gefan kunnenta ya fito. Yadda ya zare dubansa a kanta kamar kullum kamar yadda ta kula al'adarsa ce ya sake tunzurata. A koda yaushe yana nuna shi din wani tsarkakke ne wanda ita ta jima da sanin son zuciya da son rai da kuma fakewa bayan addini suna aiwatar da son rai da son zuciyarsu babu wanda yakai malami yin hakan. Wanna fusatar ta sanya ta qara taku biyu zuwa gabansa,tana son ta bambance me yakeji dashi da yake mata wani kallo sannan ya watsar ta hanyar janye idanunsa a duk sanda zasu hadu irin haka. "Kana tunanin bada aurena wani abu ne me sauqi da wasu qananun sulalla marasa darajar da ko takalmin sakawa a qafar hadimaina darajarsa tafi ta wadannan sulallan?" Ta sake fadi cike da tsiwa numfashinta yana dagawa sosai ta saman qirjinta. Numfashi ya sake ja yana aikewa cikin gangar jikinsa yana jin wataqila wannan zai taimaka wajen controlling kansa da zuciyarsa. "Wannan itace hanyar daka zaba wajen qasqantar da darajata?wajen gayawa duniya abace ni me sassauqar daraja?......darajar da baka isa ka samu kwatankwacinta ba?!" Ta sake tambayarsa tana sane takawa zuwa inda yake tsaye kamar ta manta da tana qara kawo kusanci ne a tsakaninsu. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Labarina.......sunana.....daukakata da darajata wani abun tattaunawa ne tsakanin manyan masarautu,ba na iya agadez kawai ba......dole sadakina da aurena ya bambanta dana kowacce d'iya dake jin asali da gata!.....bakasan hakan ba?" Ta sake tambayarsa,idanunsa na sake hange mata wani irin calmness a tattare dashi. Kaman ba ihu take masa ba.....kaman ba fada take masa ba,tunzura take so yayi.......tanaso yayi wani abu guda daya da zai sanyata ta yaga wannan rigar maluntar.....rigar mutuncin da yakejin yana sanye da ita. Tarin rufewa da idanunta sukayi ya sanya ya gaza ganin yadda adams apple dinsa ke sama da qasa yana qoqarin tura duk wani yunqurin bayyana fusata da fushi da zuciyarsa ke qoqarin turawa saman fuskarsa. Zuciyarsa na wani irin motsawa da mugun qarfi,yayin daya sanya kalar nashu qarfin yana danneta da dukka iyawarsa. Amanar da sultane ya damqa a hannunsa ke gilmawa cikin idanunsa........yardar sultane a kansa yake tunawa.......da rauninta na kasancewarta D'IYA MACE......d'iya macen ma da rayuwarta cikin wani yanayi na tagayyara da girman kanta son ranta da son zuciyarta ya hanata ta gane ramin da take shirin shiga ta binne kanta. Hannunsa kawai omari yake dunqulewa yana qoqarin bin umarnin haisam ta hanyar danne na'aurar warning dake tsakiyar tafin hannun haisam din. Mafi girman qarar da na'urar keyi yake gayawa omari qaqqarfan warning haisam ke masa na kada ya soma matsowa ko sanya baki kome girman abinda zai faru. "Ka qwace komai na matsayina daga hannun sultane......a zakutana mutane ma kanason qwace wannan martabar tawa?......ka gayamin......nauyin kudin da zai siya dukka ilimin da kake taqama dashi kana tunanin yayi daidai da abinda zai iya biyan sadaki na?!!". Wani abu me tsini yaji ya caki tsakiyar zuciyarsa......wani abu daya sanyashi daga dukkan manyan idanunsa ya zubesu saman fuskarta,idanun da suka nutse cikin nata ba tare data shirya ba,suka kuma soma sakin wadannan magnet din masu wani iri kaifi da girma da suka sanyata yin taku biyu baya da kanta don rage tazarar da ita ta tsuke nisan dake tsakaninsu. "Sadaki ba shine ke daga darajar mace ba ko ya sauketa......sadaki ba gasa bane.......haqqi ne da Allah yace a bawa mace.....sai kuma addininmu ya gaya mana mafi qarancin sadaki shi yafi albarka a aure......nayi abinda shari'a tafi so......idan har alfaharinki da girman kanki yana da nauyi sama MUTUNCI da KARAMCI ......wannan ba matsalata bane" Ya qarasa maganan yana zube hannayensa a aljihun jubah dinsa gami da dage dukka kafadunsa,manyan fararen idanunsa na zagayawa tsakanin blue eyes dinta,daga bayanta kuma yana hange masa kusantowar motsin da yakejin bai aminta dashi ba,saidai motsin bai janye hankalinsa daga duban kai tsaye da yake mata na ido cikin ido ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE PAGE 42* Batasan ya akayi ta samu idanunta da zame kansu da kuma qwace dubansu daga cikin nasa ba bayan ba abinda ta tsara yi kenan ba.......tana jin idan ta bari ya gayamata ko ya maida mata magana ko qwaya daya ce yayi jayayya da girmanta,don haka cikin rashin yarda da izzarta takai qasa ta sake motsa labbanta fushinta na bayyana sosai. "Me ka dauki kanka?......a tunaninka kai din waye?" Wani miskilin murmushi dake cakude da izza ya saki,wanda ya kusan tafiya da numfashinta na wucin gadi,cikin nuna halin ko in kula yana kuma sake raba hankalinsa da yadda yakejin hucin giftasu daga hagu zuwa dama ya maida mata amsa. "Muhammad haisam wani ne.....wanda ya zame miki tilas ki dakata da qidddige iya adadin ikonsa......don zaki gaza a sanda hasashenki bazai taba iya cafko adadin qarfin ikonsa ba". A karon farko iya tsaho shekarun da tayi a duniya da aka taba challenge nata......da ta taba fadin magana aka maida mata......da aka tsaya a gabanta ana dubanta da duba na kai tsaye......irin duban da mammina ko sultane kadai keda iko da lasisin yi mata shi. Koda ya samu daman tsaiwa a inda ta tsaya.....koda ya samu daman maida mata magana ba zata bari ta kwana da ciwon rai ba. "Idan kana jin dadin tozarta matan da kasan sunfi qarfin matakinka a rayuwa?,daga kaina ba zaka qara kusantar aikata hakan ba" A karo na biyu wani qasaitaccen murmushi ya subuce masa,yayi qas da kansa yana hangen tazarar inuwar boyayyen mutum daga bayanta wanda yake da tabbacin batasan da tsaiwarsa ba,sai ya daga kansa a nutse yana mata nuni da hanya cikin kamala. "Idan kin gama fadin duk abinda yake ranki kina iya tafiya" Idanunta ta qanqance sosai,reshe yana neman juyewa da mujiya. Gurbi da muhallin fushi takeson gani saman fuskarsa akan maganganun data gaya masa.......amma sai yake maye gurbin haka da wani murmushi da iya tsahon zamanta cikin da'irar sarauta,gidan mulki da iko bata taba ganin murmushin dake cakude da zallar izza irinsa ba. Yabar mata ciwon fadin maganar a ranta?,kuma yana umartarta da tafiya daga muhallin daya kasance mallakin mahaifinta?......saman QASAR data kasance cikakken ikonta.. "Ki tafi nace" Yayi maganar wannan karon yanayin fuskarsa yana juyewa da wani matsanancin tsare gida yana kuma ajiye mata wani nannauyan kallo da taji ya mata wani mahaukacin kwarjini. Wannan dabi'artata ta taurin kai da kafiya ita ta motsa.....izzarta ta taso ta lullubeta,ita dake bada umarni yau ita wani yake bawa umarni?......ita dake da iko na fada aji ita ake fadawa abinda zatayi?. Sake tsareta yayi shima da kakkaifan kallonsa,yana sake irga motsi da takun bulama. Kaucewarta a gurin yafi buqata a sannan,don yanason nunawa bulama qarshen rashin qwarewa cikin aikinsa. Saidai kuma baya qaunar wanzuwarta a gurin,saboda ba gaban idanunta yake buqatar yin kowanne motsi nasa ba.....amma yana karantar kafiyarta da taurin kanta na shirin zame masa cikas,kaman yadda ya karanci bulama yana daf da kubcewa tsarinsa,don haka dole yayi wani irin taku da bai kai biyar ba,ya miqa hannu tsakanin shukokin dake daura dasu,ya damqi wuyan bulama cikin wani irin zafin nama,sannan ya fincikoshi daga duhu zuwa cikin haske,ya kuma watsar dashi a gurin. Wani irin matsanancin bugawa kawai zuciyarta takeyi,cike da wani irin matsanancin tsoro da bata taba jin irinsa ba. Ta fidda manyan blue eyes dinta tana duban bulama din da haisam ya watsar a gurin,saidai yana riqe da hannayensa da ya banqaresu ta baya,wanda azabar irin wannan riqon da haisam yayi masa ya sanyashi fidda wani irin nishi a wahalce. Iyakar saninta da hadiman gidan gaba daya batasan bulama ba. Batasan wayeshi ba,batasan kuma wannan fuskar ba......me ya kawoshi nan?,cikin duhun da babu komai cikinsa sai hasken walqiya?,cikin duhun bishiyoyin da ba wanda zai iya labewa ciki sai wanda ke dauke da alama da tambari na rashin gaskiya?. Ba ita ba......hatta da maleek dake kallon komai daga nesa.......amma zama da haisam da dadewarsu tare ya sanya yake fahimtar lokutan da haisam din yake buqatar wanzuwa a guri shi kadai,don haka sai ya tsaya daga ness yana kallon komai. Da fari hankalinsa da nazarinsa gaba daya yana kan akhnan din. Ya cika da wani irin tarin mamakin yadda haisam yake iya hadiye maganganunta,ya sani,yana da wani irin kaifin hangen nesa da qoqarin hadiye bacin rai,saidai kuma sam sam baya daukan raini ko qanqani. Yanayin tsiwarta ya daure masa kai sosai,dukkan wannan izzar a yanzun da take magana da haisam din sai yaga ta kwaranye ta barta da iya tsiwar. Akwai wani abu da yake hanga daga can cikin dabi'unta da yake ganin zuwansa daidai da wani salon ra'ayi na haisam din. JARUMTA......irin salon jarumtar nan ta babu gudu babu ja da baya......wani irin qarfin hali da TSAIWA saman ra'ayi,sai ya saki wani sassanyan murmushi,wanda suke murmushin nasa keda wuya ya hangi yadda haisam din ya motsa cikin wani irin zafin nama ya kuma finciko bulama din. Abun ya matuqar zuwa masa a bazata da kuma bashi mamaki. Baiga wani alamun wanzuwar dan adam a gurin ba......ta yaya haisam din ya fahimci hakan?,bayan kuma da kwanyarsa ta tuna masa SHEIKH HAISAM din sai mamakinsa ya dinga raguwa,ya fara tunanin me mutumin yakeyi a tsakanin duhuwar gurin?. Kamar baisan waye bulaman ba,kamar kuma baisan wanne aiki yakeyi ya banqare hannunsa ta baya da kyau,da wani irin yanayi me cike da zafi yake duban fuskar bulama din wadda ke shimfide a qasa. "Bazan tsaya bata bakina ina tambayarka wa kake bibiya ko me kakeyi ba a nan gurin a irin wannan lokacin......kaman yadda bani da lokacin tsayawa tambayarka WAYR YA SANYAKA......Amma zan aikeka da saqo guda days ka shaidawa wanda ya sanyaka din cewa......ni muhammad ina me shaida masa,yana wasa ne da FARAR WUTA wadda cikin ruwan sanyi take qona dukkan wanda ya raina raina LAUNINTA". Sai ya saki hannuwan bulaman,wanda hakan ya bashi daman qarasa zubewa a qasa cikin wani irin matsanancin radadi da kafadunsa da gadon bayansa gaba suke masa,sannan ya yunqura da wani qaramin hanzarin da qarfin hali ne kawai ya tattara masa ragowar kuzarin,da wata irin sassarfa yake jan qafafunsa yana bacewa daga gurin. Taku uku kawai yayi ya koma zuwa bakin qarfen data sameshi a gurin,ya kuma juya mata baya yana kafe gwiwar hannunsa jikin qarfen ya koma salon durqushen da yayi dazu yana ci gaba da duban tsirran da sukaci gaba da kadawa da sauri sosai saboda qaruwar iskar data ci gaba da kadawa gami da damshin ruwa daya fara sauka yaf yaf mara qarfi. Idanu ta zubawa bayansa tana sake jin wani tsoro yana sake shigarta na wanzuwar shuru a gurin,bata ganin kowa sai shi da ita,don omar ma tun sanda yaga yanayin reaction din haisam ya matsa yana kutsawa zuwa kewayen gidan ko zai samu wani evidence motsi ko wani dake tare da bulama din. Runtse idanunta tayi da qarfi daga duban faffadan bayansa da yabar mata saboda sririyar walqiyar data haska sararin samaniya,ta kuma nuna yawan hadarin da take dauke dashi. Tsoro me qarfi dake cakude da bacin rai taji yana shigarta. Nadamar rashin amsar tayin da yayi mata tun farko na tafiya taji yana ratsata. Me yasa bata tafi ba sanda taga wani abu me nauyi cikin qwayar idanunsa?,me yasa bata tafi ba a sanda yayi mata kallo na kai tsaye......kallon cikin qwayar idanunta.....bayan taso wani kallo ne da bai taba yi mata irinsa ba. To amma duk haka ita din,GIMBIYA AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD.....har rashin darajar da zai gwada mata yakai ya juya mata baya yana ci gaba da al'amuransa kamar baisan Allah yayi tsironta a gurin ba?. Yana qarqashin cin alfarma ta mahaifinta?,yana rayuwa cikin iko na mahaifinta?. Wayeshi?,banda ordinary mutum kamar kowa?......banda ordinary hadimi kaman sauran hadiman cikin gidan,wanda suke rayuwa cikin tattalin farincikinta.....kare dokokinta da iyakokinta,yau gata a tsaye a yashe......tamkar ba itace wannan gimbiyar da ganinta yake zama GAGARUMAR SA'A GA DUK MUTUMIN DA IDANIYARSA TA SAMU NASARAR GANINTA. A cikin jikinsa yakejin tsaiwarta a gurin,saidai bayaso ya waiwaya gareta harta kalli irin nasa fushin. Yana jin tsaiwarta har cikin b'argonsa,bai kuma san abinda ya hanashi tafiya yabar gurin ba,saidai wani sashe na zuciyarsa yana nanata masa MARTABAR SULTANE ce ta jawo haka. A duk sanda zai kwanta yana jin sauti da kuma maimaicin sautin sultane a maganarsu ta qarshe cikin airport. "Dukkan masarauta......da dukkan wanda ke cikin ta na baka amanarsa......idan nace kowa da komai ciki harda AKHNAN. marainiya ce data taso batasan dadin mahaifiya ba,duk da ta shekara hudu da ita,amma kona shekara hudunma batasan dadin safeena ba,saboda ciwon hauka da safeena tayi daga randa akhnan tayi kwana arba'in a duniya.......safeena batayin cikakken wata uku da lafiya,saidai kuma a wata ukun duk sanda take a daidaita bata bari kowa yayi hidima ga biftu,kamar tasan tafiya zatayi ta barta,kamar tasan tafiyar bame nisa bace. Yana iya hangen qwayar idanun sultane a sanda yake masa maganar,yana iya ganin raunin dake tattare da sultane din ta cikin qwayar idanun nasa,raunin dake gaya masa wannan feelings din bame sauqi bane......me tsananin nauyi ne,nauyin daya gaza ture yaringar daga zuciyarsa,duk da girma da adadin kura kurenta a tare dashi,daci gaba da bijirewa zuwa ga umarninsa. Damqe qarfen yayi da kyau yana jin yadda ruwan ke qara yawa. Yanason ya waiwaya ya tambayeta me ya hanata tafiya?,amma ya tabbatar idan yayi hakan zai sake gayyatowa kansa fushin da yake yaqi dashi. Kalamanta sun soki zuciyarsa sosai,sun masa wani irin rami da ya tabbatar zaibar gurbi da miki cikin zuciyarsa. Iya adadin jurar tsaiwar da zaiyi ya kaita,sai ya zame hannunsa daga qarfen a hankali ya fara takawa. Taku hudu kawai yayi,idanunsa a gabanshi ba tare da ya ko waiwayeta ba,ya motsa labbansa da muryarsa da tayi wani irin zurfi yace. "Ba iya mulki iko da ginin doguwar katanga bane ke lullube da masarauta ba.......akwai tarin abubuwan dake buqatar zurfafa tunani da kyau.....ba dukkan murmushi bane ke nuna kulawa......ba kowacce farar fuska bace me dauke da kyakkyawar zuciya fara qal.....ka fara kula da kanka kafin kowa ya kawo maka daukin kula da kai" Ya qarashe maganan yana tafiya kai tsaye ga steps din da zasu sadashi da balcony dinsa zuwa babban sashensa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Tafiyarsa cikin izza duk da ruwan dake jiqa rigar jikinsa......da bata tabbacin barinta a gurin a yashe yafi qona mata rai da tsaye mata cikin idanuwanta da tunaninta. Maganganunsa basu kasance abun maida hankalinta ba.......face aikinsa da ya sanya taji ya sake zama LAMBA DAYA cikin manyan halittun data tsana a duniya. Ko a yanzun da birra ke taimaka mata tana rage kayan jikinta,shehnaz dake daga kwance tana qarewa fuskarta ne kawai kallo. Wani irin kwantaccen fushi ne kawai ke yawo saman fuskartata,fushin dake qara jefa shehnaz a duniyar mamaki. Me yasa komai na sheikh haisam take zafafarsa fiye da na kowa?.....me yasa ta gaza maida hankali ga aurenta dake matsowa?,take sanyawa ranta damuwa akan kowanne aiki ko hukunci da zai zartas?. Ko a yanzun da duniya ta karade da sautin saukar mamakon ruwan sama me nauyin gaske,akhnan din na gaban glass door saman sofa,sanye da wata sweeter me sulbi oversized,peach color ce data dorata saman sleeping gown din da birra ta dauko mata. Wani qawataccen blanket birra ta dora mata saman kafadunta kafin ta musu sallama ta fice bayan ta ajewa akhnan din hular sanyi me laushin gaske a gefanta. Komai na rayuwarta yi mata akeyi idan ka dauke wanka da sallah,har yanzu shehnaz tana mamakin yadda bata iya yin komai wa kanta ba. A yadda ta zauna ta wani cure guri daya,wani zama tayi me shigen tsugunno cikin kujerar wanda yawancin lokuta shi takeyi idan har ranta yana a bace. Dukka idanunta suna kallon glass dinne da yadda ruwan kebi ta jikinsa yana sauka qasa. Gajiya da kallonta shehnaz tayi,ta yunqura ta sauka daga saman lallausan gadon nasu,ta tako a hankali ta dawo gabanta tana zama saman wata qaramar ottoman. "Tunanin meye haka biftu?" Shehnaz ta tambayeta a tausashe. Kaman ba zata kalli shehnaz din ba,sai kuma ta cira kanta a hankali tana maido dubanta ga shehnaz din,kafin ta sauke dauke idonta. Ta motsa labbanta a nutse. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE PAGE 42* Batasan ya akayi ta samu idanunta da zame kansu da kuma qwace dubansu daga cikin nasa ba bayan ba abinda ta tsara yi kenan ba.......tana jin idan ta bari ya gayamata ko ya maida mata magana ko qwaya daya ce yayi jayayya da girmanta,don haka cikin rashin yarda da izzarta takai qasa ta sake motsa labbanta fushinta na bayyana sosai. "Me ka dauki kanka?......a tunaninka kai din waye?" Wani miskilin murmushi dake cakude da izza ya saki,wanda ya kusan tafiya da numfashinta na wucin gadi,cikin nuna halin ko in kula yana kuma sake raba hankalinsa da yadda yakejin hucin giftasu daga hagu zuwa dama ya maida mata amsa. "Muhammad haisam wani ne.....wanda ya zame miki tilas ki dakata da qidddige iya adadin ikonsa......don zaki gaza a sanda hasashenki bazai taba iya cafko adadin qarfin ikonsa ba". A karon farko iya tsaho shekarun da tayi a duniya da aka taba challenge nata......da ta taba fadin magana aka maida mata......da aka tsaya a gabanta ana dubanta da duba na kai tsaye......irin duban da mammina ko sultane kadai keda iko da lasisin yi mata shi. Koda ya samu daman tsaiwa a inda ta tsaya.....koda ya samu daman maida mata magana ba zata bari ta kwana da ciwon rai ba. "Idan kana jin dadin tozarta matan da kasan sunfi qarfin matakinka a rayuwa?,daga kaina ba zaka qara kusantar aikata hakan ba" A karo na biyu wani qasaitaccen murmushi ya subuce masa,yayi qas da kansa yana hangen tazarar inuwar boyayyen mutum daga bayanta wanda yake da tabbacin batasan da tsaiwarsa ba,sai ya daga kansa a nutse yana mata nuni da hanya cikin kamala. "Idan kin gama fadin duk abinda yake ranki kina iya tafiya" Idanunta ta qanqance sosai,reshe yana neman juyewa da mujiya. Gurbi da muhallin fushi takeson gani saman fuskarsa akan maganganun data gaya masa.......amma sai yake maye gurbin haka da wani murmushi da iya tsahon zamanta cikin da'irar sarauta,gidan mulki da iko bata taba ganin murmushin dake cakude da zallar izza irinsa ba. Yabar mata ciwon fadin maganar a ranta?,kuma yana umartarta da tafiya daga muhallin daya kasance mallakin mahaifinta?......saman QASAR data kasance cikakken ikonta.. "Ki tafi nace" Yayi maganar wannan karon yanayin fuskarsa yana juyewa da wani matsanancin tsare gida yana kuma ajiye mata wani nannauyan kallo da taji ya mata wani mahaukacin kwarjini. Wannan dabi'artata ta taurin kai da kafiya ita ta motsa.....izzarta ta taso ta lullubeta,ita dake bada umarni yau ita wani yake bawa umarni?......ita dake da iko na fada aji ita ake fadawa abinda zatayi?. Sake tsareta yayi shima da kakkaifan kallonsa,yana sake irga motsi da takun bulama. Kaucewarta a gurin yafi buqata a sannan,don yanason nunawa bulama qarshen rashin qwarewa cikin aikinsa. Saidai kuma baya qaunar wanzuwarta a gurin,saboda ba gaban idanunta yake buqatar yin kowanne motsi nasa ba.....amma yana karantar kafiyarta da taurin kanta na shirin zame masa cikas,kaman yadda ya karanci bulama yana daf da kubcewa tsarinsa,don haka dole yayi wani irin taku da bai kai biyar ba,ya miqa hannu tsakanin shukokin dake daura dasu,ya damqi wuyan bulama cikin wani irin zafin nama,sannan ya fincikoshi daga duhu zuwa cikin haske,ya kuma watsar dashi a gurin. Wani irin matsanancin bugawa kawai zuciyarta takeyi,cike da wani irin matsanancin tsoro da bata taba jin irinsa ba. Ta fidda manyan blue eyes dinta tana duban bulama din da haisam ya watsar a gurin,saidai yana riqe da hannayensa da ya banqaresu ta baya,wanda azabar irin wannan riqon da haisam yayi masa ya sanyashi fidda wani irin nishi a wahalce. Iyakar saninta da hadiman gidan gaba daya batasan bulama ba. Batasan wayeshi ba,batasan kuma wannan fuskar ba......me ya kawoshi nan?,cikin duhun da babu komai cikinsa sai hasken walqiya?,cikin duhun bishiyoyin da ba wanda zai iya labewa ciki sai wanda ke dauke da alama da tambari na rashin gaskiya?. Ba ita ba......hatta da maleek dake kallon komai daga nesa.......amma zama da haisam da dadewarsu tare ya sanya yake fahimtar lokutan da haisam din yake buqatar wanzuwa a guri shi kadai,don haka sai ya tsaya daga ness yana kallon komai. Da fari hankalinsa da nazarinsa gaba daya yana kan akhnan din. Ya cika da wani irin tarin mamakin yadda haisam yake iya hadiye maganganunta,ya sani,yana da wani irin kaifin hangen nesa da qoqarin hadiye bacin rai,saidai kuma sam sam baya daukan raini ko qanqani. Yanayin tsiwarta ya daure masa kai sosai,dukkan wannan izzar a yanzun da take magana da haisam din sai yaga ta kwaranye ta barta da iya tsiwar. Akwai wani abu da yake hanga daga can cikin dabi'unta da yake ganin zuwansa daidai da wani salon ra'ayi na haisam din. JARUMTA......irin salon jarumtar nan ta babu gudu babu ja da baya......wani irin qarfin hali da TSAIWA saman ra'ayi,sai ya saki wani sassanyan murmushi,wanda suke murmushin nasa keda wuya ya hangi yadda haisam din ya motsa cikin wani irin zafin nama ya kuma finciko bulama din. Abun ya matuqar zuwa masa a bazata da kuma bashi mamaki. Baiga wani alamun wanzuwar dan adam a gurin ba......ta yaya haisam din ya fahimci hakan?,bayan kuma da kwanyarsa ta tuna masa SHEIKH HAISAM din sai mamakinsa ya dinga raguwa,ya fara tunanin me mutumin yakeyi a tsakanin duhuwar gurin?. Kamar baisan waye bulaman ba,kamar kuma baisan wanne aiki yakeyi ya banqare hannunsa ta baya da kyau,da wani irin yanayi me cike da zafi yake duban fuskar bulama din wadda ke shimfide a qasa. "Bazan tsaya bata bakina ina tambayarka wa kake bibiya ko me kakeyi ba a nan gurin a irin wannan lokacin......kaman yadda bani da lokacin tsayawa tambayarka WAYR YA SANYAKA......Amma zan aikeka da saqo guda days ka shaidawa wanda ya sanyaka din cewa......ni muhammad ina me shaida masa,yana wasa ne da FARAR WUTA wadda cikin ruwan sanyi take qona dukkan wanda ya raina raina LAUNINTA". Sai ya saki hannuwan bulaman,wanda hakan ya bashi daman qarasa zubewa a qasa cikin wani irin matsanancin radadi da kafadunsa da gadon bayansa gaba suke masa,sannan ya yunqura da wani qaramin hanzarin da qarfin hali ne kawai ya tattara masa ragowar kuzarin,da wata irin sassarfa yake jan qafafunsa yana bacewa daga gurin. Taku uku kawai yayi ya koma zuwa bakin qarfen data sameshi a gurin,ya kuma juya mata baya yana kafe gwiwar hannunsa jikin qarfen ya koma salon durqushen da yayi dazu yana ci gaba da duban tsirran da sukaci gaba da kadawa da sauri sosai saboda qaruwar iskar data ci gaba da kadawa gami da damshin ruwa daya fara sauka yaf yaf mara qarfi. Idanu ta zubawa bayansa tana sake jin wani tsoro yana sake shigarta na wanzuwar shuru a gurin,bata ganin kowa sai shi da ita,don omar ma tun sanda yaga yanayin reaction din haisam ya matsa yana kutsawa zuwa kewayen gidan ko zai samu wani evidence motsi ko wani dake tare da bulama din. Runtse idanunta tayi da qarfi daga duban faffadan bayansa da yabar mata saboda sririyar walqiyar data haska sararin samaniya,ta kuma nuna yawan hadarin da take dauke dashi. Tsoro me qarfi dake cakude da bacin rai taji yana shigarta. Nadamar rashin amsar tayin da yayi mata tun farko na tafiya taji yana ratsata. Me yasa bata tafi ba sanda taga wani abu me nauyi cikin qwayar idanunsa?,me yasa bata tafi ba a sanda yayi mata kallo na kai tsaye......kallon cikin qwayar idanunta.....bayan taso wani kallo ne da bai taba yi mata irinsa ba. To amma duk haka ita din,GIMBIYA AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD.....har rashin darajar da zai gwada mata yakai ya juya mata baya yana ci gaba da al'amuransa kamar baisan Allah yayi tsironta a gurin ba?. Yana qarqashin cin alfarma ta mahaifinta?,yana rayuwa cikin iko na mahaifinta?. Wayeshi?,banda ordinary mutum kamar kowa?......banda ordinary hadimi kaman sauran hadiman cikin gidan,wanda suke rayuwa cikin tattalin farincikinta.....kare dokokinta da iyakokinta,yau gata a tsaye a yashe......tamkar ba itace wannan gimbiyar da ganinta yake zama GAGARUMAR SA'A GA DUK MUTUMIN DA IDANIYARSA TA SAMU NASARAR GANINTA. A cikin jikinsa yakejin tsaiwarta a gurin,saidai bayaso ya waiwaya gareta harta kalli irin nasa fushin. Yana jin tsaiwarta har cikin b'argonsa,bai kuma san abinda ya hanashi tafiya yabar gurin ba,saidai wani sashe na zuciyarsa yana nanata masa MARTABAR SULTANE ce ta jawo haka. A duk sanda zai kwanta yana jin sauti da kuma maimaicin sautin sultane a maganarsu ta qarshe cikin airport. "Dukkan masarauta......da dukkan wanda ke cikin ta na baka amanarsa......idan nace kowa da komai ciki harda AKHNAN. marainiya ce data taso batasan dadin mahaifiya ba,duk da ta shekara hudu da ita,amma kona shekara hudunma batasan dadin safeena ba,saboda ciwon hauka da safeena tayi daga randa akhnan tayi kwana arba'in a duniya.......safeena batayin cikakken wata uku da lafiya,saidai kuma a wata ukun duk sanda take a daidaita bata bari kowa yayi hidima ga biftu,kamar tasan tafiya zatayi ta barta,kamar tasan tafiyar bame nisa bace. Yana iya hangen qwayar idanun sultane a sanda yake masa maganar,yana iya ganin raunin dake tattare da sultane din ta cikin qwayar idanun nasa,raunin dake gaya masa wannan feelings din bame sauqi bane......me tsananin nauyi ne,nauyin daya gaza ture yaringar daga zuciyarsa,duk da girma da adadin kura kurenta a tare dashi,daci gaba da bijirewa zuwa ga umarninsa. Damqe qarfen yayi da kyau yana jin yadda ruwan ke qara yawa. Yanason ya waiwaya ya tambayeta me ya hanata tafiya?,amma ya tabbatar idan yayi hakan zai sake gayyatowa kansa fushin da yake yaqi dashi. Kalamanta sun soki zuciyarsa sosai,sun masa wani irin rami da ya tabbatar zaibar gurbi da miki cikin zuciyarsa. Iya adadin jurar tsaiwar da zaiyi ya kaita,sai ya zame hannunsa daga qarfen a hankali ya fara takawa. Taku hudu kawai yayi,idanunsa a gabanshi ba tare da ya ko waiwayeta ba,ya motsa labbansa da muryarsa da tayi wani irin zurfi yace. "Ba iya mulki iko da ginin doguwar katanga bane ke lullube da masarauta ba.......akwai tarin abubuwan dake buqatar zurfafa tunani da kyau.....ba dukkan murmushi bane ke nuna kulawa......ba kowacce farar fuska bace me dauke da kyakkyawar zuciya fara qal.....ka fara kula da kanka kafin kowa ya kawo maka daukin kula da kai" Ya qarashe maganan yana tafiya kai tsaye ga steps din da zasu sadashi da balcony dinsa zuwa babban sashensa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Tafiyarsa cikin izza duk da ruwan dake jiqa rigar jikinsa......da bata tabbacin barinta a gurin a yashe yafi qona mata rai da tsaye mata cikin idanuwanta da tunaninta. Maganganunsa basu kasance abun maida hankalinta ba.......face aikinsa da ya sanya taji ya sake zama LAMBA DAYA cikin manyan halittun data tsana a duniya. Ko a yanzun da birra ke taimaka mata tana rage kayan jikinta,shehnaz dake daga kwance tana qarewa fuskarta ne kawai kallo. Wani irin kwantaccen fushi ne kawai ke yawo saman fuskartata,fushin dake qara jefa shehnaz a duniyar mamaki. Me yasa komai na sheikh haisam take zafafarsa fiye da na kowa?.....me yasa ta gaza maida hankali ga aurenta dake matsowa?,take sanyawa ranta damuwa akan kowanne aiki ko hukunci da zai zartas?. Ko a yanzun da duniya ta karade da sautin saukar mamakon ruwan sama me nauyin gaske,akhnan din na gaban glass door saman sofa,sanye da wata sweeter me sulbi oversized,peach color ce data dorata saman sleeping gown din da birra ta dauko mata. Wani qawataccen blanket birra ta dora mata saman kafadunta kafin ta musu sallama ta fice bayan ta ajewa akhnan din hular sanyi me laushin gaske a gefanta. Komai na rayuwarta yi mata akeyi idan ka dauke wanka da sallah,har yanzu shehnaz tana mamakin yadda bata iya yin komai wa kanta ba. A yadda ta zauna ta wani cure guri daya,wani zama tayi me shigen tsugunno cikin kujerar wanda yawancin lokuta shi takeyi idan har ranta yana a bace. Dukka idanunta suna kallon glass dinne da yadda ruwan kebi ta jikinsa yana sauka qasa. Gajiya da kallonta shehnaz tayi,ta yunqura ta sauka daga saman lallausan gadon nasu,ta tako a hankali ta dawo gabanta tana zama saman wata qaramar ottoman. "Tunanin meye haka biftu?" Shehnaz ta tambayeta a tausashe. Kaman ba zata kalli shehnaz din ba,sai kuma ta cira kanta a hankali tana maido dubanta ga shehnaz din,kafin ta sauke dauke idonta. Ta motsa labbanta a nutse. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 43* "Sultane yayi sadakar mutuncina irin wanda bai taba yi ba tunda ya haifeni........inda nasan haka zai sadaka da martabata har ta bawa wani bagidajen malami daman takata ko zama a kanta......tabbas dana yarda na auri duk wanda sultane yake da ra'ayi.......KIMATA da DARAJATA shehnaz......ba wani abu da yayi daidai da ita" Ta furta tana jinjina kai,abinda ke tabbatarwa da shehnaz wannan EGO din nata baya tabuwa. "Biftu......a ganina yanzu lokacine da zaki maida hankali akan aurenki ba wadannan tunanikan bafa" "Aure?" Shehnaz din ta waiwayo tana jifan shehnaz da tambayar. Kai shehnaz ta gyada tana dubanta itama kai tsaye. "Eh aure......nan da kwanaki bakwai zuwa goma fa....." "Hmmmm" Akhnan din ta fadi d wani abu me nauyi da taji yana sauka cikin qirjinta,sannan ta maida dubanta ga qofar,wasu abubuwa suns yawo gami da kutsa kai cikin tunanikanta. "Biftu.......shin bake kika zabi almaz ba?.....auren almaz zakiyi fa?,zabinki" Shehnaz ta fada tana dora hannunta saman cinyar akhnan din. Akwai alamun shakka da kokwanto cikin muryar shehnaz,abinda ta tabbatar yana cikin sharadinsu da mammina,don haka ta sake juyowa tana duban shehnaz din "Don ni na zabi almaz......ba hakan yana nufin ra'ayina zai sauya ba......ba abinda zabin ya zamemim face zallar qasqanci.....kamarni zaya karbi sadakina da wasu tsirarun sulalla?" Tayi maganan tana nuna kanta da yatsarta,da alamun bacin ranta ya sake motsuwa. "Kuka zaki masa biftu?" Shehnaz ta furta a hankali bayan ta gama qarewa qwayar idanun akhnan kallo wadda ta hada ruwan hawaye daya sanya qwayar idanun nata qara qyalli. "Jamais de la vie(Allah ya sawwaqe)" Ta fadi tana jifan shehnaz da harara kamar wadda ta yiwa fatan mutuwa. Yadda tayin ya sanya shehnaz sakin wani qaramin murmushi. Batasan me yasa ba,batasan kuma me ya faru ba.....izzarta bata barinta nuna jin zafin abubuwa,ba'a mata ma abinda zataji zafin ballantana ta nuna,amma yanzun.....tashi daya.....lokaci daya gaba daya sheikh haisam din ya birkita tunaninta,ya dagula lissafinta,ya sanyata tanajin zafi dama haushin komai.......ME YASA?. Tambayar da shehnaz ta yiwa kanta kenan sanda akhnan take tattara ya nata ya nata. Ta tabbatar daki zata canza,wannan din kuma salonta ne,dabi'arta ne idan suka bata mata rai ita da aisa,ko sukayi mata zancan da bata so. Sai batace mata komai ba,bata kuma hanata fitan ba,don tasan zai wahala ta iya kwana ita daya yadda ake tsula ruwannan,duk kuwa da cewa wani irin kurman gini ne da bakajin qara ko sautin saukan ruwan,saidai kuma baya hana walqiya ratsowa har inda kake,mafi girman abinda akhnan din tafi tsoro kenan. "Kiyi qoqari ki tashi da wuri,don gobe ne naji nanay tana maganan za'a fara gyaran jiki" Ta gayawa akhnan din cikin daga murya kadan tana boye dariyarta can qasan ranta. Ita abun su Inda ace tana da sauran energy a tattare da ita,a yau din zata tsaya ne suyi abinda ta jima bata yishi ba,tabbas da sai an shiga tsakaninsu da shehnaz,to amma ba wannan ba......kowacce gaba ta jikinta ba abinda take buqata sai KADAICI da KEBEWA. *HAISAM* A tsaye kawai maleek din yake rungume da hannayensa daya riqe lallausan towel a tsakiyarsu yana kallon yadda haisam ke zare jiqaqqun kayan jikinsa yana zubesu saman sofa bed. Dukkan wani motsi na haisam din maleek yana biye dashi,har zuwa sanda ya rage fara qal din vest din jikinsa,ya juya a nutse yana laluben towel sai maleek ya daga masa na hannunsa yana duban qwayar idanunsa da bai kalli kowa dake tsaye carko carko ba tun a parlor. Fararen manyan idanunsa da suka sauya launi kadan ya daga ya kalli maleek din,sannan ya miqa hannu ya karbi towel din,sai maleek ya sakar masa ba tare da yace masa komai na,shima ya karba yana juyawa a nutse ya nufi toilet. Ajiyar zuciya me nauyin gaske maleek ya saki,ya jinjina kai a nutse ya tsugunna ya kwashe kayan haisam din. Yaga abinda yakeson gani din,wani irin fushi ne kwance cikin idanun haisam,irin fushin da akan samu jikin jinin SARAUTA saboda wata dabi'a ta rashin son raini dake tattare da wannan jinin wanda irinsa ne a jikinsa shi da haisam. Wannan ya sanya sau tari yafi kowa saurin fahimtar haisam.....saboda wasu irin dabi'u da jini kusan irin daya ke zagayawa a jikinsu. Abinda yake gani a idanun haisam a yanzun me zurfi da girma ne,irin abinda bai taba gani ba a idonsa akan kowa. Ya tabbatar dukka shurun da yayi da qoqarin kaucewa hada ido da kowa yana yine cikin yunqurin controlling kansa fushinsa da kuma bacin ransa. Yayi imanin inda ba tasiri na ilimin zamantakewa da addini a tattare dashi......akhnan din zata gane girman kuskuren data tafka Kai tsaye. Yana YAKANA yana da DAUKE KAI......amma a duk sanda qura takai bango yana da wahalar sarrafuwa yana kuma da wuyar sha'ani. A mganganunta yasan ta tabo abu mafi girman da yafi tsanar a taba masa ADDININSA,dole yasan fushinsa yana iya fin haka ma. Yana kammale masa kayan ya taka a nutse yana ficewa a dakin don ya bashi daman shiryawa da daukan adadin lokutan da yaga sunyi masa. Bai jima ba sosai ya fito ya fara shiryawa,yana shiryawan yana ambaton sunan Allah don neman agaji da samun sassaucin dacin da yakeji tun daga harshensa zuwa cikin maqogoronsa. Yanata qoqarin manta maganganunta,amma koda ya cillasu baya saisun dawo masa cikin kansa. "Subhanallah" Ya fadi a hankali lokacin daya kammala fesa wannan mayen turaren nasa ya ajiye bottle din saman madubi. Tafin hannunsa ya sanya ya shafa qirjinsa har sau uku yana furta addu'ar sassauta fushi da bacin rai. Baisan me yake samunsa ba a kwanakin nan.....baisan me yasa a kanta fushinsa yake yawa ba.....baisan me yasa kome tayi yake bata ransa fiye da yadda ya kamata yaji ba. Yayi iyakacin bakin qoqarinsa na kaucewa kowanne shirgi nata,don ba dominta ya shigo AGADEZ ba,ba zamanta yakeyi ba.....bata kuma cikin lissafin mutanen da yake hangen bincikensa zai iya wucewa ta kansu,amma kuma baisan me ya sanya lamuranta ke sake shiga cikin rayuwarsa ba. Duk yadda yakai ga yakicewa da dojewa amma sultane yana sake jawoshi da sakashi cikin al'amuranta......banda girmamawa ga sultane sam baiga hadinsa da karbar sadakinta da kuma zamowa waliyyinta har ya daura mata aure ba. Komawa yayi ya zauna a hankali gefan sofa bed din yana sake maimaita addu'ar. A hankali a hankali yaji yanayinsa yana daidaituwa,fushin kuma yana raguwa,sai ya miqe a hankali ya soma takawa bayan ya sanya flip flops dinsa masu tashin gaske,don kawai fitowar ta zama dole saboda maleek da omar da yasan ba gidan zasu kwana ba. "Nifa na kasa jurewa......batasan gonar da take shiga bane?......inda a Jimma ne tana zaton shekara daya ma ta isheta ta samu daman tsaiwa kawai a gabansa......iya tsaiwa kawai obbo maleek,bare harta samu daman fadin maganganu masu zafi?" Abdii dake balbalin fada ya fadi yana nuna yatsarsa ga maleek dake zaune hankali kwance yana shan coffee dinsa,da alama kuma ya tattara dukka hankalinsa akan abdii din daketa zirya yana fada. Murmushi omar ya saki yana ajiye remote din hannunsa daya dauka don kashe Ac din parlor din "Ina hakaitota ni kaina cikin masarautar jimma........rashin sani yafi dare duhu,inda cikin jimma ta fadi wadannan maganganun data zama nama". "Da ba zata sake rashin kunya a duniya ba.....da tasan ba'a tabawa oromian prinsii dinsu.....amma nan gaba sai......". Cikin tarin nutsuwarnan tashi ya saki gyaran murya sannna ya zagayo yana zaban kujerar zama. Tuni abdii ya kama kanshi,kai kace ba shine yaketa surfa bala'in nan ba. A hankali ya zauna saman kujerar a lokaci guda kuma yana aikewa abdii wani kallo daya sanya abdii din diriricewa,lokaci guda kuma ya miqe yahau hadowa haisam coffee ba kuma don ya buqaci hakan ba,sai don nauyin da idanu da kuma kallon da haisam din ya jefeshi dashi ya sanyashi qaramar rudewa. Parlor din ya dauki shuru,cikinsu ba wanda ya sake cewa komai,har zuwa abdii ya kammala hada coffee din ya kawo gaban haisam din yana cewa. "Obbo....." "Zauna nan" Haisam ya fadi kai tsaye cikin salon umarni. Bai musa ba ya zauna din,saidai ya kasa hada idanu da Haisam din kai tsaye. "Morning flight evening flight or night flight......wanne ka zaba don komawa Ethiopia kuma jimma?". Idanu abdii ya zaro yana qoqarin duban haisam da yakai cup din coffee bakinsa a nutse "Obbo......ni bance zan koma gida ba,idan nabar niger obbo tare dakai ne". "Kace mana abdii?" "Lakki(a'ah)" Abdii ya fada yana girgiza kai. "Meye alaqarka da dabbar da ba ita ka shigo farauta ba daji?,koda zata yita bibiyarka a baya?" Ya jefa masa tambayar yana ajiye mug din hannunsa. "Babu obbo" "Ergamni keenya maali?(meye mission dinmu?)" "Obbo......zaqulo mutumin daya kashe ajani,sannan mu kaishi gaban hukumar binciken sirri qasar Ethiopia kuma ta hukuntashi" Kai ya jinjina a nutse yana lumshe idanunsa gami da budesu. "Daga sanda kaji a ranka ka fara sauka daga wannan ra'ayin,to daga ranar ka siyi tikeetii(ticket)na komawa Ethiopia....banzo AGADEZ don susan waye ni ba......na yarda na zama mutum mafi qasqanci a idanun kowa muddin hakan zai zama tsani zuwa ga cikar burinmu......" "Kamar ba komai zaka iya dauka ba kaima daga gurin yarinyar ba.....kamar tana jin kanta tana da Kyau......maza suna layin mutuwar sonta tana wahalar dasu....." "Omari,Dhaabadhaa(stop it)" Yatsunsa ya saka yayi zipping bakinsa alamun yayi shuru,sai ya kalli maleek yana daukan nasa mug din ya zauna gaba kadan dasu yana fadin. "buna keessan xumurree,nuti ni deemna(idan ka gama shan coffee din sai mu tafi)". (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Kamar kowacce magana ta qare,amma can qasa maleek ya zare mug dinsa daga bakinsa yana duban haisam. "Rayuwarta na kewaye da hatsari haisam.....daidai ne ka kauda kai?" Maleek din bai zaci samun amsa daga gurinsa da wuri ba,amma kafin ya maida cup dinsa bakinsa sai yaji yana fadin. "Ani lubbuu namoota koo fi warra koo baraaruuf qofa dhufe(nazo nan ne kawai don ceton rayuwar jama'ata data iyayena)......haqqin kareta ko daukar nauyinta ba'a wuyana yake ba" Ya qarasa fada yana dire mug din gami da daukar remote ya fara canza tasha. "But she's so strong fa.... Omari ka kula kuwa?" Ya kira sunan omar din yana kanne masa ido daya. "Indeed......" Omar ya fada yana qoqarin qara wani abu,saidai haisam.ya kira sunansa da sound dinnan da dukkaninsu sunsan idan yayi irin wannan kiran me yake nufi. Hannayensa zube a aljihun trouser din jikinsa,still idanunsa kan TV da suke program kai tsaye da sheikh Dr zaakir naikh. *MAMMINA* Kai kawo kawai takeyi tsakanin falukan nata guda uku tana duban agoguna manya guda biyu dake tsaye a kusurwoyin parlor din. Har cikin jikinta tana jin yadda jininta ke tafasa......tana kuma iya jin yadda kaf dokokin haisam din sukayi mata wani irin dabaibaiyi,dabaibayin daya sake tabbatar mata cewa YA SANYA KOWACCE DOKA CE SABODA ITA. iya tuna wannan kawai idan tayi yana sanya wani zare daga tsakiyar cikinta kadawa,wanda bata sani ba,hanji ne.....zuciya ce ko wani abu na daban dake neman sanya mata tsananin tsoro,yake kuma tuna mata da ZEENATU. Zeenatun data kasance haifaffiyar Ethiopia data shafe rayuwa me tsaho a can,zeenatun da ko sunanta mammina batason tunawa ballantana ta tuna WACECE ITA?. Zeenatun da har yau ta zama silar kasa yarda aminci da sakin jiki cikin dukkan rayuwa daqiqa da awannin da zasu shude mata a rayuwa. Idan har ya sanya wadannan dokokin da suka tabata har haka,arashi ne ko kuma YAQINI?. Idan ba yaqini bane KAKKAIFAN ZATO ne?. A irin wannan daren,akwai tarin sirrika da suka kasance nata kebantattun dake gudana gabanin fitowar kowanne haske da zai bayyanar da dakushewar duhun dare,amma a wannan daren komai yana neman tsaiwa cak!. Komai ya kasa gudana yadda ya saba saboda wadannan banzayen dokokin nasa?. Duk da yalwa ta fado mata parlor din da wata irin ba zata amma hakan bai kada hankalinta sosai ba,saboda abinda takeji cikin jini da jikinta,firgici dake neman ratsa naman jikinta yakai ga jinin dake harbawa zuwa zuciyarta tana jin yafi kowanne firgici girma da nauyi. "Kiyimin aikin gafara......bulama ya qaraso.....saidai a yanayin dana ganshi ina me tabbatar miki ba lafiya.......kamar!" "Kika barshi a waje bayan kinsan tulin dokar dake yawo cikin gidan?". Mammina ta fadi tana goye hannayenta a baya gami da sassauta bugun zuciyarta da kuma qoqarin hana halittar TSORO wanzuwa a qirjinta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 44* Ko kammala rufe bakinta mammina batayi ba yalwa ta miqe da hanzari don yiwa bulama iso. Sanye cikin kalar suturar daya daya cikin hadiman sassanta wanda zai wahala ga mara zuzzurfan nazari ya zaci cewa d'a namiji ne cikin yafen da ya lullube ilahirin jikinsa dashi. Hannu yasa ya yaye lullubin,take fuskar bulama data qara wani baqi da maiqo ta bayyana,saiya sulale ya zube a gabanta yana tallafe da hannayensa da yakejinsu kamar ba'a jikinsa ba. Kasa magana mammina tayi saboda yadda qirjinta ke bugawa,tabi hannun nasa da kallo wanda duk motsi guda daya da zaiyi dashi yana jin azabar can tsakar kansa. "Ki yafemin......ki rufan asiri,ina neman sassauci ki janye aikin da kika doramin........bazan iya ci gaba da karbar ragamar aikin nan ba" Ya fada da wani matsanancin tsoro da mamaki da har yau ya kasa barinsa. "Ka bude baki kayimin cikakken bayani......bani da lokacin bata lokaci!" Mammina ta fada cikin tsawar dake cakude da fargaba da tarin tunani iri daban daban. Sosai yayi qasa da kansa,yana jin asarar dukkan wata garabasa,qarin matsayi da alfanu da zai samu baya kammaluwar aikin wuna sulalewa,saidai sulalewar aikin daga hannunsa yafi masa sauqi akan ci gaba da yinsa gami da fuskantar abinda ke tunkaroshi. Abinda ya gani ya kuma hanga tattare dashi......abinda ya gani ya hanga cikin idanunsa wani irin yanayi ne daya sanya tsoro ya tsarga masa yake shirin tsaga zuciyarsa gida biyu. "Duk da tarin qwarewata ta shekara da shekaru........duk da tarin nasarorin dana samu cikin ayyukan dana kwashe shekaru ina miki ba tare da samun matsala ko tangarda koda sau daya ba.......a yau ina me bakin haquri na janye daga wannan aikin......don ya riga ya ganni,ya kuma bani saqo da gargadi me girman gas......." Ya fara kaiwa qarshen maganar yana mata nuni da hannunsa. "Ina fata sunana baiyi kuskuren fitowa daga bakinka ba?!" Ta tambayi bulama cikin wata sabuwar tsawar tana jin wani yamutsi yana haduwa tsakanin qirjinta da kwanyarta ba tare daya damu da bi ta lafiyarsa ko bin ba'asi ba na mugun nadin da hannunsa yasha dake alamta kyakkyawar karaya ce ya samu. "Koda za'a sanya kaina gabas a yanka bazab iya aikata hakan ba......saidai akwai abinda ke nuna yuwuwar yasan wani wanda yayi.kama da wanda ya aikeni zuwa gurinsa". A wannan karon hannun kujera mammina ta samu ta zauna tana jin saman kanta ya mata nauyi kaman an jibga mata wani abu,saidai duk da haka wannan bai iya kawar da izzar da takeji ba. ★Dukkan wani shirin aure da uwa kanyi akan d'iyarta na wajibi da wanda bana wajibi ba mammina din yinsa takeyi. Ga duk wanda ya kalleta a sannan kai tsaye zai fahimci da gaske shirin aurar da d'iyar gata takeyi. Kudi kawai take zubdawa,ta kowanne fannin don ganin komai ya tafi daidai da yadda ake gudanarwa......sannna sama da abinda ya zama anayi a al'ada. Tana maimaitawa a gaban kowa cewa,aure ne na d'iyar da ba'a taba me gatanta ba a fadin qasar agadez dama niger gaba daya,dole komai yasha banbam dana sauran yaran da duniya take ganin su din qurewa ne matuqa gurin gata da girma da martaba da kuma isa. Wani irin gida ta zuba kudi me girma da daukan hankali ta siyawa almaz wanda ta mallaka komai a hannunsa a madadin nasa ne......sa'annan ta jibge kayan alfarma da dukkan nau'in abinda tasan ya kasance mafi soyuwa a zuciyar akhnan cikin gidan da take da yaqinin zasu burge akhnan din zasu kuma iya zama mataki na farko da almaz zai fara samun wani fili koda qarami ne cikin zuciyarta da har za'a cimma gaci a qurarren lokacin da takeso ya zama SANADI na tabbatuwar ragowar mafarkinta daya rage. Komai yana tafiya mata daidai ta fannin shirin biki......saidai ta kowacce kusurwa tana jin wani rashin TSARO a tattare da ita. Ta kowanne bangare tana iya riskar yadda SABBIN DOKOKIN cikin gidan suke sake tabbatuwa a kanta kowacce safiya. Kamar yadda ba wata daqiqa da zatazo ta shude bata tunasar da ita sunan HAISAM ba,da tarin yaqini da fatan ta maida aikin ragamar kula da duk wani motsi nasa hannun qwararre kuma amiñtaccen da bata da irinsa wato TAMIM. Wani irin mamaki ne yake kasheta a kowanne second a duk sa'in data tuna BULAMA ya gaza aiwatar da aikinsa?. A duk tarin shekarun daya kwashe yana hidima a gareta......tarin ayyuka masu hatsari da muhimmanci da yasha aiwatar mata,ba wani yanayi da yayi kama da alamu na rashin NASARA sai yanzu a kansa?......akan malamin da baisan komai ba sai alqalami da tawwada?.....malamin xa take da yaqinin koda cikakken sunansa zai wahala ya iya rubutashi?. "WAYE SHI?" Tambayar da take kwashe darare tana yiwa kanta ita kenan,ba kuma don saboda tana qirqirar tambayar a karan kanta ba.....aah......tana ji kamar ana tunkudo mata tambayar ne daga wani sashe daban na zuciyarta. Cikin kwanaki qalilan ta kammala komai,ta kuma sake jajircewa da raba hankalinta gami da zurfafa nazarinta akan komai. Duk da sadarwa da yawa ta yanke mata cikin gidan.....duk da saqonni da yawa sun dakata da shigo mata,amma ta zama calm tana manage da ragowar hanyoyin da suka rage mata a bude,tare da tabbatarwa kanta zata WARGAZA kowacce sabuwar doka da taci karo da muradinta da kuma cikar burikanta. ★★ Dukka tafukan hannayenta guda biyu ta shafa saman fuskarta bakinta na fidda sautin "Alhamdulillah" Ta sauke hannun nata zuwa qirjinta sannan ta masa ma'ajiya saman cinyarta. Shuru tayi tana fidda numfashi a hankali,tana mamakin yadda nutsuwa ke cika ruhinta da zuciyarta bayan shafe tsahon kwanakin da tayi tana addu'a akan lamarin akhnan. Daga randa nanay ta fita a sassanta bayan sanar mata da kwanakin da suka rage na auren akhnan,daga wannan ranar bata qara kwanciya tayi bacci a rabin daren da a baya take kwanciya tayi bacci ba bayan ta gama ibadunta. Tun asali ita din tana cikin jerin sahun mutanen da ba wani dare dake kufce musu,koda cikin jinya ko lalura take,zata daddafa ta tashi,wannan kuma tayi imani yana daya daga cikin makamai na nasararta a masarautar AGADEZ. Tayi imanin yana daya daga cikin garkuwarta daya hana zaituna ta cimmata.......yana kuma cikin manyan hijbai data tabbatar Allah ne kadai ya sanyashi tsakaninta da mammina. Ta yarda dari bisa dari sallar dare garkuwarta ne.....rigakafinta.....kuma itace qashin bayan daidaituwar dukkan al'amuranta (Kina da matsala?,kina da damuwa?,me zai hana ki gwada lazumtar sallar dare?,zakisha mamaki......kina da dare.....kina da lokacin da ubangiji ke saukowa da kansa yana tambayar ina me buqata na biya masa,ina me tambaya na amsa masa.....me ya hadaki da malaman tsubbu da bokaye?). Numfashi taja sosai cikin cikinta tana saukewa,daidai sanda muryar falaak ta ratso dakin kadan tana turo qofar da sallamar neman izini. "Qaraso" Morsa safiyya ta fada tana tattare abun sallarta a nutse. Da kamewar nan tata ta shigo tana sake jaddada sallamarta,morsa safiyya ta amsa mata rana dan binta da kallo cikin sabuwar shigar falaak din ta yanzu da take sake suturce mata jikinta ko ina da wani yanayi dake tafe da zamani. Hannunta dauke yake da wani babban kwando me daukan hankali,wanda bayyanarsa a gurin kadai ya fadi abinda ke cikinsa wato TURARE. "Momma......armelle tace saqonki ne ya iso daga nigeria". Ta qarasa maganan tana dafe kwandon tare da fatan Allah yasa irin qamshin da takeji ya zamana tana da rabo a ciki. "Ma sha Allah" Morsa ta fada cikin yabawa da gamsuwa tana gyada kai (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Incense by kabo daughter 0803 211 9803" Falaak ta karanta sunan a fili tana qarewa kyakkyawan kwandon da aka shirya da wani irin tsari na burgewa dake nuna zallar daraja girma da martabar wanda saqon zaije gurinsa. "Momma....." Falaak ta fadi a narke tana duban morsa safiyya. Da gaske tana buqatar morsa safiyya tasanmata qamshin nan,tana buqatar turare mai tsaiwa a rai kamar wannan,don tana jin dukka turarukanta suna dakushewa a duk sanda suka gauraya da sassanyan qamshin nan nasa da duk dare yake sanyata rungume pillow da kyau. "Banason magana falaak,ki koma dashi,zamuje ki rakani,ki kaiwa yayarki a matsayin kyautarki ta farko ta aurenta" Morsa safiyya ta fadi tana laluben faffadan jilbab don yau bata buqatar wata shiga me nauyi da zata bayyana sarautarta ko wani abu makamancin hakan. Fuska ta kyabe tana jin morsa safiyya ta bata mata duka tsarikanta. "Mais momma....." "Ki rufemin baki" Morsa safiyya ta buqata da yaren buzaye wanda ba kasafai ta fiya yiwa falaak din magana dashi ba,sai kawai tayi yadda morsa din ta buqata,ta juya ta fita tana jiran morsa din ta kammala shiryawa,saidai ta qudirta a ranta ko ta yaya saita samu turaren nan itama. (Kaman yadda na gaya muku,kowanne turare da zan tallata muku kanku tsaye ku siya ba haufi,zamu dawo ku godemin,tasted and trusted). *AKHNAN* Hankali kwance take zaune cikin private balcony din nata dake bata daman hangen farfajiyar gidan kusan ta kowacce fuska. Da yammacin dake dauke da wani irin lullumi bayan ruwan saman da aka sha jiya,wanda a yau ya sanya garin y wani lumshe da wata irin iska me kyau da dadi data gauraya da yanayin la'asar A yadda take zaunen zaka dauka nutsuwa ce a jikinta......saidai ba wata nutsuwa a tare da ita me yawa illa wannan miskilancin nata da izzar da suka gauraya suka bada launin nutsuwa a tare da ita. Skirt ne a jikinta sai da bai qarasa idon sawunta ba,sai wata cross front shirt data haska fatarta ta kuma dace da slim body dinta dake da wani irin ajiyayyen shape da supplement ko table basu isa su baka irinsa ba. Qaramin baby hijab ta sanya saman kanta wanda ya bayyana alamun tudun tulin gashinta dake daure tsakiyar kan nata. Qafafunta miqe suke saman ottoman,yayin data tattara hankalinta akan wayar hannunta tana danne dannenta. Ba wani digo ko alama na fara'a sam ko walwala a tattare da ita,kamar yadda ba wani abu daya sauya a tare da ita da zai sanyaka ka kirata da amarya,bayan gyaran data kasance ma'abociyarsa ce dama ita din tuntuni. Daga gefanta a qasa saman wani lallausan kilishi dan madaidaici aisa ce shehnaz kaca kaca tsakiyar invitation card,iv din da ko sau daya ta daga ido ta kalleshi ma tana jin bata da lokacin yin hakan. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 45* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ Iska aisa ta furzar tana ajiye card din hannun nata gami da dora idonta a kan akhnan din. "Biftu" Ta kirata a dan tausashe tana jin wani iri a ranta. "Ehnnnn" Kawai tace da aisa din ba tare data dago kanta ba. "Ki duba yadda aka tsara events din mana". Kaman ba zatayi motsi kowanne iri ba kafin ta ajiye wayar hannun nata,sannan ta aza idonta akan aisa. "Aisa......" "Na'am" Ta amsa mata tana dubanta hadi da karantar kafiya da tabbacin ko me zai fito daga bakinta haka yake ba sauyawa. "Bazanyi komai ba......ba abinda zanyi a auren nan,ku daina bata lokacinku bakinku da kudinku,za'a daura aure kaman yadda sultane yakeso nayi aure,amma ba wani abu da zai sanya na wahalar da jikina lokacina da kuma tunani na,daurin auren kawai nake jira na koma niamy kan harkokina". Ta sauke maganar a hankali sannan ta dauki wayarta taci gaba da danne dannenta. Sosai aisa ta zuba mata ido tana tuna badaqalar da taje ta tarar me tarin yawa a sahel couture,wata irin badaqala data tabbatar a yanzu idan akhnan ta jita sai hankalinta yayi mugun tashi,ba zata ma iya gaya mata ba,don zata hada mata tashin hankali ne bayan wanda take ciki. Ta cika da mamakin yadda cikin watanni kadan komai ya dagule haka ba,tana tsaka da bin diddigin al'amarin,saidai ta kasa gano bakin zaren matsalar. Komai ya canza a kamfanin,mutane da dama babu su,an sallamesu an dauki wasu,wasu bayanan duka sun bace suma babu su. Babban abinda yafi daga mata hankali shine,girman qarfin ikon da aka bawa wasu a cikin kamfanin,na sallama da daukar wanda suke ganin ya dace,gogayya suke da matsayinta dana shehnaz,suna qasa da nasu matsayinne kawai a yanzu a SUNA,saidai a power sun fisu. Ba komai ta bari shehnaz ta sani ba,don ta fita juriyar abu da cinyeshi,da kuma nutsuwa wajen bibiyar al'amura,shi yasa ko tafiyarta ta wancan satin ta tafi ita daya,yace shehnaz din ta zauna ta kula da akhnan,don bai kyautu su barta haka ita kadai ba. "Me yasa kike abu kaman bake kika zabi mijin aurenki ba?" Aisa ta jefa mata tambayar da ta sanya akhnan daga manyan idanunta ta zubesu kan aisa. Tambaya ce data sake tuna mata da yarjejeniyarta da mammina.......saidai tambayar da aisa din ta mata sai takejin kamar ta bude baki ta gayawa aisa EH ba ita ta zabeshi ba.......amma sam ba zata taba kwarewa mammina baya ba a sanda ta sadaukar da kanta don ganin nata farincikin. "Ni na zabeshi.......amma bawai don hakan yana nufin ina sonshi ko ina son aure ba......na zabeshi ne don na amintar da sultane daga fushi dani" Ta qarasa maganan tana sauke qafafunta qasa,sannan ta miqe tsam tana takawa a nutse zuwa gaban balcony din. "Zanyi abinda ban taba yi ba.....roqo,na roqeku kada ku sake tayarmin da zancan yin wani abu na aure" Ta qarashe maganar sanda ta tsaya gaban qarfen tana basu baya tana kuma fuskantar farfajiyar gidan da ba yawaitar zirga zirga da motsin jama'a sosai,hakan kuma tasan baya rasa nasaba da kawowar yammaci wanda zirga zirga takan ragu saboda kusantowar dokar hana yawon dare cikin masarautar. Daidai lokacin da yake takowa shida maleek,sanye da kuwaiti slim fit thobe me sulbi saqar qasar kuwait. Dogon hannu ne da ita me wani irin zagayayyen abu a hannun da kuma wuyan jallabiyyar,royal blue data wani irin haskashi da wani irin yanayi daya fidda kyansa da kuma kyan fatarsa dake da wani irin yanayi lum lum. Sak balaren da ya tashi cikin yare da al'adun qasar larabawa,don hatta da amama(rawanin da larabawa kan nada saman kansu me kama da mayafi)sak irin nadin da wayayyun matasan larabawa keyi ne. Gefansa maleek ne,hira suke abinsu,da wannan nutsuwar da izzar sarauta a jikin kowannensu da bazai sanya kaji abinda suke fadi ba ba,magana ce a nutse duk da tana basu nishadi saboda qawataccen murmushin da yake fita saman fuskarsu gaba daya. Baisan me ya sanya maleek yace zaya qara kwanakin da yayi niyyar yi masa ba,saidai koma meye hakan ya masa dadi,yana kuma kyautata zaton maleek din ya karanci yanayinsa a kwanakin ba yadda ya sanshi bane,kamar akwai wani kewa da emptiness a tare dashi,duk kuwa da cewa yana kewaye yana kuma rayuwa cikin mutane. Daddadar iskar dake kadawa taja sosai tana fitar da ita daga qirjinta a hankali,yanayin dake qara rage mata damuwar da takejin ta mata qawanya a duk sanda zuciyarta ta tuna nata kwanaki biyar suka rage mata a daura igiyarta a hannun wani d'a namiji da sunan mijinta,duk da tana samun sassauci idan ta tuna ba abinda hakan zai sauya ko ya sanya cikin rayuwarta,iya yadda bai matsa da neman sake ganinta ko.wata magana ko qulla wani dangantaka na sabo tsakaninsu ba kawai yana rage mata zullumi fargaba da quncin da takeji. Idonta ta zare daga kan flower da take kalla ta saukesu a hankali zuwa farfajiyar. Kai tsaye idonta ya sauka a kansa,yana kuma damqe da hannun maleek da yake gaya masa an samo wani littafi da haisam din ke nema shekara guda kenan,babu shi a Egypt babu shi a duk inda yake zaton za'a samu littafin wanda kudinsa ya kama million daya da rabi. "Surprise" Maleek ya furta a hankali yana jin dadin yadda alamun farinciki suka bayyana akan fuskar haisam din. Tattausan murmushin nan nasa ya saki,yana jin wani dadi a zuciyarsa. Allah ya jarabceshi da qaunar litattafan addini da kuma karatunsa fahimta da aiki dashi. "You're a rock star" Murmushi shima maleek ya saki yana duban idanunsa. "Zamanka a nan English yana qoqarin janye yaren oromo daga bakinka ba?". Kai ya girgiza a hankali,murmushin nasa yana sake fadada wanda hakan ya sake tsananta kyawunsa a bayyane. "Ba wani yare sama da nawa.....na zabi yinsa ne for security purpose". Wani abu ya tsarga cikin zuciyarta tana fatan janye idanunta a kanshi. The giant and calm sheikh din yana tafiya da wata irin nutsuwa da yanayin da bata taba ganinsa tattare da wani ba,duk da izzarta bata barinta kallon maza sam sam......wannan ya sanya take qoqarin janye idanunta a kansa,saidai ta gaza aiwatar da hakan. Tanaso ta karanci meye bambancin da yake dashi da sauran mutane da takejin kwarjininsa yana dukanta har daga inda take tsaye yanzu haka?. Tanaso ta qwaqulo dalilin da ya sanya yake da wannan IZZAR da JIN KAI da wannan calmness din data fassarashi da GIRMAN KAI?. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Kusancinta da sultane daya karbe......haduwar jikinsu har sau uku duk da har yanzu bata tsakanin yaqini da kokwanto akan shine mutumin hippodrome......shine mutum na farko.....namiji na farko a duniyarta daya taba taba jikinta. Tsaki taja dan siriri tana jin hakan yana mata wani irin zafi,ba namijin daya taba TSALLAKA layikan data shata rayuwarta saishi......a karo na farko ya tsallake mata iyakokinta masu tarin yawa,har yana iya ji da samun confidence ya tsaya a gabanta yana gaya mata magana mai cike da tsatstsauran umarni. Abinda ya faru kwanaki hudu da suka wuce ya dawo mata. Me yasa saishi kadai?,me yasa saishi kadai ne zai dinga kubutar da ita daga hatsari?. Ko hakanne ya sanya yake ganin kansa a wani abu?,har yake da confidence din challenging nata?. Aah.....ko a yanzu yanayinsa da abinda take gani a idanun nan masu wani irin haske da kwarjini,tana jin confidence din da yake dashi ba na iya kusanci da muqamin da sultane ya bashi kawai bane......akwai wata jarumta da qarfin hali tattare dashi. Wani irin taku yakeyi da a MASAURAUTA a kuma SARAUCE yake kama da takun QASAITA irin takun isashen basaraken da baya shakkar ko tsoron tunkarar komai.....baya buqatar komai daga kowa.......irin takun da sai me ilimi cikin sarauta yake iya fahimtarsa. "Me ya hadashi da izza bayan shi din qasqantaccen malami ne kawai?" Tambayar ta sake bijiro mata,wanda ita kanta batasan sau nawa ta yiwa kanta tambayar ba. Siririn tsakin da yafi na dazu ta kuma saki tana kuma tuhumar kanta kan lissafen lissafen data shiga yi marasa tushe ballantana makama. Ba lokaci bane na noticing dinsa yanzu......me yasa yake bayyana a duk sanda ranta yake a bace?,bayyanarsa me yasa take qara tunzura fushinta? "Na tsaneshi" Ta gayawa kanta da kanta da wani dan qaramin sauti tana jin gargadin da zuciyarta ke mata na dauke dubanta daga kansa. Fitar sautin sai ya zamana kamar saukar wani yanayi ne saman gangar jikinsa. Yana iya jin baqon kallo a jikinsa koda bai san ana kallon nasa ba,wani yanayi da aka haifeshi dashi,ya kuma sake masa tasiri sabda yanayin aikin intelligent security da ya zame masa jinin jikinsa. Ya sani cewa cikin lissafinsa a yanzun akwai boyayyun idanuwa masu yawan gaske dake bibiye da kowanne motsi da kuma takunsa. Yana da wani irin zurfin lissafin da yakan iya auna komai da zai iya kasancewa a lokaci na gaba,don haka cikin qwarewa ya motsa idanunsa yana dagasu a hankali zuwa sashen da yafijin tasirin kallon. Tsam tayi da ranta bugun zuciyarta yana qaruwa lokacin da taga kaman yanayin tafiyarsa ya canza,duk da a nutse dama can yake takawar amma yanzun ya sake zama low.....zuciyarta ta gaya mata yana dab da daga idanunsa zuwa inda take tsaye,sai tayi hanzarin zare idanunta daga kansa tana gayawa kanta babbar faduwa ce da asara ya sameta tana kallonsa.....ba izzarta bace wannan.....ba martabarta bace,ba kuma darajarta bace. Zaya dauka wani abun dabanne.....wataqila ya dauka yana burgeta ne,bayan a duniya ta bangaren maza shine namiji na farko da takejin taqi jininsa sama da kowa KODA KUWA ALMAZ dake dab da cakuda rayuwarsa da tata. Saidai kuma inaaaa,tayi wata kyakkyawar makara,da wani irin zafin nama irin na 'yan mazan da suke da gogewa ta fannin bincike ya sarqafe idanunsa cikin nata. Taji wani irin shocked,taji kuma wata irin faduwa da kunya gami da nauyin yadda ya kamata din. Wani bacin rai ya sauko mata sanda taga ya zare idonsa daga nata cikin kallon daya mata da duka duka bai wuce second biyar ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 46* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ____________________________ Da baya da baya ta koma tana sake sakin tsaki mai qarfin gaske. Don me yasa?,ita ya kamata ta fara dauke idanunta a kansa daga kallon farko don ta tabbatar masa da qarfin izzarta........me yasa ya rigata dauke idonsa?,me yasa ta bari har ya ganta tana kallonsa?. "Sufa irin mutanen nan qarfin kurwa garesu......har yanzu na kasa gano siffar malunta ko daya tattare dashi idan ka dauke tarin nutsuwa kwarjini da kamalarsa.....wannnanzaifi kyau da GIDAN SARAUTA BA GIDAN MALUNTA BA". a mamakance ta bude idanunta sanda aisa dake tsaye jikin qarfen balcony din. Batasan sanda aisa din ta isa gurin ba,uwa uba ma sam ta manta dasu.....mamakinta shine na dogon sharhin aisa din na yau wadda ba kasafai ta fiya magana akan mutumin ba. "Ashe bani kadai nake ganin hakan ba?.......na dade banga namiji irinsa ba......akwai maza ne hurul'eeni a duniya ne?" Shehnaz ta fada tana duban aisa. Dole aisa ta saki dariya sosai ganin yadda shehnaz tayi maganar da dukka iyakacin gaskiyarta. "Wataqila an fara kawo mana sample daga kansa". A nutse ta miqe ta fara takawa tana ficewa daga gurin,tasan muddin taci gaba da zama zasu sake bata ranta ne akan mutumin da bata qaunar zancansa kwata kwata. ★Duk da ya kasance wani irin salon kalar aure da amaryar bata buqaci gudanar da kowanne shagali a bikin nata ba,amma hakan bai hana sauyawar masarautar ba da yanayin da zai tabbatar maka akwai wani gagarumin abun farinciki da zai faru cikin masarautar kamar na aurar da d'iya me daraja ta daya a yankin agadez dama nijer gaba daya. A kowacce rana tun daga yammaci har zuwa lokacin da dokar taqaita zirga zirga zata fara aiki qananun wasanni da kide kiden gargajiya mammina ta zube akeyi. Kamar irinsu kidan qwarya wanda ake gaurayeshi da salon waqoqo da tsaffin wasannin al'adu irin na asalin buzaye. Maroqa da makada musamman mata sai suka samu gurin yasar da zango,kusan wuni mammina keyi tana fidda kyaututtuka masu nauyi ga wanda Allah ya tsaga da rabonsa,kaman yadda zai wahala ka shigo gidan da qoqon barar nema daga taskar GIWA a wannan lokacin baka samu abinda kake nema ba. Zirga zirgar hadimai ta yaiwaita sosai saboda shirye shiryen tarbar baqin da zasu iso don daurin aure. Abinciccika na alfarma,sutturu masu daraja da tsada take fiddawa kawai anata rabo zuwa ga bayi da hadimai da salon irin kyakkyawar shigar da takeso kowa yayi. Zukata da dama sun sake nutsuwa da aminta da salon soyayyar da mammina ke gwadawa akhnan. Ko iya fuskarta kadai ka kalla zakasan tana cikin matsanancin farincikin aurar da gudar diyarta a iya hange da tsinkayensu. Yadda take narkar da dukiyarta wajen komai.....kyauta ta bajinta maroqan cikin fada kakarsu ta yanke saqa a cikin kwanakin. Kwana bakwai dukka ba wanda aka daga qafa a cikinsu,har zuwa yanzu da kwanakin daurin auren suka rage biyu tal!. Ta kowanne fanni,ta kuma kowacce fuska tayi ruwa tayi tsaki,ta hana family din DIOARY HAMMANI tabuka komai akan diyar da take halalinsu ce......tsatsonsu ce. Kakannin da suka kasance su suka haifi SAFEENA amma a dole ta maidasu wash baqi ga rayuwa rai da duniyar akhnan. Bata kallonsu a matsayin wasu shaqiqai nata......ballantana kuma akai ga d'iyoyin qannen mahaifiyarta wato cousins dinta masu tarin yawa. Duk da idan qaddara ta qaddara zuwansu gurin morsa safiyya da zummar gaisheta,hanya kuma tayi sanadin da suka hadu,tana ganin wasu alamu ko kamanni na jini tattare dasu wanda yake shige da nata. Rashin wannan sabon,rashin wannan jituwar,rashin wannan shaquwar ya sanya ko a yanzun ba wata cousin dinta tattare da ita idan ka cire falaaq....aisa da shehnaz. Sai HAIRAAN data iso qasar da yaranta anwaar da Aaaron,wanda wannan karon harda me gidanta daya kasance cikakken buzu,cousin dinta NAADIR. Zata dauki wata biyu aqalla cikin agadez,don ta kwana biyu basu zo ba,don haka da kayanta da yawa ta iso ta kuma fara sauka a masarauta har sai bayan kammala biki kafin ta wuce gidanta dake daura da titin gidan gwamnati. ★★Zaune take kawai saman tattausar kujerar data kasance daga cikin kujerun hutawa na cikin kebantaccen dakin gyaran jikinta. Sanye take cikin wata baqar gown wadda ta zauna a jikinta sosai,ta kuma fidda kyawunta me sanyinnan da wani qarin fayau da fuskarta tayi saboda gyaran gashin da akayi mata jiya daya bashi daman sauka gadon bayanta ya kwanta da wani irin glowing gami da sulbi kamar na 'yar tsana. Uwa uba kuma wani irin sarewa takeji,tana rasa inner peace daga kowanne bangare na zuciyarta. Ko a yanzun data ware tafukan hannayenta tana kalla,wadanda sukasha zanen jan lalle da yake da wani irin maroon me daukan hankali saman jar fatarta dinnan dake samun tsananin kulawa da tattali......wani irin banbarakwai takejin lamarin idan ta tuna wai jibi zata zama matar aure?. Akwai wani qunci da takura da takeji sosai cikin zuciyarta,saidai kuma ta laluba zuciyarta kaf bataji tsanar almaz ba saidai wani irin haushinsa dake danqare da ruhinta. Qila bata jin tsanar nasa ne ta yadda bai sake matsa mata da zuwa gurinta ko nemanta ta waya ba.....amma ta tabbatar sai ta sanya almaz ya tsani ganinta a gaban idanunsa,tsana ta har abada,ta tabbatar wannan ne kadai abinda zai iya bata peace da kuma kalar rayuwar da takeso. Shi kanshi lallen dake hannun nata kallon baqo take masa,don ba zata iya tuna yaushe ne na qarshe data yishi ba. Kawai idan tanason taga wani launi a hannunta lokaci bayan lokaci tana saka nail polish ne kawai duk color din dataga dama,bata kuma fixing nails,saidai nata da take tarawa ya danyi tsaho kadan yadda bazai dameta ba,wanda sukayi kyau a yanzun da aka musu zanen maroon henna din. (Duk da yayi kyau haramunne barin farce a hannu ballantana kuma harka siya ka qara,shin meye marabarki da DABBA kenan?,musulunci ya lissafa yanke farce cikin tsarki na asali guda biyar da muke dashi,ciki kuma harda kaciya da akewa maza,kinga kenan barinsa najasa ne,yana jawo cututtuka na jinnu bayan na infection din mafitsara harda infection din ciki. Farce yana zama inuwar shedan ne a hannunki,kinwa shaidan inuwa kuma me ya rage?,me yayi saura....zan fadada bayaninsa a gaba in sha Allah,Allah yasa mu dace). Tana so ta roqi su shehnaz suyi nesa da ita.......tanason ta gaya musu suyi nesa da inda take,saboda tanajin maganansu tana hawan mata kai. Kuma ta zabi zama a nan ne saboda akwai qarancin jin hayaniya na abinda ke faruwa cikin gidan. Kade kaden da wasanni da aketa faman yi da kuma yadda maroqa suke wuni abu daya,neman abun duniya a hannun mammina. A nutse tayi sallama tana shigowa,bayanta hadimarta ce ta amana wato haleematu riqe da hannun kyakkyawan yaro daya kasance qaramin d'an hairaan din wato Aaron. Yayi kyau sosai cikin suspenders,kana ganinsa kaga rainon turai. Cikakkiyar buzuwar data amsa sunanta,me tsaho da kaurin jiki daidai gwargwado. Kyakkyawa buzuwa dake da wani irin kyau da ta debo wasu kamanni na SAFEENA ta wasu bangarori na jikinta dama fuskarta,sama da yadda ta debo kamannin morsa safiyya,wannan ya sanya KAMANNI na jini suke nunawa sosai tsakaninta da akhnan,duk da cewa akwai tarin banbamce babamce,don da kanta tasha fadin. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Biftu ta fini kyau,nesa ba kusa ba,inda nike da kyan biftu,zan ita gaddamewa cewa ni din hurul'eeni ce" Sosai maganan ke bawa 'yan uwa dariya,saidai kusan kowa ya sani akhnan din wani baiwar ajiyayyen kyau Allah yayi mata. Kaurewa da hayaniya dakin yayi,har tsakanin ita da shehnaz da kuma aisa wani baya jin abinda wani yake fadi. Sun jima sosai suna karadinsu,tana zaune daga gefe ba tare data motsa ba,har zuwa sanda hairaan ta miqe a nutse tana baro su shehnaz amma tana ci gaba da magana dasu "Qarfe biyar daidai za'a fara gabatar da lecture din,na minti talatin ne kawai,kuyi qoqari ku shirya don inajin saura mintuna ashirin biyar din tayi" Ta qarasa maganan tana zama gaban akhnan saman wani tattausan babban tuntum da jikinsa ke zane tsaf da tambarin masarautar agadez. Idanunsu cikin na juna ita da akhnan din,akhnan na duban kamannin da ake yawan fada hairaan ta debo na mahaifiyarta,tana kuma qoqarin tuna kamannin mahaifiyarta na zahiri ba wanda take gani a hoto ba. Murmushi hairaan din ta saki da wannan tarin nutsuwar data gada daga mahaifinta da sashen hikimar data samu daga morsa safiyya,ba abinda bata sani ba,ba abinda bata fahimta ba,kuma ko yanzu kafin ta baro wajen morsa safiyya sunyi doguwar magana sosai da morsa din. "Bana jin komai a zuciyata game da auren nan hairaan,bansan yadda akayi na wayi gari ba zuciyata tayi qaura daga tsananin quntata da labarin auren biftu ba zuwa wani irin sasssuci da tarin nutsuwa. Nayi addu'a kaman ba gobe hairaan,kuma inaji a jikina ubangiji bazai tankwabar da hannayena ba......hannun dake qarfafar zumunci yake kuma qoqarin ceton ruhin da baiji ba bai gani ba.......hannun dake qoqarin kare zumuntar Allah kada ta tozarta". Sosai maganganun morsa safiyya suka ratsa hairaan. "Barka da yammaci amarya" Hairaan ta fada da murmushi saman fuskarta,bata wani damu da rashin gaidata da akhnan batayi ba,don ta sani mulki da sarauta ba qarya bane. Ita din bata gaji sarauta ba don mahaifinta ba basarake bane,attajirin malami ne ma'abocin tsantsar ilimin addini,nata mulkin na kudi ne da ilimi da yasha banban da sarauta. "Barkanki....kinzo lafiya?" Akhnan ta fadi a hankali. Hairaan na daya daga cikin mutanen dake d'an yiwa akhnan din kwarjini kadan,ta girme ma akhnan nesa ba kusa ba,don kusan tayi quruciya sosai a gaban hairaan,kuma a wancan lokacin duk da yadda mammina taso raba tsakani da nunawa hairaan bata da hurumi akan akhnan idan tayi wani abu na rashin daidai a quruciyarta,ita din agola ce da uwarta tazo da ita gidan mahaifin akhnan cin arziqi amma hairaan din bata yarda ko aminta da hakan ba. A zamanin da ba wanda ya isa ya yiwa akhnan fada ko ya hantareta koya gyara mata idan tayi wani abu ba daidai ba,kaman yiwa babba tsawa magana a sake kota harareshi,ko wani abu daya kamata tayi taqiyi ita hairaan rufe idanunta take tayi mata. Duk da hakan ya haifar da rikici da bacin rai sosai tsakaninta da mammina din,amna taurin kai da kafiya shigen na akhnan din gareta,don haka idan anyi yau gobe ma sai an kuma,abun bazai kashe mata gwiwa ba. Ko sanda mammina ta fidda tsarin budewa akhnan aji ita kadai a dinga karantar da ita a gida saboda tsabagen gata hairaan ce tayi ruwa tayi tsakin hana hakan faruwa. Ita dinma kaman morsa safiyya a wasu lokutan,bata da shakka ko tsoro,kai tsaye ta wuce gurin sultane a sannan ta bashi hujjojinta,kuma take yaji ya gamsu,ya kuma sanya akhnan taci gaba da binsu makaranta. Makaranta ce me tsadar gaske da turawan France suka bude suke kuma koyarwa a cikinta,don haka sosai ake karatun da zaka dauka yaro ba cikin qasar niger yake karatunsa ba. "Alhamdulillah biftu.......ina fatan kin shirya saboda quracewar lokaci?" Hairaan ta fadi tana jawo akwatin dake gefanta wanda haleematu ta ajiye. Idanu akhnan tabi hairaan dashi sanda take ciro wata fara tas din gown da aka wadatata da wasu irin swarovski masu tsananin kyau da daukan hankali. "Lecture din yau akan aure da morsa ta shirya......" "Sheikh muhammad haisam ne zai gabatar,na tabbatar zamuji abubuwa da yawa......inaso naga guy dinnan a fagen aure......matarsa ta gama morewa rayuwar duniya wallahi" Shehnaz ta karbi zancan tana ajiye kayayyakin hannunta kan wani sofa daban. Murmushi hairaan ta saki zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 47* "Har yanzu shehnaz tana nan da halinta bai sauya ba" dariya ta dan saki. "Da gaske maman Aaron,ke kinfimu sanin muhimmancin auren irinsu ai ko?" Shehnaz tayi maganan da dukka gaskiyarta. Murmushi sosai hairaan ta saki tana tunawa da maigidan nata. Dan boko ne sosai,amma kuma yana da wadataccen ilimin addini daya sanya komai nasa yake me tsari da ban sha'awa. Tasha masa wauta......tasha masa abubuwa masu yawan gaske da zasu iya bata ran jahilin namiji ya tunzura harma yakai ga saki,amma a lokuta da dama yafi zabar yin shuru idan ta bata masa rai a maimakon magana,yafi zabar yayi nesa da ita har sai ya sauko,yasha gaya mata "Mafi alkhairinku shine mafi alkhairinku ga iyalinku......gidan annabi s a w nake tunawa hairaan,annabi nake tunawa nake miki uzuri,maganansa ta qarshe a duniya ina muku wasiyya ta alkhairi akan mata,ta yaya zan take wannan?". Sannu a hankali sai wannan dabi'un nasa suka dinga saitata,suka sata ta dinga jin kunya itama ta masa ba daidai ba,sai zamansu ya zama me wani irin dadi,kowannensu yana duba Allah da annabi yana qoqarin kyautatawa dan uwansa da kuma kiyaye b'acin ransa. Kai hairaan ta jijjigawa shehnaz a hankali "To kin gani?,kawai don nasan samun soyayyarsu baya zama abu me sauqi a gurin mace......banda haka Allah mom Aaron tsaf zan iya bawa jamaal haquri......" "........shehnaz?,jamaal din shima irin mijin da kike buri bane?". "Irinsa ne,amma bai kama komai na sheikh haisam ba" Ta fada tana dan hade ranta kadan. Idanu akhnan ta janye daga kan shehnaz,tana jin wani bacin rai,sannan ta aje dubanta kan hairaan. "Don Allah su fita" Ta fadi a hankali,saboda yadda zuciyarta ke tunzura a yanzu batason tayi wani abu daba daidai ba. Ta gaji dajin maganganu a kansa,dazun falaak tabar gurin suka gama zancansa,wanda ta lura ma kaman akwai wani abu a zuciyar yarinyar game dashi,yanzun gashi shehnaz ta baro wani sabon hirar. Tana qoqarin danne zuciyarta dabin maganar da suka gama dazun da sassafe da mammina. "Na gama miki dukkan abinda ya kamata ya cancanci uwa ta yiwa diyarta......duk wani motsinki akan aurennan abun bin diddiqi ne,yanayin walwala da farincikinki shine zai bawa mutane tabbacin ZAB'INKI kika aura,akasin haka kuma shine zai saka kokwanto a zuciyar mutane,ya bada qata wawakekiyar qofar zargi a kaina......akasin haka kuma zai zamana qalubale a kaina da kuma zarge zarge da zagin da ban da alhakin ayimin shi". Cikin kokwanto hairaan ta dauke dubanta daga kan akhnan ta maida gasu shehnaz. "Guys.....ko zaku bamu guri muyi shirin amarya?". "Yanzu kuwa,muma so muke mu isa gurin da wuri don muji komai sosai" Shehnaz ta fadi tana murmushi sannan ta kwashi kayanta ta fita aisa ta bita. Sama sama take fahimtar maganganun hairaan,wadda ta dage cikin hikima tana gaya mata haqqin aure da nauyin biyayyar miji dake a kanta cikin hikima. Idanunta kawai ta lumshe,cikin ranta tana fadin,inda hairaan din zatayi shuru ta hutar da sautikanta da yafi mata alkhairi,saidai dole ta qyaleta taci gaba da bayaninta ba tare da tana fahimta ko daukan komai ba. Abinda yafi yankar zuciyarta a yanzu ME YASA SAISHI?. Shi za'a sanya wai yayi mata wa'azin aure?,duk da tarin kawunnanta da take dasu?. Me yasa ya kanainaye komai ne?,me yasa komai ya karbe?,komai ya shiga ciki?,wanne irin annamimanci ne wannan?. Saita furzar da siririyar iska daga bakinta tana sake jin matsanancin haushinsa a ranta. *HAISAM* Window din qarshe ya rufe na dakin,yasa hannu ya zuge curtain din dakin wai yana sanya rai ko hakan zai rage dauko masa hayaniyar dake cikin gidan zuwa dakin nasa. Hayaniyar da tunda aka fara shagulgulan yake jinta a tsakiyar kansa tana shiga masa dukka kunnuwansa. Ya sani mutum ne da bame son hayaniya da yawa ba,amma wannan yawaitar hayaniyar batayi qarfin da zata dinga damunsa har haka ba,baisan me yasa yake jinta a kurkusa da kunnuwansa ba. Har a ransa yakejin banda amanar masarauta da sultane yabar masa da gidansa zai koma,kamar hakan zaifi sama masa nutsuwa. A hankali yake takawa zuwa gaban dressing mirror dinsa wanda a gabansa dressing table ne dake dauke da kayan shafawa na maza designers. Omar yasha tsokanarsa da cewa social sheikh,don idan kazo gurin zaka raina gayunka ne da ganin wasu irin designers perfume designers cream and oils,roll-on body mist da hair mist da baka taba ganin irinsu ba. Idan turare ake magana KAMFANIN ne shi da kansa dama,bayan personal wannan mayen turaren nasa,akwai turaruka daban daban da suke masa,kaman turaren gashi,dana underwear dinsa daya zama unique,nashi ne kawai a matsayinsa na mamallakin kamfanin. Kaman turarensa na jikin kaya,haka sanyayan body perfume dinsa da suka kama fatarsa da duk wani gashi na jikinsa babu inda zakaje kaf kasuwannin turare na duniya ka samesu. Maleek na dason turare,wannan ya sake sanya shaquwa tsakaninsu sosai,shima kuma daban ake masa nasa turaren,duk da baikai na CEO ba. A hankali maleek yake binsa da kallo har zuwa sanda ya zauna saman stool,jikinsa sanye da wata tattausar milk color din bathrobe. "Haisam" Ya kira sunansa kai tsaye,abinda ya janye hankalin haisam din kenan zuwa ga maleek. "Kana lafiya?" Ya tambayeshi yana dubansa sosai. Manyan fararen idanunsa ya lumshe sannan ya jinjina kai a hankali ya furta. "Alhamdulillah" Idanu maleek yadan kafeshi dashi,sai ya jinjina kai shima yana furta. "Ma sha Allah" Saidai cikin jikinsa yana jin ba hakan bane abinda haisam ya fadi. Maida kansa ga cream dinsa haisam din yayi,bashi da tabbacin me yakeji a jikinsa ko kuma me yake damunsa,amma yasan ba lafiya komai yake tafiya daga gangar jikinsa zuwa zuciyarsa ba. Mintuna arba'in ya kwashe aqalla kafin ya fito tsaf cikin shigar kurta pyjamas fari qal,kamar yadda tun daga half shoe din qafarsa da wani irin modern amam daya zagaye kansa dashi kaman na Indonesia ko Malaysia shima ya kasance fari din. "Ma sha Allah" Hakeem ya fadi yana duban haisam da murmushi. "Nayi burin su khadeem suna kusa.....zamana a nan sai nakejin kamar wani yawon bude ido nazo da ban taba zuwa irinsa ba" Murmushi kadan haisam ya saki,duk da yadda yakejin kansa kaman yana sara masa kadan kadan. Yasan me maleek keson fadi,ya saba da jin maganganunsu irin wannan a duk sanda yayi ado,don shi din dama ma'abocin ado ne koda ba inda zaya fita. "Ba lecture bace takai tsaye ba......muna gurinmu suna gurin su" Ya furta yana daukan turarensa ya fesa kadan saman kayansa ya ajiye. Agogonsa dake ajiye a gefe Rolex brand yana daurawa a lafiyayyar fatar hannunsa dake da wani irin kwantaccen gargasa. Murmushi maleek ya saki,haka tsarin haisam din yake,duk sanda lecture irin haka ya tashi indai ta mata ce saidai su ganshi jikin screen makeke da zaa saka musu a hall din,wannan shine abinda ya hanashi zama malamin university duk da yana da burin hakan don alfanun da ilimantarwa take dashi,ya tattara hankalinsa dukka akan kamfanonin sarrafa turarukansa da yanzu yake shirye shiryen bude branch a hadaddiyar daular larabawa wato UAE. Takawa kawai yakeyi amma bayajin wani sauran karsashi a tare dashi,ya tsammaci ganin omari a qasa yana jira amma koda suka sauko baya nan,sai ya sanya hannunsa a aljihu ya ciro wayarsa ya fara neman omar din. Bayajin zai iya tsaiwa gabatar da lecture din,don haka ya yanke kiran omar tun dazu ya jagorancin abun. Wani irin rauni yakeji a jikinsa da wani ciwon kai qasa qasa,yanayin kuma ya fara masa ne kusan kwanaki biyar baya,tun ranar da suka fara bukukuwansu na al'ada cikin gidan,a sannan yana zaune a balcony dinsa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) *AKHNAN* "Ma sha Allah,tabarakarrahman" Hairaan ta fadi tana duban akhnan din. A yau take sake gamsuwa da baiwar kyan da Allah yayi mata dari bisa dari,duk da ko a baya bata inkari,don momma safeena dama tafi kowa kyau cikin dakinsu morsa safiyya. "Wanne irin turare ne wannan biftu?" Hairaan ta dauke idonta daga kan kwalbar turaren tana duban akhnan. Nata idanun ta janye daga kan kwalbar turaren ta dubi hairaan din. Batasan yadda zata misaltawa hairaan din yadda take mutuwar son kamfanin turaren ba......bata da wani zabi a turare a duniya yanzu sama da turaren tun wata shekara data taba zuwa dubai ta siya product din ganin yadda ya mamaye shops dinsu a can da supermarket dinsu. Tana maitar son turaren kamfanin,tasha attempting halartar taron da sukeyi na product dinsu yearly a dubai amma bata samun dama,saboda yawanci yana zuwa ne a sanda sahel couture ke lissafin ribarsu na shekara da wasu gyare gyare a kamfanin. "Bansan yadda zance miki ba,amma ki gwada amfani da kayan kamfanin" Ta amsawa hairaan a taqaice. Tun daga kansa bata sakejin turaren da yayi mata ba,sai wanda birra ke turara mata kayanta dashi na kamfanin INCENSE BY KABODAUGHTER +2348032119803. Tarin Gift na turarukan da falaak ta kawo mata batayi niyyar budasu ba bare amfani dasu,amma bayan fitarta qamshin yaja hankalinta,koda ta duba dai taga kamfani daya ne da wanda birra ke mata using dashi,cikin karramawa ta sanya birra ta kwashesu ta musu gurin ajiya na musamman. Qamshin yana bata wani irin nutsuwa,yadda kuma yake dada kama kayanta da jikinta abun yana bata mamaki. Dama turaruka na gargajiya irin wannan suna da qamshi me tasiri har haka da kama jiki?. Suna shirin fita falaak na shigowa "Subhanallah" Ta fadi tana murmushi,kyan da akhnan din tayi yana ratsata,saita miqa hannu ta kama hannun akhnan din suka tako tare,hairaan a damanta falaak a hagunta,abinda ya kusa sanya qwalla fitowa daga idanun morsa safiyya kenan sannan suka fito ga farfajiyar dake a tsare da hadimai sahu sahu suna jiran isar akhnan din kebantaccen gurin da zaa gudanar da taron. Sam a zuciyarta batason auren,bata gamsu dashi ba,bata kuma nutsu dashi ba,amma batasan meye Allah ya boye ba daya dauke mata wannan quncin zuciyar,ya sanyaya mata rai akan auren. Ko iya yadda taga 'ya'yan nata data mallaka duk duniya jere da juna,abinda bata taba ganin irinsa ba shi kadai ya isheta farincikin da har ta mutu wannan hoton bazai matsa daga idanunta ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 48* Dab da zasu shiga sassan da zai kaisu parlor din dake manne da dakin gabatar da taron,wanda a nan ne zai zauna da cameras din da zasu dauke video dinsa sukutum da guda sukai qawataccen dakin taron dake kama da parlor na alfarma me girman gaske,daidai lokacin da suke fitowa sannu a hankali bisa takewar bayan hadimai masu yawan gaske. A kanta ita daya idanunsa ya fara sauka,sai ya zaresu a hankali sanda suke basu baya kan hanyar isarsu ga hall din,ya maida dubansa a hankali kan maleek,amma sai mamaki ya darsar masa sanda ya dubi idanun maleek din kafe a kansu. A nutse ya dauke kansa daga maleek yana maidawa gabansu don saita gurin da maleek keta kalla haka,kai tsaye idanunsa suka sauka akan falaak wadda ke gefan akhnan din kaman yadda suka fito a daxu. A mamakance ya maida dubansa kan maleek,still wannan basaraken murmushin yakeyi,sai ya motsa bakinsa a hankali,muryarsa can qasa ya furta. "Ina kyautata zaton samun matar aure ne ya karkato da hankalina agadez......wani rabonne yaketa kirana,shi yasa na kasa nutsuwa sai dana zo gurinka" Ya qarasa maganan yana dauke dubansa daga kansu saboda sun bacewa ganinsa ya dawo da kallonsa kan haisam. Shima haisam din shi yake kalla,yana mamakin yadda lokaci daya maleek din ya iya bayyana abinda ke ransa kai tsaye. Shi da maleek suna cikin mutum biyu a team dinsu dake da farinjini sama dana kowa kuma ake shakkar tunkararsu ace ana sonsu,amma har gwara maleek a kansa. Don maleek yakan tsaya ya saurari wadda yake ganin ta cancanci hakan na wasu kwanaki kafin ya gama karantarki,idan yaga tafiyar ba zata yuwu ba sai ya sallameki. "Da gaske nake" Maleek ya furta cikin nutsuwa yana son jin abinda haisam zai fadi. Kasa cewa komai haisam din yayi,don da gaske yakejin kanshi yana sara masa,sai ya janye idanunsa daga cikin na maleek yana cewa. "Booda haasofna(zamuyi magana wani lokaci)" Jinjina kai maleek yayi a nutse,bai sake takura masa da magana ba ya qyaleshi,don yanayinsa ya tabbatar masa da gaske baya jin dadin. *AKHNAN* Wani yanayi takeji na daban tattare da ita,wani sanyin jiki dama mutuwar jiki gaba daya,har zuwa sanda ta zauna muhallin da aka tanada wanda mammina ta shirya yi mata kamu bayan an gama lecture din. Shuru ne gaba daya ya dauka a gurin lokacin da babban allon screen din da yaci bango guda na gurin ya fitar da hotonsa. Tsaye cikin tsaiwar dake nuna zallar kamalarsa da nutsuwarsa. Murmushi me dan qaramin sautin wanda akhnan tana iya jinsa shine ya kubucewa falaak sanda idanunta suka sauka a kansa. A yau zata kalleshi son ranta,irin kallon da bata taba yi masa irinsa ba,Koda ya kasance ta cikin screen ne bawai ganin ido da ido ba.......yana da wani irin kwarjini da cika ido,tana jin ya mata wani girman da takejin nauyinsa har cikin jininta. Cikin muryarnan tasa dake da nauyi da zurfin daya kutsa har tsakiyar zuciyar akhnan da batako daga idanunta ba tunda ta zauna yayi cikakkiyar sallama. Idanunta ta lumshe a hankali tana jin yadda sautin ya karade hall din,tamkar yana tsaye a gurin,da yadda muryoyin mutanen gurin ke amsa masa can qasa. Tazarar wasu sakanni ya bada yana qoqarin hada taqaitaccen bayanin da zai gaya musu da yaren abzinawa daya soma koya......shurun daya kutsa can cikin zuciyar akhnan din,a hankali kuma ya soma tilastawa idanunta dubansa. Fes ta zube idanun nata kan babban allon dake a gabanta. Ya bayyana tarwai har fiye ma da bayyanar da zaiyi a gabansu. Fararen kayan dake jikinsa gaba daya sune abu na farko da zai fara kashema me kallonsa idanu,wani irin kwantaccen kwarjini ne saman fuskarsa da tayi wani irin fresh da fatarsa dake glowing tamkar wani wanda ke shiga gyaran jiki duk wata. Baqar sumar dake kumatunsa habarsa da qasan hancinsa ta sake fidda sirrintaccen kyan da Allah yayi masa. Uwa uba shemagh din dake kansa daya zauna masa kamar yadda matasan larabawa masu jini a jika kanyi. Idanunsa da suka dan rusuna kadan saboda ciwon kan da yakeji kadan kadan sun sake zama wani ado me jan hankali a tattarre dashi,duk da rusunawan nasu kuma hakan bai rage hasken da suke dashi da kyansu ba. Batasan sanda idanunta sunkai kan labbansa ba sanda ya fara sarrafa harshensa da yarensu na abzinawa ba. A nutse yake gabatar musu da kanshi gami da neman afuwa,gami da kuma gabatar da sunan omari a matsayin wanda zai jagoranci taron,sannan ya tura kujerarsa baya,hoton omar sanye da baqar jubah ya mamaye screen din. A hankali ta zame idanunta ta maida qasa,tana jin wani shuru cikin qirjinta,shurun daya mamaye qirjin da sautin bugun zuciyarta da takeji har cikin kunnenta. "Me yasa ko a screen ma yake min kwarjini?" Ta tambayi kanta tana jin wani haushinsa yana mamayarta. Ta tsani wannan kwarjinin......wannan kwarjinin dake tattare dashi tayi matuqar tsanarsa. Bai kamata ace yana da kwarjini har irin haka ba,baida mulki ko sarauta don me zaiyi kwarjini sosai?.....har ya zama wani abu dake ratsa tsakiyar izzarta?. *HAISAM* A hankali yake takawa shi kadai yana dawowa sassansa,can qasan zuciyarsa cike da mamakin yadda yakejin zuciyarsa wani iri cike da wani yanayi maras dadi da baisan me ya haifar dashi ba. Shamagh din kansa ya zare a nutse yaa ajiyewa gefansa bayan ya nutse sosai cikin sofa yana relaxing bayansa jikin kujerar da yake zaune akai. Idanunsa ya lumshe,a hankali yana zuqar iska sosai yana fesarwa a hankali. Ya jima a haka kafin ya bude idonsa yana furta. "Subhanallahil azeem" Sai ya miqe ya zauna sosai. Yanayin da yakeji a jikinsa da zuciyarsa wani irin yanayi ne da yakanji idan yana kewar wani abu,musamman ma nanay,wannan ya sanya ya yanke shawarar kiranta,ko wataqila zuciyar nanay din take muradi. Dab da zata tsinke aka daga kiran,nutsatsiyar fuskar matar dake cike da kamala da nutsuwar da tunda ya tashi a rayuwarsa yasan nanay din da ita ta bayyana. Murmushi sosai ya wadaci fuskarta da ganin gudan jinin nata,saidai a kallon farko kadai da yayi mata ta cikin siririn farin gilashin idanunta ya fuskanci wata qanqanuwar kwantacciyar damuwa a tattare da ita ba. Wani irin mutum ne me baiwar kulawa da duk wanda yake rayuwa dashi. Yakan damu da damuwar wasunshi,ko yaya damuwa take a tattare da kai yana iya fahimta daga kallon farko,muddin ya kalli qwayar idanunka,musamman ma mutum me matuqar muhimmanci a gurinsa irin nanay din. "Ina cikin maganarka a raina saiga kiranka ta hannun noorah". Ta fadi bayan ya gama gaidata cike da qauna da kuma kulawa cikin asalin harshen oromo me zubi da yaren fulani a Nigeria. Murmushin ya danyi kadan yana qoqarin danne harbawar da kanshi keyi. " Me ya samu nanay dina yau?" Ya furta a tausashe idanunsa a kanta. "Yau ta tuna ne da obboleetti abaayo" Siririyar muryar noorah ya shiga kunnensa. "Noorahty" Ya kira sunanta a hankali,abinda ya sanya yarinyar matsowa kusa da camera tana murmushi. "Captain obbo" Ta fadi tana murmushi gami da daga hannunta alamun saluting nasa. Maida mata shima yayi kafin ta soma gaidashi da yaren oromo. "Kina kula da nanay kuwa nurahty?" Ya tambaya da salon kulawar nan tasa. "Sosai......amma yau har qwalla nanay tayi,har hoton obboleetti abaayo ta dauko" Ta fadi qasa qasa tana saukan da camera din kan hoton. Shuru yayi yana qurawa hoton idanu kamar yau ne karon farko daya soma ganinsa. Hoton sam ba baqonsa bane,tsahon shekarun da yayi wayo a duniya yake ganin hoton,amma yau daya sai yaga hoton ya zama sabo a idanunsa. Yau daya sai yake ganin kamar yasan fuskar dake cikin hoton. "Noorahty" Ya sake kiranta a hankali "Eeyyee obbo(na'am obbo)" "Suuraa naannessaa(juya hoton nan)" Ya fadi hankalinsa yana sake kaiwa ga hoton. Yadda ya buqata haka tayi masa. Cak ya dakatar da komai ya zubawa hoton ido yana kallonsa,duk sai wani jijiya ta jikinsa yaji kaman ta tsinke. Kamar yasan fuskar,sani kuma na kurkusa ba na nesa ba......kamar akwai inda yake ganin wannan fuskar lokaci bayan lokaci. "Akhnan" Sunanta yazo ya tsaye masa a rai,abinda ya amsa kuwwa har cikin zuciya da kunnensa. "Ina nanay?" Ya tambayi noorah. Sai data waiwaya ta kalli bayanta sannan ta bashi amsa. "Gata nan ta fito daga toilet,alwala tayi" Kai ya gyada a hankali. "Idan mun gama magana da ita ki dauki hoton da wayarta ki turamin,ki tambayeta idan da wani ma ki dauka duka ki hadomin". "Me zakayi da hotunan obboleetti abaayo na?" Nanay ta tambayeshi tana karbar wayar daga hannun noorah. "Ina buqatar labarinta nanay......inaso a wannan karon ki bani labarin abaayo" Dan qaramin murmushi ta saki tana gyada kai. "Zan baka......amma ka biyoni bashi gobe.....yau din akwai.mutanen da zan rabawa tallafi,suna zauren jira suna jirana". Kai ya jinjina a hankali,ya qara da tambayarta motii. "Ya shiga hidimar al'umma sosai kwana biyu,baya zama sosai,akwai qananun qauyukan da yaketa zuwa duba mutanensa" Dan shuru kadan haisam din yayi,ya sani koda ya hana motii yace ya sa ya wakili bazaiji ba,shi kuma a wannan qadamin da ake kai yana buqatar yawaitar zaman motii dinne guri daya maimakon zirga zirga,har yanzu bai amince da safety dinsu ba,duk da tarin jami'an tsaro harda na farin kaya dake tare dashi wanda shi kansa motii din wasuma baisan suna biye dashi ba. "Allah ya tsare,a miqamin gaisuwa kafin na samu layinshi,Allah ya tsare" "Allah yayi maka albarka duniya da lahira,ya tsareka daga dukkan sharri". Nanay ta fadi cikin jin soyayyar yaron nata. Baiwar haihuwa ta farko data samu,kuma ya zame mata baiwa ta gasken gaske. "Idan na kira gobe zanyi magana da rumaisa da anani.....su zama a kusa" "In sha Allah" Nanay din ta amsa cikin tsananin kulawa. Saboda yanayin aikin sai ya kasance shi daya ke kiya kiransu,ya tsara hakanne kuma saboda tsaro a garesu gaba daya. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) ★Cikin wani irin salo gami da qwarewar da basu taba ganin irinta ba a yau karon farko yake gabatar da khudubar sallar juma'a a babban masallacin agadez me tsohon tarihi. Kyakkyawan matashin me zubi da kamanni da BUZAYE kuma ba'anzine SAK!. Wanda ke sanye da cloak robe me daukan hankali fara tas da kuma ratsin adon zaiba,kamar yadda yayi amfani da kuwaiti thobe(jallabiyya zubin saqa da adon qasar Kuwait) fara qal itama me wani irin sulbi da daukan hankali,hakanan shill shamagh din dake kansa dan asalin qasar Kuwait daya yafashi saman kyakkaywar maroccon cap din dake kansa ya sake qarawa fuskarsa wani irin kwarjini na daban. Yadda khudubar ke shiga zukatan al'umma da yadda sheikh haisam din yayi musu wani irin kwarjini da yanayin tsakanin burgewa da samun matashi me tarin ilimi haka wanda haskensa ya bayyana,yanayin ya bayyana akan duk wani wanda ya halacci masallacin da zummar yin sallar juma'a a masallacin,gami da shaida daurin auren diyar sultane din,gudan jininsa da mutane da dama suka gama saddaqarwa cewa ba'a haifi mijinta ba a duniyarmu ta yanzu. A cikin jikinsa yakejin hucin zazzabin yana ratsashi,abinda ya sanya hudubar zafafa sosai da wani irin husky voice data qara kaifi sanadin madaukar sauti masu kyau da masallacin yake dasu,take kuma watsa sautin har cikin gidan sultane har kuma kunnuwan mutane irin akhnan da mammina,wadanda zukatansu ke dauke da mabanbamtan burika da kuma tsammani. A nutse ya kammala huduba ta biyu,sannan ya sauka daga saman minbarin da wata irin nutsuwa yana fuskantar alqibla sannan ya tayar da sallah. Cikin wannan sautin.....wannan muryar wannan qira'ar dake kamaceceniya da muryar sheikh afif taj sautinsa ya fara karade masallacin,yana kuma saukar da wats irin nutsuwa a zukatan mahalarta sallar. Ba iya su kadai ba,hatta da akhnan dake kwance cikin kebantaccen dakin tana iya jin sautin tar,ta maida idanunta ta lullube sautin yana sauka saman zuciyarta duk da yadda taketa qoqarin hana kanta hakan. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 49* Wata kalar nutsuwa ce da batasan daga inda ta sameta ba take ratsa zuciyarta,duk da yadda taketa kokawa da kanta wajen hana kanta da kanta sauraro ko jin dadin sautin karatun nasa. A nutse ya sallame sallar,yana jin yadda jikinsa ke sake daukan dumi sosai da wani irin weakness. Ya waiwayo cikin girma da dattako yana fuskantar manyan mutanen dake fada aji a agadez da sukayi sallah a bayansa ya soma musabaha dasu kaman yadda ya saba yi a jimma. Maleek ne na kusan qarshe da sukayi musabaha din,sai ya riqe hannun haisam din kadan yana tambayarsa da idanu jin yadda dumin jikinsa ya qaru. Dukkaninsu magana da kuma bada umarni da ido bai zame musu baqon abu ba,saboda fita daga tsatson sarauta,tsatson izza da mulki,don haka suke da saurin karantar body language,da idanu ya yiwa Hakeem sign din baya jin dadi ne,sai ya zame hannun yana maida hankalinsa ga wazeer. Qasa qasa yake masa maganan waliyyan almaz su matso kusa,don sosai yakejin raunin yana ratsashi,yana kuma jin kamar bazai iya qara mintuna goma cikin masallacin ba. Wani babban hadimi ne ya miqe yana shelar neman waliyyan almaz din,wanda cikin qasa da mintuna uku kacal suka soma tasowa daga muhallan da sukayi sallah suna matsowa. A nutse ya daga kyawawan idanunsa yana karantar kowanne mutum dake matsowa gurin. Can qasan ransa yana wassafa abun,ba yau ne karon farko daya fara daura aure ba,daga manyan gidajen alfarmar na yankinsu,mutanen motii da yawanci suke damqa daurin aurensu cikin babban masallacinsu,wanda duk sanda ya kasance haisam din yana nan shi motii ke wakiltawa ya daura auren. Da yawan lokuta waliyyan angon yakan gansu a sahun gaba cikin sallah,wadannan sai gasu a warwatse guri daban daban suke tasowa suna isowa gurin da aka tanada don qulla auren,a haka suka kammala a gaban haisam din. Still dai a nutse yake kallonsu,can qasan ranshi yana jin wani abu yana motsuwa. Yana jin kamar ya sallamesu ya kuma hana qulla auren,akwai abubuwan da haka kawai yakejin bai masa daidai da tsarinsa ba,akwai abubuwa da yawa da yake ganin kamar basu zauna a muhallansu ba,saidai kuma ta yaya?. Ta yaya zai watsa taron wadannan mutanen da sukayi tattaki daga unguwannu da garuruwansu yace ya fasa bada auren akhnan din?.....a matsayinsa na wa?......wacce hujjar yake da ita wadda zai gamsar da sultane da dukkan me tuhuma akai?. Baya ga haka ma me yayi ruwansa da shiga sha'anin mara kunyar yarinyar da sam GIRMA baya cikin dabu'unta? Sai dukka ya kauda wannan,ya kuma lumshe idanunsa ya soma bada sigar daurin auren. Daidai sanda ya kammala bada auren,dukkanin shaidu suka shaida da AKHNAN din a yau ta zama mata ga ALMAZ IDRISSOU daidai lokacin ya miqe tsam yana bada uzuri sannan ya fara ratsa mutanen a hankali don ficewa daga masallacin yana bi ta qofar baya gami da barin wazeer dasu. Tsam maleek ya miqe ganin yadda ya wuce,sai yabi bayansa shima a nutse ta hanyar daya fita din. *_MUKAN BUDE WASU QOFOFIN QADDARA DA HANNUWANMU........YAYIN DA WASU QOFOFIN QADDARAR SUKAN BUDE KANSU DA KANSU KODA BAMU SHIRYAWA HAKAN BA_* *_NACE BA🙋🏽‍♀️,karkuyi qasa a gwiwa.....kuma kada ku sare.....ku biyoni muje_* *_Akwai QOFOFIN da suka bude kansu da kansu.....akwai wanda sheikh muhammad haisam ya budesu a wannan ranar......a wannan lokacin.....a wannan gurin ba tare daya sani ba_* Ya manta da maleek sam cikin masallacin,har sai da yaji ya taba kafadarsa,a nutse ya juya yana duban maleek gami da zura hannunsa sosai cikin na maleek din. "Gidan nan yayimin hayaniya da yawa maleek,mu qarasa gurin motoci,ka kira salana ya matso da mota kusa,zan dan fita gida kadan na huta,kaina sosai yake ciwo" Haisam yayi maganar yana dan riqe kan nasa da yatsunsa. "Yakai kwana biyar baka a daidai haisam......qin maganinka ne kawai yasa kake pretending you're okay" Maleek ya fadi yana riqe hannun haisam din sosai cikin nasa,don da gaske ya lura jikinsa yana qara zama weak ne,daya hannun kuma ya fiddo wayarsa yana qoqarin kiran omar,don yana ganin kamar zaifi salana saurin zuwa,don su din kam basa wasa da damuwar d'ayansu. Ido ya runtse sosai sanda sanarwar ta shiga kunnenta. A hankali kuma sai ta budesu,tana jan wani qaramin tsaki gami da gyara kwanciyarta sosai. Bata dauki almaz a matsayin miji ba bars ya zama takurarta,don me zata aza damuwa a kanshi?,saidai abu daya data gaza kankarewa kanta da kuma kankareshi daga zuciyarta shine TSINTACCIYAR MAGE YA ZAMA MADAURIN AURENTA? ta tambayi kanta da kanta tana jin haushin abun yana tsumata sosai,saita sake jan tsaki,fuskar sa ta jiya cikin majigin tana gilmawa a idanunta,cikin tsaiwar na tasa ta lafiyayye kuma ingarman namiji. Yatsunta ta sake azawa saman fuskarta.kamar tana gargadin idanunta da kwanyarta akan tuna komai daya shafeshi,saita girgiza kai tana hade rai kamar d wani take magana. Cike da girmamawa duka hadiman dake kai kawo suke kai masa gaisuwa sanda yake tattaki shi da maleek din da ficewa daga gidan. A hankali idanunsa suka kai kan wasu gungun motoci dake tsaye a gurin,inda maroqa da masu busa irin na sarauta suka baibaye gurin. Sosai kuma a fakaice ya saka hankalinsa a gurin yana karantar yanayin mutanen dake gurin. Daidai lokacin da wani yaketa faman rabon kudi tsakanin maroqan,yayin da idanunsa suka sauka a hankali akan fuskar almaz da tamim ke cusashi a mota. Sosai wani irin abu me kaifi da haske ya gilma ta cikin kwanya da idanun haisam,ya qanqance idanunsa a hankali yana sake kaifafa ganinsa ta guraren ko zai sake nasarar ganin fuskar almaz din,saidai bai samu nasara ba don tuni tamim ya rufe qofar motar,alamu kuma suna nuna barin gurin zasuyi. "Salaaana ya qaraso?" Haisam ya tambayi maleek dake duban wayarsa. "Ya qaraso mu yake jira" "Oya hurry up" Ya fadi yana qara daga qafa cikin wani irin zafin nama da kuzari,abinda ya sake motsa bugawar da kansa yayi har sai daya runtse idonsa. Suna shiga motar motocinsu almaz suna wucewa suka wucesu da wani irin gudu. Da zafin nama haisam ya shiga yana bawa salaana umarni da yaren oromo wanda har ya manta rabon da ya yishi cikin agadez "Ka bisu da sauri" Cikin cika umarni salaana ya tayar da motar ya kuma bi bayansu cikin qwarewa da hikimar iya tuqi gami da bin diddigi. Idanunsa kan motocin da suke bi a hankali,yana nazartar lambar kowacce mota yanayinta da kuma tsadar da take dashi. A tsakanin mararrabar titunan motoci biyu suka bi wani titi daban,dayar data rage kuma gangara wata hanya. "Wacce zamubi a ciki?" Salaana ya tambaya a hanzarce gudun kada su bace musu. Shuru yayi na second biyar sannan yace "Hannun dama" Wato mota daya data gangara kenan. A hankali suke bin titin har zuwa sanda suka fada wannan layin. Wannan layin dai daya sanya tsaro da sanya idanu a kansa,wannan layin daya dasa zarginsa a kanshi. Daga nesa ya sanya salaana ya kashe motar,ya bude murfin yana nufin sauka tare da cewa salaana din. "Ka janye motar zuwa street din dake bayan wannan.......zan qaraso da qafa idan na kammala". Har ya sanya qafa maleek ya riqe hannunsa,ya waiwayo yana duban maleek din. "Amma kasan baka da lafiya ko?" Kai ya jinjinawa maleek har yanzu yana jin yadda kansa yake sarawa da gasken gaske kaman zai fadi. "Na sani maleek.......amma akwai wani nauyi da ya hau kaina yanzu yanzunnan daya zama dole na bincika akai.....banason Allah ya tuhumeni bani da bayanin bashi ranar qiyama" "Amma bai kamata ka tafi kai kadai ba" "Ni kadai ya kamata na tafi maleek.....kada ka damu zan dawo in sha Allah" Yana kaiwa qarshe ya sanya qafafunsa cikin zafin nama ya fita. Da zafin naman kuma cikin takatsantsan yake sake kutsawa cikin layin,yanajin qarar tashin motarsu salaana a bayansa,yaci gaba da aza hankalinsa akan wannan gidan da tun ranar basu sake samun komai akai ba sai a yanxun. Qofar gidan motar ta tsaya,sannan cikin qasa da second talatin murfin ya bude. Tamim ne na farko daya fara fitowa, sannan fuskar da yake sake son gani ta sake bayyana a fili. Almaz ne,da wani irin yanayi na rashin qwarin jiki da ya riga ya zame masa al'ada saboda yawan kasancewa cikin shan kayan maye koda ba mayen yake ciki ba. Zuciyarsa ta wani motsa da qarfin gaske sanda almaz ke juyawa yana shiga cikin gidan tamim yana biye dashi. "Me ya hada tamim da angon?" Tambayar farko da taxo kansa kenan sanda yake sake laluben kwanyarsa kan neman inda yasan almaz din. "Takardun zaituna" Amsar tambayar ta haska cikin kansa. Wani mugun bugawa ya sakeji kansa yayi,har sai daya sanya tafin hannunsa ya riqe goshinsa sannan ya zare hannun nasa a hankali,zuciyarsa da kwanyarsa tana son ganar dashi tarin sarqaqiya da abubuwa masu yawa da yanzu suka harba cikin kansa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Kai yake girgizawa a hankali,ba'a iya takardar kawai ya soma ganin fuskarsa ba. A nutse sunan gidan marayun ya dawo kansa,ya soma maimaitashi a jere har sai da yaji kansa kamar zai buga.......sai kuma hoton komai ya sake haska masa......gani sau daya daya taba yi masa cikin gida marayun na YATAAMA......a bangaren wadanda ake bawa horo da tarbiyya. Da kansa yaji zuciyarsa tana kokwanton shine ko ba shi bane......sai yaji gaba daya tunaninsa yana rikicewa da wani irin yanayi daya tilasta masa juyawa yana barin gurin,saboda yana jin yadda jikinsa yayi zafi sosai da wani irin zazzabi,sai ya aikewa beeno saqo kawai,ya tabbatar zaizo yaji da komai a gurin. Ga mamakinsa maleek ya soma hangowa tsaye jikin wata motar daban bata dazu ba. Maleek din ya sauke hannayensa ya fara takowa zuwa inda haisam ke kusantoshi shima. "Kasan bazam iya tafiya na barka ba.....hankalina bai kwanta ba sam" Ya fadi yana miqawa haisam hannunsa. Zafin da yaji jikinsa ya qarayi ya sanya ya kalleshi. "Mu tafi gida" Ya fadi a hankali yana takawa,abinda ya alamtawa maleek shuru kawai haisam din yake da buqata ba tarin tambayoyi ba. Tafiyar mintuna qalilan suka qarasa gidan,dukkan wani guard da security na gidan suka soma kawo gaisuwa,don ya kusa sati biyu rabonsu dasu ganshi. Kowa yayi kewarsa a cikinsu,bawai don wasa da dariyarsa ba,aah,sai don kyautatawarsa a garesu. Maleek bai tsaya ba har sai daya taka masa har zuwa master bedroom dinsa. Yalwataccen bedroom dake nuna zallar izzar sarauta da kuma tarin dukiya dake kwance muraran a cikinsa dama tsarin ginin gaba daya. "Kana buqatar magani captain....." "......ba yanzu ba maleek" Ya dakatar da maleek din yana qarasawa saman wata irin sofa kewayayya dake da wani dan madaidaicin table wanda ke dauke da qananun na'urori. Idanu maleek ya zuba masa,yana mamakin qarfin halin haisam. Sam shi bata lafiyarsa yakeyi ba,ta aikinsa yakeyi,duk da yasan halinsa dama,ko a baya wani irin mutum ne da sai ya gama ciwonsa baisha maganin komai ba. Sau tari sanda suna secondary school sai sun hada da kiran nanay,ita zatayi tsaye cikin waya kafin ya maida hankali yasha din. Ja masa qofa kawai maleek yayi ya koma da baya,bawai don ya qyaleshi bane gaba daya,aah yayi hakanne kawai don bashi space saboda ganin yana hada system da na'urar daya samu a dakin. Cikin ransa kuma yana ganin tsananin jarumtar dake tattare da haisam din,risk da rashin sakewa dake cikin aikinsu gaba daya,lallai aikin ya dace da sunan INTELLIGENT SECURITY. Aiki ne tabbas da bai cancanci kowa ba,aiki ne kuma da ba kowa ne zai iya yinsa ba da gaske,sai jajirtacce irin haisam din,wanda kwanyarsa ke gudu yadda ya kamata.. Idanu ya zubawa system din yana jiran ta qarasa kunnuwa,cikin jikinsa yana jin yadda zazzabin ke nuqurqusar qashinsa,kansa yake sake masa nauyi har yana dan lumshesu kadan kadan saboda yadda yakejin zafin zazzabin yana shiga da kuma yadda yakejin ciwon kamar yana sauka masa a idanun ne. Yana jin ciwon sosai a jikinsa,amma baisan me yasa yakejin wani takura da qunci cikin zuciyarsa ba sama da abinda yakeji a gabbansa. Hannu ya sake miqawa da hanzari yana bude saqon da noorah tace ta aike masa,wanda ta aika ne ta email kuma system din a nan gidan ya barta,don haka koda ta gaya masa dama ya ajiye sai yau ko gobe zai ware awanni yazo ya duba hotunan. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 50* Fes suka fita hotunan,don dama yana cikin dabi'un noorah din daukan hoto. Tana da son dauke dauken hotuna,don har shi da kansa ya siya mata tarin cameras da sauran tarkacen daukan hotuna,wannan ya sanya ta cika dakinta da hotunan tsuntsayenta da take kiwo masu tsananin tsada da daukan hankali,wanda takanas tayi order dinsu daga nigeria ta hannun HALY JASHERU VENTURES 07046665338,ta samu sauqin isowar saqon saboda akwai wani company a nan Ethiopia din da suke order man kitso daga gurinsu suna kaiwa nigeria. (Suna kawo original kayan islamic chemist masu kyau,original body suit na jarirai,harda na manya ma,track suit da sauransu,masu neman nau'in aku,dawisu,irin tattabarun nan masu tsananin kyau farare qal da nau'ikan kaji masu tsada,har na million daya qwaya daya hajiya akwaisu😂,ki sana'a ki samu riba me yawa,ko kuma idan SARAUTA takai irinsu haisam maleek da akhnan,kawai sai a siya a ajjiyesu saboda su qawata farfajiyar gida ko garden idan kina da 07046665338). Zooming na hoton yayi sosai,abinda ya sanya gabansa wani irin faduwa har sai daya motsa labbansa yana furta. "Subhanallah" Kamanni yake gani sosai,duk kuwa da cewa asalin wadda ya sani da kamannin bai taba mata kallon daya wuce na minti guda ba kacal......amma yaga kamanceceniya me yawa a gurin,hatta da dimples din dake kumatunta a duk sanda qaramin bakin nan nata na rashin kunya ya motsa itama wannan tana da,banbancin wannan nata qwaya daya ne ta hannun dama. Ipad dinsa ya matso da ita,ya kunnata ya dorata a saiti,sannan ya miqe a hankali yana jin kamar jiri zai kayar dashi ya shiga toilet. Alwala ya daura ko hakan zai rage masa tururin da yakeji tun daga gangar jikinsa har zuwa zuwa zuciyarsa,bayaso kuma nanay ta fuskanci komai tattare dashi,nutsuwarta da labarin data jima tana basu shi a tsintstsinke yake nema ya jishi a yau full. Qaramin towel ya sanya ya goge damshin daya jiqa gargasar hannunsa,sannan yaja kujera ya zauna yana kunna camera din ipad din sannan ya kira nanay. Wasu bayanai ta tafa da sauri,kai tsaye kuma ya aika wa bobbo muhammad dawud yayi highlight na YATAAMAH ORPHANAGE. Bayanai yake buqata akan gidan gaba daya,da duk wani yaro da ya taba bata ko ya fita a gidan,da saninsu ko bada saninsu ba,na shekaru talatin baya. Yasan aikine babba daya bayar,amma yana buqatar gano bakin zaren komai a tsakanin nan. Ya jima yana lalubenta kafin a daga,fuskar Anaani ta fita saman screen din. "Captain obbo......barka da warhaka" Kai ya gyada mata a hankali muryarsa can qasa ya amsa mata,sai tasha jinin jikinta,zuciyarta kuma ta fara raya mata 'yan miskilancinne tabbas a kusa,don haka bata tsaya wahala ba tace "Bari na miqawa nanay" Baice komai ba har zuwa sanda wayar ta isa hannun Nanay din,Anaani ta saita mata wayar sosai sannan ta kauce ta basu guri tun kafin a qwaqulo mata laifin da zataci qaniyarta a gurin Captain din. Sassanyan murmushin nan nata daya sanya yaji wani nauyi na raguwa a zuciyarsa ta sakar masa. "Assalamu alaikum warahmatullah" Tayi cikakkiyar sallama. Zai iya cewa sallama tarbiyyarta ce,a gurinta suka fara sanin muhimmancinta da kuma tarin ladan dake cikin sallama da alfanun dake cikin yawaita yada sallama tsakanin musulmai. Murmushin ya maidata mata,murmushin da ita daya ke samunsa duk duniya,koda su anani hussam noorah da Aarif ba zasuce ga kalarshi ba,harma gwara noorah saboda ta hannun damansa ce ita din. "Nanay na biyo labarina" Ya fada cikin tausasa murya da kwantar da kai daya saba,saboda duk sanda yake gabanta yana jinsa ne kamar wani jariri,saidai yau din hakan ya hade masa da ciwon kan dake sara masa,da yadda jikinsa ke qara daukan dumi. Murmushi ta saki wanda ke qara mata wata irin kamala. "Shi alqawari abun tambaya ne,zan cikashi yanzu in sha Allah" Ta fadi tana gyara zamanta a nutse. *KHADEEJA YUNNUS JALLATA(NANAY)* "Kamar yadda ka sani,nice d'iya ta biyu da mahaifina ya haifa,bayan babban yayana Aliyyu yunnus jallata,sarki alimayu na yanzu da ya zama d'a na farko a gurin mahaifiyata data kasance mace ta biyu a gurinsa,mata ta farko a gurin mahaifina itace FALMATA,wadda sam ba 'yar qasarmu bace,kuma har yanzun mu kasa fadin ainihin sunan qasarsu,abinda ya zama silar matsala da kukan da nakeyi kenan har yanzu. Mummu falmata haka muke kiranta dashi,ta samu jinkirin haihuwa abinda yayi sanadin auren mahaifinmu ga mahaifiyarmu. Mahaifina shine sarkin gumma kaman yadda ka sani daya daga cikin yankunan da qabilarmu na oromo suke rayuwa. Samun magaji namaji abune me girma a gurin basarake,wannan shine silar auren mahaifiyata BELKIS. Gidan mahaifina wani irin zama ne da sam basusan KISHI BA,wani irin zama ake na yaya da qanwa tsakanin falmata da belkis,zaman dake bawa kowa mamaki da sha'awa. Ba wanda yayi zaton a gidan sarauta irin wannan za'ayi irin wannan zaman,wani irin xama me matuqar daukan hankali tamkar 'yan uwan da suke uwa daya uba daya. Bayan mamana ta haifi alimayu ne da shekaru biyar mummu falmata ta dauko d'iyar qanwarta da suke uwa daya uba daya data rasu,wadda tare sukazo Ethiopia gumma,kuma itama anan aka aurar da ita,don haka bayan rasuwarta mummu falmata itace UWA a gareta,kuma dole ta daukota don duka duka watan yarinyar me suna SAFEENA biyu a duniya. Ba jimawa da dauko safeena din mamana ta samu cikina,cikin wani ikon Allah sai mummu falmata ta fara ciwo,daga qarshe ya tabbata itama ta samu juna biyu ne,don haka ko da aka tashi haifarmu ni da SAFIYYA sai ya zamana tazarar kwana bakwai ne akwai a tsakanin mu,wannan ya sanya ake kiranmu da TAGWAYE. Mun tashi dukkaninmu tamkar 'yan uku,ni safeena da safiyya,har baka iya banbance uwar kowa daban,mun zama tamkar taurari da samun wata iri cikakkiyar kulawa da tarbiyya daga gurin motii yunnus. Iyamu daya samu yana jin ya toshe masa duk wata damuwa ta rashin samun haihuwa. Munyi wata irin shaquwa taban mamaki,irin shaquwar da idan ka kallemu zaka dauka mahaifa daya muka kwanta,ko bacci baya iya rabamu,komai namu daya,hatta da abinci cikin kwano daya mukeci. Daidai da dan kunne idan wannan ta canza sai wannan ta canza nata,wata iri shaquwa taban mamaki da ba zaka taba ganin d'aya bakaga daya ba,komai tsanani komai runtsi. A haka muka taso da wata mugun qaunar juna,ko ciwo daya keyi to hankalin sauran ya tashu,tare ake ciwon nan,dame ciwon dame lafiyar gaba daya...." Sai nanay ta sauke numfashi tana sakin wani murmushi me sanyi,wanda ya tabbatarwa haisam ta tuna da quruciya ne. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "A haka muka girma,muka zama yammata sosai.....abun burgewar kowanne namiji,kowa kuma qoqarin mallakarmu yakeyi,saidai wani ikon Allah nice naketa samun manema a sannan,amma naqi yarda da kowa,saboda alqawari muka yiwa junanmu babu wadda zatayi aure tabar 'yar uwarta. To amma da yake shirin Allah daban yake dana mutum,ba zato Allah ya kawo sarkin jimma kakanka kenan,ya kuma ganni,ya yiwa d'ansa yarima me jiran gado kamu,take mahaifina ya bashi ni,ban ganshi ba,bai ganni ba,amma saina samu kaina da qin musawa umarnin motii" Ta sake kai gabar maganar tana murmushi,murmushin da ya tabbatar ya boye abubuwa masu yawa data tuna. Samun kansa yayi shima da murmusawa kadan,kwanyarsa tana dauko masa banbamcin tarbiyyar yaran yanzu da na daa......tunaninsa yana kawo masa dauki ba dadin da aka dinga yi watanni kadan tsakanin akhnan da mahaifinta,sai ya zame tunanin ya watsar yana maida hankalinsa ga nanay. "Na haifi yayanka bai jima ba ya rasu,ina da cikinka kuma rigima ta barke tsakanin mummu falmata da mahaifin SAFEENA ta" Ta dakata kadan tana shan numfashi,dakatawar daya tabbatar akwai wani abu cikin qirjinta da take hadiya da bai wuce mata ba har yau. "Wannan rigimar ita ta zama sanadi na biyu da har yau ban sake ganin safeenata ba......ban sake ganin usainata ba safiyya ba,ban kuma sake kwana na tashi da farinciki cikakke ba saboda rashinsu cikin rayuwata ba tare dana shirya ba......ya dage sai an bashi safeena ya mata miji,motii ya bashi haquri akan ya bari ta zabi mijin da takeso,da yaga ya dage yace ya bashi dama yayi bincike,motii ya bincika yaga cewar akwai matsala shigar safeena wannan gidan,matansa biyu,saidai matarsa ta biyu gagararriya ce,banda uwargidan tsayayya ce da tuni itama ta fitar da ita,motii yayi qoqarin fahimtar dashi amma ya rufe idanu,duk da motii yana qarfin ikon da zai hanashi ko ya tursasa janye auren amma baiyi haka ba,yace mahaifi mahaifi ne,ya bashi safeena ta,aka aurar da ita ga mutumin da har yanzu bansan waye ba,shekara daya da auren ya saketa,a ranar da motii ya cika kwana bakwai da rasuwa. Bamusan me ya faru ba,ranar da motii ya cika kwana arba'in,muka wayi gari ba mummu falmata ba safeenata ba usaina safiyya......ba irin neman da ba'ayi musu ba har yau har kwanan gobe bamu sake jinsu ko ganinsu ba.....duk da daga baya malamai da yawa suna fadin kurciya akayi musu. Hankalin momma balkes ya tashi,mahaifiyata a sannan ta dorama kanta karan tsana.....ta dinga ganin kamar kowa zaiga ita ta kora falmata da yaranta saboda gado,amma saboda kusan kowa yasan zaman da sukayi masu zato da zargin kadanne,don dama shi dan adam baka amintar da kowa da kowa lokaci guda. Bayanai daga baya sunyita fita da rade radin kishiyarta ta biyu da tayi silar fitarta a gidan ita ta jefeta da mummunan asirin......qabilar data fito a ciki qabila ce mafi hatsari a nan qasar,ana aurensu ne kawai saboda an camfa aurensu yana zuwama mutum da arziqi,shi yasa mijinta ya kasa rabuwa da ita. Ban sakeji ta bangarensu ba haisam.....ban sake gani da jin komai daya shafesu ba tsahon wannan shekarun,suna raye?,ko dukkansu sun mutu?,ban sani ba muhammad" Nanay ta qarasa fadi muryarta a karye sosai. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 51* Sosai yaja wani irin numfashi yana lumshe idanunsa da kyau. Adadin bugawar da kansa keyi yana qara gudu. Wani irin birkicewa yakejin tunaninsa yanayi tare da hade tunanikan nasa guri guda. Tabbas wannan matar me suna safeena,kuma obboleettii lamaan din nanay dinsa(twin sister din nanay dinsa). A zahiri Kawann ne yake gani masu tarin yawa kwance saman fuskar wadda take kamanni da fuskar Akhnan din adan qanqanin ganin da yake mata,sannan ga wani kamannin ta wani bangaren kuma da suke bayyana kansu da wannan kamilar dattijuwar......matar da koda yaushe kamalarta ke mata kama data nanay dinsa wato MORSA SAFIYYA. Duk da haduwarsa da ita cikin gidan idan har yayi yawa bazai wuce sau biyar ba,ba ma'abocin iya kallon fuskokin matan al'umma bane saboda kalar nashi kishin da yake dashi,amma duk da hakan yasan akwai kamanni na gasken gaske cikin wannan labarin. Idan har hasashensa ya tabbata kenan,morsa safiyya ita dinma 'yar Ethiopia ce?,jinin sarautar GUMMA?. Amma hakan sai bai nuna a al'adunta da yanayinta ba,ko don hakan yana da nasaba da barin qasar da tayi shekaru masu yawa?,shi yasa ta juye gaba daya ta koma 'yar agadez ba'abzina ta gaske?. Dukka wadannan tunanin nasa hasashe ne.......bashi da tabbaci ko daya,ballantana ya lasawa nanay xuma a baki. Bayason ya bata tabbacin abinda ba haka yake ba. "Idan na zama silar haduwarki da obboleettii lamaan dinki nanay......wane kyauta zakimin?" Ya furta da wani sassanyan murmushi akan fuskarsa,yana jin yaqini da imanin wannan karon zai sauka daga kan layi......wannan karon zai sauka kadan daga layin aikinsa don bawa nanay farinciki. Wani irin kallo take masa,wani irin kallo dake dauke da wani kwantaccen farinciki,wani irin kallo daya bayyana adadin ruwan hawaye me yawa cikin qwayar idanunta. "Na gode Muhammad......koda baka hadani da obboleettii dina ba na gode maka,dama can kai din yaro ne daya zama sanyin idaniya ga iyayensa,kai din me share hawayen iyayensa ne da sanya farinciki a zukatansu,ba shakka rayuwarka zataci gaba da albarka......amma saidai inaji a jikina zai wahala ace safiyya ko safeena suna raye......zai wahala ace suna raye zasu kai wannan lokacin basu nemeni ba,koda asiri ne zai sakesu zuwa yanzu tabbas" Ta qarasa maganar tana qoqarin maida hawayen don kada ta raunata masa zuciya. Idanu kawai ya zubawa nanay din yana karantar zurfin ciwon dake cikin zuciyarta,can qasan ransa ya cikashi da addu'a da fatan ubangiji ya taqaita masa jarrabawa game da soyayya da qauna akan komai ma. "Shuru ba shine yake alamta mutum babu shi ba nanay,ki yarda dani kuma kimin fatan alkhairi,na miki alqawari indai suna raye zan kawo miki su......amma kafin sannan qoqari daya zakiyimin" Ya fada adam apple dinsa yanayin sama da qasa alamu ya hadiye wani abu. Yayi bala'in qin jinin zalunci,baya qaunar zalunci ko kadan a rayuwarsa,da wanna dabi'ar yayi sabo tun haihuwarsa,wannan dalilin.....wannan dabi'ar ta sanya ya tashi da KISHIN QASARSA da kuma cikakken qwarin gwiwar shiga NATIONAL INTELLIGENCE SECURITY SERVICE da yake ciki a yanxu. "Ina jinks muhammad" Ta fadi yana dauke hawayen daga fuskarta. Hawayen da haisam din yake jinsa kamar d'igar dalmar wuta saman ruhinsa. Duk wani hawaye na d'iya mace ciwo yake masa a rai,koda na wadda bai sani bane.....yana kallon kukan 'ya mace a matsayin qarshen rauninta......qarshen lafazin dake danqare a zuciyarta wanda baki bazai iya fadinsa ba......yana kuma kallonsa a abu mafi girma daya kamata aduba ga diya mace.....ballantana kuma nanay dinsa.....nanay dinsa da yakejin wani sashe ne na rayuwarsa gaba daya. "Sunan mijin da safeena ta aura kawai nakeso na samu......sai sunan da kuke kyautata zaton shine sunan qasar mumma falmata". Ya qarasa maganar yana damqr haqoransa guri guda cikin dabara,saboda yadda yakejin kamar yana shirin fita daga hayyacinsa zuwa lokacin har idanunsa suna dan lumshewa kadan. "Kana lafiya muhammad?" Nanay ta tambayeshi cikin tsananin kulawa. Murmushin qarfin hali da yabawa da tarin qauna da tsananin kulawar nanay. Duk yadda yaso ya boye mata abinda yakeji a jikinsa amma sai da yayi noticing wani abu?. "Lafiya lau nanay" Ya fadi yana sake qarfafa mata zuciya. Shuru tayi na wasu mintuna sannan ta furta. "Alhamdulillah...." "Muhammad shekarun sunja sunyi kuma nisa da yawa,amma zan gwada neman zenabu......aminiya ga mahaifanmu,ban sani ba ko falmata ta taba gaya mata sunan mijin,duk da tsufa ya risketa,amma kyautata zaton zayayi wahala ta iya tunawa" "Zata tuna nanay......zata tuna in sha Allah,ki gwada" "Zan gwada muhammad......yankin da falmata ta fito muna kiransa da birnin Aiir". Ta qarasa fada tana xube idanunta kan haisam din. Haka kawai a karon farko bayan rasa dukkan wani fata da buri a yau ya sanyata tana jin fatanta da burinta yana dawowa. "Na miki alqawari nanay" Ya fada yana yanke kiran saboda yadda yakejin komai nasa yana masa nauyi,yanke kiran kuma da yayi saiga saqo daga headquarter dinsu daga amintaccen me bincikensu. "Almaz......gudajjen yaron da har yanzu YATAAMAA ORPHANAGE HOME ya kasa tsinto inda yake,bayan sun raineshi na shekaru ta hannun wata mata data kawoshi". Daga qasa tarin nau'ikan hotunan almaz dinne daban daban. Wani irin nauyi yaji yana sake danneshi,yana shirin bude sauran hotunan da basu budu ba da hanzari video na sultane ya fado masa,sai ya canza akala ya bude hannunsa yana dan rawa kadan. Yana zaune cikin haram na makka daura da ka'aba yake bashi saqon,cikin kamalar nan tasa da dattakonsa. Godiya sosai yake masa da wani irin yanayi da yasa zuciyar haisam ta qara nauyi. "Nayi amanna da dukka kulawarka da jagorancinka,na tabbatar ban damqa amanar mutanena da iyalina hannun da zai gaza kula dasu ba,ina da labarin komai ya gudana daidai alhamdulillah,bansan da wanne abu zan gode maka ba,na yaba sosai muhammad na yaba........abinda kawai ya rage saqo na qarshe shine......kayi qoqarin damqa akhnan hannun mijinta bisa amana.....banaso ta wuce kwanaki uku a gidana kowanne kalar biki zasuyi......" Dishi dishi ya soma gani,a hankali yaji numfashinsa yana quntata a qirjinsa,tamkar qofofin fitar numfashinsa aka tsuke ko aka rage yawansu. Hannunsa ya miqa yana b'alle button din wuyan rigarsa,a hankali ya kifa kansa saman table din yana jin yadda ganinsa ke sake dishi dishi. Da sallama maleek ya shigo,amma yanayin da yaga haisam din ya daga hankalinsa. Da hanzari ya qaraso yana qoqarin daga fuskarshi. "Na fada baka da lafiya....amma ka musa hakan......" Maleek din ya fadi hankalinsa yana tashi. Da manyan idanunsa da suka lumshe a hankali ya dubi maleek,sai ya miqawa maleek hannu,ya bashi nasa hannun ya dagashi daga gurin,yana riqe dashi suke takawa a hankali suna fita a dakin. Bai fahimci likita ya kira masa ba sai bayan ya kaishi daya daga cikin bedrooms dinsa,likitan ya shigo da kayan aikinsa yana ajewa a gefe idonsa akan haisam din. Ruwa kawai ya fara qoqarin saka masa saboda yana zaton mugun zazzabin dake jikinsa ya qone ruwan jikinsa,sai daya kammala sannan ya dauki jininsa yace zaije yayi gwaji ya dawo don ganin maganin daya dace yasha. Komawa gefe maleek kawai yayi ya zauna yana duban fuskar haisam wanda bacci ya daukeshi. Mamaki can qasan zuciyarsa da wasu lissafe lissafe,akwai abubuwa da yawa dake kai kawo cikin zuciyarsa. Baisan lokutan daya dauka ba yana gadin haisam din har zuwa sanda likitan ya shigo wannan karon shida omar ne. "Banga wani matsala cikin gwajinsa ba gaskiya,nayi tunanin malaria ne ko wani abu na daban,amma ba ita a cikin jininsa......abinda kawai nafi tunani shine stress ne yayi masa yawa,so yana buqatar ya huta sosai,yayi isashen bacci,idan zai yuwu kada ya sake wani aiki me wahala ko dogon tunani da zai kawo masa damuwa ko jigata.....Allah ya bashi lafiya" Likitan ya fadi yana hada kayayyakinsa. "Mun gode" Maleek ya fadi yana bashi hannu,sannan ya ciro wayarsa ya kira su beeno yace su sallameshi su maidashi asibitin daya daukoshi. "Wai garin yaya?" Omari ya tambayi maleek damuwa fal a fuskarsa yana zama saman bedside drawers din dake gefan gadon haisam din. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Bana ce ba omar......kasan halinsa wani lokacin da zurfin ciki sosai......kusan kwana biyar kenan nake ganin bashi da lafiya,baice komai ba har sai dana gaji da ganin canzawar yanayinsa na tambayeshi,sai lokacin yake fadimin wai baya jin dadi ne.....to kuma dazun na barshi a study room dinsa mun fita dasu beeno neman likita ya dubashi,tunda nasan halinsa tun a school,muna dawowa na sameshi yana duba saqo kaman zaiyi loosing conscious nasa..." "Saqo kuma?" Omar ya tambaya cikin mamaki. Kai maleek ya jinjina "Yes.....don ban tsaya ma rufe masa system din ba......coz nasan aikin naku da tsari,kada naje naga sunana cikin suspect" Ya fada yana dan murmushi. Shima omar murmushin ya maida masa,sai ya miqe yana fadin. "Ina zuwa" Ya taka yana fita a nutse. Mintina biyar omar ya shigo da system din a hannunsa,ba personal system dinsa bane dake dauke da muhimmam bayanai sosai bane,wannan din itace ta biyu,akwai bayanai a cikinta amma baikai ta farko ba. Da idanu maleek ya bishi sanda ya dora system din saman sofa bed,yayi playing video din sultane. Dakin ya dauki shuru har suka kammala gani kafin su janye idanunsu suna kallon juna lokaci guda. Shuru ya ratsa dakin ba wasu mintuna,kafin qaramar dariya ta subuce musu lokaci daya. "Me kakewa dariya?" Omar ya tambayi maleek still da murmushi kan fuskarsa. "Kai me kakewa dariya?" Shima maleek ya tambayi omar da wannan salon na tsohuwar abota da aminci dake tsakaninsu,wanda sukan zama cikin zolaya da sakewa a junansu a duk sanda suke tare. A hankali fuskar maleek ta koma daidai,ya koma prince maleek dinsa,wannan ya sanya omar shima tattara nutsuwarsa guri daya. Numfashi maleek ya sauke,a nutse ya fara magana. "Farin shiga ne captain.......baisan daga yadda komai yake iya farawa ba......ba dole bane soyayya ta fara daga jin soyayya a zuciya ba......takan iya farawa daga fada.....rashin jituwa,tausayi da sauransu.....wani lokaci ma daga qiyayya take farawa,daga sanda na fara ganinta ido da ido.....bayan labarai na dabi'unta da naji na tabbatar itace kalar matar da haisam yake lalube a wata duniyar......gata a wannan duniyar tana rayuwa koda shi baisan hakan bane......amma baqo ne shi ta wannan feeling din dake samun zuciya,shi yasa ya kasa banbamcewa,dabi'unta da yake ganin basuyi masa ba sune su saamee suka rasa a tare dasu,wannan shi ya sanya suka gaza samun bude koda qofar farko ta zuciyarsa......inda ace irin dabi'un su saamee kawai sun wadatar dashi daga zabar matar aure......da tuntuni ya zama mijin saamee tunda dadewa.....ko ita ko......" "Menelik" Omar ya qarasa masa da hanzari,don ya hango yadda kalaman maleek suka hau kan saiti sosai,yaji kuma yana gamsuwa dasu d'ari bisa d'ari. "Yes....menelik.......so yanzun kuma,bai fahimta ba......zai mutu saboda ance a kaita gidan mijinta,bari ya farfado kaji bayaninsa bazai taba bari yayi daidai da harsashena ba". Murmushi Omar ya saki yana maida dubansa ga fuskar haisam din dake bacci peaceful,saidai yana jin wani rashin dadi da komai yazo a baibai,yana kuma jin wani iri daya kasance haisam din bai fahimci komai ba. "Yanzu meye abunyi?" Omar ya tambayi maleek yana dubansa. "Babu" Ya bawa omar din amsa kai tsaye,abinda yasa omar din xuba masa ido yana dubansa. "Eh,matar wani ce ita yanzun,kuma shine ma ya daura auren" Maganar maleek ta fita da wani sauti na daban,sautin daya haifar da shuru a cikin dakin,dukkaninsu kamar an kwashe sauran kalaman bakinsu. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 52* ★★Zaune yake saman rocking chair wadda ke ajiye cikin qawatacciyar harabar dake gurin da aka qawata da nau'in shuke shuke daidai da yadda nature dinsa yake nason tsirrai. Gefansa dan mini table din dake dauke da tarkacen kayan coffee kamar yadda yake a cikin jini da al'adar duk wani dan qabilar oromo tsananin qaunar coffee kamar rai da rayuwa. Shima nasa hannun riqe yake da mug dake tururi,yana sipping coffee din a hankali yana motsa rocking chair din zuwa gaba da baya tana dan lilo kadan kadan dashi. Tun shekaran jiya yana ciki sai yau ya fito don ya samu fresh air da yakeso ta sake buda tunaninsa da kyau,ya kwanta ne kawai saboda ya faranta ran omar da maleek daketa dawainiya dashi,amma yana kwance ne yana jin tarin matsaloli danne da kansa da kafadunsa. Yanaji a jikinsa aski yazo gaba goshi wanda hausawa ke cewa yafi zafi,yana ji a ransa komai yana kan gabar warwarewa. Ba yadda baiyi su bashi system dinsa ba da sauran wayoyinsa amma sunce sai ya gama warwarewa,shi yasa dole a yanzu ya tako ya fito,bawai don Jikinsa ya gama qwari ba. Hasalima duk da magungunan da yakesha dare yanayi yake jinsa cikin wani quntacewa da zazzabi me zafi,sassaucin abun ma'abocin tsaiwar dare ne,da zarar kuma ya fara sallarsa yake jin sassauci yana zuwa masa a hankali. Wani abu yakeji ya qulle a qirjinsa a duk sanda ya tuna fuskar almaz a wancan ranar......sannan ya hasko fuskarsa saman takardun gidan marayu,gidan marayun da suka bada tabbacin an fita dashi baa sake ganinsa ba,ba'a kuma san inda yake ba har yanxu. Abu daya zuciyarsa ke maimaita masa tun daga wancan ranar ZAITUNA ce ita shigo dashi agadez.....ita ta kawoshi ta kuma aurawa AKHNAN shi. Bayajin auren akhnan shine damuwarsa,damuwarsa shine yadda ya qulla auren da ya tabbatar AKWAI ZARGE CIKIN NADI. Da wacce fuska zai kalli sultane yace ya cika amanar daya bashi?,da wacce fuska zai.kalli sultane yace ya kare amanarsa?,da wanne harshe zaiwa sultane bayani a lokacin da GASKIYA ZATAYI HALINTA?. Ta yaya zai kare rayuwarta daga wannan baqin duhun daya tabbatar nata idanun sun makance ba tare da ita tayi zaton yana da wani interest na shiga rayuwarta ba?......ta yaya zai fahimtar da ita zuzzurfan ramin da take dab da fadawa ba tare data dauka cewa yayi ne don ITA ba?. Tafiyar da yaji a bayansa ya sakashi ajiye mug din sannan ya waiwaya a hankali. Omar ne a gaggauce maqale da waya a hannunsa. "Yes bobbo.....gashinan" Ya furta yana qarasowa gaban haisam ya miqa masa wayar,sannan yaja kujerar dake facing dinsa ya zauna. Yadda yaga omar a gaggauce yasan bobbo muhammad dawud ne,tun baice komai ba kuma yasan kiran gaggawa ne,sai ya saka wayar a kunnensa cikin cikakkiyar nutsuwarnan tasa yayi masa sallama. "Wa'alaikumussalam muhammad" Ya amsashi,har qasan ransa yana jin haisam din na daban ne,daidai da yanayin maganarsa kadai zai tabbatar maka da tambarin nutsuwar dake tare dashi. "Barka da warhaka obbo" "Barka kade captain muhammad.....ya jikin naka?" "Alhamdulillah bobbo,ba wani ciwo bane sosai". Murmushi kadan muhammad dawud ya saki. " Na jaddadawa omar su kula dakai sosai,don bansan da wanne baki zan gayawa motii gudan jininsa bashi da lafiya ba". "Na warke bobbo" Ya amsa masa murmushi can qasan zuciyarsa yana subuce masa,duk da hakan bai bayyana a fuskarsa ba. "Ma sha Allah......Allah ya qara lafiya.....naje umara muhammad,inata addu'akan aikinmu.....amma yanayin yadda naga abubuwa suna sake budewa da fitowa jikina yana ban komai yana zuwa gangara ne,komai yana zuwa qarshe,sati daya kacal zanyi na dawo gida......" "Allah ya dawo dakai lafiya" Ya Fadi a nutse. "Muhammad.....lallai Allah ne kadai yakeson Ethiopia da rahama ba qabilar oromo ba ba jimma da yankunanta ba.....ba iyayenka kadai ba da Allah yasa aka haifeka a cikinmu,sannan yayi ma intelligence security service baiwa daya sanya ka daya daga cikinmu......muhammad binciken daka tursasa ayi akan tsohuwar matar AJANI ya fito,ya kuma bada sakamakon bacewar da akace tayi ba bata tayi ba,da qafafunta ta fita daga Ethiopia ta barauniyar hanya......ta wani sashen kuma sai wani binciken namu ya nuna mana TA MUTU a wani asibiti dake daura da YATAAMA ORPHANAGE HOME. Ga certificate dinta nan na mutuwa,bayanan binneta dama kabarinta,haka 'yan uwanta dukka kowa yayi amanna da mutuwarta,don har zaman makoki anyi mata......kaga kawai ayar tambaya kenan akan matar ita kanta?". Tunda muhammad dawud ya fara magana jinjina kai kawai haisam yakeyi,tako ta ina ta share dukkan wata shaida ko alama da zata bayyana itace ta qulla kisan...... "Bobbo" "Muhammad" Ya kira haisam yana sauke gauron numfashi. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Mutumin da muke fadi tashin nema......ba bisa radin kansa ya kashe ajani ba.....daukarsa haya akayi.....sakashi akayi,matar ajani kuma da gaske ita ta saka ayi kisan....kuma tana raye,tabbas tana raye" Haisam din ya fadi kai tsaye. "Me yasa kace haka?". " Lokaci.....lokaci nakeso ka bani.....zan tabbatar maka da hakan,wacce qasa ake hasashen zata iya tsallakawa?" Haisam ya tambaya kai tsaye yana komawa ya zauna sosai saman Rocky chair din. "Qasashe biyar ne muke da iyaka dasu,Eritrea,Djibouti,Somalia,kenya,south sudan,sudan......" "Wannan shine zai sanya ta tsallakesu gaba daya,taqi fadawa ko daya daga cikinsu saboda bincike zai iya cimmata.....zata wuce kai tsaye ne daga east Africa zuwa South africa wato NIGER......Tabbas ita da duk wanda ya jibanci lamarin SUNA NIGER AGADEZ bobbo" Dif muhammad dawud yayi,yana sake jinjina girman baiwar da Allah ya yiwa muhammad haisam din. Gaba daya ya zube lissafinsa fes .....sai a yanzun da haisam yayi magana yaga tabbas maganar haisam dince akan layi. "Ma sha Allah,ma sha Allah,Rabbiin si haa eebbisu(ina fatan Allah ya albarkaceka)" Ya fadi da harshen oromo,jikinsa yana sake sanyaya da tarin baiwar haisam din.....wani farinciki yana sake lullubeshi. "Tabbas zanyi alfahari kafin na sauka daga shugabancin NISS ace a zamanina qasata ta kubuta daga wannan tuhumar.....qasata ta binciko wannan me laifin.....qasata ta hukuntasu" "Zan saka kayi wannan alfaharin tabbas bobbo" Ya furta a nutse yana zare wayar gami da miqawa omar. "Ka daukomin wayoyina" Ya bawa omar umarni nakai tsaye idanunsa cikin nasa don kada ma ya masa musu,saidai duk da haka saida omar ya kauda kansa kadan sannan yace. "Ka fara maganin abinda yake damunka mana haisam kafin ka magance matsalar qasarka." Yakai qarshen maganar sanda maleek ke qarasowa dauke da tray. Yau din duk tari sarautarsa da mulkinsa.....amma abota ta gaskiya ta sanya da kansa yake hidimawa haisam. Shi kansa haisam da kallo ya bishi yana mamakin yadda ya zubda duk qasaitarsa da mulkinsa saboda abota ta gaskiya,gefe daya kuma maganar omar tana daure masa kai. "Akwai wata matsala ne da nace maka ina da ita?" Ya jefawa omar tambayar yana tsareshi da ido,saidai sam.omar yaqi kallonsa don yasan zurfin gubar kallonsa idan yaso. Ga mamakinsa sai amsa ta fito a bakin maleek daya samu nashi gurin zaman daura da haisam din. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 53* "Damuwar da za'a barta cikin qwaqwalwa tafi kowacce kalar damuwa cutarwa,kasan da haka.........me yasa ka gaza fahimtar ka fara jin qaunarta cikin zuciyarka?......me yasa kayi fatali da komai?". Sosai maganan maleek yazo masa a bazata,ya kuma zo masa da wani irin yanayi da kai tsaye zuciyarsa ta qaryatashi. "Wace kenan?" Yayi tambayar da alamun rashin fahimtar maganar maleek din na gasken gaske. Idanu maleek ya janye,yana mamakin yadda haisam keta yin komai kaman baisan komai ba. "Ka daina pretending mana haisam.....akhnan nake maka magana" Maleek ya fadi kansa tsaye yana dubansa. Manyan idanunsa ya qanqance ciki kadan,yana ci gaba da duban maleek din. "Maleek?.....matar aure?....matar wani?,kasan inda matatace aka kama wannan hirar a kanta kowa zai iya rasa wani sashe na jikinsa?" Yayi maganar dake nuna da gaske ne abinda yake furtawa akan harshensa shine har cikin zuciyarsa. Murmushi kadan maleek ya saki yana sake karantarsa da dukka ilimin karantar halayyar dan adam din da yake dashi. "Matarka ce.....amma kayi sake kaje ka aurawa wani.....type dinka ce haisam.....itace kalar matar da kake nem......" "Stop it mana maleek!" Haisam din ya fadi da husky voice dinsa,sannan yayi shuru yana jin wani abu me kama da rai a jikinsa yana motsi. "Bakaji me na fada ba maleek?......matar wani ce.....matar aure ce,sannan a yanzun bakaga kalar aikin da yake gaba na ba?.......rayuka ake dab da rasawa amma zancan soyayya kake maleek?,soyayya fa?,a irin wannan yanayin?,a irin wannan lokacin?" Ya qarashe maganan muryarsa tana sanyi ba kaman dazu ba. Idanu maleek ya janye yana lumshesu sannan ya girgiza kai sosai. "Is okay.....shikenan......amma bayan hankula sun kwanta naka bazai taba kwanciya ba.....bayan ka kammala wannan aikin a sannan ne zakasan girman aikin dake gabanka,sabon babi zaka bude captain" Maleek yakai qarshen maganar yana miqewa tsam,ya dauki mug daya na coffee kawai ya soma takawa yana barin gurin. Wani abu yakeji yana yamutsawa a kansa da qirjinsa......yana kuma qaryata maleek karon farko a dukkanin wani hasashensa......yanaji cewa abinda ke gabansa ya danne abinda maleek din yake magana akai. Ta yaya zaiso yarinyar da bai ganta sau goma ba a rayuwarsa?,yarinya da tako ina dabi'unta basuyi masa ba?,yarinyar data shigo ne kawai cikin aikinsa da tsarinsa?,uwa uba kuma MATAR WANI?,Duk da yana qoqarin ganin WAYE WANIN nan kafin takai ga zuwa gidansa?. Yana gudun isarta ga hannun mutumin da nan gaba dashi sultane zaiyi kuka......yana gudun shiga cikin tsarikan mammina da yayi imanin ta gama hada dukkan wani target dinta. Ya tabbatar da cewa wannan auren SHIRYASHI AKAI akwai tsararru kuma shiryayyun manufofi a qarqashinsa......ta yaya zai bari daidai da taqi daya ya zamana yana da gudunmawa wajen tabbatuwar tsarinta masu rushe rayuwa?. "Bishi" Yace da omar kansa tsaye yana hade dukkanin girar sama data qasa tasa. "Yes sir" Omar ya fadi kawai yana yunqurawa gami da miqewa yana danne wani abu me kama da dariya can qasan ransa. Yana tare da maleek a wannan hasashen,daga inda yake yana ganin zurfin nazarin da haisam din ya fada,zurfin nazari kuma yana faruwa ne ga haisam a bisa dukkan abinda ya bawa muhimmanci ne kadai. *TAMIM* *_MABUDI/MAFARI_* _YANZU QADDARAR ZATA FARA_ A dukkan wani gaba ta jikinsa da jini yake iya wanzuwa a gurin....a dukkan wani tsoka dake da alhakin ji(feeling) yana jin wani gagarumin tashin hankali yana saukar masa. Ya bude yatsun hannunsa......yayi qididdigen shekarun daya dauka yana bauta mata har sau ba adadi......yayi lissafi har baisan sau nawa ba......ya sake maimaita lissafin har yana bacewa daga qa'idarsa. Yayi YAKANA yayi JURIYA ya kuma KAUDA KAI daga kan yarinyar a dukkan shekarun. Ya adana ya kuma tattala dukkan wani KWADAYINSA duk da irin tarin damarmakin da ya samu,yake dashi akan tabbas ZAITUNA zata fahimceshi tun bai furta abinda ke ransa ba......zaituna zata fahimci yaren cikin idanunsa da zuciyarsa ta kuma tattala masa TUKUCINSA a sanda zai buqaci haka. Yayi zaton shiga tsakanin burin TUKUICINSA mutuwa ce kawai,wadda yayita addu'ar kada ta daukeshi ba tare daya cika wannan burin nasa ba. Yayiya qoqarin sake tunzura wutar nesantata da kowanne d'a namiji,a fili da bayyane,ya samu nasarori masu yawa,ya kwanta duk wata qura da tashin hankali sun biyo ta kansa,sai yanzu kuma ya zamana cikin HASARARRU?. Qafarsa ya buga,yana jin wani qarfin zuciyar tunkarar duk wani abu da zai masa silar rasata ko nesantata dashi komai girmansa......ballantana almaz din da ta kowacce hanya yana da qarfin ikon ruguzashi ya kuma ruguza komai cikin sauqi. "Giwa na kiranka shugaba" Yaji an furta daga bayansa cikin girmamawa. Waiwayowa yayi ya zuba idanu akan bawan. Bawan da akayi domin ya zama photocopy dinsa,bawan daya dauka ya mallaka masa irin sunansa. "Yaushe ta buqaci ganina?". "Tace yanzun nan,don tana da baqin da take sallama". Siririn tsaki yaja,yana jin kamar yabi shawarar da daya sashen na zuciyarsa suke bashi,saidai yaka tuna da wani abu wanda shi kadai ne yake masa shamaki. Kewaye yaron yayi ya fara takawa ta gabansa,shi kuma ya rufa masa baya cikin matuqar biyayya. *MAMMINA* Idan kaga yadda take hidima cikin jama'arta,gami da kai kawo a cikinsu,ci gaba da rabon kyautututtuka masu nauyi da girman gaske ga duk wanda Allah ya tsaga yana da rabo. Ta bude qofa sosai ga.masu son ganinta da masu son gaisheta saboda yanayin farincikin da take ciki,tana so kuma ta sake jaddadawa kowa,kowa kuma ya shaida cewa da gasken gaske tana auren diyar da tafiso duk duniya ne sama da kowaaka. Daga yanayin giftawar yalwa ta tabbatar da isowar tamim,don haka ta miqe tana bada umarnin dakatar da ganinta har sai zuwa gobe. A yau akwai abubuwa da yawa da takeso ta dasa harsashinsu,harsashin da zai zama wani tushe kuma sanadin da zai qarasa tarwatsa rayuwar dukkan wani mutum daya kasance ahali ko tsatson diory hamani......zai qarasa sanya giyar takaici baqinciki da bacin rai cikin ruhi da gangar jikin duk wani ahalin safeena......giyar bacin ran da zata yita bugar da kowannensu har izuwa numfashinsa na qarshe. Yana tsaye saman qafafunsa,yana kuma goye da hannuwansa a qirjinsa,saidai takun shigowarta ya sanyashi daidaita nutsuwa da yanayinsa zuwa yanayin da suka saba. "Zauna" Tace da tamim bayan ta zauna. Zama yayi kaman yadda ta buqata,saidai kuma zuciyarsa tana gaya masa a irin wannan lokacin kamata yayi ace darajarsa ya d'aga daga wadda yake kai yanzu zuwa mataki na gaba.....matakin daya tabbatar banda tayi masa shigo shigo ba zurfi da qudundune shine yanzu akai,ba wancan tsintaccen magen ba almaz. "Ina fatan gidan ango ya kammala ko?" A nutse tamim ya jinjina kansa,yana jin wani abu me ciwo yana tsaye masa a wuya "An kammala komai" "Yayi kyau.....inajin dadin aikinka tamim qwarai da gaske......a bisa al'ada yau zataje ta kwana a gidan,gobe da asuba ya rakota da kanshi.....to amma nasan abune me wahalan gaske ta yarda da hakan,don haka na yanke shawarar fara qulla kusanci a tsakaninsu....." Saita dan dakata tana sanin murmushin dake nuna zallar farinciki. "Zai bita Niamey a satin nan kamar yadda ta tsara zata tafi,duk da har yanzu ban yarda zai iya karbarmin ragowar kamfanin sahel ba......amma tafiyarsu tare nada tarin alfanu masu yawan gaske......a yau zan tilasta mata ganawa dashi koda ba zata shiga gidanta ta kwana ba......akwai maganganun da nakeso yayi da ita,na sanya an rubucesu a killace....duka hirar da zaiyi da ita yau a killace take a rubuce,banason ya dara daga abinda na tsara. Yana da kwanya fiye da yadda kake tunani,tabbas nasan zai haddaceta kamar yadda nakeso,kaje masa da ita,da yammaci ina buqatar a rakoshi cikin ayari.......ya zamana cikin shigar alfarma ta gasken gaske......ka tunasar dashi,kada ya nuna zalama ko rawar kai.....kada ya nuna mata damuwa ko kulawa me yawa.......a jininta ta tsani wadannan dabi'un.....amma a halittarta tanason namijin dake dasu". Mammina takai qarshe tana bashi takardar dake ajiye a gefe tuntuni. "An gama....cikar umarninki shine muradinmu" Ya fada da zallar girmamawa yana hade hannuwansa guri guda. Murmushin farinciki ta saki tana gyada kai. "Saura kadan na mallaka maka shugabancin gidannan tamim......yadda kayimin rana da alfanu masu yawan gaske,dole kaima ka amfana daga falalata me fadin gaske" Ta fadi da gasken gaske saboda jin dadin yadda ko sau daya bai taba jawo mata asara faduwa ko musanta umarninta ba. Kai ya jinjina mata yana jaddada godiyarsa,saidai kuma abinda ke kaikawo a zuciyarsa yasha bambam da tazara me tarin yawa da abinda ke bayyane a zahiri. Iska ta zuqa me yawa tana fesar da ita,har yanzu murmushi yaqi gushewa daga kan fuskarta,saita kira yalwa da dama ba nisa tayi ba. "Ki daukomin alkyabbata,zani gurin akhnan". (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "An gama" Ta amsa mata tana fita da sassarfa. D'ai d'ai take takawa tana kallon gidan,da yadda ko ina dokar haisam ke aiki duk da yana kwance baida lafiya. A baya qona mata rai abun yake,amma a yanzun saita saki dariya hankali kwance. Tana wassafa yadda aikinta zai sauka a kansa hankali kwance bayan ta ga tabbatuwar dinkewar alaqa me danqo tsakanin akhnan da almaz. Taci alwashi ta kumayi rantsuwa tabbas saita sanyashi ya kwashe kayansa cikin dare yabar agadez,don ko guduwar tasa bazaya iya bari kowa ya sani ba saboda munin abinda zata sanyashi ya aikata. Da wannan hasashen ta isa sassan akhnan din hankali kwance cikin tarin girmamawa da dukkan hadiman sassan suka zube suna bata. *AKHNAN* Kwanaki ukun nan da suka shude gaba daya bata da aiki sai kwanciya,bata da wani aiki sai kebe kanta ita kadai. Bata qaunar wata hayaniya,bata son doguwar magana ko dogon surutu. Kusan salla ce kadai ke tayar da ita,sai wani lokaci da takan bude wani sashe na balcony dinta. Shima ba kasafai ba,don bata son ganin kowa kamar yadda batason kowa ya ganta. An shaida mata saqon morsa safiyya harma da Nannie dakeson ganinta,amma tayi biris da aiken kowa,kamar yadda taqi yarda kowa ya ganta. A yadda take jinta ma gaba daya ko mammina ke son ganinta saidai tayi haquri,kawai tana qoqarin digesting din komai ne,tana qoqarin haqurqurtar da zuciyarta nema tayi accepting wai an daura mata aure......wai ta zama matar aure....mafarkin da take hangoshi da nisan gaske gashi ya cimmata a lokaci qalilan. Tayi juyi tayi juyi,tayi tsaki har batasan adadinsa ba. Yanzun meye ribar wannan abun da sultane ya tursasa tayi?. Wannan aure da suka dage a kansa meye ne ribarsa?. Ita bata hangen komai a cikinsa sai wata irin rayuwa maras 'yanci,sai wata zallar takura da kashe dukkan burin rayuwa da yake cikin ruhi da gangar jiki. Saita maida idanunta ta lumshe tana qoqarin tsara yadda zata maida rayuwarta daidai kaman yadda take a baya. Kai tsaye taji an murza qofar dakin nata a hankali,bata wani damu da bude idanun nata ba,saboda tasan koma waye da zai taks dokarta,ya tsallake mata doka to bazai wuce MAMMINA ba. Bata motsa ba har zuwa sanda mammina ke takowa inda take a kwance. Can qasar zuciyarta tana mamaki,tasan da gaske taji motsinta,ta kuma ji shigowarta,amma bata motsa da nufin tarbarta ba kaman yadda ta saba?. Wani shu'umin murmushi ta saki kawai tana danne zuciyarta. "Saura qiris ki rasa wannan gatan......saura qiris ki rasa wannan izzar.....saura kadan ki fahimci ke wulaqantacciya ce abar qyama,zaki biya dukkan wani farashi da safeena ta tafi bata biyashi ba". Ta fadi qasan ranta a fili kuma tana zama daidai qafafunta. "Biftu?" Mammina ta kirata a tausashe. Kamar ba zata amsa ba,sai kuma ta tuna MAMMINA ce fa.....mammina dinta,wadda ke tsaiwa kaida fata wajen farincikinta,sai ta motsa labbanta a hankali. "Na'am" Ta amsa a hankali. "Tashi biftu" Shuru ya ratsa kadan,sannan a hankali ta juya tana miqewa,ta zauna sosai hadi da sanya hannunta tana tattare sassalkar gashinta da ya ware ribbon din yayi nasa gurin daban. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 54* Idanu mammina ta lumshe tana kuma budesu idon nata akan akhnan din. Duk da yanayin da take ciki ba abinda ya gusar da wannan sassanyan kyan......wannan kyan irin na safeena......wannan kyan da ya zamewa rayuwarta dukka qalubale da baqincikin da har kawo yau ba wani abu daya sassauta a ranta. Wannan kyan tana fatan lokacin gushewarsa ya zama a kurkusa.......a shafe tarihinsa cikin qasar agadez. Shi ta yaya ma wai zata bari AKHNAN ta fita daga tasarrufinta?. Ta yaya zata yarda tabar ruhin safeena ya kwanta lafiya cikin kusewarsa?. Yadda ta sanya darare da yawa na rayuwarta suka gagara zuwan mata da dadi,haka takeso tayita rasa nata dararen a qasan kushewa cikin baqinciki da takaici. A zahiri hannuwan akhnan din ta kamo a tausashe,har yadda tayi din ya sanya akhnan duban idanunta,tashin farko kuma ta hangi wannan tsantsar qaunar da kulawar data saba gani a tare da mammina din. "Ina cikin tsananin farinciki yau biftu,kinsan saboda me?" Kai ta girgixa a hankali. "Yadda naji sultane yana jero miki addu'o'i na sanya albarka cikin masallacin haram. Yadda sultane ya nunamin duk wani fushi da yakeyi da ke ya kau,yadda sultane ya nunamin ya.yafe miki,kuma a yanzun kin koma akhnan dinsa ta tun tale tale" Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki tana jin wani nauyi dake kwance a qirjinta yana raguwa. Wani sanyi taji gami da sassauci yana sauka saman zuciyarta,sai takejin wani girma da qaunar mammina suna saukar mata. Duk wani kyakkyawan albishir na alkhairi daga bakin mammina take fara jinsa,ita daya ce take dauke da dukkan wani albishir me dadi da zai faranta rayuwarta da duniyarta. "Amma kinsan wasu lokutan nakanji nadama tana saukarmin na hadaki da almaz?" Ta furta muryarta can qasa tana kuma sadda kanta qasa jikinta yana nuna wani irin mugun laushi da yayi. "Mammina......nadama wacce iri?" Ta tambayeta tana jin wani fargaba kadan. Kai ta daga tana sake kallonta. "Nayi wannan abunne don na samar miki da 'yancinki,ki sake cikin rayuwarki kamar yadda kikeso,amma abun mamaki shine.....sai walwalarki take raguwa,takura take maye gurbin sakewa,me yayi zafi biftu?,bayan a yanzunne kike da 'yancin yin kowacce rayuwa da kike so?" Kai ta girgixa a hankali,tana jin wannan raunin nata da bata bari kowa ya gani yana taso mata. "Ban saba bane mammina.....a hankali zan saba zan saki jikina". " Amma ko kinsan wannan rashin sabon naki yana aje ayar tambaya me yawa saman zuciyar mutane a kaina da kanki?......kinsan yau ne ranar da za'a rakaki kwanan gida?" Kai ta daga da sauri ta zubewa mammina wadannan blue eyes din. Karon farko da mammina taji kalar kallon akhnan din ya mata nauyi gami da haifar da wata jaririyar faduwar gaba. "Mammina.....kwanan gida?.....ni da almaz?" Ta furta da sigar tambaya me wani irin nauyi. Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci,sannan tace. "Haka yake a al'adar buzaye......haka yake tun kaka da kakanni,indai baso kike ki fadawa duniya cewa almaz ba zabinki bane". Shuru akhnan tayi,wai tana qoqarin daidaita kanta tana kuma qoqarin daidaita abinda takeji a qirjinta. Wani kwana ne da amarya zatayi guda daya tal a gidanta da ango,sannan washegari ya rakota ta dawo gidansu,sannan a sake shiryata a maidata. Kai ta shiga girgzawa don ta kasa tausar zuciyarta ta karbi maganar. Sam ba zata iya ba......ba zata iya bin kowacce al'ada da akazo da ita ba wai akan aure,to a wanne dalili ma?,auren da dole ce ta kaita ga yinsa,dolen amintar da sultane da maido kyakkyawan alaqansu ta baya. "Bazan iya ba mammina.....ba,bazanje ba,ko sama da qasa zata hadu bazanje kwana da almaz gida daya ba a yanzun,qarshen satinnan zan wuce Niamey,bana buqatar wani tsari da zai sanya yace zai bini,ko ke kice saimun tafi tare". Numfashi mammina ta sauke a hankali,dama ta sani,tasan za'a rina,kuma dama itama bata shirya tilastata kwana gida tare da almaz ba,to amma kuma tafiya Niamey bata hangen wani abu da zai sanya ta rushe tsarin tafiyarsu a tare. "Bazan tilasta miki ba biftu......zan sauya tsarin,saboda ya kasance dole a al'ada kuyi zaman fahimtar juna a yau,zaizo ku gana ke dashi din koda cikin gidan nan ne" Shuru akhnan tayi tana jujjuya abun. Shin meye abun damuwar cika komai da al'ada tazo dashi ne?,meye abun damuwar saita gana da mijin da HOTO ne kawai da TAKE na suna a bayan sunanta?. "Ina sake jin tsoro akan abinfa na aikata domin jin dadinki akhnan,kamar ba za'a dauki tsahon lokaci ba zaki nunawa duniya ko ki gaya mata da bakinki cewa almaz ba zabinki bane". Wani yanayi ne a fuskar mammina da yake nunawa akhnan raunin mammina da fargabar tata da gaske,sai takejin idan tayi mata hakan bata kyauta ba,bayan da qyar tasha kanta ta aminta ta zaba mata mijin auren don kubutar da ita daga fushin sultane.....bata cancanci wannan sakamakon ba,ita ta maidata cikin damuwar data kubuta ba. "Na amince zan gana dashi,saidai ba'a wani kebantaccen guri ba......ba cikin wani kebantaccen daki ko muhalli ba,zan ganshi cikin lambu na.....zagaye da hadimai da suka saba aiki a gurin,da kuma nawa hadiman da suka saba yimin rakiya" Can qasan zuciyar mammina murmushi ne ya subuce mata. Dukkan wani tsari,dukkan wani karatu da zuciyar akhnan keyi ta gama baje lissafinsa. Kai take jinjinawa a hankali,tanason gujewa qaddararta ne.....qaddarar da ita ta riga data sani ba makawa saita sameta a kurkusa ma.....saita tilastata mallakawa almaz wannana abun....wannan tutiyar wannan alfaharin.....wannan taqamar.....mallakawar kuma zata zama matakin farko ne,zataci gaba da mallaka masa ba tare data sani ba,har xuwa lokacin da adadin data shatawa qaddararsu kan ta TSAYA!. "Na gode da fahimtata da kikayi.....na gode da biyayyarki a gareni,zanci gaba da zama UWA wadda zata tsaya akan matsalolin d'iyarta. Duk qunci duk wuya. Duk tsanani,zanci gaba da tsaiwa dake a kowanne mataki ko rukuni na rayuwa har abada" Saita matsa a hankali tana rungume akhnan cikin jikinta,duk da yadda zuciyarta ke qyamtar hakan,gangar jikin keji tamkar tana hada gangar jikin nata ne dana safeena,kamar tana nutsa ruhinta tsakiyar abokan adawa masu tarin yawa. Ta gefan akhnan ajiyar zuciya take saukewa,duk sanda mammina rungumeta saita ji kamar qarshen kowacce matsalarta ne yazo,tana jin wani sassauci a tare da ita,saidai still batasan me yasa wannan EMPTINESS din da takeji a ruhinta har yanzu ba wani abu da taji ya cike GURBINSA ba. *NANAY* (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) A hankali ta shafa addu'ar data kammala bayan sallar walaha tana sauke idanunta akan saamee dake shigowa dauke da turaren wuta kamar kullum. Tausayin yarinyar ya sake tsargawa nanay,zuwa yanzu tana jin yadda kwanakin ke qara nisa,haisam da take sanyan ran hankalinsa zai kawo kanta yayi musu nisan da basu dauka zaikai har haka ba. A hankali take karantar yanayinta,kamar ta soma sarewa,kamar ta soma cire rai daga dukkan zato da kuma tsammaninta. Zuwa yanzu a wannan gabar kuma tana jin anya ba zata shiga maganar ba ko yaya ne?,anya ba zatayi wani yunquri ba don samawa marainiyar cikakkiyar nutsuwa da makoma mai inganci. "Saamee" Nanay ta kirata a hankali. "Na'am" Ta amsawa nanay din tana waiwayowa,saidai kuma tana gujewa hada idanu da ita. "Zo nan ki bani aron wayarki in kira obbo dinku". Wani faduwar gaba tayi daga kiran sunansa kawai,yayin da nanay dake karantarta a nutse ta fahimci sauyawar yanayinta daga sanda ta kira sunansa. A hankali take takowa zuwa ga nanay,tana kuma zuba numbers dinsa dake haddace a kanta,duk da cewa tayi saving nata a rubuce. Nanay ta zubawa hannunta idanu,tana rubuta number dinne da sauri sannan still hannunta yana rawa har sanda ta qaraso gabanta,ta tsugunna ta miqa mata wayar,nanay ta sanya hannu ta karba tana mata kuma alama data zauna. Duban screen din wayar tayi,sunan data masa saving dashi kaman sauran yadda 'yan uwansa suke masa ne,sai ta zare idanunta tana maidawa kan saamee wadda tayi qasa da idanunta. *HAISAM* Kacokam ya aza idanunsa akan qunshin bayanan daya kammala tattarawa,tun daga safiyar yau zuwa yanzu yammacin ranar litinin. Abu biyu yake dagashi daga gurin sallah sai kuma dauko coffee,don ba wanda ya bawa daman shigowa dakin kwata kwata a yinin ranar. Daidai da wayoyinsa dukka a kashe suke,sai bayan sallar la'asar dinnan ya kunnasu don ya kira masarauta yaji yanayin da ake ciki,ya kammala wayar kuma ya barta a silent don baya buqatar wani disturbance. Wani irin kullewa kanshi yakeyi da yadda lissafinsa da bayanan daya tattara gaba daya da bincikensa suke kaishi da direction daya. Ya sanya mutane da yawa a sahu sahu saidai duk inda ya fara bin salsalar zaren kan mutum daya suke kaishi ZAITUNA/ZEENATU/MAMMINA daya gama imanin mutum daya ne da suna uku......mutum daya ne cikin gangar jiki uku.....mutum daya ne da aikin mutum uku. "Rabbi yassir wala'ta'asir wa tammin bilkhair" Abinda ya dinga maimaitawa kenan yana zubawa allon system din idanu kaman iya aikin da aka aikoshi a yau yayi kenan cikin duniya. Idanunsa da suka nuna gajiya a fili ya janye yana maidawa saman wayarsa dake ringing,sunan nanay ne,kiran da yake jira tun kwanaki uku da suka shude,saidai yanayin rashin lafiya da kwashe wayoyin da omar yayi masa yasa dole ya daga qafa. Jawo wayar yayi,ya yanke kiran kamar yadda ya saba sannan yabi bayan kiran. Tana ringing ya sakata a handsfree ya maida bayansa jikin kujera yayi relaxing yana jin yadda qwaqwalarsa ke ninka aikinta da wani irin gudu da sauri daya wuce iyaka,har yanajin ciwon kansa kamar yana shirin motsawa,sai ya sanya hannun nasa ya dafe kansa a hankali yana lumshe manyan idanunsa da a yau suka dan canza launi kadan. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 55* Sallamar nanay dinne ta sanyashi bude idanunsa a hankali yana amsa sallamar gami da bude idanunshi. A nutse nanay ta miqawa saamee wayar sannan ta yunqura a hankali tana fadin "Ki sameni a parlor idan kin gama". Kanta a qasa tana jin takun ficewar nanay din,sai ta koma ta zauna sosai saman carpet tana jin qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba. Muryar nanay yake jiran sake ji,sai yaji muryar saamee ta maye gurbinta da sallamar nan tata cikin yanayinta me sanyi. Numfashi ya aje a hankali yana amsa mata sallamar,husky voice dinnan nashi ya ratsata ya shiga kunnenta yana motsa wani abu dake boye can saqon zuciyarta. "akkam jirta obbo(barka da warhaka,kana lafiya yaaya)" Ta fadi a hankali tana ganin kamar xai iya jiyo bugun zuciyarta daga nan inda take zaune. "Ani gaarii dha,akkamitti?(lafiya nake,kefa?) Ya tambayeta tana qoqarin kwatanta kyautatawa a gareta kamar yadda yasan tana qoqarin yin hakan ga nanay dinsa. "Alhamdulillah" Ta amsa duk wani sauran magana kuma yana dauke mata gami da tsaya mata a maqogaronta. Wani irin kwarjini yake mata koda a bayan idanunta ne,ta jima da sanin shi din wani irin namiji ne daban da sai zallar sa'a zata sanya mace ta samu damar mallakarsa. "Makaranta fa?" Yayi qoqarin tambaya don kada ta dauka ya wofantar da qoqarinta. "Komai lafiya alhamdulillah" Ta furta a hankali,har qasan ranta tana son tambayarsa sai yaushe zai shigo jimma?....don tayi wata muguwar kewarsa,amma takejin ba zata iya ba. "Ma sha Allah,Allah ya taimaka,nanay fa?" "Zan kai mata yanzun" Ta fadi a sanyaye,tana sanya rai ne hirarsu ta zarta haka,tana sanya ran maganarsu ta wuce haka,amma sai gashi da wurwuri ya gajarta maganar. A nutse ta miqawa Nanay sannan ta taka tana fita a parlor din. Nanay ta bita da kallo sanda take sanya wayar a kunnenta. "Barka da warhaka nanay" "Barka kade muhammad.....fatan ka yini cikin aminci" "Alhamdulillah nanay.....komai da kowa lafiya?" "Lafiya Muhammad,inata tunaninka omar yace wani aikin daban ka shiga,shi ya sanya ba'a samunka" Idanunsa ya lumshe a hankali yana gyada kai,cikin ransa yana jin dadin yadda omar ya boyewa nanay rashin lafiyarsa. "Na fito alhamdulillah nanay.....ko kin samu sunan abokiyar zaman Obbolettii n ki?" Kai ta gyada a hankali. "Eh muhammad.....na samu amma da qyar,na rubuta don kada na manta,duk da nasan mantuw tayi kadan ta goge sunan azzalumin mutum irinta a kaina....." "Meye sunan nanay?" Ya tambaya cikin tattarawa Nanay hankalinsa. "ZEENATU" Wuta ce ta daukewa haisam na wasu daqiqu,kafin a hankali wani murmushi me cike da madaukakin mamaki ya mamayeshi. Zeenatu a Ethiopia......zaituna a agadez? Ya tambayi kansa da kansa yana kuma sake jinjina kansa. "Matar ajani da ake zargi ZEENATU.......matar data fidda Obbolettii (sister) dinki daga gidanta ZEENATU.....ba wani alaqa tsakanin mutanen nan biyu?". Dif wuta ta daukewa nanay,tunaninta yana yin zurfi da kuma nisa. " Ajani ya taba aure shima!.....na shekara daya muhammad kamar yadda safeenata tayi!!" Nanay ta fuusgi kalaman cikin wani irin rudani. "Good nanay......zan iya samun wani abu game da rayuwar gidan ajani.....kaman ta hannun uwargidansa?" "Ta rasu muhammad.....sati daya da suka wuce.....amma,bari na kira safuura" Nanay ta fadi tana yanke kiran. Ko ina na jikinta kyarma yakeyi,tanaji jikinta kamar taga Obbolettii dinta har guda biyu,tana jin kamar an gano ind sisters dinta suke,tanajin kamar an gano bakin zaren ne. Kai kawai haisam yake juyawa a hankali,maimakon bacin rai ya mamayi fuskar nan tasa ma'abociyar Kwarjini,kawai sai wani qaramin murmushi ne yake fita a fuskarsa. Ganin komai yake tarwai.....kowanne lissafi nasa da yake sarqewa a baya a yanzun ya fara zuwa masa da warwara......yan hangen komai kamar an saka rariya ana taceshi. Hujja daya tak yake nema da zata sake bashi tabbaci itace MATAR AJANI......hujja daya tak da yakejin a yanzu ya shirya shiga kowanne sashe kowanne lungu na masarautar agadez don ya fiddo ta. Idan ya tabbata INA MAKASHIN?.....waye wanda ya aikata kisan da shima yayi batan dabo?. Ta yaya lokaci bayan lokaci suke iya aiwatar da bazaranarsu ga motii aba jifar?,ta yaya?,su waye rassansu?,su waye mataimakansu?. Yatsunsa kawai yake murzawa a hankali yana sake baje sabon lissafi. Kebantaccen dakin ajiyar mammina.....shi kadai ne abinda ke masa yawo a ransa da kansa....kebantaccen dakin da jikinsa ya bashi tabbacin lallai akwai BOYAYYUN SIRRIKA. TAMIM har guda biyu dake da alhakin kula dashi,da masu jin yaren oromo da yake da lissafin sunayensu yanzu haka fes dama fuskokinsu gaba daya!.. Turqashi......ya zuwa yanzu nasan me karatu yana tunanin KOMAI YAZO QARSHE......QARYA TA GAMA QAREWA......GASKIYA KUMA TA GAMA BAYYANA......SAIDAI NACE KUXO MUJE MAJI MA GANI Maleek ne ya shigo a nutse bayansa daya daga cikin hadiman haisam ne. Dauke da wani kyakkyawan royal tray da aka jera masa qananun bowls masu kyau. Idanunsa ya zare ya maida kan maleek,shima maleek din shi yake kalla. "Ina fata wannan aikin ya kammalu?" Tashi haisam din yayi ya zauna sosai yana duban maleek sanda hadimin ya ajiye abinda ke hannunsa yana fita. "Yadai kusa......inaso na shiga masarauta,yau zanyi kwana uku ko biyu kuma kafin na fito.....ka kira likitan nan yazo ya ciremin wannan abun" Ya fadi yana daga hannunsa dake dauke da Canular. Kai maleek ya girgiza yana zama saman sofa. "Amma kasan akwai ragowan drip da zaka sake sha?" "Ya isheni haka maleek,ina buqatar kammala wani abu dole.....inaso na gama komai qasa da sati daya". Ya amsa masa yana yarfar da hannun nasa,don har yadan fara tasawa saboda zaman allurar na kwanaki a jikinsa. "Okay " Ya fadi yana lalubar wayarsa don kiran hadiminsa da suke agadez din tare. *TAMIM* A nutse ya miqawa almaz alkyabbar data zama sutura ta qarshe da zai sanya a jikinsa,bayan tarin kayan ado da qawar daya fara sanyawa a jikinsa na tsadaddar suturar ALHARIR. Shi kansa tamim din a yau yana hangen wani irin kyau da biyayya da suturar tayi a jikin almaz din,tamkar dai dama ya saba da ire iren wadannan tufafin a jikinsa. Duk da haka ba abinda ya rage qudirinsa a zuciyarsa,ba abinda ya rage kaifin abinda yakeji a zuciyarsa.....hakanan ba abinda ya sauya daga aikata abinda yayi niyyar aikatawar. A nutse almaz ya taka cikin wani salon izza da yaji ya saukar masa,ya matsa gaban tamfatsetsen madubin dake ajiye a wani bangare na daban na dakin. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Duban kansa yakeyi cikin madubin,yana jin wani izza tana shigarsa. Tsahon rayuwarsa bai taba ganin inda yayi kyau har haka ba,koda sau daya kuwa,duk da cewa yana rayuwa cikin sutura me kyau da kuma cima me kyau,amma ba sutura irin wannan ba....ba tufafi irin wannan ba me cike da nuna qarfin izzar wanda ya sanyasu. Sosai yakeji kansa yana sake shiga charge,abinda ya qara fadada nishadin da yakeji kenan,don tun daga daren jiya ya baje dukkan kayan mayensa da aka dakatar dashi daga sha,yasha me isarsa,ya kuma dora da wani da safen nan bayan wadancan sun sakeshi. Yana jin wani banbanci da wadannan kayan da wadanda ya saba sha. Wadannan din masu taada ne sosai data sanya aka tanadar masa kwali kwali kawai don jin dadinsa,ta kuma yi masa alqawari daman,ta kuma cika,abinda ya sake saka masa nutsuwa da bin dukkan sharudda da qa'idojinta. Basa sakashi yayi mankas ya manta da abinda yakeyi,amma suna fiddashi daga duniyarsa,suna kuma fitar dashi daga ainihin duniyar da yake rayuwa a cikin ta,suna sakashi ya jishi daidai yake da kowa,yana kuma daidai da tarar kowa da komai. Waiwayowa yayi yana murmushi yana duba tamim,abinda ya sanya tamim dauke kansa daga mummunan kallon da yakewa almaz din,kallon dake cike da hassada qyashi kishi da baqinciki. "Wai nine almaz a haka?.....nine na mallaki matar aure d'iya mafi girman daraja a yankin africa......gida irin wanda nake mafarki da rayuwa cikin izza mulki da qasaita.......amma kasan meye tamim?" Yayi tambayar yana duban fuskarsa yana kuma takowa zuwa gaban tamim din. Qoqarin gaske tamim yayi wajen maye murmushi saman fuskarsa. "Na rasa wanne dalili ne ya sanya uwargijiyarka ta zaboni a cikin tarin matasan qasar Ethiopia.....a baya nayi tunanin don tana mahaifiyata ne,amma a yanzu tunanina ya gagara cafko komai" Almaz yayi maganar da tarin mamakin dake ransa daya bayyana cikin muryarsa. Murmushi tamim ya saki,yana takawa a hankali gaban wani babban glass cup daya cikashi da tataccen lemon inibi wanda ya cakudashi da sinadarai daban daban. "Kaidai ungo wannan kasha mu tafi.....yanzu ba lokaci bane na tunanin wannan.....tunda harka yadda ka shiga cikin masu sa'a ai shikenan,ba abinda ya rage maka saika zuba idanu kaci gaba da irgen lokutan sa'arka". Dan shuru almaz din yayi,kafin kuma ya saki murmushi yana miqa hannunsa ya karbi lemon hannun tamim din. "Inason lemon nan sosai,inajin dadinsa" Ya furta a hankali sannna kuma yakai cup din bakinsa. Tas ya shanye lemon a kurba daya,sannan ya miqawa tamim cup din yana cewa. "Kamar zai bani freshness din da nakeso,na gode tamim" Ya damqa masa cup din yana juyawa. Da wani kalar shu'umin murmushi yabi almaz din,rabin aikinsa ya kammala saura rabi,yana duban takunsa da yakeyi cikin wani yanayi daya bayyanar da b'urbushin qasaita. "Matsiyaci ya samu guri,wai har ya iya yanayi na masu mulki da saruta" Ya fada a fili can qasa yana jifan hanyar da almaz yabi da harara. Jerin gwanon motocin alfarmar guda shida ne cass suka takewa motor din da almaz ke ciki baya. Ya saki wani irin murmushi sanda dukkan wani hadi dake cikin lemon ya fara zagaya sassan jikinsa,ya kuma soma jinsa a sama,uwa uba yadda yaga manyan motocin alfarma irin wannan na take masa baya sai ya sake sanya yanayin yabi jikinsa sosai "Shege almaz,yau shine kamar gomna?" Ya tambayi kansa da kansa yana dariya. Sam a rayuwarsa ya rayu cikin wani madaukakin yanayi ba burinsa bane,damuwarsa daya shine ya rayu cikin 'YANCI. Bayason UMARNI,yafison ya rayu cikin sakewa da kuma zabawa kansa duk kalar rayuwar da yakeso,ba tare da an bashi umarni ba,ba tare da an sanyashi ko an hanashi ba. Ya sani......yanajin wata izza da girma a cikin jininsa da baisan wacce iri bace,wannan ya sanya sau tari yafi zabar kebance kansa tare da qin amincewa ya shiga taron jama'a. Duba daya tamim yayi masa ya tabbatar ya fara fita daga hayyacinsa,ya fara buguwa,sai ya gyara zamansa sosai yana dubansa. "Kasan meye almaz?" Kai ya girgiza yana duban tamim da idanun nan nasa da tamim din yake ganin suna masa kama da wasu idanu. "Akhnan matarka.....tana da tsananin girman kai....bata girmamawa kowa saboda tana ganin mahaifinta shine sarki a wannan yankin....." "Ashe?" Almaz ya fadi da wata irin murya yana bude idanunsa da kyau. Kai tamim ya jinjina cikin bashi tabbaci da son isar da saqonshi "Qwarai da gaske.....kai baka lura ba?,a matsayinka na namiji kuma mijin dake aurenta.....ta taba gaidaka?,kota taba zuwa gurinka nemanka?,kota taba nemanka din koda a waya ne?" Shuru almaz yayi,wasu abubuwa suna cakudewa cikin kansa tsakanin maganganun tamim da kuma abinda tamim din ya bashi yasha. Gefe daya wata izza tana huruwa cikin ransa,yana jin kansa yana girma da fadi. "Ba ko daya" Almaz ya fada muryarsa tana kaduwa da wani irin yanayi na wanda ya fara buguwa. "Ahto....to kai kuma saika bari aci gaba da tafiya a haka?" "Inaaaa......daga yau zan fara nuna mata ina da iko a kanta" Ya fada yana ji a ransa dole ya zama tsayayyen namiji. A hankali tamim ke buda masa wasu abubuwa,yana kuma sake karanta masa abubuwan da ya tabbatar zasuyi tsananin tasiri a kansa game da akhnan din. So samu komai ya fada jagule musu a yau,shi yasa ya fara da horashi da kadan daga cikin kayan mayen dana tanada,wanda wannan shine zai bashi damar dorawa kan tsarinsa d'od'ar ba tare da sunansa ko alamar ayar tambaya ta hau kansa ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 56* Yanaji a ransa,daga sanda auren almaz ya sauka daga kan akhnan,daga sannan zaiyi dukkan me yuwuwa don ganin ya mallaketa,koda meye zai faru a shirye yake,idan ta kama ma yana jin cewa a shirye yake ya dauketa cancankat ya rabata da ganin kowa ya kaita wata duniya ta daban,inda zai samu damar mallakarta ba tare da wani tarnaqi ba. *AKHNAN* Tana tsaye ne kawai tana jin yadda birra ke shiryata cikin wasu qawatattun kaya na alfarma da mammina ta aiko dasu. Iya akwatin da aka sanya kayan kawai abun kallo ne ballantana akai ga kyansa da kuma tsadar da suke da shi. Tana ji ne kamar ta sanya hannu ta ciro zuciyarta daga qirjinta,tana jin wani irin qunci da suya da zuciyarta takeyi kamar zata babbake. Maganganun mammina kawai suke bata dauriya da qwarin gwiwa.....addu'ar da sultane ya kirata jiya yayi mata wadda ta bata tabbacin ya huce da ita.....yana kuma dab da maidata BIFTU dinsa kamar yadda take a baya,su kadai ne abinda suka sanya take iya tsaiwa da qafafunta a yanzu haka. To amma yaya rayuwar zata kasance?,ta yaya zata iya carrying identity na matar aure da mutumin da shi da ZERO daya suke a wajenta. "An kammala ranki ya dade" Birra ta fadi cikin tsananin girmamawa tana komawa baya. Batako waiwaya ta kalli kanta a madubi ba kamar yadda ta saba ba ta fara matsawa inda birra ta ajiye mata takalmanta ta fara zurawa. Falaak ce tayi sallama a nutse tana shigowa,fuskarta qunshe da murmushi tana duban akhnan din. Ita kanta idan ta kalli akhnan.....ta tuna a yanzu tana amsa sunan matar aure ne saita dinga jin abun wani abu na daban. Wani al'amari ne da dukkaninsu basu kawo wanzuwarsa a kusa ba. "Ya biftu" Ta qaraso gabanta tayi kiranta da yanayin kira irin na tsakanin qanwa da yayarta. Kyawawan blue eyes dinta da kwallin da birra ta zizara mata ya qara yiwa kyau ta daga ta dubeta. "Yayanmu ya qaraso.....zan iya shiga sahun 'yan rakiya?" Ta tambaya tana dage dukka girarta sama. "Yayanmu?" Ta maimaita sunan cikin kanta,saita ware idanunta akan falaak "Me yasa kike da rawar kai har haka falaak?,yaushe ya zama yayanki?" Tayi maganar haka kawai tana jin furucin falaak din yana tabata. Bata wani damu ba,zuwa yanzu halayen akhnan din duka ba baqinta bane,sannan uwa uba tana sanya ran lokaci yayi da akhnan din zata sake janta a jiki,don zata tafi gidan aurenta ne,zata fara wata rayuwa ta daban ba wadda sukeyi ba a yanzu,dole komai zai canza. "Tunda kina nuna min careless,na sani koshi zai daukeni a matsayin qanwarsa ta gaske,irin abinda na rasa a tare da ke" Sosai maganan ya ratsata,amma duk da haka saita dauke idanunta daga kan falaak din taci gaba da sanya takalmanta a hankali,kafin ta soma nufar qofa,birra buhaina bushira barratu bara'atu dama falaak suna biye da ita. *HAISAM* Yau din tun daga nesan nesa da gidan ya sanya salaana ya ajiyesu. Akwai nazari da yakeso ya sakeyi na unguwar duka dama anihin ginin katangun masarautar. Tare da maleek suke takawa,wanda dukkaninsu suna maqale ne da Bluetooth suna hira a tsakaninsu ta conference call din da suka hada da mutallab....khadeem....amjad.....naseeb. Duk da maganarsa qalilanne cikin hirar tasu,amma hakan bai hana masa jin dadin hirar ba,wadda ta gauraya da yanayin garin daya bada lullumi na hadari. Jikinsa har yanzu bayajin qwarinsa sam,amma kuma hakan dai bai kauda wannan jarumtar qarfin halin da qarfin zuciya da qawazucin dake tattare dashi ba. Surutu ko dogon magana ba dabi'ar maleek bane,suna dan kamanceceniya ta wannan fannin,duk da wani lokaci maleek idan da zurfin sabo tsakaninku yana dogon hira,kamar dai a cikinsu su bakwai din,to amma yau tunda suka taho yake basu labarin agadez. "Nan kusa zakuzo guys....don nikam har nayi farin kamu" Maganan yaja hankalin haisam,amma sai baice komai ba da wannan salon basarwar tasa,yayi kaman baiji ba,yaci gaba da takawa abinsa yana nazarin ginin katangar masarautar da suka fara cimmata. Yanajin ihun khadeem,dan rud'u ne na gasken da kusan yafi kowa rudu a cikinsu,wannan ya sanya yafi kowa tara 'yammata. "Me nakeji kana fadi maleek?,yau kuma an biyo ta kanka?" Idanu maleek ya lumshe yana shafa qirjinsa murmushi yana qwace masa. "Wata princess tayi wuf da zuciyata daga shigowata......kuma bazan tsaya kallon ruwa ba kwado yayimin qafa.....zan zauna,zan jira mahaifinta ya dawo na nema aurenta da kaina Allah khadeem" Still haisam yaji maganan ta masa ba zata,duk da cewa yayi hasashen haka dama tun wancan ranar,amma kuma issues din da suka sakoshi a gaba ya sanya bai maida hankali ba akai. "Amma mutumina.....ya akayi ka riga dan gari yin farinjini?" Naseeb ya fadi da alamun yana danne dariya qasan ranshi. Sarai maleek yasan da waye yake,saiya saci kallon haisam sannan ya janye idanun nasa da sauri kafin ya masa wannan kallon nasa yana dariya qasa qasa. "Ya qaryata zuciyarsa ne kawai.....ina kuma masa fatan kada nan gaba kadan na sake kiranku kuzo kuyi jinyar me ci......" Qit! Haisam ya yanke kiran gaba daya,kowannensu take wayarsa tayi disconnecting,abinda ya sanya kowa dariya a cikinsu daga shiyyar da yake. Sunsan halinsa,sunsan aikinsa ne,kuma shi daya yake iya musu wannan yankar qaunar idan hira batayi masa ba,don shi kadai ne a cikinsu ya karanci sanin ilimin sanin na'ura ciki da bai dinta. Harara yadan watsawa maleek sannan yace "Ashe dama ba don Allah ko zumunci kace zaka zauna ba?....." "Ba haka bane captain......" "Haka ne.....kuma zanga waye zai baka auren....badai falaak ba?" Hannu maleek ya dora saman qirjinsa yana marairaicewa haisam. "Tsaf zaa maidawa motii ni unconscious.....a haka ma nayi kara ne ban tareta ba,inaso nabi komai bisa tsarin addini.....mahaifanta kafin ita" Kai haisam yake jinjinawa,ya sani dukkaninsu har yanzu ba wanda ya sauka daga kan tarbiyya mutunci kima da martabarsa,saidai isowarsu bakin babban qofar shiga masarautar ya sanya suka aje zancan a nan. Duk wani hadimi dake bakin kowacce qofa da zai wuce zuwa hanyar ciki rusunamasa yakeyi cikin GIRMAMAWA. Irin girman da sultane ne kawai ya cancanceshi,abun har ya fara bawa maleek mamaki. Su kansu wani jin dadin dawowarsa sukeyi,hakanan sukejin rashin karsashi na gabatar da aikinsu,da wani irin salam da gidan yayi musu a tafiyar da akace musu yayi na kwanakin. Daidai sanda suka iso farfajiya ta biyu data hada sassa da dama na gidan,daidai lokacin da falaak ke takawa gefan akhnan tana mata magana qasa qasa. "Kinyi kyau yaa biftu,kayan sun miki kyan da duk wanda ya kalleki yasan amarya ce". Wani abu taji ya sauka a qirjinta,taji kamar falaak ta qara sauke mata nauyi saman zuciyarta,abinda ya sanyata daga idanunta kenan ta saukewa falaak harara. Kan fuskarta idanunshi suka sauka,fararen idanunta dake dauke da blue din qwayar idanu da haskensu ya fita tsakiyar blue din sosai. SAK amarya saboda yanayin gown din dake jikinta wadda birra ke dage mata ita daga baya. Wani harbawa zuciyarsa dake cikin qirjinsa yaji tayi,a hankali ya janye qwayar idanunsa daga kanta yana jin yadda zuciyarsa taci gaba da bugawa kadan kadan. A lissafinsa yanzun ba lokaci bane a al'adarsu na kai amarya ba,baya kuma zaton hakan,don inda hakanne zai kasance tabbas sai an sanar dashi. Tunaninsa ya sake dawowa jikinsa.......WAYE ALMAZ bayan kasancewarsa wanda aka dauko daga gidan marayu na YATAAMA.....shin ya cancanci ya bari sultane da damqa gudan jininsa a hannun da yayi imani SHIRYAYYEN SHIRI ne da manufa da akeson cimmawa?. "Zanji da wannan tabbas" Ya samu kansa da bawa kansa da kansa yaqini. Damqo hannun maleek yayi sosai yana tsareshi da idanu. "Ina zaka?" "Ko sau daya ne ka bari nayi magana da ita mana" Maleek din ya fada cikin bawa haisam tabbaci akan abinda yake fadi. Idanunsa ya tsaurara akan fuskar maleek dim sannan ya girgiza kai. "Ba inda zakaje yanzu maleek.....tana tare da matar mutane ne,matar aure ce a gefanta,ta yaya zakaga adon daba naka ba?". Sosai maleek ya tsare haisam da kallo,sai ya zame hannunsa daga cikin na haisam din,wata irin dariya tana qwace masa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Meye naka na kishin matar wani?" Cak yaji maganar ta tsaya masa a rai,sannu a hankali ya dauke dubansa daga kan maleek,yaci gaba da takawa zuwa ciki kafin yace "Saika dawo" "Ba inda zani,na fasa nima,zanci gaba da daurewa har sultane ya qara so,na kuma nemi izini daga gareshi,hakan sai yafi kima a idanunshi". Maleek ya fadi yana bin bayansa,still murmushin dake kan fuskarsa bai bace ba. *MAMMINA* Murmushi ne kawai yake fita saman fuskarta kadan kadan,tana jin wani nishadi yana ratsata,tana kuma hangen nesanta tana dab da zuwa kusa. Tana hangen ranakun dariyarta,ranakun walwalarta,da ranakun jin dadinta suna dab da riskarta. Hankali kwance kuma cikin nutsuwa tayi zaune saman sofa,ta dora qafarta daya kan daya tana girgizata a hankali. Tana ji ne kamar an mata kyautar duniya da abinda yake cikinta. Tana jinta a wata sabuwar duniya sabuwar rayuwa da zatazo mata da FANSA akan dukka wanda ya taba yiwa rayuwarta katsalandan,ya kuma jefata a dawwamammen baqinciki. Bata da wani haufi,bata kuma da wata sauran matsala akan masaniyar abinda yake gudana tsakanin akhnan da almaz,don ta zuba dukkanin mutanenta da zasu bata labarin koda motsa yatsa ne almaz ko shehnaz sukayi. "Allah ya baki yawan rai.......tamim yanason ganawa dake,saidai dokoki da iyakoki basu bashi daman shigowa ba kamar yadda aka saba" Raliya daya daga cikin hadimanta kenan dake iya karbar aiki sanda yalwa ke nesa. Wayarta dake hannu ta dakata da dannawa,ta xubawa raliya idanu. Har tsakiyar ranta da zuciyarta tana jin yadda wadannan dokokin suke caccakar ranta. Har cikin ruhinta tana jin zafin yadda suke sake karo da muradanta,suke kuma kawo mata rauni wajen samun dukkanin wani information da take da buqatar samu. "Ya dakata a sansanun ganawa,zan fito yanzu" Ta amsawa raliya din. Cikin ranta tana jin ba normal abu bane ya sanya tamim nemanta a irin wannan lokacin ba,don haka ta miqe tsam tana gyara alkyabbarta. *AKHNAN* Dukkanin hadiman da suka mata rakiya dama wadanda ke gurin tuni sukayi biyayya suka tsaya bisa sahu da tsarin na umarni cikin salo na sarauta da akhnan ta basu. Akwai hadimai sosai a gurin,wadanda suka samu a gun suna aikin gyara shukokin gurin yankesu daidaitasu da kuma rage musu tsaho. Sai kuma nata data taho dasu wadanda suka yiwa kansu gurin tsaiwa nesa kadan da ita,ta yadda zasu iya ji da ganin komai dake gudana kamar yadda ta zabi hakan. Idanunta fes akan fuskarsa,fuskar data gaza tantance bambancinta da wancan fuskar ta waccan ranar. Ci gaba tayi da takawa a qasaice tana duban idanunsa,idanun da bata iya hangen komai ta cikinsu. Shima ita yake kallo,ya kuma qureta da dukkan kallonsa daya quntata zuciyar akhnan,sannu a hankali ta hadiye wani abu me kama da bacin rai,tana zama hannun kujerar dake kusa da ita,ta tsani yawan kallo,ta tsani a zuba mata idanu,batason a fiya kallonta,wannan ya sanya kamar ya zama doka akan dukkan wani bawa ko hadimi da zai sanya idanunsa cikin nata. Cikin izza ta motsa labbanta tana dubansa bayan tadan kalli agogo. "Kazo a makare,ina faran zaka fadi duk abinda ke ranka akan lokaci,ina da abunyi a gaba me yawa" Sosai maganar ta sauka akan kunne da zuciyar almaz,maganganun tamim kuma suna dawo masa tarwai cikin kansa kamar lokacin yake gaya masa su. "Bata da kunya,bata iya girmama kowa". Maganar kuwa ta motsashi,ya tashi ya zauna sosai yana dubanta duk kuwa da yadda yakejin kansa ya masa wani irin nauyi. Idanunsa dake lullumshewa ya waresu kadan a kanta,ware idanun kuma daya sanya akhnan din taji wani abu kadan ya fusgeta,taci gaba da barin idanunta a kansa. Tana da kyau da gaske ne,wani irin sassanyan kyau me burge idanun me kallo. Sabgar mata tana daya daga cikin sabgogin da basa cikin tsarinsa sam. Bai taba tarayya da kowacce diya mace ba ko soyayya,saboda kayan mayensa kadai sunfi masa kowacce mace a gurinsa. Amma baisan me yasa ya kasa jin komai a kanta ba,wani abu me kama da soyayya ko sha'awa sam baiji ya masa tasiri a rai ba. "Ke!" Ya kirata a dan tsawace,abinda yayi matuqar saukarwa da akhnan mamaki ta daga kanta tana dubansa kai tsaye. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 57* "Haka ake girmama......miji.....ki shigo ki sameni amma.....ba zaki....ddurd.....durqusa ki gaidanai ba?" Yayi maganar jimlar tana tsintsinkewa yana hadata da qyar. Wani zallar mamaki ne yaso kasheta daga zaunen. Mamakin farki na batun gaisuwar da yakeyi,dubansa takeyi da kyau tana son gasgata kunnenta ko kuma qaryatashi. Ita akhnan yakema batun ta durqusa ta gaidashi?. Bayan sultane ba wata halitta guda daya data samu wanna girma martaba da mutuncin. "Kana da hankali kuwa?" Ta tambayeshi fushinta yana motsawa a hankali. Idanunsa ya fidda sosai a kanta. "Ni kikeso ki kira da mahaukaci kai tsaye?...ina matsayin mijinki?" Ya fadi yana nuna qirjinsa da alama maganan ya masa zafi sosai data fadi din. "Bana daukan raini fa......ina zaman zamana bazan dauki iskanci ba......ahhhht...m.toooo,auren banza auren wofi" Ya qarasa fada yana watsa hannayensa. Mamakinta sake ninkuwa yayi,ta sake zuba masa idanu tana qare masa kallo da gasken gaske. Wanne irin mutum ne mammina ta zaba mata?,akwai hankali cikin maganganunsa da nutsuwarsa kuwa?. Idan har idanunta sun gane mata da kyau ma kamar cikin yanayin maye yake maganar,idanunsa sun nuna mata haka,hakanan dukkan wani acting nasa da yakeyi. Fidda idanunsa sosai yayi waje yana son ganinta da kyau,don ta fara yi masa dishi dishi,so yake ya nuna mata da gaske shine sama da ita. So yake ta gane shine gaba da ita,bazai yarda da yadda take wulaqata kowa ba,yana jin haka a jikinsa cewar shi din ba wulaqantacce bane. "Ni bana daukarrrrrr......raini kome za'a bani......zan iya babbbbbballlaki ko kece sarkin" Sosai zuciyarta tazo mata iya wuya,wannan narkakken bacin ran da ya dade cikin qirjinta da zuciyarta ta yunqoro mata. Tsawa ta sakar masa tana bude dukka blue eyes dinta waje,ta miqe tsam tana dubansa sanda yake miqewa tsaye shima yana dafa daya daga cikin hadiman da mammina ta bashi fa suke koya masa abubuwan da zai saje da gidan sarauta sosai,tun zuwansu kuma yana tsaye daga gefan nasa saboda nuna girmamawa. "Kabi a sannu,ka iya bakinka....koda kai din waye idan kayi kuskuren fadin wani abu mara kyau akan mahaifina zan sanya a batar dakai ne cikin agadez,za'a kuma shafe babinka,ba za'a sake jin labarinka ba" Tayi furucin tana nunashi da yatsa. Wata dariya ya saki idanunsa suna jujjuyawa gami da shanyewa,girmansu yana raguwa sosai. "Gimbiya ko?...." Ya fadi yana shammatarta,bata ankara ba ta tsinceshi dab da ita. Wani irin ja baya tayi da zafin naman da ita kanta batasan tana dashi ba. Ya sake zuba mata ido na wasu mintuna kafin ya saki wata irin dariya. "Tsammani kike zan miki wani abu?,tab.....wannan ai ba matar aure bace...ni dama can ba damuna kukayi ba" Sai ya daga hannu yana nunata da yatsa gami da fara tafiya da baya da baya yana tangal tangal kamar zai zube a gurin "Mara kunyar banza kawai....kije na sakeki.....na sakeki......na sakeki.....na sakeki....." Ya yita maimaitawa kaman wanda aka baiwa aikin ibada wata qaramar dariya kuma tana kubce masa. Bai gaji da maimaitawa ba yana kuma yunqurin fita a gurin,yana jin kamar qasar tana juyawa dashi saboda wani irin mahaukacin nauyi da yaji kansa ya masa. *HAISAM* Kebantaccen dakinsa ya wuce kai tsaye yabar omar da maleek a sitting room din farko,idanunsa saman duka na'urorinsa,ya qarasa a hankali cikin qwarewa ya fara hadasu. Wasu irin qananun device ne da idan ka kallesu ba zaka dauka suna da wani alfanu ba,dauka zakayi abun wasan yara ne kawai idan ka dauke system qwaya daya dake gurin. A nutse ya hada komai,connection ne tsakanin mutanensu dake aiki cikin gidan,location hudu,bakin babbar qofar shigowa gidan dame binta,sassan bangaren mammina,sai kuma babban kitchen na dafe dafe na gidan. Green din haske ya kama,abinda yake alamta masa kowa yana kusa. Kujera yana yana shirin zama,wayarsa tayi blinking haske kadan,ya dakata kadan yana dubawa,sai yaga nanay ce,sai ya zauna saman kujerara nutse yana furta. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Dukka sassan hudu ya aikewa hold on sign,sannan ya katse kiran nanay yabi kiran nanay din. Bugu daya ta daga,abinda ke tabbatar masa tana bakin wayar tana jiransa,tana kuma qagauce ta gaya masa koma mene "Muhammad" Ta kirashi da wani irin yanayi muryarta tana rawa,abinda ya sanya duk wani jijiyar jikinsa tayi relax. Da husky and deep voice dinnan mash ya kira sunanta. "Nanay.....Tasgabbaa'i .(calm down).......of gadhiisuu(relax)nanay........ki fadamin a hankali" Ya furta da wani irin coolness,don tuni jikinsa da zuciyarsa sun gama gaya mishi sakamakon. "tole(okay)" Nanay ta fada da wannan nutsuwartata me cike da dattijantaka da harshensa da ya riga ya narke cikin yaren oromo. Idanunsa a lumshe,zuciyarsa na wani irin gudu yayin da zuciyarsa ke sauraron sautin muryar nanay dinsa. Yadda take masa bayani daki daki,muryarta na karyewa gami da yin rawa a gurare masu yawa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Muhammad.......Nama tokko natti fakkaata,inaji a jikina mutum daya ce......zeenatun ajani itace zeenatun lamaan dina....aikin mutum daya ne muhammad wannan tabbas.....inajin shi yasanya na kasa daina mafarkin safiyyah ta.....shi yasa na kasa daina ganinta tsahon lokaci cikin mafarkaina.....safeena ina hangenta acan nesa dani,wani irin nesa da yake ban tsoro......ko ina da rabon sake ganinsu?" Nanay ta furta dukka dauriyarta tana yankewa,wani irin qauna irin na 'yan uwantaka yana ratsata. "Nanay" Ya kirata da tausasawa "Na'am muhammad" Ta kirashi da wani rauni sosai da me saurare ke iyaji cikin muryarta. "Na miki alqawari,koda ban kawo miki safeena ba,koda ban hadaki da safeena ba,zan hadaki da safiyya" Wuta ta daukewa nanay,tunaninta yana yin nauyi. "Muhammad......ta yaya?" "Nanay karki tambaya,karki tambayi yaushe,karki tambayi ta yaya,amma wannan din alqawari ne na miki,koda shine abu na qarshe daya ragemin da zanyi cikin rayuwata" Yayi furucin yanajin abinda ya fada da gasken gaske har cikin zuciyarsa. "Allah yayi maka albarka......addu'ata tana tare daku muddin numfashina" "Ameen nanay" Ya amsa yana jin wani qwarin gwiwa yana ratsashi,sannan ya yanke kiran. Dukkanin hankalinsa ya maida ya kuma tattara akan kiran da ya yiwa kowanne,ya danna madannin daya dawo da connection din daya hada da farko. "Ina buqatar tashin gobara cikin darennan daga madafa......sannan tayi kaman zata taba sasssannin matan gidan nan......amma bana buqatar ayi asarar rai ko daya.....kafin sannan,abeer....." Ya kira sunansa yana duban signal din abeer din. "Yes obbo" "Ina buqatar analysis na dukkan abinda ya halaka cikin gobarar bayan komai ya kammala,ina buqatar kuma a siya komai a maidashi muhallinsa kamar komai bai faru ba,koda tsintsiya banaso wani yayi asara" "An gama obbo" Abeer ya amsa cikin matuqar girmamawa. Kai haisam din ya jinjina yana duban lafiyayyen agogon Rolex me tsadar gaske dake daure a tsintsiyar hannunsa "Ina buqatar ta fara qarfr biyu na dare,banaso kuma ta haura awa biyu ayi a gamata" Ya qarasa fada yana sauke agogon daga fuskarsa gami da janye manyan idanun nan nasa da suka rusuna sosai. "Vous pouvez reprendre votre travail(zaku iya komawa bakin aikinku)" Ya fadi cikin harshen faransanci daya sanya kowa ya koya qarfi da yaji cikin qanqanin lokaci. Window din da iska ke kada curtains dinsa a hankali yake kalla,yanajin wani yaqini da qarfin gwiwa a tattare dashi,yana jin a yau abinda zai shiga tsakaninsa da shiga dakin ajiyar mammina shine fitar numfashi daga gangar jikinsa. *MAMMINA* zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 58* *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________ Dukkanin wanda yake a muhallin.....kunnuwansa kuma suna iya dauko masa jirkitaccen sautin dake fita daga bakin almaz sai daya rasa numfashinsa na wadansu daqiqu. Da yawansu da qyar suka iya controlling iskar da suke shaqa cikin hunhunsu wadda take iya sarrafa komai na jikinsu yake aiki daidai. Ba akhnan ba da jinta da ganinta ya dakata na wucin gadi ba......hatta da birra ji tayi a lokacin kamar idan aka tsaga jikinta ba za'a samu jini ba. Da wani irin kallo da batasan wanne iri bane.....da wani irin yanayi da take jin kamar gangar jikinta bata tare da ita.....da wani irin yanayi data gaza bambance wanne iri ne take duban hanyar da almaz yabi ya wuce,hadimansa na biye dashi ba tare da kowa a cikinsu ya iya cewa komai dashi ko da ita ba. A hankali ta daga hannunta tana shafa fuskarta zuwa kafadarta,tanason taji idan idanunta biyu ne,tanason taji idan da gaske ne.....itace akhnan,idanu biyu take tsaye da qafafunta ba cikin bacci ba,ba kuma cikin mafarki ba. Itace hamshaqiyar GIMBIYAR QASAR AGADEZ itace d'a namiji a yau ya tsaya gabanta kansa tsaye yake furta ya saketa. Ya saketa a gaban BAYI ya saketa a gaban HADIMAN da suke bauta a garesu. Ya saketa ba tare da damuwa ba,ya saketa yana me juyawa ya kuma fice abinsa hankali kwance. Idanunta ta daga a hankali tana saukewa saman fuskar kowanne hadimi. Kowa yana tsaye a muhallinsa ba tare da qwaqwaqwaran motsi ba. Ba wanda yake iya daga koda yatsarsa guda daya a cikinsu. Saidai hakan tasan bawai yana nufin basuji komai ba.....hakan bawai yana nufin komai bai faru ba,hakan kuma bawai yana nufin komai zai canza daga muhallinsa zuwa inda yake ba. SAKI UKU?,CIKIN KWANA UKU KACAL?,taji wani sashe na zuciyarsa yana jaddada tambayarsa a gareta,tambayar da batasan ita dince ko zuciyartata bane zasu baiwa kanta da kanta amsa ba. Wanne irin aure mammina tayi mata?,ta samu kanta da tambayar kanta. "D wanne idanu zata kalli duniya?,da wanne idanu zata kalli al'ummar masarautarta?,da kuma wanne idanu ne IZZARTA zataci gaba da tabbata?" Ta yiwa kanta Tambayar. Saita dinga jin kamar kowa ya tattaru a gurin yana kallonya,hadiman da dukkaninsu qasa sauke kalla saboda girmamawa a gareta saita dinga jin kamar satar kallonta suke,kamar dariya suke mata,don haka ta daga qafafunta da sassarfa ta fara barin gurin. Birra ce kawai yake da qwarin gwiwar binta,ta daga qafa da sauri tabi bayanta hankalinta a matuqar tashe. Yanayin yadda akhnan din ke tafiya da wata irin sassarfa ya sake daga hankalin birra,don wani yanayi ne da bata taba ganin akhnan din a cikinsa ba. Ba birra kawai ba,yanayin tafiyar akhnan din saiya zama abun kallo cikin masarautar. Duk inda zata jefa qefarta duk da tarin dokar taqaita kallo dake wuyan duk wani d'an masarautar,amma a yau sai kowa ke binta da kallo saboda ganin canji a yanayin tafiyarta,uwa uba kuma birra da suke gani biye da ita,abinda yabar ayar tambaya a zukatan mutane,suka kuma shiga neman ba'asin wannan sauyin tafiya tata. *MAMMINA* A nutse take karbar labarin yadda abubuwa ke tafiya na kasuwancinta dake qasar habasha,wanda ba wanda yasan itace mamallakiyar abubuwa masu yawa da kamfanoni na qasar. Adadin ribar data samu a wannan shekarar kawai take saurarar lissafinta,daidai sanda taga shigowar yalwa da wani irin yanayi da ya sanyata datse kiran ba tare data shirya hakan ba. "Al'amari ya lalace Allah ya baki yawan rai.......komai ya dagule ranki ya dade". Haka kawai mammina din taji wani matsanancin faduwar gaba ya saukar mata. Ta sani muddin tanason labarin abinda ke wakana cikin gidan,ba qarya ba gauraye a ciki to yalwa take sanyawa akan komai,kuma a yanzun tasan kalan aikin data tura yalwa din tayi mata. Ta sanya idanu akan dukkan wani abu daya gudana tsakanin almaz da akhnan. Ta tabbatar ta gama sallamar almaz da dukkan wani leakage da zai sake dasa kansa da shiga gami da bude qofar zuciyar akhnan komai qanqantarta. Ita tasan akhnan,tasan dukkan wani zabi nata,tasan meye abinda yafi komai burgeta,tasan kuma hanyoyin da zasu yiwa namiji sauqi wajen kama zuciyarta. Tunda ta shiga shekarun 'yammatanci.....shekarun da sarauta suka fara mata yawo cikin jini.....izza kuma ta soma mamayar zuciyarta,kalar izzar da mammina ta tabbatar ta mata mugun kamu,tun a sannna ta cika wani sashe na kwanyarta da karantar kalar zabinta cikin MAZA. Ta tattara komai kuma ta bawa almaz,ta tattare komai ta karanta masa,saidai yalwa ta gaya mata,bataga alamun shi din me sha'awe sha'awe bane game da harkar mata,amma tayi challenge na yalwa din "Wani lokaci kina da gajeriyar kwanya me cike da gajeran tunani.....karki mata cikin gidan da zina ta zama ado ga kowanne d'a namiji ya taso,ta yaya halittar 'ya'ya mata zata gaza burgeshi?. Abu daya na sani biftu tana da kwarjini,tana kuma yiwa maza da yawa kwarjini,zata yuwu abinda ya sanya bai gama iya dorata a hanya ba kenan". "Yalwa.....kina mantawa da cewa daurin talala nayi miki?" "Na sani Allah ya taimakeki" Yalwa din ta fada tana jin numfashinta yana mata nauyi. Wani irin tsoro ne yake kama yalwa din idan ta tuna abinda ya sanyata shigowa gaban mammina. "Meke tafe dake?" Ta tambayeta tana komawa gami da zama saman sofa tana sake hade girarta sosai. "Saqon yayimin nauyi......yanayin ya girmi abinda bakina zai iya fada.....idan kuma kin matsa zan fada din,amma saidai kiyimin aikin gafara" Bayanan yalwa ba abinda suke qara mata face adadin bugun zuciyarta,haka kawai takejin zuciyarta na wani tsinkewa,amma duk da haka ta tattara izzarta da dakiyarta guri daya. "Ci gaba da wannan banzan dogon sharhin naki shine abinda zaifi baki matsala sama da komai" Mammins ta fadi tana sake tsuke fuskarta. "Kiyimin rai....kiyimin afuwa.....almaz ya saki akhnan saki uku" Yalwa ta fada muryarta tana rawa,don tana hangen girman abinda zai iya biyo baya. Cak komai na mammina ya dakata daga aiki,wata irin tsawa ta sauka saman kanta. Duban yalwa kawai takeyi kamar itace almaz din,tsahon wasu sakanni sannan ta iya buda bakinta tana jin wani irin razani yana ratsa rayuwarta. "Sake maimaitawa yalwa......amma ki tabbatar bakinki yasan abinda yake fadi,don wannan maganar ta tabbata qarya ce,ki tabbatar da cewa hukuncin kisa ne kawai zaiyi daidai da laifinki" "Ina me miki rantsuwa da girman zatin Allah almaz ya saki sarauniya biftu saki har uku". Sam batasan ta miqe tsaye zumbur ba,sam batasan ta dora hannuwanta dukka biyu saman kanta ba,tana shirin rusa gigitaccen ihu saita tuna da yalwa a gurin,don haka saita sulale kawai,sai gata zaune a dandaryar qasa ta zauna sosai,abinda ya sake gigita yalwa kenan ta sake durqushewa sosai,ganin me bada umarnin a zauna a qasa yau shine a qasa. A zaune take amma jiri takeji,sai takejin bata da wani sauran hikima,kwanyarta ta daina aiki gaba daya,da wata irin hautsinanniyar muryar tace da yalwa. "Kiramin tafisu.yanzu yanzu" Jikin yalwa na rawa ta dauki wayar da mammina kan bada umarni a kira mata wani ta fara kiran tafisun,duka duka kuma kira biyu tak ta daga. A taqaice ta sanya yalwa isarwa da tafisu saqon,saqon da yayi masifar girgixa tafisun "Dabarar farko da zaa fara amfani da ita kafin na iso.......yalwa ta kama bakinta,kada wani a waje yasan da maganar sakin,zamu gyara komai kamar komai din bai faru ba. " Tafisu mun kusa mu talatin sanda yay furucin,bansa wa zaa hana magana ba,hasalima wasu da suke gurin ba zan ko shaida fuskokinsu ballantana a hana maganar fita ga sauran mutane". Yalwa ta fadi da dukkan tabbacinta da yaqini. Ta sani,a iya adadin gutsiri tsoma irin na gidan sarauta,a iya adadin cece kuce da qananun maganganu irin na hadimai,koda gaban mutum guda ne hakan ya faru ba shakka zai wahala a dakatar da yaduwar maganar,ballantana gaban mutanen da batasan adadinsu ba. Dubanta kawai mammina takeyi,tana jin wani tashin hankali yana ratsata,tashin hankalin da ba zata tuna lokaci makamancin wannan da taji irinsa ko shigensa ba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Tana jin wacce irin cuta ce wannan almaz yayi mata?,wanne irin asararre kuma fallasassen yaro ne irin wannan?. Tana ji a ranta da zuciyarta,ya ruguza dukkan wani aiki nata,ya ruguza dukkan wata wahala tata ta shekara da shekaru. Doguwar tafiyar dake qunshe da dubban watanni......take qunshe da miliyoyin kwanaki,take qunshe da biliyoyin kwanaki?.....a yau cikin mintuna qalilan ya bata komai?. Nasarar kwana uku kacal?,kwana uku fa kawai nasararta ta kasance. "Tafisu......nasarar kwana uku kawai zanci a iya shekarun dana nata ina jiran wannan ranar?" Ta tambayi tafisu da har yanzu take riqe da wayar,nata kan itama yana kullewa ba tare da tasan ainihin abinyi ba. "Kiyi haquri,xamu shawo bakin zaren matsalar.....komai zai koma daidai" Ta fadi cikin salon kwantar da hankali. "Ki sameni gidan yanzu" Kawai mammina ta fadi tana kashe wayar. Dubanta ta mayar ga yalwa. "Inason zuwa na samu tamim da almaz kafin maganar ta fara yaduwa,inaso na gani ko akwai hanyar gyara". Ta fada tana jin komai ya jagule mata,wayo kuma da dabararta sunata narkewa gami da sulalewa suna bin ruwa. *HAISAM* A iyaka awannin yana zaune ne kawai yana monitoring dukkan wasu cameras daya saka aka maqala masa cikin dabara tsakanin d'akunan ajiyar sultane,morsa safiyya.....da kuma mammina. Cikin awanni ya sake yaqini da samun tabbacin lallai akwai abubuwa masu tarin yawa a daidai gurin,akwai abubuwa masu nauyin da aka lullube cikin dakin ajiyar. Numfashi ya zuqa a hankali yana fesarwa,ya maida bayansa ga lallausar kujerar da yake jingine a kanta. Idanunsa ya maida ya lumshe,sai maganganun nanay suka fara dawo masa a hankali. Fuskar safeena ta soma gilmawa cikin duhun idanunsa,kafin a hankali ta juye zuwa fuskar akhnan. Wannan fuskar da bai taba ganin gilmawar dariya ta cikinta ba,sabanin ta safeena da a kowanne hoto fuskarta dauke take da murmushi. Wannan fuskar dake cike da wata irin izza tsiwa da rashin sassauci. Da dukka qarfinsa ya sanya yana ture tunaninta gefe guda,amma sai wani sashe na zuciyarsa ya turashi zuwa wani tunanin na daban. ALAQARSU da nanay dinsa......alaqar safeena safiyya da nanay dinsa......ita din wani tsatso ne daga jinin da NANAY dinsa ke matuqar so...... "Jininsa ce,yar uwarsa ce" Maganan ya harba cikin kansa,nanay na yiwa mahaifiyarta wani irin qauna,hakan na nufin KULAWA da dukka abinda zai cutar da ita zai zamana kamar kyautatawa ne kai tsaye zuwa ga safeena da bata raye?. Farantawa safeena kuma yana daidai da farantawa nanay dinsa?. Idanunsa ya bude a hankali sanda sunan ALMAZ ya harba cikin kansa. Barinta tayi tarayya da almaz din a matsayin miji ya zama tamkar CIN AMANAR amincin da sultane ya bashi......wannan ya sanya a wannan daren yake jin bazai daga qafa ba har dai yakai ga ma'ajiyar mammina......inda yake da tabbacin a can din zai samu HUJJA ta qarshe......HUJJAR da zata bashi damar fita da mammina hankali kwance zuwa Ethiopia.....hujjar da zata sanyashi dakatar da duk wata alaqa tsakanin akhnan da almaz don ceto rayuwarta. A hankali tunaninsa ya soma shawagi cikin tarin tarakunan da yake hangen yarinyar dumu dumu a tsakaninsu. Daya bayan daya ya dinga dauko dukkan wani hasashe yana hadawa da dan uwansa. Cikin dukkan wani jini da zai buga zuwa sassn jikinsa yake jin qarfin tabbacin MAMMINA HATSARI CE. ita kadai ta sarqa abubuwa masu yawa?,ita kadai ta qulla tarin abubuwan da hankalin me hankali bazaikai kai ba?,ita kadai ta zama sanadi ta bangarorin da zaka dauka basu da wani alaqa da junansu?. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 59* Qarar wayarsa ya tsinke zaren tunaninsa,a hankali kuma ya miqa wayar ya daukota,saidai.sunam sultane daya gani kan video call din dake shigo masa ya sanyashi zama sosai,cikin kuma girmamawa ya daga kiran yana aje wayar a gabansa cikin cikakkiyar sallama. Tarwai fuskar sultane ya bayyana,da wannan kwarjinin nasa. Kamalar nan tasa shimfide saman fuskarsa wadda haisam yake ganin kamar ta qaru bayan tafiyar tasa. "Da alama riqon masarauta ya shagaltar da yaro na,baya nemana sam sam.....ina nan ina masa addu'o'i masu yawan gaske na dacewa duniya da lahira". Kwantaccen murmushi ne ya qwacewa haisam,yana jin qaunar sultane har ranshi. Yadda yake masa magana tamkar yana masa magana da motii ne,cikin nuna zallar qaunar da yake ganinta cikin idanun sultane din ta gasken gaske. "Aikinku sultane ba qarami bane......na yadda da cewa kudin zababbu ne kuma na musamman ne" Murmushi sultane yayi yana gyada kai,background din bayansa kuma yana nunawa haisam a cikin farfajiyar masallacin madeena yake. "Kai dinma na musamman ne muhammad,don ba kowanne mutum bane yake iya riqon qwarya ya kuma gyara masarauta cikin qananun lokuta irin wannan ba. Koda baka gayamin ba amma komai da yake gudana cikin masarautar ina da masaniya........wannan ya sanya bazan gushe ba na juyar da mafi rinjayen addu'ata a kanka,ina fatan Allah yasa kaci gaba da zama d'ana halak malak" Sosai addu'ar sultane a guri me tsarki irin wannan ya ratsa haisam din. Wani irin yanayi yaji yana bun zuciyarsa,wani rashin jin dadi kadan daya tuna barazanar da akhnan ke fuskanta. SHIN YA KYAUTA KUWA IDAN YA BARI TACI GABA DA FUSKANTAR MUMMUNAR BARAZANA IRIN WANNAN DA ZATA IYA RUSA RAYUWARTA?. Hakan yayi daidai da kalar qauna da amincin da sultane ya bashi?. Kafin yace komai yaji wata murya na magana kusa da sultane din,muryar da yaji kamar ya santa,sani kuma na sosai sani na haqiqa tana cewa. "Yauwa.....zanso ganin wannan d'an naka kuwa muhammad" Juyawa sultane yayi ya kalli me maganar yana sakar masa murmushi. "Ako ina alfaharin nuna d'ana DAWUD.....don nasan zaiyi wahala samun irinsa a kaf matasan yanxu......kokai na samu yaro kamarsa......irinsa dai sak,ba shakka abun ayi tattakin yi maka murna ne" Qasa haisam yayi da kansa,yana jin kamar sultane yana sake jibga masa wani nauyinne,yana jin kamar sultane yana qalubalantarsa ne......kamar yana qalubalantarsa akan amanar daya bashi ta akhnan.....ME YASA BAI GAYA MASA BAZAI IYA YIN YADDA YAKE HASASHE BA?,ME YASA BAI GAYA MASA BAZAI IYA YADDA YAKESO SAK DA SAK BA?. "Muhammad" Ya tsinci muryar sultane yana kiransa. Da wannan murmushi da nutsuwa ta yiwa ado ya dubi sultane yana amsa masa,abinda ke sake jefa qaunar haisam din cikin zuciyarsa kenan. "Kasan tsohuwar zumunta nawa gurin nan ya sake hadawa bayan rabuwa ta shekara da shekaru?" Kai haisam ya jinjina a hankali. "Sau da dama zaka rabu da mutanen da zaka yita begensu,zaka yita begen haduwa dasu......amma idan har zasuci gaba da zame maka alkhairi a rayuwarka,sai kaga watan watarana kun sake haduwa dasu...... Muhammad dawud.....tsohon amini na farko dana fara gasgata amintarmu.....aminin daya bani kyautar jininsa a wani aikin hajji da muka tabayi shekaru masu dan dama abaya,jinin da a lokacin banda ya bani shi,da tuni yanzun ba nine wannan sultane din nake magana ba,ya zauna dani yayi jinyata......ya fasa barin qasar nan saboda ni,har sai da bayan na warke ya kumayi tattaki ya maidani Egypt inda daga can na taho aikin hajjin har gidan da nake zaune a sannan......" "Amma dai kana yimin rowar ganin yaronka ne kawai Muhammad" Yaji muryar tadan fadi da barkwanci,abinda ya sake saka sultane dariya. "Inaso na gaya masa ne zaman shekara goma a Egypt na nemeka na rasa,bayan an gayamin kayi qaura Ethiopia,bakai ba labarinka dawud......sai daga baya na samu lambarka,zumuncin da ba'a ganin juna yaci gaba da dorawa "Bani na fada masa da kaina" Yaji ya fada,sai sultane din ya miqa masa wayar yana cewa "Kamar zaifi" Yana dariya kadan kadan. Fuskar muhammad dawud(bobbo)ce ta mamaye screen din wayar haisam din,abinda yazo musu dukkaninsu su biyun a bazata. Wani irin mamaki ya kamasu dukkaninsu,yayin da muhammad dawud ya furta. "Haisam" Yana sakin murmushi. Murmushin shima haisam ya maida masa,don ya tabbatar tunda yaga bobbo dawud din yayi hakan,baida matsala kama sunanshi da yayi. "Ka sanshi dama?" Sultane ya fadi yana duban bobbo dawud. "D'ana ne.....dan dan uwana ne......neman ilimi ya kaishi agadez ai watannin baya da suka wuce" Bobbo ya fadi,a ransa yanajin da gaske motii aba jifar kamar dan uwa yake a gunsa,hakanan haisam din neman ilimin ne ya kaishi agadez ba qarya a ciki. "Ma sha Allah,ba banza ba nakejin qaunar haisam daban cikin raina.....sak irin qaunar da nakewa khadeejatu da falaak" Sultane ya furta maganar yana dawo da fuskarsa cikin screen din. Zare wayar a hankali haisam yayi bayan sun kammala wayar yana ajiyeta saman table din gabansa. Yatsunsa dukka ya cusa cikin tattausar sumarsa yana shaqar numfashi gami da furzar dashi ta bakinsa. Me yake faruwa ne?,ta ko ina alaqa take sake danno kai?,me yasa ta kowacce fuska ake samun ginuwar sabbin alaqoqi?. Alaman shigowar saqo cikin wayarsa ne yaja hankalinsa,yayi scrolling ya bude wayar tasa sannan ya shiga kan saqon. Daga muhammad dawud ne,ya sanya idonsa a nutse yana dubawa,rubutaccen saqon daya shigo cikin yaren oromo. "Kada ka damu,kana cikin aminci,koda abinda ka shigo yi agadez zan iya gayawa sultane,amintaccen mutum ne me wata irin nagarta,nasan kai kanka kasan da haka,QASARMU da HUKUMARMU GABA DAYA SUN ZUBA IDANU SUNA JIRAN SAKAMAKO DAGA GAREKA". Wannan kalmar tasa ta qarshe yaji ta sake zuba masa qaimi. Wannan kalmar yaji ta sake zungurinsa,wannan kalmar ta sakashi ya sakejin ya zame masa DOLE ya cika wannan imanin da dogara dashi da qasarsa dama mutanensa sukayi. *MAMMINA* A wani mugun birkice da wani fusataccen yanayi take kutsa kai cikin parlor din,ba wanda takeson gani a lokacin irin almaz da kuma tamim. Ta mance da wani sallama ballantana neman iso da dama tuncan bata sanshi ba. Itake juya komai,ita ke sarrafa komai,itake bada umarni. Tun bata qaraso ba take iya hangen almaz yashe saman kujera,rabin jikinsa saman kujerar,yayin da gwiwoyinsa zuwa qafafunsa suke dire a qasa da salon kwanciyar rub da ciki wadda tayi kama data mashaya sosai,abu na farko daya fara daga hankalin mammina din,taji kamar an dauki wani abu an doka saman kanta. Idanunta suka sauka kan tamim,yana durqushe gaban almaz din,cikin wani irin mawuyacin hali dake nuna rashin sanin abunyi. A hankali ya dabo yana duban mammina dake tsaye a kansu da idanunsa da suka canza launi,yanayin dake gayawa mammina yana cikin tashin hankali da kuma tsaka me wuya kamar dai yadda takeji a jikinta,saidai a daidai wannan lokacin akwai wata halitta data kaita shiga tsaka me wuya.....akwai wata halitta data kaita jin tashin hankali. "Meye wannan tamim?.....me nake gani?" Mammina ta tambaya tana nuna almaz dake kwance yana baccin kashirban abinsa a qasa. Baya tamim yaja yana yin qasa da kansa ba tare da sanin abinda zaice da mammina din ba,a yanayinsa na zahiri kenan,yayin da badininsa ta cika da wani irin farinciki da ya jima bai tsinci kansa a ciki ba. "Kiyi min afuwa.....nayi dukkan iyawata,nayi dukkanin qoqarina,nayi duk yadda na saba,nayi kuma abinda nasan zai gamsar dake,amma hakan bata samu ba,ya sha abun maye ba tare da sanina ba,yayi buguwar da har ya iya....." Sai ya gaza qarasawa yayi qasa da kansa ruwan hawayen dake tare a idanunsa yana disa a qasa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Da gaske ya saketa?" Mammina ta zubawa tamim idanu tana masa kallon dake dauke da tsantsar tsoro da firgicin sake samun tabbacin labarin data riga ta gama samun tabbaci din. "Ya saketa,har saki uku" Tamim ya furta da wani irin sanyi. Wani abune ya tsaye mata a wuya,tana jin kamar numfashin dake qirjinta zai tsaya cak. Ta miqa qafa ta daki qafafun almaz tanajin kamar ta shafe babinsa daga duniya. "Dan banza asararrriyar halitta.....mara alfanu,dan iskan yaro. Na gama wahalar shekara da shekaru amma ka ruguxamin dukka wata sa'ata cikin kwanaki uku kacal?,cikin awa saba'in da hudu?......wanne irin mara sa'a ne kai a rayuwa?.....wahalar dubban awanni amma lalacewar awa saba'in da hudu?.....wanne irin dabba ne kai maras amfani da bazaka iya haqurin wata uku kacal ba har sai ka samu amincinta?,har sai ka fara hada shimfida da ita!" Wani tsayewa cak maganar tayi a maqogoron tamim,har yaji bazai iya tsaiwa ba a gurin,sai ya taka yana matsawa bakin qofar parlor din,yana kallon yadda mamminan keta kaiwa almaz duka da qafafunta,dukan da sam baisan ma anayinsa ballantana yaji a jikinsa. Hannuwansa kawai ya harde a qirjinsa yana dubanta,idan har tanaso gauraya asalin yarinyar ne da wani asali mara tushe,asali maras cancanta me yasa shi ba zata zabeshi ta bashi wannan ragamar ba?. Me yasa zata dauko wani baqon yaro duk da da irin wahalar daya kwashe yana yi mata?,tun yana da qananun shekaru na can can gashi yanzu har shekarunsa sun fara haurawa?. Wani irin sauti qashin qafartata ya bayar,abinda ya dakatar da ita daga kaiwa almaz duka kenan. Wani irin sabon radadi da zafi ya soma ratsata har kwanya,abinda yasa tafisu riqeta da kyau. "Dukka wannan ba girmanki bane,idan ma hukuntashi kikeso kiyi saidai ki bada umarni kawai ayi miki duk yadda kikeso dashi". "Sai nasa yayi nadamar haihuwarshi da akayi,sai na sakashi yayi nadamar sanin kayan maye da yayi a dukka rayuwarsa" Mammina ta fadi tana nunashi da yatsa tana jin kamar ta cinna masa wuta. Komai nata ya tafi,tarin burika na shekaru masu yawan gaske,kudaden da batasan lissafinsu adadinsu ba data dauki shekaru tana batarwa,har kuma yanzu da take tsaye cikin wannan qasaitaccen gidan data siya da nufin gidan iyayen almaz dinne. "Ku killaceshi mafi munin killacewa" Abinda ta gayawa tamim kawai tana riqe da hannun tafisu suna takawa a hankali suna ficewa a gidan. Wani shu'umin murmushi tamim ya saki,dama wannan damar yake jira. A irin izza da girman kan da almaz ya dinga gwada musu a kwanakin baya kamar ubansa wani ne,yana ji a jikinsa a yanxun sai ya fanshe komai,sai ya sanyashi yayi dana sanin basu umarni cikin izza daya dinga yi a kwanakin. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 60* *MORSA SAFIYYA* Duk da cewa wani sashe na zuciyarta yana riqe da lissafin daga yanzu zuwa kowanne lokaci akhnan tana iya qaura tana iya barin gidan zuwa gidan mijin da har yanzu batasan wani mutum guda daya daya jibancesu da zai iya shaida fuskarsa ba........amma tana jin wani irin sassauci daga damuwarta data fara shiga a farkon maganar. Batasan me ya kawo sassaucin ba......batasan hujja ko dalili ba,saidai tana kyautata zaton ADDU'O'IN da take shafe dare tana yi ne. Babu wani dare da zai keto sararin subhana ta kwanta tayi bacci ta kuma qarar dashi tas ba tare data tsaida duga duganta gaban mahaliccinta ba. Tana saman dining hadimarta samiya tana shirya mata abincin rana,wanda bata samu zama ta cishi ba saboda sallamar baqi dake gabanta da suka samu halartar biki. Duk da bikin ba'a cikashi da kalolin bidi'a ba,amma kuma ahalin diory hamani sun nuna kara,sun kuma nuna zallar zumuntar data kasance abu mafi girma da qarfi a tsakaninsu. A nutse ta amsa sallamar armelle da wannan kamilar fuskartata ma'abocin tarbar dukkan wanda yazo gareta da girmamawa. "Qaraso mana armelle" Ta fada tana yin bismillah hadi da soma kai lomar abincin bakinta. Kamar yadda ta buqata haka armelle din ta qaraso,ta samu daya daga cikin kujerun dake nesa kadan da morsa safiyya din ta zauna akai. Wani abu dake bawa kusan kowa mamaki,tana da wani irin sauqin kai.....bata da izzar da zaka kiranta matar babban mutum me daraja ta daya a yankin wato sultane of agadez. Ta dauki hadimanta a matsayin nata,hadimanta wasu mutane ne da take ganin kimarsu sosai,girmamawa da mutuntawa take musu kamar yadda zata karrama kowanne dan adam. "Lafiya dai ko armelle?"Morsa ta tambayeta tana tattara hankalinta a kanta. Dub daya ta yiwa morsa safiyyan,ta kalli abincin kuma dake ajiye a gabanta,sai wani irin tausayinta ya kamata. Ta sani ta dauki darare da kwanaki masu yawa bata zauna ta sanya abinci haka a cikinta ba,ta tabbatar a yanzu idan har ta isar mata da saqon da take dauke dashi to ba shakka wannan abincin ya haramta a tare da ita. Murmushi ta sakar mata. "Ba komai....wata maganace nakeso muyi,amma da fari uwargijiyata ki kammala cin abincinki,don na tabbatar kin jima baki zauna haka don kawai kici abinci ba" Dan qaramin murmushi morsa safiyya ta saki,murmushin da ya narkar da zuciyar armelle gaba daya. Murmushinan dake dauke da tarin alkhairi.....murmushin nan dake qunshe da kyautatawa,murmushin kuma da ya sake bayyana kamanninta da SAFEENA SOSAI. Safeenar da babu wata zuciya me alkhairi da zata iya mancewa da ita....safeenan da komai butulcinka cikin gidan baka isa kace bakaci arziqinta ba.....safeenar da aka tilastawa zukata masu yawan gaske lullube sunanta....danne ambaton alkhairinta.....tunata,ambatarta,dama ambatar dukkan abinda ya shafeta,saidai ita zuciyar da alkhairi ya cikata......zai wahala wani abu ya danne ganin alkhairin waninta. Hawaye taji sun cika mata idanu sanda morsa safiyya ke cewa. "Yau lelena akeyi armelle,shikenan bari nayi na kammala saimu zauna" Saita maida kai sosai tana qara hanzarin cin abincin,tasan kuma tayi hakanne kawai don ta saurareta,abinda ya saukar da wani abu me nauyi saman zuciyar armelle wanda ta kasa daureshi,har sai da tayi qasa da kanta tana boye hawayenta. "Na kammala armelle.....amma koma meye abinda ke tafe dake da alama yana da girma" Morsa ta furta cikin nuna kulawarta ga armelle din. Idanunta da suka sauya launi kadan ta daga,ta kuma kalli morsa dashi. "Yana da girma uwar gijiyata,don na jima banga ko banji abu me girma kamar wannan ba....." Kai ta gyada ta kasa cewa komai tana ci gaba da kallonta. "Ko.meye zaki jishi daga bakina ina me roqarki ki karbeshi da sauqi ta sigar yadda zai sauka a zuciyarki.....amma ki tashi da dukkan zafinki wajen ganin komai bai sake maimaita kanshi ba" "In sha Allah armelle.....in sha Allah" Ta fada cikin mutuntawa da dattako,don armelle din na cikin tsaffin hadiman gidan dake da wani irin girma na musamman. "Auren akhnan ya mutu awa daya data wuce,mijin daya aureta ya saketa har saki uku" Wani irin abu me nauyin gaske morsa safiyya taji yana sauko mata. Banda armelle ce ga fada....banda ba wasa a tsakaninsu,banda kuma kuma ita din ba abokiyar wasanta bace bata yadda za'ayi maganan ya shiga kunnenta ya samu mazauni a zuciyarta,duk da haka sai data rutsa armelle da kallo kamar me kokwanto,kafin yanayin armelle din ya gasgata mata abinda ta fada din shine dai kwance kuma rubuce cikin idanunta. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda morsa safiyya ta maimaita har sau uku,tana sanya hannuwanta gami da dafe kanta. *MAMMINA* Tun a cikin motar tafisu ke zaune gaban mammina,tana kuma shafa mata man zafi a qafarta data fara kumbura kadan. Saidai sam ciwon da takeji a cikin qafafunta baikai koda quarter din wanda takeji a jikinta da zuciyarta ba. Ta kammala sanya mata maganin ta maidashi jikin wani abu dake maqale jikin kujerun dake a gabansu,ta daga idanunta tana duban mammina din. "Ta ina zamu fara gyara da fuskantar wannan matsalar?" Mammina tayi maganan kai tsaye ba tare data dubi tafisu ba. Numfashi ta sauke tana murza yatsunta,fuskarta da dukka yanayinta yana nuna itadin cikakkiyar baqar ba'abzina ce. "Meye hasashenki uwar gijiyata,kada na miki azarbabi......amma banajin dama ya kamata mubar wannan ranar ta wuce ba tare da hasashen komai da zai iya faruwa ba da yadda zamu tunkareshi ba. Kai mammina ta jinjina,sannan tace. "Da farko ban yanke zuwa gurin akhnan da wuri ba,domin hakan zai sanya zargi da dama a zukatan wadanda ke farautar motsina". Shuru kadan tafisu tayi sannan ta amsa mata. " Zuwanki da wuri.yana da ma'ana da alfanu,kamar yadda jinkirin zuwanki shima zai zama yana da nasa alfanun,amma a wannan gabar na bar miki dukkan zabi". Idanu mammina ta sauke a kan tafisu. "Dukka wannan ba wani damuwa bace me girma a guna,koda akhnan taga kyautatawar zuwana da wuri ko bata gani ba.....abi mafi girman damuwa a gurina shine sultane.......banaso na rasa YARDA daga gurin sultane.... Lokacin rasa yardata a tare dashi baiyi ba.....har yanzu akwai GABAR da ban isa gareta ba,muddin na rasa yarda da aminci daga sultane na rasa rabin shiri na,zai zabtare ne ya zube ya barni da tarin burikana......ta wacce hanya zan amintar da sultane tafisu?.....ta wacce hanya ce zanyi abinda zai sake karkatar da hankalin sultane zuwa gareni?,na kuma sake samun yardarsa da aminci?" "Ta hanyar amintaccensa ranki ya dade" Tafisu ta furta tana qanqantar dakai cikin girmamawa. Duban tafisu kawai takeyi cikin rashin fahimta kafin ta iya buda baki ta tambayeta. "Me kike nufi tafisu?". Murmushi ta saki sannan ta dubi mammina. "Qwaqwalwarki tafi tawa aiki nesa ba kusa a dukka shekarun da muka kwashe,amma bansan me yasa a yanzu komai nake yake sanyi sanyi ba......kinfi kowa sanin WAYE sultane wajen miqa soyayya da yarda gami da aminci ga duk wanda ya zaba da mallakawa hakan......kana sake samun aminci ne daga dan adam ta hanyar abinda ya amincewa......a yanzu ba wata hanya da zaki hana yaduwar labarin mutuwar auren akhnan......ba wata hanya da zaki hana rade radin isa ga kunnuwan sultane......amma ki tabbatar ke kika fara sanar masa.....kika hada masa kuma da mafitar komai,kinsan hikimar haka?" Kai mammina ta girgiza. "Ban fahimta ba tafisu,mafita kuma ta ina?,maida auren almaz da akhnan dai kinsan abune daya haramta.....za'a shaidawa sultane haka,ko ba ta bakin kowa ba saita bakin malaman dake zagaye dashi,malaman ma irinsu wancan SHEIKH din days mallakawa dukkan yardarsa" Murmushi sosai me kama da dariya tafisu ta saki kafin ta dago ta kalli mammina. "A idanun sultane din ke wankakkkiya ce......don bashi da wata masaniya ta kusa kota nesa akan cewa kece kika zabarwa akhnan miji.........zaki bayyana masa illar zaben da ya bari akhnan ta yiwa kanta na miji,zaki kuma kafa hujja da qoqarin da kika nuna na lallai yayi bincike akan almaz kafin daura auren......a nan kuma kin sake samun wata daman ta TARWATSA dukkan wani yarda kusanci da aminci da wancan SHEIKH din ya samu daga gareshi....nasan zaki tambayi ta wacce hanya ko?" Kai mammina ta jinjina da sauri,tana jin kamar tafisu na buda mata falle fallen littafi sosai a gabanta. "Zakiyi ruwa da tsaki ta yadda sultane zai AURAWA akhnan malamin....." Wani abu mammina taji ya saukar mata kamar ana fusgarta,ta qanqance idanunta sosai tana duban tafisu. "Kina hayyacinki kuwa tafisu?,ta yaya kike tsammanin akhnan zata auri malami?" Dariya kadan tafisu ta saki. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "A yanzu MAFITA ake nema.....ba yarda aminci ko gamsuwar akhnan nan ba.....duka daga baya zamuji da wannan" Ta fadi tana taqaitawa. Dubu bisa dubu mammina ta yarda da tafisu,tasha bata mafita da shawarwari kuma ko daya ba wanda ta taba faduwa a kansa. "Ina jinki" Wannan tunanin ya sanya ta bawa tafisu daman ci gaba da magana. "Zaku nunawa sultane a yanzu akhnan ta kawo zabinta,zabinta dinnan kuma bai haifar da d'a me ido ba,saboda haka ba wanda ya cancanci ma sultane ya sake bawa akhnan din sai amintaccensa wato malamin nan.....kinga a nan zaki sake haske a idanun sultane......zaki sake fari a idanunsa,kimarki zata dagu fiye da yadda kike tunani". Sosai mammina ke gyada kanta tana jin gamsuwa da gabar farko na bayanan tafisu. "Gaba ta biyu kuma wannan wani sirrintaccen aiki ne.....kinsan ba wanda yakai malama dake zaune basa aikin komai sai karantaswa son banza?" "Qwarai kuwa" Mammina ta amsawa tafisu kai tsaye saboda tuna wani yanki na rayuwarta na baya,mijinta na farko a rayuwarta. Kai tafisu ta jinjina. "Wannan shine dalilin da ya sanya nace miki ki zabeshi a matsayin wanda zai auri AKHNAN.......bisa sharadai da tarin dukiya me yawan gaske da zaki alqawarta masa,ki fara mallaka masa wata,idan ya cika watannin da zai saki akhnan ya saketa.......ki cika masa dukiyarsa ki sallameshi......a nan kin samu mafita biyu" Dubanta kawai mammina keyi har yanxu tanason jin qarshen bayanan tafisu. "Mafitar farko kin samu hanyar da zaki maidawa almaz akhnan.....wannan idan lokaci yayi xakiji yadda zamu maida hakan ta yiwu cikin sauqi.....na biyu kuma kin lalata alaqar dake tsakanin sultane da shiekhh. Har abada sultane bazai sake ganin farin mutumin daya saki diyarsa ba.....har abada kuma bazai sake bada dama ga mutumin daya saki diyarsa ba ya sake zama makusancinsa ba kuma amininsa." Kai kawai mammina ke jinjinawa,tana kuma jin aminci da yarda da dukka maganganun tafisu. Sai takejin kamar kowacce matsalatata tazo qarshe,saidai kuma can qasan xuciyarta da ruhinta tana jin wani irin qyashi na bawa haisam din damar maza mijin akhnan koda MIJIN WASA ne......tana jin qyashi bashi damar amsa wannan sunan koda na AWA DAYA NE TAL,mutumin da ya fara daga yatsa ga umarninta?,mutumin da ya samu wani irin kusanci da bata taba ganin wani ya sameshi ba a wajen sultane......bama sultane kadai ba,a dukka fadin masarautar. Ranar data zauna tayi nazarin kalar girmamawar da take ganin dukkan wani hadimi da bawa yake bawa haisam din sai da abun ya ratsata ainun. Kalar wani girma ne da har ya zarta wanda ake bata,duk da tarin izzarta da kuma isarta. Wani girma ne daya kusa daidai da wanda suke bawa sultane,ta kuma rasa wanda zai bata amsar DALILIN da yasa suke basa wannan girman daga dukkan hadiman data tara. Abu daya data lura dashi,yana da wani irin KWARJINI da ita kanta yakan doketa a duk sanda zasuyi gaba da gaba dashi,tasha tunanin ba ordinary sheikh bane.....amma a yanzun ta fara shiga kokwanto,don ta gaza gano komai daya kebanceshi da zai bata hujja a kansa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 61* Ba wannan ba gaba daya....,can wani sashe na zuciyarta ke tuna mata WAYESHI?. Da kalar wannan izzar da kusancin da yakeji ya samu zaya yarda da sharuddanta?. Tambayar data jefawa tafisu kenan. "Yana da wata irin izza da girman kai na banza tunda ba kowan kowa bane.....ina hangen wani irin taurin kai a tattare dashi tafisu.....ina ganin koda zai amince bazai yarda ya karba sharuddana da auren ta cikin sauqi ba". Wani murmushi dake gayawa mammina tafisu tana da kowacce mafita ta matsala da zata tunkarosu ta saki. "Ba wanda yafi qarfin barazana da takan iya juyewa ta zama gaske.....indai ba daga sama ya fado ba ai yana da ahali.....idan baida mahaifiya yana da mahaifi,idan duka babu akwai makusanta......ki tabbatar masa da daukan rayuwarsu daya bayan daya har sai sanda ya aminta da sharudanki,ruwansa ya karbi ladansa ruwansa kada ya karba". Ta fada hankali kwance. Kai mammina ta girgiza "Banajin barazana zata juya wannan.....amma a maganganunki na tanadi hanyoyi biyu da zan sashi karbar buqatata ta ruwan sanyi" Ta furta tana sakin qaramin murmushi. "Ki samomin qaramin malami,ina buqatar wasu ayoyi da hadisai da zan riqe koda qananu ne" "An gama" Tafisu ta amsa tana rusunar da kanta. *MORSA SAFIYYA* Ta jima tana maimaita innalillahi din,har zuwa sanda taji wata nutsuwa ta soma saukar mata a zuciyarta a hankali. "Rakani armelle......inaso na ganta" Ta fadi tana miqewa daga kan kujerar,tana kuma jin jiri kamar zai kayar da ita. Tafiya kawai takeyi amma tana jin kamar tana taka qasa ba daidai ba. Takawa take da wani irin yanayin da takeji kamar iskar daminar dake kadawa zata kayar da ita Qirjinta da zuciyarta a quntace,idanunta suna dauko mata shekarun baya. Sanda safeena ta amsa sunan BAZAWARA a qasa da shekara daya tal da aure.....bata fata hakan ta kasance akan akhnan,bata fata itama wannan sunan ya bita,duk da cewa ta sani basu riga da sunkaita gidanta ba,amma bata da tabbacin dukkan abinda ya faru a bayan idanunta. Da idanunta take hangen tsaiwar jama'a biyu uku daga taku xuwa wani takun nata. Mafi yawancinsu mata ne,kuma a take jikinta ya fara gaya mata suna tattaunawa ne kan al'amarin,tabbacin magana ya fara yaduwa kenan,abinda ya sake quntata qirjinta. *AKHNAN* Duhun da dakin yake dashi a yanayin yafi mata komai dadi,tanajin kamar ta tserewa duk wani kallo na tuhuma ko tozartarci da zata iya fuskanta. A wani irin soye takejin zuciyarta da wani irin yanayi da ba zata tantance wanne iri bane. Abu daya da takejin yana zagayawa a jikinta da zuciyarta gaba daya shine TOZARCI da QASQANCIN da almaz ga ajiye mata cikin tarihin rayuwarta,wani irin mummunan tarihi data tabbatar har a gama sarauta a agadez ba za'a manta da ita ba. Wannan shine ABINDA TAKE GUDU shine abinda ya sanya taketa gudun wuce sa'a tsakaninta da kalmar AURE. Ta sani cewa,ba komai a cikinsa sai tarin bin umarni da barin dukkan wani da zuciya keso ko muradi ko kuma buri,dukka don kawai ka cika muradin NAMIJI. Mammina da sultane tana iya kiransu da cewa SUNE SILA......duk da ta fannin sultane tana masa uzuri da cewa ZIGA ce da qoqarin shiga tsakaninsu da akeyi tun can can. Amma ta fuskar mammina fa?......makancewa tayi?,tunaninta ya gushe ne data dauko makakke mashayi ta damqa ragamar igiyar aurenta a hannunsa?. Me yasa mammina bata qure duba cancanta ba?,me yasa bata zagaye kusan rabin duniya ba saboda ita?....me yasa?.....me yahau kanta ta zabo mata mutumin daya munana kyakkyawan tarihinta?. A hankali morsa safiyya ta murda qofar dakin tana shigowa idanunta zube akan akhnan din. Kallon kusan sakanni talatin tayi mata sannan ta saki qofar tana takowa a hankali zuwa inda akhnan din ke zaune. Fuskarta tayi wani fayau a iya awannin kawai.....wannan blue eyes din sun rune da surkin jaja jaja a cikinsu. Kusa da window take zaune,saidai ba dukkanin fuskarta bane ke kallon window din. Sosai morsa safiyya ke hangen wani irin yanayi tattare da akhnan din,yanayin data tabbatar UWA ce kawai zata iya hangensa akan d'iyarta. A firgice take gaba dayanta,saidau rashin sanin makomar rayuwarta da abinda ke mata ciwo da zafi........abubuwan da suka cancanta da rayuwarta gaba daya ya sanya bata fahimci komai ba,ta yanke kebe kanta a matsayin wani hukunci daya dace da ita. Tana iya hangen yanayin cikin idanun akhnan din,kamar an qara mata shekaru tsakanin kwanaki ukun da aka daura mata aure. Ta sake zama wata mutual data tabbatar girman igiyar data yanke cikin kwanaki uku ne ya haifar da hakan. Har cikin jikinta taji shigowar morsa safiyyan,saidai zuciyarta na gaya mata ne.....ta shigo taga fitar hawaye ne daga idanunta?....kota shigo ta nuna farincikinta na mummunan abinda ya sameta?.....ko ta shigo ta bayyana mata cewa ta samu nasara a dukka shirinta. Yanayin akhnan bai hana morsa safiyya kusanta kanta da ita ba,daga can qasan zuciyarta takejin wani irin rauni,yanayin yana daukota mata hoton safeena sak a irin wadancan shekarun tun kafin samuwar akhnan din. Bata dakata ba har sai data isa dab da akhnan din,a nutse ta zauna saman kujerar dake fuskarta ta,kujeru qwara biyun da aka ajiyesu kawai a gurin me dauke da qaramin table a tsakiya. "Ba buqatar ki tambayeni komai......labari nasan ya riskeki,ba sai kin taso ganin hawaye a idanuna ba kafin ki samu tabbaci.....da gaske ya sakeni,ya sakeni saki uku.....shikenan dukkan wani fata da buri sun gama cika?" Akhnan ta fada da wata murya me nauyi,wanda duk daga harshen da zatayi wani irin d'aci takeji yana sauka saman harshen nata. Mamaki sosai ya saukarwa morsa safiyya,saidai har yanzu tana jin cewa ita din UWA ce......a yanzu ne kuma takejin lokaci yayi da zata kusantar da kanta da rayuwar akhnan din,wannan zargin da wannan zaton da take mata tana jin ya kamata ta maidashi reality.....abu d'aya daya rage tayi,koda zata zargeta......koda zata tuhumeta nan gaba ko bayan babu ranta zatasan bata da wata UWA a duniya bayan ita. "Ba wata uwa dake burin ganin ibtila'i cikin rayuwar d'iyarta........sau da dama fuskokin dake murmushi a garemu ba sune asalin fuskokin masoyanmu ba......hannuwan dake miqo kansu garemu,ba sune hannayen daya cancanci mu kama mu riqe don samun kubuta da tsira ba,wani lokaci suke fincikarmu zuwa ga shiga kowacce matsala da muke tsintar kanmu a ciki.......na samu amsar tambayar farko daga gareki" Morsa ta fadi da wani irin yanayi da akhnan din bata taba jin morsa safiyya din tayi magana dashi ba. Bata sake cewa komai ba,taci gaba da kallon akhnan din tana karantar wasu halaye da akayi mata horo dasu. Tana daukan nesanta kai a matsayin AMINCI,shi yasa koda wanne lokaci take zabar nesanta kanta da kowa da komai idan tashin hankali ya sameta.....saidai ba haka siddan aka koya mata hakan ba,an koya mata hakanne saboda ta zama me karbar kowacce shawara idan aka kusanceta da shawarar.......ta zama me ragaggun hanyoyin samawa kanta da zabawa kanta abubuwan da suka dace. "Zanyi nesa dake,don na samu tabbacin bai taba lafiyarki ba.....to alhamdulillah.....amma hakan ba yana nufin zanyi nesa da rayuwarki ba,zan zama maras abun cewa akan abinda ya shafi rayuwarki......sam sam.....tun kina qaramarki akwai wani SHAMAKI da aka sanya tsakanina dake......akwai wanda yake kururuta samuwar TSORO cikin kunnuwanki.......akwai wanda ya koya miki ganin ABOKAN GABA DA ADAWA a inda sam sam babu su........a wannan lokacin zan kasance tare dake koda ban zauna kusa dake ba......zan kasance me ruwa da tsaki gurin yanke hukunci akan RAYUWARKI ta gaba.....koda hakan yaha nufin ba zaki sake kallona a matsayin QANWAR SAFEENA ba har abada......ban damu ba muddin zan bawa jinin safeena qwaya daya tal daya rage kariya.....banzo don na zauna nayita tambayarki ba......don iya abinda nakeji game da sakinki na tabbatar KARIYA ce ubangiji ya baki,duk da ke a wajenki zai miki kama da MASIFA da TASHIN HANKALI.....tambayata guda daya ce......kun hada jiki dashi ko baku hada ba?" Morsa ta yiwa akhnan tambayar kai tsaye tana tsareta da wani irin zazzafan kallo. Da sauri ta daga kanta zuwa ga morsa safiyya,zuciyarta na tafasa tana amsar duk wata magana data fita a bakinta tana farfasata,ba abinda zuciyarta ke gaya mata illa mammina take toxartawa da kalamanta. A qasan ranta karon farko tunda ta zauna a gurin tana jin wani zafin mammina ne a ranta akan zaben data mata,tana jin a wannan karon tana da tarin tambayoyin da zata yiwa mammina akan mijin data zaba mata......amma batasan me yasa takejin zafi da baqar magana ko baqar kalma guda daya da aka gaya mata ba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Ta daga kai ne da niyyar tsare morsa safiyya da kallon da zai sanya ta fahimci ita din ba kowa bace da zata tasata a gaba da wannan tambayar,ba huruminta bane wannan bata da wannan ikon,amma kuma a yau a karon farko kallon dake cikin idanun morsa safiyya din wasu iri ne......wani kallo ne na daban daya sanyata dole ta juyar da fuskarta gefe tana jin wani abu me kama da tsananin nauyi yana sauka a idanunta da zuciyarta,tana kuma jin girman tambayar da nauyinta. Siririn numfashi kawai morsa safiyya ta sauke,koda akwai rashin kunya da izza a idanun akhnan,amma ta gama samun amsar ba abinda ya hadata da almaz. "Alhamdulillah" Ta furta a hankali tana miqewa. Hamdalar ta sake jawo hankalin akhnan din,me take nufi matar?,tana murna kenan da abinda ya sameta?. Me yasa wai ba zata canza ba?,me yasa ma take kiran kanta a matsayin qanwar mahaifiyarta?,bayan tana maraba da duk wani bala'i da zai sameta?. Har cikin zuciyarta takejin wata nutsuwa tana saukar mata,duk wani tashin hankalinta akan auren yana sake gushewa,tana sake gasgata girman ubangiji da buwayarsa,komai zaiyi akwai hikimarsa a ciki amma ga ma'abota hankali. *MAMMINA* Sai data koma sassanta ta sauya shigar jikinta sannan ta nufi sassan akhnan. Sassan da tana sanya qafarta zata shiga morsa safiyya na fitowa da tata,saita samu kanta da wani irin faduwar gaba. Bin juna sukayi da kallon kallo,zuciyar mammina cike da fargaba da shakku gami da tarin tambayoyin me yakai.morsa safiyya din sashen akhnan haka da wurwuri daga faruwar abun? Kada Allah ya bawa akhnan damar furta komai ga morsa safiyya din,duk da tana da yaqini,tasan abune me wahalar gaske wata magana ta shaquwa ko fahimtar juna ta shiga tsakaninsu. Ta dade da kashe wannan feeling din a tsakaninsu,ta dade da cusawa akhnan ra'ayi da hali na tsananin qyamar morsa safiyya da kuma sanyata a sahun farko na maqiyanta. To amma a yanzu bata da tabbas akan kowa da komai,har saita saita komai yadda takeso yaci gaba da kasancewa. Sassanyan murmushi morsa safiyya ta saukewa mammina sannan a hankali ta dauke kanta tana fita a gurin cikin cikakkiyar nutsuwar nan tata data jima tana huda zuciyar mammina din.. Raga raga murmushin yayi da zuciyar mammina......ya sake ajiye wata qatuwar fargaba da kuma rashin tabbas a cikin zuciyarta,wannan ya qara mata qaimin sanya kai zuwa sassan akhnan da sassarfa. Fitar morsa safiyya ta barta da wani irin tunani me zurfin gaske a kanta,tunanin da baiyi zurfi ba taji muryar mammina tana qwala mata kira da wannan muryar da kowanne lokaci take nuna zallar tashin hankali akan dukkan wani mummunan abu da zai sameta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 62* Idanunta ta lumshe kawai ba tare data waiwaya ba,idanunta ta lumshe kawai tana ci gaba da sauraron muryar mammina din maimakon ta tashi ta fada jikinta kamar yadda ta saba a dukkan wani abu da zai sameta. Haka kawai yau bata jin saukar muryar saman zuciyarta,a yau din bata jin sautin da yanayin yana ratsa zuciyarta yadda ta saba jinsa. Sak mammina tayi tana duban akhnan dake zaune kawai,ba wani alamun motsawa ko xuwa gareta kamar yadda ta saba a duk yanayi ko lokaci makamancin wannan. Gabanta ya fadi,shakkarta da kokwantonta suka dadu,amma sai tayi saurin canza yanayinta da sake takowa gaban akhnan din da sassarfa tana fadin. "Na shiga uku ni zaituna.......biftu,ya taba lafiyarki ne?" Ta qarasa maganan tana zubewa gaban akhnan,gami da sanya hannunta tana dudduba jikinta kamar me neman wani abu. "Kiyimin magana mana biftu......na rantse da ubangiji dake busa mana numfashi bazan barshi ba". " Zaki masa mene?,zaki iya goge abinda ya faru ne?,ko don bai bar tabo a jikina ba hakan yana nufin tabon dake zuciyata ma zai goge ne ko zai warke?,har abada" Akhnan ta amsa mata da wata irin dakakkiyar murya. Sosai mamaki ya tsarga a zuciyar mammina.......wanne irin magana akhnan din takeyi haka?,me takeson fadi?,anya safiyya batayi amfani da wata hanyar ba ta soma gotarwa da akhnan tunani?. "Kuskurenki ne tun farko.....kuskurenki ne mammina.....kinyimin alqawarin zaki fiddani......amma kuma sai kika sake dilmiya ni cikin wata sabuwar matsalar.....mafi munin matsalar ma da gwara bijirewa maganan sultane da umarninsa akan wannan KARYAMIN DARAJAR da kikayi" Tayi maganar karon farko hawaye na taruwa cikin idanunta,duk da batajin zata bari hawaye ko daya ya zuba daga idanunta wai don aurenta ya mutu,koda zatayi kuka ma,zatayi kuka ne kawai saboda tabuwar DARAJARTA da kuma MARTABARTA. "Me kikasha akhnan?.....baki da hankali ne?.....ni kikr tuhuma da jefa rayuwarki a wani yanayi bayan dukkan sadaukarwar da nayi?" Ta fadi da wani mugun hargagi da bata taba mata irinsa ba. Da wani irin kallo kawai takebin mammina,tsawarta tana sauka saman zuciyarta da wani irin yanayi,saboda wani abune baqo kuma sabo da bai taba faruwa tsakaninsu ba. "Ba komai biftu,na gode na gode" Mammina ta furta tana qoqarin dauke hawayen daya soma zarto mata daga ramin idanunta. Har Tsakiyar kanta takejin fitar hawayen,a tsahon shekarun rayuwarta ashirin da hudu bata taba ganin duk girman tsanani mammina ta fidda hawaye ko sau daya ba,sai yau?,kuma a kanta?. BAKI KYAUTA BA taji sautin yana sauka saman zuciyarta. A hankali ta dauke kanta gefe,muryarta dauke da izzarnan dake sake tsananta tsanarta a zuciyar mammina tayi magana. "Bazanyi magana dake ba MAMMINA.....ina roqonki ki tafi daga nan". Idanu ta zuba mata sosai,tana jin wani abu yana taso mata. Ita kadai tasan me takeji akan yarinyar.......ita kadai tasan adadin kaiwa bango da tayi. Ba shekara daya ko biyu ba,ta jima tana sanyata hidimta mata bawai kai tsaye ba.......ta jima tana bata umarni masu tarin yawa,kafin ita ta samu daman maidata qasa ta koma karbar umarninta. "Zan tafi......amma hakan bai yana nufin xan kasa yin abinda ya dace ba a matsayina na uwa.....ko yau she xanbar miki qofata a bude,duk sanda kika buqaceni ina nan ina jiranki" Maganar mammina ta qarshe kenan ta juya tana fita da wani irin yanayi dake nuna sanyin jikinta. *MORSA SAFIYYA* Wani irin shuru ne ya ratsa dakin,ba a abinda ke motsi banda bugun zukatansu dake cike da wani irin nauyi. A zaune suke suna fuskantar juna ita da hairaan,gwiwoyinsu suna gugar juna,hannuwan morsa safiyya din dukka cikin na hairaan data kama ta riqe sosai tana matsasu a hankali don samarwa da morsa safiyya nutsuwa,wadda bugun zuciyarta da numfashinta suke fita wani iri. "Ki shaqi iska sosai momma......ki fitar ta bakinki don Allah" Hairaan ta fadi cikin tashin hankali. Yanayin da take ganin morsa safiyya din a ciki yafi daga mata hankali fiye da labarin mutuwar auren akhnan din da take sanar mata a yanzu. Murmushi kadan morsa safiyya ta saki cike da wannan qarfin halin nata,idanunta akan hairaan. "Kina tunanin na rude da yawa ko zan rasa hayyacina?...." Saita girgiza kai. "Ni da naga mutuwar safeena tsakanin cinyoyina hairaan,naga mutuwar mahaifinki,bacewar ahmad a sanda nafi tsananin buqatarsa,bana tunanin akwai wani abu da yayi saura wanda zai bugani sama da buguwar da nayi a wancan lokacin. Tabbas inajin radadi,inajin tsananin baqinciki da kalar rayuwar da aka shiryawa akhnan take kuma yinta,wannan rayuwar a yanzu ba qaddararta bace.....rubuta mata ita akayi,a wannan karon kuma sai inda qarfina ya qare,koda zan rasa numfashina.....koda zata batar dani kamar yadda tayi mana a faro a Ethiopia. Barazanarta tazo qarshe hairaan.....ku shirya RASANI daga yanxu zuwa kowanne lokaci.....na yarda da amince zan narkar da rayuwata saboda safeena,saboda biftu ". Sosai zuciyar hairaan ta karye,wani irin abu takeji cikin jikinta yana ratsata da yafi girman tashin hankali. "Ki daina fadar haka momma.... Muna tare dake......tare zamu kawo sauyi wa rayuwar akhnan.....ba kuma tare da komai ya sameki ba.....gyara za'ayi kawai,ba batu ne na rasa rayuka ko salwantar wani abuba" Wani murmushi momma ta saki tana duban hairaan din. "Hairaan.....kece aminiya guda daya da nake magana da sirri dake.....kinsan komai ba abinda yake boye gaba gareki,amma har yanzu bakisan girman SHARRI da KAIDIN MAMMINA BA......bakisan wace zaituna ba....sannan bakisan wace zeenatu ba.....a kaf tarihinta ni kadaice na tsaye mata a gaba ta kasa bi ta kaina......nasan Allah ne yayimin da girman addu'a. Har yanzu tun bayan shekaru talatin da suka shude baya ban qara kwanciya nayi bacci ba irin na kowa da kowa hairaan,bacci na gaske dama bacci na ma'ana......inda ace nayi hakan da ban haifeki ba,da ban haifi falaak ba,koda tsananin rabo ya sanya na haifeku da a yanzu ba maganata akeyi a nan ba......ba komai falaak zata iya daukewa ba,shi yasa na aiketa kitchen ta kawo madara......amma ke din mun saba binnewa da rufewa dake....." ".....za kuma muci gaba tare momma.......wanne mataki ne kike ganin zai zama na farko don tseratar da rayuwar biftu". Shuru kadan morsa safiyya tayi,wani abune daya jima yana mata yawo cikin kanta,wani al'amari ne da takejin kamar ana tilasta mata. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Hairaan" Ta kirata a hankali sanda falaak ta buda qofar dakin ba tare da dukkaninsu sun sani ba,saboda wani kalan qofa ne da baya bada alamu na an budeshi. Tana sane ta dakata daga bakin qofar,don tunda momma ta aiketa kitchen tasan cewa korarta kawai tayi,akwai abinda bataso taji,yanayin momma din da sakin bazatan da mijin biftunta ya yiwa biftu din ta tabbatar wani abu ne da dole zai gigitata fiye da zatonsu. "Na dade a zuciyata inajin cewa sun dace da juna......haka kawai idan na kalleshi sai na dinga jin kamar D'ANA.....idan na ganshi hairaan sai na dinga ganin AMINCI kawai a tare dashi. Kusancin da sultane ya bashi cikin rayuwarsa da sarautarsa.......na tabbatar bayan K'AUNA da yake masa.....akwai wani abu da bai furtawa kowa shi ba......nasha mafarkinsa tare da ita.....nasha ganinsa a mabanbantan yanayi ya zame mata wata irin qatuwar GARKUWA......ina me yanke shawarar tunkararsa sheikh haisam kai tsaye......akan yayimin alfarma ya karbi auren AKHNAN.....koda bazai zauna da ita na har abada ba,ya cireta daga wannan cakurkudadden yanayin har zuwa sanda komai zai lafa,har zuwa sanda akhnan zata gane kanta.....har zuwa sanda zata fahimci WACCE RAYUWA TAKEYI.....fahimtar da sultane dama karbar yanayin shine yafi komai sauqi a gurina,don nasan tabbas shima yana burin mallakar suruki irinsa....." Duk yadda falaak taso ta hana kwanukan hannunta rawa amma ta gaza......ta gaza tsaida rawar da hannuwanta keyi wanda ya warwatsu har xuwa sassan jikinta. Ta kasa controlling komai,har zuwa sanda tea tray din ya subuce mata ya kuma tarwatse a qasa,qararsa kuma ta qara adadin razanin da takeji cikin kwanyarta,saita saka tafin hannuwanta tana danne kunnenta saboda yadda taji girman sautin yana mata yawa cikin kwanyarta. Bakin qofar suka kalla su duka biyun,morsa safiyya da hankalinta da kuma tunaninta yake a wajen ta zubawa falaak idanu. Wani abu ya harba a qirjin morsa safiyya,can qasan zuciyarta ta fara yiwa Allah magiya da ya taqaita faruwan komai. Hairaan kam da batasan dawar garin ba ta soma magana cikin fada fada,don faduwar kayan a bazata ya tsoratata. "Mene haka falaak?,wanne irin shashanci ne wannan?,daukar tray ma kawai kada kicemin baki iyashi ba". Bata iya amsawa tantee hairaan din ba,don ba ma fahimtar abinda take fada takeyi ba. Juyawa kawai tayi tana burin barin gurin kafin takai ga faduwa a gaban momma. Batasan rauninta ya bayyana a gaban momma din,muddin ya bayyana ba zata iya boyewa momma komai ba. Ta sani zata iya fighting akan batun,ba zata iya jurewa ba,saidai kuma sautin momma din shine abinda ya katse mata hanzari. "Zonan ke falaak,ba magana ake miki ba?" Ta fadi da kaushin harshe sosai. Batason ta wuce bata amayar mata da abinda ke cikinta da zuciyarta ba. Tanaso ta san mene ainihin abinda yake zuciyarta......tanason ta tabbatar da gaskiyat zarginta,idan har ya kasance haka kuwa,to lallai zata taka biriki wa tunani da hangen falaak. Qafafunta na hardewa guri guda ta qara so gaban momma ta durqusa. "Me ya sameki?" Ta sake cusa mata tambayar tana dubanta. "Kada ki tambaya momma....kada ki tambaya" Ta fadi muryarta na wani irin rawar dake nuna kuka yana dab da qwace mata. "Ki fadamin falaak nace!" Momma ta furta a tsawace. Tasan halinta sarai,idan ba hakan tayi mata ba bazataji komai ba!. Tanaso taji komai tunda wuri.....tanaso ta yiwa tufkar hanci tunda wuri. "Ki fadamin!" Ta sake tursasata a tsawace. "Inasonshi momma......ina sonsa,don Allah karkiyi yunqurin hadasa da kowa" Falaak din ta furta kanta tsaye kuka yana qwace mata,idanunta cikin na momma din. Sosai momma ta zuba mata ido,qirjinta yana bugawa,bataso haka ta kasance ba.....bataso wannan amsar bace zata fita daga bakin falaak ba,to amma ta shirya sadaukar da farinciki kowa saboda daidaita rayuwar akhnan. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 63* "Inda ya halasta ya hadaku ku biyu zanyi qoqarin hakan ya kasance ne falaak......amma tunda hakan baixo cikin halastaccen nassi ba dole ki haqura ki barwa 'yaruwarki!!!.....dole ki cireshi daga zuciyarki....daga rayuwarki!!!....dole ki sadaukarwa da akhnan shi.....ta fiki buqatarsa!!!.....ta fiki buqatarsa!!!" Momma ta fadi da wani irin zafi na tausayin falaak dake qona duk wani sashe na zuciyarta,saidai tana ji a ranta ya zama dole ta gwadawa falaak qarfa qarfa,ya zama dole ta gwadawa falaak bata tausayinta.....ya zama dole ta gwadawa falaak bata tare da ita don ta ceto JININ SAFEENA. "Momma....." Falaak ta kira sunan morsa safiyya tana jin kamar zata rasa wani sashen ne na jikinta. "Banaso ki sake cewa komai falaak.....bana buqatar ki roqeni koki nemi canza hukunci na". Tsam kawai falaak din ta miqe,tasan cewa tunda har morsa safiyya ta fadi hakan ba wani abu da zai canza mata magana. Harhada hanya kawai takeyi,tana jin kamar zata suma kafin takai ga isa dakinta. Da wani irin narkakken tausayi hairaan ta maida kallonta ga morsa safiyya. "Amma momma......" Hannu ta daga mata tana qoqarin narkar da tausayin falaak daya tsaya mata a wuya. "Kibi kawai hairaan,karki sharhi ko fashin baqi" Kai take jinjinawa hairaan din. "Na fahimta momma.....na fahimta,kuma gaskiya kike fadi,akhnan tafi falaak buqatar haisam.....duk da cewa ita din batasan darajarsa ba.....ta yaya zaki fahimtar da ita?....falaak kuma still tana buqatarki,don Allah karki tsaurara mata da yawa". Jikin morsa safiyya a mace take duban hairaan. "Bazan tsaurara mata ba hairaan,nasan wannna ciwon,nasan ciwon kubcewar abinda kakeso.....amma idan na riga falaak saukowa ba lallai na samu abinda nakeso ba,inaso ta aminta da kanta zatayi sadaukarwa.....inaso ta fahimta 'yar uwarta ta fita buqatarsa...." Saita dakata tana sauke numfashi. "Akhnan ba.......ba zata taba fahimtar muhimmancinsa amfaninsa ko gata da akayi mata dashi ba sai a nan gaba.......na gama shiryawa da karbar dukkan wani abu da zata kalleni dashi hairaan......ki dafamin kawai a inda kikaga zan gaza" "Na miki alqawari momma......sai inda qarfina ya gaza" Hairaan din ta furta tana dora hannunta saman na momma. Wannan hali.....wannan dabi'ar,wannan soyayyar da momma kewa shaqiqiyarta ya sanya itama ta tashi da qaunar 'yan uwanta,falaak da akhnan. Duk da kasancewar akhnan din me baudadden hali....duk da kasancewarta wadda ba jituwa tsakaninsu,amma wannan qaunar wannan soyayyar babu wani abu da zai canzata. *_DARE MAHUTAR BAWA_* Lokacin da gidan ya soma kaurewa da tashin hankalin ganin wutar da ba'asan daga inda asalinta ya kunnu ba......a daidai wannan lokacin ne shi kuma yayi nisa cikin killataccen dakin ajiyar mammina din. Wani irin guri ne me sarqaqiyar da bai taba tunani ba,saidai yayi amfani sosai da salon irin qwarewar daya cikin NISS ya soma karantar gurin ta qaramar na'aurar daya cilla a ciki me kama da qwaro. Tun a sannan ya gama karantar taswirar gurin,ya kuma karanci irin na'urorin da aka zuba cikin duhun gurin kawai don bashi tsaro. Kowacce na'ura idan ya juya bayanta da na'urar daya sanya a ciki din sai yaga ba wani aiki bane me wahala a kanta ba,don haka cikin kwanciyar hankali ya sauyawa kowacce na'ura fasalin aikinta kafin yakai ga shiga. Abu daya ne daya dauki hankalinsa,har zuwa sanda ya shiga gurin yakai qarshensa baiga wani abu daya da zai iya kamawa a matsayin abun zargi ga mammina ba,baiga koda wata alama qwalli daya da zai bashi haske ba. Dukkan wani tunani da yakeyi na samun komai daga cikin dakin ya yanke. Da hanzarin da bazai baka daman jin motsinsa ba yaci gaba da duba komai a gaggauce,gaggawar data cakuda da nutsuwa gudun kada ya bada wata alama ko sauti. Tas ya kammala amma bai samu koda takarda qwaya daya ba. Yayi tsaye a Tsakiyar dakin,ya sake daga hannunsa yana duban agogon dake tafiya daidai da nasu beeno dake daure a hannuwansu,wadanda ke cikin mutanen dake qoqarin tsaida wutar,wasu daga cikinsu kuma suna kewaye ne da gurin cikin duffan bishiyoyi suna masa gadin hanyar. Murza agogon yayi,ya qara mintuna goma akan mintunan da suka tsara da farko,yayin da sautin alamun qara lokacin ya isa ga agogon kowa,suka kuma fahimci me yake magana akai duk da bai furta kowacce kalma ba. Hannayensa daya riqe qugunsa dashi ya sauke,haka kawai cikin jikinsa yakejin bai gamsu da cewar ba komai a dakin ba....zuciyarsa da gangar jikinsa dukka basu nutsu ba,sai ya waiwaya yana sake duban bangon qarshe na dakin. A hankali ya zame kallonsa zuwa qasan dakin,soma lissafa adadin jajayen duwatsun dake iya bangaren yayi,wanda duka duka fadinsa bazai wuce na babban faranti ba. Ya sake maimaita irgen,yana comparing da adon cycle din dake kusa da wajen. Akwai banbancin duwatsu jajaye goma a gurin,abinda yaja hankalinsa,ya soma takawa a hankali yana kusantar gurin. Tsugunnawa yayi,yakai hannunsa ya shafa,ga mamakinsa wani shocking yaji a yatsunsa,sai ya dauke hannunsa yana kallon gurin sosai. Fes komai ya dawo masa kansa,salon kebantaccen gurin ajiya na qarqashin qasa da tsofaffin sarakunan qasar Ethiopia keyi don adana muhimman bayanansu koda yaqi xai cimmasu. Wani qaramin murmushi ya subuce masa,yana tuna yadda ya cire shocking a daya daga cikin wasu gurare da suka taba shiga don yin bincike,sai ya cire jakar bayansa ya ajiye,ya koma soma lalata tsarin tsaron gurin. Yana kammalawa gurin ya soma matsawa,yasa hannunsa ya qarasa matsar dashi gefe,take wani abu me kama da akwatin qarfe me zubin zinare ya bayyana. Shi kansa bai samu damar budeshi kai tsaye ba sai daya lalata zubinsa,bisa yaqinin zai iya maidashi kamar yadda yake. Sannu a hankali ya fara fiddo da takardun bayan ya ture wasu nau'ikan gold dake zube saman takardun. Daya bayan daya yaci gaba da fito dasu yana karanta bangon kowanne file kafin ya ajiyeshi a gefe. Sannu sannu qafafunsa yaji sun fara masa nauyi,kaman ba zasu iya daukarsa ba. Wani irin tsananta bugu zuciyarsa ta fara yi sanda ya soma cin karo da takardun da suka fara fayyace masa WACECE ZAITUNA sannan kuma WACECE ZEENATU. Wasu irin bayanai da yayi imanin bacewar basira ce ta sanya ta binne komai a guri guda a muhalli guda ba tare data rarraba gurin ajiyar bayanan ba. Katin daurin auren dake tsakiyar takardun yakai hannunsa yana budeshi a hankali. Sunanta ne da manyan rubutun da akayishi da yaren gumma......da kuma manyan sunayen AHMADE AJANI daga sama. Wani irin iska me zafi ya fessr,zuciyarsa ta fara wani irin kumbura. Ashe dukkanin hasashensa ba wani da yayishi ba daidai ba?...... "Zeenatu.....ZAITUNA" Ya maimaita sunan a fili,sannan ya miqa hannunsa yana zaro wani file gami da komawa gefe ya zauna tamkar ya manta lokacinsa qayyadadde ne. Dairy ne.....diary din mamminan data zauna ta rubutashi da hannunta cikin cikakken yaren oromo da babu algus ko kadan a cikinsa. ∞∞★ Cikin wani irin zafin jiki dana zuciya yake kaiwa da kawowa cikin bedroom din nasa. Komai ya lafa,gobarar ta dakata kamar yadda yaso,bata kuma ci wani abu me yawa ba sai tarin hayaqin data turnuqe masarautar dashi. Sunyi aiki me kyau dukkaninsu cikin tarin qwarewa da gogewar da suka samu qarqashin *obbo muhammad haisam,code name dinshi na gurin aiki AL-SAAMIT(THE SILENT ONE)* Tinjimin aiki cikin yanayi na nutsuw kamewa da yin shuru,saidai yakan fidda sakamakon da yake qarawa NISS daraja martaba da daukaka a duk sanda ya kammala wani operation nasa,wannan ya sanya ya fita da wannan sunan cikin code name da ake bawa kowa a hukumar. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Yasan komai ya tafi daidai,tunda a nutse ya kammala bincika dukkan abinda zai bincika din,sannan ya maida komai a muhallinsa kamar ba'a taba komai din ba,saidai kuma ya gaza maida wannan dairy din cikin tarin tarkacen takardun. Tarin lifidi lifidin wasu documents dake dauke da sunan sultane muhammad hammud da kuma sa hannunsa,wasu a ciki kuma suna dauke da suna da signature na khadeeja muhammad hammud qarara a cikinsu,wanda tarin abubuwan da ya gani a rubuce cikin diary din mammina din ya janye hankalinsa daga duba ko zurfafa nazarinsa akam documents documents din. Yana tattaki ne da wani irin sassarfa daya sake bayyana tsaho fadi da cikar halittarsa ta GIANT MAN,daga bango zuwa bango na dakin. Ko sau daya ya gaza ajiye wayar hannunsa da yaketa maimaita kirawa bobbo muhamamd dawud,ko sau daya kuma ya gagara ajiye diary din mammina dake hannunsa yana sake bin shafi bayan shafi yana karantawa. Mamakin tarin qarfin halinta ke sake mamaye zuciyarsa da wani irin bacin rai masa misali. Har rashin imani rashin mutunci da zallar izgilancin dan adam yakai ya zauna ya rubuta tarin rashin imanin da ya aikata a rayuwarsa?. Har yakai ya zauna ya rubuta tarin alwashinsa akan rayayyu da matattu?. Iya littafin kawai yana jin ya isheshi hujja......ya isa dalilin da zai kama mammina a safiyar gobe cikin masarautar ya kuma bayyanawa duniya samun nasarar kama me laifin da suka kwshe shekaru masu yawa suna nema. Bama iya laifin da suke hasashe bane kawai........ta dauki rayukan wasu mutane daban da bincike ma bai taba biyowa ta kansu ba. Kawai don ta kashe bakin munanan ayyukanta,kawai don ta rayu yadda takeso,kawai don taci gaba da wanzar da umarni da kuma mulkar kowa cikin wani irin SHURU da ma'abota zurfafa tunani da bincike ne kawai zasu fahimci hakan. Iska ya kaiwa naushi a sanda kiran daya yiwa bobbo muhamamd dawud ya sake katsewa,wannan kiran shine kira na ashirin da takwas da yayi masa. Yanajin kamar zuciyarsa zata fashe ne,yana jin kamar ana jan jininsa ne,so yake kawai ya samu bobbo,so yake kawai yayi accepting ya bashi daman cafke mammina. Yanajin ma kamar safiya tayi masa nisa.......yana jin kamar yayi nisa ya jirayi safiya. Ta cutar da kowa.......ciki harda nanay dinsa. Ashe itace sila na barin nanay dinsa cikin wani irin yanayi......yanayin da a kullum ta tashi a cikinsa su kansu wunin ranar baya musu dadi. Ta kife sultane ta binneshi yadda ya kamata,bama sultane kawai ba......duk wani dake rayuwa cikin masarautar a binne yake,duk wanda yake rayuwa cikin masarautar yana qarqashin sarrafawarta ne,hakanan duk wanda yake rayuwa cikin masarautar rayuwarsa cikin barazana take. SHURU da masarautar take ciki da ake masa kallon aminci......ba aminci bane......HADARI NE......wannan shurun ba ZAMAN LAFIYA BANE annoba ce......wata kwantacciyar annoba da ba wanda ya farga da wanzuwarta. Cilli yayi da wayar yana cusa yatsunsa cikin gashin kansa,ya furzar da wata zazzafar iska daga bakinsa yana sauke idanunsa akan tarin document din da yayi snapping a wayarsa ya kuma dawo dakin ya fiddasu zuwa hardcopy ta wata mini printer ta masu aikin tsaro irin nasu. Kafin yayi kowanne tunani akai kira ya shigo wayar,taku uku yayi cikin zafin naman nan na ingarman namiji ya isa ga wayar,ya miqa hannu ya dauka yana danna gurin amsa kiran da gaggawa ganin bobbo ne. "Ina ka shiga bobbo?" Ya samu kansa da furtawa abu na farko. Mamaki kadan ya kama muhammad dawud,don ya sani,komai tsanani sallama itace abu na farko da haisam yake fara yi kafin komai bayan daga wayarshi. "Muhammad mun shiga masallaci ne nida sultane......sai yanzu muka fito" "Mission accomplished sir!" Ya furta da wani irin yaqini a muryarsa,zafin rai da kuma qwarin gwiwa dari bisa dari. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 64* "Alhamdulillah" Bobbo ya fadi,yana jin wani abu me sanyi yana ratsa zuciyarsa. Wannan wahalar......wannan aikin na shekara da shekaru yau an kawo qarshensa. "Izini kawai nake buqata daga gurinka obbo muyi arresting nata,zuwa safiyar gobe ko kuma daren yau". " Zakayi hakan Muhammad da hannunka,zaka huce wahalarka gaba daya......but,inason wani yanki kadan daga hujjojin da ka samu zan duba kafin na sake maka dama". "Done" Ya fadi yana katse kiran,sannan yayi snapping wasu daga cikin takardun ya tura masa. Tsaye yayi harde da hannunsa a qirji,ba abinda yake imagination irin yadda zai shaidawa nanay dinsa ya kama azzalumar data raba soyayya da qaunarsu da 'yan uwanta na jini......ba abinda a duniya a yanzun yake buri irin Allah ya ara masa numfashi na wadannan awannin da zai kama mammina ya kuma damqata a hannun hukumar tsaro na Ethiopia. Ko a iya haka idan ya tsaya ya tabbatar yaci ribar aiki da security service. Wani irin zugi zuciyarsa take masa idan ya tuna jerin lissafin mutanen data batar wanda ta zauna da kanta cikin alfahari ta rubuta da hannunta. Ashe qeqashewar zuciyar dan adam takai ya iya zama yana tsara zunubinsa da kansa?. Kiran bobbo ne ya katseshi ya maida dubansa kan wayar da hanzari yana daga kiran. "Kama matar nan bazai yuwu ba muhammad..... Kamata zai zama abu mafi girma cikin dagulewar case dinnan" Ya tsinci muryar muhammad dawud tana sanar masa da wani mafi munin saqo. Wani irin abu yaji da bazai tantance mene ba......sam kamar kwanyarsa ta daina fahimtar komai. "Bobbo......me kake fada ne?" "Bazaiyuwu ka kamata ba muhammad" Ya sake maimaitawa haisam da karyayyar muryarsa wadda ba irin ta dazu ba kafin suyi magana. Amsar da bobbo din ya bashi sai yaji kamar ya samu wuqa ya karta saman zuciyarsa ne "Me kake fada ne haka bobbo!......na samu dukkanin hujjoji fa!" Ya fadi da fada da zafin zuciya. "Muhammad,Tasgabbaa'i (calm down),akwai abubuwan daya kamata ka tattara hankalinka ka fahimcesu". "Hankalina a tattare yake guri daya bobbo.....na gama fahimtar komai,na kuma gama hada dukkan wata hujja a kanta,ba abinda ya ragemin banda na kamata!,ba abinda ya ragemin banda na kawo qarshen zaluncinta!,.......zan kamata bobbo kamar yadda doka ta tanada,zan kamata wannan ya zama dole!!!" Yayi maganar da zafin dashi kansa baisan a haka yakewa bobbo din magana ba yana me dukan table din dake gabansa,take ya amsa ya kuma tsage daga tsakiyar glass din,Allah ya taqaita bai fashe gaba daya ba da tabbas ba qaramin mummunan ciwo zaiji ba. Kiran kawai ya katse,don a yanzu baya buqatar duk wani abu da zai dakatar dashi daga kama mammina.......a zafafe ya soma hada connection dasu beeno,yanaso a daren kowa a cikinsu ya zama cikin shiri,da asubar yau din da awanni uku kadai suka rage tayi yakeso mammina ta zama a hannunsu,a gobe warhaka kuma ya tabbatar mammina din tana hannun hukumomi a Ethiopia. Qasar data shuka manya manya laifuka ta kuma binnesu a ciki,ta dawo wani sashe daban na duniya ta samarwa kanta amintacciyar mafaka. Hakan kuma bai mata ba ta sake fesarwa sa baza gubar dake qumshe a bakinta zuwa ga duk wanda rayuwa ta kawoshi kusa da ita. Da sauri da sauri yake qoqarin hada komai,saidai gefe kansa daya da yaji ya sara,ya sara ne tare da zabge kaso tamanin na karsashinsa gami da gilmawar sunan KHADEEJATU baro baro cikin idanunsa. Sunan daya gani rubuce a documents masu yawa dake gabansa yanzu haka. A hankali ya saki wayar ya koma gefan sofa bed ya zauna akai. Sai yakejin kamar akwai wani gibi.....kamar akwai wani abu daya kamata yayi baiyi ba,a jikinsa yakejin kamar akwai wani gurbin wani abu. *MUHAMMAD DAWUD* Wani irin shuru yayi yana rungume da wayar a qirjinsa. Wani irin tsoron haisam ne yake shigarsa a karon farko. Karo na farkon daya soma ganin tsananin fushi a tare dashi,irin wanda bai taba ganin makamancinsa ba. Akwai hadari me yawan gaske game da kama matar a yanzu. Idanunsa ya sauke a hankali akan sultane da yake amsa waya,amsa wayar da tayi tsaho,kuma yake ganin wani irin yanayi na tsoro da tashin hankali yana mamaye fuskarsa. A iya saninsa matarsa ce ta kirashi,a cikin matan nasa bai tantance ko wace ba......amma yanayinsa kawai yana gaya masa kiran yana dauke ne da wani saqo na mummunan tashin hankali. Ya sani koda.muhammad ya shiga fushi irin wannan bazai aiwatar da komai ba saida izini,ya samu wani irin horo na cikakkiyar tarbiyya da bin na gaba. Rank dinsa a gurin aikin,da kuma matsayinsa na PRINCE OF OROMO bai sanya ya zama me take dabi'un musulunci ba nafin na gaba. Saidai yana jin wata shakka a tare dashi,yanayin haisam din na yanzu bai taba ganin irinsa ba,kamar yadda wayar da sultane keyi a yanzu take gaya masa akwai wani mummunan abu daya faru a qasar. Shin har ya zartar da aikin kamata dinne?. Wannan tunanin ya zaburar dashi,ya soma rubutawa haisam din rubutaccen saqo na kai tsaye yana tura masa. Me yasa haisam ya kasa ganin abinda shi ya hango wannan karan?,baya ga wancan BAQIN QULLIN da ZARGE daya hango cikin daya daga cikin file din daya tura masa......MARTABAR sultane yanzu wani abune daya kamata a dubata. Kama iyalinsa kai tsaye irin haka a wulaqantaccen yanayin daya tabbatar zai zama wani labari dake trending a dukka kafofin watsa labarai na qasa dana duniya gaba daya......zasu bar masa wani tabo da zai iya shafar rayuwarsa ma gaba daya. Duk da cewa aikine zaibi ta kanta,amma zaiso haisam ya bashi aron wannan kamilar tasa nutsuwarsa da wannan zuzzurfan hankalin nasa ta yadda kama mammina din zai zama da tarin hikima. "Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagees.....aslih li sha'ani kullah.....fala takilni ila nafsee d'arfata ainin" Ya dinga maimaitawa a hankali idanuwansa a rufe. Gilmawar sunayen sultane kawai yake gani da na akhnan rubuce saman file din,zuciyarsa na nanata masa muhimmanci daukosu ya sake nazarin files din. Kuskure daya tak! Zakayi cikin aikinsu ya ruguza komai......ko ya bawa me laifi hujja ko damar kubuta. Saidai kuma bayaso ya kalli file din......bayaso ya duba yaga abinda ya zamo doka a aikinsu da zai tilasta masa dakatar da damqe me laifi. Wayarsa ce ke maimaita masa shigowar saqo me muhimmanci daga bobbo din,dole ya bude idanunsa da suka kada,ya miqa hannu ya dauki wayar yana duba saqon. "The power of documents abbreviation........" Iya abinda bobbo ya rubuta kenan kawai. Kamar an masa allura haka yaji,ya ajiye wayar yana miqewa da hanzari zuwa gurin daya ajiye dukkanin takardun,ya kuma zubosu qasa yana waresu daya bayan daya. Awa guda cur ya share yana nazari,awa gudan data zame masa ta tashin hankali......awa dayan data bashi tabbacin da gaske bobbo ya fishi gaskiya. Ta kowacce fuska babu hanyar kama mammina kai tsaye irin kamun da yake buqatar yayi mata. Tako ina ta qulla rayuwarta ta gaba da sunan akhnan,signature din akhnan duk da baisan ainihin signature dinta ba......da muma stamp din akhnan din dake dauke baro baro da sunanta da kuma title dinta AGADEZ PRINCESS. Ta qulla dukkan wani zare na rayuwar da tayi a baya da SULTANE......sultane din daya kasance aboki ga marigayi AJANI. Sa hannun sultane caba caba a tarin yarjejeniyar kashe ajani. Stamp dinsa mafi tsaro da girma daya tabbatar iya warwareshi kadai wani abu ne da zai dauki wasu shekaru ana magana a kanshi. "Hasbi rabbi!" Ya furta a bayyane da wani irin rudadden yanayi yana dukan table din a hankali. Ta kowacce fuska,ta kowanne yanayi ta qulla rayuwarta da mutum biyu,sultane da babbar diyarsa,tayi wani irin qulli da idan ta tashi faduwa ba ita kadai zata fadi ba.......idan ta tashi rugujewa ba zata zagwanye ita kadai ba. Faduwarta daidai yake da faduwar sultane,zubewar kima mutunci da martabarsa. Sa'annan kuma daidai yake da wulaqanta image na babbar d'iyarsa. Zata rasa tarin kima.....zata rasa girmamawa zata rasa dukkan wata martabarta. Duk wata dukiya da take mallakinta zata saraya daga hannunta,zata fuskanci mafi munin wulaqanci da tozartarwa. Document of abbreviation din da bobbo ya fara magana a kansa ya dauko ya bude yana masa filla filla. Wani sabon babban tashin hankalin ya soma gani......komai na mammina ya canza,ta tashi kacokam daga haifaffiyar Ethiopia ta koma haifaffiyar qasar NIGER. Komai ya canza.....komai ya tashi daga ainihin yadda yake. Girman abubuwan daya gani ya sanya yaji kansa gaba daya ya dauki wani irin dumi,saidai kuma bai hana bakinsa da zuciyarsa kiran sunan Allah ba. Abu guda daya yayi,ya fidda wayarsa ya turawa obbo saqo a taqaice,don yanaji a jikinsa cewa yana buqatar yayi quitting.....yanaso ya yanke kowa da komai na wani dan lokaci ko kwanyarsa zatayi kalar tunanin daya dace tayi. _"I found her crime....i lost her name,she's no longer Ethiopian under the law,touching her will would ignite a diplomatic fire"_ abinda ya turawa bobbo kenan ya kashe wayarsa. Wani sashe na zuciyarsa yana son gaya masa KAYI FAILING MUHAMAMAD?,wannan jarumar zuciyar tana qaryata hakan. A karan kansa yakejin BAI FADI BA.....bai kuma gaza ba.....a cikin kansa da zuciyarsa yakejin kawai wani strategy sabo yake buqata.....a gangar jikinsa yakejin akwai sabon GAME da zasu buga tsakanin K'ARYA da GASKIYA......wani sabon shimfidadden babi ZAI BUDE kansa da kansa yanxu. Bai gaza ba......bazai kuma gaza ba......bazai kuma tafi yabar agadez ba sai da NASARA....bazai matsa daga agadez ba sai ya cika wannan alwashin......wannan alqawarin......wannan BURIN. *_NATIONAL INTELLIGENCE SECURITY SERVICE TEAM (AGADEZ_* (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Dukkanin team din dake qarqashin jagorancin Senior Field Intelligence Officer sannan kuma Deep-Cover Operative me dauke da Code Name na Al-Sāmit (The Silent One) PRINCE MUHAMMAD HAISAM ABBA JIFAR. Cikin anihin kebantaccen gidannan nasa dake dake cike da jami'an tsaro daki daki ta kowacce fuska,ta cikin gidan,ta kusa da gidan,da kuma ta nesa da gidan. Amintattun jami'ai da dukka suka samu horo ta hannunsa,ko sau daya basa wani motsi da zaibar zargi a zuciyar wanda ke rayuwa ma kusa da gidan ballantana cikin unguwar. Parlor ne na alfarma dake zagaye da wasu irin lafiyayyun sofas dake nuna zallar izza da mulkin dake tattare da mamallakin gidan,saidai a yau a safiyar da ya wayi garinta a daren jiya ba tare da ya iya baccin komai ko kuma runtsa idanunsa ba......an canzawa parlor din fasali kadan ta hanyar rarraba kujerunsa,aka kuma ajiye qananun table gaban kowacce kujera. Tun daga kan omari har salawi,beeno,abeer dama dukkan wani ma'aikaci da shigowarsa agadez ta ta'allaqa ne da gabatar da wannan aikin,dama sauran jami'ansu da suka jima cikin qasar saboda fara gano muhimman gurare a qasar. Wani irin shuru ne ya ratsa dakin,banda qamshi da tururin coffee dake sake bayyanar da cewa lallai qabilar oromia ne wanze a gurin.....qamshin coffee din daya gauraya da qamshin sassanyan freshener din data kama parlor din,da kuma sirrintaccen turaren oga me gayya me aiki muhammad haisam. Duk qaunarsu da coffee din a yau kowa nashi yana aje ne a gabansa kawai,takardun hannuwansu kowanne yake juyawa cikin zurfin tunani,mutuwar jiki da daurewar kai,yayin da haisam din ke kai kawo a tsakaninsu. Sanye da wani lafiyayyen trouser da long sleeve shirt,shigar da ba kasafai ya fiya yinta ba a yau din yadda yakejin zuciyarsa fayau sai shigar ta sake masa wani irin kyau,ta fidda kyawunsa da quruciyarsa qarara,har abdii ma yaso tsokanarsa da farkon shigowarsu gurin,saidai yanayin daya gani tattare dashi na seriousness ya sanya ya kama bakinsa ya b'ame. Hannunsa daya yana soke a aljihun wandonsa,yayin da daya hannun yake riqe da qaramin cup yana sipping coffee dinsa a hankali,kamar yadda kowanne taku nasa yake cike da nutsuwa,har ya kawo gaban table din Omar ya zuqe sauran coffee din ya ajiye mug din akai sannan yaja baya kadan. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 65* Gyaran murya yayi wadda ta sanya kowa ya tattara hankalinsa a kanshi,fuskarsu cike da damuwar da yana iya ganinta qarara a bayyane. Cikin muryar nan da sautin nan nasa dake bayyana asalin abinda ake nufi da kamala da nutsuwa ya soma musu magana yana duban fuskokinsu daya bayan daya,da wani irin accent da yaren oromo ke dashi wanda yake kama da harshen fillanci a nigeria. "Waan hunda jijjiirte(she changed everything),Ta canza sunanta,shekarun haihuwa da komai da zai nuna ita din mallaki n qasar Ethiopia ce,tana da cikakken takardu da shaidar da zata bada tabbacin bata taba rayuwa a Ethiopia ba sam sam,dukkan takardunta kuma sun nuna ta halastacciyar hanya ta samesu. Ta samu sanya hannun manya dake da ruwa da tsaki akan kowacce takarda,tayi qoqarin samun shaida da lambar yabo iri daban daban na cewa ita din mutuniyar kirki ce,mutuniyar arziqi ce.....shaida da lambobi masu tulin yawa,ba a iya niger kawai ba,harda Nigeria dama maqwabtan qasashe dake kewaye da qasar.....ta shafe duk wani jini ko suna na Ethiopia daga gareta,ta yiwa kanta garkuwa da dokar da mukeso tahau kanta.....ta lullube kanta da tarin martaba da kariya ta gidan sarauta......da kariya da kowacce matar SULTANE take da ita. Tana cikin mata masu daraja da kamasu xai iya zama wani babban abun Allah wadai ga qasarmu,zai iya kuma canzawa aikinmu suna da ma'ana gaba daya,za'a kalli abun gaba daya a matsayin wulaqantarwa da tozarta da SARAUTA.....The law has already failed once. I must let truth speak instead.” ya qarasa fadi yana duban fuskokinsu muryarsa tanayin qasa sosai. Kallon nashi dai sukeyi daya bayan daya,kalamansa na qarshe suna sakasu cikin kokwanto. Dan murmushi kadan ya saki yana goye hannunsa a baya yana ci gaba da takawa a hankali,yana kuma ci gaba da dubansu. A nutse ya sake dora maganarsa cikin qarfafa gwiwa. "Kun gama aikinku kun cika wa'adinku,ina me sanar daku cewa,kowa a yanzun yana da 'yancin komawa qasarsa.....ni muhammad haisam zanci gaba da daukar nauyin aikin a wuyana da dukkan iyawata da qoqarina......dole wasan zai sauya salo,zai kuma zuwa wani YAQI na daban,bawai binciken me laifi ba.....zan sadaukar da numfashina ga qasata,zan bada rayuwata ga qasata......You're good to go You're free to leave All set! You all did an amazing job,perfect score!.i owe you one!.....well done!!!" Ya furta yana daga hannunsa alamun jinjina a garesu gaba daya,wani siririn murmushi na qarfafa gwiwa a garesu gaba daya yana fita daga saman fuskarsa. Kamar anyi ruwa an dauke haka kowa a cikinsu ya kasa magana,ya kuma kasa cewa komai,musamman omar da yakejin wani abu yana tsargawa ta cikin jininsa da zuciyarsa. Yana son ya gaya masa labarin sakin akhnan diya ga sultane wanda yayi waliccin aurenta,yana jin kamar nauyin zaiwa zuciyarsa yawa. Ya sani faduwa a wannan aikin wani abune da zai ma haisam din wahalan dauka,sai kuma gashi dukkanin alamu suna nunawa cewa BA'A BANZA AKA HAIFESHI A MATSAYIN YARIMA BA,BA'A BANZA YA FITA DAGA JINI ABBA JIFAR BA.......ba kuma a banza yake dauke da kalar wannan nauyin ba. Baya ya basu yana fuskantar widow.......bayason ya matsantawa kowa aiki dashi......bayaso suji nauyin idanunsa suyi masa kara,baya kuma so kuma ya shiga hurumin rayuwarsu na matsa musu ci gaba da rayuwa cikin agadez. Daren jiya duka baiyi bacci ba ko sau daya,baccin da har yanzu yakejinsa cikin idanunsa,amma sai yakejin bai samu lokaci da zai kwanta ba. Ya qarasa qarar da daren jiya ne wajen yin sallah da tarin addu'oin da suka bashi cikakkiyar nutsuwa a yau din. Ya tsaya gaban ubangijin kowa yana damqa amanar kansa da kansa a hannunsa da kuma neman jagoranci daga gareshi. Salon sirrintattun addu'oin daya saba yi a duk sanda wani abu ya cakude masa ko ya shige masa duhu,wanda kuma yake da cikakken alaqa me kyau da Allah,don ko sau daya ubangiji bai taba kunyatashi ba. Yanaji a ransa zaiyi komai da dukka numfashinsa......yana kuma jin zai fuskanci komai da sadaukarwa. Hannunsa yaji an riqo ta baya,tun kafin ya juyo kuma yasan omar ne,sai ya tsinci omar din yana fadin. "Ina tare dakai a dukkanin abinda ka shirya zakayi......a iya adadin kwanaki watanni ko shekarun da zaka kwashe a agadez.....har sai mun cimma nasara" Yayi maganar yana dora hannunsa saman na haisam. Kafin haisam din yace komai abdii ya matso ya aza hannunsa saman na omari dake kan na haisam din,ya kuma sake maimaita abinda omar ya fadi. Ya daga idanunsa da sauri zaiyi magana salawi ya biyo baya,basu barshi yace komai ba har sai da dukkanin wanda ke gurin ya dora hannunsa saman nasa yana masa mubaya'a da dukkan gaskiyarsa da zuciyarsa. Wani irin abu yaji yana ratsashi,bawai don yafi kowa ba amma Allah ya mallaka masa amincin wadannna mutane dukkaninsu lokaci guda?,sai ya rasa me zaice,ya wara hannuwansa iya yadda zai iya yana rungumesu,zuciyarsa tayi wani rauni,ya rasa da wacce kalma zai nuna girman karbar amincinsu da yayi. *BAYAN AWA DAYA* *SULTANE* Tun bayan kammala wayarsa da mammina yakejin wani irin shuru cikin kansa. Tun bayan da suka gama wayar data isar da saqon da takeson isarwa yakejin komai ya dauke masa wuta. Wani abune da bai taba tunanin zai faru ba,wani abune da iya hasashensa ko lissafin rayuwarsa bai taba qiyasta zai faru ga gudan jininsa ba. SAKI irin wannan wulaqantaccen saki?. Cikin kwanaki uku kacal da daurin auren?. Da wanne idanu zai kalli duniya?,da wanne idanu zai jama'arsa?. A yanzun da yake zaune gaban ka'aba bayan ya kammala dawafi na musamman da yayi saboda akhnan din.....ya gaza tantance laifin waye?. Laifinta ne bisa bijirewa dukkanin zabin da yayi mata wanda yake da tabbas a kansa?,laifinta ne na rashin daukan zabinsa da muhimmanci ta zabi fifita nata zabin akan nasa?. Ko Laifinsa ne?. Shin laifinsa ne daya barta da zabinta?,laifinsa ne daya kauda kai daga dukkan al'amuranta?,ya kauda kai daga zurfafa bincike akan mutumin data kawo tana so ta aura?. Idanunsa kan dakin Allah......yayin da zuciyarsa ta cika da wani irin yaqini da kyautatawa Allah zato. Sawun mutane masu yin dawafi ya ragu sosai daga cunkusonsa na al'ada,wannan ya bashi damar ganin ka'aba sosai daga inda yake zaunen. Idanunsa ya lumshe a hankali na tsahon wasu mintuna,yana son tuna me ya kamata yayi?,yanason tuna me ya kamata ya aiwatar. Kamar an rada masa sunan haisam ya fado a ransa,sai ya fara laluben wayarsa. Ya tabbatar shi kadai zaiyi magana dashi yaji dadi a ransa,yana kyautata zaton baiji maganar ba tunda bayajin dadi kwana biyun shi yasa bai kirashi ba. Yanajin dadin magana dashi,yana jin nutsuwar magana da haisam sosai,wani lokaci idan yana bayyana damuwarsa a gabansa ko a tare dashi,yakanji irin yanayin nan da d'a yakeji a sanda yake magana da mahaifiyarsa. *HAISAM* Idanun omar a kansa sanda yake takowa inda yake zaunen. Cikin wata qaramar rumfa dake ta bayan gidan daura da wani garden dake dauke da wasu nau'ikan shuke shuke dake bada iska me kyau daya banbamta da iskar da gidan yake kadawa. Yayi relax cikin rocking chair yana lilawa a hankali,idanunsa a lumshe suke abinda yake alamtawa omar cewa ya lula ne duniyar tunani. Motsin da yaji ya sanyashi bude idanunsa kadan,ganin omar din kuma ya sanyashi bude idanun nasa gaba daya ya tashi ya zauna sosai cikin kujerar. "Ina maleek ya shiga ne?". Kafada omar ya daga yana neman wajen zama. " Tun sanda yaga zamu zauna meeting ya fita,kuma har yanzu bai dawo ba......hussam ne yaketa kirana yanaso na hadaka dashi........issue ne na company,order din daya saka daga India ta iso........sannan yace watanni uku suka rage a fidda sabon scents,suna buqatar hankalinka a wajen" Qaramin tsaki haisam din yaja yana shirin komawa cikin kujerar. "Ka fada masa idan bazai iya handling komai ba ya zauna ya zubawa company din ido" Yana qarasa fada ya maida idanunsa ya lumshe. Murmushi omar ya saki......haisam yana wasa da kasuwancin da Allah yayi.masa wata irin daukaka dashi kansa baiyi zato ba. Yana mamakin yadda yake fifita aikin security services akan kasuwancin da kowacce rana wasu irin mahaukatan kudi suke saukewa a account dinsa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Kaf kamfanin turaruka dake duniya a yanzu ba wanda yake daukakar nasa da karbuwarsa,amma ya tattara komai ya aza akan hussam. "Man.....yaron nan fa yana qoqari". " Kada ma yayi.....namiji ne ai,dama kuma shi namiji ai ba'a sanshi da hutu ba....banda ragonci me ya sani?,company uku kawai amma ya kasa riqesu gaba daya sai qwaya daya?,dayanma komai sai anyi guiding nasa?" Ya fadi yana bude manyan idanunsa da suka rusuna a yau din kan fuskar omar. Wannan kwarjinin nasu ne ya motsa,ya kuma daki omar din,sai kawai ya kauda idanunsa daga kan haisam din yana lalubar wayarsa don bawa hussam mafita. Shi kansa yasan a yanzu haisam din bazai saurareshi ba. "Fata dai kawai idan ka kammala branch dinka dake dubai ka nemi wani ka bawa....kada ka hada masa zafi" Yayi maganan yana danna kiran hussam,daidai sanda kiran suitane ke shigowa wayar hasaim,abinda ya sanya omari tashi yana waya da hussam din ya barwa haisam gurin. "Assalamu alaikum warahmatullah" Muryar sultane ta bayyana cikin wayar,muryar dake cike da wani irin dattako da kawaici,muryar data saukar da wani irin tausayin sultane din me nauyin gaske a zuciyar haisam. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 66* "Wa'alaikumussalam warahmatullah,barka da warhaka" Haisam ya amsa masa cikin matuqar girmamawa,girmamawar data daukar da murmushi duk da tarin zafin dake ratsa zuciyar sultane din. "Barka kade haisam,ina fatan ban shiga huruminka ba kirana kuma bai takuraka ba" Maganan saita masa nauyi,don da gaske zuwa yanzu yana yiwa sultane wani kallo na tausayi,kallo kuma na girmamawa. "Ina fata yarona yana lafiya". " Alhamdulillah,ina fatana kana cikin aminci da nutsuwa" Haisam din ya maida masa. Idanunsa ya lumshe,yaja wani numfashi can qasa,tambayar nutsuwarsa da haisam din yayi sai yakejin kamar ya fama masa wani tabo ne dake danqare qasan zuciyarsa. "Ina cikin aminci,amma nutsuwa tayi nesa da zuciyata haisam". Magana sai ta yiwa haisam wani iri,fargaba kadan taso kama zuciyarsa amma ya daidaita yanayinsa. "Ina fata kana cikin agadez?" Kai haisam ya jinjina masa kamar yana a gabansa. "Ina nan ranka ya dade.....ina riqe da amanar al'ummarka" "Ma sha Allah.....naji dadin hakan" Sultane ya furta a nutse,saidai qasan ransa yana jin nauyin furta maganar da alamu ke sake gaya masa haisam baisan da ita ba. Yanayin shurun sultane bai masa kama da amintaccen shuru ga wanda ya gama magana ba,wannan ya sake sanyashi tattara hankalinsa a kansa. "Labari ya riskeni a daren nan haisam.....auren akhnan ya qare....mijin data aura kwanaki uku baya ya saketa". Da sauri ya runtse idanunsa yana jin zuciyarsa tana wani irin harbawa. Maganar ta shammaceshi ta kuma zo masa a bazata sosai. Harshensa da zuciyarsa yaji sunyi nauyi,mamaki yana sake cika kwanyarsa. Wanne irin baqon al'amari ne wannan?,ya akayi baisan da lamarin ba a matsayinsa na waliyyinta?,shi ya kamata sultane yaji daga bakinsa bawai shi yaji daga bakin sultane ba. Wani irin nauyin sultane yaji ya saukar masa,sai yaji gaba daya kaman laifi yana laftuwa a kansa,sai yaji kamar shurun da sultane yayi yana bashi qofa ko dama na kare kansa,sai yaji kaman ya gaza da riqe wannan amanar ta wannan bangaren,sai yaji kamar ya gaza a aikin da sultane ya bashi. Ta wani fannin kuma haka kawai yaji wani nauyi yana sauka daga qirjinsa......a hankali yakejin wani abu daya tsaya masa a wuya kamar yana narkewa yana wucewa. Alhamdulillah,ya furta qasa qasa,yanajin kamar wata rahama akayi masa bushara da ita,ta wannan bangaren yanajin ya kubuta daga fadawa TARKON mammina data d'ana,ta kuma shirya akan fadawar kowanne mutum daya rabi plan dinta. "Subhanallah......" Ya furta a fili a hankali,yana saukewa muryar sultane cike da raunin da ba kasafai zaka ji sarakai da irinsa ba. Ina tsaye daura da dakin Allah haisam.....labarin sai yayimin nauyi da yawa" Kansa ya gyada a hankali,ya sani ko waye mutum dole ya fuskanci irin wannan yanayin,sakin aure ga diyar da yafi so da qauna fiye da komai ba qaramin lamari zai zame masa ba. "Haka ne.....amma sau da dama wani lokaci gaskiya takan zabi bayyana a muhallin da taga dama" "Gaskiya ne.....inajin kamar na gaza ne haisam,inaji kamar na kasa,ina jina kamar wani gajiyayyen shugaba......sau da dama shugaba yakanyi tunanin shuru hikima ce......har sai lokaci da wanna shurun ya zama KUSKURE". Yakai qarshen maganan yana tuna adadin lokutan da morsa safiyya ta kwashe tana kwabarsa akan duk wani motsi na akhnan din. Bai taba kallon hakan a matsayin tsana ga akhnan ba,saidai ya sake mata wasu abubuwa ne saboda soyayya,ya sake mata wasu abubuwa ne saboda yana gani da tunanin TSANANI baya tarbiyya. Tsam haisam ya miqe yana takawa a hankali,yana tsinkayi ma'anoni masu yawa cikin maganganun sultane din,ma'anonin da yake sanya ran su juye watan watarana zuwa fahimtar birnannun abubuwa dake lungu da saqo na masarautarsa. "Baka gaza ba ranka ya dade.....baka zama gajiyayye ba,shurunka kuma bai zama kuskure ba,kayi dukka iya qoqarinka na kula da komai,na ajiye komai a muhallinsa.....wani lokaci koda ginannen bango dake a tsaye yana iyayin rauni,akwai alaqa qarfafar gini da samun gini me kyau da inganci idan har masu jingina a jikinsa sunyi goyi bayan hakan yaci gaba da tabbatuwa" Maganan ya ajewa sultane wani tunani a ransa,abinda ya sanyashi gyara zamansa sosai,daga inda yake yana sake ganin ka'aba sosai. "Ka fadamin haisam.....a lokacin da barna ta faru a cikin iyali......wanene?.....sannan kuma ta yaya za'a iya dauko gyaranta tun daga tushe ba tare da gida duka ya samu matsala ba?". Shuru haisam yayi,yana son gane abinda sultane yake fadi. A zahiri ya fahimta,amma ainihin asalin dalilin tambayar ya shige masa duhu,amma dai koma meye,yana jin zai bashi amsar tambayar daidai da amsartata "Wani bazai hari tushe da farko ba kai tsaye.....wani zai fara da ganye ne,sanda ganye zai saitu ya gyaru,ko ya kauce daga dogara da ainihin jikin bishiya,dole tushiya ta fidda kanta da kanta". Kai kawai sultane yake jinjinawa,yana jin wata irin gamsuwa a amsar haisam din. Indai haka ne tunanin da yakeyi bai saba ba,indai haka ne mafarkan da yakeyi a kwanakin da bacci ke daukansa a masallacin manzan Allah ya kamata a tabbatar dasu......akwai wani abu a boye.....akwai wani abu a binne da Allah yakeson gwada masa. Yasha zuwa gurin ba sau daya ba basau biyu ba,amma bai taba kalar mafarkan da yakeyi cikin masallacin ba,kuma duka duka akan mutum biyu kawai,dole a gobe ko jibi ya koma madeena ya samu muhammad dawud. "Naji dadi da kiran dana maka a yau haisam" "Nima haka....ina maka fatan sauqaqar al'amuranka,tare da daidaituwar iyalinka". "Ina maka fatan alkhairi haisam,tare da addu'ar ubangiji ya shiga dukkanin lamuranka baki daya,amincin Allah ya tabbata a gareka" "Amincin Allah kaima ya tabbata a gareka" Ya amsa yana katse kiran daidai sanda idanunsa ya gane masa omar dake tsaye a gefansa,da alama bai jima da fara wayar ba ya shigo. "Me yasa ba wanda ya gayamin?" Yayi tambayar kai tsaye ba tare da ya kalli omar na,yana qoqarin cire wayarsa ne kawai daga silent. "Me yasa sai an gaya maka?" Omar ya maida masa martanin tambayar. A nutse haisam ya daga kansa yana sanya wayarsa da hannunsa duka cikin aljihun trouser dinsa. Dan kafe omar yayi da kallo,yana son gane me yasa omar yace haka?,saidai omar din yaqi bashi dama,yama kauda kanshi ne kawai daga barin kallon idanun haisam,don ya tabbatar ya qyaleshi zai karanta tunaninsa ne fes. "Saboda nike riqe da al'amuran gidan a halin yanzu......saboda nine waliyyinta" Ya fada da wani irin coolness. Murmushi omar ya saki shima,yana ajiye wayarsa gefe guda. "Akwai wani al'amari daban dake tattare da wannan maganar.......amma har yanzu ina ganin baka cancanci sani ba...." "Omar mana" Ya fada yana tsuke girarsa sosai idanunsa still a kansa. Dukka girarsa biyu omar ya daga,alamun tambayar me kuma nayi?. Numfashi yaja sosai yana harde hannuwansa a qirji "Alhamdulillah" Ya sake maimaitawa har sau uku,abinda ya sanya omar daga kansa ya kalleshi. Yayi addu'a sosai gaban Allah,ya yiwa Allah magiya akan ya kawo warwarewar komai,kada Allah ya sanya ya zama silar cutuwar kowanne bawa,gashi tun ba'a je ko ina ba.....wayewar garin yau kawai ya fara ganin warwarewar daya daga cikin abubuwan da bai gamsu kwata kwata da wanzuwarsa a muhallinsa ba. "Me kakewa hamdala a ciki?" "Kasan darare nawa na kasa bacci saboda tunanin qulla auren da ban da tabbacin sahihancinsa?....kasan sau nawa na zargi kaina akan bayar da aurenta ga mutumin da bai cancanta ba?". "Saboda me zaka zargi kanka ne?,bayan baka san wayeshi ba sai daga baya?". "Amma musulunci ya shardanta yin bincike,me yasa banyi ba?" "Me yasa mahaifinta baiyi ba shi da yafi ca cancanta yayi hakan?,yayi accepting kawai hankali kwance?" (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Amma omar......." "Haisam......stop blaming your self......ita ta kawoshi tun farko bakai ka kawo mata shi ba.....kayi gyara kawai ta fannin daya ca canta,ka bawa kwanyarka da zuciyarka dama ta fadi maka ra'ayinta.....abinda ya faru ya riga ya faru,gaba ake gyarawa ba baya ba.......Allah ma dai ya sanya bai samu ya shiga gona ba shi angon" Omar yayi maganan yana tsuke girarsa. Baisan ya zuqi sassanyar iska ba sai da yaji yana fitar da ita a hankali,amma cikin salon miskilancin nan nasa sai kawai ya janye idanunsa daga kan Omar ya juya a hankali yana takawa majestically yana barin gurin... Da kallo Omar ya bishi,qaramin murmushi yana subuce masa. Yana sane yayi maganan qarshen,yanaso ya tabawa haisam din wani turning point dashi ya gaza tabawa kansa.......yanason bude wani abu da haisam din qarfi da yaji yasa qaton kwado ya datseshi......amma miskilancinsa ya sanya ya hanashi kara ta ko fahimtar komai,saidai duk da haka yadda yabar gurin salin alin ya bawa Omar wani dan qanqanin hope a ranshi. A ranshi ya yanke ya kamata ya koma cikin gidan,ya kamata ya zamana kusa da komai,don haka kai tsaye ya bawa abdii umarnin shirya komai. Saidai baiko jima ba maher ya qaraso gidan da saqo. Rubutacciyar wasiqa ce da iya envelope din da wasiqar take ciki kadai zai gaya mata tarin izza sarauta da girmamawar da aka gwadawa shi da aka turawa saqon. "Abdii.....karbi ka karanta" Yayi maganan sanda yake qoqarin cire agogon hannunsa. Kwanciya yakeso yayi kafin yammacin da zasu koma can gidan. Yanaso yayi wani tunani,yanaso ya fadada nazarinsa.......yanason ta kowacce fuska ya tsara yadda zaiyi wasa da tunanin mammina......yanaso ya sanya mammina ta BAYYANA masha'ar data aikata......ta kuma tone dukkan wani abu mugun aikinka da kanta.....da hannunta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 67* A nutse yake sauraron saqon,saqo ne daga morsa safiyya na neman ganawa dashi a yau. Saqo ne da aka rubutashi cikin girmamawa da nuna muhimmancin dan adam. Zuciyarsa yaji tana motsawa,yanayin kalaman matar da yadda take magana kadai yana sake tabbatar masa cewa UWA take a gurinsa. Yanayin maganganunta sak na nanay dinsa,sai ya miqawa abdii hannu,abinda ya alamtawa abdii cewa yanason ya bashi takardar ne,sai ya dora masa takardar yana cewa dasu. "Ka gaya mata zanzo in sha Allah,kuna iya tafiya,bayan sallar la'asar zamu tafi.....ka fadiwa omar kowa ya duba e-mail dinsa". "An gama obbo" Abdii ya furta da girmamawa da kuma qauna da yakewa haisam din. A hankali ya zube idanunsa saman wasiqar. Duk da cewa ta rubutata da yaren hausa ne,amma yanayin zubin rubutun sak na nanay dinsa. Ba qaramin martabawa da girmamawa bace basarake ya zauna ya rubuta maka wasiqa da hannunsa,duk da cewa suna da tarin masu zama su rubuta musu saqon duk da sukeso. Ya sauke idanunsa can qasa gurin sunansa,yanayin data rubuta sunan sak rubutun yaren oromo. Hannu yakai ya shafa kan sunan yana sake zubawa signature dinta idanu,wata irin signature da bayan ya matsanta zurfafa bincike akan ma'anarta sai ya fahimci sunanta ne da sunan nanay dinsa dana safeena cakude guri daya. Murmushi ya qwace masa saman kyakkyawar fuskar nan ma'abociyar nutsuwa da hasken addini. Ya tuna da nanay dinsa.....wato komai nasu iri daya ne?,daidai da signature dinsu kowacce ta zabi ta tabbatar da sunan junansu akan kowacce alama ta rayuwarta?,duk da an nesantasu da juna?. Bayajin koda tona asirin mammina shine aikin da zai zame masa na qarshe a rayuwa zai dakata a kansa. A baya ya kwashi watanni uku,cike da matsuwa nason yayi aikinsa ya kammala,amma a yanzu yana jin koda shekara dubu zai wanzu a agadez,koda shekara dubu zaiyi yana jira zai jira din. Bazai gaji ba bazai sare ba,sai ya tabbatar da adalci akan kowa.....saiya shimfida murmushi akan fuskar kowa. *_INTERMISSION_* 😄😄😄😄 *_Me karatu?......wanne kira kake zaton morsa safiyya ta yiwa haisam?_* *_Tunaninsu yazo daya tsakanin mammina da morsa safiyya.....saidai manufa ta banbamta_* *_meye a zuciyar sultane ne?_* *_MUHAMMAD HAISAM ABBA JIFAR (THE SILENT ONE)ya dauki wani alwashi......Ta yaya zaiyi WASA da hankalin wannan BAQAR QADDARAR?_* "_YANZU SABON SALON WASA ZAI DAUKO......SABON SALON ZUBI......magana ake ta INTELLIGENCE ga kuma EVIL a gefe......MASOYA HUGUMAWA KUZO MUJE ZUWA_💃🏼💃🏼 *MAMMINA* Haka kawai ta zabi yin shawagi a yau cikin masarautar kamar yadda ta saba a lokuta masu yawa. Irin hakan yana zama wani salo ne a gareta na fahimtar kowa da komai ba tare da yanayinta ya nuna ba. Takanyi noticing yawan adadin baqin dake masarautar ba tare da tayi magana da kowa ba,saidai a yanzun ta sani ba wata baquwar fuska cikin masarautar,don wancan malamin yayi limiting na komai. Tafisu na biye da ita a hankali sunayin nazarinsu a tare ba tare da wata hira a tsakaninsu. Wannan yanayinne ya sanya kowa ke zaton ba shaquwa ba kuma kyakkyawar mu'amala tsakaninta da tafisu din. "Ina yaiwata mafarkin Ethiopia......ina yawan afkawa cikin tunaninta koda banso hakan ba,bana jin akwai sauran aminci a nan gurin tafisu,haka zuciyata da jikina suke bani" Murmushi kadan tafisu ta saki tana girgiza kai. "Nafi zaton kwadayin cikar burinki ne yake sakaki a irin wannan yanayin. A nan din uwargijiyata......babu wani abu daya isa ya karya amincin da kike dashi,ba wanda ya isa ya tsallake iyakokin da kika shata......ba wani abu komai girmansa da ya isa ya girgizaki ko ya girgiza darajarki da martabarki. Anya kina da masaniyar irin girma kima da amincin da kike dashi kuwa a zukatan talakawa?". Maganganun tafisu sun shigeta sosai. "Kin manta cewa ke a yanzun ba halak malak din qasar Ethiopia bace ke?,ke din ba'abzina ce haifaffiya uwa uba da dangi gaba daya?,kin samu wannan shaidar ta hannun mutum mafi girma daraja da kuma aminci irin sultane,kin manta ne?" Tafisu ta sake tuna mata da wani abu daya sake bata relief. "Kamar isowar tamim nake gani" Tafisu ta furta qasa qasa tana duban gabansu. "Shine.....gwara daya iso,dama yau ne rana ta qarshe cikin yarjejeniyarmu......mu qarasa can" Mammina ta fadi yana sauya akalarta zuwa wani amintaccen gurin zama daya zama kebantacce garesu kadai da kuma sultane. Idanunta akan tamim sanda yake takowa da wannan qaqqarfan jikin nasa,tana karantar wani yanayi a tattare dashi da bata saba gani ba. Cikin girmamawa ya qaraso,ya kuma zube a gabanta kamar yadda ya saba din da tarin girmamawa. "Bani labarin dukkanin abinda yake tafe dakai.....ba saura jira ko doguwar shimfida" Ta buqata cikin zaquwa da ganin yanayinsa. Qasa yayi da kansa,yana jin wata fargaba tsakiyar qirjinsa da baisan dalilinta ba. "Akwai alamun kwancewar wani noti guda daya cikin notikan da muka daure" Kai tsaye ta fahimci inda maganan ta dosa,wani irin abu taji yayi yarrrrr cikin jikinta,tsigar jikinta tayi wani irin zubawa,ta ritsashi da ido sosai. "Bani bayanin a bude". Zama yayi sosai a qasa yana sake yin qasa da kansa. "Akwai mutum daya da gilmawarsa ta qaranta cikin hukumar......akwai mutumin da aka dauki wasu satittika da kwanaki ba'a ganshi ba......bacewar motsin daya daga cikin ma'aikata kuwa a wajen yana alamta tafiyarsu izuwa wani muhimmin aiki,bacewar kowa a cikinsu bazai iya zama barazana ba.......amma BACEWARSA shi din babban barazana ne da zai iya tarwatsa KOWA!......An tabbatar min indai shidinne.....to ba shakka SHI KADAI GAYYA NE!!!" "Dakata!!!!" Mammina ta fada cikin tsawa. "Daina kurantamin kowanne mutum a gabana,ka manta a gaban wa kake?". Qasa yayi da kansa,haka kawai yana jin wani rashin nutsuwa yana shigarsa. " A bani tabbacin gurbin da ake tunanin ba kowa da gaske ba kowa din?.....muddin ya sanya qafarsa cikin agadez ne.....muddin ya sanya qafarsa cikin masarautata ne.......saina sanyashi yayi nadamar binciko laifin daya daga cikin mutanena ma ballantana ni da kaina......tabbaci nake buqatar samu da farko tukunna!!.....ka riqe wannan da kyau.....sati daya tak na baku,duk kuwa wahalar da aikin ke dashi,bazan iya jira sama da kwanaki bakwai ba". "An gama" Tamim ya furta yana miqewa da cikakken karsashin nan nasa yana barin gurin. Kasa motsawa tayi kwata kwata daga gurin,saita dinga jin wani abu yana shigarta gaba daya me kama da fargaba da razani. "Bai kamata kiji komai ba,bai kamata ki dinga mantawa da cewa ke ba jinin Ethiopia bace.....bai kamata ki dinga mantawa da al'adar agadez ba game da gwiwar sarki,ke din kina cikin kariyar sultane da alfarmar masarauta HAR ABADA!" . Wadannan kalaman na tafisu su suka suka shiga jikinta da kyau,wadannan kalaman su suka binne tsoron da yaso yayi tasiri a zuciyarta. *MORSA SAFIYYA* A nutse take gyara lullubin lafayar dake saman kanta,tana kuma sake duban fuskarta a madubi. Fuskar da wasu lokuta suke tuna mata mutum biyu da har yanzu bata maye gurbinsu ba a rayuwarta duk da tsahon shekarun. SAFEENA DA KHADEEJA. Motsa qofar da akayi shi ya sanyata waiwayawa. Armelle ce cikin kamalar nan tata. "Allah ya baki yawan rai,an kammala shirya komai,kuma sunce sheikh yana hanya,amma kuna falaak da hairaan suna buqatar ganinki". "Ki fadi musu su shigo" Kai armelle ta jinjina ta koma da baya. A nutse ta koma saman ottoman ta zauna tana fuskantar qofa. Daidai sanda hairaan ke shigowa a gaba falaak na biye da ita a baya,hairaan din riqe da hannun falaak. Cikin kwanaki qananu falaak din tayi wani fayau da ita,daga jiki har fuska sun nuna ramarta. Sau daya tak momma ta qara ganinta tun wancan ranar,duk da zuciyarta cike take da tausayin autar tata amma ta danne,saboda bata son komai da zai kawo mata cikas a tsarinta da qudurinta har sai ta cimmasa. Ta shirya fuskantar kowa......ta shirya qalubalantar kowa,koda kuwa sultane ne,shi yasa koda nanny batayi maganan komai ba,duk da awannin da suka shafe ita da nanny din suna tattaunawa game da sakin. "Ina fata ba zuwa kukayi ku batamin lokaci ba" Morsa ta fada tana wani hade rai. Murmurshi kawa hairaan ta saki. "Inamu ina batawa morsa kuma momma guda rai?....neman afuwa da yafiya kawai mukazo yi" Hairaan ta fadi tana sakin falaak,wadda bata zame ko ina ba sai gaban morsa safiyya. Sulalewa tayi ta zauna a gabanta tamkar me zaman sallah,muryarta can qasa da wani irin rauni ta soma magana kanta a qasa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Momma ki yafemin.....kiyi haquri momma,na gaza ganowa da fahimtar nufinki,duk da cewa nice na miki alqawarin tallafa miki da bada gudunmawata wajen gyara rayuwar yaa biftu,kiyi haquri bisa musun da nayi miki,kiyi haquri kan bata miki ran da nayi.....gaskiya ne da kikace yaa biftu ta fini buqatat sheikh haisam.....da gaske ne momma na yarda da hakan,ni ina iya ganinki,ina iya rabarki naji duminki.....ita kuwa ta rasa hakan,ni ban rasa gatan wanda zai dorani akan hanyar da rayuwata zata inganta ba ta kuma kubuta,amma ita ta rasa wannan.....na SADAUKARWA da yaa biftu sheikh da dukka soyayyar da nake masa,na sadaukar mata momma.....zan kuma goya miki baya ganin komai ya daidaita" Wasu hawaye ne suka taru sosai a idanun morsa safiyya,duk kuma yadda takai ga taresu amma sai hakan ya gagara,don haka ta barsu suka zubo da duminsu gaba daya,suka kuma sauka kan hannuwan falaak dake saman cinyarta,abinda ya sanya falaak din kama hannun morsa din ta saka cikin nata ta runtseshi sosai. Hannunta ta aza kan falaak a hankali tana dauke hawayen da gefan lafayar jikinta. "Ba abinda kikayimin falaak,Allah yayi miki albarka.....Allah yayi miki albarka....Allah yayi miki albarka,tabbas ina me yaqini da tabbacin ba zaki tozarta ba,ba shakka Allah sai ya maida miki madadin sheikh haisam,ina miki fatan ya zama a kurkusa ta yadda zuciyarki ba zata cika da kadaici ba,ba kuma zata tagayyara ba,soyayyar da baki hasashen samunta gurin sheik ba alfarmar manzan Allah S A W zaki sameta gurin makwafinsa har sai kinji kamar tayi miki yawa ma,Allah ya cireshi daga zuciyarki kaman yadda yake fidda gashi daga nono,ya mantar dake soyayyarsa ya cikata da qaunar Allah da manzansa dama dukkan wanda zai zama madadinsa" . Qanqame morsa safiyya tayi da kyau,tun daga nan tasan cewa addu'ar UWA ba wasa bace,wani sanyi taji yana ratsa zuciyarta,wata nutsuwa ce taji tana saukar mata,sabanin kwanakin data dauka cikin qunci da jin cewa ba zata iya barwa kowa haisam din ba. Sai hairaan ta matso itama tana cuso kanta a tsakaninsu hawaye fal nata idanun. Morsa safiyya tasan me take nufi,qarin sanya albarka itama take nema,don haka ta saki murmurshi tana shafa kanta itama gami da kwararo mata addu'a. Koda ta kammala bataji ta nutsu ba,hannuwanta ta daga tana yiwa akhnan tata daban,duk da batasan me akeyi bama,amma bata taba daga qafa ba akan mata addu'a,ko ta yiwa yaranta ko batayi musu ba. (Duk runtsi duk wuya a nemi addu'a da albarkar iyaye,karku yadda kuyi wasa da ita,wata dama ce da idan ta wuce bata dawowa kowa,idan sun rasu ka kyautatawa 'yan uwansu da qawaye da abokansu,hakan zai zama tamkar su ka kyautatawa,haka addini ya koya mana,haka yake a addininance,Wanda suka rasa nasu Allah ya jiqansu da rahama,wadanda kuma suke raye ubangiji ya qara musu lafiya da nisan kwana me amfani). *HAISAM* zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 68* *HAISAM* Qasan ransa yakejin dadi da sassauci na yadda ya samu gidan komai yana tafiya daidai da umarnin da yake bayarwa daga can ainihin gidansa. Wannan girman.....wannan martabar da kowa ke bashi ba abinda ya sauya sai sake qaruwa ma da yayi. Cikin girmamawa da martaba dan adam daya gada daga ainihin jinin OROMIA na asali yake amsa kowa gami da duba matsayar kowa a aiki da yadda kowa ke tsaye akan aikinsa. Baiyi hanzarin wucewa kai tsaye zuwa sassansa ba,sai ya zabi ya qarasa mintunan da suka rage wajen duban tsaron gidan da sauransu. Akwai kusan mintuna talatin zuwa arba'in da suka rage kafin cikar lokacin ganawarsa da morsa safiyya din. Yana ankare da lokacin,yana qiyasce yana kuma lissafe. Yana jin wani girmamawa daga qasan zuciyarsa dangane da ita,yana jin bazai qara mata koda minti daya ba cikin mintunan da ya kamata ace sun hadun. Wani girma nata yake ji,yana jinta a matsayin nanay kamar yadda musulunci ya shimfida cewa qanwar uwa itama uwa ce. Qanwar uwar ma irin morsa safiyya din,daya tabbatar rayuwarta na zagaye da wasu tarin qalubale,bai sani ba itama ta sani?,ko bata sani ba?,ta fahimta ko nata fahimta ba. Maleek yana daga gefansa yake ci gaba da duba gidan,ya maida idanunsa kan maleek a hankali. "Kowanne gidan sarauta ya banbamta da waninsa,saidai akwai gidan sarautar dake binne da tarin sirrika masu nauyin gaske dake dilmiyar dashi sannu a hankali har zuwa wani mataki" Kai maleek ya jinjin a hankali,duk da hankalinsa ma yayi nisa gurin tunani da fatan inama ace zai samu ganin falaak koda daga nesa ne. Basu kai ga cewa komai ba muryar ta soma tashi,cikin daga murya da rikici yake fadin. "Ya tsinke haadi....daya daga cikin dawakan ne......bansan me ya sameshi haka ba.....na kasa sarrafashi" Akayi maganar da yanayin daya ja hankalin haisam. A nutse ya dubi sashen da maganar ke fitowa,bargar dawakai ce dake wani kebantaccen guri a gidan. Yasan da ita,amma baisan mallakar waye ba,bai kuma taba shiga gurin ba duk da yadda yake mararin hawan doki,musamman dadewar da yayi bai hau ba a yanzu. A jininsa yake,yana jin wani iri idan yaga dawakai ko raquma,wani lokacin har cikin kansa saboda tsananin sabo da rayuwa a cikinsu,suna tuna masa da nasa dawakan daya tabbatar zuwa yanzu sosai sunyi kewarsa suma. Maleek ya waiwaya a hankali shima yana maida hankalinsa sashen da maganan ke fitowa,sannan a nutse ya dubi haisam. "Kamar fa akwai matsala.....inajin kamar akwai dokin da ya balle.....ina kyautata zaton loosing control ñasa sukayi". A nutse haisam din ya dubi maleek,sai kuma ya zare dubansa daga kansa yana maidawa qofar shigar bargar,ya fara takawa a hankali yana nufar gurin,abinda ya alamtawa maleek shiga zaiyi,miskilancinnan nasu na cikin jini ne kawai bazai barshi ya furta da baki ba. *AKHNAN* Zuwa yanzu idan tace ba komai cikin 'ya'yan hanjinta ta tabbatar batayi qarya ba. Ta manta a daidai wanne lokaci......ta kuma manta wanne abinci ne na qarshe daya shiga cikinta cikin salama. A wannan yammacinne kawai data gama tabbatarwa gami da amannar ba zata rayu ba tare da abinci ba ta amince ta karbi zazzafan ruwan tea din da birra keta mata nacin ta karba tasha din. Sanye yake da wata cotton gown ta wani irin tattausan material fari qal wanda aka yiwa adon gold d'aid'aiku a jiki. Hade yake da hularsa da kuma yalwataccen cotton din mayafin da tunda birra ta ware mata kayan batabi ta kansa ba. A yau ko hula bata sanyawa sassalkan gashin kanta ba,ta sakeshi ne kawai yana kwance a bayanta wanda tsahonsa yayi kusa da mazaunanta. Abune me wahalan gaske ka samu gashinta a cukurkude ko a yamutse,ko a yanzun ma da take cikin wani irin mode da batasan sunan da zata bashi ba,gashin a kwance yake a gadon bayanta da wani irin glowing da darkness dake nuna kulawar da yake samu,saidai daga gaban kanta yadan tashi kadan,tashin da bai hana kwantacciyar sumar data kwanta daga goshinta har gefunan kunnuwanta bayyana ba. Fuskarta tayi wani irin haske,tayi fresh sosai,blue eyes dinta haskensa ya sake fitowa qwarai. Kana iya ganin yadda labbanta suka sake sirancewa,labban da basa rabo da kyakkyawan lip gloss ko lip balm. Wani irin zurfi tayi a tunani,har yanzu tana jin emptiness dinnan a zuciyarta dama rayuwarta gaba daya,har yanzu zuciyarta ta kasa miqa wuya dari bisa dari akan cewa bada taimakon mammina ta tsinci kanta a hali mafi muni da tozarci a tarihin masarautar agadez dana family dinta ba. Bata zargin mammina da cutar da ita......amma tana zarginta da gaza maida hankali ta zaba mata CANCANTACCE da zata rayu kalar rayuwar da mamminan tasan ta jima tana mafarki,kalar rayuwar da tasan ta jima tana mararinta,RAYUWAR 'YANCI BA QARQASHIN DOKA KO UMARNIN KOWANNE D'A NAMIJI BA. "Ranki ya dade......akwai matsala....." Taji muryar bushira daga bayanta,abinda ya sanyata waigowa da sauri tana dubanta,zuciyarta kuma na cike da fata da kuma neman tsarin sake jin wani abu da zai kassara farincikin da taketa tattalin dawowa dashi. Da idanu ta tambayi bushiran,wani yare da sun jima da saba magana dashi da ita da kuma haddaceshi,don haka ba tare da jinkiri ba ta amsa mata. "Thunder ne ya tsinke.....yace ko zaki iya wani abu akai?,dukka dabarunsu ya qare". Bata tsaya sauraren sauran maganar bushira ba ta dire cup din dake saman d'an plate din da take zuqar coffee din a gaggauce,ta soma baro harabar dake liqe da dakin hutawar tata tana shigowa ciki da wannan zazzaqar siririyar muryartata take bawa bushiran umarni. "Bani mayafi". Da hanzari bushiran ta dauko mata tana yafa mata,gami da saita mata lausasan takalmanta. Bata wani damu da boyon kanta da takeyi na kwana da kwanaki ba,kamar yadda bata damu da gaisuwa da kuma kallon da hadimai keta binta dashi ba. Wasunsu kallo ne na gulma da munafunci,ta fito a yau din bayan kwanakin data shafe ba wanda yaga koda qyallin idanunta. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Hankalinta sosai yana kan dokin,doki ne matuqar tsada da sultane ya sanya zunzurutun kudade na qasar dubai ya siyo mata shi,ya siyo mata shine kawai a matsayin kyautar kammala degree dinta,ta kuma fita da kalar sakamakon da sultane din yake buri,harma sama da yadda yake hasashe. Takanas tasa aka dawo dashi agadez tun a wancan abun daya faru a hippodrome,tasa ake bashi kyakkyawar kulawa,sai ta qara saurin tafiyarta wanda duka duka baifi takun tafiyar wata macen tafiya ta al'ada ba......bata soma jin nutsuwa ba sai data kawo bakin gurin ta kuma sanya kai kai tsaye ba tare data tsaya sauraren jawabin hadimin data samu a tsaye bakin gurin ba. Tun daga nesa idanunta suka sauka a kansu,yana zaune saman bayan thunder din,saidai yayi kaman rub da ciki ya riqeshi da kyau. Sukuwa yake faman yi tare da qoqarin kayar dashi,amma cikin wata irin qwarewa yaqi bashi wannan damar. Magana yake masa da dan qarfin da zaka iya jiyowa tamkar yana magana da dan adam. Da dukka jarumtarsa ya sake rungume gadon bayan thunder din da yayi wata irin haniniya yana daga qafafunsa na gaba,abinda sukasan tabbas idan ba gwanin sarrafa doki ba ba abinda zai hana mutum faduwa qasa war was a gurin. Idanunta ta lumshe,tana jin wata irin matsananciyar faduwar gaba,tana hango yadda thunder zai watsar dashi ya kuma tattakashi yabi ta kanshi ne kawai. Faduwa a doki wani mummunan abune da bata qaunar kalla,saidai kuma yadda taji gurin ya fara nutsuwa ya sanyata bude idanunta a hankali. Ga mamakinta thunder ya fara nutsuwa,still bai sauka a kansa ba yana ci gaba da shafashi a hankali gami da yin magana qasa qasa dashi,har zuwa sanda ya tsaya cak ya daina bige bigen da yakeyi,sai yayi wani tsallae tana direwa a qasa daga bayan thunder din. Sosai ya qarewa dokin kallo bayan ya samu nasarar maidashi nutsuwarsa. Ya aza hannunsa gadon bayansa yana sake shafashi a hankali,abinda ya sake bawa dokin nutsuwa sosai,sannan yaja akalarsa zuwa gefe,ya kuma tsugunnar dshi,cikin ladabi yayi biyayya ya tsugunna saman qafafun nasa,sai shima ya tsugunna daga daya side din yana ci gaba da magana dashi,maganan da ba wanda yasan me yake fadi. Idanunta ta ware sosai,tana jin wani irin kishi yana saukar mata. Don me zai sarrafa mata doki bayan bata da tabbacin iya komai a tare dashi?,meye hadinsa ma da doki?,tunda ba magana ake ta takarda ko bada karatu ba?. Batason yayi mata komai da yayi kama da taimako tallafawa ko dafawa,da wannan tunanin nata ta fara takawa zuwa inda ya tsugunnar da dokin. Bai lura da ita ba sam,cikin sassanyan sautinnan nasa maras amo yake ci gaba da karantawa thunder wasu ayiyo na qur'ani. Yayi relaxing sosai tamkar me fahimtar ma'anonin ayoyin. Ta daya bangaren thunder din ta tsugunna,tana qanqance idanunta. Zataso ko sau daya ya kalleta don ta karanta masa a karance cewa din bashi da hurumi akan komai nata,saidai baiyi hakan ba,don baikai qarshen ayar da yake karantawa ba,wadda sautin ya fara shiga zuciyarta a hankali yana saukar da wani yanayi,saita janye dubanta daga kallon mutumin da ko sau daya bai daga idanunshi a kanta ba,ta soma shafa fuskar dokin. Shafar fuskar tasa ya sanyashi yin wani qaqqarfan yunquri kamar zai tashi,abinda.ya sanyasu dukkaninsu miqewa da hanzari da niyyar riqe akalarsa,lokaci guda.....cikin sakanni guda,abinda yayi sanadiyyar haduwarsu gaban fuskar dokin. Haduwa hannuwansu sukayi guri guda,kowanne ya janye da wani irin sauri. Lokaci guda dukkaninsu suka daga kai. Idanunsu ne suka gauraya dana juna,wani irin zuzzurfan kallo suka sakarwa junansu,iskar dake kai kawo a gurin tana kada sassanyan qamshin da ya kama jikin kowannensu. Musamman nasa scent din,wannan unique turaren da shi daya ya mallaki irin qamshin a duniya. Hasken ranar da yayi saura a sassanyan yammacin dake sake hada wani irin nau'in hadari ya haske fuskar nan tata,fuskar data mallaki wata irin kwantacciyar fata kaman da madara take wanka. A nutse ya janye idanunsa daga kanta yana mamakin samun blue eyes a yankain africa a tattare da wata mace har haka. Launin idanun da suka jima suna bashi mamaki kafin a hankali su juye su soma burgeshi tun daga sanda ya fara mallakar hankalin kansa. Nata idanun sunyi wani irin dacewa da zara zara eye lashes dinta,da kuma gewayayyar fuskarta dake dauke da kwantaccen gashin gaban yalwataccen goshinta. Wani abu ya taba zuciyarsa,sai ya samu kansa da tuhumar kansa da kansa da ganin baikensa na qare ma fuskarta kallo.ya sunkuya a hankali yana daukar akalar thunder dake zube a qasa,abinda ya sanya akhnan din ja da baya a hankali. Idanunta ta sake lumshewa tana sake budesu lokaci daya sanda ya sake zaunar da thunder sosai. Ta budesu fes a kansa,ta tsani duk wani mutum da zataji yayi mata kwarjini......ta tsani wani mutum ya fits kwarjini,ba'a taba samu ba tsahon rayuwarta tsakanin mutanen da duk suke kewaye da ita,sai yanxu?,bama kuma akan kowa ba akan wani malami can?. Iska ta zuqa sosai don daidaita nutsuwarta da hankalinta da takejin kamar tana shirin daburcewa daga sanda kallon cikin idanunsa ya zame mata wani abu na kusa kusa da tayi a yau din. Idanun da cikin mafarkinta kadai take ganin irinsu,......idanun da take tsammanin su ta gani a hippodrome,yau gasu kusa da ita ainun,kusancin da baifi banbamcin d'ani biyar ba. Kwarjinin da take hanga a nesa a kusa ya ninka wannan.......idanun sun zame mata alaqaqai din rayuwa da a yanzun cikin qasa da second ashirin na gaurayar idanunsu waje daya ta soma tunanin anya ba sihiri gareshi ba?. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 69* Ba wani ido daya taba hanata furta bacin ranta koda kuwa idanun mammina ne.....mamminan dake da girma da kima a rayuwarta,amma a yau da kallo daya da yayi mata ya shafe duk wani tunaninta na abinda ya kamata ta fada masa,na sanya masa iyakoki da tsaidashi daga shiga hurumin da ya shafeta. Da kallo guda daya tak taji ya saka mata wani irin fargaba da rudewar da batasan dalilinta ba.......da wannan kallon guda daya ta daina shaqar kowacce iska saita wannan mayataccen qamshin da har yau bata gaji da neman wanne nau'in turare bane haka?. A nutse ya miqe,miqewar data sanya idanunta sauka kan qafafunsa duk da yadda take qoqarin yiwa qwayoyin idanunta control. Kai tsaye suka fada kan takalmin dake sanye cikin doguwar qafarsa. Fes take fara sol kamar bai taba taka qasa a duniya ba,yayin da baqin takalmin da aka saqashi da magi daukakar darajar fata ta dace matuqa da gaske da qafar tasa. Karon farko wani abu ya fusgi hankalinta,ta zubawa takalman idanu sosai sanda yake matsawa baya da baya a hankali yana barin jikin dokin. Crown half shoe ne na kamfanin Dolce and Gabbana.......irin takalmin sultane sak,takalmin da aka taba bawa sultane din kyautarsa don nuna girmamawa daga sarkin tahoua. A lokacin suna tare da sultane din,tana zaune a farfajiyarsa yana duba kayan,kurkusa lokacin da take a matsayin aminiyar sultane din,ba yanzu da komai ya sauya ba. Takalmin ya burgeta sosai a sannan,don har sultane yana cewa. "Inda namiji ce ke da na bar miki shi kadeejatou" Tayi murmushi sosai a sannan,ta kuma dauki wayarta tayi qiyasin adadin kudinsa. Kanta ya kwance sosai da zallar kudin da aka buga mata lissafi da CFA din qasarsu. Idanunta take ta qoqarin zarewa,ko kuma qaryata asalin takalmin shine a qafarsa. Sam takalmin bai dace da malami ba......takalmine dake bayyana zallar kuma tsantsar mulki da iko ga duk wanda ya mallakeshi,anya ba takalmin sultane dinne ba?,idan har haka ya kasance kenan baya ga shigar sauri da yakewa sultane da dukka al'amuransa har ya fara shiga taskokinsa?. Idan hakane gaba me zai faru?,anya bazai shiga sahun mutanen da suke zuwa a madadin baqi ba amma daga baya su qwace sarauta daga anihin wanda sarautar ke hannunsu ba. "Da ambaton Allah kadai zukata suke samun nutsuwa" Yayi maganar hankali kwance yana sakin akalar dokin. Blue eyes dinta ta dauke daga saman takalmin tana maidawa kansa,daidai lokacin da ya juya baya,bata iya hangen fuskarsa sai kwanctacciyar baqar sumar da take kwance a qeyarsa zuwa dokin wuyansa kadan,shigen yadda asalin matasan samarin BUZAYE 'yan qabilarta suke. Wani irin taku da take iya hangen zallar izza a tattare dashi,izzar da har yanzu take qalubalantarsa akan yinta,izzar da takejin bai cancanceta ba.....izzar da take alaqantata da tsananin girman kai ne kawai irin nashi,tare dakai kanshi inda bai baije ba. Wani abu ya mata tsaye a wuya sanda take jinsa yana magana da hadiman gurin. "Koda dabba ne sai Allah ya tambayeku yadda kukayi kiwonta kuka kula da damuwarta,kada kuyi tunanin idan akwai zalunci gurin kula dashi Allah bazai muku hisabi akai ba,don haka ku kula" Yadda dukkaninsu suka rusunar dakai cikin girmamawa ya sake tunzurata qwarai. Me yasa yana bare zai shigo masarautarsu ne har ya dinga iko mulki da kuma izza?.....don me sultane zai bar masa riqon babbar masarauta kaman masarautar agadez?,bayan shi din baqone akan komai ma. Hasalima baisan me ake kira da sarauta ba,meye hadinsa da ita?,sunyi hannun riga ta kowacce fuska. A yanzun tsakanin ita dashi batasan waye magajin SULTANE OF AGADEZ ba. Tana hangen wani girmamawa da dukka hadimai ke.masa,har tayi kunnen doki da irin girmamawar da suke mata. Wannan bacin ran shi ya sanyata yin abinda bata taba yi ba wato kiran bawa da kanta. Yana dab da fita daga gurin yaji sautin kiran,karon farko da shima yaji bayyanar muryarta a fili irin haka,sai yaja numfashi sosai ya fesar dashi yana lumshe idanunsa gami da budesa duka lokaci guda. Kadan kadan yakejin magananta cikin fada,kalma daya tak ya iya jiyowa. "Akwai wani dama dana bayar na kowa ma zai iya shigarmin barga da duba dawakaina bayan ku?". Idanunsa ya lumshe a hankali yana maida hankalinsa ga maleek dake tattauna matsalolin daya hanga tattare da dokin,can qasan zuciyarsa kuma tana sake cika da mamakin tsananin girman kan dake damunta. Bai cewa maleek komai ba,har zuwa sanda shi da kansa ya sauya topic din. Ita kanta batasan dalili guda daya da ya sanya taketa zabga fadan ba. Saita dinga jin kamar ba ita ba,kamar an canzata sanda ta baro bargar tana takowa gami da komawa sassanta. Yanayin girman kansa da izzarsa ke sake bata mata rai. Yana da wani dabi'a data lura da ita,basarwa tare da attitude na I don't care. Komai ma yana nuna bai gabansa bai dameshi ba,abinda take gani a matsayin zallar wulaqanci da kuma girman kai. wadannan idanun suka sake gilmawa ta tsananin hijabin tunaninta,taja siririn tsaki yana qoqarin kauda tunanin gefe. Abu daya ta sani tabbas koda ba shine mutumin hippodrome ba.....komai nasu yazo da tarin tsananin kamanni,mutumin da har yanzu yaqi barin cikin baccinta,a wannan karon tana jin zata saka kudo ko nawa ne don binkito gaskiyar WAYE SHI?. "Ranki ya dade.....mammina ta aiko tana son ganinki......" "Bana sha'awar ganawa da kowa......" Ta amsawa birra a taqaice wadda ta karbo saqon daga hannun yalwa. Ko d'ar bataji ba soma takawa zuwa balcony dinta. Har qasan ranta tana jin wani zafi zafi na mammina.....tana kuma son nuna mata taji radadin da bata taba ji ba a tsahon rayuwarta don ta fahimci cewa ta bata mata da gasken gaske. Ta bata mata martabarta tarihinta da GIRMANTA da taketa fama riritawa,sai takai hannunta a hankali da zummar jawo mayafin kanta dake shirin sauka,nan take hancinta ya shaqi wannan daddan qamshin da duk sanda zata shaqeshi yake haifar mata da faduwar gaba. Sake kai hannun nata tayi hancinta da sauri,sosai qamshin ya shige mata qofofin hancinta yana ratsawa a hankali yana isa ga kwanyarta dama zuciyarta gaba daya. Dakatawa tayi da tafiyar a hankali,sunan barratu ta kira,ta qaraso a hanzarce,saita miqa mata hannunta kawai. Ta fahimci me take nufi,ta matso a hankali cikin d'ar d'ar takai hancinta ta shanshana. "Inaso ki nemo contact na kamfanin YASMEEN.....shine kawai company din daya rage bamu yiwa magana ba akan turaren nan ba haka ne?" Kai ta girgiza cikin girmamawa. "Haka ne ranki ya dade". "A siffanta musu shi,ina buqatar wannan qamshin.....indai suna dashi su fadi price din da zasu siyar dashi,ni kuma zam biya ko nawa ne.....idan ma babu,muddin sun shirya samar dashi,su fadi abinda suke buqatar a basu" Ta qarasa maganar tana wucewa ciki ba tare data tsaya ko waiwaye ba. _Hmmm,nikam akhnan me zakiyi da wannan tsadadden scent da kika qwallafa rai haka a kanshi,anya?🫣🫣....muje dai zuwa_ *MORSA SAFIYYA* Tun daga farkon sashenta yasan akwai banbamci me tarin yawa a tattare da komai ma,abinda yake bayyana masa akwai wani abu daban da yasha banbam dana sauran sassan gidan. Kowa a nutse,cikin kuma doka da order,kowa kuma cikin tsari yake a tsaye akan nasa aikin. Sam ba maza kusa da mata,hakanan basu kusa da ainihin ginin gidan,kamar yadda ba mata kusa da inda maza suke nasu ayyukan. Surutacciyar shiga dake bayyana nutsuwa kamun kai da kiyaye doka gami da kiyaye dokokin musulunci. Mewada ne yayi masa jagora cikin tarin girmamawa har zuwa sanda ya isa gurin da morsa safiyya take jiransa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Tunda ya doso gurin ta miqe don nuna girmamawa a gareshi,ya sauke dubansa qasa yana jin kaman ta aza masa nauyi. A qa'ida UWA take a gareshi,wani irin yanayi me kama da na nanay dinsa yake hanga sosai tattare da ita. Yadda ta tsaya tana jiran isowarsa da tarin girmamawa. Yadda tayi tsaye fuskarta a washe da wani yanayi da baiyi kama da murmushi ba.....amma yafi murmushi fidda nutsuwa saman fuska gami da nuna halin girma da dattako. Da cikakkiyar sallama ya qaraso gurin,ta amsa masa tana furta. "Ga guri ka zauna muhammad" Yadda ta ambaci sunan sai yaji fitar sautinta sak na nanay dinsa. Sai a sannan yake tuna me yasa lokuta da dama idan tayi magana yakejin girman maganarta,idan tayi magana yakejin kamar ya santa a wani guri?. A nutse ya zauna,itama saita koma ta zauna tana karantarsa a hankali. "Tubarakarrahman......ma sha Allah" Ta fadi can qasan ranta. Bataga lafin falaak ba data fadaawa wannan character din ba.....wannan nutsuwar.....wannan kamalar......wannan kamun kan.....uwa uba wani kebantaccen kyau da kuma gayu daya sake yiwa kyan ado da sake bayyanashi. "Na gode sosai da amsa kirana da kayi akan lokaci" Ta fada tana dan duban agogonta a sace. Baiko qara minti guda tak ba daga lokaci da ta sanya na zamansu,abinda ya sake sanya wata kimarsa da darajarsa qaruwa ainun cikin ranta da idanunta. Miskilin murmushinnan me wahalar fahimta ta saki yana gyara hannun jubah dinsa. "Babu buqatar godiya,cancanta ya sanya nazo". Ya fadi kansa tsaye fuskarsa a sake yana jin kamar yana gaban nanay. Murmushi tayi kadan daya nuna masa wani digon baqi daga qasan hancinta sak irin nanay dinsa,abinda ya sake saka zuciyarsa harbawa da sake samun tabbaci da gamsuwa,saiya zare idanunsa sanda take fadin. "Akwai magana me muhimmancin da duk duniya kai daya ya cancanta nayita da kai.....ta daya hannun kuma ALFARMA ce zan roqeka kayimin......wadda alfarmar zata shafi rayuka masu yawan gaske.....rayukan rayayyu harda na matattu". Shi din wani bangarene na tunani.....kuma shi din an haifeshi ne don ya karanta tunani yayi wasa dashi,don haka daga fitar lafazin kadai daga bakinta ya bude masa wani fage ya buda masa kuma wata hanyar me fadin gaske. "Zan iya gabatar da dukka maganganu na?" A nutse ya daga kanshi. "Nazo nan ne saboda kinyi kirana,so kiyi dukka maganganunki kai tsaye" "Na gode" Ta fadi. Sai kuma tayi qasa da idanunta gaba daya zuwa ga barin kallonsa,zuciyarta taji tana mata wani irin nauyi gami da matsewa a qirjinta. Ta sani a yau zata buda maganganun da suke da tsauri a rayuwarta zuwa ga mutumin da yake bare,saidai batasan me yasa ta gaza jinsa a mazaunin bare ba,zuciyarta ta kasa amsar haka,duk sanda zai zama a kusa da ita tamkar dai sultane,tana jinta kamar tana gaban D'ANTA tana jinta tamkar tana gaban hairaan ko falaak ne. "Akwai maganganun da me yiwuwa basu shafeka ba.....amma ya zama tilas na shaida maka,saboda qila wannan shine zai zama mabudin da zama fahimci muhimmancin ALFARMAR da zaka yi mana,ka kuma fahimci ma'anar neman ALFARMA a tare da kai" Takai qarshen maganar tana maido idanunta akan haisam din da yayi shuru yana saurarenta. Baice komai ba har zuwa yanzun,sai ta fahimci dama ya bata tayi magana yadda takeso kamar yadda ya fadi da farko. *"Sunana SAFIYYA YUNNUS JALLATA"* Ta fada da wani yanayi da ya tilastawa haisam daga idanunsa ya zubesu fes a kanta. Shikenan ta tabbata,ta tabbata wannan din Obboleettii Lamaan(twin sister) din nanay dinsa ce......dukkan wani tantama ko kowanto yakau. Jinin nanay dinsa ne zaune a gabansa,jinin da aketa kewa.....jinin dake damfare da zuciyar Nanay dinsa tsahon shekaru,jinin da har yau ba'a dains kewarsa ba......ba'a daina mararinsa ba YUNNUS JALLATA sunan daya sake amsa kuwa cikin kunnuwansa kafin sautin morsa safiyya yaci gaba. "Yar asalin qasar Ethiopia,saidai bazan iya gaya maka daga ahalin dana fito ba" Ta sake fadi tana girgiza kai a hankali. A nutse ya sake dubanta,yana son tunawa da hango abinda ya sanya wani d'aci cikin amonta da yanayinta harma da cikin idanunta. "Ba wannan bane me muhimmancin........SAFEENATA" ta furta tana yin qasa da kanta,wanda idan har haisam ya gani daidai hawaye ne suka shammaceta suka sulmiyo mata. Har cikin jininsa yakejin saukar da digar hawayen,wani abu me qarfi ya motsa cikin jikinsa. Duk da batace komai ba amma tunaninsa hasashensa masaniyarsa dama jikinsa gaba daya suna gaya masa sunan MAMMINA/ZAITUNA. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 70* "KHADEEJA ta zama wani sashe na rayuwa da zuciyata da har yanzu ban fidda ran ganawarmu ba.....duk da mutuwa ta raba tsakaninta da safeena kamar yadda ta rabata dani......mun tashi tamkar 'yan ukkun da ko bacci baya rabamu duk da mun fito daga mabanbantan uwaye......har zuwa sanda qaddara ta fara aurar da khadeeja......sannan tazo ta aurar da safeena ga hannun da bata cancanci rayuwa dashi ba.....bisa tilastawar mahaifinta. Idan nace maka SAFEENA duk cikin mu ukun nan ta fimu haquri zurfin ciki da hangen nesa kada ka qaryata,kada kuma kayi mamaki. Tun kafin ta shiga gidan mijin farkonta take ganin alamomin da suke gaya mata lallai ba za'a zauna lafiya ba daga matarsa ta biyu. Matar da take ganin ta aureshi ba bisa cancanta ba,don kyanta yafi qarfin ajinsa......amma ana kyautata zaton auren mazaje masu kudi bata maidashi a bakin komai ba shi yasa ta shiga gidan. Saidai duk gidan data shiga bata taba yarda a sake auro wata bayan ita,muddin zaka aureta.....saidai ta zama ita daya ce a wajen miji. Ba kasafai ta fiya yadda ta taras ba bare a auro mata,saidai a gidan AJANI gaba daya wannan tsarin nata ya karye. Qabilarsu suna da wani irin hadari,matsafa ne na gaske masu ta'ammali da asiri cikin qabilun Ethiopia........amma duk da haka bata samu nasarar fidda uwar gidan ajani ba,haka ta shiga da wannan haushin,bayan lokaci kadan ko amarci bata gama ci ba ajani ya hangi safeena ya qwallafa rai ya hannun MAHAIFINTA. Tun kafin ta shiga akaso maidata mahaukaciya......gane gane ta dinga yi muraran,amma ko ni bata gayawa ba bare falmaga mahaifiyata data zama itace UWARTA don ita ta riqeta tun tana da watanni a duniya. A haka safeena ta shiga gidan,ta samu tsananin soyayyar mijinta kamar bai taba son wannan matar tasa ba......ta samu wani irin tattali da kulawa da kuma soyayya.......saboda sauqin kanta,tsananin haquri,iya kula da miji miqa wuya da sadaukarwa. Kome ya fada ta zauna,wannna ya sake haukata soyayyarta cikin zuciyar ajani,ya zamana hatta da abokansa ba wanda baisan da zaman safeena ba. Zaman shekara daya kawai sukayi,amma duk wanda yasan ajani yasan safeena a bakinsa,dukkan nutsuwarsa ta duniya itace,zamansa safeena tashinsa safeena. Wannan bai daga hankalin uwar gidansa ba,don sosai safeena ke binta sau da qafa dayi mata biyayya,sannan matarsa ta biyu tafi tsaye mata a wuya,saboda izgilanci.....girman kai gadara da ganin ta isa da take dashi,ba launin wulaqanci da qasqancin da uwargidansa bata gani ba lokacin shigowar ZEENATU gidan......." Sunan data furta din ya sake sanyashi daga idanu ya dubeta. Fuskarta ta fara sauyawa daga wani mataki zuwa wani matakin.....matakin dake sake bashi tabbacin magana ce me nauyi a zuciya da bakinta. "Shekar daya safeena ta dawo da tsohon ciki gida,da kuma shaidar saki uku lokacin da muke zaman makokin mahaifina.......baiyi arba'in ba safeena ta fara naquda,ta kuma haihu cikin daya daga cikin asibitocin dake daura damu.....saidai wani abun mamaki shine,sama ko qasa aka rasa jaririn da safeena ta haifa. A lokacin tabbas inda mahaifina yana raye,lallai na tabbata zai tsaya yayi shari'a akan case din,amma sai safeena tace abarwa Allah tunda anyi dukkan iya bincike akan neman yaron da yadda akayi ya bace amma ba'a samu komai ba.....ni da falmata da khadeeja dukka mun fusata,muna ganin donme zata fadi haka?,saidai daga bisani ni da falmata muka fahimci wani mummunan aikene na saqo aka yiwa safeena.......yatsa daya na jaririnta aka aiko mata dashi daga inda dukkanmu bamusan ina bane......ana kuma shaida mata cewa muddin taci gaba da tada zancan neman abinda ta haifa nan gaba kadan kanshi za'a aiko mata dashi sukutum da guda. Wani irin mummunan tashin hankali muka shiga,baci ba sha,ga tsoro na bayyanar zancan,don sosai safeena ke kuka da roqonmu nida falmata kada mu fadawa kowa,tanaso yaronta ya rayu don sun bata tabbacin haka,ana tsaka da wannan saiga wani saqon. Gargadinta akeyi da shaidawa mutum biyu da tayi wato ni da falmata......ana kuma umartarmu da mu tattara komai namu nan da kwanaki uku mubar qasar......wannan shine zai bawa jaririnta 'yancin ya rayu,idan ba haka ba kuwa.......tabbas a asubahin kwana na ukun,ta duba randunan ruwa dake bayan masallacin kusa da masarauta ta cire gawar jaririnta,koda wasa kuma muka sake waiwayar qasar ba jaririn kadai ba.....har uwar jaririn za'a rasata. Naso mu tsaya mu tunkari koma waye.....naso mu fuskanci ko waye,saidai banason rasa safeena.....kamar yadda safeena batason rasa jaririnta wannan ya sanya mukayi baton dabon da har yanzu ba'a sake ganinmu......bisa zato da tsammanin mun tserewa matsala......saidai inaa....." Ta fada tana sauke wani numfashi. "Zeenatu ta biyo mu har zuwa agadez.......ta wacce hanya ce?,ta wanne dalili?......mutuwar ajani........ta kuma biyo sahun babban abokin da ajani baida kamarsa. Zuwan nata ya sanya na fahimci wannan zeenatu da hannunta faruwar wannan abun daya sami safeenata,amma bani da shaida ko tabbacin cewa itadin ta aikata gaba daya. Wata sabuwar babin qaddarar ce ta budewa safeena.......safeena din da sultane muhammad hammud ya soma gani a wani taron bikin al'ada da buzaye ke gabatarwa duk shekara Festival de l’Aïr. Wani irin bikine dake hada manyan mutane da sarakuna. Yada safeena ya qwallafa rai a kanta.....a sannan kuma abinda bamu sani ba zeenatu ta jawo zuciyar sultane,kafin ajani ya aureta da sultane suka fara soyayya,tayi mutuwar sonshi kamar me......amma da ajani ya nuna yana da ra'ayi sai sultane din ya barwa ajani din ita. Abun yazo mata da ciwo,ta haqura ta karbi ajani ne saboda binciken da mahaifin sultane dake raye a sannan yayi. Ya bashi tabbacin zeenatu ba matar aurensa bane.....don a sannan ya samu labarin aure auren data dinga yi. Sultane baya musu wa mahaifinsa,ya sallamawa ajani ita,sai kuma daga baya ta sake dawowa sultane a karo na biyu. Saidai ni na sani.....dawowar zeenatu a karo na biyu yasha banban da niyyarta na farko......bayan soyayya akwai wani lullubabben sirri.......wanda bincike na da Idanun dubana suke bani akwai wani abu da takeson sani na ajani,wanda ga sultane kawai zata samu amsarsa.....". Sosai maganan morsa safiyya ta sauka samam zuciyar haisam,ya lumshe idanunsa a hankali yana daidaita maganganun gami da jinjinawa kaifin basirar morsa safiyya,koda yake duka ahalin tsohon sarki yunnus JALLATA ba wanda yake koma baya gurin JARUMTA da KAIFIN BASIRA. Da gaske ne zaituna kuma zeenatu ta biyo sanin sirrin mafi girma dukiyar ajani da kuma makullin ragowar taskarsa,saidai ya raba qafa kenam?......tana harin mahaifinsa motii aba jifar daya zama amini na biyu a gurinsa......tana kuma harin SULTANE? Sai ya jinjina kansa wani boyayyen murmushi yana subuce masa. Lallai da gaske sai yayi wasa da hankalin matar nan,irin wasan da baa taba mata irinsa ba......saiya sanyata da kanta da kanta ta tonawa kanta ASIRI. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Daga sanda ta sake gane cewa safeena ce matar da sultane ke mutuwar so.....wanda shi kuma ya sota ne ba tare da yasan ma cewar matar abokinsa bace......a sannan ta sake tsananta wani kalar tsana da qiyayya a kanta. Tabi duk wata hanya don raba abun.....ni kuma naqi bata wannan damar ta cimma nasara akan hakan. Daga sanda nima na karanci ta sake shigowa rayuwar SAFEENA ta daga sannna ban sake bacci da idanu biyu ba. Safeena tana da sanyi tana da raunin dana tabbatar cikin ruwan sanyi zeenatu zataci galaba a kanta. Daga qarshe zeenatu ta bari ko ince qaddara tafi qarfinta an daura auren safeena da sultane a matsayin matarsa ta farko......saidai bata bari safeena ta tare ba,har sai daka daura nata auren ta kuma tare a gidan sultane da shekara guda cur......sannan tsananin addu'ar da family din diory hammani suka tsaya akai safeena ta shiga gidansa bayan zeenatu ta tabbatar ta gama kafawa ta tsare,ta kuma amshe sunan UWARGIDA daga hannun safeena" "Wani irin zama ne da safeena tayi gidan sultane me dadi ta bangaren mijinta,saboda samun mafificiyar soyayya daga gurin sultane din kamar yadda ta samu mafificiyarta daga gurin ajani. Wannan ya daga hankalin zeenatu da mafificin tashin hankali......tashin hankalin da ya ninku ne saboda ta gaza gusar da wannna soyayyar. Ta rayu tsakaninta da zeenatu cikin BARAZANA turata zuwa ga tarin matsalolin da batasan kansu ba batasan kuma yadda zata warwaresu ba. Saidai qarfin addu'a da na saka aka tsayawa safeena da ita komai yake zuwa da sauqi,duk da a sannan nima ina gidan nawa auren. "Ni kadai.....ni da safeena kadai muka karanci baqin matsanancin halin da zeenatu ta shiga lokacin da safeena ta haifi AHMAD......ko kadan ban bari zeenatu tasan akwai wani ciki jikin safeena ba,don jikina yana bani ba zata taba barinsa ya zauna ko a haifeshi ba. Ina da wani hali da bansani ba.....a halittata ce?,ko ina da mutanen boye dake tsartamin abu idan zai faru......inaji a jikina.....raina da zuciyata suna bani,abu qalilanne zai faru banji hakan a jikina ko zuciyata bata rayamin ba. Hatta da sultane dake neman haihuwa sosai a sannan saboda shekarun aurensa daya fara turawa ban bari safeena ta gaya masa ba,saida cikinta ya shiga wata shida,ta kuma roqeshi kada ya bari kowa ya sani,koda 'yar uwarsa nannie saboda kare lafiyar abinda yake cikinta. A sannan zeenatu tana ta fadi tashin yadda zata samu ciki da sultane,a duk duniya a wannan lokacin burinta kenan,kudade take kashewa marasa iyaka waiko zata dauki ciki dashi,saidai ko b'ari bata samu ba bare cikin dan mutum,dan mutum dinma d'a namiji. A sannan ta gama da kowa cikin masarautar,kowa kirkinta yake gani,kowa qaunarta yakeyi,ta kama nannie qam qam ta riqeta,don kusan ita kadaice ta ragewa sultane a wadda suke uwa days uba daya. Bansan me.ya faru ba,bansan ya akayi ba,ko sun manta zeenatu din 'yar Ethiopia dinnan ce da suka hana muhammad hammud aurenta?. Mun wayi gari kowa yana mata kallon cikkiyar ba'abzina,buzuwa musamman data kasance fara sol kamarmu. Sunanta da muka sani na zeenatu ya koma ZAITUNA,yaren Tuareg a bakinta fes.....al'adunsu shigarsu da komai nasu" "Haihuwar Ahmad ta qarawa safeena kima da martaba a idanun sultane.....wata sabuwar soyayya yake gwada mata wadda bata boyuwa,abinda ya sake daga hankalin zeenatu kenan,saidai da tarin kirsa irin nata da komai Ahmed ya koma kamar D'ANTA ya koma rainonta,ya koma hannunta ma gaba daya. A sannan ba abinda bance da safeena ba,amma tacemin ba zata iya gwadawa sultane zata amshe ahmad ba.....zeenatu bata isa ta masa komai ba sai abinda Allah ya rubuta qaddararsa ce......" Sai ta dakata tana hadiyar wani abu me d'aci a qirjinta. "Kasan wace safeena?" A nutse haisam ya maida dubansa kan morsa safiyya da kalar cakurkudaddiyar tambayarta. "Kasan wanne sadaukarwa SAFEENA ta mana nida sultane da bazata taba shafewa a zukatanmu da rayuwarmu ba?" Ta fadi wani irin hawaye me yawan gaske yana ballewa daga idanun morsa safiyya,wanda ko da wasa bata gwada tsaidasu ba. Bai iya amsa mata ba,amma wannan karon bai dauke dubansa daga kan fuskarta ba. "Sultane ya harbu da ciwon qoda sanda take dab da daukan cikin AKHNAN......dukka qodarsa guda biyu,kuma aka buqaci ayi masa DASHE na qoda......bada saninsa ba safeena ta sadaukar masa da qodarta guda daya,wanda baima sani ba sai bayan ya warke.......". Saita dakata tana yin qasa da kanta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 71* "Wannan ya sake sanyawa safeena ta zama wata mace da ba kamarta a gurin sultane.......ba jimawa ta samu cikin KHADEEJA wadda taci sunan 'yar uwarmu.....babbar aminiyarmu da duniya bamu da kwatankwacinta. Samuwar cikin ya sake jaddada tashin hankalin zeenatu,don cikin khadeeja yazo da banbamce babance sosai. Ciwo da laulayi sosai safeena takeyi,kamar ba cikin d'iya mace ba,girman cikin da wahalarsa daban yake,har mun fara zaton ko twins ne. Saidai daga baya zeenatu ta koma tayi relax,ta kuma maida komai ba komai ba,ta sake riqe ahmad da kyau. A wani dare da bazan manta ba,na kawowa safeena ziyara muke maganar "Duk yadda ka dauki rayuwa haka take zuwar maka,idan zeenatu ta riqe ahmad ga wani kyautar Allah zai sake bamu,Allah yana tare dame haquri safiyya,ki koyi haquri,akwai riba sosai a cikinsa,idan mace na haifa khadeeja nakeso a saka mata,ina yawan mafarkin khadeeja,inaji a jikina babu ganawa a tsakaninmu,zuciyata kullum da ciwon son ganinta da kuma ciwon son sake sanya d'ana a ido nake kwana nake tashi,duk sanda Allah ya hada fuskokinku,ki gayawa khadeeja ina qaunarta......ina qaunarta.....ina qaunarta har abada,nayi kewarta.....nayi rashinta,ki gaya mata ban tafi na barta don bana sonta ba,na tafi ne saboda tseratar da ruhin da bamusan gaba me zai zama ba......" Wani irin abune yake sauka saman zuciyar haisam,sanda morsa ke maimaita masa abinda safeena ta fada a sannan......sai yakejin kamar yana zaune a gurin.....kamar a gabansa safeena ke maganar. Wani irin rauni yaji zuciyarsa tayi,yana iya sauraren yadda morsa safiyya taci gaba da magana muryarta na rawa. "Daga ranar jikina yayi sanyi da safeena,munyi doguwar hira sosai,a sannan na yaye hairaan,tace nabar mata ita,ban musa ba nabar mata hairaan,saidai sanda zan dawo daukar hairaan na tadda wani tashin hankali ne da har yanzu bamu fita a ciki ba.......batan ahmad sama ko qasa,da fara haukar SAFEENA" Ta dakata tana sanya gefan lafayarta tana dauke hawayen idanunta da suka sake yawa kamar ana tunkudosu. "An rasa ahmad sama ko qasa,a wani dare aka wayi gari babu shi. Ba kalar nema da binciken da ba'a masa ba......a darenma yana kwamce jikin mamarsa,haka kawai kamar tasan hakan zai faru tace a dakinta zai kwana,don tun farkon cikin akhnan har girma daya fara yi bata da lafiya cikakkiya. Wayar gari tayi taga bashi a gefanta,da farko ta dauka kawai cikin gida ya shiga gurin zeenatu,nema da wasa saiya koma na gaske,amma tsahon kwanaki shuru babu shi ba alamarsa. Wani irin tawakkali safeena tayi,saidai kana ganinta kasan abun ya zame mata dafi ne kawai a zuciyarta. "Wataqila ni kuma tawa qaddarar kenan batan yarana.....wataqila tawa jarrabawar kenan,ya Allah ka bani ikon cinyeta" Ta fadi da wani irin soyewa cikin idanunta. Zeenatu ta fita haukacewa,don saida aka yita karbo mata tofin dangana,sultane yasa aka dinga kiran malamai suna mata wa'azin tawakkali,saidai tana dangana din sannan ne kuma aka wayi gari wani gagarumin hauka ya samu safeena" A hanzarce haisam ya dubi morsa cikin mamaki. "Hauka tuburan,yanzu yanzu xaku gama magana da ita lafiya lau.....amma da zarar guri ya zamana ba kowa sai ita kadai yanxu zata fara cisgar sumar kanta tana ci da yage jikinta da suturarta,wani abun mamaki indai da mutum a guri lafiya lau zata zauna,amma ko yaya ta kebe sai abinda aka gani.....naga abubuwa da yawa game da ita masu daga hankali da ban tausayi.......amma ban taba ganin abinda ya gigitamin lissafi ba irin wannan ciwon nata,komai daya sameta a baya tare muke fuskantarsa da mahaifiyata,shi kuwa wannan daya tashi zuwa ya samemu,ya samemu a sanda muka zama CIKAKKUN MARAYU,duk da tarin dangi masu matuqar riqo da zumunci da muke dasu......sannan hakan ya sameni ne a sanda nayi kwanaki bakwai kacal da fita daga takabar mutuwar mahaifin hairaan. Da hannu biyu na karbi kowacce qaddara......da dukkan imanina da yaqini na,nabar hairaan hannun qanwar mahaifiyata,na tattara na dawo cikin masarautar nan don zama da 'yaruwata mafi soyuwa a gareni. A wannan xama na saba da mutane da yawa suma suka saba dani ciki harda sultane daya tattare kulawarsa akan 'yar uwata,wannan abun ya qara kimarsa da martabarsa a idanuna sosai. Saidai wani abun mamakin shine......wata daya ya rage a haifi akhnan na kwanta wani irin ciwo,wanda daga qarshe nima ya bayyana matsalar qoda ne. Ban sani ba......bata gayamin ba.....bata bari an fadamin ba haihuwar AKHNAN akace CS zaayi mata,wanda yazo daidai da sanda zaamin aikin qoda.......ashe qodarta dayar data rage mata ga bani........" Wannan karon kasa riqe kukanta tayi,ta sanya fuskarta cikin tafin hannunta tana sakin kuka mara sauti. "Subhanal malikul quddus" Ya furta a hankali yana jin wani abu yana yawo a jikinsa. Wannan wacce irin zuciya ce?,wannan wacce irin sadaukarwa ce?......wannan wanne irin 'yan uwantaka ce?,wacce irin qauna ce haka me girman gaske?" "Ban sani ba sai dana tashi......ita ta zauna bata da ko guda daya......a ranar naji inama nasan inda ruhina yake na fusgoshi na qarawa safeena......ina riqe da hannunta cikin nawa......tana kuka ina kuka 'me yasa kikayimin haka safeena.....me yasa zakiyimin haka?,na rasa khadeeja ban shirya rasaki ba'. Budar bakinta cemin tayi "kinfini buqatar rayuwa safiyya......zaki iya abubuwa da yawan da ni bazan iyasu ba.....inata baki wahala safiyya kinata wahala dani.....rayuwarki tafi tawa muhimmanci......na baki amanar KHADEEJA don a yanxu ita kadai ta ragemin......ita kadai ce nake da tabbas akanta......ahmad da dan uwanshi bansan ya rayuwarsu zata kasance ba.......amma indai kin samu labari ko alamun suna raye.....muddin ci gaba da haquri.......muddin ci gaba da shuru akan lamarinsu ne zai basu daman ci gaba da rayuwa,don Allah safiyya na roqeki KICI GABA DA SHURU......don Allah ki barsu su rayu ta dalilin SHURUNKI" Wannan roqon......wannan magiyar.......wannan muryar.....wannan sautin da wannan sadaukarwar sune suke riqe dani har yanzu.....sune suke takamin burki akan abubuwa da dama da nake gani nakeji. Safeena ta rayu akan wankin jini na kusan kullum saboda rashin qodojin dake tare da ita,muna rayuwa cike da fata tare da ita......amma ita sam ba wani fata tattare da ita saina mutuwa. Ba yadda sultane baiyi ta bari ya fita da ita a mata dashe ba,amma sai tayi murmushi. "Ko an dasa bazan sake rayuwa me tsaho ba,iya kwanakin da aka debarmin nayi a duniya sun cika" Wata irin azababbiyar rayuwa tayi......ga ciwon rashin qoda......ga kuma wannan ciwon haukan da yake tayar mata lokaci lokaci babu qaqqautawa. Sam akhnan batasan dadin uwa ko duminta ba,sai a lokutan da safeena ke hayyacinta. Idan tana hayyacinta wuni take a hannunta,idan tana hayyacinta bata yarda kowa ya dauke mata ita,zata wuni ta kwana tana mata wasa,tana kallonta,tana mata addu'a ita da sauran 'yan uwanta,takance. "Allah nayi imani dakai,nayi imani da dukka qaddarar daka aza a kaina.....na yarda komai ka tsarawa bawanka adalci ne.... Alla idan suna raye komai dadewar zamani ka hademin kansu guri guda.....Allah ka sanyasu qarqashin wani adali......wani adalar inuwa.....wani adalin shugabanci da zai amintar da rayuwarsu......wani ruhi da zai zame musu garkuwa ya basu amincin da ni na gaza basu,Allah ka albarkaci rayuwarsu,ka aminta dasu duniya da lahira". Bansan iya adadin sau nawa take maimaita wannan addu'ar ba a rana. Ranar da aka karbe akhnan daga hannunta aka daina barinta da ita,tana tsaka da riqonta ciwonta ya tashi,haka ta dagata ta saketa daqyar numfashinta ya dawo,koda safeena ta dawo daidai aka gaya mata abinda ya faru,abinta ta tambaya kawai shine BAN MATA ILLA BA KO? Ana amsa mata da EH ta saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa,saita maida kanta ta kwantar tana fadin "Allah yasa haka ne yafi zama alkhairi a gareta" (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Bazan Manta maganar qarshe da mukayi da ita ba,ana jibi zata rasu,ta kira sunana na amsa mata,sai ta saki murmushi tana kallon bangon gabas na dakin,wanda na lura tafi sati tana kallon gurin,a duk sanda take kalla kuma murmushin takeyi "Nifa na kusa tafiya gida na,gidan daba qunci ba wahala,ba zalunci sai zallar adalci da rahama,na kusa tafiya inda zan huta....." Saita dakata murmushinta yana sake qaruwa. A sannan kowacce gaba ta jikina tayi matuqar sanyi,ina murna ne ganin kwanakin ciwonta ya rage tashi,ko wankin jininma da ake mata wanda take fita hayyacinta kafin ayi a yanzu ba wannan abun sam,ta sake wani kyau abinta,har ranar da zeenatu ta shigo dubata ta kasa shuru sai data magantu. Amma kuma a lokacin tazo da wani kalan magana daya zaremin dukka lakar jikina. "Kina da gidan da yafi wannan ne safeena?" Na fada cikin tsoro,daga kai tayi da murmushi akan fuskarta ta kalleni. "Wannan gidan?......akwai birnannun abubuwa,abubuwan da wadanda zasuzo gaba sai sunfi wanda muke ciki yanxu.....kiyi haquri safiyya.....kiyi haquri.....kiyi haquri. Karkiyi fushi da akhnan kome zaya faru.....kada ki juya mata baya don Allah,ki tsaya a tare da ita. Ni na sani komawarta hannun zeenatu ba alkhairi bane,amma na roqi Allah na ya kareta kuma nasan ya amsa min,na roqeshi ya sanyata a mafificin hannu......ya sanya kulawarta a hannun bayinsa masu tsoronsa.....ya kuma bata mafificin miji ma'abocin saninsa da tsoronsa wanda zai ja hannunta zuwa aljanna ba wuta ba......amma akwai abubuwa masu yawan gaske da zasu dinga faruwa a gidan nan,ba lallai yanzu ba safiyya....Allah ne masanin lokaci,don Allah kada ki qara bari zeenatu ta shigo gurina.....banason ganinta da gaske,wani irin baqin duhu nake gani a tattare da ita.....ta cutar dani amma na barwa Allah hukuncinsa" Ta qarasa fada wani hawaye da tunda ta shiga wadannan jarrabawar ban taba ganin ta zubdasu ba a ranar sai gasu suna fita daga idanunta. Komawa tayi ta kwanta tana murmushi sannna tace. "Kin tambayeni ina da gidan da yafu wannan ne?,ina dashi safiyya.....gidan da koda wasa wannan gidan bai isa ya hada kansa dashi ba.....tazara ce me mugun yawa,inama zaki iya vaji da na nuna miki" Ta fada still tana kallon wannan bangon,wannan bangon da har yanzu idan na shiga ta gurin saina tuna komai kamar yau ya faru. Safeenata ta rasu a tsakanin cinyoyina,a kanta na fara sanin yanayin fitar rai a jikin dan adam.....wani yanayi me wahalar gaske.....wani irin yanayi me nauyi da kai kanka da mutum yake jikinka sai kasan babban aiki ne a gabanka ba qarami ba.......magananta ta qarshe bada amanar akhnan a hannuna.....amanar akhnan a hannun sultane dake tsugunne gefe yana riqe da ita kamar zai hana a zare ranta,daga wannan sai kalmar shahadar data yota maimaitawa har sanda tabi wani abu da kallo idanunta sukayi sama,wanda nake da tabbacin ruhinta tabi da kallo......". Katsewa maganar morsa safiyya tayi,ta lullube fuskarta da hannuwanta tana sakin wani itrin kuka maras sauti me d'acin gaske. Tana tuna komai,tana jin kamar a sannan komai yake faruwa. A nutse ya zare idanunsa daga kanta,yanajin qirjinsa ya masa nauyi,wani iri zafi yakeji daga cikin qirjinsa. Ya jima baiji labarin daya taba masa zuciya tsakanin dan uwa da danuwansa ba irin wannan. Bazaice ga adadin ajiyar zuciyar daya dinga saukewa a boye ba kamar yadda ya saba a duk sanda ranshi ya dugunzuma. Ya tabbatar nanay dinsa ba zata iya jurar jin wannan labarin ba......idan nanay ce yayi imanin zata kamu da ciwon zuciya ne kawai. Labarin rayuwar safeena dinta da rasuwarta bayan rabuwarsu bame dadi bane sam. Ya miqa hannu a hankali ya jawo ruwa cikin tarin kayan ciye ciyen da aka ajjiye masa,ya dauki cup daya ya tsiyaya ruwan sannan ya miqawa morsa safiyya da batasan ma ya zuba ba. Da manyan idanunsan nan da suka rusuna yake duban yadda ta qudundune fuskarta tana boye masa hawayenta. "Kiyi kuka don yana ragewa zuciya radadi.....amma ki karbi wanna kisha tukunna". A hankali ta sauke hannuwanta daga fuskarta tana kallonsa da fuskarta da tayi jajur......wani nutsuwa taji me yawan gaske a kalamansa,saita miqa hannu ta karbi ruwan kaman yadda ya buqata. Tas ta shanyeshi,ta kuma ajiye cup din tana jin yadda zuciyarta ke samun sassauci daga radadin da take mata. Shuru ya ratsa gurin ba tare da kowa ya sake cewa komai tsakaninsu ba. Sai daya bata mintunan daya tabbatar gudun da zuciyarta keyi ya daidaita sannan ya fara magana a nutse. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 72* "Ba wani abinda yake tabbata sai ikon Allah......haramtaccen abune zalunci koda akan ubangiji daya haliccemu,ya haramtawa kansa zalunci,ya kuma sanyashi abun haramtawa a tsakaninmu,Allah yayi rantsuwa da kan kansa cewa saiya taimaki wanda aka zalunta koda bayan wani lokaci ne". Kai take gyadawa a hankali,tana jin wata nutsuwa na sake mamayarta. Tana jin wani qwarin gwiwa sosai a tare da ita.....tana jin qarfin gwiwa na gaya masa buqatarta kai tsaye......mafarkanta da safeena a satittikan suna dawo mata kanta,tana jin kamar safeena na tare dasu. "Rayuwar safeena ta riga ta wuce muhammad......rayuwar akhnan ce kadai yanzu ta ragemin......ita kadai ce abinda zan iya daukan mataki ko bada kariya akai........mammina ta shirya lalata rayuwarta fiye da yadda take a yanxu.....ni na sani....ba iya haka taso taga biftu ba.......amma ban taba bacci ba tun daga wancan shekarun har yanxu,ina mantawa da hairaan da falaak saboda na shagala da addu'a wa akhnan.....wannan sautin MIJI NA GARI da safeena taketa roqawa akhnan a qarshen rayuwarta yanata maimaituwa akaina daga sanda yarinyar ta zama budurwa.....tana da wata irin izza....na sani,tana da taurin kai na sani.....tana da wahalar sha'ani na sani......amma an qara koya mata da wasu dabi'u da ba a cikin ainihin halittarta suke ba. Na tsorata da yadda take gudun aure.....na zurfafa addu'a.....bazan boye maka ba daga qarshe na fahimci bawai wani abu bane daban......halinta ne yazo a haka koda an hada da wani abun ma daban.......muhammad" Morsa safiyya ta kirashi a wannan karon tana duba zuwa cikin idanunsa kai tsaye. Shima ita yake kalla,sai yake ganin nanay dinsa cikin idanunta. "Ba wanda ya cancanci ya auri khadeeja a wannan lokaci IDAN BAKAI BA!!!" ta furta da wani irin confidence daya bawa haisam din mamaki. Idanu ya zuba mata sosai,yana son karantar ko gano wani abu tattare da ita,saidai itama morsa safiyya din kamar kowa,kwarjinin idanunsa ya hanata ci gaba da kallonsa,saita dauke idanunta gefe,a sanyaye ta dora. "Ina me roqarka muhammad........ka auri akhnan ko bazaka zauna da ita na HAR ABADA BA......ina roqonka kayi mata ALFARMA ka zauna da ita koda na wasu shekaru ne....zuwa sanda dukkan wani buri da aka ci a kanta zai wargaje.....zuwa sanda idanu sukaja baya a kanta.....ka bata GARKUWA muhammad ta hanyar aurenka......KA TAIMAKI RUHIN SAFEENA yaci gaba da kwanciya lafiya.....wallahi nayi imanin cewa,mutuwar auren akhnan a yanzu zai buda wasu sababbin qofofi ne da Allah kadai yasan adadinsu da kuma iyakarsu.....KAYI MATA ALFARMA ka ceci rayuwarta" Takai qarshen maganar tana dawo da dubanta kansa. Wata magana ce datazo masa a bazatar da baiyi tunani ba. Wata magana ce da bai taba tunanin jinta daga bakin morsa safiyya ba. Wata irin BA ZATA CE a tare dashi data sanyashi yin shuru na wani lokaci,kaman yadda ya saba bawai kai tsaye yake amsa maka magana ba har sai ya bawa qwaqwalwarsa damar numfasawa na wani lokaci. Ta yaya zai fara auren da bai shirya masa ba?......da yarinyar da yayi imanin komai nasu baizo daya ba?. Babu ta inda sukayi tarayya ita dashi......ba wani abu dake nuna daidaito a tsakaninsu......ta yaya ma?....wanne irin aure ne haka wanda ko da wasa bai taba hakaitoshi ba?. Idan kuma yace zaiyi auren CETO na wani lokaci ne.....ai ya sani cewa haramunne a qulla aure bisa wata yarjejeniya,yarjejeniyar ma ta rabuwa.....baisan daga inda zai samo halascin haka ba. Ta kowacce fuska baiga dacewa ko yuwuwar abun ba.......don ya sani.....aure ba abune ba wasa ba......sunna ce mafi qarfi da ba wasa a cikinta ko kadan,ta yaya zai fara abinda baiyi niyya ba?,bai shirya ba?. Koda morsa safiyya bata nema ba.....koda bata buqata ba ya yankewa kansa yin revision a tarihin safeena.......ya azawa kansa wannan nauyin ba tare da shawarar kowa ko tunani na biyu tsakaninsa da zuciyarsa ba. Akwai abubuwa da yawa da yake buqatar saninsu......akwai abubuwa da yawa da bai kamata a barsu suci gaba da tabbata a haka ba. INA AHMAD ina jaririn dan yayansa?. Sun narke kenan?,sun shafe daga rayuwar safeena?,saboda tsoron salwantar rayukansu sai a tabbata a haka?. Jikinsa yana bashi tun daga farkon labarin cewa komai daya faru na farko dana qarshe a qulle suke da juna.....komai daya faru yana da alaqa da dana baya,ya zama dole GASKIYA tayi magana......ya zama dole wannan ZALUNCIN ya gushe hakanan.....ya zama dole a tabbatar da ZURI'AR SAFEENA suyi rayuwa me 'yanci kamar yadda kowacce zuri'a take rayuwa.....AMMA BANDA WANNAN AUREN.....wannan auren wani abune da bazai daukeshi a wuyansa ba sam. Shuru itama morsa safiyya din kawai tayi,yayin da zuciyarta dake lullube a qirjinta take wani irin tsalle. Rawa kawai zuciyarta takeyi,tana cike da fata da sanya rai,tana cike da zullumin me zaya amsa mata dashi?.....tana tsaka da wannan zullumin e ya dubeta a hankali. "Komai a hankali ake binsa da kuma nutsuwar da bazata kawo dana sani ba daga baya......." "Kada ka bani amsa yanzu don Allah muhammad na roqeka.....kaje kayi tunani.....kayi tunani daga yau har zuwa kwana uku hudu biyar harma sati......amma ka sani,indai ka wuce haka komai zai iya faruwa da khadeeja" Ta qarasa maganar da wani irin rauni cikin idanunta. Zare idonsa yayi yana jin raunin nata yana tabashi,ya miqe a nutse,bayanansa dukka ya adana. Bawai zai iya gaya mata a halin daya ganta cewa kai tsaye bai karbi magananta ba.....don yasan aikata hakan zai sake jefata ne kawai cikin wani rudani na daban. Ta idanunta ya karanci dukkanin FATANTA yana kansa......ta sanya buri da fata me yawa a kansa. "Na barki lafiya" Ya fada yana takawa a hankali. "Na gode sosai muhammad da amsa kirana.....da jumurin zaman saurarona da kayi......na zabeka nayi kuma magana dakai a matsayin mutum me tsoron Allah.......Allah yana taimakon bawa muddin bawa bai gushe ba yana cikin taimakon dan uwansa" Magananta ta qarshe hadisi ne......hadisin da yaji yana kakkaryashi a hankali,don haka bai waiwaya ba bai kuma tsaya ba,yaci gaba da takawa yana fita a hankali daga sassan. Ajiyar zuciya morsa safiyya ta sauke,ta gyada kanta a hankali tana daga hannuwanta zuwa sam. Wata sirrintacciyar addu'a ce tsakaninta da ubangijinta,ta shafa a nutse sannan ta waiwaya ta dauki wayarta tana laluben hairaan don ta turo mata armelle. So yake ya koma personal residence dinsa.....so yake ya sake nisa da kowa da komai ko zai samu kwanyarsa tayi resettling na magangnun morsa safiyya da yakejin sun wani irin cika masa kwanya......amma kuma bai kamata daga shigowarsa gidan ace har ya sake fita ba. Saidai duk da haka hakan bai hanashi kebe kansa ba,yabar maleek da omar a qasa,ya haura zuwa samansa bayan ya sauya kayan jikinsa,sannan yayi zaune saman bedroom balcony ta bayan wasu flowers. Relaxing yayi sosai saman wani foldable bed dake a gurin,ya lumshe idanunsa yana sake bitar dukkanin labarin cikin kansa. Ya jima cikin wannan yanayin,har zuwa sanda jikinsa ya bashi lokacin sallar magariba ya gabato,ya bude idanunsa a nutse ya jawo wayarsa dake gefansa,ya tarar da tarin miscal harda na omar da maleek,qarshe yaga gajeran saqon maleek dake gaya masa sun fita wani guri shida omar. Baibi kiran nasu ba tunda ya fahimci ma'anar kiran,sai kawai ya kira beeno ya fada masa ya duba email dinsa. Tashi yayi sosai ya zauna ya rubuta saqon da dukkan tsarin da yake buqatar ya aike masa. Yana ji a jikinsa da ranshi akwai wani personal aiki da yahau kanshi......akwai xtra bincike daban da yahau kansa,ba kuma zai dakata ba har sai ya cimma gaci,har sai yakai inda jiki da zuciyarsa suke raya masa suke masa kuma tsammani. Kamar kowanne lokaci da kansa ya dauki zafi irin wannan,sauraren karatun qur'ani da kuma karantashi ne kadai abinda yake zame masa nutsuwar zuciya da kuma hutu. Yana zaune a farfajiyar da zata bashi daman ganin zirga zirgar kowa,da kuma sake karantar yadda dokarsa take aiki. Wani nazari yake sakeyi cikin gidan,motsin kowanne sashe,motsin kowanne hadimi da yanayin mu'amalarsa. Yana daga bangaren da ba lallai ka ankare dashi ba idan ba wucewa kazo yi ta gabansa ba,kuma koda kazo wucewar zaka dauka wani sha'ani daban ya keyi bawai nazarin yanayin gidan ba. Kunnensa manne da booth yana sauraren karatun qur'anin sheikh afif muhammad taj. Yawan lokuta yakan saurari qira'ar sheikh afif din,don yanason gani ko jin kamannin karatunsu da ake yawan fada. Tun yana da shekara sha takwas a duniya yake da nasa complete qur'an din audio,karatun da yawan manyan makarantun dake jimma dama Ethiopia gaba daya da wannan sound din suke amfani. Gidajen tv dana radio dinsu gaba daya. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Kiran daya shigo wayarsa ya sakashi tsaida karatun,ya maida hankalinsa akai a nutse sassanyar iskar dake tafe da hadari tana busashi da cikin Moroccan thobe din jikinsa data kasance olive color. Yanason abu me green qwarai,daga sanda yaji favourite colour na ma'aiki annabi muhammad s a w. Sai kuma kalar take bashi wani irin kwarjini gami da bayyanar da fatarsa me haske data d'ara ta al'ummar jimma oromia haske,wataqila hakan yana da nasaba da hutu da nutsuwa da yake ciki. Nanay daya gani ya sanyashi katse karatun da yakeji,ya sanya hannu ya zare Bluetooth din ya ajiye,sannan ya katse kiran nanay yabi bayan kiran. Ajiyar zuciya ta sauke sanda taji sallamarsa,hankalinta da tunaninta ya sake komawa kan saamee dake kwance saman gadon ROYAL CLINIC dake cikin masarautar jimma din. Tun ranar qarshe da sukayi waya da haisam din ta karanci damuwa ce fal zuciyar yarinyar,amma kawaici da alkunya irin na d'iya mace ya hanata nunawa. Tana tausayin dukkan wani maraya,saboda tasan me maraici yake nufi,maraicinma irin na UWA da ba'a maida makwafinsa. "Ina fata ka yini lpy Muhammad?" "Alhamdulillah nanay" Ya amsa mata safeena da safiyya suna dawo masa tar cikin idanu da zuciyarsa. Yana jin kamar ya shaidawa nanay din cewa yaga twin's dinta......amma yanaji a jikinsa lokaci baiyi ba,ba yanxu ba. Ba yanzu bane lokacin daya kamata ya fadi mata hakan ba,tabbas zata nema tako qafarta masarautar agadez ne......a yanzu kuma da komai ya sake warware masa ta labarin morsa safiyya bayajin ya kamata nanay din ta bayyana a yanzu. "Ma sha Allah......magana zamuyi Muhammad" Ta furta a hankali tana tashi daga gaban gadon saamee gami da ficewa a hankali daga dakin. "Yanzu kike buqata nanay?,ko zaki sanya wani lokaci da yayi miki saina kiraki?". Murmushi kadan ta saki,bata shakka ko kokwanton haisam.....biyayyarsa game da iyayensa ta dabance.....wata irin soyayya da jinqai yake gwada musu data jima bataga yaro irinsa ba. "Idan nace zan bari zuwa wani lokaci muhammad sai na dinga ji kamar lokaci xai quremin......alfarma nake nema muhammad a gurinka" Kai ya girgiza da sauri kamar tana gabansa,ya zauna kuma sosai yana bata nutsuwarsa. "Kinfi qarfin alfarma nanay,saidai umarni...." Murmushi me dan sauti kadan ta saki. "Na sani muhammad.....amma wannan inaso a barshi a mazaunin alfarmar" "Ina jinki nanay" Ya fadi cikin girmamawa. "Ina tsoron wani abu muhammad......maraicin saamee yana tabani,don har yanzu bata saba da rayuwa ita kadai ba.....bata saba da rashin mahaifiyarta ba.....sai kuma na fahimci ta shiga wani yanayi da ita kanta nasan bata shirya masa ba". Shuru yayi yana saurarenta,kwanyarsa na qoqarin tattaro masa maganganun nanay guri daya ya aunasu a mizani. "Muhammad.....ko kasan akwai alqawarin aure tsakaninka da saamee ta hannun mahaifiyarta kafin ta rasu?". Shuru ne ya gilma ta cikin kansa,kafin ya maida idanunsa a hankali ya lumshesu sannan ya budesu,zuciyarsa ta dauki "Subhanallah" A hankali tana maimaitawa. Wani irin yanayi yana sake saukar masa,ya sake miqa hankalinsa akan nanay zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 73* "Ba wai hakan yana nufin lallai saika auri saame ba.....ba kuma hakan yana nufin zan tilastaka bane....aah,kamar ganin dacewar hadin mukayi dani da ita. Saidai tako ina ban hango ta yadda hakan zai kasance cikin lumana ba.....banga ta yadda zaka shaqu da saamee ba har ku fahimci juna ba saboda yanayin aikinka....a daidai lokacin na karanci kamar zuciyar yarinyar ta harbu da sonka...." Sosai maganan nanay ta shigeshi,ya fahimci hakan tunda dadewa,sannan omar ya jima yana maimaita masa. "Na sani nanay" Ta fadi kansa tsaye. Ba wani abu daya kebance game dashi wai yana boyewa nanay,nanay dinsa itace aminiyarsa ta farko dake sanin komai daya danganceshi. "Na nesanta kaina da ita ne saboda banason ta saba dani......nayi hakanne saboda banaso ya zame mata wani ciwo a zuciyarta.....saboda ina ban hangi ta inda zata samu yadda take so ba daga gareni,ban shirya ba nanay......ina da abubuwa da yawa a gabana" Ya fadi da dukka gaskiyarsa da fatan nanay ta fahimceshi. Shuru ya ratsa tsakani kafin nanay ta saki wani murmushi me sauti kadan. "Sai yaushe?.....muhammad sai yaushe?,ko kasan kwanaki kadan suka rage aje nemawa hussam aure?ana kammala bikin rumaisa?" Maganan yadan bashi mamaki,amma yasan hussam,rawar kai plus farinjinin 'yammata. "Hussam dai?" Ya maimaita da dan mamaki. Murmushi nanay ta saki. "Kowanne burina ya cika haisam banda abu biyu,ganawa da 'yan uwana da kuma ganin surukai da jikokina.....ina buqatar ganinku dukka da aure" Bai iya cewa nanay komai ba,don anzo bangaren da yakeji bashi da wani shiri akai,kuma shidin ba wani gwani bane ta wannan maganar musamman da nanay din da kunya da nauyi irin na tsakanin uwa da d'a yake ratsawa a tsakaninsu. "Kasan saamee tana kwance ana qara mata ruwa?.....ko tsananin damuwa ce a kanka ta jawo mata haka?" Maganar ta bashi mamaki sosai,ya danyi ciki ciki da idanunsa yana sauraren nanay. Koda bata ganinsa tasan yanayinsa,ta gyada kanta a hankali. "A shawarce.....me zai hana ka ceto saamee koda ta hanyar bata kulawa muhammad?,wataqila zuciyarta ta samu sassauci?". Wani shurunne ya sake ratsawa a tsakaninsu,a nutse ya motsa labbansa masu kyannan. "Indai hakan kikeso nanay sai ayi" Ya fadi a nutse yana jin wani nauyi ya sake hawa kansa. Idanu Nanay ta lumshe,murmushi mara sauti yana qwace mata,alfahari da samun yaro irin haisam din yana sake shigarta. "Allah yayi maka albarka.....Allah ya shiga dukkan al'amuranka,yadda kake qoqarin ceto damuwar wasu Allah ya ceto damuwarka" "Ameen Ameen" Yake amsawa da ita yana ware tafukan hannayensa. Addu'ar nanay wani abu ne da baya wasa dashi komai gajatarta "Zan sanya noora ko Aanani su dinga sanar maka komai a yanayin da ake ciki" Da wanna sukayi sallama da nanay din,ya zare wayar yana ajeta gefe nannauyan ajiyar zuciya tana kubce masa. "Ya ake ciki man". Maleek ya fada yana daukan gorar ruwan dake gaban haisam din ya fara zubawa da kansa a cup. Kai ya girgiza a hankali yana nutsa yatsun hannunsa cikin sumarsa wadda ya yafa amama saman kansa. Iska ya sake furzarwa daga bakinsa,saidai ba wanda ya samu daman cewa komai ta bayyana. Falaak ce,dauke da kyakkyawan kwandon data cikashi da fresh 'ya'yan itatuwa,irin wadanda tassn akhnan na matuqar so. Kai tsaye daga lambunsu ta fito,ta kuma debosu da zummar zuwa ta kai kitchen su gyara ta wucewa da Akhnan din,dukka tanayin haka ne don cika alqawarinta data yiwa morsa safiyya. Gefe daya wani sawai takejin qirjinta,nauyi me girma ya sauka ya kuma ragu daga zuciyarta. Farincikin kawai data sanya morsa safiyya ya isheta,tana jin wani dadi da yadda abinda tayi ya faranta ran morsa din. A hankali idanunsa ya sauka a kanta sanda yake tsakiyar shan ruwan,daga omar har haisam da suke magana a tsakaninsu ba wanda ya lura da ita,sai qarar tarin qwarewar maleek. Haisam ne ya fara ajiye dubansa a saitinta sanda take wucewa ba tare data ankara dasu ba,sai kawai ya janye sannun da yake niyyar yiwa maleek din ya jefeshi da harara. "Saika tashi ka bita ko?" Kamar baisan gatse ba,kamar bai fahimci gatse haisam din ya masa ba,ya kurbe ragowar ruwan daya tsaida masa tarin,ya ajiye cup din ya miqe da kuzarinnan nasa ya soma takawa yana bin bayanta. Siririn tsaki haisam yaja......wato maleek zafin kai kawai yakeson qara masa,don haka ya miqe a nutse ya dauki wayarsa kadai yana juyawa zuwa hanyar da zata sadashi da sassansa,sai suka bar omar a tsakiya a zaune ba tare da yasan shi wacce tashar ya kama ba,qarshe ya zabi satar kallonsu maleek,don ta nan bangaren yasan zaifi samun labari me kyau da armashi. Saura kadan tayi missing numfashinta sanda taji sallama a bayanta da wata irin nutsatsiyar murya. Ta tsaya cak ba tare data juya ba,muryar dai bata mata kama da muryar daya daga cikin hadiman gidan ba,to waye?. Sai maleek ya zagayo gabanta yana bayyana kamar me jiran takai ga tambayar kanta da kanta din. Kai tsaye idanunsu suka gauraya guri daya,sai taja da baya kadan tana jin wani kwarjini tattare dashi. Murmushin dake fita saman fuskarsa ya daki zuciyarta da wani irin yanayi me nauyin gaske,tana jin kamar gurbi da muhallin loneliness da takeji a zuciyarta yana cikewa. "Kawo na tayaki mana kona samu albarkacin princess?" Yayi maganan yana dage mata dukka girarta biyun. Kasa musantawa tayi,duk da batasan wayeshi ba,abu daya dake bata mamaki shine kwarjini da takejin yana mata masu cika idanu,shige wadanda take gani tattare da sheikh haisam,sai kawai ta miqa masa kwandon,yarima maleek din sai gashi da riqon kwando yana kuma jera kafada da ita a nutse suna takawa zuwa ciki ba tare da kowa yace da danuwansa komai ba. *HAISAM* A nutse yaji an kirashi da sunan da sukafi kiransa cikin masarautar na SHEIKH MUHAMMAD. Sai dakata yana juyowa a nutsensa. Me wada ne yake isowa gurin,cikin girmamawa ya rusuna yana fadin "Barka da wannan lokaci" Murmushi kadan haisam din yayi yana bawa mewada din hannu,amma sai ya noqe. Wani girma suke bashi,wanda shikuma koda a jimma ba kasafai ya fiya son irin wannan abun ba. "Musabaha a musulunci abune me matuqar muhimmanci,kankare zunubai da sadar da soyayya tsakanin bayi,assalamu alaikum" Ya qarasa fada yana sake bawa mewada hannu. Cikin jin nauyi,cikin jin girman haisam din yana kai masa ko ina ya bashi hannu suka gaisa. Me wada ya zare hannun bayan sun kammala gaisawar yana girmama zatin Allah,da yadda ya sanya wasu halittunsa tun a duniya suka banbamta da wasu,wani irin laushi da qamshi tafin hannuwansa kawai keyi. "Giwa ce tace a sanar maka tana son ganinka". Dubansa sosai haisam yayi,aiken yana dan saukar masa da mamaki qasan ranshi,amma sai ya gyara tsaiwarsa yana duban mewada. "Ka shaida mata ka sanarmin,zan kuma amsa kiranta daga yanzu zuwa kowanne lokaci" Kai mewada ya jinjina a hankali. Qarfin halinsa,jarumtarsa da yadda yake iya aikewa giwa saqo kai tsaye game da abinda yake ranshi kuma ra'ayinsa kenan yana burgeshi qwarai. "Zan shaida mata,na barka lafiya" Ya fada yana miqewa sosai ya fara takawa yana barin gurin. Hannunsa ya goye a bayansa,sannu a hankali cikin nutsuwa yaci gaba da takawa yana nufar sassansa. Tunaninsa yana zurfafa,yana kuma laluben meye dalilin kiran da mammina din tayi masa?. Daidai sanda zai gifta da qofofin da suka raba balcony dinta da nasa wadda zata kaishi kai tsaye zuwa sassan kowannensu. A hankali Idanunsa suka sauka akan sashen nata,sai ya zare idonsa dakai yana wucewa gaba. Wani bangare na rayuwarta ya soma qoqarin dawo masa fes a kansa. HADARI ne sosai take fuskanta.....hadarin da yake kyautata zaton ya kamata ace hankalinta yakai kai.....amma me ya hanata fahimtar wasu abubuwan?......me ya hanata ta gane akwai QALUBALE?.....akwai GIBI a rayuwarta?. Ta sanya girman kai da izza gaba da komai nata?,bayan akwai tarin yaran SARAUTA da basu kai kansu inda takai kanta ba?. Samun kansa yayi da jan siririn tsaki,ya dauki tunanin ya ajiyeshi gefe daya,saboda yana ji a ransa akwai wani aiki da yafi wannan muhimmanci da ya kamata ya maida hankalinsa akai. *MAMMINA* (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Yatsunta kawai take murzawa guri daya sanda mewada yake gaya mata martanin sheikh muhamma haisam. Karo na biyu.....karo na biyu kenan yana fito na fito da martabarta. Karo na biyu kenan yana qalubalantar girman matsayinta naqin amsa kiranta a sanda ta buqaci haka. Qoqarin tauna fushinta da dukkan bacin ranta takeyi ta kuma hadiyesu kada ta furtasu ko ta bayyanasu gaban mewada dake matuqar girmamata da biyayya ga dukka umarninta. "Zaka iya tafiya" Ta fadi a taqaice. Godiya yayi mata ya miqe yana barin gurin. Wani irin iska me zafi ta furzar daga bakinta,ta bude idanunta sosai sannan ta maidasu ta lumshe ta sake budesu,tana gayawa kanta ne yanzu ba lokaci bane na fushi,yanzu ba lokaci bane na bayyana zafinta ba,lokaci ne na kwantar da kai,lokaci ne na karbar duk wani abu da malamin zaiyi,har zuwa sanda haqarta zata cimma ruwa,a sannan ne zata banbance masa WACECE ZAITUNA?....WACECE GIWAR AGADEZ?. "Farisa!" Ta kirayi daya daga cikin hadimanta dake can qofa tana jiran umarninta. Da gaggawa ta iso gabanta tana zubewa. "Zan shiga naga akhnan,bana buqatar iso,bana kuma buqatar a gaya mata zuwa na". " Hakan za'ayi Allah ya baki yawan rai" Ta fadi kanta a qasa sannan ta miqe itama ta fita. Kwana da kwanaki tayi bata sanya akhnan din a idanunta ba,ba kuma wai don ta shirya faruwar hakan ba,sai don abubuwan da suka sha mata kai take qoqarin ganin komai ya tafi a tsari. Shirye shirye taketa yi,shiri kota kwana,maganan motsuwar daya daga cikin tarakuna Ethiopia ya tsaye mata a rai,shine kuma abu na farko da take kwana take kuma tashi dashi,sannan da kanta take bibiyar samun tabbacin abun,ta zare wakilci tana ganin kaman bazai mata ba. Abinda yafi sanya mata wata fargaba shine......ganin yadda aka kasa samun cikakken bayani kai tsaye cikin sauqi kan da gaske akwai wanda yayi tafiya zuwa agadez?. Abinda yake sake luguiguita mata zuciya kenan.....yake sanya mata shakka da wasi wasin ANYA ba wani gagarumin abu bane yake shirin tunkarota?. *AKHNAN* Ba zata sake bari wani abu ya taba IKONTA ba.....ba zata sake bari wani abu ya girgiza duniyarta ba......ba kuma zata sake bawa kowa dama ya bude qofar rayuwarta ba.....koda wayeshi.....komai kusancin dake tsakaninsu. Tun a dararen da suka shude ta yiwa kanta wadannan alqawuran,zata maida rayuwarta yadda take a baya a cikin satin. Zata maida kanta PRINCESS KHADEEJA MUHAMMAD HAMMUD dinta kamar yadda take a baya,zata rayu yadda takeso,ba shawarar kowa....ba sanya hannun kowa.....ba gudanarwa ko yankewar hukuncin kowa. Wannan ya sanya ba tare data shaidawa mammina ko tayi shawara da ita ba ta fara shirye shiryen komawa Niamey. Tun a daren jiya ta gayawa hannatu a gyaran gidan a maidashi kaman yadda yake a baya,a fadawa babban driver dinta na garin Niamey wato HARISU ya duba motocinta gaba daya da take fita office dasu a fita dasu a siyo wasu. Koda ta koma Niamey tana jin zatayi hutun sati daya cikin gidan kafin ta fara fita office. Zata zauna na sati daya ta maida wannan tunanin na CEO a kanta,ta sake kintsa nutsuwarta da yadda zata karbi ayyukanta. A yanzun da take zaune cikin daya daga cikin falukanta da takan huta. Baida kujera ko daya,sai wasu irin lausasan Turkish carpet da tuntum manya masu dauke da tambari na sarauta da sunanta a jikin kowanne. ABIDA me mata gyaran gashinta ce,wadda ta iya nau'ikan manyan kitso na qasashe da qabilu daban daban,da kuma kalba manya da takan yiwa akhnan din a sanda duk zata koma Niamey idan ta gama hutun qarshen mako da takeyi a baya. Tana mata kalbar data zama manya kuma tana hade jelarsu guri daya yadda ba zasu damu uwar gijiyartata ba,yayin da akhnan din ta maida hankalinta sosai ga ameesha tana sauraren bayanai akan kamfanin na watannin da tayi bata tare dasu. Kowanne bayani na ameesha sake bata mamaki kawai yakeyi,amma bata dakatar da ita ba,taci gaba da sauraronta duk da ba ganewa takeyi ba,amma ta aza hakan akan cakudewar bayanan ameesha dinne guri daya ya kawo haka,don bada wannan salon da kuma wannan yanayin suka gabatar mata da bayani ba. Kanta taji abida ta saki,abinda ya sanyata dauke kai daha system din da suke video call da ameesha ta maida ga abida,sai idanun nata suka sauka akan mammina dake takowa cikin izza,da alama kuma ita ta saka hadimanta su bawa dukkan hadiman dake dakin umarnin fita. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 74* Bata motsa ba,bata kuma ce da ita komai ba,sai kawai ta maida idanunta ga Ameesha sukaci gaba da tattaunawarsu cikin salon miskilancin nan nata da ya motsa. Idanun mammina akan ameesha bayan ta daukeshi daga kan akhnan da rabi akayi masa kalbar ta kuma sauka lambas a gadon bayanta,sai rabin gashin da yabi gefan kuncinta ya kwanta. A jikinta taji abubuwa biyu,bata kuma buqatar qarin bayani. Hankalinta ya kwanta da har take shirye shiryen komawa Niamey kenan?,sannan ya akayi ta samu access da ameesha?....me take gaya mata?. Tana buqatar fahimtar komai kafin tayi magana daukan mataki na gaba ko kuma yin wani motsin,don haka ta samu tuntum daya ta zauna akai tana harde qafarta. Still akhnan bata waiwayo ba,saidai yanayin ameesha da taga kaman yana sauyawa,kamar bayanin tana yinsa ne kawai ba tare da ita kanta tasan gundarin abinda take magana akai ba. A nutse ta lumshe idanunta sannan ta budesu a kanta. "Ameesha" Ta kirata da muryarnan tata dake cike da aji gayu da sarauta. "Ranki ya dade" "Ki tattara komai ta yadda idan na iso zanji dadin dubawa,bazan wuce gata ba in sha Allah" "To Allah ya kawoki lafiya,godiya nake" Ameesha ta fadi wani sanyi yana tsargawa qasan ranta. Tana fatan ta iso da wuri,ta kuma jima tana addu'ar dawowarta a lokaci irin wannan kafin komai ya qarasa kwabewa. "Gata?" Mammina ta furta a nutse da salon tambayar da ba iya fili kadai ba.....hatta da zuciyarta ta aikewa tambayar. A nutse ta waiwayo ta dubi mammina tana kuma dakatawa da kashe system din. "Eh gata" Ta amsa mata kai tsaye da wani irin yanayi da tasan sauran mutane kadai akhnan me magana dasu a haka ba ita giwa ba. "Gata in sha Allah......ko akwai sauran abinda ya rage da zan zauna nayi?.....kowa burinsa ya cika,an daurawa akhnan aure,ta taba aure a tarihin rayuwarta dai ko?" Ta fada da dukkanin alamun dake nuna abun yana mata ciwo.....da dukkanin alamun dake nuna cewa abun yana mata radadi tare da jefata a danasanin amincewa da wannan yarjejeniyar tunda farko. "Akhnan d'iyata" Mammina ta kirata bayan ya sake matsowa dab da ita,idanunta da jikinta dukka sunayin wani irin laushi. "Ban taba zato ko tunanin wani lokaci yana zuwa da zaki zargeni koki tuhumeni da cutar dake ba" Ta furta hawaye yana saukowa daga idanunta. Har tsakiyar zuciyarta akhnan taji hakan,a karon farko taga abinda bata taba ganina idanun mammina ba tsahon rayuwarta,kuka ko hawaye "Na rantse miki harda girman Allah......almaz shine kalar mijin da yafi dacewa dake.....kinsan a yanzu haka halin daya shiga saboda abinda ya aikata din?". Tayi mata tambayar tana tsareta da idanu tanason karantar yanayinta. Kai tsaye akhnan din take duban mammina. Haka kawai tayi loosing interest aka komai daya shafeta......tana jin tana rasa dukkan wani confidence da qwarin gwiwa akan mammina din. Batasan me yasa ba,tana jin kawai komai ma ya fita a ranta,amma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata,bai kamata KUSKURE D'AYA TAK da aka samu daga bangaren mammina din ya zama wani abu ba.....ya zama wani dalili da zai sanya ta juya bayanta daga dukkan wani alkhairan mammina din a tare da ita ba. Wata irin mutum ce ita da bata manta alkhairi komai qanqantarsa. "Wallahi akhnan ya fiki shiga baqinciki bacin rai da kuma damuwa.......a yanzun ina me baki tabbacin baisan inda kanshi da hankalinsa yake ba,kuma dukka a kanki,dukka ta sanadinki" Mammina din ta fadi yanayinta yana nuna narkewar zuciyarta. "Ta yaya zanyi saken da wani mummunan abu zai rabi diyata?.....ta yaya zanyi saken da halitta mafi soyuwa a zuciyata da rayuwata zata fuskanci wata barazana?,bayan bani da kamar wannan halittar duk duniya?. Ina jin wani irin mamaki kaman zai kasheni a duk sanda na kalli fuskarki,naga kuma ba abinda ya cikata sai tuhuma da ganin baqina" Mammina ta furta tana share qwallarta data sake gangaro mata. "Amma duk da haka ni zaituna.....nayi alqawarin saita lamuranki,koda kuwa hakan shine abu na qarshe da zan aiwatar a rayuwata.......abu daya zan gaya miki.....ko mene zai biyo baya kada ki tuhumeni.....idanunki da hankalinki kawai nake buqata......amma karki manta da wannan ko sau daya a zuciyarki......ni mammina UWA nake a gareki.....bazan kuma taba canzawa daga wannan sunan ba har abada.....kamar yadda babu wani abu da zai sauya qaunar da nake miki har gaban abada". Daga haka ta miqe da wani irin yanayi dake nuna mutuwar jiki da damuwa me yawa. Samun kanta tayi dabin mammina din da kallo,tana jin jikinta itama gaba daya yanayin wani irin sanyi. Tana jin kamar ya kamata tabi bayanta.....amma wani sashe na zuciyarta dake daqare da wannan izzar dake gauraye da jinin sarauta na gaya mata ta qyaleta. Wani irin kewa takeji a yau......wani irin kadaici takeji duk da cewa tana zagaye ne da mutane. Samun kanta tayi da miqewa tsam,ta taka a hankali tana isa bakin qofar dakin,ya maidata ta murza mata key ta kulleta. Dawowa tayi a nutse zuwa bedside drawer dinta da ba wanda yake da alhakin taba gurin,ta murzata ta budeta,ta kuma fiddo wani dan zagayayyen akwaiti me matsakaicin girma ruwan gold. Budeshi tayi a nutse,ta saka hannu tana fiddo wasu hotuna qananu guda biyu. Idanu sosai ta xubawa fuskar dake jikin hoton,fuskar dake dauke da wani lallausan murmushi. SAFEENA ce,idanunta a cikin hoton suna kallon camera ne kai tsaye,wasu irin kyawawan idanu da suke kama sosai da nata,banbamcinsa da natan ita fari da blue ne......yayin da na safeena ya kasance fari da baqi sidik...... Hannu ta sanya a hankali ta shafi hoton,a ranta tana raya abubuwa masu yawa.......a ranta tana raya inda tana raye yaya zasu fuskanci wadannan kwanakin masu tsanani da taurari a tattare da ita?,saita lumshe idanunta tana damqe hoton sosai a tafin hannunta. Haka kawai takejin akwai wani abu da ba daidai ba......haka kawai takejin akwai wani KUSKURE da yake tare da ayyukanta da zartarwata......ko kuma yake tattare da tunani da hukuncin mammina?. Amsar da bata da ita batasan kuma yadda zata fassara abun ba. *SULTANE* Cikin kamala da nutsuwa irin tasa,wadda bata taba sauyawa ba ko a wanne bigire kuma ko awanne yanayi ya samu kansa ba ya qarasa qofar dakin bobbo muhammad dawud,wanda ya kasance daura dashi cikin daya daga cikin manyan hotels dake kusa da haramin madeena. Sau daya ya nema izinin shiga,bobbo da kansa ya taso ya budewa sultane din bayan ya ajiye dan qaramin alqur'anin dake hannunsa. "Ina fata kaima qira'arka irin ta yaronka ce ko?" Sultane ya fadi yana duban bobbo muhammad wanda ya ajiye masa ruwan daya ciro masa mara sanyi sosai a fridge. Bawai don daga wani guri sultane ya taso ba,ba kuma wai don yana jin ishirwa ba.....aah,kawai don tarin girmamawa ga tsohuwar abota. Murmushi sosai bobbo muhammad dawud yayi. Zuwa yanzu har ya saba da yanda duk fitowar rana da kuma faduwarta sai sultane din ya ambaci hasaim. A irin ambaton da ko motii aba jifar baya tunanin yana ambatonsa haka. "Duk wanda ya zauna da muhammad saiya dosani wani haske na alqur'ani daga gareshi" Obbo ya fadi yana zama gefan gadonsa yana fuskantar sultane. Kai sultane ya gyada a hankali,yana sake jin nutsuwa gami da gamsuwa me yawan gaske a tare dashi game da haisam din. "Zanso nasan wadanne iyaye ne haka Allah ya yiwa baiwa da samun yaro irin muhammad.....tabbas ni na sani,suna cikin iyaye masu sa'a a duniya". Murmushi kadan bobbo yayi,ya sani ba abu bane me yiwuwa ya gayawa sultane cewa tsohon abokinsa motii aba jifar shine mahaifi ga haisam din. Yin hakan kamar ya tona asirin aikinsu ne.....komai kuma zai iya bayyana a lokaci da kuma muhallin da ba'a shiryawa faruwar hakan ba. "Abokina ne......wanda ya damqa amanar muhammad a hannuna......ya damqa min da amana da gaskiya.....wanna ya sanya sau tari ni kaina nakejin muhammad din kamar nina haifeshi" (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Wannan shine dalilin daya sanya nayi tattaki zuwa gurinka.....don ka yimin alfarma.......don kuma ka nema min alfarma". A nutse bobbo ya daga kai yana duban sultane,maganganunsu suna zuwa masa a hagunce. "Kamar yaya?" Bobbo ya tambaya kai tsaye da alamun kullewar kai a tare dashi. Sosai sultane ya gyara zamansa,yana kuma tattarawa bobbo dukkanin nutsuwarsa,abinda yake gayawa bobbo cewa maganar tana da tarin muhimmanci mara misaltuwa. "Inaji a jikina akwai qaddarar data sake hadamu a nan gurin dawud,bayan tsahon shekaru da mukayi bama tare,ba kuma tare da mun sake haduwa ba. Yanayinka da yanayin girman da muhamamad ke baka....labarin qarfi da girman amincinku ya tabbatar zaka iya tsaiwa a bigiren da mahaifine kawai yake tsayawa,Nazo ne na nemawa d'iyata khadeeja auren muhammad haisam a hannunka......kai kuma ka nema mata aurensa a hannun amininka mahaifinsa". Maganar ta zowa bobbo a bazata.....kamar yadda asalin salsalar maganar da sigar maganar ta canza daga anihin ma'anarta. Duk da yadda maganan ta saukarwa bobbo a bazata,amma hakan bai hanashi sakin dan qaramin murmushi ba. "Sultane......yaushe aka fara nemawa mace kuma auren namiji......har abada namiji ne yake neman auren mace". Kai sultane ya jinjina a nutse. "Na sani......na sauya ma'anar ne.....na sauya yadda asalin yake,cike da fatan wannan sauyin ya zama tabbatacce har a qarshen rayuwar khadeeja". Cikin nazari qwarewa da sabo da aikinsu da security intelligence bobbo ya zubawa sultane idanu. Koda sultane bai zurfafa magana ba,koda bai zurfafa bayani ba ya fahimci kai tsaye daga zuciyarsa maganar take fitowa.....kai tsaye yake maganan daga ma'ajiyar dukkan lafuzzansa na gaskiya......hakanan ya karanci wani abu lullube a bayan furucinsa dake taba zuciyarsa. "Sakin aurenta a kwanaki uku ne zai sanya sultane ka sake nema mata wani mijin?" Murmushi sultane ya saki a nutse yana girgiza kansa. "Na maimaita istikhara a kwanakinnan har bansan adadi ba Akwai abubuwa masu tarin yawa da bansan yadda zan bayyanawa kowa yadda nakejin sukarsu a qirji da zuciyata ba......amma nasan abu daya da yayiwa tunani na da fatana karan tsaye shine......MAGANGANUN SAFIYYA WANI HASKE NE.....wani mabudi ne da sai a yanzu nake zurfafa tunanin zasu zama wani SANADI a rayuwar akhnan. Ba kalar wannan qaddarar na shirya gani a rayuwar biftu ba muhammad..... Wannan ya sanya na RUNGUMI kalaman safiyya a yanzun da dukkan nazari da dacewa a bisa ma'auni.......namiji me addini shine zai zama silar bango garkuwa da kuma me jangorar rayuwar akhnan bisa hanya me kyau.......ban shirya bawa diyata kowa ba sai HAISAM.....bari kaji dawud.....na jima ina kawaici.....na jima ina bege da fatan zukatansu su hadu guri guda.....to amma abun tsoron sai na fuskanci akwai wata irin tazarar nisa a tsakaninsu. Tun daga sannan na duqufa da addu'ar haduwar zuciyarsu da kawunansu,don ko tahowa nan da nayi jigon silar zuwana itace wannan addu'ar,cike da fata da kuma sanya rai....ban kuma cire tsammani ba har sai ranar da aka gayamin shi da kansa ya bada aurenta ga wani......ashe duka duka cikin kwanaki uku jarrabawar da kokwanton amsuwar addu'o'ina dukka zasu qare......" "Dawud...." Sultane ya kira bobbo kai tsaye,bai amsa masa ba,amma kuma yaci gaba da dubansa. "Nayi bacci har sau uku cikin raudha bayan na gama addu'o'ina da istikhara ta.......haisam nake gani a mafarkina da zarar bacci ya daukeni.......yana farautar duk wani abun farauta daga namun daji da suka kawowa akhnan hari......mafarkina na qarshe kuma tana boye a bayansa ya zame mata GARKUWA......kayimin alfarma.....kayimin kuma jangora haisam ya zama GARKUWA na gaske ga marainiyar d'iyata......" Yayi maganar zuciyarsa tana motsuwa saboda tuna safeena da yayi. Wani abu ya ratsa bobbo,mamakin wani nannauyan abu me girma da yake hangowa cikin idanun sultane yana kamashi. Saidai sultane bai barshi haka ba,a nutse ya warware masa labarin SAFEENA da ya gangaro zuwa ga rayuwar akhnan. A cikin labarin ya dasa ayar tambayoyi masu yawa......a ciki ya dinga hasashen al'mura masu yawan gaske.......saidai yayi imanin muddin haisam ya wanxu cikinsu ya rayu dasu na wata guda.....yana da tabbacin zai wahala baida labarin komai. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 75* *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX "Zan shige maka gaba sultane....kafi qarfin komai a tare dani......" "A al'adarmu,magana me girma irin wannan tana farawa ne daga iyaye ba daga yaro ba,yana da kyau ta fara daga iyayensa dama wadanda suka raineshi,don haka ina son ka tambayamin iznini,Amma kuma ina neman alfarma ka barni na nema alfarma ta bangaren haisam da kaina,Zan kira haisam da kaina,bawai don na tilastashi ba....ko don yaji kunyata ya amince ba.....aah,kowanne kamilin mutum iri haisam ya cancanci a bashi zabi da dukkan girmamawa". "Nayi maka" Obbo yana sakin murmushi,saidai kuma akwai tarin tambayoyi fal kansa. Sanda sultane ya fice ya barshi a dakin shi kadai,sai komai ya dinga dawo masa. Haka kawai yakejin akwai wani abu cikin rayuwar yarinyar,haka kawai yakejin wani karsashi na yin magana da motii,don haka sai kawai ya maida dakin ya kulle,ya kuma koma saman gado ya zauna bayan ya dauki wayarsa yana laluben motii din. *HAISAM* Kamar kowanne dare yana takawa a nutse gami da bin sahu sahu na masu gadi da tsaron gidan don tabbatar da komai akan tsari. Fitowarsa kenan daga ganawar da sukayi da wazeer,duk da cewa dare ya fara yi amma hakan bai hanashi duba amanar dake hannunsa ba. Simple throbe ce a jikinsa da wasu tausasan flip-flops masu daukan hankali. Daukan hankalin har yakai kan idanun duk wani hadimi da zai giftashi. "Qasaitaccen malami ne mutumin nan.....ban taba ganin malami irinsa ba......wani irin kwarjini yakemin,idan yana guri sai naji kamar ina tare ne da sultane" "Bakai kadai ba.....kusan dukkaninmu da zaka zagaya kayi quri'a haka kowa zaice maka yana ji" Hirar da wasu hadimai biyu kenan keyi sanda yabar gurin yana takawa zuwa qofar gaba. Shi da abdii suke tattakin,duk da yadda yaso abdii yabi su maleek zuwa personal home dinsa ya kwana amma yaqi. Hannunsa cikin aljihun throbe dinsa sanda hadimin dake gabanshi yake bashi bayanin yadda suka wuni. Yana maganar ne cikin wani irin tsoro,bawai na rashin gaskita ba.....aah tsaiwarsa a gurin da yadda ya kafeshi da farare sol din idanunnan nasa kadai suna sanyashi yaji hantar cikinsa tana kadawa. A zahiri hadimin yake kalla,saidai kuma a badini maganganun morsa safiyya ne suke dawo masa akai sama da maganganun da sukayi da nanay ma akan saamee. Baisan me ya sanya ba.....baisan meye dalilin daya sanya maganganun suka tsaye masa haka a rai ba. Abinda ya dauka a wancan lokacin,koda tace yaje yayi tunani akai,yana ganin ba wani gurbi ko muhallin yin tunani akan auren da bai shirya ba.....akan kuma yarinyar da ya tabbatar kanwarsu ba zata taba jiquwa ba guri guda. Alqawari ne qwaya daya tal! Daya daukarwa ransa,kuma bayajin zai fasa ko ya ajiyeshi shine neman AHAMAD da jaririn dan uwansa dako suna ba'a bawa ubansa daman ya sanya masa ba.....wannan shurun da suke zato ko tunanin KARIYA ce.....zai ballaata da dukkan hikimarsa ikonsa dama qarfin qwanjinsa. Shuru akan wacan jaririn ya tabbatar shine ya bada qarfin gwiwa da dama me qarfin gaske akan ahmad. Hannunsa kawai ya zard daga qirjinsa yana zurawa a aljihun rigarsa saboda sassanyan ringing mara hayaniya. Da hanzari abdii ya matso yana miqa masa wayar,sai ya sanya hannu kawai ya karba don ya manta ma wayoyin suna hannun abdii. Screen din ya kalla sosai,a nutse ba tare daya daga kai ba yace. "Zaka iya komawa bakin aikinka" Ya fada still idanunsa suna kan kiran,har zuwa sanda ya fara takawa a nutse yana daga wayar hadi da karawa a kunnensa. "Assalamu alaikum warahmatullah" Yayi cikakkiyar sallamar da ko yaushe take sake tunawa sultane muhimmancin sallama,take kuma sake sanya masa qaunar haisam da nutsuwa da halayensa. "Wa'alaikumussalam muhammad haisam.....ina fatan ba takura maka ba da kirana a wannan lokacin?" Dan sirrintaccen murmushi haisam ya saki,nutsuwar kamilim dattijon tana burgeshi,tausayinsa da kuma zuzzurfan abubuwa masu nauyin gaske dake binne cikin masarautarsa ba tare daya sani ba suna dawowa haisam din. "Ko kadan,kiranka tamkar girmamawa ne a gareni" Kai sultane ya gyada a nutse,yana jin wani abu me sanyi yana saukar masa. "Na gode sosai da wannan kalar fahimta da kuma girmamawa,ban sani ba ko muhammad yana wani abu?,sultane yana so yayi magana dashi". Yanayin yadda sultane din yayi magana kadai ya sanya haisam din ya fahimci magana ce me muhimmanci da gaske,don haka ya taka a hankali ya samu wani concrete chair dake daura da sassansa ya zauna. Guri ne dake da wani irin kyau,wanda dama tun daga nan har zuwa cikin kebantattun sassanninsu gurare ne da yanayinsu yasha banban da yanayin kowanne sashe na gidan. "Kowanne lokaci da zaka buqaci magana dani a shirye nake". "Na gode haisam" Ya furta yana jin nauyi da kwarjinin haisam din,duk da cewa bawai yana kusa dashi bane. "Muhammad......inason nayi magana dakai a yau a matsayin UBA ba'a matsayin SULTANE ba" "Ina saurarenka ranka ya dade" Ya fadi da hausarsa dake gauraye da yanayin yaren oromo daya kama harshensa da kyau,kai kace bafillacen nigeria ne. Numfashi sultane ya sake,yana ji lokaci yayi da zai fidda dukkan abinda yake ransa,yana jin lokaci yayi da zaiyi wannan aikin,wannan hobbasar,lokaci yayi da zai samawa diyarsa GARKUWA BANGO KUMA MAJINGINA. Yanaji a jikinsa rayuwar akhnan haka kadai ba tare da samun TSAYAYYEN bango majingina ba.....kamar wani abu yana dab da samun rayuwarta ya kuma lalatata. Zai iya jure komai amma banda shafewar JINI kuma irin safeena daga duniya. Ya jure salwantar Ahmad saboda a sannan yana sanya rai safeena zata rayu dashi,rayuwa me tsaho,zata kuma haifa masa wasu yaran da zasu shafe fiye da rabin gurbin rasa ahamd da sukayi,walau maza ko mata,sai gashi ashe duka duka rayuwar tata gajeriya ce.....ashe ba dogon zama a tsakaninsu. "Muhammad......kana cikin mutanen dake da masaniyar komai daya shafi akhnan.....koda ban zauna maka dogon sharhi ba,tunda kusan tun daga zabar miji har zuwa mutuwar auren abune daya faru gaban idonka". Kai ya gyada a nutse,yana jin a ransa me ya hado zancan yarinyar dashi?,qasan ransa yana fata ba wani jagorancin ko nauyin sultane zai sake aza masa ba akan lamuranta. "Gaskiya ne" Ya fada a nutse. "Wannan abun daya faru wani baqon abune da bai taba faruwa ba ga diyoyinmu kaf tarihin kafa masarautar agadez haisam......inajin kamar na gaza wajen bayarwa ko yin abinda ya dace da bawa gobenta kariya a matsayina na mahaifi" Maganan ya taba haisam,tako ina jarumatar sultane yake gani da salon mulkinsa,mutum ne me jajircewa qwarai da juriya,a duk wani bincike da zaiyi akan salon mulkinsa tsarikansa da tsarin da masarautarsa take tafiya akai yana matuqar burgeshi,saidai dukkan dan adam tara yake bai cika goma ba,hakanan duk abinda akace GAIBU ne,yafi yiwa dan adam illa akan komai.......kamar yadda BOYAYYEN MAQIYI yafi komai zama dafi da guba me tsananin zafi da quna a rayuwar dan adam.....zai iya illata kowa ta inda ba'a taba zato ba. "Ina fata ubangiji ya shiga lamarin" Ya furta a nutse,har yanzu kuma yana zurfafa hasashensa kan maganganun sultane. "Ameen" Sultane ya amsa da wani irin yanayi,yanayin da sanya haisam ya sansano akwai maganan da sultane din keson fadi wadda da alama tana masa nauyi ne. "Muhammad......bazan rufeka ko na boye maka ba,tunda ka shigo masarautata nake bibiye da motsinka,dabi'unka....da halayenka......kuma tashin farko na fahimci cewa kai din ba mutum ne kamar kowa ba.....akwai tarin kamala a tattare da kai,akwai wadansu irin kebantattun gwala gwalan dabi'u da suke wahalar samu daga gurin matashi kamarka.......komai naka yana da banbamci dana dukkan wani matashi dana sani......hatta da dattijai ma masu shekaru ba kowa keda wannan baiwar ba.....kai din mutum ne da bai zabi girmamawa ba.....girmamawa da kanta ce ta zabi nagartarsa". A nutse haisam ya sauke dubansa zuwa saman qafafunsa,yana jin nauyin yabon da sultane yake masa saman dukka kafadun da zuciyarsa. Duk da cewa ba'a bakinsa kawai ya fara jin ire iren wadannan kalmomin ba.....amma a yau sai yakejinsu tamkar wasu sababbin kalmomi ne daban da bai taba jinsu ba. "Kamar darajata bata kai girman kalamanka ba ranka ya dade" Sakin murmushi sultane yayi. "Kalamaina sun gaza ne kawai gurin fadin cikakkiyar nagartarka muhammad.....ka wuce duk yadda zan fada ko na musalta ka.....zan zarce zuwa ga dalilin kirana haisam kai tsaye" Sultane ya fadi yana jin nauyi.....yana jin kamar bai kamata ya azawa haisam nauyin da baisan dashi ba......yanajin kamar zaiyi abinda zai takura haisam din da walwalarsa gaba daya.....saidai kuma can cikin zuciyarsa yana jin wani aminci da sakewa wajen magana da haisam din......yana jin wani yaqini na cewa damuwarsa akan akhnan din tattare da haisam ne kawai zai maganceta. "Ina neman ALFARMA......inaso kuma ka taimaki rayuka biyu KAYIMIN ALFARMAR". Wani motsawa zuciyar haisam tayi,saboda alfarmar da yake fadi sai yaji kamar tayi girma ya furta shi haisam yayima kamilin dattijo irinsa ALFARMA,saidai sam a muryarsa da yanayinsa ba zaka fahimci motsawar da zuciyartasa tayi ba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Indai alfarmar da nake da iko da ita ne....kayi magana kanka tsaye ranka ya dade,kamar yadda zakayi da d'iyan cikinka daka haifa". Wani lumshe ido sultane yayi,yana jin hawaye yana taruwar masa a idanunsa. Wani girman haisam yana ninkuwa a idanu da zuciyarsa. Ko iya haka haisam ya tsaya,ko a iya haka haisam yace bazai auri akhnan ba tabbas ya girmamashi. Ko a iya accepting da yayi yake kallonsa a matsayin UBA ba shakka ya gama masa komai.....bazai taba baqi a idanunsa ba.....bazai kuma taba canza masa matsayi ba. "Ina nemawa akhnan ALFARMA....nima ina neman ALFARMARKA......ina nemawa diyata akhnan AURENKA......ina neman amincewarka ka karbi auren diyata akhnan" Wani irin daukewa wuta tayi daga kowanne sassa na jikin haisam,wani irin shuru ya gilma cikin kansa dama cikin sadarwarsa da sultane,wani irin yanayi da yakejinsa kamar ya tashi daga duniyar gaske zuwa duniyar mafarki,wani irin yanayi daga gaza gasgata gaskiyarshi. Wayar hannunsa yayi jarumtar riqewa sosai cikin kunnensa. Kowanne lafazi daga bakinsa ya nema ya rasa,ya bace masa bat daga kansa. Saidai kuma wannan mazantakar.....wannan jarumtar......wannan asalin jinin ABA JIFAR din dake yawo a jikinsa na musamman ne.....kamar yadda jinin KHADEEJATU YUNNUS JALLATA yake zagaye da duk wani gaba ta jikinsa. JININ SARAUTA guda biyu ke gauraye a jikinsa,manyan masarautun da asalin tarihinsu aka kafashi da JARUMTA RASHIN TSORO DA KUMA ZALLAR HIKIMA. "Ranka ya dade......al'amari irin wannan ba qarami bane....." "Na sani muhammad" Sultane ya tari numfashin haisam din yana jin wata qanqanuwar fargaba tana saukar masa. "Aure ba kyautatawa bace kawai.....yana dauke da haqqoqi da nauye nauye masu yawan gaske....." "Wannan dalilin ya sanya nazo gareka" Ya sake fadi haisam yana sauke maganansa. Idanunsa ya maida ya lumshe a hankali,yana jin wani abu yana ratsa sassan jikinsa. Wani baqon yanayi dake qulle da cakudewar tunani. Shuru ya sake wanzuwa me dan tsaho,har sai da kowannensu yayi tsammanin d'an uwansa ya sauka daga kan layi,kafin muryar haisam me zurfin nan ta sake motsawa. "Bazan iya amsawa da komai ba a daren nan.....bazan iya cewa komai ba ranka ya dade" Murmushi me dan sauti sultane ya saki. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 76* *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX "Ba da qaramar magana nazo maka ba muhammad da zan zaci ko sanya ran samun amsarka a yanzu yanzu ba......ka dauki dukka lokacin da yayi maka kayi tunani a kai.....amma ina roqarka alfarma kada ya zarta kwanaki uku,saboda ina dab da barin madeena.......nayi magana da muhammad dawud.....na kuma buqaci yayi magana da ahalinka akan batun,saidai kasan ko yaushe namiji baya buya a bayan wani namijin....shi yasa na yanke nayi magana dakai kai tsaye kaima,kada ka damu muhammad.....idan har amsarka itace A'AH.....idan har amsarka itace BAZAN IYA AUREN AKHNAN ba,kada kaji komai,kada kuma kaji wani nauyi,ka shaidamin kanka tsaye,zan fahimceka muhammad,zan kuma amsheta da girmamawa da mutuntawa,hakan kuma bazai canza komai a tsakaninmu ba......idan kuma har ka amsa min da ZAN KARBI AUREN DIYARKA.....ZAN KARBI AKHNAN a mazaunin MATA.......amsar zata zamemin mafi kyawun kalma dana taba ji a kunnuwana.......zan samu nutsuwa da aminci koda a yau na fadi na mutu,saboda na kubutar da wani tsagin ruhi.....wani bangare na gangar jiki da rayuwar SAFEENA zuwa ga wani amintaccen hannu.....zan baka akhnan wadda ba zata kasance MATA kawai a tare dakai ba.....aah na tabbatar zakaci gaba da kallonta a matsayin MARAINIYA wadda ke rayuwa qarqashin alfarmarka.....sannan ba zaka gushe ba zaka kalleta da sunan DIYAR SULTANE". Inda a sannan za'a auna nauyin maganganun sultane a mizanin awo a sannan haisam yasan zasu rinjayi komai da za'a azasu a kai. Sun kammala waya da sultane amma maganganunsa sun masa wani tsaiwar mashi saman zuciyarsa,sun hadu sun cakude da maganganun morsa safiyya da duk motsin da zaiyi sai ya dinga jin kamar maganace kai tsaye data fita daga bakin nanay dinsa. Yana takawa zuwa sassansa amma jikinsa yayi wani irin mutuwa. Yayi imani da qaddara a rayuwar dan adam gaba daya.....amma a yanzun ya samu kansa da tambayar kansa da kansa AKWAI QADDARAR DATA SHIGO DASHI AGADEZ?. Daga can qasan zuciyarsa ake amsa masa da EH.....amma yana qoqarin ture wannan. Sassan nasa ba wani motsin da zai dameshi,don daga hadimai masu kula da buqatunsa da sassan nasa,sai kuma abdii daya baro a dakinsa a qasa. Duk da ya jima bai budr balcony din bedroom dinsa ba tun a wancan ranar na qarshe daya gama fahimta cewa gurin tsaiwarta ne,kuma suna maqwafataka ta kusa da kusa da balcony din nasu,bai sake buda gurin ba bare ya shiga. Ya taka a hankali yana qarasawa gaban qarfen balcony din,ya aza hannunsa saman qarfen a nutse,sai yaji ya sauka saman lallausan wani abu,abinda ya sanyashi sauke dubansa kenan akai. Mayafinta ne na wancan ranar,bai kwance ba har yanxu yana daure a jiki kamar yadda ya daure shi,ya manta dashi kwata kwata a gurin,sai ya janye hannunsa a hankali gefe,abinda ya faru a ranar yana dawo masa. Me yasa qaddara takeson tursasasu bisa dole,me yasa qaddara ta dage saita hada tarayyarsa da tata guri daya?. Bayan akwai nisan tazara me yawa tsakaninsu. Ya santa sanin da ita kanta bata taba tunani ba,yayi zuzzurfan bincike game da dabi'unta abinda baisan dalilin daya kaishi ga aikata haka ba. Baiga wata dabi'a tata guda daya data masa ba banda ciyarwar JUMA'A data wajabtawa kanta. Ta kowacce fuska dabi'arta bame kyau bace,dabi'arta bata siffantu da kalar dabi'ar macen da za'a kwadaitu ga aurenta bane. Idan yace zai dorata bisa mizanin dacewa da cancanta.....ko daya bata isa ta tsaya a gurbin da nagartar dabi'un Menelik ba ballantana akai ga saamee. To amma baisan me ya sanya daga Menelik har saamee din suka kasa samun gurbin da ya kamata ace sun samu daga gareshi ba. _"zuciyarka nason kayi yaqi wajen nema da samun soyayya ne.....bawai ka samu soyayya a bagas har zuwa inda kake a zaune ba"_ wasu daga cikin maganganun maleek suka dawo kanshi. Kai ya girgiza a hankali,koda haka ne.....amma yana buqatar neman soyayyar a gurin da GIRMA da GIRMAMAWA suke aiki.....ba gurin da wasu dabi'u suke taka rawarsu ba da salon mummunar rawa da ba girmamawa sam a cikin ta. *AKHNAN* A daren batasan me takeji ba,tsakanin duniya da lahira batasan inane zaifi mata dadi da sauqin rayuwa ba. Saqon data samu na kaitsaye daga gurin SULTANE kan cewa kada ta kuskura ta fita daga masarauta shine abinda yafi komai gigitata. Batasan daga inda yaji batun ba,duk da kusan dukka hadiman sassanta sun sani cewa tana shirin komawa Niamey ne,to amma kuma ba wanda yake da access da sultane da har zai shaida masa hakan. Mammina bata sani ba,bata ma saurareta sunyi magana ba ballantana ta gaya mata,koda mammina din taji bata tunanin zata gayawa sultane wata magana a kanta da zata sanyata tunzura. Morsa safiyya ce tazo ranta,idan ita keda alhakin gaya masa ya akayi tasan da tafiyar?. Wadannan tunani da bacin ran daya hade mata guri daya ya sanya takejin zuciyarta da kanta kamar zai fashe. Ta yiwa sultane abinda takeso a tunanin ta,ta daura aure,auren kuma baije ko ina ba.......wanda hakan tana kallonsa a matsayin nasu laifin. Tayi iya nata qoqarin na cika musu burinsu,don me yasa ita din ba za'a qyaleta ta koma rayuwarta ta baya ba?. Ko meye ya faru BATA DA LAIFI ba ita keda alhakin faruwar komai ba. Ta nuna musu illar sanyo rayuwar wani d'a namiji cikin rayuwarta,amma sun gaza fahimta,in da ace sun barta da tsarin ta,tunanin ta dama rayuwarta,da tuni yanzu wannan abun daya faru da ita bai faru ba. Ganin kamar kwanyarta zata buga ya sanyata zura baby hijab baqi saman kanta bayan ta daure gashinta a tsakiyar kanta,wannan ya bawa wannan fuskar me dauke da wani irin kwantaccen kyau daman fitowa das tsakiyar fuskar hijab din,fuskar data wani fada,tayi fayau da ita,ta sanya flip flops baqaqe a qafarta,ta sauko daga saman gadon tana nufar qofar balcony dinta. A jikinsa yaji an bude qofar,abinda ya sanyashi daga manyan idanunsa a hankali yana maidasu qofar data raba nata balcony din da bedroom dinta. Kyakkyawar farar fuskarta ta bayyana tsakiyar baqin hijabin saqar qasar Malaysia. Kan qafafunta ya maida dubansa,tana takowa zuwa tsakiyar balcony din da wannan takun nata. Wani irin taku daya fita daban,yana gauraye da tashen quruciya gata izza da kuma mulki. Mamaki kadan ya kamashi,yadda take tafiya da raina ciki jama'a,haka still takunta dai yake a sanda ta kebe ita daya cikin duhun dare CHARACTER ce kenan,ba izza bace.....ba kuma wani salo bane na jin kai. A nutse ya dinga tafiya da idanunsa jikin cotton sleep wear din jikinta fari qal. Kaman wani character dinta ne yawan amfani da abubuwa masu hasken kala da dare irin haka. Tsaf idanunsa suka tsaya saman baby face dinta,almond eyes dinta sun qara girma kadan,abinda ya sanya blue eyes dinta fita sosai. Idanunsa ya lumshe a hankali yana qoqarin janye kallonsa daga kan fuskarta,saidai kuma maimakon hakan ta faru,sai idanun nasa suka sauka kan dan qaramin bakinta dake dauke da wani nau'in siraran lips marasa kauri. A tsuke bakinta yake guri guda,abinda ya sanyashi tunawa sa noorah.. Hanya guda daya da kake gane ran noorah ya baci,zata tsuke lips dinta ne,sannan ta samu guri kawai ta zauna tana tara ruwan hawaye. A yanzun koda bai san mood dinta ba,amma tsaf ya karanci itama irin noorah dince. Akwai alamun bacin rai sosai tattare da ita,kamannin safeena kuma suna bayyana sosai saman fuskarta. Takun data qara yi tana zama saman ottoman ya sanyashi zare idanunsa da wani mugun qarfi yana jin zuciyarsa tana wani irin bugawa. Zaman da tayi ya fidda shatin cinyoyinta ya kuma fidda shape din cinyoyin sosai,abinda ya sanya shape dinta ya bayyana. Ya sauke idanunsa a nutse yana qoqarin saita tunaninsa gami da tuhumar kansa daya gaza kame ganinsa kamar yadda musulunci ya tanada. Wayarsa tayi burari,sasaanyan ringing din maras hanayaniya daya saci kunnuwan akhnan,ya sanya hannu ya fidda wayartasa yana duban me kiran,daidai sanda ita kuma take aje dubanta a kansa. Wani abu ya matse mata qirjinta. Me yasa duk sanda take cikin yanayi irin wannan.....yanayin baqinciki da bacin rai shi kuma a sannan yake bayyana a gabanta?. Me yasa sai sanda ranta yake a bace sannan take ganinsa?,wannan alama ce bame kyau ba.....alama ce dake nuni da rashin alkhairin dake tattare dashi. Kiran bobbo muhammad dawud ne,baya jin zai iya daga kiran bobbo din a yau,yana buqatar nutsuwa,yana buqatar dogon nazari,yana buqatar ya yanke hukuncin daya gamsu dashi,hukuncin da bazai taba rayuwarsa ko aikinsa ba. Zai iya aminta yayima sultane kowanne irin taimako.....zai iya aminta ya soma dora sultane akan hanyar da zata masa jagora ya fahimci tarin baragurbin daya bawa muhalli cikin gidansa......amma ba lallai bane ya sanya kansa a matsala ba. Don haka ya maida wayarsa a aljihu,ya juya kuma a nutse yana komawa ciki abunsa ba tare daya yarda ya kalli koda sashen da take zaune ba. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Wani mugun tsaki taja,a jikinta takejin yasan ta shigo gurin,a jikinta takejin yasan tana gurin,tsabar izza ce kawai......da zallar rainin wayo. Yadda yake bagarar da dubanta idan tana guri wani abune da yake mata ciwo gami da bata haushi,mutum ce da batason kallo.....amma batasan me yasa abinda yakeyi idan ya ganta din yake qona ranta ba,duk da haka tafiso,bata qaunar ta daga idanu ta samu idanun namiji qur a kanta,amma nasa kauda idanun haushi yake bata,tana ji a ranta yana yin hakanne kawai don ya nunawa duniya itadin tozartacciya ce.....yana yine kawai don ya iyakance matsayinta da isarta,tunda ta sani,duk yadda takai gason a dinga qauracewa hada idanu da ita wannan abun yana yiwa maza da yawa wahala. Tana da wani irin kyau me sanyi da fusgar hankali qwarai. Idanunta ta maida ta lumshe,tana shaqar wannan qamshin nasa. Duk yadda take avoiding qamshin,duk yadda ta jima tana gayawa kanta da koyawa ruhinta yadda zai qyamaci qamshin amma abun yaci tura,sannu a hankali saita tsinci kanta ba wani scent dake mata dadin shaqa irinsa,idan kuma ta jishin sai taji dukka sauran turarukanta basuyi mata ba. Qarar shigowar saqo wayarta ya sanyata bude idanu. Daga fareeda ce daya daga cikin ma'aikatanta take shaida mata cewa sun samo kamfanin dake fidda wannan turaren,kuma sun tura musu saqon buqatar irin qamshin,da kuma fadin dukka adadin da suke buqata daga garesu,saidai branch dinsu na asali yana Ethiopia,akwai kuma biki bude sabon babban branch a dubai da india. Saqon ya mata dadi,musamman daya iso a daidai sanda ya dace,ta maida fareeda amsa,tana shirin ajiye wayar saqon aisa ya fado cikin harshen faransanci kamar yadda suka saba _"Komai yana sake dagulewa a sahel couture,zuwa kowanne lokaci komai yana dab da durqushewa akhnan,bansan ya zamu shawo kan matsalar ba,kin kuma sake dage dawowarki bisa umarnin sultane,zanyi dukkan iyawata,amma nan da kwana goma dole na dawo agadez Festival de l’Aïr saura 'yan kwanaki"_. Ajiyar zuciya ta sauke,hankalinta a yanzu dukka ya tattara kan sahel couture,warning signs da aisa da shehnaz suke bata akan company din yayi yawa,batasan me yake faruwa har haka ba,batasan wanne irin matsala ce haka take ta qwaqular kamfanin ba. _"Ina bakin qoqarina aisa,komai zai daidaita in sha Allah"_ abinda ta maidawa aisa kenan,don batasan wanne bayani zata mata ba. Sultane ya kamata ya fara fahimtar matsalar,shi ya kamata ya fara fahimtar akwai buqatar komawarta kan dukiyarka,kan kamfanin ta,amma a yanzun ko giyar wake tasha ta sani ba ita ba tunkarar sultane da kowacce magana. Qasan ranta taji zuciyarta tana baci,inda ta iya zagi ko mummunar magana ko fata,tabbas data aikesu ga duk wadanda suka shiga cikin wannan qaunar da soyayyar da fahimtar junan dake tsakaninta da mahaifinta na tsahon shekarun da tayi a raye,tu daga sanda aka haifeta zuwa yanzu. Calendar ta shiga sanda ta tuna da Festival de l’Aïr. Wani bikin al'ada guda daya da cikin bukukuwan al'adunsu na buzaye da take matuqar so take kuma ji dashi. Biki ne da bata taba bari ya wuceta ba,saboda yadda yake bata nishadi sosai,yake kuma bata daman yin rayuwa cikin qawaye,rayuwa me 'yanci dake mantar da ita wacece ita. Amma wannan yanayin da aka jefata a ciki ya sanya ta manta da lissafin kwanaki?. Kai ta juya a hankali,koda sultane ma ya bata daman komawa Niamey,zataje ta dawo,don ba abinda zai sanya ta bari tayi missing wannan festival din. ★★★A makare ya tashi washegari,wannan ya sanya bashi ya zauna breakfast ba sai kusan sha biyu na rana. Breakfast dinsa ba wani me zafi bane tunda yazo agadez,sam ya kasa sabawa da salon tsarin abincinsu,komai baqo ne a harshensa,ya riga ya saba da abinci irin na qabilae oromo. A abu daya nasu yake sakin jiki sosai yasha shine shayinsu da yake dan kamanceceniya da al'adun qabilar oromo. Nutsuwa ta kama komai nasa,don haka a komai nasa sai kaga nutsuwar ta bayyana kanta da da kanta. Kamar yanzu da yake zaune yana breakfast din,kansa da jikinsa dukka sun masa nauyi saboda rashin samun isashen bacci a daren jiya. Daya daga cikin hadiman sassansa ne ya shigo,ya kuma zube kaman yadda al'adarsu ta sabar musu. Ba kasafai yake hanasu ba duk da bayaso,yana kiyayewa a komai kada yayi abinda ya saba da al'adarsu da har zai sanya a fahimci wani baqon abu tattare dashi ko yabar zargi kokwanto ko ayar tambaya a kansa. "Giwa ce take sake sanarmaka da buqatar ganinka da gaggawa" zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 77* *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX A nutse ya ajiye mug din hannunsa,don dama ya gama breakfast dinsa,ita gejin cikinsa kenan. Maganan zuwansa da ya amsa a jiyan yana sane dashi,kuma koda bata aiko ba tunda ya amsa zaije din zaije. Inda baiyi niyyan zuwa ba,baiga dalilin da zai sanyashi ya amsa mata ba. "Ta dakaci zuwana daga yanzu zuwa kowanne lokaci". Ya amsa masa yana jawo wayarsa dake gefe. Mutum ne shi ma'abocin son cika alqawari,kyautatawa da kyakkyawar mu'amala tsakaninsa da duk wanda yake rayuwa a qarqashinsa. Ballantana nanay dinsa,da niyyar kiran saamee ya tashi,ya kuma gamsu da ya kirata din saboda farantawa nanay rai,da kuma samar da relief ga Yarinyar. Duk da ta bangarensa baya duban hakan a matsayin maslaha sam.....baya son abinda zai sanya ta sake aza ranta ga komai daya shafeshi. *SAAMEE* A hankali ta waiwaya tana duban wayarta dake ajiye saman abun sallar da take kai daga gefanta. Idanunta ta ware sosai,zuciyarta tana wani irin bugawa da ganin sunan dake harbawa a fuskar wayartata. "Captain obbo" Ta karanta sunan a fili tana jin yadda zuciyarta ke bugawa b'al b'al kamar zata huda qirjinta. Wani yanayi ne daban.....wani abune na daban me matuqar shammata da bata taba zaton faruwarsa ba. Ko ina na jikinta rawa yakeyi,ta daga wayar ta karata a kunnenta. Sallama tayi masa,irin sallamar dake bayyana yadda muryarta ke sake raunana da wani irin rawa na zallar kwarjinin da yake mata. "Barka da warhaka Obboleettii" Ta fada a sanyaye bayan ya amsa sallamartata. "Barkanki sameera.....ya jikin naki?" Sai data lumshe idanunta a hankali,dadin muryarsa yana ratsata. Wani irin amo mejan hankali daya saukar mata da wata irin nutsuwa,har batasan ta saki siririyar ajiyar zuciya ba. "Alhamdulillah obbo....da sauqi". "Ma sha Allah" Ya fadi sannan shuru na wasu sakanni ya biyo baya kafin ya dora. "A rayuwar dan adam gaba daya lafiya itace gaba da komai....yana da kyau ki sanya lafiyarki gaba da kowa da kuma komai.....ki zabi kanki kafin komai da kowa......sannan ki kusanta kanki fiye da baya da karatun qur'ani,domin da ambaton Allah kadai zukata suke samun nutsuwa". "Na gode obbo" Ta fadi da wani irin sanyi,tana jin dadi yana sauka mata a ranta. Ba'a banza zuciyarta take nacewa da soyayyarsa ba,ba'a banza takejin ta kowanne taqi na rayuwarta yayi mata ba,ba'a banza takejin da ita kadai ya dace ba. Miji take nema dan gaske me kamala koda shigen tasa ce.....mijin da zai kama hannunta ya kusantata zuwa ga Allah da kuma dokokin Allah,sai akayi sa'a idanunta suka sauka a kanshi. Duk kuwa da cewa zuciyarta tasha gargadarta akan cewa haisam din ya mata NISA.....ya mata TAZARA ya d'ara ajinta. Tana jin kamar ba zata sameshi ba......tanajin ita din sam ba ajinsa bace,to amma kuma ta rasa ta yadda zata fara tanqwara zuciyarta ta cire hakan daga ranta. "Ki kula da nutsuwar ruhinki,abinci sannan magani". Ya furta cikin yanayin kulawar daya sanya murmushi qwace mata. "In sha Allah obbo,na gode" Da godiyar tata da bataji abinda ya fadi ba kiran nasa ya tsinke,tana jin kamar ta tambayeshi yaushe zai dawo?,yaushe zata ganshi?. Rungume wayar tayi a qirji tana lumshe idanunta. Wani irin murmushi ne kawai yake fita saman fuskarta. A iya maganganunsa na yanzun takejin basai ta sake shan wani magani ba kuma a yau din. Bata zata ba ta tsinci muryar nanay saman kanta. "Ikon Allah......bacci kike ko idanunki biyu?" Nanay ta tambayeta tana ci gaba da leqa fuskarta dake shimfide da wani kalar murmushi. Da sauri ta miqe ta zauna tana sunkuyar da kanta. "Idona biyu nanay,sallah na gama yi". Kallo Nanay tabi hannunta dashi,sai ta ganta damqe da wayarta,murmushi ya subuce mata. Da alama sirrin walwalarta haisam ne,taji hakan a jikinta,don ta tabbatar haisam din bazai tsallake alfarmar data nema ba dama. "Shikenan yi kwanciyarki,zamu fita gidan marayu ne,nace bari na leqo naga jikinki" "Saikin dawo nanay,Allah ya bada sa'a,na gode sosai" Ta fadi still tana kasa hada idanu da ita,itama saita juya ta fice ranta yana mata dadi ganin karon farko yanayin saamee din yana daidaita. *HAISAM* Samansa kawai ya koma,ya kuma wuce bathroom yana fidda kayan jikinsa. Faffada kuma lallausan towel ya daura a qugunsa,abinda ya bawa lafiyayyar qirar jikin nan nasa dama fitowa sosai. Faffadan qirji me dauke da mayalwatan kafadu......muscles da suka cika dantsensa wadanda yawan daga qarfe ya sanya suka zauna masa sosai. Tun daga saman cikinsa har zuwa qirjinsa lallausan gashi ne baqi sidik da ya yiwa fatar jikinsa qawanya,hakanan gwiwar hannunsa har zuwa tsintsiyar hannunza,kaman yadda cinyoyinsa har zuwa idanun sahunsa sassalkar gargasa ce dake qara nuna ainihin qirar cikakken lafiyayyen namiji. Bai wani damu da adadin lokutan daya dauka ba,ya shirya fes cikin daya daga cikin throbe din da wani company daga qasar oman. Silk ce irin silk dinnan me asalin tsada da daukan idanu,sai ya daura amam a kansa da wani irin yanayi me birgewa,irin salon nadin matasan qasar saudiyya. Kusan deal ne tsakaninsa da fitattun kamfanonin throbe(jallabiyya) dake qasashen sudan,oman,saudiyya,dubai,Morocco,qatar,Kuwait. Duk bayan watannin da sukan fidda sabbin design na throbe na maza shine mutum na farko a Ethiopia gaba daya dake fara sanya new arrivals na throbe dinsu. Kusan duk wani malami ko diyan sarauta dake ji da kansa cikin Ethiopia da zagayenta yana kwaikwayo ne da sheikh muhammad haisam aba jifar. Yana da wani irin salo na iya ado tamkar dawisu,adon da har a yanzu a agadez bai canza ba. Dressing dinsa a koda yaushe unique ne,cikin wani irin yanayi da idanu basu saba ganinsa ba. Ya zamewa yaran sarakuna da yawa a Ethiopia role model,wajen qurewa ado gudu ba'a kaishi ba. Tun daga kan cloak thobe.....jubahs da fitattaun kurta pyjamas a gurinsa ake fara ganin sample. Hakan kuma ya zame masa jiki. Tun yana da shekara goma a duniya ya zama DAN SARKI DA YASHA BANBAM DA SAURAN YARAN SARAKUNA.....kuma har yanzun da yake kan ganiyar samartakarsa ba abinda ya canza,saima sake daukan hankulan 'ya'yan manya dana malamai da yake sakeyi cikin qasar tasa. Qamshin nan dai nasa da shi kadai ya mallakeshi ke tashi a jikinsa,ya zura wasu budaddun takalma masu wani irin aji a zubi da tsarinsu. Yana saukowa daga sama idanun omar a kansa,suka hada ido sai ya janye dubansa yana duban maleek da ya miqe qafafunsa saman center table na glass yana aiki cikin system dinsa. "Nidai kawai jikina yake bani akwai abubuwa da yawa da ake binnewa.....jiya bobbo dawud ya kirani yace komin dare na hadaka dashi......amma koda nazo tun daga babbar qofar shigowa sabuwar dokarka cikin masarautar nan ta hanani daman shigowa" Duk da ba haka yaso ba,amma yaji dadin jin hakan,hakan yana nuna masa da gaske ana tafi da dokar yadda ta dace kenan kamar yadda ya shimfida. Sai daya gama saukowa gaba daya sannan maleek ya dauke idanunsa daga kan system din ya maida kan haisam sanda ya dauki dabino bakwai cikin wanda ke zube a wani qawataccen gold plate dake ajiye a gurin. "Sai ina?" Maleek ya tambaya kai tsaye,don yanason ya zauna suyi magana da haisam akan falaak. Abinda yakeji tattare da ita ya girmeshi,yana jin kamar kwanakin da motii ya dauka be dawo ba suna da nisan gaske. "Zanje.....zaituna nason ganina" Haisam ya fadi yana cire qwallon dabinon daya dauka din. Sosai omar ya koma ya zauna yana duban haisam. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Kiranka kuma?,to ko nazo muje?" Sosai maganan ta bashi dariya,amma sai ya saki murmushi sanda yake jefa dabinon bakinsa yana taunashi a hankali. Ya yadda qwarai da gaske garin suna da albarkar dabino suma kamar qasarsu,a wasu abubuwan hana hangen kamanceceniya kadan kadan. "Ka rakani?,saboda me?" "Saboda tsaro mana haisam" Omar ya furta da dukkan gaskiyarsa. Murmushi ya kuma saki,sannan ya fara takawa a hankali da alama yana nufar hanyar fita ne. "Shi zaki koda ba'a cikin gandun dajinsa ba ya tsinci kansa yana yin farautarss ne yadda yaga dama,duk wani kira.....duk wani kebewa,duk wani magana da zata nemi tayi dani yana zamantowa kaman qarin dama ce a tare dani,qarin daman da zan samu na buda mata hanyar da zata dilmiya kanta da kanta" Ya qarasa maganar a huce kuma hankali kwance. "Amma ko connection ya kamata ka hada dani" "Babu buqata.....saina dawo" Ya fadi yana saka qafafunsa waje. Ajiyar zuciya maleek ya sauke,ya kuma maida dubansa ga omar da har yanzu yabar bakinsa a sake. "Duk inda kake ajiye haisam ya wuce nan gurin.....ya wuce hasashena da naka,hakanan ya zarta tunaninmu,duk wani motsi da taku da zaiyi lissafinsa daban yake da namu.....yanayin jarumtarsa yana bani tsoro a wasu lokuta. Baisan tsoro ba....baissn fargaba ba,baya banbamce guri me hadari da akasin hakan a duk sanda ya sanya gabansa gaba a kan aikinsa.....yana da yaqini cikakke ga mahaliccinsa......zai dawo omar.....zai dawo lafiya ina da yaqini da hakan.....addu'a ta ratsashi fiye da zatonmu da kallon da muke masa,a kwanakin nan ni kaina nasan da haka,shi yasa baya shakkar kowa da komai,baya kuma shakkar tunkarar komai din" Sosai omar ke jinjina kansa,yana kuma sake gamsuwa dari bisa dari da maganganun maleek. *MAMMINA* Wannan karon kuma a wannan lokacin da kanta take takawa zuwa bakin iyakar gurin,cikin salo na kai kawo tare da tarin tsammanin jiran isowar haisam din. Har wani zabalbala takeji jininta yana yi idan ta tuna cewa yau itace ke maimaita kiran wani d'ana adam dake rayuwa cikin masarautar agadez qarqashin alfarmarta?,bayan yayi watsi da kiran kuma har sai ya zabi lokacin zuwa?. Ranta yana son ya cimma qololuwar baci,amma kuma tana danne hakan daga ranta,don a yanzu ba fusata ko tursasawa take buqata suyi mata aiki ba. Kwantar da kai,maida komai ba'a bakin komai ba da kuma nuna masa zallar karamci da tarin abun duniyar da zai iya rabauta dashi,su kadai ne makaman da tafi buqata a yanzu. Tana juya baya tana komawa ciki a karo na barkatai taji sallamar tafisu. Saita waiwayo da wani irin yanayi tana dubanta. Dubanta itama tafisu takeyi,cikin girmamawa take dubanta. "Ki dade kiyi qarko,Allah ya baki yawan rai.....mene yake faruwa haka ne?". Wani bacin rai ya tasowa mammina,ta kasa amsawa tafisu har sai data samu guri ta zauna. "Nida wancan wulaqaccen malamin mara asali ballantana tushe.....mutumin da har yau jiya zuwa yau dana shirya zama dashi an kasa ganomin danginsa ko daya na kusa ko na nesa.....sai almajiransa mutum uku da yake tare dasu,don na ukunma baiyi cikakken sati biyu cikin masarautar nan ba" Mammina tayi furucin tsananin fushi yana nunawa kan fuskarta. "Ki kwantar da hankalinki ranki ya dade.....iname tabbaci da yaqinin komai zai tafi yadda akeso,kinsan abu me qarko bai fiya zuwa da sauqi ba......yanzu haka tamim ne ya tasomin,ya kusa isa diffa amma ya juyo,yace yana buqatar ganinki da gaggawa". Kai ta jinjina a nutse,don hankalinta a yanzu ba'a kan tamim yake ba. Hankalinta yafi karkata ga yadda zata tsara auren haisam da akhnan,tayi imani shi daya ne zata juya yadda takeso cikin sauqi tayi amfani kuma da wannan damar ta bata tsakaninsa da sultane,ta nesanta tsakaninsa dashi har abada. "Wannan mutumin tafisu.....har yanzu na kasa samun gamsuwa da aurensa da akhnan" Murmushi tafisu ta saki tana waiwaya kadan,sai itama idanunta ya sauka inda mammina ta kafe da kallo. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 78* Haisam ne yake takowa a nutse,shi daya da wani irin haiba kwarjini da kamala. "Zaki ruftashi ne ramin rubutaccen alqawari da yarjejeniyar da bazai iya tsallake mata ba.....zaki daureshi da sasarin da bazai iya kunceshi ba dole saiya amince miki. Yasan girman alqawari,yana tattalin mutuncinsa da kimarsa,ko don gudun sarayar mutuncinsa da tsare tsaren da muka tanada zamu masa barazana dasu zai saketa salin alin". Kai mammina ke jinjinawa,maganganun tafisu kuma suna bata wani qwarin gwiwa na musamman. Cikakkiyar sallama yayi yana takowa cikin nutsuwa,sai mammina din ta miqe cikin yanayi na girmamawa. Fuskarta dauke da wani kwantaccen murmushi take fadin "Lale maraba da zuwan amintaccen sultane......ga gurin zama" Ta fadi tana nuna masa kujerar dake fuskantarta. A nutse ya zube idanunsa ga kujerar,ya taka a hankali yana komawa bayan kujerar ya jawo wata can daban da bata cikin jerin jadawalin tsarin ya ajjiyeta a daidai inda yakejin ya gamsu dashi. Wani boyayyen murmushi ta saki,a hankali ta maida idanunta kan fuskar tafisu. Cikin harshen afaan oromo,cikin yaren daya zame mata garkuwa,yaren da bata yarda ta yarashi sam a gabab mutane,saidai a kebantaccen guri irin wannan tace. "Ko don na karya izzarsa....ko don na nuna masa shi din ba kowan kowa bane.....tabbas sai nayi amfani dashi......na rusa sultane na kuma rusa ragowar rayuwar AKHNAN,lokuta kadan ya rage,zai zamemin makami ba tare da shi kansa yasan da hakan ba" A wani irin jere maganganun suka shiga kunnen haisam wanda ya sanyo qafafunsa dab da gurin. Ya kamata ace yayi mamaki matuqa ko ya girgiza da jin futar furucin daga bakin ta,amma sai baiji komai ba. Mamakin daya mamayeshi kadai shine yadda yaren oromo daya dade da sanin tana jinsa a yau yake fita saman harshenta radau. Cikin rashin sani ta aza idanunta akan haisam tana me sakin fuska,sannan ta maida dubanta ga tafisu saboda tanaso ta sallameta kafin su zauna da haisam din. "Tabani tamkar taba masarautar agadez ne tafisu,yayi ganganci daya aikata haka,don baisan yadda makomarsa zata kasance mafi muni ba.....baisan cewa ni zaituna bazan tabu ba.....ta kowacce fuska biyayya a gareni ne kawai zaman lafiyan kowa.......zan tilastashi ya karbi aurenta koda ya nuna wannan girman kan da kuma izzar da dagawar.....a shirye nake na sanya a batar da kafatanin ahalinsa muddin mazauna qasar nan ne da kewayenta" "Kin dade da makara zaituna zeenatu" Haisam ya furta can qasan ranshi,saidai ko daya ba wata alama da zata baka cewa wai yana fahimtar yaren oromo gaba daya. A yau yaga amfanin adana yare da gasken gaske......a yau kuma da mammina ke sake fardewa cikinta wuqa zayaso ace NAMIJI ce ita. Zayaso wannan wasan......wannan yaqin......wannan farautar dan uwansa namiji ne a cikinta,saidai koma meye yayi imanin kawai BOYAYYUN MAZAJE cikin duk wani shirinta......wanda suma a kowanne mataki yake da lissafinsu da kuma alwashin birkitosu cikin da'irarsa. Hakanan tafisu takejin maganar kamar tayi nauyi da yawa. Duk da cewa bayajin yaren amma wanda ake shirya komai a kansa?,kuma don saboda shi yana tsaye a gurin?. "Maleeka......kibi a hankali kada ya fahimci wani abu" Murmushi ta saki me cike da izgili,sannan ta maida dubanta ga haisam dake takowa saman shimfidadden lallausan kilishin da aka qawata gurin dashi,ta saki masa murmushi cikin nuna alamun girmamawa. "Qaraso sheikh,bismillah". Kai ya jinjina a hankali,yana sake riqe kansa da kyau gami da hanawa kansa nuna wani alama dazai bayyana shi din jinin OROMIA ne. Maida kallonta tayi kan tafisu da wani salon kallon izza da isa. "Ba wani alama tattare dashi dake nuna yasan yaren oromo.......oromia basa buya.....basa iya boye yarensu,yanayi da zubinsu da al'adunsu basa canzawa da wuri,ko ke kin manta yadda dukkanin ayarinku akasha wahala daku kafin ku saje ku koma ABZINAWA?" Murmushi tafisu tayi tana jinjina kai. "Anyi haka maleeka". Sai itama mammina din ta jinjina nata kan "Iya wannan ya isa amsa tafisu,kina iya tafiya,kafin mu kammala din naga tamim" "A kammala lafiya" Ta fadi ta yunqura tana miqewa. Saida tafisu ta kammala fita gaba daya sannan ta tattara hankalinta akan haisam,haisam din dake riqe da wayarsa yana sarrafata hankali kwance,saidai kunnuwansa da kwanyarsa suna bibiye da kowanne lafazi da zai fita a bakin mammina din. "Ina neman afuwa sheikh......duk da tarin uzurori da nauyin masarauta dake kanka amma na matsanta game da batun neman haduwarmu dakai" Ta fada cikin kwantar dakai sosai,nuna karaya da tausasawa. Sai a sannan ya daga kanshi daga wayar,bai kuma kalleta kai tsaye ba saida ya yiwa wayarsa ma'ajiya sannan ya zube dukkanin idanunsa a kanta yana soke yatsun hannunsa cikin na juna. Wani irin magnet ya fusgeta da kyau,wasu kamanni suka gilma daga tsakiyar qwayar idanunsa cikin nata,sai tayi saurin janye qwayar idanunta a nashi can qasan ranta kuma tana tambayar kanta "MENENE WANNAN?" Maganarsa ta kawar da tunaninta. "Ba damuwa ranki ya dade". Har tsakiyar kanta taji kiranta da yayi ranki ya dade din bai zauna mata ba,don yau din a wannan lokacin kuma shine karo na farko data fara jin kalmar a bakinta. "Aiki ne me muhimmanci a gabanki ZEENATU... Meye tattare da matashin malamin da zai firgitaki har haka?!!!" Wata zuciyar ta tsawatar mata,abinda ya sanya ta sake maida dubanta kansa a karo na biyu,saidai wannan karon ta kaucewa duban tsakiyar qwayar idanunsa kamar dazu,shima kuma ya karanci hakan. "Na gode" Ta fada da murmushin nan. "Bismillah.... Ga kayan sha da naci" Ta fadi tana nuna gaban shimfidarsa inda aka shirya komai. Sai daya dubi dukka tulin kayan da bai amince da koda cup daya dake gurin ba ballantana su kansu tarkacen cimar da aka cika gurin da ita,tamkar wanda aka gayyata wani party sannan ya maida dubansa a kanta. "Godiya nake" Kawai ya furta a nutse. Ko a rayuwarsu ta yau da kullum,a tsarin aikinsu na security ba'a kowanne guri suke amincewa da kowa ba,kaman yadda ba'a hannun kowa suke amsar abu suci ba. Koda a office dinsu dake hukumar tsaro ta farin kaya masu girkinsu amintattu ne,musamman irinsa da suka zama manya. Uwa uba ma kuma shi din yana da bala'in tsantsami,ba kowacce mace ke masa girki yaci ba,wannan ya sanya Aanani ke yawan gulmarsa a bayan idanunsa. "Captain din tsirfa......captain obbo inda macene nanay mun shiga uku" Bakinta baya gajiya da fadin hakan,musamman duk sanda zata tarara da nanay da shekarunta da komai.....duk da tarin hadimai dake gudanar da komai na gidan amma zaka sameta a kitchen a tsaye akan abincin Muhammad haisam din. Randa ta karkace tanaga gulmarsa,sam batasan yana qofan kitchen din ba,ya shigo gaida nanay dinsa ba,saida saamee ta tabata suman zaune tayi,baice mata qala ba ya qarasa shigowa kitchen din,ta samu ta sulale,sai data debi sati guda cur bata bari sun hadu ba,duk da sau tari shirunsa tasan wani punishment ne me zaman kansa,ta samu da qyar dai tasha zancan yabi ruwa,sai bayan wani lokaci ya tarfata. Bata da hanyar goge kanta,sai kawai ta fashe masa da kukan da tasan ya tsana,tattarata yayi yace ta bace masa da gani. "Akwai muhimmiyar magana da nakeso muyi dakai.....wani muhimmin abu nake dauke dashi,wanda ba wanda ya cancanci samun wannan abun.... Wannan damar ta musamman face kai" Kai ya gyada a hankali yana ci gaba da dubanta don tabbatar mata yana tare da ita. Zamanta ta gyara sosai,tana kuma sauya yanayin fuskarta zuwa jimami da rashin sukuni. "Ba shakka kai din wani babban mutum ne da ake girmamawa a nan,sunanka tsaftatacce ne......sannan mu'amalarka da jama'a me kyau ce kowa ya shaida hakan...." Saita dakata a hankali sannan ta dora. "Magana ce akan shalelen sultane wato akhnan....." Wani yanayi ne a hankali ya ratsashi,ya kuma sake sanyawa ya tattara hankalinsa. Ba wani magana a bakin matar da zata zama me muhimmanci matuqa a tare dashi,amma kuma dole ta zama wani abu da za'a bawa nutsuwa....duk wani motsi nata.....duk wani fitar furuci daga bakinta ya sani tabbas YANA IYA KASANCEWA WATA SABUWAR RAYUWA.....WANI SABUWAR MASIFA GA RAYUWAR WANI,walau ta ambaci sunansa ko bata ambata ba. "Duk da abubuwa da yawa sun faru,wadanda suka darsa fushin sultane a kanta,suka koma jawo raunin mu'amala a tsakaninsu,amma hakan ba abinda zai canza game da matsayinta a zuciyar sa......sannan kuma babu abinda zai hanashi yaji ciwo,kuma yaji zafi idan wani abu mara kyau yasameta". Still yana ci gaba da saurarenta ne ba tare daya furta komai ko ya motsa ba. "Akhnan ta hadu da jarrabawar rayuwa ita sahihi kuma ingantaccen mijin data zaba....wanda a zahirin gaskiya ba qarya bane ya dace da ita. Suna yiwa junansu wani irin so dani kaina bansan dashi ba sai a yanzu bayan ya saketa kwanaki uku bayan daura aurensu,bisa makircin wasu da har yanzu ban gane su waye ba. Sun bugar dashi sun sanya ya fita hayyacinsa a ranar farko da zasu fara ganin juna,ya kuma yi mata mafi munin saki wato saki har uku" Saita dakata tana wani ajiye numfashi cikin nuna yanayin alhini na gasken gaske. Idanunsa ya lumshe a hankali ya sake budesu a kanta. Yana yabawa da jinjina yadda ta iya tsara wasan kwaikwayo me kyan gaske irin wannan. Yadda ta zama gagarumar me laifi da yadda ta maida qarya ha'inci da zamba cikin aminci ne kawai ke tafasa masa zuciya. Ba abinda yafi tsana kaf rayuwarsa irin qarya,ita kuma ya lura cewa tafi girmama QARYA sama da komai. A yadda take maganan nan banda dashi muhamamd haisam take magana.....mutumin dake kallonta tarrr a tafi hannunsa ba abinda zai hana tausayinta ya kama wanda take maganar dashi,ba abinda zai hana imani ya shiga zuciyar dan adam a kanta,wannan kadai ya sake tabbatar masa ME HADARI CE ita. "Saki sheikh hasaim,wani abune dake barwa mace tabo koda bata da laifin komai yayin sakin......musamman saki irin wannan da aka yoshi a sanda ake ganiyar dokin haduwa da juna,ake kuma tsananin qaunar juna......" "Ina ganin zaifi kyau ki wuce kai tsaye zuwa dalilin kiran" Ya samu kansa da katseta haka kawai yana jin bayanan nata sun fara cika masa kai. Cikin wata irin dabara ta qare masa kallo. Cikin izza yayi mata magana,tamkar dai tana magana da sultane. Ta sake duban yanayin zamansa dake nuna zallar QASAITA irin xaman da ba wani bawa ko hadimi daya taba zuwa gabanta yayi irinsa. Wani abu ta hadiye ta turashi can cikin maqoshinta,sannan ta qwaqulo murmushi ta aza saman fuskarta. "Inaso na samar mata da nutsuwa,inaso na samar mata da daidaito cikin rayuwarta a matsayinta na amanar Allah a hannuna" Ta fadi tana dunqule hannunta. Sosai maganar ta wani irin ratsashi AMANAR ALLAH data kira ya sanya ya sake bude idanunsa sosai a kanta. Tabbas batasan girma da illar maganarta ba,tabbas batasan waye ALLAH ba......babu ko shakka batasan matsayin AMANA a musulunci ba,da bazatayi wannan furucin ba,sai ya sakejin matar gaba daya tana saare masa a rai....duk dama bai kamata ma ya tsammaci imani ko sanin Allah a tattare da ita ba. "Naji cewa a musulunci ba laifi ko kuskure game da hada AUREN KISAN WUTA ko kuma AUREN YARJEJENIYA muddin bada sanin mace ba ko?....ko bada sanin miji da matar ba......muhammad,kaf duniya sultane bashi da wanda ya aminta dashi sama dakai......da kai kadai ne nima na aminta,na kumayi amannar cewa zaka iya taimakawa akhnan kamar yadda itama zata taimakeka" Sai ta dakata tana dubanshi kafin ta qarasa farke manufarta gaba daya,duk da tasan zuwa yanzu koda bai fahimceta gaba daya ba ya fahimci fiye da rabi na abinda take nufi. Shima dubanta kawai yakeyi,hauka qarara kuma yake gani shimfide cikin maganganu da kalamanta. Jira yake ta qarasa fadin abinda take niyyar fada din a yanzu,abinda kawai ya rage masa kenan. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 79* "Nayi imani kai ka dace.....auren KWANGILA AUREN YARJEJENIYA......bisa dokoki bayyanannu......ba takura ba matsantawa......ba sanya qa'idojin da zasu takuraka......ka auri akhnan na watanni biyu zuwa uku kawai.....don ka kubutar da ita daga fushin sultane,don kuma ka bata daman komawa abinda ranta yakeso......wanda dukkanin haka idan ya tabbata,ba shakka zakayi bankwana da sunan SHEIKH zuwa MILLONIER". Tana kaiwa nan ta dakata zuciyarta na wani far far da yadda taba ya zuba mata ido calmly yana kallonta,saidai abinda bata sani ba,wannan calmness din ya bayyana ne kawai iya saman fuskarsa......wani irin zafi yakeji zuciyarsa tana masa...... A zahirin gaskiya ba zaituna idanunsa suke gani ba,hakanan ba zeenatu idanunsa suke gani ba.....wata halitta ce daban datayi nisa da tsarin halittar dan adam. A kudin duk da take ganin zata bashi baya tunanin zasu kai adadin kudin ciyar da marayun da yake fitarwa a shekara daga cikin dukiyar da Allah ya bashi. Me yasa ita kanta yarinyar ta maida kanta tamkar wata HAJA a kasuwa?. Me yasa ta kasa fahimtar MARTABAR kanta?,me yasa take damqa dama da ragamar rayuwarta a hannun matar?. Me yasa GIRMAN KAI take bari yake yaudararta?. Koda wasu abubuwan shirya mata ake tsara mata ake.....amma lallai akwai hadin kanta me yawa a tattare da faruwar komai. Wani irin hatsari ne girma yake hanga tattare da rayuwarta,ita me yasa ko sau daya ta kasa hangowa kanta wannan?. "Kada kace zakayi jayayya sheikh haisam.....Allah yana sonka da rahama shi yasa ya watsoka cikinmu a irin wannan lokacin.....shi yasa ya kawoka ya damqa wannan damar ta fado hannunka,wadda dama ce dana tabbatar miliyoyin maza suke nemanta koda ba za'a biyasu da komai ba......kawai su amsa sunan mijin GIMBIYA KHADEEJA SULTANE MUHAMMED HAMMUD kadai nasara ce a tare dasu" Tayi saurin fadi saboda tsoron kar amsarsa ta fito ba yadda takeso ba. "Amma me yasa sai ni?" Yayi mata tambayar da salo na titsiye yana dubanta kai tsaye cikin idanunta. Kanta ta kawar kadan,da gaske idanunsa yana mata wani irin nauyi da kwarjini tamkar dai idanun IBRAHEEM. "Saboda kai din ba dan nan bane.....kai din ba jinin SARAUTA bane......sannan na sani mutane ire irenka da dama suna zauna a masarautar nan.....amma basa dogon zango suke tafiya suyi gaba". Akwai wani abu cikin maganganunta daya tsinkaya. "Kin saka zato da yawa a kaina" Ya fadi kansa tsaye. Kai ta gyada "Saka zatona me yawa a kanka yana da alaqa da kula da mu'amalarka motsinka da takunka" Idanunsa ya lumshe sannan ya budesu lokaci daya. Koda batayi subutar bakin fadin hakan ba ya sani......har yanzu akwai wanda ke bibiye dashi,kuma yana dab da durqusar dashi a gabanta saman gwiwoyinsa ya kuma tilastata bada ba'asin hakan. Tsaf ya karanci tsoron a idanunta,kuma yanaso ya tabbatar mata da wannan tsoron,don haka ya miqe a nutse yana zube hannuwansa cikin aljihun jubah dinsa,abinda ya sake qara masa kwarjini kenan,idanunsa fes cikin nata. "Lokacin da mabuqata akan samun wata dama suka yawaita......wani mutum qwaya daya yace baya buqatar wannan damar da shi ta fara zuwa hannunsa......ina kyautata zaton sauran da zasu samu hakan zai faranta musu fiye da zato......bana cikin wannan tsarin ranki ya dade,na gode sosai da tayin dama". Ya qarasa fada cikin nutsuwa yana takawa a hankali ya doshi qofa. Wani irin tashin hankali ne ya bijiro mata,ta miqe tsaye cak tana kallon yadda yake yakunsa a nutse hankali kwance. "Muhammad.....kada zuciyarka ta yaudareka kayi gangancin barar da buqatata.....yin hakan tamkar kirawa kanka masifu ne da bakasan iyakacinsu ba......komai zai iya faruwa da kai,komai zai iya faruwa da ahalinka dama dukkan wani makusancinka......" Tayi maganar da hargagin daya tilasta tafisu shigowa gurin da sassarfa,saboda yadda harshenta ya dagu har sautin yana yin nisa da inda suke tsaye. Cak yatsaya,tsaiwar kuma data bawa mammina relief,har ta fara tunanin samun saukowa daga gareshi. Saidai koda ya juyo gareta yanayin fuskarsa kadai sai daya sanya hanjin cikinta curewa guri daya. "Kiran sunan AHALINA kawai lokutan shirme irin wannan akan harshenki zaituna zai iya zama babban kuskure a gareki" Iya gajeriyar kalmar daya fada kenan ya sake juyawa,saidai kuma girman kalmar ya daki zuciyar mammina da wani irin tarin mamaki da jin QASQANCI a tare da ita. Babu wata rana a rayuwarta da zata iya tunawa wadda aka tsaya a gabanta aka gaya mata magana me kama da wannan. Ba wani dan adam me rai me qafa biyu ido biyu hanci daya daya taba jefa mata magana me tsauri irin wannan. "Damar da qasqantaccen mutum irinka ya samu shine yake zaton KIMARSA da martabarsa takai da zai iya tsayawa gaba gareni ya gayamin duk maganar da tazo ranshi?......kana zaton akwai wani DARAJA da kake da ita ne da har ka cancanci ka rabi koda sunan SULTANE MUHAMMAD HAMMUD?. Kana zaton banda ni da zan zameka maka tsani har ABADA ka isa ka amsa sunan MIJIN GIMBIYA KHADEEJA koda na rabin second ne?.....baka da wannan damar HAR ABADA baka da wannan MARTABA DA DARAJAR......qasqantacce dama zai tabbata a yadda Allah ya halicceshi ne....koda kuwa an nufeshi da arziqi ne.....ka rubuta ka ajiyr har abada kaida samun wata martaba ko daukaka a rayuwa....zaku tabbata a qasqantattu qarqashin alfarmar wasu KAIDA DANGINKA GABA DAYA....KUDA MARTABA HAR ABADA!!!" Ta fadi maganganun da wani irin zafi har sai da tafisu ta riqeta. Tsaf dukka kalamanta sukayi masauki a kunnensa. Wani iri murdawa zuciyarsa takeyi.....wani irin tashi jijiyoyin kansa kawai sukeyi. Wani irin fushinsa ne daya jima bai motsa ba yake motsa masa. Kansa ya wani harba da kalar bacin ran da yakejin dacinsa har saman harshensa. AHALINSA da DANGINSA da take fada ya hada da NANAY da kuma MOTII ciki. Tsigar jikinsa ta zuba hannuwansa suka dauki rawar daya tabbatar idan fushinsa yakai wannan gejin akwai matsala ta gasken gaske,kuma komai yana iya faruwa,don haka ya sauya akalarsa zuwa daya daga cikin kebantattun guri na gidan. Yatsunsa kawai yake cusawa cikin sumar kansa yana zarewa,can qasan ransa yana maimaita fadin. "A'uzubillahi minash shaidanirrajeem" Ya sani,fushi irin wannan daga shaidanne.....kuma a hankali yaji qirjinsa yana sassauta daga yanayin da yakeji. Nutsuwarsa ta dawo jikinsa,ya dinga zuqar iska yana fesarwa. Ya zama dole ya nunawa matar cewa YA ISA isar kuma da bata da alaqa sam da samuwarta. Zai sanya wani tabbataccen alqalami,ya kuma zana mata rubutun da ko nan da shekara dubu duk inda taji ance wannan sunansa MUHAMMAD sai hantar cikinta ta kada......zai sanyata da bakinta da kanta ta bawa wasu labarin wannan ISA da take inkarin yana da ita. Kiran daya shigo wayarsa ya dauki hankalinsa kadan,kamar bazai duba ba sai ya tuna jiya bobbo yanata kiransa,abinda ya sanyashi cusa hannunsa a jubha dinsa ya fiddo wayar. Bobbo dinne yake kiransa,ya fesar da iska kadan daga bakinsa yana daga Kiran ya saka a kunnensa. "Kana lafiya kuwa Muhammad?" Shine abinda ya fara tambayarsa bayan sallama "Alhamdulillah bobbo" Shuru ya ratsa kadan,yanayin muryar haisam din tana qaryata masa maganarsa. Ya san halinsa sarai,idan ya boye maka abu,bai shirya gaya maka ba,barinsa shine yafi,don haka ya sauke ajiyar zuciya yana cewa. "Shikenan.....Allah yayi muku jagora......kunyi magana ne da sultane." Kai ya gyada tamkar yana gaban bobbo din. Har yanzu yanajin daci saman harshensa "Munyi magana.....inaso ka shaida masa na amince......ka gayawa motii amincewata shima". Sosai bobbo yayi shocked,maganan na zuwa masa a bazata. "Muhammad.....wanne irin hukunci ne haka da sauri?" Kansa ya sake girgizawa yana hadiye wani abu da qyar. Banda bobbo dinne tsinke wayar yafi muradin yi baci gaba da magana ba,don a duk sanda yake cikin fushi irin wannan yana taqaita magana ne qwarai gudun dana sani (Wannan din koyarwar ma'aiki ce,idan har kana da dabi'ar yin shuru a sanda ranka ya baci ko yake bace,to tabbas ba zaka zama me nadama ba,amma muddin ranka yana bace kuma kace sai kayi magana,ko sai ka dau mataki,to akwai yuwuwar nadama da danasani me yawa a tare da kai) "Wannan hukuncin dana dauka bobbo shine abinda ya kamata nayi.....shine abinda ya dace kowanne da na halak yayi". "Amma kana tunanin d'iyar abokin mahaifinka ta zame maka wata garkuwa ne bayan garkuwar da akayi da ita ba tare da tasan da hakan ba?". Sai a sannan maganar bobbo ma ta harba masa wani abu cikin kansa.....sai a sannan yasan AUREN zai iya zamewa mammina wani BABBAR BARAZANA koda bai nufaci ya zame mata barazanar ba,koda iya manufarsa ta nuna mata ISA ce kawai. Baisan murmushi ya subuce masa har sai da shuru ya gilma. "Zanji komai daga gareka bobbo bayan wani lokaci......zan zameta GARKUWA ne bawai ita din ta zamemin GARKUWA BA. Namiji ako yaushe zama yake madubi bawai ya buya a bayan wani ba ya zame masa madubin ba.....namaji GARKUWA ne bobbo.....zan zame mata garkuwa saboda albarkacin SAFEENA albarkacin NANAY......zan zameta GARKUWA ne zuwa lokacin da zan amintar da rayuwarta......zan sakar mata 'yancinta a sanda dukka wasu kuraye dake farautarta suka kwanta dama.....suka tsoraci kusantar inda take. Taci albarkacin SAFEENA taci albarkacin NANAY......uwa uba kuma ZUMUNCI ya siya mata wannan damar ta qayyadaddun lokuta.....badon MORSA SAFIYYA BA....ba don SULTANE Ba......albarkacin IGIYAR ZUMUNCI.....Albarkacn nagartacciyar uwa da QODARTA har yanzu ke rayuwa jikin YARUWA GA NANAY DITA. Zamuyi sauran magana bobbo.....amma a yanxun shuru nake buqata,amma Amincewata ta isa ga sultane da motii,kome sukace bobbo na baka dama akan hakan.......TA KIRA WUTA da kanta batasani ba......tayi wasa da DAFIN MACIJI tana tunanin ordinary ruwa ne kamar kowanne kalan ruwa" Yana kaiwa nan ya katse kiran a hankali yana jin wani sassauci a ransa. Ya sani bobbo zai iya qalubalantarsa......amna a yanzun da kwanyarsa ta harbo masa tarin gajiyar da auren Akhnan zata mallaka masa gurin sake dulmiya mammina da sanyata fiddawa duniya da nunawa duniya cewa itadin asalin CRIMINAL ce,sai yake sakejin ba wani abu da zai dakatar dashi daga karbar auren Akhnan din. *MAMMINA* zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 80* "Allah ya taimakeki.....ba girmanki bane,kinfi qarfin kiyi jayayya da wani....kinfi qarfin wani dan tsako ya daga hankalinki wallahi" Tafisu ta fada cikin tsantsar girmamawa tare da son kwantarwa da mammina hankali. Da idanunta da suka sauya launi ta dubi tafisu dake durqushe a gabanta kamar me neman rahama,kamar itace tayi laifin,kallonta take sosai,tana son taji ko yaya ta yarda da kalaman tafisun akan cewa haisam din dan tsako ne,amma kuam zuciyarta ta gaza gasgata haka. "Ina me tabbatar miki koda ace ya nuna miki taurin kai.....koda ace ya nuna miki yana kan bakansa.....koda ace ya nuna jarumtarsa.....tabbas can qasan zuciyarsa cike take da TSORO da kuma d'ar d'ar.....don ba wanda ya isa yayi jayayya dake ya kwana lafiya......ya tashi qalau cikin zuciyarsa.....kwarjininki da girman ikonki cikin qasar nan kadai ya isa kowanne dan adam shiga fargaba da zullumin saba miki". Wani numfashi sosai mammina taja. Karon farko da taji zuciyarta sam bata aminta da zantukan tafisu ba,karon farko da taji har cikin jikinta cewa zantukan tafisu na faranta mata ne zallah bawai na fadin anihin abinda yake shine gaskiyar magana ba. Sai data tabbatar ta soma dawowa saitinta ta hanyar zuqar iska da fesarwa sannan ta kalli tafisun. "Na rantse shine zaiyi wannan aikin.....don shi na hangowa cancantar yin aikin a sauqaqe.....sannan duka tsarin dukkanin plan din nasa ne.....QADDARAR wannan karon tashi ce" Ta fada da wani irin zafi "Tabbas....babu ko makawa" Tafisu ta jaddada tana gyada kanta,wanda basu kai qarshen zancan ba yalwa ta shigo duka ilahirin jikin yalwa din yana tsuma. Ido mammina ta tsareta dashi,yayin da yalwa din tayi qasa da kanta tana jiran umarnin fara magana daga gurin mammina,duk da yadda hanjin cikinta yake kaduwa. Cak mammina ta dauke kanta daga duban yalwa din,ta maida dubanta wani guri daban. "Ki gaggauta fadin abinda yake tafe dake kafin fushina yakai ga sauka a kanki" "Allah ya taimakeki.....tamim ne ya iso.....yace kuma cikin gaggawa yakeson ganawarku sama da duk irin gaggawar daya taba gabatarwa a gabaki". "Ya shigo......yalwa" Ta bada umarni gami da kiran sunanta. "Ina amsawa ranki ya dade" "A tabbatar an nesanta duk wani me rai daga wannan area din" Ta fadi still idanunta na kallon wani guri daban,tana sauraron wani irin bugu da zuciyarta takeyi. Wani yanayi ne da muddin ta jishi tattare da ita yake alamta mata sunan MATSALA. Wani yanayi ne data tsani jinsa a tare da ita,yayi da can qasan zuciyarta yake danqare da tsanar haisam. Silar banzayen dokokinsa ya sanya zata gana da tamim a karon farko kan wata magana da tafi.mata rayuwar duk wani me numfashi dake masarautar muhimmanci.....zata gana dashi a budadde guri irin wannan da bai dace da sirri irin nata ba. Tafisu ta gani tana miqewa tsaye,saita waiwaya a hankali tana duban inda tafisun ke kalla. Tamim ne ke takowa da wani irin sassarfa.....da wani irin yanayi me nuna zallar rudewa da dimuwa a tare dashi. Abinka da dogo kuma zabgegen mutum,ko ina na jikinsa gaf gaf yakeyi,har zuwa sanda ya qaraso gabanta ya kuma zube kamar me shirin tafiya sujjada. Samun kanta tayi da gaza tambayarsa.......saita bishi da idanu sanda yake cusa hannunsa cikin babbar rigar jikinsa dake dauke da tarin aljihun da wani ma baisan da zaman wani ba,ya zaro wasu takardu yana miqasu kai tsaye ga mammina. Hannunsa dake riqe da takardun wadanda suke rawa tabi da kallo,dukkaninsu daga su har takardun shaking suke,sai kawai ta miqa hannunta ta karba din,ta koma da baya ta zauna ta fara budesu. Wani irin yanayi taji yana saukar mata,a hankali taji ta fara daina gane komai daga karanta layi uku kadai da tayi na takardar wanda yake dauke da rubutaccen saqo da yaren oromo. Gumi na lokaci daya ya yanko mata,iya abinda idanunta suka iya hange qwaya daya ne da take ganin kamar ga cika takardar gaba daya "ABA JIFAR ROYAL BLOOD". Bata sani ba.....tsohon karonta da MASARAUTAR karon da bai mata dadi ba ko qanqani shine yake son farautarta a yanzu?,yake mata yawo da qwaqwalwa da kuma tunaninta?,ko kuma da gaske sunan take gani jikin takardar. Sakin takardar tayi ta sulale tana duban tamim. "Ba karatu a takarda nake buqata ba.....don ba ita na aika ta samomin muhimman bayanai ba.....NAMIJIN DUNIYA TAMIM nake buqatar gani a gabana.....ba zaburarren bawa ba,me kama da kazar da aka tsoma cikin ruwan sanyi". Wadannan maganganun nata sun dan tattaro kadan daga cikin qwarin gwiwar dake maqale a wani saqo na zuciyarsa,sai ya zauna sosai yana qoqarin share zufar fuskarsa. "Uwar gijiyata....bincike ya cimma agadez!!" Ya fada da wani sauti daya aike da wani kalar razani kowanne lungu da saqo na jikin mammina. Wani irin abu yarrr ya sauka a jikinta yana zartawa har tsakiyar kwanyarta. Wani abu takeji yana kurkkurdawa kowanne lungu da saqo na jikinta,wani irin matsanancin mamaki yana cikata. Koda ace tana zaton anaci gaba da bibiyar sawunta ne.....amma koda wasa.....ko a mafarki bata taba tunanin akwai wanda hasashensa zai kawo ga AGADEZ din ba.....bata tunanin akwai wanda zaiyi tattaki ya tsoma kansa a bala'i wajen tunkararta cikin agadez ba. Agadez din da take jinta tamkar wani GIDA nata mallakinta da take da ikon sarrafashi da kuma juyashi. Agadez din da take da tabbacin ta kowacce fuska cimmata a cikinta zai zama abu me wahalar gaske. "Wa ya taka wannan hanyar?" Ta jefawa TAMIM tambayar da idanunta da suka sauya launi tana dubansa. "Ba'a ambaci suna kai tsaye ba......saidai inkiyar dana jima da saninta.....inkiyar dana jima da sanin tasirinta da kuma hadarin da take dashi.....bansan ma'abocin inkiyar ba......amma kuma hadarinsa kaifin kwanyarsa da tasirinsa a hukumar ya zarta na kowa.....naso sanin fuskarsa tun a wancan zamanin.....amma akwai wani irin amana da kutsen me kutse gurin samo sahihan bayanai yake wahalar gaske......" "Duk inda kaji jita jita akwai qamshin gaskiya tattare da wannan labarin,koda kuwa zai kasance kaso casa'in cikin dari na labarin qarya ne.....mece inkiyar tasa?" "Al-saamit......the silence one.....mai shuru" Sunan ya harba wani abu cikin kwanyar mammina sosai,ta girgiza kanta da gaske kafin tace. "Shuru makami ne na gasken gaske,makami ne na masu hikima dabara da tsananin wayo.......waye ya aikoshi?" "Ba'a bayyana ba.....amma dai hukumar tsaro ta masu tsananin kaifin basira.....wayeshi kai tsaye da kuma wanda ya aikoshi abune da bai gama bayyana ba,an boye bayanan sosai". "An boye ko kuma an kare?" Sosai tamim yakejin wani gumin yana tsatsatsafo masa. Yanayin tambayoyin uwar dakin nasa yana jinsu a yau da wani irin tsauri da nauyi a kansa. "Dukka zai iya yiwuwa.....saidai a dabi'unsa baida yawan magana.....baida yawan tambaya.....saidai yawan sauraro....sanya idanu cikin hikima har zuwa sanda zai gano bakin zaren". Shuru tayi me wani irin zurfi,tana kuma zubawa guri daya idanu. "Yasan abinda yake nema.....tabbas ko waye suka aiko yasan abinda yake nema" Ta fada tana jijjiga kai "Yana cikin mu.....yana a kusa damu,alamun da jikina ya dade yana bani ba qarya bane,alamun da jikina yaketa karantamin gaskiya ce da ba qarya a cikinta....wasu abubuwan sunzo a rufe....amma ba zasu gagari zeenatu ba" "Zanci gaba da bincike ne?" Tamim yayi tambayar da madaukakin tsoro da fatan a bashi dama ya toshe duk wata hanya duk wata kafa da qofa. Wani kallo ta watsa masa tana qanqance idanunta. "Karka qara kowanne motsi,kada ka qara kowanne taku,ci gaba da bincike yana iya fadakar da maciji.....amma kuma......me sunan ABA JIFAR yakeyi jikin takardar?". Zama ya koma yayi sosai yana jin yadda cikinsa ke hada gangamin zazzafar gudawa,shi kansa iya bayyanar sunan kadai ya masa wani irin gigita da kuma ba zata. "Akwai kyakkyawan zaton ya fito daga masarauta.....akwai kyakkyawan zaton Prinsii ne cikin jerin masarautu ukun da aka bani......masarautar jimma......." "Dakata!" Mammina ta dagawa tamim hannu tana tsaidashi da wani irin mahaukacin bugun zuciya. "Kada ka qarasa lissafo kowacce masarauta a ciki......tafisu...." Ta kirata tana maida dubanta kanta. "Allah ya taimakeki" Ta amsa tana rusunawa. "Jinin IBRAHEEM kenan fa?.....indai ya tabbata prince of jimma ne ya shigo AGADEZ?" "Qwarai kuwa" Tafisu ta amsawa mammina da wani irin qaqqarfan amo dake bada tabbaci ga mammina din. Cak mammina ta miqe tsaye,tana jin kamar zama yana shirin gagararta. Gwara kowanne dan aike.....gwara kowanne dan leqen asiri da ace JININ IBRAHEEM ke farautarta. "Wanne D'A ibraheem ya sake samu?.....wanne d'a ibraheem ya sake haifa dake da tsananin tsaurin ido haka?. Hala ibraheem bai gaya masa wacece ZAITUNA ba kafin ya jefo kansa da kansa a da'irata?.....kafin ya jefo kansa da kansa a TASKU na da BALA'I na?" "Wanne tabbaci kike dashi dan masarauta jimma ne ranki ya dade?". Wani irin murmushi mammina ta saki,sannan ta juyo tana duban tafisu. " Kinsan QARFIN JININ OROMO?.....KINSAN JARUMATA DA SADAUKANTAR DA SUKA GADA SAMA DA KOWACCE KINGDOM data taba wanzuwa a HABASHA?.....Kinsan waye ibraheem?......kinsan meye zai iya aikatawa da wanda bazai.aikata ba?.....ibraheem shine mutum qwaya daya da yafi kowa sanin sirrikana......mutum daya days gagareni na kauda shi,mutum daya da yafi SULTANE sanin wacece zeenatu zahirinta da badininta.....masarautarsu ba banzar masarauta bace....masarauta ce da JARUMTA da SADAUKANTAKA ce ta ginata.....masarauta ce da tun a baya ta gagari QABILATA dama sauran QABILU.....IBRAHEEM shi daya ne nake qarfafa zargina a kansa......masarauta OROMO....amma zan gani.....zan gani....zan gani,kafin sannan.....tamim.....na baka nan da awa daya kawai,ina neman alqalumma da jadawalin baqin da suka shigo shiyyar na dama cikin masarautar nan gaba daya". "An gama" Ya fada yana miqewa,gami da tsatstsafe gumin daya jiqa masa gaban riga da hannun babbar rigarsa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 81* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX *BAYAN AWA DAYA* A iya awa dayar data bawa tamim,ta kasa zama ta samu nutsuwa koda na minti biyar ne. Kaiwa kawai da kawowa takeyi tsakanin parlor dinta data koma,saboda tana jin iskar gurin da hasken gurin kamar sun mata kadan gaba daya. Duka ta tsiyayar da tunaninta ta kuma qarar dashi akan hango wani abu da taga ya sauya tattare da ita mu'amalarta da mutane ko jama'ar da suka shigo rayuwarta suka kuma fita a watannin. Tako ina idan ta zagaya tunaninta mutum DAYA take gani.....hasashenta mutum daya yake hanga......saidai ba wani dalili ko hujja me qarfi da zata iya riqa. Zama tayi bayan cikar awa dayar,tana jin gaba daya tunaninta ya gama jigatar da ita. "Akwai wanda kike zargi?.....akwai wanda hasashenki yake kaiwa kansa?" Mammina ta tambayi tafisu idanunta a kanta. A nutse tafisu ta girgiza kai "Zuwa yanzu tunani na baikai kan kowa na tukunna......amma mu jira.....mu dakaci dawowar tamim....zai iya yuwuwa mu samu haske daga alqalumansa" "Amma baqon malamin da na yiwa tayin auren akhnan fa?" Daga kai tafisu tayi tana dubanta,kafin a hankali tace. "Me yakai tunaninki kansa haka?". Shuru mammina tayi na wasu sakanni,sannan ta sake fesar da iska. "Akwai tarin wasu abubuwa dana jima ina mamaki tattare dashi.....har yanzu banga alamun rauni ko qasqanci tattare dashi ba,mutuwar zuciya,fadanci neman shiga iin wanda nake gani tattare da dukkan malamin daya rayu cikin fada qarqashin umarnin masu mulki......irin dabi'ar data assasa gaba me yawa tsakanin biftu da dukkan wani malamin addini.....MAKAMIN da na fara taqar d'a namiji a zuciyarta dashi kenan. Tun ranar da naji safiyya na fadin burin safeena zai cika na samarwa akhnan miji ma'abocin addini....tun a ranar na daura damarar saqa tsana da gaba tsaninta da dukka wani me irin wannan siffar,.....daga qarshe kuma na tsara idan hakan ta yiwu ma zan sake sanyawa su zama wani dalili na sake bacinsu a idanunta. Ban samu wannan damar ba sai a kansa,don shi daya ne matashin malamin dake da dukka qualities din da nake hange......saidai yana da wani abu cikin jininsa da na kasa gane meye shi.....yana da wata IZZA yana da ZARRA yana da KWARJININ da jikin BASARAKE kawai ake samun kalar wannan kwarjinin......." Maganarta ta yanke da sallamar yalwa. "Tamim ya dawo" "Ya shigo" Ta bada umarni nakai tsaye. Dan jim yalwa tayi. "Shigowarsa nan zata karya doka ne....." "Ya shigo inji ni ni giwa!" Mammina ta fada da wani irin zafi daya sanya yalwa juyawa ba shiri tayi masa iso. Kai tsaye ya miqa mata takardar,tafisu ta karba a nutse ta wareta. List na jerin sunan mutanen daya bayan daya ta fara bi tana karantowa mammina. Yayin da parlor din ya dauki shuru,kowa kuma yayi shuru din yana sauraronta. "Sheikh muhammad haisam......." "Aba jifar?" Mammina ta samu kanta da qarasawa ta salon tambayar data daukewa kowa wuta a cikinsu,don dukkaninsy basu fahimci abinda take nufi ba,sai kallon kallo a tsakaninsu. Yayin da cikin kanta kuma takejin wata irin zabura sanda lokaci guda sautin haisam din ya karade kunnuwanta da sirrintaccen sunanta na ZEENATU Sake miqewa tayi tana nufar tafisu,jikinta yana son ya dauki rawa,ta sanya hannu tana zare takardar daga hannunta tana kai idanunta kan list din,saita saki takardar tafisu ta saka hannu ta cafeta. "Tun daga labarin zuwan.....zuwa hasashen sunansa......karanta sunansa da kuma sake kallon sunansa da nayi a yanzu jinina ke zabalbala.....nakejin wani abu yana harbamin kwatankwacin wanda nakeji game da IBRAHEEM......Bana ko shakka sheikh haisam shine ABUN ZARGINA a yanzu......zan JARRABA hakan.....idan kuwa ya tabbata da gaske.......lallai ya jefo dansa ga halakarsa" Ta fada da wani irin yanayi tana dukan tsakiyar tafin hannunta. "Prince haisam zaiyi magana.......ba shakka zai bayyana kansa" "Idan yaqiyi fa?" Tamim da yakejin rayuwarsa ta gama kaiwa ko ina yayi tambayar da bai shirya yinta ba. Shi kadai yasan yadda shehin malamin yake masa barazana a idanunsa.....shi kadai yasan irin yadda kallon idanunsa kadai yake sanya masa firgici......yayi imani idan ta tabbata SHINE lallai zai faraucesu daya bayan daya kamar yadda damisa ke farauta cikin daji. "Kowanne mutum yana magana tamim....indai ansan yadda ake magana dashi.....TAMIM.......a shirya farmaki.......mafi bada barazana......mafi bada girman gargadi.......qarfafan dakaru nakeso a aika......amma kuma BA RAYAYYU BA......da matattu nakeso nayi amfani,saboda shafe duk wani sahu ko alama da maibin diddigi zai iya bi......Al-SAAMIT the silent one zaiyi magana da gasken gaske.....da kansa.....zai saki signals da alamomi da zai bani hasken shiga lamarin kai tsaye". "An gama" Ya fada cikin tsoro shakka da kokwanto. Halittar tsoro data jima da mutuwa cikin qirjinsa da zuciyarsa,sai gashi yau THE SILENT ONE da sunansa kawai ya raya wannan halittar. "Farmakar motii ba wani qaramin abu bane me sauqi.......ka kula......ka kula.....ka kula" Ta maimaita masa sau uku tana masa alama da hannu akan ya wuce. *HAISAM* Da wannan zaman nasa dake nuna SARAUTA dake yawo a jininsa yake duban na'aurar dake gabansa. Abood daya daga cikin ma'aikatansu na hukumar sirri ne ke ci gaba da bashi bayanai daki daki kaman yadda ubangidan nasa sheikh muhammad haisam ya buqata da gaggawa. "Komai data fadi maka ya faru a asibitin haka ne ya faru......saidai kuma tun daga kwanan watan shekaru rana da lokaci dana samu a record dinsu dukka yasha banbam da wannan daka bani a rubuce........iya abinda na fahimta shine,ba wani tsohon ma'aikaci cikin asibitin,dukkaninsu sababbi ne,kuma basusan salsalar asalin labarin ba......suma sunzo ne kawai sun tadda komai a rubuce yadda suka nunamin suka kuma bani. Kowacce qofa obbo a kulle take ta samun komai daya danganci lamarin batan jaririn......ba wata sauran hanya don na gwada duk wata dabarata ban samu wani sabon abu ba kuma" Kai ya jinjina da wannan cikakkiyar nutsuwar tasa da ba komai ke girgizata ba,ya raba yatsunsa dake soke cikin na juna tun dazu. "Kayi aiki me kyau abood......a huta gajiya,na gode" "Obboo galatoomaa (thank you" Abood shima ya fada cikin rusunawa da girmamawa. Idanunsa ya daga a hankali ya zubesu akan omar dake zaune a gabansa yana dubansa. A iya tsahon rayuwar aikinsu omar din bai taba jin wani aiki daya masa nauyi akai.....aiki me wahala.....aiki dake cike da mugun mummunan qulli ba irin wannan. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Shekara talatin ta binne komai?". Idanunsa haisam ya lumshe sannan ya budesu,a zahiri murmushi ne qasan zuciyarsa,amma kuma ya kasance salon murmushin nan nasa dake cakude da miskilanci,don haka ba kowa ke fahimta ba. Ya sani......aiki ne me girman gaske a gabansa......amma baisan me yasa wasan yake masa dadi ba. Komai idan ya tabo ta kowanne bangare sai ya dinga ganin qofa ce me girma take bude masa. "Shekara talatin bata birne gaskiya ba......tadai lullubeta ne kawai". "Amma ta wanna fuskar haisam ka fahimta.....komai ya qare fa,ba sauran wani abu da bazai bada haske" Kansa ya girgiza a nutse "Komai bai qare ba omar......hasalima komai yana sake saitamu ne akan hanya,yana qara nuna mana hanya ne kawai" "Nuna mana hanya?" Yayi tambayar yana duban haisam cikin mamaki,ta ina ya hango hanyar?. "Sosai.....ka fadamin.....waye yake da iko ko qarfin gwiwar shiga dakin haihuwa ba tare da barin sunansa ba?" Shuru kada omar yayi kafin ya amsa. "Only someone above the hospital administration" "Good" Ya fadi yana gyada kansa da lumsassun idanunsa. "Waye kuma zai sace yaro ba tare da ya kasheshi ba?" "Wanda yake buqatar yaron a raye" "Exactly" Haisam ya sake amsawa omar da wani low tune. "Amma koda hakan gaskiya ne.....there's no way to prove it now" "I'm not looking for proofs.....I'm looking for pressure" Ya amsa masa calmly da wani accent cikin English dinsa me wani irin dadi saboda saboda da oromian language da yayi. "Pressure on whom?" Wannan karon dole wannan sassanyan murmushi ya subuce,kyawawan labbansa suka motsa kadan. "On the person who has spent thirty years protecting silence" "Mammina?" Kai tsaye omar yayi tambayar yana duban haisam" "May be.....amma ka sanya idanu.....mutanen dake dauke da tsaffin sirrika suna da saurin nuna kansu fiye ma da masu laifi a wadansu lokutan". Komai omar ya gama fahimta.....ya gama gane kuma inda haisam ya sanya gaba. Shuru kawai maleek yayi dake zaune a gefe sannan ya saki qaramar ajiyar zuciya. Iya zaman da yayi da aminan nasa a wannan dan taqin ya bashi tabbaci cewa aikinsu sai CIKAKKEN NAMIJI JARUMI daya amsa sunansa. Ya fahimci abubuwa masu yawa,yarukan da baka isa ka iyashi ba idan kai din ba mallakin intelligence agency bane......da gaske aikin na masu INTELLIGENT ne. " Aure zanyi" Haisam ya saki maganar hankali kwance sanda ya jawo system dinsa da zummar turawa bobbo wasu bayanai *_Ayimin afuwa,yau dai baqi nayi,ban samu daman rubuta abun arziqi ba,ina fata za'ayimin uzuri,naso yau muzo gurin😂,don nasan abinda duk muke jira kenan harda nima😂_ _na gode sosai,na gode da qaunarku da jumurin bibiyata_🙏🏽 SON SO🥰🥰🙏🏽 zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 82* Dif wuta ta daukewa omari da maleek,kada ma omar yaji labari shida yafi kasancewa da haisam tsahon lokaci sama da kowa. Yadda sukayi shuru haka yaci gaba da matsa system dinsa hankali kwance,ya basu isashen lokaci da zasuyi mamakinsu su gama,saboda ya sani mamaki dole ne......basu kadai bama,koma waye yazo da wannan maganar tsakaninsa dashi mamakin shine abu na farko da zai fara yi. Sunsan halinsa dukkaninsu,tunda har yayi shuru bazai sake cewa dakowa komai ba,sai idan kai ka buqaci qarin bayanin. "Wai.....da gaske kake ko wasa?" Omar ya fadi ba tare da samun yaqini cikin maganarsa ba,saboda kuwa yafi kowa sanin halin haisam din,baya fadin magana sau biyu......baya qarya koda kuwa da wasa ne......sai wasan ma da baya cikin tsarin yanayin dabi'ar halittarsa gaba daya. "Aure zanyi omar,da gaske nake" Ya sake maimaitawa very calm,abinda ya sake tsumasu da gaske,ya sake kuma tabbatar musu abinda yake fadi din da gaske yake. Tashi maleek yayi daga relaxing din da yayi cikin kujera,ya zauna sosai yana duban idanun haisam dake saman system abinsa hankali kwance. A hankali dariya ya kubcewa omar,don hankalinsa ya gaza gasgata abinda kunnuwasa suka ji masa,duk da baida yaqinin ba gaskiya haisam yake fadi ba. Bai motsa ba bai kalli omar ba,ya barshi yayi dariyarsa yadda yakeso. Sosai maleek ya tsareshi da idanu,yana karantar gaskiyar dake sama fuskarsa. Sai ya motsa labbansa a hankali. "Haisam......aure fa?,a daidai wannan lokacin?" Sai a sannan ya dauke dubansa daga kan system din ya zubesu a fuskar maleek. Ya karanci maleek ya soma gasgata maganarsa shi yasa yaga yana da lokacin sake fahimtar dashi. "Yes.....aure maleek,nan da juma'a in sha Allah.....kwana uku kacal masu zuwa" Idanu suka waro gaba dayansu,omar yana jin kamar wata dabi'a da basusan haisam da ita bane yake qoqarin fara kwatantawa. Suman wucin gadi sukayi,kafin maleek ya qara aro qarfin hali "Amma haisam wanne irin cin amana ne wannan?......ba sign ba signal......ba alamar komai?". Ya fada yana jin nauyi da girman al'amarin. Bai ce masa komai ba......har zuwa sanda omar yayi nasa qoqarin. "Wacece wannan a kwana uku kawai haisam?......kwana uku fa?,ko saamee ce?" "Akhnan ce" Yayi maganar sanda ya zubewa omar dukkanin manyan fararen idanun nan nasa dake da wani irin kwarjini me narka zuciya. Zabura omar yayi ya miqe tsaye,fuskarsa da wani irin mixed emotion,mamaki......kokwanto.....farinciki da kuma zallar rudewa. "Akhnan.....akhnan Muhammad hammud?......dama kuna soyayya haisam baka taba bari na fahimci komai ba?" Omar yayi tambayar wadda maleek ma shi sam a wannan karon ya kasa tambaya. Idanunsa ya janye daga kan omar,sai kawai ya fara tattare kayansa da xummar barin gurin,bayajin zai iya zama ya amsa tarin tambayoyin daya fuskanci sun shirya yinsu a kansa d'aya bayan d'aya. Caraf maleek ya riqe hannunsa gam,sanin halinsa sarai zai iya barinsu cikin rudaninsu. Ba kowanne lokaci yake zama yayi dogon bayani ba. "Bakka eessayyuu deemuu hin dandeessu (ba zakaje ko ina ba).......akhnan dai kake magana akai kaman yadda omar ya fada?,nima inaso na sani" Maleek ya fadi shima yana tsareshi da idanunsa. "Eh.....itace" Ya amsawa maleek kai tsaye yana duban cikin idanunsa kamar yadda shima yake duban nasa. Sake masa hannu maleek yayi yana sakin wata dariya shida omar me cike da nishadi,yasan kwanan zancan......yasan kuma me zai faru,idan ma ya tafi a yanzu be tsira ba,tunda suka fara wannan dariyar,sai kawai ya koma ya zauna salin alin,yayi relax sosai cikin lallausar sofa din yana qare musu kallo. Tsam maleek ya miqe,ya soma takawa yana nufar briefcase dinsa yana fiddo system dinsa. "Wannan labarin bazai cika ba,bazai kammala ba sai dasu khadeem a kusa......nikam bazanyi wannan cin amanar ba,ayi wannan sha'anin babu su?" Ya qarasa fada yana daidaita system din nasa gami da qoqarin kiran kowa a cikinsu. Idanu kawai ya lumshe,gwara ya barsu suyi iyayinsu,ba lallai su fahimci komai ba......ba kuma lallai yayi musu bayanin komai da komai ba. Bayaso su kalli lamarin da wani idanu daban,shuru shi yafi dacewa ya zama amsa......koda kuwa hakan yana nufin zasu amince da cewar SHI YA ZABOTA.....shi yake sonta. Wani irin aminci ne a tsakaninsa da zai wahala wani yaga kiran wani ya share,don haka cikin qaramin mintuna ya hadasu gaba daya,sai gasu sun cika su bakwai cif harda haisam da omar da maleek din dake guri daya a gari daya. "Me yake faruwa da mr lowering gaze?". Naseeb dake zaune ciki parlor din gidansa yana shan fruit da alamu ke nuna matarsa ce a gefe tana yankawa tana miqa masa ya fadi,ganin har suka gama zama online dukkaninsu haisam bai motsa ba bai kuma ce komai ba. Murmushi da yafi kama da dariya maleek yayi,irin wanda sunsan ba dabi'arsa bace. A cikinsu dukka shida haisam dinne keda wannan jinin sarautar a jikinsu,so izza wani lokacin zuwa musu kawai takeyi. Dariyar maleek taja hankalin kowa,don Omar gabadaya ya kurumce,bayajin yana da bakin bayani,yayin da ta wani gefe kuma zuciyarsa ta kasa gasgatawa da kuma yarda da inganci da sahihancin auren. "Lowering gaze ya qare daga yau......mr man aure zaiyi,nan da kwanaki uku masu zuwa kawai". Dariya suka sanya gaba daya,kowa da irin abinda zai fada,abinda ya sanya haisam zama sosai yana ware idanunsa da suka dan sauya launi a kan screen din,wannan ya basu daman ganinsa sosai,sai kuma kowa ya fara komawa nutsuwarsa. Shuru ya ratsa ko ina,ya bude baki da nutsuwar nan da suka sanshi da ita. "Da gaske maleek yake gaya muku.....ruwanku ku yarda.....ruwanku kuci gaba da duban abun ta fuskar wasa" Yana kaiwa nan ya sake relaxing abinsa,saidai kunnuwansa suna tare dasu,duk da qasa qasa yake kallon screen din da salon kallon da zaka dauka bacci yakeyi. Maganan ta saukarwa kowa a bazata. "Haisam dinnan da baya iya kallon mace sai biyu?......guys a duba maganan nan fa?" Amjad ya furta sounding so amazing. "I'm serious" Ya fada da wata murya kaman mejin bacci,yanayin dake nuna musu ya gundura da yadda suketa avoiding labarin. "Wacce jarumar?.....wacce kuma me tsananin sa'ar ce?" Mutallab ya tambaya cikin son jin wadda tayi nasarar. "Akhnan" Omar ya amsa wannan karon kai tsaye yana tallabe da kumatunsa,irin mamaki ya masa kisan mummuqe. Yadda suka kama sunan kusan lokaci daya ya sanya haisam sake girman idanunsa yana jifan omar da kallo. Da alama akwai wani labari nata da suke dashi?. Tambayar data girmi tambaya a wajen haisam saidai qarin tabbaci,don kowa maganan naseeb ta tabbatar masa da haka. "Akhnan?......the princess of agadez?.....stubborn and silly girl?" Naseeb ya jero gaba daya. Maganan ya sakashi qarasa bude idanunsa gaba daya ya azashi kan omar. Omar din da yaqi yadda ya kalleshi. Komai kenan da yake fadi akan yarinyar akan kunnen omar ne?,komai omar yana hankalce dashi kenan?,komai omar ya labartawa su khadeem. "Amma Captain......waye ya tilastaka.......gaya mana sai inda qarfinmu ya qare" Mutallab ya fadi yana matsowa dab da screen din gami da lowering muryarsa irin sirrin nan za'a gaya masa. Yadda mutallab din yayi ya sakasu dukkaninsu kwashewa da dariya,banda haisam daya murmusa kawai yana bin fuskokinsu da kallo daya bayan daya. Har abada ba abinda zai sauya wannan amincin.....wannan yardar.....wannan damuwa da lamuran junan dake tsakaninsu,sirrin dayansu na kowane a cikinsu,saidai wannan SIRRIN nasa ne shi kadai.....wannan SIRRIN na hukumarsu ne kawai.....wannan SIRRIN kareshi yana jin ya zama tamkar wani abu na dolensa. "Babu.....ba kowa my guy" Haisam ya amsa da muryarsa data qara dadi saboda laushi data sakeyi. "Gangan kenan.....kaima ka fadi ne kawai khadeem,banda haka......captain ne fa?......ka manta?.....dama akwai wani abu da yake tsoro a rayuwarsa?.....akwai abinda ke razanashi?.....ka manta da forest din da kowa zai kasa shiga ya koma amma saboda yanayin weather na gurin shi dayanshi yake shiga yayi abinda ya kaishi ya dawo?". Amjad ya furta yana tuna musu lokuta masu dadi na rayuwarsu. "I remembered" Ya amsa wa Amjad yana girgiza kai da qarfi. "Duk da haka komai yana da dalili......meye boye a bayan wannan auren da wuri haka?.....ko dama can da wani abun kuka boye mana yaa omar?" Naseeb daya ajiye qaramar wuqar hannunsa ya fada yana sake fuskantar screen din sosai. Da hanzari omar ya daga hannuwansa dukka biyun sama,kamar me surrender,alamun ba ruwansa,bai kuma san komai ba. Sai maleek ya gyada kai yana sake tabbatar musu da reaction din omar. Shuru kadan ya ratsa,kafin ya motsa da cikakken nutsuwarsa yana duban fuskokinsu still. Shi ya sani,ba komai bane zai iya boye musu ba,kamar yadda suma bass iya boyewa junansu komai. Duk da cewa ba'a rasa jituwa me qarfi tsakanin wani da wani a cikinsu,kamar yadda maleek ya zama mafi qarfin jituwa shida omar a tsakaninsu,saboda gidan da suka fito shida maleek din,daidaito da kamanceceniyar jini da rayuwar yau da gobe da suka tashi a ciki me shigen kama da juna.....saidai hakan bai sauya wannan AMINCIN dake tsakaninsu ba. Akwai dalili.....tabbas da akwai dalili.....saidai dalilin wani dalili ne da bazaiyuwu a yanzu na fadeshi ba" Ya furta a nutse. Ya riga ya barwa ransa kansa da zuciyarsa.....a gefe guda kuma yana jin dole ya kare MARTABARTA koda ba zata shiga rayuwarsa don ta wanzu har abada ba.....hakanan dole ya kare martabar sultane shima saboda AMANA ba abinda yakai girma da qarfinta. "Hakan yana nufin ba don SOYAYYA bane captain?" Naseeb ya fadi cikin yanayin hankali da nutsuwa irin ta wanda ya ajiye iyali. Idonsa ya lumshe sannan ya budesu lokaci daya akan naseeb din. "Ba ko yaushe bane soyayya yake zama dalilin yin komai naseeb" Shuru ya sake ratsawa,kowannensu da nazarin da yakeyi,saidai dukkaninsu sun fahimci da gaske akwai dalilin,ba kuma soyaya bace.....amma tunda har baiji ya kamata ya fadi dalilin ba,suma ba wani hurumi ko dalili na matsa masa. Dukkansu sun yarda da haisam,dari bisa dari,yana da wani irin hankali da dattako cikin dabi'u halaye da kuma jininsa,tun sanda suka hadu a haka yake.....har yanzu kuma ba abinda ya sauyashi. "Idan da rai....idan da rabo komai yana iya canzawa.....kabi a hankali.....wataran zaka iya b'urmawa cikin soyayyarta". Naseeb ya fadi cikin bashi tabbaci. Murmushi ya saki kadan,can qasan ransa yana basu uzuri da RASHIN SANI. "Bazaiyuwu bane na sota.......bana planning din son kowacce diya mace a rayuwata.....don zata iya zame min BARAZANA......zata iya kuma zama itace RAUNINA.....samun RAUNI ga ma'aikacin security intelligence kuwa barazana ne ga rayuwarsa......ka auri wadda ke sonka.....wadda kawai zata yarda ta sadaukar maka" "Ba'a yiwa so iyaka.....ba'a yiwa so irin wannan dabarar" Naseeb ya fada yana girgiza kansa sosai. "Inaji kamar akai naseeb,saboda banga kuma banji muhallinsa ba sam sam" Yana kaiwa qarshe qarar wayarsa ya dauki hankalinsa. Ya aje dubansa a nutse,sai yaga motii ne yake kiransa. Hakan ma ya masa,don yasan a bakunansu,maganganu ne fal tarin tambayoyi da kuma qalubale masu yawa. Da hannu ya basu uzuri,ya miqe kuma anutse yana haurawa zuwa sama,yayin da dukkaninsu suka bishi da kallo had ya bace,sai kuma tattaunawa ta koma tsakaninsu. Duk wani magana da yayi akan auren suka ajiye gefe,suma tashin nasa yayi musu,sai kawai suka fara tsara yadda komai zai gudana,koda kuwa bazaiso hakan ba,amma sunsan bata yadda za'ayi captain sheikh din zai daura aure koda sadaka za'a bashi matar subar komai ya tafi a haka. Koda ba a ranar da za'a daura auren ba,dole suyi wani abu da shi kansa zaisan YES aure zaiyi. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 83* *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX "Assalamu alaikum warahmatullah" Haisan yayi sallamar da cikakken nutsuwa sanda yake zama saman stool din dake gaban madubin. "Wa'alaikumussalam" Motii aba jifar ya amsa muryarsa dauke da wannan tarin dattakon kamala da kuma kamewar. "Barka da warhaka ranka ya dade" Haisam ya furta da yaren oromo yana rusunawa tamkar motii aba jifar yana gurin. "Barka kade muhammad". Cikin asalin girmamawar da yakewa me martaba aba jifar ya soma gaidashi,cikin tsananib kulawa da tarin girmamawa. Shuru ya ratsa na sakanni,yanajin nauyin abinda zaice da motii dinne,yana jin kamar baiyi abinda ya kyauta ba. Aure rana tsaka?,aure kuma a kwanakin da duka duka ko bakwai basu kai ba?. Sai yakejin nauyin motii sosai,abinda kuma ya hanashi kiran nanay kenan,don baisan da yadda zai mata bayani ba. Kamar me martaba aba jifar yasan tunanin dake ran yaron nashi,sai ya kira sunansa da wani irin nutsuwa qauna fahimtar juna da girmamawa. "Muhammad" "Ranka ya dade" Haisam ya fadi da harshe na girmamawa yana rusunar da kansa kamar yana a gabansa. "Naji saqo daga bakin bobbo......na kuma karba dukka bayanai daga bakinsa,na kuma fahimci komai,kuma koda baimin kalar wannan bayanin ba......ni nasan yarona bazai taba tozartani ko ya kunyatani ba......ko kuma ya aikata wani abu na ba daidai ba......na amince na kuma yarje maka ka auri diyar Muhammad hammud......domin kuwa shi din mutumin kirki ne,tsohon aboki daya kasance amintacce,kuma ma'abocin halaye da kuma dabi'u masu kyau. Na aminta bazan bayyana ga muhammad hammud ba saboda yanayin tsarin aikinku.....zan bada goyon baya dari bisa dari......saidai kuma abu guda daya da zan gaya maka muhammad....." Me martaba ya fada yana dan dakatawa. "Muhammad" Ya sake maimaita kiran sunansa "Na'am me martaba" "Kaji tsoron Allah......aure ba wasa bane,nasan ka fini kusan sanin hakan,domin kai me karantarwa da nusashe da mutane ne akan hakan........kada ka yarda koda wasa ka qudurta a ranka zaka auri d'iyar hammud don ka fake a bayanta......don ka cimma wata manufa taka......koda sultane ya roqi ALFARMAr ka auri diyarsa.....kada ka manta hakan bazai canza MARTABA KIMA DARAJA DA TATA ALFARMAR BA......koda yace GARKUWA kawa yakeso ka zame mata......bafa hakan yana nufin yayi wasarere da ita da qaunar da yake mata ba,don haka kaji tsoron Allah,ka tsarkake niyyarka" Sosai maganganun motii ke masa yawo saman kai,sai ya tuna masa da maganganun sultane a jiya. "Na gode sosai muhammad.......na gode daka martabani.....ka karramani ka kuma karbi qoqon barata hannu bibbiyu.....ko iya haka ya isheni muhammad,ka kuma nunamin halascin D'A na halak.....don Allah na roqeka.....koda baka zamo miji cikakke ga akhnan ba kaji tsoron Allah kada ka cutar da ita.....koda baka zamo miji cikakke gareta ba.....ina nema mata ALFARMA ka zame mata GARKUWA......ka zame mata GATA ka zame mata SUTTURA" Dukkaninsu kalamansu idan aka tattarasu abu guda suke nunawa. Dukkaninsu kalamansu idan aka tattarsu guri daya zasu hadu,sai yakejin kamar sunason sauya masa manufar komai a zuciyarsa ta qarfi da yaji. "Ina fata komai yana tafiya lafiya?" Haisam ya tambayi motii bayan sun gama maganan data shafi auren. "Komai lafiya Alhamdulillah.....bisa dafawar ubangiji da qoqarinka". Kai ya jinjina a nutse,a duniya to su waye yake dasu sama dasu din?. A koda yaushe yana nan ne amma hankalinsa yana can jimma. Abu daya yanzu da yadan sake saka masa nutsuwa,gano anihin kan matsalar,sanin wacece ZAITUNA ya sauqaqe masa abubuwa masu yawan gaske,ya sake saka qarin saka idanu sosai a kanta da wata irin boyayyar matsin lamba da ita kanta batasan da ita ba.....abu daya ya rage masa a yanzu........iya adadin rassan da take dasu a Ethiopia......iya adadin idanunta a Ethiopia din. "Ma sha Allah......" "Ranar juma'ar nan ma da izinin Allah zanje na duba al'ummata na qauyen Dass" Motii ya fada a nutse yana duban nanay data shigo wanda tun dazu ya nemi ganawa da ita. Sam abun sai yaji bai kwanta masa ba,ya miqe a nutse yana duban fuskarsa a madubi. "Amma motii.....wakilci kawai bai wadatar ba?" Kai ya girgiza yana murmushi. "Ambaliyar ruwa aka samu......lamarin yafi qarfin wakilci muhammad,ina tsoron ranar da Allah zai tsaidani ya tambayeni ne nayi akai?,wacce gudunmawa na basu?" Shuru haisam yayi.....su din rainon me martaba aba jifar ne,wannan ya sanya zukata da ruhika suke da wata irin nutsuwa. "Hakanma yayi motii,amma da zaka iya jinkirtawa,zan aiko da wasu qari da kuma musaye na masu tsaron lafiyarka daga hukuma" Kai motii ya girgiza yana sanya hannunsa cikin na nanay daketa kallonsa "Babu wani abu da zai faru damu sai abinda Allah ya rubuta masa,ga Allah ne kadai muminai suke dogara" Kansa ya gyada,motii na sake zama masa wani role model a rayuwarsa,tun daga quruciya har kawo yanzu. "In sha Allah motii.....in sha Allah". Sauke wayar me martaba aba jifar yayi daga kunnensa yana duban khadeeja data zuba masa idanu. Mace daya tamkar da dubu a gurinsa.....uwar gidansa kuma uwar dukkanin 'ya'yansa......matar da har yanzu ba wata mace daya taba jin zuciyarsa tanaso koma bayan ita. Murmushi ya saki a hankali yana ajiye wayar a gefansa. "Irin wannan kallon kamar ranar da muka fara haduwa?" Ya fadi yana kashe mata ido daya. Qaramar dariya ta saki,tana jin kunyarsa kadan tana saukar mata. Duk tsahon shekaru da kuma haife haifen da tayi ba abinda ya sauya tsakaninta da IBRAHIM. Har yanzu wannan kallon qauna rahama da soyayyar yana nan a inda yake,takan kalli haisam a yawancin lokuta,tana kuma rayawa a ranta tana yiwa diyar duk data sameshi a matsayin miji murna,musamman idan ya dauki halayen mahaifinsa. Wannan dalilinne ya sanya take tsananin yiwa saamee sha'awarsa,ko don maraicinta,ko don kuma nata nutsuwar da kuma hankalin. "Allah yasa ba wani laifi nayi ba ake tuhumata da idanu.....abu daya dana karanci a gurinki muhammad haisam ya gado" Sake sunne kanta tayi a nutse tana murmushi. "Ko daya Allah ya baka yawan rai,....ina na isa na tuhumi mijina haka?" Murmushin ya maida mata shima yana dan jan hannunta. "Magana nakeso muyi Allah yasa aban aron hankali duka da tunanin a nan" "Ba aro za'a baka ba,domin kuwa hankalin tunanin da wadda ta mallakesu dukka naka ne" "Na sani,na gode da aka sake tabbatarmin" Ya furta yana murmushi. "Khadeeja....." Ya kirata da sunanta na asali. "Sanin kanki ne komai muqaddari ne daga Allah,sannan sanin kanki ne muna rayuwa ne akan rubutacciyar qaddararmu......sannan sau da dama akwai abinda muke hanga ga yadda zai kasance sai Allah ya canzashi ya kasance daban da yadda muke tunani.....duk Allah yana yine don zaba mana maslaha da kuma abinda xai dace damu....wasu suna shiga rayuwarmu a sanda bamu zacesu ba,wasu kuma suna fita a sanda bamu tsammacesu ba.....haka rayuwa take. Ka marabci dukkan wanda Allah ya kutso dashi rayuwarka don bakasan dalili ko manufar haka ba....kada ka koreshi kada ka qyamci kalar qaddararsa.....hakanan duk wanda ya zabi fita daga rayuwarka kada ka tsaidashi,.......bakasan manufar Allah na koreshi daga cikin rayuwarka ba,wataqila bai cancanci zama da kai ba......wataqila wanzuwarsa a rayuwarka matsala ce" Kai ta jinjina a nutse tana jin jikinta yana sanyaya,hankalinta kuma yana gamewa guri daya. "Kin tuna sultane hammud na yankin sahel?" Ya tambayeta yana duban idanunta. Nazari kadan tayi sannna ta girgiza kai da sauri tana murmushi. "Wanda yazo barkar haisam?.....yace in sha Allah shi din babban malami ne da ba'a taba irinsa ba?.....ga sarauta ga ilimi.......dan gatan malami.....isa takai isa kenan malamin dake da sarauta" Sosai murmushi ya qwacewa motii,ya sani zai wahala nanay ta manta sultane ko don saboda wadannan kalaman. UWA bata manta wanda yayi KYAKKYAWAN FATA ga yaronta.....kamar yadda bata manta wanda yayi mummunan fata a gareshi. Lokaci lokaci takan tambayeshi ina hammud na sahel?,saidai shi kansa bayace ba,don baisan ainihin sunan qasar ba har suka rabu,sadarwa ta yankewa kowa a cikinsu,tun a Egypt. "Yana ina kuwa?,har yanzu ba wani labarinsa?" (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Ya dawo khadeeja......ya dawo rayuwarmu ta hanyar bawa haisam auren diyarsa me sunanki khadeeja......auren da zaa daurashi nan da kwana biyu ko uku a madeena". Wani iri taji xancan,kwata kwata saita gagara fahimta,ta zubawa motii idanu tana neman qarin bayani. Murmushi ya saki,ya miqa hannu yana lakace mata hanci. "Dauke idanuwannan ma'abota kwarjini.....irin idanun sheikh muhammad haisam sak" Tare murmushi ya qwace musu,tana kallonsa ne bawai don bata aminta dashi ba,ta yarda da mijin nata dari bisa dari,da wata irin yarda da d'a yakewa iyayensa. "Bani labari motii" Ta fada cikin son jin yadda wannan bahagon al'amarin ya kaya. Nutsuwa yayi sosai yana sake riqe hannunta cikin nasa. "Gidan sultane haisam ya sauka,acan kuma yame gudanar da bincikensa,saidai cikin binciken ya samu gidan sultane a hargitse......ya samu komai baya tafiya daidai dalilin hatsabibiyar matarsa......akwa tarin abubuwan da suke a rufe da sultane bai sani ba bai kuma fahimta ba har yanxu......akwai abubuwan da suke tafiya akan hadari da ba daidai ba......ciki kuwa harda d'iyarsa da aka yiwa saki uku kwana uku kacal da daura auren da ko tarewa batakai gayi ba.......MARAINIYA ce data rasa uwa......marainiyar data rasa UBA ba kuma don baya raye ba......sai don kawai yadda aka kifar da tunanin mahaifin da nata tunanin dukka,bara gane daidai daba daidai ba cikin rayuwarta,an amintar da ita duk wani kuskure da za'a yiwa rayuwarta daidai ne.....duk wata halaka da za'a jefata daidai ce...... Bamu sani ba addu'a ce?,Allah masani,sultane ya yanke bawa haisam diyarsa wanda haisam din ya dade da zama cikakken d'a a gidan.....ya kuma dade da zama amintacce ga sultane din ba tare da yasan daga inda ya fito ba......sun sake haduwa da bobbo.....yasa bobbo ya nema masa izini,ni kuma na yarje......haisan ya yarje shima saboda ceto......duk da banda tabbaci d'ari bisa d'ari akan dalilin da ya sanya ya amince haka da wurwuri shi din.....wannan shine abinda ya faru". Yayi mata bayanin a dunqule ba tare daya buda mata dukkanin abinda ya shafi aikinsu haisam ko hukumar tsaro ta sirri ta farin kaya ba. Shuru tayi tana rasa abuncewa,wani bahagon al'amari ne daya kamata ya zame mata me nauyin gaske,auren d'anta a wata qasar,a sanda ba'a shiryawa komai ba. D'anta mafi soyuwa a gurinta,d'anta na fari.....to amma kuma komai tasan tsarin Allah ne kamar yadda motii ya gaya mata a yanzu. Uwa uba kuma MARAICIN yarinyar da rayuwarta a baragurbin hannu shine abinda yafi tsaya mata. Tana tausayin maraya sosai,tun sanda ta fada nata maraicin. Batun shiri akan aure ko biki dukka tasan wasu abubuwa ne da za'a iya yinsu daga baya......wasu abubuwa ne da za'a iya maye gurbinsu a wani lokaci na daban,bata da haufi ko matsala a kansu. "Shi kuma muhammad tasa qaddarar ta auren marayun mata ce....Allah ya qara cika zuciyarsa da tausayinsu da kyautatawa" Ta furta a sanyaye. Furucin yaja hankalin motii a kanta. "Marayun mata?" Ya sake tambayarta. Murmushi ta saki tana dubansa. "Eh.......ina da burin ya auri saamee Allah ya taimakeka......saidai hakan baya nufin na tursasashi.......zan bashi dama har sanda zaiji ya gamsu,zan bawa saamee dama itama idan tana jin zata iya riqe soyayyar ita kadai.....kada kace komai don bazan tilasta daya daga cikinsu ba,duk yadda nakai gason wanzuwar abun" Idanu ya zuba mata sosai,yana jin kamar ya hadiyeta. Komai nata akwai sauqin kai a ciki,komai nata akwai hankali nazari da kuma fahimta,bata da zafafawa akan komai,mu'amalarta sassauqa ce,iya wannan yana qara yawan sonta a zuciyarsa,yana jin bazai samu wata mace kamarta ba. (Yake me karanta wannan littafi.....muddin kina biyayya ga mijinki da kuma qoqarin kyautatawa tuquru,soyayya da zama bisa amana,ina roqa miki Allah ya kadaitaki a gidan mijinki......ya kadaitaki a zuciyarsa dama rayuwarsa gaba daya ki zama KE DAYA CE TAK!). "Zan aika jama'ata in sha Allah zuwa nan da gobe ko jibi zuwa madeena,zan yiwa sarkin Gibe da sarkin kaffa. Ki sanar da me martaba sarkin gumma don ya zama wakilin mahaifiya da d'an yar uwarsa" Murmushi ya qwacewa nanay......yadda motii ke girma ahalin yunnus jallata na dada burgeta,har yau har gobe ba abinda ya sauya. Yayanta sarkin gumma motii yana kallonsa ne a matsayin mahaifinta,duk da kuwa kusan sa'anni suke da junansu. Murmushi ya saki,ga jawota kadan yana rungumeta cikin jikinsa zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 84* "Ya kamata a samu yawaitar shaidu......kowa yasan ibrahim aba jifar ya aurar da sheikhun malamin d'an nashi,duk da mun boyewa sultane har yanzu baisan nine asalin mahaifinsa ba.....har yanzu kuma baisan daga wanne DANGI daga wanne AHALI haisam ya fito ba......duk wani hidima da shirye shirye zasu biyo baya......ba abinda xan hanaku aiwatarwa khadeeja......haisam na musammanne,kuma na dabanne a raina" Kanta ta ajiye a qirjinsa tana sauke ajiyar zuciya,gurin da kullum idan ta sanya kanta a gurin sai taji wata tarin nutsuwa da kasancewa cikin aminci a zuciyarta da jikinta. "Allah yayi mana zabi mafi alkhairi,ya shige mana gaba" "Ameen......a ranar ina da tafiya duba mutancan da asara ta samesu na qauyencan,inaso a duba yadda za'a biyasu diyya su rage radadin asarar da sukayi" Hannunsa ta matse cikin nata tana sake alfahari da kasancewarsa mijinta uban 'ya'yanta. Ba shakka da yawa daga cikin halayen nagartar haisam daga gurinsa ya gado. "Allah ya qara maka suttura arziqi da rufin asiri" "Ameen ya rahman ya raheem" Ya amsa mata yana jin wani farinciki yana ratsashi. *WHEN FATE SPOKE IN MASJID ANNABAWI* _(MADEENA ALMUNAWWARA)_ Tun asubahin ranar juma'a ya fita kamar yadda ya saba duk lokaci irin wannan don samun sallar juma'a a masallacin ma'aiki a guri na gaba daura da liman. Duk kuwa kasancewar yana cikin jerin sahun manyan mutanen daka iya tsaiwa dab da liman a kowacce sallah,amma yafi zabar sammako don dacewa da dukkan falalar da ranar ke dashi. A yau din juma'ar ta zame masa ta daban,juma'ar ta zame masa ta musamman,juma'ar da yakejin kamar itace juma'a ta farko a gurinsa. Da qyar a jiya bobbo ya tilastashi kan ya koma masauki yayi bacci koda na awa uku ne kafin asubahi tayi. Baisan iya adadin addu'ar da yayi akan auren ba a kwanaki ukun kacal,baisan iya adadin rahamar Allah daya nema ya sauka akan auren ba,kariya da albarka. Baisan kalar addu'ar samun shaquwa da qauna me zurfi da yayi ma ma'auratan ba. Tunda ya sani.....wani aure ne da dukkaninsu zaizo musu da wani bahagon yani bahagon al'amari. Yasan haisam me sauqi ne,kamala dattako da sanin ya kamata,ya san muddin maganan sauke haqqi na iyali da kulawa ake magana akai bazai bashi da haufin khadeeja dinsa ta gama samun dukkan wadannan,saidai bayan wannan din......yanaso ta samu SOYAYYA soyayyar ma irin ta haisam daya tabbatar muddin ta sameta ta gama samun cikakkiyar kamala dacewa da jin dadin duniya harda na lahiran ma yana sanya mata rai. Shi kansa bobbo muhammad dawud bai sake gasgata yadda sultane ya dauki girman al'amarin ba sai da baqi suka iso daga agadez. Aqalla mutum biyar dukkaninsu saboda halartar daurin auren da kuma sauke umra. Sun hadu da sarkin nigeria daya kasance amini na sosai ga sarki sultane.....wanda a take ya baiwa muhammad sunusi lamido sunusi waliccin daura auren da zaa daura din bayan kammala sallar juma'a a masallacin manzan Allah. Sarkin Cameron Gabon da ghana dukkaninsu suna hade a gurin,wanda kusan ibadar umara ce ta kaisu abun kuma yazo a daidai. A gefe ga sarakunan Ethiopia din da motii ya aiko wakilci,abun ya zama na SARAKAI kawai.....sarauta kawai ke magana. A babban hotel na five-star hotel dake dab da haramin madeena sukayi masauki dukkaninsu. Royal suit dake dauke da dakunan alfarma. Cikin babban parlor din da yake dashi,ana raha da hira irin ta manya.....hira irin ta sarakai hira irin ta tsaffin abokai,an saje gaba daya harma da wanda ba'asan juna ba. Shiga ce ta alfarma jikin kowannensu,sutura dake nuna zallar sarauta da kashe ido,sassanyan qamshin turarukan da zai nuna maka manyan mutanene kawai a gurin,masu ji da ilimi dattako mulki dama sarauta din gaba daya. A nutse sultane yabar gurin yana fita zuwa private balcony din da suit din yake dashi,ya ciro wayarsa yana laluben nannie. *AGADEZ* Tun a daren jiya da sultane ya gaya mata abinda ya yanke da yadda komai ya gudana tsakaninsa da haisam ta kasa bacci. Ta rasa da wanda zatayi maganan,don ya umarceta dayin shuru har zuwa sanda komai zai tabbata. Yace don wannan din HUKUNCINSA Ne baya buqatar wani gyara ra'ayi tsaiko ko dakatarwa.....koda kuwa daga bakin AKHNAN dinne. Tayi imanin koda morsa safiyya itama bata sani ba.....ta tabbatar inda ta sani tabbas zata ganta tazo gareta.....zata ganta tazo gareta don kawai ta fadi mata. Murmushi nannie ta saki,haka kawai takejin wani farinciki da nishadi da batasan na meye ba,haka kawai takejin wani abu me dadi yana ratsa zuciyarta tun safiyar ranar. Abu daya tayi shine ta kira aisa kan tanason ganinta a yau juma'a,tace tabar kome takeyi ta iso agadez kafin sha biyu na rana,ta siya ticket ta biyo jirgi. Ta san tabbas sai an samu tashin qura,so dole Akhnan din tana buqatar su aisa din a gefanta. Aisa din taso bata uzurin matsalan da company yake ciki da kuma ganin cewa kwana nawa duka duka da komawarta amma nannie bata tsaya sauraren wannan ba. Idan ta tuna da waye sheikh muhammad haisam din,sai taji tabbas ne ya dace.....ya cancanta........an ajiiye qwarya a gurbinta. Tana kammala sallar walaha qarfe goma da rabi na safe kiran sultane din dan uwanta shaqiqi ya shigo mata. Da cikakkiyar sallama,muryarsa da tata dukka wani irin wasai suka amsa da junansu. "Imam da wazeer dukka sun qaraso ko?" Kai sultane ya gyada. "Dukkaninsu muna tare,nan da mintuna talatin zamu wuce masallaci in sha Allah......" "Allah ya tabbatar da alkhairi,yasa wannan din ya zama sanadin zuwan qarshe duk wani damuwa tata da gyaruwar komai". "Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ya amsa mata sannan ya dora. "Na gode......fatima.....inaso Akhnan ta shaida d'aurin aurenta da idanunta,bawai don ban ban isa bane....aah.....inaso ta samu yaqini da tabbaci har cikin jinin jikinta......inaso ya zama rubutacce cikin idanunta da zuciyarta cewa ita din mallakin sheikh Muhammad haisam ce ta har abada......ki shaidawa morsa safiyya,ki shaidawa zaituna,ku isa sashenta,zan kiraki ko kuma ita na kirata,ina buqatar ki ajiye mata video call din a gabanta don ta shaida komai" Kai nannie ta gyada a hankali. Har ranta taji hakan yayi,hakan kuma zai sauqaqa musu komai.....zai sauqaqa musu wani bayani na gamsar da ita faruwar komai. Basu jima ba suka yanke kiran,ta miqe a nutse ta sanya aka nemo mata aisa da shehnaz......sannan tayi tattaki zuwa sashen morsa safiyya da kanta,bayan an tabbatar mata mammina din bata gidan,ta fita tunda safe duba marasa lafiya gami da basu tallafi,kaman yadda ta saba tana yi lokaci lokaci. Ta samu morsa safiyya din da baqi,saidai tana kan sallamarsu sanda ta shigo,don haka ta samu guri ta zauna tana monitoring yadda morsa safiyya din zataji da labarin. Yanayinta yana burgeta,komai zatayi na kyauta sadaka ko kyautatawa tanayin abinta ne a qunshe cikin sashenta,ba tare da kowa ya sani ba sai wanda akayi abun dominsa wato Allah da kuma shi wanda aka taimakawa din. Wani irin yabo take samu a zukatan al'ummar agadez,wanda ba kowa yasan dashi ba,wani irin matsayi na yadda take lullube asirin ne neman taimako,ta taimaka da dukkanin iyawarta ba tare data fallasa asiri ko ta bayyanawa duniya kalar buqatar ka ba. "Saqon alkhairi nake tafe dashi" Nannie ta fadi tana murmushi idanunta akan morsa safiyya. Murmushi ta saki itama.....bataji wani tashin hankali ko d'arrr ba,don mafarkin da tayi daren jiya har yau yanzunnan shine a ranta. Dalilin daya sanyata fidda sadaka me yawa kenan a safiyar juma'ar yau ta bayar,duk da dama ta saba,halinta ne kuma dabi'arta ce. A daren jiyan taga safeena cikin wani kyakkyawan yanayi,cikin farinciki tarin walwala da annashuwa,cikin taron wasu mutane dake da kyakkyawan shiga. Sunyi hira me yawa amma bata iya tuna komai da sukace,abu daya ta iya riqewa a kanta. "Na gode safiyyah.....ina cikin farinciki sosai yau,kinga kowa ma yana tayani murna?.....ki gaidamin khadeeja,ina kewarta,duk dadai tana kawomin ziyara ma". Maganan ya tsaya mata sosai a rai,saidai hankalinta be tashi ba,saboda koma meye tasan alkhairi ne. Mafarki mamaci yana cikin farinciki da taron jama'ar da suke cikin kyakkyawan kamala da siffa alkhairi ne ta sani.....saidai maganan khadeeja daya tsaya mata arai,don ko bayan ta farka a wannan mafarkin mafarkin khadeeja din tayi,saidai ita din daga nesa suka hango juna,sunata yiwa juna murmushi a wani guri da suka saba haduwa a shekarun quruciyarsu suyita wasa,har sai falmata ko bilkeesu maman khadeeja din ta sanya bayi sun daukosu. Idanunta akan khadeeja sai kuma taga ya juya ta shige wani guri,ta bita da sauri amma bata ganta ba,tana tsaye taji ana jan hannunta zuwa hanyar,batasan waye yake jan nata ba kiran sallar asuba ya farkar da ita. "Allah yasa muji alkhairi" Safiyya ta fada tana zama gefan nannie. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Alkhairi ne safiyya.....don kuwa a wannan juma'ar sultane ya yanke shawarar daura auren diyarmu Akhnan da sheikh haisam a masallacin madeena" Idanu morsa safiyya ta kulle gam gam,wai tanaso ta tabbatar da cewa mafarki take ko idanu biyu ne?. Dama sultane yayi accepting maganar yayi mata shuru kamar bai gamsu ba?,dama sultane ya gamsu da abinda ta fada amma yayi bakam kamar bai gamsu ba?. Bata kai ga bude idanunta ba ruwan hawaye suka silmiyo mata. "Kuka safiyya?.....baki ganin gurin akwai hadimai?" Nannie tayi saurin fada tana riqe hannunta. Idanun ta bude murmushi yana mamaye fuskarta. "Duk wanda ya yarda da Allah bazai taba tozarta ba......duk wanda ya damqa amanarsa a hannun Allah ubangiji bazai taba cin wannan amanar ba.....ubangiji ba maciyin amanar bayinsa bane.......sai yanxu na sake tuna maganan da mukayi jiya safeena a mafarki.....wadannan kalaman tayita maimaitamin.....kana mace ko kana raye muddin zaka bawa Allah amanar rayuwarka dama amanar abinda ka mallaka....lallai ne Allah xai cika wannan amanar musamman ga zukatan da suka miqa wuya ga Allah.....ba kokwanto.....ba shakka......ba munana zato.....nannie,ko a yau na mutu burina ya cika.....nasan gudar halittar data ragewa safeena da qarfin ikon Allah ta kubuta.....ta kuma tsira" Morsa safiyya ta fadi hawayenta suna qaruwa tana kuma riqr da hannun nannie sosai. Dubanta sosai nannie takeyi,ta gane zancanta,amma bata fahimci maganarta ta qarshe me take nufi ba,amma farincikin dake ranta,dama abinda yake gabanta ya shafe komai,ya shafe tsayawa sauraro ko neman fashin baqi. "Zaki iya shiryawa muje gareta?,don sultane yana son ta shaida komai a idanunta" Murmushin nan yana kwance saman fuskarta ta zame hannunta daga cikin na nannie. "Banaso naci gaba da bata alaqata da d'iyata.....bayyanata a yanzun a gurin bazai bata daman kwantar da hankalinta ta fahimci abinda akeso ta kalla ba.....zan shigo daga baya....sanda komai ya gama bayyana a idanunta....inanan tafe koda zata gutsiremin kai. Kome akhnan zataji a kaina tuwo sunansa bazai taba canzawa ba....". Kai Nannie ta gyada tana miqewa a hankali,ita kanta tana jin wani iri,tana jin ba dadi na yadda har yanzu alaqa taqiyin kyau.....taqi daidaituwa tsakanin morsa safiyya da akhnan din,duk kuwa da cewa a gabanta ta girma.....a gabanta ta zama mutum,bawai baqin juna bane ga rayuwar kowannensu. *AKHNAN* Cikin lafiyayyen daya daga cikin bedroom dinta cikin bedrooms din da take dasu daban daban har guda uku take kwance. Bedroom ne dake dauke da wani irin weather me sanyi da dadi.....bedroom din da tattausan qamshin turarukan icce dana ruwa da tsirrai na kamfanin INCENSE BY KABO DAUGHTER 0803 211 9803 ya kama dukkan wani curtain duvet bedsheets dama towels harda lallausan Chinese Carpet dake malale tsakiyar dakin. Hatta da pillows dinta qamshin ya kamashi sosai,batasan da hakan bama sai a kwanakin nan data koma kwana a dakin,don tabar kwana sauran bedrooms din,saboda dukkaninsu ba wanda bai bata bad memories ba. Tsakiyar lafiyayyen royal bed din take kwance rub da ciki,ta toshe kunnuwanta dukka biyun da earpiece tana sauraren waqar nan tata ta love story. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 85* Ta love story. Sanye take da qananun kaya.....Palazzo ne a jikinta da kuma crop top wadda hakan ya bawa plate tummy dinta bayyana sosai kaman zai hade da bayanta,kamar bata zubawa cikin nata wani abu me suna abinci a cikinsa. Gashinnan nata na asalin BUZAYE me tsahon da ya sauka har kusa da mazaunanta ya baje saman pillow din data dora kanta akai,wani kuma ya sauko a sashe da sashen fuskarta,har yana neman tsone mata idanu,lokaci lokaci tana sanya hannunta tana maqale shi a bayan kunnenta. Kyawawan idanunta suna rufe,tana sauraren waqar da tunanin zata samu sassauci zata rage kewa kamar yadda ta saba,amma kuma a yau sai takejin gaba daya waqar tana mata wani irin sautin amo mara dadi,kamar ma tana sake dagula mata sauran lissafinta da d'an guntun nutsuwar da kwanciyar hankalin data samu. Siririn tsaki taja,ta zura hannunta tana zare earpiece din daga kunnenta,kaman hakan kuwa ake jira taji an fara knocking na qofar tata. Manyan fararen idanunta masu sirkin blue ta bude cikin dakin dake da matuqar qarancin duhu ta zubawa qofar dakin idanu. Wasu sakanni suka biyo baya anaci gaba da knocking din can qasa kamar ana tsoron buga qofar ne. Ranta ya sake baci.....me yasa idan ta sanya dokar kada a nemeta kuma kada a dameta su birra ke gaza kiyayewa a kwanakin nan?. Bata buqatar kowa.....bata buqatar magana da kowa,jiran dawowar sultane kawai takeyi. Sultane kawai take dako,ya dawo su fahimci juna ta tattara ya nata ya nata ta wuce Niamey ita kuma da agadez ba rana ballantana wata,wataqila sai kuma zagayowar wani festival de l'Aïr din. Batace ma mai bugun ko cikanka ba,har sai data miqe a nutse tana gyara zaman shirt din jikinta data bayyana dukiyar fulaninta da suka cika qirjinta sosai kamar sun raina fadin rigar,wanda banda ta gurin qirjin kota ina rigar tayi mata daidai,ta sanya hannunta ta tattara sassalkan gashinta guri daya ta daure da siririn band din data cire ta ajiye gefa a dazun don taji dadin kwanciyar,ta zira qafafunta qasa cikin tattausan royal bedroom flip flops dinta. A yangance da wannan yanayin nata mai cike da qasaita me yawan gaske ta furta. "Waye ne?" Cikin harshen faransanci da ya zauna sosai saman harshenta da wani irin qwarewa da gwaninta. "Birra ce ranki ya dade" Ta amsa mata cike da ladabi da kuma yaren faransancin. Dokarta ne tama magana da wani yare ka maida mata amsa da wani yaren daban,koda yarensu na buzaye kuwa. Bata qaunar jahilci don haka duk cikin hadimanta na kusa ba wanda baiyi karatu ba,ba wanda bayajin faransancin tas a bakinsa. Don ko sanda zata tafi France karatu da dukkaninsu su biyar din ta tafi,kuma ta sanya kowacce a makaranta daidai da matsayinta,ta rarraba musu lokuta yadda bazaici karo da lokacin hidimarsu a gareta ba. Shuru tayi kaman ba zata amsa ba....wanda banda da birran take magana inda wani ne da yake baqo ga sanin halayyarta zai tafi ne ya dauka ba zata amsa din ba.....sannna ta sake magana tana saka qaramar hula me sauqi saman gashinta. "Yaushe kika fara karya doka da umarnina ne birra?". Ta fadi da wannan muryatata dake cike da yauqi da gayu. Duk da bata iya ganinta amma hakan bai hanata rusunar da kanta ba "Kiyi haquri ranki ya dade.....an kammala hada ruwan wankanki ne". Mamaki kadan ya kama akhnan. "Sau nawa zan maimaita miki idan ina buqata zan sanar miki?" "Eh na sani.....bawai ina jayayya dake bane.....nannie ce tace ki tashi ki shirya" Maganan ya sanyata dakatawa daga qoqarin bude scrub dinta da takeyi tana kallon qofar kai tsaye "Nannie kuma?.....zaki barmin qofar daki birra ko saina hukuntaki?" Maganan ya sanya birra janyewa babu shiri ba kuma tare data sake cewa komai din ba. Wani siririn tsakin ta saki,wankan zatayi din......amma izzarta ba zata barta ta tsaya yiwa birra bayanin saita gama goge gogen fuskarta da cleansers dinta da take amfani dasu ba kafin ta shiga din,wanda aqalla suna daukarta kusan minti talatin kafin ta gama hidimarsu ta shiga wankan gaba daya. Stool ta jawo ta zauna gaban mirror din,sannan ta miqa hannunta ta kunna makunnin qwan dake zagaye da mirror din nata wanda ke bata haske sosai a duk sanda za'a gyara mata fuska ko zatayi wani abu irin haka. A cikin jininta yake,son ado da gyara,tana kula da lafiyar jikinta da kuma fatarta sosai fiye da kima,wannan ya sanya ba wani halitta da zai kalleta bai sake marmarin kallonta ba,mace ko namiji babba ko yaro. Ta mallaki dukkan wata sura ta kyau,wata irin lafiyayyar fata diri da zubi da kowacce mace zata buraci inama ace nata ne?,sai ya hadu da mulki sarauta izza da kuma dukiya.....uwa uba gata da kwanciyar hankali,wannan ya bawa dukkanin siffofin damar fitowa dayin tasiri yadda ya kamata a tattare da ita. Knocking ta qaraji anyi,zuwa yanzu ta fusata da wannna fusatacciyar zuciyartata. Ta waiwaya a hankali ta lumshe idanunsu ta kuma budesu lokaci daya tana bude bakinta da zummar yin magana,saidai kuma batakai ga cewa komai din ba hairaan ta murza qofar ta tura ta shigo. Dama a bude take qofar,saidai kuma ba wanda ya isa ya shigo din idan bada izininta ba. Idanunta suka gauraya daya hairaan,saita janye dubanta a kanta a hankali tana maidawa kan dressing table din. Batasan me yasa ba.....hairaan din tana mata wani nauyi.....tana dan jin shakka kadan kadan a kanta,batasan ko abubuwan da suka dinga gudana tsakaninta da ita zamanin quruciya bane yayi tasiri?. A nutse hairaan tayi sallama a yau din,ba wani qorafi fada ko mita ta dubi akhnan din. "Ki ajiye wannan aikin,ki shiga kiyi wanka....so samu ki shirya yau da kanki,yau dai sau daya tak.....amma idan hakan ya gagara birra zata shigo ta shiryaki yadda kika saba" Hairaan ta qarashe maganar tana ajiye wasu kayayyaki da akhnan din batasan meye ba saman bedside drawer. Bin hairaan din tayi da kallo sanda taga ta juya salin alin tana fita a dakin ba tare data sake ce mata komai ba. Ta danyi mamaki,don ta saba duk sanda zasuyi face to face haka bata gaidata ba sai tayi magana.....hakanan sai tayita qorafi da mita kamar zata balbaleta da fada. Zuwanta ne kawai qasar wannan karon ya sassauta wasu abubuwan. Haka kawai taji jikinta yayi wani iri sanyi. Duk abinda zai hana hairaan qorafi haka to lallai babba ne. Samun kanta tayi da saka hannu ta ciro dump face wiper ta goge scrub din data fara shafawa,ta miqe daidai sanda birra ke shigowa. Ido ta zubawa birra din,kanta a qasa taqi duban uwar dakin nata tazo ta giftata zuwa toilet don hada mata sabon ruwan wanka a nan. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Har ta fito tana tsaye,ta sake binta da kallo. "Saboda nace a qyaleni bazanyi wanka yanzu ba shine kikaje kika fadiwa titi hairaan?" Tayi tambayar da wani irin quruciya da sakalci cikin muryata,wanda ba kasafai wannan sifar ke nunawa a tattare da ita ba.....duk da lokaci lokaci takanyi abubuwa da yawa da birran ke hangen quruciya sakalci da ta taso a ciki,wanda idan itace ba zata yisu ba. Fushi taqiyin wani abun,ko fushi tayi wani abun duka wani lokaci birran ke boye tayi dariya. Duk inda izza da sarauta suke a jikinka,indai akwai wannan gatan ya maka yawa.....indai akwai wannan quruciyar lallai wataran saita bayyana kanta da kanta. "Kiyi haquri" Kawai birra tace da ita,saita gyada kai kawai taja qwafa tana nufar bandakin. Har takai qofa ta dakata,ta waiwayo tana qarewa birra kallo. "Waime meye na sanyani a gaba yau nayi wanka?,bayan ina da dukkan zabi nayin yadda nakeso a sanda nakeso naga dama?,ko wani sabon munafuncin ne?,naga fuskarki kamar kina murmushi?" Akhnan din ta fada still yanzu ma da sakalcin nan sosai a tattare da ita. Allah ne ya taimaki birra,kadan ya rage murmushi bai fita a fuskarta ba. Tunda samia baiwar morsa dake hidima a sassanta ta tsaigunta mata maganar da taji anayi ta samu kanta cikin matsanancin farincikin daya gaza boyuwa. Ta sake samun tabbaci sanda nannie ta shigo sassan,ta kuma wuce can kebantaccen parlor din akhnan din dake qasa,wanda ita daya ke shiga ciki saiko su shehnaz,ta kuma kirata ta gaya mata dukkan abinda take buqatar ayi. Ganin birran bata amsa mata ba,tsaiwar kuma kamar tana bata mata lokaci ne sai kawai taja tsaki yana wucewa cikin toilet din qasa qasa tana gunaguni. Tsalle birra ta buga ta sake juyawa. Sukam tako ina sheikh muhammad haisami yayi musu,ba ita daya ba,dukkan hadiman sashen da tasu tazo daya da suka fara tseguntawa juna kowa tsalle yake bugawa. Kai tsaye ta juya zuwa sassan walk-in closet din akhnan din,ta shiga lalubar mata kayan da zasu dace da yanayin,wadanda ba zasu nuna wani gagarumin abu ba,ba zasu kuma takurata ba a dukka yanayin rudanin da zata shiga,don ta tabbatar rudani kam akwaishi.....daaru na akwaishi,kallo kam su hadiman da suke kusa zasu shashi,fatan da takeyi kome zai biyo baya yazo da sauqi,ya kuma zamanto me sauqin gaske ga uwar dakin nata. Don har ga Allah suna sonta,suna qaunarta qwarai da gaske,tana da tarin akkhairanta garesu,tana da matuqar kirkin da idan kana nesa da ita ba lallai ka fahimci hakan ba,sai zama ya kawoka kusa da ita,kuma ka zauna da ita lokaci me tsaho. Wasu dabi'un nata basa damunta,tunda ita din an haifeta cikin gidan sarauta ne,tasan duk wasu dabi'u da halaye da JININ sarauta ke sanya diyoyinsa aikatawa,wanda haka yake kawai a dabi'arsu,ba rashin kyautawa bane,gado ne kawai a cikin jini ya zame musu normal life. Kaman kowanne lokaci wankanta yakan dauki lokaci kafin ta kammala. Tazo ta zauna birra na tayata shiryawa,harta kammala. Kayan data bata ta sanya ya sakata daga kai ta kalli birra din,kamar zatayi magana amma sai kuma ta fasa ganin birra din ta saukar dakai qasa. Tsaf ta fita cikin wani cotton material me asalin tsada da daukan hankali. Butter milk me adon red roses manya a jiki. Daga qirjinsa yasha wata tattarar roba,wadda take bawa rigar daman budewa daidai da fadin qirjin wanda ya saka rigar. Cup hand ne da rigar wanda duka duka iya damtsenta ya tsaya,ya bada wani style me kaman cup. Earrings ta miqa mata red color ta saka a kunnenta a hankali,idanunta still yana kan birra dai,birran daketa nuqu nuqu tana qoqarin boye duk wani baqon mode nata. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 86* Sake kallonta tayi sanda ta miqa mata awarwaraye da suka dace da kayan jikinta. Ta zubawa birra din idanu,haka kawai takejin yau bata yarda da birra ba,haka kawai takejin wani baqon yanayi a tattare da ita. "Maidasu basai na saka ba" "Nannie tana dakin hutu tana jiranki" Birra tayi saurin fadi ganin akhnan din ta juya a hankali tana nufar sashen da aka ware mata cikin tafkeken dakin da wasu qawatattun kujeru biyu da mulmulallen table saboda daura tarkacen system dinta da sauransu akai. Cak ta tsaya ta waiwaya tana duban birra,still taqi bari su hada idanu. "Tun yaushe kika barta tana jirana?" Ta fadi Kai tsaye. Sosai take ganin girma da kimar Nannie,don soyayyar da Nannie din take nuna mata a bayyane take. Uwa uba daga sultane har mammina tana ganin irin yadda suke girmamata. Dan sosa kai kadan birra tayi tana kaucewa hada idanu da ita. "Kafin ki shiga wanka ne......kuma itace tace kije kiyi wankan ai". Idanunta ta maida ta lumshe. Ta manta sai yanzun da birra ke sake gaya mata. Amma haka nan takejin wani faduwar gaba da bata saba da ita ba,ta taka anutse da wannan qasaitartata,ta isa inda takalman da birra ta ajiye mata suke,ta zura dogayen qafafunta da suke subul kamar bata taba taka qasa ba tunda aka haifeta. Da dan mamaki kadan a ranta sanda take ratsa falukanta ganin hadimanta kusan dukka suna nan. Kamar tun dazun basuyi ayyukansu bane sai yanzun. Kadan kadan take amsa gaisuwarsu,murya can qasa cike da wannan izzar. Tayi wani iri kyau,fuskarta tayi fayau saboda damuwar data shiga kwana biyu. Material din ya karbeta,ya kuma fidda qirarta da kyau. Bata yada mayafin da birra ta miqa mata ba,ganin bawai wani guri zata fita ba,tayi gaba ne tabar birra da mayafin a hannu tana binta dashi. Tayi wani irin kyau wanda va zaka gaza ganinsa ba koda daga ness ka hangeta. Wani irin sassanyan kyau take dashi,wanda yake iya fusgar hankalin d'iya mace ta maimaita kallonta akan akhnan din ballanta namiji. Qirarta ta fita sosai kamar wadda sam sam.bata cin abinci a rayuwarta. A haka take takawa a nutse zuwa kebantaccen falon nata wanda takeson xama sosai a cikinsa saboda ba abinda ya rabashi da cikin mini garden din datasa aka mata a gefan parlor din sai wata glass door me murfi biyu. Idan tanaso tana budeta,iska me kyau tana shigo mata,sai yanayin yake sake qawata zamanta a gurin. *_WHEN THE CALL CHANGED HER LIFE_* Da siririyar sallama a saman siraran labbanta da suke qyalli da hasken lip gloss ta tura qofar falon. Daidai sanda Nannie dake zaune gaban system din da aka aza saman side table din da aka jawoshi gaban three sitter din da take zaune ta zube idanunta akan akhnan dake shigowa. Wani irin kyau.....wani irin haske da qyalli taga akhnan din tayi mata. Sai take ganin kamar ba akhnan din data gani bace jiya.....kamar wani abu ya sauya tattare da ita. Fuskarta ta nuna GIRMA irin girman dake hawa kan kowacce mace a sa'o'in da aka kammala daura aurenta......gashi yanzu tana ganinsu muraran a fuskar akhnan din,duk da ana kan daura auren ne ba tare da an kammala ba. Mamaki ne ya darsu akan fuskar akhnan din,ya kuma bayyana kansa da kansa ganin aisa da shehnaz harda falaak a gurin. Gefe daya ga Nannie data dasa system a gabanta abinda bata taba gani ba tattare da Nannie din. Don ita ko waya bata dameta ba,idan kaga waya ta dameta to tabbas dan uwanta sultane ne ya kirata ko ita take nemansa. Daga gefanta kuma yakumbo ce. Yakumbon da take jimawa bata ganta ba saboda shekaru da suka fara ja,saidai kuma dattijuwar a nutse take tsafff.....akwai tarin nutsuwa tattare da ita....hangen nasa da hikima gami da tarin ilimi me yawa a tattare da rayuwarta. "Yakinan.....qaraso" Yakumbon ta fada tana yafitarta da hannu. Haka kawai taji gaba daya gwiwoyinta sunyi wani irin sanyi......yadda suka zuba mata idanu a yau sai takejin kamar idanunsu sun mata kwarjini da yawa. Mamakinta ma yadda aisa din tazo amma bata nemeta ba,yaushe ma aisa din tazo?,yaushe ta bar agadez harta dawo ba tare da ita tasan zata shigo ba?. Kodai festival d l'Aïr dinne ya kawota tun yau?. A hankali take takawa tana maida dubanta ga yakumbo,kafin ta qaraso Nannie tuni ta miqe,ta kuma kamo hannunta har zuwa gaban kujerar da suke kai,har kuma gaban system din da ta zaunar da ita a tsakiyarsu ita da yakumbo. Sai a sannan idanunta suka sauka kan screen din,fuskar sultane ya bayyana tarwai cikin masallacin madeenar daya bada background me kyau da haske,kaman yadda kowa ya saba ganinsa. Idanunsa ba screen din yake kalla ba,idanunsa suna gaba da screen dinne,amma zamanta a gurin ya sanya sultane din saka qwayar idanunsa a kanta a nutse,abinda ya sanya taji wani abu ya tsarga mata tun daga saman kanta har qafafunta,kafin ta sakeji ko fuskantar komai ya karkatar da fuskar tablet din zuwa ga inda idanunsa suke. Daya bayan daya takebin mutanen dake zaune saman lausasan carpet din masallacin da kallo. Daidaiku ta gane,kaman imam dinsu da wazeer. Kanta ya kulle da yanayin data gansu a zaune sunyi da'ira. Zaman kaman na masu daukan karatu,idan kuma ta lura da kyau ma kaman wata tattaunawa sukeyi a tsakaninsu,kafin kuma taga an ajjiye daurin kudi CFA dinsu me yawa da daurin goro da wasu kwalaye data fahimci alawa ce a ciki. "Me sukeyi ne haka?,me sultane yake nunamin?" Ta tambayi kanta da kanta ba tare data iya fidda tambayar sarari ba saboda yadda taji tana neman shiga rudani. "Daurin aure ne" Taji zuciyartata tana bata amsa saboda tunawa data tabayi. Cikin wani film data taba gani shehnaz na kalla ta taba ganin irin wannan zaman,don itadin ba ma'abociyar kalle kallen finafinansu na gargajiya bace. Fina finanta dukka basa wuce na fada da gwagwarmayar rayuwa,saina soyayya da takan kalla a sace gudun kada su aisa su sanyata a gaba. "Ni sarki abubakar al'assad.........na bawa sheikh muhammad haisam ibraheem auren d'iyata khadeeja muhammad hammud.......bisa sadaki na sisin gold dubu d'ari da hamsin,lakadan ba ajalan ba,bisa sharadin ciyarwa tufatarwa da Matsugunni......bisa kuma sunnar annabi muhammad S A W". Yayi maganar cikin girmamawa yana duban bobbo muhammad dawud dake sanye cikin manyan kaya da suka sake kwarxantashi. "A matsayina na waliyyin muhammad haisam.....na karba masa auren 'yar abokinmu khadeeja,bisa sunnar ma'aiki S A W da kuma yarda da duka sharuddan da addinin musulunci ya tanadar mana". "Kun amince?" Me martaba sarki abubakar al'assad ya fadi har sau uku,bobbo muhammad dawud yana fadin "Mun amince mun karba" . Sai sarki abubakar al'assad ya juya zuwa ga sauran dake zaune a guri dama hausawa da mutanen niger da suka marmatso wadanda jin auren diyar sarkin agadez ake daurawa a gurin wanda wasu daga cikin su tuni suka fara nad'ar recording na video don su samu abun dorawa da bada labari.....sai ya dan daga sauti kadan daidai da yadda kowa zaiji yace. "Jama'a kun shaida?" Har sau uku nan ma kowa yana amsawa da "Mun shaida" "Ma sha Allah,salati goma ga annabi". Sarki abubakar al'assad ya furta yana hada hannuwansa guri guda ya fara karanto sigar daurin aure. *HAISAM* Baya ya koma a hankali yana jingina bayansa da sofa din da yake kai. Bai taba yarda da gaske aure wani abu ne me girma da nauyi ba sai a yanzu daya tabbatar kammaluwar bayarwa da karbar sadakin da baisanma wanda ya biyashi ba ya gama maida akhnan din sunan MATARSA HALAK MALAK ba sai yanzu. Abinda yakeji a dukka jikinsa dama kansa bai dauka zaiji wani abu me nauyi kwatankwacin wannan ba. Aikin na nasaeeb ne,yana Riyadh gurin wani aiki da aka turashi gurin aikinsu,ya katse dukkan abinda yakeyi yayi tattaki har zuwa madeena,yayi umra kuma yayi joining wadanda suka zauna don shaida daurin auren,takanas kuma ya kirasu sanda yake tare dasu omar. Su sunsan da kiran.....shine kawai abun yazo masa a bazata. "Congratulations captain" Ya tsinci muryoyinsu a sanda bai taba zata ba. Da hanzari ya buden idanunsa,sai suka sauka akan khadeem......mutallab da Amjad. Idanu ya zuba musu,kaman yadda suka zuba masa idanu. Wani murmushi na fita a fuskarsu,wanda a hankali tasa fuskar ta soma washewa da murmushi. Miqewa yayi da wani irin kuzari da zafin naman daya rasa a dazu ya qarasa gaban khadeem yakai masa wani naushi da hannu,sai khadeem din ya tare yana dariya,sai kuma suka cakume juna suna huggin din juna. "Komai Nisan inda kake obbo....komai nisan tazarar dake tsakaninmu hakan bazain hanamu zuwa a lokaci me muhimmanci irin wannan a rayuwarka ba. Koda ma yaya ne kayi auren nan congratulations.....congratulations once again Capt sheikh" Amjad ya fada yana suna sakin juna shida haisam gami da sake bawa junansu hannu sukayi musabaha me zurfi da kyau. Yasan wannan aikinsu maleek ne.....yasan sunsan da komai,sun kuma shiryawa komai,gaya masa ne kawai basuyi ba. Zuwan ya masa dadi,bai kuma San yayi kewarsu haka ba saida suka wanzu a gurin,sai kawai ya yanke su wuce zuwa personal home dinsa. Ya waiwaya ya dubi abdii da ya fahimci walwalarsa kawai yakeyi,da gaske farinciki yakeyi da auren ta kowacce fuska. "Idan ka kammala ka samemu a gida" "Tom in sha Allah" Ya fada yana hada kayayyakin da haisam din ya sanyashi hadawa. "Awa biyu ta ishemu,don dole mu dawo muyi sallar juma'a cikin gida" Haisam din ya fadi yana jin wani sassauci cikin ransa. *AKHNAN* Yadda dakin yayi shuru haka akhnan ta tsinci wani irin shuru cikin kanta. Shurun data jishi ne kawai bawai don ta gama fahimtar ahinda ma yake shirin faruwa da ita ba. Abu daya ne kawai ya tsorata tunaninta,yake kuma yi mata kai kawo. "Ina nemawa sheikh muhamamd haisam ibraheem auren d'iyarku khadeeja muhammad hammud.......na bawa haisam auren diyata khadeeja hammud?..... Wannan wacce irin rubututacciyar qaddar ce da zata hada sunayensu guri guda?.....wanne irin mummunan arashi ne da sunayen wadannan ma'auratan yazo iri daya nata dana wancan bagidajen malamin?......malamin da ko sunasa bata qaunar taji an kira?.....malamin da take da imani da kuma yaqinin yana dasa hannu gurin faruwar abubuwa da yawa a rayuwarta. Tushen baqincikinta shine....tushen takurarta,silar nesantata da masoyinta mahaifinta da bata da kusanci da kowa a duniya sama da irin kusancin dake tsakaninta dashi. "Wai meye amfanin zaunar dani a nunan wadannan abubuwanne?" Ta fadi tana raba idanunta tsakanin shehnaz aisa da nannie don batabi takan yakumbo ba,saboda tasan harkar na'aura ba cikin lissafinta suke ba. "Ke kika hadamin AI ko?" Akhnan tayi tambayar tana dage dukka girarata biyun tana duban shehnaz fuskarta na nuna tsananin bacin rai. "Amma dai wannan ba wasa bane shehnaz.....shine kika saka aka tasoni a lokutana masu muhimmanci irin wannan.......yakumbo" Ta fadi tana waiwayawa ga yakumbo din,saidai idanun yakumbo dake kanta ya daketa sosai. "Juya zuwa ga mahaifinki,yanason yayi magana dake" Yakumbo ta fadi kai tsaye da wannan dattijankar tata dake qara mata kwarjini itama. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 87* Wani mummunar faduwa gabanta yayi,kamar wadda aka riqewa wuya ta juya a hankali zuwa ga screen din karo na biyu tana maida dubanta ga sultane. Yana tsaye a wani guri na daban,a wani guri can wajen masallaci gefe inda ba zirga zirgar jama'a,ba kamar dazun da yake cikin masallacin ba. "Khadeejatu" Yayi kiranta da wani sauti,da wani yanayi daya sanyata shiga hankalinta tilas. "Na'am bappi" Ta samu kanta da amsawa da wata irin nutsuwar dole datazo mata,nutsuwar dake cakude da zallar tashin hankali daga can qasan ranta. "Haqqine na iyaye su zabawa yaransu mijin aure.....mijin aure na gari daya dace da rayuwarsu......na baki wannan damar duk da cewa ina da ikon yin hakan,haka ne?" Ya jefeta da tambayar data saukar da wani abu me nauyi saman zuciyarta. Qasa tayi da kanta,tana jin kamar ba abinda ya rage a duniya a sannan sai sautin bugun zuciyarta. "Haka ne" Ta amsa masa da wani irin nauyi,tsoro da tarin fargabar abinda zataji a gaban bayanan nasa,wanda tafi damuwa da qaguwa kawai yayi mata conclusion ba tare da wani tsawaita bayani ko shimfida ba. "To alhamdulillah....akwai wani haqqi dana tauyeki dashi tsahon haihuwarki kawo yau?" Ya tambayeta idanunsa car bisa kanta. Kai ta girgiza. "Da baki nakeso ki amsamin" "Babu" Ta sake amsawa muryarta kamar zata yanke daga maqogoronta. "Kin shaida har a gaban Allah baki da hujjar da zaki kai qarata gurin Allah?.....na cika miki komai.....na baki dukkan wata dama....na cike miki dukkan gurbi?". Kai ta daga da hanzari,maganar kaisa qara gaban Allah ta mata nauyi da yawa,amma sai ya sake tabbatar mata. "Eh.....baki da hujjar kai qarana gaban Allah?" Kai ta girgiza da sauri,hawayen da take qoqarin riqeshi ya silmiyo mata. "Babu bappi...babu,ka cika dukkan wani ma'auni,ka cika dukkan wani mizani,kai din uba ne daya tamkar da million,kaidin ubane daya cika dukkan ma'auni bappi". "To alhamdulillah.......a yau abu guda daya zaki sakamin dashi shine......zama gidan sheikh hasam.....rayuwa ta dindindin a mazaunin matarsa.......a yau ni mahaifin dana haifeki,na aurarwa da sheikh haisam ke bisa sunnar manzan Allah...sadakinki in sha Allah zan taho miki dashi na damqa miki,dukkan wanda ya dace ya shaida ya shaida.....dabi'ata tason bawa me haqqi haqqinsa ya sanya na saka a zaunar dake don kema ki shaida hakan,kuma alhamdulillah kin shaida,ki zauna kuma da shiri na komawa qarqashin ikonsa da kulawarsa,daga yanzu zuwa kowanne lokaci" Dif ya yanke kiran,ya kuma maida akalar kiran nasa ga morsa safiyya daya lura bata agurin,don yasan mammina bata nan. Shuru ya sake ratsa falon,kafin a hankali ta soma jin wasu maganganu a kunnenta. "Alhamdulillah,sai kiyi biyayya ga umarnin mahaifinki,donn yaron duk da bansanshi ba amma ya samu yabo qwarai daga bakin kowa.....ballantan sultane da nayi imanin bazai aura miki qasqantacce ba wulaqantacce b....." "Qasqantacce mana.....kuma wulaqantacce yakumbo,fadi ki qara fada!!!" Akhnan da take tunanin zata iya shanye abinda ta soma ji yana taso mata kaman zai hallakata ta fada cikin qaraji tana duban yakumbo. "Baida asali.....baida dangi.....bawa ne kuma hadimi kaman sauran hadiman dake gidannan......kamar sauran hadiman dake rayuwar qarqashin ALFARMARMU......shikenan ni na zama tamkar wata mara galihu?,shikenan saboda mahaifiyata ta rasu sai yadda akaga daman yi dani?" Ta furta tana nuna yatsarta da qirjinta. "Me yasa ya gaza fahimtar gwara ya auramin kowa da malamin can?.....me yasa ya kasa ganewa zuciyata da tasa ba daya bace?,don zuciyarsa taso shi ni ba dole na bane na soshi......bakusan me nakeji a qirjina ba ko?" Ta fada tana fashewa da kuka,idanunta cikin na yakumbo kamar itace ta aikata laifin. Tsam aisa ta miqe daga mazauninta,ganin maganganu sosai akhnan ke fadi kamar ma wadda tayi loosing control nata. Kafadunta ta kama tana zama daga bayanta. "Shuru mana akhnan?.....akwai nadama me yawa cikin magana cikin fushi fa!" "Dalla ki sakeni.....akwai wata nadama data ragemin aisa?....akwai nadamar da tafi auren malami ga diyar BASARAKE irin akhnan zama mafi girman nadama?.....idan akwai KI FADAMIN". Da gaske fushi ne yake neman cire akhnan daga saitinta,da gaske tashin hankali ne yake neman gigita mata tunani,don haka aisa ta zare hannuwanta daga kafadarta,hakan kuma ya bawa akhnan din damar miqewa da wani irin hanzari,aisa ta miqe itama,saidai suna taku daya biyu ana uku akhnan din ta sulale tana zubewa a gurin,Allah ya bawa aisa iko ta nufeta tana tarbeta a hannuwanta suka zube qasa tare aisa din tana qwalla kiran sunanta kusan lokaci daya da kiran sunanta da shehnaz tayi,abinda ya sanya dukkanin wanda ke parlor din miqewa yayo kanta. *HAISAM* Duk wani shaqiyanci da suke masa yana jinsu. Duk wani shaqiyanci da suke masa yana binsu da idanunsa ne kawai. Suma sunsan bazai ta ka din ba,saidai abinda basu sani ba nasa tunanin yana nesa dasu,yana can gurin kallon da tunanin QADDARAR yau me zata canza?.....rayuwar wa zata canza?,rayuwar wa zata taba?,meye MAKOMA na al'amarin gaba daya?. Wani sashe na zuciyarsa ya harbo masa tunaninta,yata tsinci batun?.....ta yaya ya risketa?. Yanzun qila tana can tana ji a ranta shi ya zabeta ko?,.....tana can tana tunanin shi ya bayyanata a zuwan ita din ZABINSA CE. Siririn tsaki yaja....qaddarar mammina ina ta jona tasa qaddarar da tata,banda hakan baya tunanin ita din tana cikin sahun matan da zai karba da hannunsa da sunan MATAN AURE. Lafiyayyen abinci cook dinsa ya shirya musu saman dining,dukkaninsu kuma suka wuce can din don cika cikinsu. Ba ma'abocin cin abincin a waje bane shi sam,duk da irin wayewa tarin dukiya da matsayin da yake dashi yafi aminta dacin abincin gida. Uwa uba da kare lafiyarsa ma,don ya sani masu sana'a da aiki irin nasa koda yaushe ababen farautar masu laifi ne,tako wacce fuska ana iya shiga a cutar dasu. Baya ga haka kuma albarkar dake cikin abincin da aka girka cikin gida,ya sani tana da banbanci da abincin siyarwa na waje. Rudu kawai ake saman dining din,hira ce irin ta amintattaun shaqiqan abokai,hira ce irin ta yaushe gamo tsakaninsu,jifa jifa kuma sunqi barin haisam,lallai saisun taboshi. Yana jinsu bai hanasu ba bai saka musu baki ba kuma,sunata tsara yadda zasu gudanar da biki sosai idan komai ya lafa. Ajiye spoon dinsa yayi yana duban idanunsu. "Biki?.....wanne biki khadeem?......auren da za'a yiwa biki nayi?" Ya tambaya yana duban su. Dariya sukayi suna kallon juna,sai ya lura kaman akwai magana a qasa. "Aure dai ai duka sunansa aure.....manufar cikinsa mu da duniya duka babu ruwammu a ciki. Abinda muna sani kawai captain dinmu yayi aure,so zamuyi duk kalar bikin daya halasta ayi.....ba ruwanka" Amjad ya fadi yana daga hannunsa. Da kallo yabi Amjad din,don dama kusan duk a cikinsu shikam yana son hidima sosai ta tasowa dayansu,kan jiki kan qarfi yake tsayawa akai. "Ya kamata ma mu nemi gafarar dukka 'yammatan da kayi rejecting a baya" Khadeem ya fada yana daukan tissue gami da matse hancinsa kaman irin wanda yake qwalla. Harara ya bisu da ita yana watsa musu daya bayan daya. Maleek ya saki dariya yana dan kare fuskarshi. "Ka rufa mana asiri ango da wadannan manyan idanun naka......suna saka mutum yana feeling guilty bayan baiyi komai ba.....muma labarin auren mukaji daga sama" Numfashi yaja sosai ya fesar,ya lura ba wanda ya gasgata magananshi,wanda kuma yana da kyau su fahimci baiyi aure saboda SOYAYYA BA.....yayi aure ne don ya D'ANA TARKO.....yayi aure ne don ya ceci rayuwar dake cikin halaka da musiba ba tare da girman kanta ya bata daman fahimtar hakan ba. Baiyi alqawarin saki ba.....amma kuma baiyi alqawarin zama na har abada ba. "Mijin wata" Omari ya fada qasa qasa har yanzu yana shan mamaki qasan ransa. Harara ya balla masa yana dubansa. "Ka sake fadin haka sau daya saina koreka daga gidana". "Wallahi ba zagi ko tsokana bane.....bazan boye maka ba dukkaninmu mamaki muke har yanzu......mr lowering gaze?....kai?.....aure kuma da akhnan?". Idanunsa ya maida ya lumshe kawai yana relaxing bayansa jikin kujera. "Kuci gaba da mamaki.....lokaci ne dashi,zaizo zai wuce,zakuma miyi accepting abinda dukka na fada muku" "Amma mutumin da bai taba kallon mace da idon aure ba......" "Har yanzu ban fara ba" Ya katsi numfashin Amjad. "Ka jishi......yana magana kamar auren wata takarda ce kawai" Khadeem ya fadi yana duban fuskokinsu "A wannan halin dai tamkar takardar yake" Ya amsa musu still idanunsa suna a lumshe har yanzu. Sake kallon junansu sukayi,haisam din sake shayar dasu mamaki kawai yakeyi "Kana wasa da mace fa haisam duk da ka fimu karantarsu.......zakasha mamakin nan da kwanaki kadan zaka fara sanya ido kan yadda take tafiya.....yanayin maganarta....." "Omar!" Haisam din ya fada da sauri yana dan dukan table din gabansa kadan. "You know my mission omar.....kada ka lalatamin target mana.......baya ga haka I married her to protect her,she was in a tough spot ba tare da tsukakken tunaninta ya barta ta fahimci haka ba......zanyi hakanne kuma ba don ita ba.....zanyi hakanne badon so ko qauna ba.....zanyi dukka haka ne saboda JININ SAFEENA da take tare dashi.......saboda darajar wasu mutane data d'amfara da rayuwarsu.....nothing more.....hope you understand guys?" Ya qarashe maganan yana bude idanunsa sosai a kansu yana duban fuskokinsu daya bayan daya. "It's okay.....mun fahimta......amma,why not ba zaka bude mata zuciyarka ba......why not ba zaka bada qofa zuwa ga wannan killatacciyar zuciyar ba?" Maleek ya fada a nutse dukkaninsu fuskokinsu suna nuna seriousness dinsu. Girman idanunshi ya rage ta hanyar lumshesu sannan ya budesu fes akan fuskar maleek. Baisan me yasa suke putting pressure a kanshi ba game da maganan ba. "Wannan zuciyar budeta shine babban kuskuren da zan aikata.......na gaya muku a baya.....yanayin aikina banajin zai bani daman budewa wata mace zuciyata harta shiga ciki.....zata iya zama weakness dina....mafi girman abinda na tsana kuma kenan......wannan zuciyar" Ya furta yana nuna qirjinsa da yatsarsa "Idan tanayin so bata yinsa d'an kadan......bata kuma yinsa da sauqi.....wannan ne ya sanya nake qoqarina sosai gurin ganin ban tsani mutum ba.....gurin ganin ban tsani kowa ba,saboda nasan idan na fara QIYAYYA itama bata zuwarmin da sauqi......ina dukka qoqarina na canza kaina.... Amma haka aka halicci wannan zuciyar.....shi yasa nake qoqarin fahimtar kowa....shi yasa nake qoqarin bada uzuri ga kowa.......shi yasa bake qoqari sosai kar naqi kowa......ina fatan wannan bayanin ya gamsar?". Shuru ne ya dauki falon gaba daya,na wasu sakanni ba wanda ya motsa ba wanda kuma ya sake cewa komai. Ya musu magana da wannan yanayin nasa na seniority da dukkaninsu suke shakkarsa idan ya juye,sun gama fahimtar kuma da iya gaskiyarsa yake maganar. Tsam ya miqe a nutse bayan ya tura kujerarsa baya "Bazan hanaku yin komai ba.....don kun isa ku zartar da komai a kaina.......amma kuyi qoqari kada ku zafafa abun da yawa,don ba tabbas a cikin komai" zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 88* "In sha Allah saika jarabtu da soyayyar da zaka zauna a gabanmu kamar haka kana maimaita bayanin mahaukaciyar soyayya" Dan dakatawa kadan yayi daga saukar da yakeyi daga step din dining area din,wani murmushi ya subuce masa,yana jin maganar omar cikin kansa kaman wani wasan yara,murmushin ya zarce har cikin zuciyarsa yana sake jin abun da fatan omar ba wani magana bace me muhimmanci ba a gurinsa,sai kawai yaga tsayawa yayi magana dashi tamkar batawa kai lokaci da baki ne.....don TABBAS yasan abune da bazaiyiwu ba. Samansa ya haura ta stairs din baya,saboda yanason sake wankan juma'a irin na sunnah da shari'a ta koyar saboda qarin samun ladan ranar,yana taka step din a gaggauce yana duba agogonsa. Yana shiga dakin tunanin motii ya fado masa,sai ya tuna jiya sunyi dashi xaije qauye,don haka ya kira number dinsa kai tsaye yana zare kayan jikinsa yana musanyasu da towel. A kashe wayar tasa take,haka na'ura ta fada masa,sai ya maida akalar kiran nasa ga hussam da hanzarce. Ya kirashi ya kusa sau uku ba amsa,sai ana hudun ya daga. Ya hasala sosai,don ko waye kai idan ya maka kira daya baya sake qarawa,duk kuwa muhimmancin kiran da yayi makan,saidai idan ka gani ka biyoshi daga baya,abinda ya sake tunzurashi kenan amma yayi qoqarin calming kanshi. "Barka da warhaka captain obbo" Hussam din ya furta da girmamawa,can qasan maqoshinsa kuwa maganganu ne fal da kwarjinin haisam din dake bugunsa cikin waya ne kadai hanashi xolayarshi da sunan ango. "Barka.......motii fa.....ina fata kuna tare?" "Ya fita wani aiki obbo...." "Shi kadai?" Ya tambayi hussam a hanzarce. Adan tsorace hussam ya amsa masa "Eh obbo.....ni" Bai ko tsaya yaji bayaninsa ba yau balbaleshi da masifa. Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Shuru kawai hussam yayi,baice komai ba,saidai zuciyarsa cike take da mamakin abinda ya hasala obbo din nasa har haka. Har sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita yana maida numfashi,haka kawai yakejin wani bacin rai duka yau din,yana qoqarin dannewa ne kawai. "Kayi haquri obbo,aikin company ne ya tsareni,kace lallai lallai mu tsaya mu lissafa adadin masu shops na saida turaruka da zaka bada tallafin manyan drum na turaruka a qarshen shekarar nan......inataso na gaya maka kaman shops din suna da yawa....." "Ina ruwanka?....ko adadin shops nawa ne a lissafa,masu qananun tebur fa?" "Su mun gama dasu" Ya fada a raunane. Bayason fadan obbo din nasa,kuma shima din ba kasafai ya fiya buda baki ya masifeka ba,amma kuma duk sanda ya fusata shikam ko fuskarsa baison kallo,saboda baida sauqi idan ya hasala. Ajiyar zuciya ya sauke don sauqaqawa zuciyarsa abinda yakeji. "Amma ka manta na gaya maka.......kulawa da motii yana hannunka har zuwa sanda zan dawo?". "Ina bakin qoqarina obbo......kafin su fita na tabbatar ya fita qarqashin security da guards masu yawa......sannan Aareef ma yana tare dashi". "Aaareef fa?......makarantar fa?" "Obbo an musu hutun tsakiyar zangon karatu ne". "Karka sake turashi nesa shi da yazo baqunta.....Kun maraatummaadha(rashin hankali ne wannan)" "Dhiifama obbo(I'm sorry big brother)" Shuru ya sakeyi "Tole(alright),yana dawowa gida ka sanarmin.....sannan ka bibiyi isarsu lafiya,inaso ka sake kula da duk wani tsaro na gidan.......ina ebba da adeel?" "Dukkansu kowa na bakin aikinsa" "Shikenan.....sai munyi waya" Ya fadi a nutse yana yanke kiran. Wayar ya ajiye yana fesar da iska daga bakinsa,a hankali ya kira sunan Allah yana qoqarin bawa zuciyarsa daidaito,sannan ya taka a nutse yana wucewa toilet din sabe da lallausan towel a faffadar kafadarsa. *MORSA SAFIYYA* Cikin lokaci qanqani ta sanya aka tashi qwarya qwaryar abinci. A yau din a wannan rana ta juma'a tanaso ta ciyar da adadin mutane masu yawa........tanaso cikin masarautar kowa ya shaida abun alkhairi ya fara samunta....abun alkhairi ya fara samun me babban daki ta farko wato safeena. Tanason nunawa Allah godiyarta abinsa amsa addu'arta da yayi.....a bisa ceton rayuwar akhnan da yayi.....bisa cika fata buri da kuma addu'ar 'yar uwarta dake kwance cikin kushewarta tsahon shekaru masu yawa. Komai akwai,don haka lokaci qalilan girki ya kusa kammala,wanda takeso bayan sallar juma'a ciyar da mabuqata. Ranta fes ta shiga tayi wanka,ta kuma fito ta soma shiryawa cikin wata atamfa 'yar gaske,daya daga cikin kayan atamfofin da falaak tayi musu order daga HUGUMA CLOSET 08187255862(maza garzayo ki gwangwaje da laces da atamfofinmu,masu sauqi da rahusar da gurinmu kawai zaki samu,kizo kiyi joining group dinmu ki rabauta da kaya 'yan gaske,online business kikeyi ko boutique gareki,ko kuma shaguna kika bude?). Tana ji da atamfofin qwarai,dinkuna ta sanya aka musu na isassun mata,wannan ya qara fidda kyansu da martabar atamfofin ya kuma qara mata kwarjini sosai. Tana cikin lanqwasa tattausan dankwalin atamfar da har wani qamshi ita kanta atamfar take,wadda aka saqata da rose water daya sanyata qamshin da taushin taji an buda qofar da sauri. Da saurin itama ta waiwaya,sai suka hada idanu da falaak. "Ke lafiyanki kuwa?" Morsa ta fadi cikin mamakin yanayin da taga falaak din a ciki. "Ya biftu ce momma......" "Me ya sameta?" Morsa ta fada tana jin wani abu yana tsarga mata,dankwalin dake riqe a hannunta yana zamewa. "Suma tayi......kuma bata farfado ba har yanzu......ya hairaan tace kizo". Da sauri ta lanqwasa dankwalin saman kanta,ta dauki yalwataccen mayafin dake ajiye gefe ta lullube jikinta,sannan ta zura bedroom slippers dinta tana yin gaba ba tare data jira falaak bama. A hanya suka kusa karo da samia. "Ranki ya dade......an kammala,za'a iya fara rabawa?" Samia din ta tambayeta tana binta da kallo cikin mamakin saurin da taga tanayi,don ko kallon fuskar samia dake mata magana batayi ba. "A raba samia......da alama uzuri ne me qarfi ya taso mata" Armelle da itama tayi sararo da farko a tsaye ta fada. "Tom" Samia ta amsa cikin girmamawa tana juyawa. Shuru armelle tayi tana sake bin bayan falaak data wuce da kallo. Fatanta daya addu'arta daya kada Allah yasa wani mummunan abune kuma ya sake tasowa. Ita kadai a karan kanta tana tsananin tausayin wadannan bayin Allahn......zuwa yanzu tana ganin ya kamata hankulansu ya fara kwantawa. Dauke idanu kawai hadimai da bayi suke don girmamawa ga morsa safiyya din ganin yanayin tafiyarta na gaggawa ba yadda suka saba ganinta ba. Ma'abociyar nutsuwa ce da kamala amma a yau hankalinta kamar baya tare da ita,abinda ya sake tsananta tsaigumin dake tashi a gidan tun daga awannin dazu na jita jitar daurin auren sheikh Muhammad haisam da kuma gimbiya akhnan din. Wasunsu sun samu damar ganin daurin auren ta wayoyin hannunsu ta manhajar YouTube,take kuma suka fara yadawa a tsakanin dukkan wani me wayar hannu,wanda baida itama yana kalla a hannun dan uwansa,wannan ya sanya cikin qasa da awa biyu tsaigumin ya zagaye ko ina ya kuma yawata,maroqan fada da masu busa kuma suka fara tunanin ta inda bushasharsu sabuwa zata balle,suna fata tafi ta wancan auren da akayi,don alamu suna nunawa kowa cewa wannan shine auren da mai martaba yake maraba dashi. *MAMMINA/HAISAM* A sukwane motar dake dauke da giwar sarkin wato hajja zaituna ta qaraso makekiyar qofar masarautar agadez din,wanda a wannan karon shiga da fita daga cikin masarautar yake bisa tsari doka da qa'idar da sheikh haisam ya zartar. Qa'ida ce tsaiwar motar na mintuna gaban gate din kafin a bata daman shiga da sauri idan ta zama motar sultane ne kota iyalinsa. Ko yanzu motar mammina din gangarawa tayi zuwa bakin gate din ta tsaya tana jiran cikar mintunan. Duk da cewa zuciyarta cike take da wani irin nishadi da annashuwa na samun cikakken tabbacin plan dinta a yau zai tafi yadda takeso. Sun samu motii ya fita da kanshi da kanshi daga masarautarsa zuwa qauyen da suke kyautata zaton hanyar zatafi musu sauqin kai masa harin jan kunne da neman girgiza ko motsuwar mutumin dake maqale cikin agadez din.....mutumin da hukumar binciken farin kaya ta turo musu zuwa agadez. Abune sun sani me wahalar gaske kai masa hari cikin masarautar,zai iya zame musu barazana me yawan gaske. Sun samu bayanan a yanzu cikin dukka masarautun da Ethiopia ke dasu ba masarautar da takai ta JIMMA qarfin iko......qarfin tsaro da qarfin dakaru. An shaida mata D'ANSA jarumin namiji ne da yake tsaye da qafafunsa kan tsaron masarautar da kuma lafiyar iyayensa. Ya haifi ZAKI da Ethiopia gaba daya take alfahari da samunsa. Bayanansa ba abinda suke mata sai sake jijjigata da qoqarin sanya shakka da razani a cikin zuciyarta abinda yafi garata,yafi kuma bata mamaki shine.......kasa samun koda gilmin hotonsa guda daya da zai sanya ta iya gane sura ko siffarsa......ta kuma daidaitata da siffar wadanda take yawaita zargi a kansu. Ta sani.....ta kuma dade da haddace cewa,SHURU yafi zama hatsari a gurare da dama sama da MAGANA. Shuru yana da wani irin tasirin karya komai wanda MAGANA bata da wannan tasirin a gurare masu yawa. THE SILENT ONE.....sunan da tun daga ranar data jishi yake mata kai kawo cikin kwanyarta,ya kuma hanata zama lafiya. A iya sunansa kawai ta sani akwai hatsari,ballantana da ake qarfafa zato da zargin cewa jinin IBRAHIM ne.....wai yaushe Ibrahim ya maida asarar BABBAN D'ANSHI DA YAYI?.....yaushe waccar matar tasa ta sake haifa masa wani dan damisar bayan wanda ta murje?. Idonta ta daga cike da haushi tana son bin ba'asin abinda yayi sanadin tsaiwarsu a nan kamar sun manta girman matsayinta ita da take tsaye a bakin gurin,sai idanun nata suka sauka akan motar dake bayanta. Wannan ganin data yiwa motar ya shafe tambayar da tayi niyyar yi,ta zubawa gaban motar idanu ta glass din jikin tata motar. Haka kawai takejin wani abu a jikinta......motar bata qananun mutane bace.....mota ce da ita kanta har yanzu sha'awar mallakarta takeyi. Ga wanda yasan mota duban farko zai mata ya fahimci me ake kira da KUDI DUKIYA DA KUMA MULKI.....amma ga WAWA a mota bazai mata wani duban ariziqi ba. "Maher" Ta kira sunan maher dake zaune gaban motar,wanda ya jima da zama dan gida kuma n jikinta. "Allah ya baki nasara" "Inason sanin waye a motar bayan can" Dubansa ya maida ga motar,a take kuma ya fahimci sheikh haisam ne a ciki,saiya saki boyayyen murmushin da bata kula dashi ba yana fadin "Umarninki shine burina" Ya balle murfin motar yana sauka daga ciki. Har yanxu bakunansu basuyi shuru ba,har yanzu hira suke abinsu kamar ba zasu sake haduwa ba. Banda haisam dake riqe da tablet yana sake duba wasu bayanai da kyau. Wani irin sassanyan kyau yayi,cikin shigar kurta pyjamas farare tas,sun zauna masa sosai a jiki da wani irin yanayi me daukan hankali daya fidda qirar ginannen jikinsa da koda ba'a gaya maka ba zaka fahimci yana bawa motsa jiki da daga qarfr muhimmanci. Wasu irin tufafi da a hausance sukafi gama da Pakistan na maza suturar jama'ar qasar Pakistan da india,saidai kuma ya sake banbamta dasu ta hanyar farin amam din daya nada a kansa da wani irin salo da zai gaya maka ya gwanance wajen nadin da sanyashi,jelar amam din guda daya ya zagayo da ita kafadar damansa. Dukkanin sassalkan gashinnan nasa ya shige cikin amam din,bata inda zaka iya ganinsa sai ta wajen dokin wuyansa da wasu qananu masu santsi suka fito kadan. Gaba daya motar ta gauraye ne da qamshin sanyayan turarukansu,saidai nashi turaren na dabanne,ya danne na kowa,ya kuma gauraya da sanyin AC din dake cikin motar ya haifar d wani irin yanayi me sanyaya zuciya. Mutum shidda dukka dake cikin motar buri kowacce diya mace ne,zaratan samarin da ba ta inda Allah ya ragesu,abinda Maher ke rayawa a ransa kenan,wani murmushi yana subuce masa sanda yake isa bakin window din motar,daidai sanda kuma aka dagewa motar mammina ta wuce ciki. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 89* Omar ne ya fara hangoshi,ya kuma sauke glass din kadan don ya samu daman masa magana gudun kada yayi wani reaction da xai sanya asa ayar tambaya a kansu. Ya masa signed da idanu ya kuma fahimta,don haka ya daure fuskarsa idanunsa akan haisam. Yaga tahowarsa ta qaramar computer din dake maqale a seat din gabansa,wadda ke baka bayani da kuma nuna maka mutumin dake gaban motar bayanta da kuma hagunta,sai yaci gaba da abinda yakeyi kawai ba tare daya dago ko ya motsa ba,har zuwa sanda Maher ya qaraso. "Giwa ke buqatar sanin su waye a cikin motar?". "Ka gaya mata sheikh muhammad haisam motii ibraheem ne" Haisam ya furta kansa tsaye da wata irin zarra da rashin tsoro. Dif kowa yayi,amsar daya bayar takai tsaye tana bawa kowa mamaki,musamman Omar ma. "Idan kuma ba maher bane bafa captain?" "Shima hakan zan gaya masa" Ya qarasa bawa omar amsa yana daga kansa izuwa omar din. Dauke idanunsa omar yayi,haka kawai yake ganin rigima kaman yakeji yau haisam din,hakan ya sanya waiwayawa yana duban maher,duban daya sanya kwarjininsa taba maher din har sai daya sadda kai qasa. "Amsar da nake buqatar ka bata kenan idan ta tambayeka" "In sha Allah" Maher ya fada yana janyewa da baya,daidai sanda motar tasu suma ta sanya kai ciki bayan gama nadar bayanan cewa yau sheikh haisam dinne a cikin ta,abinda basu taba gani ba,amma wasu daga cikin wadanda ba mutanensu ba dake bakin gate din sai suke tunanin ko saboda ya zama surukin sultane ne ya sanya tun a ranar farko aka fara nuna masa alfarmar gidan sarauta aka mallaka masa mota?. "So nake na tayar da kasar dake bacci.....inaso na tunasar da ita akwai babban yaqi a gabanta" Ya furta yana maida idanunsa kan tab dinsa cikin izza. Maganansa a bayyane take,ta kuma fahimtar da kowa abinda yake nufi,don haka sai basu sake tayar da zancan ba. Daidai sanda mammina ta bada umarni a yau a tsaida motarta a babban parking lot na gidan,wanda a qa'ida za'a wuce da ita ne kai tsaye zuwa muhallin ajiyar motoci na sassanta. Da jin girman nan.....izza da mulki ta sauka a motar,saidai tayi tsaye kawai jikin motar tata tana dakon shigowar maher koshi ko motar da takeson sanin mallakar waye?. "Allah yaja zamaninki" Muryar yalwa daga gefanta ta cika mata kunnuwa,wadda batasan sanda yalwar ta iso ba. A qasqancs ta waiwayo tana duban yalwa din,saidai yanayin data gani a tare da ita ya sanyata jifanta da tambaya takai tsaye. "Mene?" "Sultane ya daura auren gimbiya akhnan da haisam a yau awa guda kacal da fitaki a madeena garin manzo" Wani irin hautsina kanta yayi lokaci daya. Badon maganar baquwa bace a kunnenta ba. Hasalima wannan shine burinta......shine kuma plan dinta,amma bata haka ta shirya yazo mata ba,zuwan komai kuma a hakan ba shakka wani babbar alama ce dake nuna HATSARI ko rashin DAIDAITO cikin tsarinta. "Kamar yaya yalwa?" "Bana ce ba uwar gijiyata,mun tsinci maganar haka kawai ta fara yaduwa,saiga tabbatuwarta ta faifan video". "Ina akhnan din?" Ta tambaya da sauri tana jin hankalinta yana tashi. Bata fatan kowa ya shiga gaban plan dinta,batason kowa yayi wani abu da zai bata tsarinta. "Tana can sassanta.....na samu labarin ta suma daga samun labarin.....kuma tunda ta suma bata farfado ba" "Yayi kyau" Ta fada da hanzari tana takawa a gaggauce zuwa nahiyar da zata sadata da sassan akhnan din kai tsaye. Wata gauruwar ajiyar zuciya Maher ya sauke,yana dab da qarasowa gurin mammina ta juya zuwa sassan akhnan. Hakan ya masa,don baisan yadda zai gaya mata cikakken sunan haisam ba. Bai shirya gaya mata abinda zai bata daman cutar musu da haisam din ba. A iya zamansa da matar ya gama karantar wacece ita,wani irin karatu daya girgiza zuciyarsa. Suna yiwa haisamd in wani irin matsanancin qauna irin ta jini da jini. Qauna irin ta 'yan uwantaka. Kusana jininsa ne wannan,duk wanda ya zauna dashi sai ya soshi,duk wanda ya rabeshi sai ya qaunaceshi,wata irin baiwa daban Allah yayi masa tun yana qaraminsa,har kuma kawo yanzu....wannan ya bayu ga samun tarin matsananciyar soyayya da farinjini daga gurin tarin tulin 'yammatan da da yawansu baisan da zamansu ba. Cikin ransa yakejin bazai gaya mata yadda obbo haisam yace ba,bai shirya ganin cutarwa tattare dashi ba,ta kusa kota nesa. Bashi kadai ba,kowa yana mamakin irin jarumta da kafiya da yake da ita,bai tsoron duk abinda waninsa yake tsammanin abune me hatsari,dan kai tsaye ne sosai,bai mantawa akwai sanda motii yaja hankalinsa akan hakan,nanay ta daga hankalinta,wannan ne kadai abinda ya kawo sassauci ya rage kasada da rayuwarsa. *MORSA SAFIYYA* A jikin aisa ta sameta da shehnaz,kowanne a cikinsu hankalinsa a tashe,kowanne a cikinsu yana tsaye a kanta,kamar yadda nanay da yakumbo ke tsaye,nanay din tana ta yayyafa mata ruwan dake hannunta,saidai kuma hakan bai amfana komai ba,don bata motsa ba ko daya. Qarasawa morsa safiyya din tayi zuciyarta na karyewa,ta karbi kan akhnan dake saman cinyar aisa,idanunta suna saman fuskarta,tana jin zuciyarta na wani irin karyewa. Hannu tasa ta shafi fuskartata wadda ke jiqe sosai da ruwan da nanay keta yayyafa mata da zummar ko zai taimaka ta farfado,ta shafe ruwan tas har zuwa saman kanta da ba dankwali,sai yalwataccen sumarta dake kwance luf saman kanta ta bazu zuwa kafadarta da gadon bayanta. Dukka jikinta a sake yake,tamkar dai mutu,bugun zuciyarta dake wani bugawa da wani irin yanayi ne kadai zai baka relief da tabbacin tana raye. Bata ce komai ba sai hawayen daya soma taruwa cikin idanunta. Tana fata da addu'ar rayuwar akhnan ta daidaita. A yanzu tana ji a jikinta yarinyar tafi kowa galabaita,rayuwarta tafi ta kowa shiga cikin ibtila'i da jarrabawa iri iri. Ko kafin tace komai ba aka buda qofar da qarfin gaske,qarfin daya ja hankalinsu su duka zuwa bakin qofar. Mammina ce,wadda kai tsaye ta fara shigowa da sassarfa cikin dakin. Fuskarta jiqe da hawaye,tashin hankali da rudani yana bayyana qarara saman fuskarta. "Biftu?.....ina biftu?" Ta fada tana laluben akhnan din dake kwance saman cinyar morsa safiyya duk kuwa da cewa ta ganta. Ba wanda ya iyace mata komai,saboda zukatan da yawa daga cikinsu tausayin mamminan sukeji. Suna duba da soyayya da kuma shaquwa ta ZAHIRI dake tsakanin mammina din da akhnan..... Suna duba da idanun zahirin da zai gaya maka mammina din ita zatafi kowa shiga rudani akan duk wani abu daya shafi akhnan din. Mammina din ita zatafi kowa damuwa akan komai da zai shafi akhnan din. Idanu kawai morsa safiyya ta zuba mata sanda tayi gurfane gaban akhnan din. Saidai duk siyasarta da yadda taso maida akhnan cikin jikinta morsa safiyya ta hanata wannan damar.......taqi matsar da koda yatsanta daga jikinta,koma baya yadda ta saba a baya. Tana ja da baya ne a duk sanda mammina tazo kan al'amarin akhnan,tana matsawa ne ta bata dama da fili a duk sanda take ganin ita tafi cancanta da ita. Amma a yanzu.....a kuma yau din,tana jin komai yana canzawa game da ita,tana jin jinin nan na UWA yana dawowa jikinta game da akhnan......tana jin ba wata sauran dama da zata sake bawa mammina game da akhnan daidai da d'anin yatsa guda daya tak!.....don haka a daidai sanda take kiran yalwa da sauran hadimanta da sukayi mata rakiya kan su dauko wheelchair su dauke mata akhnan su wuce mata da ita sassanta......a daidai sannan ta kalli falaak da armelle. "Maza ku gaggauta kiran MIJINTA.....ku gaya masa ni morsa safiyya ina kiransa da gagggawa,yazo matarsa bata cikin hayyacinta" Yadda morsa safiyya din ta basu umarnin da wata irin murya mai cike da zarra da kuzari kawai ya qarawa armelle da falaak qaimi. Su dukka sunsan me yake faruwa,bawai a boye komai yake a gurinsu ba,don haka da sassarfa suka soma takawa suna ficewa. Wani irin duka kalmar MIJI da morsa safiyya ta fada ta yiwa mammina. Sai a sannan tunaninta ya sake dawowa jikinta. Da gaske a yanzun akhnan din ta zama MATAR BABBAN ABOKIN BURMINTA.....to amma hakan yana nufin zata saki kambunta?,hakan yana nufin zata sakar masa zaren?. Samun kanta tayi da bawa kanta amsa da "A'ah" Wannan amsar ita ta yaudareta da bata qwarin cewa. "Amma safiyya,ta yaya zamu zauna jiran wanda ba'asan yana kusa ko a nesa ba?,ki duba ki gani Yarinyar nan bata numfashi.....marabarta da gawa bugun zuciya!" Mammina ta fada a tsawace tana fidda idanunta cikin son nuna rudanin data shiga. "MIJINTA.....shine mafi cancantar haqqi a kanta.....MIJINTA shine Allah ya dorawa alhakin kula da lafiyarta,MIJINTA shine majibancin lamarinta a yanzu BA MU BA" Kowacce kalmar MIJI guda daya da morsa safiyya ke fadi cikin kunnenta......tana maimaita kanta da kanta ne a zuciyar mammina din sau DARI. Tana jin bugawar sunan a kowanne jini da zai harba zuwa sassan jikinta. "Ashe?.....ina soyayyar da kike iqirarin kina mata?,ashe ba zaki iya cetonta ba a sanda tafi buqatar ceto safiyya?.....sai mun jira zuwan wani?". Kai tsaye morsa safiyya take kallonta ido cikin ido,tanajin zuciyarta tana soyewa. "Idan har shekaru ashirin baya basu kashe akhnan ba......a yanzun 'yan qananu kuma gajerun mintuna irin wadannan ba zasu taba daukan rayuwarta ba.......ta mutu a hannuwan MIJINTA yafi mata daraja akan ta mutu a hannun daya daga cikinmu,bamu da wuta ko aljannar da zamu bata.....amma kuma MIJINTA fa?" Ta tsaida ayar tambayar tana duban tsakiyar idanun mammina kai tsaye,abinda ta jima batayi ba......abinda ta dauki shekaru bata yi ba. A duk sanda ta kalli idanun mammina din SAFEENA take hanga a ciki........a duk sanda ta kalli idanun mammina MUTUWAR SAFEENA take gani.....WAHALA da GALABAITAR safeena a kafatanin rayuwarta take kalla......QADDARAR safeena take gani rubuce cikin fuskar mammina din.....wannan ya sanya kallon fuskartata ya zama wani abu na qarshe a rayuwarta da takan jima bata yishi ba *HAISAM* Ya dauki wasu mintuna cikin masallacin yana gaisawa da mutanen maimartaba,karbar koke da sauran abubuwan daya zamana sultane dinne yakeyi duk bayan sallar juma'a,kafin daga bisani ya samu ya baro masallacin. Shi da khadeem da maleek suke takowa,don abdii omar da Amjad sunyi gaba. A hankali suke tattaunawa akan lamarin kasuwancin da kowannensu yake gudanarwa. Hirar kusan duka kan duniyar kasuwanci ce,saidai kuma tattaunawa ce dake muna zallar nutsuwa da ilimi a maganganunsu. Kusan baya cikakken taku biyar ba tare da gilmawar hadimai ba,kuma su tsaya su gaidashi cikin girmamawa sannan su wuce. Da yawansu murna ce fal cikin ransu game da labarin daurin aurensa da gimbiyarsu da liman ya sanar bayan gama khudba. Da yawansu kuma suna son masa Allah ya sanya alkhairi ne,saidai yana musu wani irin mugun kwarjini da yake sanyawa daga gaisuwa saidai kawai su wuce ba tare da sun iya ce masa komai ba. Shi ya fara hango abdii yana tahowa,yana magana da amjad amma sai ya tattara hankalinsa akan abdii din har zuwa sanda ya qaraso. Da ido ya tambayeshi,don kusan dabi'arsa ce magana da ido,duk kuma wanda ya saba rayuwa dashi ya saba karbar kalar tambayoyinsa da tuhumarsa da qwayar idanunsa. "Aike akayi yanzu......ana buqatarka a sassan amarya......gimbiya....." Abdii ya rarraba zancan yana kallon idanun haisam din don duba sunan dashi haisam din zai iya karba. "Akhnan?" Haisam din ya furta kai tsaye yana duban abdii. Kai ya jinjina masa.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 90* "Gwaggonta morsa safiyya ta aiko.......tace kirane na gaggawa" Idanunsa ya janye daga kan abdii din a hankali cikin nutsuwa. A musulunce kuma a al'adance kiran morsa safiyya yana daidai da kiran nanay dinsa. Koda ita batasan hakan ba shi ya sani......she earn some respect kasancewarta UWA a gurinsa. "Okay" Ya fada da wani coolness yanna motsa labbansa sannan ya fara takawa a nutse yana barinsu amjad a gurin. "Idan da buqatar wani taimakon let us know" Amjad ya furta da nuna supporting zuwa ga abokinsa. Kai kawai ya gyadawa amjad din ba tare daya waiwayo ba,yayin da abdii yaji zuciyarsa ta tafi,bazai iya barin haisam din yaje shi kadai ba,sai kawai ya fara binsa a baya a nutse. Suna dab da sassan haisam ya ankara da abdii. Cak abdii din ya tsaya yana duban haisam daya waiwayo yana dubansa. "Don Allah obbo" Ya fadi cikin karyar da murya. Idanun nasa ya dauke ya juya yana ci gaba da takawa,abinda ya gayawa abdii kenan ya barshi ya biyoshi,don haka ya qara hanzari kadan yana taddoshi. Kai tsaye yake takawa cikin sassan akhnan din,karo na farko tunda yake a gidan,don ba wani abu da yake ganin zai hadashi da gurin. Iyakacinsa daga bedroom balcony dinsa,sai kuma dogon veranda din da ta hada sassan nasu,wanda yawancin lokuta ma bata nan yake biba. Cikin girmamawa bayin dake hidima ta kowanne sashe na sassan nata suke zubewa suna gaidashi,kawunansu a qasa cikin salon da suke gaida uwargijiyar tasu. Koda a baya yana da girman matsayi cikin gidan,amma a yanxu matsayinsa da girmansa sun ninku a zuciyarsu saboda zamowarsa mijin gimbiya akhnan. Tun hankalinsa baikai kai ba har yakai din,ya lura kamar sashin nata yafi kowanne sashi na gidan yawan bayi da hadimai,duk da cewa kusan mafi yawansu mata ne amma adadinsu ya ninka na kowanne sashe. Kai tsaye birra dake daga bakin qofa ta juya itama tana sadda kanta qasa. "Zan iya maka jagora zuwa muhallin da suke" Ta furta a hankali tana jin yadda kwarjininsa a yau yake dukanta sosai. "Dama haka yake?" Ta tambayi kanta,don yau din shine karo na farko data fara tsaiwa a muhallin da yake tsaye. Bai amsa mata ba,tadai juya da zummar yin gaba,saidai kuma a qasaice ya umarceta da cewa ta koma bayansa. Da dan mamaki ta dakata tana komawa bayansa,shi kuma ya shige gaba. Abdii ya sani,yasan tsarinsa shi yasa baiyi mamakin hakan ba. Baya taba yarda macen da take ba muharramarsa ba tayi tafiya a gabansa,saboda koyi da sunnar annabi musa. Ya taba tambayarsa bai kuma zargi tambayar abdii din ba ya zaunar dashi yana karanta mass k'issar. Lokacin da ya shayar da dabbobin daya daga cikin annabawan Allah,kuma d'iyoyin annabin da suka kasance mata suka dawo domin kiran annabi musa,ta shaida masa mahaifinsu yana son ganinsa don ya saka masa ko ya biyashi shayar da dabbobinsu da yayi kaman yadda qur'ani ya bada labari cikin suratul qasas......a yadda k'issar tazo cikin sauran litattafai ta nuna tayi gaba ne don ta masa jagora xuwa gidansu,sai iska ta daga zaninta kadan,sashen dugaduginta ya bayyana,sai annabi musa ya runtse ganinsa,ya kuma umarceta ta koma bayansa. Sosai abdii ke jinjina kai,lallai akwai hikima kenan cikin abinda haisam din yakeyi duk sanda tafiya irin haka ta hadashi da mace,zama da me ilimi akwai dadi,dole abubuwa da yawa naka zasu gyaru,al'amuran duniya dana lahira ma gaba daya. Tun daga wannan lokaci shima abdii sai ya zame masa dabi'a. (YAKE UWA!!!.....akwai abubuwa masu kyau da yawan gaske daya kamata ki koyawa diyarki.....kunga diyoyinkunnan mata SUNFI ZINARE SUNFI LU'U LU'U DARAJA DA TSADA.....kyan diyarki ba'a fuskarta yake ba,kyan diyarki yana ga kyawawan dabi'u halaye da tarbiyyar da zaki bata....KADA KI YARDA DIYARKI TA ZAMA BARAGURBI ki sanyata ta zama kyakkyawan fure me qamshi ga al'umma,abar rububi ga dukkan namiji wajen son mallakarta. Ki koya mata kaucewa maza a hanya yayin tafiya.....koda tana tafiya wani yana binta a baya,ki koya mata tsaiwa ta rabe ya wuce gaba ita ta bishi a baya....YIN HAKAN KARE MARTABARTA NE.....YIN HAKAN KARE KIMARTA NE.....YIN HAKAN KOYA MATA MUHIMMANCIN KUNYA NE.....Allah ka bamu ikon fidda yabanya masu kyau). Mamaki kadan yake kama birra ganin yana bin duka hanyoyin da zasu sadashi da gurin kanshi tsaye kamar dama yasan ya gurin yake,bai kuma tambaya ba saida suka zo mararrabar da zaka hau stairs din akhnan din da kuma inda zaka zarce hanyar parlor din. "Hannun dama" Ta bashi amsa cikin kamewa. A nutse ya waiwaya ya bawa abdii umarnin dakatawa daga nan,sannan yaci gaba da shiga kai tsaye da wannan kuzarin nasa. Kallon kallon sukaci gaba dayi da morsa safiyya bayan takai qarshen maganganunta. Sosai take hangen wani abu me tsananin zafi da tsini daga idanun morsa din,irin wanda bata taba ganinsa ba sai yau din. "Sanyi zeenatu.....sanyi......zafi ba komai yake bayarwa ba" Wani sashe na zuciyarta ya d'arsa mata kaman yadda wasu lokutan yake gaya mata. Janye idanunta tayi kadan tana hadiyar wani abu a zuciyarta,tana jin wani irin nau'in qasqanci da morsa safiyya ta gwada mata gaban tarin bayi?. "Lokaci yayi da ko yaya ya kamata itama na tabata.....ya kamata taji a jikinta" Ta furta can qasan muguwar zuciyarta tana hadiye bacin ranta. Daidai sanda takai qarshen maganar,daidai lokacin haisam ya bayyana bakin qofar parlor din da sallamar dake nuna nutsuwa me yawa a tare dashi. Wani irin muguwar faduwa gabanta yayi,yana tsaye kyam saman qafafunsa da cikakkiyar tsaiwar da a yau karon farko ta fara ganin murjewa jiki da tsahon da yake dashi. Giant ne sosai wanda qirarsa ta sake d'arsa mata zargi na biyu a ranta. Ko ba'abzine ko dan qasar habasha wanda suke kadai keda wannan siffar a qabilun data sani. Kwarjininsa da haibarsa gaba daya taji sun cike dakin,qamshinsa kuma ya fara gayawa kowa isowarsa. "Wa'alaikumussalam" Morsa safiyya data daga kanta daga kallon akhnan da har yanxu bata motsi ta fadi tana sauke idanunta akan haisam din. Wani irin abu taji ya tsarga mata me dadi,tsoronta taji ya zabge daga kaso dari zuwa kaso.ashirin cikin darin. Bayyanarsa kawai a wajen sai takejin kamar bayyanar haske a yayin da duhu ya yiwa wani kogo mamayar gaske. A kanta idanunsa ya sauka,sanda take rungume jikin morsa safiyya din. Tashin sheshsheqar kuma yakeji cikin kunnensa,sautin da baisan daga inda yake fitowa ba don ba ma'abocin aza dubansa akan komai da komai bane,saidai koda bai qarewa dakin kallo ba ya tabbatar akwai mutane da dan yawa a cikinsa. Hannunsa dake cikin aljihun kurta dinsa ya zare,yaci gaba da takowa tsakiyar parlor din. "Me yake faruwa?" Ya tambaya a nutse idanunsa akan morsa safiyya duk da yaga mammina a gefe. "Suma tayi muhammad......kuma da alama suma ne me zurfi,don duk abinda ya kamata ayi mata an mata amma bata farka ba" Morsa safiyya ta furta cikin nutsuwa saidai akwai wani nauyi cikin muryarta da ya jiyo can cikin kunnensa zuwa zuciyarsa. Matsowa yayi dab da inda kafadunta suke,ya tsugunna saman qafafunsa yana duban fuskarta kai tsaye karon farko tun shigowarsa. Sumarta me santsinnan har yanzu tana baje saman fuskarta sassan wuyanta dama kafadunta,saita zamewa tattausar farar fatarta kamar wani ado na musamman. Idanunsa ya zare a hankali daga kan fuskartata,wani abu yana kadawa can qarqashin zuciyarsa da wani yanayi.....da kuma wani amo mara qarfi. "Ya isa.....muna buqatar shuru" Ya fada da coolness dinsa,don sai a yanxu ya fahimci muryar falaak ce tafi fitowa sosai. "Muna buqatar iska......ya kamata kowa ya matsa" Ya sake fadi yana miqewa tsam sannan ya fara tattaki yana nufar windows din gurin. Sum sum hadimai da bayin dake dakin suka fara hada kansu suna ficewa,ya rage shehnaz aisa falaak nannie yakumbo da morsa safiyya. A nutse yake bude windows din da glass doors din parlor din,take iska fresh ta fara wadatar parlor din. "Magana ake ta rai da rayuwa,dawowar ruhi gangar jikin mutum,me ya hada hakan da bude windows?......baku lura da halin da ake ciki bane?,tana buqatar taimakon gaggawa.....bawai a tsaya wasu hirarrki ba" Mammina tayi maganar tana nuna akkhnan da hannu,tana kuma nuna fushinta cikin maganarta. Baiko nuna yasan tayi magana ba.......duk wani kallo da take binsa dashi tun shigowarsa dakin yana jinsa a jikinsa,saidai yau deciding nuna mata rashin muhimmancinta ne....don baiga muhimmancin da take dashi ba,lokacin da zata tonawa kanta asiri da kanta kadai ya rage mata yanzu a duniya. "Ko zaku sake bamu space?" Yayi tambayar haisam kai tsaye yana duban fuskar nannie. "Me zai hana.....saimu jira daga waje ko?" Nannie ta fada tana duban mammina. A nutse morsa safiyya ta zame akhnan daga cinyarta tana kwantar da ita sosai saman couche din da suke zaune akai. "Yakumbo keda shehnaz ku zauna ko zaa buqaci wani abun" Tayi maganan ne don yankewa mammina duk wani hanzari ko qoqarin zama da akhnan din. Ta santa farin sani,wannan din ba baqon abu bane a wajen morsa safiyya. A komai daya shafi akhnan saita nuna kusanci,a komai daya shafi akhnan saita nuna itace ahaqqu dashi,ita kuwa a yanzu ta shirya kashe dukkan wadannan abubuwan da take ganin tana da tasiri a kansu. Sai data zubewa morsa safiyya wani iri kallo sannan ta juya tana bin Nannie dake fita,sannan morsa safiyya ta zamana a qarshe ta take bayan mammina din. A nutse ya tsugunna gaban couche din da take kwance,karo na farko wani irin kusanci mafi kusa ya wanzu tsakanin shi da ita. Idanunsa ya sake zubewa kan fuskar tata,wani irin skin dake glowing kaman bayan tarwada. Idonsa ya lumshe a hankali,yana jin yadda bugun zuciyarsa ya soma canzawa. Kusancin ya masa kusa da yawa.....har yana iya jiyo qamshin hair mist da take amfani dasu saboda inganta sumarta. "Nauyi ce ita a kanka.....haqqine a wuyanka lafiyarta" Can wani sashe na zuciyarsa ya tunasar dashi. Hannunsa ya cire a hankali ya miqa ga hannunta dake kwance sambal gefanta. Hannunsa ya sanya ya kama hannun cikin nasa da nufin duba bugun jijiyar dake tsintsiyar hannunta. Har cikin bargonsa yaji wani irin abu ya harba yana kuma ratsashi. Karo na farko daya soma hada hannunsa da wata diya mace har haka.....karon farko da hannunsa ya manne jikin hannun wata 'ya mace da zurfin alaqa har haka. Jijiyar tana bugawa,ya sake janye idonsa daga kan hannun yana maidawa ga qirjinta. Idanu ya zubawa gurin yana lissafa bayan kowanne second nawa zuciyarta ke harbawa don tantance daga inda matsalar take. Second daya biyu kawai yaji kamar ana zare masa duk wani laka dake jikinsa. Akwance yake plate,a miqe sambal,wannan yanayin kwanciyar kuma ya bawa dukiyar fulaninta dake zaune das a qirjin nata cikin tattararar dinkin material din jikinta damar fitowa das kamar an dorasu. "Ko akwai wani abu da ake buqata?" Muryar aisa data roqa itama a barta ta ratsa kunnensa,abinda ya sanyashi tattara dukka jarumtarsa ya sake maida dubansa saman qirjin nata karo na biyu. "Pulse Oximator" Ya fada a taqaice. Tsam aisa ta tashi da wani irin hanzari tana ficewa. Idanunsa ya daga kadan ya kalli shehnaz da idanunta suka fito saboda kuka. Sumar kan yakeso a tattare a kuma saka mata hula da dankwali. Janye idanunsa yayi daga fuskar shehnaz din,ya lumshe idanunsa yana sake budesu sanda ya sake dora hannunsa saman tsintsiyar hannun nata,yana sake jin bugun jijiyar hannun nata. Sake maida idanun nasa yayi still,yana jin kamar wani weakness yana bin kowacce jijiya ta jikinsa dake bashi kuzari. "Ba'a samu pulse Oximator ba......sai stethoscope" Aisa ta fada tana miqa masa. Alama ya mata da inda a inda zata ajiyeshi,ta ajiye din tana komawa da baya ta zauna hankalinta da idanunta akan akhnan din. Ya sani dukkaninsu suna ganin kamar zasu rasata ne......dukkaninsu sun damu da ita ne,damuwar da ya tabbatar ita bata damu dasu din kamar haka ba.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 91* Sake matsawa yayi dab da ita,ya miqa hannunsa da wani irin sanyi yana tattare mata sumar tata dukka zuwa gefe guda,abinda ya sanya fuskar ta wuyanta da qirjinta fita fes. Wani nauyi dukkansu sukaji ya kamasu su da suke gefe sanda ya aza hannunsa saman qirjinta nata ya dora bakin stethoscope din bayan ya sanyashi a kunnuwansa. Bugun zuciyarta ya fara ji sosai cikin kunnuwan nasa,abinda ya sanyashi lumshe idanu sosai. Zaka dauka wani hasashe yakeyi,saidai wanzuwar hannunsa a gurin kawai yana sanya wani abu harbawa da gudun gaske cikin jijiyoyin jikinsa. Yadan cije lips dinsa kadan yana jin nasa gudun zuciyar kamar yana neman haura nata,kamar yana neman hautsinewa da nata gaba daya,yaja iska sosai yana bude idanunsa wanda yayi qoqari sosai kada su sake kai kansu zuwa ga qirjin nata. Xare abun gwajin yayi daga kunnensa yana ajiyeshi a gefe.....ya fahimci tana buqatar iska ne sosai kafin dawowar numfashinta yadda ya dace. Ya sani,akwai mutane a dakin,akwai mutanen daya kamata aji nauyinsu,amma muma ceton numfashinta da lafiyarta ya zame masa kaman dole. "Ko zan sake samun raguwar mutane?" Ya fada a hankali yana sake kusanta fuskar sa da tata,abinda ya sake sanyashi qara ganin komai dake saman lafiyayyar fatar fuskarta. Kusancin daya qara a tsakaninsu ya saka kunya ta kama kowa a dakin,falaak da yakumbo suka juya suna neman hanyar fita,yayin da aisa tayi qasa da kanta,shehnaz kuma abun taji ya fara mata wani tasiri a ranta. Tana cikin yanayin son ceton ran akhnan din da gaske ne.....amma wanzuwar shiekh haisam a gefan akhnan din kamar me shirin bata kyakkyawar runguma sai taji yana sauya komai a ranta. Kamar wanda wani magnet yakeja haka yake sake rage tazarar dake tsakanin fuskokinsu.....bugun zuciyarsa na sake ninkuwa da gudun dashi kansa ya d'arsa mamaki a ransa,dab da zai aza bakinsa saman nata ya lumshe kyawawan manyan idanunsa yanajin bugun zuciyarsa yana ci gaba da sauyawa. Kyakkyawan mazauni lips dinsa suka samu saman nata,ya miqa hannunsa yana riqe hancinta me tsaho da dan tudu kadan wanda ya dace da kyakkyawar fuskarta. Iska ya shiga hura mata sosai don taimakawa numfashinta da yake fita ba yadda ya dace ace ya fita din ba,tsahon wasu sakanni kafin a hankali ta amsa ta hanyar zuqar iskar daya aikamata din da kyau,taja wani irin numfashi daya sanya qirjinta dagawa sosai ya mannu a jikinsa,sannan ta saukeshi duka lokaci guda. Ganin ta amsa ya sanyashi ya janye bakinsa daga cikin nata,saidai kuma bai janye fuskarsa ba dab da tata. Mannuwar da tayi a jikinsa ya sanyashi damqe tafin hannunsa da yake cikin nata yana kiran sunan Allah can qasan zuciyarsa,yanayin daya sanya fitar sassanyar iska daga bakinsa dake gauraye da qamshin fresh mint mouth fresh na brand din bonjour care breath spray. A hankali idanunsa suka sauka kan wani dan digon baqi dake saman lips dinta,daidai sanda labbanta masu wani irin color me daukan hankali suke motsawa. Idonsa ya maida ga lips din,kafin a hankali ya maida dubansa kan kyawawan idanunta ma'abota yalwataccen eye lashes da suka yiwa idanun rumfa. Motsasu take a hankali tana qoqarin budesu. Bai taba zaton haka take tamkar tangaran ba.....bai taba zaton wannan taurin kai da kafiyar nata zaibar dabi'ar firgici da tsoro su wanzu a zuciyarta ba,ya tabbatar abu guda ne kawai ya sanyata a wannan yanayin....labarin aurensa. Inda tayi haquri,inda ta kwantar da hankalinta duka duka kwana nawa ne?.....wani mataki kawai yakeso ya taka,wani tsani kawai yakeso ya hau,wani guri yakeso yakai. Duk wani tunani da ma'ana data bawa aurensu zata fahimci yaudara kanta kawai tayi......zata gane fahimtarta yasha banbam da ainihin ma'anar aikin. Ya zubamata ido sosai,kafin a hankali cikin laushin nan nasa yace. "Alhamdulillah" A fili. Wani irin sauka maganar tayi mata a kunne,da wani irin kusanci da bata taba kawoshi ba. Ta ware idanunta a hankali,zuciyarta na sake qoqarin komawa yanayin bugunta na dazu,saidai hakan bai hanata waiwayawa gefan hannun damanta ba. Fes fararen blue eyes dinta suka sauka cikin nasa. Wadannan dream eyes din......wannan tattausan qamshin daya zame mata jarrabawa.......wannan kallon daya jima da sauke wani nauyi saman zuciyarta yau gasu dab da ita da taqin da bai wuce d'ani daya ba. Kusancin ya saukar da wani rudewa a tattare da ita,wani irin take ganin kamar a mafarkan data saba yi. Ta yaya zaizo ya zauna dab da ita har jikinsa yana gogar nata?......ta yaya zai kasance kusa da ita da mugun kusanci har haka?.....ta yaya zai samu daman sanya idanunsa cikin tsakiyar nata qwayar idanun har yana iya sarrafa tunaninta da qwayar idanunta?. Ya riqe dubanta sosai cikin nasa idanun......yana sane kuma ya hanata katabus saboda wani karatu da yakewa tunaninta. Ya fahimto tsoro mamaki da motsawar wannan izzar lokaci guda daga cikin Jininta,har yanzu bai sakar mata ido ba kamar yadda bai bata daman motsawa ba. "Ki nutsu.....ina nan tare dake......nauyinki a yanzu na wuyana" Ya fadi da wani irin sanyi da nufin sanya nutsuwa cikin tunaninta. Wani birkicewa ta sakeji tunaninta yayi,sanda kwanyarta ta dawo mata da abinda ya faru da ita a dazu,dazun da batasan adadin awa ko mintuna nawa bane da suka shude. "Malamin nan dai......ma'abocin girman kai......malaminnan dai ma'abocin izza.....malamin nan dai data tsani komai daya shafeshi.....shine yanzu tsugunne dab da ita?,shine take shaqar numfashin dake fita daga qofofin hancinsa?,numfashinsa ke sauka saman fuskarta?,wani irin numfashi me dumi dake gauraye da wannan qamshin da yake shiga rayuwarta a duk sanda zata shaqeshi.....shine MIJIN AKHNAN....shine sultane ya aura mata.....ba yardarta.....ba amincewarta....ba saninta,sai labarin da ba'a sanya rai dashi ba koda cikin mafarkai?. Baqinciki haushi da bacin rai suka turnuqeta gaba daya.....haushin kanta shine abu na farko data sake tana duban cikin idanunsa har tsahon wadannan mintunan,wani abu dabai tana hadata da wani d'a namiji ba tunda ta fado cikin duniya. Da dukka qarfinta take yunqurin tashi bayan ta fahimci tafin hannunsa manne yake cikin nata.....bayan ta fahimci ko dankwalin arziqi babu a kanta.....bayan ta fahimci yadda suturar jikinta ta bayyana kowanne tudu na sirrin jikinta. "Calme-toi" Ya furta da tataccen yaren faransancin daya kusa sanya numfashinta wucewa. Mamaki da razani da suka cakude guri daya suka sanya numfashinta sarqewa,saita fara jansa da qyar tana jin kamar duk wata qofar shaqar iska ta mata kadan. Ba wani tashin hankali ko rudewa sam a tare dashi ya qara kusancin dake tsakaninsu,ya riqeta da kyau ganin yadda qirjinta yake sake dagawa da alama tana yaqi da numfashinta ne. "Kija iska sosai sannan ki fitar da ita ta bakinki" Ya fadi da nutsuwarnan da ba komai ke sanyawa tabar cikin jikinsa ba. Batayi yadda yace ba.....ya kuma fahimci taurin kai da gasken gaske a jininta yake,sai yadan tsaurara muryarsa kadan,don da gaske idan bataja numfashin ba komai zai iya faruwa. "Karkice zaki yaqi jikinki zuciyarki da hunhunki da suke buqatar iska don su rayu.....su din basusan ke GIMBIYA bace....basu da masaniyar yawan izzar da kike da ita.....numfashi kadai suka sani.....kija numfashi don ki rayu!!" Ya sake fadi yana jin ransa ya soma baci da kalar taurin kanta. A lokacin ta soma jin wahala a qirjinta da hunhunta,bata da wani sauran zabi illa yin yadda yace din,taci gaba da maimaitawa,sai ya zare hannunsa cikin nata,ya dinga matsawa da baya da baya har ya bada tazara a tsakaninsu,sai ya zauna saman sofa din dake facing kujerar da take kai yana ci gaba da kallonta. Tsahon wasu mintuna numfashinta ya sake daidaita. A hankali ta maida idanunta ta lumshe tana jin yadda gabbanta gaba daya suka saki. Ko bata bude idanunta ba,koda bata kalleshi ba tasan idanunsa yana kanta ne,tasan kallo yake qare mata,wataqila ma qirjinta kadai yake kalla. Ta sani....ta kuma sani bata buqatar a maimaita mata. Maza irinsa mayun mata ne,wadanda sau da dama suke fakewa da addini su dinga kallon mata yadda sukaga dama. Ballantana shi din. Har yanzu tana iya riqe adadin haduwar hannayensu guri daya data tabbatar intentionally ne bawai arashi ba. Me ta yiwa sultane data cancanci irin wannan hukuncin?......me ta aikata ga sultane data cancanci wannan izayar ta auren MALAMI?. Malamin ma datayi imani bata taba jin haushi tsana ko qin jinin wani malami kamarsa ba. Ya qwace mata sultane dinta.....ya qasqantar da darajarta......ya kuma nesantata da sultane ta hanyar taba kusancin dake tsakaninsu. Samun tabbacin daidaituwar numfashinta ya sanyashi miqewa a nutse,ya soma takawa cikin nutsatsen takunsa daya hana akhnan fahimtar yama fita a dakin,taci gaba da kwanciya cikin qunan rai da baqincikin wanzuwarsa a gurin,yayin da shi kuma ya jima da ficewa a dakin. "Sannu" Kalmar ta sauka a kunnenta. Taji aisa ce,don haka ta bude jiqaqqun idanunta a hankali ta saukesu a kanta. Kallon kallo suka yiwa junansu na wani dan lokaci,tambayoyi ne masu yawa cikin kanta.....tambayoyine tuli da takeson ta yiwa su aisa su. Dama can sunsan da plan din aura mata mutumin kowacce ta kama bakinta ta tsuke?,dama suna da labari amma sukaci amanarta sukayi shuru?,ko kuma yadda labarin yazo mata haka suma yazo musu?. "Ki rufa mana asiri don Allah" Taji muryar shehnaz kuma daf da kafadarta inda yake zaune a dazu wanda ta jima da dauke kanta daga gurin gudun kada yaga fitar hawaye daga idanunta. Abinda take ganin zai zame mata qarshen abun kunya.....yaga weakness dinta?. Ta bari yaga hawaye daga idanunta?. Idanunta ta bude akan shehnaz dake dafe da qirjinta,duk da fuskarta ta nuna tashin hankalin data shiga a dazun amma bata fasa fadin abinda ke zuciyarta ba. Kai ta gyadawa akhnan "Eh ki rufa mana asiri karki sake suma.....don idanunmu ba zasu iya sake daukan nauyin kallon abinda muka kalla a yanzu ba.......bamu iya jura bama.....fita mukayi. Wani irin shauqi tun a yanzu akhnan?.....ya cika dakin da kwarjininsa gaba daya....." Idonta ta runtse da kyau. "Don Allah shehnaz.....don Allah" Ta fada da wani irin sanyi. Maganganunta suna tuna mata yadda hannuwansa suka samu daman taba sassan jikinta ne kawai......hannunta.....gashinta.....bayan nan me dame ya taba ma?. Tambayar da tayi tsawa a kanta kenan,harta bude idanunta da sauri ba tare data shirya ba ta watsasu akan fuskar shehnaz,da murya me qarfi wanda sautinta ke fita da wani irin rauni don har rawa sound dinta yakeyi "Don Allah shehnaz......me dame ya taba a jikina?" Sak aisa tayi,don tambayar ta mata girma saboda,amma ga shehnaz 'yar katobara sam.bataji komai ba,saima dadin tambayar dataji. Tana murmushi abinta ba tare da duba da yanayi da dalilin tambayar da akhnan din tayi mata ba ta gyara zamanta tana blushing. "Connexion profonde(deep connection)Mouth to mouth resuscitation" Ta fadi kanta tsaye abun yana sake dawo mata a kwanyarta tana sakin murmushi. Idanu sosai akhnan ta fidda tana fara shiga tunanin yadda bakinta ya hadu da nashi. Wani matsanancin bacin rai ya sauko mata,sai kawai ta fashe da kuka tana jujjuya kanta da sauri,wasu tawagar hawaye masu dumi suna sauko mata. "Allah zai sakamin......wallahi Allah zai sakamin" Ta fara fadi kaman wadda zatayi iska. Tsoro abun ya baiwa aisa,ta watsawa shehnaz harara. Muddin akhnan din ta fara bore irin wannan abund me wahala sauko da ita ta sauqi,batasan ma ta inda zata fara ba indai itace zata gyara Barnar shehnaz din. "Kowacce tambaya ma wai tana da amsa ne?....."💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 92* Idanu shehnaz ta fidda tana kallon aisa. "Meye laifi na?,tambaya tayi na bata amsa fa.....aisa mana....me nayi?,gaskiya na fadi mata fa" Iska sosai aisa ta furzar a bakinta,ta sauke hannuwanta tana nufar akhnan dake kuka sosai kamar qanqanuwar yarinya. "Biftu mana.....kin manta wacece ke?,ya zaki abinda zaki zubda martabarki?,sassanki cike yake da hadimai kin sani....kinaso suji ne?". Wani kallo ta watsawa aisa din da jiqaqqun idanunta. "Hardaku aisa.....hardaku aka auramin shi.....me zakucemin?....aisa banason ganin kowa!!" Ta fada cikin daga murya da qaraji. Baya aisa taja tana duban yadda gaba daya akhnan din ta birkice kaman ba ita ba. Ta iya rigima ta kuma iya tuburewa akan abu,wannan din wata dabi'arta ce da aisa ta jima bataga ta motsa ba......amma ta sani yau kam saita Allahu. Duban juna sukayi ita da shehnaz,saita soma takawa tana fita. Ta gama yanke abinda zatayi,gwara kawai ayi.maganin akhnan din me gaba daya. Banda iya shegen banza da wofi......idan aka cire SARAUTA da take taqama dashi ba wani abu data hanga wanda akhnan din zata gwadawa sheikh haisam. Ta wata fuskar ma idan aka cire SARAUTA din sheikh haisam din irin mazan nan ne da ake cewa KODA KUDINKA saida rabonka,bataga wani abu qwaya daya da zai sanya a gujeshi ba. Idan aka azata a mizanin aji.....idan aka dora a sikelin dacewa bata isa ta tsaya matsayi daya dashi ba,wai bahaushe yace IDO BA MUDU BA YASAN KIMA wannan karin maganar da haisam din kawai tafi dacewa. Taso ta tarar da haisam din,saidai ta samu tuni ya wuce,sai yakumbo morsa safiyya da mammina dake yunqurin dawowa ciki duba jikin nata. "Gwara ku shiga kuga abinda takeyi,nikam bazan iya ba" Aisa ta fadi tana ratsasu ta wuce abinta,saidai taci alwashin nan da wanni uku zuwa hudu muddin akhnan din bata shiga hayyacinta ba sai tayi maganinta. Ta tafi bawai don ba zata dawo ba,ba kuma wai don ba zata bibiyi al'amarinta ba,ta tafi ne ta lissafa awannin,ta kuma jira taga hankalin akhnan,taga ME ZAI SAUYA?. Juyi tayi kawai tana yin rub da ciki saman gadon data tashi ta koma kai,ta jawo fiber pillows dinta masu tsananin laushi ta cusa kanta a qasansu. Kuka take sosai,tana sake jin baqinciki yana ratsata. Kuka take har zuciyarta,irin kukan data manta rabonta da yinsa. Gefe guda tana jin wannan qamshin turaren nasa a duk wani motsi da zatayi baibaye da jikinta,abinda yake sake matse zuciyarta kenan,kukan yana sake narkewa gami da gangarowa tun daga tsakiyar zuciyarta. Itakam ta sani,nata ya riga ya qare,ta sani ba qaramin abu bane zai sanya sultane daura mata aure irin wannan. Ba shawara da ita ba kuma neman yardarta. Ta sani ba jiya ba ba yau ba,ba qaramin ganin girma da martabar malamin yake ba. Abu na farko daya sake jawo tsanarsa kenan a zuciyarta bayan zargin da take dashi me qarfi na cewa shine mutumin hippodrome. Ta tsani tana gaba wani ya tako ya karbe matsayinta. Ta sani tana sama wani ya jawo hannunta ya sauketa qasa. Bata ga maciji da duk mutumin da zai musa girmanta da martabarta. A cikin dukkanin wadannan abubuwan ba wani abu da bai aikata mata ba.....AKAN ME ZATA QAUNACESHI?. Uwa uba ma shi din tsintacciyar mage ne. Bata da tabbacin akwai wani cikakken nasaba da yake da ita dangi ko ahali. Koda yana dasu wanne MATSAYI yake dashi a rayuwa?,wanne FADA AJI yake dashi?,wacce wayewa ya mallaka?. A sanda duniya ta dade da yin gaba,a sanda duniya ta jima da wayewa,a sanda idanu suke a bude da sanin ME AKE NUFI DA RAYUWA bataga wani abu daya hada MALAMI da dukkanin wadannan abubuwan ba. MALAMI FA!.....ORDINARY MALAMI! Sunan ya sake bugawa cikin kanta,take wani sabon kukan ya barke mata. Tana jin maganganunsu morsa safiyya,muryar dake sake qona mata rai,taji muryar mammina da dukka irin salon gwanancewarta da sanin yadda zata shawo kanta,amma dukka a banza. Nannie tayi nata haka yakumbo,ammo ta daga kai ta kalli wani a cikinsu ta qiya. Tsaf morsa safiyya ta karanci yanayinta,wannan tsoho halin....wannan kafiyar,saita juya dukkaninsu ta kallesu. "Ina ganin muje haka.....duk randa taga damar samawa kanta salama zata fahimci kalar abinda akeson gaya mata.....aure ne dai biftu ya gama dauruwa......haquri da kuma fuskantar gobenki ce kawai ta rage miki". Wani irin suka maganganun sukayi mata. Aita sani basai ta nuna mata ba.....ta sani cewa tana farinciki da hawayenta.....ta sani cewa tana walwala da dukka abinda zai bata mata rai,ta tsani jin dadinta ko dariyarta,tana kuma da yaqini da saninta da hadin bakinta sultane ya shirya wannan BARAGURBIN AUREN. Wani irin murmushin nasara da mugunta mammina ta saki can qasan ranta. Duk da zuciyarta na mata kokwanto da suya na canjin data fara gani tattare da akhnan. Tun daga ranar da almaz ya saketa bata sake bata wata fuska ko dama kamar yadda take bata a baya ba.....to amma yanzun wata dama ce a wajenta na gyara wancan alaqar......wata dama ce a gareta na maido komai kan hanya.....na maido komai kaman yadda yake a baya. "Bada wannan harshen ya kamata kiyi magana da wanda ke cikin damuwa bafa morsa......hankalinki har yanzu bazai taba zuwa daya daga akhnan ba". Wani kallo morsa safiyya ta watsa mata,kaman zatayi magana sai kuma ta juya abinta a nutse tana ficewa bayan ta ajewa mammina wani kyakkyawan murmushi. Murmushin da mamminan tayi imanin ba REAL MURMUSHI bane.....murmushin da tayi imanin akwai wani abu a bayanshi. Duk da tana benefiting da yawan fushin morsa safiyya da dabi'arta na gaza boye fushinta da abinda ke cikin zuciyarta......amma tana tsoron AMSA CIKIN SHURU irin wannan na morsa din. "Muje mammina......wannan 'yar kashin bata inda zata fahimci mutane......amma ta bakin safiyya ai shima kuka yana da iyaka idan ba me rarrashi" Yakumbo ta fadi tana sanyasu a gaba suna ficewa,duk da ba haka mammina taso ba......ta kuma ci alwashin YANZU ZATA DASA SABON HARSASHI ta tafi badon ta tafi bane gaba daya......ta tafi amma kuma ZATA DAWO a nan kusa bawai a nesa ba. *HAISAM* Strange feeling kawai yakeji cikin jikinsa. Wani irin yanayi yakeji da bai saba jinsa tattare dashi ba. Wani irin mutuwar jiki,yana takawa da nutsuwar da bazata baka daman fahimtar abinda yakeji din ba ya nufi sashensa. Iska ya furzar daga bakinsa. Wani abun ne da bai taba faruwa dashi ba tsahon rayuwarsa. Cakudedeniya da jikin diya mace. Mutum ne shi me yawan nesanta kansa da ire iren wadannana abubuwan qwarai da gaske. Ya sanyawa ransa akwai LOKACI. Lokacin dashi kansa ya tabbatar idan yazo bazaiji bari ba.......ya killace kansa ga HALAL dinsa kawai.....ya killace kansa wa halastacciyar matarsa. Matar da a sannan shi kansa bai taba hasashe ko tunanin WACECE BA....kawai ya sanya a ransa ME RABO,shine sunan kawai da yakan furta. Sake fesar da iska yayi daga dogon hancinsa daya tsaya sosai saman fuskarsa. Baisan me yasa qamshin hair mist dinta ya maqale a hancinsa ba.....baisan me yasa qamshin turarenta ya nace shima a hancinsa ba. Gaba daya kansa sake tariyar moment din yake masa wanda duka duka yanzu ya baro gurin. Idanunsa ne suka sake hasko mata qirjinta dake zaune cif tsakanin kafadunta guda biyu. Wani irin zubawa tsigar jikinsa tayi har sai daya dunqule hannunsa da kyau yana furta. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Can qasan ransa. Duk yadda aka jarrabi maza da son gurin.....wanda bai tsame kansa da kansa ba.....don daya daga cikin abinda ya sanya ya wajabtawa kansa lowering gaze dinsa akan kowacce mace.......amma bai taba hasashensu haka kusa da kusa dashi ba. "Idan ka samu kusanci sama da haka dasu fa?.....inda ace zaa bude......." Cikin azama ya tsawatarwa sashen zuciyar dake qoqarin qawata masa wannan tunanin cikin ransa......wanda ko a yanzun qoqarin yakice wancan image din dake cikin idanunsa da kwanyarsa yake. "Halal dinka ce fa" Wata zuciyar ta tunasar dashi. Murmushi ya yiwa kansa da kansa,yana tuna cewa tuna hakan da maido hoton ga idanunsa ba haramun bane.....to amma kuma aurensa ba yana nufin wanzuwar komai a tsakaninsu ba. Aurensu yafi cancanta da a kirashi GARKUWA......zata zame masa garkuwa da zai wasa da hankalin mammina yadda ya kamata......ita kuma zai mata ALFARMA kamar yadda kowa nata ya buqata. Da wannan kasalar ya murza handle din sassansa ya shiga. Still suna zaune suna hira abinsu,kamar wadanda suka shekara goma basu hadu ba. Wannan karon harda naseeb daya basu tabbacin ya koma Riyadh lafiya. "Wancan angon har ya dawo daga gurin amaryar ne?" Naseeb ya fadi wanda shi daya ne ya hangi shigowar haisam da fara haurawa zuwa stairs dinsa,ya kuma qare masa kallon tsaf sanda yake takawa din. Waiwayawa sukayi suna dubansa kafin maleek ya dawo da kallonsa akan naseeb yana danne dariyarsa "Bari naje na sameshi" "To kabi dai a hankali......kasan tsohon tuzuru ne......idan kuma kaje kayi abinda zaka tunzurashi yaqi shige maka gaba shikenan". " Bazan fara ba.....don idan na rasata mutuwa.zanyi" Ya fadi yana haurawa ta bayan kujerun ya dirga yana wucewa stairs din. Yana jinsu suna masa dariya su dukka. "Nidai naga alama sarakan nan basu iya zarmewa ba idan suka fada soyayya.....duk wani maintaining pride da sukeyi sai ya dinga rawa.....me yasa?" Khadeem ya fadi,yana jinsu omar na goyawa maganansa baya,sai ya saki murmushi kawai baibi ta kansu ba. Shidai ya sani da gaske ne mutumin daya fiya shuru kamun kai da nutsuwa abune me sauqi soyayya ta rikitashi. Ya yadda da gaske falaak ta rikitashi,shi kansa idan ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa sai ya dinga ji da ganin kamar ba shine maleek ba. To amma baida wani qwarin gwiwa ko tabbacin haisam zai fada haka da sauri. Ya sani ba wanda zaice yafi qarfin siyayyay,tana da wani irin qarfi da take iya wargaza komai da kowa.......to amma bashi kadai ba,dukkansu sun sani ba abu bane me sauqi hakan ta kasance akan mr lowering gaze dinsu. _uhmmmm.....nidai nace banda cika baki_ Sai daya zauna ya jirashi ya fito daga toilet. Kansa da damshin ruwan dake nuna alwala ya daura. Dubansa yakai ga agogo,akwai sauran kusan awa daya ko mintuna arba'in kafin lokacin la'asar yayi,to daura alwalar kuma ne meye?. Kallo daya tak maleek yayi masa ya janye idanunsa daga kansa. Idanun nan na captain din.....wannan manyan idanun dake da wani irin kaifi da tsini gaba daya sun koma sun rusuna,sunyi wani irin laushi. Tattara duk jarumtarsa yayi yakai dariyanshi qasan ransa ya danneta,sannan ya debo tambaya ya dora akai. "Wai me ya faru?.....wani abunne me tsanani?". " Me ka gani?" Haisam ya jefawa maleek din tambayar da wani irin coolness. Yadda ya zuba masa ido yasan yanason samo.amsar tambayarsa ne daga kallon da yake masa,don haka sai ya basar yana amsa masa tare da sake danne dariyarsa qasan ransa. "Aah....yanayinka ne yake nuna kaman ba lafiya ba". Shuru yayi kawai,ya maida idanunsa ya lumshe sannan ya budesu akan maleek. "She was so fragile maleek......ina mamakin yadda stubbornness dinta yake da yawa bayan tasan duk wani strength nata bame yawa bane......ta dauki kanta da fadi maleek......" Haisam yayi maganar da alama dabi'un nan nata biyu suna ci masa rai. Yana iya jin maganganunta dasu aisa a kunnensa bayan ya fita,don bai nisa ba yadan tsaya yana amsa godiyar da morsa ke masa. "Tana zaton ina da interest ne a kanta?.....kota dauka ina cikin jerin lusaran mazan da suka dinga zuwa neman yardarta ta auresu kaman ita kadaice diya macen data rage a duniya?.....to hell with her sarautan.....to hell with her mulkin.....da tasan yadda komai yake da bata suma ba.......sultane kawai nake kalla da morsa safiyya maleek " Ya qarasa maganan fushi yana nunawa qarara saman fuskarsa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 93* Zallar mamaki ya kama maleek,sai kawai ya zuba masa ido yana kallonsa. Yau a karon farko bayan dogon lokaci haisam din yana fada saboda wata mace ta bata masa rai?. Shi baya complain completely akan mata.....in fact ma bashi da wani hadi dasu,yana qoqarin avoiding nasu ne kawai akan komai nasa. "What about this" Maleek ya fadi yana pointing qasan labban haisam din. Wani haushi ya kama haisam,yana masa maganan abinda yakeji yana bata masa rai yana nuna masa fuskarsa?. Duk da hakan baiqi ta maleek din ba,ya miqa hannunsa qasan lips din nasa yana dangwalo gurin,sai yaji danqo. Koda ya dawo dashi zuwa ga idanunsa lipstick ya gani baby pink in color. Wuta tadan dauke masa,kafin ya mutstsuka yatsunsa yana batar da kalar dake jikin yatsunsa. Qaramin tsaki ya sake ja,mintunan suna dawo masa akai. Baisan me ya jashi bata irin wannan taimakon ba.....baisan ya akayi ya hada jikinsa da nata ba har haka. "Saboda ka ceci rayuwarta......saboda ganin girman sultane da morsa safiyya right?" Yaji maganan maleek tsakiyar tunaninsa. Kallonsa yayi kafin ya sake kauda kai yana cirar tissue guda daya yana goge duka area din lips dinsa. "Ko ka karbi first kiss ne?" Maleek ya fadi qasa qasa yana duban haisam. Yi yayi kamar baiji ba,sai kuma ya shammaceshi yakai masa naushi,yayi kyakkyawar sa'ar samunsa a kafadarsa. Gurin ya dafe yana yamutsa fuska yana duban haisam. "Yanzu idan kayi nasarar karyani me zaka cewa me martaba?....me kuma zaka cewa falaak?". "Idan kaga na shige maka gaba an baka ita kenan ba" Ya amsa masa yana nufar hanyar toilet,don ya fahimci a wannan karon dukkaninsu sun toshe kunnuwansu ne da idanunsu,dukkaninsu ba wanda ya daura aniyar fahimtarsa,kawai su auren yayi musu......kome meye a ciki nasa lissafinne shi kadai. "Kada muyi haka daki mana.....ka dawo muyi magana,nayi alqawari zan fuskanceka" "Bana buqata.....a yanzu dai bana buqata. Tunda kazo agadez soyayya sun hadu da omar sun lalatawa me martaba yaro. Ba zaka gane zancena ba,ba zaka gane maganata ba muddin ba zancan soyayya bane zan maka. Na yafe kaje,wanka zanyi,zan kwanta kuma idan na fito,sai lokacin sallah yayi zan fito da kaina.....na roqeku ku barni hakanan" Ya fadi yana tsaye bayan qofar toilet din yana hade hannayensa biyu alamun roqo. Fuskar tausayi maleek yayi masa sannan ya juya yana jan qafa alamun yayi giving up ya fice. Duk da bai shirya ba amma sai da murmushi ya subuce masa. Ya yarda da maganar nan da ake cewa abokinka matattarar sirrinka ne,dukkaninsu idan suka hadu kaman yara suke ga junansu. Idan suna wani abun a tsakaninsu,yakanyi tunani musamman a inda yake komawa da baya yayi relaxing,sai yaga meye na musamman a tare dasu mata ke nacin binsu haka?. Tambaya ce dake dauke da daruruwan amsoshi da zai miqata ga dubbannin 'yammatan da burinsu shine ta mallaki guda daya a cikinsu. *TAMIM* Zufa kawai yakeyi wadda ta wankeshi tassss tamkar wanda aka dauki botikin ruwa aka watsa masa. Wani irin fushi ne yake bayyana kansa da kansa saman fuskarsa.....fuskar da a yau tsananin fushin ya sauya mata kamanni zuwa wani yanayi me ban tsoro maras kyan gani. Hancinsa ya bude sosai,ya kuma ninka girman da yake dashi,hakanan idanunsa gaba daya sun juye sun sauya launi. Bai taba zaton komai zai juye haka da hanzari ba......bai taba hangenta a matsayin MATAR WANI BA baya ga shi,tun sanda ya samu nasarar qara bugar da almaz ya samu ya rattaba mata saki uku. Gwara auren almaz sau million akan wannan auren. Akan wannan auren bashi da wani sauran hange......akan wannan auren bashi da wani sauran tunani,akan wannan auren fatan a saketa nan da SHEKARA dubu ma gani yakeyi yayi kadan. Matashin malamin nan fa?.....shi aka bawa,mutumin da tsaiwa kawai kusa dashi sai me dakkakiyar zuciya. Mutumin da har yanzu ba kowa ke iya kallon qwayar idanunsa ba.....mutumin da tun daga nesa kwarjininsa yake kasheka gaba daya,ta yaya zai iya warware wannan lamarin?. Bazai taba yarda ba.....bazai taba aminta wahalarsa ta shekara da shekaru su tashi a banza ba. Ba kalar bautar da bai ma mammina ba.....ba kalar hadarin da bai jefa kansa ba,ba kalar barazana da rayuwarsa data ahalinsa da bai gani ba.....hasalima ya rasa iyalinsa ne saboda sadaukarwa ga mammina......ya rasa kowa nashi saboda sadaukarwa......shi me yasa zata bari ya RASATA?. Yarinyar data girma a gabansu?.....yarinyar da yasha duqawa.....yarinyar da yasha kwanciya ta takashi tabi da kansa. Tsawa umarni kala kala ba wanda baibi ba nata. Dukkan wata kariya ta fili data boye ya baiwa yarinyar saboda TANADIN WANNAN RANA. saboda ya sani cewa komai da kowa na masarautar agadez yana qarqashin umarnin zeenatu.....komai da kowa yana qarqashin sarrafawarta,sai abinda ta tsara ya faru shi zai faru.....Cewa kawai zatayi NA BAWA TAMIM ya tabbatar kuma ta badu har abada.....amma sai gashi a karon farko bata masa kara ba......a karo na biyu ma haka?. Tattare rigar jikinsa yayi ya watsar a saman shimfidar dake gurin. Abinda yake hange yana tasiri kadan kadan shine.....kamar K'ARFIN juya komai da zeenatun ke dashi kamar yana raguwa.....kamar yana ja da baya. Shi kuma ya sani,yayi rayuwa da sarakuna kala daban daban,a duk sanda irin haka ya fara faruwa,to tamkar fa komai yana shirin kwabewa ME IKO KENAN. Idan kuwa haka ne ko yaya ya kamata ya fanshe wahalarsa ta shekaru. "Koda baka mallaketa qarqashin aurenka ba.....koda bata zama taka ta har abada.......ko sau d'aya tak ka d'ana wadannan abubuwan da kake kwana kana hasasosu,ko sau daya ka ratsa wannan ma'ajiyar izzar.....ko yaya KA GAURAYA JINI DA JINI TSOKA DA TSOKA" Wata mahaukaciyar dariya ya saki saboda yadda tunanin yayi masa dadi,ya sake qyaqyacewa yadda tunanin yayi masa daidai. "Matar sheikh haisam take a yanzu fa?" Wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa tamkar me tunasar dashi. Wani mahaukacin tsaki yaja,yana jin a yanzun koda babanta ne ke aurenta shima sai ya d'ana,koma waye mijin tabbas shima sai ya huce wahalarsa. Koda daga sannan fuskarsa zata bace Bat daga agadez,ballantana KWANYARSA tana wani irin mugun ja da bashi da kokwanton komai zai tafi cikin sirrin da saidai idan shi yaga dama ya yayeshi. Zubewa yayi saman kujerar yayi d'ai d'ai yana ci gaba da qyaqyata dariyarsa cikin nishadi. *_TURQASHI!.....AH NACE TURQASHI.......LALLAI,ANYA TAMIM BAKA DEBO RUWAN DAFA KANKA BA KUWA?_* *_KALLON MUHAMMAD HAISAM KAWAI KAKEYI BA TARE DA KASAN TRUE COLOR DINSA BA.....amma hausawa sukace shi me rabon shan duka ai bayajin bari sai yasha,muje zuwa_* *AKHNAN* Ba abinda ya canza tun daga awannin dazu har zuwa yanzun da yammaci tayi magariba kuma ke shirin kawo kai. Kuka kawai takeyi kaman ba gobe....kuka takeyi kamar ta rasa komai nata. Duk da tanajin ta rasa komai dinne,tanajin rayuwarta ta naqasa,tana kuma jin duk wani buri nata ya gama mutuwa murus. Ina zata iya buda baki tace wai MALAMI ta aura?,dame zatayi tutiya?. Tana neman wayayyen namiji ne.....tana neman namijin da zai tsaya gaban duniya yayi magana da dukka yaren da ake buqata. Namijin da zai kama hannunta ya sakar mata dukkan 'yanci......ya sakar mata dukkan dama,ta jagoranci rayuwarta da kamfaninta daya kasance zuciyar dukiyarta zuciyar SULTANE zuwa matakin da ba wani company daya taba kaiwa har haka. Birra tayi dabarun,tayi maganan duka a banza,don daga qarshe ma tsawa ta bugawa birra din ta koreta. "Kada na sake ganin fuskarki a nan munafuka" Ta fada a tsawace kamar zata cinye naman birran danye. Sum sum birra ta miqe zata fice. "Zoki tattara komai ki fita dashi,.....banason ganin kowa.....banason komai kuma" Ta sake fadi da fuskarta datayi jawur saboda awannin data dauka tana kuka. A nutse birra ta qaraso tana kwashe kayan abincin da tun dazu take jerasu,tana satar kallon yadda ta tura kanta qasan pillow taci gaba da kukanta. Tausayinta takeji har qasan zuciyarta,tausayinta takeji sosai,tana da kirki wanda saika zauna da ita sosai zaka fahimci haka,tana da qoqarin kyautatawa wanda yake hidima a qarqashinta,duk da tana da fada tana da zafi tana da izza amma hakan bai sauya kirkinta ba. Duk da kukan da takeyi ita har ga Allah tana murna da wannana auren. Jikinta yana bata abubuwa masu yawa game da mammina da rayuwar Akhnan din,saidai abune me razanarwa a iya zuciyarta ma kawai ta zargi GIWA ballantana akai ga furtawa. Mamaki yana qara cika birra,ta rasa kukan mene ma Akhnan din keyi?. Ta yarda da gaske ne idan dadi ya yiwa bawa yawa sai yace ALLAH KASHENI NA HUTA. A iya rayuwar masarautu da sukayi tun tana mitsitsiyarta har kawo yanzu,bata taba ganin NAMIJI da ya dauki hankalinta ba kamar sheikh haisam ba. Ta gaza gamsuwa cewa ordinary sheikh ne......komai nasa yasha bambam da kowanne malami da idanunta suka taba gani ko suka taba zama dashi. Kwarjininsa yafi mata kama dana BASARAKE ko jinin sarauta. Sukan zauna wani lokaci su yasu suna gulmar kyansa. "Jinin annabi yusuf" Shine sunan da sukan kirashi a boye. Yana da tarin ilimin daya sanya kwarjini da nutsuwa suka masa wani irin ado......to dukka bayan wadannan me Akhnan din take nema?. Sarauta ce kawai za'a ce bashi da ita.....ko kuma ace shi din ba jinin sarauta bane,a dabi'unsa da yanayinsa kuma bayyana SARAUTAR kawai sukeyi......amma baya ga wannan bataga wani abu na aibu ko tawaya a tare dashi ba,saidai idan kukan BADAN SARAUTA BANE Akhnan din takeyi. "Zaki fita ko sai na miki duka!" Ta sake fadi ga birra wadda ke tsugunne tana tattare kayan tunani yaci qarfinta. "Tuba nake" Ta fada tana qara hanzarinta,tana kuma jin wani dumi yana busowa daga inda Akhnan din ke kwance. Babu ko shakka zazzabi ne,zazzabi takeyi,tana dadewa batayishi ba,amma birra ta sani,duk ciwo idan Akhnan ta tashi yinsa da qarfi yake durfafarta,sai taji a jikinta don tana dadewa bata yishi ba. Tana tsoron kada ya kwantar da ita yadda ya saba mata,tana kuma tsoron gayawa kowa kada ya zamana tayi laifi,da wannan tunanin ta isa kitchen ana qwala kiran sallar magariba a babban masallacin dake manne da gidan sultane. Umarni ta bayar dasu tattara komai da aka dafa su bayar,ta basu simple recipe na lite abu tace su dafa a ajjiye. Tayi hakanne incase don tasan dole ba zata bari Akhnan din ta kwana da wannan uban zazzabin ba,dole saita gayawa wanda ya dace don a samu a bata kulawa kada yayi mata yadda ya saba,don zafin yayi yawa,kada yakai matakin convulsion. Kebantaccen parlor dinsu da aka ware musu hadimanta mafi kusanci su biyar dinnan. Birra buhaina bushira barratu da bara'atu. Su biyu ta tarar,suka bita da kallo sanda take zama gefan kujera tana daukar daya daga cikin wayoyin da ake ajiye musu saboda buqatar kiran gaggawa ga wani sashen ko wani a cikin gidan. "Har yanzu bata haqura ba?" Buhaina ta fada tana duban birra. Kai ta jinjina cikin alhini tana lalubar number aisa. "Wannan mahaukacin zazzabinne ma a jikinta,tsoro nake kada ta shiga convulsion ma" Tayi maganan daidai sanda ta danna kiran aisa. "Ikon Allah......lallai dadi idan ya yiwa mutum yawa ba abinda bazaiyi ba......anya wannan karon qwaqwalwar gimbiya lafiya qalau take?" Buhaina ta fadi qasa qasa tana kama haba idanunta akansu dukka su biyun. "Kema kina mamakin yadda take bore akan auren mutum kamar sheikh muhammad ko?" Barratu ta fada tana duban buhaina. Kai ta jinjina "Sosai fiye da yadda kike zato......inama inama.....inama ace....." "Dakata malama" Birra ta fada tana dariya. "Ai karma ki qarasa.....aljanna tafi qarfin arne" Dariya suka saka su dukka ukun don kowacce ta karanci hasashen kowa. Maida idanunta birra tayi kan wayar ganin an daga,gabanta yadan fadi tana fatan Allah yasa aisa bataji abinda suke magana akai ba. Sake jaddada sallamarta aisa tayi tana basarwa birra kamar bataji tattaunawarsu ba. Bataga laifinsu ba ko d'is,don basu ba,ko ita tana wannan tunanin,ko ita tana cewa inama inama din...... Ba wata isashiyar mace da zata mallaki haisam ta raina.....kome isarki kome kuma matsayinki a duniya. Wani irin namiji daya zama LU'U LU'U cikin maza.....diamond ne uban gold kuma kakan azurfa. Amma batasan da wanne idanu Akhnan ke kallon abubuwa ba,ta iya yiwuwa bada irin idanun mutane take kallo ba,ta iya yuwuwa zuciyarta ta qarfe ce kota roba data kasa jin amincin da dukkaninsu sukaji da labarin aurenta da haisam din.. Amma ta sani,ko ba jima ko ba dade wataran zata fahimci cewa DIAMOND Allah ya dauka ya bata. "Ya ake ciki?" Aisa ta tambayi birra. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 94* "Ba wani sauyi,kuka take har yanzu,tun abincin safe bataci komai ba.....zazzabinnan nata me wuyar sauka ne yanzu haka a jikinta,kuma kaman ya fara qarfi" Kai aisa ta jinjina,itama ta sani,zazzabin Akhnan idan ya fara yana da wahalar magani yana da wuyar sauka kuma. Jini yake qone mata wani lokacin idan yaso tsiyarsa,wannan ya sanya ake tattalinta sosai,daya fara kuma ake tsayawa a kanta. "Kici gaba da kula da ita,zan gyara lamarin". "Godiya muke" Birra ta fadi aisa ta yanke kiran tana yabawa kalar hadiman da Akhnan din ta samu. Dukka yaran suna qaunarta qauna ta fisabilillahi,suna kuma dukkan qoqarin su a kanta gurin kula da ita da kula da abinda zai cutar da ita. Wayar ta ajiye a nutse,ta kuma shiga closet dinta ta samu wadatacciyar abaya ta saka da baby hijab me dan girma,sannan ta yiwa hadimarta guda daya maganan tazo ta rakata. *HAISAM* Sam ya mance da abinda ya faru a dazun,saidai abu daya dake dawo masa cikin kansa lokaci bayan lokaci. Doguwar waya da maganganun da sukayi da sultane kamar me masa ban kwana ko wasiyya. A dukkanin hirarsa ya fahimci girma da tarin qaunar da yakewa Akhnan zallah cikin maganganunsa. A maganarsu ya sake fahimtar kamar akwai wani abu a boye dame damun sultane din wanda shima qila baisan meye ba.....kawai dai ya fahimci akwai wani abu da bai zama comfortable dashi ba. Bai iya dannewa ba,bai iya kawaici kaman yadda yaso ba,sai daya rufe maganan tasu da fadin. "Don Allah.....kayi mata alfarma koda ita bata fahimci haka ba....taci tawa alfarmar......kayi mata riqo tamkar riqon da zaka yiwa qanwarka uwa daya uba daya. Ka maye mata gurbin ubanta sultane.....ka maye mata gurbin mahaifiyarta SAFEENA" Maganan ya tsaya masa sosai a rai. A duk sanda ya tuna labarin safeena sai ya sake jin girman baiwar Allah ya qaru a ransa......sai ya sake jin kamad ya zama WAJIBI a kansa ya tone JININTA GUDA BIYU data bar irinsu a duniya ake neman birnesu saboda rufewa da yanke bayanta.....saboda shafe IRINTA a duniya gaba daya. Ta fuskanci wata irin birkitacciyar rayuwa......tayi sadaukarwa da dukkan qauna da soyayya,kalar sadaukarwar dake wahalar samu a yanzu. SOYAYYAR GASKIYA datayi wahala......tatacciyar qauna mara algus a cikin ta ko kadan. Yakanji kamar wani alqawari ne me girma a kansa da tuna labarin safeena kawai. Zuwa yanzu da suke takowa daga masallaci zasu koma sassansa ransa fresh yake jinsa. Yana tsara yadda bazai kwana bane yau a gidan,so samu ya kwana a personal house dinsa,amma kuma bayaso hankula su fara kaiwa ga tunanin inda yake fita ya kwana din. "Ta yaya wai zakaje damu gida captain?.....ka manta kana da iyali yanzu cikin gidan nan?" Muryar khadeem ta sanyashi daga kai yana dubansa. Bazaice ya manta duka ba.....amma tunaninsa ya aje zancanta a gefe,yanzun hankalinsa yafi karkata ga wancan asibitin na Ethiopia,don ya tabbatar akwai wata qura a lullube a gurin. Kaman zaiwa khadeem din magana sai kuma ya dauke dubansa kawai. Ya karanci abun dadi kawai yake musu,shi baisan har haka sukeso ma yayi aure ba sai yanzu,baisan me yasa sukafi son suga yayi aure akan kowa ba,bayan dukkansu ba auren ne dasu ba saidai niyya. Sallamar da akayi daga dan gabansu kadan da muryar mace ya sanyasu sukayi dif gaba Dayan su. Fuskar aisa din adan sake take gaidasu,suka amsa banda haisam daya maida hankalinsa ga wayarsa data dauki haske alamun shigowar saqo. "Ko zan iya magana da sheikh muhamamd?" Aisa ta fadi tana duban haisam din kai tsaye,izzarsa da kamewarsa tana burgeta. Sai a sannan ya daga manyan fararen idanunsa ya sauke a kanta,tadan sassauta dubanta a kansa saboda yadda taji idanunsan sun mata nauyi. Kai ya daga mata alamun eh,sai khadeem da maleek suka fara tawa zuwa gaba kadan. "Basai kunyi nisa ba........qarar amarya na kawo" Aisa ta fadi tana tattaro qarfin halinta idanunta akansu khadeem,don tana jin muddin suka bar gurin,muddin suka barta daga ita saishi ba lallai ta iya fadin komai. Tana jin tsaiwarsu zata taimaka,don tana hangen wani zuzzurfan sabo a tsakaninsu kamar shigen wanda ke tsakaninta da shehnaz da kuma akhnan din. Qawataccen murmushi khadeem ya saki yana dubanta. "Kamar a yarenku ance amarya bata laifi ai ko?" Yayi maganar da hausarsa shima da bata gama fita sosai ba. Murmushi aisa tayi,hausar tasu tana mata dadi sosai,yanayinsu kamar na sheikh haisam din,nutsuwa da kwarjini da wani irin kamewa a magana dake nuna zallar haiba. "Wannan amaryar nata laifin yana da yawa,tun abincin safe bata sakecin komai ba.......kukanta bai yanke ba,babban abun zazzabi ne a jikinta,kuma zazzabinta yana da wahalar sha'ani,nan da nan yake mata illa,kowa ya kasa shan kanta......ko zaka taimaka......don Allah?" Ta fada tana duban fuskar haisam ba tare data iya kallon qwayar idanunsa ba. "Subhanallah" Ya furta can qasan zuciyarsa da wani irin yanayi. Har saman ransa yaji ba dadi,ko ba komai amanace yanzu a hannunsa,haqqinta ya sauka daga kan kowa ya koma wuyansa. Cinsa shanta da lafiyarta gaba daya. Kome zataci yanzu a gidannan ko tasha a qa'ida haqqinsa ne......be kamata ace bai sake duba lamarinta tun dazu ba. Sultane baya nan,shi ya kamata koda ba igiyar aure a tsakaninsu ya kula da lamarinta tunda kusan haqqin kowa a masarautar yanxu a wuyansa yake. "Ba komai,kije zanzo yanzu in sha Allah" Ya fada cikin kamala da kamewa. "Na gode sosai da fahimta" Aisa ta fadi,mamakin sauqin kansa takeyi,a yadda take yawan kallonsa zaiyi wulaqanci izgili da wahalar sha'ani,yadda yake da yawan tsare gida haka take hasashen zai zama me wulaqanci ne kawai. Takawa yayi zuwa ga inda su maleek ke tsaye,idanunsa akan khadeem dake bin aisa da kallo a sace. Dauke kansa yayi,bai masa magana ba bai kuma nuna masa ya gani ba,ya fidda wayarsa yana kiran number abdii. Bugu daya ya dauka,ya saka wayar a kunne yana amsa gaisuwarsa. "Ka yiwa hussam waya,ya saka maka kudi a canzaminsu zuwa CFA a darennan please da sauri.......adadi me yawa nake buqata,zan tura maka list na wasu abubuwa yanzu kaida salaana da sauran CFA din hannunka kayi amfani dasu a siyosu gaba daya" "In sha Allah obbo" Abdii ya amsa masa a ladabce. Wayar ya tsinke yana sauke ajiyar zuciya,iska ya furzar a bakinsa yana sake lalubar wani number. "Ka gayawa muminai maza da muminai mata suyi qanqan da ganinsu..." Ya furta a nutse,maganan ya jawo hankalin khadeem zuwa jikinsa,saiya kalli haisam din ya saki murmushi me sauti. "Mr lowering gaze......wallahi nima inajin 'yar agadez ta kamani.....an samu wata buzuwar tayi wuf da zuciyata" Ya qarasa fada yana dora tafin hannunsa kan qirjinsa. Da hanzari haisam ya daga kansa yana duban khadeem,maleek na gefe yana dariya amma ya dake kaman bai fuskanci komai ba. Ci gaba yayi da kallon khadeem,idanun khadeem din kuma suna gaya masa ba gaskiyar abinda ke zuciyarsa khadeem din yake gaya masa. Su kuma wacce qaddara ce haka ta kirasu agadez daya bayan daya?. Anya wannan qaddarar zata tsaya a iya tona asirai na masu laifuffuka kuwa kadai?,kuma anya wannan qaddarar zata tsaya kawai akan aurensa da khadeeja?. Kasa bawa khadeem amsa yayi,kawai sai ya maida wayarsa aljihu yana duban maleek. "Dame dame ya kamata ace na siya?" Ba maleek kawai ba,hatta da khadeem sosai tambayar ta bashi dariya. Hade fuska yayi yana dubansu su dukka. "Wai yaushe na zama abun wasanku ne guys?" Kai kawai maleek yake girgizawa. "Idan ance ka shigo sha'anin bikin auren wani saika doje.....kafi ganewa ka rayu kai kadai kaida tunaninka.....yanzu qananun siyayya daya dace ka fara yi ma baka sani ba?" Bude musu wadannan kwarjantattun idanun yayi yana binsu da kallo,sai kawai yaja musu siririn tsaki yana takawa zuwa hanyar da zata sadashi da shiyyarta ba tare daya sake cewa da kowa komai ba. Sunsan bazai tsaya ba tunda ya tafi,bazai kuma sake sauraren komai daga bakin kowa ba a cikinsu a yanzu dai,don haka suka rabu dashi,saidai khadeem bai haqura ba "Saida safe kenan?...." Ya jishi sarai,bai kuma juyo ba,ya kuma fahimci fes abinda suke nufi,sai ya saki qaramin miskilin murmushinnan nasa ba tare daya nuna alamun yaji ba. Ba zasu taba yarda ba,ba kuma zasu gane ba......idanunsu ya rufe,fatansu kawai da burinsu auren ya juye zuwa irin wanda sukeso,abinda shi kuma ya riga ya sani bame yuwuwa bane. Ba wani muhalli ko gurbin soyayya ko daya a zuciyarsa ba,bazaiso abinda zaizo yana wahalar dashi ba,bazaiso abinda zai tafi ya barshi ba watarana..... Babban kuskuren da zai tafka ma gaba daya a yanzu shine yaso yarinyar. Ya tabbatar za'a iya amfani da ita ta kowacce fuska......SONTA shine RAUNINSA da za'a iya cin galaba dashi. Don zuwa yanzu mammina kawai ya gani.....amma bai yarda cewa ITA DAYA bace......bai gamsu ita kadai ta shirya ta tsara ta kuma aiwatar ba.....yayi imani akwai SAURA akwai RAGOWA kuma akwai wasu,yayi alqawari kuma sai ya tattarasu gaba daya cikin da'ira guda sannan ya sanyasu su fallasawa duniya SU SU WAYE?. *AKHNAN* Da qyar ta bude idanunta ta kalli lokaci,abinda ya tabbatar mata wunin wannan ranar duka data tsara zata fita tasha iska,zata fita tahau doki don ta huce takaicinta,zata fita tayi abubuwa da zasu bawa zuciyarta nishadi a yau dukka sun rushe. Maimakon hakama baqinciki qunci da tashin hankali su suka zama makwafi. Zazzabin dake cin naman jikinta tana jin kamar yana dab da gama tsotse jinin jikinta,ta fara jin wani yanayi da yake alamta mata yana dab da shiga hadari,don haka ta yunqura ta motsa ta miqe a daddafe. Rigar jikinta data sanya tun dazun ta cire,wani abu da bata taba yiba tunda take. A qalla a rana tana wanka biyu har uku ma idan garin da zafi,sutura tana iya sauya kala uku zuwa hudu kawai sai taji ta dace da yanayinta. Rigar ta zame daga bakin qofar da zata kaita closet dinta,ta zare brazier din jikinta duka ta zubesu a gurin,sannan ta qarasa ciki. Rigar farko data fara tararwa a hanger ta cire,silk sleeping gown ce wadda duka duka tsahonta bai wuce gwiwoyinta ba,armless ce wannan ya sanya kana iya hangen gefe da gefan breast dinta. Wuyanta ma lace ne me v-shape,shima hakan yake bawa idanu daman ganin tudunsu da tsaiwarsu daga sama. Da qyar ta jawo kanta zuwa saman gadon nata,ta koma rub da ciki ta kwanta,lulluba takeson yi amma duvet din ya mata wani irin nauyi,dole iyaka qugunta duvet din ya tsaya,ta dunqule tana sake sakin sabon kuka a hankali. Daya bayan daya take wuce parlors dinta da setting room dinta. Bai kuma sha wahala ba ya gano dakin da take ciki cikin dakunan dasuke mallakinta ne gaba daya. *MAMMINA* "Daga Ethiopia......daga yanzu zuwa kowanne lokaci daddadan labaei zai riskeki....ki zamana cikin shiri" Saqon muryar data samu kenan daya sanyata sakin dariya cikin nishadi tana ajiye wayar gefe. Ba abinda ke mata yawo irin yadda yaron yake neman zame mata qarfen qafa. Ba abinda yanzu yake damunta yake tashinta a barci irin al'amarin yaron. Abu mafi daga mata hankali shine sanin WAYESHI?......idan daga daya daga cikin masarautun ya fito tanason tasan wacece a ciki. Masarautar JIMMA zatafi zame mata suna mafi girman barazana ga kwanyarta.....masarautar GUMMA kuma zata zama ta biyu. Amma tayi imanin wannan MATAKIN shine zai bayyana mata SHIEKH HAISAM ne?. Koma waye tana jin zaizo mata da sauqi muddin bashi bane,hakanan tayi imanin indai shine JININ IBRAHEEM bazai lamunci yin shuru ba. Akhnan a yanzu itace gaba ta biyu da takeso ta saita,bai kamata ta bari al'amarin yayi nisa a haka ba,dole komai ya zamana akan sarrafawarta tsarinta juyawarta da kuma umarninta,wannan ne kadai zai bata dama da ikon isa ga muradanta. Dole safeena ta fuskanci wannan uqubar a cikin kabarinta.....dole ta dandana dacin da yafi na mutuwa a gurinta.....dole ta sanyata ta nemi tsarin sake zama KISHIYARTA koda a aljanna ne.....dole ta sanyata fahimtar illa qwace abun ZAITUNA ko qwace abinda zaituna keso daga hannunta. Kai tsaye ta nemi alkyabbarta ta zura saboda iskar dake kadawa wadda ke bada tabbacin kwantaccen hadarin da zai samar da ruwan sama daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ta shirya tsaf,tayi tsaye kuma a gaban madubi tana kallon kanta da kuma salon kirarin data saba yiwa kanta da kanta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 95* "Zaituna ikon Allah....zaituna iccen kabari......zaituna kabewar kan kabari......zaituna zamani goma sarki goma...zeenatu kuma me zamanai daban daban" Ta qarasa maganan tana sakewa kanta murmushi. Tana marmari,tana muradi tana kuma burin ganin yadda fuskar shiekh haisam zata sauya a sanda yaji wani abu ya faru da mahaifinsa. Wani dariya ta kuma saki.....da gaske ta sani,tayi kuma imanin koda wanne irin suna ne laqabinsa a wannan gabar shuru bazai yuwu a tare dashi ba. Jinin OROMO jinin IBRAHEE suna da wani irin TSAIWA da JAJIRCEWA akan martabarsu.....ta yadda bazai qyale ba....dole!. Shiga takun saqa da wasa irin wannan da jinin jimmawa ta sani ba abu bane me sauqi.......saidai kuma a wannan karon zata shige yaqi dasu da dukka QAWAZUCINTA. Zata maida martanin da abaya bata maidawa IBRAHEEM ba,har yayi zaton TA KASA har yayi zaton TA TSORATA ne ta janye....akwai HATSARI akwai WUYA amma dukka ita wadannan abubuwan basa sanyata janyewa daga yin dukkan abinda tayi niyya. Indai D'ANSA ya aiko mata zata tabbatar masa KUSKURE mafi girma da muni a tarihin rayuwarsa. Sai kuma taja da baya da sauri daga gaban madubin sanda wani tunani yazo mata. "Kada ya nemi kusanci ko kasancewa da ita!!" Maganan daya sanya zuciyarta wani irin bugawa da qarfin gaske. Sai kuma murmushi ya subuce mata data tuna WACECA AKHNAN. Tayi imanin akwai qura me kaurin gaske ga kowanne d'a namiji kafin ya samu daidaito cikin wannan zuciyar data sanya aka cika mata ita da izza da ganin fifikon saman kowacce halitta koma bayan ita. Hanya dayace take sanya rai wataqila ya samu sassucin isa gareta shine HANYAR YADDA DA DUKKA SHARUDDANTA na auren yarjejeniya.... Babban abinda yake sake jefata a duhu da take neman hanyar warwareshi shine. Me yasa bayan ya amince bai magana da ita ba?....a maimakon haka sai ya zabi yayi magana da sultane?. Tambayar da bata da amsarta kenan,amma ko yaya tasan zata iya samun haske ta bangaren sultane,don haka ta sanya takalmanta tana takowa zuwa waje tana kuma kiran sultane kai tsaye. Koda ya daga wayar narke masa tayi sosai,harda guntun kukan munafuncinta kamar qaramar yarinya. "Ta yaya za'a yimin haka?......ta yaya za'a shammaceni?,a lokaci irin wannan daya kamata ni UWA niya kamata ace na fara sani kafin kowa ya sani?". Murmushi ya saki,murmushin daya sake bawa mammina tabbacin zuciya da ruhinsa gaba dayansu qulle suke da madaukakin nishadi. "Kina da rauni me yawa zaituna wani lokuta akan diyarki.....zamu iya gama magana na waiwayo naga kun hademin kai ke da diyarki". Maganan yadan tabata kadan ta fuskar RAUNI daya dangantata dashi. Tana tsoron kada yaci gaba da aiwatar da komai daya shafi akhnan bada saninta ba,kada ya maida akalar shawara cikin rayuwar akhnan ga safiyya. Ta wani fuskar kuma yabo da tabbaci gami da yaqinin data samu saiya mata dadi ainun,ya gama sakankancewa da soyayyar da takewa akhnan din.....tabbas wannan din WANI MAKAMI NE dazai mata wani sabon amfanin a gaba. "Amma ranka ya dade.....banda zabar mata abokin rayuwa nagartacce.....abokin rayuwarma irin sheikh muhammad....Nagartaccen da kowanne ahali zasuyi alfaharin hada nasaba dashi" "Ban sake jin alfahari da hakan ba sai dana sake samun tabbacin daga irin zuria'ar daya fito da jama'ar da suke kewaye dasu" Saura kadan qafarta ta zame daga stairs din da take saukowa,haka kawai gabanta ya fadi amma zuciyarta na mata zillo AKWAI.HASKE wataqila da zata sake samu game da rayuwarsa. "Dan babban gida ne kenan kamar yadda muke fata?" Tayi tambayar zuciyarta cike da zullumi da addu'a. Kai sultane ya jinjina a hankali "Iyayensa ba masu sarauta bane.....ba kuma attajirai bane.....amma dai.manyan mutanene masu tarin ilimi" Ajiyar zuciya ta sauke,har takai kunnen sultane ya kuma tambayeta. "Nayi murna da naji samun tabbacin ilimin addininsa na gado ne tun daga gida,rayuwar diyarmu zata daidaita da yardar Allah,bari na qarasa zan hadaka da ita,amma na roqeka kalaman kwantar da hankali kawai a gareta" Ta fada tana narke murya da.langabar da kai. Murmushi me sauti sultane ya saki "Har abada diyarki zakita zaba sama da kowa zaituna?" "To ina da wata diyanne duk duniya bayan ita?" Ta fada a raunane. Tausayinta ne ya sauka a zuciyar sultane,ka rayu baka taba haihuwa ba abune me ciwo,tabbas inda yana da halin siyawa zaituna haihuwa daya siya mata,don ta kowanne fuska ta cancanta. "Tunda ina da khadeeja kuma ai ta isarmin,sai kuma inda qarfina ya qare" Ta rufe maganan da kalar kalaman da kullum suke qara mata girma da soyayya a zuciyar sultane din. Da kuma wadannan mayaudaran kalaman ta katse kiran,tana sake jin ta samu sassaucin rudanin da take ciki. Tayi imanin inda haisam jini ne na sarauta dole sultane zaiga alamu,zai bayyana ma,ta tabbatar da hannunsa sultane bazai bada auren akhnan baida wata makama me qarfi akan nasaba da alaqar sheikh haisam ba,duk kuwa yadda yaso ga hada auren. Ta samu relief sosai.....wataqila masu nata binciken ne basu gano daidai ba.....idanma sun gano din,daren yau zuwa safiyar gobe zasu bata alarm. *BIRRA* Su dukka biyar din tayi shawarar su shiga su lallashi uwar dakin nasu ko zata samu ta sanya ko ruwan zafi ne a cikinta. Suka shirya komai suka kuma wuce kai tsaye zuwa dakin. A sannan kukanta ya zama mara sauti sai digar ruwan hawaye kawai. Jikinsu a sanyaye suka jere komai sannan suka zauna daga qasan gadon. "Muna neman afuwarki a madadinmu dama kowa dake cikin gidan nan.....cikin nuna damuwa da yanayin da kike ciki,ki taimaka koda ruwan zafi kofi daya kisha saboda lafiyarki" Idanunta kawai ta lumshe tana sake jin yadda azabar zazzabin yake dukan qasusuwanta,ga wani irin hautsinewa da cikinta yayi guri daya. Har sun fidda rai da zata amsa sai sukaga ta motsa. Birra ta tashi da sauri tana tayata yaye duvet din,sannan suka taimaka mata ta zauna sosai ta jingina bayanta da fuskar gadon tana share damshin hawayen saman fuskarta. Tea foldable table ta bude mata daga gefanta,ta kuma zaunar dashi saman gadon sosai,ta hada tea din ta dora mata akai ta koma tana tattara kayan,duk da akwai sauran farfesun danyan kifi daya wadata da spices,amma ba zata mata tayinsa ba yanzu tukunna har sai an samu ta shanye tea din,daidai sanda aka murda handle din qofar dakin. Qamshinsa shine abu na farko daya soma musu sallama. Yana sanye da Moroccan thobe olive green me kyau da daukan idanu. Sallama yayi da tattausan nutsatsiyar muryarsa. Qasa dukkaninsu sukayi da kansu,kowacce tana qoqarin kame kanta da jikinta,kafin su fara miqewa a hankali suna dosar qofar fita a dakin. Cikin qasa da second biyar dakin ya zamana shuru,kamar ba'a wani me numfashi daya taba wanzuwa cikin dakin. Wani irin nauyi takeji cikin qirjinta,zuciyarta na matsewa guri daya,sanda ta tabbatar shi da ita yanzu suna musayar numfashi ne iri daya...qarqashin roofing daya.....cikin tsakiyar dakinta da take ganin baida hurumin shiga mata. Dakinta sirrinta ne......sirrinta guda dayan da bai kamata ya keta alfarmarsa ya shigo mata ba,tunda dai batajin matsayinsa yakai ya wanzu a qarshen sirrinta. Zuciyarta ke wani irin bugawa da kyau,tana jin yadda qamshinsa ya cika dakin gaba daya tamkar tun asali a nan ake ajiye turaren. Batasan wanne irin bugu zuciyarta keyi ba a duk sanda zataji qamshin,ko hakan yana da nasaba da ranar data fara jin irin qamshin ne a hippodrome?. Ko wannan lokacin baqincikin take tunawa?,shi yasa bugun zuciyarta yake banbamta dana kowanne lokaci?. Ko sau daya bai dubi sashen da take zaune ba,sai yaci gaba da takawa abinsa yana nufar windows din dakin dukka yana budesu don samun wadatacciyar fresh air bawai ta ac din da suka balbalawa dakin ba. A asalinsa mutum ne shi me son natural air,shi yasa yake yawaita shuke shuke a duk gurbin da yake rayuwa,yake matuqar son yawo kuma cikin guraren da suke da yawaitar tsirrai. "Me ya dauki kansa ne?,waye shi?!" Ta tambayi kanta tan ajin zuciyarta na mata zugi na yadda yake tafiya cikin dakin hankalinsa kwance yana bude mata curtains ba tare da izininta ba cikin wannan izzar tasa data tsana tamkar ma shine mamallakin dakin ba ita ba. Bakin qofa ya sake komawa,ya sanya hannu yana daidaita hasken dakin,yana kuma daukan remote na Ac da fitilar tsakiyar dakin don ya daidaita sanyi da hasken gaba daya. Wani irin bugawa zuciyarta takeyi kamar zata fita daga qirjinta,ba zata jurewa zama dashi a daki daya ba......a yanayin da ba kowa daga ita saishi,ba zata juri shaqar iska guda daya dashi ba......wannan tunanin bai barta ta fahimci yadda jikinta yake rawa ba......wannan tunanin bai barta ta fahimci zazzabin jikinta yakai iyaka ba.....wannan tunanin still dai ya sake mantar da ita kalar suturar dake jikinta,sai kawai ta zuro qafafunta qasa ta miqe harda saurinta,saurin daya sanya kanta wani bugawa har sai data dafeshi kadan ta sake miqewa tsaye tana takawa da burin kaiwa qofa ta fice ta bashi guri. Sosai silk rigan ya lafe a jikinta,sosai ya nuna dukiyar fulaninta da mazaunin kowanne da kuma space din dake tsakaninsu,shape dinsu ya fita sosai kamar yadda qugunta ya bude sosai ta cikin rigar dake mannuwa da fatarta. Sumarta me santsin nan ta warwatsu daga kafadarta zuwa gadon bayanta,tana dafe da gefan kanta da hannunta guda daya tana kuma nufar qofar da ayau take ganin tazarar dake tsakanin bed dinta zuwa bakin qofar,wanda bata taba ganinsa ba sai yau. Baiji takunta ba saboda a hankali lallausan tafin qafarta yake sauka saman marbles din dakin me wani irin santsi da daukar idanu,don haka sanda ya kammala saisaita komai sai ya waiwayo a nutse da nufin komawa ainihin cikin dakin. Kyakkyawan gani yayi,don tana takowa ne dab dashi da zummar giftashi ta fice ba tare data kalleshi ba. Dukka idanunsa suka zube akan fuskarta,kafin wani abu me qarfi ya fusgeshi zuwa ga cikakkun dukiyar fulaninta. Numfashinsa ne yaji kamar zai dauke daga hunhunsa. Zuciyarsa ta wani irin bugawa data tilasta masa lumshe idanun nasa wanda kafin ya budesu sun rusuna qwarai sun kuma sauya launi. "Subhanallah" Ya furta a hankali can qasan ransa yana motsa kyawawan labban nan nasa masu daukan hankali. Sanda ya bude idanun nasa ta gotashi,ya kuma fahimci waje takeson fita cikin qasa da second biyar. Baisan yadda akayi ba.....baisan me ya saukar masa da jin wani mummunan tashin hankali ba daya ingizashi riqo hannunta da sauri,sannan yayi taku biyu ya isa gefanta. Dukka idanunsan nan masu wani irin kwarjini ya zube mata,duk da cewa sumar kanta me santsi ta rufe wani sashe na fuskarta. "Ina zaki?" Ya fada da salon tambayar dake nuna wani irin zafi da zurfin muryarsa,girarsa tana tattarewa guri daya yana jin wani abu me zafi a qirjinsa. Sama sama takejin abinda yake fadi,don jiri takeji sosai,burinta kawai ya saketa ta qarasa parlor ta kwanta,amma hakan bai hanata bude masa manyan fararen blue eyes dinta ba,sannan ta zame hannunta daga cikin nasa da dan guntun qarfin da take dashi "Ka sakeni.......Ne me touchez plus jamais(don't touch me again)" Ta fadi da harshen faransanci,duk da tana ji a jikinta ba lallai yana jin abinda take fadi ba. Wani irin kallo yake watsa mata,yana jin wani abu me zafi yana sauka saman zuciyarsa. Ya qyaleta ta fita?,a haka?,da wannan kayan a jikinta?,fitarta na nufin kowa ya kalleta?,fitarta na nufin kowa yana da damar ganin surar jikinta? Wataqila ma wani cikin hadimai ya shigo isar da aike ko kawo wani saqo?. Bai jira ba,bai kuma bawa kwanyarsa daman yin tunani na biyu ba ya sanya hannunsa dukka biyun ya rabata cak da qasa. Wani abune da yazo mata a mugun bazatar da bata taba kawota ba. Bata taba hasashe ko tunanin faruwar hakan ba,shi yasa tayi wani irin mugun kaduwa ga tunaninta faduwa ce bawai daukarta ba,wannan ya sanyata cukuikuyeshi gaba daya numfashinta yana shirin daukewa. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 96* Jikinsa ta shige sosai kamar wadda ke neman mafaka sanda wani abu na tsoro ya biyota,wannan ya bawa qirjinsa daman haduwa da nata da wani irin yanayin da sai daya sanya yaji kamar shocking aka jona masa. Hakan bai sanya yayi sako sako da ita ba,bai bata dama ba har sai daya isa saman gadon ya kuma duqa yana sauketa. Yadda tayi zullon kubuta daga hannunsa ya sanya saura kadan ta sanyashi ya fada saman gadon,amma yaja ya turje ya tsaya kyam saman qafafunsa yana zube hannunsa a aljihun Moroccan thobe din jikinsa yana fidda wata irin iska daga bakinsa. Wani irin abu yakeji yana yawo cikin tafukan hannayensa yana bin duk wasu hanyoyin jini zuwa gangar jikinsa. Wani irin yanayi daya kusa kamanceceniya da yanayin dazu,saidai har yaso yafi yanayin dazu qarfi da qoqarin d'ai d'aita masa tunani. Tsaiwar kimanin mintina biyar yayi saman kanta kafin ya samu ya daidaita numfashinsa da nutsuwarsa. Ya hade ranshi tsaf yana ware idanunsa kadan a kanta. Tana qudundune cikin duvet tunda ya sauketa tana jin yadda kanta ke sara mata. Mamaki kadan ya kamashi jin sautin kuka can qasa yana futa daga boyayyar fuskarta. Bai taba tunani ko zaton zata zama me saurin kuka har irin haka ba......duk wannan taurin kan?,duk wannan musu da kafiyar gami da gaddamewar?. Hannayensa ya fidda duka biyun yana murxasu a hankali. Zafin da yaji cikin jikinta a dazun shine abinda ya fara fusgar hankalinsa. Dole akwai buqatar ta rage zafin jikin,idan ba haka ba komai yana iya faruwa. Amma ya fahimci da wannan taurin kan nata da kafiyar nata dole sai yazo mata da zafi,cikin lokaci qalilan,wasu alaqoqi da sukayi daga nesa,jin halayenta daga mabanbantan bakuna ya fahimci zuma ce ita sai da wuta. Takawa ya sakeyi yana komawa bakin qofar dakin,ya murza handle din ya budesa,sanda wata irin iska me dadi dake bushawara ga mutane na tahowar ruwan sama ta fara busawa. Komawa yayi ya duba sashen da yasa ana ajiyar waya a kowanne daki na gidan,ya danna yayi kira ga sassan hadimanta. Birra ce ta daga kamar ko yaushe "Shigo" Ya bata umarni a taqaice yana ajiye wayar. Kamar tana bakin qofar sai gata ta iso,ya fara nufar qofar fita yana bata umarni. "Ki hada mata ruwa mara zafi tayi wanka yanzun nan.....kada ku haura mintuna biyar,idan bata tashi ba ki sanarmin kawai" "In sha Allah" Ta fada da matuqar girmamawa,bata kuma daga kanta ba har sai daya fice a dakin. "Jikinki yayi zafi da yawa,kiyi haquri ki watsa ruwa.....wataqila yace kiyi wankanne sabo....." "Ya isheni haka birra!" Akhnan ta fadi da qarfin hali duk da yadda muryarta da labbanta ke rawa. Bata qaunar qara maganarsa ballantana wanzuwarsa a gurin,don haka ta miqe da taimakon birra ta shige toilet din. Zama tayi a gefan tafkeken bath tub dinta,har birra ta gama hada mata ruwan,kanta a qasa tana jin yadda hawayenta yake diga. Saida birra takai qofa sannan tace mata. "Ki ciremin kaya masu kauri ki kawominsu nan,ki ajiyemin,ki kuma kullemin qofata idan kin fita......ban yarda a bawa kowa izinin sake shigomin ba.....ko wanene" Ta fada da mugun bacin rai tana miqewa. Cikin girmamawa birra ta amsa mata,ta kuma duba closet dinta ta fitar mata da irin kayan da tace tana so din. A sashen shiryawa bayan gama wanka na tafkeken bathroom din nata ta ajiye mata,ta juya tana fita don cika umarninta. Saidai sanda take sako qafarta cikin dakin baccin,daidai lokacin yake shigowa dakin a karo na biyu. Wayace maqale a kunnensa,da alama kira yake amsawa,yayin da hannunsa daya yake riqe da wata madaidaiciyar jaka me jikin kwali. Qasa birra tayi da kanta,ta kuma tsaya gefe guda har ya kammala shigowa,sannan ta juya da hanzarinta tana fita a dakin. "Wai Allah na,wannan bawan Allah badai kwarjini ba" Ta fada qasa qasa bayan ta samu ta fito din tana raba idanu,sai kuma murmushi ya qwace mata. Ita dai har ga Allah wani dadi takeji,dadi takeji sosai idan taga uwar gijiyartata tare dashi. Duk da ta fuskanci tsananin taurin kan nan nata take take taken gwada masa,to amma ta sani yanayinsa sam baiyi kama da yanayin wanda zai dauki wannan ba. Da lallausan towel din ta tsane jikinta,ko tarin creams din da aka shirya a gurin kamar wani qaramin shago bata kalli ko daya daga cikinsu ba,ta zanya riga da wandon masu kauri gami da tsananin taushi. Ta lumshe idanu tana jin yadda sama ta fara bada qarar rugugin hadari. Cikin ranta take tambayar kanta ya zatayi yau ta kwana ita daya?. Duk tsanani idan ana ruwa.....duk yadda sukai fada dasu shehnaz ko aisa sai tasan yadda aka shirya. Ko ita ta bisu dakinsu,ko tasan yadda zatayi suzo a kwana tare. A yau kam batajin zata nema,koda kuwa tsoro zai kasheta,don bata ma tsara bude dakinta ba kwata kwata har nan da awa ashirin da hudu. Kai hasalima daga aisa din har shehnaz ba wanda batajin haushinsa. Saidai kuma tana sanya qafarta cikin dakin bayan ta dauke qafafunta daga saman water proof door mat din turarensa ya ajiye mata tabbacin yana dakin. Tsaye yake yana fidda wasu abubuwa daga madaidaiciyar jakar kwalin daya ajiye saman bedside drawer dinta da bata gama gane meye da meye ba. Wani irin bugawa taji zuciyarta tayi,idanunta suka sauka kan dokin wuyansa dake kwance da wani sashe na sumar kansa me santsi. Hasken fitilar daya dan sake qarota ya haskeshi fes cikin Olive color Moroccan thobe din jikinsa. Ta karanci waya yakeyi,amma abun mamakin ba'a jin abinda yake fadi sam. Izzarce da girman kan nan nasa abinda zuciyarta ta gaya mata kenan,tayi taku biyu kamar zata koma toilet din,amma wata zuciyar ta gaya mata DON ME?,keda dakinki?,ashema kin damu dashi.....ya isama ashe yakai kenan. Wannan tunanin ya sanyata ci gaba da takowa tana dauke kanta daga gareshi,tana fatan kafin ya waiwayo ya kalleta ta isa ga gadonta ta nade cikin duvet. Dukka addu'arta ba wadda taci,don tana isowa tsakiyar dakin ya waiwayo da wannan shimfidaddiyar nutsuwar yana zube idanunsa a kanta. Maida idanun nasa yayi ya lumshesu kana ya ciresu daga kanta. Butter color din sleep wear ne a jikinta masu tsananin laushi da bonnet cap a kanta data cusa gashinta gaba daya,amma hakan bai hana wani daga ciki bullutsowa ta gaban goshinta da qeyarta ba. Wani irin sassanyan kyau kayan sukayi mata,sun hadu da ramar da tayi iya yau kadai,da ramar da tayi kwanakin da suka shude duka sun sake fidda zallar quruciyarta Wannan kayan da sauqi,ba wani abu nata daya fito don long sleeve ne rigan,amma duk da haka wannan faffadan qugun sai daya bayyana kansa da kansa ta cikin wandon kayan. "Zan kira" Ya fada kalar hausar nan tasa da take kama da wani yaren daban ba hausa ba yana sauke wayar a kunnensa. Tsaki yaja qasa qasa,kwanyarsa na maido masa da hoton fuskarta daya kalla a yanzu. Qiyasin shekarunta ya tafi yi sanda yake latse wayar gami da maidata silent. A iya abinda nazarinsa da qididdigar lissafinsa yake bashi,ba zata haura sa'ar Aanani ba,bama rumaisa ba. "Sai rashin kunya da zallar girman kai" Ya fada can qasan zuciyarsa. Kwatanta shekarunta dana Aanani qanwarsa na kusan uku ya sanya ya sakeji a jikinsa kawai kaman Aanani dinne a gabansa. Sai ya dauki jakar kai tsaye yana nufar gadon,gadon da tuni ta haura tana kwashe qafafunta zuwa sama. Ranta a quntace tana jin wani irin dan banzan haushi yana cikata. Koda su shehnaz akwai sanda take tafiya abinta ta kwana ita daya idan 'yan halin nata suka motsa. A sanda sam batason damuwa ko takura,a sanda take buqatar kadaici takan so zama shuru kawai......saidai a yanzun shi gashi cikin al'amuranta,wani BAQO cikin rayuwarta gaba daya,wanda sam ba wani abu da takejin ya hadata dashi. Tanata qoqarin gyara hannun rigarta dana wandonta tana karance dashi. Cup din da birr ta hada mata tea ya matsar. Ya tsiyaya wani ruwan zafi sosai da batasan dashi ba,ya bude zuma ya zuba,ya kuma bare dabino ya zare qwallonsa ya dora duka saman qaramin madaidaicin tray. Zuwa sannan ta maida qafafunta saman gadon,ta kuma jawo duvet tana shirin lullube. Caraf taji an kama duvet din an riqe tamau,a hankali ta sauke idanunta saman hannunsa dake riqe d duvet din. Zara zaran yatsuntsa sun shige sosai jikinsa wanda dukka alamu suka nuna mata ba qaramin riqo ya masa ba,don tana ganin lafiyayyun jijiyoyin hannun nasa dake lullube qasan lallausar gargasarsa. Tasan koda wasa bata da qarfin da zata qwata,saita daga idanunta a hankali da xummar zube masa kallon gargadi,saidai kuma inaaaa...... Kallo daya tak ya bata daya qarasa zare dukkan wata guntuwar karsashi da take dashi,kallo Dayan daya hanata sakewa har ta kalli qwayar idanuwansa.... Kallo daya da taji ya mata wani irin girma. Bai magana ba bai kuma saki duvet din ba,yaci gaba da tsareta da ido ne yana hukuntata da idanuwan nan dake dauke da wani maganadisu,har a hankali ta zare yatsunta daga jikinsu,saiya tattara duvet din ya tureshi gefe,ya kuma maida nini foldable table din ya maye gurbinsa tsakanin cinyoyinta. "Dauki kisha" Ya fadi yana tsare gida da kyau cikin siga ta umarni irin nakai tsaye. Idanunta ta lumshe tana jin wani irin bacin rai yana taso mata. Taja numfashi me zurfi sannan ta sauke tana jin wani tarin tawagar hawaye suna yo gangami don isowa ga idanunta. Shanyesu tayi da wani irin taurin kai da kafiya. Ba zata taba bashi daman ganin hawayenta a karo na biyu ba.......kome da yakeyi yanzu kuma na lokaci ne,rashin lafiyarta da rashin qwarin jikinta shine sila......amma daga yau.....daga wannan ranar taci alwashin bazai sake samun kusanci da rayuwarta haka ba. "Bai kamata kisha wannan yanzu ba......amma gangar jikinki tana buqatarki a raye" Ya fadi cikin I don't care manner ba tare daya dubeta ba. Ya fara jin komai so boring.......sultane da morsa safiyya kawai yake hangowa suke sanyawa yake sake bawa kansa qarfin gwiwa. Yanaso ya kula da amanar sultane yadda ya dace,yanason sultane ya tabbatar da kansa da kansa cewa ya kula da kowa da komai kamar yadda ya dace ace yayi. Maganarsa sai tazo mata a hagunce......bacin ranta ya sake motsuwa,hawayen da take riqewa suka samu hanyar fita kansu tsaye,ba wani shamaki ba kuma wani abu da zai taresu. Fuskarta takeson boyewa amma ba komai kusa da ita,wannan ya sanya tayi amfani da bayan tafukan hannayenta ta lullube idanunta irin yadda yaro keyi a sanda ya fashe da kuka. Qaramar stool ya jawo hankali kwance zuwa gabanta. Zaman nan nasa yayi wanda ya zame masa jiki,zaman dake qara masa haiba,yake kuma zake nuna SARAUTA dake cikin jininsa. Kamar kowanne kuka na diya Mace,wannan ma sai yaji yana sauka masa saman zuciya. Sai yaji yana masa wani iri ba dadi daga can lokon zuciyarsa......sai kuma ya dinga jin wani irin weakness da bacin rai suna ratsashi. Wai dukka wannan kukan saboda kawai ta gani ta samu tabbacin shi muhamamd haisam ya aureta ne?. Ta dauka komai na gaske ne?,ta dauka komai zai tabbata ne?,ta dauka zata zama kamar kowacce matar aure ne?. Hakan mazan da suka auri matan da basa sonsu suke ji a ransu?. Ya lumshe idanunsa yana sake budewa a kanta,can cikin ransa yana sake bawa kansa alwashi da tabbacin har abada bazai taba yarda ba,bazai taba sakewa ya auri macen da bata sonshi ba. Dama can tsarinsa ne......zabinsa ne ya auri macen da soyayyarsa a zuciyarta ya haura wanda shi yake mata.....a yanzun ya sake samun yaqini da tsaiwa saman ra'ayinsa dari bisa dari. *MAMMINA* Cikin taku daya daya ta dinga ratsa falukan akhnan tana kuma mamakin qauracewar hadimai haka tunda wuri,don duka duka a sannan data duba agogo tara ne da mintuna na dare. Kusan ma kowanne living room da sitting room qwayayensu a kashe yake,abun yadan bata mamaki,amma saita alaqanta hakan da yanayin da akhnan din take ciki. Parlor na dab da qarshe wanda daga shi sai sassan stairs din akhnan da down stairs bedrooms dinta ta iske birra. Burners din dake kowacce corner da kusurwa na falukan take kashewa. Wani sirri kenan na daban da sassan akhnan din ya kebanta dashi. TAMBARIN QAMSHI,komai na sashenta zaka samu tambarinsa kenan,da wannan kadai ya isa ka gane ababen sassan gimbiya akhnan. "Dukka ina sauran hadimai da suka tafi haka da wuri?,waye ya sallamesu bayan nasan zai wahala zuwa yanzu biftu tayi bacci?" Dan rusunar da kanta tayi. "Eh bata jin dadi ne......" "Kuma kuka barta ita kadai harda tafiya da wuri?" Mammina ta fada cikin hargagi tana fiddawa birra idanuwanta. "Ai tana tare da sheikh muhammad" Birra ta amsa mata a ladabce. Wani irin abu mammina din taji kamar an doka mata tsakiyar kanta,tana tare da haisam?......har sun samu kebewa?,akan wanne dalili?. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 97* "Tun yaushe ya iso?" Ta tambaya tana jin qirjinta yana wani irin bugawa. "Tun bayan sallar isha". Ta amsa mata. A sace mammina din ta kalli agogo,aqalla awa guda kenan?. "Shikenan.......zan zauna a nan,ki shaida musu na qaraso ina jira" Qasa birra ta sakeyi da kanta sanda mammina ke neman gurin zama. Tanaso ta gaya mata inda zai yuwu mafi alkhairi shine ta koma,don bataga alamun fitowarsa yanzun ba. Banda ma rigima irin ta giwa,ta yaya sabon aure irin wannan a irin wannan lokaci ki buqaci shiga shiyyarsu?. "Kamar dai ma saida safe fa ranki ya dade" Wani kallo ta watsawa birra tana kallonta. "Kamar yaya kenan?" "Ya kulle qofar daga ciki ranki ya dade" Birra ta amsa mata a ladabce. Wani irin fushi ne ya taso mata gauraye da tashin hankali. Har tana iya jin yadda qirjinta yake bugawa. Me ya kaishi wanzuwa da akhnan din a ranakun da ko bisa al'ada ba'a bawa namiji daman kadaicewa da matarsa ba. Don dai kawai batajin dadi?,ita akhnan din ita ta bashi fuska?,har ta warware daga suman qiyayyar data masa a dazu?. "Tun yaushe ya shiga?" Ta sake tambaya gumi yana tsatstsafo mata,ta manta da cewa birran ta bata amsa a dazu. "Bayan sallar isha'i" Shuru kawai tayi tana jin wuta tana dauke mata gaba daya. Birra taci gaba da tsaiwa tana jiran umarninta. Mintina kusan biyu suka shude dukkaninsu suna tsaye a haka,mamaki fal zuciyar mammina naci gaba da zamansa a ciki,zuciya kuma tana mata kalar saqe saqe daban daban. Qafafunta sukayi wani irin sanyi kamar ba zasu dauketa ba,sai kawai ta koma da baya ta zauna saman kujera. "Jeki....zan jirayesu" Ta fadawa birra. Rusunawa birra tayi tana yin gaba,zuciyarta fal da mamaki,wannan sanya idanun da bin diddiqin har ina?,mema ya kawo irin wannan sanya idanun na giwa?,mutum da matarsa?,auren sunnar da kowa ya tabbatar an daurashi?,a muhallin da yafi kowanne tsarki da daraja duk duniya. *HAISAM* Ci gaba yayi kawai da sauraren kukan da take rairawa ba tare da yayi yunqurin dakatar da ita ko hanata ba kwata kwata. Yanaso tayi yadda zai isheta,ta yadda idan ta gama din ba zata sake damun kanta da nasa kunnuwan ba da qirqirarrun hawaye ba. Bai zaci fara hawayenta da ganin kukanta haka da wuri ba,bai dauka tana da rauni ta wannan bangaren ba sam. Taurin kanta izzarta dama kafiyarta dukka basuyi daidai da raunin da yake gani yanzu a tare da ita ba. Idanunsa ya lumshe sannan ya sake zubesu saman tafukan hannunta dake a bude saboda idanunta data rufe da bayan hannunta. "Ya isa......ya isa" Ya fada da wani irin coolness. Abinda ya bata mamaki yadda ta samu kukan yana zuqewa a hankali a hankali,kafin ya tsaya cak tamkar suma idanun nata suna bin umarnin haisam dinne. "Dauki kisha.....idan kukan yana burgeki ne daga baya kina iya ci gaba dayi" Ya fadi yana sauke idanunsa akan mug din dake tururin zafi. Wani abu ya matse a qirjinta,wato ko ta mutu ko tayi rai duka wannan shi ba damuwarsa bane?. Ya shigo mata daki,ya mata bake bake kuma yana gaya mata duk maganan da yaha dama,yana bata umarni bisa zaton tabi umarninsa,wanne irin mutum ne shi me shegen jin kan tsiya da wulaqanta mutane?. To amma a wannan gabar yadda takejin hanjin cikinta suna murdewa guri guda kamar zasu tsinke,ba wani abu da tafi buqata irin ruwan zafin. Bakinta da jikinta dukka basu da wani energy da zata iya nuna masa kuskuren shiga sharafinta da yayi.......so take ko harara ta watsa masa,amma kuma sanda ta daga idanunta a kansa,qwayar idanunsu suka gauraya sai taji kaman tana neman daburcewa,sai kawai ta zarce da daukan cup din duk daba abinda tayi niyyar yi ba kenan. Kallon cikin cup din take,tana tunanin wanne kalar tea ne wannan,kuma an hadashi ba madara sai honey?. Bata taba sha ba,amma hakanan takai bakinta tunda ta riga ta dauka din,kada ya rainata,ya dauka bada niyyar sha ba dama ta dauka. Tsam ya miqe daga saman stool din sanda yaga ta fara sipping tea din. Idanunta ta lumshe sosai ba tare kuma data budesu ba. Duk da bakinta ba taste,zazzabin daya dan sauka yakeson ya dawo mata,amma hakan bai hanata jin wani dadi ya ratsa harshenta ba. Kurba daya tayi niyya,amma sai gashi yana sha kadan kadan har sai data kusa shanye duka cup din. Qwayar idonta ta sauke cikin cup din,tana jin wani kunya yana saukar mata ganin yadda ta kusa tashi dashi gaba daya,a hankali ta ajiye saman foldable table din tana sauke idanunta daga kanshi sanda yake takowa zuwa bakin gadon,hannunsa riqe da wani abu da batasan meye ba don bata kalleshi ba. Ajiye drip din da cannula din daya dauko yayi daga gefe,ya sunkuya a hankali yana nade foldable table din da yake saman cinyoyinta. Wani irin faduwa gabanta yayi,zuciyarta ta soma qara adadin bugun da takeyi,yayi mata kusa da yawa.....kusar da har tana iya jin hucin numfashinsa dake gauraye da wannan mayen turaren daya zame mata jarrabi. A duk sanda zataji scent din saita samu kanta da wata irin kasala......a duk sanda zata shaqi scent din sai taji wani emotions daga can qasan zuciyarta wanda batasan asalinsa ba.....a duk sanda zataji qamshin sai taji tasirin wani abu qasan zuciyarta me kama da nishadi wanda batasan meye yake kawoshi ba. A nutse yake nade table din,ba tare daya daga kai ya dubeta ba. Idan yace zaiyi hakan tazarar inches ne kawai zai zaman tsakanin fuskokinsu. Tanason masa wani abu da zai sanya ya janye daga kusancin daya haifar tsakaninsu.....amma tana jin koda ta buda baki zatayi magana bugun da zuciyarta takeyi ba zata bari kalaman bakinta su fita daidai ba. A hankali taji wani irin sanyi yana ratsa qasusuwanta,wanzuwarsu a hakan sai takejin kamar ba mintuna ya dauka ba,kamar shekaru ya dauka a duqe yana maida table din yadda yake. Sanda ya kammala ya miqe a nutse yana ajiyeshi a qasa,ji tayi kamar wani qatoton fili ya bayar na tazara a tsakaninsu,saidai bata ajjiye wannan numfashin ba ta tsinci husky voice dinsa yana furta. "Gyara" Idanunta nan da suka qara wani jeme jeme saboda kuka ta daga tana dubanshi dasu. Ta lura tunda ya dawo dakin bai kalleta koda sau daya ba,wannan girman kan da jin ya wuce ajin ya kalleta ne yake motsa masa?. Tambayar da batasan amsarta ba,saidai maida dubanta ga allura da cannula harma da drip din hannunsa ya tashi hankalinta. Idan a duniya akwai abar data tsana take sanyawa tsigar jikinta tana zubawa lokaci guda itace cannula,tana iya haqura da ciwo duk nauyinsa da zurfinsa muddin akwai allura a lamarin maganinsa. Zubawa allurar idanu tayi,bataso ya rainata da yawa,bataso ya gane rauninta,rainin zai yawa idan ta bashi hannunta don mata allura,hakanan rainin zai yawa idan ya fuskanci tsoron allura takeyi. Batajin zata yarda da wannan mulkin kama karyar da yake mata......ya isa haka,ya tilastata tayi abubuwa da yawan da ko shine sultane sai haka,a wannan lokacin zata gwada masa har yanzu AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD take. Ya samu access da ita da yawa dalili dame?. Ya jefata a qunci amma kuma yanayin kamar baisan komai ba?. Dama akwai wata manufa a ransa game da ita?. Dukkaninsu tunaninsu ya yanke sanda wayarsa ta dauki wani daddadan sautin kukan tsuntsaye. Wani abu ya sauka a ranta tare da fitar sautin. Kukan tsuntsaye na daya daga cikin abubuwan da takeso sosai,don haka kusan komai nata da zai bada ringing da notifications duka shine. Ganin sunan sultane yana yawo saman video call din ya sanyashi takawa a nutse saman stool din daya tashi ya zube ruwan da alluran gaba daya,sannan ya koma saman dressing table ya zauna a nutse yana daga kiran. Fuskar sultane da muryarsa gaba daya ta bayyana cikin wayar da dakin,muryar daya sanya akhnan tattaro dukka nutsuwarta ta aza cikin ranta,wani bangaren na zuciyarta kuma wani dadi taji. Zataga yadda zai kalli sultane ya fadi masa yana daki daya da diyarsa......zataga da wanne idanu zaiwa sultane bayanin dalilin zamansa a dakinta a daren nan. Wani irin murmushi ne yake fita daga fuskar sultane din,wanda yake zaune cikin haramin makka. Tun daga wadancan awannin da suka shude zuwa yanzu zuciyarsa ke cikin wani kwanciyar rai da walwala gami da nutsuwar da bai taba jin irinta ba. Yaso ya daure zuwa gobe ya kira akhnan da haisam don ya sake tabbatar da lafiyar komai amma ya gaza daurewa,ya kikkira akhnan bai sameta ba,don haka ya maida kiran ga haisam,sai gashi cikin sa'a ya sameshi. Daga inda ta cure ta ware idanunta sosai akan fuskarsa. Kyawawan idanunsa da lips dinsa da hasken screen ya sake fidda color dinsu da kyansu sun bayyana tarwai kamar glass. Ba murmushi bane saman fuskarsa......amma akwai wani sakakken yanayi daya qara masa wani irin ajiyayyen kyau. Madaidaitan Lips dinsa suna motsawa a hankali wadanda suke ajiye tsakanin gashin qasan habarsa dana saman lips din nasa da suka sake qawata kyau da darajar fuskarsa na cikakken namiji. An ornament for a man.....he has completeness. Wasu words guda biyu suka fado a kanta,tana tuna wani lokaci a French,sanda ta shiga cin breakfast a kitchen nasu na school,ta zauna gefan wasu 'yammata da suketa hira a tsakaninsu,qarshe dayar ke nunawa dayar hoton saurayinta. Yana da gemu da cikakken saje,kuma da kalmomin data yabeshi dasu kenan. Idanunta ta janye a kanshi,tana jan qaramin tsaki. Haushi yana qara cikata,yana kuma sake tunzura zazaabin da takeji a jikinta. Don yana da gemu sai me?,don yana da saje meye damuwarta?,wanne kyau zai nunawa sauran maza?,tambayar data sake sanyata maida idanunta a kansa kenan da zummar tantance tambayar. Cikin girmama juna suka gaisa,wani abun mamaki shine yadda haisam din a wannan lokaci yaji nauyi da girman sultane ya dadu a ransa. Wannan transparency din da yakeji a baya game dashi a yanzun wani abu ya sauyashi. "Inata kiran khadeejatu amna na kasa samunta" Sultane ya fadi yana kai dabino bakinsa. A nutse da wani irin ba zata ta saman wayar ya daga wadannan idanun nasa masu kaifi yana saukesu a kanta. Ya shammaceta,bata dauka zai kalleta ba,da bazata taba bari ya ganta tana kallonsa ba. Ranta ya bace ta rufe qwayoyin idanunta,yanzu zai dauka yana da kyau ne.....yanzu zai dauka yaci galaba a kanta ne,yanzu zai dauka cewa ya isa ne ko dama can tana kallonsa,maganganun data dinga tattaunawa ita da zuciyarta kenan wadda ke bugawa da sauri da sauri. "Bataqi kiranka ba.....zazzabine kadan ya kamata......gata muna tare ruwa za'a saka mata da allurai ko zai sauka da wuri.....na fahimta ranka ya dade" Amsoshin haisam din kawai kunnuwanta suke iya ji,tana mamakin yadda ya fadiwa sultane kansa tsaye suna daki daya. "Allah ya sawwaqe.....jeka saka mata ruwan.....amma nasan halinta da tsoron allura muhammad......ka ajiye wayar a kusa na gani ko zan taimaka da wani abun" Sultane ya fadi ransa yana masa fari. Wani irin alfahari da haisam din yakeji. Tun a ranar farko ya fara ganin muhimmancin zaben NAGARTA akan komai. Ya tabbatar haisam ya karbi auren akhnan ne bisa ALFARMA amma hakan bai sanya ya watsar da ita ba. Hakan bai sanya ya gaza sauqe haqqin da yace zai iya riqewa ba,wanzuwa sultane din ko rashin wanzuwarsa a gurin bai sanya ya sauya hali ko dabi'a ba. A nutse ya miqe da wayar a hannunsa,ya qarasa gefan bedside drawer ya ajiyeta. "Khadeejatu" Ta tsinciki muryar sultane daga gefanta,abinda ya sanyata daga kai da hanzarinta. Murmushi yane mata,murmushin da tashin farko ya daki zuciyarta. Ta zubawa mahaifin nata idanu tana hangen wani walwala da farinciki me yawan gaske a tattare dashi. Kuka takeson sake masa.....roqonsa takeson yi ya raba wannan auren,alfarmarsa takeson nema ya barta ta rayu ita kadai.....amma kuma irin walwalar data gani a idanunsa.....irin farincikin data gani shimfide saman fuskarsa sai taji ya kashe duk wani karsashi nata......sai taji ba zata iya ba.....ba zata iya hanashi yaci gaba da jin wannan farincikin ba. Ya bata duk wani kulawa.....ya bata duk wani 'yanci.....ya bata duk wani dama a yanzun itama sai takejin kamar ya kamata ta barshi yaji wannan dadin.......kamar akwai WATA HANYA......akwai wani damar da zata warware matsalarta ba lallai saita cutar da farincikin sultane ba,ta cikin ruwan sanyi koda ba ayau yau ba....koda ba'a yanzu yanzu ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 98* Cikin kulawa yake mata sannu,tana amsa mata tana kuma qoqarin boye rauninta da tashin hankalinta. Hankalinsa sam bayakan maganganunta da mahaifinta,ya tattara nutsuwarsa wajen zuqe ruwan allurar a syringe daya da kuma fasa drip din ya masa gurin tsaiwa. Dukka cikin horon aiki da suka samu ne.....sun koyi abubuwa masu yawa da kowannensu zai iya buqatar yiwa kansa ko dan uwansa na taimakon gaggawa wato emergency a bakin aiki. Karo na biyu suka sake hada idanu dashi,shi ya fara janye nasa idanun yanajin qosawa a tare dashi. Babban syringe din tabi da kallo da cannula din daya riqo yana takowa a hankali. *MAMMINA* Kasa cikakken zama tayi cikin kujerar gaba daya kaman yadda ta kasa samun cikakkiyar nutsuwa. Tun tana zaune daidai har ta fara motsawa kamar wadda ke zaune saman qayoyi. A hankali zufa ke karyo mata lokaci lokaci tana sanya tafin hannunta tana sharewa. Duk da sassanyan iskar Ac dake parlor din,da kuma daddadar iskar dake kadawa a waje wanda zuwa lokacin yayyafi ya fara sauka sirara marasa sauti. To wai me yakeyi?,me yakeyi a dakin yarinyar mutane sama da awa daya?. Me yake gayawa akhnan?,ita data sani da kafiya taurin kai da dan uban miskilancin da shi kadai ya isa ya sanya namijin shayin kallonta ko matsowa kusa da ita?. Me yake gaya mata har haka da dukkaninsu sukayi luf a dakin,ba alamun motsin koda me rai da take iya jiyowa duk kuwa da adadin kasa kunnen da tayi?. Sanda agogo ya nuna mata zaman awa biyu cur tayi a gurin sai taji haqurinta yana qarewa. Ta miqe tsam tana kaiwa da kawowa kamar wadda takejin ba haya. Zuciyarta nata saqa mata ta shiga kawai duk da ta sani cewa a dokar masarautar aikata hakan laifi ne babba. Tsaki taja tana Allah wadai da tsayawa tambayar birra da tayi,inda ta shige kanta tsaye ma da laifin zai zamana da sauqi akan yanzun da tabbas birran tasan ta gaya mata. A mamakance birra ta dakata tana dubanta,wadda tayi mantuwar kashe socket na Ac din parlor dinne,abinda ya sanyata dawowa kenan,don har bacci ya fara awon gaba da ita. Sosai mammina ta hade rai,duk da tasan birran bata da hurumin kallonta. "Allah ya taimakeki ko....." "Kiyi abinda ya kawoki ki tafi" Ta fada mata a kausashe,saita gotata ta kashe sannan ta dawo ta sake ficewa tana barinta,can qasan ranta mamakin giwar yana sake kamata,tana kuma sake gamsuwa da yadda da halayenta wasu lokutan da basu da kyau. Ci gaba tayi da irga lokaci,tun tanayi da yatsun hannunta har abun ya soma gagararta ta maida idanunta kacokam ga agogo. Tana jin yadda gari yake sake sanyi,tana kuma jin yadda gaba daya ruwan yake qara qarfi. Zafi kawai zuciyarta keyi mata,banda gayawa kanta da taketa faman yi na cewa ba girmanta bane,bataga abinda zai hana hawaye zubowa a idanunta ba. Dole ta san yadda zatayi ta sake samun yarda da amincin akhnan,idan ba haka ba komai zai iya faruwa.....komai zai iya wargaje mata. Bata shirya barin zuciyar akhnan a yanzu taso kowanne d'a namiji ba,bata shirya barin akhnan ta yiwa kanta zabi akan kowanne d'a namiji ba....bata shirya qyale akhnan ta zabarwa kanta komai ba a yanzu. Wannan lokacin baiyi ba,wannan lokacin baizo ba tukunna. *HAISAM & AKHNAN* Cikin dauriya da dakiyar da batakai ko ina ba ta miqa masa sambalelen hannunta. Ya kauda idanunsa daga kallon sambala sambalan yatsunta da yake da ragowar jan lalle na wancan lokacin da akayi mata. Ya fidda cannula din ya cire tsinin allurar. Kallonsa kawai takeyi tana kuma kallon allurar hannunsa. Ranta a shaqe fal da baqincikin taba mata hannu da zaiyi,zuciyarta kuma na cikin kokwanto tanaso ta gani zai iya kama hannunta gaban sultane?. Saidai kamar jira yake ta qarasa yiwa kanta wannan tambayar ta tsinciki lallausan tafin hannunsa cikin nata. Har tsakiyar kanta taji tsigar jikinta ta zuba. Wani irin sanyi da laushi me ratsa jijiya da kuma jiki,wani abu ya harba cikin jininta da wani irin sauri,saita maida idanunta ta lumshe tana tambayar kanta. "MENENE WANNAN?". bata samu amsa ba,sai amsar da daya sashen na zuciyarta ya fada mata,ya kuma tunasar da ita. "Shi din malami ne fa kawai" Kalmar data sauka a zuciyarta da wani irin nauyi,ta kuma sanyata bude idanunta gaba daya tana kuma zare hannunta dake tsakiyar tafin hannunsa da wani irin sauri. "Me haka biftu?....ke har yanzu ba zaki daina tsoron allura ba?,kin girma fa?" Sultane ya fada da wani yanayi da yafi kama da lallashi. Hawaye ne sosai cikin idanunta tana kallon haisam din,wani irin duba take masa wanda ta kasa kallon qwayar idanunsa,sai kyawawan lips dinnan nasa da taga sundan motda kadan. Wani zafi takeji har cikin ruhinta a sanda duk ta tuna MALAMI yake aurenta. Me yasa sultane zai mata haka ne?. Wannan tambayar ta nanatawa kanta ita tafi sau dubu,saidai ba amsa ko daya gamsashiya data samu. "Muhammad.....bari na barku,ga daya daga cikin halinta nan tsoron magani da allura.....nasan zakaji dasu.. Mu tashi lafiya" Sultane ya furta,ba tare kuma daya bar kowa a cikinsu ya masa magana ba ya kashe wayar murmushi na fita a fuskarsa. Yau biftu dinsa ta samu me kula da ita,yau biftunsa ta samu wanda zaiji da wannan rigimar. Shikam baisan sai yaushe zata fahimci ta girma ba,amma koma meye yasan tabbas ta samu wanda zaiji da dukkan komenta. Ci gaba yayi da kallon screen din wayar daya zama.blanck bayan yankewar wayar. Qoqari yake ya hadiye wani abu......yana jin girman yardar da sultane yayi dashi,yana jin kamar yadda sultane ya amince dashi abun yayi yawa,kamar abun yayi zurfi,kamar bai kamata ya yarda dashi aka diyarshi har haka ba. Bai bashi wannan assurance din ba,me yasa ya zurfafa a aminci dashi har haka?. A nutse ya maido idanunsa a kanta ya zube mata su. Sosai ya kafeta da kallon da aqalla saida ta kusa sakanni goma sha biyar ba tare daya qifta ba,sai ya bude hannuwansa yana miqa mata tafin hannunsa ba tare daya janye kallon ta akanshi ba. Hawaye ne sosai kwance cikin qwayar idanunta,saita samu kanta da bashi hannun kamar yadda ya buqata tana jin wani kuka yana qwace mata. Meye haka a idanunsa me tasirin da yake iya sarrafata a duk sanda yaso?......wanne irin magnet ne a idanunsa masu tsananin qarfin da suke sarrafa tunaninta a sanda bataso ba bata kuma shirya ba.....wanne irin qarfi gareshi da iya umarnin ido kawai yake samun nasarar sarrafata ba tare da yace da ita komai ba?. (Nikam nace uhmmm yarinya,an gaya miki duk makarancin alqur'ani mutumin banza ne?,duk wanda ya aboci qur'ani ba shakka zai rabauta da wani irin haske da kwarjini). Kyakkyawan mazauni hannun nasa ya samu cikin nata,a nutse ya dora babban yatsarshi saman hannun nata ya soma sama da qasa dashi yana laluben jijiya,abinda ya haifar musu da wani irin yanayi dukkaninsu shi da ita. Wani irin tashi tsigar jikinta tayi,ta same curewa guri daya hawayenta da bataso ya gani suna qaruwa,yayin da wani abu me nauyi shi kuma ya fara danne zuciyarsa. Numfashinsa ya soma qoqarin canza yadda yake shiga da fita,da farko ya qaryata yanayin,saidai daga baya da dukka gangar jikinsa ke neman amsawa sai ya hada dukka jarumtarsa yana bawa kansa qwarin gwiwa tare da canza yanayin zuwa yanayinsa na Muhammad haisam. Karo na farko kenan a rayuwarsa daya taba riqe hannun wata diya mace har haka cikin tafukan hannunsa,sai yakejin kamar komai yana shirin kwance masa. Har cikin qasusuwansa yakejin saukar kukanta sanda ya nutsa allurar cikin fatarsa. Ya tsani kuka,banda kuma haqqinta dake wuyansa da tuni ya jima da barin dakin. Qasa qasa ya saki tsaki saboda yadda sam baya son noises a rayuwarsa,kukanta yana masa waninirin kud'a cikin kunnensa. Tsakin kuma ya sauka a kunnenta sosai,ya wuce zuciyarta yana aje mat wani tabo daya sanya kukanta ya qara tsananta. Allurar jijiya ce don haka dole ya dinga turata a hankali,yana dakatawa gami da dubanta,ta riga ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta tana sauke kukanta a hankali. Idanunsa ya sauke a hankali kan dogon dokin wuyanta da gashinta daya fito ta qasan hularta yayi masa rumfa. Kamar rad'a abinda ya taba karantawa cikin littafin ibnul qayyum Aljauzy na RAUDATUL MUHIBBEEN. Cikin sifffofin kyau na diya mace daya lissafa,soyayya tsakanin mace da namiji. Hannunsa daya masa nauyi kadan ya daga ya sake tura ruwan allurar cikin jikinta kamar me tsoron turashi a hankali,sai ya sake dakatawa don bawa ruwan daya tura din damar bin jikinta. Gudun sake fadawar idanunsa inda yakejin bai cancanci ya sauka din ba,sai yabar kansa a qasa,saidai kuma a hankali idanun nasa suka zame,kai tsaye kuma suka sauka kan dogayen qafafunta da suke hade guri daya. Wasu zara zaran yatsu,lallausar qafar da idanu kadai sun isa su gaya maka hakan. Fatar dake lullube da qafan itama me sheqi ce da daukan hankali kamar ba fatar qafa ba. Akwai gashi qananu saman kowanne yatsar qafar. Kaman tasan su yake kallo,ta motsa qafar tata a hankali,sai ya sake zare idanunsa daga kai yana jin yadda numfashinsa yake sake sauyawa. Ya gaji da gane gane,don haka a wannan karon koda ya maida idanunsa ga allurar bai dauke idon nasa ba,sai daya qarasa tura mata ruwan allurar gaba daya,sannan ya zare syringe din. Drip din ya matso dashi ya jona mata,idanunsa akan iv flow regulator din yana qoqarin daidaita ruwan,da deep and husky voice dinsa ya furta. "Zaki iya kwanciya" Kamar haka take jira kuwa ta koma a hankali ta kwanta tana sake fashewa da kukanta. "Ya salam" Ya fadi qasan ransa,saidai duk da haka bai kalli fuskarta ko sau daya ba. Bayason yayita kallon abubuwan da xasu zame masa matsala,wannan kusancin tsaf zai iya zame masa ciwo koda bai shirya hakan ba. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 99* A nutse ya taka yana sake rage hasken qwayayen dakin,ya kuma sake daidaita iskar sannan ya maida windows din dukka yadda weather din dakin yasan zaiyi mata,yadda yasan zai dace da yanayinta. Ya zuba allurai cikin drip din daya tabbatar zasu saukar mata da zazzabinta,zasu kuma sanyata zuwa gobe ta tashi da qwarin jikinta. Har zuwa sanda ya qarasa saman daya daga cikin sofa din dake can bangare daya na dakin ya zauna akai yana jin sautin kukanta can qasa. Idanunsa ya lumshe yana furzar da iska daga bakinsa. Shi kansa shi daya yasan me yakeji a ransa da jikinsa,gajiya.....kasala da wani irin qosawa. Qafarsa ya dora daya kan daya,ya kuma rungume hannayensa a qirjinsa sosai yana lumshe idanunsa a nutse. Cikin wata irin nutsuwa,da wannan daddadan muryar tasa....da wannan daddadan sautin nasa yayi gyaran murya a hankali,sannan ya fara rera karatun qur'ani da wata tattausar murya,wannan qira'ar dake matuqar kama data sheikh Muhammadu afif taj. Laushin muryar......zaqin karatun,da nutsuwar da qur'ani ke sanyawa a zukatan bayin dake karantashi ya cakuda da sassanyan yanayin saukar ruwan sama a wannan daren. A hankali sautin muryarsa ya fara ratsata,a hankali ta dinga jin wani yanayi me cike da nutsuwa yana saukar mata.....a hankali kuka da bugun zuciyarta suna fara daidaita,saita lumshe idanunta a hankali,komai tana jin yana mata shuru,sautin kawai ke shiga kunnenta,yayin da ruwan dake diga a jikinta a hankali ya soma wanzar da wani irin sassauci a jikinta,ruhinta kuma yaci gaba da samun nutsuewa da karatun dake tashi cikin dakin. *MAMMINA* Sau uku tana diba fuuuu tana nufar qofar dakin,saidai kuma data isa saita tsaya cak ta kasa qarasawa. Ita kanta batasan abinda yake tsaidata ba. Ita kanta batasan me yasa take juyowa tayi reverse ta koma parlor din data tashi da farko ba. Wani irin zafi takeji ba iya zuciyarta kawai ba,harda gangar jikinta. Wani irin zafi takeji idan ta tuna yanzu haka haisam din ya kebe da akhnan......ya kwashi wasu a wanni a inda ba kowa daga shi sai ita,waye yasan me ya faru ma?,wa yasan me yake faruwa kuma?. Komai ma zai iya kasancewa. Iska me zafi ta furzar daga bakinta,tana ji kamar hawaye na shirin balle mata,abinda ta manta rabonta da tayi. Tunda yaron ya shigo masarautar gaba daya komai yake zuwa mata a hagunce,ta lura abubuwa da dama basa tafiya daidai,indai kuwa ba jinin IBRAHEEM bane to waye?. Kai ta girgixa da sauri ganin tana neman kaiwa sama da sha biyu na dare a zaune a gurin. Ya zuwa yanzu ya zama dole ta tafi,dukkanin alamu sun bata cewa kwana zaiyi kenan a dakin?. Tambayar data sauka zuciyarta da wani irin zafi da takaici. Wanne irin rashin ta ido ne wannan?,wanne irin soyewar idanu ce wannan?. Me ya gayawa akhnan har ya amintar da ita tayi ladab. A tarin aure auren yankin agadez bata taba gani ko jin labarin inda ango yakai kanshi dakin amarya ya kwana da ita ba,amma koma meye yakeji,koma meye yake taqama dashi dole gobe ta yiwa tufkar hanci. Da mutuwar jiki kasala baqinciki da bacin rai ta juya ta fara komawa inda ta fito. Batajin duka yau zata iya kwanciya tayi bacci......ta sani zata yita lissafi ne tare da jiran awannin da zasu kaita wayewar gari. A hankali ya soma slow da muryarsa sanda yakai qarshen surar,ya sauke idanunsa a kanta yana karantar yanayin fitar numfashinta. Tayi relax sosai,abinda yake gaya masa cewa bacci ya dauketa. Ya qarashe ayar qarshe yana lumshe idanunsa,shima yana jin wata nutsuwa me yawa da nauyi tana saukar masa. Tsam ya miqe cike da nutsuwa kasala da mutuwar jiki ya kalli agogo. Sha biyu harda rabi na dare,sai ya taka a hankali ya qarasa gaban gadon don tattare kayan magungunan dake ajiye a gurin. A hankali idanunsa suka sauka saman fuskarta,wadda kusan rabinta a duqunqune take cikin duvet,amma hakan bai hana manyan idanunta da zara zaran eye lashes da eye brows dinta bayyana ba. Idonsa ya dauke a kanta,ya matsar da komai yadda ya dace,ya saka hannu yana kashe hasken beside lamp dinta daya fuskanci digital ce. Daukarta yayi a hannunsa yana duba wanne company ne. Yadda yaga gurin da ake kunna bangaren qur'anin da seal a jiki ya tabbatar masa bata taba kunnuwa ba. Yadan tabe baki kadan,wataqila batasan ma da qur'ani a jiki ba kenan?,tabbacin baime dameta ba?. Baya yaja kadan ya cire seal din yana sake duba sunan company din. Sanda zasu fara fidda irin design na fitilun sun nemi izininsa kan karatunsa ya zama daya daga cikin karatuttukan da zasu dora akan na'urarsu,ya kuma basu dama,don haka yana kunnata kai tsaye ya tafi ga zabin farko qira'ar SHEIKH MUHAMMAD HAISAM. Suratul baqra ya saka,ya kuma daidaita sautin sannan ya ajeta nesa kadan da ita ta yadda sautin bazai takura baccinta ba. Yadda karatun yake fita duk kuwa da cewa muryarsa ce qira'arsa ce amma shi kansa sai daya lumshe idanu,tsaiwar sakanni yayi sannan ya matsa ga wayar girke dake cikin dakin,ya kuma kira sassansu birra. Birra dince ta daga,ya umarceta data zo yanzun,ya maida wayar ya ajiye idanunsa suna sauke sauka akan fuskarta. "Stubborn girl" Ya fadi can qasan zuciyarsa. Bai taba ganin mutumin da bai damu da kansa ba irinta. Abubuwa masu yawa ne tattare da ita zagaye da ita amma anyi sealing tunaninta gaba daya an dunquleshi guri daya,kuma a hakan gani take tana da lissafi sama dana kowanne d'a namiji. "Zamanka a rayuwarta taimako ne....lada ne me yawa ka fidda mutum daga hatsarin da baisan dashi ba" Yaji wani sashe na zuciyarsa yana gaya masa. Kai ya girgixa,baison raini,bazai sanya kasan canciki da rayuwarta ba.....zaiyi aikinsa ne kawai ya qare......sauran abinda Allah ya qaddara a rayuwarta da tashi a gaba shi kadai ya barwa kansa sani. A ladabce birra ta shigo kanta a qasa. Muryarsa a sauqaqe ya bata umarnin shigowa ciki. Ita kanta yanayin dakin a yau sai ya burgeta,duk da dakin bawai baqonta bane,ba kuma yau ta saba shiga cikinsa ba,amma a yau sai take ganin kamar an sauya dakinne. Umarnin zama ta kwana da ita ya bata,sannan ya nuna mata yadda zata kula da drip din har ya qare,da kuma yadda zata zareshi ta tsaidashi idan ya qare din gudun kada ya fara zuqar jini kuma. Ya sake gaya mata wasu abubuwan da zatayi bayan ta farka koda safe ko cikin dare "ki tabbatar bata rasa sallar asuba ba" Ya fadi daga qarshen maganganunsa duka. Wayoyinsa ya tattara da komai nasa ya juya yana fita a dakin cike da gajiyar zaman guri daya,kasancewarsa mutum me kazar kazar da yawan motsi,shi yasa zai wahala ka ganshi a zaune a guri daya. *W A S H E G A R I* A hankali ta bude idanunta sanda taji ana dan bubbuga pillow din da take kai ana kiran sunanta cikin girmamawa. Gefe daya daddadan sautin karatun qur'anin dake can qasa yana shiga kunnuwanta a hankali yana samar da nutsuwa cikin bude idanunta na farko da tayi a safiyar. Fes ta bude idanunta da suka sauka kan fuskar birra dake rusune a gabanta. "Allah ya taimakeki......lokacin sallar asuba yayi" Ta fada tana rusunar da kanta qasa. Kaman ba zatayi.magana ba,ta xubawa birra idanu tana mamakin yadda yau ta gaza jin alarm dinta. "Ina fashin sallah....ina wayata?" Ta tambaya da muryar masu bacci bugu da qari da wani yanayi a cikin muryar tata da wani irin sanyi sosai. "Bari a duba miki ita" Birra ta fadi tana miqewa,saidai batayi nisa ba ta ganta kusa da bedside lamp din. Idanu akhnan ta sauke kan fitilar,mamaki kadan yana kamata. Bata taba zaton akwai qur'ani a jikinta ba,tana daga kwancen ta miqawa birra hannu tana karbar wayar gami da jefa mata tambayar "Waye ya kunna karatun nan?" Tayi tambayar sanda take sauke idanunta akan fuskar wayartata "Sheikh muhammad ne" Ta amsa mata a ladabce. Qaramin tsaki taja tana jin wani haushi yana kamata. Ba professor ba ba doctor ba......sheikh?...sheikh?.....itama matar sheikh kenan nan gaba kadan za'a kirata?. "Idan kin gaza samarwa kanki mafita ba,....idan kika yarda kika rayu dashi" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa. "Ya akayi wayar ta mutu?" Ta sake daga kanta tana daga kwancen ta tambayi birra. "Shine ya kasheta da zai fita" Mamaki yadan kamata,taja qaramin tsaki tana jefa wayar bayanta ta maida kanta ta kwantar. Har birra din ta juya sai ta sake bude idanunta. "Waye yace ki tayar dani sallar subh?" "Sheikh muhamm....." "Ya isa haka nan" Ta katse birra da hanzari tana sake jan wani dogon tsakin tana maida idanunta ta lumshe. Tanason sanin waye ya cire mata ruwan ma amma tasan qilan idan ta tambayi birra zatace mata shine,don haka gwara ta riqe tambayarta a ciki tafi mata alkhairi. Tayi zaton zata koma bacci ne,amma abun mamakin sanda ta rufe idanunta sai daren jiya ya dinga dawo mata,wani sashen na tunaninta kuma yanata dibansa kan daddadan sautin karatun qur'anin da har yanzu ke fita can qasa ta cikin fitilar. Kamar tasan muryar,da gaske kaman tasan malamin,amma tunaninta daya lula da ita can duniyar abinda ya faru tsakaninta dashi a jiya ya janye zurfin nazarin bin qwaqwafin inda ta sanshi din. Fes wadannan idanun suka dawo mata.......lips dinsa da suke motsawa da wani irin yanayi.....kwantacciyar sumar dake fuskarsa data qara cika siffarsa da kamalarsa ta kwarjini,laushin tafukan hannunsa da suka nutse cikin nata. Bata farga da lokutan data bata ba a kwance tana tilawar abinda ta gayawa kanta daga baya baida amfani ba sai bayan wani lokaci. Wani tsaki taja me qarfin gaske tana bude idanunta. Cike take da tuhumar kanta,ba wannan tunanin ya kamata tayi ba.....wayeshi da zata bata lokutan masu tsada a kansa?. Samun kanta tayi da tula tarjn zarge zarge da laifuka ga zuciyarta data dauko mata wannan shirmen a cewarta. Koda ta bude idanunta saita riski birra harta kimtsa dakin tsaf. Taja numfashi sosai da nufin furzarwa.....amma saita riqe numfashin ta gaza fiddashi har na tsahon wasu sakanni kafin ta sakeshi. Wannan qamshinne sosai take jinsa cikin hancinta,wannan qamshinne yake ratsa qofofin hancinta sosai. Saita ware idanunta sosai tana a kwance tana juyasu tsakanin inda ya zauna a daren zuwa yanzu. Fari qal din handkerchief ta hanga zaman stool din daya zauna a jiya. Ta zuba masa idanu kamar haisam dinne zaune a gurin. Wannan abun kadai ya manta amma kuma yake isar da qamshi haka har cikin kwanyarta? Wanne irin turare ne wannan? Ta jefawa kanta tambayar. Sake jin qaunar mallakar turaren tayi ya kamata. A nata hasashen sam ba dashi kalar turaren ya dace ba......irin wannan turaren a hannun sarakuna da JININ SARAUTA ya kamata a sameshi ba hannun malami ba. Muddin kamfanin suka bata tabbacin mallaka mata qamshin saita haramta fidda sample dinsa a kasuwa gaba daya ballanta ya samu ya siya. Ta sake jan tsaki,waya sani ma ko da qyar yake iya hada kudin siya?,tsabar girman kai da son nuna izza a muhallin daba nata bane kawai ya sanyashi lallai saiya mallaka. Tafi kyautata zaton na wasu daga cikin manyan shugabannin larabawa ne qilan aka taba bashi kyautarsa.....ko kuma da dagiya irin ta malamai ya nace sai daya siya. Ta tabbatar badai a ce ya iya mallakarsa ta sauqi ba. "Ya kukayi da company perfume dinnan?,wacce amsa suka bayar?" Akhnan ta fadi bayan ta fito daga wankan data sanya birra ta hada mata ruwa me zafin gaske,birran kuma tana tayata tsane jikinta don tayata ta shirya. "Sun maido amsa.....wannan yanayin da aka shiga ya sanya tace kada mu sanar miki yanxu....mu bari sai komai ya lafa" Fararen blue eyes dinta ta daga ta jefi birra dasu. "Bayan auren wancan mutumin na farko?....kina nufin a yanzu kowa yasan ni matar malamincan ne?" Ta fada da wani irin emotions me zafi da suke tasowa daga zuciyarta. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 100* Qasa birra tayi da kanta,batasan amsar da zata bata da zata gamsar da ita ba. Yadda tayi maganan kawai tasan akwai wutar dake ruruwa cikin zuciyarta.....to amma maganan gaskiya ba cikin masarautar agadez kawai ba......maganan daurin aurenta a yanzu da sheikh haisam ya bazu a yankunan niger dama maqwabtanta. To amma wani hanzari ba gudu ba....tafi kowa sanin QARYA na cikin halin akhnan na qarshen qarshe. QURU QURU CE ita,kome zata fadi zata fada maka kai tsaye,koda kai hakan bai.maka ba,koda kai hakan bai dace da abinda kakeso kaji ba.....zata fadi maka ne da iyakar gaskiyarta,duk yadda zaka dauki abun kuma ya rage naka....wannan halin nata ya sanya ta tsani ayi mata qarya.....ta tsani HA'INCI....ta tsani YAUDARA kamar yadda tayi matuqar tsanar CIN AMANA. "Shuru ba shine abinda na tambaya daga gareki ba" Akhnan din ta fada tana jin zuciyarta tana mata rauni. "Tabbas.....kowa ya sani....ba a iya....." "Ya isa.....me company sukace?" Ta sauya akalar maganar,don iya amsar birra ta farko kadai ta wadatar da ita. "Sunce qamshine da mutum daya kawai yake da haqqin mallakarsa......amma zasu tura buqatar zuwa gareshi.....idan ya amince ya sanya hannu zasu iso da saqon amincewarsa......idan kuma bai amince ba,saidai ki zabi wani scent din na daban zasuyi miki shi". Kai ta girgixa a hankali. "Tunda wancan malamin ya samu qamshin to tabbas sun fada ne kawai......duk da banda tabbacin waye ya bashi.....don tunda suka fadi hakan alamace na sammasa qila akayi.....maganace ta kasuwanci da kudi,ki gaya musu su shaida masa ko nawa ne zan biya.....yau nakeso ki gaya mata,kada kuma ta wuce kwana biyu zuwa uku bata isar musu da saqona ba" "In sha Allah" Birra ta amsa mata tana ci gaba da taje doguwar sumarta kafin ta saki kanna hankali ta tafi ta dauko hair burner da take zuba mix na turarukan wuta masu dadi daga kamfanin INCENSE BY KABODAUGHTER 0803 211 9803. Tsaf ta gama gyara mata gashin ta kuma daure mata shi yadda ba zata takura ba,ta shirya cikin wasu sauqaqaqqiyar doguwar riga me dogon hannu. Koda ta kalli fuskarta a madubi sai taga kaman tadan qara kyau kadan. Tsaki taja,wanne kyau za'a samu cikin tashin hankalin da malamin ya sanyata?. Na nutsuwa ba kwanciyar hankali ba walwala?. Ta rantse har gwara lokacin maganan auren almaz akan yanzu,batasan wanne irin nisan qin jini tayima mutumin ba. Cannula din hannunta ta daga ta kalla. "Banason wannan abar birra,a cireta" "Kiyi haquri yazo,baice a cireta ba" Harara ta watsa mata wadda ta tilastawa birra din sadda kanta qasa. "Dama shima ba aikinsa bane.....bansan wanne shishshigi ne ya hada malunta da harkar lafiya ba....." Ta fadi har cikin ranta tana shan mamaki. Wancan karon ance shi ya mata allura sanda ake suspecting guba taci,yazun gashi ya sanya mata qarin ruwa,bayan abune da da yawa ma wasu masu aikin jinya saka cannula ke musu gardama,amma shi tsirawa daya taga ya samu kan jijiyar "Ni bamma yarda da mutumin nan ba.....baida gaskiya,ya kamata sultane yasan ainihin waneneshi" Ta samu kanta da fadi tana duban inda ya ajiye paper bag din me wani irin daukan idanu,tana tuna tea din daya bata jiya. Me yasa ta karba?,inda kuma ya zuba mata wani abu a ciki fa?. "Muje ki ban breakfast.....ki fita da wancan jakan" Ta fada tana nuna mata inda jakar take ajiye sannan ta juya a hankali cikin rashin qwarin jiki tana fita zuwa babban setting room dinta. Ko zama batakai gayi ba shehnaz da aisa suka shigo,shehnaz ce tayi sallama don aisa amsa waya takeyi. Daga amsa sallamar bata qara komai akai ba ta zarce kai tsaye zuwa ga dining,aisa ta zauna saman kujerun parlor din tana ci gaba da amsa wayar da da alama taja hankalinta da yawa,shehnaz kuma ta tako tana biyo bayan akhnan. Kujera birra taja musu su dukka suka zauna a kusan tare. "Shi cin abincin safen amare ma daban yake.......yanzu qarfe sha biyu sannan zaki karya?" Ta fada tana duban idanun akhnan. Bata amsa mata ba,har birra ta gama shimfida mata fari qal din lap napkin dake dauke da tambarin masarautar agadez ta kuma ajiye mata abubuwan buqata a kusa kaman tissue.....toothpick da sauransu sannan ta koma ta fara serving dinsu da plate uku,don ta hangi shigowar aisa ma. "Ki kira barratu ta hadamin tea" Ta fada da miskilar tattausar muryarta sannna ta maida fararen blue eyes dinta ga shehnaz. "Ba yau ba shehnaz.....ba yau ba....idan rigimar kike buqata ki bari na zama free.....ko na maida hankalina jikina" Maganan ya bawa shehnaz dariya sosai. Duk abinda zai sanya akhnan tayi magana haka da ita with calmness lallai babba ne,yana kuma taba zuciyarta da gaske. Saidai tasan halinta,tana kuma tsoron tattalin energy dinta kawai takeyi. "Ta yaya zanyi fada da amarya?.....amaryar ma ta manyan mutane,babban makarancin qur'ani irin sheikh muhammad haisam......kawai jiya na zauna kallo abinda na dade banyi ba,dana gaji na fara lalube laluben channels..... Kinsan wani abu?....manyan channels uku na kama kawai sai naji karatunsa sun saka da hotonsa yana rotating?" Shehnaz ta fada da mamaki sosai saman fuskarta. Har akhnan takai chips na farko bakinta ta fara taunawa ta tsaya tana watsawa shehnaz harara. Abinda zuciyarta ta bata kawai shehnaz tazo tayi mocking nata ne don ta auri malami.....abinda taketa gudu kenan,idandai har shehnaz zata zama ta farko da zatayi mocking nata to waye kuma bazai mata ba?. Waye haisam din da har wasu kanyan channels data lisaafo zasu saka hotonsa ko karatunsa?. Waye ma ya sanshi a iya agadez kawai kafin akai ga niger gaba daya?.. Banda kalar girman da taga kowa yana bashi da shugabancin riqon qwayar da sultane ya bashi wanda ya qara masa girman kan da yakeji tsaf zata iya cewa a masarautar ma ba kowa ya sanshi ba balle a tafi ga wani abu me fadi irin duniya. "Idan a jaridun duka duniya na jiya kikaga an sakashi ba damuwata bace.....ki riqe labarinki....banason qarin bacin rai.....aisa ki mata magana tun kafin aji kanmu" Ta fada da wani rauni da bacin rai tana maida dubanta ga aisa. Dariya kadan da mamaki suka kama aisa wadda ke takowa gurin bayan ta kammala waya. Duk da wayace me wani irin girma da nauyi a qirjinta,amma yadda yau kai tsaye akhnan ke kawo qarar shehnaz sai da abun ya sakata boyayyen murmushi. "Da alama bakiji abinda nannie ta fadi ba kafin mu fito ko?" Ta qarasa maganan tana jan Kujera a tsakiyarsu ta zauna. Hannu shehnaz ta saka alamun tayi zipping bakinta,saima ta jawo farfesun kayan cikin da birra ta zuba mata tahau ci,ita kuma aisa ta maida hankalinta akan akhnan tana tambayarta jikinta ba tare data dauko mata maganan jiya ba. *H A I S A M* Wani irin bacci yayi me nauyi daya sakashi makara a komai ma,don ko yanzun da yake breakfast shi da maleek ne kawai zaune cikin setting room din dake gefe daban na gidan. Yana breakfast din yana sauraren maleek da list din yadda zasu gabatar da bikinsa. Tissue ya ciro yana goge hannunsa gami da aza manyan fararen idanun nan nasa akan maleek. Tunda ya tashi yau kawai yakejin yanayinsa wani irin,sai yakejin yau yafi buqatar kebewa da zaman shuru akan kowanne lokaci na rayuwarsa. Amma indai yana tare da wadannan mutum shidan,koda bai shirya ba ya sani lallai sai sun sakashi ya magantu. "Da zaku fahimta da kun ajiye komai yanzun" "Zuwa yaushe kenan?" Maleek ya tambayeshi kai tsaye. Hannunsa ya sanya ya dauko system dinsa ya kunna ya fara daidaitata kafin ya amsawa maleek. "Aikina......sanda aikina zai cika.....sanda aikina zai kammala" Ya amsa masa yana soma duba emails din da bai duba a jiya ba,gudun kada ya samu kwantan emergency message. "Captain" Maleek ya kirashi bayan ya ajiye wayar hannunsa. "Ba wanda zaka hana yin biki tsakaninmu ko nanay haka ne?" Kansa ya dago yana duban maleek kafin ya dauke dubansa. Ya sani tunda maleek ya ambaci sunan nanay tabbas akwai magana da sukayi da ita,saidai bakai ga cewa komai ba abdii ya shigo da sallama. Yanayin yadda sallamar abdii din ta fita ya sanya haisam daga kansa yana aje dubansa a kansa. Wani irin rikici yake ganin cikin idanu da fuskar abdii din daya sanyashi zare hannuwansa daga kan system din gaba daya ya zuba masa ido kafin yace masa. "Shigo abdii" Kaman jira yake yace hakan ya fara takowa da wani irin rauni,idanunsa akan haisam din. "Kanata tsaiwa.....ka zauna abdii ko ka tafi" Haisam din ya fada wani abu yanajin yana dan taba zuciyarsa. A hankali ya sauke gwiwoyinsa yana kuma zama saman throw pillows din dake gaban haisam inda ya miqe qafafunsa a tsakaninsu ya aza system dinsa akai. "Labari yazo daga jimma" Abdii ya fada muryarsa da wani nauyi. Idanun kawai haisam ya zuba masa,har na tsahon wasu sakanni saidai abdi bai sake cewa komai ba,don haka yace dashi. "Ina saurarenka" "Motii was attacked" Ya fada yana sauya harshe,don yanajin yayi nauyi ya furta da yaren oromo ko hausa. Daidai sanda omar ya fado dakin shima fuskarsa na nuna tashin hankali sosai. A hankali haisam.ya maida idanunsa ya lumshe yana kiran sunan Allah daga can qasar zuciyarsa. Ci gaba da maimaitawa yayi,yana jin wani abu yana ratsa jikinsa gaba daya,innalillahin da maleek ke maimaitawa a sarari tana cakuduwa da tasa da yake maimaitawa a zuciyarsa. "Da yaushe?" Haisam din ya sake tambaya bayan ya bude idanunsa da wata iri jarumta yana daidaita bugun zuciyarsa. "Dazu da sassafe......ya baro inda yaje ya kwana daya,sai sukayo tafiyar asubah.....a hanya akayi attacking nasu". Omar ya bada amsa wannan karon. "Wanne yanayi suke ciki gaba daya?" "Akwai wadanda sukaji ciwo......saidai dukkaninsu ba wanda ya rasa ranshi.....don guards din dake tare dashi Allah ya basu ikon yin abinda ya dace,da qwarewar aiki kuma da suka samu daga gareka". Wani irin shuru ya ratsa cikin kansa.....wani irin shuru daya zarce har cikin kwanyarsa na wasu daqiqu,duk da tambayoyi da tattaunawa da sukaci gaba dayi su da maleek. Wani abu ne ya harba cikin kansa,yayin da wani irin bacin rai ya mamayeshi lokaci guda. Yatsunsa dake harde cikin na juna tun dazun ya rabasu da 'yan uwansa.....ya jinjina kai da wani irin yanayi daya sanya kowa juyowa yana dubansa. "Kiramin beeno" Ya bawa abdii umarni kai tsaye. "Beeno kuma?,na dauka zata shirya wucewa Ethiopia yau......ya kamata kaje kaga condition din da motii din yake ciki,a halin yanzu nasan ba wanda zaiso gani a kusa dashi sama dakai" Omar ya fada fuskarsa a rikice. Idanu haisam ya lumshe sannan ya budesu akan fuskar Omar din,ya kada kansa a hankali kafin ya motsa labbansa da yanayin fuskar nan tasa data tabbatar YAU SAI TA ALLAH......HALIN YA MOTSA ya kuma cakuda da bacin ran da sukaga ya sauko masa lokaci daya. "Bazan samu xuwa Ethiopia ba omar.....ba Ethiopia kawai ba.....bazan motsa ko ina ba daga cikin masarautar nan" "Me yasa captain?" Maleek ya tambaya cikin tsananin mamaki. Abune da basu taba zata daga gareshi ba,fadin irin shaquwa qauna da soyayyar dake tsakaninsa motii ma bata bakine.....koda yau ya sauka a addis ababa,anjima kadan akace masa motii yana ciwon kai,to tabbas zai juya ya koma jimma. Har tsokanarsa suke wani lokaci da sunan DAN BABA.....amma a yau babban abu ya samu motii irin wannan kuma yace bazaije ba?. "Ta zabi motii ne.....saboda tanason gwada SHURU ya koma SAUTI....if i leave i confess.....if i rage.....i reveal......i will do neither" Ya fada yana fidda wani irin numfashi. Abdii da omar kai tsaye kansu ya kawo wuta,duk da maleek ya gano wani abu amma ba duka ba. Wani irin kallo omar yakewa haisam din,yana sake girmama kaifin kwanya da basira da Allah ya bashi. Tashin farko shi daya.....shi kadai ya gano abinda cikin dukka su ukun basu ganeshi ba......ta zunguri motii ne saboda tana zargin haisam daga nan ya fito,ta zunguri motii saboda tanason yiwa haisam hukunci da reaction dinsa. "Saidai abu daya da bata sani ba......tasa muqulli ta budewa kanta da kanta qofar farko ta BAYYANAWA DUNIYA DA KANTA DA KANTA ITA WACECE" Ya fada da wani irin qawa zuci da fushin da yakejin yana tasowa daga qasan ransa. A duniya ba wanda zai taba mutum biyu halittu biyunnan ya qyaleshi,ko wayeshi,muddin da rai da lafiya a gangar jikinsa. Wayar abdii ya miqa masa bayan ya hadashi da beeno. "Wannan gidan.....wannan ajiyar da take ciki inason TA BACE BAT!.....Ayi mata kuma kyakkyawan guri,bincike na farko nakeso a zurfafa a kan ajiyar......ba dare ba rana,banason a jima komai bai kammalu ba" Ya furta da salon bada umarnin daya tabbatarwa da beeno babban aiki ya fara ballowa.....hakanan abdii da omar dake zaune dukka a falon. Awanni ya kwashe yana kiraye kirayen waya tsakanin jimma da Ethiopia......sai daya tabbatar da komai lafiya da kuma qarin samun tsaro,saidai bai magana da nanay ko motii din ba,yace a barsu su nutsu tukunna. Zuwa sanda ya kammala qarfe daya harda rabi,sai sukayi alwala gaba dayansu,omar ya jasu sallah a nan setting room din nasa. 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 101* *M A M M I N A* Cikin wani irin walwala take jin ranta,gaba daya fresh takeji a yau din saboda samun tabbacin qaddamar da harin da tayi imanin shi zai bata haske akan komai. "The silent one" Ta furta sunan a fili tana duban fuskarta a madubi "Al_saamit" Ta sake fadi tana sakin murmushi. Tabbas indai har shi din jinin aba jifar ne.....tabbas a yau zata naqalci hakan. Ta dakatar da murmushinta,ta saka hannu cikin jewelry organizer dinta tana fiddo warwarayen da sai sanda takejin girma da izzarta cikakkiya take sanyashi. Sanyashin yana tuna mata da abubuwa masu yawan gaske,sanyashin yana tuna mata da cewa ita dinfa me nasara ce. Dan dakatawa kadan tayi tana kallonsa ganin yadda ya shige hannunta zuruf,ba kaman a baya ba idan zata sakashi saita dan turashi saboda matseta da yayi,don asalin mamallakinsa batakai cikarta ba. Juyashi ta sakeyi cikin hannunta tana mamaki,to ramewa tayi?,ta tamabayi kanta da kanta,tambayar data sakata dauke dubanta ta mayar ga fuskarta a jikin madubi. Sam a zahiri bataga wata rama ba,ta sanya hannunta jikin wuyanta tana shafawa. Mamaki ya sake saukar mata,ta sake duban abun hannun da takeji kamar nauyinsa ma bai qarasa wannan ba.. Haka kawai taji wani faduwar gaba ya kamata,ta xareshi daga hannunta tana sake kallonsa,shine dai,ba wani banbamci,to meye ya sanya takejin kamar akwai wani abu na daban a tattare dashi?. Ta jima a tsaye bata hango komai da zai bata yaqinin abinda takeji ba,ta tabbatar kuma zata batawa kanta lokacine kawai,don haka ta qarasa shiryawa tana riqe da abun hannun ta fito. Tafisu ta samu,ta zube bisa gwiwoyinta tana gaidata kanta a qasa "Mun tashi lpy alhamdulillah.....naji dadin zuwanki yanzu,don zamu shiga duba akhnan ne.....idan da hali kuma ina buqatar ganin malamin can,saidai banason kiranshi kai tsaye,don zuwa yanzu ya kamata na fara tattalin izzata,ya kamata kuma yasan girman da izzata ke dashi da gasken gaske" Ta fadi tana miqawa tafisu abin hannunta. "Dubamin wannan......" Hannu biyu tafisu ta sanya ta karba abun hannun,don kusan tafi kowa sanin darajarsa. Juyashi tayi da kyau na wasu mintina,kafin ta maida dubanta ga mammina data xuba mata idanu tana jin gabanta yana faduwa. "Kinga wami abu daya canza daga gareshi?" Kai tafisu ta girgiza. "Ba komai ranki ya dade,yana nan kamar yadda yake,akwai buqatar ma a wankeshi don yafi haka haske". Shuru tayi na sakanni sannan ta girgiza kai,ta miqa hannu ta karba ta saka a hannunta tana cewa. "Muje". Kamar ko yaushe duk wani bawa ko hadimi dake hanyar wucewarta ya shiga kawo gaisuwa,a hankali a hankali har ta isa sassan akhnan. Fes abinda ya faru jiya ya dawo mata,zuciyarta ta matse bacin ranta ya dawo sabo. Wani tsanar matashin taji tana neman fara tofo a ranta. Bata tana haduwa da mutumin data gaza juyashi ta kuma sarrafashi ba sai SHEIKH HAISAM DIN. Ibraheem ne na farko wannan ya sanya take sake jin tabbaci da yaqinin cewa shi din JININ IBRAHEEM ne. Fruit salad ne a hannunta,tana zaune cikin wasu manyan throw pillows masu tsananin laushi. Madaidaicin parlor ne cikin parlours dinta,wanda kusan komai na ciki fari ne qal. Aisa na daga gefe ta saka system a gaba,cikin kwanakin kawai qarfin hali takeyi,ta shiga bincike ne kawai cikin sirri a SAHEL COUTURE ba tare da sanin kowa ba. Saidai yanayin abubuwan da take gani da report din da take dubawa daki daki lamarin b'arnar da akewa company din ya fara bata tsoro. Duk da haka bata bari tsoron ya mata tasiri ba......tanason lallai saita cimma gaci,tanason lallai saita tono tushiyar matsalar. Saidai duk da haka bata hana hankalinta wa shehnaz dake zaune tana bata labarin wani film data kalla ba,bara'atu kuma tana gyaran farce wa shehnaz na qafafunta dana hannu. A cewarta ba zata sake lalle ba sai idan an tashi biki. Da aisa da akhnan din dukka kallon shehnaz din sukayi,suna buqatar qarin bayanin bikin wa?. Aisa ce ta fara dago me take nufi,saita watsa mata kallon gargadi abinda ya sanya shehnaz boye dariyarta kenan,amma cikin dakewa tace. "Allah dai ya dawo da sultane lafiya,bamu yafe kowacce hidima ba ta al'ada data zamani" "Shehnaz mana" Aisa ta fada tana bata rai "Nayi shuru" Ta fada tana mazewa. Hankalinta aisa ta sake maidawa ga abinda takeyi din,sai gurin ya dan dauki shuru kafin sallamar mammina ta maida hankulansu bakin qofar. Idanunta a zube fes kan akhnan,idan bata manta ba idan kuma bawai tayi lissafi ba daidai bane......kwanakin data dauka bata ganta ba wasu kwanaki ne da basu taba faruwa ba a tsakaninsu a rayuwarsu. Koda tana Niamey ne bata rabo da kiran mammina din,video call ma,su kuma jima suna magana,komai zatayi saida shawarar mammina din,koda yanzun nan suka gama waya wani abun ya tashi to zata sake kiran mamminar. Cikin girmamawa shehnaz ke gaidata,ta amsa musu sanda take shirin zama saman daya daga cikin throw pillows din dake kusa da akhnan,daidai sanda idanunta suka sauka kan system din aisa. A nutse aisa din ta juyo da zummar ta gaida mammina din itama,idanunta suka kai kan mammina wadda ta zubawa allon system din idanu tanason hango da karanto manyan rubutun dake jikin system din. Da dan hanzari aisa takai hannunta tana kife fuskar System din,abinda yaja hankalin mammina din ta dauke idanunta ta maida ga fuskar aisa din. "Barka da warhaka mammina" Aisa ta kutso da gaisuwa tsakanin kallon qurillar da mammina ta kafeta dashi. Murmushi ta wanzar saman fuskarta cikin qasa da second daya tana gyara zamanta sosai. "Barka kade.....aisa sarkin aiki,har a nan ma ba zaki huta ba?" Kai ta dauke daga kan mammina din,tana jin wani abu a kanta wanda bata taba jin makamancinsa ba,saidai hakan bai hana aisa sakin murmushi ba. "To ya za'ayi......amana abace me nauyi da girma" Tace da mammina din tana dauke system din ta cusata cikin briefcase dinta. Kai mamminan ta jijjiga,har yanzu bata dauke dubanta daga kan aisa din ba "Gaskiya ne.......Allah ya taimaka,yayi kuma jagora.....ai muna sanya rai in sha Allah 'yar uwarku tana dab da komawa bakin aikinta itama" Mammina tayi maganar tana maida dubanta ga akhnan fuskarta na fidda murmushi. Still dai akhnan bata kalleta ba,idanunta na zube cikin bowl na fruit salad din da take diba a hankali. "Ya kamata mammina......kamfanin gaba daya ba dadi,abubuwa da ama sun dakata" Shehnaz ta fadi tana narke murya da kanta. "In sha Allah shehnaz" Mammina ta fada cikin qarfin gwiwa da bada tabbaci. Duk da bata kalli mammina din ba,amma zuciyarta ta harba ta kuma motsu da kalamanta. Wanne tabbaci take dashi na daidaituwar rayuwarta harma da komawa bakin aikinta a dan qaramin lokaci?. Tambayar data tsayewa akhnan din kenan a ranta. A nutse shehnaz da aisa suka miqe suna fita don basu guri. Hakan ya yiwa mammina din dari bisa dari. Ta sani yaran suna da wani irin hankali,suna da nutsuwa still,amma kuma hakan bazai sanya tayi sake akan canzawar motsi ko sanya idanun daya daga cikinsu ba. "Na yiwa 'yan uwanki albishir.......amma ke kuma banji kince komai ba biftu" Mammina ta fadi tana tsare akhnan din da kallo,tana son karantar ko akwai wani abu a daren jiya daya sauya tattare da ita?. Cikin izzar nan da mammina tayi mutuwar tsana.....cikin miskilancin nan da mammina din ta jima da sanin cewa rubutaccen abune a jininta,ta daga wadannan idanun dakema mammina din kanta kwarjini da zubesu akan mammina din. Banda mammina dince.....inda ace wani ko wata ne tabbas da bai isa ta sake koda kallonsa ba. Inda wani ne tabbas data jima da shafeshi daga babin rayuwarta.....data jimda taka masa burki gami da yi masa burki akan kowanne abu da ya shafi rayuwarta,to amma mammina ce......ko ba komai ita bata manta alkhairi a rayuwarta. A nutse ta motsa bakin ta bayan ta hadiye fruit din dake ciki "Bansan me ya baki qwarin gwiwar yi musu kalar wannan albishir din ba.......ko kina tunanin akwai wani qwarin gwiwar ko wata kalma da kike da ita wadda tafi girman yardar da sultane ya yiwa malamin?. Ko kina zaton akwai wani qanqanin shiri dalili ko gajerun kalmomi da zasu amintar da sultane?". Murmushi mamminan ta saki,kamar ba zatayi magana ba kafin ta saki wani irin shu'umin murmushi. "Yaro yaro ne.....kuma ta yaro kyau take bata qarko" Ta fadi idanunta zube a kanta. Da wani kallo tabi mammina,tana jin wani abu me kama da hope yanason taso mata. "Hannu daya baya daukan jinka fa biftu......a sanda ka tasamma sauya wani abu,idanuwa da yawa kake kallo dasu,kunnuwa da yawa kake saurare dasu.....sannan kana qara adadin hannuwanka ne don sarrafa abinda qafafunka ba zasu samu isa ga gurin ba". Shuru ya wanzu a dakin,tana sake jefa shakka da buri a zuciyar akhnan. Kallon da akhnan din tayi mata ya gaya mata neman qarin bayani take. "Eh.....kina tunanin zan bari burinki ya tafi a banza?.....baki mamakin yadda UWA me share kukan diyarta a wannan karon tayi wasarere da buqatar diyarta ba?....ta bari aka hadata da TAUYAYYEN mutum wanda yaci karo da dukka buri da muradan d'iyarta ba?" Shuru akhnan tayi,wani abu yana fusgarta game da maganganun mammina. Murmushi mammina taci gaba da jifanta dashi,kafin daga bisani wasu qananun qwalla suka fara zubo mata a fuska,ta sanya hannu tana sharesu,still bata daina murmushi wa akhnan ba "Kina zaton cewa sa nayi zan tsaya miki......zan kasance tare dake da dadi ba dadi da wasa nake?.....kina tunanin don kin juyan baya ni hakan zai sanya na gujeki?" Saita girgizawa akhnan din kanta. "Idan uwa tace tana son d'anta da gaske take tana sonshi,dadi ko wuya ba wani abu da yake sauya wannan......dadi ko wahala ba abinda zai sanya ta sauka daga kan wannan maganar tata.......Ban taba zaton KUSKURE daya tak zai iya zama sanadin rushewar alaqar dake tsakaninki da uwarki ba. Ban taba zaton AKASI guda daya da kika samu daga tarin shawarwari da uwa a gareki ta jima tana baki ba zaki kasai mata uzuri ta zama abar zargi a gurinki ba" Ta fadi hawayen still suna sauka.. Wani irin sanyi jiki da gwiwoyin akhnan sukayi,wani irin yanayi takeji a ranta maras dadi.....saidai duk da wannan akwai wani sashe daban na zuciyarta da bai sauya daga yanda yake tun a wancan ranar ba. "Sultane bazai sauka ba bazai sauka ba bazai kuma warware abinda ya qulla ba.....saidai shi da kansa wanda aka daurawar zai warware da kansa.....sai sallameki ta hanyar da zata nesantashi da sultane har abada.....soyayyarki kusancinki da sultane zai koma kamar yadda yake harma ya rubanya na baya" Duban mammina takeyi cike da kokwanton abinda take fadi. Fuskar haisam na gilmawa cikin idanunta. Wannan kafaffen malamin da bata hangen sassauci ko sauqin kai a tare dashi?. Ta yaya mammina zatace zai sallama haka da sauri da kuma sauqi?. "Kina mamaki ko?,to aurenki bai dauru dashi ba sai bisa sharadin AUREN YARJEJENIYA ne zaku qulla ke dashi.....don ki wanku a idanun sultane.....ki kuma samu irin 'yancin da kike fata" Da wani irin shuru bayanan suka wuce ta cikin kan akhnan din,tana jin sam sun gaza hawa mizanin da takeson dorasu. Mizani na farko.....da irin idanun data karanci mutumin.....yana da wata irin izza da girman kan da bata taba ganinta jikin mutum me maqasqancin matsayi irinsa ba. Na biyu halayensa kaf basuyi kama da halayen mutum sassauqa da zai karbi duka wani sharadi doka ko umarni ba. A tsanake ta maida dubanta ga mammina,tana jin tarin kokwanto,tana jin tarin rashin nutsuwa da aminci. "Karfa ki sake aikata wani abun da zai janyomin sabuwar matsala.....karki damqa ragamar rayuwata a hannun mutumin da zai sarrafata yadda yaga dama" Murmushi mammina ta saki,ta karanci tarin kokwanto a tare da akhnan,ta karanci shakkar abun sosai a tare da ita......saidai ta tabbatar zata bawa akhnan hujja da gamsuwa. "Nasan kina shakka ko?.....shikenan,kiji dadinki,ki kuma kwantar da hankalinki,lallai babarki zata tabbatar miki da komai,zaki gani a gaban idonki" Mammina ta fada hankali kwance tana miqewa da wani kwataccen murmushi akan fuskarta. Murmushin da akhnan ta dade da saninsa,murmushin da idan ta yishi yana nufin ZAN AIKATA ko kuma ZAN TABBATAR.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 102* *HAISAM* A nutse ya ajiye wayarsa bayan sun kammala waya da sultane,wanda yake fadi masa kwanaki bakwai ko shida kawai zai qara ya dawo. Wani irin nauyi sultane ke aza masa,yanata qara kusanci tsakaninsu. Duk sanda zai waya da sultane din cikin hikima ya fahimci yake sake tabbatar masa da amanar akhnan a hannunsa,cikin hikima yake sake gaya masa AMANNAR da yayi dashi,abinda ke sake sare gwiwar haisam kenan. Baiyi alqawari ba.....amma maganganun sultane suna zame masa kaman wani ginannen rami. Ko a yau din duka ya sha'afa da lamarinta,musamman daya tashi da mummunan labari akan motii,bai kuma yi niyyar sake zuwa inda take ba,don ya tabbatar taimakon daya bata jiya yana kyautata zaton yau zata tashi da cikakken sauqi,to amma kuma aiken kayan abinci niqi niqi dafaffe cikin Warmers na alfarma da morsa safiyya tayo masa ya sanya ya tuna da yarinyar. Duk da haka bai niyyar shiga ba,saida sukayi waya da sultane. Yardar da yayi dashi a kanta dari bisa dari ce.....ba wani abu dake nuna kokwanto ko shakka a kansa. Wannan yardar kuma itake sakashi jin nauyin sultane din,ko sanda suna wayar yace masa. "Biftu bata taba ciwon da naji hankalina bai tashi a kansa ba irin wannan.....na tabbatar tana hannu da qarqashin kulawar wada zai bata kula da kariya sama da yadda ni zan bata" Ajiyar zuciya ya sauke yana balle maballan jallabiyyar jikinsa da zummar shiga wanka sannan ya fita ya leqata,daidai sanda kiran beeno ya shigo masa. A nutse ya saka wayar a kunnensa,kuma cikin qasa da second biyu ya isar masa da saqon da dama shi yake kyautata zaton zaiji daga bakin beeno din. "Tun dazu aiki ya kammala,kuma ko yanzu haka na lura da qaqqarfan motsi a gidan,da alama suna neman inda ya bace ne" "Da kyau.....saina nemeka" Haisam ya fadi da husky and calm voice dinsa yana katse kira. Maher ya kira kai tsaye a amintaccen layin daya ware kawai saboda kiran nasa. Saidai tunda ya kira daya bai daga ba yasan qila yana bakin aiki,yayi kuma nisa da wayar. Sai ya aike masa gajeran saqo. _"akwai wani boyayyen abu da takewa wani bala'in boyo a villa street,haske kawai nake buqata akai ba duka bayanan ba.....ragowar aikin na haisam aba jifar ne"_ abinda ya aikewa Maher kenan,sannan ya ajiye wayar. Karatun qur'ani ya matsa gaba kadan ya kunna ta jikin fitilar tsakiyar dakin,qira'ar sheikh maher almu'aiqaly da sasaauqan sauti mara amo sosai,sannan ya dauki lallausan babban towel din yana zarcewa bandaki. Karatun yana sake saukar masa da nutsuwa,yana kuma sake buda masa qofofin tunaninsa sosai. Awa daya ya kammala shiryawa cikin black emirati kandora me wani irin sulbi da daukan idanu. Shemagh ya nada a kansa fari qal me adon black mara hayaniya da yawa,ya saye qafarsa cikin fari tas din half shoe. Wani irin kyau yayi me daukan hankali da idanu,baqar kandora din ta fidda asalin kyansa da haibarsa. Bai sanya agogo ba tunda ba nisa zaiyi ba,yadai saqala counter dinsa a yatsarsa saboda gudun tozartar da lokaci ba ambaton Allah a cikinsa. Wani irin counter ne da zaka rantse da Allah qawataccen zobe ne me asalin kyau da tsada. New model 2028 da company din suka fidda sample dinsa suka kuma aiko masa dashi saboda girmamawa. Ba kowa a sassan nasa,sai abdii kawai dake siyan zaune saman kujera da system yana cinikin wasu litattafai daga Egypt misra. Dubansa kadan haisam yayi,kasuwancin litattafan ya fuskanci kamar sun karbi abdii din,don shima idan ya nema wani cikin wasu litattafan bai samu ba yana yiwa abdii din magana yake kawo masa. Ya yanke shawarar idan komai ya nutsa ya qara masa jari me kauri ya sake buda harkar tashi,duk da so yayi dukkaninsu ya zubasu a harkar kamfanin turarukansa,tunda ba yadda za'ayi kana aiki irin nasu ya zamana baka wata sana'ar daban da zata kadar da hankalin mutane daga ainihin aikinka. "Obbo.....an samu naka littafin.... Million daya da dubu dari biyar" Abdii ya fadi yana sanya qwayar idanunsa akan haisam din,sai kuma maganar ya qarasa maqalewa saboda wani irin kyau da kwarjini da haisam din yayi masa. "Ba damuwa,a aika dashi jimma.....ka fadawa mansoor(me kula da katafaren library dinsa) a bangaren da zai sakashi,ya hadashi da sauran" Ya amsa masa yana nufar qofa. "Am....amma obbo....library dinka ya cika fa duk kalan littafin daya kamata ace akwai...." Abdii ya fada har qasan ransa shigar haisam din tana sake burgeshi,still kuma yana mamakinsa. Yadda yake sanya ko nawa ne ya siya littafi,duk da kudi ba matsalarsa bace,amma girman library dinsa ya isa. Yana daya daga cikin manyan dakin karatu da ake recommending ma mutane shi. Yana matuqar ji da ita sama da komai daya mallaka,don haka ba kowa yake samun dama ko izinin shiga ba. "Bakasan girman ilimi ba abdii?,daga inda kake zaton ka qure masa,daga nan wani ya fara ma......ilimi.kogi ne,yana da girma da fadi,saidai kawai kayi iya yinka" Ya amsa masa sanda yake.murda handle na qofar parlor din. Dasauri ya miqe abdii din yana kashe system din. "Zan iya rakiya?" Ya fada yana daga yatsarsa. A nutse haisam ya juyo ya kalleshi,sai yaga ya wani narke alamun roqo yake yana tsoron kada ya hanashi. "Bismillah" Ya fada yana motsa kyawawan labbansa. Wani dadi abdii din yakeji,jerawa da captain obbo din kawai wani dadi da alfahari yake sanyashi ji,yana jin zuciyarsa cike da fatan shima wataran ya zama kamar haka. A duk sanda suke tafiya kaman haka cikin gidan,yaga yadda hadimai ke gaida obbo din dariya abun ke bashi,ba shakka inda sunsan LU'U LU'UN da suke rayuwa tare dashi....ba shakka idan da sunsan YARIMAN dake rayuwa a masarautarsu qila da jan ciki zasu dinga wucesa,saidai shi din ko acan Allah ya masa daukan rayuwa da sauqi,baya daukan kansa a bakin komai. ∞Tun daga nesa idanunta suka hange mata shi,nesan data zame mata kamar wata kusa saboda tarin kwarjinin da taji ya fara dukanta. Idanunta ta rufe ta kuma budesu tana gayawa kanta da kanta cewa itadin mutum ce me daraja da tafi qarfin wani qaramar halitta irin wannan ya qalubalanceta ko ya saka mata shakka. "Ku gaya masa ya dakata inason magana dashi" Tayi magana da tafisu da sauran hadimai biyu maza dake bayanta. "An gama" Suka fadi suna qara sauri don su riski haisam daga inda yake su sanar masa da saqon mammina. "Inason naga yanayin fuskarsa.....inaso in samu tabbacin saqon dana aike masa ya riskeshi?" Ta fada qasa qasa,tana magna da tafisu,idanunta akan haisam. Sau daya tak ya kalleta yayi zuzzurfan karatu game da abinda ke shimgide a zuciyarta. Siririn murmushi ya saki cikin qasaita da izza wanda kai tsaye ya wuce ya kuma zarce zuciyar mammina duk da daga nesa take hangensa. "Na bata wannan damar" Ya bawa hadimin amsa. Da mamaki yadan dubeshi na yadda yake fadin ya bawa giwa damar ganinsa amma sai kwarjininsa ya hanashi qarasa kallonsa da kyau. A nasa sanin,muddin ta buqaci ganinka kokai waye ba amincewarka take buqata ba,sanarwar da tayi yana gaya maka cewa ka tsaida duk wani uzurinka ne kawai ka saurareta. Isowarta daura dasu yayi daidai da dauko kujerar da hadiminta yayi ya dasa mata a nan tsakiyar hanyar,tunda hanya ce dama ta iya su isassu ba kowa ya isa ya bita ba. Wani abu ya tasowa abdii,girma martaba dama isar da masarautar JIMMA ke da ita ya motsa masa.....jinin jimmawa da martabar sarautarsu,sai shima ya taka da hanzari ya dauko kujerar yana ajiyewa haisam din. Maimakon ya zauna saiya karbi kujerar kawai ya maidota gabansa yana dafe dukka hannayensa akai idanunsa akan mammina data zubawa abdii su tana kallonsa cike da mamakin WAYE SHI KUMA?. Ya lura da kallon da takewa abdii,kuma shi kansa yasam abdii din yayi mafi girman motsin dabai kamata yayi ba. "Ka bamu guri abdii" Haisam ya fada don kade kallonta dama dukkan tunaninta akan abdii din. Murmushi ta saki tana girgiza kai a nutse,nutsuwar da sam babu ita a zahirin zuciyarta. "Yayi zamasa......ka zauna mana?" Ta fada tana masa nuni da kujerar dake gaban nasa wanda abdii ya miqo masa. Kai ya girgiza,sannan ya rusunar dakai cikin girmamawar da ita kanta bata zauna mata a inda duk wani girma da ake bata yake zama ba. "Bai kamata ba.....tsaiwa ita ta kamata ranki ya dade" Shuru tayi tana juya amsarsa a ranta. Shurun ya wanzu,kafin a hankali yaren oromo ya harba a gurin "Haleellaa du'aa Motii irratti raawwatame(Harin mutuwa akan motii)" Ta furta da haruffan da suka fita a bakinta daya bayan daya,labbanta suna motsawa,amma idanunta a kafe saman fuskar haisam din. Neman reaction take a tare dashi komai qanqantarsa.....neman wani canjin yanayi takeyi a tattare dashi ko yaya da zai bata haske,amma abinda ya jefa shakku da kokwanto a ranta shine. Ko yatsarsa bai motsa ba ballantana ta sanya rai zaiyi wani motsi da zai bata wata alama komai qanqantarta. Shock ta shiga sosai,ta sauke hannunta daga fuskarta tana sake qare masa kallo. "Haleellaan hanga namni dhokataan of mul'isutti hin dhaabbatu(kai harin bazai dakata ba.....har sai sanda wanda ya boye kansa ya bayyana kansa da kansa)" Ta sake fadi tana hada dukkan fuskarta guri guda. Wani murmushinne can qasan ransa shima,wanda ko kusa ko alama bai bada alamu ko qwaya daya ba. Saqonta ya isa gareshi fes.....wawancinta yana sake bayyana. Duk inda mace take macace,hakanan duk inda takai ga zurfafa tunaninta ta qureshi tunanin d'a namiji a nan ya tsaya. Ba abinda yake kalla a yanzu sai ZAITUNA A TAFIN HANNUNSA.....bayan ta kashe asalin ZEENATU ta shafe babinta a Ethiopia ta maye gurbin suna tarihi da kuma dukiyarta.....TA'ADDANCINTA NA FARKO da take tunanin ya jima da bacewa!. "Daga gurin waye ka samu iznin kwana dakin akhnan a daren jiya?.....baka da masaniyar a al'adarmu hakan haramun ne?" Tayi tambayar da nuna izza da isa,can qasan zuciyarta kuma da manufar kunyatashi gaban hadimai da bayin da take tare dasu. "A al'adar ba'abzine.....bata inda namiji yake da ikon kwana dakin matarsa harsai an miqata gidansa......kana da qarancin sani game da al'adunmu.....nme yasa zaka takesu kayi gaban kanka?" Ta sake fadi cikin izgili da nuna isa. Bayason ya zuba mata dukka idanunsa ya hanata cewa komai,yanaso ya karanci abinda ke sakaye a zuciyarta......don haka bai kalli cikin idanunta kai tsaye ba sai fuskarta kawai,wani irin abu yana tasiri a ransa......JININ OROMO da asalin sarautar gidan aba jifar suna motsa kowaccs jijiyar jini ta jikinsa. Sosai abdii dake tsaye a bayansa ya zuba mata idanu. Cikin ranshi yakeji inama ace cikin jimma suke a yanzu haka?,inama ace ba boyayyen aiki bane ya kawosu agadez?,shakka babu da sai ya sanya matar ta cika da nadamar yadda take magana da prince din nasu. Baisan me yasa haisam yaketa dauke abubuwa da yawa daga gareta ba,bata ca canci wannan kawaicin ba. A nutse ya juyo da kujerar yana dora tafin qafarsa guda daya akai. Idanunsa fes a kanta,muryarsa da wani madaidaicin sauti dake nuna qarfin da zuciyarsa dama dukka gangar jikinsa suke dashi. Qafarsa dake sanye cikin takalmin asalin fata saqar qasar italy tabi da kallo. Gabanta yayi wani mummunar faduwa,wannan din wani sign ne na alamun qanqantarwa da rashin bada girma a qabilar oromo,saita zarce da duban fuskarsa da sam bata nuna fushi ko dimuwa ba. Kai tsaye yake duban idanunta a wannan karon "Bana buqatar neman izini a sanda zan shiga halastaccen muhalli a gurina.....na shiga a matsayin MIJI ba dan aike ba.....ba bawa ba ba kuma hadimi ba.....sannan kuma na shiga a matsayin me ceto.....shi kuwa me ceto baya jiran umarni kafin yayi ceton,a al'darmu ceto gaba yake da neman izini.....ceto baya jiran ixini,izini ne yake jiran ceto a koda yaushe......a tamu al'adar.....MIJI yana zama abun tir a sanda ya gaza kare MATARSA da nauyinta yake wuyansa,bawai a sanda ya karya wata al'ada ba da bata da alaqa da addini......amma idan kina ganin kasancewata da ita a daren ya zubda mutuncinta.....kina iya shelantawa duniya ki fadiwa kowa laifina a fili" .💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 103* Idanunta ta lumshe a hankali tana jin yadda ya sauke mata magana masu zafi,amma cikin wani salo na taushi da kwantar da harshe,ba hayaniya ba daga murya,amma nauyinsu da zafinsu a gurinta yakai wani mizani me girma a zuciyarta. Yanason mata rami ya jefata ne a ciki,me zata ce ya kaita gurin Akhnan din a irin wannan daren?,wanne amsa zata bayar a sanda idanuwa zasu kalleta da tuhumar ya akayi tasan da wanzuwarsa a dakin duka daren?. Fes ta sake bude idanunta a kanshi,baici banza ba,ba kuma zata qyaleshi ya bata kalar wannan amsar gaban hadimanta ba kuma ya tafi salin alin "Ku matsa ku bamu guri" Ta fada cikin bada umarnin daya sanyasu watsewa da sauri. Yatsa kawai ya murzawa abdii ya motsa daga gurin,yadda ya murza yatsan yaja hankalinta matuqa. Wani yanayi ne na salon izza da sarautar Ethiopia.......salo ne na isar sarauta ga BASARAKEN oromo. Saita sake zuba masa idanu gabanta yana faduwa,amma wani halin na rashin son faduwa ya mamayeta. "Ni na fara nemanka da wannan auren" Ta fadi tana dakatawa "Baka bani amsa ba" Ta sake dakatawa,yanayin daya tabbatar masa maganar tana da girma da nauyi a zuciyarta. "Saika barni.....mahaifinta kuma ya kiraka,saika amsa masa ka kuma karba" Ta sake fadi tana nutsa idanunta cikin nasa,sannan cikin daga murya kadan da kaurarata ta dora. "Me yasa baka sanar dani ba.....me yasa naji labarin daura auren nan kamar bani da hannu a ciki?" Ta fada cikin fushin da taketa qoqarin danneshi tana kokawa dashi,maganar tafisu tana mata yawo akai inda tace 'kamar akwai izza a tare dashi,idan kikace ta fada ta umarni nakai tsaye zaki biyo masa ba zaki taba nasara ba giwa.....kamar dabi'unsa na SARAKI ne' Wani irin shuru yayi mata yana dubanta,irin shurun nan me sanya shan jinin jiki ga mutum,shurun daya sanya mammina komawa hayyacinta,saidai ba zata barin ba ya gane hakan bane. "Ki kula da yadda kike tambayata" Amsarsa ta fito da wani yanayi daya sanya mammina buda idanunta dukka a kansa. Kansa ya jinjina mata shima yana ci gaba da dubanta,abinda yake bata tabbacin eh maganar daya fada din yana nufin ita dince daga bakinsa kuma ta fito. "Ka kula da wadda kake magana da ita" Itama ta mayar masa da shigen salonsa. Wani murmushi yayi na gefan baki kadan,sannan ya sauke qafarsa ta dama dake saman kujerar ya maida ta hagu. "Ba dole bane saina sanar dake.....duk da kafin ke wasu mutane da sukafiki cancanta da kusanci da ita sun nema min ita?.....ko sun nema mata ni?" Ya fadi kaman ya rasa yadda zai bada maganar. Shigarta maganar tayi......kafin ita kuma?,waye ya rigata?.......SAFIYYA? Ta tambayi kanta tunaninta yana girgiza. "Lokacin da kika nemi aurena.....ban amsa ba saboda ban shirya ba....duk da ba kece ta farko data nema hakan ba....." Ya sake maimaita maganan yana duban idanunta sannna ya dora. "Sanda mahaifinta ya kirani ya bani aurenta.....na karba ba kuma don roqo ba....sharadi ko wata qa'ida ba.....na karba ne saboda na yanke shawara" Ya sake fadi kansa tsaye cikin wani coolness da mammina ta tabbatar ba iyakarsa kenan ba......akwai wani abu a badini "Bana dawowa na nema izini ga wanda bai mallaki shawarata ba" "Wannan auren baizo da tsari ba sam....yazo da gaggawar da zata iya kai hankulan wasu akan manufar yinsa" Ta fada da hanzari ganin yana sauke qafafunsa qasa......tana tsoron rasa control nashi.....tana tsoron rasa wannan gabar......tana buqatar juyashi daidai da buqatar ta. Wani kalan murmushi ya sauke yana daidaita tsaiwarsa sosai,da wani yanayin da zai gaya mata CIKIN IZZA DA IKO AKA HAIFESHI. "Idan labarin yazo miki ba zato ba tsammani to haka rayuwa take ga mutumin da bai zama cibiyar hukunci ko yanke hukuncin ba" Wani abu ya naushi zuciyarta,magana ce ya yaba mata me girman gaske,ta maida dubanta a kansa sanda yaci gaba da takawa yana barin gurin,alamu dukka suna gwada mata gurin Akhnan zai shiga. "Ki saba da jin labarai daga waje.....ba daga bakina ba" Ya qarasa fada da wani salon izza da yakejinta a yau mamminar ta motsa masa shi.....jinin aba jifar ya soma harbawa a jikinsa da qarfin gaske. Dukka wannan suffar daya azawa kansa yaji kamar zai gagarata riqeta nan da wani dan lokaci kadan. Da sauri tafisu ta dafeta wadda ta garzayo kusa da ita da gaggawa ganin yadda komai ya gudana. Ta tabbatar komai zai iya sake damalmalewa tsakaninsu. "Kada kice komai.....akwai wani abu cikin jininsa,tabbas akwai wani abu me qarfi a jininsa,ki lallabashi harki cimma burinki" "Tafisu?....meye banbancinsa da sauran mazan dana taba sarrafawa?" Mammina ta jefa tambayar ga tafisu tana dubanta duba na mamakin da haisam ya shayar da ita "Baki buqatar fushi a daidai wannan lokacin sam,bashi da amfani a tattare dake" Tafisu ta fadi tana dannar mammina. "Akwai lokaci....a sannan ne zaki nuna masa qaryarsa.....a sanda rayuwar Akhnan ta dawo hannunki zaki sarrafata yadda kikeso ki kuma b'alb'alta rayuwarta dama ta ubanta data uban dukkan wanda kikaga dama" Maganganun suka sauka a kunnen haisam daidai sanda idanunsa suke sauka saman fuskar Akhnan din. Har yanzu tana zaune tsakiyar throw pillows din,idanunta wannan karon akan system din dake gefanta suna magana da ameesha,dankwalinta yadan zame kadan wannan ya bawa kwantacciyar sumarta me sulbi daman fitowa ta gaban goshinta,fuskarta tayi fayau tayi wani haske me daukan hankali. Hannu ya sanya yasake danna Bluetooth din cikin kunnensa sosai,yana jin maganarta ta qarshe haka kawai ta sauka zuciyarsa da wani irin nauyi a kunnensa da qirjinsa. Ya yarda device dinne dan qarami a gurin,bai dauka zaiji wani abu me muhimmanci da yawa ba. "Ya jawowa Akhnan.....gwargwadon wahalar daya bani.....gwargwadon yadda zan sauyawa rayuwarta fasali da la'antaccen yanayi....." "Allah ya baki yawan rai" Maganan mammina yaji ta katse a kunnensa,muryar tamim cikin yanayi na haki ya maye gurbin tata. Shigar qamshin cikin qofofin hancinta ya sanyata daga kanta a hankali daga fuskar ameesha dake system din zuwa bakin qofar,inda haisam yadan dakata kadan yana bada hankalinsa ga maganganunsu mammina......saidai kuma hakan ya sanya su aisa sun zaci kamar yana buqatar gusawarsu ne daga gurin,don haka aisa ta tattare kayanta,hakama shehnaz suna gaidashi cikin matuqar nutsuwa saboda tsananin kwarjinin da yayi musu. Da kai kawai ya amsa musu yana qarasa shigowa ciki don ya basu daman fita daga dakin,kowacce kaman zata kifa haka sukeji suka fice daya tana bin daya,abinda ya bashi daman maida qofar ya kulleta,ya kuma ci gaba da tsaiwa hannunsa saman handle din. Ci gaba da duban ameesha tayi,amma kuma a wannan lokacin ta soma daina fahimtar bayanan ameesha din. Shuru takejin kanta da qirjinta,sai qamshinsa daya cika dakin ya kuma sanya bugun zuciyarta ya tsananta. Lumshe idanunta tayi tana tambayar kanta,meye dalilinsa na tsaiwa mata a qofa?,jiran girmamawa ko gaisuwa yakeyi?... "Bazai yuwu ba" Ta fadawa kanta da kanta ba tare da tasan dukka kunnuwansa dama fiye da rabin hankalinsa akan maganganun mammina da tamim suke ba. A hankali ta matsar da idonta zuwa ga siririn madubin da bai rabin fadin hannu ba,saidai yana da tsaho sosai wanda akayi wani ado daga gefan inda take zaune. Fes idanunta suka sauka a kansa,tsaf ya fito ta cikin madubin,still hannunsa yana kan handle din,idanusa sunyi qasa yadda baka iya ganin qwayar idanun. Idonta ta sauke daga kan qafafunsa. Ma'abotan dogayen yatsu farare sol,dogayen yatsun da kowanne samansa yake da wata gargasa a kwance. A hankali tayi sama da idanunta. Saidai kafin takai qarshe kwanyarta da zuciyarta sun gama lissafa mata "GIANT ne" Tsahon data tabbatar idan ta tsaya a gabansa zata zama yana kallon tsakiyar kanta ne. Kwantacciyar sumar dake habarsa zuwa kuncinsa guda biyu,cikakkiya da aka yiwa wani gyaran daya gagara tsallake qawar zuciyarta,idanunta suka gangara ga lips dinsan nan masu daukan hankali kamar wanda ke using lip balm. Shape din hancinsa daya zauna da wani irin yanayi me ban qaye tabi da kallo,wanda ya kaita ga girarsa wadda ta kusa haduwa da juna,kafin idanunta su zarme su sauka cikin manyan idanunsa da iya saninta ba'a bude suke ba a dazu,saidai a yanzun tana kai qwayar idanunta cikin nashi qwayar idanuwa hudu suka sarqafe cikin na juna. Wani irin mugun kaduwa tayi,ta kuma janye idanunta da wani irin sauri tana maidasu kan system din,saidai banda wuyanta ba abinda ya nuna motsawar da tayi,abinda ya sanya wani miskilin murmushi yana subuce masa. Murmushin abu biyu ne. Da gaske tana da GIRMAN KAI DA IZZA irin na kowacce isashiyar mace. Ta sakankan kan ta cikin madubin kawai take qare masa kallo a fakaice,a nata tsammanin ita kadai tasan da zaman madubin. A sanda ta tabbatar kuma ya ganta tsabar JINKAI da K'I FADI ya sanya tayi wani reaction da zaka dauka arashi aka samu na haduwar idanunsu,bawai kallo take qare masa ba,tabbas ta gwanance wajen iya kare kai da maintaining steex dinta. Da gaske bata yarda komai ya taba wannan MARTABAR tata. Murmushinsa na biyu muryar tamim....muryar mammina......rudewar mammina da tashin hankalin da sound dinta ya gwada masa "AN DAUKE ALMAZ RANKI YA DADE!!!".duk da baisan kalar ashar din qabilar abzinawa da yarukan da suke iya amfani dashi ba.......amma kuma zagi jikinsa yake bashi ta auna me qarfin gaske. "An dauke almaz?.....waye?....yaushe?.....a ina?" Duka ta aunawa tamim wadannan tambayoyin da muryarta kamar wadda ta zare.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 104* Disconnecting device din yayi,ya fara takowa zuwa cikin parlor din. Sallama yayi da muryarsa wadda a yau ta bada wani irin taushin amo.....taushin amon daya tuna mata da karatun qur'anin daya kwana jiya yanayi,ya bata wani yanayin bacci me dadi da kwantar da hankali. Karon farko ta daidaita muryar qira'ar jiya da tasa,sai a sannan ta tuna,ta lumshe idanunta tana sake budesu kan system din da ita kanta ba zatace ga abinda takeyi a ciki ba. Sai taji a sanda karatun yake dab da ita kamar yafi dadi akan daga nesa da take jinsa. " Can qasan ranshi yana maimaito kalaman mammina......yana hasashe da hangen yanayin mammina da yadda zata fuskanci wannan qalubale. Ba wannan ne kadai challenge din daya shirya bata ba.....ba wannan ne kawai rudanin daya shirya bata ba.....amma wannan shine abu na farko da zai fara aike mata a matsayin gargadi. Sau daya tak ya kalleta ya zare idanunsa daga kanta. Sanda tayi zurfi wajen satar qare masa kallo,shima nashi idanun suna kanta,yana jira yaga adadin gudun ruwanta. Tana latsa system din amma kuma tana jin takunsa har cikin jininta,duk taku daya da zaiyi sai taji kamar yana matse space din dake tsakaninta dashi fiye da kima,qamshinsa yana sake cika mata hanci,yana kuma tsananta bugun zuciyarta. Ga mamakinta sai taga ya wuceta,ya zarce zuwa window din dakin ya budesu sosai kaman yadda yayi a daren jiya. Ya juyo ya dawo da cikakkiyar nutsuwarsa. A hankali ya tattako zuwa gabanta,ya tsugunna saman qafafunsa idanunsa aka hannunta. Cak wuta ta dauke mata,taqi daga idanunta ta kalleshi kamar batasan da wanzuwarsa ba a gurin,yayin da zuciyarta kuma ke wani irin bugawa,qofofin hancinta kuma suna zuqo mata qamshinsa sosai fiye da kullum,dakatawa da motsa yatsunta dake saman system din tayi,tana jin kusancin sun mata yawa,tana jin kamar ya cike gurin gaba daya,tana jin kamar ko yaya tayi motsi jikkunansu suna iya taba na juna. Idanunsa sosai cikin fuskarta,yana dubanta da wani irin yanayi na sake karantar halayyarta. Jin kai izza da qi fadi,kamar ba ita bace jiya ke tsoron qanqanuwar aba irin allura ba,kamar ba ita ta suma kawai saboda ance an daura mata aure ba......kamar ba ita ta kwanta tana rusa kuka kaman jaririya ba. Duka a bayan wannan izzar akwai wadannan dabi'un na tsoro raki da sakalci a tattare da ita?. Hannunsa kawai ya shimfida yana miqa mata,taja wasu sakanni kafin ta daga kanta tana duban idanunsa. Wani irin abu ya sake sauka cikin nata idanun. Baqar rigar jikinsa ta haskashi da yawa,ta kuma haska fatarsa da yawa,tana shirin janye qwayar idanun nata ya mata nuni da alamar ta bashi hannunta,jim tadan tsaya tana tunani,ta yaya zata dora hannunta saman nashi?,to amma kuma idan bata bashi ya cire mata cannula din ba sai yaushe za'a rabata da ita?. "Idan na tashi bazan sake dawowa na zauna ba" Ya furta da zaratan idanunsan nan dake kafe a kanta. A hankali ta daga hannun nata tana miqa masa gami da sake daure fuskarta,ta kauda fuskar gefe tana hada rai kamar wadda aka yiwa dole,can qasan zuciyarta tana wani irin bugawa,tana jira taji hannunta sun sauka cikin nasa tafin hannun,saidai ga mamakinta sai tajisu saman pillow. Qaramin pillow ya sanya a tsakaninsu,wannan ya bawa hannuwanta daman zama saman pillow din,baiko taba koda fatar hannunta ba,ya soma cire plaster din a hankali. Idanunta ta runtse,yayin da kuma can qasan zuciyarta wani abu me kama da haushi ya d'arsu a ranta. Me yake nufi da ajiye hannunta saman pillow?,don ya samu daman ganin hannun nata ma cikin sauqi har haka?,ko yana zaton son hada hannu takeyi dashi?. "Wash" Bakinta ya subuce ta furta a hankali tana sake runtse idanunta saboda fara taba cannula din da yayi. Dakatawa yayi daga qoqarin zareta da yakeyi,ya daga idanunsa a hankali ya ajiye a kanta. Fuskarta tana kallon wani gurin ne daban......kai tsaye dubansa ya sauka akan dogon wuyanta daya bayyana saboda zamewar dankwalin kanta. Ragowar gashinta me sulbi wanda ko tayi parking baya kamuwa yana kwance saman farar fatar wuyanta,hakan sai sake qawata gurin sosai. Idanunsa ya janye yana lumshe idon nasa,har cikin jininsa yaji wani abu ya harba,sai ya maida dubansa a nutse kan hannun yana qarasa janye cannula din,ya kuma maida cotton wool gurin sannan ya miqe a hankali ba tare da yace komai ba ya taka a nutse ya fice bayan ya jefa cannula din cikin dust bin. A hankali ta waiwayo,idanunta suka sauka akan inda ya tashi,saidai tamkar bai tashi ba,kamar yana gurin har yanzu sanadin qamshin lallausan turarensa daya bar mata. Qaramin tsaki taja kadan tana shafa inda aka cire cannula din. MALAMI NE KO LIKITA?,ta yiwa kanta tambayar da sai gata a zahiri ta bakin shehnaz data fado parlor din. "Wannan man din naki.....MALAMI ne ko likita?,na kasa banbancewa" Cewar shehnaz hankalinta kwance tana qarasowa ciki. Idanunta ta daga ta watsa mata harara. "Da zai fita da kin tsaidashi kin tambayeshi......amsar da nakeso na sani kenan nima.....don ku kanku bakusan wanda kuka bawa d'iyar da kuka gaji da ita ba saboda bakwa sonta......ko tsafi ma yakeyi duka ba wanda ya damu da hakan don salwantar rayuwar akhnan ba komai bane". Wani irin dariya shehnaz ta saki tana kwantawa. "Allah bazai taba bawa mutumin banza kalar kwarjinin da wannan guy din yake dashi ba......na rantse idan har zan samu irinsa inaso koda ba'asan asalinsa ba......nidai an gama min komai......kin ganshi kuwa yau?" Shehnaz ta fada ta miqe tana zama sosai tana duban akhnan. "Ina kyautata zaton ya hada jini da larabaw......." "Shehnaz!.....ya isheni hakanan" Akhnan ta fada murya a kaurare,idanunta da fuskarta dukka suna nuna fushi. "Nifa sai kinyi haquri dani,bazan fasa fadin abinda na gani ba......kuma wallahi kome zaki fadi akan shi din TSINTACCIYAR MAGE NE bazan taba yarda da hakan ba.....komai nashi perfect ne,bani kadai kuma na fada ba" Shehnaz ta sake fadi tana kwanciyarta abinta ba tare data samu da yanayin akhnan ba. "Me yasa kowa yake yabonsa?,me yasa suka kasa gane cewa yana da naqasu?,me yasa suka kasa gane cewa ya gaza?......a dauke ilimin addini.....eh ta yarda yana da daidai nasa......amma kuma ilimin zamani fa daya zamana shine JIGO kuma JAGORA a idanun kowa?". "Ki shirya wasu abubuwa mana.....ki tsarawa kanki yadda kowa zai gane bai iya komai ba.....bai kuma san komai game da ilimin zamani ba......kiyita kunyatashi mana harsai ya tabbatar da cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE......har sai ya gane zaren ba kalar yadin bane" Wani qaramin murmushi ya subuce mata saman fuskarta,ta girgiza kai a hankali. Tabbas wannan itace hanya mafi sauqi da zata nuna masa TAZARAR DAKE TSAKANINSU......itace sassauqar hanyar da zata nusar da sultane kalar rashin dacewar dake tsakaninsu,wataqila ma ya hango illar da hadin auren zai haifar tsakanin DIYAR BASARAKE da malami. Wani murmushi ya sake subuce Mata.....qila ta samu mafita ne a sauqaqe,ba tare da tabi doguwar hanyar tsarin mammina ba. *M A M M I N A* Tsaye take a filin gurin ita da duk wani boyayyen hadimi nata dake mata gurbatacciyar hidima. Mutane ne dake rayuwa cikin gidan sultane suka kuma saje da bayi da hadiman gidan ba tare da sanin mutanen gidan ko nuna wata alama da zata bayyana maka akwai wani rayuwa suna da identity a jikinsu a boye ba bayan wanda ake ganinsu dashi. Tun daga wancan ranar da aka rasa almaz har zuwa yau bata kwanta tayi bacci ba,idan bacci ya dauketa to barawo ne. Tana lissafa ta yaya zata dauko tsintuwa daga wata qasar,tana riritata da zummar cin gajiyarta da alfanunta,kuma katsam kawai sai ace ta bace cikin rairayi da sahara?. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Ina me sake maimaita muku tambayar da har yanzu na kasa sanin amsarta a karan kaina da kuma ku kanku......su waye suka shigo har cikin gida suka dauki AJIYATA cikin sauqi har haka?,harda sukunin ajiye rubutacciyar takarda suka samu.....wanne irin sakaci ne da sassauci da aikinka TAMIM?" Ta jefa tambayar ga tamim wanda kiran sunansa kadai da tayi ne abinda ya dawo dashi cikin tunaninsa. Fes abinda take magana akai baiji ko ya riqe ko qwaya daya ba,don shima a yanzu a wannan qadamin mafitarsa yake nema....nasa tunanin ya karkata ga yadda zai lashi kalar ZUMAR daya tabbatar tunda uwarsa ta kawoshi duniya bai taba lasar irinta ba. Qasa yayi da kansa yana nuna girmamawa a fili,saidai badini zuciyarsa da gangar jikinsa ta fara gajiya da tattali da kuma binciken KAB'AKIN da ba'asan ranar samuwarsa ba. Kowanne shekaru watanni kwanaki da darare suna qarar dashi ne wajen shiryawa wannan lokaci,saidai a yanzu jikinsa da hasashensa suna bashi akwai wani babban qalubalen da yake tunkararsu. "Wannan ya nunamin ya kuma bani tabbacin lallai Al-saamit yana tare damu.....yana kallonmu kuma yana rayuwa damu.....indai sheikh haisam shine Al-saamit.....lallai zai ruga zuwa Ethiopia don duba mahaifinsa motii,jininsu qarfi ne dashi,sukan zabi JINI akan NASARARSU......idan kuma ba shi bane.......TO WAYE?" Tayi musu tambayar tana duban fuskokinsu daya bayan daya. Shuru ce ta kasance amsar kowa a cikinsu. Dukkaninsu kusan basa fatan sheikh haisam ya kasance wanda suke zargin,don sun sani muddin ya kasance shi dinne.....basa jin qamshin nasara a tattare dasu......kowanne FADUWA kawai yake hangowa qasa warwas a kansu,faduwar kuma tana shirin RASA RAYUKA MASU YAWA. "Ba bada kwana uku......kwana uku kawai duk inda almaz yake.....muddin yana qasar niger da maqotanta a nemoshi" Ta fadi maganar tana juyawa da sauri tana barin sansanin. "A gayawa me wada......ina buqatar ganawa da dukka bayi da hadimai dama duk wanda ke rayuwa qarqashin umarni doka da tsari maza da mata na gidannan,yaro da babba a filin taro na bayan gida.......a shaidawa sheikh haisam" Ta sake fadi wasu abubuwa suna qulluwa a zuciyarta. "Me hakan ke nufi?" Tafisu ta tambayi mammina dake takawa don komawa zuwa ga motarta. "Inason sake gwaji a kansa tafisu,har yanzu ban yarda shi din ba jinin aba jifar bane.....ban yarda shi din ba jinin ibraheem bane" Idanu tafisu ta zuba mata,kamar zatayi magana sai kuma tayi shuru,ta saki qaramin murmushi sannan a hankali tace. "Allah ya taimaki uwar dakina" Cikin nuna kambamawa da bayar da qarfin gwiwa. *MORSA SAFIYYA* Wata cikakkiyar nutsuwa ta samu a kwanakin,irin nutsuwar da ta jima rabonta da ita. Irin nutsuwar da tayi hannun riga da ita tun shekaru masu tsaho da suka shude. Shirye shirye takeyi sosai na gudanar da duk wani abu daya shafi auren D'IYA ga mahaifiyarta,shiri takeyi na gaske tamkar wadda zata aurar da yara goma. Cikin tsanaki take shirya komai,kama daga dukkan wani kayan qawata gida da diya macen da za'a aurar take buqata.....shirin gudanar da baki na alfarma,suturar da akhnan zata sanya,falaak da ita kanta. Kudaden gudanar da hidimar bikin,sabon dinki ga kowanne hadimi da bawa na gidan....sai kuma babbar shahararriyar me gyaran jikin nan data karade qasashen sudan niger mali dama sauran qasashen africa. A jikinta takejin aurar da diya zatayi kamar a karon farko,don haka gagarumin shiri takeyi silently ba tare data qara bi takan akhnan ba ko wani magana ya sake hadasu. Kawai abu daya ta sani shine.....a wannan karon zata fitowa da akhnan zafinta a duk sanda tace zata bijirewa duk wani shirye shirye nata......zata gwadawa akhnan ita din UWARTA ce da gaske,kuma ba'a sauyawa tuwo suna.....lokaci yayi da zata gwadawa mammina JINI YAFI RUWA KAURI,lokaci yayi da zata tunasar da mammina ZUMUNCIN MAHAIFA ba wani dan guntun makirci daya isa ya rabashi. Tun a yanzun ta fara aike zuwa ga kowanne dan uwa da dangi na kusa dana nesa tana shaida musu kowa ya zama cikin shirin auren diyar safeena. Abinda kawai ya rage mata jiran dawowar sultane,su tattauna idan akwai inda yake buqatar gyaran shiri sai a gyara. Bata jiran sultane don karbar ko sisi a hannunsa......tana ji cewa koda zata qarar da dukka abinda ta mallaka akan diyar safeena wannan karon bata biya koda digo daya na zumuncin safeena da halascinta ba a kansu. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 105* Tare da falaak da hairaan suke gudanar da komai,hatta kuma da falaak bata gwadawa akhnan akwai gagarumin shirin biki ba da momma din keyi ba. Abu guda daya ne kawai ya tsayewa morsa safiyya a rai. Ta yaya za'a lanqwasa akhnan a maidata MATAR AURE TA GASKE?. A nata tsarin a nata burin a kuma nata mafarkin,kaman yadda ta horar da hairaan.....har hakan ya siya mata soyayya me girma a zuciyar mijinta.... Kamar yadda ta horar da falaak kuma ta tabbatar ba zuciyar wanda ba zata mallaka ba ba tare da asiri ba......haka takeso akhnan ta kasance. Tanason akhnan tasan me ake kira da AURE......tanason akhnan tasan me ake kira da BIYAYYAR MIJI......tanason akhnan tasan sirrikan mallakar miji da sake shiga zuciyarsa.....don ta tabbatar akan AURE gaba daya akhnan din bata da sani kwata kwata. Sun zauna da hairaan sun tattauna,amma a wannan karon hairaan kanta dariya ta dinga yi. "Momma wannana aikinki ne......ke zakiyishi.....bana tunanin akwai wanda biftu zata zaunawa yayi mata wannan karatun,saidai ki dauki wannan nauyi kawai,ki koya mata ki kuma karanta mata abinda ya samu.....sauran aikin sheikh haisam ne,nauyin ya hau wuyansa........sauqinta daya maza irinsu dama hatta ga matansu malamai ne.....suna kuma zurfafa nazari da uzuri ga matansu,balle irin sheikh haisam.....tabbas zata samu rayuwa sama da duk yadda take mafarki,kuma kuma zaku sameshi sama da yadda kuke fata,ni nayi imani da wannan". Maganganun sun shigi momma,to amma a yanzun ita da bata da cikakken zama a kwanakin bata jin tana da chance,saidai ta yanke shawarara duba qwararriyar malama me hikima koda na sati daya ne su zauna da akhnan din ita saita qarashe sauran aikin. ★Takardu biyu ne suka iso gabansa da dukkaninsu suka sanya murmushi subucewa saman kyawawan labbansa. Takardar farko ta mammina ce wadda itace silar asalin murmushin nasa......takarda ta biyu kuwa daga akhnan ne. Rubutacciyar saqon gayyata zuwa bikin yaye dalibai a babbar makarantar secondary ta kwana ta 'yammata dake garin agadez. Already wannan sultane ya kirashi,sunyi magana,ya kuma nema alfarmar "Ina nemawa diyata alfarma mijinta ya rakata,itama da kanta ta buqaci hakan" Maganar ya zowa haisam a bazata,mamaki kadan ya kamashi,saidai isowar takardar gayyatar a yanzu gabansa hade da wani qaramin akwati me dauke da kayan sawa ya bashi mamaki. Yana daga zaune yayi relaxing ya sanya abdii ya dinga daga kayan daya bayan daya. Murmushi ya subuce a hankali,abinda ya sanya abdii dubansa cikin mamaki. "Ka ninkesu,ka bawa salaana" Ya fadi a taqaice kawai Yana maida hankalinsa akan aikinsa. Tsaf ya karanci inda komai ya dosa,wani abubuwan yanzun yadda suke tafiya murmushi kawai suke bashi. "Amma kamar basu qarasa kayan da kake raba musu obbo" Abdii ya fadi yana daga kayan gami da sake jujjuyasu. Kai ya daga ya kalli abdii kadan sannan ya gyada kai. "Na sani.....wannan kyauta ce kawai,ba lokaci ne na rabon sutura ba". Bai sake cewa komai ba abdii din ya ninke yana maidasu jakar,ya dauka yana ficewa. *JIMMA(Ethiopia🇪🇹)* *_Abba jifar palace_* Cikin makeken dakin da aqalla zai iya daukan kayan gado na alatu set biyar.....tafkeken bedroom dake dauke da gadaje qwaya biyu,wall wardrobe da komai set biyu da sukayi nesa da juna saboda yalwar dakin. Daga saman daya daga cikin gadajen take kwance. Saamee ce kwance rub da ciki. Manyan curtain masu nauyi tsada da alfarmar daraja da aka zagaye dakin dasu ya sanya ba wani cikakken haske a dakin,uwa uba kuma ta lullube kanta da duvet fuskarta na tsakiyar pillow. Hawaye takeyi sosai,har tana jin jijiyoyin kanta suna bugawa saboda ciwon da suka fara. Ta tsincin zancan ba tare da tasan zata jishi ba.....zancan da ya kusa sanya zuciyarta ta buga saboda fargaba da kuma tsananin razani. AUREN CAPTAIN OBBO. Idan tace ya mata kama da mafarki ma tayi qarya.....wani abune daya zame mata sama da mafarki wajen sanyata a tsananin razani da tashin hankali. Ta jima tana fargabar zuwan wannan ranar......ta jima tana tunanin yadda haisam din zaici gaba da kasancewa me sauqaqa kallonsa akan diya mace ba tare daya samu wata ta fusgi hankalinsa ba. Koda shi bai qawatu da kowacce mace ba,lallai ba shakka ta sani wataran zaa samu wadda zatayi nasarar janyeshi gareta. A jigace ta miqe tana ture bargon jikinta,sannan ta lalubi hanya zuwa toilet don rage fitsarin daya cika mata mararta,tana kuma jin zuciyarta kamar zata fashe. Daidai lokacin kyawawan 'yammatan oromo din guda biyu suka tura qofar dakin suna shigowa. Rumaisa aba jifar da kuma Aanani aba jifar. A halittar ne yawan magana......fara'a da son tsokana,har wani lokaci yayarsu KANSAA wadda ita ke bin sheikh haisam takance. "Kamar ba daga jinin aba jifar kika fito ba?" Aanani din ita da hussam su kadai ne halinsu daban,amma za'a iya cewa dukkanin yaran nanay suna da wani hali na miskilanci da jinin sarauta da sukayi gado daga bangaren nanay da motii din gaba daya. Shi yasa izzarsu ta daban ne,da gaske kuma jinin yake zagayawa a jikinsu saboda gadonshi da sukayi ta uwa da uba. Saidai kuma tasirin ilimi da tarbiyya sosai yake gwada aikinsa a kansu. Basu iya wulaqantar da d'an adam ba komai kashinsa. "Har yanzu mamaki nake yaa rumaisa.......kaman ina mafarki fa......Captain da aure?.....yaushe yaa rumaisa?......yaushe ya tsayar da idanunsa ya kalli macen har tantance tayi masa?. Yaushe dukka ta cancanta ta tsallake tulin uban tsarikansa?,yaushe ta cinye dukka wadannan jarabawar tasa?" "Aanani mana?....ahaan?,daukomin kawai na wuce,idan ya dawo kya ita tambayarsa kamar zaifi sauqin samun amsoshinnan" Rumaisa ta fadi cikin daurs girarta. Baki Aanani ta rufe da tafin hannunta tana dariya. "Koda wuqa bazan iya ba kin sani,shine zakimin turin mutuwa." Goye hannuwanta sosai rumaisa tayi a qirji tana duban Aanani din. Ta sani,tafi kowa sanin Captain sheikh din. Har yanzu tana tuna yadda ya kori abeed da salon tambayoyinsa?,wai aure ba abun wasa bane.....koda nanay tayi magana sai ya bata haquri,ya fadi mata ko shine idan ya tashi aure sai matar ta cinye tarin jarabobin da tambayoyinsa harma da gwaji. Yaaa khansaa tayi dariya sosai a sannan "Duka ban manta ba,kuma nima ina yiwa kaina wannan tambayar,amma ni dake duka wazai iya tunkararsa?. Mu tsaya kawai mu gani,lokaci zai bayyana komai" Rumaisan ta amsa mata gudun kada ta tsaidata,don hadimanta suna waje suna jiranta da zasu rakata daukan jarabawar da zatayi ayau din.. Wani dan juyi Aanani ta saki,ta dauki remote ta danna wani wani locker dake gefan gadonta ya bude kanshi da kanshi,ta qarasa tana cirowa rumaisa takardun. "Naga yaaa kansaa tazo,sun qule da nanay......nasan duka shirye shirye ne......kaman bazan iya jiran lokacin da Captain zai iso da amaryarshi ba.....inaso.inga gwanar sa'ar nan ta duniya" Ta qarasa maganan tana miqawa rumaisa takardun,saidai bayanta da taga rumaisa din tana kallo ya sanya itama ta waiwaya. Saamee ce ke takowa a hankali,hirarsu tana sake kashe mata jiki gaba daya da dukka wani hope nata. "Baki da lafiya ne saamee?" Rumaisa ta tambaya cikin kulawa. Da qyar ta iya qaqalo murmushi tana kada kai. "Lafiya lau nake....ciwon kaine,amma nasha magani,ina sanya rai zai sauka in sha Allah a kusa". Kai rumaisa ta jinjina,ba kuma don ta yarda ba " Allah ya sawwaqe" Ta fadi daidai sanda ake na'aurar dake maqale da qofar dakin kaman yadda yake a sauran dukkanin manyan dakuna na gidan take shaida musu isowar mutum da neman izinin shigowa. Haka hake a tsarin gidan,kowacce qofa saida izinin me dakin,saidai dukkanin 'ya'yan motii anyi register na finger print din kowa da sauran qofofin da suke da alaqa dasu na al'amuran yau da kullum,kai tsaye suna iya buda kowacce qofa su shiga,saidai duk da hakan idan ba dakunansu ba sukan tsaya na'aura ta shaidawa mamallakin dakin,sai idan shigar ta gaggawa ce ta taso. Sunga me neman izinin,obsa ce,daya daga cikin bayin rumaisa. Sanye da asalin tufafin da dukkan wani bawa dake qarqashin gidan sarautar aba jifar ke amfani dashi muddin macace. Tufafi ne me launin fari da aka yiwa ado me kyau da jan zare,cikakkiyar sutura da aka dinka daga zare me laushi kyau da daraja da sheikh muhammad haisam ya sanya aka samar da ita wadatacciya ga kowanne bawa da hadimi na gidan. Be yarda kowa a cikin su yayi maimaicen sutura ba,kwanaki biyar dinnan da suke sanya kalar kayan kowacce rana wami daban kake sakawa saboda tabbatar da tsaftarsu. Sannan da zarar ka gaji dasu kana iya bayarwa,zakayi magana ne kawai cikin dakin ajiya na gidan a sake baka sabo dal adadin da kake da buqata,kamar yadda ranakun alhamis da juma'a suka kasance ranakun da duka wunin zaka sanya kalar tufar da kakeso,duk da ragowae ranakun ma a iya awannin aikinka ne kawai zaka sanyasu saboda fidda tsari da cikakken tsaro na gidan,abinka da JININ hukumar binciken sirri da qwarewa ta farin kaya. Hadimai dake sashensa gaba dayansu maza ne.....tasu suturar kuma tasha banban data kowanne hadimi.na gidan,launinta da kuma tsarinta,kamar yadda girma da kimarsu a gidan fita daban dana saura. Kai tsaye ta nufi inda rumaisa ke tsaye,saidai kafin takai gwiwoyinta qasa yadda suka saba ta miqa mata takardun idanunta akan saamee din amma obsa take bawa umarni cikin tataccen yaren oromo. "Ki magana da masu bangaren clinic na gida,suzo su duba saamee....." Kai a qasa ta amsa mata tana ficewa a ladabce. "Aanani ki dinga dubata,idan da akwai wani abun ki fadiwa nanay.....Allah ya sawwaqe" Rumaisa ta furta ga saamee tana dosar qofar fita zuciyarta fal da tausayinta. Ta jima tana zato me qarfi akan saamee din ta fada tarkon son captain obbo din. Saidai ta dade tana addu'ar Allah yasa ba gaske bane,domin kuwa ita kanta da suke ciki daya ta sani,haisam din ba shakka allura ce cikin ruwa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Tana da alaqa me kyau da 'ya'yan sarakuna irinta na cikin Ethiopia dama wajenta. Wasunsu tare da ita sukayi degree dinsu,a makarantar da tayi,batasan kuma adadin wadanda har yanzu suke kamun qafan son haisam din daga gurinta ba. Abinda basu sani ba ko ita din bata iya tsaiwa suyi magana makamanciyar wannan dashi. Yana da sakewa 'yan uwansa da kuma nuna girma ta hanyar basu lokacinsa ya saurari damuwoyinsu. Amma kuma yana da tsare gida,yana kuma da wani irin kwarjini da duk yadda kaso masa wata magana idan dai har bashi ya bada qofa da fuska ba baka iyayi masa ita. Da idanu saamee ta rakasu,saita maida idanunta ta lumshe tana sakin wani numfashi me nauyi. A hankali wani sashe na zuciyarta ke tambayarta. "Anya haisam baifi qarfinki ba?,anya wutsiyar raqumi batayi nesa da qasa ba kuwa?" Iya su rumaisa kawai idan ta kalla wani lokaci zuciyarta tana yin rauni. Tana ganin girman matsayi na iko da mulki da suke dashi,saita dinga jin kamar haisam din ya mata nisan nisa....kamar haisam din yafi qarfinta,kamar haisam din ba sa'anta bane. Ajiyar zuciya ta subuce mata,ko yaushe tana jin hakan,tana kuma gayawa kanta hakan,amma ta kasa cireshi daga zuciyarta. Wacece ya aura yanzu? Tambayar da taketa nanatawa kanta tun daga wancan lokacin kawo yanzu. *N A N A Y* Cikin qawataccen setting room din daya kasance shine dakin hutawarta na shidda cikin dakunan hutawar data mallaka,zaune take saman wani ottoman me tsananin laushin da har nutsewa takeyi a ciki. Daga opposite dinta kyakkyawar mata ce da tashin farko zaka kirata da MATASHIYA. Saidai ko kadan,tsabar dukiya hutu kwanciyar hankali da kula da kaine zai sanya ka dauka shekarun nata kadanne. Wani irin salon kula da kai da jiki ta hanyar tsara cima me kyau da itatuwa da suka koya daga UWA TA GARI wato khadeeja yunnus jallata(nanay). Hansaa kenan da suke kiranta da khansaa......itace 'ya ta biyu a gurin ibraheem aba jifar da kuma khadeeja yunnus jallata bayan yaronsu na farko daya rasu. Yaya ce ga haisam,wanda shi ya biyota sai NUDRA kuma ta biyo haisam din,amma dukka ya hadiyesu ya zama Kamar shine yayansu gaba daya. Lullube jikinta yake da wata lafiyayyar laffaya milk color daya kusa sajewa da kyakkyawar fatar nan dake kwance lumui. Idanunta akan nanay,murmushin nan irin nasu dake nuna zallar nutsuwa take jifan nanay dashi "Da gaske nanay,har yanzu mamaki yaqi sakata.....da gaske sheikh dinmu ne ya zabi mace?,da gaske sheikh dinmu ne yau ya zama me aure.....nanay idan ana maimaita maganan saina dinga ji kamar za'a dawo ace bashi bane abdii ne" Ta qarashe maganan da qaramar dariyar da zata tabbatar maka ra gaske take maganartan. Murmushi nanay din ta sauke,har abada dai girma baya taba nunawa ga mutumin da yake da iyaye a raye,komai girmansa saiya taba wani aby na quruciya. Ita kanta banda waya da sukayi dashi ta samu tabbaci daga gareshi ta dade tana juya abin,saidai har yanzu bata zauna sunyi wani cikakken magana akan auren ba. Motii ya mata daidai bayanin da ita ta gamsu,abu daya ta yarda dashi,aure dai ko ya yake aure ne,kuma alqawari ne wannan zata yiwa DANTA mafi soyuwa a ranta duk wani abu daya dace uwa tayi a al'ada da kuma addini,zata kuma tayashi karbar duk kalar macen da yazo da ita,duk da abun yazo ba zata,ga saamee da tausayinta yake maqale a ranta. Kafin takai ga cewa komai sallamar Aanani ya katse maganan. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 106* Idanun nanay a kanta tana duban nanay din sanda take qarasowa cikin yaren oromo dinnan da yake kama da yaren fullanci. "Don Allah nanay kiwa yaa hussam magana magana mana.....ya barni na fita ni kadai.....kawai karbowa zanyi na dawo" Ta furta a shagwabe kamar noorah auta ke magana. "Bazaiyuwu ba Aanani,kin manta da dokar haisam ne?,ko har kin manta da abinda ya faru kwana biyar kawai daya wuce?.....dukka ice cream da kalar madarar da muke dasu don kawai ba flavours din da kikeso sai kice saikin fita da kanki?,kuma ke daya?,ba hadimai ba kowa?". Jikin Aanani din ya danyi sanyi,tana tuna tashin hankalin da suka shiga a sannan,har ana tunanin cikin motii din ko Aarif an rasa wani,amma cikin taimakon Allah dukka aka shigo dasu guda s raye cikin kuma qoshin lafiya,saidan bubbugewar da ba za'a rasa ba. "Ba suna delivery ba?" Hansaa ta katse maganar tana duban Aanani din. "Kiwa abla magana ko ke magana dasu su kawo miki" Ta fadi tana wurga mata key. Da farinciki tabi key din ta dauka,tasan key din meye,aljihun motarta ne da take ajiyar kudin,tunda yaa hansaa din tayi mata haka,hakan yana nufin kona nawa ne ta dauka a siya,saita juya tana duban qaramin gadon yara da aka kawoshi aka ajiye musamman daga gefansu saboda zuwan hansaa din. Kyakkyawar yarinya ce kwance a ciki,wadda fatarta gaba daya taqi biyo kalar fatar qabilarsu. Fara ce tas 'yar kululluba,baccinta take haiqan hankali kwance,kaman tasan tana qarqashin kyakkyawan tsaro cikin iyali masu girman daraja aba jifar Royal blood. "Allah ya rayaki housanna" Tana dan gwalo wa hansaa. Bata bi ta kanta ba,don indai Aanani ce zaka gaji,uwa uba kuma maganansu da nanay yanzu yafi daukan hankalinta kan yadda zasu shirya komai. Duk da basu da tabbacin lokacin isowar haisam din,amma ta sani,ko a yau ta cewa haisam din ya iso Ethiopia to komai dare zai iso. Dawowar anani yasa hansaa zuba mata harara "Afwan yaaa hansaa.....nanay saamee fa bataji dadi ba,amma yaaa rumaisa tasa an kira clinic su dubata". Motsa fuska Nanay tayi tana dubanta. " Me yasa batayi magana ba kuma?" "Tace da sauqi ne". " Ki biya ta gurinta ki tabbatar kinbar wasu hadiman a gurinta kafin na shigo". "An gama" Tace da nanay tana sake ficewa. Fuskarta da damuwa sosai take kallon hansaa,wadda rashin 'yan uwanta biyu ya sanya ta zame mata itace aminiyarta(kamar yadda hairaan ta zama aminiyar morsa safiyya). "Kinji maganan da nakeson miki.....yarinyar nan tana shan wahala saboda muhammad.....anya bazan sanya motii ya daura auren nan ba idan yaso ya riqesu gaba daya,zai fara sonta idan har ta zama mallakinsa,kuma na sani,koda baya son saamee bazai cutar da ita ba,bazai kuma mata rashin adalci ba" Tayi maganan da damuwa sosai. Idanu hansaa ta fidda tana kallon nanay. "Nanay.....ki rufa mana asiri......muhammad din da ban taba tsammanin zaiyi aure da quruciyarsa ba?,fada miki ne fa ban taba yi ba,saboda kada na tada miki hankali. Munsha hira dashi,duk kuma da bata da tsaho sosai amma na fahimci ya saka aikinsa gaba da komai. A yadda na fahimci muhammad koda zaiyi aure ba yanzu a nan kusa ba. Tsarin matar da yake muradi kuma daban take da namu tunanin.....bance kada ki masa maganan saamee ba.....amma karki matsa,karkuma ki bayar da abun ta fuskar umarni. A fara samun fahimtar juna ma tsakanin su tukunna,komai da zai biyo baya me sauqi ne" Kai nanay ke gyadawa,ita din macace me fahimta,bata da tsauri sam ko matsantawa akan komai ma. "Na fahimceki hansaa" "Ki addu'a diyar mutane guda dayan nan ma ta samu cikakken lokacinsa" Hansaa ta fada tana murmushi,sai nanay dinma ta saki murmushin. *A G A D E Z P A L A C E* Umarnin giwa a masarautar kadan ya rage yayi daidai da dukkanin wani umarni da sultane zai bayar,wannan ya sanya gurin da mammina ta ayyana saboda halartar taron ya zama a cike maqil. Isowarta gurin ya sanya shuru ya wanzu a gurin,a daidai lokacin da haisam ke kwance cikin sofa a parlor din gidansa,yana kuma saurare da kallon komai kamar a gabansa yake faruwa. Cikin nuna tsananin izzarta ta qaraso gurin,ta kuma zauna a kebantaccen gurin da aka tanada saboda ita idanunta d'ai d'ai akan kowa. Taji mamaki sosai cikin ranta na rashin samum ganin haisam a gurin,ranta ya wani sosu,wanda shi dake zaune daga parlor dinsa yana kallon komai ya fahimci ya kuma raya daya daga cikin abinda ya sosa ranta. Sallama tayi musu,saidai ita dimma cikin izza,dukkaninsu suka hada baki don amsawa kafin shuru ya sake biyo baya. Koda bata ce komai ba sun sani,bayyanar giwa a yanayi irin wannan da kowa zai samu daman ganinta kai tsaye ba qaramin muhimmi bane "Ku saurareni da kyau.....gajeran saqo ne amma mai matuqar muhimmanci" Maganar ta ratsa shurun gurin,kowa kuma yana sake bata hankalinsa da wani irin yanayi. "A yau ba muna fuskantar barazanar b'arayi bane.....ko wani qaramin laifi....a yau babbar barazana ce ta shigo cikin agadez,ta kuma riskemu har cikin masarautarmu" Sake yin shuru tayi tana aje numfashi gami da duban fuskar kowa don fuskantar yadda maganar ta ratsasu. "Bama fuskantar maqiyi na fili,boyayyen maqiyi ne wannan wanda ya shigo cikinmu ba tare da mun lura ba" "Baqo ne" "Me hatsarin gaske" "Mai nutsuwa fiye da DIYOYIN CIKIN GIDAN NAN" Ta fada qirjinta yana nuna nauyin abinda take dauke dashi. Miqewa tayi tsaye tana dubansu da kyau gami da matsowa gaba sosai. "Ya zama dole kowa ya lura ya maida hankalinsa.....saboda babbar barazana ce da zata iya shafar kowa.....ciki kuwa hardani mata ga sarki ba lallai na tsira ba". Sosai maganan ta kada kowa,don sai da yawancinsu suka daga kai suna kallonta. Maganan ya musu girma sosai,tunda indai har ita giwa bata tsira ba?,to waye yake ta batunsu?. "Qwarai kuwa.....kada ku yarda da shuru......kada ku yarda da murmushi......wanda yafiyin shuru shine yafi sanin abinda yakeyi" Ta sakeyin magana tana ci gaba da dubansu. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Aiki ne yanzu akan kowa.....aiki ne da ba'a daukewa kowa ba.....dole kowa ya sanya idanu akan kowa.....ba wanda aka yarda dashi a yanzu. Dole kowa ya sanya idanu ga tsaron masarauta. Kome muqamin mutum idan har ka karanci wani abu na rashin yarda a tattare dashi to kayi gaggawar sanarwa.....karku nuna kun ganshi...ku barshi yayi tunanin shine yayi nasara.....domin wanda yafi wayo shine wanda yabar maqiyinsa ya bayyana kansa" Kalamanta na qarshe suka sakashi sakin murmushi,don yana jin a ransa kalamaine da suke aiki tsakanin shi da ita,sai ya zare device din kunnensa,ya kuma kashe system din. Iya wannan kawai da yaji.....iya wannan kawai daya gani ya isar masa. Tabbas yayi nasarar dasa tsoro me girma a zuciyar mammina....ya sani,ya saka zargi da hasashe gami da rudewar lissafi me yawa a tattare da ita. Da gaske hakanne,don kuwa ko bayan rufe taron ta bada umarnin a maida qofar shiga da fita daga gidan guda daya. Tana zaton wannan ce kawai kyakkyawar hanyar da zata bata wani kaifi da hange akan komai. Tsananin tashin hankali takeji a ranta a duk sanda ta tuna AN DAUKE ALMAZ. Almaz qarfinta ne,kuma wani mahadin sirrinta. Ta tayar da nemansa da wani salo a boye,don ta tabbatar zaman almaz a hannunsu barazana ce me girma a tattare da ita. ★★★★Sake tsaiwa tayi gaban babban madubin da birra ta ajiye mata kamar ko yaushe. Sosai take sake duban kanta,ita kanta shigar tayi mata wani irin kyau. Ta jima rabon da tayi ado irin wannan,saidai hakan ba yana nufin ta saki wannan muguwar tsaftar da qamshin dake tattare da rayuwarta ba. Ta motsa kadan tana saka takalmin qafarta buhaina ta nemi izni ta shigo dauke da wayarta dake ruri. "Allah ya taimakeki sultane ne yake kira". Kyawawan idanunta da aka zizarawa baqin kwalli wanda yasa suka qara haske da kyau ta daga,sannan ta miqawa buhaina din hannu tana karbar wayar,ta taka a hankali ta koma saman sofabed ta zauna,sai dukkaninsu suka juya suka fice saboda bata daman amsa wayar sultane din. Wannan cikakkiyar sallamar tasa,da wannan muryar tasa da ita kadai ta isa ta gaya maka farincikin da zuciyasa take ciki. Idanunta ta lumshe kadan,har ga Allah tanason wannan walwalar ta sultane,har ga Allah tana jin dadij yadda kulawarsa da nuna qaunarsa da dukka suka dawo a kanta,amma tana jin haushi idan ta tuna dukka hakan ya faru ne ta sanadin malamin.....tana jin wani qunci idan ta tuna anya zata iya jurar auren bare farincikin sultane ya dawwama?. Saidai wani sashen na zuciyarta yana gaya mata farincikin sultane din gaba yake da komai a wajenta. Cikin girmamawar da duk duniya shi daya yake iya samunta cikakkiya kamar haka ta gaidashi,ya amsa mata kuma cikin kulawa. "Kun fita ne biftun bappi?" Ya kirata da wani suna can da yake kiranta,sunan da take matuqar so amma abubuwa daketa faruwa suka rabata da jin sunan daga bakinsa. Dan murmushi ta saki kadan,tunda ta shaida masa tare takeso suje gurin bisa rakiyar haisam ta fahimci walwalarsa da komai nasa ya qaru. Ta tabbatar inda yasan abinda ke shimfide a ranta bazai tana goya masa bayan ya bita ba . Itakam a yau.....tun a yanzu tanason tantance masa TAZARAR DAKE TSAKANINSU.....tanason ya gane cewa ruwa ba sa'an kwando bane. "Yanzun nan zan fita bappi" Ta amsa masa da lallausar muryar nan da ko yaushe take sake bayyana qasaitarta. Kai ya gyada kamar yana ganinta "Ma sha Allah biftu....ma sha Allah,don Allah biftu,kibi mijinki,ba wani sauran buri yanzu a duniya irin na ganki qarqashin mijinki. Ko yaya ki daure ki dauki halin safeena.....har yanzu inajin ciwon rashinta,har yanzu ban maida madadinta ba,ta mutu tana biyayya ga mijinta,safeena ta sadaukarmin da komai,harda rayuwarta" Ya fada da wani sanyi a muryarsa. Numfashi sosai taja ta sauke,har ga Allah wannan soyayyar ta sultane da mamminta tana burgeta. Tsahon shekaru komai bai sauyashi ba?,komai bai sauya zuciyarsa ba?. Yaushe?,a ina?,kuma ta yaya ma zata zamu miji irin bappinta?. A tare dashi kadai take ganin irin soyayyar dake burgeta,a tare dashi kawai take ganin kalar soyayyar da takeso namiji yay mata,amma kuma bata tunanin AKWAI KAMAR BAPPINTA.....babu kamarsa shi daya ne tak!,safeena har yanzu itace akan gaba a zuciyarsa,duk da cewa ya samu jininta ta qut da qut. Macen data samu miji kamar bappinta.....ya cancani kowanne soyayya a bashi....amma nata fa?. Malamin da baisan komai ba.....malamin da wataqila koda cikakken sunansa bazai iya rubutawa,don itakam bataga alamu ba. Tana mamakin yadda kowa ya gaza fahimtarta,abu daya ta sani shine KYANSA da suke kodawa.....wanda ta tabbatar shi ya rufe musu ido a kansa. Tasha nanatawa kanta BA KOWANNE ABU ME KYAU BANE yake da qarko da ingancin daya isa ya tsaya a kowanne gurbi da muhalli ba. ZAKI take nema.....jarumin namijin da zai iya tsaiwa ya qalubalancin duniya saboda ita,karantar ba zata samu haka ba ya sanya tayi condemning mazan gaba daya......taga kuma ba wanda ya cancanta ya sameta sam. "Kina jina biftu?" Kai ta gyada a hankali "Inaji bappi.....in sha Allah" "Allah yayi miki albarka" Ya maimaita har sau uku tare da qarin wasu addu'o'in. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 107* *_Assalamu alaikum warahmatullah_* *_Kina neman inda zaki saki samu TSALA TSALAN backpack/school bags masu kyau inganci da rahusa?_* *_To huguma na muku promo nasu,akan farashin 9k da 7500_* *_Free delivery free waybill idan har sunkai pieces shida zuwa sama_* *_Direct zan miki refund idan sukazo hannunki basu miki ba,foreign ne sabbi dal_* *_Akwai Abun hannu(bracelet)na gayu,unique one shima akan farashin promo,6pcs 2above free delivery free waybill_* *_Ba iya wannan kayan suke available a qasa ba,akwai soft tops da shorts/lounge wears/short gowns sababbi dal na musamman_* *_zaki iya magana dani kai tsaye koki tuntubeni a wannan number wayar_* 08187255862 ____________________________ Shuru tayi tana jin muryar sultane da addu'o'insa cikin kanta,wani irin dadi sautin yake mata cikin kwanya,da yawan addu'ar data samu a yau din,saidai kuma tana tuna SABODA WAYE yayi addu'o'in gaba daya sai komai ya dagule mata,taja qaramin tsaki tana miqewa a hankali gami da duba lokaci. D'ai d'ai take taku da wani irin kyau da kayan suka mata. Wine color gown ce wadda ta dace da qirarta da kuma jikinta,shigarta na nuna zallar zamani.....sarauta gogayya a ilimin zamani qasaita da kuma wayewa. Duk inda ka kalleta sau daya idan tayi ado zakasan cewa KWALLIYA tazo gidanta,saidai hakan bai hanata lullube kanta ko yafa madaidaicin mayafin da zai lullube qirjinta zuwa mazaunanta ba,wanda ko ba'a gaya mata ba,ko ba'a mata fada a kansu ba tasan Allah ya albarkaceta dasu,wanda sau tari a yanayin slim body dinta ba zaka dauka tana da ajiyayyun kaya irin haka ba. Cak mammina ta dakata daga takowar da takeyi xuwa sassan akhnan din saboda hango fitowarta. Idanunta ya sake sauka sosai akan akhnan din,wani abu me tsananin tsini da zafi ya sauka saman zuciyarta. Ba abinda take hangowa sai SAFEENA a tattare da ita,wannan sassanyan kyan na safeena daya xame mata barazana a dukka gidajen da tasha buri da alwashin rayuwa a cikinsu,ta qwace mata mazan da sukafi dukkan mazan data aura dacewa da ita,mazan da bata kawo rabuwa dasu a kusa ba. Wannan kyan dai data tabbatar yana daya daga cikin abinds ya qara tumbatsa farinjinin akhnan din da qarin izzar da takeji. Gaskiya ne.....ba qarya tana da wani irin kyau da sai an tara mata masu yawa kafin a samo kamarta,amma a nata gurin wannan kyan daidai yake da DAFIN MACIJI. Gefen zuciyarta kadan ta matsa tana saurare. Mamakin inda zata je?,har ta kammala shiryawa kuma ba tare data sani ba. A baya kome akhnan din zatayi,ko ina zataje ita take fara shaidawa.....da ita take fara shawara,sai abinda ta yanke,amma yanzun har ankai matsayin da akhnan din zata dinga zartarwa da kanta?. Bata lura da mammina ba,har sai data kusa da inda take tsaye sannan. Idanunsu suka hadu guri daya,mammina ta sauke mata wannan murmushin,yayin da akhnan ta janye idanunta daga kanta cikin salon wannan miskilancin basarwar da qasaitar da yake iya gwadawa kowa shi. Duk sanda zataga mammina din sai taji wani abu me ciwo ya motsa a ranta,takanji a ranta,zuciyarta kuma na raya mata itace sila. Inda ace ta zaba mata namijin daya dace da haiba da kamalarta,da tuni yanzun wani zancan ake ba wannan ba......amma ta dauko mutumin da sam bai dace da basarakiyar mace irinta ba,ya dagula komai,ya dawo lissafi baya,ya gwamutsa mata qaddara da amsa sunan MATAR MALAMI. Wani irin zafi mammina taji a ranta,ba kallo kawai ba,koda motsin yatsar akhnan kadai tana iya fassarashi......motsin yatsar akhnan kawai tana iya fadin ME TAKE NUFI?,ME YAKE DAMUNTA?,MEYE A ZUCIYARTA? ballantana kallo da wannan blue eyes din nata masu kama da idanun safeena sak. Hakan bai kassarata ba.....bai karya mata gwiwa ba,bai kuma hanata furta. "Maraba da d'iyata,.....sai ina kuma?" Kaman ba zata amsa mata ba haka ta gotata a hankali,kafin ta motsa labbanta da lip gloss ya yiwa wani irin kyau me daukan hankali. "Zan fara gwada tawa sa'ar" Ta amsa mata a taqaice tana yin gaba. Bata gane sam inda maganar ta dosa ba,amma tana jin ba zata bar yarinyar haka ba,saita tako bayanta tana fadin. "Wacce irin sa'a akhnan?.....wacce sa'a kike nema ke da kika mallaki uwa irin ZAITUNA?". Taji murmushi iya qasan ranta,duk da yadda zuciyarta ke quna,ta lumshe kyawawan idanunta da sukayi kama da wadda ta saka eyelashes. " A yanzu na gane kuskure ne dogara da mutum daya....ko yaya a rayuwa ya kamata ka koyi yanke wasu hukunce hukunce akan qashin kanka.....don kaine shiga a rayuwarka.....kaine CEO na kanka da kanka" Wani irin duka maganar akhnan din tayi mata duka bana wasa ba. Ta sani....tana da dabi'ar fadin magana kai tsaye......tana da hali na gaza boye abinda yake zuciyarta wanda ya mata dadi dama wanda bai mata ba,sau tari furta wasu abubuwan miskilanci ne kawai yake hanata,amma idan ta tashi furtawa zata furta gaba daya ne. Wannan bai sanya tayi zaton akhnan din zata bata amsa kai tsaye irin haka ba,saidai mamakinta ya cakude da wani abu na daban sanda ta hangi haisam gurin parking lot na musamman na gidan. Lafiyayyen yadin cashmere me asalin tsadar ne a jikinsa baqi,wanda aka yiwa dinkin kufta riga da wando sai wata riga ta musamman da ake dorawa a sama wadda ke kama da cloak thobe din da yake amfani da ita. Duhun yadin yayi wani masifar haskaka farar fatarsa.....kamar dai ranar daya shigo mata sanye da baqar jubah a jikinsa,saidai a yau din hular dara ce a kansa wine color data dace da wine color fij half shoe din qafarsa. Wani irin ajiyayyen kyau yayi,karon farko daya soma saka sutura da dinki irin na mutanen nigeria dama niger din. Fuskar nan tasa wani irin kwantaccen kyau da kwarjini ne yake tashi,yana tsaye kusa da wasu hadimai yana sanya hannu kan littafin report din aikinsu don zasu shiga hutun kwana bibbiyun daya raba wasu zasu karbesu,saboda bawa kowa daman yin rayuwa bisa sakewa bawai ka qare a bakin aiki ba. Zuba masa idanu tayi a hankali tana takawa xuwa inda ta sanya aka shirya motocin da zasu fita ciki. A hankali kamar da gayya iska ta soma kwaso wannan fitinannen qamshin nasa tana aikewa dashi zuwa ga qofofin hancinta. Karon farko da taga irin shigar ta kwanta jikin matashi tayi ladabi har fiye da yadda ake buqata. Ba murmushi yake ba,amma wani sakakkiyar fuska ce yau kwance a fuskar tasa sanda yake magana da hadiman. Magana suke me dadi da alama,don dukkaninsu sun rusuna suna sauraronsa,basu miqe sun gwada tsaho dashi ba,hakanan basu zube a qasa ba kamar yadda ya hanasu yin hakan,yace qasqantar da kaine. Littafin ya miqa musu,ya kuma juya da nufin takawa ya koma bakin motocin abdii yana biye dashi. Wani mahaukacin bugawa zuciyar mammina taji tayi,a yau kawai tana ganin wani abu tattare dashi. Shugaba take hanga kuma jagora bawai gama garin malami ba. Shigar ba abinda ta tuna mata dashi sai shigar tufafin manyan malamai daga Nigeria da niger sukeyi,musamman qasaitattun malaman da suka hada karantarwa da kasuwanci. Takunsa kadai ya ajiye mata wata qatotuwar ayar tambaya. IZZA DA QASAITA kawai take hanga muraran a cikin takunsa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Ta bangaren akhnan itama takun nasa ne abu na farko daya fara janye hankalinta duk da ya juya baya bayan ta gama samun tabbacin ba suturarta bace a jikinsa......ba suturar data saka kudade masu yawa ta siya masa bace ya sanya. Ta lumshe idanunta tana budesu mamaki yana sake saukar mata,mamakin inda ya samu nau'in sutura data dace da al'adar qasar dama qasashen kusa dasu. Zuciyarta ta quntata guri daya,tana sake amanna da kalar girman kansa,karo na farko data fara kyauta aka wofantar da hannuwanta. Tana iya tuna samarin da suka dinga zuwa neman aurenta,duk cikinsu ba wanda sunansa bai zama fitacce a agadez ba......ba wanda bata hada da kyauta me nauyi ba a sanda zai koma zuwa ga ahalinsa don yaje musu da shaidar zuwansa agadez......amma a yau din,shi da yake malamin da bai da wata sana'a qwaqwara guda daya ya ture kyautar tufafin data masa?. Idanunta ta ware a hankali cikin bacin rai tana duban takunsa,wata nutsatsiyar tafiya me nuna kuzari da kamewa,sai kace toron mai cikakken iko cikin dajinsa. Kamar idanu yakeji a jikinsa,saidai hakan bai sanyashi waiwayawa ba har ya iso bakin daya daga cikin motar yana sauraren driver din da me wada yace sultane ya bada izini ya jagoranci tafiyar,ya tsaya jikin motar yana kuma juyawa cikin hikima a nutse zuwa ga bayansa. Da wani irin mugun hanzari ta kwashe idanunta daga kansa,qirjinta yana wani irin bugawa. Ba zata taba yafewa kanta ba muddin ta bari ya kamata tana kallonsa. Ba zata taba yiwa kanta afuwa ba muddin ya zamana yaga idanunta a kansa. Wai meye ma abinda yaja idanunta gurin qarewa shigarsa kallo?. Sai taja siririn tsaki tana sake shimfida wannan miskilancin saman fuskarta. Qasan ranta wasai takejin kanta,duk da bacin ran qin saka tufafin data aike masa dashi,don kuwa tabbas tun a yau zata sanyashi ya fara danasani da karbarta a matsayin matarsa.....bayan banda kyau batasan wani abu na daban da zaiyi tutiya ko ya nunawa kowa ba. Fes idanunsa ya sauka a kanta. Tana takowa cikin jin tata izzar da isar. Idanunsa ya lumshe a kanta ya kuma bude,yayi hakan har sau biyu waiko zaiji bugun da zuciyarsa keyi zata daidaita,hakanan fitar numfashinsa da yakeji ta masa nauyi ko zai koma daidai shima. Zuciyarsa fayau take a kanta,saidai can qasan zuciyarsa wani irin qunci yakeji da takura me yawan gaske daga kallon fuskarta wanda shi kansa baisan dalili ba. Idanunsa ya janye yana furzar da iska daga bakinsa waiko hakan zai sanya yaji sanyi ko ya samu daidaito akan abinda yakejin din,saidai hakanma ba abinda ya rage sai qara masa wani yanayi na takura da quncin zuciya da yayi. "Me yasa?" Ya tambayi kansa da kansa. Wani yanayi na kishi yakeji,kishin daya d'ara yadda yakeji akan rumaisa da Aanani da noorah. Me yasa zaiji haka a kanta bayan ita din bata cikin jerin sahun dukka wadannan da zuciyarsa ta lissafa masa?. "Martabar aure" Zuciyarsa ta amsa masa. Ya yadda da wannan amsar.....martabar aurensa a kanta yafi gaban komai.....martabar aurensa yafi gaban ya bari ta fita da duk shigar data mata. Ya sani tun asali,yana da kishi koda ba'a akan abinda yakeso bane.....ya sake tabbatar da haka a kanta. Ba so koda na wasa nata a zuciyarsa......amma zafin da yakeji a yanzu ya tabbatar yana tuna cewa duk wanda ya kalleta abinda zai fara fadi shine.....zai dangantata da kansa.......zaice matar HAISAM ce.....shi kuwa sunan MATAR HAISAM wani abune da bazai bari ya tozarta ko ya wulaqanta ba koda kuwa auren wasan yara ne a kansa. Tana takowa zuciyarta na mata zafi,yadda ya dauke idanunsa ya maida wani sashe kamar baisan Allah yayi da wanzuwarta a gurin ba. Ta dade da fassara hakan da sunan GIRMAN KAI,ta dade da bawa wannan dabi'a tasa suna da JIN KAI IZZA DA FADIN RAI. Qaramin tsakin da ba wanda zaiji ta saki,taci gaba da takowa har zuwa bakin qofar motar. "Koma ki canza wannan shigar" Ya fadi a taqaice da wata tattausar murya daba wanda zaiji daga shi sai ita,don hatta da birra kwarjininsa ya cikata,ta gaza qarasowa har bakin motar yiwa uwar dakinta rakiya kaman yadda ta saba. Cak ta dakata daga takawar da takeyi,mamaki ya cika fuskarta sosai. Ta zube masa duka blue eyes dinta,saidai bata samu daman kallon fuskarsa sosai ba,don ya karkatar da ita yana kallon gefensu,sai kwa tacciyar sassauqar qasumbarsa mara cika da yawa data zama wai adon girma akan kyakkyawar fuskarsa data samu gani da kyau. Hasken ranar daya fito bame kashe idanu ba yana sake bayyana qyallin da takeyi,irin qyallin da zai baka tabbacin tsafta kulawa da kudaden da takeci kawai don a gyarata. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 108* Da wani irin salo ya bata umarni,salon da ko sultane ba zata iya tuna yaushe da yaushe ya mata magana dasu ba. Idan hani ne ko umarni sultane yakan fadi mata dalilinsa ne na hani ko umarnin bawai iya umarni ko hanin tsurarsu ba. To amma shi fa?,yana bata umarnin ne kai tsaye,ba kuma alamun sassauci daga fuskarsa da yanayin maganarsa,sai tayi tsaye tana ci gaba da zuba masa idanu tana son ganin adadin zarrarsa. Shurunta ya gama saqa masa komai game da ita,cikin kamewar nan....cikin kwarjinin nan nasa ya waiwayo a nutse yana zube mata idanunsa,waiwayowar data bata cikakken daman ganin fuskarsa tarwai. A hankali taji wani abu yana shiga jikinta ta cikin idanunsa.....wani uba kwarjini da bata taba ganin irinsa ba ya soma tsintsinka duk wani kafiya da takeji a tare da ita. Jikinta gaba daya ya amsa,wani irin weakness ya fara qoqarin mamayarta,saidai ta kori hakan ta hanyar janye dubanta daga kansa tana maidawa ga motar gami da daga qafafunta. "Zan zabi duk shigar data dace dani.....zan kuma ci gaba da saka duk tufafin da suka kasance zabi na" Ta fadi tana ci gaba da takawa. Bawai don tana qwarin gwiwa da gaske bane....bawai don zuciyarta ta daina bugawa da dukka maganar data fito daga bakinta bane....aah dukka tayi haka ne don kada ta fado,dukka tayi hakanne don kada ta bashi dama ya juyata. "Kada ki kuskura ki gwada iyakar da bakisan inda zata qare ba.....karki dauka qauna da kulawa ta sanya duban natsayin shigarki.....bana buqatar sani ko tantance zabinki.....zabinki naki ne.....amma mutuncinki amanar Allah ce". Ya qarashe fada da wani irin nutsuwa me sanyi data sauke maganarsa a hankalin tamakar saukar sassanyan ruwa daga sama. Wani irin tsaiwa cak maganarsa ta mata a cikin kanta. Kalmar MUTUNCI tana mata nauyi da yawa....wannan ya sanya koda wasa bata taba sanya wajen sanya suturar da ba zata fidda wani sashe na jikinta ba. Bata ko yarda sun hada idanu ba sanda yake juyawa a nutse tana takawa tana kuma komawa hanyar data fito,wata zuciyar na qalubalantarta "Akan me zaki koma?" Wani sashe na zuciyarta kuma yana karanta mata MUTUNCINKI DA DARAJARKI gwara ki sauya,kada ma ya dauka ko yayi tunanin don ki burgeshi ne kika canza din. Daga inda mammina ke tsaye kuwa,tana karantar komai,zuciyarta kuma tana mata hasashen komai.....saidai wani irin zafi firgici da qarin tsoro ne suke sake mamayeta. Bayan firgicin da take ciki,na yau ko gobe?,a ina zaa samu almaz?. Waye HAISAM DIN?. D'a ne ga ibraheem?,ko kuma ba shine al-saamit ba. Sunan da idan ta kwanta duk dare yake cika mata kunnuwa da qirji,sunan da idan ta runtse idanunta shi take gani a rubuce cikin inuwar idanuwanta. Matsowa birra tayi don tayata zare kayan,zuciyar birran cike da mamakin uwar gijiyartata. A tarihinta bata taba fita wani abu ko wani ya dawo da ita ba.....kaman yadda ba'a taba tsaidata ba ko ta rushe plan dinta saboda wani ko wata ba,sai gashi yau itace da dawowa harda canza shiga?,to me ya faru haka?. Matsowa tayi donta tayata,amma saita dakatar da ita,ta mata alamu data debo wasu kayan. Cak birra ta tsaya cikin closet din,tana qarewa tarin tulin suturun dake jibge a gurin kallo. Tana da experience na zabar mata kayan da zata sanya,shi yasa tafi kusa da kusa da ita a duk sanda zata shirya din. Tunani ya fado daga wani sashe na zuciyarta,a yanzu uwar dakin nasu MATAR AURE CE.....matar auren ma ta kamilin sheikh irin sheikh muhammad haisam din,to meye yafi dacewa da ita?. Juyawa tayi don sake duba wani sashen kayan,idanunta suka fada kan sashen da lafayas dinta suke. Tuli masu yawan da aqalla sun tasamma guda talatin,saidai bata taba gwada saka ko qwaya guda ba. Duk sanda zata gwada dauko mata zatace ta maida,amma a yau din saita samu kanta da dauko mata ita,saidai kuma riga ta dauko mata long sleeve da straight skirt na long sleeve shirt din da zata bata daman samun sakewa ta fito daga gurin. Idanu kawai akhnan ta zubawa birra har ajiye kayan. "Allah ya taimakeki,ki gwada wannan" Shuru kawai tayi tana dubanta,zuciyarta tana rabuwa kaso biyu. Yanason ya tauyeta ne?.....tun a lokaci na farko xai fara juya akalar rayuwarta?. Ashe hasashenta akan naqasu game da cikakken ikon mace idan tayi aure ba kuskure a ciki?. "Damuwar me zakiyi?,kwana nawa ne komai yazo qarshe?" Ta fada kanta,saita sassauta yanayinta tana karban riga da skirt din,birra ta kauce mata ta sanya sannan ta dawo ta fara nada mata lafayar. "Ma sha Allah.....tabarakarrahman" Birra ta samu kanta da yin abinda bata taba yi ba wato koda uwar gijiyartata. Tana da baiwar kyau da ake kira da kyau,kowacce shiga idan tayin tana mata kyau,amma saidai ta koda hakan cikin ranta. Ba yau ta fara yin kyau me sanyi haka ba,saidai a yau din birra sai taga ta qara wani haiba da kwarjini,sannan a yau din ta sake zama wata BABBAR MACE. Taji gamsuwa da abinda zuciyarta ta gaya mata AURE girma da martabarsa shine ya lullube akhnan din a wannan lokaci. Wannan ba akhnan din kwanakin baya bace....wannan din wata akhnan ce da aka lullubawa igiyoyi masu daraja....igiyoyin kamilin mutum irin haisam din. Sau biyu tana kallon kanta cike da mamakin yadda shigar ta karbeta,dama zata mata kyau har haka bata taba gwadawa ba?. Ko sanda take takawa tana komawa gurin ta dauka ba zata iya tafiya da ita ba.....sai gashi tana tafiyar tana kuma jinta SAFE saboda yadda a jikinta takejin ko ina nata.....komai nata ya rufu ba kaman dazu ba. A hankali mammina ta waiwaya zuwa ga akhnan dake sake fitowa cikin sauyin suturar daxu. Wani abu ya samu kyakkyawan mazauni a qirjinta,tsoronta kuma ya zarta na baya. Tsoron SARRAFAWA kada ya zamana ya fara samun power na sarrafa akhnan din?. "Kada ki yarda ki rasa ikonki....kada ki yarda ki rasa izzarki,kina da cikakken iko har yanzu......auren YARJEJENIYA ne me cike da 'yanci" Abinda mammina tace da ita kenan sanda zata sake giftawa tana saukewa akhnan din murmushi. Dubanta kawai tayi,batace komai ba,abu daya ke bata qwarin gwiwa AUREN YARJEJENIYA da mammina take sake tabbatar mata. Tunds ta tashi tasan mammina din na magana daya ne......idan tayi mata albishir baya faduwa sai ya tabbata. Da kallo tabi akhnan din data wuce kawai,a cikin idanunta taga tabbacin maganar dazu data gaya mata. Da gaske take zata raba qafa,itama zata gwada tata sa'ar,saidai a ranta tana jin ba zata bari akhnan din ta gwada kowacce dama tata taci nasara ba ballantana ta fara yunqurin fara dogara da kanta da kuma fara dogara da tunaninta. Idaninshi a qasa suke,amma iya lissafin takun tahowar akhnan din da tsaikon da aka samu na sakanni sittin ya tabbatar masa ta tsaya kadan gurin wani. Lokacin da lissafin tunaninsa yake gaba,ya tsaya cak akan mammina.....gurinta ta tsaya... Ya fahimci hankalin mammina din ya fara rasa kwanciya. Kenan duk sanda zai KUSANTA KANSA DA AKHNAN hakan yana nufin rasa kwanciyar hankalinta?. "TARKON FARKO" Ya furta can qasan maqoshinsa har adam apple dinsa yana motsawa,wani miskilin murmushi da bai siffantu akan fuskarsa ya harba kadan. Bai kalleta ba,amma kuma yasan ta iso gurin,ya juya da wannan takun nasa yasha gabanta yana tafiya ba tare daya waiwayota ba,ya tsaya gaban motar,ya kuma sanya hannu da kansa ya bude mata. Wani mamaki je ya tsarga mata,ya kuma sanyata jinkirin shiga. Jinkirin daya sanyashi daga manyan fararen idanunsa a nutse ya zubesu cikin nata,yaci sa'a tana kallonsa ne itama a sannan. Da body language yayi amfani,da wadannan qwayar idanun da ganinsu kullum yake tuna mata hippodrome ya mata sign na ta shiga. Wani irin abu taji ya zarce daga cikin idanunsa zuwa nata,ya kuma harba cikin jikinta har sai da taji wani iri. Salon qwarewa ne na qarshe ga duk wani basarake da izzarsa takai,iya magana da qwayar idanuwa kawai. "Ina ya samo izzarsa?" Ta tambayi kanta da kanta sanda take shigewa motar da wani yanayi na jan aji da kamewa. Murfin ya maida ya kulle,sannan a hankali ya daga idanunsa cikin ba zata ya zubesu kan mammina dake can a tsaye yana sauke wani qaramin murmushi ne taushi Sai a sannan jinin jikinta days daskare na wucin gadi sanda ta ganshi yana budewa akhnan qofa ya harba da wani irin gudu,gudun da banda tayi gaggawar janye dubanta daga nasa,ta kuma zame kadan ta zauna kamar wadda ta zauna ne kawai don ta huta,ta tabbatar da sai ta samu wata qaramar matsalar. Abdii yaja baya kadan yana bashi guri,shima nasa jinin yana daskarewa. Wani irin mugun tafiya dashi abun yayi......yau prince haisam din da ake budewa mota ya shiga bayan an shimfida tattausan qawataccen carpet a dukka hanyar da qafafunsa zasubi su taka......yau shine da budewa wata qofa? "Turqashi.....ina omar?" Abdii yayi gulmar a ransa. Yana shiga motar yanayin fuskarsa ta sauya zuwa wani lafiyayyen msikilanci hade rai da hade tsokokin fuskarsa guri guda. Seat biyu ne da motar kawai,wanda suke facing juna. So zabin biyu ne,koka zauna akusa da mutum,ko ka zauna opposite nasa,ya kuma zabi zama opposite nata yana maida hankalinsa ga system dinsa da abdii ya ajiye masa a gurin. Akwai wasu bayanai da yakeson dubawa daga gurin Maher dama wasu daga Ethiopia,don haka ya kunnata ya kuma daidaitata saman cinyarsa Sanda motar ta miqa saman kwalta,wani shuru mars hayaniya ya wanzu a motar,sanda system dinsa ta daidaita ya kuma shiga bangaren saqonnin,sai ya motsa labbansa da wata irin nutsuwa data zame masa dabi'a (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Ban karbi aurenki don ina hada rayuwata da taki ba....ban aureki kuma don na murqusheki ba......baki zama cikin lissafina ba tun daga farkonsa har qarshensa......ki kwantar da hankalinki,idan kin zabi tafiya ba tare da rikici ba.....zan zareki cikin lissafina cikin sauqi kamar bamu taba haduwa ba,idan komai ya daidaita,zan barki kamar yadda na sameki.....amma kuma daga yau....sunan da kike dauke dashi.....da sunan da zaki ci gaba da dauka zuwa wani lokaci duka ba naki kadai bane.......bana buqatar soyayya domin na kare mutuncin aure na da sunana.....wata kariya ce ta gajeran lokaci". Maganarsa ta gilma sosai cikin kanta,ba abinda kuma ta sake bude mata sai linking da tayi da maganar mammina. Kalamansa suna sake bata tabbacin auren yarjejeniya ne.....saidai wasu alamu suna neman qaryata mata hakan. Yadda yake magana da ita cikin kwanciyar hankalinsa ya sanyata daga idanu,saidai bata iya kallon qwayar idanunsa ba. "Kada ka rudi kanka,ban nemi shiga cikin lissafinka ba,kuma bazan tsaya jiran a zareni ba.....nima nasan inda zan tsaya......kamar yadda nasan lokacin da zan fice" Ta furta cikin tsiwar da takejin zataso kallon qwayar idanunsa ta masa ita kai tsaye. Zare idanunsa yayi daga system din sanda ya bude wani email na manager din kamfanin turarensa dake Ethiopia wanda baima kai ga karantawa ba. Idanu ya zuba mata sosai,har sai dataji kallon har bargonta,sai da taji kamar ba wani sauran space daya rage mata da zata iya cikakken motsi. A wannan yanayin kuma,ya sake matsowa dab da ita.....ba kuma don ya samu kusanci da ita ba.....don sai ya ajiye mata nauyin maganar sosai a qirjinta. "Qaddarar wasu tana zuwa musu ne daidai da yadda sukayi sakaci da rayuwarsu......daidai da yadda basu iya tabukawa rayuwarsu komai sai abinda xaren tunanin wasu ya qulla a kansu......da zaki dan sanya haquri kadan na zuwa wani lokaci zamu gani......kina cikin wadanda qaddara take basu zabi?,ko kuma qaddarar ce take zabarsu......duk da banajin ke kina cikin wadanda take bawa zabin.....don inda tana baki zabi da baki kasance a wannan bigiren ba gimbiya akhnan" Yana kaiwa qashe ya koma da baya a nutse yana relaxing bayansa jikin fuskar kujerar yana maida idanunsa ga email din,saidai ko daya fara karantawa har yakai qarshe baiji ya fahimci komai ba. Ya zuqo qamshin turarenta sosai a hancinsa wanda yaci gaba da kaiwa da kawowa tsakanin kwanyarsa da hancin nasa. Yadan lumshe idanu kadan yana mamakin yadda zuciyarsa ke bugawa sosai,bugawar da baisan dalilinta ba. Daidai sanda taja nata numfashin d qyar tana daidaitashi itama. Qarin taku daya da yayi a tsakaninsu sai taji kamar ya zuqe iskar motar gaba daya,kamar ya tare mata duk wani sarari. Wani abu taji yana sauka a gabbanta sanda ta shaqi iska sosai wadda ke cakude da fitinannen tutarensa. Ya dauki wasu sakanni kafin ya bude idanunsa a hankali a hankali,fararen idanun da suka kada kadan suka kuma sauya launi,ya saukesu kawai saman saqon,wanda sunan da abbakar yayi highlight akai shine abinda ya fara jan hankalinsa. *_prince khadeeja muhammad hammud of agadez_* kaman zai daga idanunsa ya kalleta sai kuma ya fasa,ya maido saqon farko yana duban abinda ya qunsa. Neman iri ne na turaren da yasan shi kadai ya mallaki irinsa,da kuma tayin kudade ga kamfaninsa,da kuma bada damar yiwa turaren dukka price din da sukaga dama muddin zai samu. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 109* Cikin wani yanayi da salo na kallon mutum ya saci kallonta kadan. Fuskar nan a hade cikin miskilanci,wanda ya tabbatar da cewa tana jin wannan izzar ne a ranta,tana jin kamar an takura mata aurenshi,auren da baya nufin komai dashi a gurinsa,auren da inda tasan haqiqanin me yake cikinsa tabbas da zatayi gudu ne saboda rayuwarta......quruciya ne?ko rashin dabara ke damunta. Ya sake saukar da idanunsa kadan,saidai still ita yake kalla,yadda take basarwa saika rantse da Allah ba ita ke neman turaren dake jikinsa a yanzu haka ruwa a jallo ba,tana nema......amma batasan wa take nema ba. Ya janye idanunsa kadan wani boyayyen murmushi yana subuce masa,sannan ya fara maidawa abbakar amsar da yake buqatar su tura mata. _Akwai qamshin da ba'a qerashi don kasuwa ba,ba kowa ke dacewa dashi ba,wasu suna ganinsa abu ne me sauqi,amma gaskiyar itace qamshi ne dake neman wanda zai zauna dashi,idan ya dace dake zaki sake jinmu ba tare da kin nema ba_ _sashen gudanarwa_ Turawa abbakar yayi,ya kuma bashi umarnin ya turashi kai tsaye kamar yadda ya tura masa yanzu yanzu. Ya sake dora masa da cewa idan sun sake magana akai kafin ya amsa musu ya fara shaida musu,kada ya yarda ya daga kira,musayar saqonni kawai tsakaninsu. Yana kaiwa nan din ya soma shutting down system din da rufe duk wani guri da yasan ya shiga. Haka kawai yakejin bashi da energy din yin komai,ya xubawa system din idanu yana kallonta sanda take kulle kowanne sashe da kanta da kanta kamar yadda ya budeta daya bayan daya a dazun,daidai sannan wani sassanyan ring tone ya kada. Kadan ta motsa,tana yamutsa fuskarta. Ta sanya hannunta a jaka tana ciro wayar data katse mata tunani da lissafin ME YASA YA BUDE MATA MOTA?,ME YASA YA HANA TARIN HADIMANTA MAZA BUDE MATA QOFAR?. Wataqila wani salon makircinne,ko ba komai ko banza kuma mutane da yawa dake gurin zasu tayashi shaida gurin sultane kan yana bata kulawa,ta yadda ko yaya tayi wani abun laifin zai zama nata ita kadai? Ta yiwa kanta tambaya. Shehnaz ce take kiranta,kamar kada ta daga amma kuma darajarsu tafi gaban taqi daga wayarsu. "Hello" Ta furta da wani sauti daya sauka a hankali.....wani sauti dake cike da yauqi.....gayu da kuma sarauta. Idanunsa ya maida a hankali ya lumshe,shurun da tayi yana zarcewa gaba daya ilahirin motar,kafin a hankali sautin muryarta da yake da wani taushi da tsari ya sake ratsa shurun. "Dites-moi votre excuse directement,ne perdez pas mon temps(Ki fadi uzurinki kai tsaye,karki batamin lokaci)". Wani dariyan shaqiyanci shehnaz ta saki,a hankali cikin nishadi tace. "Me zai hana ki magana da yaren abzinanci ko hausa?" Ta maida mata da yaren France. Qaramin tsaki taja,itama dai cikin harshen France tace mata "Voilà ce que je veux être ahjourdh'hui(haka na zabi na zama yau)". "Oh.....ba laifi ai,amma akhnan......wai idona kemin gizo,ko zallar munafurcin hadimai da bayin gidan nan ne?,naga kamar a mota daya kuka fita da sheikh muhammad dinmu.....yawon amarci ne ko shan iska?" Ta fada tana qunshe dariya. Dariyar data qular da akhnan sosai,wato har ya zama wani topic na tattaunawa fitarsu tare dashi a yau?,ta diga masa ta goga masa wata daraja tata kenan da har aka fara maganan?. "Zan shayar daku mamaki.....baku kadai ba harshi din. Na nema mu fita ne don ya ganewa kansa da kansa tazarar dake tsakaninmu......inaso ya kunyata gaban kowa da kowa a sanda zai kasa magana cikin harshen qasarmu.....kuma na shirya nayita yi masa haka har sai da kansa ya banbance matsayina da nasa......shehnaz,bashi da abinda zai ja zuciyata dashi,kyanshi baya rudata baya kuma burgeni sam" Ta qarasa maganan da harshen faransanci tana daga idanunta a hankali ta zube saman fuskarsa kamar meson tabbatar da managarta ta qarshe da gaske ta fadeta ko kawai fita tayi a abakinta don ta gamsar da shehnaz. "Biftu?,tozarci fa kenan?" "Yakai kalar tozarcin da yayimin na sakani amsa sunan matar malam?.....ku zuba ido kawai labari zai dawo muku" "Idan kuma labarin ya sauya salo fa kinga ai shikenan ko?". Wani tsaki akhnan taja sosai kamar ta tsinke harshenta. " Ai sai kiyita yi.....idan na yar ai zaki iya dauka kem halal ne" Daga haka saita yanke kiran. Haka kawai ta sake samun kanta da daga idanunta ta zube a kansa,saidai dukka hankalinsa yana kan wayarsa yana dannawa,ta janye duban nata daga kanta tana jan tsaki mara sauti. Rashin sani ai masifa ne,a zage mutum tas amma bai fahimci ma cewa dashi ake ba?. Ko ita da ba rainon english ba amma tana ji tana kuma maidawa sosai,iya wannan kawai ya isa ya gaya mata hausa ce kawai a bakinsa,itama bata fita yadda ya kamata,to wai shi menene yarensa?. Amsar data sanyata sake waiwayowa tana dubansa. Kyakkyawar fuskar nan cikin nutsuwa take ci gaba da kallon screen din wayarsa,ganin ya motsa saita kauda idanunta da hanzari,tana gudun kada ya ganta irin na wancan lokaci yayi alfahari ko ya dauka tana kallonsa ne da wani abu. Wani irin murmushi kawai yake saukewa qasan ransa,zuciyarsa tana sake jaddada girman kai da stubbornness irin nata. Ya tura saqon qarshe wa beeno wanda ya tura masa duk details na gurin taron,awannin da zaa kwashe a gurin,su waye suka halarta,dame dame za'a gabatar,dama tabbacin cikakken tsaro da gurin ya samu,wanda shi ya bada umarni a tabbatar da hakan a gurin. Daidai sanda ya sauke wayar daga idanunsa motocinsu suka iso bakin gurin. Cikin girmamawa da mutuntawa aka wangale musu babbar qofar shiga gurin. Hannu ta sanya zata bude qofar don ta qagauta ta sauka.....ta matsu a fara gudanar da taron don ta samu mission dinta ya fara cika,amma sai taji kawai an danna locked dukka qofofin motar suka maida kansu suka kulle. Da sauri ta waiwayo tana dubanshi cike da mamaki,shima ita yake kalla,ya zuba mata wadannan idanun nasa masu tsananin kwarjini da sanya mutum ya rusuna komai taurin kanshi. Ta dauka zata iya ci gaba da kallonsa,amma sai taji ta kasa,dole ta tattare tsiwar data taso mata ta maidata cikinta,sannan ta dauke idanunta a hankali tana maidawa farfajiyar gurin. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Wani abu ta hadiye,tana jin ba zata karya izzarta.....ba zata karya martabartabarta gurin tambayarsa dalilin saka lock a qofofin,gashi alamu suna nuns dukka guard din da dogarai da suka musu rakiya sunyi gaba abinsu. A hankali ya zare idonsa daga kanta yana sake ganin wannan izzar a tattare da ita. Baisan me yasa takejin kamar tafi dukka sauran matan duniya ba.....baisan meye nata daya banbanta da sauran mata ba daya sanya takejin izza har haka ba,sai ya maida idanunsa ya lumshe yana saka hannunsa ta gefe yadan kwantar da kujerar kadan,abinda zai bashi daman yin relaxing sosai cikin nutsuwa. A mamakance take kallonshi da gefan idanu,yadda yayi relax cikin kwanciyar hankali,hasalima earpiece taga ya jawo ya sanya a kunnensa,sannan ya maida idanunsa ya lumshe yana sauraren karatun qur'ani cikin suratu taubah. "Kai" Ta fada cikin ranta tsananin mamaki yana cinta. Me malamin nan yake nufi?,fitar ce ba zatayi ba kwata kwata?,ko kuma sanda yakeso?,sai sanda yaga dama?,sai sanda ya bata izini?. Magana yakeso tayi?,idan haka ne kuwa ya makara. Babu ta yadda za'ayi ta nema ALFARMA daga gareshi,don kuwa bashi da ita,shi kansa alfarmar tata yakeci. Shuru yaci gaba da wanzuwa cikin motar,saboda dukka gilasan motar a rufe suke ruf. Mintina suka ci gaba da harbawa suns niyyar hada awa guda. Zuwa sannan zuciyarta ta gama tunzura,ranta ya gama baci,ta daga idanunta zuwa ga glass din gaban motar,sai taga qananun yayyafi sun fara sauka,abinda ya sake tunzurata kenan,har taji kamar zata fashe,sai kawai ta fidda wayarta ta soma kiran shehnaz kai tsaya. Bugu biyu aka dauka,cikin muryarta da ko fushi takeyi ba zakaji ta kaurara ko ta canza salo maras dadi ba. "Shehnaz kinga abinda mutumin nan yayimin?,ya kulleni a mota yana jiran saina karya girmana na masa magana?". "To meye a ciki biftu,karyowa miji faduwa ne ko asara ce?" Muryar aisa ta mamayi kunnenta a madadin shehnaz data kira. Sosai akhnan taji ta hasala "Kinsan abinda yakeyi ne yanzu aisa?,ya kulleni a mota kamar wata yarinyarshi?,wai ba'a gayawa malamin nan wadda ya aura bane?" Maganar ta tsaya a zuciyar aisa,ta kuma sauka a kunnen haisam daya saki boyayyen murmushi. WANNAN IZZAR.....WANNAN GIRMAN KA?. Ya fada can qasan zuciyarsa. "Akhnan.....miji ne wannan.....ba ordinary malami ba akhnan......" "Wai me yasa ba zaki gane ba aisa?,tozartani yakeson yayi aisa......yana kwance abinsa yana lumshe idanu kaman ban wanzu a gurin ba". Tana iya jin dariyar shehnaz ta cikin wayar,wadda ita abun ma dadi yayi mata. Zataso ace tana gurin,ta tabbatar yadda yanayinsan nan yake cike da miskilanci idan baiso ba da aji abun zai dadin kalla. Shi qasaita ita izza. "Nice scene" Ta fadi daga kunnen aisa har sai da aisan ta juya ta tureta. "Akhnan,ki tambayeshi me yasa yayi hakan,ta yuwu akwai dalili...." "Bazan tambayeshi ba Allah aisa......bazan bashi wannan nasarar ba" Sai ta gintse wayar kawai don ta fuskanci ita aisa ma sam bata fahimtar abinda take fada......kamar aisa haisam ta sani,dukkansu ma ba wanda yake ta tata,kowa kaman goyon bayansa yake. Wani miskilin murmushi na qasan zuciya ya saki,tana magana hankalinta kwance bisa dukkanin tsammanin baya jin yaren France,hakan ma yayi masa,kuma zaici gaba da barinta cikin duhunta. Motsawa yayi a nutse yana duba kiran beeno. "Obbo.....gurin yayi clear,komai yana a daidai,nan da mintuna talatin taron zai iya tashi" "Okay" Kawai ya furta ta hanyar motsa kyawawan labbansa,muryarsa can qasa da wani irin zurfi da nutsuwa. Da cikakken kuzarinsa ya miqe yana zama sosai,yadda ya zauna cikin zafin nama yaja hankalinta,amma saitaqi waiwayawa ta dubeshi,saboda idanunta dake cike taf da hawaye. A wannan lokaci ita kanta ta yabawa kanta qoqarin da tayi na riqe kukanta. Bata qaunar abinda zai sanya aga faduwarta ko kasawarta,wannan dalilin ya sanya bata taba yarda wani yasan rauninta bare ya cusguna mata har yaga hawayenta. Ya riga ya tsada yadda zai fara mata karatun da zata san rayuwarta a yanzun ba daidai yake data baya ba. Ya sani,wani aiki ne da dole sai ya yishi,a kafiyarta da taurin kanta zai iya zame masa me wahalar gaske.....amma ya shirya fahimtar da ita da dorata bisa tsarin tarbiyya. Ya kamata tasan cewa zuwa yanzu tana da iyaka,ba komai ne zataci gaba da yinsa yadda takeso ba da kuma yadda ta tsara....akwai umarni ko hani daga wani da zai iya zuwa mata kowanne lokaci,dole ta koyi saurara,ta koyi bin tsarin da zai ci gaba da zaba mata.....zata fahimci kuma ba duk inda takeso zata dinga tafiya ba......saidai izininsa da amincewarsa. Dole ya riqe martabar igiyar aurensa,koda auren kwana daya ne tal!. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira 1,000 kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 110* A nutse ya bude idanun nasa,sannan a hankali ya miqa hannunsa ya cire lock din. Sai daya zura qafafunsa dake saye cikin tsadajjen royal half shoe din qafarsa sannan ya furta kalaman a jejjere cikin izza. "Idan zaki shiga ki shiga yanzu,lokutana masu muhimmanci ne,bazan sake tsayawa ba" Sai ya qarasa fita waje yana tsaiwa saman qafafunsa gami da barin qofofin motar duka a bude. A nutse yake gyara rigar jikinsa,yana kuma qarewa gurin kallo. Da a haka takeso su shiga?,sanda gurin yake a yamutse da mutane?,daidai mintunan data bayar don isowarsu gurin?. A lokacin ya tabbatar kowa yana qagauce da ya ganta,tunda wani abune da bata taba yi ba. Cikin kwanaki uku ya binciki komai daya shafeta,mu'amalarta da mutanenta dama komai. Yaji wani abu kadan daya burgeshi a halayenta,duk da ita bada wannan manufar tayi ba BATA DA YARDA SAM bata kuma yarda da abinda zai taba izzarta. Abune me kyau gurin mace,ki zama me izza.....ki zama maras yadda amma akan MAZA KAWAI. Dabi'a ce ta jin isa daga jininta,amma kuma siffa ce me kyau ba tare da ita tasan da hakan ba. Kusan wannan shine karo na farko ma da zata bayyana a taron jama'a irin haka. Ba kowa bane yasan fuskar princess akhnan din ba,ya tabbatar akwai dimbin masu jiran ganin bayyanuwar fuskarta,abinda idan ya tuna hakanan sai yaji kamar su koma a fasa shiga. Baisan dalili ba,bai kuma san me yasa yakejin hakan ba,kawai yabar yanayinne akan AMANARTA da sultane yaketa maimaita masa. Gwagwarmaya sosai tayi da zuciyarta kafin ta maida hawayen da suka cika mata idanu. Ba wani dan adam daya taba baqinciki irin wanda haisam din yake bata.....WAYESHI WAI?,ya akayi ya samu power da yake iya sarrafata haka cikin sauqi? "Meye na damuwa?,ke da kika kawoshi gurin da zaiji kunya ya kuma muzanta sama da abinda yayi miki?". Wannan tunanin ya sanya taji zuciyarta ta sassauta sosai,wannan tunanin ya sanya taji relief. Daidaita mode na fuskartata tayi,sannan cikin irin tata nutsuwar ta miqo qafafunta a hankali ta saukesu qasa,wanda suke saye cikin high hill shoe me igiyoyin da birra ta tsugunna ta dauresu saman kyakkyawar fatar qafarta. Idanunsa suka sauka akai a hankali,sai ya dauke kansa da sauri gudun faruwar wani abu,yaja numfashi yana duban hanyar da zata kaisu babbar farfajiyar taron kai tsaye. Tayi mamakin ganin ya fara takawa kai tsaye,ba wani hadimi ko bawa ko dogari a tare dasu. Wani iri taji,wani banbarakwai,wanne irin raini yakeson jawo mata cikin al'ummarta.?. A duk sanda zataje guri irin haka koda ba cikin qasarta da yankinta ba,cikin tarba ta musamman ake tararta. Koda taron qarawa juna sani zataje a france ko dubai,hagu da damanta duka dogarawa ne suke tsaye da ita,amma a yau din sai gata suna takawa daga ita saishi su biyu qwal?. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Me yasa sultane bai gano wannan ba?,me yasa sultane be gane banbamcin dake tsakaninsu ba?. Tayi imanin inda ace JININ SARAUTA NE SHI wani Dr ko professor din da tuni gurin ya cika da tarin 'yan biko suna marabtarsu,koda kowa ace ba JININ SARAUTA BANE. Amma yadda yake takawa hankalinsa kwance haka kawai ya nuna nata BAI SABA da duk wata girmamawa ba. Wai me yasa kyansa yake rudarsu?,me yasa kyanshi kawai suke hangowa?,me yasa basa hangen kowanne quality a tattare dashi?. Tsakiyar tunaninta beeno abdii salawi Aabeer da salaana suka bayyana,saidai da idanu ya musu alamar kada su qaraso,kada ma su nuna suna da wani alaqa ta girmamawa tsakaninsu idan ta wuce ta gaisuwar abota kawai. Take suka janye suka kuma saje da mutanen gurin. Hangota ya sanya hadimanta dake tsaiwar jiran isowarsu suka taso musu,abinda yaja hankalin me gabatarwa da sauran mutanen dake gurin. Sanarwa aka fara yi kai tsaye da yanayin daya bawa akhnan mamaki. "Muna maraba da isowar wakilin me martaba.....sheikh muhammad haisam tare da me dakinsa" Sanarwa ya mata wani banbarakwai,komai ma sai taji kamar baizo akan tsari ba saidai kuma hankalinta ya sake daidaita a jikinta duk da mamakin da yake mintsinarta sanda taga dukka manyan baqi dake gurin sun fara tasowa. Kai tsaye haisam din suke dosowa,murmushi ya subuce mata daga can qasan zuciyarta. Lokaci yayi da zai fara fahimtar ba kowanne dan adam bane kake kutsa rayuwarka cikin tasa ba......a yanzu zai fara jin me ake nufi da KUNYA da toxarci.....zata ga da wanne yare zai iya magana da wadannan mutanen daketa wani girmamashi sama da yadda suka nuna mata bangirma,tamkar sunga me martaba. Ta tabe baki tana dubansa qasa qasa,sun taso sunyo gunsa gaba daya kamar shi ta yowa rakiya taron. Da wannan murmushin nasa dake sake bayyana kamalarsa dama nutsuwarsa yake basu hannu,a hankali tataccen larabci taji ya soma tashi daga harshen haisam din zuwa ga manyan mutanen da yake musabaha dasu daya bayan daya. A mamakance ta daga manyan blue eyes dinta tana saukewa a kansa. Fuskarsa a sake da wani irin yalwataccen yanayi,daya bayan daya kuma cikin girmama juna yakeci gaba da musabaha da mutanen,kowa kuma kaman yana qoqarin lallai saiya gaisa dashi kamar wadanda sukaga wani babban basaraken da babu irinsa. "Me yasa?" Ta tambayi kanta "Ko suma yana musu kwarjini ne?" Ta sake tambayar kanta a mamakance,saidai bata ko musa hakan ba sanda taga alqalin alqalai na niger gaba(chief justice ahmadu hambali) ya riqe hannun haisam din da kyau cikin rusunawa. "Me kenan?,meye wannan?" Ta tambayi kanta. "Duka wannan girmamawar ta meye?" Ta sake tambaya still ganin yadda ya tattarawa haisam hankalinsa yana saurarensa. Cikin nutsuwa Haisam ke magana dashi,cikin yaren larabci da ya sanya ta gaza fahimtar akan meye suke magana haka me muhimmanci?. "Muje ko?" Ta tsinci muryarsa daidai kunnenta,abinda yazo mata a bazata saboda lulawa da tayi duniyar tunani. Kamar ko yaushe kusancinsu taji ya mata kusa sosai,qamshinnan da tun dazun ya zame mata jarrabawa yana sake kusantar hancinta,kafin ta daga qafa har ya soma yin gaba,saita taka tana biye dashi daidai sanda mutanen suka soma gaisheta itama. Hakanan taji idanuwa sun mata yawa,har taji qafafunta kamar sun mata laushi. Ba wannan ne karo na farko data tsaya cikin taron jama'a ba kamar haka. Ta tsaya a taron da yafi wannan girma da tara manyan manyan mutane daga qasashen duniya,amma me yasa wannan yafi ratsa da tsaye mata a rai?. Saidai sanda ta daga idanunta a hankali saita fahimci......ba sauran idanun bane suke damunta ba.....ba sauran kallon da ake mata bane damuwarta ba.....aah idanunsa shi kadai.....kallonsa shi kadai ya hadiye dubbannin kallon da ake mata na bayyanar fuskarta a karon farko cikin taro cikin qasar agadez kamar haka. Idonsa ya dauke a kanta,ya kuma karanci me yake damun zuciyarta da kallo daya tak,abinda tayita qoqarin tarewa saidai bai samu ba. Sassauta yanayin tafiyarsa yayi,ya rage karsashinta don ya bata dama su jera kafada da ita ko hakan zai rage mata nauyin da takeji. Ci gaba da marabtarsa mutane daban daban sukaci gaba dayi cikin nuna kulawa da girmamawa. Bai fasa ba,da wannan karamcin nasa.....da wannan dattakon nasa yaci gaba da bada kulawa,saidai gaba daya sai yake jinsa kamar an masa dabaibayi. Idanun da suke kansu sunyi yawa,idanu ne dake cike da kallo na burgewa,sai yakejin kamar idanun sunfi yawa a kanta,kamar sunfi yawa akan fuskarta kasancewarta MACACE. Ya saka samun sukuni sam qasan ransa,har zuwa sanda suka isa mazaunin da aka ware musu,ita tana side din mata daga hannun hagu,shi yana side din maza daga dama,seats din sai suka kasance opposite na junansu. Ya taka sau daya zai zarce mazauninsa kamar yadda itama ta doshi mazauninta bisa takewar bayansu birra barratu buhaina bushira da bara'atu. Tsintar yatunsa guda hudu tayi cikin wani abu me dumi da laushi ta qasan lafayarta,wanda sai bayan ta samu taja numfashi sannan ta fahimci hannunsa ne. Wani irin abu taji ya tsarga mata saboda yadda yake murza yatsun nata sosai cikin tsakiyar tafin hannunsa. "Ki gyara lullubinki,ki maida qafafunki ciki sanda kika zauna a seat dinki" Ya furta adan rarrabe saboda yadda zuciyarsa ke bugawa da qarfin gaske,sai ya saki yatsun nata yana wucewa mazaunin nasa cikin kame kansa da qoqarin daidaita nutsuwarsa. Wani yanayi yakeji sosai cikin jikinsa,ya murza yatsunta ne kawai don ya fahimtar da ita maganarsa tafe take da kyakkyawan gargadi.....saidai kuma abun yazo masa da akasin abinda yayi niyyar aike mata. Murmushi take qoqarin azawa kawai saman fuskarta ganin yadda kowa ke qoqarin gwada mata qauna da kulawa,saidai sam murmushin ba zaka kirashi da murmushi ba saidai washewar fuska,har zuwa sanda komai ya daidaita na murnar zuwansu aka dora da gudanar da taron. Wani numfashi taja me nauyin gaske har qirjinta yana dagawa a hankali. Har yanxu jikinta amsawa yakeyi,ta lanqwashe hannunta cikin lafayar,ta saka daya hannun tana riqe yatsun daya riqe mata dazun tana murzasu a hankali waiko hakan zai.maye gurbin dumi da taushin tafin hannunsa da tambarinsu yaqi matsawa daga fatarta dama zuciyarta. Tanata jin abunne cikin jikinta,zuciyarta na sauyawa da wani irin yanayi,yanayin daya dinga tunzurata lallai saita kalli fuskarsa......lallai tanaso ta gani ya yanayin nashi fuskar?. Da gayya yayi mata ko kuma arashi ne,sannu a sannu ta dinga wasa da idanunta a kewayensa,tana son duban yanayinsa,tanason duban me yakeyi?,ita yake kallo ko wani gurin,amma bataso ta zubda kimarta,saidai kuma da wani saurin idanunta suka fada a akansa ba tare data shirya ba. Dukkanin hankalinsa ya tattara kan me jawabin da yake magana cikin harshen larabci,wanda ba duka take gane me yake cewa ba don bata da sani ta wannan bangaren. Kyakkyawan gemunsa da gashin dake kwance gefe da gefan fuskarsa yanata glowing da wani yanayi daya qarawa lafiyayyar fatar fuskarsa me wani irin haske me daukan idanu kyau. Ya dan karkata fuskarsa wannan ya sanya taga shape na lips nasa.....shape na manyan idanunsa da suke lumshe kadan,da hancinsa daya zauna sosai saman fuskarsa kamar an ajiyeshi. Bame tsini ko tsaho bane sosai,yana da tsaho din amma yana da dan tudu daya sanya qwayar idanunsa ta fidda yadda ya kamata. Motsawar da taga yayi ya sanyata dauke idanunta da sauri,saidai kuma ko data sake dubansa sai taga idanunsa ya maida kan wayarsa. A hankali ta sauke dubanta kan zara zaran yatsun hannunsa da yake danna wayar da sauri,yanayin da zai gaya mata qwarewarsa wajen sarrafa waya. Daga nan inda take tana iya ganin fararen yatsunsa dama fararen nails dinsa da suke wani irin tarwai kamar glass. Zoben azurfa ne qwaya daya kawai a hannun nasa me dauke da wani irin blue din stone a samansa da yafi mata kama da DIAMOND saboda yadda blue din ya kasance wani me sheqi da dukan hankali. Agogon Rolex din dake dake tsintsiyar hannunsa ya kwanta luf cikin fatar nan tasa ma'abociyar gargasa sosai. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira 1k kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 111* Batasan ya akayi ba wani numfashi ya qwace mata,zuciyarta kuma taso tsaiwa a qirjinta sakamakon dago kansa da yayi suka kuma hada idanu cikin ba zata. Da wani irin hanzari ta qwace idanunta tana jin zuciyarta tana lugude "Me yasa?" Ta tuhumi idanunta da zuciyarta da suka tunzurata kallonsa har haka. "Sheikh haisam ne fa?,ordinary malam?" Ta fadiwa kanta da kanta. Bata sake kowanne tunani ba taji me gabatarwa yana magana ta mic "Muna neman alfarma ga sheikh muhammad haisam yazo ya wakilci me martaba gurin miqa certificate na girmamawa ga zaqaquran dalibanmu". Idanu ta qanqance,zuciyarta tana matsewa a qirjinta. Wannan matsayin nata ne.....inda babu shi,banda ya wanzu a gurin itace zata wakilci sultane,sai taji wani bacin rai yana lasarta,ta sake daga idanunta tana dan satar binsa da kallo sanda yake takawa a qasaice zuwa saman steps din,duk da sunyi nufin matsowa da abun maganar gurin ya basu daga inda yake a zaune. Yadda yadin cashmere din jikinsa ke daukan idanu wani abune na daban na musamman kuma da zai sake bayyana maka tsadarsa. Hakanan tsarin dinkin da akayi masa kawai abun burgewa ne. "Yana da daukan hankali malamin nan......irinsu cikin malamai ne qalilanne......ga izza ga ilimi" Maganan ya sauka daga bayanta wadda taja hankalinta. A hankali ta soma maido da dubanta da nufin fahimtar wadanda ke maganar. Saidai kafin takai garesu ma idanunta sun nuna mata yadda dubban idanu suka raja'a a kansa kafin muryarsa me zurfin nan data sake kwarjini ta soma fita ta cikin mic din. Kujera ta musamman suka aje masa still a gurin duk da ya taso din,sannan ya karbi mic din ya fara da sallama. Kai ka sani koda ba'a gaya maka ba zaka fahimci gwani ne wajen magana cikin mutane. Sallama yayi wadda ta bada wani irin sauti me daukan hankali,dukka suka amsa suna tattara hankalinsu a kanshi. Cikin taqaitaccen lokaci ya gabatar da jawabi cikin harshen larabci,jawabin data fahimci kusan duk wanda kejin harshen larabci a gurin yana ratsashi. A nutse idanunsa da bakinsa ke juyawa,bakin dake fidda haruffan larabcin cikin wani irin zallar qwarewa da fahimtar harshen. Tana numfashi sosai taja fiddashi a hankali. Karon farko data tsaya ta saurari yaren larabci zalla irin haka da kyau,batasan me yasa ba batasan kuma dalili ba,sai taji yaren yana mata wani irin dadim da farko ta dauka ba yaren da yakai yaren abzinanci da French dadi......amma a yau sai takejin wani irin yanayi daban yana ratsata. Yana kammalawa dukkanin gurin ya dauki kabbara me qarfin gaske,mc din ya qarasa ya karbi mic din cikin girmamawar dashi kansa baisan yana yinta ba,ya saka mic din a bakinsa ya fara magana cikin yaren Tuareg. "Na jima banji tataccen larabci daya tsumani da harshe me kyau irin wannan ba......nasan dukkanin udaba'u masana yaren larabci a yanzun sheikh muhammad haisam ya tayar musu da shauqi,muna godiya sosai" Ya fada yana rusunawa. Daya bayan daya ya fara kiran 'yammatan daliban da suka cancanci girmamawar yana miqa musu certificate din,karbar certificate din daya zama jidali ga dukkan 'yammatan. Ba wadda bata bar gurin da wani irin bugun zuciya ba saboda wani irin kwarjinin tsayawa a gabansa. "Khadeeja rabi'ou sa'adou" Mc din ya kira sunan dalibar me suna khadeeja har sau biyu. Ta tsakiyar daliban ta fara takowa da dan hanzarinta. Baqar buzuwa ce wadda bata cika hasken fata ba,saidai tana da kyanta daidai gwargwado. Kallo daya ne haisam din keyi bisa al'adarsa,baya kuma d'ara hakan,ya dauke idanunsa yana miqewa a nutse,miqewar data bawa kowa mamaki. Tsaiwa dalibar tayi a gabansa,saita sad da kanta qasa kwarjininsa yana cikata,daidai sanda yayi magana da abdii dake gefansa. Murmushi abdii din yayi,ya matsa ya yiwa MC din magana,sautin murmushin Mc din ya harba ta cikin mic din yana duban kowa d'ai d'ai. Karbar nata certificate din haisam yayi,yadan duba kadan,sannan ya miqa mata,ta sanya hannu biyu ta rusuna cikin girmamawa tana karba. "Muna miqa saqon godiya ga sheikh muhammad haisam....ya miqe don karrama khadeeja da kansa,saboda ita din taci sunan mahaifiyarsa ne......dalilin wannan sheikh muhammad ya bayar ga kyauta ga kowacce daliba har na CFA 390,000 yayin daya ninka wannan adadin ga daliba khadeeja" Wani irin abune a hankali taji yana saukar mata a gangar jikinta,wani abu da batasan meye ba. A nutse ta dora idanunta akan dalibar,wadda duka duka batafi sa'ar falaak dinta ba. Idanunta sukayi kyakkyawan gani,don kuwa lura tayi da idanunta suna kan haisam din dake saukowa daga step din a nutse don komawa muhallinsa. Murmushi takeyi sosai wani irin murmushi dake nuni da farincikin da zuciyata take ciki. "Kyautar CFA 390,000 ga kowacce daliba?.....daliban da aqalla sun kusa sun tamanin?. A ina ya samu wadannan kudaden?,yasan ma abinda yake fadin yayi kyautar dashi kuwa?,yasan kuwa adadin kudaden daya ambata kuwa?" Ta tambayi kanta da kanta tana son maida idanunta kan fuskarsa,saidai zuciyarta tana gargad'arta game da hakan. "Daliba guda daya an ninka mata adadin?" Ta sake tambayar kanta tana maida idanunta kan yarinyar da tuni ta koma ta zauna. Murmushi takeyi sosai,dukkan alamu na matsanancin farinciki sun nuna akan fuskar yarinyar,lokaci lokaci tana daga idanu ta kalli sashen da haisam yake tsaye yana sallama da manyan mutanen daya samu a gurin. Wani harbawa guda daya taji zuciyarta tayi,ta lumshe idanunta tana tambayar kanta DALILI?. Saboda kawai sunanta khadeeja?,me yasa yake iya ninka kyauta saboda suna daya?. Sauke numfashi tayi sanda birra ta rusuno tana gaya mata "Zamu wuce ne ranki ya dade......yallabai yayi umarni" Idanunta ta daga a hankali ta kalli birra jin sunan data sauya masa,saita miqe a nutse abinda ya sanya hankula suka sake yowa kanta. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Bata manta ba,batayi qasa kuma a gwiwa ba ta waiwaya a hankali tana sauke idanunta ga mutum biyu dake bayanta. Suka hada idanu sai suka sakar mata murmushi. Shugabar hukumar ilimin bai d'aya ce ta qasa,hajiya nihla Ousmane......da baquwar da batasan wacece ba. Kudi kyau gami da dukiya dukkaninsu nihla tana dasu,tana cikin mata matasa masu qananun shekaru da suka samu aiki me girma cikin gwamnati,saidai duk da haka nihla din bata taba aure ba. Hada idanu sukayi,cikin girmamawa hajiya nihla wadda ta miqe tana miqawa akhnan hannu. Duk da cewa ta girmi akhnan nesa ba kusa ba.....akhnan din kamar qanwa take a gurinta,qanwar ma ta bayan baya,amma hausawa sukace sawun giwa ya take na raqumi,dole ta bawa akhnan din girma kamar nata shekarun sunfi nata. Wani kallo ta sakewa nihla din na cikin idanu,'yan abun miskilanci sun motsa,a nutse cikin wannan fuskar da sarauta da izza ke kaiwa suna kawowa ta zare idanunta,ba tare data maidawa nihla hannunta su gaisa ba.......ta zare idanunta tana juyawa a nutse ta fara takawa su birra suna take mata baya. A nutse sukaja da baya sanda take dab da riskarsa. Yana takawa hankali kwance yana amsa waya da hausarsa da bata gama fita gaba daya. Idanunta ta lumshe tana budesu,tana tuna komai daya faru a yanzu. Damuwarta alqawarin daya dauka na kudade masu nauyi da yace zai bayar ga daliban. Ta sani,baida abinda zai iya biyan wadannan kudaden daya ambata,zai karya siffarsa yayi musu qarya ya gudu?,ko kuma karba daga lalitar mahaifinta da sunan shine ya bayar?. Haka kawai a jikinta taji bata gamsu da dukkanin wadannan amsoshin ba. A jikinta take jin indai wannan mutumin ne.....indai wannan malaminne ba daya daga ciki da zaiyi. Ta saci kallonsa kadan sanda ya sake matsawa da kansa ya kuma bude mata qofar motar a karo na biyu. Ganin zai waiwayo ta dauke dubanta a kansa. Tana jin wani d'aci a ranta,wannan nutsuwar rashin fushin da take gani saman fuskarsa bata sonsu. Ko data maida idanunta sai taga seat din gaba ya bude mata. Mamaki yadan kamata,a iya rayuwarta idan ba Niamey ta shiga ba bata taba zama gaban mota,kullum a baya take,driver yana janta. Ta sake daga idanunta cikin alamun rashin fahimta tana dubansa,tsareta yayi da kallo da wannan zafafan idanun nasa,sannan ya mata sign din ta shiga. Wannan zuciyar.....wannan kwanyar data soma jin haushinsu sai suka bata qwarin gwiwar shiga din. Ta sauke numfashi me nauyi sanda ta daidaita cikin seat din. Wai me yake faruwa?,me yasa komai ya juye?,me yasa komai ya sauya daga asalin yadda yake?. Shi ya kamata ya zama cikakken d'an rakiya a idanun kowa.....amma ita ta buge da zama 'yar rakiyar.....shi ya kamata ya shiga qunci kunyata da takura amma ita dince ranta a bace bashi ba......me yasa haka?. "Bismillah" Taji an ambata a hankali. Wani irin baqon yanayi ne a hankali ya mamayeta,qamshinsa yana sake kusantarta da wani irin yanayi dake jefa zuciyarta zuwa ga wani irin shauqi. Ta saba jin hakan a duk sanda qamshin zai bugeta,zuciyarta wasai.....qirjinta wasai,nutsuwa kuma zataji tana mamayarta. Wannan zuciyar dake bugawa cikin qirjinta itace ta soma tambayarta SHI ZAI DRIVING?.....ina driver na?. Zuciyarta taci gaba da bugawa cikin qirjinta da tsoro,tana tsoro kada bai iya motar ba....kada yayi ganganci da rayuwarta,abinda ya sanyata bude idanunta da sauri,daidai sanda ya miqa hannunsa don kunna motar. Da wani irin tsoro ta miqa hannunta da zummar dakatar dashi,tafin hannunta ya sauka a bayan hannunsa,dumin jikin junansu ya harba cikin kowacce magudanar jini ta jikinsu,yakai kuma saqo kwanyarsu. A tare kuma lokaci guda wuta ta daukewa dukkaninsu. Ya daga idanunsa a hankali ya aza saman nata adam apple dinsa yana motsawa da wani irin sauri. Kaifi da tasirin idanunsa suka ratsata,tunaninta da jinin jikinta suka koma daidai,ta samu nasarar janye hannunta da sauri daga saman nasa. Kauda kanta tayi tana son bugun zuciyarta ya daidaita sosai. Me yasa taketa yin shirme ne?,me yasa ta kasa mallakar kanta?,me yasa taketa abubuwan da bai kamata tayisu ba?. Idan ya rainata fa?,idan ya zaci wani abu a kanta fa?. Saita lumshe idanunta sanda taji ya tayar da motar,cikin wani irin coolness yayi reverse ya soma fita da ita daga gurin. Sai daya daidaita motar saman kwalta sannan ya miqa hannu ya kunna A.c din motar saboda yadda yakejin kamar suna cudayyar numfashi da yawa shi da ita. Wani irin shuru ya ratsa motar,tuqi yake cikin nutsuwa mutuwar jiki da kuma kasala. idanunsa akan lafiyayyar kwaltar dake shimfide saman titin,koda batayi magana ba yasan tanason sanin inda zai kaisu ne,bai kuma shirya magana da ita ba. Yanaso ta fahimci IKO da yake dashi a kanta......yanaso ta fahimci maganarsa dama tsarikansa sama suke da nata. Sai ya fara zare mata UMARNIN MAMMINA daga ranta gaba daya,sai ya fara fahimtar da ita tana da wata rayuwa......tana da wani umarni......tana da wani IKO sama da ikon mammina saman wuyanta. Sai ya fara tabbatarwa mammina akwai tazara yanzu tsakaninta da ita,sai ya fara koyar da mammina akwai wani QARFIN IKO daya fara mallaka daga cikin nata kason ikon. Sanda ya rage gudun da yake ya gangara zuwa wani street din daban saita bude idanunta a hankali. Mamaki ya sake cikata ganin ba kowa tare dasu. Basu birra,ba sauran guard's dinta maza da suke kula da tsaronta a duk sanda zasu fita din. Idanu tabi ginin dashi,tunda take a agadez ma batasan gurin ba,saidai koda ba'a gaya mata ba,ta fahimci kodai hotel ko kuma wani hamshaqin guests in dinne. Amma kuma gaba daya ba symbol ba alamu na sunan gurin,saidai girma da tsaruwar ginin kawai ya sanya ta gaza gasgata gida ne. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1,000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 112* Ta daga idanunta sanda aka zuge makeken gate din tana duban layin. Dukka gidajene a tsare masu matuqar daukan hankali da bada sha'awa. Wani qawataccen parking lot ya sanya motar,bai wani damu da daidaita tsaiwarta a gurin ba yadda ya dace,abinda zai nuna maka alamun ikon da yake dashi a gurin. Wani farin matashine sanye da baqaqen uniform ya qaraso,ya kuma rusuna ta bakin window din. Batasan me haisam din ya miqa masa ba,kamar yadda bataji me yace dashi ba tunda yayi magana dashi ne da wani yare da batasan wanne yare bane,amma.kamar tana jin wani sashe na yaren daga bakin morsa safiyya ko mammina jifa jifa. Maida glass din yayi ya rufe "Alhamdulillah" Taji ya furta can qasa da muryarsa me nauyin nan.dogayen yatsunsa ya sanya ya kwashe wayoyinsa dake gurin,sannan ya zura qafarsa ya fita,sai a sannan ya lura da yayyafin daya fara sauka. Ya taka a hankali ya zagaya inda seat dinta,yasa hannu yana sake bude mata motar. Manyan blue eyes dinnan nata da hasken garin da bame kaifi ba saboda yanayin hadari ta daga tana dubansa dasu. Still da ido ya sake mata maganar ta fito. Sauke qwayar idonta tayi,me yasa idanunta da zuciyarta dukka basa iya qureshi da wannan kallon nata dake nunawa mutum kuskure idan ya mata abu?,me yasa basa iya jurewa ne?. Wanne irin izza gareshi haka da zai dinga tafi da ita da umarni da idanu kawai?. Aurensa tayi ne don yayita bata umarni?,anya mammina bata sake cutarta ba?,anya bata jefata inda ba zata taba fita ba?. Bata hangi ta inda wannan kafaffen me shegen izza da girman kai zai sallameta ba. Bataga muhallin da maganganun mammina zasu samu gurin zama ba. "Fito" Yayi magana a karo na farko yana dubanta. Umarnin nan na kai tsaye,magana da izzar nan ya fara cikata,ta tattara dukka jarumtarta guri daya. "Bazan sauka ba,don nan din ba gidana bane" Tayi maganan tanason nuna jarumta,saidai tsakiyar hakan ya hangi tsoro qarara tattare da ita. Wani siririn murmushi ya subuce masa can qasan zuciyarsa ba tare da hakan ya bayyana akan fuskarsa ba. Dole saita nuna yanayin tata jajircewar,kuma alhalin idanunta suna qaryatata suna kuma bada ita wajen fallasa masa labarin zuciyarta. Kyam ya tsaya da dukka wannan tsahon nasa daya biyu da murjajjen jikinsa ya nada structure me kyau. Wani kallo yake aje mata,irin kallon da zai sanya har cikin jininka kaji ana aunaka ne,ya zuqi iska ya fesar,ya daga kansa yana kallon sama dake zubda wani yayyafi siri siri,ya sauke kansa a hankali a kanta karo na biyu. "Ki sauka" Ya kuma maimaitawa hankali kwance. Fusatattun idanunta ta daga tana dubansa,yadda yake magana hankali kwance kaman baisan yana tana ranta ko yana bata mata rai ba shine abinda yafi komai baqanta mata "Na fadi maka nan din ba gidana bane". "Na sani" Ya amsa mata a nutse yana duban yanayin fushinta da yadda izzarta take magana. Idanunta ta mayar gefe,tana jin hawaye suna son ciko mata amma ta hana hakan faruwa. Tanaji a ranta yanason nuna mata iko,yana son karyata da izzarsa,ita kuma karaya da faduwa wasu abubuwa ne da bata yarda dasu a rayuwarta ba. Agogonsa ya daga ya kalla a tsanake,muhimmiyar magana zasuyi da omar da shine ya jagoranci zaman da aikin da kansa. Bai saba bata lokaci ba,bai saba saba magana ko canza lokaci ba,baya so kuma ayau ya fara,saboda aikine me girman gaske. "Kina da zabi biyu......daqiqa goma kawai zan baki ki tunani....ko ki saiko da qafafunki ki shiga.....ko na maida motar na rufe ki zauna ciki,don bazaki koma gida ke daya ba". Mamaki ya sake kamata,sai kawai taji hawayen suna shirin gangaro mata,tayi saurin sadda kanta qasa. A rayuwarta ba'a taba matsanta mata haka ba.....a rayuwarta bata taba ganin juyawa da bada umarni kai tsaye irin haka ba. Tana baqincikin yadda SHURUNSA kadai yake da ikon sarrafata.....tana takaicin yadda ya samu ikon sarrafata da sauqi haka ta cikin qwayar idanunsa kawai. Kamar yana gaya mata ne a sauqaqe IKO BAYA BUQATAR HAYANIYA. "Sakanninki suna dab da cika...." "Bazan shiga ba.....ni ban yarda ba" Ta fada still tana jin zuciyarta tana quna. Abu na farko da yafi tsana MUSU TAURIN KAI abinda ya sanya Aanani qanwarsa tasha wahala sosai a hannunsa kenan har sai daya lanqwasata ta koma tsarin tarbiyyar qabilad oromo. Hannunsa guda daya ya dora saman roofing motar,ya sunkuyar da kansa sosai samanta kamar me shirin mata rumfa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Wannan tsaiwar da yayi saman kanta.....wannan kusancin daya qara a tsakaninsu ya qarasa tsinke duk wata jijiya a jikinta dake bata qwarin gwiwa da damar yin musu. "Dole ki shiga duk inda na kaiki gimbiya akhhnaan" Wani abu yaso sarqe numfashinta yadda ya furta sunan da hausar nan tasa da bata zama tattacciya ba,yadda taji iskar bakinsa dake gauraye da qamshin mint leaves ta fito a hankali tana sauka a fuskarta,sai komai ya qarasa jagule mata,lissafin ya fara harhadar mata guri guda. "Second uku ya rage miki.....ko kikai kanki da qafanki....ko kum...." Bata tsaya ya qarasa fadi ba ta sauke qafarta ta farko a qasa ganin yaja baya yana nade hannun rigarsa. Sai ya dakata da abinda yakeyi a nutse,ya matsa gaban motar ya bude mata murfin sosai yadda zataji dadin fita gaba daya,yayin da idanunsa suka sauka kan zara zara yatsun hannunta data damqe wayarta da kyau a ciki,sai yaga kaman hannun nata rawa yake kadan. "Matsoraciya" Ya fadi can qasan ransa yana sake gasgata kalar tsoron daya gani shimfide a idanunta dazun. Gaba yayi ta soma binsa a baya a hankali,murmushi ya qwace masa kadan bayan wani tunani ya d'arsu a ransa,ya kuma furta "Allah ya sawwaqe" Ya sani wataqila zuciyarta tana raya mata zai nema tarayya ne da ita.....shi ya saukar mata da wannan tsoron?. Ko daya baima shiryawa kalar wannan rayuwar ba,bada ita bama da kowacce mace,koda zai karba yana jira ne daga halittar data mutu a sonshi ne,ba wadda bai tunanin ba qaddarar halittar so a tsakaninsu ba. Tun daga qofar farko data kasance kamar wani lobby ne tsararre idan an budeta mamaki ya cikata. Cikin gidan yafi wajen kyau,wani irin tsari ne me daukan hankali daya kusa kulle mata kai. "Gidan su waye ya kawoni?" Abinda take fadiwa kanta kenan. Gaba daya ta gama tsinkewa sanda sukabi wani dogo kuma siririn hallway,sai taga sun bace daga ainihin lobby din sun balla wani dan guri kamar reception sannan suka sake shiga wata qofa data kaisu wani irin parlor. Kai tsaye ba zatace parlor bane,kuma bai kamanda bedroom ba,hakanan bai kama da office ba,amma dukka zai iya daukan wadannan ma'anonin gaba daya. Akwai wasu irin lafiyayyun sofas da zaka iya maidasu gado ko kujera da aka qawata gurin. Wasu iri marbles masu tsananin kashe idanu da daukan hankali,wasu irin curtains da suke fusgar idanu,dunqulallen table madaidaici sai qananun side tables da aka qawata tsakanin kujerun dasu. Wani irin freezer dispenser da qawatattun trays da cups da butucin shayi masu tsananin kyau. Komai na gurin fari ne qal ba wani sirki ko kadan,banda daukan idanu ba abinda yakeyi. Gagara zama tayi,sosai take jin kanta a baqon guri,shi kansa gurin kwarjini da daukan hankali ne dashi. A nutse kuma kansa tsaye taga yana ci gaba da takawa. Ya fara zare rigar alkyabbar saman kayan nasa a wani irin nutsuwa,abinda ya sake nuna fadin kafadunsa da kuma murjajjen jikinsa ta cikin doguwar rigar cashmere din ta sama da aka mata dinki me zubin kaftaan. Jikin wani abun rataye kaya me qyalli dake tsaye da qafafunsa ya rataye rigar,sai ya taka gaba kadan yana cire agogonsa yana ajiyewa,ya jawo wani qaramin na'ura ba tare da saninta ba ya soma searching network din wayarta yayi connecting da na'urar,sannan yayi disabled na network dinta. Baya buqatar doguwar magana ta hanyar amsar wayarta da kasheta,amma kuma baya buqatar kowa ya kirata ya sameta ko ita ta sameshi. Yanason tsahon awannin da zasu zauna cikin gidan a rasa gane inda suke. Yanason hankalin mammina ya tashi koda na wunin yau ne kawai,yanason ta kasa nutsuwa,yanaso tayita cigiyarsu ba tare data isa tayi cigiyar tasu a fili ba......wannan din kadan tashi da hankalin Aareef yayi ne.....shine dan abinda zai iya rama masa dashi sanda tasa akayi attacking nasu,bawai kuma don yaji ciwo ba,don subul ya fita,motii ne kawai yadan buge kadan a qafar hagunsa.. A nutse ya maida na'urar yadda ba zata lura da ita ba,ya miqe ba tare daya kalleta ba dai,ya fara takawa yana nufar waje. "Ki duba ko ina ki dauki abinda kike buqata.....idan baki samu bama ki danna madannin dake jikin switch na fitilan can,za'a zo a saurari buqatarki. "Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana jin tsoro yana shigarta. Tsoron yadda zai fita ya barta a gurin da yake mata wani irin kwarjini,ta yaya zai killaceta haka ita kadai?. "Zaki zauna ki jira har zuwa sanda zan kammala tattaunawa da mutane". " You speak as if......" "As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da tataccen turancin nan da ko yaushe nasa yana fita da wani tone saboda zaman yaren oromo a bakinsa. Idanunsa sun mata nauyi,saboda ya datsi numfashinta ne ya fada kai tsaye yana kuma waiwayowa bayan ya tsaya daga bakin qofar. "Yes.....because you're" Ya qarasa bata cikakkiyar amsa. "Amma ni ba yarinya bace" Ta maida masa tana qoqarin tattara qarfin halinta. Murmushi yayi can qasan zuciyarsa,wannan qarfin halin nata da kafiyarta yana fusgarshi wani lokaci. "Na sani.....yara basa cikin tsarin mammina.....shi yasa na gasgata ke ba qanqanuwar yarinya bace me girma gimbiya......amma dai....ni nake da zabin sanda zamu tafi.....rest well" Ya furta yana saluting nata sannan ya juya a nutse yana ficewa. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 113* Wani irin numfashi taja tana saukewa a hankali "Yara basa cikin tsarin mammina?" Ta maimaita maganasa. Me ya kawo maganan mammina cikin wannan al'amarin?,me maganarsa take nufi da haka?. Rikicewa lissafinta yayi gaba daya,ta sanya hannu tana dafe goshinta duk da haka idanunta suna yawo cikin gurin. Wani irin gurine da har yanzu tsaruwarsa yake bata mamaki,saidai abinda takeji game dashi daga qasan ranta ya sanya tana danne komai. Qofa bayan qofa yaci gaba da kutsawa cikin gidan,gidan daya zama killatacce kuma na musamman. Cike gidan yake da wani irin tsaro tako ina,shi kuma ya tsara gidan daidai da yadda yakeso. Wani irin tsari da yakan iya sarrafa wayar mutum daga sanda ya shigo gidan har ya fita. Irin wannan gidan kamar mini copy ne na babban ainihin gidansa dake Ethiopia. Wani irin cabinet ce da zaka dauka litattafai ne a shirye a gurin,saidai ko daya matsa wani guri sai ga qofa ta bayyana. Dakine da ko ba'a gaya maka ba kasan an tanadeshi ne saboda aikin sirri,a gaggauce ya shirya komai,ya zauna gaban wani siririn screen da sam baiyi kama da system ko babban computer ba,fuskar omar ta bayyana. "I'm sorry omar" Haisam din ya fada yana jawo mug din coffee dinsa ya surba. Murmushi kadan omar yayi,bada haquri gurin haisam din ba wani bane me wahala,saba alqawari kuma ba halinsa bane sam sam,inde kaga hakan ta faru saida babban dalili. "Ai sai an maka uzuri captain" "Go straight mana omar" Ya fadi yana komawa serious. Shima omar din yasan aikin babba ne,don haka ya koma serious dinsa. Saluting na haisam ya fara yi yana daga hannunsa zuwa gefan kansa. Tsaiwa haisam yayi yana dubansa kafin omar ya sauke hannunsa a hankali. "Dukkan hasashenka ya zama gaskiya,tabbas kawai wani babban abu da take boyewa a gida.....hasashenka ya tabbata,saidai kuma gidan zagaye yake da wani irin tsaro me tsananin gaske. Fiddo da wadanda ke cikin gidan ko cimmasu kamar yana buqatar muyi wani adjustment dan kadan....." Kai kawai haisam yake gyadawa a hankali,yana jin qirjinsa yana yin wani irin wasai. Da gaske ubangiji yana jin dukkan addu'ar me neman d'auki,da gaske ubangiji na tare da dukkan wanda aka zalunta,fadarsa ne cewa zai taimaki wanda aka zalunta koda bayan wani lokaci ne. "Muyi focusing akan gidan omar.......juyar da camera.......inaso cikin sati daya kacal a gama da batun gidan......kamar inaji a jikina shine abu na qarshe daya rage mana" Yayi maganar da dukka seriousness dinsa,yanayin da yake gayawa omar da gaske haisam din ya shirya koda kwana ne a tsaye. "Ka hada connection dasu beeno,kowa ya kasance a matsayarsa" Ya fadi yana tattare hannun rigarsa,abinda ya baiwa kwantacciyar gargasarsa daman fitowa sosai ya aza manyan idanunsa dinnan masu haske saman system din da dukka bada hankalinsa. Batasan adadin sau nawa taja tsaki ba tana duban lokacin daya fara gudu yana qara zurfi. A qalla ta zaci bazasu haura awa daya ba komai dadewar da zaiyi,sai gashi qarfe biyu na rana na dab da hada kanta. Miqewa tayi ta fara takawa kadan kadan a hankali,a ranta tana raya gwara tayi alwala tayi sallah,qila kafin ta kammala sallar ya gama shigo. Ci gaba tayi da kewayawa cikin dakin tana laluben qofar toilet,saudai har ta dawo zuwa anihin inda ta baro bataga wani alamun qofa ba. Mamaki ya sake kamata,ta sake takawa a hankali tana dawowa,saidai still kaman dazun ne. Ganin zata batawa kanta lokaci ne kawai ya sanyata komawa ta zauna tana zubawa sarautar Allah idanu. Ta maida idanunta zuwa ga wayarta a mamakance sanda taji tana qwala kiran sallah. A iya saninta ba wani alarm ko app data taba azawa wayartata don tunasar da ita lokutan sallah,ta miqa hannu ta dauki wayar ta soma sarrafata. Kaf bincikenta bataga wani app ko wani abu daya kawo dalilin kiran sallar ba,har tayi kiran ta qare,sai kawai ta maidata ta ajiye a ranta tana saka ran qilan wani automatic abune ya soma aiki a ciki. A hankali taci gaba da duban lokaci da yake wucewa da sauri,yayyafin dake sauka a sararin sama yana dan qara qarfi. Ranta ya soma baci ganin lokacin sallar azahar ya kubce mata. Duk yadda taso ta hana zuciyarta baci amma abun yaci tura,quna kawai zuciyarta takeyi. Wai a haka basa ganin aibunsa har yanzu?. Ashe bayaga abinda take gani ya hada da wulaqanta dan adam da banzatarwa. Ba zata juri wannan ba sam,saboda komai da yayi tasan yana sane yayi,yayi ne kawai don ya wulaqantata,yayi ne kawai don ya tozartata. A komau nasa idan baiyi qoqarin kai kanta qasa ba bayajin dadi,a yau itakuma tayi alqawarin zaiga irin tsaiwar da take dashi,sai ta jawo wayarta tana laluben wanda zata kira. Kiran duniya kowanne kira yaqi isa ga wanda aka yishi,data kira sai kiran ya yanke,data kira sai kiran ya katse,sai kawai ta ajiye wayar tana dora hannunta akan fuskarta. "Bazan iya wannan tafiyar ba.....bazan iya ba" Ta fadawa kanta da kanta. Har tsakiyar zuciyarta takejin ta gashi dashi,har tsakiyar zuciyarta takejin ya isheta,har qasam zuciyarta takejin ta qosa da wannan tarin umarnin nakai tsaye da yake bata. A hankali kiran sallar ya sake maimaituwa a wayar tata,wanda koda ta kalla sai taga lokacin sallar la'asar ne ya shigo. Zuciyarta ta sake tunzura,ta fara tuhumar kanta me yasa taci gaba da zama ne a gurin?,me yasa ba zata tafi ba tunda tana da qafafu koda kuwa a qasa ne?. Da wannan shawarar tayi amfani ta miqe a hankali ta dauki jakarta da wayarta tana nufar qofa. Hankali kwance ta bude qofar,don shigen qofofin gidanta ne na Niamey. Ta fara takawa ta hanyar da suka shigo,saidai tun bataje ko ina ba ta rude ta kasa tantance waccece hanyar?. Koda ta zabi hanyar da take ganin itace,sai gata ta bulla wata farfajiyar ta daban. Wani irin guri dake cike da shuke shuke masu daukan hankali. Turus tayi tana kallon yadda ruwan sama ke sauka a hankali,abinda tafi tsoro kenana duniya irin wannan yanayin. Lokaci na ruwan sama da zata kasance ita daya koda da rana bare dare,saboda tsoron walqiya da tsawa. Ta taka baya a hankali tana girgiza kai saboda tasan ta bace hanya,saita juya zuwa baya da sassarfa hawaye na sauko mata,amma saita sanya hannu ta dauke tana fadin. "Ba yanzu ba" Kamar jira ake ta sanya qafafunta aka saki wata irin walqiya data haska sararin samaniya da wani irin matsanancin haske,ta runtse idanunta ta kuma toshe kunnuwanta zuciyarta na wani mugun gudu tana jiran jin saukar tsawa,abinda ya sanayata ci gaba tayi da tafiya da wani irin sassarfa,saidai kuma still dakin dazu kawai ta gane hanyarsa,dole ta yanke shawarar komawa ciki.gudun kada ta sake qoqarin fita a samu wata walqiyar me hade da tsawar. Zubewa tayi gaba daya saman daya daga cikin luxury sofas din dake dakin tana sakin ajiyar zuciya. Sosai tayi yaqi da kanta da kanta,ta kuma hana kanta da kanta kuka,saidai zuciyarta kawai suya take mata,ta sake duban lokaci wanda ya nuna mata biyar harda rabi da wasu mintuna na yammaci,nan da awa daya ko da rabi ana iya kiran sallar magariba,sai kawai ta cure guri daya ta sanya fuskarta tsakanin cinyoyinta. Kukan takeso tayi,amma ta hana kanta,abinda ya taru kenan ya tsananta xafin da zuciyarta takeji. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Subhanallah" Ya furta da sauri yana ajiye paper din daya dauko saboda tunawa da yay cewa tare suka shigo gurin shi da ita. Miqewa yayi da hanzari ba tare daya damu da sauke hannun rigarsa daya nannadeshi zuwa gwiwar hannunsa ba,ya kashe system din gaba daya da sauran na'urori da fitilar dakin,ya kuma kwashi takardun da zai kwasa a gaggauce ya fito daga gurin bayan ya maida komai kamar yadda yake. Da sassarfa yake takowa zuwa dakin,yana kuma duba agogon hannunsa. "Ya salam" Ya sake furtawa a hankali. Har cikin zuciyarsa da gasken gaske yana ji ba dadi,kwata kwata ya manta tare suka shigo,duk da cikin jikinsa time to time yana jin kamar yayi mantuwa ko akwai wani abu daya kamata yayi baiyishi ba. Binciken yazo masa da wata irin nasara,aikin ya daukesu dogon lokaci,amma yana sanya ran duk ranar da suka nufi gurin zasu samu dukkan wata nasara da suke sanya rai. Ya sanya ayiwa komai sakin talala,saidai suna biye da motsin komai kuwa. A nutse wannan nutsuwar da ta zame masa jiki yayi scanning fuska da hannunsa qofar ta bude masa kanta da kanta ya tura yana shiga. Bakinsa dauke da sallama,da wannan muryar tasa me wani irin laushi da zurfi. Tana zaune kawai,kanta a qasa kamar me duban cinyoyinta. Sallamar ta sauka a kunnenta tana tattaro dukkan wani rauni da take ta boyewa ta aza saman zuciyarta da wani qarfi daya wancakalar da duk wata juriyarta. Idanunsa a kanta yake takowa a hankali yana qoqarin karantarta,saidai bai samu daman ganin fuskarta gaba daya ba,ya qarasa saman wani abu ya dora takardun gaba daya yana fadin. "Afw........" "Mu wuce gida" Muryarta ta fita da wani irin sanyi duk da ba wannan sautin taso maganarta ta fita ba. A nutse ya waiwayo,idanunsa suka sarqe da nata,abubuwa da yawa ya karanta ya kuma fahimta a tattare da ita,ya jisu ya kuma fahimcesu har cikin jikinsa,sai ya zare idonsa daga kanta yana qoqarin karantar yanayin dakin ya gani ko wani abu ya sauya. Baiga komai ba,koda bottle na ruwa kuwa,hakan yana nufin ba abinda taci ko tasha?. Baiga komai game da cima ba. Mamaki ya kamashi,ya soma takowa inda take idanunsa a kanta fuskarsa tana nuna wani yanayi. "Bakici komai ba?......akwai komai a dakin nan fa" Ya fadi da tausasawa yana dubanta yana sake nazartar yanayinta. Batace masa uffan ba,saboda idan ta tuna cewa batayi sallolinta ba duka tana jin kamar tayita kurma ihu. Tana da riqe lokutan sallah,tun wani fada da suka taba yi da hairaan a lokacin duka duka shekarunta sha biyu hairaan tana da biyar. Tun daga wannan lokacin abun ya zaunar mata akai,bata sake fashin sallah ba,bata kuma sake bari lokacin ta ya wuce ba. Hasalima ita din tana da wani abu.....tana masifar ganin girma da kimar duk wanda ke qoqarin kiyaye sallah,ko wayeshi kuwa. Abun yana burgeta sosai,takanyi lamo tana duban birra wani lokaci idan ta ganta tana sallar dare,abun yana burgeta,amma sai take ganin kamar idan tace ita zatayi ba zata iya ba,kamar ba zata jura ba,wannan yana daya daga cikin dalilan daya sanya birra din ta shiga ranta sosai fiye da sauran hadimanta. "Khadeeja" Ya kirayi sunanta na asali da wani irin sauti me taushin gaske. Idanunta ta runtse da kyau saboda matsananciyar faduwa da gabanta yakeyi,tanason yana hawaye tsatstsafowa a idanunta. Tana jin bugawar zuciyarta da kyau har cikin kunnuwanta. Batasan yaushe ya qaraso gabanta ba,tadai jishi ya kira sunanta ne kawai yana tsugunne saman qafafuwansa. Batasan me ya kawoshi gabanta ba ya tsugunna irin haka yana bar mata qamshinsa ba. Ta bude idanunta a hankali jin bai sake magana ba tana zaton ko ya tashi ne,saidai dukkanin idanun nata sun sauka ne saman lafiyayyar fatar hannunsa dake kwance da gargasa me santsi data bayyana sosai a nade hannun rigarsa take har zuwa gwiwar hannu. "Khadeeeejaah" Ya sake kiranta da asalin yadda sunan yake a larabce da bayyanar kowanne harafi yadda yazo a larabci,saidai kafin ta sauke wannan tunanin taji kalma mafi girma a bakinsa. "Kiyi haquri......na manta ne.....na manta ne kwata kwata". Kalmomin biyu suka daketa sosai,har ta samu kanta da daga idanunta da sauri a kansa tana dubansa. "KIYI HAQURI" Da sauri haka?,kalmar haquri daga bakinsa a sauqaqe har irin haka?. "NA MANTA NE" Ya manta yace.......yana nufin ya manta da ita kenan fa?. Raurau idanunta sukayi har yana iya gani sosai. Wani abu ya sauka saman zuciyarsa,rauni qarara yake gani daga idanun wannan gimbiyar......wannan gimbiyar me tarin IZZA da jin QASAITA?. Kamar tasan me yake yawo a zuciyarsa sai tayi qasa kawai da kanta tana hana mishi ci gaba da kallon qwayar idanunta. Ya lura da yanayin data shiga,sai ya miqe lallausan tafin hannunsa yana miqa mata ta qasan fuskarta,daidai lokacin da hawayen masu dumi suka gangaro suka kuma diga akai. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 114* Wani irin abu yaji ya sauka a jikinsa da saukar hawayen. Ya lumshe idanunsa a hankali ya bude saman tafin hannun nasa Kamar yadda itama ta ware dukka idanunta tana kallon tafin hannun ba tare data dago ba. Hawayen da take boyewa ne gasu a tafin hannunsa?. Saita daga fuskarta da niyyar maidata gefe,amma cikin wani shammatarta yayi ba tare data ankara ba,ya saka yatsunsa biyu yana riqe habarta gami da waiwayo da fuskarta zuwa saitinsa. Batayi qoqarin qwacewa ba,tunda me ya rage?,abinda take gudu ya riga daya gani,ba gani kawai ba.....hasalima ya sauka ne a tafin hannunsa,kawai saita barshi,ya saki hawayen suka fara zuba abinsu,don dama sun mata qoqari riqe kansu da sukayi kusan awa hudu zuwa biyar baya. "Ya salam.....kuka?" Ya fada a hankali yana duban yadda kyakkyawar fuskarta ta fada baci da hawaye. Duk da kukan take da gaske tana jin radadin yana fita,amma kuma tana karantar yadda yanayinsa yayi irin sauyawa. Yadda ya furta.. "Ya salam.....kuka?" Da yanayin mamaki da nauyi cikin al'amarin sai ya bata mamaki. Dukka jikinsa ya amsa gaba daya,da gaske ya tsani kuka......kukanma na mace da ya sani ko Allah baya sonshi. Ya sani ko ubangiji ya rarrashi mata cikin qur'ani a gurare da dama,kamar mahaifiyar annabi musa.......nana maryam da sauransu. Sake mata fuskar yayi,ba zato ta tsinci hannuwansa masu taushi da duminnan cikin nata. "Kiyi haquri" Ya sake maimaitawa yana jin saukar furucin daga qasan zuciyarsa. Nauyi kalmar take mata,duk da tana cikin fushi da bacin rai,amma duk sanda zai furta TAYI HAQURI din bata mamaki sosai yake sakeyi. Har cikin qasusuwanta takejin riqon da yayi mata. Wani irin yanayi ne yake bin jinin da yake harbawa zuwa kowanne sashe na jikinta,turarensa da yanayin kusancinsu tana jinsa har b'argonta. Hannunta ta zame kadan cikin qarfafawa kai gwiwa,sai shima ya zame nasa hannun a hankali. Miqewa yayi tsaye,yayi taku biyu baya yana zube hannuwansa cikin aljihun wandonsa. Zuciyarsa yaji tana nauyi a qirjinsa,bayason ya zama silar kukan wani ba bisa kowacce hujjs ba,muryar sultane kawai yakeji a kunnuwansa sanda yake sake jaddada masa. "Ka riqemin amanar biftu.....na sani tana da wahalar sha'ani.....amma har yanzu qaramar yarinya ce....shekarunta ba masu yawa bane,akwai quruciya akwai wauta na sani sosai tattare da ita". Taku biyu yayi da baya da baya a hankali kafin ya juya zuwa wani abu me kama da fridge kusa da fridge din. Koda ya bude sai ya zamana kamar wani qaramin kitchen ne a ciki. Mini coffee maker ya jona,ya kuma hada kayan coffee din dake jere a gurin cikin qananun mazubi. Cikin sakanni ya hada komai ya.maida ya rufe,yayi tsaye a gurin hannunsa rungume a qirjinsa. Lokaci lokaci yana daga idanu ya kalleta,har yanzu kukan takeyi,ya lumshe idonsa da qarfi yana sauke ajiyar zuciya. Da gaske kukan dagula masa lissafi yakeyi,yana jin kamar ya mata wani zalunci ne da zata kaishi qara gaban Allah. "Ya rahman.......ka dafamin,kasa mu gama da ita lafiya qalau" Ya fadi yana kashe na'urar. Har a ransa yana ji bayason ya dauki nauyinta har biyu a kansa. Yayi amfani da ita gurin aiki sannan kuma ya cusguna mata a zamansu?. Bayason wannan taurin kan,bayason wannan musun,wannan rashin ganin girma da darajar dan adam din dukka baya sonsu,to amma shima da kansa ya sani dole saiyayi aiki kafin ya rabata dasu. Duk da komai ma temporary ne,koda zataci gaba daga baya kenan bayan komai na aikin ya kammala. Qaramin table din gefe ya jawo zuwa gabanta,ya ajiye tray din daya saka cups na coffee din akai sannan ya jawo wani qaramin ottoman ya zauna sun saka tray din kenan a tsakiya. Cup daya ya dauka na coffee din ya miqa mata. Ta daga idanunta da taji suna mata yaji yaji ta kalla. Tun bai iso gabanta ba qamshin komai ya cika mata hancinta. "Karbi" Ya fada a tausashe yana tsareta da idanunsa. A hankali ta miq hannunta ta karba din,don ita kanta tasan qarya take tace bata buqatarsa,saidai taji wani banbarakwai saboda bata saba cin komai gaban maza ba. Gaban sultane kawai take iya cin komai,ta miqa cup din zuwa bakinta a hankali zata kurba amma maganansa ya dakatar da ita. "Bismillah" Ya furta a nutse idanunsa a nutse a kanta saman dan qaramin bakin nan nata masu wani irin siraran lips masu kyau. Dubansa tayi kadan sannan ta janye cup din daga bakinta,tana jinta kamar a takure,fahimtar hakan ya sanyashi zare idanunsa a hankali daga kanta ya maida kan cups din shima ya dauki daya. Kusan lokaci daya sukakai cup din bakinsu,don haka bismillah din da kowa ya fadi ta fito daga bakinsu kusan lokaci guda,wannan ya sanya kowa kallon dan uwansa,kafin kuma dai su sake janye idanunsu dukka a tare. "Sallah....banyi sallah ba" Ta fada bayan ta jiye mug din hannunta wanda koda yakai idonsa ya fuskanci ba wani shan kirki tayi masa ba. Haka take tun asali,tana iya kwana da kwanaki dama bataci cikakken abinci ba sai qananun abubuwa irin haka. "Subhanallah" Ya fada a hankali yana ajiye nashi cup din "Duka?" Ya tambayeta da wani irin yanayi yana duban tsakiyar qwayar idanunta. Kai ta gyada a hankali tana jin kallonsa yana mata nauyi. "Garin yaya?,sallah fa.....aikin bawa na farko da za'a fara dubawa ranar qiyama?" Kai ta dauke gefe,tana jin haushi yana kamata. Tana cika sallarta,bata wasa da ita sam sam,kada mana yayi mata kallon me wasa da salla bayan yau dinma laifinsa ne,shine yaja mata?,saita tura bakinta gaba kamar na qaramin yaro dake jin rigima. Sarai ya gani,abun kuma sai yaso sanya murmushi a fuskarsa. Da gaske abubuwan quruciyarta suna da yawa,ya tura ottoman din yana miqewa sanda take fadin. "Ba toilet din da zan alwalan" Murmushi yayi kadan ya soma takawa yana nufar wani bango. A sace ta bishi da kallo,wannan tafiyar me izza ba abinda yake canzata ne?,ta tambayi kanta da kanta. Ga mamakinya hannunsa ya dafa kawai ya motsa gefe qofa ta bayyana,gabanta ya wani irin faduwa,tayi qasa da kanta tana ware idanu a hankali. Ya akayi bata lura ba?,ya akayi bata gwada ba?,kada fa ya dauka bata iya bane?. "Amma da gaske ban dauka bangon zai bani qofar toilet ba" Ta fadawa kanta da kanta,saidai kafin ta sake tuna komai taji lallausar muryarsa. "Bismillah" Ya ambata idonsa akan wayoyinsa dake ajiye a gefe wadanda suke haske. Omar ne yake kiransa,ya daga wayar a nutse yana sakata a kunne daidai sanda take takawa tana nufar bandakin kamar wadda bata da kuzari. Idonsa ya dauke a hankali daga kanta,daga can qasan zuciyarsa yana jin ba dadi kadan. Ya amsa sallamar omar yana aje numfashi,saidai kafin yace komai kiran ya katse,don haka ya maida wayar ya ajiyeta yana sakata a silent. Idanunta ta ware a hankali tana duban toilet din,tsarinsa yana wani burgeta sosai. Tayi mamakin yadda aka sarrafa ginin har ta gaza fahimtar ina qofar toilet din yake. Ta shiga qasashe da dama taga gine gine iri iri,don haka komai!na toilet din bazai mata wahalar sarrafawa ba,saita taka a nutse tana nufar inda zaifi dacewa da alwalarta. Yana nan tsaye yana jin motsin ruwa har zuwa sanda ta kammala ta fito. Fatarnan da bata riqe ruwa saboda santsinta tayi damshin ruwa da digo digon ruwa kadan kadan. Da hannu ya mata nuni,ta maida idanunta gurin. Lallausar dadduma ce shimfide a gurin,da babu ita a gurin,sai bayan shigarta toilet din,hakan yana nufin shine ya shimfida mata da kanshi kenan?. Ta daga idanunta ta maida kansa a sace,saita samu ba ita yake kallo ba,ya maida hankalinsa ga cire agogon dake daure a hannunsa. Haka kawai taci zuciyarta tadan matse kadan,tayi tsammanin zata ganshi tsaye ne yana dubanta,saita juya tana takawa a hankali zuwa saman abun sallar,shi kuma ya juya yana wucewa bandakin. Tafin qafarta ya nutse saman lallausar daddumar,ta daidaita nutsuwarta ta kabbara salla. Sanda tayi sujjada sosai hancinta ya zuqo mata wannan qamshin. Wannan qamshin nasa da ta tabbatar zuwa yanzu a duniya ba wani turare da yayi daidai dashi a gurinta. Wannan qamshin da tayi imanin ta gama son kowanne turare bayanshi. Ta sauke ajiyar zuciya sanda take zaman tahiyya na farko. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Cikin zuciyarta takejin wani irin nutsuwa,a yau sai takejin kamar sallarta ta banbanta data ko yaushe. A yau din tana jin kamar sallar daban take da wadda ta saba yi duka shekarun baya,wata irin cikakkiyar nutsuwa dake sauka a dukka ruhi da gangar jiki,wanda kafin ta kammala ramuwar azahar dinta tana jin yadda wannan nauyin da quncin zuciyar ya dauke gaba daya. Tana tsaka da ramuwar la'asar ya fito,tayi sallame tana karkatar da kanta kafadar damanta. Idanunta ya sake sauka a kansa,qaramin towel ne fari qal a hannunsa dan qarami yana rage damshin ruwan dake hannuwansa saboda leman dakan zauna a hannun duk sanda ya taba ruwa sakamon gargasar dake kwance a gurin. Ta motsa idanunta kadan tana duban girarsa data jiqe da ruwa,dogayen eye lashes dinsa suma sun harhade dana juna saboda lema,karon farko idanunta yakai kan sumarsa itama data warwatsu saboda shafar kan da yayi lokacin alwala. Wani abu ya harba kadan a qirjinta,suma ce me santsi da yawa kamar sumar yawan yawan mazan buzaye,saidai tasa ta dabance,tana da santsi sosai da baqin da koda baka taba ba a idanu kawai zaka iya gani,ta kwanto masa kadan ta gefan fuskarsa da kuma gaban goshinsa. Gabanta ya fadi sanda take dauke idanunta a kansa saboda daga kansa da taga yayi. Kadan ya bita da kallo,yaji a jikinsa kamar ana kallonsa,amma koda ya daga idanunsa baiga kowa ba,sai ya kautar da kansa gudun raunanar alwalarsa yana sake dawowa cikin dakin sosai. Wani guri ya daga,ya sake ciro wani abun sallar ya shimfida daga gaban tata kadan. Ya sake matsawa kusa da freezer din ya ciro ruwan gora maras sanyi yana takowa a nutse zuwa saman shimfidar. Tayi shuru tana tattara hankalinta guri daya,tana jin kamar zata narke saboda zama da yayi sosai saman abun sallar suna facing din juna. Qamshinsa ne kawai ke kai kawo a tsakiyar gajeruwar tazarar dake tsakaninsu,ya zube mata manya farare tas din idanunsa dukka a kanta. Idanunta taja ta lumshesu,tana jin wani abu me suna KWARJINI dan gaske yana dukanta kamar zai hallakata. Mamakin bugun da zuciyarta keyi ya saukar mata,kafin kuma a hankali muryarsa ta mamayi kunnenta. Duk da akwai tazara tsakaninsu amma sai takejin muryar cikin kunnuwanta sosai. "Sallah tana daya daga cikin manyan ayyukan da ba bawan da zai tsallake ba tare daya samu cikakken report na ingancinta ba. Itace ta farko da Allah S W T yake fara dubawa cikin littafin aikin bawa,idan tayi kyau sallarka azuminka sadakarka da hajjinka umararka da sauran ibadu sun tsallake,idan batayi kyau ba dukka wadannan ibadun ba zasu amfaneka da komai ba. Daga cikin alamun sallarka tana karbuwa,akwai gyaruwar dabi'u da halayenka,komai naka zai sauya zuwa ga yanayi zubi da suffa ba mutumin kirki,haske zai yalwata a fuskarka,muhimmancin sallah ne ya sanya Allah ya umarci mu fara koyawa yaranmu ita tun suna da shekara bakwai,idan sunkai shekara goma basayi a nan gurin kadai Allah ya yarda a daki yaro,idan ya balaga baya yinta Allah yace a kasheshi,itace ibada mafi girma bayan kalmar la'ilaha illallah wato kalmar shahada,itace kadai saboda nauyinta darajarta da kimarta a gurin Allah,saida annabi muhammad S A W yayi tattaki yaje da kansa ya karbota daga gurin Allah,ita daya ce annabi muhammad ya yiwa wannan tattakin. Ba'a taba wanda ya riqe Allah gurin sallah ya wulaqanta ba,ba'a taba wanda ya nemi arziqi gurin sallah ya rasa ba" Ya qarashe maganan da wani irin cool tone. Wani abu me sanyi taji yana sauka a zuciyarta gaba daya,girman sallah taji yana sake qaruwa cikin zuciyarta,ta lumshe idanu maganganunsa suna mata amsa kuwwa a kunne. Ashe tun daga shekara bakwai ne ake fara umartar yaro da sallah?. A hankali sai tunaninta ya koma baya,a hankali saita koma tata rayuwar shekara bakwai baya. Komai ya fara dawo mata tarwai kamar wadda aka dauko faifan CD aka saka mata. "Duka duka nawa take da za'a dameta?,batakai minzali ba ki qyaleta kawai.....don dai bakyason yarinya saiki addabeta da sanyin nan a dinga tashinta sallar asuba?,tana tsakiyar wasa kisa hadimai su daukota su kaita tayi alwala?,kinfi kowa sanin Allah ne safiyya?,wanne irin matsi ne wannan?.....dondai bake kika haifeta ba?" Wasu daga cikin maganganun mammina suka dawo mata a sanda morsa safiyya ke qoqarin sanyata ta fara tsaida sallah a lokacin. Ta tuna sanda takai guraren shekaru goma,a sannan ma mammina ta daina tare mata,duk wani bawa ko hadimi daya matsa mata tayi sallah ranar yaga ta kanshi. Zata masa kome taga dama,zata gaya masa maganganun duka da sukazo ranta,daga qarshe kuma ta kaishi qara gurin mammina. Sanadin wannana abun kuma saiya karbi hukunci kamar wanda yayi wani mummunan laifi. Hairaan itace mutum daya data gagari mammina,zatayi mata dirar mikiya a dukka lokutan sallah,tana kuka tana zumbura baki haka zata tilastata suyi alwala tare suyi kuma sallar tare. Ba zata manta dambarwar da suka sha tsakaninsu da hairaan ba,baran baram sai daya zamana ba shiri tsakaninsu,amma daga qarshe ba zatace ga yadda akayi sallar tabi jikinta ba. "Morsa safiyya tafi mammina gaskiya kenan a wannan lokacin?" Ta yiwa kanta tambayar da taji ta tsaya mata cak! Cikin kwanyarta. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 115* Duk da idanunta suna qasa,amma kamar ya fahimci akwai abinda take nazari. Ya maida idanunsa kan agogon hannunsa,lokacin sallar magariba yayi,don kamar yana iya jiyo kiraye kirayen salla. Idanunsa ya sauke kan ruwan gorar,ya dauka yana budeshi gami da juyawa ya bata baya ya fuskanci alqibla. Tana jin yadda yake zuqar ruwan a hankali,yanayin shan ruwan nasa sai takejinsa da wani sauti da yanayi daban kamar ba yadda mutane suka saba shan ruwa ba. (Eh,da gaske ne,hatta da shan ruwa akwai hanyoyin shansa,musulunci ya koya mana yadda zakasha ruwa,wani daga annabi,wani daga malamai don rayuwa tayi albarka,musamman yaro anaso a tarbiyyantar dashi yanayin shan ruwa sosai don ya girma ya kuma saba da hakan,addinin musulunci yana da ban sha'awa sosai,kawai mun rufe idanunmu ne rayuwar yahudawa tana burgemu sama da wannan,bayan rashin fahimtar addinin yasa muke masa kallon kamar bagidajen addini ne,saidai kash.....duk wata wayewa da muke kalla me kyau da tazo duniya asalinta daga musulunci tazo.....daga larabawa take). Tana jin sanda ya kammala ya ajiye gorar ruwan gaba daya,da tattausar muryarsa dake can qasa tajishi yana addu'ar. "Zahabaz zama'u,wabtallatil uruuq,wasabatal ajru in sha Allah". Shuru ya ratsa dakin,ta daga idanunta a hankali ta gefansa sai taga kaman ya hade lausasan fararen tafukan hannayensa ya budesu guri daya yana addu'ar da bata iya jin komai a cikinta. Yatsunta ta kalla tana irga ranakun mako,yau litinin,tabbas yau litinin,hakan yana nufin azumin litinin da alhamis yakeyi?,da wannan matsanancin zafin daminar da ake fama dashi cikin agadez?. Bata sake wani tunani ba taga ya miqe. "Muyi sallah" Ya furta yana gyara tsaiwarsa,sai kuma ya waiwayo a hankali yana dubanta ba cikin idanunta kai tsaye ba. "A bayana daga bangaren dama na zaki tsaya,nan ne gurin tsaiwar mace idan zatayi sallah da namiji" Ya fadi yana saita mata daidai gurin da yatsunta. Motsawa tayi kadan zuwa inda yake nuna matan,tana jin wani nauyi a ranta da zuciyarta. Bata taba sani ba,hasalima bata taba sallah cikin jam'i ba idan ba umra taje ba. Ta lumshe idanu tana tayar da kabbara itama bayan ya tayar da tasa,tana jin wani irin sakeena cikin zuciyarta. *M A M M I N A* Duk adadin masu tsaro da sanya idanun data baza tsakanin qofofin gidan dama qofar data zama ita kadai ce yanzu ta shigowa cikin gidan ba wanda ya bata labarin ganin dawowar sheikh muhammad haisam ballantana princess akhnan. Tun daga sanda ta koma ciki nutsuwarta ta sake qaurace mata. Dukka kwanakin dama gatanan gata nan ne,bacci cikakke bata iya yinsa,daga ta kwanta take tashi saboda zulumi da fargabar INA ALMAZ?. Duk irin kudin data narkar akan jami'ai kala kala na shige da fice cikin sirri wajen gano mata koda footprint na almaz yaci tura,sai kuma a yau din ta soma hango wata babbar faduwar da jikinta yake bata tana tunkararta. A kaf tarihin rayuwar akhnan din.....wannan shine karo na farko data fara karbar umarni daga WANI ba ita ba ba sultane ba.......umarnin da binsa ya zama wani sassauqan abu har ita dake nesa ta shaida haka. Tuna hakan kawai yana harba wani abu me qarfin gaske a zuciyarta da jikinta,yana saka wani babban shakku akan anya wannan din BA D'AN IBRAHEEM bane?. Tun tana lissafin awa daya kacal zasu dawo,har ta koma lissafin zuwa azahar ne. Daga azahar ta maida fatanta ya koma la'asar,saidai shigowar magariba ya sanyata ta gaza haqurin hadiye maganar a cikinta. Sassan akhnan din ta fita da kanta,su birra da taga dawowarsu tun kafin azahar din tayi suka sake bata tabbacin tana tare da sheikh haisam din,kuma har yanzun basu shigo ba. "Wanne irin take al'ada ce haka?,wanne irin rusa lissafi ne wannan?,ba izini ba komai ka dauki 'yar mutane?,shin ina ya kaita ma kenan?" Ta tambayi kanta saidai tambayar ta kasance a bayyane,abinda ya dasa mamaki sosai azukatansu buhaina din. Birra ta gaza daurewa,don zuwa yanzu ta gaza fahimtar meke daga hankalin giwa ne a duk sanda wata kebewa ta ratsa tsakanin sheikh haisam da uwar dakin nasu?. A iya nata sanin aure aka daura musu,kuma aure na sunnah ma me daraja cikin raudar ma'aiki,ba kebewa kadai ba......tana ganin ko meye a yanzun sheikh muhammad zaiyi halas ne. "Lafiya ce take buya Allah ya taimakeki....ina ganin tunda akwai mijinta a tare da ita ba ita kadai bace komai mai sauqi ne" Idanu ta zubawa birra tana qanqancesu ciki,saidai kuma duk kalar magana da hukunci da take qiyastawa akan yarinyar ya rushe sanda zuciyarta take nanata mata. "Lullubabben sirri ne zeenatu,duk sanda aka matsa akan komai kowa zaiga abun banbarakwai,tabbas a idanun kowa yake mijinta,amma a naki idanun lamarin dabanne,ke kadai kikasan komai" Ta fadawa kanta. "Haka ne...." Ta amsawa birra a taqaice ta miqe tana takawa a hankali tana barin gurin. Kallon kallo suka koma yi a tsakaninsu,sai buhaina ta sheqe da dariya. Idanu suka fidda cikin tsoro suna yiwa buhaina alamar tayi shuru. "Aita tafi....wallahi saina fada....hala ta manta sheqe ayar data dinga yi da me martaba farkon aurensu?,batasan iyayenmu sun bamu labari ba?,haka kawai ki tsagal ki dinga shiga tsakanin miji da mata?,na meye?,idan tazo tana mutuwar son mijinta maga yadda za'ayi". Dariya dukkaninsu suka saka,banda birra data murmusa. "Kuma jikina yana bani kwanan nan haka zata faru......akwai abubuwa da yawa da nasan tanaso tattare da namiji.....wallahi dukka yana dasu" Ta fadi gana gyada kanta a hankali. Idanu suka zuba mata son son jin gulma "Allah ko?" Bara'atu ta fadi,saboda ta sani dukkaninsu ta fisu kusanci sosai da akhnan din. Tafi kiran sunanta kafin na kowa,tafi nemanta kafin kowa. "Jinin annabi yusuf kam koda baida abubuwan da takeso zaiyi saurin jan hankalin mace tabbas" Bushira ta fada tana girgiza kai. "Yana dasu.....harda qari,wani LU'U LU'U ne dake sheqi wanda ba kowa ke gane qyallinsa ba,sai a hankali sanda ruwa ya wankeshi da kyau ya sake bayyana" Birra ta fadi tana murmushi,tana fata inama zata samu koda kwatansa ne,can qasan zuciyarta tana jin fata da burin ya zama mallakin uwar dakinnata na har abada. Babbar balcony dinta na qarshe da zai bata daman ganin farfajiyar ajiyar motocinsu ta zauna,saman qananun kujerun dake gurin,ta sake daukar wayarta tana sake neman number akhnan din,ba kuma wai don tana da tabbacin samunta ba. Still dai kamar dazun wayar tsinkewa takeyi kawai,don ko computer bata tsaya fadi mata dalilin tsinkewar wayar. Ta kalli fuskar wayar tana jin jininta yana tafasa. Wannan shine kira na ashirin da tara data mata daga dazun zuwa yanzu,amma ba wanda aka bata dalilin qin shigar wayar ma ballantana kiran yakai ga shiga. "Tafisu" Ta kira sunanta da wani irin birkicewa. "Allah ya taimakeki" "Ina gudun faruwar wani abu" "Me kenan?" Ta tambayeta cikin kulawa. "Zuciyar mace tafisu,tana da wani irin saurin aminta saurin yarda da saukowa gami da bada kai.....musamman zuciya irinta JININ SAFEENA......ta yarda ta auri ajani duk da bata sonshi,amma hakan bai hana hada jiki dashi ba harta haifa masa yaron da ko duniya zata tashi zai tabbata a maras alfanu har ABADA.....ya komai zai kasance idan zuciyar Akhnan ta zama irin ta uwarta?" Ta qarashe maganan tana duban tafisu dake rusune a gefanta kamar tana neman ainihin sahihiyar amsa. *AKHNAN/HAISAM* "Komai ma yana da tsarinsa?,komai ma yana da addu'a?" Ta yiwa kanta tambayar idanunta qasa qasa tana takawa cikin kamewa tana biye da haisam din. Kowacce qofa da zai maidata ya kulle sai taji ya ambaci wani abu,abin ya dinga mata yawo akai,har zuwa sanda suka kawo bakin babbar budaddiyar balcony din data cikinta zaka wuce zuwa ainihin cikin gidan inda suka fito. Tana lura dashi,ya daga kansa sama a hankali yana duban yadda ruwan sama ke sauka da qarfinsa. "Allahumma sayyiban nafee'an" Ya maimaita a hankali har sau uku kafin ya sauke kansa qasa a nutse. Addu'ar ta shiga kunnenta sosai,ta fara juyata a ranta tanason gane ita kuma addu'an mecece?. Wani gefen na zuciyarta kuma yana cike da taraddadin yadda zata shiga ruwan har takai bakin motarsu. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Cikin muryar nan tasa mai taushi da nutsuwa wadda ke da zurfi a wasu lokutan taji yana magana qasa qasa wadda bata haura ta second uku ba kafin ya kashe wayar. Aljihu ya jefata,yana ci gaba da kallon zubar ruwan saman. Addu'a yakeyi kala kala cikin ransa,wanda ya riga daya zame masa jiki,saboda lokaci irin wannan lokaci ne na amsar addu'a. Yaji kewa sosai cikin ransa,yaji kewar jimma tana taso masa,yaji kewar library dinsa. A irin lokaci irin wannan jimma tana zama koriya da Tarin tsirrai masu ban sha'awa. Kamarshi me son tsirrai da gandun daji,yana jin dadin yawon bude idanunsa sosai,ba qura ba zafi,duniya tana yin wani irin sanyi dake bawa zuciya da ruhi nutsuwa. A hankali ta cure jikinta guri daya saboda sanyin da yake kadata na ruwan. Ya daga idanunsa ya aza a kanta yana karantar yanayinta. A nutse ya saka hannunsa ya zare rigar samanshi ta yadin cashmere din me zubin alkyabba sannan ya fara takowa inda take idanunsa a kanta. Ba zato ba tsammani taji wani abu me taushi cakude da sassanyan qamshin nan daya zame mata JARRABI sun mamayeta. Wani abu ya tsarga mata tun daga tafin qafarta zuwa tsakiyar kwanyarta,ta lumshe idanunta tana jin yadda numfashinta yake fita da sauri. Taku uku kawai yayi ya sake bata tazara bayan ya tabbatar rigar ta zauna a kafadunta,sai ya dauke dubansa daga kanta don ya bata daman gyarawa yadda zaiyi mata dadi. Dukka hannuwansa ya cusa cikin aljihun rigarsa yana dage kafadunsa sama gami da hade jikinsa kadan,still idanunsa kan farfajiyar dake da yalwa da haske tarwai. "Mota ta kusa qarasowa" Ya fadi a taqaice sanda ta sanya hannuwanta dukka biyun tana qanqame rigar a jikinta,wani yanayi da tunda aka haifeta yana taso mata karon farko a matsayinta na cikakkiyar 'ya mace me cikakkiyar lafiya. Hasken motar da aka rage da tahowarta gurin ya sanya ta daga kanta a hankali har zuwa sanda motar ta tsaya daidai gabansu dab dasu,ta yadda feshin ruwan ne qila kawai zai iya tabasu. Wanda ya tuqa motar ya fito,maleek ne saidai yayi shigar basaja ta yadda sam ba zaka gane shima nasa matsayin ba. Suka hada ido da akhnan suka janye kuma lokaci daya,saidai haka kawai cikin jikinta take ganin wani abu daban tattare dashi bawai driver ba. Shi da maleek din ba wanda ya cewa da kowa komai,ya bashi key din kawai,shi kuma ya karba yana cewa. "Na gode" Sai ya waiwaya gareta ya kalleta sau daya,yanayin daya alamta mata yana gaya mata suje ne. Ya rigata isa bakin motar,kamar daxun yanzu ma hannu ya saka ya bude mata qofar motar. Takowa take a hankali,kasala yana lullubeta,qamshin yana kassara jikinta,mamakinsa kuma yana saukar mata. Ya maida motar ya rufe,ya kuma zagaya da sassarfa don komawa nasa side din,ta bude idonta a hankali ta zubesu a kansa sanda yake zagayowa ta gaban motar zuwa nasa seat din. Sake maida idanun nata tayi sosai ta rufe su,tambayoyi fal cikin kanta,tana jin sanda ya furta. "Bismillahir rahmanir rahim" Sanda yake qoqarin kunna motar. "Me yasa yake hidima da ita?" Tambayar datafi tsaya mata kenan da tarin ban mamaki. A dazu da yake bude mata mota cikin gida kafin su fito,ta dauka yayi ne kawai don idanun mutane dake kansu,yayi ne saboda ya burge,yayi ne don ace yana da kirki,sai gashi yanzun,a gurin daba kowa sai su biyu,a gurin da idan yana so zai iya wulaqantata,a gurin da idan yanaso zai iya tozartata,amma girma yake bata. "Kiyi haquri" Ta sake tunawa da kalmarsa ta dazu daya maimaita har sau biyu. Shuru motar ta sake dauka,saidai cikin kwanyarta da zuciyarta hayaniya ce kala kala take tashi. Ya mata zafi.....ya mata sanyi duka lokaci daya,wanne irin mutum ne?. Abinda bata sani ba manufar zuciyarsa daban. Har yanzu yana iya tuna wani sashe daya karanta na tarihin annabi muhammad. Sanda yaci garuruwa da yaqi bai wulaqanta manyan mutane masu daraja ba,ya girmamasu daidai da yadda mutanensu kafin musulunci suke girmamasu,har yanzu wannan din halin da yake qoqarin koyi ne dashi. Yana cikin MULKI yana cikin SARAUTA yasan yadda sukebin jini suke barwa mutum wasu dabi'u koda bakayi nufin aiki dasu ba. Shurun ya masa yawa,sai ya lalubo karatun sheikh sudais ya saka cikin suratul rahman. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 116* Wata irin sabuwar nutsuwa taji tana sake saukar mata,ta sake narkewa sosai cikin seat din tana jin kamar zata hade su zama abu guda dashi. Sosai ta sake qanqame rigar cikin jikinta,wani dumi takejin tana bata.....wani irin yanayi da ita kanta ba zata iya tantanceshi ba. Kiransa da akayi a waya ya sanyashi rage kashe dukka volume na karantun,tana fahimtar komai,girmamawarsa ga alqur'ani. A wacan ranar cikin dakinta ya barta da karatun qur'ani sanda zai fita,wanda kafin sannan ya rage volume dinsa gaba daya sanda yake magana da ita. Omar ne,sai ya saka wayar a kunnensa yayi cikakkiyar sallamar data qarawa muryarsa da yanayinsa kamala. "Maannn......kada kacemin har yanzu kuna gurin taron kammala karatun?" Muryar omar kawai da yanayinsa sun isa su tabbatar masa kiran bana Allah da annabi bane.....baya ga haka kuma Omar din da yasan gidan da yake?,duka duka awa nawa sukayi da rabuwa bayan sun kammala aikinsu?. "Omar...." Ya kira sunansa da wannan serious voice din nasa data ratsa akhnan. "Yana da mabanbantan siffofi" Ta fadawa kanta da kanta. "Na dauka honeymoon ne ya fara,mu tattare kayanmu tun yanzu mubar agadez,mission accomplished tunda mun samu wadda tayi mana wuf da captain jagoran tafiya" Sarai yaji saukar dukka kalamansa,amma da wannan izzar da miskilanci ya sake basarwa. "Muna kan hanya" Ya kuma amsa masa a taqaice yana fatan ya barshi haka. "Kan hanya tun kusa awa hudu kenan?,hanyar ce ta qara tsaho?,ko kuma akwai wadda ta riqe hanyar da kyau?" Ya fadi yana dariya. Ba iya omar kadai ba,yaji alamun khadeem da amjada gurin,alamun sun hada baki kenan suka kira su tsuyeshi?. Numfashi yaja a hankali yaja saukeshi a boye. "Ka kira ne don kayi tambaya ko don ka qure mutum?" "Duka biyun" Yaji amjad ya karba. "Amjad mana" Haisam din ya fadi,saboda bayaso suja doguwar magana da zata fahimci wani abu. "Ka manta muna jiranka ne?" Amjad ya sake tambaya. "Akwai abubuwan da ba'a gaggautasu" Yayi qoqarin kaucewa zancan. "Wannan sabuwar magana ce.....haisam da baya bata lokaci,baya qyalewa a jirashi?" "Ya samu babban dalilin da ya sanya lokaci ma ya daina biyayya a gareshi....duka ma yana mantawa da wannan lissafin nasa na kiyaye qa'idar lokaci" Ya jiyo omar ya fada yana dariya. Lips dinsa ya cije kadan da wani miskilin murmushi saman fuskarsa,yana kuma sarrafa steerig motar da kyau cikin wani irin gwanancewa. Wasu irin abokai ne na amana,da suka zame masa tamkar uwa daya uba daya,suna jin junansu har cikin jikinsu. "Ka kiyaye kalamanka" Ya aikewa omar gargadi. "Na kiyaye.....amma mun samu shaida mun kuma bada uziri,daga yanzu a duk sanda ka makara a wani abu.....tabbacin abinda ya sanyaka makara ba qarami bane......ya shiga cikin tsarin doka" Amjad ya fadi suna dariya sosai abinsu. Koda baiso ba saida murmushi ya wanzu akan fuskarsa na wani dan lokaci kafin ya daidaitata. Ya saci kallonta don ba abune daya kamata ace taji ba,saidai gefe ya samu tana kallon titunan da suke wucewa. "Zan iso in sha Allah,ku fara" Ya furta yana katse kiran,ya kuma maida karatun daidai yadda yake. Duk wata fitar kalma guda daya daga bakinsa tana fita ne da wani irin tsari gami da iya tafi da wanda yake magana dashi,bada uzuri da kaucewa samun sabani,wannan shine abinda zuciyarta ta rubuta mata daya sanya ajiyar zuciya subuce mata. Karatun shi yaci gaba da musu rakiya,har zuwa sanda suka isa masarauta. Masu tsaron qofofin suka dinga dage masa kai tsaye cikin girmamawa yana sanya motar a hankali cikin qwarewa. Kaman ruwan yafi yawa a ta nan,ko kuma jira yakeyi su iso sai ya qara qarfi,daidai sanda yake ajiye motar a kebantaccen gurbin ajiyar motoci na gidan.......daidai lokacin da mammina ta sauke idanunta akan motar. Ido ta zubawa motar,cikin nazari da mamakin su waye a cikin ta. Sai ta zabi ci gaba da duban motar daga nan inda take zaune. A hankali ya kashe motar gaba daya,ya zare belt din jikinsa cikin nutsuwa yana ajiyeta a gefe. Duban saukar ruwan kawai takeyi da idani,ta qiyasta yadda zai tabata da kyau kafin ta samu qarasawa ga sassan nata,gabanta yadan fadi ganin ya bude murfin motar ya fita. Saman idanun mammina ya fito,ta qanqance idanunta da kyau tana jin wani abu me nauyi yana sauka a qirjinta. Daga nan inda take kwarjininsa ne still yake iya taras da ita harma yana dukanta,abinda ya sake qara gudun zuciyarta kenan,ta kuma samu kanta da kanta da tambayar ME YASA YAKE MATA KWARJINI NE HAR HAKA?. Ita da akhnan din dukkansu suka bishi da kallo sanda yake zagayawa daya seat din da akhnan din ke zaune. Saidai dukkaninsu ba wanda yasan da kallon da daya yakewa daya. Babbar lemar dake riqe a hannunsa ya matsa,sai gata ta bude,ta kuma bada yalwatacciyar rumfa da zata hana ruwan sama cimmata. Bata lura da hakan ba,har zuwa sanda ya bude murfin motar,ya kuma ja da baya kadan yana dubanta da manyan idanunsa. Qasa ta rusunar da idanuwanta,tana jin abun da wata matuqar martaba da girmamawa,ta kuma motsa a hankali tana fita a motar,yayin da shi kuma ya saita lemar daidai kanta don hana ruwa daman tabata. Batasan ruwa akeyi haka sosai ba sai data sanyo qafarta waje,ta bayanta ya zura hannu daya ya maida motar ya kulle,daidai sanda ta waiwayo saboda jin yadda kusanci yayi yawa a tsakaninsu. Saura qiris fuskokinsu su hadu guri daya,sukayi musayar numfashi shi da ita,abinda ya sake kassarata gaba daya har sai data riqe numfashin nata na wasu sakanni. Ta budesu a nutse,daidai sanda ya kawo hannunsa saitin yadda zata gani yana mata nuni da hannunsa da hanya alamun suje. Tsam mammina ta miqe tana jin zama yana gagararta. Ta matso bakin qarfen balcony din tana qarewa duk wani dagawa da saukar qafafunsu kallo.. A sanda yake biye da ita a bayanta.....a sanda yake maida qafarsa a duk wani gurbi data dauke nata.....a sanda ya sanya lema ta zame mata rumfa da kariya daga ruwan sama,ba kkmai yake hangowa ba sai ZAKI dake bada kariya ga ZAKANYARSA. Wani irin gizo suke mata dake sanya zuciyarta bugawa. Wannan tsahon daya maidashi GIANT na anihi,gaba daya ya laqume akhnan din a gabansa. Manyan kafadunsa da qirarsa me bayyanar da qarfi kai tsaye,gaba daya ya katangeta wanda yake bayansa ma ba lallai ya iya ganinta da kyau ba. Tamkar dama wannan tsaron masa......tamkar dama wannan qirar tasa dukkaninta an halicceta ne don AKHNAN kadai. Tana takawa ne cikin tsantseni saboda yadda yake dab da ita,ta tabbayar motsi kadan zatayi jikinta ya gogi nasa. Ta sani lemar ba lallai ta iya daukesu ba ita dashi,bata da tabbacin ruwa baya tabashi koda ta baya ne. Saidai kuma duk yadda taso kiyaye alaqar jiki a tsakaninsu hakan ya faskara. Don kuwa kyakkyawar walqiya akayi wadda ta sanyata tsaiwa cak ba tare daya waiwayo ba. Banda yana da hanzari da zafin nama,tsaiwarta katsam zata iya jawo cakuduwar jikinsu koda basu shirya hakan ba,saidai ya tsaya cak saboda zafin naman daya nuna gurin tsaiwar da ainihin tazarar dake tsakaninsu na farko. Bugawa kawai zuciyarta takeyi,ta riga ta camfa muddin akahi walqiya tsawa tana tafe,to yaya zata Fahimtar dashi tsoronta?,idan aka samu tsawar yaya zatayi?. Tsawar kam bata barta ta samu amsa ba,ta tarwatse cikin sararin subhana tana me isar da saqon da mahaliccinta ya bata. Wata qaramar qara ta saki,ta juyo da wani mugun hanzari,ba tare data tsaya tantance me takeyi ba ta fada jikinsa tana masa wani kyakkyawan riqo. Kyakkyawan masauki ta samu cikin qirjinsa,tana cusa kanta cikin qirjinta kamar wadda wani mummunan abu ya biyo zai kama,zuciyarta na wani irin bugawa da sauri da sauri. Cak komai ya tsaya masa......cak mumfashinsa buguj zuciyarsa jinsa dama ganinsa ya na wasu daqiqu kafin ya zuqosu da qyar yana fesarwa. Hannunsa ya daga a hankali da zummar dagota,yana iya jin bugun zuciyarta cikin allon qirjinsa,kaman yadda yake iya jin riqonta har cikin bargonsa........amma sai ya samu kansa da aza tafin hannuwan nasa saman bayanta a hankali. Da gaske ya fahimci takeyi,da gaske ya fahimci tsoro takeyi,sosai kuma ya fahimci ba qaramar razana tayi ba. Ya dauka minti daya ko biyu ne kawai zata dago.....ya dauka sakanni qalilan zatayi ta tashi,amma sai yaji abun yana niyyar zarcewa wadannan mintunan saboda ci gaba da haskawar walqiya a sararin samaniya bayan kowanne second. Idanunsa ya lumshe,tashi zuciyarce take bugawa,tashi zuciyarce ke wani irin tsalle a qirjinsa. "Alhamdulillahil lazi yusabbihur r'adi bi hamdihi wal mala'ikatu min kifatih" Ya furta a hankali yana ci gaba da maimaitawa. Sannu a hankali addu'an ya soma shiga kunnuwanta,sannu a hankali numfashinta ya soma daidaita,sannu a hankali tafin hannunsa dake tsakiyar bayanta ya soma nutsar da wani abu cikin b'argonta da jininta,nutsuwa ta fara saukar mata. Kamar wadda aka radawa. "A jikinsa kike" Tayi azamar miqewa daga jikinsa bugun zuciyarta yanaso yaci gaba da harbawa,saidai maganarsa ta bada wani irin relief me shiga zuciya da wani irin sanyi. "Tsoro halitta ne.....amma ba abinda ke kwantar da zukata irin ambaton Allah a lokutan tsoro da fushi". Idanunta ta lumshe tana jin wani nauyi yana saukar mata. Wai me yasa yau komai yazo a haka?,me yasa yau komai yake zuwa a hagunce?. "Bismillah" Ya furta a nutse da wannan coolness din nasa,wanda a yau har cikin gabbansa yakejin wannan sanyin da mutuwar jikin. A nutse ta soma takawa tanayin gaba,yaci gaba da biye mata riqe da lemar. Har cikin ranta takejin wani safety da tsaro me girman gaske,sosai takejin aminci da wani irin girma sanda yake biye da ita. Wani irin numfashi mammina taja ta kuma sauke tana jin yadda qirjinta ya riqe. Hannu tasa ta dafe gurin sosai tana runtse idanu saboda wani irin suka da yake mata. Biftu?,akhnan?,akhnan dince a kwance qirjin wani?,akhnan dince rungume da wani namiji?,hakan fa yana nufin abubuwa masu dama....hakan fa yana bude qofofi ne masu yawa da girman gaske. Ta juya da dan zafi da nufin fita ta sauka ta cimmata,amma sai tafisu da taga komai daya faru ta riqeta da sauri. "Kada kiyi gaggawar zuwa yanzu Allah ya baki nasara.....karki zama cikin alamun matsi da takura. Matsanta mata da takura mata a yanzu ba abinda zasu haifar sai qarin bijire miki". " Tafisu.....bakiga yadda yake juya akalar komai yadda yaga dama ba?,bakiga yadda komai yake canzawa daga muhallinsa ba duk don saboda shi?,bakya hangen akwai yuwwar hurewa biftu kunne?,dole inason haduwa da ita,inason in sake karantar inda tunaninta ya dosa". "Za'a kira miki ita,amma bada kanki ba" Tafisu ta furta cikin girmamawa. Shuru ta danyi kaman me nazari,kafin ta zame hannunta daga riqon da tafisu tayi mata,ta taka zuwa bedroom dinta,wannan ya bawa tafisu tabbacin ta aminta da wannan,don haka tabi bayanta ta kuma sauka tana umartar yalwa da kiran gimbiya akhnan din. Sanya qafarta cikin balcony dinta,da samun tabbacin zuwa inda ruwa bazai tabata ba ya sauke lemar a nutse yana lanqwasheta. Taci gaba da takawa da wani irin sanyi zuwa babbar qofar sashenta dake maqotaka da tashi,tana jin wani abu cikin jikinta sosai yana mamayarta. Yau din ta tabbatar tun daga nan ta ajiye mata wani memory me girma da kuma nauyi,abubuwa da yawa basuzo yadda ta tsarasu ba,sun faru kaman yadda Allah ya hukuntasu,amma kuma akwai wani abu me qarfin gaske daya tsaye mata cakkk wanda batasan meye ba. "Barkanku da isowa" Da ita dake qoqarin qarasawa sassanta,dashi dake tsaye qyam saman qafafunsa,hannayensa zube a aljihun rigarsa yana duban inda duk take saukewa da dauke qafarta yana son tabbatar da shigarta sashenta kafin ya wuce nasa sashen muryar armelle ta sauka a kunnensu. Fuska ya saki a hankali yana amsa mata gaisuwar data masa sannan ta maida dubanta ga akhnan.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 117* "Komai dare morsa safiyya tace a shaida miki tanason ganinki lallai lallai" Maganan yazo mata a wani iri,karon farko data taba kiranta kai tsaye zuwa sassanta. A duk sanda takeson ganinta ko magana da ita idan haka ya kama ko ya zama dole,tana tattaki da kanta tazo ta sameta ne,idan taga dama ta ganta,idanma bataga dama ba taqi bari ta ganta. "Ki shaida mata......" "Zatazo.......zatazo yanzu in sha Allah" Muryar haisam ta mamayi tata. Murmushi ya subuce a fuskar armelle,murmushin farinciki,murmushin jin dadi,yaqini yana sake sauka a zuciyarta TABBAS TSAYAYYE NE SHI DIN ta fadawa kanta da kanta. "Muna godiya" Armelle ta furta cikin tsananin farinciki sannan ta taka a nutse tana barmusu gurin. Da kallo tabi armelle,yayin da shi kuma ya zubawa fuskarta idanu. Ido ya lumshe a hankali yana janye dubansa daga gareta. Wannan baby face din ta cika da dan siririn bacin rai,ita dole ance taje ga matar da take a mazaunin mahaifiya a tare da ita?. Wannan girman bacin alaqar har ina?.....wanne irin aiki akayi haka me zurfi wajen raba wannan qarfi da kaurin JININ?. "Komai zai gyaru....komai zai gyaru in sha Allah.....bazan jewa nanay da albishir din ganin obboleettii lamaan dinta da wannan mummunan yanayin ba......diyar safeena bata dauki safiyya a matsayin uwa ba?. Dubansa takeso tayi cikin tsakiyar idanunsa,taga wanne qarfin gwiwa ne ya bashi daman yanke mata hukunci?,me ya dogara dashi da zai tilastata ko ya sanyata zuwa ga morsa safiyya a sanda batayi niyya ba?. Yau kadai yana zaton ta bashi wannan zarrar?. Yau kadai yana tunanin ta bashi wannan damar?,ta bashi wannan qwarin gwiwar?. Duka tayi wannan tunanin ne a sanda take duban idanunsa kai tsaye,duk da wani irin nauyi dake cikin nasa idanun dake barazanar durqusar da nata qarfin gwiwar. Shima yana tsaye......da wannan tsaiwar dake fadiwa me kallonsa tsayayyen ne tun daga haihuwarsa har kawo yau.....wanda bai gajiya da tsayawarsa akan dukkan komai. Tsaf ya karanci abinda ke kai kawo a zuciyarta. Sai ya zare idonsa a hankali ya kuma fara juyawa. "Qanwar uwa a matsayin uwa take a musulunci,kyautata mata daidai yake da kyautatawa mahaifiyar data haifeka......hakanan munana mata kai tsaye kamar munanawa mahaifiyar taka ne" Bai dad'a ba bai qara ba,yaci gaba da sauka a nutse,bai kuma sake koda waiwayarta ba. Duk yadda taso kada maganansa ya mata tasiri ko kadan amma hakan ya faskara,tabi yalwatattun kafadunsa da kallo har ya bacewa ganinta,saita juya tana murda handle din qofar data kasance kebantacciya saboda ita kadai ta tura tana saka qafafunta. Taku daya tak masu kula da qofar suka fara mata maraba. Ba wanda ta kula don kanta cike yake kawai da kalamansa. A haka ta ratsa dukka parlors dinta ta haura zuwa bedrooms dinta. Har ta gifta bedroom din dake fuskar gaba sosai ta ginin nata saita koma da baya,abinda ya sanya birra takowa da sassarfa ta bude mata don ta karanci nan take da sha'awar kwana,idanun birra dai akan rigar dake maqale saman dukka kafadunta,wanda ta tabbatar rigar sheikh haisam ce. Da mamakin birra tayi tsaye yau da kanta tana fidda dankunnenta da sarqarta ba tare data jira an cire mata ba. Sai datazo zuge zip na rigarta sannan ta waiwayo ta kalli birra. Ta tako a hanksli hankali ta tsaya gabanta,amma saita kalli rigar saman jikinta. Itama dubanta takai ga jikin nata,rigar ta kwanta luf tana fidda qamshin nan nasa saika dauka yana cikin dakin. Ta manta kwata kwata da ita,birra ta miqa hannu zata janye mata ita,saita samu kanta da dakatar da ita,ta saka hannu ta zareta a hankali tana jin yadda yadin yake wani yauqi yauqi a hannu ne dadin tabawa. A nutse ta ajiyeta gefan gadon,sannan ta juyawa birra ta tayata rage kayan jikin nata. "Yalwa ta shigo yanzu yanzu kina dab da shigowa" Birra ta fadi tana qoqarin ninke rigar data cire din. Bata amsawa birra ba,tana zare band dinta daga kanta,abinda ya bawa doguwar yalwatacciyar sumarta daman warwatsuwa a kafadunta zuwa gadon bayata daura da mazaunanta. Shurunta ya ganar da birra komai,don haka ta wuce zuwa ga fadin saqon. "Tace giwa na buqatar ganinki a daren nan" Sai maganan ta tsaya iya nan kawai. Ko daya bataji a ranta zata je ba,to taje tayi me?,tana zaton duk wani deal tsakaninta da mammina din ya qare,abinda ya rage kawai ta bata dama taga nata qoqarin ba tare data nemeta kota gaya mata komai da takeyi ba. Kaman yadda zata bawa mamminan dama itama,zata tantance NASARAR WAYE akan gaba. Bata amsawa birra ba ta wuce zuwa toilet kawai abinta. Wanka takeson tayi,don ta tabbatar da wannan qamshin da take jinsa a jikinta gaba daya ba lallai ya barta ta sake ba. Shuru birra tayi tana zaton zata amsa mata,saidai ganin har ta shige batace komai ba saita tattara kayan data watsar a nan kamar yadda ta saba ta killacesu a inda kowannensu ya dace,ta juya don bawa yalwa amsa. Turus yalwa tayi,abun yana daure mata kai,maganan tana mata girma da yawa. Giwa ce a yau zata nema ganin akhnan amma ba bijirewa hakan?. Maganan ya mata girma da yawa,a gefe daya ita kanta tana wassafa yadda zata shaidawa mammina din ba tare da tayi laifi ba,saita juya kawai tana ficewa a sassan ba tare da tace da birra komai ba,tunda ta sani daga ita har birra din kowa aiki yake,umarni kuma yake bi na uwargijiyarsa. Tayi kwance kawai cikin bathtub tana maimaita maganganunsa. Bata rayu rayuwa me tsaho da annee dinta ba,amma har yanxu tana iya tuna sunanta,har yanzu tana iya tuna yadda take kiranta,har yanzu kuma tana iya tuna yadda take zaunar da ita ta gyara mata gashinta......ta mata wanka,ta shiryata,sannan ta zaunar da ita saman cinyoyinta ta bata abinci a baki. Wani abu guda daya wanda bata sake samunsa ba duk da tarin gata da kulawar da ake nuna mata. Ta rasa macen nan me suna UWA guda daya da zata jingina da cinyarta taji irin wannan dumin na UWA. Ta rasa macen nan guda daya da zata mata wanka ta shiryata irin yadda UWA kewa d'iyarta. Har sanda take shiryawa cikin sassauqar doguwar riga me rubi biyu ta barci tunanin baibar cikin kwanyarta ba,komai da komai daya faru a ranar,ta sauke idanunta a hankali saman rigarsa dake gefan gadon nata. Wani numfashi taji taja a hankali ta kuma saukeshi. Alama ce ta girmamawa,tabbas alama ce ta girmamawa,dabi'a ce da idan basarake ya maka ya gama girmamaka. Ya dauki suturarsa tufafinsa ya lulluba a gareka,koda normal yanayi ne ya kawo hakan bada kyautar rufar dake a jikinka zuwa ga wani alama ce ta girmamawa ta gaske. Ta tuna a duka rayuwarta sultan ne kadai yake mata kalar wannan girmamawar. Neman rikicewa tunaninta yakeyi. Bata hangi sauqi ko sassauci a tare dashi a kanta ba,amma kuma irin wannan girmamawar daga ina ta samo asali? "Baki sani bane.....ba wanda yakai malami iya riqe mace da tattalinta inde yasan abinda yakeyi,suna girmamawa matansu,akance da matar malami data basarake ba kowa ke iya aurensu ba idan suka sakesu,saboda riqon mahaukaci sai sarki". Ta tuna wani hira da taji shehnaz sunayi ita da aisa. A sannan ma qaramin tsaki taja,ta kuma tattare kayanta tabar musu gurin saboda gani take shirme ne kawai a hirarsun. Haka abun yake?,ko kuwa dai kawai yayi ne saboda wani dalili nasa na daban?. Qarasa jan zip din rigarta tayi daidai sanda biftu ta shigo mata da abinci shirye saman wani tray me kyau da dukan hankali. Shimfida ta mata,ta zauna akai tana cewa da ita. "Karki zuba komai.....bani fruit da madara kawai" Tace da ita a taqaice. Hada mata tayi kaman yadda ta buqata ta miqa mata,tana shirin miqewa ta fita ga dakatar da ita. "Zauna na qarasa,zan shiga gurin momma". Maganan yadan bawa birra mamaki,amma batace komai ba ta zauna tana jiranta kamar yadda ta buqata. Sanda suka fito ruwan ya janye sosai,sai sanyi da ruwan ya sakarwa garin. Akwai kebantacciyar hanyar da take iya tasu ce wadda ba lallai ruwa ya tabasu harsu isa inda zasuje din. *MORSA SAFIYYA* Cikin qwataccen parlor din dake dauke da wasu gajerun kujeru masu tsananin taushi. Wani irin pink color ne komai na parlor din,pink me taushin kala da haske. Saman kujerun suke zaune,ita da falaak da kuma hairaan. Aaroon da Aeeda na kwance saman mabanbantan kujeru da alama bacci ne ya kwashesu,don ga kayan wasansu nan barbaje a qasa. Anwar yana saman cinyar hairaan din. Wani nutsatsen qamshi ne yake tashi cikin parlor din,qamshin daya hadu da sassanyan ni'imar garin ya bada wani qamshi me aji na hadadden turaren wuta daga kamfanin SHUWA INCENSE AND MORE(0704 229 3387).....wani sirrin qamshi guda daya da morsa safiyya din keji dashi. Qamshi ne da mammina ke matuqar adawa dashi,saboda yadda ta fahimci yana daya daga cikin sirrikan daya sanya sultane ke mararin kebancewa da morsa safiyya,kuma qamshin da har yau mamminan batasan sirrinsa ba.....batasan kuma daga inda ake samoshi ba. A iya parlor da dakunan me martaba kadai zakaji wannan qamshin,sai kuma lokaci irin wannan idan tana kewar me martaba din takan saka a wannan parlor din Shima qwalli daya tak. Kusan hirar tasu akan akhnan ne da shirye shiryensu da sukeyi wanda ba kama hannun yaro. Dawowar sultane ne kadai ya rage musu,sai gyaran jiki da lecture class dim da morsa safiyya keson akhnan din ta fara,daga bisani kuma hirar tasu ta sauya akala ta koma basu labarin safeenarta wadda ba wanda ya santa a cikinsu,don ko hairaan ba komai take iya tunawa ba. Hira ce wadda zai wahala a farata a kuma gamata lafiya lau ba koke koke. Tana jinta cikin kadaici,tana jin kamar ita kadai take rayuwa a duniya,saboda ba khadeejanta ba kuma safeenarta. Wani lokaci takance. "Baisan wacce hikima Allah ya boye ba wajen barina a duniya ni kadai naci gaba da rayuwa......lokuta da dama nakanji mutuwata ce kawai ta ragemin,ina son na kwanta na huta nima,ina shauqin na tafi na ruski safeena da khadeeja ta. Kamar yau din da hotunan safeena din ke gabansu,wanda yawanci a Ethiopia aka daukesu,sai yanzu kuma wasu daga ciki da aka daukesu cikin agadez a sanda safeena din ke sharafin kyau da quruciya,kamanni na sosai suna bayyana tsakaninta da akhnan din. Sallamar akhnan din ya sanyasu maida hankalinsu dukka a kanta. Morsa safiyya tasa tafin hannunta tana share hawayen da yake kwance. A dukka tunaninta safeena ta tafi bata tafi bane,a sanda ta rasu tabar akhnan.....saidai a yanzun tana ganin safeena ne kawai daga wani sashe daban na jikin akhnan din,bawai safeena take gani completely dukanta ba. Zuciyarta ta mata sanyi sosai sanda ta binciki dabi'un akhnan din......tana cike da fata ko yaya a kanta ta samu wani abu daya da zai sake bata nutsuwa a kanta. Ta samu labarin sirri data aminta dashi......tana wata irin kyauta da sadakar da bata yarda asan ita bace....bata kuma amince sunanta ya fito ba. Taji wani irin dadi daya sanyata sakin zallar hawaye,irin sadakar safeena,irin halayyarta. Ta yiwa mutane da dama da yawan gaske alkhairi,irin alkhairin da sai bayan ranta sannan aka yita sani,sannan aka yita fadinsa,sannan yayita bayyana. A hankali ta dauke idanunta daga fuskokinsu ta maida saman hotunan dake zube a tsakiyarsu,tun bata qaraso ba kuma ta fahimci hotunan waye?. Inda ace ba'a kanta ya faru ba zata qaryata. Kaso mutum bayan rasuwarsa ka kuma kasa mancewa da soyayyarsa. Soyayyar mahaifiyarta daban ce,daban takejin soyayyarta a zuciyarta. Koda me irin sunanta taji sai taji kamar an fusgi hankalinta a kanta. Soyayya takewa me irin sunan na daban,a yanzun da take hangen hotunanta masu girma da wankuwa sosai fiye da wanda take dashi ita sai takejin wani abu yana taso mata. Sanda take zama a gurin shuru ya mamayi ko ina,sai takejin jikinta kamar wata baare a cikinsu. "Gani momma" Ta fada a hankali ba tare da tasan meye ya sanya ta fadi hakan ba. Wani abune da bata taba yinsa ba tunda suke da morsa safiyya din,abun kuwa ya saukar da murmushi saman fuskarta,ta kalli su hairaan tace dasu. "Ku bamu guri" Haka suka miqe kuwa,falaak ta dauki Aeera.....Aafreen ta dauki Aaroon,falaak ta saba anwar a kafadarta suka fice. 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 118* Batasan ya akayi ba wani numfashi ya qwace mata,zuciyarta kuma taso tsaiwa a qirjinta sakamakon dago kansa da yayi suka kuma hada idanu cikin ba zata. Da wani irin hanzari ta qwace idanunta tana jin zuciyarta tana lugude "Me yasa?" Ta tuhumi idanunta da zuciyarta da suka tunzurata kallonsa har haka. "Sheikh haisam ne fa?,ordinary malam?" Ta fadiwa kanta da kanta. Bata sake kowanne tunani ba taji me gabatarwa yana magana ta mic "Muna neman alfarma ga sheikh muhammad haisam yazo ya wakilci me martaba gurin miqa certificate na girmamawa ga zaqaquran dalibanmu". Idanu ta qanqance,zuciyarta tana matsewa a qirjinta. Wannan matsayin nata ne.....inda babu shi,banda ya wanzu a gurin itace zata wakilci sultane,sai taji wani bacin rai yana lasarta,ta sake daga idanunta tana dan satar binsa da kallo sanda yake takawa a qasaice zuwa saman steps din,duk da sunyi nufin matsowa da abun maganar gurin ya basu daga inda yake a zaune. Yadda yadin cashmere din jikinsa ke daukan idanu wani abune na daban na musamman kuma da zai sake bayyana maka tsadarsa. Hakanan tsarin dinkin da akayi masa kawai abun burgewa ne. "Yana da daukan hankali malamin nan......irinsu cikin malamai ne qalilanne......ga izza ga ilimi" Maganan ya sauka daga bayanta wadda taja hankalinta. A hankali ta soma maido da dubanta da nufin fahimtar wadanda ke maganar. Saidai kafin takai garesu ma idanunta sun nuna mata yadda dubban idanu suka raja'a a kansa kafin muryarsa me zurfin nan data sake kwarjini ta soma fita ta cikin mic din. Kujera ta musamman suka aje masa still a gurin duk da ya taso din,sannan ya karbi mic din ya fara da sallama. Kai ka sani koda ba'a gaya maka ba zaka fahimci gwani ne wajen magana cikin mutane. Sallama yayi wadda ta bada wani irin sauti me daukan hankali,dukka suka amsa suna tattara hankalinsu a kanshi. Cikin taqaitaccen lokaci ya gabatar da jawabi cikin harshen larabci,jawabin data fahimci kusan duk wanda kejin harshen larabci a gurin yana ratsashi. A nutse idanunsa da bakinsa ke juyawa,bakin dake fidda haruffan larabcin cikin wani irin zallar qwarewa da fahimtar harshen. Tana numfashi sosai taja fiddashi a hankali. Karon farko data tsaya ta saurari yaren larabci zalla irin haka da kyau,batasan me yasa ba batasan kuma dalili ba,sai taji yaren yana mata wani irin dadim da farko ta dauka ba yaren da yakai yaren abzinanci da French dadi......amma a yau sai takejin wani irin yanayi daban yana ratsata. Yana kammalawa dukkanin gurin ya dauki kabbara me qarfin gaske,mc din ya qarasa ya karbi mic din cikin girmamawar dashi kansa baisan yana yinta ba,ya saka mic din a bakinsa ya fara magana cikin yaren Tuareg. "Na jima banji tataccen larabci daya tsumani da harshe me kyau irin wannan ba......nasan dukkanin udaba'u masana yaren larabci a yanzun sheikh muhammad haisam ya tayar musu da shauqi,muna godiya sosai" Ya fada yana rusunawa. Daya bayan daya ya fara kiran 'yammatan daliban da suka cancanci girmamawar yana miqa musu certificate din,karbar certificate din daya zama jidali ga dukkan 'yammatan. Ba wadda bata bar gurin da wani irin bugun zuciya ba saboda wani irin kwarjinin tsayawa a gabansa. "Khadeeja rabi'ou sa'adou" Mc din ya kira sunan dalibar me suna khadeeja har sau biyu. Ta tsakiyar daliban ta fara takowa da dan hanzarinta. Baqar buzuwa ce wadda bata cika hasken fata ba,saidai tana da kyanta daidai gwargwado. Kallo daya ne haisam din keyi bisa al'adarsa,baya kuma d'ara hakan,ya dauke idanunsa yana miqewa a nutse,miqewar data bawa kowa mamaki. Tsaiwa dalibar tayi a gabansa,saita sad da kanta qasa kwarjininsa yana cikata,daidai sanda yayi magana da abdii dake gefansa. Murmushi abdii din yayi,ya matsa ya yiwa MC din magana,sautin murmushin Mc din ya harba ta cikin mic din yana duban kowa d'ai d'ai. Karbar nata certificate din haisam yayi,yadan duba kadan,sannan ya miqa mata,ta sanya hannu biyu ta rusuna cikin girmamawa tana karba. "Muna miqa saqon godiya ga sheikh muhammad haisam....ya miqe don karrama khadeeja da kansa,saboda ita din taci sunan mahaifiyarsa ne......dalilin wannan sheikh muhammad ya bayar ga kyauta ga kowacce daliba har na CFA 390,000 yayin daya ninka wannan adadin ga daliba khadeeja" Wani irin abune a hankali taji yana saukar mata a gangar jikinta,wani abu da batasan meye ba. A nutse ta dora idanunta akan dalibar,wadda duka duka batafi sa'ar falaak dinta ba. Idanunta sukayi kyakkyawan gani,don kuwa lura tayi da idanunta suna kan haisam din dake saukowa daga step din a nutse don komawa muhallinsa. Murmushi takeyi sosai wani irin murmushi dake nuni da farincikin da zuciyata take ciki. "Kyautar CFA 390,000 ga kowacce daliba?.....daliban da aqalla sun kusa sun tamanin?. A ina ya samu wadannan kudaden?,yasan ma abinda yake fadin yayi kyautar dashi kuwa?,yasan kuwa adadin kudaden daya ambata kuwa?" Ta tambayi kanta da kanta tana son maida idanunta kan fuskarsa,saidai zuciyarta tana gargad'arta game da hakan. "Daliba guda daya an ninka mata adadin?" Ta sake tambayar kanta tana maida idanunta kan yarinyar da tuni ta koma ta zauna. Murmushi takeyi sosai,dukkan alamu na matsanancin farinciki sun nuna akan fuskar yarinyar,lokaci lokaci tana daga idanu ta kalli sashen da haisam yake tsaye yana sallama da manyan mutanen daya samu a gurin. Wani harbawa guda daya taji zuciyarta tayi,ta lumshe idanunta tana tambayar kanta DALILI?. Saboda kawai sunanta khadeeja?,me yasa yake iya ninka kyauta saboda suna daya?. Sauke numfashi tayi sanda birra ta rusuno tana gaya mata "Zamu wuce ne ranki ya dade......yallabai yayi umarni" Idanunta ta daga a hankali ta kalli birra jin sunan data sauya masa,saita miqe a nutse abinda ya sanya hankula suka sake yowa kanta. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Bata manta ba,batayi qasa kuma a gwiwa ba ta waiwaya a hankali tana sauke idanunta ga mutum biyu dake bayanta. Suka hada idanu sai suka sakar mata murmushi. Shugabar hukumar ilimin bai d'aya ce ta qasa,hajiya nihla Ousmane......da baquwar da batasan wacece ba. Kudi kyau gami da dukiya dukkaninsu nihla tana dasu,tana cikin mata matasa masu qananun shekaru da suka samu aiki me girma cikin gwamnati,saidai duk da haka nihla din bata taba aure ba. Hada idanu sukayi,cikin girmamawa hajiya nihla wadda ta miqe tana miqawa akhnan hannu. Duk da cewa ta girmi akhnan nesa ba kusa ba.....akhnan din kamar qanwa take a gurinta,qanwar ma ta bayan baya,amma hausawa sukace sawun giwa ya take na raqumi,dole ta bawa akhnan din girma kamar nata shekarun sunfi nata. Wani kallo ta sakewa nihla din na cikin idanu,'yan abun miskilanci sun motsa,a nutse cikin wannan fuskar da sarauta da izza ke kaiwa suna kawowa ta zare idanunta,ba tare data maidawa nihla hannunta su gaisa ba.......ta zare idanunta tana juyawa a nutse ta fara takawa su birra suna take mata baya. A nutse sukaja da baya sanda take dab da riskarsa. Yana takawa hankali kwance yana amsa waya da hausarsa da bata gama fita gaba daya. Idanunta ta lumshe tana budesu,tana tuna komai daya faru a yanzu. Damuwarta alqawarin daya dauka na kudade masu nauyi da yace zai bayar ga daliban. Ta sani,baida abinda zai iya biyan wadannan kudaden daya ambata,zai karya siffarsa yayi musu qarya ya gudu?,ko kuma karba daga lalitar mahaifinta da sunan shine ya bayar?. Haka kawai a jikinta taji bata gamsu da dukkanin wadannan amsoshin ba. A jikinta take jin indai wannan mutumin ne.....indai wannan malaminne ba daya daga ciki da zaiyi. Ta saci kallonsa kadan sanda ya sake matsawa da kansa ya kuma bude mata qofar motar a karo na biyu. Ganin zai waiwayo ta dauke dubanta a kansa. Tana jin wani d'aci a ranta,wannan nutsuwar rashin fushin da take gani saman fuskarsa bata sonsu. Ko data maida idanunta sai taga seat din gaba ya bude mata. Mamaki yadan kamata,a iya rayuwarta idan ba Niamey ta shiga ba bata taba zama gaban mota,kullum a baya take,driver yana janta. Ta sake daga idanunta cikin alamun rashin fahimta tana dubansa,tsareta yayi da kallo da wannan zafafan idanun nasa,sannan ya mata sign din ta shiga. Wannan zuciyar.....wannan kwanyar data soma jin haushinsu sai suka bata qwarin gwiwar shiga din. Ta sauke numfashi me nauyi sanda ta daidaita cikin seat din. Wai me yake faruwa?,me yasa komai ya juye?,me yasa komai ya sauya daga asalin yadda yake?. Shi ya kamata ya zama cikakken d'an rakiya a idanun kowa.....amma ita ta buge da zama 'yar rakiyar.....shi ya kamata ya shiga qunci kunyata da takura amma ita dince ranta a bace bashi ba......me yasa haka?. "Bismillah" Taji an ambata a hankali. Wani irin baqon yanayi ne a hankali ya mamayeta,qamshinsa yana sake kusantarta da wani irin yanayi dake jefa zuciyarta zuwa ga wani irin shauqi. Ta saba jin hakan a duk sanda qamshin zai bugeta,zuciyarta wasai.....qirjinta wasai,nutsuwa kuma zataji tana mamayarta. Wannan zuciyar dake bugawa cikin qirjinta itace ta soma tambayarta SHI ZAI DRIVING?.....ina driver na?. Zuciyarta taci gaba da bugawa cikin qirjinta da tsoro,tana tsoro kada bai iya motar ba....kada yayi ganganci da rayuwarta,abinda ya sanyata bude idanunta da sauri,daidai sanda ya miqa hannunsa don kunna motar. Da wani irin tsoro ta miqa hannunta da zummar dakatar dashi,tafin hannunta ya sauka a bayan hannunsa,dumin jikin junansu ya harba cikin kowacce magudanar jini ta jikinsu,yakai kuma saqo kwanyarsu. A tare kuma lokaci guda wuta ta daukewa dukkaninsu. Ya daga idanunsa a hankali ya aza saman nata adam apple dinsa yana motsawa da wani irin sauri. Kaifi da tasirin idanunsa suka ratsata,tunaninta da jinin jikinta suka koma daidai,ta samu nasarar janye hannunta da sauri daga saman nasa. Kauda kanta tayi tana son bugun zuciyarta ya daidaita sosai. Me yasa taketa yin shirme ne?,me yasa ta kasa mallakar kanta?,me yasa taketa abubuwan da bai kamata tayisu ba?. Idan ya rainata fa?,idan ya zaci wani abu a kanta fa?. Saita lumshe idanunta sanda taji ya tayar da motar,cikin wani irin coolness yayi reverse ya soma fita da ita daga gurin. Sai daya daidaita motar saman kwalta sannan ya miqa hannu ya kunna A.c din motar saboda yadda yakejin kamar suna cudayyar numfashi da yawa shi da ita. Wani irin shuru ya ratsa motar,tuqi yake cikin nutsuwa mutuwar jiki da kuma kasala. idanunsa akan lafiyayyar kwaltar dake shimfide saman titin,koda batayi magana ba yasan tanason sanin inda zai kaisu ne,bai kuma shirya magana da ita ba. Yanaso ta fahimci IKO da yake dashi a kanta......yanaso ta fahimci maganarsa dama tsarikansa sama suke da nata. Sai ya fara zare mata UMARNIN MAMMINA daga ranta gaba daya,sai ya fara fahimtar da ita tana da wata rayuwa......tana da wani umarni......tana da wani IKO sama da ikon mammina saman wuyanta. Sai ya fara tabbatarwa mammina akwai tazara yanzu tsakaninta da ita,sai ya fara koyar da mammina akwai wani QARFIN IKO daya fara mallaka daga cikin nata kason ikon. Sanda ya rage gudun da yake ya gangara zuwa wani street din daban saita bude idanunta a hankali. Mamaki ya sake cikata ganin ba kowa tare dasu. Basu birra,ba sauran guard's dinta maza da suke kula da tsaronta a duk sanda zasu fita din. Idanu tabi ginin dashi,tunda take a agadez ma batasan gurin ba,saidai koda ba'a gaya mata ba,ta fahimci kodai hotel ko kuma wani hamshaqin guests in dinne. Amma kuma gaba daya ba symbol ba alamu na sunan gurin,saidai girma da tsaruwar ginin kawai ya sanya ta gaza gasgata gida ne. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1,000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 119* Ta daga idanunta sanda aka zuge makeken gate din tana duban layin. Dukka gidajene a tsare masu matuqar daukan hankali da bada sha'awa. Wani qawataccen parking lot ya sanya motar,bai wani damu da daidaita tsaiwarta a gurin ba yadda ya dace,abinda zai nuna maka alamun ikon da yake dashi a gurin. Wani farin matashine sanye da baqaqen uniform ya qaraso,ya kuma rusuna ta bakin window din. Batasan me haisam din ya miqa masa ba,kamar yadda bataji me yace dashi ba tunda yayi magana dashi ne da wani yare da batasan wanne yare bane,amma.kamar tana jin wani sashe na yaren daga bakin morsa safiyya ko mammina jifa jifa. Maida glass din yayi ya rufe "Alhamdulillah" Taji ya furta can qasa da muryarsa me nauyin nan.dogayen yatsunsa ya sanya ya kwashe wayoyinsa dake gurin,sannan ya zura qafarsa ya fita,sai a sannan ya lura da yayyafin daya fara sauka. Ya taka a hankali ya zagaya inda seat dinta,yasa hannu yana sake bude mata motar. Manyan blue eyes dinnan nata da hasken garin da bame kaifi ba saboda yanayin hadari ta daga tana dubansa dasu. Still da ido ya sake mata maganar ta fito. Sauke qwayar idonta tayi,me yasa idanunta da zuciyarta dukka basa iya qureshi da wannan kallon nata dake nunawa mutum kuskure idan ya mata abu?,me yasa basa iya jurewa ne?. Wanne irin izza gareshi haka da zai dinga tafi da ita da umarni da idanu kawai?. Aurensa tayi ne don yayita bata umarni?,anya mammina bata sake cutarta ba?,anya bata jefata inda ba zata taba fita ba?. Bata hangi ta inda wannan kafaffen me shegen izza da girman kai zai sallameta ba. Bataga muhallin da maganganun mammina zasu samu gurin zama ba. "Fito" Yayi magana a karo na farko yana dubanta. Umarnin nan na kai tsaye,magana da izzar nan ya fara cikata,ta tattara dukka jarumtarta guri daya. "Bazan sauka ba,don nan din ba gidana bane" Tayi maganan tanason nuna jarumta,saidai tsakiyar hakan ya hangi tsoro qarara tattare da ita. Wani siririn murmushi ya subuce masa can qasan zuciyarsa ba tare da hakan ya bayyana akan fuskarsa ba. Dole saita nuna yanayin tata jajircewar,kuma alhalin idanunta suna qaryatata suna kuma bada ita wajen fallasa masa labarin zuciyarta. Kyam ya tsaya da dukka wannan tsahon nasa daya biyu da murjajjen jikinsa ya nada structure me kyau. Wani kallo yake aje mata,irin kallon da zai sanya har cikin jininka kaji ana aunaka ne,ya zuqi iska ya fesar,ya daga kansa yana kallon sama dake zubda wani yayyafi siri siri,ya sauke kansa a hankali a kanta karo na biyu. "Ki sauka" Ya kuma maimaitawa hankali kwance. Fusatattun idanunta ta daga tana dubansa,yadda yake magana hankali kwance kaman baisan yana tana ranta ko yana bata mata rai ba shine abinda yafi komai baqanta mata "Na fadi maka nan din ba gidana bane". "Na sani" Ya amsa mata a nutse yana duban yanayin fushinta da yadda izzarta take magana. Idanunta ta mayar gefe,tana jin hawaye suna son ciko mata amma ta hana hakan faruwa. Tanaji a ranta yanason nuna mata iko,yana son karyata da izzarsa,ita kuma karaya da faduwa wasu abubuwa ne da bata yarda dasu a rayuwarta ba. Agogonsa ya daga ya kalla a tsanake,muhimmiyar magana zasuyi da omar da shine ya jagoranci zaman da aikin da kansa. Bai saba bata lokaci ba,bai saba saba magana ko canza lokaci ba,baya so kuma ayau ya fara,saboda aikine me girman gaske. "Kina da zabi biyu......daqiqa goma kawai zan baki ki tunani....ko ki saiko da qafafunki ki shiga.....ko na maida motar na rufe ki zauna ciki,don bazaki koma gida ke daya ba". Mamaki ya sake kamata,sai kawai taji hawayen suna shirin gangaro mata,tayi saurin sadda kanta qasa. A rayuwarta ba'a taba matsanta mata haka ba.....a rayuwarta bata taba ganin juyawa da bada umarni kai tsaye irin haka ba. Tana baqincikin yadda SHURUNSA kadai yake da ikon sarrafata.....tana takaicin yadda ya samu ikon sarrafata da sauqi haka ta cikin qwayar idanunsa kawai. Kamar yana gaya mata ne a sauqaqe IKO BAYA BUQATAR HAYANIYA. "Sakanninki suna dab da cika...." "Bazan shiga ba.....ni ban yarda ba" Ta fada still tana jin zuciyarta tana quna. Abu na farko da yafi tsana MUSU TAURIN KAI abinda ya sanya Aanani qanwarsa tasha wahala sosai a hannunsa kenan har sai daya lanqwasata ta koma tsarin tarbiyyar qabilad oromo. Hannunsa guda daya ya dora saman roofing motar,ya sunkuyar da kansa sosai samanta kamar me shirin mata rumfa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Wannan tsaiwar da yayi saman kanta.....wannan kusancin daya qara a tsakaninsu ya qarasa tsinke duk wata jijiya a jikinta dake bata qwarin gwiwa da damar yin musu. "Dole ki shiga duk inda na kaiki gimbiya akhhnaan" Wani abu yaso sarqe numfashinta yadda ya furta sunan da hausar nan tasa da bata zama tattacciya ba,yadda taji iskar bakinsa dake gauraye da qamshin mint leaves ta fito a hankali tana sauka a fuskarta,sai komai ya qarasa jagule mata,lissafin ya fara harhadar mata guri guda. "Second uku ya rage miki.....ko kikai kanki da qafanki....ko kum...." Bata tsaya ya qarasa fadi ba ta sauke qafarta ta farko a qasa ganin yaja baya yana nade hannun rigarsa. Sai ya dakata da abinda yakeyi a nutse,ya matsa gaban motar ya bude mata murfin sosai yadda zataji dadin fita gaba daya,yayin da idanunsa suka sauka kan zara zara yatsun hannunta data damqe wayarta da kyau a ciki,sai yaga kaman hannun nata rawa yake kadan. "Matsoraciya" Ya fadi can qasan ransa yana sake gasgata kalar tsoron daya gani shimfide a idanunta dazun. Gaba yayi ta soma binsa a baya a hankali,murmushi ya qwace masa kadan bayan wani tunani ya d'arsu a ransa,ya kuma furta "Allah ya sawwaqe" Ya sani wataqila zuciyarta tana raya mata zai nema tarayya ne da ita.....shi ya saukar mata da wannan tsoron?. Ko daya baima shiryawa kalar wannan rayuwar ba,bada ita bama da kowacce mace,koda zai karba yana jira ne daga halittar data mutu a sonshi ne,ba wadda bai tunanin ba qaddarar halittar so a tsakaninsu ba. Tun daga qofar farko data kasance kamar wani lobby ne tsararre idan an budeta mamaki ya cikata. Cikin gidan yafi wajen kyau,wani irin tsari ne me daukan hankali daya kusa kulle mata kai. "Gidan su waye ya kawoni?" Abinda take fadiwa kanta kenan. Gaba daya ta gama tsinkewa sanda sukabi wani dogo kuma siririn hallway,sai taga sun bace daga ainihin lobby din sun balla wani dan guri kamar reception sannan suka sake shiga wata qofa data kaisu wani irin parlor. Kai tsaye ba zatace parlor bane,kuma bai kamanda bedroom ba,hakanan bai kama da office ba,amma dukka zai iya daukan wadannan ma'anonin gaba daya. Akwai wasu irin lafiyayyun sofas da zaka iya maidasu gado ko kujera da aka qawata gurin. Wasu iri marbles masu tsananin kashe idanu da daukan hankali,wasu irin curtains da suke fusgar idanu,dunqulallen table madaidaici sai qananun side tables da aka qawata tsakanin kujerun dasu. Wani irin freezer dispenser da qawatattun trays da cups da butucin shayi masu tsananin kyau. Komai na gurin fari ne qal ba wani sirki ko kadan,banda daukan idanu ba abinda yakeyi. Gagara zama tayi,sosai take jin kanta a baqon guri,shi kansa gurin kwarjini da daukan hankali ne dashi. A nutse kuma kansa tsaye taga yana ci gaba da takawa. Ya fara zare rigar alkyabbar saman kayan nasa a wani irin nutsuwa,abinda ya sake nuna fadin kafadunsa da kuma murjajjen jikinsa ta cikin doguwar rigar cashmere din ta sama da aka mata dinki me zubin kaftaan. Jikin wani abun rataye kaya me qyalli dake tsaye da qafafunsa ya rataye rigar,sai ya taka gaba kadan yana cire agogonsa yana ajiyewa,ya jawo wani qaramin na'ura ba tare da saninta ba ya soma searching network din wayarta yayi connecting da na'urar,sannan yayi disabled na network dinta. Baya buqatar doguwar magana ta hanyar amsar wayarta da kasheta,amma kuma baya buqatar kowa ya kirata ya sameta ko ita ta sameshi. Yanason tsahon awannin da zasu zauna cikin gidan a rasa gane inda suke. Yanason hankalin mammina ya tashi koda na wunin yau ne kawai,yanason ta kasa nutsuwa,yanaso tayita cigiyarsu ba tare data isa tayi cigiyar tasu a fili ba......wannan din kadan tashi da hankalin Aareef yayi ne.....shine dan abinda zai iya rama masa dashi sanda tasa akayi attacking nasu,bawai kuma don yaji ciwo ba,don subul ya fita,motii ne kawai yadan buge kadan a qafar hagunsa.. A nutse ya maida na'urar yadda ba zata lura da ita ba,ya miqe ba tare daya kalleta ba dai,ya fara takawa yana nufar waje. "Ki duba ko ina ki dauki abinda kike buqata.....idan baki samu bama ki danna madannin dake jikin switch na fitilan can,za'a zo a saurari buqatarki. "Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana jin tsoro yana shigarta. Tsoron yadda zai fita ya barta a gurin da yake mata wani irin kwarjini,ta yaya zai killaceta haka ita kadai?. "Zaki zauna ki jira har zuwa sanda zan kammala tattaunawa da mutane". " You speak as if......" "As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da tataccen turancin nan da ko yaushe nasa yana fita da wani tone saboda zaman yaren oromo a bakinsa. Idanunsa sun mata nauyi,saboda ya datsi numfashinta ne ya fada kai tsaye yana kuma waiwayowa bayan ya tsaya daga bakin qofar. "Yes.....because you're" Ya qarasa bata cikakkiyar amsa. "Amma ni ba yarinya bace" Ta maida masa tana qoqarin tattara qarfin halinta. Murmushi yayi can qasan zuciyarsa,wannan qarfin halin nata da kafiyarta yana fusgarshi wani lokaci. "Na sani.....yara basa cikin tsarin mammina.....shi yasa na gasgata ke ba qanqanuwar yarinya bace me girma gimbiya......amma dai....ni nake da zabin sanda zamu tafi.....rest well" Ya furta yana saluting nata sannan ya juya a nutse yana ficewa. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 120* Ta daga idanunta sanda aka zuge makeken gate din tana duban layin. Dukka gidajene a tsare masu matuqar daukan hankali da bada sha'awa. Wani qawataccen parking lot ya sanya motar,bai wani damu da daidaita tsaiwarta a gurin ba yadda ya dace,abinda zai nuna maka alamun ikon da yake dashi a gurin. Wani farin matashine sanye da baqaqen uniform ya qaraso,ya kuma rusuna ta bakin window din. Batasan me haisam din ya miqa masa ba,kamar yadda bataji me yace dashi ba tunda yayi magana dashi ne da wani yare da batasan wanne yare bane,amma.kamar tana jin wani sashe na yaren daga bakin morsa safiyya ko mammina jifa jifa. Maida glass din yayi ya rufe "Alhamdulillah" Taji ya furta can qasa da muryarsa me nauyin nan.dogayen yatsunsa ya sanya ya kwashe wayoyinsa dake gurin,sannan ya zura qafarsa ya fita,sai a sannan ya lura da yayyafin daya fara sauka. Ya taka a hankali ya zagaya inda seat dinta,yasa hannu yana sake bude mata motar. Manyan blue eyes dinnan nata da hasken garin da bame kaifi ba saboda yanayin hadari ta daga tana dubansa dasu. Still da ido ya sake mata maganar ta fito. Sauke qwayar idonta tayi,me yasa idanunta da zuciyarta dukka basa iya qureshi da wannan kallon nata dake nunawa mutum kuskure idan ya mata abu?,me yasa basa iya jurewa ne?. Wanne irin izza gareshi haka da zai dinga tafi da ita da umarni da idanu kawai?. Aurensa tayi ne don yayita bata umarni?,anya mammina bata sake cutarta ba?,anya bata jefata inda ba zata taba fita ba?. Bata hangi ta inda wannan kafaffen me shegen izza da girman kai zai sallameta ba. Bataga muhallin da maganganun mammina zasu samu gurin zama ba. "Fito" Yayi magana a karo na farko yana dubanta. Umarnin nan na kai tsaye,magana da izzar nan ya fara cikata,ta tattara dukka jarumtarta guri daya. "Bazan sauka ba,don nan din ba gidana bane" Tayi maganan tanason nuna jarumta,saidai tsakiyar hakan ya hangi tsoro qarara tattare da ita. Wani siririn murmushi ya subuce masa can qasan zuciyarsa ba tare da hakan ya bayyana akan fuskarsa ba. Dole saita nuna yanayin tata jajircewar,kuma alhalin idanunta suna qaryatata suna kuma bada ita wajen fallasa masa labarin zuciyarta. Kyam ya tsaya da dukka wannan tsahon nasa daya biyu da murjajjen jikinsa ya nada structure me kyau. Wani kallo yake aje mata,irin kallon da zai sanya har cikin jininka kaji ana aunaka ne,ya zuqi iska ya fesar,ya daga kansa yana kallon sama dake zubda wani yayyafi siri siri,ya sauke kansa a hankali a kanta karo na biyu. "Ki sauka" Ya kuma maimaitawa hankali kwance. Fusatattun idanunta ta daga tana dubansa,yadda yake magana hankali kwance kaman baisan yana tana ranta ko yana bata mata rai ba shine abinda yafi komai baqanta mata "Na fadi maka nan din ba gidana bane". "Na sani" Ya amsa mata a nutse yana duban yanayin fushinta da yadda izzarta take magana. Idanunta ta mayar gefe,tana jin hawaye suna son ciko mata amma ta hana hakan faruwa. Tanaji a ranta yanason nuna mata iko,yana son karyata da izzarsa,ita kuma karaya da faduwa wasu abubuwa ne da bata yarda dasu a rayuwarta ba. Agogonsa ya daga ya kalla a tsanake,muhimmiyar magana zasuyi da omar da shine ya jagoranci zaman da aikin da kansa. Bai saba bata lokaci ba,bai saba saba magana ko canza lokaci ba,baya so kuma ayau ya fara,saboda aikine me girman gaske. "Kina da zabi biyu......daqiqa goma kawai zan baki ki tunani....ko ki saiko da qafafunki ki shiga.....ko na maida motar na rufe ki zauna ciki,don bazaki koma gida ke daya ba". Mamaki ya sake kamata,sai kawai taji hawayen suna shirin gangaro mata,tayi saurin sadda kanta qasa. A rayuwarta ba'a taba matsanta mata haka ba.....a rayuwarta bata taba ganin juyawa da bada umarni kai tsaye irin haka ba. Tana baqincikin yadda SHURUNSA kadai yake da ikon sarrafata.....tana takaicin yadda ya samu ikon sarrafata da sauqi haka ta cikin qwayar idanunsa kawai. Kamar yana gaya mata ne a sauqaqe IKO BAYA BUQATAR HAYANIYA. "Sakanninki suna dab da cika...." "Bazan shiga ba.....ni ban yarda ba" Ta fada still tana jin zuciyarta tana quna. Abu na farko da yafi tsana MUSU TAURIN KAI abinda ya sanya Aanani qanwarsa tasha wahala sosai a hannunsa kenan har sai daya lanqwasata ta koma tsarin tarbiyyar qabilad oromo. Hannunsa guda daya ya dora saman roofing motar,ya sunkuyar da kansa sosai samanta kamar me shirin mata rumfa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Wannan tsaiwar da yayi saman kanta.....wannan kusancin daya qara a tsakaninsu ya qarasa tsinke duk wata jijiya a jikinta dake bata qwarin gwiwa da damar yin musu. "Dole ki shiga duk inda na kaiki gimbiya akhhnaan" Wani abu yaso sarqe numfashinta yadda ya furta sunan da hausar nan tasa da bata zama tattacciya ba,yadda taji iskar bakinsa dake gauraye da qamshin mint leaves ta fito a hankali tana sauka a fuskarta,sai komai ya qarasa jagule mata,lissafin ya fara harhadar mata guri guda. "Second uku ya rage miki.....ko kikai kanki da qafanki....ko kum...." Bata tsaya ya qarasa fadi ba ta sauke qafarta ta farko a qasa ganin yaja baya yana nade hannun rigarsa. Sai ya dakata da abinda yakeyi a nutse,ya matsa gaban motar ya bude mata murfin sosai yadda zataji dadin fita gaba daya,yayin da idanunsa suka sauka kan zara zara yatsun hannunta data damqe wayarta da kyau a ciki,sai yaga kaman hannun nata rawa yake kadan. "Matsoraciya" Ya fadi can qasan ransa yana sake gasgata kalar tsoron daya gani shimfide a idanunta dazun. Gaba yayi ta soma binsa a baya a hankali,murmushi ya qwace masa kadan bayan wani tunani ya d'arsu a ransa,ya kuma furta "Allah ya sawwaqe" Ya sani wataqila zuciyarta tana raya mata zai nema tarayya ne da ita.....shi ya saukar mata da wannan tsoron?. Ko daya baima shiryawa kalar wannan rayuwar ba,bada ita bama da kowacce mace,koda zai karba yana jira ne daga halittar data mutu a sonshi ne,ba wadda bai tunanin ba qaddarar halittar so a tsakaninsu ba. Tun daga qofar farko data kasance kamar wani lobby ne tsararre idan an budeta mamaki ya cikata. Cikin gidan yafi wajen kyau,wani irin tsari ne me daukan hankali daya kusa kulle mata kai. "Gidan su waye ya kawoni?" Abinda take fadiwa kanta kenan. Gaba daya ta gama tsinkewa sanda sukabi wani dogo kuma siririn hallway,sai taga sun bace daga ainihin lobby din sun balla wani dan guri kamar reception sannan suka sake shiga wata qofa data kaisu wani irin parlor. Kai tsaye ba zatace parlor bane,kuma bai kamanda bedroom ba,hakanan bai kama da office ba,amma dukka zai iya daukan wadannan ma'anonin gaba daya. Akwai wasu irin lafiyayyun sofas da zaka iya maidasu gado ko kujera da aka qawata gurin. Wasu iri marbles masu tsananin kashe idanu da daukan hankali,wasu irin curtains da suke fusgar idanu,dunqulallen table madaidaici sai qananun side tables da aka qawata tsakanin kujerun dasu. Wani irin freezer dispenser da qawatattun trays da cups da butucin shayi masu tsananin kyau. Komai na gurin fari ne qal ba wani sirki ko kadan,banda daukan idanu ba abinda yakeyi. Gagara zama tayi,sosai take jin kanta a baqon guri,shi kansa gurin kwarjini da daukan hankali ne dashi. A nutse kuma kansa tsaye taga yana ci gaba da takawa. Ya fara zare rigar alkyabbar saman kayan nasa a wani irin nutsuwa,abinda ya sake nuna fadin kafadunsa da kuma murjajjen jikinsa ta cikin doguwar rigar cashmere din ta sama da aka mata dinki me zubin kaftaan. Jikin wani abun rataye kaya me qyalli dake tsaye da qafafunsa ya rataye rigar,sai ya taka gaba kadan yana cire agogonsa yana ajiyewa,ya jawo wani qaramin na'ura ba tare da saninta ba ya soma searching network din wayarta yayi connecting da na'urar,sannan yayi disabled na network dinta. Baya buqatar doguwar magana ta hanyar amsar wayarta da kasheta,amma kuma baya buqatar kowa ya kirata ya sameta ko ita ta sameshi. Yanason tsahon awannin da zasu zauna cikin gidan a rasa gane inda suke. Yanason hankalin mammina ya tashi koda na wunin yau ne kawai,yanason ta kasa nutsuwa,yanaso tayita cigiyarsu ba tare data isa tayi cigiyar tasu a fili ba......wannan din kadan tashi da hankalin Aareef yayi ne.....shine dan abinda zai iya rama masa dashi sanda tasa akayi attacking nasu,bawai kuma don yaji ciwo ba,don subul ya fita,motii ne kawai yadan buge kadan a qafar hagunsa.. A nutse ya maida na'urar yadda ba zata lura da ita ba,ya miqe ba tare daya kalleta ba dai,ya fara takawa yana nufar waje. "Ki duba ko ina ki dauki abinda kike buqata.....idan baki samu bama ki danna madannin dake jikin switch na fitilan can,za'a zo a saurari buqatarki. "Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana jin tsoro yana shigarta. Tsoron yadda zai fita ya barta a gurin da yake mata wani irin kwarjini,ta yaya zai killaceta haka ita kadai?. "Zaki zauna ki jira har zuwa sanda zan kammala tattaunawa da mutane". " You speak as if......" "As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da tataccen turancin nan da ko yaushe nasa yana fita da wani tone saboda zaman yaren oromo a bakinsa. Idanunsa sun mata nauyi,saboda ya datsi numfashinta ne ya fada kai tsaye yana kuma waiwayowa bayan ya tsaya daga bakin qofar. "Yes.....because you're" Ya qarasa bata cikakkiyar amsa. "Amma ni ba yarinya bace" Ta maida masa tana qoqarin tattara qarfin halinta. Murmushi yayi can qasan zuciyarsa,wannan qarfin halin nata da kafiyarta yana fusgarshi wani lokaci. "Na sani.....yara basa cikin tsarin mammina.....shi yasa na gasgata ke ba qanqanuwar yarinya bace me girma gimbiya......amma dai....ni nake da zabin sanda zamu tafi.....rest well" Ya furta yana saluting nata sannan ya juya a nutse yana ficewa. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 121* Ta daga idanunta sanda aka zuge makeken gate din tana duban layin. Dukka gidajene a tsare masu matuqar daukan hankali da bada sha'awa. Wani qawataccen parking lot ya sanya motar,bai wani damu da daidaita tsaiwarta a gurin ba yadda ya dace,abinda zai nuna maka alamun ikon da yake dashi a gurin. Wani farin matashine sanye da baqaqen uniform ya qaraso,ya kuma rusuna ta bakin window din. Batasan me haisam din ya miqa masa ba,kamar yadda bataji me yace dashi ba tunda yayi magana dashi ne da wani yare da batasan wanne yare bane,amma.kamar tana jin wani sashe na yaren daga bakin morsa safiyya ko mammina jifa jifa. Maida glass din yayi ya rufe "Alhamdulillah" Taji ya furta can qasa da muryarsa me nauyin nan.dogayen yatsunsa ya sanya ya kwashe wayoyinsa dake gurin,sannan ya zura qafarsa ya fita,sai a sannan ya lura da yayyafin daya fara sauka. Ya taka a hankali ya zagaya inda seat dinta,yasa hannu yana sake bude mata motar. Manyan blue eyes dinnan nata da hasken garin da bame kaifi ba saboda yanayin hadari ta daga tana dubansa dasu. Still da ido ya sake mata maganar ta fito. Sauke qwayar idonta tayi,me yasa idanunta da zuciyarta dukka basa iya qureshi da wannan kallon nata dake nunawa mutum kuskure idan ya mata abu?,me yasa basa iya jurewa ne?. Wanne irin izza gareshi haka da zai dinga tafi da ita da umarni da idanu kawai?. Aurensa tayi ne don yayita bata umarni?,anya mammina bata sake cutarta ba?,anya bata jefata inda ba zata taba fita ba?. Bata hangi ta inda wannan kafaffen me shegen izza da girman kai zai sallameta ba. Bataga muhallin da maganganun mammina zasu samu gurin zama ba. "Fito" Yayi magana a karo na farko yana dubanta. Umarnin nan na kai tsaye,magana da izzar nan ya fara cikata,ta tattara dukka jarumtarta guri daya. "Bazan sauka ba,don nan din ba gidana bane" Tayi maganan tanason nuna jarumta,saidai tsakiyar hakan ya hangi tsoro qarara tattare da ita. Wani siririn murmushi ya subuce masa can qasan zuciyarsa ba tare da hakan ya bayyana akan fuskarsa ba. Dole saita nuna yanayin tata jajircewar,kuma alhalin idanunta suna qaryatata suna kuma bada ita wajen fallasa masa labarin zuciyarta. Kyam ya tsaya da dukka wannan tsahon nasa daya biyu da murjajjen jikinsa ya nada structure me kyau. Wani kallo yake aje mata,irin kallon da zai sanya har cikin jininka kaji ana aunaka ne,ya zuqi iska ya fesar,ya daga kansa yana kallon sama dake zubda wani yayyafi siri siri,ya sauke kansa a hankali a kanta karo na biyu. "Ki sauka" Ya kuma maimaitawa hankali kwance. Fusatattun idanunta ta daga tana dubansa,yadda yake magana hankali kwance kaman baisan yana tana ranta ko yana bata mata rai ba shine abinda yafi komai baqanta mata "Na fadi maka nan din ba gidana bane". "Na sani" Ya amsa mata a nutse yana duban yanayin fushinta da yadda izzarta take magana. Idanunta ta mayar gefe,tana jin hawaye suna son ciko mata amma ta hana hakan faruwa. Tanaji a ranta yanason nuna mata iko,yana son karyata da izzarsa,ita kuma karaya da faduwa wasu abubuwa ne da bata yarda dasu a rayuwarta ba. Agogonsa ya daga ya kalla a tsanake,muhimmiyar magana zasuyi da omar da shine ya jagoranci zaman da aikin da kansa. Bai saba bata lokaci ba,bai saba saba magana ko canza lokaci ba,baya so kuma ayau ya fara,saboda aikine me girman gaske. "Kina da zabi biyu......daqiqa goma kawai zan baki ki tunani....ko ki saiko da qafafunki ki shiga.....ko na maida motar na rufe ki zauna ciki,don bazaki koma gida ke daya ba". Mamaki ya sake kamata,sai kawai taji hawayen suna shirin gangaro mata,tayi saurin sadda kanta qasa. A rayuwarta ba'a taba matsanta mata haka ba.....a rayuwarta bata taba ganin juyawa da bada umarni kai tsaye irin haka ba. Tana baqincikin yadda SHURUNSA kadai yake da ikon sarrafata.....tana takaicin yadda ya samu ikon sarrafata da sauqi haka ta cikin qwayar idanunsa kawai. Kamar yana gaya mata ne a sauqaqe IKO BAYA BUQATAR HAYANIYA. "Sakanninki suna dab da cika...." "Bazan shiga ba.....ni ban yarda ba" Ta fada still tana jin zuciyarta tana quna. Abu na farko da yafi tsana MUSU TAURIN KAI abinda ya sanya Aanani qanwarsa tasha wahala sosai a hannunsa kenan har sai daya lanqwasata ta koma tsarin tarbiyyar qabilad oromo. Hannunsa guda daya ya dora saman roofing motar,ya sunkuyar da kansa sosai samanta kamar me shirin mata rumfa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Wannan tsaiwar da yayi saman kanta.....wannan kusancin daya qara a tsakaninsu ya qarasa tsinke duk wata jijiya a jikinta dake bata qwarin gwiwa da damar yin musu. "Dole ki shiga duk inda na kaiki gimbiya akhhnaan" Wani abu yaso sarqe numfashinta yadda ya furta sunan da hausar nan tasa da bata zama tattacciya ba,yadda taji iskar bakinsa dake gauraye da qamshin mint leaves ta fito a hankali tana sauka a fuskarta,sai komai ya qarasa jagule mata,lissafin ya fara harhadar mata guri guda. "Second uku ya rage miki.....ko kikai kanki da qafanki....ko kum...." Bata tsaya ya qarasa fadi ba ta sauke qafarta ta farko a qasa ganin yaja baya yana nade hannun rigarsa. Sai ya dakata da abinda yakeyi a nutse,ya matsa gaban motar ya bude mata murfin sosai yadda zataji dadin fita gaba daya,yayin da idanunsa suka sauka kan zara zara yatsun hannunta data damqe wayarta da kyau a ciki,sai yaga kaman hannun nata rawa yake kadan. "Matsoraciya" Ya fadi can qasan ransa yana sake gasgata kalar tsoron daya gani shimfide a idanunta dazun. Gaba yayi ta soma binsa a baya a hankali,murmushi ya qwace masa kadan bayan wani tunani ya d'arsu a ransa,ya kuma furta "Allah ya sawwaqe" Ya sani wataqila zuciyarta tana raya mata zai nema tarayya ne da ita.....shi ya saukar mata da wannan tsoron?. Ko daya baima shiryawa kalar wannan rayuwar ba,bada ita bama da kowacce mace,koda zai karba yana jira ne daga halittar data mutu a sonshi ne,ba wadda bai tunanin ba qaddarar halittar so a tsakaninsu ba. Tun daga qofar farko data kasance kamar wani lobby ne tsararre idan an budeta mamaki ya cikata. Cikin gidan yafi wajen kyau,wani irin tsari ne me daukan hankali daya kusa kulle mata kai. "Gidan su waye ya kawoni?" Abinda take fadiwa kanta kenan. Gaba daya ta gama tsinkewa sanda sukabi wani dogo kuma siririn hallway,sai taga sun bace daga ainihin lobby din sun balla wani dan guri kamar reception sannan suka sake shiga wata qofa data kaisu wani irin parlor. Kai tsaye ba zatace parlor bane,kuma bai kamanda bedroom ba,hakanan bai kama da office ba,amma dukka zai iya daukan wadannan ma'anonin gaba daya. Akwai wasu irin lafiyayyun sofas da zaka iya maidasu gado ko kujera da aka qawata gurin. Wasu iri marbles masu tsananin kashe idanu da daukan hankali,wasu irin curtains da suke fusgar idanu,dunqulallen table madaidaici sai qananun side tables da aka qawata tsakanin kujerun dasu. Wani irin freezer dispenser da qawatattun trays da cups da butucin shayi masu tsananin kyau. Komai na gurin fari ne qal ba wani sirki ko kadan,banda daukan idanu ba abinda yakeyi. Gagara zama tayi,sosai take jin kanta a baqon guri,shi kansa gurin kwarjini da daukan hankali ne dashi. A nutse kuma kansa tsaye taga yana ci gaba da takawa. Ya fara zare rigar alkyabbar saman kayan nasa a wani irin nutsuwa,abinda ya sake nuna fadin kafadunsa da kuma murjajjen jikinsa ta cikin doguwar rigar cashmere din ta sama da aka mata dinki me zubin kaftaan. Jikin wani abun rataye kaya me qyalli dake tsaye da qafafunsa ya rataye rigar,sai ya taka gaba kadan yana cire agogonsa yana ajiyewa,ya jawo wani qaramin na'ura ba tare da saninta ba ya soma searching network din wayarta yayi connecting da na'urar,sannan yayi disabled na network dinta. Baya buqatar doguwar magana ta hanyar amsar wayarta da kasheta,amma kuma baya buqatar kowa ya kirata ya sameta ko ita ta sameshi. Yanason tsahon awannin da zasu zauna cikin gidan a rasa gane inda suke. Yanason hankalin mammina ya tashi koda na wunin yau ne kawai,yanason ta kasa nutsuwa,yanaso tayita cigiyarsu ba tare data isa tayi cigiyar tasu a fili ba......wannan din kadan tashi da hankalin Aareef yayi ne.....shine dan abinda zai iya rama masa dashi sanda tasa akayi attacking nasu,bawai kuma don yaji ciwo ba,don subul ya fita,motii ne kawai yadan buge kadan a qafar hagunsa.. A nutse ya maida na'urar yadda ba zata lura da ita ba,ya miqe ba tare daya kalleta ba dai,ya fara takawa yana nufar waje. "Ki duba ko ina ki dauki abinda kike buqata.....idan baki samu bama ki danna madannin dake jikin switch na fitilan can,za'a zo a saurari buqatarki. "Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana jin tsoro yana shigarta. Tsoron yadda zai fita ya barta a gurin da yake mata wani irin kwarjini,ta yaya zai killaceta haka ita kadai?. "Zaki zauna ki jira har zuwa sanda zan kammala tattaunawa da mutane". " You speak as if......" "As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da tataccen turancin nan da ko yaushe nasa yana fita da wani tone saboda zaman yaren oromo a bakinsa. Idanunsa sun mata nauyi,saboda ya datsi numfashinta ne ya fada kai tsaye yana kuma waiwayowa bayan ya tsaya daga bakin qofar. "Yes.....because you're" Ya qarasa bata cikakkiyar amsa. "Amma ni ba yarinya bace" Ta maida masa tana qoqarin tattara qarfin halinta. Murmushi yayi can qasan zuciyarsa,wannan qarfin halin nata da kafiyarta yana fusgarshi wani lokaci. "Na sani.....yara basa cikin tsarin mammina.....shi yasa na gasgata ke ba qanqanuwar yarinya bace me girma gimbiya......amma dai....ni nake da zabin sanda zamu tafi.....rest well" Ya furta yana saluting nata sannan ya juya a nutse yana ficewa. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 121* "nan diwa kike fa.....meye zai dinga zauta tunaninki irin haka?" Tafisu ta fada cikin sassauta magana,muryarta acan qasa. Wannan lafazi na tafisu shine abinda ya zaburar da ita.....wannan magana ta tafisu shine abinda ya tilastata gayyato dukkanin nutsuwa ta azawa fuskarta. Wani irin gumi takeji yana tsargawa daga tafin hannunsu dake manne da juna yana bin sassan jikinta,idanma taji da kyau,idanma ta lura da kyau kamar jikin nata shaking yake kadan kadan. Kusancin ya mata yawa......ga jarababben turaren nan dake sake daga mata hankali. A nutse yake takawa da ita a gaban tawagar madame soufiane aghaichata guichene,minister al'adu ta qasar niger. Taku kadan ya rage tsakaninsu,sai ya sassauta tafiyar yana zame hannunsa daga cikin nata. "Ki nutsu,akwai idanu da yawa a kanki.....ki qarasa ki fara marabtarsu" Ya fadi da wani sauti me taushi can qasa kamar wanda ke mata rada,abinda ya sanya tsigar jikinta zubawa gaba daya. A hankali take nufar Madame aghaichata,fuskarta sake da dan murmushi kaman yadda fuskar Madame aghaichata take a sake sosai. Cikin zuciyarta tanajin wani abu yana sauka a hankali......ya girmamata kenan?.....ya karramata ya mutuntata,ya kuma bata damar data zama tatace. Damar fara tarbar baqin da suke na masarautarsu,ko kuma rashin iya boko ne?,tsoron magana da harshen France da bai iya bane?. Farar matashiyar buzuwa data kasance fara sol,ba wani sofanin baqi sam a tare da ita. Kyakkyawar minister din data zama mace ta farko data fara zama minister cikin zuri'ar buzaye. Yare daya qabila daya.....murmushi sukewa junansu ita da akhnan din. Akwai tarin sanayya sosai tsakaninsu,don kusan akwai abota me qarfi tsakanin kakanninsu,abotar data sanya iyayensu da wasu sashe cikin dangin biyu suke da kyakkyawar mu'amala. A hakam akhnan din bame sakewa bace.......bata da saurin sabo,uwa uba yawa izzarta ya sanya shehnaz da aisa ne kawai take mu'amala dasu a sake. Irinsu Madame aghaichata suna da yawa da saidai idan sun hadu a taro ko kawo ziyara irin wannan su gaisa cikin mutunci da kimanta juna. "Amaryamu.....gimbiya akhnan......magana a kanki ya cika garin agadez gaba daya.....boyayyar gimbiyar nan da ba kowa ke samun iko da damar ganinta ba.....amma fa a yau na sake ganin dalilin da ya sanya akeyin shuru cikin jin nauyi da girma kafin a ambaci sunanki" Murmushi akhnan ta saki me taushi wanda sam bata shirya fitarsa ba. Ta sani Madame aghaichata nada barkwanci sosai,tun a wata seminar da suka hadu da ita a france ta lura da wannan. "Na gode matashiyar minister dinmu" Tayi qoqarin maida mata barkwancinta. Gaishe gaishe suka fara gudana a tsakaninsu ita da akhnan din,da hirarrakin da ba masu tsaho ko tsauri ba,yayin da haisam ke musabaha daya bayan daya da permanent secretary,jami'in protocol,diministerna tarihi da al'adu na minister,da secretary din yada labarai. A hankali hankali da idanuwan akhnan suka sauka a kansa. Karon farko data fara ganin fitar murmushi saman fuskarsa.....karon farko da murmushi ya zame mata wani abun kallo a duniyarta. "Haka murmushi yakewa kowa kyau?,ko a iya shi kadai ne?" Ta tambayi kanta da kanta. Abu mafi girma da yafi bata mamaki yadda taga bakinsa yana juyawa a hankali. Kyawawan labban nan nasa suna motsawa da alama magana yakeyi. "Da wanne yaren?,da wanne harshen?" Ta tambayi kanta da kanta. A dukka tawagar minister data kalla ta tabbatar ba wanda kejin wani yare na daban idan ka cire yaren Tuareg da france. ta sake juya idanunta a hankali.....wani abu take gani......tarin banbanci me yawan gaske tsakaninsa da dukka mazan dake kewaye dashi suna gaisawa. Koda daga nesa idan ka hangesu zaka iya fiddashi daban a cikin su. Wani irin kwarjininsa ne yake fasuwa yana bayyana kansa. Maganarsa motsinsa dama kallonsa gaba daya yana bayyana asalin banbancinsa da dukkan mazan dake gurin. Ta sake motsa idanunta kadan,dukkaninsu suna masa magana ne amma kowa zaka iya hangen tsantsar girmamawa daga gareshi zuwa ga haisam da har yanzu yake sakin murmushi yana kuma saurarensu da nutsuwar nan tasa. Da sauri ta dauke idanunta a kansa sanda hannunsa ke cikin na protocol,ta saukesu a qasa tana jin bayanan madame aghaichata. Can qasan ranta take tuhumar zuciyarta. "Me yasa?.....me yasa ta damu da sai ta kalleshi bayan bata taba kallonsa a sa'a ba?.....me yasa zuciyarta ke yawan zugata da tunzurata ta kalleshi,bayan duk sanda zata kalleshin sai ya kamata?....kada ka kije ki zuba ajinki.....karki je ki zubda kima da martabarki.....kada ki sa ya dauka saboda wani abu daban kike kallonsa?". Abinda zuciyarta keta nanata mata kenan,wanda ya bata dukkan qwarin gwiwar qin sake yarda ta kalleshi. "Sheikh muhammad haisam" Ta kira full name dinsa tana dubansa fuskarta dauke da murmushin nan nata dake bayyana kalar kirkinta da sauqin kanta,kaman yadda idanunta tsaye a kansa,saita dakata kamar me zaben kalmomin da zatayi magana dashi. Da gaske taji kwarjininsa sosai,har ya sanya take laluben kalmar daya kamata ta fara magana dashi,wannan dakatawar tata kuma ya tsaida komai a qirjin akhnan. Sassanyan murmushi ya saki me nuna sanin kima da darajar kai. "Madame aghaichata" Ya kirata a taqaice shima. Tsoro take......tsoro take kadda ta zarce da masa magana da france......gurin cike yake da 'yan press,batasan ya zai amsa mata ba,batasan ya zai fahimta ba. Cikin qasa da second daya wai tsoro ya zarta a qirjinta sanda taji muryar Madame aghaichata tana magana cikin faransancin nan nata. "Ina ganin akwai mutanen da ake gabatar dasu ta hanyar muqami......amma akwai wadanda kasancewarsu ce kadai take gabatar dasu" Tayi maganan da girmamawa sosai cikin muryarta. Kai ya gyada a hankali cikin nutsuwa,ya fahimci ita dinma tana cikin jerin sahun mutanen da basa iya boye haqiqanin abinda ke ransu. "Kwarjinka yafi jin labarinka yin magana" Ta sake fadi da dukka gaskiyarta. Zuwa sannan tsoro ya hana akhnan sakat,ta daga kanta a hankali ta zubesu akan haisam. Haka kawai takejin kamar ta zama me masa tafinta,idanunsu suka hadu dana juna,yadan zuba mata idanu na wasu sakanni yana karantar tsoron dake cikin idanunta. Mamaki kadan ya kamashi,idan ya fahimta daidai irin wannan ranar irin wannan lokacin take fata,sanda zata tabbatarwa da duniya bai iya faransancinsu ba,yanzu me ya canza mata wannan ra'ayin?,me yasa manufar ta sauya?. Amsa bai sani ba,don haka ya dauke kansa ya maida zuwa ga minister "Son charisme resplendit,pas le mien,je me contente de baigner dans son aura(Kwarjinin nan nata ne,ba nawa ba.....kawai nima ana rabani ina amfana ne kawai)" Wani irin sake numfashi tayi kamar wadda numfashin ke shirin tsinke mata. Da wani irin yanayi.....da wani irin accent yaren ke fita daga bakinsa. Wani irin accent me matuqar jan hankali da nuna zallar qwarewa. Murmushi madame aghaichata ta saki a nutse,yadda ya sarrafa faransancinsa a baki yana burgeta. "Na fahimci dalilin da yasa ake saurarenka ba tare daka daga murya ba" Ta furta tana jinjina kai da gaske. Qaramin murmushi da iyakarsa lebe kawai ya saki. "Masarauta na maraba dake cikin farinciki wannan ziyara da girmamawa" Ya fada cikin nuna girmamawar. Gaba daya Madame rose dake gefe,matar da aqalla zata kai shakarun haihuwa hamsin haisa din ya gama burgeta,ya kuma gama tafiya da ita,don haka sanda ta lura bai ganta ba saitayi masa sallama da gurbataccen yaren da harshen nasara dake kan harshenta. Sai a sannan ya lura da ita,cikin hikima da sanin darajar girma koda na kafiri ne ya sakar mata murmushi,yabi hannunta data miqo masa da nufin suyi musabaha da kallo,sau ya hade dukka tafukan hannayensa kawai yana gaidata,ganin alamun bazai bada hannun ba itama saita amsa da yanayin da ya gaidata din. A biye take dasu kawai,yawun bakinta yana daukewa gaba daya. So take ta tuna dame dame ta fadi masa a gabansa da yaren France bisa tsammani da tunanin baya ji. Waye ya koya masa?.......ya akayi yakejin yaren da wani irin yanayi dako ita kanta bata iya sarrafa harshenta kamar haka?. Haisam din da sauran directors na Madame aghaichata suna gaba,ita da Madame din da mata biyu da suke mata rakiya hadi da Madame rose suna biye dasu. A nutse yake karantar mammina,wadda ke tsaye daga qofar qarshe da zata sadasu da cikin gidan. Dab da ita suka dakata,ya janye a hankali yana basu space suka gaidata,suka fara yin gaba kafin Madame aghaichata ta qaraso. "Gaisuwa nake giwar me martaba.....nace wannan karon biftu aka miqawa ragamar aikin gaba daya kenan" Madame aghaichata ta fadi da wannan salon barkwancin nata. Wani murmushi ya subuce mata,ko banza tasan cewa matsayinta yana nan,ko banza kuma 'yan press dake tare da minister ta tabbatar zasu haskawa duniya da abokan adawa na boye da baka sansu ba,dana filin ma da suka bayyana cewa har zuwa yanzu ba abinda ya canza daga wannan matsayin nata. "Kinsan kana girma kana dora 'yan baya akan turba me kyau,sabida yanayi na rayuwa" "Gaskiya ne" Madame aghaichata ta amsa mata,suka sake gaisawa. "Ku qarasa......haisam zai jagoranci komai shida matarsa,bayan kun kammala saimu zauna tattaunawar" Mammina ta fadi saboda tana buqatar kebewa koda na minti ashirin ne tayi tunani akan haisam din. Komai akan idanunta ya faru,komai saman idanunta ya wakana. Riqon da yayi mata....maganar rada qasa qasa ba abinda yake sake shaidawa duniya da masu kallo aurensu akwai qauna da fahimtar juna. Ba haka takeso ba,ba haka taso ya faru ba,saboda samun tabbacin mutanen duniya a soyayyarsu ba abinda zai kawo sai tarnaqi ga nata plan din. Kai tsaye suka wuce zuwa kebantaccen kuma makeken parlor din sultane na alfarma wanda ya saba ajiyar baqi irin haka. Tsarin kayan ciye ciye ne kala kala aka gabatar musu,basu dade da ba suka wuce qaramin gurin tarihi dake cikin masarautar daura da babbar fadar sultane. Baya yaja sanda aka shiga gurin,karon farko yake duban akhnan din. "Ranki ya dade ke zaki wannan bayanin" Ya fadi kai tsaye yana janyewa baya. Murmushi dukka suka saki,musamman Madame aghaichata da komai yake burgeta dangane dasu. Haka kawai taji hadin yayi mata,tsarin kuma ya burgeta sosai,tana ta karantar wani abu me nutsuwa sosai a tattare da komai nasu. Nauyi taji ya aza mata sosai,tadan lumshe idanunta tana fidda numfashi,sannan ta taka zuwa gaba a hankali. Tana sane ta zabi tayi bayanin da yarenta harshen Tuaregh. Shuru ya ratsa gurin,haisam ya saki murmushi kadan. Koda batace komai ba,koda bata furta komai ba yasan dalilin da yasa tayi hakan,sai yayi kaman bayaji din,sai yayi kaman baya fahimta har zuwa sanda ta kammala bayanin. Kai Madame aghaichata ta jinjina. "Da gaske daga gidan sarautar agadez kika fito" Ta fadi da murmushi me laushi akan fuskarta tana duban akhnan da take kallonta kamar qanwarta ta jini. Itama qaramin murmushi ta saki,murmushin daya tilastawa haisam dauke kansa daga kanta a hankali,sannan ya jagoranci tawagar zuwa gidan museum din dake daura da gidan sultane din. A qafa suke takawa,wata nutsatsiyar tafiya a hankali. Yana dage gefan akhnan din,suna kuma magana da Madame aghaichata,saidai ga mamakinta da hausar nan tasu da dukka bata nuna ba suke magana. Abinda ya sake daure mata kai,ta shiga shakka da kokwanto,france din yakeji?,ko kuma dai yayi yaren ne kan sa'a. Jin qafafunta kawai takeyi kamar ba'a jikinta ba. Duk taku daya biyu sai kafadarta ta gogi tasa. Bata sani ba,shima yana ji?,nunawa ne baiyi ba ko kuma ita daya ce?. Nan da nan security suka zagaye museum din,sannan aka buda musu hanya suna wucewa ciki.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 122* A nan din akwai ma'aikaci dake qarin bayani akan komai daya shafi gidan tarihin da kayan dake ajiye a ciki. Har xuwa sanda suka kammala suka kuma yada zango suda manya managers na gidan ajiyar kayan tarihin don tattauna yadda za'a gyara gurin da kawo sauye sauye da ci gaba. Relaxing yayi sosai cikin kujerar,kunnuwansa suna biye da dukka tattaunawar da akeyi da kuma musayar ra'ayin da suke a tsakaninsu,saidai idan ka dubeshi yadda yake zaune zaka dauka baya gurin,don idanunsa na saman wayarsa ne yana duba wani aiki da aka turo masa daga hukumar national intelligence security services. Saqo yake tafawa,amma sai yadan dakata kadan sanda ta fara magana. Cikin izzar nan dake qara mata nutsuwa. Kusan itace ta qarshe data fara magana,bayan ta gama satar kallonsa tana jira taji ko zaice wani abu. Can qasan zuciyarta zuciyartata take raya mata qila ma baya gane me ake magana akai,qilan ma maganar dazun yaje ya haddace duk abinda zai fada ne,kuma komai yazo da arashi din. "Kinyi magana me kyau me ma'ana.......ranka ya dade ba wani abu da zaka dora?" Madame aghaichata ta fadi da murmushi tana duban haisam. A nutse ya ajiye wayarsa a gefensa,ya motsa idanunsa gefansa suka fada cikin na akhnan. Wani siririn muskilin murmushi ya saki. Ya sani idanuwa dukka suna kansu shida ita,koda bai kallesu ba yana ji a jikinsa,sai ya kashe mata ido daya a hankali yana zare dubansa a kanta ya maida kan Madame aghaichata. " Elle est vraiment brillante,elle a fait un excellent travail,et j'ai quelques idées à(Tana da fikira,tayi qoqari sosai kuma,saidai akwai wasu qarin shawarwarin da zan bayar)" Tamkar daukewar ruwa dakin ya dauki shiru,sai sautin muryarsa dake zarcewa har ta saje da shurun dakin. "A ina ya koyi faransanci ne?" Madame aghaichata ta tambayi kanta da kanta,saidai idanunta suna kansa tana gyadasu a hankali cikin gamsuwa da dukka kalamansa. Batasan mutum yana jin bugun zuciyarsa daga qirjinsa zuwa kunne ba sai a sannan,tun daga kashe kashe mata idon da yayi,zuwa kalamansa na yanzu da bata da tabbacin yabonta yayi ko akasin haka?,accent dinsa me wani irin kashe jiki da nuna zallar salon iya sarrafa harshe tayi qasa da idanunta bata kuma iya sake dagosu ba. "Nasan zamu samu fa'ida sosai daga tsarinka,muna saurarenka ranka ya dade" Madame aghaichata ta fadi tana gyara zamanta cikin jin kwarjininsa yana sake mamayarta. A nutse ya maida bayansa ya jingina da kujerar,yadda suka cika dakin da hayaniya da fadin ra'ayiyyika abun yadan bashi murmushi kadan. A tsarin aikinsu wannan yanayin ba abun karba bane.....sannan duk abinda suketa cecekuce a kansa me sauqi ne,don haka cikin qwarewa da iya sarrafa harshe ya fara magana da tattaccen harshen faransanci kamar dama can yarensa ne na gado. "Ba gyara kawai muke buqata ba,muna buqatar labari.....kowanne abu anan ya kamata ya samu murya" "Ta wacce hanya?" Madame aghaichata ta tambayeshi cike da son jin qarin bayani. Yadan motsa kadan,yana ji a ransa ba halittar da takai ta mace gaggawa. "Ta hanyar qananun na'urorin sauraro,mutum zaizo ya saka a kunne,yaji tarihin abinda yake gani cikin harshen daya zaba" Batasan ta daga kai ta kalleshi ba saida suka hada idanu. Wani idea me girman gaske....wani tunani me kyau data tabbatar zai daga daraja da martabar gidan kayan tarihinsu,me yasa su basu taba irin wannan tunanin ba?. "Merveilleux(wonderful)" Madame aghaichata ta fadi tana jinjina kanta. Ba ita kadai ba,kowa a gurin saida fuskarsa ta bayyana yadda idea din ta qayatar dashi. "Kan tsarin gyara kuma.....banso a rufe gidan gaba daya ba,hakan zai dakatar da kudin shiga na wannan jahar,zanso muyi gyaran sashe sashe,don kada al'umma su rasa alaqa da tarihinsu zuwa wani lokaci sanadin gyaran" "Gaskiya ne" Minister ta sake fadi cikin jinjina kaifin basirarsa. Tana jin inama zai karbi wani muqami cikin tafiyarsu?,inda zai amince da zataji dadi da hakan,ta tabbatar ba qananun ci gaba za'a haifar ba. "Dan gane da ganuwa da manyan katangun tarihi da kukayi magana akai kuma......" Ya fadi yana aje numfashi a hankali. Mamaki ya sauka a zuciyar akhnan,wanne irin mutum ne shi?,dama yana sauraren komai?,amma yayi kaman baya gurin?,yayi kamar besan me ake fadi ba?. "Guraren tarihi basa buqatar ado me yawa,abinda suke buqata shine tsaro,haske......da bayanai na asali" Ya sake tsayawa yana sauke numfashi,abinda yake sake gayawa minister tsantsar nutsuwar dake gareshi. "Zamuyi amfani da matasa masu koyon tarihi daga yankinnan,su zama sune jagorori ba baqi ba". "Yana hada ilimi da martaba" Zuciyar akhnan ta fadi a hankali tana jin gamsuwa da bayanan suna sauka saman zuciyarta. "Baya magana har sai an nemi yayi....har sai an sanyashi cikin al'amarin" Madame minister ta furta qasan zuciyarta tana jin yadda gaba daya haisam ya hade bayanansu ya rushesu,yana basu bayanan da zasu dace da yanayin,ba tare daya qalubalanci bayani ko qoqarin kowa a cikinsu ba "Tarihi baya buqatar yabo,yana so a barshi ne yayi magana da kansa" "Wannan ba malami kawai bane......jagora ne" Madame aghaichata ta raya hakan a ranta. Kasa boye abinda yake ranta tayi,ta sake gyara zamanta kamar yadda takeyi tun dazu saboda yadda har yanzu takejin kwarjininsa. "Amma.....muna neman wata alfarma guda daya mana idan ba damuwa" Ta sake fadi da harshen faransanci. Agogon hannunsa ya kalla sannan ya maida dubansa a kanta. "A gurguje.....lokacin sallah yana dab da shiga" Maganan ya sakata murmushi,ya kuma sanya kowa mamaki. Karo na farko da wani ya taba magana da minister din kai tsaye irin haka,karon farko kuma da wani ya nuna muhimmancin lokacinsa sama dana minister. "Me zai hana kayi aiki da hukumarmu?" Shuru ya ratsa na sakanni,yayin da akhnan ta tattara dukka hankalinta akan amsar da zai bayar. Zai amsa.....zai karba abinda zuciyarta keta fada Mata. Dama ce babba ga kowa miqa qoqon bara harda neman alfarma daga minister din,don haka shima bata zaton zai tankwabe dama irin wannan. Yawanci abinda kowa ke buri da mafarki kenan,don haka shima bazai tsallake ba. Saidai kuma ya bata mamaki Kamar yadda ya saba,ya hada yatsunsa cikin na juna ya fara magana da wannan salon nasa me nutsuwa. "Ina godiya qwarai Madame minister,wannan gayyata alfarma ce babba,kuma tana nuna amincewa da yarda" Idanu minister ta zuba masa tana gyada kanta a hankali,tana fatan amincewarsa ta biyo bayan bayanansa. "Amma ina da dabi'ar yin aiki ne idan na tabbatar zan iya bada gudunmawa me amfani,bawai suna kawai ba" "Idan manufarku itace kiyaye tarihi da al'adu,zanyi farincikin baku duk gudunmawar data dace.....banqi karbar tayinki ba......saidai Inaso a bani lokaci na duba tsarin aikin,in duba inda zan iya shiga da iyakacin iyakokina...." Ya daga idanunsa a hankali,ba zato yana saukewa akhnan dake satar kallonsa qasa qasa. Tayi matuqar qoqarin ganin ta janye idanunta daga kansa,saidai yayi mata wani daidabayi ta hanyar sarqafe kallonsu. "Idan gimbiya ta amince,zanji dadin yin aiki tare da hukumarku". Yayi maganan idanunsa suna cikin na akhnan. Dariya gurin ya dauka da surutai kadan kadan,yadda yayin ya burge kowa......yadda yayin ya isarwa da minister saqonsa kai tsaye. Baida sha'awar aikine dasu,amma bazai gaya mata kai tsaye ba saboda kare matsayinta da girmanta......kada kuma ya bari taji ya tozartar da matsayinta. "Ranki ya dade muna neman alfarmar ki sake mana wannan fasihin al'ummarmu su qaru dashi" Madame aghaichata ta fadi tana dariya idonta akam akhnan. Wani irin abu taji,da qyar ta fusgo murmushi saman fuskarta. Me yasa yake kasheta?,me yasa yake kasheta haka?,me yasa yake dasa mata abubuwa masu qarfi har haka?,me yasa yake kafa mata hujja a gaban mutane?. Wannan girmamawar.....wannan bada damar?.... Wai me yasa murya guda daya tal daga bakinsa take sawa kowa yayi shuru?,baya daga murya.....amma kowa yana saurarensa........ Karon farko da taga namijin da bai nemi burgewa ba amma kuma yake burge kowa. Bai nuna kansa ba.....amma so ake aji ra'ayinsa, Ta maimaita kalmarsa ta. "Inaso in duba inda zan iya shiga,da iyakacin iyakoki na" Kalaman sun mata kama da kalaman mutumin da baya neman matsayi,.....matsayinne yake nemansa da kansa.....AMMA HAR ZUCIYARSA HAKANNE?. Tambayar data maqale mata cak tsakiyar zuciyarta......tunaninta ya fara dawowa daga nisan kiwon da yayi sanda ya miqe a nutse yana tunasar dasu lokacin sallah. "Ina fatan zaka sake bamu lokaci bayan mun kammala sallar,ka tayamu rubuta jadawalin komai a sauqaqe,don bamu da tabbacin daga nan idan ka kubce mana zamu sake samun dama irin wannan" Murmushin da kumatunsa ne kawai suka motsa yayi ya jinjinawa Madame minister kai,sannan ya juya yana ficewa sauran mazan suna rufa masa baya. Tayi zaune tana duban minister da baturiyar dake gulmar haisam bayan sun kammala sallar magariba,sallar magaribar da haisam din yayi limancinta,sautin karatunsa kuma ya ratsa kowacce kusurwa cikin masarautar da sauran sasannin unguwar. "Ma sha Allah.....ma sha Allah" Kawai Madame minister ke fadi tana juya kai. A nutse kuma ta sauke idanunta akan akhnan. "Idan naji labari daidai khadeeja.....kamar haisam.bai kasance zabinki ba da farko?" Ta qarashe maganar da tambaya. Idanu kawai akhnan ta lumshe ba tare data bawa minister amsa ba. Ta sani,ba lallai tayi magana ba dama,bata damu da wannan ba ta jinjina kai. "Hakan ba laifi bane,ba kuma kuskure bane,saidai inda zai zama laifin dama kuskuren gaba daya idan kika kasa riqeshi da kyau......kinsan ina da labarinsa tun kafin na sako qafata masarautar nan?......hirarsa ta zagaye agadez da yadda ya maida masarautarku cikin tsari?.....naji hirarsa ba daya ba biyu ba....nayita addu'a na sameshi,don haka na buqaci sultane ya bamu wakili yayin ziyara,bisa zato da yaqini na kuma ya bamu sheikh muhammad haisam.....". Fararen blue eyes dinta ta daga tana duban minister. "Yes.....ki ribaceshi khadeejah......na gano abubuwa masu yawa da alfanu tattare dashi......ba shakka LU'U LU'U ne wannan" Murmushin qarfin hali kawai ta sakewa minister din tana dubanta,hakan ya bawa Madame damar ci gaba da magana.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 123* "Sheikh muhammad ba irin mutanen da ake gani bane yau da kullum.....naga kalar mutumin da qasashe ke neman irinsa,saboda ilimi da kwarjinin dake lullube dashi......irin wannan mutumin idan kina tare dashi zaki kasance me ninkin qarfi,ki kula da wannan ni'imar" . Kai ta jinjina a hankali,me yasa suke iya ganin abinda har yanzu bata gama gani ba?.me yasa kowa ke ganin qarfin ikonsa?,me yasa kwarjininsa bai bar kowa ba?" Ta tambayi kanta. Batasan ya akayi ba,batasan me yasa ta tsinci kanta da lafewa cikin kujeru ba,ta zubawa dogaye kuma zara zaran yatsunsa farare tas idanu sanda yake rubutu cikin wani yanayi me daukan hankali saman doguwar takardar tsare tsare kamar yadda minister ta nemi alfarma. Ya sake zama,ya kuma rubuta komai kaman yadda yayi alqawari. "Ba mutumin banza ne yake iya cika alqawari ba" Madame minister ta fadi qasa qasa saitin kunnen akhnan. Madame rose ta gyara abun jin magana dake kunnenta,wanda yake iya fassara maka magana daga duk yaren da akayi magana zuwa yaren da kai kakeji,wanda akwaishi a kunnen kowa dake cikinsu. Kasa daurewa tayi,itama qasa qasa ta fara magana da minister. "There was an unmistakable aura of authority around him.....he carried him self with quite dignity" Murmushi Madame minister tayi tana jinjina kai. Ko Madame rose da take me banbancin aqida.....banbamcin al'ada da banbancin yanki ta fahimci abubuwa masu yawan gaske a tattare dashi. "Seriously madame......he had a commanding presence quite dignified and impossible to ignore" Sauran maganar Madame rose ya maqale sanda ya ajiye abun rubutun yana tura takardar gaban Madame minister. "J'ai tenu ma promesse(na cika alqawari na)" Hannu tasa tana daukan takardar cikin jin dadi. "Merci,vous avez tenu parole(tabbas ka cika alqawari,na gode)". Cikin wani yanayi suke mata rakiya har zuwa bakin motocin da suka kawota a dazu,fuskarta cike da murmushi ta sake cewa cikin harshen faransanci "Na dade banji dadin ziyara irin wannan ba saboda haduwa da mutane irinka abune sai mai sa'a....muna godiya da karramawa......sannan muna me miqa saqon goron gayyata a gareku,duk da cewa zamu turo wasiqa officially......zaku zama manyan baqinmu na wannan gurin......zaka zame mana me tsara komai.....kwanaki biyar zuwa bakwai kadai zakayi cikin sahara.....zaku zama baqin ma'aurata na musamman.....muna fatan hakan bazai takuraku ba?" Madame minister ta fadi tana murmushi da raba dubanta tsakanin fuskar haisam da akhnan. Haka kawai taji tanason ta qulla wannna kusancin,haka kawai taji ya kamata ko yaya wannan kyakkyawan hadin ta bashi gudunmawar qara danqo da wanzuwa. "Na tabbatar dukkaninku ba zaku wofantar da gayyatata ba......ina fata zaku riqe kwanan watan da komai.....zan shaidawa sultane da kaina,za'a tsara komai yadda zai dace da tsarinku.....na gode qwarai" Ta fadi tana miqawa akhnan hannu. Da wani irin faduwar gaba ta bawa minister hannu sukayi musabahan qarshe. Gabanta ke wani irin faduwa,me yasa madame zata mata haka?. Yaya take nufin komai zai kasance akan tsarin?. "Sheikh muhammad....ina fata qasata zata koyi yadda kuke hada zamani da kuma girmamawa" Yadan murmusa kadan,da alama gwanar hira ce,yana ganin kimarta sosai saboda aure dake wuyanta,amma yayi magana yau harta zarce qa'idarsa da yadda ya saba. "Muna maraba da duk wanda wanda ya girmama abinda muka gada" Kai ta jinjina sosai tana daga masa hannuwanta biyu alamun girmamawa,sannan ta shiga motar da aka bude mata. "A bawa giwa haquri,akwai wadanda ke jirana yanzu haka,lokaci na gaba idan na shigo xamu xauna sosai da ita". Kai akhnan ta gyada a hankali,don da alama ita aka bawa saqon. A hankali motocin minister da jama'arta keyin nisa da gurin,wannan nisan dake qara wani irin nauyi da kunya a qirjin akhnan. Batasan da wanne idanu zata waiwaya ta kalleshi ba,tunda batasan adadin meye da meye ta fadi da France ba a kansa,idan taje har zaginsa tayi batayi qarya ba,ashar ne kawai bata d'ura ba. Iska yake zuqa a hankali shima da wani irin nutsuwa yana fesarwa. Wani qamshi na daban daya tsinkaya yau a tattare da ita yana busawa da wani irin yanayi zuwa ga qofofin hancinsa. Abu na farko daya fara jan hankalinsa ya kuma sanyashi baiwa mazan dake biye da ita umarnin dakatawa da binta gaba daya a wunin yau. Yasan fitinar da qamshi yake dashi a gurin d'a namiji.....ya sani yana daga cikin girman abinda ke motsa sha'awar dan adam,tuna wannan kawai ya sanya sanda ya gansu biye da ita duk da su birra dake tsakani yaji kamar wani abu yana yankewa daga qirjinsa yana faduwa. "Muje na maidaki ciki" Ya fada da wani irin dakewa. Har ranta taji maganan tasa da wani irin nauyi. Kamar zata bata?,ko.kamar batasan kan gidan ba?,kamar ma itace baquwa bashi ba?. Saidai wani irin borin kunya takeji a zuciyarta,ba zata iya tsaiwa jayayya da musu dashi ba,fatanta ta isa sassanta ta samu ta zauna ta nutsu,ta kuma tariyo dukkan maganar da tayi a gabansa a wadancan kwanakin da wancan yaren. Har jikinta ta dinga jin wani abu sanda ya sanyata a gaba yana biye da ita a baya,tamkar wanda aka bawa gadinta. Batasan me yasa yake son take mata baya har haka ba,ina tashi izzar?,ya sarayar?,ko kuma yana da wata manufa na qare ma bayanta kallo,kamar yadda yawan maza suke da wannan dabi'ar. Iya tuna wannan kawai ya sanyata taji qafafunta sun sarqe saboda tuna yadda taji shehnaz na fadin daurin lafayar ya fidda shape na mazaunanta kadan. Ta tafi luuu zata fadi,cikin wani irin zafin nama taji ta fada a jikinsa. Daga idanunta tayi a tsorace idanunsu suka gauraya da juna. Da sauri ta dauke idanunta tana jin wani nauyinsa karon farko......karo na farko a rayuwarta da nauyin wani mutum data yiwa ba daidai ba ya mamayeta. Jikinta ta fara qoqarin zarewa daga jikinsa da hanzari,saidai da zafin nama ya furta. "Attendez(wait)" Ya fadi,kalmar ta sauka saman zuciyarta tana qara gudun zuciyarta. Still dai da France zai mata magana?,sai taji kaman yana zaginta ne ko maida mata baqar magana. A nutse ya saketa ta tsaya da qafafunta,saidai bata iya tsaida qafarta dayar sosai ba,sai kuma a sannan ta fahimci abinda ya sanya yace ta dakata din. Dogon hill shoe dinta ne ya gurde,a nutse matsa gaba kadan. Ga mamakinta sai ta ganshi yana duqewa saman qafafunsa yana tsugunnawa a gabanta. Hannunsa ya miqe a hankali ya kamo lallausar farar qafarta,wadda gyaran jikin da ake mata ya sake qarawa fatar haske laushi da kuma sulbi. Zara zaran yatsunta yabi da kallo,kafin yaji wani abu yaarrrr ya sauka zuwa dukka gabansa. "Hasbiyallahu wa kafa" Ya fadi can qasan maqoshinsa,adams apple dinsa yana motsawa sama da qasa a hankali. Takalmin ya kama ya cireshi dukka daga qafarta,yana kuma mamakin qarfin halin mata da suke iya sanya takalma irin wannan,kuma ace wai duka wadannan awannin suna qafarta?bata gaji ba?bata kuma tsoron faduwa kamar haka?. Ajiye mata yayi a gabanta yana miqewa tsaye,saita soma tura qafar tata ciki mamaki yana sake kasheta,ta daidaitashi a qafarta,mamakin ya kasa barinta ko yi mata linzami,tilas ta daga kanta a hankali tana saukewa a kansa don tabbatar da cewa shi dinne?. "Vous n'êtes pas blessée(bakiji ciwo ba?)" Yayi tambayar da seriousness dinnan nasa. Idanunta ta lumshe a hankali tana daga masa kai. Bata hangar komai cikin idanunsa sai kwatankwacin girman nan da YAYA yake dauka akan QANWARSA. Sake goge mata hadda yakeyi gaba daya akan haddar daya goge mata dazun. Dukka wannan jarumtar tsaiwar da iya tsara komai ina ya samota?. Haka malaman suke?,ko kuma shi dinne haka?. A duk sanda yayi magana da France yana sake sanya fargabarta qaruwa,yana sake sanyata feeling guilty sosai a jikin jininta. Kamar me tafiya akan qwai har suka isa mararrabar da zata sadata da sassanta. Bata waiwayo ta dubeshi ba,amma a cikin jikinta takejin ya tsaya ne kawai cak. Ya tsaya ne kawai ba tare daya qara taku ko daya ba,sai tafiyarta ta sake zama slow,a hankali har ta gifta ta wata doguwar bishiyar turare dake gurin. Samun kanta tayi da tsaiwa jikin bishiyar,ta yadda ba yadda za'ayi ya ganta,saidai ita tana iya hangensa. Ya saki hannuwansa dake goye a qirjinsa a nutse ya juya. Saidai baiyi taku ko daya ba wata murya ta wanzu a gurin,tare da kukan yaro qarami "Inda kinsan darajar abun nan da baki yar dashi ba.....ni bazan iya tsaiwa tayaki nema ba,idan kin ganshi kya taho" Idanunsa da suka dan rusuna saboda gajiya ya daga zuwa sashen. Daya daga cikin hadiman gidanne,shi da matarsa itama dake aiki cikin gidan,tana dauke da yaronsu daya hannun kuma torch light ce,duk a gigice take,da alama wani abu me girma suke nema. "Akaramakallah....dakata mana" Haisam ya furta a nutse. Da sauri ya tsaya ya waiwayo,sai gashi kuwa sa sassarfa ganin wanda ke kiran. Zubewa yayi niyyar yi,amma haisam din ya riqe kafadarsa yana fadin "Tashi abinka" Sannan suka fara takawa zuwa inda matar keta dube dube,wanda yake daura da inda akhnan ke tsaye tana kallon komai. "Jeka karbi yaron hannunta da fitilar hannun nata" Kwarjininsa ya isa ya hanaka tambaya akan duk hukuncin daka yanke,jikinsa na rawa saboda yadda ya hada kafada dashi,harda aza hannunsa saman kafadar tasa ya isa inda take. Sororo tayi da mamaki tana kallon mijin sanda yake karbar yaron da fitilar. Abune da bata zata ba,sai kuma hankalinta ya kawo kan haisam a sannan,ta durqusa da nufin gaidashi,sai ya daga mata hannu yana mata nuni data koma cikin gida. Hannu yasa ya karbi yaron daga gurinsa,idanu sosai yaron ya zuba masa,sai haisam din ya sake masa murmushi. Tamkar yaron yasan hannun kyakkyawan ruhi me taushi da tausayi da yazo,sai kukan nasa ya ragu a hankali,ya sauke kansa yana kwantarwa a qirjin haisam din,sai haisam din ya sake gyara riqonsa sosai yana rungumeshi cikin qirjin nasa,yaron ya sauke ajiyar zuciya sannan yayi luf a qirjinsa.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 124* "Dan bayi?" Ta tambaya can qasan ranta cikin mamaki. A nutse ya dubi mutumin "Lawan ko?" Cike da mamakin yadda akayi ya iya shaidashi ya kuma fadi sunansa haka kai tsaye ya gyada masa kai. "Kasan wacce wasiyya ce annbi muhammad S A W yayi ta qarshe?.....mece maganarsa ta qarshe?" Kai lawan ya girgiza da sauri yana saukar da kansa qasa. "Rifaqan bil qawarirr.....istausu binnisa'i khaira........yace kuyi a hankali,ku kuma lallaba wadannan kayan qarau din wato mata.....sannan yace kuyi wasiyya da alkhairi wa mata........annabi muhammad bai tsaya a nan ba sai daya qara da fadin. Ba me karrama mata sai karimi,babu me wulaqantasu sai wulaqantacce.....mafi alkhairi a cikinku shine mafi alkhairi ga iyalinsa....manzon S A W yace nine nafi zama mafi alkhairi ga iyalaina. Allah yanason mutum me tausayi me rahama koda akan dabba bare dan adam....me yasa ba zaka zama me rahama da tausayi ga matarka ba?,uwar 'ya'yanka?,me kwantar da hankalinka?,meye a cikin tsugunnawa kawai ka tayata neman abinta daya fadi......kasan taimama?" Kai lawan ya gyada yana share gumi. "Kasan asalin halascin taimama a musulunci?" Kai ya sake girgizawa. Sai ya saki tattausan murmushin da hatta akhnan dake tsaye tana iya hangen haskenshi. "Sanadin ummuna nana aisha R.A. qarqashin tawagar yaqi bisa jagorancin mafi alkhairin halitta manzo S A W,abun adonta ya fadi,take manzan Allah S A W ya shelanta,yasa aka tsaida wannan tawaga gaba daya ana neman abun adonta ita kadai......an tsaida dubban maza saboda ita,akayita nemansa har lokacin sallah,gashi ba ruwa a inda suke,mahaifinta sayyadina abubakar RA yazo yana zungurinta gami da tuhumarta akan ta tsaida annabin Allah da sahabbansa saboda ita kadai?. A nan ne Allah ya halasta taimama idan an tsinci kai a inda ba ruwa......kuma kasan me?" Haisam ya fadi very friendly murmushi na sake kubce masa. "Ana motsa raquminta yana miqewa sai gashi,ashe shi ya danneshi.......kaga anan sanadin mace sauqi ya zowa al'umma har ranar da za'a tashi duniya......sarki me girma da darajara da tafi ta kowanne dan adam ya dakatar da tawagar yaqi guda saboda matarsa......kai waye da ba zaka dakata saboda matarka ba?". Idanunta ta lumshe a mugun slow,tana jin wani abu me sanyi yana sauka a zuciyarta. Rana ta farko data fara jin wani abu me tsaho da fadi daya danganci annabi muhamma irin haka,tausasawarsa da nuna kulawarsa..... "Shine dalilin da yasa nake samun wannan kariyar dake gareshi?,koyi yake kenan?" Ta tambayi kanta da kanta tana jin wani abu yana ratsa zuciyarta. Wani irin kwadayi taji yana taso mata nason karanta tarihin manzan Allah S A W gaba daya.....da kuma rayuwarsa a cikin gidansa. "Nayi kuskure tabbas,kuma daga rana irin ta yau in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba". Kai haisam ya gyada cike da gamsuwa da jin dadi. " Muje ka duba mata......idan mace t qwallafa rai akan abunta bai kamata a karya mata zuciya ta hanyar hanata samunsa ba" Yayi magana yana soma takawa lawan yana gefansa yana sake haska masa duk da cewa akwai haske. Cak ya tsaya sanda ya hango qyallin dan kunnen,saidai koda ya sanya qafa da niyyar motsashi yaga ko shine sai idanunsa suka sauka kan dogayen yatsunta,tsaiwa yayi na sakanni,sai qaramin murmushi ya subuce wanda ba lallai ka iya gani ba. "Me takeyi a nan?" Tambayar daya yiwa kansa kenan,sai ya umarci lawan ya sauke fitilar qasa,da hannu ya masa nuni ya ciro dan kunnen,don bayajin ya dace ya taba abun da yake rayuwa jikin matar wani. Cire yaron daya fara bacci yayi daga kafadarsa yana miqa masa shi. "Allahumma bareek" Ya fada yana jin yaron yana burgeshi. Dan lukuti dashi,baccinsa kuma yake hankalinsa kwance ba tare da yasan a kafadar wa yake ba. Godiya ya dinga masa sosai,ya sanya yaron a kafadarsa jiki a sanyayr ya juya yana wucewa. Hannayensa dukka ya zube a aljihun rigarsa,shuru ya ratsa gurin,yayin da akhnan ke lullube cikin shuke shuken zuciyarta na bugawa fat fat a qirjinta. "Na tafi?,ko zaki fito na qarasa dake?" "Ya Allah.....me yasa bata sa'a akan komai?" Ta fadi cikin zuciyarta. Bata taba kawawa zai ganta ba,tunda kuma ya riga daya ganta me ya rage?,sai kawai ta fito,ta dauke kanta tana basarwa. Ba wanda yace da dan uwansa komai,har suka qaraso mararrabar sashen,sai kawai ya zabi shiga sashen nasa ta baya duk da ba a nan ya shirya kwana ba,don aiki yakeso yayi me yawa a daren nan,ya taka bai waiwayeta ba yana wucewa ta tasa qofar. *T A M I M* Dukka akan idanunsa suka wuce shi da ita. Ya koma baya ya zauna yana sakin wani irin murmushi. Murmushi ne najin dadi,murmushi ne dake nuna NESA TA MATSO KUSA. Idan yace ga adadin farincikin da yakeji yayi qarya,sam bai dauka ba baiyi kuma zaton komai zaizo da sauqi har haka ba. Bai taba daukan Festival de l’Aïr zai masa rana ba irin yau......bai taba zaton zai samu wani alfanu me tarin yawa ta dalilinsa ba. Miqewa yayi tsam,yana daukan wata rigar fatar damisa ya sanya a jikinsa,ya jawo manyan takalmansa da suka zama abokan rayuwarsa,don duk wanda ya sanshi dasu ya sanshi,ya soma takawa yana ficewa daga kebantaccen dakinsa dake cikin masarautar. ★★★ *_W A S H E G A R I_* Komai ta kammala na kwanciya bacci tana jin gajiya tana bin qasusuwanta,bugu da qari wani abu na daban takeji yana mata yawo a dukka jikinta. Wani kalan magani daban yau yaa hairaan ta bata,bayan wunin gyaran jiki da aka wuni anayi mata,don za'ayi hutu na kwanaki uku ne kafin a sake dorawa. A gobe kuma suke sanya ran dawowar sultane,har cikin zuciyarta takejin wani irin farinciki yana saukar mata. Idan face tayi kewarsa daya ma kenan. Wani irin mugun zaquwa takeji taga sultane dinta,da wannan sakakkiyar fuskar,da tarin soyayyarnan da yake nuna mata da kulawa wadda tayi tsananin kewarta. Ta maida idanunta a hankali ta lumshe sanda ta narke cikin lallausan duvet dinta tana sauke numfashi a hankali. Saidai kuma sake zuqar numfashin da zatayi sai ta sheqi daddadan qamshin nan har tsakiyar kanta. "Ya salam" Ta furta a hankali,gabanta yana faduwa tana bude idanunta,tsoro yana kamata,kada fa ace bayan tunanin komai daya faru daya fara kawo mata ziyara cikin madaidaicin duhun dakin still kuma qamshinsa ya fara biyota?. Saidai ko data bude idanun nata saita Fahimci meya kawo hakan. Lallausan rigar cashmere dinsa dake ninke saman kanta. Ta zuba mata idanu sosai kwanyarta na dawo mata da yanayin dukka shigarsa a wancan ranar. Ta sake lumshe idanunta tana budesu a kan rigar,zuciyarta na hasko mata kyawawan labbansa dake motsawa a hankali,sanda yake karanta addu'ar saukar ruwan sama.....sanda yake karanta addu'ar tsawa. Batasan ya akayi ba wani siririn murmurshi ya subuce mata saman labbanta,ta miqa dogayen yatsunta a hankali ta dora saman rigar. Kawai tana tuna ba zatar da yayi mata ne,yadda taji a sanda taji yana yara yaren France. Tsahon rayuwarta bata dauka ba sam cewa zataji nauyi ko kunya saboda shi ba,bata taba zaton akwai sanda zata zauna tana lissafin me dame ta cewa wani dan adam ba. Ta yamutsa yadin cashmere din cikin tafin hannunta. Koda ba'a gaya mata ba ta sani me daraja ne da tsananin tsada "Baimin kama da ordinary malam ba" Ta tsinkayi muryar shehnaz "Shemagh dinsa kamar a kansa aka halicceshi.......jinin annabi yusuf,tana tuna kayan data aike masa dashi.......bai saka ba,ya zabi kalar shigarsa....baiqi zuwa gurin ba,saboda sultane ya sanar dashi......ya girmamata da dukkan girmamawa.......ya kuma bata kariya irin wadda take so. ZAKI takeso......amma wani lokaci DAMISA ma take gani tattare dashi......nutsuwarsa da da kwarjininsa batasan me yasa suke tilastawa kowa girmamashi ba.....batasan yadda ya akeyi yake iya sarrafa kowa da shirunsa ba........batasan ta yadda yake iya bada umarni da idanu kawai ba tare daya daga hannu ba. Dukkan wani yanayi nasa yana gaya mata BANASON RAINI......yana da alamun dabi'ar girmamawa. Kaman anyi mix cikin halayensa ne......taushi da tsauri,batasan wanne ne yafi yawa ba a ciki. Batasan ta jawo rigar cikin jikinta ba......batasan ta qanqameta ba sosai sai da taji birra na magana. "Na kammala ranki ya dade,shikenan zan iya tafiya?" Ta tambaya tana rusunawa. Rai ta hade sosai tana shan mur,ta manta tana gurin,batasan kuma yaushe ta dauka a tsaye tana mata magana ba. "Ki ajiyemin madara me dumi da cup da ruwa saiki wuce. Ta fada tana maida kanta saman pillow gami da sakin rigar kadan. Samun kanta birra tayi da sakin dariya gami da sanya bakinta tana rufe bakin nata gudun kada ta jita. Shi yasa ta hana taba gurin?....ko shi yasa ta hana a dauke rigar?,ta hana koda hannunta yaje kusa da ita?. Ita din da bata bari abar mata komai saman gado idan ka dauke pillows din da ta saba bacci a cikinsu,ta saka wasu daga bayanta ta rungume wasu?. "Turqashi" Birra ta fadi murmushi still yana subuce mata. Abun yana da girma.....abun zai zama wani na daban na musamman idan har ya kasance abinda zuciyarta ke mata hasashe ya tabbata.....amma anya kuwa?,anya?,badai akhnan din ba. Tana jin sanda birra ta dawo ta ajiye komai,sannan cikin takatsantsan ta kashe mata dukka fitilun kamar yadda ta saba tamkar wata qaramar yarinya,ta rufe dakin bayan ta fice. Idanunta ta bude a hankali,sannan ta juya zuwa hannun hagunta,tana jin yadda bacci yayi wani irin nisa da idanunta. Ta lumshe idanunta cikin duhun ta sake budesu tana sauke ajiyar zuciya. Batasan me yasa komai nasa yake dawo mata a kai ba,tafiyarshi maganarshi yanayin magananshi da tafi mata wani irin idan yana magana da harshen France.......sai kuma uwa uba qamshinsa da tafi jinsa fiye da ko yaushe saboda rigarsa dake cukuikuye cikin duvet dinta. "Turaren kawai yake burgeni.....inason turaren nan,dole na mallakeshi" Ta fadawa kanta da kanta tana cusa kanta tsakanin rigar,saidai kuma hoton fuskarsa ne ya gilma mata. Wannan tattausan murmushin da lokaci na farko kenan data fara ganinsa saman fuskarsa. Murmushin daya soma jefa mata tunanin DAMA YANA MURMUSHI?.....da gaske kyau yana qarawa mutum kyau?. Wani irin emptiness takeji cikin zuciyarta da gangar jikinta. Ji take kaman ita daya take rayuwa cikin dakin,bugu da qari idanuwanta sam babu bacci,saita ture duvet din,ta miqe a hankali ta zura qafafunta qasa ta sanya bedroom slippers dinta tana gyara maballin silk sleep wear din dake jikinta daya zame. *H A I S A M* Private bedroom balcony din na daya daga cikin guraren da yakan zabi zama idan zaiyi aikin sirri daya shafeshi ko ya shafi gidan,saboda yana da tabbacin area din was secured hundred percent. A yanzu yana tsaye ne,sanye da da lausasan cotton wool sleep wear da dukkansu suka kasance kalar sararin samaniya. Wando ne dogo har qasa,sai rigar data kasance long sleeve ce. Takalmin qafarsa me tsananin taushi shima blue color ne,sai mug na zazzafan coffee dake riqe a hannunsa yana sipping a hankali. Baya buqatar yau yayi bacci da wuri,aiki ne me matuqar muhimmanci da yake sanya rai zai zama wani mataki na qarshe da zai warwarewa NIGER da ETHIOPIA wacece mammina?. Yana tsaye qyam.....the giant sheikh dinnan,hannunsa daya soke cikin aljihun wandon kayan baccin nasa,hannun damansa kuma riqe da mug din. Idanunsa a zube fes saman system din dake ajiye saman daya daga cikin kujerun dake zaman banza a gurin,yana kallon progress din da aka fara samu akan request din daya tura game da takardun. Cikakken information ya fara nema kan waye ya yiwa mammina su?,cikakken details na ma'aikatar da aka yisu,wanda yayi dama dukkan wanda ya jagorancin aikin. Ya gama tsara yadda zai bullowa kowa da komai,tabbas a wannan karon akwai buqatar ya shigo da yaudara barazana da wasan kwaikwayo a ciki. Yanaso ya kaucewa zuwa festival din,saidai sultane dama madam minister sun gama masa dabaibayi. "Kwana uku ne kawai haisam,ka daure ka fidda masarautar agadez kunya a matsayinta na me masaukin baqi" Sultane yace dashi yanayin muryarsa kamar yana roqonsa. Yanayin ya masa nauyi da yawa,don haka dole ya amsawa sultane din,saidai yanaso kafin gobe sultane ya dawo.....kafin gobe da zasu wuce festival din ya kammala da kaso mafi girma na wannan gagarumin aikin na qarshe. Dukka hannuwanta biyu ta sanya ta daure gashinta a baya,kafin tayi pulling qofar ta turata tana budeta a hankali. Iskar damina me kyau ta taso da hanzarinta tana shigewa hancinta gami da sanyaya fuskarta,abinda ya sanyata lumshe idanunta a hankali tanajan iskar sosai tana kuma jin wani numfashi sassauqa yana kubce mata. Ta saman screen din system dinsa yaga alamun motsi ta nahiyar cameras daya saka a gurin,bai motsa ba,bai kuma nuna alamun yaga dan adam ba,yaja arrow zuwa kan sashen camera din dake harbawa ya bude hoton gurin tarwai,wanda ya bude masa da cikakken hotonta live daya cika screen din system din gaba daya. 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 125* Lumshe idanunta tayi,sannan ta bude hancinta sosai ta shaqi sassanya kuma tatacciyar iskar da Allah ya yiwa halittunsa baiwa da ita.... Ba don kowa ya biya ba ko kuma yana biya,sai don zallar rahama da kuma ni'imarsa ga bayinsa. Fesar da iskar tayi a hankali,ta taka sosai zuwa tsakiyar balcony din tana jawo wata qaramar cushion chair,a nutse ta zauna,sannan ta ware idanunta a hankali tana saukesu akan balcony din dake fuskantarta. Balcony din sheikh muhammad haisam. Kamar haka yaga budewar idanunta ta cikin allon system din,wadannan blue eyes din,idanun dake da wani launi da suka sanya ya dade yana girmama zatin Allah. Tun yana shekarar farko a university yayi binciken dalilin samuwar hakan. Da farko ya dauka cuta ne ko lalura,saidai shi tun da can baya zama da abinda baisan meye ba.....bai iya zama cikin duhu ba kuma baya bari kansa yayi murfi,daga baya ya fahimci low melanin ne da kuma gado na halitta. Tamkar tasan yana kallonta kamar tana a gabansa,tamkar tasan idanunsa yana kanta ta juya idanun nata a hankali tana dora hannunsa saman sassalkar sumarta. Idanunsa ya lumshe sannan ya budesu duka lokaci guda yana jin zuciyarsa tana bugawa a hankali. "Subhana khalequ kulli shay'in" Ya furta can qasan zuciyarsa. A qasar da yawancin idanun mutanenta brown ko black......ga wani ido daban daya banbanta dana kowa.....ba kalan blue sosai kaman fenti ba,wani irin quite sky blue. Tana sauke hannun nata gashin ya biyota ya warware gaba daya yana lullube kafadunta zuwa gadon bayanta. Qaramin tsaki taja,wannan santsin nasa yana daya daga cikin abinda ya sanya sau da dama sai birra ta taimaka mata wajen daureshi,har yanzu bata iya daureshi yadda ya kamata ba. Hannu ta sake sakawa tana gwada tattareshi din kamar dazun,wannan yanayin ya bawa qirjinta da ko brazier bata saka ba daman gantsarowa gaba. Sauran kadan......saura qiris mug din hannunsa ya subuce ya fadi a qasa,saidai cikin zafin naman nan nasa ya saka daya hannun nasa ya tallafoshi. Wani irin abu me kaifin gaske yaji yana tsarga masa,sai ya koma da baya ya zauna saman qanqanuwar kujerar dake gefansa yana ajjiye mug din hannun nasa. A hankali ya maida idanunsa saman screen din,haka kawai,duk da yadda zuciyarsa ke gargadarsa ya kauda idanunsa akai smma sai ya samu kansa da miqa hannu ya jawo system din sosai gabansa. Ya sani ba zata iya ganinsa ba idan bashi yaso hakan ba,saboda yana bayan wata qatuwar flower guda daya da aka ajjiye a gurin don bada iskar oxygen me kyau. Tafukan hannunsa ya hade guri daya yana matsesu sosai gami da fidda siririyar iska daga bakinsa. Ta kasa daure gashin,ta sake sakinsa tana yamutse fuska gami da jan siririn tsaki. Sakewarta a gurin ya tabbatar masa tana jin amincin ita kadai ce a gurin. Hannayensa ya sake rabawa daga cikin na juna a hankali,wani abu yakejin yana fusgarsa,so yake yayi closing side na camera din inda take zaune,saidai kuma zuciyarsa na ingizashi sosai. "Halal dinka ce.....idan ka kalla baka sabawa Allah ba......sau daya kawai.....sau daya a dukka rayuwarka muhammad" Zuciyarsa ke fadi masa cikin taushi. Miqa hannunsa yayi da wani irin zafi zuwa kan system din,sai a sannan ya lura,sai a sannan ya gani. Rawa hannunsa yakeyi sosai,kamar wanda sanyi ya kama. Meye dalili?,me yasa dukka bai sani ba,abu daya kawai ya sani,abu daya yake iya ji cikin jikinsa,abu daya yake iya fahimta,yanaso yayi zooming video din sosai,yana so ya matso da video din dab dashi......yanason karon farko lokaci na farko a rayuwarsa ya qarewa wata mace kallo. Ya kalli abubuwa da dama,ya kalli abubuwa da yawa da yakejin matasa na fadi akan halittar diya mace. Ya karanta.....ya kuma haddace.....ya karanta komai daya shafi halittarsu har kamar yana jinsa shi wani likita ne a kansu,ya karanta komai daya shafi hali da dabi'arsu har kamar ya gama sanin halayyarsu gaba daya......amma ko sau daya bai bari ya sauka daga umarnin Allah ba. "Ka gayawa muminai maza da mata su runtse ganinsu,su kuma kiyaye farjinsu" Ya sani,yayi dukkan iyakacin iyawarsa.....yayi dukkan qoqarinsa na ganin ya kiyaye,bai taba yarda zuciya ta tunzarashi ba ya tsallake doka ko hurumin ubangiji......ya riqe kansa,ya yiwa zuciyarsa linzami.....duk da irin abinda yakeji,duk da irin yanayin dashi kadai yasan yadda yake wanzuwa a tattare dashi. Wannan din dai yayi imanin ko meye ya kalla Allah bazai taba rubuta masa zunubi ba,saidai tarin lada me yawan gaske. Koda ba don so ba.....ko da ba wani qaqqarfar alaqa ko dangantakar zuciya tsakaninsu......amma yana da tabbacin wannan halal dinsa ne.....wannan IKOnsa ne.....wannan damarsa ce Allah ya bashi. Wani irin abu yaci gaba da zagayawa kowacce jijiya ta jikinsa,tafin hannuwansa da qafafunsa dukka sukayi sanyi,kamar yadda numfashinsa ya soma sauya yanayin fitarsa. Yayi relaxing sosai cikin kujerar kamar zai narke su zama abu daya shida kujerar,idanun sun masa wani irin nauyi,idan yaji da kyau ma kamar hawaye ke taruwa a cikinsu. Hankalinta kwance take kai kawo tsakanin qarfe zuwa qarfe na balcony din,cikin wani nutsatsen taku. Tana jin ko hakan zai taimaka mata wajen zazzage dukkan wani tunani nasa. Idan tace shine abu na farko a duniya daya taba tsayewa tunaninta batayi qarya ba. Bata taba damuwa da komai da kowa ba,bata taba damuwa da wani abu ba......amma me yasa ya tsayewa tunaninta haka?. Meye dalili?. Amsar itace bata sani ba. Lokaci lokaci take duban balcony din nasa. Wani abu takeji can qarqashin zuciyarta da ruhinta. Ba motsin kowa,ba motsin komai,hasalima a iya abinda idanunta suke gani fitilun bedroom din a kashe suke. "Qila ma ya dade da yin bacci" Taji zuciyarta na gaya mata. Tsaiwa cak tayi tana dawo da maganar a kanta. Ya dade dayin bacci?dama saboda shi na fito?,meye damuwa na da baccinsa?,meye damuwana da motsinsa?. Tambayoyin da suka dinga dawowa cikin kanta kenan,suka sanyata kuma a hankali a hankali ta dinga takawa da baya da baya,har takai bakin qofar da zata maidata bedroom din ta shige da sauri. Wani irin numfashi ya sauke yana runtse idanunsa gami da matse jikinsa guri guda. Wani irin numfashi yaci gaba da saukewa yana jin zuciyarsa na wani irin qarfi,har yana jin alamun sautinta cikin kunnensa. Iskar da yake shaqa da komai ma yana jin kamar an sauya masa su ne gaba daya. Baisan adadin mintunan daya dauka a haka ba,ya sani dai yaji motsin bude qofar balcony din,ya kuma bude idanunsa yaga system din har ta shiga sleep mode saboda rashin wani motsi cikakke a tattare da ita. Idanu suka zubawa idanu shida omar din,omar din da bai sake bari sun hadu ba tun wancan ranar da yayi subutar baki. Ba yadda baiyi ba yazo su qarasa aiki yace masa shikam ya tafi hutu. Maleek ne dan sasanci a tsakaninsu,dariyar da maleek yayi a wannan lokacin bata da iyaka. Ga sasanci ga gulma da nashi dariyar yana cinsa. "Haisam dai?......zasuga yadda wannan al'amarin zai kaya.....zasuga yadda zai kasance.....baya sonta amma yana kishinta......auren CIMMA MANUFA ne amma komai yana tabashi game da ita?. " Kana lafiya?" Omar ya tambayeshi yana tsareshi da idanu. Besan me zai cewa omar din ba.....baya fatan ma ya fahimci komai,don haka ya daga masa kai kawai yana janye lumsassun idanunsa daga kanshi. Sake zuba haisam din idanu omar yayi,a jikinsa yakeji bai yarda da maganan haisam din ba. "Captain......" Daga masa hannu haisam yayi,bayaso yace komai,don yana jin yafi buqatar kadaicewa a yanzu. Takowa omar yayi,yana sake nazartarsa "Idan bakajin dadi ka tashi muje kasha magani zaifi kyau,baka zauna yadda ka saba ba......ga wasu document can dana shigo maka dasu". Idanu ya waiwayo ya zubawa omar,idanun da omar yaji kallonsu har cikin jininsa,kwarjinin nan ya dakeshi a hankali,sai ya dakata daga takowar da yake. Mamaki kadan yana sauka fuskar omar din,meye haka ya birkita haisam?. Bai taba ganinsa a bikice haka ba koda fushi yayi. "Kaje zan fito" Ya bawa omar din umarni nakai tsaye. Yana jin ta yaya?,ta yaya zai iya miqewa a yanayin da yake ciki har yayi tafiya. "Haisam....." "Omarrrr" Ya kira sunansa yana danjan sunan. Sak omar din yaya,kafin kuma ya juya yana ficewa a hankali,bai kuma tsaya a nan ba,koda ya fita din daga bedroom din gaba daya ya qarasa ficewa yana bar masa saqon daya shigo dashi. Ya sani bashi da tsawwalawa.....baida zafi baida yawan fushi,shi yasa duk yanayin daya nuna musu suke qoqarin yi masa abinda ya nuna yanaso. Idan baison magana da gaske yake baya so,idan ya nuna beson tambaya da gaske yake baya so,hakanan idan ya nuna bayason kusanci da gaske shima baya so. Da wata irin mutuwar jiki ya fito daga wankan daya zame masa tilas yayi,jikinsa gaba daya yayi wani irin laushi,ya zauna da bathrobe a jikinsa na lallausan auduga da zare yana sauke ajiyar zuciya. "Me nayi haka?" Ya tambayi kansa da kansa bawai don yasan wacce amsa ce daidai da tambayarsa ba. "Haisam ka nutsu......ka nutsu haisam,me kakeyi haka?,akhnan ce fa?" Ya gayawa kansa da kansa. Sai tunaninsa ya koma can baya.....farkon fara sanin wanzuwarta a gidan,farkon fara sanin WACECE ITA.....maganganunta a kansu hakeem da ire irensa,sai yaja qaramin siririn tsaki yana miqewa a hanksli. Tabbas kome Allah yayi hani akai akwai hikima a cikinsa. Yanzu irin wannan yanayin ko makamancinsa mazaje masu kallon haramci ga matan wasu suke tsintar kansu?. Me yayi zafi?,yanzu shima banda halal dinsa ya kalla yana da zunubi cikin littafin ayyakansa. "A'uxubillah" Ya furta a hankali,ya dora hannunsa yana shafar qirjinsa yana jin wata qanqanuwar nutsuwa data saukar masa. "Halal is the best.......tabbas halal is the best" Ya furta can qasan ransa. Koda ya sake shiryawa cikin wasu kayan baccin,yayi sallolinsa daya saba sai kawai yaja files din yana dubawa. Ya zauna sosai yana nazarinsu daya bayan daya. Wani abu ya saki a hankali daga qirjinsa tamkar qullewar wani bahagon dauri. Fuskarsa ta sassauta daga daurewar da tayi. LALLAI BA SHAKKA AKWAI TARIN BIYAN BUQATA GA DUK ADDU'A DA LAMARIN DA AKA SANYA ALLAH A GABA,ya fada can qasan ransa yana sake girmama hukuncin ubangiji da yace zai sauqaqewa bayinsa abu me wahala. ★★★ A washegarin ranar tamkar wata sabuwar duniya haka masarautar ta kasance. Sultane ya kasance na musamman a zukatan al'ummar agadez gaba daya,kamar yadda ya kasance wani jigo kuma abun soyuwa ga al'ummarsa. Adalcinsa,tausayinsa da yadda yake bada kulawa me girma ga talakawansa ya siya masa wata qauna a zukatansu,bawai iya cikin masarautar kadai ba.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 126* Awanni uku da dawowar sultane din,can cikin kebantaccen parlor din daya kasance guri ne na musamman,guri ne da ba wanda yake iya kaiwa wajen sai iyalin me martaba,sai kuma kebantattun bayinsa dake hidimar kula da gurin,wanda hidimar gurin ma ya zamana kamar gado ne. Asalin masu hidima da gurin idan sun rasu 'ya'yansu ake dorawa akai. Su biyu ne rak cikin parlor din,sultane wanda ya gama hutawa bayan shigowarsa,da kuma sheikh muhammad haisam. Dukkaninsu suna zaune saman lausasan sofas dake parlor din. Hira suke shida haisam din,wani irin kalar hira da kana kallonsu zaka tantance zallar aminci da yarda daga idanun sultane din zuwa ga haisam din. Cikin nutsuwar nan tasa.....cikin kamewar nan tasa yake amsawa sultane din. Dashi aka dauko sultane din daga airport......tare suka shigo da sultane har cikin gidan,saidai kuma suna dab da shiga sassansa ya samu ya zame ya shige cikin jama'a ya fice daga gidan. Akwai aikin da zausuyi da beeno a ranar......wannan gidan dake kan hanyar villa street,gidan daya tabbatar akwai wani killataccen abu me tsananin darajar da girmansa yakai qololuwa a gurin zaituna. Bai kuma shigo gidan ba sai ana dab da sallar la'asar,a masallaci suka hadu da sultane din,sukayi sallah a sahu daya "Ina ka shiga ne muhammad?.....na tambayi iyalinka itama batasan inda kayi ba" Maganan yazo masa a wani ba zata,iyalinsa kuma?. A hankali sai kansa ya kawo wuta,ya tuna yana magana ne akan akhnan. "Wani uziri ne na gaggawa ya tasomin ranka ya dade" "To ba laifi,idan ka kammala ina buqatar ganawa da kai". "In sha Allah" Ya fadi. Can qasan ransa yana sake yaba dattako da kamalar dattijon. Yana da ikon bashi umarni kai tsaye a matsayinsa na wanda ke rayuwa qarqashin masarautarsa da dokokinsa.......saidai kuma duka baiyi hakan ba,ya zabi bashi zabi.....ya zabi neman ALFARMA a madadin bada umarni nakai tsaye. Wanka kawai yayi,ya kuma shirya cikin wata maroccon jallab me sulbi da daukan idanu. Hasken fuskarsa ya fita ta qarqashin kalar maroccon jallab din jikinsa data kasance ruwan sararin samaniya,hakanan kwarjininsa ya sake fita sosai. A yau nauyin sultane yakeji sosai,nauyin da shi kansa baisan dalilinsa ba. Amma yadda sultane din ya sake sosai kamar yadda motii ke sakewa dashi ya sanya ya tattara nutsuwarsa a kansa. Yadda yake bashi labarin komai daya shafi tafiyar yake sake azawa haisam din wani nauyi saman zuciyarsa. "Ya yarda dani fiye da tunani na......yaya zaiji a duk sanda ya fahimci cewa na aminta na auri diyarsa ne saboda na danawa MATARSA TARKO?". Iya wannan tambayar kawai ta sanya yaji wani nauyi saman zuciyarsa kamar sultane din yana fahimtar abinda yake tunani a daidai lokacin. *MORSA SAFIYYA* Rana ta farko a rayuwarta da takejin wani nutsuwa a zuciyarta. Rana ta farko da takejin wani alfahari yana ratsata,rana ta farko kuma da takejin kome sultane yayi mata ya gama wankuwa a idanunta. Ta gaza hana kanta murmushi a duk sanda ta tuna akhnan din a yanzu tana qarqashin iko da mulkin sheikh muhammad haisam. Mutumin da dukka addu'arta a kansa nutsuwa take bawa zuciyarta. Ko zatayi addu'a dubu,ko zata maimaita istikhara irin wadda ma'aiki ya koyar guda dubu tabbas shi din takejin hankalinta yana sake kwanciya dashi. Batasan me yasa sultane ya gayyaceta a wannan yammacin ba,amma abinda tafi sanya rai shine wani liyafar cin abinci ne ya shirya saboda dawowarsa,kaman yadda tayi masa ba zata ta hada masa wani qaramin liyafar a dazun. Tsaf ta shirya cikin wani qawataccen shadda me tsananin tsada da daukan hankali,marron color ce wadda aka zuba mata wani qasaitaccen aiki da yake tabbatar da cewa ita din jinin BUZAYE ce. Wani irin kyau ta ajiye.....wani irin ado data manta yaushe rabon da tayi irinsa. A yanzun take jinta a matsayim rayayya,a yanzunne take jinta a matsayin mutum kamar kowa,tunda tana da dukkan yaqini da nutsuwar jinin safeena ya isa ga SAFE ZONE. A baya ba zata iya dorar da komai ba. Duk wani dare da wuninta da zai gilma ya kuma gushe cikin rudani da lissafin wanne hali AKHNAN take ciki?,wanne hali zata kasance.....wannan tunanin shine abinda yake kassarata a kowacce rana. Da karsashinta take isa sassan sultane,a yau din hatta da hadiman da sauran bayi dake da aikin kula da wadannan hanyoyin sunsan akwai wani ajiyayyen farinciki tattare da morsa safiyya. *AKHNAN* Ba abinda ya dagata daga gurin sultane sai don ta barshi ya huta,dukkan wata qauna da soyayya tana jinta tsakaninta da mahaifin nata a yau kamar an sabuntata. Wani wakeken gibi....wani babban space da takeji a rayuwarta a yau yana cike gurbinsa a hankali. "Ashe akwai wani gurbi da muhallin daya zamana MALLAKAR UBA ne shi kadai?" Ta dinga tambayar kanta sanda take komawa sassanta. Mamaki ne yake maimaituwa cikin kanta,tanason banbance yanayin da dana yanzu......tana banbance yanayin data tsinci kanta a sanda sultane ya miqa mata ragamar komai......ya barta ta auri zabinta,da kuma yañzun da ta aminta da abinda yakeso. Tabbas nutsuwar ta dabance.....tabbas farincikin na dabanne......wannan yanayin baya mata kama da kowanne. Iya aminta da tayi da auren da sultane ya rataya mata shine abinda ya haifar da wannan walwalar aminci da kuma gyaruwar alaqar a tsakaninsu?. Wannan tambayar ta yita maimaitawa kanta.....wannan tambayar da take buqatar amsarta......tambayar data sanyata tsaiwa gaban madubi tanata duban fuskarta daketa glowing saboda yadda fatarta ta karbi gyaran da ake mata fiye da yadda take zato. "Farincikin dake cikin yin biyayya ga umarnin iyaye ya haura duk yadda zaki fasalta biftu......" Aisa dake hada wasu document ta fadi kamar tasan abinda yake zuciyar akhnan kenan. Wannan abun kadai shi ya haifar da zaquwarta wajen ganin yammaci ta sake komawa ga mahaifinta sultane. Tsaf ta kammala shiryawa cikin Egyptian abayar me wani irin sulbi qyalli da daukan idanu. Maroon color ce,budaddiya sosai wadda aka zuba mata wasu irin stones masu kyau da daraja. Ita kanta data tsaya gaban madubin da birra ta ajiye mata kamar yadda ta saba ajiye mata shi a duk sanda ta gama tayata ta shirya sai da taga yadda ta kwanta a jikinta da wani irin yanayi me daukan hankali. Socks ta zauna birra ta zira mata. Umarnin yaa hairaan ce,batasan me yasa tazo yau din da kuma wannan salon ba,amma akwai wani sashe na respect da take bawa hairaan din,kuma socks din basa daya daga cikin abinda ke takurata don haka ta sanya,ta kuma zura qafarta cikin qawataccen takalmin da yazo mahadin rigar. Ta miqe tsam,taku daya biyu aka murda handle din qofar,sannan kuma kai tsaye ba tare da jiran umarni ba aka shigo. Mammina ce......murmushi kuma shine abu na farko data fara saukewa akhnan din tana qarewa shigarta kallo. "Tabarakarrahman........diyata tafi ta kowa" Mammina din ta fadi a fili,amma can qarqashin zuciyarta kuwa,wata irin wuta ce ke kunnuwa......can qasan ranta wutar kota halin qaqa saita soma ganin tagayyarar akhnan da tabuwar rayuwarta shine abinda ke kunnuwa. Wani abun mamaki......a yau din da take yabonta,a yau din da take kodata.......a wannan lokacin ba komai cikin zuciyarta game da dukka maganganunta. Wani yanayi da yasha banban da yadda ta saba ji akan kalaman mammina din,tun daga sands ta mallaki hankalin kanta zuwa yanzu. Kalaman mammina a gareta suna da wani irin tasiri......suna da wani irin kaifi da suke sanya kanta kumbura da kuma huruwa,amma a yau sai taji bataji ko daya a kai ba. "Zuwa nayi na biyo mu wuce sake gaida sultane ni da d'iyata" Ta fada tana neman gefan sofa bed ta zauna,abinda ya sanya birra fita a hankali tana bar musu dakin. Dan duban mammina tayi kadan,sai kuma ta basar da salon miskilancinta. A duk sanda ta waiwaya ta kalleta sai taga ba abunda take gani sai sakinta BARO BARO sama da guda goma da mahaukacin mutumin da itace silar shigowarsa rayuwarta yayi mata.... Tana jin ba dadi.....tana jin wani irin ciwo har qasan zuciyarta idan ta tuna cewa......ita kadaice keda tarihi irin wanna.....ita akhnan da labarinta ya shiga bakunan 'ya'yan sarakuna dana manyan attajirai da dama. Sake dauke kanta tayi,duk yadda taso ta amsawa mammina din koda da qanqanuwar kalma ce ta kasa amsa mata. Sai ta fara takawa zuwa bakin qofa,a sannan ne ta samu ta fusgo kalmar. "Na gode" A taqaice. Qanqance idanu mammina tayi tana kallonta,wani irin mamaki yana ratsata "Ta canza.....tabbas ta canza" Ta fadi qasan ranta. Canji ne ba qarami ba,ba kuma na taqaitaccen lokaci ba,canji me girma da nauyi wanda koda yaushe yake zame mata barazana zuwa ga tabbatuwar tsarinta. "Khadeeja" Ta kirata da wani yanayi me nauyi a muryarta. Mamaki ne ya sakata tsaiwa,saboda tunda take da mammina din bata taba jin ta kirata sunanta na asali kai tsaye ba sai yau. Bata umarceta tazo ba,saita tako ta cimmata. "Meye yake damunki?,wannan yanayin naki yana sakamin shakku da kokwanto akan matsayin da kika daukeni a yanzu" A nutse ta waiwayo ta zubawa mammina idanu,bada kowanne nufi ba.....amma sai kallon ya yiwa mammina din nauyi,a karon farko taji akhnan a yau kawai ta mata kwarjini. Kwarjinin da tabbas tasan dashi,amma bata daukeshi da zurfi har haka ba,bata daukeshi da zurfi da nauyi kamar yau ba. "Wani abu ya faru?" Ta tambayeta kai tsaye tana jin kamar tana bata mata lokaci. Mamaki ya sake shigarta,ta qanqance idanu tana dubanta sosai. "Baki amince da dukka tsarina bane akhnan?" Idanunta sosai ta zuba cikin na mammina din na wasu daqiqu kafin ta janye dubanta,sannan taci gaba da takawa tana yin gaba,abinda ya sanya mammina din mara mata baya itama tana biye da ita. "Basai na furta da bakina ba......ba kuma saina dakatar da aiwatar da abinda nima nakejin zan iyayi ba.....idan kin yarda da kanki mammina.....kawai kici gaba da abinda kika tsara.....basai kin gayan tsarikanki ba......basai kin tuhumeni nima akan tsarikana ba" "Ta canza!" Ta fadi can qasan maqoshinta. "Zaituna dole kema ki canza taku!!!" Zuciyarta ta gargadeta da mafi girman gargadi. Cikin sakewa.....cikin rashin nuna damuwa ta saki murmushi. "Zaitunan nan dai ta jiya da shekaran jiya har yauma itace,....ba kuma zata canza miki ba,ba zata kuma fasa shiga lamuranki ba har sai sanda kika cimma gaci" Haka kawai taji kalaman basu burgeta ba,mutum ce ita da sau tari take zabar zaman lafiya da kwanciyar hankali sama da rikici da tashin hankali,wannan ya sanya take da dab'ar miskilanci.......wannan ya sanya take da dabu'ar kebe kanta a mafi yawancin lokuta ma.......a yanzun a wannan lokacin......tana jin nutsuwa da Kwanciyar hankali sama da sanda zaituna ke tsara al'amuranta dama bibiyarsu. Tare sukaci gaba da takawa,saidai akhnan din ta zabi shuru sama da magana......ko dama can tafi zabar shurun,a yanzun kuwa ta fifitashi ne. "Zan tabbatar miki da AUREN YARJEJENIYA ne tsakaninki da wancan malamin......alqawari na yiwa mahaifiyarki zan samar Miki da dukkan wani farinciki.....alqawari nayi mata bazan bari rayuwarki ta taba toxarta ba,alqawari ne zan samar miki da dukkan abinda kikeso......bazan bari komai da bakiso ko baki qauna ya shiga rayuwarki ba" Ta fada da marairaicewa,harda guzurin qwalla cikin idanunta daidai sanda suke dab da shiga farfajiyar da kebantaccen dakin hutawar sultane din yake. Waiwayowa tayi kadan ta kalleta,wani abu yana tsalle da rarrabuwa a qirjinta. Wanne ne yafi dacewa ne?......ta tabbatar mata da MURADIN ZUCIYARTA?.......ko kuma zata tsaya wajen zaba mata abinda ya dace da ita?....koda zatayi kuka......koda zata quntata......koda zataji ba dadi?. Rasa banbamce amsar tayi.......kasa tantance wanda yafi kamata ta zaba a ciki tayi saboda daddad'an qamshin nan nasa da ya shaida mata YANA GURIN. Saukar da kanta da kuma idanunta qasa shine abinda takeso tayi,amma haka kawai taji ana sarrafa zuciyarta dama idanunta wajen watsasu a dakin hutawar sultane din,labbanta masu kalar ruwan hoda me haske suna motsawa da siririyar cikakkiyar sallamar data samu kanta da yinta,sallamar data zarce ta kuma hade da fadawar idanunta cikin nasa. 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 127* Kamar kowanne lokaci da zata ganshi......yana zaune cikin wannan nutsuwar.......wannan kwarjinin......da wannan zaman da yake nuna wani babban abu tattare dashi.....babban abun da har yanzu ta gaza canko MENENE?. Da qyar ta zare idanun nata daga kanshi da wani irin sanyi da batasan na meye ba. Kwana daya kwana biyu kwana na uku kenan bataga koda gilmawarshi ba. "Kwana uku?" Ta tambayi kanta,sai taji wani abu ya mata tsaye a wuya,wani abu da batasan meye ba......wani abu me nauyi mara dadi a qirjinta. Ko a dazun cikin wadanda suka yowa sultane rakiya,ta samu kanta,ta kuma samu idanunta da jujjuyawa ba tare da tasan me take nema ba?. Haka kawai taji kamar akwai wani gibi ko wani gurbi ko muhallin da ba'a cikeshi ba. "Taho ki zauna a nan" Kalmar data iya ji qwaya daya kenan Sultane yace da ita yana nuna tazarar dake tsakaninsa da haisam din. Idanunta ta sauke a gun,tazara ce maras nisa sam,koda tayi kusa da sultane yayin zamanta.....dole zatayi kusa dashi ainun. Ta yaya?,ta yaya zata iya dauke wannan kusancin?,ta yaya zata iya shanyeshi?. Idanunta ta lumshe a hankali sannan ta bude lokaci guda. Ta tabbatar yau sai abinda ta gani.....qamshin nan......wannan qamshin tana jin zai iya hallakata tsaf kafin ta tashi daga tsakiyarsu. Batasan idea din wanne shu'umi bane......batasan wanne shu'umin ne ya samar da wannan qamshin ba. "Wai zaman me kukeyi safiyya da baku miqawa muhammad matarsa ba tun ranar da aka daura aure?" Sultane yayi maganar kansa tsaye,idanunsa kan morsa safiyya. Morsa safiyya din da a yau takejinta tamkar an bata kyautar duniya da abinda yake cikinta. Wani lafiyayyen murmushi ta sauke.....wannan murmushin dai dake kashe zuciyar mammina da wani irin makami da takejin ba na biyunshi a duniya wajen iya illata ZUCIYA......(zuciya irin tata ba......zuciyar maqiyi,zuciyar abokin adawa,ya rabbussamawat Allah ka doramu akan maqiya,Allah ka sani mu bama qin kowa......bama tsanar kowa,saboda mun sani duk wanda ka halitta bawanka ne,kuma kana qaunar abinka,bamu da hurumin da zamu tsaneshi ko mu qishi,tunda bamu muka halitta maka shi ba,ya Allah kai mana tsari da duk wanda yake da mummunar nufi a kanmu don isar shugaba S A W har izuwa ranar qarshe). Maganar data saukarwa akhnan a bazata da wani mummunan faduwar gaba........ta kuma sanyata qarasa zama duk da bata gama kaiwa qasa ba. Ta saukar da wani nauyi a zuciyar haisam me yawan gaske.......a nasa plan din koda a haka aka tafi komai zaiyi daidai da tsarinsa......basai ankai nan ba......basai ankai inda za'a tattarata dukka a damqa masa ba. "Idan da ace ka bada umarnin aikata hakan......la budda da sai mun zartar......saidai muna buqatar kimtsa diyata da kyau" . Ido mammina ta lumshe,ta kuma ja numfashi sosai tana qoqarin kimtsa kanta. "Ki nutsu zaituna......NUTSUWA MANA ZAITUNA!" Ta samu kanta da tsawatarwa kanta da kanta. Maganan yayi tasiri,don haka ta qaraso tana zama daga gefan morsa safiyya gami da fidda murmushi a fuskarta. "Haka maganan yake ranka ya dade........d'iya ce ta musamman......wanda nima nake dakon safiyya ta gama nata shirin na dora da nawa" "Ban yarda da wannan tsarin ba......shirin meye haka?". Numfashi haisam yaja,yana jin maganan tayi nauyi suci gaba da yinta a gabansa. Sultane yayi mugun bashi matsayin da yakejin bai kamata ya bashi ba. Ya kamata ko yaya ya rage wannan girman matsayin daya bashi,tunda komai TEMPORARY ne,komai FAKE ne......komai na WUCIN GADI NE. "Zan iya qarasawa?" Ya tambayi izinin sultane cikin girmamawa. "Au.....tafiya zakayi ka barni da yaqin karba maka mata?,kai ba zaka tsaya su baka matarka ba?" Sultane ya fadi cikin barkwanci . Dariya akayi,saidai tsakanin shi da mammina da akhnan data sadda kanta qasa cikin wani yanayin bugun zuciya dariyar kowa tasha banban data d'an uwansa. "Ku gama duk abinda zakuyi ku bashi matarsa,don rana ita yau in sha Allah zasu wuce umra shi da ita.......kana da zabin dawowa nan?.....ko zaku wuce gida?". Kai ya jinjina a hankali. Ya akayi kwanakin da sultane ya yanke suke daidai da kwanakin CIKAR AIKINSA?.......ya akayi kwanakin da sultane ya dauka suke daidai da kwanakin KAMMALUWAR KUNDIN ZAITUNAN ZEENATU?. Ya akayi suke daidai da ranar farko da zai bude bakin BOMB din da zai fara kada rayuwar zaituna?. "Zamu wuce ETHIOPIA" haisam ya fada kansa tsaye. Sunan Ethiopia ya buga da wani irin qarfi a kunnuwa da zuciyar mammina. Sunan ETHIOPIA kadai barazana yake zame mata ballanta tuna QASAR. Ethiopia din da yanzu ta zame mata JARRABAWA na dukka darenta,duk wani dare da zata sanya kafadunta saman gadonta sai Ethiopia gaba daya tazo mata duk da kasancewarta qasa ba dan adam ba. A manya burikanta da tasan basu da ranar cika shine......shafewar Ethiopia gaba daya......shafewa ta har abada,inda tana da hali.....inda tana da dama da shafe qasar zatayi daga doron duniya dama dukka abinda ya shafeta. Sunan qasar ya sake dokawa a kunnuwan morsa safiyya,ya taso da tsohon ciwon dake kwance a cikinsa. "KHADEEJA" shine sunan data furta a hankali tana dauke wata qwalla data sauko mata. Haisam shi daya ya lura da wannan,haisam shi daya ya lura da motsawar labban morsa safiyya. Wani abu yaji ya sauka saman zuciyarsa.....bazai iya haqurin ci gaba da kallon morsa safiyya a haka ba.....bazai kuma iya haqurin ci gaba da barin nanay dinsa cikin duhu ba.....saidai ba yanzu ba.....ba'a cikin agadez ba......ba a wannan lokacin ba......sai a sanda yakai mata diyar safeenarta gabanta......a sanda ya hada hannun nanay dinsa da hannun copy na safeenarta. "Ma sha Allah.....hakan yayi,to kunji.....saiku gama duk uzurinku,gobe zasu wakilceni a festival......kwana biyu nakejin zasuyi saboda visa dinsu ta fito tun ina can......khadeejatu" Sultane ya fadi yana duban akhnan. "Na'am bappi" Ta furta da wani irin sanyi,da wani irin yanayi da yake sauyata daga akhnan dinnan.....wannan biftu din me tsananin kafiya da taurin kai......zuwa new version na princess khadeeja muhammad hammud. "Naji dadi sosai.....naji dadi sosai yadda nazo na samu ba wata matsala,naji dadi sosai yadda na tarar da komai fiye da zatona.....na kuma sake alfahari dake sanda haisam ya tabbatarmin komai lafiya.....naji alfahari dake da ban samu labarin tarzoma ko wani abu makamancin haka daga gareki ba.....Allah ya albarkaci rayuwarki......ya baki ikon yin biyayya ga mijinki kwatankwacin yadda SAFEENA ta bini" "Ameeeenn" Amsawar morsa safiyya da wani sauti dake nuna zallar qwarin gwiwa ta sauka a kunnen mammina,ta kuma gauraya da sautin sunan SAFEENA. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Qasa tayi da kanta tana jin wani ciwo yana diga saman zuciyarta. "SAFEENA.....SAFEENA" Wai sai yaushe kunnuwanki zasu daina jin wannan sunan?,sai yaushe wannan sunan zai daina gilmawa cikin rayuwarki?,sai yaushe zaki samu AMINCI?,sai yaushe zaki huta?,yaushe SAFEENA ZATA daina zame miki barazana?. "ETHIOPIA" sunan ya sake dawo mata fes cikin kanta,dawowar sunan daya sanyata daga kanta da hanzari takaisu ga haisam. Cikin wata irin sa'a idamunsu suka gauraya guri daya. Wani irin bugawa zuciyarta tayi da ganin wadannan idanun bisa kanta. "The silent one......jinin ibraheeem" Taji ana fadi tsakiyar kanta. Wasu irin idanu irin na ibraheeem sak.....wani irin kallo irin na ibraheeem......kallon da bazata manta dashi ba muddin numfashinta(WAYE IBRAHEEEM DIN?.....MEYE TSAKANINTA DASHI?.....AKWAI WATA A QASA NE TSAKANINTA DA MAHAIFIN HAISAM BAYAN WADDA TAKE TSAKANINTA DA MAHAIFIYARSA?). Wannan kallon......wannan idanun.....dama dukkan abinda ya faru ranar a parlor din shine abinda ya tsaye mata a kai. Sunan Ethiopia ya dinga wanawa cikin kwanyarta kamar ana buga gwangwanaye kusa da kunnuwanta. "Tafisu......inaji a jikina jinin ibraheeem ne wannan" Abinda ta kira tafisu kenan tana gaya mata. Kai tafisu ta girgiza cikin nutsuwar nan tata da kaifin basira. "Idan kuma bashi bane bafa?,idan kuma wasa kawai yake miki da hankali fa?,idan kuma so yake ya dauke hankalinki kawai daga kan komai fa?" Sosai maganganu tafisu suka ratsata. Ta miqa hannunta tana dafa na tafisu. Tana jin gaba daya a yanzu rayuwarta kamar ta ta'allaqa da ita,tana jin a yanzu kamar bata iya wani tunani me kyau,kamar kwanyar tafisu ce ke iya hange mata komai.....kamar wata Katanga ta kusa GINE tunaninta. "Gidancan na villa street" Shine abu daya dake kwanyarta a yanzu. Duk da tasani.....wani kebantaccen abune da ko tafisu batasan dashi ba,amma DAUKE ALMAZ tana kallonsa a matsayin gargadi.....daukeshi akayi da gasken.....ko yasha ta gaya masa qarya ya gudu da qafafunsa ya shriya daukeshi akayi?. Koma meye yana fatan ALMAZ ya narke har abada......koma tafiya yayi tana fatan ya tafi kenan har abada........tunda ko be tafi ba.....dashi da duk wanda jininsa yake yawo a jikinsa irin jinin nan data tsana......dole ne babinsu ya shafe gaba daya daga doron duniya. *_FESTIVAL DE l’AÏR_* *_Sanda sabbin shafuka zasu bude.......tsaffin shafuka kuma zasu rufe kansu da kansu_* Cikin wani irin yanayi da tsari na girmamawa sultane yasa aka shirya aka kuma tsara komai,yadda tafiya zata kasance daga nan har zuwa sansanin da za'a gabatar da bikin. Sansanin da zuwa yanzu idan ka kalleshi zaka rantse ba shimfidaddiyar sahara bace a kwana uku baya daya wuce ba. An qawata gurin da komai na buqata,an gina tent tent na kwana da canopy saboda zama,bandakunan tafi da gidanka na wucin gadi,kujeru qawatattun na zama don hutawa.....hakanan baqi da suka fara sauka daga kowanne sashe na qasar niger dama qasashen duniya gaba daya. Wani yanayi aka samar me cike da daukan hankali da ba'a taba samun irinsa ba a tarihin festival de l'Aïr....tun daga yadda aka tsara tent din layi layi unguwa unguwa.....kamar yadda tsaron gurin ya zama na daban saboda kusan komai bisa shawara da tsarin sheikh muhammad haisam aka gabatar dashi a wannan shekarar. *AGADEZ PALACE* Har cikin jininta takejin jinin BUZAYE yana mata a yau,a yau din ta jita a cikakkiyar buzuwa wadda ta amsa sunanta,musamman data kalli kanta cikin shigar suturar al'adar buzaye. Wata irin shadda ce a jikinta data fidda ainihin zallar al'adar buzaye,wata irin color take bayarwa,ita ba dark purple ba.....ita ba ruwan hanta ba hakanan ita ba baqa ba,saidai kalar da tazo da ita me duhu ta haska ainihin fatarta gami da fidda zallar kyanta. Irin wannan rana tana zame mata ranar alfahari.....ba ita kadai ba,rana ce me muhimmancin gaske agun kowanne buzu dama al'ummar niger mali da burkina faso gaba daya. Baya kawai birra taja tana dubanta,murmushi na fita daga saman fuskarta. Wani irin kyau akhnan din tayi mata yau din. "Kinyi kyau ranki ya dade" Ta furta cikin girmamawa. Maganan birra din ta sanyata maida dubanta ga madubin tana qarewa kanta kallo. A yau sai take ganin kamannin data gani saman hoton mahaifiyarta akan fuskarta. Hannu tasa ta jawo Locker din gabanta,ta zaro hoton tana kallonta. Murmushi take,murmushi takeyi sosai cikin hoton,tamkar ba abinda yake damunta.....kamar ba ita ta rasa yaranta har guda biyu ba,akwai alamun tawakkali sosai da imani da yarda da qaddara a tattare da ita. Tana da blue eyes irin nata......hancinta shape din fuskarta da sauran wasu abubuwan da suke sake bayyana tsananin kamanninta da ita. Tare da birra suka dauke idanun daga kanta,ta sauke ajiyar zuciya,daidai sanda birran take cewa "Allah ya gafarta mata" Samun kanta tayi da waiwayowa tana duban birra din,sai taji qafafunta sunyi sanyi "Ameen" Ta fadi a hankali tana maida idamunta ga madubi. "Allah ya gafarta mata" Itama ta samu kanta da fadi can qasan maqoshinta,tana kuma sake maimaita kalmar. Ba zata iya tuna rana ta qarshe da tayi wannan addu'ar a kanta ba.....ba zata iya tunawa ba,tana dai tuna sabani na qarshe da suka samu da morsa safiyya. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 128* "Hairaan,duk sanda ta gama sallar nan ki sanyata ta yiwa safeena addu'a" A wata rana kenan bayan hairaan ta sakata a gaba tayi sallah. Ranar mammina bata nan,ta fita dubiyar marasa lafiya asibiti kaman yadda ta saba. Kusan dukanta hairaan tayi kafin ta fara sallar,tanayi kuma tana kuka,daga qarshe kuma hairaan din tace lallai saita yiwa safeena addu'a. A sannan bata gama tantance wace safeenar da ake damunta a kanta ba......ko sanda zata ta tance wace kuma tuni mammina ta sabar mata da kammala sallarta ta tashi ta kama sabgogin gabanta,ita kanta bata saba ta daga hannu ta yiwa kanta addu'a ba bare a sako da mahaifiyarta. A yanzun.....a daidai wannan lokacin sai komai ya dawo mata kamar yanzu yake faruwa. Morsa da sultane a bakinsu kawai takejin "Idan kinyi sallah ki yiwa safeena addu'a" Me yasa mammina bata taba gaya mata haka ba?. Wannan tambayar itace ta tsaya mata cak a rai,ta kuma hade da alamun bude qofar dakin da taji anyi. Hairaan ce,sanye da tufafi itama shigen nata. Tana dauke da Aaron a kafadarta. Tayi wani irin kyau,irin wannan asalin kyan na buzaye wanda suka gajeshi tun daga salsalar turkawa. Yaron tabi da kallo tana amsa sallamar tata,wani abu da hairaan ta lura ta koya kwanan nan. Tanason yara sosai.....ita kanta ta sani,saboda ta rayu tsakanin manya ne,ta rayu a inda bata ganin yara,amma wani abu ya taso ya danne wannan feeling din daga ranta. Rashin ganinsu da rashin sanin yadda idan an batasu koda riqewa na wasu mintuna yadda zatayi handling nasu ya binne komai daga ranta. Ko zamansu Aaera da Aafreen basu wani dameta can can ba,amma zuwan yaaa hairaan da qaramin yaron Aaroon kullum idan ta kalleshi sai taji yaron yana burgeta. "Ma sha Allah" Hairaan ta fadi tana murmushi,ita kanta kyan akhnan din ya daketa,ya bugeta da wani irin burgewar data gaza boyuwa. Karon farko ta samu kanta da sakin wani qaramin murmushi mara zurfi,mamaki ya sake kama hairaan sanda taga akhnan din tana miqa hannu zuwa ga Aaroon. Sai data kalli akhnan din sosai,tanason tabbatarwa kanta itace?. Kallon daya sanya akhnan taji nauyin hairaan din ya saukar mata. Tunda take haife haifen yaranta ko Allah ya raya bata taba cewa ba ballantana akai ga yunqurin daukarsu. Batace komai ba ta zame Aaroon dake bacci daga kafadarta ta miqa matashi,ta sanya hannu biyu yadda taga anayi ta tallafeshi sannan ta rungumeshi a jikinta. "Ashe haka akeji?" Ta tambayi kanta sanda dumin yaron ya ratsa jikinta. Shehnaz itace sarkin rakace rakacen yara,takance mata. "Yaro.....yana da nishadi da debe kewa,akwai wani abu na musamman tattare da yara.....ko dabba idan kikaga ta cutar da yaro ba qaramar azzaluma bace". Idanunta ta dauke daga fuskar yaron ta maida ga hairaan "Bacci yake" Kai ta gyada mata,tana jin dadi da mamakin sauyin dare daya haka?. Duk da ba'a mamaki da ikon Allah,ba'a kuma raina qarfin addu'a,addu'a ma irinta momma data dauki sama da shekaru ashirin kullum sai tayi. "Tunda abida ta gama shiryashi yahau bacci....." Ta amsa mata,kafin shuru ya sake mamayar dakin. Neman izinin shigowa daga birra kuma ya katse shurun. "Me wada yace na shaida miki komai na tafiya ya kammala" Kai ta gyadawa birra ta fara yunqurin miqewa da Aaroon a hannunta,sai hairaan ta miqe da sauri da zummar karb'arsa. "Ki qyaleshi,zan iya" Ta fada da qarfin zuciya,duk da ita kanta mamakin qarfin halin da tayi takeyi. Bata taba daukan yaro ya jima haka a hannunta ba,yau gata itace rungume dashi har zasu fita. "Anya akhnan sheikh haisam zai bari ki fita a haka?" Hairaan ta furta tana tsaiwa a bayan akhnan din. Gaba daya shigarta ta fidda sigar kyanta,wanda dama hakan kamar wani abune daya zama jiki. A duk shekara a gurin bikin princess of agadez din daban take fita,kyanta kwarjininta dama kamalarta. Fuska kadan ta kyabe tana duban hairaan. "Meye aibun shigata ummin Aaroon?" Murmushi hairaan ta saki,yau tanata ganin abun mamaki tattare da akhnan din. Ummin Aaroon ba a bakin akhnan take jinsa ba,saidai ta jishi a bakin falaak ko wasu cikin causing dinta. Tare suka jero da hairaan da falaak wadda tayi wani irin kyau itama cikin shigar suturar al'adar,saidai wasu kaloli da suke bambanta kadan kadan dana wasu. A yau sai takejin kamar festival din ya banbanta dana kullum,haka kawai takejin wani irin sanyi da sakewa a ranta,nutsuwa ta musamman takeji a tattare da ita. Saidai kuma haka kawai ta dinga jin faduwar gaba kadan kadan sanda suke dab da qarasowa farfajiyar farko da zata fiddosu zuwa ga babbar harabar gidan data tabbatar kowa da kowa yana jira. Abinda ta lura dashi,a yau din ba wani cikin hadimai ko bayi maza tare da ita,daga ita saisu birra din,sai hairaan da falaak dake biye dasu. Duk da ba zuzzurfan sabo bane da sanayya tsakaninta da falaak din ba,amma ta fuskanci akwai wani kwantacciyar walwala tattare da ita. Sau uku kuma suna hada idanu da ita tana sake mata murmushi,ana hudunne ta kalli hairaan. "Ummin Aaroon......wai ba zaki gayawa yaa akhnan bane?". "Me?" Hairaan ta fadi tana duban falaak din,sai kuma ta furta. "Au.....sannu mara kunya.....wai tanaso saita gaya miki itama sultane ya bada ita......ya bada ita wa maleek......aboki ga sheikh haisam" Daga kanta tayi da sauri tana duban falaak,ta dauka zataga samu yanayinta ya canza......ta dauka zata ganta yanayinta ya sauya zuwa yanayin bacin rai ko kuma qunci,amma ga zallar mamakin ta sunne kai ma falaak din tayi tana murmushi. Idan har idanunta sun gane mata daidai,idan har idanunta ba qarya sukayi mata ba falaak dariya take me cike da walwala da annashuwa. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Abokin sheik haisam" Maganar ta sake maimaituwa cikin kanta. Inde hakane me ya banbamta yanayinta dana falaak?,me yasa falaak take walwala ita kuma ta kasa samun wannan yanayin?,me falaak ta hango wanda ita bata hangeshi ba?. Me yasa falaak take farinciki da samun abokin shiekh muhammad amma ita ta gaza jin hakan a tattarr da ita?. Bata samu sararin amsa wannan tambayar ba,ta tsinci sautin mammina tana isowa gurin itama. Ji tayi kamar wani abu yayi disturbing nata da bayyanar mammina din. Ta daga idanunta a nutse tana dubanta sanda take dubanta itama. "Meye haka?" Mammina ta mata tambayar da dukkaninsu ba wanda ya gane ma'anarta ballantana amsarta. Cikin nutsuwa hairaan ta tako gaban akhnan. "Kawo Aaroon din mu wuce kafin ku gama" Janye yaron dake kafadarta akhnan tayi. "Qyaleshi bacci yake.....zamu taho" Hairaan batace komai ba ta juya tana kama hannun falaak sukayi gaba. Ba tun yau ba.....ba tun yanzu ba,haka kawai Allah ya zuba mata tsanar matar. Tana dannewa ne kawai bata nunawa,don ta tabatar morsa safiyya ba zata bari ta nuna ko tayi wani abun na ba daidai ba. "Ms kike shirin nunawa duniya ne?" Mammina ta fadi fuskarta na nuna zallar bacin rai qarara. Irin bacin ran da idan ta nunashi a baya yake daga hankalinta,irin bacin ran da idan ta nunashi a baya koma me take buqata ta gama samunsa daga gurin akhnan din,saidai a yau.....a kuma yanzu gaba daya batajin komai game da yadda ranta ya baci. "Auren da nake shirin 'yantaki a kanshi?,shine kike shirya jere kafada dashi?,a gurin taron al'adun da duk duniya idanunsu yana kai?,zakije dashi a sunan mijinki?,MALAMIN AKHNAN?". Sam sam bai lura ba tahowarsu ba,saboda hankalinsa yana kan qaramar na'uarar dake kafe a filin festival din,wanda yake sarrafata daga inda yake tsaye. "Gata nan fa.....ya subhanallah" Muryar maleek da wani irin amo taja hankalinsa,ta kuma sabbaba masa daga kansa zuwa gareta ba tare daya shirya hakan ba. Idanunsa ya dauke yana jan siririn tsaki. "Ka nutsu maleek.....ka nutsu.....bazan tolerating wannan susucewar da kayi ba". Haisam din ya fadi a dake idanunsa akan na'urar,saidai kuma can qasan ransa yake jin kamar akwai wani abu da aka rasa a gurin,kamar daya kallesu akwai wani abu daya da bai cika ba a gurin. "Saidai kayimim afuwa da gafara mr lowering gaze......na yarda na yarda na yarda akan mace ba wani wada yake da sauran IZZA ko SARAUTA......na rantse maka har ga Allah,ban dauka akwai macen da zata kwacemin kai haka ba a duniya......sai ga wani irin so daga falaak muhammad hammud" Da wani irin nauyi yanayi da amo yayi maganar,abinda ya sanya haisam daga kai ya dubeshi don ya tabbatar da gaske yake?. Sai a sannan ya kula.....wai ashema ya baje ne ajikin amjad ne yana suburbudo wadannan kalaman,shi kuma amjad din ya wani tallafeshi kamar a film din india. Haushi sosai ya cika haisam.....baisan yaushe maleek yakeso yabi sahun su omar ya koma dan wasan kwaikwayo ba. "Buzuwar nan ta tafi dani" "Aiba kai kadai ba dan uwa.....gwara kai ka kama dahir.....ni bansan a wane matsayi nake ba" Amjad ya furta yana shafa kafadar maleek kamar me lallashin qaramin yaro. Cak haisam ya dakata,sai ya ajiye na'aurar a wani abu me kama da side table dake gaban seat din da yake zaune,yasa yatsunsa ya kama habarsa kawai yana kallonsu,ya rasa me zaiyi,fada zaiyi ko kuma me?. "Obbo.....gimbiya ce kawai ta rage" Abdii ya leqo daga seat din bayansa da nasa tsurkun yana fadi. "Nima ban hangeta ba" Khadeem ya fada. Waiwayowa yayi yana raba dubansa tsakanin abdii da khadeem. Kenan duk wata fitowa tata suna ankare da ita?,ko kuma aikin hakan ya basu?. Yaji a jikinsa dama akwai wani abu da yayi saura,kuma ko a yanzun da 'yan riga malam masallacin nasa suka gane masa jikinsa ya bashi wani abu. Yaga fitowar mammina da mutanenta......ta ganshi ya ganta sunyi idanu hadu,ya sauke kansa daga dubanta,saidai bai sake bibiyar motsinta daga kwanyarsa ba,don haka koda ta juya tana komawa hankalinsa da nazarinsa yana lissafe da ita. "Ku canza mota please kafin na fito" Kawai yace dasu bayan ya bude murfin motar a taqaice yana sauke qafarsa qasa wadda ke sanye da wani kyakkyawan rufaffen takalmi. Bai ko waiwayo ya dubesu,bai kuma damu da kallon kallon da sukewa juna ba ya fara takawa zuwa hanyar da zata sadashi da sassan akhnan din kai tsaye. Dukka masu tsaron hanyoyin,kowanne ya janye masa yana sadda kansa qasa cikin girmamawa da yadda kwarjininsa ke bugarsu a kullum. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 129* *M A M M I N A* "Ki dawo hankalinki akhnan.....ki dawo cikin hayyacinki mana......ta yaya zaki dinga aminta kina fita da mutumin da baki shirya zama dashi ba?,ta yaya zan samu nasarar yi miki abinda kikeso bayan kina nunawa duniya kina tare dashi?,yana nunawa duniya yana baki kulawa.....me kikeso ace?,ya kikeso a kalleki?.....ke da kanki zaki jera da malamin daya kasance qarqashin inuwa da alfarmar mahaifinki?". Idanu sosai ta xubawa mammina,karon farko a rayuwarta da taji gaba daya maganganun mamminan suna sauka mata a zuciya da wani irin rashin tsari. Sai data sha numfashi sosai,ta lumshe idanunta sannan ta sake budesu fes akan fuskar mammina din. "Eh......tsarin sultane ne.....abinda kuma zai iya bawa sultane farinciki kenan a daidai wannan lokacin" Tayi maganar tana duban idanun mammina kai tsaye. Wani murmushi mammina ta sake,a bayan burin sultane.....a bayan tsarin sultane daya tilastata,tana hangen wani abu daban daga can wani nisan nisa. "Tsarin sultane?,ko kuma kece aminta da hakan?" Ta fadi tana son auna gwargwadon abinda ke shimfide a zuciyarta. Kanta ta karkatar gefe tana cije lips dinta,tana jin gaba daya mammina a yau ta cikata,tana jin kamar daidai da iska me kyau ta hanata shaqa. "Kina so nayi fito na fito kai tsaye da tsarin sultane?" Tayi tambayar tana dagewa mammina dukka girarta sama. Maganan ya danso taba mammina,abinda ya sanyata saurin gyara harshenta dama tsaiwarta kenan. Tana jin wani matuqar tuqewa,tana jin matuqar kaiwa maqura. A yau din itace tsaye gaban akhnan suna musayar ra'ayi?.....suna musayar yawu?,suna kuma musayar maganganu?. "Ko kadan.....saidai kin saki zaren ne yayi sakwa sakwa........baki da zarafin kaucewa maganan sultane,.......amma hakan bawai yana nufin kiqi nuna ra'ayinki ba.....ke sarauniya ce akhnan......bai kamata ace kina yawo da namiji ba,wanda har yanzu na tabbatar ke kanki bakisan ASALINSA BA!.....Wayeshi?" Tayi maganar da wani irin nauyi daya daki qirjin akhnan. Wannan maganan ya samu matsugunni sosai cikin zuciyarta. WAYESHI?,da gaske batasan wayeshi ba.....da gaske batasan komai a kansa ba,da gaske ba zata iya dorar da komai daya shafeshi ko ya danganceshi ba. "Ki tuna matsayinki mana......ki tuna kanki biftu ki tuna wacece ke!.....baki cancanci mutum mara asali ba!" Tayi maganan da karyewar zuciya,tanason BUDE WATA QOFA......tanaso ta budewa akhnan wata qofar da zata zama me nisan zango,qofar da zatayi tafiya me matuqar nisa a cikinta. "ASALI shine mutum,ba wanda ya damu ya duba miki wannan,ba wanda ya damu ya tabbatar da nutsuwarki wajen sanin hakan,kowa idanunsa ya kulle....kiyi aure......kiyi aure,haka soyayya take?....da uba ake ado! Kamar yadda kike ado da taqama da naki uban!.....waye nasa UBAN?". Ta sake fadi tana waro idanunta waje tare da qoqarin nunawa akhnan girman abinda ke fuskantota. Shuru ne ya wanzu a gurin,yayin da zuciyarta ta fara mata wani karatu. "Karki kuskure akhnan......karki kuskuren fahimtar littafin da yake a rufe.....karki kuskuren fahimta littafin da baki bude koda shafi guda kin karanta ba". Kamar wani abu ya fusgi hankalinta,saita dauke idanunta a hankali daga kan fuskar mammina dake sake bata yaqini da kuma dasa mata zargi,sai gashi sun sauke kansu da kansu a hankali a bayan mammina da tazarar takun da yakai goma sha biyar. Da farko farin zabgegen buxu ta gani......irin jinsin da yafi kowanne jinsi nasaba da qarfi cikin jinsin buzaye. Giant zabgege fari tas,sanye da wannan turkudin(wani nau'in abu kamar rawani me kalar bula bula da sirki sirkin ruwan hanta da buzaye ke amfani dashi a taruka da dama irin nasu. Gwanintarsa da qwarewarsa wajen sarrafa rawani......sarrafawa irin ta matasan malamai da sukasan sirrin ado da gayu daga matasan larabawa ya sanya nadin turkudin ya zama na musamman a kanshi da kuma fuskarsa,zabgegiyar takobi ce rataye a kafadarsa ta dama tayi crossing a jikinsa zuwa cinyarsa ta hagu. Kaman a wancan ranar......zagayen idanunsa kadai......zagayen idanunsa kawai take iya hange,wasu irin idanu masu matuqar haiba da kwarjini. Yayi wata tsaiwa hannuwansa goye a qirjinsa ya sarqafe su yana dubansu. Wani namijin damisa take hange......a tsaye a kafe kamar gini ko zanen daya tsaru daga hannun qwararrun masu zane,masana kan yadda zaka sarrafa alqalaminka. Sanda ta qifta ido a karo na biyu tana son sake tantancewa,sai SHEIKH MUHAMMAD HAISAM ya fito mata sak da dukka kamanninsa,qifta ido na biyu da tayi kuma tana bude idanun sai taga ya fara motsi yana takowa a hankali zuwa inda suke tsaye,tabbacin ba ZANE ko GINI bane.....shine din dai. Shine dindai jinin IBRAHEEEM da YUNNUS JALLATA.....gadon sarauta ta kowanne fani na uwa da uba. Kalaman mammina na ASALI sune abinda ke masa kururuwa a kunnensa. "WAYE UBANSA?" maganar da tayi tsaiwar mashi cikin tsakiyar zuciyarsa. "Ki tsaya ki zuzzurfan tunani biftu.....nidai ina kar......" Maganan ya tsaya mata cak a maqoshi saboda inuwarsa data hanga,wanda cikin qiftawa da bismillah kuma ya bayyana gaba dayansa. Abinda ya haifar mata da wata irin firgita,wata irin firgitar da tunda take tsahon rayuwarta bata taba jin irinta ba,don kuwa cikin qasa da second goma da yayi na kafeta da idanuwan nan nasa dake da tsananin KAIFI gumi ya jiqe mata fuskar tamkar wadda ta daura alwala. Cikin nutsuwar nan tasa yake takowa zuwa gaban akhnan,wani irin taku cikin QASAITA da GINSHIRA. Cak ya tsaya a gabanta yana zube idanunsa cikin tsakiyar nata. Wani abu ya tsarga mata,wani irin abu mai kaifin gaske.....wani irin abu me tsananin nauyi da ratsa jini har zuwa b'argo. "Ya isa......ya isa" Ya maimaita sau biyu yana lumshe idanunsa gami da budesu a tare,idanunsa fes akan fuskar Akhan da wani irin kusanci don tazarar daya rage tsakaninsu qilan yaro me qananun shekaru ne kawai zai iya shiga ya cike gap din. Hannu ya miqa a hankali ba tare daya dauke idanunsa daga kanta ba,ya riqe jelar dogon gashinta masu kauri guda biyu da aka kitsata ta zubo a gefe da gefen fuskarta yana maida mata su baya,don kadan ya rage su saukar fuskar Aaroon dake baccinsa abinsa.. Still idanunsan nan suna kan fuskar Akhan din,ya sanya hannu ya karbe Aaron daga hannunta,sai ta samu kanta da sakar masa yaron. Wannan shine maslaharta,koda bata bata Aaroon bama taji jikinta gaba daya ya gama mutuwa,hasalima rawa takeji ya soma mata,wannan kallon tana jin kamar dafi ya tattara ya zuba mata a jikinta gaba daya. Baice komai ba,ya zura hannunsa ta gefanta ya kamo lallausan tafin hannunta ya runtse cikin nata,sannan ya fara takawa a nutse ta gaban fuskar mammina. "Abu mafi kyau ga kowanne dan adam shine......ya gina kansa fiye da yadda sunan uba zai ginashi.......sunan uba yana daga mutum ne idan ya dace dashi......amma mutunci.....mutum ne yake ginawa kansa shi......idan wani yana iqirarin baisan mahaifinka ba.....ba hakan yana nufin babu shi ba". Wani hazo hazo ta fara gani,kamar jiri yana shirin kayar da ita. Babu shiri ta soma lalubar duk abinda ke kusa da ita,cikin taimakon Allah ta samu nasarar damqe daya daga cikin bishiyoyin da aka yiwa gurin ado dasu,wannan ya taimaka mata gurin tsaiwa saman qafafunta. Wani irin mamaki.....zallar mamaki ne kawa ke yawo cikin kwanyar akhnan. Maganganunsa dake nuna zallar jarumta.....sanin ciwon kai da kuma sanin darajar kai din suke bata mamaki. Ya iya maida amsa.....ya iya bada amsa a taqaitattun kalaman da amsar zata kai maka ko ina. Hannunta.....hannunta dake cikin nasa shine wani hanya guda daya da take aike kasala da mutuwar jiki zuwa kowanne sashe na jikinta. Gumin da tafin hannun nata ya fara yi kuma.......yadda tafin hannun nata ya nutse tsakiyar nasa saita dinga jinsa kamar ba'a jikinta ba. Cak ya tsaya da ita,dab da hanyar qarshe da zata fiddasu zuwa farfajiyar. Yatsunsa kawai ya murza,daya daga cikin hadiman dake qoqarin kwashe busassun ganyen dake tsakanin flowers din ta dago.kai da hanzari. Mutuwar tsaye tayi.....yadda ya qware wajen bada umarni?. Da murza yatsa kawai duk wani bawa duk wami hadimi yana iya fahimtar saqon da yakeson isarwa?. Aaroon ya saka mata a tafin hannuwanta,da qasaitacciyar muryar nan tasa idanunsa suna kallon wani guri ya mata magana da kalaman da basu da tsayi sam. "Ki kaiwa mamansa shi.....ki aiko da birra" Cikin girmamawa ta rungume Aaroon,da sassarfa kuma ta fara takawa tana barin gurin. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Ita dashi din gaba dayansu da kallo suka bita harta bacewa gurin. Shuru ya ratsa gurin,baka jin komai sai kukan tsintsaye dake yin masauki saman tarin bishiyoyin daka gurin. Ba iya wannan kadai akhnan ke iya ji ba,tana iya jin fitar numfashinta dama bugun zuciyarta gaba daya a lokaci guda,kafin husky voice dinsa ta ratsa shurun da wani irin kakkaifar tambaya. "Wa ya baki damar fitowa a haka?". Cak tambayar ta tsaya cikin iska da wani irin yanayi,wani irin yanayi me ban mamaki.....wani irin mamakin daya sanyata dole ya tilastata daga idanunta ta zube akan fuskarsa ba. Bata iya ganin fuskarsa,don ya bata baya,amma tana iya ganin kadan daga cikin sumarsa me santsi da bata samu shigewa cikin nadin turkudin kansa ba. Izzar tadan motsa mata.......cakude da mamakin yadda bata masa KWARJINI ne kaman kowa?,har yake iya bata umarni kai tsaye gami da qalubalantarta?. "Banga aibun shigata ba......" "Kece bakiga aibun shigarki ba" Ya furta da wani yanayi na fusata yana kuma juyowa zuwa gareta da wani irin zafin nama. Juyowar tazo mata a bazata,juyowar ta bata wani irin ajiyayyen tsoro daya sanya tayi baya da sauri ba tare data shirya ba. Idanunta cikin nasa tana hangen wani abu......fushi ne?,baiyi.kama da fushi completely,wani abune dake da tsananun zurfi da kuma kaifi daya taso tun daga zuciya. Step biyu ya tako zuwa gaba......sai ta janye baya da sauri ganin yadda ta rage gap din dake tsakaninsu. A hankali yake ajiye takunsa duk inda ta dauke nata,sannu a hankali yake sake matsarta yana kuma cike duk wani tazara data bayar a tsakaninsu,sai jinta tayi ta hade da babbar bishiyar dake bayanta. Da sauri ta waiwaya tana duban bayanta,ba wani sauran taku daya rage mata da zatayi,ta maido dubanta kansa,sai taga still matsota yake sakeyi. Idanun nan dake zagaye tsakiyar nadin kansa da habarsa.....idanun nan dake kasheta alhali da ranta da numfashinta. Wani irin abu me kama da fushi take hanga mamaye da fuskarsa duk da bata iya ganin fuskar tasa gaba daya. Duk wani taku qwaya daya da zaiyi sai taji kamar numfashinta zai dauke....duk wani taku qwaya daya da zaiyi sai taji girman kusancinsa har tsakiyar tsokar zuciyarta,zuciyarta ta qara gudu,qirjinta ya soma dagawa a hankali da wani kalar tsoro ganin inches ne da basu fi biyu suka rage a tsakaninsu ba. Taku daya ya rage yayi filling gap din.....taku daya bame nauyi ba,don haka ta runtse idanunta a hankali,tsoronta yana ninkuwa,tsoron daya sanya qirjinta dagawa sosai saboda kokawar jawo numfashinta da fidda she da takeyi saboda yadda takejin kamar qofofin shaqar iskarta sunyi mata kadan. Tana iya jinsa cikin jikinta,tana iya jinsa sanda ya raba qafarsa tsakanin nata qafafun,tana iya jin wannan qamshin.....tana iya jin wani irin dumi dake tsakanin cinyoyinsa suka ratsa nata suna kuma aike mata da wani irin shock zuwa kowanne sashe na jikinta,kafin a hankali hannunsa saman qugunta. Idanunsa ya ware sosai saman matsoraciyar fuskarta data sake wani kyau saboda yadda tsoro ya bayyana qarara saman fuskartata. Karon farko da yaga tsoro shimfide akan wannan fuskar ma'abociyar kafiya da kuma taurin kai. Sam bada niyyar wanzar da irin wannan kusancin tsakaninsu ba ya waiwayo,saidai wani irin qyalli daya hanga cikin idanunta.....da kuma matsoraciyar fuskarta sai ya tuna masa da wancan dare. Yadda fuskarta take cikin screen......yadda dukiyar fulaninta take cikin rigar baccin data kwanta a fatarta sosai.......take wani abu ya d'arsu cikin zuciyarsa. Yanason yaga da gaske abinda ya gani a na'urar shine a zahiri?..dagawar da numfashinta yakeyi shi ya sabbaba dagawar qirjinta,abun sai ya zame masa tamkar wata tsokana ne. Cak ya tsaya yana dubansu,yadda suke dagawa sama da qasa a hankali da bugawar zuciyarta da yana iya ganisa sosai. Zai iya irga sakanni nawa yake bugawa tsakiyar qirjin nata,duk da yanajin wani abu me nauyi yana qarawa fitar nasa numfashin shima nauyi amma ya tantance zuciyarta a lokacin bata bugawa daidai. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 130* A hankali yayi sama da idanunsa......kafadunta da suka dan bayyana kadan wadanda sukayi wani irin kyau da siririyar silver sarqar data zauna a dogon wuyanta. Ya lumshe idanunsa a hankali yana tuna wani baitin mawaqin balarabe daya qware wajen siffanta mata. Yasha karanta waqar....yasha maimaitata da cin karo da ita a litattafai da dama......amma a yau yaga zahirin ainihin maganar mawaqin ido biyu. Idanunsa suka sake sauka akan lips dinta,take yaji maqogoronsa ya bushe har zuwa saman nasa lips din,sai yakai harshensa a hankali yana lashe labban nasa kafin ya turasu ya maidasu cikin bakinsa gudun samun kuskure. Yadda jikinta ke rawa sai yaji kamar nasa jikin yana dab da fara rawan shima.....saidai faruwar hakan yana nufin abubuwa da dama.....cikin taimakon Allah wannan zuciyar tasa ta maidashi hayyacinsa. Tunawa yayi inda ta fita haka,maza nawa ne zasu kalleta?. Wuyanta.....lips dinta.....qirjinta.......da dogon gashin da ya maidashi baya a dazu. Numfashinsa yaji yana sake nauyi da zuciyarsa ta tuna masa da haka,sai yaji kaman shima numfashin wahalar fita yake neman yi masa. Shuru ya wani ratsa a tsakaninsu,saidai wannan shurun bai dauke bugun zuciyar kowannensu ba......a hakan zuciyarta ke raya mata ta bude idanunta.....ta cire wannan tsoron......ta gaya masa ya matsa daga gareta......idan batayi hakan ba zuciyarta na gaya mata bata da jarumtar ci gaba da daukan wannan yanayin..... A hankali kamar me ganin wani abu ta fara ware manyan blue eyes dinta. Ta zubesu a kansa,saidai ta gagara budesu gaba daya a kansa,dole ta zabi maidasu ta lumshesu tana ci gaba da kokawar yadda numfashinta zaici gaba. Kai ya girgiza yana ja baya a hankali bayan da kunnuwansa suka jiye masa alamun taku nesa kadan daga inda suke. Besan wanne kalar kishi gareshi ba,saidai shi kansa yasan me tarin yawa ne. Kalar kishin daya sanya hatta dasu Aanani rumaisa da nanay kanta kishinsu yake. Ya hana musu drivers maza......ya hana musu bayi maza......duk wata harkarsu da maza zasu shiga ya soketa. "Gani Allah ya taimakeka" Akhnan da hat yanzu bata farfado daga suman da tayi ba ta fada tana duban haisam. Baya yaja kadan ya bata umarnin da ko akhnan bataji me yace mata ba,saidai qasa da minti uku sai gata ta fito da abinda yace tana miqa masa. Karba yayi yana warwarewa. Babbar lafaya ce fara qal me wani irin taushi da daukar idanu. "Get on your feet" Ya fadi kafin kuma ya koma ya gaya mata da france. "Tenez-vous debout" . Kamar wata statue haka tayi tsaye,yana kewayeta a hankali har ya kammala nade adonta tsaf cikin fara lafayar. Gabanta ya zagayo yana dauke da ragowar sashenta,ya tsaya sosai da tazarar da dukka dukka bame nisa ba. Hannunsa dukka biyu ya saka ya dorata a saman kanta,ya qarasa rufe wadannan dogayen gashin nata. Wani sabon salo kyan da tayi ya dauka....wani yanayi na daban ba irin na adon dazu ba. Taku biyu yayi baya,sannan ya juya bayansa a hankali. Har yanzun bai gamsu ba.....har yanzun yanajin kamar akwai sauran abinda bai rufe ba,kamar ma be rufe komai ba. Bai daina ganin wani yanayi me fusgar hankali yana tashi tattare da ita ba. Wannan karon kafada da kafada suka jero ita dashi. Jerowar da taja hankalin dukkan wanda ke gurin. "Ya subhanallah" Aisa ta fada da wani irin yanayi. A yau tana jin yadda suka tafi da imaninta,a yau tana jin an gama tashin kanta gaba daya. Zata iya cewa a duniyarta bata taba ganin couples da sukayi matching iya matching ba irin muhammad da khadeeja din.......kasa dauke idanunta tayi daga kansu,tana jin ko taku days nasu bataso tayi missing. "Innalillahi.....aisa.....kalli takunsu fa......hatta qafarsu tare suke ajiyeta da dagata" Shehnaz da take qare musu kallo ta video din data fara musu bayan ta zuge window din motar ta fadi a matuqar gigice da yadda suka fita kamar wasu taurari. "Na gani shehnaz.....na gani wallahi" Aisa ta fadi tana jin yau ko ita me iya biyewa shehnaz ce akan batun akhnan da haisam. A cikin jikinsa yaji dukkanin adadin idanun da suke kansu....cikin idanun kuwa harda idanun mammina........idanun da suka cika da fusata,idanun da a yau takejin duk wani juriya tasu ta qare "Muddin kika zabeshi....muddin kika yarda kyanshi ya rudeki kika fada soyayyarsa.......lallai a sannan zakisan me ake kira da ainihin AZABAR RAYUWA.....mission dina zai sauya a kanki.....zaki gaje kujerar SAFEENA da kyau,daga dukkan nau'in kalar wulaqantacciyar rayuwar dana jefata. Ta shayar dake a sanda take cikin HAUKA.....zai zama kuskure ko laifi idan rahoton yazo da bayanin KIN TSOTSI KALAR HAUKAR NE A NONON DA KIKA SHA NATA?" ta fadi can qasan ranta idanunta zube fes a kansu,tana kallom yadda suke takawa da salon tafiya daya......tana kallon sanda ya sanya hannu cikin wani girmamawa me nauyi data hanga daga dukkan motsinss,daga wani dogon nazari da tsinkayen data tabbatar ko akhnan din bata hangeshi ba,sannan ya zagaya da qasaitacciyar tafiyarsa me cike da shan qamshi izza da ginshira zuwa daya side din shima ya shige. "Bazan bari hakan ta faru ba.....na kasa gano komai a tare dakai.....amma tabbas jikina da hasashena sun bani amannar KAI DIN JININ IBRAHEEM da KHADEEJA ne" Ta fada still a ranta tana dukan qafen veranda da hannunta data dunqule tana kuma cizon lips dinta na qasa. Wani irin shuru ne ya ratsa cikin motar,kamar ba kowa a cikinta. Idanuwanta na gefan window tana kallon titunan da suke wucewa da matsakaicin gudu. Shimfidaddu tituna kuma lafiyayyu wadanda aka samar dasu a mulkin mahaifinta sultane muhammad hammud. Bawai titunan kawai take kalla ba,ba kuma wai don bata sansu ba.....a'ah. Wani abune lullube da zuciyarta me matuqar nauyi da take jin nauyin har saman qirjinta. Yatsunta take murzawa a Hankali,har yanzu tana jin kamar hannunsa yana cikin nata. Har yanxu tana jin zaman zara zaran yatsunnan nasa cikin nata,har yanzu wannan bugun zuciyar......fitar numfashin dama komai nata bai koma daidai ba. Batasan wanne irin nau'in mutum bane shi da yake mata kwarjini har irin haka. Rauni......rauni takeji sosai a zuciyarta,wannan jarumtar tana ji tana zagwanyewa a jikinta a duk sanda yayi kusa da ita. Wannan jarumtar tana jin tana yin nisa da ita......tana jin tana nesa da zuciyar ta dama gangar jikinta gaba daya. Tun suna dab da isa gurin abubuwa da tsarin suka fara daukan hankalin haisam. Karo na farko da zaiga biki na al'ada irin wannan a tsakiyar sahara. Wani abu da bai taba sanin dashi ba. Duk irin sonshi da zuwa yawon bude idanu,bincike akan nature da gurare masu dadin zama da wanzar da nishadi bai taba zuwa takan niger ba ballantana al'adunsu. Wata qesa ce da yake kallonta nesa dasu sosai. Ko sanda ya fara bincike a kanta.....bincikensa ya tsaya ne akan zargin wanzuwar me laifinsu da suke tuhuma SAMUUD. A hankali motocin masu manyan tayoyi suka fara keta cikin saharar. Wata nutsatsiyar tafiya data sanya haisam bude manyan idanunsa a hankali yana duban yadda suke keta yashi. Daga nesansu sai yaga kaman wani tsuburin amma da sun kusanci gurin sai ya fahimci tudun yashi ne kawai. "Innafi khalqissamawaati wal'ardi wakhtilafil laili wannahari la'ayatil li'ulil albab" Ayar tazo masa cikin kansa. Tabbas a iya halittar sama da qasa kawai ya ishi bawa imani.....ya ishi me rabo ya fahimci da gaske Allahn Allahn ne. Wata halittar tafi gaban abun halitta ya tsarata ko ya qirqireta.....ka kalli guri shimfide da wani irin lallausan rairayi,haka kawai aka halicci gurin,ba deboshi akayi aka zuba ba. A hankali takejin wani siririn nishadi yana ratsa mata zuciya. Jinin nan na Tuareg jinin nan na ABZINAWA jinin BUZAYE yana motsa mata. Tana tsananin son festival din,yana daya daga cikin abinda ke bata sakewa nishadi da walwalar da batayi ba a baya. Suna hango gurin amma tun daga nesa security ne a zube tako ina. Riqe da manya bindigu da wadanda ke nesa kadan da abubuwan bada kariya da kayan hangen nesa. Akwai tsaro sosai.....saidai qarin samun tsaron ya ta'allaqa da wanzuwar haisam da shawarwarin daya bayar,ya kuma gutsira musu idea 'yar kadan wadda ba zata bankada WAYESHI ba daga cikin tarin hanyoyi da dabarun bada tsaro na hukumar qwararru kuma gogaggu kan binciken sirri da kuma bada tsaro. A nutse dukka jerin gwanon motocin masarautar agadez suka karkata kadan suna isa inda aka tanada domin ajiyar motoci. Kyakkyawar matashiyar minister din itama yau da kanta tana tsaye sanye da tufafinsu na al'ada cikin tsaro na guards dinta da sauran ma'aikatanta na kusa. A yau itama ta fita a matsayin cikakkiyar BUZUWA ta fita sak! Cikin shiga da kamanni na al'adar festival de l'Aîr,ta zabi zuwa da kanta ta marabci sheikh muhammad da princess akhnan hammud. Tunda tabar masarautar agadez couples din suke fado mata,lokaci lokaci kawai saita saki murmushi. Wani irin match da zazzafar soyayya take hango musu a gaba. Dukkaninsu bata hangen akwai wanda zai samu ya tsallakewa dan uwansa. Tayi zaton zai bude murfin motar kaman yadda sama da motoci goma da sukazo dasu suka bude,sai taga driver din ya fita ya kuma rufesu cikin motar. Shuru ya wanzu,tana tuna abinda ya faru ranar taron makaranta,yauma yanason maimaita irin hakanne. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) A hankali taji zuciyarta tana motsawa,musamman data karkatar da kanta zuwa sashen da minister ke tsaye. Sunata wasa da dariya dasu aisa. Akwai sanayya da sabo sosai tsakaninsu da ita sama da yadda ita ta saba da ita,saidai tsananin kirkinta da kuma girmamawarta ga sultane ya sanya janta sosai a jiki. Gaba daya gurin ya zama wata qaramar unguwa,jama'a ne masu yawa suketa kai kawo a gurin. Maza da mata,yara da manya harda tsofaffi da al'adar festival din take tsaye tsaf cikin jini ruhi da zukatansu. Garin agadez yana daya daga cikin garuruwan da suka riqe al'adunsu da kyau sama da kowanne gari a niger,kama daga gine ginensu aurarrakinsu da sauransu,wannan ya sanya ya zama kamar wata cibiya ta gudanar da al'adu. A nutse ya zaro wayarsa bayan ya sauke siririyar ajiyar zuciya. Yana jin ta yaya zata fita a haka?. Zagaye suke da maza muqarraban minister da sukazo tarbarsu,haka kawai yakeji zuciyarsa ta masa nauyi kadan,saiya rubuta gajeran rubutaccen saqo ya aikewa beeno. A tsakanin tazarar dake tsakaninsu ya ajiye wayar a hankali. Wanda da ajiye wayar da soma janyewar maza ba'ayi minti biyar ba. Ta glass din gaban motar ya hangi tahowar minister din,sai ya bude murfin motar,tana zuwa ta qarasa budeshi ta shigo. Da cikakkiyar sallama,fuskarta shimfide da murmushi,cikin harshen France ta dubi haisam bayan ta dauke dubanta daga kan akhnan. "Je m'excuse,monsieur(i apologize sir)" Kadan ya murmusa yana gyara zaman agogon hannunsa a nutse. "Le festival se passe bien? C'est super de te voir gérer tout ça(Managing the festival okay?,great to see you working the crowd)" Murmushi tayi a nutse tana dors hannunta saman na akhnan. Dukkaninsu sun mata kyau.....sun mata wani irin kyau daya sake sanyawa take jinsu har cikin ranta take kuma fatan kasancewarsu tare. Ta gyada kai da sauri. "Alhamdulillah.....komai lafiya,muna matuqar godiya bisa gudunmawarka......anjima da yamma mr President zaizo,yace a miqa maka saqon gaisuwa da godiya dama masarauta gaba daya da suka bada aron mutum irinka,komai yasha banban da yadda muka saba gudanar dashi,wannan karon kowa yana jin abun zaifi armashi" Kai ya gyada a hankali. "Naga sabon tsari......na tashin kiran sallah jikin na'aurori a duk sanda lokaci yayi" Minister ta fada abun yana burgeta tana duban idanun akhnan da murmushi. "II est très sincère dans sa religion et c'est vraiment admirable(He's very sincere about his religion and that's really admirable).....ya gina mana masallacin tafi da gidanka na maza da mata a sansanin nan....wannan shine karon farko da muka fara tunanin yin haka......raye raye na al'ada ya kebe gurin da mazan zasuyi nasu daban mata ma haka......sai abun ya bani sha'awa sosai " Ta fada tana qanqance idanunta da wani murmushi na burgewa. Idan har tace bataji wani RESPECT ya sauka a hankali saman zuciyarta ba tayi qarya.....kwatankwaci saukar qaramin tsuntsu saman bishiya. Ta karkata kanta a hankali ta saci kallonsa kafin ta dauke idanunta da sauri gudun kada ya kamata. "Na karbi amanarta yallabai.....zan kula maka da ita in sha Allah" Minister ta fadi tana murmushi tana kuma sake riqe hannun akhnan cikin nata. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 131* Wannan karon murmushinsa sai daya d'ara labbansa,ya sauka kadan zuwa saman fuskarsa. Bai kuma ce komai da ita ba,ya danna locked ne kawai qofofin sun bude,tana riqe da hannun akhnan din suka fice. "Soyayyaaaaaaa.........Allah yabar soyayyaaaaaaa" Shehnaz ta fadi tana daga hannu sama da salon waqar nan ta sogha. Murmushi madame minister tayi tana nuna shehnaz da yatsa. "Ba zaki canza ba shehnaz?". Juya idanunta tayi tana dariya. "Soyayya kala kala ce.....soyayya iri iri ce,soyayyar maso wani cuta to kowa yaso me so nai" Dariya sosai dukkaninsu ta basu,banda akhnan data tamke fuska tana jifan shehnaz da harara. Hannun akhnan ta sake riqewa cikin nata. "Ki rabu da ita....nasan yadda zamu hukuntata....bata iya tsere ba.....anjima shi zamu sakata a raqumi" Wani murmushi ya subucewa akhnan din,har cikin ranta.....har cikin ranta taji dadi sosai,ta dade bata hau raqumi ba.....har dawakanta ma kusan duka ta manta dasu saboda rudanin nan data shiga,amma a yau tana jin saita cike wannan gibin. Kusan tun daga saukarsu hidima ake akwai da hada hada. Baqi daga kowanne sashe da nahiya na duniya. Turawa larabawa harda faransawa da sukafi yawa,china india dukka suna cikin qasashen da suke halartar festival din. Karbar baqi kawai akaci gaba dayi ta ko ina. Akwai VIP tent da shiyyarsu ta zama daban dana sauran al'umma. Tent ne da aka tsarasu harda bandakunansu a ciki,sannan akwai spare daban da aka yisu kamar qaramin parlor,saidai an qawatashi da carpet carpet da kuma lausasan kujerun zama na wucin gadi. Ac ne na tsaye cikin dukkanin VIP tent din da parlor din,an samar da yanayi me kyau da zai sanya kaji kamar kana gida. Ita karan kanta sai dataga banbanci me nisan tazara na gaske da minister ke fadin ya samar. Komai na wannan karon yasha banban dana ko yaushe. Komai a tsare,wani irin yanayi da zaka dinga jin kamar kwanaki ukun da za'ayi kada su qare. Daya daga cikin parlor din suke zaune,da minister da sauran manyan baqi. Hira ake cikin sakewa da juna da qaunar juna,ba wani banbancin launi ko na yanki ko kuma qabila. Duk da cewa daga nesa ne,kaeo na uku kenan da take iya ganin mutanen da yaketa magana dasu. Kai kawonsa tare da manyan baqi daga qasashen waje,qasashe daban daban yare daban daban. Ta kafeshi da idanu sanda suke musabaha da wani balarabe,bakinsa yake motsawa a hankali cikin fara'a da sakin fuska. Batasan me yasa yake janye tunaninta ba,batasan me yasa yake janye hankalinta ba. A duk sanda zai gilma ta gurin,sai taji kamar an fusgi hankalinta zuwa gurin. A hankali ta sake daga idanunta tana kai dubanta zuwa inda yake tsaye. Wannan karon a gefan mutumin,matashiyar balarabiya ce,sanye da baqar abaya me sulbi sosai. Tayo rolling da mayafin abayar har kana iya ganin gashinta daya sauka a bayanta. Sake maida dubanta tayi fuskar mutumin,babu ko shakka dukkan alamu sun nuna mahaifinta ne. Hannunta cikin na mutumin ta kwantar da kanta a kafadarsa. A nutse akhnan ta gyara zamanta,tana dora qafarta daya saman daya idanunta zube fes saman fuskar yarinyar da aqalla zasuyi sa'anni da ita. Direction na qwayar idanunta tabi kai tsaye kuma suka kaita fuskar haisam. "Shi take kallo?,shi ta zubawa ido haka?" Taji wata murya can qasan zuciyarta tana tambayarta. A hankali ta sake maida dubanta kan idanun yarinyar......da gaske haisam take kalla.....da gaske idanunta yana kanshi,har kamar ma bata qiftawa. "Saboda me?" Muryar ta sake tambayar akhnan da wani irin yanayi daya disa mata wani abu me zafi saman zuciyarta. Haka kawai taji kamar zuciyarta tana tattarewa tana kuma matsewa a qirjinta da wani irin yanayi data fara jinsa tsakanin qirjin nata tafin hannunta da qafafunta. Taci gaba da raba kallonta a tsakaninsu,zuciyarta tana sake tsukewa guri guda,saidai abu daya daya bata mamaki,abu daya data iya gani ta kuma fahimta,ko sau daya haisam bai aza idanunsa a kanta ba. Kanta ta girgiza a hankali,still hakan be mata ba,haka kawai takejin tsaiwar batayi mata ba. Me suke fadi masa haka sama da abinda sauran suke gaya masa?. Me suke fada masa haka da suka dade dashi sama da kowa?. A hankali ta waiwaya inda birra ke zaune daban. Birran kawai ta ware ta yiwa umarnin zama cikin nasu tent din. Hannu tasa ta kirata a hankali,tana jin kamar ana tunzurata,tana jin tana da buqatar sanin abinda suke tattaunawa akai. Da idanu ta yiwa birra nuni,duk da birran ta fahimta,duk da birran ta gane me uwar gijiyartata ke nufi amma abun sai ya mata banbarakwai,sai kuma ta miqe a hankali tana ficewa don cika umarnin uwagijiyarta. Cikin rashin jin sukuni tun daga zuciyarta zuwa ruhinta ta sake aza idanunta a kanshi,still idon nasa yana kan mahaifin,still dai ko sau daya bai kalleta ba,amma haka kawai takejin wani abu yana ci gaba da matse zuciyarta. Bayan idanun yarinyar dake kansa.....kamar daga can nesa yanaji a jikinsa akwai wani abu na daban. Wannan wani horo ne da suka samu da baiwa da yake da ita wadda ta shafi aikinsu. Miqawa muhseen hannu yayi sukayi musabaha,yanason kawo qarshen hirar don mutanen dake jiransa yawa ne dasu. Yana zame hannunsa daga nasa yarinyar ta miqa masa nata hannun tana murmushi. Karon farko daya aza idanunsa a kanta tsahon tsaiwarta. "Tanason ku samu fahimtar juna da kusanci sosai" Mahaifin nata ya fada yana murmushi gami da duban fuskar haisam. Kadan ya jefi uban da murmushi,ya fahimci irin 'yan modern Muslim ne,a tsaiwar da sukayi na mintuna ya tabbatar duk yadda zai masa bayani game da komai bazai fahimta ba,don haka yayi taku biyu baya still yana duban uban "Na gode qwarai sayyed muhseen" Cikij sanyin jiki yarinyar ta sauke hannunta qasa,sai uban ya kama hannun ya riqe cikin nasa cikin rashin jin dadin yadda haisam din yayi ya qiriqiri murmushi shima yana masa godiya. Sanda suka taka suna barin gurin saita sauke wata boyayyar ajiyar zuciya,abun mamaki a hankali taji qirjinta yana sassauta,still dai ta kasa dauke idanunta daga kanshi,yana tsaye sosai cikin rairayin saharar......BUZU sak,sai taga ya zaro wayarsa daga aljihunsa yana dannawa da wani irin qwarewar da zata gaya maka gwani ne gurin sarrafa na'ura. Sassanyan murmushi madame agaichaata ta sake. Ita days ce ta lura da komai,ita kadai ce akayi komai saman idanunta. Ta tabbatar inda shehnaz ta gani da zuwa yanzu ta cika tent din da karadinta da kuma tsokana. "Ba wanda zai qwace miki shi.....yadda yake tsaye kafe cikin rairayin saharar agadez.....na rantse miki yanayinsa yamin kama da irinsa mazannan ne da idan suka fara so ba gudu ba ja da baya......yana da kyau dai kawai ki koyi yadda zaki adana zuciyarsa...... Ki killaceta,don na fahimci taki zuciyar itama kamar tana da muradinsa". Ta qarashe maganar can qasa,yadda b wanda zaiji me suke fada daga ita sai akhnan din. Bata tantance wanne yanayi taji game da maganan madame ba taji qarar shigowar saqo wayarta. _Ki rage kallona madame princess.....ina da hadari fa ni kaina na sani_ Wani irin bugawa zuciyarta tayi,ta zubawa saqon idanu sosai tana sake karantashu. Da sauri ta daga kanta zuwa inda yake tsaye a dazun saboda hasashen da zuciyarta tayi mata. Take idanunta ya manne cikin nasa. Ta tsakanin wannan rawanin.....wannan nadin dake qarawa idanunsa wani irin kyau da kwarjini. Girarsa dukka biyin ya dage mata,bai kuma barta tayi tunani na biyu ba ya juya yana takawa a nutse yana barin gurin. Da wata irin kasala ta janye idanunta da sauri,ji take kamar zata narke a gurin,wai me yasa?,me yasa bata iya kaucewa kallonsa?,me yasa muddin yana guri saita kalleshi?. A kansa ta fara sanin NACIN KALLO wata dabi'a ce data tsana.....wata dabi'a data saka ta sanya aka hukunta mata mutane da yawa tsakanin agadez da Niamey,ta tsani a yawaita kallonta,ta sani mutum me KALLO,amma ya akayi a kansa shi kadai!....a kansa SHI DAYA TAK! take neman jarabtuwa da wannan dabi'ar?. "Bazan bari haka ta faru ba" Ta gayawa kanta qasa qasa tana tuhumar kanta da kanta. Tana jin murmushi madame agaichaata......amma kuma kunya da nauyi sun hanata motsi. *S* ake narkewa tayi gaba daya cikin mazaunin sahun farko na manyan baqin da aka tanada sanda ake gudanar da bikin bude fara festival din. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Ba ita kadai ba kawai.....hatta da manyan baqin dake zazzaune a mazauninsu.....baqin da suka fito daga qasar faransa gaba daya ya tashi hankulansu da yadda yake sarrafa french akan harshensa. Yadda yake gabatar da jawabinsa cikin wata irin tarin nutsuwa,nutsuwar data dauki hankulan daruruwan mutane dake gurin,da miliyoyin mutane dake iya kalla daga akwatin talbijin dinsu daga gida ciki kuwa harda mammina da wani mummunan ciwon kai ya hanata zuwa ko ina. Nutsuwar dake cikin bayanin ya sanya shuru ya wanzu a ilahirin gurin gaba daya. Murmushi kawai mademe minister ke saki,tana jin gaba daya an tashi kanta. Duk wani qwarewa da take taqama dashi.....duk wani tutiya da take dashi akan yaren a yau akhnan tana jinta kamar 'yar koyo.....kamar me gwagwarmayar son iya yaren bawai yaren qasarta bane. Wasu kalmomi da wasu jimlolin yadda yake fadinsu kamar a duniya bai taba sanin wani yare ba daban bayan France. Ta lumshe ido a hankali tana jin yadda yake gauraya jawabansa da ayoyin qur'ani. Lokacin da yake karanto ayar da cikakkiyar qari'ar nan tasa......cikin microphone din daya gaurayr nisan saharar da tafiya me tsayi sai da taji tsigar jikinta ya tashi. "Mene nasa naqasun?,meye nasa aibun?" Ta samu kanta da tambayar kanta da kanta. Duk wani motsi da tayi duk wani tunani da zai fado mata tana ganin lokacin da zaiji kunya yazo sai ya juye zuwa wani qarin tarin girmamawar daga mutanen ma da basusan wayeshi ba. Sanda ta bude idanunta sai suka sauka kan yarinyar dazu dake zaune rukunin kujerun dake facing nasu. Ta zuba mata idanu sosai tana kallon yadda take nadar video din haisam din a babbar iPhones din dake hannunta. Wani abu taji ya zarta ta maqogoronta,hoto na biyu sai ya sake dauko mata wata budurwar ta daban daga bayanta da itama ta saita tata wayar. A hankali ta dinga bin fuskokin matan da kallo,sai taga fiye da rabin kyawawan 'yammatan buzayen dake gurin Idsnunsu da hankulansu dari bisa dari yana kanshi. Wani abu taji ya tsaya cak a kwanyarta,daidai sanda shima ya dakata cak da bayanin da yakeyi,yayin da kiran salla ya mamaye gurin gaba daya. Yadda yayi shuru haka kowa yayi shuru,kowa yana sauraren kiran sallar dake tashi cikin wata kwantaciyyar murya. Wani irin nutsuwa da haske ya mamayi musulmin gurin,manyan baqi dake gurin musulman cikinsu wani irin nutsuwa ta sake shigarsu kaman yadda tsarin ya burgesu. Qasa qasa yake karanta addu'ar bayan kammala sauraren kiran sallah,baka jin abinda yake fadi tar amma kadan kadan muryarsa tana motsawa ta mic din. "Allahumma rabba hazihid da'awatittaammah.....wassalatil qa'imah.......aati muhammadanil waseelata wal fadeelah,waddaraja'tur rafee'ah......waba'ashullahumma maqaman mahmudanillazi wa'adtah......innaka la tukliful mi'ad" Dukka akhnan taji addu'ar sosai cikin kunnuwanta,tamkar yayita ne a bayyane,kamar ya furta da murya me qarfi da kowa zai iya ji. (Manzan Allah da kansa yace mu dinga wannan addu'ar......yace mu roqa masa Allah,annabi da kansa yace ku roqamin Allah maqaman mahmuda.....karki xama shugabar marowata mana....ma'aiki ya mana gatan da duk duniya daga farkonta har qarshenta ba wanda yayi mana,daure ki nuna halasci ko yaya a duk sanda kikaji kiran sallah idan an gama kiyi wannan addu'ar,sai kuma ki biyo baya da taki addu'o'in biyan buqatar,saboda lokaci ne na amsa addu'a,Allah ya qara mana soyayyar shugaba ya sadamu dashi S A W,kar a manta har yara a koya musu 🙏🏽). A gurguje ya qarasa kammala jawabansa saboda qaratowar lokacin sallah,ya rufe da gajerun addu'o'i masu ma'ana. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 132* Duban birra takeyi sanda take zura safar hannunta,ta shirya tsaf cikin wata doguwar rigar data dace zatayi daidai da tsarin tseren. Ta batad da duk wani shape nata,kamar yadda ta boye ainihin kamanninta. Bata zato ko tunanin a tanadin shigar da tayi akwai wanda zai shaidata da sauqi. "Kaman yadda na gaya miki dazu.....'yar qasar Morocco ce,kuma ta qware wajen sukuwar dawakai a qasarsu,hasalima idan kika dubata a Instagram da TikTok duka an santa,an shirya tseren ke da ita kamar yadda kika buqata,an kuma boye sunankin kamar yadda kikace an shaidawa madame hakan.......na samu dauko wayartata" Kai akhnan ke gyadawa a hankali,jinin SARAUTA yana tafasa cikin jinin ta. Tun daga ranar da abun ya faru a hippodrome daya ja mata matsaloli da yawa,bata sake hawa doki ba koda kuwa da nishadi ne,amma a yau ta shirya hawa saboda abubuwa da dama. Daya daga ciki yarinyar.....yarinyar me suna yumna. Tanaso ta nuna mata qasarta ta shigo,tanaso kuma taga iyakarta. "Bana buqatar wayarta,kawai duk wani video da yake kai nakeso ta rasashi". "Na wayoyin sauran 'yammatan fa?" Taji muryar shehnaz tana fadi. A nutse ta waiwaya tana dubansu,dukkansu sun sake shiga akasin ta dazu a tent dinsu da yake daban da nata. Idanu ta zubawa shehnaz.....amma da yake 'yan miskilancin suna kusa saita dauke kai taqi tanka mata,ta jawo qaramin hijabin da zata fara dorawa saman kanta don ya sake boye fuskarta da tudun gashinta kafin ta saka medium din. Shigar black tayi gaba daya tun daga takalman qafarta har tufafin jikinta. Idanun aisa a kanta sanda take zama gefen wata lallausar kujera,tsarin dakin kuma yana burgeta sosai. "Shirinki fa kamar na masu tseren dokin nan biftu" Aisa ta fadi. Taji aisa din tsaf,amma sai tayi banza da ita,batajin akwai wanda zai dakatar da ita,don haka ba buqatar shawararsu takeyi ba. "Akhnan.....karki fara inde hakan kike shirin yi" Aisa ta sake fadi idanunta akan akhnan din. Still bata kulata ba sai data kammala gaba daya sannan ta juyo ta kalleta. "Na roqeki....karki bata bakinki.....na yau ne kawai aisa....komai an hanani.....komai ban samu yadda nakeso ba.....hawa dokinma sai a hanani?,ba don kaina zan hau ba.....Saboda qasata ne" Tana kaiwa nan tayi gaba birra na biye da ita. Duban aisa dake zaune shehnaz tayi. Tana tsoron doki sosai,wani lokaci gwara mata raqumi a kansa,tsaf zata hau ta sarrafashi,saidai hakan kuma bai hanata sha'awar dokin ba da kuma yadda akhnan ta qware wajen sarrafashi. Idan taga akhnan na sukuwa tana bata lokaci sosai wajen zama kallonta,wanda idan itace ko yaya za'ayi da ita ba zata hau ba.. "Kizo muje.....gaba kadan da nan za'ayi,awa daya ne an tashi zuwa da rabi saboda sallar magrib" Dubanta aisa tayi. "Ke kam ma ko a jikinki.... Kina zaton ta shaidawa mijinta?" "Zata fara hawa ne bata gaya masa ba?" Ta fadi tana waro idanunta waje. Shuru aisa tayi,ta sani inde shagala ce shehnaz tana kan gaba,bata bakinta kawai zatayi wajen fahimtar da shehnaz. "Anjima da daddare zaki rakani zan sake siyan turkud'i" Aisa ta fada tana miqewa. "Dazun ban samu shiga kasuwar ba,duk da wannan karon naga itama na canza tsarin saida kayyayakin al'adun" Dubanta shehnaz tayi "Tarhanine zaizo anjima kin sani?kinsan kuma yadda nake mutuwar son waqoqinsa,banajin zan bar gurin har sai sanda aka tashi" "Ko shekara zaki a gurin ki rakani na fara siyayyata tukunna,saboda zan koma Niamey ne ranar litinin da safe.....ya kamata shehnaz ki saki komai ki dawo muyi gyaran nan tare,b'arna ce ba qarama na shehnaz,bakya gani?". Shuru ya ratsa tsakaninsu,shehnaz na kada kanta a hankali kafin tace. "Na sani aisa....na sani,haka kawai aiki a qarqashin wadannan mutanen nakejin bai kwanta min a rai ba,kamar tafiyata zatafi zama alkhairi" "Ba zaki tafi ba.....tare zamu gyara". " Zanyi shawara da nannie" Ta abawa aisa amsa a taqaice ba kuma don tanajin zata iya komawar ba. Duk da yanayinta da yadda wasa yayi mata yawa,amma wani lokaci tana da dogon nazari da tsinkaye. ★Kebantaccen guri ne da aka zuba duwatsu da kwalta sosai,tafiyar kilometers bame yawa ba. A kewaye yake yana da fadi da tsaho daidai yadda zai isa wasan tsere a nishadance. THUNDER shi ta zaba......ta aika takanas daga gida aka dauko mata shi,dokin da takejinsa a ranta sosai.....dokin da bata da kamarsa a dawakanta. Bawai don ya fisu tsada bane.... Aah,hatta kyansa na dabanne,da kuma wanda ya mallaka mata shi kyauta wato SULTANE. Dukkaninsu suna saman dawakansu,saidai akhnan din ba wani abu nata daya bayyana saboda hijabin dake jikinta. Yumna ta gyara gashinta da iska ke wasa dashi. Ta yaya matar dake lullube da hijabi haka tayi nasara a kanta?,nasara kawai take hangowa tattare da ita. *T A M I M* Ta gaban idanunsa suka wuce yana kallon inuwarsu dama wucewarsu gaba daya,wannan ya bashi daman motsawa da zummar shiga dakin,saidai yana daga qafarsa daya daga cikin masu bada tsaro a gurin ya iso bakin tent din. Tsaiwar mutumin a gurin da dadewar da yayi yana kai kawo a gurin ita ta bata masa lokaci. Yaci gaba da duqewa a gurin,wani irin gumi yana yanko masa. Bai taba zaton samun cikas me girma har haka ba,don a iya saninsa da dukka festival din a shekarun da yayi a qasar,tsaron da ake bawa gurin baikai koda rabin haka ba,sai gashi a wannan karon......a wannan lokacin da yake da babbar buqata komai yana zuwa masa da wani irin wahala. Numfashin gushewar tsoro ya sauke sanda yaji takunsa yana wucewa zuwa rukuni na gaba,cikin takun dudduqe da sanda ya dawo ta gaban tent din ya buda ya shige. Qarewa dakin kallo ya yakeyi,yana duba area din da zata bashi sauqi da damar buya cikin kwanciyar hankali. Idanunsa suka fada saman kayanta data cire birra ta adanasu saman kyakkyawar luggage dinta ruwan gold,ya miqa hannu ya daukesu yana kaiwa hancinsa. Sosai ya zuqi daddadan qamshin da suturar tata me laushi da santsi take fitarwa. Yaji wani abu ya motsa masa,qarin qaimi da qarfin mallakarta da dukkan qarfinsa. Wani murmushi ya qwace masa,wanda banda yanayin da yake ciki dariya zai saki,nishadi ya samu sosai,musamman da kwanyarsa ke gaya masa wannan qamshin ya kusa zama mallakinsa na har abada. Zata bace bat daga DUNIYAR da aka santa......zai tafi da ita dangin mahaifiyarsa can wani qauye da basa rayuwa da baqi. Qauye ne da duk baqon daya shigo sunansa gawa. Tun daga sanda aka taba cinsu da yaqi,abinda yayi silar kama mahaifiyarsa aka fito da ita zuwa wata masarutar a matsayin baiwa,har aka samu cikinsa aka haifoshi,bata sake komawa garinsu ba saida wani fada ya harqe a masarautar da suka ribatota din,ta samu ta falle zuwa qauyensu,tun daga sannan suka saka tsaro me qarfi da doka akan yankinsu,don haka yasu yasu suke rayuwa,ba kowa ma yasan da zaman wata qabila a gurin ba. Kayan ya saki a nan inda suke......ya soma birkita kaya dake ajiye tsaf a dakin don samun muhimmin gurin buya. "Commenc!(start!)" Me kula da tsarin fara tseren ya fadi da madaukakiyar murya. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Sautin ya sauka a kunnen haisam,daidai sanda yake saukowa daga can sama inda yahau yana sake duba tabbacin tsaron gurin. Baya daukar komai da sauqi.....duk abinda aka dorashi a kanshi a matsayin amanar al'umma dukiya ko rai baya taba bari gangar jikinsa da ruhinsa su huta. Tun daga nesan yadda ake sarrafa dokin ya dauki hankalinsa......tun daga nesa yake iya hangen banbanci qarara daga mahayan dokunan guda biyu. Yana iya gane fuskar dayar,yana iya gane wacece......saidai dayar dake sanye da baqar sutura wadda take neman yin wasan kura da yumna itace wadda tafi daukan hankalinsa. Duk da yana nesa amma sai yake jin wani irin kusanci da sanayya me qarfi tsakaninsa da dayar.......tamkar ana fusgar hankalinsa zuwa kanta duk da irin gudun da take tsulawa akan dokin. Cikin filin duka ba wanda yakejin muryar wani saboda karadi sowa ihu da fito da suka rude dashi. Gaba daya larabawan nan......mazansu da matansu hankalinsu ya tashi akan akhnan din. Sun jima basuga mace da bata tsoron sarrafa doki irinta ba,ako ta ina manyan wayoyi da cameras ne kawa suke haskawa. Har cikin zuciyarta takejin wani sanyi da aminci sanda ta fara hangen tsoro da sarewa daga yumna. Murmushi take saki kawai ta qasan qyallen data yane fuskarta dashi. Wannan din ya tuna mata zamanin quruciya. Sanda take biftu dinta 'yar shekara goma sha daya zuwa sha biyu. A tsakaninsu yaran sarakuna,duk wadda take bata haushi,duk wadda take matsanta mata bata tashi koya mata hankali sai lokacin taro irin haka. Zata kadaki ne ta daga miki hankali har sai ta tabbatar kin horu,wannan ya sake bata qaimi ta bawa thunder qaimi da kyau......qaimin da batasan shine zai zama SILAR MATSALARTA BA......QAIMIN DA BATASAN SHINE ZAI XAMA SILAR RABUWARTA DASHI BA HAR ABADA. Zuciyarsa yaji tayi wani motsi me qarfin gaske sanda yaji wani sashe can daga zuciyarsa yana gaya masa. "Akhnan ce" Ya zuba mata idanu sanda take surfa wani irin gudu yana lissafa adadin tsahonta da fadinta daya dade da riqeshi cikin kansa. Tsaf lissafinsa ya bashi itane,ya sauke dubansa kuma dai akan dokin da take kai. "Thunder?" Ya fadi a hankali yana jin ransa yana sake ninka baci. Dokin da yayi mata magana a kansa?,dokin daya gaya mata a taqaice yana buqatar kulawa ta lafiyar kwanyarsa?. Ya riga ya zabura tun a wancan ranar.......ya dauka zata bari ne ya samu cikakkaken hutu?. "Ba zaki sake ba" Ya fada da wani irin coolness yana zaro wayarsa daga aljihun rigarsa duk da cewa zafi kawai zuciyarsa take masa. "Ka gayawa kowanne dan jarida ya sauke camera dinsa.....wannan daukar kada ya fita daga nan inda aka yita......idan kuma wannan sukuwar ta qare......akwai sabon wasa da wani mutumin" Abinda ya fada kenan duka a dunqule a kuma jere,sannan ya sauke wayar yana katseta gami da furzar da iska me dumi daga bakinsa,sannan ya taka a hankali yana sauya akalarsa daga gurin. Cikin qasa da minti talatin takai yumna ga faduwa. Ta cinye wasan da wani irin salo na cinyewa da kuma qwarewa. Kowa nata ne.....kowa kuma da yazo baqonsu ne......amma haka kawai Madame minister takejin wani irin farinciki da qarin alfahari da akhnan din yana ratasata. Tabbas princess dinsu ta dabance......ta sake gasgata hakan bayan ta sake samun kusanci da ita na wanacan ranar da kuma yinin yau. Duk labarin da ake a kanta.....duk zuzutatan da akeyi sai take ganin yayi kadan ma,kamar ma basu gama saninta bane shi yasa zantukansu suka tsaya a haka. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽 💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 133* Lokacin da me sanarwa yake sanar da neman lokacinta don tsere na biyu saita tsaya cak,muryarsa tana ratsa dukka lasifiqar dake daure a gurin wadda take qarawa sautin qarfi. Wancan lokacin shine abinda ya dawo mata a idanu..... Sak komai yake dawo mata kamar a wancan karon. Sanda baqin dokinsa yake takowa da wani irin qasaita da taku d'ai d'ai. Qafafunsa suna bada wani sauti kamar yana bata tabbacin wani abu ne. Idanu ta zuba masa sosai kaman yadda ya zuba mata idanu cikin wani kwantaccen bacin rai.....yauma nannade da wannan rawanin......nannade cikin hiramin da yabad zagayen idanunsa a wancan lokacin. Idanunta ta lumshe sannan ta budesu dukka lokaci guda a kansa. Wani irin buguwa zuciyarta takeyi kamar zata ballo qirjinta ta fado qasa. Kamar shine take gani ake dawo mata dashi.....kamar faifan video dinsa aka sanya mata take sake maimaicin kallo. Sanda yazo ya daidaita tsaiwar sa kuda da nata don karbar umarnin fara tsaren sai taji kamar an zare mata dukka lakarta sakamakon qamshin nan.....wannan qamshin turaren da ba wata rana da zata fito ta fadi bata shaqeshi cikin rigarsa da bai sake bi ta kanta ba. "Idan har shine,....inde ya tabbata shine......a nan gurinne kawai ya kamata ki rama.....kyakkyawar dama kika samu da zaki maida masa zazzafan martani,dama ce me kyau a tare dake khadeeja muhammad hammud.....ahalin abun ce ke.....ya kamata ki gwada masa BANBANCIn JIMIN SARAUTA da gama garin mutane" Taji wata zuciyar tana qarfafarta.. Iska ta sake zuqa me kyau ta fesar a hankali,tana jin qwarin gwiwarta dama komai nata yana dawowa. Qaimi ta bawa thunder sanda aka furta kalmar "Start" Da faransanci,gurin ya cika da ihu da sowa,sowar dake sauka har tsakiyar zuciyarsa tana sake tunxurashi da bata masa rai,saidai kwance kwance yayi mata,ya barta da murna da karsashin ganin ta tsere masa. Sau uku tana dubansa da wani irin kallo dake furta ma'anar. "Ba tsararka bace ni" Da wani murmushi da ba kowa zai iya ganinsa ba cikin idanunta,saboda boyayyar fuskarta. Ya bata dukkan nasara da dama a zagayen farko dana biyu,ya bata dama me kyau a zagaye na uku,kafin ya yiwa dokin wani irin qaimi da umarnin daya soma cilla wani irin gudu me daukan hankali. Bata zata ba.......bata kuma taba kawowa ba. Nasara kawai take hanga dab da ita,saidai cikin mamaki ta jiyo taku me matuqar qarfi. Hankalinta yayi matuqar tashi sanda ta jishi dab da ita,abinda ranta ke gaya mata kawai ya taso ne don ya wuceta ya isa ga finished line. Saidai kuma sanda ya cimmata saiya saisaita gudun dokin. Waiwayowa tayi a hankali,idanunta ya fada cikin nasa. Wani irin kallo yayi mata,kallon da ya zuba wani irin rudewa a zuciyarta gaba daya. Idonsa da kansa ya dauke daga kanta,sannan ya sake miqewa saman bayan dokin yana gigitashi kamar yadda umarnin ya hada harda thunder ya gigitasu gaba daya. Fara ruda mata hankali yayi,ya fara kadata daga hagu zuwa dama,daga dama zuwa hagu da wani irin salo daya qarasa gigita nutsuwarta. Thunder taketa qoqarin controlling......amma kamar yadda ya faru a wancan ranar ya gigice mata. Cikin qasa da mintina goma sha biyar ya goge mata hadda gaba daya.....cikin qasa da mintina goma sha biyar ya sanyata ta manta cewa ITA GWANA CE,qasa da mintina goma sha biyar ya sanyata tayi loosing control na thunder kwata kwata tamkar bata taba sarrafashi ba. A gaban idanunta ya isa finished line,ya kuma cire tutar gurin ya dagata,abinda ya sake hautsina gurin da mabanbantan sautukan burgewa. Ba cinyeta da yayi a yanzu ne damuwarta ba,damuwarta a yanzu shine irin gudun da dokin yakeyi da wani wajigata. Tana dab da isa inda haisam din ke tsaye.......amma sam bataga alamun thunder zai tsaya ba......ta tabbatar muddin ya wuce nan kuma zai nutsa da ita cikin sahara ne kai tsaye,batasan kuma inda zata tsaya ba....batasan inda zai dosa da ita ba. Bacewa bat.....bacewa ta har abada a cikin sahara ba wani baqon abu bane,abinda ya sake daga hankalinta kenan musamman da taji fit sun wuceshi sun kuma soma nausawa cikin saharar. Hannu ya dagawa kowa yana bashi tabbacin aminci,sannan ya zunguri nasa dokin gami da juya akalarsa yabi bayansu. Wani irin kaduwa zuciyarta kawai takeyi.....wani irin tashin hankali takeji sanda taga kai tsaye ya tunkari tulin lallausan yashin da zai.kaisu ga gangarawa,gangarawar data tabbatar idan ta yita Allah ne kadai yasan me zai faru da ita. Kan nasa dokin ya miqe gami da ranqwafawa ya riqe linzamin da kyau,cikin wani irin sauri.....cikin wani irin karsashi ya kamo thunder. Da hannu daya ya samu nasarar dauketa cak zuwa saman nasa dokin bayan ya samu nasarar dukan thunder da qafa,dukan daya sanyashi jan wata turjiya yayi haniniya yana juyawa,saidai bai sake takun gudu guda ba saboda wani abu da taji haisam din ya fadi cikin tsawa wanda batasan meye ba,sai dokin yaja ya tsaya cak,saidai kuma yana ci gaba da haniniya kamar idan aka bashi dama kuka zai saka. Saman dokin suka koma suka zauna dabas ita dashi,yayi mata rumfa cikin yalwataccen qirjinsa saboda ajiyeta da yayi a gabansa,hannuwansa kuma suna riqe da linzamin dokin. Baya taji ba shiri saboda miqewar da dokin yayi kamar zai zubar dasu,ta samu wata kyakkyawan mazauni a qirjinsa kafin a hankali dokin ya ajiye qafafunsa a qasa. Dukkaninsu ba wanda yayi qoqarin motsawa,daga ita har shi suna saman dokin a zaune. Tana jin yadda yayi mata rumfa da hannuwansa,tana jin yadda qamshinsa yake sake mamayarta,tana jin yadda wani irin dumi daga faffadan qirjinsa yake mamayar ilahirin zuciyarta da gangar jikinta,yana kuma haifar da wata nutsuwa yana amintar da ita daga dukkan tsoron daya taso ya soma lullube mata zuciya. A hankali kamar wandada ke shirin narkewa taji tana qara shiga jikinsa sosai.....a hankali taji habarsa saman kafadarta.....a hankali hucin numfashinsa dake fita daga dogon hancinsa ya soma sauka a fatar fuskarta,abinda ya sanya tsigar jikinta zubawa. Da wani tattausan harshe amma mai cike da kaushi a maganganunsa.......da wata magana dake fita daga can qasan maqoshinsa......wata magana me kama da maganar da akeyinta cikin sirri,sirrin da ba'a buqatar kowa yaji yace. "Ki daina gwada kanki a inda hatsari yake.....Ba'a shiga tseren doki don nuna girman kai.....musamman ba tare da izini na ba". "Izini?" Ta fada can qasan ranta. Har yanzu idan ya fadi hakan tana jin mamaki......ta kasa sabawa. "Izini fa.?" Ta maimaita maganar zuciyarta tana lumshe idanunta zuciyarta tana bugawa. Kusancinta dashi yana haifar mata da wani abu,tana jin kamar ba zata iya riqe kanta ba,kawai saita zabi ta shammaceshi,ta sauka daga saman dokin da wani irin sauri. Saukar da tazo mata da tsautsayi......tana dire qafafunta qafartata ta bada wani sauti daya tilastata furta. "Wash Allah na" A mugun wahalce tana dafe qafartata. Cikin qiftawar idanu...cikin wani yanayi na zafin nama.kamar sadaukin daya dawo daga yaqi ya dire a qasa da dukka qafafunsa. "Kin rasa hankalinki ne?" Ya fadi da wani irin yanayi daya tilastata daga kanta tana duban qwayar idanunsa duk da irin zafi da radadin dake ratsata har kwanyarta. Wani irin rudewa take gani cikin idanunsa,kafin ya qaraso ta tattara dukka juriyarta ta miqe,saidai ta tsaiwa din batasan sanda ta sake furta. "Wayyo Allah na" Da siririyar muryar nan tata data karye sosai ba. Da wani irin zazzafan taku ya isa gareta kafin takai qasa yana riqe dayar kafadar tata,riqon daya sanya mata tsoro,tafin hannunta yakai saman faffadan qirjinsa. Daga kai ta sakeyi a karo na biyu tana duban fuskarsa dake shimfide da rudani. Bugun zuciyarsa take iya jiyowa......bugun zuciyarsa sosai da wani irin qarfi da bata taba kawowa ba. "Tsorata yayi?,me yasa ya damu haka?" Ta tambayi kanta da kanta tana sauke dubanta kan qafarta. Kamata yayi ya maidata ya zaunar da ita sosai yana miqe mata dukka qafafunta. Hannu ya saka ya dago dayar,dagawar data sanyata runtse idanu ta kuma saka hannunta ba shiri tana riqe hannunsa idanunta a runtse tana furta. "Wayyo Allah bappi". Yadda ta furta din ya ratsa kunnuwansa da wani irin yanayin. Muryarta ta sauka sosai cikin kunnensa saboda kusanci da fuskarsa tayi da tata. " Ki nutsu" Ya furta a tausashe yana qoqarin daidaita nutsuwarsa. " Da zafi" Ta fada tana yarfa hannu cikin tsananin azaba. Sake kama gurin yayi,saita sake cafke hannunsa da hanzari,abinda ya sanyashi daga kansa yana dubanta a hankali. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Da gaske zafi takeji,ya fahimci hakan saboda kalar gumin data hada sosai cikin qanqanin lokaci. "Don Allah" Ta fada a narke,saboda ta fuskanci da gaske so yake ya taba ciwon,tare da manta cewa roqonsa ma takeyi. Wani abu daya zamana na farko a rayuwarta.....roqon ALFARMA da neman alfarma daga gurin wani mutum na daban......ba SULTANE ba. Yadda tayi maganan a shagwabe ya sanya yaji wani abu ya tsarga cikin kansa. Ya daga kan nasa a hankali ya zube idanunsa saman fuskarta. A shagwabe tayi maganan sosai.....da shagwaba irin wadda a baya mammina da bappi sultane kawai take iya yiwa su. Ruwan hawaye yake gani sosai cikin idanunta a kwance,karon farko da yaji wani rauni me kama da tausayi ya saukar masa. Bayason kuka,bayason hawayen mace. Tunda ya karanta cikin qur'ani a nazarin da yayi masa sanda yake karatun qur'anic science,yazo ya kammala tafseer dinsa gaba daya. Cikin qur'anin ayoyin da dukka sukazo akan MACE Allah yana tausasa mata kalamai ne da lafuzza,sai abun ya zame masa jiki. Zare nadin dake kansa yayi a hankali,abinda ya bawa sassalkar sumar nan tasa me santsi baqi da cika kai daman bajewa saman kansa da wani sashe na fuskarsa. A hankali idanunta suka kai......yawan sumar ya bata mamaki don bata taba ganinta full kamar haka ba. Duk da duhun magariba daya shigo amma kana iya ganin qyallin da take bayarwa. Warwareshi yakeyi a nutse,yayin data samu kanta da kafeshi da idanu,tana kallon yadda sumar ta sake canza kamanninsa. "Wanne yare ne?.....balarabe?" Ta tambayi kanta da kanta tana lumshe idanunta gami da budesu lokaci guda saboda radadin ciwon dake ratsata. Daga idanunsa yayi,sai suka hada ido,tayi saurin kauda idanunta shi kuma yayi kamar bai ganta ba. Ya miqe yana wareshi sosai ya shimfidashi a qasa ba tare daya damu da rairayin dake gurin ba. Ya tako a hankali zuwa gabanta,ya miqa mata hannunsa kai tsaye yana dubanta. Nauyi taji ya aza mata,ta fahimci me yake nufi sarai......amma kuma ita kadai tasan me takeji duk sanda ya hade tafukan hannunsu guri daya. To amma ya zama dole ta tashi,don ba zata iya takawa da qafafunta ba ita kadai. "Levez-vous(Stand up)" Ya fadi da wannan karya harshen da yake sanyata takejin wani yanayi a cikin ranta duk sanda zai furta France. A nutse ta miqa masa dogayen yatsunta,ya runtsesu tsakiyar lallausan tafin hannunsa sannan ya dagota. Ido ta runtse,zata sake fadin. "Washa Allah" Sai ya rigata. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ya maimaita har sau uku. Kasa fadin wayyo Allah din tayi,a hankali sai taji zuciyarta tana maimaita abinda ya fadi din. Sai da yaga ta samu daidaito a tsaiwar sannan ya umarceta ta taka,saidai hakan yaqi yiwuwa. Har cikin zuciyarta takejin radadin sosai. Kaman daga sama ya shammaceta,sai jinta tayi yayi sama cak da ita da hannuwansa biyu yana mata kyakkyawan riqo cikin jikinsa. Ji tayi kamar numfashinta zai dauke,tsoro sosai ya kamata. Ko nauyinta baiji ba?,ko girmanta shi baya gani?. Idanunta kawai ta zube akan qirjinsa,qirjin da zuciyar dake cikinsa take bugawa da wata irin nutsuwa ba kamar dazu daya tallafeta ba. "Me ya hautsina bugun wannan nutsatsiyar zuciyar a dazu?" Ta tambayi kanta da kanta. A yanzu da take kallon qirjinsa da yake dage.....dagewar da take tabbatar mata cikakken qarfi ne kwance a gurin. Sai taji tana sha'awar sake aza tafin hannunta a gurin,sau taji tana sha'awar sake jin wannan kyakkyawan bugawar dataji a dazu,bugun zuciyar tasa daya dinga ratsa jininta da wani irin gudu yana son samar da connection da wani sashe na jikinta. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 134* Gaban Shimfidar ya tsaya,ya sauke dubansa a kanta,daidai sanda itama ta daga kai tana dubansa. Shi ya fara dauke kansa wannan karon,ya tsugunna saman gwiwoyinsa a hankali yana ajiyeta gefan Shimfidar. Tana zama suna jin taku daga bayansu,don haka kai tsaye ya miqe yana waiwayowa. Wasu daga cikin guards na gurinne da kuma na masarauta. "Minister tace fatan komai lafiya?" Kai ya gyada a nutse yana basu alamun tabbacin lafiyar. Thunder yasa suka janye suka bar nasa dokin,sannan suka juya suna barin gurin. Idanunsa a akanta,ya sake haurowa saman Shimfidar. Zama yayi sosai a gabanta yana tanqwashe qafafunsa,wani irin zama me tsananin kusanci a tsakaninsu. Hannu ya sake kaiwa zai kamo qafar ta zabura ta riqeshi,sai ya dakata cak,ya zuba mata idanu da kallon data gaza jurewa,abinda ya bashi daman kama qafan cikin zafin nama,don ya fuskanci idan ya biye mata fa to zasuyita zama ne a gurin. Idanun ta bude a tsorace,saidai ta sameshi ya kafeta da wani irin kallo me tsananin kaifi. "Kalleni" Ya fada da wani irin coolness ganin tana son janye qwayar idanunta. "Cikin idanuna" Ya fada yana nuna nata qwayar idanun nasa da yatsarsa. Batasan me yasa ta gaza janyewa ba,batasan me yasa ta gaza masa musu ba,sai tayi yadda yace din. Tayi yadda yace din.....tayi kuma yadda yaso ba tare da tasan SAKAMAKON da hakan zai haifar mata ba. Duban idanunsa kadai sai taji kaman yana zuqeta daga ainihin duniyar da take ciki......kamar yana zuqeta daga ainihin gangar jikinta zuwa wata gangar jikin ta daban. Kamar yana zuqeta zuwa DUNIYARSA.....wasu irin magnet masu tsananin qarfi taji a hankali suna janta. Wani iri yanayi.....wani irin kallo.....wasu irin idanuwa data dinga ji kamar ana jifanta da wasu abubuwa masu sanyi dake sauka saman zuciyarta suna narkewa suna kuma bin sassan jikinta. Wani zuzzurfan kallo da bata taba yiwa wani d'a namiji irinsa ba.....wani zuzzurfan kallon da itama ba wani d'a namiji daya taba yi mata irinsa. "An gama" Lafazin ya sauka a kunnenta yana kuma maidota duniyar ta daya saceta daga ciki zuwa wata daban. Zare idanunta tayi a kansa duk da shi yaci gaba da kallonta ne. Takai dubanta ga qafartata. A hankali wani mamaki yake lullubeta. Yaushe yayi gyaran?,yaushe kuma ya gama shi duka bata sani ba?. "Kiyi alwala.....lokacin magarib yana kusa da fita" Tana kallonsa yasa hannu ya share rairayin gurin ya Ciro ruwa daga jikin dokinsa ya soma alwala, Hankalinta ya dauku sosai,yadda yake alwala da wata irin nutsuwa da kamewa,gami da cika dukkan sunnoninta da farillanta sai abun ya kasa wucewa a idanunta. Sai ya matso bayan ya gama,ya tsugunna a gabanta ya fara zuba mata ruwan a hankali ta fara alwalar. Idanunsa ya sauka akan fararen tafukan hannunta da sukayi kwanciyar jini saboda tsananin hasken fatarta. Samun kanta tayi da halarto kalar tasa alwalar tana bibiya itama daki daki,gabanta yana faduwa. Haka kawai takejin ya mata wani kwarjini,ga tsugunnonsa dab da ita dake sake yin kaca kaca da nutsuwarta. Wai itace a yau take alwala da takatsantsan kada wani yaga kuskurenta?. Dakatawa ta danyi sanda tazo shafar kai. Ya daga manyan idanunsa ya zube a kanta,kafin a hankali ya dauke dubansa yana maidashi wani gurin daban. Ya fahimci ne ta tsayawa.....itama ta fahimci ya bata space ne nayin shafar kan. Qafafunta ya zubawa ruwan tana wankewa,saidai tsigar jikinsa ce yaji tana zubawa lokacin da take wanke sambala sambalan fararen qafafun nata. "Ina zuwa" Taji ya fadi bayan ta kammala. Narai narai tayi da idanu,ina zaije a wannan fili saharar da baka ganin kowa da komai?. Fitilar wayarsa dake kunne ce kawai take basu haske. "Ba nisa zanyi ba" Ya fadi yana bata qwarin gwiwa da kuma tabbaci da idanunsa. Daga inda ta tsaya tana hangensa,mamaki ya kamata ganin ya sake sauya alwala bayan yanzu ya gama. Dawowa yayi,ya tsaya daga gabanta kadan ya fara tayar da iqama,ya kabbara sallar yana daidaita tsaiwarsa sannan ya fara rera karatun nan nasa. Da wannan muryar.....wannan sautin me kama da qira'ar sheikh afif,cikin suratul furqaan da wani kwantaccen sauti daya soma sanya nutsuwa tana lullubeta. A nutse ya kammala ba tare da jan dogayen ayoyi ba...ya zauna kadan sannan ya fara gabatar da nafilolin bayan sallar magariba din. "Baya gajiya ne da sallah?" Ta tambayi kanta tana satar kallonsa sanda yake sake zaman tahiyar qarshe. Itakam sai take ganin kamar sallarsa tana da banbaci da tasu,kamar akwai wasu abubuwa wata nutsuwa da wani tsantseni a sallarsa da suka rasa a tasu. Kwarjinin da yayi mata ya sanyata yin qasa da kanta sanda ya waiwayo bayan ya kammala sallar. Kamar tsakanin fara sallar da kammalata ana qara haske fuskarsa ne. "Zaki iya takawa?" Ya fada da kulawar da taji ta ratsa har tsakiyar zuciyarta. Kanta ta daga masa,sannan ta yunqura ta miqe a hankali. Ga mamakinta ba wani ciwo me zafi,ta dinga takawa a nutse a nutse har suka kai bakin dokinsa daya rage. Tsayawa tayi ranta da zuciyarta fal saqe saqe. Saman doki daya zasu zauna?,tabbacin fa kenan zasuyi sharing muhalli daya?. Idan ma haka ne ta yaya zata iya dokin?,tsahonta baikai ba,ta riga ta saba duk sanda zata hau sai an saka mata abinda zata taka ko an samu wadda zata tallafeta. Wani irin mamaki ne ya soma narkar da ita sanda taga ya tsugunna saman gwiwoyinsa yana daidaita gaban dokin. Ko baiyi magana ba,ko baice komai ba ta fahimci abinda yake nufi. Durquso ne da akewa sarakuna don su tattaka su samu hawa doki,duk da cewa a tasu masarautar sultane ya haramta hakan. Suna da abubuwan takawa masu kyau na musamman da aka ajiye don hawa doki bawai dan adam ba. Ji tayi kamar tana narkewa sanda ya daga manyan idanun nan da koda ace da duhu a gurin bata iya ganinsu tarwai amma tana iya jin tasirin kwarjininsu a jikinta. Sanda yake fadi mata. "Ki hau mu tafi" Sai takejin kamar ba zata iya ba. Ta yaya zata taka gadon bayansa don tahau doki?,gadon bayansa fa?,abun ya mata girma da nauyi. "Taka ki hau mu tafi" Ya sake maimaitawa da wani sauti daya sanyata takowa a hankali kamar wadda ke tsoron taka qasa. Takalmanta ta kalla,sai takejin ba zata iya taka gadon bayansa da takalmi ba. Tsugunnawa tayi a hankali ta zare takalman daga qafafunta. Sannan ta matso tana jin wani abu yarr yana tsirgawa a jikinta,ta sanya qafarta ta dama kafin ta dago ta hagun itama. Cak ta jita tsaye saman bayan nasa,ba wani girgidi ko lagwai lagwai na nama ko fata. Kaman tana zaman wani abu dake shimfide saman doron qasa,sai curi curi na muscle da dumin jikinsa da yake ratsa tsakiyar fatar qafafunnata. Bismillah tayi tana hawa ta zauna sosai,bismillah din data sauka a kunnensa,karon farko da yaji tayi wani abu daya burgeshi. Hagu da dama ya zagaya yana dubawa,kaman bai amince da iya zamanta saman dokin ba,tana jira taga yahau bayanta,sai taga kawai ya kama linzamin dokin sun fara tafiya a hankali. *T A M I M* Daga gurin da yayi kyakkyawan boyo tsakanin tent din akhnan dana maqotanta,daga nan din yana iya ganin kai kawo da motsin duk wanda zai shiga ciki ko kuma ya fita. A irge yake da shudewar kowanne minti,a lissafe yake da shudewar kowacce daqiqa. Akan idanunsa komai yake faruwa,saidai a yanzu fatansa daya shine dawowar akhnan da kuma shigarta cikin tent dinta kamar kowa.... Baida yaqinin inda ta shiga daga sukuwar dokin daya kubcewa saitinta,duk da bai ganta a kasuwar bajakolin kayan al'adu dake ci a sansanin ba.....amma ya tabbatar duk inda take zata kwana ne dole a tent dinta. Tsakiyar dare zuwa asuba sune awannin sa'arsa.......daga tsakiyar dare zuwa asuba mummunan labari zai tarwatsa taron festival de l'Aîr gaba daya. Zabi biyu ya aje mata a ransa,idan ya samu nasarar tafiya da ita lafiya lau haka yakeso,idan hakan kuma zai zame masa kaya zai aikata abinda yakeso da ita a gurin,ko banza ya kashe wata wutar kafin ya samu sararin hada target na gaba. ★Wata irin tafiya data saukar mata da wani yanayi a zuciyarta....wata irin tafiya da take jinta kamar cikin litatattafai da finafinai. Hasken farin wata sai ya zame musu tamakar wata fitila tsakiyar duhun daren daya keto. Samun kanta tayi da zuba masa idanu. Yadda yake takawa cikin sahara da wani irin yanayi dake gwada jarumtarsa da rashin tsoronsa. A iya saninta baqo ne shi a yankinsu,a iya saninta baisan kan sahara da hanyoyinta ba,amma kuma sai gashi yana taka saharar da wani confidence da rashin DAMUWA. A duk sanda ta tuna yadda ya bata gadon bayansa ta taka sai taji wani tashin tsigar jiki.....a duk sanda ta tuna da wannan sai mamaki ua mamayeta. Tana zaton yana da girman kai......amma kuma wannan abun ba wanda keda girman kai komai qanqantarsa da zai iya aiwatar dashi. Tana ganin wata kulawa a tare dashi.....kalar kulawar da sultane kadai take ganin makamanciyarta a gurinsa. Tun tana ganin NA GANIN IDO ne.....tun tana ji a zuciyarta na NEMAN SUNA ne gurin sultane,ya zuwa yanzu zuciyarta ta gama sallamawa DABI'A CE A CIKIN JINI. Ya girmamata ta hanyoyin da bai girmamata din ba a gaban mutane.....ya girmamata da nau'in abubuwan da take jinsu sun tsaye mata sosai a zuciyarta. A inda ba kowa daga shi sai ita sai Allahnsu,.....a inda idan yaga dama zai iyayi mata komai,ba wanda zai hanashi.....bame qwatarta.....a irin wannan gurin sai ya zabi girmamata,sai ya zabi kare mutuncinta sama da komai. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Sanda suka fara hango haske sansanin festival din.....saita dinga ji kamar su rage saurin tafiyar da sukeyi. Duk da tafiya ce sannu sannu cikin nutsuwa......amma sai takejin kamar karsu iso gurin. Ita dashi dukka sun hangi maleek da falaak zaune saman rairayin,da alama cikin wani yanayi suke na zallar shauqi da qauna.....har basaji basa ganin kowa dake daura dasu. Ga mamakinta sai taga ya dauke kansa,ya kuma ja akalar dokin sun dan sauka daga kan hanya kadan yadda ba zasu ji motsin tafiyarsu ba,ya yanke ta wani hannun daban can qasan ransa yana sakin murmushi. Ya aminta da gaske maleek yake,baida zaqewa haka.....baida rawar kai akan diya mace iya saninsa dashi,saidai zuwa yanzu ya gasgata da gaske yake yarinyar ta zautashi da yawa. Ta sake binsa da idanu sanda yake miqawa birra akalar dokin yanayin gaba,bayan ya danyi magana da birra din da batasan me yace mata ba. Sai sake waiwayarta,bai sake juyowa ba ya taka yana shigewa cikin mutane har ya bacewa ganinta. "Zamu iya tafiya ranki ya dade?" Taji birra tana fada cikin girmamawa "Muje" Ta amsa mata a taqaice,saitayi gaba da dokin kai tsaye zuwa ga tent hanyar tent dinta. Wani shu'umin murmushi tamim ya saki,yana jin wani dadi yana kamashi sanda ya hangi isowar akhnan da shigewarta tent dinta. Akan idanunsa Madame minister......da sauran ministoci mata suka dinga shiga duba lafiyarta suna fita,kuma akan idanunsa aisa da shehnaz da suka zama fitar qarshe suka fita suma,bayan shehnaz ta gama cakar da ita da wannan kalar tsokanartata. Yau bata da bakin cewa komai.....a yau bakinta da zuciyarta sun wani mutu murus. Komai game dashi ne yake dawo mata,idan tace komai tana nufin komai da komai din. Nutsuwar nan data mamaye komai nasa......miskilancin nan data lura yana iya hanaka ganin murmushinsa.....kwarjinin nan da har yanzu take tambayar kanta INA YA SAMOSHI?,INA YA GAJESHI?. Uwa uba.....tana ganin wani good sign da wani good character da riqo da addini yake iya bawa d'a namiji ashe?. Wani kalar shiriya kusanci da Allah da Allah a dukka lamura. Komai zaiyi a iya tsahon awannin da suka taba yi tare sai taji ya kira sunan Allah. "Bismillah....alhamdulillah.....a'uzu billah.....astagfirullah......subhanallah" Bata taba jin wata mummunar kalma ba......bata taba jin wata kalma mara kyau daga bakinsa ba. Ta juya tana gyara kwanciyarta da kyau bayan birra ta taimaka mata tayi wanka,ta kuma canza kayan jikinta zuwa wani riga da wando masu taushi na bacci farare tas. "Yace idan kinyi wanka ki rama sallolinki saikisha wannan" Ta tuna maganar birra a dazu data bata ruwan wani abu me dumi tasha. Wanda tana kammala sha da mintuna kadan taji gajiya tana warware mata gami da barin jikinta. A hankali idanunta suka fara lumshewa,wani irin ni'imtacen bacci da ta jima bataji irinsa ya lallabo ya dauketa. Sannu a hankali sawu ke daukewa.....sannu a hankali gurin yake qara cika da shuru saboda kwanciyar jikkuna izuwa makwancinsu don huce gajiyar ranar farko ta festival din,don samun cikakken baccin da zai basu daman tashi da karsashi me yawa a rana ta biyu. A wannan lokacin burin tamim yake sake kusanta zuwa ga cikarsa.....a wannan lokacin kowacce daqiqa dake gotawa take sake cika zuciyar tamim da madaukakin farinciki. A wannan Lokacin ne kuma haisam ke dawowa sansanin,bayan ya sake tabbatar da tsaro a kowacce fuska da nahiya na gurin,cikinsa da wajensa. Wani irin gumi me dumi ya yankowa tamim ganin yadda haisam ke tunkaro gurin. Ba yau ba ba jiya ba ba kuma shekaran jiya ba. Tun a ranar farko daya fara ganin sa yakejin wani abu me qarfi da girman gaske a kansa. Tun daga wancan ranar yakejin wani kwarjini na bala'i yana dukansa a kansa. A duk sanda zasu hadu dashi,a hanya ko a wajen sultane,dukka wannan ranar yana yinta ne cikin rashin sakewa da kuma d'ari d'ari. Numfashinsa gaba daya ya dauke ganin ya tako dab da inda yake yayi tsaye. Baibar gurin ba saida ya kusa rasa numfashinsa saboda riqeshin da yayi,ya zuqi iska yana riqe wuyansa da kyau ganin yadda tsaiwarsa ke shirin hallakashi,idanunsa a kansa har sanda ya shige tent din da Akhnan ke ciki. Bai damu ba....koda ya rasa samunta a tsakiyar dare,ya shirya samunta lokacin sallar asuba.... Lokaci ne daya tabbatar haisam zai fita da sauran dukka maza don bada faralin sallar asuba din.....saidai daga yanzu zuwa kowanne lokaci inde dama ta bashi iko.....zai iya aiwatar da qudurinsa,don haka ya zauna sosai yana ci gaba da gadin komai gami da ci gaba da daidaita numfashinsa da har yanzu bai dawo daidai ba. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 135* Sassauqan haske ne a dakin,wanda sam baiyi yawa ba,kusan ma za'a iya cewa hasken fitilun dake zagaye da tent din sune suke haske dakin,hasken da zai iya nuna maka komai ka ganshi fes. A nutse ya dinga takawa zuwa cikin dakin,idanuwansa akan fuskarta,yana shaqar qamshin dake manne da d'akin. Sosai ya shaqi iska ya fesar,yana qarasawa saman kanta da wani irin taushi yana dubanta. Bacci takeyi sosai,da alamun tarin gajiya a tattare da ita. Dazun zuciyarsa ke dawo masa da komai daya faru. Tana da jarumta can qasan zuciyarta......tana da tsaiwa da rashin tsoro akan abinda takeso da dukkanin abinda ta sanya a gabanta. Ya tuna yadda tayi da yumna,duk da irin qwarewa yumna din wajen sarrafa doki da babanta ke gaya masa,da yadda shima ya fahimta. Baisan meye mafarin abun ba,besan meye ya jawo hakan ba,amma abinda ya lura kawai FANSA take nema daga yumna din. "Rigimammiya" Ya fadi sanda yake matsawa daga inda take,saidai idanunsa suka sauka kan yadda hannunta ya lanqwashe. Kamar zai gyara mata sai kuma ya fasa,bayason abinda zai kawo haduwar jikinsa da nata. Komawa yayi da baya ya soma rage jayan jikinsa a nutse,ya wuce toilet yayi wanka sannan ya fito ya tsane jikinsa ya kuma shafeshi da lausasan lotion dinsa da kuma turaren daya saba amfani dasu. Abun sallah ya shimfida,yayi shafa'i da wuturi da sauran addu'o'insa. Yayi zaune saman abun sallahr yana qarasa azkar na yammaci da bai samu yayisu ba a yau,jifa jifa yana tsintar idanunsa suna fadawa kanta. Baccinta take hankalinta kwance,baccin daya tabbatar qila inda tasan yana gurin ba zata sake har haka ba. Hular kanta ta zame tayi nata gurin,wannan ya bawa gashin kanta me santsi da sheqi daman bayyana. "Alhamdulillah" Ya furta yana miqewa a nutse,ya ninke abun sallar. Fita yakeso yayi ya sake tabbatar da tsaron gurin,sannan ya qarasa gurinsu omar ya karbi coffee da yasa suka ajiye masa. Yayi missing coffee yau duka,wani abu da ba kasafai yake yinsa ba saboda tsananin amincin dake tsakaninsa da coffee din. Har yayi taku uku zuwa bakin qofa,sai ya sake dawowa ya kalleta. Maimakon fita kamar yadda ya tsara,sai kawai yayi kwana yana dawowa inda take kwance. Cikin wani irin taushi ya tsugunna a gabanta,qamshin nan nata daya mamaye dakin ya cakude da nasa qamshin yana bada wani yanayi na daban. Hannunsa ya miqa gareta,sai kuma ya janye. Idan ta farka fa ta ganshi haka dab da ita?,idan ta bude idanunta kuma ta ganshi a gabanta fa?. To amma kuma zai iya fita ya barta haka hannunta a lanqwashe?. Idan yayi hakan zai iya cutar da ita,xata iya tashi da ciwon hannu kuma bayan qafarta. Koma yayi ya zauna sosai,wannan ya kashiginda kan hannunsa daya tamkar yadda uwa keyi idan zata lallaba yaronta yayi bacci ko zata gyara masa kwaciya. Hannunsa ya miqa a hankali yana zare mata hannun,zuciyarsa na bugawa da wani irin sanyi,yana jin kusancin har cikin zuciyarsa. Can cikin hancinta takejin qamshin,can cikin duniyar baccinta takejin qamshin sosai kamar yadda ta saba jinsa a duk wani.mafarki nasa da zatayi. A yau bayan qamshin tana jin wani abu tattare da mafarkin,wani abu da yake mata kama da wanzuwarsa dab da ita. Wani irin sanyi nutsuwa da sukuni takeji sosai tattare da qamshin a yau cikin baccinta fiye da wanda ta saba ji,fuskarsa tsaye a gabanta,da wannan kalar fusatar data faru a dazu bayan ta sauka daga saman dokin ba tare daya tsammaci haka ba,don haka tayi wani kyakkyawan juyi tana yamutsa fuska kadan,tana gyara kwanciyarta sosai muryarta can qasa take fadin. "Kayi dariya mana......kafi kyau idan bakayi fushi ba,hai.....haismmmm". Idanunsa ya lumshe a hankali,wani murmushi da baisan daga inda ya taso masa ba ya subuce masa,wani murmushi da baisan daga inda ya taho ba ya subuce masa,duk da yadda ta danne masa dantsen hannusa ta kuma zagaye hannun nasa da kyau da dukka hannuwanta biyu kamar ta samu kyakkyawan pillow,kamar kuma wadda ta samu abun kamawar da take tsoron faduwa. A hankali ya motsa bayan ya tabbatar tayi relax ta kuma sake komawa baccinta da nufin zaren hannun,saidai tuni ya fahimci ba abu bane me yuwuwa. Ta qanqameshi sosai,idan kuma ya matsanta yace sai ya cire hannun farkawa zatayi,idan kuma ta farka din bashi da kalmar da zai mata bayani da ita kan abinda ya kawoshi gurin har hakan ta faru. Mintuna masu yawa suka shude,idanunsa suna sauka a kanta. Kyakkyawan fuskar da a yau tayi kusa dashi sama dako yaushe,kyakkyawan fuskar da wannan gashin ma'abocin tsahon santsi da silki ya rufe rabinta,saidai hakan bai hanashi ganin tattausan labbanta ba dake tsuke kadan,alamun kodai still tana cikin mafarkinne,ko kuma dai ranta ne ba dadi. "Me ya kawo sunana mafarkin ta?" Ya tambayi kansa da kansa har yanxu yana jin mamaki cikin ransa. Ya lumshe idanunsa sannan ya budesu duka lokaci daya,yana jin yadda wata muguwar kasala ke lullubeshi. Sosai lips dinta ke jan hankalinsa,ya zuba musu idanu yana kuma lumshe idanun nasa a hankali. Kaman ta sani yana kallonta ne.....ta sake motsawa da wani irin yanayi daya sanya qirjinta shafar qaurin hannunsa tana sake qanqame hannun nasa da kyau. "Ya salam" Ya fadi labbansa suna rawa kadan,wani irin zubawa tsigar jikinsa tayi.....wani abu yaji me girma da qarfi ya tsarga masa tun daga saman kansa zuwa kowanne sashe na jikinsa,yadda suka taba hannunsa wani abune da ba wani namiji da zai iya tsallakewa abinda yaji. Suna cikin silk rigar bacci,yadda yajin kuma ya tabbatar babu bra a jikinta. Numfashi ya sauke me matuqar nauyi,yana ji a ransa tabbas yau yana cikin tarko. Don yana iya jin yadda jikinsa ya fara rawa kadan kada. Baida wani sauran mafita,illa kawai kwantar da kansa da yayi sosai a kafadarsa yana ambaton sunan Allah. Kwanciyar kuma ba kuma ta samar masa da sauqi bane,saima qara kusanci da tayi a tsakaninsu. Musayar numfashi suka fara yi a hankali shi da ita,musayar numfashin data sake masa nauyi ainun,iskarsa yaji ta fara canzawa da wata kalar iska dake shigar da saqo kowanne lungu da saqo na jikinsa. Wanda ta fitar shi yake shaqa,wanda ya fitar itama shi take shaqa. Yatsansa ya daga a hankali yana ajewa saman dogon hancinta medan tudu kadan daya qawata fuskarta,sannan kuma a hankali ya janyeshi yana kaiwa saman tausasan lips dinta. Komai nasa ya fara rikicewa,komai nasa ya fara neman fita daga saitinsa. Dumin jikinta.....kusancinsu musayar numfashin dake gauraye da tattausan qamshin jikinta. Ya lumshe idonsa da kyau yana kiran sunan Allah a jejjere can qasan ransa,yana jin yadda yanayin bugun zuciyarsa da fitar numfashinsa suke sauke hargitsewa. "Ya Allah.....not now.....not yet" Ya fadi yana qoqarin controlling kansa. Ya jima idanunsa a rufe,ya jima da zame kansa qasa kadan saboda rage musayar numfashin dake tsakaninsu kafin ya samu ya rage dan wani abu kadan cikin abinda yakeji. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Ya sake bude idanun da suka sauya launi suka kada sukayi jaa yana sake zubesu a kanta. Kamar wani annuri da nishadi ke fita daga kan fuskartata,kaman yanayin yayi mata dadi cikin baccinta sama da kowanne yanayi. Ya sani muddin ya bari sukaci gaba da kasancewa a haka,muddin ya qyaleta cikin jikinsa tayi kyakkyawan matashin kai da hannunsa to komai yana iya faruwa........ya qaryata dukkanin wata jarumatarsa a yanzu.....ya yadda bazai iya ci gaba da mallakar kansa ba........don haka ya tattara dukkan wata jarumatarsa ya zare hannunsa a hankali yana maye mata gurbinsa da pillow. Ko a yanzun sai data turo baki fuskarta tana yamutsewa,kamar dai tasan canjin pillow yayi mata daga hannunsa xuwa pillow din fiber. Kamar dai tana qorafi akan wancan yanayin yafi mata dadi,sai ya miqe a hankali yana jinsa kamar iska zata daukeshi,still idanunsa a kanta. Matsawa yayi daya side din,ya dauki lallausan duvet din ya lullubata a hankali ganin yadda ta qanqame pillow din,yayi tsaye saman kanta yana kallon fuskarta. Wato ba qaramin kariya da ni'ima Allah yayi masa ba daya sanyashi ya zamana cikin masu kame kansu,ba qaramin taimakonsa Allah yayi ba daya sanyashi cikin masu bin umarninsa na RUNTSE GANINSU......ya sani inda ace ya shigo a sahun 'yan duniya......inda ace ya shigo a sahun mutane banza ba qaramin b'arna zaiyiwa yaran mutane ba. "Alhamdulillah" Ya fada yana shafa qirjinsa da tafin hannunsa har zuwa saman cikinsa. Har ya juya sai yaji kamar kada ya fita kuma,amma yanason ya qarasa karya wannan feelings din da yakeji a jikinsa. Yana son yayi nisa da abinda yakeji.....uwa uba kuma bayason yaqi fita ya bawa su omar daman sakashi a gaba. Ya lura.....dama ya lura da kallon da suketa masa tunda aka warewa kowa tent dinsa,nasa tent din ya zamana daya da Akhnan din. Sam bai shiga ba ko sau daya,baima bata daman da zata gane a tent daya zasu zauna ba.....amman ko dazun da yace zaije ya watsa ruwa yana kallon yadda idanunsa da fuskokinsu ke cike da gulma. "Ku ajjiyemin nawa coffee din" Ya fadi da yaren oromo sanda yake takawa zai fice. "Anya kuwa?,kaidai kawai idan ka dawo shikenan.....idan baka dawo bama shikenan.....bazai kayi alaye ba" Omar ya fada yana wani mazewa. Harara kawai ya jefawa omar din sannan ya fice,yana jinsa kuma yana masa dariya qasa qasa,to tabbas idan bai fita ba yanzun ya bawa omar dasu khadeema abun fadin da zasu addabeshi dashi gobe. Tunda yaga shigar haisam din hankalinsa yake a tashe,wani irin gumi yake yana lissafa lokacin fitowarsa. A iya saninsa bata zama tasa ba ta hanyar damqa masa ita officially bare su fara kwana tare guri daya,amma yanayin dadewarsa yanzu a ciki ya fara saka masa shakkar anya ba kwana zaiyi ba?. Fitowarsa ta sauke masa wani gingimemen abu me nauyi daga saman zuciyarsa,ya sauke ajiyar zuciya yana share gumin fuskarsa. Gwara kawai yayi me yiwuwa a yanzu,don a yanzunne kawai zai samu bugar da ita ta kwanciyar hankali tunda bacci take,xai masa sauqin tafiya da ita kuma. Haka kawai yaji ya kamata a qara haske gurin,yana takawa zuwa gurinsu omar yana fidda wayarsa,ya kuma kira daya daga cikin security na gurin ya bada wannan umarnin yana isa bakin tent din su omar din. Taku uku yayi haske ya gilma a gurin,taku uku yayi haske ya ninka na dazun,wani irin haske da yasa gabansa faduwa,wani irin haske daya haska can nesa da inda sansanin yake bama sansanin kansa ba, "Akwai matsala tamim ka gaggauta" Abinda zuciyarsa ta gaya masa kenan,don haka da sassarfa a dudduqe ya durfafi tent din. Tsaiwa yayi kamar wani sakarai yana dubanta yana sakin qaramar dariya sanda ya hangeta nade cikin duvet din. Duk wata tsohuwar qwalamarsa dama sabuwar zalamarsa yaji sun motsa gaba daya. Burinsa da karsashinsa ya qaru sanda zuciyarsa ke gaya masa,wanna halittar dake kwance tana zuba qamshi dab take da zama mallakinsa......wannan halittar dake kwance awanni kadan suka rage masa ya mallaketa dama komai daya shafeta. Sai yaci gaba da takawa cikin zafin nama kamar wani mahaukacin kare,har zuwa sanda ya isa gaban gadon. Har zai fara hura mata abinda ya ruqo saboda gusar mata da hankali sai kuma ya fasa. Ko yaya yanason ya fara kallonta sosai don ya sake samun karsashi da qwarin jiki,don haka ya saka hannu ya fara zame qaton duvet din da haisam ya rufeta kafin ya fita Daidai lokacin da haisam din ya saka hannu don bude labulen tent din.....daidai lokacin yaji zuciyarsa tayi wani mummuna dokawa......wani irin bugu da yasa yaji kamar zuciyar tasa tana shirin tsinkewa ne daga qirjinsa. "Hasbiyallahu la'ilaha illa huw,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ya fada yana lumshe idanunsa cikin tsananin mamakin nau'in faduwar gaba da mummunan bugun zuciyar da yakeji lokaci daya. Sanyin da taji ya fara ratsata,da yadda takejin wani abu yana zamewa daga jikinta shine abinda ya sanya ta bude idanunta a hankali. "Gimbiya" Taji an kira sunanta da muryar rada saidai kuma sam muryar bame dadi bace. "Gimbiya Akhnan" Taji an sake maimaitawa da muryar da bata da dadin amo. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 136* Wani irin tsoro ya kamata,tayi wani irin juyi ta miqe tana zama,saidai kuma da wani irin zafin nama ta kama duvet din dake barin jikinta ta qanqameshi zuwa qirjinta. Dukkanin idanunta ta fiddo waje da wani irin mahaukacin mamaki. TAMIM take gani zaune gefan gadonta......tamim wannan dadadden amintaccen bawan gidan nasu?. Duk yadda zuciyarta taso kawo mata uzuri a kansa a sannan amma taqi karba,abu daya tafijin zata aminta dashi shine. "Me kakeyi a nan tamim?.....kasan girman laifin dake tattare da qetare iyakokin iyalin sultane?,a cikin dakin da nake bacci,?har kana saka hannunka kana janye abun lullubata tamim?,a hayyacinka kake?" Dariya ya saki wadda bame qarfi ba. "Wallahi bana cikin hayyacina......saboda tun kina shekara bakwai a duniya nake kwana da sha'awarki nake tashi......karamcin mahaifinki yasa bazan iya keta miki haddi ba......ko a yanzunma sai idan ke kika zabi hakan.......na sani,ba zaki bini mu tafi salin alin ba,saboda nasan girman taurin kanki da kafiyarki.......zan tilasta miki mu tafi tare saboda na samu nasarar mallakarki ta hanyar aure,shine kawai halaccin da zanwa sultane daga tarin karamcinsa......amma inda ace ke din diyar MAMMINA CE da ba shakka a nan zan kaca kaca dake nabar mata jinyarki........wannan kuma kadai bazai isa na rama abinda tayimim ba.....zan dan huce ne kadan kafin na sake waiwayarta.......ki tashi mu tafi" Ya fadi yana zaro kakkaifar wuqarsa,ya kuma yage bangon tent din ya zube gefe daya,abinda ya sanya take iya hango duhuwar cikin sahara me nisan gaske daga inda take. Wani irin tsoro da firgitar da bata taba shiga irinta ba ta saukar mata. Ba kowa a bayan tent dinsu tabbas ta gani tunda rana.....amma a lokacin akwai tarin guards da security,saidai a yanzu bataga kowa ba.....wanne irin kaifi takobinsa ke dashi haka?,ta tsaga tent din cikin sauqi ba tare da qara ba. Tabbas zargin farko na amfani da sihiri da aka taba yiwa tamim shekarun baya can mammina ta wankeshi a yau cikin wannan rudadden yanayin ta aminta da haka. "Tashi mu tafi gimbiya" Tamim ya fadi yana mata murmushi,murmushin da yayi mata kama sak da hammar kare. Kai ta gara girgizawa tana sake tamke duvet din da taga yana sake kamowa da nufin zameshi,zameshin kuma da yake daidai da ganin surar jikinta ta kayan baccin da suke jikinta,duk da cewa masu kauri ne. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya qara fada yana jin kansa ya wani sara masa kamar an lafta masa itace. "Man.....yadai?.....ka qaraso" Muryar omar ta sauka a kunnuwansa. Saidai bayan kallon omar da yayi baice komai ba,sai ya samu kansa ya sake bude wayarsa da wani irin sauri yana jin yadda zuciyarsa keci gaba da bugawa a jajjere kamar zata tarwatse. Red light daya gani a sashen security na tent din Akhnan ya sanya yaji hannuwansa sun fara rawa. "Me yasa baka da juriya akan komai daya shafeta?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar duk da rudanin daya samu kansa a ciki. Haka kawai yaji tsaiwa duba na'urar ma akwai bata lokacine. Kai tsaye ya soma takawa zuwa ga tent din,saidai bawai kai tsaye irin na wanda baisan kan tsaro ba.....ba kai tsaye irin na ordinary mutane ba. Tun daga nesa idanunsa suna kan tent din,ba wani alamun rikici ko hargitsi ko hayaniya daga qofar da dukkanin idanu suke iya kalla. Ji yakeyi kamar na tunzurashi.....ji yakeyi kamar ana jansa zuwa cikin tent din,amma wannan kalmar.....wannan kalmar daya dade yana horas da na qasa dashi cikin aikinsu ta taso ga danneshi *"WANDA YASAN YAQI.....BAYA SHIGA TA QOFAR DA YASAN ANA JIRA"* Wannan wata babbar magana ce cikin aikinsu.....wata babbar qofar nasara ce ga aikinsu. Abu daya kacal ya danna a wayarsa duk wai security dake gurin ya koma bakin iyakarsa da shirin kota kwana. Cikin qasa da minti daya gurin ya zama kewaye dasu da wani yanayin da ba lallai yasan gurin ya samu tsaro da kewayewarsu ba. Sawu ya fara dubawa......yana daya daga cikin dalilin da ba wanda ya sanshi saishi. Shi ya sanya aka yiwa dukkan wani wanda zai aikin bada tsaro a gurin takalminsa na daban......sawu yana daya daga cikin abu me amfani a aikinsu. Kuma ko a yanzun ya gane,ya iya tsame sawayen security din duk da suka wuce,saidai kafcecen sawu guda daya daya gani ya sake harba wani abu a zuciyarsa. Kama me laifi a guri irin wannan dake da tent ba gine gine ba,abune da yake buqatar qwarewa. Motsi ko gilmawarka tana iya bada inuwa da haske ga wanda ke giftaku ta waje,don haka yayi plate a gurin,da wani salon tafiya kamar me ninqaya ya soma zagayawa zuwa bayan tent din. "Da alama kinaso kisha wahala" Ya fada yana sakin duvet din,sannan ya fara ware tsummar hannunsa. Cikin wani dan qaramin hanyoyin kariya da aka koya musu kasancewar yana daya daga cikin abinda jinin sarauta ya kamata ya iya cikin masarautu irin nasu ta dauke numfashinta sanda yake karkade tsumman hannun nasa cikin mugunta yana dariya,kafin ya cillar da tsummar yana haurawa saman gadon da wani irin kuxari yana jin cewa lokaci yayi da zai dauketa su wuce. Muguwar razanar da tayi ganin yana haurowa ya sanyata bude bakinta da nufin qwalla qara.....wannan abun yayi sanadin shaqar kadan daga cikin qurar hodar daya badeta da gurin don gusar da hankalinta. Yadda yaga bayan tent din a fafaye a qasa tamkar an zubda tabarma ya sakashi mqewa cikin zafin nama. Baisan yadda akayi yakai kansa cikin tent din ba.....bai sani ba da qafa ne?,ko saman iska ne duka bazai tantance ba.......saidai kuma abinda ya gani ya zane masa wani abu mafi munin kallo a rayuwarsa gaba daya. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) Tamim baqe baqe saman gadon da yabar Akhnan tana bacci cikin kwanciyar hankali?. Bai gane komai a sannan......baya fahimtar komai a lokacin......lokacin da tamim hankalinsa ya karkata kan yadda xai jawo Akhnan daga saman gado zuwa qasa donsu fice daga tent din.....daidai lokacin yaji wata azaba tana ratsa tsintsiyar hannunsa,azabar data sanyashi buga wani irin gigitaccen ihu kafin ya kalli hannunsa dake lilo jikin tsoka da fatar jikinsa,saidai ko wanda ya aikata masa hakan bai samu daman daga kansa zuwa gareshi ba yaji an fincikoshi zuwa qasa an watsar duk da irin girma jiki nauyi da qarfinsa,kansa ya bugu da gefan qarfen tent din guda daya,ya runtse idanunsa yana jin wata sabuwar azabar. A hautsine ya haura saman gadon yana yayubo dukka duvet din,duk da nauyinsa.....duk da girmansa da fadinsa turashi yake kawai a jikin Akhnan din yana lullube jikinta kanta dake a bude iskar data samu cikakkiyar hanyar shigowa tana kada gashin nata. Zuciyarsa ke wani irin bugu kamar ta shirya tarwatsewa tayi pieces a qirjinsa,baya gane komai sai yadda zai suturce duk wani abu tattare da ita da idanu ke iya gani,cikin wani rudewa da rawar jiki,duvet din yana zamewa saboda yayi kauri da yawa amma yana sake tattareshi a jikinta. "Bai miki komai ba.......bai miki komai ba?" Ya samu kansa da maimaitawa. Idanunta a kansa.......duk da nata kalar tashin hankalin da takeji sai taga salaama ne.....duk da rudewar da takeji da yadda taji numfashinta ya fara mata nauyi a qirjinta sai take ganin kamar cikin aminci take akan abinda take iya hanga daga qwayar idanunsa. Sanda ya bude idanunsa......sanda ya sauke idanunsa akan haisam daya samu nasarar lulluba mata babban mayafi sai yaji ALQIYAMARSA TA TSAYA.......sai yake hangen wata irin jar wuta tana fita daga fuskarsa dama motsinsa gaba daya. "Ko bazaka tsira ba.....ka gwada guduwa" Zuciyarsa ta raya masa,saiya miqe da hanzari saidai rudewar da yayi tasa ya manta da ragargajajjen hannunsa yayi nufin dafa qasa dashi. Azabar da yaji ya sakashi sakin wani nishin yana danne ihun daya taso masa. Yadda yaga hankalinsa ya raja'a a kanta,ya sani yana sakin ihu zai tuna dashi dake yashe a wajen wannan dalilin ya sakashi danne ihunsa,ya miqe ya soma takawa da wani irin gudu ta inda ya yage tent din,zuciyarsa tana yaudararsa da cewa tabbas yana haurawa nan ya tsira. Yadda jikinta yayi week ya sanya ta aza kanta samam kafadarsa,tanason gaya masa ne numfashinta yana riqewa......tanason gaya masa tana jin kamar numfashinta zai kubce mata amma ta kasa bude bakinta. Sosai ya riqeta cikin jikinsa yana zube idanunsa akan tamim dake kwasar gudu iya qarfinsa. Da hannunsa yakeson ya kamashi......da hannunsa yakeson ya damqeshi,.....kamar yadda da kansa yakeson duk wani abu da tamim ya kamata ya fuskanta ya zamana shi ya zaba masa. Sakinta yayi a hankali a hannun birra data dimauce,birran da ita kadai ta shigo tent din ita shehnaz da aisa,kowa yana daga wajen tent din saboda bin qa'ida da kiyaye haddi. A rungume take a jikin aisa da shehnaz......saidai kuma duk yadda idanunta sukaso su lumshe su rufe kansu da kansu ta hanasu yin hakan. Shi take hange daga inda take kwance,kai tsaye shi kadai idanunta suke hange. Wani irin gudu yake kamar mayunwacin zaki......wani irin gudu yake cikin yashi duk da wahalar da hakan yake dashi ga dabbobo ababen hawa ballantana kuma dan adam......yana kuma dakatar da duk wanda yayi yunqurin biyoshi,har zuwa sanda ya saka hannu ya damqo tamim yana warwaro dashi da hannu daya daga tudun yashin da yahau,sannan ya jashi kamar kayan wanki yana adanashi zuwa duhuwar bayan yashin. *_SHUD'EWAR MINTUNA BIYAR_* "Ku adanashi beeno.....a raye nake nufi" Haisam ya fadi yana tsallake tamim da ya yiwa wani d'aurin butar malam,hanyar fitar numfashinsa kawai yabar masa,shima saboda da gaske yana buqatar tamim din a raye kaman yadda yace. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal* *Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank* *KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN* 09166221261 KO 08187255862 *Al'ummar qasar nijer 🇳🇪* *2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000* *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI* 09166221261 *GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE* *MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261 *SHAIDAR BIYA* 09166221261 *_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_* *QASAITA👑* *HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 137* ★Gaba daya qwayar idanunta tana cikin nasa......kamar yadda nashi qwayar idanun dama fuskarsa suke dab da tata fuskar. Yanayi ne da takejin ya kamata ta damu da wani abu daban.......yanayi ne da takejin ya kamata ta ace wani tsoro.....firgici da rudani ne yake mamaye da ita.......amma dukka sabanin wannan takeji a tattare da ita. Idanunsa kawai take kalla.....fuskarsa kawa take iya gani wadda inches kadanne suka rabata da tata fuskar. Tana iya gane wasu abubuwa......amma abubuwan dashi kadai suka shafa. Numfashinta yana barazanar dauke mata.....bata iya gane ko tantance komai........bata kuma iyajin sautin komai......amma tana iya jin nasa sautin......tana iya jin sautin muryarsa,tana kuma iya jin tattausan tafin hannunsa da yake cikin nata. Cikin harshen French yake mata magana.....cikin wannan yanayin karya harshen.....wannan accent din da tafison ji sama da sauran sautika tun wandancan satittikan. Tana iya jin dumin daya tafin hannun nasa dake kwance gefan fuskarta yana shafawa a hankali daga sama zuwa qasa,tana kuma iya ganin zallar tashin hankali saman fuskarsa. Fes take hangen yadda launin fuskarsa ya sauya,har wani jajajaja take......tana iya ganin kuma zallar madarar fushi dake yawo tsakanin idanuwansa guda biyu. "Kija numfashi......karkiji tsoro......ina tare dake......ba abinda zai cutar dake......ba wanda ya isa ya sake cutar dake.....kijia numfashi......ja numfashi akhnaaann.......a hankali......kija saiki saukeshi ki sake jan wani......zaki iya,.......zaki iya......zaki iyaaaa" Ya fada yana matsa hannunta dake cikin nasa. Wani qaimi maganganunsa suka bata,wani tabbaci maganganunsa suka bata,ta fusgi numfashin da wani irin qarfi ta sauke. "Eheeen......sake ja.....sake maimaitawa" Ya fadi da confidence yana sake matsawa sosai dab da ita kamar yana bata support da nashi numfashin da kuma bugun zuciyarsa ta hanyar matso da hannunta cikin qirjinsa yana sake sarqafe yatsunsu. Sake maimaitawa tayi yana kuma cewa ta sake. Sannu a hankali numfashin nata ya fara daidaita,abinda ya saukar da relief cikin zuciyar morsa safiyya sultane,nannie shehnaz aisa birra dama sultane dake tsaye a gurin cikin babban bedroom din haisam din dake bangarensa cikin masarautar agadez din. "Kawomin ruwa kadan" Haisam din yace da birra cikin bada umarni,still hannunsa dama idonsa suna kan Akhnan din. A gaggauce birra ta kawo,yakai cup din bakinsa ya tofa gajeriyar addu'a sannan ya saka mata a bakinta bayan ya tallafota. Kadan ya bata tasha ya janye,ya saka mata pillow yadda zai dago mata kanta sosai,ya sake jan kujerar gaban gadon sosai kaman zai haura yana duban yadda numfashinta ke sama da qasa. "Astagfirullahal azeem.....astagfirullahal azeem" Ya fara maimaitawa can qasa da wani irin softness sosai cikin muryarsa. Lumshe ido tayi tana jin wani hawaye yana taruwa a idanunta. Wani irin abu me girma da tasiri take hanga cikin idanunsa......abunda yafi girma da nauyi a zuciyarta sama da abinda ya sameta.....domin kuwa tayi imani da yaqinin Allah bazai taba bawa tamim ikon keta mata haddi ba. Istigfar din da yakeyi dab da kunnuwanta shike saukar mata da nutsuwa. A hankali taji ta soma motsa labbanta,a hankali taji ta fara maimaitawa itama. Wani hawaye ne ya cika idanun sultane harma da morsa safiyya,wani yanayi sukeji su kansu me saukar da nutsuwa. Zuciyar sultane din ta karye sosai.......tabbas akwai wata nutsuwa da hangen nesa ga ma'abota addini,sai ya daga hannu yana yiwa kowa da kowa alamun ya fice ciki kuwa harda shi. "Alhamdulillah......na gode,na gode da baki gaza ba.....na gode da bakiyi qasa a gwiwa ba,na gode da kika dage sai an jona rayuwar Akhnan da mijin da zai ma rayuwarta jagora duniya da lahira" Sultane yace da morsa sanda suke komawa sassansa yana damqe hannunta cikin nasa. Hawaye ne ya sauko zuwa saman fuskar momma,tayi qasa da kanta tana duban sultane. "Tsoro nakeji bappi.....me yasa tamim ya aikata haka?....tsoro nakeji kada ya sake dawowa ya sake cutar da ita,tunda ba tabbacin an kamashi". Murmushi ya sake me sanyi.....wani kalar murmushi dake nuna tsantsar kwanciyar hankalinsa. " Be fada bane......kuma nasan bazai fadawa kowa ba......amma tabbas tamim yana hannunsa. Yadda be fada ba bazan nuna masa na gane na,bazan kuma matsa da tambayar ina ya kaishi ba?,ko kuma wanne hukunci zai masa ba.....abu daya zanyi......zan tabbatar sati be zagayo ya samesu a agadez ba......ya dauki matarsa sudan matsa daga nan.......idan sun tashi dawowa ina fatan ganin kusancin da yafi wannan.....na godewa Allah.....ko a yanzu na fadi na mutu zan kwanta a kabarina cikin salama......nasan inda nakai diyar safeena". Karyewa zuciyar morsa tayi,saita samu kanta da shigewa jikin sultane din tana hawaye sosai. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Ka daina fada......bakai ba safeena ba KHADEEJA......me zan zauna kenan nayi a duniya" Murmushi ya saki yana riqe hannunta sosai a nashi. "Wataqila ke zaki riqe jikokina....ke kadai zaki dauki jikokin safeena da hannunki" Kuka ne me nauyi ya balle mata,kukan da daga qarshe sultane ya fahimci daga zuciyarta yake,kuma da gaske ya taba zuciyarta da abinda ya fada din,tilas yaja hannunta ciki yana qoqarin lallashi. *M A M M I N A* Idan akace jikin mutum yana rawa kamar mazari a baya daukan abun takeyi da wasa. Saboda abu daya ta sani,rawar mazari da ba abu bane na wasa da jikin dan adam zai iya yinsa,amma kuma a yau ta tabbatar bisa yaqini da abinda taji nata jikin yanayi da gaske har sama da haka dan adam zai iyayi idan tashin hankali ya girmama. Sanda ta miqe daga labarin da daya daga cikin hadimanta suka bata na abinda ya faru a gurin festival jiya......jiyan data zo mata da wani asararren bacci da batasan me yasa ta yishi ba.....baccin daba wanda ya tadata sai bayan sallar asuba data tashi da kanta. Ba farmakar Akhnan bane damuwarta ba......ba yadda aka ceto Akhnan din da qyar ne damuwarta ba......damuwarta shine B'ATAN TAMIM. Tana ji a jikinta ba guduwa tamim yayi ba kamar yadda kowa yake fada......tana jin cewa qirqirarren labari ne wannan......an shirya a fadi hakanne saboda akwai wani birnannen abu a qasa. "Idan tamim ya bata......idan ba'a gama tamim ba ya tabbata daukeshi akayi kaman yadda aka dauke almaz.......ya tabbata wanda ya dauke almaz shine ya dauke tamim......inde kuma wanda ya dauke tamim shine wanda ya dauke almaz tabbas ba kowa bane wannan sai sheikh muhammad haisam!!!" Mammina ta furta a sarari dukkanin muryarta da jikinta suna rawa. Qasa tafisu tayi da kanta,cikin nuna salo na girmamawa. "Ranki ya dade......karki jefa zargi a inda zai iya jawo miki matsala......nutsuwa itace jigon komai.....ki nutsu tukunna". "Bazan iya ba tafisu.....bazan boye miki ba.......a yanzu na fara jin tsoro......ya kamata na fara kammale jama'ata da dukkan wanda yasan sirrin ciki na........ina yalwa?" Qasa tafisu ta sakeyi da kanta,tana jin da wanne irin yare zata gayawa mammina?. Saidai tasan dole ta gaya mata,don nan bada jimawa ba zata sake neman yalwa din. "Yalwa......ba'aga yalwa ba tun daren jiya". Maganar ta sauka saman kan mammina,ta kuma tilasta mata durqushewa tana zama dirshan a gurin. "Ba'a ganta ba?,taje wani gurin ko itama ta bace?" "Zargin dauketan yafi qarfi ranki ya dade.....don har gidanta nasa an duba don tazo ta kula dake jiya da naga kinyi nauyin bacci,amma har yanzu ba wanda ya bani tabbacin inda take" "Innalillahi....innalillahi" Mammina ta fada tana dafe kanta. "Kan dai?" Tafisu ta daga kanta a hargitse tana tambayar mammina. "Shine tafisu.....maganina". Da sassarfa ta saketa ta kuma juya zuwa inda tasan an zube magungunan. ★Da wani irin naiyun qirji yake takowa zuwa sassan Akhnan din,da wani irin yanayi da duk wanda ya kalli fuskarsa yasan ba yanayinsa bane. Baida yawan fara'a,baida yawan sake fuska,amma kuma wannan hasken......wannan haibar tasa ya sanya zakaga fuskarsa da wani annuri koda yaushe. Cikin girmamawa dukkan hadiman ke gaidashi.....cikin wani qarin girma da karamci bisa yadda labarin kariyar daya bawa diyar shugabansu mafi soyuwa a zukatansu kariya. Har zuwa sanda ya isa qofar da zata sadashi da living room din da birra tace masa suna ciki. Da nutsatsiyar sallama ya tura qofar dakin ya shiga,sallamar da taja hankalinta momma dake zaune tana shafa mata man zafi a qafarta,yanayin daya sanya Akhnan ta dinga satar kallonta. Sallamar da still ta fusgi zuciya da hankalin Akhnan din wadda ke riqe da bowl tana shan farfesu a hankali. A jiyan ta sani....har sanda bacci ya dauketa yana zaune a gabanta. Har sanda bacci ya dauketa hannunsa da Jikinsa yana manne da nata,abinda ya bata wani irin peace da bata taba sanin akwaishi ba a rayuwarta. Abubuwan dake faruwa da ita wadanda basu kai girma da hatsarin wannan ba sunsha gigitata,to amma batasan me yasa ba.....wannan din yakai girman da zata gigice.....amma wani peace take samu a ranta. Me yasa?,SHINE SILA.....SANADINSA NE. abinda zuciyarta ke gaya mata kenan. Sanda ta farka momma ta samu ta maye gurbinsa,ita ta kwana da ita.....ita ta zauna a gabanta,ta kwana a gabanta idanunta biyu. Taga zahirin maganar nan da ake cewa yadda naga rana haka naga dare......tsakanin momma da haisam din dukkaninsu tana iya ganin yadda suka raba daren a tsakaninsu suka raba baccinsu. Ko qarfe uku da rabi na dare ta jishi ya sake shigowa,ta jishi yana tambayar momma game da ita,saidai daga wannan lokacin bata sake ganinsa ba sai yanzu. Da wani irin qauna da girma momma ta sauke man tana rufeshi,fuskarta fal da murmushi tana gyara zamanta,irin yadda kowacce uwa keji a sanda surukinta yake gurin. "Sannu muhammad......sannu da qoqari" Momma ta amsa masa sanda yake gaidata da wani irin girma da martabawa. Ko meye zai mata yana jin kamar ya yiwa nanay dinsa ne. Kowacce girmamawa yana jin kamar ya girmama nanay dinsa ne,ya cancanci kalar kowanne girmamawa. Miqewa tsam momma tayi,saidai ya dakatar da ita ta hanyar fadin. "Ba jimawa zanyi ba......akwai inda zanje,wataqila na kwana biyu" Maganan ya tsaida momma. Tana jin meye dalilin da ya gaya mata zaije wani guri?,bata da hurumin tambayarsa......amma a ranta tana jin kamar ba lokacin da zaice zaije wani guri bane. Tafiyarsu duka duka ba zata haura kwana hudu ba,don sultane ya kammala shirin komai,to amma kuma hakan sai takejin kamar wata qarin dama ne da zata qarasa shirya Akhnan din. "Allah ya bada sa'a.....yayi jagora yayi riqo da hannaye" Kai ya gyada a hankali,zuciyarsa tana masa nauyi. Tausayinsu ne dukka yake kamashi......ita nanay dinsa.....na Akhnan me sauqi ne don yana jin a yanzu a wannan lokacin,a kuma wannan qadamin ko mummunan quda baida ikon qarasowa gurinta,baida ikon sauka a jikinta ballantana wani dan adam. Sultane mutum ne na gaske.....me nuna qauna ta gaske.....ya cancani komai don kare gudan jininsa. SAFEENA wani ruhi ne da kadan Allah ya halitta a jikin mutane......dattakonta da sadaukarwarta da tata kalar qaunar ta gaske ta cancanci KARIYA da KAARA. Shuru ya wanzu a dakin sanda momma ta fita zuwa daya parlor din,ta zabi ta basu guri ne saboda tana ganin abinda ya dace kenan. Idanunsa kar a kanta,ba abinda yake dawomasa a duk sanda zai kalleta sai abinda ya faru. Har yanzu yanajin wani abu daya dunqule masa tsakanin wuyansa da qirjinsa me d'aci "TAMIM FA?" Abinda yaketa maimaitawa kenan cikin ransa,saidai mamakinsa ya sassuta ya juye zuwa tsananin fushi a sanda omar ya fara turo masa wasu bayanai. Ya kasa haquri omar din,ya kasa jurewa kaman yadda haisam ya buqata,bayanan kawai da haisam din ya gani daga omar ya sani.......za'a samu ninkinsu daga gurin tamim....muma qila sune cikamakin bayanan da yake jiran samu,don haka ya yanke kawo qarshen komai a kwana biyu kacal. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎 *H U G U M A* *BOOK 02///PAGE 138* Tazara ce sosai a tsakaninsu,amma tana jinsa ne tamkar kusa da ita.......yana ci gaba da kallonta shima yana ganin wani irin sanyi a tattare da ita. Kwana daya kacal amma kuma fuskarta ta nuna wata irin rama ta fitar hankali a tattare da ita. Ya motsa bakinsa zai magana,na'ura ta nuna masa kira daga abeer. Abeer din yaketa jira.......jiran Aberdeen yafi zame masa wani mafi munin jira daya zauna yana lissafa wucewar kowanne second da mintuna da suka shude tsakani awanni sha biyun nan. Ta qasan ido take satar kallonsa sanda ya danna wani button jikin agogon dake daure a hannunsa. Wani irin sassanyan kwarjini fuskarsa yake fitarwa,wani irin yanayi daya cakuda da daurewa da miskilancin da a yau ta fara ganinsa qarara tattare dashi. Fuskarsa a daren jiya......yanayin daya shiga wanda batajin akwai d'a namijin data taba ganin haka tattare dashi saboda ita. "Sun kammala obbo......an gamasu gaba daya". "Ma sha Allah.....on my way" Ya furta yana jin wani abu guda daya ya saki daga abubuwan dake danne da zuciyarsa. Idanunta ta lumshe a hankali,tana jin wani abu me kama da BURGEWA yana sauka saman zuciyarta. Yadda yayi maganar da wani irin nutsuwa da maturity sai takejin kaman a yau ne ta fara ganinsa yana magana. Kujerar da momma ta tashi ya qarasa,ya zauna akai yana sake janta gaba kadan idanunsa a kanta. Ta motsa labbanta tana sarrafa tunaninta,zata gaidashi ne yadda take gaida sultane?,ko zataci gaba da shuru?,. Kamar ya karanci haka daga gareta saiya hutar da ita ta hanyar fadin. "Kin tashi lafiya?,ya jikin naki?" "Alhamdulillah" Ta samu kanta da fada tana danyin qasa da kanta. Kai ya jinjina,shuru yana sake ratsawa a tsakaninsu,kafin ya sake magana yana miqewa. "Koda wani abu zai taso......ban aminta ki dorawa sultane nauyin komai ba.....kisa a kira miki abdii,yawan saurare da karanta qur'ani ya sanyawa zuciya nutsuwa,kiran sunan Allah da tunashi" Yayi maganan yana dosar qofar fita, Samun kanta tayi da binsa da kallo,tana jin kamar tace masa ya dakata,tana jin kamar tace masa INA ZAKA?,tanajin kamar ta tsaidashi tayi masa tambayoyi masu yawa......amma tana jin wani nauyin hakan. "Na gode" Bakinta ya subuce ta furta a hankali. Maganan ya bashi mamakin da yaji saukarsa har saman tsakiyar kansa,amma kuma bai juyo ba bai kuma tsaya ba,yadai amsa mata a taqaice da. "Haqqina ne" Kawai yana qarasa ficewa,saitaja iska qamshin nan nasa yana ratsa kowacce kafa ta kwanyarta da zuciyarta yana hudawa da wani abu me sanyi. ★Ba zuciyarsa kadai ba.....hatta da gangar jikinsa sun qagauta su isa gidan,wannan dalilin ya sanya yau shi da kansa......prince muhammad haisam aba jifar ke driving motar da kansa,salaana yana zaune a gefe yana jin shugaban nasa kamar ya aza masa wani irin nauyi da tuqashi da yakeyi shi kuma yana zaune cikin motar. Wani irin gudu yakeyi sosai daya basu daman isa gidan a qasa da awa daya,maimakon awa daya harda wasu mintina daya kamata su dauka a baya. Sanda suke gifta gidan idanunshi akan tsarin tsaro da aka bawa gidan. Villa street data zama qarin wani matattarar sirri ga zeenatun zaitunaa. Gidan da a yau yakejin muddin bai sanya qafarsa a cikinsa yayi bajakolin komai dake cikinsa ba shi ba jinin aba jifar bane. Ya dauke idanunsa daga kai yana qarawa motar gudu. Sanda idanunsa suka sauka akan tamim da ya wani kumbure sama da ainihin halittarsa sai yaji jininsa yana tafasa. Ya dauke idanunsa daga kansa yana bulla qaramin garden din dake manne da dakin da tamim din yake yashe. Omar......beeno salawii dama sauran duka manyan team dinsa na agadez ya samu zaune a gurin. Duk da kana ganinsu kasan kowa jininsa akan farce yake......amma hakan bai hanasu shan coffee ba,don ga cups da trays din duka a gurin. Shigowarsa ya sanya kowannensu miqewa......hatta da omar idan aka shiga irin wannan yanayin zare alaqar abota yake dake tsakaninsu. Yana jin haisam a matsayin OGANsa bawai aboki kuma amini ba. Miqewa ce ta grimamawa......miqewa ce ta mutuntawa,dukansu sai yabisu daya bayan daya suna musabaha gami da tambayar kowa lafiyarsa cikin yaren oromo. "Ku zauna" Ya fada yana miqa hannunsa ya kuma karbi takardun dake liqe da wani takarda me qarfi daga hannun abeer. Bai iya minti biyu a tsaye ba ya koma ya zauna......ya koma ya zauna yana qara kallon takardun......ya koma ya zauna yana qara ganin girma istigafari da kiran ismullahil A'azam din daya dinga yi a sanda yake ganawa da mutanen da online direct video call. Dukkanin takardun zaitunaa ne......dukkanin wani takarda da mammina ke taqama dashi......dukkan wata power da take ganin ta mallaka......power din data dauketa ta dauke asalinta da komai daya shafeta daga ETHIOPIA ya maidata NIGER. A yau komai nata ya canza......a yau gaskiyar asalinta ta canza a dukkan wata ma'aikata......dukkan wata hukumar shige da fice......a yau daga yanzu ba wani abu.....ba wata hujja data ragewa mammina da zatayi riqo da ita kota nunawa duniya da sunan ita din JININ QASAR NIGER CE. da kanta......da kanta zai sanyata ta gayawa duniya ITA MAQARYACIYA CE... Da kanta zai sanyata ta gayawa duniya TA HA'INCI AL'UMMAR NIGER ta musu cushe da qarfa qarfar shigo musu qasa,tare da mallakawa kanta shaidar zama tasu bayan ba haka bane. Idanunsa ya lumshe yana gyada kai.......ko a iya nan nasararsa ta tsaya yana maraba.....ballantana komai ya gama hawa kan saitin da yakeso. (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862) "Waye zai iya?" Yayi tambayar a taqaice yana duban fuskokinsu. "Zanyi obbo" Dukkaninsu sukayi maganar a kusan tare. Duk da bayajin wani yanayi na dariya ko murmushi,duk da bayajin wani yanayi na nishadi sam a tattare dashi,amma hakan da sukayi sai daya sanya murmushi me sanyi qwace masa. Wannan murmushin nasa da dukkaninsu yake burgesu,wannan murmushin nasa dake cike da kamewa da maturity. Ya tambayesu ne bawai don yana shakka ko kokwanto ba,ya tambaya ne saboda yasan dukkaninsu zasu ce zauyi. "A zabi mutum daya.....na bude wata sirrintacciyar hanya.....sirrintacciyar hanya takai tsaye zuwa dakin ajiyar mammina. Takardunta nake buqata gaba daya,sannan a maue gurbinsu da wadannan" Ya fada yana daga takardun dake hannunsa. "Ni zan saka obbo....don Allah" Salawi ya fada yana riqe takardun da sauri. Ido ya bisu dashi,ba wanda yayi challenge nasa,abinda yake gaya masa sun barwa salawi din. Ya dasa wannan a zukatansu,ya koya musu yadda zasu so junasu,ya koya musu fifita buqatar dan uwansu akan tasa buqatar......a yanzun shi kansa yana cin moriyar hakan. "Ya sake cewa wani abu?". Ya kuma tambaya bayan shuru ya ratsa gurin " Ya bayyana komai" Omar daya qagu ya gayawa haisam wannan amsar ya amsa masa. Idanu ya zubawa omar yana dubansa. "Da sauri haka?,garin yaya?" "Waccan hanyar yabi" Beeno ya amsawa haisam,maganan data sanya haisam juyawa ga beeno sannan ya sake maida hankalinsa ga omar. Dukka girarsa biyu omar ya dagewa haisam din. "Meye amfanin mazantakar tsinanne......kasan mata nawa ya yiwa fyade?,ka sani ko a musulunci hukuncinsa jefewa ko?" Shuru haisam yayi yana jin wani sanyi yana ratsashi. Samun amini na qwarai....aminin daya fahimci burinka da fatanka ya idar maka dashi tun bakace komai bama rahama ne. Sai ya kasa cewa Omar komai.....ya gama hukunci na farko daya kamata tamim ya karba. "Omar.....beeno......zamu shiga gidan can,qarfe daya na rana daidai" Ya furta yana miqewa da takardun a hannunsa. Wani murmushi omar ya saki,burinsa kenan....abun kuma ya masa dadi. "Ko sha biyunnan kace mu shiga a shirye muke" Ya amsa masa yana murmushin jin dadin zabarsa da haisam din yayi. Qaramin murmushi ya saki kawai,kafin yace komai kuma Aateeq dake kula da motsin komai na gidan ya shigo. "Obbo.....me wada ya iso" "Kaishi daya parlor din" Ya fadi yana miqewa a hankali. Sunan me wada ya sanya omar bin haisam da kallo,kallon da yake cike fal da tambaya da mamaki. "Me ya kawo me wada kuma gidan nan?" Tambayar dake cizon omar kenan,amma bayan haisam ya kalleshi sai yayi kaman bai fahimta ba ya dauke kansa yana takawa zuwa gaba abinsa. A nutse yayi sallama,me wada ya amsa yana rusunar da kai cikin girmamawa. "Bismillah.....zauna" Haisam yace dashi yana zama. Zama shima yayi,yana tattara dubansa ga haisam din. "Farko dai godiya zan miqa maka......kayi qoqari qwarai......ka kuma taka dukkan rawar daya dace" Haisam ya furta yana jinjina kai. Qasa da kansa me wada yayi yana amsa masa. "Nine da godiya da wannan damar da aka bani,nine da godiya da akaban damar da zan samu 'yanci bayan shekarun dana kwashe ina bauta" Kai haisam ya gyada a hankali. "Wannan aikin na wannan zangon ya qare......abinda ya rage yanzu kawai shine.....kasa hankalinka akan kitchen.....akan abincin sultane" Yayi maganan yana duban me wada. Kai ya jinjina yana kallon haisam shima. "Abun nufi ungo wannan" Yayi maganan yana danna wani madanni daga gefan kujerar da yake kai,budewa gurin yayi,ya sanya hannunsa ya ciro wani abu. Siriryar kwalba cw me dan tsaho kadan,saidai a cikinta akwai wani baqin abu da koda baka tsiyayoshi ba zaka fahimci yana da kauri. Kai tsaye haisam ya zube idanunsa akan me wada. "Zaka iya shayar da sultane wannan a duk sanda na buqaci haka daga gareka?" Haisam ya jefa masa tambayar fuskarsa tana tsukewa daga sakewa da sukunin da take dashi a dazu zuwa wani yanayi na daban *_TOFA!......MEYE HAKA HAISAM KE SHIRIN SHAYAR DA SULTANE?,......SULTANE FA?_* *_WANNE GIDANNE?,MEYE NE WAI A CIKIN GIDANNAN NA VILLA STREET?.....MAMMINA?......ANYA KUWA ZAKIKAI LABARI?_* *_AKWAI WANI QUDURI NE AKAN HAISAM DABAN BAYAN QUDURIN CAFKE MAMMINA?,KO KUMA AKWAI WANI ABU DABAN DAMU BAMUSAN DASHI BA?_* *_A YAU IN SHA ALLAH NAKE SANYA RAN ZAMU SAUKE PART 2 NA LABARIN NAN_* (Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)