❤️🤍 RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🤍 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E__________________1🔥 GIDANSU KHADIJAH 😥💔 Daga Zainab har mamanta an ransa wanda zai kalli ɗan uwansa ya ce ya yi shiru, sun shiga tsananin tashin hankali. Basu ƙara tsorata bama sai da suka kalli baban Zainab ɗin ya dai'na motsi, ya yi tsit alamar rai ya yi halinsa. Wani irin ihun da Maman Zainab ɗin ta kurma mai sauti sai da yasa Zainab ta tsorita sosai ta miƙe tsaye. Daga wannan ihun da ta kurma bata sake yin kwakkwaran motsi daga in da take ba, kawai ta sulale ƙasa ne, kan ka ce me ta dai'na numfashi, numfashinta ya ɗauke diff alamar ta sume. Da gudu Zainab da diro ƙasa daga saman gadon, har lokacin kuma jini na cigaba da malala daga cikin babanta, yadda kuka san hanyar ruwa ta fashe, kuma babban abin takaicin ma faɗuwar da ya yi yana murkusoso sai ya kwanto a kan wukar dake cikin nasa, hakan yasa wukar ta kara lumewa a jikinsa, shiyasa jinin ya yawaita sosai, dan ba ƙaramin ciwo ya ji ba, ga shi a tsakiyar cikin nasa ta caka mashi wukar, abin ya munana sosai!!. Waje Zainab ta nufa domin ta duba Khadija, ta rasa me zata yi wa iyayen nata ne yasa ta bi bayan yar uwarta. A takaice dai maman Zainab bata tashi farkawa ba sai da ta ɗauki awa uku masu kyau a sume, an zuba ruwa an zuwa ruwa, amma shiru bata farfaɗo ba, daga karshe suka kyaleta suka zubawa sarautar Allah ido. Lokacin da ta farfaɗo kuwa sai ganin kanta ta yi a wani irin ɗaki mai kama da cell na ƴan'sanda. A hankali ta fara bin saman celling da kallo, idanunta sun kumbura luhu luhu, sun kuma yi jajir kamar jini ne kwance a cikinsu. Tunanin baban Zainab ne ya faɗo mata a ranta, hakan yasa ta yunƙura zata miƙe da zafinta kuma a ruɗe. Sai dai kash ta kasa iya miƙewar, sakamakon jikinta duk ciwo yake yi mata, gaɓɓanta sunki koda motsawa. Hakura ta yi ta cigaba da kwanciya a saman tabarman da take ɗin. A hankali ta fara sauko da kallonta da kallon celling da take yi izuwa ƙasa dan taga a ina take a kuma wani hali take! Wasu irin siraran hawayen takaici haɗe da danasani mai girma ne suka fara zirara daga idanunta izuwa saman ƙuncinta. Kwatsam ba zato ba tsammani tana sauke idanun nata ƙasa sai saman kofar shigowa wanda yake kofa ce ta burglaris, wato kofar cell kenan. Zaro idanu ta yi a tsorace, jikinta har kerma ya fara yi, cike da mamaki take tunanin ina su Khadija da baban Zainab ɗin? In da take ɗin babu kowa bare ta yi tambaya. Sake yunkurin miƙewa ta yi a karo na biyu, cikin tashin hankali da ruɗani take. Jikinta sai kerma yake yi, idanunta sun cicciko da kwallah sosai ga kuma wasu na zuba. A wannan karon ma kasa miƙewar ta yi, saboda jikinta duk a mace yake, ga bala'in ciwo da yake yi mata. Tunani ta fara yi a kan me ya kawota cell kuma? Me ta yi?. Rasa mai bata amsa ta yi, hakan yasa bata gaji ba ta sake yunkurin miƙewa a karo na uku, sai a lokacin ta fahimci cewa kafarta na ɗaure da wani sarka irin na ɗaure manyan ɓarayi. Kara zaro idanu ta yi tare da fara ƙoƙarin tunawa ko zata iya tunano abin da ya faru a baya?!. A can gida kuwa sai kuka Zainab take ta yi, ta ƙunshe kanta a cikin ɗaki tun bayan da ƴan'sanda suka tafi da mamar ta su. Abin da ya faru shi ne, fitar da Khadija ta yi domin zuwa kiran mutane su zo su taimaka masu, tana fita bakin gidan nasu bata ga kowa ba, babu mutane, dukka mazan unguwar tasu sun tafi masallacin jumma'a, dan lokacin an fara sallar jumma'a. Ganin hakan yasa a ruɗe ta nufi hanyar fita daga unguwar nasu izuwa bakin titi ko zata haɗu da wasu su taimaka mata, basu da nisa da titi. Bata ƙarisa fita ba wata dankareriyar mota kirar Bugatti la voiture noiro baka kirin sai kyalli take yi ta faka a gabanta. Tana ƙoƙarin kaucewa motar ta raɓa gefenta ta wuce sai gani ta yi an buɗe kofar motar. Wasu maza biyu kyawawa farare tas tas masu sanye da suit ash color ne suka ɓalle kofar motar suka fito. Daga ganin mazan nan ba Nigerian mens bane, daga gani daga ƙasashen masu jajayen kunnuwa suke, dan kuwa jajir suke kamar ka taɓa jini ya fita, ba irin farin Nigeria bane, ga kyakkyawan gashin kai bakin kirin, sannan idanunsu tas kamar an ɗiga zaiba, kwayar idanun kuma bakin kirin har wani ɗan kyalli yake yi, suna da kyau kam masha Allah, matasane da ba zasu wuce 25 years ba a duniya. Sai dai da kallo ɗaya zaka yi masu ka san basu da imani, saboda fuskokinsu babu alamarta ko kaɗan, a turnuke fuskokin nasu suke sosai. Ga su dai dirarrun maza ne sosai sosai, kira kamar su suka yi wa kansu. Da yake tana cikin ruɗani da tashin hankali sai bata ma bi ta kansu ba, hasalima bata ɗaga idanun ta kalli koma su waye bane, kai tsaye ta raɓa gefensu zata wuce, kamar wata mahaukaciya haka ta zama. Bata kai ga wucesu ba suka damketa suka wurga cikin motar tasu, ga motar da tinted a jikinta. Ihu ta fara kurmawa da karfi karfi. A hanzarce suka faɗa cikin motar suma, suna shiga kuma bayan sun rufe kofar ji kake tsit Khadija ta dai'na wannan ihu, kamar waɗan da suka yi mata wani abin...... To fa, su waye su?. Cikin kwanciyar hankali suka yi reverse na motar tasu, a hankali suka takata suka bar unguwar, suka miƙi hanya. Abin da yasa kenan su Zainab suka ga ta jima bata dawo ba, ita kuma Zainab ɗin bayan mamarta ta suma sai ta fito a guje kamar mahaukaciya, dan ta nemo jama'a da kuma ƴar uwarta. Kasancewar ta fito a guje kamar mahaukaciya yasa ta shiga gaban wani mai mashin da ya ɗauko wata mata, ai kuwa bata ankara ba sai jinta ta yi a ƙasa. Ko kaɗan bata wani damu ba, da yake Allah ya takaita mashin ɗin bai ji mata ciwo sosai ba, tureta kawai ya yi ta faɗi ƙasa, ƴar kwarzanewa ta yi a hannunta sakamakon wani dutse da yake a kusa da ita ta faɗa kansa. Baiwar Allah hankalinta baya a jikinta, sai ta miƙe cikin kaɗuwa da tashin hankali. Da gudu ta nufi bakin titi. Mai mashin da yake ƙoƙarin banka mata ashariya saboda shiga gabansa da ta yi, kafin ya buɗe baki ma ta miƙe da gudu ta barshi da baki a buɗe, bai san me take ji ba, bai san bala'in da yake kanta ba. Bata ƙarisa isa ga bakin titi ba sai jin jiyar motar ƴan'sanda a gabanta ta yi, birki ta ja ta tsaya da nufin idan sun wuce sai ita ma ta nufi bakin hanyar, kasancewar hanyar fita daga unguwar tasu zuwa bakin titin babu wani faɗi sosai. Ganin Hauwa a gaban motar ƴan'sanda ne yasa Zainab ɗin bata san lokacin da ta juya ta fasa isa ga bakin hanya dan neman mutane ba, ta juya ta bi bayansu, dan tasan cewa definitely gidansu wannan mota ya nufa tun da ga Hauwa a ciki....... Ashe ƴan'sanda Hauwa ta je tattarowa. Suna isa bakin gate ɗin suka fara dirowa ƙasa daga saman bayan motocinsu, ba tare da ɓata lokaci ba suka nufi cikin gidan, ƴan'sanda shidda ne cif suka zo, sai Hauwar da ta kirasu, shegiya ko ɗan'kwali babu a kanta. Ita ta yi masu jagoranci har izuwa ɗakin nasu in da maman Zee ta kashe baban Zainab ɗin. Suna shiga suka sami maman Zee a sume, duk da take a sumen kuma bai hana sun tafi da ita ba, hands gloves suka sanya a hannayensu kafin su taɓa baban Zainab ɗin, sai da suka ɗauke shi a hotuna kala kala ma kafin su taɓa shi. A takaice dai wannan shi ne abin sa ya faru. Zainab tana kuka kada su tafi mata da mamarta, amma haka suka wuce da ita tana sume bata san me yake faruwa ba, sannan suka tafi da Hauwar ma, dan kara gudanar da bincike, shi kuma baban Zainab wasu ƴan'sanda ne na daban suka zo suka ɗauki gawarsa izuwa asibiti, dan a yi gwaje gwajen da za'ayi. Hauwa a police station ɗin ne da suka je ta kira Hajiyarsu baban Zainab da wayar baban Zainab ɗin ta sanar mata da cewa maman Zainab ta kashe baban Zainab, gawarsa tana police hospital, dan haka su zo. Ai kuwa babu ɓata lokaci sai gasu sun hallara a station ɗin bayan Hauwar ta gaya masu a division ɗin da suke. Ƴan'sanda sun yi sun yi maman Zainab ta farfaɗo daga sumar nan da ta yi sun ƙasa, sun yi ta zuba mata ruwa, amma bata farfaɗo ba. Hakan yasa suka yi duk gwaje gwajen da zasu yi ɗin tana sume. Shatin zanen hannunta ne a jikin wukar dake lume a cikin baban Zainab ɗin, suna gwajin farko ya tabbatar masu da hakan, hakan yasa suka gasgata dukkan zantukan da Hauwa ta gaya masu, sun yarda, duk wani bincike da zasu yi ya tabbatar masu da lallai maman Zainab ce ta yi wannan kisan kan, wannan dalilin yasa suka jefata cell tun kafin manyansu su iso kan case ɗin. Ita kuwa Hajiyarsu baban Zainab ɗin da take ta faman kuka tun da ta zo, ƴan'sanda sun ce ta koma gida, kin yarda ta koma ta yi, faɗi take sai maman Zainab ta biyata ran ɗanta, azzaluma ta kashe masu bangonsu, da shi kaɗai suka dogara, shi ne mai yi masu komai, dan haka wlh sai ta biyata ɗanta, maman Zainab dake sume bata san wainar da ake toyawa bama baiwar Allah, sai banka mata ashariya kala kala suke yi tana sume. Maman Haidar kam ma har da wani cewa wlh ba zasu yarda ba dole ita ma a kasheta kamar yadda ta kashe shi azzaluma kawai. Da kyar dai aka samu ƴar'sanda mace ta ja Hajiyar suka tafi zata mayar da ita gida, haka su Maman Haidar suka bisu, Maman Hanif kam ta ƙasa iya furta ko kala bayan ruwan hawaye da take yi, banda ruwan hawaye babu abin da take yi, ita dai tasan maman Zainab ba zata taɓa kashe baban Zainab haka kawai da gangan ba, dan ita ta san soyayyar da yake a tsakaninsu, ta san irin yadda baban Zainab ya rinƙa jigila a tsakanin Kano da Kaduna saboda ita, sannan ta san yadda maman Zainab ɗin ma take son shi, so ita bata ma yarda cewa maman Zainab ɗin ce ta kashe shi ba, zargin Hauwa ce ta yi hakan take yi a ranta, dan ita fa kwata kwata bata kaunar Hauwa, amma Hajiyarsu da Maman Haidar fa suna kaunar Hauwar duk da balai'n da take surfa masu, da alama ta kai sunansu wajen bokanta ne, sai dai aikin bai kama maman Hanif ba, dan dai ita kam babu son Hauwar ko ɗigo a ranta, sai ma zallar tsana da take yi mata. Ko da aka mayar da su gidan baban Zainab ɗin, a bakin kofar gidan suka isko Zainab a zaune tana tikar kuka kamar ranta zai fita, ta rasa ina zata sanya rayuwarta, babu uba yau, sannan ƴan'sanda sun tafi da mamansu, ga kuma Khadija shiru bata dawo ba. Ƴar'sanda da ta rakosu ta dawo da su gidan tana juyawa suka fara halin nasu, tana barin gidan maman Haidar ta fara surfe da nikar bala'in a kan wlh ba zasu taɓa hakura su yafewa maman Zainab ba, dole a kasheta kamar yadda ta kashe masu bangonsu ma jingina. (Ni kam na ce sai yanzu kenan suka san cewa shi ɗin bango ne a gare su?🤔) Kasancewar har da Hauwa ƴan'sanda suka saki da nufin idan wani abin ya taso zasu nemeta, hakan yasa ita ma ta fara rera nata kukan munafurcin tana faɗin wlh haka ne ba zasu yafe jinin baban Zainab ba. Dama fa ita Hauwa idan baku manta ba dukiyar baban Zainab ɗin kawai take so ba shi ba, so ita mutuwar tasa ma rage mata hanya ya yi, ya zame mata tsanin da zata taƙa ta cinma burinta ne, dama ko maman Zainab bata kashe shi ba ita Hauwar ta shirya yadda zata sanya a ɓatar mata da shi bayan ta gama kwasan abin da zata kwasa, so ita wannan kasheshi da maman Zee ta yi hanya ta rage mata, wani dama ne ta samu, yanzu tunanin da yake a cikin ranta kawai shi ne ta yadda zata yi ta rufe bakin kowa ta kwashe komai na marayun Allahn nan Khadija da Zainab ta gudu abinta, shiyasa ma kuka ga ta yi saurin zuwa ta kira ƴan'sanda domin su tafi da maman Zainab, tasan idan maman Zainab ɗin tana cikin cell abubuwa zasu tafi mata yadda take so saɓanin idan tana gidan, bokanta ya gaya mata asirinta ba zai ci maman Zainab ɗin ba, ba zata iya rufe mata baki ba, domin a yanzu maman Zainab ta tsaya tsayin daka a kan ibada, ta koma ga Allah sosai, hakan yasa babu wani aiki da zai iya kamata. Sanin hakan yasa Hauwar ta yi azaman jefata a cell, dan in tana gidan zata katse mata duk wani abin da ta shirya, kuma bata isa ta ɗauki ko tsinke a gidan ba, amma yanzu kunga maman Zainab tana cell, iyayen baban zee ɗin kuma ta sanya an yi masu aikin cusa masu kaunarta, saura mata aiki ɗaya shi ne ta rufe bakunansu ta yadda zata gudanar da komai babu wanda zai iya ce da ita uppan........ E lallai akwai kura, ina Khadija? Sai Allah kaɗai yasan su waye suka ɗauketa, ina kuma zasu kaita baiwar Allah. Wani irin tsananin tsana Hajiyarsu baban Zee ta ji take yi wa maman Zee da ƴaƴanta gabaɗaya...... Ni kuwa nace to me laifin ƴaƴan nata? Su suka yi laifin ne? Ko a wajen Allah laifin wani baya shafar wani, amma jahilci yasa Hajiyarsu ta haɗe da su dukka ta tsana kamar ta kashesu, sai faɗi take maman Zainab ta gama da su ta tona masu asirin da Allah ya rufa masu, shikenan sun shiga uku sun lalace. Maman Hanif kam har izuwa yanzu ta kasa iya furta ko uppan. Banda zagi babu abin da maman Haidar take surfawa Zainab dake zaune a bakin kofa tana tikar kuka, yarinyar nan kamar ranta zai fita, kuka take yi ba ji ba gani, idanunta har ƙanƙancewa suka yi, sun kumbura sun yi jajir, idan ka ganta sai ta baka tausayi, sai kuma ka tsorata da ganin idanun nata, saboda yadda suke jazur da su. Ko sannu bata ce da su ba, duk zagin da maman Haidar take yi mata bata ko ɗago idanu ta kallesu ba, hasalima hankalinta baya a tattare da ita ne, bata jin me ma suke faɗe. Maman Haidar na zagi Hauwa na ƙara ingizata, har da kara cewa ai dama maman Zainab ta kai sati tana cewa sai ta kashe baban Zainab, dan haka wlh har su Zainab ɗin ma kada su bari, ai suma mugun iri ne, dan halin uwarsu suka ɗauko. Ita fa Hauwa fama take yi taga yadda zata yi ta kawar da su Zainab ɗin, sannan ta rufewa kowa baki ta kwashi dukiya ta yi pacakanta da su son ranta, ta haɗa kayanta ta koma Kaduna....... Gaskiya ba karamar mayyar son abin duniya bace Hauwar nan, ba kuma ƙaramar azzaluma bace ba. Da dai suka ishe Zainab da zagi kamar zasu cinyeta ɗanya, sai ta miƙe ta nufi cikin ɗakinsu, ji take kamar zuciyarta na ƙonewa da wuta, su barta ta ji da abin da take ji mana, amma suna kara mata wani. Ko da ta shiga ɗakinma ba su barta ba, maman Haidar ta ce ta fito daga ɗakin nan munafuka, yadda kuka san ba jininsu ba ce, kamar ba jinin baban Zainab ɗin ne yake gudu a jinin Zainab ɗin ba, suka murje idanu, suka sanya yarinya a gaba da zagi da baƙaƙen maganganu kamar ita ta aikata laifin ba mamanta ba. Da maman Hanif ta yi ƙoƙarin basu hakuri su rabu da ita, ai kuwa ita ma maman Haidar ta hau zaginta babu kakkautawa, wai bata kishin jinin ɗan uwanta, kamar ba yau bawan Allahn nan ya rasu ba, sun zauna sai kace nace suke yi, tun ruhinsa bai gama sauka a masaukinsa ba sun fara walaƙanta bayansa, sun fara cin zarafin ƴaƴansa kamar ba nasu ba. A takaice dai Zainab da ta ga ba raga mata zasu yi ba, sun isheta da magana, sai ta kama hanyarta ta nufi barin gidan. Maman Haidar ce ta ce ina zata je munafukar banza. Ko sannu bata ce masu ba, bata ma sake ɗaga idanu ta kallesu ba, abin da take ji a cikin zuciyarta ma ya isheta, haka ta yi banza da su ta nufi waje, sai magana suke ta yi mata, ina ko waigowa bata yi ba, sai kiranta suke yi. Tana fita ta fara neman ina Khadija take, tana tafiya tana hawaye bibbiyu, wani na bin wani gwanin ban tausayi. Ni kai'na na tausayawa maman Zainab da ƴaƴanta wlh, kowa da kalar tasa ƙaddara a rayuwa, ba ta yadda Allah baya jarabtar bawa, amma kuma my people's ina son ku san wani abu, duk wanda kuka ga yana shiga cikin kaddarori to wlh Allah ya fi sonsa, Allah yana jarabta imanin bawa ne kawai idan yana kaunarsa, kada ki ga kina shiga cikin wasu matsaloli ki yi tunanin ko Allah baya tare da ke har ki fara tunanin kauce hanya, wlh wlh wlh Allah yana jarabtar wanda yake so ne kawai, to fata na dai a nan shi ne Ubangiji Allah ya bamu ikon cin rabawarmu a rayuwa koma wace iriya ce, sannan ƙarin wata haske shi ne duk abin da kike so kike kauna a rayuwar nan ki saki a nan kaddararki da jarabawarki take, hadisi ne in gantaciya, domin na baku misali a aikace yasa na zaje na yi rubutu a kan part ɗin su maman Zainab, duk abin da ya faru da maman Zainab mu kaddarine da ga Allah, kuma ku sani kaddara da jarabawar ta faru da ita ne a kan abin da ta fi so ta fi kauna wato baban Zainab, a dalilinsa komai ya faru, saboda son da take yi mashi yasa har ta kauce hanya, dalilin son da take yi mashi yasa abubuwan duk suka faru da ita, da bata son shi da hakan ba zai faru ba, so misali na baku a aikace ba a labarce ko a kwatance ba. Ƴar uwa ki kasance mai yawan rokon Allah a kan abin da kika fi kauna, hakan zai sa idan kaddara da jarabawa zasu afka maki bisa wannan abin ya zo maki da sauki, saboda yawan addu'a, fatan kun gane? To rayuwar maman Zainab tarin karatu na tara maku a wajen dan ku ilmantu, Allah ya bamu dacewa ya kuma yafe mana kura kuranmu. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ KINGDOM OF POWER💪🔥💘 A karo na almost 8 Yah Jawad ya sake gwada kiran number Jaish, sai ya ji number a kashe. Guntun tsaki ya ja kafin ya ce. "Aikin me ka yi jiya da har yanzu baka tashi daga barci ba? Wato na dameka da kira shi ne har da kashe wayar ko? Zamu haɗu ne". Ya kai karshen zancen zucin nasa tare da kai kallonsa kan Chuchu dake goge ɗan bakinta da tissue. "Kin gama mu je ko?". Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e. "Amma Yah Jawad ka ɗan ci abincin mana". Ta faɗa kamar zata yi kuka, sam bata ji daɗin yadda yaki cin abincin bane. "Kina son in ci ne?". Ya faɗa tare da ƙaƙalo murmushin dole dan ya kwantar mata da hankali, amma zancen gaskiya hankalinsa a tashe sosai yake, kawai Rizwan ya gaya mashi kada ya bari kowa yasan me yake faruwa ne yasa ya danne, amma ga dukkan alamu maganar da suka yi da Rizwan ta yi mugu mugun ɗaga mashi hankali. A hanzarce cikin farinciki ta furta. "E Yah Jawad ina son ka ci". "Zaki bani a baki?". Ya faɗa yana kura mata ido, kuma ya yi maganar yana ƙara ƙaƙalo murmushin. Kai ta gyaɗa mashi. "E zan baka a baki Allah in dai zaka ci". Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da alama maganar ta yi mashi daɗi sosai. Gaya mata abin da zai ci ya yi, da sauri ta zuba mashi tare da ɗaukar spoon na fara ɗebo mashi. Saitin ɗan bakinsa ta kai mashi tana sunkuyar da kanta ƙasa. A fili ya furta. "A matsayin wa zaki bani abincin a baki?". "Yayana da na fi kauna". Ta bashi amsa. "Da gaske kin fi kaunata sama da kowa?". Ya yi tambayar da alamar mamaki a saman fuskarsa. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Meyasa kika fi kaunata?". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara jero mashi bayani. "Saboda kafi sake mun fuska sama da su Yah Bilal, sannan ka fi su kaunata, kana mun duk abin da nace nake so, kana wasa da dariya da mu saɓaninsu Yah Bilal da ko murmushinsu ma ban taɓa gani ba, sannan kan......." Katseta ya yi da cewa. "Meyasa kika ce nafi kaunarki Jannat?". Girgiza kai ta ɗan yi. "Yah Jawad ni ma ban sani ba, kawai dai nasan kafi kaunata shiyasa na fi kaunarka sama da kowa, daga kai kuma sai Yah Rizwan, sai Yah Raj, ku kaɗai nake so". Ajiyar zuciya ya sauke tare da kai hannunsa ya riƙo hannun nata, bakinsa ya kai spoon ɗin, a tare da shi da ita suka juye mashi abincin a cikin baki yana kallon face ɗinta. Sake mayar da spoon ɗin ta yi zata ɗebi abincin bayan ya saki hannun nata. Hannun nata ya sake riƙewa yana faɗin. "Ajiye spoon ɗin ki ciyar da ni da hannunki". Ba musu ta ajiye ta fara ɗiba da hannunta tana bashi a bakin. Sosai ya ci abincin, bai yi zaton zai ci mai yawa har haka ba, amma da yake suna hira tana bashi sai ya ci mai ɗan yawa. Bayan sun kammala ya ce su je ya kaita school akwai in da zai je. Miƙewa ta yi tare da ɗaukar jakarta suka nufi waje. Dai'dai zai fita part ɗinsu mai gabaɗaya, family part na King kenan, a dai'dai katafaren gate ɗin suka ci karo da Mammie tana shigowa, da alama ta biyo bayan Aliyah ce. Shi kuwa Jawad yana riƙe da hannunta, sai hira take zuba mashi suna tafiya, dama zai je amsa kiran mammie ɗin ce kafin ya wuce ya kaita school, shiyasa suka nufo kofar fita ba tare da mota ba, shi fa Jawad gabaɗaya ya mance da cewa Mammie ta ce kada ta kara ganinsa a tare da Chuchun. Dakatawa daga tafiyar da yake yi ya yi. Da kallo ya bi Mammien, bata ce mashi ko kala ba saboda jiga jigan zakunan matasan mayakan dake tsaron gate ɗin, saboda su yasa Mammien bata tanka masu ba ta wuce kawai. Ganin ta wuce bata ce masu ko sannu bane yasa shi ma ya juya ya bi bayanta, kuma har lokacin yana riƙe da hannun Chuchun. Parking space suka nufa, bai bi Mammaien cikin gida ba, ya shiga motarsa kawai dan ya kai beb ɗinsa school, lokaci ya tafi sosai, ta kusa yin latti, su Fanan har sun tafi sun barta, sun nemeta dan su tafi tare, da suka san tana tare da shi sai suka tafi abinsu. Wucewa da ita school ya yi, ita kuwa Mammie tana shigowa part ɗin kai tsaye wajen Momma ta nufa. My people's duk yadda kuke tunnin makircin Mammie ya wuce tunaninku, lumbu lumbuce ita ɗin, nunawa take yi babu wanda ya kaita son zaman lafiya, nunawa take yi tana kaunar Momma kamar ranta, ta manne da Momma kamar me, suna shiri, Allah sarki Momma bata san true colonta ba, bata san cewa ita ɗin musa ce a zahiri fir'auna a baɗini. Haka take nunawa Mummyn Gimbiya Chuchu ma kauna over, Maman Gimbiya Aneesa ce kawai basu shiri, basu haɗa inuwa da Mama, kamar wuta da audiga haka suke, kar ta san kar ne, dukkansu sarakan makirci ne, kun san idan fa kana aikata abu sai kaga kamar kowama aikatawa yake, hakan yasa basu zama inuwa ɗaya, in dai suka haɗu sai aikawa juna baƙaƙen maganganu da habaici game da harare harare suke yi, sukam sun fitar da kishin balbalin nasu a fili. Kuma yadda kuka ga Mammie da iya makircin nan haka Gimbiya Sarina take, Fanan dai babu ruwanta, nutsatsiya ce, ba ruwanta da makirci da kirsa, amma Sarina kam ita ta sha nonan Mammaie ɗin haikam, Mammaien na cire kafa ita kuma zata sanya nata kafan a munafurci da kirsa da kisisina haɗe da makirci, ƴar karama da ita amma idan ta haɗa maka wani makircin sai ka yi zaton macece yar shakaru 50 wadda ta ga jiya ta ga yau, ba'a banza ta zama master team ɗin su Obaid and Omaid ba ai, iyashegensu ne kusan ɗaya, sai dai su sunfita, amma akwai kamanceceniyar halayya da wasu dabi'u a tsakaninsu. A parlourn ta isko Momma, kusa da ita ta zauna tare da sakar mata fuska kamar wata ta Allah, sannan ta ɗaga mata gaisuwa. Mommar ma duk da murmushi bai wani dameta ba, ba zaka taɓa ganin tana murmushi da waɗansu ba sai da yaranta, su ne kawai suke ganin murmushinta sai King namu, amma ganin Mammie ɗin ta sakar mata murmushi yasa ita ma ta ɗan saki ɗan siriri murmushi kafin ta amsa gaisuwar tata. Cike da kwarewa a iya kirsa da makirci ta fara janta da hira, ba komai yasa take son jan Momma da hira kuma take yawan zuwa wajenta sannan ta nuna tana kaunarta over ba face dan san sanin wani sirrin Momman, gabaɗaya matan gidan banda Mummyn Gimbiya Chuchu duk suna zargin Momma tana ɓoye masu wani sirri tsawon shekaru, sun buga sun buga suna son sanin gaskiya, amma da yake ita bata ma san suna yi ba, kuma da zuciya ɗaya take zaune da su, shiyasa Allah bai basu ikon sanin komai a kan hakan ba. Wannan dalilin yasa ita Mommar da Mama basu shiri ko kaɗan, dan mama tana zargin tabbas akwai abin da Momma ta ɓoye masu a tsakaninta da King. Sosai Mammie ta zage tana ta janta da hira, Momma fa bata da yawan magana wlh, amma nacin Mammie take sawa ta rinƙa ɗan tayata hirar jefi jefi. Ba komai yasa bata da yawan magana ba face faɗar da mahaifiyarta take yawan yi mata a kan kada ta bari kowa ya san sirrinta, kishiya fa ba'a bar bawa yarda gabaɗaya bace, shi ne yasa bata sakewa ta saki baki tana magana, in kunji tana hira sosai to da yaranta ne ko kuma da masoyinta King. Mommar izuwa yanzu ta fara mamaki a kan yanayin hiran Mammie a duk lokacin da ta zo in da take, a duk lokacin da ta zo bata da hira da ya wuce na shekarun baya, ba zata taɓa yi mata hira kan abubuwan yanzu ba, sai dai ta yi ta kaƙale kaƙalen abubuwan da suka suɗe. A gaskiya da can baya an yi wani irin zama a cikin family part ɗin nan, ba ƙaramin faɗa aka yi ba, Momma ta sha bakar wahala a gidan fiye da tunaninku, bata shiri da kowa, kusan haukatata aka yi a cikin gidan, akwai lokacin da har ya zamana tana zaune ita kaɗai tana magana, wani lokaci sai ta yi ta buga kanta a bango har sai ya fashe ya yi ta jini, wani lokaci kuma ta yi ta faman kuka babu gaira babu dalili, abubuwa dai kala kala, to babban abin da yake damun Mammie har ita da Mama suke zargin akwai abin da Mommar ta ɓoye masu shi ne lafiya da ta samu sosai, yadda take gudanar da rayuwarta yanzu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, abin ya basu mamaki, suna son sanin ya aka yi hakan ta faru?. Haka dai Mommar ta cigaba da biye mata suna hira sama sama, ita kuma Aliyah tana wajen Mummyn Gimbiya Chuchu, sai hira suke yi kamar kawaye, Allah sarki Mummy fa bata san mijinsu Aliyah take hari ba. Mama kuwa sai yanzu jikinta ya fara ɗan rage raɗaɗin da take ji na azabtarwan su Omaid da suka yi mata. After some hours. Da misalin karfe ɗaya na dare, shirye take cikin wasu irin baƙaƙen kaya, doguwar riga ce tana ja a ƙasa, sai ta ɗaura bakar alkyabbarta a saman kayan, shi ma alkyabbar yana jan ƙasa, cikin wani irin tafiya wadda takun sahu baya bayyana ta fito daga cikin ɗakinta. Ta kofar baya ta fita daga part ɗin nasu. Tafiya ta fara yi cikin taku kamar na marasa gaskiya ta miƙi wata hanya mai tsawo. Ta ɗan yi tafiya mai ɗan nisa kaɗan, duk in da ta zo giftawa idan ta kalli warriors a wajen sai ta laɓe, da yake warriors ɗin suna kai komone a cikin masarautar sai ya zamana idan sun wuce sai ta fito ta cigaba da tafiya. Wani irin canza kala idanunta ya yi izuwa red color sosai lokacin da ta kusa isa bakin babban gate na farko na masarautar. Bakin gate ɗin shake yake da manya manyan zakunan warriors a wajen, jiga jigai masu ji da karfi ranon commander Zafar, a tsaye suke kamar waɗan da aka sassaƙa. Ta gabansu ta zo ta wuce amma basu sami damar iya ganinta ba, canza taku ta yi izuwa takun ƙasaita lokacin da ta zo giftawa ta gabansu. Wucewa ta yi kai tsaye ta nufi waje. Tana fita wajen gate ɗin kuma ta ɓace ɓat, babu ko alamarta............... To fah, dama ta kira waya ɗazun ta ce karfe ɗayan dare su haɗu a in da suka saba haɗuwa, ko da waye zasu haɗu? Me zai yi mata? Dama ita matsafiya ce? Ƴar surkulle ne ita kenan?. Ku ɗan lallaɓa da wannan page ɗin kafin mu fara yin long pages.🔥💘 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E__________________2🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ FOREST🏞️🔥 Tafiya yake yana layi ba tare da ya san in da ya dosa ba, burinsa kawai ya ganta, ita ce a cikin tunaninsa. Cigaba da zuba jini ya rinƙa yi a duk wata kafa da wannan damisar ta yakushesa. A hankali hankali ya fara ganin dajin na juya mashi, idanunsa na ƙoƙarin rufewa ruf, sai ƙoƙarin buɗesu yake yi, amma abin ya ci tura, domin already duk wata gaɓa a jikinsa ta yi la'asar, duk wata karfi ta kare mashi a yanzu. Har ya iso bakin wata rami mai kama da karamin rafi, cike ramin take tab da ruwa, kasancewar baya iya gani sosai sai bai kalli rafin ba, cigaba da saka ƙafafunsa kawai yake yi yana tafiya ba tare da yasan in da yake takawa ba, shi dai Pretty kawai yake tunanu. Wani irin jiri da ta ɗebesa ne ya tafi luuuu zai kifa gabaɗayansa a cikin wannan ramin. Kamar walkiya haka mutun ya bayyana a gabansa tare da tareshi ya faɗa saman kirjinsa. Kamar dai kullum, fuskarsa na sanye da wannan rawani da yake rufe fuska, iya kan idanunsa irin na Pretty kawai zaka iya gani. A lokacin kuwa idanun Kamran ɗin sun gama rufewa, baya iya ganin kowa kuma baya gane komai, bai dai suma ba kam. A saman shoulder ɗinsa wannan jarumin sadaukin ya saɓa shi, sannan ya nufi wata hanya da shi, tafiya yake cikin nuna tsantsar jarumta, daga ganinsa kasan dakakken namiji ne mai ji da lafiya. Saman wasu ganyayyaki ya kwantar da Kamran ɗin bayan sun yi tafiya mai ɗan nisa, da alama shi ya shirya ganyayyakin. Hannu yasa ya ƙarisa yage rigar jikin Kamran ɗin, dama already damisar ta ɗan yayyageta, so sai ya ƙarisar da yageta kawai. Wasu kwarya dake gefe guda ya buɗe ɗaya, cikin zafi zafi yake aiki, da alama jininsa a tafashe yake, kwayar idanunsa duk in ya lumshe ido ya sake buɗewa sai sun tafi da imanin mutun, saboda kyansu, sak idanun Pretty and Sweetie, ga idanun nasa shi ma dara dara. Maganin launin green color ne a cikin kwaryar, duk wani waje da wannan damisa ta fasa a jikin Kamran sai da ya bi ya zuba mashi wannan maganin. Cikin ƙanƙanin lokaci Kamran ya fara dawowa cikin hayyacinsa, da alama maganin aiki yake yi kamar magic. Miƙewa ya yi daga wajen ya nufi wajen wata bishiya dake gabansu ya tsaya a wajen bayan ya mayar da kwaryar gefe ya ajiye. Shi kuwa Kamran a hankali idanunsa suka fara washewa, da alama ya dawo cikin hankalinsa. Ɗan dishi dishi ya fara ganin mutumin, da yake a ta gaban ganinsa mutumin ya tsaya, sai kara waro waɗan nan manyan idanun nasa yake yi yana son ganin wanene? Amma ganinsa bata gama washewa ba, dishi dishi yake gani. Mutumin ya juya mashi baya, iya bayansa kawai yake iya gani. Jin alamar Kamran ɗin ya fara dawowa dai'dai ne yasa ba tare da ya juyo ba, in a low voice sosai ya furta. "Where's Nufaysat?" Haƙiƙa yana da sanyin murya tamkar Sweetie ce ta yi magana, kun san dama ita tana da sanyin muryar, Pretty ce mai zazzakar murya kamar busar sarewa, amma Sweetie ko ɗaga murya ta yi sai kun ji shi a sanyaye, saboda sanyinta, ga daɗin saurare, dukkansu ita da Pretty voice nasu akwai daɗin saurare sosai, sai ma idan suna karatun Alkur'ani mai girma. Mamaki ne ya kama Kamran ɗin, dan shi bai san su waye Nufaysat ba, kuma ya ji voice ɗin mutumin tamkar na Sweetie, sai abin ya ɗaure mashi kai. A hankali ya fara ƙoƙarin motsa laɓɓansa alamar yana son ya yi magana, sai dai kuma tongue ɗinsa ya yi mashi mugun nauyi, ya kasa iya motsa ta. Still wannan mutu bai juyo ba, jiran amsa kawai yake yi a kan ina su Nufaysat?. Kamran kuma baki ya kasa buɗuwa, saboda azaban da ya sha a hannun bakar damisar nan, duk ya jigata. Motsin da suka ji alamar mutun ya tinkaro in da suke ɗin ne yasa wannan sadaukin ya bar wajen a ɗari, da alama ɓoye kansa yake yi ga kowa. Yana barin wajen Mamma ta iso wajen cikin zafinta, tana tafiya kamar wata jarumar mayakiya, gefen face ɗinta yana ɗan zubar da jini, alamar damisar ta ji mata ciwo a wajen, ta biyo sahun ɗan ta ne. Dai'dai lokacin da ta iso wajen, a dai'dai lokacin shi kuma Kamran ɗin ganinsa ya gama washewa, ƙoƙarin miƙewa ya fara yi, amma sai ya kasa, kamar wadda aka ɗaɗɗaurewa gaɓɓan jiki. Da sauri mamman ta ƙariso wajen nasa, a gabansa ta tsugunna tare da kura mashi idanu tana ganin maganin da Sadauki ya sanya mashi. "Kamran who did all this thing to you?". Ta faɗa tana kara zaro idanu. Girgiza mata kai ya yi tare da cewa. "I don't know him". Sosai take ganin maganin, a matsayinta na babbar likitar gargajiya bata taɓa ganin irin wannan magani ba, bata san wani ganye bane, ga shi babu halin ta sani, saboda ganyen an murjeta sosai, so ba zata iya ganewa ba. Yau tsawon shekaru 25 zuwa 26 tana wannan aiki na likita, amma bata taɓa sanin irin wannan magani ba. Yau a karo na farko ta shiga cikin mamaki sosai, hannu ta kai ta ɗauki wannan kwaryar, zubawa maganin idanu ta yi tana mamaki sosai, yau dai an samu wani abin da ya bata mamaki a wannan dajin. Dawo da idanunta a kan shi ta yi. "Kamran tell me who treat you? Who help you?". Sake girgiza mata kai ya yi tare da ce mata bai sani ba shi ma. Miƙewa tsaye ta yi da kwaryar a hannunta, tafiya da shi zata yi ya je ta yi bincike a kan wani irin ganye ne wannan. Hannu ta miƙa mashi a kan ya riƙe ya miƙe tsaye su tafi. Kasa iya miƙewar ya yi duk da ya riƙe hannun nata, hakan yasa ta ajiye kwaryar tare da duƙawa kamar ɗan baby ta saɓe shi sai saman shoulder ɗinta, sannan ta ɗauki kwaryar maganin ta nufi hanyar komawa...... Kai Mamma ba dai karfi ba kam, kakkarfan macece sosai. Suna tsaka da tafiya ya ce. "Mamamma take me down zan iya tafiya yanzu". Ba musu ta sauke shi, dan ya ɗan ji kwari. "Mamma ki je zan zo in sameki". Ya faɗa tare da gyara tsayuwansa. Kallon tuhuma ta wurga mashi kafin ta ɗaure fuska sosai. "Ina zaka je?". Kai tsaye ya ce mata. "Neman Pretty zan je, ban san in da ta nufa ba, kuma kin san dajin nan yana da haɗari sosai, kada ta je ta faɗa wani wajen mugayen dabbobi su cutar mun da ita, gaskiya ba zan iya zama ba". Bawan Allah ita ce kaɗai a cikin tunaninsa, dan yana ganin kamar Sweetie tana mazauninsu, dan a tunaninsa ai ita bata fita, kuma haka ne, da ni da ku duk mun san bata fita, so ya yi tunanin Pretty ce kawai ta fito damisar ta ritsata, shiyasa baya zancen Sweetien. "Who's she?!". Ta faɗa murya a kausashe. "My pleasure". Ya bata amsa cikin halin ko in kula, ba wani damuwa a tattare da shi. Da alama fa Kamran hankalinsa baya jikinsa, da alama ya manta cewa da Mamma yake magana. Gyara tsayuwa da kyau ta yi, wani irin kallo da ta wurga mashi sai da tasa ya haɗiyi yawu da kyar, da alama kallon yasa ya dawo cikin hankalinsa. "Your pleasure?!". Ta maimaita kalmar cikin kausasshiyar murya. Nan take ya ji harshensa ta yi mashi nauyi, sai a lokacin ya fahimci ya yi kuskuren suɓutar baki, yanzu idan ta rabasu fa ya zai yi? Idan ya gano Pretty ta ce kada ya sake zuwa in da suke ko kuma ta koresu a dajin ko ta bi dare ta salwantar masu da rayuwarsu ya zai yi? Wannan tunanin yasa ya fahimci ya tabka babban kuskure a magana, yasan da cewa tsab Mamma zata iya bin dare ta kashesu, ba zuciyar imani ne da ita ba, amma duk da haka yana yi mata biyayya, shi kansa bai san meyasa yake yi mata biyayya sosai har haka, a yanayin renon da ta yi mashi bai kamata ma ace yana tsoronta ko yana yi mata biyayya har haka ba, duk da cewa e munsan ko faɗa zasu yi zata yi mashi dukan mutuwa, dan ba sa'arsa bace a fagen iya faɗa, ƙashinta ya rigada ya yi dahu da faɗa, amma biyayyar da yake yi mata har ta yi yawa, baya taɓa ja da maganarta, yanzu haka da ya kasance yana karatun Alqur'ani mai girma ma kullum kara kaunarta yake yi, dan yanzu yana kara sanin girma da darajar mahaifiya. "Kamran amsa me a ina ka santa? Ashe kana da wata pleasure bayan ni?". Shiru ya yi ya kasa yin magana. Tsawa ta daga mashi mai karfi a kan ya buɗi baki ya bata amsar da take tambayarsa a kai ko ransa ya ɓaci. Wani irin raɗaɗi yake ji zuciyarsa take yi mashi, burinsa kawai ya je ya ceci Pretty, ya nemo in da take kada wani abin ya cutar da ita, amma mamma tana neman dakatar da shi, shi gaskiya a wannan gaɓar baya jin zai iya yi mata biyayya ya kyale ran Pretty ya salwanta. Saukar wani irin gigitattacen mari da ya ji a saman ƙuncinsa ne yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka. Nan take ya kai hannunsa ya dafe kumatun nasa tare da sauke kallonsa a kanta, tun da yake da ita ko da sukan wasa bata taɓa dukansa ba, wannan mari da ta yi mashi ya kara tabbatar mashi da abin da yake zargi na cewa bata da gaskiya ne yasa take ɓoye rayuwarsu ga kowa, rashin gaskiya ya bayyana karara a tatare da ita, in dai kuwa haka ne yau sai ta gaya mashi wanenen shi wanene babansa? Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da yes kada ya yarda sai ta gaya mashi wanenen shi?. Cikowa tab idanunsa suka yi da kwallah saboda zafin marin da ta dalla mashi, marinta ba wasa ba, akwai tsananin zafi. Da yake fatarsa akwai haske hakan yasa shatin yatsunta biyar da Allah ya bata suka fito ɓaro ɓaro a saman face ɗin nasa. Wani irin raɗaɗi zuciyarsa take yi mashi, ji yake tamkar an ɗaurata a saman wuta. Dannewa ya yi tare da furta. "Mamma please ki barni na je na cece rayuwarta, idan ta mutu me zan cewa ƴar uwarta Sweetie? Idan mum ɗinsu ta bayyana ta tambayeni amanar da ta bani me zan ce mata? Ni kai'na nasan idan ta mutu nima ba zan rayu ba, in dai kina sona da gaske to ki barni na je na nemota!". Yana kai karshen maganar wasu siraran hawaye suka fara ganganrowa a saman ƙuncinsa, ba kukan marin da ta yi mashi yake yi ba, kukan rashin Pretty ya fara yi, idan mamma bata barshi ba da alama zai iya mutuwa, da alama Pretty ce rauninsa dan ga shi duk jarumtarsa yau a kanta yana kuka!. "Kamran ba in da zaka je, kenan dama kullum wajensu kake zuwa? Who're they? Har amanarsu kenan aka baka? A ina kasan amana? Who told you this word?". "Mamma ki bari idan na je na nemota na dawo sai mu yi magana, please kada mu tsaya magana a yanzu ta yi mun nisan da ba zan iya ganeta ba, duk wani lokaci da zamu ɓata a nan ki sani rayuwar Pretty ce taka cikin haɗari, kin fa san yadda Forest ɗin nan yake, please mamma........." Tsawar da ta daka mashi a kan babu in da zai je ne yasa ya haɗiye sauran maganar dake bakinsa bai amayar ba. "Kamran kamar yadda na gaya maka tun farko babu kai babu mutane to hakance har yanzu, babu ruwanka da mutane, ko mutuwa mutun zai yi a gabanka ka tsallake ta kansa ka wuce, babu ruwanka da kowa, ni kaɗai ce kake da shi a duniya, haka kuma zamu cigaba da rayuwarmu, dan haka babu in da zaka je, ka wuce mu tafi!!". Cikin ɗaka murya ta yi maganar, da alama ta fara hasala sosai. "I can't go anywhere without seeing my Pretty! Mamma meyasa kike yin hakan? Kenan nima kina son idan wasu suka ganni ina bakin mutuwa su tsallekeni su wuce ba tare da sun taimaka mun ba?..........." Katse shi ta yi da cewa. "Kai ba zaka mutu ba! Kai daban kake da mutane, babu wanda ya isa ya kasheka, ba mutun kake kamar sauran mutane ba, dan haka kamar yadda na ce babu in da zaka je to babu in da zaka je, ka wuce mu tafi, babu mutuwar da zaka yi da har mutane suki taimakonka!!". Yanzu ma a kausashe ta yi maganar, da alma ranta ya fara ɓaci sosai. "Mamma na gaya maki ni ba zan je ko'ina ba sai naga Pretty, amanatace, bazan taɓa bari rayuwarta ya salwanta ba, dan haka ki tafi kawai ni zanje nemanta, she's my wife my everything, mum ɗinsu ta bani aurenta, ita ce bugun numfashina, idan har kina son na cigaba da yin numfashi a duniya to ki barni na je na nemota kada ta yi mun nisa, please mamma ki fahimceni, nasan halinta sosai, yanzu haka tana can tana gudu tana kara afkawa cikin daji, kada ta je ta afaka wani wajen, please ki tausaya mana.....". Katse shi ta sake yi da cewa. "Waye ya gaya maka aure? Waye ya baka wannan kalmar? Wanenen ya gaya maka me mata yake nufi? Yaushe kasan soyayya? Wani maci amanar ne ya gaya maka dukka wannan?". A karo na biyu mamaki ya bayyana a saman fuskarta. Gyara tsayuwarsa ya yi, ido cikin ido ya kalleta, babu ko shakka, duk wasu shakkarta dake cikin kwayar idanunsa sun kau, cike da rashin tsoro ya furta. "Okey mamma daman kenan da gangan kika ɓoye mun dukka waɗan nan abubuwa da kika tambayi waye ya gaya mun su? Kenan kin san komai kika reneni cikin duhun kai?! Sai kika koya mun ilimin da ba amfanata zai yi ba, wanda zai amfaneni kuma sai kika ɓoye mun kika ki sanar da ni, to amma kin tabka babban kuskure da kika koya mun reading, na iya karatun da zan karanta storys, sannan kin yi kuskuren ajiye litattafai a ɗakinki da har na gani na karanta, ni yanzu dukka bama wannan ba, ki gaya mun ina babana yake tun da kin san komai......." Tashin hankali, wani irin zaro idanu ta yi, bata taɓa zaton abin zai kai masu haka ba, wani irin bugawa da zuciyarta ya yi ne yasa cikin hanzari ta dafe saitin kirjinta, kanta har juya mata yake yi jin ya ambaci ina babansa? Nan take ta ji jiri na ƙoƙarin ɗibarta. "Ki bani amsata! Where's my father? Yau ina son sanin wanene ni?!". "Kamran ni kake yi wa magana haka?". Babu ko shakka ya gyaɗa mata kai. "Yes Mamma ke nake yi wa magana haka, kawai amsa my questions...." Wani irin zufa ne ya fara tsastsafo mata a gefe da gefen face ɗinta, ji ta yi duniya ya yi mata zafi, nadamar hanashi tafiya neman Prettyn da ta yi ta fara yi, yanzu ga shi allura tana ƙoƙarin tono mata garma. "Kamran baka da wani baba sai ni, ni ce kaɗai kake da shi, dan haka kada ka sake yin magana a kan hakan......" "Mamma i knew everything now! Mace bata taɓa haihuwa ita kaɗai! Dole sai da namiji! Dan haka tell me where's my father?!". Shiru ta yi ta kasa iya sake buɗe baki, ta rasa me zata ce da shi. "Mamma ki bani amsar ina babana!!......". Ya faɗa da karfi. Katse shi ta yi cikin ɗaga murya. "Idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu, zaka mutu Kamran....." Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon yadda ta yi maganar cikin tsarguwa da alamun rashin gaskiya ya bayyana sosai a tattare da ita. "Mamma koma me zai faru ni dai ki gaya mun ina babana? Wanenen ni? Ina familyna suke! Yanzu duk nasan komai". "Kamran wai wani maci amanan ne ya gaya maka dukka wannan? Wani azzalumi ne yake son raba uwa da ɗanta?! Wani bakin mugu ne wannan?! Waye ya ce maka kana da baba? Waye ya koya maka wannan karatun?! Ka gaya mun shi!". Cikin tsawa ta yi maganar. "Mamma ni kawai ki faɗa mun ina babana? Idan kika faɗa mun zan faɗa maki daga baya sai ki yi duk tambayar da zaki yi, yanzu dai ina babana? Wanenen ni". To fa yanzu an bar maganar zuwa neman Pretty ma, abu ya ɗau zafi kenan, mamma ta tonawa kanta bala'in da yake ƙoƙarin fin karfinta, saboda kafiya da kafurar zuciya irin tata ga shi yanzu ta ja wa kanta yaronta na cikinta yana jayayya da ita, abin da bai taɓa yi ba, bata taɓa yin magana ya tsaya yana mayar mata da martani ba sai yau, yau ɗin ma ya tsaya yana kallon cikin kwayar idanunta yana faɗa mata magana dai'dai gwargwado, Hasbunallahu wani'imal wakil, duk abin da ya faru ita ta jawa kanta, ai yaro ba'a yi mashi kafiya irin haka, barema shi da ya girma har haka? Ai yama yi kokarin na danne son sanin wanenen babansa da ya yi na tsawon lokaci, kowani ɗa zai so ace ga babansa a tare da shi suna zane cikin farinciki, amma saboda biyayya da kaunarta da yake yi yasa ya danne bai buƙaci lallai sai ta faɗa mashi in da baban nasa yake ba, ya hakura ga shi yanzu ta ja yana fito na fito da ita a kan hakan. Wani irin yawun wahala ta haɗiye, ji take maƙogoronta ya yi wani irin bushewa da jin tambayoyin ɗan nata, yawun bakinta ya kafe kamar mai yin azumi, da kyar take iya kakalan yawun ta haɗiye, da kyar ma yake wuce maƙogoronta, ji take maƙogoron nata kamar an toshe mata shi ne. "Kamran idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu nace maka, mutuwa kuma mafi muni a rayuwa, kamar yadda ka taso baka san kowa ba, sai ni, to haka zaka riƙe ka manta da duk wasu tunanin banza". "But Mamma why? I want to know my father ko da kuwa hakan ce zata zama sanadiyar numfashina na karshe, just tell me where's he? Ni zan je in da yake koda kuwa ya fi wuta zafi dole na tinkaresa!! Na kusancesa!!". Tsawa ta daka mashi mai sauti, cikin fusata, idanunta sun kaɗa sun yi jajir, jijiyon kanta har wani mimmikewa suka yi, da alama ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci take yi kamar zakanya. "Kamran ina gaya ma zaka yi mutuwar walaƙanci in dai ka sake yin magana a kan babanka! Kai ba mutun ne kamar kowa ba! Kai ba kamar sauran mutane kake ba! Kai na daban ne, farautarka ake yi kamar yadda ake karautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana! Zaka mutu idan ka fita! Zaka! Dan haka ka tsaya a in da na tsayar da kai!!". "Mamma i can't! I can't gaskiya! Idan kuma kina son na bi maganarki so tell me who I am?! Where's my father and my family?! Why are you hiding our life anytime?! Am tired! Am tired Mamma! I want to see my father and my family, cos I can't stay with you again! Tafiya zan yi na nemo babana and Prettyta even wannan shi ne ganina dake ta karshe!"......... Tashin hankali. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E__________________3🔥 Wani irin gigitacen mari ta sake dallah mashi wanda ya sanya shi yin tangal tangal kamar zai faɗi ƙasa. Cikin ƙunar rai ta ce. "Babu in da zaka je! Daga yau idan ka sake yi mun magana a kan babanka ko wasu banzaye can tsinannun da suka kurɓata maka tunani sai ranƙa ya ɓaci fiye da tunaninka, ni kaɗai kake da shi a duniya, dan haka ka goge komai dake cikin ranka, daga yau ma ba zaka sake fita ko nan da can ba..." Ta kai karshen maganar cikin tsananin ɓacin rai tana furzar da huci mai zafi, tana kai karshen maganar kuma ta finciki hannunsa da karfin tsiya har sai da ya furta wash da karfi. Cikin fusata ta jashi da karfin gaske suka kama hanya, azaban zafin jikinsa yake ji saboda fincikarsa da ta yi da karfi, ciwon da damisar ta ji mashi wajen duk yana yi mashi raɗaɗi, amma haka ta cigaba da fincikarsa har suka isa gida. Zuciyarsa tafasa take yi mashi, gabaɗaya gaɓɓan jikinsa yana yi mashi ciwo. Wani ɓangare na zuciyarsa tana gaya mashi ya tirge yaki binta, ya bijirewa maganarta kawai ya gudu ya tafi neman Pretty da babansa amma kafin nan ya fara zuwa ya duba lafiyar Sweetien da yake tunani tana cikin ramin can. Ɗayan ɓangare na zuciyar tasa kuma tana ƙara gaya mashi girman uwa, tuna mashi da irin fafutuka da famar da Mammar ta yi a kansa take yi, tunawa ya rinƙa yi da yadda ta sha wahala a kansa, ta sadaukar da komai nata dan shi, har rayuwarta ta sha sanyawa a haɗari dan ta ceci tasa rayuwar, a yanzu idan ya bijire mata sam bai yi mata adalci ba, a yadda kuma yake karatun Alkur'ani yake karanta fassararta da English yasan cewa in dai ya yi wa Mamarsa haka Allah ba zai barshi ba, uwa ta wuci wasa. Amma kuma yana son sanin babansa, yana son sanin ƴan uwansa, zuciya bata da kashi, ba zai iya hakura bai je ga su Pretty ba, ba zai iya hakura bai nemo in da take ba. Wasu irin zafafan hawaye ne suke bin ƙuncinsa, a tunanin mammar saboda marin da ta yi mashi ne yasa yake wannan kukan, bata san cewa shi ko zata ɗaure shi ta kwana tana dukansa in dai zai rayu da safe ta rabu da shi ya je ga Pretty da babansa zai yarda da hakan ba, sam bai ma ji zafin marin da ta yi mashi ba, azaban zafin dake cikin zuciyarsa ta take zafin marinta. Raɗaɗi zuciyarsa take yi mashi, ya rasa mafita. Haka ta cigaba da jansa har izuwa cikin ɗakinsa. Da karfi ta turashi ya faɗa saman gadonsa, da alama ta manta da cewa yana da ciwo a jikinsa, ɓacin rai ya rufe mata idanu bata ganin komai face ta san yadda zata yi ta hana shi ko leƙa waje......... Lalla Mamma ta ɗebo da zafi, da karfi da ya ji zata raba soyayyar da Allah ya haɗa, Allah ne ya sanyawa Kamran kaunar Pretty, ba dan komai yake sonta ba face dan Allah, shi kansa ko kashe shi zaka yi ka tambayi meyasa yake sonta sai dai ka kashe shi, dan ba zai baka dalili ko guda ɗaya ba, saboda tun ranar da ta faɗo duniya, ko cibiya ba'a yanke mata ba, a haka yana ɗaura idanunsa a kanta zuciyarsa ta kamu da kaunarta, a wannan lokaci me zai so? Shiyasa nace maku ba dan komai yake sonta ba face dan Allah, son da yake yi mata kaddararsa ce, a tare aka haifesu da Sweetie, meyasa bai taɓa jin son Sweetien ba sai Prettyn? Dame tafi Sweetie? Babu abin da ta fita da shi, amma a haka zuciyarsa ta kafe Pretty take so while ita kuma Sweetie tana sonsa, son yaya da kanwa kawai yake yi wa Sweetie, Pretty ce kaddararsa, ita farincikinsa, sau ɗaya ya ganta ranar da aka haifeta, a ranar ya ɗauketa da hannunsa, ya ceci rayuwarta, tun daga lokacin kuma sai da ya shafe shekaru goma bai sake ganinta ba, amma dai'dai da rana ɗaya bai taɓa mantawa da ita ba, kullum tana cikin tunaninsa, a tsawon waɗan nan shekaru da suka yi basu tare kullum yana cikin ƙunci da damuwar rashinta, ya zo ya ganta sun sake sabo, har soyayyarta mai zafi fin na baya ya kara shigansa, sun saba, ita ma tana son kasancewa a tare da shi kullum, rana tsaka kawai mamma ta rabasu? Ta ce kada ya sake fita ma bare ya nemosu? Yanzu bashi da tabbacin suna mazauninsu ko basa nan? Bai san ina takamaimai suke ba, wannan abin da taɓa zuciya, anya zai yarda da hakan kuwa? Ku dai kun san yadda yake jin sonta a ransa. Cusa kansa ya yi cikin katifar tasa, wani irin kukan zuciya yake yi mai tsuma rai, har wani irin shessheka yake yi kamar wanda ake zarewa rai, ji yake yi kamar zai iya haɗiyar zuciya ya mutu, gabaɗaya zufa ta wanke mashi jiki. Ko kaɗan a wannan lokaci mamma bata ji tausayinsa ba, ta ɗauka soyayyar wasa yake yi wa Pretty, dan tana ganin kamar bai san menene so ba, ta ɗauka haɗuwar yau ce kawai ko na ƴan kwanaki, bata san sun jima a tare ba tare da saninta ba, batasan soyayyar bata wasa bace, sannan bata yanzu bane, soyayya ce da ta faro tun ranar da aka haifeta, rashin sanin daraja da mutuncin soyayya yasa sam bai bata tausayi ba. Da alama zuciyar mamma ya rigada ya bushe, ta kekashe bata jin tausayin komai da kowa, har shi kansa ɗan nata bata tausaya mashi, ashe ba'a banza take bashi irin horon da take bashi ɗin nan ba, babu tausayi a ranta yasa komai magiyar da zai yi mata a kan ya gaji ta bari ya huta, amma bata ɗaga mashi kafa har sai ya cike lokacin da ta ɗeba mashi, bawan Allah. Tana jin irin kukan da yake yi mai tsananin ratsa zuciya, amma ta yi burus da shi tasa kai ta fice daga ɗakin. Kai tsaye waje ta nufa domin ta samo igiya irin na jijiyar itace mai karfi ta ɗaure shi, dan ta ci alwashin ba zai sake fita waje ba bare ya je gurin waɗansu har su sake kurɓata mashi tunani. Kukansa ya cigaba da yi yana addu'ar Allah yasa ya mutuma kawai ya huta, dan zuciyarsa ba zata iya jure rashin Pretty ba, ga tunanin Sweetie da yake a ɗayan ɓangaren zuciyar tasa, yana tunanin makantar nan nata, yanzu idan Pretty ta ɓata ita kuma ya zata yi? Yasan da wuya Pretty ta iya dawo da kanta cikin wannan ramin nasu, dan hanyar da ta bi ma sam sam bashi da haɗi da in da suke, dajin nan yana da girma kuma yana da haɗari, akwai namun dawa sosai a cikinsa, da wuya Pretty ta iya kai labari, da wuya ta rayu in dai ta cigaba da tafiya a kan wannan hanya da take, tunani yake ya Sweetie zata rayuwa ba mai yi mata jagoranci zuwa in da take da buƙata kamar yadda Pretty take yi mata?. Addu'a yake yi Allah yasa wannan sadaukin ya haɗu da Prettyn ko kuma ta haɗu da mai tamakonta. Tun yana iya kuka mai sauti har sautin ta dai'na fita, ban da ruwan hawaye babu abin da yake fita daga idanunsa. Babban damuwansa ma amanarsu aka bashi, bai riƙe amana ba, ya karya yardan da aka yi mashi, idan ya tuna da hakan sai kara rushewa da kuka, yarda da shi yasa mum twins ta bar sakon ta bashi amanarsu, ta san zai iya riƙesu ne yasa ta bashi, amma ga shi yanzu mamma tasa ya kasa cika amanar da ya karɓa. Saboda tsananin sabo da yake a tsakaninsa da Rocky ne yasa Rockyn ya zo bakin kofar ƙogon yana ta zuba masu kurnani, da alama yana jin kamar Kamran ɗin bashi da lafiya ko wani abin makamancin haka, kun san fa ita dabba idan ka yi sabo sosai da ita sai ku zama kamar twins, bare shi da a gabansa aka haifi Kamran ɗin, tun Kamran yana jariri suke tare, ai dole ma ya ji hakan a jikinsa. Ko da Mamma ta dawo hannunta a ɗauke da igiyoyi masu karfin gaske, a bakin kofa ta isko Rocky, kun san ba zai iya shiga ciki ba. Yana ganinta ya nufeta yana gurnani. Sarai ta san me yake yi wa, amma sai ta yi kamar bata sani ba, ta sharesa zata wuce. Tsalle ya fara yi yana kama jikinta alamar baya son ta tafi. Sam taki yarda ta bi ta kansa, sai ma ture shi da ta yi ƙoƙarin yi ta wuce, hakan yasa ya yi tsalle sosai zai capketa, da sauri ta wuce ciki ta barsa. Ai kuwa da karfinsa da Allah ya basa ya fara ƙoƙarin lallai sai ya bita cikin wannan kogon yau, sai dai ina, kogon dutsene mai karfin gaske, wane shi ya iya fasata ya shiga, haka ya rinƙa gurnani yana tsalle ya bugi jikin kogon har ya jiwa kansa ciwo. Har cikin ransa Kamran ɗin ya ji zafin wannan ciwo da Rocky ya ji, haka kawai ya ji zuciyarsa ta tsananta zafin da take yi mashi, hakan yasa ya fahimci lallai wani abin yana faruwa da wanda yake kauna, so sai ya ɗaura zarginsa a kan Pretty, ya yi tunani ko itace wani abin yake faruwa da ita, sam bai kawowa ransa Rocky ne ya ji ciwo ba, dan baya tunanin akwai wanda zai zalinci Rocky ko ya yi mashi wani abin a wannan dajin, shiyasa sam bai kawowa ransa shi ɗin bane. Da gaske babu tausayawa Mamma ta haɗa kafafunsa dukka biyu ta ɗaure yana daga kwance. Yana jin duk abin da take yi mashi, amma ko kwakkwaran motsi bai yi ba bare a sa ran zai tirje mata, shiru ya kwanta yana cigaba da kukan zucinsa, irin wannan kuka babbar haɗari ce kuma babban barazana ce ga lafiyar ɗan Adam, tana taɓa zuciya, kuma tabbas mamma ta san da haka, amma gudun kada ya fita ya ce zai tafi neman babansa yasa ta danne duk wani zafin da take ji a zuciyarta na kukan da yake yi ta ɗaure shi hannu da kafa. Ko kaɗan bata yi ƙoƙarin rarrashinsa ba, saboda tana ganin kamar idan aka kwana biyu haka shikenan zai sauko ya hakura da komai ya kuma manta komai su koma kamar da, wannan dalilin yasa bata yi ƙoƙarin rarrashinsa ba. Allah sarki rayuwa kenan, waɗan nan bayin Allah ya suke ji a cikin ransu?. Sweetie da Pretty da suka kwanta ciki ɗaya, aka haifesu tare, suka sha nono tare, basu taɓa rabuwa da juna kona wuni ɗaya ba, koda yaushe suna tare, suna kaunar junansu fiye da tunaninku, basu da kowa sai junansu, rana tsaka aka rabasu, ko ya Pretty take? Ta mutu ko tana da rai? Ina Sweetie?. Shi Kamran da ya zo ya samesu a tare ma ya ji zafin rabuwa da su har haka bare kuma su da suke tamkar chewing gum da gashi, hanta da jini, kun san idan chewing gum ya manne gashi baya saki gabaɗaya, haka zalika hanta bata rabuwa da jini, to haka Sweetie da Pretty suke. Fatana dai Allah yasa suna da rabon sake ganin juna, Allah ya haɗa fuskokinsu. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 1:30 Am. Karfe ɗaya da rabi na dare. Kwance Gimbiya Chuchu take a saman gadonta bayan ta kammala wayar da take yi da Rizwan, har 12:30 suka kai suna waya, sai zuba mata kalaman soyayya yake yi, yana ta kara sanya zuciyar baiwar Allah tana narkewa a sonsa, yau Yah Jawad bai zo in da take ba sam sam, da alama akwai abin da ya riƙesa, tun safe da ya kaita school sai kuma da daddare da suka haɗu a dining room ya rinƙa tsokanarta ta ƙasan table kamar ranar har sai da ta kusa saka mashi kuka sannan ya rabu da ita ta ci abinci. To tun lokacin ba su sake haɗuwa ba, tana kewarsa sosai da sosai. Barci na ƙoƙarin ɗaukarta sai ji ta yi an turo kofar ɗakin nata. A hanzarce ta juyo da kallonta izuwa kofar ɗakin nata. Sanye yake da single fara tas, sai short da bata wuci zuwa tsakiyar cinyarsa ba, gashin kansa a hargitse sosai, kamar wanda ya taso daga barci ko kuma wanda ya fito daga gidan mahaukata ko dai wanda aka yi wa kirso aka warware ba'a taje an gyara ba. Zaro idanu ta yi tana kallonsa da mamaki ta kasa yin magana, ita dai tasan wlh Yah Jawad baya yin irin wannan dressing ɗin ya fita haka, ko part ɗinsa suka je idan babu full kaya a jikinsa baya basu izinin shiga room ɗinsa har sai ya zura jallabiya a jikinsa, amma yau sai ga shi tsakar dare da irin wannan shiga, ga kansa kamar bayan bushiya, duk ya wargaje gashin, yanayinsa ma kamar wanda ya yi tatul da giya, dan har wani layi layi yake kamar zai faɗi. Zabura ta yi ta miƙe zaune tare da faɗin. "Yah Jawad lafiya? Meyasa baka yi barci ba?". Wani irin mayen kallo yake binta da shi wadda bata taɓa ganin ko da sunan wasa ya yi mata irinsa ba. Haka kawai ta ji wani irin tsoronsa ya dira mata. Kallonta yake yi kamar zai cinyeta ɗanya. Ta yi magana almost baki biyar, amma yaki tanka mata, murje idanunta ta fara yi domin ta tabbatar bafa mafarki take yi ba. Duk murje idanun da zata yi tana cire hannu sai ta ganshi a tsaye yana dai cigaba da binta da wannan mayen kallon. Dallawa kanta mari ta yi duk dan ta farkar da kanta daga barcin da take yi a tunaninta, dan ta kasa yarda cewa zahiri take gani. Ko da ta mari kan nata ma still dai shi ɗin ne a tsaye da gaske ba mafarki ba. Kamar wani tsohon maye ya fito da harshe ya ɗan lashi red lips ɗinsa yana binta da mayen kallo. Ƙara tsorata ta yi da ganin hakan. Ai bata san lokacin da ta diro ƙasa daga saman gadon ba, duk ta ruɗe, jikinta nan take ya fara kermar tsoro, hankali a tashe ta nufi in da yake, a cewarta zata fice daga ɗakin ta bashi waje, dan kada ya yi mata wani abin duk da cewa har yanzu ta kasa yarda cewa ba mafarki take yi ba. Tana zuwa kusa da shi da nufin ta raɓa gefensa ta wuce, sai zuba sauri take yi jiki na kerma. Da hannu ɗaya ya fisgota ta faɗa saman kirjinsa. Tsoro ne ya kara kamata, zuciyarta na dukan uku uku kamar zai fasa kirjin nata, jiki sai kerma yake yi. Murya na rawa ta ce. "Yah Jawad wajen Momma zan je". Kara matseta ya yi a jikinsa. Da jin haka sai ta fara ƙoƙarin kwatar kanta, da karfi ya ƙanƙameta kamar zai ɓallata. Ƙoƙarin kwala ihu ta yi, toshe mata baki ya yi da karfi yana ƙoƙarin cire mata kayan jikinta. Izuwa yanzu gabaɗaya tsoro ya gama dabaybayeta, karfi tasa tana ƙoƙarin kwatar kanta. Ai kuwa haka ya haɗe hannayenta dukka biyu ya riƙe da hannunsa ɗaya, ya matse mata baki da ɗayan hannunsa, haka ya jata izuwa saman gadonta, tirgewa take yi a kan ita ba zata hau gadon ba, sakin hannayen nata ya yi da nufin ya ɗagata cak ya wurga a gadon. Ai kuwa yana sakinta ta samu hanya ta watsa a guje zata fita. Da gudu ya bi bayanta ya damkota, wage baki ta yi zata kurma ihu, a ɗari ya kai............. Ko me ya shiga kan Yah Jawad yau kuma? Anya lafiya yake kuwa? Fyaɗe yake ƙoƙarin yi mata kenan? Meya fito da shi karfe ɗaya na dare? Anya bai sha wata kwayar ba?. (To ni dai na ce su twin's Obaid and Omaid basa nan bare na ce ya yi masu ba dai'dai ba sun yi mashi wata tsiyar da suka saba😅) 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 17/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E_________________4 Ai kuwa yana sakinta ta samu hanya ta watsa a guje zata fita. Da gudu ya bi bayanta ya damkota, wage baki ta yi zata kurma ihu, a ɗari ya kai ya rufe mata bakin. Ƙoƙarin rabata da kayan jikinta ya fara yi ta karfin tsiya. Ai kuwa ta gartsa mashi cizo a hannu da karfin gaske har sai da ya saketa ba shiri, dan ta fasa mashi fatar hanni. Ihu ta kurma tare da ƙoƙarin gudu a karo na uku. Sake damkota ya yi da karfin gaske, hannunsa in da ta cijesa sai jini yake yi, wani ihu da ta daddage ta kurma da iya karfinta na karshe ne ya daki dodan kunnen momma dake zaune a saman dadduma tana karatun Alkur'ani mai girma. Sosai ihun ya daki dodan kunnuwanta, da yake room ɗin chuchu and auta a part ɗin ta yake, Chuchun tana da ɗaki a part ɗin mummynta ma, amma ta fi kwana a part ɗin momma, ita fa renon Momma ce, bata shaku da mummynta kamar yadda suka shaku da Momma ba, shiyasa ita da Auta akwai amana sosai, tare suka taso ne. Shiru mommar ta ɗan yi tana tunanin ihun Auta ne ko na Chuchu? Dan voice ɗinsu kusan iri ɗaya ne saboda tsananin shakuwa, kuma ai jini ba wasa ba, mamaki momma take yi a kan ihun me suke zundumawa cikin tsakar daren nan. Tana tsaka da tunanin ihun ya kara dira a kunnenta a karo na biyu, a wannan karon ihun haɗe yake da kuka, da alama kuka take yi, cikin nutsuwa Mommar ta rufe Alqur'anin dake hannunta, sannan ta miƙe tsaye, door room ɗin ta nufa da nufin ta fita waje izuwa wajensu taga me yake faruwa?. A hankali ta murɗa handle na kofar da nufin ta buɗe ta ta fita. Sai kuma me? Sai jin kofar ta yi a datse kamar an datse shi da keys sama da goma, kofar a datse take gam gam tamkar ba'a taɓa yin amfani da ita bama. Gabaɗaya gidan babu wanda ya ji ihun da Chuchun take yi kuma sai ita Mommar kawai, ita ma dalilin ɗaya zuwa biyu ne yasa ta ji, na farko bata yi barci ba, na biyu kuma karatun Alkur'ani da take yi ya kore duk wasu shaiɗanun da suke arear room ɗinta waɗan da zasu iya hanata jin ire iren hakan, wannan dalilin yasa ta ji ihun. Sake murɗa handle ɗin ta yi da karfi a ƙoƙarinta na buɗewa, amma ina kofar taki buɗuwa, mamaki ne ya kamata sosai, haƙiƙa tasan ire iren wannan abin yana faruwa da ita, shiyasa tun farko da ta ji ihun Chuchun bata ɗaga hankalinta ba, dan tana tunanin irin abubuwan da ake yi mata a baya ne yanzu abin ya sake dawo mata, idan baku manta ba a baya ana yawan yi mata ihu ko kuka da muryar Gimbiya Zunaira, so yanzu ma ta ɗauka hakance, sai dai abin da ya bata mamaki shi ne, ba'a taɓa riƙe mata kofar ɗaki ba, gara ma na toilet. Karfi ta sanya wajen sake gwada buɗe kofar, amma ina abin ya ci tura, tun daga nan ta fahimci ba lafiya ba, tun daga nan hankalinta ya yi mugun tashi, tasan koma waye mai wannan ihun yana tsaka mai wuya, kuma ba lafiya. Sautin ihun ne ya kara dokan dodan kunnuwarta a karo na uku, hakan yasa hankalinta ya kara tashi, jikinta har tsuma yake yi, burinta kawai ta je taga me yake faruwa saboda karfin hali, babu tsoro a tattare da ita. Da sauri ta juya ta koma wajen bed ɗinta, wayarta ta ɗauko jiki na kerma, har wani tsuma take yi. A hanzarce take daddanna numbers ɗin da take buƙatar kiran, bayan ta gama shigar da number sunan my world ne ya bayyana. Kira ta danna mashi, amma ina kirar taki tafiya, sai wayar ma ya nuna mata sam babu network, da ta matsa ma sai wayar ta ɗauke gabaɗaya. Wurgi da wayar ta yi a saman gadon, a hanzarce ta juya ta koma bakin door ɗin, jikinta na kerma ta fara karanto duk adduar da ta zo bakinta, da karfi ta sanya hannu tana jan handle ɗin kofar tana rero addu'a. Cikin ikon Allah kofar ta buɗe, kamar wadda bata da cikakken hankali haka ta nufi waje. Kai tsaye ɗakin Auta ta fara nufa, tana buɗe kofar ta hangota kwance a saman gado, wutar lamp ya haske kyakkyawar face ɗinta, sai sharara barci take yi cikin kwanciyar hankali. Da sauri ta janyo kofar ta rufe mata tare da nufar ɗakin Chuchu. Murɗa kofar ta yi domin ta buɗe, amma sai kofar taki buɗuwa, tamkar yadda kofar ɗakinta ya yi haka shi ma wannan ya yi. Kofar a datse gam. Gabaɗaya jama'ar gidan barci suke shararawa kamar gawarwaki, duk abin da yake faruwa basu ji ba, shi kuwa King da bai yi barci ba yana saman dadduma part ɗinsa yana da ɗan nisa da nasu, akwai ratar da ba zai iya jiyo su ba, hakan yasa bai ji me ake yi ba. Ganin kofar a rufe kamar yadda nata ya yi ruf ne yasa ta gane cewa lallai lallai akwai matsala, ya fahimci daga ɗakin Chuchun wannan ihun yake fitowa. Addu'a ta fara yi tana tura kofar da karfi karfi!. Ta ɗauki almost 5 mins a wajen kafin ta samu kofar ta buɗe, kasancewar da karfi karfi take tura kofar sai yasa da kofar ta buɗe ta kusa faɗuwa kasa, da karfi ta shiga cikin ɗakin a tare da kofar. Jujjuya fararen idanunta ta fara yi tana bin ko'ina da kallo. Tsit ɗakin ya yi kamar babu kowa, a hankali hankali shesshekar kukan Chuchun yake tashi, tana kwance a saman gadon, ta yi ruf da ciki, kayan barcin jikinta duk an yagesu kamar wadda ta yi faɗa da damisa, fuskarta gabaɗaya ya yi jaga jaga da hawaye baiwar Allah, har da majina. Mamaki da al'ajabi ya hana Mommar motsawa daga in da take tsaye, ta rasa me zata yi, ganin abin take yi kamar a mafarki, ga shi dai bayan Chuchun babu kowa a cikin ɗakin. Ni kam na ce toh ina Yah Jawad ɗin?. Ta jima a tsaye tana bin ɗakin da kallo, sai jujjuya idanu take yi, jin sautin shesshekar kukar Chuchu yana kara karuwa ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka. A hankali ta ɗaga kafarta ta fara takawa. Kai tsaye wajen bed ɗin ta nufa. Cak ta tsaya a tsakiyar ɗakin sakamakon motsin da ta ji kamar mutun ne a bayanta. Fargabar juyawa ta ji gudun abin da zata gani, ga shi kuma tsakar dare ne sosai, a lokacin almost karfe ɗaya da minti talatin. Wani irin kasala da tsoro ne ta ji ya rufeta, a hankali ta fara jiyo sautin kuka kamar na mage a kunnuwarta ta baya. Ajiyar zuciya ta sauke tare da furta Hasbunallahu wani'imal wakil. Nan take ta ji kwarin gwiwa da kwarin zuciya ya ziyarceta. Da karfi ta juyo domin ta ga me yake motsi a bayanta?. Sai dai ko da ta juyo bata ga komai ba. Sake sauke wani ajiyar zuciyar ta yi tare da ɗaga kafafunta ta cigaba da tinkarar gadon. A karo na biyu ba ta ƙarisa isa wajen bed ɗin ba ta sake jiyo takun sahun mutun a bayanta yana biyota. A wannan karon cikin sauri ta juya. Ai kuwa tana juyowa wani irin haske ne ya kashe mata idanu, yadda kuka san an dalla mata wutar fitillah mai bala'in haske. Karfin hali irin nata yasa bata datse idanunta ba, cigaba da zarosu ta yi a cikin wannan haske. Wani irin idanu ta gani a cikin haske, green eyes irin masu hasken nan ta gani, ga idanun dara dara suna bala'in kyalli, idanu kawai ta iya gani, sam bata ga mamallakin idanun ba, bata ga face ɗinsa ko face ɗinta ba, idanu kawai ta gani suna yawo a cikin wannan hasken. Da yake akwai ta da karfin hali da jajircewa sai ta kara zaro idanunta tana kallon wannan idanun ido cikin ido, babu ko tsoro a ranta, da alama ta saba da irin waɗan nan masifun sosai, gidan King zama cikinsa sai masu karfin imani da kuma karfin hadda dan faɗa da shaiɗanu, idan ba haka ba kana cikin gararin, dan idan ka yi ba dai'dai ba da daddare ba kai ba barci............ A takaice dai duk yadda aka yi a tsoratar da ita ta gudu abin ya ci tura, ba su san da jinin Modarawa suke tare ba, ai Modarawa basa gudu kuma basa ja da baya, duk wuya duk daɗi, komai bala'i sai sun isa in da suka tinkara matikar Allah ya basu tsawon kwana, so basa ja da baya bare gudu, bare kuma ita Momma da take da shegen karfin hali kamar Akka ce ta haifeta, ko da yake babanta ai yayan Akkar ce, Husaininta ne, so fin haka ma zata aikata. (Ni kam my people's zan so ganin Akka na yaki😅 wato tarihin Akka a lokacin ƴanmatantaka fa zai bada citta 🤔🌝 dan haka kada ku ga laifin su Omaid, sun gada ne har ya yi masu yawa, ta gefen uwa da uba dukka ba sauki, kun ga su Chuchu ai suna da mix, dan mummy ba jinin Akka ba ce, ba jinin Modarawa bane, amma su twin's fa? Gaba da baya jinin Akka ce ke gudana a jikinsu, uwa ba sauki haka uba ma, sannan kakarsu ta gefen uba, ta gefen uwar ma duk tsatso ɗaya ne da gefen uban, ai kunga su kam sai shirin Allah kawai, sai abin da kuka gani, Zunaira ce kawai ta fita zakka a cikinsu, ita ce mai sanyi hali sai Guyson da sai ka taɓo shi yake faɗa, su twin's kuwa ba sai ka taɓosu ba, idan baka burgesu bama sai sun maka azaba😅) Da dai suka fahimci ba zata tsorata ba, sai suka yi ƙoƙarin canza salo ta hanyar sanya mata kuka da muryoyi kala kala dan su doɗe mata kunne ta dai'na jin sautin komai. A nan ne ita kuma ta fara rero masu karatun Alkur'ani mai girma na duk wata sura da ta zo bakinta. Ai kuwa ko aya ɗaya bata gama karantawa ba wannan haske ya ɓace ɓat, nan take ɗakin ya yi wani irin tsit, sai a lokacin ita ma Chuchun ta iya ɗago kanta daga kifuwar da ta yi a saman gadon. A zabure ta miƙe zaune, jikinta sai kerma yake yi, wani irin razana ce bayyane a saman face ɗinta, da alama ta tsorata sosai, a ruɗe take bin ɗakin da kallo kamar mai neman wani abin. Tana sauke idanunta a kan Mommar ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, da gudu ta diro ƙasa daga saman gadon. Tana zuwa ta faɗa jikin Mommar tana kara tsananta kukanta. Ita kuwa Momma ta yi shiru tana ƙoƙarin fahimtar wani abin, sai da Chuchun ta faɗa jikinta ne ta sauke ajiyar zuciya tare da rungumeta. Cike da al'ajabin abin ta fara tambayarta me ya faru?. Kuka take yi sosai ta kasa iya yin magana, ganin haka yasa Mommar ta kara rungumeta sosai tana ɗan bubbuga bayanta, a haka suka nufi room ɗinta. A saman gado ta zaunar da ita, sannan ta janyo bargo ta lulluɓeta da shi. Har lokacin jikinta na kerma, gani take kamar Yah Jawad ɗin yana nan. Da kyar Mommar ta iya lallaɓata ta yarda ta kwanta, bayan ta kwanta ne Mommar ta miƙe ta ciro mata wasu kayan barcin Auta da suke ɗakin nata. Da kanta ta sanya mata su sannan ta tofa mata addu'oi, bayan ta kammala sai ta haye gadon suka kwanta tare. Ba jimawa barci ɓarawo ya yi awon gaba da Chuchun, ita kuma Momma kamar yadda taga rana haka ta ga dare, sai tunani take yi a kan to me yafaru? Waye ya yi yunkurin yi wa Chuchun fyaɗe? Ga shi har an rabata da kayan jikinta gabaɗaya saura pant kawai, sosai ta afka duniyar tunani a kan wanenen? Meyake faruwa? Dan dai ita bata ga mutun ba a ɗakin da ta shiga, ko dai da ya ji motsin fitowarta ne ya gudu? Ko kuma ya ɓuya a cikin toilet ko wani wajen?. Haka dai ta rinƙa tunane tunane har asuba. Washegari da safe da zazzaɓi mai zafi Gimbiya Chuchu ta farka, jikinta zafi kamar wuta, da alama zazzaɓin firgici ne, ta ƙasa iya tashi ma, ko sallar asuba a kwance ta yi bayan Momma ta yi mata alwala kenan. Sai kuka ƙasa ƙasa take yi saboda zazzaɓin, da alama bata da juriyar ciwo, tana da raki sosai. Sosai momma ta rinƙa rarrashinta, da kyar ta samu ta yi shiru, miƙewa ta yi da nufin ta je ta sanar da King batun zazzaɓin. Zata fita kenan a bakin kofa suka ci karo da Auta tana shigowa, gaisuwa ta ɗaga mata, cigaba da tafiya ta yi tana amsa gaisuwar. Ko da ta je part ɗin King sai ta isko shi a tare da Mummyn Chuchun da kuma Yah Jawad sai Aunty MieMie suna hira, gaisuwa ta ɗagawa King, bayan ya amsa ta gaishe da mummyn ma, sannan Yah Jawad da Aunty MieMie suka ɗaga mata nasu gaisuwar. Cikin nutsuwa ta sanar da King abin da yake faruwa na Chuchu tana zazzaɓi, amma bata sanar da shi abin da ya faru a daren jiya ba, ta ɓoye saboda dalilin ɗaya zuwa biyu, ba wani dalili bane kuma face ta yi tunanin koma wanenen ya shiga ɗakinta ya yi ƙoƙarin keta mata mutunci to ɗan gidan ne, dole kuma tsakanin Jawad da Jaish ne, ita bata san Jaish baya nan ba, so ta ce dole tsakanin su biyun nan ne, dan sune kawai mazan gidan da suke nan, wannan dalilin yasa ta yi shiru bata yi maganar ba, tana son idan Chuchun ta samu lafiya sai ta tambayeta wanenen ya yi ƙoƙarin yi mata hakan? Idan ta gaya mata sai ta san matakin da zata ɗauka, wannan dalilin yasa ta yi shiru bata yi magana ba. King ya ce mata yana zuwa ya duba jikin nata, Aunty MieMie da Yah Jawad suka miƙe tare da faɗin bari su dubo jikin nata, mummy dai tana zaune bata ce ko uppan ba, kamar Chuchun ba yarta na cikin ta bace, da alama tana da alkunya da kawaici sosai, tun da taga momma ta tsaya a kan rashin lafiyar ƴar tata sai ta kawar da kanta kamar bata jin zafin a kirjinta, alhalin kuma ta shiga damuwa sosai. "Raeesa ki zauna akwai maganar da zan yi dake, idan mun kammala sai mu dubo jikin nata kafin na wuce fada". Cewar King, ya yi maganar ne kuma da Aunty MieMie, ita ce sunanta na gaskiya Raeesa, MieMie kawai sunan gida ne da mummyn tasu ta sanya mata, kasancewar ita ce ƴar farin mummyn shiyasa bata kiranta da Raeesan ta sanya mata MieMie, da haka sunan ya bita har izuwa yanzu, Raeesan ma ya ɓace, King ne kawai yake kiranta da sunan, da yake shi da sunansu da ya yanke masu yake kiransu dukkansu, Guyson ne kawai baya kiransa da Omar ɗinsa sai kuma Zunaira da yake cewa Auta, my Saeadati ya ke kiran Guyson, wato farincikinsa kenan, su biyun nan ne yake kiransu ba da sunansu ba. Komawa Aunty MieMie ta yi ta zauna kamar yadda daddyn nata ya bukata, ita kuma Momma suka tafi tare da Yah Jawad ɗin. Suna shiga ɗakin suka sami Chuchun ta miƙe zaune suna hira da Auta, da alama ma kamar labarin abin da ya faru da ita daren jiya take gayawa Autar, dan ga alamar tashin hankali game da mamaki haɗe da tsoro sun bayyana a saman fuskar Autar. Suna jin motsi shigowa ɗakin suka kai kallonsu izuwa bakin kofar ɗakin. Ai kuwa Chuchu na yin ido huɗu da Yah Jawad ta kusa haukace masu. Ihu ta fara zundumawa tana ƙoƙarin gudu ta sauka daga gadon, ko ina zata je idan ta sauka?. Da kallon mamaki bawan Allah shi da mommar suka bita da shi, ta datse idanunta gam tana zunduma ihu, sai ƙoƙarin sauka daga gadon take yi, ita kuma Auta ta riƙeta gam ta hana ta sauka, sai tambayarta lafiya me yake faruwa take yi. Ƙarisowa cikin ɗakin suka yi, da sauri momma ta riƙeta tana faɗin. "Jannat lafiya? Meyake faruwa ne?". Banda ihu babu abin da take zundumawa, da alama bata jin me suke faɗe. Saman bedside drawer Yah Jawad ya zauna, cikin sanyin murya ya furta. "Jannat lafiyarki kuwa?". Habawa ai tana jin muryarsa ta kara zunduma wani irin ihu mai sauti, ga shi kuma ta kasa iya yin magana, kamar wadda aka shaƙewa maƙogwaro magana ba zata fita ba. Kallonsa Mommar ta yi da mamaki fal a face ɗinta. Zarginsa ne ya dira mata a ranta, dama su biyu ta ɗaurawa ayar tambaya shi da Jaish, to kuwa tun da Chuchun ta gansa ta birkice masu har haka dole a sanya mashi ayar tuhuma. Bawan Allah shi kuwa da bai san komai ba sai ƙoƙarin rarrashinta ma ya fara yi, dan zuciyarsa tana yi mashi zafi na wannan ihun da take yi, ji yake yi ba zai iya jurewa ba. Ita kuwa Chuchu ta ki bada haɗin kai ta yi magana, banda ihu ba abin da take yi, idanunta ma a datse gam, bazama ta budesu ba bare ta yi ido biyu da shi. "Jawad jeka kai kam, barni da ita". Momma ta faɗa tana hayewa saman gadon. Ba musu ya tashi ya fice, sai dai ransa bai so ba, ya so ya rarrasheta ya ji me matsalarta? Amma bai isa ya ce da momma ta bari ya rarrasheta ba, sai kawai ya bi umarninta ya tashi ya fita fuskarsa a ɗauke da damuwa fal. Mommar kuma ta yi mashi hakan ne domin ta tabbatar da zarginta, so take ta ga da gaske saboda shigowarsa yasa Chuchun kuka ne ko dai me?. Ai kuwa yana fita ta rage sautin kukan nata sosai tana sauke ajiyar zuciya game da shessheka. "Jannat wai me yake damunki ne? Me yake faruwa ne?". Ta yi maganar tana ɗan rungumota. Lafewa a jikinta ta yi, cikin shesshekar kuka ta furta "Momma ni bana son na sake ganin Yah Jawad, please ki ce kada ya sake shigowa cikin ɗakin nan"...... Babbar magana!!. Da mamaki Mommar take sauraron kalamanta har ta kai karshen, tambayarta ta yi me yasa bata son ganinsa?. Shiru ta yi ta ƙasa iya bada amsa, ita dai bata son ganinsa kawai ta sani. Ganin ta kasa iya faɗar dalilin nata ne yasa Mommar ta fara zargin wani abin, da yake ita akwai ta da kaifin basira sosai, su twin's ma a wajenta suka gado rabin nasirarsu, tunani ta rinƙa yi anya Jawad zai aikata abin da take zarginsa a kai ɗin nan kuwa?. Ni ma dai PRINCESS TEEMA ina tantanma a kan hakan, ga shi shima dai Yah Jawad ɗin ya nuna kamar bai san komai ba, ko dai lumbu lumbu yake yi mana ne?🤔 Amma bari mu leƙa wani bangaren mu dawo, watakila kafin nan zamu samo mafita, dan komai a kulle yake yanzu, kila mu iya warwaresu idan muka dawo!!. Amma kafin mu leƙa wani part ɗin bari na ɗan yi maku wani bayani a kan tambayoyin da nake sha, yau bari na baje maku amsar a faranti😂 to masu tambayata wanenen star na littafin RAWANIN ZALINCI, and wacece star mace, kun kasa iya gane star mace da star namiji bari na fara da amsa tambayoyinku, dan tun farko farkon book 1 nake samun waɗan nan tambayoyi, yau dai nace bari na amsa. Amsarku a nan shi ne kun manta nace maku littafin RAWANIN ZALINCI zai zo maku da sabon salon da baku taɓa ji ko karanta irinsa bane? Ton idan kun manta na tuna maku! Littafin RAWANIN ZALINCI yana da ɓangarori da dama! Sai dai shi salonsa daban ne, a kowani ɓangare suna da nasu rikicin da cakwakiyar, ba wai rubutu nake yi a kan abu guda ɗaya ba! No kowace ɓangare jigon labarin daban yake, ba family guda bane a cikin labarin, kowace family da nasu cakwakiyar da kuma saƙon da nake son isarwa, in short a kowace family tana da star ɗinta namiji da kuma mace, haka labarin yake, sabon salo ne da na tabbata baku taɓa jin irinta ba! Amma a gabaɗaya littafin akwai star guda ɗaya wanda ya fita daban da kowa, haka ita ma macen akwai guda ɗaya da ta fita daban da kowa, ku cigaba da hasashenku daga macen har namijin kila zaku iya ganesu kafin alkalamina ya afka cikin labarin sosai ta yadda zamu zaƙulosu😅 so a takaice dai RAWANIN ZALINCI yana da ɓangarori da dama, sannan ba family guda nake rubutu a kansu ba, family's ne daban daban, kuma kowani family da cakwakiyarsa na daban, sannan yana da star ɗinsa mace da namiji, sabon salo na kawo maku ai🤨 Sai masu yawan tambayata tun lokacin da nake tubuta littafin TRIPLETS har izuwa kan RAWANIN ZALINCIN a kan rubutun, kuma bari na baku amsa. Ana yawan yi mun tambaya a kan yadda nake rubutu part part daban daban and kowani part da nashi cakwakiyar, sannan familys daban daban, nasamu tarin tambayoyi a kan cewa labarin baya haɗe mun ko kuma akwai wanda take tayani rubutu ne yasa baya haɗe mun kuma bana mantuwa sannan bana ɗauko cakwakiyar familyn nan na sanya a cikin familyn nan dan mantuwa, to ga amsarku, a gaskiya babu wadda ta taɓa rubuta mun ko A a cikin rubutuna, ni da kaina nake zama na ɓata awa huɗu zuwa biyar ina rubuta maku labarin, haka nake raba dare ina rubutu, haka zan sanya ƙwaƙwalwata busy, zama nake yi in kirkiro labarina, na tsara shi yadda zai kasance a cikin ƙwaƙwalwata kafin na fara rubutawa, babu wanda ta taɓa taimaka mun da ko A, wai taya ma za'ayi wani ya yi maka rubutu ne?🤔 Ai ba zai yiwu ba, domin labarinka a cikin ƙwaƙwalwarka yake ba'a ƙwaƙwalwa wani ba, ai ba zai taɓa iya rubuta maka shi yadda zaka rubuta ba, in short babu wadda ta taɓa tayani da ko A, ni nake zama in kirkiro labarina in kuma tsara kayana, sannan in hau rubutu na ni kaɗai har in kammala shi, kamar wata computer nake aiki, ni ko irin true life story da ake karɓa a rubuta ma bana yi, akwai wadda ta taɓa cewa zata bani labarinta na rubuta a cikin grp ɗina, duk wadda take cikin grp na PRINCESS TEEMA ina tunanin taga hiranmu da matar a lokacin da ta ce zata bani labarinta na rubuta nace mata a'a banaso, abin da yasa kuma shi ne, labarin da zan ƙirƙiro da ƙwaƙwalwata sai ya fi bani damar isar da saƙona ga al'umma cikin sauki, duk ta yadda nake so zan tsara labarina da na ƙirkira saɓanin true life story, so ni ba zan iya karɓar labarin wani or wata ma na rubuta ba, na fi son na ƙirƙiro kayata da kai'na ta yadda zan sarrafa shi yadda nake so, na isar da saƙona ta sigar da nake so, na ilmantar da al'umma ta sigar da nakeso, na tafi da komaina ta sigar da nake so, na juya kayana upside down yadda nake so, wannan shi ne, fatan kun gane?! Yau dai kun samu amsoshinku dukka!!. To mu cigaba da labarinmu. JIMETA..........NIGERIA💘🔥 Wasu irin uban lodin shanayene (Cows) suke ƙetarawa ta gefen wani katafaren kogi mai girman gaske, kogin yana da matuƙar girman da ya keta har ta maƙotan garuruwa, ta gefensa shanayen suke wucewa, da alama kiwo zasu tafi, shanayene masu matikar yawan da sun kai a kallah 1000 da ɗoriya, haka suka rinƙa wucewa, buguma buguman cikinsu ne a tagaba, harda boƙolaye ƴan kasar Cameroon a cikin shanayen. Bayan bujumayen sun wuce ne kananan cikinsu suka rufa masu baya, suma kananan suna da uban yawa ba kaɗan ba, ga shanayen da kyan gani sosai, ɓul ɓul da su, sun samu kiwo mai kyau, jikinsu tas, ɗaiɗaikun cikinsu ne zakaga jikinsu da ɗan baki baki, amma tas suke. Bayan kananan sun wuce uban tilin garken raguna ne suka biyo masu baya, raguna ne irin masu tsawo da dogayen kunnuwar nan, kala biyu ne jikinsu, akwai mai brown da fari akwai kuma mai baki da fari. Suma ragunan suna dayawa sosai, zasu iya kai 300 haka, kuma maza ne da mata. Bayan sun gama wucewa sai awakai suka bi bayansu, suma suna da yawa gasu manya manyan, sun ji kiwo sun ƙoshi. Bayan su sai jakuna da basu wuce guda 20 ba. Dukka waɗan nan uban tilin dabbobin da suka wuce wata yar kyakkyawar yarinya ce riƙe da sanda take daga karshensu tana kaɗasu, yar ƙarama da ita, ba ta wuce 8 to 9 years ba a duniya, ita ce ta kaɗo waɗan nan uban tilin dabbobin har da bujumayen saniyoyin nan, duk suna a ƙarkashin kulawarta. (Ni kam abin ya bani mamaki, yarinyar da idan ta shiga cikinsu ko alamarta ba za'a gani ba wai a ƙarƙashin kulawarta suke?🤔 abin da mamaki da kuma burgewa. Kai wayaga PRINCESS TEEMA a cikin shanaye?🤔😅 Tab da na yi suma goma wlh, kai ni ai tsakanina da su in gansu a soye🥱😅🌝 na ci na kora Maltina mai sanyi!. Kar fa ku ce tsoronsu nake ji, sam bana tsoronsu💪 ni kanwar Mammar Kamran ce, 💪 jarumta a jininmu take😅 tsaro zai sa ba ma zan je in da suke ba ba tsoro ba, fatan kun gane?🌝) Sanye take da takalmar kiwo a kafafunta, ga zanin da ta ɗaura sai ta baka dariya, ɗaurin zanin ma bata gama iyawa ba, na ciki ya fi na waje tsawo ta ɗaura kayanta, rigar kayan fulani ne a jikinta, sai dressing natan ya kara bawa mutun dariya, barema wannan uban kwadaram ɗin takalmi da tasa na kiwon, kai ba ɗan'kwali, wasu kumbusa kumbusan kitso ne a kanta guda huɗu, da yake tana da tsawon gashi sosai sai jelar kitson ya sauko mata har bayanta, ga gashin nata baƙin kirin da shi sai tsantsi. Kyakkyawar gaske ce sosai yarinyar, sai dai idanunta a tsaitsai a tsakar ka suke, da alama bata da kunya, dan akwai bushewar idanu sosai kam, ga ɗan bakinta ɗan ƙarami da alama zai yi rashin kunya da surutu dai'dai gwargwado. Ta cancaɗa wani irin mahaukacin kwalliya da idan ka gani sai dariya ya kashe ka, wannan idan ka ga kwalliyar nan da daddare sai ka sume ko ka ruga a guje a zatonka aljana ka kallah, amma ita a haka gani take tafi kowa yau, ji take kanta ya yi kato saboda ta yi kwalliya, ji take babu kamarta a duk faɗin rugar Lamiɗo, har wani taku take yi irin na wadda ta fita daban yau.......😅 Sai ƴar wakarta take rerawa cikin harshen fullanci tana cigaba da bin dabbobin tana kuma kaɗa sanda, idanunta tas suke kamar farin cikin kwai, ga idanun kam sai dai muce masha Allah, dara dara da su. Cigaba da tafiya da dabbobin ta yi har suka keta ta cikin wasu gonakin suka bar kusa da wannan kogin. Da ɓacewarsu a arear wajen ba jimawa sosai wata kyakkyawar matashiyar yarinya fara tas tare da wani dattijo suka zo giftawa ta wajen kogin, da alama duk a tare suke. Cikin nutsuwa suke tafiya suna hira, daga ganinsu kasan baban da ƴa ce ba sai ka tambaya ba, dan suna kama sosai, sai dai yarinyar ta fishi hasken fata sosai, tana da tsawo sosai kamar shi, a shekaru ba zata wuce 14 to 15 years ba, kyakkyawa ce ajin farko. Zanin dake jikinta irin na wancan yar yarinyar da ta kaɗa dabbobin nan ne, sai dai ita tana sanye da hijabi mai ɗan girma zuwa gwiwarta, da alama tana da nutsuwa sosai, dan yadda take magana da baban nata cikin girmamawa da yin kasa da murya a kan nasa ne zai tabbatar maka da nutsuwarta. "Bappa zan sha ruwa". Yarinyar ta faɗa cikin sanyin murya, tana murya mai daɗin gaske wanda zai dace da rera kira'ar Alqur'ani mai girma. Cikin harshen fillanci ta yi maganar!. "Tom Mahnoor jeki sha sai ki sameni a wajen Mahreen, ki kula sosai fa". Ya bata amsa tare da wucewa gaba, haƙiƙa muryarsa sak irin tata yake, sun yi kama. Nufar gangaren da zai sauketa izuwa bakin kogin ta yi, dan a saman tudu suke, shi kuma Bappa kwairaga ya bi bayan ƴar yarinya mai kaɗa dabbobin nan. Cikin nutsuwa take sauka izuwa bakin kogin, daga ganin wannan kyakkyawar innocent face ɗin nata da akwai damuwa a kanta, tana da fuskar tausayi sosai. Bakin ruwan ta tsugunna tare da kai kyawawan fararen tafukan hannunta ta ɗebi ruwan ta kai baki, da yake ruwan gudu ne yana da haske sosai, ba'a tsaye ruwan yake ba, yana gudu ne. Bayan ta sha dai'dai yadda take buƙata sai ta miƙe tsaye, bin kogin da kallo ta fara yi tare da sanya hannayenta ta riƙo ƙugunta. Can ta hango wani abin jibgi kamar kaya a can gefe a bakin kogin. Ɗan zaro ido ta yi tare da kurawa wajen idanu, bata iya ganin menene sosai daga in sa take tsaye, hakan yasa ta yi tunanin bari ta ƙarisa wajen ta ga menene?. Ai kuwa babu tsoro ba komai ta nufi wajen cikin nutsuwa. Tun bata gama ƙarisawa ba ta ja wani uban birki tare da gwalalo ido waje sosai kamar zasu faɗo ƙasa. A ɗari ta ɗan ja baya tare da wage cool voice ɗinta tana kwalawa Bappa kira. Da ƙarfi ƙarfi take kwala mashi kiran, amma ina, kasancewar tana da sanyin murya sai voice ɗin nata baya fita sosai sam............. Da yake dajin yana amsakuwa hakan yasa kiran nata ya dira a kunnen Bappa dake ƙoƙarin rabon faɗa tsakanin............ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 19/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 Da yake dajin yana amsakuwa hakan yasa kiran nata ya dira a kunnen Bappa dake ƙoƙarin rabon faɗa tsakanin Mahreen da wata ƴar matashiyar yarinya da zata iya finta a shekaru, a kallah yarinyar zata kai shekaru goma sha biyu haka, amma Mahreen ta tsaya sai gwabza faɗa suke yi har zani ya faɗi saura pant kawai. Sandar kiwon nata ta rarumo zata bugawa yarinyar a tsalar ka Bappan da ya iso wajen yanzu ya yi maza ya riƙe sandar yana faɗin. "Haba gajin Bappanta (Auta kenan shi ne gaji da fillanci), meyasa zaki bugeta da sandar nan har haka?". Gashin idanu a tsastsaye kamar wadda tasa na kanti, idanu a bushe kwalam ba alamar kunya, Bappan yana idasa maganarsa ta sanya mashi kuka kamar ba ita take jibgar ƴar mutane a yanzu ba, sake mashi sandar ta yi tare da yin zaman ƴan bori a kasan wajen, kan kace me ta fara birgima a kasan kamar mai shafan aljanu, yi take yi tana kukan shagwaɓa ita a dole Bappa ya kyaleta ta cigaba da jibgar ƴar mutane kamar ita ta haifota izuwa duniya. Yarinyar kuma da ta samu Bappa ya kwaceta ai sai ta danna a guje, dama ta daku a hannun Mahreen ɗin, ta germe mata a shekaru, amma saboda bala'in Mahreen ɗin nan sai da ta daka yar nan lilis kamar an aikota, har kuka sai da yarinyar ta yi, tana kukan ne kuma dama zata kara kwala mata sanda a kanta dan iyashege. Sai rarrashinta Bappan yake yi, da alama shi ya ɓatata da shagwaɓa da kuma faɗa, dan baya yi mata faɗa da nasiha a kan idan tana faɗa da mutane ko tana shagwaɓa, sai dai ya biye mata ya yi ta rarrashi, yanzu ma faɗi yake yi tom ta tashi ta dage shi da sandar shi tun da ba zata hakura ba, ai kuwa make kafaɗa ta yi tana faɗin ita dole ya barta ta kwalawa yarinyar can sandar, idan ba haka ba yau ba zata ci abinci ba. Ita kuwa yarinyar da Allah yasa Bappa ya kwaceta ta ruga da gudu wajen shanayen kiwonta, sai da ta kusa isa wajen ta juyo tare da faɗin. "Mahreen mai kwalliyar mahaukata na faɗa ɗin ki lilili ki liƙeni ki mai dani cikin uwata ki fitar dani ta bakin allura idan kin isa ba iya duka kawai ba! Na faɗa kin yi kwalliyar aljanu karya na yi ne? Fuska a dame kamar fura........" Habawa a wani irin zabure ta yunƙura, an fasa yi wa Bappa shagwaɓa, aljanun dukan sun motso, Mahreen mai karɓawa wata ƴancinta ma bare kuma ace ita aka tsokano? Ita fa take tsayawa ta yi dambe da duk waɗan da suka taɓo Mahnoor, dan ita Mahnoor ɗin sam bata da faɗa, tana da sanyi, idan anyi mata ba daɗi sai dai ta samu waje ta zauna ta sha kuka, to Mahreen take tsaya mata a buga dambe, tsabar faɗarta yasa yanzu aka dai'na tsokanar Mahnoor mai idon mujiya a kauyen, ai ganganci ne ma ka taɓo Mahreen ka yi tunanin zata barka, wlh komai daren daɗewa ba zata manta ba kuma bazata hakura ba, duk randa kuka haɗu sai ta rama, gata da iya faɗa, duk ta yagushe maka jiki da faratun hannunta, kamar wata mage, idan kuna faɗa tsalle take yi ta haye jikin mutun ta shakesa kamar mage, ta yi ta yagushe maka fuska, bazata taɓa bari kuma ka yakiceta ba, sai ta yi ta zullewa har sai ta yi maka lahani, duk kuma abin da zata yi Bappa baya taɓa ganin laifinta, shiyasa ko ta jibgi ƴaƴan mutane ba'a kawo kara wajen Bappa ko Nennenta, dan kuwa basu karɓar laifinta, gara ma Bappa zai bawa waɗan da suka kawo karan tata hakuri ya ce yarinya ce, ranar kam ma da ta fasawa wata baki sai da Bappa ya basu kyautar ɗan marakin saniya kafin suka hakura, sun ce sai sun ɗauki fansa sai sun rama, hakan yasa dole ya basu wai aje a yanka a gasawa yarinyar nama ta ci bakin nata ya koma normal, sai da ya yi haka suka hakura, ita kuma Nenne idan kika kai mata karar Mahreen uban masifa zata hau surfa maki ta ce ƴarta kawai aka sakawa ido a kauyen nan, yarinya kamara zasu cinyeta da baki!. Mahreen akwai shagwaɓa sosai dan Bappa ya shagwaɓata sosai ba karya, sannan akwai faɗa dan faɗarta ma gado masifar ta yi daga wajen Nennenta, in tana masifa fa har wani rufe idanu take yi hannu na rawa ya yi sama ya yi ƙasa, ƙugu na rawa kamar ana kaɗa burugalin burga nono, haka take riƙe ƙugu tana sama tana ƙasa, ta in da take shiga ba tanan take fita ba, sai dai bata shiga harkar kowa ne, haka kawai bata kama mutun da faɗa, idan kunga tana faɗa to tabbas taɓota aka yi, idan kuma aka taɓota wlh wannan faɗar bata karewa cikin sauki, idan yarinyar bata gudu ko ta miƙa wuya ta bada hakuri ba, wlh sai Mahreen su kwana suna gwabza faɗa ba zata gaji ba, so bata faɗa sai an tsokaneta ko kuma an taɓa mata ƴar uwarta Mahnoor, nan ne zaku ga balbalin bala'i in mai tafasa in jita. Yarinyar nan ta yi suna a wannan kauyen fiye da tunaninku, manya da yara kowa ya santa, gata da ɗan banzan farinjini, bata isa ta gifta wani guy ɗin saurayin bai ce mata hllo ƴan mata ba.........😎🌝 Su fulanin daji kunsan suna auren wuri gaskiya, kamar Mahreen ɗin nan takai ayi mata miji idan an samu, wadda bata kaita bama ana yi masu miji har ma aure, shi dai Bappa ya bar ƴaƴan nasa ne a cewarsu yana jiran ƴaƴan yayansa maza da suka tafi kiwo na tsawon shekaru biyu, sun tafi yawon kiwo har ƙasashen makota, dama kun san suna yin haka, to su yake jira idan sun dawo zai aura ma ɗaya Mahreen sai a haɗa da Mahnoor dake da nata saurayin shi ma na gida ne, yana son haɗa aurensu lokaci guda ne yasa bai aurar da Mahnoor ɗin ita kaɗai ba. Da sauri Bappan ya riƙota. "Haba gajin Bappa, ki kyaleta mana tun da dai ta gudu, ai ta ji tsoronki ne yasa ta gudu, tun da tana tsoronki yi hakuri ki ɗaga mata kafa". Ya faɗa cikin sigar rarrashi. "Da gaske bappa ta ji tsorona?". Ta faɗa tana zaro idanu. Duk wannan faɗuwa ƙasa da ta yi tana birgima tana kuka ashe babu hawaye ko tsilo a face ɗinta, ashe ihunta kawai take kwararawa babu hawaye, kai wannan yarinya sai shirin Allah. Amma dai wani lokaci tana da gaskiya wajen kwatawa kanta ƴanci har ma da ƴar uwarta. "Kwarai kuwa gajin Bappanta, ta ji tsoronki sosai ma kuwa". Wani irin tuntsirewa da dariya ta yi tare da fara yin tsalle tana faɗin. "Shikenan Fatu ki je na yafe maki tun da kin ji tsorona, yeee ta ji tsoro a bata kunun zakin da ya yi sati ta sha ta bugu ta hau aiki". Mahnoor dake tsaye tun ɗazun tana kallonsu ne ta ce. "Mahreen Allah ya nuna mun ranar da zaki dai'na faɗa, Bappa kazo muje ka ga wani abu a bakin ruwa, sai kiranka nake yi baka amsa ba". Yana ƙoƙarin yin magana Mahreen ta rigasa da cewa. "Adda Mahnoor zan daina faɗane kawai idan suka dai'na zagin kwalliyata". Ɗan girgiza kai ta yi kafin ta amsa mata da. "Ai Mahreen ba zagin kwalliyar taki suke yi ba, na sha faɗa maki saboda basu iya haɗaɗɗen kwalliya irin taki ɗin bane yasa suke zaginsa, da zaki koya masu irinsa tsab zasu dai'na zagin su fara yin irinsa...." Ƙara zaro fararen idanun nata ta yi. "A'a gaskiya wlh ba zan koya masu ba munafukai kawai". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai. "Bappa zo mu je ka ga wani abin, ke kuma Mahreen ki dawo da dabbobin nan kusa, sun yi nisa sosai". To ta amsa mata tare da sanya kai da ƴar gudunta ta wuce tana murmushin da ya kara mata kyau sosai, ta ji daɗi ƴar uwarta ta ce tafi kowa iya kwalliya a kauyen........ E da gaske wannan yarinyar akwai shiga rai, nima dai ta shiga rai na. Wucewa Bappa ya yi izuwa in da Mahnoor ke tsaye, a cikin ransa yana addu'ar Ubangiji Allah ya shirya mashi Mahreen ɗin nan nasa, Allah ya rabata da shegen son faɗar nan, fargaban da yake yi kada wata yara ta taɓo wadda zata yi mata duka, ba zai iya jure a daketa ba, yana kaunarta sosai, duk wadda ta taɓa mashi lafiyarta sai sun buga shariya a wajen Arɗo da shi, so shiyasa yake yi mata addu'ar Allah yasa ta dai'na faɗar ma tun kafin a kai ga haka. Daga ɗan baya baya Mahnoor ta tsaya bata iya ƙarisawa bakin kogin ba. Shi kuwa Bappa da ganin kamar mutun ne a wajen yasa ya yi saurin ƙarisawa wajen dan ya ganewa idanunsa. Zuba mashi ido sosai Bappan ya yi yana kallon yadda fuskarsa take da kuma yadda yake kwance a bakin ruwan, rabin jikinsa duk a cikin ruwan, kyakkyawa ne sosai, farine tas da shi, soft skin ɗin nan nasa sai wani sheki yake yi, ga fatar tasa luwai luwai kai ka ce bai taɓa fita rana ba. Yanayin yadda yake kwance a bakin kogin ba ƙaramin mamaki ya bawa Bappa ba, abin ya ɗaure mashi kai. Ita kam Mahnoor ta tsorata sosai, ta koma baya tana faɗin. "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun ". A cikin zuciyarta, dan a nata tunanin aljani ne ba mutun ba, dan kyakkyawan gaske ne, ga wannan dark black curly hair nan nasa ya kwanto mashi har saman goshinsa, da yake ruwan kogin ya jiƙa gashin nasa, sai ya manne mashi a fuska, duk da idanunsa a rufe, hakan ba zai hana ka gane cewa yana da manya manyan idanu ba, ga lips ɗin nan nasa ya yi pink color sosai kamar na mata, ɗan ƙarami da shi, yana da dogon hanci sosai, hancin nasa kuma bai yi irin dogo zur ɗin nan ba, a'a ya yi ɗan dai'dai mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ya kuma yi dai'dai da face ɗin nasa, ya kara kawata kyansa ba kaɗan ba. Kwata kwata bai yi kama da Nigerians ba, suit ce mai bala'in kyau da tsada a jikin sa, launin ask color ce, daga ta ciki kuma, long sleeve shirt ce fara tas. Duk da yana kwance, hakan bai hana ka ga cikakkiyar tsuransa ta kiran karfi da lafiya tare da jini a jika a tattare da shi ba, ga dukkan alamu yana da alaƙa da manya manyan mutane, duba da irin tsadaddun kayan da suke jikinsa, watch dake hannunsa ma kawai abin kallo ne, diamond watch ce mai matukar kyau da ɗaukar hankali, kafarsa na sanye cikin wata dankareriyar half cover ash color mai bala'in kyau, neck tight dake wuyarsa ta manne mishi a wuyar tasa ta samar lallausan fatarsa, saboda ruwa da ya jika shi, yana da tsawo sosai, ga faɗin kirji tamkar wani zaki. Tsugunnawa a kusa da shi Bappa ya yi babu ko tsoro tare da sanya hannunsa a bakin kofofin hancinsa dan ya ji shin yana numfashi ne ko baya yi. Ko kaɗan baya numfashi kamar ma babu rai a tattare da shi, duba da yanda ya yi wani yellow sosai, ga kuma face nasa da alamar kumbura a tattare da shi. Ɗagowa Bappan ya yi cikin harshen fillanci ya ce "Mahnoor ɗin Bappa ki kaɗo mun jakin guda ɗaya bari na ɗaura shi a kanta mu je gida". "Bappa kada ka ɗauke shi, aljanine fa, ni ban taɓa ganin mutun mai shegen kyau irin haka ba". Ta yi maganar tana zaro idanu. Cike da ɗa zolaya ya ce. "Kin taɓa ganin aljani ne? Kuma waye ya ce maki aljani yana da kyau? Ko dai kin taɓa ganin kyakkyawan aljani ne ban sani ba...?" Kara ja da baya ta yi, jikinta har ya fara kerman tsoro, ita dai bata taɓa ganin kyau irin nasa ba, sannan ga shi kwance a cikin ruwa, sai hakan ta kara sanyawa fuskansa ya yi wani iri a gareta. "A'a bappa, ban taɓa ganin aljani ba, amma dai ban taɓa ganin mutun irin wannan ba". A takaice ya ce mata. "Nima ban taɓa ganin mutun irin wannan ba kam, ina dai ganin masu irin yanayinsa, amma ina da yaƙinin ba aljani bane, mutun ne wannan In Sha Allah, kada ki damu je ki kaɗo mun jaki bari na nemo wani ya tayani kama shi mu ɗaura a saman jakin". To ta amsa da shi tare da wucewa da sauri, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, addu'a take yi Allah ya sa dai mutun ne ba aljani ba, dan ita dai bata taɓa ganin mutun kamar haka ba. Cikin hanzari ta je ta kaɗo jakin ta dawo, ko da ta dawo wajen bata sami Bappan ba, hakan yasa ta tsaya daga ɗan nesa da kogin kaɗan, taki yarda ta ƙarisa wajen, dan gani take kamar idan ta je aljaninne zai tashi ya kamata, ita dai bata gama yarda cewa mutun bane. A wajen ta tsaya har Bappa ya dawo tare da wani mutun, sanin halinta yasa Bappan bai ce lallai dole sai ta matso kusa da mutumin ba, karɓar jakin kawai ya yi tare da ce mata ta koma wajen Mahreen bari ya kai mutumin gida. Da sauri ta juya, kamar zata kifa ƙasa, sai waigo su take yi, tana gani suka ɗaura shi a kan jaki, jikinta na kerma ta wuce wajen Mahreen. Zaune ƙarƙashin wata bishiya ta isko Mahreen ɗin tana shan raken da ta karyo a gonar Bappa. A kusa da ita ta zauna tare da fara gaya mata cewa Bappa ya tsinci wani aljani mai kama da mutun. A ɗari Mahreen ta zaro idanun nan nata. "Aljani kuma Adda Mahnoor?". Ta zaro ido alamar mamaki da tsoro tana magana, amma hakan bai hana ta karyi rakenta ta cigaba da sha ba....... Wannan yarinyar akwaita da abin dariya, tana tambaya tana shan rake. "E Mahreen aljani, idan kika ga kayan jikinsa ban taɓa ganin irinsu ba, har da wani igiya ya ɗaura a wuyansa, kinga takalmarshi? Ya so ya yi iri ɗaya da na kafarki, ga shi nan fari tas, kuma shi kalar fatar jikinsa sam sam ba irin namu bane, shi fatarsa ma ban san ya zan ce maki ba, amma dai ba irin na mutane bane, dan ban taɓa ganin irinsa ba, ya ɗaura wani abin mai ɗaukar ido a hannu (agogo) kin ga ga shin kansa? Ba irin namu bane, yana da kyau sosai ba irin kyau ɗin mutane ba......" (Magana ta Allah Mahnoor ta cuci Jaish da ta haɗa takalmar ƙafafunsa da na ƙafafun Mahreen, gaskiya ta gama cutarsa😅 Mahreen mai takalmar kiwo me haɗinsa da tsadaddiyar cover fisabilillahi?🤌) Zubur ta miƙe. "Adda Mahnoor bari na je na gansa, riƙe mun sandar nan....." Tun bata kai karshen maganar ba ta miƙa mata sandar tare da sanya kai da gudu ta wuce, maganar ma a hanya ta ƙarisa ta. Tana barin wajen sai ga wani kyakkyawan matashi chocolate color ya ƙariso wajen, hannunsa na riƙe da sandar kiwonsa. Matashi ne da ba zai wuci shekaru 22 ba a duniya, ba karya yana da kyau sosai, suna ɗan yanayi da Mahnoor ɗin ma, daga gani ba tambaya zaka san dangi ɗaya ne, dan waɗan nan dara daran idanun nasu kusan iri ɗaya. Ɗaure fuska ta ɗan yi da ganinsa. A kusa da ita ya zauna yana washe baki. "Mahnoor ina Bappa da Mahreen yau kuma?". Cike da nuna kulawa ta fara magana, sai dai ta ɗaure fuska alamar tsare mutuncinta. "Ina kwana Hamma Faisal". Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mata da lafiya lou, sannan ya ɗaura da maimaita tambayar inasu Bappa?. "Bappa ya je gida, Mahreen kuma yanzu ta bar nan ta bi bayansa". Ta faɗa tana ɗan murza sandar Mahreen dake hannunta a ƙasa, ta kuma yi maganar tana kallon ƙasa, ko da sunan wasa bata ɗago sun haɗa ido ba. "Mahnoor meyasa a duk lokacin da muke tare kike ɗaure fuskarki ne? Sai na ganki kina hira da murmushi da su Bappa, amma ni baki yarda ki yi hira da ni ma bare har ki mun murmushi, sai ki ɗaure fuska sosai mena yi maki ne?". Ajiyar zuciya ta sauke, ba tare da ta ɗago kai ba ta amsa mashi da. "Hamma Faisal babu abin da ka yi mun..." "To ko kin dai'na sona ne?". Kai ta girgiza mashi. "A'a ban dai'na ba". "To meyasa baki son yin hira da ni ko ki yi mun murmushi kamar yadda kike yi da Bappa da kuma Mahreen?". Sam babu alamar zata yi murmushin a saman face ɗinta, tamkar bata taɓa yin murmushin bama, fuska kala biyu take da shi yarinyar nan, idan ta ɗaure fuska sai ka rantse da Allah bata taɓa sanin me murmushi ba, ɗaurin fuska yana zama a face nata sosai kuma yana yi mata kyau, haka zalika idan ta yi murmushi sai ta baka sha'awa, sai kaga kamar kullum haka fuskar tata take, musamman idan dimple nata ya lotsa, so in ma murmushi ko akasinta duk suna dacewa da face ɗinta kuma suna ƙara mata kyau. "Hamma Faisal ai baka yi abin da zai sanyani yin murmushin bane, ita kuma Mahreen ai kasan halinta, in dai kana zaune da ita dole sai ta baka dariya ma ba murmushi kawai ba, shi ne yasa kawai bana murmushi ba dan wani abin ba". Cikin sanyin murya sosai ta yi maganar. "To amma dai kin san ina sonki ko?". "E na sani, nima ai ina sonka". Guntun murmushi ya yi. Shiru ne ya biyo baya na ɗan lokaci, shi ya katse masu shirun da cewa. "Ya aka yi yau kika biyo Bappa kiwo ne ma?". Har lokacin bata ɗago ta kalle shi ba ta amsa mashi da cewa. "Bappan ne ya ce nazo mu tafi, kuma ai dama kaga idan yana nan muna binsa kiwo sosai, idan baya nan kuma Nanne ce take hanamu bin kawu Ibrahim, shiyasa bama zuwa". Zai sake yin magana Mahreen ta iso wajen da gudu tana haki, da alama ta ci gudu ne ta ƙoshi. "Adda Mahnoor wlh da gaske maganarki take, kin ga mutumin nan kuwa? Tabbas ba mutun bane, Bappa kuma fa gida ya kaishi, yanzu faɗa suke yi da Nenne a kan Bappa ya ce in dai mutumin yana da rai to shi zai yi jinyarsa har ya warke, idan kuma suka bincika ya mutu to sai a binnesa, shi ne Nenne ta ce wlh Bappa ba zai ajiye mata aljani a gida ba, salon tsakar dare ya tashi ya shake mata wuya ya kasheta, Bappa kuma ya ce ba zai je ya wurga da shi ba, ya shigar da shi ɗakinsa har da kwantar da shi a saman tabarman da yake jinyar marasa lafiya, ya kafe sai ya yi jinyarsa idan yana da rai, Nenne kuma ta ɗauki mayafinta ta tafi gayawa Arɗo abin da Bappa ya yi, kuma ta ce ba za ta dawo gidan ba har sai Bappa ya fitar da aljanin nan". Ta ƙare maganar tana tsugunnawa a kusa da Mahnoor ɗin tare da sauke ajiyar zuciya. Get "Ke chali chali, wai bana ce ki rinƙa nutsuwa idan zaki yi magana ba? Yanzu dai babu abin da na gane a maganar nan taki, yarinya sam bata da nutsuwa, kai na rawa kamar mazari.." cewar Faisal. "Babu ruwanka da ni Hamma Faisal, tun da nazo nan ai ban yi magana da kai ba, kuma ai na ganka, maganarce kawai ba zan yi maka ba, ni fa nace ma ka dai'na shiga harkarta, kasan bana sonka tom!"......... Tab mai kankanta kenan, yau ga ikon god, wato ita idan bata son mutunma kai tsaye zata gaya mashi, a tsirara zata fitar da kalmar sai dai ayi wacce za'ayi, aiki ga mai kareka!!. "To dama wayace ki so ni? Nima ai kin san ba sonki ɗin nake yi ba, waye zai so aljana ma irinki? Yarinya kamar jikar Lami mai kafar shamuwa, Mahnoor idan ana iska kada ki bari ta rinƙa fita na sha gaya maki, idan ba haka ba wata rana zaku nemeta a rugar nan ku rasa, dan tsab iska zai yi sama da ita............" Ai kuwa bai ƙarisa maganar ba ta zunduma ihu tare da miƙewa ta miƙi hanya sai wajen Bappa. Ɗan siririn murmushi Mahnoor ta saki kafin ta ce. "Hamma Faisal yau babu kai babu zaman lafiya tsakaninka da Bappa". Miƙewa tsaye ya yi yana faɗin. "Shiyasa zan gudu yanzu, kuma ba zan dawo ba sai gobe, ba zan bari mu haɗu da shi ba yau, sai zuwa gobe idan ya huce". Murmushi kawai ta ɗanyi bata ce komai ba, sa kai ya yi ya wuce yana tunanin yadda zai kauce haduwarsa da Bappa a yau, ƴaƴan gwaggo da ƴaƴan kawu suke shi da su Mahreen ɗin, maman Faisal kanwar Bappa ce, kuma shi Faisal shi Bappa ya baiwa auren Mahnoor ɗin, yanzu mijin Mahreen ake jira ya dawo sai a aurar da su. Nikam har na ji tausayin mijin da zai auri Mahreen gaskiyar, za'a sha dambe, dole kuma ya koyi rarrashi kamar Bappa. Yau dai Mahnoor ita kaɗai ta zauna tare da waɗan nan uban tilin dabbobin, Mahreen tun da ta kai karar Faisal wajen Bappa bata dawo ba, lallashinta Bappan ya yi tare da kwantar da kanta a saman cinyarsa har ta yi barci, amma kafin ta yi barci sai da Bappan ya yi mata alkawarin zai yi maganin Faisal ɗin, ta ce ita dai ya ce kada Faisal ɗin ya sake yi mata magana, idan ba haka ba watarana sai ta fasa mashi kai da itace idan yana zaune bai sani ba, zata zo ta bayansa ta buga mashi, har da nunawa Bappan yanda zata yi ta fasa mashi kan nasa, da kyar ya shawo kanta, sai da ya yi alkawarin zai shiga tsakaninsu, daga yau Faisal ba zai sake kulata, sannan ne ta hakura ta kwanta ta yi barci. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 19/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 Mahreen da Faisal kamar wuta da audiga haka suke, basu shiri kuma basu haɗa hanya, kullum bata da aiki sai zaginsa, ta ce da Mahnoor kada ta yarda ta aure shi, in dai ta aure shi to wlh ba zata je gidanta ba, haka dai suke ta fama, ita Mahnoor da bata san me soyayyar ko daɗinta ba jinsu kawai take yi, ita ina ma ruwanta da wani soyayya, Faisal ɗin ne ma ya koya mata cewa tana sonshi shiyasa take faɗa mashi kalmar, amma bata san me soyayya ko me ake ji idan ana yi ba, bare wannan uwar rawan kan, yo ita idan ba faɗa da kukan shagwaɓa da kuma cin abinci ba me ta sani? Ai ba ruwanta da zancen banza, ta dai san ance za'ayi masu aure, ita kanta Mahnoor da take matsayin babba ma bata san me ake nufi da auren ba bare kuma uwar rawan kai, su dai za'ayi masu aure kawai, kila sai anyi zasu san me yake nufi ko me amfaninsa. Sai bayan la'asar Bappa ya dawo wajen kiwon hannunsa riƙe da kwanon sha mai rufe da paipai. A saman ɗan'kwalinta ya sameta zaune ƙarƙashin wata bishiyar ɓaure, da alama bata jima da idar da sallah ba, ta buga uban tagumi, idanunta sun ɗan ciko da kwallah, da alama tunanin wani abin take yi wanda ya sanya ta kusan kuka. Sallamar da Bappan ya yi mata ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka, da sauri ta goge idanunta tare da cewa. "Bappa ka dawo?". Zama ya yi a gefenta. "Na dawo Mahnoor, kiyi hakuri ban kawo maki abinci da wuri ba, Nennenku ce ta yi tafiyarta, taki dawowa ta yi girki, ni da kai'na na yi girkin sai yanzu na kammala, ga shi kici sai mu kaɗa dabbobin mu koma gida ko?". Kallonsa ta ɗan yi tare da yin ƙasa da kai. "Bappa meyasa zamu koma gida da wuri yau? Ai naga kamar karfe 6 bata yi ba, ban jima da yin sallar la'asar bafa". Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce. "E haka ne lokacin komarmu bai yi ba, amma zamu koma ne saboda dalilai biyu, na farko Nennenku bata nan, kuma naje gidan Arɗo ɗaukarta ta ce ba zata dawo ba, kinga ba wanda zai yi girkin dare sai ke, dan haka zamu koma ne ki dafa mana abin da zamu ci, sai kuma batun mutumin nan da muka tsinto, ina bincike a kan lafiyarsa, har yanzu ban iya gano yana da rai ko ya mutu ba, shiyasa zamu koma gida yau da wuri, dan haka ci abinci da wuri mu tafi". Ya kai karshen maganar tare da buɗe mata paipain da ya rufe kwanon shan da shi. Abinci ne mai rai da lafiya, tuwo ce da miyar ɗanyar kuɓewa ta ji man shanu, ga nama zuƙu zuƙu. Hannu tasa ta fara ci, dan hannunta a wanke tas, ba jimawa ta je ta yo alwala a bakin kogi. "Bappa ina Mahreen?". Ta yi maganar tana cigaba da cin abincinta. "Mahreen tana gida tana zuba barci". Ya bata amsa tare da miƙewa ya nufi wajen dabbobin nasu in da suke ɗan nesa da su, sai gabsarar ciyawa suke yi. Haɗa kansu ya yi ya kaɗasu tare da fara zuba masu surutu a kan su yi hanyar walde wato in da suke kwana a bayan gidansu kenan, a bayan gidansu walden dabbobin yake, akwai tirke dayawa a wajen, wasu shanayen suna ɗauresu saboda ƴaƴansu su samu damar shan nono kada iyayen su ɓace cikin garke ƴaƴan su sha wahalar nemansu, shiyasa suke ɗaure masu ƴaƴan, wasu kuma saboda mafaɗata ne yasa suke ɗauresu a tirken, saura kuma sai su barsu a sake haka basa ɗauresu, kuma babu in da suke zuwa suna tsaye a wajen. Ita kuma cinye abincin tas ta yi tare da miƙewa ta nufi bakin kogi da kwanon, wankosa tas ta yi, sannan ta bi bayan Bappan, dama bai yi mata nisa ba, ba jimawa ya wuceta duke tana wanke kwanon. Kai tsaye walde Bappa ya nufa da shanayen, ita kuma ta nufi cikin gida. Tana shigowa ta nufi kitchen, bayan ta ajiye kwanon a ma'ajiyinsa ta ɗauko wani ɗan madaidaicin bokiti, ruwa ta ɗebo a cikin ɗaya daga cikin randunar dake cikin kitchen ɗin. Kai tsaye bayi ta nufa, a gurguje ta yi wanka ta fito, da sauri ta shige cikin ɗakin bukkarsu, sai sauri take yi kamar zata kifa, duk dan ta ɗaura zani a kirji, kuma ta sanya hijabi, amma da yake hijabin zuwa gwiwarta kuma shima zanin da ta ɗaura a kirji bai kai gwigwa ba, so singalalin kafafunta a waje shiyasa take zuba sauri dan kada wani ya shigo ya kalleta. Zama ta yi a bakin ƴar karifarsu, man shafawa ta ɗauko, mai ne irin wannan vaseline ɗin na 150 ƴan kananan mazubin nan, shi ta ɗauko ta murje jikinta da shi, da yake sun wadatu da nonon shanu skin ɗinsu yana da kyan gani sosai, kun san madarar saniya tana gyara jiki, so jikinta ya yi luwai luwai. Bayan ta gama shafa man sai ta janyo wani jaka da aka ɗinka da buhu, kayan kwalliya ta fitar a ciki, powder ce da ƴar janbaki za irin mai green ɗin bayan nan, shi ta ɗauko ta hau murje fuskarta tana gyarawa. Lips ɗinta da suke pink sosai ma kamar an sanya janbaki pink sai da ta sa mashi red janbakin, sam jan kalar bai yi mata kyau ba, kalar lips ɗin tata ya fi yi maya kyau, amma da yake suna kaunar kwalliya ita da Mahreen sai sun sanya, ita iya power da janbaki take sakawa, bata sanya kwalli ko da a iya ido ne kawai, Bappa ne ya hanata sanya kwallin, a cewarsa idan tana sanya kwalli a ido bakin mutane zai yi mata yawa over, yanzu ma jama'a suna yawan magana a kan kyan idanuta, to idan ta sanya kwalli ƙara kyau sosai idanun suke yi, gasu farare tas, hakan ya ja duk wanda ya ganta sai ya yi maganar idanun nata da kyanta, shi ne yasa Bappa ya dakatar da sanya kwalli, kuma ya hanata yin kwalliya idan zata fita, shi yake sayo masu kayan kwalliyar idan ya je cikin gari, amma ya hanata yi idan zata fita, shiyasa kuka ga ita bata yi kwalliya ba time da zasu je kiwo, tana kuma kaunar kwalliyar sosai, ita ma Mahreen duk randa Mahnoor ta yi mata kwalliyar kirki ta yi kyau sai jama'a sun yi ta magana, shiyasa Bappan ya hana Mahnoor ta yi mata kwalliya, ya ce a barta ta rinƙa yi da kanta, dan idan ya hanata yin kwalliyar nan ba ƙaramin rigima zai yi da ita ba, amma idan ya barta tana yi da kanta ta zama kamar mahaukaciya ai kunga ba wanda zai yaba, ba wanda zai kallah ya ji ta burgesa, sai dai ma a mata kallon mahaukaciya, duk ta ɓata fuska, har a kumatu take sanya janbaki, kun ga kuwa ai sai dai ayi mata dariya, ta wannan hanyar ita kuma Bappan ya biyo mata suka zauna lafiya. Bayan ta gama kwalliyarta ta ɗauko wata koɗaɗɗiyar goduwar riga ta atamfa daga cikin kwallar da suke saka kayansu ta sanya a jikinta, sannan ta ɗaura ɗankwalin rigar. Kasancewar ita yanzu ta ɗan fara girma, akwai tula tula a kirjinta sai hakan yasa bata taɓa yarda ta yi yawo babu hijabi koda kuwa a tsakar gida ne, kullum da hijabi, har barci bata cirewa, tana manne da shi, dan tana jin kunyar a ga tula tulan a kirjinta, sai wahalar da kanta take yi wajen nokesu, idan tana tafiya ta yi ta faman sanya hannu a hijabi wai dan kada ma alamarsu ya fito. Ita kuwa Mahreen da ɗan'kwalin ma sai randa aka ga daman sakawa ake sawa, idan kun ganta da ɗan'kwalin to fa ranar da ta sanya kayan sallarta ta ci kwalliya mai kyau, to a ranar ne za'a ganta da ɗan'kwali an sheƙa ɗauri kamar bukkar mahaukaciya, sai a ƙwama wani kwandaram ɗin takalma, Allah sarki suna son yin gayu irin na ƴan birni da suke gani idan suka shiga birnin da Bappansu, amma basu da kayan ƴan birni kuma bama su iya irin kwalliyar ba, sai dai su yi iya kar yinsu. Tana gama shiri ta ɗauki hijabi ta sanya sannan ta fito waje ta ɗauko tsintsiya, ɗakinsu ta fara sharewa kafin ta fito ta share na Nennensu ta gyara, sannan ta nufi na Bappa. Tana shiga ta ɗan ja birki ganin Jaish da basu san wanenen shi ba kwance a cikin ɗakin na Bappan, ita kwata kwata ta manta da cewa Mahreen ta gaya mata Bappan ya kai shi ɗakinsa ya kwantar, da ta san yana nan ba zata shigo ba, dan tsoronsa take ji, ga shi Bappa da ƙoƙari bawan Allahn nan ya raba shi da suit ɗin jikinsa, ya rage daga shi sai singlet ɗinsa fara kal, daga ta ƙasa kuma wani wandon yadin shadda green color Bappan ya sanya mashi, wandon tana da tsawo, a dai'dai saitin tsakiyar faffaɗar kirjinsa Bappan ya manna mashi wasu ganyayyaki, da alama magunguna ne na gargajiya da zasu taimakawa bugawar zuciyarsa, gaban goshinsa ma hakan ce, Bappan ya janye gashin kan nasa baya ya bi gaban goshin nasa duk ya mammanna mashi ganyen. Hasbunallahu wani'imal wakil ta furta saboda bugawa da kirjinta ya yi na ganinsa a kwance haka, juyawa ta yi da sauri da nufin ta fice daga ɗakin, dan ba zata iya yin wannan gyaran ba, har ga Allah face ɗin Jaish yana tsoratata, ita ba ta yarda mutun bane. Mahreen kuwa da yake ba tsoro a ranta tana kwance saman katifar Bappan tana zuba barci, sam bata ji tsoronsa ba, ta dai yi mamakin ganinsa, amma har da taɓa fuskarsa ta yi dan ta tabbatar ba face ɗin ƴar tsana bane, dan a cewarta fatarsa ta yi mata kama da irin fatar ƴar tsana da Bappa ya taɓa saya mata lokacin da ya je gembu wajen kakansa, da zai dawo ya saya mata kyakkyawar ƴar tsana fara tas, to shi ne take ganin fatar jikin Jaish ɗin kamar na ƴar tsanan, bata yarda ba har sai da ta taɓa shi ta ji, sannan ne ta yarda ba ƴar tsana bace, dan tasan ƴar tsana roba ce, shi kuma ta ji nasa fatar da laushi sosai. Yana a wannan hali da basu tabbatar yana raye ko ya mutu ba, haka Mahreen ta rinƙa mulmula mashi kumatu wai akwai daɗin taɓawa...........😅 Kumatunsa ya yi mata laushi, kafin ta yi barci har da wani cewa Bappa kumatunsa laushi kamar breadi. (Ni kam nace ina Yah Jawad ya zo yaga yau yadda mace take mulmulawa Jaish sarkin kunya kumatu😅 wlh idan ka biye Mahreen sai ka mutu da dariya 😅 Jaish dai yau yaga ta kansa, ya faɗo hannun Mahreen sai yadda kuma hali ya yi😅) Na fara yin wani tunani fa, idan Allah yasa yana da rai ya farfaɗo ma kenan haka zata rinƙa taɓa mashi kumatu tana mulmulawa ta ce kamar breadi? Tab hmmmm.....🤔 MAHNOOR. Tana juyowa suka yi ido huɗu da bappa da yake tsaye a bakin kofar shigowa. "Ina zaki je Mahnoor?". Ya faɗa tare da shigowa cikin ɗakin. Muryarta har kerma yake yi saboda tsoro ta furta. "Bappa Allah tsoronsa nake ji, ni har yanzu gani nake yi kamar aljani ne, dama Nenne ta taɓa gaya mun cewa akwai aljanu a kogin nan mu dai'na zuwa wajen ba Bismillah, to yau wlh na manta ban yi Bismillah ba ina ga shiyasa naga wannan aljanin, dan Allah Bappana kada ka ce na share ɗakin nan ka ji? Allah ba zan iya ba". Da yake ya san halinta da tsoro sai ya ce to ta bashi tsintsiyar bari ya sharo ɗakin ya fitar mata da dattin sai ta share tsakar gidan. Ai a dubu ta miƙo mashi tsintsiyar tare da fita waje da sauri. Shi dai Bappa bai ga abin tsoro a tattare da Jaish ba, ba karya yana da kyau sosai, jinin larabawa, amma da yake shi Bappan yana shiga garuruwa da dama a faɗin Nigeria da Niger har ma da Cameroon, so wani lokaci yana haɗuwa da turawa da larabawa, ya sha ganin kyawawa sosai, har Nigerians kyawawa masu kama da larabawa da turawan ma ya sha cin caro da su, so kyan Jaish bai ɗaga mashi hankali ba, haka ita ma Mahreen. Ko da yake wannan yarinyar kam me ma zai bata tsoro? Ina ga sai idan ta ga aljanin gaske kila ta tsorata. Sharo ɗakin ya yi ya fito mata da dattin, sannan ya bata tsintsiyar, da sauri ta karɓa ta fara sharar tsakar gidan. Wata yar yarinya da bata wuci sa'ar Mahreen bace ta yi sallama a kofar gidan tare da yaye labulen buhun ta shigo. Amsa mata sallamar Mahnoor ɗin ta yi tare da ɗagowa ta kalleta. "Adda Mahnoor gwaggo Rabi ta ce in zo in tambayi meyasa baku zo karatun ba?" Islamiya ce suke zuwa a gidan maƙota kullum daga karfe uku zuwa shidda ake tashi, wata mata ce wadda suke cewa gwaggo Rabi ita ce malamar, naira 50 ake biya duk sati idan ta zago, shi ne kuɗin islamiyar. "Mahreen ce ta yi barci, ni kuma yau Bappa yana aiki sosai, bai zo wajen kiwo ya karɓeni ba sai yanzu na dawo, shiyasa bamu zo ba, amma zamu zo karatun dare In Sha Allah". Ta bata amsa tare da duƙawa ta cigaba da yin shararta. Tom yarinyar ta amsa mata tare da juyawa da sauri ta koma islamiyar, dan ana can ana ta karatu. Share gidan tsab ta yi kafin ta fito da wanke wanke ta wanke tas, da alama tana da tsabta sosai, ga nutsuwa. Bayan ta kammala wanke wanken ne ta nufi kitchen, sai da ta share shi tsab, sannan ta hau hura wutar itace ta ɗaura tukunyar ƙasa mai ɗan girma tare da sanya ruwa rabi a cikinta, ta tada wutar sannan ta fito. Tana fitowa Mahreen ma ta fito daga cikin ɗakin Bappa tana zuba uban hamma kamar zata ci babu. "Adda Mahnoor ina abincina?". "Kai Mahreen daga tashi? Ba batun yin sallah bare ki tuna yau bamu je islamiya ba, bare kuma wanka, ke dai abinci kawai daga tashi? To ga shi a rufe a cikin kitchen, idan kin gama ci sai ki zo mu je gidan Arɗo mu duba Nenne". Tsalle ta yi ta dire kafin ta ce. "Wlh ni dai ba zan je ba, wai ke Adda Mahnoor bama zaki yi murna da Nenne ta tafi ba sai ki ce mu je mu dubata dan ta dawo? Ke wato ma baki damuwa da shegen masifarta ko? Tom ni ban son ta dawo, da sassafe ta tashi mutum da faɗanta da awaki, sai ta yi ta zagin awaki da karfi karfi kamar sun ce mata suna jin magana, duk ta bi ta tashi kowa daga barci, ni babu in da zanje, gara ma da Bappa ya kawo wannan aljanin, kinga yanzu dole ta koma gidan Arɗo da zama ai, ni kam ma aljanin kyau ya yi mun". Baki Mahnoor ta saki tare da gwalalo ido tana kallonta, tasan halinta sarai fin hakan ma zata aika, amma abin da ya bata mamaki ta saki baki tana kallonta shi ne cewa da ta yi aljanin ma kyau ya yi mata, wato ya burgeta, ko tsoronsa bata ji ba. Tana tsaka da tuna Mahreen ɗin ta katseta da cewa. "Adda Mahnoor wlh kumatun aljanin nan kamar irin breadin da Bappa yake kawo mana idan ya yi tafiyar nan, idan kina taɓa kumatunsa zaki ji daɗi".......... Hasbunallahu wani'imal wakil, Mahreen zata kashe mutun da dariya. Zaro idanu sosai Mahnoor ta yi. "Kumatun nasa kika taɓa? Ke Mahreen ina kike son ki tsaya ne wai? Ai dolema kanki ya rinƙa rawa, aljanu wasa ne, daga gani sun shiga kanki shiyasa baki tsoronsu, dole zan gayawa gwaggo Rabi idan muka je karatun dare, dan ta yi maki addu'a, yanzu dai zoki ci abincin ki je ki yi wanka sai muje wajen Nenne". Ta yi maganar cike da tsoron jin cewa Mahreen ta taɓa kumatun aljani. Sake yin tsalle ta yi ta dire. "Wlh Adda Mahnoor ni ba zan je wajen Nenne ba, ke ni fa banson ta dawo nace maki". "Mahreen kina da hankali kuwa? Wato duk nasihar da gwaggo Rabi take yi mana a kan bin iyaye ke bakya ji ko? Kina son Allah ya la'anceki ne? Mahaifiya fa? Wlh tun wuri ki yi istigifari sannan kizo ki wuce ki yi abin da nace maki mu gama aiki mu je wajenta, da take yin masifa da akwaki dake take yi ne? Ba shegen kunnenki na jin gulma yasa kike iya jiyota ba? Ni meyasa bana jin faɗar safen nata da awakin?". Turo bakin nan ta yi kamar zata sa kuka, cikin kuncin rai na bata son Nenne ta dawo ta nufi cikin kitchen ɗin dan ta ɗauki abincinta, yadda kuka san Nennen nan kishiyar mamarta ce ba mahaifiyarta ba, wai ta cika masifa. Cigaba da aikace aikacenta ita kuma Mahnoor ɗin ta yi, sai sauri take yi dan ta gama suje wajen mahaifiyar tasu a gidan kansu Arɗo kenan, shi ne mahaifin mahaifiyar tasu, kuma shi ne sarkin wannan ruga, kawu yake wajen mahaifinsu kuma, duk dangi ne. Ita kuwa Mahreen abincinta ta ɗauko ta zauna a saman kujera irin na zaman tsakar gidan nan ta fata ci tana turo baki dan bata son zuwa gidan kakan nata, kuma kakan nasu fa yana kaunarsu sosai, dan su kaɗai ne jikokinsa, amma da yake ita Mahreen bata son gaskiya, bata son ayi mata faɗa yasa ta tsanesa, dan kawai yana yi mata nasiha a kan ta nutsu. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 Yau kwana uku kenan da kai baban Zainab makwancinsa, wato gidansa na gaskiya. Khadija dai shiru babu ita babu labarinta, su kuma dangin babanta basu ma bi ta kanta ba, bama su san tana nan ko bata nan ba, kuma basu damu da su sani ba, sun mayar da hankulansu kan zuwa station da hanyar kotu wai lallai dole sai an biyasu jinin Baban Zee da maman Zainab ta salwantar, sun kafe sam ba zasu ɗaga kafa ba. Sadiq ya ji duk abin da ya faru, amma ya ɓoye ya kasa iya gayawa mamarsu saboda tana da hawanjini haɗe da ciwon suga, yasan in ta ji me ya faru da maman Zainab zata iya haɗiyar zuciya ta mutu, ko hawanjininta ya tashi, shiyasa ya ɓoye mata. Ya zo Kanon amma an hana shi ganawa da ita, almost kafa uku yana zuwa cell ɗin, amma sun hana ya ganta, tashin hankali iya tashin hankali ya shiga, wannan ba maganace da zai ɓoyewa mamarsu ba, amma ya rasa ta yadda zai iya gaya mata, ko dan ta sanya maman Zainab ɗin a cikin addu'a yakamata ya gaya mata, amma ya rasa hanya, bawan Allah ya rasa mafita. Ita ma Zainab dake ƙunshe a cikin ɗaki tana fama da zazzaɓi mai zafi babu wanda ya kulata, basu bi ta kanta ba, ba dare ba rana tana cikin ɗaki, bata taɓa leƙowa ko parlourn, har ɗaki Sadiq yake binta da abinci idan ya faki idanunsu Maman Haidar basa gidan, idan sun fita sai ya shigo gidan ya kawo mata abincin, sun hana shi shiga gidan ne yasa yake shiga a sace. Yanzu haka sai haukar neman Khadijan yake yi ba dare ba rana, har ma ya shigar da report, dan Zainab ta gaya mashi cewa Khadija tun ranar da maman nasu ta kashe babansu bata sake ganinta ba, tashin hankalin da Sadiq ya shiga sam ba zan iya fassara maku ba, kusan hauka ɗan tahalikin nan ya yi. Haƙiƙa ya tabka babban danasani na barinsu da ya yi ya koma Kaduna, kukan zuci yake yi yana faɗin laifinsa ne, da yana nan koma yaya zai hanata aikana wannan babban kuskuren. Yarinyar nan Zainab duk ta fita a hayyacinta, ta dawo shiru bata magana, ko ka yi mata magana sai dai ta girgiza maka kai kawai ko ta gyaɗa ta, amma ba bakin magana, ta zama abar tausayi, har rama ta yi!. Shi kam Haidar ma da alama baya garin, dan shiru kake ji, da yana nan dai zai ɗan leƙo koma yaya ne Wannan shi ne halin da familyn Baban Zee suke ciki, bari mu leƙa wani season ɗin. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 20/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ ❤️𝐓𝐇𝐄 𝐂𝐑𝐎𝐖𝐍 𝐎𝐅 𝐈𝐍𝐉𝐔𝐒𝐓𝐈𝐂𝐄💔🥺 𝐎𝐑 🖤𝐀 𝐃𝐀𝐑𝐊 𝐖𝐎𝐑𝐋𝐃🌑 RAWANIN ZALINCI ko BAKAR DUNIYA. Shi ne sunan da suke kiran wannan birni da shi, ɗayawa daga cikin mazauna wannan birnin ne suke kiranta da CROWN OF INJUSTICE, wasu kuma su kirata BLACK WORLD. Meyasa sunanta ya kasance a haka? A tarihi ya nuna cewa shekaru da dama da suka suɗe, babu kasa a wannan wajen ma bakiɗaya, daga baya aka kirkireta, Amma mu shiga cikin labarin, koma menene dalili a hankali zamu ji komai. Dark world, birni ce mai matuƙar girma, akwai tsawo da kuma faɗin kasa gabaɗaya, sannan birni ce mai yelwar abubuwa da dama, irinsu abinci nauika daban daban, dan suna noma sosai, ruwan sha mai tsabta da masana'antunsu ke bugawa, ga ishasshen ruwan noma koda rani ne, dan suna da tapkeken teku dam mai matuƙar girma da sarkinsu ya kaddamar masu shekarun baya, suna da yelwar isassun kayan sakawa, dan suna da manyan camfanoni dake sarrafasu a birnin, wanda suke sarrafa kayan sakawa da sauran abubuwansu na amfani, suna da yelwar kasar noma, kaso sittin cikin ɗari na mazauna wannan birni da noma suka dogara, da akwai makiyaya, sai dai basu da yawa, akwai ƴan kasuwa, ma'aikata da dai sauransu. Birni ne mai cike da kawa tare da ɗaukar hankali, suna da matuƙar tsabta ta yanda ko leda ba zaki gani a kan hanya ba idan kana tafiya, akwai masu sharan kan hanya kullum safe da yamma, sannan a kowani lungu da saƙo akwai manya manyan abubuwan zuba datti ta yadda ba zaka ga datti a kan hanya an zubar ba, idan abin zuba sharan ya cika sai a kai bayan gari a zubar, shi ma wannan akwai masu kula da wannan ɓangaren, haka zalika suna da gine gine masu matukar kyau da ɗaukar hankali, ga manya manyan tituna da suka keta har ta cikin unguwanni, wajajen wasanni haɗe da wajajen yawon buɗe idanu, manya da ƙananan jiragen ƙasa, jiragen sama, manya manyan buses, danƙara danƙaran motoci da dai sauransu. Komai nasu abin burgewa ne, ga su da tsari wa rayuwarsu, kama da ga shigarsu mu'amalarsu, yanda suke rayuwa, cuɗanyarsu, tsabta da dai sauransu duk abin birgewa ne. Ga dukkan alamu kuma basu son hayani, kuma basu son faɗa. Sai dai kuma babban abin birgewa da birnin nan shi ne, duk wanda ka ɗaga idanu ka kallah in ma matashi ko dattijo, to sai ka gan shi da kirar mayaka, abin da abin mamaki, mafiya yawan waɗan da suke simtiri a tsakiyar birnin kuma mata ne, zaka iya wuce mata hamsin ba tare da ka kalli namiji ɗaya ba, kasuwanninsu, gonakinsu da sauransu, dukka mata ne zaka tarar a wajen ba maza. Yanayin dressing na kayan jikin matan wannan birni ya kasance irin dogayen sket ɗin nan ne zuwa har ƙasa, da riga zuwa ƙugu, yanayin yanda sket ɗin nasu yake sai ya baka sha'awa, dan daga ta sama ya kamasu tare da fitar musu da shapes nasu, daga zuwa dai'dai gwiwa kuma, ya buɗe sosai kamar umbrella har zuwa ƙasa, sannan suna da wata shiga da suke yinta a duk ranar jumma'a da kuma ranar lahadi, ita ma ta kasance shiga ce mai matuƙar burgewa da ɗaukar hankali, riga ce dogowa zuwa ƙasan gwiwarsu, rigar tana da maɗauri a tsakiyar cikinsu, sai kuma ƴar karamar hannun ke gareta, shi ma rigar like A shape take, shi ga ce ta zuwa wajen bautarsu. Ko wacce mace ka kallah zaka tarar da irin ɗinkisu kenan, kuma yana da matukar kyau tsantsa a jikkunansu, duba da yanayinsu na rashin kiba, ga bala'in shape mai tsananin kyan gaske da suke da shi, shape nasu akwai matuƙar ɗaukar hankali, daga manyansu har yara, tamkar su suka yi wa kansu. Kuma abin mamaki da burgewa kusan kamanninsu iri ɗaya, fararene kal, zaka iya wuce mata hamsin farare ba tare da ka haɗu da baka or chocolate color ba, gasu da bakin gashi tamkar su suka bawa kansu. Sai dai ga dukkan alamu gabaɗayansu mutanen birnin suna da addini na daban, akwai abin da suke bautawa dukkansu, ba musulmai ba ne, kuma da yuwuwar addini ɗaya suke bi, abu ɗaya suke bautawa, suna da yelwar tsawon gashi wanda mafiya yawansu ya kai musu har tsakiyan bayansu wasu kuma har ƙugunsu, basu ɗaura ɗankwali sam sam a kawunansu, suna yin abubuwansu bisa bin doja da oder. Sai harkokin gabansu suke yi, ba su wani damuwa da komai da kowa ba, da alama akwai halin ko in kula a tattare da su sosai. Daga gefe tsallaken titi wajen wani makeken rumfa taron wasu gungun matasa ne wanda za su iya kai su 20 a wajen suke zaune, wani kayatatcen rumfa mai matukar kyau wanda yake tamkar da zinari aka yi shi saboda tsantsar kyau. Dukka mazan dake wajen shigarsu iri ɗaya, sannan dukkansu kirar warriors ne a tattare da su, wandon jikinsu ya kasance brown color mai ɗan faɗi, sai riga mai maɗauri a dai'dai ciki, while faffaɗar kirazansu a buɗe, dan gaban rigar a buɗe take, shi kalar rigar ta kasance milk color, gabaɗaya mazan suna da yalwar tsawon gashi sosai, da alama irin kiristocin nan ne masu tsananin tsauri a kan addininsu, waɗan da suke koyi da annabi isa, su ne masu barin gashinsu ya yi tsawo sosai irin na Annabi Isa, haka suka kasance. Suna koyi da shi amma basu yarda su musulunta ba, da ni da ku dai duk mun san annbi Isanmu musulmi ne, su dai ina sun dai yarda shi ne Allansu ba Ubangijinmu ba. Ga wasu kananan yara da suke ta wasanninsu a wajen, mata suna ta kai kawo cikin wannan shigar tasu mai ɗaukar hankali da matuƙar kyau. One thing about DARK WORLD shi ne, kewayayyen birni ne yana da kofifin shiga da fita, tampatsa tampatsetsan gates ne kamar dai masarautun zamanin da suka suɗe. Lokacin guda gabakiɗaya gungun mazan dake zaunen suka mike tsaye gabaɗayansu. Gabaɗaya harta mata dake bakin hanya suna kasuwancinsu da harkokinsu, da mata masu wuce duk sai da suka wani ja birki suka tsaya tare da kamewa kam, komai dake arean wajen sai da ya dakata cak, harta kananan yara da suke wasa a wajen sai da suka shiga taitayinsu. Nan take wani tsananin tsoro ya bayyana a saman fuskokinsu, fargaba da tashin hankali ya ziyarci zukatansu, kallo ɗaya zaka yi musu kasan suna cikin tsananin tashin hankali. Abin da ɗaure mun kai!. A wani irin mahaukacin gudu wasu danƙara danƙarar motoci bakake kirin suka shararo ta saman wannan tabkeken titi da waɗan nan jama'a suka kame kam ɗin. Sosai motocin suke zabga uban gudu tamkar zasu tashi sama. A yawa ba zaka iya ganin karshensu ba, dan a kalla zasu kai 50 haka, dukkansu kala ɗaya suke except 1, sannan kuma dukkansu motoci ne da suka amsa sunansu motoci motocine masu numfashi wanda tamkar da gold aka yi su tsabar kyau da ɗaukar idanu, sun haɗu iya haɗuwa, gabakiɗayansu bakake ne kirar *BUGATI* tayun motocin ma kawai abin kallo ne, tamkar ba'a kan ƙasa suke tafiya ba, saboda tsananin kyau, ga wani kuka da suke yi mai fita a hankali hankali tamkar ba kuka suke yi ba. Da zarar sun dimfari waje to tun daga farko hanyar jama'a suke fara kafesu da idanu, kirazansu na dukan uku uku har motocin su wucewa ganinsu! Suna matuƙar ɗaukar hankulan mutane na wuce misali. Sai dai fa ganinsu ba alkhairi ba ne sam sam a cewar jama'ar wannan birni, duk wanda yake cikin wannan birni babu wanda yake sha'awa da kuma fatar yin ido huɗu da su, suna da kyau da ban sha'awar gani a ido, amma kuma ganin nasu yana matuƙar gigita duk wata halitta dake a cikin wannan birnin, yana razana ƙwaƙwalwar manya da yara, yana tsantsar birkita mata da maza, suna dimfarowa waje zaka ga gabakiɗaya kowa ya sha jinin jikinsa, hankula sun tashi, masu ɓari kayansu suna yi, masu sakin fitsari a wando suna yi, masu ruwan hawaye suna yi, wannan ma a iya wucewa kawai motocin zasu yi, ba tsayuwa zasu yi ba, amma har wani ɓarin abin hannunsu mutanen suke yi, wata ma ko da abinci ta ɗauko bata sanin time ɗin da abincin yake kifewa ya zube saboda tsananin fargabar wucewar motocin. TO SU WAYE SU? MEYASA JAMA'AR WANNAN BIRNI SUKE TSORONSU HAKA? PRINCESS TEEMA CE KAWAI ZATA BAKU WANNAN AMSA, DAN ALKALAMIN TA NE KAWAI ZAI RUBUTA MUKU KOMAI, KU DAI KU KASANCE DA NI DAN JIN KOMAI DALLAH DALLAH!!. Waƴannan dankara dankaran tsadaddun motoci guda hamsin ne ciff, dukkansu bakaƙen ne kirin, gudaɗaya ne ya kasance FARI kal a cikinsu, da alama ma tsadadden fenti na daban aka yi mishi, dan irin farin shi na daban ne, up white ne sosai. Kai tsaye suka nufi wajen wani tafkeken gida wanda bama zaka ce mishi gida ba, sai dai gari guda, gida ne da babu makamancinsa ma a wannan birni. Wani irin tampatsetsen gate ne wandan girmansa ma kawai abin kallo ne, shi ne a manne a kofar wannan aljannar duniya, daga gefe da gefe gate ɗin gumakai ne na bakar damusa ya buɗe baki aka sassaƙa, sun yi zaman kasaita tare da wage baki, ga zabga zabgan hakwara a waje, wannan makeken gate ɗin da zallar gold akayi ta. A saman aihanin kayin gate ɗin shi ma da zallar gold aka yi gunkin bakar damisa a wajen, daga kasar gunkin an yi rubutu da manyan baki wanda ya kasance shi ma da zallar gold aka yi shi. Ba komai aka rubuta a wannan waje ba kuma fa ce 𝐁𝐋𝐀𝐂𝐊 𝐓𝐈𝐆𝐄𝐑 𝐄𝐌𝐏𝐈𝐑𝐄, wato Daular black Tiger. Gate na shiga cikin gidan har guda huɗu ne, gate na farko an yi shi ne tamkar na kariya daga mayaƙa, saboda yanayin yanda yake a dafe babu abin da zai iya fasa shi. Gate na biyu ma kusan haka ne, jikinsa ma dukka kifiyoyin yaki ne wanda zai nuna maka cewa gidan zaratan jaruman mayaƙa kazo. Gate na uku kuma fashion gate ne mai bala'in kyau, sai gate na karshe da zai sadaka da cikin Daular, ya kasance gate ne da aka yi shi shi ma da zallar gold kamar gate na farko, sai ɗaukar idanu yake yi, yana wani walwali na wuce misali, a kowani gate sai da aka yi irin rubutun dake jikin gate na farko, wato 𝐁𝐋𝐀𝐂𝐊 𝐓𝐈𝐆𝐄𝐑 𝐄𝐌𝐏𝐈𝐑𝐄. Daular black Tiger, Daula ce mai matuƙar girman gaske wanda ya amsa sunansa Daula, fili ne mai girman ikka 150, idan ana magana ikka 150 ya kai wani garin mai girman gaske, Daula ce wanda a cikinta akwai dogaye gine ginen zamani na gani a faɗa, har ta high rise building akwai a cikin ta, sannan akwai kanana kananan gine gine, har da bukkoki da akwai a ciki, suna da yelwar abubuwa da dama ciki Black Tiger, shi ne sarkin wannan daula dama birnin 𝐃𝐀𝐑𝐊 𝐖𝐎𝐑𝐋𝐃 bakiɗaya, shi ne yake mulkan kowa dake cikin birnin, black tiger da yawan mutanen garin suna cewa ba mutun bane, wasu su ce mutun ne wasu akasin haka. Sai dai kaso 80 cikin ɗari sun fi raja'a a kan cewa shi ba mutun bane shi aljani ne!. Ko me dalili?. Babu wanda ya taɓa ganinsa ido da ido! Babu wanda ya taɓa jin sautin muryarsa! Yana mulki ne son ransa! Yana juya duk wanda ya ga dama! Bakin azzalumin ne number ɗaya! Mulkin zalinci yake gudanarwa! Zallar rawanin zalunci ne a ɗaure a kansa wanda babu ɗigon adalci ko kaɗan!! Sai dai idan ka bi ra'ayinsa zaka zauna lafiya! Akasin haka kuwa, watar tashin hankali da shiga bala'in ka ne ya tsaya kai da danginka! Baya kisa kai tsaye idan ka yi mashi ba dai'dai ba! Sai ya azabtar da rayuwar bawa fiye da tunanin mutun kafin ya kashe shi! Ba ruwansa da wata doka! Hukuma bata isa ta tinkari 𝐃𝐀𝐑𝐊 𝐖𝐎𝐑𝐋𝐃 ba! Shi ne hukumar kansa! Shi ne shugaban ƙasa, gwamna, minister, Sarki, da duk sauran jami'an doka! Shi ne komai na birnin nan! Shi ya kafa ɗaularsa da kansa! Da dukiyarsa ya gina komai dake cikin birnin! A baya shekaru da dama da suka shuɗe wajen daji ne! Shi ya zo ya kafata tare da kawatata da ɗunbin dukiyarsa! Yana da dukiya fiye da tunaninku. Sannan ƙasar DARK WORLD tana da ɗunbin albarkatun ƙasa irinsu ɗanyar gold, ɗanyar manfetir, aluminum na haɗa baturan mota! Kai suna da tarin albarkatun ƙasa sosai, so ta hakan ya tara ɗinbin dukiya na wuce misali, shiyasa harta gate na shiga daularsa ma ɗanyar gold ce, saboda suna da ita wadatatciya a ƙasar, duk wata ƙasa da ta yi yunƙurin shiga DARK WORLD domin ta cucesu ta kwashe masu albarkatun ƙasa to fa Black tiger sai ya yakesu, sai ya kifar da su komai girman daularsu, bashi da imani sosai, yana da tarin sadaukan warriors fiye da tunaninku, yana ji da su, dan sune suka sa yake murza kambun RAWANIN ZALINCI son ransa, sune suka sanya ake TSORONSA over. Abu na farko da yasa jama'ar wannan birni suke kiran black tiger da bakin azzalumi shi ne, in dai mace ta haifi yaro namiji a cikin birnin DARK WORLD to fa babu ita babu wannan yaron, tun yana jajiri black tiger zai sanya a ɗaukosa, tun yana ƙarami bai san komai ba zasu fara horar da wannan yaro, haka zai taso ɗaya daga cikin mayaƙan DARK WORLD, uwarsa kuwa sai dai idan ya girma ya zo wajenta in yana ra'ayi, amma ba shakka mukarraban black Tiger ke renan yara maza su mayar da su mayaƙa, hakance ta bashi damar tara uban ɗinbin mayaka da yake amfani da su wajen kara karfin iko ya kuma yaki duk masarautar da bata yi mashi ba, haka zai yakesu ya kuma zauna lafiya ya ci banza. Duk in da ya sami labarin masaurata sun girma suna da karfin iko, to shi kuma yana haɗa dakaru ne su je su yake su, dole ya tilastawa masarautu su yi mishi mubaya'a, hakan tasa karfin ikonsa a kullum sai kara hauhawa yake yi, dole dole idan ya ɗaura idanuwansa a kan masarauta sai sun dawo karkashin kafarsa! Ko su so ko suki! Zai saka musu karfin damtse! Yana da dakarun yaki ƴaƴan mutane da ya tattaro dan zalinci sosai, an horar dasu ta yanda basu san ja baya a yaki ba, basu da imani ko ɗigo a ransu, duk da cewa kullum suna cikin kayan yaki, amma ganinsu kawai babban tashin hankali ga ɗan adam mai rai, idan mutun yana da zuciya a kusa, take zai mutu idan ya yi arba da dakarun yakin 𝐁𝐋𝐀𝐂𝐊 𝐓𝐈𝐆𝐄𝐑. Haka fa yake raba ƴaƴa maza da iyayensu tun suna jarirai dan mugunta, amma ba ruwansa da ƴaƴa mata, in zaki haifi mata ɗari a birnin babu ruwansa da ke, mafiya yawan ƴan'matan birnin basu da aure, saboda duk ya tattare mazan ya mayar da su warriors ɗinsa, sai dai ya turasu yaki a kashe na kashewa a yaki, gobe baya hanashi idan aka haifo maza ya tattara, kamar bai san darajar rayuwa ba shi dai. Kuma fa idan suka je yaki suka yaki masarauta baya barinsu haka kawai, dan mugunta sai ya tabbatar ya kwashe masu warriors ɗinsu sun dawo masarautarsa dan ya kara karfi, ya kara tara tulin mayaƙa ta yadda zai sa a cigaba da jin tsoronsa yana azabtar da mutane son ransa. Wannan shi ne ga mari ga tsinka jaka hmmmmm. Sai dai kana da damar da zaka so yarinya a cikin birnin har ma ku yi aure a matsayinka na warriors, idan ba yaki za'a tafi ba zaka iya kasancewa a tare da ita har ku samu ciki, kuna haifar ɗa namiji Black Tiger kuka haifawa, idan kun haifi mace kuma to wannan takuce, ku reni kayarku ku bata tarbiya yadda kuke so, idan aka kashe mijinki a wajen yaki kuma adalci ɗaya yake yi wa mace, shi ne ya ɗauki nauyinta ci da sha da komai na bukatun yau da kullum. Shi fa bai tsaya iya nan ba, ina ina zalincinsa ya wuce haka. Daga ta cikin gidansa ko in ce daularsa kuma........ Yana da zaratan maza ƴan Wrestling wanda su horo na musamman ya sa master ya basu, su ya ajiye sune saboda nishaɗinsa, a ko da yaushe ana zubo sabbin ƴan Wrestling ɗin, matasa masu jini a jiki ake kwasa a ɗauki tsawon watanni ana basu training ɗin Wrestling sosai. Su ƴan Wrestling ɗin yana ajiye su ne duk ranar da yake cikin nishaɗi, sai ya sanya biyu Wrestling, duk wanda ya faɗi, to kashe shi za'ayi, dan a rayuwarsa ba kalmar da ya tsaya irin kalmar faɗuwa, shiyasa duk ranar da ya fitar da sanarwa za'ayi Wrestling a birnin gabaɗaya hantar ƴan Wrestling ɗin sai ya kaɗa, saboda sun san dole ɗaya daga cikin sai ya faɗi, haka kuma wanda ya ci shi zai kashe wanda ya faɗin a gaban kowa da kowa! Abu ne wanda aka saba yin shi ba sau ɗaya ba sau biyu ba!. Kuma koma waye ne ya faɗi haka za'a kashe shi a gaban kowa ba ɗaga kafa, baya yafiya sam sam, bai ma san menene yafiya ba, kuma ko zaka mutu baya canza magana, wannan shi ne zalincinsa na biyu kenan, idan za'ayi wasan harta mutane gari suna zuwa kallon, dan shi dole a gaban jama'a yake sakawa a kashe mutun bayan an azabtar da shi kowa yana gani, shi dai baya fitowa, amma duk abin da yake faruwa a birnin yana sane da komai, shiyasa suke ce mashi ba mutun bane aljani ne, yana sanin komai tsab, ko Wrestling idan ana yi yana ganin komai, amma su basa ganinsa, bama su san takamaiman ina yake ba a cikin Daular tasa. A takaice dai sam bai san kalmar faɗuwa ba a rayuwarsa, nasara ya sani, shiyasa duk wanda ya faɗi ake kashe shi, dan baya haɗa hanya da faɗuwa sai nasara, azzalumin ne number ɗaya a duniya, sunansa kawai tana girgiza alkarya! Tana jijjiga manyan masarautu dake kewaye da shi! Shiyasa da yawan masarautu basu son su yi abin da zai sa su cigaba, dan kada idanunwan black Tiger ya hau kansu, amma a hakan akwai masarautun da suka haɗa kai ta bayan fage suna shirya ta yadda zasu yi su yakesa dan su sami ƴanci su huta da zalincnsa da ukubarsa. Wani lokaci tsabar zalinci idan muguntar ta motsa haka kawai zai sanyawa matasan mayakansa gasa, duk wanda ya faɗi kuma kashe shi zai yi, shi fa har wani nishaɗi yake yi idan ana kashe mutane. Abin mamakin kuma a nan shi ne, duk lokacin da na hannun damansa ya fitar da sanarwa a kan Black Tiger ya sanya wata gasa, wlh har rige rige matasan suke yi a kan cewa su zasu buga gasan, saboda suna da jajircewa da karfin zuciya, duk da sun san idan ɗaya ya faɗi gasan kashe shi za'ayi, amma hakan baya hana su ce lallai zasu yi, dan kowannensu gani yake yi babu mai iya ja da shi, shi ma ya cika kuru kuma Barde!! A haka suke ta kashe kawunansu!. A duk lokacin da 𝐁𝐋𝐀𝐂𝐊 𝐓𝐈𝐆𝐄𝐑 yake son ya yi magana da mutanen garin ko mutanen gidansa or ma'aikatansa, in dai yana son fitar da wata sanarwa na za'ayi abu ko biki ko wani abin, ko sabuwar doka, ko dai wani shirginsa can or za'a tafi yaki, to yana da na hannun damarsa har mutun biyu, ɗaya macece mai suna Delisha sai kuma namiji mai suna Devil wato shaiɗan kenan, shi da sheɗan ɗin ma ake kiransa tsabar iya kwarewa a mugunta, to ta hannunsu duk wani saƙonsa yake isa ga jama'ar birnin DARK WORLD. karin wani haske a kan dark world, duk wanda ya shigo cikinta ya shigo kenan, baya iya fita, komai zalincin da za'ayi mishi, zai ji ba zai iya rayuwa a wani ƙasa ba sai nan ɗin. Burin black Tiger abu ɗaya ne a duniya, shi ne mulkar duniya bakiɗaya, bashi da burin da ya wuce wannan, a kullum lissafinsa shi ne ta yaya zai yi ya mallaki duniya kamar shi ya kafata! Ya zama shi ne mai juya kowa da komai kamar shi ya haliccemu!! Ya zama mai ikon faɗa kuma dole a ji shi. Tamkar hauka! Tamkar mayunkacin zaki haka yake farautar yadda zai yi ya mulki duniya. Sai dai kuma kafin mulkar duniyar yana da bukatar ƙarin karfin iko da zai iya kwatanta hakan. Matuƙar yana son ya kara karfin ikon da zai iya kwatanta mulkar duniya kuma to dole sai ya kasance yana tare da 𝐒𝐏𝐈𝐍𝐃𝐄𝐑, shi ne kawai zai bashi karfin ikon da zai iya kwatantawa. A halin yanzu a yunwace yake yana haukar neman 𝐒𝐏𝐈𝐍𝐃𝐄𝐑, sai dai fa kafin ya samu 𝐒𝐏𝐈𝐍𝐃𝐄𝐑 sai ya haɗu da mutane mafiya haɗari a duniya guda biyu a hanya, cikon na ukun idan ya yi wasa ita ce zata iya zama ajalinsa! Idan kuma ya zage, to zai iya zama ajalinta ya karɓi 𝐒𝐏𝐈𝐍𝐃𝐄𝐑. Waɗan nan mutane biyu da zai wuce kafin ya isa ga na uku, akwai green eyes wanda shi ma a yunwace yake yana neman 𝐒𝐏𝐈𝐍𝐃𝐄𝐑 ɗin kamar hauka, dan shi ma burin mulkar duniyar ce a ransa, shi kuma mutun na biyu, tare yake da 𝐒𝐏𝐈𝐍𝐃𝐄𝐑 waje guda, sai dai bai san a dai'dai ina yake ba, babu kuma wanda ya sani sai wannan cikon ta ukun. A takaice dai yanzu burin Black Tiger shi ne ya isa ga 𝐒𝐏𝐈𝐍𝐃𝐄𝐑 ko ta halin ƙaƙa!!..........E LALLAI AKWAI AIKI BA KARAMA BA, AKWAI TAKUN SAƘA TARE DA CAKWAKIYA, YANA DA KYAU MU SAN AINAHIN TARIHIN BLACK TIGER, MEYASA YAKE SON MULKI HAR HAKA? MEYASA DUK WANDA YA SHIGO DAULAR DUK MIN ZALINCIN DA ZA'AYI MISHI ZAI JI BAYA SHA'AWAR FITA DAGA CIKINTA? DUK DA SUNA TSORONSA AMMA BASU DA BURIN DA YA WUCE SU ZAUNA A DARK WORLD, MEYASA? SHIN DA GASKE 𝐁𝐋𝐀𝐂𝐊 𝐓𝐈𝐆𝐄𝐑 BA MUTUN BA NE? MU JE DAI ZUWA, ALKALAMIN NA NE KAWAI ZAI WARWARE MUKU ZARE DA ABAWA, KOMAI ZAI WARWARE A CIKIN NATSUWA!!. One thing about BLACK TIGER shi ne bashi da kowa na daga ƴan uwa, shi kaɗai ne ya zo ya gina birninsa har mutane suka taru a cikinta, babu wanda ya taɓa sanin labarin wani dangi nasa, hakan ma yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa mutanen birnin suke cewa shi ba mutun bane, ga shi basu taɓa ganinsa ba bare su ce ko zasu ga mai kama da shi su ce ɗan uwansa ne!!. TUN DA MUN ƊAN JI TAKAICE LABARI A KAN KING 𝐁𝐋𝐀𝐂𝐊 𝐓𝐈𝐆𝐄𝐑 TO MU KOMA KAN LABARINMU. Wasu jiga jigan zaratan Warriors, wato mayaka ne suke gadin gate na farko, wanda already shi a buɗe yake. Kutsawa ciki waɗan nan motocin suka yi, cikin girmamawa waɗan nan mayaka masu tsaron gate ɗin suka risinar da kansu ƙasa har sai da gabaɗaya motocin suka gama wucewa, sannan suka ɗago tare da binsu da kallo. A gate na biyu da na uku ma hakan ce ta kasance kamar yanda ta faru a na farko, sai dai a gate na karshe da zai sadaka da cikin gidan sai da suka tsaya, suka jira jaruman mayakan suka buɗe musu kofar, sannan suka danna ciki a guje, gabaɗaya glass na motocin bakake ne, baka iya ganin kowa da yake ciki. Tsabar girman Daular tasa ta kwashe motoci hamsin ɗin nan cif tamkar bata ɗauki komai ba, motocin sun jeru layi mai matuƙar kyau, a wajen da ya kasance parking space na gidan, dama already sun saba tsayuwa a hakan, abin dai gwanin ban sha'awa a idanu. Almost 10 mins da tsayuwarsu kafin a buɗe kofofinsu bakiɗaya lokacin guda daga ta ciki, gabakiɗaya cikin Empire ɗin daga yara har manya, mata da maza ko wannensu ya kame waje guda, duk sun sha jinin jikinsu, zaratan jiga jigan mayakan dake shawagi a cikin daular duk sun kame waje guda, ko numfashi da kyar suke yinta, gabaɗaya cikin Empire ɗin jiran suke yi a buɗe wannan farar motar kawai, sun takura sosai saboda numfashi ma basu iya ja sosai. Ko da aka buɗe motocin sai da suka sake ɗaukar good 5mins kafin wasu jiga jigan zaratan maza lafiyayyu masu kiran karfi su sako kafafunsu wajen motar, sannan suka fito waje gabaɗaya. Maza ne madaka katti, suna da tsawo da lafiyayyen jiki, dukkansu suna sanye ne cikin maroon suit, sannan dukkansu akwai black zane na Tiger irin na saman tambarin bakin gate ɗin shigowa Empire ɗin a fuskokinsu. Zanene wanda idan aka yi shi ba zaka iya gane fuskar wanenen ba ne, kamkar dai wani abin ne suke sakawa. Geruwa suka yi layi guda tun daga farkon bakin motocin nasu har izuwa karshe. Wani ƙosasshen mayaki ne ya ƙariso wajen ya buɗe kofar wannan white car ɗin, da alama dukkansu dakon na cikin white car ɗin suke yi ya fito. Suna buɗe mashi motar ya sanyo kansa waje. Matashin saurayi ne da ba zai wuce 17 to 18 years ba a duniya, matashi ne mai ɗan madaidaicin jiki. Yana sanye da face mask a face ɗinsa. Sanye yake da tsadaddun kaya wandon jeans da riga ya ɗaura coat a sama, sannan ya sanya hular malafa a kansa, hannunsa na riƙe da sandar sarauta wanda aka yita da ɗanyar gold, takalmar kafafunsa masu bala'in tsada ne, duk abin da zaku gani a wannan birni mai tsada ne sosai, basu da talauci sam, dan Allah ya albarkacesu da tarin arzikin ƙarƙashin ƙasa da kuma ta teku, wannan teku dam da King Black Tiger ya janyo masu ya zo masu ta tarin arziki sosai, ga shi suna samun ishasshen ruwan noma ta yadda amfanin gonansu yake yin kyau, ga su da cin abinci mai gina jiki sosai, saboda akwai wadataccen ɗinbin dukiya a ƙasar. KARFIN IKO, KARFIN MULKI, ƊINBIN TARIN TULIN DUKIYA, ƊINBIN TARIN ALBARKATUN ƘASA, ƊIN BIN UBAN TULIN DAKARUN JIGA JIGAN WARRIORS, ƊIN BIN DAWAKAI NA ZUWA YAKI KAMAR JININ ALNAAS MAE ALKHUYUL, SAI KASAR DARK WORLD ZA'A SAMU IRIN HAKA. Wannan matashin yana wucewa gaba wannan matashiyar budurwa da ta ɗauki Sweetie a dajinsu ta fito daga cikin white car ɗin, nan take duk jama'ar wajen suka kara nutsuwa, da alama sun fi jin tsoronta sama da yadda suke tsoron wannan matashin. Hannu tasa ta ɗauko Sweetie dake sume ne ko ta yi barci ne Allah masani. A saman shoulder ɗinta ta saɓata suka nufi katafaren kofar gold da zata sadasu da cikin daular tasa. Tsayawa zayyana maku haɗuwar parlourn Black Tiger ma ba zai yiwu ba, dan baki ya yi kaɗan ya faɗesa, sai dai abin da zan ce maku shi ne kusan komai na cikin wannan parlourn da gold aka yi su, masha Allah, suna da arzikin gold sosai, da ita Black Tiger yake yin amfani wajen kara gina ƙasarsa, ya kara karfin iko da karfin warriors ɗinsa dan yaƙan duk ƙasar da bata burgesa ba, yana kula da warriors ɗinsa sosai ga horo na musamman da suke karɓa wajen master. Ya sanya an kyara mashi kujerar mulkinsa da zallar madarar gold, ya haye saman kujerar yana zartar da zaluncinsa son ransa, sam ba zaku so ku ji yadda Black Tiger yake azabtar da bawa idan ya yi mashi ba dai'dai ba, wani ma dalma yake sanyawa a dafa, dalmar yana tafasa ya sa a kamosa a gaban kowa a zuba mashi dalmar, haka duk namar jikinsa zata zagwanye ta dube ƙasa ya mutu, kuma shi fa idan zai yi kisa ko wani hukuncin wlh sai ya taro gabaɗaya jama'a, ko baka son gani dole sai ka kalli yadda yake sakawa ayi kisa, dan dole yake tilastawa mutane ganin hakan, masu raunin zuciya haka za su yi ta kuka, masu zuciya a kusa kuma nan take suke suma a wajen, hakan ba zai hana shi gobe idan wani ya yi mashi ba dai'dai ba ya sake sakawa a taro jama'a a zartar mashi da hukunci gaban kowa. Hakan yasa jama'ar birnin suke kara mahaukacin tsoronsa, dan suna ganin irin izayar zaluncinsa kala kala, wannan kujera ta mulkin nasa da take na zallar madarar gold idan ya hayeta fa sam baya tunanin mutuwa, ko da yake su da ba Allah suke bautawa ba ina zasu yi tunanin mutuwa? Su ba musulmai bane. Sai dai Black Tiger yana aikata wani aiki guda ɗaya a rayuwarsa na alkhari, wannan aikin kuma ba komai bane face renon marayu, duk in ya samu labarin yara marayu basu da uwa basu da uba, to zai sanya a ɗaukosu, za'a renesu a cikin ɗaularsa tamkar ƴaƴan sarakuna, za'a kula da su tamkar basu rasa iyayensu ba, damkar kuma yayan shugabanni ƙasashe, cikin gata sosai, sai ya mantar da su sun rasa iyayensu, a haka yake renan marayu. DELISHA. Kai tsaye saman wani electric stair case Delish ta nufa da Sweetie, stair case ne wanda yake amfani da wutar lantarki, da ka hau zai yi sama da kai, babu ruwanka da tafiya da kafarka bare ka sha wahala. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 20/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 DELISHA. Kai tsaye saman wani electric stair case Delish ta nufa da Sweetie, stair case ne wanda yake amfani da wutar lantarki, da ka hau zai yi sama da kai, babu ruwanka da tafiya da kafarka bare ka sha wahala. Hawa ta huɗu Delisha ta wuce. Kai tsaye wani haɗaɗɗen luxurious bedroom ta nufa. Ɗaki ne iya ɗaki, ko ɗakin shugaban kasa bai kai wannan haɗuwa ba, dan wannan fa kusan komai na cikinsa na zallar madarar gold ne. Saman wani katafaren luxurious bed Delisha ta kwantar da Sweetien, gadon nan headboard ɗinsa har yana taɓo saman ɗakin saboda girma, kuma gabaɗaya headboard ɗin da gold aka yi shi. (Gaskiya ku zo mu je DARK WORLD haƙar gold, ina dalili? Sai pacaka Black Tiger yake yi da gold😥 Allah ya masu tarin arziki dayawa, ga ƙasar tasu bata da wani girma sosai, shiyasa suke pacakarsu, dan arzikin har ta yi masu yawa, ga Black Tiger da yake yana da dabara kuma yana da buƙatar cinma wani buri nasa sai ya zamana yana ta amfani da wannan tarin albarkatu da ni'imomin dukiya da Allah ya basu yana ta ƙoƙarin kara gina kasarsa ta yadda zata yi girma sosai ta fi kowace ƙasa, sai kara gina ma'aikatu, asibitoci, haka zai sanya mayaƙa su yi ta saran dajukan kusa da su yana yin gine gine dan ƙara faɗaɗa ƙasar, yana kuma ta ƙoƙarin kara karfin iko, so yake ƙasarsa ya haɓaka ya fi kowa, yana son ƙasarsa ta zama ta ɗaya a duniya, gaskiya my people's mu ma kuzo mu je DARK WORLD ko da a sace ne mu sato ɗanyar gold, kada ku ji tsoro, idan Black Tiger ya gano mu zan tsaya maku💪😅🌝🥱) Ƙoƙarin juyawa Delisha ta yi dan ta fice daga ɗakin. A hankali sautin dasasheyar muryar Sweetie ya fara tashi cikin kuka. Ƙasa ƙasa ta fara kukan nata haɗe da sambatun ina Prettynta and Kamran? Da alama ta sha kuka na wuce misali ne yasa voice nata baya fita sosai. Juyowa Delishan ta yi ta kalleta. Tana kwance yadda ta kwnatar da ita, bata motsa ba, kukan da sambatun kawai take yi. A hanzarce ta fice daga ɗakin domin ta je ta karɓo umarni a kan me zata yi wa Sweetien, bata isa ta ce mata ko uppan ba har sai wanda ya ce su je su ɗaukota ya bada umarni. Jim kaɗan da fitarta ta sake dawowa cikin ɗakin, a bakin bed ɗin ta zauna tare da fara magana cikin harshen turanci. Kalma ta farko da ta fara furta wa Sweetien shi ne ina Spender? Cigaba da kukanta ƙasa ƙasa ta yi ba tare da ta yi magana ba, sai dai ta yunƙura ta miƙe zaune. "Ɗago idanunki da kyau ki kalleni, sannan kuma ki yi mun shiru, a nan ba'a son hayaniya, kada ki bari a jiyo ki". Ni kam na ce ku bama ku san bata da idon kallon ba bare ta kalleku?. Shiru dole ta yi ba dan ta so ba, sai dan tsoron irin muryar da ta ji anyi mata magana da shi, tabbas wannan murya da ta ji ba muryar wasa bace, kuma da alama babu imani a tattare da mai wannan murya ko ɗigo. "Ina Spender yake? Shi kawai muke da buƙatar ki bamu, kina bamu zamu sakeki, mu bamu da bukatarki a nan wajen!". Wannan murya ce ta sake katseta da faɗin hakan. Menene Spender? Ina kuma yake? Me zasu yi da shi?. Murya a dashe saboda kukan da ta rinƙa sha tun safe, murya ya dashe, da kyar ta iya furta. "Menene Spender?". A fusace Delisha ta ɗaga wannan katakon katon hannu nata kamar na adawa zata zabga mata mari, dan a ganinta Sweetien ta raina masu wayo ne, ta isa tace bata san Spender ba? Ba zai yiwu ba dole ta basu yau, abin da suke haukace suke nema, nemansa suke yi kamar hauka, kuma sun san yana wajenta, sama da shekaru biyar suna nemanta, da kyar suka ganota, sun sha bakar wahala a nemanta, amma ta nuna masu bata ma san shi ba? Tama isa?!!. Shin da gaske Sweetie ta san Spender? Idan ta sani ina yake? Kuma waye ya bata shi? Da alama dai sun san yana wajenta shiyasa basu nemi Pretty ba suka ɗauketa ita kaɗai, kenan kunga sun san lallai lallai a wajenta yake ba wajen Pretty ba, bana jin cewa Pretty ma ta san da zancen, dan da ta sani ita ma ba zasu barta ba, da tsab zasu tafi da ita ko dan ta gaya masu a ina yake idan Sweetie taki gaya masu. Lallai akwai cakwakiya, kenan dai Sweetie akwai abubuwan da ta sani sosai ta ƙunshisu a cikin cikinta taki amayar da su ga kowa ne ko yaya? Mu dai je zuwa, Allah dai ya kawomu RAWANIN ZALINCI, mun zo SEAT OF INJUSTICE. Zamu ga ya wasan nasu su kuma yake, zamu ga wannan family kuma ya suke rayuwa!!. Tana ƙoƙarin sauke mata wannan katon hannun nata a saman lallausan kumatunta kwatsam ta ji hannun nata ya sage a saman iska bai ƙarisa kai saman kumatun Sweetien ba. Yar karar azaba ta saki kafin ta furta......... Kai bari mu leƙa wani season ɗin mu dawo, dan bana son rubuta complete page a part na family guda ɗaya, gara mu ɗan yawata muga ya wasu kuma suke...........🥱🤪 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ FOREST 🏞️ Yau tsawon kwana biyun kenan da Mamma ta ɗaure Kamran, sam bai yi ƙoƙarin kwance kansa ba, bawai dan ba zai iya kwance kan nasa ba, a'a sai dan kawai shi a yanzu burinsa shi ne ya mutu, ya ce ba zai iya rayuwa ba tare da Pretty ba, tun da Mamma ta hana shi zuwa ya dubasu ko suna nan ko basu nan to shi bai ga amfanin rayuwarsa ba, ya dai'na cin abinci, ko ta kawo mashi abinci ta kwance mashi hannu ma baya ci, haka zata zo ta ɗauki kayanta, shaiɗan sai zugata yake yi a kan kada ta rarrasheshi, ta barshi bayan ɗan lokaci zai manta da komai su koma kamar da, hakan yasa sam bata yi ƙoƙarin lallashinsa, ta zuba mashi ido, a cikin zuciyarta azaban zafin hakan take ji, tana cikin tsananin tashin hankali na ganinsa a cikin wannan halin da yake ciki, har ga Allah tana kaunarsa fiye da kanta, amma a ganinta abin da ta yi mashi shi ne mafita a gareta. Bawan Allah bashi da aiki sai ruwan hawaye, ko kwanciya baya yi, yana zaune a saman gadon ya jingina bayansa da jikin ƙogon, ya haɗa kai da gwiwa, ya sha kukansa ya ƙoshi har barci ta ɗaukesa a haka, cikinsa sai ciwo yake yi mashi saboda yunwa, ya kuma ki yarda ya ci abinci, cewa yake yana fatan yunwa ta zama ajalinsa ya huta. Tun ranar da abin ya faru Rocky ya ki barin kofar ƙogon, Allah sarki ya kuma ƙasa iya shiga ciki. Ita kuma Mamma taki yarda ta fito waje, dan tasan in ta fito wlh tsab Rockyn zai yi mata mummunar lahani, saboda ta harzuƙa shi ba kaɗan ba, ta ɓata mashi rai, coz tasan idan ta fito ba barinta zai yi ba, ita kuma ba zata iya faɗa da shi bama bare har ta yi ƙoƙarin kashe shi, dan tana kaunarsa sosai, jinsa take yi kamar ɗanta, dan fa sun kwashi shekaru a tare, sun yi matuƙar shakuwa sosai, shiyasa ma taki fitowa wajen gabaɗaya, tana jinsa sai ya kwana yi masu kurnani, yaki matsawa daga wajen, amma ta yi banza da shi kamar bata ji ba. Banda tunanin Pretty babu wani abin da yake cikin ransa, jefi jefi yana tunanin Sweetie, kuma ya fi yin kuka mai tsuma zuciya idan ya tuna Sweetien, yana matuƙar tausayawa rashin idanunta, baya damuwa sosai idan ya tuna Pretty, saboda tana da idon ganin koma inane, amma Sweetie bata gani, idan Pretty bata dawo ba ya rayuwarta zai kasance? Wannan shi ne tunanin da yake cikin ransa a kowani lokaci. Yana shiga matsanancin damuwa tare da fargaba sosai idan ya tuna cewa Pretty ta bazama cikin dajin nan, fargabansa kada ace wani abin ya sameta, kada ace ta mutu, kuma da alamun wani abin ya sameta ɗin, dan duk lokacin da ya tuno sunanta kirjinsa ne yake duka da sauri sauri, gabansa sai ya yi ta mummunar faɗuwa, hakan yasa ya fara yanke kauna tare da daina tunanin tana raye ko ta mutu? Yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa yake horar da kansa da kin cin abinci dan ya mutu ya bi Prettynsa, zuciyarsa ta gama saddakarwa da ta mutu. Har izuwa yanzu kuma Mamma bata jin kamar zata iya lallashinsa, ji take yi ta barshi dan dole zai sauƙo da kansa idan ya ji azaban wahala, ta manta da cewa ɗan na gada ya fi ɗan na koya, ita ma ta yi kafiya da zafin zuciya bare shi? Ai kuwa yana da kafiya sosai tare da jajircewa a kan sai ya cika muradinsa haɗe da taurin kai da taurin zuciya. A takaice kenan halin da Mamma and Kamran suke ciki a yanzu. Bari mu leƙa wasu Familyns kuma muga halin da suke ciki. KINGDOM OF POWER.💪🔥💘 Wasa wasa har kwana uku yau Chuchu bata yarda su haɗa hanya da Yah Jawad, babu kuma wanda ya san da wannan abin sai Momma. Duk yadda Yah Jawad ya so su haɗu taki yarda, ta tattara ta koma part ɗin Mummynta, dan can ne bai cika zuwa ba, idan ta ji zai zo sai ta koma part ɗin Mammiensa ko kuma na Mama, dan part biyun nan ne baya taɓa zuwa sai idan su ne suka kira shi, bai ma san a wani part takamaime take ba. Ya tambayi Auta sai dai ta ce nashi ita ma bata ganta ba sam sam, kuma wlh tasa san in ta take, amma da yake kun san shakuwar da take a tsakaninsu, bakinsu ɗaya sun iya rufawa juna asiri, yanzu haka Autar ma haushinsa take ji haɗe da tsoronsa, dan Chuchun ta gaya mata komai. Abin ya dame shi matuƙa, ko ya kira numberta bata ɗauka, yau kwana uku bata zuwa school, ya shiga damuwa matuƙa, ya rasa ina zai sanya ransa, abubuwa sun haɗe mashi, ga shi idan ya kira number Jaish bata shi ga, yana cikin tashin hankali a kan hakan! Sannan ga wani tashin hankalin da ya faru a Dubai wanda Rizwan ya sanar da shi ya ce kada ya gayawa kowa dan suna iya ka bakin ƙoƙarinsu dan su shawo kan matsalar, sannan yanzu ga shi baya samun damar ganin sanyin idaniyarsa bare ta rage mashi raɗaɗin da yake ji, har zazzaɓi sai da ta kama shi, a halin yanzu ya fi shiga damuwa sosai a kan Jaish, shi ne a ransa, ƙoƙari yake yi ya ɗan samu lafiya ya ji kwarin jikinsa sai ya bi bayansa, dama ƙasar England ya ce mashi zai je, so yasan hotel ɗin da ya sauka ma, dan da ya sauƙa ya tura mashi saƙon a kan ya sauƙa lafiya da sauran bayanai, coz yanzu yana son ne jikinsa ya ɗan warware daga damuwar da suka yi mashi yawa sai ya bi bayansa ya je ya gani shin aiki ne ta yi mashi yawa har ya kashe wayarsa ne ko kuma dai wani abin ne ya faru?. A safiyar yau ma sai da King ya tambaye shi ina Jaish? Da ya rasa me zai ce mashi sai ya ce ya tafi ƙasar Brazil wajensu uncle Jahiz yau da safen, ya rasa amsar da zai basu ne yasa ya ce masu haka, dan kullum idan suka tambaye shi sai ya ce masu bai dawo office da wuri bane, ya yi dare shiyasa yana dawowa ya kwanta, da sassafe kuma ya sake fita saboda aiki ta yi mashi yawa, kullum amsa ɗaya shiyasa yau ya canza amsar. Sosai King ya yi faɗa a kan ya za'ayi ya yi yafiya ba tare da ya sanar da su ba? Idan wani abin ya je ya farufa? Allah ya tsare!. Sai hakuri Jawad ɗin ya rinƙa bashi, ya yi ƙoƙarin kiran number Jaish ɗin amma bata shi ga, sai ya yi tunanin ko dai yana cikin jirgi bai sauka bane yasa wayar bata shiga ba, da haka dai ya samu suka rabu da King ɗin. Yana barin part ɗin King ya kira number uncle Jahiz ɗin nasu, wato ɗan autan Akka kenan kaninsu King. Yana kiransa bai ɓoye mashi komai ba ya sanar da shi gaskiya, sannan ya ɗaura da cewa King zai kirasu dan ya tabbatar da cewa Jaish yana tare da su, idan ya kirasu dan Allah su amsa da e, idan ba haka ba sun san halin King sarai. Da yake uncle ɗin nasu ma irin uncle Abbas ne, yana kaunarsu sosai kuma ya iya goya masu baya, sai ya yarda a kan e lallai za'ayi yadda suke so, amma Jawad ɗin ya yi saurin nemo in da Jaish ɗin yake, cikin raunin zuciya ya amsa da tabbas zai yi duk yadda zai yi ya dira a ƙasar England gobe ko jibi domin ya duba shi, idan ba haka ba za'a samu matsala, da haka dai suka bar zancen suka shiga hirar duniya. Suna tsaka da yin hiran ne Momma ta kira numbersa, sallama ya yi wa uncle ɗin nasu ta hanyar sanar da shi cewa Momma na kiransa bari ya ɗauka, okey ya amsa mashi kafin su yi sallama ya ɗauki kiran nata. "Jawad ka sameni a parlourna yanzu". Shi ne abin da ta faɗa. Cikin sanyin murya ya amsa mata da okey ga shi nan zuwa. Katse kiran ta yi shi kuma ya nufi part ɗin nata. Zazzaɓi sosai yake ji a jikinsa, da alama shakuwarsa da Jaish yasa yake yi mashi ciwon wahalar da ya shiga, kun san idan mutun biyu suka shaƙu, in ma mata da miji ne ko ƴan uwa, in dai shakuwarsu ta kai shaƙuwa zaku ga ko basa tare idan ɗaya ya shiga wahala ko tashin hankali sai kuga shi kuma ɗayan ya kamu da wani ciwo, ba dai ciwo mai tsanani can can bane, amma sai ku ga yana ta fama da ciwo, daga ya ce kansa na ciwo, sai ya ce zazzaɓi, mutuwar jiki, ko zafin jiki, haka zai yi ta fama da rashin kwarin jiki har sai randa wancan ya fito daga cikin matsalar da ya shiga, ana samun irin haka sosai a cikin al'umma. So shi dai ga shi yana yi wa Jaish jinya ba tare da ya sani ba. A parlournta ya iskota zaune cikin kwalliya irin na hamshaƙan gimbiyoyi, da alama ma wajen King zata je, dan kwalliyar ta musamman ce. Saman carpet ya zauna ta kusa da ita kafin ya ɗaga mata gaisuwa cikin girmamawa. Amsa mashi ta yi fuska ba yabo ba fallasa, sannan ta ɗaura da cewa. "Jawad ina Jaish? Yau kwanansa huɗu kenan ban sanya shi a idanu na ba, kuma sanin kanka ne baya taɓa yin kwana guda cur ba tare da ya zo in da nake ba, na kira numbersa bata shiga, na je part ɗinsa daren jiya misalin karfe 1 ban samesa ba, ɗakin nasa ma ya nuna mun alamar kamar ya kwana biyu babu mutun a ciki, saboda curtains na windows and balconynsa duk sun nuna alamar an kwana biyu ba'a taɓasu ba, kuyangun da suke gyara ɗakin nasa basa taɓa wajen, meyake faruwa? Ina ya tafi?". Wani irin yawu mai wuyar wuce maƙogwaronsa ya haɗiye da kyar, sannan ya ɗan ɗago da kallonsa izuwa kanta. Ya rasa me zai ce mata, yasanta da kaifin ƙwaƙwalwa, sannan ita ta renesu shi da Jaish ɗin, yana yi mata karya zata ganosu, ta yi masu farin sani, ko da sunan wasa ya yi mata magana ba dai'dai ba tana ganewa cikin ƴan sakani bare da gaske, to yanzu ya zai yi da ita? King ya fita sauki, shi bai cika tsawwalawa sosai ba, ko ya gane ba gaskiya ka faɗa mashi ba yana kawar da kai sai ya yi bincike da kansa, ita kuma sai ta tirkeka ka faɗi gaskiyar da bakinka. "Shirun da ka yi mun Jawad ya tabbatar mun da abin da zuciyata take raya mun, tun jiya bani da kwanciyar hankali, ina jin faɗuwar gaba da fargaba kamar wani abin ya samar mun ɗaya daga cikinku, duk na kira ƴan uwanka a waya suna lafiya, kai kuma muna tare da kai a nan, shi kaɗai ne ban samu damar yin magana da shi ba, kuma shi kaɗai ne idan na tuna shi nake jin faɗuwar gabana ya tsananta, ka gaya mun gaskiya me yake faruwa?". Wani irin nisawa ya yi wadda da ka jita kasan yana cikin mawuyacin hali, muryarsa har wani ɗan sarkewa ta yi, ɗan gyaran muryar ya yi kafin ya ce. "Momma babu abin da ya samu Jaish, In Sha Allah yana cikin aminci tare da kariyar Ubangiji, tafiya ya yi izuwa ƙasar Brazil wajensu uncle Jahiz........" Bai ƙarisa maganar ba saboda wani irin kallo da ta wurga mashi yasa ya shanye sauran maganar tasa. "Jawad ka manta cewa da Mommarka kake magana ne? Sam babu kamshin gaskiya a maganarka, faɗa mun gaskiyar dai ina sauraro". Haƙiƙa sai da ya ji kirjinsa ya bada dum dum, dama yasan halinta sarai, ba zaka mata karya kuma kasha lafiya ba, sai ta kamoka, bashi da zaɓin da ya wuce ita dai ya gaya mata gaskiya ko dan ta tayasu da addu'a idan ma wani abin ne ya samu ɗan uwan nasa. Ya sha madarar mamakin ganin fuskarta bai sauya ba duk da ya gaya mata gaskiyar halin da ake ciki, shiru ya yi yana tunanin ko dai dama tasan gaskiya ne? Ko dai gwadasa kawai ta yi?. Katse mashi tunanin nasa ta yi da cewa. "Kana mamaki ya aka yi ban shiga damuwa ba duk da na ji abin da yake faruwa ko?". Da sauri ya gyɗa mata kai alamar e. "Dama nasan dole wani abin ya saɓa, domin kai da Jaish tamkar ƴan biyu kuke, tun kuna yara idan ɗaya ya yi rashin lafita da safe to ɗayan zai kwanta nasa ciwon da yamma, tun jiya da naga yanayinka na fahimci kana taya Jaish ciwo ne, ka dawo wani sukuku da kai, kai da kanka baka san me yake damunka ba, hakan ce ma yasa na biɗi ganin Jaish ɗin dan na tabbatar da abin da yake damunka, shin ciwon gaskiya ce ko dai ciwon shaƙuwa ce? Yanzu na tabbatar, coz ban yi mamaki ba, kuma ban ji cewa Jaish ya aikata ba dai'dai ba, a jikina ina jin ba lafiya yake ba, amma koma menene ni ban haifi rago ba, jarumta a jininmu take, a ko'ina yake ina da yaƙinin da izinin Allah zai fidda kansa, dan babu rago a zuri'armu, bamu san komai ba sai jarumta, dan haka kai ma ka warware ka taya shi da addu'a, Allah kuma yasa ya cinma burinsa a kan abin da ya je nema, zan yi mashi addu'a, sannan bana son ka gayawa kowa wannan magana, dan sanin kankane a gidan ba kowace magana ake yinta da mutane ba, wani lokaci is better ka haɗiye magana a cikinka sai ya fi maka sauki, ko daddynku kada ka gaya mashi, dan zai shiga damuwa, and lastly ka gaya mun gaskiya duk da ni kai'na ban yarda da abin da zuciyata ta gaya mun ba, amma zanso in ji gaskiya daga bakinka". Dakatawa da yin maganar ta yi tana kallon face ɗinsa. Tattare nutsuwarsa waje guda sosai ya yi, dan ya ji ta ɗauko wani maganan na daban. "Ka faɗa mun gaskiya kai ka shiga ɗakin Jannat kwana uku da suka wuce?". Tana magana tana kara kura mashi idanun, dan ta kalli yanayin da fuskarsa zata yi. Zaro idanu ya yi kafin ya ce. "Momma ina zuwa ɗakin Jannat, amma kwana uku da suka wuce ban shiga ba, kwana huɗu da suka wuce dai na shiga da daddare sosai wuraren karfi 12 haka, har daddy ya zo ya samemu a tare na ɓuya a cikin toilet, bayan haka kuma babu wani abin". Tabbas ta yarda da maganarsa, tasan gaskiya ya faɗa, dama kuma tasan ba zai aikata wannan ɗanyen aikin ba, ta san halin ƴaƴan nata sosai, amma sai ta ce. "Me kake zuwa yi a ɗakin nata a irin wannan lokacin haka?". Ƴan kame kame ya fara yi mata yana faman sunkuyar da kai. "Yau kuma ka dawo Jaish ne da kake ɓoye mun fuska? Yaushe kunya ta ratsa jinin jikinka kai ma? Jaish ma ina ganin rashin kunya ce take damunsa da idan ya zo yake ɓoye mun fuska yake wani sunkuyar da kai, ashe ko dai hakance tun da gashi kai ma ka fara ɓoye fuska". Ɗan ƙaƙalo murmushi ya yi kafin ya ce........ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 23/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E___________9 Ɗan ƙaƙalo murmushi ya yi kafin ya ce. "Kai our Momma, bafa kunyarki nake ji ba, abin da zan gaya maki ɗin ne yasa na fara jin kunyarki a yanzu". "Mmmmmm to dai faɗi na ji menene? Me yake kaika wajen ƴata da tsakar dare haka?". "Kai Momma addu'a nake zuwa yi mata fa, daga nan sai mu ɗan yi hira kaɗan haka, bafa dayawa ba, kuma a hiran dukka karatu nake koya mata". Ya faɗa yana ɗago da kallonsa izuwa kanta. Wani irin kallo da take binshi da shi mai nufin ni zaka yi wa karya ne yasa shi sakin siririn murmushi tare da ɗan dafa kafafunta kafin ya ce. "Kai our Momma, to zan faɗa maki gaskiyar". "Oya go ahead". Ta faɗa tana kara kallon face nasa da kyau, while shi ma kallonta yake yi. "Magana ta gaskiya zan gaya maki, dan ko zan ɓoyewa kowa ban da ke our Momma, zance ta gaskiya son Jannat nake yi kuma ina fatan ta zama matata, amma da alama bata sona, dan yau kwana uku kenan tana guduna ba tare da ta tsaya ko kallonta na yi ba, taki tsayawa ko tambayarta me nayi mata take gudu na ma taki, ban san me yake faruwa ba, ban san laifin da na yi mata ba, amma a baya tana nuna mun kauna, kwana huɗu da suka wuce ma da na je ɗakinta da daddaren lokacin da zan koma nawa part ɗin sam bata so hakan ba, ta so na zauna mu yi ta hira har wayewan gari, duk da bata fito ta gaya mun hakan ba ni naga hakan a cikin kwayar idanunta, amma haka dai na danne na koma part ɗin na, na rasa me yasa yanzu take guduna, sam bata sonna, ban kuma san laifin da na yi mata ba, please Momma ki tayani da addu'a, wlh ina kaunar Jannat sosai". Ya kai karshen maganar cikin wata iriyar raunanniyar murya. Saboda kaifin ƙwaƙwalwa irin nata nan take ta gane lallai lallai akwai mai son shiga tsananinsu a cikin gidan nan, tabbas akwai mai son rabasu, to wanenen? Ta tambayi kanta, sai dai abin da bata gane ba a nan shi ne meyasa Chuchu take gudun Jawad ɗin tun da ba shi ya shiga ɗakin ya yi ƙoƙarin keta mata mutunci ba? Dole wani abin ya saɓa, dole akwai wata makarƙashiya da basu san menene bane. Shiru ta yi tana tunanin ta gaya mashi gaskiyar abin da ya faru domin ya yi ƙoƙarin yi wa Chuchun bayani yadda zai shawo kanta ne? Ko dai ta yi shiru sai ta gama bincikenta?. Voice ɗinsa ne ya katse mata tunanin da take yi ta hanyar cewa. "Momma please ki tayani da addu'a, wlh ina kaunar Jannat sosai, yau tsawon kwana uku kenan ban sanyata a cikin idanuna ba, ki taimakeni na ganta, idan ba haka ba zan iya cutuwa". Cikin raunin murya tamkar zai saka mata kuka ya yi maganar. Ajiyar zuciya ta sauke tare da fara magana. "Eyeee wato Jawad sam baka kunyata ko? Kai tsaye kake gabatar mun da yadda kake kaunar ƴata ko? Ba irin jin kunyar surukai da ake yin nan?". Kamar zai sa mata kuka ya ce. "Momma please ki daina faɗin hakan mana, ni ban yarda ba, ke mahaifiyar miji kike bana mata ba, ki bar batun surukuwar nan, mummy ce zata zama surkuwa, ni yanzu please Our Momma a samo min mafita, in dai ba so kike yau na ki cin abinci na zauna nan nayi ta yi maki kuka ba to a haɗa ni da Jannat ɗita, Kila ma Momma ke kika ɓoye mun ita saboda kina son na gaya maki me yake tsakaninmu, to dai na faɗa maki surukarki ce, dan Allah a haɗani da ita ko na minti biyar ne". Dan siririn murmushi ta saki kafin kuma ta sake ɗaure fuska sosai kamar bata taɓa yin dariya ba, a tsanake ta fara bashi labarin abin da yake faruwa dukka, bata ɓoye mashi komai ba, dalilin da yasa Chuchu take gudunsa duk ta gaya mashi da abin da ta ganewa idanunta, daga karshe ta rufe mashi da cewa lallai lallai ya kula sosai, sannan ya kara tsananta addu'a, yanzu haka Chuchun tana part ɗin Aunty MieMie, ya je ya sameta shi yasan ta yadda zai shawo kanta, kada ya yi ƙasa a gwiwa, ya jajirce sosai zai yi nasara. Sosai ya shiga tsananin ɓacin rai da jin anyi ƙoƙarin yi mata fyaɗe ne, jikinsa har wani tsuma yake yi, bai damu da cewa zarginsa take yi a kan hakan ba, damuwarsa a yanzu shi ne ya gane wanda ya yi mata hakan domin ya hukuntasa, uncle Taheer ƙanin mama baya ƙasar, ya tafi wajen iyayensa dan sada zumunci bare ya ce ko shi ne ya yi mata hakan, Jaish ma baya nan, kuma koda yana nan ma ko giyar wake ya sha ba zai aikata hakan ba, a mazan gidan dai shi kaɗai ya saura a gidan. Tashin sense!! Ganin alamar ransa ya ɓaci sosai ne yasa ta fara rarrashinsa tare da ƙara mashi kwarin gwiwa. Ina ai yanzu duk maganar da take yi ma bata shiga kunnuwansa, ya yi nisan kiwo wajen tunanin mafitar yadda zai kama wanda ya yi mata wannan aikin, faɗi yake yi a cikin zuciyarsa wlh idan ya kama wannan mutumin koma wanenen sai dai uwarsa ta haifi wani. Tsabar ya afka kogin tunani da tsananin ɓacin rai bai ma san time ɗin da ya miƙe ya nufi hanyar fita ba, ko sallama bai yi wa Mommar ba, da alama ma ya mance cawa a wajenta yake, kawai ya nufi waje. Har ta buɗi baki zata kira sunansa sai kuma ta fasa, saboda ta lura baya tare da ita, ko ta kirasa ba lallai ya jita ba, dan haka sai ta bishi da kallo tare da fatan nasara. Yana fita kai tsaye wajen Aunty MieMie ya nufa, zuciyarsa na tafarfasa sosai, tsikar jikinsa har tashi yake yi. Tsabar ya shiga damuwa ko sallama bai yi ba ya afka cikin parlourn, babu kowa shiru, da yake already ya san in da zai sameta a part ɗin idan ta shigo sai ya nufi stair case kai tsaye. Sama ya haura, kai tsaye ya nufi wani katafaren luxurious bedroom wanda yake zaton zai sameta a ciki. Babu ko sallama ya tura kofar ya afka ciki. Tana kwance a saman gado, bata jima da gama yin waya da Rizwan ba, da ga ita sai kayan barci, da alama a part ɗin ta kwana, har yanzu kayan barcin jiya ne a jikinta, bata yi wanka ta canza ba, haka zalika bata fito ta ci abinci ba, tana kwance shiru tana fuskantar celling ɗin ɗakin. A tunanin Aunty MieMie ma barci take yi shiyasa bata zo ta ce mata ta tashi ta yi breakfast. Jin motsin mutun yasa ta sauko da kallonta izuwa bakin kofar room ɗin, a tunaninta ma Aunty MieMie ce. Tana sauke idanunta a kanshi ta wani irin zabura tare da miƙe zaune a dubu, nan take ta yi ƙasa da kallonta tare da fara ƴan kame kame, tsabar razana har kerma jikinta ya fara yi. Tura kofar room ɗin ya yi ya rufe, sannan ya tako a hankali ya nufo in da take. Kara tsorata ta yi da ganin ya tura kofar kuma ya tunkaro ta, muryarta na karma yana sarkewa ta fara faɗin. "Yah Jawad dan Allah ka yi hakuri, na shiga ukuna, Momma, mummy kuzo ku ceceni, Aunty MieMie kizo Yah Jawad zai kashe ni, dan Allah Yah Jawad idan wani laifin ma na ya yi maka ka yi hakuri, wlh ba zan sake ba, dan girman Allah........." Ka sa ƙarisa maganar ta yi dan ganin ya zauna a saman bedside drawer tare da zuba mata idanu, tana magana muryarta na sarkewa, ga shi ta datse idanu gam tare da sanya hannunta ta tare fuskar tata duk wai dan kada ya taɓata. Jin ya zauna a kusa da ita ba tare da ya taɓata ko ya yi mata magana bane yasa ta ɗan buɗe idonta guda ɗaya a hankali dan ta saci kallonsa. Ganin yana zaune shiru ya kura mata idanu ne yasa ta mai da idon nata ta rufe tare da fara yin tunanin to ko dai ya zo bata hakuri ne? In kuwa haka ne wlh ba zata saurare shi ba, kuma ba zata sake jin maganarsa ba, daga yau ta dai'na kula shi. Shiru shiru almost 10 mins bai ce da ita uppan ba, da ta gaji da datse idanun nata ne sai ta buɗesu tana kallon ƙasa, taki yarda ta ɗago su yi ido huɗu, tunane tunane kala kala ne a ranta. "Jannat". Ya ambaci sunanta a wani irin low voice sosai. Kin amsawa ta yi kuma taki ɗago kai, ko ɗan motsawa ma bata yi ba tamkar ba ita ya kira ba. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Yanzu Jannat ko wata aka ce maki na shiga ɗakinta da nufin na keta mutuncinta zaki yarda?". Still bata motsaba kuma bata amsa ba. Cigaba ya yi da cewa. "Jannat kenan da gaske zaki yarda da cewa zan iya shiga ɗakin wata ma ba ke ba?". Har yanzu dai shiru bata amsa ba. "Shirunki ya nuna mun cewa kin yarda kenan ni ne?". A wannan karon kai ta gyaɗa mashi alamar yes she's agreed!. Ɗan zaro idanu ya yi tare da bayyanar mamaki a face ɗinsa. Hannayensa ya kai ya riƙo nata cikin nasa. Wani irin zabura ta yi tare da yin baya a ɗari tana ƙoƙarin kwace hannayen nata. Bai saketa ba sai ma ƙara ƙanƙame ƴan hannayen nata ya yi, ƙasa ƙasa kaman mai raɗa ya furta. "Jannat menene hujjarki na cewa tabbas ni na shiga ɗakinki? Ki gaya mun! Idan na ji hujjar taki na kuma gamsu da ita zan karɓi laifin da bani na aikata na, zan yarda da cewa ni na aikata". In a low voice sosai ta fara magana kamar wadda aka sanya dole. "Wlh Yah Jawad kai ne! Kai ne ka shigo mun ɗaki, face ɗinka ne, jikinka ne, komai nake n........." Bata iya kai karshen maganar ba sakamakon sauke kallonta da ta yi a kan hannayensa dake riƙe da nata. Ɗan zaro idanu ta yi tare da juyar da nata hannayen ta riƙo nasa, kurawa hannun nasa idanu sosai ta yi, har da ɗan ɗagosu tana kara dubawa da kyau, duk bata gamsu ba sai da ta fara jujjuya hannun nasa. Kura mata idanu ya yi yana binta da kallon mamaki, abin ya ɗan ɗaure mashi kai. "Lafiyarki kuwa Jannat?". Ya faɗa tare da zame hannayen nasa daga riƙon da ta yi masu. Da sauri ta ɗago da kanta haɗe da kallonta izuwa garesa, a ɗan ruɗe ta furta. "Yah Jawad ina tabon cizon da na yi maka na fasa maka fatan hannu? Izuwa yanzu wlh wannan cizon ba zai yiwu ace ya warke ba, dan na fasa fatar wajen har ta yi jini, ko da jinin ya tsaya da zuba ba zai yiwu a ce babu tabo ba". Tsabar ta ruɗe har ta kare maganar tana kallon cikin kwayar idanunsa, yau ba sunkuyar da kai, da alama bata san ido cikin ido suke kallon juna ba saboda ruɗu. "Jannat ni babu wanda ya cijeni bare tabo ya zauna, a yaushe aka yi hakan? Yaushe kika cijeni?". Still har lokacin tana kallon cikin tsakiyar kwayar idanunsa, mamaki ne ya kara bayyana a saman fuskarta, ta kara shiga ruɗani ta furta. "Ranar da ka shigo ɗakin nawa ne ina ƙoƙarin kwatar kai'na na cijeka har na fasa maka fatar hannunka, wlh kuma ya yi jini sosai". Wani irin sanyi ya ji ta ratsa shi, Allah ba azzalumin bawansa bane, ga shi cikin sauki ya kawo mashi mafita ta yadda zai wanke kansa, Allahu Akbar, gaskiya ne Ubangiji baya barci, kai ko gyangyaɗi baya yi bare barci, Allahu Akbar, Allahu Akbar. Ya faɗa a cikin zuciyarsa. Miƙewa tsaye ya yi tare da fuskarta gabas, ya zube gwiwowinsa a ƙaya ya gabatar da sujjudur shukur tare da miƙa ɗinbin godiya ga Ubangiji. Bayan ya miƙe ya koma ya zauna, cikin hanzari ya riƙo hannayenta a cikin nasa, cikin tsantsan farinciki tare da murmushi a saman face ɗinsa ya furta. "Allahu Akbar my Jannat, Ubangiji ya wankeni daga zargin da kike yi mun, na gaya maki ba ni na shiga ɗakinki ba, jannat ko ƴar wani can da ban ba zan iya keta mata mutunci ba bare ke da kike kanwata, jinina, farincikina, wannan ke kin sani ba tarbiyar gidan nan bane". Ɗan sakin jiki ta yi da shi kaɗan, izuwa yanzu ta fara yarda da cewa e ba shi bane, amma kuma da yake shi sheɗan munafuki baya son yaga ana zaman lafiya sai ya rinƙa zuga zuciyarta yana sanya mata wasi wasi a kan idan ba shi bane to wanene? Ga kamanninsu ɗaya, komai nasu iri ɗaya ne da wanda ya shigo ɗakin. "Yah Jawad amma idan ba kai bane ya aka yi komai naku kai da wancan ɗin iri ɗaya? Na kasa yarda da hakan wlh". Ƙara matsowa ya yi dab da ita, har lokacin tana kallon cikin idanunsa, mamaki da al'ajabin abin yasa ta kasa kawar da kallonta daga kansa, ta kasa iya tunano ko abu guda ɗaya da ya banbanta Jawad ɗin da wanda ya shigo ɗakinta, babban tambayar da yake cikin zuciyarta ma shi ne, idan ba shi bane to wanenen? Ita dai tasan shi ba twin's bane bare ta ce ko ɗan uwansa ne. "Tunanin me kike yi kuma Jannat?". Ƴar razana ta yi tare da ɗan kyafta idanunta kaɗan, ta sake kura mashi ido tana kallonsa. A hankali ta zame hannunta ɗaya daga riƙon da ya yi mata ta kai hannun nata saman kumatunsa, ta dage ne tana son nemo banbancin dake tsakanin shi da wancan, tun da dai taga babu tabon cizon da ta yi wa wancan a hannunsa. Zuba mata idanu ya yi yana kallonta, shafa kumatun nasa ta fara yi har izuwa saman lallausan sajensa, ita kanta da taɓa fatarsa a yanzu sai ta ji yana da banbanci da na wancan, wancan fatarsa tauri gareta kamar jikin samudawa, shi kuma Yah Jawad jikinsa da laushi sosai. Sam bai yi ƙoƙarin katseta ba, ya zuba mata idanu yana kallon yadda take ta shafa mashi kumatu har izuwa hannunsa. Shiru ta luluƙa duniyar tunani, nan take kuma ta ji kanta na sara mata, ta gaza gane me yake shirin faruwa da ita ne, wani irin jiri ne ya fara ƙoƙarin ɗibarta, kanta ya kulle ruf. Sarai ya lura da ta shiga halin ruɗani sosai, hakan yasa ya ɗan jawota jikinsa, murya ƙasa ƙasa sosai ya ce. "Baki yi addu'ar barci lokacin da zaki kwanta ranar ba ko?". Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e. Cikin nutsuwa ya yi mata faɗa a kan wasa da addu'a, sannan ya bata labarin da Momma ta bashi na abin da ya gani, daga karshe ya rufe mata da cewa ta zage da yin addu'a sosai, kada ta kuskura ta yi wasa da addu'a, idan ba haka ba wlh akwai babbar matsala sosai. Kasa iya amsa mashi ta yi, ta kwanta a jikinsa shiru, izuwa yanzu ta yarda ba shi bane ya shiga ɗakin nata, saboda ta gano ko fatar jikinsa da wancan ma ba ɗaya ba ne, ga ba tabon cizon da ta yi mashi. Tsoro da ruɗa ne ya ƙara kamata yasa ta ƙara shigewa jikinsa, yau ta shiga uku taga Yah Jawad guda biyu take faɗa a ranta......... Ni kam na ce ai dama dole ki tsorata, irin wannan ruɗani haka? Mutun ɗaya ya zama biyu, kin ma yi ƙoƙari da baki suma ba bayan jin wannan labarin. Turo kofar da Aunty MieMie ta yi ne yasa shi saurin kai kallonsa wajen. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallonsu, hararar wasa ya wurga mata lafin ya ce. "Ya da shigowa ɗakin mutane ba neman izninsu?". Dakuwa ta ware yatsunta biyar ta watsa mashi da hannu kafin ta ce. "Me kazo yi a nan? Kazo kana tsara yar mutane ko? To zo ka wuce". Da sauri Chuchun ta yi ƙoƙarin barin jikin nasa jin voice ɗin Auntyn tasu. Ƙanƙameta ya yi ya hanata barin jikin nasa. Cikin zolaya ya furta. "Aunty MieMie gaskiya zaki takura mun, yanzu me kika zo yi a nan?". "Zo ka fita nace ko na kira Akka, ke kuma Chuchu zo ki wuce ki yi breakfast ki yi wanka, uncle Dr yana zuwa ya dubaki, dan ina son gobe ki je school". Dawo da kallonsa kan face ɗinta ya yi tare da faɗin. "Dama baki da lafita ne yasa 3 days baki zuwa school?". Ɓoye fuska ta yi a kirjinsa dan kada Aunty MieMie ta ganta, ƙasa ƙasa ta ce lafiyarta lou, zuwa ne bata son yi yasa ta ce masu bata da lafiya. "Kus kus ɗin me kuke yi?". Cewar Aunty MieMie. "Kash Aunty MieMie wai ba zaki barmu mu ɗan zanta ba, ina ruwanki tsakanin yaya da kanwa, ni ki tafi zata zo". Ya faɗa yana juyo da kallonsa a kanta. "Babu in da zanje, zo ka wuce ka tafi ko na kira Akka, ke kuma zo nan ki je ki yi breakfast". Tana magana tana wurga mashi harara, saboda su abokan wasa ne sosai. Raba jikinsu ya yi, ya riƙo hannunta tare da sauko da ita daga saman gadon. "Zo mu tafi kada ta kira mana wannan masifaffiyar tsohuwar ta jiƙa mun aiki. Ya yi maganar tare da nufar kofar fita hannunsu cikin na juna. "Tun da ba zaki barni na yi hira da farincikina ba ai sai mu tafi tare ko?". Ya faɗa bayan ya zo raɓawa ta gefenta zai wuce. Harara ta bishi da shi tana faɗin. "Oho dai kaje dai, ko na kira wayar Akka". "Ni Aunty MieMie ki daina kiran sunan tsohuwar nan, kina sanya na ji kai na na sara mun". Ya karesa zancen nasa a waje, saboda yana tafiya ne bai dakata ba. Juyawa ta yi ta bi bayansa tana zolayarsa a kan Akka ce maganinsa, kuma sai ta sanar da ita yana tare mata jika a lungu ya kalailameta da kalamai. Duk zancen da suke yi suna ta raha tare da tsokanar juna sam Chuchu bata a tare da su, ta afka duniyar tunanin ya aka yi aka samu mai kama da Yah Jawad a gidan nan? Wannan abin ya tsaya mata a rai matuƙa. Sam bata san lokacin da suka isa saman dining table ɗin ba, ta luluƙa duniyar tunani, sai da ta ji spoon na abinci yana taɓa lips ɗinta ne ta farga ashe sun iso wajen cin abincin har ma ya zuba masu ya fara bata a baki. Ɗago idanu ta yi sai saman fuskarsa, wani irin faɗuwar gaba ta ji ya ziyarce, lokaci guda ta fara jin sauyin yanayi a cikin zuciyarta a kansa, taga ya kara yi mata kyau sosai. Buɗe baki ta yi ta fara karɓar abincin, ita kam Aunty MieMie ta kama kanta abinta ta basu wuri. A can cikin babban family part kuwa, sai shiryawa Auta take yi tana tsantsara kwalliya mai kyau cikin Turkey gown brown color mai matuƙar kyau, ya ji duwatsu sosai a jikinsa, sai kyalli yake yi, kun san yanda kayansu yake ai, daga ta sama ya yi dai'dai da jikinsu, ya bi shape ɗinsu, daga wajen kugunsu zuwa ƙasa kuma a buɗe a bage kamar umbrella. Kayan yana da kyau sosai, yana ƙara fito masu da ainahin kyansu. Tamkar wadda zata je wani wajen mai muhimmanci, sosai ta tsara kwalliya, ta ɗaure gashin kanta kashi biyu, ta kuma kitsa bakin gashin tare da ɗaure karshen jellar gashin da roba saboda tsantsin gashin zai sanya kitson nata ya warware, ta saki jelar a saman shoulder ɗinta sun zubo mata har saman ciki. Ba karya kam ta haɗu iya haɗuwa, ta ɗauko wani malesian cap mai tsadar gaske ta sanya a kan nata, sai ta ƙara kyau sosai. Flat smooth shoe ta sanya a kafafunta, wanda ko tana taka ƙasa ba zaka ji tafiyarta ba. A hankali ta fito waje, kai tsaye ta hau elevator ta yi kasa mai gabaɗaya, sai sauri take zubawa tana yi tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Kai tsaye wannan wajen hutawa na musamman ɗin na mussan dake cikin family part ɗin ta nufa, wajen wasu kyawawan tsuntsaye dake cikin keji ta nufa a hanzarce. Tsuntsaye masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali ne suke birjik a wajen, a kallah kejunansu sun kai guda 20 a wajen, tsuntsaye ne different types and colos. Kai tsaye wajen wasu fararen tattabaru ta nufa, guda biyu ta damko bayan ta buɗe kejin, ta riƙosu da kyau a hannunta, suna ta faman ƙoƙarin kwacewa su tashi sama, amma ta riƙe su gam dan kada su gudun. Da sauri ta nufi waje, har da ɗage doguwar rigarta dake sharar ƙasa saboda sauri. Wani hanya da ya raɓa da wajen da ake gabatar da gasar tsaren doki duk sati ta nufa, a hanzarce take tafiya kamar zata kifa, tana yi tana waigawa bayanta dan taga shin akwai wanda ya ganta ne? Sai laɓewa take yi a duk lokacin da taga wani warriors ya zo zai gifta, da alama bata ƙullo gaskiya ba. Wasu jiga jigan warriors ne suke gadin gate ɗin in da ta dosa ɗin. Mayaƙa biyu ne a wajen, sun ji horarwar yaki sosai, commander Zafar ya yi aiki a jikkunansu wajen basu horo mai lafiya, sun ginu tamkar wasu dakuna, ga faɗin kirji da baya kamar na zaki, ganinsu da ido kawai sai sun tsorata ka, suna tsaitsaye cikin kayan yaƙinsu, ɗaya daga cikinsu yana sanye da hular yakinsu a kansa, ɗayan kuma ya cire shi, sai hira suke yi da junansu, dukkaninsu larabawa ne tas tas da su, ga kyau sosai da bakar gashi haɗi da saje. Suna ganinta tun bata iso wajen ba suka tinkarota da sauri. Ƙara ɗaga kafa ta yi wajen yin sauri, dan bata son su tareta a hanya, ta fi son ta isa in da suke. A kusa da bakin gate ɗin suka haɗu. Cikin girmamawa ɗaya daga cikinsu ya ce. "Barkanki ranki ya daɗe, shin kina da buƙatar wani abin ne?". Shiru ta ɗanyi tana tunanin abin da zata ce masu, dan wlh yau ko zasu yi yaya sai ta je gonar ɗawisun daddynsu, so take yi ta je ta gani kuma ta ɗauki hutona da su, sai dai kash saurinta yasa ta manta ma bata ɗauko wayar da zata ɗauki hoton da shi ba, kuma har izuwa yanzu bata tuna cewa babu waya a hannunta ba. King Zuhair ya hanasu kusantar gonar ba tare da shi bane saboda sanin halinsu, basu taɓa shiga cikin gonar ba, ita kuma Auta ta ɗaukarwa kanta alkawarin sai ta shiga taga me a ciki, akwai mugayen namun dawa sosai a ciki, akwai kuma dabbobi masu ban sha'awa sosai a ciki, irin su ɗawisu akwai su dayawa kala daban daban, su kuma ba'a cikin keji suke ba, an sakesu suna yawo a wajen, akwai su jimmina, su kifaye kala kala na gida dana waje waɗan da suke cikin wani haɗaɗɗen glass mai matuƙar ɗaukar hankali, an zuba masu ruwa sai shawagi suke yi abinsu, akwai tsuntsaye kala kala, ga su dila, Zomo, bushiya, a manyan dabbobi da aka killacesu a cikin keji akwai su zakuna, damisai, kuraye, da dai sauransu, duk wasu dawakai da King yake hawa suna cikin wajen an kewaye masu nasu ɓangaren daban ana kula da su sosai, akwai dai tarin abubuwa dayawa a ciki, wasu suna cikin keji, wasu kuma an sakesu suna ta shawagi a cikin katafaren filin tsakiyar wajen. To ita bata san saboda haɗarin da yake a ciki bane yasa King ya hana su ko tinkarar wajen, ta ɗauka baya son ta yi hoto da su ɗawisan ne kawai, shiyasa ta saci hanya ta zo ba tare da sanin kowa ba. Ganin ta yi masu shiru ne yasa suka sake tambayarta cikin girmamawa a kan ko dai tana buƙatar wani abin ne?. Ɗago idanun ta yi ta zuba masu kallo, cikin dabara ta saki tattabara ɗaya ya tashi sama, kukan gulma ta sanya masu a kan lallai su kamo mata tattabararta kafin nan su zo ta gaya masu abin da take buƙata a wajensu. Mutun ɗaya ne ya yi saurin bin bayan tattarabar da ta tashi sama ta bi ta wajen tseren dawakai da suke gudanarwa a cikin masarautar duk sati. Ɗayan warriors ɗin kuma sai ya hau bata hakuri yana faɗin za'a kamo mata shi ta yi shiru. Sake fakar idanunsa ta yi ta saki ɗayar tattabarar ma, kara fashewa da kuka ta yi mai sauti tana faɗin ɗayar ma ta sake guduwa lallai lallai ya kamo mata abinta. Sanin ita wacece da kuma girman kaunar da ake mata a gabaɗaya faɗin kingdom ɗin yasa ya bi tattarabar da gudu yana mai gaya mata zai kamo mata amma dan Allah ta yi shiru. Ai kuwa suna barin wajen ta yi saurin ƙarisawa wajen gate ɗin. Ƙoƙarin tura gate ɗin ta yi dan ta buɗe, amma ta ƙasa saboda karfi da nauyi irin ta kofar, kamar zata rushe da kuka ta sanya dukkanin karfinta tana turawa. Ko gezau kofar bata yi ba, bakin ciki kamar ta haɗiyi zuciya, sai waigowa take yi tana kallon bayanta dan taga ko suna dawowa. Ta yi iya yinta kofar ko motsawa bata yi ba, tamkar dasata aka yi, fara bin jikin kofar da kallo ta yi, can ta hango wajen key ɗin datse kofar, ashe a rufe take, sai dai tsawonta ba zai kai ta iya taɓa wajen key ɗin ba, dan kofar tana da tsawo kuma key ɗin a sama yake. Ciccikowa da kwallah idanunta ya yi dan haushi, kamar ta ɗaura hannu a kai ta zunduma ihu. Juyawa ta yi cikin sanyin jiki, har zata nufi hanyar komawa kuma sai wani dabara ya faɗo mata, da sauri ta juyo tare da janyo kujerun da warriors ɗin suke zama a wajen ta kawo shi wajen saitin key ɗin, takawa ta yi ta haye dan ta ƙara tsawo. Ta kuma yi sa'a tsawonta ya kai wajen makullin, da sauri ya kama key ɗin dake manne a wajen ta hau murɗa shi, tana yi tana waigo bayanta. Tana buɗe key ɗin ta hau tura kofar, Da kyar ta iya buɗesa, a hanzarce ta afka ciki, tana shiga ta datse kofar da wasu keys da suke ta ciki, a kallah key zasu kai uku a jikin kofar ta ciki, sai ta sanya ɗaya wai dan kada idan warriors ɗin suka dawo su zo su fitar da ita, yau ta ci alwashin sai ta kewaye cikin wajen gabaɗaya duk girmansa, waje ne fa mai matuƙar girma sosai, amma wai sai ta kewaye dukka. Tafiya ta fara yi a cikin wajen tana kallon halittun dake wajen, wasu halittun su bata dariya, wasu su bata tsoro, wasu kuma su sanyata afkawa kogin mamaki. Sai da ta iso wajen wasu ƙanana ƙananan fararen zomaye waɗan da suka so su yi kama da wolf ɗinta ne ta tsaya, nan ta fara neman wayar da take tunanin ta ɗauko shi dan ta yi hoto, sam babu wayan a jikinta, kuka ne kawai bata yi ba, amma ta ji haushin manta wayar, ta so ɗaukar zomayen hoto. Wucesu ta yi ta cigaba da tafiya ba tare da tasan in da ta nufa ba, kwatsam ba zato ba tsammani ta ganta a gaban bushiya, da gudu ya yi kanta yana son kama kafarta ya gwaguya, kun san halinsa dama, ga iya sake kifiya. Ai kuwa watsawa ta yi a guje tare da sanya hannu ta toshe bakinta dan kada ta yi ihu wani ya jiyota. Garin gudunwa bushiya ta je ta faɗa cikin dawakan da ba'a ɗaure suke ba, ai kuwa watsewa gabaɗaya dawakan suka yi a guje, wasu suka yi kanta, a haukace ta zunduma ihu tare da fara ƙoƙarin cetar ranta. To bari dai muga zata iya cetan ran nata kuwa? Ga shi da iya ƙoƙari irin nata har da rufe kofar da key, ko taya ma za'a shigo a kawo mata ɗauki idan an ji ihun nata ma kenan? To ni dai bari na leƙa ƙasar DARK WORLD mu gani, wata kila kafin mu dawo dawakan nan sun gama take Gimbiya Zunaira ta yi laushi tilis tun da bata jin magana.......🥱 DARK WORLD💪🔥😥💔 Yar karar azaba ta saki kafin ta furta. "Am so so sorry sir". Slowly aka sakar mata hannun nata, wani irin haki take saki tamkar wadda ta yi gudu ta ƙoshi, kamar wadda ake horar da cikin kashi da ɓargon jikinta, har wani gumi take haɗawa kamar ba lafiya ba, abin da abin mamaki, yadda kuka san azabtar da ita ake yi, har sauyawa kalar idanunta ya yi izuwa jan kala. Turo kofar ɗakin aka yi, a hankali ya sako kafarsa a cikin ɗakin, gently yake tafiya kamar baya son taƙa ƙasa. Kyakkyawan matashi ne da ba zai wuci 19 to 20 years ba, kyakkyawan gaske ne sosai, idan ka gansa ba tambaya kasan koreans guy ne, sam babu zanen black Tiger a face ɗinsa, jikinsa kamar madara, ga idanu manya manya farare kal kal, soft skin ɗinsa har wani sheki yake yana glowing kamar mirror, shi ma ya bar dogon ga shi kamar dai sauran gabaɗaya mutanen cikin birnin DARK WORLD, na gaya maku su ɗin Christians ne masu koyi da Annabi Isa, ga su da shegen tsauri a addinin nasu, waɗan nan zasu yi wuyar musulta over, dan su ɗin tsauri garesu sosai fiye da tunaninku, kun san dama akwai Christians masu tsauri sosai da sosai haka, to haka suke, kun san Annabi isa yana barin dogon gashi sosai, so shi ne suke koyi da shi, kuma gabaɗaya mutanen birnin haka suke, basu da wani addini face wannan ɗin, duk abu ɗaya suke bautawa wato Annabi Isa. Sai dai launin kalar gashin kan nasa fa up white ne ba baki ba ko wata kala daban, up white ce. Sanye yake da three cuter jeans baka and shirt blue, da yake yana da haske sosai sai ya yi wa kayan kyau matuƙa, hannunsa na ɗaure da wani gold chains mai tambarin Black Tiger, duk yadda aka yi shi ɗin maraya ne ɗaya daga cikin marayun da Black Tiger ya rena, dan na gaya maraku in dai kai maraya ne to tabbas kafi ƴaƴan sarakuna gata a wannan Daular, zaka taso tamkar wani yarima, ko tambarin Black Tiger baka sanyawa a fuska, saboda darajarka, kuma marayu basa zuwa yaki, and kuma akwai wani mask na ɗanyar gold da Daular suke da shi, matasansu suke sanyata idan za'ayi gasa, da ɗanyar gold aka yi ta, design of black Tiger face ce, idan sun sanya fuskokin bakar damisa fuskokinsu yake komawa. To marayu basa saka ko shi wannan mai daraja mai tsada na gold ɗin. Sai Allah kaɗai sai kuma alkalamina ne zai warware maku dalilin Black Tiger na ririta marayu tamkar jinin jikinsa. Gefen bed ɗin ya zauna, cikin Korean language ya fara magana, sai kuma ya ɗan shafa white hair ɗinsa tare da juya yare zuwa English, da alama yasan Sweetie bata jin Koreans language. "Sorry beautiful Queen, ki nutsu ki daina kuka kin ji? Ba zamu cutar da ke ba, kina bamu Spender zamu sake ki, ba da nufin komai muka ɗaukoki ba kin ji? Ki dai'na kuka yanzu ki kwanta ki huta za'a kawo maki abinci ki ci, sai ki yi wanka ki kwanta ki huta, kin ga tun safe kuka kike yi ko? Zaki jawa kanki wani ciwon da zaki wahalar da jikinki". Cikin wani irin sanyin murya da sigar jan hankali haɗe da rarrashi ya yi maganar, da alama sam bashi da bakar zuciya, da alama zuciyarsa fara ce tas, ko da yake su renon ƴan gata ƴaƴan sarakuna aka yi masu, shiyasa bai san zalinci ba bawan Allah, zuciyar zinari da azurfa ke garesa. Haƙiƙa yana daɗin murya da sanyi sosai. "But Ronnie why? Why zaka tausasa murya a gareta bayan kuma kasan komai, kasanta tana da taurin kai? Dole sai an tursasata zata faɗi gaskiya, idan ta kama ma sai mu daka mata wutar azaba da sai ta buɗi baki, idan ta ji barbalin wutar azaba zata yi bayani ma ba wanda ya sani, mu da muke saka kurma ma yin maganar dole idan ya ji azaba bare kuma wannan ƙaramar kwaruwar? In taki sai mu bawa karnika ita su yi watandarta, su lamusheta ni na je na nemo Spender da kai'na". Juyo da kallonsa a kanta ya yi, cikin harshen Korean ya fara yi mata magana. "Why Delisha? Meyasa kika cika zafi ne har haka? Abin da hankali bai bada shi ba tashin hankali ba zai bada shi ba, tashin hankali sai dai ma ya lalata komai". Da alama Black Tiger yana da matuƙar wayo over, yasan idan suka bita a hankali suka lallaɓata da wuya ta iya ketare tarkonsu ba tare da ta biya masu buƙatarsu ba, shege Black Tiger ya san kan duniya, ko da yake mutumin da yake haukar neman ta yadda zai yi ya mulki duniya ai fin haka ma zai sani. "Ni bana son ɓata lokaci a kan abu ne ka sani Ronnie". Cewar Delisha. Jan dogon hancinta ya yi kafin ya furta. "Sarkin gaggawa ba? To sai a yi hakuri a kan wannan case ɗin kam". Kallon Sweetie ta yi. "Ɗago ido ki kalleni da kyau! Bani da wasa kuma bana ɗaukar wasa, bana son wargi da rainin wayo, yanzun nan zan saɓa maki kamanni ta yadda ke da kanki ba zaki iya gane kanki ba, kada ki bari mu yi haɗuwa ta biyu baki sanya a ranki zaki gaya mun gaskiya ba!!". Ta kai karshen maganar cikin kaifin harshe tare da miƙewa tsaye. Janyo hannunta Ronnie ya yi a kan ta koma ta zauna yana faɗin. "My Delisha ita fa wannan yaya (Black Tiger) ya ce bata gani, so ki dai'na wahalar da kanki wajen faɗin ta ɗago ta kalle ki". Wani ɗan iskar kallo ta wurga mata kafin ta sanya kai fuuuuu kamar kunfar teku ta wuce ba tare da ta yi magana ba. Da kallo ya bita har ta fice waje, da alama yana da sanyi hali over. Shesshekar kukan Sweetien ne ya dawo da kallonsa izuwa kanta daga kallon fusatatciya Delisha mai kan giginya............😅😌 Ita a dole mai fusatatciyar zuciya, da katon katakon hannunta kamar katako ko todi za'a ce ne, goshi kamar durom, amma ba laifi dai akwai ta da madarar kyau, wlh na ce maku mutanen garin yanda kuka san su suka yi kansu saboda kyau. Ni kam na ce bari na bawa Delisha shawara, ta fita harkar Sweetie kafin Kamran Allah ya ɗaura shi a kan mamma ya samu ya gudo ya zo cetarta, idan bata yi sa'a ba a cikin masai zai jefata ta mutu........(😅) Kun san Kamran namu ba wasa ba.........💪🔥 Ɗan rungumota Ronnie ya yi a jikinsa tare da fara bubbuga bayanta ya hau yin rarrashi, sai yi mata tausasan kalamai yake yi masu tausasa zuciya, ya nuna yana kaunarta, tsantsar tausayinta ya bayyana a saman face ɗinsa...... To Allah yasa ba basaja kake yi mana ba Ronnie, Allah yasa ba dan ka yaudareta ta gaya maku in da spender yake kake yi ba ato, dan ku ɗin ba abin yarda bane. Cigaba da shesshekar kukanta ta yi bata iya amsa mashi maganar tasa ba.......... 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 27/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 Cigaba da shesshekar kukanta ta yi bata iya amsa mashi maganar tasa ba. Shi kuwa bai rabata da jikinsa ba har sai da ta dai'na kuka, ya tabbatar da zuciyarta ta ɗan yi sanyi, ba karya ya lafazata da kalamai masu tsayawa a rai, ya rarrasheta tamkar wata ƴar baby. Bayan ta yi shiru ne ya rabata da jikin nasa, sannan ya ce ta kwanta ta ɗan huta bari ya kawo mata abinci da kansa. Ya kai karshen maganar tare da janyo ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman pillows ɗin dake saman bed ɗin ya matso mata da shi izuwa tsakiyar gadon, sannan ya kwantar da ita, sai hamma take yi alamar barci da yunwa take ji. Bayan ta kwanta sai ya miƙe da nufin zai fita. Tattare up white hairn nasa ya yi ya watsa shi baya har tsakiyar bayansa, nan take wasu ƴan kananan kyawawan diamond earrings suka bayyana a kunensa, ya huda kunne har huji shidda, ya zuba diamond earrings masu bala'in tsada da kyau a kunnen, sai ɗaukar idanu suke yi, a sama ta kusa da kunnen waje da gashin sage yake zama amma ta sama kusa da kunne ya kuda wajen ma tare da zuba diamond pin a wajen, harta tsakiyar harshensa akwai wannan pin ɗin ya sanya, and one thing yana da zanen tattoo a tsakiyar bayansa, sannan yana da shi a saman hannunsa wajen damatsansa...... Ni kam ina son sanin waye Ronnie gaskiya!. Har ya kama hanyar fita sai ya lura da tana rawan sanyi, alamar karfin gudun Ac ɗakin ya yi mata yawa. Juyowa ya yi tare da rage mata gudun, sannan ya rufeta da duv kafin ya sanya kai ya wuce. Tana kwanciya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita, dan ta ci kuka ne over, sannan kuma ta gaji ga yunwa and barcin dukka sun haɗe mata. Sai ajiyar zuciya take saukewa a cikin barci. Yana fitowa ya nufi electric stair case ɗin dan ya yi ƙasa, sai wai saiɓi yake yi a tafiya kamar wata mace, da alama hutu ce ta yi mashi yawa. A main parlourn ya isko Delisha dake zaune gabanta da uban kayan motsa baki tana aikin ci. Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da wucewa ya nufi wani katafaren dining room wanda girmansa ya wuci tunaninku, ya haɗu sosai, ya ji komai na more rayuwa, ai bama sai na tsaya ɓata lokacina wajen faɗa maku haɗuwarsa ba, domin komai na cikin Daular Black Tiger fa kun san ya amsa sunansa, dan kuwa daloli ne suke kuka a Daular bama Nairori ba, dukiya ta yi mubaya'a har ƙasa ta kwanta a wannan masarauta, sun jiƙu da ɗinbin arziƙi daga Ubangijin, dan Allah ne kawai mai bada arziki musamman ma na ƙarƙashin ƙasa dana cikin ruwa. So sun cika sun batse shiyasa suke tunanin mulkar duniya. Sai dai da ni da ku dukka mun san babu wani mutun ɗaya da Ubangiji ya ambata wanda zai mulki duniya, ace duniya ta zama shugaban ƙasa guda ɗaya gareta? Ina ba zai yiwu ba, wane mutun, sai dai mahdi da zai bayyana a gaba wanda shi kuma zai zo ya cika duniya ne da adalci a lokacin da zalunci ya yi ci karfin bayin Allah, Allah ka iya mana, wlh Ubangiji yana sonmu, kullum yana cikin kawo mana mafita a lokacin da abubuwa suka yi mana tsanani, Allah ka bamu ikon yin bautarka yadda ka umarcemu......... 💔😥 (Amma ni tambayata ma a nan wai ko ta ya Black Tiger zai iya rike duniyar idan ya samu karfin ikon mulkin?🤔 Yanzu ma kowacce ƙasa da shugabanta, governors, ministar's, hukuma, kai da dai sauransu ma ya aka kare? Bare kuma ace shi kaɗai yake mulkar ko'ina? To ko dai zai gina mana ƙasa kuda ɗaya ne ya haɗemu waje guda?😅🤔 Is just a jock.) Saman ɗaya daga cikin wani gold chair of gold dining table dake dining room ɗin Ronnie ya zauna, sai wani lumshe ido yake yi kamar mai jin barci, kayan abinci iya kayan abinci ne a saman table ɗin, suna maƙare, table ne mai girman gaske, dan chairs dake ta side ɗaya kawai sun kai 28, ɗayan side ɗin ma haka, gaba da baya kuma two two chairs ne a wajen. Kai my people's naso ace kunga haɗuwar wannan dining table ɗin, wayyo duniya Allah ka yi mana arziki mai albarka wanda zamu taimaki bayinka mu yi wa addinin musulunci hidima Amin. Wato chairs na dining ɗin nan sun rikitani a wajen kallon, sai ka wuni wajen sakin baki kana kallon haɗuwarsu, komai na girma na manyan kai ne a cikin wannan Daula, komai wayewarka idan ka shigo wannan Daula fa sai ka zama ɗan kauye, abin ya wuci tunaninku, haɗuwa iya haɗuwa!!. Wasu irin saƙaguna ne tsaye a gaban table ɗin, su shidda ne cif, gabaɗayansu kuma robot ne ba mutane ba, da naura suke aiki, kuma chajinsu ake yi, sai dai kirar mutane ke garesu, idan ka gansu ma ba zaka taɓa zaton ba mutane bane, sai in suna tafiya ko suna yin wani abin zaka ga sun banbanta maka da mutane. Akwai irinsu sosai a cikin Daular, daga ƙasar China Black Tiger ya sayosu da ɗinbin dukiya mai yawa, duk ya sayosu ne dan ya kara karfin wajen tara uban yawan warriors ta yadda zai cigaba da karin samun karfin iko ya mulki duniya, burinsa dai mulkar duniya, kamar hauka haka yake farautar wannan matsayin, shiyasa ya sayo robot guda ɗari biyar, suna ɗaya daga cikin abin da yasa ba'a cin nasara a kansa a yaki, dan mafiya yawan lokuta idan za'a tafi yaki robot ɗin sune a kan gaba, duk da cewa a yanzu ba'a gama shigarwa da robot ɗin dukkanin horon yaki ba, basu wuci guda ɗari aka shigarwa da horon yaki a cikin jadawalin naurar ƙwaƙwalwar kansu ba, saura suna nan a killace cikin wani ɗaki ana basu horo, duk wanda horon ya shiga jadawalinsa sai a fitar da shi izuwa cikin sauran warriors na mutane shi ya yi free, so Black Tiger ya ware robot guda 30 yasa an basu horon yi mashi hidima a cikin Daular tasa, su suke share ko'ina su goge ko'ina, sannan na wajen dining table dan serving abinci suma ya ware guda shidda, so a takaice dai haka suke a cikin Daular..... Wai akwai karfin iko iya karfin iko kam a DARK WORLD, ai dole a rinƙa jin tsoron Black Tiger, dan shi ɗin wuta ne mai balbali, gobara daga kogi kasheka sai dai lillahi, dole duk sauran masarautu su ja baya!. Ni kam nace ba? Anya za'a iya samun wanda zai yaki Black Tiger kuwa? Irin wannan warriors da ya tara majiya karfi! Kuma harda robot da bindiga bata fasasu bare wuka? Ta yaya za'ayi nasara a kansu a fagen yaki? Hmmmm akwai cakwakiya, zan so naga karshen wannan game ɗin. Yanzu su kuma nasu wasan zai fara, fata na dai shi ne Allah yasa kada Sweetie ta yi masu taurin kai daga lallaɓawa su juya su fara azabtar da ita idan taki basu haɗin kai su samu Spender! My people's ku ce amin, dan Sweetie ba zata iya ɗaukar azabtarwan waɗan nan masu Black heart ɗin ba, Black Tiger with black heart gaskiya abin ya munana kam, ya haɗe ya yi mashi yawa idan ma mutun ne!!. Ronnie Da yaren English ya yi wa robot ɗin magana a kan su haɗa mashi abinci mai rai da lafiya bari ya kaiwa bakuwarsu, da alama ba'a shigar masu da jadawalin yarika dayawa a cikin head ɗinsu ba, dan kuwa Ronnie ya fi iya yaren Korean akan English, amma haka yake yin magana da su da English ɗin dan su fahimce shi sosai kada su yi mashi shirme, kum san sufa robot ba wani hankalin azo a gani ne da su na, yanzu zasu tabka maka ba dai'dai ba. Zuba mashi abincin suka fara yi, wani katafaren luxury glass try suka ɗauko daga wajen makeken drawer dake cikin dining room ɗin, glass drawer ne na shirya kananan kwanikan da ake amfani da su a cikin room ɗin, irinsu cup's, spoons, small plates, and tray's different types, design, and colors, dan kaiwa wanda bai fito cin abinci ba nasa ɗaki aka ajiye tray's din, kai ai na gaya maku dining room ɗin nan duniya ne, baki bai isa ya faɗi haɗuwarsa ba, wane mutun!. Abinci suka hau shirya mashi lafiyayyu kala kala, da yake tray ɗin yana da girma sai ya kwashe abincin da ya buƙatar kaf a ciki, wajen kala biyar suka sanya mashi, amma tas ta ɗauke, sun kuma sanya wasu irin fresh kayan marmari masu kyau da ɗaukar ido, har tissue basu bari ba sai da suka sanya mashi, sun dai haɗa komai normal da yake umarni suke bi su kam, kana bada umarni zasu aikata dai'dai abin da kace masu, basu kara komai kuma basu ragewa. Yana zaune har suka gama, sannan ya miƙe ya ɗauka tare da nufar hanyar fita. Still Delisha tana zaune a parlour tana cika tana bashewa. Sake kashe mata ido ɗaya ya yi, harara ta wurga mashi irin ta ji haushi ya shiga mata cikin aikinta, ya hanata sumar da Sweetie da mari. Shi kuwa bawan Allah ko da ta hararesa ɗin ma sake kashe mata ido ɗaya ya yi tare da sakin murmushin da sai da ya kusa sakani suma saboda kyan da ya ƙara, ban taɓa sanin dimple na yi wa namiji kyau ba sai a kansa. Wucewa ya yi saman stair case ɗin ba tare da ya ce mata uppan ba, harara ta cigaba da binsa da shi har ya wuce abinsa. Kai tsaye ɗakin Sweetie ya nufa. Sai dai ko da ya je har barci ya ɗauketa, ajiye mata kayan abincin ya yi a saman haɗaɗɗen luxury glass table dake saman carpet dake gaban bed ɗin nata, sannan ya nufi waje. Da fitarsa ba'afi minti 2 ba sai ga wata kyakkyawar farar matashiyar budurwa ta shigo cikin ɗakin, shigar jikinta sak na ƴaƴan sarakuna, a gefen bed ɗin ta zauna tare da zubawa Sweetie idanu, da alama ita ce zata kula da ita har izuwa lokacin da zata basu abin da suke da buƙata su saketa ta tafi. MY PEOPLE'S NA CE BA? WAI IDAN BLACK TIGER ZAI MULKEMU YA ZAKI YI? AKWAI TARIN ARZIKI KAM, SAI MUN ƘOSHI DA ƊINBIN DUKIYA, AMMA ZAMU ƊANƊANI KUƊARMU FA. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ JIMETA............ NIGERIA🛫 Mahreen🔥😅 Bayan ta kammala cin abincinta tana dai ta kunkuni bata dai na ba, ita a dole bata son zuwa wajen mahaifiyarta. Mahnoor dai bata sake bi ta kanta ba, ta cigaba da yin abin da yake gabanta. Wanka ta je ta yi ita ma, ta zo ta yi zaman ƴan bori a tsakiyar katifa ta hau yin wannan mahaukaciyar kwalliyar tata, shiyasa fa kwata kwata powder baya jima masu idan bappa ya sayo masu, saboda Mahreen ke karar da shi a face ɗinta, damɓarashi take yi kamar an aikota, ga power irin jajayen powder nan ne, wlh sai fuskarta ya tashi daga farar fata izuwa jan ƙoshe, abin dai sai wanda ya gani, kuma a haka take hauka da faɗa idan aka yi wa kwalliyar tata dariya, wannan yarinya ni dai in ce sai shirin Allah. Yau dai sai sauri take yi tana son ta gama da wuri ta je ta cigaba da taɓa kumatun aljanin nan da bappa ya kawo, tana son ta je ta yi ta mulmula mashi ne kafin Mahnoor ta gama kwashe tuwo su tafi. Kaya irin na jikin Mahnoor ɗin ta sanya a jikinta, da alama bappansu ɗinki iri ɗaya yake yi masu, duk abin da Mahnoor take da shi ita ma Mahreen tana da shi. A hankali ta gama ta miƙe tare da tattare komai ta mayar mazauninsa, ba karya suna da tsabta kam, basu son datti, komai nasu tsab tsab. A ɗari ta fito ta afka cikin ɗakin bappa dan ta fara aikin mulmula mashi kumatu..... Ni kam na ce su Mahreen an samu sabon business, Allah ya fitar da kai Our Jaish. A gabansa ta zauna, ta kura mashi idanu kamar mai nazarin wani abin, yadda kuka san itace likita an kawo mata mai jinya tana nazarin yanayin jikin nasa, haka ta nutsu tana kare mashi kallo, ita dai a duniya Jaish ya yi mata, bata ki a barta ta mayar da shi Tv ta yi ta kallo ba. Ta ɗauki tsawo lokaci a haka tana ta kallonsa, jin sautin muryar Mahnoor na kiranta tazo su tafi ne yasa ta yi saurin kai hannunta saman jajir ɗin lallausan kumatun nasa ta fara shafasa a hankali kafin daga baya ta fara mulmula mashi kamar wadda take mulmula gullinsuwa. "Wai Mahreen ba zaki fito mu tafiya ba?". Mahnoor ta faɗa daga waje, tsoro ya hanata shigowa ta janyo Mahreen ɗin. "Ni fa Adda Mahnoor ban fa gaji da taɓa kumatunsa ba, kizo kema ki taɓa jiki akwai daɗi". "Allah ki fito daga cikin ɗakin nan tun kafin in shigo". Da yake kwararriya ce a iyashege sai ta ce. "Idan kina son na fito muje gidan Arɗo to fa sai kin shigo kin kama hannuna, idan ba haka ba ni babu in da zan je". "Ayya gajin Bappanmu kin ga ina jin tsoron aljaninnan, dan Allah ki fito, wlh ba zan iya shigowa ba, ki zo kinji ko? Idan muka je kiwo gobe zan ciro maki kanya". Kin fitowa ta yi, ta kafe sai Mahnoor ɗin ta shigo in dai tana son su je. Tana surutu tana ɗan murguɗa baki, gashin idanunta kam ba'a magana, suna tsaitsaye zara zara dasu na rashin kunya. Cigaba da yi mata magiya daga waje ta yi, amma ta ki fir, sai cigaba da mulmulawa bawan Allah kumatun nasa take yi. Ai kuwa kamar daga sama ba zato ba tsammani kwatsam ya wani irin zaro idanu waje, ga idanun nasa sun yi jajir tamkar wadda aka watsawa barkono a cikinsu. Subhanallah wani irin ihu da Mahreen ta zunduma mai sautin toshe jin mutun, ta yi wani mahaukacin razana, dan bata yi excepting zai buɗe idanunsa ba, sam bata kawo hakan a ranta ba. A dubu ɗari ta miƙe ta fasa waje tana ihu. Ai kuwa tun da ta zunduma ihu farko Mahnoor ta arta waje a guje, dan a tunaninta aljanin ne ya tashi ya kama Mahreen ɗin yasa take ihu, a maimakon ta shiga ciki ta kai kama agaji idan ma hakan ne, ina ai sai ta yi ta kanta a ɗari, dama kamar a kan kaya take, tana jin tak ta arta waje a dubu abinta. Haba wa hajiya Mahreen ana firowa sai kofar gida, ihu take har da cire takalma da ɗan'kwalin kamar su ne suka sanya Jaish ya buɗe idanu, yau har da karanta suratul fatiha a cikin ihun nata. Bata zame ko'ina ba sai gidan kakansu Arɗo, duk ta zubar da takalma and ɗan'kwali a hanya. Can ta isko Mahnoor har ta isa gidan sarkin tsoro, tuni har ma ta shige cikin ɗakin kakarta mace tana kuka da hawayenta duk da ita bata ga abin da Mahreen ta gani ba, ihu kawai ta ji amma har da kukanta. Kakar su dake cikin madafa bata san da zuwan Mahnoor ba dan ita bata yi ihu ba sai hawaye gudowa kawai ta yi, sai da Mahreen ta shigo a haukace tana ihu ne duk wata halitta mai rai dage gidan har da magensu sai da suka fito, manyan mata an shigo waje ai dole a fito a tarbeta, Mahreen manyan ƙasa. Mata uku ne a cikin gidan, so bukkoki huɗu ne da na Malam Arɗo biyar kenan a cikin gidan. Harta Arɗo sai da ya fito a hanzarce jin irin ihun da ta afko masu cikin gida da shi. Da sauri kakarta ta yi ƙoƙarin kamata tana kiran sunanta, ina kin basu haɗin kai wajen riƙota da suke yi ta yi, faɗi take. "Hande mi woni, ina Nennenmu? Ashe da gaske ne aljani Bappa ya kawo gida, wlh aljani ne idonsa ba irin na mutane bane, kamar wuta idanunsa suke, na shiga uku, ga idanunsa wlh sun kai ukun na Adda Mahnoor a girma, kato kato da su, yau kam mutuwa zan yi na kalli idanun aljani". Sai ƙoƙarin nutsar da ita suke, amma ina yadda kuka san iska haka take yawo a sama dan sun rirriketa, sai ta ɗage kafa sama tana wuwwuntsiyasu tana ihun ina Nenne. Nennen nasu dake tsaka da barci ne ta tsinkayo muryar ƴar tata a cikin kunnenta, a hanzarce ta zabura ta taso ta fito, kusan a tare suka fito da ainahin Kakansu Mahreen ɗin. Matan Arɗo uku ne, so biyun da suka tari Mahreen ɗin suna ƙoƙarin rarrashinta kishiyoyin kakar tasu ce, ita kuma ainahin wadda ta haifi Nennen tana banɗaki lokacin da Mahreen ɗin ta afko masu, so yanzu fitowarta kuma a tare da Nennen kenan. Kanta suka yi a tare da gudu kakar tata ta ainahi tana faɗin. "Cikinku wace shegiya ce ta dakar mun jika?". Sake Mahreen ɗin suka yi, ai kuwa a guje ta yi wajen Nenne tana ihu. Arɗo na ƙoƙarin yin magana ɗayar matar wadda ake kira da Diddi ce ta rigasa da cewa. "Ai babu shegiya a cikin gidan nan ko kin manta ne? Ko wacce da ubanta". "To rasa kunya ɓerar tanka, wacece ta dakar mun jika na ce?". Cewar kakan Mahreen da suke kira da gwaggo. Sa kai ɗayar matar da suke kira da Inna ta yi ta wuce izuwa nata ɗakin abinta, bata tofa ko uppan ba, da alama bata son hayaniya. Su kuwa suka tsaya kace nace, gwaggo ta zage sai ta ji uban waye ya dakar mata jika. Inna na shiga ɗakinta ta ci karo da Mahnoor a zaune tana ta kuka, dan ba karya ta tsorata. A hanzarce ta ƙariso wajenta. "Mahnoor lafiya me ya faru?". Tana ganinta ta yi maza ta miƙe ta faɗa jikinta tare da kara sautin kukanta. "Mahnoor ki gaya mun me ya faru mana? Meyasameki?". Ƙasa yin magana ta yi tana cigaba da yin kukanta. Nasan zaku yi mamakin ganin Mahreen ta nufi wajen gwaggo ita kuma Mahnoor ta nufi ɗakin Inna ko? To barin baku kaɗan daga labarinsu dan ku fahimci ina muka dosa. Mahnoor Inna ce kakarta a gidan, ita ta haifi mahaifiyarta, ita kuma Mahreen gwaggo ce kakarta ita ta haifi Nennenta. Mahaifiyar Mahnoor bata gidan Bappa kwairaga, Inna ƴaƴanta biyu rak a duniya, daga mahaifiyar Mahnoor mai suna Halima, sai kuma kaninta Ibrahim. Bappa kwairaga mahaifiyar Mahnoor ya fara aura, ita ce matarsa ta farko, Nenne kawarta ce da aka maye mashi gurbin mahaifiyar Mahnoor da ita bayan ya rasata, ƴaƴan kishiyoyi suke da Mahaifiyar Mahnoor da Nenne, kuma kunga gidan Arɗon ba zaman lafiya suke yi ba, akwai kishi a tsakaninsu, lokacin da Bappa ya rasa mahaifiyar Mahnoor Mahnoor ɗin tana yarinya bata wuci 2 years ba, shiyasa Arɗo ya bashi auren Nenne dan ta riƙe Mahnoor ɗin tunda ƴar ƴar uwarta ce, suna ganin zata kula da ita sosai. Hakan kuma aka yi, da farko Nenne ta riƙe ta sosai da sosai, tamkar ƴar cikinta, har ta haifi Mahreen, ta haɗasu ta riƙe da amana, sai dai kash mahaifiyarta ta canza mata tunani daga baya, a in da suka fara sakawa ɗinbin uban tulin dabbobin bappa ido, daga nan ta fara sanyata ta fara juya riƙon amanar da take yi wa Mahnoor izuwa nanzalinci, duk lokacin da Inna ta yi wa gwaggo ba daidai ba, sai gwaggo ta ce da Nenne ta azabtar da Mahnoor, ta hakan suke cusawa Inna bakinciki, dan Mahnoor ita ce kaɗai jikarta, ita take kallah ta tuna ƴarta, bappa kwairaga kuma yaki bata Mahnoor ɗin ta riƙe, wai shi ma yana tuna mahaifiyarta a duk lokacin da ya ɗaga idanu ya kalleta, so ba zai iya rabuwa da it ba. Sannan su gwaggo suna bakincikin irin kauna da bappa yake nunawa Mahnoor ɗin dan maraicin rashin uwa, sai ya zamana yana kula da ita sosai fiye da kansa, kuma yana ƙoƙari dannewa fa baya nuna banbanci a tsakaninsu da Mahreen, amma saboda shegen makirci irin na gwaggo ta zuga Nenne wai Bappa ya fi kaunar Mahnoor a kan Mahreen, hakan yasa ta kara tsananta wahalar da Mahnoor ɗin. Duk kuma wannan abin da yake faruwa Bappa ko Arɗo ba wanda ya sani a cikinsu, bappa bai san ana wahalar mashi da ɗiya ba, kuma bata taɓa gaya mashi ba baiwar Allah, idan ya yi tafiya har talla Nenne take ɗaura mata, amma da ya dawo zata dai'na ta nuna tana kaunarta ma a gaban idanunsa. Ita kuma Mahreen da kuke ganin nan, rikici suke yi da Nenne, saboda ita tana kaunar ƴar uwarta, tana sonta fiye da tunaninku, ba ruwanta da zancen su ƴaƴan kishiyoyi ne, babu wannan a ranta, kuma kullum Nennen nata tana gaya mata ba ɗaya suke da Mahnoor ba, Mahnoor ƴar kishiyarta ce dan haka dole ta tayata kishi, ita kuwa ta ce ba dai ubansu ɗaya ba? Ai tun da ubansu ɗaya ita kam ba ruwanta da wani banbanci uwa, koma yaya ne Mahnoor ƴar uwata ce. Idan Nenne tasa Mahnoor aiki to fa ko zata mutu sai Mahreen ta tayata, bata yarda ta barta ta yi ita kaɗai, duk faɗar da Nenne zata yi mata zata ce wlh ita sai ta taya ƴar uwarta, tun Nenne tana faɗa har ta hakura, dan ta lura Mahreen zata tona mata asiri wajen bappa idan ta matsa. Wannan dalilin yasa Mahreen ɗin take cewa bata son Nennen ta dawo gidan, dan tana wahalar da Mahnoor, ita kuma bata son hakan, shiyasa ta ce kada Nennen ta dawo, ita fa Mahreen wlh sam bata son zalinci, bata son abin da zai taɓa mata Mahnoor ɗinta, ƴar uwarta ɗaya tilo a duniya. Bata bin bayan rashin gaskiya! Ga iya kwatar ƴancinta abinta, ko ba karfi akwai baki, da bakinta zata ɗaure mutun har igiya ya saura!!. Wannan a takaice yadda suke kenan, fatan kun gane?. Lallashinta sosai Inna ta yi har barci ya ɗauketa a kwance a saman cinyar Inna ba tare da ta gaya mata dalilin yin kukanta ba. Ita kuwa Mahreen da kakarta gwaggo ta jata suka yi ɗaki bayan sun gama masifar tasu Arɗo ya fice ha basu waje dan yasan sun saba. Da kyar suka iya lallashin Mahreeh ta yi shiru, ai kuwa tana yin shiru ta yo waje sai wajen ƴar uwarta Mahnoor a ɗakin Inna, suna kiranta tana ce masu tana zuwa bari ta dubo Mahnoor, ɗakin Inna ta shige abinta. Ko da ta zo Mahnoor ta yi barci har ma Inna ta kwantar da ita a saman gado ta fita waje dan cigaba da aikace aikacenta. Ita ma tana shigowa ta kwanta kusa da ƴar uwar tata tana fuskantar saman zanar bukkar kamar mai tunanin wani abin. A can ɓangaren Jaish kuwa, bayan ya buɗe idanu da Mahreen ta tsorata ta guda sai ya sake mayar da idanun nasa ya rufe, da alama baya cikin hayyacinsa sosai sosai, dan da alama bai ma san in da yake ba, ya rufe idanu ya kwanta shiru har barci mai nauyin gaske ta ɗaukesa. Bappa kuma a lokacin ya fita zuwa wajen wani abokinsa likitan gargajiya irinsa dan ya ɗauko shi ya zo ya yi nashi gwaje gwajen ko Allah zai sa Jaish ɗin ya farfaɗo, shi ya yi iya ka yinsa tun safe shiru, shi ne ya ce bari ya jarraba kiran ɗayan dattijon likitan, dama su uku ne kawai likitocin gargajiya a kauyen, to ɗaya ya rasu, kuma shi ne babbansu dama, yanzu sun rage su biyu ne kawai likitocin kauyen. Da yake wajen yana da ɗan nisa sai da ya sha tafiya kafin ya isa wajen, sai gab da mangariba suka ƙariso shi da likitan. Har lokacin barci Jaish yake zubawa. Sun sha madarar mamakin ganin yana numfashi, kun san dama already bappa ya barosa baya numfashi, bama su da tabbacin yana raye ko ya mutu. Da sauri bappan ya yi yo waje dan ya tambayi Mahnoor yaushe wannan bakon ya farka?. Sai dai ko da ya shiga cikin ɗakinsu basu nan, mamaki ya fara yi a kan ina suka tafi? Can ya tuna sun ce zasu je wajen Nennensu, tuna hakan yasa ya ce nan suka tafi sai kawai ya fito ya koma nasa ɗakin. Sun yi murna sosai na ganin bakon nasu yana numfashi, dan haka sai suka hau aikin da zasu taimaka wa rayuwarsa shi da likitan abokin nasa. TO ALLAH YA BAKA LAFIYA OUR PRINCE JAISH. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 A takaice dai yau aka yi arba'in na baban Zainab, Maman Zainab dai in short hukuncin ɗaurin rai da rai aka yanke mata, a hakan ma dan ta ce bada gangan ta yi hakan ba, amma kotu bata yarda da kalamanta ba, saboda su Hauwa sun fita makirci, sannan kuma su sun ɗauki makirin lauya da ya kware wajen take gaskiya a kullum, hakan yasa dole ta hakura ta karɓi kaddararta na ɗaurin rai da rai. Zainab kuwa tana gadon asibiti saboda ciwo, Sadiq ya ɗauketa ya kaita asibiti ba tare da sanin su maman Haidar ba, kuma tsabar basu kaunar Allah ko nemanta basu yi ba da suka dawo daga kotu, ko a jikinsu kamar ba ɗan mutun ne ya ɓata ba, sai ma tunanin abin da zasu ci suke yi. Shi kuwa Sadiq ya kaita asibiti ne dan jikin nata ya yi tsanani, kuma tsawon wannan lokaci da ta fara jinya tun rasuwan baban nata babu wanda ya sai mata ko paracetamol a cikin ƴan uwan baban nata, Maman Hanif dai bata cikin gidan, dan kuwa kaca kaca suka yi da Maman Haidar shi ne ta wuce gidan mijinta, ita kuwa Maman Haidar taga wajen zama, ta share mazaunanta ta yi zamanta, ko ina gantalallen mijin nata ne kuma ya shiga sai Allah ya san mashi. Ita dai Maman Hanif ta ce wlh abin da baban Zainab ya yi masu a rayuwa bai cancanci irin wannan sakayya daga garesu ba, a halin yanzu addu'a yake da buƙata ba duk wannan balaja'un da suke ta yi suna up and down within karya and gaskiya ba, shi ne fa Maman Haidar da yake ita ce babba ta hauta da ruwan masifa, ai kuwa a wannan karon bata raga mata ba, ta yi mata wankin babban bargo har da ce mata babbar banza sai girma a shekaru babu girman kwakwalwa, daga karshe ta ce zata ɗauki Zainab su wuce da ita gidanta ta je ta yi jinyarta kuma ta cigaba da riƙeta tun da dai ita kam Maman Haidar shashasha ce babu tunani a cikin kanta, to ita dai tana da tunani kuma tasan ya kamata, dan haka zata riƙe Zainab duk da tasan bata da karfi mijinta ma haka, amma ba zata bar bayan baban Zainab ya walaƙanta ba, zata san ta yadda zata yi ta kula da Zainab ɗin. Nan fa Maman Haidar ɗin ta yi tsalle ta dire ta ce bata ga uban da zai ɗauki Zainab da Khadija ya fitar da su daga cikin gidan nan ba, ai ita ce babba, ita ce zata yanke me za'ayi. Kuma duk borin kunya take yi, dan tana bakin cikin Maman Hanif ɗin ta yi mata zagin kare dangi kuma ba halin ta daketa, dan kuwa tsab Maman Hanif zata karye banza ta ajiye, so tana tsoron fara kwatantacewa ma zata mareta, dan a lokacin Maman Hanif ɗin ta fusata sosai, komai aka yi mata ba zata kyale ba, coz shi ne take hucewa ta hanyar hanata ɗaukar Zainab. Maman Hanif kuwa, sai a lokacin da ta shiga ɗakin Zainab da nufin ta ɗauketa ɗin ne sai ta ga ba Khadija, ta tambayeta ina Khadija ɗin kuma?. Dan su hankalinsu na a kan kotu duk tsawon kwanakin nan, sannan ƴan gaisuwa sun cika gidan, bugu da ƙari basa shiga in da su Zainab ɗin suke, suna ta fama da jama'a. Hajiyarsu da izuwa yanzu ta gama nadama da danasani, ko uppan bata iya furtawa, banda kuka ba abin da take yi, Maman Hanif ɗin ce ke zama kusa da ita tana rarrashinta, time to time Hauwa na zama kusa da ita dan makirci, so maman Hanif abubuwa sun taru sun mata yawa shiyasa bata farga Khadija bata gidan ba, ita kuwa maman Haidar dama can bata nemesu ba bare ta san Khadija bata nan, tana can tana gantali a tsakanin police station and court ita da Hauwa! Yanzu Hauwa kawarta ce, Allah sarki ta rigada ta shanyeta. Ko da maman Hanif ɗin ta tambayi Zainab ina Khadija ta yi?. Zainab baiwar Allah ta kasa iya yin magana, ciwo ya ci karfinta, zama kusa da ita Maman Hanif ɗin ta yi tana ƙoƙarin lallaɓata ta gaya mata ina Khadija, a wannan lokacin ne Maman Haidar ta biyo bayanta tana bala'i a kan bata ga uban da ya isa ya ɗauki Khadija daga wannan gidan ba. Da maman Hanif fa taga ba iya masu da balai'n nan zata yi ba sai ta kama kanta, ta bawa Zainab hakuri tare da gaya mata cewa wlh tana kaunarsu har cikin ranta, kawai ba yadda zata yi ne da balai'n dangin nan nasu, dan haka Zainab ta kula da kanta ta cigaba da addu'a, idan Khadija ta dawo ma ta gaya mata hakan, dan a tunaninta Khadija ɗin ta fita sayan wani abin ne. A takaice dai wannan shi ne abin da ya faru a kwanakin baya kafin kwana arba'in da rasuwar bbn Zainab ɗin. One thing da ban sanar da ku a nan ba shi ne, mu koma baya mu ɗauki farkon labarin A'isha wato maman Zee. Maman Zainab and Hauwa they're very very close friend. Unguwa guda suka taso, makarantarsu ɗaya, islamiya ma ɗaya, coz ita Hauwa tun suna ƴan'mata mayyar kuɗi ce, a hanyar islamiya idan suna dawowa duk namijin da ya ɗan yi masu wasa irin matasan unguwa haka sai Hauwa ta ce ayya wane ɗan saya mun gyaɗa dafaffa ko wani abin makamancin haka, idan zai saya sai ya saya tare da Maman Zainab, ita bata karɓa, dan mamarta ta hanata. So a haka suke rayuwa, mayyar kwaɗayi ce ga rokon bala'i, lokacin da Sadiq ya san da hakan dan tana yawan rokonsa, ko abu ta gani a hannunsa sai ta roƙesa, shi ne ya gayawa mamarsu halin Hauwar, gata da yayuɓen samari kamar wata ballagaza, Sadiq ya ce wa mamarsu kullum saurayin da zaka ganta da shi na safe daban na yamma daban, kuma dukka yara ne da basu wani isa aure ba, ba iya riƙe mata zasu yi ba, amma sai ta biye masu tana cinye masu kuɗi, ga shegen kaifin harshe kamar reza, nare nare zata kalailame ɗan mutane da kalaman yaudara ya ɗebi duk ɗan cinikin kuɗin da yayo a kasuwa ya bata, ta karɓe ta shige gida. Hajiyarsu Sadiq da ta ji haka ta bincika kuma ta gane hakan sai ta ce da Mmn Zainab maza maza ta kama kanta, ta yi maza ta fita harkar Hauwa dan ba kawar zama bace, duk mace mai kwaɗayi da rokon maza da mata abu to tabbas tana gab da jefa kanta ga halaka, dan kuwa kwaɗayinta zai kaita ya barota. Da Hauwa ta biyo mata zuwa Islamiya Sadiq da kansa ya kora mata jawabin kada ta sake zuwa gidan, kuma kada ta sake ko ɗaga idanu taga maman Zainab, kowa ta yi rayuwarta, ta so ta masa rashin kunya ta zage shi, sai Hajiyarsu ta taka mata birki ta kara mata da bayanin ko sannu kada ya kara haɗata da maman Zainab basu so, kowacce ta bi nata layin. Abin ya baƙanta mata rai sosai, already dama ita Hajiyar tasu tasan yaran gidansu Hauwa ba yaran kirki bane, uban nasu ne wato kanin baban Hauwa shi ne mutumin banza maras zuciya da kwaɗayin abin duniya, shi ne ya koyawa yaran kwaɗayi da roƙo yana zaune su ciyar mashi da gida, har tutiya yake yi ya haifi jari, ɗiyar arziki su suka riƙe mashi gida. Coz Hajiyarsu tasan da wannan, amma da taga Hauwa na zuwa makaranta har da Islamiya sai ta yi tunanin to kila ita ta fita zakka a cikinsu, ashe kuwa duk kanwar ja ce bata sani ba, shiyasa bata ɓata lokacinta wajen cewa zata yi wa Hauwar nasiha ba kawai ta yanke hukuncin rabata da ƴarta, dan tasan duk gidansu haka suke ba kamun kai ga ɗan banzar rashin kunya da rena manya, komai girman babba ya yi masu zage shi fes zasu yi babu ruwansu. To a takaice a haka aka raba maman Zainab da Hauwa, bayan kamar sati biyu suka sake jonewa, sai dai basu bari an gane suna tare ba, suna kawancen ne kawai daga islamiya sai school, a cikin unguwa basu taɓa nuna kamar sun san juna, ko sannu basu yi wa juna. A haka suka cigaba da yin rayuwa har lokacin da aka zo neman auren Hauwa, wani bakano da ya zo biki a garin Kaduna, a unguwar su Maman Zainab ɗin za'a ɗauki amaryar a kaita Kano, so Hauwa tana cikin kawayen amarya, a nan dai suka haɗu da mijin nata har ta kawo shi gida, aka yi abin da za'ayi, a lokacin mijin nata yana ji da ɗan dukiyarsa dai'dai gwargwado, shiyasa ta yarda ta amince ta aure shi ya tafi da ita Kano, amma a lokacin sun kammala secondary sai dai babu abin da Hauwa kam ta iya in ba satar amsar ƴa'ƴan jama'a ba, dama ita fa ba karatu take zuwa ba, yawon neman samari take fita ato, kuɗin makarantar ma daman yayan mamanta yake biya mata ba bappan nata da ya riƙeta ba, shi yaransa ai basa makaranta, Hauwar ce kawai ta shiga makaranta a cikinsu. In short bayan aure Hauwa da kamar wata biyar baban Zainab ya zo wajen wani abokinsa a Kaduna, a hanya suka haɗu da maman Zainab ta je wajen kanwar mamarta tana dawowa, ta tsaya a bakin hanya zata nemi abin hawa dan ta dawo gida, a nan ya ganta, sai dai bai tare ta a hanya ba, ya bi bayanta shi da abokin nasa, abokin nasa yana da mota, so basu yi mata magana ba ta hau abin hawa suka bi bayanta har sai da ta shiga gida. Da ta shiga gida sai suka yi sallama da babanta, Sadiq baya nan lokacin sai Hajiyarsu ta sanya katuwar hijabi ta fito, a takaice suka faɗi abin da ya kawo su, ganin irin abin da suka yi yasa Hajiyar tasu ta fahimci lallai lallai baban Zainab yana da hankali da kuma ilimi, kuma ya cancanci a bashi aure, saboda alama ya nuna shi ba wasa ya zo yi ba, da wasa ne ba zai nemi gidansu ko iyayenta ba, ita kai tsaye zai tara, amma ya biyota gida, bayan ya biyota gidan ma bai dakatar da ita ba ya nemi ganin babanta, lallai ba shakka yana da hankali sosai. Hakan yasa ta ce mashi ya yi hakuri ya dawo gobe, dama a ranar zai koma Kano, ai kuwa ya ce ina kwana Kaduna ta kara kama shi, kun san kanawa da son fararen mata (😅) ya kuwa ce dole ya jira amsar Hajiyarsu. Ita kuwa ta ce mashi haka ne dan tana son su yi maganar da ƴaƴan nata barema Sadiq da yake da hankali sosai, ƙaramin yaro ne a lokacin amma akwai hankalin manya sosai kamar wan da ya girma a cikin dattijawa. In takaice maku labari wannan shi ne sanadiyar aure baban Zainab da maman Zainab bayan anyi bincike da komai da komai. Baban Zainab ya sha jigila tsakanin Kano da Kaduna yana zuwa hira. Lokacin da aka yi auren su maman Haidar kamar su cinyeta saboda so, ko kwatancen haske fata suke yi a magana to da nata fatar suke kwatantawa, suna bala'in sonta barema Hajiyarsu da ta ɗauketa kamar ƴarta, suna zaman lafiya da kaunar juna haɗe da girmama juna, ganin mutuncin juna. Rana tsaka kawai Maman Zainab da jajuɓowa kanta wahala ta nemo number Hauwa ta hannun wata kawarsu ta Islamiya, ta kirata ta sanar da ita ai ita ma a Kano ta yi aure, yadda kuka san Hauwa ta shanye mata kurwa. Haba Hauwa kam bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen karɓar address ta ce gobe gata nan zuwa. Wannan shi ne musabbabin sake haɗuwarsu a Kano, suka cigaba da kawance, Hajiyarsu maman Zainab bata sani ba, Sadiq bakinciki ta isheshi kamar ya kashe Hauwa, amma haka ya danne, kuma bai gayawa Hajiyar tasu ba, dan shi tun ainahi ba mutun ne mai faɗar duk abin da ya gani ba, baya son gutsiri tsomi, yana da kawar da kai a kan abubuwa ba komai yake nacewa ba. Lokacin da baban Zainab ya sanya Sadiq ɗin a school daga nan ne Hauwa ta fara jin wani iri a ranta, dan kuwa mijinta ko naira baya bawa kannenta, zasu taso daga Kaduna su zo wajenta ko kuɗin motar komawa baya basu, ta yi mashi ƙorafi har ta gaji ta hakura. Baban Zainab tun da suka yi aure da maman Zainab arzikinsa sai kara bunƙasa yake yi, da farko ƙaramin makaranta ya sanya Sadiq, daga baya ya ɗauko Haidar ya haɗasu. Bayan an haifi Khadija da Zainab ya canza masu Sadiq ɗin makaranta zuwa ta ƴaƴan masu kuɗi, nan fa Hauwa hankalinta ya tashi, abinku da mai kwaɗayi, mai hali baya fasawa, ga maman Zainab da iya bata labarin abin kyautatawa da baban Zainab yake yi masu sannan yake turawa Hajiyarsu ma Kaduna. Hauwa zuciya ta yi bakinkirin kamar gawayi saboda haushi ita ba'ayi mata mai kyau ma bare ayi wa danginta. Ita kuwa maman Zainab tana gaya mata wai dan ta tayata murna ta samu miji na gari, bata san hasada take yi mata ba. A haka dai suka cigaba da tafiya, Hauwa fa taga ba zata iya jurewa ba hasada zai kasheta, nan ta bazama ta fara nemanwa kanta mafita, to a wannan gaɓar ne ta haɗu da wata kawar banza ta jefata bin bokaye, farkon abin da ta fara yi ta mallake mijinta ta rufewa danginsa baki a kanta. Tana mallakesa ta fara kwasan kuɗinsa ta shiga harkar dillanci, duk tana rame tana bushe, Maman Zainab kuwa ko'ina a cike ɓul ɓul gwanin sha'awa. Bayan ta kwashi kuɗinsa ta bi sahun dillalai sai ta sake kwasan dubu ɗari biyu nasa ta koma wajen boka dan a shiga tsakanin maman Zainab da dangin mijinta da mijin nata gabaɗaya, a lokacin asirin ya ki kama baban Zainab, sai dai su maman Haidar, ta raba maman Zainab ɗin da dangin mijin nata, su maman Haidar suka dawo basu kaunarta, su da a baya kamar su cinyeta saboda so, amma suka zama basu kaunar ganinta sam sam, aka rasa daga ina matsalar take, ashe Hauwa ce ta hassasa komai. Wannan shi ne farkon shiga matsalar maman Zainab kenan a rayuwarta, amma ta cigaba da hakuri har duk abin da ya faru ya faru. A takaice kenan abubuwan da suka faru a baya, nasan zaku fahimta duk da in short na baku labarin, idan zaku lura a rubutuna ban cika tsawaita bada labarin baya ba, zan dai yi maku yadda zaku fahimta, amma bana son dogon labari a kan abin da ya wuce, ayi wanda ake yi a yanzu, dan ban son ɓata lokaci. Coz yanzu nasan kun fahimci labarin maman Zainab ko?. To maganar da zan yi a nan shi ne, abin da ma yasa na kawo tarihin maman Zainab a nan shi ne dan na baku darasi mai girma, ku sani ita uwa ba'a bijire umarninta matuƙar bai saɓawa Allah ba, uwa ta wuci wasa, ta wuci tunanin mutun, duk lokacin da kika bijire maganar iyayenki to ko bajima ko ba daɗe sai kinga ba dai'dai ba, mahaifiyarki ba zata taɓa hanaki yin abu haka kawai dan ra'ayin kanta ba, saboda duk duniya babu wanda ya kaita kaunar taga farincikin ƴaƴanta, dan haka duk abin da zata haneki da shi ki daure ki hakura, gaba zaki gane illar abin da yasa ta hanaki wannan abin, abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba, to dan Allah idan mama ta ce abari a bari ɗin shi ne yafi. Da maman Zainab ta rabu da Hauwa tun lokacin da mamarta ta umarceta da duk abin da ya faru da ita bai faru ba, amma taki wai ita a dole tana da wayo ta yi wa mama wayo suna ƙawance da Hauwa a ɓoye. Ta manta da cewa zata iya yi wa mama wayo amma ba'a yi wa Allah wayo, Allah ba abin wasa ba ne! Wane ɗan adam ya ce zai yi wa Allah wayo! Daga ƙarshe dai rashin jin maganar mahaifiya ya jefata duk cikin wannan bala'in da ta shiga, yanzu ga shi tana danasani maras amfani!!.......... My people's mu gyara halalenmu, mu bi iyayenmu sau da kafa dan samun ribatuwar duniya da lahira, wani lokaci ki na ɗaukar maganar mamarki ai karamar magana ce ba wata babba ba bari ki shareta kawai, wlh babu karamar kalma a maganar uwa, duk abin da zai fita daga bakinta babbar kalmace da garinku ya yi kaɗan ya ɗauketa idan za'a mai da kalmar dutse, dan haka ki lura da komai ƙanƙantar maganar mama kada ki yi wasa da shi, dan kuwa maganar mahaifiya yana bin bawa har tsufa, Mama ta wuci wasa, ina faɗa ina karawa, a kula sosai. Kun dai ga maman Zainab dai ta bijire maganar Mama ta kare a prison tare da tarin uban danasani maras amfani! Allah ka kiyashemu yin danasani, Allah kasa mufi karfin zuƙatanku. Yanzu mu koma kan labarinmu, dan gidansu Zainab akwai tarin darusan rayuwa sosai, kuma duk abin da yake faruwa a cikin gidan abu ne wanda yake faruwa a cikinmu sosai da sosai, labarin kamar true life story nake jinsa a rai'na, fata na dai ƴan uwana mata zaku ɗauki darasi domin gyara, waɗan da irin haka ya faru da su sai dai muce Allah ya kiyaye gaba, waɗan da kuma bai faru da su ba sai ku ɗauki alluran rigakafi daga rayuwar maman Zainab, a rashin jinta ta cuci harda rayuwar ƴaƴanta gabaɗaya!. Ni yanzu damuwata ma ko ina Khadija?......😥💔 STORY🔥❤️ Sadiq dai shi yake jinyar Zainab a hospital, yarinyar ba um bare um'um, shiru, sai waɗan nan dara daran idanun nata da suka kara girma saboda rama take bin mutun da su (Amanar Jehan, Leesharh, Ummu Sudais, Maman Sultan, Sumayya, Daughter in low, Adama, babyn Oumma, Oumu Amjad, Zubaida Abdullahi, Zaituna, Shafa'atu Adam, Princess, Meerah, Maryamcy, wlh sunan ma ba zasu ƙirgu na, da dai sauranku dukka yau ku tashi kai'na da ruwan commenters, kamar yadda na sanyaku hawaye a page ɗin nan ni kuma ku sanyani dariya na gaya maku😅 maman Sultan Allah ya jiƙan Sweetie na gaya maki💔😥🥳 Maltina mai sanyi yana jirana🥱👋) 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 Sadiq dai shi yake jinyar Zainab a hospital, yarinyar ba um bare um'um, shiru, sai waɗan nan dara daran idanun nata da suka kara girma saboda uban rama take bin mutun da su..................., kome Sadiq zai ce mata sai dai ta bishi da ido kawai, duk ta rame ta zama abin tausayi, kamar ba Zeezeen babanta ba, ta yi wani haske fau kamar bata da jini a jikinta. Ita kaɗai tasan raɗaɗin da yake cikin zuciyarta ƴar tahaliƙar nan, azabar da ta yi mata yawa ne ma ya hanata buɗe baki, ta ci kuka har hawayen sun dai'na zuba izuwa yanzu, babban damuwarta shi ne ina Khadija? Ina ta tafi? Yau kwana arba'in da wani abu babu ita babu labarinta, a wani hali take ciki? Wannan shi babban abin da ya fi damunta, gara mata iyayenta ta rigada tasan babanta ya rasu, ya tafi in da ba'a dawowa, yanzu ba zata sake ganinsa ba, wlh har gizo sautin muryarsa yake yi mata a cikin kunne yana faɗin Zeezeena zan kawo maki lemu mai zaki sosai, Zeezeena yau kam lemun nan dukka naki ne ke kaɗai kada ki bawa mamanki ko ɗaya, Zeezeena mu je kasuwa ki zaɓi duk kalar abayar da kikeso kala biyar mu dawo. Duk in ta motsa baiwar Allah sai ta ji sautin muryarsa yana dakar dodan kunnenta, ta rasa ina zata sanya ranta, hakan ne ya jawo mata ciwon kirji, kirjin nata yana tsananta gudun bugu fiye da yadda yake yi saboda tashin hankali. Mamanta kuma ta rigada tasan tana prison, kuma izuwa yanzu ba'a bawa kowa damar zuwa ganinta ba, kome dalilinsu oho? Case ɗin ma kamar akwai ƙullalliya a ƙasa. So tasan maman nata ba lallai ta sake sanyata a idanunta ba tun da ɗaurin rai da rai ne, idanunta sun kasa dai'na ganin face ɗin maman nata ta lokacin da babansu yake tsokanarta yake cewa ya fita kyau hasken fata kawai zata gwada mashi, ta kafe ita kuma a kan lallai ta fishi, har yanzu Zainab tana ganin face ɗin maman tata a idonta cikin wannan yanayin, sai kuma idan tana murmushi babansu ya kawo mata abin da take so. Waɗan nan abubuwa suna neman zautar mata da ƙwaƙwalwa, in da Allah ya taimaketa dai bata magana, da tana magana kam da anji sambatu kala kala, sai dai fa da alama bata cikin hayyacinta sam sam, dan kuwa irin kallon da take yi wa Sadiq abin da mamaki, in ta kafe shi da ido bata ko kyaftawa har sai idan shi yaga kallon ya yi yawa sai ya matsa daga saitin idanun nata, haka kuma zata sake binsa da kallo. Idan ya bata kankana ko lemu haka zata zubawa lemun idanu ta yi ta kallo kamar wadda taga abin da bata taɓa gani ba. Tun abin bai dame shi sosai ba yanzu har ya fara ɗaga mashi hankali sosai da sosai, bawan Allahn sai tausar zuciyarsa yake yi a kan ya yi hakuri zata ji sauki. Duk hakuri da dauriya irin nasa sai da ya zubarwa da Zainab kwallah, ba dan shi namiji bane kuma yana da tawakkali wlh da shi ma ya zube a gadon asibiti irin wannan tsananin tashin hankali, ba ƴar uwa, sannan ba Khadija! Zainab na asibiti! Babu babansu ya iyali ya lilliahi, lokacin guda gidan farinciki ya ruguje ya koma na bakinciki. Har yau ya gagara iya gayawa mahaifiyarsa abin da yake faruwa, kullum idan ta kirasa a waya ta ce ina maman Zainab tana kiranta wayar bata shiga, sai ya yi mata karyar wayar ce ta lallace, in ta ce ya haɗasu a waya sai ya ce yana kasuwa, last week kam ma sai ce mata ya yi ai baban Zainab da maman Zainab ɗin sun yi tafiya zuwa wajen wasu ƴan uwan baban Zainab dake jihar Bauchi. Sam bata yarda da maganarsa ba hakan yasa tasa ayi mata bincike ba tare da saninsa ba, dan tana ji a jikinta ba lafiya ba, uwa kenan, babu kamarki a duniya!!. A ɓangaren neman Khadijan kuwa, Sadiq ɗin ya je station ya fi a kirga, zuwansa na ƙarshen nan ma sai ce mashi wanda case ɗin yake hannunsa ya yi cewa ai ƙasar waje aka fita da Khadija, bata Nigeria, a ranar da aka ɗauketa a ranar aka bar ƙasar nan da ita, dan haka suna cigaba da binciken wace ƙasa aka tafi da ita, ya je ya yi ta tayasu da addu'a kawai. A lokacin ji ya yi tamkar zai haɗiyi zuciya ya mutu, ga shi Zainab bata magana bare ya tambayeta ko akwai abin da ta sani dan gane da Khadija ko zai iya samun damar yin hasashen su waye suka ɗauketa, ya kashe kuɗi tun yana lissafi har ya dai'na, ya shiga damuwa na wuce misali, ko abinci bashi da lokacin ci bare wanka, da kyar yake samu ya yi wanka a rana sau ɗaya, da farko hotel ya kama, daga baya ya haɗa kayansa ya koma tsohon ɗakinsu a tsohon gidansu Khadija ya zauna, bige kwaɗon kofar gidan ya yi ya sayi sabo ya saka. Haidar kuwa sai Allah kaɗai yasan a wace duniya yake yanzu, dan baya garin Kano ganaɗaya. A ɓangaren Hauwa mai bakar kafa kuwa, sai shirye shiryen ta yadda zata fara kwasan dukiyar gabaɗaya ta gudu take yi, tana ta ƙara ingizata su Maman Haidar tana hure masu kunne. _____________________________🔥💘 DUBAI😇 A hankali ya yi ƙasa da kallonsa izuwa kan kafafun nasa. Kwata kwata Leesharh bata cikin hayyacinta saboda marin da ya wanke mata fuska da shi, tana can tana ganin jiri, sai ƙoƙarin faɗuwa ƙasa take yi, sam kunnuwanta sun daina jiyo mata sautin komai. Kasancewar wajen babu wadataccen haske yasa bai iya gane menene ya same shi a kafafunsa ba, ya dai ji raɗaɗin zafi ta ziyarcesa kawai. Ƙoƙarin gano me ya same shi a kafafun nasa ya fara yi ta hanyar sanya hannu a aljihunsa zai ciro wayarsa dan ya kunna light ɗin ta. Dai'dai lokacin Sharifat ta iso wajen, idan baku mance ba dama ta biyo bayan Leesharh ɗin. Ganinsu a tsaye cirko cirko yasa ta ja binki ita ma tana faɗin. "Leesharh meyasa kika tafi kika barni bayan nace ki jirani?". Ina ai Leesharh bata iya jinta, kunnuwanta sun doɗe. "Leesharh lafiya kike kuwa?". Ta sake jefa mata tambayata tare da kwalalo idanunta da kyau dan ta samu damar ganin Leesharh ɗim da kyau. Shi kuwa Obaid sai ƙoƙarin kunna wayarsa ta ya yi switch off ɗinta a wajen walima yake yi. "Obaid meyake faruwa? Me ya haɗaka da Leesharh?" Ta tambaya tare da dawo da kallonta a kansa. A dai'dai wannan lokacin kuma Leesharh ɗin ta fara dawowa cikin hayyacinta. Addu'a ta fara yi a cikin zuciyarta Allah ya kuɓutar da ita daga hannunsu, zuciyarta tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje saboda tsorata na halin da ta shiga. "Leesharh meya haɗaki da Obaid?". Ta yi maganar tare da dawowa kusa da ita ta ɗan riƙonta. Ganin tana dafe da kumatu ne yasa ta sake cewa. "Marinki ya yi ne?". Wannan magana da ta yi a kan kunnen Guyson da ya iso wajen a yanzu ta yi shi, sai sauri yake zubawa zai je wajen Ramish kafin ya fita, bai san cewa already Ramish ya jima da fita ba, wannan stair case da Leesharh ta tsaya a kusa da shi ɗazun da Sharifat ta ce ta jirata a bakin part ɗin nasu hanyar sirrinsu ce na fita part ɗinsu ta kofar baya ba tare da elevator ba kenan, ta nan Ramish ɗin ya fita, da alama ba kowa yake son ya san da fitarsa ba, dama kuma already kun san shi baya yarda da kowa, fitarsa ta wannan kofa hanya yasa suka samu saɓani da Guyson dake shirin komawa ƙasar Tunisia, da Abu Abdussalam ya ki yarda ya barsa ya koma, amma da King Zuhair ya matsa mashi sai ya hakura zai mayar mashi da shi, dan fa ya riƙewa King yara dayawa yaki bashi, kowanne ya ce yana so, shi kaɗai ya tattaresu dukka. "Obaid yanzu sake marin yarinyar nan ka yi? Wai me ta yi maka ne? Meyasa baka sonta? Kafa san wannan hannun naku kai da Omaid kamar na a'dawa yake ga shegen zafi, kun karɓi horo iya horo da ake bawa manyan mutane, kuzo kuna gwada marin ƴar tahalika da bata yi maku komai ba?". Cewar Guyson. Shi duk abin da suke faɗa ma ba ta kansu yake ba, burinsa wayarsa ta karisa kunnuwa ya ga ƙafarsa me ya taka take yi mashi zafi. Sharifat ce ta amsawa Guyson ɗin da cewa. "Dama Yah Guyson ya taɓa marinta ne na ji kace ya sake marinta?". "Kwarai Sharifat, ɗazun ya mareta a wajen grass carpet dake kusa da hall". Ganin suna magana a tsakaninsu yasa Leesharh cikin dabara ta tsugunna ƙasa, a cikin wannan duhu babu tsoro tasa hannunta ta fara laluɓar kwalaben sauri sauri tana tattaresu. Fargaba da faɗuwar gaba saura kaɗan yasa zuciyar ƴar tahaliƙar nan ta buga, sai bada bugun dum dum yake yi, jikinta na kerma, kun san idan mutun yana aikata rashin gaskiya yana kuma tsoron a kama shi haka zaku ga jikinsa har wani kerma yake yi yana tsuma, to da yake ita kamma kun san akwai ta da karfin hali na gasken gaske, in ta sa kai zata yi abu to fa bata jin shakkar kwatantawa koda kuwa tasan ba zata yi nasara ba, irinsu ne wlh idan suka samu karatu mai kyau haɗe da kula ba kananan mutane masu kaifin ƙwaƙwalwa za'ayi ba, akwai ta da jajircewa sosai, ga kaifin ƙwaƙwalwa sai dai kash bata da kaifin hangen nesa, kunsan hangen nesa daban ne da kaifin ƙwaƙwalwa, shi wannan baiwa ne da ba kowa yake da shi ba sai wanda Allah ya zaɓa ya baiwa, zaku iya samun yaro karami mai kaifin hangen nesa irin na manya, za kuma ku iya samun babba mai hankali amma ba hangen nesa. So ita akwai kaifin ƙwaƙwalwa babu hangen nesa sosai, tunaninta ko yaushe a iya yadda take yake, bata tuna makomarta gobe ko anjuma. Ganin ya kunna hasken wayarsa ne yasa ta zabura ta yi wani irin miƙewa tsaye, kai jama'a Leesharh ba dai karfin hali ba, ko da yake tana da gaskiya iyaye ba wasa ba, dole ta ceci ran mahaifinta tun da tana da dama, kuma da alama akwai matuƙar shaƙuwa a tsakaninta da mahaifin nata. Allah yasa da ya kunna hasken wayar kafafunsa kawai ya nufa da hasken ba ta kanta ya bi ba, shiyasa basu ga ta tsugunna ba. Sai magana Guyson da Shafita suke yi mashi dama bai amsa ba, yana kunna hasken wayar a ƙafafunsa suka ga jini jajir da shi na lafiyayyen mutun yana zuba daga ƙafan nasa. Ai a ɗari suka yi kansa suna rige rigen tambayarsa me yake faruwa? Meyasame shi a wajen?. A take suka ruɗe, Guyson har idanunsa sun kawo kwallah, dan fa shi rago ne a fanni ciwo, amma ban da fannin karatu, a fannin karatu guru ne shi ɗin, amma in bashi da lafiya ina ga duk duniya yafi kowa ragonta, kuka yake yi sosai wani lokaci harda haɗawa da cewa shikenan zai mutu ya dai'na kallonsu Yah Ramish, bawan Allah yana kaunarsu sosai. Duk sun ruɗe sai tambayarsa suke yi, ko uppan bai ce masu ba ya sauke yatsun kafafunsa a ƙasa da nufin ya taka izuwa cikin parlourn dan ya zauna kafin su kira Dr Raj a san me ya ji mashi ciwon. Haba tuni Guyson ya sa hannu ya ɗauke shi cak, dan fa bashi da ragonta ta fannin karfi ma, kuna ganinsa haka har gym nasu Ramish yana zuwa kullum safiya, shi dai da ya fara ciwo ne ya zama jariri, sai kuma idan yana son abu wajen ƴan uwan nasa, yauwa to a nan zaku ga shagwaɓa dan su biya mashi buƙatarsa. Cak ya ɗauki Obaid, da yake Obaid ɗin ma yana motsa jiki bashi da wani nauyin kirki. Bai zame da shi ko'ina ba sai part ɗin su Dr Raj. Da gudu Sharifat ta bi bayansu tana ruwan hawaye. Leesharh abin nema ya samu, jiki na kerma ta tsugunna ta hau tattare kwalaben da suka yi saura, dama ɗazun ta tattare wasu, tana yi tana dafe saitin zuciyarta, dan ji take saboda tsabar bugawar da zuciyar take yi mata tamkar zata fasa kashin kirjinta ta fito waje, Allah sarki, wlh ko da iya wannan fargaba da faɗuwar gaba masu nikaf suka barta mutuwa zata yi baiwar Allah. Tattare komai ta yi da sauri ta nufi ɗakinta, tana zuwa ta wuce toilet ta zuba kwalaben a cikin wc sannan ta bishi da ruwa ya tafi. Tana yi ta dawo ɗakinta da gudu kamar wadda wani abin ya biyota, a saman gadonta ta faɗa tare da sake kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yau Allah ya taimaketa ta sha a hannunsu da kyar, ya iyahi ya lillahi, sai dai faɗuwar gaba yana gab da kasheta kuwa. Kuka take wanda duk mai zuciyar imani idan ya jita sai ya tausaya mata, duk wanda ya ji irin kukan nan sai ya san zuciyarta ta zo har wuya. Tana tsaka da wannan kuka ta tsinkayo vibrate na wayarta a kunnenta, ko bata duba ba tasan masu nikaf ne, hakan yasa ta sanya hannunta dukka biyu a kanta tare da fara birgima a saman gadon tamkar wata zararriya, Allah sarki suna neman haukata yarinya, kuka take yi sosai da sosai har tana wani irin shessheka mai matuƙar ban tausayi. Har wayar tata ta katse kira na biyu ya sake shigowa, a ƙage masu nikaf ɗin suke da ta ɗauki wayar su ji cewa ta zuba maganin, ita kuma fargabar ɗaukar kiran take yi dan tsoron abin da zasu sake ce mata kuma. Ta jima a haka tana juyi tana kuka sosai, su kuma sai kiranta suke yi basu fasa ba, almost miss calls 15 suka yi mata. Can kuma ta zabura ta miƙe zaune a tsakiyar gadon, jikinta na tsananta kerma sosai, gashin idanunta sun yi sharkaf da hawaye, saboda birgiman da ta rinƙa yi har ɗan kwalin kanta ya fita, yadda kuka san zararriya haka ta zama. A ɗari ta janyo wayar tata, tsabar yadda jikinta yake kerma da kyar ta iya riƙe wayar. A hanzarce ta yi picking call ɗin da ya shigo yanzu. Voice ɗinta har ya canza saboda kuka, da kyar ta iya furta. "Hello". Daga ɗayan ɓangaren aka ce. "Leesharh lafiya kike kuka? Meyasameki?". Babu komai ta amsa masu da shi. Shiru matar ta ɗan yi kafin ta sake cewa. "Ina kika jefar da wayarki na yi ta kira baki ɗauka ba". A takaice ta ce. "Bana kusa ne ina waje wayar na ɗaki". "Okey kin aiwatar da aikinki ne?". Kai ta gyaɗa kamar tana a gabansu tare da amsa masu da e. Tana ƙoƙarin ce masu ina baban nata su haɗata da shi tun da ta yi masu aikin. Bata kai ga gaya masu hakan ba kawai ta ji diff sun katse kiran, bukatarsu ta biya sun ji ta aiwatar da aikin. Ciro wayar daga kunnenta ta yi ta fara bin screenshot ɗin da jajayen idanun nan nata tana kallo, tunani ta fara yi a kan me hakan yake nufi kenan? Sun kashe waya basu ji uzurinta ba, anya kuwa ba ayar tambaya a kansu?. A ɓangaren su Sharifat kuwa, kai tsaye emagency room dake cikin part na su Ramish suka wuce da Obaid da yake ta faman cewa Guyson ya sauke shi zai iya takawa da kafafunsa, ai shi ba rago bane, dan haka ya sauke shi. Ina ko sauraronsa Guyson ɗin bai yi ba, sai da ya kwantar da shi a saman ɗaya daga cikin katafaren beds dake cikin emergency room ɗin, sannan ya ɗago yana kallon face ɗin. "Sharifat go and call Yah Raj, he has a patient here". Cewar Guyson. Da sauri ta juya ta fice daga room ɗin. Hararar wasa ya wurgawa Obaid tare da faɗin. "Ji wani ɗan bakinka a wajen kamar in saukeka kai jarumi ne, you're not a hero at all, because hero never treat a woman like the way your doing, hero never beat woman's or shout for them, if you're a hero go and fight with strong man not small innocent girl". "Yah Omar stop it, i don't want, am a hero, and who tall you that am fighting with her? Am not her mate, about beating she did a wrong think to me that's why i teach her a lesson". Ya kai karshen maganar yana ɗaure fuska sosai. Cigaba da harararsa Guyson ya yi ba tare da ya yi magana ba, dan yawan magana sam shi ba nasa ba ne, bata a tsarinsa. Dr Raj ne suka shigo a tare da Sharifat cikin sauri, daga shi sai jallabiya a jikinsa, da alama daga masallaci sallar isha ya dawo. Cikin zafin nama ya zo ya kama kafan Obaid ɗin tare da ƙurawa jinin dake zuba ɗin idanu. "What happened to him?". Ya jefa masu tambaya. Guyson ya amsa da suna tsaye a wajen wannan ɗan hanyar kawai sukaga ya haska hasken wayarsa sai jini suka gani a kafar tasa. Tambayarsa Dr Raj ɗin ya sake yi a kan meyasame shi?. Bai ɓoye mashi ba ya gaya mashi gaskiya. Wani irin ɗaure fuska sosai Dr ya yi, rai a matuƙar ɓace ya fara faɗa a kan cewa duk laifin masu aikin gidan ne da basu goge komai yadda ya dace da har za'a sami wani abin da zai ji ma wani ciwo a wannan wajen, gaskiya dole duk wata mai aiki dake cikin gidan yau sai sun karɓi hukunci na gaske ma kuwa, sai faɗa yake yi sosai ya ɓata rai. Shi kuwa Guyson binsu da ido kawai yake yi, yana jin tamkar jikinsa wannan kwalba ta fasa, Sharifat dake tsaye a gefe ne ta fara cewa yayan nata ya yi hakuri. Ransa a ɓace ya fara duba kafan ƙanin nasa. Da gudu Omaid ya faɗo masu cikin ɗakin har yana haki, tun ɗazun yake ta neman Obaid ɗin. Haka Dr Raj ya gyara mashi kafar tasa tare da yi mashi abin da ya dace, sannan ya ce Sharifat ta gayawa Ummie ta tara mashi duk masu aikin gidan nan ta miƙasu ga Discipline master ya basu ajikinsu, dan gobe su ɗauki aikinsu da mahimmanci, shi fa wannan discipline master ɗin wani shirgegen jami'in Special weapons ne, ya kware a iya casa mutane, duk wanda ya yi laifi a ma'aikatan gidan shi ake damkawa ya yi mashi hukunci, duk ma'aikatan gidan suna matuƙar tsoronsa kamar menene, saboda bashi da mutunci, bakin mugu ne, ya iya tabka ba karya, ga wata shegiyar zabgegiyar bulalarsa wadda aka yi ta da fatar macijin mesa, duk in ya hukunta yarinya ko wani ma'aikaci to fa sai wan da aka hukunta ya yi jinya sosai, saboda bulalar bata wasa bace, akwai shiga jiki. Sosai Sharifat ta shiga bashi hakuri a kan ya hakura ayiwa ma'aikatan faɗa dai, ayi masu afuwa na yau kawai. Rai a ɓace Omaid ya ce. "Aunty Sharifat kin san me kike faɗa kuwa? Sakacinsu fa ya ja jinin Obaid ya fita, gaskiya ba zan iya yafe blood na ɗan uwana da ya fita ya tafi a banza ba, i can't, dole a hukuntasu, ai wannan basu san aikinsu bane, wai ma manene suka bari a kan tiles ɗin har ya ji maka ciwo haka Obaid? Kuma a ina ne?". Guyson da yake shiru tun ɗazun ne ya ce. "Yah Raj please and please for give them kamar yadda Sharifat ta nema masu alfarma, and Omaid I don't want to hear your voice here again, ka mun shiru". Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa Omaid ɗin ya wurgawa Guyson ɗin kafin ya ce. "Yah Omar my Obaid fa! Blood ɗin Obaid fa suka zubar mun, am sorry to say i can't for give them wlh". Yana kai ƙarshen maganar ya juya da nufin ya fice daga ɗankin, dan ya lura basu san irin tafarfasar da zuciyarsa take yi mashi a kan zubarwa da ɗan uwansa jini da aka yi ba, da shi suka sanya jininsa ya zuba zai iya yafe masu, amma Obaid gaskiya ba zai iya hakura ba, ransa ya ɓaci sosai, zuciyarsa na ƙuna. Yana juyawa Obaid ɗin ya riƙo hannunsa yana faɗin. "Don't go anywhere my blood, please stay with me". "I want to talk to Abbie ne, zan dawo yanzu, you know i can't stay in other place without you". Da ido suke binsu, Guyson bai sake cewa ko uppan ba, dan yasan a kan Obaid Omaid zai iya haukacewa, shi ma Obaid a kan Omaid ba abin da ba zai iya aikatawa ba, su ɗin kamar chewing gum suke, idan ka taɓa ɗaya ka shiga uku, ɗaya baya hakura ya yafe ɓacin ran ɗaya, sun san kome zasu yi yanzu Omaid ba zai hakura ba, ko da kuwa duka zasu yi mashi bafa zai hakura ba, shi ne yasa kawai suka bishi da ido. Dr Raj da yake ya yi masu farin sani, dan ya fi kowa daga cikin ƴan uwan nasu kai masu ziyara a makaranta, kullum kuma ya je complain kala daban daban malaman makaranta suke bashi a kan waɗan nan ƴan albarka, so sanin su in and out yasa ya ce da Omaid ɗin. "Ba sai ka ɗauki wani mataki ba, just leave the case in my hand, I will handle the case". Juyawa Guyson ya yi ya fice daga ɗakin, da kallo Dr ya bisa, tabbas ya fahimci ransa bai so ba, Obaid kaninsa ne, ba zai zo wani abin ya cutar da shi ba, amma duk da haka bai kamata a hukunta waɗan da basu da laifi ba, a haɗa masu aiki dukka a hukunta a kan haka ai bai dace ba, wasu ai suna aikinsu da kyau. Bin bayan Guyson ɗin Sharifat ta yi da sauri, dan ita ma ta lura ransa ya ɗan ɓaci, Dr Raj kuwa ya tsaya da su Obaid yana kara yi masu nasiha. Sai huci Omaid yake yi shi a dole ba zai hakura ya yafe jinin ɗan uwansa da ya zuba ba. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 After some minutes. Da misalin karfe 8:10pm. Wani irin jiniyace ta fara tashi tun daga farkon shinfiɗaɗɗiyar titin da ta keto har cikin gidan Abu Abdussalam, jiniya ce ta daban, ba kamar yadda suka saba jin jiniyar ba, ta yau yadda kuka san filin yaki suka dinfara, kaki ne kala kala har wajen kala huɗu, dukkansu sun saki jiniya, mitocin jami'ai ne gaba da bayan, a tsakiya kuma familys car's ne. Gudu suke shararawa na gasken gaske tamkar zasu tashi sama. Tun daga nesa suke danna horn tamkar zasu tashi unguwar gabaɗaya. A ɗari securitys dake tsaron gate ɗin suka wangaleta. Yadda suka taho a haukace suna gudu haka suka danna hancin motocin ciki. Leesharh dake kwance a saman bed ɗinta tana aikin kuka ne ta zabura ta miƙe zaune, tun da Allah ya kawota wannan gida bata taɓa jin jiniya irin haka ba, tamkar zasu tashi garin, sannan bata taɓa jin motocin gidan sun shigo a haukace haka ba. Hakan yasa ta diro ƙasa daga saman gadon nata, da gudu ta nufi wajen windown ɗakin nata domin ta leƙa taga su wanene?. Dai'dai lokacin da ta leƙa dai'dai lokacin Bilal ya zo wucewa ta tsakar harabar gidan ɗauke da Ramish a saman shoulder ɗinsa ga jini na zuba kamar an buɗewa ruwa hanya, ko motsi Ramish ɗin baya yi, manya manyan jami'an special weapons uku ne suka takewa Bilal ɗin baya suka nufi cikin gida. Dafe saitin zuciyarta dake barazanar tarwatsewa ta yi da hannu, salati ta fara sakawa tare da tambayar to me ya sami Ramish ɗin kuma? Ya mutu ne?. Babu mai bata amsa, hakan yasa ta yi ƙasaƙe a wajen jiki ba kwari, yadda kuka san wadda aka zarewa laka. Ta ɗauki a kallah 20 mins a wajen tana tsaye, kukan da ta ji yana tinkaro room ɗin nata ne ya dawo da ita daga duniyar da ta afka. Da kyar ta iya janyo kafafunta ta koma wajen bed ɗinta, ta kasa iya zama, zuciyarta ce ke bugawa da sauri da sauri, tsoronta dai kada ace ya mutu, tunani ta fara yi a kan to meyasame shi?. Sharifat ce ta afko cikin ɗakin nata tana kuka wiwiwi hawaye bibbiyu kamar ƙaramar yarinya. Tana zuwa ta faɗa jikin Leesharh tare da ƙara sautin kukan nata. A ruɗe Leesharh ɗin ta ce. "Sharifat lafiya me yake faruwa?". Cikin kuka ta amsa da. "Harbin Yah Ramish da bindiga aka yi, kuma ni ina ganin kamar ya mutu, wayyo yau na shiga uku na, in ya mutu ya zan yi ni kuma?". Buɗe baki ta yi da nufin ta fara rarrashinta kenan Guyson ya faɗo cikin ɗakin yana kiran sunan Sharifat ɗin, sahunta ya biyo, tun daga emergency room yake ta aikin rarrashinta amma taki yin shiru, Ummie ma ta saka baki, amma taki ta yi shiru, gabaɗaya family sun taru a cikin room ɗin, ba wanda bai ce ta yi shiru ba, amma taki ta yi shirun, da suka matsa mata da rarrashin ne ma ta fito ta basu waje. Jin abin da Sharifat ɗin ta ce yasa Leesharh sake shiga tsananin tashin hankali, amsa ɗaya take son sani shi ne ya mutu ko yana raye? Shi ne abin da kawai take son ji. Riƙo hannun Sharifat ɗin Guyson ya yi da nufin su tafi. Yah Rizwan ne ya shigo cikin ɗakin, ya biyo bayanta ne shi ma, hannunta ya riƙo suka fice dan su je su rarrasheta, shi Yah Rizwan sarai yasan Sharifat tana son Ramish, dan in baku manta ba a baya na gaya maku tafi shaƙuwa da shi a kan sauran ƴan uwan nata, Rizwan abokinta ne sosai kamar dai Guyson, so saboda kusanci da suke da shi yasa ya fahimci tana son Ramish, amma bai gaya mata ya gane hakan ba, ya dai rabu da ita tana dakon kauna. Yau dai gabaɗaya hankalin kowa a matuƙar tashe yake, Guyson ma ya sha kuka, da yake shi da Sharifat akwai saurin kuka, Obaid and Omaid kuwa idanunsu a bushe, shi Obaid ma cewa ya yi bari ya je ya yi wanka da kafar ciwon nasa, yaran nan sam sam babu wani tausayin kirki a ransu, abin kirkinsu ɗaya dai shi ne kaunar juna da suke yi, amma kome zai faru zuciyarsu bata karaya sam sam. A haka dai yau gidan ta kwana hankali a matuƙar tashe, kowa yana cikin damuwa, amma King Zuhair bai da kabari, sun ki sanar mashi abin da ya faru. Da Abu Abdussalam, Rizwan, Bilal sai Dr Raj sune suka kasance a tare da Ramish ɗin, sai fama Dr Raj yake yi a kansa dan shawo kan matsalar, Guyson ma ya kasa iya yin barci, sai shige da fice yake yi daga room nasa zuwa wajen ƴan uwan nasa. Ba yadda su Rizwan basu roƙi Abu Abdussalam ba a kan ya yi hakuri ya je ya kwanta dare ya yi, amma ina ya kafe ya ce in sunga ya fita daga ɗakin nan to fa ya san a wani hali Ramish yake ciki, dan yanzu su dukkansu har Dr Raj ɗin basu san a wani mataki yake ba. Sharifat da ta tare a saman dadduma tun karfe 10 sallah take yi tana kuka, addu'a take yi Allah yasa kada ya mutu, bata damu da son jin meyafaru har aka harbesa ba, ita dai burinta kawai ya farka. Ita ma Leesharh ta ji tausayinsa sosai, kuma tasha kuka, duk sai ta ji tamkar ɗan uwanta aka harba, ta shiga damuwa sosai, hakan yasa ta yi mashi addu'a sosai kafin ta kwanta, sai dai ko da ta kwanta bata iya yin barci ba, tunani ya hana ta rintsawa, sai kuka take yi masu nikaf basu haɗata da babanta ba, bama su sake kiran ta ba, tun da suka yanke call ɗin ɗazun, basu cika alkawari ba. A ɓangaren Obaid and Omaid kuwa, suna cikin room ɗinsu dake part na su Ramish ɗin, dama idan sun zo gidan a nan suke zama, ko a jikinsu suka yi shirin kwanciya Obaid kafa ta dai'na zogi, shirin kwanciya abinsu suka yi, dan a cewarsu ai ragonta ne dan an harbi mutun da bindiga su wani tsaya ɗaga hankalinsu, Yah Ramish ai jarumi ne, ba rago bane, sun tabbata da Yah Bilal aka harba haka Yah Ramish ba zai tashi hankalinsa har haka ba, dan shi ɗin jarumi ne baya son harkar ragonta, dan haka su basu ga wani abin ɗaga hankali ba, Allah ne yake riƙe da ransa, idan ya tashi fine, idan ma bai tashi ba fine, kowa ma zai mutu, su basu son shirmen banza, ba zuciyar mata ne a kirazansu ba da zasu tsaya yin kuka ko su hana kansu barci, dakakkun maza suke shiyasa suka yi kwanciyarsu basu sake leƙawa wajen Ramish ɗin ba!. Yo su dama ta ya za'ayi su damu? Kada ku manta suna da tsama tsakaninsu da Ramish ɗin da kuma Mama, duk cikin kingdom of power Ramish ɗin ne kawai yake iya nutsar da su su nutsu, shi ne mai ci masu ƙaniya dai'dai gwargwado, ba wanda suke shakka da tsoro sai shi, shiyasa ba wani kaunarsa suke yi ba, kunga kuwa fin haka ma zasu faɗa, ga maman Ramish ɗin ta sako Mommarsu a gaba, ta takura mata, kunga ai dole su ce su ba ragwaye bane. Amma fa da yake jini ba wasa ba har cikin ransu abin ya yi masu zafi, sun ji babu daɗi, kuma sun ji a ransu da zasu kama wanda ya harbesa tsab zasu kashe banza, yaran nan baka iya gane masu sam sam. Haka suka yi shirin kwanciya suka kwanta abinsu, kafin su yi barci ma sai da suka sha hira tare da cewa gobe da safe zasu bar gidan nan dan basu son wani koke koken da shirmen banza, jibi zasu wuce school, zasu koma gidam King Badeen su ƙarisa shirinsu a can. Obaid ne ya fara yin barci ya bar Omaid, shi kuwa Omaid ɗin har wajen karfe 3 yana latsa waya bai kwanta ba. Washegari da safe, shiryawa sosai suka yi kafin su fito, kai tsaye palace na Abu Abdussalam suka nufa, dan su yi mashi sallama. Sai dai ko da suka je baya nan, hakan yasa suka dawo wajen Ramish. A nan suka sami family gabaɗaya. Allah sarki Sharifat idanu sun kunbura luhu luhu sun yi jajir kamar mai ciwon ido saboda kuka da ta kwana yi, shi ma Guyson idanu sun kumbura saboda kuka da rashin samun barci, yau gabaɗaya kowa da yake cikin gidan Abu Abdussalam sai da yasan ba lafiya, jami'an special weapons sun yi tururuwa zuwa gidan, kaki sun ƙaru a cikin gidan sosai, tamkar ba lafiya ba, sai kai komo manya manyan motocin kaki suke yi, waɗan nan su shigo waɗan nan su fita, babu wanda ya sami damar ganin Ramish ɗin. Harta air force, wato ma'aikatan Bilal sun cika gidan, sai up and down suke yi suna wani muzurai kamar zasu cinye mutun ɗanye, ga su mafiya yawancinsu idanunsu jajir, sannan ga wasu jiga jigan bindigu a hannunsu wanda ko baka yi laifiba ka fito tsakar gidan nan ka gansu sai ka razana ka ruɗe ka rasa ina zaka sanya ranka, idan ma kana da zuciya a kusa yanzun nan zaka haɗiya ka mutu saboda razanar da zaka yi da ganinsu. Yadda kuka san ɓarayi ne suka hauro gidan suka yi ɓarna, sai wani kaiwa suke yi suna komowa haɗe da gyara bindigunsu kamar masu jiran kiris su saki wuta. Abu Abdussalam suka fara gaisarwa kafin su gaida Ummie, sannan suka bi sauran ƴan uwan nasu dukka suka ɗaga masu gaisuwa. Da yake yau kowa yana cikin tashin hankali sama sama suka amsa gaisuwar tasu. Cikin girmamawa suka ce da Abu Abdussalam zasu koma gidan King Badeen dan gobe zasu koma school. Ba musu Abu Abdussalam ya ce okey Rizwan ya rakasu waje yasa a ɗaukesu a cikin motan jami'ai, sannan jami'ai kamar guda 10 su rakasu har gida dan tabbatar da tsaro. Da okey Rizwan ya amsa kafin ya wuce gaba su rufa mashi baya. Kowa dake cikin ɗakin banda Ummie duk suna tsaitsaye ne cirko cirko sun zubawa Ramish dake kwance kamar gawa idanu. Ummie kuma tana zaune a bakin bed ɗin da yake kwance ta tsare shi da kallo, Guyson kam ya kifa kansa a jikin bangon ɗakin yana ruwan hawaye. Kai tsaye Rizwan ya je ya faɗawa securitys dake bakin gate umarnin Abbie, yana gaya masu kuma ya juya izuwa cikin gida, dan suna tsaka da aiki ne. Nan take jami'ai 10 cif kamar yadda minister Abu Abdussalam ya faɗa suka shirya tare da fito da mota har izuwa gabansu in da suƙe tsaye, sannan suka buɗe masu kofar motar a kan su shiga a mayar da su. Obaid ne ya fara ƙoƙarin shiga. Basu kai ga shiga cikin motarba jiniya ya ƙaraɗe ko'ina a cikin gidan. Dakatawa daga shiga suka yi, Obaid ya ce su jira bari yaga su waye kuma suka zo? Ba yadda jami'an suka iya dole su jira, haka suka tsaya cirko cirko suna jiransu, yarana kanana sai sakawa manyan mutane ciwon kai. Wasu daga cikin Jami'an Swat ne suka danno hancin motocinsu guda uku cikin gidan, yau gidan minister ya zamana tamkar filin yake, ko'ina ka juya kaki daban daban ne suke kai komo. Wasu jiga jigan jami'ai guda biyu ne suka fito daga cikin mota ta tsakiya, suna fitowa wasu matasa guda biyu suka fito suma. Damko matasan suka yi suka nufi hanyar discipline room dake cikin gidan ta kusa da apartment na jami'an dake cikin gidan gabaɗaya, a nan ɗakin discipline room ɗin nasu yake, wannan ɗaki wlh da'a kai mutun ciki gwara mashi su harbe shi da bindiga kawai ya mutu ya huta. Wlh idan suka shiga da mutun wannan ɗakin da wuya uwar da ta haife shi ma ta iya ganesa a lokacin da zasu fito da shi. Ɗaki ne katafare gaske, babu kalar nau'in azaba da babu a cikinta, kayan azabtar da bawa birjin suka tara a ciki, ko ɗan'sanda or soja ko dai swat or wani kaki dai idan ya yi laifi, shi da yake da horo a jikinsa ma kuka yake yi idan aka ce a kaisa wannan ɗakin a bashi punishment bare kuma wanda bai da kaki bai da horo a jiki, sam babu imani a wannan ɗakin. Dama tun da motocin suka shigo cikin gidan Obaid and Omaid ɗin suka nufesu dan su ga su wanenen? Su da zasu tafi amma sun tsaya ganin gulma, jami'an da zasu raka sun ɗin kuma sun tsaya kamar wasu tsaƙaguna suna jiransu. Sun zo dai'dai tsakiyar harabar gidan suka ci karo da jami'an swat ɗin guda biyu suna riƙe da mutane guda biyun da suka fito dasu daga cikin motan, sun riƙe masu kunkumin wandunansu kamar dai yadda suke damke criminal. Kallon Omaid Obaid ya yi kafin ya furta. "They looks like a criminals". Jinjina kai Omaid ɗin ya yi alamar e zancen Obaid dutse tamkar wani babban mutun. Ga ƴan rakiyansu a can suna jiransu sun zo yin abin da ba'a aikesu ba. Da sauri Obaid ɗin ya dakatar da jami'an tare da tambayarsu me waɗan nan kuma suka yi? And su waye su?. Cikin girmamawa ɗaya daga cikin jami'an ya buɗe fasasshiyar voice ɗin nan nasa kamar na adawa ya furta. "They're criminals, we're suspect that they are one of those who shot sir Ramish with gun, Sir Bilal told us to bring them home because he cannot go out today". Da sauri suka juyo suka kalli juna kamar abin haɗin baki, zaro idanu suka yi a tare, da alama yaran nan sun saba magana ƴar kurma kurma da ido haɗe da ɗan motsa lips ɗin bakunansu, duk wata kafa ta munafurci sun santa kusfa kusfa, kana zaune ka saki baki zasu yi cinikinka su saidaka ko su haɗama boom da zata yi maka mummunar fashewa ta hanyar yin magana da ido baka sani ba. Haɗa ido kawai suka yi wajen kallon juna, basu furta ko uppan wa junansu ba, amma haka suka sake juyo da kallonsu izuwa kan jami'an, a tare suka kai wa criminal ɗin mutun ɗaya wani irin bahagon naushi a baki, Obaid ta gefen hagu ya naushi shi, shi kuma Omaid ta gefen dama kamar an aikosu. Nan take bakinsa ya fashe hakwara biyu suka fita, da alama hakwaran a mace suke, sun ji busar sigari har sun gaji. Sake kaiwa ɗayan ma naushi suka yi a tare. Tsabar iya mugunta har da naɗe jallabiyar jikinsu zuwa gwigwa zasu fara labta masu duka kamar su aka kawowa su basu horo. Ƙoƙarin janye criminals ɗin jami'an suka yi, aikuwa Obaid ya ce. "Kai ku dakata mu basu a jikinsu tukun nan, yau saboda su ma a gidan nan zamu sake kwana, da safe zanzo in ɗan yi Wrestling a jikinsu ko na 30 mins ne haka, naga sun ruɓe da shaye shaye, ba su da kuzarin da zasu iya jurar azabata na 1h". (Ni kam na ce ko ba su ruɓe bama yaushe zasu juri azabanku? Ai ku wlh ko mai lafiya kuka kama sai abin da hali ya yi, Hmmmm jikokin Akka waye ya ce ba ku ba? Yanzu duk rikicin da kuka rinƙa yi a cikin gida bai isheku ba sai kun karawa wasu ma? Kai my twin's sai shiriyar Allah.) Omaid ne ya amsa da. "Sure, ni ma da safe ina zuwa, kune kuka harbi yayanmu ko? To ku shirya karɓar azabanmu". Wucewa da su jami'an suka yi, amma sai da Obaid ya kara masu naushi ɗaya a ciki. Juyawa suka yi tare da cewa ƴan rakiyan nasu su koma bakin aikinsu su sun fasa komawa yau, sai gobe da sassafe zasu koma bayan sun ci ƙaniyar waɗan can criminals ɗin, daga haka suka wuce cikin gida abinsu, abin nema ya samu, dama ba'a taɓasu ba ma sun iya mugunta bare kuma Allah ya kawo masu mai laifi? Ai shikenan kuma. Tun daren jiya Dr Raj yake fama a kan Ramish amma har yanzu shiru, waya ya yi wa hospital ɗinsa a in da ya ɓuƙaci da a kwararrun Dr's guda biyu and nurses uku su zo gida dan su taya shi aiki, ya dai yi nasarar cire bullet ɗin dukka biyu, amma dai har yanzu bai iya shawo kan matsalar ba, basu ma ta tabbacin Ramish ɗin yana raye ko ya mutu. Tun jiya Dr yake ƙoƙarin gano wani abu, yana zargin kamar a cikin jinin Ramish ɗin da akwai wata kwaya ta ruwa da ya sha kafin faruwar abin, dan tabbas alamu sun nuna jinin jikinsa a gauraye take, hakan tana ɗaya daga cikin dalilan da yasa Dr Raj ɗin ya kasa shawo kan matsalar, dan jinin jikin Ramish ɗin akwai matsala a tattare da ita kuma jinin tayi sanyi over ta yadda Dr ya kasa iya aikinsa, duk wani allura da ya yi mashi jinin taki ƙarɓa sai ta fara ƙoƙarin canza mashi position na aikinsa, kamar jinin matatce.... Tashin sense. Nasan kun ƙagu ku ji me ya faru, to ku saurara, bayan fitansa gida da nufin ya halarci meeting da zai yi shi da ƴan cikin team ɗinsa. Shi da wani jami'in swat mai tuƙa motar tasa kawai suka fita, bai ɗauki wasu jami'ai ba, ya fita shi kaɗai, dan yana tunanin meeting ne na sirrin, a ganinsa babu wanda ya san da batun, kuma kunga babu wanda ya san da batun sai Leesharh da ta yi mashi laɓe sai kuma ƴan uwansa. Yana kan hanyar tafiya ne Bilal ya kirasa a waya, a nan ne yake sanar da Bilal ɗin yana hanyar zuwa guest house ɗinsa domin yin meeting da yaransa kafin su wuce ƙasar Tunisia gobe. Okey Bilal ya amsa mashi da shi tare da ce mashi gashi nan biyo bayansa, daga haka suka yi sallama. Sun ɗan yi tafiya mai nisa tsakaninsa da kiran da Bilal ya yi mashi, kwatsam ba zato ba tsammani wata mota ta tari gaban motarsu, da kyar driver nasa ya iya taka birki, saura kaɗan su yi karo da motan da ta shiga gaban nasu. Jin cewa Ramish ɗin bai yi magana bane yasa drivern bayan ya dai'dai ta nutsuwarsa ya juyo tare da cewa. "Sorry sir". Ya yi saurin ce mashi sorryn ne kuma saboda sun san halin Ramish ɗin yana da zafi, yanzu zai iya hukuntasa a kan haka, dan zai ce tuƙin ganganci ne, ba zai yi la'akari da cewa wata mota ce ta sha gabansu ba, zai hukunta shi ne kawai, shiyasa ya yi saurin cewa sorry. Sai dai ga mamakinsa Ramish ɗin bai amsa mashi ba, yasan cewa dama ba wani amsa masu magana yake yi ba, amma abin ya ɗaure mashi kai yadda suka kusa yin accident kuma bai yi magana ba. Juyowa ga Ramish ɗin da kyau ya yi da nufin ya sake yin magana, sai ji ya yi anyi knocking na glass ɗin motar. Zuge glass ɗin ƙasa ya yi da nufin ya yi magana, dama so yake yi ya gama da Ramish ɗin kafin ya fita ya ci uban koma waye mai wannan mota da ya shiga gabansu, sai ga mai motan ma ya kawo kansa yana yi masu knocking na glass ɗin. A fusace ya zuge glass ɗin, har da ɗaure fuska sosai irin ba wasan nan, dan kudirin cin uban komawaye mai motan ya yi a ransa. Bai kai ga buɗe baki ba sai ganin ya yi mai motan ya sanya mashi bindigar silent gun a kai, cike da bada umarni ya ce ya yi maza ya yi waje. Ramish kuwa yana zaune kaman gunki, yadda kuka san an sassaƙasa a wajen, idanunsa kuma a buɗe garau yana ganin komai, sai dai ko yatsa daga jikinsa ba zai iya motsawa ba, tamkar ba shi ya yi waya da Bilal ba jimawa ba, in short bayan idanun babu wani abin da yake amfani a jikinsa a halin yanzu, sai kallo kawai, ga kuma wayarsa a hannunsa yana kame kam. Ba musu wannan jami'in ya fito, saboda babu bindiga a hannunsa, ita kuma bindiga fa kunsan idan tana waje to umarninta ake bi, dan haka wannan jami'in ya bi umarnin bindigar dake kansa dan dole ya fito daga cikin motar. Sai dai akwai kudirin in ya fito ya samu sarari ya ci uban mai motar ya kwaci bindigar a ransa. Yana fitowa mai motan dake sanye da mask baka a face ɗinsa, ga hand gloves ita ma baka, takalmar kafarsa Booth ce baka, a takaice baka iya ganin komai na jikinsa face ido, ƙara sanya mashi bindigar da kyau ya yi a kai, da alama ya san halin jami'ai zasu yi ƙoƙarin kwatar kansu, sai ya kara sanya mashi bincigar da kyau, abinku da babban gari kuma cikin yankin manyan kai na ƙasar ko'ina shiru tsit, dan dare ne kowa ya wuce gida, dama su manyan nan ba wani fita suke yi ba, suna cikin gida abinsu, to me zasu fita su nema?. Wani irin fito mai motar ya yi sai ga wasu maza guda uku masu irin shigarsa sun fito daga cikin motar tasa. Kai tsaye gidan baya na motar su Ramish ɗin suka buɗe, kamar sun san ba zai iya taɓuka komai ba, da zafinsu suka ɓalle kofar motar. Janyo shi suka yi suka fito da shi, har lokacin idanunsa a buɗe suna kallon komai ba zai dai iya motsawa ba. Fito da shi suka yi da nufin su sanya shi a cikin motarsu su tafi da shi, a dai'dai lokacin Bilal ya iso tare da motar sojoji guda ɗaya, shi baya kasada da rayuwarsa wajen tafiya shi kaɗai, duk in da zai je da ƴan rakiya dan tsaro ba dan tsoro ba, inma sojoji or ƴan'sanda ko kuma jami'ansa wato air force su take mashi baya, baya dai fita shi kaɗai, shi da ma ba farautar rayuwarsa ake yi ba yana kula sosai, amma shi Ramish yasan nemansa ake kamar hauka, yasan da cewa yana da tarin makiya gaba da baya amma sai kuga ya yi fitowansa shi kaɗai, wani lokaci ma da kansa yake jan motar shi kaɗai, ba ya wani damuwa da ƴan rakiya, yana kasada da rayuwansa, sai ya ce shi ba rago bane, zai iya kwatar kansa a koma inane. Isowar su Bilal wajen yasa mutanen suka yi azama tare da kara zafin nama wajen ganin sun tura Ramish ɗin cikin motarsu sun gudu da shi. Ai kuwa drivernsa ya ɗaga murya wajen gayawa su Bilal ɗin abin da yake faruwa. Da farkoma wucewa motocin su Bilal ɗin zasu yi, sai kuma yaga kamar ba gaskiya ake ƙullawa a wajen ba, a matsayinsa na Jami'i sai ya ce su dakata su ga menene yake faruwa a wajen?. Suna dakawata ne mutanen suka fara saurin tura Ramish cikin mota su gudu da shi dan sun ga wasu sun dakata a wajen ga jiniya. Shi kuwa drivern Ramish da yake yasan cewa motar gidansu ne sai ya yi saurin sanar da su da su yi sauri su zo kar waɗan can su tafi da Ramish, Allah sarki bai gama ihun gaya masu ba mai motan da ya sha gaban nasu ya ciro bindiga ya harbesa. Ganin haka yasa Bilal ya ɗauko nasa bindigar tare da fitowa da sauri. Kan kace me sauran da suka ɗauki Ramish ɗin suka sauke shi ƙasa suka ciro nasu bindigar. Musayan wuta suka fara yi Bilal ya harbi ɗaya saura suka gudu, sojojin suka rufa masu baya. Ƙarisowa wajen Bilal ɗin ya yi yana bin Ramish da kallo. A gabansa ya tsugunna yana yi mashi magana, amma bayan wannan ido da yake binsa da kallo bai iya amsawa ba. Ganin hakan yasa Bilal ɗin ya yi tunanin ko dai sun yi mashi wani abin ne? Dan haka sai ya miƙe ya saɓe shi sai saman shoulder ɗinsa. Yana juyawa da shi da nufin ya kaishi cikin motarsa sai suka ji harbi from nowhere, ba kowa aka harba ba kuma face Ramish ɗin, kafin Bilal ya juyo sun ƙara mashi wani harbin, so suke kada wannan dama da suka samu ta ƙubce masu, so suke su kashe shi ta kowacce hali tun da ɗaukarsa su tafi da shi ya gagaresu, harbi biyu suka yi mashi, wannan harbin ya ja hankalin sojojin da suka bi masu motan nan, hakan yasa suka dawo a guje suka bi in da harbin ya fito. Shi kuwa Bilal da karfin hali kai shi cikin mota ya yi, zuciyarsa na tafasa, yana son bin ƴan ta'addan ya kamosu dan yana ganin kamar yaran nasa ba zasu iya kamasu ba, yana son binsu ya kamosu amma ran ɗan uwansa yafi mashi mahimmanci, hakan yasa ya ja motar kawai da wani mahaukacin gudu ya nufi hanyar komawa gida. A lokacin kuma wani daga cikin sojojin ya yi waya gida a kan wasu jami'an su taho akwai matsala, a hanya Bilal ya ci karo da motocin jami'an gidan nasu wajen motoci goma, umarni ya yi masu a kan su juya ba wasu ƴan ta'addan azo a gani bane. Ba musu suka juya suka takewa Bilal ɗin baya suka nufi gida. Wannan shi ne abin da ya faru da Ramish ɗin. To bari mu leƙa wani part ɗin kuma mu ga wani hali suke ciki. Amma kafin nan meyasa suke son kafin su kashe Ramish sai sun kamashi sun kai shi in da suke? Da suka gagara kamashi ɗin ne suka fara yunƙurin kasheshi kada damar ta wucesu, sun fa san kama Ramish yana cikin hayyacinsa ba abu bane mai yuwuwa ina ga shiyasa suka ɓullo mashi ta wata hanyar, to fatana dai ni kam Allah yasa RAMISH ɗin yana raye, bari mu leƙa wani part ɗin dai mu gani. _________________________________🔥💘 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E______________13 and 14 FOREST😇 Mamma ta shiga tashin hankali da damuwa sosai na ganin halin da Kamran ya shiga, yau tsawon kwana bakwai kenan ya ki ya yarda ya ci komai, tun yana rashin lafiya kaɗan kaɗan har abin tazo ta fi karfin sa, yunwa ba wasa ba, tuni ya fita daga hayyacinsa ga shi da kafiyar bala'in, ya fi mammar tasa iya kafewa a kan abu, komai wuya komai daɗi idan ɗan tahalikin nan ya yi magana baya canzawa, shi burinsa kawai ya mutu ya huta, Allah mun gode maka da kayomu a musulmai, muka taso cikin ni'ima mai girman da babu wanda yake da shi sai musulmai, Alhamdulillah. Mamma fa da taga da gaske Kamran zai yi wa kansa illah, dan a halin da ake ciki yanzu yana zube ne ko magana bayayi, gabaɗaya ya fita hayyacinsa, ga idanunsa a datse gam yaki buɗe su ma bare suyi four eyes da mamman zuciyarsa ta karaya, suna rufe ruf, yanzu fa sai idan mammar ta ɗaga shi ko ta kwantar, duk wani karfi na jikinsa ya kare. Da taga da gaske zai iya mutuwa sai tsoro ya shigeta, ta tsorata sosai ta yadda ta fara nemanwa kanta mafita, tana ganin kamar idan ta kyaleshi ya je nemansu Pretty or mahaifinsa fa to kamar ta sallama shi ne, gani take yi kamar sai dai ta nemi wani ɗan ba dai shi ba, kaunarsa yasa bata son ya fita, tana jin tsoron rabuwa da shi kamar hauka. A kusa da shi ta shigo ta zauna hannunta ɗauke da kayan abinci kamar yadda ta saba kawo mashi, wuka tasa ta yanke igiyar da ta ɗaure shi da shi ɗin. Duk in da ta ɗaure shi wajen igiyar ta shata layi, da yake yana da hasken fata, sai zanen igiyar ta fito ɓaro ɓaro kamar menene, ya yi ba kyan gani, wani wajen kam ma ya ji mashi ciwo har da jini. Ganin yadda igiyar ta lallata mashi jiki ne yasa mammar ta fara nadamar meyasa ta ɗaure shi? Gaskiya bai cancanci irin wannan hukuncin daga garetaba, duk da su ba musulmai bane, a irin renon da ta yi mashi na rashin imani ma duk ya danne ya yi mata biyayya a matsayinta na mahaifiyarsa, abin da mamaki gaskiya, ita kanta ta jinjina mashi sosai, duk yadda ya kai ga kaunar Pretty kuma yana da damar da a lokacin zai iya kwace kansa ya gudu ya je nemanta ɗin, amma bai yi hakan ba, ya daure ya bi mammar tasa dan baya son zuwa ko'ina ba tare da izininta ba. Tuna hakan yasa ta fara tunanin bata kyauta mashi ba, tsawon shekaru yana bin umarninta bai taɓa saɓawa ba, duk abin da ta ce shi yake yi, yanzu ya nuna abin da yake so meyasa ba zata bi ra'ayinsa ba? Ai a yanzu ya kawo karfi, ko ya buƙaci soyayyar mace shi ma ai bai yi laifi ba. Ɗaugo shi ta yi ta zaunar, ya kasa iya zama sai langwaɓewa yake yi yana ƙoƙarin sulalewa ya kwanta against, dan bashi da karfi ko na miskala zarratin. Cikin azama ta jinginasa da jikin bangon dutsen, murya a sanyaye ta fara ƙoƙarin rarrashinsa, dan tasan yana jinta, sai dai bata san cewa baya cikin hayyacinsa ba, kunnuwansa dai suna jin komai. Ta yi magana mai ɗan tsawo ko motsawa daga in da yake bai yi ba bare a sa ran ya ji abin da ta ce. Ganin hakan yasa ta ɗauko tea mai zafi na green tea leaf ta fara ƙoƙarin ɗura mashi, dan tasan yunwa ce ta yi mashi over. Wajen ɗura mashi sai da suka kusa kokawa, dan kuwa baya cikin hayyacinsa, yana jin abu mai zafi a bakinsa ya fara ƙoƙarin furzarwa ya kwaci kansa, bashi da karfi ko kaɗan, hakan yasa Mammar ta danne shi ta fara ɗura mashi da gasken gaske kamar yaro, dan dole ya fara haɗiyewa ba dan ya so ba, ta toshe mashi hanci ne kungakuwa dole ya haɗiye. Sai dai ko da ta samu ya sha ba dayawa ba tana cire cup ɗin ya fara tikar amai kamar zai amayar da ƴaƴan hanjinsa, bata wani damu da hakan ba, dan tasan fin hakan ma zai aikata, ai ya ji yunwa over. Basket ɗin magungunanta na gargajiya ta ɗauko, cikin zafi jini ta fara haɗa mashi magani babu wasa, jikinta har wani irin tsuma yake yi. Haka ta rinƙa ɗura mashi haɗe haɗen nata babu kama hannun yaro, yanzu dai burinta ta ga ya warke ya koma kamar da. In short sai da ta ɗauki kwanaki uku tana ta faman jinyarsa, ta wahala shi ma ya wahala, banda tarin danasani babu wani abin da yake cikin ranta, duk ta shiga damuwa na wuce misali, da kyar da suɗin goshi ta iya samu ta shawo kan matsalar tasa ya dawo daidai. Sai dai kuma ko da ya dawo dai'dai ɗin baya magana, dama can kun san ba yawan magana ne da shi ba, yanzu da ya yi ciwon sai abin ya kara tsananta, abinci ma a baki take bashi, yana karɓa ya ci sai dai baya ce mata ko uppan, abin da yasa yake karɓar abincin ma dan ya ga tashiga damuwa ne sosai, har rama ta yi sosai, yana kaunar mammar tasa sosai, kuma yana yi mata biyayya sosai da sosai, son da yake yi mata ya kai ya iya sadaukar da komai nasa dan ita, hakan yasa ya hakura yake ƙoƙarin cire duk wani tunanin su Pretty a ransa, dan Mamma ita ce duniyarsa, ita ce komai nasa, tun bai san kansa ba take kula da shi fiye da kanta, komai wuyar da zai sha ya gwammaci ya tabbata cikin wannan wuya amma bai saɓa maganarta ko ɗaya ba, ba zai gaji da yi mata biyayya ba, badan ta kula da shi ta rainesa ba yaushe zai girma har ya san da su Pretty a duniya? Da ta yi watsi da rayuwarsa ya makomarsa kenan? So Mamma ita ce gaba da komai kafin sauran abubuwa su biyo baya. Allah sarki, da ni da ku dukka mun san mantawa da su Pretty a rayuwarsa ba abu bane mai yiwuwa, sun zame mashi wani ɓangare na rayuwarsa, zai azabtar da zuciyarsa ne kawai a banza, amma mantawa da su ba abu bane da zai yiwu mashi. Ganin ya kara samun sauki sosai ne yasa ita ma Mamma ta samu sukuni har ta ɗan fara mai da jikinta. Sai dai rashin maganar nan tasa ya dameta sosai, ba um bare uh uhm, ko ta yi mashi magana sai dai ya ɗaga mata gera ko kai, abin yana damunta sosai da sosai. Kamar kullum zaune yake a saman gadonsa ya haɗa kai da gwiwa yana aikin tunani, ba tunanin kowa yake yi ba face na su Pretty and mahaifinsa, yana son sanin wanenen babansa? Wannan itace burinsa a yanzu. Har Mamma ta shigo cikin ɗakin bai ji shigowarta ba yana can yana tunani, kafin ta shigo kuma sai da ta tsaya almost 10 mins a bakin kofa tana kallonsa, ganin bashi da niyar ɗago kai ya kalleta ne yasa ta ƙariso ciki. A bakin bed ɗin ta zauna tare da kai hannu ta ɗan shafi wannan tulin uban gashin kan nasa. Yana jinta amma bai ɗago kai ba, dan kwata kwata baya son motsawa komai ƙanƙantarta daga in da yake, a yadda yake zaunen nan ba ƙaramin daɗin zaman ya ji ba. "Kamran lafiya kake kuwa?" Ta faɗa a sanyaye. Kai kawai ya gyaɗa mata alamar e yana lafiya ba tare da ya ɗago ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa. "Tashi ka je ka yi wanka". Nan ma girgiza mata kai ya yi alamar a'a ba yanzu ba. Wannan hali da yake yi mata na rashin magana sai dai girgiza kai yana matuƙar damunta, sannan halin da yake ciki yana matuƙar ɗaga mata hankali ba kaɗan ba, kawai dannewa take yi. "Kamran meyasa kake mun haka ne? Kasan dai duk abin da zan yi a duniya ina yinsa ne domin kai ko? Domin farincikinka nake yin komai! A takaice ma dominka nake zaune a cikin wannan dajin na tsawon shekaru, meyasa ka kasa gane hakan? Meyasa ka kasa gane cewa uwa tana sadaukar da komai domin ƴaƴanta? Meyasa ka kasa gane cewa uwa ba zata taɓa cutar da ƴaƴan da ta haifa ba? Meyasa a yanzu zuciyarka take ƙoƙarin zaɓar wasu da ka haɗu da su daga baya ka manta da wadda ta haifeka ta sha wahala a kanka? Ni nasan da a ce in ka tafi babu wata haɗari to da ba wanda zai kai ni murnar da ɗaukin ganin cewa ka nemo Prettyn taka, amma ka kasa gane hakan, why my son, why?". Ta dagata da maganar tana mayar da numfashi tare da kura mashi idanu. Ba tare da ya ɗago kan nasa ba ƙasa ƙasa muryarsa bata fita sosai ya fara magana. "Mamma ki bar maganar su Pretty, saboda ke na hakura da su, saboda farincikinki na mance da su, ki sani Mamma kin fiye mun su, kin fiye mun komai a rayuwata, sai da kika kula da ni na girma na zama mutun sannan na haɗu da su, da baki kula da ni ba a ina zan girma har na san su na kaunace su, dan haka ki dai'na zancensu, ki manta da su kawai, ni ma na ciresu a raina....." Kasa ƙarisa maganar ya yi sakamakon kuka da ya kubce mashi mai karfin gaske, Allah ya gani tilastawa zuciyarsa da yake yi a kan ya manta da su Pretty yana cutuwa sosai kuma ba abu bane da zai yiwu gaskiya, kawai dai mahaifiyarsa ta wuci wasa kuma ta wuci tunanin duk wani mai tunani a ransa ne yasa yake ƙoƙarin yi mata wannan sadaukarwan da in ya cigaba da matsawa yana iya rasa ransa. Ita kuwa Mamma tana son ganin farincikin ɗan nata ɗaya tilo a duniya amma kuma fargabar rasa shi yasa ta gwammaci ganinsa a cikin bakinciki. Wani irin tausayinsa ne ya kamata, ita tasan zafin so, kuma tabbas soyayya ta gaskiya kamran yake yi wa Pretty, taga hakan a cikin idanunsa tun ranar, tun da take bata taɓa jin zuciyarta ta karaya ko ta ji tausayin wani abin ba sai yau a kan ɗan nata, musamman yadda ya ce ya hakura da first love ɗinsa yarinyar da yake matuƙar kauna saboda farincikinta, tsabar zuciyarsa na son Prettyn ma da kuka ya kai karshen maganar ya hakura da ita, nan take zuciyarta ta ji in ta yi mashi haka ta rabasu magana ta gaskiya bata yi mashi adalci ba, ta cutar da shi sosai, in dai har zai iya sadaukar da soyayyarsa saboda farincikinta meyasa ita kuma ba zata so ta cika mashi burinsa dan ya yi farinciki ba? Abubuwa nawa ya yi ta sadaukarwa waɗan da yake kauna saboda ita? Ba zasu kirgu ba, ya sha hakura da abu saboda ita, ya sha danne zuciya ya yi mata biyayya koda baya so, meyasa ita yanzu ba zata hakura ta mashi abu ɗayan nan ba? Meyasa?. Haka ta rinƙa faɗa a cikin zuciyarta. Shesshekar kukansa ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. Matsowa kusa da shi ta yi cikin karayar zuciya tare da raunin murya ta fara magana. "Sam ba zaka hakura da Prettynka ba, ka je ka ɗaukota a koma inane, ka dai'na kuka ya isa haka, yau ina maka izinin ka je ka ɗaukota, nasara tana tare da kai my son". Ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka. Sai a lokacin ya ɗago kansa, idanunsa a datse gam, hawaye sun wanke mashi fuska, gefe da gefen kunnensa dukka ya jike sharkaf da gumi, ga kuma wani zufar tana cigaba da tsasstsafo mashi, in ka gansa a haka sai ya baka tausayi sosai, mai saurin kuka ma sai ya zubar mashi da kwallah. Girgiza kai ya shiga yi hawaye na cigaba da gangarowa da gudu daga idanunsa zuwa saman face ɗinsa, tamkar am buɗewa ruwa hanya. Saboda kuka da ya ci karfinsa da kyar ya iya buɗe baki zai yi magana. "Bana da buƙata Mamma, no need, saboda nasan Pretty ta mutu, ta mutu Mamma, nima mutuwa kawai nake son yi a yanzu, dan nasan na rasa Pretty, babu wani amfanin fita nemanta". Yadda yake magana sai ya baka tausayi, yana maganar ne kawai amma babu wani kuzari ko sanyi a muryarsa, bawan Allah ya zama kaman zararre, ga idanu a datse yaki buɗe su. Nisawa ta yi tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta. "Bata mutu ba, kuma ba zata mutu ba, saboda bazaka taɓa faɗuwa ba my son, komai kasa a gaba sai ka yi nasara, kai ɗin jinin nasara ne yake gudu a jikinka, nasara a jininka yake, babu faɗuwa a jininka, mahaifinka bai taɓa faɗuwa ƙasa ba a komai da ya sanya a gaba, mahaifinka wuta ne mai balbali, jarumi ne, daga ni har mahaifinka nasara muka sani kuma a jininmu take, dan haka zaka yi nasara, ka dai'na tunanin faɗuwa, idan ka nuna sarewa da gazawa hakan yana nuni da cewa kai ba jinin damisa bane! Dan damisa bai san sarewa ba!". Wani irin buɗe idanunsa ya yi a ɗari jin cewa yau da bakinta ta ambaci cewa yana da mahaifi! Abin ya ruɗar da shi ya kuma bashi mamaki. Cigaba da magana ta yi. "Ban so na sake yin magana a kan mahaifinka ba a rayuwata, amma yau kasa na yi magana a kansa saboda Pretty, ka je yarona, kaje zaka yi nasara dawo da Pretty, na yarjema kaje ka kawo mun ita nan". Wani irin nisawa ya yi tare da furzar da iska, nan take hawayen dake zarya a saman face ɗinsa suka dakata cak, wani irin wasai ya ji a jikinsa, harshensa da yake ji ta yi mashi nauyi yin magana a ɗazun ne ya ji yanzu ta sake shi wasai, cikin tsantsar ƙaguwa da son jin wanenen mahaifinsa ya ce. "Mamma ki bani labarin babana, and please ki barni na je garesa ko da sau daya ne na gansa da idanuna kinji?". Ɗan daure fuska ta yi kafin ta ce. " kamran ba zan baka labarin babanka a yanzu ba, ni dai Pretty zaka je ka ɗauko mana a yanzu". A take ya riƙo hannayenta a cikin nasa, muryarsa har sarkewa yake yi saboda saurin magana ya furta. "Please Mamma na ji ba zaki bani labarinsa ba, to please ki gaya mun in da yake na je na gansa, na yi maki alkawarin ba zan yin mashi magana ba ganinsa kawai zan yi na dawo". Wani irin canzawa fuskarta ya yi daga annuri izuwa zunzurutun baƙinciki, idanunta a take suka yi jajir, ji take kamar ta fashe da kuka. Amma sai ta danne ta ce. "Shikenan Kamran, zan barka ka je neman nasa, amma ba zan taɓa gaya maka in da yake ba, ka nemosa da kanka, idan har jinin damisa ce take gudu a jikinka to tabbas ba makawa zaka kai kanka in da yake, dan damisa baya sanya kai a waje bai cinma in da yake da burin zuwa ba, dan haka ka kaikanka gare shi". Cike da zumuɗi ya ce. "Mamma ni kuma na yi maki alkawarin tabbas zan kai kaina gare shi, tabbas zan nemo babana". Ya yi maganar tare da sake fuskarsa kamar ba shi yake kuka a yanzu ba, farincikin jin cewa yana da uba kuma Mamma ta bashi izinin isa ga babban nasa yasa ya mance da duk wata ƙunci da yake ciki, Allah sarki iyaye kenan. "Mamma in je in shirya in tafi?". Ya yi maganar yana kallon face ɗinta. Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a kafin ta ce. "Kamran ka nutsu, mahaifinka ba yadda kake tunani yake ba, ya wuci tunaninka, zan barka kaje neman nasa ne ma domin ka matsa mun kuma ina son farincikinka, tabbas nasan zaka iya isa garesa, sai dai kuma kafin na barka ka tafi ina da sharaɗi guda ɗaya". Da sauri ya ce. "Wani irin sharaɗi ne Mamma? Ki faɗi koma menene zan yi na yarda". Nisawa ta yi kafin ta fara magana. "Sharaɗin shi ne zaka yi ɓaddakama, ba zaka tafi a haka ba, ba zaka tafi da kamanninka ba, dan bana son kowa ha ga face naka". "Mamma why to?". Ya faɗa da alamar mamaki a saman face ɗinsa. "Because duk wanda ya san babanka idan ya ganka zai gane cewa kai ɗin ɗansa ne, kuma kaga alkawari muka yi da kai a kan ba zaka bari kowa ya san kai ɗan damisa bane, sannan kuma kusantar hanyar in da babanka yake da ainahin kamanninka ba abu bane mai yiwuwa, dan kafin ma ka kai garesa za'a iya hallakaka, wannan dalilin yasa na ɓoye maka wanenen kai, kuma saboda haka yasa nake koya maka faɗa dan watarana ko bananan ka kwaci kanka a koma inane, nasan da cewa ko ba jima ko ba daɗe mutanen mahaifinka zasu cinmana, in ma su ganmu a tare ko kai ka ɗai, shiyasa na ke koya maka kare kanka da kuma kwatar kanka a koma inane, dan haka dole sai ka yi ɓat da kama idan kana son na yarda ka tafi neman babanka". Shiru ya yi yana jinjina wannan al'amari, Mamma ta gindayar da shi ta kuma ruɗar da shi, shi yarasa to wani irin family ne da shi........ gaskiya nima narasa wani irin rikitarwa ne wannan. "Mamma na yarda da sharaɗinki, amma taya za'ayi na ɓoye kamaninna kuma?". A takaice ta ce. "Kai dai jeka ka yi shirin tafiya ninzan ɓatar maka da kamannin naka". Tana kai karshen maganar ta miƙe da sauri ta bar ɗakin dan bata son yaga hawayen da take ƙoƙarin dannewa. Allah sarki bata son rabuwa da shi, tsawon shekaru 26 kenan yanzu kullum ba dare ba rana suna a tare, bai taɓa matsawa daga kusa da ita ba, duk in da zai je a faɗin dajin nan dai zai dawo wajenta, ba dan su Pretty bama shi baya zuwa ko'ina, bayyanar su Pretty suka koya mashi fita har ya je wajensu ya yi awa ɗaya zuwa biyu. Kuka ne sosai mai karfi ya zo mata, ɗakinta ta shiga ta fara murzan kuka sosai, rabuwar uwa da ɗa babu daɗi ko kaɗan. Shi kuwa tashi ya yi ya fara shiri, har wani karfi ya ji ya zo mashi. Duk wani abin da su Pretty suka bashi sai da ya ɗauka, ya ɗauki wukarsa sannan ya ɗauki al'qura'ani mai girma da Sweetie ta bashi. Ya dai gama shirinsa tsab abinsa bai san cewa Mamma tana can tana kuka ba. Bayan ya kammala duk abin da zai yi ya fito ya nufi in da take. Jin motsin yana nufo wajenta yasa ta yi saurin goge hawayenta tare da fara fito da wasu abubuwa nata dan ta ɓatar mashi da kamanni. Cike da murna ya shigo cikin ɗakin nata, sai zumuɗi yake yi zai je ya duba su Pretty daga nan ya ɗaukesu su je neman babansa, a lissafinsa ba zai iya tafiya ya barsu a dajin ba, zai je ya ɗauki Sweetie ya kawota wajen Mamma ɗin tun da ita bata gani, ita kuma Pretty ya tafi da ita neman babansa.......... Tab da kuwa akwai cakwakiya in dai da Pretty zaka tafi neman baban naka. Zaunar da shi a bakin gadonta ta yi tare da ɗauko abubuwan nata ta fara aikin ɓatar mashi da kamanni. Tas ta yanke mashi dogon gashin kansa saɓanin kullum da take rage mashi tsawon, yau dukka ta yanke, sannan ta aske mashi sajensa ma tas da wani irin ɗan ƙaramin wuƙa na gold mai kama da aska sai kaifin bala'i, tun da yake da ita bai taɓa ganinta da irin waɗan nan abubuwa ba, ko daga ina ta samosu yau kuma? Ya tambayi kansa, gudun kada ya yi mata laifi ta ce ta fasa ya zauna a gida yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai tambayi daga ina ta samo waɗan nan abubuwa ba. Bayan ta aske mashi sajensa sai ta aske gashin gera ma, ta sanya mashi wani irin powder a wajen da ta aske gashin, wlh sai ya canza kamanni gabaɗaya, kun san idan aka cirewa mutun gashin gera yadda yake canzawa kamar ba shi ba. Haka dai ta zage ta canza mashi kamanni, wlh ba zaka taɓa zaton shi bane. Ta ɗauko wani dogon towel da ta saƙa ta naɗa mashi rawani da shi, ya fito kamar irin larabawan ƙasar Iraq ɗin nan, ba zaka taɓa cewa shi bane. Fatan nasara da fatan alkhairi ta yi mashi, sannan ta bashi umarnin tafiya. Duk zumunɗin da yake yi na son tafiya sai ya ji jikinsa ta mutu da ta ce ya tafi, nan take ya ji idanunsa sun cika da kwallah, damuwa ce ta bayyana a saman fuskarsa. Juyowa ya yi suka kalli juna, ganin idanun Mammar tasa ms a cike da kwallah yasa na sa hawayen da suka cika mashi idanu suka fara zubowa. "No Kamran no, kada ka yi kuka, ka tafi kawai, sai dai ina son ka mun alkawarin zaka dawo gareni! Ina zaune ina jiranka". Matsowa ya yi tare da riƙo hannayenta. "Mamma zan dawo gareki, duk wuya duk daɗi zan kasance da tunaninki a duk in da nake, please Mamma kema kada ki yi kuka kin ji?". Hug na juna suka yi, hawayen da take ƙoƙarin dannewa ne suka fara zubo mata, tana jin kamar kada ta barshi ya tafi, dan tana ganin kamar za'a gane shi ɗan cikin damisa ne a kashe shi, tana jin kamar zasu rabu rabuwa ta har abada kenan. Sun jima rungume da juna suna kuka kafin daga karshe ta yi ta maza ta raba jikinsu tare da riƙo hannunsa ta fito da shi waje. A wajen ma tsayawa suka yi tana goge mashi hawaye shi ma yana goge mata nata, da kyar suka iya rabuwa bayan ta bawa Rocky amanarsa. Da gudu ta juya ta koma cikin gida shi kuma ya nufi kasa har lokacin ya ƙasa dai'na kuka, Rocky ya rufa mashi baya suka tafi a tare. Rocky da Kamran akwai amana, wannan rashin lafiya da Kamran ya yi Rocky ma har ƴar rama ya yi, saboda baya fita ya fatauci nama sosai, koda yaushe yana zaune a bakin kogon nasu yana dakon jiran fitowar Kamran ɗin tun da ba halin shiga ciki. Kai tsaye wajensu Pretty ya nufa cike da kaguwa na son ganinsu. TO KAMRAN ALLAH YA TSARE HANYA YA KUMA HAƊAKA DA CIKAN BURINKA NI DAI SHI NE FATANA🥰😇 _____________________________😇❤️‍🔥💫 DARK WORLD😇❤️‍🔥 Saboda kuka da wahalar da ta sha yasa ta yi barci mai nauyi wanda bata farka ba sai can wuraren karfi 9 na dare. Tana farkawa kuma abin mamakin da bata taɓa zato ba a rayuwarta shi ne ta farka idanunta suna gani, tamkar a mafarki ta ji kuma take ganin abin. Tana farkawa kuma da kyakkyawar fuskar Ronnie ta fara cin karo, yana tsaye a gaban gadon nata hannunsa riƙe da wani allura da ya haɗa yake son yi mata, ko alluran menene oho masu, idanunta dai ba aiki suka yi mata suka buɗe mata su ba, su kaɗai suka san me suka yi mata idanun suka buɗe. One thing about Ronnie shi student ne. Har yanzu bai kammala karatu ba, kuma yana zuwa school, sannan yana ɗaya daga jikin ɗaliban likitoci da Dark world suke alfahari da su, yana da kwazo ta fanni karatu sosai, ya kerewa tsaransa. So duk lokacin da yake da class yana zuwa school, suna da babban university da black tiger yasa aka gina masu, ga manya manyan asibitoci da dai sauransu, shi fa black tiger kullum burinsa ƙasarsa ta zamana tana da komai na more rayuwa, ta zama number ɗaya, sai dai akwai ɗan banzan zalinci kuma kamar kafurin farkon zamani. So Ronnie kwararrene a fannin nan na likitanci, riƙe yake da allura zai yi mata. A duniya Sweetie bata da burin da ya wuce idanunta su buɗe ta yi tozali da Kamran, sai ga shi yau sun buɗe ta yi tozali da madarar kyau da ya take na Kamran, sai dai kallon kamar idon sani ta yi wa Ronnie ɗin, ta ji kamar ta sansa. Mamaki da al'ajabi ya hanata motsawa daga in da take kwance, wai yau itace idanunta suka buɗe tana gani? Kai abin da mamaki, Pretty and Kamran ne kawai a cikin tunaninta, sai ayyana yadda zata kalli Kamran take yi, Pretty kam already ta san ya kamanninta yake, Kamran take mararin gani. Shekara bakwai tana tare da Pretty idanunta suna gani, so tasa kamanninta saura Kamra Tuna cewa ga fa in da take yasa idanunta suka ciko da kwallah, zuciyarta na sanar da ita cewa shikenan ba zata sake ganin Pretty and Kamran ba. Kan kace me hawaye sun fara zuba daga idanun nata. Ronnie bai lura da hawayen nata ba bai ma lura da ta farka ba, hankalinsa naa kan wanna kyakkyawar yarinya mai kula da Sweetien da ta shigo yanzu. Jikinta na sanye da wani guntun wandon jeans baki da t-shirt mai laushi pink color wanda ya tsaya mata a iya kunkuminta, ta ɗaure gashin kanta ta zuba jelar a baya, ta bar wani guntun gashi a gaban goshinta wanda ya ƙara mata kyau sosai, fara ce tas amma bata kai Ronnie ba, a gaskiya ma idan tana gabansa za'a iya ce mata bakar fata, dan shi fa koreans ne, jikinsa kamar madara, tas yake. Ƙarisowa kusa da shi yarinyar ta yi, ɗan rungumar juna suka yi irin welcome ɗin nan kafin ya sumbaci kumatunta, ita ma sumbatar nasa lallausan kumatun ta yi. A shekaru wannan yarinya ba zata wuci 12 years ba, sai shegen kyau irin na mutanen cikin Dark world ɗin. "Beb go and bring food for her, ina ga yanzu zata iya farkawa......." Bai kai karshen ba idanunsa suka sauƙa a kanta tana hawaye. A hanzarce ya ce. "Kash beautiful Queen why are you crying? Baki san kuka a yanzu isn't ur own bane? Kina son kuka ya yi affecting na idanun naki su sake rufewa ki daina kallo ne? Please stop this crying because bana son ki dai'na kallo". Ya kai karshen maganar tare da zama a kusa da ita ya ajiye alluran hannunsa a gefe ya hau goge mata kwallah. Juyawa Floria ta yi ta nufi room door ba tare da ta yi magana ba. Shi kuma bayan ya goge mata hawaye ya ɗago ta dan ya ƙara rarrashinta da kyau. A kirjinsa ya mannata yana ce mata sorry, sannan ya ɗauko injection ɗin da ya ajiye a gefen, cikin wannan sanyayyar voice ɗin nasa ya fara yin magana tare da matso da bakinsa dab da kunnenta, dan a hankali ya yi magana. "Bari na yi maki injection a jijiyar hannunki ko?" Ita dai har yanzu gani take yi mafarki fa take yi ba gaskiya ba, gani take yi kamar idan ta farka zata ga idanunta sun rufe, haka yasa ta kafe shi da idanu tana kallonsa, dan ya yi mata mugun kyau, bata son ta yi missing wannan kyau bata gani da kyau ba ta tashi daga mafarki da take zaton shi take yi taga ta koma makauniya. Sosai take ta kallon kyansa bata ce ko uppanba, shi kuma kallon kalar idanunta da suka burge shi yake ta yi, ya ji kamar ta bashi idanun nata ya ƙara kyau kan kyau. Shigowar Floria cikin ɗakin ne yasa Ronnie kawar da kallonsa daga kanta tare da ɗauko alluran ya gyara hannunta da nufin ya yi mata. Tana ta kallon shi ita kuma bata ankara ba bata ji time ɗin da ya ɗaure hannunta ya nemi jijiya ba sai ji ta yi zafin tsira alluran ya ziyarceta. Wani irin ƙanƙanme shi ta yi tare da fasa kuka. Zare injection ɗin ya yi a hankali tare da fara ce mata sorry. Ita kuma Floria ta ɗaura katon glass tray ɗin abincin a saman carpet ta haye saman gadon ita ma. Haɗuwa suka yi ita da Ronnie suka rarrashi Sweetien har sai da suka tabbatar ta yi shiru. Sannan ne Ronnie ya rabata da jikinsa ya sauko ƙasan gadon. "Beb ki kula da ita ta ci abinci sai ta yi wanka ku zo mu je muga wasan su Ovil". Yana gama magana bai jira amsarta ba ya nufi waje. A kowace Daula akwai jarumi da yake gaba da kowa. To a Daular Dark World dai Ronnie ne jarumin da yake cinye duk wata gasar da black Tiger zai sanya, yana da karfi sosai da kuma dabara, ga ilimi, idan suna Wrestling in dai ya shiga shi zai yi nasara, kasancewar suna cikin ɓata ba musulmai bane yasa a duk lokacin da ya yi nasara zai kashe wanda ya faɗin kamar yadda yake a dokance ba tare da ya ji wani ɗar ɗar ba. Kakkaifar wuƙa yake ɗauka ya datsewa wanda ya faɗi ɗin wuya ba tare da tausayi ko makamancinsa ba, sai dai bai cika shiga gasar ba, dama dan ra'ayin kansa yake shiga, sai ranar da yake cikin nishaɗi yake shiga kuma ya yi nasara. Duk ƴan'matan cikin birnin Dark world suna mahaukacin son suga zai yi wasa, suna son ganin wasan sa, domin idan ba'a wasa ba ba sa samun damar ganinsa, baya fita, ko school kaisa ake yi a mota mai tinted, kowa tana santin kyansa kuma tana kaunarsa, sannan suna son ganin wasan sa ne dan suka ga jarumta, jarumin gaske ne wanda yake da karfi. Yana fitowa daga cikin ɗakin suka ci karo da Delisha a kusa da ɗakin ta nufo wajen. Harara ta wurga mashi ba tare da ta ce mashi uppanba. Wani irin ƙayatatcen murmushi ya sakar mata har sai da dimples ɗinsa suka lotsa sannan ya kashe mata ido ɗaya kamar wani tsohon kwarto. Hannunta ya riƙo tare da jawota jikinsa, a kunne ya raɗa mata cewa. "Sarkin faɗa sai ina kuma?". Sake banka mashi harara ta yi, shi ko ya sake sakar mata wani lallausan murmushi, shi fa har daɗi yake ji idan tana wannan hararar tasa, kyau take karawa. "Sake ni in tafi ka ji?'. Ta faɗa a sanyaye kamar ba ita ce mai shegen tsiwa da faɗa ba. "Haba mana beb kafin na sake ki gaya mun in da zaki je tukun nan". Yana magana yana wani lumshe idanu kamar wanda yake cikin yanayi. "Wai kai meyasa a rayuwarka ka cika neman faɗa ne? Yanzu ina ruwanka da in da zanje?". Matso da face ɗinsa dab da tata ya yi kafin ya ce mata. "Saboda haka nake, kuma ai ke da kanki kinsan ni jarumi ne dole na takali faɗa dan nasan zan kare kai'na na kuma kwaci kaina". Cigaba da banka mashi harara ta yi tare da faɗin. "Wajen wannan yarinyar zanje". "Dama ai na sani, kin ɗebo zafinki zaki je ki sauke a kanta ko? To zo mu je ki bani abinci a baki yunwa nake ji ka fin ki dawo ki je ki zalinci ƴar mutane". Yana kai karshen maganar bai bari ta yi magana ba ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa ya nufi downstairs da ita. Shi fa Ronnie idan ba su Delisha dake cikin Daular black Tiger ba baya kula kowa, a waje cikin birnin ɗaukin ganinsa da ido ma kawai suke yi, bege jin zazzaƙar voice nasa suke yi, saboda kowa yasan shi ne mafi kusanci da black Tiger, black tiger yana kaunarsa kamar me, kowa yana son ganinsa da ido, shi kuwa yana nan yana biyewa su Delisha ko a jikinsa, bai ma san ana haukar son ganinsa a cikin birnin ba. Idan ya fita wajen gasa ya zama cikakken jarumi da babu biyunsa a kaf faɗin birnin, idan kuma ya dawo cikin Daular ka gansa tare da su Delisha sai ya zama kamar na mata wanda bai da karfi ko kaɗan haka yake. Ɓangaren su Sweetie kuwa Sosai Floria ta hau lallaɓa Sweetien a kan taci abinci, amma ta kafe a kan ba zata ci ba har sai taga Pretty and Kamran. Da kyar ta iya shawo kanta ta yarda zata ci, sai da ta yi mata karyar gobe da safe za'a kawo mata Pretty and Kamran ɗin nata, sannan ne ta yarda ta ci. Mandi rice Floria ta zuba mata ɗan dai'dai a plate, sannan ta zuba mata watermelon juice a wani haɗaɗɗen kuma tsadadden cup. Ɗan kaɗan ta ci abincin saboda yunwar ta rigada ta yi mata yawa, kaɗan ɗin nan da ta ci ma har wani murɗawa cikinta yake yi saboda yunwar. Bayan ta ci ta sha ne Floria ta ce taje ta yi wanka. Ƙasa iya miƙewa ta yi har sai da ta taimaka mata ta riƙeta. Bayan ta miƙema sai da ta taimaka mata izuwa bakin toilet ɗin. A bakin ta saketa ta juya ta dawo, ta barta da nufin ta ƙarisa shiga cikin toiletɗin, sai kallon ɗakin take yi, komai ya ruɗar da ita, dan Allah yasa tana da nutsuwa sosai ne yasa ta danne tsoronta da kauyancinta haɗe da al'ajabinta tana dai bin ɗakin dakallo, da Pretty ce ai da ta yi masu hauka, dan bata taɓa ganin irin wanna ɗaki ba. A hankali ta ja kafafunta da suka yi mata nauyi ta ƙarisa shiga cikin toilet ɗin. Tsantsar tsoro ne cike fal a cikin ranta, gani take kamar ɗakinma gabaɗaya zai ruguzo mata a kanta, gani take kamar zata faɗi ƙasa ta ƙasa ganewa. Amma dai ta yi jarumtar danne tsoronta. Tana shiga cikin toilet ɗin Tv dake manne a bango yana magana ya haukatata. Ga wata kyakkyawar ƴar tsana dake ta kusa da kofar shigowa wadda take amfani da battery ta yi mata welcome ta hanyar furta hakan da turanci. Ƴar tsanan ƴar babbace da zata kusa kaita tsawo, kawai ta ce mata welcome, unexpected ta ji maganar. Ai a wanna karon tsoron nata yaki dannuwa, da gudun gaske ta juya ta nufo waje tare da kurma ihu wandan sai da ta tsorata Floria tasa ta ta kusa rugawa a guje. Kai tsaye Florian ta nufa tana ihu. Da yake mutanen birnin Dark World ba dai jarumta ba sai Floria ta tsaya tare da tambayarta me ya faru take wannan ihu. Ƙasa yin magana ta yi sai nuna mata toilet da hannu take yi tana kuka. Riƙota ta yi, dan ta fahimci Sweetie fa ƴar kauyece bata san komai ba shiyasa ta tsorata. Hakan yasa ta kama hannunta tana gaya mata ta yi shiru ba komai, haka ta rakata har cikin toilet ɗin. Gane cewa bata san komai bane yasa ta tsaya ta hau nunnuna mata abubuwan da yadda zata yi amfani da su. Ai ina Sweetie ta ce bata san wannan ba, Floria ba zata bar wannan toilet ɗin ta barta ita kaɗai a ciki ba, sai dai ta hakura da yin wankan su fita a tare. Da yake suna son ta yi wankan sai Floria ɗin ta ce to ta yi wankan bari ta jirata. Nan ma kuma sai ta maƙe mata kafaɗa a kan a'a ita ba ta yarda ba, ba zata iya cire kaya a gaban kowa ta yi wanka ba, ko da take makauniya idan Pretty ta rakata wajen da zata yi wanka tafiya take yi ta bata waje, dan haka ita ba zata cire kayanta a gaban Floria ba. Nan ta ta fara sakawa Floria ciwon kai, zata fita ta ce ba haka ba, zata zauna nan ma ta ce ba zata cire kaya a gabanta ba, to wani irin masifa ce wannan?. Dafe kai ta yi tana tunanin ya zata yi da wannan yarinya? Ga shi dai shekarunsu kusan ɗaya, da ƴan watanni ƙalilan Floria zata fita, amma ta kafe ita fa ba zata cire kaya a gabanta ba, abin ya bawa Floria mamaki sosai, dan ita dai tasan a tsakar gida ma mamanta tana yi mata wanka kafin Ronnie ya ɗaukota ya dawo da ita cikin Daular black Tiger, kuma da dawowarta cikin Daular bai wuce 1 year ba, so da girmanta ma a tsakar gida ake yi mata wanka, kowa ya shigo zai ganta kuma ba abin da ya dameta, yau taga sabon salo wajen Sweetie mai kunyar nuna jikinta a gani. Floria fa ba marainiya bace, da mamanta da babanta a raye, kuma suna cikin birnin Dark World, Ronnie ne kawai ya ga ta burgesa ya roƙi alfarman da black Tiger ya sanya a ɗaukota ta dawo cikin Daular da zama, shi ne sanadiyar dawowarta cikin Empire ɗin. Da kyar da suɗin goshi Sweetie ta yarda Floria ta fita ta barta a ciki. A gaggauce ta yi wankar, ruwa ta kwarara kawai, ba wani fitan da ta yi, sam bata yarda ta kunna shower ko wani abin ba, fanfo ta kunna ta tari ruwa a borket ɗin da ta gani a cikin toilet ɗin, ruwan da sanyi haka ta zuba a jikinta daga kai bata surka da na zafi ba, jikinta duk dauɗa, da yake tana tsoro sosai ne yasa ta kwara ruwa bata wanke dauɗar ba ko soso ma bata nema ba. A gurguje ta sanya kayanta ta fito. Sai muzurai take yi, a tsorace take da komai na ɗakin sosai. A zaune saman gadon ta isko Floria, ganinta yasa ta miƙe ta sauƙo ƙasa tana binta da kallo. "Har kin yi wankar?". Ta faɗa tana mai da kallonta kan yatsun kafar Sweetien waɗan da suke dogaye ba sosai ba, ga su farare tas suna kyalli gwanin birgewa, yana yin yatsun nata masu ɗaukar hankali, ita kanta Floria ɗin da take mace sai da ta ji Sweetie ta yi mata, ta tafi da imaninta, a hakan ma wai dan cikin wahala suka taso, da sun samu hutu kamar na wannan Daula ai da anyi kyau na ban mamaki. Ga gashin kanta da yake golden white ta jiƙa shi da ruwa ya kwanto a hayanta wasu sun zubo mata ta gaba, wayyo abin ba'a magana, sai ta ƙara tafiya da imannin mutane, sai ma ta ɗan zaro idanu, wannan gurun wuyar tasu ita da Pretty yana matuƙar ɗaukar hankalin duk wata idanu da zata sauka a kansu, suna rikita mutane sosai. Sweetie hasken fatarta ita da Pretty ya kai na Ronnie ko ma ya ɗan ɗara shi ƙaɗan. A duk cikin birnin Dark world kuma ba wanda ya kai Ronnie ɗin haske, to ku kwatanta ya hasken su Pretty yake kenan a ranku. Katse su Ronnie ya yi ta hanyar shigowa cikin ɗakin. Wani irin faɗuwar gaba ya ji lokacin da ya sauke idanunsa a kanta, tun da yake ganinta a kwance ko a zaune yake ganinta, yanzu dai tana tsaye a kan kafafunta, ga shi gashin kanta a wargaje bata tara shi ba saboda tsoro, ta fito ne kawai a guje dan kada wani abin ya kamata. Yanayin kayan jikinta kuma kayan sakar da Kamran ya basu ne, kun san yadda kayan yake idan baku manta ba, kuma bashi da ɗan'kwali dama. Sosai Ronnie ya zaro idanu yana kallonta, bai taɓa tunanin haka take da kyau ba. Kamo gashin kansa ya yi a in da ya dawo da shi ta gaba yana kallon na kanta. Nata gashin golden white mai matuƙar kyau ga sheki mai daukar idanu, nasa gashin kuma up white ne wanda ya fi nata haske sosai, sai abin ya ƙara burgesa sosai. Dama tun da ya sauke idanunsa a kan nata idanun ya kamu da kaunar idanun nata, sun burgesa idanun sosai har ya ji kamar ya kwacesu. Ita kuma a ruɗe take binsu da kallo while su kuma suna binta da kallon mamaki, ita Floria kallon mamaki na ta yi saurin gama wanka take binta da shi, shi kuma Ronnie kallon mamakin haka take da tsantsar kyau dama yake yi mata. Ƴar karama da ita sai cikar halittar good bye, kamar ita ta bawa kanta su, ga tsokar gurun wuyar nan nata ba'a magana. A hankali ya dawo da kallonsa kan tsala tsalan cinyoyinta dasu da matuƙar ɗaukar hankali, ɓul ɓul da su, ga sket ɗin nata dama ɗan gajere. Ronnie fa ya ruɗe da alama. (Mumcy, Ummu Sudies and Maman Sultan yau dai black Tiger ya yi maku abin arziki ya buɗewa Sweetie idanunta 😇 Allah yasa ba ya buɗe mata bane dan ya tasata a gaba ta kaisu ga Spender 😅😆 idan ta ki tasha bugu hannunsu Davil😂 ina daga gefa🤓) Dukkansu an rasa mai bakin magana a cikinsu, Floria da Ronnie sun shagala da kallonta, ta tafi da imaninsu, ita kuma jira take yi ta ji me zasu sake ce mata......... 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E_____________14 Dukkansu an rasa mai bakin magana a cikinsu, Floris da Ronnie sun shagala da kallonta, ta tafi da imaninsu, ita kuma jira take yi ta ji me zasu sake ce mata. Floris ce ta ƙatsesu da cewa. "Am ki cire kayan jikin nan naki akwai kaya a clothes set dake cikin room glass ɗin can, ki je ki zaɓi wanda kike so sai ki sanya, kayan jikin nan naki sun yi datti ai". Wani irin dogon numfashi Ronnie ya ja tare da sauƙewa a hankali, ko me ya tuna sai ya saki cool murmushin mai wuyar fassaruwa, sannan ya ƙariso in da suke a tsaye. Hannu yasa ya tattarewa Sweetien gashin kanta tare da cewa Floris ta haɗa mashi hair dryer bari ya busarwa da Sweetien gashin kanta. Okey ta amsa mashi da shi tare da ɗauko luxurious dryer ta juna mashi, sannan ta wuce ta ɗaukowa da Sweetien kayan da take ganin sun dace da ita ta kawo mata saman bed ɗin ta ajiye. Kaya ne irin nasu shigar ta wannan birni, sket ce mai bala'in kyau kasarta kamar umbrella launin blue black, sai riga t-shirt mai karamar hannu launin white, a iya west ɗinta rigar ya tsaya mata, shi kuwa sket har ƙasa ya kai mata, ya fito mata da shape ɗinta kamar dai mutanen cikin birnin. A takaice dai Ronnie shi ya busar mata da gashin kanta, ba ƙarya gashin kan nata ya tafi da imaninsa, ta burge shi sosai da sosai, yana busar mata yana shafawa. Ya kuma iya gyaran sosai, dan gashin nata ya yi matuƙar kyau sosai, da ya gama sai ya ciro pil daga nasa kan ya ɗaure mata nata gashin da shi, ta yi kyau sosai. Bayan sun kammaka floris ta taimaka mata ta sanya kayan a jikinta, Ronnie ya riƙo hannunta a kan ta zo su je ganin wasa. Abin mamaki sam bata yi mashi musu ba, ta bi su kawai suka tafi. Tun da suka nufo waje ta saki baki tana kallon hanya, mamaki da al'ajabi sun hanata magana, floris da Ronnie sai hira suke zubawa, ita kuma sai kalle kalle take yi. A haka suka nufi stair case. Nan fa ta ce ba zata hau wannan electric stair case ɗin ba, ya tsoratata sosai, gani take yi kamar zata faɗi. Da dai Ronnie yaga da gaske ta tsorata da ganin stair case ɗin sai ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa suka sauƙo ƙasa. Ita dai ta datse idanunta gam bata son sake ganin komai, dan gabaɗaya gidan tsoro da al'ajabi yake bata. Sai haɗuwa da ƴan'matan da samari suke yi a hanya, kowannensu cikin girmamawa yake gaishe da Ronnie, dan shi ne shugabansu a nan, saboda yafi kusanci da Black Tiger. Ƴan'matan kuwa duk wacce suka haɗu da ita sai ta ɓallawa Floris and Sweetie da ya ɗauko a saman shoulder ɗinsa harara, sai harararsu suke yi, da alama ƙishi suke ji, dan fa kowacce bata da burin da ya wuce ta mallaki zuciyar Ronnien da bai ma san suna yi ba. Kai tsaye wani katafaren waje suka nufa, girman wajen nan ya wuce tunaninku, yanayin tsarin ginin wajen kamar football stadium aka tsara shi, wajajen wasanni daban daban ne a cikin wajen, filin da aka tanada dan zaman al'umma suga wasa an ƙawata wajen da luntsuma luntsuman kujeru masu shegen laushi kamar a gidan gwamnati, kowani kujera kuma akwai wani luxury glass table a gaban kujerun, sun ƙawatu iya ƙawatuwa kamar ba na ƴan kallo bane, yadda kuka san manyan sarakuna aka tanadawa saboda haɗuwarsu, gabaɗaya kujerun launin ash colors ne masu haske. Daga wani ɓangare na musamman a cikin wajen kuwa wasu shegun kujeru ne waɗanda tsarinsu ya fita daban da kowacce sofa dake wajen, daga ganin zaka shaida na musamman ne, suna da yawa a wajen, dukkan kuma one one seaters ne, kai an fa zuba kayan alatu a wajen, ga girman stadium ɗin zai iya kwashe rabi da kwantan mutanen cikin birnin DARK WORLD. Daga ta ɓangaren hagu kuwa waje ne mafi haɗari, wato wajen da ake datse kan duk wanda ya faɗi gasar, shi ma wajen tsabar mugunta irin na Black Tiger har da ƙawata wajen kamar wajen abin kirki ne, sharɓa sharɓan wuƙaƙe masu bala'in kaifi ya tanada a wajen, sannan ga head lock da aka ƙawata shi sosai, waje ne da mutun zai sanya kansa sai a rufe, iya kan nasa kawai wajen da za'a datse zai saka a wajen, daga nan sai mai datsewa ya sanya wuƙa ya cire mashi kan nasa shikenan an kashe shi. Haka suke yi gaban jama'ar birnin ba tausayi bare inami, ba kalmar da black tiger ya tsana irin kalmar faɗuwa, sam baya son wannan kalma, nasara kawai yake so, coz baya haɗa hanya da wanda ya taɓa faɗuwa ma, nasara a jininsa take!!!. Saman waɗan nan kujeru na musamman ɗin Ronnie ya zaunar da Sweetie, a gefenta Floris ta zauna, shi kuma Ronnie ya zauna kusa da Floris ɗin, sai banka masu harara Delisha dake gefe guda take yi, ita ma ta halarci wajen, ji take yi kamar ta shaƙo Sweetien nan ta naɗa mata ɗan banzan duka, ita tun ainahi jininsu bai haɗu ba, ita kuwa Floris tana kaunar Sweetie sosai, tun ganinta da ita na farko ta ji yarinyar ta burgeta ta shiga ranta. Sweetien dai ta yi shiru tana bin uban dubbannin jama'ar da suke cikin wajen da kallo, mamaki ne duk ya bi ya isheta, ga tsoron da ya mamayeta, bata taɓa ganin jama'a haka ba, kunsan Kamran da Pretty sai mum ɗinsu kawai ta sani, to yau dai gata ga jama'ar birnin Dark world!!. Wajen da ƴan wasan zasu yi wasa an ƙawata shi over, sannan wajen a kewaye yake ta yadda zasu yi wasansu cikin aminci, kun dai san yadda wajen ƴan wasan Wrestling yake ai, to haka aka kawata masu nasu wajen ma. Wani irin ihu da fito da jama'ar wajen suka fara yi ne yasa Sweetien yi wani irin razana tana ƙoƙarin guduwa, a garin ƙoƙarinta na miƙewa ta gudu ne idanunta suka sauƙa a kan Devil dake gefenta yana zaune saman nasa sofar. Habawa ai bata san lokacin da ta kurma ihu ba, saboda ba karya Devil ya tsoratata fiye da tunaninku, kun dai san yadda jikin ƴan Wrestling yake ko? Suna cike, damatsan hannun nan nasu kamar zai fashe, ga uban tattoo da suke zanawa a jiki, su tara gashin kai mai tsawo wanda wannan kuma dama al'adar birnin Dark world ne, sannan abu na biyu da ya kara tsorata Sweetien shi ne Devil fuskarsa a turɓune kamar an aiko mashi da cewa uwarsa ta mutu, daga ganin wannan fuska babu imani a tattare da shi, ga idanu manya sai muzurai yake yi, shararren ɗan Wrestling ne wanda shi ne master dake basu horo a kan Wrestling ɗin, shi ya koyar da Ronnie ma, amma shi yanzu baya wasa, dan babu mai yin winning ɗinsa, har yanzu ba'a samu wanda zai iya dokesa ba, shiyasa ya daina shiga wasan yana cigaba da horar da masu tasowa kawai, a yanzu dai Ronnie shi ne zakara a cikin duk ƴan wasan dake cikin empeir ɗin, da yake shi Ronnie yana da siririn jiki kalar nasu na Koreans sai ya zamana shi duk horon Wrestling ɗin da ya samu wajen Devil damatsan hannunsa basu wani cika sosai ba, bai da wani cika, idan ka gansa sai ka yi zaton ba zai iya taɓuka komai ba, sai an haɗu a filli wasa kaga in da yake zubar da maza yana ɗagawa yana wurgi da su kamar yasamu kwalaye. Sannan shi Ronnie bai wani ɓata jikinsa da tattoo sosai kamar na master Devil ba, tattoo ɗan daidai ya zana na zanen bakar damisa, shi kam Devil duk ya zane ko'ina na jikinsa, ganinsa da ido sai ya baka tsoro, ba'a banza Sweetien ta tsorata ba, rashin mutuncinsa ya yi yawa, kowa tsoronsa yake yi a cikin birnin except Ronnie, ga shi kullum cikin wando three cuters and riga mai gajeran hannu yake, duk ya saki damatsan hannu duk tattoo nasu kunama, damisa da sauransu yana kara razana zuƙatan bayin Allah dan iskaci ya yi mashi yawa. Ihun da ta zunduma ya janyo hankalin mutane dayawa a kanta har shi Devil ɗin, idanu suka yo kanta. Da sauri Ronnie ya miƙe ya dawo kusa da ita ta ɗayan bangaren da Master Devil yake kenan. Riƙo hannayenta a cikin nasa ya yi tare da tambayarta lafiya?. Nan take jama'a suka tsareta da ido, sun ga kyau iya kyau, sai suka kasa tantance ita da king of beautyn nasu wato Ronnie ma wanene ya fi kyau?. Ita ma Floris matsawo ta yi suka fara tambayarta me yake faruwa?. Da kyar ta iya ce masu. "I'm afraid". Ta yi maganar kamar zata yi kuka. "I'm here to take care of you, don't be scared of anything, nothing will happen, just watch the game let me watch your beautifull face like television". Cewar Ronnie, ya kai karshen maganar yana ɗan murmushi. Ƙanƙame hannunsa ta yi tana tunanin Kamran and Pretty, zuciyarta tamkar zata fashe saboda tsoro, daga karshe ma kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana cigaba da tunaninta. Shigowar wani ƙaƙƙarfan matashi cikin wajen wasan ne yasa jama'ar wajen suka sake saka fito tare da ihu, wasu suna sakin tafi da hannunsu rap, rap, rap. Matashi ne ƙaƙƙarfa madaki katti, shi ma jikinsa duk zanen tattoo na Black Tiger, chocolate guy ne, jikinsa duk jijiyoyi a tsaitsaye, karfi kam ba'a magana, ga shi kuma kyakkyawa sosai, gashin kansa bai da tsawo sosai, a iya wuya ya tsaya mashi, sannan ya watsa gashin nasa kamar dambun rama bai ɗaure ba. Sai tafi ake yi ana jiran wanda zai iya gwabzawa da shi ya fito. Almost 10 mins da shigowarsa cikin filin kafin wani haɗaɗɗen matashi ya shigo, na gaya maku mutanen birnin Dark world fa ni har yanzu banga mummuna ba, kyawawa ne sosai kamar su suka yi kansu, ga cikar duk wata halinta na mata da maza, abin dai ba'a magana, sai dai kash ba musulmi ko guda ɗaya a cikinsu, dukkansu abu ɗaya suke bautawa, Christian's ne...... Fata na dai Allah ya kawo maku shiriya ku gane gaskiya wata kila zaku daina zalincin da kuke yi, dan musulunci rahmace babba da babu irinta a duniya. Wani irin fito mai sauti Ronnie ya yi shigowan wannan guy na biyun, bayan ya yi fiton ne ya ce da Floris. "Our Oxil ne zai yi winning". Delisha ce ta amsa da cewa. "No Feros ne winner". Har ta yanke hukunci. Harara ya wurga mata da ido tare da cewa zamu gani. Ita dai Sweetie da bata ma san me za'ayi a wajen ba ta kwanta shiru a saman shoulder ɗinsa abinta, bata san wani irin wasa za'a gudanar ba, ita dai tana ta ganin ƙosassu kuma lafiyayyun maza sai tururuwan zuwa wajen suke yi. Ga ƴan'mata ma nan birjin, kowacce tana ta kallon wanda take burin aura. Hannu ƴan wasan suka haɗa suka gaisa da juna, dama a ƙaidar wasan kenan, sai an gaisa an rungumi juna kafin a fara. Suna gaisawa jama'a suka sanya ihu haɗe da fito, kowa ka ɗaga idanu ka kallah a cikin jama'ar zaka gansa da murmushi a face ɗinsa, da alama suna cikin annasuwa, tabbas mutanen birnin nan suka jin daɗin ganin wannan wasa, sai murna suke yi. Master Devil da yake a matsayi commissioner wasannin ne ya miƙe tsaye, yana da tsawo sosai ga faɗi, taku ya fara yi cikin jarumta ya isa cikin tsakiyar filin wasan, Sweetie tana ganin ya miƙe ta ƙara ƙanƙame Ronnie, dama tun ɗazun sai satar kallonsa take yi ya tsoratata ya kuma bata mamaki, bata taɓa ganin mutun irin haka ba a rayuwarta, ko Kamran da yake da damatsan hannu manya saboda horon da Mamma ke bashi bai kai rabin Devil ba, shiyasa ta ruɗe baiwar Allah. Hand gloves na wasan master Devil ya ƙarɓa a waje rappern wasannin, irin hands gloves ɗinsu masu kauri sosai ɗin nan, shi ya karɓa ya sanya masu a hannu tare da ɗaura masu maroon ɗin handkerchief a gaban goshinsu, sannan ya sanya hannu a tsakiyansu ya yi counting from 1 to 10 kafin ya furta start. Yana faɗin hakan ya bar wajen. Wasa aka fara bugawa, mazan nan kowannensu ya zage dantse, bugun juna suke yi babu wasa, kowa yana son ya rayuwa, wannan wasa ce tsakanin mutuwa da rayuwa, duk wanda ya faɗi shikenan ya bar duniya, kuma a haka suke yarda su yi, dama murnarsu suke shiga cikin wasan. Jama'a sai fito suke yi, su dama kun san ƴan karawa abu armashi ne, ai kuwa sai yi suke yi. Wasa ya fara ɗaukar zafi, wasu maza dake zaune a saman nasu sofar sai kace da su ake faɗar, sai wani wuwwurga hannu suke yi, idan ƴan wasan ɗaya ya ɗaga ɗaga zai buga da ƙasa sai kagansu su sanya hannu kamar zasu tare shi, yadda kuka san da su ake yi, ƴan karawa abu armashi wato masu ihu da fitoma suna yin nasu, yanzu almost karfe 11 na dare amma babu alamar zasu je su kwanta su yi barci, ita ma Sweetie yanzu ta ware idanunta tana ganin wannan wasa mai abin al'ajabi a gareta, sai dai kuma tausayi ne cike taf a ranta, dan yadda suke jibgar juna tsakaninsu da Allah sai da idanunta suka kawo kwallah, abin ya ɗaga mata hankali sosai, amma ba yadda zata yi dole ta hakura ta kallah. Wasa ta ɗauki zafi, Feros ya fasawa Oxil baki, nan take Ronnie ya ɓata rai, dan Oxil mutuminsa ne, ita kuwa Delisha murmushi ta fara yi dan ita tana backing na Feros ne, Floris da dama bata bin bayan kowa wasa kawai ta zo gani hankalinta a kwance yake abinta, duk wanda aka daka shi ya sani. Wasa fa ta yi tsamari sosai, Feros ya sake fasawa Oxil hanci, nan fa hankalin masoya Oxil suka tashi, ciki kuma harda Ronnie wanda yake jin kamar ya je ya karɓawa Oxil ɗin, ransa ya ɓaci, shi gani yake naushi ɗaya ya ishe shi ya gama da Feros, faɗi yake yi a ransa in dai Feros ya yi winning ya ja aka kashe Oxil to tabbas next wasa da shi zasu buga ya ɗaukarwa Oxil fansa....... Babbar magana, yau dai ake yinta, wato wasan ma wasu suna shiga ne dan ɗaukar fansan ƴan uwansu kamar dai yadda Ronnie ya kurta a ransa yanzu! E lallai black tiger kafi kowa tara makiya a duniyar nan, dan kai ne silar komai, tab da mutanen birnin nan zasu samu dama ina ga cinyeka ɗanya zasu yi, dan dai kawai ba wanda ya san kai mutun ne ko aljani, amma fa my people's akwai matsala babba a wannan birnin, Allah ka dawwamar da mu a cikin addinin musulunci addinin ni'ima, yo idan ba rashin musulmar zuciya ba zasu yi irin wannan wasa da ransu haka ne? Sun ɗauki rai ba'a bakin komai ba! Allah yasa su samu dai su musulunta ko a rage zalinci kam in ba haka ba akwai babbar matsala. A hankali tausayi yasa Sweetien ta fara kuka da hawayenta, musamman yadda taga sai jibgar Oxil Feros yake yi, abin ya yi matuƙar ɗaga mata hankali, kamar ba jini da tsoka bane a jikunansu, sun zage sai jibgar juna suke yi kamar basu jin zafin jikinsu?. Wani irin naushi da Feros ya kaiwa Oxil ne yasa shi ya yi baya baya yana ƙoƙarin faɗuwa, cikin zafin jini Feros ɗin ya sake binsa da nufin ya ƙarisa shi kawai ya cinye gasar. Rai a matuƙar ɓace Ronnie ya kurma ihu da sunan Oxil ɗin wanda hakan ya yi sanadiyar sanya Oxil ɗin ya farga tare da dawowa cikin hayyacinsa, cikin fusata ya sanya hannusa ya kare naushin da Feros ya kawo mashi, da karfin gaske ya murɗe hannun Feros ɗin baya tare da miƙewa tsaye da kyau ya fara ƙoƙarin kwatar kansa. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya Ronnie ya sauke tare da yin fito da bakinsa, ita dai Sweetie sai kuka take yi ba tare da kowa ya lura da ita ba, duk hankulansu na kan wasa. Ronnie ji yake yi tamkar ya tashi ya taya Oxil faɗar nan, har wani tsuma jikinsa yake yi, sai ciza lallausan laɓɓansa yake yi, shi ala dole bugun da Oxil yake yi wa Feros ta yi mashi kaɗan........... Kash ana ƴan iska a cikin birnin Dark world wlh, kun ji mun Ronnie fisabilillahi my people's wai jibgar da ake yi wa Feros ta yi mashi kaɗan, Allah gamu gareka, Allah ka shirya mutanen birnin nan........😅 An gwabza wasa iya wasa, sun jibgi juna iya jibga, daga karshe Oxil ya yi nasarar kayar da Feros kasa a in da ya kasa tashi har commissionern wasannin wato master Devil ya ƙirga daga ɗaya zuwa goma bai miƙe ba, ya sha jibga ba kaɗan ba, shi ma Oxil ɗin dai da kyar ya sha, da kyar da suɗin goshi ya iya yin galaba, ya ci wuya, shi ma sai ya yi jinyar kansa, dan ya daku. Ganin bai tashi bane yasa commissionern ya kama hannun Oxil tare da ɗagata sama a zuwan shi ya yi nasara. Nan take masoyansa suka fara ihu suna fito kamar zasu tashi wajen. Ronnie har da miƙewa da sauri ya raba Sweetie da jikinsa, cikin sauri ba tare da ya bi ta kanta ba ya wuce ya shiga wajen wasa, rungumar Oxil ɗin ya yi kafin ya sakesa suka fara taka rawa kamar me.......... Ashe dai Ronnie ya iya rawa. Rawa sosai suka taka kamar west ɗinsu zai ɓalle shi da master Devil, da alama master ma yana team na Oxil ne, shi ko Oxil girgiza kai kawai ya tayasu, dan ba zai iya rawa ba, jiki duk ta yi tsami. Kiɗa mai dukan sautin gaske Dj Jack ya sakar masu, ba karya sun taka rawa, suna yi Ronnie yana fito da karfin gaske, da alama wannan winning ɗin da Oxil ya yi fa ya yi masu matuƙar sugar. Suma masoyansa sun takarawan nasarar da ya samu. Sai da suka taka rawansu mai isarsu jama'a suna yi masu fito sannan ne Ronnie ya dawo wajen zamansa, sai a lokacin ya lura da Sweetie ta sha kuka har ta ƙoshi, ɗazun duk bai gani ba hankalinsa na'a kan wasan, burinsa kawai Oxil ɗinsa ya yi nasara. Rarrashin ta ya hau yi tare da tambayar meya sameta me aka yi mata take kuka?. Shi kuwa master umarni ya baiwa wasu jaruman mayaƙa da su ɗauki Feros su sanya shi a wajen da suke datse wuyar wanda ya faɗi wasan wato head lock kenan. Ai kuwa basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen aiwatar da hakan, bayan sun kaisa wajen ne master ya ce Oxil ya je ya ƙarisa aikinsa, Allah sarki Feros da bai gama dawowa cikin hayyacinsa daga dukan da ya sha a hannun Oxil ɗin ba zai bakunci lahira.......Abin ya taɓa mun zuciya sosai. Babu imani bare tausayi Oxil ya ɗaga wuƙa ya datse mashi wuya da ita, habawa sai jini ke feshi kamar fanfo. Fito jama'a suka sanya suna jinjinawa Oxil a zuwan ya yi jarumta ya yi abin kirki. Wani irin azabbabbe kuma razanannen ihu Sweetien ta kurma na ganin ya fillewa ɗan uwansa wuya da wuƙa a gaban dubbannin jama'ar birni kuma sai jinjina mashi suke yi babu wanda ya ce ya yi ba dai'dai ba. Ihu ta kurma saboda razana kan kace me numfashinta ya ɗauke diff, bata taɓa ganin irin wannan bala'i ba a rayuwarta, a kullum fatanta idanunta su buɗe taga Kamran, ga idanun sun buɗe kuma ta fara cin karo da tashin hankalin da ta gwammaci makantarta ma ya fiye mata alkhari. Ganin ta kurma ihu kuma ta sume ne yasa Ronnie ya kalli Floris kafin ya dawo da kallonsa kan Delisha. "Wai me yake damun yarinyar nan ne? Ɗazun na ganta tana kuka, yanzu kuma ta suma, to me aka yi mata?". Ronnie ya tambaya da mamaki a saman face ɗinsa, wato dai shi wannan tashin hankali duk ko a jikinsa, kun ji ma wai tambaya yake yi me aka yi wa Sweetie ta suma?. Allah mai iko. Jama'a sai ihu suke yi suna murna, su kuma team na Feros idanunsu sun yi jajir masu saurin kuka har sun fara yi, abin nasu dai babu tsari sam, ina laifin wanda ya faɗi wasan a bashi horo na mai tsanani, amma a kashe shi abin ya munana, ku duba kuga Feros fa ko dawowa cikin hayyacinsa bai yi ba suka cire mashi wuya, a gaskiya Black Tiger bakin azzalumi ne na karshen kasasheshe, irin wannan zalinci haka, Allah dai ya kawo karshen wannan irin mulki taka ta zalinci, Allah ya kawo wanda zai cire wannan RAWANIN ZALINCI ya ɗaura CROWN OF JUSTICE, PEACEFUL AND FREEDOM. Ganin da gaske ta sume ne yasa Ronnien ya miƙe ya ɗauketa cak, da alama Ronnie shi aka bawa gadin Sweetie, da alama ya roƙin alfarman a barsa ya karɓo Spender daga hannunta cikin sauki, dan yadda yake yi matan nan da biyu, dole akwai abin da suka shirya mata na dabara. Kai tsaye ɗakinta ya mayar da ita, da kansa ya ɗauko ruwa ya yayyafa mata. A haukace baiwar Allah ta farka, ihu take tana faɗin shikenan ya mutu, ya mutu, sun cire mashi kai. Rungumota Ronnien ya yi tare da hawa rarrashinta. Cigaba da sambatunta ta yi da alama ta fita a hayyacinta. A cikin sambatun nata ne ta yi suɓul da baka ta ce. "A irin wannan ɗanyar zalincin da kuka aiwatarwa ne kuke tunanin zan gaya maku in da spender yake har ku mulki duniya? Da kuwa Allah ya kamani, da karshena ba zai taɓa yin kyau ba, tun da ni zan taimaka a azabtar da bayin Allah, wlh ko ina tare da ainahin Spender ba.........." Dakatawa da maganar ta yi sakamakon wani irin azabbabben mari da ta ji saukarsa a ƙuncinta. Ai tuni ta dawo cikin hayyacinta, kwalalo idanu waje ta yi dan taga waye ya mareta, ina idanunta sun ƙasa iya gane mata komai da kowa, face ɗakin empty babu kowa, tabbas ta jita a jikin mutun, amma ta ƙasa iya ganin fuskarsa, kuma ba makancewa ta yi ba, kawai fuskar ne ya ɓacewa ganinta saboda marin da ta sha ɗin. Tsoro iya tsoro ne ya dira a ranta, hawaye kuwa yadda kuka san an buɗewa ruwa hanya haka suke gudu a saman face ɗinta, jikinta nan take ya fara kerma ya kuma ɗau zafi sosai, addu'oi ta fara jerowa wanda ita kanta bata san wasu iri take yi ba, sai a lokacin kuma ta tuna da cewa bata yi sallah ba. Wani irin banko kofar ɗakin da aka yi aka shigo ne yasa ta ƙara tsorata, ji take kamar bugawa zuciyarta zata yi ta mutu kawai. Faɗi take yi a ranta koma me zai faru ko kasheta zasu yi wlh ba zata taɓa gaya masu in da spender yake ba, dan wannan alkawari ta ɗauka, (ta ɗaukawa waye?) a wani ɓangare na zuciyarta kuma addu'a take yi Ubangiji Allah yasa Kamran ya riƙe kayan da suka bashi da amana, Allah kuma yasa kada su kama Kamran ɗin and Pretty, in dai basu kamosu ba, to wlh ba zata gaya masu in da spender yake ba, idan kuma sun kamosu ko dan Pretty dole ta faɗa........... Ni kam nace akwai tashin hankali kenan, wato dama Sweetie tasa abin da suke nema kenan? Tab lallai yarinyar nan ta wuci tunanin mai tunani, gata makauniya, ƴar karama kuma shiru shiru ashe ta san abubuwa da dama! Lallai yau ake yinta kuwa, fatanmu dai shi ne Allah yasa kada su azabtar da ita baiwar Allah, ko me da me ta sani baiwar Allah, tabbas tun da tasan labari a kan Spender ta kuma san da cewa yana da karfi iko na musamman, sannan tasan ana nemansa ruwa a jallo to tabbas da wuya idan bata san tarihinsu ba. Allah dai yasa kada ta ji wahala ta basu spender su cigaba da zalunci, karfin ikon Black Tiger ya ƙaru, yanzu ma yaya bare ya samu Spender?. Tab akwai cakwakiya. Amma ina da tambaya, ya aka yi Sweetien tasan abubuwa da dama Pretty bata sani ba? Ko dai ita ma Prettyn ta sani ne? Waye ya sanar da Sweetien dukka wannan abin?. And meyasa duk yadda da suke da Kamran bata sanar da shi komai dangane da hakan ba? Kuma dai ta yarda da shi sannan tana sonsa! Sannan meyasa kai tsaye mun ɗinsu ta bawa Kamran auren Pretty ba Sweetie da take babba mai hankali da nutsuwa ba? Daga karshe a tsakanin su ukun nan wato Sweetien, Pretty and Kamran a hannun wanenen Spender yake takamaime? Waye yasan hakikanin in da yake? Akwai babban buhun bala'i kam a cikin wannan birnin tab. Ba kowa bace ta banko wannan kofa ta shigo face Delisha, sai wani huci take yi, daga ganin yadda take tafiya zaka fahimci sam bata ƙullo mutunci ba, rashin mutunci ne cike a face nata haɗe da mugunta. Tana zuwa ta fimciko Sweetien daga jikin Ronnie da tun ɗazun da ya zabga mata mari ya kasa motsawa daga in da yake...... Me dalilinsa na zabga mata mari to?. Ya kasa yin wani kataɓus har Delisha ta fincikota tare da janta kamar kayan wanki ta nufi waje da ita. Sai bayan sun fita ne Ronnie ya iya sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin muryar ya furta. "Kin yi kuskure". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya sauko ƙasa daga saman gadon....... To fa ta yi kuskure? Wacece ta yi kuskure? Kuma kuskuren me? Mu je dai zuwa. Waje ya nufa wato ya bi bayan Delishan kenan, da alama duk jikinsa ta yi sanyi, tafiya yake yi kamar wadda aka zarewa laƙa. Kai tsaye sama ya sake haurawa yana tafiya kamar zai faɗi ƙasa............. ___________________________🔥🤍 GIDANSU KHADIJAH.💔😥 Satin Zainab guda a asirbiti tana fama da jinya, yanzu Alhdulillah jiki ya fara kyau, ita kuwa Hauwa da maman Haidar sai cin karensu suke yi babu ɓaɓɓaka. Yau ta kama ranar jumma'a satin baban Zainab bakwai kenan da rasuwa, Hauwa da Maman Haidar suna zaune a parlour suna hira kamar wasu ƙawaye, a yanzu suna shiri sosai, Hauwa ta yi masu mage mai kwanciyar ɗaukar rai, da biyu ta yi shiri da su, akwai abin da take hara ne yasa ta kwantar masu da kai suna zaman lafiya. Hajiyarsu kuma tana cikin ɗaki tana kwance, fama take yi da ciwon zuciya, ga hawan jininta ya taso, so bata da lafiya sosai, ko magana bata iya yi, sai an kwantar sai an tayar, rasuwar baban Zainab ya jefata cikin wani halin da baki ya yi kaɗan ya faɗesa, Hauwa da maman Haidar basu wani damuwa da halin da Hajiyar take ciki, maman Haidar dama sai abin da Hauwa ta ce take yi, shiyasa bata kula da mahaifiyar tasu, kullum maman Hanif ce take zuwa tana jinyarta, a gida likita yake zuwa ya dubata, maman Hanif ita take zuwa ta bata magani da duk abin da ya dace. Har yau Hauwa da Maman Haidar basu nemi Khadija ba, Hajiyarsu kuma bata magana a yanzu bare ta ce ina yaran suke, Maman Hanif kam ta san komai, dan har asibitin da Zainab ɗin take kwance ta je wajen ta dubata yafi sau a ƙirga, yadda aka yi tasan komai kuwa shi ne, tun ranar da suka yi kaca kaca da maman Haidar ta tafi bata sake zuwa gidan ba har sai da Hajiyarsu ta kwanta jinya, a ranar ta zo suka je asibiti dan a lokacin jikin ya tsananta sai suma Hajiyar take yi tana farfaɗowa, shiyasa suka je hospital. Bayan sun je anyi duk gwaje gwajen da zasu yi ne aka basu magunguna haɗi da nurse guda ɗaya suka dawo gidan, a nan ne ta shiga ɗakin su Zainab da nufin ta dubasu, sai bata gansu ba dukkansu biyu. Hankali a tashe ta fito ta tambayi Maman Haidar ina su Khadijah? Maman Haidar ta ce bata sani ba tun da dama ba'a bata ajiyarsu ba. Nan fa ta shiga tashin hankali ta fara tunanin waye zata kira ta tambaya ina suke?. Can sai Sadiq ya faɗo mata cikin tunaninta, shi ne ta nemi numbersa ta kirasa, da farko har ya ɓoye mata gaskiya, daga baya kuma sai ya tuna cewa ita da maman Haidar akwai banbanci, dan haka sai ya gaya mata gaskiyar abin da yake faruwa. Tsabar shiga tashin hankali jikinta har kerma yake yi, nan take ta ce ya bata address na hospital ɗin gata nan zuwa, to kunji yadda aka yi tasan batun ɓatar Khadija da rashin lafiyar Zainab, ita kam maman Haidar ko nemansu ma bata yi ba ita da take da alhakin kula da su ma bare Hauwa gayyar tsoɗi. Sai hira Hauwa da Maman Haidar suke zubawa maman Hanif ta koma gidanta, kamar daga sama suka ga an banko labule an shigo masu cikin parlourn. Saboda sun tsorata miƙewa tsaye suka yi cikin sauri. Ganin Haidar ne yasa mamar tasa ta ce. "Kai lafiyarka zaka shigowa mutane ɗaki babu sallama? Daga ina ma kake ke? Ina ka fito? Yau fa wajen wata biyu ban sanyaka a idanu na ba, ina kaje!". A maimakon ya amsa mata maganar da ta yi ɗin sai ya ce. "Ni mama ba wannan ba, ina Khadijah? Kin san cewa lokacin aurenmu ya yi ko? Satin nan za'a ɗaura auren". "Ina kaje tukun nan? Faɗa mun naji kafin na gaya maka in da Khadijah take". Ɗaure fuska sosai ya yi. "Wani waje na je ni da abokaina da nufin mu yi sati biyu, shi ne muka yi wata biyu, dan wajen ta yi daɗin, to ina Khadija da kawu suke? Kawu ya zo yau idan an sauko daga sallar jumma'a ya ɗaura mana auren kawai". Yana magana kamar yana baiwa mamar tasa umarni. "Haidar maman Zainab ta kashe maka kawunka, Khadija kuma ina jin cewa tana ɗakinsu". Wani irin ihu ya kurma irin na ƴan daban nan, muryarsa ƙato ya ce. "Kutumar ubancan, lallai yau akwai durun uwa, A'isha ce ta kashe kawu? To akan me? Meyayi mata? Tukun nan ma kisan gaske ko ma wasa?". Charap Hauwa ta caɓe zancen da cewa. "Tsabar mugunta ce kawai, ta kasheshi mana shi har lahira". Ta kai karshen maganar tare da fashewa da kukan kinibibi da munafurci. Wani irin kallon rainin wayo ya wurga mata kafin ya ce. "Ke kuma daga ina gayyar soɗi? Kaji munafuka, kina da wani haɗi da kawun ne da zaki tsaya wani ƙaƙalo kukan munafurci? Ke daga ganinki fuskar bakaken munafukai ne da ke, ni mama ki bani amsata me yake faruwa ne?". Cikin bokarewa ya yi maganar babu respect ko kaɗa. Tsit Hauwa ta yi, ta haɗiye kukan gulmarta, dan Haidar dai bata ga alamar mutunci a tattare da shi ba, jahilci cike da kai yanzu zai yi mata mummunar aiki, tasan matasa irinsu sarai, dan haka sai ta kama bakinta ta yi shiru. Mamarsa bata ɓoye mashi komai ba ta zayyana mashi yadda abin ya faru kamar yadda makira Hauwa ta zayyana masu, da karya da gaskiya duk ta kwasa dama ta gaya masu, dan haka ita ma Maman Haidar haka ta kwasa ta gaya mashi. Wani irin buga center table na tsakiyar parlourn ya yi da karfi, cikin fusata da ɗaga murya ya fara zazzaga jajjagen masifa. "Kutumar uban can, wlh in na yarda Allah ya tsinemun, kamar yadda A'isha ta kashe kawu nima sai na kasheta, wai wace shegiya ko shegen ne ma ya kaita kotu? Ai barin mun ita zasu yi na zo na feɗe shegiya, wlh na rantse da Allah sai ta fito daga prison ɗin nan na yi mata yankar rago, su ma su Khadijah ɗin ba barinsu zan yi ba, ƴan iskan banza, su ma mugun iri ne sosai, basu da amfani a cikin al'umma, kashe su shi yafi". Yana kai karshen maganar ya nufi ɗakunan gidan yana tambayar ina su Khadijah zai kashesu dan basu da amfani, ya fasa batun aure. Kun ga kaɗan daga cikin aikin jahilci kenan, Allah da kansa baya hukunta wani da laifin wani, laifin wani baya shafar wani, amma shi Haidar saboda jahilci da ya yi mashi katutu shi ne yake neman su Khadija ya kashe su dan mahaifiyarsu ta yi laifi bisa kuskure. Kai Allah ka buɗa mana ƙwaƙwalwarmu ka bamu ikon neman ilimi ka rabamu da jahilci. Sai kiransa mamarsa take yi a kan yazo kada ya taɓa su Khadija, amma ina ya yi gaba sai faman banke kofofi yake yi yana shiga cikin ɗakuna shi a dole sai ya fito da su ya kashesu. Ganin basu cikin ɗakun nan sai kakarsu dake kwance kamar gawa ne yasa ya fito ya dawo parlourn ya fara tambayar mamar tasa me ya samu kakarsu kuma?. Nan fa ta sake gaya mashi ai saboda mutuwar baban Zainab ne yasa hawan jini da ciwon zuciya suka kamata. Sake haukace masu ya yi yana faɗin ai ga irinta nan, wlh ba zai bar gabaɗaya dangin maman Zainab ba, duk sai ya kashe su kamar shi ne dama ya kawosu duniya. Sai tausarsa mamar tasa take yi, amma ina sai kara haukace masu yake yi, har da wani cewa zai kwashi abokansa su tafi Kaduna su je su farwa maman maman Zainab ɗin su kasheta, sannan ya kashe Sadiq kafin ya san ta yadda zai yi ya fito da maman Zainab daga prison ita ma ya kasheta. Hauwa kam abin nema ya samu, daɗi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, ita gani take yi idan ya kashe mata Khadija and Zainab shikenan ta ci dukiya, ita dai matsalarta abin duniya. Suna tsaka da wannan hayaniya kwatsam ba zato ba tsammani suka ji sallama a bakin kofa. A tare suka kai kallonsu wajen, ba kowa bace face Khadija. Binta da kallo suka fara yi, dama can su basu san bata nan ba, basu san da ta ɓace ba bare su yi mamakin dawowarta, kallon tuhumama suke binta da shi, tuhumanta suke yi a kan ina kuma ta je? Da a tunaninsu ai suna ɗaki basu fitowa sai in zasu girka abin da zasu ci ko makancin haka ne suke fitowa, kuma basu haɗuwa da su ko a kitchen amma basu damu da su san wani hali suke ciki ba bare har su je ɗakinsu su dubasu. Sanye take da doguwar riga abaya maroon color mai matuƙar kyau da tsada, riga ce mai tsadar gaske, takalmar dake kafafunta ma masu tsadar gaske ne, ta yafa gyalen rigar a kanta, hannunta na riƙe da irin school bags ɗin nan mai matukar kyau, bata goya a back ɗinta ba sai ta riƙe a hannunta, ta ƙara kyau ta kuma yi haske sosai, ta yi ƙiba matuƙa, kamar ba Khadija ba, gabaɗaya ta canza. Kanta Haidar ɗin ya yi da nufin ya aiwatar da kudurinsa na kashesu dukka, da sauri mamar tasa ta yi ƙoƙarin riƙesa dan kada ya ɓallo masu ruwa, ba hankali ne da shi ba, kada ya jajumo masu abin da ba zasu iya ba. Hauwa kuwa cewa take Maman Haidar ɗin ta kyalesa ai gaskiya ya faɗa, su Khadijah mugun iri ne, sun tsotsa a nono, dan haka su rabu da shi. Maman kuwa ta ce a'a bata shirya ɗanta ya tafi prison ba, dan haka ita bata yarda ya kashe kowa ba. Kin yarda ya yi shi kuwa, ya kafe sai ya kashe su, marika ya fara kaiwa Khadija ɗin kamar an aikosa, bata ko motsa daga in da take tsaye ba, da alama zuciyarta ya rigada ya bushe, da alama ita ma mutuwar take da muraɗin ta yi. Dukan gaske ya fara kai mata tana tsaye tana kallonsa ko gezau, sai ƙoƙarin riƙesa mamarsa take yi. Kwashe kafafun Khadija ɗin ya yi da nasa kafafun ta zube ƙasa, still dai kallon face ɗinsa take yi ba tare da ta ce mashi ko uppan ba, kuma bata motsa ba, sai dai ruwan hawaye da take yi saboda zafin dukan da yake yi mata. Allah sarki ko daga ina ta dawo? Suwaye suka ɗauketa? Daga dawowa kuma ta hau karɓar dukan mahaukaci Haidar, baiwar Allah daga ganin face ɗinta cike take tab da damuwa, idanunta sun sha kuka har sun gaji, ga dukkan alamu koma daga ina ta fito bata yi zaman daɗi a wajen ba, sai dai kuma jikinta ya nuna ta samu kula sosai duba da yadda ta yi ƙiba ta kuma yi haske, da alama wlh zuciyar Khadija a yanzu ya bushe bata jin tausayin komai. Ganin da gaske zai iya hallaka ƴar mutane yasa mamar tasa ta fara ihun neman taimako, a guje ta yi waje dan ta nemo mai agaza mata. Haniyarsu dake kwance rai a hannun Allah ne ta ji Haidar zai kashe mata jika Khadija da duka, nan take jikinta ya tsananta ciwo, tana kaunar jikokin nata a yanzu kam, dan ta yi nadama, su Khadijah ɗin zata gani ta tuna babansu, kuma ace Haidar zai kashesu ai ba zaman lafiya. Nan take jininta ya sake haurawa sosai, jiki ya tsananta ciwo, suna can su kuma suna hauka babu wanda ma yasan ciwon nata ya tashi, sai numfashi sama sama take yi tamkar rai zai yi halinsa. Sadiq dake asibiti yana ƙoƙarin haɗawa Zainab tea ta sha kafin a kawo masu takardar sallama ne ya ji wayarsa tana ringing, yau dama za'a sallami Zainab ɗin, dan ta ji sauki sosai, sai dai rashin maganar ne har yanzu dai shiru ba wani cigaba, komai kace mata sai dai ta ɗaga maka kai sama kawai alamar ta ji. Haɗa mata tea ɗin ya yi ya miƙa mata tare da ciro wayar tasa daga aljihunsa, my friend shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Picking ya yi ƙoƙarin yi call ɗin ta katse, dama call ɗin farko ta katse saboda yana haɗa tea, hakan yasa bai samu damar ɗauka ba. Cire password na wayar ya yi tare da fara ƙoƙarin kiran abokin nasa sai ga kiran ya sake shigowa. Picking na call ɗin ya yi tare da kara wayar a kunnensa. Tun kafin ya yi magana ya tsinkayo muryar abokin nasa cikin tsananin tashin hankali yana faɗin. "Sadiq duk in da kake ka yi maza kazo, kome kake yi ka yi maza ka bari mama ta faɗi yanzu zamu kaita asibiti". A ruɗe ya ce. "Meyasameta ta faɗi?". "Nima dai ban sani ba, na zo gaisheta ne na sameta tana waya, ina ga a wayar ne aka gaya mata wani magana mai ɗaga hankali da har yasa ta faɗi, ka yi sauri kazo". Bawan Allah tsabar ruɗewa da shiga tashin hankali bai san lokacin da ya fice daga ɗakin ba, sai ya mashi kamar a Kaduna yake ba Kano ba, ko katse kiran bai iya samun dama ya yi ba, shima abokin nasa bai katse kiran ba ya tura wayar a aljihu suka ɗauki maman zuwa asibiti, shima Sadiq ɗin haka ya tura wayar a aljihunsa ya fice daga hospital ɗin, tashin hankali yasa ya mance da Zainab a asibitin ya tafi, wlh Sadiq yana da karfin imani da tawakkali, da wani ne irin wannan tashin hankali daga wannan jarabawa sai wannan wlh da wani ne da ya jima da haɗiyar zuciya ya mutu, wannan bala'i sai kace ba lafiya ba, ko da yake Ubangiji ya fi jarabtar wanda yake kauna, Allah dai ya baku ikon cin wannan jarabawa, amma gaskiya wannan family na Baban Zainab kuna ganin rayuwa, Allah dai ya saka maku da mafificin alkhrinsa bayan kunyi hakuri da juriya kun cinye jarabarwarku. Haka Sadiq ya tafi ya barta kwance a asibitin, Dr ya kawo mata takardan sallama, zaman jiran kawun nata ta yi har dare bai dawo ba, hakan yasa ta fara tunanin ko dai ta koma gida ne? Wani zuciya kuma ya ce mata idan ta koma gida ya dawo bai sameta bafa? Tun da rana wannan tunani na idan ta tafi ya dawo bai sameta bafa ɗin nan shiyasa ta zauna a asibitin har dare ta kasa tsayar da hukuncin da ya dace da ita. Sai da ta ji ana sallar isha ne ta ce bari dai ta lallaɓa ta tafi gida in yaso idan ya zo gida sai ta bashi hakuri. Wannan shawara da ta yanke shi ta bi a in da ta tashi ta haɗa komai nasu, da kyar take tafiya har ta fita daga asibitin, bata da ko naira biyar haka ta tari abin hawa ta hau da nufin ya kaita gida. A ɓangaren Khadija da Haidar kuwa, kafin mamarsa ta samo maza su kama mata shi har ya jiwa Khadija rauni, ya fasa mata baki sai jini yake yi. Da kyar aka iya kama shi, sai huci yake yi yana faɗin wlh sai ya kashesu kamar shi ya kawosu duniya. Haka matasa suka jashi izuwa waje, jin yana ambatar sai ya yi kisan kai ne yasa matasan basu yi ƙasa a gwiwa wajen miƙashi ga hukuma ba, dan kar ya jajumo masu masifa irin na sati bakwai da suka wuce da mmn Zee ta kashe bbn Zainab, ranar sun ga tashin hankali a unguwar, so gudun kada Haidar ɗin ya kara jajuɓo masu wata bala'in yasa suka wuce station kai tsaye da shi...... _________________________🔥 A bakin kofar gida mai mashin da Zainab ta tara ya kawota. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 3/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E_______15 A bakin kofar gida mai mashin da Zainab ta tara ya kawota. Sauƙa ta yi tare da kayan nata, nan fa ta tsaya shiru tana tunanin waye zai bata kuɗi ta biyasa hakkinsa? Ita dai tasan bata da ko sisi, sannan mamarta bata gidan bare ta yi tunanin shiga ciki ta karɓa, to ya zata yi kenan?. Ta jima a tsaye a wajen tana tunane tunane har sai da mai mashin ɗin ya ce mata. "Malama sallame ni in tafi". Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali. Murya a sanyaye ta furta. "Ka yi hakuri bawan Allah, wlh bani da ko naira biyar, dan Allah ka yafe mun kuɗin". Ɗago idanu ya yi ya kalleta da kyau, sannan ya mayar da kallonsa kan gidan nasu, ɗan taɓe baki ya yi, ko ba'a gaya mashi ba ya gane Zainab ƴar matar da ya ɗauka zuwa bayan gari wajen boka ne ranar, dan har yau kamannin maman zainab ɗin yana face ɗinsa ya kasa mancewa da ita, dan abin da ya jiyo da kunnuwansa a gidan bokan ya tsaya mashi a rai, sannan yasan a unguwar nan ya ɗauki mamarta ya kuma kaita ya dawo da ita, dan haka a cikin zuciyarsa ya furta. "Tun da uwarki tana da kuɗin zuwa wajen boka to wlh ba zan yafe kuɗina ba sai an biyani, dama ku mutanen arziki ne sai na iya yafe maki". "Ke malama bani kuɗina kawai, ni ba wai na fito dan na ɗauki mutane irinku na kuma yafe masu kuɗi bane, nema na fito yi! Dan haka biyani hakkina kawai na wuce". Shiru ta yi tana tunanin ya zata yi ta biya wannan bawan Allah. Tsawa ya daka mata a kan ta bashi kuɗinsa shi yana son ya tafi. Narai narai ta yi mashi da idanu, babanta ne kawai ya faɗo mata a ranta, da yanzu yana nan waye ya isa ya yi mata walaƙanci irin haka, da yanzu yana raye ai ko mashin ɗin haya ma ba zata hau ba bare har ta rasa kuɗin biya, baiwar Allah tasan gayyar shaiɗanu ne kawai a cikin gidan nasu, ko ta shiga ma babu wanda zai ɗaga idanu ya kalleta bare har ya taimaka mata da ko sisi. Can kuma tunanin maman Hanif ya faɗo mata, nan take ta fara addu'ar Allah yasa maman Hanif ɗin tana gidan nasu, tasan ita ce kawai zata iya taimaka mata, a lokacin kuma mai mashin ɗin ya fara surfa mata ruwan balai a kan lallai ta bashi kuɗinsa. "Kayi hakuri malam, bari na shiga cikin gida na karɓo maka kuɗin". Da kyar ta iya idasa maganar saboda tsananin nauyi da tongue ɗinta ya yi mata, maganar tata ma bata fita sosai saboda wahala, ga bakin nata babu ɗanɗano ɗaci rok kamar shuwaka. "Wlh ba zai yiwu ba, babu in da zaki shiga, a nan zaki bani kuɗina, salon ki shiga ki gudu ki barni, wlh ba zai yiwu ba, kawai fito da kuɗi ki bani kayana hakkina". Wasu zafafan hawayene suka cika mata idanu a in da suka fara ganganrowa da ƙaɗan da kaɗan. "Ke ko kukan jini zaki yi yau sai kin bani haƙƙina, ai ba irinku musrikai mutanen banza ake yafewa kuɗi ba!!" Jin ya dangantasu da musrikai ne yasa ta ɗago da idanu cikin sauri ta wani wurga mashi wani irin kallo wanda yasa sai da ya haɗiyi yawu ba shiri, dama fa kun san ita Zainab ruwa ne ya daki babban zakara, badan haka ba mafaɗaciyace number ɗaya, dan haka ranta a ɓace dama ga ciwo ga bakinciki tana neman in da zata amayar da bakincikin dake cikinta ko abu zai ragu mata. Cikin fusata ta ce. "Musrikai kuma mutanen banza? Su waye kenan?". Ta yi maganar tana goge hawayen dake fita daga idanunta. "Gaku kuwa, wlh tun da kuna da kuɗin zuwa wajen boka sai an biyani hakkina makiya Allah da Manzonsa kawai". Ai tsabar haushi bata san lokacin da ta cire hannu zata zabga mashi mari ba, duk ta saki abubuwan hannunta har flask ɗin da Sadiq ya saya mata na sanya ruwan zafi a asirbiti ya fashe saboda sakinsa da ta yi, ranta ya sosu da jin maganarsa, bata san cewa yana da gaskiya shi ne nan ya kai mamanta har wajen boka ba, sai dai ya yi kuskure tun da ba tare da su ya kai maman nasu ba, ta kan iya yiwuwa su bama su san ta je ba, ya zo ya haɗesu ya yi masu kuɗin goro. Bata kai ga sauke hannunta a saman face ɗinsa ba ta dakata, ba komai kuma yasa ta dakata ba face ta gansa babban mutun ne har da furfura a gemunsa, da yara matasane babu abin da zai hana ta maresu sai dai duk abin da zai faru ya faru, amma a irin tarbiyar da iyayenta suka bata ba zata iya marin wanda ya haifeta ba, dan haka sai ta juya cikin fushi zata wuce cikin gida, ranta a matuƙar ɓace ta fasa marin nasa. Da sauri ya sauƙa daga kan mashin ɗin ya sha gabanta yana faɗin. "Aww dama marina kenan zaki yi dan nace ku makiya Allah ne? Karya na faɗana ne? Ni malama ki bani kuɗina! Babu in da zaki motsa ba tare da kin biyani hakkikana ba! Da kuma kin mareni da daga yau baki sake marin wani ba!!". Cikin faɗa ya yi maganar. Datse idanunta gam ta yi kafin ta ce. "Ka matsa mun a hanya malam, ina ganin mutuncinka, idan ka cigaba da yin abin da kake yi wlh zan yi maka rashin mutuncin da har ka mutu ba zaka mance da shi ba, kuɗin naka kuma na cinye ba zan biya ba kayi duk abin da zaka yi!!". Da kyar ta yi maganar kamar wadda aka sanya dole. Ai kuwa shi ma ransa a ɓace wai ta yi mashi rashin kunya, cikin jin haushi ya cire hannu zai mareta. Kaucewa marin nasa ta yi tare da ja da baya tana wani layi kamar zata faɗi, bata da kuzari ne a jikinta ko kaɗan. Wasu matasa da suka zo wucewa ne suka ga abin da yake faruwa, nan fa suka tsaya suka tambayi me yake faruwa, mai mashin ɗin ne ya amsa masu da cewa. "Wannan yarinya zata raina mun hankali, na ɗaukota daga hospital zuwa gida ta bani kuɗina wai ba zata bayarba bata da kuɗi, tasan bata da kuɗi ne ta hau abin hawana? Da nace ba in da zata je sai ta biyani shi ne ta tsaya tana zagina ni kuma zan ɗauki mataki, ba zai yiwu ace yarinya kamar wannan wadda na haifa ace tana gaya mun magana ban zaneta ba!". Ita dai shiru ta bishi da ido tana jin sharrin da yake yi mata, ita burinta ma kawai ta shiga cikin gida ta kwanta, dan jiri take gani yana ɗebarta. Nan fa matasan suka ce zasu biya kuɗin nawa ne ya yi hakuri. Ana cikin hakan sai ga Khadija da hayaniyarsu ya isheta ta taso ta fito dan ta ga su wanenen? Dama tun da yamma take neman Zainab ɗin, ga jikinta da yake yi mata ciwo na dukan Haidar da ta sha, bakin nata ma in da ya fasa mata har ya ɗan kumbura. Ganin hayaniyar da Zainab ake yi yasa ta yi saurin ƙarisawa wajen tana tambayar lafiya me yake faruwa?. Zainab da take begen ganinta ne ta buɗi baki da karfi ta furta sunanta Khadija. Nan take ta ji jikinta ya watsake, a ruɗe ta rungumeta tana faɗin. "Ina kika je? Ina kika tafi kika barni? Meyasa kika tafi kuma? Kin san wahalar da na sha da baki nan? Babu mama babu baba, kema babu ke! Iya kawu Sadiq ne kawai ya rage mun a duniya! Dan Allah ina kika je?......" Da kyar ta iya kai karshen maganar saboda kuka da ya ci karfinta. Ita ma Khadijan kuka take yi sosai ta ce. "Ba tafiya na yi ba, ɗaukata aka yi aka rabani dake, nayi kewarki sosai, na yi kuka rashinki tun hawaye na zuba daga idanuna har suka daina zuba, ina kaunarki ƴar uwata, ina mama take?". Daga mai mashin ɗin har matasan dake gefe zuba masu idanu suka yi suna kallonsu, a yanzu fa gabaɗaya unguwar su Zainab ɗin zagin gidansu ake yi ana tsine masu albarka wai su ɗin annoba ne, daga dawuwarsu unguwa sai masifu kala kala yake faruwa, har da kisan kai aka yi a gidansu, maganganu dai kala kala marasa daɗin ji ake jefansu da shi. Sai murna da ganin juna suke yi. "Me ya tsayar dake a waje? Daga ina ma kike haka tun ɗazun ina nemanki? Ya na ganki duk a firgice and ina mama?". Dukka Khadija ce ta jero mata waɗan nan tambayoyin. Fuska duk a jiƙe da hawaye ta amsa mata da. "Daga asibiti nake, mai mashin ɗin da ya dawo da ni ne ya tsayar da ni wai na bashi kuɗinsa kafin na shiga cikin gida, ni kuma bani da kuɗi, kawu Sadiq bai bar mun kuɗi ba". Ta kai karshen maganar hawayenta na ƙara tsananta gudu a saman face ɗinta. "Meya kai ki asibiti? Amma dai bari mu shiga ciki sai ki gaya mun, yanzu jirani bari na ɗaukowa mai mashin ɗin kuɗinsa". Tana kai karshen maganar ta raba jikinsu dana juna tare da sa kai da sauri ta wuce cikin gidan. Matasan da suka ce zasu biya mata kuɗin ɗin jin cewa Khadija zata ɗauko kuɗin ne yasa suka hakura suka wuce abinsu, dama kawai dai dan sun ga macece yasa zasu biya mata ba wai suna da wani ishasshen kuɗi a jikinsu ba, kun san mu a arewacin Nigeria Allah ya horewa matasanmu zuciyar taimakon mata a duk lokacin da suka ga za'a ci zarafinsu, basu bari a ci zarafin mace koma ya take, in ma matar aure ko budurwa or bazawara, su dai koma wace iriyar macece zasu taimaka mata matuƙar suka ga za'a ci zarafinta musamman ma kanawa suna da wannan dabi'a, sai dai muce Allah ya ƙarawa zuciyarsu taimako da tausayi. Mai mashin ɗin kuwa yana tsaye yana bankawa Zainab da hankalinta baya a kansa harara, hankalinta na'a kan kofar gidansu tana jiran fitowar ƴar uwarta Khadija, ta yi kewarta sosai, badan bata son masifaba da ta bi Khadija ɗin cikin gida, amma idan ta ce zata bita mai mashin ɗin nan zai sake tsayar masu da tijara, so gara mata ta daure kawai ta jirata har zuwa ta fito. Da sauri Khadija ɗin ta fito har kamar zata kifa ƙasa, Allah sarki duk dan kewar ƴar uwarta, hannunta na riƙe da dala ba naira ba, tana zuwa ta miƙawa mai mashin ɗin dollar dubu ɗaya sabuwa kal sai kyalli take yi. Ai wannan mai mashin ɗin bai san lokacin da ya sauko ƙasa daga saman mashin ɗin nasa ba, zaro idanu waje ya yi yana kallon kuɗi ya kuma ɗago ya kalli Khadija da ta tsugunna ƙasa tana kwashe kayan da Zainab ta zubar, ita sam bata ma san yana kallonta ba, ita kuwa Zainab ta tsaya sai banka mashi harara take yi na yana kallon mata ƴar uwa, bata san shi al'ajabi da mamakin kuɗin da ya fito daga hannunsu ma yake yi ba, dala dubu ɗaya a yanzu wajen million ɗaya da dubu ɗari shidda kenan take, amma Khadija ta zo ta miƙa mashi ta kama harkar gabanta tamkar wadda ta bashi naira ɗari ko ɗari biyu, ko a jikinta, ko daga ina ta samo dala sabuwa kal haka?. Kwashe kayan tsab ta yi tare da miƙewa tana faɗin. "Zainab mu shiga ciki dan Allah ki gaya mun ina mama kuma me kika je yi a hospital?". Wucewa suka yi ba tare da Khadija ta sake bi ta kan mai mashin ɗin ba, ko kallon in da yake ma ba ta sake yi ba ta ja hannun yar uwarta suka nufi ciki. Shi kuwa mai mashin sai Allah Allah yake yi su shiga ciki basu tambayi canji ba ya samu ya gudu da kuɗin ya ci bulus a ganinsa, e mana a ganinsa ne ya ci bulus ya samu kuɗi a sama, da ni daku kuma duk mun san cin hakkin wani dai ba cin bulus bane, akwai ranar biya, dan Allah baya yafe hakkin wani a kan wani, dole sai mai shi ya yafe maka, laifi tsakaninka da Allah ne wannan idan ka tuba Ubangiji gafurur rahim zai yafe maka, amma tsakaninka da wani, dole sai ka nemo shi ya yafe maka tukun nan, in ba haka ba Allah ya bi mashi hakkinsa. Ai kuwa suna shiga gida ya yi maza ya haye mashin ɗinsa, jikinsa har yana kerma wajen yin saurin kunna mashin ɗin, da gudun gaske ya bugata ya bar unguwar, sai murna yake yi ya samu kuɗi har naira miliyan ɗaya da ɗauri. Suna shiga cikin parlour suka isko Hauwa da maman Haidar suna zaune suna aikin da suka saba wato hira, maman Haidar ta ce a rufe Haidar na kwana biyu a cell sai ya nutsu a sako mata shi, ita kanta bata iyawa da haukarsa, ita da ta haife shi ma kenan, amma dan tsabar son zuciya da mugunta a haka take son a ƙaƙabawa Khadijah ƴar marainiyar Allah shi, kai wlh jama'a mu rage son kai da son zuciya, ba in da hakan zai kaimu face halaka, Allah mun tuba ka yafe mana zunubanmu, a yawaita tuba jama'a, dan babu wanda yasan a ina karshensa zata zo, yawaita tuba zai sa koda kana da zunubi mutuwa ta riskeka zunubin naka su ragu koma Allah ya yafe maka gabakiɗaya, dan haka mu yawaita tuba kafin mutuwarmu, Allah kasa mu dace. "Ku zo nan munafukai! Ina kuka fito?". Cewar maman Haidar. Khadija ce ta amsa mata da. "Daga waje muke gwaggo". Zainab sai aikin binsu da wani matsiyacin kallo take yi, da yake akwai solar a gidan haske ya gauraye parlourn sai ya zamana suna ganin juna sosai, hakan yasa Hauwa taga irin kallon rainin wayon da Zee take binsu da shi. "Ke rasa kunya ɓerar tanka uban waye kike harara? Ko akwai sa'an ki a cikin nan ne?". Cewar Hauwar. Khadija ce ta amsa mata da. "Kina ji ko Hauwa kike ko wa? Koma ya sunanki dai ina son ki tsaya a iya matsayinki, kada ki sake ki shiga harkarmu wlh, idan kuma kika ki wlh sai na sa kin gane Annbi isa ba ɗan Allah bane manzon Allah ne". Tana kai karshen maganar ta ja hannun Zee suka wuce cikin ɗakin. "E lallai Khadija kin girma, wuyarki ya yi kwari ya isa yanka kenan!". Cewar Hauwa. Zee ce ta capki zance da cewa. "Tun da ya isa yanka ai sai kizo ki yanka ai!". Daga hanka suka banko masu kofa da karfin gaske, irin su suka sani nan. Taɓe baki maman Haidar sarkin tsoro ta yi, dan ita fa tsoron masifaffu take yi kada su naɗa mata duka ato, ta ji daɗi ma da Khadija ɗin ta amsa mata magana cikin mutunci har ta ce mata gwaggo, dan haka gara ta kama girmanta ta cigaba da samun suna ce mata gwaggon, dan yanzu ta lura yaran nan suna ji da tashen girman, tsab zasu dakata ta yi laushi, gara ta shafawa kanta lafita ta ja mutuncinta. Hauwa kuwa da yake ƴar balaja'u ce sai ta fara surfa masu masifa, a can ƙarƙashin zuciyarta kuwa tana tunanin ta yadda zata yi ta yi maganin yaran nan, dan ita ma ta lura Khadija tana ji da tashe girma a yanzu, tsab zata iya cewa zata yi faɗa da ita, idan kuma faɗar zasu yi wlh tsab Khadija zata lakaɗa mata shegen duka, dan Khadija fa sai dai muce masha Allah, Zainab akwai rashin kunya ba karfin kirki, Khadija kuwa shiru shiru amma in ka kureta karfi ne da ita sosai, haka suke, dama kunsan mai hakuri fa kada ka kuskura ka kuresa wlh, in ka kuresa abin baya kyau sam sam. Suna shiga ɗaki Khadija ta ce. "Zainab kin yi sallah ne?". Kai ta girgiza mata alamar a'a. "Okey yi alwala ki yi sallah kizo ki gaya mun me yake faruwa ne a gidan nan?". Da okey ta amsa mata tare da wucewa cikin toilet, wanka ta fara yi da ruwa mai zafi sosai kafin ta ɗauro alwala ta fito. A saman gado ta isko Khadija ɗin tana duba magungunar da aka bata a asibiti. "Zainab wannan uban tulin magunguna kuma na waye? Naga har da na zuciya duk na waye haka?". Kamar zata yi kuka ta ce. "Magunguna na ne, yanzu ma zan zo in hau shan su". Zaro idanu ta yi kafin ta ce. "Dukka uban magungunar nan? Ji wannan manya manyan kamar shanu ce zata sha? Dukka kuma zaki sha?". Ta yi tambayar fuskarta ɗauke da mamaki. Kai ta gyaɗa mata alamar e, abin gwanin ban tausayi. "To me ya sameki har zaki zuba waɗan nan magunguna a cikinki? Meyake damunki?" "Bari na yi sallah sai na gaya maki me ya faru". Nan take idanun Khadija suka ciko da kwallah, rayuwa kenan, yau sun dawo yin rayuwa su biyunsu Allah sarki gwanin ban tausayi. Sallah Zee ta yi, bayan ta idar ne ta yi addu'a sosai, ta ɗauki lokaci mai tsawo a wajen jero addu'oin nata kafin nan ta shafa, sannan ta miƙe ta dawo saman gadon ta zauna. Khadija da ta ƙura mata idanu tun ɗazun tana kallonta cike da tausayi ne ta ce. "Dan Allah Zee kada zuciyata ta fashe ki sanar da ni meyake faruwa? Ke kaɗai nake jira, a ƙage nake wlh". Ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙarisa hayewa saman gadon da kyau, sannan ta riƙo hannun ƴar uwar tata, nan ta fara bata labarin abin da ya faru tun fitar ta gida lokaci da mamarsu ta cakawa babansu wuƙa har izuwa yanzu da suke zaune. Ya ilahi ya lilliahi, kuka Khadijan take yi sosai da sosai, hawaye a saman face nata gudu suke yi kamar ba gobe, jikinta har rawa ya fara yi saboda tsananin tashin hankali, babanta ya rasu, mamarta ta ci life in prison, innalillahi wainna ilaihir rajuun, wannan masifa ko makiyin ka ba zaka so ka yi mashi fatan shiga makamancinsa ba. Rungume juna suka yi suka hau murzan kukansu, wannan hawaye nasu Allah ne kaɗai yasan ranar da zata dakata daga zuba a idanunsu, ya ilahi ya lilliahi. Allah sarki babu mai rarrashinsu, haka suka ci kukansu har ya ishesu suka rarrashi kansu da kansu, Zainab sarkin zuciya sai shessheka haɗi da ajiyar zuciya take ta faman saukewa. Sai da suka ɗan ji dama dama ne Zainab ta ce. "Ina ke kuma kika je? Ina kika tafi kika barni ni kaɗai na rinƙa faɗa tsakanin rayuwa da mutuwa? Na sha wahala! Na rasa wa zan yi wa kuka, babu mai rarrashina, babu wanda zan gani na ji sanyi a rai'na, ta ko'ina na juya zafi ne kamar wuta a gareni, sam babu wani sassauci, na ce kawu Sadiq ya kaini wajen mama ya ce shi ma ya je an hana shi ganinta, zuciyata zafi take mun kamar zan mutu, shiyasa kika ga maganin zuciya a cikin magungunana, wlh Aunty Khadija gara mun mutuwa akan azabar nan da na shiga, irin wannan tashin hankali bana fatan ko makiyina ya shiga cikinsa". Ta kai karshen maganar wasu zafafan hawaye suna ganganro mata a saman kumatunta. Matsowa Khadija ɗin ta yi ta fara goge mata hawaye tana faɗin. "Kiyi hakuri Zainab, na tabbata Allah bai mance da mu ba, na tabbata yana sane da mu kuma zai yi mana sakayya, sannan shi ne kawai zai share mana hawaye, ina son ki sani duk halin da zaki shiga kada ki manta Allah yana tare da ke, kuma shi kaɗai ne zai kawo maki sauyi a lokacin da baki taɓa zato ba, dan haka ki goge hawayenki, addu'a baba yake da buƙata, mama kuma da izinin Allah Ubangijinmu zai dubeta da idon rahama tun da ba da gangan ta kashe baba ba, ban taɓa yankewa daga fatan samun nasara daga wajen Ubangiji ba, nasan shi ɗin mai rahma ne a kan bayinsa, da izininsa zai saukar mana da rahmansa, kuma baya mantawa da bawa ko guda ɗaya, Allah zai kawo mana mafita". Maganganun Khadija sun ratsata sosai, hakan yasa ta goge hawayenta tare da yin alkawarin zata yi ƙoƙarin ta dai'na zubda hawaye duk da tasan abu ne mai wuya a gareta, dan kuwa wani lokacin idan ta yi kukan ne take samun sauki a zuciyarta. "Aunty Khadija ina kika je har tsawon wata biyu to?". Ta yi tambayar tana kallonta har cikin ido. A takaice ta ce "Russia!". Zaro idanu sosai waje Zee ta yi tare da maimaita sunan Russia ɗin. Jinjina mata kai Khadija ɗin ta yi kafin ta ce. "Yeah kamar yadda kika ji hakan ce ƙasar Russia aka kai ni". "Waye ya kaiki can? And me kika yi a can?". "Saceni suka yi suka kaini can, ni ban san na yi wata biyu da tafiya bama sai da kika faɗa mun yanzu, dan tun da naje ina ga na ɗauki kwanaki ko satuttuka a sume, ni ban san komai da ya faru ba". Ƙara zaro idanu waje Zee ta yi. "Na shiga uku ni Zainab! To amma ya aka yi kika dawo? Sannan kuma basu yi maki komai ba ko?". Tana ƙoƙarin firfito da magungunar Zee ɗin da ta mayar ɗazun ta amsa mata da. "Waɗan da suka ɗaukeni su suka dawo da ni har kofar gida, kuma ni ba abin da suka yi mun, ban ga alamar sun cutar da ni ko wani abin makamancin haka ba, kamar yadda suka ɗaukeni a kofar gida haka suka dawo da ni, sannan suka bani wancan jakar mai cike da kuɗi suka ce na tafi gida wai na rinƙa cin abubuwa masu kyau da kuɗin da suka bani". Shiru Zainab ta yi tana tunanin anya hakan zai yiwu kuwa?........ Ni ma dai nace anya hakan zai yiwu kuwa? Su zo har kofar gida su ɗauketa su tafi da ita ƙasa mai nisa haka, sannan su riƙeta na tsawon sati bakwai ace sun sake dawo da ita da kansu kamar yadda suka ɗauketa? Sannan su bata maƙudan daloli ma ba nairori ba su ce ta tafi ba tare da sun yi mata komai ba! Anya hakan abu ne mai yiwuwa kuwa? Kai akwai dai abin da ya saɓa wanda ita bata sani ba. Hmm akwai dai wata a ƙasa, haka kawai ba zasu yi abin da suka yin nan ba. Katse mata tunani Khadija ɗin ta yi ta hanyar cewa. "Zo ki sha magani, dan ina fargabar wani abin ya saman mun ke, ke kaɗai kika rage mun sai Allah da ya haliccimu sai kuma kawu Sadiq, dan haka ba zan barki ki yi wasa da magani ba, zo maza ki sha bari na nemo waya mu kira Kawu Sadiq mu ji ina yake kuma me ya faru ya fita asibiti da sauri haka?". Ta kai karshen maganar tare da turo mata tulin kwalin magungunar a gabanta. "Aunty Khadija ban fa ci abinci ba, magungunar nan kuma suna da karfi in ji Dr, dole na ci wani abin kafin na sha su". "E haka ne, to ki jirani bari na nemo maki abin da zaki ci, daga nan na nemo mana waya". Tana kai karshen maganar ta zuro kafafunta kasan gadon ta sauƙa. Kai tsaye wajen jakar kuɗin nata da taho da shi ta nufa, dala ɗaya ta zara, wannan shi ne dare ɗaya Allah kan yi bature, yau dai ga Khadija da dukinyar da babanta ma bai mallaki ko kwatansa ba, wannan maƙudan dukiya da yake cikin jakar nata duk familynsu daga ɓangaren mamarta har na babanta babu mai kwatan wannan dukiya, dan zallar dollars ne a ciki, gasu da uban yawa, Allah sarki a kan dukiya aka kashe babanta kuma Hauwar take son kashesu, dukiyar baban nasu ma da bai wani taka kara ya karya ba, to ita gata da dukiyar da zai isheta rayuwa ita da familyn nata gabaɗaya ba tare da sun juya shi bama ma, su ajiye suyi ta zara kawai zai ishesu har su mutu....... Hmmm tab yau ake yinta, wannan uban kuɗin dukka da suka bata kuma ace basu yi mata komai ba? Kai ina akwai ayar tambaya gaskiya. Da yake su basu ɗauki dollars da mahimmanci ba, kai bama su san banbancinsa da kuɗin Nigeria ba, ita dai da taga dubu ɗaya a rubuce a jiki sai ta yi tunanin ko irin dubu ɗayan Nigeria ne, bata san wajen miliyan ɗaya da rabi ake magana a kan dollar dubu ɗaya ba. Dan haka rashin sani yasa ta sake zarar dubu ɗaya ta nufi waje abinta bayan ta ɗauki hijabi Zee ɗin ta sanya a jikinta. Har lokacin su maman Haidar suna parlourn. Maman Haidar ce ta ce. "Khadija ina zaki je a daren nan?". Cikin halin ko in kula ta ce. "Abu zan saya a waje gwaggo". "To amma kada ki jima kuma ki kula kin ga dare ya yi"...... Kash wato a duniya idan ba ka nunawa wasu kai ma ɗan iska bane fa bazaku zauna lafita ba, yanzu dai ga shi maman Haidar ta fara yin biyayyar dole gasu Khadija, ta fara tausaya masu dan dole ba dan tana so ba sai dan gudun kada Khadija ta daketa, wannan shi ne maganin shege sai ɗan iska, maganin biri karen maguzawa. "A daren nan ne zaki fita?". Cewar Hauwa da bata gajiya da shegen shisshigin tsiya. Ko sannu Khadija ɗin bata ce mata ba, bama ta kalli in da take ba, dan wani irin haushin Hauwa da take ji kamar ta shake shegiya ta kashe, idan ta ce zata kulata to wlh za'a sake tabka irin kuskuren da aka yi sati bakwai da suka wuce, dan wlh yadda Zainab ta bata labarin abin da ya farun nan ji take ta kashe Hauwar kawai ta huta. "Khadija ba dake nake magana bane? Nace kada ki fita da daddaren nan ko?". Hauwa ta sake faɗa kamar wata uwarsu, hegiya bata gajiya da shisshigi a lamuran mutane. Yadda kuka san da mutun mutumi take magana ba Khadija ba, ko juyowa bata yi ba bare ta ganta, ta sanya kai ta yi waje abinta, dan wlh in ta juyo zata iya sumar da Hauwa da duk abin da ta gani a gabanta ɗauka zata yi ta bugawa hegiya, amma gudun kada shaiɗan ya yi galaba a kanta ne yasa taki juyowa, addu'a take yi Allah yasa tafi karfin zuciyarta, da haka ta nufi waje. Kai tsaye shagon mai sayar da provision ta nufa. Kayan tea masu inganci ta sayawa Zainab ɗin, bayan mai shagon ya haɗa mata komai sai ta bashi wannan dalar da ta ɗauko. Zaro idanu ya yi yana kallon kuɗin, ya kasa iya gaya mata cewa a shagon nan nasu basu da kuɗin da zasu iya bata canjin wannan kuɗin nata. Ya saki baki yana ta kallon kuɗin har ta kwashi abubuwan da ta saya ta ƙara gaba abinta, bata tsaya neman canji ba, bama ta san tana da canji ba, dan abubuwan dubu ɗaya dai'dai a kuɗin Nigeria ta karɓa, na gaya maku ganin kuɗin take yi kamar dai'dai yake da kuɗin Nigeria, ita dama ba shiga media take yi ba bare ta iya sanin farashin dollar, ba waya ne da ita ba, idan kunga ta riƙe wayar mamarta ma to game take bugawa da wayar, so bata san komai dan gane da fashin kuɗin ba. Hanyar gida ta nufa sai sauri take yi, kamar daga sama daga bayanta ta ji ance. Khadija................. A hankali ta juyo domin taga wanenen da ƙoƙari ya iya ganeta a daren nan, hanyar ba wani haske ne sosai da shi ba, bugu da ƙari sabuwar unguwa suke, bata san kowa a unguwar ba to waye ya ambaci sunanta? Tana juyowa sai taga......................✍️🔥🦋 ___________________________🔥🌹 KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 Gimbiya Zunaira🌹 Ihu sosai take kurmawa da iya karfinta na karshe, wani ƙosasshen doki da ya yi kanta a guje ne yasa ta sanƙare waje guda tare da kurma ihu mai sautin gaske, ga shi dai dokin da babanta yake yawan hawa ne, amma saboda rashin mutunci irin na dokin nan bai ji tausayinta ba ya yi kanta da nufin ya murkusheta, ko tsayawa bai yi ya ga kamanninta da King Zuhair ba bare ya tausaya mata...........😅 (Wai doki bai san kamanni bane?😫 Meyasa ba zai tsaya ya fahimci tana kama da King Zuhair kuma jininsa bace?😫) Kanta kawai ya yi da nufin ya tattaketa, haba tsabar tsorata har sai da numfashinta ya ɗauke cak, tana ƙoƙarin zubewa ƙasa Hoorain ya tareta da hannu ɗaya ta faɗa saman faffaɗar chest ɗinsa, hannunsa ɗayan kuma da yake riƙe da yellow da jan kyallen ne ya fara ƙaɗawa dokin a face ɗinsa. Ai da gudu dokin ya juya ya bar wajen a in da ya bazama cikin sauran dabbobin, dukkan sauran dawakan sun watse sun bazama cikin gonar. Jefar da kyallen ya yi tare da riƙota da kyau yana kallon face ɗinta, kamar dai kullum kayan warriors ne a jikinsa. Dama kun san tsakaninsa da Auta akwai amana sosai, to tun fitowarta daga family part ya hangota, yana tsaye da abokansa suna hira suna nishaɗi ya hangota, tun daga kan yadda yaga tana tafiya ƴar tsanɗo ya fahimci bata da gaskiya, ya fahimci akwai abin da take son aikatawa na rashin gaskiya, hakan yasa ya ce da abokan nasa yana zuwa. Bai jira amsarsu ba ya bar wajen cikin takun jarumta, a hankali ya bi bayanta ba tare da ya bari ta sani ba, duk in taga mayaƙa sai ta ɓuya, shi ma sai ya dakata da binta, idan ta cigaba da tafiya sai ya bi bayanta, idan yaga zata juyo sai ya ɓuya, haka suka rinƙa tafiya har izuwa bakin gonar. Lokacin da ya ga ta yi wa mayaƙan bakin gate ɗin wayo ta saki tattabarun nan sun tashi sama sai da ta kusa sanya shi murmushi, ƴar karama da ita wai ita ma ta yi wayo, ta yi wa manyan warriors wayo, bata san cewa ba wayo ta yi masu ba, kawai dai a matsayinta na Gimbiya ne basu isa su ki bin umarninta ba shiyasa suka bi tattabaru, bugu da ƙari ta kasance Auta a cikin family, sannan ita ɗin sanyin idaniyar kowa na cikin family ne, wannan dalilan yasa suka yi hakuri suka bi tattabaru. Hoorain dai saura kaɗan ta sanya shi murmushi, haka ya laɓe ya zuba mata idanu yana ganinta har ta yi dabara ta buɗe kofar gate ɗin ta shiga. Cikin tafasar jini ya rufa mata baya, sai dai yana zuwa ya tarar da ta kulle gate ɗin ta ciki. Ganin haka yasa bai yi ƙasa a gwiwa ba ya yi zafin naman haurawa ta dogon kakkarfan katangar wajen, dan gudun kada wani abin ya sameta, shi yasan me a cikin gonar, sannan idan wani abin ya sameta ya shiga tara ba uku ba, dan shi King Zuhair zai hukunta, saboda alhakin kula da ita a wuyarsa yake, shi aka damƙawa kula da duk wata motsinta, so ko ciwo ta ji shi za'a hukunta, hakan yasa ya haura ta gini ya bi bayanta dan gudun kada babansa commander ya jibgesa, kunsan commander shi ne mai hukunta duk wani mai laifi, kuma gara mashi ace wani ya hukuntasa a kan Abbu ɗinsa, dan in ya kama shi mantawa yake yi da shi ɗansa ne, sai ya lallasashi idan sun je part nasu ya yi jinyarsa.........😅 Commander namu baya wasa kuma baya son kai, aiki yake gudanarwa dai'dai tsakani da Allah. Sosai ya ƙurawa face ɗinta ido yana kallo, ta tafi da tunaninsa, ga kuma tumatunta luwai luwai irin na Jaish in ji Mahreen kamar bread........😅 Ya shagaltu da kallon kyanta ya fara jin ihun wasu daga cikin dabbobin wajen, gonar yana ƙoƙarin ruɗewa da kukan dabbobi daban daban, ba komai bane ya ja hakan kuma face ɓallewan da dawakan nan suka yi, sun bazama cikin gonar, so sun watsa wasu daga cikin dabbobin ma. Kafin ya yi wani yunkuri sai ganin wasu daga cikin dabbobin ya yi suna ta watsewa, Auta ta ja komai na ƙoƙarin rikicewa. Ɗago kai ya yi yana tunanin yadda zai yi da ita ya samu ya kaɗa dawakan nan ya mayar da su wajensu, tunani yake yi a ina zai kwantar da ita, ga shi ta suma. Yana tsaka da tunani wani ƙosasshen doki ya yo kansu a haukace. Ai kuwa bai san lokacin da ya kwantar da Autar a ƙasa a wajen ya miƙe ya tinkari dokin gadan gadan ba. Cikin jarumta ya yi nasarar kama linzamin dokin tare da daka wani uban tsalle ya haye bayanta. Haba wani irin haniniya dokin ya yi tare da ɗaga kafafunsa biyu na gaban nan sama yana cigaba da yin haniniya, jan linzaminsa ya yi da karfi nan take ya kaɗashi suka nufi wajen da suke dama. Da gudun gaske dokin ya nufi wajen. Ciki ya mayar da dokin kafin ya dawo ya saɓi Autar a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye ya nufi wajen da King yake zama idan ya kawowa gonar ziyara, akwai waje na musamman da aka tanada, ya sha kayan alatu da luntsuma luntsumar kujeru, an ƙawata wajen matuƙa da kayayyaki masu ɗaukar hankali, sannan ga shinfiɗu na alfarma irin na gidan sarauta masu kwalliyar gashin jimmina. Ga throw pillows da aka zuba a saman shinfiɗun. A saman doguwar sofa ya kwantar da ita ya juya, yadda yake tafiya a buɗe zaka gane yana da jarumta sosai, babu tsoro ko kaɗan a tattare da shi, ko da yake assistant commander ne shi ɗin, dole ya yi namijin jarumta sosai. Wannan kyalle yellow and red ɗin ya ɗauko ya nufi dawakan dake ta gudu a cikin gonar, haɗa kansu ya fara yi yana kaɗasu dan ya mayar da su in da suka fito. A lokacin kuma warriors dake gadin gate ɗin suka fara knocking na gate ɗin ta waje cikin tashin hankali, dan kuwa sun san King ya hana kowa shiga wajen ba tare da izininsa ba, so idan suka yi wasa yau sai sun shiga hannun commander!....... Tab lallai kuna tsaka mai wuya, shiga hannun commander ai ba alkhari bane, kowa baya kaunar hakan!!. Hoorain yana jinsu amma bai tanka masu ba, sai da ya mayar da dabbobin dukka, sannan ya nufi in da take kwance. Ruwa ya ɗauko a cikin freezer dake wajen ya ƙariso wajen nata. Cike da fargaba ya tarbo ruwan a hannunsa, hannun nasa na karma kamar wanda zai taɓa wuta ya nufi face ɗinta da ruwan. Sarai yasan dokar masarautar ce, idan aka kamaka wani warriors ya taɓa ko da yatsar gimbiya ce to zaka fiskanci mummunar hukunci, akwai wani warriors da suka taɓa yin karo da Gimbiya Sarina, hukuncin yanke mashi hannu commander ya yanke mashi, sannan ya watsa shi prison na masarautar har na tsawon shekara ɗaya, shi ne hukuncin taɓa jikin Gimbiya Sarina da ya yi. Amma ba'a yanke mashi hannun ba, uncle Abbas ya hana a in da da kyar ya shawo kan King Zuhair ya yarda ya yafe mashi aka mashi hukuncin shiga yarin masarautar na shekara ɗaya. So shi Hoorain yasan da wannan hukuncin shiyasa yake fargabar taɓa jikinta, ɗazun da ya kamata bai bari ta ƙarisa zubawa ƙasa bama bai san ta ya aka yi ya rumgumota haka ba, bai san ina hankalinsa ya shiga ba har ya riƙota haka, shi bai ma san ya aka yi ya iso gareta da zafi da kuma sauri haka ba, shi dai kawai yaga ya rumgomota bata isa ƙasa ba, yanzu kuma da yake ya dawo cikin hayyacinsa shiyasa ya tuna da wannan hukunci yake kuma fargabar taɓata. Amma da yake babu kowa a gonar sai ya daure ya shafa mata ruwan a lallausan kumatun, yana yi kamar maras gaskiya ko kamar wani yana yi mashi laɓe in ya taɓata za'a gansa, bawan Allah sai waige waige yake yi. Da kuka ta farka daga sumar tata, dan a tsorace ta sune, hakan kuma ya yi dai'dai da shigowar warriors dake bakin gate ɗin cikin gonar, ta saman ginin suma suka hauro, dan suna zargin akwai mutum a ciki, saboda rufe kofar ta ciki da aka yi, kuma sun fi zargin Autar ce, dan ita kaɗai ce ta zo garesu yau. Ganin warriors ɗin sun shigo wajen yasa bai san lokacin da ya yi saurin kai hannunsa ya toshe mata baki ba, duk da yake matsayin assistant commander yasan ya karya doka, kuma duk da yake gaba da waɗan nan warriors da suka shigo, in fact umarninsa ma suke bi dan shi ya basu horo, amma dole ba zasu rufa mashi asiri ba, shi ya shigo aikinsu, a tsarin masarautar babu rufawa kowa asiri idan ya yi laifi, koda gaba yake da kai ya yi ba dai'dai ba dole ka faɗa, idan aka kama ku da wannan laifi na rufawa juna asiri a kan laifi dukkanku zaku fiskanci mummunar hukunci a hannun commander, coz su ma basa yarda su rufawa juna asiri gaskiya, suna da kula da doka basa karyawa. Kewaye warriors ɗin suka fara yi a cikin gonar suna neman wanene a ciki?. Ita kuwa Auta ganin shi yasa ta ƙara tsorata, dan bata yi expecting ɗin ganinsa a wajen ba, ga face ɗinsa dake cikin hular yakin nan ya ƙara tsoratata. Ya toshe mata baki yaki yarda kuma su haɗa ido dan baya son ganin yanayin dake saman face ɗinta, yasan zata sha madarar mamaki na ganin ya taɓa jikinta, dan hakan abu ne da ko da sunan wasa bai taɓa kwatantawa ba. Ta yi ƙasaƙe tana kallonsa, ga ragowar guntun hawaye a face ɗinta. Dalilai biyu yasa ya rufe mata baki kuma yake ƙoƙarin ɓuyanwa waɗan nan warriors ɗin, na farko ita kanta Autar zata fuskanci faɗa a wajen King na ya hanasu zuwa wajen ita saboda rashin ji sai da ta zo, so sai ya yi mata faɗa, domin gudun gobe kada ta sake zuwa ta shiga wata muguwar dabba ta yi mata illa, so dalilinsa na farko Autar baya son ayi mata faɗa, dalili na biyu kuma shi kansa, shi ma ya karya doka ya shiga cikin wajen, sannan kuma ya taɓa mata jiki laifi mafi girma ma kenan ya aikata. Ganin warriors ɗin suna rinkaro ta in da suke ne yasa ya yi saurin zame hannunsa daga bakin nata ya miƙe tsaye, a hanzarce ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa suka ɓuya a bayan wasu dogaye kuma cunkusassun flowers dake ɗan nesa da wajen da King ɗin yake zama. Ita kam ta kasa iya ko motsawa, abin ya yi mugun bata mamaki, bata taɓa tunanin zai taɓa jikinta ko da sunan wasa ba. Ko da suka ɓuya a bayan flowers ɗin bai sauketa daga jikinsa ba, da alama baya son ta taɓa ƙasan wajen, dan ba takalma a kafafunta, ta zubar da su a garin gudunwa dawakai, kuma fa yaki yarda ya juyo su haɗa ido ko da sunan wasa, duk da a takure suke a bayan flowers ɗin dan ba faɗi ne da wajen ba, sai ya mannata da faffaɗar kirjinsa ya juya mata face ta wani ɓangaren. Ita kuwa da bata da burin da ya wuce daga face ɗinsa dama sai ta kai hannunta saman face ɗinsa, juyo da face ɗinsa ta yi ya zamana suna fuskantar juna, ƙasa ya yi da idonsa yaki yarda su kalli juna, ɗayan hannunta ta kai zata cire hular yakin nasa dan yau kam ta ga face ɗinsa. ____________________________🔥 CHUCHU AND JAWAD A can cikin gida kuwa bayan sun kammala cin abincin nasu ne ya ce ta tashi su je wajen Momma, daga nan sai ta yi wanka ta cire kayan barcin jikin nan nata. Da okey ta amsa mashi. Ko sallamar Aunty MieMie basu yi ba, su Yah Jawad buƙata ta biya masoyiya ta dai'na zarginsa ko neman Aunty MieMie ba za'ayi ba, Aunty MieMie kam tana nan zaku zo ku sameta ne, zata yi maganinku ne. Kai tsaye cikin gida suka nufa, ya riƙo hannunta suna tafe suna hira kamar wasu abokai, sai rigima take yi mashi yana biye mata, yau dan dolensa ya koyi rarrashi dan kada ta sake gudunsa kamar na baya. Dai'dai tsakanin part nan mummyrta da hanyar zuwa part ɗin King, hanyoyin sun rabu uku ne a wajen, akwai wanda zai sadaka da parlourn King, ɗayan kuma part na mummynta da yake itace uwargida ran gida, ɗayan kuma hanyar zuwa part na momman Auta, to a jikin na mommar ce na Maman Gimbiya Aneesa yake. To a dai'dai tsakiyar hanyar ne suka hango Akka tana nufar parlourn King, sai kaɗa kai take yi a cikin alkyabbarta, daga gani wani ya yi mata ba dai'dai bane zata kai shi ƙara wajen King, wlh Akka duniya ce, ka sake ka shiga gonarta ka shiga uku, yanzu fa wai kwana biyu bata ga Jaish bane take wannan sababin, za ta je ta kai kararsa wajen King a kan baya zuwa gaisheta ne, idan kuma suka je wajenta nan ma rigimace, in basu je ba laifi, kai wannan tsohuwa ba mai iya mata sai su Guyson. Cike da murna Chuchu ta wage baki ta ce. "Akka ina zaki je?........". Ai bata ƙarisa maganar ba ya toshe mata baki tare da fisgota ta faɗa jikinsa, kafin Akka ta juyo ya yi baya baya ya shige hanyar ɗakin Mummynta. Shiru Akka ta tsaya tana jin kamar dai an kira sunanta, juyowa ta yi sai taga hanyar wayam babu kowa, girgiza kai ta yi tare da cewa tabbas ta ji an kirata, amma bari ta duba ko su waye ne?. Ita kuwa Chuchu yanzu ta fahimci cewa Yah Jawad yana gudunwa Akka ne a duk lokacin da suke tare, dan haka sai ta ƙudurta a ranta wlh sai ta rinƙa yi mashi tsiya a duk lokacin da suke tare suka haɗu da Akka, ba zata kyale shi ba, lokacin ɗaukar fansar wahalar da ya rinƙa bata a baya ya yi. Motsin alamar kamar mutun na zuwa ta part na mummyn nata ne yasa suka mayar da kallonsu wajen, ga kuma Akka tana zuwa duba waye ya ƙirata?..............................Fata na dai Allah yasa Akka ta kamasu ta yi wa Yah Jawad ihun kwarto🤣 dan wlh kaɗan daga aikin Akka ta ce lalata mata jika zai yi, dama suna da jikakkiya a ƙasa, ta ce su yi aure sun kai karanta wajen yayanta King Badeen wai ta saka masu ido, shiyasa kuka ga ake ta wannan ƴar tsaman tsakaninta da su, dan kuwa sun kai karant an yi mata faɗa a kan ta kyalesu su ƙara girma kafin su yi aure ne😅 wlh King Badeen ma ya iya goya masu baya, shiyasa fa Akka bata raga masu, dan suma basu raga mata wajen kaita kara, gaba da gabanta ne, to su sun riƙe can ƙololuwa sun fita iko, ita kuma ta riƙe iyayensu tana sanyasu yin abu dole🤣 ana show a wannan kingdom ɗin wlh. Na yi maku long page a tashi Kaina da ruwan Comments dan gobe na yi maku fin haka yawa, ga shi gobe zamu shiga weekend, so a zage ayi comments kila na baku update weekend din ma idan kun farantan. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 4/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘STEP TWO....✍️📚🔥 E__________16 KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 Motsin alamar kamar mutun na zuwa ta part na mummyn nata ne yasa suka mayar da kallonsu wajen, ga kuma Akka tana zuwa duba waye ya ƙirata?. Rasa mafita Yah Jawad ya yi, tunani yake yi ya zai yi da Akka? Dan da Mummyn Chuchun ta kama shi da ƴarta gara mashi Akka ta kamashi, yana jin kunyar mummy sosai, Akka kuma gobara ce daga kogi, sai Allah ne kaɗai zai iya kashe ta, idan ta fara bala'i ba mai iya mata sai yayanta su King. Da alama mai nufosu ta part ɗin mummyn waya yake yi, dan yana irin ya je gaba ya dawo bayan nan alamar waya tana daɗi. Shiru ya ɗan yi yana sauraron takun tafiyar mai nufosun, sai ji ya yi kamar Gimbiya Sarina ce, wato sistersa ƴar Mammie kenan, hakan yasa ya ƙara ɗaure fuska sosai, dan in ta gansu a tare da Chuchu raini ne zai shiga tsakaninsu. Bashi da mafita dai a yanzu, ita kam Chuchu ko a jikinta, sai ma tsiya da take son yi mashi idan Akka ta ƙariso wajen. Ɗan raba jikinsa da nata ya yi tare da zuwa hannun a aljihun wandonsa. Handkerchief fara tas mai shegen kamshi ya ciro, sannan ya matso bakin hanyar. Haba wa Akka na isowa wajen saboda tsiya irin nasa sai ya ware handkerchief ɗin nasa ya rufe mata fuska da shi tare da toshe mata baki dan kada ta yi mashi ihu. Da ido ya nunawa Chuchun hanyar part ɗin momma a kan ta tafi. Ita kuwa dan tsiya sai ma kara jingina da jikin bangon wajen ta yi alamar ba zata tafi ba, baya son buɗe baki kada Akka ta ji voice ɗinsa, yasan tsohuwar nan sarai ta haddace voice ɗin kowa a gidan nan except voice na twins Obaid and Omaid, ai waɗan nan twins ɗin wlh ko Jaish baya rabe voice nasu, ko King baya rabesu, mommarsu ce kawai take rabesu, ita kaɗai ce ko a duhu ta laluɓasu zata rabe Obaid ta cire Omaid. Yanzu yana yin magana zata gane voice ɗinsa. Dan haka sai ya sake nunawa Chuchun hanya a kan ta gudu, ai kuwa make mashi kafaɗa ta yi a kan ita gaskiya ba zata tafi ba. Kamar zai yi kuka, ga Akka kuwa tana ta ƙoƙarin kwace kanta ya toshe mata baki ga rufe mata ido da ya yi, sai ƙoƙarin taɓa jikinsa take yi dan ta tantance jikin waye ne ya yi mata wannan ɗanyar aiki, tab wlh idan ya kuskure Akka ta kwaci kanta ya shiga ɗari biyar ba uku ba. Chuchu da tsiya taki tafiya, kamar zai yi kuka ya marai rai ce mata fuska yana bata hakuri ta hanyar motsa lips ɗinsa, kin yarda ta yi ta make kafaɗa tana toshe baki da hannunta saboda dariyar mugunta da ke son cubce mata. Sai da ya wahala, Akka ta kusa kwatar kanta sannan Chuchu ta fara tafiyar yanga dan iya shege, har da wani murguɗa bashi good bye ɗinta tana tafiya cikin saiɓi kamar hawainiya, ji yake kamar ya jawota ya kifa mata mari, amma ba hali, zaman lafiya yake so da ita, haka ya hakura ya toshewa Akka baki yana kallonta har ta wuce ta hanyar part ɗin momma ta kurewa ganinsa. Sai da ya tabbatar ta yi nisa sosai, sannan ya ja Akka har parlourn King, yana zuwa ya turata saman sofar King ya juya da gudun gaske ya bar parlourn. Ai kuwa a ɗari Akka ta miƙe ta fara surfa bala'i wai tasan wlh ɗaya daga cikin jikokinta ne suka yi mata hakan, ko Jaish ko Jawad, dan sun fi kowa rainata a gidan nan, wlh ɗaya daga cikinsu ne ya yi mata hakan, dan haka ba zata kyalesu ba, dole King Zuhair da uncle Abbas su zo su ɗauka mata fansa, wlh ba zata yafe ba, har da cewa ita dai bata yi sa'an jikoki ba, har da karawa da cewa jikokin nata kamar masu karɓar huɗubar shaiɗan..........😂 King dake ɗakinsa yana shirin fita fada ne ya jiyota sai surfa masifa take yi. Hakan yasa ya fito da sauri. A zaune saman sofa ya sameta. A hanzarce ya kariso wajenta yana tambayarta lafiya?. Ai ina a fusace ta ce ya kira mata Abbas da Jahiz a waya duk su bar abin da suke yi su bi jirgin safe su zo, sai sun zo sun haɗu zata faɗi abin da aka yi mata.......... Kai wannan mata akwai rikici, rikitacciyar tsohuwa ce, uncle Jahiz dake ƙasar Brazil, shi kuma uncle Abbas ya tafi ƙasar China baya nan, amma dan balai saboda ta nunawa su Jawad ita take da su shi ne sai an haɗo mata kan iyayen nasu dukka, kai Akka duniya ce, kar ka sake ɓatacciya ta haɗoku, ba zata kyaleka ba, iyayenka zata sa a gaba, kana ji kana gani ranka na kuna ta zagesu tsab shi ne ta ɗauki fansa.........😂 King dai bashi da zaɓin da ya wuce ya bi umarninta, dan sai surfa masifa take yi, ɗaki ya koma ya ɗauki wayarsa, yau Yah Jawad ya ɓallo ruwa, kingdom of power yau ba zaman lafiya. Number uncle Jahiz king ya fara kira. A lokacin da kiran ta shigo wayarsa yana zaune a saman wata iriyar luxury sofa wadda babu irinta ma a yankin Africa, kuɗi ta zauna mashi, tsayawa zayyana maku Daular guy ɗin nan ma ba zai yiwu ba, domin kuwa babu irin wannan ginin a Africa ma gabaɗaya, dollars ta yi kuka ta kuma yi mubaya'a, kun fa san manyan ƴan kwallon nan ba ƙaramin dukiya ne da su ba, bare shi Jahiz da yake shararren ɗan kwallo da kowacce team ke son sayansa ya buga mata kwallo, dan kuwa in ya shiga filli fa jama'a har wani irin ihu da fito na musamman suke yi, idan ya riƙi kwallo ba mai iya kwata ta daɗi a hannunsa. Sai dai fa shi ɗin jinin mulki ne ke gudana a jininsa, akwai shi da izza ga shegen iya shariya, baya kula masoyansa ko kaɗan, ko ɗaga idanu baya yi ya gansu, amma a haka kuma suke haukar kaunarsa, idan ba wasan team nasu ba ma dayawan jama'a basu son zuwa. A baya Manchester united yake bugawa kwallo daga baya real Madrid suka saye shi da, billions suka sayesa, dan yana da tsada sosai, ɗan kwallo ne mafi hazaƙa. A gaskiya ma shi ya fi King Zuhair ma kuɗi ba uncle Abbas ba tukun nan, ya samu duniya kam iya duniya saura lahira. Zaune yake a saman sofa daga shi sai short jessy trouser zuwa gwiwa, ta sama kuma single ce fara tas, jessyn jikinsa ma ba ƙaramin dukiya aka narka wajen sayansa ba, ga su da shegen kyau. Guy ne iya guy, da ka gansa ka ga King Zuhair, babu banbanci kamar shi yake binsa wajen haihuwa, amma bashi bane, uncle Abbas ne, arab guy, fari tas da shi, ga hanci har baka, dollars ta zauna sosai, jikinsa har wani kyalli yake yi, cikakken namiji ne sosai, da ka gansa ka san ɗan kwallo ne na gasken gasken. Kafafunsa na sanye da sillpers na cikin gida masu bala'in laushi, ya yi crossing leg ɗinsa, hannunsa na riƙe da tsadaddiyar cup na cappuccino haɗaɗɗiya yana sha cike da class. Tsadaddun wayoyinsa ne a saman luxury glass table dake gabansa, ga wata tsadaddiyar laptop a gefe guda saman table ɗin, wannan parlourn nasa kamar ba'a duniya kake ba zaka ji idan ka shiga, su kansu sofas ɗin nasa kamar wasu jirage luntsuma luntsuma da su. Wani irin daddaɗar kamshin mai kwantar da hankali ne yake yashi a ko'ina cikin parlourn, ga sanyi Ac mai ratsa zuciya. Sai dai kash dukka wannan alatun nasa bashi da mata, katan gwauro ne bai cika cikakken namiji ba. Picking call ɗin ya yi cikin nutsuwa, da alama yana da nutsuwa sosai da sosai, komai cike da class yake yi. "Good morning bro!". Ya faɗa kamar baya son motsa baki, voice ɗinsa sak na King Zuhair, sun yi kama sosai gaskiya, jini ba wasa ba. Daga can King ya ce. "Akka ta ce ku bar duk abin da kuke yi tana son ganinku yau". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Bro I have something very important to do, but me yake faruwa take son ganin mu? Ina da wasa champions league gobe fa". Nisawa King ya yi. "Kai da ita ne wannan, ni dai na isar da saƙo, ka kira Abbas ka sanar da shi". Daga haka King ya katse kiran. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mayar da wayar ya ajiye. Shi kuwa King komowa parlourn ya yi ya hau rarrashin Akka a kan tazo su je ciki ta gaya mashi me aka yi mata?. Shi kam Yah Jawad bin bayan Chuchun ya yi izuwa part na Momma abinsa, bai san Akka ta tada balli ba. A parlourn ya iskota tana tsaye, ai tana ganinsa ta watsa a guje ta nufin ɗakin Momma, sai dai kafin ta shiga shi ma ya tako da gudu ya riƙota, ashe tasan ta yi mashi laifi, tasa shi ya kusa yin kuka. Riƙo west ɗinta ya yi, wage baki ta yi zata yi mashi ihu ya yi saurin rufe mata baki. "Yau sai kin gaya mun idan ni sa'an wasan ki ne? Nace ki tafi sai kika tsaya kina ganina ko? Wlh saura ki gayawa Akka ni na rufe mata ido zaki ga yadda zamu ƙare". Ya faɗa yana ɗaure fuska kamar ba shi ne ɗazun ya marairace mata fuska kamar zai yi kuka ba, yanzu kuma da ya samu ya kuɓuta daga haɗuwa da Akka shi ne zai nuna mata jan ido. Fitowar Momma daga room nata zuwa parlourn ne yasa ya saketa tare da juyawa zai bar part ɗin. "Zo nan Jawad". Momma ta faɗa tana nufar saman sofa. Da gudu Chuchun kuwa ta nufi cikin room ɗin abinta, ta samu Momma ta kwaceta. Tana shiga ta faɗa saman sofa dake cikin room ɗin ta hau tiƙar dariya kamar zararriya, sai ta yi dariya sosai sai ta ɗan tsaya shiru, idan ta tuna yadda ya marairace mata fuska kamar zai yi kuka ɗazun sai ta sake watsewa da dariya kamar ba lafiya ba. Shi kuwa Momma ta zaunar da shi ta shiga gaya mashi ya kula sosai, dan yana da tarin makiya a tarayyarsa da chuchu, dan haka ya ɓuye soyayyarsa, kada ya bari ma a rinƙa ganinsu a tare, ya yi kamar ya mance da ita ko sun rabu, dan wanda ya yi ƙoƙarin rabasu ɗin ya ji daɗi ya kuma ciresu a ransa kada ya kara haɗa masu wani tuggun, idan ta samu lokaci ta zauna da king zata gaya mashi batunsu, sai a sanya masu rana ayi bikin kowa ya huta, amma yanzu ya kula ya kuma ɓoye batun, sannan ya tsananta addu'a sosai, dan abu ne da ya haɗu da mushirikai, so ya kula sosai. Sosai ya ji daɗin maganganunta, addu'a ya yi ta zuba mata, sannan ya ce mata ta yi mashi izini gobe yana son zai bi bayan Jaish ya duba shi. Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Bin bayan Jaish ba zai yiwu ba, zan kira yayansa ya bi bayansa, amma kai kam ba zai yiwu ba, dan kasan cewa baya nan kai ma baka nan daddynku ba zai yarda ba, dole zai san akwai matsala, dan haka kai ka tsaya a nan kana ɗebe masa kewa kuma kasan yadda zaka yi da shi idan ya tambayi ina Jaish ɗin, zan sanar da yayanku ya nemo Jaish ɗin a koma ina yake". Jinjina kai ya yi, ya gamsu da maganarta, amma kuma yana tunanin anya zai iya hakuri bai je ya duba ɗan uwansa da kansa ba kuwa? Kai abin akwai wahala. _________________________🔥 Auta. Hannu ta kai zata cire mashi hular, a hanzarce ya riƙe hannun nata da nashi hannun ɗaya, sannan ya ɗago idanu yana kallonta. Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. "Fuskarka nake son gani fa! Kullum kana tare da ni amma ban taɓa ganin kamanninka ba, to ni ba zan yarda ba, kai ba ka kalli face ɗina ba?". Mai da kallonsa kan warriors dake nufar gate ɗin fita dan basu ga kowa ba ya yi, sun hakura zasu fita daga wajen kawai. Zuba masu ido ya yi har suka fice a wajen, sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Sake hannunta ya yi tare da miƙewa tsaye da ita, sauketa daga jikinsa ya yi, sannan ya nufi hanyar ficewa daga wajen ba tare da ya yi magana ba, da alama magana tana yi mashi wahala. Tafiya yake yi yana tunanin ta ina zasu fita wajen nan ba tare da angansu ba? In dai suna son fita salum alum to dole sai dare, fitarsu da rana ba zai yiwu ba. "Hoorain". Ta ambaci sunansa tana kumbura kumatu. Tsayawa cak daga tafiyar da yake yi ya yi, a hankali ya juyo gareta, sai kuma ya kawar da kallonsa a kanta, da alama yana ƙoƙarin hana idanunsa kallonta ne dan tsaro ba dan tsoro ba. "Na'am ranki ya daɗe". Ya amsa yana mayar da hannayensa baya ya harɗesu. "Meyasa baka son na kallin face ɗinka?". Ta faɗa tana ɗaure fuska. Ɗan risinar da kansa ƙasa ya yi. "Sorry ranki ya daɗe baya daga cikin aiki na ne shiyasa". Hannu tasa ta riƙo west ɗinta tare da ɗaure fuska. "Dama aikin da kake yi ma akwai wanda yake ce maka ga abin da zaka yi ne? Ai na ɗauka kawai aiki zaka yi". Jinjina mata kai ya yi alamar e umarni yake karɓar kuma ganin fuskarsa bata daga cikin umarnin da aka bashi a wajen aiki. "To ni yanzu na baka umarni ina son ganin face ɗinka". Ta yi maganar tana nufo shi. Ɗan juya idanunsa ya yi yana kallon hanyar da take takawa, da alama shi ma baya son ta ga face ɗin nasa, ko me dalilinsa? Wannan sai alƙawarina. Ƙasa ƙasa yake satar kallon yadda take tafiya cikin nutsuwa sosai har ta ƙariso gabansa. "Please remove this thing let me see your face". "Sorry ranki ya daɗe, why are you want to see my face?". Still yana kallon ƙasa ya yi maganar. "Because you're the only person da ban san yaya face ɗinsa yake ba a cikin warriors mafi kusa damu, kuma i want to see it now". Dawo da kallonsa cikin idanunta ya yi, wani irin faɗuwar gaba ya ji da ganinta cikin idonta da ya yi, bai san meyasa yake jin faɗuwar gaba a duk lokacin da suka haɗa ido ba, shiyasa baya son haɗa ido da ita, yana jin wani irin shock a jikinsa duk lokacin da ya ga face ɗinta, ko daga nesa ya ganta sai ya ji zuciyarsa ta amsa. "Please ranki ya daɗe kada ki sanya na karya dokar aikina, kinga yau a dalilinki na aikata abinda King ya hana, na aikata laifi, yanzu haka ni mai laifine sosai, and am sorry to say please ki daina yi mun magana kada ki ja wani lokaci ƴan uwanki su yi maki faɗa, kinga gabaɗaya ƴan uwanki basu son kina yi mun magana, a gaban idanunki ranar Prince Jaish ya daka mun warning a kanki, and kin ji abinda Prince Ramish ya gayawa Abbuna a waya wancan karon, a gaban idanunki dukka aka yi hakan, ni bawa ne kawai mai baki kariya, ko ba haka Prince Jaish ya ce mun wacan ranar a gabanki ba? Please ki bari kin ji? Bana son Abbona ya ɓata rai saboda hakan, ba zai ji daɗi ace ya hanani yin abu kuma ina yi ba, ke yarinya ce mai zuciyar zinari, amma am sorry to say ƴan uwanki ba haka suke ba, ke baki banbanta bayi da kanki ko mayaƙa da kanki dan kina kallon darajan ɗan adam, amma ƴan uwanki ba haka suke ba, bayi ko mayaƙa daban suke a gabansu..........". Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon ido da ta zaro mashi, ta ɗan bashi tsoro kuma ta ƙara yi mashi kyau. "Yanzu Hoorain ƴan uwana kake zagi a gabana?". Tana faɗar haka ta fara ruwan hawaye. Dukar da kansa ƙasa ya yi yana faɗin. "Am so sorry princess, na yi kuskure ina neman ki mun afuwa". Kin kula shi ta yi, kuka ta cigaba da yi har da cewa sai ta gayawa Abbonsa abin da ya yi mata, ya ci mutuncin ƴan uwanta a gabanta. Hakuri ya fara bata yana faɗin ta yi mashi duk abin da zata yi mashi na hukumci, amma dan Allah kada ta gayawa Abbonsa, baya son ɓatawa mahaifinsa rai. Wucewa ta yi ta nufi cikin wasu bishiyoyin lemu dake ɗan nesa da in da suke. Cikin takun jarumta ya rufa mata baya yana cigaba da bata hakuri. A jikin bishiya ɗaya ta jingina tana cigaba da kukanta. Gabanta ya ƙariso, cikin girmamawa yake bata hakuri. Rufe idanu gam ta yi taki kallon in da yake ma bare yasa ta dai'na kuma. Zubawa face ɗinta idanu ya yi yana kallon yadda zara zara eyelashes ɗinta da suka jike da hawaye, ga hawayen a saman kumatunta, ji yake yi kamar ya sanya hannu ya goge mata hawayen nata, baya son ganinsu a face ɗinta, amma yana tsoron ƙara laifi kan laifi dan haka sai ya shafawa kansa ruwan sanyi ya haƙura. Yana ɗago idanu sai kan wani katon kunama a jikin bishiyar da ta jingina ɗin yana nufota, ga shi ya ɗana ƙarinsa zai yi harbi. Ai bai san lokacin da ya matso dab da ita ya sanya hannu ya kamo kunamar ba. Ita kuwa jin mutun ya matso kusa da ita yasa ta waro idanun nata waje, ganin shi ne ya matso dab da ita yasa ta yi ƙasa kaɗan ta matsa gefe guda sosai. Tana yin gefe ta ga ya kama kunama, ai ƴar kara ta saki tare da barin wajen a guje ta nufi wajen da King yake zama in da ya kwantar da ita ɗazun kenan. Shi kuwa ya yi saurin kaiwa kunamar hannu, ga shi ta ɗana zata yi harbi, aikuwa yana sanya hannu ta sake mashi harbi, sam bai damu ba tun ya kamata bata harbi gimbiyarsa ba. Sakinta a ƙasa ya yi ya taketa da wannan kakkarfan takalmar nasa ya kasheta. Nan take hannunsa ta fara yi mashi zogi ta kuma kumbura sosai. Da yake jarumin gaske ne sai ya juya ya bi bayanta ba tare da ya damu da zogin da hannun nasa take yi mashi ba. A saman shinfiɗar carpet ɗin dake wajen ya zauna. Tun da ya nufota ta zubawa hannunsa da ya kama kunamar idanu tana ganin yadda wajen ya kumbura sosai, zaro idanu ta yi tana cigaba da kallonsa har ya ƙariso ya zauna. Nan take ta dakatar da kukan da take yi. Yana zama ta sauko ƙasa kusa da shi, duk da tana tsoron kunamar hakan bai hana ta kama hannun nasa dan ta gani ba. Wash ya ɗan furta saboda riƙo hannun da ta yi. Cikin sauri da raunanniyar murya ta ce mashi sorry, ta yi maganar kamar zata yi kuka. Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma so da yake yi ya kwaci hannunsa daga riƙon da ta yi mashi. "Me zan kawo maka ka shafa a wajen?". Still kamar zata yi kuka ta yi maganar. Ɗago da kallonsa izuwa kanta ya yi da nufin ya ce mata ta bari amma sai ya kasa, da suka haɗa idanu sai ya kasa iya ce mata ta sake mashi hannu, shiru ya zuba mata idanu, ita ma kallonsa take yi tana begen ganin face ɗinsa, bata san meyasa yake mugun burgeta ba, ko dan yana bada ransa dan kula da ita ne? Sun shagaltu da ganin juna, a hankali ta ɗago ɗayan hannunta ta kawo saman face nasa da nufin ta shammacesa ta cire mashi wannan hular, ita dai ta matsa sai ta kalli face ɗinsa. Ai kuwa shima ɗago ɗayan hannunsa ya yi ya riƙo hannun nata ya hanata. Turo baki ta yi tare da fara ƙoƙarin kwace hannunta daga nashi. Ba musu ya saketa, yana saketa ta sake kai hannun nata ita a dole yau sai ta cire taga face ɗinsa. Ai kuwa wannan karon da karfi ya damko hannun nata tare da janyota ta faɗa jikinsa, matso da face ɗinsa dab da tata ya yi da nufin ya yi mata magana yadda zata fahimtar ta daina ƙoƙarin cire mashi hular, amma suna haɗa ido sai ya kasa yin magana, zubawa juna idanu kawai suka yi, sai kallonsa take yi tana mamakin irin idanunsa, suna burgeta sosai da sosai, ita gabaɗayansa ma daga sama har ƙasa burgeta yake yi. She love everything about him. Da kyar muryarsa ta iya fita, sai sarkewa yake yi ya furta. "Please ranki ya daɗe ki yi hakuri, dan Allah kada ki ja mun aiki babba da ba zan iya ɗauka........." Dakatawa da maganar ya yi sakamakon gera ɗaya da ta ɗaga mashi. "Ka buɗe mun face naka na gani, daga nan ba zan sake abin da nake yi maka ba". Bai san lokacin da ya ce mata. "Waye kuma ya koya maki ɗaga gera ɗaya?". "Yah JAISH". Ta bashi amsa bata kawar da kallonta daga kansa ba. "Kuma ya yi maki kyau sosai". A sanyaye ya faɗi hakan. Mamakin jin abin da ya faɗa ta yi, bai taɓa yi mata magana haka ba, shi daga karɓar umarni sai aiwatarwa ya iya. "Kin barni? Kin hakura da cire mun hula?". Ya faɗa ƙasa ƙasa. Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata hakura ba idanuta a tsaye kyam a cikin nasa. "But why?". Yadda ya yi maganar zaka fahimci ya yi nisa, baya tare da ita, da alama ya mance da wanda yake tare magana kawai yake yi. Mamaki ne ya kara kamata, tunani ta fara yi a kan anya Hoorain ɗinta ne wannan? Guy shiru shiru baya magana, yau tana son ɓata shi da magana, har tunani take yi dama yana magana bayan e da a'a kenan? Yau maganar tasa ma ta musamman yake yinta kamar ba shi ba. "Hoorain to please meyasa kake ɓuye mun face naka?". Kamar zata saka mashi kuka ta yi maganar. "Babu komai, kawai dai baya a tsarin aiki na ne". "Tom shikenan sai wace rana zaka nuna mun?". A takaice ya ce mata. "Sai ranar da Abbona ya yarda na yi hakan". Sai yanzu ta fahimci cewa shi yana aiki ne bisa umarnin babansa, Allah sarki, sai ta ji ya ƙara burgeta, baya son ɓata ran babansa "Amma kai kyakkyawa ne ko?". Da alama ta mance cewa a jikinsa take kwance. Shi ma da alama ya mance. "A'a bani da kyau, ai babu wani kyau da kyansa zata yi tasiri a waje idan kina nan". Ya bata amsa yana cigaba da kallon face ɗinta, daga karshe ma sai ya sanya hannu yana goge mata hawayen face ɗinta na kukan da ta sha. "Yanzu kana nufin kamar yadda Yah Jaish yake cewa nafi kowa kyau a gidan nan da gaske ne?". Jinjina mata kai ya yi alamar e da gaske ne tare da lumshe idanunsa. Cool murmushi ta saki wanda ya ƙara mata kyau dimple ɗinta suka lotsa sosai kafin ta ce. "To bari naje naga madubi". Cikin sauri ya ce "Ai bamu ba fita daga nan sai dare, dan ba hanya". Zaro idanu sosai ta yi har sai da tasa ya kawar da nasa kallon daga kanta. "To ni yanzu me zan ci? And idan uncle na islamiyanmu ya zo karantar da mu ya zan yi? Wanka da sallama dukka a ina zan yi?". Ɗan shafa kumatun nata ya yi bayan ya gama goge mata hawayen nata. "Nima ban san me zaki cewa uncle naku ba, amma dai zan nemo maki abin da zaki ci, sannan zaki yi sallah a nan, kamar yadda na gaya maki sai dare zamu fita daga nan to hakan ne, dan dole fita zamu yi a sace ba tare da kowa ya ganmu ba". Ta fahimci me yake nufi, sai dai tsoro ya kamata, me zata ce wa Mommarta da uncle ɗin islamiyarsu and Gimbiya Chuchu, sannan idan Yah Jaish ko Yah Omar suka kira Momma zasu yi waya da ita ya zata yi?. Katse mata tunanin nata ya yi ta hanyar taɓa mata lips ɗinta a garin shafa kumatunta da yake yi, shi kansa bai san ya yi hakan ba sai da ta zaro ido tana kallonsa ya farga, dan yana shafa kumatun nata ne ya afka duniyar tunani wani abin da bai bayyanar mana ba ya barwa zuciyarsa. Sorry ya furta mata tare da sauketa daga jikinsa ya miƙe tsaye, sai zogi wajen wannan cizon kunama yake yi mashi. Wucewa ya yi ya nufi wajen bishiyoyin dake wajen dan ya nemi maganin da zai saukaka mashi wannan zogin ya kuma cire dafin kunamar tare da ce mata yana zuwa. Da kallo ta bishi da shi har ya kurewa ganinta, yana tafiya cike da jarumta sosai. Yana kurewa ganinta ta koma saman sofar ta kwanta tare da lumshe idanu, kafin wani dan lokaci barci ya ɗauketa. Ko da ya dawo sai ya samu ta yi barci. Tsayuwa ya yi ya zuba mata idanu yana ta kallonta, tsabar shagala da kallonta har ya mance da zogin da hannunsa ke yi mashi, hankalinsa ya bar jikinsa. ________________________🔥💘 A can cikin gida kuwa. Wanka Chuchu ta yi ta canza kayan jikinta, kwalliya sosai ta cancaɗa, kun san ta da shegen iya kwalliya dama, ta yi kyau sosai cikin riga da wando Pakistan dress, ta yafo gyalen kayan a kanta kamar wata amayar, ga shi kalar kayan pink and black sun yi mata kyau sosai. Waje ta nufa bayan ta zuba perfume masu kamshi sosai. Room ɗinta ta nufa. Wayarta ta je ta ɗauko, a bakin bed ɗinta ta zauna ta fara lalauɓar number Yah Rizwan, tana kewarsa sosai da sosai. Bugu ɗaya ya katse kiran ya kirata, shima yana kewarta sosai, sai kiranta yake tun ɗazun bata ɗagawa, yanzu da ya ga call ɗinta ba ƙaramin daɗi ya ji ba, duk da suna tare da Ramish da har yanzu bai motsa ba hakan bai hana shi fitowa waje ya kirata ba, dan yana kewar voice ɗinta sosai. Hira suka fara yi cikin nishaɗi, rigima ta sanya mashi wai ta yi kewarsa kuma tana son ya zo gaskiya ta ganshi ai dama ya ce mata zai zo, hakuri ya shiga bata tare da gaya mata zuwansu ba zai yiwu ba, sai dai wani lokaci. Sam yaki gaya mata saboda an harbi Ramish da bindiga yasa ba zasu zo ba, sai ya ɓoye mata ya ce mata dai sun fasa zuwa wannan karon sai wani lokacin. Kuka ta sanya mashi a kan ita lallai tana son ganinsa, shi ma da yake ya iya sai ya sanya mata rigima a kan to su yi video call su ga juna, kukan shagwaɓa ta sanya mashi a kan ita a zahiri take son ganinsa. Sai da ya rarrasheta sannan ya ce mata dole zai zo ko dan aurensu, yana zuwa kuma ba ɓata lokaci za'a ɗaura aurensu ya wuce da ita Dubai, jin hakan ne yasa ta hakura ta dai'na kukan. Part ɗin Akka ta nufa tana tafiya tana waya, a hanya ta ci karo da Gimbiya Fanan. "Chuchu Mammie na kiranki, wai ki zo yanzu". Cewar Fanan ɗin. "To Aunty Fanan ina nan zuwa yanzu bari na gaishe da Akka tun safe bamu gaisa ba". Da okey Fanan ta amsa mata tare da wucewa room ɗin Momma......... Hmmm Fanan tana son zuwa part ɗin Momma, kuma Mammien ɗin tasu ce ta ce ta rinƙa zuwa dan ta rinƙa yi wa Momma abun kirki tana nuna mata halin kirki ta yadda ko sun samu sun shawo kan Jaish ya yarda zai aureta kada Momma taki yarda, kunga Mammie ta yi dabara, Momma zata ce Fanan yarinyar kirkice mai kyan zuciya, a wayo zasu saye zuciyar Momma, amma kam Mammie ta iya basaja. Amma my people's me kuke tunani game da kiran da Mammien ta yi wa Chuchun? Menzata ce mata?................. ____________________🔥💘 NIGERIA...............JIMETA 🔥💘 Har dare can wuraren 9 bappa yaga su Mahreen basu dawo ba, ya san dai basa kwana a gidan Arɗo, kome za'ayi masu basa yarda su kwana, dan bai koya masu hakan ba. Shi kuwa Jaish tun da ya buɗe idanu ya sake rufewa bai sake buɗewa ba, wannan abokin bappan shi ma ya bada nashi gudumawar magungunar kafin ya wuce nasa gidan. Bappa bayan son fita ya bar Jaish ɗin shi kaɗai, dan haka sai ya leƙa waje ya kira wani matashi dake zaune cikin matasan da suke kofar gidan suna hira. Ko da matashin ya zo sai ya ce mashi jeka gidan Arɗo ka kira mun su Mahreen, and ku taho tare fa. Da to matashin ya amsa sannan ya wuce. Shi kuma Bappan ya koma cikin gida, ya ɗauki abincinsa da Mahnoor ta zuba mashi a kwanonsa ya zauna kusa da Jaish ɗin ya fara ci. Wannan matashi kuwa ko da ya je Mahnoor dai ta ce yau a gidan Arɗo zata kwana saboda tsoron aljani Jaish, Mahreeh kuwa da yake bata da wani tsoro, dama yadda Jaish ɗin ya waro idanunsa ne yasa ta tsorata sosai, hakan yasa ta bi bayan matashin suka komo gida, in takaice maku ma Mahreen kam ta mance ma da idanun Jaish sun bata tsoro, tuni ta shiga shargallen duniya. Tana shiga ɗakin Bappan ta hau gaya mashi ɗazun aljanin nan da ya kawo ya buɗe idanu, ba ko sallama fa ta fara bashi labari, shi kam matashin nan ya juya ya koma abinsa. Mamaki ne ya kama bappa a in da ya ce. "Mahreen kema yanzu kin yarda wannan bawan Allahn aljani ne? Kece kaɗai dama a kauyen nan baki yarda da cewa aljani bane, ko bappa geɗe da ya zo yanzu ya duba shi shi ma ya tsorata da ganinsa, ya dai daure ne kawai ya yi mashi magani, amma ya tsorata da ganinsa" Zama ta yi tare da sanya hannu suka fara cin girkin Mahnoor a tare. "Bappa aljani ne nima na yarda, saboda idanunsa wlh sun kai ukun na Adda Mahnoor da ya buɗesu, suna da girma sosai gasu jajir kamar jini, amma fa ni bana tsoronsa koma aljanin ne, ai ina da karfi, kuma wlh ko aljani ne sai na taɓa kumatunsa, yanzu ma bari mu gama cin abinci nazo na taɓa, ni inaruwa ya je ya yi ta aljanancinsa a can ni dai kumatunsa yana mun daɗin taɓawa, amma bappa wai daman menene aikin aljani ne da kowa yake tsoronsa?". Ta kai karshen maganar tare da ɗage kai sama kamar mai tunanin wani abin, irin bari ta tuna wai shin menene ma aljanin?...... Mahreen manyan ƙasa, wato ita fa dama bata ma san meyasa ake gudun aljani ba, in fact bama tasan me aljani yake nufi ba, wato dai ko Jaish aljani ne sai ta taɓa kumatunsa, gaskiya justice for kumatun Jaish, ya shiga uku da Mahreen, kai wannan yarinya sai shirin Allah. "Mahreen ɗin Bappanta, babu abin da aljani yake yi, kawai dai mutane ne suke tsaronsu, ina Mahnoor take? Taki shigowa saboda tsoron bakon nawa ko?". Cewar Bappa kwairaga. "A'a bappa Mahnoor tana gidan Arɗo, wai a can zata kwana ba zata dawo gida ba dan tana tsoron wannan aljanin". Tana magana tana kai loma abinci bakinta. "Kai kai kai aikuwa ba zai yiwu ba, bari na gama cin abincin nan ki zauna tare da bakon nan nawa in je in ɗaukota". Da to ta amsa mashi ba ko tsoro. Haka suka cigaba da cin abincin suna zuba hira har suka kammala, Bappan ya miƙe ya fito. Wanke hannunsa ya yi ya fice daga gidan zuwa gidan Arɗo. Ita kuwa yana fita ta yi tsalle sai kusa da Jaish, hannunta duk miyar kuka ta rinƙa shafe mashi a kumatunsa mai kama da madara saboda haske, duk da haka bai isheta ba sai da ta lakato ragowar miya daga cikin kwanon nasu, ta sanya ɗayan hannunta ta matse mashi ɗan red lips ɗinsa ta tura mashi miyar da ta ɗebo a cikin baki tana faɗin. "Aljani kai ma yau ka ci abincin da Adda Mahnoor ta girka, wlh Adda Mahnoor ta iya girki sosai, idan ka ci sai kace a ƙara maka, sai ma idan ta dama fura ka ji shegen daɗi". Tana magana tana tura mashi miyar a bakinsa............. Tab ina ga wlh idan Jaish ya kama Mahreen ba mai karɓarta, rayuwa kenan yau Prince Jaish da kansa ne yake shan miyar kuka a hannun Mahreen, wai lallai kuwa wani abin sai ciwo, shi da yake da shegen kyankyani, kuma tsabar iskanci irin na Mahreen miyar da suka ci suka rage take cusa mashi a baki, Innalillahi wannan yarinya ta gama da Jaish kaca kaca, subhanahu ni dai kam kome zata yi ina team ɗinta iya wuya......😂 Duk ta shafe mashi kumatunsa da miya, bayan ta gama ne ta zo ta zauna ta nutsu a gabasa tare da kura mashi idanu kamar mai tunanin wani abin a kansa. Can kuma ko me ta tuna ta hau zuba mashi surutu. "Aljani ka tashi mana, ko dai ku a garinku na aljanu baku tashi daga barci ne? Ka tashi muje kaga masarana a gonar bappa sun fara girma, kullum ina addu'a ruwan sama dayawa ya zo dan masarana ya nuna, zan tsamma idan ya nuna, ka tashi ka ci abinci dayawa, ko dai in ɗebo maka zaka ci ne?". Sam yarinyar nan bata da tsoro. Shi dai yana kwance ko motsawa bai yi ba, yana dai numfashi da take nuna yana raye, bayan haka ba wani abin da zata tabbatar maka da a wani hali yake ciki. Miƙewa ta yi kamar wadda aka mintsina ta fito waje, kitchen ta shige wai zata ɗebo mashi abinci ta zo ta ciyar da shi....... Allah sarki bawan Allah ya samu gata har ciyar da shi za'ayi........😂 Ta ɗebo abincin kenan sai ga bappa, Nenne da kuma Mahnoor ɗin, bappa ya je ya tasosu a gaba, amma da kyar suka yarda suka biyosa, sai da Arɗo ya ɓata rai, shi ma fa Arɗon ganin kyan Jaish yake yi kamar aljani ko rafani haka, dan kuwa shi ma bai taɓa ganin mutun irinsa ba, kawai dai ya daure ne ya ce Nenne ta bi mijinta ita kuma Mahnoor ta bi babanta tun da ya zo da kansa a karo na biyu. Habawa suna shigowa Nenne ta yi maza ta shige ɗakinta da gudu, wai dan ma kada aljanin yasan ta dawo da daddare ya shigo ɗakinta ya shaƙeta. Ita kuwa Mahnoor ta kanƙame bappa tana zare idanu. "Gajin bappa me zaki yi da abincin da kika ɗebon nan? Ko dai baki ƙoshi bane zaki kara?". Cewar Bappan. "A'a bappa na ƙoshi, wancan aljanin zai je na bawa rabonsa a baki, shi kaga bai ci abincin ba". Zaro idanu Mahnoor ta yi tare da cewa. "Ke Mahreen baki da hankali ko? Ke baki tsoro ko? Wlh yanzu dare ne sai kin je ya shakeki kin mutu ai". Ko a jikinta ta ce. "Adda Mahnoor kin cika tsoro, bappa ya ce aljani baya komai, kawai kune kuke tsoronsa, amma baya komai, to ni ko yana komai ma sai na je wajensa tun da yana burgeni". Tana kai karshen maganar ta yi maza ta afka cikin ɗakin. Da sauri bappa ya saki hannun Mahnoor ya bi bayanta dan kada ta je ta yiwa bawan Allah Jaish ɗuren abincin dole, yasan kaɗan daga aikinta kenan. Ita kuwa Mahnoor juyawa da sauri ta yi zata gudu cikin ɗakinsu saboda tsoro sai ji ta yi Hamma Faisal ya kirata daga ta kofar gida. Dakatawa ta yi tare da juyowa. Da yake akwai hasken wata tankar sai ta iya gajinsa. "Hamma Faisal kai ne a daren nan?". A sanyayye ta yi maganar. "Ni ne, na zo gidan nan kafa uku bana samunki sai bappa kawai, ni kuma na kasa iya komawa gida ba tare da na ganki ba". Ya kai karshen maganar tare da shigowa cikin gidan. Kujera ta ɗauko mashi daga cikin kitchen ya zauna a tsakar gidan, sannan ta ɗauko mashi rabon abincinta daga cikin kitchen ɗin ta kawo mashi, ta koma ta ɗebo mashi ruwa a cikin kwarya, ta rufe kwaryar da pai pai, baiwar Allah bata sanar da shi rabon abincinta bane, saboda kyan zuciya irin nata sai ta hakura ta bashi. Ta ci abinci a gidan Arɗo wajen kakanta Inna. Da yake gidan kawunsa ne sai bai nuna wani pulako ba, da alama ya saba cin abinci a gidan, dan haka sai ya buɗe abincin ya fara ci, ɗakinsu ta shige dan ita bata yarda ta yi hira da shi a cikin gida, kai ko a idanun Mahreen bata yarda su yi hira, Mahreen ɗin ma kunyarta take ji, in kunga ta sake tana hira da shi to sun haɗu a wajen kiwo ne ya sameta ita kaɗai tana zaune, daga lokacin da Mahreen ta bayyana a wajen to hiranta da shi ya ƙare, dan ko zai yi magana sau dubu ba zata amsa shi ba, sai Mahreen ta tafi, bare kuma ace bappa ko Nenne suna kusa, ai nunawa take kamar bata taɓa saninsa ba, kullum dare idan ya zo hira to shi da bappa suke hiran, ita dai idan ta kawo mashi abinci sai ta shige ɗaki, idan ya gama hiransa da bappa sai ya tafi sai da safe in sun haɗu a daji, haka ake soyayyar gwanin ban dariya. Tana shiga ta haye gado ta kwanta, already ta yi sallah a gidan Arɗo, kwanciya ta yi ta takure waje guda, dan tana tsoron gidan a yanzu, gani take yi kamar Jaish aljani zai zo ya shaƙeta, sai tunani take yi a kan ita ta ganshi ma ta sa bappa ya kawo shi gidan, idan ma kashewa ne ita zai fara kashewa kenan, tuna haka yasa ta kara takurewa waje guda ta dunkule kamar maggi star. Mahreen kuwa da kyar Bappa ya hanata ɗurawa Jaish abinci, sun sha fama kafin ta hakura, zama ta yi kusa da bappan suka fara hira yana biyewa shirmenta da tambayoyinta marasa kan gado a kan Jaish ɗin ko in ce aljanin nasu, haka bappa ya rinƙa biye mata har san da barci ya ɗauketa, sannan ne ya ji iskar duniya tana kaɗawa, haka ya miƙe ya ɗauketa sai ɗakinsu, a kusa da Mahnoor ya kwantar da ita, hasken farin wata na haska masu har cikin ɗakin nasu. Yana kai ta ciki ya fito tare da zama kusa da Faisal saman kujera da ya ɗauko daga kitchen, hira suka fara yi da Faisal ɗin, kun san fulanin daji da iya hiran dare kamar rana, tsakar dare, zaka samesu zaune suna hira kamar wasu aljanu, ko tsoro basa ji, dare tamkar rana yake a wajensu. Haka bappa da Faisal suka yi ta hira har almost 11:40pm. Sannan ne suka yi sallama, Faisal dai ya cinye rabon abin Mahnoor tas ba tare da yasan rabonta ya ci ba. Dayawan lokuta rabonta take bashi ita ta hakura, dan Nenne kam bata bashi abin. Bayan tafiyarsa ne Bappa ya koma cikin ɗakinsa tare da ɗauko wani tsummar rigarsa ya fito ya jiƙata da ruwa, ɗakin ya koma ya gogewa Jaish ɗin miyar kukan da take saman kumatunsa wanda Mahreen ta shafe shi da shi, tas ya goge mashi kafin ya kwanta a gefensa tare da yin addu'ar barci..ASUBA TA GARI IYALAN BAPPA KWAIRAGA. Washegari da safe kamar yadda suka saba ne, bayan sun yi sallar asuba Mahnoor ta fito ta share gidan tsab, sannan ta je bakin kogi ta ɗebo ruwa kafa uku ta cikasa randunar dake cikin kitchen, bayan ta gama ta hura wuta ta sanya ruwan wankanta ita da Mahreen, da ruwan ya yi zafi ta juye a bakiti ta ɗaura ruwan turo, already suna da ragowar miyan jiya, dama idan zasu yi miyar dare haɗe da na safe suke yi, da safe sai su yi sabon two su dumama miyar su ci da shi. Da yake wutar tana ci sai da ta yi talge kafin ta shiga wanka, ita kaɗai a tsakar gida kamar aljana, tun karfe biyar take wannan aiki, ita kam Mahreen kafin bappa ya samu ta tashi ta yi sallar asuban ma ai sai an kai ruwa rana, wani lokaci da kuka take tashi har ta yi sallah tana kuka, tana idarwa a wajen zata baje ta cigaba da yin barcinta, bata tashi sai an tasheta su tafi karatu, nan ma wani lokaci da kuka take tashi. Nenne kuwa sarauniya uwar mugaye, bata firowa sai karfe bakwai kafin nan Mahnoor ta gama girki ta gama komai, wani lokaci ma har sun tafi karatu. Haka ta kammala duk wani aiki da kuka san mace tana yi a gidanta, kamar matar aure baiwar Allah, ta yi shirinta sannan ta tashi Mahreen a kan ta tashi ta je ta yi wanka su wuce karatu. Da kyar ta yarda ta tashi, tana turo baki ga shegen iya shagwaɓa ta nufi cikin toilet ɗin, ruwan wankan nata har ya huce, dan ma da zafi sosai Mahnoor ta surka mata, ya huce ya zama ba sosai zafin, haka ta yi wankan ta fito, kaya iri ɗaya suka sanya doguwar riga ta atamfa koɗadɗiya. Alqur'aninsu da bappa ya saya masu time da ya je Niger suka ɗauka suka nufi ɗakin bappa, a bakin kofa Mahnoor ta tsaya taki shiga, Mahreen kam tuni ta afka cikin da sauri ta je ta fara taɓa kumatun Jaish, wlh har ja kumatun nasa suka yi saboda taɓasu da Mahreen take yi, sun yi jajir da su, Bappa yana tsoron hanata kada ta tsayar mashi da kukan da ba karewa, rufin asirinsa ya rabu da ita, Mahreen ba kowa yake taɓata ya zauna lafiya ba. Gaishe da bappa Mahnoor ta yi sannan ta ɗaura da cewa. "Bappa zamu tafi karatu". "To Mahnoor ku kula sosai, sai kun dawo". Cewar bappan. "To bappa, Mahreen zo ki wuce mu tafi". Da kyar ta fito daga cikin ɗakin, wai ita a dole a barta ta zauna tare da aljaninta....... (Wayyo Jaish yana ganin rayuwa wai aljaninta kai jama'a maman Yasmin Mahreen bata da kirki sam sam😂) Suna fitowa Nenne na fitowa daga nata ɗakin, nan ta fara surfa masifa a kan ina awakin ta? Ai Mahnoor bata isa ta bar gidan nan ba idan bata je ta kamo awakin nan ta zo ta ɗauresu a cikin walden dake kusa da kitchen wanda aka ɗan kewayesa da ɗan gajeran matanga sannan aka yi runfa da zana daga ta sama, sai tirken awakai da aka kafa a wajen. Miƙawa Mahreen Alqur'anin hannunta ta yi tare da cewa. "Mahreen ki je karatun kada ki yi lattin bari na kamo awakan nasan suna cikin awakan bappa ne, bari na kamosu na dawo da su sai in sameki a karatun". Karɓar Alqur'anin ta yi ta shige ɗakunsu ta ajiye ta fito. "Muje mu kamosu tare, ke kaɗai zasu wahalar dake, kuma zasu sanya ki watsa awakin bappa su baki aiki, muje in tare maki". "Wuce ki ɗauki littafinki ki wuce karatu ba zaki tayata ɗin ba". Cewar Nennen. Ai a take ta turɓune fuska zata saka kuka, ganin haka yasa Nennen ta ce. "Sai ki wuce ki bita ɗin ai chewing gum". Wannan shi ne biyayyar dole, idan aka ki yi mata biyayya taja asiri ya tonu wajen bappa, kai Mahreen duniya ce, yanzu zata yi wa Nenne hauka mai lasisi, rufin asirinta kawai ta barsu su tafi tare. Bappa kuwa yana fama da Jaish da ya ɗan motsa kaɗan, sam hankalinsa baya a kansu bare ya jiyo hayaniyar da suke yi. A tare suka fita, suna fita Mahreen ta ce. "Baga irinta nan ba, ai dama nace maki ki rabu da Nennen nan ta yi ta zama a gidan Arɗo, amma ke gaki mai tsoron Allah, to wlh Nenne ba zata barmu mu zauna lafiya ba da batun shegun awakin nan nata, ni watarana sai na kashesu dukka ma mu huta da masifar safe". Ita dai Mahnoor shiru bata ce ko uppan ba, cikin garken awakin bappa suka nufa. Wata yarinya ce ta zo wucewa ta ce. "Ku ba zaku tafi karatu bako? Lokaci ya yi, sai Inna Rabi ta yi maku shegen duka ai, ku kullum baku gajiya da zuwa a makare, ko da yake baku gajiya da shan duka ne shiyasa". Dakatawa Mahreen ta yi da tafiya tare da riƙe west ɗinta, cikin tsiwa da masifa ta ce. "Ke Abu da su waye kike yi?". Ganin Mahreen ce ta amsa mata yasa a hanzarce ta ce. "Ni ba daku nake yi ba". A tsorace ta yi maganar, da alama tun farko bata lura da Mahreen ɗin a wajen bane, yarinya ƴar karama ta zama zakanya a cikin kauyen, duk ƴan mata tsoron masifar ta dana Nennenta suke yi. "Da mu kike yi nafikijo (munafuka) ai mune kawai a nan wajen, zo nan munafuka!!". Cewar zakanya Mahreen, cikin tsawa ta yi maganar, irin ba wasa a tattare da itan nan. Ai a ɗari da hamshin Abu ta watsa, gudu take yi da iya karfinta. Ɗage rigarta sama Mahreen ɗin ta yi zata rufa mata baya. Da sauri Mahnoor ta riƙota tana faɗin. "To Allah ya yi dare gari ya waye, rikicin duniya dukka sun tashi, wuce mu tafi ki rabu da ita, ke kowace safiyarki da faɗa take farawa, haba Mahreen yakamata ace yanzu kam kin rage jibgar ƴaƴan mutane". Sai wani cija laɓɓa take yi, taso ne ta bi yarinyar ta lallasa mata jiki, har da wani ɗage riga zata yi gudu dan iya balai. Kwafa ta yi tare da cewa. "Wlh idan muka haɗu da ita a karatu sai na cire mata hakwaran bakinta na gaba, gobe ba zata sake kulamu ba, ɗan banza duka zan yi mata sai dai Inna Rabi yau ma ta dakeni, amma sai na gwada mata na fita rashin ji". "To na dai ji, zo ki wuce mu kama awakin nan mu mayar da su mu wuce karatun". Da kyar ta jata suka shiga cikin garken awakin. Awakin Nennen ƙanana ne guda biyar da take kiwatasu a cikin gida, ita sune arzikinta, ji da su take yi, da daddare tana kwamcesu su sha iska, su shiga gidan mutane su yi ta ɓarna a kitchen suna kalitan ƙanzo a tukunya, idan sun gama ne sai su shiga cikin awakan bappa su kwanta, da safe kullum sai Mahnoor ta kamosu ta zo ta ɗaure mata su. Ita kuma Nennen idan ta tashi ko sallar asuba ne taga awakin wasu a kitchen ɗinta ta rinƙa surfa masifa kenan ba ɗaga kafa, ta kama akuya ta yi ta jibga dan ba nata bane....... Allah dai ya shiri Nenne, amma akwaita da son zuciya kam. Ɗaure awakin suka dawo suka yi kafin su ɗauki Alqur'aninsu suka wuce makaranta. Bayin Allan da suka je sai da suka sha bilala bibbiyu na latti. Ana tashi karatun kuma Mahreen ta capke Abu da duka kamar an aikota, kafin Inna Rabi ta zo ta rabasu faɗar Abu ta sha ɗan banza duka da cizo haɗe da yagushi, ta ji mata ciwo a fuska da yagushi. Ai Inna Rabi na dososu ta saki Abu ta watsa a ɗari sai hanyar gida, wlh duk iya shegen Mahreen bata tsayawa a daketa, kaunar lafiyar jikinta take yi amma ta iya jibgar jikin wasu ta yagushesu. Hanyar gida ta nufa sai taga ai Inna Rabi zata iya biyota gida, dan haka sai ta nufi hanyar wajen kiwonsu, saboda izuwa yanzu tasan bappa ya tafi kiwo, a wajen kiwo kuma ko Inna Rabi ta zo hakuri bappa zai bata ta tafi, ba zai taɓa bari a dakar mashi autarsa ba, kafin zuwa gobe su je karatun kuma bappa ya je ya bada hakuri haka ake fama da ita kullum. Ai kuwa hasashenta gaskiya ne, a can ta isko bappa yana zaune ƙasan bishiya. Ita kuwa Mahnoor gida ta nufa dan ta mayar da qur'anansu kafin ta wuce wajen kiwon nasu. Inna Rabi kuma ta ɗauko bayafi tare da riƙo hannun Abu suka bi bayan Mahreen dan ta je ta haɗesu ta ji me ya haɗasu faɗa, bata yanke hukunci ba tare da ta ji ta bakin kowa ba, sai ta haɗesu ma take tambayarsu ta yadda ɗaya na zai cuci ɗaya ba. Ko da Mahnoor ta shigo gidan babu kowa, Nennensu ta shiga maƙota, kun san fulanin daji da shegen iya zuwa maƙota, suna ɗaukar kamar gida ɗaya suke, yanzu yanzu zakaga wannan ta shiga maƙota wannan ma ta shiga nan, rayuwarsu dai akwai ban sha'awa yadda suke kamar ahali ɗaya. Ganin Nenne bata nan ne yasa ta wuce ɗakinsu ta ajiye Alqur'anan, tana fitowa shi ma Jaish yana fitowa daga ɗakin bappa, ya dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi da hannu ɗaya, jiri ne yake ɗebarsa, ya dafe jikin kofar fitowa Ai a ɗari ta.............. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 7/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E_________17 Ai a ɗari ta kurma ihu tare da nufar waje da gudu. Ko kallon in da take ma bai yi ba, shi gidan ma yake bi da kallon kyama da ƙaskanci, daga sama har ƙasa yake karewa gidan kallo, har wa yau idanunsa suna nan jajir kamar jini, da alama akwai abin da ya sami idanun nasa. Mahnoor kuwa bata zame ko'ina ba sai wajen bappa, tana zuwa ta iskosa ya gama case da su Inna Rabi na jibgar Abu da Mahreen ta yi, ya shiga cikin dabbobinsa yana raba wasu shanu guda biyu faɗa. Da kyar ta iya ƙarisawa wajensa a cikin tsakiyar dabbobin, sai haki take yi tana numfashi sama sama. Sam bai lura da ita ta zo da gudu ba, hankalinsa yana kan dabbobin, ita kuma Mahreen tana zaune tana cin gwaiva da bappa ya tsinko mata dan ya yi mata nasiha. Idan kana son zaman lafiya ka yi mata nasiha kuma ku zauna lafiya sai ka bata wani abin. Haka bappa yake yi mata, sai ya bata gwaiva ko rake ta nutsu tana sha sai ya yi mata nasiha a nutse, a haka sai kuga ta ɗauki maganarsa in ta yi niyya, tafa san daidai yarinyar nan, kawai dai idan anyi mata ba daidai bane take mantawa da wani daidai ta rama abinta, amma sarai ta san me take yi. Ganin ta ƙariso wajensa tana ta zuba uban haki ga numfashinta na fita sama sama ne yasa ya yi saurin riƙota yana faɗin. "Mahnoor lafiya kuwa?". Kasa amsa mashi ta yi, saboda uban gudun da ta sha, numfashinta bai dai'dai ta ba bare ta iya yin magana. Hannunta ya riƙo suka fito daga cikin dabbobin, in da Mahreen ke zaune suka nufa. Gorar ruwansa dake wajen ya ɗauko ya bata tare da zaunar da ita a kan ta zauna ta nutsu ta sha. Ba musu ta karɓa ta sha sosai, gabaɗaya a rikice take, sai zare idanu take yi kamar wadda taga wani abin da babu irinsa a duniya, ko da yake a wajensu babu irin Jaish a duniya, dan basu taɓa ganin mai kyau irinsa ba, dole su ɗaukesa kamar babu irinsa a duniya........ Ni kam na ce dan ma ba kuga Guyson nawa and Auta Zunaira ba, ai da kun mace saboda kyau. Sai bayan ta samu nutsuwa ne Bappan ya ce. "Me ya faru Mahnoor?". A matuƙar tsorace take ta amsa mashi da. "Wannan aljanin da ka kawo ne ya fito daga ɗakinka". Yadda ta yi maganar a ruɗe take. Ai bata ƙarisa maganar ba ya yi saurin wucewa yana ce masu. "Ku jirani ina zuwa, ai abin da muketa tsumayi kenan tun jiya, farkawarsa kawai muke fata dama". Kallon Mahreen dake ta sabgar gabanta hankalinta baya a kansu ta yi tare da cewa. "Ke gaji aljaninki ya tashi har ya fito waje". Ta yi maganar tsoro na kara bayyana a saman face dinta. Ai kuwa ita kam Mahreen tsalle ta buga tare da miƙewa tsaye ta ce. "Dan Allah? Wayyo Allah bari na yi sauri na je na gansa". Tana kai karshen maganar ta watsa a guje sai hanyar gida kamar ba yanzu bappa ya ce su jira shi yana zuwa ba. Kafin Mahnoor ta buɗe baki ta dakatar da ita tuni ta wuce kamar wata walkiya, fiw ta wuce kamar iska tsabar iya gudu, daga karshe ma ta riga Bappan nasu isa gidan, a hanya ta wuce shi, kamar bata gansa ba, shi kuwa da ya ganta kafin ya buɗe baki ya kirata tuni ta wucewa ganinsa, yadda kuka san iska haka take da gudu. A dubu sittin ta shiga gidan babu ko sallama. Yana tsaye a in da Mahnoor ta barosa, yana dafe da bango da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya ya dafe kansa yana kallon ƙasa ya sunkuyar da kansa. Kai tsaye gabansa ta nufa a kuje, da kyar ma ta iya taka birki ta kama kanta bata afka jikinsa ba, tsabar yadda ta shigo gidan a guje, gudu ta yi da iya powerta dukka. Sarai ya ji motsinta kuma ya ji gudun da ta yi har ya zamana da kyar ta kama birki a gabansa, amma yadda kuka san babu shi a wajen, sam bai motsa ba bare a yi tunanin ya ji shigowar mutum, da ni da ku dai mun san halin kayanmu daman, mun san ya yake, su Mahreen ne baki a sanin halinsa. "Yauwa ginnaji amin a fini ko? (yauwa alajinmu ka tashi ko)?". Yadda ta yi maganar tana haki zaka fahimci ta saba dallawa a guje, ma'ana ta saba yin gudu, dan bata wani wahala ba, ita kuwa Mahnoor wannan gudun da ta yi sai wani irin haki take yi kamar numfashinta ba zai dai'dai tu ba, amma Mahreen ai shar, wannan da za'a saka gasar gudu a kauye na tabbata sai ta fi kowa, ita zata zo na ɗaya, gata ƴar siririya, haba my people's karku ga yadda take pella kafafu idan ta arce a gujen. Sarai ya ji anyi magana, amma bai san da wani yare bane, dan haka bai gane me aka faɗa ba, kuma dai yaki ɗago kai ya kalli wace aljana ce take a gabansa, dan ma Allah ya rufa mashi asiri yau kwalliya kaɗan ta ɗan yi kafin su tafi karatu da suka yi wanka, sai dai ta cika powder nan nata da ta saba a fuska, amma ba'a lapka janbaki sosai ba, dan Mahnoor ta ce mata idan tasa kaɗan ta fi kyau, sannan yau bata ɓata fuskar da bakin kwalli sosai ba. Ganin bai amsa mata bane yasa ta ɗago da kallonta a kansa, sai a lokacin ta zaro idanun tana kallon tsawonsa da ya fi bappanta, kun san tun jiya a kwance yake, sai yanzu ta gansa da kyau. Ai a ɗari ta ɗaga kanta sama ta kai kallonta saman fuskarsa. Da yake kan nasa tana duƙe ƙasa sai bata wani iya tantance face ɗinsa da kyau sosai ba, amma dai taga kumatunsa da yake jajir saboda mulmula mashi da ta rinƙa yi. Saboda rashin tsoro irin na yarinyar nan hannu tasa ta ɗan taɓa plat tummynsa, dan a iya nan taawonta ya tsaya, ba zata iya taɓa shi a sama da haka ba. Taɓa shi ta yi tare da cewa. "An kam a wala volwa na? (Kai kam baka magana ne?)". Daga hannun nata da ta taɓa shi ya fara bi da kallo kafin ya kai kallonsa saman face ɗinta. A lokacin ita ma tana kallon face ɗin nasa da kyau, ai kuwa suka yi four eyes. Ɗan zaro idanu ya yi da ganin face nata da ya yi, ba komai yasa ya zaro idanu ba face kwalliyar dake saman face ɗinta. Ai kuwa yana zaro idanun nasa da suke ja ta sakesa tare da kurma ihu ta yi baya baya ta faɗi ƙasa, dan kuwa ya bata tsoro, ga idanu manya manya, sannan gasu jajir kamar jini, duk yadda aka yi akwai abin da ya samu idanunsa wlh, dole akwai abin da aka sanya mashi a cikinsu ko kuma ya sanyawa kansa, dan sun yi wani irin ja mai ban tsoro, duk wanda ya kalli cikin idanun nasa sai ya tsorata sosai. Dani da ku dai mun san idanunsa farare ne. Tana faɗuwa ƙasa numfashinta ya ɗauke diff, shi kuwa yana ganinta ta zube ƙasa bai taimaka mata ba, sai ma hannunsa da ya cire daga saman goshinsa ya dafe cikinsa da shi, dan wani irin murɗa mashi da cikin nasa ya yi da karfi, wani irin zafi ya ji shiyasa ya dafeta. Wani irin kwaɓe fuska ya yi saboda kyama, shi Mahreen kyama sosai ta bashi, a ganinsa ta yi datti over, bai san nan ta sha wankarta ba, kayan nata ne kawai suke koɗe kamar masu datti, amma ba wani datti, dan suna da tsabta sosai. Shi kuwa mugun kyama ta bashi, barema gidan nasu da ya kallah, dama tun da ya buɗe idanu ya kalli in da yake cikinsa ta fara murɗa mashi, wannan dalilin yasa ya fito waje ko zai samu sassauci. Ai kuwa yana fitowa ya ci karo da su bukka gidan ƙasa nan take kansa ya fara sara mashi, hakan yasa ya dafe kan nasa ga cikinsa na juyawa. Wani irin amai ne ta kwace mashi. Da kyar ya iya jan kafafunsa ya matsa daga bakin kofar, a tsakar gidan ya dakata ya fara tikar amai mai sautin gaske, kamar zai amayar da ƴaƴan hanjinsa. A wannan hali bappa ya shigo ya samesa, ga Mahreen a sume kwance a ƙasa. Ganin yana ta amai yana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa dan jikinsa babu kuzari ko kaɗan ne yasa bappa bai bi ta kan Mahreen ba ya yi kansa yana yi mashi sannu da harshen fillanci. Hannu yasa ya ɗan riƙosa dan kada ya faɗi, sai layi yake yi kamar wanda ya sha wani abin na maye, a hakan ma kuma wai ya yi ta maza ya rike kansa da ɗan sauran karfin da ya rage mashi. Bawan Allah sai Allah ne kaɗai yasan kwanansa nawa rabonsa da abinci........... Tab akwai cakwakiya, anya Jaish zai iya cin abincinsu kuwa? Anya zai iya yarda ya ƙara minti ɗaya a cikin gidan kuwa? Akwai matsala, already kun san shi da muguwar kyankyani dama, ga shegen izza da suna isa, akwai dai matsala babba!!. A hanzarce bappa ya riƙesa, a lokacin amai ɗin yake tiƙawa da gasken gaske, bai ma san an riƙesa ba, duk in ya tuna kwalliyar kan fuskar yarinyar da ya kallah yanzu wato Mahreen sai cikinsa ta sake murɗa mashi, aman nasa ma banda zallar ruwa dake fita kaɗan kaɗan babu komai, dan babu komai a cikinsa, bai ci abinci ba, sai uban kakari da karfi da yake yi ba wani aman kirki. Ya ɗan jima a sunkuye a wajen kafin ya fara sassauta mashi, wlh ba karya ya wahala matuƙa, dan wannan kakari da yake yi duk ta ƙara nukurkushe mashi ɗan karfin da ya rage mashi, ba dan bappa da yake rike da shi ba da ya jima da zubewa ƙasa, amma Allah yasa bappa ya riƙesa, ya wahala idanunsa sun ƙara yin jajir kamar wuta, wasu siraran jijiyo ne suka fito mashi a forehead ɗinsa, ga wani uban zufar wahala dake tsastsafo mashi a face ɗinsa, harta zara zaran eyelashes ɗinsa sun jiƙe da gumin da ta wanke mashi face ɗin nasa, red lips ɗinsa sai kerma suke yi alamar yana jin sanyi kuma babu kuzari a tattare da shi, arab hairn nan nasa ya watse caka caka kamar bai taɓa sanin menene gyara ba. Lokacin da ya ɗan dawo dai'dai aman ya tsaya, a hankali ya ɗago idanunsa da suka yi mashi nauyin ɗagawa, kai kallonsa ya yi ta gefen da bappa yake dan yaga waye ya riƙesa?. A dai'dai lokacin kuma bappan ya ce. "Allah sarki a yari bone sosai, sannu, joɗu bari mi wandina ma diyam a lota hundukoma be ɓanduma, (Allah sarki ka sha wahala sosai, sannu, ka zauna bari na kawo maka ruwa ka wanke jikinka da bakinka..........." Ai bai ƙarisa maganar ba ya dakata sakamakon turesa da Jaish ɗin ya yi gefe guda har sai da ya faɗi ƙasa. Tattare dukkan sauran karfi da suka rage mashi ya yi ya ture bappan tare da zubewa ƙasa a saman gwiwowinsa ya cigaba da yin kakarin amansa, sai dai aman taki fitowa, da alama ruwan dake cikin nasa ne ya ƙara. Ba komai yasa ya ture bappa ba kuma face kyama, a cewarsa bappa na wari, sannan ya ji kyamar kayan jikinsa......... Ni kam nace zan ga wannan cakwakiyar ya zata ƙare, yo idan bappa yana maka wari zanga mai yi maka magani, kai in short ma zan ga wanda zai taimaka maka ka tashi daga wajen da kake yin aman ma kafin aje ga batun magani, gaskiya da babbar matsala!!!. Bappa dattijon kirki miƙewa ya yi tsaye, sam shi bai kawowa ransa kyamansa yasa Jaish ɗin ya turesa ba, ya yi tunanin ma ko dai Jaish ɗin ya ɗan samu wata matsala a ƙwaƙwalwarsa ne, dan haka sai bai damu ba ya kaɗe jikinsa tare da sake matsowa ya riƙe kafaɗun Jaish ɗin ya yi mashi sannu cikin sanyin murya, ga Mahreen kuwa a sume kwance a ƙasa, duk yadda bappa yake kaunar yarinyar nan amma ya nufi Jaish dan ya karrama kalmar nan ta bakonka annabinka, sarai kuma ya ga Mahreen ɗin, amma saboda kyan zuciya irin nasa sai ya zaɓi ya fara taimakawa bakon nan nasa, bai san cewa bakon nasa iyashegensa in ji Yah Jawad tana da yawa ba, i really like Yah Jawad, musamman yadda yake faɗarwa Jaish ɗin gaskiya, ga shi ya gaya mana gaskiya rashin kunya yake damun Yah Jaish ba kunya ba...........😂 Ko ya zai yi a karo na biyu idan ya ɗago ya ga still bappa da yake kyama ne ya riƙesa?...... To ni dai bari na leƙa Dubai mu gani. DUBAI.......ABU ABDUSSALAM EMPIRE🌹 Kamar yadda ƴan tahalikan nan suka faɗa haka kuwa a kayi a gidan suka sake kwana. Washegari da safe tun karfe biyar da suka tashi suka yi sallar asuba basu mayar da barci ba. Misalin karfe 5:30 suka tsala wanka, Obaid ne ya fara yin wankar bayan ya fito Omaid ya shiga. Da yake su a dukkannin gidajen uncles ɗin nasu suna da kaya a rooms ɗinsu sai suka shiga dressing room ɗin suka fara shiri. Wando three cuter na ɗaya daga cikin uniform nasu na swat suka sanya a jikinsu, sai farar t-shirt mai karamar hannu mai laushi sosai. Wow arab hairn nan nasu ya sha gyara na ƙin ƙarawa, sun yi kyau sosai, bafa zaku taɓa iya rabesu ba. Komai nasu gwanin birgewa da ban sha'awa, suna kaunar junansu over, ga su da shegen son wasa da juna, yanzu haka da suka shiga yin brush bayan tashin su daga barci sai da suka yi ta tsokanar juna, Obaid na goge bakinsa yana wani lumshe ido irin barci bai isheshi ba, ya ratayo karamar towel a wuyarsa yana goge bakin kamar yana jin tsoron taɓa hakwaran nasa. Da gangan Omaid ya shigo cikin toilet ɗin ya salallaɓo a hankali ya zo ya kwace brush ɗin da yake goge bakin nasa da shi ya sanya a nasa bakin ya fara goge nasa fararen hakwaran. A kule Obaid ya buɗe baki zai yi magana, ruwa Omaid ɗin ya tarfo daga pampom dake wajen wash hand base ɗin ya watsa mashi a fuska, shi ma a fusace ya tari ruwan ya fara watsa mashi ba dakatawa har sai da Omaid ɗin ya gudu ya fita daga toilet ɗin da brush ɗin a bakinsa, ɗauko wata brush ɗin Obaid ɗin ya yi tare da haɗa wani tsadaddun mayukan goge bakin nasu, sannan ya cigaba da goge bakinsa, haka zaku gansu suna wasa gwanin birgewa, amma kada kuso ku gansu suna shiryawa wani mugunta, a wannan part ɗin sam sam basu da daɗin kallo. Bayan sun kammala shirinsu Obaid ne ya fara ficewa waje daga ɗakin. Omaid ya rufa mashi baya, sai dai shi Omaid yana fitowa part ɗin brothers ɗinsu ya nufa, domin ya gaishesu ya duba jikin Ramish, shi kuwa Obaid da hannunsa take ta faman yi mashi kaikayi na ya je ya jibgi waɗan can criminals ɗin ai waje gabaɗaya ya nufa. A ɓangaren Leesharh kuwa, tasata a gaba Sharifat ta yi a kan lallai ta zo su je ta gaishe da Yah Ramish ɗinta. Sosai Leesharh ta tsorata, tana tsoron shiga ta gansu, dan da yake bata da gaskiya sai taga kamar idan suka ganta zasu gane abin da ta zo yi, wannan dalilin yasa bata son zuwa in da suke ko da Sharifat ta buƙaci hakan. Amma da yake yau rashin lafiya ne sai ta ce to su je ta gaishe da su ɗin. Wanka ta yi ta shirya cikin arab abaya mai shegen kyau launin maroon color, ta yi matuƙar kyau sosai da sosai, ta yafa gyalen kayan a kanta, ba make up sai natural beautynta. Fitowa suka yi suka nufi part na su Ramish ɗin, zuciyarta sai dukan uku uku yake yi, fargabarta ɗaya me zata je ta tarar? Wannan shi ne fargabar da take yi. Baki a ɗauke da sallama suka shiga room da Ramish ɗin yake kwance, gabaɗaya family suna a tare da shi except Obaid da yake ɗakin horo yana aikin da ba'a sanya shi ba. Omaid kuwa yana tsaye a kusa da Guyson yana latsa wayarsa, hankalinsa ma baya a tare da su, sai magana Abu Abdussalam yake yi mashi hankalinsa ya yi nisa, chatting yake yi da wata class mate ɗinsu da ta kasance kawar Obaid, Obaid suna shiri da yarinyar, sabuwar zuwa school ɗin ce, ni da ku dai mun san sai hali yazo ɗaya ake abota, to dai da walakin goro a miya a kan wannan yarinyar. Chatting yake yi da ita in da take gaya masu yanzu daddynta zai mayar da ita school su kuma sai yaushe zasu dawo?....... Nikam nace baban wannan yarinya da kasada yake, yarinya mace da aikin swat fisabilillahi, gaskiya bai kyauta mata ba, daga gani ita ma bata jin magana a gida kamar dai su ɗin. Wani irin muguwar faɗuwar gaba Leesharh ta ji lokacin da ta sauke idanunta a kan ƴaƴan King Zuhair, musamman ma Bilal da yake tsaye a kan Ramish dake kwance kamar gawa, haƙiƙa Bilal ya shiga tashin hankali sosai, idan ka gansa gabaɗaya a hargitse yake saboda tashin hankali, sai ka tausaya mashi. Tun da suka shigo ta tsaresa da idanu tana ƙoƙarin tuna a ina ta taɓa ganin face ɗin nan, tabbas ta taɓa ganin face ɗin Bilal a wani waje, to a ina ne? Ta mance, amma tabbas daga fitanta a gidan AAJ zuwa yau akwai in da ta taɓa ganinsa. Sai dai kuma da ta sauke kallonta a kan Dr Raj sai ta kasa iya banbancesa da Bilal ɗin kuma, sai ta shiga ruɗanin waye ta taɓa gani a cikinsu? Kuma basu wani kama sosai, kawai dai jini ba wasa ba, sannan kuma kowani ɗan adam da yadda yake kallon mutun, kai zaka iya ganin kamannin wane da wane amma ba lallai wani kuma ya ga kamannin ba. Bata ƙara shiga fargaba da faduwar gaba ba sai da ta sauke idanunta a kan Ramish dake kwance, Allah ya gani tana tsoron wannan bawan Allah, ba komai ya ja mata wannan tsoro ba kuma face rashin gaskiyarta, yanzu a jikinta tana jin cewa tabbas cutar da shi masu nikaf suke son yi, amma duk da haka bata tunanin kin taimaka masu saboda tana son babanta sama da kowa a rayuwarta. Shiru ta tsaya tsoro da fargaba ya hanata yin magana kuma ta kasa ƙarisawa cikin ɗakin. Omaid ne ya nufo hanyar fita daga ɗakin yana latsa waya, hankalinsa ya yi nisa wajen chat da wancan yarinyar. Yana can yana taɓa waya har ya ƙariso tsakiyar ɗakin, bai ankara ba ya bangaji Leesharh dake ƙoƙarin kauce mashi hanya da ta gansa ya nufo in da take tsaye. Ai kuwa yana bangazarta wayar hannunsa ta faɗi ƙasa. A ɗari ya ɗago kansa tare da zare idanu, ganin itace bai yi wata wata ba ya cire hannu ya dalla mata mari mai sautin gaske wanda yaja gabaɗaya ɗakin suka ɗago idanu suna kallonsa. Ita kuwa a ɗari ta sanya hannun ta dafe ƙuncinta, wani irin azaban zafin marin da ta ji ne yasa ta fara ruwan zafafan hawaye ba tare da ta sani ba. Shi kuwa dama haushinta yake ji saboda suna zargin bata da gaskiya Guyson ya ce su rabu da ita kada su sake dangantata da mutanen banza, haushin hanasu bincike da ɗaukar mataki a kanta da Guyson ya yi ne gaja suka tsaneta sosai. Haushinta da yake ji yasa ya sake ɗaga hannu zai kara dalla mata mari a karo na biyu. Da gudu Sharifat ta ƙariso wajen ta riƙe hannun nasa tare da saka mashi kuka, kafin ta iso wajen ta riƙe hannunsa ma Dr Raj da Rizwan har suna haɗa baki wajen cewa kada ya yarda ya kara mata mari, yanzu ma wannan da ya yi mata bata gama dawowa cikin hanyacinta ba, idan ya kara mata ai sai ta sume. Abbie ne ya kalli Omaid ɗin. "Jeka abinka my son". Ya faɗa. Wucewa ya yi ba tare da ya ɗauki wayar tasa da ta faɗi ƙasan ba, a cewarsa wlh shi ba zai duƙa ya ɗauki wayar ba, idan kuma ya ce lallai sai Leesharh ta duƙa ta ɗauko mashi wayar ba zasu wanye lafiya da brothers ɗin nan nasa ba, bare ma yadda ya ji har suna haɗa baki wajen hana shi kara mata mari lallai ya tabbata ba zasu wanye lafiya ba, hakan yasa ransa a ɓace ya fice daga ɗakin ya kyale wayar a ƙasa tare da fisge hannunsa daga riƙon da Sharifat ta yi mashi......... Ran maza ya ɓac!!. Sharifat ɗin ce ta tsugunna ta ɗauka mashi wayarsa tare da riƙo hannun Leesharh ɗin tana hawaye ta nufi waje. Bata kai ga fita ba Abbie ya dakatar da ita a in da ya ce ta zo. Ba musu ta juya ta dawo garesa, gefensa ya nuna mata ta zauna, hannu yasa ya kwantar da kanta a saman laps ɗinsa har lokacin tana riƙe da hannun Leesharh ɗin bata saki ba. Goge mata hawaye Abbie ɗin ya fara yi tare da tambayarta me abin kukan to, shi ma Yah Rizwan tamyar da ya gefa mata kenan. Cikin kuka ta ce. "Abbie Yah Rizwan wlh I really like Leesharh, because she's so silent innocent and good girl, and marainiya ce, no dad no mum, bata da kowa sai Allah sai kuma ni, meyasa Omaid zai mareta dan sun bugi juna? Jiya Obaid ya mareta bata yi mashi komai ba, su idan basu son mutun sai su yi ta yi mashi mugunta, to ni ina son Leesharh sosai........". Da kyar ta ƙarisa maganar saboda ta tuna cewa Leesharh bata da iyaye. Shi kansa Abbie sai da ya ji wani irin tausayin maraicinta ya soki zuciyarsa, bayin Allah suna da zuciya mai kyau suna kuma da zuciyar kaunar marayu, nan take suka ji kaunar Leesharh ɗin ya kamasu, shi kuma Bilal da hankalinsa baya kan hiran nasu sai bai ji komai ba, gabaɗaya hankalinsa kacokam yana kan Ramish. Riƙo hannun Leesharh ɗin Abbie ya yi tare da zaunar da ita a ɗayan gefen nasa, wlh Abu Abdussalam sarkin kaunar yara ne, duk ƴaƴan King Zuhair da ya tattare suka dawo gidansa bai ishe shi ba, har Auta Zunaira son ɗauketa yake yi King yaki yarda, shi fa bai ki ace gidansan nan a cike yake da ƴaƴansa ba, sai kuma Allah bai bashi aihuwa dayawa ba, ƴaƴansa uku ne kawai a duniya, shiyasa ya kwaso ƴaƴan King, bai ma ki a ƙara mashi wasu ba. "Rizwan bani handkerchief a wajen kan nan". Cewar Abbien. A hanzarce ya ciro daga aljihunsa ya miƙa mashi, gogewa Leesharh ɗin hawaye ya karɓa ya fara yi yana bata hakuri, nan take ya ji yana kaunar yarinyar, ji ya yi gaskiyar saboda maraicinta shi zai maye mata gurbin mahaifinta, dan gaskiya yana son ƴaƴa mata sosai, amma Sharifat kawai Allah ya bashi, dan haka yanzu a ransa ji yake bayan Sharifat ya samu Leesharh. A ɓangaren Ummie kuwa haka kawai ta ji wani irin tsanar Leesharh ɗin ya kamata, ko me dalilinta Allah kaɗai masani komai da komai na fili da na ɓoye. Shi ma Rizwan da yake yana da saukin kai sosai sai ya ji yana kaunar Leesharhn, sai ya ji ta bashi tausayi sosai, ƴar yarinya da ita ta rasa iyayenta, Allah sarki ita da ya kamata a ce yanzu tana tare da iyayenta tana jin ɗumin jikinsu, amma saboda babu su gata a in da ma bata sani ba ta zo aikatau, to daga yau gaskiya ta bar yin aikin komai duk da dama ba wani aikin kirki take yi ba, amma daga yau ta zama ƴar gida ita ma, kuma zai riƙeta matsayin kanwa kamar yadda ya riƙi Sharifat, haka yake tunani a cikin ransa. Shi kuwa Guyson da ya fisu zuciyar tausayi sosai har da hawaye ya yi mata, shi dama already tausayi take bashi, tun da ya ganta an kawota gidansu da sunan aiki tun kafin ma yasan ita marainiya ce yake tausaya mata, dan a cewarsa ƙaramar yarinya kamar wannan ta zo aiki ai akwai tausayi. Shi kuwa Omaid sarki bakar zuciya yana fita waje harabar gidan ya nufa, kai tsaye in da Obaid yake ya nufa, haushin da ya ji a cikin gida zai je ya sauke a kan criminals ɗin nan......... Tab ni kam na ce criminals kunga ta kanku. Yana shiga ya samu Obaid yasa jami'an Swat guda biyu sun ɗaure mashi criminals ɗin a jikin wasu kujeru da suke ɗaure masu laifi su yi masu tambayoyi, yasa an ɗaure mashi su kamar wani babban mutun ya ɗauko chair ya zauna a gabansu, kai daga ganin yadda ya zauna a gabansu zaka fahimci lallai suna samun horo a makaranta yadda ya kamata, waɗan nan yara wlh idan aka yi wasa sai sun fi Ramish ɗin da ya kaisu school ɗin ma sanin aiki yadda yakamata, dan su baiwarsu ta musamman daga Allah ce, idan suna yi abu sai ka rantse da Allah sun haura shekaru 25, suna karatu ne yadda yakamata, duk wani dabaru da zasu yi wa mai laifi ya faɗi gaskiya sun san shi, gasu da iya zaƙulo mai laifi a cikin dubban jama'a, da ido idan suka ga maras gaskiya suna iya ganesa, kai yaran Momma ba dai ƙwaƙwalwa ba, sun gada baiwa daga iyaye, kada kuso ku ki ganin Guyson a class, bai taɓa tsalleke first class ba, gabaɗaya ƴaƴan Momma a school ɗinsu da su ake kwantance ta kowace halaiya, idan karatu ne da su akeyiwa sauran student kwatance, idan ma da rashin ji ne da su ake kwantance, mugunta da su ake kwantance, kyan zuciya da iya kyauta dukka dai su ne, su fa ba abin da basu iya ba idan sun ga damar yi, in basu ga dama ba ba uncle ba ko uban waye a school ɗin nan bai isa ya sakasu yi ba, ga su kuma tun daga farkonsu har zuwa kan Auta Zunaira shegen mugun shiga rai ne da su, ga ɗan banzan farinjini kamar su suka bawa kansu, komai muguntar da yaran momma zasu yi maka ba zaka dai'na sonsu ba, saboda shegen shiga ransu, kamar ba lafiya ba, haka ita ma Mommar take. Tambayarsu Obaid yake yi a kan waye ya turosu su kashe masu yayansu? Yadda kuka san da gaske kaunar Ramish ɗin suke yi, kawai tsabar iya mugunta ne, amma ba wani kaunar Ramish da suke yi, hasali ma haushinsa suke ji, dan yana takura masu. Chair shi ma Omaid ya ɗauko ya zauna, jami'an swat dake gadin room ɗin sun zuba idanu suna kallo yara masu aiki da cikawa, gani suke yarannan kamar sun fi su sanin aikinsu wlh, abin har mamaki yake basu, yadda kuka san wasu manya general's na ƙasa baki ɗaya. Shiru criminals ɗin suka yi suka ki amsa masu tambayarsu, sake maimaita masu tambayar Obaid ya yi a karo na uku yanzu kenan. Habawa Omaid da ya kwaso ɓacin rai daga cikin gida ne ya miƙe tsaye tare da sanya kafarsa da karfi ya taƙa ɗayan criminal ɗin a kirjinsa, ai kuwa baya baya ya yi shi da kujerar tasa suka zube ƙasa, wani irin belt na kaca ya ɗauko, jikin belt ɗin duk kifitoyi masu zafi. Kansu ya yi da belt ɗin, cikin fusata ya fara zabga masu shi a jiki, ba bu imani bare tausayi, yadda kuka san su fa aka kawowa su hukuntasu, duk in ya zabga masu wannan belt ɗin sai waɗan nan kifiyoyi sun caku har cikin namar jikinsu, amma duk da hakan bai sa tausayi ko mai kankantar ta bayyana a saman face ɗinsu ba, sai ma miƙewa da Obaid ɗin ma ya yi ya je ya tattaro wasu kayan hukunta masu laifin da ya yi. Jami'an dake wajen ne suke faɗi a ransu cewa zaku yi ku gaji ne dan har shi kansa Bilal ya yi iya yinsa criminals ɗin su buɗi baki su yi magana amma sun ki, da alama irin criminals masu sayar da rayukansu a kan aiki ne, kun san akwai waɗan da su idan kuka ɗaukesu su yi maku aiki to fa idan aka kamasu asirinsu ta tonu ko kashesu za'ayi ba zasu buɗi baki ba bare ma har su tonawa wanda ya sanyasu aikin asiri, su sai dai a kashesu, amma ba tona asiri, to irinsu ne waɗan nan, daren jiya saura kaɗan Bilal ya harbesu da bindiga saboda bakincikin sun ki yin magana. Sosai Omaid ya farfashe masu jiki jini yana ta zuba, sun galabaita iya galabaita, sun wahala, amma duk da haka babu alamun zasu buɗi baki su yi magana. Sai da ya ji ya gaji ne ya rabu da su ya koma saman chair ɗinsa ya zauna yana mayar da numfashi, shi kuma Obaid cewa da jami'an dake wajen ya yi su zo su ɗaga masu criminals ɗin su mayar da su su zaunar da su. Ba musu suka zo suka ɗaga masu su tare da kujerar tasu suka zaunar da su. Zama suka yi suna fuskantar juna, sai wani irin numfashin azaba sama sama criminals ɗin suke yi tamkar ba zasu rayu ba, sun ci bakar wahala ƴan banza, daren jiya Bilal ya jibgesu, sassafe kuma su twin's su ɗaura nasu. Plastic and cotton Obaid ya ɗauko, miƙewa ya yi ya koma ta bayansu, da karfi ya damki gashin kan ɗaya, jan gashin ya yi baya da karfi dan dole guy ɗin ya ɗaga kansa sama, babu alamar tausayi ko kaɗan a saman face ɗin yaran nan, yadda kuka san ba rai suke azabtarwa har haka ba. Cutton ɗin ta cusa mashi a baki kafin ya bi da plastic ɗin ya manne mashi baki, shi ma ɗayan haka ya yi mashi. Bayan ya kammala ya koma saman chair ɗinsa ya zauna, yana zama ya dubi Omaid ya ce. "Me and you zamu ga waye zai fara sanya nasa criminal ɗin ya buɗe baki ya yi jawabi". Yana kai karshen maganar ya sanya hannunsa ya fara fito da wasu mugayen makamai daga cikin box ɗin da ya ɗauko. Small silent pistol gun Obaid ɗin ya ɗauko, saita babban yatsar criminal dake gabansa na kafa ya yi, fasa mashi yatsar da bulle ya yi ko a jikinsa, sai gani kake jini ya tallatsa. Wani irin sama da kai criminal ɗin ya yi yana son ya yi ihu ba hali, dan bakar muguntar Obaid ya toshe mashi bakin nasa ba halin yin ihun. Bai kula shi ba, sai ma sake fasa ɗayar babban yatsar na kafar hagu ya sake yi. Wannan mai laifi dai yau ya ji azaba, girgiza kai ya fara yi idanunsa sun yi jajir kamar jan gauta, alama ce ta yana cikin azaba. Tsabar mugunta irin na Obaid sai ya ɗauko chimical mai suna plutonium-239 ɗaya daga cikin wanda ake haɗa atomic booms da shi, chemical ne mai bala'in zafi, ko da yake ku daga jin boom ai kun san wuta ce, ba chemical ce ta wasa ba, haka ya ɗauko chemical nan ya zuba mashi a kafar tasa, dai'dai in da ya fasa da bindiga. Azaba kan azaba, wannan mutumin kamar zai mutu, idanunsa sai sun baka tsoro saboda yadda suka yi ja sosai. Kallonsa cikin ido ya yi tare da cewa. "Zaka bada bayanai ko dai har yanzu baka niku ba?". Girgiza kai mutumin ya yi alamar a'a shi ba wani bayanai da zai bada sai dai ya mutu. Omaid da ke binsu da kallo ne ya ce. "Kai Obaid matsalata da kai baka iya bada punishment ba". Yana kai karshen maganar ya sanya hannu ya ɗauko wata ƙatuwar almakashi daga cikim box ɗin........... Ni kam nace duk wannan bakar azabar da Obaid ya gana mashi Omaid ya ce wai bai iya horarwa ba? To ya yake son ya yi kenan? Waɗan nan yara da abin al'ajabi suke, tun basu kai ko'ina bama kenan, waɗan nan idan suka girma a school na swat wlh ba kananan muguye kuma jami'ai mafi hazaƙa kuma mafi haɗari za'ayi ba, idan suka kama mai laifi wannan gara ya kashe kansa a kan hukuncinsu, kun ga wata lukutar masifa tun suna yara, ga babu tausayi ko kaɗan, Leesharh Allah ya hanaki kara faɗawa hannun waɗan nan yara. Sanya almakashi Omaid ya yi ya fara yanka short ɗin jikin criminal ɗinsa dake gabansa, dama tun jiya Bilal ya cire masu kayan jikinsu kafin ya basu a jikinsu, so yanzu iya short ce kawai a jikinsu. Yanka short ɗin gabaɗaya ya yi, ya yi wa mutumin zindir. Bayan ya yanketa sai ya dubi jami'an da suka saki baki suna ganin ikon Allah, ce masu ya yi su sauyawa criminal ɗin kujera, tun da suka ga ya faɗi haka suka gane nufinsa, dan haka sai suka kawo wata kujera wandda tsakiyarta a fafake babu komai take, a nan suka ɗaura shi suka ɗaure hannunsa da kafafunsa, sai dai fa wlh jami'an da kansu jikinsu ya yi sanyi da ganin irin hukuncin da Omaid yake son yi wa wannan mai laifin, su kansu sau ɗaya suka taɓa ganin Ramish ya yi wa wani irin wannan hukunci, ko a ina Omaid ya koyo irin wannan mugunta? Dama na gaya maku Omaid ya fi Obaid iya mutunta sosai, shi idan zai yi nashi muguntar wlh sai ya tayarwa da kowa dake wajen hankali, baya nuna kamar yasan me imani da tausayin ma, gara Obaid sau dubu a kansa. Ɗauko wata igiya mai karfin balai ƴar siririya ya yi tare da ɗaukar hands gloves. Sake baki Obaid ya yi yana kallonsa, suma jami'an nan dai bakin suka sake suna kallonsa. Bayan ya sanya hands gloves ɗin ya ɗauki wannan igiyar ya ɗaurewa criminals ɗin a gabansa, daga farkon tushen bananarsa ya ɗaure, sannan ya ɗauko wata ƴar kwallo ya ɗaure a karshen jelar igiyar ya saki tana lilo ta ƙasar kujerar, idan baku manta ba dama tsakiyar kujerar a rarake take babu komai. Kafarsa ya sanya a ta ƙasar kujerar ya kama wannan igiya tare da sanyata a tsakanin yatsun ƙafafunsa, da karfi ya ja igiyar ƙasa kamar zai tsinkewa guy ɗin bananarsa. Wani irin ɗaga kai sama guy ɗin ya yi tsabar azaba har sai da wasu jijiyoyi zara zara suka fito ɓaro ɓaro a wuyansa kamar zasu fito waje, idanunsa wlh zaku ce jini ne a ciki saboda ja, azaba ta yi azaba bai san lokacin da ya fara girgiza kujerar da yake zaune a kanta ba, alamar yana son ya yi magana. Sarai Omaid ɗin ya fahimci criminal ɗin yana son ya yi magana, amma da yake mugunta ta yi mashi yawa sai bai kula shi ba, ya cigaba da jan wannan igiyar kamar zai tsinke mashi banana. Obaid dai yau yaga abin da bai taɓa gani ba, zaro idanu ya yi yana kallon ɗan uwan nasa da ko a jikinsa yana ta janwa mutumin abarsa. Su kansu jami'an nan Allah sai da suka tsorata, sai da jikinsu ya yi sanyi, wlh matasan nan sun basu tausayi, sun yi masu jajen shiga hannunsu Obaid, ɗayan jami'in kam ma har sai da idanunsa suka cika da kwallah, ya sanya hannunsa ya tallabo bananarsa, ji yake kamar bananar tasa Omaid yake fincika haka, yau sun ga rashin imani zallarta babu mix, anya Obaid da Omaid lafiya suke kuwa? Ni dai PRINCESS TEEMA na saka ayar tambaya a kan irin rashin imanin da suke da shi tun suna yara, anya ba'a samu wani da ya sanya zuƙatan yaran nan ya bushe haka ba?. Sai da ya ji jinin bananar guy ɗin ta fara ɗiga mashi a saman kafafunasa sannan ya saki igiyar tare da komawa ya jingina bayansa a jikin kujeran da yake zaune ɗin, duk tsoratar da Obaid ya yi bai sa ya ce ɗan uwan nasa ya rabu da mutumin ba tsabar shi ma ba tausayin ne da shi ba.... Ko da yake ba su da a laifi irin hukuncin da suka yi wa criminals ɗin, saboda kashe mutun ai criminals ɗin suka yi ƙoƙarin yi, da an barsu suma kisa zasu yi babu tausayi, to kunga kuwa su Obaid basu da laifi, sun yi dai'dai, kawai tsantsar madarar rashin tausayin nasu ne dole ya girgiza bawa. Omaid shiru ya yi tare da zubawa criminal ɗin idanu yana masa wani irin ƙasƙantacen kallo, sai girgiza kai guy ɗin yake irin azaba tana kara ratsa shi, Omaid ɗin ya kusa tsinke mashi bananarsa, ya datse idanu gam kamar zai fasasu. "Zaka gaya mun gaskiya ko kuma na mayar da kafata na tsinketa mai gabaɗaya?". Cewar Omaid ɗin, cikin kwanciyar hankali ya yi maganar, word ɗinsa na fita one by one kamar ba shi ya yi wannan azabar yanzu ba, cikin nutsuwa sosai yake abinsa............ Yaseen Omaid shegen kaya ne na karshe, wato hankalinsa a kwance? Ni dai yana burgeni ato.........😂🌝 A hanzarce criminal ɗin ya gyaɗa mashi kai sama alamar wlh zai basu amsa zai buɗe baki. Zaro idanu Obaid haɗe da jami'an dake wajen suka yi, su dai jami'an nan sun san irin jibgar criminals ɗin nan da Bilal ya yi jiya amma suka ki buɗe baki, yanzu dai ga shi da suka shiga cikin azabar Omaid and Obaid ai sun buɗe baki ƴan banza. Ba ƙaramin jinjinawa twins ɗin nan jami'an suka yi ba, sun sara masu, yara masu aikin manyan kai. Hannu yasa ya cire mashi plastic dake bakinsa tare da cutoon dake cikin bakinsa dan ya bashi damar yin magana. Wani irin numfashi guy ɗin ya ja kafin ya fara ƙoƙarin buɗe bakinsa, jikinsa sai kerma yake yi kamar mazari,....... Lallai ƴan ta'addan nan suna da taurin zuciya, ko da yake dama ai dole su yi jarumta shegu, saboda zuciya babu imani, su yi kisa ko a jikinsu, sun ga abubuwa kala kala dole, sun saba da azaba kala kala shiyasa dole su koyi dauriya. "Give me your phone Obaid". Cewar Omaid ɗin, dan shi ya baro wayarsa a ɗakin da Ramish yake kwance. A hanzarce ya ciro wayar daga aljihunsa ya miƙa mashi. Video recorder ya kunna tare da miƙawa ɗaya daga cikin Jami'an a kan ya riƙe ya ɗaukesu bari ya yi mashi tambayoyi tun da ya aminta zai buɗe baki. Karɓa jami'in ya yi tare da fara ɗaukarsu kamar yadda ya bukata. A tsanake ya fara jera mashi tambayoyin da yake da buƙatar amsarsu. Haba my people's yau sai ga ɗan ta'addan da ko za'a kasheshi baya tona asiri yau sai gashi da ya ji azabar Omaid ya buɗe baki tiryan tiryan yana zuba jawabi kamar wani computer. Haƙiƙa jami'an nan sun sha madarar mamaki da ganin wannan al'amari, su ma yau sun samu ƙarin haske wajen horarwa, Omaid ya basu caurse yau. Tiryan tiryan wannan criminal ɗin ya faɗi duk wani abin da ya sani ba tare da ƙarya ko ɓoye ɓoye ba. Shiru suka yi suna sauraronsa har ya kai aya, miƙewa Omaid ya yi tare da cewa. "Ƙananan ƴan iska, ina kuka ce baku ji? Ashe dai ku karnukar farauta ne ma na tsaya ɓata lokacina a kanku". Ya kai karshen maganar tare da jan siririrn tsaki sannan ya sanya kai ya nufi kofar fita daga wajen. Sai da ya ƙarisa wajen jami'an sannan ya ce. "Mun yi namu aikin, saura naku, idan kun gama abin da zaku yi ku bawa Obaid wayarsa". Yana kai karshen maganar ya fice waje abinsa. Shi kuwa Obaid ko da ya miƙe sai da ya dallawa wanda ya yi jawaban mari mai rai da lafiya sannan ya ce. "Ɗan iskan banza, ashe kana son shegiyar taka, to wlh sai na yanketa, tun da Omaid bai guntuleta ba, ni ka jira dawowata da yamma zaku gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah ne, duk sai na cire maku shegiyar taku na bawa karnukan Yah Ramish ɗin tun da dama shi kuka karɓi kwangilar kashewa, dan haka karnukansa sai su yi party da ayabar taku". Yana kai karshe maganar ya kara masu marika tas tas a saman kumatunsu kafin ya bi bayan ɗan uwansa zuwa cikin gida. Suna shiga cikin gida wanka suka yi tare da fara shirin wucewa gidam King Badeen dan su wuce school, cikin nutsuwa haɗe da wasa da juna suke shirinsu, tamkar basu suka gama tsala mugunta tsala tsala yanzun nan ba. Guyson ne ya shigo cikin ɗakin nasu hannunsa riƙe da wayar Omaid da ya baro a A and E room ɗinsu. Omaid ne ya ce "What happened Yah Omar i saw you like you aren't happy?". Yana ɗan turo baki ya amsa mashi da cewa. "Akka said that she wants to see everyone at home today, that we all need to go home". Ya kai karshen maganar tare da hayewa saman bed ɗinsu ya kwanta. Obaid ne ya tari numfashinsa da cewa. "But she's calling only her own children right? Dan ni dai i can't go anywhere". "Wait mana Obaid, ka cika gaggawa fa, first of all Yah Omar a kan me take nemanmu? For what reason? Shin akwai wanda ya yi mata wani abin ne da zata nemi ta takurawa rayuwarmu?". Cewar Omaid sarkin iya tsari a magana. Siririn tsaki Obaid ya ja kafin ya ce. "Wlh Akka she's totally bad old woman". Shi dai Omar bai sake yi masu magana ba, ya kwanta shiru tare da binsu da kallo kawai, dan yasan fin haka ma yaran nan zasu faɗa a kan Akka, saboda bata shiri da su, ita take sanya Ramish ya saka masu ido sosai, shiyasa suka fi kowa tsanarta, basu shiri ko kaɗan, kun dai ji dalilin da yasa basu son Akka su kuma yau kam, kowa da dalilin da yasa suke rikici da tsohuwar nan, duk ta bi ta takura masu, ga uncle Jahiz uncle nasu mai shekaru 38 yanzu a duniya bai yi aure ba, kuma tana ganinsa bata ce komai ba, amma ta takurawa Jaish and Jawad wai su yi aure, kuma fa iya su ta takurawa ɗin, bata maganar su Ramish sam, mancewa ma da su take yi, Jaish da Jawad ne suka tsole mata ido, su ta saka a gaba take gasawa aya a hannu ta hanyar haɗasu da iyayensu ta ja King da uncle Abbas su yi ta yi masu faɗa ba gaira ba dalili. "Obaid ai ka rage mata ma idan kace bad old woman, Akka she's like nuclear, duk in da ta nufa sai ta banbanme wajen, i don't like her, wai meyasa nema bata mutu ba tun kafin mu girma ba?". Ya kai karshen maganar yana jan tsaki. "Do you know something blood?". Obaid ya tambaya. Girgiza mashi kai Omaid ɗin ya yi alamar a'a bai sani ba. "At all ban so ace Akka ce kakarmu ba, because she's to stubborn, and then dad and uncle Abbas har uncle Jahiz sai su rinƙa biye mata, bamu yi abu ba ta yi mana sharri a wajensu a kan mun yi, su kuma su yarda da ita like they don't know us or they're not the one who give birth to us, sometimes ji nake kamar kada na je gida hutu, but if I remember that I missed my momma and that mama is there sai na ji i want to go even dan na yi punishing na mama if she did something wrong to our Momma". "Kurinƙa sassautawa dai, ni dai kam na wuce, kuma daga nan sai ƙasar Tunisia, dad yana buƙatata a kusa da shi, and lastly Akka dai dama bata ce ku take son gani ba, a waɗan da ta lissafama babu ku a ciki saboda ita da kanta ba kaunarku take yi ba". Cewat Guyson, yana kai karshen maganar ya miƙe tare da ajiyewa Omaid ɗin wayarsa ya nufi waje, zai je ya shirya Abbie ya yarda ya koma kingdom of power ya cigaba da karatunsa. Suma ƙarisa shirinsu suka yi suka je suka yi wa uncle ɗin nasu tare da ƴan uwansu sallama, daga nan sai gidan King Badeen............ Leesharh and Sharifat Abbie ya ce yanzu ɗaki ɗaya zasu rinƙa kwana sun zama ƴan uwan, tuni Sharifat ta jata suka tafi ɗakin nata sai murna take yi ta samu ƴar uwa. Rizwan ma ya tafi yana shiri dan yana son shima a satin nan ya dira kingdom of power saboda aurensa da Gimbiya Chuchu..... Akwai cakwakiya sosai, to ni dai bari na leƙa Dark world. _______________________💔🔥 DARK WORLD🔥😥💪 Bayan Delisha Ronnie ya bi, jikinsa duk a mace kamar wanda aka yi wa dukar tsiya, da kyar yake iya jan kafarsa ya nufi sama. Ba karamin mamaki ya ji ba lokacin da ya kalli delisha ta shiga ainahin babbar parlourn black tiger da babu wanda ya taɓa shiga sai shi Ronnie, bayan shi a gabaɗaya masarautar babu wanda ya yaɓa shiga cikinta, yau Delisha ta ja Sweetie har ciki.... Tashin sense........... Meyasa aka kai ta can? Me zasu yi mata?. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 8/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E18 DARK WORLD🔥😥💪 Bayan Delisha Ronnie ya bi, jikinsa duk a mace kamar wanda aka yi wa dukar tsiya, da kyar yake iya jan kafarsa ya nufi sama. Ba karamin mamaki ya ji ba lokacin da ya kalli Delisha ta shiga ainahin babbar parlourn black tiger da babu wanda ya taɓa shiga sai shi Ronnie, bayan shi a gabaɗaya masarautar babu wanda ya yaɓa shiga cikinta, yau Delisha ta ja Sweetie har ciki.... Tashin sense........... Meyasa aka kai ta can? Me zasu yi mata?. Da yake shi ya saba shiga cikin part ɗin, ba bakon bane a part ɗin sai ya bi bayanta har zuwa ciki, Delisha ɗin ita ce ma bakuwa da bata taɓa shiga part ɗin ba sai yau a dalilin Sweetien. Ya yi matuƙar mamaki a kan meyasa yau Black Tiger zai sanya Delisha irin aikin da shi kaɗai yake sakawa ya yi mashi? Meyasa ya yi hakan? Yau da kansa ya bar wata ta shiga part ɗinsa da ba wanda ya taɓa shiga sai shi Ronnie! Lallai akwai matsala. Da wannan tambaya da mamakin cike a ransa ya shiga gold parlourn......... Hmmmm alƙalamina ya yi kaɗan ya iya zayyano maku yadda haɗuwar wannan gold parlourn yake, alƙalamina ba zai iya ba, dan karshen haɗuwa ne, abin da zan ce maku kawai a nan shi ne four in one ne parlour, parlours har kala huɗu ne a cikin guda ɗaya, dukkansu kuma an ƙawatasu a luntsuma luntsumar kujesu wanda aka yi su da gold, kun sansu arziki mafi yawaita a cikin birnin gold ne, dan haka akwai shi wadatatce, kusan komai na Daularsa da gold aka yi ta....... Babban kai kenan. Haɗuwar parlourn nan ya wuci tunaninku, ga shi gari guda a girma, kofofin shiga sauran ƙananan parlourn guda ukun manya manyan luxurious glasses ne, center table dake tsakiyar kowani sofa set ma kawai abin kallo ne, haƙiƙa idan ka shiga wannan parlourn zaka yi zaton ba'a duniyar nan kake ba, babu hasken rana dake shigowa wajen, luxury curtains ɗin parlourn masu kauri ne sosai da sosai, gabaɗaya parlourn kuwa gauraye yake da white light na flourescent bulbs, shi babban parlourn ma flourescent bulbs ɗinsa yana da tsayi sosai, duk da ya kasance ginin yana da tsawo sosai, amma flourescent bulb ɗin centern parlourn ta sauko dai'dai, and design na flourescent bulb ɗin tamkar wasu kyawawan flowers haka aka yi su, sun haɗu har sun gaji da haɗuwa, haske ne da su sosai da sosai ta yadda su kaɗai ne a kunne a parlourn amma sun haske ko'ina duk girman parlourn, gasu golden color sai suka kara fito da gold parlourn. Irin wannan parlour sai dai baki ta yi shiru kawai, wani irin makeken Tvn dake cikin gold parlourn nan idan yana kunne sai kaga mutanen ciki kamar ka kirasu su amsa saboda girma, jiga jigan manyan Ac's kam ba'a magana, Daula iya Daula sai bakin zalinci. Har tsakiyar gold parlourn Delisha ta jata, sai kuka take yi babu wanda ya saurareta. Dakatawa ta yi a tsakiyar parlourn tana binta da wani irin matsiyacin kallo, ta ji haushi ne da ya zama bata taɓa zuwa wannan part ɗin ba sai a dalilin Sweetien yau, bata so ace hakan ta faru ba, ta so ace ta shigo ba ta dalilin kowa ba, isarta yasa ta shigo kawai ba wani ya yi mata alfarma ba, ba dai yadda ta iya ne kawai, sai dai ita kanta tana tunanin meyasa Black Tiger bai sanya Ronnie wannan aiki ba ya sanyata ta je ta ɗauko mashi Sweetien? Bayan kuma da Ronnie kawai ya aminta a cikin Empeir ɗin, abin dai ya bata mamaki. Haka zalika duk da ta kasance wayayyiya yar boko kuma ƴar cikin empeir ɗin, sannan ta saba ganin kayan alatu na more rayuwa very expensive ones, amma da ta shigo cikin gold parlourn nan sai da ta zama cikakkiyar ƴar kauye babu mix, sai satar kallon ko'ina da ina take yi, bare kuma ita Sweetie da take girman forest! Ai kauyanci dole!. Shi ma Ronnie ya shiga ruɗani da har ya fara zargin kansa ko dan ya mari Sweetien ne yasa yau Black Tiger ya sharesa? Sai a lokacin kuma ya tuna cewa shi ma ya yi kuskure ba iya Sweetie kawai ba, dan kuwa ya san duk abin da suke yi a kan idanun Black Tiger ɗin suke yinsa, a tafi hannunsa suke, duk wani motsinsu yana sani kamar wani aljani, dole mutanen birnin su ce shi ɗin ba mutun bane, yana ganin komai da ake yi a faɗin birnin, shi kuma a lokacin ransa ne ya yi mummunar ɓaci da har ya kasa control ɗin tempersa har ya mareta, shi kansa bai san dalilin wannan marin ba, abin ne ya zo mashi unexpect kawai. Wani irin tsawa Delisha ɗin ta daka mata wadda ya sanyata kara ruɗewa, dama can ba ta cikin hayyacinta sosai, tsawa ta daka mata a kan ta gaya mata in da Spender yake ko kuma ta kasheta a nan. Harɗe hannayensa a bakin kofar shiwo gold parlourn ya yi, shi kansa kofar shigowar abin gani ne, na farko kofar bullet proof ce, babu bullet ɗin da zata iya fasashi, sannan water proof ce, design of the most expensive door in the world, kai kofar ta haɗu ta gaji da haɗuwa, sannan da gold aka yi ta. Zubawa Delisha waɗan nan kyawawan idanun nasa ya yi yana kallonta, ji yake yi tamkar ya yi kuka, shi bai taɓa jin tausayin wani abin ba a rayuwarsa kamar yadda Sweetie ta bashi tausayi a yau, idan kaga tashin hankalin da yake kan face ɗin yarinyar nan wlh sai zuciyarka ta karaya, a tsananin tsorace take, sai dai kuma babu alamar zata amsa masu tambayar da suke yi mata a tattare da ita, sam bata nuna alamar kamar ta san abin da suke tambaya ɗin bama. Shiru bata yi magana ba sai kerma da jikinta yake yi, hakan ba ƙaramin kara fusata Delisha ya yi ba, wani irin mari da ta dallamata ne yasa sai da baiwar Allahn nan ta yi wani ni irin juyawa tare da kifawa ƙasa. Idan ran Ronnie ya yi dubu a kan wannan marin to ran nasa ya ɓaci, cikin fusata ya tako ya ƙariso in da suke, daga ganin yadda yake tafiya kai kasan ba rago bane, jarumin gaske ne. Dai'dai lokacin da ya ƙariso wajen ita kuma Delisha ta ɗagota da dogon gashin kanta tana ƙoƙarin dalla mata wani marin a karo na biyu, ga shi ta damke mata gashi tana ja da karfi. Yana zuwa ya riƙe hannunta ta baya, a fusace ta juyo dan taga wanene? Ai kuwa tana juyowa ya ɗauketa da nasa marin mai doɗar da jin bawa. Wani irin jiri ta gani ya ɗebeta da karfi, ta ji hannun maza, dan fa marin Ronnie ba wasa, wurgi da hannunta da ya riƙe ya yi da nufin ya kama Sweetien dake ƙoƙarin zubewa ƙasa saboda marin da ya ɗauke Delisha ɗin da shi yasa Delishan ta saki gashin kan Sweetien da ta riƙe ba shiri. Tana sakinta kuma ta tafi zata faɗi ƙasa, shi ne ya yi wurgi da hannun nata zai taro Sweetien. Yana ƙoƙarin kama Sweetien Delisha da ta dawo dai'dai ta cire hannu zata dallah mashi mari ita ma ko tsoro babu, ta fa san wanene shi sarai, amma take ƙoƙarin rama marin da ya yi mata dan nemanwa kai rugugin balai. Ai kuwa cap ya capke hannun nata da hannunsa ɗaya tare da ƙara dallah mata wani gigitattacen marin mai karfin gaske da ɗayan hannunsa, sannan ya riƙo Sweetie da hannun da ya mareta ɗin, cikin ɓacin rai ya kwashe kafafunta ta zube ƙasa, abin da yasa ya yi mata hakan kuma ba komai bane face renin da take ƙoƙarin kawowa a tsakaninsu, a iya saninsa yasan cewa ko master Devil ya mara bai isa ya ce zai rama ba bare ita, saboda shi ɗin kowa yana girmamasa kamar yadda suke girmama Black Tiger, sanin Black Tiger ɗin ya fifita shi sama da kowa a cikin birnin, dan dole ake yi mashi biyayya, da yara da manya waɗan da suka fisa, kai har dattawa suna yi mashi biyayya, dan ya mareta shi ne ita sarkin bala'i zata rama? Tab dan ma ta samu hankalinsa na kan Sweetie ne, ai da ya yi mata one blow seven die. A fusace ta miƙe tsaye, kansa ta yi da iya karfinta a dole ba zata kyalesa ba, gani take yi yanzu ta kawo karfi ita ma, ji take kamar zata iya dukansa, mutumin da tun yana ɗan shekara biyar ya fara koyan Wrestling shi ne wai take tunanin zata iya dukansa. Ai kuwa sake Sweetien ya yi ya juya kanta kamar wani zaki, kan kace me suka fara gwabza faɗa kamar wasu zakuna. Ronnie yana da karfi sosai, wani irin damƙa ya yi mata a gashin kanta wanda sai da yasa ta yi ihu, da karfi ya ja gashin kan nata tare da ce mata ta ji yadda Sweetien ma ta ji lokacin da ta ja mata nata gashin, ashe ba daɗi? Ashe da zafi?, yana yi mata magana yana ƙara fisgar gashin nata da karfin gaske. Azaban da ta ji ne yasa cikin dabara ta juya tare da damko dogon wuyar nan nasa da karfi ita ma, hakan yasa ya saki gashin kan nata da sauri, yana sakinta ta juyo da kyau tare da shake mashi wuya da karfin gaske. Sweetie kam kara tsorara sosai ta yi, musamman yadda taga suna faɗa cikin rashin tausayin juna, kamar basu taɓa sanin juna ba, duka sosai Ronnie ya yi mata tamkar bai taɓa saninta ba, duk da hakan kuma ta kasa daddara a cewarta ba zata barshi ya sha a banza ba, kenan ya daketa ya daki banza? Ba zai yiwu ba, ga shi sai kara cin jibga take yi. Da dai yaga dan yana yi mata a hankali ne take ƙara zaƙewa, sai ya cire duk wata sanaiya ya kama hannunta dake wuyarsa ya ɓanɓarota, da karfi ya murɗe hannun nata ta baya, ji kake ƙad ya ɓalle mata ƙashin hannu. Bai barta ta yi ihun hannun ba ya jajumota sama cikin fusata zai yi wurgi da ita saman glass table dake kusa da su. Ihun da Sweetie ta kurma tare da rufe idanu ne yasa ya farga da kisan kai da yake son yi, dan kuwa in dai ya yi wurgi da ita a wajen sai dai wata ba ita ba, ba zata yi saura ba, dan babu abin da zai hana ƙashin bayanta ballewa sai dai wani ikon Allahn. Jin ihun Sweetien yasa ya wurgata saman sofa tare da matsowa ya riƙo hannun Sweetien wanda ta ɗaura a saman face ɗinta ta rufe idanunta da shi dan kada taga yadda zai yi kisan kai. Yana riƙe hannunta ya miƙar da ita tsaye kenan kwatsam sai ji ya yi Delisha ɗin ta buka mashi wani abin saka flowers a ciki, wadda ya kasance shi ma da gold aka yi shi, haka ta daddage ta ɗaga shi da hannunta ɗaya ta buga mashi a bayan ƙeyansa, tana buga mashi kuma ta fara layi kamar zata faɗi ƙasa, ga bakin azaba da hannunta da ya karya mata yake yi mata. Ai kuwa sakin hannun Sweetien ya yi tare da juyowa ya capki wuyarta, da karfi ya shaƙeta, ga kansa in da ta buga mashi abin zafi yake yi mashi over, kamar yadda yake jin raɗaɗin wajen haka yake ƙara shake mata wuya da karfin gaske, nan take idanunta suka firfito waje ta fara ƙoƙarin faɗa tsakanin rai da mutuwa, ƙoƙarin shakar numfashi take yi, amma ina ta kasa, dan ba riƙon wasa ya yi mata ba. Ta kasa iya kwatar kanta. Sai da ya tabbatar ta dai'na numfashi, sannan ne ya hankaɗata da karfi da kuma hannun ɗaya, gabaɗaya ta tafi ta kifa a ƙasa kamar gawa, ko motsi bata yi kamar ta mutu. Ɗaga idanunsa ya yi yana kallon ɗan siririn gold stair case dake cikin gold parlourn kusa da dining room, stairs case ne mai design of indomie ɗan siriri na wucewar mutun ɗaya, na haurawa ne sama in da ainahin room ɗin Black Tiger yake. Ajiyar zuciya ya sauke, dan yasan duk abin da suke yi tsab Black Tiger yana kallonsu, yasan komai, kawai dai bai tanka masu bane, ya barsu suka gwabza abinsu. Stair case ɗin ya nufa kai tsaye, babu ko tsoro bare shakka, haka ya bar Sweetie a wajen tana zaune ta rasa madafa, ga dukkan alamu ya saba haurawa wajen. A can wajen wasa kuwa, sai raƙashewa suke yi, an saki sauti sai rawa suke yi, master Devil ma fa ashe ya iya taka rawa over, Floris ma rawa ta taka sosai kamar babu ƙashi a jikinta yarinyar nan, suna chashewa son ransu, sharholiya iya sharholiya, dama haka suke yi duk idan aka gudanar da gasa. Makudan kyauta masu tsada Black Tiger ya aikowa Oxil da shi kamar yadda yake a dokar gasar, ba'a karya doka sam sam, ko ma waye ya ci ko ya faɗi a gasar doka zata hau kansa. Almost 1 hour Ronnie ya ɗauka a saman kafin ya sauƙo, yadda ya shiga ba'a haka ya sauƙo ba, daga ganin yadda face ɗinsa take a yanzu zaka san yana cikin tashin hankali da damuwa, idanunsa sun yi jajir sosai, alamar ran maza ya ɓaci. Ga dukkan alamu ya yi katari da abin da bata yi mashi daɗi ba a saman!!. Kai tsaye waje ya nufa bai sake bin ta kan Sweetien ba, yadda yake tafiya cikin jarumta zaka fahimci lallai ransa a ɓace, ya fusata sosai. Da kallo Sweetien ta bishi har ya kurewa ganinta. Zama ta yi a ƙasa a wajen gwanin ban tausayi, kallon Delisha dake baje a ƙasa kamar gawa ta yi kafin ta mayar da kanta ta kifa a saman gwiwowinta, shiru ta yi tana tunanin yadda za'ayi ta gudu ta bar wannan Daula. A hankali voice ɗin mummynta ya fara ratsa kunnuwanta, tana tunano zantukan da suka yi kafin mum ɗin ta ɓace masu. "Sweetie duk wuya duk daɗi kada ki yarda ki bawa wani mahaluki wannan abin, ki kasance mai dauriya a duk halin da zaki shiga, in dai kika bada wannan abin to tamkar ki sadaukar da ran mahaifinki ne, ni nasan ba zan taɓa kai labari ba, shiyasa na zaɓi na baku shi ɗin, dan ba kowa zai yi zaton abin yana hannunku ba, ki kula da Pretty sosai, magana ta karshe a nan shi ne ki sani wannan abin yana da matuƙar haɗari sosai, manya manyan sarakuna na sama da masarautu biyar ne suke neman wannan abin idanu a rufe, zasu iya aikata komai dan su same shi, nasan rayuwarku zata iya shiga haɗari a dalilin wannan abin, amma bani da wani zaɓin da ya wuce in damka maku shi kamar yadda mahaifinku ya bani shi amana, ki sani wannan makulli ne na rayuwa ko mutuwa na mahaifinku". Ajiyar zuciya ta sauke tare da sake waigawa ta fara tunanin yadda suka yi da Pretty a kan Spender ɗin bayan ɓatar mum ɗinsu. "Pretty kin san yadda zamu yi da wannan abin da mummy ta bamu ɗin?". Pretty dake zaune saman gado ta buga uban tagumi ta amsa mata da a'a bata sani ba. "To ni dai wannan abin ni zan baki ki riƙesa, saboda ke kina da ido ni bani da shi, dan haka ke zaki fi kula da shi, sannan ki kula sosai kin dai ji abin da mum ta ce a kansa ko?". Kai ta gyaɗa mata tare da amsa mata da e. Hakan yasa Sweetien ta cire abin ta bawa Prettyn a kan ta ajiye shi, dan haka yanzu Spender dai yana hannun Pretty ba hannun Sweetien ba, in dai har Sweetie tana son rayuwarta kuma tana son barin wannan Daula to dole sai Pretty ta zo, dan ita ke rike da Spender, ita tasan in da ta ajiye shi..... Tashin hankali gaskiya Sweetie tana tsaka mai wuya, yanzu ma shin ina Prettyn take? Sannan a ina ta ajiye Spender ɗin? Lallai ya tabbata ita ma Pretty tana da shegen wayau, duk yadda suke da Kamran bata taɓa gaya mashi ba ko da sunan wasa, amma ni tambayata a nan shi ne, ta ya aka yi Black Tiger yasan mum ɗinsu Sweetie ta bawa Spender ba Pretty ba? Dan kunga dai kai tsaye Sweetien suka nufa, and shin sun san su twin's masu kama ɗaya ne ma ko dai basu sani ba kawai sun kama Sweetien ne? Wa ma ya gaya masu Spender na hannunsu? Anya basu kama mum ɗinsu ba kuwa? To idan ba ita ba ai babu wanda yasan ta bawa Sweetie abin, ko ita mum ɗin kuma bata san da cewa Sweetien ta baiwa Pretty abin ba, ita dai tasan Sweetie ta bawa ba Pretty ba, akwai cakwakiya babba kuwa, ta ina za'a nemo Pretty ta zo ta kuɓutar da ƴar uwarta daga RAWANIN ZALINCI? Dan kuwa sai ta zo kam, saboda ko ita Sweetien bata san a ina Prettyn ta ɓoye shi ba..... Wannan shi ne babbar magana!!!. Tunanika kala kala take ta faman yi a ranta, kamar ance ta ɗaga kanta sama ta ɗaga. Tana ɗagawa ta kalli flourescent bulb da take a zaune saitinsa yana ƙoƙarin faɗo mata a kanta, sai wani jijjiga yake yi da karfi kamar zai ɓallo. Ihu ta kurma tare da fara ƙoƙarin tashi ta bar wajen dan kada ya faɗo mata a kanta, sai dai ta kasa iya motsawa daga wajen, ihu ta rinƙa yi tare da datse idanunta gam ta kuma takure jikinta waje guda, sai ƙoƙarin miƙewa take yi amma ta kasa. Ganganrowa ƙasa flourescent ɗin ya yi har gabanta, ihu ta rinƙa kurmawa, kuma ihun nata baya fita, ga dai ɗan bakinta ta wagesa tana kurmawa, sai dai ba wani sautin da yake fita daga cikin bakin nata, abin da ɗaure kai sosai........ Ni ma dai ya ɗaure mun kai sosai gaskiya. Nan take ta ji kamar ana juyata, a ɗari ta buɗe idanunta, me zata gani? Sai ganin parlourn ta yi yana wani irin jujjuyawa kamar fanka, komai na cikin parlourn juyawa yake yi, gabaɗaya light na cikin wajen bulbs sun fi gida 30 suka fara kawo light suna mutuwa lokaci guda, bulbs dake cikin gold parlourn sun kai guda 20 sai kawowa suke yi suna ɗaukewa suma, lokaci guda suke ɗaukewa su sake kawowa kamar ba lafiya ba, idan suka ɗauke kuma wani irin duhu mai ban tsoro ne yake sake bayyana a gabaɗaya gold parlourn, sai ta rinƙa ganin wasu irin halittu da bata taɓa ganin irinsu ba a cikin duhun kafin hasken ya sake dawowa, idan haske ya dawo kuma sai ta ga komai normal babu waɗan nan halittu. Kanta ne ya fara juya mata ta fara fita daga cikin hayyacinta saboda bala'in tashin hankali, jikinta sai kerma yake yi. Da alama sun lura Sweetien fa bata da niyar basu Spender ne yasa suka fara azabtar da ita da tashin hankali kala kala haɗe da yi mata gizo, a tunaninsu idan ta sha azaba dole ma zata gaya masu in da yake,.........Babbar magana!!. Tun tana iya gane in da take, tun tana iya ganin hasken light dake ɗaukewa yana sake dawowa har ta dai'na gani, idanunta suka rufe ruf ta sulale ƙasa ta kwanta a wajen. Kafin wani lokaci komai na gold parlourn ya koma normal in da yake. Ita kuwa sai farkawa ta yi ta ganta a saman wani haɗaɗɗen bed cikin wani irin haɗaɗɗen ɗaki wanda ya fi ɗaki na farko da aka kaita kyau, ko kamshin dake tashi a cikin ɗakin na musamman ne, bata taɓa jin irinsa ba a duniya, kamshi ne mai kwantar da hankalin mai shaƙa!!. A hankali ta waro idanunta da suka yi mata matuƙar nauyi waje, gabaɗaya jikinta ciwo yake yi mata, yadda kuka san wadda aka yi wa duka da itace, gashin kan nan nata a watse kamar na mahaukaciya, olive eyes ɗin nan nata har sun kumbura saboda kuka. Yunkurawa ta yi zata miƙe saboda ta tuna da sallah. Kasa mikewar ta yi, saboda tsami da jikinta ya yi mata, kuka ta fara yi tana ji kamar ta gaya masu cewa Spender yana hannu Pretty su ɗaukota ta zo ta basu sai su sakesu su koma wajen zamansu, dan ba zata iya jurar wannan azabar ba, amma da ta tuna mum ɗinta ta ce in dai ta bada Spender ɗin nan to tabbas ta sadaukar da rayuwar babanta da kanta ne, to me haɗin ran babanta da spender? Akwai rina a gaba sosai ma kuwa. Tuna hakan yasa ta ji ba zata iya gaya masu ba, zata haƙura ta jure azaban!!. Ajiyar zuciya ta sauke ta rasa mafita, sake yunkurawa ta yi cikin dabara, da kyar ta iya miƙewa zaune, ƴan kafafunta ta zuro ƙasan gadon, tsabar yadda gadon yake sama kafafunta basu iya taɓa kasa ba, mattress na bed ɗin ƙaton ƙosasshe da dollof ne sosai, ga shi gadon bango ne guda, tsab zai kwashi mutane 10 manya ba yara ba, har filli ta rage, king bed ne na musamman. Dirowa ta yi ƙasa, wani irin zafi ta ji gaɓɓan jikinta suna yi mata. A hankali ta miƙe ta nufi kofar da take zaton toilet ne, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, fargaba kamar zai kasheta. A guje ta fito daga cikin toilet ɗin, saboda irin abin da ya faro a toilet ɗinta na farko ne ya sake faruwa a nan ma. A tsakiyar ɗakin ta tsaya, wasu irin siraran hawaye masu zafin gaske ne suka fara bin ƙuncinta, ta rasa me abin yi. Turo kofar ɗakin aka yi aka shigo. A ɗari ta kai kallonta wajen. Harɗe hannunsa ya yi a saman faffaɗar kirjinsa tare da zuba mata idanu, ya yi matuƙar kyau a cikin dressing ɗin nasa, hoodie ce a jikinsa, ya sanya hular kayan a kansa, ya yi matukar kyau, daga school ya dawo, yau yana da class, da yake ɗakunan cikin daular rana bata ratsa har ciki sai ba zaka iya sanin shin dare ne ko rana ba, yanzu haka almost karfe ɗaya na rana, tun jiya bata samu ta yi sallah ba, dan bata san time ba. Ganinsa yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, shi da Floris kawai take son rinƙa gani a cikin empeirn nan, bayan su bata kaunar ganin kowa, dan duk wanda zata gani bayansu bala'i ce a gareta. Wani irin haɗaɗɗen murmushi ya sakar mata kafin ya tako ya ƙariso cikin ɗakin, tana tsaye bata motsa ba har ya ƙariso in da take tsaye. Yana zuwa ya kyasta mata yatsunsa a saitin face ɗinta, dan ya kalli ta tsaresa da ido tun da ya shigo bata iya kawar da kallonta ba har ya iso wajenta, shiyasa ya kyasta mata yatsunsa. Ajiyar zuciya ta sauke, taga kyau iya kyau shi ne ta tsare shi da kallo, ta shagala da kallon nasa har bata san ya iso gababta ba sai da ta ji kyas ɗin yatsunsa. "Mekike yi a nan?". Ya tambayeta cikin sanyin murya. Da kyar ta iya kawar da kallonta daga kansa, sannan ta amsa mashi da. "Ina son ne na yi alwala na yi sallah amma ina tsoron wajen da ruwan alwalan yake". Ba abin da ya gane tsakanin alwala da sallan, dan haka sai ya yi tunanin ko dai wani al'ada ne nasu na daban? Tuna hakan yasa ya ce mata. "Ruwa kenan kike so yanzu?". A hanzarce ta gyaɗa mashi kai. "To ki shiga cikin toilet akwai ruwa, ko dai ruwan sha kike so?". Girgiza kai ta yi tare da cewa. "A'a ba ruwan sha ba ruwan alwala dai". "Menene alwalar?". Ya gefa mata tambayar idanunsa na'a kan face ɗinta, tana matuƙar yi mashi kyau haɗe da burgesa. "Alwala da ake yi kafin ayi sallah mana". Sanin cewa bai gane ina ta dosa bane yasa ya ce. "Ruwa mai kyau dai kike so ko idan na fahimta?". Ya ce mata hakan ne kuma dan baya son wahalar da kansa wajen tsayawa sai ya gane nufinta, dan yasan ba wani ganewa zai yi ba tun da ita ba ƴar cikin birnin nace bare ya ce al'adunsu iri ɗaya, shi bai taɓa ɗauka ma akwai wasu al'adu a duniya da suka sha banban da al'adun su na birnin ba, shi ya ɗauka kowa ma christian ne kawai kamar su. Toilet ya nuna mata. "Akwai ruwa mai tsabta a ciki". Girgiza kai ta fara yi mashi, tsoro ne bayyane karara a saman face ɗinta. Ya lura da hakan, ya lura a tsorace sosai take, dan haka sai ya ce su je ya rakata. Ba musu ta yarda, ya wuce gaba ta bi bayansa. Har cikin toilet ɗin ya rakata, sai da ta shiga ya juya ya fita. Yana fita bai kai ga karasawa tsakiyar ɗakin bama ta fito a guje, saboda ta je neman kwano ta ɗebi ruwa a cikin bokitin da ta gani a wajen pampom kusa da wash hand base, tana zuwa kusa da wajen ɗin wata ƴar baby dake wajen ta ce mata welcome to wash hand base side, wannan ne abin da ya ruɗata ya ja ta fita a dubu, dama idan ba ka saba da su ba dole ka rinƙa tsorata, unexpect ka ji an yi maka magana a cikin toilet kuma kasan kai kaɗai ne a ciki ai dole mutun ya razana tun da ba ya saba bane, da ta saba ne lafiya lou...... Gaskiya Daular Black Tiger duniya ne, wato duk in da zaka je a cikin toilet ma akwai na'ura mai yi maka welcome haɗe da gaya maka side ɗin da kake a cikin toilet ɗin, wannan ko baka san komai dan gane da toilet ɗin ba kamar dai Sweetien ba sai ka nemo mai yi maka bayanin komai ba, na'urorin cikin toilet ɗin zasu gaya maka komai, kuma idan ka taɓa abu a toilet ɗin ka tambayi menene wannan menene kuma amfaninsa tsab zasu yi maku bayani menene da kuma amfaninsu, ba a iya yiwa mutun welcome na'urorin suka tsaya ba, har da yiwa wanda ya shigo bayanin komai idan ma bai sani ba. Kowa ni side da na'urorinsa har da wc. A guje ta fito waje, jin motsin ta fito waje yasa ya juya, yana juyowa ta faɗa jikinsa bata ankara ba. Wani irin shock ya ji tun daga tafin kafarunsa har tsakiyar kai, haƙiƙa yana rungumar ƴan'mata da dama, su Floris duk yana rungumarsu, dan su basu ɗauki hakan a bakin komai ba, amma bai taɓa jin abin da ya ji yanzu da Sweetie ta faɗa jikinsa ba, duk sai ya ji kasala ta sauko mashi a jikinsa. Ita kuwa a hanzarce ta raba jikinta da nasa tare da komawa gefe ta tsaya tana zare idanun kamar ball, ita wannan Daula masifa ce a gareta, ta gaji da fargaba da faduwar gaba, tashin hankali ne zai kasheta, ita ko da iya waɗan nan ƴan iskan na'urorin dake cikin toilet ɗin aka barta mutuwa zata yi da tsoronsu, ba sai an kara mata wani azaban ba, gida ne babu setting a ganinta, wai na'urorin dake magana ne yasa take ganin gidan babu setting, a haka ma bata taɓa cin karo da robot na gidan ba, da sai yaya kenan? Da kila cewa zata yi bata duniya, ko da yake yanzu ma bata yarda a duniya take ba, dan ita rayuwar Forest kawai ta sani. "What happened kika fito a guje haka?". Da kyar ya iya tambayarta, cikin kasalalliyar murya ya yi maganar. "I am very afraid of going to the toilet" "afraid of what your feeling?". Kamar baya son motsa baki yake maganar, dan ta kashe mashi jiki faɗawa jikinsa da ta yi. "There is something in the toilet that talks, I'm afraid of that". Ya fahimci me take tsoro a yanzu, dama kuma yasan in dai baka saba da waɗan nan na'urorin ba dole ka tsorata idan sun yi magana, dan magana suke yi unexpect, da zarar ka doshi waje zasu yi maka welcome tare da ambatar sunan wajen, kunga ai dole bawa ya tsorata. "Okay, let's go, I'll accompany you, then do what you have to do and we'll come back". Kasancewar tasan iya alwala zata yi sai ta aminta da ya rakata ɗin. Haka suka juya a tare tana gaba yana biye da ita izuwa cikin toilet ɗin, yana tafiy a kasale. Tsayuwa ta yi a cikin bata san komai ba, ko iya kunna ruwa a panpo bata yi ba, roba ma ta fara nema ta yi alwalar. Ganin haka yasa ya tambayeta me take nema?. Abin da zata saka ruwa a ciki ta bashi amsa, ƙarisowa cikin ya yi, panpon dake dai'dai da tsawonta wajen kusa da bath pan ya kunna mata tare da cewa ta matso taga yadda ake kunnawa ko dan anjuma. Ƙarisawa wajen ta yi, tana zuwa sai da wannan na'ura ya yi mata welcome, a yanzu kam bata tsorata ba, dan yanzu tasan akwai su a wannan toilet ɗin ma, dama ɗazun rashin sanin suna nan ne yasa ta tsorata. Kunna mata ya yi tare da ɗan jan gefe ya bata waje, tsayuwa yayi ya tsareta idanu, komai nata makurar burgesa yake yi. Ai ba batun tsarki kawai ta hau yin alwala, da kallo ya bita yana mamakin abin da take yi ɗin. Bayan ta kammala ta ce mashi su tafi. Kaman zai tambayeta me ta yi kenan, sai kuma ya ce bari ya zuba ido ya gani, dan yawan tambaya ya kansa mutun baya cin moriyar gani ko kuma jin labari, dan haka bari dai ya bita ya ga me zata aikata. Cikin room ɗin suka koma, saman bakin bed ya zauna ya tsareta da ido, ita kuma ta tsaya turus kamar wata sakarya. Sai da ya tambayeta me ya tsayar da ita ne ta gaya mashi kaya wanda zasu kai mata har ƙasa sosai da kuma abin rufe kai take so. Dressing room na ɗakin ya nuna mata, dan kuwa yasan tun da aka kawota wannan ɗakin to ba makawa akwai abubuwan da zata iya yin amfani da su. Cikin ta nufa, duk wasu drawers dake cikin ɗakin akwai na'urar da zata gaya maka wani irin kaya ne a cikin drawers ɗin bayan ta yi maka welcome, ba sai ka sha wahalar buɗe drawers ɗin ba na'urar zata gaya maka kaya iri kaza ne a ciki, kana dosowa wajen zata yi maka welcome sannan ta sanar da kai. Sam a wannan karon bata tsorata da jin maganar na'urar ba, dan ta fara sabawa da abubuwan al'ajabin dake cikin wannan Daula. Duba abin da zai yi mata dai'dai ta yi sallah ta fara yi, da kyar ta iya samun doguwar rigar da zata kai mata har ƙasa, ta laluɓi hijabi har ta gaji bata samu ba, ko gyale ma babu a wajen bare hijabi, kaya ne kawai da suka saɓa da addinin musulunci cike a wajen shagon kayayyaki, ganin babu hijabi ko gyalene yasa ta laluɓi wata doguwar riga ta ɗan lulluɓa ta fito cikin ɗakin. Ɗan waro idanu waje ya yi yana kallonta, bata san ina ne gabas ba, dan haka sai ta tambayesa ina ne east? Da hannu ya nuna mata a tunaninsa wani abin take nema, bai san ma sallah ba bare yasan gabas ake duba ayita. Gyara tsayuwarta ta yi ta fiskanci gabas ɗin. Mamaki ne ya bayyana a kan fuskarsa na ganin ta tada kabbara ta fara sallan da ita kanta bata san na wani lokaci take yi ba a yanzu. Shiru ya bita da kallo har ta idar da raka'a huɗu ta sake miƙewa ta fara wani, shima raka'a huɗun ta yi ta sallame, a lissafinta azahar da la'asar na jiya kenan, haka ta yi mangariba da isha, sannan ta yi asubar yau, bata san azahar ta sake yi ba, da ta sallame asuban sai kawai ta yi addu'oi tare da rokan Ubangiji da ya yafe mata jinkirta sallah da ta yi da kuma haɗesu da tayi. Bayan ta shafa addu'ar ne ta miƙe ta nufesa, sam bata jin tsoronsa shi kam, dan shi da Floris ne kawai masu sakar mata fuska. Gefensa ya nuna mata a kan ta zauna, cikin ɗari ɗarin jiki ta zauna, sai binta da kallon mamaki yake yi. Kasa hakura ya yi har sai da ya tambayeta me ta yi yanzun nan kenan?. Sallah ta bashi amsa a takaice. "Sallah?". Ya mainaita kalmar mai haɗe da alamar tambaya. Kai ta gyaɗa mashi tare da cewa e. "Menene shi sallah ɗin?". "Gaishe da ubangijinmu". Ta bashi amsa a nutse Ubangiji ya maimaita kalmar. "To ai mu ba haka muke gaishe da Ubangijinmu ba". Cikin nuna halin ko in kula ta ce. "To ya kuke yi kenan?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Anjuma zamu je church ai, idan mun je zakiga yadda muke yi, zan roki yaya ya bari mu je tare da ke sai ki gani, ko da yake ma ai dole ki je tun da kike nan, dole ki girmama ubangijinmu ki je church". A takaice ta ce mashi. "Mu bama zuwa church, a gida muke sallah, ni musulma ce ba Christa ba". "Musulma kuma? Menene musulman?". Ya tambaya yana ɗan kai kallonsa saman room ɗin. Bata san ta yaya zata bashi amsa ba sai kawai ta yi shiru. Shi ma kawar da zancen ya yi da cewa. "In ba damuwa zaki iya bani storynki? Ina son sanin wacece ke?" Tunani ita kuma take yi a kan maganar da ya yi na cewa dole ta je church, kuma haka zancensa yake, in dai tana cikin birnin nan to fa dole ta zayarci church ɗinsu yau da yamma, wannan dokace, suna da ranakun yin ibadunsu, a sati sau uku suke ibadan nasu, ranar Wednesday, Friday da kuma Sunday, a cikin waɗan nan ranaku suke ibada, Friday da Wednesday da yamma suke ziyartar church ɗin, Sunday kuma da safe. So yau zasu je da yamma kenan, lallai akwai kura, Sweetie ta zuwa church, kuma ya zame mata dole yin hakan ba yadda zata yi, tabɗijam!! Kai ta gyaɗa mashi a kan babu damuwa zata bashi labarin nata. Go ahead ya bata a kan ta fara bashi ɗin, yanzu fa ya dawo daga school ko abinci bai ci ba ya tare a wajenta, to Allah dai yasa da gaske har cikin zuciyarsa yake tausaya mata ba haɗa baki aka yi da shi za'ayi mata wayo ba, kafin ta gama bashi labarin nata bari mu leƙa wani ɓangaren mu gani... ______________________🔥💘 PARIS____________FRANCE 55 RUE DU FAUBOURG SAINT-HONIRE _______ELYSEE PALACE🔥💘 Elysee palace wato president house ne na kasar Faransa, kun dai san yadda gidan shugaban ƙasa yake ba sai na tsaya ɓata lokaci na wajen yi maku bayani ba, Daula ce guda, duniya ce guda, to mu shiga cikin gidan ba ɓata lokaci. Ta ko'ina jami'ai ne uniform kala daban daban ke gadin gidan, rike suke da manya manyan bindigu, sai muzurai suke yi, suna ta kewaye a tsakiyar harabar gidan, yadda suke ɗin nan bana jin ko tsuntsuwa zasu iya bari ta iya giftawa ta tsararin samaniyar tsakar gidan, duk da cewa akwai satellite dake ɗauko rahoton duk wani abin da zai gifta ta sararin samaniyar gabaɗaya arear gidan, komai kankantar abu bai isa ya gifta ta arear ba tare da wannan satellite ɗin ta zakulo shi ta turawa na'urorin dake cikin gida bayanai ba, amma duk da haka waɗan nan jiga jigan turawan jami'an riƙe suke da bindigu suna wani kewaye suna ganin sama da ƙasa, kunsan dai yadda ake jibge jami'ai a gidan shugaban ƙasa, to suma hakan ce. Daga kilometer biyu da gidan jami'ai ne jibge ta ko'ina, kai daga gani ƙasan ka doso gidan shugaban ƙasa. Elysee palace ya kasance hawa uku ne kuma duniya guda, mu haura hawa na biyu kai tsaye ba ɓata lokaci. Wani irin................🥱🌝 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 10/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E19 Elysee palace ya kasance hawa uku ne kuma duniya guda, mu haura hawa na biyu kai tsaye ba ɓata lokaci. Wani irin babban parlour ne sosai mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Daga yanayin design ɗin jikin parlourn kaɗai ya isa ya kashe idan mutum, ga wasu manya manya chenese chairs da sukayi matuƙar ƙawata parlourn. Daga gefen hagu wasu irin set ɗin kujerun Dubai set ne a wajan kalar milk da sukayi matuƙar dacewa da parlourn. Babban main parlourn na ƙasa dai parlours ne four in one, saura na sama kuma parlours ne three three in one. Sofa set kala huɗu aka yi amfani da su, akwai milk color, coffee color, ash color sai white colors. So na parlour hawa na biyu akwai milk color set uku, sai parlors dake gefe cikon three in one ɗin su kuma akwai mai sofa set coffee set biyu, ɗayan kuma white color shi ma set biyu. Hmmmmm gidan nan ba'a magana sam sam. Komai na cikin ya yi matuƙar dacewa da yanayin tsaruwar parlourn. Ga wani irin London carfet mai matuƙar laushin a tsakiyar ko wana sets ɗin kujerun parlourn. Daga gefen hagu wani babban glass ne mai ɗauke da manyan abubuwan masu matuƙar tsada a cikinsa. Babbar plasma ɗin parlourn sosai yake da girma, ta ko ina sanyin Ac ne yake tashi saboda manya manya Aç da suke cikin parlourn. Wani irin haske ne yake tashi a cikin saboda yadda manya manyan chandeliers ɗin cikin parlourn suka haska ko ina da hasken su. Daga ɓangaran dama wani irin dining room ne a wajan, mai ɗauke da step huɗu da zai kai ka zuwa inda dinning ɗin yake. Sosai dinning room ɗin yake da girma, ga kujeru na set ɗin dinning ɗin yayi matuƙar dacewa da yanayin tsaruwar wajan. Daga saman dinning ɗin wani farar mini chandelier ce a wajan me ɗauke da zagayayyun fitulu ƴan ƙanana, sai mirror ɗin dinning da aka ƙawata shi da wasu manya manyan warmers, a jikinsa a wajan show class me ɗauke da cups da mini plate a ciki, sai wasu irin chocolate da cookies da aka saka ko wannan cikin mahallin da ya dace. A cikin wajan dinning ɗin akwai mini plasma ita ma mai matuƙar kyau na kallan labarai, sa cuttons ɗin labule white colours ne, ga babbar Acn wajan da take faman hura sanyi ta ko ina a cikin dining room ɗin. Iya haɗuwa da tsaruwa parlourn yayi sama da tunanin mai tunani. Ta ko wani ɓangare idan mutum ya kalli parlourn sai ya sake ɗagowa ya kallesa. Akwai elevator a gidan, sannan akwai stair case mai design of fish da yake da matuƙar ɗaukar hankali. Kun dai san duk wani ginin zamani ya ƙare wajen masu jajayen kunnuwar nan, daga wajensu ake ɗaukar designs. Wasu kyawawan stage ne guda uku a kusa da dining room ɗin, wata ƴar siririyar corridor ce a wajen. Tafiya kaɗan zaka yi ka shiga wata haɗaɗɗiyar parlourn na wani part wadda komai na cikinsa milk and white ne, daga gani wannan part ɗin zaku san na ganiyar na musamman ne a cikin gidan, daga gani mai wannan part ɗin one in million ne, ya ji komai da komai na more rayuwa bawa, komai burinka ba zaka kure part ɗin nan ba, kana shigowa cikinta zaka ce baka da sauran buri kuma. Luxury bed room ne fiye da tunaninku a cikin wannan parlourn, tun daga kan gado zuwa labulaye har zuwa kan chandelier izuwa kan tiles ɗin ɗakin, glass na dressing room and bath pan na toilet, komai da komai white and milk colour ne, komai na cikin room ɗin nan the most effective thing ne, tamkar ba za'a mutu ba, komai ya ji a room ɗin, su kansu furnitures da aka zuba a part ɗin zaka san e lallai wannan part na musamman ɗin na musamman ne, furnitures ne da a wannan part ɗin kawai zaka iya samun irinsu, dan gabaɗaya furnitures ɗin haɗe suke da computers haɗe da na'urori, ko drawers na room ɗin baka isa ka buɗesu ba sai da izinin mai shi, da alama koma waye mai wannan part ɗin mutun ne da ake kauna over, dan tun daga kan matakan tsaron da suke kewaye da wannan part ɗin zaka fahimci e lallai ba ƙaramin kai bane a wajen, ku dubi yadda gidan yake da uban tsaro amma a haka aka gargame wannan part ɗin da uban tsaro har haka. Alkalamina bai isa ya zayyana maku haɗuwar part ɗin nan ba, kawai dai abin da zan ce maku shi ne wannan part ɗin karshe ne wajen haɗuwa. Wani irin fitinannen kamshi mai kwantar da hankalin mai shaƙa ne yake tashi a gabaɗaya arear part ɗin, kana dosowa wajen zaka ji hankalinka ya kwanta a lokacin da ka shaƙi kamshi, shi yake fara yiwa kowani kofar hanci bawa welcome a duk lokacin da ka doso, kana saka kafarka a ciki kuma wani irin sanyin Ac mai haɗe da kamshin ne zai yi maka welcome. Komai na cikin part ɗin tsabar tsabta tamkar yanzu aka buɗesu a leda, kar kar suke!!. Kwance yake a saman wani irin haɗaɗɗen King bed mai bala'in kyau da tsada, shin fiɗe yake da zannuwar gado masu bala'in kyau, laushi da kuma tsada, ya lume cikin bargo ya kuma rufe gabaɗaya jikinsa gar zuwa wuyarsa da haɗaɗɗen bargonsa mai bala'in laushi, jikin bargon tamkar jikin mage, idanunsa a rufe da eyes care mai shegen kyau, gashin kansa ta sauko mashi har gaban goshinsa, baka iya ganin face ɗinsa, saboda gabaɗaya room ɗin duhu ne, ko light ɗin wajen drawers ba'a kunne suke ba bare a je kan sauran bulbs ɗin. Sai dai akwai light mai bada haske ɗan kaɗan a jikin na'urar dake jikin bed side drawers ɗin dake kamar waya. Wani mutun ne ya shigo cikin room ɗin, kai tsaye wajen drawer ya nufa, kasancewar room ɗin babu haske sosai sai yasa ba'a iya ganin wanenen ya shigo. Remote ya ɗauko a cikin drawers ɗin bayan ya sanya fingerprint ɗinsa, a saman drawers ɗin ta side guda akwai wani wajen da yake tamkar waya da glass a jikinsa, akwai password sannan akwai fingerprint a jiki duka, haka dukka furnitures na part ɗin suke, shiyasa nace maku idan bada izinin mai part ɗin ba ko tsinke ba mai iya taɓawa a ciki!. Kunna wutar ɗakin ya yi da wannan remote da ya ɗauko, iya wutar chandelier dake tsakiyar room ɗin ya kunna, nan take wani irin haske ya gauraye cikin room ɗin gabaɗaya, a haka ma bai kunna wutar ɗakin gabaɗaya ba, iya chandelier kawai ya kunna. Hasken da gauraye room ɗin ne yasa wanda yake kwance a saman wannan King bed ɗin ya ɗan matse idanunsa alamar baya son hasken......... Wow duk da bai buɗe idanunsa ba ni dai nasan ban taɓa ganin kyakkyawan guy irinsa ba, ban san ma ya zan gaya maku haɗuwar guy ɗin nan ba........ (Saura na ji kun ce na juyawa Romeo baya🥱 yo na ga kyau iya kyau, ni fa ina son kyau sosai. 🌝 Domin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana matuƙar kaunar kyau, yana matuƙar son kyau da kuma kamshi, kunga a matsayinmu na masu koyi da shi ai dole mu so kyau mu kuma so kamshi🤸💃 sai dai fa babu mummuna a halittar Allah, komai na Ubangiji mai kyau ne sosai, duk wanda ya ga cewa yana kallo wani mummuma a cikin halittar Allah to maza ya yi saurin korar shaiɗanin dake kusa da shi, dan shaiɗan ne yake son zugasa ya kaisa ga halaka, dan babu mummuna a halittar Allah, komai na Ubangijinmu mai kyau and tsabta ne sosai.) My people's guy ɗin nan ya haɗu maƙurar haɗuwa, skin ɗinsa yadda kuka san Korean guy, tamkar madara, a kwance luf, ya ji hutu har ya gaji, hancin nan nasa masha Allah kawai zan iya cewa, wayyo ɗan bakinsa ɗan ƙarami da shi, lips ɗinsa na ƙasa yana da ɗan kauri kaɗan, na sama kuma ɗan pelem pelem design of heard, yawancin maza zaka ga lips ɗinsu yakasance red color, amma shi wannan guy ɗin nasa pink color ne kamar na mata, kun san mata aka fi sani da pink lips, to shi nasa gaskiya pick ne mai matuƙar ɗaukar hankali sosai, yadda gashin kansa yake kwance mashi a gaban goshinsa ba'a magana, bakin kirin da shi yana wani shaki, ba ƙaramin kyau ta ƙara mashi ba, face ɗinsa ta fita ras, kumatunsa ɓul ɓul dai'dai da su, tamkar bai taɓa fita waje ba, hasken fatarsa yana da matuƙar ɗaukar hankali, gashin gerarsa tana nan yadda kuka san zana mashi ita aka yi, tana kwance luf sosai, garasan wajen sajensa basu da yawa sosai, ƴan dai'dai suke a kwance luf, kai guy ɗin nan fa kyansa ya zarce tunaninku, ga wasu zara zaran eyelashes kamar wanda ya sanya na kanti. Kyakkyawar lallausan wuyarsa tana da tsawo ɗan dai'dai, gata a cike da tsoka, sai wani ƴan jijiyo da suka ƙarawa wuyar kyau, sun mashi kamar kwalliya. Ɗan tsuke fuska ya yi sosai kafin ya fara motsawa a hankali, da alama baya son haske a lokacin barcinsa. Idanunsa a rufe ruf ya ɗan motsa lips ɗinsa kaɗan, nan take wasu haɗaɗɗun dimples masu matuƙar ɗaukar hankali suka lotsa a kumatunsa gefe dukka biyun, saura kaɗan na sume saboda wani irin kyan da fuskarsa ta ƙara yi. A hankali kamar baya son motsa bakinsa ya furta. "Why dad?". Haƙiƙa daɗin muryarsa zai iya sanya mutun ya yi shekara yana sauraron maganarsa, in dai ba zai gaji da yin magana ba to haƙiƙa jama'a ba zasu gaji da sauraransa ba saboda tsananin daɗi da kuma laushin muryarsa, gata a sanyaye. Sai dai a kaifafe voice ɗin take, lion voice ke garesa, harshensa da kaifi sosai. Wani irin cool murmushi daddyn nasa ya saki, shi kansa dad ɗin abin kallo ne, hadaɗɗe ne sosai duk da tsufa ta fara bayyana a tattare da shi, jajir yake tamkar ka taɓa jini ya fita, fatarsa luwai luwai. "Wake up, now is our time". "Dad". "Son". "Dad". "Son" "Dad". "Son". Idan ya ce dad sai dad ɗin ya ce son, abin nasu gwanin ban dariya. Ganin daddyn nasa ba zai amsa masa bane sai dai ya ce mashi son sai ya fara ƙoƙarin waro idanunsa dan ya ga daddyn su fuskanci juna. Tamkar baya son buɗe idanun nasa haka ya warosu waje, da alama barci bai ishesa ba............. Subhanallah!! Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu, shin kunga irin wannan haɗuwa kuwa my people's? Idanun guy ɗin nan wani irin idanu ne kaifafa masu cike da gwarjini, tamkar eagle eyes, ga wani shining da suke yi, farin cikin idanun nasa bai yi fari tas ba, ya yi milk milk haka, kwayar idanun nasa kuma hazel ne masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, idanun nasa kaifafa ne sosai da sosai, ba kowa zai iya juriyar ganinsa ido cikin ido ba, da wuya a samu mai kure mashi kallo cikin idanun su ga juna kenan, ga idanun nasa dara dara, kila idan baya kallon mutun mutumin yakan iya kallon cikin idanun nasa, amma su kalli juna ido cikin ido abu ne mawuyaci gaskiya, saboda kaifin idanun da kuma gwarjininsa. Yana buɗe idanun nasa sai kan daddyn nasa dake zuba mashi murmushi mai kwantar da hankali. "Dad why are you always d........." Hannu dad ɗin ya ɗaura mashi a saman bakinsa tare da cewa. "Your mum is waiting for you, zata fita office ne". Wani irin kallon kauna ya wurgawa daddyn nasa kafin ya ɗan kawar da kallonsa yana ɗaure tiger face ɗinsa, dama fuskar a ɗaure, sai ya ƙara ɗaureta. Hannu daddyn ya miƙa mashi. Ya gane nufinsa ya kama hannun nasa ya miƙe kenan. "Daddy now ba zaka iya ba". Ya faɗa yana ƙoƙarin yin ƙasa da bargon jikinsa alamar zai miƙe...... Kada ku mance da English suke magana. Hannun nasa dad ya sanya ya kama kumatunsa tare da cewa. "Before na zama president am a general of SSS". Shiru ya yi bai sake yin magana ba, dan yasan magana kawai daddy yake nema da shi, wai general na SSS! Shi da tun da ya taso siyasa yake bugawa amma wai general ko a ina ya zama general ɗin? Idan dad da mum basu ja shi da magana ba a gidan sam basu jin daɗi, ga shi shi kuma magana wahala take yi mashi!. Miƙewa zaune ya yi..... Ya subhanallah! Iya single da short farare ne kawai a jikinsa, yana da kyan jiki kamar madara, sai dai yana da zanen tattoo a hannunsa ta sama sai kuma a bayansa in da a bayan nasa ya yi zanen eagle mai ɗan girma, ya yi wannan zanen ne kuma saboda da sunan da wasu da dama suke kiransa kenan wato mikiya, shi ɗin tamkar mikiya yake, dan kuwa idan ya doso waje sai ƙananun tsuntsaye sun gudu, tamkar zaki a faɗin dokar dawa yake, shiyasa ya yi zanenta a bayansa, a damatsan hannunsa kuma zanen Tiger ya yi, tattoo ya fito sosai, saboda hasken fatarsa da ta haɗu da bakin zane ai kunga dole ta fito ta yi kyau sosai. Cikakken namiji ne da a shekaru zai iya kai 30 haka, very very smart guy ne na gasken gaske, idan ka gansa ko kai makiyinsa ne sai ka yarda ya ci sunansa na smart gentle guy. Kwakwalwa garesa sosai, yana da baiwa matuƙa, ƙasashe da dama sun so ɗaukarsa aiki amma daddynsa yaki yarda, yana da ƙwaƙwalwar matuƙa, idan ya yi wani abin in ba ka yarda Allah ba yadda baya yin mutun ba ba zaka yarda da shi ya yi ba, sai mai imani da Allah yake iya yarda da baiwar guy ɗin nan, sai kana da imani ka yarda Allah na iya yi wa duk wanda ya so baiwa na musamman a lokacin da yake so ne zaka iya yarda cewa ɗan adam ne ya yi wannan abin da guy ɗin yake yi kuma da ƙwaƙwalwarsa yake yinta, wane computer idan ya yi wani abin, scientist wato ilimin kimiya ne da shi ɗin matuƙa. Ga bala'in ilimin haɗa makamai da yake da shi, wannan dalilin yasa America, England, Russia, south Korea, China duk suke bala'in son ɗaukarsa aiki, amma daddynsa yaki. Sai dai kuma fa shi da daddyn nan nasa da kuke ganinsu ku gansu ne kawai ku barsu a yadda suke, abin ba'a magana, sun munafurci sauran kasashen duniya da suke ƙawance da su irinsu England da sauransu, sun munafurci ƙasan a in da suke haɗa muggayen makamai a ɓoye dan kariya ga ƙasarsu, a matsayin dad ɗinsa na president sai ya yi amfani da wannan dama suke mallakar manya manyan makaman ƙare dangi, duk ƙasar da ta yadda ta takalosu da yaki, to wlh sunan wannan ƙasa shafaffiya a doron duniya, domin kuwa sai Allah ne kaɗai yasan iya adadin mugayen makaman da guy ɗin nan ya jagoranci yaransa suka haɗawa ƙasarsa, wajen da suke haɗa makaman waje ne na sirrri da yake under grawn, daddynsa ya ƙaddamar masa da wannan wajen dan kawai su rinƙa haɗa mugayen makamai, kai guy ɗin akwai basira fiye da tunaninku, irin makaman da yake jagoranta su haɗa sam sam babu wata ƙasa da ta mallaki irinsu, manya manya ne sosai, mugayen makamai ne fiye da tunajinku, ga wasu makaman masu karfi da ya haɗawa kasarsa wadda ake kira da defense system, makami ne mai iya tare makamai masu linzami komai karfinsu, ga shi da shegen sani dan gane da computer kamar wani aljani, Allah ya bashi in dai ƙwaƙwalwa ne. Yana da kishin ƙasa sosai da sosai. Sai dai wannan batu na makaman iya shi da daddynsa ne kawai suka sani, sai kuma yaran team nasa da suke su huɗu, mum ɗinsa bata san da hakan ba, da ta sani ba zata taɓa yarda ba, dan tasan yaronta zai zama abin farautar manya shugabannin manya kasashen duniya, tasan kowa zai farauci ransa ne, dan ku dai kunsan manyan ƙasashen nan basu son ace kowacce ƙasa ta fisu, suna son su zama su ne a kan gaba da kowa, shiyasa zasu nuna suna tare da ku suna sonku dan su leƙi asirinku su rinƙa ganin me ake ciki, amma da yake daddyn nasa shi ma ba baya ba wajen kaifin ƙwaƙwalwa ga iya siyasa, sai ya zamana yana yarda ya yi abota da kowace ƙasa a baki, amma a ƙarƙashin ƙasa munafurtarsu yake yi, baya taɓa yarda kowa yasan halin da yake ciki, ya iya siyasarsa ne fiye da tunaninku, yasan takunsa, akwai shi da shegen wayo sosai. Mum dai sun barta a duhu bata san komai ba, kuma saboda sun san zata hana ɗan nata ne yasa basu bari ta sani ba, in takaice maku dai daddyn nasa ne ya ɓata shi kuma ya mayar da shi haka, saboda haɗa waɗan nan makamai ɗin ya zana wannan tattoon a jikinsa, sannan saboda haɗa wannan makaman ya yi abubuwa da dama kuma ya koyi abubuwa da dama, lokuta da dama yana cikin chemical kala kala na haɗa booma boomai da su roket, ga uban tarin computers a gabansa kamar ba gobe, hakan yasa yake da shegiyar zafin rai kamar zaki, ga shegen saurin fusata kamar me. Zuro kyawawan fararen ƙafafunsa ƙasan bed ɗin ya yi, miƙewa ya yi ya nufi toilet ba tare da ya sake yiwa dad ɗin nasa magana ba. Yana miƙewa wani dogo da shi ga cikar halitta ta jaruman maza, yana da Lion chest faffaɗa sosai. Da kallo kauna daddyn nasa ya bisa har ya shige cikin toilet ɗin, suna kaunar juna shi da dad ɗin nan nasa over, sannan haka suke rayuwa kamar abokai, idan ka gansu zaka rantse abokai ne, shi kaɗai ne ɗansu a duniya, sai ƴar kanwar mum ɗinsu da suka ɗauko suka riƙe, da alama suna son ƴaƴa Allah ne bai basu ba, suna bala'in kaunarsa fiye da tunaninku, yadda kuka san zasu yi mashi numfashi saboda kauna. Izuwa yanzu my people's nasan kun fahimci dalilan da yasa matakan tsaro suka yawaita a part ɗinsa sosai ko? Idan ma baku fahimtar bari na yi maku bayani, abin da yasa duk da yawan matakan tsaron da suke tun daga farkon unguwar har izuwa cikin gidansu, ta ko'ina tsaro ne amma duk da haka sai da aka kara jibge mashi tsaro ta ko'ina sosai, to ba komai bane yasa hakan face haukar buƙatarsa da manyan ƙasashen duniya suke yi, kowacce ƙasa tana son ɗaukarsa saboda kaifin ƙwaƙwalwarsa ba ƙaramin cigaba zai kawo masu ba, America ta yi ta yi ta ɗaukesa amma ta rasa damar samun hakan, duk yadda England take ƙawance da France ɗin amma dad ɗinsa yaki yarda su raba shi da ɗansa ɗaya tilo, kuma bama dan shi kaɗai suka haifa bane yasa yaki yarda ya basu shi, kawai saboda shi ma kunga abin da yake yi shi da ɗan nasa, shi ma gina ƙasarsa yake son yi ya fi kowa, wayo ne da shi shima kamar me, kuma mum ɗinsa ma ba zata taɓa yarda ba, ta ce komai zai faru tana kusa da ɗanta. Coz yanzu dai haukar rububinsa da ƙasashen duniya suke yi ne yasa daddyn nasa yake matuƙar kula da shi sosai, tsaro ta ko'ina tana tare da shi, dan kuwa shi dad ɗin nasa yasan su waye ne ƙasashen da suke neman nasa, suna nan suna shirya duk ta yadda zasu yi su ɗaukesa su sanya shi dole ya koyar da mutanensu haɗa abubuwan da ya iya, kuma matsalar a nan shi ne misali ko da ya koya masu ɗin da wuya su barshi ya rayu, dan basu son cigaban kowace ƙasa sai ƙasarsu kawai, idan sun barshi ya rayu bayan ya koyar da su ma sun san zai yi wa ƙasarsu makaman da ya fi nasu ne dan ai ƙwaƙwalwar tasa ce ba tasu ba, dan haka fasa ƙwaƙwalwar tasa zasu yi da bindiga, hasada ziryan, sai dai fa sun makaro, dan shi ɗin zaki ne na gasken gaske, basu isa su kama shi kuma su tursasa shi yin abin da bai yi niya ba, ba zai yiwu ba, guru ne shi ma sosai, kamar yadda yake haɗa makaman boom masu tafasa haka jininsa yake a tafashe, sannan kuma shi mutun ne da baya yafiya, in dai ka yi mashi laifi to tabbas sai ya hukuntaka, baya yafiya, amma kuma baya kula kowa bare ya shiga harkar mutun, sai in kai ka taɓosa. Ƴar autar sarkin England ake son a aura mashi, manyan ƙasashe da dama suna son aura mashi ƴaƴansu mata duk dan saboda baiwar ƙwaƙwalwar da Allah ya yi mashi da kuma jarumtarsa, in yasa kai a abu fa sai ya aikatasa komai wahalarsa, duk yarinyar da mahaifinta ya yi wa dad ɗinsa magana a kanta sai dad ɗin ya ce baya so, shi guy ɗin ma bai san da wannan zance ba, dan basu isa su tunkaresa da maganar ba, daddynsa suke yi wa maganar, shi ma dad ɗin a siyasance suke yi mashi maganar ba wai zahiriya ba, kowa dai farautarsa yake yi shi kuma basu isheshi kallo ba. Haƙiƙa idan mace zata so guy ɗin nan sai dai dan baiwarsa, kuɗinsa, muƙamin gidansu, ko kuma kyan da Allah ya yi masa, yana da ɗinbin dukiya fiye da tunaninku, dan ba haɗa makamai bane kawai aikinsa, haɗa makamai aikin daddynsa ne wannan, kuma shi baya taƙama da matsayin dad ɗinsa na president, sannan baya taƙama da kuɗin dad ɗinsa, yama fi dad ɗin kuɗi. Mum ɗinsa prime Minister ce fa, sannan ƴa ce ga tsohon shugaban ƙasa da ya sauƙa kafin dad ɗinsa ya hau, in short ma mahaifin mum ɗin nasa shi ya tsayar da dad ɗinsa takara ma, kunga kuwa dan dai dukiya basa magana ne da sun ce sun yi uban yawa a gidan nan a kaisu gaba. Zama daddyn nasa ya yi yana jiransa har ya yi wanka ya fito ɗaure da towel launin milk color a west ɗinsa, ya subhanallah my people's guy ɗin nan ya haɗu iya haɗuwa, ga tsawo da cikar halitta. Ganin dad ɗinsa a room ɗin bai fita bane yasa ya nufi dressing room ɗinsa. Da sauri dad ɗin ya miƙe ya ƙarisa wajensa, yana ƙoƙarin sanya yatsarsa a jikin glass door na dressing room ɗin dan ya buɗeta ya shiga ne dad ɗin ya riƙo hannun nasa, kusan tsawonsu ɗaya da dad ɗin, sai dai ya ɗan fi dad ɗin nasa kaɗan. Jan hannunsa ya yi suka isa wajen gaban luxury mirror ɗin nasa. Zaunar da shi a saman wata haɗaɗɗiyar chair ya yi kafin ya fara kwaso lotion masu tsada yana bubbuɗesu, tsab ya shafa mashi kamar wani ƙaramin yaro. Shiru bai yi wa dad ɗin magana ba har ya kammala. "Let's go in let me dreass you well". Wani irin kallo da ya wurgawa daddyn ba tare da ya yi magana bane yasa dad ɗin cewa. "My smart sarkin faɗa, go and do it by yourself". Bai ce ko uppan ba dai ya wuce ya nufi room ɗin, shi kuma dad waje ya nufa, da alama office zai je, dan shirin suit masu bala'in tsada ce a jikinsa. Kai tsaye dining room dad ya koma. Zaune ya isko wata kyakkyawar farar mace mai gashi har karshen gadon baya, tana sanye cikin wani haɗaɗɗen wandon jeans blue mai bala'in tsadar gaske, ta ciki kuma farar long sleeve t-shirt ce a jikinta, sai ta ɗaura wani haɗaɗɗen long coat launin blue kalar wandonta a sama, ta sanya kular malafa fara kal kalar t-shirt ɗin cikin a kanta, kyakkyawar gaske ce sosai, sannan daga ganinta ƴar wanka ce ta musamman, dan tundaga sama har ƙasa kayan ƴan gayu ne a jikinta, matar ta haɗu sosai, takalamar kafarta kawai ya ishi mutun jari. Ɗan rungumarta dad ya yi tare da manna mata sumbata a kumatu kafin ya wuce ya zauna saman chairs kusa da ita, bodyguards manya manyan guda shidda ne suke wajen table ɗin dan serving mutane abinci. Wata ƴar siririryar matashiyar budurwa ce ta shigo cikin room ɗin, sanye take da wani ɗan iskan crazy jeans dogo har ƙasa da kuma t-shirt ɗan figalalle. Ta saki gashin nan har gadon baya, gashin nata launin dark brown ne mai kyau, kyakkyawa ce sosai ita ma, kamarta ɗaya da mum ɗin smart eagle, ko ku ce mashi smart Tiger. Kamanninsu ɗaya da mum ɗin. Shi kuwa smart Tiger ya fi kama da daddynsa, sai dai basa wani kama sosai can can, amma akwai kamar jini, da gani ba tambaya zaka san daddynsa ne. Tana da zanen tattoo na kunama a saman wuyarta ta gefen hagu, sannan tana da wani zanen a kafaɗarta na flowers, zanen ya fito sosai saboda hasken fatarta. Siririn wuyarta sanye yake da wani diamond chain mai ɗauke da tambarin cross a gaba, hakan yana nuna cewa ba musulma bace ba. "Mum I want to go to office". Cewar matashinyar yarinyar, a shekaru zata iya kai 23 to 25 haka. Da yake su jikinsu baya nuna girma sai ka rantse shekarunta 17 to 18 haka. "You didn't eat your breakfast Heleena". Cewar mum ɗin, tana da sanyin murya sosai, mutuniyar kirkice sosai mum ɗin nan. Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Am okey mum". Muryarta akwai tsiwa a ciki sosai, da alama mafaɗaciya ce sosai. "No I don't agree! Come and have your breakfast before you go out". Cewar daddy. "No dad I can't eat anything now, am late". Tana magana tana kallon ɗan siririn diamond watch dake manne a hannunta, ga wani haɗaɗɗen diamond earrings ƙanana a kunnenta. "No, sit down and have your breakfast". Cewar daddyn, ya yi maganar tare da juyar da kallonsa a kan bodyguards dake tsaye. Umarni ya yi masu a kan su zuba mata abincin nata. Ƙoƙarin tirjewa take yi a kan ita ba zata ci abinci a gida ba dan ta yi latti, ta buɗe baki zata yi mashi tirjiya kenan ta ja burki babu shiri sakamakon kamshin perfume ɗinsa da ya daki kofofin hancinsu. Gabaɗayansu harta bodyguards ɗin kai kallonsu a kan kofar shigowa cikin room ɗin suka yi. Nan take bodyguards ɗin suka kara nutsuwa tun bai ƙariso ba, ita kuwa wannan figaggiyar masifaffiyar yarinyar a hanzarce ta haye saman chair ta zauna tare da ƙara nutsuwa, da ta tsaya zata yi wa dad musu saboda ba shi ya haifeta ba, na gaya maku ƴa ce ga kanwar mum, shi ne ta tsaya zata gwada mashi bai isa ya sanyata yin abin da bata yi niya ba, ko da yake su turawan nan dama can ko iyayensu da suka haifesu ba jin maganarsu suke yi ba, saboda su suna ganin da zarar sun kawo karfi shikenan sun sami ƴanci, iyayensu basu isa da su ba, amma dai ba'a rasa masu natsuwa kamar yadda a ko ina akwai na gari kuma akwai na banza, sai dai su gaskiya gwammatinsu ne ma ta bawa kowa ƴanci, iyayensu kuma suka kara lallatasu, dan tun farko iyayen ne ke biye masu suna yin abin da suka ga dama har su zo su fi karfin iyayen ya zama sune suke komawa kamar su ne iyayen........ Na kara jin sanyi a rai da Allah yasa ni musulmace da na san darajar duk wani babban mutun ba ma iyayena kawai ba!!. A hankali yake takowa tamkar baya son taka ƙasa. Yana isowa wajen kofar ta buɗe mashi kanta, dan da na'ura take amfani, da zarar ka dosota zata buɗe kanta, kofofin gidan dukka suna da tsaro sosai, kun dai san yadda gidan his excellency mr President yake ba sai na tsaya ɓata bakina wajen yin dogon bayani ba. Yana shigowa ɗaya daga cikin bodyguards ɗin dake wajen ne ya janyo mashi chair baya ya zauna. Shirye yake cikin wandon jeans white color, rigar jikinsa round neck t-shirt ce milk color, kasancewar akwai sanyi matuƙa sai ya ɗaura wata haɗaɗɗiyar white jacket, ya sanya hular jacket ɗin a kansa, kyawawan fararen ƙafafunsa suna cikin black socks and luxury booth mai kyau fari, wuyarsa da wani ɗan siririn chain mai bala'in tsada, hannayensa ɗaya ɗaure yake da danƙareren agogo diamond, ɗayan kuma ɗaure yake da chains na hannu na zallar madarar zinari masu bala'in tsada, kai guy ɗin nan ɗan wanka ne na bugawa a jarida, akwai iya ɗaukar wanka ga shegen tsabta kamar me, ya haɗu iya haɗuwa. Kara ɗaure tiger face ɗin nan nasa ya yi kafin ya ɗan motsa lips ɗinsa a hankali furta. "Good morning mum". Ta tsare shi da kallo kamar zata mayar da shi cikin cikinta saboda tsananin so da kauna, kai daga ganin yadda take kallonsa zaka san tana bala'in kaunar ɗan nata fiye da tunaninku. "Morning my baby, how was your night?". Shiru ya yi bai sake amsawa ba. Umarni dad ya bawa bodyguards a kan su zuba mashi abinci. Abincin gidan nan fa idan aka girka shi kafin a kawo shi saman dining table sai an yi scanning ɗinsa, sai na'ura ta tace shi an tabbatar babu wani abin cutarwa a cikinsa, duk dan saboda tsaro, ga shi abincin different kala suke dafawa, sai ayi girki sama da kala 10 lokaci guda........ Ni kam nace koma me zaku yi da zarar wa'adin da Allah ya ɗebawa bawa ya cika dai mutuwa dole ce babu tantama kuma babu wanda ya isa yasa a fasa mutuwa.......... Irin wannan tsaro haka! Dama kunsan shuwagabannin ƙasa fa haka suke, komai nasu daban ne, komai zasu ci kuma sai an bincikesa tsab. Hannu ɗaya ya ɗaga masu alamar baya buƙatar cin komai tare da miƙe tsaye. Wata black zazzafar luxury glass ya ciro daga aljihunsa ya sanya a idanunsa, nan take ya kara wani masifaffen kyau. Tun da ya shigo wajen Heleena ta tsare shi da ido, da alama tana tsoronsa sosai, dan yadda ta zauna ta nutsu daga jin kamshin perfume ɗinsa ya nuna basa shiri sam sam, dan kuwa ita ɗin bata da kunya ko kaɗan, idan ta tashi rashin kunyarta bata ragawa kowa a cikin gidan sai shi ɗin, idanunta a tsai tsaye a tsakar ka na rashin kunya, ko daddy bata raga mashi, duk abin da ya zo bakinta take faɗa masu ba tace magana, shi kaɗai take mahaukacin tsoro, kuma tun da yake da ita sau ɗaya ya taɓa dallah mata wani marin da yasa sai da ta sume aka kaita gadon asibiti, daga nan take bala'in tsoron ma su haɗa hanya, dan kuwa ya sauke mata aljanun iskancin da suke kanta na rashin kunya, duk abin da take yi idan ta gansa zata bari ta nutsu sai ya wuce. Mum ce ta ce ina zai je bai yi breakfast ba?. A takaice ya ce mata yana da meeting ne da wasu yaransa. Daga haka ya sanya kai zai wuce. Miƙewa mum ɗinma ta yi ta bi bayansa. Ɗaure fuska sosai Heleena ta yi, da kallo ta bisu. Riko hannunsa mum ta yi suka fice daga room ɗin kamar wadda zata je ta gaya mashi wani abin, amma nan raka shi wajen motarsa zata yi kafin ita ma ta wuce nata office ɗin, tun da ba zai yi breakfast ba ita ma ba zata yi ba kenan, akwai shaƙuwa da kauna sosai a tsakaninsu. Suna futa a filli Heleena ta furta. "I already knew that you didn't love me at all". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye cikin ɓacin rai, ba komai ya ɓata mata rai ba kuma face yadda suke a gidan, shi Smart idan ya yi magana ɗaya iyayen nasa basa jayayya da shi, ita kuma idan ta yi magana sai sun ja da ita, yanzu ta ce ba zatayi breakfast a gida ba sun ce basu yarda ba dole ta yi a gida, shi kuma daga ya ce ba zai ci a gida ba sun yi shiru basu kara magana ba, sai ma fasa yin breakfast ɗin su ma da suka yi, to hakan ne yake ɓata mata rai, sai ta rinƙa ganin kamar suna nuna mata banbanci da shi......... Ni kam na ce Heleenar nan yadda take jin haushin nan tsab idan aka kawo mata contract na kashe smat zata karɓa, gaji yarinya ai sonki ma akeyi da aka matsa maki ki ci abinci amma baki gane ba. Kai tsaye harabar gidan mum ta fita tana riƙe da hannunsa. Suna fitowa ji kake dip! Dip! Dip gudun manya manyan jami'ai ƙosassu masu ji da lafiya kuma madaka katti, dukkansu jami'an dake gidan fararen turawa ne masu jajayen kunnuwa. Da hannu ya nunawa jami'ai guda biyu su fito mashi da motocinsa fita zai yi ba tare da ya yi magana ba, da alama magana tana yi mashi wahala. Ko da yake irin wannan kyau da Allah ya yi mashi dole ya ja aji sosai, dan yasan shi ɗin one in million ne. Hira mum ɗinsa take yi mashi ba tare da ya amsa mata ba, yana dai jinta kawai, sai bashi labari a kan wajen aikinta take yi, daga karshe ta ce mashi ko dai zai kaita wajen aiki ne yau?. A takaice ya ce mata no mum. Bata ja da shi ba kawai ta ce a fito mata da jerin gwanon nata motocin. Haka kuwa aka yi, wata dankareriyar mota aka fito mashi da shi, motocin jami'ai kala huɗu ne suka take mashi baya, mota ɗaya na swat ne, mota ta biyu na special emergency unit wato SEU ne, su ɗin tamkar wuta suke, aiki da cikawa, baku ji sunansu bane? Emergency suke, abu yana faruwa faka faka zasu dira a wajen su yi handle na komai and they solve everything, so motarsu ce ma a gaba kafin nasa, dan su tabbatar mashi da tsaro, jama'ai ne da suke na musamman. Mota na uku kuma jami'an SSS ne a ciki, suma jami'ai ne masu zafi, duk waɗan nan jami'an sun take sojoji a iya aiki, jarumta, ilimi haɗe da zafin nama, jami'ai ne na musamman masu aiki da ƙwaƙwalwa mamar computer, sannan suna aiki da karfin damtse kamar me. Smart Tiger a da can baya baya taɓa yarda a take mashi baya, dan a cewarsa ai shi ya fi sojoji da ƴan'sanda power to bai ga abin da zai sa su take mashi baya ba tun da ko wani abin ya faru ma sai dai shi ya karesu ba dai su karesa ba, sai dai ya agaza masu, dan haka shi bai ga amfanin su take mashi baya ba, ragwaye ne a cewarsa, wannan dalilin yasa daddynsa a matsayinsa na president ya ƙaddamar mashi da jami'ansu na musamman waɗan da suka take sojoji da ƴan'sanda a tafasar jini da iya aiki, shi ne yasa ya yarda suna take mashi baya, dan ba kananan jarumai bane, nan ma fa sai da mum ɗinsa ta saka baki ne ya yarda su rinƙa take mashi baya su ɗin ma, idan ba haka ba yaki yarda, ya ce suma ƙananan kwari ne, daddynsa kuma yana jin tsoron kada wata ƙasa ta yi kwantan ɓauna ta sace mashi yaro shiyasa bai yarda yana barinsa ya fita shi kaɗai ba. Duk da hakan kuma wlh smart sai ya fita shi kaɗai ɗin, shi fa gani yake shi ɗin zaki ne a cikin namun dawa, gani yake yi babu wanda ya isa ya ce zai kawo mashi wargi, kuma haka ne, yasan abin da ya taka, ba ƙaramin kwaro bane shi ɗin. Mota ta huɗun kuma jami'an NDLEA, motocin biyu suka yi gaba, sannan nasa a tsakiya, sai biyu suka rufa mashi baya. Juyowa ya yi ya ɗan yi hugging na mum ɗin tasa, sannan ya manna mata sumbata a kumatu bayan ya raba jikinsu, ita ma sumbatar kumatun nasa ta yi tare da ɗaga kafafunta tana son shafa kansa, sai dai bata iya yin hakan ba, dan ya fita tsawo sosai. Ɗan sunkuyo mata kaɗan ya yi ta shafa kan nasa. Sannan suka yi sallama tana sakar mashi lallausar murmushi. Motar tasa ya nufa, ita ma ta nufi nata jerin gwanon motocin ta shiga. Da gudu securitys suka buɗe masu kofofin motocin nasu, gidan baya ya shiga, ita ma mum a nata motar hakance, gidan baya ta shiga. Wani katon bature fari tas ne yake tuƙa nasa motar, ita ma mum haka. Jerin motocinsa ne suka fara dallawa waje a tsananin guje, sun ɗan jima da tafiya kafin motocin mum ya tashi, dan ta tsayar da su tana waya da dad da ta barosa a cikin gida, sai da ta gama da shi sannan ta ce su wuce. Gudu suke shararawa da motocin nasu kamar zasu tashi sama har suka fita arear Elysee palace dake jibge da securitys ta ko'ina kamar zasu tashi arear, duk in da suka gifta da sunan zasu wuce sai securitys ɗin wajen sun ɗaga hannu sun sara masu cikin girmamawa. Kai tsaye Avenue Montaigne Suka nufa, unguwa ce ta manya manyan kai bana ƙananun kwari ba. Duk gidajen dake arear sun amsa sunansu gidajen gaske. Manya manyan luxurious highrise buildings ne kawai a arear, idan ka shiga wannan arear kauyanci ma kawai zai hanaka motsawa daga in da kake Ya ilahi ya lillahi, my people's ku zo ku ga aljannar duniyar da babu irinta a nan, tun daga kan titin da zata sadaka da cikin gidan wasu irin mahaukatan securitys aka suba a wajen, securitys ne wanda ko giftawarsu ka gani a cikin Tv sai hantar cikinka ya kaɗa, jiga jigai ne masu lafiya, sai safa da marwa suke yi a wajen, ga wani uban zare jajayen idanunsu da suke yi suna muzurai kamar mutun ya ruga a guje, yadda suke tsaye suna kewaye ko'ina a wajen bana jin kamar zasu iya barin ko tsuntsuwa ne ta gifta ta tsakar sararin samaniyar harabar wannan gida. Babban gida ne sosai mai matuƙar girma da ɗaukan hankali. Daga yanayin tsarin gidan mutum zai tabbatar da maƙudan kudin da aka zubar wajan tsara shi ba zai ƙirgu ba. Ta ko wani ɓangare gidan ya haɗu sosai da sosai. Daga wajan gidan akwai wasu flowers da masu kyau da aka ƙawata wajan da su, sai babban gate ɗin gidan mai matuƙar girma da ɗaukar hankali, ga securities ta ko ina da suke shawagi hannayensu ɗauke da bindigu, har zuwa second gate ɗin da yake wajan, wanda tazaran sa da fırst gate ɗin mutum sai yayi kusan 5 minutes a hanya . Daga harabar gidan babban fili ne me ɗauke da shuke shuke masu kyau da ɗaukar hankali, sai babban titin da zai kai mutum har zuwa main building. In short wannan gida ya kai filli girman plot 50. Parking space na wannan gida kawai ya kai girman fili plot 10, tsab zai iya kwasan motoci sama da guda hamsin, a haka kuma cike yake tab da zafafan moto. Pentin gidan gabaɗaya ya kasance white color ne, my people's wannan gidan ya haɗu, Allah ya bamu aljannatul firdaus my people's, ku ce amin!. Da electric stair case suke amfani, amma akwai elevator ma, sai dai sun fi yawaita yin amfani da electric stair case ɗin, komai na cikin gidan nan ba ƙananan ƙuɗaɗe aka zuba wajen sayansu ba, lallai ba shakka dollars sun yi kuka kuma sun yi mubaya'a a wannan ginin. Tampatsa tampatsan gate ɗin gidan dukka biyu wasu irin jiga jigan securitys ne suke tsaronsu. Suna dakatawa a parking space na gidan, gabaɗaya jami'an suka sauƙo ƙasa. Bai bi ta kan kowa ba suna buɗe mashi kofar motar yasa kai ya nufi cikin gida. Wani irin azabbabben daddaɗar kamshi ne yake tashi tun daga ɗan nesa da hanyar nufa cikin parlourn gidan, idan nace zan tsaya zayyana maku haɗuwar wannan gida sai mu kwana mu wuni bamu kammala ba, dan haka ku ƙawata shi a ranku, ni na yi gaba na je na leƙo maku ciki ba zan ɓata lokacina a wajen harabar gida ba. Shi kaɗai ya shige cikin parlourn, duk sauran securitys da suka rakosa sun tsaya a waje wajen securitys da suka samu a gidan. Yana shigewa cikin parlourn ya nufi luxurious dining room ɗinsa, wannan gida dai ba gidan kowa bane face gidansa, bashi da mata, bashi da budurwa, hasali ma bai taɓa yin soyayya ba, kuma bashi da niyar yin matar amma yana da tampatsetsan gida irin wanna, bama wannan ne kawai ba, yana da gidaje sosai, sannan shi mutun ne mai yawan kyauta sosai, yana sadaka fiye da tunaninku, idan zai yi kyauta kuma baya zaɓar wa zai bawa, duk wanda ta faɗa kansa kawai bashi zai yi, duk da bashi da sauƙin kai da tausayi amma yana da zuciya mai kyau, ga taimakawa gajiyayyu, kuɗinsa basa tafiya a banza. Yana zama saman table ɗin sai ga wani na'ura mai siffar ɗan adam ya shigo wajen. A gabansa na'uran ya tsaya yana jiran umarni. Ya ɗauki tsawon lokaci yana latsar wayarsa wadda shi kaɗai company ta kerawa irinsa, shi ya bada design da duk wasu abubuwan da yake buƙata da yadda yake so wayar ta kasance, wane mutun ya iya bibiyarsa ta wannan waya, a garƙame take da matakan tsaro na ban mamakin gaske, komai maitancinka a iya computer baka isa ka datsi tsaron dake tattare da wannan waya ba har ka shiga cikinta, dan shi ma guy ɗin shegene a fagen iya computer So ya jima yana latsa wayarsa kafin nan ya bawa na'uran umarni ya kawo mashi breakfast da ya fi kauna, ya haɗa mashi da Espresso strong coffee...... Ko meyasa yaki yin breakfast a gida ya zo gidansa?. Da sauri na'urar ya juya ya bar wajen. Cigaba da latsa wayarsa shi kuma ya yi. A hankali sautin ringing ɗin wayarsa ta fara tashi, shiru ya zubawa wayar sexy eyes ɗin nan nasa masu shegen shining kamar me. Har wayar ta katse bai ɗauka ba, ƙira na biyu ne ya sake shigowa, a dai'dai lokacin kuma wannan na'ura mai yi mashi aikin ya dawo hannunsa ɗauke da wani jibgegen glass tray mai bala'in kyau. Kayan abinci kala kala ne a saman wannan haɗaɗɗen tray ɗin tare da spoon, knife da sauransu. Saman table ɗin ya ɗaura trayn, sannan ya tsaya a gefe yana jiran umarnin ya hau yin serving. Kira na uku ne ya sake shigowa, a lokacin ne ya yi pick tare da sanya wayar a hand-free ya ɗaura saman table ɗin a kusa da shi tare da ɗauko tsadaddiyar cup dake cikin tray ɗin mai shaƙe da Espresso strong. A hankali ya kai ɗan bakinsa, lips ɗin nan nasa ba'a magana, yana ɗaukar hankali matuƙa. Kaɗan ya ɗan kurɓa ya cire, a nutse yake bin komai daki daki, cikin class mai jan hankali. Daga cikin wayar tasa wata ƙatuwar fasashiyar murya ta furta. "Sir the RS52-nuclear was mistakly feared". Cikin tashin hankali mai maganar ya yi ta, yadda yake maganar har word ɗinsa suna haɗewa. Shiru ya yi bai yi magana ba, kuma bai nuna alamar kamar ya shiga tashin hankali ba duk da ya ji cewa sun yi mistake sun saki nuclear bom ɗin, basu yi setting ɗinta ba aka samu akasi suka saketa, amma hankalinsa a kwance, cigaba da shan espresso strong ɗinsa ma ya yi. Daga cikin wayar wanda ya yi maganar ya sake cewa. "Hello sir I said the RS.........". Bai bari ya ƙarisa sake faɗa ba ya sanya kyakyawan hannunsa ya katse kiran. Lallai akwai cakwakiya, wannan guy ɗin gaskiya bana ce komai ba, ace maka nuclear ta kwace ta fita amma yana zaune yana sharholiyarsa?🤔 Akwai matsa in dai haka ne, ni dai bari na hau jirgi sai ƙasar Nigeria cikin birnin jimeta Yola mu dubasu mu gani, kila kafin mu dawo ya farka daga barci, dan ni ban yarda cewa baya barci ba, nuclear bom fa ake magana amma yana zaune, kuma shi kaɗai zai iya shawo kan matsalar, to ni dai kada nuclear nan ta yo Nigeria ato, ta tsaya a ƙasar tasu ko kuma ta yi ta yawo a sararin samaniyarsu, na dai gudu abina. _________________________🔥💔😥 JIMETA🔥 Duk wani karfi dake tattare da shi ne ya kare sakamakon wannan aman, kan kace me ya zube ƙasa ya kwanta, sama sama yake numfashin tamkar ba zai rayu ba. Bappa dai bai karaya ba kuma bai ji komai ba ya matso ya fara yi mashi sannu. Wani irin fita da karfi karfi numfashinsa ta fara yi tamkar zai sume, bawan Allah dama bashi da lafiya ya zo kuma ya ƙarisar da ɗan karfin da yake da shi a wajen yin amai. A ruɗe bappa ya miƙe tsaye ya nufi waje har yana haɗawa da gudu. Matasa ya nemo a kan su zo su taimaka mashi ya kai Jaish ɗin ɗaki ya taimaka mashi da agajin gaggawa kada ya mutu......... My people's ina son ɗaukar hutu, kuma ina son in bari sai mun kai ƙarshen book 2 ko tsakiya sai na ɗauki hutun, wanne kuke ganin ya fi? In ɗauki hutu yanzu ne ko sai na kai tsaki ko kuma karshen book 2? Ina son in ɗan huta kwakwal ta yi fresh ta ƙaro walaƙanci, 😅 ku tayani da addu'a.......✍️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 11/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E20 Matasa ya nemo a kan su zo su taimaka mashi ya kai Jaish ɗin ɗaki ya taimaka mashi da agajin gaggawa kada ya mutu. Kama shi suka zo suka yi izuwa cikin ɗakin, a saman gado bappa ya ce su kwantar mashi da shi. Duk kyakkyamin nan nasa yana ji yana gani suka kamashi izuwa cikin ɗakin, kamar ba zai rayu ba! Sai ma da suka kama shi ne jikin nasa ya ƙara tsananta ciwo, dan kuwa da alama wannan uban kyakkyamin nasa a jini take, shiyasa yake fama bawan Allah, kun san akwai waɗan da abin a jininsu yake, akwai waɗan da kuma tsabta ce ta ja masu hakan, idan kana da tsabta sosai tana iya ja maka hakan, to shi bayan tsabta ma a jininsa take abin, shiyasa ko ya ce zai bari ma zai sha bakar wahala ne a banza, dan ba abu bane da za'a iya barinta kamar yadda kuke tunanin nan. Datse idanunsa gam ya yi baya son ganin cikin ɗakin bappan, saboda kyama, ga shi bashi da wani zaɓin da ya wuce ya kwanta shiru, saboda ko motsawar kirki baya iya yi, cikinsa ne yake bala'in murɗa mashi kamar zai mutu. Magunguna bappa ya hau jiƙa mashi tare da yi wa mutane da suka taimaka suka kamashi izuwa cikin ɗakin godiya. Idanunsa a datse gam yana numfashi sama sama har bappa ya kammala jiƙa magungunar, su kuma samarin suka yo waje, ɗaya daga cikinsu ya ɗauki Mahreen izuwa cikin ɗakin ya kwantar da ita a gefen Jaish ɗin, sannan suka fice daga gidan. Idanunsa a datse bappa ya fara ɗura mashi magunguna masu uban ɗaci kamar me, abin da bai taɓa sha ba, ko a mafarki bai taɓa mafarkin zai sha irinsu ba, ga shi bashi da zaɓin da ya wuce ya haɗiye a cikin cikinsa dan dolensa, dan kuwa kansa yana ɗage da pillow ne, yadda bappa ya sanya mashi bakin kwaryar a ɗan bakinsa dan dole ya haɗiye, dan bashi da karfim da zai iya ture maganin ko kuma ya iya ture bappa or ya yunkura ya ce zai fitar da maganin, bashi da kuzarin iya motsa kansa ma bare iya amayar da maganin, haka ya ƙara datse idanunsa ya jin maganin tana ratsa maƙogwaronsa izuwa cikinsa, wani irin takaici da yake ji kamar zai mutu, ji yake yi kamar ya tashi ya shaƙe bappan har sai ya mutu, amma dukka babu halin yin hakan. Tsab bappa ya yi mashi duk abin da ya dace, sannan daga karshe ya ƙara mashi da maganin cin abinci na gargajiya, a lissafin bappan idan ya bashi maganin da zata sanya shi cin abinci zai ci abinci sosai dan ya samu kuzarin jikinsa.......... Ni kam na ce lallai ba shakka bappa ya gama da Jaish tabɗijam, yanzu yunwa da ba kanwar kowa bace zata nukurkushe mana Jaish na mu ta yadda dan dolensa ya nemi abinci ko dan ya rayu. Akwai matsala gaskiya, bappa dai bai kyauta ba da wannan magani na cin abincin gaskiya .......😥💔 Cin abincin ruga ya kama Jaish Innalillahi. Ko da yake Mahreen zata yi mashi gata wajen bashi a baki, idan ya ki ci ma zata iya yi mashi ɗure wannan yarinyar kam........ Duk kuma cikin gata ne!.😎 Barci mai nauyin gaske ne ta ɗaukesa. Fitowa waje bappa ya yi, ruwa ya ɗebo ya zo ya yayyafawa Mahreen, abin mamaki a nutse ta farfaɗo, tana farfaɗowa kuma ta fara rambayar bappan nata ina aljaninta yake?. Da hannu bappan ya nuna mata shi, sannan ya ce. "Jeki ki kira mun hammanku Faisal kin ji?". Turo baki ta yi, a shagwaɓe kamar zata yi kuka ta ce. "Amma bappa kasan dai bana son hamma Faisal ɗin nan ko?". "Yi hakuri gajina jeki ki kira mun shi kin ji ko? Daga yau na yarda baki son shi". Miƙewa ta yi tana turo baki ta nufi waje. Kai tsaye gidansu Faisal ɗin ta nufa. Tana shiga ta gaida Innarsu, sannan ta ce bappa na kiran hamma Faisal, bata jira amsar Innar ba ta wuce ta fice abinta. Gida ta koma, a lokacin bappa yana hura wuta a kitchen, Nenne kam har yanzu bata dawo ba. Wuta ya hura ya ɗaurawa Jaish ruwan wanka, bayan ya ɗaura ya fito waje, Mahreen kuwa ɗakinsa ta shiga, a kusa da Jaish ta zauna ta tsare shi da idanu, ita dai a duniya aljanin nan nata yana matuƙar burgeta, ya yi mata kyau sosai, bata gajiya da kallonsa, sannan bata son kawar da kallonta a kansa, sai dai yau bata taɓa mashi kumatu ba, domin shakkarsa ya ɗan shiga ranta, ta ji tana ɗan shakkarsa. Sallama cikin nutsuwa Faisal ya yi a bakin kofar gidan kafin ya shigo ciki. Har ƙasa ya duƙa ya ɗagawa bappa gaisuwa, cikin so da kauna bappa ya amsa mashi tare da ce mashi. "Yau Shehu ne ya tafi kiwon shanun bappanku ko?". Kai ya gyaɗa mashi alamar e. "Tom dama so nake ka je ka karɓawa Mahnoor kiwon nan ta dawo gida, ta zo ta yi mana girki, ni yau ba zan samu fita ba". Da to ya amsa mashi tare da miƙewa tsaye ya nufi waje. Ruwan albarka bappa ya fara sanya mashi, da amin amin ya yi ta amsawa har ya fita, bappa yana kaunar Faisal sosai, a yanzu bashi da burin da ya wuce yaga ya ɗaura mashi aure da Mahnoor, haƙiƙa Faisal yaron kirki ne sosai, ga girmama manya da sanyin hali sosai da sosai, baya son yanayina kuma baya yi, bashi da faɗa kamar na sauran matasan ƴaƴan fulani, ko takalarsa faɗa kayi baya kula mutun, yana da hakuri sosai da kawaici haɗe da kunya, idan kunji yana magana ma to sun haɗu da abokiyar faɗarsa ce wato Mahreen wanda dama can ita bata zaman lafiya da kowa, duk wanda ya ce mata kule sai ta ce cas, to da ita kawai zaku ji yana magana mai sauti, sai masoyiyarsa abar kaunarsa wato Mahnoor. Yana fita ba jimawa sosai sai ga Mahnoor ɗin ta dawo, tana shigowa Nenne na shigowa tamkar a tare suke. Ai Nennen tana shigowa nata ɗakin ta nufa da sauri saboda tsoron Jaish, tana bala'in tsoronsa sosai. Ita ma Mahnoor akwai tsoron nasa dai, amma haka ta nufi kofar ɗakin bappan jiki na kerma, kirjinta sai dukan uku uku yake yi. A bakin kofa ta tsugunna tare da cewa bappan. "Bappa jamɓandu?. (Bappa ina wuni?)". Yana daga cikin ɗakin zaune a kusa da Jaish da kuma Mahreen ya amsa mata gaisuwar tata sannan ya ɗaura mata da cewa abinci zata girkawa bakonsa mai daɗin gaske. Ɗan zaro idanu ta yi kafin ta ce. "Bappa dama aljanu ma suna cin abinci ne?". Kyakkyawar murmushi ya sakar mata kafin ya bata amsa da. "Mahnoor baki yarda da bappanki bane?". Girgiza kai ta yi tare da cewa. "A'a bappa na yarda da kai". "To idan har kin yarda dani kuma zan yi magana ki ji to na gaya maki wannan bawan Allahn ba aljani bane, mutun ne kamar kowa, ku dai'na ɗaukarsa a matsayin aljani, sannan batun kyansa da kuka damu sosai a kansa ku sani akwai mutane kyawawa sosai a duniya, ba yadda Allah baya halittar bawa, amma na maku alkawari ke da Mahreen in zan sake fita Nigeria zan tafi daku, ko Cameroon kuka je akwai turawa mazauna can sosai bama sai a Nigeria ba, akwai larabawa, to wannan bawan Allahn yana ɗaya daga cikinsu, ko bature ko balarabe, ni nasaba ganin irinsu shiyasa ban damuba, dole ma idan zan sake tafiya in tafi daku dan ku kalli irinsu saboda ku rage tsoro". Ya kai karshen maganar yana kallonta. Ɗan karkatawa ta yi ta leƙo fuskar Jaish ɗin kafin ta sake dawo da kallon nata a kan bappan. "Tom shikenan bappa, na yarda ba aljani bane, amma ni dai ina jin tsoronsa har yanzu, bari na je na dafa mashi tuwo dawa da miyar zogale". A hanzarce bappan ya fara girgiza mata kai tare da cewa. "A'a Mahnoor ba zai iya cin irin abincinmu ba ai, su basa cin tuwo, kinga yanayinsa ya yi maki kama da wanda zai iya cin tuwo ne?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a. "Yauwa ai ba zai iya cin irin namu abincin ba, yanzu dai zan yanka mashi zabbi da kaji ko guda goma ko ashirin haka, sai ku gyara ku soya mashi, nasan nama kam zai iya ci tun da suna ci, sai a rinƙa dama mashi fura yana haɗawa kafin ya samu sauki ya koma garinsu". "Tom bappa, bari na sanya ruwa a wuta dan gyara kajin". Da to ya amsa mata, miƙewa ta yi ta nufi kitchen, shi ma bappa ya miƙe ya fito waje, wajen kajinsu da zabbin nasa ya nufa, haka ya zaɓo manya manya guda ashiri, kaji goma zabo goma, ƙosassu ya zaɓo, sannan ya tsinto kwan zabi dayawa ya dawo da su cikin gidan. Mahreen ce ta riƙe mashi wuyar kajin ya yankesu dukkansu, Mahnoor bata taɓa yarda ta riƙe mashi kaji ya yanka, saboda tsoro irin nata, sannan tana da raunin zuciya sosai, idan ana yanka kaji tana wajenma har kuka take yi, dan tausayi suke bata, ba zata iya ganin ana yankasu ba, sai ma idan ransu ya zo fita, a wannan lokacin kuka sosai take yi, shiyasa bata tsayawa a wajen da ake yankan, ita kuwa Mahreen sarkin taurin zuciya da rashin tsoro, ai tuni take riƙewa bappa ya yanka, ita ko wukar aka bata tsab zata karɓa ta yanka da kanta, ai wannan yarinya special ɗin specials ce. Dukka ya yankasu, da shi da Mahreen suka haɗu suka taya Mahnoor gyara kajin, Nenne dai taki fitowa daga cikin ɗakinta, tana kwance tana tunanin wani irin mugunta zata ƙullawa Mahnoor wanda zai sanya bappa ya tsaneta ya dai'na sonta, ya jima tamkar ya kasheta idan ya ganta, abin da kawai ta kwanta take tunani kenan. Baiwar Allah Mahnoor kuwa tana can tana aikin farantawa mahaifinta rai tana samun lada ba tare da tasan me Nenne ke shirin kullah mata ba. Sai misalin karfe 3 ta gama soya kajin nan dukka, dan ma Bappa da Mahreen sun tayata sosai, ta gama bappa ya ce ta dafawa Jaish ɗin kwan zabbi bari ya duba gonarsa ko akwai nunannun kaya itatuwa ya taho mashi da su a haɗa mashi a kayan abincin nasa kila zai ɗan iya ci. To suka ce mashi, wucewa ya yi ya fita ita kuma Mahnoor ta juye ruwan zafin dake saman wuta ta je ta yi wanka. Mahreen kuma ta kwashe namar ta kai shi cikin ɗakin bappa. Mahnoor bayan ta fito daga wanka shirin zuwa Islamiya ta yi fes abinta ta fito, sannan ta ce da Mahreen ta fito daga ɗakin bappan nan ta wuce tazo ta yi wanka ta yi shirin zuwa Islamiya bari ita kuma ta tattare gidan ta share kafin lokacin yin sallar la'asar ta yi sai su yi sallah su wuce islamiya, sam basa jin yunwa dan sun ci namar kajin sosai sun ƙoshi, da yake su kam ma ba bakin nama bane, kullum Friday bappa yana tanka masu ƙaton rago ƙosasshe guda ɗaya, kaji kuwa duk lokacin da yaga dama yana yanka masu, so su nama baja baja suna da shi. Tsintsiya ta ɗauko da nufin ta fara share gidan, dai'dai lokacin Nenne da ta tashi a barci yanzu ta fito waje. "Ke Mahnoor ɗauko mun jakar littattafan bappankun nan bari na duba wani littafin addu'oi a ciki zan kai wa gwaggona". Cewar Nennen, tana maganar tana jefawa Mahnoor ɗin wani irin kallon tsana. Narai narai baiwar Allah ta yi da idanu, tamkar zata rushe da kuka ta ce. "Nenne dan Allah ki yi hakuri Mahreen ta ɗauko maki, wlh ina bala'in tsoron wannan mutumin da bappa ya kawo, dan Allah Nennen ki yi hakuri, Mahreen ce bata jin tsoronsa, zata iya..........". Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon wani irin matsiyacin kallo da Nennen ta wurga mata, shiru ta haɗiye sauran maganar tata, nan take idanunta suka ciko da kwallah. "Lallai Mahnoor kin girma, yanzu ni ce zan aikeki ki ce mun in aiki Mahreen? E lallai kuwa, yanzu ai da uwarki ce ta aikeki ba zaki ce mata hakan ba ko? Shekiyar idanunki manya manya kamar na mayun nan kina kallona da su in zo in kwakwale maki su in zubar, wlh tun wuri ki wuce ki je ki ɗauko mun jakar nan ko in zo wajen in shakeki sai kin mutu"............ Hasbunallahu wani'imal wakil. Wai menene amfanin mugunta ga ɗan uwankan a duniya my people's? Kun ga dai wannan zallar madarar mugunta ce Nenne take ji da shi, idan ba mugunta ba fisabilillahi ita da kanta tana bala'in tsoron Jaish ɗin nan, dalilin tsoronsa har ta koma gidan babanta, amma tsabar mugunta zata ce Mahnoor ta shiga in da yake ta ɗauko mata jaka fisabilillahi, ai wannan zalinci ne, meyasa ita ba zata iya shiga ba hegiya. Mahreen da take jiyo duk abin da suke faɗa ne ta fito riƙe da jakan bappan a hannunta tana faɗin. "Nenne Adda Mahnoor fa tsoron aljaninna ɗin nan take yi, ni ne kawai bana jin tsoronsa, ga jakar nan na kawo maki......" Wani irin uban harara da ta wurga mata ne yasa ta tsaya ta kasa ƙarisowa in da take da jakar. "Wuce ki mayar da jakar nan ta shiga ita ta je ta ɗauko mun, ai Mahnoor na ce ta ɗauko mun jaka ba Mahreen ba uwar goninta". Turɓune fuska ta yi tamkar zata sanya mata kuka. "Ko kukan jini zaki yi yau sai dai ki yi, kuma idan baki wuce kin mayar da jakar nan ba wlh in na damkeki a cikin gidan nan sai buzunki". Sanin cewa bappansu bayanan kuma tasan halin Nenne nasu sarai ne yasa ta juya tana turo baki ta wuce mayar da jakar. "Sai na sake gaya maki abin da zaki yi ne?". Ta jefawa Mahnoor dake tsaye idanunta cike tab da kwallah tambaya. Allah ya sani my people's kun sani Mahnoor tana bala'in tsoron Jaish, tsabar tsoronsa da take ji ma ko bappanta yana cikin ɗakin bata shiga, amma saboda bakin mugunta irin na Nenne wai sai ta shiga, ga shi Bappa baya nan ma bare ta ji confidence na shiga. Wasu zafafan hawaye ne suka fara bin ƙuncinta, ji take yi kamar shikenan yau ta mutu, abin gwanin ban tausayi sosai. Jikinta har kerma ya fara yi, Allah sarki haka ta nufi cikin ɗakin tana karanto duk addu'ar da ya zo bakinta saboda tsoro. Wani irin shu'umin murmushi na mugunta Nenne ta saki, cikin ranta ta furta. "Ai tun da na gano kina jin tsoron wannan aljani wlh kullum sai na haɗaki hanya da shi, shegiya shi ne ma zai zama ajalinki, ko bani da aika cikin ɗakin bappanku sai na ƙaƙalo ko na karya ne na aike ki ciki sai dai ki mutu in zaki mutu, dama ni fatana kenan ki mutu kowa ma ya huta annoba kawai". Dai'dai zata shiga ɗakin bappan Mahreen ta fito ta nufi waje tana turo baki alamar ta ji haushin Nenne, Mahnoor tana son cewa Mahreen ɗin ta juya ta koma ciki dan ta rakata, amma ba hali, dan Nenne na tsaye ta tsareta da ido. Ciki ta shiga tana kuka, kamar ranta zai fita, har zufar dole ta fara haɗawa. Ganin idanun Jaish ɗin a rufe alamar yana barci ne yasa ta yi saurin ƙarisawa wajen da jakar yake a in da yake maƙale a jikin wata itace da ya sanya a jikin bangon wajen. Jakunkuna kala uku ne a wajen. Hannunta nata kerma da kyar ta iya ciro wanda Nenne ta aiketa, juyawar da zata yi caraf suka yi ido huɗu da shi, yanzu ya farka daga nannauyar barcin da ta ɗaukesa tun safe. Ai a dubu ɗari ta kwala ihu tare da jefar da jakar a ƙasa ta fasa waje a guje tana ihu. Tana fitowa Nenne ta damkota ta hau jibga da bata ga jakar a hannunta ba, dama kiris take jira ta naɗa mata duka, dan kwana biyu bata daketa ba, saboda Mahnoor yarinya ce mai kiyaye dokoki, komai a nutse take yi, da wuya ka samu ta yi wa wani laifi, tana taka tsantsan da komai, komai aka sanyata a hanzarce take yi, hakan yasa Nennen bata samu ta rinƙa jibgarta, dan bata yi mata laifi, shiyasa take ta neman laifinta komai ƙanƙantarsa ta ci zalin yarinya ta zalunceta a banza. Ai kuwa jibgarta ta fara yi da karfi, kuka ta fara yi tana faɗin. "Dan Allah Nenne ki yi hakuri, wlh ya buɗe idanunsa ne yasa na gudo, wayyo Allah!". Gwanin ban tausayi. Ina ai Nenne bata saurareta ba, kai mata duka da hannun take yi ta ko'ina tana faɗin. "Har na aikeki ki ki yi mun abin da nace, dan kinga ina yi maki dariya ko? Ni sa'ar wasarki ce? Yau sai kin gaya mun na haifeki ko ban haifeki ba?". Tana magana tana haki saboda muguntar da take yi. "Wlh Nenne kin haifeni, dama ni a uwa na ɗaukeki, dan Allah ki yi hakuri". Ina ai cigaba da dukanta Nennen ta yi tana faɗin. "A'a baki ɗaukeni a uwa ba, da kin ɗaukeni a uwa ai da kin yi mun abin da nace, kuma wlh ko zaki mutu yau sai kin je kin ɗauko mun jakar nan, ki wuce ki ɗauko mun jakar nan in ba haka ba wlh sai na takaki har hancin cikinki sai sun zubo waje". Kamar daga sama tana tsaka da jibgarta ta ɗago idanunta sai a kan kofar ɗakin bappan, hakan yasa suka yi ido cikin ido da Jaish ɗin da yake tsaye ya dafa bango da hannu ɗaya ya kuma ɗan rage tsawonsa saboda ciwo da cikinsa yake yi mashi. Ya ɗaura hannunsa ɗayan a saman cikinsa alamar cikin yana yi mashi tsananin ciwo, ihun da Mahnoor ɗin take yi ne yasa shi lallaɓawa ya fito waje, dan sun takura mashi, sun toshe mashi kunne, ya fito ne yaga su wanenen suke matsawa rayuwarsa?. Ai kuwa tana sauke idanunta a cikin nasa idanun by mistake, wani irin mahaukacin ihu ta zunduma, a dubu ɗari ta saki Mahnoor ɗin, kada kuso ku ga yadda ta wantsala waɗan nan siraran kafafun nata kamar na shamuwa ko balbela za'a ce ne, wasu sirara da su ga uban tsawo, ai a ɗari ta watsa a guje sai waje tana ihu kamar wata zararriya, sai faɗi take. "Yau na shiga uku na, yau na yi ido huɗu da aljani shikenan zan rasa hankalina da ganina, shikenan zan dawo aljana nima". Ai bata zame ko'ina ba sai gidan Arɗo, sai ihu take a kan hanya, ta ja matasa da dama suka rufa mata baya da nufin su kamata, dan a tunaninsu ta rasa hankalinta ne take wannan ihun a kan hanya, shiyasa suka bita dan su ji me yake faruwa. Ita kuwa Mahnoor tana ganin Nennen ta saketa ta yi waje da gudu ne yasa ta fara waige waige tana son ganin me ya sanya Nennen ta saketa? Ita dai tasan idan Nenne ta fara dukanta sai ta gaji take rabuwa da ita, komai magiyar da zata yi mata bata haƙura har sai san da ta gaji, to yau me ya faru ta saketa?. Ai kuwa unexpect ita ma ta haɗa ido da shi, yana tsaye, yadda yake bin su Gimbiya Sarina da kallon walaƙanci haka yake binsu da irin wannan kallon, irin wannan kallon nasa yana mugun karyawa mutun zuciya, dan kallo ne mai kama da mugun harara, ta gefen ido yake wurgawa mutun irin kallo, ko ya kake idan aka yi maka irin wannan kallon walaƙancin sai ka ji ka shiga wani irin yanayi, sai ka zargi kanka ko baka da gaskiya ko kuma ka yi laifi ne, irin wannan kallo wlh sam bashi da daɗi idan aka yi wa mutun, duk sai yasa gaji kai ba komai bane a duniya, to haka dama yake kallon su Sarina, ya kware a iya irin wannan kallon walaƙancin, kuma Sarina da Fanan yafi yi wa irin kallon, dan ya tsane yaran nan bare ma Fanan da ake son ƙaƙaba mashi ita, ya tsaneta, tsanar kuma ta samo asaline daga kan Mammiensu, tsanar da ya yi mata ne ya shafesu suma. Ai kuwa suna haɗa ido ta kwala ihu, a guje ta nufi waje. Karaf suka ci karo da bappa dake shigowa cikin gidan hannunsa ɗauke da ɗan ƙaramin buhu da ya zuba kayan fruits a ciki. Baya baya ta yi ta faɗi ƙasa. "Subhanallah Mahnoor lafiya kika fito a guje haka?". Cewar bappa. Kasa iya amsa mashi ta yi, fuskarta jaga jaga da hawayen dukan da Nenne ta yi mata. Mahreen dake biye da shi a baya ne ta yi kan Mahnoor ɗin tana faɗin. "Adda Mahnoor meyasameki? Naje gonar bappa ne fa na gaya mashi Nenne ta saki zuwa wajen aljani, dukanki Nennen ta yi ne?". Kai ta girgiza alamar a'a Nenne bata daketa ba. Kama hannunta Mahreen ɗin ta yi a in da ta taimaka mata ta miƙe tsaye. Hannu tasa tana goge mata hawaye. "To waye ya dakeki?". Ta sake jefa mata tambaya. Da kyar ta iya saita nutsuwarta tare da cewa. "Babu wanda ya dakeni, aljanin ne ya tashi ya fito waje shi ne ya bani tsoro". Da sauri bappa ya ce. "Yauwa masha Allah to mu koma ciki bari naje na bashi abinci, dan nasan yanzu abincin kawai zai buƙata, saboda yasha maganin cin abinci". Ba musu suka wuce gaba riƙe da hannun junansu, ya rufa masu baya. Jaish dai yana tsaye a in da yake, bai motsa ba, ya kasa iya komawa ciki ne saboda rashin karfi, dama da kyar da suɗin goshi ya iya fitowa wajen, yanzu kuma ya kasa motsawa ma daga in da yake, ga wani irin azabbabben yunwa da yake ji, ji yake tamkar ana yayyanke mashi ƴaƴan hanjinsa saboda azabar yunwa, a wannan yanayi da yake ciki wlh kome ya samu zai iya ci bawan Allah, maganin cin abincin bappa ta fara aiki gadan gadan. Suna shigowa ya bawa Mahnoor buhun hannunsa a kan ta je ta wanke fruits ɗin ta kawo mashi. Shi kuma ya matso ya kama Jaish ɗin yana yi mashi faɗa a kan ya dai'na tashi kada ya je ya faɗi ya jiwa kansa ciwo, ya bari zuwa gobe ko jibi idan ya ƙara samun karfi sai ya rinƙa fita. Ko kallonsa bai yi ba, hasalima ba jin yarensu yake yi ba, dan haka bai ji me bappan ya ce ba, shi dama yare biyu ya iya, daga larabci yaren iyayensa sai kuma turanci yaren masu jajayen kunnuwa. A wannan karon sam Jaish ɗin bai yi wani yunkuri ture bappa ko wani abin magamancin hakan ba, saboda bashi da wani karfi, yana ji yana gani bappa ya ɗan rungumosa suka koma cikin ɗakin, zaunar da shi bappan a saman tabarma ya yi, sannan ya janyo mashi kwaryar namar da Mahreen ta kawo cikin ɗakin ta ajiye da suka gama suya, bayan ya janyo mashi kwaryar namar ne ya sake janyo mashi kwaryar dake shake da ruwan sha mai sanyi na randar taɓo, ya kuma yi sanyi tamkar a fridge aka ɗauko shi. Buɗe mashi paipain dake rufe da kwaryar namar ya yi tare da tura mashi gabansa. Habawa azababben yunwar da yake ji yasa ya mance da cewa ma ana yin brush a duniya, ai hannu kawai yasa ya fara ɗaukar namar, ya mance da cewa yana jin kyamarsu. Haba ai yunwa ba kanwar uwar kowa bace bare ta tausayawa bawa, kowa ta kama kifar da shi take yi ta nukurkushesa har sai ya zama abin tausayi, duk wani iyashegen mutun da tsiyarsa duk sai yana ƙoshe yake yi, komai ji da kan mutun yunwa tana sanya shi ya yi ladab ya miƙa wuya, to yau dai ga Prince Jaish yunwa ta kifar da shi ta nukurkushesa har ya zama tamkar ba shi ba....... Allah mai iko yau Jaish ne a Nigeria, a Nigeria ma a Adamawa, a Adamawan a rugar fulani zaune yana cin abincin da suka girka da hannunsu, rayuwa kenan ba ta yadda bata juyawa bawa, ina son ku kara tunawa da cewa yau idan kai ne gobe ba kai bane, duniyar ma gabaɗaya nawa take? Wuni guda ɗaya fa take a wajen mahaliccinmu, Allah kasa mu cika da kyau da imani haɗe da kalmar shahada!!. A bakin kofa Mahnoor ta tsaya ta miƙawa Mahreen kwayar fruits ɗin da ta wankosu tas, sun yi fresh da su. Ɗan satar kallon Jaish ɗin ta yi yadda yake cusa namar nan a bakinsa tamkar wani ya ce zai kwace mashi, bawan Allah yadda kuka san shi da wasu zakunar da suka shekara basu ci abinci ba yake ci, sai cusawa yake yi a cikin bakinsa, irin kada su cinye su barshin nan, bai gama cinye na bakinsa ba zai sake ɗauki wani ya cusa a bakin masa, shi da yake cin abinci cikin class mai ɗaukar hankali, cikin nutsuwa da jan aji, yau sai ga shi yana cin abinci tamkar almajirin da ya kwana uku bai ga idanun abinci ba, har ya karyar mun da zuciya, shi ma aya ce mai zaman kanta a garemu, yau da gobe sai Allah, yau da gobe ta wuci wasa, dan haka kada ki ga Allah ya baki wani matsayi a rayuwarki ki ce zaki walaƙan wasu, a kowani lokaci Allah na iya canza abubuwa ba tare da ya nemi shawarar kowa ba, Allah na iya kwace abinsa ba tare da neman shawararki ba, dan kuwa lokacin da ya baki ma ai bai nemi shawararki ba, dan haka ina fatan Jaish ya zamar mana aya ku ɗauki darasi........ Ni dai bari na leƙa wani ɓangaren. ___________________________🔥💔 KHADIJAH 💔😥 A hankali ta juyo dan ganin wanene?. Wani matashi ne da ba zai wuci shekaru 25 zuwa 27 ba. Ƙarisowa in da take ya yi, murmushi ya sakar mata yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi magana ta rigasa da cewa. "Ina wuni malam?". "Lafiya lou Alhdulillah Khadija Ahmad, ya gida yasu mama?". A takaice ta amsa mashi da lafiya lou Alhdulillah. Shiru suka ɗan yi, shi ɗin malaminsu ne na islamiya ɗinsu. Katse masu shirun ya yi da cewa. "Khadijah Ahmad duk abin da ya faru da ku na samu labari, Allah ya jiƙan baba da rahma ya kuma sanya mama ta iya cin wannan jarabawar tata". Shiru ta yi ta kasa iya amsawa da Amin ɗin, saboda wani irin tukukin bakinciki da ya taso mata, yanzu kenan labarin abin da mamarsu ta aikata ya baza ko'ina? Yanzu duk in da zasu wuce nunasu za'ana yi kenan ana cewa ga waɗan da mamarsu ta kashe babansu? Innalillahi wainnailayhir rajiun! Hasbunallahu wani'imal, wannan wace iriyar musifa ce?!. "Kiyi hakuri Khadija komai mai wucewa ne, sannan ko wani bawa da irin tasa ƙaddara da jarabarwar, fatana dai Ubangiji Allah ya baku ikon cin jarabawarku, ki cigaba da addu'a". Ɗan dakatawa ya yi da maganar yana kallon face ɗinta, duk da ba wani hasken kirki ne a wajen ba amma suna iya ganin juna, shi da kansa yasan ta yi kiɓa kuma ta yi haske, ta ƙara kyau sosai, dama kun san Zainab ta fita haske, to yanzu har ta kusa ɗara Zainab ɗin a hasken fata. Cigaba ya yi da cewa. "Dama naga kun jima baku zo islamiyya bane yasa na ce bari na zo na duba meyasa baku zo ɗin ba? Allah yasa dai kuna lafiya?". Daga yadda yake magana da ita cikin mutunci da girmama juna zaku iya fahimtar kaunarta yake yi, ba shakka akwai soyayyarta a zuciyarsa ga kwayar idanunsa ma ya nuna hakan. Wani irin wahalallen ajiyar zuciya ta sauƙe, murya a karaye kamar zata sa kuka ta ce. "Malam muna nan lafiya, sai dai islamiyyar ce ba zamu iya cigaba da zuwa ba, duk fa yanzu kowa yasan abin da ya faru da mu, kasan dama can ƴan islamiyyan namu ba kaunarmu suke yi ba saboda bamu kula kowa muna yin rayuwarmu ne kawai, yanzu idan mun je islamiyya ai kanmu muka jawa bakinciki, dan dai babu wanda zai hana yaran islamiyyar nan tsokanarmu a kan mamarmu ta kashe babanmu, dan haka mu ba zamu sake zuwa ko'ina ba". Ta kai karshen maganar siraran zafafan hawaye na bin kuncinta. Hakika shi kansa yasan da haka, kuma yana matuƙar tausaya masu, saboda zasu zama abin tsangwama a cikin mutane, amma hakan ba shi ne zai sa su ki neman imili ba, a zamanin yanzun nan ka nemi ilimin ma idan aka ƙunsa maka wani bakinciki in ba ka kai zuciya nesa ba sai ka aikata saɓon Allah bare ace kuma baka nemi ilimi ba ai sai abin ya kwaɓe maka, amma hakika ya matuƙar tausaya masu na irin rayuwar da zasu fara fuskanta a wajen al'umma a yanzu. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Nasan da haka Khadijah, amma ba hakance zata sa ku ƙi neman ilimi ba, kin san da cewa ilimi yana da matuƙar mahimmanci sosai, dan haka ku kawar da kanku a kan duk abin da zaku gani kuma zaku ji, ku daure ku nemi ilimi, kada ki manta babanku bashi da burin da ya wuce ya ga kun yi karatu mai zurfi, to meyasa ba zaku kokarta ku cika mashi burinsa ba? Ki yi tunani a kan hakan mana". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a kan mutumin da yake fitowa daga cikin shagon da ta fito a yanzu. "Tom shikenan malam zamu yi shawara da ƴar uwata da kuma kawunmu Sadiq, kowani hukunci ya yanke mana shi zamu karɓa tun da shi ne mamarmu kuma babanmu a yanzu". Tana magana zafafan hawaye ne suke cigaba da bin ƙuncinta. "Dan Allah Khadeejerh ki daina kukan nan haka ya isa, addu'a kawai zaki rinƙa yi, addu'a makamin mumini, kada ki zama kamar baki da tawakkali sannan wadda bata yarda da ƙaddara ba mana! Dan Allah kukan ya isa haka, Allah ya gani ba zan iya jurar ganin kukanki ba........." Wani irin ɗaugo kai haɗe da kallonta a kansa ta yi na jin kalamansa na karshe in da yace ba zai iya jurar kukanta ba. Ɗan kawar da kallonsa daga kanta ya yi ya mayar da kallon nasa a kan mutumin da ɗazun ya fito daga cikin shagon, so ya tsaya ne a ta bakin shagon yana making call. "Kamar yadda kika ji na faɗa ne Khadeejerh, ba zan iya jurar ganin kukanki ba, zuciyata tana sosuwa sosai saboda ba zan ɓoye maki ba ina sonki, ba kuma tun yau na fara sonki ba, ya kai shekara biyu ina dakon sonki, ban samu damar furta maki bane sai yanzu, ki sani aurenki nake son yi". Wani irin zaro idanu waje ta yi, kirjinta ta ji ya bada dukan uku uku, bata taɓa zaton hakan daga garesa ba. A dai'dai wannan lokacin kuma wannan mutumin da ya fito daga shagon tun ɗazun yake tsaye yake waya ya zo wucesa ta kusa da su. A ɗari ta wani irin toshe hancinta da hannunta saboda wani irin bala'in warin da kamshin turaren bawan Allahn nan ya yi mata, duk da ta toshe hancinta nan take cikinta ya murɗa zuciyarta ya fara tashi, kan ta yi wani yunkuri amai mai karfin gaske ya kwace mata....... Tashin sense. Bata iya matsawa daga in da take tsaye ba ta fara tikar aman, hakan yasa ta ɓatawa malamin nata jikinsa da aman, da yake yana kusa da ita ne. Ƙasa ta tsugunna ta cigaba da sharara amanta. A ruɗe shi ma ya tsugunna yana tambayarta lafiya me yake damunta. Ina ai bata iya bashi amsa ba amai kawai take yi. Sosai ta yi aman har ta galabaita, idanunta suka yi jajir kamar jini, ta sha wahala sosai. Ganin aman ya dakata ne yasa malamin nasu ya yi saurin nufar shagon mai provision ɗin na bayansu ya karɓo mata ruwa. A harzarce ya zo ya fasa ruwan ya bata. Da kyar ta iya karɓa ta fara wanke bakinta da shi, da kyar ta iya miƙewa tsaye, bata sake ce da shi ko uppan ba ta nufi hanyar gida, tana tafiya tamkar wadda ta sha wani abin, sai layi take yi kamar zata faɗi ƙasa. Bin bayanta ya yi yana yi mata sannu har suka isa bakin titi, sai tambayarta yake yi dama bata da lafiya ne? Me yake damunta? Har da ƙarawa da an kaita asibiti ne ko ba'a kaita ba?. Ita dai ko sannu bata sake ce mashi ba, haka ta samu da kyar ta tsallaka titin ta nufi hanyar gida. Binta ya yi yana cigaba da yi mata magana bata kula shi ba har ta shiga cikin gida ta barshi tsaye a waje. Hauwa kawai ta isko a parlourn, tamkar bata ganta ba ta wuce ta nufi ɗakin nasu, har lokacin kuma tana layi kamar wadda ta sha wani abin. "Ke Khadeejerh lafiya kike kuwa?". Cewar Hauwa uwar shisshigi a lamuran mutane. Ai yadda kuka san da bango take magana haka Khadeejerh bata kulata ba, cigaba da tafiyarta kawai ta yi har izuwa cikin ɗakin nasu, ta banko kofa ta murza key. Tana shiga bata kula Zainab bama ta wuce cikin toilet ɗinsu. Wani aman ta je ta sakeyi saboda yadda cikinta yake murɗa mata sosai, har lokacin tana jin warin turaren mutumin yaki sakar mata hanci, shiyasa ta sake zuba wani aman. A ruɗe Zee dake kwance a saman gado ta diro ƙasa, ita ma ba wani karfin kirki bane a jikinta amma haka ta bi bayan Khadeejerh ɗin da gudu izuwa cikin toilet ɗin. Ganin tana ta amai ne yasa ta ƙara ruɗewa, a rikice take tambayarta meyasameta, ta yi maganar tare da ƙarisowa ciki ta riƙeta. Bata iya amsa mata ba sai amanta da take yi, sai da ta yi mai isarta, sai da zuciyarta ya ɗanyi sanyi sosai sannan ta wanke bakinta tare da cewa Zee ta saketa ta fita bari ta yi wanka. Cikin kuka Zee ta ce. "Amma Aunty Khadeejerh ki gaya mun me yake damunki tukun nan in fita". "Kije ɗaki idan na fito zamu yi magana". Ta faɗa da kyar. Tana kuka ta nufi wajen ba tare da ta sake yin wata magana ba. Wanka ta yi tare da ɗauro towel ta fito. A zaune a bakin gado ta isko Zee ɗin, wucewa ta yi ta nufi wajen jakar kayan da Zee ɗin ta dawo da su daga asibiti, dukkansu basu da kaya sai wanda Sadiq ya kwasowa Zee ɗin daga tsohon gidansu ya kai mata asibiti lokacin da take kwance, kayansu duk yana tsohon gida. Wata doguwar riga ta ciro ta sanya a jikinta, tsawon bai kai mata har ƙasa ba kam, amma ba laifi ya ɗan yi mata daidai, sai dai ya matseta sosai, dan ta fi Zee ƙiba kaɗan. Gadon ta zo ta haye ta kwanta, zannin gadon ta ɓangaren da take ta yaye ta lulluɓa da shi, nan take ta fara rawan sanyi alamar zazzaɓi. Ganin haka sai yasa Zee bata iya sake tambayarta me yake damunta ba, sai ta yi shiru kawai, daga karshe ma lallaɓawa ta yi ta dawo kusa da ita suka kwanta a tare, kafin wani ɗan lokaci barci ya yi awon gaba da su ba tare da sun ci abinci ba bayin Allah, ga Zainab bata sha magungunarta ba, basu yi waya da Sadiq ba haka barci ya yi awon gaba da su. ______________________🔥💔 KINGDOM OF POWER. Dai'dai Gimbiya Chuchu zata shiga bedroom na Akka ta ji an rufe mata idanu ta baya. Murya a sanyaye ta ce. "Yah Jawad me haka ne wai?". Zame hannayen nasa ya yi tare da cewa. "Waye ya ce maki ni ne?". Juyowa ta yi suna fuskantar juna tare da ciro wayarta daga kunnenta. "Ba wanda ya gaya mun kai ne face kamshin perfume ɗinka". Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da cewa. "Da waye ake waya to? Naga kina kan call". Dawo da kallonta kan screen ɗin wayar ta yi. "Yah Rizwan ne". Jinjina kai yayi ba tare da ya sake yin magana ba, gera kawai ya ɗaga mata alamar ta cigaba da yin wayarta mana. Mayar da wayar kunenta ta yi tare da cewa. "Yah Rizwan zamu yi magana anjuma, zan yi hira da Yah Jawad yanzu". Bata jira amsarsa ba ta katse kiran. Tana katse kiran ta ɗago da kallonta a kansa, while shima kallonta yake yi, suna haɗa idanu suka sakarwa da juma murmushi. Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tana cigaba da murmushi. "Me kuke tattaunawa ne da Yah Rizwan ɗin namu?". Ya jefa mata tambayar yana ɗago haɓarta, dan ta sunkuyar da kai ƙasa. Haƙiƙa ya ji matuƙar daɗin yadda ta bashi mahimmanci, ta bar abin da take yi ta ce wannan lokaci nata nashi ne yanzu bana yin magana da kowa ba ne, ya ji matuƙar daɗin hakan, bawan Allah bai san soyayya take yi da yayan nasu ba!. Hmmm akwai gagarumin matsala ranar da ɗaya ya fahimci ɗaya yana sonta, sai Allah ne kaɗai yasan irin bala'in tashin hankalin da bayin Allahn nan zasu shiga, waye zai hakura ya barwa ɗan uwansa? Ko dai dukkansu biyu hakura zasu yi ne? Anya ma a cikinsu akwai wanda zai iya hakura kuwa? Dan fa dukkansu suna yi mata zazzafar so ne fiye da tunaninku!! Gaskiya Mammaiensu nan bakar azzaluma ce, zata azabtar da su cikin ruwan sanyi ta hanyar sanya masu ciwon zuciya, bayin Allah marayun Allah masu kaunar junansu zata shiga tsakaninsu ta rabasu, wato idan Allah ya haɗaka da mai bakar zuciya fa kai kam ka shiga uku wlh, Allah dai ya kyauta ya shiga tsakanin nagari da mugu!. "Hira kawai muke yi da shi, ya ce mun zai zo a satin nan saboda Akka sannan kuma saboda au........." Wani irin kunya ne ya rufeta ta kasa iya ƙarisa gaya mashi sannan kuma saboda aurensu, kasa karisa maganar ta yi, ta yi shiru. "Awww sai a zauna ayi ta hira da su Yah Rizwan ni ba za'a zo ɗakina a tayani yin hiran ba ko?". Cikin zolaya ya yi maganar. A ɗan shagwaɓe ta ce. "Kai Yah Jawad kai fa Momma ta hanani zuwa room ɗinka, ta ce kada na sake shiga ciki, ko naje kai maka wani abin na tsaya a iya parlour kawai". Ɗan leƙo face ɗinta ya yi. "Eyeee momma zata shiga tsakaninmu kenan? Ni ba zan yarda ba gaskiya, ni dai ki rinƙa zuwa ko a parlourn ne ma mu zauna ki yi mun hira dan ki rage mun kewa". Ɗan zaro idanu ta yi tare da cewa. "Yah Jawad kai kuma wani irin kewa zaka ji? Kana ganin yadda face ɗinka take wani shining daga gani kullum hira kake yi a waya da Auntynmu da zaka auro......" Ta kai karshen maganar tare da sanya hannu ta toshe bakin nata tana ɗan murmushin. Damko west ɗinta ya yi yana faɗin. "Waye ya gaya maki ina da budurwa da nake yin hira da ita?". Wage baki ta yi da karfi ta furta. "Akka ga Yah Jawad nan zai......" Ai bai bari ta ƙarisar ba ya toshe mata bakin nata da hannun ɗaya, sanin cewa in dai Akka tana cikin room ɗinta to ba abin da zai hanata fitowa ne yasa ya yi saurin zame hannunsa daga bakin nata ya fara ƙoƙarin cicciɓarta sama su bar wajen. Tsabar tsiya irin nata sake cewa. "Akka ki zo ki ceceni a hannun Yah........." Ai dan dole ƙaniyarta ta dakata bata ƙarisa maganar ba saboda abin da ya yi mata a wannan karon, ya ɗauketa cak da hannayensa, ga shi tana son ƙira mashi ruwa hakan yasa ya rufe mata baki da ɗan bakinsa tun da ba hannu. Dama ta ce tun da ta gane baya son Akka ta gansu a tare ta ce zata fara rama abin da ya yi mata, to ga shi ta fara ramawa kuma ta samu kyautar sumbata, karon farko kenan a rayuwarta, dan ma Allah ya taimaketa mutumin kirki ne ai da kiss ma mai gabaɗaya zai yi mata ba iya sumbata ba, to na dai yi shiru. Nutsuwa tsit ta yi tare da datse idanunta gam, kai tsaye room ɗinta dake kusa da na Akka ya shiga da ita, a tsakiyar ɗakin ya sauketa yana kawar da kallonsa daga kanta izuwa kofar shigowa, dan ya ji motsi a waje wanda yake kyautata zaton Akkar ce, dan yasan dama in dai tana nan wannan ihun sunanta da Chuchun ta yi zata jiyota shi, idan ta ji kuma tabbas zata fito waje, haka kuwa aka yi, ita ɗince ta fito duba waye ya kirata...... Yah Jawad yana wasa sosai, Momma ta ce ya ɓoye soyayyarsa kada ya bari kowa ya sani, amma yana wasa da hakan sosai, har ɗaukar Chuchun yake yi a tsakar rana ido na ganin ido, sam baya gudun ya haɗu da wani a cikin family. A hanzarce ita kuma Chuchun ta raɓa gefensa zata wuce ta gudu ta bar ɗakin. Riko hannunta ya yi tare da dawo da kallonsa a kanta. A hanzarce ta yi ƙasa da kanta, dan wani irin kunyarsa ta ji, sunbatar tasa ta tsaya mata a rai, ga shi unexpect ya yi mata shi, a lokacin idanunta suna a kan face ɗinsa, sun ga juna ido cikin ido a yayin da ya sauke ɗan bakinsa a saman nata, duk abin ya tsaya mata a rai, yanzu ba zata iya haɗa ido da shi ba. "Ina zaki je kuma Jannat?". Yana magana yana kallon face ɗinta, shi ko kunyar abin da ya aikata ma bai ji ba. Ƙasa ƙasa kamar wadda bata son yin magana ta ce. "Wajen Mommana". Ɗan ɗago habarta ya yi dan su kalli juna, sai dai taki yarda ta ɗago idanunta su ga junan. "Faɗa mun waye ya gaya maki ina da budurwa kafin ki tafi?". A hankali ya yi maganar kamar wani mai faɗawa wani gulmar wani. Ɗan turo baki ta yi. "Su Aunty Sarina naji suna faɗa ita da Aunty Fanan wai kana da budurwa saboda ranar ta jika kana waya da budurwar taka". Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin ko shi a yaushe ya yi waya da wata? Amma yaran nan sun iya sharri da shegen sa ido, kawai dan sun ji yana waya sai aka ce masu da budurwarsa yake waya?. "Yah Jawad Mammie ma fa ta aiko naje na manta, ka sakeni na tafi wajenta". Ta faɗa tana ɗan ɗagowa ta saci kallonsa. "Jannat yanzu ni dan na yi waya da mutun sai nace da budurwa nake waya?". Ƙasa ta ƙara yi da kai kafin ta bashi amsa da cewa. "A'a da Aunty Fanan ta ce baka da budurwa sai Aunty Sarina ta ce ta jika ka yi ƙasa da murya sosai kana gaya mata kalamai na soyayya masu daɗi, wai in ba budurwarka ba ba zaka gaya mata hakan ba". Innalillahi Chuchu ta buɗe aiki, dama zama suke yi suna yin gulmarsa kenan, yau ta tona asiri. Zaro idanu ya yi sosai. "Dama zama kuke yi kuna magana a kai'na ko Jannat?". Yadda ya yi maganar murya a kausashe ne yasa ta ɗago ba shiri ta kallesa. Ganin ya ɗaure fuska ne yasa ta fara bashi hakuri tana gaya mashi wlh ita bata yi gulmansa ba, Sarina da Fanan and Aneesa ne suka yi. Sosai ya ji babu daɗin abin da suka yi mashi, ya kuma yi alkawarin sai ya hukuntasu tun da zama suke yi suna gulmarsa. Ganin yadda ta ɗan tsorata tana bashi hakuri ne yasa ya saki face ɗinsa tare da ce mata ta je ta amsa kiran Mammie ɗin ta dawo ta same shi a room ɗinsa. Ya kai ƙarshen maganar tare da sakin hannun nata. A hanzarce ta amsa da okey tare da sanya kai ta wuce, da kallo ya bita har ta kurewa ganinsa. Sai da ta kurewa ganin nasa ne ya rufa mata baya a in da ya nufi part ɗin su Sarina dan hukuntasu, haka kawai zasu sanya beb ɗinsa ta fara tunanin yana da burdurwa ta yadda ko ya bayyana mata soyayyarsa taki yarda ta ce yana da wata, lallai basu nemi zaman lafiya ba dole su sha hukunci. Kai tsaye part ɗin uncle Abbas ta nufa ita kum, zaune kamar kullum ta isko Mammien a saman sofa tana wani shan kamshi kamar ita ce Princess na kingdom ɗin. Har ƙasa Chuchu ta tsugunna ta gaisheta, sai sakin wani irin murmushin mai wuyar fassaruwa take yi tun lokacin da Chuchun ta shigo, dan haka fuska ɗauke da murmushi ta amsa gaisuwar tata tare da ce mata ta zauna a saman sofa...... Kai yaran King Zuhair sun samu tarbiya, ji yadda Chuchu ta gaisheta cikin girmamawa, da wata ce yadda take ji da ita ƴar sarki ce ai ba zata zube a ƙasa dan gaishe da Mammie ba, amma su babu ruwansu suna girmama Mammien. Zama ta yi a saman sofan ba musu, wani kwalban turare Mammien ta ɗauko daga in da ta ajiye saman hannun sofan, miƙa mata shi ta yi tana faɗin. "Ga wannan turare ne da nasa aka haɗa maki, na sanki da shegen son gayu kakar Guyson ɗinmu, shiyasa na saya maki wannan zazzafar perfume ɗin, ke kaɗai zaki yi amfani da abinki kada ki tsamma kowa......." A hanzarce ta tari numfashinta da cewa. "Mammien har da Auta ma kada na bata ta sanya a jikinta?". Kai ta gyaɗa mata alamar e sannan ta cigaba da cewa. "Ke kaɗai na sayawa, dan nafi kaunarki fiye da kowa, dan haka karɓa abinki". Ta kai karshen maganar tare da miƙo mata. Hannu tasa ta karɓa jikinta duk ya yi sanyi, dan ance kada ta tsamma Auta sai ta ji jikinta ya mutu, amma haka ta karɓa ta miƙe ta nufi waje bayan ta zuba mata godiya. Da wani irin shu'umin kallo ta bita da shi har ta fice waje, murmushi mai wuyar fassaruwa ta saki. Ita kuwa Chuchun tunani take yi a kan babu wanda ya isa yasa ta hana Auta wannan perfume ɗin, a tare zasu yi amfani da shi sai dai mutun ya mutu, yo ita in za'a bata abu a bawa Auta bama ba gara a hanata kawai ba, dan in dai aka bata sai ta bawa Autar......... Cakwakiya kenan, anya turaren Allah da annabi Mammie ta bata kuwa? To ga shi dai ta ce tare zasu yi amfani da shi ita da Auta bayan ance nata ne ita kaɗai, tab akwai rugugin aradu kam. Aftar some hours.🔥 ___________________💔🔥 AUTA AND HOORAIN🤍🕊️ Zaune take a saman kujera, gari ya yi duhu, amma wajen nasu haske ne tamkar rana, saboda kwayayen bulbs dake ta ko'ina a wajen. Ta tada kai da laps ɗin Hoorain dan ta ce mashi tana tsoron wajen, dan dole ya matso kusa da ita, sun yi shiru kowannensu da abin da yake tunani, shi ya jingina kansa da jikin kujeran ya ɗaga kai sama, ita kuma tana kwance shiru ta haɗa hannayenta waje guda tamkar mai jin sanyi. Tamkar a mafarki sadauki Hoorain ya ji busar yaki, a wani irin zabure ya furta Hasbunallahu wani'imal wakil, yaki kuma a masarautarsu da daddaren nan? Innalillahi wainnailayhir rajiun!. Kafin ya yi wani yunkuri tuni masarautar ta gauraye da busoshin yaki, ta ko'ina buga bososhin yaki ake yi, daga in da suke suna iya jiyo gudun dakarun yaki gabaɗaya suna hallara a harabar kingdom ɗin.......... Tashin hankali! Yaki unexpect kenan, kuma da daddare fisabilillah?! Subhanallah, ko suwaye da wannan ɗanyar aikin na kawo masu farmaki da daren nan?!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E21 Kafin ya yi wani yunkuri tuni gabaɗaya masarautar ta gauraye da busoshin yaki, ta ko'ina buga bososhin yaki ake yi, daga in da suke suna iya jiyo gudun dakarun yaki gabaɗaya suna hallara a harabar kingdom ɗin. Jin irin yadda ya furta Hasbunallahu wani'imal wakil ɗin ne yasa Auta ɗago kai haɗe da kallonta a kansa. "Hoorain lafiya kuwa?". A sanyaye ta faɗi hakan. Kallon face nata ya yi tare da jan doguwar numfashi, a gaskiya Kingdom of power ta jima rabonta da yaki, tun Zunaira na jaririya, shiyasa ta kasance bata san ya busoshin yaki ma yake ba, tana dai jin labarin yadda masarautar tasu ta sha gwagwarmaya a baya, ta san yadda suka shiga filin daga a can baya, sun fafata da makiya ba kaɗan ba, dan a caf faɗin ƙasar Tunisia kujeran mulkin babanta gaba yake dana kowa, wannan dalilin yasa kowa yake farautar kujerar yake neman samun damar mallakarta. Sai dai kuma basu iya samun damar mallakar ba, dan fa gabaɗaya ƴaƴansa su Ramish da kuke ganin nan ba baya ba wajen tsayawa mahaifin nasu tsayin daka, a lokacin suna Dubai, amma sun tasowa su zo a duk lokacin da aka kawowa mahaifin nasu farmaki, basu ɗaga kafa har sai sun rama sun mayar da martani, commander Zafar and Hoorain ba karya sun hidimtawa masarautar nan tamkar nasu ne, akwai yakin da aka taɓa gwabzawa a masarautar wanda a lokacin an kashe mutane da dama shekarun baya da suka wuce, to jama'a suna kyautata zaton cewa a wannan lokacin aka kashe Mahaifiyar Hoorain, dan tun daga wannan yakin ba'a sake ganinta ba, a lokacin da aka kawo masu hari bata nan ta fita daga cikin masarautar ita da wasu kuyangu, ba'a sake jin ɗuriarsu ba har yau, commander ya sha kuka da hawayensa tamkar karamin yaro, da alama suna son juna sosai, shi ma Hoorain ya sha kuka sosai, a lokacin yana ƙarami ma. A can cikin gida kuwa gabaɗaya ƴan'matan King suna part ɗin Akka, duk cikinsu babu wadda ta ji tsoron busar yakin da ya karaɗe masarautar, dan fa wlh jinin Modarawa basu da tsoro ko ɗigo, abin a jininsu yake tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci haka suke, ka taɓosu ka shiga ɗari uku bama uku ba, komai tsawon shekaru suka samu dama sai sun rama babu yafiya a cikin lamuransu!! In dai baka taɓosu ba basa zalunci zaku zauna lafiya! Ka taɓosu su rama ba ɗaga kafa!. Yah Jawad and uncle Taheer kanin mama ne suka fito daga cikin part ɗinsu a zafafe, kowannensu da abin da yake tunawa, shi Yah Jawad kai tsaye part na King ya nufa, dan kaunar da yake yi wa dad ɗin nasa, a cewarsa bari ya fara da tsare ubansa kafin kowa. Shi kuma uncle da yake shima ya taɓa renon Commander Zafar yana ji da karfi kai tsaye waje harabar gidan ya nufa, ko'ina yau a cikin kingdom ɗin zaratan zakunan warriors na masarautar ne waɗan da ake kira da dangerous warriors. Wasu warriors ɗin sai haɗa kan mata bayi suke yi izuwa wajen da ya dace su ɓoyesu dan basu tsaro, wasu kuma sai shirin yaki suke yi, wasu suna shirya zafafan makaman yaki, Allah yasa ma a ko da yaushe da shirin yakinsu suke, saboda sun san su ɗin kowani sarki farautar kujerar King Zuhair yake yi, sun san a koda yaushe zasu iya afkawa yaki ba tare da saka time ko date ba, ba yau suka fara samun harin yaki unexpect irin wannan ba, an jima ana yi masu irin wannan shammatar Allah yana basu nasara a kan makiya. Habawa ai a ɗari commander Zafar ya fito daga part ɗinsa, ban da Hoorain babu wanda yake nema, nemansa yake kamar hauka a kan ya zo ya jagoranci ɓangaren da suke kula da makamai bari shi kuma ya kula da zakunar mayakansu da zasu fara yin gaba wato masu harbi da kifiya kenan, akwai abokin Hoorain ɗin wanda kuke ganinsu kullum a tare mai suna Ansar, shi kuma commander ya ce mashi ya haɗa kan dakarun da zasu fita da dawakai, ya ce su haɗa dawakai guda 400 ma ya isa, dan ma sun ga ba ƙananan mayaka bane suka kawo masu hari, sannan kuma suna dayawa sosai suma, gasu da manya manyan kayan yaki sosai. Kan kace me masarauta ta ruɗe, dan ma suna da tsari sosai. Yah Jawad yana ƙoƙarin shiga part ɗin King Aunty MieMie tana shigowa, a tare suka ƙarisa ciki, ba wanda ya iya yi wa ɗan uwansa magana, saboda dukkansu hankalinsu baya jikinsu, yana wajen mahaifin nasu. Ba komai ya ja haka ba face sun san dayawan lokuta idan aka kawowa masarauta hari fa mayakan kwantan ɓauna suke yi su nufi in da sarki yake, shi suke fara kashewa kafin su yi ƙoƙarin ruguje komai, shi ya ɗaga masu hankali sosai, sannan abu na biyu sun san kafin a kawowa masarauta hari fa dole sai an santa ciki da waje, dole akwai ƴan leƙen asirin wasu masarautun a cikinsu ba tare da sun sani ba, so sun san da wuya idan waɗan da suka kawo masu harin a yanzun nan ba'a gaya masu in da King Zuhair yake ba ta yadda kai tsaye zasu hari wajen da yake ɗin dan su fara kashe shi. Ai kuwa suna shiga suka wani irin jan burki ba shiri, dukkansu zaro idanu waje suka yi tamkar idanun nasu zai faɗi ƙasa. Ba komai suka gani ya sanyasu jan wannan birki ba face yadda suka sami King a tsaye cikin uniform na mayaƙa, ya yi tsayuwar jarumta tamkar wani zaki, ga Momma a tsaye kusa da shi tana ƙoƙarin taya shi shiryawa, da alama ita ta sanya mashi kayan, sai jan mashi gemu take yi tana yaba shi tare da yi mashi kirari a kan ba'a taɓa samun wanda ya ci nasara a kan modarawa ba tun farkonsu har izuwa yau, su ɗin jarumai ne na bugawa a jarida, dan haka ta sani da izinin Allah koma su waye suka kawo masu hari da izinin Allah sune zasu yi nasara, sai kara kuranta mijin nata take yi, ko a jikinta, babu karaya ko tsoro a tattare da ita, tsabar zafin zuciya da karfin hali irin nata ta yarda mijinta ya shiga filin daga duk da yake sarki, dan ita gani take in bai shiga filin dagar nan ba za'ayi nasara a kansu tun da ƴaƴan cikinsu basa nan, ita fa Momma ta yarda da jarumta King, tasan sarai zai iya, su Mama dai sun ki yarda a kan ya shiga fili, tun ɗazun suke yi mashi magiya a kan ya hakura a matsayinsa na sarki ya haura sama ya kalli yakin daga sama, momma ta ce a'a dole ya fita saboda al'ummarsa, shi ma ya ce a matsayinsa na adalin sarki dole ya fita saboda al'ummarsa, ya ce kowa dake cikin kingdom ɗin nan mutun ne kamar shi kuma kowa yana son ransa kamar yadda shi ma yake son nasa, dan haka kamar yadda yake son kansa da lafiyarsa, matansa da ƴaƴansa suke sonsa suma al'ummarsa haka suke son kansu da kuma matansu da ƴaƴansu suke sonsu, dan haka dole ya fita ya gwabza dan ya samu hujjar kare kansa a gaban Allah a kan amanar talakawa da ya bashi....... Gaskiya King Zuhair adalin sarki ne over wanda samun irin sa zai yi matuƙar wahala a duniyar yanzu!!. Akka ma tace ya fita ta bashi goyon baya, kun san jinin Modarawa yake gudu a jikin Akka, ita da Momma ba sarewa ko karaya a lamuransu, basu san menene ja da baya ba, akwaisu da taurin zuciya kam sosai da sosai. Tun ɗasun suka rinƙa dragging da su mama and Mummy a kan sun ce su basu son ya fita, hankalinsu a tashe har kuka Mummyn Gimbiya Chuchu ta yi, amma daga karshe ma ce masu ya yi su fice mashi a ɗaki fita babu fashi tun da su basu san hakkin bayin Allah da yake rataye a kansa ba, dan haka su fice mashi a part, shi ne yasa suka fita Akka ma tace tana zuwa ta wuce part ɗinta, ya rage daga shi sai momma dake ta kara mashi kwarin gwiwa shi kuma yana ta bata wasiya a kan koma bai dawo a raye ba, sam bata wani ɗauki wasiyar tasa da mahimmanci ba, dan tana ji a jikinta zai dawo garesu, su fa Modarawa wlh basa taɓa yin tunanin faɗuwa, kullum tunanin sune da nasara suke yi. Da sauri Yah Jawad ya ƙariso wajen nasu da nufin shima ya dakatar da daddyn nasu daga fita filin, ita kuwa Aunty MieMie da yake jinin King ɗin ne a jikinta habawa juyawa ta yi sai part ɗinta ta fara shirin yaki ita ma, dan na gaya maku mayakiya ce sosai a baya, har mutunmutuminta aka sassaƙa a kofar masarautar tasu, so jaruma ce sosai da sosai, haka ta hau shiryawa dan ta takewa babanta baya zuwa wajen yakin, a nan ta sami mijinta ma yana shirin yakin, kai kingdom of power gabaɗaya babu ragwaye, gabaɗayansu a shirye suke, a koyaushe suna shirye su afkawa yaki bayin Allah, jininsu a tafashe yake!!. Kallon Momma dake ta zubawa King kirarin kara mashi kwarin gwiwa fuskarta ba yabo ba fallasa Yah Jawad ya yi kafin ya ce. "Momma ba zaki hana dad fita ba?". A ruɗe ya yi maganar!!. Bawan Allah bai taɓa ganin dad ɗinsu a filin yaki ba, dan lokacin da ake gwabza yaki shi da Jaish suna Dubai basu dawo ba, shiyasa hankalinsa ya tashi sosai. "A kan me zan hana shi Jawad?". Ta jefa mashi tambayar tare da ɗauke hannunta daga kan gemun King ɗin tana dawo da kallonta a kan Jawad ɗin, while shi ma King kallonsa yake yi da waɗan nan idanun nasa kamar shi ya arawa gimbiya Zunaira su. "Momma yaki fa? Haba bai kamata dad ya fita yaki ba! Duk yawan mayakan da muke da su basu isa ba sai dad ya fita?". "Jawad ina son ku sani su kansu mayaƙan dake cikin kingdom ɗin nan nauyinsu ya ratayane a kan daddynku, matsawar daddynku adalin sarki ne to fa dole hankalinsa ya tashi ya shiga filin daga domin kare al'ummarsa, duk wasu adalan sarakuna haka suke, kuma mu jininmu basu san sarewar gwiwa ba! Dan haka ka kawo wata zancen ba wannan ba!!". Cewar Momma, murya a ɗan kausashe ta ƙarisa maganar. Tana rufe baki King bai bari Yah Jawad ɗin ya sake yin magana ba ya ce mashi. "Kaje ka haɗa mun kan ƴaƴana dukka ka sauke mun su izuwa under ground, sannan umarni ne ka tsaya da su a wajen, duk da mayakan da zasu basu tsaro ban yarda ba, dan mutun bare ba abin yarda bane, ana iya haɗa baki dasu ko a sayesu a cutar mun da family, dan haka ka tsaya da su kada kaje ko'ina,". Fuska a ɗaure ya yi maganar, hakan yasa Yah Jawad bai ja da maganar ba, dan kuwa bai ga alamar wasa a tattare da dad ɗin nasu ba, in a serious note ya yi maganar, dan haka sai ya karɓi umarni ya juya ya fita kawai. Shi da Jaish mafa sun taɓa renon Commander Zafar, jarumta a jininsu yake, suna da karfi sosai, amma su wajen Ramish and Bilal suka koyi wannan training ɗin kafin commander!. Yana fita ya nufi part ɗin Akka, a nan ya samesu gabaɗayansu except Auta, harta Mammiensu da su Mummy sun haɗu a wajen. Yana zuwa ya ce da su su tashi su tafi, Chuchu na ganinsa ta taso da gudu ta nufesa tana faɗin. "Yah Jawad Aunty Sarina ta ce mun yaki za'ayi kuma Auta ban ganta ba, na shiga uku dan Allah Yah Jawad ka nemo mun ita, na je part na Momma bata nan, na je ɗakinta bata nan, na duba ko'ina ban ganta ba, kuma ni yau since morning fa bamu haɗu da ita ba". Wani irin zaro idanu ya yi tare da mayar da kallonsa kan su Fanan ɗin. Tabbas bata cikinsu, a ɗari ya fara tambayarsu ina take?. Cikin girmamawa su Fanan ɗin da suka sha duka a hannunsa ɗazun suka amsa mashi da suma basu ganta ba, ɗazun sun ci duka sosai a hannunsa, lilis ya yi masu kamar an aiko shi, su Sarina iyayen rashin kunya sai da idanu ya rena fata, an daku, shiyasa suka nutsu suka kara bashi girma suna girmamashi dan dole ƴan ƙaniya. Jin cewa kowa ya ce bai ganta bane yasa ya ce yana zuwa bari ya dubata ko tana barci a wani ɗakin. Da sauri Chuchun ta ce. "Yah Jawad zan bika". Girgiza kai ya yi. "A'a Jannat ki zauna a cikin ƴan uwanmu, dan kinga yadda Kingdom ɗin nan yake a rikice ban lamunta ki bini ba, ki zauna ina zuwa yanzu zan tambayo Hoorain ko ya ganta ne, in dai bata cikin nan kinga ta fita waje kenan, idan ta fita kuma dole Hoorain zamu nema, dan shi ne mai alhakin kula da ita a duk lokacin da ta fita". Ya kai karshen maganar tare da nufar waje. Kuka ta sanya mashi tana yi mashi magiya a kan dan Allah ya tafi da ita, tana son ta raka shi ta riga kowa ganin ƴar uwarta autansu. Tsawar da Mammie ta daka mata a kan ba zata bishi ba ta wuce ta dawo ne yasa ya juyowa tare da dakatawa daga tafiyar da yake yi. Da farko bai da niyar juyowa ya saurareta saboda baya son fita waje da ita, amma da Mammie ta yi magana sai ya ji yana son fita da ita, dan haka da ya juyo sai ya miƙa mata hannu kawai. A guje ta nufesa, a hanzarce ya riƙo hannunta kafin Mammie ta yi wani magana ya fice waje abinsa. Kai tsaye part part na kowa suka fara shiga suna nemanta. A can cikin gonar kuwa, cemata Hoorain ya yi ta tashi a kafarsa yana zuwa, tashi ta yi tana mai cigaba da tambayarsa lafiya kuwa?. Bai iya amsa mata ba ya yunkura zai tashi domin ya nemo masu hanyar fita daga wajen nan. A hanzarce ta riƙo hannunsa tare da cewa. "Hoorain kasan dai ina tsoro shi ne zaka tafi wani wajen ka barni ko?". Kamar zata yi kuka ta yi maganar, ta yi maganar kuma cikin shagwaɓa tana turo baki. Ita sam bata san bala'in da yake faruwa a cikin masarautar ba. Ɗan kawar da kallonsa daga kanta ya yi, wannan yarinya ta rantse sai ta jefa shi cikin wani hali, shi idan tana irin wannan magana tana sawa ya ji tamkar yana a sararin samaniya, irin wannan shagwaɓa ta rinƙa yi mashi ɗazun har tasa ya yarda ta kwanta a saman laps ɗinsa ba tare da ya sani ba. Hannunta ya riƙe ba tare da ya yi mata magana ba. Miƙewa tsaye ta yi suka fara kewaye a cikin gonar suna neman hanyar da zasu iya fita ba tare da sanin masu gadin bakin gate ba. Tafiya kaɗan ya yi ta fara yi mashi shagwaɓa a kan ita ta gaji da tafiya sai dai su koma su zauna. Da yake shi yasan me yake faruwa baya son gaya mata ne yasan halinta sarai, yanzu idan ya gaya mata me yake faruwa a cikin kingdom ɗin in ta fara yi mashi kuka sai tasa ya ruɗe ya fita hayyacinsa, dan zata yi kuka ta ce sam ya mayar da ita cikin gida taga ƴan uwanta suna lafiya ne, sanin hakan ne yasa ya saki hannunta tare da tsugunnawa a gabanta ya bata baya almar ta hau tun da ta gaji da tafiya. Da sauri ta haye bayan nasa ya miƙe da ita. Cigaba da tafiya ya yi ba tare da ya ce mata ko uppan ba, sai jero mashi tambayoyi ta rinƙa yi kamar wata ƴar jarida. Shi kam sai tafiya yake yi cikin jarunta, jikinsa har tsuma yake yi saboda bala'in dake faruwa a cikin kingdom ɗin. Wajen kusa da gate ɗin suka nufa, sun kusa isa bakin gate ɗin ya ce mata ta sauko bari ya yi wani abin, make mashi kafaɗa ta yi tana faɗin. "Ni wlh tsoro nake ji ba zan iya saukowa ba sai ka mayar da ni cikin gida". Wannan ma bai sanar da ita abin da yake faruwa ba ta makalemashi wai tana jin tsoro, ina kuma ace ya gaya mata, ai ya shiga uku ko nan da nan ba zata yarda ya kara motsawa ba. "Ranki ya daɗe duba mana hanyar fita fa zanyi". Cikin wannan sanyayyar kuma daddaɗar voice ɗin nasa ya yi maganar, kuma ƙasa ƙasa kamar mai jin tsoron yin maganar ya yi ta. "Ni dai a'a muje koma inane a tare". Ta faɗa a shagwaɓe. Sh dai Allah ya gani wannan shagwaɓa tata tana kashe mashi jiki. Lallashinta ya fara yi yana lallaɓata a kan ta sauƙa yana son ya lallaɓa a hankali ya leƙa securitys dake wajen gate ɗin suna nan ne ko dai sun nufi wajen sauran warriors dake cikin kingdom ɗin?. Kafewa ta yi taki yarda ta sauƙo, shi kuma sauri yake yi saboda yadda busar yakin nan take tashi ta ko'ina ya ɗaga mashi hankali sosai, hakan yasa ya damko hannunta tare da fisgota ya dawo da ita ta gabansa da nufin ya sauketa tun da ta baya ba zai iya sauketa ba ta riƙe mashi wuya, har sai idan ita ta sakesa zai iya sauketa, shiyasa ya dawo da ita ta gaba. Wani irin zaro mashi waɗan nan dara daran idanuwan nata ta yi, an kuma yi sa'a shima face ɗin nata yake kallah, hakan yasa ya ji ba zai iya abin da ya yi niya ba, ɗan kawar da kallonsa daga kanta ya yi yana bata hakuri. Hakika ta lura da cewa Hoorain baya son kallon cikin idonta, in dai tana kallonsa baya taɓa yarda ya kalli cikin nata idanun, kawar da kansa yake yi. Modarawa sarakan zuciya sake shi ta yi tana ƙoƙarin sauka daga jikin nasa, ta yi fushi ne saboda ya yi yunkurin sauketa daga jikinsa ta karfin tsiya, bawan Allah bata san abin da yake gabansa ya fi wuta zafi ba, ba laifinsa bane, hankalinsa ne a matuƙar tashe, Abbonsa kawai yake tunawa, yasan yanzu yana can yana nemansa, idan aka fara yakin nan bai kai kansa ga mahaifinsa ya taimaka mashi ba baya jin zai iya yafewa kansa, yana cikin tashin hankali da tsaka mai wuya shiyasa ya yi mata hakan!. Ganin alamar tayi fushi zata sauka daga jikin nasa ne yasa ya yi saurin ƙanƙameta, har yanzu duk tashin hankali da yake ciki ba zaka ga hakan a kan face ɗinsa ba, cikin tausasawa haɗe da rarrashi ga voice ƙasa ƙasa ya ce. "Am so so sorryyyyyyy ranki ya daɗe". Bata yi mashi magana ba, hasali ma bata ɗago ta sake kallonsa ba, sai ƙoƙarin barin jikin nasa kawai take yi. Shi kuma yaki saketa sai bata hakuri yake yi, wlh sam taki kulasa, ashe ita ma tana da zuciya ta iya fushi. Ba yadda bai yi da ita a kan ta yi hakuri ba taki, ko magana ma bata sake yi mashi ba, dan gani take ma ya yi mata karshen walaƙanci a duniya, dan ya samu ma ta hau bayansa saboda tsoro shi ne zai yi ƙoƙarin sauketa ta karfi? Lallai ba laifinsa bane, laifinta ne da take sakar mashi fuska. Baiwar Allah baki san shi ma ba laifinsa bane, tashin hankali ne ya kai tashin hankali shiyasa ya yi maki hakan, ita ma dan bata san me yake faruwa bane, da ta sani ba zata yi fushi da shi ba. Bashi da zaɓin da ya wuce ya saketa ta sauƙa, dan ta fara yi mashi kuka tana ture shi, ga shi taki ta yi magana, hakan yasa sai ya saketa kawai, dan baya son ganin kukanta. Yana sauketa ta nufi gate ɗin kai tsaye zata fita. Cikin zafin nama ya riƙo hannunta, dan kuwa idan ta fita sun shiga uku, zargine ma zai hau kansu sosai, za'a ce tun safe me suke yi a cikin goner su biyu kawai? A cikin gida kuma ba'a nemeta ba tun safen, saboda suna da parts dayawa, kowa zai yi tunanin tana wani part ɗin ko tana wajen Mammiensu Sarina ko part na Aunty MieMie, shiyasa ba wanda ya ce ina take sai yanzu da abin nan ya faru aka fara nemanta. Juyowa ta yi a fusace zata yi mashi magana sai gani ta yi yana ƙoƙarin zube gwiwowinsa a ƙasa dan ya bata hakuri tun da taki yarda da kalaman bakinsa. Cikin sauri ta yi ƙoƙarin hana shi, sai dai kafin ta kaiga yin magana har ya aiwatar da hakan. A hanzarce ita ma ta zube nata gwiwon a ƙasa tana faɗin. "Dan Allah ka yi hakuri ka tashi ka ji? Kuma ai ranar nace kada ka ƙara tsugunnawa ka bani hakuri ko?". Tana magana tana cigaba da hawayenta tun na ɗazun da yaki sauketa. "Sai kin amsa da kin haƙura zan tashi". Ya faɗa yana kawar da kallonsa daga kan face ɗinta, saboda kukan da take yi baya son gani. "Na hakura Allah kuwa". Ta kai karshen maganar tare da faɗawa jikinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sanya hannunsa ɗaya ya fara goge mata hawayen da yake jin zafin zubowarsu. Hannunta ta zura ta bayansa ta ɗan rungumosa tana ɗan shesshekar kuka............ Ni kam nace Auta yanzu fa kada ki manta kin fara girma sai a dai'na rungumar kowa, dan an fara zama ƴan'matan.......💃🤸 Da yake hankalinsa duk yana wajen Abbonsa sai ya yi mata dabara suka miƙe tsaye, haka ya nufi bakin gate ɗin riƙe da hannunta. Kash an rufe gate ɗin ta waje, da alama warriors dake wajen sun tafi cikin kingdom suma. Dafe kansa ya yi tare da fara tunanin ta yadda zai hau gini da ita a bayansa, dan dole ya nemo hanyar fita idan ba haka ba yana cikin bala'i ba kaɗan ba, rashinsa ma zai iya sanyawa makiya su yi galaba a kan Abbonsa, domin kuwa idan har Abbo bai gansa ba zai shiga tashin hankalin da zai sa ba zai iya taɓuƙa komai a filin yakin ba, hakan zai sanya makiya su iya kai mashi hari har su yi nasara, ya shiga tashin hankali iya tashin hankali bawan Allah. A can cikin gida kuwa tsab aka haɗa kan mayaƙa sannan aka umarce masu riƙe da kwari da baka da su fara fita waje, dan a dokar kingdom of power basu yarda yaki ta zo cikin masarauta ta samesu, sai dai su su tunkareta su tareta a waje su gwabza, hakan kuwa aka yi suka tunkareta. Wasu tsirarun warriors da ba zasu wuci guda ɗari bane suka kukkunna wuta a jikin itace suka rufa masu baya da shi domin ganin haske yadda zasu ji daɗin gwabza yakin da kyau. Sai dai abin da basu sani ba mayakan da suka kawo masu hari fa sun kewaye masarautar gabas da yamma kudu da arewa, kwantar ɓauna suka yi masu, sun kasa kansu wajen kaso biyar duk dan cinwa burinsu....... Tashin hankali!!. Mayakan commander Zafar kaso na farko da suka fara fitowa wato masu kwari da baka a can kusa da mayakan da suka kawo masu harin suka dakata, a nan commander ya umarcesu da su tsaya su kuma shirya yadda ya kamata, da yake ba yau suka fara yakin ba sai ya zamana sun jera kansu da kansu ba tare da wani ya basu umarni ba, sun yi tsayuwar mazajen gaske, kudai kun san duk wata jarumta to ta biyo bayan mayaka, baku jin ko kwatance za'ayi da namiji jarumi to da sadaukan yaki ake kwatantashi bane? Da mayaka ake kwatance dan an san sune jarumtarsu ta kai jarumta babu wani mix ko kaɗan. Naɗe kafafunsu suka yi tamkar waɗan da suka yi kneel down, sannan suka lankwashe kafa ɗaya baya ya yin da suke ɗago kwari da bakarsu suna saitata yadda ya dace, ga dakaru masu riƙe da wuta a tsakiyarsu dan su samu haske. Daga cikin kingdom ɗin ma fa akwai manya manyan makamai na kwari da baka wadda daga can za'a iya yi wa abokan hamayyar nasu ruwan kibau, kowani makami kuma yana iya ɗaukar kifiya sama da ɗari, yanzu haka wasu mayaƙan suna ciki suna zubawa makamin kifitoyi sosai a cikinsa tare da jerasu da kyau ta yadda zasu ji daɗin yi masu ruwan kibau. Daga in da suke suna iya gani da kuma jiyo maganganun mayakan da suka kawo masu harin. Babban cikinsu ne ya ce da su. "Get ready is time to fight now, kuje!! Kada ku kuskura ku dawo ba tare da kun dawowa da Queen ZARINA spender ba, dole ku kwato mata shi domin ta yaki duniya!!".......... Tashin hankali, spender kuma?. To me haɗin King Zuhair da Spender? Dama yana wajensa ne ko yaya? Gaskiya akwai sarkakiya haɗe da cakwakiya!! Me haɗin kingdom of power da spender? To fah wata sabuwar cakwakiya kenan!!. Shi BLACK TIGER ya ce yana son ya karɓi Spender dan ya mulki duniya, ita kuma wannan QUEEN ZARINA ɗin ko wacece ita? Kun ji ita kuma tana neman SPENDER ne dan ta yaki duniya, tabɗijam! To wai shin menene ma wannan Spender ɗin? Ainahinsa mallakin wanenen? Sannan a yanzu takamaime yana hannun waye? Lallai akwai gagarumin matsala, akwai gagarumin rugugin aradu da cakwakiya mai matuƙar sarkakiya, KING ZUHAIR kuma da Spender?! Tabɗijam!! Commander Zafar dake tsaye a tsakiyar warriors dake riƙe da kwari da bakan ne ya ɗaga murya da karfi ya ce masu. "Ready!!". Nan take suka ja kifiya da karfi suna jiran umarninsa na gaba kuma. Commander dai duk hankalinsa wlh bata jikinsa, ɗansa ɗaya tilo a duniya kawai yake tunawa, ya nemesa kamar hauka bai gansa ba, sai dai kasancewar bai ji fargaba ko faɗuwar gaba ba yasa ya ji a ransa koma a ina ɗan nasa yake yana cikin ƙoshin lafiya, sai dai damuwarsa ɗaya, yasan halin ɗansa da zafin nama haɗe da tafasar jini ga zafin rai, sannan yasan shi da bakar kishi, yana kishin masarautar sun nan over, kuma yana matuƙar kaunarsa, amma ace ya ji an buga busoshin yaki kuma duk in da yake duk abin da yake yi bai bari ya hallara a gaban baban nasa ba? Kai abin da ɗaure kai sosai, abin ya damu commander a cikin zuciyarsa, sai waige waige yake yi yana duba ta ina zai ga ɓullowan zakin nasa, hazikin jamumin mayaki abin alfaharin KINGDOM OF POWER!. Sai dai har yanzu shiru ko alamarsa bai gani ba. Suma mayaƙan can riƙe suke da sandar wuta a hannayensu, hakan ya bawa su Commander damar ganinsu da kyau, da kallo ɗaya commander ya yi masu ya gane daga wace masarauta suke, dan haka sai ya ƙara gayawa dakarunsu a kan irin kisan walaƙanci zasu yi masu, sannan su ƙara jajircewa tare da fito da jarumtarsu su baje basirarsu a fili, dan wannan shi ne karo na uku kenan suna gwabza yaki da wannan masarauta, dole wannan karo su yi masu mai kankat. Masarautar Queen Zarina hatsabibin masarauta ne wanda yaƙarsa ba abu bane mai sauki, karfinsu kusan ɗaya ne da kingdom of power ɗin, amma su sun haɗa ne da karfin sihiri ba iya karfinsu bane kawai, shiyasa karfin nasu yake kusan ɗaya da kingdom of power, duk faɗan da suka yi a baya sai dai su gwabza su gaji su hakura, ɗaya baya cin galaba a kan ɗaya..... Babban magana, akwai matsala fa, da alama KINGDOM OF QUEEN ZARINA nan wannan karon da gagarumin shiri suka taho, dan kunga unexpect suka kawowa su commander hari, idan har basu yi gagarumin shiri ba kunga ba zasu fara ba, dan sun taɓa yakin ai, kowanne yasan karfin ɗan uwansa, dan su gwabza a baya sosai!!. A saman dawakai gabaɗaya mayakan masarautar Queen Zarina suke, hakan yasa commandersu suma yana ce masu ku afka suka kaɗa kan dawakan nasu suka nufo su commander Zafar da gudun gaske. Habawa shi kuma commander da karfi ya ɗaga murya ya furta. "Fire!!". A ɗari dangerous warriors suka kara jan kifiyoyinsu kan kace me sai ganin ruwan kifiyoyi suna shawagi a sararin samaniya, commander yasa sun saki wuta.................... To fa babban aiki. Ina Chuchu and Jawad? Sun koma cikin gida ko yaya? King ya fito kuwa? Babban tashin hankalin ma shi ne, Uncle Jahiz, Yah Rizwan, Guyson suna hanyar dawowa, daga yanzu izuwa kowani lokaci jirginsu zai iya sauka, tashin hankali! Zasu shigo su tadda yakin da basu san da shi ba, fatan mu dai Allah yasa kada su yi wannan mummunar gamon, Allah yasa wani abin ya riƙesu a airport har izuwa a gama yakin, dan ba da shirin yaki suka fito ba. Ga shi a yanzu yadda ake cikin tashin hankalin nan duk cikin family ba wanda yake da nutsuwar tunawa da su bare har ya kirasu a waya ya ce kada su nufo gida ana yaki, yanzu hankalin kowa a tashe yake, Innalillahi wainna ilaihir rajuun akwai matsala babba kuwa! Ya su Auta zasu yi su fito? Idan sun fito zai iya kaita a cikin family part kuwa? Yana da kwarin gwiwar yin hakan kuwa? Zasu rayu ma tukun nan? Dan dai kunga mayakan can sun kewaye ko'ina na kingdom ɗin ba tare da su King sun sani na, shigar dare suka yi masu, da alama kuma sai da suka kewaye ko'ina suka gama shirinsu kafin su busa masu busar isar da saƙon ga mayaka sun kawo masu hari, idan Auta ta samu ta koma cikin gida ya za'ayi ta gane ƴan uwanta suna part na ƙarƙashin ƙasa an ɓoyesu? Akwai matsala babba, shin su Mummy zasu rayu kuwa? Dan kunga an kewayesu ta ko'ina!! To ni dai bari na leƙa wani wajen na dawo daga baya in ɗauko maku rahoton me ya faru a wannan yakin!!. _______________________🔥💔😥 JIMETA.................NIGERIA. Sosai ya ci namar nan kamar ba gobe, dan ya ji yunwa sosai matuƙa, sai kallonsa suke yi, tsananin tausayinsa ne cike fal a ran bappa, bayan ya ci ya ji cikinsa ya ɗauka ne ya miƙe ya kwanta a wajen, saboda yadda cikinsa yake tsananin murɗa mashi, dan ya jima bai sanyawa cikin nasa komai ba, dole dama ta yi mashi ciwo. Bappa ne ya ce mashi ya tashi ya hau gado cikin harshen fillanci. Sam bai gane me suka faɗa ba, in takaice maku labarima shi Jaish yana jin duk abin da suke faɗa duk da bai san wani yare ko me suke nufi a kalaman nasu ba, amma bai kurmance ba yana jinsu, yaren ne kawai bai sani ba. Da bappa ya lura da yana jinsu magana ce baya yi ko baya son amsa masu, sai ya yi tunanin ko dai tun ainahi dama bebene?. Mahreen dake zaune shiru ne ta ce. "Aljanina cikinka ne yake ciwo?". A yanzu Mahreen tana tsoron taɓa shi, yi mashi magana ma a yanzu tana jin shakkar hakan, sosai take shakkarsa, kuma kunsan yadda ta yi shiru har ya gama cin namar bata ce zata bashi namar a baki ko kuma ta ce su ci tare ba ai daga nan zaku gane lallai tana shakkarsa ko ma tsoronsa. Jin maganar Mahreen ɗin yasa ya ɗaga idanu ya kalleta ba tare da ya yi magana ba, hasalima bai san me ta faɗa ba, kawai dai ya ɗago ya kalleta ne. Bappa ne ya ce mata. "Mahreen aljaninki baya magana, ina tunanin shi ɗin bebene". Ɗan zaro idanu ta yi tare da cewa. "Bappa shikenan shi haka zai zauna?". Kai bappan ya gyaɗa mata alamar e. Marairace fuska tayi tamkar zata rushe mashi da kuka ta furta. "Allah sarki ya bani tausayi, yanzu kowa yana magana ban da shi? To bappa ka samun mashi magani mana, dan dai ni ina son jin ya muryar aljanu suke?". Mahnoor dake tsakar gida tana zaune ta buga uban tagumi tana jiyosu ne ta ɗan taɓe baki tana mamakin hali irin na Mahreen, yarinya ne baka taɓa gane mata, bata san cewa ita kanta aljana bace ba iya Jaish ba, in za'a cewa Jaish aljana to tabbas ita kam itace sarkin aljanu, ban da nemanwa kai masifa me na yi wa kai fatan jin sautin muryan aljani fisabilillah? Tana zaune ƙalau zata jazawa kanta masifa, ai idan tana son jin muryan aljani sai ta saurari nata muryan, dan ita ma aljana aljana mutun mutun ce. "Mahreen ban tabbatar da cewa yana magana ko baya yi ba bare na bashi magani, amma bari na gwada mugani ko zai iya amsa maganata". Cewar bappan. Ya yi maganar tare da matsowa kusa da shi sosai. Ɗan zuba mashi idanu sosai ya yi yana kallonsa yadda yake kwance ya datse idanu gam, shi kansa bappan a yanzu ya fahimci dalilan da yasa dole a kirasa da aljani, wani irin shape mai bala'in kyau face ɗinsa take da shi, hancinsa ta zauna ta kuma tsaru dai'dai da face ɗinsa, ga gurbin idanunsa da girma, duk da idanun suke a rufe zaka iya gane cewa manya manya ne sosai, ɗan bakin nan nasa ba'a magana sai dai shiru, dole mutane su kirashi da aljani, shi ma yanzu ya ɗan ji wani irin yanayi a tattare da shi daya kurawa face ɗinsa idanu, da duk bai lura da hakan ba. Amma sai ya yi shiru bai ce komai dan gane da kyansa ba, ya dai matso kusa da kunnensa a ina ya fara yi mashi magana da fullanci a kan cewa ya dubi girman Allah kada ya wahalar da su ya sanar da su idan yana iya yin magana ko kuma idan yana jinsu. Sarai ya ji sun yi magana amma bai san me suka ce ba, dan haka sai bai motsa daga in da yake ba, shiru bappa ya yi yana tunani, da yake tattijon kirki ne ga tunani mai nisa, sai ya yi tunanin to taya ma za'ayi Jaish ya ji fulatanci tun da shi ba a ruga yake ba, ƴan cikin rugarma gudunsa suke yi hakan ya nuna bashi da wata alaƙa da fulani, duk yadda aka yi shi ɗin ɗaya daga cikin biyu nan ne, wato ko bature ko balarabe, hakan yasa bappan da ya tuna hakan sai ya sake matsowa kusa da kunnensa cikin dattaku ya ce mashi. "Kanajin larabci?". Cikin harshen larabcin ya yi mashi magana. A hankali ya ɗan motsa idanunsa kafin ya warosu a hankali izuwa kan face ɗin bappan! Sake mayar da su ya yi ya datsesu ba tare da ya ce ko uppan ba. Bappan ya lura da cewa tabbas yana jin larabci, dan tun da suka yi ta yi mashi magana bai motsa ba sai da suka yi mashi larabci, hakan na nufin yana ji sai dai kamar ba zai iya buɗe baki ya yi magana ba. Sake ce mashi bappan ya yi. "Dan girman Allah idan har kana jin larabcin ka nuna mana alamar hakan ko ka amsa mana, dan Allah kada ka wahalar da mu ka ji?". Shiru ya yi nan ma bai motsa ba, sai dai tsab ya ji me bappan ya ce. Ya ɗauki a kallah tsawon 2mins har bappa ya cire ran zai tanka masu, yama cire rai a kan yana iya magana, sai kuma ya ga ya ɗan buɗe idanu kaɗan tare da gyaɗa mashi kai alamar e yana jin larabcin, amma bai buɗi baki ya yi magana. Wani irin daɗi na musamman bappan ya fara ji na ganin cewa an samo yaren da bakon nasa yake ji, abin ya yi mashi daɗi sosai, bai damu da rashin amsa mashi da bakinsa da bai yi ba, saboda dama yana son ya san cewa bakon nasa yana jinsu shi ne burinsa, dan ko baya magana in dai yana jinsu to Alhdulillah zai iya yi mashi bayani kuma su fahimci juna, dan shi yana da baiwar iya yin magana da kurame, ya iya maganarsu da ƴatsun hannunsa, dan haka bashi da damuwa a kan wannan!!. Gyara zama da kyau bappan ya yi a in da ya shiga yi mashi bayanin halin da yake ciki da abin da ya faru da shi na tsintarsa a cikin ruwa da suka yi, ya yi mashi hakan ne kuma dan ya samu Jaish ɗin ya saki jiki da su ya san su ba cutar da shi zasu yi ba, dan ya fahimci sarai Jaish ɗin yana gudunsu, bai kawowa ransa cewa saboda kyamarsu yake ji yasa yake gudunsu ba, ya ɗauka saboda yana tsoron kada su cutar da shi ne yasa yake guduwa! Basu san dalilinsa daban ba, ai duk yaran King Zuhair babu matsoraci a cikinsu bare ace yana jin tsoronsu kada su cutar da shi ne!. Duk abin da bappan ya faɗa yana jinsa sarai, ya ji dukkanin bayanansa, sai dai sam bai motsa daga in da yake ba, sai ka yi zaton bai ji me aka ce ba. Mahreen dai ta ji bappanta yana wani yare daban da bata taɓa ji ba, sai ta zaro idanu tana kallonsa. Bayan ya gama yi wa Jaish bayani ne ta ce. "Bappana dama kaima ka iya yaren aljanu ne?". Kai kawai ya gyaɗa mata alamar e. "To bappa dan Allah ka koya mun, kaga dai shi ɗin aljanina ne, zan rinƙa yin magana da shi". Shiru ya ɗan yi mata kafin ya ce. "Ba shi ne idan nace ki nutsu ki karanta NAHHU a islamiya zaki iya larabci sosai sai ki ce mun yana da wahala Nahhu nawa hore ba? (Nahhu ciwon kai take cewa) To ai a cikin Nahhu nima na koyi yarensu". Da sauri ta ƙara zaro idanu waje. "Bappa kenan aljanu yarensu shi ne larabci?". Girgiza kai ya yi. "Larabci yaren kowa ne, aljanun gaske ma akwai masu jinsa kuma suna magana da shi, yaren annabinmu ne, da shi za'ayi magana a lahira". Shiru ta yi kamar mai nazari a kan maganganun bappan nata, can kuma ta ce. "Bappa daga yau zan fara koyan yaren, kuma zan fara karatun Nahhu har da muɗalaa da malumat, duk zan rinƙa karatunsu, kaima ka rinƙa ƙara mun da naka karatun a gida yadda zan iya yaren sosai". Jinjina mata kai ya yi alamar to shikenan babu damuwa. Ita dai Mahnoor tana jin larabci dai'dai gwargwado, dan tana mayar da hankalinta sosai a kan karatun islamiyar, bata wasa da shi haka zalika bata fashin zuwa sai idan bappan nasu ya yi tafiya, in baya nan bala'in Nenne yake hanata zuwa, sai ta yi ta sanyata aiki har lokaci ya ƙure bata samun zuwa, amma idan bappansu yana nan lafiya lou take zuwa, sai dai fa bappan idan ya tafi yana kai irin wata biyar haka bai dawo ba, idan kuma ya dawo baya wuce yin wata uku zuwa huɗu ya sake tafiya, bappa yana jin yaruka da ɗan dama, ciki har da yarabanci, dan yana zuwa har kudu a wajen yawonsa, yana jin broken English sosai, haka yaren ibo sosai, yana jin Hausa sosai, yana da baiwa ta iya yarika daban daban, kun san mutun mai yawo irin haka ba yaren da ba zai iya ba, sannan kun san akwai fulani irin bappa sosai masu yawan fita yawata ƙasashe da dabbobinsu, wani lokaci ma idan suka bar gida sai sufi shekaru 2 basu dawo ba, sai ka manta da su ma rana tsaka sai kaga kiwo ya juyo da su ta wajenku kwatsam sai ka gansu, kamar wasu aljanu ta bakin Mahreen ɗin. Sai dai shi bappa baya jimawa sosai, idan ya yi nisa ne wata biyar, ko dan saboda Mahnoor yana dawowa gida!. Kuma sanadiyar wannan kiwon da yake tafiya wurare daban daban Allah ya albarkace shi da samun shanu dayawa gasu suna ƙoshe ɓul ɓul sosai gwanin ban sha'awa. In short wannan labarin da bappa ya bawa Jaish ne yasa shi ya ɗan yi sanyi ya kuma daure ya dai'na nuna masu cewa yana kyamarsu, dan kuwa jinin King wlh basu manta alkhari ko mai ƙanƙantar idan aka yi masu, haka zalika komai ƙanƙantar sharri idan ka yi masu basa mantuwa, kar suke ba wata kwana kwana, yanzu yasan bappa ya taimakesa sosai, dan haka sai shi ma ya kudurta a ransa zai yi ƙoƙarin dai'na nuna masu kyama ya kaunacesu. In short sai da ya shafi wata biyu dai'dai a tare da su kafin ya fara sakin jiki da su, a wata biyun da suka shuɗen sam baya yarda ya yi kusa da su, dan kada ya yi amai a gabansu su ji babu daɗi, baya son ya ƙuntata masu hakan yasa yake daurewa yana dannewa ya kawar da kai, haka zalika bai taɓa yin magana ba a tsawon wata biyun nan, sai dai bappa ya yi mashi magana kuma yana jinsu, ko meyasa baya amsa masu?. Mahreen ta zage sai koyan larabci take yi dan ta rinƙa hira da shi, bata san shi kam ba abin da ya tsana a rayuwarsa kamar surutu ba, ita kuma Mahnoor har yau har gobe ita da Nenne suna tsoronsa, sai dai Nenne ta fi jin tsoronsa sosai, Mahnoor tsoron ya ragu, ba komai kuma yasa ta rage tsoronsa ba face muguntar Nenne, Nennen tana yawan aikanta cikin ɗakin na bappa dan tsabar mugunta, tana jin tsoronsa shi ne take aikata wai dan kawai taga Mahnoor ɗin tana zubar da kwallah, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai yasa Mahnoor ɗin ta fara sabawa da shi, ta rage jin tsoronsa, yanzu ta san ba cutar da su zai yi ba, dan a koda yaushe idan ta shigo ɗakin bappan ma har ta ɗauki abin da zata ɗauka ta fito yana kwance ko kallon in da take bayani, yana dai jin motsin shigowarta a koda yaushe, baya ɗagowa ne ya kalli wace? Kun dai san halinsa dama, akwai miskilanci da shege izza. Amma fa har yanzu a matsayin aljani yake a idanunta, ta ƙasa yarda cewa mutun ne!!. Har yau har gobe wannan kunyan na Jaish tana tare da shi, wlh baya taɓa yarda ya haɗa idanu da bappa sai idan by mistake, amma kunyar haɗa idanu da bappan yake yi, tsawon wata biyu suna kwana a ɗaki ɗaya amma baya yarda su haɗa idanu, kunya gareshi sosai, halittarsa ce a haka. Sarai bappa ya lura da cewa yana da kunya sosai, hakan bai yi mashi daɗi sosai ba, saboda yaso ya saki jiki da shi su saba sosai, amma ina kunya ta hana shi, ga rashin yin magana da yake fama da shi, lokacin da ya samu lafiya sosai tsakaninsa da bappan ya bashi hannu kawai su gaisa, shikenan ko hira bappa yake yi mashi baya cewa ko uppan ko kuma ya nuna alamar ya ji me bappan ya ce. Mahreen tana shakkarsa sosai, bata yi mashi magana idan bappa baya nan, yanzu ta ja baya da shi dan tun ranar da ta shigo ta same shi babu riga a jikinsa saboda zafi da ta kusa haukata shi bawan Allah abin da bai taɓa ji ba bai saba ba, da zafin ta isheshi ne ya cire riga, to tun da ta shigo ta same shi a haka ta fita a guje daga ranar ta ja baya sosai da shi, tsoron shi ma take ji dan taga kirar karfi. Ƴan kauye har cincirindon suke yi suna zuwa leƙensa idan bappa ya tafi kiwo, dan izuwa yanzu labari ya baza ko'ina a kauye cewa akwai wani aljani kyakkyawan gaske a cikin gidansu Mahnoor, hakan yasa ake zuwa leƙansa, shi kuwa yana kwance yana ganin masu zuwa leƙan nasa. Ita kuwa Nenne bata taɓa yarda ta wuni a gidan saboda shi ɗin, dan taki yarda cewa mutun ne har yanzu, tuni ta je ta kai wa gwaggonta labarinsa, tsabar mugunta irin na gwaggon sai ta ce ai wlh kada ta bar Mahnoor ta huta, lallai dole ta rinƙa turata wajensa yana bata tsoro dan su kuntata mata........ Ɗan adam kenan, ko me ribarsu idan sun ƙuntata wa baiwar Allah? Allah kasa mu fi karfin zuciyarmu, dan wannan duk kaɗan ne daga sharrin zuciya idan ka yi sake tafi karfinka, duk bala'in da za'ayi gara ka yi gwagwarmaya ka fi karfin zuciyarka, hakance kawai zata sanya ka ji daɗi duniya da lahira. Yau ma kamar kullum duk sun tafi kiwo, sun bi bappa, Nenne da ta dawo wuni gidan Arɗo bata nan, ta wuce gidan Arɗon, a gidan take zama sai yamma idan bappa ya dawo daga kiwo sai ita ma ta dawo. Kamar kullum Jaish ɗin kaɗai suka bari a gida yana kwance, ya taɓa zuwa wajen ciwo bappan sau ɗaya, lokacin tun bai jima sosai da su ba, bai wuce sati 2 da su ba lokacin, daga nan bai sake zuwa ba, saboda aman da ya rinƙa yi kamar zai mutu, wai wajen akwai datti, hakan yasa bappa ya fahimci yana da kyakkyani sosai, shi ne yasa bai sake yarda ya bisu ba, gara su bar shi a gida kada kyama ta yi mashi illar. Gajiya ya yi da kwamciyar da yake, hakan yasa ya miƙe tsaye, yau yana sanye cikin kayan fulani da bappa ya saya mashi, har yau ya kasa iya buɗe baki ya yi magana, yana jin duk abin da suke faɗa kuma, maganarce dai shiru har yau. Waje ya nufa, kayan fulanin sun yi mashi kyau sosai, saboda launin navy blue ne ba farar ba, kasancewar yana da hasken fata sosai sai kayan suka yi mashi kyau sosai. Waje ya nufo, cikin nutsuwa yake tafiya. Wasu takalmar bappa dake bakin kofa ya sanya a kafafunsa, takalmar sun yi mashi yawa kaɗan, amma haka yasa ya nufi hanyar fita daga gidan. Ya subhanallah, ai yana fitowa waje gabaɗaya matasan da suke yawan zama a ƙarƙashin bishiyar dake kofar gidan suka watse da gudu, dan tsoronsa. Ko kallon in da suke bai yi ba yasa kai ya nufi hanyar wajen kiwon su bappa, sau ɗaya ya taɓa zuwa amma saboda kaifin ƙwaƙwalwarsa bai manta hanyar ba. A kan hanyarsa na tafiya ya haɗu da Mahreen and Mahnoor sun ɗebo itace zasu koma gida Mahnoor ta yi masu abinci, ita kuma Mahreen ta tayata da ɗan aikace aikace, idan sun gama girki sun ci sun ƙoshi sai su ɗauki na bappa su koma mashi da shi wajen, su taya shi hira har zuwa lokacin tafiya islamiyya su dawo gida, kafin a tashi islamiyyar kuma bappa ya dawo gida, haka suke yi yanzu tun da Jaish ya zo, Nenne ta dai'na zama a gida bare ta yi girkin rana, dama ita take yin na rana idan bappa yana nan, zata yi na rana ta kai masu wajen kiwo, Mahnoor kuma zata yi na safe da dare haɗe da sauran aikace aikace!. Kallo ɗaya ya yi masu ya kawar da kansa, dan ya ganesu, ƴan gidansu ne. (Yanzu sun zama ƴan gida ɗaya kuma jini ɗaya🤣 Allah sarki Prince Jaish namu na amana🥱) Mahnoor ce ta ce mashi ina wuni da larabci. Mahreen kuwa duk da tana shakkarsa bai hana ta ce mashi. "Aljani ina zaka je? Kasan hanya ne? Ko dai garinku na aljanu zaka koma?". Da fulatanci ta yi maganar, dan har yanzu ba'a ƙarisa iya larabcin ba. Cigaba da tafiyarsa ya yi har ya ƙurewa ganinsu, su kuma tsayuwa Mahreen ta yi tana ganinsa har ya wuce, ita Mahnoor dan dole ta tsaya tana jiran Mahreen ta gama kallonsa, dan tasan ko ta ce mata ta zo su tafi ba zata zo ba har sai ya wuce, dan haka sai ta tsaya kallonsu kawai. Sai da ya kure masu ne Mahreeh ta juyo suka cigaba da tafiya tana faɗin. "Aljanin nan ban san yaushe zai fara yin magana ba, bappa kuma ya ce shi ba kurma bane, amma ya ki ya yi magana". Shiru Mahnoor ta yi mata bata amsa taba, dan tasan in ta biye mata zasu kwana su wuni Mahreen tana sanyata magana, ba zata kyaleka ba............ Kai tsaye wajen bappa Jaish ya nufa............. ____________________🔥🌼❤️ SMART TIGER. Sai da ya sha daidai cikinsa ya ajiye cup ɗin, sannan ne ya miƙe ya nufi stair case. Haurawa hawa na sama mai gabaɗaya ya yi, yana sanya kafarsa a saman wani haɗaɗɗen white Tiger ya yi kansa da gudu, irin foreas Tiger nan ne, ya ji kiwo ya ƙoshi sosai, ga shi fari tas da shi, idanunsa ba kamar na sauran damisoshi da kuka sani bane, na shi ligh blue ne, kun san dama su haka idanunsu yake. Tiger ta yi kyau sosai ba karya. Rungumar damisan ya yi yana shafa jikinsa, saman gabaɗaya grass carpet ne a wajen, a nan damisan yake yin rayuwarsa, bai cika fita da shi ba kuma bai cika barinsa ya sauƙa ƙasa harabar gidan ba, time to time dai yana sauƙa da shi zuwa harabar gidan, amma fa ɗaki ɗaya suke kwana, da daddare idan har zai kwana a gidan, idan kuma ya koma gidansu to a sama Tiger yake kwana. Da kyar damisan ya yarda ya sake shi suka ƙarisa cikin fillin, akwai pool mai girma a saman, sannan akwai Librarynsa na karatu a wajen mai shake da litattafai daban daban a ciki, sai wajen hutawa dake gefe mai shake da kayan alatu iri iri dan more daɗin rayuwa. Kai tsaye wajen hutawarsa ya nufa, wajen an kewaye shi da transparent glass, sannan an ƙawata shi da luxurious furnitures masu ɗaukar hankali, wajen dai ya tsaru iya tsaruwa. Wani haɗaɗɗen laptop MJ SWAROVSKI ne a saman center table dake tsakiyar kujerun. A kallah kuɗin wannan laptop ɗin ya kai dala miliyan uku da rabi, biliyoyin kuɗi ake magana. Daga ganin laptop ɗin a ido ma kawai kasan ta ci kuɗinta. Yana zama ya jawo laptop ɗin, Tigersa kuma ya kwanta a kusa da shi........... One thing about him, shi fa bisa ƙaida sannan ta halattacciyar hanya yake haɗa makamansa, kowace ƙasa tana iya nemanwa kanta abin da zata iya kare kanta da shi idan aka zo yakarsu su iya kare kansu. Ga shi kuma ya ci karo da tsawon shekaru familynsa ke mulkar ƙasar. Yana da ilimin addini sosai, mahaddacin Alqur'ani ne, yasan duk wasu dokokin Allah dan haka ba zai yi abin da ya saɓawa Allah ba, yana da kula da taka tsantsan, ya riki addininsa da muhimmanci fiye da tunaninku, a kan addininsa ma yana iya sadaukar da ransa. Nasan yanzu zaku yi matuƙar mamakin jin cewa mahaddaci ne shi ɗin bayan kuma kun san iyayensa christians ne, to ku saurara kuji labarinsa. Daddynsa d............. Na manta sai typing nake na bako long page sosai, dole na dakata a nan.🥱 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 15/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E22 Daddynsa dai musulmi ne cikakken mahaddacin Alqur'anin mai girma, ya yi wa addini hidima da karfinsa da kuma dukiyarsa, kusan halinsu ɗaya da Smart ɗin, mum ce taki musulunta, tana da kirki da farar zuciya sosai, kuma tana balain kaunar ɗan nata da mijinta, kawai musulunta ne ba zata yi ba, gabaɗaya familyn nasu christian ne, amma shi da dad ɗin ranar jumma'a tun karfe 10 suke masallaci har izuwa 1:30 ayi sallar jumma'a, suna sauraro huɗubar liman, kun san manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce duk wanda ya riga liman zuwa masallacin jumma'a ya zauna yana addu'oi haɗe da kararun Alqur'anin mai girma har liman yazo su yi sallah, kuma ya saurari huɗuba, to kamar yadda jariri yake zuwa duniya babu zunubin ko miskala zarratin to haka wannan bawa zai zama kafin ya fita daga cikin masallacin nan, Ubangiji ya shafe komai na daga laifukan da ya yi a baya, haba ƴan uwa me kuke jira, ai duk abin da kuke yi ranar jumma'a kam a daure a bada awa uku zuwa huɗun nan domin samun wannan garaɓasa. To shi dai Smart and dad musulmai ne cikakku masu kaunar Allah da Manzonsa, kuma dan mum taki musulunta bai sa basu zaman daɗi ba, zaman farinciki sosai suke yi, kullum basu gajiya da yi mata nasiha da nuna mata girman Allah dan ta musulunta........ Fatana dai Allah yasa tana da rabon musuluntar. Ya ɗan ɗauki lokaci kaɗan yana latsa laptop ɗin nasa kafin daga bisani ya kashe laptop ɗin ya miƙe tsaye. Kai tsaye haɗaɗɗiyar bedroom ɗinsa ya nufa. Wanka ya sake yi ya fito........... (Wai ni kam my people's ba Smart ɗin nan aka kira a waya a kan roket ta kwace masu ba? Ga shi ba'a gama haɗata ba bare a shigar mata da control 🤔 amma yana zaune ko a jikinsa🤔 da alama guy ɗin nan zai azabtar da ni 🤔 ka ji mun ɗan abin da babana ya hanani faɗa.) Shiri ya tsake yi cikin ƙananan kaya, ko da ya gama shiri ya dawo cikin room ɗin sai ya isko Tigersa kwance a kan gadonsa, a takaice ya ce mashi ya tafi. Da farko damisan ya so binsa, hana shi ya yi ya ɗauki wayarsa kawai ya fito waje, sai gurnanni damisan yake yi amma bai kula shi ba ya wuce kawai. Wani irin haɗaɗɗen mota ya ɗauko ba wanda suka zo da shi ba, wannan mota da ya ɗauko motace mai tuƙa kanta da kanta, ba sai ka wahala wajen tuƙata ba, da zarar ka shigar mata da location ɗin in da zaka je a map ɗinta zata bi komai a sannu ta kaika in da ka buƙata, idan gudunta bai yi maka ba kana da damar cewa ta ƙara gudu kuma zata ƙara sosai, haka zalika idan kana son ta kara gudun Ac ma zata kara maka, abin dai ba'a magana, shegiyar tsada ce da motar nan fiye da tunanin ku, billions of dollars ne. (Kun san ni bana son kiran sunan kuɗin abubuwan dan kada mu sume da jin kuɗinsu🤣 wlh ban san meyasa ba ban son faɗan kuɗin duk abin da na rubuta😅 ya fi mun in ce yana da tsada kawai, kuma wlh kuɗinsu na gaskiya ne, kiran ne kawai ban son yi.) To billions of dollars motar nan take, ta haɗu ta gaji da haɗuwa, ita ya ɗauko ya shiga, gidan baya ya shiga, kai tsaye ya shigarwa motar in da yake son zuwa. Securitys ɗinsa sun so su raka shi ya hanasu, dama dan kada ya rinƙa yawo da kowa a bayan idanun daddynsa ne yasa ya sayi wannan motar, sannan baya son driving da kansa, kunga a saukake motar zata kaisa in da yake da buƙata. Haka shi kaɗai ya bar gida, duk wannan uban tsaro da dad ya haɗa mashi kullum a nan yake zuwa ya jibgesu ya yi fitarsa shi kaɗai, dad yana can ya saki baki a kan ya bawa ɗansa tsaro na musamman, bai san jibge tsaron ɗan nasa yake yi a gida ya yi fitarsa shi kaɗai ba........... Kai tsaye bayan gari ya nufa, wato daji kenan, gabaɗaya wajen ƙanƙanra ne, ice palace kenan, motar tasa ma ba dan ta amsa sunanta mota ba bata isa ta keta wannan hanya ba, wajen akwai sanyi sosai da sosai, dusar ƙanƙara sai zuba take yi kamar ruwan sama. Ya yi tafiya mai nisa a cikin ƙanƙaran nan kafin ya dakatar da motar, sannan ya ɗauko wani jibgegen jacket mai bala'in kyau ya sanya a jikinsa, dan ba karya akwai sanyi kam, komai sabonka da sanyin ƙasar idan kazo wannan wajen sai ka haɗawa kanka kayan sanyi ko kuma sanyi ya busar da kai. Already dama kun san ƙasar France ba dai sanyi ba, suna da ita sosai, to amma dole wajen da za'a haɗa boma bomai irin waɗan nan ya kasance da sanyi, shiyasa suka nemi in da yake da matuƙar sanyi, dan idan baku manta ba nuclear bom's fa wuta ne, wuta kam mai rai da lafiya ma kuwa, kunga dole a nemi waje mai sanyi domin haɗa su, idan ba haka ba in waje mai zafi ne sai ma'aikatan su yi ta mutuwa, zafin sai ya yi masu illah over, kai bama zai yiwu a waje mai zafi bane. Fitowa daga cikin motar ya yi bayan ya sanya jacket ɗin, nufa kofar shiga underground ɗin ya yi.............. Kana sako kafarka a cikin wannan katafaren wajen nasu gabaɗaya warin chimical na haɗa nuclear bom's irin su, Uranium-235 U-235, Plutonium-239, Pu-239, Deuterium D2, Tritium T2, Lithium-6 Li-6 zaka ci karo. Dukkansu is for atomic Bombs Fission, gabaɗaya wajen idan baku saba ba kuka shiga sai mutun ya mutu har lahira, cikin tamkar engine bread, saboda zafi, ga wasu chimical ɗin yadda suke tafarfasa kamar wuta, kai abin dai sai wanda ya gani. Yana sanya kafarsa a wajen wani katon ƙosasshen bature fari tas mai rai da lafiya dake tsaye a wajen bakin kofar shiga ya yi hanzarin ɗauko mashi wani irin riga mai ɗan tsawo zuwa gwiwowinsa da kuma face mask and katon glass mai haske. Sanya rigar a saman kayan jikinsa ya yi tare da ƙarɓar glass ɗin haɗe da mask ɗin ya sanya a face dinsa. Yana yin tsarin wajen fili ne mai matuƙar tsaro wadda wane mutun ya iya gane me ake yi a wajen, duk munarfurci wata ƙasa bata isa ta iya gane abin da ake yi a wajen shagon ba, ga wajen underground, sannan ga uban tsaro da aka yi amfani da na'urori wajen sanya mata mahaukatan mataƙan tsaro na ban mamaki. Wasu irin jiga jigan fararen turawa ne birjik a cikin wajen, kowanne da aikin da yake yi, yadda kuka san wani irin katafaren Company ne a wajen, ko da yake wannan ya ci uban company ma, dollars suna kuka a wajen nan, dan ana cin uban kuɗi kam, kuɗin da ake zubawa a wajen nan wane budget ɗin Nigeria. Gabaɗaya cikin wajen tiles ne a kasan floor, ga wasu irin engines masu matuƙar girma, side da suke haɗa chemicals kala kala har su sarrafa shi su mai da shi wuta filin ɗan adam bai isa ya tunkara ba idan ba aikinsa bane, daga jefe guda ga wasu irin na'urori wanda da wuya ka iya samun irinsu a ko wace iriyar ƙasa, dan kuwa Smart shi ya kyara kayansa, a cikin wajen ta can gefe akwai wani part da aka ware na daban, system ne birjik a wajen, duk wasu irin nau'in abin da ya shafi system irin su laptop, desktop computer, kai duk dai abin da ya shafi system akwai shi a wannan wajen Duk in da ya sanya kafarsa zai wuce sai waɗan nan jaruman ma'aikatan nasa sun bar abin da suke yi sun ɗaga hannu sun sara mashi. Kai tsaye wajen system ɗin ya nufa, har ya kai tsakiyar wajen sai kuma ya juyo ya nufi wajen chemicals ɗin da suka haɗasu cikin wani irin jibgegen engine da yake buɗe kamar baf, a nan suke zuba chemicals ɗin sai engine ya yi masu mixing ɗinsa, sai ya haɗu sosai kafin su tura shi izuwa wajen da zai narkasu kuma. Ma'aikata sama da guda biyar ne tsaye a gaban chemicals ɗin suna aikinsu, yana dososu suka buɗa mashi hanya tare da ɗaga hannu suka sara mashi. Ɗaya daga cikinsu ne ya yi hanzarin ɗauko hand gloves ya sanya mashi a hannunsa, ƙurawa chemical ɗin idanu ya yi na ƴan sakanni. Chemicals ne irinsu Deuterium-Tritium D-T, Fusion fuel, Lithium Deuteride LiD. Slowly ya dawo da kallonsa a kan ma'aikatan nasa, shiru ya yi yana kallonsu kamar ba zai yi magana ba, can sai kuma ya ce. "This chemicals is it not for Hydrogen Bombs?". A hanzarce suka amsa mashi da e sune cikin girmamawa. Juyawa ya yi ya nufi wajen systems ɗin nan. Binshi da kallon mamaki suka yi, kai guy ɗin nan ba dai ƙwaƙwalwa ba, an cakuɗe chemicals ɗin waje guda ma amma ya iya tantance na wani irin nuclear bom ne, kuma chemicals ɗin kusan kala ɗaya suke a kamanni, amma a haka yana iya tace kowanne koda kuwa zasu haɗa da na nau'in boma bomai daban daban su cakuɗa ba'a gabansa ba yana zuwa kallo ɗaya zai yi masu ya ce masu ya suka haɗa na kaza da kaza? Tun suna mamakinsa har sun hakurar da zuciyarsu sun dai'na, dan sun gane baiwa ce daga Allah ke garesa. Yana isa wajen systems ɗin wani katon bature mai rai da lafiya a hanzarce ya cire mashi hand gloves da waɗan can suka sanya nashi, bayan ya cire sai ya cire mashi glass dake face ɗinsa ma, wani wajen ya nufa dan ya je ya ajiyesu, shi kuma Smart ɗin wata black glass ya ɗauko daga cikin drawers da wasu daga cikin nau'i na laptop suke ɗaure a kai. Sanya glass ɗin ya yi tare da shiga cikin na'urar da kyau ya fara ƙoƙarin control na nuclears da suka tattasa sama ɗasun dan gwaji, harta nuclear da ya kwacewa ma'aikatan nasa ma ya iya sarrafata, saboda already ya shigar mata da control su ne basu sani ba, dama ɗazun lokacin da yake gidansa ma'aikatar nasa sun gwada wasu nuclears abin da ya duba kenan a laptop ɗinsa da ya ɗauka a lokacin da ya haura sama a gidansa, to information da ya samu kenan shiyasa ya taso ya zo wajen dan ya ga ya nasarar aikin ya yake da idanunsa. Abin da kuma masu karatu baku sani ba, idan baku manta ba na ce maku yana da aikinsa na daban, to shi ɗin jami'in Secret Intelligence Service, the most powerful Jami'an sirrine in the whole kasar France, haka zalika ma'aikatansa dake wajen nan dukka aikinsu ɗaya, yaransa ne, dukka waɗan da kuka gani a cikin wajen zaƙaƙuran masu kishin ƙasarsu ne, basu da wasa ko kaɗan, da ka shiga hannun waɗan nan gara maka mutuwa, ko da yake ba sai na ɓata bakina ba wajen dogon bayani, mutanen da suke cikin irin wannan waje mafi haɗari a duniya ai bama sai an ce maku komai ba, wajen da in suka yi mistake kaɗan gabaɗaya birnin Paris zata bambame da wuta ne, babu abin da zai rage, dan kuwa ba ƙananan boma bomai ake haɗawa a wannan wajen ba, yadda suke haɗa chemicals suke tafasa suna ci da wuta haka zuƙatansu yake. Kowani jami'i aikin dake gabansa kawai yake yi, sai ku rantse da Allah basu san juna ba, babu irin hiran nan na sanayya bare raha, tamkar ma basu san da junansu a wajen ba, kowa ka gani fuska a turɓune tamkar waɗan da aka cewa wutar jahannama zasu shiga, kunga kuwa ai karshen ɗaure fuska kenan zasu yi. Ya ɗauki almost 1h a cikin na'urorin nan, yana tsaye a kan kafafunsa ko ɗar na gajiya baiyi ba, tamkar wani saƙagon da aka sassaƙa. Yawan ringing da wayarsa ta yi ta yi ne yasa ya ciccire duk wasu na'ura dake jikinsa ya fita daga wajen, sai kaga tamkar ma'aikatan nasa basu ganin komai face aikin dake gabansu, amma da zarar ya dososu zai wuce sai kuga sun ɗaga hannu sun sara mashi kamar wasu masu idanu a bayan wuya. Wani hanya mai ɗan tsawo ya bi, duk a cikin wajen ne, wani katafaren luxurious parlour ya shiga, yadda kuka san ba'a underground suke ba, ga wani irin daddaɗar kamshin da sanyi dake tashi a wajen, ba abin da ya fi bani mamaki ma irin furnitures dake cikin parlourn, sun haɗu kam, luntsuma luntsuma da su. Jami'ai biyu ne ke gadin room door ɗin, yana dososu suka kame waje guda tare da sara mashi, bai tankasu ba, tamkar ma bai gansu ba ya sa kai zai shiga ciki. A hanzarce ɗaya daga cikinsu ya tsugunna ya riƙe ƙasan takalmarsa hakan yasa takalmar suka fita daga kafafunsa, ɗaukarsu ya yi ya sanyasu a cikin shoe dryer dake ta bakin door ɗin ta ciki. Ɗayan jami'in kuma ya yi saurin sanya hannu ya zame mashi rigar dake jikinsa da jami'an farko suka sanya mashi a yayin shigowarsa wajen, yana cire mashi ya fice da rigar daga wajen...... Kai kaga wani isa da iko!! Takalma da rigar ma sai an cire mashi?!! Wannan guy daga gani akwai girman kai!!. Shi kuwa Smart ɗin toilet ɗinsa dake cikin parlourn ya nufa, akwai socks a kafafunsa, a haka ya zura toilet shoe ɗinsa ya shige ciki. Kai tsaye wash hand base ya nufa, wash hand sanitizer mai kyau da tsada ya ɗauko, wanke hannunsa tas ya yi da shi, yana da tsabta sosai, komai nasa very clean gwanin ban sha'awa. Waje ya fito bayan ya kammala, a saman sofa ya zauna, kafin ya fito wannan jami'in nasa da ya cire mashi takalma yasata a dryer ya ɗauko mashi ruwa mai sanyi and glass cup ya kawo mashi saman table kusa da sofar da ya zauna, su dai waɗan nan jami'ai guda biyun nan aikinsu kenan su hidimta mashi!. Yana zama ya ciro wayar tasa, gayyar miss calls dayawa ya samu, mum ɗinsa kawai ta yi mashi 10 miss calls kamar ba ɗazun ba jimawa suka rabu ba. Miss calls na dad ɗinsa ya kai 20, ɗan girgiza kai ya yi tare da furzar da iska mai ɗan zafi daga bakinsa. A hankali ya jingina bayansa a jikin sofar tare da fara kiran number mum ɗin nasa, da alama yafi sonta sosai sama da dad. Bugu ɗaya ta ɗauka, tana daga zaune a office nata ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ga sanyin Ac na bugata, sannan ga kamshi mai kwantar da hankali a gauraye a cikin office ɗin ta ko'ina, securitys biyu suna gadin kofar shigowa, hannunsu ɗauke da manya manyan guns masu lafiya ba saɓa saiti. Cike da tsananin so da kaunarsa ta ce. "Hello my baby". Wani daddaɗar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Mum.........." Katse shi ta yi da cewa. "I hope you get to the office safely?". Ɗaga kai ya yi yana kallon cikin parlourn nasa, wato ita mum duk a tunaninta wajen aikinsa ya tafi, har da tambayar ya isa lafiya? Bata san yana nan yana aiki daddynsa da suka ɓoye mata ba, lallai akwai kura ran da ta gane gaskiya kuwa. "My baby". Ta sake kiran sunansa jin bai amsa mata ba, bata san ya aka duniyar tunaninta a kan idan ta ganosu daddynsa yana ruwa tsundum bane, dan kuwa zai sha hukunci a hannunta ba kaɗan ba. (Ni kam na ce idan ma bata ce ta saki daddyn ba🤣🤣 e mana su ai kunsan mata tana saki a wajensu🤣 ba wani cikakken hankali ne ya ishi wasun su ba, amma ba ruwana na yi nan kada Smart ya ji abin da nace.) "Mum everything is going well like the way you think". Ya faɗa a sanyaye, yana magana yana bin parlourn da kallo kamar bai san komai da yake ciki ba. "How's your work? Hope you're enjoying the day?". Ta sake jefa mashi tambaya. "My mum". "My baby". "My mum". "My baby". Shiru ya yi tare da ɗaura hannunsa a saman forehead Mum da dad ɗinsa suna yi mashi son ransu, sai ya kira sunansu suma su kira nasa, sun saba mashi da wannan abin tun yana ɗan shekara bakwai, sai ya ce mum ta ce baby, idan ya ce dad ya ce son, abin gwanin ban dariya. Call ɗin dad ne ya shigo wayarsa, dukka fa a kan abu ɗaya suke son tambayarsa, shi ne kuma ya isa office lafiya sannan ya aiki, a kan wannan tambayar fa suka tara mashi miss calls har haka, kullum haka suke yi mashi, sai sun ji ya isa lafiya kuma yana cikin aminci sannan suke kama nasu aikin, wannan ɗan nasu mugun ji da shi suke yi, suna kaunarsa fiye da kansu,....... Ni kam nace ai dole su so shi, dan kuwa shi kaɗai kamar rai ne ke garesu, ga shi sun tsufa, dan shi kansa Smart ɗin ya kai 30 years a duniya, kunga kuwa ai sun fara tsufa, basu ma sanya rai a kan samun wani yaron ba, dan a tunaninsu ba samu zasu yi ba, shiyasa suke bashi kulawa fiye da kansu, one in billions yake a garesu. "Mum dad is call me let me pick his call". Ya faɗa a kasale. Da okey ta amsa mashi kafin ta jero mashi jawaban da ta saba a kan lallai ya yi breakfast mai kyau tun da yaki ya yi a gida, sannan lallai idan ya yi aiki na awa ɗaya ya kwanta ya yi barci na awa biyu dan ya huta, kada ya yi wani tunani idan ba nata ita da dad ɗinsa ba, ya kula masu da kansa sosai, haka dai ta rinƙa jeramasa su kamar yadda ta saba, kullum haka take yi mashi. Wani irin haɗaɗɗen sumbata ta mannawa wayar tata a zuwan shi ta sumbata. Okey kawai ya ce tare da katse kiran, dan in ya biyewa mum sai su kai yamma basu yi sallama ba, jawabinta baya karewa, idan ya ce mata shi fa yanzu ba yaro bane, sai ta ce mashi har gobe shi babynta ne, a baby take kallonsa, hakan bata yi mashi daɗi sam sam, mum ta ki yarda ya girma.........😅 Yana ɗaukar call ɗin daddyn ma abin da mum ta faɗa shi ya sake nanata mashi, okey nan dai ita ta raba shi da su. Yana katse kiran ya ajiye wayar, sam bai bi sauran miss calls ɗin ya kira ba, dan dama shi idan ba mum and dad ba baya bin miss calls na kowa ya kira, duk mai buƙatarsa sai dai ya Kiransa. Shiru ya ɗan kwantar da kansa yana kallon sama kamar mai nazarin wani abin, Allah ya gani yana kaunar iyayen nan nasa, yana jinsu a ransa tamkar ya yi masu numfashi. Wayar tasa ce ta fara ringing again, ɗaukota ya yi ya kawota dai'dai saitin face ɗinsa. Ganin sunan dake yawo a saman screen ɗin ne ya sanya shi yin hanzarin picking tare da miƙewa ya nufi waje, dukkan nutsuwarsa ya tattara waje guda dan yin magana da wanda ya kirasa ɗin, da alama mutum ne mai muhimmanci a garesa. Kai tsaye wajen ya nufa, yana waya yana tafiya har ya je ya shige cikin motarsa. Da gudun gaske motar ta tashi ya bar wajen. Office ɗinsa ya nufa wato ma'aikatansu na jami'an Secret Intelligence Service. ______________________🔥🌼❤️ DARK WORLD🔥 Idanun Ronnie cika suka yi tab da kwallah a lokacin da Sweetie ta kammala bashi labarinta, sosai ya ji tausayinta ya kamashi, bai taɓa jin tausayin wani ba a rayuwarsa sai yau, ajiyar zuciya ya sauke tare da sanya hannu ya ciro handkerchief daga aljihunsa, goge kwallan da suka cika mashi idanu ya yi, sannan ya matso kusa da ita sosai, sai kuka take yi hawaye duk sun wanke mata fuska, da alama labarinta ba mai daɗin saurara bane, handkerchief ɗin ya sanya ya fara goge mata hawayen nata da shi........ Abin da mamaki, ashe Sweetie ta san labarinsu kenan? Ta san su waye su?! Tabɗijam!. Amma yarinyar nan akwai basira da nutsuwa. Rarrashinta ya fara yi a kan ta yi shiru. Da kyar ya samu ta dai'na kukan, ruwa ya ɗauko mata ta karɓa ta sha. Shiru ya zuba mata idanu yana kallonta, ita kuma ta duƙar da kanta ƙasa tana ɗan shesshekar kuka...... Abin da mamaki sosai gaskiya, Ronnie da yake irin wannan masarauta mai cike da zalinci kala kala, azaba kala kala mai taɓa zuciya bai taɓa zubar da kwallah wai dan an zalintar wani ko kuma yaga zalincin da ta ɗaga mashi hankali ba sai a kan labarin Sweetie, wannan wani irin labari ne to? Kada ku manta ɗazun fa aka datsewa wani wuya a gabansa amma rawa ma ya rinƙa tiƙa shi da master Devil ko a jikinsu, yanzu sai ga shi kwatsam yana yi wa labarin Sweetie kwallah, kai da mamaki sosai abin, shi fa bai taɓa zubar da kwallah a kan wani abin ba, tabɗijam lallai da matsala in kuwa hakan ne, ko me ta gaya mashi?. Zuciyarsa ta karaya matuƙa yau a karon farko a rayuwarsa, bai taɓa jin karaya ko wani rauni na sai yau, duk sai ya jikinsa ya yi sanyi, har wani guntun ciwon kai ya ji. Hannu ya kai ya riƙo nata hannayen, hakan yasa ta ɗago kanta tare da sauke idanunta a cikin nasa. "Where's your mum now?". A hankali ya faɗi maganar. "I don't know where is she". Ta bashi amsa. Sake sauke ajiyar zuciya ya yi kafin ya matso da bakinsa dab da kunnuwanta, ƙasa sosai ya yi da murya tamkar munafukin da zai kai gulmar kishiya ga kishiyarta, a haka ya fara yi mata raɗa a kunne kamar haka. "Ya isa haka kukan please, I promised you that ba zan taɓa bari ki sake yin kuka ba, kuma na yi maki alkawarin tabbas duk yadda za'ayi zan kuɓutar dake daga gidan nan, ba zan taɓa bari yaya ya azabtar dake kamar yadda ya yi wa wasu a baya ba, ya sha kashe mutane a kan neman Spender, ya sha wahala kafin ya iya nemo in da kike, ya taɓa kama wata yarinya ta so ta yi kama da ke, kai kuna ma kama sosai da ita, a tunaninsa lokacin kece ya kama, ya buƙaci Spender daga hannunta sai ta ce bata san menene bane ma, haka ya kasheta da azaba haɗe da razanarwa, sai da ta haukace kafin ta mutu saboda razanata da yake yi, na yi maki alwarin zaki gudu daga gidan nan, sai dai ki mun alƙawarin ko da yaya ya kamaki ba zaki ce da sa hannuna ba?". Dakatawa da maganar ya yi yana jiran ya ji me zata ce! Ya kurawa face ɗinta idanu kamar zai cinyeta ɗanya. A hanzarce ta gyaɗa mashi kai alamar ta yarda ba zata ce da sa hannunsa ba ko da an kamata. Nisawa ya yi tare da sanya hannu ya kwantar da kanta a saman kirjinsa. Cigaba da magana ya yi a cikin kunnenta. "Queen of beauty tun kafin a kawo ki nan wajen na san labarinki". A hanzarce ta ɗago da kanta. Mayar da ita ya yi tare da cigaba da maganarsa. "Bawai labarin tarihin rayuwarki na sani ba, no, labarin cewa Spender yana hannunki na sani, sau da dama na buƙaci ganin hotonki yaya yana hanani, dan ya ce har ni a wannan karon bai yarda da ni ba, saboda ya sha nemo hotunan mutanen da yake samun labarin Spender yana hannunsu, zai sha wahala ya nemo hotunansu, sai dai kafin ya kai ga isa garesu wasu sun rigasa, hakan yasa yake tunanin ko ni nake gayawa mutane, dan yasan ni kaɗai yake gayawa rahoton, amma magana ta gaskiya bana gayawa kowa, kawai dai abin da na lura da shi shi ne masu neman Spender suna da yawa ne". Ɗan dakatawa ya yi da yin maganar yana mayar da numfashi a hankali hankali. Shiru ta kwanta tana sauraronsa, ƙwaƙwalwarta sai saƙa mata waye shi wannan yayan nasu? Meyasa ya zama bakin azzalumi har haka?. "Yanzu kin san me nake so da ke?". Ya katse mata tunanin nata. Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Dole ki saki jikinki a gidan nan, domin kada wani ya gane shirina, sannan ki nuna tamkar baki cikin damuwa, ki yi rayuwa tamkar yadda kike yi a forest ɗinku, ki ƙirƙiro farincikin dole domin mu cinma burinmu, lastly kada ki ƙara mun zancen Kamran a nan, zancen Pretty is okey for me". Mamakin kalamansa na karshe ne ya kamata, dama tun ɗazun ta lura da shi ya canza fuska, tun lokacin da ta gama bashi labarin mum ɗinsu ta shigo labarinta ita da Kamran and Pretty a forest, tun daga nan ya canza fuska ya ɓata rai kamar ba shi ba, bare ma da ta ce mashi bata da wani burin da ya wuce ta buɗe idanu ta fara kallon Kamran lokacin da suke Forest kenan, ta ƙara mashi da cewa bata yi farincikin buɗewar idanunta ba tun da bada shi ta fara yin tozali ba, tana kewarsa tamkar hauka, daga nan face ɗinsa ta sauya ya ɓata rai, ji yake yi kamar ya tashi ya tafiya ya barta Black Tiger ya cinyeta ɗanye ma idan yana so, ya ji kamar kada ya taimaka mata, amma sai ya daure, ko me dalilinsa oho dai. Okey ta ce mashi tare da cewa ba zata sake ba. Hannu ya kai saman gashin kanta. "Beautiful Queen gashinki ya so ya yi kama da nawa, amma naki ya fi nawa kyau sosai". Rasa me zata ce mashi ta yi, dan ita ba wani hira ta iya ba, kun san dama da Pretty kawai take hira, ko Kamran sai dai gaisuwa ce take haɗasu, so bawani iya dogon magana ta yi ba. "Baki ce komai ba". Ya sake faɗan. "Nakama yana da kyau". Da kyar ta iya faɗan hakan. "Golden white ya fi up white kyau fa, i really like yours, and see this your eyes is very very sexy nice and........" Sai ya ƙarisa mata sauran maganar a cikin kunne kamar wani maras gaskiya.......... Ya yi maganar ta yadda ban ji me ya ce ba!!. Kuma yana zuba mata kalaman yana wani lumshe idanu kamar ba lafiya yake ba!!. Ba wani abin da ta gane da kalamansa, ita dai bayan cewa da ya yi nata ya fi nasa kyau, sai kuma kalmansa na karshe da ya ce ita ɗin kyakkyawace ta karshe sannan kuma tana da sexy body kakar babbar mace, daga haka bata san ma'anar sauran kalaman nasa ba, shi dai ya sani! Kuma sexy kalamai ya rinƙa gaya mata a cikin munnen nata, to ita da take girman forest dama ta ina zata gane wannan karatun nasa fisabilillah? Ai sai shi ɗin zai gane. (Summy princess zan yi wa Ronnienki ihun kwarto fa, ta ya zai wani zauna yana gayawa baiwar Allah irin waɗanga kalamai? Aisha baita jidda Maman Sultan Ronnie zai ɓata maku tarbiyar da kuka yi mata, ku kama sumayya ku jibgeta zata ja mashi kunne in ta ji wuya) Shiru ta yi bata bashi amsa ba, dan ita bata san me zata ce ba. Jin ta yi shirun ne yasa ya ɗan lankwasa dogon wuyar nan nasa ya leƙo face ɗinta. "Queen of beauty why kika yi shiru? Give me my amsa mana, i said why are you so beautiful like that, do you look like mom or dad?". A sanyaye ta amsa da. "I don't know what to say, that's why am silent, but ka manta na ce maka we don't know our dad?". Ɗan shafa gashin kan nata ya yi tare da cewa. "Oh oh eyya na manta ne, zaku ga dad ɗinku nan ba da jimawa ba, in dai na samu na kuɓutar dake daga hannun yaya to ba shakka nima zan biyo bayanki daga baya, zan tayaki neman dad and mum with our Pretty". Yana magana kamar wanda yake jin barci ko maras lafiya. Godiya ta yi mashi sosai, daga haka bata sake yin magana ba ta yi shiru. Sarai ya lura da bata iya magana bama bare ajega sexy words masu daɗi, daga e sai a'a ta iya. "Ronnie". Ta ambaci sunansa ƙasa ƙasa. Miƙar da wuyarsa ya yi kafin ya amsa. "Ina son sanin wanenen ya kawo ni nan? And me zai yi da Spender? Waye wannan yayan naku? Sannan ina su mamanku ku kuma suke?". Wani irin yanayi ne ya bayyana a saman face ɗinsa jin tambayar da ta yi na wanenen Black Tiger? Alamar tsoro haɗe da tashin hankali ne suka bayyana a saman face ɗin nasa, nan take ya shiga taitayinsa, idan da daɗin hira da ita yasa ya mance in da yake, to yanzu ta tuna mashi dalilin wannan tambaya tata, fuskarsa ta canza daga annuri izuwa tashin hankali. Rabata da jikinsa ya yi tare da yunƙurawa zai miƙe ba tare da ya bata amsa ba. Ɗago idanu ta yi ta kallesa da kyau, tabbas ta lura da canzawar da ya yi lokaci guda, sai dai bata kawo wani banzan tunani a ranta ba, ta yi tunanin ko kawai zai tafi ne babu dalili. Haƙiƙa ya ji babu daɗi sosai a ransa, ba komai yasa hakan ba kuma face ta yi mashi tambayar da ba zai iya amsa mata ba, bai isa ma ya amsa mata ɗin ba, bai so kuma ace ta nemi wani abin a wajensa ta rasa ba, amma ko zai mutu ba zai iya gaya mata wanenen Black Tiger ba! Da alama shi yasan Black Tiger ɗin sosai, kawai dai ya nuna kamar bai san shi ba ne, idan kuka yi duba da yadda yake shiga har cikin bedroom ɗinsa kunga da wuya idan bai san ya kamanninsa suke ba. "Zan roƙi yaya da ya bar Floris ta rinƙa zuwa kuna yin hira idan na tafi school, zan so ace tana koya maki wasu abubuwa, ko ba komai idan kika bar gidan nan zasu amfaneki......". Da kyar ya iya ƙarisa maganar, daga jin yadda yake magana zaka fahimci ransa a ɓace yake. Yana gama maganar ya nufi waje da sauri ba tare da ya sake kallonta ba. Yana fitowa ya shiga bedroom ɗin Black Tiger dan ya roƙesa a kan Floris ta zo ta rinƙa zama da Sweetie. Ya ɗauki tsawon 20 mins a ciki kafin ya fito ya nufi ɗakin da aka kwantar da Delisha tana jinya, duba lafiyar jikinta ya je ya yi tare da fitowa. Nasa room ɗin ya shiga, wanka ya fara yi kafin ya shirya cikin sport wears masu tsada, ya yi wa kayan kyau sosai. Ƙasa ya sauƙo da nufin ya ci abinci ya je buga ball, zakarar Dark world kenan, a komai shi ne a gaba, ball ɗin ma ba'a barshi a baya na, ga shi yau ba zuwa church, dan pastor ya faɗi bashi da lafiya yana kwance a hospital, yanzu shigarsa wajen yayan nasu ya samu labarin hakan. A parlourn ya isko Floris na zaune a saman sofa tana jera abubuwan game ɗinta dake saman trayn wasan. Ta bayanta ya lallaɓo ya zo ya sanya hannu ya watsa mata cubs ɗin da ta sha wahala ta jera. A dubu ta juyo domin taga wanene?. Tana ganin shi ne ta haɗe rai tare da ajiye tray ɗin, cikin dabara ta ɗauki pillow ta harbesa a fuska da shi. Kamar ya san zata yi hakan ya yi carap ya capke pillown ba tare da ta taɓa fuskar tasa ba. Haushi ne ya kamata ta nufesa gadan gadan irin ta zuciyan nan. Sai da ya bari ta iso in da yake ta ɗaga ɗan hannun nan nata kamar bulala zata kai mashi naushi a ciki ne ya riƙe hannun nata, wurgi da pillown hannunsa ya yi ya haɗe ƴan hannayen nata ya riƙe da hannunsa ɗaya. Sumbata ya manna mata a dogon wuyar nan nata yana faɗin. "I really missed you my beb, yaushe kika dawo daga school?". Ƙoƙarin kwace kanta take yi dan ta samu ko naushi ɗaya ne ta yi mashi. Ɗagata sama ya yi sai saman kirjinsa, a kunne ya raɗa mata. "Tsaya ki ji wani magana" kin yarda ta yi tana ƙoƙarin barin jikin nasa. Cigaba da gaya mata magana a kunnen ya yi kan kace wani abin har ta fara dariya kamar zararriya. Dining room ya nufa da ita sai dariya take yi, ko me ya gaya mata yasata dariya? Oho mashi. Wato shi Ronnie har da sarrafa mata ya iya, daga ya sanya wannan dariya sai ya sanya wancan kuka, kai anyi ɗan duniya da babu biyunsa a Dark world ɗin nan wato Ronnie, shi dai babu ruwansa, bashi da wata matsalar rayuwa. Zama suka yi ya ce ta bashi abinci a baki, ai kwana biyu bata bashi ba. Make mashi kafaɗa ta yi tare da cewa a'a ba zata bashi ba. Marairace mata ya yi tare da shagwaɓe fuska kamar ba shi ne zakin Dark world ɗin ba, kamar zai yi kuka ya ce mata please ta yi hakuri ta bashi mana. Jan mashi aji ta fara yi. Hannu ɗaya yasa ya damko wuyar rigarta zai jawota jikinsa, dama mini sket and vest ce kawai a jikinta. Ganin ya damkota ne yasa ta fara ihun wasa tana faɗin zata bashi abincin. Kashe mata ido ɗaya ya yi, ya yi ƙasa da murya sosai. "Da baki amsa ba yau da kinga aiki da cikawa". Harara ta wurga mashi, ido ya sake kashe mata yana sakin cool murmushi dimple nasa mai tafiya da imani maza da mata yana lotsawa. "Zero tension kawai". Ta faɗa haɗe da murguɗa baki. Kwaikwayan yadda ta murguɗa bakin shi ma ya yi sai dai bai iya ba, daga karshe ma sai dogon harshensa ya fitar ya lashe lips ɗinsa wai shi ma a dole ya murguɗa baki. Su dai robbot suna tsaye suna kallonsu har sai da ya ce su zuba mashi abinci. Da farko Sweetie ya so ta bashi abincin a baki shi ma ya bata dan yasan bata ci komai ba, shiyasa yana dawowa daga school ya nufi wajenta dan ta ciyar da shi, amma ta zo ta ɓata komai ta hanyar kawo mashi zancen wanenen Black Tiger? Tana son kasheshi tun kwanansa bai ƙare ba, zata ja mashi rugugin bala'i ai gara mashi ya kama kansa shiyasa ya bar ɗakin. Wai ni kam to menene dalilin Black Tiger na ɓoye kansa? Dole akwai wani ƙwaƙƙwaran dalili kam, ba haka kawai banza zai boye kansa yana wanzar da zalinci ba!!. Ciyarda shi a baki ta yi har sai da ya ƙoshi, sannan ya miƙe ya ɗauketa cak suka nufi wajen buga kwallo. Jama'a sun cika stadium ɗin tab, komai ya kankama shi kaɗai ƴan team ɗinsa suke jira. Yana sako kafarsa a fili jama'a suka hau tafi da ihun murnar zakinsu ya shigo fili. Ɗaure fuskar nan tamau ya yi tamkar ba yanzu ya gama wasa da Sweetie and Floris a cikin gida ba, shi fa Ronnie ɗan rai'nin wayo ne na bugawa a jarida, mata kawai ne suke ganin murmushinsa, kuma su kaɗai ne yake sakarwa fuska, matan ma dama da Floris ce sai Delisha, to yanzu sun yi faɗa ya kakkarya Delisha sai ya maye gurbinta da Sweetie, su biyu yanzu yake sakarwa fuska, idan ya fita waje tamkar wani zaki haka yake, sai ya turɓune fuska over, kowa ka tambaya zai ce maka bai taɓa ganin dariyarsa ba sai waɗan nan mutane biyun yanzu da Sweetie uku. Wasa aka fara bugawa jama'a sai murna suke yi, dama kowa ya rigada yasan team ɗin su Ronnie ne zasu yi nasara, dan in baku mantaba shi ne zakaransu a empire ɗin. Haka kuwa aka yi, su suka ɗauke cup ɗin wannan wasan, jama'a ihu suke kurmawa sosai kamar ba daga cikinsu ihun yake fita ba saboda sautinsa. Master Devil dake zaune a saman haɗaɗɗiyar kujerarsa ne ya ce yau dole ayi shagali a case dan kwana biyu ba'a yi ba. Jin furucinsa yasa jama'a suka kara kurma ihun suka ruɗe da murna. Master Devil fa ya ɗauki Ronnie kamar ɗan cikinsa ne, dan shi ne horonsu ya yi dai'dai, yana ji da shi sosai......... Sai da daddare suka shirya partyn da master ya ce. Tsala tsalan ƴan'mata waɗan da suka iya taka rawa sosai ne aka kira, sun iya rawa da har idan suna takawa ma zaku ga tamkar basu da ƙashi a jikinsu, su yi wani irin lankwashewa kamar macizai, su uku ne matan gasu kyawawan gaske........ To ni dai na ce a gaskiya rashin addini dai bai yi ba, idan ka bar addinin musulunci wlh ka shiga uku ka lalace. To su dai haka suka shirya partynsu, ga kwalaben giya gana dreaks kala kala, saniya da raƙumi aka gasa tun da rana, shagali iya shagali suke yi idan master ya shirya masu party, ga rawan da suke yi innalilahi ba'a magana, sai ma idan Ronnie ya shiga filli yana rawa, guy ɗin nan ya kware kam, in dai rawa ne to daga kansa an rufe kofa, dama ga jikinsa ɗan dai'dai ya taka son ransa babu nauyin jiki bare ciwo. Kowa yana zazzaune a saman chairs ɗinsa, kiɗa kawai ake jira sai a fara takawa, shi kuwa mai sakin ƙiɗan wato Dj yana jiran ne Master ya bada umarni aci a sha sannan a sha giya a yi tatul ta yadda zasu ji daɗin casunsu a buge, su haukata kansu su yi ta rawa kamar waɗan da aka zarewa duk wani hankali da sani. Ai kuwa master na bada umarni ba wanda bai kwankwaɗi wine kwalba biyu zuwa sama ba, wasu iyayen rashin hankali kam ma giyar zallarta ba'a sirka ba suka sha har kwalba uku zuwa biyar, duk kuma abin da suke yi Black Tiger yana ganinsu, dama shi baya hana a cashe, su yi duk abin da suke so, shi ma idan ya tashi yana yi masu son ransa ne. Sai da suka bugu iya buguwa saura Master da Ronnie, su basu shan wine, sai dai su sayawa masu sha, Floris da Delisha ma basa sha, Ronnie ya hanasu, dan shi ɗin ɗalibin lafiya ne. Dukka ƴan Wrestling nasu da kuma dakarun yakinsu ma Black Tiger ya hanasu shan wine, dan in suka shata nan take zata yi masu mummunar illar, saboda kullun cikin yin training suke, zasu mutu a banza in suka ce zasu haɗa hanya da ita. Matan da zasu yi rawan ma fa sai da suka kora rabin kwalabe, lokacin da Dj ya saki waka ya subhanallah, idan kuka gansu yadda suke cin uban rawa sai kunce kun godewa Allah da ya yo ku a musulmai. Lokaci da Ronnie da master suka fara rawa, basu fili aka yi ana ihu haɗe da tafi, masu fito suna yi, sai dai fa komai rashin son rawanka idan kaga yadda Ronnie yake rawa sai ya burgeka, ya kware iya kwarewa, wannan da zai shiga gasar rawa na duniya shi zai zo na ɗaya. Yana tsaka da rawa ya tuna cewa dole ya ɗauko Sweetie su yi rawa a tare, zai koya mata idan ma bata iya ba, dan haka bari ya ɗaukota ita da Floris, dole ya roƙi Black Tiger ya barta su taka rawa yanzu kam tun da a cikin gida ne ya barta ta fito su taka............... Tab Sweetie da rawa, e lallau kinga ta kanki, Ronnie dai anyi ɗan duniya wlh.....🤣 To na dai barku a nan bari mu leƙa wani wajen mu dawo kafin nan kila Black Tiger zai aminta Sweetie ta fito ta taka rawan. ___________________🔥🌼❤️ DUBAI 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E23 DUBAI_____🔥🤍🔥 Izuwa yanzu Leesharh ta yi mugun sabo da Sharifat sosai, sun zama kamar ya da kanwa, har Abbie yana batun saka Leesharh ɗin a school ɗin su Sharifat, sai dai a nan matsalar take, dan dai da ni da ku munsan takardunta dai na karya ne, kuma hakikanin malamai idan suka ga takardun nan dai zasu gane gaskiya, matsala ta biyu kuma bata kammala secondary school ba a gaske, a takardu kuma ta kammala, yanzu Abbie magana yake a kan zata shiga jami'a fa kenan, jamb zata rubuta yanzu....... Babbar magana!!. Tabɗijam! Dan ma tana da ƙwaƙwalwa yarinyar da lallai za'a shiga babban makaranta da dolanci, dan kuwa ba wani abin kirki ta iya sosai ba, matsala ta uku 15 to 16 years take da shi kada ku manta, gata ƴa mace, a wannan zamani a ɗan shekarun nan nata ake son ta goga da manyan mata ƴan jami'a, ita da ba wayewa ne ke gareta ba, ba ishasshen ilimi ba, da alama Abbie yana son ɗaukar dala ba gammo, domin kuwa kamar yadda masu nikaf suke beating na brain ɗinta da wuya idan ta shiga jami'a manya mata bazasu kwatanta beating na brain ɗin nata ba suma, koma su yi mata wayo su ɓata mata rayuwa, ga maza sosai, tsab wlh zasu mata wayo su buɗe mata idanu, dan ba ƙarya ta yi ƙanƙanta, ga shi ba uwa kusa bare uba, Ummie dai kun ga bata sonta, bata ko kulata bare ace zata maye mata gurbin uwa ta rinƙa bata ƴar shawarwari ta jata a jiki. Sannan ga dukkan alamu Leesharh bata taso da uwa kusa ba, saboda yanayin yadda take gudanar da rayuwarta zai tabbatar maku da cewa ba shakka ta jima bata a tare da mahaifiyarta, duk macen da ta taso a tare da uwa ba zata yi irin shirmen da take yi ba, ga ƙwaƙwalwar dai tana da shi, amma an rasa wanda zai sarrafata ta hanya mai kyau har ƙwaƙwalwar tata ta amfaneta, kuna gani dai yadda take ta fama a kan tunanin masu nikaf, sai ta yi kamar zata ɗago gaskiyarsu sai kuma ta sake komawa ruwa, sai ta yi tamkar ta gane gaskiya, sai kuma ta sake faɗuwa, gabaɗaya gata gatan nan kawai, tana da buƙata uwa ko kuma mai irin zuciyar uwa wanda zai cike wancan gurbin. Shi kansa Abbie yanzu da ya jawota a jikinsa sosai ya fara lura da cewa da wuya idan wannan yarinya ta kammala secondary, sannan yanzu ya ga ƙanƙantar shekarunta a yanayinta da ta matso kusa da shi, sai dai bai wani ɗauki wannan tunani nasa da mahimmanci ba, daga karshe ma ya watsar da tunanin a in da ya umarce Dr Raj ya tsaya mata ya yi mata duk abin da ya dace!!. Yah Rizwan and Omar wato Guyson sun shirya komawa ƙasar Tunisia a yau, shi Yah Rizwan batun aurensa da Gimbiya Chuchu zai kaisa sai kuma Akka da ta ce lallai lallai ya zo, dan tana zargin Jaish ko Jawad ne suka yi mata wancan tsiyar, shiyasa ta ce Rizwan ɗin ma ya zo, a cewarta shi ne uwarsu ɗaya da Jawad, dan haka kome za'a yanke a gabansa za'ayi, Su King basu taɓa rabe ƴaƴansu ba shi da uncle Abbas, amma Akka tsab take rabasu, ba wani haɗesu da take yi da sunan family, wani lokaci idan gigin tsufan ma ya bugota sai ta kira Yah Jawad da Abbas ɗin ma mai gabaɗaya, wannan tsohuwa dai sai dai muce Masha Allah, rigimamma ce number ɗaya. A ɓangaren Yah Ramish kuwa, Dr Raj ya sha matuƙar wahala a kansa, Bilal ma ba'a magana, har rama bawan Allahn nan ya yi, ya shiga matsanancin damuwa sosai, baya fita office, baya samun ishasshen barci, haka zalika baya nutsuwa ya sanyawa cikinsa wani abin kirki, sai gayyar coffee or cappuccino, idan ya ɗan gaji da su ne sai ku ga ya sha cold brew, aikin kenan kullum, ya rasa ina zai sanya ransa ya ji sanyi, suna kaunar junansu ne, in short Ramish ɗin dake kwance yana jinya ma ya fisu kumari da kyan gani, sai jigila suko suke yi suna going up and down a kansa. Idan baku manta ba dama harbi biyu aka yi mashi, dukka biyun kuma sun ɗan taɓa yi sosai, ɗayan kam ma a gefen cikinsa ne bullet ɗin ta fasa, ɗayan kuma a hannunsa wajen damatsansa, na hannun nasa kam Alhamdulillah ba laifi an shawo kan wannan matsala, na cikin ne dai aka samu matsala saboda abin da ya sha kafin harbin ɓille ɗin. A iya binciken da Dr Raj ya yi a cikin jininsa ya gano an bashi wata magani ne mai suna arm bars an kwaɓa shi da joins locks da wani shegen magani mai karfin iya ɓacewa a cikin jini wanda ya ƙasa iya gane wanenen, duk iya binciken da ya yi ya kasa ciro maganin, shegen magani ne mai wuyar ganewa idan ya ratsa jini, da ace ba Ramish aka haɗawa wannan ba, kai ace ba wani na jikin Dr Raj ɗin aka yi wa hakan ba tsab zai iya bincika ya gane wani irin magani ne. Amma ɗan uwansa da suka shaƙu aka yi wa hakan, baya cikin ishasshen nutsuwa da zai iya yin wani dogon bincike, yana tafiya ma tamkar zai kifa saboda tashin hankali, aikin nan yinta kawai yake yi dan tabbatar da ɗan uwansa ya kuɓuta daga haɗari, amma a wahalce yake bawan Allah. A ɓangaren Leesharh tun ranar da masu nikaf suka katse mata kira a kan ta ce su haɗa ta da babanta, to tun ranar basu sake kiranta ba, ba wai kuma basu nemanta ɗin ba ne, nemanta ma suke yi kamar hauka dan su tambayeta shin Ramish ya mutu ne ko kuwa harbin bata same shi a in da ya kamata ba? Kun san idan ba ita da take cikin gidan kuma hawan da su Ramish ɗin suke ba da wuya masu nikaf ɗin su san halin da ake ciki ta wajen wasu, dole sai ta wajenta, dan idan baku manta ba a baya sun faɗi cewa suna da ma'aikata a gidan, amma ba'a can ciki ba, har suka kara da cewa Leesharh yarinya ce za'a barta ta yi aiki a can ciki, to shiyasa suke nemanta dan su samu rahoton meke gudana a cikin gidan. Sai dai kash a yanzu ko sun kirata wayar baya shiga, ba komai yasa hakan ba kuma face sun koma kwana ɗaki ɗaya da Sharifat, gudun kada asirinta ya tonu yasa ta kashe wayar mai gabaɗaya ta cusata cikin wani aljihun wandonta ta danna a can kasar echolac ɗinta, ta yadda hankalin Sharifat ba zai kai wajen ba. Abin da Leesharh bata sani dan gane da masu nikaf a nan ba shi ne, a wannan rana da ta zubawa Ramish wannan maganin da suka bata, da Ramish ya mutu tamkar yadda suka shirya ko sun kamashi sun tafi da shi kamar yadda suke so, to da ba shakka ba zasu sake nemanta a waya ba, aikinsu da ita ya ƙare, zasu san ta yadda zasu yi ne a cikin gidan su tona mata asiri ta yadda Abbie zai binneta da ranta, ko kuma su Yah Bilal su kasheta su miƙawa karnika namarta, sannan su kuma su kashe babanta dake hannunsu, kunga sun rufe babinta kenan, a tunaninsu asirinsu a rufe hankalinsu a kwance dan sun san bata san komai dan gane da su ba bare ta tona masu asiri. Da Allah yasa bata da hakkinsu, Allah ba azzalumin bawansa bane, sai Allah ya nufa burinsu bai cika ba, Allah ya aiko Bilal ya ceci ran ɗan uwan nasa, Ramish bai mutu ba!! Wannan dalilin yasa yanzu suke neman Leesharh ɗin kamar hauka, dan kuwa kunga idan ya kasance Ramish bai mutu ba dole su nemota ta koma bakin aiki, dan su fa sun kwallafa rai a kan sai sun ga bayansa, ba gudu ba ja da baya, wannan abinfa ba iya masu nikaf bane kawai, akwai manyan jiga jigai daga sama waɗan da su suka ƙaddamar da contract ɗin, dan haka Leesharh rayuwarta yana cikin gagarumin haɗari, tabbas idan ta yi sanadiyar mutuwar Ramish kamar yadda suka tsara, to su ba zasu fitar da ita daga gidan Abu Abdussalam ba, a nan zasu tona mata asiri su Bilal su ji da ita, su kuwa kunga a tunaninsu dama bata san face ɗinsu ba bare idan suka tona mata asiri ita ma ta ce zata tona masu. Gaskiya akwai gagarumin cakwakiya zallarta, dan kuwa Leesharh tana tsaka mai wuya ne, saboda wannan aiki da aka bata jiga jigai manyan kai a ƙasar ne suka ƙaddamar da shi........ Ni dai fatana a nan shi ne kada Leesharh ta sake ta kunna wayarta, dan dole ta nan zasu sameta, idan bata kunna ba ai shikenan, Allah yasa kamar yadda ta kashe wayar ta manta da ita shikenan a tafi a hakan kawai mugayen mutane kawai, zasu zalinci marainiyar Allah!. Yau ta kama Friday sai murna Sharifat take yi idan aka sauko masallacin sallar jumma'a Abbie ya aminta za'a kaita gidan King Badeen ta wuni sai dare a dawo da ita, ba yadda bata yi ba a kan Leesharh ta zo su je, amma ina ta ce wlh ba zata je ba, kuma tun farko Sharifat ɗin ce ta ja ta ce ba zata je ba, dan tana zaune a tsakiyar gado daga ita sai kayan barci, basu jima da tashi daga barci ba, Sharifat ta tafi gaishe da Abbie, a nan ta tambayesa zata je gidan kakan nasu, ya ce idan an sauƙo daga jumma'a za'a kaita, shi ne ta shigo room ɗinsu da gudu tana murna ta ce. "Leesharh ki shirya Abbie ya yarda za'a kaimu gidansu abokan faɗarki wato su Omaid sarakan zuciya". Ai daga jin sunan su Omaid ta ce wlh har ta mutu ba zata je wannan gida ba, sai godiya ga Allah dama take yi da Allah yasa ba'a gidan nan suke da zama ba, sun tafi nasu gidan, kawai rana tsaka Sharifat ta wani ce mata tazo su je gidansu? A kan wani dalili? Ai ba wannan magana, shi ne ta ce ba zata je ba. Magiya sosai Sharifat ɗin ta rinƙa yi mata tana gaya mata ai basa nan suna school, ina ai taki yarda, ta ce wlh ba wannan zance. Daga karshe dai Sharifat ta haƙura ta shirya ita kaɗai. Gidan Abu Abdussalam a manne yake da katafaren masallacinsa da ya gina a waje, a nan suke yin sallar jumma'a, amma fa saboda girman gidan sai sun shiga mota daga cikin gida izuwa mallacin. Haka suka shirya, su Sharifat sun yi kyau a cikin black abayn da suka sanya, sunyi rolling mayafan abayan a kansu, kayan ya fi karɓar Sharifat sosai, saboda ita farace tas, Leesharh kuma kunga ai chocolate ce, kalar fatanta ya ɗan saje da kayan, sai bata wani haska sosai can ba. Ga shi suna son saka kaya iri ɗaya, Yah Rizwan ne kafin ya tafi Tunisia suka je ya saya masu kayayyaki komai iri ɗaya, shiyasa suke saka kaya iri ɗaya yanzu. Abbie yana jin daɗin ganinsu a shiga iri ɗayan kenan, idan ya ga Leesharh na murmushi har wani sanyi yake ji tana ratsa ransa, ya rasa dalilin hakan, amma ya danganta hakan da cewa, dan yana jin daɗi ya sanya marayun Allah farinciki ne, bai san abin ya wuci haka ba, tabbas yana matuƙar jin sanyi a ransa idan ya ganta, Hakan na matuƙar ƙonawa Ummie rai, sanadiyyar haka har shaiɗan ya samu matsuguni a cikin zuciyarta in da yake saƙa mata cewa tabbas Abbie son Leesharh da aure yake yi, idan kuma Ummie ta yi sake to nan ba da jimawa ba zata ji diran kishi ƴar cikinta a cikin gidan, wannan dalilin yasa ta kara tsanar Leesharh ɗin fiye da tunaninku.......... Tashin hankali, tab lallai gidan Abu Abdussalam zai kama da boma bomai ma kuwa, jama'a kun ji wata lukutar masifar da Ummie take tunani? Tana son tasa su Bilal su yi wa karnikansu kilishi da namar jikin Leesharh, ai idan suka ji Abbie zai kara aure ko da babbar mace ma zai aura akwai yaki ba kaɗan ba bare Leesharh da Sharifat ma ta fita a shekaru, lallai ummie ta zo da babban al'amari, amma kuma fa tun da ta fara tunanin hakan kila akwai kamshin gaskiya, dan fa mai ɗaki shiyasa wajen da yake yi mashi yoyo, ta san halin mijin nata in and out, lamarin abin dubawa ne. (Ni kam nace da kuwa abin zai bada citta, kash wayaga Leesharh ana buga kishi da Ummie🤔 wayaga ta ce kai Ramish zo kayi driving ɗina muje shopping 🤣 yau zan kwana cikin farinciki dan za'a samu mai saukewa ƴan gidan dukka jijida kansu na jinin sarauta, haba idan Leesharh ta aure mana Abbie da takalma zamu rinƙa shiga parlon muga uban da zai hana mu🥱 mu kaka yaro kneel down😎🤣 uhmm babu ruwa dai.) A motar Bilal Sharifat da Leesharh suka shiga dan zuwa masallacin, sai bata labarin yadda gidan king Badeen yake Sharifat take yi, tana ta kwaɗaita mata son ta ce zata bita gidan, amma ina ta ce ai koma menene a gidan ba zata je ba, ita ai bata fatan ta sake haɗuwa da su Omaid a rayuwarta. A haka suka nufi masallacin, ƴaƴan larabawa sai kallon Leesharh suke yi, dama last week ma da suka zo da ita Sharifat taga idanu a kansu kam har ta godewa Allah, tun bata magana har ta gaji ta kira securitynsu guda ɗaya ta sanar da shi cewa kallon da jama'a dake cikin masallacin nan suke yi masu ya isheta, dan haka a taka masu birki. Haka kuwa aka yi, securitys suka ja masu layi tare da daka masu warning, sai ya zamana a sake suke satar kallonsu, basu fitowa kai tsaye su kallesu bare a kamasu su sha hukunci. To wannan satin ma haka suke ta faman kallon Leesharh ɗin, tabbas ba dan komai suke kallonta ba face kyanta, gata dai chocolate color, amma kuma za'a iya cewa duk ƴan'matan dake cikin musque ɗin ta fisu kyau nesa ba kusa ba, shi ne abin yake ta basu mamaki, basu yi zaton za'a samu kyawawa a bakake fata ba, da sun ɗaukemu kamar a kanmu aka sauke muni gabaɗaya. Motocin Abu Abdussalam yana shigowa cikin masjid ɗin sai da gabaɗaya jiniya ya karaɗe ko'ina, yau Bilal bai jira Abbie ɗin nasu bane, kawai ya ɗauko su Sharifat sun yi gaba, sai yanzu su Abbie suka iso, motocin a jere sun kai guda 10, daga gida zuwa masallacin kawai, Allah sarki Ramish yau jumma'a na biyu kenan za'ayi sallah ba tare da shi ba, abin tausayi, a gaskiya masu nikaf ɗin nan bakaken mugaye ne, sun dagula mashi jini sosai da makirin maganin nan nasu, da kyar aka iya shawo kan jinin aka sarrafata, yanzu dai ikon Allah kawai ake jira, kila ya farfaɗo ko akasin haka, su Dr Raj kam dai sun gama nasu aikin. Mata kenan, mu ɗin ƴan albarka ne, kowa da abin da yake yi a cikin masallacin kafin a tada hiƙama, wasu ƴan'matan suna latsa waya a cikin masjid ɗin ma, sam ba zasu hakura ayi askar ba, ayi karatun Alkur'ani a bar wayar sai an koma gida kuma, kwana shidda a week ana tare da waya ana latsawa, amma tana ɗaya, a ranar ma ƴan awannin biyu zuwa uku kawai ake da buƙata ka ware dan samun falala da lada, amma a'a, sai dai anyi abin da ba shi ba, ya Allah ka rabu da sharrin waya ka haɗamu da alkhairinta, kasa ya kasance mune zamu moreta ba itace zata moremu ba. So wasu suna latsa waya, wasu sun haɗu suna ta hira maras amfani, wasu suna riƙe da Alqur'anin basu buɗe ba suna ta kallon mutane, kuma wlh wannan ɗabiar dayawan mata ne, haka suke yi, meyasa zaku bari sheiɗan ya hanaku samun wannan garaɓasa mai girma da daraja haka? Please mu daina bari shaiɗan yana zugamu yana hanamu aikata aikin da ya dace damu, yasa muna zuwa muna aikata aikin da bai dace da mu ba, kowani wayewan gari ki tabbata kin tuna mutuwa fiye da yadda zaki tuna rayuwa, hakance zata baki damar gina lahirarki mai kyau, Allah ka bamu dacewa. Alqur'anin mai girma Leesharh ta ɗauko daga wajen ajiye Alqur'anai, tana ƙoƙarin dawowa mazauninsu Sharifat ta nuna mata da hannu a kan ta ɗaukomata ita ma, komawa ta yi ta ɗauko. A tare suka buɗe suratul Maryam suka fara karatu, Sharifat ta yi mamaki sosai na jin yadda Leesharh ta iya karatu sosai, da kamar zata tambayeta a ina ta iya karatu nan, sai ta fasa ta ɓoye mamakinta suka cigaba da karatu har liman ya fara ƙoƙarin tada kabbara, sannan suka miƙe suka fara kikkimtsawa yin sallah. Tun daga masallaci bayan sun idar da sallah Sharifat ta ce da Abbie daga nan a wuce da ita kawai, ita ko gida ba zata koma ba, saboda murna yau an barta ta je, tana fin wata biyar haka wani lokaci bata samu daman ko leƙa waje ba idan ba school ba, shiyasa idan aka bata damar zuwa gidansu uncle Rahab ko dai gidan kakan nasu mai gabaɗaya ba ƙaramin daɗi take ji ba. Saka Bilal Abbie ya yi a kan ya kai masa ita can, sannan ya yi umarni da motocin securitys da dama su raka su. Haka kuwa aka yi Bilal ya wuce da ita, ita kuma Leesharh Abbie ya ce tazo ta shiga nasa motar. Sosai Sharifat ta ɗan yi mamaki, dan kuwa Abbie ba zaka taɓa ganin wani a cikin motarsa ba, ko ita da take ƴar cikinsa sau biyu ta taɓa binsa a cikin motarsa, yau rana tsaka kawai ya ɗauki Leesharh, abin da mamaki. Shiru ta ɗan yi shaiɗan ya fara raya mata anya babu kamshin gaskiya a zargin Abbie da Ummie take yi na yana son Leesharh da aure kuwa? Dan kuwa yana yawan lallaɓa Leesharh ɗin sosai, wani abin idan ya yi ma sai ka zaci Leesharh ɗin ce yarsa ba Sharifat ba, abin da mamaki kam. Dannewa ta yi ta shiga motar Bilal, shiru ta yi tanata saƙe saƙe har suka bar gidan, dama Ummie ta sha gaya mata tana zargin Abbiensu da soyayyar Leesharh a ransa, har ta ce mata ta daina janta a jiki, ita kuwa taki fir, ta ce ai Abbie ba zai taɓa yin haka ba, yana da ɗa mai 25 years a duniya ai ba zai ce zai ƙara aure ba, bata san a nata wautar bane hakan, dattijo mai yaro mai shekaru wajen 40 ma ya kara aure bare Abbie, nawa yake?....... Ni dai na ce akwai tashin hankali gaskiya ba kaɗan ba a gidan nan my people's, bala'in can kai jama'a!!. Ummie ma fa ta zo masallacin, dan haka tsarin gidan Abu Abdussalam yake, sai dai ita ma a nata jerin gwanon motocin ta zo, haka zalika da zata koma, bata lura yau Leesharh ta shigar mata motar miji ba, da yau anyita kuwa. Bayan sun koma gida ma a elevator ɗaya Abbie ya haura sama da tare da Leesharh ɗin, ya riƙe hannunta ɗaya da hannunsa ɗaya, ya kuma riƙe wannan sandar girman tasa da hannu ɗaya, yana dake cikin alkyabbar nan nasu na larabawa, kansa ya sha naɗi da rawani ya fita sosai. Sai kamshi haɗaɗɗe ne yake tashi a cikin elevatorn. Suna haurawa parlourn sama suka fito, Abbie ya wuce part ɗinsa yana cewa Leesharh bye bye, ita ma nata room ɗin ta shiga. Tana zuwa ta haye saman gado ta kwanta tana tunanin rayuwa, yau da Sharifat bata nan sai gabaɗaya ta ji gidan babu daɗi, hakan yasa ta miƙe ta fara tunanin me zata yi dan ya ɗebe mata kewar Sharifat kafin zuwa dare. Sai a lokacin ne tunanin wayarta ya dawo cikin kwakwalwata, dan ba abokiyar hira sai tunane tunanen banza, a haka ta je ta afka tunanin wayarta ko nace barazana ga rayuwarta. A hanzarce ta miƙe ta ɗauko wayar dan ta kunna ta gani, sai a lokacin ne ma ta tuna da abin da ya kawota gidan, babanta ya faɗo cikin ranta, nan take zuciyarta ta karaya jikinta ya yi sanyi sosai, har kerma hannayenta suke yi wajen kunna wayar tata. Yana kawo wutan screen ya ɗauke saboda babu chargi, a hanzarce ta miƙe ta koma saman sofa dake kusa da switch, chagern Sharifat ta ɗauko ta sanya wayar. Tana sawa kuma ta kunna shi, kawo wutan screen ɗin ya yi. Wayar dake saman bedside drawer ne ya fara ƙara, irin emergency phone ɗin nan ne. Da farko kamar ba zata je ta ɗauka ba, sai kuma dai ta ce tun da Sharifat bata nan bari ta je ta ɗaga ta ji wanenen? Dan tasan iya ƴan cikin gidan ne kawai suke amfanai da wayar. Hannunta na kerma alamar a tsorace take haka ta ɗauki wayar tare da karawa a kunnenta tana faɗin hello. "E lallai ya tabbata kin zama yar gida kenan, wato har kin ma iya ɗaukar call na emergency wanda ya kamata ace ƴan gida ne kawai suke picking ko? To maza ki fito main parlourn ki ɗauki abincin su Bilal ki kai masu tun da Sharifat bata nan". Sautin muryar Ummie ce ta daki dodan kunnuwarta da waɗan nan maganganu. Wani irin dukan uku uku da ta ji kirjinta ya yi ne yasa bata san lokacin da ta yi saurin ɗaura hannunta a saman saitin zuciyarta tana sauke numfashi ba. Murya a raunace ta amsa da. "Okey Ummie gani nan zuwa". Kit ta ji an katse kiran ba tare da an sake yin magana ba. Wani irin fargaba ne ya dira a ranta na tuna yanayin su Bilal, ita shiyasa ko zuwa gashesu ta duba jikin Ramish ɗin ma bata yi, ko Sharifat ta ce su je sai ta ƙaƙalo wani uzurin wanda zai sa dole Sharifat ta tafi ita kaɗai, sai ga shi yau Sharifat ɗin bata nan dan dole ta je part ɗin nasu, kai amma wannan abin bai yi mata daɗi ba sam, jikinta sai kerma yake yi ta miƙe ta nufo waje, sai kuma ta baro wayar tata a saman hannun sofa. Kai tsaye ta nufi main parlourn, Allah ma yasa bata cire kayan jikinta ba, gyalenta ma yana kanta, a shirye take. Kirjinta sai dukan uku uku yake yi har ta kai bakin kofar parlourn. Dab zata shiga ciki Ummie da Hajiya two seater suka danno kai zasu fito. Karo Leesharh ta yi da Ummie dan ita ce a gaba, wani irin baya baya ta ja tana layi. Dama kun san haushinta Ummien take ji, ai kuwa bata yi wata wata ba ta dallah mata wani irin mari wanda ya sanyata dafe ƙuncinta a hanzarce, ita ta sara me ta yi wa ƴan gidan nan kumatunta yake shan marika daga wajaje daban daban...... Abin da baku sani ba a nan shi ne, Hajiya two seater kawar Ummie ce sosai, yanzu Ummien ta kirata ne a kan tazo su yi shawara a kan zargin Abbie da take yi na yana son Leesharh, shi ne dalilin zuwarta gidan a yau. Shawarar suka yi, hajiya two seater ta bada shawarar Ummie ta ɓatar da Leesharh daga doron duniya kawai, idan ba haka ba irinsu yara ne masu mugun shiga rai, kuma idan Abbie ya aureta idanunta suka buɗe wlh Ummie bakin ciki ne zai kasheta, cewar Hajiya two seater kenan, shi ne suka tsayar da magana a kan lallai dole a san ta yadda za'ayi a fitar da Leesharh daga gidan a ɓatar da ita a shafe babinta, kun fa san larabawa da shegen iya bakin kishi, to Leesharh dai ta shiga uku, tana tsaka mai wuya! Can ga masu nikaf, nan kuma ga Ummie......... Su da basu da tabbacin Abbie sonta yake yi ko tausayinta ya ji, amma suke batun a shafeta daga doron duniya kamar su suka halicceta, kai jama'a, bakar zuciya dai ko a ina take sai ta nuna kanta!. Amma ni ina da tantanma, tantamata a nan shi ne! Idan baku manta ba Leesharh ta taɓa cewa wannan Hajiya two seater da take zuwa wajen ummie tabbas ita ce wadda ta ɗaukota daga gidan AAJ, to idan ko haka ne kunga kenan da biyu hajiya two seater ta ce Ummie ta ɓatar da Leesharh a shafe babinta, zasu jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya...... Kai jama'a mutun abin tsoro, Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu kawai, amma ta kan iya yiwuwa ba ita ɗin ba ce wancan hajiya two seater daban, dan da wuya ace mutun ɗaya ce dukka, idan mutun ɗaya ce kenan Ummie ma munafuka ce? Munafurtansu take yi? Ko yaya ake son ce mana?!!. Tabɗijam!!. Ƴan siraran hawaye ne suka fara bin ƙuncinta. Tsawar da Ummie ta daka mata a kan ta bata hanya ne yasa ta ja baya da sauri jiki na kerma. Wucewa Ummien ta yi, bata san da cewa akwai hajiya two seater a bayanta ba, dan haka tana na wucewa ta sa kai zata shige cikin parlourn, wani irin baya baya ta yi ta faɗi ƙasa saboda karo da ta sake yi da giwar mata wato hajiya two seater, wannan ai doke mutun ya faɗi ƙasa idan ya yi karo da ita, idan kun yi karo mai kyau ma sai ka ji komai ya tsaya ma, ka yi tunanin da trailer ka yi karo ba mutum ba saboda ƙiba irin nata, tsokoki ta ko'ina. Ɗan kawar da kanta hajiyar ta yi kamar wata maras gaskiya ta tsallake Leesharh ɗin ta wuce abinta. Miƙewa ta yi tana hawaye ta ƙarisa cikin parlourn tana waigen Hajiyar. Da kyar ta iya ɗaukar trayn abincin su Bilal ɗin, trayn ya yi mata girma, haka ta nufi part ɗin nasu. Tana ta jan kafafu har ta isa, fargaba kamar zai kasheta. Sanya kai cikin room ɗin ta yi, bata san cewa a saman dining table ɗinsu na parlourn part ɗin nasu zata ajiye masu ba, ita kam kai tsaye ta wuce emergency room ɗin nasu. Tana sanya kai Bilal da ya kai Sharifat gidan King Badeen ya dawo ba jimawa ya sako kai zai fita domin ya ɗebowa Dr Raj wasu allurorin da zai yi wa Ramish. Karo suka ci tray ɗin abincin ya faɗi ƙasa a kan kafarsa, gabaɗaya kayan abincin suka tarwatse, suka ɓata ko'ina jaga jaga. Cikin fushi ya cire hannu zai mareta, dai'dai lokacin ta ɗago face ɗinta dan ta ga waye ta yi karo da shi a karo na biyu kuma? Ita dai ta shiga uku kawai take faɗa a cikin zuciyarta, duk ta ruɗe har ta ji kamar fitsari na ƙoƙarin zubo mata a wando. Yana ɗago hannunsa ita kuma ta ɗago face ɗinta, cak ya tsayar da hannun nasa bai kai ga sauke mata marin ba, kallon tsab ya yi wa face ɗinta na ƴan sakani kafin nan slowly ya mayar da kallonsa ƙasa ƙan kafafun nasa, ya ga ɓarnanar da ta yi masu, ta ɓata masu waje kaca kaca, dan fa kayan abincin ya watse ta ko'ina a cikin room ɗin, kayan fruits duk sun watse. Dama already da hawayenta na marin da ta sha a wajen Ummie ta shigo cikin room ɗin, dan haka sai hawayen suka tsananta gudu a saman face ɗin nata, jikinta na kerma ta zube gwiwowinta a ƙasa ta shiga furta kalmar sorry. Dr Raj dake zaune kusa da Ramish ɗin ne ya zuba masu idanu yana kallonsu, yana jiran yaga me ɗan uwan nasa zai yi mata, dan yasan Bilal sarai ba baya ba wajen saurin ɗaukar zafi, akwai zafin rai ga shegen fushi da fusata. Abin mamaki sai bai yi mata komai ba, sai ma hannun da yasa ya ɗagota daga zubewa da ta yi a saman gwiwowin nata. Ai tsabar mamaki da kallon kwakwab Dr Raj bai san lokacin da alluran da yake riƙe da shi yana haɗawa Ramish ɗin ta cake shi a hannu ba, ya ga abin da bai taɓa zato ba. Yana ɗagota ya raɓa gefenta ya fice daga ɗakin abinsa. Ita kanta ta sha madarar mamaki kuma ta sha jinin jikinta, dan kuwa Sharifat tana yawan bata labarin zafin rai irin na Bilal da Ramish and Dr Raj, basu da saukin kai ko kaɗan, Rizwan ne dai ya fita zakka a cikinsu, yana da saukin kai da kirki sosai. Kawar da kallonsa daga kanta Dr Raj ya yi tare da ɗaukar cutton ya goge jininsa dake zuba in da ya cakawa kansa allura a wajen ganin gulma. Turus ta tsaya ta rasa me ma zata fara yi a wajen. Har Bilal ɗin ya ɗauko sauran alluran ya dawo tana tsaye in da ya barta, ga jiki sai kerma yake yi. Miƙawa Dr Raj alluran ya yi tare da zama a gefen Ramish ɗin ya zuba mashi idanu tamkar zai ti mashi kwallah, Allah ya gani yana kaunar ɗan uwan nan nasa fiye da kansa. Ta kai almost 30 mins a tsaye ta rasa abin yi, su kuma sai aikin gabansu suke yi ba wanda ya sake bi ta kanta, da alama ma sun manta da ita a wajen. Sai da suka gama abin da suke yi ne Bilal ya miƙe zai fita waje, zai je ya yi wanka a room ɗinsa ne. Yana juyowa suka haɗa idanu da ita, dan sai kallon shi take yi, ita dai wlh tabbas tasan ta taɓa ganinsa a wani waje, kuma tabbas bayan fitowarta daga gidan AAJ ne, hakan yasa duk in da ya yi take binsa da idanu ta kasa tuna a in ta taɓa ganin nasa. Suna haɗa idanu ya sake yi wa face ɗinta kallon tsab kamar ba lafiya ba, bai taɓa ɗaga idanu ya kalleta ba sai yau, ga shi kuma ya zo yana ta yi mata kallon tsab, anya kuwa lafiya?. My people's kallo me kuke tunanin BILAL yake yi mata?. "Just leave it here and go". Bilal ɗin ya faɗa mata hakan, ya yi maganar tare da nuna mata kayan abincin da yatsarsa, tamkar ba shi ya yi maganar ba, dan ba zaka yi zaton ya motsa lips ɗinsa ba, a hankali ya yi ta. Abin mamaki baya ƙarewa a duniya, wai yau Bilal ne da yi wa wata saukin kai? Anya kuwa ba wata a ƙasa? Abin da mamaki, daga kallon farko, gaskiya kamar dai zan saka ayar tambaya a nan. Ai a dubu ta juya ta fice daga ɗakin, kai tsaye ɗakinsu ta nufa, tana zuwa ta faɗa saman gado. Waya Bilal ya ciro ya kira number Ummie a kan ta turo a gyara room ɗin, sannan ta haɗa masu wani abincin tun da wannan kam ya zube. A takaice ta ce mashi me ya faru da wancan abincin da ta haɗa masu yanzu?. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce ya kifar da shi by mistake, dan haka ta haɗa masu wani. Okey ta amsa mashi da shi tare da ce mashi zata aiko Leesharh ta gyara room ɗin, ita kuma bari ta shirya masu wani abincin. A ɗan dakile ya bata amsa da Leesharh ai ba ƴar aiki bace bare ace ta zo ta yi gyara ɗaki. Daga haka ya katse kiran. Ummie ta saba da halinsu, dan haka sai ta kira phone dake cikin kitchen dan ta kira ƴar aikin da ta aminta da ita ta je ta gyara masu room ɗin, emergency room ƴan aiki suna iya shiga gyara shi, can cikin ainahin part ɗinsu ne basu shiga. Tamkar a mafarki ta fara jiyo vibrate ɗin wayarta. A razane ta miƙe zaune a tsakiyar gadon. Kai tsaye wayar ta nufa, wani irin dukan uku uku da kirjinta ya yi ne yasa sai da kanta ya sara mata. Kiran masu nikaf ne ya shigowa wayar, hakan zai tabbatar maku da lallai nemanta suke kamar hauka. Da farko zama ta yi a gefen hannun sofa taki ɗaukar kiran, amma abinku da shaiɗan suna kiranta na huku sai ta ji tana son ɗagawa ta ji me zasu ce mata. Ɗauka ta yi murya na rawa ta furta. "Assalamu alaikum". Daga ɗayan ɓangaren namiji ne ya amsa mata sallamar tata. A hanzarce ta ciro wayar daga kunnenta ta duba ta gani shin da gaske su ɗin ne? Ta saba yin magana da mace, yau kuma ta ji muryan namiji? Dole ta shiga ruɗani. "Aisha Aliyu Haidar". Namijin ya furta. Muryarta tsananta kerma ya yi a in da ta amsa mashi da na'am. "Ina son ki saurarin wannan da kyau ki ji kafin nayi magana da ke". Kai ta gyaɗa mashi alamar to tamkar tana a gabansa. "Innalilahi wa inna ilahir rajiun, bayin Allah dan girman Allah me na yi maku? Su waye ku? Kada ku kasheni, wlh ina da yarinya, kuma ni kaɗai ne gatanta, da ni kaɗai ta dogara, ku dubi girman Allah ku tausayawa maraicinta, wlh idan ma kuɗi kuke so a wajen mu wlh bamu da shi, mu talakawa ne! Dan Allah kada ku yanke mun.........." Kit ya katse voice record ɗin da suka kunna mata ɗin, wannan shi ne maganar dake fita daga cikin voice ɗin. Da larabci shi ma na cikin voice ɗin ya yi maganarsa. Ai a wani irin haukace ta miƙe tsaye, ko mutuwa zata yi ta dawo ba zata taɓa manta voice ɗin babanta ba, tabbas shi ne, wasu irin hawaye tamkar hanyar ruwa ne ya buɗe suka fara gudu tsere a saman fuskarka, da yake bata san voice record suka kunna mata ba, ta yi zaton baban nata ne a wajen, hakan yasa cikin ɗaga murya tana kuka ta fara ambatar. "Baba bazaka mutu ba, tabbas zan yi abin da suke so dan su sakeka, na shiga uku!........." Tsawar da mutumin ya daka mata ne yasa ta haɗiye kukan nata ba dan taso ba, tsit ta nutsu tana zare idanu. "Ki saurareni da kyau ki ji abin da zan ce maki, mu ba ke ko babanki muke da buƙatar kashewa ba, Ramish muke da buƙata, ki bamu haɗin kai mu same shi sai mu kuma mu baki babanki ku tafi duk in da zaku je". Cewar mutumin, da kausasshiyar murya tamkar na ƴan shaye shaye ya yi maganar. Tsabar zufa dake tsastsafo mata har face ɗinta ya jiƙe sharkaf, ga kuka, majina haɗi da yawu dukka, ta sanya hannunta ta toshe bakinta dan ma kada sautin kukanta ya fita wani ya jiyota. Sai haɗe word's take yi, murya a sarke ga kuka ta ce. "Wai me zaku yi wa Ramish ɗin? Meyasa sai ni kawai zan yi maku aikin? Ku nemi wata mana! Me nayi maku da kuke azabtar da ni ta hakan?". Tana kai karshen maganar ta zube ƙasa a saman gwiwowinta tare da kifa kanta a saman sofa ta saki wani irin kuka mai azabbabben ciwo da kuna. Kai tsaye ya ce mata. "Fasa kirjin Ramish muke son yi mu tsinko zuciyarsa, mu cinyeta a ɗanyarta, batun aiki kuma ke muka ga damar sanyawa, ki yi ko kuma mu shafe babinki a doran duniya!!". Cikin fushi ya yi maganar yana ɗaga murya, da alama ransa ya yi mugun ɓaci sosai da jin kalamansa. Kamar zata yi hauka, cikin wata iriyar murya da bata fita sosai ta furta. "Ni na yarda ku kasheni kawai, ku yi wa girman Allah ku kasheni, dan hakan sai ya fi mun sauki a kan in tallafa maku wajen kashe bawan Allah da bai ji ba bai gani ba, ba zan iya yin wannan aikin ba, wlh na yarda ni ku kashe ni, amma ku sake mun babana ya koma gida, ku dubi girman Allah ku tausaya mun". Wani irin shu'umin dariya mutumin ya saki mai sautin da ya ratsa dodan kunnenta da kyau, hakan yaja ta ɗan sassautan kukan da take yi tana sauraron sheɗanin dariyar nasa. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya dakata cak, cikin wani irin shu'umin murya ya furta. "Ƴan'matan ki tabbata wannan shi ne jin sautin muryar babanki na karshe kenan a duniya, dan kuwa Aliyu Haidar zai fuskanci ukubata yanzun nan, daga yau ya fara fuskantar masifa da bala'i kenan har izuwa ranar da zai mutu, ki sani kullum sai na cire mashi wani abu daga jikinsa, kullum zan yanki wani abin daga jikinsa in jefawa karnikana su cinye, a haka zan kashe shi, adadin join da suke jikinsa adadin rayuwar da zai yi cikin azaba da jin ciwon duk in da nake yanke mashi babu magani har ya mutu kenan.........." Yana kai karshen maganar kit ya katse kiran. A zabure ta miƙe tsaye, cikin ɗaga murya ta fara furta. "Dan girman Allah kada kayi haka, na amince zan yi duk abin da kuka ce, wlh na yi alkawari kawai ku bani umarni". Tana magana tana kewaye ɗakin ta ɗaura hannu ɗaya a kai kamar mahaukaciya. Duk wanda ya ganta a wannan hali sai ya zubar mata da kwallah Jin ba'a yi magana bane yasa ta ciro wayar daga kunnenta. Ganin sun katse kiran ne yasa ta furta. "Lahhh shikenan sun katse wayyo babana na shiga uku na". Kamar fa ta zare. Ta kai karshen maganar tare da sakin wayar ya faɗi ƙasa ya gangara ƙasan sofar dake wajen, ihun sunan baban nata ta fara yi tare da cire gyalen da yake a kanta ta yi jifa da shi gefe, tamkar wata zararriya haka ta watsa gashin kanta, kai tsaye ta nufi jikin bangon ɗakin, buga kanta da karfi karfi ta fara yi tana kiran sunan baban nata. A hankali jini ya fara bulbula daga gaban goshinta, sai bugawa take yi da karfi karfi tana kiran sunansa, sosai jinin ya ɓalle daga wajen, da karfi yake zuba kafin wani lokaci ta zube ƙasa bata numfashi................... Tab a gaskiya Leesharh kina cikin wani hali, kina tsaka mai wuya, ke baki ma san koda kin taimaka masu hakansu ya cinma ruwa suka cinwa burin nasu ba barin ki ke da baban naki zasu yi ba, wannan wace iriyar masifa ce? Fatan mu dai Allah ya kuɓutar da ke daga sharrinsu. ______________________🔥🤍 GIDANSU KHADIJAH. A hankali wani sautin murya ya fara yi mata yawo a cikin dodan kunnenta, wani irin jiri take gani daga kwance. Bayan sallar asuba ne, sun yi sallar sun idar, Zainab ta yi ƙoƙarin tambayarta me ya sameta daren jiya ta rinƙa amai? Sai dai Khadeejerh bata bata damar hakan na, ta ɗaure fuska ta haye gado ta kwanta, taki sakewa bare Zee ɗin ta kusanceta har ta kawo mata wani maganar na daban. Ganin haka yasa Zee ɗin ta miƙe ta haye gadon ita ma, haka suka kwnata shiru. Kafin wani ɗan lokaci barci ya kwashe Zee. Ita kuwa Khadeejerh shiru ta yi tana tunanin. A hankali wani sautin muryar ya fara dokan dodon kunnuwanta, datse idanunta gam ta yi tare da fara tunani yadda mai wannan murya ta cutar mata da rayuwarta, a hankali sautin yake tashi a cikin kunnuwanta in da take faɗin. "Dr ka tabbatar da cewa wannan injection ɗin zai cire mata cikin nan da yake jikinta? Dan fa na bata kwayoyi kala kala har bleeding ta yi, amma cikin yaki fita, bana son kowa ya san da wannan maganar ne"........ Ya ilahi ya lillahi wasu irin zafafan hawaye ne suka fara bin ƙuncinta. Waro idanunta waje ta yi tare da miƙewa ta nufi toilet. Tana shiga ta datse kofar da key, a saman gefen jacuzzi ta zauna tare da kifa kanta da jikin bango, kuka ta fara rerawa tare da toshe bakinta da hannu ɗaya, wani irin raɗaɗin azaba da zuciyarta take yi mata tamkar ta kashe kanta take ji........ Innalilahi wa inna ilahir rajiun, my people's me yake faruwa da Khadijan kenan? Hasbunallah wani'imal wakil!!. Ta sha kuka tun da daɗin rai har ta fara jin numfashinta na fita sama sama tamkar zata sume, jin hakan yasa ta daure ta miƙe daga wajen, hannunta da ta toshe bakinta da shi ne ta ciro ta fara goge hawayen da suke ta ƴar tsare a kumatunta. Gaban wash hand base ta nufa, kunna ruwan ta yi ta sanya hannunta dukka biyu ta taro ta fara wanke face ɗinta. Idanunta sun yi jajir gwanin ban tausayi, bayan ta gama wanke face ɗin nata, dafa jikin base ɗin da hannu ɗaya ta yi, ta sanya ɗayan hannu nata kuma ta dafe cikinta dai'dai saitin mararta. A hankali ta motsa bakinta wajen furta. "Allah shi kaɗai ne zai iya saka mun, In Sha Allah ba zan taɓa zubar da cikin nan ba, sai ya zo duniya, kuma Allah sai ya saka mashi shi ma"............. Tab zance dai ya tabbata, Khadeejerh da ciki? To cikin waye? Waye kuma take cewa Allah zai saka mata abin da ta yi mata? Da alama macece ta cutar da ita! To wacece? Akwai matsala babba kuwa! Innalilahi. Ta jima a tsaye a wajen tana surutai kafin ta lallaɓa ta dawo cikin ɗakin nasu, har lokacin Zee tana barci bata motsa ba, a gefenta ta zo ta rakuɓe ta kwanta tare da janyo bargo ta shige ciki ta ƙudundune kanta. Haka rayuwa ta cigaban masu cikin ƙunci da halin ko in kula, sun zama marasa gata karfi da ya ji, Hauwa tana rayuwarta suma suna yin nasu, maman Haidar time to time tana shiga harkarsu, Khadeejerh ta ɓoye cikinta tana renonsa, ko Zainab bata bari ta gane ba. Haidar kuwa a binciken da ƴan'sanda suka gudanar a kansa an go cewa babban mai laifi ne da ake nema dama, ashe tafiyar da ya ce sun yi na wata biyun nan fashin banki suka je suka yi, dama ana nemansu ruwa a jallo sai ga shi Allah yasa mamarsa bisa rashin sani ta miƙa shi ga hukumar, yanzu haka case ɗin an miƙa shi sama, sai ta Allah shi kam. Mamarsa ta yi kuka har ta godewa Allah, yanzu tsawon wata biyu kenan ko in da yake bata sani ba, ance manya ɓarayi ne su ɗin ba za'a bar kowa ya gansu ba har sai an gama bincike a kansu dan a san matsayin da suke, dan fa har mutane uku suka kashe a bank ɗin lokacin da suka yi fashin..... Tashin sense. Yanzu a kallah cikin Khadeejerh yana cikin wata na huɗu, ta canza sosai kamar ba ita ba, kuɗin da suka bata ma tun ranar da ta je saya masu kayan tea ta haɗu da malaminsu, tun daga lokacin ta ɓoye kuɗin a bayan gado bata sake fitarwa ba, wani lokaci haka suke wuni da yunwa ba mai basu abinci, ta mance ma tana da kuɗin, sun kira number Sadiq har sun gaji a kashe, sun kira number maman Sadiq ɗin ma a kashe, da yake basu san gidan kakan nasu a Kadunar ba sai kawai suka hakura suka cigaba da zama cikin ƙuncin rayuwar. Malamin islamiyyan nasu ya zo wajenta yafi kafa hamshin, ko sau ɗaya taki yarda su haɗu da shi, abin ma kamar ba lafiya ba yanzu sai cincirindon lafiyayyun samari masu ji da kuɗi suke yi masu a kofar gida, kowa sai ya ce ya zo neman auren Khadeejerh, ita kuwa tana can tana fama da bakin zaluncin da aka yi mata, dan ma Allah ya taimaketa cikin nata ba laulaui kuma bai da girma, hakan yasa har wata uku ba wanda ya gane. Mamarsu kuwa shiru kake ji tamkar an shuka dusa. Idan muka koma kingdom of power kuwa. ___________________🔥🌼❤️ KINGDOM OF POWER. Abubuwa ne ta ko'ina suka ɗauki zafi 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 18/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E24 Commander ransa ya ɓaci iya ɓaci, hankalinsa a matuƙar tashe na rashin ganin Hoorain, ya shiga damuwa, baya tunanin ko an cutar mashi da ɗan nasa ne, dan already ya san cutar da Hoorain a ƙanƙanin lokaci irin haka ba zai yiwu ba, da alama ya yi wa ɗan nasa kyakkyawar shaida saboda renonsa ne. Ji yake yi tamkar ya tafi nemansa, dan yana kyautata zaton akwai abu mai matuƙar muhimmanci da ta riƙesa ne, yasan halin kayansa sosai. Haka suka kacame da yaki tamkar ba za'a mutu a bar duniya ba, maza sai zubewa suke yi kamar menene, mayaƙan commander Zafar fa ba wasa ba, suna zuba jarunta sosai da sosai. Mayaƙan Queen Zarina da suka fito da nasu salon yakin ta hanyar amfani da zaratan takuba ne ya bawa commander mamaki, dama ya yi tunanin akwai abin da suka taka da yasa har suka iya karya ka'idoji da dokokin yaki suka kawo masu hari unexpect, dole da man sun taki wani abin ne, ashe kuwa hakan ne, sabon zaƙwaƙwurin commander suka samu wanda ya kwashi watanni 6 yana horar da su. Shi commander Zafar ma duk ba wannan ne ya fi ɗaga mashi hankali, yaddà aka yi suka iya keto cikin masarautar nasu har suka san lagonsu ne ya ɗaure mashi kai, yasan da cewa a dokokin yaki, a shekaru 30 zuwa 35 da ya kwashe yana shiga filin daga ya san cewa irin wannan farmaki da suka kawo masu unexpect dole sai da ƙwaƙwaran information da suka samu, dole suna da ɗan leƙen asirin a cikin kingdom ɗin wanda yake leƙan masu abin da yake faruwa, kuma duk yadda aka yi ɗan leƙen asirin nasu na jikin su commander Zafar ɗin ne sosai, dole na kusa amintacensu ne, to waye kenan?. Wannan ya fi komai ɗagawa commander hankali, dan kuwa akwai matuƙar ciwo irin wannan abin, addu'a yake yi Allah yasa ba na jikinsa wanda suka saba sosai ba ne ya ci amarsu, dan in kuwa aka samu hakan yana iya haɗiyar tafasashiyar zuciyar nan tasa ya mutu gaskiya........ Tirƙashi!!. A farkon yaƙin haƙiƙa kingdom of power bata ɗauki zafi sosai ba, suna yin yakin ne bisa bin dokokin yaki, kun san fa ko hari aka kawo maku to in dai kuna san zaman lafiya kuma kun san me kuke yi to dole ku bi dokar yaki, sai dai idan abin ya fi karfinku ne, nan ne ake iya baku duk wata dama na ɗaukar kowace irin mataki domin kare kai da kuma duniya. So a farko dai'dai wa daida suke yakin, dama jikin commander a mace yake sosai, saboda ba Hoorain, yana fafatawa yana waige waige ta ina zai ga zakin ɗansa, sun saba idan zasu yi yaki Hoorain ɗin yana gefensa ta dama, kamar wasu tagwaye haka suke gwabzawa, yau kuma babu shi ai dole hankalinsa ya tashi sosai. Shi kuwa Yah Jawad lokacin da ya fito shi da Gimbiya Chuchu neman Hoorain sai hanya ya kwace masu, saboda mayaƙan da suka kewaye masarautar sun shigo ta baya ba tare da sanin su commander ba, su suna waje suna gwabzawa basu san mayaƙan sun yi kwantan ɓauna sun shammaci sauran mayaƙansu dake cikin kingdom ɗin sun shigo ciki ba. King Zuhair kawai mayakan suka fara neman ko da suka shigo, hakan yasa sauran mayaƙan kingdom of powern da commander ya shirya su ne suka fara fafatawa da su ba tare da jiran umarnin commander ba, kacamewa da yakin da suka yi ne ya ja Yah Jawad da chuchun hanyar komawa cikin family part ya kwace masu. Lokaci da King ya fuskanci lallai an shammacesu an yi masu kwamtan ɓauna, sai ya buƙaci fitowa waje. A nan ne ya fahimci Yah Jawad bai aiwatar mashi da abin da ya sanya shi na saukar fa su Mummy underground ba, rai a ɓace ya nufi part ɗin Akkar kafin ya fita. A zazzaune ya samesu a saman sofa, cikin magana ɗaya ya tambayi mummy ina Jawad ya nufa?. Kafin mummy ta buɗe baki ta ce zata bada samsa tuni Mammiensa ta ce. "Waye ya san mashi ina ya tafi! Tun ɗazun shi muke jira". Ta yi maganar tana ɗaure fuska. Dukkansu dawo da kallonsu a kanta suka yi, dan yadda ta yi maganar kamar dama jira take yi a tambaya ta bada amsa, sannan kuma da alama ta manta waye ya yi tambayar, a tsarin Kingdom of power ba ya taɓa yiwuwa King ya yi magana da wani wani can daban ya amsa, idan hakan ta faru to fa mutun yana fuskantar hukuncin mai tsanani, na gaya maku su suna da tsari sosai, kalma ɗaya ke garesu. Ko kallon in da take King bai yi ba, ya zubawa mummy da ya tambayaya idanu alamar yana jiran amsarsa. A sanyayye ta amsa mashi da cewa. "Ya fita duba Zunaira ce, dan bata nan". Ai a dubu ɗari ya juyo da kallonsa a kan Momma dake tsaye a bayansa. Alama da idanu ya yi mata a kan abin da ya ji gaskiya ce?. Ɗan yin ƙasa da kanta ta yi cikin girmamawa ta amsa mashi da. "Nima yanzu nake jin hakan kamar yadda kaji ranka ya dade". Dawo da kallonsa a kan Akka dake zaune a gefe guda saman sofa ya yi, yana son ya yi magana sai sautin karan tashin egwa suka fara ji, hakan yasa a matsayinsa na commander mayaƙa a lokacin da mahaifinsa King Abdul Malik yake kan mulki, sannan a matsayinsa na King a yanzu ya san cewa karar makaman egwa a yaki hakan yana nuni da an rikita mayakan masarautar an kuma kusa yin galaba a kansu ne hakan yasa dole su fara fito da manya manyan makamansu dan su ceci kansu dukiyarsu, da kuma al'ummarsu, abin da ba'a taɓa yi ba a Kingdom ɗin ko da sunan wasa, a ko da yaushe suka gwabza yaki sune da nasara, to how cames yau abin ya juye?......... Bai san yau a tsananin shirya Queen Zarina ta nufesu ba, ga shi ta shammacesu ne. Ai fasa maganar ya yi, duk yadda ya kai ga kaunar Auta haka ya ja baki dan dole ya yi shiru a in da ya sanya kansa a ɗari ya nufi waje, yana tafiya cike da jarumta sosai. Ya kai dab da kofar fita room ɗin ya juyo ya kalli Momma, da yake shi da itan sai Allah kawai, da idanu ya yi mata magana alamar ta aiwatar da abin da ya sanya Yah Jawad, wato ta haɗa kan su Mummy su sauƙa kasan kenan, yasan ita kaɗai ce zata iya yin hakan, dan jaruma ce!!. Waje ya nufa yana tunanin kala kala, kansa har sara mashi take yi a kan batun Auta, duk sai ya ji jikinsa ya mutu, ba dan ƙarar egwa da suke ji bama da a kan Zunaira zai fasa fita ya tafi nemanta, amma ba yadda zai yi, dole ya kaiwa jama'arsa ɗauki dan cikar tabbacin adalin sarki!!. Haɗe kansu Momma ta yi suka nufi in da ya buƙata ɗin. A ɓangaren Chuchu da Yah Jawad kuwa, dan dole Jawad ya goyata a bayansa ya shiga faɗa dan ya ceci rayuwarsu su rayu, dan kuwa mayaƙan Zarina sun bazu a cikin kingdom ɗin ta ko'ina, so yana tafiya dan neman hanya suna shan gabansa tare da kawo mashi hari, hakan yasa dole ya fafata ya kwace takwabin hannunsu dan cetan kansa. Kuka sosai chuchu take yi mashi, bata taɓa zaton yana da taurin zuciyar iya kashe mutun ba, dan kuwa ita a mai raunin zuciya take ganinsa, bata san ba haka abin yake ba, hmmmm ba'a shiga fili bane kawai, amma ai a yaran King ba rago, dukkansu masu iya ƙare kansu ne har ma su tsayawa wasu. Tsabar fafatawa yaki har Jawad ya fita daga cikin masarautar ba tare da ya ankara ba, faɗa kawai yake........... Fatana dai Allah ya maku ikon kare kanku ku rayu!. A ɓangaren Hoorain kuwa, tamkar zai yi hauka, ga Auta a gefe tana ƙara mashi ciwon kai ta hanyar kukan da take yi mashi na cewa ya mayar da ita wajen ƴan uwanta, tana son ganin Aunty Chuchunta, tun safe basu haɗu ba, wlh ba zata kara hakura ba kawai ya mayar da ita. Da kyar ya shawo kanta ta yi shiru. Daga karshe bashi da zaɓin da ya wuce dole ya goyata su haura katanga, hakan ce kawai zata taimaka mashi, a lokacin kuma har an ci rabin yakin, ba karya a wannan karon waɗan can mayaka sun yi masu muguwar ɓarna, dama ance ba kullum ake kwana a gado ba, kullum su suke yin nasara, to yau dai sai shiru, dan kuwa ta kansu abin ya juye. Kum san ba ta yadda za'ayi ace kullum su suke nasara, ina hakan ba zai taɓa yiwuwa ba, akwai jarabawa da sauransu ai!!. "Ranki ya daɗe ki hau bayana ki riƙe ni da kyau kin ji?". Ya faɗa yana sakin hannun nata da yake riƙe da shi. "Me zaka yi idan na hau bayan naka?". Cikin muryar kuka ta yi maganar. "Hawa saman katanga zan yi mu dira ta baya tun da babu hanya". Zaro idanu waje sosai ta yi. "Hoorain ni tsoro nake ji, idan muka dira muka ji ciwo fa?........" Bata iya ƙarisa maganar ba saboda yadda ya ɗago idanu ya tsareta da kallo, ya kalleta ido cikin ido, hakan yasa dan dole ta yi shiru tana kallonsa. Ɗan kawar da kallonsa ya yi, a hankali ya ce. "Duk wanda zai yarda da ni a cikin kingdom ɗin nan ina tunanin bayan Abbona babu wanda zai kai rabinki a yarda dani, amma meyasa a nan kike ganin kamar zan gaza?". Shiru ta yi tana ƴan kame kame, hakika ta yarda da shi fiye da tunaninku, tasan shi ɗin jajirtatcene mai aiki da cikawa, amma haka kawai sai ta tsinci kanta da jin karayar zuciga a kan bin nasa su dira ta saman katanga, gani take yi kamar zata karye. "Kina tunani akwai abin da zan iya bari ya cutar dake ne?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a. "Ko kina tunanin zan iya wahalar da ke ce?". Nan ma kai ta girgiza mashi alamar a'a. Tafin hannunsa ya buɗe tare da miƙo mata. "Trust me babu abin da zai faru In Sha Allah........". Ƴan hannunta ta ɗaura a saman nasan alamar ta yarda da shi, ta yi hakan tana ɗan murmushi fuska duk hawaye. A dubu ɗari cikin tafasar jini ya ɗagata sama tare da kaucewa gefe da ita, yana ɗagata kifiyar da aka harbo da nufin a harbeta ɗin ne ya wuce fiw da karfi ya caki itacen da yake bayansu. A dubu ya juyo yana kallon kifiyar kafin ya dawo da kallonsa a kan bujumin mayakin da yake tsaye a can ɗan nesa da su. Tamkar a mafarki Hoorain ɗin ya hangosa lokacin da ya ja kifiyarsa ya saita Zunairan zai harbeta, hakan yasa bai san lokacin da ya ɗagata sama suka kauce ba!!. Kafin su yi wani yunkuri mayaka ne suke tururuwar haurowa saman katangar wajen suka fara dirowa cikin gonar. Wani irin ɗaure fuska sosai ya yi, sauketa ƙasa ya yi, jikinsa har wani tsuma yake yi, ransa idan ya yi dubu ya ɓaci, dan kuwa tun da yaga mayaƙan har cikin gonar nan hakan na bashi tabbacin an cisu da yaki kenan? Abin ya yi bala'in ɗaga mashi hankali, tunaninsa ɗaya ina Abbonsa da ya yi saken hakan ta faru?. Kewaye shi mayankan suka yi, a kallah sun kai su 20, gasu bujumaye da su, sun horo iya horuwa, tamkar wasu dodanni masu cin ɗanyar namar ɗan adam, sam basu da kyan gani, suna da muni sosai. Tamkar ba zaƙaƙuran dodannin mayaka ne suka kewayesu ba, sam babu alamar tsoro a idanunsa, sai ma tafasa da jikin jikinsa yake yi mashi, jikinsa na tsuma, burinsa kawai su zo ya sauke zafin da zuciyarsa take yi mashi a kansu, dan shi gani ma yake waɗan nan ai ƙananan kwari ne, matsalarsa ɗaya Autace, ita ce zata iya sanyawa a ci nasara a kansa, da dai zata tsaya shiru a gefensa shi kuma zai tsaya mata da izinin Allah zai ceceta. Gadan gadan mayakan suka tunkaresa, bayansa ya mayar da Auta tare da ce mata kada ta matsa daga in da take kome zai faru, sannan ta dubi girman Allah kada ta yi mashi kuka. Ina tuni jikinta ya fara kerman tsoro, hawaye ta fara yi tun ma bai gama cewa kada ta yi kuka ba, tuni face ɗinta ya wanke da hawaye, haƙiƙa ta yi matukar tsorata da ganin waɗan nan dodannin, zufar tsoro ta fara haɗawa. Bashi da mafitar da ya wuce ya kawar da kai kawai, hakan kuwa ya yi ya kawar da kansa yana ƙoƙarin ciro takwabinsa, dan waɗan nan dodannin ba zasu saurara mashi ba, hakan shi ma ba zai saurara masu ba. Riƙo hannunsa da yake ƙoƙarin zaro takwabinsa dake manne a ƙugunsa ta yi tare da sanya mashi kuka tana faɗin tsoro take ji, dan Allah ya mayar da ita cikin gida, waɗan nan mutanen abin tsoro ne sosai........... Bata idasa maganganun nata ba ɗaya daga cikin mayakan da suka iso ne yasa kafa ya take Hoorain ɗin a dai'dai shouldersa sai da ya tafi luuuuu ya kifa a ƙasa. A wani irin ɗari ya ɗago kansa tare da buga ƙasa da hannunsa ɗaya kafin ya miƙe tsaye a kan ƙafafunsa. Nan take ransa ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci yake yi, zuciya na tafasa, har wani tashi tsikar jikinsa yake. Duk da bata taɓa ganin face ɗinsa a zahiri ba, bata san yana murmushi ko baya yi ba, bata san ya yake ba, amma a wannan lokacin sai da ya yi mugun bata tsoro, dan kuwa har idanunsa sai da suka yi wani irin sauyawa lokaci guda, jikinsa nan gabaɗaya wani irin kerma yake yi saboda ɓacin rai, ya zama tamkar zakin gaske kamar yadda Abbonsa yake kiransa, ashe zakin ne da gaske. Zaro takwabin nasa ya yi, sabuwa dal da ita, tsabar kyallin da take yi har mutun ya kan iya kallon kansa a jikinta, gata da kaifin bala'i. Cikin nuna tsantsar jarumta ya nufosu, a dai'dai lokacin mayakin da ya taka shi ɗin ya sanya hannu zai kama Autar. Ai kuwa a tsananin fusace yana zuwa ya datse mashi hannun nasa daga saman wajen shoulder ɗinsa, pit hannun ta fita daga jikinsa, wage baki ya yi da wani irin katuwar murya ya kurma kururuwa mai saurin gaske, ga muryar nasa ƙato babu daɗin ji ko kaɗan, sautinsa mai doɗe sautin ji. Haba ai a dubu sauran suka afka mashi da faɗa, fafatawa suka fara yi babu kama hannun yaro, sai ƙoƙarin kashe shi suke yi ko su kama shi, sai dai ya fisu sanin dabarun yaki, da alama su horon kawai aka basu ba'a koya masu dabarun yakin ba, gina masu jiki da horo kawai aka yi dan su razana zuƙatan mutane a gani da ido, sai dai ko a gani da idon ma basu razana zaki Hoorain ba kam, sai ma haushi da suka bashi suka sa ya ji tamkar zai haɗiyi zuciya saboda bakin ciki......... Auta kam ta gama tsorata a in da ta kame kam waje guda ta kasa motsawa, sai ruwan hawaye dake tsere a saman face ɗinta, tamkar wadda ta yi tsumar tsaye. After some hours Idan muka koma wajen su commander Zafar kuwa, haƙiƙa sun jigata sosai, sun wahala, commander ma baka iya ganesa, saboda jinin da ya wanke mashi jiki daga sama har ƙasa, fuskar nan tasa jinin jama'a ne kala kala da ya yi ta datsewa wuya, an kashe masu mayaka a kallah zasu kai 100, sannan wasu sun jigata sosai an rautasu. Raga irin na kama zakin nan suka jefawa commander suka kama shi, dan kuwa sun kasa kama shi da hannu, shi ne kuma har yanzu yake da kuzari sosai a cikin mayaƙan, sannan shi ya tsaya tsayin daka a bakin gate na farko na kingdom ɗin ya hana kowa wucewa, shiyasa suke son kama shi dan su sami hanyar wucewa ciki su haɗu da sauran ƴan uwansu da suke ciki su ƙarisa kashe kowa a tunaninsu. Commander ba zai kamun masu da hannu ba, dan shi ɗin bujumin zaki ne a cikin zakuna, namijin gaske ne. Ko da suka kama shi mayaƙa shidda ne suka riƙosa, sannan mayaƙa biyu suka cire mashi ragar da suka sanya suka kama shi ɗin. Ƙoƙarin azabtar da shi su kashesa suka fara yi, bawan Allah ya jigata ya wahala. Wani warriors maras imani ne ya ciro takwabinsa zai datsewa commandern kai. Yana ƙarisawa ya ɗaga takobin kenan tamkar daga sama suka ga an fille mashi wuya. Yana datse mashi wuyar kuma dokin da Hoorain ɗin yake kai ta ɗaga kafafunta sama tare da yin haniniya da karfin gaske........ Tab ta ina Hoorain ya bi ya fito har yazo cetan babansa?. Kafin sauran warriors dake riƙa da commandern su yi wani yunkuri tuni Hoorain ɗin ya datsewa uku daga cikinsu kai, cikin zafa ya diro ƙasa daga saman dokin nasa, fafatawa suka fara yi da su, duk ya kashe banza, sannan ya rungumi Abbon nasa yana mai bashi hakuri. Uban tulin mayakan da suke bayansa Abbon yake gani. Kasa iya hakura ya yi har sai da ya ce. "Hoorain waɗan nan warriors ɗin fa? Kai ka jagorancesu kuka fito ne?". A takaice ya ce. "Abbo ba lokacin yin magana bane a yanzu". Ya kai karshen maganar tare da juyo da kallonsa a kan mayakan da ya fito tare dasu daga cikin kingdom ɗin, fafata yaki suka yi, ya gwabza da mayakan da suka yi masu kwantan ɓauna suka shiga cikin, da ya shigo cikin kingdom ɗin bayan ya fito daga cikin gonar ne, da yaga abin da yake faruwa na galaba a kansu da ake ƙoƙari yi, ransa idan ya kai dubu saba'in to ya ɓaci a lokacin, shi ne ya ɗaga murya a in da ya fara yi wa mayaƙansu faɗa a kan ta ya za'ayi su bar hakan ya faru? Daga nan ya ƙara masu kwarin gwiwa a in da suka ji sabon jarunta ya diro masu, suka ji jinin jikinsu na tafarfasa tamkar an ɗaura dalma a saman wuta, hakan yasa suka ji wani irin karfi ya zo masu, gadan gadan suka miƙe suka tunkari mayaƙan, Allah ya basu nasara suka cinmasu, kisan walaƙanci suka rinƙa yi masu bisa umarnin Hoorain ɗin, a tare aka gwabza da shi, kafin wani lokaci sai ga mayakan suna gudu suna ihu ancisu da yaki, kaf suka bisu suka kashe shegu, shi ne Hoorain ɗin ya yi masu umarni a kan su fito waje su taya su comments. Ko da suka fito da yanayin buɗaɗɗiyar jikin Abbon nasa ya iya ganesa, ba dan haka ba da ba zai ganesa ba, dan na gaya maku jini ya wanke ko'ina na jikinsa, baka iya ganesa, shi kansa Hoorain ɗin jini ne ta ko'ina a jikinsa, ya yi wanka har face ɗinsa dukka, ya gwabza ba kaɗan ba, amma har yanzu jininsa a tafashe yake, ji yake yi tamkar yanzu zasu fara yakin ma, tsabar taurin zuciyar irin nasa sam bai ji kamar ma ya fara yakin ba, sai tsuma jikinsa yake yi, jarumin jarumai ba!!. Haƙiƙa commander ya ji matuƙar daɗin ganin ɗan nasa, rungumesa ya yi tamkar zai mayar da shi cikin cikinsa, wani irin annashuwa na musamman ne ya bayyana a saman face ɗinsa, haka suka cigaba da gwabza yaki a tare kamar wasu yaya da kani. Cikin ikon Allah, Allah ya basu nasara suka kashe mayaƙa da dama, sauran da suka ga abin ya juyo ta kansu ne sai suka fara artawa a guje, da gudun gaske warrios na kingdom of power suka rakasu. Hoorain ya kama babansa suka nufi ciki, mayakan da suka saura a cikin kingdom ɗin ne suka firfito domin kwasan waɗan da suka jigata izuwa ciki........... To fah a nan ne kuma matsalar take, ina Yah Jawad da chuchu? Ina King Zuhair da ya fito domin jama'arsa? Ina Auta? Hoorain ta yaya ya iya fitowa daga cikin gonar har ya zo ya taimakawa mahaifinsa? Wacece Queen Zarina?. Amsoshinku suna cikin alƙalamina, mu dai je zuwa. ______________________ 🔥🔥🔥 ----------------------------------🔥🔥🔥 ______________________✍️🔥🔥 DARK WORLD🔥💘 Ko da Ronnie ya je ɗaukarta Black Tiger ya hana shi, bai ɓata rai ba ya dawo wajen rawar tasu. A daren ranar dai sun cashe iya cashewarsu, anci an sha, anyi rawa sosai, masu buguwa sun bugu matuƙa, abin dai ba'a magana. Sai around karfe ɗaya da rabi na dare kowa ya watse, room ɗinsa Ronnie ya nufa. Wanka ya je ya tsala tare da shiri cikin kayan barcinsa masu tsada, riga mai kajeran hannu ne sai dogon wando black color, saboda hasken fatarsa sai ya yi wa kayan kyau matuƙa, sai zuba haɗaɗɗen kamshi yake yi, handout ɗinsa ya kwasa tare da pen and phone ɗinsa mai shegiyar tsada ya nufi waje. Babu kowa a parlour, Floris ma ta yi barci. Dining room ya nufa, abinci ya ɗeba daidai yadda yake ganin zai ishesu, da kansa ya zuba abincin ma tare da ɗauka ya fito. Kai tsaye ɗakin Sweetie ya nufa, fuskarsa sai kyalli take yi alamar yana cikin annashuwa. Tana zaune a tsakiyar gado, sam babu alamar barci a tattare da ita, tana dai zaune shiru ta buga uban tagumi, da alama tunani take yi, ga kuma tarin damuwa a saman face ɗinta!. Turo kofar ya yi tare da shigowa. Su fa da alama basu san cewa dare mahutar bawa bane, dan wani lokaci sai su kai asuba suna party abinsu, kamar wasu ƴaƴan aljanu basa barci. Ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da fara binsa da kallo, ya yi matuƙar yi mata kyau sosai. Ita tana ganin shi ne karshen haɗuwa a kyau tsabta da komai, shi ma kuma yana ganin itace karshen haɗuwa, magana ta gaskiya shi Ronnie kyanta ne yake ruɗarsa, bai taɓa yin soyayya bama, bai ma santa ba, shi dai duk macen da ta burgeshi sai ya sanya a ɗauko mashi ita ya kawota cikin empeir ɗin su yi rayuwa a tare, misali kamar Floris kenan, so a zuciyarsa babu banbancin a tsakanin Floris da Sweetie face kyanta, tsantsar kyan Sweetien kawai ya ja sa har yasa ya fara bawa ta hankalinsa da komai da komai nasa fiye da Floris, idan har akwai wani abin dan gane da ita ma a zuciyarsa to bai wuce sha'awar surar jikinta haɗe da kyanta ba, sai kuma batun Spender, bayan wannan babu komai. And one thing about him, shi fa bai taɓa yin zina ba, amma su master Devil suna yi, kun san waje idan ba addini ba abin da ba zaku samu a wajen ba, to bai taɓa yin zina ba gaskiya, shi dai yana son ganin ƴan'matan kyawawan fararen tattabaru a kusa da shi, ya yi ta rungumarsu yana gaya masu kalamai masu daɗi suna murmushi yana ɗaukarsu hoto, shi ne kawai buƙatarsa, amma ko da sunan wasa bai taɓa kwatanta zina ba, haka zalika ko kiss bai taɓa yi wa mace ba, a kyaleshi dai idan ta yi mashi kyau ya bata sumbata, yana son yawo da kyawawan mata a gefensa, shiyasa zaku gansa tare da Floris and Delisha kullum, dan kyawawane suma, yanzu kuma ya samu Sweetie da ta ninnikasu a kyau, da alama ya fara mancewa da su, ba wanda yake gani yanzu sai Sweetie............. Ni kam nace Allah ya kamaka yasa sonta na gaskiya ya shigeka in ga ta tsiya, yaro sai iyashege kala kala, kawai kai ka tattaro kyawawan ƴaƴan mutane ka tarasu a gefenka dan ka yi ta kallonsu kawai? Wlh ana tsiya a Dark world, Ronnie ɗan duniya ne, wato shi baya son munana sai kyawawa, justice for kyan Sweetie!!. A gaskiya yana kaunar kyau ne sosai!!. Sai ka rasa ganewa guy ɗin nan, komai nashi sai shi kaɗai, shi kaɗai yasan me a cikin ƙarƙashin zuciyarsa. A gefen bed ɗin ya zauna tare da ɗaura kayan abincin a saman side drawers. Cool murmushi ya sakar mata kafin ya ce. "What are you thinking queen of beauty?". Ƙara ruɗewa ta yi da ya yi murmushi, dan kuwa wani irin sihirtatcen kyau ne ya sake bayyana, ga dimples ɗin nan nasa masha Allah. Jin bata amsa mashi bane yasa ya ɗan kwanto da kansa kaɗan ya leƙa face ɗinta. "Ko dai barci kike yi a zaune ne?". Ajiyar zuciya ta sauke. "A'a idanuna biyu, kawai ina ganinka ne?". "Na yi maki kyau ne?". Cikin wani irin murya ya yi maganar tamkar mai jin barci, bayan kuma yanzu ya gama tikar rawansa. Kai ta gyaɗa mashi tare da cewa. "Sosai ma, kana da kyau matuƙa". Ɗan matsowa kusa da ita sosai ya yi. "Na kai ki kyau ne?". Kamar mai raɗa ya yi maganar. "Har ma ka fini". Siririn murmushi mai ƙayatar da mai kallonsa ya saki. "To taso ki bani abinci a baki, daga nan sai na gaya maki gaskiyar cewa kin fini kyau na kuma tabbatar maki da hakan". Ɗan zaro idanu ta yi. "Abinci a baki kuma? Ka zama Pretty ne? Ni gaskiya ba zan iya baka abincin a baki ba ka yi girma, kawai ka ci da kanka". Maƙe mata shoulder ɗinsa ya yi tare da shogwaɓe fuska sosai, kamar zai sa mata kuka ya ce. "Ni bana iya cin abinci har sai idan ƴan'matan kyawawa kamar kece suka bani a baki"........... Wlh Ronnie yana iyashegensa son ransa, sai kyawawan tattabaru ne zasu bashi abinci ya ci. Aikuwa sake baki ta yi tana binsa da kallom mamaki, wani irin kyau na musamman ya yi mata da ya yi shagwaɓar nan, ashe ya iya shagwaɓa kamar Pretty?....... Ni kam na ce menene ma Ronnie bai iya ba, ai wannan ku gansa ne kawai ku barsa. Sai ya tuna mata da Pretty sarkin shiririta da shagwaɓar, nan take face ɗinta ya sauya na tuna ƴar uwar tata da ta yi. "Haba mana queen of beauty, ba zaki bani a baki ba? Ko kina son na zauna da yunwa ne?". Ya faɗa a shagwaɓe har da turo baki....... "Idan fa ina jin yunwa bana iya yin komai, kuma kuka nake yi, idan na yi kuka kuma Floris ba zata barki ba, dan kin saka mata beb ɗinta kuka! Sai ta zaneki, yaya ma ba zai barki ba". Omg yadda ya yi maganar sai wanda ya gani!!. Ƙara zaro idanu ta yi, bata ki ya yi ta yin magana cikin shagwaɓar nan kada ya dai'na ba, ya tashi kanta matuƙa. Ganin sai kallonsa take yi babu ko kyaftawa kuma ta ki ta yi magana ne yasa ya kai hannu ya kyasta mata yatsunsa a saitin fuska. Lumshe idanunta ta yi tare da sake buɗe su, sai ta sakar mashi cool murmushin da ya sanya shi lumshe idanu shi ma, ta tafi da imaninsa, yatsa ya sanya mata a dimple ɗinta yana faɗin. "Like mine". Jinjina mashi kai ta yi alamar e haka kamar dimple ɗinsa. "Will you going to give me the food or zaki barni da yunwa na kwana". Kai ta fara girgizawa. "A'a i will, ba zan barka ka kwana da yunwa ba". Jan karan dogon hancinta ya yi tare da ɗauko trayn abincin ya ɗaura a saman gadon. "On bed kuma? Why not mu sauƙa ƙasa?". Cewarta. Girgiza kai ya yi ba tare da ya yi magana ba ya fara bubbuɗe abincin. Da mamaki take ganin irin abincin nasu, nama ya sanya wuƙa ya yanko mata jajir ya ji kayan haɗi sai zuba kamshi yake yi. Saitin ɗan bakinta ya kawo mata namar alamar ta buɗe baki ta karɓa. Har zata buɗi bakin sai kuma ta ce mashi. "Namar menene wannan?". Ba komai yasa ta tambaye shi ba face ɗazun ya gaya mata shi christian ne, annabi isa suke bautawa, shi bai san wani Allah ba bayan Jesus, wannan dalilin yasa ta tambayesa. A takaice ya ce mata namar ɗawisuce da na jimmina. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wanda yasa sai da ya kura mata idanu. "Lafiya kike sauƙe ajiyar zuciya haka?". "Nagodewa Ubangijinmu da yasa ba namar pig bane, shi ne yasa na sauke ajiyar zuciya". "Baki cin namar pig ɗin ne?". "Allah ya haramta kai kana ci ne?" Kai ya fara girgizawa tare da faɗin. "No am not, kai ni kwata kwata ma bana cin nama idan bana ɗawisu ba, shiyasa kika ga shi ne kawai a cikin abincin nawa". Jinjina kai ta yi alamar ta ji daɗi a ranta, daga nan ta fara buɗe baki yana bata abincin yana zuba mata hira mai daɗi. Sam bata san lokacin da ta ci abincin mai yawa ba, tun da ta zo gidan dama ban da ruwa babu abin da take sha, sai ta ɗan tsakuri abincin ta bari, to yau dai ya ɗebe mata kewa ta hanyar daɗaɗan kalamansa, sai ka rasa a ina yake koyo kalamai masu kwantar da hankali, wanda zasu sanya mutun yin abu ko bai yi niya ba. Sai da ya tabbatar ya cika mata ciki tab, sannan ya bata izinin ta bashi a baki. Ba musu ta karɓi spoon ɗin ta fara ciyar da shi. Tun da ƴan'matan nasa wato su Floris suke ciyar da shi a baki bai taɓa jin daɗin da ya ji a yanzu da ta fara bashi ba, har wani lumshe idanu yake yi idan zai karɓi abincin. Yau yawan abincin da ya ci wlh a iya saninsa bai taɓa cin abinci mai yawan shi ba, abin ya bashi mamaki. Bayan sun kammala cin abincin ne ya buɗe takardunsa da ya zo da su ya fara karatu, sun kusa fara Exams na karshe, duk tsiyar da yake yi baya wasa da karatu, dan in ya sauka daga kan turbar first class ya yi alkawarin ba zai yafewa kansa ba, shiyasa yake warewa karatun lokacinsa baya haɗa shi da komai saboda sanin mahimmancinsa. Shiru ta zuba mashi idanu tana ta kallonsa har misalin karfe 3 na dare, a nan ne barci ɓarawo ya fara ɗebarta, gyangyaɗi ta fara yi ta zo zata kifa a kan gadon kamar wani walkiya ya tareta da hannunsa, tun ɗazun rubutu yake yi tamkar baya kallonta, ashe dai yana kallon duk abin da take yi, sai da ta zo zata faɗi ne ya nuna yes yana kallonta. Tarota ya yi a in da ya kwantar da ita a saman laps ɗinsa ya cigaba da abin da yake yi. Sai misalin karfe 4:30 sannan ya kammala, a hankali ya jawo pillow ya kwantar mata da kanta tare da miƙewa da nufin ya fice, duƙawa a kanta ya yi tare da manna mata sumbata a goshi kafin ya nufi waje. Abin mamakin kuma shi ne yana fita ɗakin Black Tiger ya nufa a wannan tsohon daren, koma ace gari ya kusa wayewa, to me zai je yi a can?............... PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA. ________________________🔥🤍 JIMETA..............NIGERIA After some times. (Bayan wani lokaci) Sosai Jaish ya yi sabo da Bappa, sai dai har yau har gobe yana nan da wannan balai'n kunyar tasa, a tsawon zaman da suka yi da Bappan bai taɓa ɗago idanu ya kalli cikin idanun Bappan ba, wani irin azabbabben kunyarsa yake ji, a tare suke zuwa kiwo, yana rakasa, amma ko Bappa zai yi yaya ba zai taɓa yarda su ci abinci a tare ba, idan Mahreen ta kawo masu abinci a wajen kiwon kwanika biyu take zuwa da shi, Bappan ya zuba mashi namarsa daban ya zauna a gefe can ya ci, har yau har gobe kuma bai taɓa kwatanta ɗanɗana irin abincinsu ba, ko kallon abincin ma baya son yi, sai dai kuma a yanzu ko magana da fillanci Bappa ya yi wa su Mahreen yana iya gane me yake nufi duk da baya magana. Kun san yaran Momma fa da shegen kaifin basira, to tsab yake gane duk abin da zasu faɗa, magana ne dai shiru har yanzu baya yi, Bappan ya yi iyaka yinsa amma har yanzu Allah bai buɗe mashi bakin nasa ba. Mahnoor yanzu ta rage tsoronsa sosai, ita kuwa Nenne har yau har gobe tsoronsa take ji sosai, dan kuwa yanzu ne ma yake bawa jama'a tsoro, idan yana tsaye sai su ga ya ƙara kyau sosai, bare kuma idan ya ɗago idanu ya kalli mutun, ya ilahi sai mutun ya ji kamar ya yi ta kallonsa a sace ba tare da sun haɗa idanu ba. Har yanzu kuma idanunsa suna nan jajir da su, da alama dai akwai abin da ya ɓata mashi idanu, bappa ya yi zaton a haka idanunsa suke shiyasa bai yi ƙoƙarin nema mashi magani ba!. Mahreen kuwa iyashege da faɗa sai abin da ya cigaba, baka isa ka taɓota ka kwana lafiya ba, bare ma yanzu da ake bala'in jin tsoron gidansu saboda Jaish ɗin, ai sai iyashegen nata ya ƙara gaba da lasisinta, idan ka yi mata abu sai ta ce wlh sai ta gayawa Hammanta aljani ya zo wa mutun da daddare ya sumar da shi ko ya kashe, in takaice maku yanzu ko manya basu dukanta, Allah sarki Inna Rabi, tana ji tana gani Mahreen zata daki ƴaƴan mutane a islamiya amma saboda tsoron Hammanta aljani bata hukuntata, duk yarinyar nan Mahreen ta gama baza sunan Jaish a kauyen nasu da sunan ya ce zai ramata duk wanda ya taɓata, shi kuwa bai ma san tana yi ba, dan shi ko kallonsu ma baya son yi, saboda tsoronsa da suke nunawa a filli yana mugun ɓata mashi rai......... Mahreen fa da alama zuwan aljani Jaish gidan nan nasu gaba ya kaita, ga shi yanzu har respect ake bata a kauyen gabaɗaya dan tana da Hamma Alhaji..........🤣 Kamar kullun Bappan ya kaɗo shanayensa zasu dawo gida, dabbobin suna gaba shi da Jaish kuma suna baya, Jaish baya taɓa yarda ya jera kafaɗa da shi, dan kunyarsa da yake ji. Tun daga nesa suka hango cincirindon matasa da ƴanmata. A takaice Bappa ya ce. "Na tabbata da Mahreen a wannan wajen". Ai kuwa bai gama rufe baki ba ya hangota Mahnoor da wata ƴar budurwa ta wajen Inna Rabi sun riƙeta suna bawa wani matashin bafulatani hakuri, ita kuwa sai surfa mashifa take yi a kan wlh ba zata barshi ba. Ɗaga kafa da sauri Bappa ya yi domin ya isa garesu, ganin yana sauri yasa Jaish ma yin saurin bin bayansa. Ko da suka isa wajen Bappa ya tambayi me yake faruwa? A gefe guda Jaish ya tsaya tare da juyawa yana kallon dabbobin nasu yadda suke tafiya. Mahnoor ne ta ce. "Bappa muna tafiya ne wannan yaron Inna Rabin ya cewa Mahreen ta yi kwalliyar aljanu, shi ne ta zagesa shi kuma ya mareta". Sai ta ce ba zata barsa ba, tun ɗazun muke bata hakuri taki hakura, shi kuma ya ce mu saketa ta zo sai ya yi mata ɗan banzan duka. Bawan Allah bai san wacece Mahreen a kauyen ba, bai san tana da Hamma aljani ba, yau ya dawo daga wajen kiwo, ya tafi bayan dutse ne na tsawon shekaru da dama!. Hakuri Bappa ya fara bata tare da lallashi yana cewa tazo su tafi gida ta bar yaron, ina ai kafewa ta yi a kan ba zata zo ba sai ta rama marinta, anyi juyin duniyar nan taki, daga karshe ma ihu ta fara kurmawa tana faɗin Bappan ya kyaleta ta rama marinta. Da yake shi Jaish yana ganin yadda bappa yake fama wajen rabon faɗarta kullum, idan ba'a barta ta rama abin da aka yi mata ba faɗar bata karewa, ko an rabasu anjuma sai ta koma, dan haka sai ya juyo yana kallon Bappan. Haƙiƙa ya tausayawa dattijon nan yadda yake ta faman rarrashinta tana tirjewa. Hakan yasa ya matso in da suke tare da dallawa yaron da ya mareta ɗin mari a matsayin ya ramata dan faɗar ta mutu kawai. Haba bawan Allah ya ji hannun maza sai zubewa ƙasa ya yi, ko kallon in da yaron yake bai yi ba yasa hannu ɗaya ya ɗauki Mahreen ɗin sai saman shoulder ɗinsa ya nufi hanyar gida da ita ya baro su bappa a wajen........ Ai wani musulmin nutsuwa a jikinsa ta yi, dan tana bala'in shakkarsa. A guje matasan wajen suka watse yau aljani ya mari wani ya suma............. Nima tsabar tsorata na haɗa kayana sai gidanmu har ina jefar da camerata na ɗauko maku rahoto........ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 21/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 25 A guje matasan wajen suka watse yau aljani ya mari wani ya suma. Kan kace me zance ya baza kauye ai aljanin gidansu Mahreen ya mari yaron Inna Rabi ya suma, abin ku da kauye nan take suka canza mashi suna daga aljani zuwa maye, dama can kun san ba yarda da shi suka yi ba, to ga abu kuma ya zo ya faru, kun san kauye da iya champa abu, take suka champa shi (champi), sai dai kuma duk kauyen babu mai iya tinkarar Jaish ɗin ya ce mashi ya bar garin ko wani abin makamancin hakan, dan tsoronsa suke ji, sai gangami ake yi ana kaiwa Arɗo complain a kan shi a matsayinsa na Arɗon kauyen ya ɗaukar masu mataki a kan Jaish, su sun kasa. Shi kuwa Jaish ɗin bai sauke Mahreen a ko'ina ba sai a tsakar gidan nasu, sai dai kafin ya sauketa sai da ta taɓa mashi gashin kansa, dan ta jima ita da Mahnoor suna gulmar arab hairn nan nasa, suka ce ba gashi bane, to yau da ya ɗauketa sai da ta taɓa ta tabbatar gashi ne, kyallin da gashin yake yi ga shi bakin kirin da shi ne yasa suke ganin kamar ba gashi irin na mutane bane da shi, Mahreen kam da hankali ya yi mata yawa ma har da cewa ai roba ce ba gashi ba, Mahnoor kuwa ta ce a'a gashi ne amma ba irin na mutane ba, na aljanu ne, to yau dai ta taɓa ta ji bana aljanu bane na mutane ne. Ɗakin bappa ya shige bayan ya sauƙeta, binsa da kallo ta yi har ya ƙarisa shigewa ciki, ajiyar zuciya ta sauƙe, wasa wasa fa ita Mahreen ta fara son shi, tun asali kun san dama tana sonsa, lokacin da kowa yake gudunsa ya ce aljani ne a lokacin ita da bappa kawai suke kusantarsa, kunga kuwa idan tace tana sonsa ma bata yi laifi ba!. Bappa kuwa da yake dattijon arziki ne sai da ya kira matasan da suka watse ɗin ya sanyasu suka kama yaron Inna Rabin suka nufi gida da shi. Da kafafunsa kuma ya taka izuwa gidan Inna Rabin dan ya bata hakuri, idan kuka lura da yanayin bappa zaku ga shi mutun ne mai son zaman lafiya, baya son yin hayaniya da kowa, haka zalika baya son ɓatawa kowa rai, shiyasa baya ganin cewa shi babba ne yake bawa kowa hakuri, har yara matasa ya kan basu hakuri idan suna faɗa, shi bai ɗauki bada hakuri a bakin komai ba face tubali ko ace makulli na zaman lafiya. Da kyar ya iya shawo kan Inna Rabi ta yi shiru, da kuka take ta yi, dan tana tsoron Jaish ɗin ita ma. Allah da ikonsa kuwa tun marin da Jaish ɗin ya yi wa yaron sai Allah ya rabbeshi da wani irin ciwon ciki mai tsanani wanda yasa jama'ar kauyen suka kara tabbatarwa da cewa Jaish fa mayen gaske ne, hakan yasa suka fara shirya ta yadda zasu koresa daga garin, sai dai suna tsoro, Allah ya bawa yaran Momma kwarjini sosai, komai zafin da ka ɗebo da nufin ka yi masu faɗa ko ka ga ya masu sun yi maka ba dai'dai ba, to kuna haɗa ido ko kana ganinsa zaka ji ina ka kasa, duk sai ka nemi kalaman bakinka ka rasa, wasu irin su Mama gani suke yi tamkar asiri Momma ta yi wa ƴaƴan nata suka kasance a haka, bata san daga Allah bane kwarjinin nasu. Ai Nennen da ta ji wannan labari haukacewa ne kawai bata yi ba, ta ce wlh ba zata koma gidan bappa ba, dan ita bata shirya mutuwa ba, haka kawai ta je Jaish maye ya cinyeta, wlh ba zata saƙu ba, shi kansa Arɗo mahaifin nata cewa ya yi ya fara tsoron Jaish gaskiya, dole su bulbula hayakin mayu a kauyen, gobe za'ayi gayya na jama'ar kauyen dukka izuwa kofar gidan Arɗon, dan shi ne Arɗon kauyen gabaɗaya, kamar ace sarkin kauyen kenan gabaɗaya, to Arɗon ya sanya sanarwa gobe da yamma kowa ya hallara a kofar gidansa, dole za'ayi turaren mayu, duk kuma mayen da aka kama wlh kashe shi za'ayi. Yadda Arɗon ya rinƙa nanatawa bappan kwairaga a kan lallai ya tattare gabaɗaya jama'ar gidansa ya zo da su ne yasa Bappan ya fara tunanin ko dai Arɗo ma ya yarda da maganganun ƴan kauye ne da suke zancen cewa Jaish maye ne?. Da yake bappan mutun ne mai ɗan wayewa saboda tafiye tafiyen da yake yi kasashen daban daban, shiyasa bai yarda da duk abin da suke faɗa ba, dan kuwa yasan da Jaish maye ne ko wani mugun to da shi zai fara cutarwa, dan a ɗaki ɗaya suke kwana, su wuni a daji wajen kiwo tare ba abin da yake yi mashi, sai ma tallafa mashi sosai da yake yi, dan ko jiya da suna wajen kiwo bappan yana zaune a ƙarƙashin bishiya wata kunama ta zo kusa da shi ba tare da ya sani ba, saura kaɗan ta harbesa Jaish ya ganta, da hannunsa yasa ya kamata ta harbesa a hannu, bappan ya sanya mashi maganinta, to da shi mugu ne ko mayen da suke faɗa da ba zai taimakesa daga harbin kunama ba, sai dai ma ya kara mashi wasu kunamun, amma da yake su kauye sai a hankali akwai karanci wayewa ga karanci addini shiyasa. Ai Nenne dai ta koma gidan Arɗo da zama, ta ce wlh sai randa Jaish ya bar gidan zata dawo. Arɗo fa mutun ne mai zafi sosai, amma a wannan karon dole ya hakura ya bar Nennen a gidansa ta cigaba da zama, dan kuwa gwaggo ta hayayyako mashi da ruwan bala'i a kan ƴarta ba zata koma gidan bappa maye ya lashe mata kurwa ba, idan ana son ta koma ɗakinta dole mayen nan ya bar gidan. Yaron Inna Rabi dai tun daga aka kaisa gida cikinsa ke matsanancin ciwo tamkar ba zai rayu ba, idan cikin ta wani irin murɗa mashi har wani irin sandarewa yake yi yana miƙewa kamar ransa ta zo fita, abin gwanin ban tausayi, sai kuka Innar take yi baiwar Allah. Da daddare misalin karfe 9 suna zaune a tsakar gida da bappa da Jaish a saman tabarmar da Mahnoor ta shinfiɗa masu, abinci ta kawo masu, yau dai Jaish ya nunawa bappa alamar baya son cin nama, bappan ya ce mashi to me zai ci, ko dai zai iya cin irin abincinsu ne?. Hakika bappa ya ga ƙoƙarinsa ma na juriyar cin nama na tsawon lokaci haka da ya yi, dan ma dai bai da yawan ci ne, bai wani cin abincin rana, wata rana ma sau ɗaya yake cin abinci a rana, shiyasa namar ma bata yi saurin ginsarsa ba. Cikin harshen larabci bappa ya tambayesa me zai ci?. Shiru ya yi kansa a ƙasa, baya yarda ya kalli face ɗin bappan a lokacin da yake kallonsa, sai ya kauce, idan ya kauce kuma sai ya yi ta kallonsa yana jinjinawa kyawawan halayensa da tarin alkairansa, da zarar ya juyo da kallonsa a kansa kuma zai yi maza ya kawar da nasa kallon, abin ma wani lokaci gwanin ban dariya. Shiru ya yi bai amsa ba. A karo na biyu bappan ya sake tambayarsa me zai ci? Kai ya ɗan girgiza alamar shi ba zai ci komai ba. "A'a ban yarda ba dole ka ci wani abin, da safema fa kaki cin komai, kai haka zaka yi ta horar da kanka da yunwa?". Cewar bappa. Ƙara yin ƙasa da kansa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Miƙewa bappan ya yi yana faɗin. "Akwai wata kauye a gabanmu can su suna da shago, bari na je na duba maka ko suna da fanta da bread ne na saya maka sai ka sha". Kunsan fulani da kallon darajar bread and fanta...........🤣 (To fulani masu karanta book nan ayi hakuri amma gaskiya na faɗa, kuna daraja bread and fanta 🤣💃🤸) Miƙewa shi ma Jaish ɗin ya yi tare da nunawa bappan alamar a'a kada ya fita, shi ba zai ci komai ba, a daren nan ya tafi har wata kauye kai gaskiya a'a ya barshi kawai. "A'a ka bari na sayo maka, dan ba zan iya barinka da yunwa ba, kai bakona ne, dole na kula da kai, kamar yadda ba zan iya barin su Mahreen su kwana da yunwa ba haka kai ma ba zan iya barinka da yunwa ba, dan haka ka zauna dai bari na zo". Rike hannunsa Jaish ɗin ya yi ya shiga nuna mashi alamar a'a shi dai bai yarda ba, ya yi hakuri ya bari shi baya jin yunwa. Kuma haƙiƙa yana jin yunwar, kawai baya son wahalar da dattijon nan ne, saboda yana hidima da su sosai, ya gaji da cin nama, ga shi babu wani abincin, tunani yake yi a cikin ransa ko dan ya faranta ran bawan Allah nan bappa, ya rage masa wahala dole ya koyi cin irin abincinsu ko da fura da nono ne kawai, idan ba haka ba wahalar da bappan da yake yi ta yi yawa, kullum sati sai an yanka mashi kaji guda goma, ai abin ta yi yawa, shi bai taɓa tunanin akwai irin dattijawan arziki irin bappa na, gaskiya mutum ne mai farar zuciya sosai. Da kyar bappan ya yarda ya koma ya zauna. Mahreen and Mahnoor ne suka fito daga nasu ɗakin suka ɗauki abincinsu, a kusa da bappan suka zauna dan su ci. Sai leƙen Jaish Mahreen take yi, ga hasken wata tankar tana haska shi, ya sunkuyar da kai tamkar mai tunanin wani abin ko kuma mai ɗaukar darasin karatu. Sallamar da Hamma Faisal ya yi ne yasa suka kai kallonsu a kan kofar shigowa. Kusa da Jaish ya zauna tare da miƙa mashi hannu kamar kullum. Kin bashi hannu su gaisa Jaish ɗin ya yi, har yau har gobe bayan su bappa mugun kyamar jama'ar kauyen yake yi, baya taɓa yarda ya gaisa da kowa, dan zai yi amai, su bappan ma ba karamin fama ya sha ba wajen ƙoƙarin cire kyamarsu a ransa. Already Faisal ya saba da cewa Jaish baya yarda su yi musabaha, amma kullum yana gwada bashi hannu idan suka haɗu, dan a kullum gani yake yi tamkar zai yarda ya bashi hannun nasa su gaisa, sai dai ba wani canji, bai da ko alamar niyar gaisawa da kowa, ko bappa baya musabaha da shi sai dai ya nuna mashi alamar gaisuwa kawai idan suka tashi da safe. Faisal baya jin tsoron Jaish, dan kuwa tun da yaga bappa bai guje shi ba, kuma Jaish ɗin ma bai cutar da bappan ba sai ya share zancen mutanen kauye shi ma. Hira sosai suka fara yi tsakanin bappa da Faisal Jaish ya yi shiru kai a ƙasa yana sauraronsu, ita kuwa Mahnoor ta je ta ɗaukowa Faisal ɗin abinci, ta zo suka gaisa sannan ta ɗauki abincinsu tare da cewa Mahreen su wuce cikin ɗakinsu. Ba musu ta miƙe dan su tafi ɗin, saboda idan baku manta ba dama Mahreen ba shiri suke yi da Faisal ba, dan haka basu haɗa inuwa sam sam, shiyasa ma ta yarda ta bi Mahnoor cikin ɗaki ba dan ta so ba, saboda bata gajiya da kallon Jaish. Suna shiga cikin ɗaki Mahreen ɗin ta ce. "Adda Mahnoor kin san me?". Kai ta girgiza mata tana ƙoƙarin kawar da fitillar kwai dake wajen da suke zama su ci abincin nasu. "Allah Adda Mahnoor da Hamma aljanina ɗin nan ya ɗaukeni ɗazun sai da na taɓa gashin kansa naji, ashe ba roba bace, gashi ne mai laushi kamar namu, kawai dai dan nashi ya fi namu baki kuma kinga yana sheƙi shi ne kawai banbancin". Ɗan zaro idanu Mahnoor ɗin ta yi tare da cewa. "Haba da gaske?". Kai ta gyaɗa mata. "E da gaske, kuma gashin nasa wlh kamshi yake yi, akwai daɗin taɓawa". Harara ta wurga mata tare da cewa. "Ke Mahreen dama ai komai na Hamman daɗin taɓawa yake yi maki, haka fa kika rinƙa taɓa mashi kumatu a gidan nan har sai da kumatun nasa ta kunbura ta yi ja, to dan Allah kada idan yana barci ki je ki yi ta taɓa mashi kyakkyawan gashin kan nasa har kisa ta fara muni tana zamowa ja ko kuma ma dai yawan taɓawan naki yasa gashin duk su cire, dan Allah ki bar masa kayansa kin ji yar kanwata?". Turo bakin nan ta yi, a shagwaɓe ta ce. "Gaskiya a'a, Allah Adda Mahnoor idan dai na samu dama sai na taɓa, in yana barci zan rinƙa taɓawa, idan yana zaune da bappa ma sai na taɓa, dan in bappa yana nan ba zai yi mun komai ba, ke dan baki ji laushin gashin nasa bane shiyasa kike cewa kada na taɓa". Ta kai karshen maganar tana turɓune fuska irin na shagwaɓa. Shiru Mahnoor ta yi, dan kuwa tun da ta ce sai ta taɓa gashin nan to fa ba makawa sai ta taɓa ɗin, kome za'a ce sai ta taɓa, kai ko Jaish zai daketa sai ta taɓa, bare ma sun san ba zai dakesu ɗin ba, ai shikenan. Suna cin abincinsu suna hira gwanin birgewa, har suka kammala, sannan suka miƙe Mahreen ta tattare komai ta gyara wajen, sannan ta haye saman gado ta kwanta. Ita kuma Mahnoor sai da ta yi wanka kafin ta kwanta, saboda zafi da ake yi, kuma ita ta saba yin wankar dare kafin ta kwanta, Mahreen ce randa ya gameta ta yi wankar daren, ran da bai gameta ba kuma wankar da ta yi da rana ma ya wadatar. Amma fa duk ranar da ta yi wanka da daddare to tabbas sai ta yi kwalliyar nan nata na aljanu, ta mammaka kwalliyar sannan ta kwanta......... Ni kam na ce ai wannan kwalliyar kawai ya isa idan aljanu masu yawo tsakar dare suka zo giftawa ta ɗakin nasu suce ga ƴar uwarsu a nan a kwnace bari su ɗauketa su tafi da ita........🤣 Washegari da safe kamar yadda ta saba ta tashi da aikin gyaran gida haɗe da girki. Bayan ta gama komai tsab kamar kullum, sai ta ɗauki hijabinta ta nufi gidan Arɗo. Gaishe da su ta je ta yi a lokacin ita kuma Mahreen ta shiga wanka, dan ta ce wlh ba zata je gidan ba, dan Arɗo ya ce Jaish maye ne, dan haka tun da suka zagar mata Hamma aljaninta wlh ta raba gari da su, kowa ya yi ta kansa, Mahreen manyan ƙasa. Tana dawowa a hanya, sai bitar karatunta da Inna Rabi ta kara mata take yi, cikin nutsuwa take tafiyarta, kwatsam taga mutane a gabanta kamar wasu aljanu. Zaro idanu ta yi tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, yaran Inna Rabi guda biyu ne sai abokansu. Murya na rawa ta ce "Hamma Salisu ina kwana". Yaron Inna Rabin kenna, kanin wanda Jaish ya dallawa mari. Sandar kiwon dake saman shoulder ɗinsa ya sauke ƙasa tare da ce mata. "Yanzu ina mayen naku mai rama maku duka idan anyi maku?". Narai narai ta yi da idanu, dan tasan yaran Inna Rabin da shegen zuciya ga faɗa, saboda zafin zuciyarsu yasa wancan yaron da Jaish ɗin ya mara ya yi saurin kaiwa Mahreen duka a maganar da bata kai ta kawo ba, suna da saurin hanu wajen duka ga fushin bala'i. "Kayi hakuri Hamma Salisu". Ta faɗa kamar zata yi kuka. "Ba hakuri na ce ki bani na ai, kin ganmun nan ramawa Hammanmu abin da mayen gidanku ya yi mashi muka zo yi a kanki, sai ki kira mayen naku mu gani, ya zo ya hanamu in ya isa". Wani irin faɗuwar gaba ta ji, dan ita wlh bata son abin da zai taɓa mata lafiyar jikinta, kwana biyu Nenne bata taɓa mata lafiya ba dama, sai bin sandar hannunsa da kallo take yi, addu'a take yi Allah ya hana hannunsa ɗaga sandar nan har ya ce zai buga mata shi, ƴan hannayenta sai kerma suke yi, alamar ta tsorata, ga manyan idanun nan nata sun fara cika da kwallah. Daga ta bayansu kamar daga sama suka ji muryan wani dattijo ya ce. "Kai Salisu me kuke yi a wajen?". A hanzarce suka kai kallonsu wajen, mahaifinsu ne. A daƙile Salisun ya ce. "Bappa ba komai......". Bai ƙarisa maganar ba Mahnoor da ta ga sun juya suna kallon bappansu haba ai sai ta watsa a guje, ta samu hanya kafa me naci ban baka ba? Sai hanyar gida. Da gudu suka rufa mata baya, sai kwala ihun sunansu bappan nasu yake yi, amma ina basu tsaya ba. Gudu take yi da iya karfinta. Da karfi ta nufi kofar gidan tana ƙoƙarin banke buhun kofar gidan ta shiga Salisun ya capko hijabin jikinta da nufin ya janyota baya kada ta shiga gidan, dan su samu su daketa koda sanda uku ne su yi mata kafin su sake haɗuwa da ita a wani wajen sai su ɗauki fansa na gaske, dan sun ce wlh ba zasu barta ba ita da Mahreen, ko dare ne sai sun bi su rama abin da aka yi masu, dan a cewarsu su Mahreen ɗin ne silar da yasa mayen ya kama masu ɗan uwa......... Kenan yanzu idan Allah ya karɓi rayuwar yaron su ma fa haka zasu ce zasu kashe su Mahreen dan rashin ilimi da hankali, kai wato wani lokaci mutane masu zuciyar gado ma fa basu yi ba a rayuwa, dan irinsu basu yafiya kuma basa manta gaba wlh. Yana damko hijabinta while tana ƙoƙarin shiga cikin gidan suka ci karo da Jaish da bappa da suke ƙoƙarin fitowa, sun gama cin abincin safe zasu fita zuwa gona. Da karfin Salisu ya ja hijabinta ta yi baya, bayan da ta yin nan kuma a tunanin Jaish ɗin faɗuwa ƙasa zata yi saboda karon da suka yi, sam bai lura da su Salisun a bayanta bane, hakan yasa ya kai hannu da sauri ya riƙo hannunta. Sai da ya riƙe hannunta ne ya ji daga bayanta ana jan hijabin jikinta, sun shaƙe mata wuya kan nata ya yi sama. Hakan yasa ya riƙeta da kyau take da fitowa wajen. Subhanallah, ai suna ganin Jaish ɗin suka saketa tare da watsawa a guje suka bar wajen, ashe rashin kunya suke ji da shi, balai'n tsoron Jaish ɗin suma suke ji. Da kallo ya bisu kafin ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta, ruwan hawaye take yi saboda shake mata wuya da hijabin nata da suka yi. Sake mata hannunta ya yi tare da sa kai ya wuce gaba abinsa. Ƙarisowa wajenta bappa ya yi da sauri, tambayarta ya fara yi a kan meya haɗata da su Salisu? Ya yi maganar yana goge mata hawaye!. Bata ɓoye mashi ba ta sanar da shi duk abin da ya faru. Shiru ya ɗan yi yana tunanin wannan rikicin kuma tab, shi yasan halin mutanen nasu, tun da suka fara hakan ba barinta zasu yi ba, sai sun ɗauki wannan fansa da suke ikirari, tabbas dole ya san abin yi a kan hakan kada wannan matsala ta girma, kar ya yi sake a illata mashi ƴaƴa, hakan yasa ma ya ce yau ba zai barsu a gida su kaɗai ba, gara ya tafi da su gona, in yaso idan sun je wajen Arɗo da yamma ya gaya mashi a yiwa su Mahreen tsakani da su Salisu, dan baya son abin da zai taɓa mashi lafiyar ƴaƴansa. A takaice dai yau a tare suka wuni wajen kiwo, sai yamma suka dawo gida, yau dai basu ci abincin rana ba, saboda babu wanda zai yi girkin. Mahreen fa sai da ta taɓa gashin Jaish ɗin kamar yadda ta faɗa, yana zaune a ƙarƙashin bishiya shi da bappa ta zo ta shafa gashin nasa. Ai a ɗari ya ɗago yana kallonta, ko a jikinta ta cigaba har da murɗa mashi gashin nasa, da yake a yanzu gashin nasa yana da tsawo zuwa bayan wuyansa, kun san larabawa da gashi, sannan kuma ga shi ya kai almost 3 to 4 months a kauyen bai yi aski ba, sai gashin ta kara tsawo sosai, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa suke ce mashi aljani, dan yadda gashin nasa ya yi tsawo, sannan kun san yadda gashin larabawa yake, akwance ga tsantsi da sheki, ku kanku ku kwanta yadda fatar jikinsa yake fari tas kyakkyawan gaske, ga uban bakin gashi mai tsawo da sheki ai dole ku ɗan tsorata da kyansa, sai ma ya zaro idanun. Yau wuni Mahreen ta yi tana mummurɗe mashi gashin kai kamar an aiketa, tana fa shakkarsa, amma tsabar ita ɗin in ta faɗa sai ta cika, sai da ko ta cika, tun yana mamaki har ya dai'na, kuma sam bai nuna alamar kamar ya ji haushin abin da take yi mashi ba, bappa ma bai hana ta ba, dan shi kansa yana son su rinƙa jan Jaish ɗin da maga ko Allah zai sanya watanara bakinsa ya buɗe ya yi masu magana, ya gaya masu daga ina yake dan su samu su mayar da shi in da ya fito. Duk ta watsa mashi gashi, ta bi ta mummurɗesa ya zama kamar indomie, yau ya sha aikin Mahreen manyan ƙasa Time da zasu koma gida da ya yi sam bata ji daɗi ba, ranta bai so ba, ta so ne Jaish ya cigaba da zama a wajen tana murɗe mashi kai har gobe, ita fa bata gajiya in dai tana tare da shi. Haka dai suka koma gida, wanka Mahnoor ta yi suka shirya zuwa wajen Arɗo. Jaish dai ya nuna ba zai je ba, da kyar bappa ya lallaɓashi suka tafi. Jama'a duk sun hallara, kowa sai baya baya yake yi da bappa, sauran manyan dattawan kauyen ne kawai suka ɗan yarda suka gaisa da shi, su ɗin ma sai ɗari ɗari suke yi, shi kam Jaish dama bai nemi su yi mashi magana ba, dama ko sun yi mashi ma ba kula su zai yi ba, dan haka tsayuwarsa a gefe ya yi yana kallon gefen da babu mutane. Sai gulmarsa jama'a suke yi ƙasa ƙasa, masu satar kallonsa suna yi, masu rufe idanu wai suna tsoron ganin maye suma suna yi, haka dai suka tsaya har lokacin da Arɗo yasa su gwaggo suka banka maganin mayu a wuta hayaki ya fara balbalowa, jama'a basu da masaniyar hakan kawai unexpect suka ga hayaki yana bulbulowa. Nan take dayawa daga cikinsu suka fara tari mai sautin gaske, gwaggo bakar muguwa har da dumbulo maganin cikin hannayenta dukka biyu ta sake bankawa a cikin wutar, dan a cewarta idan Jaish maye ne ma ya ji azaba sosai......... Wato mutun dai ko ya mutu sai an ɗaure shi!!. Sai tari jama'a suke yi shi kuwa Jaish yana tsaye yana binsu da kallon mamaki, bappa ma bai yi tari ba, haka su Mahreen ma. Kan kace me ainahin masu aljanu a kai sun fara faɗuwa ƙasa suna ihu, nan take wajen ya hargitse da masu aljanu da almatsotsai dukka, ihu sautin muryoyi kala kala ne suka fara karaɗe kauyen gabaɗaya. Mahnoor kam gam ta ƙanƙame bappa jikinta na kerma, shi kuwa Jaish da ba mayen bane sai ma harɗe nannaye a saman faffaɗar kirjinsa ya yi yana ta kallon ikon god. Duk shakkarsa da Mahreen take ji bai hana ta riƙo hannunsa tana tambayarsa menene wannan ba?. Kallonta ya yi tare da yi mata alama da hannu a kan shi ma bai sani ba, hakan yasa ta yi shiru tare da ɗan kwantar da kanta a hannunsa tana binsu da kallo, bata taɓa ganin irin hakan ba, dan da wayonta dai ba'a taɓa kama mayya ko makamancin haka a gabanta ba!. Sai da gabaɗaya masu almatsotsai a kai ɗin suka sume a ƙasa sannan Arɗo ya fito. Ba ƙaramin tsorata ya yi ba a lokacin da ya fito ya ga Jaish a tsaye a kan kafafunsa, abin ya ruɗar da jama'a dayawa, wanda suke zaton shi ne mayen sai ga shi a tsaye cak a kan kafafunsa, wanɗan da basu taɓa zato ba kuma sune suka zube ƙasa matsayin masu lalurar. Abin ya ɗaure masu kai, ya kuma jefasu cikin ruɗani, a maimakon su yarda da cewa Jaish fa mutum ne kamar su, amma ina sai ma suka sake kai abin gaba, a in da suka fara cewa ai Jaish shi ne shugaban mayun duniya gabaɗaya, wai shi ne sarkinsu, dan haka wannan magani ya yi mashi kaɗan ne shiyasa bai faɗi ƙasa ba, sai sun nemo magani mai karfin gaske, dan haka dole su shiga kauyukan Cameroon wajen ƴan uwansu sulluɓawan fulani su nemo magani, sam sam su ba zasu taɓa yarda cewa shi ɗin mutun ne ba, dan kyau ɗinsa fa daban yake, ga shi ya mari yaro ya fara ciwo kamar zai mutu. Bappa dai da yake ya yarda da Jaish ɗin ko a jikinsa, sai ma cewa da ya yi su wuce gida, ɓacin ran kalmar da suke jefar Jaish ɗin da shi ne yasa ya wuce gida ya manta bai ce da Arɗo a yi wa su Mahreen tsakani da su Salisun ba, ya mance suka wuce gida. Da Arɗo ya dawo cikin gida ya gayawa su gwaggo Jaish fa shugaban mayu ne, wannan maganin ta yi mashi kaɗan, wani irin tsoro ne ya ƙara kamasu, haba kan kace me sun shige cikin ɗaki har suna rige rige, Innar Mahnoor ɗin ce kawai bata gudu ba, kowa ya ƙara tsorata da lamarin aljanin Mahreen sosai. Shi kuma bawan Allah da Allah yasa ba jin fulatancin sosai yake yi ba, sam bai san me suke ciki ba, a tunaninsa ma wani al'ada ne nasu na banka hakaƙi a gari su saka mutane tari har da suma, shi bai ma san wasu halitta wai su mayu ba a duniya, tunani ma yake yi a kan wace iriyar al'adance wannan ta cutar da mutane da hayaki har su suma?........ Babbar magana, to jama'ar ruga shi fa Jaish bai ma san kuna yi ba bayin Allah, sai ku kara himma wajen banke kowa da hayaki kuna tonawa kanku asiri, ku yi maza ku kashe kowa sai naga waye zai gaji kauyen, yau ance wasu dayawa ne mayu a maimaikon Prince Jaish namu, gobe kuma sai a haɗa da Arɗonma mai gabaɗaya..........🤣 Duk wani mayen da ya suma a wannan wajen Arɗo ya ce kashe shi za'ayi har lahira tun da su mugaye ne, nan fa kauye ya riƙice, kowa sai cewa yake yi a'a wlh nasa ba maye bane, kawai ya suma ne, sun ki yarda a kashe masu ƴan uwan nasu, nan fa Arɗo ya ce dole a kashesu, dan kuwa basu da amfani a cikin al'umma. Su Mahreen dai gida suka wuce abinsu, Mahnoor ta je ta hau yi masu girkin dare da zasu ci. Nenne dai ta zama yar gidan Arɗo yanzu,............. A gaskiya Jaish kana wuta a kauyen nan, duk ka sanya jama'a bala'in tsoronka, mata sun bar gidan mazajensu sun koma gidan uba kamar babu mutuwar a can gidan baban nasu, duk saboda kai?..... To ni dai bari na leƙa wani ɓangaren. __________________________🔥🌼❤️ DARK WORLD🔥🌹 Washegari da safe Ronnie ya tafi school, a tare da Floris Sweetie ta wuni, sai hira su ke yi, a nan Floris ta bata labarin iyayenta da suke a cikin birnin, sosai Sweetie ta sha madarar mamakin irin halin Ronnie, kawai ka ɗauko ƴar mutane ka ajiyeta a nan haka ake rayuwa, su iyayen nata ai rashin addini ne duk ya ja haka, idan ba rashim addini ba yaushe zaku ɗauki ƴarku budurwa ku baiwa Ronnie ya dawo da ita cikin empeir ɗin ya ajiye fisabilillah?. Ko da yake suna a ƙarƙashin ikon Black Tiger ne dole su bi ra'ayin Ronnie su bashi ƴa. Sai around 1:30 Ronnie ya dawo daga school, kai tsaye room ɗin Sweetie ya nufo, a lokacin ta shiga cikin toilet dan yin alwala, Floris kawai ya isko a kwance saman gadon. Tana ganinsa ta miƙe zaune. Ƙariso ciki ya yi, ɗan rungumarta ya yi tare da bata sumbata a kumatu kafin ya zauna a gefen bedside drawer. "Hiran me kuka yi yau?". Ya faɗa murya a kasale. Kashe mashi ido ɗaya ta yi kamar yadda ya saba yi mata, da alama akwai abin da suke ɓoyewa. Jinjina kai ya yi kamar mai sauraren wani abin mai daɗi. Dai'dai lokacin Sweetie ta fito ta ɗauro alwala. Kamar yadda ta saba yin sallah haka ta tsaya ta tada sallah ba tare da ta ce da Ronnie ɗin ko uppan ba. Binta da kallo shi da Floris suka yi, sun kasa iya cigaba da hiran da suke yi, sai kallonta suke yi har ta idar da sallar, addu'oi sosai ta yi tare da shafawa, sannan ta miƙe ta dawo kusa da Floris ta zauna. "Welcome Ronnie" . Ta faɗa a sanyaye. "Queen of beauty ya naga kin ƙara kyau ne yau?". Tamkar bai san motsa lips ɗinsa ya yi maganar, sai ka ji tamkar shagwaɓa yake yi, saboda a gajiye yake, ga kasala........... Ni kam nace ai dole ta ƙara kyau, dan kuwa ta samu hutu, ga Ac na bugata, sannan ga sabulai masu tsada, kwanciyar hankali ne dai kawai bata da shi, hankalinta gabaɗaya yana kan ƴar uwarta Pretty and Kamran, amma ta samu abin da take fata kam dukka saura wannan. Miƙewa ya yi ya nufi waje tare da ce masu yana zuwa, dama Sweetie yake ta marmarin gani yasa yana dawowa daga school ya zarcu nan. Da sauri Floris ta miƙe ta bi bayansa suka bar Sweetie ita kaɗai. Shiru ta buga tagumi tana tunani rayuwarsu a baya ita da su Kamran, har yau har gobe son Kamran yana nan a cikin zuciyarta, shi take buri da muradin gani, ance so mugun wasa, so tabarmar kaya, idan ka iya zama kaji daɗi, akasin hakan kuma ka ji a jikinka. Tana zaune a wajen bata motsa ba har Ronnie ya dawo hannunsa ɗauke da trayn abincin kamar yadda ya saba kullum. Yau tracksuit ce a jikinsa daga wandon har rigar, launin ash color mai ɗan duhu, ya yi wa kayan kyau, ya ɗaure korean up white hairn sannan sai ya baro wani mai ɗan tsawo kaɗan a gaban goshinsa, ya ilahi, ni kam naga madarar kyau da ban taɓa gani ba a nan, Koreans fa akwai madarar kyau matuƙa. In da ya saba ajiye abincin ya je ya ajiye, tun da ya shigo take kure mashi kallo, har ya ƙariso gabanta, kamar dai kullum yatsunsa ya kyasta mata a saitin face ɗinta haɗe da sakar mata lallausan murmushi mai narkar da zuciya. "What are you thinking?". Ya yi maganar yana wani karyar da murya tamkar budurwar da ta shirya yaudarar saurayi ta karɓe mashi kuɗi. Macewa ta kara yi da kallonsa, ta rasa meyasa shi wannan Ronnien kome zai yi sai ya burgeta, abin ya fara bata mamaki, komansa gwanin birgewa da shiga rai, ga shi da shegen salo kala kala, yanzu idan ya yi maka wannan, to fa anjuma wani daban zai yi maka, sai ka rasa daga ina yake koyosu. Ganin bata yi magana bane yasa ya matso kusa da ita tare da ciro tsadaddiyar haɗaɗɗiyar wayarsa, ya saita camera haɗe da saita fuskokinsu ya ɗaukesu a hoto yana faɗin. "Bari na ajiye tarihi, a duk cikin waɗan da yaya yake kawowa cikin empeir ɗin nan dan buƙatar Spender daga wajensu babu wadda na taɓa kulawa ma bare mu yi hoto, gaskiya ke you're the best my queen". Ya kai karshen maganar tare da zama a gefenta yana jin wani irin burgesa da take yi yana ratsa zuciyarsa. "Ronnie kai ɗin kyakkyawa ne ajin farko". Ta faɗa kamar mai raɗa. Da sauri ya juyo da kallonsa a kanta, gera guda ya ɗaga yana murmushi tare da ɗan ɗaga kansa sama, shi kansa yasan shi ɗin kyakkyawa ne, amma idan kyawawan fararen tattabaru irinsu Sweetie suka faɗa cewa yana da kyau sai ya ji daɗi sosai. "Ronnie ina Floris?". Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dakatar da murmushin da yake yi ya bata amsa da. "Floris ta tafi wajen wasa". Shiru ta ɗan yi tana tunanin akwai wani abin a ƙasa da yasa baya zama tare da ita da Floris waje guda, idan suna tare da Floris da zarar ya shigo Floris ɗin zata yi dabara ta zulle ta bar wajen, idan shi ne yake tare da ita da zarar Floris ta zo zai miƙe ya fita ya ce yana zuwa, daga haka ba zai sake dawowa ba sai Floris ɗin ta fita, kuma ita dai tasan da cewa ba faɗa ya yi da Floris ɗin ba, to meyasa basu haɗuwa su uku su zauna su yi hira?. Ta jefawa kanta wannan tambaya da bata da amsarsa. Ganin alamun ta shiga duniyar tunani ne yasa ya ce mata. "Come let's eat food first before you continue what ur doing, thinking thinking lady kawai". Siririn murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Am okey, we eat together with Floris since 12:30". Ɗan lumshe idanunsa ya yi kafin nan ya sake warosu a kanta. "Ban yarda ba, let's go kawai my Queen, if not ba zan ci abincin ba nima". A shagwaɓe sosai ya yi maganar har yana ɗan turo baki. Habawa shagala ta yi da kallonsa, in ya yi wannan shagwaɓar a gaskiya yana kifar da Gwamnatin mata da maza dake kallonsa. Ta shagala da kallonsa bata ankara ba sai jinta ta yi a sama ya ɗauketa cak, kai tsaye sai wajen da ya ajiye abincin ya direta. Ƙasa ƙasa ya furta. "Meyasa kike son saka gown ne ke kam? Ki rinƙa sanya kaya irin na beb Floris mana". "Addinina bai aminta da irin waɗan nan kaya ba, addininmu ya ce mu suturta ko'ina na tsiraici a jikinmu, mu rufesa mu killacesa, dan duk abin da yake a buɗe ba abu bane mai daraja, mai daraja shi ne wanda ake rufe shi ruf babu wanda zai kallah sai mamallakinsa". Shiru ya ɗan yi yana tattauna maganganun nata, can kuma sai ya ɗauko spoon tare da fara zuba abincin yana faɗin. "No ba haka bane, duk abin da yake buɗe ana ganinsa dole za'a fi sonsa, saboda kinga za'a ga kyansa har aji ana sha'awarsa, abin da yake ɓoye kuwa ai ba wanda zai gani bare ya ji sha'awarsa"............. A wannan magana ta Ronnie fa idan kuka mayar da hankali da kanku zaku fahimci darasin da yake ciki, dan kuwa ya buɗe maku gaskiya ce a fili. Cewa ya yi abin da yake buɗe shi jama'a suke kallah har su ji sha'awarsa, me yake kawo zinace zinace? Amsar ita ce sha'awa, kenan kunga wani lokaci mu da kanmu muke jawo irin su fyaɗe a'a saurayi ya yaudari yarinya ya lalata da dai sauransu, ya ce abin da yake rufe babu wanda zai kallah ma bare ya yi sha'awa, na san nan kun gane ma da kanku ba sai na tsaya dogon bayani ba, dan haka duk macen da ta suturta kanta a ko'ina daraja ne da ita, Allah dai yasa mu gyara laifukan da muke yi na fili da na ɓoye ya kuma yafe mana kura kuranmu. Amin. Kawo mata abincin da ya ɗeba a spoon ɗin ya yi saitin bakinta. Buɗe bakin ta yi ya zuba mata, sannan ya tsareta da idanu yana kallon yadda take taunar abincin a hankali cikin nutsuwa. Sai bayan ta haɗiye ne ta bashi amsar sa da cewa. "Duk abin da jama'a zasu gani su yi sha'awarsa su kuma yi rububinsa kai kuma a matsayinka na mai zuciya me zaka yi da shi? Ai babu wata daraja a wajen abin da kowani shashashan kare da doki zai gani ya ji ya burgesa, wanda ya kai da wanda bai kai ba duk ya ji ta burgesa kenan? Hakan na nufin baka cika na daban ba kuma baka cika zakara a cikin empeir ɗin nan ba kenan?!". Ƙura mata idanu sosai ya yi har ta kai karshen maganar, nazari ya fara yi a kan maganganun nata. Cigaba ta yi da cewa. "Idan har kai ɗin zakara ne ko kuma kai na musamman ne to kamata ya yi komai naka ya fita na musamman, kamata ya yi ka nunawa jama'a da banbanci a tsakaninku, kamata ya yi ka zama cewa abin da kake so babu wanda ya isa ya gansa bare ma har ya so ko ya ji sha'awarsa". Ban da kallo babu abin da yake binta da shi, kalamanta kamar sun yi tasiri a cikin zuciyarsa. Ganin ya nutsa cikin kogin nazari da tunanin yasa ta kai hannu ta karɓi spoon ɗin hannun nasa. Nisawa ya yi tare da ɗan kawar da kallonsa daga kanta alamar ya dawo cikin hayyacinsa kenan. Abincin ta cigaba da ɗebawa tana kai mashi saitin bakinsa, a hankali yake karɓa yana tauna. Tabbas ta lura da yanayinsa gabaɗaya ya canza, abincin ma taunarta kawai yake yi, amma ga dukkan alamu bata yi mashi ba. Ta yi nisa cikin ciyar da shi ɗin da take yi ta ji sautin daddaɗar sexy voice ɗin nan nasa ya daki dodan kunnenta a in da ya ce. "Waye ya koyar dake abin da kika gaya mun ɗin nan?". A takaice ta ce da shi. "Addinina". Adadi ya maimaita kalmar, jinjina mashi kai ta yi alamar tabbatarwa ba tare da ta yi magana ba. Shiru ya yi suka cigaba da cin abincin har suka ƙoshi sosai, bai sake yin magana ba. Miƙewa tsaye ya yi jiki ba kwari ya ce. "Ba zan gaji da rokan yaya da ya barki muje wajen wasa ba, yanzu ma bari na je na roƙesa ya barki mu je fili ki ga wasana da zan buga, zan ji daɗin hakan". Yana kai karshen maganar ya nufi waje ba tare da ya jira amsarta ba. Da kallo ta bi bayansa tana mai cigaba da yabawa tsantsar madarar kyau da Allah ya yi mashi, ga tsawo da faɗin kirji irin nasu na ƴan Wrestling. Tana zaune a wajen har ya je ya dawo. Fuskarsa a ɗauke da annashuwa, da alama yau dai ya yi nasara sosai. Yana zuwa ya ja hannunta da nufin su tafi. "Ka tsaya na gyara ɗakin mana". Ta faɗa a hanzarce. "No ki barshi za'a gyara". "To ka bari in ɗauko wani abin na rufe gashin kaina". Nan ma a'a ya ce mata, daga karshe ma sai ya ɗagata cak, shi fa da alama yana jin daɗin ɗaga ƴan'mata kyawawa sama. Kai tsaye wajen wasa ya nufa, yau wasan takalmin taya zai buga, su shiddane dai'dai zasu yi gasar, dukkansu sanye suke da tracksuit masu bala'in kyau da tsada, sai dai na Ronnie ya fi nasu kyau, dan shi na musamman ɗin na musamman ake buga mashi, tun daga company design ɗinsa daban dana kowa, babu kuma wanda ya isa ya sa ayi masa irin nasa ya sanya, idan ya yi hakan zai fuskanci mummunar hukunci daga hannun Black Tiger, hakan yasa ba wanda ya taɓa kwatantawa ma. Gabaɗaya ƴan wasan jikin kayansu wajen cikinsu an rubuta number, kowa da numbersa, na Ronnie shi ne number one, shiyasa yau kuka ga ya ɗaure gashin kansa, dan ya ji daɗin gudu. Yana sako kafarsa a filin aka fara ihu ana tafi haɗe da fito, a kujeransa da yake zama kallon wasa ranar da ba zai buga ba ya zaunar da ita, Floris tana gefen master Devil tana aikin yin tapi jaruminta Ronnie ya shigo fili. Takure jikinta waje guda Sweetien ta yi, ba komai yasa hakan ba kuma face master Devil da ta gani, tana bala'in tsoronsa, bare ma kirar jikin nan nasa dole aji tsoronsa, shekaru da dama yana Wrestling, yanzu kuma ya dawo horar da ƴan Wrestling ɗin, ai kunga dole ya razana duƙata, dole hantar ciki ta kaɗa da ganinsa!!. Fili Ronnie ya nufa, bayan ya tsaya a bayan red line dake zane a gaban dukkannin ƴan wasan ne ya ɗago da kansa tare da ƙara ɗaure fuskarnan tamau tamkar bai taɓa yin dariya ba a rayuwarsa. Kallonsa ya kai kan Sweetie dake ta kallonsa tamkar zata taso ta zo ta manna mashi hut rumguma, ji take kamar ta ganta a gabansa kawai. Kashe mata ido ɗaya ya yi fuska a haɗe, hakan wani irin cool murmushi ya sanyata saki ba tare da ta san lokacin da ta saki ɗin ba, saura kaɗan ta sanya shi yin murmushin shi ma, sai kuma ya sake dakewa ya ɗaure fuskar tamau. Wannan abin da suka yi kuwa a kan idanun master Devil suka yi shi, hakan yasa master ya jinjina kansa tare da fara tunanin Ronnie yana son jiƙa masu aiki, dan kuwa in dai suka barsa ya saba da Sweetie to tabbas ba zasu samu abin da suke so cikin daɗin rai ba, dan ba zai barsu su azabtar da ita har sai ta buɗi baki ba, zai rinƙa shiga tsakaninsu ya yi ta yi masu kuka har sai sun hakura sun rage mata azabar da suke kan tanada mata idan bata basu Spender ba, hakan yasa master ya miƙe ya nufi cikin gida, da alama wajen Black Tiger zai je. Shiryawa ƴan wasa suka yi, wasu irin hut luxurious taya shoe aka kawo masu, na Ronnie ya fita daban da nasu, dama na gaya maku ai shi kayansa daban da na kowa. Sanyawa suka yi a kafafunsu tare da yin ready. Commissionern wasannin yana hura usir suka tashi a guje kamar zasu fasa kirazansu saboda karfin gudu. Nan take jama'a suka ɗauki tafi ta ko'ina haɗe da fito, sai watsa flowers a sama jama'a ke yi, wasu sai rawa suke yi suna ile, kowa ihun sunan jaruminsa yake yi, amma a gaskiya ban ji sun ambaci sunan kowa ba face sunan Ronnie mai tarin uban masoya ta ko'ina. Gudu suke yi tamkar masu gudun cetar rai, ga tayan takalmar nasu ba'a magana....... 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 22/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 26 Gudu suke yi tamkar masu gudun cetar rai, ga tayan takalmar nasu ba'a magana....... Miƙewa tsaye Floris ta yi tare da haɗe hannayenta dukka biyu ta ɗaura a saman kirjinta ta lumshe idanu tana faɗin Jesus yasa Ronnie ya yi nasara. Da kallo Sweetie ta bita tana mamakinsu, ita dai bayan addinin musulunci bata san yadda ake yin kowani addini ba, sauran addinan ma mum ɗinta ta basu labarinsu a lokacin da take koyar da su karatun Alkur'ani mai girma, a lokacin tana basu tarihin annabawa da yadda magabata suka sha gwagwarmaya duk da cewa gobenmu ta yi kyau, ta hakan tasan cewa akwai wasu addinai na daban bayan musulunci, amma bata san ya ake yi sun ba. Kowa da yake cikin wannan fillin addu'a yake yi a kan Ronnie ya yi nasa, duk da sun san cewa kullum shi yake zuwa na ɗaya, har yau babu wanda ya kai kusan shi ma, amma abin ya zame masu jiki yi mashi addu'a a ya yin da yake buga koma wace iriyar wasa ce. Number one dai shi ya zama number ɗin kamar kullum, ihu da fito a wajen jama'a ba'a magana, tamkar maƙoshinsu zai ɓalle. Ita kam Sweetie nata idanu kawai.......... Kamar daga sama ta ji an riƙo hannunta, a hanzarce ta ɗago kanta dan ganin wanenen?. Wani irin razana ta yi haɗe da zaro idanu waje sosai, mutumin da ta fi tsoro a rayuwarta wato master Devil shi ne ya riƙo hannunta tare da yi mata alamar ta tashi su tafi. Da sauri ta juyar da kallonta izuwa kan Ronnie da yake tsaye a saman wani irin shinfiɗa mai kyau za'a sanya mashi tambarin zakara a wuya, shi dai a rayuwarsa yana matuƙar kaunar wasanni, yana kuma bugasu son ransa, Allah kuma ya bashi, kowace wasa zai buga shi yake zama zakara. Tamkar zata ce ba zata bi master ba, sai dai tsoro ya hanata ko motsawa ma, jikinta har kerma ya fara yi, ta gaza iya sake juyowa ta kalli face ɗinsa, addu'a kawai take yi Allah ya juyo mata da kallon Ronnie a kanta, dan tana ganin cewa shi kaɗai ne zai iya dakatar da master daga ɗaukarta su tafi. Sai dai har ya jata suka fita daga wajen hankalin Ronnie bai juyo kanta ba, yana can yana karɓar lambobin yabo kala kala, ga wata haɗaɗɗiyar box mai girma da Black Tiger ya aiko mashi da shi a matsayin gift ɗinsa, sai yaba kyan box ɗin yake yi duk da bai san me a cikinta ba, abi da ya sani kawai shi ne wajen box ɗin ta yi mashi kyau. Sai tafi jama'a suke yi, da sauri Floris ta sauƙo izuwa cikin filin. Kai tsaye wajensa ta nufa, sam ita ma bata lura da cewa master ya tafi da Sweetie ba. A gefensa ta zo ta tsaya aka fara ɗaukarsu hoto, sam yaki yarda a ɗaukesa hoto da sauran ƴan wasan da suka buga a tare, da Floris kawai ya yarda su ka yi hoton. Tana zuwa da aka fara ɗaukarsu hoto sai ya ɗago da kallonsa zuwa in da Sweetie take zaune da nufin ya kirata ita ma tazo su yi. Wayam ya ga kujerar da take ɗin babu kowa, zaro korean eyes ɗin nan nasa ya yi yana kallon filin da kyau. Wata haɗaɗɗiyar tattabara ƴar siririya fara tas da ita zubin bebs ɗin Dark world ɗin take da shi ita ma. A gabansa ta zo ta tsaya, wasu kyawawan fararen ƴan'mata su biyu ne a gefe da gefenta hannunsu ɗauke da aword plate gift. Suna isowa gabansa matar ta kai hannu ta ɗauko wani kyakkyawar aword towel ɗan siririr mai tsawo, a wuyarsa ta nufo da nufin ta rataya mashi abin, ya fita tsawo sosai, kuma high heel sosai ta sanya a kafafunta, amma ina hannunta bai iya kai wuyarsa ta rataya mashi abin ba. Ɗan duƙa mata kaɗan ya yi ya rage tsawonsa dan ta sanya mashi, yana yi hankalinsa a kan jama'ar dake kusa da in da ya ajiye Sweetie, one by one yake bin mutanen wajen da kallo ko zai hangota, sai dai wayam bata ba alamarta. Wannan mata tana ƙoƙarin sanya mashi gold na girma wanda ita ce gold na winner wajen na 35 da ya ci a ƴan shekarun nan nasa, awajen takalmin taya kawai ya ci 15, haka a sauran wasanin irinsu foosball da sauransu, ya tara ɗanyen gwalgwalai dayawa, harta takalmar da yake sakawa wajen buga kwallo ta ɗanyar gold ce wanda Black Tiger ne ya yi mashi gift ɗinta lokacin da ya ɗauki cup. Bai bari ta sanya mashi wannan gold ɗin ba ya sanya kai da sauri ya wuce tare da cire wanda ta sanya mashi a wuyar tasa ma ya riƙe a hannu. Kai tsaye wajen da ya zaunar da Sweetie ya nufa, sam hankalinsa baya jikinsa ita kawai yake tunani. Sosai Floris ta yi mamaki, yau Ronnie ne ana karrama shi ya tafi ba tare da ya jira an gama ba? Kai abin da mamaki, to ina zai je?. Tambayar da take ta jefawa kanta kenan. Ganin ya nufi cikin gida ne yasa ta yi saurin barin wajen ita ma, bayansa ta bi zuwa cikin gidan. Yana shiga ciki room ɗinta ya nufa kai tsaye. Sai dai ko da ya je bata ciki, ai bai san lokacin da ya yi wurgi da gift dake hannunsa a tsakar ɗakin ba, a hanzarce ya nufo waje. Yana fitowa suka ci karo da Floris da ta biyo bayansa. "Beb what happened? Naga ka bar wajen taron lafiya?". Cikin sanyin murya ta yi maganar, dan ta lura tamkar hankalinsa a tashe, ta kuma san halinsa sarai, wlh idan ya fusata ransa ya ɓaci ko master Devil ya bashi hanya a zafin zuciya, kun dai ga yadda yake rayuwa dasu so simple ga shi so silent, amma kada ku ga ɗayar zuciyarsa ta ɓacin rai kenan, a wannan lokacin bashi da kyan gani, kun dai ga yadda ya ɓaɓɓallah Delisha duk da take ƙawarsa, to wlh a haka ransa bai ɓaci ba, da ya ɓaci ina mai tabbatar maku Delisha ba zata rayu ba. Sam bai amsa mata maganar tata ba, da alama kamar bai ji abin da ta ce ba, kai yasa zai wuceta. Da sauri ta sake cewa. "Beb are you okay? What's going on? What are you looking for?". A wannan karon a ruɗe ta yi maganar. A karo na biyun ma bai amsata ba, cikin zafin nama ya nufi part ɗin Black Tiger kai tsaye, har wani irin zafi ya ji zuciyarsa tana yi mashi, ya saba da Sweetien sosai, ba zai ji daɗi ba idan aka rabasu, kuma yasan tabbas Black Tiger ne ya ɗauketa, dan kuwa idan ba shi ɗin ba ba'a haifi mutumin da zai iya ɗaukar ta ba, kai koma ba'a cikin empeir ɗinsa take ba, ko a iya cikin birnin take wlh babu wanda ya isa ya fitar da ita ba tare da izininsa ba, kada ku manta komai da suke yi a tafin hannunsa suke yi, Ronnie ya fi kowa sanin hakan, shiyasa ma bai tuhumi kowa ba ya nufi yayan nasa kai tsaye, yasan ko master Devil bai isa ya gwada mashi sani a kan black tiger ba, duk cikin birnin shi kaɗai ya san shi. Abin da baku sani ba shi ne, duk wanda ya yi kuskuren shiga wannan ɗakin da Ronnie yake shiga da sunan ɗakin Black Tiger, duk wanda ya yi kuskuren shiga wannan ɗakin shikenan an shafe babinsa, magana ta gaskiya in dai ka shiga wannan ɗakin to fa ka tafi kenan har abada, wlh mutum baya rayuwa, Ronnie kawai yake iya shiga kuma ya fito lafiya lou, wani lokaci ya fito da farinciki idan ya shiga, wani lokaci kuma ya fito fuska a ɗaure, idan abin ta yi tsamari ma har da hawaye yana iya fitowa idan abin tafi karfinsa, duk da haka baya ɗaukar good 5 hours ba tare da ya ziyarci cikin ɗakin ba, to me a cikinta kenan?. A yanzu ma bai kula Floris ba kai tsaye ya nufi wannan ɗakin, da yake ita Floris ɗin tasan me tsarin wannan ɗakin sai ta ja da baya tare da nufar parlon dan ta jira shi a can. A wannan karon ya jima a cikin ɗakin, ya ɗauki a kallah awa ɗaya da rabi kafin ya fito, fuskar nan tasa a ɗaure tamau kamar hadari, kai tsaye wajen part ɗin ya nufa. A parlon ya isko Floris sai safa da marwa take yi tana jiran fitowarsa....... Yana fitowa ko kallon in da take bai yi ba ransa a matuƙar ɓace ya nufi nasa room ɗin. Da sauri ta rufa mashi baya, sai dai kafin ta iso ya banko kofar ya murza key ta ciki. Ƙasake ta tsaya a wajen tana mamakin abin da bai taɓa yi ba yau ya aikata, to me yake damunsa har haka? Ta jefawa kanta tambaya. Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta ja ƙafafuwanta, jiki duk a mace ba kwari ta nufi hanyar nata room ɗin............ To fah me ya ɓatawa Ronnie rai har haka? Me aka yi mashi? Ina aka kai Sweetien? Me zasu yi mata? Da alama nasu game ɗin yanzu zai fara, sai ku gyara zama my people's, amma ni dai bari na leƙa wani part ɗin kafin mu dawo kan wannan cakwakiyar, dan su sai anyi masu shiri na musamman. ____________________🔥🌼🌹 DUBAI Sanyin Acn da yake a ɗakin ne ya fara ratsa ƙashin jikinta har izuwa cikin ɓargo, hakan yasa ta fara motsawa, kyawawan yatsun kafafunta dake motsawa ne ya ja hankalinsa. A hankali ya furta. "I will call you back uncle". Yana kai karshen maganar ba tare da ya jira amsar da za'a bashi ba ya katse kiran. Kusa da gadon da take kwance ya matso, three cuter and t-shirt mai laushi na shan iskace a jikinsa, ya yi kyau sosai, arab hairnsa ya sha gyara matuƙa, sai tashin kamshi yake yi. Number Dr Raj ya danna, short sms ya rubuta mashi tare da tura mashi, sannan ya zauna a gefen bed ɗin yana kallon face ɗinta. A hankali yatsun hannunta ma suka fara motsawa, tamkar wadda aka dannawa allura da karfi ya karye a cikin jikinta haka ta waro idanunta da suke jajir kamar wuta waje, idanun nan nata a kumbure sosai saboda kuka, gabaɗaya from head to toe idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk da tana sume kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci lallai ba shakka a birkice take, sam bata da nutsuwa ko na second ɗaya. Mai da idanun nata ta yi ta datse su gam tare da fara faɗin. "Wlh zan yi, zan yi kome kuke so, kada ku cutar da rayuwata, wlh ni marainiya ce, ku ji tausayin maraicina............" Shiru ya zuba mata idanu yana sauraron sambatun nata, ga dukkan alamu baya son taɓata ta daina sambatun, kamar akwai abin da yake son ji. Sallamar Ummie a cikin room ɗin yasa ta dakata da surutan da take yi, kai kallonsa kan room door ɗin ya yi. Ummie ce da Sharifat suka shigo a tare. Da farko Ummie ta ce ba zata zo ta dubata ba, amma da Sharifat ta matsa mata sai ta hakura ta zo. Ummie fa har da launin fatar Leesharh da take chocolate yasa ta tsaneta ba iya dan tana zargin mijinta yana sonta ba, kun san wasu larabawan dama da tsanar bakake fata ba gaira babu dalili. Zame haɗaɗɗen white glass dake face ɗinsa ya yi, a hankali ya mai da kallonsa a kan Ummie dake ƙoƙarin zama a saman haɗaɗɗun kujerun dake room ɗin........... Da sauri Sharifat ta dawo kusa da ita, a hankali ta fara ruwan hawaye tana faɗin. "Leesharh ki tashi dan Allah, tun jiya fa nake ta kiran sunanki amma kin ki tashi............" Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon hannu da ya ɗaura mata a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru. A daƙile Ummie ta ce. "Ya jikin nata Bilal?". Shiru ya kafeta da idanu ba tare da ya amsa ba, dan kuwa mugun zarginta yake yi sosai, dama da shi da Ramish sam basu shiri da ita, shi Ramish dama baya shiri da kowa kamar wani aljani, gara Bilal ɗin sau dubu. Ganin bashi da niyar amsa mata ne yasa ta miƙe ta nufi waje, sai ɗari ɗari take yi, dan kuwa yadda taga ya tsareta da idanun nan tasan akwai wani abin a ƙasa da yake zargi, nan take ta ruɗe, tunanin kashe Leesharh ɗin da suka shirya ita da hajiya two seater kawai ta fara yi, tasan su waye su Bilal ɗin sarai, ita ta renesu, zaƙwaƙuran jami'ai ne masu aiki da ƙwaƙwalwa, tun da suka sanya hannunsu a kan Leesharh is better for her da ta janye ƙudurinta, idan ba haka ba zata jawa kanta balai'n da dukka danginta babu mai iya tare mata, dan idan abin nasu ya motsa wlh ko maganar Abu Abdussalam basa saurara bare ta sa ran zasu ɗaga mata kafa, ta san pata pata zasu yi da ita, bare ma Ramish da dama shi ba wani jin maganar mutane yake yi ba, idan ya tsara abu fa to sai ya yi shi, idan ya tsara abu yasan cewa King Zuhair ba zai aminta ba to wlh baya taɓa yarda ya yi magana da King ɗin a lokacin har sai ya kammala abin da zai yi ɗin sannan ya nemi daddyn nasa haka yake wannan tafiyar, a duniya mamarsa ce kawai take yi mashi magana ɗaya baya bata hakuri bare ya ce zai kwatanta yin wannan abin, da zarar ta ce Ramish ka bar wannan abin bana so, to fa a lokacin zai share wannan abin daga ƙwaƙwalwarsa ya ce ya barta har abada, ita kaɗai take yi mashi magana ɗaya ba ƙari kuma ya bi cikin hanzari, uwa uwace, yana girmamata sosai. Amma King idan ya ce mashi baya son abu ya rinƙa takura mashi kenan har sai ya kyaleshi ya yi. Ummie na fita Dr Raj na shigowa, saura kaɗan ma su ci karo. Sannu ya yi wa Ummien tare da ƙarisowa ciki ba tare da ya jira amsarta ba. Sanye yake da kaya irin na jikin Bilal ɗin sai!. A gaban gadon Leesharh ɗin Dr ya zauna. Kallon Sharifat dake ruwan hawaye Bilal ya yi. "Little tashi ki je room ɗinki". Ya faɗa a sanyaye. Miƙewa tsaye ta yi tare da nufar wajen da Ramish yake kwnace, bawan Allah ya yi wani irin haske sosai a kan wanda yake da shi, ba shakka wannan magani da Leesharh ta bashi yana da tsananin karfi sosai, ya sha wahala sosai ɗan tahaliƙin nan, ga shi sun ɓoyewa King Zuhair abin da yake faruwa, saboda sun san King yana matuƙar kaunar ƴaƴan nasa, idan ya ji labari komai zai iya faruwa, shiyasa suka ɓoye mashi, dama idan baku manta ba a baya ya buƙaci su Ramish ɗin su je, kunga a kan washegari zasu tafi ne wannan abin ya faru, shi ne Bilal ya sanar da King ɗin anyiwa Ramish kiran gaggawa a wajen aiki ya tafi, dan haka sai ya dawo zasu zo, to a haka suka rabu da King ɗin lafiya, basu je sun duba jikin Mama ba har ta warke. Sai dai abin da basu sani ba shi ne tabbas King ya san komai da yake faruwa dangane da su, dan kuwa yadda yake bibiyar rayuwarsu yana kula da su tabbas ko kansa baya kula da shi haka, duk wani abin da suke ciki yana sani, ya sanya masu kula da matakan tsaronsa a matsayinsa na uba na gari, su sam basu san da hakan ba duk da suke jami'ai, shiyasa wanda ya haifeka fa komai iliminka komai baiwarka da wayonka sai dai ka gwadawa wasu ba dai shi ba, dan kuwa shi dai a tsirara yake kallonka ato, gara ma mutun ya san da hakan. King yasan komai, yana da niyar yi masu dirar mikiya a Dubai ɗin ne ma wannan yaki ya riskesu, da zuwan bazata zai masu, a tunaninsu sun ɓoye mashi. A kansa ta ɗan tsaya tana kallon face ɗinsa, har cikin ranta take bala'in kaunar Ramish, mafarkinta a kullum su yi aure, Allah sarki shi kuma bai ma san tana yi ba, bashi da ma wata kusanci da ita, yasan dai yana da kanwa mai kawo mashi abincin, sannan autarsu a gidan, shikenan, ba kaunar uwarta ma yake yi ba bare ace ita ma zai kaunace ta, uncle nasu kawai suke so ƴan albarka. Dr Raj ne ya ce mata. "Little zaki iya tafiya ba wata damuwa kin ji?". Jinjina kai ta yi tare da nufar waje da gudu saboda wani irin kuka da ya kubce mata. Duk abin da ya faru a kan idanun Leesharh da tun ɗazun ta dawo cikin hayyacinta ya faru. Tabbas tasan da cewa Sharifat na son Ramish, ta gaya mata tun lokacin da suka koma kwana ɗaki ɗaya, a lokacin ne ta fara nadamar abin da ta yi wa Ramish ɗin, saboda ba karya Sharifat ta nuna mata kauna na wuce misali, idan ta cutar da Ramish tamkar ita ta cutar, a yadda ta kaunacetan nan kuma wlh tasan idan ta cutar da ita Allah ma ba zai kyaleta ba. Idanunta ne suka cike tab da kwallah, ta ji matuƙar tausayin Sharifat ɗin matuƙa, mayar da idanunta ta yi ta datse su, zafafan hawayen da suka cika idanun ne suka fara bin gefen ƙuncinta da ɗuminsu, ta rasa mafita, idan ta juya gefe guda babanta, idan ta juya zata aiwatar da aikinta dan ta ceci baban nata kuma sai ta tuna Sharifat dake da tsohuwar soyayya a zuci, in ta ja Ramish ya mutu ya Sharifat ɗin zata yi? Tasan zata cutu matuƙa. In ta juyo ta wani gefen kuma Abbie bawan Allah ya nuna mata kauna, shi take tunawa, duk sai ta ji tamkar ta kashe kanta kawai ta huta, ta gaji da wannan azaba, kullum bata cikin nutsuwa, zuciyarta cike da ciwo matuƙa, kullum tana cikin tashin hankali da fargabar asirinta zai tonu!. Kallon Dr Raj Bilal ɗin ya yi. "Dr i think Ummie ce ta azabtar da yarinyar nan, dan a sambatun da ta yi lokacin farkawarta tana ambatar aji tausayin maraicinta a kyaleta, kaga kuwa hakan na nufin wani daga cikin gidan nan ne ya yi mata wannan aika aikan!"............. Tab tashin hankali, wato shi Bilal ma zargin Ummie yake yi a kan ita ta fasawa Leesharh kai? E lallai kuwa, Leesharh tana zarginsa a kan yana tare da masu nikaf, dan yanzu ta gane cewa wlh shi ta gani a gidan masu nikaf, wlh shi ne ba kama ba, domin kuwa farfaɗowar da ta yi jiya kafin ta sake suma ta ga kayan da ya sanya ya je gidan masu nikaf shi ya sanya a jikinsa jiyan, ya fito a sak yadda ta gansa, sannan yana da zanen kunama a wuyarsa, kuma ta ga zanen, kai wlh shi ne ya je wajen masu nikaf, kunga ita tana zarginsa a kan da sa hannunsa wajen kashe Ramish, shi kuma yana zargin Ummie wajen cutar da ita, tab akwai cakwakiya, idan kuwa haka ne an samu babbar matsala ba kaɗan ba! Amma meyasa duk zafin rai da zafin kai irin na Bilal ɗin daga kallonta a karon farko ya yi mata saukin kai? Meyasa ya zaɓi ya taimaka mata bayan su da basa yarda wani ya raɓesu? Su da basu yarda da kowa ba?! Har ma yake zargin Ummie a kanta! Meyasa ya ɗauketa da mahimmanci lokaci guda haka?. Sannan kuma ta wani ɓangaren idan har yana son cutar da Ramish meyasa zai taimaka mashi a lokacin da suka zo kashe shi? Meyasa ya shiga damuwa sosai na rashin lafiyar Ramish ɗin? My people's akwai matsala fa, wannan cakwakiya ta kusa sanya ƙwaƙwalwata ta ɗauke ɗif na wucin gadin. Mu koma baya kaɗan dan jin abin da ya faru. Abin da baku sani ba Bilal ne ya shiga ɗakinta dan ya yi magana da ita ya ganta kwance cikin jini, shi da tun da Allah ya yi Sharifat a cikin wannan gidan bai taɓa taka kafafunsa ya shiga ɗakinta ba sai jiya wai yana son ganin Leesharh, shi ne ya je, idan baku manta ba a lokacin ta baro part ɗinsu ba jimawa masu nikaf suka kirata, to ya biyo bayanta kenan, yana shigowa ya sameta kwance a ƙasa cikin jini, kanta a fashe saboda bugasa da bango da ta rinƙa yi, a hanzarce ya ɗauketa cak zuwa room da Ramish yake kwance, a nan ya sanya Dr Raj ya bata taimakon gaggawa, da yake kanta ta rinƙa bugawa sai yasa jinin nata ya yawaita zuba, a jiyan ta farfaɗo ta sake sumewa, dan ciwo a kai ba karamin abu bane. Wannan shi ne abin da ya faru, tsayuwa tsayin daka a kanta Bilal ɗin ya yi har sai da Dr Raj ya kasa danne hakurinsa ya ce mashi wai ko ya san yarinyar nan ne da ya tsaya tsayin daka a kanta haka? A'a ya amsa da shi tare da ɗaurawa da cewa kawai tausayi take bashi.............. To mu koma kan labarinmu tun da mun ji ya aka yi Bilal ya taimaki Leesharh!. Siririn tsaki Dr Raj ya ja tare da sanya hand gloves a hannunsa ya kwaso wasu allurai da nufin ya haɗa ya yi mata, dama jiran farfaɗowarta suke yi ya yi mata allura. "Dama kai Yah Bilal ka yarda da Ummie kenan? Ai ko dan waɗan nan shashashun friends ɗin nata da suke zuwa gidan nan ita ba abar a yarda da ita bane, tsab zata iya cutar da ƴar mutane, kasan dai babu wata maikaciya a gidan nan da zata yi wa wannan yarinyar irin wannan rauni, dole Ummien ce mana". Shiru ya yi kamar mai nazarin wani abin. Kamar daga sama idanunsa suka sauƙa a kan Ramish, a hankali ya ga yatsun hannunsa suna motsawa, a lokacin kuma Dr Raj yana ƙoƙarin yiwa Leesharh allura, ai tana jin za'ayi mata ta waro idanunta waje, da a tunaninsu barci ma take yi shiyasa suka tsaya suna hiran Ummie a wajen, ashe basu san ta ji komai ba. Tana buɗe idanu sai kan alluran hannun nasa idanunta suka sauƙa. A ɗari ta yunkura zata tashi, dan tana tsoron allura kam sosai. Da kallon mamaki Dr ya bita tare da daure fuska sosai kamar ba shi ba, dama dan dole Bilal ya sanyasa kula da lafiyarta. "Gyara na yi maki". A dake ya yi maganar, irin babu wasa a tartare da shi ɗin nan. Jin ya yi magana yasa Bilal dawo da kallonsa a kansu, sai gani ya yi Leesharh ta manne da bango dan bata son ayi mata alluran, ga shi kuma ba zata iya miƙewa ta gudu ba, jikinta dukka tamkar an ɗaure mata shi da igiyoyi. Motsawa gaɓɓan jikin Ramish suka cigaba da yi, nan take bugawar zuciyarsa ta fara aiki daidai wa dai'da, sautin numfashinsa ya fara dai'daituwa, hakan yasa duk suka kai kallonsu a kansa jin na'urorin dake wajen bed ɗin nasa sun fara ƙara. Cikin zafin nama Bilal ya fara isa wajensa, shi ma Dr ajiye alluran hannunsa ya yi suka nufi ɗan uwansu. Ajiyar zuciya Leesharh ta sauke, dan a tunaninta sun fasa yi mata alluran ne. Suna isa Dr ya fara aikinsa, shi kuwa Bilal cikin ƙaguwa da tsananin kaunar ɗan uwan nasa ya fara ambatar sunansa a hankali a cikin kunnensa. Kamar daga sama a hankali ya ji Ramish ɗin ya amsa da. "Yes blood". Wani irin annashuwa ne ya bayyana a saman face ɗinsu, wani irin sanyi suka ji, tsabar daɗi Dr bai san time ɗin da ta furta. "Yes, oh my god, Allah Alhamdulillah, Alhamdulillah!". Shi kam Bilal matsowa ya yi ya rungumi Drn, dan ya rasa ina zai tsoma kansa saboda murna. Sautin muryar Ramish ɗin yasa suka raba jikinsu da juna suna sauraron me zai ce dasu. Girgiza kai ya fara yi a hankali, idanunsa a rufe ruf ya fara faɗin. "Bilal don't let this people's to go anywhere, kill them all, the hut me to much.............." Bai ƙarisa maganar ba tari ta kwacemashi wanda ya yi sanadiyar waro idanuwansa da suke kamar wuta waje. A hanzarce ya mayar da idanun ya datsesu, saboda wani irin haske da ya kashe mashi idanu, ya jima idanun a rufe ruf shiyasa, ga idanun sun kumbura sosai sun yi jajir kamar ba waɗan nan idanu kyawawa irin na King ba. Da sauri suka yi kansa, Dr yana ce mashi ya yi shiru kada ya yi magana, shi kuwa Bilal yana gaya mashi ai bai bar mutanen sun tafi ba, ya kamasu dan haka ya kwantar da hankalinsa ya yi shiru kada ya sake yin magana dan kada ya ja wani ciwon ta tashi kuma. A hankali ya sake gwada buɗe idanun nasa. A wannan karon ma haske ne ta kashe mashi idanun, sai dai bai rufesu ba, ya barsu a buɗe har lokacin da haske ya ɗan washe, sannan ne ya fara iya ganinsu Bilal ɗin. Yana ɗaura ganinsa a kan Bilal ɗin ya sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, har cikin ransa ya ji wani irin sanyi ta ratsa shi na ganin ɗan uwan nasa, Dr Raj fa shi ne ƙaninsa da suke uwa ɗaya, amma ga dukkan alamu ya fi kaunar Bilal, bai yi farincikin ganin Dr kamar yadda ya ji wani irin sanyi lokacin da ya ɗaura idanun a kan Bilal ba. Hannunsa dake ɗaure da drip ya buɗewa Bilal ɗin. Da sauri ya kai hannunsa saman hannun Ramish ɗin suka haɗa hannu, saman shoulder ɗinsa Bilal ɗin ya damko tare da ɗan jijjigasa alamar ya cigaba da kasancewa da jarumtarsa, jinjina kansa Ramish ɗin ya yi alamar In Sha Allah jarumta a jininsu take, Dr Raj dai ya zama ɗan kallo, ya tsaresu da idanu kawai yana kallonsu. Ita ma Leesharh tv ta mayar da su, wani irin abu ta ji a kan Ramish ɗin, kura mashi idanun sosai ta yi tana kallon yadda yake magana ƙasa ƙasa da Bilal, wani irin jiri ne ta ji ya wani ɗebeta, ta rasa gane irin wannan wahalallen cakwakiya, kenan shi Ramish yana bala'in kaunar wanda yake neman rayuwarsa fiye da ɗan uwansa da suka fito ciki ɗaya ba tare da saninsa ba? Anya kuwa hakan zai yiwu? Ko da yake mutun fa ko ya mutu sai an ɗauresa, Allah dai yasa mufi karfin zuƙatanmu. Nan take Dr Raj ya hau kiran ƴan uwansu a waya yana sanar da su ɗan uwansu ya farfaɗo kuma ya farfaɗo ba tare da wata matsala ba, sai dai jikin ne da za'a cigaba da kula da shi har ya ƙara warwarewa. Murna a wajen su Yah Rizwan ba'a magana, Abbie yana jin wannan labarin ya baro office ɗinsa ya dawo gida, kan kace me gida ya cika tab da family, su uncle Rahab duk sun zo, Sharifat sai kuka murna ake yi masoyi ya farfaɗo. Duk wanda ya zo gidan sai ya tambayi wacece Leesharh? Tun Abbie nacewa Allah ne ya kara mashi kyautar ƴa bayan Sharifat har ya gaji da basu amsa. Mahaifiyar mommar Gimbiya Zunaira wato uwar gidan King Badeen ce da ta samu labarin Leesharh ta ce a kawo mata ita zata riƙeta, dan ita a yanzu babu wata ƴa a gabanta, su Obaid and Omaid ne kawai suke gabanta, su kuma kunga suna school, sai an yi hutu suke dawowa, ko sun dawo kuma Tunisia suke tafiya yin hutunsu, basu wani zama da ita, dama tana neman yarinya mace dan su rinƙa zama a tare tana ɗebe mata kewa, idan baku manta ba Momma ce kawai yarta mace dama. Nan fa Abbie ya ce shi dai a'a bai yarda ba, a barmashi ƴar marainiyarsa ya riƙe abarsa, ba yadda ba'ayi ba ya ce ina Leesharh shi zai riƙeta. Yadda ya kafe a kan babu in da zata je ne yasa Ummie ta ƙara tsananta zarginta a kansa, wani irin bakinciki ne ya rufeta, faɗi take wlh ko zata mutu sai ta san ta yadda zata yi Leesharh ta bar mata gidanta. A takaice dai Leesharh ta yi tarin masoya, da alama tana da farinjini sosai, kowa son ɗaukarta yake yi Abbie ya hana, Ummie ce dai kaɗai bata sonta. Kwana uku a jere family suna tururuwar zuwa duba jikin Ramish, a kwana na ukun ne ya tashi, dan ya ce kwanciya ta ishe shi, ya ɗan samu karfi ya tashi, yana tashi kuma ya fara shirin komawa bakin aiki, ba yadda basu yi da shi ba ya ce ina dole ya koma bakin aiki, dole a koma bakin rai bakin fama. In takaice maku dai dole suka haƙura suka kyalesa, dan sun san kome zasu ce sai fa ya koma kamar yadda ya yi niya. Leesharh kuwa ta samu lafiya sosai, dan Bilal yasa Dr Raj ya bata kulawa sosai. Daga haka suka koma bakin aikinsu kamar yadda suka saba, batun zuwa ƙasar Tunisia dai sun shafeshi, sun ji labarin harin da aka kaiwa King, amma jin cewa daddyn nasu ya yi nasara sai suka ce to ai ba sai sun je ba, suka cigaba da abin da suka saba yi............✍️🔥 _________________________________🔥 KINGDOM OF POWER.💪🔥💘 Mu koma mu duba yadda aka yi Hoorain ya fita daga cikin gonar nan bayan an kai masu hari!!. Fafatawa ya fara yi da mayakan nan, yana kashesu wasu suna shigowa, abin mamakin kuma duk wani warriors da zai shigo wajen Auta kawai yake hara, ita kaɗai suke son kamawa, abin tun bai dami Hoorain ɗin ba har ya fara ɗaure mashi kai, meyasa shi basu kawo mashi hari sai ita? Ya jefawa kansa tambaya. Wani mayaƙi ne da ya kusa cin galaba a kanta a in da ya zo datse mata wuya Hoorain ɗin ya kare mata da nasa takobin, amma duk da haka sai da wukar ta taɓata a saman shoulder ɗinta, ya yanketa sosai, hakan yasa ta kurma ihu mai sauti, kan kace me jininta ya fara bulbula daga wajen. Haba idan ran Hoorain ya kai dubu to fa ya ɓaci a wannan lokaci, wani irin tafasa da zuciyarsa take yi mashi ne yasa a tsananin fusace ya ɗaga takobin nasa ya raba wannan warriors ɗin gida biyu, nan take ya fara yi masu yakin a haukace, kashe su kawai yake yi tamkar mai kashe karnika ba mutane ba, ransa ya kai kololuwan ɓacin rai. Da suka ga ya haukace masu kisa kawai yake yi babu kama hannun yaro sai suka fara yin ta kansu, kowa ya fara gudun cetan ransa. Bai bi ta kan Autar ba ya raka warriors ɗin da gudu yana yi masu kisan ƙasƙanci da walaƙanci, pata pata ya rinƙa yi masu ɗaya bayan ɗaya sai da ya tabbatar ba mai shaƙar iskar numfashi a cikinsu, sannan ne hankalinsa ya dawo jikinsa. Jefar da takobin nasa ya yi ya nufe ta da gudu, tana zube a saman gwiwowinta, ta riƙe in da aka yanketa ɗin tana kuka hawaye tamkar ruwa ya ɓalle hanya ya fita, kunsan a guje zai fita ai, haka hawaye ke tsere a saman face ɗinta. A guje ya taho, yana zuwa ya zube gwiwowinsa a ƙasa a gabanta tare da kai hannunsa ya riƙo hannun nata. Yadda jininta ke zuba ba ƙaramin ɗaga mashi hankali ya yi ba, jikinsa har wani tsuma yake yi ya kai hannu zai rago rigar jikinta ya ɗaure mata hannun nata. Ai a ɗari ta riƙe rigarta da ɗayan hannun nata tana girgiza mashi kai a kan bata so kada ya yaga mata riga, dan an fara kirgan dangi kar ya kalle mata kayanta. Bai yi mata musu ba ya sake mata rigar tata tare da miƙewa ya ɗauketa cak suka nufi saman kujeran King, zaunar da ita ya yi, sannan ya kama sket ɗinta zai yaga, nan ma a hanzarce ta riƙe ta hana shi. Miƙewa tsaye ya yi, ya shiga tashin hankalin da ta haifar mashi da ruɗu, ji yake ana caka mashi wuƙa mai kaifi a ƙawon zuciyarsa, ita aka yanka da wuƙar amma zuciyarsa tafi tata jin raɗaɗin hakan. Matsawa daga in da take ya yi, can gefe in da ba zata iya ganinsa ba ya nufa, yana jinta tana kuka tana faɗin. "Hoorain kada ka tafi ka barni, dan Allah ka dawo tsoro nake ji". Sam bai kulata ba, ya tafi abinsa, zuciyarsa na ƙuna. Sai da ya tabbatar ya ƙurewa ganinta sannan ya dakata a bayan wata bishiya, cire rigar mayaka dake jikinsa ya yi ya ajiye a gefe, nan take wani farar single ta bayyana a kakkarfar kyakkyawar surar jikinsa, tamkar yanzu ya ɓare single ɗin daga ledarta, haka ya cirota ya ajiye a gefe, sannan ya ɗauki kayan yakinsa ya mai da jikinsa. Single ɗin ya ɗauka ya koma in da take. Farar single tas haka ya sanya cikin wannan jini nata ya ɗaure mata hannun, saboda zubar jinin ya yi yawa, sai kallonsa take yi tana kuka, sam yaki yarda ya ɗago su haɗa idanun, duk jikinsa jini shi ma, dan ya yi kisa ba karya. Yana gama ɗaure mata ya miƙe ya nufi gate ɗin gonar, still dai a rufe. Haurawa ta saman katanga ya yi ya dira baya ya barota a ciki. Wani jibgegen dutse ya ɗauko, kwaɗon dake jikin gate ɗin ya zo ya fara duka da wannan dutse yana son ɓalleta. Duk wasu warriors a wannan lokacin suna harabar Kingdom ɗin, hakan yasa har ya ɓalle kwaɗon ba wanda ya gansa. Allah ma yasa kwaɗo guda ɗaya suka sanya, sauri yasa basu rufe gate ɗin da kyau ba, da kwaɗi 6 ake rufe gate ɗin da su, sannan a sanya mashi kuba, to tsabar sauri ko kubar ma basu sanya ba saboda sauri. Ya yi sa'a yana ɓalle kwaɗon gate ɗin ta buɗe, godiya ya yi ga Allah, sannan ya nufi in da take. Yana zuwa bai yi magana ba ya saɓeta sai saman shoulder ɗinsa, da alama yana cikin matsanancin ɓacin rai, dan yadda yake taku ma zaka fahimci ran maza fa a ɓace yake. A hanyarsa ta nufa cikin kingdom ɗin ma sai haɗuwa yake yi da warriors ɗin Queen Zarina, abin da ya kara kona mashi rai ya sanya shi fafata yaki cikin fushi kenan, duk mayakin da ya kama wani irin kisan walaƙanci yake yi mashi na ƙin karawa. Da kyar da suɗin goshi ya iya samun dama ya ƙariso kusa da cikin harabar kingdom ɗin da ita, a maimakon ya bi ta hanyar da zata sada shi da cikin harabar, sai ya kauce hanya, da yake kingdom ɗin tana da girma kuma tana da kofofin sirri sosai a cikinta, sannan a matsayinsa na assistant commander kuma wanda ya yi wasan kasansa a cikin kingdom ɗin ba wata hanya ta sirri da bai sani ba, dan haka sai ya ɓad da kafa. Yau har cikin family part ya shiga da ita amma ta kofar baya. Yana shigowa ta kofar baya ya hango King Zuhair yana fita ta kofar gaba, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da yiwa Allah godiya da Allah yasa babu wanda ya kamashi ya taɓa jikin Gimbiya har ma ya ɗauketa, da sun yi katari da King ai shikenan kwanansa ta kare, dan da ya shiga ɗari uku ba uku ba. Ciki ya shigar da ita, a dab kofar underground ɗin ya sauƙeta, sai shesshekar kuka take yi. Hannu yasa ya kwance mata single ɗinsa da ya ɗaure mata hannu da shi, sannan ya ce. "Ranki ya daɗe ki je ciki su momma suna wajen, nan shi ne mazauninsu a duk lokacin da aka kawo mana hari irin haka". Ya faɗa cikin kunar rai, har wani huci yake yi, da kyar ma ya iya yin maganar. Kura mashi idanu sosai ta yi, ya kawar da kallonsa bai san su haɗa idanu. Faɗawa saman faffaɗar kirjinsa ta yi tare da ce mashi. "Nagode sosai Hoorain, ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata, dan Allah kazo mu gudu wajensu momma tare kada ka je mutanen nan su kasheka ka ji?". Hannu yasa ya cireta daga jikinsa, yana tsaye kyam cikin jarumta. "A'a ranki ya daɗe, ki je kawai kekam, nima zan je wajen Abbona, In Sha Allah babu abin da zai faru, amma dole na fita yaki kam!". Kuka ta saka mashi mai sauti a kan ita ba zata yarda ya je yakin ba, dan kada a kashe shi a banza. Lallashinta dan dolensa ya fara yi, hankalinsa duk ya tafi wajen Abbonsa, da kyar ya samu ta yarda zata shiga ciki. Matsowa ya yi da kyar ya iya cire tiles dake wajen ya buɗe mata kofar sirrin da idan ba a cikin family kake ba ba zaka iya sanin wannan waje akwai kofa ba, shi ma dai kasancewarsa zakara abin alfaharin KINGDOM ɗin ne yasa King ya yarda da shi sosai haka har yasan duk wasu kofofin sirrin dake masarautar. Tana kukan bata son rabuwa da shi haka ta shige ciki, tsayuwa ya yi yana kallonta, tana tafiya tana waigoshi har ta kurewa ganinsa, sannan ne ya mayar da tiles ɗin ya rufe bayan ya rufe kofar cikin kenan, ya miƙe tsaye cikin zafin nama, jininsa na tafasa ya nufi waje. A nan ne fa ya je ya ƙarawa mayaƙansu kwarin gwiwa a in da suka shiga fillin daga gadan gadan har ya taimakawa Abbonsa. TO KUN JI ABIN DA YA FARU, MU KOMA KAN LABARINMU. Alhamdulillah kingdom of power dai ta yi nasara a wannan yakin, sai dai sun rasa mayaka a kallah guda ɗari, amma gaskiya sun yi namijin ƙoƙari ba kaɗan ba, dan kuwa irin wannan yakin da aka shammacesun ai ba wanda ya yi zaton ma zasu yi nasara, sun ɗin jajirtattune na haƙiƙa gaskiya. Bayan komai ya lafa ne kowa ya fara neman ɗan uwansa, mayanƙan Queen Zarina da suka kama kuma sai suka watsasu cikin gidan yarin masarautar sai King ya zo ya yanke masu hukuncin da ya dace da su. Commenters and Hoorain suka ja ragamar duba mayakan da suka rasa da kuma ƴan uwan su wanenen, suka yi wa kowa adalci, suka ja ragamar har aka shirya mayakan aka kaisu makwancinsu na gaskiya. Commenters and Hoorain suna da ƙoƙari sosai, ga jajircewa matuƙa, duk suka juri ɗawainiyar kowa, waɗan da aka ɓarnatar masu da duniya ma sun tarasu waje guda a kan idan King ya fito duk zai fito da dukiya a mayar masu da abubuwan da suka rasa cikin aminci. A can ciki kuwa, sai da komai ya lafa sannan suka fito, Momma ce ta ja ragamar kula da su ita kuma, Akka dai ta ce a barta ta fita ta yi yaki, Momma ta rinƙa bata hakuri. Amma fa Aunty MieMie da mijinta sun gwabza, Allah kuma ya tsare babu abin da ya samesu, yanzu da komai ya lafa ne suka shigo family part, dai'dai lokacin suma su momma suka fito waje, duk a ruɗe suke saboda ganin Auta da suka yi da ciwo a jikinta, sannan an tambayeta ina su Yah Jawad da suka je nemanta? Ta ce ita bata gansu ba, me ya ji mata ciwo in kuma ta je? Nan kuma taki bada amsa, anyi anyi ta faɗi ina taje taki faɗa, da suka matsa mata ma sai ta ce masu ai daga part ɗin uncle Abbas ta fito, tana ƙoƙarin dawowa nan ne wasu mutane suka tareta zasu kasheta sai wani mayaki ya taimaka mata, taki yarda ta kawo ko alamar sunan Hoorain a cikin maganar tata ma bare har ayi zargin wani abin, sai ta yi ma kamar bata san da wani Hoorain a duniya ba. Uncle Taheer kanin mamane ya fara duba hannun nata zai yi mata ɗinkin wajen, sai kuka take yi, Momma kuwa ficewa ta yi daga part ɗin King da suke ɗin ta nufi fada dan ta duba mijinta, da sauri Aunty MieMie ta bi bayanta, dan ita ma daddyn nata kawai take son gani a halin yanzu. Mummyn Gimbiya Chuchu ne ta ce da uncle Taheer. "Attaheer ina su Jawad da chuchu ne?". Sai a lokacin suka farga suma basu dawo ba. Ita ma Momma ta je fada King bayanan, babu shi babu labarinsa. Ai idan hankalinta ya kai dubu to gabaɗaya ya tashi, nan take ta shiga ruɗu. Dakarun dake gadin fadan ta umarta da su kira mata commander Zafar yanzun nan. Aunty MieMie da yake irin matan nan ne masu zubin halittar ruɗani, nan take ruɗanin nata ya ninninka na momman, kun san akwai masu irin zubin halittar ruɗani, wanda ko hankalinsu a kwance idan suna magana sai ku gansu kamar a ruɗe suke, akwai su sosai a cikin mutane, to ita ma haka zubin halittarta yake. Commander na zuwa Momma ta gaya mashi dalilin kiransa. Cikin tashin hankali ya ce mata ai shi kwata kwata basu haɗu da King ba a wannan yakin, ai shi bai ma san King ya fito ba da ba zai barshi ya gwabza yaki ba. Nan take hakalin masarauta gabaɗaya ya tashi, ba'a ga sarki ba ai kunga ba zaman lafiya. Ba yadda ba'ayi ba Momma ta koma cikin gida kada ta fito wajen fada, amma ina taki yarda. A dokar Kingdom of power Queens wato Momma Mama and Mummy basu fitowa wajen fada, kullum suna cikin family part ko kuma iya fada kawai zasu tsaya, jama'ar da suke waje basa ganinsu, idan ma tafiya wata ƙasa ko wani garin zasu yi motor da zasu shiga akwai tinted, sannan daga cikin family part suke shiga mota, babu wadda ta taɓa fita waje a cikinsu. Amma yau ba yadda commander bai bawa Momma hakuri a kan kada ta fita za'a nemo King ɗin ba, amma ina taki yarda, gani take yi kamar ta fi su idanun ganinsa......... A hanzarce ta nufi kofar fita, gabaɗaya dakarun dake cikin fadar zaro idanun waje suka yi, dan sun san dokar masarautar, in ta fita tabbas King zai hukuntata. Dab zata buɗe kofar da zai sadata da wajen ne daga bayanta ta ji ance. "Kada ki kuskura ki yi wannan gangancin Rahilarh!". Ko bata juyo ba ta san mamallakin wannan muryar. Dan haka ba tare da ta juyo ba ta ce................ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 23/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 27 Ko bata juyo ba ta san mamallakin wannan muryar. Dan haka ba tare da ta juyo ba ta ce. "Gwaggo bayanan fa, bai dawo ba ne". Akka dake tsaye a bayan nata ne ta sake maimaita mata abin da ta ce tun farko a akan ta koma kada ta kuskura ta fita waje. Rai a matuƙar ɓace, ba dan ta so ba ta juyo, kofar da zata sada ta da cikin gida ta nufa rai a ɓace. Da kallo Akkar ta bita har ta wuce, sannan ta dawo da kallonta a kan su Commander dake tsaya, umartarsu ta yi a kan su nemo mata ɗanta, tana kai karshen maganar ta juya ta bi bayan Mommar. A parlon King suka isko family, kai tsaye room ɗinta Momma ta nufa, bata bi da kan kowa ba, bata jin kamar King ya rasu, infact bata jin kamar wani abin ma ya same shi, tana ji a jikinta yana nan lafiya lou, sai dai a ina yake to? Wannan shi ne matsalar. Hankalin kowa a tashe, dan sun sami labarin King fa baya fada. Gabaɗaya sun haɗe a main parlon har Aunty MieMie dukka. Mommar ma ta dawo parlon ta zauna shiru tare da buga uban tagumi. Akka dai babu ruwanta, hankalinta a kwance dan ta ce ita bata haifi tagwaye ba, dan haka ita jarumin jarumai ta haifa, kuma tana ji a jikinta yana nan dawowa, shiyasa kamar ba ita ta haife shi ba, bata wani damu ba. A dai'dai lokacin call ɗin uncle Jahiz ya shigo wayar Momma dake hannunta, sai a lokacin suka tuna da bayin Allahn nan. Picking ta yi tare da karawa a kunnenta. Daga ɗayan ɓangaren ya ce. "Amarya kullum amarya ce fa bakya laifi". Bata cikin mood mai kyau amma sai da ya sanyata sakin fuska kamar zata yi murmushi. "Ban san yaushe zaka canza ba Jahiz". Ta faɗa tana kallon Akka. Carap ya capki maganar da cewa. "Babu rana, ba zan taɓa canzawa ba har abada". Ɗan siririn murmushi ne ya kubce mata, idan baku manta ba ita da su King ƴaƴan gwaggo da ƴan kawune, akwai wasa sosai a tsakaninsu, shiyasa take yawan wasa da Jahiz bama dan kanin mijinta ba, ya haɗu da jini, har uncle Abbas idan kuka ji irin wasan da suke yi sai sun burgeku. "Momma since one hour ago fa muna airport, sai kiran numbers ɗinku muke yi bakwa picking lafiya?". Kai kallonta kan jama'ar parlon dake ta faman kallonta ta yi. "Wato kenan shiyasa ka fara da amayar bakya laifi ko? Saboda kasan mun yi laifin na barinku a airport, to muna bada hakuri yanzu za'a zo ɗaukarku". Cool murmushi ya saki, daɗinsa da Momma akwai saurin gane abubuwa. "Tom shikenan ƴar kanwata na yafe maki". Ya faɗa cikin zolaya. "Jahiz Allah ka fita idona, banson yin dogon magana yanzu, ka kyaleni haka, amma kafin nan ka sani ni dai na haifeka ba kanwarka ba". Kafewa ya yi a kan sam ita sister shi ce, dama sun saba tun kafin King ya aureta, sai ya ce ya fita shekaru, in ya je Dubai a gidansu yake tarewa dan neman magana, ya yi ta tsokanarta kawai, da kin ya aureta sai abin ya kara yi mashi sugar, ya ji daɗin yin tsokanar da hujja. "To shikenan dai ni kam, na yarda ke kanwata ce". Yana kai karshen maganar ya yi maza ya katse kiran dan kada ta ce ita yayarsa ce, hegen son girma ne da shi kamar me, wani lokaci ma sai ya ce uncle Abbas da kaɗan ya girme sa, bayan kuma uncle Abbas ɗin ya fisa da almost 15 years, shi fa 35 years yake da shi, ko aure bai taɓa yi ba, ga uncle Abbas da yake da Yah Rizwan mai 28 to 29 years, kunga ya kusa haifar Jahiz ɗin ma ai, amma sai son girma kamar me. Kallon uncle Taheer ta yi kafin ta ce. "Attaheer ka jagoranci zuwa ɗauko su Jahiz a airport". A hanzarce Mammien ta capki zancen da cewa. "Sun zo ne dama?". Kai Momma ta gyaɗa mata alamar e ba tare da ta yi magana ba. Wani shu'umin murmushi Mammien ta saki tare da wurgawa Aliyah dake zaune kusa da mummyn Gimbiya Chuchu wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, ita dai ta zage sai ta haɗa Jahiz da Aliyah aure kamar dole, Aliyah ta ce King take so ana dolene wai?. Tunani take yi tayadda zata haɗasu aure kafin ya koma Brazil, dan tasa baya taɓa wuce kwana biyu zuwa uku idan ta yi yawa in yazo. Jugum jugum suka cigaba da zama a cikin parlourn, Auta ta yi barci saboda alluran da uncle Taheer ya yi mata, kowannensu da abin da yake tunani, uncle Abbas ma yana hanyar zuwa, saboda ya ji labarin abin da ya faru. Muryar Yah Jawad ne ya karaɗe kunnuwansu a in da ya yi masu cikakkiyar sallama ta addinin musulunci. A ɗari kowa ya kai kallonsa kansu, tare yake da Chuchu, tamkar basu san anyi yaki bama, dukkansu biyu sun yi wanka, Chuchu kayan Gimbiya Fanan ce a jikinta, shi kuma Jawad kayansa, da alama akwai in da suka tsaya suka kwana har zuwa wayewan gari. Miƙewa tsaye Momma ta yi tana faɗin. "Jawad ina kuka je? Ina kuka tafi kuka sanya mu cikin tashin hankali da jimami, tun daren jiya bamu da nutsuwa, mun rasa kwanciyar hankali da walwalarmu, babu ku babu daddynku". Ƙarisowa cikin parlourn ya yi tare da sake hannun Chuchu da yake riƙe da shi, da alama ta sha kuka dan ga idanunta nan suna kumbure jajir da su. A gefen Auta ya zauna, a maimakon ya basu amsar da suke dakon ji daga bakinsa, sai ya ce. "Momma menene ya samu Auta?". Gabaɗaya parlon binsa da kallo suke yi, Mammien dai da yake bata so dawowarsu a raye ba sai ta haɗe rai, ta ƙasa hakuri da son jin daga ina suke ta ce. "Ana tambayarka daga ina kuke kana sake jefa mana wani tambaya?". Dawo da kallonsa a kanta ya yi tare da cewa. "Daga part ɗinki muke, a nan muka kwana". Wani irin ƙululun bakin ciki ne ya tokare mata maƙoshi, danasani ta fara yi na barin gate ɗin part ɗin a buɗe da ta yi, duk sai ta ji dama bata tambayesa ba, yanzu amsarsa ya ƙona mata rai matuƙa. Haƙiƙa Momma ta lura da cewa Mammie bata ji daɗin bayyanarsu a parlon ba, sai dai bata munana mata zato wajen tunanin ko bata sonsu ne yasa ba ko tana yi masu fatan mutu, sai ta kyautata mata zato ta hanyar cewa kila dan basu dawo da wuri bane sun wahalar da zuƙatansu wajen tunani ina suke ne yasa Mammien ta ji babu daɗi har alamar jin haushin ganinsu ya bayyana a saman face ɗinta. Mummyn Chuchun ce ta ce. "Kai amma masha Allah, Allah mun gode maka da ka kare mana ƴaƴan nan namu, Allah ka kara kare mana su da kariyarka a koma ina suke". Da amin dukka parlon suka amsa. Kuka Chuchun dake tsaye bata iya ƙarisowa cikin ba ta fara yi. Hankali a tashe Jawad ya tambayeta lafiya take kukan? Da kyar ta iya bashi amsa a kan saboda Auta take kuka. Hakuri ya shiga bata tare da gaya mata ai zata samu sauki. Ƙarisowa wajen Autar ta yi tare da kai hannu tana taɓa kumatunta tana mai cigaba da kwallah haɗe da sambatu ƙasa ƙasa. Akka ce ta ce. "Zo nan Jannat!". Da kyar ta iya miƙewa, kusa da ita ta je ta zauna, goge mata hawaye Akkar ta fara yi haɗe da lallashinta har sai da ta yi shiru. Mummyn Gimbiya Chuchu ta sake cewa Yah Jawad. "Jawad zama bai kama ku ba ai, domin kuwa daddynku bai dawo ba". Hankalinsa na'a kan Auta ya amsa da cewa. "Daddy ya tafi fillin kaka ai, mun haɗu da shi a lokacin da muke ƙoƙarin shiga part na dad". Momma dake ƙoƙarin komawa ta zauna ne ta dakata tare da cewa. "Alhamdulillah, Alhdulillah ya Allah, to Allah ya dawo mana da shi lafiya". Gabaɗaya suka amsa da amin, mummyn Gimbiya Chuchu har da sakin murmushi, nan take farinciki ya bayyana a saman fuskokinsu. Akka kuwa cewa ta yi. "Meyakai Zuhair wannan wajen? Shin harin da aka kawowa masarautar nan tana da alaƙa da wajen ne?". A hanzarce Jawad ɗin ya amsa da. "Gaskiya akwai alaƙa, domin kuwa daddyn ya ce mun saboda Spender suka kawo wannan harin, kinga kenan Queen Zarina ita ma a yanzu ji take yi ta kawo karfin da zata iya kwatar Spender a hannun daddy". Shiru gabaɗaya parlon suka yi, can Mammie ta ce. "Amma dama Spender baya gidan nan ne?". Da wani irin kallo Momma da Jawad suka bita, tambayar tata ya yi kama da na wadda take son a kwace Spender daga hannun King, yadda kuka san ita ce ma ta turo a kwace, dan yadda ta ce dama baya gidan ne ya yi kama da kamar ta gayawa wasu cewa yana gidan ne dama. Sai dai kuma duk parlon Momma da Jawad ɗin ne kawai suka lura da ita, ba wanda ya gane hakan. Akka kam ma sai cewa ta yi. "E Spender baya gidan nan, Zuhair ya kawar da shi daga nan saboda irin su King Abdulkarim". Shiru ta yi kamar mai tunanin wani abin, sarai Yah Jawad ya lura da yanayinta ya canza kamar bata ji daɗin cewa Spender baya nan gidan ba, sai dai bai kawo wani mummunar zargi a kanta ba..... Spender a hannun King Zuhair? Black Tiger ya kama Sweetie saboda bukatar Spender? Queen Zarina ta turo a kwatar mata shi ta karfin tsiya! Me alaƙar waɗan nan mutane da suka haɗe wajen buƙatar abu guda? Ainahi shi Spender na wanenen? Kuma a halin yanzu ina ma Spender yake? Yana hannun wanene? Mu je dai zuwa akwai rikici a gaba!. Shiru gabaɗaya parlon ya yi, can Chuchu ta miƙe tare da faɗin. "Mummy bari na je nayi wanka, kayan Aunty Fanan ɗin nan sun yi mun yawa, so nake in ciresu". Ɗan satar kallonta Jawad ya yi ta wutsiyar idanu, dama ya yi mamakin tun da suka shigo bata wuce nata room ɗin ba, dan ita ta takura mashi su dawo cikin ƴan uwanta dan ta yi kwalliya ta sanya kayanta, ba dan haka ba bai yi niyar dawowa yanzu ba, ya yi niya sai da rana zasu dawo, ya fi son ya ajiyeta ya yi ta kallonta yana samun nishaɗi kawai. Daren jiya kwana ya yi bai yi barci ba, zama ya yi tana barci yana gadinta, saboda gani yake kamar mayaƙan Queen Zarina zasu shigo su cutar da ita, shi bama ta kansa yake yi ba, ita yake tunawa, tana barci yana ta kallon face ɗinta, Allah ya gani yana kaunarta fiye da kansa, ko ganinta da ido kawai ya yi yana tsintar kansa cikin matsanancin farinciki sosai. Amsa mata da okey mum ta yi, da sauri ta wuce sai satar kallonta yake yi, shi fa baya gajiya da ganinta sam sam. Aneesa da Fanan ma a tare suka miƙe suka fita waje, suna fitowa Fanan ta ce. "Wai Aneesa ina Yah Jaish ne? Kwana biyu ban sanyasa a idanuna ba, ko ya yi tafiya ne?". Girgiza kai ta yi tare da cewa. "E to ya yi tafiya sai dai kuma na ji dad da momma suna magana a kan ansamu matsala a tafiyar tasa, in da ya ce zai je an duba baya can, babu kuma wanda ya san in da ya tafi, yana lafiya ko yana da matsala ba wanda ya sani, yanzu haka dad ya ce su Yah Ramish su fara binciken ina yake, momma kuma ta ce a'a ya bari zata sanya yayanta ya nemosa, hakan zai sa cikin ƙanƙanin lokaci a gansa". Idan baku manta ba na taɓa gaya maku cewa duk wani labari idan kana son sani to ka tambayi Aneesa zaka sami bayani dallah dallah kamar wata aljana, sai ka rasa a ina take samo gaskiyar labarai waɗan da babu alamar karya a cikinsu, komai yadda ya faru take faɗa, yanzu batun ɓacewar Jaish daga Momma sai Yah Jawad and Dad ne kawai suka sani, amma kunji ita har ta samu labarin da mamanta ma bata sani ba. Zaro idanu waje sosai Fanan ta yi, nan take ta yi narai narai kamar zata yi kuka, dan ita fa yanzu da gasken gaske take bala'in kaunar Jaish, bata san kudirin Mammienta na son haɗata aure da shi ba, abin da ta sani kawai shi ne tana son shi da iya gaskiyarta. Murya a karaye ta ce. "Innalilahi wa inna ilahir rajiun, hasbunallah wani'imal wakil, ya Allah a duk in da wannan bawan naka yake ka taimaka ka kare mana shi da kariyarka, ya ilahi ya lilliahi, wayyo Allah, dan Allah Aneesa duk halin da ake ciki dan gane da shi ki rinƙa sanar da ni kin ji?". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga face ɗinta. Sake baki Gimbiya Aneesa ta yi tana mamakin Fanan ɗin, dan ita bata san da cewa tana dakon son Jaish ɗin ba, abin da ta sani dai basu sonsa saboda mugu ne, iyakarta kenan, amma yau ga Fanan har da kwallah dan ance ya ɓata? A baya kuma ba wanda ya kaita zaginsa na cewa shi mugu ne bashi da imani, abin da mamaki. Shiru ta yi tana kallonta bata bata amsa ba har suka shiga cikin room ɗin Fanan ɗin, suna zuwa ta faɗa saman gadonta ta hau murzan kuka, mamaki ya hana Aneesa tambayar me ya sameta............ A ɓangaren Chuchu kuwa, tana shiga cikin ɗakinta wayarta dake saman bed ya fara ruri, a hanzarce ta ƙarisa wajen. My Yah Rizwan shi ne sunan da ya bayyana a samam screen ɗin. Jikinta har kerma yake yi wajen tsumayar ɗaukar wayar, ta yi kewarsa sosai. Picking call ɗin ta yi tare da kara wayar a kunnenta fuska ɗauke da murmushi. Cikin sanyin murya ya ce. "Assalamu alaiki my jannaty". Wani irin cool murmushi ta saki kafin ta amsa da. "My Yah Rizwan wlh na yi kewarka sosai, tun jiya fa ban ji daddaɗar voice ɗinka ba". Kamar zata yi kuka ta kai kashen maganar. Siririn murmushi ya saki tare da cewa. "Am so sorry my Jannaty, ni kai'na na shiga damuwa sosai na rashin jin voice ɗinki, amma ayi hakuri kada ayi mun kuka, fatana dai Allah yasa my baby tana cikin ƙoshin lafiya haɗe da farinciki?". Cool murmushi ta kara saki kamar tana gabansa kafin ta bashi amsa da. "Ina nan lafiya my noor, bari na yi wanka nazo mu yi hira ka ji?". "Okey ayi mun kwalliya sosai yanzu bai wuce saura 5 mins mu sauka a gida ba, kece burina da nake son fara yin tozali da kyakyawar face ɗinta kafin kowa, dan haka ki shirya mun sosai". Wani irin tsallen murna ta buga tare da ɗan yin kara ta ce. "Wayyo Allah daɗi, Yah Rizwan ni kai'na burina na yi ido huɗu da kai, kada ka cinye mun lokacina, bari na yi maka kwalliya na musamman ka ji?". Kana ganin face ɗinta zaka fahimci cewa tana cikin tsantsar farinciki mara misiltuwa, sai murmushi take yi baki ya ki rufuwa. Shi kansa sai murmushi yake yi uncle Jahiz na ta tsokanarsa, dan a tare suka taho, jirgi daban daban suka hau, amma kusan tare suka sauƙa, sai dariya uncle ɗin yake yi yana cewa Allah ya yi Rizwan ya fara soyayya, saura su Ramish, sai dai shi kansa uncle Jahiz ɗin bai san da waye Rizwan ɗin yake waya ba, shi dai ya gane da mace ce, kuma soyayya suke yi. Okey ya amsa mata da shi tare da katse kiran. Ɗaura wayar a saman bed ɗin ta yi, da gudu ta nufi toilet tana murna. A hanzarce ta shirya wankanta mai kyau, ta fito, cikin wani dandatsetsen doguwar riga mai matuƙar kyau launin purplish red, kayan ya yi matuƙar zama a jikinta, da yake calar tana da ɗan duhu sai hasken fatar ya ƙara fitowa sosai, umbrella gown irin na ƴaƴan sarakuna ne, haka ta ɗauko wani tsadadden alkyabbarta da ya sha kwliyar duwatsun gold, abaya ne na musamman wanda uncle Rahab ya saya masu ita da Auta iri ɗaya, yana da bala'in tsada saboda gold ɗin da yake ji, sai kyalli yake yi yana ɗaukar idanu, shi ta sanya a jikinta saman doguwar rigar tata. Wai my people's nace ba? Shin kunga chuchu a cikin wannan haɗaɗɗen alkyabbar kuwa? Ya ilahi, kyau kam ya fita tsantsar fita, ta zuba perfume ɗin nan tamkar anyi ɓarinsa a jikinta, simple make up ta yi wanda zai ƙara fito mata da natural beautynta, lips balm ta sanya ba jan baki ba, hakan sai ya ƙara fito mata da pink lips ɗinta tamkar ta sanya jan baki. Cover high heel ta ɗauko kalar alkyabbar tata wato golden color ta sanya a kyawawan kafafun nata, ya ilahi ta yi kyau my people's, Chuchu ta cika ƴar wankar kuwa da gaske, ba dan ba dan ba da sai in ce tafi Guyson ɗinmu iya ɗaukar wanka, sai dai Guyson ɗin ma fa ba baya ba, gwanine number ɗaya. 40 mins ta ɓata wajen yin wanka da shiryawa haka, da yake ta saba yi sai bata wani ɓata lokaci ba, idan baka saba bane zaka ɗauki lokaci mai tsawo, amma ita ƴan mintuna sun isheta. Jama'a ita da kanta ta san ta haɗu, kai duk wanda ya ganta sai ya kai zuciya nesa zai iya tsalle faɗawa tarkon sonta. A gaban dressing mirrornta ta tsaya, ta juya ta nan ta sake juyawa ta nan, sai dubawa take yi ina ne yake neman gyara ta ƙara gyarawa. Ganin ko'ina ya zauna dai'dai ne yasa ta ɗauko wayarta zata fara aikin ɗaukar hoton da ta saba, zuciyarta na can wajen masoyin nata wato Yah Rizwan, tunaninsa kawai take yi, tana son zuwa suga juna, amma ta tsaya ɗaukar hoto da yake abin ya zame mata jiki. Wajen hotuna kala goma ta kashewa kanta. Bayan ta gama hoton ma sai da ta sake ƙurawa kanta idanu a cikin mirror, sai ɗan jujjuya face take yi dan ta ƙara tabbatarwa da kanta yes ta yi kyau. Daga bayanta wajen room door cikin sanyin murya ta ji ya ce. "Jannat kin yi kyau har kin gaji da kyau, please kallon mirrorn nan ya isa haka kada ki kwashe mana kyan naki gabaɗaya". Lallausan murmushi ta saki. "Kai Yah Jawad ka barin na kalli kaina da kyau, dan kada na bar wani waje bai gyaru da kyau ba ya rage mun kyauna ko ma ya ɓata gabaɗaya". Ta yi maganar tare da juyo da kallonta a kansa cikin wani irin salo na rigima da yanga mai jan hankali. Bawan Allah ba da gangan ta yi mashi irin wannan salon ba, kawai rigima da yanga ce saboda ta ɗauki wanka. Shi kuwa wannan kallo da yadda ta juyo da yangar nan ne ta kara ruɗar mashi da ƙwaƙwalwarsa, ga shi ta yi kyau iya kyau, haba me Yah Jawad zai yi? Ai sai suman tsaye ya yi tare da ƙura mata idanu sosai. (Na ce ban gane ba! Yah Jawad ya da haka? Komai Chuchu zata yi wa Yah Rizwan sai ka riga shi sani da gani🙄 watarana ma ka wani shiga tsakaninsu suna waya ka dakatar ka sanya chuchu katse kiran, nace ya ne? Yanzu ta tsara mashi kwalliya a matsayinsa na mijinta ka zo ka wani rigashi gani a kan menene wai?😒 Rai na ya fara ɓaci da abin da kakewa Yah Rizwan namu na zamani fa🌝 kabarsu su shana tun da kai ka ɓoye naka soyayyar haba mana, ko ya kuka ce my people's, sai ya rinƙa wani shiga tsakaninsu haka ake yi ne? Yanzu dai ga shi ya riga Rizwan ganin wannan tsadaddiyar kwalliyar, wannan abin ya sakani kuka😥😌) Ganin ya kafeta da idanu ya kasa yin magana ne yasa ta ɗage dara daran idanun nan nata sama tare da yin wani irin fari da su mai ɗaukar hankali tana faɗin. "Yah Jawad wai kyau na yi maka ne da ka tsare ni da idanu haka?". Shiru bai amsa ba, dan baya tare da ita, ganin face ɗinta kawai yake yi yana hasaso gasu sun yi aure shi da ita........ Tab gaskiya da matsala idan har bai aureta ba, wlh idan aka hanashi ita da matsala, har wani hasasowa yake yi an ɗaura masu aure, toh gaskiya akwai matsala. Jin still bai amsa mata bane yasa ta sauko da idanun nata a kansa. "Yah Jawad!". Ta ambaci sunansa tamkar zata yi mashi kuka. Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da kawar da kallon nasa daga kanta izuwa ƙasa, ingazashi kawai zuciyarsa take yi a kan ya gaya mata abin da yake ransa kawai, dan a gaskiya yau ya ji ba zai iya hakuri sai ta ƙara girma ba, wani ɓangare na zuciyarsa ne ta ce mashi a'a ya bari ba'a irin wannan lokacin ya dace ya gaya mata ba, ya bari sai ya ɗauketa sun fita yawo sannan ya sanar da ita, hakan zai fi ɗaukar hankalinta. Aminta da hakan ya yi sannan ya dawo da kallonsa a kan nata, sai tura baki take yi wai yaki kulata dan haka ta yi fushi. "Jannat ke ɗin duniyar kyau ce, sannan ta musammance kuma ta daban". Ya faɗa can ƙasan maƙoshinsa ta yadda ita kanta bata ji me ya faɗa ba. Ganin sai turo mashi baki irin ta yi fushin nan take yi ne yasa ya tambayeta me ya faru?. Kin yi mashi magana ta yi, sai ma ɗan murguɗa mashi baki cikin yanga tare da juya mashi baya da ta yi ita a dole ta yi fushi. A hankali ta ji saukar hannunsa a saman shoulders ɗinta, ya ɗan rage tsawonsa tare da saita fuskokinsu suna fuskantar mirror, ta cikin mirrorn suka kurawa juna idanu babu ko kyaftawa. Gera guda ya ɗaga mata tare da kashe mata ido ɗaya. Ai bata san lokacin da ta manta da fushi ta saki ƙayatatcen murmushi ba. Shima ɗan siririn murmushin ya sakar mata. "Sarkin rigima kawai, yanzu me na yi maki da kika yi fushi?". Ɗan turo baki ta yi tare da juyowa ta shige jikinsa da kyau kafin ta ce. "Ina ta tambayarka na yi kyau ko ban yi ba kaki ka kulani, shiyasa na yi fushi". Matso da ɗan bakinsa saitin kunnenta ya yi, can ƙasa ƙasa ya fara yi mata raɗan kalamai masu daɗin gaske kamar haka. "Am sorry my sister, ke kanki fa kin san ke ɗin makura ce wajen kyau, meyasa zaki ɓata bakinki wajen tambayar kin yi kyau ko baki yi ba? Kin san cewa a kan kyanki faɗema ɓatawa ne amma sai ki rinƙa sanya mutun ɓata komai, babu wasu kalamai a duniyar nan da suka isa su zayyana yanda kyanki yake, duk abin da kika ji ana faɗensa to bai kai bane, abin da ya kai babu wasu kalaman da zasu iya zayyana shi, dan haka ke makura ce my lovely sister". Mata mu da shegen son a yabemu tuni wani irin farinciki na musamman wanda bata taɓa jinsa ba ya cika mata zuciya tab, hannu tasa ta rungume shi sosai tana murmushi. Bawan Allah duk ta sanya ya susuce kamar ba shi ba, tsabar iyashege kuma wai bata fahimci cewa sonta yake yi ba, ta ɗauka kaunace ta tsaknin yaya da kanwarsa, akwai matsala kam babba. Kasa yin wani kataɓus ya yi, kwantar da kanta a saman kirjinsa ta yi, ƙasa ƙasa ta ce. "Yah Jawad duk cikin yayyunmu Allah nafi sonka, kana da kirki sosai". Nisawa ya yi, ya ƙasa iya magana, saboda shi kaɗai yasan halin da yake ciki. Cigaba da yin maganarta ta yi. "Yah Jawad ina son kasancewa a tare da kai kullum, idan muna tare in jin daɗi sosai, kafi su Yah Rizwan sosai, kasan me?". Shiru bai amsa mata ba, hakan kuma bai hana ta cigaba da cewa. "A duk lokacin da muke tare sai in rinƙa jin kamar ba'a duniya nake ba, ko guduwar lokacin bana iya gani, kana ɗauke mun komai a duk lokacin da muke tare, ina manta kai'na da kai'na saboda farincikin Allah". Da kyar ya iya jan dogon numfashi tare da sauƙewa a hankali, yatsansa guda ɗaya ya ɗaura a saman lips ɗinta, alamar ta yi shiru, saboda ba zai iya cigaba da sauraren kalamanta ba, hakan yana kara jefa shi cikin yanayi, dama a kullum yana addu'ar Allah ya tsareshi kada ya wuce gona da iri idan suna tare, Allah yasa kada ya yi abin da zai sa ta dai'na ganin girmansa, shiyasa baya son jin kalaman nata, saboda daɗinsu suna ratsa ƙashi da ɓargonsa. Ita kuwa da bata san a wani hali yake ciki ba, sannan a yaya mafi soyuwa a gareta ta ɗauke shi, sai ta buɗe baki ta sanya hakwara ta kama yatsan nasa tana ɗan cizawa a hankali. Ai bai san lokacin da ya furta wash da karfi ba, da sauri ya rabata da jikinsa, lumshe idanu ya yi kamar wani mara lafiya, kasa iya riƙe kansa a tsaye ya yi, dan jikinsa tamkar wadda aka zarewa laka, dan haka sai ya koma saman bedside drawer ɗinta ya zauna yana cigaba da lumshe idanu tare da shaƙar daddaɗar kamshin perfume ɗinta da ya gauraye ko'ina a ɗakin. Yana zama kuma Momma tana shigowa cikin room ɗin nata, Allah ya taimakesa, da kuwa yau zai sha faɗa a wajen Mommar, dan kuwa dama ta gaya mashi yanzu ya sani son Jannat da aure yake yi, dan haka ta tashi daga kanwarsa, duk wani rungume rungume da suke yi na oyoyo tsakanin yaya da kanwa to ya dakatar da shi, in kuma ba haka ba ba zai ga da kyau ba, sosai dai ta yi mashi faɗa, amma bai ji ba, to dai Allah ya rufa mashi asiri yana raba jikinsu Mommar ta shigo. Ganinsu a tare yasa Mommar ta fasa yin abin da ya kawota, dama wajen Chuchun tazo zasu yi magana a tsakanin uwa da ƴa, amma da ta ganshi a ɗakin sai kawai ta juya, dama room nata zata wuce ta biyo nan, daga parlon King take. "Momma lafiya?". Da kyar ya iya jefa mata tambayar, muryarsa sai sarkewa yake yi. Jin yadda ya yi maganar yasa Mommar yi mashi kallon tsab kafin ta ce. "Babu komai, Jannat idan kin gama ki zo kin ji?". Tana magana tana kare mashi kallo. Ya fahimci ta gane wani abin, dan haka sai ya kawar da kallonsa daga kanta kawai, tunani ya fara yi a kan yau zai sha faɗa a wajenta in suka haɗu, dan bashi da kalaman kare kansa, sai dai fatansa Allah yasa kada ta yi wa Jannat ɗinsa faɗa. "To Momma". Chuchun ta amsa. Wucewa ta yi ta fita, ita kuma Chuchun ta zauna a saman mirror chair ɗin tana sakarwa yayan nata murmushi. "Ina zaki je ne ma da kika yi irin wannan kyalliya mai tsayawa Jawad a zuciya?". Ya faɗa yana ɗaure fuska alamar kishi ta motsa. "Yah Rizwan zan je in yi wa oyoyo". Ba tare da tunanin komai ba ya ce. "Shi ne sai an ɗauki irin wannan kwalliya haka tamkar zaki je neman saurayi ko mijin aure? To ban yarda ba, canza kayan nan ki sanya normal kayanki na gida, kuma ki saka hijabi, shi ne cikar mace ta gari". Fuska a ɗaure ya yi maganar.............. (My people's kun ji Yah Jawad da karfin hali, shi ya ganta da irin shigar da ta yi ɗin amma wai bai kamata kowa ya gani ba, yau ga ikon Allah.) Turo baki ta yi kamar zata yi kuka ta ce. "Yah Jawad na sha wahala fa wajen tsara wannan kwalliyar, please ka bari mana". Ƙara ɗaure fuska sosai ya yi tamkar bai taɓa yin dariya ba, alamar babu wasa fa. "A'a ban yarda ba, ki cire kayan ni sai na tayaki yin wani dressing ɗin". Sam bata san yin ja in ja da shi, dan tana jinsa a ranta sosai, kuma tana respecting ɗinsa sosai, hakan yasa tana tura baki ta nufi dressing room ɗinta. Mikewa ya yi ya bi bayanta yana faɗin. "Ni zan zaɓa maki kayan da ya dace ki fita da su". Sarkin kishi ba, yaga ta yi kyau sosai ne a cikin kayan shi ne bari yasa ta canza dan ma kada ta burge wani.............. Yah Rizwan ka yi sauri ka zo ga nan Yah Jawad zai ci amanarka ya yi maka kwacen mata. Wata simple gown wanda babu kwalliya a jikinta ya zaɓa mata, rigar mai tsada ce sosai, amma babu wani kwalliya da zai ja hankali a jikinta, ita ya bata dan ta sanya, sannan ya zari mayafin rigar ya miƙa mata. Ba dan ranta ya so ba ta karɓa ta wuce toilet, shi kuma ya koma saman bedside drawer ya zauna. Jim kaɗan ta fito, da yake ita ɗin kyakkyawace sosai kuma munafikin jiki ke gareta mai ɗaukar kowani irin kaya ya yi mata kyau, sai kayan ya yi mata kyau sosai. Ɗan dafe kansa ya yi tare da cewa. "Sister har yanzu dai kin yi kyau sosai, kamar kada na barki ki je nake ji". Turo bakin nan ta yi, a shagwaɓe ta ce. "Kai Yah Jawad wai ni kam me matsalarka da idan na yi kyau kada na fita ne?". A takaice ya ce mata. "Saboda ina kaunarki mana, dole na kula da ke". Da yake ya saba cewa yana kaunarta sai ta ɗauka yau ma irin dai kauna ta tsakanin yaya da kanwa ne, bata kawo komai a ranta ba sai ma cewa da ta yi. "Nima ai ina kaunarka". Wani irin sanyi ya ji ta ratsa mashi ƙashi da ɓargon jikinsa, miƙewa tsaye ya yi. "Zo mu je to in ɗan rakaki dan zan je wajen Aunty MieMie ce, ta ce nazo yanzu na sameta a part ɗinta mu tattauna, nace mata a'a sai naganki naga da kika cire kayan Fanan ɗin wani irin kwalliya kika yi". Guntun murmushi ta saki tare da ƙarisawa gabansa, hannunta ya riƙo suka nufi waje, har cikin ransa yake jin daɗin lallausan hannun nan nata yana ratsa shi. A dai'dai tsakanin part ɗin Momma da Mama ya saki hannun nata tare da manna mata sumbata a goshi, sannan ya ce. "To a gaishe da Yah Rizwan". Da okey ta amsa mashi, daga haka suka raba hanya, shi ya yi wajen Aunty MieMie ita kuma ta nufi wajen Yah Rizwan ɗin. Sai zumuɗin son ganinsa take yi, baki a ɗauke da ɗan siririn sallama ta shiga part ɗin uncle Abbas. Babu kowa a parlour, dan haka sai ta nufi part ɗinsu, already ta san a in da part ɗin yake. A bakin kofar shiga parlonsa ta tsaya ta yi sallama. Shiru ba'a amsa mata ba, sake yin sallama ta yi a karo na biyu, nan ma shiru ba'a amsa mata ba. Hakan yasa ta kutsa kai ciki kawai. Babu kowa a parlourn nasa face sanyi Ac haɗi da kamshin perfume dake tashi. Ajiyar zuciya ta sauke tare da nufar kofar master room ɗinsa. Dab zata shiga shi kuma yana fitowa manne da waya a kunne yana waya, ya ji alamar kamar anyi sallama a kofar parlour ne yasa ya fito dubawa. Karo suka ɗan yi ya ja baya kaɗan da sauri. Ita ma bayan ta ja a hanzarce tana sunkuyar da kanta ƙasa haɗi da ce mashi sorry. Subhanallah tsayuwa ya yi tare da zuba mata idanu yana kallonta, ya manta yana waya ne, ashe a hoto bai ga komai ba, yanzu ne ya ga madarar kyau, wai a hakan ma Jawad ya sa ta canza kwalliyar farko, da se yaya kenan?. "Yah Rizwan sannu da zuwa, ina wuni?". Ta faɗa kai a ƙasa. Subhanallah, ai ƙasa iya amsa mata ya yi, sai ma fitowa parlon da ya yi yana kare mata kallo da kyau da kyau, da yake yasan halinta da shegen son ace mata ta yi kyau, nan fa ya hau yabon kyanta da ya sanyata farinciki da annashuwa. Da hannu ya nuna saman sofa tare da cewa. "Zo ki zauna". Kamar wata bakuwa haka ta zamto, ba karya zuciyarsa ya kamu da matuƙar sonta. Zama ta yi sai faman ɓoye fuska take yi, haka kawai take jin kunyarsa saɓanin Yah Jawad da suke ƙurawa juna idanu suna karewa juna kallo. Saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna while ita tana saman mai zaman mutun ɗaya, sai satar kallonsa take yi, ya yi kyau cikin arab jallabiyar tasa, da alama bai jima da fitowa daga wanka ba, dan kuwa ga shin kansa da sauran danshin ruwa, alamu sun ya nuna wanka ya yi ya biya basussukan sallolin dake kansa. "A fili kuma kunyata kike ji my Jannaty?". Ya yi maganar idanunsa a kanta babu ko kyaftawa. Ƙara ɓoye fuska ta yi tana ɗan murmushi ta ce. "A'a kawai dai na ji ba zan iya haɗa idanu da kai bane". Ajiyar zuciya ya sauke. "Yanzu nake cewa zan shirya ya je part ɗin dad in sameki, idar da sallah na kenan". "Ai ba zan iya jiranka ba, ina marmarin ganinka, dama nasan zakazo ai shiyasa na yi saurin rigaka". Ta bashi amsa ba tare da kallon in da yake ba. "Wow ashe my wife ta girma sosai fa! Kai shi ne na tsaya yin sanya salon wani ɗan sarkin ya mun kwace, gaskiya da na yi shirme babba". Seriously ya yi maganar. "Kai yaya Rizwan ni fa yarinya ce". Ta faɗa a shagwaɓe.Ɗan leƙo face ɗinta ya yi yana faɗin. "E wato yau dai ba za'a ce mun my husband ba kenan ko?". Girgiza kai ta yi alamar a'a tare da cewa. "Zan kira mana" "To shikenan a kirani in ji". Hannayenta dukka biyu tasa ta rufe fuska tana murmushi ba tare da ta kira ɗin ba. "Kin gani ko? Ai nasan a waya ne kawai aka iya yi mun wannan soyayya, yanzu gani nan an ɓoye mun fuska, a barni naga kayana ma an hanani ni da fuskarta, kuma naga alama a iya waya kawai ake mun shagwaɓa yanzu ba za'ayi ba ko?". "Kai Yah Rizwan ni fa ban hanaka ganin face ɗina ba". "To meyasa aka rufe mun shi?". Zame hannayenta daga saman face ɗin nata ta yi tare da faɗin. "To ga shi nan na buɗe shi ka gani". Ta yi maganar tana ɗan turo baki alamar shagwaɓa. Habawa nan take ta ƙara tsunduma shi cikin gogin kaunarta. Zuba mata idanu ya yi yana rakon Allah da ya kara mallaka mashi ita, a gaskiya yana yi mata wani irin son da bai taɓa yi wa wani abin ba, yana jinta har cikin ƙarƙashin zuciyarsa. "My Jannaty". Ya ambata a hankali. Ɗan ɗago da kallonta a kansa ta yi, karaf suka haɗa idanun. Nisawa ya yi kafin ya fara magana. "Ina sonki my Jannaty, ina kaunarki sosai da sosai, da ban yi niyar maganar aurenmu a yanzu ba, ganinki kawai na zo yi, nace zan barki ki kammala secondary sannan na yi wa daddy magana, amma ganinki yasa na ji ba zan iya hakuri ba, gara kafin na koma na sanar da dad abin da yake a tsakaninmu, in yaso idan kin kammala koda Jss 3 ne sai ayi auren mu koma Dubai ki cigaba da karatu a can, please promise me that ba zaki bar wani ya shiga mun cikin zuciyarki ba, wlh ina sanki da dukkanin zuciyata..........". Dakatawa ya yi da yin maganar ba dan abin da zai gaya mata sun kare a bakinsa ba sai dan ya ji amsar da zata bashi kafin ya ɗaura mata da wasu maganganun. Har lokacin kallonsa naa kan face ɗinta. Ita ma bata kawar da kallonta daga kansa ba, sai dai bata kallon cikin idanunsa sosai, cikin sanyin murya ta ce. "Ina sonka Yah Rizwan, ina sonka sosai nima, kuma na yi maka alkawarin ba zan kula kowa ba, kuma ai kasan daddy ma baya barin wani ya zo wajen mu, ni bani da wanda nake so sai kai, kuma In ba zan taɓa son wani bayankai ba". Ji ya yi Dr Raj da suke waya da shi ya katse kiran, idan baku manta ba ya fito manne da waya a kunnensa yana magana, to ya mance da wayar ya afka duniyar soyayya, sai yanzu da Dr ya ji zancen nasu fa ba mai karewa bane ya katse kiransa abinsa. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa tsaye. "Wait for me ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da nufar kofar room ɗinsa. Sai a lokacin ne ta samu damar ɗaga idanu ta bishi da kallon tsab, bashi da wata maraba sosai da Yah Jawad, kana ganinsu zaka san ciki ɗaga suka fito, sai dai Jawad ya ɗan fisa hasken fata, kuma ya fisa tsawo duk da yake shi ne ƙarami. Ba karya tana jin son Rizwan ɗin sosai a ranta, ya iya kalamai masu kwantar da hankali........ Ni ma na iya yi wa my people's kalamai masu daɗi, ko me Rizwan zai yi a cikin ɗakin da ya wani shige, to ni dai bari na leƙa Jimeta Yola wata kila kafin mu dawo ya ɗauko abin da zai ɗauko ya dawo mu zo mu ji kalaman kauna!.😎 _________________________🔥🌹 NIGERIA________________JIMETA Wasa wasa dai haka rayuwar Jaish ta cigaba da kasancewa a cikin wannan ƙauye, jama'a sai gudunsa suke yi, shi kuma ko a jikinsa, Mahreeh tana cigaba da tsula tsiyarta sosai, Jaish kuma kullum sai ya shigar mata faɗa in dai ta tsokalo, baya gajiya saboda bappa. A hankali saboda shegen son faɗarta yana shigar mata yasa shaƙuwa ta fara shiga tsakaninsu, ya zama kullum in dai yana zaune sai ta zo ta zauna ta yi ta faman murɗe mashi arab hairnsa, bata gajiya, shima kuma bai taɓa hanata ba, har ta kai ta kawo idan bata taɓa mashi gashin nasa bama sam baya jin daɗi, ya saba da hakan sosai. Ita ma Mahnoor a yanzu ta dai'na tsoronsa, sai dai shakkar yi mashi magana kawai take ji, Mahreen kuwa har hira take yi mashi duk da baya gane ina take dosa a maganar tata har ta karesa. Hakika bappa ya yi farinciki sosai na sabon Mahreen da Jaish, dan kuwa ko ba komai a ganinsa zata sanya watarana ya buɗi baki ya yi magana. Nenne har yau har gobe tana gidan Arɗo, suna can suna ta faman shiryawa Mahnoor mugunta, a cewar Nennen idan ta dawo gidan sai Mahnoor ta mutu ko kuma ta ɓatar da ita. Ita kuwa baiwar Allah a kullum safe da yamma sai ta je ta gaisar da Nennen. Kamar kullun yau ma suna wajen kiwo, Mahreen da Mahnoor suna bakin kogin da suka tsinci Jaish suna wanke kayan sakawarsu, sai tiƙar wanki Mahnoor take yi ita kuma Mahreen ta zauna a bakin ruwa tare da tsunduma kafafunta a cikin ruwan tana wasa. "Adda Mahnoor kin san......... 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 25/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 28 "Adda Mahnoor kin san me?". Girgiza kai ta yi tana mai cigaba da matsan kayan da take wankewa. Sai wasa da ruwa take yi ta ce. "Su Hamma Salisun gidan Inna Rabi ne suka tareni ɗazun da zan je kwaso kayanan wankina a gida, wai sai sun dakeni, ni kuma na yi masu aljanun karya, kin ga yadda na yi wa su yayan Abu a hanyar islamiya ranar ko? Har kika yi ta kuka kamar zaki mutu kina cewa na tashi ba?...........". Ta dakata da yin maganar tana dawo da kallonta a kan Mahnoor ɗin, dan ta ga shin tana sauraronta ne ma ko dai ta shareta kamar yadda ta saba. Aikuwa hakan ce, ta shareta kamar yadda ta saba tana cigaba da dirzan kayan nasu tana ɗaurayewa da ruwan gudu. "Adda Mahnoor wai meyasa kike yi mun haka ne?". Ta faɗa tana ruro baki. Ba tare da ta kalleta ba ta amsa da. "To me nayi maki kuma?". "Sai mutum yana yi maki hira sai ki yi banza da shi". "Mahreen wai kunne ne yake jin magana ko ido da baki?" Still dai bata ɗago ta kalleta ba, aikin da yake gabanta kawai take ta faman yi ta yi maganar, sai haɗa uban gumi take yi saboda hasken rana da yake haskasu. "Kunnene yake saurara". Ta bata amsa tana turɓune fuska. "To masha Allah da kika fahimci kunnene yake ji, dan haka ki yi maganarki ina jinki". Miƙewa tsaye ta yi tare da cewa. "Na fasa gaya maki ma, kuma wlh yanzu zan kai ki kara wajen Hamma, kin san cewa ni nafi son idan ina magana a rinƙa kallona ana amsa mun da e e e haka, amma ke kullum sai ki mayar da mutun ɗan iska ya yi ta yin magana shi kaɗai baki ko ɗan cewa e ina jin nan, sai ki wani ce ai kunnene mai ji dan haka kina jina, da ga yau ba zan sake yi maki hira ba". Tana kai karshen maganar fuuuuuu kamar wata kumfa ta wuce izuwa wajen su bappa. A hanzarce ta miƙe tana ihun sunant Mahreen!! Mahreen!! A kan ta dawo zata saurareta kada ta kai ta kara, amma ina fuuuuu ta wuce. Ganin ta rigada ta tafi ne yasa ta koma ta zauna tare da cigaba da abinda take yi. Jim kaɗan sai gata ta dawo hannunta sarƙafe a cikin na Jaish, dole dole ta je ta takura mashi a kan ya zo yaga kogin garinsu yaga yadda suke wanki. A tunanin Mahnoor kararta ta kai wajensa shi ne ya zo rama mata, hakan yasa ta miƙe tsaye da ta gansu, sai uban gumi take haɗawa, kuma taki yarda ta cire hijabin jikinta, dan kada a kalla tana da tula tula, kullum tana kakabe da hijabi ba dare ba rana kamar wata mai takaba. Tana ɗago kai suka haɗa idanu da Jaish ɗin, ɗan zuba mata idanun ya yi yana kallon yadda gumi ya wanke mata fuska kamar wadda aka watsawa ruwa, ga wasu sai tsastsafo mata a gefe da gefen face ɗinta suke yi. Mayar da kallonsa a kan tulin kayan da yake gabanta ya yi, mamaki ne ya kamashi a kan wankin nata, lokaci guda kuma ya ji duk sun bashi tausayi, irin wannan aikin wahala da suke jibga, sau da dama idan ya fito da sassafe haka zai sameta tana tikar aiki komai sanyin safiya, abin da ya yi ta bashi mamaki da tausayi kenan, gata yar karama da ita amma bata da son jiki ko kaɗan, saboda tun tana karama aka horar da ita, jiki ya saba da wahala har in bata yi bama bata jin daɗi. Cikin rawar murya ta ce mashi. "Ka yi hakuri Hamma, wlh sharri Mahreen take yi mun ni ban yi mata komai ba, kuma nace tazo zan saurari hirar tata amma taki ta yi tafiyarta". Baiwar Allah a tunaninta ƙararta Mahreen ɗin ta kai, bata san cewa Mahreen kam tana zuwa da ta ga Jaish ta mance da cewa ƙara ta kawo bama, sai kawai ta hau zuba mashi rigima da shagwaɓa. Ɗan jinjina mata kai kawai ya yi, alamar ya ji me ta ce, daga haka ya mayar da kallonsa a kan ruwan dake ta gudu. Sau da dama Mahreen tana ce mashi ya zo ya shiga cikin ruwan amma sai ya ki, sai dai ya tsaya a bakinta yana ganin irin nisan tafiyar da take yi. Komawar da ta yi ta fara tikar wankin nata, sai shi kuma ya dawo da kallonsa a kanta yana mamakin ƙoƙari irin tata. Sosai ya jinjina mata. "Hamma kazo mu shiga cikin ruwa ka ji?". Cewar Mahreen sarauniya a son shiga ruwan kogi ta yi bulel. Kai ya girgiza mata alamar a'a shi ba zai shi ga ba. Turo baki ta yi kamar zata yi kuka ta fara yi mashi magiya. Kin yarda ya yi dan shi ruwar ma kyama take bashi, dan ma dai ruwan gudu ce kawai, ita ruwan gudu ai bata da datti. Zare hannunta daga cikin nasa ta yi, sannan ta sauƙo daga saman dutsen da suke, dan akwai tudun dutse tsakanin bakin kogin da gonakin mutane wanda idan baku manta ba a baya na gaya maku hakan. Da kallo ya bita yana jiran yaga me zata yi. Aikuwa tana zuwa bata yi wata wata ba ta daka tsalle ta afka cikin ruwan abinta. Tana afkawa ta lume ƙasa tare da toshe hancinta da bakinta wanda hakan ya yi sanadiyar dan dole Jaish ɗin ya bita cikin ruwan, dan a tunaninsa ruwan ya tafi da ita ya kuma fi karfinta ne, bai san cewa ita ɗin gwanace wajen shiga ruwa ba, ta saba, ruwan kuma ta can tsakiya tsakiya akwai zurfi sosai, ta baki baki in da suke wanki ne babu zurfi, amma can ta tsakiya ya kai tsawon Jaish ɗin a zurfi. Ku kanku kun san ruwan da zai kawo Jaish wannan gari ba karamar ruwa bace ba. Wani irin dariya ne ya so kubcewa Mahnoor lokacin da ta ga Jaish ya tsorata ya bi bayan Mahreen a dubu dan kada ta mutu. A zuciyarta ta furta. "Ai in dai Mahreeh ce watarana sai ta sanyaka shiga cikin wuta ma ba tare da ka sani ba, kaɗan daga aikin wannan yarinya ƴar albarka". Shi kuwa bawan Allah haka ya zunduma tsulumdum cikin ruwan ba shiri, tana jin alamar ya tsundumo cikin ruwan ta ɗago kai a ɗari tana fitar da numfashi sama sama kamar zata mutu ƴar ƙaniya. Ƴan sakanni ta ɗauka tana jawo numfashinta da kyar da kyar, sai da ta dawo dai'dai ne ta daka tapi da ƴan tafukan hannayenta tana faɗin. "Na yi nasarar sanya Hamma shiga cikin ruwan nan". Ƙatsake ya tsaya yana kallon ikon Allah, Mahreen zata iya mayar da mutum ana yi mashi kallon mahaukaci bayan yasan shi mai hankali ne, ita dai Mahnoor ta ɓoye fuska ne tana yi masu dariya, shi ma bappa da tun kafin Mahreen ta faɗa cikin ruwan yake tsaye a bayansu yana kallonsu dariya ya shiga yi masu, Mahreen da karfi da yaji tana son mayar da Jaish irinta, in dai zai cigaba da biye mata tsab watara za'a kirasa da abin da ya fi maye a wannan ƙauye. Haka nan ya fito tsamo tsamo daga cikin ruwan ya yi sharkaf yana zuban ruwa, sai dariya bappa yake yi mashi, ita ma Mahnoor ta ɓoye fuska dan kada su haɗa idanu ko ya ganta tana yi mashi dariya, ita kuwa hajiya Mahreen tamu a bayyana take yi mashi dariyar tana murna tare da faɗin ta yi nasarar sanya shi shiga cikin ruwan. Yana fitowa gida ya nufa ba tare da ya yi wajen bappan ba, dakatawa da yin dariyar da yake yi bappa ya yi, dan ya lura kamar ran Jaish ɗin ya ɓaci, sai dai kafin ya yi mashi wani magana tuni ya sa kai ya wuce............. Abin da baku sani ba my people's, Jaish ɗin nan fa ba Jaish da kuka sani bane, yes hakance kamar yadda kuka ji hakan dai na faɗa, ku kanku kun san Jaish na King Zuhair dai ba zai yi irin wannan abin da su Mahreen yana cikin hayyacinsa ba, to ya abin yake ne?. Wannan Jaish ɗin dai ga shi nan ne, shi kansa bai san wanene shi ba, rayuwa dai yake a tsakanin mutane da kuma mutuwa, a halin yanzu dai iya cema ku zan yi bai san wanene shi ba, baya iya buɗe baki ya yi magana, ga dai shi nan babu wanda ya san hakikanin abin da yake damunsa, saboda babu wata asibitin da aka kaisa bare a san damuwar da take cikin kwakwalwarsa, kawai dai yana rayuwa ne. Sai dai kuma akwai ɗabiunsa da dama wanda har yau har gobe suna a tare da shi, which means da su aka haifesa kenan, irinsu kyamar abu, rashin son magana, shariya, halin ko in kula, izza, isa da taƙama, da dai sauransu, bayan su duk wasu dabi'un da ya ɗaurawa kansa daga baya ya watsar da su. To me ya sameshi? Meyasa baya magana? Meyasa har yau har gobe idanunsa da suka kasance fararetas kamar madara an lalatasu izuwa jajir kamar wuta? Meyasa suka ki washewa idanun? To mu je dai zuwa, alkalamina zai warware maku komai, amma wannan littafin akwai cakwakiyar da ni kai'na suna sanya ƙwaƙwalwata ɗaukar zafi, sai na yi da gaske wlh, amma idan ba haka ba kowani ɓangare da rikicinsa mai zafin gaske, mai kuma bala'in ɗaure kai. Bayansa bappa ya bi, dan ya lura sam bai ji daɗin abin ba, sau da dama idan Jaish ɗin ya yi wani abin bappa yana yi mashi kallon kamar jinin sarauta ne shi ɗin, saboda su basa ɓuya, a jininsu izza take, hakan yasa bappa yake yi mashi kallo duk yadda aka yi ya haɗa alaƙa ta jini da sarauta, ba'a haka ɗai watarana idan izzansa suka motsa yake zuba masu mulki ba, bappan baya hana shi ko ya ce mashi ya rinƙa sassautawa, dan yasan su fa a jininsu abin yake, ko ya yi mashi magana ba dai'nawa zai yi ba, sai dai ya wahalar da kansa a banza kawai.............. Dama da ni da ku kam my people's ai mun san halin Jaish namu na gaskiya, watakila laluran da yake ciki ne ma yasa ya yiwa su bappan saukin kai wallahu ahlam, amma dai mu je zuwa koma menene zamu sani ai. Dap bappa zai shigo gida ita ma Nenne tana shigowa, da mamaki cike a ransa yake kallonta, da bakkwan kayanta da komai ta tattaro ta dawo, sai dai da ganin face ɗinta zaka iya fahimtar akwai abin da take tafe da shi, da alama akwai zantuka a bakinta. Sannu da dawowa kawai bappan ya yi mata, tsabar makirci irin na mace har da tsugunnawa ta yi ta kwashi gaisuwa haɗe da bada hakuri. Kai mata duniya ne, muna shagalinmu wlh, mu dai ɗuwawune dole a zauna damu ko anki ko anso..........💃🤸 Mamaki ne ya kara kama shi, amma bai kawo komai a ransa ba, bawan Allah ya karɓi kayan hannun nata da take tafe da su suka shiga ciki yana ta yi mata sannu da dawowa. Haƙiƙa bappa ya kaunaci maman Mahnoor a rayuwarsa fiye da tubaninku, su bama haɗasu aure aka yi ba, soyayya suka yi har zancen ya kai ga iyaye, Nenne ba ita ce zaɓinsa ba, amma rashin maman Mahnoor ɗin yasa ya hakura ya karɓi Nenne, dan gara mashi ita a kan bare, yana kaunar Mahnoor sosai, dan idan ya ganta tana ɗebe mashi kewar mamarta, hakan yasa ya yarda ya karɓi auren Nennen, dan a tunaninsa zata kula mashi da ita tunda ƴar ƴar uwarta ce, bai san ya makaro ba, dan kuwa kamar yadda iyayensu wato su gwaggo basa shiri basa zaman lafiya haka su ma Nenne da maman Mahnoor ɗin ma basa shiri, dan kowacce tana taya mahaifiyarta kishi, tun suna ƴan'mata ake buga gaba, kunga kuwa Nenne zata iya sauke haushin mamarta da take ji a kanta, matsalar ta samo asaline daga irin zaman kishin da ake yi a gidan Arɗo, shi ne yasa babban kuskure ne ku yi zaman kishi a gaban ƴaƴanku suna gani, hakan ba ƙaramin gurɓata masu tunani da tarbiya zai yi ba, zaku zo ku aurar dasu da nufin hankulanku da nasu ya kwanta ku samu nutsuwa, amma sai ku gaza samun hakan, saboda irin zaman da kuke yi ya gurɓata masu tunani, to dan Allah ku rinƙa sassautawa a gaban yara ko dan gobensu ya yi kyau, ku aurar da su ku samu kwanciyar hankali da nutsuwa, suma su ɗauki duniya da sauki, yanzu dai kunga aya illar yin irin wannan zama a kan Nenne da mahaifiyar Mahnoor, aka ce idan gemun ɗan uwanka ya kama da wuta sai ka yi maza ka shafawa taka ruwa, Allah yasa mu dace!!. Suna shigowa ɗakinta ta wuce, da alama dai har yau har gobe akwai tsoron Jaish a ranta. Ɗaki bappa ya bita da kayan, bayan ya ajiye mata ya wuce nasa ɗakin izuwa wajen Jaish ɗin, ko sannu bata sake ce mashi ba bare ta tambayi ina zai je, dan magana ta gaskiya ita ma bappan ba shi ne zaɓinta ba, tana da nata saurayin, suna tsaka da soyayya aka rabasu wai dan ta auri bappa ta kula da Mahnoor, kunga kuwa ko dan haushin rabata da saurayinta ma ba zata bar Mahnoor ɗin ba, ta dinga azabtar da ita kenan dan ta huce, kun san shi fa so mugun abu ne wani lokaci, sai ya iya saka ka yi kisa a kan abin da kake so ba tare da ka sani ba. Da kallo ta fara bin ɗakin nata da shi. Duk tsawon lokacin nan da ɗauka bata nan wlh kullum sai baiwar Allah Mahnoor ta share mata ɗakin ta gyara shi fes, abin har ɗan mamaki ya bata, amma da yake kishi da bakar zuciya sun rufe mata ido da kuma zugin gwaggonta, ga ɗan banza jahilci a cike da kai, dan ita ko karatun addinin ma bata samu ba, gwaggonta mayyar son kuɗi ce, tun tana yarinya bata barta ta samu ilimin addini ba, yara rabi duk su tafi islamiyya amma ita kuma da sauran yaran da iyayensu ke son kuɗi sai a ɗaura masu tallar nono su tafi, haka ta taso kan fanko babu komai sai shirme da wauta, shiyasa da zarar gwaggon nata ta kitsa mata wani abin tsab zai shiga kunnenta ya yi kane kane ya yi tasiri. Ba abin da take tunani face kudirin da ya dawo da ita gidan, a burinsu na son suga sun ƙuntatawa Inna kakar Mahnoor ɗin zasu je su jefa kansu ga halaka. Shi kuwa bappa nasa ɗakin ya shiga, kwance ya isko Jaish a saman gado ya yi flat tare da ɗaura hannu ɗaya a saman face ɗinsa tamkar mai yin barci, sai dai idanunsa biyu, ya canza kaya ne ya kwanta. Kusa da shi bappa ya zo ya zauna tare da fara ambatar sunansa da Hamma Hamma kamar yadda su Mahreen ke kiransa. Kada ku manta shi kansa bai san wanenen shi ba bare har ya sanar da su sunansa, so sai kawai suka sanya mashi Hamma!. Shiru bai motsa daga in da yake ba, dama idan jiji da kan mulki jinin sarautar tasa ta motsa sai ayi ta yi mashi magana yana ji amma ba zai motsa ba bare ya nuna alamar ya ji me suka ce, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa bappa yake zargin ko dai shi ɗin jinin sarauta ne, ya iya miskilanci da shegen izza na karshe. Lallashinsa tare da bashi hakuri sosai bappan ya fara yi, dan ya fahimci tabbas ransa ne ya ɓaci, wato fushi yake yi yanzu kenan. In short bappa ya ɗauki almost 40 min a wajen yana yi mashi magana, amma ɗan tahaliƙin nan yadda kuka san mutum mutuminsa ne aka sassaka a wajen, ko ɗagowa ya kalli bappan yaki, duk da dama can baya yarda su haɗa idanu da shi, amma ko motsawa daga in da yake yaki yi. Sai da bappan ya gaji dan kansa ya hakura ya rabu da shi, amma ransa bai so hakan ba sam sam, shi da burinsa a kullum Jaish ɗin ya saki jiki da su, ya zama kamar jini ɗaya suke kawai, amma sai ga shi yau Mahreen ta ɓata komai, abin ya ƙona mashi rai matuƙa. Miƙewa ya yi ya nufi waje, wlh idanun Jaish biyu yana jinsa, kawai ransa ne a ɓace, baya son ya yi wa dattijon nan wani abin da babu daɗi ne yasa ya danne zuciyarsa ya kuma riƙe harshensa, yasan yadda zuciyarsa take tafasa in bai yi da gaske ba wlh tsab zai iya dallawa bappan maruka, ku da kun san halinsa, to shiyasa ya kwanta shiru ya danne zuciyar yana jiran har ta sauƙa, kun ji dalilinsa na share bappan, ya yi kokari matuƙa gaskiya na iya danne zuciyar tasa. Gona bappan ya koma, kai tsaye wajen Mahreen da Mahnoor ya nufa, sai hira suke yi suna wanki gwanin birgewa. Yau karo na farko a rayuwarsa da ya fara yi wa Mahreen faɗa dan kawai ta sanya ran baƙonsa ya ɓaci. Tsabar mamakin hakan yasa Mahnoor miƙewa tsaye tana tambayarsa meyake faruwa?. Bai ɓoye mata komai ba ya gaya mata Mahreen ta ja Jaish ya yi fushi sosai, mamaki ne sosai ya kama ta sosai baiwar Allah, ita dai tasa wlh ko Arɗo Mahreen ta yi wa laifi bappan nasu baya taɓa yi mata faɗa, amma yau akan bare da basu san saga ina yake ba yake yi mata faɗa? Lallai wai wani irin kauna bawan Allahn nan yake yi wa Jaish ne? A gaskiya yana kaunarsa over, ku duba ku gani, kun san yadda fulanin daji suke kaunar dabbobinsu sosai, amma a haka bappa yake zubar da dabbobin nan nasa yana yankesu wa Jaish, a gaskiya ya nuna mashi kauna sosai, ya cancanci a jinjina mashi, yau a kansa aka yi wa ƴar gabar goshi, ƴar Auta, kuma ƴar zinarinsa faɗa? Lallai Jaish ya ciri tuta. Wlh haka yaran Momma suke da shegen farinjini da shiga rai, shiyasa ya shiga ran bappa sosai. Ita ma fushi ta yi da ya yi mata faɗan, fuuuuu ta wuce gida abinta, cikin raunin murya Mahnoor ta ce. "Bappa kaga ta tafi gida fa". Rai a ɗan ɓace ya amsa mata da. "Kyaleta ta tafi ɗin, yau wata da watanni ina ta shan wahala wajen ganin bakon nan nawa ya buɗi baki ya samu lafiya sosai, amma na lura Mahreen tana neman ta lalata mun komai, yanzu idan ta sanya yana shiga ɓacin rai komai ya zo ya lalace ya take son nayi?". "Ka yi hakuri bappap In Sha Allah zata dai'na". A sanyayye ta faɗa. Albarka ya sanya mata tare da juyawa zai koma cikin gonarsa, har ya fara tafiya sai kuma ya juyo. "Nennenku fa ta dawo". Ya faɗa fuska ba ya bo ba kuma fallasa. Ɗan zaro idanu waje ta yi tare da cewa. "Kai masha Allah, amma ba zata sake tafiy ba ko?". Wallahu a'alam ya amsa mata da shi tare da wucewa in da ya nufa. Cigaba da yi wankinta ta yi har izuwa azahar, ta kammala ta je ta shanyasu a farar yashin dake gefen kogin, sannan ta ɗauro alwala ta nufin in da bappan nata yake. Ga mamakinta sai ta iskoshi a tare da Mahreen suna ta zuba hira kamar ba ita ce ta yi fushi ta tafi gida ba, yanzu ta dawo, abinci ma ta kawo masu Nenne ta yi girki mai rai da lafiya yau, sai mamaki bappa yake ta yi, ita kanta Mahnoor ta sha madarar mamaki na ganin Nenne ta yi girki, ta kai tsawon shekaru 5 bata girki kamar matar aure a gidan, Mahnoor ɗin ce ke yi, yau rana tsaka ta yi girki abin da mamaki, amma duk basu kawo komai a ransu ba, suka ci suka sha, suka yi sallah, sannan suka zauna yin hira kamar yadda suka saba. Nasiha bappan ya rinƙa yi masu sosai mai ratsa zuciya, sai kuka Mahnoor ta rinƙa yi saboda nasihar ya taɓa mata zuciya sosai, bappa ya iya yi masu nasihar da ya kan sanyasu su ji duniya ma gabaɗaya ya fice masu daga ransu, bawan Allah ne sosai, uba ne na gari sosai. Ita kuwa Mahreen da harkar tsoro baya a tsarinta, idanunta a bushe garau ba ko alamar hawaye, kun san ita harkar jarumta ta tasani, sai kace wata renon Commander Zafar, idanu a bushe, komai nasihar da bappa zai yi masu, zai ratsa zuciyarta, amma hawaye? Tab baya fitowa daga idanun yarinyar nan, sai ka yi zaton ma bata da ruwan hawayen a duniya, amma akwaisu, kukan ne kawai ba za'ayi ba. Sai karfe uku Mahreen and Mahnoor suka dawo daga wajen kiwo, abin mamaki kuma yau Nenne dai bata yi masu tijarar da ta saba ba, salum alum suka yi wanka, suka ɗauro alwala, har da abinci ta basu suka ƙara ci suka ƙoshi, sai ɗari ɗari Mahnoor take yi da ita, dan bata taɓa ganin ta yi masu makamancin haka ba, ita dai tasan tsakaninta da Nenne duka, zagi da kuma hantara. Sai tunani take yi a kan to ko dai yau lafiya Nennensu take? Abin da ɗaure mata kai. Islamiyya suka nufa kamar yadda suka saba, yau bata hanasu tafiya da wuri bama. Ko da suka tashi daga islamiyyar sai da su Salisu suka biyosu da nufin su dakesu, duk da yayan nasu ya sami sauki saboda bakar zuciya sunki hakura sai sun ɗauki fansa. A hanya suka taresu, suka sha gabansu sun hanasu hanya. Mahnoor dai hakurin nan da ta saba shi ta shiga basu da wannan sanyayya muryar tata. Ita kuwa Mahreen Mahnoor na tsaka da basu hakuri kamar wata zararriya ta zunduma ihu tare da bajewa a ƙasa ta fara birgima tana watsi da wulli da kafafunta sama. Zaro idanu gabaɗayansu suka yi, da sauri Mahnoor ta tsugunna a gabanta, murya na rawa ta fara tambayarta me yake damunta?. Sam bata kulasu ba, ihun ta ta cigaba da yi tana birgima, sai da ta babbatar zuƙatansu sun gama tsinkewa, sannan ne ta wani irin girgiza jikinta yadda kuka san wata bujumar saniyar da aka zubawa ruwan sanyi, kunsan zai karkaɗe jikinsa ya yi wani irin girgiza ai? To haka ita ma ta yi tamkar mai wani motsi a kai. Zaro idanu suka yi suna cigaba da kallonta, da wani irin murya kamar na ƴan shaye shaye da suka jima a harkar murya ta gama lalacewa ta ce. "Kai Salisu zo nan gabanmu!!". Tun da Mahnoor ta ji haka ta gane iskancin da ta saba yi wa waɗan da suka fi karfin ta iya dukansu ne ta yi masu, dama idan ka fi karfinta, ta san cewa zaka iya dukanta sai ta yi masu aljanun karya, a haka take kwatar kanta a koma inane, lafiyar jikinta ne ba zata bari a taɓa mata ba yar albarka. Da farko Salisu dai an gwada jarumta, nunawa ya yi kamar baya tsoro har da wani ɗaure fuska sosai. "Ba zanzo ba, idan ma kai aljani ne to ka fito ina dai'dai da kai, ba kana ganin da safe kasa mun gudu ba? To yanzu aradun Allah babu in da zanje har sai na ci uban yarinyar nan". Wani irin zaro idanu waje ta yi tare da sake yin wani irin girgiza, sannan ta kara kausasa murya tare da yunƙurawa a haukace zata tashi tana faɗin. "To jiramu gamu nan zuwa!!". Habawa ai tana yunƙurowa da karfinta a guje Salisu ya watsa sai hanyar gida har wando na faɗuwa, takalma kam ba'a maganarsu, tuni ya watsar da ƴan banza, hege ko waye ya ce mashi barno a gabas take, ai Mahreen ba taya baya bace, kuma she's know how to act well well ƴar albarka, ji yadda ta taso fisabilillah har da wani cewa gamu nan zuwa, oh ni princess Teema ina ganin rayuwa wajen wannan yarinya, ko da yake jikar gwaggo ce fin haka ma idan ta aikata ba abin mamaki bane, dan faɗa dai kun gani da idanunku a jininsu yake, gwaggo ce ko bala'i, ga Nenne ma ta gado.......... Ni kam na ce to da ta tason nan in da Salisun bai gudu ba ya zata yi kenan? Ita dai tasan ba iya dukansa zata yi ba? Amma dai koma me yarinyar akwai bala'in karfin hali tare da sanyawa ranta koma me itace da nasara, bata tunanin ɓacin rana sam sam............ Na ce ba Allah ya haɗa mun ita da Obaid and Omaid, ƴan amin ku ce amin......🤣 Tana ganin sun gudu ta miƙe tsaye tare da buga tsalle tana faɗin. "Gobe ma ku dawo mana, na fiku iya shan kunun tsiya". Tana magana tana karkaɗe kasan da ya ɓata mata jiki saboda kwanciyar da ta yi a ƙasan.......... Oh ni ƴar mamata, har da kunun tsiya ma Mahreen take sha? Allah mai iko!. Ko sannu Mahnoor bata ce mata ba suka nufi gida, sai addu'ar neman shiriya a wajen Allah Mahnoor ɗin take ta yi wa ƴar kanwar tata a cikin zuciyarta. Suna shigowa suka isko bappa a tsakar gida yana gyaran harawa, sam basu ji daɗin rashin ganinsa a tare da Jaish ba, da alama kenan har yanzu zuciyar tasa bata sauƙo ba, kullum a tare suke komai da bappan, amma yau yana ɗaki yana kwance shiru, sai tafarfasa zuciyarsa take yi mashi. Shi kansa bappan zuciyarsa zafi take yi mashi na fushin da Jaish ɗin yake yi, haka ya shiga gyara harawansa shi kaɗai yana zubawa awakansa da suka kusa haihuwa ya tsamesu daga cikin sauran ya dawo da su cikin gida. Wajensa Mahreen ta nufa, ita kuma Mahnoor nonon da suka tatsa da safe suka ajiye shi a ɗakin bappa ya yi bacci dan ya yi kauri ta shiga ciki ta ɗaukowa. Ƙasa ƙasa ta yi sallama cikin natsuwa, yana kwance ko gezau bai yi ba. Wucewa ta yi ta ɗauko kwaryar nonon ta fito, dama haka suke yi kullum, idan ta ɗauko sai ta damawa Jaish, tun baya iya sha har ya koya dan dolensa, da idan ya sha sai ya yi ta amai tamkar zai akayar da komai na cikinsa saboda karninta, amma yanzu lafiya lou yana sha, rayuwa kenan, wuya mai koyawa mutun abin da yake ikirarin bai iya ba kuma ba zai yi ba, sai ga shi dai yau kun gani a kan Jaish, duk wanda ya ce bai iya kuka ba to ku ce mashi mahaifiyarsa bata mutu bane, tana mutuwa dole ya yi dan gidansu!!. Dama mashi fura da nonon ta yi ya damu sosai, haƙiƙa Mahnoor yarinya ce mai abin birgewa, dan kuwa a kullum ta san kowani aiki da ya rataya akanta, ku duba ku gani ko ina ta je tana dawowa dallah dallah zata fara yin duk abin da ta san aikinta ne baiwar Allah, ba sai ta jira an ce ta yi ba, fatan Allah ka shirya mana ƴaƴanmu da jikokinmu. Bayan ta kammala ta miƙe ta ɗauko mashi ɗan ƙaramin kwaryarsa mai kyau ta zuba a ciki, sannan ta zubawa bappa da Nenne, ta bar masu sauran ita da Mahreen a cikin wannan babban kwaryar, ta ɗauki paipai ta rufewa kowa nasa, ta ɗauki na Jaish ta nufi cikin ɗakin bappan. Tana shiga ita kuma Mahreen ta zo ta ɗauki na bappa ta je ta miƙa mashi, karɓa ya yi ya ajiye a gefensa ya cigaba da aikinsa. Sannan ta ɗauki na Nennen ta kai mata, sai ta ɗauko wani ludayi ta zo ta zauna tana jiran Mahnoor ɗin ta fito su sha a tare. Ihunta da suka ji daga cikin ɗakin bappan ne yasa suka kai kallonsu a bakin kofar, da sauri Nenne ta fito daga cikin nata ɗakin dan tsabar gulma. Da gudu bappa ya ajiye harawar hannunsa ya nufi ɗakin nasa, da gudu ita ma Mahreen ta rufa mashi baya, Nenne kuwa a bakin kofar nata ɗakin ta tsaya tana jiran ta ji menene? Sai addu'a take yi a kan Allah yasa kashe Mahnoor ɗin ma Jaish ya yi kowa ya huta. Turus suka tsaya a tsakar ɗakin suna ganin abin da yake faruwa, gabaɗaya Mahnoor ɗin jikinta ya sha wanka da furar da ta kawo mashi ɗin, tana tsugunne a gaban gadon nasa. Abin da ya faru shi ne, ta saba idan ta kawo mashi furar ko da yana kwance ne zata zo gabansa ta tsugunna ta miƙo mashi, wani lokaci har hannu take sawa ta ɗan bubbuga katifar ta ce ya tashi ga furarsa. To yau dai da ta zo ta yi mashi na farko bai motsa ba, sai ta yi zaton bai ji bane yasa bai motsa ba, dan ta san dai in ta yi mashi magana yana ɗaga mata kai kawai alamar ya ji, yau sai taga akasin hakan, kuma idanunsa biyu ba barci yake yi ba. Shi ne ta sake buga jikin katifar ta maimaita abin da ta faɗa da farko, ita gabaɗaya ta manta cewa da safe ya fusata. Nan ma bai motsa ba, ganin hakan ga idanunsa biyu sai yasa ta kai hanni ta ɗan taɓa hannunsa zata yi magana kenan a fusace ya kai hannu zai dallah mata mari, zaro idanun da ta yi ta sha jinin jikinta tare da kamewa waje guda ne yasa ya fasa marin nata ya sauke haushinsa a kan furar a in da ya yi fatali da shi, ya yi mata wanka da shi, gabaɗaya jikinta ya ɓaci, har face ɗinta, hakan ya ɗaga mata hankali har ta yi kara, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba, Allah ya ceceta, wlh da ya sauke mata wannan marin da ya yi niya in da yake cikin fushin nan in bata mutu ba zata sume, amma sai ya danne, tun safe yake ta ƙoƙarin danne zuciyar nan nasa na Modarawa, amma abin ya ci tura bawan Allah. Ba laifinsa bane, zuciya gadon modarawa ne kowa yasan da hakan!. Bappa yana ɗaura idanunsa a kansu ya fahimci abin da ya faru, hakan yasa ya ce mata ta je ta canza kaya ta wanke jikinta. A hanzarce ta miƙe, sarki tsoro jikinta har kerma yake yi ta fito waje a tsorace. Tana fitowa Nenne ta dakatar da ita a kan ta gaya mata me ya faru a cikin ɗakin?. Murya na rawa ta bata labarin abin da ya faru, wani irin murmushin mugunta ta saki tare da juyawa ta shige cikin ɗakinta. Bayan Mahnoor Mahreen ɗin ta biyo tana bata hakuri. Shi kuwa bappa rarrashin Jaish ɗin ya shiga ya fara yi. Da yake ya ɗan samu ya yi wa Mahnoor patali da furarta sai ya ɗan ji zuciyar tasa ta yi sanyi, hakan yasa ya kara zagewa wajen dannar zuciyar har ya iya amsawa bappan ta hanyar jinjina kansa alamar ya ji. Sosai bappa ya ji daɗin hakan tare da sanya mashi albarka. Shi ma ya ji daɗi da Allah ya taimakesa wannan bakar zuciya tasa bata ja mashi ya cutar da bappan ko ya yi mashi wani abin da ba dai'dai ba, godiya ya yi ga Allah. Kiraye kirayen sallar mangariba da yara suke yi ne yasa ya ce mashi lokacin sallah ya yi ya fito su tafi masallaci. Alamar wanka zai yi ya nunawa bappan. To ya amsa mashi da shi tare da fitowa ya umurci Mahnoor da ta sanya mashi ruwa a wuta. Baiwar Allah haka ta tafasa mashi ruwan tare da surkawa dana sanyi, ta kai mashi banɗaki ta fito. Yana fitowa da nufin ya shiga wanka da ita suka fara haɗa idanu, kawar da kallonsa daga kanta derect ya yi tare da satar kallonta ta wutsiyar idanu, sai ya ji bai kyauta ba abin da ya yi mata, ta mashi alkhairi ya sauke haushin laifin da ba nata ba a kanta, dama idan baku manta na yana jin tausayinsu ita da Mahreen. Toilet ya nufa yana aikin satar kallonta, ita kuma a tunaninta baya kallonta sai ta tsare shi da idanu tana ta kallonsa har ya shige. After some minutes. Bayan sun yi sallar mangariba da isha'i sun dawo, zaune suke a tsakar gida kamar yadda suka saba, sai hira suke zubawa abin gwanin birgewa, bappa, Mahreen and Mahnoor ne suke yin hiran, Jaish dai shiru yana sauraronsu, Hamma Faisal bai rigada ya ƙariso ba. Fitowa daga ɗakinta Nenne ta yi, a kusa da bappa ta zauna, ko wanka matar nan bata yi ba tun da ta dawo, da alama dai akwai wata ƙasa. Cikin rawar jiki bappa ya ce. "Kin fito ne?". Kai ta gyaɗa mashi hasken fitullun kwai na haska su, da dayake wata ta ɗan yi nisa. "Wata magana nake son yi da kai". Ta faɗa da wata iriyar murya kamar masoyiyarsa ta gaske, da alama wani makircin zata haɗa. Jin ta ce tana son yi magana da shi ne yasa Mahreen and Mahnoor suka miƙe tare da shiga kitchen suka ɗauki abincinsu suka wuce nasu ɗakin. Shi kam Jaish miƙewa ya yi ya nufi waje mai gabaɗaya, a karkashin bishiyar kofar gida ya zauna yana ganin yadda mata da maza suke zirganiya tamkar ba dare bane, kowa da firillar kwai a hannunsa yana haskawa, ƙananan yara sai yawo suke yi a tsakanin gidan makota. Dawo da hankalinsa kacokam a kanta ya yi tare da ce mata yana sauraronta. Gyara zama ta yi tare da lankwashe kafafunta ta juyo suna fuskantar juna. Cike da makircin ta ce. "Wani alfarma nake nema idan ba damuwa?". A takaice ya ce. "Ba damuwa ki faɗa ina jinki". Sai da ta sakar mashi murmushi kafin ta fara kora mashi jawabin abin da take buƙata. "Ina son in ba damuwa ka aurawa wannan bakon namu Mahnoor, nasan zata samu kulawa daga wajen shi, ai kama fini sanin halinsa, kuma.........." Ɗaga mata hannun da ya yi ne yasa ta dakata da yin maganar. "Ba sai kin ƙarisa ba, duk abin da kike so shi kowa zai yi a gidan nan". Ya faɗa a sanyaye. To fah, a gaskiya Nenne muguwa ce ko kuma in ce gwaggo bakar muguwa ce, wai dan ance Jaish shi ne sarkin Mayu shi ne suka zauna ita da gwaggon nata suka shirya ta yadda zasu rufe bakin bappa ya aurawa Jaish ɗin Mahnoor dan ya cinyeta, sun yi imanin shi ɗin mugu ne na karshe, burinsu kuma ta wahala sosai, a tunaninsu idan aka aura mata shi zata zama abin tausayi koma ta mutu, shi ne har da zuwa kauyukan Cameroon suka samo magunguna da zasu rufewa bappan baki ta yadda zai yarda da maganarsu kai tsaye, su dai kawai suga sun sanya yarinyar nan cikin wahala, sai dai basu san cewa boom suke shirin haɗawa kansu ba, dan kuwa da ni da ku dai munga soyayya a tsakanin Mahreen da Jaish ɗin, akwai shaƙuwa, ya zasu yi kenan a lokacin da Mahreen zata ce masu idan ba shi ba sai mutu? Mu dai mun san jinin Modarawa jinin Akka wato Jaish namu ba maye bane, kunga kuwa ai baya cinye Mahnoor ko ya azabtar da ita ba, in da tsawon kwana muna nan Mahreen zata kara girma kuma shaƙuwa ta kara shiga tsakaninsu, a wannan lokaci ni kam zanga ya zasu yi, akwai matsala wlh babba, idan zaka gina ramin mugunta dai ka gina shi dai'dai kai, dan watan watarana kai zaka afka a ciki, Allah dai ya kyauta ya kuma sa mu dace. Wani irin sanyi ta ji a ranta, burinta ya cika, a tunaninta Jaish irin gama gari banzan nan ne, wanda bashi da gata bashi da galihu, shirinsu shi ne su sanya bappa ya yi wa Jaish ɗin nasa ɗakin daban can gefe da su idan aka yi auren, bappan kada ya taimaka masu da abinci da komai, su barsu su sha wahala su sha gararin rayuwa, wato dai shi mugu fa kawai ka yi addu'ar Allah ya rabaka da shi shi ne kawai mafitarka, wannan ma jini ɗaya suke duka, amma ku dubi muguntar da take ta bibiyar ƴar tahaliƙar nan da shi fisabilillah. Hira suka cigaba da yi, bappa bawan Allah ya ma mance da cewa ya yi wa Mahnoor ɗin baiko da Hammanta Faisal, duk abin da Nennen ta ce sai ya aminta da hakan kawai, ya manta da cewa bai fa san wanene Jaish ɗin ba, basu san asalinsa ba, kawai dai alamu sun nuna maganin gwaggon Nennen ne yake aiki ba shi ba. Sai tsara yadda abubuwan zasu kasance Nennen take yi, duk kuma zallar zalinci take tsarawa babu tausayawa, dukka kuma bappan ya aminta, har da wani cewa gobe suna idar da sallar asuba za'a ɗaura auren kamar yadda ta buƙata, shi ya yafewa Jaish ɗin ma sadaki, ma'ana zai biya mashi kenan, daga Jaish ɗin har ita Mahnoor basu san me yake faruwa ba, Nenne ta shirya komai har da cewa Jaish ɗin ya tafi garinsu da Mahnoor ɗin ma idan ya tashi tafiya dan tsabar mugunta, a ƙaramin tunaninsu da wautarsu sun ɗauka idan ya tafi da ita garinsu shikenan ba zai sake dawowa ba, a shirmensu wai shikenan sun rabu da ita rabuwa ta har abada sun huta, wato idan aka ce maku mutun jahiline kawai ka barshi a yadda ka gansa, jahilci kanin hauka kenan. Shi dai bappa umarni kawai yake karɓa abinsa. Hakan kuma aka yi kamar yadda ta buƙata washegari suna idar da sallan asuba bappa ya sanar da liman aka ɗaura auren, abin ya yi mugun bawa Jaish mamaki jin sunansa na Hamman a bakin liman, sai dai bai yi wani yunkuri ba, sai ma miƙewa da ya yi ya nufi waje abinsa, sai gida ya nufa....... Allah sarki Faisal bawan Allah yana jin wannan magana ya yanke jiki ya zube ƙasa sumamme a cikin masallaci, shi kansa kawun Mahnoor ɗin kanin mahaifiyarta wato Ibrahim sai da ya girgiza da jin maganar, Arɗo da bappan su Faisal babu wanda bai razana ya kuma yi mamaki ba, faɗi suke yi bappa ya haukace ya aurawa ƴarsa maye. Ai Arɗo bai yarda ba, bai yi ƙasa a gwiwa ba yasa a kama mashi bappa a kai mashi gida, wai dole a ɗauresa a yi mashi magani dan ya haukace, faɗi ƴan uwan Inna suke yi wlh ko zasu mutu sai dai su mutu amma Jaish bai isa a aura mashi Mahnoor ba, an gaya mashi bata da gata ne? Ko bata da ƴan uwa mahaifiya ne? Wlh ba zasu bawa wani bare ƴarsu ba, wani irin hatsaniya ne ta kacame a masallacin, tuni labari ya karaɗe kauyen, shi dai Jaish yana gida bai san wace waina ake toyawa ba. Nenne kam tambaya take yi shin an ɗaura auren ko ba'a ɗaura ba? Amsar ne burinta a yanzu. Akwai wani kanin Inna mai bala'in ƙabilanci da zafin rai, ai kuwa ya ce idan bappa ya isa Allah ya tsine mashi, sune dangin uwar yarinyar nan, basu ga uban da ya isa ya ɗauketa ya bawa baren banza ba wanda ake zargin maita a tattare da shi, dole Mahnoor Faisal zata aura, idan ba haka ba ayi ambaliyar ruwan bala'i a kauyen, Haka ya haɗa matasa a kan su je su yi wa Jaish ɗan banzan dukan mutu su ɗaukeshi su fitar da shi daga cikin ƙauyen....... To fa tashin hankali, cikin ƙanƙanin lokaci Nenne ta haddasa boom a cikin ƙauyen, da alama kuma tashin boom ɗin nan sam ba zai yi kyau ba, zai yi mugun munana, kai mata mata Allah ya shiryamu shirin addinin musulunci, ji fa cikin minti ɗaya ta rikita gari guda. Tana gida sai fargaba take ji kamar zai kasheta, sai safa da marwa take yi a tsakar gida, burinta kawai ta ji an ɗaura auren nan, tana fargabar ace ba'a ɗaura ba, duk wani shirinta zai lalace. Mahnoor kuwa suna can suna shirin bin bappa kiwo, dan kuwa basu san me yake faruwa ba, basu san Arɗo yasa a capke bappansu an ɗaure shi da sunan ya haukace ba, dan kawai ya ɗaura mata aure da bare ko in ce maye da suke kiransa, shikenan shi ma ya haukace sai ɗauri, kai ƙauye duniya ne jama'a. Gungun matasa da a kallah zasu kai su 20 ne suka nufo gidan bappan, kowanne rike yake da sanda, ƙanin Inna ya basu umarni su tabbatar sun fasawa Jaish jikinsa ta ko'ina kafin su fitar da shi daga cikin ƙauyen nan, su kai shi can su jefar, sai wani tayar da kura suke yi a hanya suna tafiya, da ganinsu kasan waɗan nan sun ƙunso ƙunshin mugunta, fuskokinsu babu alamar imani, sai wani haki suke yi kamar waɗan da suka ci uban gudu suka ƙoshi, suna wani muzurai da idanu kamar ka arta a guje idan ka gansu. Shi kuwa bawan Allah Jaish da bai ma san me yake faruwa ba, fitowa tsakar gida ya yi hannunsa riƙe da sandar kiwon bappa, fita waje yake son yi ya je wajen dabbobin nasu ya tatso nono kamar yadda yaga bappan yana yi, bai taɓa kwatantawa ba sai yau ya ce bari ya yi, kuma ya yi alkawarin dama daga yau shi zai rinƙa tatsanwa bappa yana rage mashi wahala. Ganin ya fito yasa Nenne ta yi maza ta shiga cikin ɗaki ta cigaba da safa da marwanta har tana haɗa uban gumi yadda kuka san wadda take gudanar da wani aiki na alkhari, gabaɗaya a ruɗe take, tsantsar rashin gaskiya ne tab a saman face ɗinta, a hakan ma bata san me yake faruwa a cikin ƙauyen ba, bata san babanta ya sa an ɗaure bappa ba, da ta sani kam ina ga ruɗewar da zata yi sai Allah ne kaɗai ya sani. Bokitin tatsar nonon ɗin ya ɗauka, shi dai baya ɗaga idanu ya kalli kowa, haka zalika fuska kamar hadari kullum a ɗaure tamau, ga iya shariya, aikin gabansa kawai yake yi, sai ka rantse ma babu shi a gidan idan ba ganinsa ka yi ya fito ba!. Yana ɗaukar bokitin ya juyo zai nufi waje kenan waɗan nan matasan suka banko labulen buhun kofar gidan, tsundum suka afko cikin gidan gabaɗayansu, sai kaɗa sandunar kiwon nasu sama suke yi. Da gudu Nenne da su Mahnoor ɗin suka fito waje jin irin wannan hayaniya. Gabaɗaya matasan suka rufa kansa da gudu haɗe da ɗage sandunarsu da nufin fara kai mashi jibga ta ko'ina................. TASHIN HANKALI, A GASKIYA NENNE DA GWAGGO HEGU NE, JI LOKACIN ƘANƘANI SU HARGITSA KAUYE GABAƊAYA, DAMA AI ABU NE DA BA ZAI YIWU BA ƳAN UWAN MAMAN MAHNOOR ƊIN SU YARDA DA WANNAN ABIN, AKWAI GAGARUMIM RIKICI A WANNAN ƘAUYE, GA SHI DAI BAPPA MAI SHIGARWA JAISH ƊIN FAƊA TSAKANINSA DA ƳAN KAUYEN MA AN ƊAURESA DA SUNAN MAHAUKACI, MY PEOPLE'S AKWAI BALA'I BA KAƊAN BA, NA BARKU LAFIYA NA TAFI KINGDOM OF POWER, KAFIN MU DAWO WATA KILA SUN GAMA KASHE JAISH ƊIN. _____________________🔥🕊️ KINGDOM OF POWER💪🔥💘 Jim kaɗan ya fito daga cikin room ɗin nasa, saman sofar da ya tashi ya koma ya zauna hannunsa janye da katuwar echolac mai bala'in kyau da tsada. "Before I came, before I actually see your face I already knew that my wife is gorgeous, beautiful and Pretty, you're a so special my Jannaty". Ya yi maganar kallonsa a kanta babu ko kyafta idanun. "I never thought there is a woman who will make me fall in love at this moment, I was so surprised, one time like a dream you stole my heart, wow my Mammien is special, ta iya zaɓe gaskiya, dole na yi mata gagarumin kyau"........ Duk ya ruɗe ne, ya susuce kalaman kauna kawai yake ta zuba mata.............Hakiƙa a wannan wajen ɗai zuciyata ta karaya my people's, dukkansu suna bala'in kaunarta, ya zasu yi a lokacin da zasu san cewa mace ɗaya suke so? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, waye zai hakura kenan? A gaskiya Mammie bakar muguwace kuma silent killer ce ta gasken gaske wlh, wato da bata da hanyar da zata bi ta kashesu ne yasa ta haɗa masu tarkon da ciwon zuciya zai kashesu gabaɗaya, domin kuwa dole ɗaya ya hakura ko kuma dukkansu biyu King ya hanasu dan ya raba gardama, kai koda an bawa ɗaya ya aureta ba zai taɓa jin daɗin zama da ita ba, saboda zai rinƙa jin raɗaɗin cewa ya auri abin da ɗan uwansa yake kauna, dole zuciyarsa ta yi ta yi mashi zogi, kai Allah ka rabamu da masu bakar zuciya irinsu Mammie. Sai sakin cool murmushi take aikin yi, tana mayar mashi da amsa cikin jin kunya. Sun jima suna hira kafin ta ce mashi zata je Momma na kiranta, dama zumuɗin son zuwa ta gansa ne yasa bata fara zuwa kiran Mommar ba. Okey ya amsa mata da shi sannan suka miƙe a tare. Da hannu ya nuna mata ta yi gaba mana, ba musu ta wuce gaba ya rufa mata baya. Suna fitowa parlour suka isko Mammien and Aliyah suna zaune, har ƙasa ta tsugunna ta gaida Mammien, sai wani uban washe masu baki na munafurci take yi. Gera guda ya ɗagawa Mammie tare da cewa. "Mammie bari na raka Queen ɗina in tabbatar ta shiga ciki lafiya ina dawowa mu yi magana". Cike da kaunar Mammien ya yi magana. Kara faɗaɗa murmushinta ta yi tare da amsa mashi da okey ya kula da ita dai sosai kamar da gaske take yi. Gaba chuchun ta yi da sauri dan kunya da ya lulluɓeta, bayanta ya bi yana yi mata dariya wai tana kunyar Mammie. Suna fita Aliyah ta dubi Mammie ta ce. "Aunty ina na ji kincewa Mama Jawad ne yake son Jannat? Ko dai ba Jannat ɗin bace wannan? Dan ni ƴaƴan King ɗin nan ruɗar da ni suke yi, kamanninsu kusan ɗaga, duk da shi suke kama da kuma wannan hegiyar tsuguwa mai idanu manya manya kamar na mujiya, wlh banson tsohuwar nan, haushi take bani". Ta kai karshen maganar tana kwaɓe fuska kamar an naushi kashi. My people's nace mu gayawa Aliya gaskiyar wacece Akka ne ko dai mu yi shiru Akka ta bayyana mata wacece ita? Ana bala'i a kingdom of power, wai tana son King ya aureta amma bata son Akka, kam balai'n can, e lallai kin ɗauko dala ba gammo hajiya Aliya, dan kuwa Akka kam mai sonta ma bata so shi ba bare marasa sonta, ai duk bala'in ki a tafin hannun Akka ki ke, ita ɗin wandon robace dai'dai da ƙugun kowace maras kunya, ita gobara ce daga kogi wanda kasheta sai dai lillahi, dakalin majina a hau a zame, kai Akka bala'i ce, Akka duniya ce, zaki sameta daram yarinya, zata cire maki hayakin da kanki yake fitarwa, su Mama jiga jigan mata ma ya suka kare da ita bare ke tsutsar masai?. Wani irin ɗaure fuska Mammie ta yi kafin ta ja dogon tsaki. "Ita ce Jannat ɗin dai, Jawad yana sonta ni kuma na cusawa Rizwan kaunarta, kinga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, daga karshe dukka zasu yi mutuwar kasko, kinga babu wanda zai ce da sa hannuna, ina da tabbacin dukkansu biyu King ba zai basu aurenta ba, dan kuwa shi King adalin mutun ne, idan yasan suna son mace ɗaya zai hanasu dan ya kwatanta adalci, kinga ciwon zuciya ce zata nakastasu". Ta kare maganar tana sakin wani ɗan iskan dariya kamar wata mai motsi a kai. Wani irin shu'umin murmushin ta saki. "Shegiya Aunty gaskiya kin iya plan, amma nasan mama ce ta shirya komai, dan ke baki da irin wannan ƙwaƙwalwar........" Cak ta tsaya da dariyar tare da ɗaure fuska ta wurga mata wani matsiyacin harara wanda yasa ta haɗiye maganar. Zata yi magana kenan Rizwan ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama. Tsabar iya munafurci a wajen mammie har da wani cewa. "Kai har ka fara kamshin ango, wai ma me ka sayawa amaryar ne cikin katon echolac haka?". Hegeya Aliya ita ma har da wani sakin murmushin munafurci tana faɗin. "Yah Rizwan wlh har wani kyalli face ɗinka ta fara yi, e ango, wai yaushe ne ma abin?". Zama ya yi kusa da Mammien yana murmushi, aka ce rashin sani yafi dare duhu, Allah sarki da kansa ya zauna kusa da makashiyarsu shi da marayan kanin nasa. "Mammie bafa yanzu bane auren, zan barta ta kammala junior secondary school kafin nan na yi wa daddy magana......" Bata bari ya ƙarisa zancen ba ta tari numfashinsa da cewa. "A'a ban yarda ba, zuwan nan naka za'ayi komai a gama, ni da bani da burin da ya wuce ku yi aure shi ne kuma Allah ya kawo lokacin kana ƙoƙarin ka kawo mana wani zancen da ba shi ba? Shekara nawa ina dakon jiran wannan rana? Ko so kake na mutu da tsumayin zuwan ranar aurenka a raina". Fuska a ɗaure ta yi maganar. Aliyah ce ta capki zancen da cewa. "Gaskiya kam nima ban yarda ba, kawai ka shigo mun da Auntyta". Tana magana tana turɓune fuska yadda kuka san da gaske suke yi bayin Allahn nan, amma tsagwaran iya makircine da munafurcin ne kawai, idan ka faɗa tarkonsu ba zaka taɓa tunanin ba sonka suke yi ba hegu. Fuska ɗauke da ƙayatattcen murmushi ya ce. "Kai mammie Jannat fa yarinya ce, zan bari kafin ta kammala dai zata kara girma, kinga hakan zai fi". Girgiza kai ta fara yi. "A'a ban yarda ba, idan wani ya yi saurin shigowa ya ɗauketa fa? Kasan ƴaƴan sarakuna nawa ne suke rububinta? Jannat fa ba mace kamar sauran mata bane, ta fita daban, shiyasa na zaɓa maka ita dan kaima na daban ne, dan haka ka gayawa daddynku, zai ma fi kowa murna, jumma'ar nan a ɗaura aure kowa ya huta". "Haka kike so our Mammie?". A hanzarce ta gyaɗa kai. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce. "An gama, bari zuwa dare zan sami dad a part ɗinsa, kafin nan kinga daddy ma jirginsu zai dira, kinga shikenan sai ayi komai ko?". Murmushin makirci suka saki a tare ita da Aliya. "Kwarai kuwa, ai ka yi kyan kai, ka je ka kwanta ka huta, na san a gajiye kake, saboda nasan tun ɗazun hira ake yi da surukata kuma ƴata". Ƙara fadaɗa murmushinsa ya yi tare da miƙewa. "Our Mammie kamar kin sani, yanzu ma ban gaji da hira da ita ba, itace dai ta ce mun zata koma, shi ne yasa na kyaleta sai zuwa anjuma da yamma zan sameta a cikin gidan". "Eyyye wato kai baka kunyata ko?". Kai yasa ya nufi part ɗinsa yana faɗin. "Mammie kunyarki na me zan ji? Ke fa kika zaɓa mun ita, ai daga nan kunya ma ta kare, bari dai na yi barci na tashi zan zo ki tayani zabawa ɗan uwana rabin jikina mata, dan kin iya zaɓa". "Kai ai Jawad baya son batun aure, gara ma kada ka yi mashi yanzu, ka kyalesa sai gaba"... ......Munafuka ta faɗi hakan ne dan kada ya je ya ce zai yi wa Yah Jawad maganar aure har su fahimci mace ɗaya suke so, ba'a yanzu take son su fahimci hakan ba, ta fi so sai ranar auren ko kuma sai an bawa Rizwan ɗin Jawad ɗin ya san da hakan, daga nan komai na kwaɓe, shiyasa ta yi saurin dakatar da shi. Da yake yana bala'in kaunar kanin nasa, kada ku manta shi kaɗai garesa, kunga kuwa dole ya kaunacesa, sam baya son ɓacin ransa, sai ya ce. "A'a ba sai ya ɓata rai ba, na kyalesa ya yi rayuwarsa, idan ya kara girma shi da kansa zai buƙaci yin auren". Yana kai karshen maganar ya shige ciki abinsa. Ya manta Yah Jawad ya taɓa ce mashi ya samu matar aure. Wani irin murmushin mugunta suka yi tare da miƙewa a tare suka wuce room ɗin Mammie, dan su je su cigaba da kullah tuggunsu kada ya jiyosu. ___________________🕊️💘 A can cikin gida kuwa, sai can dare King Zuhair ya dawo, kai tsaye master room ɗinsa ya shige. Momma na jin labari ita da Akka suka yi maza suka garzaya izuwa room ɗin nasa. Tsaye yake a tsakiyar room ɗin, ya harɗe hannayensa ta bayansa, daga ganin yanayinsa zaka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali, damuwace a kewaye da shi, kamar ma zai faɗi kasa sabdoa ɓacin rai, ba dan Allah ya tsare yana da taurin zuciya ba da ba abin da zai hana shi faɗuwa. Tun daga ganin yanayinsa su Momma suka san ba lafiya ba, hakan yasa suka haɗa nutsuwarsu waje guda. Akka ce ta fara tambayarsa menene yake faruwa?. Wani irin yawu mai ɗaci ya haɗiye tare da furzar da wani irin isaka mai tsananin zafi daga bakinsa, sannan ya ja dogon numfashi, a hankali ya sauke. A hanzarce Momma ta ɗauko mashi ruwa, hannunta har yana ɗan kerma wajen balle marfin bottle water. Tana mika mashi ya sa hannu ya karɓa, tun da ya kafa a bakinsa bai cire ba sai da ya shanye tas, karbar robar Momma ta yi. A hankali ya fara sauke numfashi mai tsananin zafi!. A karo na biyu Akka ta sake tambayarsa meyake faruwa?. Ajiyar zuciya ya sake saukewa, da kyar ya iya furta. "Akka babu Spender, sun ɗaukesa daga gareni"....... Tashin hankali, ai wani irin jirine ya ɗebi Akkan, tafiya ta yi luuuu zata faɗi ya yi zafin namar tarota ta faɗa saman kirjinsa. Ita kanta momma ta shiga tsananin tashin hankali na wuce misaltawa, har wani juya mata kanta ta ji yana yi. A saman gadonsa ya kwantar da Akkar tare da zama a gafenta yana mai bata hakuri tare da yi mata alkawarin tabbas koma a ina Spender yake dole zai kwato kayansa ya dawo da shi. Me alaƙar King da Spender ne wai?. To ku buɗe kunnenku ku ji, Spender dai mallakin King Abdul Malik ne wato mahaifin su King Zuhair mijin Akka kenan, a yanzu da baya raye kunga kuwa mallakin ƴaƴansa ne wato King Zuhair, uncle Abbas and uncle Jahiz, nasan kowa zai so jin menene wannan Spender, amma mu je zuwa zaku ji komai a hankali, sai dai kuma abin tambayar a nan shi ne, King Zuhair da yake babban sarki da kowace kujerar mulki a faɗin ƙasar Tunisia take ƙarƙashin tasa kujerar, suna da karfin iko da isa, kada ku manta ko gate ɗin masarautarsu babu wani mahalukin da ya isa ya nuna da ɗan yatsa, jarumai ne waɗan da akewa mayaƙansu ma laƙabi da dangerous warriors, amma duk da haka ya aka yi Spender ta bar hannunsu take hannun Pretty? Akwai bala'i gaskiya, wai ni ina mummyn twin's ɗin ne ma kam? Tana raye ne ko ta mutu? A ina ta samu Spender har ta nasu? Kai mu je dai zuwa, dan waɗan nan tambayoyi ma kara jefa mun ƙwaƙwalwata cikin zafi zasu yi. Tana daga kwance tana ganin jiri ta fara faɗin. "Zuhair kada ka yarda ka fitar da zancen Spender ya ɓata saboda abokan gaba, kawai ku nemosa ta ƙarƙashin ƙasa". Hannayenta ya riƙo cikin nasa tare da yi mata alkawarin aiwatar da hakan cikin ƙanƙanin lokaci. A takaice a cikin wannan dare ya bugawa duk wasu amintattun cikin fada busar gayyata, sai hidimar gyaran masarautar ake yi saboda yakin da aka buga. Yana buga masu busar gayyatar ba'afi minti biyu ba suka hallara a cikin meeting room ɗinsa, zama ta sirri ya gudanar a tare da su, ko ni kai'na basu bani damar jin abin da suka tattauna ba bare na kawo maku labari, sai dai ga dukkan alamu sun gamsu da tattaunar tasu, dan sun tashi taron fuskokinsu ba yabo ba fallasa, dama dai kunsan su ba dariya suke yi ba, musamman ma commander Zafar, ai shi wannan fuska kamar hadari take kullum. King bai iya kwanciya barci ba har sai da ya samu matsaya a kan ta yadda zasu nemo Spender!. Sannan ne ya yi wanka ya samu ya sanya haƙarkarinsa a gado. Haka ita ma Momma sai da ta samu tabbacin mijin nata ya samu nutsuwa ya dawo cikin hankalinsa sannan ta iya kwanciya. Kafin King ya dawo uncle Abbas da ya yi isowar yamma ya zo dan su gaisa sai bai samesa ba, shi ma Rizwan ya zo da nufin ya sanar da shi batunsa shi da Chuchu a lokacin bai dawo ba, hakan yasa ya wuce part ɗin Momma suka sha hira da chuchu, Jawad kuma yana tare da uncle Abbas a lokacin, sai tsokanarsa daddyn nasa yake yi yana tambayarsa ina Jannat? Sai ya wani kafe wai shi bai san in da ma take ba dan bashi da wata relationship da ita. ____________________________🔥🕊️ Washegari da safe, uncle Abbas and uncle Jahiz sai Akka suka zauna zama ta sirri, sai dai King bai iya sanar da su cewa Spender ta ɓata ba, dan in ya gaya masu za'a samu matsala, Akka ta hana ma ya sanar da su, sun dai yi zama na tattaunawa a kan ɓatar Jaish da sauran matsalolinsu. Mummyn Gimbiya Chuchu ce ta buƙaci King da ya yarje mata zata shirya gagarumin walima na dawowar Guyson kamar yadda ta yi alkawarin kuma kamar yadda take shiryawa duk wanda ya dawo daga cikin ƴaƴan nasu, sai dai wannan karon zata haɗa da walimar nasarar yakin da suka ci, da yake ita bata san da batun ɓacewar Spender ba yasa ta bukaci hakan, su suna cikin jimami ita kuma murna ma take yi, ko da yake dole zata yi murna dan a ganinta sun ci nasara a yaki ai abin murna ne. Da farko King ya so hanata shirya walimar, amma sai Akka ta yarje mata, ta yi mata hakan ne kuma dan kada a fahimci batun ɓatar Spender, dama a duk lokacin da suka ci nasara a yaki sukan shirya walima da manya manyan masarautu zasu halacta, duk wani mai riƙe da muƙami zai hallara, suci su sha, su yi kyaututtuka, ayi abubuwa dai na bajinta da taimakawa talakawa, to kunga idan ba'ayi ba wannan karon dole jama'a zasu ce akwai wata a ƙasa, hakan yasa Akka ta ce mummyn ta yi. Kan kace me aka hau shirin walima. Shi kuwa Yah Jawad yau tun da sassaqfe ya shirya dan yana da gagarumin aiki a office, jiransa ma ake yi, sai kiransa a waya suke yi, sun takura mashi. Jiya a tare da Rizwan ya kwana ɗaki ɗaya, kamar zasu cinye juna saboda so, ko shirin tafiya office da ya yi yanzu sai da Rizwan ɗin ya taimaka mashi saboda kauna. Yana fitowa daga part ɗin daddyn nasu ya nufi part ɗin King dan ya gaishe da su Momma kafin ya wuce office. Yau kingdom of power a cike take da baki, su uncle Jahiz sun zo, Guyson tun da suka zo yana tsakanin mummyn Gimbiya Chuchu da mommarsa, shi fa irin mutanennan ne mai ƙulafucin uwa, sai dai suna mugu mugun shiri da mummy, badan kaunar da yake yi wa mummyn ta musamman bace bama da ba zai iya motsawa daga kusa da mommarsa ko nan da can ba, amma yana kaunar mummyn, dan tana da farar zuciya tana kuma kaunarsa. Duk girmansan nan, yana da kanne uku a duniya, amma tsabar shagwaɓa da kulafucin uwa a ɗakin momma saman gadonta ya kwana, bai san da batun dawowar King ba, tun karfe 8 ya yi barci abinsa, a saman cinyarta ma ya kwantar da kai ya yi barci, sai da ya yi barcin ne ta lallaɓa ta kwantar da shi ta tafi wajen King. JAWAD Dab zai shiga ɗakin Momma ita kuma tana fitowa, karo suka yi a in da kanta ya bugi faffaɗar kirjinsa. Baya ta ɗan yi tare da sanya hannu t........ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 28/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E29 Baya ta ɗan yi tare da sanya hannu tana murje gaban goshinta, da alama ta ɗan ji zafin karon da suka yi. From toe ya fara kallonta yana ɗagowa har izuwa face ɗinta, da sanyi safiyar nan har ta tsantsara kwalliya, kai Chuchu duniyar kwalliya, idan ka ji mutum ya ce make up bata burgesa to fa bai haɗu da na Chuchu bane, ita ɗin duniya ce. Har ta tashi ta yi wanka, tsantsara kwalliya ta yi dan Yah Rizwan ɗinta, wandon jeans doguwa ce sai riga zuwa gwiwarta a jikinta, a takaice dai Pakistan dressing ta yi, mayafin kayan babba ne yana ja mata har a ƙasa, ga shi kuma net ne da ya ji flowers, haƙiƙa kayan sun yi mata kyau sosai, gata fara kayan launin maroon and milk, abin ba'a magana. Shakar daddaɗar kamshin perfume ɗinta ya yi tare da lumshe idanunsa, a hankali ya sake warosu a kanta. "Ina kwana Yah Jawad?". Ta faɗa a sanyayye. Kawai kura mata idanu ya yi babu ko kyaftawa tamkar idan ya rufe idanun zata ɓacewa ganinsa. Sake maimatawa ta yi. "Yah Jawad ina kwana?". Hannu ya kai saman kansa ya ɗan shafa arab hairnsa tare da sauke ajiyar zuriya. "Jannat ki na yi mun son ranki a gidan nan". Ya yi maganar ce a zatonsa a cikin zuciya ya yi, sai da ya ji ta ce. "To ni Yah Jawad me kuma nayi maka?". Tana magana tana turo baki. A san nan ne ya fahimci ashe a fili ya yi maganar ba'a ɓoye ba. Girgiza mata kai kawai ya yi tare da cewa. "Babu komai, yanzu dai da kika yi wannan tsantsararren kwalliya ina zaki je? Kuma yau ba school ne?". Tana ƙoƙarin yin magana sai ga Momma ta fito daga cikin room ɗin. Shiru ta yi shi kuma ya ɗagawa Mommar gaisuwa. "Office zaka je yau ɗin nan hakan zata yiwu kuwa?". Momma ta tambaya. "Yeah Momma, sai kirana ake ta yi ne, wani aiki ne da muka yi apply since last two months ago sai yanzu fa daddy ya sanya baki aka sakar mana aikin, shi ne zan je in saka hannu". "Tom shikenan ka kula sosai, dad ɗinku dai ya ce su Jannat su zauna yau kada su je school saboda wannan yaki da aka yi, su dakata tukun nan zuwa kwana biyu komai ya koma normal". Tana magana tana kallon shi. Sa kai Chuchu ta yi zata wucesu, dan ta lura hiransa da Momma ba karewa zai yi ba. Cikin sauri ya riƙo hannunta yana kawar da kallonsa daga kan Mommar. Harara Mommar ta watsa mashi tare da sa kai ta wuce abinta. Tana wucewa ya matso kusa da ita. "Ina zaki je bamu gama magana ba? Ko kallonki mafa ban gama yi ba". Cike da so da tsantsar kaunarta ya yi maganar. Cigaba da turo mashi baki ta yi bata yi magana ba. "Lafiya naga kin ɓata rai kuma? Yanzu fa face ɗinki ɗauke da ƙayatattcen murmushi amma daga Momma ta fito ta wuce shikenan kika dai'na murmushi why?". Girgiza kai ta yi tare da cewa babu komai. Ƙara matsowa kusa da ita sosai ya yi tare da rage tsawonsa ya ɗan rankwafo kanta kaɗan. Ƙasa ta yi da kai tare da ɗan ja baya kaɗan, dan har sautin numfashin juna suna ji, hakan yasa ta ɗan matsa. "Menene ya faru? Faɗa mun kin ji ko?". Ya faɗa murya kamar mai raɗa. Still dai girgiza mashi kai ta yi tare da cewa babu komai. Hannayensa da ya harɗesu a saman kirjinsa ne ga saukesu, ɗaya ya ɗaura a saman handle ɗin kofar Mommar, ɗayan kuma ya yi kamar zai ɗaura a saman jikin bango, sai kuma ya sauke shi a bayanta tare da janyota ta faɗa jikinsa, bai cire hannun nasa ba ko da ya janyota, sai ya kara ɗan haura da shi sama daga mazaunanta izuwa tsakiyar bayanta. Ƙara rankwafo kanta ya yi, a dai'dai saitin kunnenta ya fara yi mata raɗa. Ɗan zaro idanun nan waje ta yi. Dukan wasa ta kai mashi a kirji bam tana turo baki tare da fara ƙoƙarin ture shi, hannunsa na saman handle ya sauke tare da haɗawa ya rungumeta da kyau yana murmushi. "Ni Yah Jawad ka kyaleni ko na je na gayawa Akka!". Tana magana tana ƙara ɗaure fuska kamar wadda aka yi wa wani abin. "Da gaske?". Ya faɗa kamar mai taɗa. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Okey tom yanzu dai a gaya mun meyake faruwa ko dai na aiwatar da abin da na gaya maki a cikin kunne zan yi". "Please my sister, gaya mun me ya sameki kin ji?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar. Kwanciya a jikin nasa ta yi tare da fara magana a shagwaɓe. "To Yah Jawad ba kai bane". "Ni kuma?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Menayi to?". "Ba kai ne kullum sai nace zan bika office ɗinka sai ka ce mun a'a ba, to yau Allah na ɓata da kai, ni nasan Allah da Yah Rizwan ne nace zan je office ɗinsa zai tafi da ni". Nan take face ɗinsa ya sauya, kishi ta motsa, sai dai kuma bai bari saiɗan ya yi tasiri a ransa ba, ya yi ƙoƙarin kawar da hakan a in da ya ƙaƙalo murmushin dole, sannan ya ce. "Am so so sorryyyyyyy my sister, jeki shirya ki zo mu tafi, amma kada ki gayawa kowa har Auta ma, dan bana son dad ya samu labarin kin bini, bama dad ba kada kowa ya san kin bini, dan kinga dad ya ce kada kuje school yau, kada ku fita ko'ina duk dan saboda yakin nan da aka yi, dan haka kin ga ba zai ji daɗi ba idan na fita da ke, so kada ki bari kowa ya sani kin ji?". A hanzarce ta ɗago daga kirjin nasa, murmushi ne ya bayyana a saman face ɗinta, daɗi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, dama kunsan basu fita daga kingdom ɗin, kullum suna ciki, idan aka ce zasu fita sai su yi ta murya tamkar waɗan da zasu je aljanna. Haka kawai ya ji shaiɗan yana raya mashi da akwai wani abin a tsakanin Rizwan da ita, saboda idan suna magana tana yawan sanyo zanjen Rizwan a ciki, abin ya fara jefa shi cikin tunani, amma yana ta ƙoƙarin koran shaiɗan dake faman zugasa, faɗi yake bai kamata ko zai yi kishi da kowa ya yi da Rizwan ba, domin kuwa irin kaunar da yayan nasa yake yi mashi ya wuci tunaninku. Wata ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da ai koda da gaske Rizwan yana sonta ma ya cancanci ka bar mashi ita. Ɗayan ɓangaren zuciyar tasa ta ce mashi ina hakan ma ba zai yi wu ba, ba wata alaƙa a tsakaninta da Rizwan face alaƙa ta yaya da kanwa, shakuwa ce kawai dan yana kyautata mata. Haƙiƙa dai yanayinsa ya sauya, ga dukkan alamu ya shiga damuwa sosai, dan har bugawar zuciyarsa ta canza daga yadda take da, amma dai yana ƙoƙarin ya kawar da tunani, sai da ya sanya a ransa idan suka je office zai tambayeta me a tsakaninta da Yah Rizwan? Idan ta gaya mashi saɓanin abin da yake zargi to tabbas a yau zai bayyana mata soyayyarsa, idan kuma ba haka ba........ Hmmmm akwai matsala kuwa!!. Ta lura da canjin da face ɗinsa ya yi, ta lura da damuwa ta bayyana a tattare da shi, dan haka sai ta ce. "Yah Jawad tunanin me kake yi?". Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakar mata murmushi kafin ya bata amsa da. "Ina tunani ne a kan yau zaki ga budurwata abar so na, kina son ganinta ko?". Ya jefa mata tambayar yana kura mata idanu, dan yana son gane shin ita ma tana son shi ne ko dai kawai shaƙuwa ce a tsakaninsu? Zuciyarsa sai harbawa da sauri take yi, yana fargabar amsar da zata bashi. "Dama kana da burdurwa da gaske kamar yadda su Aunty Sarina suka faɗa?". Ta jefa mashi tambayar tana ɗan turɓune fuska. "Yeah Jannat, ina da budurwa kyakkyawa sosai fara mai kama da dad ɗina, yau idan mun je office zaki ganta ai". Har lokacin fargabar jiran amsarta yake yi. Ɗaure fuska sosai ta yi kamar ba ita ba. Murya ƙasa ƙasa kamar wadda bata son motsa bakinta ta ce. "Tom shikenan mu je". Ya lura da ita sosai, sam ranta bai so jin zancen nasa ba, da alama ma hankalinta ya tashi, murmushi ya kau daga saman face ɗinta. "Jannat lafiya kuwa?". Ya faɗa yana leƙo face ɗinta, dan ta sunkuyar da kai ƙasa. Idanunta ne suka cicciko tab da kwallar da ita kanta bata san na menene bane, haka ɗai ta ji komai ya canza mata, har sara mata kanta ta ji yake yi mata, nan take ta ji kamar zazzaɓi ne yake son kamata, duk sai ta ji bata ma son sake ganin face ɗinsa, kishi ne ɓaro ɓaro ya bayyana a tattare da ita, tabbas kuma ya lura da hakan, ya lura da kishinsa ne fal a tattare da ita, abin ya yi mugu mugun yi mashi daɗi, ransa ta yi sanyi sosai, zuciyarsa har wani irin sanyi ne ya ratsata, ya samu abin da yake so. Ita kuwa da yake kishin fa a jininsu yake, abin nasu na gado ne tun daga kan King Abdul Malik, bala'in kishi ne da kakan nasu, haka ita ma Akka, tsabar bala'in kishin Akka yasa King Abdul Malik duk zafinsa bai iya yi mata kishiya ba, dan yasan duk wanda ya auro wlh kishin Akka ba zata taɓa barin ƴar mutane ta zauna lafiya ba, shiyasa ma bai fara ba, an san sarki da mata huɗu cif, amma ban da King Abdul Malik, duk kuma saboda kishin bala'i da suke da shi, so ku sani abin nasu na gadone, a jininsu yake, kada ku ga laifin Chuchu, gado ta yi, sai dai ko a cikin nasu ma na wani ya fi na wani zafi kishin. "Jannat lafiya kuwa? Menake gani a idanunki kamar hawaye?". A ɗan ruɗe ya yi tambayar, dan bai taɓa tunanin kishinsa zai sanyata kuka ba. Yana magana yana wani waskewa kamar bai san me take yi wa hakan ba. Raɓawa ta jefensa ta yi zata wuce da gudu, dan ta ji ta gaza tsayuwa a wajen ne, ba zata iya ba. A zafafe ya riƙo hannunta tare da jawota jikinsa. "Jannat menene?". Ya faɗa still yana ruɗe. "Ni Yah Jawad ka sakeni!". Ta faɗa da ɗan ɗaga murya. Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaukarta cak sai saman shoulder ɗinsa. Kuka ta fara yi mashi sosai tana bubbuga bayansa a kan ya sauketa sun ɓata kowa ya kama kansa, bai kula ta ba sai saman bed ɗinta ya sauketa tare da duba watch dake manne a hannunsa, kirar Rolex deepsea wadda a ƙalla darajar kuɗinta ya kai dollars 10,000, naira kuma ta kai naira million dubu goma sha biyar. "Tashi ki shirya mu tafi kin ga lokaci yana ta kurewa". Kuka take yi sosai wanda ita kanta bata san dalilin yin sa ba, da kyar ta iya cewa. "Ni Yah Jawad babu in da zan je, ka yi tafiyarka kawai". Tana kai karshen maganar ta kifa kanta a saman pillow ta cigaba da rera kukanta. A can wajen su Mummy kuma sai shirin yin walima ake yi, da misalin karfe huɗu za'ayi walimar. Ya janyowa kansa rigima, dole kuma ya kashe wutar da ya kunna. A hankali ya zauna a gefen gadon, hannu biyu yasa ya ɗagota daga kan pillown, a kirjinsa ya manta, sai ƙoƙarin ture shi take yi, idanu a datse gam take faɗin. "Ni ka kyale ni, ka tafi kawai, kuma ni bana son ganin burdurwar taka, kuma ba zan taɓa zuwa office ɗin naka ba, na tsani zuwa, ni ka barni". Sai sambatu take yi idanu a rufe. Dariya ce ma taso kubce mashi, su Jannat ma ansan kishi, Allah mai iko, ji yadda take kuka kamar wadda aka cewa mummynta ta mutu, ta haƙiƙance sai zabgar kuka take kamar ba gobe, yanzu da zaka tamnayeta dalilin yin kukan nata ba ta da amsa. "Yanzu dai na ji zan tafi, amma kafin nan sai wannan kyakkyawar tawa ta gaya mun me nayi mata take wannan kukan?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar. A faɗa ce ta ce. "Ni ba kyakkyawa bace, budurwarka ce kyakkyawa ko ka manta haka kace a bakin kofar Momma? Har da cewa kyakkyawace sosai, wato ta fini kyau ko?........" Ta ɗan dakata da yin maganar saboda jan numfashi da ta yi irin na mai kuka. "Kuma kai ne ka ce nafi kowa kyau a duniya ranan a parlon dad, ashe kenan Yah Jawad kai ma kana faɗar magana biyu ko?". Tana kai karshen maganar ta sake rushewa da kuka mai sauti. Yau ga ikon Allah yana gani, ji yadda ta haƙiƙance tsakaninta da Allah take murzan kukan nan nata, Chuchunmu mai abin mamaki, ko ina ta baro soyayyar Yah Rizwan da take kishin Yah Jawad a nan kuma? Yau muna ganin ikon god. Ƙasa sosai ya yi da voice ɗinsa a in da ya kawo bakinsa dai'dai saitin kunnenta, magana ya fara yi mata cikin sigar rarrashi haɗe da tsantsar so da kauna. "Am so so sorryyyyyyy my Jannat, wlh ba da wasa nake yi maki ba, kuma ni ba mai magana biyu bane, kamar yadda na gaya maki a idanuna wlh babu wata mace da ta fi mun ke kyau, kyanki ke kaɗai ce babu mai irinta kin ji ko? Dan Allah ki dai'na kukan nan haka ya isa". Hannu ta ɗaga ta fara kai mashi dukan wasa a kirji tana faɗin. "Koma me zaka ce tun da kana da budurwa babu ruwana da kai........." Katse mata maganar ya yi da cewa. "To meyasa? Meyasa zaki ce babu ruwanki dani dan ina da budurwa? Ko dai kina sona ne?". A hanzarce kuma ta fara girgiza kai tana faɗin a'a bata son shi. "To baki sona kuma ki ce kada na yi budurwa? Ke zan aura ne?". Kai ta girgiza alamar a'a. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "To tashi ki je ki shirya mutafi ko?". Ya kai karshen maganar tare da ɗago haɓarta ya shiga goge mata hawayen face ɗin nata da white handkerchief da ya ciro daga aljihunsa. Shiru ta haɗiye kukan nata a in da ita da kanta ta shiga tambayar kanta kukan me ma take yi ne kam? Ina ruwanta da budurwarsa? Ita da take da Yah Rizwan meyasa zata ji babu daɗi dan shi ma yana da budurwa?. Haka ta rinƙa jefawa kanta tambayoyin da babu amsarsu, daga ni sai ku my people's muka san wannan amsa ko ba haka ba? Mu mun san kishinsa take yi, dan a ƙarƙashin zuciyarta akwai kaunarsa da bai taso izuwa saman zuciyar tata ba, hakan kuma bai faru bane dan bai bayyana mata nasa son ba, da zai gaya mata tabbas nata ma zai bayyana. Ita fa bata san menene son soyayya ba, ba kuma ta iya banbanta so da son ƴan uwantaka ba, tabbas tana son Yah Rizwan haka zalika tana son Yah Jawad ɗin ma, sai dai banbancin son da take masu a nan shi ne, Yah Rizwan daɗaɗan kalamansa yasa take jinsa a ranta, ya kuma haɗu da jini, sannan kuma akwai son ƴan uwantaka. Shi kuma Yah Jawad, na farko akwai shaƙuwa mai karfi a tsakaninsu, sannan akwai son yaya da kanwarsa da take yi mashi na daban, dan ko Bilal da suke uwa ɗaya bata yi mashi son da take yi wa Jawad ɗin, sannan akwai soyayya mai karfi ta aure da take yi mashi wanda ita da kanta bata san hakan ba, so ta yi ƙanƙanta iya banbance waɗan nan abubuwa, shiyasa zaku ga zata nunawa Rizwan so ta kuma nuna kishi a kan Jawad, dan a cikin duhu take ita yanzu, babu mai iya kunna mata haske ta fita daga cikin wannan ruɗani sai Jawad ɗin, shi kuma ya biyewa gurɓataccen tunanin da zuciyarsa take sanya shi, ya tsaya kallon ruwa kwaɗo zata yi mashi kafa. Raba jikinta da nashi ta yi, sannan ta sauƙo ƙasa ta nufi dressing room ɗinta, jim kaɗan ta fito riƙe da wasu kaya a hannunta, toilet ta nufa. Da kallo ya bita yana jin wani irin sanyi tana ratsa shi, ko ba komai yau ya san yadda Jannat ta ɗaukesa, yasan yadda take jinsa a ranta, irin wannan kishi haka ai sai wanda ake matuƙar kauna ne zai samu haka. Wayarsa ya ciro ya shiga amsa kiraye kirayen da ake ta yi mashi, jiransa ake yi yazo ya sanya hannu, tun wuraren karfe 6 bakin nasa suka zo, suna ta jira yasa masu hannu a takarda su mayarwa minister, amma ya zauna biyewa Chuchu. Wanka ta yi ta shirya cikin wandon jeans white and t-shirt pink, ta yi wa kayan kyau sosai, sai ta ɗaura after dress a saman kayan, ta yi rolling gyalen after dress ɗin a kanta, a cikin toilet ta kammala shirin nata tsab, sannan ta fito. Tun da ta fito ya kura mata idanu babu ko kyaftawa, tana kallonsa amma sai ta yi kamar bata gani ba. Dressing room ɗin ta koma, simple make up ta ɗan yi da yake akwai kayan make up a ciki, sannan ta sanya lips balm a ɗan bakinta, ta ɗauki high heel ta sanya a kafafunta, kun santa da iya zuba perfume, haka fa ta zuba sosai. Sai da ta gama fesa perfume da Momma ta bata ne idanunta suka sauƙa a kan kwalbar perfume da Mammie ta bata, ji ta yi ai da shi ta fesa, kamar zata ɗauka ta ɗan fesa sai kuma ta ce kamshin zai yi mata yawa over bari ta barshi sai ta yi wanka da daddare......... Tirƙashi!! My people's akwai kallo! Kuna tunanin perfume ɗin Allah da annabi Mammie ta bata kuwa?! Muje dai zuwa. Fitowa ta yi yana zaune yadda ta bar shi, zuba mata idanu ya yi har ta ƙariso gabansa, tana tafiya tana wani yauki kamar hawainiya rai a ɓace, sai tura baki take yi dan tsabar kishi. Miƙewa tsaye ya yi tare da riƙo hannunta yana faɗin. "Jannat duniyar kyau, haba akwai wanda ya isa ma ya ce akwai wadda ta fiki kyau ne? Wane mutum! Ke ɗin ta daban ce". Shiru bata amsa mashi ba, dan har yanzu kishi ne yake cin mata ƙarƙashin zuciya, bata son yin magana da shi, idan ta ce zata yi magana kuka ne zai kubce mata. Mata kenan, mu ai daban muke da kowacce halitta ato, manzon Allah (S.A.W) ya ce a karkace muke babu wanda zai yi dai'dai damu, sai dai a lallaɓa a bimu yadda muke a karkace ɗin dan a samu zaman lafiya. Wasu malamai suka ce kamar aljanu muke.......🤣😂 Jin bata yi magana ba sai bai wani damu ba, dan yasan me take yi wa fushi, burinsa kawai su je office ɗin ya nuna mata wacece budurwar tasa dan ta samu kwanciyar hankali ta kuma koma cikin farincikinta kamar ɗazun, yau ransa tas, duk wani fargaba da yake ji na tana son shi ko bata son shi yau ta kau daga zuciyarsa, dan ya tabbatar so mai karfin gaske ma take yi mashi. Suna fitowa waje ya saki hannunta tare da ce mata ta yi gaba ta jirasa a wajen motarsa, baya son a gansu a tare ma bare ace shi ya fita da ita in ba'a ganta ba. Wucewa ta yi ba tare da ta yi mashi magana ba, sai wani shakar daddaɗar kamshin perfume ɗinta yake yana lumshe idanu, har wani barci barci yake ji saboda daɗi. Da tafiyarta kamar da minti biyar sai ya bi bayanta, a lokacin su Akka suna meeting a kan Jaish, so sai bai je in da suke ba ya nufi office kawai. Bai yi sallama da Rizwan ba, tsabar hankalinsa yana a kan Chuchunsa, burinsa kawai su tafi office ɗin ya je ya yi ta tsokanarta tana ɓata rai, yau dai ya samu damar ƙaɗaicewa da ita su wuni a tare, yana matukar farinciki da hakan. Tana fitowa motarsa ta nufa, securitys suna ganinta suka rufa mata baya, suna isa wajen da take ta ce masu su buɗe mata motar. Cikin girmamawa ɗaya daga ciki ya ce mata key baya hannunsu sai dai su jira shi ya zo. Ɗaya daga cikin securitys ɗin ne ya sake ce mata. "Ranki ya daɗe ko kina bukatar wani abin bayan buɗe kofar motar kafin ya zo". Kada ku manta da larabci fa suke yin magana, dukkansu larabawa ne har securitys ɗin. Da yake dai izza a jininsu take sai ta girgiza mashi kai kawai tare da ɗaga masu hannu alamar zasu iya tafiya bata bukatar komai, ta yi hakan ba tare da ta yi magana ba, ko kallon in da suke ma bata yi ba, sai kawai ta jingina bayanta da jikin motar ta hau latsar waya. Chat ta shiga yi da Rizwan dake kwance a saman bed ɗin Jawad daga shi sai short and single. Har ya iso in da take bata sani ba, daddaɗar kamshin perfume ɗinsa da ya cika mata hanci ne yasa ta ɗago kai, ya harɗe hannu a saman chest ɗinsa tare da zuba mata idanu yana ganin yadda take sakin murmushi, hankalinta na a can Rizwan yana zuba mata kalamai tana sakin murmushi, massage na karshe da Rizwan ɗin ya tura mata shi ne ta kawo mashi breakfast yana ɗakin Jawad a part na King Zuhair kenan, sai dai bata ga wannan massage ɗin ba, dan a lokacin ta dawo da kallonta kan shi. Tana sauke idanu a kansa ta ɗaure fuska kamar ba ita ce ke murmushi a yanzu ba, kalamar Rizwan suna yi mata yawo a cikin kwakwalwarta. "Sarkin buga game and ɗaukar hoto, meyafaru kike ta murmushi haka? Sannan me na haɗa fuska daga ganina?". Ya faɗa tare da cire hannunsa daga saman chest ɗin nasa, gently ya tako izuwa gabanta. Securitys ɗin da suka biyosa da ganin fitowarsa ne suka tsaresu da idanu, su kansu sun ga dacewarsu a matsayin mata da miji ba yaya da kanwa ba. "Ni babu abin da nake yi, kuma ni dama can face ɗina a ɗaure take". Cikin fushi ta yi maganar. Ajiyar zuciya ya sauke. "Haba my sister! To shikenan dai muje ko?". Jin ya ce muje yasa da sauri wani katon dakakken arabs man daga cikim securitys ɗin ya matso ya sanya hannu ya ɓalle kofar motar back seat. Da hannu ya nuna mata ta shiga. Ɗan murguɗa baki ta yi a tunaninta bai ganta ba, sarai kuma ya ganta, sai dai ya yi kamar bai gani ɗin ba. Ciki ta shiga tana tura baki kamar wadda aka yi wa dole zuwa office ɗin, bayan kuma ita ta ce zata bisa. Tana shiga ta matsa can jikin ɗayar kofar, rufa mata baya ya yi, a maimakon ya zauna a kusa da nasa kofar, amma sai ya matso kusa da ita. Wannan securityn ya rufe kofar sannan ya shiga driving teas ya zauna. Sauran securitys da a kallah zasu kai goma da hanzarin suka juya zasu nufi nasu motocin Jawad ɗin ya ce da drivern nasa ya dakatar da su, dan yau baya da buƙatar gayya. Da sauri securityn ya risinar da kansa alamar ya karɓi umarni, sannan ya isar da sakon kamar yadda ya faɗa. Juyawa suka yi suka koma muhallinsu. "I'm late dan haka ka taka motar nan da kyau dan mu isa da wuri". Ya faɗa yana duba agogon dake hannunsa, ga uban miss calls da suka cika mashi waya na ana jiransa. Haba ai a dubu ya taka motar suka nufi gate one. "Yah Jawad yanzu ita budurwar taka a companynka take aiki ne?". Ɗan satar kallonta ta wutsiyar idanu ya yi, wani irin sanyi ya ji a cikin zuciyarsa, wato har yanzu batun yana cinta a cikin zuciyarta, Allah ya gani yana jin daɗin wannan kishi da take nunawa a kansa. "Yeah a can take". Ya bata amsa ba tare da ya kalleta ba. Harɗe hannayenta a saman kirjinta ta yi. "To Yah Jawad yanzu idan muka je zan ganta kenan tana aiki?". Gyaɗa kai ya yi tare da tabbatar mata da hakan. Switch off na wayarta ta yi mai gabaɗaya sai kace wayar ce ta yi mata laifi, sannan ta ɗaure fuska kamar hadari. "Yah Jawad kuma idan muka je dole sai na ganta ne?". "Kwarai kuwa, zaki je har office ɗinta ki gaisheta tun da Auntynki ce". A dake ya yi maganar tamkar da gaske yake yi, yana yi yana satar kallonta, yadda ta haɗe rai kamar wata jagaba, ita a dole kishinsa take, daga ta cikin zuciyarsa dariya sosai yake yi mata, da kyar ya iya danne dariyar na fili dan ya samu damar cigaba da ganin turo wannan ɗan bakin kamar ya yi kissing ɗinsa. "Yah Jawad please ka mayar dani gida dan kai'na yana yi mun ciwo, ni na fasa zuwa". Ta faɗa tana dawo da kallonta a kansa. Da yake dukka yare ɗaya suke yi sai ya zamana driver yana jin duk abin da suke faɗa, mamaki Chuchun ta bashi na yadda take da wannan kishi haka, sannan abin ya so bashi dariya yadda Jawad ɗin yake yi mata yawo da hankali. Shi ma juyowa ya yi suka kalli juna ido cikin ido, nan take dukkansu wani irin saƙo na musamman daga zuciya izuwa zuciya ya isan wa zuƙatansu a lokaci guda, a wani irin yanayi na tsananin ƙishin ruwan son kallon juna suka tsinci kansu, kurawa juna idanu suka yi kowannensu da abin da yake tunawa a ransa. Shi hangosu yake yi a matsayin mata da miji cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ita kuma tunanin yadda zata ga budurwar tasa kawai take yi, tsabar kishi har haskowa take a idanunta ga shi a tare da wata a cikin office nasa suna kashe juna da hira, ita ina zata sanya ranta yau? Ta jefawa kanta tambaya. Jin sun yi shiru yasa wannan securityn ya fara satar kallonsu ta cikin mirrorn motar, haƙiƙa sun yi matuƙar burgesa, har ya ji dama ace shi ne, ji yake da zai samu dama tabbas yadda suka mace da kallon junar nan sai ya ɗaukesu hotuna, amma ina babu damar yin hakan, dan bai isa ba, bashi da wannan dama da kwarin gwiwa. Ya dai'na ganin hanya sosai, ya koma kallonsu ta cikin mirror, ya ga madarar kyau sun haɗe waje guda. Dukkansu sun mance da in da ma suke, sai da driven ya taka wani irin birki wanda yasa suka yo gaba, ta tafi zata buga kanta da jikin kujerar motar yasa hannunsa a tsakanin kan nata da kujerar, hakan yasa kan nata ya sauƙa a kan hannunsa, abin gwanin birgewa, duk da accident suka kusa yi amma shi hankalinsa yana a kanta, tabbas soyayyarsa a gareta ba ta wasa bace. Dawo da ita saman kirjinsa ya yi tare da juyo da kallonsa a kan drivern domin ya tambayesa me ya sanya zai ja irin wannan birkin?. Suna haɗa idanu tun bai yi magana ba drivern ya shiga bashi hakuri, ya je yana satar kallonsu ne ta cikin mirror har motar tasu ta kauce daga kan hanya tana ƙoƙarin sauka daga titin, shi ne da ya farga ya taka wannan irin burki mai rikitarwar. Ita kuwa da ta gama tsorata ta kwantar da kanta luf a saman chest ɗinsa tare da datse idanu kam tana sauke numfashi, ta wani ƙanƙame jikin rigarsa kamar ya ce zai gudu ya barta. Jin ya fara bashi hakuri yasa sai bai yi magana ba, da hannu ya yi mashi nuni a kan ya tada motar su tafi. Haka kuwa aka yi, a hanzarce ya yi mata key, da gudun gaske ya bar wajen. Dawo da kallonsa a kanta ya yi, ta tsorata sosai, kamar zai ambaci sunanta, sai kuma ya fasa, dan ya tuna ashe faɗa suke yi, gara ya kyaleta har sai sun isa kawai. After 10 mins. A marking space na katafaren Companyn nasa drivern ya yi parking. Jin motar ta tsaya ne yasa ta buɗe idanu a hankali tana jin tsoron abin da zata gani. Like wow a cikin zuciyarta ta furta, ashe haka Companynsa take duniya guda, gabaɗaya ginin glass and tiles ne, ba shakka dukiya ta yi kuka a wannan wajen, ta yi mubaya'a. Da sauri drivern ya fice waje ya barsu a cikin motar, a dai'dai lokacin kuma wasu jiga jigan securitys dake Company suka ƙariso wajen motar, dakatar da su drivern ya yi a in da ya ce kada su buɗe motar dan yau yallaboi a tare da madam suke, dan haka su dakata, sai ka ce an ce mashi madan ɗinsa ce ko kuma ita yake son aura, shi dai tun da yaga sun dace mashi sun kuma birgesa shikenan ya ɗaura masu aure a ɓangarensa. "Jannat ta shi mu je ko? Ana jirana". Ya faɗa tamkar mai raɗa. "Yah Jawad ni fa bana son ganin budurwar nan taka, ka ce kada ta zo in da nake, kuma ni ma ba zan je in da take ba". "But why?". Ya yi maganar yana riƙo hannunta da yake saman kirjinsa ta ƙarƙame rigarsa saboda tsoro. "Ni dai babu wata dalili kawai bana sonta ne". Tamkar zata rushe da kuka ta yi maganar. "Jannat baki son abin da nake so?". A takaice ta ce. "Ina son duk abin da kake so amma ban da budurwarka". Tana kai karshen maganar ta raba jikinta da nashi tare da juyawa zata buɗe door ɗin side ɗinta. Hannunta dake sarƙafe cikin nasa ne ya dakatar da ita daga yunƙurinta na buɗe kofar ta fita. Ɗan juyo da gefen face ɗinta ta yi tana kallan hannun nata. "My Jannat uwar rigima, to dai yanzu komai zai wuce mu je, za dai ki ga budurwar nan tawa yanzu". Ya kai karshen maganar tare da sakar mata hannu. Bata sake ce mashi uppan ba ta buɗe motar ta fito. Ganin ta fito yasa securitys ɗin har suna rige rigen buɗe door ɗin side ɗinsa. Cikin izza ya zuro kafafunsa waje kafin ya fito gabaɗaya. Wani irin ɗaure fuska na musamman ya yi, cikin isa da izza ya fara takawa ya kewayo ta side ɗin da take, tana tsaye shiru. Hannunta ya riƙo ba tare da ya yi magana ba, ciki suka nufa, kai tsaye sai wajen haɗaɗɗiyar elevatorn da zata sada shi da office ɗinsa ya nufa. Tunda Allah yasa suka sako kafafunsu cikin companyn duk wasu ma'aikata suka fara binsu dana mujiya, ga wasu rikaƙƙun securitys dake gadi tun daga farkon corridor da elevator yake saukesa wajen office ɗinsa kenan har izuwa bakin door office ɗin, dukkan securitys ɗin sanye suke da pea suit, ga wani uban black glass kamar dai yadda kuka san dressing na securitys, dukkansu arabs mens ne, farare kal da su. Kafin ya kai ga wajen elevator ransa ya gama ɓaci, dan kuwa yaga idanu iya idanu a kan Chuchunsa, sai kallonta suke yi, kishinsa ta motsa shi ma. Wasu suna yi masu kallon suna kama, wasu kuma suna yi masu kallon mata da miji, wasu su ce sun dace, wasu kuma da yake duk wanda ya kwana ya tashi a Companyn yasan Jaish sai su ce ai da Jaish ta fi dacewa, wasu kuwa su ce daga gani wannan kanwar Jaish ce dan sun fi kama da shi, kowa dai da abin da yake faɗe, tamkar zasu cinyeta da idanun. Sai tambaya suke yi wai master ya yi aure ne? Da yake master suke ce mashi. Duk in da zai wuce sai securitys sun girmama shi haɗe da sara mashi, gabaɗaya ma'aikatan wlh tsoronsa suke ji, dan yadda suke bashi girma mugu mugun shakkarsa da tsoro suke ji. Duk wani ma'aikaci ya zo wucesa sai ya gaishesa cikin tsananin girmamawa, abin ya yi mugun bata mamaki, bata taɓa tunanin haka yake da girma sosai a waje ba, ga shi ya wani ɗaure face no respect. Bata tashi shan ainahin madarar mamaki bama har sai da suka hau elevator ta kai su hawa na huɗu in da office ɗinsa yake. A nan ne taga abin al'ajabi, yadda ƴan wannan hawa suke girmama shi jiki na kerma, yadda kuka san yana dukansu ko yana basu hukunci mai tsanani. Ga company nasa duniya ce guda, number one ce, a kallah ba'a ƙasara ba ma'aikata zasu kai dubu goma da suke aiki a ƙarƙashinsa. Duk securitys dake wajen wani irin girmama shi na musamman suke yi, bata gama tsinkewa ba har sai da ta kalli office ɗinsa, a ranta take faɗin. "Ashe Yah Jawad haka yake a waje? Ji yadda kowa yake bashi girma matuƙa, amma a gida na mayar da shi abin wasa na?". Abin ya bata mamaki sosai. Yana shiga waiting room ɗinsa wata matashiyar budurwa ta iso wajen cikin kerman jiki, dama waiting room ne a farko kafin office na P.Ansa sannan sana shi ne a canciki. Sanitizer ne mai kyau da tsada rike a hannunta, a gabansa ta tsaya cikin girmamawa, while shi ma ya dakata da tafiya, tafukan hannunsa ya buɗe mata, matsa mashi sanitizer ta yi. Cike da class ya murje hannun nasa da kyau, sannan ya riƙo hannun ita ma Chuchun ya buɗewa yarinyar tafukanta ta matsa mata a ciki. Da kansa ya murza mata shi, sannan suka wuce ciki, sai binsa da kallon mamaki yarinyar take yi, ita kuma Chuchu sai banka mata harara take yi kamar ba lafiya ba. Suna shiga ta hango P.A a hakimce a saman kujera, sai juyi take yi a saman kujerar, ga sanyin Ac na bugata, ita ma da take P.A office ɗinta ba ƙaramin girma bane da shi, akwai komai a ciki har da toilet. Tana ganinsa ta miƙe tsaye tare da fara kwasan gaisuwa haɗe da yi mashi sannu da zuwa. Ɗaure fuska sosai Chuchu ta yi, dan a tunaninta wannan ce budurwar tasa, dan taganta a office. "Barkanki da zuwa ranki ya daɗe". Cewar P.A ga Chuchu. Wani irin kallon ƙasƙanci da walaƙanci ta bita da shi ba tare da ta amsa gaisuwar ba. "Yah Jawad ina ne office ɗinka? Dan ni wucewa can zan yi". Yadda ta yi maganar sai ta baka dariya, kishi kiri kiri, ko waye ya ce mata ita ce budurwar tasa? Kai Chuchu ikon Allah. Ita kanta P.A ta lura da balai'n kishin da yake kwance a cikin idanunta, hakan yasa ta fahimci duk yadda aka yi Chuchu matar ogansu ce ko kuma wadda zai aura, ɗaya cikin biyu, dan haka sai ta kama kanta kada ta ci duka, a cikin ranta faɗi take. "Shiyasa master baya ɗaga idanu ya kalli mutane kenan? Allah mai iko, dama kana da wannan haɗaɗɗiyar beauty flower yaushe zaka kalli wasu matan? Yanzu kenan master a maza fa yake kallonmu, dan idan irin waɗan nan mata suna a gabanka a maza zaka rinƙa kallon sauran mata, ni kam yau ina Rashidah take ne? Ita sarkin ji da kyau har tana ikirarin zata iya sace zuciyar oga da wannan ɗan guntun kyan nata, to yau ta zo ta ga kyau a nan, ai tana zuwa kusa da wannan zata zama kamar namiji, Allah ya yi halitta a nan, ga iya ɗaukar gayu, ji yadda kayan jikin nan nata ya zauna mata da kyau kamar dan ita aka yi su, master ban ga laifinka ba na kin ɗaga idanu ka kallemu, dole ka ruɗe a nan gaskiya, ashe a maza muke a gabaka, yau ina Rashidah ne". Sai sambatu take yi a cikin zuciyarta, da alama wannan P.A ƴar iska ce, dan har da fa wani lashe baki take yi tana karewa Chuchunmu kallo. Ta kai karshen zancen zucin nata bata san lokacin da dariyar mugunta ya kubce mata ba, ba dariyar komai kuma ba ne ya kubce mata face dariyar Rashidah da take jiji da kai ita kyakkyawace, to ashe dai a namiji ma Jawad yake kallonta, shi ne abin da ya bawa P.A dariya. Ganin Chuchu ta dalla mata harara ne yasa ta yi cak ta tsayar da dariyar. Shi kuwa ko kallon in da table ɗin P.An yake bai yi ba, kamar bai ji ta yi dariya ba "Fuck dirty girl!". Chuchun ta faɗa a bayyane.......... Ni kuwa nace ashe dai Chuchun mu ta iya faɗa, ashe ba'a iya gayu aka tsaya ba har da tsiwa, kunji ta kama zagin mata ba gaira babu dalili, sai kace ance mata ita ce budurwar yayan nata. "Jannat lafiya?". Ya faɗa a sanyaye yana kallon face ɗinta dake ɗaure kamar hadari. "Ni dai ka nuna mun office ɗinka kawai". Kamar zata sa kuka yi maganar. Cigaba da tafiya ya yi suka shiga cikin nasa office ɗin. Suna shiga a maimakon ya wuce saman kujerarsa, sai ya zauna a saman ɗaya daga cikin sofars set dake cikin office ɗin, a saman three seater ya zauna. Yana zama sai ga wani matashi da ba zai wuci 20 years ba, a gabansa ya zo ya tsugunna ya hau cire mashi takalma izuwa sock. Bayan ya kammala ya miƙe ya kaisu ma'ajiyarsu, sannan ya fice, shi ma miƙewa ya yi izuwa saman nasa kujerar ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. "My Queen zan iya samun ruwan sha?". Ya faɗa yana kallonta, ta zauna saman sofa tana ta aikin turɓune fuska. Shi fa duk abin da take yi yau kara sanyayya mashi zuciya take yi, dan kishin da take nunawa a kan nasa ma ya ja sonta ya ƙara ninninkuwa sosai a ransa. Miƙewa ta yi ta isa gaban freezers dake cikin office ɗin. Buɗe ɗaya ta yi ta ciro ruwan, ta dawo wajen kyakkyawan show glass da ta gani a ta kusa da shi, a shake yake da cups and small plates kala kala for snacks. Guda ɗaya ta ɗauko mai kyau, a gabansa saman table ta ajiye mashi da nufin ta juya. Hannunta ya riƙo, da sauri ta juyo, saman laps ɗinsa ya nuna mata a kan ta zauna. Babu musu ta zauna tana mai kallon face ɗinsa. "To zuba mun ruwan". Yana magana yana ɗaga kansa izuwa kallon pop. Ɗaukar robar ruwan ta yi tare da fara ƙoƙarin buɗewa, kasawa ta yi hakan yasa ta ajiye tana faɗin. "Yah Jawad ya yi tauri sosai ba zan iya buɗewa ba, amma ka kira budurwar nan taka ta zo ta buɗe mana, dan naga ita lukuta ce kirar adawa ko sumudawa zata iya". A ɗari ya sauƙo da kansa haɗe da kallonsu izuwa kan ɗan bakin nata, wato dai a fakaice ita a dole ta zagi P.A da take yi wa kallon budurwarsa ce, ba shakka Chuchu ita ma akwai faɗa kam. Ɗaukar ruwan kawai ya yi tare da buɗewa ya zuba a cup ɗin bai ce ko uppan ba. Sosai ya sha sannan ya cireta daga bakinsa. Kawo mata saitin bakinta ya yi, dama ita ma tana buƙatar shan ruwan, dan haka sai ta buɗe baki ya sanya mata. Ɗan dai'dai tasa ta cire baki. Tunani ya fara yi ta yadda zai bayyana mata soyayyarsa a gareta, can dabara ya faɗo mashi ya ce ta rufe idanu sai ya kaita gaban mirror dake cikin office ɗin, sannan ya ce ta buɗe idanu taga budurwarsa, tana buɗewa sai taga kanta a cikin mirror hakan zai ƙayatar. Na'am ya yi da wannan shawara da zuciyarsa ta basa, yana ƙoƙarin yi mata magana aka yi knocking na kofar. Shiru ya ɗan yi na na ƴan sakani kafin ya ce wanene?. Daga waje P.A ta e ita ce. Izinin shigowa ya bata, a ɗari Chuchu taso barin jikinsa ya yi saurin riƙeta yana kallon face ɗinta. A gaban table ɗinsa ta ƙariso, cikin girmamawa ta ce. "Sir daman waɗan nan bakin namu ne suke jiranka a meeting office". Tana magana tana aikin satar kallonsu, sun yi mugun dacewa sun kuma tafi da imaninta sosai. Kai kawai ya jinjina mata alamar ya ji ba tare da ya yi magana ba. Juyawa ta yi ta tafi tana mai ɗan waigowa ta saci kallonsu. Muguwa tunanin Rashidah ce kawai a ranta, tana ta faman dariyar mijinta ta ciki, su Rashidah masu kyan sace zuciyar oga. "Jannat ban aran minti biyar ina zuwa ko?". Ya yi magana yana kallonta. Okey ta amsa tare da barin jikin nasa. Miƙewa ya yi a hanzarce ya fice. Yana fita ta koma saman chair ɗin ta zauna. Shiru ta yi tana tunanin Yah Rizwan ɗinta, a haka har ya dawo ya sameta, ya je ya sanya hannun. Yana zuwa ta miƙe ta bashi waje, zama ya yi tare da mayar da ita saman laps ɗin nasa. "Yah Jawad wai ina budurwar taka ne?". Ta faɗa kamar zata yi kuka. Tausayinta ne ya ji ta kamashi, wato har yanzu abin yana cinta a rai, hakan yasa ya ji gara ya gaya mata abin da yake ran nasa kawai, dan ya saukaka mata abin da take ji na zafin kishi. Juyowa ya yi tare da matso da face ɗinsa daf da tata har suna iya jiyo sautin numfashin juna, wani irin ƙurawa juna idanu suka yi, jiran amsarsa kawai take yi, shi kuwa ya zubawa kwayar idanunta ido yana kallon tsantsar soyayyarsa dake kwance a cikinsu. Saƙo na musamman zuciyoyi suka shiga aikawa juna, a hankali ya haɗe face ɗinsu waje guda, wani irin duniya na daban ya tsinci kansa a ciki. Ƙasa ƙasa cikin salo mai matuƙar jan hankali ya furta. "My Jannat". Sarƙewa muryarta ya yi a in da ta kasa amsawa da na'am ɗin, saboda yadda ya haɗe fuskokinsu ya jefata a cikin ruɗani da fargabar me zai biyo baya. "My Jannat bani da kalaman da zan iya bayyana maki abin da nake ji a yanzu, baki bai isa ya faɗi abin da suke tare cunkushe a cikin zuciyata ba, ba abin da zan iya cewa face in ce maki..............". Knocking na kofar da aka yi ne ya sanya ya dakata da maganar bai iya kai karshenta ba. Cikin wani irin kasala ya ɗan yi baya kaɗan ya raba fuskokinsu ya koma ya jingina bayansa da jikin chair ɗin. Kasa jurewa ta yi da sauri ta kwnatar da kanta a saman kirjinsa tana sauke numfashi a hankali hankali, ɗazun ta rasa ina hankalinta ya shiga da har ta iya tsayuwa tana kallon cikin idanunsa ya kuma haɗe fuskokinsu waje guda, har yana ƙoƙarin kamar zai yi kissing ɗinta kuma duk tana kallon cikin kwayar idanunsa, abin ya bata mamaki, soyayya yasa tama mance a wace duniya take. Da kyar ya iya motsa lips ɗinsa wajen furta. "Come in". Dan yasan P.A ce. Turo kofar ta yi ta shigo, a karo na biyu ta same Chuchun kwance a saman kirjinsa, abin dai ya yi matuƙar ƙayatar da ita, sai ta ji ina ma ace ita ce, sai dai matsalar ita ɗin hajiya one seater ce a ƙiba, ai kunji ma Chuchun ta faɗa da bakinta ɗazun, tana da kiɓa sosai. Idanunsa a lumshe ya ce. "Lafiya?". "Sir dama sir Rizwan ne yake neman iso". Ai da jin sunan Rizwan bai san time ɗin da ya waro idanunsa waje na. A ɗari ita kuma ta ɗago kanta daga saman kirjin nasa, kai tsaye face ɗinsa ta kai kallonta, while shi ma juyo da kallonsa a kanta ya yi. P.A dai mamaki suka bata, daga jin sunan Rizwan duk sun ruɗe kamar marasa gaskiya, shi Jawad tunani yake yi ya za'ayi ya bari yayan nasa ya kamashi da ita a nan? Ai sai ya ce dama ya saba. Ita kuma tunani take yi shikenan ya zo sai su yi hira. "Zan iya tafiya sir?". P.A ta katse masu kallon juna da suke yi, dan ta lura kamar sun manta da ita. Kai kawai ya gyaɗa mata, a hanzarce ya ce wa Chuchun ta shiga ƙasar table ɗinsa ta ɓuya, tun da in ta shiga babu mai iya ganinta sai shi da yake ta wajen, waɗan da zasu shigo daga baya ba zasu ganta ba. A hanzarce ta sauƙa daga jikin nasa ta shige ƙasan table ɗin, dan ta lura ba da wasa yake yi ba, so kada ta ja ransa ya ɓaci a banza. Tana shigewa shi kuma Rizwan ya shigo, ƙananan kaya ne a jikinsa, ya yi kyau fresh da shi. Tun da ya ɗaura idanu a kan kanin nasa ya fahimci akwai wani abin, dan har lokacin a ɗan ruɗe yake, Yah Rizwan ya ɓata mashi komai, ya so gaya mata abin da yake ransa, ya kuma yi kissing nata kamar yadda ya yi niya, amma idan ya kama shi yana aikata hakan ko ya kamashi da ita a tare a nan ai ya shiga talatin............ My people's shin me kuke tunanin zai faru a cikin wannan companyn yau? ________________________🔥😥💔 GIDANSU KHADIJAH.😥💔 Ya ilahi, my people's Khadijan ta koma tamkar ba ita ba, kullum ɓoye kanta a cikin ɗaki take yi ta murji kuka kamar me, tun Zainab na tambayarta me yake damunta har ta hakura ta daina tambaya, taki yarda ta sanar da kowa abin da yake faruwa, cikin nata kuwa ya kusa isa level ɗin da ba'a isa a ɓoye shi ba, dan ma cikin fari ne, bashi da girma sosai ita ma bata da babban ciki, kuma Allah ya rufa mata asiri bata laulayi sosai, sai uban faɗa da tsanar mutane ta iya, ko Zainab dan dole suke tare da ita, dan ba yadda zata yi ne, amma ta tsani ganinta a kusa da ita sosai, ga dukkan alamu duk yadda aka yi uban cikin nan mafaɗaci ne sosai, dan kuwa abin da baku sani ba shi ne a ciki akwai ilimi biyu zuwa uku da ba kowa ne yake iya gane hakan ba sai wanda ya kasance mai ilimin addini sosai, domin kuwa faɗar Allah ne wannan ba faɗar bature ba, amma a hankali zan warware maku komai In Sha Allah. A ɓangaren malamamin makarantarsu kuwa, kullum sai ya zo, amma Khadijan ta ki yarda ko da sunan wasa su haɗu, kwata kwata ma ta dai'na fita, saboda matsa mata da samari suke yi, tamkar abin ba lafiya ba sai da abin nan ya faru da ita ne suka fara tururuwar zuwa neman aurenta. Sannan makudan kuɗaɗen da ta dawo da su ko naira bata sake taɓawa ba, tun da ta cusasu a bayan gado ta fita harkarsu. Yau tun safe basu ci komai ba daga ita har Zee ɗin, Amma bata fito da kuɗin dan ta saya masu abinci ba, da alama ta mance da kuɗin. A yau ne kuma suka tashi da mummunar al'amari na rasuwar Hajiyar su baban Zee wato kakarsu kenan, Hajiya lokaci ya yi, sai dai mu ce Allah ya jikan musulmi. Kakarsu ta wajen uwa wato Hajiyar su Sadiq kam ma basu san a wani hali take ciki ba, tun da Sadiq ya tsallake ya bar Kano ba su sake jin ɗuriyarsa ba, Zee ta nemo waya a maƙota wajen wani mai shago ta kirasa numbersa a kashe, kusan kullum sai ta kira shi domin ya zo ya kawo masu ɗauki a kan wannan wahala da suke ciki, amma ina basu samunsa, sun kira number kakar tasu ma a kashe. Yanzu haka wani irin cin kashi Hauwa take yi masu, Khadeejerh mai iyawa da ita ɗin kunga tana fama da kanta, ita kuwa Maman Haidar tana can tana hidima ta yadda zata yi ta fitar da ɗanta daga halin da yake ciki, bata da nutsuwa, hankalinta a tashe yake sosai, bata ma garin, tana can Abuja wajensa, zuwanta na biyar kenan yanzu ana hanata ganinsa, har yau bata samu damar sanyashi a idanunta ba, bata san a wani hali yake ciki ba, duk ta firgice, ta rame kamar ba ita ba. Ta zama kamar mai cutar ƙanjamau, rasuwar Hajiyar tasu ma ita bata da labari, tana can tana up and down, sai bin manya take yi duk dan ta samu mafita, ta samu ko da sau ɗaya ne taga ɗan nata, sai ta je wajen wannan ta sha bakar wahala wajen sati tana biɗar ganinsa, idan ta samu da kyar ta gansa sai ya ce mata case ɗin a sama da shi yake, ya fi karfinsa, dan haka ta kara gaba zuwa sama ko zata dace, haka dai take ta fama, ta sayar da gidan mijin nata, dan kuwa shi kaɗai ne kadarar da suka mallaka, shi kuma mijin kunga ga shi ne ga kalarsa, in dan ta shi ne Haidar ɗin ya mutu a can ba ruwansa, ita ce dai ta tsaya tsayin daka wajen ganin ya fito. Ta juri rana, ruwa, iska da zafi dukka!!. In takaice maku kuɗin gidan da ta sayar wajen 10 million ɗin ma ta kusa cinyesu a neman ganin manya, duk in da ta je sai ta bada kuɗin goro kafin ma ta samu a haɗata da P.An wanda ta je nema, shi ma P.A ya kwashi rabonsa, gata wawuya ba ilimi ba, sai ayi ta cutarta, wani ma karya yake yi mata ya ce zai haɗata da wanda zai fitar mata da ɗan nata amma sai ta biya, haka zai karɓe mata makuɗan dubbanin ɗaruruwa ya gudu ya barta, sai dai ta yi ta jan Allah ya isa. Wani abin da wani ya yi mata sai da ya sanyani kwallah, dan kuwa sati tana bibiyarsa, ta je office ɗinsa ya fi kafa talatin, yana ciki amma sai P.A ya ce mata baya nan, haka mai gadi zai ce kada ta zauna a ciki dan tana wari, sai dai ta fito waje ta zauna, komai zafin rana haka take zama a tsakar ranar, uwa kenan, komai lalacewarta dai daban take da kowa. Ko ruwan sama ake yi haka zata zauna, ta gama cin bakar wahala, ta basu kuɗi kamar ba gobe, P.A ɗin ma mugu ne sai ya yi ta karɓar mata kuɗi yana kuma ce mata ta dago gobe ogansa baya nan, abin dai ba daɗi, koda baka kaunarta sai ka tausaya mata a wannan gaɓar. Daga karshe randa Allah ya nufa ta samu damar ganin mutumin ya fito daga cikin mota zai shiga office, tana ganinsa ta ruga da gudu ta nufesa, securitys ɗinsa suna tare ta kada ta isa garesa ta bangajesu ta isa gabansa, har ƙasa ta zube gwiwowinta tana kuka tana ce mashi dan girman Allah ya ceci yaronta. Mutumin nan ba kunya bare tsoron Allah har a kai ga tausayi yasa ƙafa ya hamɓareta ya wuce gaba fuskar nan kamar na shanu, har da dakawa securitys ɗin nasa tsawa a kan su fitar mashi da wannan almajira da talauci yasa ta sami taɓin hankali a nan hai, sai warin datti take ta cika masu waje, ya ce kada a sake barinta ta doso mashi office baya da buƙata. Ya bi ta kan yatsun hannunta ya takesu ya wuce, yatsun nata sai da suka fashe suka fitar da jini, saboda takalmar kafafunsa masu ƙarfin gaske ne. Haka securitys ɗin suka kamata suka jefa waje, sai kuka take yi......... Yanzu wa gari ya waya fisabilillah?. Da ace sun yi zaman mutunci da su Sadiq, da shi kaɗai bai isa ya tsaya mata ya yi iya bakin ƙoƙarinsa har a samu Haidar ɗin idan yana da rabon fita ya fito ba?! Wlh da Sadiq yana nan ba sai ta zo nan tana shan wannan bakar walaƙanci da kaskaci haka ba, da tana gida zai yi komai, amma ga shi nan tana ganin illar mugunta ai, su ba tsayayyen namiji suke da shi a cikin familyn ba, ga rashin ilimi da rashin wayo, kowa ya ce mata kuɗi ta ɗeba ta bayar, sai ma ta tambayesu nawa zata kawo, mugaye su suke yanke nawa zata kawo, ita kuwa ta cire ta miƙa, Allah sarki ita dai ɗanta kawai take son ya fita, duk da haka ko ta bada a walaƙantata, yanzu duk ta yi yaushi ta rasa ina zata sanya rayuwarta ta ji sanyi. Duk wannan halin da take ciki kawarta hajiya Hauwa tana gida ta baje tare da ɗaura ɗamarar cin dukiya da gasken gaske, idan ta yi crossing leg ɗin nan nata a saman sofa, ta tasa su kaji gassasu and yogurt a gaba tana cin duniyarta da tsinke babu wanda zai takura mata, ga shi Hajiyar tasu ma rai ya yi halinsa, gidan babu wani tsayayye, Hauwa kam duniya sabuwa abinta. Zata yi saye sayen kayan daɗinta, su Khadeejerh suna ji suna gani zata ci ko a gabansu ko ɗanɗane bata yi masu. Allah ya rufawa Khadeejerh ɗin asiri ma cikin nata bashi da kwaɗayi kuma baya zaɓe, ai da ta wahala ƴar tahaliƙar nan a hannun Hauwa. Hajiyar tasu da ta rasu ma ba wanda ya sani a tsawon awanni, su Khadijah suna ɗaki kamar kullum, ita kuma Hauwa sai abin da hali ya yi, ta fita ya kai sau uku tana zuwa unguwa ta je ta dawo, ta kuma yi girki amma duk da haka bata san cewa surukartata ta rasu ba tsabar bata da albarka. Sai da Maman Hanif ta kawo masu ziyara gidan ne ta iya ganewa, ta zo ne dan ta ji ko ya labarin ƴar uwarta maman Haidar ake ciki, sai kawai ta tadda bakar labari na rasuwar Hajiyarsu. Ta yi matukar kiɗima tare girgiza, hankalinta idan ya yi dubu ya tashi!. Duk da ba shiri su Khadija suke yi da kowa a gidan ba haƙiƙa sun sha kuka na rasuwar Hajiyar. Hauwa kuwa wani irin daɗi ta ji, faɗi take gara ya karun mata, jin daɗi babu tsayawa, ita fa ga dukkan alamu bata tuna akwai ranar tafiya gidan gaskiya, anya jahilcin Hauwar nan ma ya barta ta yarda da lahira kuwa? Akwai matsala, wannan wutarta daban yake idan bata tuba ba, Allah baya yafe laifin wani, ko ta tuba a ina zata ga baban Zainab har ya yafe mata abin da ta yi mashi, dan shi ta cutar da shi cuta mafi muni a rayuwa, duk wannan abin shi ta yi wa, ta ja Hajiyarsu ma ta rasu saboda bakin cikin abin da ya faru ne yasa hawan jininta ya tashi har zuciyarta ya kumbura, yanzu rai ya yi halinsa, rayuka biyu Hauwa ta salwantar waɗan da basu ji ba ba kuma su gani ba. Innalilahi wa inna ilahir rajiun, ga maman Zee a can prison tana karɓar azabar laifin da a kan Hauwa yakamata ya rataya. Haka maman Hanif ta kira jama'a aka yi kira mai wankar gawa ta yi wa Hajiyar tasu, daga haka aka je aka rufeta a gidanta na gaskiya. Bayan rasuwarta da kwana uku ne Maman Hanifa tana zaune a parlour, ta buga uban tagumi tana tunanin rayuwa. Fitowa daga cikin ɗakinsu Khadija ta yi, ta zo wucewa zata shiga kitchen, idan baku manta ba dama kitchen ɗin a parlour yake. "Zo nan Khadija". Ta faɗa tana kallonta sosai, da alama tana zargin wani abin. Ba musu ta juyo ta zo, dan koba komai maman Hanif tana nuna masu so, tana kuma tausaya masu. A saman sofa ta zauna kusa da gwaggon nata. "Gwaggo gani nan". Da kyar muryarta ya iya fita har ta furta hakan, saboda kukan da ta rinƙa sha, ga kukan cikinta da take ɓuya a cikin toilet kullum dare ta ɗirka, ga kukan rasuwar kakar tasu, ga shi bata san a wani hali kawunsu mai kaunarsu Sadiq yake ciki ba, hakan yasa yanzu sai dai ka kalli bakinta ka fahimci me take faɗa, muryanta kam sam baya fita. "Khadija me nake ganin nan? Ya naga jikinki haka?". Maman Hanif ta faɗa da mamaki a saman face ɗinta!. Wani irin dukan uku uku kirjinta ya bada, nan take ta nemi nutsuwarta ta rasa, tsuru tsuru ta yi da idanu, duk da muryar tata baya fita zaka iya fahimtar muryar tata tana sarkewa, da kyar ta furta. "Me kika gani gwaggo? Me jikin nawa ya yi?". Sarai maman Hanif ɗin ta lura da ruɗewar da ta yi daga tambaya, hakan yasa ta ji zuciyarta ya tsinke, addu'a ta yi a cikin ranta Allah yasa ba abin da take zargi bane ya faru da ƴar ɗan uwan nata, da sun shiga uku sun lalace.............. Ai kuwa sai dai ki fara kukan kun shiga ukun, dan kuwa abin da kike zargi ne in ji ni princess Teema!.......🌝😥 Zuciyarta a tsinke ta ce. "Khadija naga jikinki ne wani ɗanye ɗanye ban gane ba, kamar mai ƙaramin ciki kamar kuma period ne, menene yake faruwa?". Ta jefa mata tambayar kirjinta na dukan uku uku, fargabar abin da zata tono ne yake neman kasheta. "Gwaggo nima ban sani ba". Ta faɗa tamkar zata rushe da kuka, wani irin ƙululun bakinciki mai matuƙar bala'in tsaci ne ya tokare mata maƙoshi, wani lokaci ji take yi kamar ta kashe kanta kawai ta huta, Zee ce take ce mata ko ta kashe kanta bata huta ba, hasali ma a lokacin da ta kashe kanta a lokacin ne babin wahalarta mai lasisi zai buɗe, dan kuwa duk wanda ya kashe kansa dai yasan makomarsa, to gara mata azabar duniya da ta lahira, tun da Allah ya ƙaddara basu da rabon duniya to su tsaya su nemi lahira kawai kada su yi biyu babu, wannan maganganu na Zainab suke sanyawa ta daure ta fasa kashe kan nata. Ban da haka wani lokaci har wuƙa take ɗauka ta ce zata kashe kanta!. "Anya kuwa Khadija? Ko dai mu je asibiti ne? Dan gaskiya alamar mai ƙaramin ciki ne a tattare da jikin nan naki". Zaro idanun nata da rama suka kara masu girma ta yi, nan take wani irin faɗuwar gaba ya dira mata, da kyar ta haɗiyi yawun wahala a wahalce, sannan ta ce. "A'a gwaggo ni bana jin komai wlh". Shiru ta ɗan yi kamar mai tunanin wani abin, can kuma sai ta ce. "To shikenan ta shi ki je". A hanzarce ta miƙe har kamar zata kifa ƙasa, duk saboda saurin ta bar wajen kada ma gwaggon nata ta sake jefo mata wata tambayar da ƙwaƙwalwarta ba zai iya jura ba. Da kallo ta bita har ta shige cikin kitchen ɗin, ajiyar zuciya ta sauke, a fili ta furta. "Ya tabbata baki da gaskiyar Khadija, wlh akwai abin da kike ɓoyewa, ya Allah gamu gareka, ka dubemu da idanun rahma, ya Allah kada ka sa abin da nake zargine yake a gaske, ya Allah ka kare mun mutumcin dangina". Tana magana idanunta ne suka ciko tab da kwallah, zuciyarta yana yi mata wani irin suya, yau da bata yarda da Allah da Manzonsa ba da ta shiga uku ta lalace, irin wannan jarabawa sai mai karfin imani zai iya ɗauka, duk rintsi duk wuya my people's kada ku kaucewa Allah, kowace irin hali zaku shiga kada ruɗu da tashin hankali yasa ku manta Allah ne kaɗai zai iya fitar da ku. Duk abin da ya faru a kan idanun Zee dake bakin kofa tana ƙoƙarin fitowa ya faru, zata fito ne ta taya Khadijah ɗin aiki ne dama, jin suna magana da maman Hanif ɗin ne yasa ta tsaya tana sauraro, wani irin bugawa da zuciyarta ya yi na jin abin da gwaggon nasu take zargin ƴar uwarta da shi. Da karfi ta dafe saitin zuciyarta tare da furta. "Ciki? Kuma Khadija gwaggo kike zargi? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, na shiga uku ni Zain........." Bata kai karshen maganar ba ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, idan baku manta ba dama tana da ciwo a zuciya baiwar Allah, sai hakan ya fama mata ciwon ya ja mata wata bala'in. Kuma haƙiƙa ta yarda da zancen gwaggon nasu ne ya ja mata wannan matsalar, dan dama ta jima tana zargin Khadija na ɓoye mata wani babban al'amari dangane da ita, sai dai bata kai abin har ga ciki ba gaskiya, amma da gwaggon nasu ta yi magana sai ƙwaƙwalwarta ta tariyo mata komai da ya rinƙa faruwa a tsakaninta da Khadija. Na farko tun da Khadija ta dawo bata ga ta yi fashin sallah ba wato period, sannan sau da dama tana kamata a cikin toilet tana kuka, idan ta tamnayeta sai ta ce ta tuna baba da mama ne, kuma tasan karya take yi mata, dan bata saba yinsa ba, idan ta yi dole a ganeta, amma duk da haka bata nuna cewa ta gane karya take yi mata, sai ta yarda kawai a wuce wajen, to yau ga gaskiya ya bayyana innalilahi wa inna ilahir rajiun wannan wace iriyar bahaguwar ƙaddara ce?......................... 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 29/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E30 A guje maman Hanif ta miƙe ta yi kanta, sunanta take ambata babu kakkautawa cikin tsananin tashin hankali take!. Jin tana ihun sunan ƴar uwar tata yasa Khadija ɗin fitowa daga cikin kitchen ɗin da gudu a kuma ruɗe, haka zalika ita ma Hauwa a guje ta fito daga nata ɗakin. Kansu Khadija ta yi tana ambatar sunan Zee ɗin, ita kuwa Hauwa ganin cewa Zee ce ta suma ba wata masifar da ta zata bace sai ta ja birki ta tsaya a tsakiyar parlourn tana binsu da kallon walaƙanci. A ruɗe Khadijar ta bar kan nasu ta juya da nufin ta je ta ɗauko ruwa su zubawa Zee ɗin, tana juyowa suka yi karo da Hauwa dake tsaye a tsakiyar parlourn tana yi masu kallon rashin mutuncin. Bangajeta Hauwar ta yi har sai da ta yi baya ta faɗi ƙasa, hakan yaja hankalin maman Hanif ta juyo da kallonta a kansu. Yunƙurawa ta yi ta miƙe tsaye, a tsiyace haɗe da walaƙance ta ce. "Ke amma dabbace ko? Ƙwaƙwalwar ki ta jakuna ce da alama". Da yake jahilar ce bata ma san zafin abin da Khadija ɗin ta faɗa ba, sai bata wani ji zafin maganar ba, amma saboda a cewarta Khadijar ta rainata da zata yi mata magana ba respect haka sai ta cire hannu zata dalla mata mari. Kaucewa ta yi marin bai sameta ba, cikin fushi ta ɗago kai, dama ga cikin nata ya mayar da ita mafaɗaciya. Kanta ta yi da nufin ta daddallah mata maruka, dan kuwa duk yadda kake kai zuciya nesa sai Hauwa ta kureka, duk yadda take dannewa ta kawar da kai yau sai da ta kure ta, sam bata so wani abin ya sake haɗasu ba, amma Hauwa muguwar ƴar shisshigi ce. A hanzarce maman Hanif ta riƙeta tana faɗin. "A'a Khadija ki rabu da ita, jeki ki kawo ruwa mu zubawa ƴar uwarki kin ji?". Wani irin hucin da ta fara fitarwa ne zai sa ku gane lallai yau ranta a matuƙar ɓace yake, ta zo har wuya. Zata wuce Hauwar ta danko rigarta ta wajen shoulder ɗinta tana faɗin. "Dawo nan dan ubanki! Da kenan faɗa da ni zaki yi ko? To bismillah, ba kin san abin da uwarki ta sani ba? Ai dole ki ce zaki yi faɗa dani ina matsayin uwarku a cikin gidan nan". Ita fa Hauwa a dole dole so take yi su yi faɗa ta samu wani abin ta buga mata yadda zata raunatata. Aikuwa a wannan karon Khadija tana juyowa ta ɗauketa da wani irin gigitattacen mari mai rai da lafiya. Ihu ta saki kamar wata mai motsi a kai, cukumo wuyar rigar Khadija ɗin ta yi da nufin ta lakkaɗa mata dukan tsiya. Kunsan dai tana fama da kanta, ba wani karfin kirki bane gareta, ba ci a ƙoshi ga ciki, hakan yasa Hauwar ta jefar da ita ƙasa, tana ƙoƙarin hayewa kan ruwan cikinta ta yi mata dukan kawo wuƙa. Aikuwa maman Hanif ta ce ba'a haifi uwarta ba, dankota ta yi, hankaɗata ta yi sai da ta tafi ta kifa a kusa da sofa two seater. Bin bayanta ta yi ta hau jibgarta kamar ba gobe, dama ta jima da takaicin Hauwar nan a ranta, kullum idan ta ganta sai ta ji tamkar ta kasheta kowa ta huta, to yau dai Allah ya yi ta samu dama jibgar banza. Dukar takaici ta rinƙa kaimaya ta ko'ina tana sauke numfashi mai kama da huci, ihu mai sauti Hauwar ta fara fitarwa dan jama'a su kawo mata ɗauki, kunsan akwai ɗaiɗaikun ƴan zaman makoki a waje da suka yi saura. Jin ta dameta da ihu zata iya tara masu jama'a yasa ta dunkule hannunta ta dakarkare ta danna mata naushi a bakin nata. Habawa kan kace me sai jini ya ɓarke, duka ta ko'ina take sauke mata tamkar wadda aka yi wa wahayin duka. Lallaɓawa Khadija ɗin ta yi ta miƙe tsaye, baiwar Allah har wani irin jiri jiri take gani. Kai tsaye kitchen ta wuce tana ɗan dafa bango, ruwa ta ɗebo a bowl ta zo ta fara yayyafawa ƴar uwarta, bata sake bi ta kansu maman Hanif ɗin ba. A ruɗe Zee ta farka, kuka ta shiga yi hawaye bibbiyu haɗe da sambatu wadda sai ka yi zaton yaren China take yi, ko ita kanta bata san me take faɗa ba, surutu kawai take barƙate da yaren da bana mutane ba, kamar wadda ƙwaƙwalwarta ya samu matsala. Rungumota Khadija ɗin ta yi a kirjinta, wani irin tausayinta ne ya kamata, ji take tamkar ta fasa ihu mai sautin dode jin kowa ko zata huta, wannan shi ne rana zafi inuwa ƙona. "Zainab dan Allah ki daina waɗan nan surutan haka ya isa, dan Allah kada ki bari wani abin ya sama mun ke, kada ki manta ke kaɗai ke gareni, ko kina son wani abin ya sameki zuciyata ta buga na mutu ne?". Tana magana tana matsar kwallar da suka cika mata idanun, abin gwanin ban tausayi. Ina ai Zainab kamar ta samu matsala fa a ƙwaƙwalwarta, dan kuwa duk bata jin me ƴar uwar tata take faɗa ba, cigaba da sambatunta kawai take yi. Abin idan ka gani sai ka matsa masu kwallah. Khadija ta rasa ina zata sanya ranta ta ji sanyi, rarrashinta ta shiga yi tana ruwan hawaye tamkar ruwa ya fasa hanya ya ɓallo. Ita kuwa maman Hanif da zuciya ya ɗebeta sai da ta ga Hauwa ta daina wani motsin kirki ga jini da yake bulbula daga bakinta, bakin ya sunduma sum, sannan ne ta kyaleta tana sauke numfashi da sauri sauri, haki ta shiga yi yadda kuka san wadda ta tiki uban gudu ta ƙoshi. Kan su Zainab ɗin ta koma, kama hannun Zee ɗin ta wajen shoulder ɗinta ta yi, ɗagota ta yi suka koma saman sofa. "Khadija jeki ki kawo mata magungunanta da sauri". Ta yi maganar har lokacin tana haki sosai, dan fa ba karya ta jibgi Hauwa iya jibga, wannan shi ake cewa dukan huce takaici. Da gudu ta watsa cikin ɗakin, jikinta sai kerma yake yi ta kwaso magungunar ta fito. "Zainab ɗin ta ci abinci ne?". Cewar maman Hanif. Girgiza kai ta yi, tana kuka sosai ta ce. "A'a bata ci komai ba". Shiru maman Hanif ɗin ta yi tana tunanin ya zasu yi kenan? Dan babu komai da ya danganci abinci a cikin wannan gida, ga shi ita bata da ko sisin kwabo. "Gwaggo dan Allah ki bata maganin mana". Cewar Khadija da voice baya fita. "Khadija ba ta yadda za'ayi ta sha magani ba tare da ta sanya komai a cikinta ba, maganin ba zai yi mata wani amfani ba, dan haka dole mu nemo mata wani abu mai ɗumi wanda zai ɗumama mata ciki ta ci". Zaro idanu ta yi, jikinta sai kerma yake yi, ta gaza tsayuwa waje guda, kamar zata faɗi tana ta tangal tangal. "Na shiga uku na ni Khadija, Zee dan Allah kada ki mutu, kowa sai mutuwa yake yi yana barina, baba ya tafi ya barmu da kewa, yanzu kuma Hajiya ta tafi, ke kam Zee ki tsaya da ni, ko kuma ni gara na tafi na barki". Tana magana tana mai cigaba da tangal tangal. Ba kara ɗaga hankalin maman Hanif suka yi ba, ga abin tausayi marayun Allah. Ta ruɗe sosai a in da take ta faɗin. "Khadija ya isa kukan nan ki yi shiru, Zainab ki yi wa Allah ki daina sambatun nan, kinga kin jefa ƴar uwarki ita ma ta fara sambatu ko? Kin ɗaga mana hankali sosai, dan Allah ki yi shiru". Ita kanta da take maganar kwallah ne a cike tab a idanunta, dan kuwa dole su bawa mutum tausayi. Kamar daga sama suka tsinkayo muryarta tana faɗin. "Gwaggo wlh na yarda ciki Khadija take da shi, tana yawan yin amai a toilet, ga yawan barci da faɗa, idan na yi mata abu kaɗan zata hau zagina abin da a baya ko da sunan wasa bata taɓa yi mun ba, sannan ga kukan da take ɓuya tana yi, na sha kamata tana yi a cikin toilet, innalillahi wlh tun da ta dawo gidan nan dama na ƙasa gane mata". Cewar Zee mai sambatu. Jin zantukan Zee ɗin yasa maman Hanif da tashin hankali ya kusa yin ajalinta ta miƙe tsaye, a razane take kallon Khadija dake tsaye tana layi. Ƙurawa cikinta idanu ta yi, duk da hijabi ne a jikinta amma tabbas cikin ya bayyana, ga alamar ya fara girma. Ai maman Hanif bata san lokacin da ta ɗaura hannu bisa kanta ta kurma ihu mai sautin gaske wanda ita kanta bata san ya aka yi ta yi shi ba. Ihun ya yi sanadiyar buɗewar idanun Zee ɗin. Wani irin bugu da karfi karfi zuciyarta ya fara yi, ita ma da take gwaggonsu kenan, yau da ace babansu yana raye ina da tabbacin wannan mummunar labarin ce zata zama ajalinsa, dan kuwa yana da kishin familyns matuƙa. Zubewa ƙasa ta yi a saman gwiwowinta, dan kafafunta ya kaza iya ɗaukar gangar jikinta, ita ma maman Hanif ɗin zubewa ta yi a saman nata gwiwowin tare da rushewa da kuka mai sauti, tamkar wata ƙaramar yarinya ta shiga rera wi wi wi gwanin ban tausayi. An rasa waye zai rarrashi ɗan uwa, Hauwa dake kwance magashian tana numfashi sama sama ne kunnuwanta suka tsinkayo mata wanna bakin labarin. Ai bata san lokacin da ta waro idanunta waje ba, faɗi take a cikin zuciyarta ta samu damar korarsu daga cikin gidan, a cewarta yanzu maman Hanif ɗin ce kawai ta rage ta yi maganinta shikenan komai ma baban Zee ya zama nata, yanzu dai shirin korarsu daga gidan zata yi, dan dama ta jima tana tunanin hanyar da zata bi ta aiwatar da hakan, ta ƙasa iya kashesu. Abin da baku sani ba, sau biyu tana shirya masu gadar zare Allah yana tsaratar da su, taso salwantar da rayukansu, ko kuma ta turasu waje mai nisan da ba zasu iya dawowa ba, amma duk haƙarta bai cinma ruwa ba, to yanzu dai da alama ta sami abin da take so, a tunaninta zata iya cinma burinta..... To fah!! Akwai matsala, amma dai mu je zuwa ni ina ma zarginta a kan mutuwar Hajiya, dan wannan Hauwar a kan duniya babu abin da ba zata iya ba. "Khadijah wanenen ya yi maki wannan abin? Waye ya cuceki ya kashe mu innalilahi wa Inna ilahir rajiun........". Cewar maman Hanif. Yadda take magana wlh sai ta ɗagawa bawa hankali, saboda wani irin kuka take yi mai tsuma zuciya, tamkar ranta zai fita take ji, hmmmm da mamaesu na nan ta sami wannan labari da sai yaya kenan? Ina ga ita ma shi ne zai yi sanadiyar rayuwarta. Zata gwammaci gara mata zaman prison ɗin. Kuka ita ma Khadijah ɗin take yi tamkar ranta zai fita. Da kyar ta iya faɗin. "Gwaggo nima ban san shi ba, ban sansu ba, kawai ɗaukata suka zo suka yi a kofar gidan nan, daga nan suka wuce dani ƙasar Brazil, a can na yi wata ɗaya da sati biyu cikin wani irin gida da ban isa in fita ko nan da parlonsu ba, kuma wlh gwaggo daga ni sai shi ne kaɗai a cikin gidan, ko parlonsa bana iya kai kaina saboda yanayin tsarin gidan, kofofin gidan dukka sai da password suke buɗuwa, kuma shi kaɗai yasan password ɗinsu, bana fita ɗakin da ya ajiyeni, haka na shafe wannan lokacin, daga nan kuma sai ya ɗaukeni muka je wani gari ne ko wace ƙasa ce ban sani ba, sai da dai muka hau jirgi........." Dakatawa da yin maganar ta yi tana tari mai sauti, irin tarin nan mai kwarzane kirji, mai zafin gaske. Sosai ta yi tarin, tun tana tsugune kan gwiwonta tana yi har ta zauna dirshan mai gabaɗaya. Maman hanif bata da zaɓin da ya wuce ta matso ta riƙeta dan ta tallafa mata, ita ma Zee da sauri ta sauƙo ƙasa daga saman sofar, rungumarta ta zo ta yi. "Zee kawo mata ruwa". Cewar maman Hanif ɗin. A guje ta miƙe, sai dai kuma ta ƙasa yin gudun, saboda ba lafiya ne da ita ba, dan dole ta hakura ta ja kafafunta a hankali ta nufi kitchen, gaɓoɓinta duk ciwo suke yi mata. Ruwa ta ɗebo a cup ta kawo. Karɓa maman Hanif ta yi ta sanya mata a saitin bakinta, a hanzarce ta karɓa ta fara sha ba kakkautawa, Allah sarki har maƙoshinta ya bushe ne saboda tashin hankali. Tas ta shanye ruwan kafin ta cire kai, kifa kan nata a saman shoulder ɗin gwaggon nata ta yi tana mai cigaba da kuka ƙasa ƙasa. "Ban san ƙasar da ya sake tafiya dani a karo na biyu ba, shi ma Brazil ɗin abin da yasa na san a ƙasar nake shi ne, a lokacin da jirginmu da ya ɗaukomu daga Nigeria ya sauƙa a airport ɗinsu, a nan ne na ga kasar da muke, to ɗayan ƙasar da muka je ɗin kuma lokacin da muka sauƙa ina barci, sai dai buɗe idanuna na yi na ganni a wani ɗaki na daban, babu kowa a cikin ɗakin, sai dai hayaniya da na ji a wani ɓangare na cikin gidan, hakan yasa na miƙe da nufin in je in ga su wanene? Ko da na fito na rasa hanya, haka na yi ta bin daga in da sautin hayaniyar yake tashi har Allah ya kaini main parlon ƙasa na gidan..........". Ɗan dakatawa ta yi tana mai jan numfashi, kuka yana neman cin karfinta. "Wanene shi Khadijah?". Cewar gwaggon nasu, a ƙage da son jin amsar ta yi tambayar. "Kin san shi ne? Aina kuka haɗu? Meyasa zai ɗaukeki? A ina yake yanzu?". A cikin tsananin fargabar amsar da zata ji ta jefa mata tambayoyin nan. "Gwaggo ban sani ba, wlh ban taɓa ganinsa ba sai ranar da waɗan da suka ɗaukeni suka kaini gidansa, bani da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da shi, yanzu haka ban san a wace ƙasa yake ba, ban san ɗan wace ƙasa bace, ni sau ɗaya ma na taɓa jin sautin muryarsa, ranar da zamu rabu, a ranar ne ya taɓa yi mun magana, ba komai kuma ya ce mun ba face na kula da kaina sosai sai haɗuwa ta gaba idan Allah ya ƙaddara, shikenan abin da ya ce mun, daga haka ban sake sanin komai ba, tsawon sati ina sume, bayan na farfaɗo da kwana uku aka dawo dani Nigeria, kuma ko da na farfaɗo ban gansa ba, boys ɗinsa ne suka dawo dani kamar yadda suka zo suka ɗaukeni". "Har kofar gidan nan suka dawo dani, sannan suka bani kuɗi suka ce oga ya ce na rinƙa cin abubuwa masu daɗi, kuma na tabbata ya bani waɗan nan kuɗaɗen ne dan a tunaninsa cikin jikina ya fita kamar yadda suka yi yunƙurin zubar da shi tun farko, so shi ne yasa ya bani kuɗin dan na yi jinyar kai'na......" Ta kai karshen maganar tana sake rushewa da kuka mai sautin gaske. Wani sabon kuka maman Hanif ta ɓarke da shi, da yake Zee tasan wacece ƴar uwar tata sosai, sai ta iya gano cewa tabbas karya take yi, duk yadda aka yi ta san uban cikin nan, wlh ta san komai dangane da shi, watakila tasan ba kaunar cikin ake yi bane yasa ta ɓoye dan ma kada maman Hanif ta ce zaa je wajensa har yasan da cikin ya yi yunkuri yi mashi wani abin, amma ba ta yadda za'ayi ace mutum ya ɗauketa tsawon wata biyu suna tare, kuma ya yi mata ciki sannan ta ce bata san shi ba, karya take yi, dole ta san shi! To a ina ta san shi? Ita dai Zee bata yarda da wannan magana ba, dan idan baku manta ba Khadijah ɗin ta yi mata karyar cewa bata san in da aka kaita ba har da ce mata tun da aka kaita a sume take tsawon wata biyu nan, har da ƙarawa wai ƙasar Russia aka kaita, kunga kuwa ai dole ta karyatata a yanzu ma. Sai dai abin da Zee ɗin bata sani ba a nan shi ne, wlh maganganun Khadeejerh a wannan karon kam zallar gaskiya ce, duk abin da ta faɗa hakance ta faru, dama da farko taso ɓoye abin ne shiyasa ta yi wa Zee karya, to yanzu da komai ya tuno kansa me amfanin ɓoye gaskiya? Ai kunga babu, to wlh gaskiya ta faɗa, shi dai uban wannan ciki bata san shi ba, hasalima ba a nan Nigeria yake ba, ɗan Nigeria ne ko ɗan waje ne duk bata sani ba. Ko a ina ya santa? Wannan ne abin tambaya, yanzu kuma a ina zata gansa har ta kai mashi ɗansa ko yarsa idan Allah yasa ta haife? Sannan ɗan wani ƙasa ne uban? Ina yake a halin yanzu? Shin yasan tana ɗauke da cikinsa? Wacece wadda Khadijah ɗin take yawan tunano muryarta tana ƙoƙarin zubar mata da cikin? Ya tabbata kenan kamar yadda Zee take hasashe ba'a kaunar wannan cikin kenan? Tun da ga shi har alluran zubar da shi aka yi mata! Lallai akwai cakwakiya sosai, haƙiƙa akwai abin da Khadijah ɗin ta rage bata sanar da su ba, dan kuwa bayan rayuwar da ta yi daga ita san uban cikin nata tabbas ta yi wani rayuwa da wata na ɗan lokacin, dan in baku manta ba bata tuna uban cikin nata kamar yadda take tuna sautin muryar wannan mata da zata zubar mata da cikin, ta ɓoye wannan labarin baya gaya masu ba. To wacece wannan mata?. Ni kam na ce amma lallai wannan uban ciki na Khadijah anyi ɗan duniya na bugawa a jarida, tsabar isa da iskanci kawai kasa a ɗauko maka yarinyar mutane, ka ɗirka mata ciki ba gaira ba dalili, sannan ka yi yunƙurin zubar da ciki, ka kuma sakota a jirgi a dawo da ita Nigeria kamar yadda ka ɗauketa, wai ma a ina ya santa? Da alama guy ɗin ɗan balai ne, fata nama dai ni kam Allah yasa musulmi ne ba kafuri ba, amma dai wannan ya kai duk in da ɗan iska dan duniya ya kai wlh, anya yana da iyaye ma kuwa? Daga gani da wuya idan yana da mafaɗa gaskiya!. Ɗan rungumuta maman Hanif ta yi tare da shiga rarrashinta sosai. After some minutes, da kyar suka samu ta yi shiru, bayan ta yi shirun komai ya lafa sun kudundune waje guda ita da Zee. Kallonta da kyau maman Hanif ɗin ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Khadijah to me zai hana mu je asibiti a zubar da cikin nan, kinga sai ki fito da miji kawai ki yi aure ki hutawa ranki". Zaro idanu waje sosai ta yi, tamkar zata sa kuka ta ce. "A'a gwaggo, ina son cikina, idan na zubar da shi me ribana? Mutumin nan ya zalunceni, ya cuceni, ya lalata mun rayuwata, sannan da ya fahimci ina da ciki shi ne yasa a zubar mun, yanzu a tunaninsa an zubar da cikin, da alama babban mutum ne wanda baya son sunansa ta lalace na ya haifi ɗan shege, shi ne yasa ko ta halin ƙaƙa a zubar mun da cikin, ba abin da basu yi ba sai dai jinina ya zuba, amma cikin yana nan, tun da kika ga haka cikin nan yaki fita gwaggo to tabbas akwai wata aya da Ubangijinmu yake son nuna mana, kuma ni kai'na ina son haifar cikin, ko dan na ɗauki fansar abin da suka yi mun". "Kullum mama tana yi mana nasiha, hakan yasa ta ja na yi wa ɗan shege muguwar tsana, sai ga shi yau ni ce da kai'na zan haifi ɗan shegen kuma a cikin gidanmu innalilahi wa inna ilahir rajiun....." Wani sabon kuka ta fashe da shi. Shiru maman Hanif ta yi tana jinjina wannan al'amari a ranta, tabbas Khadija tana da gaskiya, tun da ba abin da ba'ayi wa wannan ciki ba yaki fita to gara kawai su barshi kada su ja rayuwar yarinya ya salwanta a banza, sannan kuma kamar yadda ta faɗa ne, tun da uban cikin baya son ɗan har ya yi yunƙurin zubar da ciki to tabbas yana da kyau ta haifi ɗan, idan ma uban nasa babban mutum ɗin ne ta yi amfani da wannan dama shi ma ta rusa mashi farincikinsa kamar yadda ya lalata mata tata, dan haka ya cancanci a bar wannan ciki ta haifesa, kuma cikin ma ya wuci munzalin zubarwa a yanzu, dan ya kai ɗa......... Tirƙashi ana yinta a RAWANIN ZALINCIN!!.🔥 Wunin yau cikin tsananin rashin daɗi suka yi shi, duk suna cikin damuwa, walwala ya kau daga tattare da su, Hauwa kuwa ta ja jiki ta kai kanta hospital dan ta jibgu ba karya. Sai da aka yi kwana bakwai da rasuwar Hajiya sannan maman Hanif ta koma gidanta, maman Haidar dai shiru bata ba labarinta bata san mamansu ta rasu ba. Allah sarki, time da maman Hanif take tare da su a gidan Khadija taga kula sosai irin wadda kowace mai ciki zata buƙata, tana komawa gidanta kuma suka fara fuskantar matsala da Hauwa, da maman Hanif tana nan sam bata shiga harkarsu, dan kuwa tana tsoron ta sake cin jibga, da farko ƴan'sanda taso kirawa maman Hanif ɗin, sai kuma ta fasa, dan bata son case ɗin ya zama babba, saboda tana son maman Hanif ta koma ita kuma ta fara gallazawa su Khadija har sai sun gudu da kafafunsu sun bar gidan, shi ne shirinta, sannan tana son yi wa maman Hanif ɗin wani mugun abin dan ya zama ita ce kaɗai zata cinye dukiyar bb Zee, shiyasa bata kira ƴan'sanda ba, dan idan ta yi mata abin ya faru ƴan'sanda zasu iya shiga case ɗin, idan suka shiga kuma za'a iya bukatar waɗan da suka taɓa sa in sa da maman Hanif ɗin dan bincike, kunga a nan asirinta zai iya tonuwa, shi ne yasa ta hakura bata kirasu ba Ai kuwa haƙarta yana son cinma ruwa a wannan karonma, dan kuwa da alama burinta zai iya cika, saboda kuntata masu da take yi tana shiga harkarsu ta yi ta lalata masu abubuwa idan suka ajiye, idan suna girki ta zo ta zuba omo ko ta juye kedar gishiri a ciki, da kyar da suɗin goshi suke samun abin da zasu sanya a bakin salati, sai suna girkawa ta lalata masu. Wani lokaci haka suke kwana su wuni da yunwa, hakan yasa Khadija ta fara bawa Zee shawara a kan su je Kaduna su nemo su Sadiq, daga nan su nemi aikin yi wanda zasu rinƙa yi dan su rufawa kansu asiri, yunwar nan ta yi yawa. Da Zee ta ce. "To Aunty khadina baga kuɗin da kika dawo da shi ɗin nan ba, ki fitar mu fara sana'a da shi". Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Zee ki bar batun wannan kuɗi, ina tanadinsu ne domin in ɗauki fansa a kan wannan mutumi, jira nake yi na haifi cikin tukun nan, dan mu gwabza shari'a, shiyasa bana son taɓa kuɗin". Tana magana tana shafa cikin nata da a yanzu ya kai almost 6 to 7 month. Ashe dai tasan da zaman kuɗin ba mantawa ta yi da su ba, ashe tanadinsu take yi dan gwabza faɗa ta kwatarwa da kanta ƴanci, akwai cakwakiya kenan, muje zuwa, da alama Khadija zata ɗauki dala ba gammo, idan babban mutum ne kuna tunanin zata tona masa asiri kamar yadda take tunanin nan kuma ta zauna lafiya? Ya zuba idanu yana kallonta?. Hmmmm akwai matsala gagarumin ma kuwa!!. "Haka ne kuma, nima zanso ki ɗauki fansa a kan wannan bakin shaiɗani azzalumin". Cewar Zee. "Yauwa ashe kin gane, yanzu kinga mu shirya mu sa ranar tafiya Kadunar nan, dan na gaji da zaluncin Hauwa, banda RAWANIN ZALINCI da mugunta babu wani abin da yake kanta, gara mu tafi wajen kawu sai ya fi mana, kinga ba iyawa da ita zamu yi ba, ni bani da karfi a halin yanzu, ke kuma baki da lafiya, ba zamu iya da ita ba, gara kawai mu bar mata gidan. Na'am da zancen nata Zee ta yi. "To amma Aunty khadina kuɗin motar zuwa fa? Sannan a ina zamu ga su kawun?". Tana magana tana ɗan zaro idanu alamar ta shiga ruɗani. "Kuɗin mota kam zan ɗauka mana a cikin kuɗin da na zo da shi, su kuma su kawu In Sha Allah zamu gansu". Ta kai karshen maganar tare da karkatawa ta kwanta a saman gadon ta tada kai da laps ɗin Zee. Duk waɗan nan maganganun da suke yi a kan kunnuwar Hauwa suke yinsa, ta yi masu laɓe tana jinsu, burinta kawai ta ji sun faɗi a in da suka ajiye kuɗin, dan ta sha alwashin sace kuɗin nan ko ana ha maza ha mata, Allah Allah take yi wani tsautsayi ya ja su fita daga cikin ɗakin ta shigo ta kwashi kuɗin abinta. Bakar mugu ba, to ta Allah ba taki ba, In Sha Allah ba zaki gansu ba bare har kwashe. Shafa kan Khadijah ɗin ta farayi suka cigaba da yin hira a in da Zee take ta yi mata magiya a kan idan mace ta haifa dan Allah ta yi mata takwara. Alkawari ta yi mata a kan za'ayi haka, koda ta mutu idan yarinyar ta zo da rai to ta rinƙa kiranta da Zainab. Girgiza kai ta yi tare da cewa ba zata mutu ba, In Sha Allah ita zata shayar da ƴar tata. Amin kawai ta amsa da shi, amma ita a jikinta bata jin zata cigaba da rayuwa mai tsawo........... __________________________🔥 DUBAI🛬 Leesharh, kwance take a saman bed ɗinsu tana fuskantar saman celling, ta yi shiru da alama duniyar tunani ta luluƙa, wayarta ce ta fara ringing, ba wayar da masu nikaf suka bata ba, a'a, wayar da Bilal ya saya mata ita da Sharifat iri ɗaya, jiya ya sayo masu wayar ya kawo masu, akwai sim card da komai a ciki. Ganin sunan my brat ne yasa ta yi saurin picking. Sharifat ce. "Hllo Bloody". Daga ɗayan ɓangaren Sharifat ɗin ta faɗa. "Naam Brat". Ta masa mata tana miƙewa zaune, ta kara kyau sosai, har ɗan cika ta yi, ta yi kumari saboda kwana biyun nan ta rabu da su annoba wato masu nikaf, tun da ta jefa wayarta a cikin echolac bata sake bi ta kansa ba. "Bloody ki zo ɗakin Abbie yanzu". Cewar Sharifat ɗin. Da okey ta amsa tare da miƙewa zaune tana katse kira , wandon jeans fari ne a jikinta, daga ta sama kuma riga ce black color mai karamar hannu iya daidai shoulder ɗinta, kanta babu ɗan'kwali, ta saki gashinta da yake shan gyara sosai a hannun Sharifat, sai kyalli yake yi. Kasa ta sako, mayafinta mai ɗan girma ta ɗauko, yafawa ta yi tare da ɗaukar wayar tata, ta sanya parlourn sillpers masu kyau da laushi a kafafunta, sannan ta fito. Kai tsaye part ɗinsa ta nufa, tana kan tafiya ne massage ya shigo cikin wayar tata, ƴar kara wayar ta yi, haka yasa ta kunna wutar screen ɗin dan ta duba saƙon wanene?. Tana yi tana cigaba da tafiya, bata ankaraba dab zata shiga parlon Abbie shi kuma yana fitowa, karo suka ci a in da dukkansu wayoyinsu suka faɗi ƙasa, shi ma yana tafiya ne yana latsa waya kamar dai ita, shiyasa suka ci karo ba tare da sun farga ba. Wani irin tsoro ne ya kamata, tsoron ɗagowa ta kalli wanenen ma ta ji, ƙasa motsawa daga in da take ta yi. Hakan ba ƙaramin haushi ya bashi ba, ta buge mashi waya kuma ta ƙasa tsugunnawa ta ɗauko ta bashi hakuri? Lallai yarintar nan da me take taƙama? Ya jefawa kansa tambaya. Ai ko da wuta take tafiya a bakinta sai ta san yau ta haɗu da Ramish ya faɗa a ransa. Wani irin marin da ya dalla mata a kumatu ne yasa ta dai'na gane komai, ji ta yi kamar ba a duniya take ba, duk da take chocolate color sai da yatsun hannunsa suka fito a saman face ɗinta, alamar ta maru kenan, har wani jiri ne ta ji yana ƙoƙarin ɗibarta, hankalinta sai da ya gushe na wucin gadin. Bilal da yake bayansa da suka fito a tare ne ya ce. "Ramish yau kai ne da sanya hannunka a jikin mace? Abin da mamaki, what kind of sadness did you feel da har ka mareta?". Yana magana yana kallon ta ta yi mutuwar tsaye, ko motsawa ta kasa yi. Dr Raj dake bayan Bilal ɗin ne ya amsa da. "Dole ya mareta mana, kana gani ta buge mashi waya amma taki tsugunnawa ta ɗauko ta bashi hakuri!"............ Aka ce so so ne amma sonkai ya fi, karo fa suka yi, ba ita ta buge shi ba, duk suna kan latsa wayar ne suka bugi juna, amma sun ɗaura mata laifi sun bi bayan ɗan uwansu, sun haƙiƙance itace ta buge mashi waya. A tare suka fito daga ɗakin Abbien nasu, gaishesa suka je suka yi. Tsugunawa Bilal ya yi ya ɗauko wayoyin dukka biyu, ya damƙa mata nata a hannunta tare da kama hannun nata ya turata cikin parlourn, sannan ya miƙawa Ramish ɗin ma nasa yana faɗin. "Sorry bro". Ɗan binsa da kallon mamaki Dr Raj ya yi. "Amma Yah Bilal ni kam me haɗinka da wannan aljanar yarinyar ne?". Kasa hakura ya yi sai da ya tambaya, dan abin yana bashi mamaki yadda Bilal ɗin yake yi mata mugu mugun saukin kai, ko Sharifat baya yi mata irin hakan. Wucewa Ramish ya yi ba tare da ya karɓi wayar tasa ba, bayansa suka bi Bilal yana faɗin. "Dr tausayi take bani kawai". Ya faɗa yana cusa wayar Ramish ɗin a cikin aljihunsa, dukkansu shigar Arabs jallabiyas ne a jikkunansu. Ta jima a tsaye a bakin kofar parlourn ta gaza motsawa daga in da take, raɗaɗin marin nasa ne yake ratsa tsoka da jijiya har izuwa ɓargon kashin jikinta, bata taɓa jin mari mai zafin wannan ba, kai ko marin gandurobobin gidan yarin AAJ bai kai ko rabin nasa a zafi ba, ko marin su Omaid da suke twins bai kai nashi zafi ba, har ta ji duniya ya canza mata. Sautin muryar Ummie da ya daki dodan kunnuwanta ne yasa ta farga ta dawo cikin hankalinta, firgita ta yi tare da zaro idanun, ba komai Ummien ta ce mata ba face me ya kawota part ɗin mijinta?. Murya na rawa ta ce. "Sharifat ce ta kirani wai na zo". Da hannu ta nuna mata hanyar barin parlourn ba tare da ta yi magana ba. Da sauri ta juya har tana haɗawa da ɗan gudu gudu. Tamkar zata kifa ƙasa, a haka ta wuce ta koma ɗakinsu. A saman gado ta kwanta tare da kunna wutar screen ɗin wayar tata. Ajiyar zuciya ta sauke ta sanya hannunta guda ɗaya a saman kumatunta in da ya mareta, ƙasa ƙasa ta ce. "Mugu azzalumi Allah zai saka mun, ashe haka kake bakin mugu, ai dole ne ma jama'a su nemi kashe ka, daga gani ka zalunci mutane dayawa ne, sai Allah ya saka masu, idan ka yi wasa ma makiya ne zasu kasheka a kan titi, daga ɗan yi karo da kai kawai ka sauke mun wannan hannun naka kamar na samudawa, Allah ya isa na". Tana surutan tana cire password na wayar dan ta duba massages ɗin da ya shigo cikin wayar tata ɗazun kafin su yi karo da shi. A wani irin zabure ta miƙe zaune, wani irin razana ce ta bayyana a saman face ɗinta lokacin da ta ɗaura idanunta a kan saƙo. A ruɗe kuma a fili ta furta. "Who give them my number? A iya sanina only Sharifat ce kawai take da numberta, ko shi Yah Bilal da ya saya mana wayoyin bana tunanin yana da number. Mamaki ne ya kusa kasheta, har ta kasa karanta sakon, wani irin fargabar abin da zata ji dangane da sakon ne ya kamata, yau kuma dame suka zo? Infact a ina suka samu contact ɗinta?...... Idan kun fahimci wani abu my people's, masu nikaf fa basu da wani zaɓi ne da ya wuce dole su sake nemanta, dan itace kawai ta samu damar da babu wata da taɓa samun makamancinsa a gidan, babu yar aikin da aka taɓa yantawa sai ita, sun san yanzu ta zama yar gida zata ƙara kutsawa cikin family sosai, ta samu wajen zama, yanzu ne ma aikinsu zai tafi yadda suke so cikin farinciki, dole su nemota su lallaɓata, shiyasa suka sake yi mata text a kan zasu sanyata aiki na karshe wanda ba mai wahala ba ne, amsa kiran waya ce kawai zata yi idan lokaci ya yi, daga wannan aikin amsa call ɗin da zata yi shikenan zasu bata babanta su kuma mayar da ita kasarsu. Jin hakan yasa ta miƙe zaune, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata daga gefe fuskarta. Tunani ta fara yi a kan in dai amsa call ne kawai ai gara ta yi masu su bata babanta. To amsa kiran me? Magana zata yi da wani? Leesharh ta kasa gane cewa yanzu fa time ɗinta ne, ta kasa fahimtar cewa yanzu fa sai dai ita ta juya masu nikaf ba dai su su juya taba, yanzu Allah ya ara mata dama, tana da damar da zata iya ce masu idan basu yi mata kaza ba ita kuma ba zata yi aikin ba, ba su da zaɓi kuma ba yadda zasu yi da ya wuce dole su yi abin da take so, dan kuwa ita kaɗaice zata iya yi masu wannan aiki, dole su lallaɓata idan suna so, amma duk bata gane hakan ba, bata gane cewa yanzu ita fa abin su lallaɓane idan suna son aiki, ba wai su rinƙa yi mata barazana ba, da yake tun farko da tsoronsu a ranta, sun rigada sun sanya mata tsoro azzalumai sai ta ƙasa gane komai. Shiru ta luluƙa duniyar tunani, bata san da shigowar Sharifat ɗakin ba sai tsinkayo muryarta ta yi tana faɗin. "Bloody me ya sameki a kumatu? Waye ya mareki? Kuma ya baki zo kiran da Abbie ya yi maki ba?". Ƴar firgita ta yi alamar mutum yana cikin tunani, a hanzarce ta shiga sharce gumin dake saman face ɗinta. Da mamaki ɗauke a fuskarta Sharifat ta ce. "Bloody lafiya kike kuwa? Gumi fa naga kike yi? Ko dai gudun Acn ne ya yi maki kaɗan ko baki da lafiya ne?". Duk tana ruɗe, hannunta har yana kerma wajen fita daga kan massages ɗin ta kashe wutar screen ɗin, murmushin dole ta ƙaƙalo tare da faɗin. "Brat babu komai fa, kawai ina tunanin mamata ce, Abbie kuma kin san har yau bana iya gane wasu hanyoyi na cikin gidan nan, na fita zanje wajen nasa sai na rasa hanya". Ajiyar zuciya ta sauke tare da zama a kusa da ita. "Allah sarki my bloody, da na yi zaton wani abin ne ya sameki, kada ki damu ki rinƙa yi wa mama addu'a Allah yasa tana cikin rahmarsa". Da amin ta amsa tare da ɗan runtse idanunta, tunanin Jasrah ce ya faɗo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, Allah sarki baiwar Allah, yadda Sharifat take bata shawara a kullum, yadda take nuna mata girman Allah a kullum sak yadda Jasrah take yi mata, suna yi mata kamanceceniya, ga shi bama su san juna ba bare ta ce suna da alaƙa ta jini, haka kawai Allah mai halitta sai komai nasu yana zuwa kusan iri ɗaya, wani lokaci idan Sharifat ta yi magana sai ya yi mata tamkar Jasrah ce a wajen take magana, tana yawan yi mata addu'a a kullum, dan tasan yanzu ƴan watanni ne da basu wuci biyar zuwa shidda ba suka rage a yanke mata hukuncinta, a ratayeta a kashe, innalilahi wa inna ilahir rajiun. A wani ɓangaren na zuciyarta kuma wani tunani ne ya faɗo mata, shiru ta yi tana tuna lokacin da mahaifiyarta take magagin mutuwa ga wuƙa a saman tsakiyar ruwan cikinta, ya fasa fatarta ya shiga har can ciki, faɗi take. "Leesharh ki yafe mun, ki yafe mun duk abin da na yi maki, nasan na cutar dake na ɗauki alhakinki, duk abin da kika yi a duniyar nan ba laifin kowa bane laifina ne, na yi danasani a lokacin da na rigada na san lokacin ta kure mun, amma dai ina sa ran zaki yafe mun, idan kin haɗu da Abbanki ki ce ya yafe mun, haƙiƙa na cutar da ku, sai magana ta karshe kuma shi ne........". Wani irin zabura ta yi tare da furta. "Hakan ba zai yiwu ba mama, ni ba zan taɓa yarda da waɗan nan kalaman naki ba". Tsoratar da Sharifat ta yi tare da miƙewa zata gudu ne yasa ta farga ashe a duniyar gaske ta yi maganar ba'a duniyar mafarki ba, hakan yasa ita ma ta miƙe tsaye tana faɗin innalilahi wa inna ilahir rajiun. Ta lura idan bata yi hankali ba watarana tunanin mahaifiyarta zai iya sanya a ce mata tuburar mahaukaciya. "Bloody zaki sa na gudu, tunanin me kike yi haka har zancen zucin naki ya fito da karfi?". Komawa ta yi ta zauna tana wani irin sauke numfashi kamar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi, dafe saitin zuciyarta ta yi tana huro iska daga bakinta, bata iya amsawa Sharifat amsarta ba saboda ruɗewa. "Bloody yakamata ki dai'na yawan tunani, kinga a yanzu tunani ya fara sanyaki kin fara surutai da karfi a bayyane, na ce maki addu'a zaki rinƙa bin mama da shi, ni tashi mu je mu yi breakfast ma, amma kafin nan ki rakani na kaiwa su Yah Ramish abincinsu, mu dawo mu yi namu breakfast ɗin, Abbie kuma yana kiranki a kan result ɗinki ne, dan ya ce yana son week ɗin nan ki fara zuwa school". Shiru ta ɗan yi kafin ta amsa da. "Ni dai Brat ba zan je wajensu Yah Ramish ba, sannan ni breakfast ɗin ma mu yi namu a nan ba sai mun je main parlourn ba, sai ki rakani wajen Abbie ɗin daga haka na amsa kiran nasa". "Oh oh oh yanzu na gane dalilinki na kin zuwa amsa kiran Abbie kika wani fake da cewa baki gane hanyar ba, dama naji ne kawai amma ban yarda ba, wai bloody sau nawa zan gaya maki ki dai'na ɓoye mun abin da Ummiena take yi maki? Dama na yi tunanin yadda ta baro room ɗin Abbie ɗin nan da wuya idan baku ci karo ba, ban yi tunanin zata fita a lokacin bane shiyasa nakiraki nace ki zo, nasan ita ta hanaki shiga ko?". Ta kai karshen maganar tare da komawa ta zauna. Girgiza kai ta fara yi. "A'a ni Ummie bata yi mun komai ba, kuma bata hanani shiga ba, ban ma haɗu da ita ba, kawai dai hanyar ce ta ɓace mun". Ta yi maganar kai a ƙasa. "Bloody kenan, watanninki almost 6 a gidan nan amma ki ce wai hanyar zuwa ɗakin Abbie daga nan ne ba zaki gane ba? Anyway yanzu dai zo mu je mu kaiwa su Yah Ramish abinci, kin ma san me nake tunani ne?". Girgiza kai ta yi alamar a'a, a cikin zuciyarta kuwa ta furta Alhamdulillah da Allah yasa zata canza masu topic na hira. "Addu'a nake yi Allah yasa Yah Bilal ya kamu da sonki, kinga ina son Yah Ramish sai kawai a haɗa aurenmu, matsalar ma ke ɗin nan wawiya wawiya ce, sai ki rinƙa cewa kina jin tsoronsu, ba fa abin da zasu yi maki, dan kuwa su ɗin basu dukan mata, Yah Ramish ya ce me abin duka a jikin mace? Wai idan ya ce zai daki mace mutuwa zata yi, shiyasa baya farawa, nima idan na yi masu laifi harara ta kawai suke yi a wuce wajen, dan haka ki dai'na tsoronsu kema kin ji?". Kai kawai ta gyaɗa mata alamar to, amma batun ta dai'na jin tsoronsu kam babu shi bai taso ba, dan fa dole a ji tsoronsu, zaratan samari irin haka ai dole hantar ciki ta kaɗa idan ta gansu. "Yauwa my gurl, ki rinƙa tsara kwalliya idan zamu je wajensu, Ummie na ta ce in dai ina son shawo kan Yah Ramish har ya fara ɗaga idanu yana kallona to sai da hakan, dan haka kema ki ɗaura ɗamayar sace zuciyar Yah Bilal saboda mu auri yaya da kaɗin zan yi farinciki da hakan". Okey nan dai da shi kawai ta bita, dan kuwa dai ba ɗaukar shawarar nan tata zata yi ba, ita kaɗai tasan abin da ya kawota gidan, ba auren ɗan gida ta zo yi ba, dan haka babu ruwanta da su, yanzu ma jiran ranar da masu nikaf zasu ɗauketa kawai take yi, dan tasan dole zasu ɗauketa kamar yadda suka kawota, ta san suna kewaye da ita, duk wani motsinta suna samun information a kai, ga shi yanzu ma daga saya mata waya jiya har sun sani sun kuma samu number. "Yanzu gaskiya ki yi wanka ki canza kayan nan mu je kai masu breakfast, sai mu zauna mu ɗan yi hira a wajensu, dan ma dai Yah Rizwan baya nan, shi ne abokin hirana, su sauran basa magana, sai dai ki zauna shiru kina kallon film". Ta kai karshen maganar tana miƙewa tsaye. Okey nan dai shi ta sake amsa mata da shi tare da miƙewa ita ma, har ga Allah bata so binta part ɗinsu ba, dan ita bata son hanya ma yana haɗata dasu ba batun zuwa in da suke ba ma tukun nan. Sharifat fa wayayyiyar yarinya ce sosai, idanunta a buɗe suke, gata da iya soyayya dan mayyar kalle kalle film ɗin turawa ce, kada ku manta na gaya maku tana da yawan karance karance da bincike bincike, ta iya bada shawarar yadda za'a sace zuciyar namiji, amma ita kuma ta kasa sace zuciyar Yah Ramish ɗin nata, ko kallon ma bata ishe shi ba, dan shi ɗin wani irin bahagon mutum ne ba mai iya mashi sai Bilal and mamarsa, ko King Zuhair wani lokaci hakuri yake yi kawai ya kyalesa, ita maman nasa kawai ya san girma da darajar mahaifiya ce yasa baya musa maganarta komai ƙankanta, hakan yasa ake ganin kamar ita ce kawai take iya mashi, ba wani nan, kaunarta yasa hakan. Shi kuma Bilal shakuwar da take a tsakaninsu da tsananin kaunar juna yasa idan ya ce yana son Ramish ɗin ya yi abu to yana yi dan kauna, suna iya sadaukarwa juna da abubuwa sosai, hakan yasa ake ganin kamar Bilal ɗin yana iya mashi, kaunace kawai shi ma. Toilet Sharifat ta nufa, wanka ta yi, yau da kanta ta ciro masu kaya masu shegen kyau, Italians gown ta fitar masu, kayan daidai yake da shape ɗin jikinsu, yana ɗaya daga cikin kayan da suka sayo lokacin da Bilal ya kai su shopping. Ita ma Leesharh wanka ta yi suka tsara shirunsu, yau Sharifat ɗin ce ma ta yi wa Leesharh kwalliya, wai duk dan ta sace zuciyar Bilal, ni kam naga ikon Allah, ita ta kasa iya sacen zuciyar nata masoyin amma tana tsarawa wata yadda ita kuma zata saci zuciyar wani, abin dariya wai yaro ya tsinci hakwara. Ba karya sun yi kyau kam matuƙa, kayan ya bi shape ɗin Leesharh sosai, dama na gaya maku tana da shape mai tafiya da imanin duk wani lafiyayyen namiji, mata ma idan suka ganta sai sun sake juyowa sun kalla bare maza. Haƙiƙa Sharifat ɗin ta ɗan ji wani abin a ranta na ganin duk kayan da zasu sanya sai ya fi zama a jikin Leesharh tamkar dan ita aka yi, kuma komai na kayan iri ɗaya, amma sai ya fi bin shape ɗin Leesharh ya fita zat, ta kasa yarda cewa Leesharh ta fita good bye and welcome, da alama Sharifat tana da kishi sosai gaskiya. Amma bata bari hakan ya yi tasiri, tana kore tunani, yanzu ma kore tunanin ta yi tare da riƙo hannunta suka nufi waje, kamar wasu taurari haka suke haskawa........... Eyeee my people's yara sun shirya sace zuƙatan zaratan samarin Abbie, gaskiya ne!! To dai mu je zuwa muga su zasu yi nasara ko dai samarin Abbien ne zasu yi nasara.( Ni dai na ce Leesharh Sharifat zata kai ki ta baroki ar To🥱🤣) Kayan abincin nasu Sharifat ta ɗauko, a parlon suka isko Ummie and Abbie suna yin breakfast, cikin girmamawa ta ɗagawa Abbie gaisuwa, da yake shi ba mutun ne mai fara'a ba, kamar dai Mommar Zunaira yake shi ma, bashi da fara'a sai waɗan da yake kauna sosai yake sakarwa fuska, hakan yasa face ba yabo ba fallasa ya amsa mata gaisuwar tata tare da zuba masu ruwan albarka. Amin suka amsa da shi, sannan suka juya, Leesharh ta ɗagawa Ummie gaisuwa, ita kuma Sharifat ta ɗan yi gaba da kayan abinci. Rai a jagule ta amsa a takaice da lafiya, da alama amsar ma bata kai zuciya ba, saboda Abbie yana wajen ne ma yasa ta amsa. Bayan Sharifat ta bi suka nufi part na samarin Abbien. Yau a parlon ta samesu dukkansu, sun sauya shigar da yake jikinsu daga jallabiya izuwa ƙananan kaya. Bilal and Ramish suna sanye da hoodies dan ana ɗan sanyi sanyi, shi kuwa Dr Raj t-shirt and Jeans ne a jikinsa. Ramish yana riƙe da cup mai ɗauke da cappuccino, yana tsaye a tsakiyar parlourn, ga zura hannu ɗaya a aljihun wandon jikinsa. Bilal yana tsaye wajen center table, ya ɗaura kafarsa ɗaya a saman center table ɗin tare da haɗe hannayensa dukka biyu waje guda ya zubawa Ramish ɗin idanu, shi kuwa Dr yana zaune saman two seater yana binsu da kallo, da alama magana mai mahimmanci suke tattaunawa. Sallamarta yasa suka dakata da maganar da suke yi, dama Dr Raj ne yake magana a lokacin. Da kallo Dr ya bi Sharifat ɗin, shi kuwa Ramish da kallonsa yake a kan Bilal bai yi mashi kamar ma mutane ne suka shigo cikin parlourn ba, ko gezau bai motsa ba. Bilal ma dai satar kallonsu ya yi dan gulma. "Hakan ba mai yiwuwa bane, is better for you to look for another way". Ramish ne ya yi maganar a sanyayye, har lokacin kallonsa naa kan Bilal. Mamaki ne ya kama Leesharh na jin maganarsa, tamkar ba muryan maza ba, ba kuma muryan mata ke garesa ba, da yawan maza suna da ƙaton murya, muryarsu a fashe yake, amma shi muryarsa tana da sanyi sosai ga daɗi sauraro sai kaifi irin na King Zuhair. Ajiyar zuciya Sharifat ta sauke domin wani sanyi ta ji a ranta na sauraron voice ɗinsa, baya da yawan magana, ko kana tare da shi zaka jima baka ji maganarsa ba, muryarsa mai tsada ce. A saman table ta ɗaura masu abincin nasu tare da nufo saman sofa kusa da Dr Raj ta zauna tama murmushi. Turus Leesharh ta tsaya a wajen table ɗin, already Sharifat ta wuce gaba ta barta, ita kuma tana tsoron ƙarisawa wajen nasu ita kaɗai, sai kawai ta tsaya turus a wajen. Bilal da tun da suka shigo yake satar kallonta ta wutsiyar idanunsa ne ya juyo da kallonsa mai gabaɗaya a kanta, ta tsaya kamar wata sakarya tana raba idanu. Kamar zai yi mata magana sai kuma ya fasa, saboda Dr Raj ya saka mashi idanu a kanta, sai ya basar kamar bai ga tana tsaye ba. Ganin tana tsaye yasa Sharifat ta ce. "Leesharh ki zo ki........". Ƙasa ƙarisa maganar ta yi saboda idanun masoyin nata da ya sauka a kanta, maganar da ta yi ne yasa ya kawar da kallonsa daga kan Bilal izuwa kanta, kaifafan idanun nasa suka sa ta kasa idasa maganar tata, Sharifat tana da abin dariya sosai, yayanta ne, gidansu ɗaya, tana bala'in sonsa amma tana bala'in tsoronsa, ko cikin idanunsa bata iya gani, ko maga take yi idan ya kalleta sai ta haɗiye maganar, ni kam zan ga ta yadda za'ayi wannan soyayya, na tausaya mata, dan kuwa shi dai Ramish bai san tana yi ba, infact yama tsani mahaifiyarta, ita ɗin ma albarkacin Abbiensu take ci ya barta tana zuwa part ɗinsu, ku kunsan yadda ya tsani Ummien nan da wuya idan zai yarda da wani zancen sonta, sai dai idan dole Abbien zai yi mashi, kuma wlh shi ba kunya ce da shi ba, dan ya zauna ya gayawa Abbie baya sonta ƙaramin aikinsa ne, mutum ne mai magana kai tsaye, ba ruwansa da abi da maganar zata haifar, shi dai zai faɗi san ransa ato, ga shi idanunsa babu kunya ko ɗigo, a bushe suke. Jin takasa ƙarisa maganar yasa tun basu ganta ba suka gane Ramish ya kalleta kenan, dan kuwa ba ita kaɗai ba ko jami'ansa idan suna magana da zarar ya sauke idanunsa a cikin nasu sai sun sha jinin jikinsu su ɗan daga ta da yin maganar, sai daga baya su cigaba, yana da idanu masu kaifi ne sosai. Ta wutsiyar idanunsa Ramish ya kalli Leesharh ɗin jin Sharifat ta ce ta zo ta zauna, shi ne bari ya ga wacece ma?. Ga mamakinsa sai ya ga yarinyar da ya mara ɗazun ne, tunani ya fara yi a kan wacecec ita ɗin? Dan lokacin da Abbie ya ƴantata ai kunga yana sume. Wata zuciya ce ta ce mashi bai wuce kwashen ƴan uwan Ummie bane, tuna hanan yasa ya nufi saman table ɗin dan ya yi breakfast abinsa, a cewarsa dik abin da ya shafi Ummie bashi da lokacinsa. A hanzarce Sharifat ta miƙe, fuska a ɗauke da ƙayatattcen murmushi, tana murna ta ce. "Yah Ramish bari na yi serving ɗinka". Allah sarki soyayya kenan, har wani nishaɗi take ji a duk lokacin da take yi mashi hidima, daɗi sosai take ji, shi kuwa tamkar gunki bai san tana yi ba. Yana isowa kusa da ita ta datse idanu gam, tun da ta ji marinsa ta ƙara jin tsoronsa sosai. Kamar bai ganta a wajen ba ya wuce ya zauna a saman chair, cike da murna Sharifat ta fara serving ɗinsa. Zama Bilal ma ya zo ya yi a chair dake kusa da shi yana faɗin. "Lil zuba mun nawa abincin sai ki ɗauki sister nan taki ku tafi". Ɗan turo baki ta yi tana satar kallon Ramish. "Ni Yah Bilal hira nazo taya ku". Sarai ya kalleta tana satar kallon mashi ɗan uwa, a ransa ya ce zaki yi ki gaji ki bari. Ita dai Leesharh tana tsaye shiru, Dr Raj kuwa shiru ya yi yana nazarin maganganun da suka tattauna, da alama ba zai yi breakfast yanzu ba. Zuba masu abincin ta yi, cike da class suka fara ci, ita kuma sai ta zauna a saman chair ɗaya tana ta aikin satar kallon shi. Shi kuwa Bilal duk ransa bai so tsayuwar Leesharh a tsaye ba, duk ya takura, yana cin abinci ne amma hankalinsa kacokam yana a kanta, ya rasa sukuninsa, amma kuma baya son kulata bare ya ce ta samu waje ta zauna, Dr Raj ya saka mashi idanu, haka dai ya daure ya danne yana ganinta a tsaye ba yadda za'ayi. ________________________🔥🤯 JIMETA YOLA NIGERIA. Gabaɗaya matasan nan kansa suka nufa, suna zuwa da nufin su hau jibga mashi sandunar nasu yasa hannu ya kwace sandar mutun ɗaya tare da rage tsawonsa sandar da wani ya zo buga mashi ta wuce fiw bata same shi ba. Cikin ɓacin rai ya fara jibgarsu da sandar hannun nasa da ya kwata yana kaucewa nasu dukan da suke kawo mashi, su da suke kiwo ma sun san ta yadda zasu daki mutum bare shi da yake renon Commander Zafar? Ai wlh lilis ya dakasu kamar ai aikosa, yana dukansu yana tunanin me ya yi masu suka zo jibgarsa haka?. Tsurewa Nenne ta yi har ta ji cikinta ya murɗa, nan take ta ji tana son shiga banɗaki, wani tunani ne ya faɗo mata a ranta na cewa anya kuwa ba garkuwa ma ta haɗa Mahnoor da shi ba kuwa? A tunaninsu bashi da karfin iya nemo masu abinci da zasu ci ma bare har ya bata kulawa, sai ga shi ya jibgi matasa wajen guda 20 shi kaɗai, kuma ya iya kauce dukan da suka rinƙa kawo mashi bai taɓasa ba, gaskiya da sake, in dai haka ne wannan zai iya zamawa Mahnoor babban garkuwa ma kuwa, ba zai bari ta walaƙanta ba. Nan take Nennen ta ji ina dole a raba wannan aure idan ma an ɗaura, dan su ba garkuwa suke neman mata ba, wanda zai walaƙantata suke neman mata...... Lallai akwai cakwakiya babba ma kuwa, tabɗijam!!. Mahreen dake tsaye a bakin kofa ita da Mahnoor suna kallonsa ne ta daka wani irin uban tsalle tana faɗin. "Hammana jarumin namiji ne! Adda Mahnoor kina ganin yadda ya yi masu bahagon makahon duka! Wayyo daɗi kasheni, Hamma dan Allah ka koya mun irin wannan faɗar ka ji? Ina son in ga nafi kowa karfi a garin nan, dan na rinƙa dukan kowa a garin nan". Tana kai karshen maganar ta watsa a guje ta nufi she babu ko tsoro a tatare da ita. Tana zuwa ta daka tsalle. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E31 Kash! Kullum sai kun mun magana Pretty and Kramer, har da masu ce mun ko na manta da su ne, ta ya za'ayi na manta da su? Bayan ni na zauna na ƙirƙirosu! Suna nan labari ne kawai bai juyo ta kansu ba, kunga lanarin part part ne da dama, so ko wanne kuma ina tafiyar da shi ne bisa ga yadda na tsara kayana tun farko! Komai zai zo maku daki daki, me kuke ci na baka is falling down? Calm down my people's duk wanda story ya juyo ta kansa zaku ji labarinsa dallah dallah, dan haka let's go kawai!!. Tana zuwa ta daka tsalle ta haye jikinsa tana murna. Jefar da sandar hannun nasa ya yi tare da sanye hannu ɗaya ya tallafeta da kyau dan kada ta faɗi, ya gyarata izuwa saman kirjinsa fuskar nan kamar wadda aka cewa Mommarsa ta rasu. Karo na farko a rayuwarsa yau ya ɗago idanu ya kalli Nenne dake tsaye a bakin kofar nata room ɗin. Ya kalleta ido cikin ido Ai a ɗari da sittin ta shige cikin ɗaki tana faɗin. " Hasbunallahu wani'imal wakil, innalilahi yau na yi gamo". Dariya sosai Mahreen ta ɓalle da shi, mayar da kallonsa a kan Mahnoor dake tsaye ya yi, ƙasa da kai ta yi ta fara ƴan kame kame kamar maras gaskiya. Muryar Mahreen ɗin ne ya karaɗe kunnuwansu a in da take faɗin. "Hamma Nenne fa tsoronka take ji, ka jita har da cewa hasbunallah, ni kam ban san meyasa suke tsoronka ba, ni kuma kyau kake mun wlh". Tun da ta fara maganar ya dawo da kallonsa a kanta, while ita ma Mahnoor ɗin sai ta dawo da kallonta a kansu. Matasan da ya jibgan ne suka fara motsawa, dama already akwai masu motsawa a cikinsu, duk sun watsa cikin gidan a garin faɗarsu, sun tumurmushewa bappa harawarsa dukka, gidan dai ya zama kamar bola. Sallamar Arɗo tare da bappa ne yasa Nenne sake fitowa daga ɗakin nata, dan ta ji muryar mahaifin nata. Mamaki ne ya kamata na ganinsu a tare, Arɗo bai taɓa zuwa gidan nasu ba sai yau. Kawar da kallonsa daga kansu Jaish ya yi, dan baya son haɗa idanu da bappa, kada ku manta kunyarsa yake ji dama. A hanzarce Mahnoor ta shiga ɗakin bappan ta ɗauko masu tabarmar sakar mafici, a tsakar gidan ta zo ta tattare abubuwan da suke wajen ta shinfiɗa masu. Zama suka yi idanun bappa a kan Jaish, shi kuma ya yi ƙasa da kai, ga Mahreen data ɗale jikinsa ta saƙalo wuyarsa da hannunta ɗaya tana shafa mashi arabs hairnsa ta bayan wuya, tana ta zuba mashi surutu, yana gane wasu, wasu kuma sai dai ya ji kawai. Nasan zaku so jin me ya kawo bappa a tare da Arɗo bayan kuma Arɗon ya ce aje a ɗaure mashi shi, to ku saurara. Kamar yadda ya buƙata haka aka je aka ɗaure mashi bappan, yasa su gwaggo suka kawo mashi garwashin wuta mai ci dan ya yi mashi hayakin kaikayi koma kan mashekiya, dan a cewarsu wani ne nan ya yi wa bappan asiri har ya samu matsala a ƙwaƙwalwarsa, dan sun san yadda suke basa bawa bare auren ƴaƴansu, haka kawai Bappa ba zai bada Mahnoor ga Jaish ba duk yadda yake son shi kuwa, shiyasa basu yarda ba dan sun san halinsu su da kansu!. Ai kuwa hantar cikin gwaggo ne ya kaɗa jin cewa Arɗo zai yi mashi hayakin ƙaiƙayi, nan take ta sha jinin jikinta, dan tasan idan fa aka yi kashi hayakin nan shikenan maganin da suka yi mashi zai karye, a tsure ta fara ƙoƙarin dakatar da Arɗon cikin ƙissa da kisisina. Sai dai ina bata yi nasara ba, tana ji tana gani ya banka wannan garin ƙaiƙayi a cikin wutar, kan ƙace me hayaki ya bule cikin gidan nasa, dama a cikin gida wajen bishiyar mangoron dake tsakiyar gidan aka ɗaure shi, aikuwa Arɗo kam ya banka maganin abinsa. Nan take bappan ya sume, wani irin zaro idanu sosai Arɗon ya yi a lokacin da ya ga bappan ya sume, hakan na nufin da akwai asiri a jikin nasa kamar yadda suka yi hasashe kenan?. Gwaggo kuwa tana ganin haka cikinta ya murɗa ta ƙara tsurewa, me zata yi banda ɗaukar buta ta nufi banɗaki, zawo ta fara yi cikin ya ɗuri ruwa, Allah Allah take yi kada asirinta ya tonu, addu'a take yi Allah yasa kada aljanin da suka turo masa ɗin ya fito ya yi magana ya ce su suka sanya shi ya gusarwa da bappan hankali. Tun da ya shiga banɗaki ta kasa fitowa, sai zata fito cikin nata ya sake murɗawa ta koma, ba komai kuma ya razanata har haka ba face sanin halin mijin nasu, idan baku manta ba a baya na gaya maku mafaɗaci ne, yana da tsauri sosai, so tsoron halinsa da sanin abinda zai iya aikatawa yasa hakan. Sai dai fa Allah ya taimaketa da ƙaiƙayi Arɗo ya yi amfani da garin makarin asiri, da da ayoyin Allah ya yi amfani to da babu abin da zai hana aljanun magana, amma wannan hanya da ya bi asirin komawa kan wanda ya yi kawai zai yi, hakan kuwa aka yi, kan gwaggon abin ya koma, dan ita ta haɗa komai ba Nenne ba, Nenne tana gida sai dai aka kawo mata maganin ta zuba mashi a abinci!!. Bayan ya tabbatar asirin ya koma kan wanda ya haɗasa sai ya buƙaci da a kwance mashi shi a kwarya, matasan da suka ɗauresa ɗin ne suka kwance sa, ya buƙaci tabarma daga wajen Inna. Da sauri ta kawo masu ta shinfiɗa. A kai suka kwnatar da shi, ruwa ya buƙata, nan ma Inna ce ta kawo mashi. Karɓa ya yi, sai a lokacin ne ya tofa ayoyin Allah, suratul iklas, suratul nasi and falak sai ayatul kursiyu and amanarrasu. Ya tofa a cikin ruwan sannan ya ɗabo kaɗan a hannunsa ya shafa mashi a face ɗinsa. A lokacin already abin ya koma kan gwaggon. Sanadiyar waɗan nan ayoyin yasa bappan farkawa a nutse cikin kwanciyar hankali kuma cikin hayyacinsa. Abin da ya basu mamaki ya kuma kara tabbatar masu da cewa asiri aka yi mashi shi ne, da bappan ya farfaɗo sai ya kama tambayar me ya kawo shi gidan Arɗo kuma?. Bayani Arɗon ya yi mashi dallah dallah a kuma nutse, sai da ya tabbatar ya fahimta sannan ya kyalesa. Ruɗu iya ruɗu Bappan ya shiga. To kun ji abin da ya faru, Arɗo ya sanar da shi dik abin da yake faru, daga haka suka nufo gida, dan bappan ya ce yana son ganin Jaish and Mahnoor ɗin...... To fa, ko ya makomar wannan aure. Da farko fa musawa bappan ya yi a kan shi wlh ba shi ne ya ce a ɗaura auren ba, dan shi ai already ya bawa Faisal ita ta yaya kuma zai sake cewa a aura mata wani? Sai da sirikin nasa ya yi masa bayani da kyau ne ya ɗan yarda da zancen. Miƙewa suka yi suka nufo gida. Story Kusa da bappan Nenne ta ƙariso ta zauna, cikin harshen larabci ya yi wa Jaish kira a kan ya zo su yi magana. Sauke Mahreen daga jikin nasa ya yi, cikin nutsuwa ya nufesu, sai dai bai kai ga ƙarisawa ba sai ga kanin Inna da wasu zugan matasa sun banko cikin gidan yadda kuka san waɗan da aka jefosu daga sama. Sai wani irin huci kanin Innan yake yi, shi ala dole ba za'a bawa jikarsa bare ya aura ba. Miƙewa tsaye bappa da Arɗo suka yi a tare cikin ruɗu, ita kam Nenne yau tana ganin bala'i, ta haddasa abin da tun ba'aje ko'ina ba tana tabka danasani mai girma kuma maras amfani. A guje ta watsa sai cikin ɗakinta, ta fasa jin gulmar da ta fito da ita, dama ba ta zauna zata ji me su bappan zasu tattauna ba?. To ganin tawagar Inna yasa ta fasa. Da farko da zafansa kanin Innan ya shigo, harda wani huci yake yi irin ran maza ya ɓacin nan. Yana sauke idanunsa a kan matasan da ya aiko da farko Jaish ɗin ya jibgesu sai ya ji tsoro ta ɗan kama shi, nan take ya lafa, ya shafawa kansa ruwan sanyi dan samun lafiya. Bai ma karasa razana ba sai da ya ɗaura idanunsa a kan Jaish ɗin, yaga dakakke tsayayyen namiji! Ai nan take ya nemi nutsuwarsa ya rasa, sai da hantar cikinsa ta ƙaɗa. "Lafiyarku kuwa Shehu?". Cewar Arɗo, ya tambayi kanin Innan. Jaish kuwa yana tsaye yana binsu da wani irin kallon da duk bala'inka ba zaka iya fassara wani irin kallo bane, sai shi kaɗai da ya yi ta yasan wace iriyace. Ɗan ja da baya Shehu dai ya yi, dama bai san Jaish ɗin ba, sunansa kawai yake ji na aljani da ake mashi ikirari da hakan, wato yau da ya ɗaura idanu a kansa sai da zuciyar maza ta karaya, ya tsorata sosai, hakan yasa ya ƙara ja da baya. Kafin Arɗo ya sake yi masu wata tambaya ma suka juya a hanzarce suka bar gidan, suma matasan dake zube a ƙasan, waɗan da suka dawo cikin hayyacinsu sai suka tashi da gudu suka bi bayan Shehun, waɗan da suke kwance basu dawo cikin hayyacinsu kuma suka cigaba da kwanciya kamar waɗan da suka suma. Komawa su bappan suka yi suka zauna, da yake already sun san su waye ne su Shehun, and sun san a kan me suka zo. Nunawa Jaish saman tabarma bappa ya yi a kan ya zo ya zauna. Ba musu ya zo ya zauna, a tsanake cikin sanyi da nuna kulawa bappan ya gaya mashi dik abin da yake faruwa, daga karshe ya ce. "Banso hakan ba, kuma Allah ya ga zuciyata Faisal na so ya auri Mahnoor, amma kuma ba zan iya kiran ƴata da bazawara ko kuma in ji wani ya kira mun ita da hakan ba, abin kunya ce babba mu a wajenmu, bani da zaɓin da ya wuce in..........." Dakatawa ya yi da maganar bai kai karshenta ba sakamakon sake bankowa cikin gidan da aka yi a karo na biyu. A lokacin Mahnoor tana tattare gidan tana gyara abubuwan da faɗar da su Jaish ɗin suka yi suka watsa komai, ita kuma Mahreen tana zaune kusa da Arɗo ta buga uban tagumi tana tuna yadda Jaish ya yi ta jibgar matasan can, a gaskiya abin ya yi mata mugu mugun daɗi kuma ya ƙayatar da ita. Ba kowa bane ya banko cikin gidan ba face Faisal, kamar wani zararre, yana wani zaro idanun, ga dikkan alamu baya a cikin hayyacinsa, sai wani huci yake yi, ga shi babu ko riga a jikinsa, daga shi sai wando dogo ta wata shadda koɗaɗɗiya, gashin kan nan nasa kamar dambu mahaukaciya ko ace bukka, ya tara gashin sosai, gata da cika, da alama ya yi birgima da gashin nasa a cikin turɓayar ƙasa ne, dan gabaɗaya gashin nasa ta zama yadda kuka san power aka zuba mashi, saboda ƙasa da ta wankesa. Jikinsa duk ƙasa, kai in takaice maku ya fita a hayyacinsa, ya fita sahun mutane. Yana shigowa a gaban bappa ya zube gwiwowinsa, yana zaro idanu, ga idanun nasa alamar ya ci kuka ya ƙoshi, sun yi jajir gulu gulu da su, haka kamar mahaukaci ya fara sambatu. "Wlh bappa ina son Mahnoor, kuma kowa ma ya san da haka! Kai kanka ka sani, ba ka bani aurenta ba ma? Dan Allah bappa kada ka ɗauketa daga gareni ka bawa wani ƙaɗo can bare da bai san darajarta ba, ka ji tausayi na bappa, zan iya mutuwa a kanta, aradun Allah ina kaunarta, wayyo na shiga ukuna......." Yana tsaka da yin maganar ne idanunsa suka sauka a kanta, ta tsaya turus a tsakar gidan baiwar Allah, Allah ya gani tana son Faisal ɗin, ita yanzu ma ƙoƙari take ta fahimci wani abin, tana son ta san menene ya sanya Hamma Faisal ɗin nata ya birkice haka? Ta ji yana faɗin kada a rabasu, to waye zai rabasu? Ta gaza gane kada a rabasu kamar yaya? Bata fahimci komai ba. A zabure ya miƙe tsaye, hannunta ya zo ya ruƙo, ya jata har gabansu bappan, kuka bawan Allahn nan ya shiga yi da hawaye bibbiyu kamar ƙaramin yaro, faɗin ya fara yi. "Mahnoor ki gayawa bappa kina sona, dan Allah ki gaya mashi ba bakon ƙaɗon nan nasa kike so ba, ki gaya mashi kada ya rabamu kin ji?". Yana magana hawaye da gudun gaske suka cigaba da wanke mashi fuska, ya haɗa uban gumi, fuska kamar wanda aka watsawa ruwa saboda gumi, jikinsa har kerma yake yi, tsikar jikinsa duk sai tashi suke yi, wlh sai ya baka tausayi idan kaga yadda ya mace a kanta. Daga Arɗo har bappan an gaza samun mai kwarin gwiwar iya yi mashi magana, ko ya taushesa, sun zuba mashi idanu kawai. Ƙoƙarin kwace hannunta daga nasa ta yi, dan ta gudu izuwa cikin ɗaki, baiwar Allah ba zata iya tsayuwa wannan rashin kunyar ba, yanzu ta fagimci batun aurenta kenan ake yi, sai dai ta gaza gane da waye a cikinsu ake batun auren nata? Me kuma yasa Hammanta kuka?. Mahreen ce ta miƙe tsaye tare da ƙarisowa in da suke, hannu tasa ta fara ƙoƙarin taya Mahnoor ɗin kwace hannunta daga riƙo da ya yi mata, da yake kunsan ita fa bakinta baya shiru, kuma kun san ba shiri da Faisal ɗin suke yi ba dama sai ta ce. "Kai Hamma Faisal ai dama bama sonka, dama Adda Mahnoor ba zata aureka ba, dan ni bana sonka, ka sake mata hannu........." Bata ƙarisa maganar ba ya ɗauketa da wani irin gigitattacen mari wanda yasa sai da ta yi baya baya ta faɗi ƙasa. Zuciyarsa tafarfasa yake yi tamkar an ɗaura dalma a wuta, dama shi ma yana da zuciya har haka?. Yana ji da tsananin bakinciki tazo tana sake gaya mashi mai ɗaci, ai dole ya dallah mata mari. Yadda kuka san zuciyar Jaish zata fashe, yadda kuka san shi ya mara ba Mahreen ba, a wani irin zuciye ya miƙe tsaye, nan take ransa ya ɓaci, da hannu ɗaya yasa ya pincike rikon da ya yi wa Mahnoor ɗin, wani irin mari mai tsananin zafin da ya sauke mashi a saman ƙuncinsa ne sai da yasa shi ganin wasu irin taurari masu hasken gaske suna gilma mashi, sake ɗaga hannu ya yi a karo na biyu zai ƙara mashi wani marin. Da saurin bappa ya miƙe ya riƙe hannun nasa ta baya, a fusace ya juyo tare da damko wuyar bappan ba tare da ya lura cewa shi ɗin bane, a tunaninsa wasu ne irin su Faisal ɗin. Ya juyo da kyau da niyar ya karya hannun wanda ya rikesa ɗin, duk da ɓacin rai da zafin zuciya da ta rufe mashi idanu hakan bai sa ya gaza gane cewa bappa ya shaƙe ba. A hanzarce ya zame hannunsa daga wuyar nasa yana sunkuyar da kansa ƙasa, ransa ya ɓaci ne na Mahreen da Faisal ɗin ya yi wa mutuniyar tasa. A hankali ya sakar mata hannunta da ya kwace daga cikin na Faisal. Yana saketa ta kwasa a guje sai cikin ɗakinsu tana sauke numfashi. Hannunsa ya miƙawa Mahreen dake baje a ƙasa tana kuka. Da sauri ta riƙo ta miƙe tsaye. Ɗakinsu ya nuna mata da ɗayar hannun nasa alamar ta je. Ai da gudu ta wuce. Shi kuwa Faisal da ya yi suman tsaye ko motsi bai yi ba ne bappa da Arɗo suka ƙariso kusa da shi, bappa nasa hannun ya taɓashi kawai sai ga Faisal ya tafi luuu sai ƙasa, da karfi ya furta. "Shikenan ni Faisal na mutu". Yadda ya yi maganar gwanin ban dariya gwanin ban tausayi, ya ji marin manya ne yasa ya zama kamar ya zare, kamar ƙwaƙwalwar ta samu matsala, shiyasa zaku iya jin abin da ya fi wanda ya faɗa yanzu ma, ba laifinsa bane, ya ji hannun jinin Modarawa ne. Cikin harshen fillanci Arɗo ya ce da bappa wannan magana ta batun auren nan a barta sai komai a daidaita, sai a san abin yi, yanzu dai su ɗauki Faisal a sama mashi magani ya samu lafiya, dan da alama hankalinsa ta gushe ƙwaƙwalwa ta taɓu. Na'am da zancen sirikin nasa bappa ya yi, matasa suka nemo aka ɗauki Faisal ɗin zuwa gidan Arɗo, a tare suka wuce da bappan, amma kafin su tafi sai da suka zubawa sauran matasan da Jaish ya jibga waɗan da basu farfaɗo ba ruwa. Baya sun farfaɗo ne suka tasasu a gaba suka tafi. Nenne tana can cikin ɗaki tana ciza yatsa tammar zaga yi hauka, ban da nadama da danasani babu wani abin da yake ranta, ta yi babban danasani na sanyawa a haɗa wannan aure......... Ni kuwa nace danasani tun daga yanzu Nenne? Kada ki bada mata mana! Ai bai kamata ki fara danasani tun yanzu ba! Yana da kyau ki kara ɗaura ɗamara ne hegiya!. Ai duk wanda ya gina ramin mugunta to ya jira ranar afkawarsa ciki! Ai baki ga komai bama tukun nan. Dama ke kin taɓa gani ko kin taɓa jin zalinci ta ɗaure ne? To jama'a sai a kula, komai yana da iyaka yana da karshe musamman ma zalunci!!. Aka ce idan jemun ɗan uwanka ya kama da wuta?? Ku ƙarasa mun!!. Baiwar Allah Mahnoor tun da ta shiga ɗaki kuka take yi sosai har Mahreen ta shigo ta sameta. A gefenta ta zauna suka cigaba da kuka a tare, ba mai rarrashin ɗan uwan. Shi kuwa Jaish da ko a jikinsa, shiryawa ya yi ya fito ya kaɗa dabbobin bappan ya tafi kiwo abinsa, yau bai ma jira bappan ba, dan ya ji lokacin da suka ce zasu je su nemawa Faisal magani, dan haka sai kawai ya tafi abinsa. Bai dawo ba sai can yamma kamar yadda suka saba, bappan har lokacin bai dawo gida ba, dan kuwa Faisal dai a maimaikon sauki sai abin ya kara gaba sosai, kamar ya zare ne fa!. Lokacin da ya dawo daga kiwon babu kowa a tsakar gidan, ɗakin bappa ya nufa dan ya ɗan huta sannan ya je ya yi wanka. Yana shiga ita kuma tana fitowa, baya ta ɗan ja dan ta bashi hanya ya wuce. Ta sunkuyar da kanta ƙasa ta mannu da jikin bango. Shiru bai wuce ba ya tsaya a bakin kofar. Ganin haka yasa ta ɗan ɗago idanunta dan ta saci kallonsa ko me ya hana shi wucewa?. Tana ɗago kai suka yi four eyes, dan kuwa idanunsa yana kanta, ba komai yake gani ba kuma face hawayen da yake saman face ɗinta ga idanunta a cike tab da wasu zafafan hawayen. Ƙasa ta sake yi da kai tana ƴan kame kama kamar maras gaskiya. Hannu ya kai ya ɗago haɓarta, wani irin dukan uku uku kirjinta ya yi, wiki wiki ta fara yi da idanu kamar an tare ɓera a tarko. Da hannunsa ɗaya ya yi nuna mata alamar meyasameta take kuka?. Kai ta fara girgiza mashi alamar babu kenan. Tabbas yaga tsoro a kwance a cikin idanunta hakan yasa ya yi tunanin duk yadda aka yi Nenne ce ta daketa, shiyasa ma taki faɗa, saboda tana tsoron bala'in Nennen. Shiru ya ɗan yi yana tunanin irin rayuwar nan tasu, shi dai kunga ya taso ya samu King matansa har uku, kuma kowacce da ƴaƴanta, amma basu yin irin wannan zaman kishi na cutar da ƴaƴan nasu haka, su ba ruwansu suna kaunar ƴan uwansu, ba ruwansu da uwa daban daban suke, su dai sun san ubansu ɗaya, ba ruwansu da kishin da iyayensu mata zasu yi, amma a nan ya rasa me matsalar Nennen nan, dan ba ke kika haifi yarinya ba sai ki yi ta gallaza mata? Ke kika halicceta ne?. Zame hannunsa daga haɓar tata ya yi tare da shigewa ciki. Bappa da yake tsaye a bayansu tun ɗazun yana ganinsu ne ya fara zubawa Allah godiya a cikin ransa da Allah yasa aka ɗaura auren nan, a cewarsa soyayya suke yi da ya gansu a tsaye haka, bai san cewa shi Jaish tun da yake ma bai taɓa shigar mata faɗa ba, kai bai ma taɓa matsowa kusa da ita kamar yau ɗin ba, yana dai shigarwa Mahreen faɗa, dan ita kunga ai mutuniyarsa ce, amma Mahnoor gaskiya babu wani abin da ya taɓa haɗasu ko da sunan wasa. Yana sake haɓar tata ta nufo waje da sauri, karaf suka ci karo da bappa. Gaisuwa ta ɗaga mashi tana goge hawayen face ɗinta. Hannunta ya riƙo suka koma cikin ɗakin. Yana zaune a bakin bed suka isko shi, ya kurawa yatsun hannunsa idanu yadda kuka san yana son tuna wani abin. Kusa da shi bappa ya zauna tare da sanya hannu ya kamo nasa hannun da ya kurawa idanun. Ita dai tana tsaye tana ganin ikon Allah, tana jiran ta ji me bappan nata zai ce?. Buɗe tafukan hannun Jaish ɗin ya yi tare da matso da ita ya ɗaura nata hannun da ya riƙe a kan nasa. Cikin harshen larabci ya yi mashi bayanin cewa ga amanarta nan ya bashi ya ga dai marainiyar ce, ya dubi girman Allah ya riƙe mashi ita amana, kada ya kuntata mata, kada ya zalunceta, yana da tabbacin Mahnoor yarinya ce mai biyayya, kuma In Sha Allah zata yi mashi biyayya fiye da yadda yake tunani. Shiru bai ce komai ba, sai ma sunkuyar da kansa ƙasa da ya yi, bashi da wata damuwa da wannan aure, dan bai san wanene shi ba ma. Slowly ya ɗago da kallonsa, saman face ɗinta ya sauke kallon nasa. Kana ganin face ɗinta zaka san a firgice take baiwar Allah, tana son ta tambayi bappa meyasa za'a aura mata shi? Amma kuma kunya ya hanata, ita ba shi take so ba! Hamma Faisal shi ne zaɓinta, shi ne ta buɗe idanu ta kallah a matsayin masoyi, tsawon shekaru 5 kenan suna tare a matsayin masoya, tun bata fi ƴar 9 years ba kenan, kawai rana tsaka a zo a canza mata da wannan mutumi da take tsoro? Kai gaskiya abin da sake. Amma dai haka ta daure tana tunanin wa kanta mafita. Haƙiƙa Jaish ya ga wasu abubuwa kwance a cikin idanunta, sosai ta bashi tausayi, shi ba yana tausayinta dan auren da aka yi masu aka rabata da Faisal bane, a'a, yana tausaya mata halin da take ciki a cikin gidan, dama Allah ya gani ba shi yake yi waɗan nan ayyuka da take yi ba, amma wlh ganinta kawai yake tana aikin ya gaji, wlh ya gaji da ganinta tana bautatuwa da tsabar bakar wahalar da take sha. "Hamman Mahreen". Bappan ya ambaci sunansa. Dawo da hankalinsa haɗe da kallonsa a kan bappan ya yi, sai dai side ɗinsa ya kalah, ya ki yarda su haɗa idanu. "Baka amsa mun ba, ka karɓi amanar da na baka? Zaka riƙe mun ita da amana?". Shi kam me bappa zai nema a wajensa da zai ki yi mashi? Irin yadda bawan Allahn nan ya nuna mashi kaunar da iyayensa ne kawai zasu iya nuna mashi irinta a duniya, ai koma me ya yi bai biyasa ba, kuma koda bai ce mashi ya riƙe mashi ƴa da amana ba wlh dole zai riƙeta, saboda shi tun ainahi ma ai ba maci amana bane, babu cin amana a jinin Modarawa. Dan haka sai ya gyaɗa kansa sama kawai alamar zai cikawa bappan maganarsa. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, koba komai ya ji sanyi a ransa, kuma a yanzu duk duniya ba wanda ya kaishi sanin wanene Jaish ɗin, yasan yana da zuciya mai kyau. Sake hannayen nasu ya yi, da sauri ta juya zabar ɗakin dan wani irin kuka da ya zo mata, tun bayan kukan rashin mahaifiyarta da take dirza sai yau ne ta ji kuka mai zafi irinsa ya zo mata, duk azabar da Nenne take yi mata ko kaɗan baya taɓata kamar idan ta tuna rashin uwa a duniya, yau kuma ga rashin masoyin da ya sota tun tana ƴar shekara biyu a duniya, an haɗata da wani mutum mutumi kawai. "Waru haɗo (zo nan)". Bappa ya faɗa cikin sanyin murya. Ba musu ta dawo ta tsugunna a gabansa. Miƙewa Jaish ya yi ya fice waje. Hannunta bappa ya riƙo, cikin sanyin murya ya fara bata hakuri tare da yi mata nasiha a kan ta karɓi kaddararta, ta dage ta ci jarabawarta, sannan ta sani Jaish ya fi Faisal nagarta da komai da komai, in ta yi hakuri a hankali komai zai dai'dai ta, sai magana ta karshe kuma shi ne. "Duk da nasan kina da kula da takatsantsan, amma ina son ki kara kulawa sosai, ki mayar da hankalinki wajen ganin kin gujewa abin da baya so, kin san cewa yana da zafin zuciya, kuma nasan ita ce kaɗai zata rinƙa kawo saɓani a tsakaninku, yana da zuciya da zafin nama, jininsa a tafashe yake, baya son abu sanyi sanyi da ɓata lokaci, ke kuma kina da sanyi over, dan haka sai ki kula, ki guji abin da zai sanya ransa ya ɓaci, dan idan zuciyarsa ta matso kusa komai yana iya faru, nasan kin san hakan, ina kara tunatar dake ne kawai, ki kula sosai, na mai tabbatar maki zaki ji daɗin zama da shi". Kanta a ƙasa, ban da aikin kuka babu wani abin da take yi, ita dai Allah ya gani Faisal take so, bayan shi bata jin zata so kowa. Rarrashinta bappan ya rinƙa yi, a haka Mahreen ta shigo ta samesu, ta dawo daga aikan da Nenne ta yi mata gidan Arɗo. Ganin ƴar uwarta tana kuka ne yasa ta faɗo cikin ɗakin da sauri tana tambayar ba'asi. Rungumo juna suka yi tana gogewa Mahnoor ɗin hawaye tana mai cigaba da tambayar bappa waye ya dakar mata ƴar uwa yaga tijara yau!!. "Babu wanda ya daketa Mahreen, nasiha nake yi mata shi ne take kuka, ku tashi ku tafi ɗakinku Allah ya yi maku albarka". Da amin Mahreen ta amsa, sai ta ɗaura da cewa. "Bappa ina Hammana?". "Ya fita waje". Miƙewa ita kuma Mahnoor ta yi ta nufi waje da sauri tana mai cigaba da dirzan kukanta. Da sauri Mahreen ta bi bayanta, suna shiga ɗaki ta kwanta a saman gado tare da ƙara rushewa da wani sabon kukan. Sai aikin rarrashinta Mahreen ta fara yi, bata kulata ba kukan nata kawai take yi. Can kuma ko me ta tuna sai ta miƙe zaune a zabure. Da sauri ta diro ƙasa ta nufi waje tana goge hawaye. Bokiti ta ɗauko ta juyo ruwan zafin dake saman wuta a kitchen, ta ɗebo na sanyi daga randa ta surka, sa hannu ta yi ta taɓa ya yi dai'dai. Ta ɗauka sai cikin toilet, tana ajiyewa ta fito da sauri. Already kunsan akwai hijabi a jikinta kullum dama, dan haka sai ta nufi waje kai tsaye. Yana zaune a ƙarƙashin bishiyar kofar gida kamar yadda ya saba zama, gabansa ta ƙarisa, cikin girmamawa ta ce. "Hamma ga ruwan wankan can na kai ma, ka yi hakuri na manta ne yasa tun ɗazun ban kai maka ba". Tun da ta fara magana ya kafeta da idanu yana kallonta, bai san meyasa yau ya ji kamar ta yi mashi kama da wata wadda ya sani ba, sai yake jin kamar ya taɓa rayuwa a wata duniya ta daban, kansa ya ji tana ɗan sara mashi a hankali hankali, Magana ta gaskiya a lokuta da dama yana jinsu kamar Gimbiya Zunaira ce, baya cikin hayyacinsa, amma tabbas soyayya da yake yi wa kanwar tasa a jinin jikinsa yake, sau da dama yana jin kamar yana da wata wadda yake matukar kauna, yafi yawan ganin Mahreen a wannan matsayi shiyasa yake yawan sake mata, yau kuma sai ya ga hakan a tattare da Mahnoor, musamman ma yadda ta yi magana a kusa da shi, sai ya ji tamkar sun taɓa yin wata rayuwa a wata duniyar da ita, a zahiri ba da ita bane, da Zunaira ce. Jin ya yi shiru bai ko motsa ba ne yasa ta ɗago da kallonta dan taga me yake yi. Tana ɗagowa suka kalli juna ido cikin ido. Gabanta ne ya bada ras a hanzarce ta yi ƙasa da kanta. "Hamma in tafi?". Muryarta ya daki dodan kunnuwarsa. Miƙewa tsaye ya yi ya wuce gaba ba tare da ya yi mata magana ba. Da sauri ta miƙe ta bi bayansa. Kai tsaye cikin toilet ya nufa ita kuma ta wuce ɗakinsu. Yau dai abincin dare turasa kawai baiwar Allah ta yi, amma ba dan daɗi ta ci shi ba, tunanin Hamma Faisal ɗinta ne kawai a ranta, abin ya yi mugun sosa mata rai. Haka baiwar Allahn nan yau sam bata rintsa ba, kamar yadda taga rana haka taga dare. Sai dai ba ita kaɗai bace bata rintsa ba, bappa kwana sallah ya yi yana rokon Allah da yasa Jaish ba mugu bane zai riƙe masa ƴa da amana, Allah Ubangiji ya bashi lafiya, sosai ya yi masu addu'a, shi kuwa Jaish yana ta barci abinsa. Nenne ma bata yi barci ba, kwana ta yi tana tsinewa tunanin gwaggo na ce wa a haɗa Mahnoor and Jaish aure, ga shi yanzu tun ba'a je ko'ina ba ya fara tare masu faɗa, a kan Mahreen ya daki Faisal da safe, to ina ga kuma Mahnoor da take matsayin matarsa? Zai iya kisa a kanta kenan?. Abin ya tsaya mata a rai matuƙa, duk sai ta ji kamar ta kashe kanta, sai tunanin ta yadda zata bi ta ruguje wannan aure take yi, ta yi wa kanta alkawarin ko ana ha maza ha mata wlh sai ta ruguje wannan aure ta mayar da yarinya ƙaramar bazawara ko 15 years bata cika ba, sannan ta ƙuntatawa rayuwarta, shi ne next plan ɗinta. Washegari da safe daga bappa har Nennen idanunsu a kumbure suka wayi gari, saboda rashin samun barci, gara ma shi bappa a kan dadduma gaban Ubangijinmu ya kwana, ita kuma fa? A tawagar shaiɗan ta kwana? Idanun sun yi jajir. Mahnoor da bata samu barci daren jiya bane na asuba ya ɗauketa bayan sun yi sallah, kun san shi fa barci ba'a cin bashinsa, idan ka ci sai ka biya a time ɗin da baka yi zato ba, aikuwa tana sallah tana gyangyaɗi, da kyar ta iya samu ta daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallarta dai'dai. Daga nan ta ɓige da barci, tana tsaka da barcin ne ta ji saukar duka a jikinta ta ko'ina da bulalar itaciyar gwaiva. A razane ta miƙe, bama ta yi ihu ba dan tasan wanenen mai dukan nata, waje kawai ta fita da gudu. Nan take hawaye suka cika mata idanu tab da kwallah. Aikinta ta fara yi tana sharar kwallah da ya fara bin saman ƙuncinta. Karfe shidda ne dai'dai a lokacin. Tsintsiya ta ɗauka ta fara ƙoƙarin share gidan tas. Ita kuwa Nenne ta koma ɗaki bata ko kalli in da Mahreen take ba, saboda ƴarta ba ƴar wahala bace a cewarta, ƴar gata ce ta sha barcinta. Bayan ya gama sharar sai ta kwashe dattin cikin wani marfin langa ta nufi bayan gida zata je ta zubar a can wani rami wajen dabbobinsu bayan ta gama sharan kenan, dama a nan suke zubar da shara kullum, tana yi ma tana kuka baiwar Allah, ga yunwar safe da take ji, idanunta ita ma a kumbure saboda rashin barci jiya, jikinta duk babu kuzari, zuciya a raunace, tana tafiya tana jan kafafu kamar zata kifa ƙasa. Garin yana haɗe bakin kirin da hadari, yau da alama ruwa zasu sha ba kaɗan ba. Tana zuwa ta juye sharar a ramin, juyowarta ke da wuya ta ci karo da shi a in da ta buga kanta a saman kirjinsa, baya kaɗan ta ɗan yi dan ta samu damar ganin face ɗinsa. Ko yaushe ya tashi barci har ya fito ya zo cikin dabbobin zai tatso nono? Ta jefa wa kanta tambaya. Ƙasa ta yi da kanta tare da cewa. "Hamma ina kwana?". Bai motsa ba bare tasa ran ya jita, hannunsa riƙe da bokiti wanda ya tatsi nonon a ciki. Kyawawan yatsun hannunsa ya ɗago ya ɗaura a saman kumatunta a in da ya nuna hawayen face ɗinta tare da yi mata alama da hannun na meyasameta da sanyin safiyar nan take kuka haka?. Ta gane me yake nufi, dan haka yake tambayar Mahreen ma idan ya ganta tana kuka, dama dayawan lokuta tana kukan yunwar safe idan ba'a gama abinci da wuri ba, ai Mahreen manyan ƙasa ne. Girgiza mashi kai ta yi alamar babu abin da ya sameta. Zuciyarsa ce ta zarga mashi Nenne, dan yasan ita ce mai sanyata aikin sassafe kuma tana zazzaga mata masifa. Wucewa ya yi izuwa cikin dabbobin ba tare da ya sake bi ta kanta ba. Ɗan binsa da kallo ta yi tana mamakin hali irin nasa, wani irin mutun ne a murɗe haka? Abin dai sai a hankali, shi baya tambaya sau biyu, idan ya yi ɗaya ba'a amsa ba shikenan kai ka jiyo, gaskiya yana da abin mamaki. Sa kai ta yi ta wuce, a hankali take tafiya tana goge hawayen nata. Tana shigowa ta sami Nenne a tsakar gida, a lokacin kuma bappa ya tafi gidansu Hamma Faisal ya je duba jikinsa. Wani irin tsawa da Nennen ta daga mata a kan ta je ta jima ne sai da yasa ta ji duk wani kasala da yunwa da take ji sun gudu, nan take jikinta ya soma kerma. "Uban me ya tsayar dake daga zuwa zubar da shara?!" Shi ne tsawar da ta daka mata. Murya a sarƙafe ta furta. "Hamma na tsaya gaisarwa". Har lokacin hawaye suna cigaba da gudu a saman face ɗinta. Gadan gadan ta tinkarota da nufin ta fara aikin da ta saba na jibgarta, dan a cewarta wato yanzu ta yi girman da har zata iya bata amsa idan tana magana, kuma dai kuna ji ita ta tamnayeta me ya tsayar da ita, ta bata amsa kuma abu ya zama bala'i, wato dai idan mutun mugu ne kawai ka barsa, dan kome zaka yi mashi sai ya gallaza maka. Wani tray irin na kwano na mutanen da ɗin nan ta rarumo a fujajan zata maka mata a kai dan tsabar bakar zuciya irin na matar nan, ga jikin tray ɗin duk a farfashe ya yi lamba, wanda kuma kun san lambar jikinsa tsartse ne da yana iya fasa fatar jikin mutun ya shiga cikin nama, yana yi wa mutum illah sosai. Amma tsabar mugunta sai ta rarumo shi zata rafka mata a kai, ita kuma tana tsaye baiwar Allah, da yake tasan ko ta gudu ma ba tsira zata yi ba, sai dai ta kara wa kanta wani bala'in, dan idan ta gudun ma dole a gidan zata dawo ta kwana, idan ta dawo kuma ninninka mata azaba zata yi, so is better for her to stay kawai. Da iya karfinta ta ɗaga trayn zata buga mata, runtse idanu ta yi gam tare da sanya hannu ta tare kanta da fuskarta tana jiran saukar trayn a kan nata. Shiru bata ji an rafka mata ba, hakan yasa ta ɗan motsa zara zaran eyelashes ɗinta tana son buɗe idanun ta ga me yake faruwa bata ji anfasa mata kai na?. Aikuwa tana buɗewa cak ya riƙe hannun Nenne da tray ɗin gabaɗaya. Tsabar tsoro yasa Nennen ta yi suman tsaye, yau ga aljani ya riƙe mata hannu ko in ce maye da suke ce mashi. E lallai ba shakka yau Nenne taga bone, maye ya riƙe mata hannu ba kanta, me kuke tunanin zai faru a wannan ƙauye? Ya kuke ganin zamansu zai kasance a yanzu? Shin Nenne zata iya samun nasarar raba wannan aure kamar yadda ta shiga ta fita ta haɗa kuwa? Me makomar Jaish? Shin zai yarda ya zauna da Mahnoor matsayin mata kuwa? Dan ni dai ban ga alama ba!. Akwai cakwakiya fa sosai, yanzu muke ƙoƙarin afkawa cikin littafin mu gadan gadan, ku gyara zama akwai......... Ba sai ma na faɗa ba, muje dai zuwa. ________________________🔥🤯 FRANCE🔥🌹 Hakimce yake cikin katafaren office ɗinsa, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, sanye yake cikin shigar ƙananan kaya wandon jeans milk color and flannel shirt coffee color masu bala'in kyau da tsada, ya ɗaura denim jacket a saman kayan nasa, dan kowa yasan ƙasar faransa suna da balai'n sanyi mai dusar ƙanƙara, mai daskarar da abu, sai da jackets manya manya ma kuwa. Ya fito a ainahin Smart ɗinsa, ko mai kiyayyarka da shi sai ka amincewa ranka shi ɗin smart ne, komai ya yi guy ɗin nan dai'dai take tafiya da shi. Jiga jigan jami'ai ne ta ko'ina suke ta shawagin shige da fice, wani irin sanyin Ac da kamshin office perfume ne yake tashi a office ɗin. A ainahin office ɗinsa yake ba'a ma'aikatan haɗa nuclears ɗinsa ba, nan yana bakin aikinsa ne. Wayarsa dake saman desk ɗin gaban nasa ne ta fara ruri alamar shigowar kira. Yana tsaka da yin aiki ne ba kama hannun yaro. Jajirtattun jami'ansa guda ɗai ɗai ɗai har guda shidda ƙasar America ta kama masu a matsayin ƴan leƙen asiri ƙasa da ƙasa, kuma hakance, leƙen asiri suka je yi Allah ya bawa American dama suka kamasu, sun jima suna yi mata leƙen asirin kamar yadda ita ma take yi masu, sai dai Smart hege ne na karshe, maye ne a basira, duk wasu ma'aikatansa ya zuba masu matakan tsaro na na'urori, harta na'urar ɓadda kafa yana da shi wanda shi da kansa ya ƙirƙireta, amfaninta shi ne ba'a isa a bibiyesa a lamuransa ba, komai bala'in ƙasa haka zata gansu ta barsu. Da su da America fa ana mugun tare, kawaye sosai, amma dukkansu basu yarda da juna ba, suna leƙar asirinta ita ma tana leƙar nasu, kunga duk suna munafurtar juna ta ƙarƙashin ƙasa kenan, a fili kuma idan suka haɗu sai kuga kamar zasu cinye juna saboda so, amma American ce ta fara leƙar asirinsu shiyasa suma suka koya, sai dai America ɗin ko ta leƙi asirin nasu bata samun komai, duk min karfin na'urar da zata yi amfani da shi bata iya hango komai daga sararin samaniyarsu, har tauraron setline system suka sanya dan su leƙi asiri amma ina basu iya ganin komai, hege Smart ya juyar masu da kwakwalen kai. Hankalinsu ya gaza kwanciya dan suna ganin kamar tabbas yadda Allah ya baiwa Smart wannan basira daddynsa ba zai barshi haka ya tafi a banza ba, suna zargi lallai lallai yana amfani da ƙwaƙwarar nan tasa suna gina ƙasarsu, shi ne yasa suke leƙe leƙe ko zasu iya ganin ko da ɓirɓishin makami ne haka irin abin zargin nan. Sai dai basu san Smart ya wuce tunaninsu ba, duk ya rufe komai abinsa. Sau da dama jami'an Smart ɗin suna zuwa laƙar asiri ba'a taɓa kamasu ba sai yau, dama ai ba kullum ake kwana a gado ba. Yau dai an kamasu shi ne ya ɗaga hankulan sauran jami'an, dukkansu jira suke yi suga matakin da zata ɗauka a kan jami'an nasu, kansa ya ɗau zafi, sai aiki yake yi tukuru dan ya yi amfani da basiransa wajen kwato jami'an sa cikin sirri, baya son maganar ta baza duniya. Mummynsa ce take ta kiransa a kan ya zo gida da wuri akwai ɗan ƙaramin party da suka shirya, yau iyayen Heleena sun zo daga ƙasar England, shi ne suka shirya party, ba komai ne kuma ya kawo iyayen Heleena ɗin ba face sun zo ne domin ayi maganar aurensa da Heleenar....... Babbar magana, har sun bani bazawarar dariya 🤣 Abin da baku sani ba shi ne, Heleena zaman Smart take yi a cikin gidan, tun da ta yi wayo ta san menene soyayya, ta san kanta take fama da son shi, ta kafe shi take so, tana bala'in tsoronsa sannan tana haukar sonsa, iyayenta sun san da zancen, shi ma mummynsa ta sani, shi da daddynsa ne kawai basu san da zancen ba, dan su fa idan daddy ya san abu to tamkar shi ne ya sani, idan kuma shi ya san abu to tamkar daddyn ne ya sani, yadda kuka san twin's wlh, kuma wai uba da ɗa, ko da yake shaƙuwa ce ta yi yawa. Mum ta ƙasa iya gaya mashi Heleena fa shi take jira, shi take so yasa ma ta yarda har yanzu take tare da su, tana tsoron gaya mashi ne kada ya tayar mata da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali, tasan a duniya ya tsani mutum maras kunya, ita kuwa Heleena badan badan bama sai ace ita ta kawo rashin kunya duniya, tsabar bata da shi ko ɗigo, shiyasa ya tsani ganinta kamar ba gobe, sam basa shiri. Sun gama shirin komai shi da daddynsa kawai ake jira su zo a tattauna a tsayar da magana, daddy ma yana office yana ta tikar aikinsa bisa gaskiya da amana, yana ta ganin call ɗin mum ɗin amma yaki ɗagawa, dan yasan ita fa idan bata je office ɗinta ba bata da aiki da ya wuce ta zauna ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ta yi ta danna masu kira a kan su dawo suma su haɗu su jibge a gidan suna kallon juna, ba aikin fari bare baki da zasu yi mata, kawai su zauna suna ta ganin juna, ai mummy duniya ce. To da suka gane mata ne sai basu wani cika ɗaukar call ɗinta idan bata je office ba. Wani call ɗin ne ya sake shigowa cikin wayar a karo na biyu, sai dai ba call ɗin mum bace. Bluetooth dake kunnensa ne ya isar mashi da saƙon cewa ga number dake kiransa. Jin bana mum bane yasa ya yi picking. Yana ɗaga kiran daga ɗayan ɓangaren a ruɗe wani fasashen murya ya fara faɗi. "Sir remain s few minutes, the bomb went off". Ba tare da ya amsa ba ya miƙe tsaye, cikin nutsuwar nan tasa ya nufi waje wayar na'a hannunsa. Kai tsaye wajen wata F-15E Strike Eagle ya nufa, ɗaya ne daga cikin jiragen da air force suke amfani da shi, shi ba air force bane amma yana amfani da irin jirgin a duk lokacin da yake son isa waje cikin gaggawa, dan jirgin tana da mugun gudun gaske. Yana saƙo kafarsa waje wasu irin jiga jigan zaratan maza ne suka fara aikin sara mashi, tamkar zasu bauta mashi saboda biyayya. Ba tare da ɓata lokaci ba ya bar headquarters ɗin nasu cikin wannan eagle ɗin. Bai jira a ko'ina ba sai a lotus forest, gabaɗaya wajen harta bishiyoyin dake kewaye da wajen snow na mamayesu except wajen da jirgin nasa ta sauƙa. Wajen ana tsabtace shi ba'a barin snow a nan. Already an rigada an shirya komai shi kaɗan ake jira, jami'ai ne da dama cike a wajen, dukkansu fararen fata ne tas. Suna ganinsa a guje suka nufosa, jami'a,i zasu kai goma karti da su, haka suka nufosa, wasu daga cikinsu suna riƙe da bomb hand gloves, wasu kuma bomber jacket. A tsananin zafafe suka fara sanya mashi bomber jacket and hand gloves ɗin, sauri sosai suke yi domin bomb ɗin saura ƴan mintuna ya tashi. Cikin nutsuwa yana taku a hankali ya nufi wajen, ji jami'an suke yi tamkar su janyoshi da sauri su ƙarisa da shi wajen, dan rayukan ƴan uwansu ne yake a haɗari, kuma shi kaɗai zai iya cetansu, sai dai ɗan banzan jan ajine da shi na masifa. Wayarsa ce ta fara kara, call ɗin mum ne, dan ya tsokaneta sai ya yi picking, bai bari ta fara jefa mashi tambayoyi ba ya ce. "Mum i am near the bomb, I will remove it from some of our officers, so i will call you later". Habawa ai mum tana jin wannan labari ta miƙe tsaye, duk da tasan wanenen shi ɗin a kan aikinsa, amma ita wannan batu na bomb yana ɗaga mata hankaki sosai,........ Ni kam na ce dan ma baki san har nuclear ɗan albarkar ɗan nan naki yake haɗawa ba kenan! Da kin sani sai yaya kenan?. A ruɗe ta fara faɗin. "My baby, take care of yourself, don't let something to happen to you, take care". Katse kiran kawai ya yi tare da tura wayar a aljihunsa, dama dan ya tsokaneta ya yi hakan. Jami'ansa tsabar ƙaguwa da son ya zo ya ceci rayukan ƴan uwansu har kamar su kai hannu su janyo shi izuwa wajen bomb ɗin, tsabar isa da jan aji shi kuma ya tsaya yana waya. Abin abin takaici Nasan zasu ce wani bomb ne akewa haka? To dai sai gobe zaku ji komai........🥱🤪 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 31/10/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E32 Jami'ansa tsabar ƙaguwa da son ya zo ya ceci rayukan ƴan uwansu har kamar su kai hannu su janyo shi izuwa wajen bomb ɗin, tsabar isa da jan aji shi kuma ya tsaya yana waya. Abin abin takaici. Kowannensu zuciyarsa sai bugawa yake da sauri sauri, a cikinsu akwai jami'in da duk jarumtarsa kuka ya fara yi, idanunsa sun cika tab da kwallah, saboda akwai yayansa a cikin jami'ai shidda da suke sarkafe da rigar boma boman, shiyasa ya fara kuka, dan Smart ya ɗaga masu hankali, baya abu da sauri dan iskanci, saboda yasan shi kaɗai ne zai iya, dole a jirasa idan ana da buƙata. Gabansu ya ƙariso, shi kansa ya girgiza da ganin jami'an nasa, gabaɗayansu ɗaure suke da rigar bomb, jami'ansa da ƙasar America ta kama ne, da Smart ɗin ya buƙacesu a hannunsu ne suka yi masu wannan abin, duk suka sarƙafesu da boma boman da koda minti goma aka baka ka kashe bomb ɗin har ya tashi ba zaka iya sanin me yakamata ka taɓa a jikinsu dan kashe su ba. Ga shi su dukka shiddan aka ɗaurawa, bayan haka dukkansu time na tashin bomb ɗin nasu lokaci guda ne, kafin ya cire na wasu na wasu zai iya tashi, wannan dalilin ya ɗaga hankulan sauran jami'an da suke wajen, shiyasa kuka ga wancan jami'in ya fara kuka, sai dai dukkansu sun san in dai Smart ya ce zai cire, to ƴan sakanni sun isheshi, dan yana haɗa boma boman da suka fi waɗan nan haɗari. A gabansu ya tsaya dukkansu suna zaune saman chairs da sauran jami'an suka kawo masu. Tsabar suna cikin haɗari ma a jiragen Rockwell B-1B Lancer aka turo su, sun ki sanyasu a normal jirgi, saboda gudun fashewar bomb ɗin. Calmly ya furta. "Jack come and remove all the camera's that have installed for them". Zaro idanu suka yi, fuskokinsu ɗauke da mamaki, kallon kallo suka fara yi wa junansu, gaskiya Smart ya cika ɗan baiwa, sun duba jikunan jami'an nan nasu tas su basu ga wani abin ɗaga hankali a tattare da su ba, shi daga zuwa ya ga an sanya masu camera a jiki, wato dole dai America tana son kama shi da komai kanƙantar abar zargi, kunga idan ya cire ko ya kashe masu wannan bomb na jikin nasu cikin ƙanƙanin lokaci, in America ta ga da gaske shi ya cire ta hanyar waɗan nan camerorin to fa zasu ce wlh duk yadda aka yi yana haɗa irin boma boman, tarko suka haɗa mashi. Cikin sauri suka fara ciccire masu camera's ɗin, shi kuma yana nuna masu in da suke, irin ƙanaƙnanan cameran nan ne waɗan da ake ɓatar dasu a jikin botrin riga, sai ka cika mai kaifin basira zaka iya zaƙulosu. Gabaɗaya bombs ɗin saura five minutes su tashi, jikin wasu jami'an har kerma yake wajen cire camera's ɗin, dan tsoron kada ya tashi da su. Shi kuwa yana tsaye yana aikin shafa lallausan hair ɗinsa. Bayan sun gama cirewa ne ya ɗan rage tsawonsa ƙaɗan ya fara aikin kashe bombs ɗin, bai yi yunkurin cire masu ba, kasheta ya yi kawai, dan cirewa zai ja lokaci. Na karshe da ya zo cirewa saura one minute ta tashi, boma boman da kafin ka ciresu a matsayinka na kwararema sai sun ɗaukeka sama da ten minutes, amma shi ya ciresu dukka in less than five minutes tsabar ya kware a iya haɗasu, kuma yana da tsananin nutsuwa ne, irin wannan aikin kuma dama tana buƙatar nutsuwa sosai, ga misali ma kun gani, jami'ansa da yake suna cikin tashin hankali kunga ai basu ga camera's dake jikinsu ba, shi kuwa kunga ai yana zuwa ya gani. Umarni ya basu a kan su kwashi jami'an izuwa hospital ɗinsu na headquarter. Allah sarki har sun cire rai da rayuwa, dan basu taɓa tunanin za'a cire masu wannan bombs ɗin ba, sun jigata sun sha bakar wahala, kafin ya sanya daddynsa ya yi magana da America ta sakar masu jami'an wlh sun azabtar da su ba kaɗan ba, da kyar ma suka samu aka sakesu. Sai da daddy ya ratse masu ba leƙen asiri jami'an suka je yi ba, da yake suna matsayin kawaye sai ta hakura zata basu su, amma mugun munafurtar juna fa suke yi, dukkansu suna yi wa junansu kallon wawaye, a duniya idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba wlh. Smart dai da daddynsa sun zama ƴan duniya, wato sun iya siyasa ne na bugawa a jarida, yanzu sai su saka mutum a kwana. Sai da ya tabbatar antafi da jami'an cikin aminci, sannan ya kwashi boma boman da ya cire masu bayan ya kashe ɗin ya nufi eagle ɗinsa. Office nasa ya koma, a can ya ajiye boma boman a kan idan ya samu time zai dubasu, daga haka ya wuce gida, dan mom taki barinsa ya huta, sai kira take ta danna mashi babu kakkautawa. Ni dai securitys dake tsaron gidan nan nasu suna ɗaga mun hankali har bana son zuwa ɗauko maku labarai, waɗan nan ganinsu kawai ya isa ya sanya mutum sakin fitsari a wando, dan ma dai na riƙi Allah ina da kwarin zuciya ne, kuna ganinsu wasu jiga jigan turawa, sai dai kyawawa ne kuma duk da fuskokinsu babu alamar annuri bare imani, ga su ta ko'ina tun daga farko titin ketowa unguwar har izuwa cikin gidansu, ai kunsan yadda gidan shugaban ƙasa yake, ba'a wasa da tsaro!!. Yana shigowa main parlourn ƙasa wani irin ɗaure fuska na musamman ya yi, ya cunkushe rai dan kawai ya ga baƙi a gidan nasu. Ko kallon in da suke bai yi ba bare su sa ran zai ce masu sannu, kai tsaye ya nufi elevator domin ya wuce room ɗinsa. Da sauri mom ta miƙe tana faɗin. "Baby come here". Wani irin kallo ya wurga mata, irin kallon nan na mom kin fara ko. Mayar mashi da makamancin irin kallon ta yi na e ɗin na fara maza zo nan. Abin gwanin birgewa da ban dariya. Tsayuwa ya yi kusa da elevator ba tare da ya ƙarisa in da take ɗin ba, ƙarisowa gabansa ta yi tana faɗin. "Baby don't you see ur uncle? Come and greet them". "Mom i have a lot to do now, you just go and greet them for me". Ya yi magana ba tare da ya kalli in da suke ba, yana kai karshen maganar ya haura sama. Haushinsu yake ji dan ba yadda dad ɗinsa bai yi da su a kan su musulunta ba sunki, a haka kuma suke son haɗa alaƙa da shi, tab lallai kuwa!. Bin bayansa izuwa saman ta yi, already har ya shige toilet dan yin wanka, a gefen bed ɗinsa ta zauna dan ta jirasa, ita kanta kirjinta bugawa yake yi da sauri sauri, tana jin tsoron bayyana mashi maganar da ta zo da shi, tasan ba wanda ya tsana biyun Heleena a gidan, baya son ganinta sam, tana fargabar yadda zasu kwashe da shi, ita ma kenan da yake matuƙar kauna yake kuma jin maganarta, ina ga ace uncle ɗin nasa ne zai yi mashi maganar, me kuke tunanin zai faru?. After 40 mins Bathrobe ce a jikinsa fara tas ya fito daga toilet ɗin, da yake tsakanin in da bed ɗinsa take da toilet ɗin akwai nisa saboda girman bedroom ɗin, sai bai san tana cikin ɗakin ba, ya yi zaton tana parlourn, duk da ta san password na buɗe kofar room ɗin nasa dan ba iya fingerprint bane kawai da kofar, zaka iya buɗewa da password ma, duk da yasan tasan password ɗin bai yi tunanin zata biyo bayan shi ba. Dressing room ya shiga daga toilet ɗin, girman room ɗin nan ba'a magana, gabaɗaya show glasses, transferred glasses su ne cike a ciki, kowani irin kaya da glass wardrobe ɗinsa, daga waje kana iya ganin duk wasu kayan da suke ciki kowanne, ba sai ka sha wahalar neman in da ma'ajiyinsu take ba, part na set ɗin takalma daba, abubuwa dai sai wanda ya gani. Shiri ya yi cikin denim short mai bala'in tsada, and white single, da alama kwanciya zai yi. Ya zuba wani haɗaɗɗen perfume ɗinsa mai kamshin kwantar da hankali a jikinsa. Cikin room ɗin ya nufa bayan ya kammala shirin nasa. He was so surprised ganinta da ya yi a zaune a bakin bed ɗin. Ɗan kara cukule fuska ya yi, dan yasan takura mashi kawai ta zo yi. Ganin ya kara cukulewa yasa ta saki murmushi tana binsa da kallo from down to up. Haye gadon ya yi da nufin ya kwanta, cikin sanyin murya ya ce. "Mom what are you doing here again?". Ya yi maganar yana sauke kansa a saman lallausan pillownsa. Juyowa ta yi garesa da kyau, cikin sigar rarrashi da lallaɓa mutum ta fara magana. "My baby please come and greet ur uncle and ur aunty, i will be happy if you do thet". A marairace ta kai karshen maganar. Yana cigaba da cukule fuska ya ce. "Mom i want to sleep, because am feeling to much of sleeping, if they're here, they haven't left, by the time I wake up we should say hello". Yana kai karshen maganar yaja katuwar lallausan duv ɗinsa ya rufe harda face ɗinsa gabaɗaya dan ma tasan da gaske barcin yake ji....... Smart wato idan kun lura shi fa jan ajin nan kamar a jininsa take, komai sai ya ja aji a kanta kafin ya aikata kamar ba gobe. Miƙewa tsaye ta yi, sam bata ji daɗin hakan ba, amma kuma farincikin ɗanta yafi mata komai, wannan barcin da ya ce yake ji to ya yi sa ya fi mata auren ma gabaɗaya, tana kaunarsa sosai. Parlourn ta iskosu suna zaune, hakuri ta shiga basu tare da gaya masu cewa ai ya dawo a gajiye ne shiyasa, yanzu ma haka ya yi barci, su yi hakuri sai ya tashi. Baban Heleenar ne ya nuna ɓacin ransa a kan hakan, ya ce dan Smart ɗin yaga Heleena tana haukar sonsa ne zai na yi wa mutane walaƙancin? To su wlh sun ma fasa ba zasu haɗa wannan aure ba. Nan fa Heleena dake zaune tana cikin wani irin tantirin shiga nasu na turawa ta fara faɗin wlh baban nata bai isa ba, ita Smart take so, shi take son yin rayuwa da shi, dan haka dole su jirashi kuma su yi duk abin da yake so, bata son ma su ɓata mashi rai....... Idan kana raye dai babu abin da ba zaka gani ba, kuma su fa hakan a wajensu normal ne ƴa tasa iyayenta dole su nema mata soyayyar wadda take so, su kuma kaunar ƴaƴan nasu ne yake rufe masu idanu ya kaisu ga halaka. Hakuri mom ta basu a in da ta ce musu shi fa Smart bai ma san Heleena tana son shi ba, infact bai ma san me ya kawosu gidan a yanzu ba, dan haka su bi a hankali, gaya mashi batun auren ma sai an bishi a hankali. Taɓe baki baban Heleenar ya yi, yana mamakin irin son da suke yi wa ɗan nan nasu, shi baya laifi, komai ya yi daidai ne, ita kuwa mum Heleenar bata ji komai ba, ita burinta yarta ta samu abin da take muradi. Haka suka yi ta zaman jiransa har barci ya ɗauki mum Heleenar. Dad kuwa shi ne bai dawo ba sai can da yamma, shi ma a tare da manya manyan bakinsa ya dawo. Mom ta sha mamakin ganinsa da baki, har ƙasa hakuri ta yi sai da ta tambayesa waɗan nan kuma daga ina? Taga mace da namiji masu kama ɗaya, kuma ga dukkan alamu dangin gidan sarauta ce, sarauta ma mai karfin iko duba da yanayin shigarsu, sun haɗu sosai, da alama maƙudan dukiya ta yi masu mubaya'a, domin kuwa sun jiƙu da dukiya ba kaɗan ba, shi namijin ma takalmar sarauta dake kafarsa ta zallar madarar gold ce. Shi ma dad he was so surprised na ganin iyayen Heleena a gidan nasu, da izinin mom kenan suka iya ketowa cikin gidan, dan babu wanda ya isa ya keta arearsu ba tare da izinin ɗaya daga cikinsu ba bare har ya iya shigowa cikin gidan, koda kuwa securitys ɗin sun san kasan mutumin to fa dole sai ka sanar da su zai zo zasu bashi hanya bayan sun gama cajesa in and out tsab!. Gaisawa suka yi cikin mutunci da mutunta juna, sannan ya wuce izuwa sama bayan ya damka amanar bakin da ya zo da su a hannun mom ta kula mashi dasu bari ya duba Smart sai ya yi wanka ya zo su tattauna. Lokacin da ya shiga ɗakin ɗan nasa barci ya iskosa yake yi, har lokacin bai farka ba, a hankali ya lallaɓa kamar wani ɓarawo ya fito waje, wai duk dan kada ya tashesa daga barcin. Nasa room ɗin ya nufa, a nutse ya yi wanka, ya shirya cikin hoodie, kyakkyawa ne dad ɗin nan fa sosai. Ƙasa ya sauko, a lokacin already mom ta sa masu aiki sun tashi kan bakin dad da kayan abinci masu rai da lafiya, president food ma ta sa suka shirya masu, wato irin abincin da dad ɗin yake ci, na gaya maku mom mutuniyar kirkice mai zuciyar zinari, musulunta ne dai har yanzu taki yarda ta yi. A rest parlourn suka haɗu dukkansu bayan bakin sun gama kwasan abinci daidai gwargwado. A nan dad ya ce da bakin nasa su zo ayi magana, da yake ita ma mom tana son su yi magana da shi da iyayen Heleena sai ta ce duk su haɗu a rest parlourn kawai. A cikin bappan parlourn wannan rest parlourn yake, ya ji komai na more rayuwa, waje ne da suke yawan zama dan hutawa ko su tattauna abubuwa masu mahimmanci. Saman sofa suka zazzauna, a nan dad ya gabatarwa da Mom bakin nasa, ya nuna namiji tare da ce mata shi ne Prince mai jiran gado na ƙasar England, macen kuma babar yayarsu ce, kara gaisawa suka yi cikin mutumci. Ƙarawa dad ya yi da cewa. "Prince they came for the issue of their sister's marriage which they are asking for Smart to do, saying that the girl is determined that she want him to marry her or she will kills herself". Prince sun zo ne a kan maganar auren sistersu da suke son Smart ya yi, wai yarinyar ta ce tana son ya aureta ko ta kashe kanta. ______________ Ai tun dad bai kai karshen maganar ba Heleena ta miƙe a zabure. Su mom kuwa binsa da idanu suka yi tun da ya fara jawabi suna jiran ya direta. Cikin tsawa Heleena ta ce wlh bata ga ƴar iskar da ta isa ta ce tana son Smart ba, dan ita kaɗai aka yi shi, wlh mace ko da wuta take tafiya a jikinta bata isa ta ce zata aure shi ba, tafi karfin yarinta sai dai uwar yarinyan ita, ba sarauta suke takama da shi ba, ko uban sarauta ne basu isa ba. Tashin sense! To fa, nan fa kallon kallo ya koma a parlon, shi dai dad bai taɓa sanin wannan zancen na son da Heleenar ke yi ɗan nasa ba, yau ake yinta, Heleena zata taro mach, kishi da ƴar sarki, to ni dai ina daga gefe ni da Smart bamu san komai ba. Yau ga ikon god, haɗaɗɗun chikun turawa masu kama da ƴan tsana suna faɗa a kan Smart namu na amana, shi da bai ma san me ake ciki ba, ni kam princess Teema na ce duk mai son Smart a cikinsu to ta musulunta ko ba haka ba my people's? Idan ta musulunta da ni da ku my people's zamu tayasu gaya mashi ko? Har ma tayasu shawo kansa zamuyi, duk tsaurin nan nasa tsab zamu jure mu sadaukar da rayukanmu mu tayasu neman soyayyarsa ba sai sun yi faɗa ba, su karɓi kalmar shahada kawai su ga ikon god!! Ko ya kuka ce?🤨 Dad kam bin Heleena da ido ya yi, ta wani tsaya a tsakiyar mutane tana huci kamar wata zakanya. Mom ce ta ce mata ta kwantar da hankalinta Smart nata ne ita kaɗai. Nan fa ta dakawa mom ɗin ma tsawa wai ta kyaleta, yau sai taga waye uban yarinyar da aka kawota talla wajen Smart ɗinta. Kun ji mun karfin halin irin na Heleena, wai an kawo yariya tallah, sai kace ita ma ba tallar kanta take yi ba, abin takaicin ma wajen wanda sam bai san suna yi ba, hasalima tsoronsa take ji ƴar ƙaniya, rashin kunyar tata mom and dad kawai take yi wa. Da yatsa ta nuna Prince dake zaune yana binta da kallon mahaukaciya, cikin tsawa ta fara da fuck kafin ta ƙarisa da tun kafin ta rufe idanu ta buɗe su tabbatar sun bar gidan nan, har da wani cewa kada su yarda su bari ta sake ganin waɗan nan dattin kafafun nasu a ƙasar nan ma bare gidan nan. Nasan yadda take surfa masifar nan zaku yi tunanin ko dai ubanta wani hege ne a ƙasar ko, to ubanta ba kowan komai bane, duk taƙamarta dai muƙamin daddyn Smart ne da kuma shi Smart ɗin, hasalima iyayenta bayi ne a ƙarƙashin masarautar England ɗin suke, a can suke da zama, amma sai shegen baki gareta da gadarar tsiya. Ku dai kunsan jinin sarauta basu ɗaukar wargi komai ƙanƙantarta, dan haka Prince bai yi wata wata ba ya miƙe ya ɗauketa da wani irin kafirin mari mara mix, sai da ta yi wani irin tangal tangal kamar wadda ta yi tatil da wine ta bugu. Har wani gaba ta yi kamar zata kifa a kansa, sannan ta ɗan yi baya. Da farko ma shi Prince da ya shigo ya ganta har ya ji ya fara kamuwa da sonta, dan fa wlh ba karya kyakkyawa ce sosai, sai bala'in rashin kunya da masifa ga iya makirci. A fujaje dad ya miƙe tsaye, ita ma mom miƙewa ta yi suna jinjinawa karfin hali irin na wannan Prince ɗin, kazo gidansu yarinya neman alfarma kuma ka mareta a gaban iyayenta?! lallai ka kai ɗan duniya. Iyayen Heleenar kuwa suna zaune sun yi shiru, dan kuwa su sunsan ya karfin iko England kingdom yake, basu isa su ce zasu ja da su ba, shi dai dad yana da damar iya yin magana a matsayinsa na mai riƙe da muƙamin president, amma su sai dai shiru da ido kawai. Dad ne ya dakawa Prince ɗin tsawa a kan meyasa zai maran masa yarinya a kan dan ta ɗan yi waɗan nan maganganu?. Rai a daƙile ya ce shi ba zai iya ɗaukar rainin nan ba, dama shi bai so zuwa ba, saboda takurawa mahaifinsu da kanwar tasu ta yi ne yasa aka wakilta shi dan dole, su basa ɗaukar walaƙanci. Tsawa mai sauti dad ya sake daka mashi a kan dan baya ɗaukar walaƙanci sai ya dakar mashi yarinya a gabansa ne? Ai tun da su suka zo neman alfarma har gidansu sai su yi hakuri da duk abin da zasu gani. "I can't tolerate nonsense you already knew that!!". Cewar Prince, ya yi maganar yana nuna dad da yatsa!. Mom ce ta tari zancen daddy da yake ƙoƙarin faɗa da cewa. "It's okay, please and please we're so sorry for all...........". Katse mata maganar dad ya yi da cewa. "Which kind sorry are you talking about? Shin mun yi masu something wrong ne?". Lumshe idanun ta yi ta sake warosu a kansa, tasan halin daddyn dama, shi ma dai yadda kukan san jinin sarauta haka yake da kafiya, zafin rai, izza da rashin yafiya cikin sauri. Baiwar Allah ta so ta kashe wutar tun bai yi nisa ba, amma haka daddy ya murje idanu, cikin ɓacin rai ya kira securitys a waya, tana ce mashi a'a, dan ita tana son zaman lafiya da kowa, idan ma rabuwa ne su rabu da kowa lafiya cikin mutunta juna dan baka san me gobe zata haifar ba. Tana hana shi amma yaki kulata ya damka Prince ga securitys, ya ce maza aje a ladaftar mashi da shi. Mom kamar zata yi kuka, tana a'a yana yi. Cikin ɓacin rai yayar Prince ɗin ta fita daga parlourn, mom na kiranta tana tafiya. Wajen jerin gwanon dallah dallah motocin da ya kawosu gidan ta nufa, kai tsaye ta buƙaci da su mayar da ita airport, abin ya kwaɓe masu, dole ta isar da labarin ga mahaifinsu cewa an rufe yarima da hanzari. Sai magiya Mom take yi mashi a kan yasa a saki yarima ya koma kasarsu please, ina ya ce sai ya ɗanɗana kuɗarsa, zai san cewa shi ba sa'ansa bane da zai zo har cikin gidansa ya marar mashi ƴa. Hajiya Heleena kuwa sai cika take tana ɓatsewa, rarrashin ta dad ya rinƙa yi, da alama shi mutum ne mai shagwaɓa yara sosai. Cikin fushi fuuuu ta wuce room ɗinta ta barosu a parlour, da wani shegen takalmarta masu uban tsini. Da sauri mum ɗinta and mom Smart suka bi bayanta dan su je su rarrasheta. Zama dad ya yi a saman sofa yana sauke ajiyar zuciya. Shi kuwa daddyn Heleenar ya yi shiru yana ganin ikon god kamar wanda ruwa ya cinye. Duk wannan abin da yake faruwa Smart yana zuba barcinsa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa su suna nan suna faɗa a kansa. _______________________🔥🌹 KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 JAWAD AND RIZWAN. "Jawad what's going on? Your face looks like you're hiding something for me". Cewar Rizwan, ya yi maganar yana ƙoƙarin zama a saman visitor's chair. "Kai yaya Rizwan zaka fara ko? Ni babu wani abin da nake ɓoye maka". "To why ka tafi baka mun sallama ba? And where's Jaish? Nasan dai kullum kuna tare, but tun da nazo ban gansa ba". Nan take face ɗinsa ta sauya, ya sosa mashi in da yake matuƙar yi mashi kaikayi, dama da kyar ya iya danne tashin hankalinsa yana ƙaƙalo walwala da farincikin dole. Kasancewar yasan Chuchu tana cikin office ɗin sai ya ce. "Jaish yana nan, abubuwa ne suka sha kansa yasa baka ganinsa". Idan baku manta ba Momma ta ce kada ya yarda ya fitar da zancen ɓatar Jaish ɗin, da ace shi da Rizwan ɗin ne kawai a office ɗin, to da zai iya gaya mashi gaskiya, amma Chuchu tana ƙarƙashin table. "Jawad seriously you're not okey". Ya faɗa yana kare mashi kallo, sai wani sunkuyar da kansa ƙasa yake yi, yau dai ya dawo kamar Jaish, kunya yake ji. "Me ka gani da kace am not okey?". Ya yi maganar dai still bai ɗago ba. "Abin ne da mamaki, yau na zo office ɗinka ko ruwa baka bani ba bare black coffee, sai wani sunkuyar da kai kake yi abin da ban taɓa gani ba". Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Am so sorry aiki ne suka mun yawa yasa na manta, amma bari na ɗauko maka". Yana ƙoƙarin miƙe ya yi saurin ce mashi. "No, go back and sit down to continue doing your work, ni tafiya ma zan yi, i want to go to the supermarket, there is something I want to buy for your Aunty".". Ɗan zaro idanu ya yi. "Yah Rizwan kana bani mamaki fa! Wai yanzu da gaske kai ne kake batun aure? Ni ban ma ga wacece Aunty tawa ba, baka nuna mun ita ba". Cool murmushi ya saki. "Ba dole na yi batun aure ba, Auntyn taka special ce, ta ruɗar dani sosai, a duk time da na kalli face ɗinta bana iya rintsawa a wannan daren ranar, kwana tunaninta nake yi, she is different from everyone else, ban ma san ta ya zan gaya maka yadda take a raina ba, abin ya wuci tunaninka, and babu wasu kalmomi da zasu iya zayyana yadda nake jinta a rai'na, amma dai bari na je na dawo zamu haɗu a gida in gaya maka yadda nake sonta". Jawad since he started talking, he was silent and listened to him while smiling, and he noticed that they're in the same situation, because he also don't have the words that he could describe how's he love his chuchu. Sai da ya kai aya ne ya ce. "Yah Rizwan now ka zama ɗan love wlh, seriously zaka yi kyau da aure sosai wlh". Yana magana yana murmushi. Murmushi shi ma ya yi tare da miƙewa tsaye. "Idan na biye maka tabbas ba zan yi abin da zan yi ba, dama kewarka yasa na fara zuwa dubaka". Ya yi maganar cikin tsantsar kaunar ɗan uwan nasa. Miƙewa Jawad ɗin ma ya yi tare da miƙa mashi hannu suka yi musabaha, sannan Rizwan ɗin ya nufi waje, Allah ya tsare ya yi mashi, da amin ya amsa tare da ficewa waje. Komawa ya yi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Duk abin da suka faɗa tana jinsu, haka kawai ta ji Yah Rizwan ɗin nan ya kara burgeta saboda yadda yake nuna kauna da kulawa ga Yah Jawad ɗinta...... To fah e lallai Chuchu ta yi nisa. Tana tsaka da tunani sai ji ta yi ya shafa face ɗinta tare da cewa. "What are u thinking?". Ƴar firgita ta yi, da sauri ta ɗago da kallonta izuwa kansa, lokacin guda suka sakarwa da juna cool murmushi, sai kuma ta ɗan shagwaɓe fuska. "Yah Jawad ni matsa na fito zafi nake ji". Ƙasa ƙasa ya furta. "Da gaske?". Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e da gaske. A maimaikon ya matsa ɗin sai ya kara matsowa kusa da ita. Ƙara turo baki ta yi. "Yah Jawad zafi fa nace maka nake ji". Kumatunta ya sumbata tare da ɗan yin baya ya miƙar da jikin nasa, ya koma ya jingina da jikin chair ɗin nasa. Fitowa ta yi tana faɗin. "Sai na gayawa Yah Rizwan cewa lokacin da ya zo office naka ka sakani ƙasan table wai dan kada ya ganni, bari kaga mu koma gida". Tana magana tana kwaɓe fuska irin ita a dole zata yi mashi barazanar nan. Riƙota ya yi, da murya kamar mai jin barci ya fara faɗin. "Da gaske zaki iya tona mun asiri?". Kai ta gyaɗa alamar e. "Okey bari dai na yi maki wani abin ma dan idan mun koma ki haɗa har da shi ki faɗa mashi". "Wani abin kuma?". Ta tambaya tana ɗan zaro idanu, addu'a take Allah yasa ba zaneta zai yi ba. Matso da face ɗinsa dab da nata ya yi, kamar zai haɗe fuskokinsu waje guda, in a whisper ya ce. "Rufe idanunki ki gani". Ɗan siririn haɗaɗɗen hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Yah Jawad to wai ina budurwar taka ne?". Yadda kuka san wanda yake cikin maye haka ya zama, kamar ya sha wine. A kasalance ya ce. "Jannat wai meyasa kika damu da zancen budurwa ta ɗin nan ne? Ko dai kishina kike ji?". Da sauri ta girgiza kai. "A'a ni bana kishi, kawai ina son in ganta ta fini kyau ne ko na fita?". "Are you sure that's all?". A hanzarce ta gyaɗa kai. "Okey yanzu kuwa ba sai anjuma ba zan gaya maki wacece ita, amma kafin nan rufe idanunki". Kamar dai bata yarda da shi ba, kamar tana ɗan tsoron wani abin haka ta ɗan datse idanun nata. Kara matso da face ɗinsa dab da tata ya haɗesu, suna iya jiyo sautin numfashin juna suna kuma iya shaƙa. A hankali ya........ ___________________🔥 Sautin tashin kiɗa ne ya karaɗe gabaɗaya kingdom ɗin, an gama shirya komai, an ƙawata komai yadda ya dace, dukiya ta yi kuka a wannan party da aka shirya, daga walima mummy ta mayar da shi yazama party, dan an haɗa ne da na murnar cin nasara da suka yi a yaki. Sai neman Chuchu Auta take yi bata ganta ba, dukka princess sun ci kwalliya na gani a sake kallah, sun fito reras da su, komai cikin tsari da nuna tsantsar mulki ake gudanar da shi, zakarun mayaƙan da suka fi kowa a cikin kingdom ɗin ne suka kewaye hall ɗin da ake gudanar da partyn, Hoorain yana tsaye daga bakin kofa shigowa cikin tsantsar jarumta, Auta dake zaune saman stage, ta tsantsara kwalliya, ta fito a ainahin jinin sarautarta kuma princess, in ma mace ko namiji duk wanda ya kalleta sai ya juyo ya sake kallonta, kai kace ba ita bace, tana zaune kusa da Guyson ɗinta, ga Gimbiya Aneesa na zaune a gefenta. A gabaɗaya taron jama'ar dake cikin hall ɗin nan ba wanda ta kurawa idanu sai shi, ga Guyson ɗin nata ma yau yana kusa da ita yadda take damunsa a waya a kan ya dawo amma bata mayar da hankali a kansa ba. So take ta karɓi single ɗinsa da ya ɗaure mata hannu da shi ranar, amma bata san ta ya zata sake samun damar keɓewa da shi su biyu a keɓaɓɓen waje ba, ranar ma Allah ya tsare zasu samu wannan damar ne, tana da buƙatar sake haɗuwar nasu kuma, to me yakamata ta yi? Dole ta nemowa kanta mafita. Shi ma ɗin dai tun da ya harɗe hannayensa a saman lion chest ɗin nan nasa ita ya zubawa idanu, ba zaka taɓa iya famintar cewa yana kallonta ba har sai idan kana tare kusa sosai da shi. Baiwar Allah yau ko damar yi mashi magana bata da shi, idan tana son zamansa lafiya to kada ta kula shi, dan kuwa dai yau idan ta ce zata kula shi zata ja mashi wani bala'in ne, barema yadda uncle Taheer yake wajen ai ba zai bari ba. Tunanin yadda zata yi ta fara yi. Can sai wani tunani ya faɗo mata. Da sauri ta miƙe tsaye, sai sakin wani irin murmushi take yi ta samu mafita. "Where are you going?". Guyson da wanka ta bi jiki ne ya yi magana, guy ɗin nan yau haɗuwa ta musamman ya yi, shigar henley shirt and cargo trouser ya yi, kaya sun bi jiki Masha Allah. "Yah Omar zan je duba Aunty Chuchu ne, kaga bata zo ba". Ɗan wawwaigawa ya yi domin duba Chuchun, a nan yaga tabbas bata a wajen. "Okey sit down let me look at her". Ya faɗa a tsanake. Tamkar zata sa ihu ta ce. "No Yah Omar, ka zauna kawai kada ka wahala bari ni na dubata by my self ka ji?". Da yake basa son ɓacin ran juna sai ya yi na'am da zancen nata, amma sai ya ce ta samu ɗan rakiya. Rai a farance ta amsa da. "Already ni ina da ɗan rakiya ai, Hoorain zai rakani". Ya yi mamakin ganin karuwar farinciki a tattare da ita lokaci guda, amma bai kawo komai a ransa ba ya amsa mata da to kada ta jima. A hanzarce ta nufi step na sauka daga wajen, da ido uncle Taheer dake zaune kusa da mama suna hira ƙasa ƙasa ya bita, yadda kuka san son Autar nan yake, ya cika nuna kishi da kulawa a kanta, da yanzu zai ganta a tare da Hoorain ba ƙaramin faɗa zai yi mata ba, kuma zai ce sai ya hukunta Hoorain ɗin, yana ɗaya daga cikin waɗan da suka hanata yiwa Hoorain magana bayan Jaish kenan. Miƙewa ya yi da nufin ya bita dan ya ji ina zata je ƴan uwa dukka suna nan? A lokacin King bai kai ga shigowa cikin wajen ba, babu tabbacin ma zai halarci taron, dan yana can suna zama ta tattaunawa da dattawan fada, duk zama ce a kan Spender, duk wani amintaccen dattijo na fadan ya halarci tattaunawar, commander Zafar kam shi ne ma a kan gaba. "Koma ka zauna ai bamu gama maganar ba". Cewar mama. Ba dan ya so ba ya koma ya zauna dan su kammala maganar, ya so bin bayanta yaga ina zata je sai ya rakata, amma ya kudurci niyar in har bata dawo ba suka kammala magana sai ya bi bayanta. Ita kuwa cikin nutsuwa tana taku wanda ya ja hankulan jama'a da dama a kanta, da yake takalma high ta sanya, kuma ƙasar wajen tiles ne, sai yake bada sauti duk in ta yi one step, ga manya manyan ƴaƴan sarakuna, ƴaƴan shuwagabannin ƙasashe da dama, baki dai iya baki sun halarci wannan taro na mummy. Yadda take tafiya suna binta da kallo hakan ba ƙaramin ƙona ran Hoorain ya yi ba, ya ji babu daɗi, haushin takalmar nata ne ma suka kama shi, kamar ya je ya ciresu ya jefar, amma bai isa ba, bashi da damar yin hakan. Ya luluƙa duniyar tunanin haɗe da bakincikin yadda maza suke binta da kallo, bai ankara ba sai jin sautin ɗan siririn muryarta ya yi tana faɗin. "Hoorain mu je ka rakani garden ɗin babban yaya". Ta kai karshen maganar tare da wucewa gaba. Bayanta ya bi, yana taku cike da tsantsar jarumta sosai. Suna fita daga hall ɗin ta fara faɗin. "Hoorain yanzu haka zamu iya samun gonar daddy a buɗe?". Yadda suke tafiya gwanin birgewa, gata ƴar karama a gabansa, dan Hoorain yana da tsawo da cikar halitta sosai, ya tasata gaba, ita kuma ta ja mashi tafiya irin na mata, dan kuwa yadda take tafiya a hankali hankali sai ya ji kamar ya ɗagata sama kawai sai ya fi mashi, yana da zafin nama, ba zai iya jurar irin wannan tafiya tata ba, tafiyar tata kayan haushi ne a wajensa, dan bata sauri. Shiru ya yi tamkar ba zai amsa ba, sai da ta dakata daga tafiyar da take yi ta juyo da kallonta a kansa, sannan ne ya ɗan kawar da kansa tare da buɗe baki zai amsa mata kenan suka ji sallamar wani ta bayansu. A tare suka kai kallonsu kansa. Wani matashin balarabe ne da ba zai wuci 23 years ba, ɗa ne ga sarki Egypt. Hoorain ne ya amsa mashi sallamar. Wani irin ƙasƙantacen kallo ya wurgawa Hoorain ɗin, a gadarance ya ce. "Bada kai nake yi ba malam bodyguard, ko an gaya maka prince kamar ni ina magana da irinku ne? Ni idan ina waje ma waɗan da suka fiku ma basa magana bare ire irenka". Ɗaure fuska sosai ta yi, maganar ta mata zafi, ta ji babu daɗi sosai, a kan me wannan ƙazamin zai ce wa Hoorain ɗinta bodyguard ya kuma yi mashi magana a gatse haka?. Ƙarisowa wajensu ya yi yana sakin murmushi, ita ya nufa da nufin ya yi mata magana. Gabansa Hoorain ɗin ya tare ba tare da ya yi mashi magana ba, ya dai hanasa isa gareta ne kawai. Hannu yasa da karfi zai hankaɗe Hoorain ɗin, ya turesa ya wuce ya isa gareta, sai dai ina ko motsa Lion chest ɗinsa ya kasa, kamar dutse haka ya jisa. "Hoorain ka kyale wannan mu tafi da wuri ka ji? Dan bai san ciwon kansa ba da alama". Ta fa tana ƙara ɗaure fuska sosai. Dan jinjina mata kai ya yi tare da juyawa, ta wuce gaba ya rufa mata baya. Da sauri wannan guy ɗin ya sake shan gabanta yana faɗin. "Magana nake son yi dake". "Bani da lokacin yin magana da ire irenku da basu san darajar ɗan adam ba, Hoorain ka ce ya tashi mun daga hanya na wuce". A dake irin babu wasa a tattare da itan nan ta yi maganar. Aikuwa da hannu ɗaya Hoorain ya cakumosa ya watsar gefe guda, dama ga shi kamar bulala ɗan siriri. Cigaba da tafiya suka yi tana tambayarsa ina wancan single ɗin da ya ɗaure mata hannun da shi ɗin nan ranar. Shiru ya yi, har ga Allah baya son bata single ɗin, dan haka sai ya ce mata ya jefar, dai'dai lokacin kuma suka shiga cikin garden ɗin. Kuka tasa tana faɗin dole ya je ya ɗauko mata, wato dama kyamarta yake ji da dan jininta ya taɓa rigarsa shi ne zai jefar ko?. Rarrashinta ya fara yi tare da ce mata ta bashi daga nan zuwa dare tabbas zai nemo mata. Da kyar ya samu ta yi shiru, bayan ta yi shirun ne ta zauna saman sofa tana aikin binsa da kallo, ya yi ƙasa da kai kamar mai tunanin wani abin. Sai da Guyson ya kira wayarta dake hannunta ne ta ce su koma, tana son yin hira da shi, shi kuma bai iya surutu ba, sai dai ya tsaya shiru kamar mutum mutumi. Suna a hanyar komawa suka ci karo da uncle Taheer, cikin ɓacin rai ya fara tambayar ina suka je, ita ce nan ta bashi amsa. A takaice ya ce ba da ita yake magana ba, da Hoorain yake yi. Murya a sanyaye ya maimaita abin da ta faɗa na in da suka je. Cikin bada umarni ya ce daga yau ma kada ya sake jin ta yi wa Hoorain magana, zai yi magana da dad ma a kan yanzu bata buƙatar mai kareta ko kula da lafiyarta, gasu a cikin kingdom ɗin me amfaninsu? Dan haka ya haramta sake ganinsu a tare. Yana kai karshen surfa masifar tasa ya ja hannunta suka koma cikin hall ɗin. Ba zaka taɓa fahimtar a wani irin hali Hoorain yake ciki ba, bakinciki ne ko farinciki ne Allah masani, cikin takun jarumta ya bi bayansu izuwa cikin hall ɗin, suna tafiya tana juyowa ta kallesa, har suka shige ciki. Ko da suka shiga cikin ma idanunta na'a kansa, shi kuwa gani take yi baya kallonta, alhalin kallonta sosai yake yi kamar zai cinyeta da ido. Sai gudanar da party ake yi cikin tsantsar girma, harkar ta manya ce. Ba Chuchu ba Jawad a wajen. _______________________🔥🌹 A hankali ya furta. "Ke dai Jannat kin cika tsoro, jibi yadda eyelashes ɗinki suke ɓari kamar ba lafiya ba?". "Ni Yah Jawad yanzu budurwarka kawai nake son gani". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. Raba face ɗin nasu ya yi yana sauke ajiyar zuciya, idan bai nuna mata kanta ba ba zata barshi ya sarara ba, kai mata kishinsu sai su. "Tashi mu je in kaiki in da take". Da sauri ta waro idanun tare da sauka daga jikinsa, sai dai kuma ta ɗaure fuska sosai, sai kunkuni take yi ciki ciki wadda ba zaka iya jin me take faɗa ba, da alama tsinewa budurwar tasa ma take yi. Miƙewa shi ma ya yi, sarai ya lura da kunkunin da take yi, ta wani cunkushe rai, ta haɗe jeran sama da na ƙasa, bai ce mata uppan ba. Tafukan hannayensa ya kai ya rufe mata idanunta da su, a hankali ya ce. "Let's go". Fara tafiya ta yi tana faɗin. "Yah Jawad to sai anrufe mun idanu ne za'a nuna mun ita?". "Yeah, saboda ita ɗin special ce da babu irinta a duniya, dole na rufe maki idanu, a gabanta zan buɗe maki idanun naki sai ki fara yin tozali da kyakkyawar face ɗinta". Shiru ta ɗan yi suna cigaba da tafiya. Can kuma ko me ta tuna sai ta ce. "Wlh nama san mummuna ce budurwar taka, duk yadda aka yi kanta ƙato ne". Yana jinta dai bai tanka ba. Gaban mirror dake cikin office ɗin ya dakata. "Get ready". Ya faɗi hakan a saitin kunnenta na dama. "Ni a shiryena nake". Da alama ranta a ɓace ta yi maganar. "Gaskiya beb ɗin ta kyakkyawa ce sosai Jannat? Ki shirya wanke idanunki da kyanta yau, dan nasan da wuya yau ki yi barci matuƙar kin ganta". "Wlh nama tsani ganinta, ni Yah Jawad na fasa ganin nata sakeni na koma office ɗinka". Tana kai karshen maganar tana ƙoƙarin juyawa har da ɗan ture shi. Da ɗan kasasa murya ya ce. "Ki nutsu!". Ba dan taso ba ta dakata tare da nutsuwa tsit. A hankali ya zame hannunsa daga saman idanun nata, cikin zumuɗi da son ganin wacece mummuna ce budurwar tasa ta waro idanunta. Subhanallah zaro ido ta yi, she was shocked and so surprised na ganin kanta kuma, hannu ta kai saman face ɗinta a fujaje ta fara murje idanunta dan ta tabbatarwa da kanta abin da take gani. Ganin da gaske fa ita ɗin ce yasa ta kai kallonta a kansa ta cikin mirror, cool murmushin da ya sakar mata ne yasa ta tabbatar da gaske ne. Tafukan hannayenta tasa ta rufe fuskar tata tana sakin cool murmushin da bata taɓa yin irinsa ba....... Ni kuwa nace Chuchu ban da cin amana, shi kuma Yah Rizwan ɗin ina zaki kaisa dan gidanku?. Hannunsa ya sanyo ta saman shoulders ɗinta, a hankali ya riƙo hannayenta dake saman fuskar ɗin tata, janyesu ya fara ƙoƙarin yi dan ya samu damar ganinta da kyau. Juyowa ta yi ta faɗa jikinsa tana dariyar da sautinsa yake fita a hankali hankali, wani irin kunyarsa ta ji ya kamata, kenan yanzu duk zagin budurwar nan tasa da ta rinƙa yi kanta ta zaga? Ta manta da zancen Yah Rizwan ta wani shige jikinsa. Rungumeta shi ma ya yi, cikin wata iriyar sigar soyayya dake fusgarsa ya fara zuba mata uban tulin kamalan da ya tarasu a cikin ransa na tsawon shekaru, yadda yake magana sai kaji kai ma ka kamu da kaunarsa. Cikin sanyin murya ga magana one by one ya fara faɗin............ Ba dai zasu ji me ya faɗa yau ba sai gobe🥱🤪🤣 su maman Yasmin, Mumcy, Sumy sarakan gulma da sauran my comments section grp in kunji babu daɗi ina gidanmu kuzo ku sameni🤣 ba za dai ku ji wasu irin kalamai zai kashe Jannat ɗinsa da su ba🥱 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/11/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 E33 Rungumeta shi ma ya yi, cikin wata iriyar sigar soyayya dake fusgarsa ya fara zuba mata uban tulin kamalan da ya tarasu a cikin ransa na tsawon shekaru, yadda yake magana sai kaji kai ma ka kamu da kaunarsa. Cikin sanyin murya ga magana one by one ya fara faɗin. "My Jannat i don't know how can i tell you the way i love you, your love has been in my heart for a long time, it melted and made me feel the lump inside my heart, no person in this world that can remove it, is something that will never be possible, unless i will die with it, your love has melted and mixed with the blood that circulates in my body, know that every beat of my breath is beating with your name, a kowace rana na kwanta ɗayan biyu ne, dole sai na yi mafarkinki ko kuma tunaninki ya hanani barci, zuciyata ta jima tana azalzata a kan lallai na isar da saƙonta a gareki, please tell me with your mouth, I want to hear the sound of your sweet voice when you say that you love me?". He asked the question full of fear of the answer she would give him, even though he knew that she will love him, but he found himself afraid of what would come out from her mouth in this moment. "Yah Jawad, I can't talk right now, leave it until after some hours, I can't tell you what kind of situation I'm in right now, just leave me alone". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. "Na ji zan barki, amma har sai kin furta mun abin da nake son ji, ko dai kina son in shiga tashin hankali ne?". Kai ta fara girgizawa alama a'a bata so. "Okey to ki gaya mun, kina sona?". A shagwaɓe ta ce. "Yah Jawad ni bana sonka, ina da wanda nakeso, sai dai ba shakka na ji daɗin sona da kake yi, kada ka damu idan na yi aure na haifi yaro namiji zan saka mashi sunanka, kaga kenan na baka cukuicin son da ka yi mun ko?". Ta kai karshen maganar with full confidence a voice ɗinta, yadda kuka san da gaske take yi. Ai a fujaje ya sauko da kansa a kanta yana ƙoƙarin raba jikinsu dan ya kalli face ɗinta da kyau. Ƙara ƙanƙameshi ta yi, taki bari ya raba jikin nasu, ta ƙara kwantar da kanta a saman kirjin nasa luff. Wani irin bugu da ta ji kirjinsa na yi da sauri sauri ne yasa ta yi hanzari ɗago da kanta ba dan ta so ba, a tsorace ta kai kallonta kan face ɗinsa. Wani irin razana ta yi na ganin a take har kalar idanunsa sun sauya, lallai da ita ce ta yi ta mashi irin wasa da hankali da ya rinƙa yi mata ɗazun na yana da budurwa ashe da zuciyarsa zata buga, haƙiƙa ta yarda ba karamin so yake yi mata ba. "Yah Jawad ka yi hakuri ka ji, ni idan ban soka ba waye kake tunanin ni Jannat zan so? Dole kai ne mana". A shagwaɓe sosai ta yi maganar, tana kai karshe kuma ta mayar da kanta saman chest ɗin nasa ta kwanta. Wani irin dogon haɗaɗɗen numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, ƙasa ƙasa tamkar zai yi kuka kamar kuma mai raɗa ya furta. "Kin gama yi mun komai my Jannat, ban san da me zan biyaki ba, tun bayan da na yi wayo nasan cewa a duniya bani da mahaifiya, tun daga lokacin farinciki kaso hamsin da biyar cikin ɗari na rayuwata babu shi, ina rayuwa ce bisa farincikin cewa ina son Allah da Manzonsa, bayan haka sai farincikin sanin cewa ga family na, amma a yau ina da farinciki kaso tamanin cikin ɗari saboda ke, i really love you...........". Shiru ya yi sakamakon hannunta da ta ɗaura a saman face ɗinsa tana laluɓar lips ɗinsa, so take yi ta ce ya yi shiru, kalamansa suna neman fasa mata kai, ruɗar da ita kam sun jima da yi. Ƙasa ƙasa da wata iriyar murya wadda za'a iya kiranta da raunatatcen murya ya furta sunanta. "Jannat". yau cikin wani irin tsantsar farincikin da yake ciki har wani kyalli face ɗinsa ta fara yi, baki ya yi kaɗan ha zayyana yadda yake ji a yau, kawai ga shi nan ne. Ita kanta baki ba zai iya zayyana abin da take ji a kansa ba, kamar yadda yake kaunarta ita ma haka Allah ya sanya mata matuƙar kaunarsa a ranta sosai. Shiru ya yi tamkar mai tunanin wani abin, kamar a mafarki ya ji sauƙar hawayenta mai ɗumin gaske a jikinsa, hakan ya ja ya yi hanzarin ɗago da haɓarta tare da ɗan raba jikinsu. "Subhanallah Jannat menene ya faru kike kuka a maimaikon farinciki kuma?". A ruɗe ya yi maganar, ta ɗaga hankalinsa ne sosai kukan nata. "Yah Jawad ni ma ban san meyasa nake hawayen ba, kawai zuba yake yi, ina matuƙar murna da farinciki, yau burina ya cika, ina sonka Yah Jawad, ina sonka sosai, ban ma san ya zan gaya maka ba, kawai ka barni na cigaba da yin kukana ko zan samu sassaucin abin da nake ji a raina". "No Jamnat, ba kuka zaki yi ba, addu'a zaki yi mana tare da godiya ga Allah kin ji?". Kai kawai ta gyaɗa mashi, handkerchief ya ciro, wanda ya goge mata hawaye a gida kafin su zo ne, da shi ya sake goge mata hawayen a yanzu ma. Komawa jikinsa ta yi ta kwanta shiru tana mai matuƙar farinciki sosai yau, da alama ta mance da cewa suna soyayya da Yah Rizwan. Shi kuwa Yah Rizwan bawan Allah kayan make up ya je saya mata a shopping, dan a ɗan zaman shi da ita ya fahimci akwai abubuwa da dama da take balai'n so wanda bai saya mata a cikin tsarabarta ba, dalilin zuwansa shopping kenan yau. Yana yi yana jin faɗuwar gaba, hankalinsa ya gaza kwanciya har sai da ya kira number Jawad ɗin, yana son ya ji ko yana lafiya, saboda idan baku manta ba dama yana zargin bashi da lafiya kafin ya fita daga office ɗin nasa, so sai ya ta'allaka faɗuwar gabar nasa da ɗan kanin nasa abin soyuwa a garesa............. Ni kam nace baka san amanarka suke ci ba, soyayya ɗan kanin naka yake zubawa da matar da kake burin aura, wlh wani tsiyar sai a RAWANIN ZALINCIN.....🤣 A lokacin da kiran ta shigo suna manne da juna yana ta zuba mata kalaman da suke sanya ta kuka sosai kamar ƙaramar yarinya, yana sake aikin goge mata hawayen kuma. Jin wayarsa tana ringin ne yasa ya ambaci sunanta a hankali. Ɗago kai ta yi tare da kai kallonta kansa. Wani irin sarƙafewa idanunsu suka yi cikin na juna, yau burinsa ya cika, wani irin kallo yake binta da shi mai wuyar fassaruwa, ji yake yi idan bai mayar da ita cikin cikinsa ba ba zai samu nutsuwa ba, yana yi mata wani irin soyayya wanda bai san iyakarta ba....... E lallai soyayyarku daga Allah ne mutanennan. Shigowar call na biyu ne yasa suka ɗan farga da kallon juna da suke yi, da sun macewa juna basa gane komai. Juyo da ita ya yi suna fuskantar mirror. Ƙasa ta yi da kai, sai yanzu ta ji ba zata iya haɗa idanu da shi ba. Ƙayatatcen murmushi ya sakar mata tare da ɗan rage tsawonsa ya sureta sai saman shoulder ɗinsa, luf ta kwanta tana wani irin jin daɗi na musamman. Wajen table ɗin suka koma, zama ya yi da ita a jikinsa, a saman cinyarsa ya ɗaurata, sannan ya ɗauko wayar tasa dake ta rurin neman agaji, Yah Rizwan ya gaza samun kwanciyar hankali shi ne yake ta kiransa. Dai'daita nutsuwarsa ya yi tare da gyara voice ɗinsa, sannan ya yi picking. Daga ta cikin wayar yana iya jiyo sautin wani irin ajiyar zuciya da ɗan uwan nasa ya sauke alamar ya ji matuƙar daɗin ɗaga call ɗin da ya yi. "Yah Rizwan lafiya kuwa?". Ya jefa mashi tambayar idanuwansa suna a kanta babu ko kyaftawa, ta wani yi ƙasa da kai kamar mai ɗaukar darasi gaban malami. "Lafiya lou, kawai kewarka na yi ne yasa na kiraka, hope kana normal cikin amincin Allah?". "Da izinin Allahn ina cikin amincinsa kuma ina cikin ƙoshin lafiya fatan ɗan uwana ma hakan ne?". Yadda ya yi maganar zaku fahimci ba shakka suna masifar kaunar juna. "Da izinin Allah nima ina nan cikin ƙoshin lafiya, ka kula mun da kanka ka ji?". Gyaɗa kai ya yi tamkar yana a gabansa, sannan ya ce. "In Sha Allah ɗan uwana, kai ma ka kula mana da kanka, muna kaunarka sosai, kana da mahimmanci over a cikin rayuwarmu". Murmushin kawai ya saki. "Sai mun haɗu a gida ko?". Okey ya amsa da shi tare da ciro wayar daga kunnensa. Kit Rizwan ya katse kiran tare da dakatawa da zaɓar kayan da yake aikin yi, tunani ya fara yi a kan to wai meyake faruwa ne yake jin irin wannan faɗuwar gaba? Shi dai yasan a kan Jawad ɗin kawai yake fuskantar irin wannan faɗuwar gaba, amma ya aka yi yau Jawad yana cikin amincin Allah da ƙoshin lafiya amma still yake jin faɗuwar gabar nan?. Abin ya bashi mamaki matuka, sai kuma ya fara tunanin bai taɓa jin voice ɗin ɗan uwan nan nasa cikin tsantsan farinciki haka ba, amma bai kawo komai a ransa ba, ya cigaba da ɗaukar kayayyakin da yake da buƙata, sai dai kuma ya zama wani sukuku da shi saboda rashin samun kuzari da kwanciyar hankali, wannan faɗuwar gabar ta haifar mashi da kasala sosai. Kada ku manta dama tun zuwansa office ɗin yake zargin Jawad ɗin, sheiɗan kuma da shegen son haɗa bomb sai ya ƙara ingiza zuciyarsa!. Shi kam Yah Jawad cigaba da zibewa juna madarar kalaman soyayya suka rinƙa yi, tamkar zasu cinye juna da hira. Sai around karfe 11 Momma ta kirasa a waya dan ya tambayesa ina Jannat?. Dan tasan shi ne wanda ta gani last a tare da Jannat ɗin, wato da safe kenan, kunga a tare ta barosu a kofar room ɗin. Yana picking ta fara faɗin. "Meyasa ka fita da Jannat?". "Sorry our Momma". "Sorry for what? Kadai san idan daddynku ya ji labari ba zai ji daɗin hakan ba ko?". Sake ce mata sorryn nan dai ya yi. Shiru ta ɗa yi kafin ta ce to su dawo da wuri ba sai sun kai lokacin da yake dawowa ba, dan kada kowa ya farga cewa Chuchun bata gidan. Da okey ya amsa mata. Amma sai misalin karfe 8 na dare suka koma, ya biyewa Chuchun suka zauna sai hira suke yi manne da juna, bai fargaba sai gani ya yi karfe 8 ta yi, ko sallar mangariba ba su yi ba, hankalinsa ya tashi sosai, tunanin yadda zasu kwashe da Momma ya fara yi, a ransa ya ce ai ina yau ba zai je part ɗinta ba. Ko da suka komo gida har angama walimar jama'a sun watse, an sha kyaututtuka na girma kam ba'a magana. Part ɗinsa ya wuce da sauri dan kada ma Momma ta kama shi, ita kuma Chuchun part ɗin Momma ta wuce. Tun da yamma mummynta take nemanta, ta ɗaga hankalinta sosai har sai da Momma ta ce ai ta aikesu ita da Jawad, sannan ne ta samu natsuwa. Da yake da Momma ta saba tana dawowa bata nemi kowa ba ta wuce wajen Auta dan ta faɗa mata yau Yah Jawad ya ce yana sonta, kun san dai ita da Auta hanta ne da jini, ba'a rabasu. Ko da Momma ta ganta bata ce mata ko uppan ba, dama dai saboda tsaro ne yasa take yawan yi masu magana. Wanka ta tsara tare da tsala kwalliya, ɗakin Auta ta nufa domin su ga juna daga nan su je wajen mummynta. Kwance ta iskota tana latsa waya, da alama tana cikin farinciki sosai, dan sai sakin murmushi take yi wanda yake ƙara mata kyau sosai, dimples ɗinta suna lotsawa, duk yadda aka yi chatting take yi da wanda yake sanyata farinciki. Hayewa saman gadon ta yi tana kaiwa Autar duka a baya. A fujaje ta ɗan ɗago kai, ganin ita ce yasa ta ɗan turo baki. "Kai Aunty Chuchu sai yanzu Yah Jawad ɗin ya dawo mun dake?". "Ke duk ba wannan ba, zo ki rakani wajen mummy idan mun dawo sai na baki labarin abin da ya faru yau". "A'a Aunty Chuchu ni babu in da zanje, ki je kawai, yanzu ma ni wajen uncle Jahiz zan je, ya ce idan na yi sallar mangariba na zo, kin ga kuma lokacin sallah saura ƴan mintocin da basu fi 15 ba". Ta kai karshen maganar tana miƙewa zaune. "To shikenan jeki, ni ma dai zan je duba uncle Abbas, dan bamu gaisa ba yau, idan mun yi sallar isha'i mu haɗu a part ɗin Akka". Da okey ta amsa mata, a tare suka fito waje, ita ta nufi part ɗin mummynta, Auta kuma ta nufi part ɗin uncle Jahiz kamar yadda ta faɗa, sai dai kuma ba can ɗin ta je ba, hanyar baya na sirri ta je dubawa, hanya take nema ta yadda zata fita da daddare idan kafa ta ɗauke, ko ina zata je?. After some hours. Bayan sun yi sallah sun ci abinci, kowa ya wuce part ɗinsa. Room nata da yake part ɗin Akka ta nufa, dan ta ce su haɗu da Auta a wajen. Wayarta ta ɗauko suka fara chatting da Yah Rizwan ɗin da bata san matsayinsa a gareta ba yanzu, tabbas bata dai'na jin sonsa a ranta har yanzu.... E akwai cakwakiya kam. Ita kuwa Aura fitowa ta yi daga nata room ɗin, kayan barci wando da riga launin pink ce a jikinta, kayan sun yi mata kyau, ta sanya hular barci a kanta. Kamar wata maras gaskiya haka ta wuce ta fara sanɗo, tana yi tana juyowa. Karaf suka ci karo da uncle Taheer da ya fito daga wajen King zai koma part ɗinsa. Wani irin zabura ta yi, a take ta yi ƙasa da kai, rashin gaskiya ce zalla ta bayyana a tattare da ita. "Baby ina zaki je kike tafiya haka kina waige waige kamar maras gaskiya?". Ya yi magana yana bin bayanta da kallo ko zai ga mai biyota da yasa take irin wannan waige waigen. Babu kowa da yake zuwa. Murya na sarƙafewa ta ce. "Wajen dad zan je". Ɗan zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda ta yi wa kayan barcin nata kyau matuƙa. "Uncle Taheer in tafi?". Ya shagala da kallonta ne muryarta ya daki dodan kunnensa. Kai kawai ya gyaɗa mata alamar e. A hanzarce ta wuce har kamar zata kifa ƙasa saboda sauri. Da kallo ya bita, sai faman waigowa take yi, duk in ta waigo sai su haɗa idanu, dan yana tsaye yana kallonta, dan dole ta shiga part ɗin dad ba dan nan zata je ba, sai dan bata da zaɓi yana tsaye yana kallonta. Laɓewa ta yi a bakin kofar ta ciki tana leƙarsa har sai da taga tafiyarsa, sannan ta fito da sauri ta nufi kofar bayan. Ko tsoro bata ji, ga shi dare ne, bata ji tsoron ko wani zai iya biyo bayanta ba. Kai tsaye wani sassa tangameme mai girman gaske a cikin gidan ta nufa, tana tafiya tana ƴan waige waige, duk in ta ga wani daga cikin mayaƙa zai gifta sai ta laɓe a wani wajen har sai ya wuce, sannan ta fito ta cigaba da tafiya. Bata kai ga shiga cikin part ɗin ba, tana a tsakiya tsakanin part ɗin uncle Abbas da in da zata je ɗin, dai'dai wajen wasu flowers masu kyau da aka shuga, wajen akwai ɗan duhu duhu sakamakon bishiyoyin mangoro guda uku dake jere a wajen. Tana ta zuba uban sauri kwatsam ta ji an toshe mata baki ta baya an kuma jata an nufi wata hanya ta daban da ita. Ga shi an rufe mata baki ba halin yin ihu.......,. To fa wanenen da wannan aiki kuma? Sannan ita Auta me ya kaita fitowa waje da middle night ɗin nan? Ina zata je?. _____________________________🔥💘🕊️ Chuchu kuwa, hira ta biyewa Yah Rizwan suna yi, daga karshe ma sai ya kirata suka cigaba da zuba soyayya, ya ce yana son ganinta dan yau gabaɗaya bai ganta ba, shi ma dai bai zauna ba, amma idan ba damuwa zasu iya haɗuwa yanzu. Ɗan juya idanu ta yi da nufin ta bashi amsa, kwatsam idanun nata suka sauƙa a kansa. Yana tsaye a bakin kofar shigowa ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa. Kayan barci ne a jikinsa shi ma, ya yi ta kiran layinta ne yana nuna mashi busy shiyasa ya tako da kafafunsa ya zo ya ganta, ya je room nata a part ɗin momma bata nan, yasan tabbas tana nan, shi ne ya zo. A fujaje ta cire wayar daga kunnenta tare da miƙewa zaune, sai a lokacin kuma ta tuna ashe shi take so ba Yah Rizwan ba. A gaskiya wautar Chuchu na dayawa wlh, kuruci dangin hauka. Shi dai bai ce mata ko uppan ba ya tsareta da idanun, nan take ta tsargu ta kuma shiga ruɗu, ƴan kame kame ta fara yi kamar zata yi kuka. My people's me kuke tunani? Shin Jawad ya ji hiran da take yi da Rizwan ko bai ji ba? Idan ya ji me zai faru? Tun wani lokaci yake tsaye a bakin kofar tata? Shin da gaske Jawad ɗin take so ko Rizwan?. Akwai badaƙala a cikin kingdom ɗin nan, ni dai bari na leƙa Black Tiger kafin na dawo wata kila Jawad zai iya ƙarisawa ciki mu ji da me ya zo?. ______________________________🔥🌹 BLACK WORLD🔥😥💔 Wasu irin jiga jigan jirage waɗan da suka amsa sunansu jirage ne suke shawagi a sararin samaniyarsu, jirage ne masu kirar Mirage 2000, A400M Atlas, suna da matuƙar girma fiye da tunaninku. Kowani jirgi kansa na tambarin bakar damisa ce, sannan a jelarsu ma akwai tambarin black tiger, sun kai su 20 a sararin samaniyar suna shawagi, ba jiragen ko'ina bane face na Black Tiger, mallakin black tiger ne dukkansu, idan baku manta ba na gaya mu shi fa kowace ci gaba yana kawowa birninsa, baya wasa, dan burinsa ya zama number ɗaya a duniya, dan haka ya mallakawa birnin tasa jirage dayawa wanda suma zasu goga da kowace ƙasa, maƙudan dukiya yasa ya sayi jiragen, in dai dukiya ce Allah ya mallakawa Black Tiger, yana amfani da ita ta hanya mai kyau kuma, matsalarsa ɗaya shi ne wannan burin nasa na son ya mallaki duniya, wannan ita ta riƙiɗar da shi izuwa baƙin azzalumi, yana nemanta ne a fujajan, hakan yasa yake taka kowace irin doka. So a takaice dai gabaɗaya jiragensa ne, bayansu ma yana da wasu, ita kanta dukiya idan ta gansa sai ta durƙusa mashi. Kai tsaye katafaren airport ɗinsu suka nufa, shi kansa airport ɗin sunan Black Tiger ne a manne a jikinsa, sannan ko'ina jikin bango akwai zanen bakar damisa, hakan zai kara tabbatar maku da karfin ikon da yake ji da shi. Abin da waɗan nan jirage suka ɗauko zai baku mamaki sosai, ba komai bane face robbot da ya saya daga ƙasar China, duk dan shirin yakar duniya. Robbot guda 500 daidai ya sawo abinsa, kada kuso ku ji maƙudan kuɗaɗen da yake zubawa wajen sayan Robbot ɗin nan, billions of dollars ake maku magana, amma haka yake zube kuɗin ya sayesu, kuma ko jijjiga bai yi, da yake kullum suna kan haƙar ɗanyar gold, ga kuma ɗanyar mai da sauransu. Master Devil ne ya jagoranci zuwa sayan waɗan nan Robbot ɗin, ya tabbatar da ingancinsu, haka shi ya jagorancesu izuwa cikin Black Tiger empire. Gabaɗaya Robbot ɗin kuma mazane, an zuba masu kirar karfi kamar samudawa, ga su da tsawo, sai sun baka tsoro idan ka gansu, da alama Black Tiger ya gama shirinsa na fita yaki Spender kawai ta dakatar da shi. After some minutes. Kwance yake a saman katafaren bed ɗinsa, ya yi shirun yana fuskantar celling, da alama wani tunanin yake yi, pajama ce milk color a jikinsa, da ganin face ɗin nan nasa zaka fahimci yana cikin damuwa sosai, tun jiya da ya rufe kansa a ɗaki yaki buɗewa, da yunwa ya kwana, ba yadda Floris bata yi ba a kan ya buɗe kofa amma yaki, ta buga har ta gaji, yaki kulata, kuma yana jinta, daga karshe ita ma a bakin kofar tasa zaune ta kwana, dan bai taɓa yi mata irin hakan ba, yau ne farko kuma ta kasa jurar hakan. Ta saba kafin su yi barci sai sun sha hira, wani lokaci sai su kai karfe 2 na dare suna hira, kuma shi yake rakata room nata, ya yi mata abin da ya saba wato sumbata, sannan ya rufa mata barko tare da kashe mata wutar ɗakin kafin ya wuce nasa ɗakin, amma yau shiru, ko abinci ta gagara ci, dan shi ma bai ci ba, Allah sarki sabo fa wani lokaci bashi da daɗi, dan idan anzo rabuwa ko wani abin ya faru akwai wahalar iya jurewa, to ita dai Floris ta gaza jurewa, babban matsalar ma shi ne bata san me yake damunsa ba. Yana jin sai kiran wayarsa ake yi amma ko kallon wayar yaki yi, kansa ce take ɗan sara mashi kaɗan kaɗan saboda yunwa, yau yana da buga wasa, amma ya sanya a ransa ba zai je ba, dan ya yi alkawarin matsawar yayan nan nasa bai dawo mashi da Sweetie ba sai dai ya mutu a cikin wannan ɗakin, sai dai kuma yana son ya fita ya je ya samu master Devil. Yau sai ya ji dalilin da yasa master zai shiga rayuwarsa, a kan me zai wani cewa yayansa ai shi ya gaya mashi yana son Sweetie? Duk dan mugunta, dan yana son a rabasu, da yake shi kansa Black Tiger yana zargin hakan, saboda yana ganinsu, yana ganin dik abin da suke yi, hakan yasa ya fara zargin cewa akwai wata a tsakaninsu, shi kuwa master ya tabbatar mashi da hakan, har da karyar cewa wai Ronnie ne ya gaya mashi yana sonta, gaskiya master bakin mugu ne, ya iya shirya kutunguila. Daga karshe da kiran wayar ma ta dame shi sai ya ɗauketa ya makata da jikin banko yana huci kamar wani tiger. Watsa watsa wayar ta tarwatse. Yana maka wayar da bango ya yi dai'dai da fara cirewar password ɗin door room ɗin nasa. Abin mamaki ga waɗan da basu san Dark world ba, amma shi a wajensa hakan ba komai bane, dan yasan yayan nasa ba abin da ba zai iya ba, password na kofarsa dai shi kaɗai yasan kayansa, ko Floris bata sani ba. Yana ji aka buɗe password ɗin ɗakin nasa. Wata iriyar iska mai karfin gaske ce ta banko kofar ta shigo, duk yana ji ɗan tahaliƙin nan ko motsawa bai yi ba. Komai da kuka sani na cikin wannan haɗaɗɗen luxurious bedroom ɗin nasa sai da wannan iska ta kifar da shi saboda karfinta, yadda kuka san wani walkiya haka iskan ta shigo. Wani irin haske na ban mamaki ne ya bayyana a cikin wannan iska mai kama da guguwar, gabaɗaya glasses na cikin ɗakin sai da suka tarwatse, show glass dake kusa da bed ɗin mai shake da Bibles kala kala ma haka ta jijjigo ta faɗi ƙasa, gabaɗaya glass ɗin ya tarwatse ya Bibles suka fara watse ƙasa. Dressing mirrorsa ma ya tarwatse watsa watsa, chandelier ɗakin ma jijjigowa ya yi da karfi ya yo ƙasa zai faɗi, in kuma ya faɗo to fa a tsakiyar cikin Ronnien ɗin zai faɗi, in kuma ya faɗi a kansa to fa da wuya ya rayu, dan chandelier tana da girma sosai. Aikuwa yana kwance yana fuskantar sama, dan haka yana ganin yadda chandelier nan ta jijjigo ta yo kansa, amma ina ko motsawa bai yi ba, tamkar babu shi a ɗakin. My people's wani irin iska ce wannan? Su ba'a cikin daji suke na! Sannan ba lokacin iska ba! Anya lafiya kuwa? . Amin afuwa yau bana jin daɗi ne, zazzaɓi da ciwon kai, amma duk da haka nace bari na ƙokarta kada na barku a cikin kewa, shiyasa kuka ga short page, da babu gara ba daɗi, sai mun haɗu on Monday In Sha Allah, idan kun ban hot comments na yi maku weekend. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 4/11/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 34 Aikuwa yana kwance yana fuskantar sama, dan haka yana ganin yadda chandelier nan ta jijjigo ta yo kansa a dubu, amma ina ko motsawa bai yi ba, tamkar babu shi a cikin ɗakin. A fujaje chandelier tayo kansa, ko datse idanu irin tsoron nan bai yi ba, idanunsa kar a kanta, yadda kuka san wanda ya yi suman kwance. Dai'dai saitin daf zata sauka a cikin nasa ne sai kuma ta tsaya cak tamkar wadda aka riƙe, babu kuma wanda ya riƙeta. Ɗan Lumshe idanu ya yi tare da sake warosu, a hankali ya miƙe zaune yana fuskantar wannan haske da yake ƙoƙarin riƙiɗewa alamar halittar ɗan adam yana bayyana a cikinsa. Abin gwanin ban mamaki da ban tsoro, haka ya zuba idanu yana kallo daga wannan haske har ya riƙiɗe ya zama complete halittar ɗan Adam. Babban mutum ne sosai ya bayyana, sai dai yana da karfi da kwarin jiki sosai, baka iya ganin face ɗinsa bare ka iya tantance wanenen?. Ya fito cikin wata iriyar dressing wanda kai daga gani kasan dukiya tana cin ƙaniyarta a wannan Daula. Hannunsa na riƙe da irin sandar nan na sarauta mai tambarin kan bakar damusa ta wage baki, ga garma garman hakwara tamkar zata cinye ni. Takalmar dake kafafunsa sun kasance covers ne masu bala'in kyalli kashe ganin idanu, na zallar madarar gold ce, doguwar alkyabbar jikinsa ta sauka har tana ja a ƙasa ta rufe takalmar tasa, kansa na sanye da hular alkyabbar tasa, from up to down ɗinsa komai na jikinsa fararene ƙal except takalmarsa da suka kasance gold, ya rufe komai na jikinsa, ko kalar fatarsa ba zaka iya ganewa ba. Baka iya ganin face ɗinsa sakamakon wannan haske da ta fara bayyana a farko ta tattaru ta koma saitin face ɗin nasa ta rufeta, hakan ya hana damar ganinsa. Abin dai ba'a magana. Wace iriyar haske ce mai karfin kashe idanun gani ta bayyana a bayansa, idanun bawa ba zai iya kurawa wannan haske idanu ba, sai kashe mashi karfin gani da kwarin idanun. A hankali hasken ya fara riƙiɗewa yana komawa golden color. Babu ko alamar mamaki da al'ajabin abin a face ɗin Ronnien, da alama ya saba da ganin fin hakan ma, hankalinsa a kwance, shi sai yunwar dake damunsa ne ma take murɗa mashi ciki. A hankali wannan farin haske ta riƙiɗe ta koma wani irin dandatsetsen katafaren the most powerful seat of king in the world da ba'a taɓa yin irinsa a duniya ba, kujerace wadda aka ƙawata ta musamman, gabaɗayanta da zallar madarar gold aka yita, sannan gabaɗaya jikinta an yi mata kwalliya ne da wasu irin wuƙaƙe masu bala'in kaifi ta bayanta kenan ba ta wajen zama ba, ta jikinta kenan, wuƙaƙen ma na zallar madarar gold ne, kujerar tana da tsawon kai sosai, koda an zauna a kanta, duk tsawon mutum kansa ba zata yi dai'dai da kanta ba, sai dai ya lume a cikinta, daga can karshen kayinta kuwa an yi shi ne design of black tiger, shegen damisa mai haɗarin gaske kenan, yafi jar damisa haɗari, shi yana iya kashe zaki har lahira idan ya fusata. Design ɗin damisan ya fita sosai, a takaice dai kujerar nan ya wuce tunaninku a ƙawatuwa, ga wasu duwasun zinari masu haske tas dake manne a jikinsa ta ko'ina, abin dai sai wanda ya gani, bana jin a duniya ma akwai kuɗin da zai iya sayan wannan gold kujerar. Tana da girmar two seater wajen zama, kyallinta sai ɗaukar idanu yake yi. Cikin wata iriyar ƙasaita ya zauna a samanta, duk tsawon kan da kujerar take da shi sai da kansa ya kusa kai tsawonta da ya zauna, saboda tsawonsa dogo ne sosai, duk da yake babban mutum yana da wani irin jiki tamkar wani tsohon ɗan Wrestling ɗin da ya shafe tsawon shekaru ana gwabzawa da shi a fili, a murɗe yake sosai. Yana zama ya ɗaga wannan scepter king ɗin nasa ya fara nunnuna dukkan wasu kayan da suke cikin room ɗin. Abin al'ajabi baya ƙarewa a duniya matuƙar kana raye, gabaɗaya kayan da suka fashe a ɗakin ne suka fara komawa da kansu yadda suke. Duk abin da ya nuna da wannan scepter king ɗin nasa sai ta koma yadda take kamar bata taɓa tarwatsewa ba, gabaɗaya glasses ɗin sun koma, Bibles da suka zube a ƙasa duk sun koma cikin glass ɗin da kansu, a hankali chandelier ma ta bar saitin kan Ronnien ta koma sama mazauninta. Wani irin fitinannen kamshi mai kwantar da hankalin mai shaƙa da ban taɓa jin daɗin kamshi irinsa bane ya gauraye gabaɗaya ɗakin, sai wani irin iska from nowhere mai daɗin gaske ne ya fara kaɗawa a hankali hankali, kofofi da winduna fa a rufe, sai Allah kaɗai yasan daga ina Black Tiger ya ƙaƙalo wannan daddaɗar iska dake ƙaɗawa gwanin birgewa da sanya zuƙata nishaɗi musamman ga masoya, sai dai kash su dai yaya ne da kaninsa ba masoya ba!. Har lokacin idanun Ronnie yana a kansa babu ko kyaftawa, duk kaifin ganin wani idanu ba zai iya ganin cikin wannan haske ba, amma shi Ronnie ya sanya kwayar nasa a ciki ba tare da ya ji komai ba, da alama dai kaifin ganinsa daban yake da sauran mutane, ga shi babu alamar tsoro a cikinsu ko ɗigo. Aka ce kowa a duniyar nan in ma mutun ko aljani yana da weakness ɗinsa, dole akwai in da ake gazawa, babu wanda yake dai'dai sai Allah, to hakance, shi ma Black Tiger dai Ronnie ne weakness ɗinsa a duniya, ya ƙasa jurar halin da Ronnie ɗin ya shiga ne yasa ya taso da kansa ya zo in da yake. Tun da yake a rayuwarsa a empeir ɗin nan bai taɓa fitowa daga wannan room ɗin nasa ba sai yau, kuma duk a dalilin Ronnie ya fito, to why Ronnien ya samu wannan matsayi haka? Kome alaƙarsu? Meyasa duk wannan zafin nasa, zalincinsa! Muguntarsa! Karfin ikonsa! Ronnie ya zama shi ne rauninsa? Me dalili? Komai dai dole yana da dalili! Dan haka suma dai akwai dalili. Kuma shi Black Tiger tabbas bashi da ƴan uwa kamar yadda yan cikin birnin suke faɗa, hakance, Ronnie ba ɗan uwansa bane, shi shiƙaɗai yake tun bayan ɓacewar mahaifinsa a doron duniya, a idanun mutane mahaifinsa ɓacewa ya yi, a idanunsa kuma mutuwa baban nasa ya yi, abin da yasa mutane suke cewa ɓacewa babansa ya yi ba mutuwa ba shi ne, ranar da baban ya mutu, insect of a sanya shi a akwati a kaisa kabarinsa sai suka ga gawar ta ɓace ɓat daga saman gado mulki da yake kwance. Ranar Black World sunga tashin hankalin da basu taɓa zatan zasu gani ba!!. Sai dai kuma tun ranar da ya bar duniya ya bar cikin kwakwalen mutanen birnin, tamkar an shafe masu saninsa, shiyasa suke cewa basu taɓa ganin wani ɗan uwan Black Tiger ɗin ba a duniya!. A lokacin da baban nasa yake raye shi ne yake zaune a kujerar da Black Tiger ɗin ya zauna a yau, shi baya ɓoye kansa, kowa ya san shi a birnin, sai dai kuma shi yake ɓoye Black Tiger tun yana ƙarami hakan yasa ya taso a mai ɓoye kansa, shi kaɗai yasan dalilinsa na yin haka. My people's izuwa yanzu me kuka fara tunani a kan wannan Daula ta Black Tiger? Alamu dai sun nuna mutanen birnin suna da gaskiya na cewa Black Tiger ba mutum bane kenan?. Ƙaɗan daga cikin labarinsa kenan, shi ya ƙirƙiro birnin Dark world, bayan ya gama ƙawatata ne ya ɗauko dattijon mahaifinsa wanda a lokacin bai wani tsufa ba, to daman tun kafin zuwan Black Tiger kirkirar Dark world mahaifin nasa yana ɓoyesa, shi ya kasance ɓoyayye ne, a cewar baban nasa shi ɗan baiwa ne na musamman wanda abin bautarsu ya sa mashi albarka, kun ji dalilin fara ɓuyarsa har lokacin da ya ƙara girma sosai, babansa ya mulki Dark world cikin zalunci da azabtar da bayin Allah, ga tsafin bala'i, kome suke yi a tafin hannunsa suke na tsawon shekaru, ya ɓata tsawon shekarunsa kuma a kan neman Spender dan yunwar mulki da suke da shi!! Haka ya mulki mutane yana azabtar dasu a kan Spender kafin tsufa ya cin masa, Black Tiger ya karɓesa, shi ma cikin zalunci ya cigaba da gudanar da mulkinsa yana neman Spender kamar hauka dan ya cika burin mahaifinsa, yanzu ita kaɗaice a gabansa, kunga kuwa ai dole ya ɗaga hankali yana nemanta, ace warsa dan ruhin babansa ya samu salama dole ya nemota ya cika mashi burinsa!. Tun da ya mutu kuma babu wani mahaluki da ya yi gigin zama a wannan kujerar tasa sai yau da Black Tiger ɗin ya fito da ita ya zauna, wannan shi ne kaɗan daga labarinsa, saura bayanai zasu biyo daga baya. To wanenen Ronnien? Ina iyayensa? Ya aka yi suka haɗu da Black Tiger da ya kasance ɓoyayyen mutum tun tale tale? Akwai dai badaƙala a gaba, ku shirya!!. STORY🔥🕊️ Cikin wani irin yare Ronnien ya fara yi mashi magana kamar haka. "Hyeongnim hwan yeonghaeyo, dangsin- i anjeon hagil balabnida nae hyeong". (To ni dai ba abin da na iya ganewa a wanann yare nasu face nae hyeong wato ɗan uwana kenan, my people's ina kuke masu jin yaren Koreans? Maza ku zo ku fassara mana me suke faɗe? Dan ni ina son jin abin da suke faɗa gaskiya kada a barni a baya.😥🥱 Su maman Yasmin ku zo ku fassara mana, ina mumcy, Sumy kin dai san Ronnien naki ne, maza zo ki fassara mana wannan yaren Korean nasu, zo ki gaya mana me suke cewa, dan nasan bani kaɗai ba har da my people's ma suna son jin wannan tattaunawa na tsakanin babban yaya da kaninsa, kada su je su sayar mana da Sweetienmu da wannan yaren nasu ba tare da mun sani ba, gara a fassara mana.🤣😂 Ko da yake maganar sirri ce tsakaninsu🥱🕊️) Sun yi magana mai ɗan tsawo ko kuma in ce Ronnie ya yi magana mai ɗan tsawo wannan dakakken namijin yana zaune, kamar wani jarumin bujumin mayaki, ga shi dai da alamar dattaku wato manyanta a tattare da shi, ba yaro bane, amma yadda kuka san wani dakakken namiji ɗan shekaru 23 zuwa da 25, ga shi da kirar ƴan Wrestling, kai abin dai sai wanda ya gani. Yana zaune kamar gunki bai furta kalma ba!. Sun tattauna sosai a in da daga karshe Ronnien ya ce. "naneun geunyeoleul nae hyeongjeleul salanghaji anhgo danji geunyeoleul dongjeonghago ma-eum sog-eulo geunyeoga nae dongsaengcheoleom neukkyeojibnida. naleul geunyeowa hamkke namgyeodueoseo eolmana mianhanji" Wato da Hausa cewa ya yi. Bana sonta dan uwana, kawai ina tausaya mata ne, kuma a cikin zuciyata nake ji kamar kanwata ce. Yaya ka yi hakuri ka barmu a tare da ita. Shi ne maganar da ya faɗa ta ƙarshe, daga haka wannan mutumi ya rikiɗe ya koma haskensa kamar yadda ya shigo tun farko, waje ya nufa ba tare da ya sake yin yunkurin wani abin ba. Yana fita ita ma kujerar da ya zauna a kanta ta ɓace ɓat!. Kifa kai a saman mattress ɗinsa ya yi tare da sanya hannu ya fara dukan jikin mattress ɗin kamar wanda bashi da cikakken hankali. Da karfi ya furta. "Why nae hyeong?". Wato meyasa ɗan uwana?. Wato dai Black Tiger yaki sauraronsa a kan batun Sweetie, ya ce mashi ya mance da ita a rayuwarsa tamkar bai taɓa saninta ba, domin kuwa in dai bata basu Spender ba babu abin zai hanashi kasheta already ya rigada ya da san haka, so ya daina wahalar da kansa a banza, dan yasan dai shi bai taɓa ƙudurta yin abu kuma ya janye ba, so ya kiyaye!. A can waje kuwa, bayan Master Devil ya isar da waɗan nan Robbot ɗin wajen da ya dace da su, sai ya koma bakin aikinsa, ba ko'ina bane bakin aikin nasa ba face azabtar da ƴaƴan mutane, to mu je dai mu gani me ake ciki. TRAINING HALL💔😥 Shi ne sunan da aka rubuta a jikin katafaren gate ɗin shiga wajen, duk a cikin empeir ɗin yake, yana ta kusa da wajen buga basket ball ɗin su Ronnie. Katafaren waje ne yadda kuka san stadium na kwallon, duk wasu kayan training na ƴan Wrestling da mayaƙa akwaisu a wajen. Yadda kuka san kung fu place, haka wajen yake, yara ne birjik a wajen, matasa ne masu ji da rai da lafiya waɗan da daga 20 years ya yi sama side ɗinsu daban, akwai masu daga 30 years up, daga masu shekaru 40 suka tsaya, Black Tiger baya sanya waɗan da suka haura 40 a sahun warriors ɗinsa, daga 40 ya yi ƙasa yake shiryawa a cikin dakarun yakinsa. Duk wanda ka ɗaga idanun ka gani a wajen sai ka razana, master ya iya bada horo, sun horu kam ba karya. Sun cika zakarun mayaƙa Daga wani waje mai girman gaske, sannan wajen yana keɓene, yara ne ƙanana a wajen wanda a kallah zasu kai su 100, dukkansu babu wanda ya haura 10, sai dai kuma babu wanda yake da ƙasa da 5 years. Mafiya yawa daga cikinsu idan kaga fuskokinsu sai ka zubdar masu kwallah, dan dayawansu busassun hawaye ne a kan fuskokinsu, idanu sun yi jajir, wasu ma idanun sun kumbura saboda kuka. Bayin Allah basu saba ba, dama idan baku manta ba shi Black Tiger idan kika haifo ɗa namiji a cikin birnin ko wani shayar da shi ba za'a bari ki yi ba za'a karɓesa. Allah sarki su yara ba wani samun nonon uwa suke yi ba, ga bakar horo tun suna ƴan shekaru uku a duniya ake fara lallankwashe masu ƙasusuwar jiki kamar wasu ƴaƴan Chinawa, tun suna ihun neman taimako har su haƙura su fawwalawa Allah komai, har su zo su saba, suna tasowa suna tashi da wannan horo a jikinsu, da zarar sun kai 15 years fa to wlh duk ranar da basu yi training ɗin bama basa jin daɗi, duk sai su ji duniyar babu daɗi. Haka zasu taso babu tausayin uwa bare na uba, ko iyayensu sun zo ganinsu basa jin kamar iyayensu ne ma, saboda basu saba da su ba, master shi ne zai zama kamar iyayensu, sai sun fi tausayinsa fiye da yadda zasu ji na iyayensu, wani ma idan horon ta ratsa shi wlh da za'a bashi izini ya yi wa iyayensa wani abin tsab zai yi masu, gara ma iyayensu mata, ko yaya suna jin iyayensu mata a ransu ba kamar maza ba, uwa ko bata shayar ba ta wuce wasa, ita soyayyarta a jini yake, abin ya wuci tunaninku. Haka dai suke tasowa, wani ko ance mashi ga mamarsa ta zo ganinsa kai tsaye zaku ji ya ce bashi da lokaci yana training ko yana yin wani abin makamancin haka. Wannan shi ne babban cuta kuma babban tabo da ya yi wa mutanen birnin da bazasu taɓa mancewa da shi ba a rayuwarsu, ya cuta masu matuƙa, raba uwa da ɗa wlh ba wasa ba, zunubinsa daban ne, kina ji kina gani ki haifi yaron, kuma kuna waje guda da shi amma baki da iko da shi, sai dai ya bi tsarin wani, ko ganinsa zaki yi sai da izini, wani lokaci ma ace ki tafi yana aiki ki dawo anjuma ko gobe, abin da matuƙar takaici na wuce misali ga ban tausayi da taɓa zuciya!. Abin dai babu daɗi sam, Black Tiger ya kai azzalumi ta wannan ɓangaren kam, ba karya yana cutar da iyaye da dama, wani irin fargaba da balai'n tsoro mutanen birnin suke yi na su haifo ɗa namiji. Kai har ta kai ta kawo idan mace ta fahimci tana da ciki, tun daga ranar da ta san da cikin tana cikin tashin hankali da fargaba ga azababben tsoro, kullum haka zata kasance cikin addu'ar Allah yasa mace zata haifa ba namiji ba, ba wai dan basa son ƴaƴa maza ba, dan dole yasa suka tsanesu, dolen dole aka cusa masu tsanar maza, dan dole suka koyi addu'ar idan ɗa namiji ne a cikin cikin nasu to gara cikin ya zube kafin su haifesa, ko kuma idan sun haifo najimi ya mutu a lokacin da ya faɗo duniya!. Kun san uwa da ɗa, da a rabata da shi a turasa yaki gara mata ya mutu ko kuma cikin ya zube tun ba'a je ko ina ba. Sai dai kuma kash gabaɗaya mutanen birnin sun fi haifar ƴaƴa maza a kan mata, sai ku tarar mace ɗaya zata haifo maza 8 mace 1, idan ya yi yawa ne ma mata 2, haka suke, sun fi haifar maza, shiyasa Black Tiger yake alfahari da su, yake kuma da tarin gayyar warriors and ƴan Wrestling masu ɗebe masa kewa su sanya shi nishaɗi. Wato shi Black Tiger ayi Wrestling a kashe wanda ya faɗi a zubar da jini shi ne yake sanyashi nishaɗi, gaskiya yacika azzalumi, da gaske RAWANIN ZALINCIN ce a kansa. (Zan so ganin wanda zai cire wannan RAWANIN ZALINCIN gaskiya akwai badaƙala ba kaɗan ba.😥💔) Wani irin katafaren ruwa ne mai matuƙar zurfi a farfajiyar wajen horon nasu, ruwace mai bala'in sanyi, har da ice a cikinsa. Wasu yara da ba zasu wuce 8 years a duniya ba, tsaye suke a gaban ruwan jikkunansu na kerma, kana ganin face ɗinsu alamar tashin hankali da firgicice sosai a ƙwance. Idanunsu gabaɗaya ya rena fata, a tsananin tsorace suke, fighter uniform ce a jikinsu, yanayin kayan nasu yaso ya yi kama da kayan mayaƙa, sai dai su nasu hular ta roba ce, and nasu kamar over roll suke, wato a haɗe rigar take da wando suke kamar kayan Spider-Man. Kowani yaro a jikin hularsa akwai sunansa da sunan babansa complete a rubuce a jiki. Dukkanninsu sun riƙe hulunar nasu a hannunsu dake ta faman kerma tamkar hulunar zasu faɗi ƙasa, babu takalma a kafafunsu, gabaɗaya yanayin kamanninsu iri guda ne kamar yadda nace maku mutanen birnin suna kamanceceniya. Master Devil yana tsaye a gaban ruwan ta ɗayan side ɗin suna fuskantar juna da yaran, ya harɗe hannayensa a saman wannan buɗaɗɗiyar kirjin nasa, fuskar nan a ɗaure tamau, ga wani ɗan iskar gashin bakinsa kamar na bunsuru da ya tara, idanunsa jajir kamar jini, bashi da imani ko miskala zarratin. Da wannan buɗaɗɗiyar fasasshiyar muryar tasa ya fara ƙirga from one to three. Yana kaiwa three ko yaro ɗaya bai rage a bakin ruwan nan ba, duk wannan firgici da tashin hankali da yake a saman face ɗinsu bai hanasu yin azaman faɗawa cikin wannan ruwan ba, ji kake zundum sun afka ciki!. Abin tausayi ba su iya iyo a cikin ruwan ba, sai lumewa ƙasa suke yi suna ƙara ɗagowa sama, duk in suka lume kuma sai sun sha ruwa sosai kafin su iya ɗagowa su shaƙi kamshi duniya wato numfashi. Nan take idanunsu ya kaɗa ya yi jajir, sun sha ruwa tamkar cikinsu zai yi bindiga, sun kasa iya yin iyo su kai baƙin gaɓa su fita, suna nan a in da suka faɗa basu motsa ba sai ƙasa da suke yi suna ɗagowa. Wlh yadda kuka san mutum mutumi ne ba mutum ba haka master yake tsaye yana kallonsu babu ko tausayi bare imani, tamkar karfe ce a kirjinsa ba zuciya ba, yara ƙanana haka, ina ma laifin ace manya ne? Ai da da sauki, amma su waɗan nan abinci ma yaushe suka gama iya ci sosai bare wannan horon mayakan, abinci ma har yanzu sai an nuna masu yadda zasu ci da kyau, wasu har yau na tabbata cusa hannunsu a baki dukka suke yi a yayin cin abinci, amma saboda shi master dama sunansa na sheɗan ne mai gabaɗaya babu imani a ransa, shi kuma Black Tiger ina ga ma uban shaiɗan ne mai gabaɗaya a zallar mugunta. Wani shirgegen katon mayaƙi ne ya shigo cikin wajen. Kai tsaye in da master yake tsaye ya nufo, yana tafi har wani amshi ƙasa take yi. Sanye yake da kayan warriors a jikinsa, sai dai bai sanya hularsu ba, daga ganin face ɗinsa kasan ɗan cikin birnin ne shi ma, a kallah zai kai 35 years haka. Kusa da master ya tsaya, cikin dakiya da katon murya kamar engine niƙa ya fara magana kamar haka. "Na gama bincikena, duk tsawon tarihi ba'a taɓa yin wata masarauta mai ji da karfin iko da jaruman mayaƙa ba biyun wannan KINGDOM OF POWER, masarauta ce a gabaɗaya faɗin ƙasar Tunisia babu irinta, kujerace da kowani sarki zai ci burin ɗale kanta, in takaice maka labari ɗagun kansu yafi na wannan empeir ɗin, suna ji da kansu, King Zuhair shi ne sarkinsu, mutum ne mai kafiya, jajircewa, jarimta, karfin iko, isa, taƙama, karfin faɗa aji dole, sannan kuma adalin sarki ne, yana kuma da zaratan jaruman ƴaƴa haɗe da wani bujumin namijin zakin commander mayaƙansu mai suna Zafar wanda ya kware wajen sanin duk wasu dabarun yaki, yana da wani yaro guda ɗaya mai suna Hoorain, namijin gaske ne mai firgita hantar manya manyan sarakuna wannan yaron, a yadda bincikena ya nuna mun da wuya ko in ce zamu sha bakar wahala kafin mu iya tankwarasu su dawo ƙarƙashin ƙafafamun kamar yadda muke yi wa sauran masarautun da suke kawo karfi a idon duniya". Ya kai karshen maganar cikin jarumta babu alamar jin ɗar ko wani fargaba a tattare da shi. Idan baku manta ba a baya na gaya maku a cewa duk wata masarauta da Black Tiger ya ji labarin suna da karfin iko to fa sai ya san ta yadda ya yi ya shirya dakaru ko ta halin ƙaƙa su je su yakesu, su kashe sarkin, sannan su kwaso mashi mayaƙan dake masarautar su kawo mashi master ya ƙara masu horo su zama nasa, yana amfani da karfin sihirinsa wajen control na ƙwaƙwalwar duk wani mayaƙi da zasu kamo daga wata masarauta, yana juyar masu da kwakwalensu yasa su mancewa da tsohon masarautarsu ya zama nasa kingdom ɗin kawai zasu tuna, fatan yanzu kun tuna?. To a wannan karon kuma idanunsa sun kyalla sun kyallo mashi kingdom of power, ya ji labarin suna da karfin iko fiye da tunaninsa ne yasa a ƙara bincika mashi da kyau, duk da cewa ya ga karfin ikon nasu a cikin ruwan tsafinsa, amma duk da haka yasa aka ƙara bincika mashi dan ƙara tabbatarwa, yanzu a shirinsa kingdom of power zai yaƙa, a hakan ma bai san cewa King Zuhair shi ne mamallakin Spender ba, ina ga da ya sani ai da a yau ba sai gobe ba zai ce aje a kifar da su a shafe tarihinsu a doron duniya...... Tashin sense, akwai gwarama wlh ba kaɗan ba!. Amma wani hanzari ba gudu ba, my people's shin kuna ganin a gwabzawar Black Tiger and King Zuhair waye zai yi nasara? Shin Black Tiger zai iya yakar Kingdom of power? Me zai faru a tsakanin waɗan nan masarautu biyu masu ji da balai'n karfin iko dukkansu? Ga Queen Zarina a gefe! Sai dai Black Tiger ya fisu arziki nesa ba kusa ba, bazama a haɗa ba, su kuma sun fishi kwararrun dangerous warriors masu lafiya renon Commander Zafar, shi kuma ya fisu da Robbot masu haɗari, sun fishi da ayar Allah, shi kuma karfin tsafi, ya kuke tunanin wannan wasa zata kaya? Su waye masu nasara? Daga karshe waye zai kasance mammallakin Spender? Akwai gagarumin cakwakiya, masarautu uku zasu fara farautar junansu kamar hauka, dan kun dai san King Zuhair ba zai kyale Queen Zarina harin da ta kawo masu ya tafi a banza ta ci bulus ba, ta ƙetare iyakokin yaki, a dokikin yaki yanzu suna da damar mayar mata da martani dan ta ketare iyakarta, akwai tashin hankali. King Zuhair zai yaki Queen Zarina, shi kuma Black Tiger zai yaki King Zuhair, su kuma turawan yamma suna shirin yaƙar Black Tiger ɗin dan su kwashe mashi arzikin Daula, shin ya kuke tunanin wannan game ɗin zata kaya? Ya kuka hango wannan cakwakiya? Muje zuwa, yanzu wasan zata fara da zafi zafinta ko in ce da tafasarta. Dan haka ku gyara zama, mu je zuwa, yanzu ne zaku ji ainahin daɗin shan maratu ni kuma na sha Maltina mai sanyi ina suburbuɗo maku update!!. Master Devil. Suna tsaka da yin maganarsu da wannan mayakin kwatsam ba zato ba tsammani master ya ji an cukumi ruyar rigarsa. Wani irin zaro idanu wannan warriors ɗin ya yi, saboda ko da gigin wasa bai taɓa ganin wanda ya yi wa master magana cikin ɗaga murya a cikin birnin nan bama bare har a kai ga nuna mashi matsa, sai ga shi yau an cakumi wuyar rigarsa?! Abin dole ta tashi hankalin kowa. Shi kansa master ya girgiza da ganin cakumar wuyar rigar nasa da aka yi tun ma kafin ya ɗago idanu ya kalli wane? Yasan cewa Black Tiger ne kawai zai iya yi mashi hakan a cikin birnin nan, bayan shi kowa mahaukacin tsoronsa yake ji. Zuciyarsa tafasa take yi tamkar anɗaura dalma a wuta, jikinsa sai wani irin tsuma na ban mamaki yake yi, gashin jikinsa duk sun mimmiƙe, duk wata alama ta zarra na cikakken namiji ta bayyana a jikinsa a wannan lokaci, tamkar wanda ya ci uban gudu ya ƙoshi haka yake huci haɗe da haɗa uban gumi, idanun nan sun kaɗa sun yi jajir da su kamar wuta, tamkar ba Ronniensu Floris ba. Da kyar ya kawar da tunaninsa ya furta. "Ronnie are you out of your sense? Am I your mate?!". Cikin ɗan ɗaga murya ya faɗa. Ronnie da ya gama fusata, zuciya ta zo har wuya, ransa ya gama jagulewa, jikinsa na wani irin zafi, ya rasa hukuncin da ya dace ya yi wa master a yau, dan dama ya jima yana tara mashi ne, master ya jima yana shiga harkarsa sosai, yau kam ya ƙuresa ba zai iya ɗaga mashi ƙafa ba. Ganin haka yasa wannan mayaki da ya kawo rahoto a kan Kingdom of power ya salallaɓa ya gudu ya bar wannan waje, domin yasan faɗan na manyan kai ne, duk cikin birnin nan banda Black Tiger babu wanda ya isa ya ce zai saka baki a wannan faɗa wane ƙaniyarsu. Zuciyarsa na tafasa, da kyar ya furzar da iska mai zafin gaske daga bakinsa, cikin ɗaga murya ya ce. "Akan me zaka je ka yi mun karya? Ni nace maka ina son Sweetie?! Me yarinyar nan ta yi maka da zaka ja mata irin wannan hukuncin? Shin ta cancaci haka daga gareka ne ko ni na cancanci hakan?!". Ya ƙare maganar yana wani irin huci, ran maza ya ɓaci!. Tamkar bai taɓa yin shagwaɓa a rayuwarsa, kamar ba Ronniensu Floris mai zuba masu shagwaɓa idan suna a tare ba!!. Rai a ɓace ya bashi amsa da. "Awww kai ta yarinyar kenan ma kake yi?! Kai baka kishin yayanka? Baka masa fatan burinsa ya cika? Baka son mu samu Spender mu cinma burinmu? Saboda yanzu zuciyarka ta mutu shi ne kake bin bayan mace a kan yayanka?........" Tsawar da ya daga mashi cikin fushi da kausasshiyar murya ne yasa ya dakata da yin maganar ba dan ya kai in da yake son dasa aya ba. Da kausasshiyar murya mai amo haɗe da zafin rai ya fara magana kamar haka. "Kai har ka isa kace ni bana kishin yaya? Ka isa kace zuciyata ta mutu? Har yau har gobe nine zakarar Black world!! Ba'a taɓa yin namijin da ya kaini ba kuma ba za'ayi shi ba!! Ra'ayi nane na yi magana a kan Sweetie or not, daga yau kada ka kuskura ko da sunan wasa ka sake ce mun zuciyata ta mutu a kan mace!!". Zaro mashi waɗan nan jajayen idanun nasa master ya yi. Shi ma cikin ɗaga murya ya ce. "Ronnie na gaya maka ka zama rago mai matatccen zuciya a kan mace!! A kan yarinyar da baka san asalinta ba, ka haukace a kan abin da ba zai taimake ka ba, ka zubarwa da y............". Azababben marin da ya dallah mashi cikin fusata ne yasa ya dakata da yin maganar, al'ajabi da mamaki ne suka kusa sanya shi sumewa a wajen, bai taɓa tunanin Ronnie yana da gwanin gwiwar da karfin zuciyar iya ɗaga mashi murya bama a rayuwarsa, duk da yasan cewa tabbas ya fisa matsayi da komai da komai, amma bai taɓa kawowa a ransa ya yi ƙasƙancin da zai iya ɗaga hannu ya dallah mashi mari ba, abin da mamaki. "Master kada ka jawa kanka bala'in da ba zaka iya ɗauka ba, kada ka ƙureni! Kada ka ɓata mun rai! Kai kanka kasan ɓacin raina girgizan rugugin aradu ce ga birnin Black world! Kada ka ja na kasheka a nan kuma na kashe banza karen farauta!!..............". Bai iya kai karshen maganar bane sakamakon zuciya da ya yaudari master ta ja shi ya ɗaga hannu da nufin ya kai mashi mari, hakan yasa ya dakata da yin maganar tare da kaucewa marin. Shi kansa mastern bai san ya aka yi ya yi yunƙurin marin nasa ba, ya san duk abin da yake faɗa gaskiya ce, ɓacin ransa rugugin aradu ce ga birnin, amma aka ce zuciya bata da ƙashi, sai ta ingiza shi a kan kada ya bari ɗan yaron nan yana gaggaya mashi baƙaƙen maganganu hakan zai sa mutumcinsa ya zube ya kuma sa jama'a su rage jin tsoronsa. Ransa ne ya ƙara ɓaci, wato yanzu master har zai iya cire hannu ya ce zai maresa? E lallai dole yau su cire raini a tsakaninsu, dole kowa ya san matsayinsa, hakan yasa cikin fushi ya jijjiga wuyar rigar master da karfin gaske, da hannu ɗaya ya jinjigasa sai da gabaɗaya jikinsa ta girgiza, sannan ya ɗan yi baya tare da ɗaga kafarsa ya takashi da karfi a kirji sai da ya tafi ta baya da karfi ya faɗa cikin wannan ruwa da yaran suke ciki suna ta faman ɗirkar ruwa, wasu daga cikinsu ma sun sha ruwa ta yi masu yawa har sun sume a ciki master yana can suna tafka faɗa da Ronnien, yara abin tausayi. Wani irin daka sufa Ronnien ya yi tare panjamawa cikin ruwan. Faɗa suka farayi a matsayinsu na zaratan zakaru masu ji da rai da lafiya. Abin mamaki abin al'ajabi, master dai shi ya bawa Ronnie horo, shi ya koya mashi komai, amma sai ga shi Ronnie ya bashi kashi, ya sha kashi a hannun ɗalibinsa, da kyar da makyarkyata ya iya kwace kansa yana haki ya samu ya fito daga cikin ruwan, kamar zai mutu ya fara ƙoƙarin gudun cetar ransa, dan ya wahala, Ronnie ya kama kansa ya danna a cikin ruwar almost 10 mins yana ta shan ruwa, dama Ronnien yasan suna da horon iya riƙe numfashinsu har na tsawon 5 mins a cikin ruwa, shiyasa kuka ga yana ƙoƙarin koyawa waɗan can yaran irin wannan ne yasa ya jefasu cikin ruwan, su sun samu wannan horon ne kuma daga wajen master ɗin tun suna yara, shiyasa ya danne shi har ya kai 10 mins a cikin ruwan, kunga ya wuce adadin da ya iya. Sai shan ruwa yake yi yana fafutukar neman numfashi, ashe shi ma Ronnie ya iya mugunta, haka yasa karfi ya dannesa yaki bashi wata damar da zai iya shaƙar numfashi!. Ya sha ruwa kam babu karya, har idanunsa suka kara wani uban ja kamar wutar dake ruruwa. Gudun cetar ransa ya fara yi. A fusace Ronnien ya fito daga ruwan, a fujaje ya bi bayansa, shi kansa ya yi mamakin yadda aka yi ya iya dukan master har haka, mutumin da ba wanda ya taɓa iya ja da shi a fagen faɗa ne ace yau shi da yake matsayin ɗalibinsa kuma kusan ɗan cikinsa ne ya dakesa har haka? Abin da mamaki! Power da ya samu a jikinsa yanzu ta bashi mamaki ba kaɗan ba, bai taɓa zaton hakan yake ba....... Ran maza ne kawai ta ɓaci!. Bayan master ɗin ya bi domin har izuwa yanzu bai huce ba, sai ma ƙara tafarfasa da zuciyarsa take yi. Basu zame ko'ina ba sai cikin main parlourn, a lokacin Floris tana zaune a saman sofa ta buga uban tagumi, ga busassun hawaye a face ɗinta alamar ta ci kuka ta ƙoshi. Da gudun gaske master ya haura sama yana haki kamar numfashinsa zata ɗauke, jikinsa dukka sai ɗigar ruwa yake yi. Ronnie na danno kai da dugu Floris ta miƙe tsaye, da gudu ta nufesa, yana wani irin huci zai nufi sama ta yi saurin faɗawa jikinsa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Kowani mutum da rauninsa, shi kuma Ronnie kyawawan ƴan'mata ne rauninsa, yana matuƙar son ganinsu cikin farinciki. Na gaya maku baya zina, kuma bai taɓa yi ba, amma dai yana kaunar kyawawan mata a kusa da shi kam ba karya. Wannan kuka nata yasa ta ɗan taɓa mashi zuciya, hakan yasa dan dole ya dakata da bin master da yake da niyar yi, ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya. A saman shoulder ɗinta ya kwantar da kansa yana jin kamar zai haɗiye zuciyarsa ya mutu. Ita ma kuka take yi sosai, dan ta yi kewarsa over, yau ya yi mata abin da bai taɓa kwatantawa ba ko da sunan wasa. Jin kukan nata na taɓa mashi zuciya ne yasa ya ɗauketa can jikinsa duk ruwa suka koma saman sofa suka zauna. Goge mata hawayen nata ya fara yi tare da fara aikin rarrashinta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta yi shiru, da yake ya kware a fannin sanin me mata suka fiso, ya iya rarrashi da kalamai irin na soyayya masu sanyaya zuciya, sai dai shi ba soyayyar yake yi ba ɗan albarka...........🤣 Ya dai zuba masu kalaman ya kwantar masu da hankali, yagansu a gefensa suna murmushi, shikenan fa. "Beb yunwa nake ji". Ta faɗa cikin muryar kuka. Ba tare da ya sake furta kalma ba ya miƙe ya ɗauketa suka nufi dinning room. Shi kuma master ko ina ya yi? Yau Floris kyakkyawar tattabara ta cecesa. Me kuke tunanin Black Tiger zai ce a kan wannan faɗa nasu? Kun dai san yana ganin komai! Shin zai yi shiru ne ko dai zai gayawa kowa matsayinsa ne?! Hmmmm mu je dai zuwa!. _P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A__🔥🌹🕊️ JAWAD and CHUCHU🔥🕊️ Murya a ɗan ruɗe ta furta. "Yah Jawad kai ne da middle night ɗin nan?". Ta yi maganar tare da miƙewa zaune cikin sauri, ta zuro kafafunta ƙasan gadon sannan ta miƙe tsaye. Harɗe hannayensa da kyau ya yi a saman chest ɗinsa, sannan ya jingina da jikin door room ɗin. A hankali ya lumshe idanunsa ya sake warosu a kanta. "Mekike yi baki yi barci ba har yanzu?". Tamkar mai magagin barci ya yi maganar, kana jinta kasan yana tare da kasala sosai. "Nakasa yin barcin ne". A shagwaɓe ta yi maganar. Wani irin yanayi ya ji ta ratsa shi tun daga tafukan kafafunsa har izuwa tsakiyar kansa. "Jannat kina mun son ranki kam, yanzu dai meyasa kika kasa yin barcin?". Ya kai karshen maganar tare da ɗaga mata gera guda alamar yana jiran amsa!. "Yah Jawad na kasa yarda cewa wai kai ne kake sona, abin ya tsaya mun a rai'na, idan na rufe idanuna kalamanka ne kawai suke neman fasa mun kai'na, jin abin nake yi tamkar a mafarki, na ƙasa yarda gaskiya ce, na kasa samun wanda zai mareni na farka daga wannan daddaɗar mafarkin, ina ma na farka naga gaskiya ce ba mafarki ba, da kuwa sai na yi azumi guda biyar ina godiya ga Allah". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar. Gently ya fara takowa izuwa in da take tsaye, tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki yake tafiyar. Tana tsaye ya ƙariso gabanta, cike da tsananin kaunarta ya furta. "Har yanzu gani kike yi a mafarki kike?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e ba tare da ta yi magana ba. A hankali ya sauke hannunsa daga saman kirjin nasa, jikinsa duk a wani irin mace sosai kamar mai jin barci, komai a kasalance yake yinta. Hannunsa ɗaya ya kai saman waist ɗinta. Ɗan zaro idanu ta yi sakamakon wani irin shock da ta ji tamkar wadda aka jonawa wutar lantarki. Iskar bakinsa mai tsananin kamshin mouth perfume deference type and toothpaste ne ya hura mata a cikin kwayar idanun da ta zaro mashi ɗin. A hankali ta lumshesu tana turo baki alamar shagwaɓa. "Kai Yah Jawad me hakan to?". Ƙasa sosai da voice ɗinsa ya yi wajen furta. "So da kauna mana". Wani daddaɗar ajiyar zuciya ta sauke, a fili ta ce. "Yah Allah kasa ba mafarki nake yi ba, Allah kaga zuciyata ina son Yah Jawad so mai tsanani, Allah ƙasa gaskiya ce ba a mafarki ya zo ya ce yana sona ba, Allah ka cika mun burina ka mallaka mun shi a matsayin miji". Tana magana nan take idanunta suka cicciko da kwallah. Hannunsa dake saman waist ɗin nata ya fisgota da shi ta faɗa saman kirjinsa. Wash ta ɗan furta sakamakon faɗawa da ta yi babu excuse ta buga kanta a dai'dai saitin ribs ɗinsa. Hannu ta zura ta bayansa ta rungumo waist ɗinsa ta baya, shiru ta kwantar da kanta a saman kirjin nasa tana addu'ar Allah yasa kada ta farka daga wannan mafarki a yanzu sai gobe. Rankwafo da kansa a kanta ya yi. Cikin wani irin salon soyayya mai jan hankali ya fara magana kamar haka. "My kaunaty har yanzu baki farka daga mafarkin bane?". Tana daga kwance ta gyaɗa kai alama e, sai ta ɗaura da cewa. "Yah Jawad ka bari kada ka tasheni, kaga a zahiri ka cika yi mun faɗa da bada punishment, amma a mafarkinka da nake yi kullum soyayya kawai kake nuna mun, ina sonka my melody". Hannu ya ɗaura saman bayanta yana ɗan shafawa a hankali kamar mai rarrashinta. Cikin sigar soyayyarta da ke wani irin fiagarsa ya fara faɗin. "My kaunaty ki buɗe idanunki, tabbas ba mafarki kike yi ba, ni ɗin ne da gaske, amma bari na yi maki abin da zai sa ki yarda". Shiru bata iya amsa mashi na, sakamakon wani irin kaunarsa dake ƙara ratsa fata, nama izuwa ƙashi da ɓargon jikinta, duk wasu kofofi na jikinta sun buɗe suna karɓar soyayyarsa da salonsa dake ratsata, duk sai ta ji wani iri daɗin da ya rufe mata baki, ta ƙasa iya furta kalma, sako kawai take ƙarɓa yana ratsata. Ƙara yafe mashi a jiki ta yi kamar mage. Sai kiran layinta Yah Rizwan yake ta sake yi, amma basu ji ba, da yake wayar tata yana vibrate ne kuma tana kan gado pillow ya ɗan danneta. "My kaunaty please talk to me nown, kin san yadda nake marmarin jin voice ɗinki a kullum kuwa?". "Ni Yah Jawad ka barni please". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar, a salon irin shagwaɓa mai kara fisgar zuciyar masoyi ta yi shi. Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. Hannu ya kai ya ɗan ɗago haɓarta yana mai cigaba da ɗan shafa tsakiyar bayanta. "Wahalar dani kike son yi ne kaunatyna?". Idanunsa a ɗan limshe ya yi maganar. Waro nata idanun ta yi, nan take suka sarƙafe juna da kallon so mai tafiya da imani. Almost 5 mins idanunsu sarƙafe cikin na juna, a hankali ta hura mashi iskar bakinta a face ɗinsa wanda hakan yasa ya ɗan limshe idanun nasa, soyayyarta ce kawai ke wani irin fisgarsa tamkar zai sa hannu a kai ya yi ta zunduma ihun daɗi. Ɗan turo baki ta yi, shagwaɓa mai kara rikita mashi ƙwaƙwalwa ta fara zuba mashi tana turɓune fuska. "Ni Yah Jawad ka kura mun idanu duk ka kwashe mun kyau ɗina, yanzu idan na farka daga wannan mafarki sai naga kyauna ta rabu..............". Ƙasa ƙarisa maganar ta yi sakamakon saukar kyawawan lips ɗinsa da ta ji a saman tata, ta rikita bawan Allah sosai ne, shiyasa. Suman tsaye ta yi tana jiran ta ji me zai yi mata da ya haɗe lips ɗinsu waje guda. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A__✍️🔥🕊️ AUTA ZUNAIRA🕊️🌹 Ga duhu ga toshe baki sai abin ya matuƙar daga mata hankali tare da bata tsananin tsoro, a ruɗe ta fara ƙoƙarin kwatar kanta dan ta samu ko ihu ne ta kurma ko za'a kawo mata ɗauki. Saukar zazzakar voice ɗinsa a cikin kunnenta in da yake cewa. "Ki nutsu ni ne". Yasa ta nutsu tsit, amma jikinta na kerma, saboda ta rigada ta tsorata tun farko. A hankali ya zame hannunsa daga bakinta tare da saketa ya ɗan yi baya kaɗan kamar taku biyu daga kusa da ita. Bata iya ganinsa sosai, amma ta samu nutsuwa matuƙa da jin voice ɗinsa. Ƙasa ƙasa ta ce. "Hoorain me kake yi a nan? And meyasa ka rufe mun baki ka jawo ni wajen duhun nan?". A maimakon ya amsa mata tambayar tata sai ya jefa mata nasa tambayar shi ma. "Ina zaki je a daren nan? Meya fito dake?". Da alama ransa a ɗan ɓace ya yi maganar, saboda ba da irin muryar da ya saba yi mata magana bane ya yi ta. "Sai ka amsa mun nawa tamnayar tukun nan ni ma zan amsa maka, domin ni na fara tambayarka ai". A ɗan shagwaɓe da irin muryar da take yi wa Yah Omar ɗinta magana ta yi mashi. Daddaɗar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Afuwan ranki ya dade, tuba nake yi bisa jefo maki tambaya da nayi ba tare da na baki amsar wanda kika tambaye ni ba, rai'na ne a ɗan ɓace, amma ki yi hakuri". Wayyo shi dai kullum muryarsa cikin sanyi da nutsuwa, sam babu hayaniya abinsa, very gentle guy. "Ba komai, yanzu dai ka gaya mun me kake yi a wajen nan?". Ta yi maganar da alama son jin me yake fito da shi da daddare haka, meyasa shi ba zai je ya kwanta ya hutawa ransa ba? Ta damu sosai a kan hakan, tana tausaya mashi sosai. Shi kansa ya fahimci cike da damuwa sosai a tattare da ita ta jefa mashi wannan tambayar, ya kuma ji matuƙar daɗi a ransa na yadda ta nuna damuwarta sosai a kansa, sai dai kuma bai bari hakan ta yi wani tasiri a cikin zuciyarsa ba, dan shi yasan da wacece yake tare, yanzu haka ma idan aka kamasu ai ya shiga dubu ɗari uku bama uku ba, so baya barin duk wani abin da zai shafeta ya ratsa fatarsa ma bare har ya fasa tsoka da ƙashin jikinsa ta shiga mashi cikin zuciyarsa, Allah sarki har ya bani tausayi ya kuma taɓa mun zuciya bawan Allah. "Gadinki nake yi shiyasa kika ganni a wajen". Allah sarki ya bata amsa, bai iya yin karya ba, baya iya samun nutsuwa a kullum, sai ya fito kusa da part ɗinsu ya zauna dik dan saboda ita, Hoorain sam bai iya karya ba, yanzu haka da commander ya tambayesa ina yaje lokacin da aka kawo masu hari kai tsaye ya gaya mashi gaskiyar komai na cewa yana tare da ita ne a lokacin, sosai baban nasa ya ja mashi kunne tare da daka mashi warning a kan ya kula kuma ya yi baya da ita. Amma dik da haka baya iya janye jikinsa daga in da yasan tana wajen, ko barcin kirki baya iya samun yi, shi kansa bai san me yake damunsa ba. Wani irin sanyi taji ya ratsata, haƙiƙa ta yi matuƙar farinciki na jin cewa saboda ita yake kusa da part ɗinsu, tsabar daɗi sai ta ji tamkar ta daka tsalle ta rungumesa, amma sai ita ma ta danne ta ce. "Yanzu saboda ni kake tsayawa a wannan waje? Meyasa to?". Ta gefa mashi tambayar idanunta a kan face ɗinsa duk da bata ganinsa sosai saboda duhun wajen. "Babu komai, kawai zuciyata ce take kasa samun nusukuni idan har ban kasance a dik in da nasan kina wajen ba". Ya bata amsa kansa a ƙasa. Shi dai ya ji daɗi baya karya kuma bai iya bama, kun ji ya buɗe mata gaskiyar dake cikin zuciyarsa. Ai wani irin daɗin da ta ji ne yasa bata san lokacin da ta matso ta faɗa jikinsa tana murmushi ba. Bai so barinta a jikin nasa ba dan gudun kada a gansu, amma kuma ya ƙasa iya rabata da jikin nasa, sai ya tsinci kansa da jin daɗin hakan. "Ke kuma baki faɗa mun me ya fito dake a wannan daren ba?". Kamar mai raɗa ya yi maganar. Hannunta ta zura ta ƙugunsa izuwa ta bayansa ta rukunkumesa, ta kwantar da kanta a saman lion chest ɗinsa. "Kai mana na fito gani". A shagwaɓe ta bashi amsa. Wani irin yanayin da ya tsinci kansa a ciki na farinciki ne har bai san lokacin da ya sanya hannayensa dukka biyu ya rungumeta da kyau ba. Yaji matuƙar daɗi over, ashe shi ta fito nema dan ta gansa. Ta fahimci ya ji daɗin maganarta, dan haka sai ta ɗaura da cewa. "Na ji ina son ganinka ne, sannan kuma ka bani wancan rigar taka idan ba haka ba ba zan koma cikin gida ba, a wajen nan zan kwana". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. Da kyar ya iya buɗar baki ya furta. "Meyasa zaki zo ganina? Kina son su Prince Jaish su hukuntani ko?". "Babu wanda zai hukuntaka, ai ba kai ka kirani ba, ni da kai'na nazo". Tana magana tana ɗan motsa hannayenta dake saman bayansa. Hakan da take yi ba ƙaramin rikitar da shi take yi ba, tana ƙara jefasa cikin yanayi, bare ga shi ga yadda yake dama, kunga mutane masu shiru shirun nan, idan kuka kuskura suka buɗe baki sai kun gudu, sannan ga yanayin aikinsa aiki ne wanda kullum jinin jikinsa yana cikin busy, bai san wani rauni ko gazawa or sanyin jini ba, jininsa a tafashe yake sosai, irinsu sai an bisu a hankali idan ba haka ba ayi ɓatacciya. Shiru bai iya furta kalma ba, ya kasa koda motsawa saboda wani irin bakon yanayi mai raɗaɗin daɗi dake ratsa shi. "Hoorain ina tambayeka........". Bata kai karshen maganar ba a fujaje ya rufe mata baki da hannunsa dake saman bayanta. A hanzarce ta ɗago da kallonta izuwa kansa, ganin yana kallon wani wajen yasa ta kai kallonta nan, inuwar mutum ta hango kamar uncle Taheer. Wani irin dum dum ta ji kirjinta ya bada bugu, ya biyo bayanta kenan? Hakan na nufin yana ankare da ita kenan? Yanzu me abin yi?. Ta luluƙa duniyar tunani sai jinta ta yi a saman shoulder ɗinsa, cikin sanɗa ya matsa da ita gaba, dan wannan inuwa mai kama da uncle Taheer ɗin yana tinkarosu kamar ance mashi tana wajen, ko da yake kamshin perfume ɗinta ya bi, da shi ya yi amfani ya iso in da take. Ganin da gaske yana cigaba da biyosu ne yasa ya dakata tare da sauketa ƙasa. A cikin kunne ya raɗa mata. "Kina da vest a ciki?". Ɗan zaro idanu ta yi, ganin babu lokacin tsayawa ta ce zata yi mashi shagwaɓa ko gardama ne yasa kawai ta gyaɗa mashi kai alamar e tana vest a ciki. A hanzarce ya kai hannunsa saman maɓallan rigar barcin jikinta. Ɓallesu dukka ya yi ya rabata da rigar, ya rage saura white vest na ciki kawai. Sauri sauri ya tsugguna ta haye bayansa, bayan bishiyar mangoron dake karshen wajen ya laɓe, yana ganin uncle Taheer ɗin yana tafiya cikin sanɗo har ya iso in da suke. Har zai rufe mashi fuska da rigar tata sai kuma wani tunani ya faɗo mashi, tunawa ya yi da idan ya kuskura ya rufe mashi fuska da rigarta fa to ba shakka zai gane cewa Autar tana wajen, dama ya yi niyar ya ɗaure mashi fusa da rigar tata ne sosai sai su gudu, kunga kafin ya samu ya kwance face ɗin nasa ya bisu ma sun kurewa ganinsa sun yi nisa, amma sai ya tuna to ai zai gane rigarta ce, in hakan kuma ya faru to fa tabbas yau ba zaman lafiya a wannan masarauta, tabbas sai hankalin kowa ya tashi. Tuna hakan ne yasa ya fasa kudurin nasa, a hankali ya fara sanɗo da ita a bayansa suka bi ta bayan bishiyar, uncle Taheer yana ta gaba su kuma suka bi baya, cikin dabara ya samu ya bar arear wajen. Suna fita kuma ya rasa ina zai yi da ita, ga ko'ina da haske tamkar rana, mayaƙa suna ta shawagi, idan aka gansu a tare kawai ma ya shiga uku bare kuma a ganta goye a bayansa. Duk ya ruɗe hankalinsa a tashe bawan Allah, sam bai ma san lokacin da ya wuce room ɗinsa da ita ba, ba zai iya sauketa a wajen ya ce ta tafi ba, dan babu riga a jikinta, ɗan banzan kishi ba zai iya barinsa ya yi hakan ba, zai ga ai kowani mayaki idan zai wuce zai ganta kafin ta isa cikin part ɗinsu, idan kuma ya ce zai tsaya sanya mata rigarta to fa tabbas za'a iya ganinsu, dan mayaƙa masu gadi suna ta going up and down a cikin harabar kingdom ɗin dan tabbatar da tsaro. Suna shiga ɗakin nasa ya banko kofa tare da murza key, a hanzarce ya sauko da ita daga bayan nasa, jikinsa har tsuma yake yi wajen miƙa mata rigarta dan tasa yasan ta yadda zai yi ya mayar da ita cikin gida. Yana jiyowa da nufin ya miƙa mata rigar idanunsa suka sauƙa a kan haɗadɗen lallausan surar jikinta, fata kamar na jarirai. Ai a dubu ya kawar da kallonsa while ita ma ta yi ƙasa da kai. Miƙa mata rigar tata ya yi ba tare da ya sake juyowa ba, da kyar ta iya karɓa ita ma saboda kunyarsa da ya kamata, ga shi vest ɗin jikin nata a dai'dai cibiyarta ya tsaya mata, ya kalle mata plat tummynta da sauran sassan jikinta. Mayar da rigarta jikinta ta yi, wani irin yanayi na tsananin kunyarsa ta tsinci kanta a ciki. "Muje na rakaki ko?". Ya faɗa ba tare da ya juyo gareta ba. Ɗakin nasa ta fara bi da kallo tana mamakin irin tsabtarsa, komai nasa kamshi yake zubawa, ga ɗakin nasa ɗan dai'dai, sai dai akwai komai da duk wani ɗan adam zai buƙata a cikin bedroom dan more rayuwa, bed ɗinsa dake shinfiɗe da up white bedsheet ne ya yi matuƙar burgeta, ashe dai ya iya aikin mata. Kallonta ta kai saman zabgegiyar takobinsa dake rataye a jikin bango, abin ya burgeta. Can ta hango wani hoto dake saman bedside drawer ɗinsa cikin frame, an ƙawata shi sosai da kwalliyar flowers masu ɗaukar hankali. Dawo da kallonta a kansa ta yi tana mamakin hali irin nasa, idan ka gansa a dake cikin jarimta kamar bashi da wani shaukin a kan soyayya, ashe ɗakinsa harda kwalliyar flowers, ashe dai ya san love kawai dai jarumta ce ta fi soyayyar yawa a jinin jikinsa har ta rikiɗar da shi har haka, da zai samu wadda zata farfaɗo mashi da soyayyar tuni zai taso da tasa, irinsu ne idan suka fara zuba love sai ka rasa ta ina suka koya. Raɓawa gefensa ta yi zata wuce dan ta je ta ɗauki hoton taga su wanene? Ta dai hango har da ƙaramin yaro a cikin hoton, ga kuma mace da namiji wanda idan ba gizo idanunta suke yi mata ba sai taga kamar commander Zafar ne lokacin yana ɗan matashi matashinsa, to waye ƙaramin yaron kenan?. Ta jefawa kanta tambaya, taso amsar ya kasance Hoorain ɗin nata ne dai, hakan yasa ta nufi hoton da sauri dan ta tabbatar, sai dai bai bari ta ƙarisa wajen ba ya yi saurin riƙo hannunta. A hanzarce ta juyo da kallonta a kansa, da sauri ya kawar da idanunsa daga kanta dan baya son su haɗa ido. "Hoorain ka bari mana, hoton can zan je na kallah". Kamar zata yi kuka ta yi mashi maganar. Jin ta ambaci hoto yasa ya yi saurin kai kallonsa kan hoton, ai kuwa a fujaje ya saki hannunya ya je ga ɗauke hotonsa da nufin ya ɓoye. A hanzarce ta ƙariso wajensa tana yin ɗan kukan shagwaɓa a kan ya bata ta ga su wanene?. Kin bata ya yi saboda baya son ta gansa yana yaro, ga shi a hoton mamarsa ta haɗa shi da nama a hannu ta kuma cusa mashi wani a baki bai gama haɗiyewa ba, duk dan ya yi shiru a ɗaukesu hoto, kuka yake ta yi, hakan yasa kumatunsa suka kumburo a hoton, abin gwanin ban dariya, shiyasa baya son ta gani. Kuka ta fara yi mashi tare da fara ƙoƙarin kwatar hoton daga hannunsa. Hannun nasa ya ɗaga sama kafin ya ce. "To ki kwata ki gani mu gani idan kina da tsawo". Tsalle ta fara yi tana son kwata sai dai ina ta kasa, dan kuwa komai tsallen da zata yi bata kusa kamawa ma. Dakatawa da yin tsallen ta yi tare da juya mashi baya ta harɗe hannayenta a saman kirjinta a dole ta yi fushi. Ganin haka yasa ya sauke hoton, a hankali ya dawo ta gabanta ya zamana suna fuskantar juna. Hoton ya miƙo mata ba dan ya so ba sai dai fushin da ta yi bai so hakan ba, cikin sanyin murya da sigar rarrashi haɗe da tausasawa ya ce. "Am so so sorryyyyyyy ranki ya daɗe, tuba nake yi, ga hoton nan ki gani". Yadda ya yi maganar da ka jita zaka san bata kai har cikin zuciyarsa ba, saboda baya son ta gani gaskiya. Ba tare da ta ɗago da kallonta a kan hoton ba ta furta. "Dukkan abin da my hero zai ce baya so to nima bana buƙata, dan haka na fasa ganin hoton ka ajiye shi kawai". Maimaita sunan my hero da ta faɗa ya yi a cikin zuciyarsa, haƙiƙa ba yau ta fara ce mashi jaruminta ba, amma na yau da ta faɗa sai ya ji sunan ya yi mashi wani irin daban. "Da gaske nake yi ranki ya daɗe ki ƙarɓa ki gani kin ji? Dan Allah ki dai'na yin wannan fushi ko?". Cool murmushi ta sakar mashi tare da dawo da kallonta a kansa, tamkar wata babbar mace tasa hannu ta karɓi hoton, ba tare da ta kallah ba ta nufi saman drawer ta ajiyeta, a hankali ta juyo garesa, murya mai cike da kulawa ta furta. "Wani lokaci idan na zo zan kalli hoton, yanzu dai bani rigar taka na tafi". Tana magana tana matsowa in da yake tsaye, kallonta kar a kan face ɗinsa. Ajiyar zuciya ya sauke, yau jin kansa yake yi tamkar ba'a duniya yake ba, ya kasa yarda cewa yau Gimbiya Zunaira ce a cikin ɗakinsa, abin ya tsaya mashi a rai, anya zai iya rintsawa yau kuwa? Ya jefawa kansa tambaya. Ya shagala da tunani bai san lokacin da ya kafeta da kallo har cikin ba, sai dai jinta ya yi ta sanya tafukan hannunta cikin nasa tana faɗin. "Tunanin me kake yi kuma kallon me kake mun?". Nisawa ya yi tare da buɗe baki zai yi magana kenan suka jiyo knocking na kofar ɗakin da karfi. A tare suka wani irin zaro idanu kamar kwayar idanun nasu zai faɗi ƙasa. My people's wa kuke tunanin ya buga masu kofa? Me zai faru a wannan dare?. A can cikin gida kuwa, nemanta King Zuhair yake ta faman yi a ɗakunan ƴan uwanta, dama kunsan yana zuwa yi mata addu'a a kowani dare, to ya je room nata zai yi mata addu'a ne bai sameta ba, ya je ɗakin Mommarta bata nan, ya leƙa na Chuchu bata nan, izuwa yanzu hankalinsa ya fara tashi, ga shi Guyson ma yana ɗakin Mommarsu bare ace suna tare, sarkin kwalafucin uwa ba, yaka manne da ita yaki matsawa. Me kuke tunanin zai faru idan King bai ganta ba? Akwai cakwakiya gobe, ni dai suna yi ina shan Maltina mai sanyi, to me yafi rai'na?. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 6/11/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 35 A tare suka dawo da kallonsu a kan juna, sun kasa motsawa daga in da suke, dukkaninsu faɗawa suka yi duniyar tunani. Ita kanta Autar ta yi matuƙar tsorata, zuciya da iya shegen jefa mutum cikin mugayen tunani da saƙe saƙe, musamman idan mutum yana tsorace da abu to wlh zuciya ta rinƙa kara mashi tsoro ta hanyar jefa mashi munana tunane tunane. Tunani ta fara yi a kan idan Yah Jaish ne ya zo fa? Ta shiga uku ta lalace! Ita da kanta ma kenan, ina kuma ga shi? Kamar ba yanzu ta gama ce mashi ba mai hukunta shi ba, ta yi mashi daɗin baki, ashe dai ita da kanta ta san bakar zuciyar ƴan uwanta, tasan idan hakan ya faru ta ja mashi babbar aiki ne da kaf kingdom of power babu wanda zai iya tare mashi, a gaskiya ta tafka babban kuskure wanda sai a yanzu ta fahimci hakan, addu'arta ɗaya shi ne Allah yasa Yah Guyson ɗin ta ne idan ma ɗaya daga cikin ƴan uwanta ne, shi ne kawai a gabaɗaya familyn nasu wanda tasan zai iya fahimtarta ya kuma rufa mata asiri ba zai gayawa kowa ba, bayan shi wlh ko Gimbiya Chuchu da suke tamkar chewing gum ba barinta zata yi ba, sai ta sanar da King, dan ita ma bata wani sonta da Hoorain ɗin, bata son ganinsu a tare. Sake buga kofar da aka yi ne yasa suka dawo cikin hankalinsu, dawo da kallonsa daga kan kofar izuwa kanta ya yi, while ita ma shi take kallo, sun rasa mafita, yadda suka tsaya a tsakiyar ɗakin sai sun baka tausayi ga kuma abin dariya na yadda suke kallon juna sun rasa mafita. "Zan ɓuya a cikin toilet ɗinka kai kuma sai ka duba wanenen ka ji?". Ta yi maganar ƙasa ƙasa kamar mai yin raɗa. Kai kawai ya gyaɗa mata, da alama jikinsa duk a mace, bashi da wani kuzari, dan kuwa shi ba ƴan uwanta ne ma suka damesa ba, idan sun kamashi karkari dai bai wuce su kashe shi bane kawai, shi damuwarsa yadda Abbonsa ya ja mashi kunne a kanta, ya yi mashi faɗa, sai a ce mashi yau an kama shi da ita a ɗakinsa a irin wannan daren? Ya kuke tunanin commander zai ji a ransa? Shi ɓacin ran mahaifin nasa ne baya so, gara mashi su kasheshi idan suna so amma kada Abbon nasa ya sami labarin hakan, yasan zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba. Wato commander yana balai'n kaunar ɗan nan nasa ɗaya tilo a duniya, shiyasa duk abin da zai zama mashi matsala a rayuwarsa yake saurin taka mashi birki a kan abin, kunga yasan kasancewarsa kusa da ita zai haifar mashi da matsala ne yasa tun wuri ya daka mashi warning a kan, amma bai ji ba, ko da yake ba laifinsa bane bawan Allah. Tun da yake bai taɓa sallake ko A a maganar da Abbonsa zai gaya mashi ba, yana yi mashi biyayya sosai, yana gudun ɓacin ransa sosai, da ya yi abin da zai ɓata mashi rai gara mashi ya yi kwana biyar a ɗaure babu ruwa babu abinci, a kanta ne farkon fara tsallake maganar commander, a hakan ma kullum yana cikin danasani tare da ƙoƙarin nesanta kansa da ita, amma ya ƙasa. Kofar ɗakin ya nufa ita kuma da sauri ta shige cikin toilet. "Wanene?". Ya faɗa muryarsa tana sarkewa. Ya yi tambayar cike da tsoro da fargabar muryar wanda zai bashi amsa. Kirjin maza yau sai dukan uku uku yake yi dan tsoron kada ace Abbonsa ne, Allah sarki shi commander ne ma kawai a ransa. Daga wajen ya amsa da. "Lafiya yau ka kulle kofar Hoorain?". Wani irin sauke nannauyar ajiyar zuciya ya yi, to fah ya zai yi kenan? Abin da yake gudu dai da alama shi ne yake shirin faruwa. "Babu komai Abbo". Ya bashi amsa tare da sanya hannunsa dake ɗan ɓari saboda tashin hankalin da ta jefasa a ciki, da kyar ya murza key ɗin ya buɗeta. Commander ne a tsaye cikin wannan irin tsayuwar tasa ta manyan jiga jigan jaruman, hannunsa riƙe da kayan abinci cikin wani babban tray. Hannunsa dake ɓari ya kai ya karɓa mashi abinci yana faɗin. "Sannu da zuwa Abbo". Miƙa mashi abincin ya yi a tare suka ƙarisa cikin ɗakin commander ya rufe kofar. A saman gefen bed ɗinsa ya zauna yana faɗin. "Hoorain wani irin kamshin perfume ne wannan?". Wani irin dukan uku uku ya ji kirjinsa ta bada, Abbonsa akwai kaifin ƙwaƙwalwa, wai yanzu har ya iya tantance cewa akwai wani kamshi na daban da ya shigo ɗakin?. Kai shi ma dai ya iya sa ido gaskiya. "Kamar wani kamshi fa?". Ya yi tambayar cikin dakiya, yadda kuka san bai san me commander yake nufi ba. "Na ji kamshin perfume irin na mata ne a ɗakin, kuma tamkar kamshin perfume ɗin princess Zunaira ko Jannat, su ne suke amfani da irin wannan turaren". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya sauƙo ƙasa saman dadduma ya zauna. Tun da ya fara magana kirjin ɗan nasa take harbawa pat, pat, pat da karfi karfi, addu'arsa ɗaya kada ya titsiyesa a kan sai ya ji dalilin zuwan wannan kamshi ɗakin, bawan Allah duk yana cikin firgici da tashin hankali, Auta tana neman jefashi cikin bala'i, da yake bai taɓa aikata hakan ko da sunan wasa bane sai tsoron nasa ya tsananta. "Zo nan na baka abinci yau barci da wuri nake ji". Abbon nasa ya katse mashi tunanin da yake yi. Wani irin ajiyar zuciya da ya sauke ne yasa Abbon nasa ɗagowa ya zuba mashi idanu. "Hoorain ya na ganka tamkar a ruɗe haka? Lafiya kake kuwa?". Da sauri ya furta. "E a'a e". Ya yi maganar ma murya na sarkewa alamar rashin gaskiya, wlh bai iya karya ba, ga shi wane shi ya ce zai faɗi gaskiya a yau, zai jawa kansa bala'i ne, amma kuma ya rasa ta ina zai fara yin karyan dan kare kansa, shi ne yasa ya ruɗe yake ta faɗin eh kuma a'a. "E a'a kuma?". Ya sake jefa mashi tambaya. A karo na biyu ma cewa ya yi e a'a e ya sake yi. Zuba mashi idanu sosai ya yi yana son karantarsa. Ganin hakan yasa sai ya yi saurin miƙewa, a ruɗe ya nufi toilet duk dan ya kaucewa zargin da yake gudun Abbon nasa ya fara jefansa da shi. Da kallo ya bisa har ya shige cikin toilet ɗin, bai kawo komai a ransa ba, sai ma tunani da ya yi a kan ko dai toilet da yake son shiga ne ya rikitashi har haka? Ko da wasa bai bashi wani zargi maras kyau ba, dan yasan da wuya Hoorain ya aikata wani abin rashin gaskiya, yasan irin tarbiyar da ya bashi. Jim kaɗan ya fito daga cikin toilet ɗin ya dawo ya zauna, sai a lokacin kuma ya rage kayan jikinsa, ya kuma cire wannan hula tasu, ya zauna a gaban Abbon nasa, zaman cin abinci da kyau. Abinci commander ya zuba masu da kansa, a tare suka fara ci suna tattaunawa a kan rayuwa, haka suke yi kullun, commander yana bala'in kula da ɗan nan nasa, baya yarda Hoorain ya ci abinci har sai ya zo sun ci a tare, shiyasa baya barinsa ya ci shi kaɗai. Duk abinda suke yi tana jiyosu daga cikin toilet ɗin, sun yi matuƙar burgeta, uba da ɗa ne kamar wasu abokai haka abin da birgewa matuƙa. Hira commander yake ta zuba mashi amma hankalinsa baya a tattare da shi, yana can ya tafi duniyar tunanin yadda za'ayi ya mayar da ita cikin gida. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ Sosai hankalin King ya fara tashi, sai yanzu yake danasanin saba mata da zuwa kowani ɗaki ta kwanta da yake yi, kun san tana kwana da Chuchu ko su Sarina idan ta yi ra'ayi, sannan tana kwana wajen Momma, har part na Jaish tana kwana da shi idan tana so, yau dai King ya yi nadamar hakan. Bai sanar da mommarta ba, ya nufi part ɗin Akka domin dubata a can, a jikinsa yake jin bata cikin arear wajen, saboda bata taɓa wuce wajen su Mommarta ba, in ta ɗan yi nisa ne room na Jaish, yasan bata zuwa wajen mama and mummy, amma haka ya je can ya duba, duk dan kawar da zargi. Duk wasu ɗakuna da suke part ɗin na Akka sai da ya shiga, wayam babu kowa, yau ko su Sarina ma basu kwana a part ɗin ba, har ɗakin uncle Jahiz dake cikin part ɗin sai da ya duba, wayam bata a ciki, uncle Jahiz ɗin ne kawai kwance yana zuba barci cikin kwanciyar hankali. Tsayuwa ya yi a main parlourn part ɗin yana tunanin ina ta shiga a wannan dare? Baya son shiga ɗakin barcin Akkar dan kada ya tasheta ko wani abin makamancin hakan. Tunani ya fara yi ta ina zai fara nemanta a daren nan? Ina ma taje? Yasan dai babu wanda ya isa ya shigo part ɗin nan nasu har ya ɗauketa ya fita da idan ba dai aljani ba, domin masu tsaron wannan part ɗin ko ƙuda idan zasu gani ba zasu barshi ya giftasu har ya wuce ciki ba, so idan ma bata nan to wlh da kafafunta ta fita ko kuma wani daga cikin family ya fita da ita!!. A hankali ya juya zai bar part ɗin, amma sai ya ji zuciyarsa ta ƙasa yarda da hakan, ya kasa samun sukunin aikata hakan, damuwa mai tarin yawa ce take cunkushe a cikin zuciyarsa take ƙoƙarin taso mashi izuwa maƙoshinsa. A hankali ya juya ya nufi ainahin bedroom na kwanar Akka, bai so shiga ba, amma haka ya tsinci kansa da leƙa wajen dan ya samu damar cewa babu in da bai duba ba a gidan. Ba karamar madarar mamaki ya sha ba na ganinta kwance a kusa da Akkar, idanunta a rufe alamar barci take yi, shi dai yasan bai taɓa samunta a wannan part ɗin da sunan zata kwana ba, tana shiga, amma banda batun kwana kam. A hanzarce ya ƙarisa cikin ɗakin domin ya tabbatar ba kaunarta ce take sa take yi mashi gizo ba. Kamar zai kunna wutar ɗakin domin ƙara tabbatarwa, sai kuma ya fasa dan kada Akka ta farka, wutar lamps ɗin ma sun wadatar ya iya hango face ɗinta. Tana kudundune a cikin bargo, sai zuba barcinta take yi abinta. Ina ai duk da haka bai yarda ba sai da ya hau saman bed ɗin ya taɓata dan dai ya kara tabbatarwa da kyau. To shi ma kenan da bai san cewa ta fita ba ya sha madarar mamakin ganinta a saman bed ɗin Akka, to ina kuma ga mu da muka san tana a tare da Hoorain, wai me ya faru? Ya aka yi ta dawo room ɗin Akka?. To mu koma baya kaɗan mu gani. Bayan sun kammala cin abinci ne commander ya buƙaci da su yi hira, a nan shi kuma ya nuƙe ya ce barci yau yake ji, sosai commander abin ya bashi mamaki, domin kuwa tun da yake da Hoorain yau almost 26 to 27 years bai taɓa ce mashi Abbo ina jin barci ba, hasalima shi ne yake matsa mashi a kan ya kwanta ya yi barci, amma sai ya ce a'a shi bai ji. Tun yana ƙarami haka yake baya son yin barci dare, gara na rana ma yana ɗanyi bisa ga na dare. Amma sai bai kawo komai a ransa ba, saboda yarda da ya yi da ɗan nasa, bai kuma sake ta da batun kamshin perfume ɗin Auta da ya ji a ɗakin ba, saboda ya yi tunanin ai Hoorain mai kula da lafiyar ta ne, ta yiwu basu jima da rabuwa bane, hakan yasa ya yi shiru bai sake tada maganar ba. A ɓangaren shi kuwa Hoorain addu'a kawai yake yi Allah yasa mahaifin nasa kada ya jefa mashi wata tambaya ko kuma wani magana, dan bashi da amsa ta karya da zai iya bashi, bai iya ba. Sai dai kuma ya gudu bai tsira ba, sai da Abbon ya ce. "Baka da lafiya ne Hoorain?". Kai kawai ya girgiza alamar a'a, yau yaki yarda su haɗa idanu da shi, ya kuma ki yarda ya buɗi baki ya yi magana sosai. "Hoorain me kake ɓoye mun ne? Alamu sun nuna akwai abin da ka ɓoye mun ko dai baka son na san baka da lafiya na tashi hankalina ne?". Kallonsa na'a kansa babu ko kyaftawa ya yi maganar. Tunani ya shiga yi a yanzu idan ya yi karyar bashi da lafiya ma ya ƙara ɗaure kansa ne, dan kuwa Abbonsa zai ce ba zai fita ya barshi shi kaɗai a ɗakin ya kwana ba, sai dai su kwana a tare, dan kada jikinsa ta tashi da tsakar dare, dan haka karyar bashi da lafiya ma bata taso ba, dole ya nunawa mahaifin nasa cewa lafiyarsa lou dan ya samu ya tafi ya barsa shi kuma ya mayar da ita cikin gida. "Abbona lafiyana lou, yau na gaji dayawa ne, barci sosai nake ji". Kana jin yadda ya yi maganar zaka fahimci ba'a cikin nutsuwarsa yake ba, bawan Allah abin da bai taɓa kwatantawa bane, ko tuna hakan a ransa bai taɓa yi ba Auta ta ja mashi, shiyasa ya ruɗe, kuma ga dukkan alamu Hoorain baya magana da mata, bai saba ba, bare kuma ace ya kawosu cikin ɗakinsa, kai bai taɓa, da akwai bayi mata masu hidima sosai a cikin gidan, amma shi baya daga cikin layin masu yi masu magana gaskiya, dan ruɗewar da ya yi wanda ya saba kasancewa da mata sam ba zai ruɗe har haka ba!!. "Tom shikenan, ni na manta ma ban gaya maka ba, batun neman Prince Jaish mai martaba ya ce a barshi yayyunsa suna aiki a kansa a kimiyance, dan haka mu maida hankali a kan neman Spender kawai, ka shirya gobe akwai in da zan aikeka kafin nan mu fara shirin mai da wa Queen Zarina martani, kada ku kyaleta idan kuka je, ku tabbatar sai ta fito daga cikin fadarta ta zube gwiwowinta a gabanku ta bada hakuri a fatar baki a kuma rubuce a takarda ku dawowa da King da shi, matar nan ta ketare duk wasu iyakoki, duk wasu dokokin yaki ta takesu ta kawo mana hari ba gaira babu dalili, dan haka yanzu a dokar yaki muna da damar yi mata duk abin da ya dace, ku ladabtar da ita, lastly ka da ka mance da riƙe addu'a dan kai kanka kasan in da zaku dosa". Ya kai karshen maganar tare da ɗan kawar da kallonsa a kansa......... Da alama wannan karon ba tare da shi za'a fita yakin ba. Ni kuwa nace rashin sani yafi dare duhu, da kunsan balai'n da yake tinkaroku na harin da Black Tiger yake son kawo maku wlh da ba zaku ɓata warriors ɗin yakinku, ku wahalar da su, ku jigatar da su a kan wata Queen Zarina karamar kwaruwa ba, ga babban sheɗani ifiritu mai shafe Daula duk girmanta daga doron duniya, ya rufe babinta a manta da an taɓa yin irin ta a duniya nan yana dinfaroku! Zaku wani tsaya biyewa Queen Zarina! Ai kawai fara shirin gagarumim yaki na a mutu ko a rayu kawai zaku yi! Hmmm akwai dai gagarumim matsala sosai gaskiya. Jinjina kansa ya yi alamar ba matsala ya ji zantukan baban nasa, daga haka suka yi sallama, commander ya fita ne kawai amma ba dan ya so hakan ba, saboda yana son sanin me yake damun ɗan nasa. Yana tafiya kamar da minti biyar haka sai ya ɗauko holarsa ya mayar kansa, sannan ya ce da ita ta zo ya mayar da ita dare yana kara yi. A hanzarce ta fito daga cikin toilet ɗin, yana tsaye ta ƙariso gabansa. Kansa a ƙasa ya nufi hanyar fita daga ɗakin!. Bayansa ta bi da sauri, ita kanta izuwa yanzu a tsorace take kada a nemeta a cikin gida, ga kuma uncle Taheer da ya biyo bayanta tasan za'a iya samun matsala. Buɗe kofar ɗakin nasa ya yi tare da fara fitowa, ya yi mata alamar ta tsaya bari ya duba ko akwai wani motsi a wajen!. Ɗan wawwaigawa ya fara yi domin dubawa. Ganin babu kowa ne yasa ya yi saurin, yi mata alama da hannunsa a kan ta fito. A hanzarce ta fito, jikinta har kerma yake yi ƴar ƙaniya, hannunta ya riƙo suka nufi hanyar komawa. Kamar wasu marassa gaskiya a duk in da suka ga mayaki na shawagi sai su laɓe a wani wajen har sai kafa ta ɗauke ta wajen sannan su cigaba da tafiya. A bakin kofar bayan nasu ya dakata, da hannu ya nuna mata hanya a kan ta wuce kenan ba tare da ya furta kalma ba. Da sauri ta wuce ita ma bata furta kalma ba, dan a tsorace take. Zuba mata idanun ya yi yana kallonta har ta shige ciki ta rufo kofar. Ya ɗan jima tsaye a wajen kafin daga bisani ya ɗan matsa kaɗan. Ita kuma tana shiga ta hango King ya fito daga part ɗin Mommarta zai shiga na mama, tasan ita yake nema hakan yasa dabarar guduwa part ɗin Akka ya faɗo mata, tasan idan ta shiga part ɗin Momma to zai gano ta fita, saboda ai ya duba wajen da farko bata nan, shi ne yasa ta gudu wajen Akka ta haye gadonta ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda wasu kattin gani kasheni suka biyo ta sha da kyar. To kun ji yadda aka yi, mu cigaba da labarinmu. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ Ɓangaren Jawad kuwa, yau kusan a ɗakin Chuchun ya kwana, domin kuwa lokacin da ya haɗe bakinsa da nata, ya kasa iya aikata abin da yake da niya wato kissing ɗinta, ya kuma ƙasa iya rabata da jikinsa, shiru suka tsaya ita tana jiran ta ji me kuma zai yi mata, shi kuma Allah ne kaɗai yasan me a ransa. A dai'dai wannan lokacin King ya yi knocking na kofar ya zo neman Auta. Ba ƙaramin razana suka yi ba, domin kuwa dukkansu sun san dole King ɗin ne, idan ba shi ba babu wanda zai zo a cikin wannan dare ya buga mata kofa. Tuni Yah Jawad ya dawo cikin hayyacinsa, kamar dai yadda ya yi ranar yau ma hakan ya yi, cikin toilet ya shige ya ɓuya, ita kuma ta haye saman gado da sauri ta shige cikin bargo tana zare idanu kamar antare ɓera a tarko, yanzu kam ta yarda ba mafarki take yi ba ƴar ƙaniya. A karo na biyu King ya kara yin knocking jin na farko shiru ba'a amsa ba. Shiru ta lume a cikin bargon har da rufe kanta irin idan ma ya shigo ya ce barci take yin nan, kai Chuchu ma fa ƴar duniya ce wlh, tasan komai kawai shiru take yi. A karo na uku ya sake knocking, shiru da ya ji ba alamar motsi ne yasa ya murɗa handle ɗin kofar ya tura ya shigo. Daga bakin kofa ya ɗan tsaya yana kallonta, kowani ɗansa yasan kalar perfume ɗin da yake amfani da shi, saboda yawan zaman da suke yi a tare da shi, so ya ji mamakin jin kamshin perfume ɗin Jawad a cikin ɗakin, ga shi kuma ya ga Chuchun barci take yi. A ransa ya furta zan kamaka ne, da ni kake yi Jawad, wato idan mun ce maka kana son Jannat sai ka ce mana ba haka ba, ko jiya mun yi maganar nan da Abbas, shi ma ya kafe a kan lallai son Jannat kake yi, in muka yi maka magana kuma sai ka ce mana bahaka ba, amma ka iya zuwa mun ɗakinta cikin dare ku sha hira ba? Ina nan lokacin yin maganinka ya yi, Allah ya kaimu da safe. Karisawa ciki ya yi yana zancen zucin nasa, cike da so da kaunarta ya haye saman bed ɗin, tana jinsa ya fara tofa mata addu'oi kamar yadda ya saba yi masu kullum. Bayan ya kammala a fili ya furta Allah ya yi masu albarka ya cigaba da basu kariya. A cikin zuciyarta ta amsa mashi da amin. Ƙasa ya sauko ya nufi waje. Yana fita Jawad ya fito, a saman bedside drawer ya zauna tare da faɗin. "Gaskiya ya isheni wasan ƴar tsere da nake yi da dad, dole na ɗauki mataki a yanzu, dole kawai na gaya masu gaskiya dan su mallaka mun ke na huta ki huta". Shiru ta yi bata amsa mashi ba, ta yi kamar ta yi barci da gaske. Hannunsa ya kai ya yaye bargon da ta kudundune a ciki. Idanunta a datse kamar mai barcin gaske, sai dai kuma shi barcin karya asirin mutum tonuwa yake yi ida ya yi shi. "To kaunaty sai ki buɗe idanun naki ai, bama ki iya barcin karyar ba, ji yadda eyelashes ɗinki suke kerma". Can ƙasan maƙoshinsa ya yi maganar. Turo baki ta yi, ba tare da ta buɗa idanu ba ta furta. "Kai Yah Jawad me haka ne wai? Na yi barci na kazo ka tasheni". "Tom shikenan ayi hakuri, cigaba da barci ni ma bari na je nayi nawa barcin". Jin ya furta kalmar tafiya ne yasa ta yi saurin waro idanu tare da miƙewa zaune. "Kai Yah Jawad dare fa bai yi sosai ba, yanzu karfe 12 ma bata cika ba ne zaka tafi?". A shagwaɓe ta yi maganar. Cikin zolaya ya ce. "Awww dama a duniyar mafarki ma akwai time ne? Ko dai yanzu kam kin gane ba mafarki bane?". Hannu tasa ta rufe fuska na rashin kunya tana ɗan sakin murmushi, kumatu a kumbure cike da iska data hura ta ce. "Kai Yah Jawad nasan ba mafarki bane yanzu, kuma ni ka dai'na tsokanata". "Eyyeeee Jannat matar Jawad, dan ni aka haifeki, kin ma ji sunanmu kusan iri ɗaya, Jannat and Jawad". Yana magana yana murmushi cikin sigar zolaya. "Kai Yah Jawad ni ban san yaushe ka zama haka na". Ɗan matsowa kusa da ita ya yi. "Tun lokacin da Jannat ɗita ta fara girma na zama hakan". Kamar mai raɗa ya yi maganar. Pillow ta ɗauka ta jefa mashi a fuska tana ɗan dariya maras sauti sosai. Bai bari pillown ta sauƙa a face ɗin nasa ba ya riƙeta tare da ɗan kara matsowa kusa da ita. "Idan kina turo mun wannan ɗan bakin kina sakawa na ji ina buƙatarsa, kwanta ki yi barci sai da safe". Yana kai karshen maganar ya miƙe tsaye. "Yah Jawad meyasa zaka tafi yanzu?". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. "Saboda dare ya yi". Ya bata amsa a takaice. "Tom shikenan ka kula mun da kanka, sannan ka yi mafarkina". Jinjina mata kai kawai ya yi alamar to ya ji, baya son sake yin magana dan kada ta tsayar da shi. Kwanciya ta koma ta yi ya ja bargo ya rufa mata izuwa wuyarta, sannan ya tofa mata addu'oi kafin ya manna mata sumbata a goshi. Kofar fita ya nufa ba tare da ya sake furta kalma ba, da kallo ta bishi har ya fice ya rufo mata kofa. Yana fita ta miƙe ta ɗauko remote daga cikin drawer bedside, kashe wutar ɗakin ta yi, ta koma ta kwanta bayan ta ajiye remote ɗin. Yana shiga room ɗinsa shi ma ya haye saman bed, sai dai kuma ya ƙasa iya yin barci, tunaninta ya tsaya mashi a rai. Kamar yadda ya ga rana haka ya ga dare......... To asuba ta gari malam Jawad namu na zamani jikan Akka tamu ta amana. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ Shirye suke cikin uniform ɗinsu gabaɗaya ƴan'matan, suna zaune a saman dining table chairs dake part ɗin King, su momma kowa yana zaune, Akka ma tana wajen, yau sun haɗu fa, ga uncle Jahiz and uncle Abbas. Sai kallon uncle Jahiz mammie take yi tana ayyana yadda zamansa zai kasance shi da Aliya bayan an haɗasu aure. Ita kuwa Aliyah ayyanawa a ranta take yi yadda zamanta zai kasance da King Zuhair.........E lallai waɗan nan sun yi nisa, akwai cakwakiya gaskiya. Cikin nutsuwa suke cin abincin nasu, gabaɗaya room ɗin tsit kake ji, babu abin da yake tashi a cikin face ƙarar spoons. Kuyanga Zubaida sai aikin serving ɗinsu take yi, duk wanda yake da bukatar zai ƙara wani abin haka zata ƙara mashi. Guyson dai yana zaune kusa da Mommarsa, har da wani ɗan kwantar da kansa a saman shoulder ɗinta, kamar kullum ya dauki wannan kwalliya tasa mai ruɗar da masu kallo su yi ta santin kyansa, kansa sanye da hular sanyi mai gashi sosai a jiki, ya yi shiru baya ma cin abinci, shagwaɓa kawai yake ta aikin zubawa Mommar tasu tana biye mashi, dan son da take yi mashi na daban ne, musamman ma yadda ta sha wahala a kan na wannan ciwon cikin nasa, shiyasa yake manne mata, saboda ya saba idan ta je Dubai ciwonsa ya tashi to wlh duk girman nan nasa yana saman jikinta, ko lafiyarsa lau ma yana jikinta kullum abinsa. Yaki cin abinci wai sai anjuma around 9 zai yi breakfast sai ya sha magungunarsa, dan dole suka haƙura suka kyalesa, amma sun so ya yi breakfast a lokacin. Rizwan yana cikin room ɗinsa yana zuba barci, bai fito ba, dama shi baya cin abinci a tare da su, shi kansa Jawad idan baku manta ba tafiyar Jaish yasa ya fara shiga cikin iyayen nasa suna ci a tare domin ya rage kewar ɗan uwan nasa. Shirye cikin wani irin luxury pea long coat, daga ciki kuma tuxedo shirt ce mai bala'in kyau fara tas, ƙasa kuma blue jeans ne kalar pea coat ta sama. Ya shigo wajen, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ɓarin perfume a jikinsa, bakinsa a ɗauke da cikakken sallama, cikin nutsuwa ya shigo. King and Uncle Jahiz har suna haɗe baki wajen amsa mashi sallamar. Sai a lokacin da ta gansa ne ma Akka ta tuna da dalilin da yasa ta kira su uncle Jahiz su zo, wannan yakin da aka yi yasa ta manta da dalilin, amma yanzu ma da ta tuna bata yi maganar ba, dan yanzu suna cikin tashin hankali na ɓatar Spender daga hannunsu, yanzu ta Spender take yi ba tsayawa wani shirirta ita da jikokinta ba. Tun da ya shigo take ta aikin satar kallonsa, ya yi kyau sosai, da alama office zai tafi, shi kuwa da yake ba kunya ne garesa ba, tun da ya shigo idanunsa a kanta, sai kallonsa King and Uncle Abbas suke yi ko a jikinsa. Kusa da uncle Jahiz ya zauna yana ɗagawa King gaisuwa, bayan sun gaisa sai ya dagawa uncle Abbas sai uncle Jahiz, sannan ya gaida Akka, da yake tana cikin tashin hankali sai bata tsaya wasa da shi ba, kawai ta amsa gaisuwar a takaice. Ya yi tunanin ko dai gigin tsufarta ce yau ma ya tashi take share mutane, hakan yasa bai wani damu da ganinta so silent ba, ya cigaba da gaisawa da iyayensa. Gabaɗaya jikokin nata sun sha madarar mamakin ganin yadda yau ta amsawa Yah Jawad gaisuwa kai tsaye kuma cikin sanyin murya ba tare da sun kai ruwa rana ba, abin da mamaki sosai gaskiya, a cikin jikokin nata kuma babu wanda yasan da batun ɓatar Spender, bama su san menene shi Spender ɗin ba. Dannewa ya yi ya ɗagawa su momma nasu gaisuwar, sannan suka yi musabaha da uncle Taheer. Umarni ya yi wa kuyanga Zubaida a kan ta zuba mashi abinci da sauri dan zai fita ne. Uncle Abbas ne ya ce. "Jawad ina Rizwan?." "I think bai tashi ba daddy". Ya bada amsar yana ɗauko spoon ɗaya daga cikin waɗan da kuyanga Zubaida ta jeresu a wajen. Cikin nutsuwa ya fara cin abinci, sai satar kallonsa take yi, shi kuwa tsaboda tsokana sai ya fara yi mata abin da ya saba yi mata idan suka zauna saman table, wato ya yi ta taɓa mata kafafunta da nasa kafar ta ƙasan table ɗin. Duk abin da suke yi wlh King yana ganinsu tsab, kuma ya ci alwashin yin wani abin a kan hakan, jira yake yi su gama cin abinci zasu je su tattauna da uncle Abbas and uncle Jahiz a kan hakan, daga nan sai su yanke hukuncin da ta dace. Sai da suka kammala cin abincin ne ya miƙe da nufin ya tafi office, dan sauri yake yi. "Zauna ina da magana". Cewar King Zuhair. Komawa ya yi ya zauna. "Gabaɗaya ku bani hankalinku a nan". Cewar King again. Gabaɗayansu nutsuwa sosai suka yi, suka tattara mashi hankulansu haɗe da kallonsu a kansa. Ɗan gyaran murya ya yi tare da gyara zamansa, cikin ƙasaita ta jinin sarautar haɗe da a dake ya fara magana kamar mai bada umarni. "Sarina, Fanan and Aneesa ku shirya zuwa yamma zaku yi baki". Ya yi maganar idanunsa a kansu dan yaga reaction ɗinsu. A fujaje Sarina ta zaro idanu, kamar zata yi kuka ta ce. "Dad baki kuma? To su waye?". Fanan da Aneesa kuma kallon kallo suke fara yi wa juna haɗe da bin fuskokin iyayen nasu ma da kallo. Cigaba da yin magana ya yi ba tare da kawar da kallonsa daga kansu ba. "Na samu takarda daga masarautu daban daban a kanku, ɗa ga sarkin Sudan ya turo mun sako yana neman wa ɗansa alfarmar a bashi dama yana son Sarina, a taron da aka yi jiya suka samu damar ganinku, so sun nemi alfarmar zuwa su haɗu da ku". Ya ɗan dakata da yin maganar yana kallon fuskokinsu gabaɗayansu har da iyayensu mata. Duk cikin room ɗin face ɗin mama, Mammie and uncle Jahiz ne kawai suka nuna alamar basu ji daɗin maganar ba. Shi uncle Jahiz abin da yasa bai ji daɗin hakan ba shi ne, a ganinsa an yi masu sauri, wai basu girma ba, Sarina almost 20 to 21 years take da shi a yanzu a duniya, amma haka yake cewa basu girma ba, dan kawai shi boko tafi arabiya yawa sosai a kansa, kuma shi girman cikin turawa ne ba larabawa ba sai yake ganin aibun hakan. Ni kuwa nace to yau dai su Omaid basa nan waye zai taya Sarina koran wannan ɗan sarkin da zai zo? Akwai matsala to! Za dai muga ya zasu kaya, dan dai da alama ba zata so shi ba tun da ta fara da complain tana ɗaure fuska. Cigaba ya yi da cewa. "Ƴaƴan sarakuna ne mabanbanta suka nuna sha'awarsu na son haɗa danganta da mu, sai dai sai da na zaɓi waɗan da suka dace ne na basu izinin su zo ku gansu su ganku ku tattauna a tsakaninku, dan haka sai ku shirya". Dawo da kallonsa a kan Momma ya yi, ba tare da ya basu izinin yin magana ba ya ɗaura da cewa. "Rahilarh kema fa aiki ya ganki sai ki shirya". Ɗan zaro mashi idanu ta yi tare da cewa. "Aikin kuma? To aikin me?". Tsayar da kallonsa a kanta ya yi. "Aiki a kan shirya Autata mana, a saƙon ai harda ita, ɗa ga sarkin Egypt wai ya ganta kuma yana so". Kun tuna guy ɗin da ya bisu lokacin da ta fita daga cikin taro ita da Hoorain? To shi ne ya matsawa babansa a kan a nema mashi izinin ganawa da ita haɗe da aurenta, ya bi ya matsa shi da gaske yake yi har sai da aka yi mashi abin da yake so ya sakar masu mara suka samu damar yin fitsari. Ai uncle Abbas bai san lokacin da dariya ta kubce mashi ba, wai ƴar Autar nan ce da yanzu take kirgan dangi ne wani zai wani turo ya ce a nema mashi izinin ɗansa na so?. To me zai aura a nan? Ita Auta yanzu yaushe ma tasan wani aure bare soyayya fisabilillahi?. Ni kuwa nace tab aikuwa ba yaran yanzu ba, dan ku kuna can kuna wasu tunaninku na banza Auta kam ta jima a cikin kogin kaunar Hoorain ma idan baku sani ba, ai yaran yanzu da sanin komai ake haifarsu ato........😂 Uncle Jahiz kuwa bakincikin ne ya hanasa furta kalma, dan sai ya ga abin nasu ma kamar da rai'nin hankali a ciki, idan ba rai'nin hankali ba yaushe yarinya kamar Autar nan zasu wani ce suna neman izinin aurenta fisabilillahi? Abin sai ya bakanta mashi rai, kawai dai baya son yawan magana ne yasa bai tanka su ba, dan idan ya ce zai buɗe baki to babu wanda zai ji da daɗi a wajen, kuma shi da alama ya fi King and uncle Abbas ɗaukar zafi da wuri, da alama shi ne ya ainahin gadar King Abdul Malik, wato marigayi babansu kenan. Yah Jawad da ransa ya ɓaci shi ma a kan batun autar ne ya ce. "Dad Auta kuma? Amma dai wannan bashi da hankali ko?". Uncle Taheer da ya gama zuwa har wuya da ɓacin rai ne ya ce. "Dad ga dukkan alamu bashi da hankali ko dai babu ƙwaƙwalwa ma a cikin kansa mai gabaɗaya, idan ba dabbanci ba yaushe Auta ta isa aure? Kuma ko ta isa aure ma sai aka ce mashi bata da masu sonta ne da zai wani gwada mana shi ya isa?". Sarai Momma ta fahimci maganganun uncle Taheer akwai wata a ƙasar zuciyarsa, shi kansa King ya fahimci haka duba da yadda uncle Taheer ɗin ya wani harzuƙa ya hayayyaƙo da masifa kamar anfaɗi wani abin da ba dai'dai ba, daga tambayar aure ai ba bashi aka ce za'ayi ba yake wannan surfen masifar. Shi ma Yah Jawad ya fahimci ina uncle Taheer ɗin ya dosa, shi kuwa uncle Jahiz da ra'ayinsa baya son auren wurin sai ya yi tunanin kawai halinsu ne yazo iri ɗaya da uncle Taheer ɗin, bai kawo komai a ransa ba!. Su Sarina da suke zaune shiru ne Mummy ta ce su tashi su je abinsu, su tafi kada lokacin tafiya school ya wucesu su yi latti, su dai su sani suna da baki da yamma kamar yadda dad ɗinsu ya faɗa. Ai tun mummy bata kammala dasa aya a zancen nata ba Sarina ta miƙe rai a matuƙar ɓace tana wani uban turɓune fuska ta nufi waje, a ranta tunanin yadda zata yi da guy ɗin idan ya zo kawai take yi, dan wlh ita ba wanda take so face babban yayansu kamar yadda mamminta ta kwaɗaita mata aurensa, in bashi ba ba ita ba aure a duniya, saboda shi take koran samari in suka zo, shi da bai san da zamanta a duniya ba amma ta mallaka mashi kanta gabaɗaya. Zan so ganin wannan cakwakiya wlh, mammie wlh muguwar silent killer ce ta ƙarshe ma kuwa, ta iya haɗa boma bomai. Fanan ce ta rufa mata baya ita ma rai a ɓace, dan ita idan baku manta ba Jaish take jira ya dawo su yi aure kamar yadda mammiesu ta tsara mata, tashin hankali akwai fa kura. Anya Fanan zata yarda da wannan yariman kuwa? Shin Mammie zata yarda? Zata karɓi sabbin surakanen nata kuwa?. Aneesa and Chuchu ne suka rufa masu baya, auta kuma uncle Jahiz ne ya miƙe tare da riƙe hannunta ya ce su je, dan shi ba zai tsaya jin wannan kayan haushin ba, yana ɓata rai a kan za'ayi wa su Sarina auren wuri, ashe bai sani ba ga kayan haushi kam na Auta. Kallon Mommyn King ya yi. "Sai ki shirya masu komai, na basu izinin zuwa wajen Sarina Fanan and Aneesa, ban da Auta, dan bata kai aure ba". Guyson ne ya ce. "Dad koma ta isa aure ita ba zata yi ba, dan ba wani katon da ya isa ya zo ya rabani da ita, su kara gaba, Auta tana nan tare da ni". Ba ƙaramin dariya ya basu ba, sai dai King ɗan siririn murmushi kaɗan kawai ya yi tare da mai do da kallonsa a kan Akka, Allah sarki lallai ba shakka duk yadda aka yi Spender yana da matuƙar girma da amfani a tattare da su, dan kuwa abin da zai sanya Akka yin laushi haka a gaskiya ba karamin abu bane, ɓatar Spender ya jefata cikin tunani da damuwa, yanzu tsabar tunanin da take duk hiran da suka yi a saman table ɗin nan bata jinsu. Allah sarki ita ta san babban haɗarin da yake tare da Spender shiyasa ta damu, addu'a take yi kada Allah yasa ya faɗa a hannun azzalumai waɗan da suka san amfaninsa, idan hakan ya faru za'a samu gagarumin matsala, ta yi wa King Abdul Malik alkawarin ba zata taɓa barin ya shiga hannun mutanen kirki ba ma bare azzalumai, domin cika alkawarinta da ta ɗauka yasa ta bawa King Zuhair dan ya ɓoye shi, rana tsaka kawai ace babu shi ai dole ta shiga tashin hankali, haɗarinsa ya wuce duk yadda kuke tunani. Idan yana hannun mutun su kansu aljanu tsoron isa in da kake zasu yi, ba abin wasa bane, King Abdul Malik ɗin ma mahaifinsa ne ya ainahin kirkireta domin karin karfin ikonsa a mulki a zamaninsa, abin dai a takaice ba abu bane da zasu yi wasa da shi. A saƙon da aka turo domin neman auren su Sarina har da Chuchu a ciki, ita Chuchu da Auta ma wajen yarimomu daban daban har sama da biyar ne suke neman aurensu, amma King bai bayyana har da Chuchu a ciki ba, ya ɓoye masu Momma, sannan ya sanar da masu neman auren nata a kan already ya yi mata miji. Miƙewa Jawad ya yi yana duba agogo kamar wani mai gaskiya, da sauri ya nufi waje. Da kallo dad and uncle Abbas suka bisa. Yana fitowa kai tsaye room ɗinta ya nufa. Tana ƙoƙarin fitowa riƙe da katan school back ɗinta suka ci karo shi kuma zai shiga. "Ina kwana Yah Jawad?". Ta yi maganar kai a ƙasa, dan yanzu ita kunyarsa ma take ji, kuma ta yi maganar tana ɗan ja da baya. "Wato haka zaki tafi school baki nemeni mun ga juna ba ko?". Kai ta fara girgiza mashi tare da faɗin. "A'a ai na ganka a dining room yanzu". Cikin sanyin murya ta yi maganar. Jinjina kai ya yi. "Amma ai ni wannan kallon bai wadaceni ba! Ko dai baki damu da abin da zai wadaceni bane?". A hanzarce ta girgiza mashi kai alamar a'a, sannan ta ɗaura da. "Nadamu sosai ma". "Okey muje na kaiki school ɗin kafin na wuce office ko?". Kai ta gyaɗa mashi alamar to. "To ba za'a ɗago kai mu kalli juna bane my kaunaty?". Ai bata san lokacin da cool murmushi ya ƙubce mata ba, ba ƙaramin kyau ta ƙara ba da ta yi murmushin, ita school ma za'a je sai an sanya su lips balm, kai Chuchu duniyar gayu ce. "Kai Yah Jawad zaka fara ko? Ni ka dai'na kada nazo na yi latti, su Aunty Sarina sun tafi sun barni". Ta kai karshen maganar tare ɗan ɗago kanta, ta sauke kallonta a kansa. Suna haɗa idanu suka sakarwa juna haɗaɗɗen murmushi mai kara haɗe juƙatan masoya su cure su zama abu guda. _____________________________🦋🔥 "Ke Chuchu zaki zo mu tafine ko kin tsaya a nan kina ɓata mana lokaci? Ina da class by 8 daidai, yanzu kuma 7:35 yaushe zamu isa har na san abin yi kina wani tsaye a nan........." Sarina dake bayansu wadda ta zo yanzu ne ta ɗauko wannan masifa, sai dai bata diresa ba ya juyo da kallonsa a kanta wanda hakan yasa ta haɗiye sauran maganar a cikinta ba tare da ta shirya ba. Wani irin kallo ya wurga mata wanda ya sa ta haɗiyar yawu da kyar, ƴan kame kame ta fara yi tana addu'ar Allah yasa kada ya yi mata komai. "Ka yi hakuri Yah Jawad". Ta faɗa tana ƙoƙarin juyawa ta bar wajen. "Aunty Sarina ku je Yah Jawad ya ce zai kaini da kansa". Cewar Chuchu. Ai cikin girmamawa da mutumtawa ta amsa mata da okey, yau ba tsawa da tsiwa, Chuchu ta zama Auntynta a gabansa, da baya nan rashin mutunci zata yi mata, dan Sarina wlh ba dai masifa ba. "Muje ko?". Ya faɗa yana kai hannu ya karɓi school back ɗin nata, shi ya riƙe mata suka nufi wajen mota. Su Sarina kuma drivern da ya saba kaisu ne ya ɗaukesu, sai kallonsu Sarina take yi tana mamakin yaushe Yah Jawad ya zama haka Chuchun bata gaya masu ba?! Ta ci alwashin in dai suka je school sai ta tambayeta me a tsakaninta da Yah Jawad ɗin. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ A can cikin gida kuwa zaune Momma take a cikin room ɗinta bayan sun kammala hiran da suke yi a dining room kenan, kowacce ta wuce nata part ɗin. Kuyanga mama Haulat ce zaune a gefenta ƙasa saman carpet, while ita kuma tana saman sofa. Cikin sanyin murya ta ce. "Ranki ya daɗe asirin da kika jima kina rufewa Mammien tana shirin bankaɗosa, tana ta ƙoƙarin bincike a kan". Ta kai karshen maganar kanta a ƙasa cikin girmamawa. Shiru ta ɗan yi na ƴan mintocin kafin ta ce. "Dama nasan za'ayi hakan, nasan ba dan Allah take sona ba, nasan da biyu take zuwa nan, hankalina bai kwanta da ita bane yasa na sa ki saka mun ido a kanta". A fujaje kuyanga mama Haulat ta ɗago kanta tare da zaro idanu tana kallon Mommar, while ita ma Momma ita take kallo........ A dai'dai lokacin ni kuma nace bari na leƙa Jimeta Yola Nigeria na dawo. To amma my people's wani irin asiri kuke tunanin Momma take ɓoyewa da har bayyanarsa zai iya zama babbar tashin hankali ga kowa dake cikin kingdom ɗin? Akwai kallo a gaba, kada dai ku matsa daga in da kuke, a cikin wannan lokaci kada ki yarda ki yi missing na koda rabin page ne, dan ki kalli wannan cakwakiya da idanunki ba ki ji labari ba. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ JIMETA YOLA_________✍️🔥🦋 Ganin ta yi mashi suman tsaye ne yasa ya saki hannun nata tare da tray ɗin. Yana sakinta ta zube ƙasa kamar gawa, aikuwa tana faɗiwa tray ɗin ya kwaɗe mata kanta ya kuma rufe mata fuska. Dawo da kallonsa a kan Mahnoor baiwar Allah da ta tsare shi da idanu ya yi, hannu ya............ Kana naka Allah na nashi, my people's bana jin daɗi, zazzaɓi kamar me, da kyar na iya yi maku wannan page ɗin, idan Allah ya bani lafiya zaku ga update gobe, ku tayani da addu'a, zazzaɓin nan ta addabi kowa, Allah ya bamu lafiya gabakiɗayanmu. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 11/11/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 36 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ JIMETA YOLA_________✍️🔥🦋 Ganin ta yi mashi suman tsaye ne yasa ya saki hannun nata tare da tray ɗin. Yana sakinta ta zube ƙasa kamar gawa, aikuwa tana faɗuwa tray ɗin ya kwaɗe mata kanta ya kuma rufe mata fuska. Dawo da kallonsa a kan Mahnoor baiwar Allah da ta tsare shi da idanu ya yi, hannu yasa ya nuna mata hanyar tafiya, a kan ta tafi abinta. Da sauri ta bar wajen har kamar zata kifa ƙasa. Shi ma juyawa ya yi ya bar wajen bai ƙara bi ta kan Nenne ba. Suna barin wajen bai fi da ƴan mintoci ba sai ga bappa ya shigo cikin gidan, ya je ya duba Faisal, bawan Allah dai jikinsa har yanzu, soyayyar Mahnoor tana neman zautar da shi, bayan sunanta yaki yarda ya furta ko wace iriyar kalma, Mahnoor, Mahnoor kawai yake kira. Bappa zuciyarsa ta fara karaya, ji yake yi tamkar yasa Jaish ya saketa, dan kuwa ba zai iya jurar ganin halin da ɗan nasa yake ciki ba, kuma ba karya dan ya yi hakan ba wani abin bane, fin haka tana iya faruwa da shi, domin kuwa soyayyar da ta faro tun daga yarinya ai wlh kun san ba ƙaramar so bace, tun yarinta fa! Wlh Faisal yama yi ƙoƙari da ƙwaƙwararsa har yanzu take iya kira mashi sunanta bai zauce gabaɗaya ba. Sai dai idan kuma bappan ya waiga ya waigo ya tuna cewa Mahnoor da Jaish ɗin fa suna son junansu, nan kuma sai ya ji ba zai iya raba auren ba saboda kada marainiyar Allahn nan ta shiga damuwa. Kun tuna lokacin da bappa ya gansu a bakin kofar ɗakinsa? Ai a lokacin na gaya maku yana zargin soyayya suke yi ko? To wannan ita ce kaɗai hujjarsa na cewa ai san junansu suke yi yasa ba zai iya raba su ba. Wlh duk wanda ya ga halin da Faisal yake ciki sai ya tausaya mashi, tun jiya yaki ya sanya komai a bakin salati, ba yadda ba'a buga ba yaki, idan ma ka yi mashi magana sai ya ce maka Mahnoor kawai, bayan wannan Mahnoor kawai da yake faɗa baya kara komai. Iyayensa sun yi sun yi amma ina yaki sauraran kowa, yanzu da bappa ya je wajensa kuka yake yi da hawaye bibbiyu, ya riƙe kafafun bappan yana haɗasa da girman Allah da kada ya raba shi da Mahnoor, iyayensa sun yi mamakin jin yadda yake roƙan bappa, dan su idan ba sunan Mahnoor ba yaki ya yi magana da su, amma yana ganin bappa ya fara rukonsa yana kuka. Ga shi bappa bai isa ya bashi Mahreen madadinta ba, saboda basa shiri, wuta ne da auduga su ɗin, ba zasu taɓa haɗuwa inuwa guda ba, idan aka haɗasu gida ɗaya wlh tsab zasu tashi kauyen nan su hana kowa yin barci, kai ita fa Mahreen uwar watsice, dan ta watsa kowa ƙaramin aikinta ne. Bappa bai isa ya kawo batun bashi Mahreen ba, Arɗo ya gwada ce mashi ya bashi Mahreen madadinta mana, ya ce a'a kawai, dan ba wanda yasan irin kiyayyar da take tsakaninsu sai shi. Shi kansa Faisal ɗin ba zai taɓa yarda a haɗa shi da ita ba, dan wlh kullum addu'a yake yi Allah yasa su dai'na haɗuwa inuwa guda da ita, shi kansa shakkar bala'in masifarta yake yi, to ina ga kuma an haɗasu aure? Fisabilillah ku gaya mun ya rayuwar Faisal zai zama a gabanta? Yanzu ma bata ga wajen kwanansa ba, tana ganinsa da sutura a jiki ma ya aka kare da uban rai'nin da ta yi mashi, bare ace ta gama ganin komai nasa! Ai wlh ya shiga uku, kai yama shiga dubu uku ba uku ba, dan Mahreen sai ta kwance mashi notikan ƙwaƙwalwa gabaɗaya tasa ya zama zazzare da gaske. Kuna gani dai faɗa take yi a kan kada ƴar uwarta ma ta auresa bare ita!. Shiyasa ya shafawa kansa ruwan sanyi yake ta aikin tunanin ya zai yi da wannan al'amari, kansa ya ɗau zafi...... Ni kam nace ka cigaba da addu'a Allah zai kawo maka mafita cikin ƙanƙanin lokaci, idan raba auren ne mafita, to cikin sauki Allah zai kawo maka hanyar da kowa ba zai wahala ba, ai kawai ka barwa Allah zaɓi ka zuba idanu kaga sakamako. Ganin Nenne a sume a ƙasa yasa bappan ƙarisowa wajen da sauri yana tambayar me yafaru kuma?. Ganin babu kowa a tsakar gidan ne yasa ya fara kwalawa Mahnoor kira. A lokacin ta fita ta bayan ɗakinsu ta nufi wajen dabbobin nasu dan ta kamo awakin Nennen ta dawo mata da su cikin gida kamar yadda ta saba. Jin Mahnoor bata amsa ba yasa ya fara kwalawa Mahreen dake barci kira. Ina ai ko alamar jinsa ma bata yi ba, tana wata duniyar a barci. Shi kuwa Jaish yana ɗaki yana jinsa, fitowa ne kawai ba zai yi ba, dan yasan ihun sunansu a kan me yake yi, dan haka bashi da lokacin bi ta kan wannan matar. Jin duk babu wanda ya tanka shi ne yasa ya fara ƙoƙarin yadda zai farfaɗo da ita. Kitchen ya shiga ya ɗabo ruwa a moɗa. Da azama ya zo ya yayyafa mata a fuskar yana salati, duk ya ruɗe. A haukace ta tashi tana faɗin. "Na shiga ukuna shikenan rayuwata ta zo karshe, zai shanye mun kurwata na mutu, dan Allah baffana ka kawo mun ɗauki". Tun da ya ji irin sambatun nan da take yi ya fahimci ita da Jaish ne, tunani ya yi wata kila hanya ce ta haɗosu har ta sume, sam bai kawo cewa Jaish ya yi niyar ramawa Mahnoor zaluncin da take yi mata bane, saboda bai ma san tana yi mata ɗin ba. Cikin nutsuwa ya ce. "Babu abin da ya sameki, kuma shi Hamman nasu ma baya nan ya yi wucewarsa, ke kincika tsoro, sai ki tashi ai, na gaya maku na kara gaya maku wannan bawan Allah ba azzalumi mugu kamar yadda kuke tunani bane, bawan Allah ne, amma kunki yarda, yanzu sai ki gaya mun da hanya ta haɗaku ɗin ba ga shi kin tashi lafiya lou ba? Ko akwai in da yake maki ciwo? Kin wahalar da kanki wajen suma a banza!". Ya kai karshen maganar cikin faɗa yana ɗaure fuska. Wani irin kallo uku saura kwata ta wurga mashi kafin ta miƙe ta fara karkaɗe jikinta na ƙasa da ya buɗeta, cikin tsiwa ta fara faɗin. "To kai yanzu me ya dameka? Ina ruwanka da tsoronsa da muke ji? Sai ka rabu da mu ai tun da kai ya rigada ya shanye kurwarka ka zama nasu, ni bari ma nazo na haɗa kayana na yi gidanmu, dan kai ma yanzu ban yarda da kai ba, dole kai ma maye ne irinsa, idan ba haka ba meyasa komai zai yi a ƙauyen nan zata zama matsala amma banda tarayyarsa da kai?!". Tana magana tana kwaɓe fuska tana kuma harare harare, ta daiki yarda su haɗa idanu, sai ta rinƙa hararar gefe gefensa kamar dai tana jin tsoronsa. Miƙewa tsaye shi ma ya yi tare da faɗin. "Menene kuma ya yi a wannan ƙauye da ta zama matsala ban da tarayyar tamu?". Cike da mamaki a face ɗinsa ya yi maganar. "Kafini sani ai tun da jinsinka ne, kana gani da ya mari yaron Inna Rabi mai islamiyya sai da yaron nan ya yi ciwo, sannan yanzu ya mari Faisal jiya shi ma ga shi can kwance an rasa gane kansa". Mamaki kamar zata kashe shi ya ce. "Amma dai Nafisa baki da hankali, Allah ba zai saukowa da bayinsa jarabawa ba? Yanzu waye ya ce maki saboda marin da ya yi wa ɗan wajen Rabi ne yasa ya fara ciwo? Sannan shi kuma Faisal ai ciwonsa a bayya ne yake, kina dai ji sunan Mahnoor da yake kira ko ita kaɗai ta isa tasa kowa ya fahimci ina ciwon nasa ta dosa, ko kin ji yana kiran sunan Hamman nasu ne? Wai meyasa ku baku da adalci ne wani lokaci?". Cikin nutsuwa ya kai aya a maganar. Cikin tsiwar nan dai nasu ma gadon masifa da faɗa ta ce. "Sai kuma ka yi, kanka ake ji, ni dai ba zaman a gidan nan zan yi ba koma me zaka ce, bari ma kaga tafiyara". A takaice ya ce. "To Allah ya bada sa'a". Yana kai karshen maganar ya juya ya bar wajen. Mamaki ne ya kamata, bata yi zaton zai ce mata ta je ba, ta yi zaton hakuri zai bata ita kuma ta yi mashi walaƙanci dan ba son shi take yi ba, sai ta ji ya ce Allah bada sa'a. Jikinta ne duk ya mutu, bata taɓa zaton hakan ba, dan haka sai ta wuce sumumui sumumui kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tsaye take a gaban garken dabbobin nasu tana tunanin rayuwa, tana tunanin yadda aka rabata da Hammanta Faisal wanda take masifar so. Daga ta bayanta ta ji an yi mata sallama. Da sauri ta juyo da kallonta. Ƴar matashiyar yarinyar Inna Rabi ce, yarinyar da zata iya kai shekaru 14 zuwa 15 haka, da kaɗan ta fi Mahnoor ɗin girma. "Ina kwana Mahnoor". Yarinyar ta faɗa tana kallonta. "Lafiya lou jumma, yasu Inna?". Da lafiya ta amsa mata kafin ta ɗaura da cewa. "Mahnoor na ji daɗi da Allah yasa aurenmu zai kasance a cikin sati guda, wannan chewing gum ne na kawo maki, kada ki gayawa kowa na sayesa, jiya ne da muka shiga birni da bappa na saya dan na bawa kawayena, na aurena ni da bobbo Bello ne". Ta kai karshen maganar murmushi a kan face ɗinta. Ƙaƙalo murmushin dole baiwar Allah ta yi tare da cewa. "Amma gaskiya Jumma na maki murna da Allah yasa kika yi nasarar samun dama zaki auri wanda kike so, Allah ya kai mu jibin Allah kuma ya baku zaman lafiya, na ji maki daɗi sosai, sai dai ni kuma an rabani da Hamma Faisal ɗina, ina jin kamar in yi ta kuka kada na dai'na". Ta kai karshen maganar idanunta a cike da kwallah alamar tana son yin kukar. Matsowa kusa da ita Jumma ta yi, shoulder ɗinta ta dafa da hannu guda, cikin sanyin murya ta fara faɗin. "Mahnoor ki yi hakuri, nasan da ciwo a rabaka da wanda kake so, amma kuma ki sani bappa ba zai taɓa haɗaki da abin da zai cutar dake ba, sanin kanki ne yana kaunarki fiye da kansa, kuma ke ki godewa Allah ma ɗan birni aka aure maki, kin dai san wannan Hamman naku bai yi kalar ƴan rugar nan ba, ga shi kyakkyawa wanda gabaɗaya kauyen nan suke son kallonsa idan ya fito......." Katse mata maganar ta yi da cewa. "Suna son kallan kyansa amma kuma suna jin tsoron haɗa idanu da shi ba". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. "Haka ne muna jin tsoron haɗa idanu da shi, amma ina son ki sani har laɓewa muke yi mu leƙesa dan muga kyansa, wlh ki godewa Allah da wannan ni'ima da ya baki, ni ba dan tsoronsa da nake ji ba wlh da babu abin da zai hanani tinkararsa in ce ina sonsa, yana da kyau sosai, ki duba gashin kansa sam ba irin namu ba, har kyalli nasa yake yi, kai koya zan gaya maki ba zaki gane ba, amma dai yana da kyau ki san cewa kin yi sa'a, wannan ko da haɗi a kwatance ba za'a haɗa shi da Hamma Faisal ba". Shiru ta ɗan yi tana tattauna maganganun a cikin kwakwalwarta, dan ita a gaskiya Faisal take so, da wuya zuciyarta ta yarda da wani bakon. "Kada ki tsaya yin wani dogon tunani Mahnoor, tunani ba naki bane, kawai ki rungumi mijinki ku zauna lafiya, idan ma baya sonki ki koya mashi sonki, idan ma kece baki sonsa to ki koya, yana da kyau ki dai'na tunanin Hamma Faisal a yanzu, yin hakan kin dai san Inna ta ce babban kuskure, da auren wani a kanka kana tunanin wani hakan sam bai dace ba, ba tana karantar da mu hakan a islamiya ba?". Ta jefe mata tambayar tana leƙo face ɗinta, while hannayenta suna a saman shoulder ɗinta har lokacin. "Amma kuma Jumma kin ji fa jama'a suna cewa maye ne shi ɗin?". A tsorace ta yi maganar, muryarta har kerma yake yi. "Ke kin yarda shi mayen ne?". A hankali ta ɗago kai suka kalli juna ido cikin ido, wani irin tausayinta ne ya kama Jumma, tasan yadda zafin so yake, yarinya baiwar Allah, marainiyar Allah, sam kukanta baya da kyan gani ga koma waye ne idan ba bakin azzalumi irin Nenne ba. "Jumma a da can baya na yarda Hamma aljani ne, amma ban taɓa yarda cewa shi maye bane". Tana kai karshen maganar hawayen da suka cika mata idanu ne suka gangaro mata sama face ɗinta gwanin ban tausayi. "A yanzu fa? Kin yarda shi aljanin ne?". Ta sake jefa mata tambayar tana mai da kallonta a kan shanu biyu da suke ƙoƙarin fara faɗa a bayansu. "A'a yanzu na dai'na tunanin shi aljani ne, shiyasa ma na dai'na jin tsoronsa, amma kuma ba zan iya zama da shi ba Jumma, wlh idan ni da shi ne kawai zan ji tsoro, har yau har gobe ina jin tsoron haɗa ido da shi". Tsananta kukanta ya yi a lokacin da ta ce idan shi da ita ne kawai zata ji tsoro. "Shin ya taɓa yi maki wani abin na mugunta ko na ban tsoro ne?". Ta yi maganar tana kai hannu saman face ɗinta dan ta goge mata hawaye. "Bai taɓa yi mun komai na mugunta ko ban tsoro ba, sai dai ma taimakona da ya sha yi, ko ranar da su Hamma Salisunku suka biyoni zasu dakeni shi ya tare mun ya hanasu dukana........". A hanzarce ta tari numfashinta ba tare da ta barta ta kai aya ba ta ce. "Yauwa Alhamdulillah, to kin gani, kinga shi bangone ma a gareki, ki riƙesa hannu biyu zaki sha mamakin kulawar da zai baki, ina mai tabbatar maki watarana zai hana Nenne ma zalincin da take yi maki, ki jarraba ki gani". Tunanin abin da ya faru a yanzu na hana Nenne dukanta da ya yi ne ya faɗo mata a rai, da alamar kamshin gaskiya a maganar Jumma fa, amma to taya zata fara iya zama da shi waje guda? Wannan abu ne mai matuƙar wahalar gaske a gareta. Ganin ta afka duniyar tunanin ne yasa Jumma ta katseta da cewa. "Yanzu abin da nake so dake ki je ki faki idanunsa ki kure mashi kallo anjuma idan kin zo islamiyya sai ki gaya mun me kika ji a ranki lokacin da kika kare mashi kallon". Ta kai karshen maganar tare da kara goge mata hawayen da har yanzu suka ki dakatawa daga zuba. Kai ta ɗago da nufin ta yi mata magana karaf idanunta suka sauka a kansa, yana tunkaro in da suke tsaye hannunsa riƙe da sandar bappa na kiwo, da kuma igiyoyi da zai ɗaure kananan shanu, basa fita kiwo da kananan ciki irin waɗan da suka kusa kai yayen nan, tsaka tsakiya kenan, a haka ake koya masu yaye, za'a rinƙa fita da uwar ana barin ƴaƴan, tun suna kuka har su zo su fara sabawa da rashin shan nonon, a hankali hankali har su manta da shi su dai'na sha, koda uwar ta dawo sai kuga basu wani damu da su zo su sha ba, saboda sun ci abincin da ya dace da su a gidan sun ƙoshi sosai, so basu wani damuwa da nonon, a haka dai har su yaye kansu da kansu daga shan nonon. So ya nufosu da nufin ya ɗaure yaran kafin bappa ya fito su tafi, yau bata dama mashi fura da nono ba ta zo ta tsaya suna hira da Jumma, ko ɗumamen safe bata ɗaura ba, ko wutar ma bata hura ba. "Jumma idan na zo islamiyya zamu ƙarisa maganar ga Hamma nan yana zuwa, sannan In Sha Allah na san bappa zai barni na je dandali shagalin bikinki". Tana kai karshen maganar bata tsaya jin maganar da Jumma zata sake cewa ba ta yi saurin wucewa. Jumma kuwa tun daga nesa ta kafe shi da idanu tana kallonsa babu ko kyaftawa, tamkar taga bako daga wani duniya. A cikin zuciyarta sai santin kyansa take yi, Allah ya gani tana bala'in son ta yi ta kallon face ɗinsa, kun san larabawa da turawa kyan gani ne da su ga daɗin kallo.........😂 Sai dai kuma tana tsoron ya kalleta su haɗa ido, dan haka da ya kusa isowa sai ta yi maza ita ma ta bar wajen ta nufi hanyar gidansu, tana tafiya tana waigosa, shi kuwa in da yasa gaba kawai yake kallo, ko ya ɗago ya kalli amaryar tasa ma yaki har ta zo ta wucesa tamkar bai santa ba. Tana shiga cikin gida ta isko bappa da ya fito daga banɗaki a yanzu, hannunsa na riƙe da buta. Cikin girmamawa haɗe da nutsuwa ta ce. "Bappa ina kwana". Ganin alamar kamar ta yi kuka ne yasa ya amsa da. "Lafiya lou me ya sameki kika yi kuka?". Ƙasa ta yi da kai ta rasa abin faɗa, sai ta fara ƴan kame kame kamar wata maras gaskiya. "Mahnoor ba dake nake yi bane? Meyafaru kika yi kuka?". Fuska a ɗan ɗaure ya sake tambatar tata, dan a duniya babu abin da ya tsaya da ya wuce ya ganta a cikin damuwa. "Babu komai bappa, wani abin ne ya shiga idanu na". Ta bada amsa a tsanake. Ya fahimci karya ta yi mashi, amma bai nuna ya gane karya take yi ba, sai ya ce mata. "Ina hammanku?". Da hannu ta nuna hanyar fita tare da faɗin. "Yana walde". Shiru ya ɗan yi yana tunani a kan abin da ya sanyata kuka, to kenan kukan nata yana da alaƙa da hammansu? Dan yaga waje guda kenan suke, daga wajensa ta fito kenan, to me ya haɗasu ya sakata kuka kuma?. Ya jefawa kansa tambaya yana mai cigaba da zancen zucin nasa. "Bappa in tafi ne? Ina son na je na kunna wuta na yi maku ɗumame kafin ku tafi kiwo". Jin muryarta yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka, dawo da kallonsa a kanta ya yi. "Jeki ki ce Hamman naku ya zo, sannan yau ba zamu je kiwo ba". Da mamaki ta ɗago ta kallesa. "Bappa ba zaku je kiwo ba kuma? To meyasa?". "Saboda bikin aurenki za'ayi, ba zan je kiwo ba zamu zauna ni da Hammanki mu gyara maku ɗaki, anjuma da yamma a dandali za'ayi bikin bidirin aurenki kamar yadda ake yi wa kowacce yarinya a kauyen nan, ba zamu bar al'adarmu ko guda ɗaya ba, kamar dai yadda ake yi tun iyaye da kakannin, ke ma dole za'ayi maki". Zaro idanu waje ta yi, tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa, da yake ita tasan yadda al'adun nasu suke, sai yasa ta ji kanta na juyawa, yanzu fisabilillahi yaushe zata iya aikata irin waɗan nan abubuwa da suke gudanarwa a biki da Hamman nasu, to shi ma zai iya kuwa? Shi da yake sarkin kunya, har yau ya ƙasa haɗa idanu da bappa, yaushe zai iya waɗan nan abubuwa, karami daga cikinsu ne ma bata abinci a baki, wai hakan ne zai sa a yarda zai iya kula da ita, sannan ya goyata a bayansa ya hau saman wani dutse dake kusa da dandanli mai tudun gaske, sai ya kwana yana tafiya bai isa sama gabaɗaya ba, kuma a haka zai ɗauketa a daren ya haura sai gobe da safe zai iya saukowa, a cewarsu wai hakan ne zai tabbar masu da zai iya ɗaukar nauyin ɗawainiyarta, kamar yadda ya ɗauketa ya juri wahalar haurawa da ita sama, ya je can ƙololuwa ya sake dawowa, to haka ɗaukar ɗawainiyarta ba zai yi mashi wahala ba acewarsu. Sannan idan suka sauƙo ga girki da zai yi mata, sannan zai yi mata tsantsarerren kyalliya irin nasu na al'ada da ake yi wa amarya kamar yadda ake yi, ya ɗaura mata ɗan'kwali ɗaurin amarya, waɗan nan kaɗan ne daga cikin al'adun nasu, sai dai mun haɗu a dandali kwaga sauran. Kuna tunanin Jaish zai yarda ya yi dukka waɗan nan shirme kuwa? Wajen sati fa ake ɗauka kowacce rana da abin da za'a gudanar, tabɗijam! Akwai kallo sosai wlh, wayaga Jaish da yi wa Mahnoor kwalliya, yaseen ba mai hanani sai na yi dariyata, ina ma emojin dariyar yake........😂😂 Yo hauka ake da ba zan yi dariya ba, Prince Jaish da kansa da hura wuta ya dafawa amaryar da bai ce yana sonta ba abinci a bainar nasi! Sannan ya yi mata kwalliya, ya bata abin da ya girka ɗin a baki, ga goyata su hau dutse, tun farkon dare suna tafiya har daren sai ta tsala zasu isa, kuma suna isa su sake juyowa su dawo, tab e lallai bappa baka son zaman lafiya, to ni dai ina daga gefe ina kuma kora maltina mai sanyi ina binsu da eyes, babu wanda zai hana ni shan maltina ta kuma in yi dariya ato. Zaro idanu ta yi, tunani ta fara yi a kan lallai za'a samu matsala in kuwa haka ne. Jiki ba kwari ta nufi waje, bappa da kallo ya bita, sarai ya fahimci ta shiga damuwa na jin abin da ya faɗa, amma kuma dole ayi waɗan nan al'adu kamar yadda ake yi wa kowace ɗiya, shi kansa yana fargaba yana ɗari ɗarin yadda zata kasance idan har aka ce Jaish ya yi wannan abin, yana ganin kamar da wuya, amma ba shi da niyar fasawa a ransa. Can wajen dabbobin ta iskosa yana ta ƙoƙarin ɗauresu, yanzu gabaɗaya ya canza, kamar ba Prince Jaish namu ba, har duhu soft skin ɗinsa ta yi, dark black arab hairnsa har ta ɗan yi brown kaɗan, saboda yanzu baya sanya mata mayukansa da ya saba, bata samun gyara sosai, kuma ga shi yaki yarda bappa ya datse mashi gashin nasa, ba yadda bappan bai yi ba amma yaki yarda, ya ce a bar mashi kayansa a haka yake sonta. Cikin sanyin murya ta ce. "Hamma bappa ya ce kazo". Shiru bai motsa ba bai kuma dai'na abin da yake yi ba, tamkar bai ji metace ba. Ganin haka yasa ta kuma cewa. "Hamma bappa ya ce yau ba zaku fita kiwo ba, ba sai ka sha wahalar ɗaure dabbobin ba, ka barsu kawai". A wannan karon cikin harshen fillanci ta yi mashi magana, izuwa yanzu yana jin yaren nasu sosai, baya magana ne da tsab zai iya mayar masu da amsar dik abin da suka buƙata, yawan zamansa da Mahreen inuwa guda ne yasa ya iya yaren sosai, dama ita ai ko baka kaunar Allah sai ta sanya ka fara kaunarsa, yo dan dole yake sauraran hirarta, tun baya gane komai har ya fara fahimtar wace duniya ta dosa dan dolensa. Sai a wannan lokacin ya ɗago kansa jin cewa ba zasu je kiwo ba, idanu ya zuba mata ba tare da ya yi wata alama ba. A yanzu tana fahimtar dik wata motsinsa me yake nufi, dan haka ta fahimci tambaya yake son yi a kan me zai hanasu zuwa kiwo dik da bai nuna alamar hakan ba, baiwar Allah tana da basira. "Ni ma ban san dalilin da zai hanaku zuwa ba, kawai dai ya ce na kiraka ba zaku je ba yau". Ta bashi amsa tana yin ƙasa da kai. Ba zata iya gaya mashi za'ayi bikin aurensu bane, kunya abin ya bata yasa ta yi karyan bata san dalili ba. Aikuwa bai gamsu da maganarta ba, dan kuwa ya gano karya take yi, hakan yasa sai bai motsa daga in da yake ba. Ta fahimci dalilin rashin motsawar tasa, wato gaskiya yake son ji kenan, lallai ma ya iya tsiya shi ma. Kara yin ƙasa da kai sosai ta yi, kunya kamar zata nutse cikin ƙasa ta ce. "Da gaske Hamma ni ban san dalili ba". Still bai motsa daga in da yake ba, dan bai gamsu da zancen ba. Ganin haka yasa ta ji a ranta ko dai ta watsa a guje ta yi cikin gida ta barshi a wajen ne? Tun da ta isar da sako ya ji da kunnensa bappa na kiransa ai dole ya je. Sai kuma ta yi tunanin idan ta yi hakan ai raini ne, bappa ya gargaɗesu sosai a kan rai'na na gaba da su, dan haka bai dace ta yi hakan ba, to ya zata yi? Ita dai a gaskiya ba zata iya gaya mashi shirye shiryen bikinsu ake yi ba. Tana tsaka da tunanin mafita ne sai gani ta yi ya ɗaga hannunsa yana yarfarwa kamar wanda wani abin ya kama mashi hannun ya maƙale. A ɗari ta ɗago da kanta haɗe da kallonta a kansa. Cigaba da yarfar da hannun nasa ya yi yana son cire kaskar jikin shanu da ta maƙale mashi jikin fata tana son shan jininsa, cizonsa ta yi a hannun yasa ya farga da ita. Ai data ga haka bata san lokacin da ta manta da cewa tana jin kunyarsa ba, a fujaje ta matso kusa da shi tare da riƙo hannun nasa. Bai yi kokarin kwacewa ba, saboda dayawan lokuta yana gani idan suka kama jikin bappa ita take cire mashi ta sanyasu cikin wuta, babu kaskar dayawa a jikin dabbobin nasu, saboda bappa yana yawan duba gabaɗaya jikin dabbobin, rana yake warewa a kowace karshen sati ba ya zuwa kiwo, zama yake ya hura wuta kusa da su ya yi ta cire masu kaskar yana sanyawa cikin wuta, hakan yasa basu da yawa, kun san suna yawan maƙale jikin shanu su yi ta shan mashi jini, wanda bai sansu ba wasu irin kwari ne kanana kamar ƙuda da suke maƙale jikin dabbobi suna shan masu jini, sun iya cizo sosai fa. Har kashe shanu suna iya yi idan suka yawaita a jikinta, suna da haɗari gaskiya, sun iya ɓarna, dole ka rinƙ kula da jikin dabbobinka idan ba haka ba su kamu da cuta ka rasa daga ina matsalar take, kan ka ankara idan ka yi wasa sai ka ji dabbarka ta mutu. Zuba mata idanu ya yi yana kare mata kallo a lokacin da take cire mashi wannan kaskar, haka kawai yake jin tausayinta, tana da innocent face, fuskar ban tausayi, ga shi kullum na duniya sai ya ci karo da ita tana kuka Nenne ta yi mata wani bakin izayar, hakan tasa ko bata kuka sai ya rinƙa kallon face ɗinta kamar tana kuka, sai ya rinƙa jin tausayinta yana ratsa shi. A lokacin da ta kama yatsun hannun nasa tana son cire mashi kaskar sai da ta ji kirjinta ya bada dum dum, saboda yadda yatsun nasa suke dogaye kuma gasu ba sirara can ba, ƴan ɓul ɓul dai haka, ga su da haske kamar madara, yau dai ta taɓa jikinsa, duk sai ta ji kamar ba jikin mutun ta taɓa ba, ga wani haske da faratunan hannun nasa suke yi, har wa yau skin ɗinsa is very soft. Kerma hannunta ya fara yi wajen kama kaskar, sarai ya lura da a tsorace take, sai ya basar kamar bai ganta ba. Da kyar ta iya kamar kaskar ta cire mashi, a can gefe ta jefar da ita, sannan ta ɗan ja baya kaɗan daga kusa da shi tana yi mashi sannu, dan kuwa ta cijesa a hannu, ga wajen har ya yi alamar jini. Shi kam face ɗinta yake ta kallo, cikin ransa yake jin kamar ya taɓa rayuwa da ita a wata duniyar, wato tunanin gimbiya Zunaira ce take yi mashi gizo a ƙwaƙwalwarsa ta dalilin ganin face ɗinta a kusa da shi................ Ni kuwa nace anya face ɗin Mahnoor idan ta cigaba da matsowa kusa da shi ba zai sa ya dawo cikin hankalinsa ba kuwa? Kuna dai ganin a duk lokacin da ya ganta kusa da kusa sai tunanin gimbiya Zunaira ta yi mashi gizo, ya rinƙa jin kamar ya taɓa yin rayuwa a wata duniya ta daban, to mu je dai zuwa, lokacin zai warware mana komai. "Hamma in tafi ne?". Ta faɗa kallonta a ƙasa, tana son ɗago idanu ta saci kallonsa dan taga me yake yi, amma ta kasa gudun kada ta tsinci yana kallonta su haɗa idanu. Shiru shiru bai amsa mata ba, sai dai kallonta da yake ta yi yana jin ƙwaƙwalwarsa tana wani irin juyawa tamkar agogo. One step ta yi baya kafin ta ɗan ɗago da kallonta a kansa. Ai a fujaje ta sake yin ƙasa da kai ganin ita yake kallo sun kalli juna ido cikin ido. Shi dai ba komai yasa ya ƙasa dai'na kallonta ba face wannan tunani da yake ji na daban idan yana kallonta, abin yana bashi mamaki da yasa baya son kawar da kallonsa daga kanta. Ita kuma sarkin tsoro, ganin yana ta kalleta yana kalle kayansa, e mana kayansa tun da dai aure ya ɗauru in ji ni princess Teema taku ta amana..........😂 Yana ta kalle kayansa yasa ta tsorata, nan take kirjinta ya fara dukan uku uku, a tunaninta wani abin zai yi mata, shege shaiɗan da kuma munafukar zuciya mai sake sake sai ta fara saka mata cewa ai dama jama'a sun ce maki shi maye ne, ba ga shi yanzu yana kalle maki jiki yana neman ta in da zai fara cinye maki tsokar jiki idan ya samu dama ba. Ai kuwa wani irin ihu ta zunduma wanda bata san ta yi ba, kamar mai wani motsi a kai, kawai zuciya ya kai ta zai barota, wlh yarinyar nan ta zaci a cikin zuciyarta ta kurma wannan ihu, bata san a fili ta yo shi ba. Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin ihun nata, kamar wadda aka yi wa allura ko wadda aka kwalawa guduma a kai, ta wani kware baki ta zundumota, anya ma lafiya take kuwa?. Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa. Ita kuwa ihun da ta yi ya yi dai'dai da ta ɗago kai ta kallesa, ai kuwa hakan ya yi dai'dai da idanun da ya zaro dan mamakin abin da ta yi. Habawa tana haɗa ido da shi taga ya zaro nasa me zata yi? Ai sai ta zunduma a guje ta yi wani irin juyawa da karfi ta nufi hanyar gida, kafa me na ci ban baka ba? Ai sai gida. Bata ma san lokacin da takalmar kafafunta suka cire ba, ita dai gida kawai take burin ta shiga. Sai dai bata kai ga isa gidan ba ta faɗi ƙasa tare da kurma ihu mai sautin gaske. Yana dai tsaye yana kallon ikon god da wannan yarinya, yana gani ta watsa a guje bai yi wani motsi ba, sai da ya ga ta faɗi ƙasa ta kuma zunduma wani ihun ne ya ɗan lumshe idanunsa tare da jan dogon numfashi. Ni kuwa nace har yanzu dai wannan fadanci ta jinin sarautar tana nan bata rabu da shi ba. A hankali ya fara takawa ya tinkari in da take, a gabanta ya tsugunna dan yaga me yasameta ta faɗi take yin wannan ihu kuma. Jini ne yake zuba daga kafarta ta dama, da sauri ya kai hannu ya riƙo kafar tata, jini sosai yake zuba, sam bai iya gane me ya sameta a wajen ba, saboda jinin ya wanke wajen, shin yankace ko dai wani abin ne ya soketa har ya fasa fatar kafar haka? Jini sosai ya rufe wajen ciwo baka iya gani, ga jinin nata jajir da shi. Dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, ta datse idanu gam, ba abin da zaka gani face hawaye dake bin ƙuncinta kamar ruwa ya faso hanya. Da alama bata ma san yana kanta ba. Ɗan miƙewa ya yi, ya duƙa ya ɗauketa cak suka nufi cikin gida. Bappa dai yana ta ƙoƙarin gyara wajen da zasu yi bukkar kusa da ɗakinsu Mahnoor ɗin ta gefe haka. Gabaɗaya kunya ya ji tamkar ƙasa ta tsage ya shiga ciki na ganin bappa a tsakar gidan, sai ya ji dama bai ɗauketa ba, wato shi fa wlh kunyar a jininsa take, ba wai tsiya bace kamar yadda Jawad yake tsokanarsa da shi, ai kunga ko zai ji kunyar kowa ban da Yah Jawad, so shiyasa Jawad ɗin yake ganin kamar iyashege ne ba kunya ba dan shi baya nuna mashi yana jin kunyarsa. Ko kallon in da bappan yake yaki ya yi, yadda kuka san ya gefar da ita a ƙasa haka yake ji, sam bai yi tunanin zai isko bappan a tsakar gidan ba, da Allah ba zai ɗaukota ba sai dai ya taimaka mata ta miƙe ta taka da kafafunta su dawo. Shi fa wlh ko da Mahreen baya son jerawa mutanen gari su gansu bare kuma bappa, kunya hakan take bashi. Allah sarki yaron Mommarsa mai alkunya.........😂 Saman wata dutse da suke zama su goge kafa idan sun fito daga wanka ya zaunar da ita, sam ɗan tahaliƙin nan yaki yarda ya juyo in da bappa yake, yana ganin kamar idan ya juyo zasu haɗa idanu ne. Shi kansa bappa abin ya yi matuƙar bashi kunya yadda ya ɗaukota ya keta wajen nan jama'a suna wucewa ya shigo da ita, amma da yake yana kaunarta sosai sai ya danne kunyar a ruɗe ya fara tambayarsu meyafaru kafarta ke jini?. A dai'dai lokacin Mahreen ta fito daga cikin ɗaki tana zabga uban hamma kamar zata ci babu, da alama da yunwa ta taso daga wannan barci. Ganin abin dake faruwa yasa ta yi saurin ƙarisowa wajen tana tambayar hamman nata me ya faru?. Bai kulasu ba ya yunƙura zai miƙe ya bar wajen, cikin jin raɗaɗin ciwo ta riƙo wuyarsa yadda ta saƙalosa lokacin da ya ɗauketa haɗe da faɗin zafi kafarta yake yi mata, su taimaka mata su cire mata zafin. Shi kuwa kunyar bappa yasa zai bar wajen dama, baya son su haɗa ido, ba wai dan baya son taimaka mata ko bai ji tausayinta ba, aa, ko ɗaya, hasali ma ya so ya wanke mata kafar, ya wanke jinin sai ya duba menene ya ji mata ciwo a wajen. Bappa ya lura da kunyarsa yasa Jaish ɗin yake son gudu ya bar wajen, bai san cewa shi kansa abin ya bashi kunya ba, in gaya maku Mahreen ce kawai bata ji komai ba, dan kun san ita kunya ya yi gabas ne ita kuma ta yi yamma, sam basu da haɗi. Ganin yadda ta riƙe mashi wuya gam tana kuka haɗe da magiyar a cire mata zafin ne yasa ya koma ya tsugunna a gaban nata, a hankali ya kai hannunsa ya fara ƙoƙarin cire hannunta da ta sarkafe wuyarsa da shi. Hakan yasa bappa ya ji ba zai iya ganinsu ba, sai kawai ya fice daga gidan ya basu waje, ya nufi gonarsa na su tomatoes dake kusa da gidan, dan ya je ha fara saro itacen da zai haɗa masu bukka da shi kafin su gama abin da suke yi. Ganin bappan ya fice ya basu waje ne yasa sai ya fasa cire hannun nata daga wuyarsa, dama wai zai cire hannun nata ne dan ya samu ya bar wajen, yana son taimaka mata amma idan bappa na wajen ba zai yi ba, da tafiyarsa zai yi abinsa, amma tun da bappan baya nan sai ya kai hannu ya kamo kafar tata. A gabansu Mahreen ta tsugunna, idanu jajir da su saboda barci, ga yunwa, sai daka hamma take yi, kamar zata yi kuka ta kai hannu ta saƙalo wuyarsa saman hannun Mahnoor dake wuyar tasa, lallausan kumatunsa ta shafa da ɗayar hannun nata, cikin fuskar tausayi ta ce. "Hamma meyasami Adda Mahnoor ɗita?". Dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, hannunsa ɗaya ya kai ya shafi face dinta kafin ya yi mata alama da ba komai, sannan ya yi mata alamar ta kawo mashi ruwa. Ba shakka akwai shaƙuwa sosai a tsakanin shi da Mahreen, shaƙu kam mai karfi ma. Da sauri ta miƙe ta nufi cikin kitchen, ruwa ta ɗebo a cikin butar karfe irin na mutanen da ɗin nan ta dawo da shi in da suke. A gabansu ta tsugunna ta miƙa mashi. Karɓa ya yi, hannunsa yasa a saman wajen ciwon ya fara zuba ruwan yana wanke mata jinin. Sosai ta kara tsananta kukan nata, saboda ruwan sanyi da ya taɓa ciwon, sai ya kara azabar zafi. Yana wankewa wata jinin tana ɓulɓula, sai dai kuma da ya wanke ya gano babbar ciwo ta ji sosai, wani kwalba ne ya fasa mata fatar har nama, ya yanketa sosai da sosai. A hankali wani irin tsananin tausayinta ya ratsa zuciyarsa sosai, tsumma mai tsabta ya buƙaci Mahreen da ta kawo mashi. Ɗaure mata kafar ya yi ko zai samu jinin ya ɗan tsagaita su saka magani, dan shi ma a yanzu ya san magunguna da dama na gargajiya. Miƙewa ya yi ya ɗauketa izuwa ɗakin bappa, da sauri Mahreen ta rufa masu baya. Saman gado ya zaunar da ita, sai a lokacin ta sakar mashi wuyarsa, dan ta ɗan ji sassaucin zogin. Juyawa ya yi zai fita sai kuma kamar wanda aka cewa ya juyo, yana jiyowa suka haɗa idanun, dan jin zai fice yasa ta yi saurin waro idanu dan tagansa kafin ya fita. Yana haɗa idanu da ita tunanin yadda ta tashi hankalinta a ɗazun da kaska ta hau hannunsa ya faɗo mashi, ya ji daɗi sosai yadda ta ruɗe ta kuma taimaka mashi, ta nuna tsantsar tausayinta a gare shi, tuna hakan yasa ya juyo ya dawo, ya fasa ficewa. Da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mamakin me ya dawo da shi kuma?. Sai surutu Mahreen take zuba masu babu wanda yake iya jin me take faɗa, dan kuwa duk sun afka duniyar tunani. A kusa da ita ya zauna yana kai hannu ya riƙo kafar tata, mamaki ne ya kusa sanyata suma, bata taɓa zaton hakan ba. Ita dai Mahreen sai tambayar ina Nenne take take yi, ba wanda ya bata amsa, ni kuwa princess Teema na ce Nenne ai ta saki kanta da kanta, bappa dai ba ruwan, ta haɗa kaya sai gidan Arɗo abinta, dan dai bappa namu na gargajiya kam bai sake ta ba, kuma bai ce ta tafi gidan Arɗo ba, rashin albarka ne irin tata da rashin ilimin sanin darajar miji, kai ita bama tasan me ake nufi da miji ba, kan fanko ne. Alama ya yi mata da hannu a kan har yanzu wajen yana yi mata zafi?. Mamaki ya hanata iya amsawa, ta yi suman zaune, kanta a ƙasa ta kasa iya ɗagowa. Ya fahimci ita ma kunya ce da ita sosai kamar shi, hakan yasa ya saki kafar tata tare da miƙewa ya nufi waje da nufin ya je ha tsinko magunguna ya zo ya haɗa mata, sam baya son su haɗu da bappa a yau ɗin nan, dan haka yana fitowa ya bi ta baya dan karsu haɗu. Ai kuwa ya gudu bai tsira ba, dan kuwa bai yi zaton bappa yana wannan gona na su tomatoes ɗin ba, can kuma ya shiga dan ya ciro abin da zai ciro. Yana sanya kai unexpect suka yi ido huɗu, ai wani irin kunyar da ya ji tamkar ya ce ƙasa ta tsage ya shige ciki, sai ya ji kamar ya juya ya fasa shiga, gabaɗaya sai ya ji ya rasa sukuninsa. Shi kam bappan da yake yasan halin kayansa sai ya kawar da kansa kamar bai gansa ba, dan baya son ganin ɗan nasa a cikin takura, bayan son yaga ya takure kansa saboda kunya, sai ya matsa can cikin gonar ma ya bashi damar shiga ya yi abin da zai yi ba tare da ya takura kansa ba. Ya fahimci sarai bappa ya gano yana tsananin jin kunyarsa, ya fahimci da gangan ya wuce can cikin gonar ya bashi waje, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ƙarisawa wajen bishiyar zogale, dan ganyenta yana tallafawa wajen tsayar da jini, idan jinin ya yawaita over wajen zuba to yana ragesa, idan kuma ba dayawa sosai bane yana ɗauketa gabaɗaya. Bari na baku magunguna biyu zuwa uku dangane da zogale domin mu karu da juna kafin na wuce. Ina masu ulcer? To zogale takuce, ku matso kusa. Komai karfin ulcerki idan kika samu furen zogale, ki gyarata ki wanketa tsab, sannan ki zuba a tukunya, ki sanya ruwa kada ya wuce litter ɗaya, sai ki ɗaurata saman wuta, idan ta tafasa sosai, ki sauƙeta ki tace, sai ki zuba zuma a cikin ruwan ki sake ɗaurata a wuta ta tafasa na minti uku zuwa biyar, sai ki sauke, da ɗan ɗuminta zaki rinƙa sha, da izinin Allah zaki rabu da ulcer. Magani na biyu, ki yi wa ganyenta shanyar inuwa, idan ta bushe ki dakata ta yi laushi sosai, ki samu nonon shanu mai kyau, sai ki rinƙa zuba tea spoon uku na garinta a cikin nonon kina zuba zuma tea spoon biyu, ki garwaya sosai ki sha, wlh yana matuƙar saukarwa da mace ni'ima, yana kuma maganin sanyin ciki sosai. Na uku, ki rinƙa dafa ganyen zogalen kina tace ruwan, ki zuba zuma ki sha, yana matuƙar wanke jini, yana kashe kwayoyin cutar sanyi na ciki, tana matuƙar saukarwa da mace ni'ima sosai, ki gwada zaki sha mamaki In Sha Allah. Kina iya dafa ruwan ganyen, ki zuba a cikin buta kina tsarki da shi, yana matuƙar gyara wajen sosai, yana kashe kwayoyin cuta, sannan yana ɗauke duk wani wari. To ya isa haka mu koma kan karatunmu, sai kuma wani lokacin.......... A karshen littafin nan da izinin Allah zan baku wasu sirrika, ina matan da mazansu ke biye biyen matan banza a waje? Ina iyayen da suka fuskanci jarabawa na ƴaƴansu suna shaye shaye da bin matan banza? Ina iyayen da ƴaƴansu basa jin maganarsu? Sun bijire masu basa ji? Ina iyayen da suke fuskantar matsalolin tsakaninsu da ƴan uwan miji? Baki yi masu komai ba su ɗauki karan tsana su ɗaura maki? Ina matan da mazansu suke wahalar da su ba tare da kina da hakkinsu ba? Baki yi wa namiji komai ba kawai ya rinƙa azabtar dake yana cusa maki bakinciki? Ina masu son mallake zuciyar mai gida? To duk ku matso, a karshen littafin nan zan baku wani sirri na musamman, amma ki tabbatar da cewa tsakaninki da Allah kike zaune da kowa, kada ki cutawa kowa, sirri ce ta musamman, magani ne irin ta addinin Musulunci, in dai zaki yi shi yadda yake to da izinin Allah duk wata damuwarki zata warware, zaki samu waraka da yardan Allah, sai dai ina kara haɗaku da Allah da ku zauna da kowa da zuciya ɗaya, domin da ki cuci mutum gara shi ya cuceki, kada ki je Allah ya mallaka maki zuciyar oga kuma ya zamana kina da kishiya ki cuta mata! Ki ji tsoron Allah ki sani akwai mutu, ni dan saboda iyayen da yaransu ke biye biyen mata, da matan da mazansu ke biye biyen matan banza a waje ma yasa zan bada, a dai ji tsoron Allah na faɗa na kara faɗa, wlh duk wadda tasan da kudurin niyar cutar wata ko wani a ranta ya Allah kasa ko zata yi sau miliyan kada bukatarta ta biya ato, babu ruwana, In Sha Allah a karshen littafin nan na yi maku tanadi na musamman, fatana dai Allah ya kaimu da rai da lafiya, ina kaunarku my people's.......💘 STORY 🔥 Sinko dik abin da zai buƙata ya yi, ya dawo cikin gidan. Kai tsaye bappa room ya nufa, zaune ya iskota ita da Jumma ƴar Inna Rabi, sun yi wa Mahreen wayo sun koreta, sai suka kama hira a kan aurensu, Jumma tana kara bata shawarar ta yarda ta zauna da Jaish, kun san fa ita Jumma ta ɗan waye, dan tana zuwa cikin birni tallar nono, so ta fi Mahnoor wayo nesa ba kusa ba, ta san wasu abubuwan na duniya, sannan bugu da ƙari mamarta malamar addini ce sosai, ta koyar da su daidai gwargwado, so yanzu sai ƙoƙarin wayarwa da Mahnoor kai take yi a kan ta yarda ta zauna da shi zata ji daɗi. Aikota fa Inna Rabin ta yi a kan ta zo ta kira mata Mahnoor ɗin, dan Innar ma ta samu labarin auren da aka ɗaura wa Mahnoor ɗin, shi ne ta ce ta kira mata ita tana son yin magana da ita. Shi ne da ta zo ta samu ta ji ciwo a kafa sai ta samu waje ta yi zamanta suka kama hira a kan gidan miji, yara sun girma Inna Rabi bata sani ba. Wani irin tsoro ne ya kama Jumma na ganin yau gata ga Jaish a ɗaki guda, ta kafeshi da idanu tamkar zata cinye shi, shi kuwa da bai san da wata halitta a wajen ba, abin da yake gabansa kawai yake yi, a kusa da ita ya tsugunna tare da kamo kafar tata, cikin nutsuwa yake murje ganyayyakin magungunan da ya tsinko yana sanya mata a ciwon. Sai washe take faɗa, sai ma da ya sa hannu ya buɗe ciwon nata da kyau zai ɗiga ruwan ganyen zogale da ya murje ya matse, datse idanu ta yi tana kuka a hankali hankali. Jumma kam tamkar zata sume, abin ya yi matuƙar burgeta yadda yake yi wa matarsa magani cikin nutsuwa da takatsantsan ga tsantsar kula, sai dai kuma a tsorace take, dan har yau har gobe yana ruɗar da ita idan taga kyansa. Ba ita yake yi wa magani ba, amma it ce jikinta yake kerma. Bayan ya gama abin da yake yi ya mayar da tsummar ya ɗaure mata kafar, dik da jinin ya tsaya da zuba hakan bai sa ya cire tsummar ya jefar ba, saboda yana son maganin ta nutsa ciki ciwon sosai. Miƙewa ya yi tare da ɗan ɗaura hannunsa a kanta alamar sannu ya yi mata, daga haka ya nufi waje. Kamar jira take yi ya fita, yana kurewa ganinsu ta yi maza ta ce. "Amma gaskiya Mahnoor baki da hankali!". Cikin jin zafin ciwo ta zaro idanu kafin ta ce. "Mekuma na yi na rashin hankali Jumma?". "Mema baki yi ba! Yanzu dan tsabar rashin hankali da rashin mafaɗi ne kike ƙoƙarin haɗa hamma Faisal da wannan jarumin namijin? Me kuma wani hamma Faisal? Ki duba fa ki ga yadda ya yi maki magani a yanzu, komai cikin natsuwa, ki ga kalar jaruntarsa a jikinsa fa! Ke kam baki da hankali wlh". A kule ta kai karshen maganar, ji take yi dama ita ce ta same shi!. "Jumma amma dai kin san cewa hamma Faisal ɗin ma idan ya ga naji ciwo irin haka hankalinsa zai ta shi ko? Kuma da kike maganar Hamma ya yi mun magani ki sani shi ma hamma Faisal ɗin fa wlh tsab zai yi mun magani kamar yadda hamman ya yi mun a yanzu, ko ma dai fin hakan". Tana magana tana ciza laɓɓanta alamar tana jin zafin kafar tata. A hanzarce ta capki zancen da cewa. "A'a wlh Mahnoor, baki son gaskiya ne kawai, amma ke kanki kin san hamma Faisal dai ba zai yi maki magani kamar yadda wannan hamman naku ya yi maki ba, ki duba kiga yadda yake gudanar da komai nasa, abin gwanin ban sha'awa, wlh da ma nice na same shi ai da na more". Da iyaka gaskiyarta take magana kuma cike da confidence!. Harara ta wurga mata da waɗan nan idanun nata da suke jajir ɗin, sannan ta ce. "Hmmmm Jumma kenan, ni dai koma me zaki ce hamma Faisal shi ne a raina, shi nake so! Da shi kuma na saba". Ita ma hararar ta wurga mata kafin ta amsa da. "Ai kuwa gara ki fara son wannan hamman naku, dan wlh babu kwatan kwacinsa a garin nan, amma a juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe, idan bappa ya miƙa mashi ke ki ce ba zaki je ba mu gani". A kule ta ce. "Ba zan je ba ɗin kuwa". Tuntsirewa da dariya mai ɗan sauti Jumma ta yi, cike da shakiyanci da iyashege tana dariya ta ce. "Allah da gaske ba zaki je ba amaryar hammanta?". Kai ta gyaɗa bilhakki da gaskiyarta ba zata je ba. Kara faɗaɗa dariyar tata ta yi, cike da tsiya ta ce. "Kada fa watarana a wayi gari na zo kawo maki ziraya kina cikin ɗaki ki ce mun hamma yana nan in tafi ba zaki fito ba". A harzuke ta ce. "Me zan yi da shi a cikin ɗakin da har idan yana nan zan ce ki tafi?. Wai ke waye ya ce maki ma ni zan yarda mu zauna ɗaki ɗaya ne? Tab ni ai ina ɗakinmu ni da ƴar uwata! Hauka nake yi zan zauna da shi?!". Ta kai karshen maganar tana banka mata harara. "Me ake yi a cikin ɗaki dama? Ai na gaya maki idan bappa ya miƙa mashi ke kice ba zaki je ba". Tana kai karshen maganar ta sake tuntsurewa da dariya, Inna Rabi tana can tana jiranta ta tsaya nan tana iyashege. Shiru ta yi mata bata amsa ba, dan ta lura idan ta biyewa Jumma wlh tsab zata sanyata kuka. Ɗan matsowa kusa da ita ta yi, da kyar ta dakatar da dariyar tata, kamar wata maras gaskiya ta yi wani ƙasa da murya, sai dai cike da iyashege ta fara magana kamar haka. "Kin san me Mahnoor?". Girgiza mata kai ta yi alamar a'a bata sani ba. "Akwai wata uwar ɗakina a birni, matar suna da kuɗi sosai, gidansu akwai kyau, tana sayar nono cikin katon kwarya su saka a cikin wani abin da yake yin sanyi (freezer) baya lalacewa, sannan tana sayan man shanu sosai a wajena, kullun ina kai mata nonon kwarya guda, matar tana bala'in sona, ta ce ina yi mata kyau, ita take koya mun wasu abubuwa, da kam ma ta ce wai ɗanta zai aure ni, shi kuma yaron ya ce shi baya son wadda bata yi makaranta ba, baya son yar kauye mai tallar nono, har da cewa ya yi ya tsaneni, amma mamarsa tana da kirki sosai, ta bani hakuri ta ce idan aure na ya zo har nan garin zata zo ta kawo mun abubuwa kyauta, kema zan koya maki duk abin da ta koya mun dangane da miji". Ɗan dakatawa ta yi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa. "To a gidan na ji suna faɗin mazansu wato mazan birni suna da shegen jarabar tsiya sosai, dan haka sai ki shirya, kinga ke mijinki wlh ɗan birni ne, dan ni ba zan taɓa yarda daga kauyen yake ba, saboda bai yi kalar kauye ba". Ta kai karshen maganar tana ɗan karkata kanta ta leƙo hanyar fita daga ɗakin dan taga babu mai zuwa dai ko?!. A ɗan tsorace ta zaro idanu tare da faɗin. "Me kuma wani jaraba?". Matsowa ta yi dab da kunnenta, ƙasa ƙasa ta yi mata raɗar menene jaraba tana ƙunshe dariyar iyashege. Ko me ta gaya mata? Su dai suka sani, a dubu ta zaro idanu tare da juyowa suka fuskanci juna. Tuntsurewa da dariya Jumma ta sake yi tare da kawar da zancen ta hanyar canza topic na magana a in da ta ce. "Allah Mahnoor ina gaya maki ko a birni da nake zuwa, dik yawace yawacen da nake yi Allah ban taɓa cin karo da jarumin namiji kyakkyawar gaske irin mijinki ba, gara maki ki farka tun wuri ki rungumi abinki". Sai a lokacin ne ta amsa da. "Dama nace maki barci nake yi ne? Duk kyansa babu ruwana da shi, Hamma Faisal nake so". Tana magana tana harara. Siririn murmushi Jumma ta yi, sannan ta ce. "Tom shikenan, ni dai bari na zo na wuce gida kada Inna ta yi mun faɗa, koma menene sai mun haɗu da yamma a dandali, zan so ganin yadda hammanki kuma mijinki zai yi maki kwalliya......" Datse mata numfashi ta yi da cewa. "Waye zai yi wa kwalliyar?". "Amaryarsa Mahnoor zai yi wa mana, idan ya zo yi sai ki hana shi mu gani, ke anya Mahnoor ba sai ya yi maki ta karfi bama zaki yarda da shi kuwa? Bari zan gayawa Inna, wlh zan gaya mata zagin mijinki kike yi". Da sauri ta riƙon hannunta, marairace murya ta yi kamar zata sa kuka, ta ɗan tsuke fuska kafin ta ce. "Dan Allah Jumma ki yi hakuri kada ki cewa Inna ina zaginsa, kin san dai zata yi mun faɗa koma ta dakeni ko? Dan Allah kada ki faɗa". "To naji ba zan faɗa ba, amma ki yi mun alkawarin zaki yi mashi duk abin da Inna take karantar damu dangane da miji? Sannan kuma ki mun alƙawarin zaki dai'na tunanin hamma Faisal, tunaninsa kawai zaki rinƙa yi!". Tun da ta fara magana take gyaɗa kai sama alamar ta yi alkawarin, sai da ta dasa aya ne ta ce. "Na yi maki alkawari In Sha Allah zan yi dik abin da na sani iyakar iyawata, dan Allah dai kada ki gayawa Inna komai". "To ba zan faɗa ba, yanzu dai bari na je gida sai mun haɗu da yamma a wajen shagalin bikin, akwai shagali yau, wani irin kwalliyar kece raini zan yi, a matsayina na babbar kawar amarya sai na fi kowa kyau, harta amaryar da angonta zai yi mata kwalliyar ma sai na fita kyau". Ta kai karshen maganar tare da mikewa tsaye. Sakar mata hannunta Mahnoor ɗin ta yi tare da yi mata sai anjuma ta gode da ziyara da kuma shawara. To kawai ta amsa da shi, sannan ta fice waje. Karkatawa ita kuma ta yi ta kwanta abinta, tunani cike fal a ranta ta lumshe idanunta kamar mai jin barci. Ita kuwa Jumma tana fitowa ba zato ba tsammani kwatsam ta gansa a kusa da ɗakin bappan yana gyara itatuwan da bappa ya saro dan su haɗa bukka, a yanayin yadda ta gansa sai taga kamar ya jima zaune a wajen, dan kuwa har yana ɗan haɗa zufa, rana ta iso in da yake. Gabanta ne ya yi wani irin faɗuwa, addu'a ta fara yi a kan Allah yasa bai ji abin da suka yi ta faɗa ba, ga shi ta yi ta sakin baki ita sarkin magana. Shi kam tamkar bai san da ita a wajen ba, har ta wuce bai ɗago ya kalle ba. Ita kuwa Mahreen da suka yi wa wayo suka kaɗata wajen bappa dan su yi hira, wlh laɓewa ta yi ta baya tana jin maganganunsu, sai da ta ji komai sannan ta gudu wajen bappan a cikin gona, tana zuwa a fesa mashi komai tsab, ta fara bashi labarin tun daga farko tiryan tiryan, wai ai ga su Mahnoor can suna hira a kan yadda zata zauna da Hamma, ta tona masu asiri yarinyar nan. Bappa dake ta ƙoƙarin saro wasu itatuwan ne mamaki tasa sai da ya dakata, dama ya saro wasu ya kawosu gida Jaish yana gyarawa, sai ya dawo karo wasu. Bai taɓa tunani su Mahnoor sun san wannan karatun ba, bai san cewa Jumma take koya mata ba. A ransa ya kara jin cewa lallai Mahnoor tana son Jaish tun da har take bada labarin yadda zata zauna da shi, bai san cewa Mahreen ta kwaɓe maganganun bane, shi ne bai fahimce ta da kyau ba, ta ɗauki labarin da Jumma ta bayar sai ta bashi a matsayin Mahnoor ce ta faɗi hakan, maganganun Mahnoor ɗin kuma sai ta bashi labari a matsayin Jumma ce ta faɗi hakan, ta juya kan zancen gabaɗaya. Bawan Allah mamaki yasa ya ajiye addar wukar dake hannunsa yana tunanin gara dai ya samu ya miƙawa Jaish wannan yarinya ya huta, ayi masu ɗakinsu su koma can, ko yaushe ta yi wayo haka bashi da labari? Mahreen uwar haɗa bomb, ta bashi labarin da ya ɗaga hankalinsa, ta kama kanta ta haye saman bishiyar gwaiva tana aikin tsinka ko a jikinta, ta barosa a tsaye a wajen. My people's ya kuke tunanin wannan zama zata kasance, shin Jaish zai yarda ya yi biyayya ga al'adunsu? Mahnoor zata yarda bappa ya yi masu ɗakinsu su biyu kawai? Zata yarda ta zauna da shi? Ya makomar Faisal bawan Allah? To dai dukka nan da lokacin ƙanƙani zaku ji komai, mu leƙa KINGDOM OF POWER mu dawo. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ ___________KINGDOM OF POWER💪🔥 MOMMA AND KUYANGA MAMA HAULAT. A fujaje kuyanga mama Haulat ta ɗago kanta tare da zaro idanu tana kallon Mommar, while ita ma Mommar ita take kallo. "Ranki ya daɗe gimbiya Momma kina nufin dama kin san mammie green snake under green grass ce?". A ruɗe ta yi tambayar. Jinjina mata kai ta yi alamar tabbatarwa da tasan komai shiru kawai take yi, duk wasu bibiyarta da suke yi tana sane, duk wani makirci da munafurcin da suke shirya mata tana sane da su, lokacin su ne kawai adbata da, ba su isheta kallo ba, dan ita tasan ta riƙe Allah, ta yarda da tauhidinta, dan haka bata da wani sauran fargaba. Da hannu ta yi wa mama Haulat nuni da ta je kawai ta bata waje. Jiki ba kwari ta miƙe, cike da ruɗu da damuwa ta nufi waje, ita ce amintaciyar Momma, duk wasu sirrukan da Mommar take ɓoyewa ta sansu, babu abin da bata sani ba, shiyasa ta girgiza da jin zancen cewa Mommar tasan duk wasu abubuwan da suke faruwa shiru kawai take yi, akwai matsala. A can cikin fada kuwa, sai tattaunawa King yake kara yi da dattawan cikin fadan, yanzu aiyuka biyu ne a gabansu, na farko yakar Queen Zarina wanda ya zamar masu dole, dan su basa yafiya in dai aka taɓosu, sun ma yi kokarin da suka ɗaga mata kafa har ta ɗan kwana biyu basu ladabtar da ita ba, ba dan komai suka yi hakan ba kuma face saboda rashin nutsuwa da suke ciki na ɓatar Spender. Abu na biyu kuma da yake gabansu shi ne neman dik in da Spender yake su dawo da shi, yanzu dik hankalinsu a tashe, kullun suna cikin zaman tattaunawa ta yadda zasu shawo kan matsalarsu, abin ya ɗaga hankulansu. After some hours. Rana ta yi sanyi alamar ta kusa faɗuwa, garin ya yi tsit tamkar babu mutane, sai harkokin gabansu kowa yake yi, kafa ta ɗauke har a kan tituna, akwai alamar hadarin ruwan sama sosai a sararin samaniya. Sanye take da doguwar malesian gown, ta ɗaura short winter jacket mai hula a sama, ta sanya hular a kanta. Fitowa ta yi daga part ɗin Momma zata nufi part ɗin Akka, da farko a tare suka fito da Auta, sai Autar ta ce bari ta koma ta canza kaya dan tana jin sanyi. Shi ne ta koma ta sako Turkish casual warm ware a jikinta, tana fitowa domin ta bi bayan Chuchun sai ta haɗu da uncle Taheer da ya fito daga part ɗin mama, shi ne ya ce tazo su je lambun dad su yi hira ta ɗebe mashi kewa, ba dan ta so ba ta bi bayansa suka tafi. Ita kuma Chuchu sarkin waya, tana tafiya tana latsa waya bata ganin gabanta, saura kaɗan su yi karo da Yah Rizwan, ambatar sunanta da ya yi ne yasa ta farga tare da ɗago kai a hanzarce, sai ta yi baya kaɗan. "Wani irin danna waya ne wannan my Jannaty? Idan kika je kina bugu da wani abin fa?". Cikin sanyin murya ya yi maganar. Ƙasa ta yi da kai. "Ka yi hakuri Yah Rizwan zan gyara". Siririn murmushi ya saki. "To shikenan, amma yanzu kin yi wuyar gani my Jannaty, tun jiya nake magiyar a bani dama mu ga juna anki ko? To laifin me na yi?". Cikin zolaya ya kai karshen maganar. "Baka yi laifin komai ba Yah Rizwan, kuma kai ai baka laifi, Allah ya hanani ganin ranar da za'a ce ni Jannat ka yi mun laifi, kawai dai barci ne jiya ya ɗaukeni muna waya, da safe kuma na je school, da muka dawo na gaji sosai sai na kwanta sai yanzu na samu na tashi na yi wanka na fito, dama kai nake ƙoƙarin kira yanzu". Wani irin sanyi ya ji a ransa na yadda ta ce shi take ƙoƙarin kira a yanzu, ya ji daɗi, a ganinsa ta damu da shi, zuciyarsa tana yaudararsa akan ta damu kuma tana sonsa sosai, ita kuwa a duk lokacin da take tare da ɗaya, in ma Jawad ko Rizwan ɗin to mantawa take yi da tana soyayya da ɗaya, abin kamar ba lafiya ba, sai ta haɗu da ɗaya take tunawa da suna soyayya ashe. "Ina zaki je yanzu to?". Cikin nutsuwarsa sosai yake, yana da kamala da nutsuwa matuƙa, ga hankali da sanin yakamata, ga kuma kaunar ƴan uwansa. "Part ɗin Akka zan je". Ta bashi amsa kanta a ƙasa, tana jin kunyarsa sosai ba kamar Yah Jawad da suke karewa juna kallo har cikin ido ba. "To yaushe zan samu a bani dama mu zauna mu yi hira?". Ya yi maganar haɗe da leƙo face ɗinta. Tana ta sakin murmushi ta ce. "Anjuma da daddare, yanzu zan je part ɗin Akka ne mu tafi gaishe da mijin Aunty Sarina da ya zo ni da Aunty Fanan". Ɗan zaro idanu ya yi tare da faɗin. "Wace Sarinar kuma wani miji? A yaushe ta yi miji ban sani ba?". Idan baku manta ba da safe lokacin da King ya yi sanarwar shi baya wajen, so bai san da batun zuwan saurayin ba. "Da safe ne dad ya ce akwai wasu yarima da zasu zo wajen Aunty Sarina da kuma Aunty Fanan, to su ne suka zo yanzu, baka ji jiniya da busoshi ta ko'ina bane ɗazun?". Sai a lokacin ya tuna da ɗazun ya ɗan ji jiya kaɗan, sai dai hakan bai wani ɗauki lokaci ba ya ji komai ya yi shiru tsit, abin bai sa ya yi tunanin ko baki suka yi ba, dan yadda ya ji jiniyar bata wani yawaita ba kuma ba'a jima ba ta ɗauke, bai san cewa commander Zafar ne ya taka masu birki yasa suka kashe jiniyoyin nasu ba, basu san dokokin kingdom of power ba, sun wani shigo da jiniyar motocin ƴan'sanda, a dokar masarautar kuma babu wanda ya isa ya shigo masu cikinta kamar wani shegen kwaro, kowa kansa a ƙasa zai zama idan zai shigo, baka isa ka zo ka ce zaka nuna kaima wani shegen bane, dan fa wajen manyan kai ka zo, dole ka rusuna ka zama tamkar bawa a gabansu, hakan yasa commander ya daka masu warning ya kuma sanya suka kashe jiniyar suka ƙariso ciki suna masu ƙasƙantar da kansu ƙasa. Kai kingdom of power duniya ne, dik wani ji da kanka da isarka sun take ka, suna mulki bisa dokokinsu masu ƙarfin gaske, sun ci ka masu power ɗin da gaske, ba mai keta dokokinsu ya zauna lafiya, wane mutun!!. "Okey na gane, to jeki zamu yi magana da su dad ɗin". Ya kai karshen maganar tare da sa kai ya wuce yana mai kallon face ɗinta. Ita ma wucewa ta yi tare da cigaba da latsa wayar ta, ta sunkuyar da kanta ƙasa, bata sanin in da take takawa saboda hankalinta gabaɗaya yana kan waya, hotunan sabbin kaya take dubawa wanda zata nunawa Aunty MieMie ta buga masu odersu ita da auta. Tafiya kawai take yi saura kaɗa ta buga kanta da jikin bangon wajen kwanar da zata sadaka da part ɗin na Akka, ba zato ba tsammani kwatsam sai ji ta yi ta buga kanta da kirjin mutum. A hanzarce ta ɗago kai dan taga wanene?. Yana tsaye ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, tun daga nesa ya hangota tana zuwa tana latsa waya, shiru ya zuba idanu yana ta kallonta, sai da ya ga zata buga kanta da jikin bangon wajen ne ya yi maza ya shiga tsakaninta da bangon ta faɗo saman kirjinsa. Ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da mayar da kanta a saman kirjinsa ta kwantar. "Yah Jawad ɗina ina kewarka sosai, ina ka shiga tun safe?". (Wato ana iya hege a cikin kingdom ɗin nan, shi Rizwan ya ce yana kawarta ta yi wuyar gani, bata ce tana kewarsa ba bata ce mashi komai ba, amma ta zo ta wani ce wa Jawad tana kewarsa, wato wani abin ma sai gaba fa my people's.............😂) Kura mata idanu ya yi yana kallonta ba tare da ya furta uppan ba. Tana daga kwance a kirjin nasa ta turo baki. "My melody ka yi magana mana! Wai ko kai baka yi kewata bane?". A shagwaɓe kamar zata yi kuka ta yi maganar. Shiru bai amsa mata ba, kuma bai dai'na kallonta ba. Yunƙurawa ta yi zata bar jikinsa tana faɗin. "Kenan ni kaɗai ce na yi kewar ka ko? Ba damuwa". Ita a dole ta yi fushi ne zata tafi. Hannunsa dake saman kirjinsa ya saukar tare da rungumota da su da kyau, cikin wata iriyar kasalalliyar murya ya furta. "Yau da rigima ake ji kenan? To ban da abinki Jannat ai kin san dole zan yi kewarki ko? Kewar taki ce ma tasa na ƙasa yin magana da na ganki, kin san ya nake ji a rai'na kuwa?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a idanunta a tsaye cikin nasa, while shi ma kallonta yake yi. "To ji nake yi idan ban mayar dake cikin kirjina mun cure mun zama abu guda ba ba zan ji sanyi a rai'na ba, dan haka a daina yi mun rigimar nan haka.......". Da kyar ya iya kai karshen maganar sakamako ido ɗaya da ta kashe mashi dan tsokana. Ajiyar zuciya ya sauke ya kasa yin magana, ta goge mashi hadda, ashe ita ma ta iya kashe ido ɗaya. "Yah Jawad yauwa ka ɗaukeni hoto ina tsaye full ka ji?". Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya iya furta kalma ba. Wayar dake hannunta ta miƙa mashi tare da raba jikinta da nasa. Baya kaɗan ta ɗan koma tare da tsara style na yadda za'a ɗauketa hoton. Ba musu ya shiga camera, sai dai kuma saboda neman tsokana irin nasa sai ya sanya mata filter kare, ta zama mai doggin kunnuwa da katon hanci, a haka ya yi mata hotuna kala biyar. A hanzarce ta ce ya kawo ta gani, ba musu ya miƙa mata wayar yana ƙunshe dariyar muguntar da ta ciyosa, dan yasan zasu kai ruwa rana yau. Tana ɗaura idanunta a kan hotunan a fujaje ta ɗago da kallonta a kansa, ai a ɗari wata iriyar dariyar mugunta ta kubce mashi, da gudu ya bar wajen ya nufi part ɗinsa. Aikuwa da karfi ta furta wlh ba zata hakura ba, ba zata barshi ba, tana magana hawaye yana zuba, da gudu ta bi bayansa dan ta ɗauki fansa, ta ci alwashin ba zata kyalesa ba. Kai my people's na rubutu yau fa, kai kun samu long page over. Saura ku bani hote comments kuma. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/11/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 37 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ A can part ɗin uncle Abbas kuwa, manya manyan motoci ne shake a parking space na part ɗin, bakin Sarina and Fanan ne suka iso, ga manya manyan bodyguards masu tsaronsu, ga jama'ar fada wato dogarawa, harabar gidan a cike yake da jama'a, su kuwa bakin an wuce da su wajen saukar baki bisa jagoranci uncle Abbas da ya tarbesu hannu bibbiyu. Sun samu tarba ta girma da girmamawa. Sarina tana can tana shiri, muguwar makirace yarinyar nan, tasan da cewa tana da diri mai kyau, kuma my people's kun sani dai a dik cikin ahalin King Abdul Malik daga kan ƴaƴa har izuwa jikoki babu munana, gabaɗayansu kyawawan gaske ne, sai dai kyan wani ya fi na wani, coz tasan tana da kyau, gata doguwa, dik wasu shika shikan kyau ta cikasu, haka ta zauna ta tsara kwalliyar da dik wanda ya ganta sai ya sake waigawa, ta sanya wasu shegun matsastsun kaya da su ka bayyanar da surar jikinta. Burinta a nan shi ne ta kwaɗaita masu surar jikinta ta yadda ko sun tafi tunaninta zai hanasu sakat, sannan ta tabka masu rashin mutuncin da sai sun yi danasanin zuwansu wajenta, tana burin su tafi suna masu danasanin zuwansu, sannan kuma su tafi suna masu kwadayin surar jikinta, sha'awarta ta hanasu sukuni, su sha bakar wahala wajen yaki da zuciyoyinsu dan su cire tunaninta, wannan shi ne dalilin da yasa dik namijin da aka ce zai zo wajenta sai ta tsaya ta tsantsara kwalliya na wuce tsara, sannan ta tunkari in da yake. Shegiyar mata ce yarinyar, ta san kan duniya sosai, sai dai ni kuma na ce in ta san wani ai bata san wani ba ko my people's? Mu je dai zuwa. Wani irin ɗan iskan athletic wear ta sanya, kayan sun matseta sosai, dik wasu albarkatu na jikinta sai da suka bayyana, ta sake arab hairn nan nata har baya, sannan ta sanya wani sheɗanin high heel, daga karshe sai ta ɗaura wani irin after dress mai kama da transparent net a saman dressing ɗin nata, ta ɗaura silk scarves a kanta, wasu irin siraran doggin diamond earrings ta sanya a kunnenta, ta yi kyau kam na karya. Yanayin dressing ɗin nata dai tafi kama da tantiriyar shaiɗaniyar karuwa, sam bata yi kama da mutanen kirki ba, dik kuma abin da take yi kada ku manta mammie ɗinsu ke goya masu baya. Sai dai kuma hali ya sha banban a wannan waje, dan kuwa lokacin da Mammie ta saƙawa Fanan ga yadda zata yi ta kori wannan yariman nata sai ta ce wlh ba zata iya ba, ita ba zata yi mashi rashin mutunci ba, su kyaleta tasan ta yadda zata yi ta rabu da shi lafiya, sosai mammie ta ji haushin hakan, amma ba yadda ta iya face ta kyaleta ɗin, dan idan ta ce zata ɗaga murya uncle Abbas zai iya sanin me yake faruwa, idan kuma ya sani kun san ba zasu wanye lafiya ba, asirinta ne zai tonu. Wani irin luxury glass cup ta ɗauka, abin sha ta zuba a ciki dai'dai tsakiyar cup ɗin, sannan ta shiga room ɗin Mammienta ta yi mata sallama. Sai sa mata albarka Mammien take yi tana yi mata fatan nasar. Me kuke tunani Sarina zata yi wa wannan guy ɗin? Muje dai zuwa. Ita kuwa Fanan dressing ta yi tamkar ƴaƴan manyan sarakuna da ake ji dasu, dressing irin ta addinin musulunci, har da alkyabbar ta ɗaura a saman kayan jikin nata, ta fito a jinin sarautarta da kyau. Ita kam Sarina ai ta yi nisa bata jin kira, cikin wani irin shaiɗanin takun da dik in da ta taka sai halittun jikinta sun motsa ta nufi wajen nasu. Duk wasu bodyguards kai har da mayakan dake cikin part ɗin sai da suka ji wani abin ya motsa masu a lokacin da suka sauƙe kallonsu a kanta, dik sai da suka kwaɗaitu da surar jikinta, ta ja hankulan su sosai, ta tafi da imanin dayawa daga cikinsu. Harta tsofaffin dake cikin dokaran yariman sai da suka haɗiyi yawu na ganin santala santalan cinyoyinta game da coca colar shape ɗinta, ga bayanta yadda yake wani juyi. Tana dinfarar bakin kofar shiga ta kara canza salon tafiyarta izuwa mai jan hankali sosai, sam bata ɗaga idanu ta kalli ko mutun ɗaya daga cikin waɗan da suke harabar gidan da suka shagala da kallon surarta ba, kai tsaye ta afka ciki abinta. Sam bata yi fargabar ko zata ci karo da uncle Abbas ko wani nata a ciki suna gaisawa da bakin ba! Ba shakkar kowa bare tsoro yarinyar nan ta afka ciki ba tare da ta yi sallama ba sai wani ɗan iskan excuse da ta ce masu. Ta kuwa yi sa'a babu kowa a ciki sai yariman da wani abokinsa ɗaya, sai dogarawa guda biyu da suke tsaitsaye a kansu ta bayansu dan basu tsaro. Hannunta na rike da wannan cup mai ɗauke da abin shan a ciki, wani irin ɗan iskan taku ta iya izuwa tsakiyar parlon, idanunta na'a kan abin shan nata, sam bata ɗago ta kalli in da suke ba!. Ai yarima da abokin nasa basu san lokacin da suka miƙe tsaye ba, gabaɗaya kallonsu a kanta yake, da alama fa haƙanta ya cinma ruwa ta ɓangaren sace zuciyar yarima, ko da yake dama can soyayyarta ta kawo shi, ba dole aka yi mashi ya zo ba!. Wani irin ɗan iskar kallo ta bi dogarawan dake bayansa da shi, cikin tsantsar nuna isa da jiji da kai irin na jinin sarauta ta furta. "Me waɗan nan ƙazaman kuma suke yi a nan? Ko da su zan yi hiran?". Da alama yarima dai sai sorry za'ace, dan kuwa kamar fa ya tafi, dama tun da ya ganta a wajen taron da mummy ta haɗa yake ta faman santin kyanta da surar jikinta, sai kuma yanzu gata a gabansa cikin shiga mai tada hankalin lafiyayyun maza, ai dole ya rikice. Ga shi namiji har namiji, arabs guy ne lafiyayye kuma ɗan gayu da ba zai wuci 28 to 30 years ba, ya yi shiga irin ta prince masu ji da kansu, yana wani shan kamshi ga mutane, sai dai a gabanta tuni ya mance da cewa shi yarima ne mai ji da isa da izza, muryarsa har tana ɗan kerma wajen buɗe baki zai bata amsa, sai dai bai kai ga furta uppan ba abokin nasa ya rigasa da cewa. "Ranki ya daɗe dogarawa ne masu bada tsaro............" Hannu ɗaya ta ɗaga mashi alamar ya dakata da yin maganar, cikin wani irin isa ta juyo da kallonta a kansa, ga idanun nata sun kara haske saboda bakin kwallin da ta sanya masu, idan ta juyasu sai kaga wani irin fari na musamman, ga shi ta iya juyasu kuwa, matsiyacin kallon up and down ta yi mashi kafin cikin nuna isa a walaƙance ta ce. "Who the hell are you da zan yi magana da wani ka tsoma mun baki a cikin maganata? I think bakaga kalar hakan a tattare da ni ba ko?!". Wani irin shan jinin jikinsa yarima ya yi, domin kuwa bai taɓa zaton haka take mafaɗaciya ba, shi kallon so silent ma ya yi mata a karon farko, bai san cewa ja'irar yarinya bace. Shi kuwa abokin nasa da ya kasance ɗa ne ga kanin mahaifinsa, dikkansu dai jinin sarautar ne suma, suna ji da izza da isa sai ya wani uban ɗaure fuska, ya dubeta da kyau up and down, sannan ya ja wani ɗan siririn tsaki, a tsiyace ya furta. "Rubbish! Yana da kyau ki san da wanda kike magana fa, am not your mate, and am n...........". Katse shi ta yi ta hanyar ɗaga mashi hannu a karo na biyu, sannan ta kawar da kallonta izuwa kan wanda take zaton shi ne yariman, dan ita a cikinsu bata ma san wanenen yarima na ainahi ba. "I don't have time for listening all this your nonsense! What i want to know here is between the two of you who's the prince? Is it you or him?" Ta yi maganar tana nuna su da ɗan yatsar hannunta manuniya. "And among the two of you who should I going to talk?, answer me as soon as possible because I have something a lot to do!". Ta kai karshen maganar tana tsayar da kallonta a kan dogarawan da suke bayan nasu. Abokin nasa zai sake yin magana cikin fushi da fusata dan a ganinsa ta raina mashi wayo, kun san jinin sarauta basu ɗaukar wasa. Dakatar da shi yarima ya yi ta hanyar ɗaga mashi hannu, sannan ya furta. "Ni ne yarima gimbiya Sarina". Nisawa ta ɗan yi tare da nuna abokin nasa da manuniyar yatsarta haɗe da dawo da kallonta a kansa, cike da class take magana, babu hayaniya sai zallar jiji da kai, yadda zaku san e ba wawiya bace, wayayya ce mai ji da kanta. "Okey ban san kai ya kake da shi ba, even do dai bana son ɗaga idanu na sake ganinka a cikin parlourn nan, coz ba kai kazo neman auren ba, shi da ya zo neman auren ma i don't have time for him ma bare friends or familynsa, you have to go out now!". Tana kai karshen maganar ta maida kallonta a kan dogarawan nasa. "Sai na furta maku ku fita ku bani waje ne kuma?". A tsiyace sosai ta yi masu magana, cikin nuna ƙasƙanci a garesu. Daga dogarawan har abokin nasa shi suka zubawa idanu suna kallo, ta bakinsa kawai suke jira su ji. Wani irin murmushi ya saki wanda da ka ganta kasan e lallai ƙaƙalota ya yi, dan kuwa murmushin takaicice, ya ji haushin abin da ta yi masu, a ɗan tsagaice ya furta. "You can go outside by her permission, I don't have to say anything, coz my words and hers will all go together" Zaro idanu abokin nasa ya yi, da mamaki yake kallonsa, kenan yarima ya goyi bayanta a kansa? Lallai to da matsala, wannan yarinya maras kunya da idanunta a tsaitsaye a tsakar ka, bata jin kunya ko nauyin zagin babban ne yarima yake tunanin ita ta dace da rayuwarsa? Har yake ƙoƙarin nunawa tun yanzu ta fi mashi kowa? To da matsala gaskiya. "Adam har da ni yau kake cewa zan iya fita waje bisa umarnin wata ba sai ka ce komai ba? Ni ne fa?". A ɗan takaice ya ce. "And so?! Ko dai ba zaka fita ɗin bane?". A dake ya yi maganar. Tun da dogarawansa suka ga haka sai suka kama kansu salum alum suka fice, da farko sun so su ce mashi ya yi hakuri ya barsu saboda mai martaba mahaifinsa ya ce in dai ba toilet ya shiga ba to su tabbatar duk wani motsin da zai yi suna a tare da shi, su bashi kula na musamman, amma ganin harda abokinsa tun na yarinya da suka taso a tare ya dakawa magana maras daɗi a kanta sai suka shafawa kansu lafiya suka yi ta kansu. Daga haka abokin nasa bai kara furta ko uppan ba ya nufi waje zuciyarsa tana tafarfasa kamar an ɗaura dalma a wuta, faɗi yake yi a ransa wlh ba zai bar Sarina ba, kuma in dai yana raye yarima ba zai auri wannan shegiyar yarinyar ba, dik wanda ya ci tuwo da shi wlh miya ya sha, za ta gane annabi Isa ba ɗan Allah bane annabin Allah ne. Suna fita ta ɗaga cup ɗin dake hannunta ta kai saitin bakinta, kaɗan ta ɗan yi sipping na drinks ɗin ta cire, matsowa kusa da shi kaɗan ta yi, ya saki ido, hanci da kuma baki yana ta kallonta, ya manta da shi fa Prince ne. _________________________💘🦋 "Ban san ya kake da suna ba, kuma bana da buƙatar na sani, dan babu abin da zai kare ni da shi, but let me tell you abin da kai zaka karu da shi kuma it will help you so much". Tun da ta fara magana ɗan bakin nata yake kallo ba tare da ya motsa daga in da yake tsaye ba, shi a duniya yana bala'in son mace haka mai cike da kwarin gwiwa a kan dik abin da tasa a gaba, sannan ta zamana bata tsoro ko shakkar kowa, mai furta magana one by one cike da class kamar dai ita, dan haka wannan abin da take yi sai ya ƙara tafiya da imaninsa sosai da sosai. A dab gabansa ta matso ta tsaya, sannan ta sake kai cup ɗin bakinta ta yi sipping kaɗan ta cire, ido cikin ido ta kallesa, babu ko shakka bare tsoro ko kunya, cike ma da walaƙanci a muryar tata ta fara magana. "Ban sani ba ko kana da ƙwaƙwalwar gane abubuwa ne, ko dai fanko ne kan naka, but even do dai nasan ba zaka rasa brain na ɗaukar waɗan nan maganganun nawa da zan faɗa ba, dan maganganu ne da komai dakikancin mutun dole ya fahimcesu!". Tashin sense. Dakatawa ta yi tana kara yatsune fuska haɗe da nuna gadara. Still har a lokacin yarima dai bai furta kalma ba, sai dai shi ma ya kurawa tsakiyar kwayar idanunta kallo. "I don't want to see your legs in this kingdom again, because i really hate u! Ka koma ka sanar da cewa baka yi nasara a soyayyarka ba! A nema maka haɗin gida kamar yadda aka saba yi maku!!". Sake yin sipping na abin shanta ta yi dan ta ji daɗin shuka mashi rashin mutuncin nata son ranta, kun san ko masifa zaka yi idan kana kora abu mai sai komai ya fi tafiya dai'dai.............😂 Ki ji maƙogwaro sanyi na ratsata, sai kin ma fi tuna irin rashin mutuncin da zaki zabga sosai, a duk lokacin da sanyi ta ratsa sai kin tuna shika shikan rashin mutun kala goma......😂 In ji wata ta yi wani magana ku gani, ai gaskiya na faɗa!!. Shi ko bawan Allah yadda kuka san mutun mutumi haka yake tsaye kikam, sai ma mujiya da yake binta da shi. "Kai baka ga kalarka bane? Irinku ai basu da wata zaɓi a rayuwarsu sai abin da dattawa na gida suka zaɓa masu, irinmu ne ke da zaɓi a duniya, even do dik wanda ya yaudareka da sunan kana da zaɓi kuma zaka iya playing roll naka a kan hakan to he really done bad and he lied to you !!". Ta kai karshen maganar tana ɗan zaro mashi idanu, alamar yasan da gaske take yi!. Sai a lokacin ya nisa tare da sauke hannunsa daga saman kirjinsa da ya harɗe, da alama ko kaɗan bai ji zafin maganganunta ba, dik da ta sako iyayensa a cikin maganganun nata, dan su ta kira da dattawa a baya, shi ya fahimci maganar tata da ta yi su a dunkule, dik ya faɗaɗasu a ma'aunin ƙwaƙwalwarsa ya kuma gane in da ta dosa. Dan haka sai ya kai hannu da nufin ya karɓi cup ɗin dake hannunta. Ba musu ta sakar mashi cup ɗin tare da janye hannunta da sauri wai dan kada ya taɓa mata jiki. Cikin nutsuwa ya kai cup ɗin bakinsa, one sipping ya ɗan yi tare da cirewa, cikin ƙasaita da kwanciyar hankali ya ɗan yi step biyu, ya ɗan wuceta kaɗan sai ya tsaya, ba tare da ya juyo gareta ba, ya bata baya kenan, cikin kwarewa ya furta. "Zazzafa kuma kyakkyawa, you really try beb". Yadda ya kai karshen maganar cikin wani irin slow a hankali ga salo mai ɗaukar hankali!. Zaro idanu sosai ta yi, ba na mamaki ba, na tsantsar haushin abin da ya faɗa, da alama shi ma cikakken ɗan duniya ne sosai, ita ta yi shigar banza ta zo gabansa ba tare da ta tuna abin da zai je ya dawo ba, yanzu ya yi maganar banza a kanta kuma tana ɓata rai game da jin haushi. A fujaje ta juyo garesa, ya bata baya haɗe da harɗe hannayensa a saman kirjinsa. Wani irin matsiyacin ɗan iskar kallo ta wurga mashi kafin ta buɗi baki da nufin ta yi magana, sai dai kuma ya rigata furta. "Yana da kyau na lashi zumar zazzafa gimbiya gaskiya, Gimbiya Sarina ko ya kika ce?". Ya yi maganar tare da juyowa gareta a wannan karon. Yana juyowa saura kaɗan su mannu da juna, saboda ta juyo gare shi ita ma. Wani irin kallon tsana take bin shi da shi, tamkar ta shaƙesa ya mutu take ji. Wani irin shu'umin murmushi ya sakar mata kafin ya kyasta mata yatsunsa a saitin face ɗinta cike da duniyanci. Wani irin ɗan iskan kallo ta watsa mashi kafin ta sake yunkurin buɗe murya dan ta yi magana, sai dai a wannan karon ma bai bari ta furta uppan ba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu, ba dan ta so ba ta yi shiru. A maimakon ya sauke hannun nasa da ya ɗaga mata ƙasa, sai ya sauke a saman lallausan wuyarta, cike da iyashege ya furta. "Yanzu lokacin yin magana na ne ba naki ba gimbiyata, the way na barki kika yi maganganunki son ranki har kika gama, the waye zaki dakata dan sauraron nawa!". Yana magana yana shafa neck ɗin nata, a hankali yake gangaro da hannunsa izuwa saman kirjinta, idanunsa suna tsakiyar tata. A hankali ya wani lumshesu da alamar daɗin latsa skin ɗinta da yake yi tana ratsa shi, har da wani furta ishiiiiiii irin ya ji zazzafar nan. Wani irin zaro idanun waje ta yi, bata taɓa zaton haka daga garesa ba, tunani ta fara yi a kan ko dai ya sha irin abin da Yusuf ya sha ne shi ma? Amma kuma da ya zo gidan ai bai ci komai ba, kuyangun da zasu kawo mashi abinci ma ai basu rigada sun ƙariso ba, fruits da aka kawo masu ma ga shi nan basu taɓa shi ba, to me ya shiga kansa kenan da zai latsa mata jikinta a cikin gidansu? Ta jefawa kanta tambaya. Ya lumshe idanu yana wani shafe mata jiki, dab da zai shafa mata kirji ba zato ba tsammani kwatsam ya ji saukar dalleliyar mari mai tsada a saman lallausan kumatun nan nasa mai kama da bread, ga kumatun nasa da tsoka a cike ɓul ɓul hannun zai ji laushin mari, dan yana da ɗan cika. A gaskiya ya maru kuwa, ji kake tasss, sai da ta dakarkare tsakaninta da Allah sannan ta dalla mashi ita, da yake yana da hasken fata, balarabe ne, sai da yatsun hanunta suka kwanta a saman fatarsa, har wani irin ɗan jiri jiri ya gani. One step ta matsa baya da shi, cikin kunar rai na taɓa mata jiki da ya yi ta furta. "Banza ƙazami jahili! Ashe dai ban yi karya ba da tun farko na kiraka da jahilin daƙiƙi, wannan jikin da kake gani dan mutum ɗaya aka yi shi a duniya, babu wanda ya isa ya taɓata ya zauna lafiya! Shashasha kawai". Tana magana tana sauƙe huci kamar wata zakanya, ta kai karshen maganar cikin masifa haɗe da ɗan ɗaga murya, sannan ta kara two step tsakaninta da shi. Idanunsa ne suka kaɗa suka yi jajir kamar wuta, ransa idan ya kai dubu to yau ya ɓaci, tun da uwarsa ta haifesa ba'a taɓa marinsa ba, shi ɗin ɗan gata ne, sai yau wata ta maresa? Lallai kuwa ta ɗebowa kanta ruwan zafin dafa kanta da kanta. A dai'dai wannan lokacin wasu kuyangu biyu suka shigo cikin parlourn bakinsu a ɗauke da sallama, ƴan'mata ne masu ƙananun shekarun da a ƙallah zasu kai 22 haka, hannunsu ɗauke da tray ɗin abinci mai girma wanda yake shake da cima iri daban daban a ciki, dukka tray guda biyun a shake suke tab. Ƙarisowa ciki suka yi, a tsakiyar parlourn saman carpet suka zubesu, sannan suka zube gwiwowinsu a ƙasa domin su kwashi gaisuwa a gun yarima. Basu kai ga buɗe baki su furta uppan ba Sarina ta kai hannu ta fisgi cup ɗin drinks ɗinta dake hannunsa, babu tsoro bare shakkar komai ko tunanin abin da zai je ya zo kawai ta watsa mashi wannan drinks ɗin gabaɗaya a face ɗinsa ta gangaro har jikinsa. Rai a matuƙar ɓace ta yi wurgi da cup ɗin ƙasa ya faɗi ya tarwatse, bata jira ganin reaction da zai ɗauka ba ta juya cikin ɓacin rai ta nufi waje. Yadda take tafiya da sauri sauri ya ja hankalin kowa dake harabar gidan har da abokin yariman a kanta, gabaɗaya suka bita da na mujiya, bata zame ko'ina ba sai room ɗin Mammienta. Tana shigowa parlourn ta ci karo da Rizwan da ya fito daga part ɗin King, ya je sun gaisa da Akka ce ya kara yi mata batun aurensa da chuchu da yake son ayi cikin satin nan kafin ya koma. Akka dai ta yi na'am da hakan, har ma ta ce mashi on this coming Friday za'ayi komai, sosai ya ji daɗi, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin farinciki ainun. Amma dik wannan farincikin da yake ciki suna cin karo da Sarina cikin irin wannan shiga da yake jikin nata sai da farincikin ta kau daga kan face ɗinsa, nan take ya ɗaure fuska sosai. Sai dai kafin ya yi mata magana har ta shige room ɗin Mammienta, dan wani uban sauri take zubawa, tamkar bata gansa ba ta wucesa da sauri, da alama kasancewarsa shiru shiru mai sauki kai sosai yaja suka rena shi. Dan a dik jikokin Akka babu mai saukin kansa, ga fara'a, kunga ai basa gigin kawo wa Jawad iyashege, da Jawad ne wlh kome ta kwaso, ko da wuta take tafiya sai ta tsaya ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa, amma da yake wannan gajeran dangarta ne sai ta wucesa fuuuu kamar kunfa. Da ya so ya bi bayanta izuwa ɗakin mammie ɗin, sai kuma ya fasa ya nufi nasa part ɗin a zuwan zai yi mata magana idan suka sake haɗuwa. Shi kuwa yarima wani irin murmushi ya saki na abin da ta yi mashi, sai dai da alama murmushin takaici ce, a face ɗinsa bai nuna ya damu ba, daga ta cikin zuciyarsa kuma tamkar ya murɗe wuyarsa ya mutu yake ji saboda wani irin ɗacin takaici da ya ji, ba'a taɓa yi mashi irin wannan cin mutuncin da ta yi mashi ba, ace dik izzarsa da isar nan tasa Sarina ta walaƙanta sa har haka?! Abin da kunar rai gaskiya. Waje ya nufo shi ma ba tare da ya ɗaga idanu ya kalli kuyangun da suka kawo mashi abincin ba. Yana fitowa ya nufi motarsa tare da bada umarnin su tashi motoci su tafi. Da ido abokinsa ya bisa da shi yana addu'ar Allah ya kara, dan ko ba'a gaya mashi ba ya san rashin mutunci Sarina ta yi mashi, da yake abokinsa ne sai ya iya gane hakan y a face ɗinsa!. A dai'dai lokacin kuma ita ma Fanan ta fito a tare da nata yariman daga ɗayan part ɗin, sai murmushi yake yi ita ma tana murmushi kuyangu biyu suna take mata baya, shi ma dogarawa biyu suna take mashi baya. A haka ta rakosa har wajen mota, sai kwasan gaisuwa sauran dogarawansa dake jiransa a wajen suke yi a wajenta. Cikin mutunci ta rinƙa amsa masu. A jikin motarsa ya jingina bayansa, cikin sanyin murya ya furta. "Na ji matuƙar ɗaci da takaici na rashin samunki a matsayin mata da na yi Fanan, amma ba komai kana naka Allah yana nashi, na gode da karranawa kuma na ji matuƙar daɗi, ina yi maki fatan Allah ya haɗa kanku ke da wanda kike so ɗin ya kuma baku zaman lafiya". Kanta a ƙasa ta furta. "Amin ya Allah, ina godiya sosai da addu'a, ni kai'na na ji babu daɗi da zuciyata ta riga fara son wani ba kai ba, ina yi maka fatan samun mace tagari tamkar yadda kake nagari mai tsoron Allah". "Amin Fanan, amma ba zan gaji da faɗin na yi babban rashi ba, na kuma ji ciwon hakan sosai a zuciyata, kuma na tabbata zan cigaba da jin zafin hakan na har abada, na so ki sosai Fanan, tun da na ɗaura idanuna a kanki sonki ya shigeni, amma babu komai na barki lafiya, please keep smiling like the way you're, murmushi tana yi maki kyau sosai". Yana kai karshen maganar ya matsa daga jinginar da ya yi da jikin motar. Wani dogari ya yi saurin zuwa ya buɗe mashi kofar motar, a back seat ya zauna idanunsa a kanta. Kanta a sunkuye tana kallon ƙasa ta jinjina mashi kai tare da furta. "In Sha Allah ko dan kai zan cigaba da kasancewa da murmushina, nagode sosai da ka fahimceni, ina yi maka fatan alkhairi". Kawar da kallonsa daga kanta ya yi cikin jin kunar rasata da ya yi, dogarin ya rufo kofar motar, sauke glass ya yi a in da ya ce mata ya gode, daga haka bai kara furta uppan ba aka tashi motocin nasu. Tana tsaye a wajen tana kallonsu har suka danna hancin motocinsu waje da gudu. Shi ma idanunsa a kanta har suka bar gidan, motocin yariman Sarina na fita ne nasu ya take masu baya. Ajiyar zuciya ta sauke na ganin sun fice, godiya ta ɗaga hannu ta yi wa Allah da ya sanya ta rabu da wannan yariman lafiya, yarinyar kirki, ita dai bata bi shawarar Mammienta ba, ta fito fili ta gaya mashi gaskiyar dake cikin zuciyarta na cewa tana son Jaish, ba faɗa ba komai, suka gaisa cikin mutunci, ya isar mata da kudurinsa a kanta, bata katse shi ba har ya gama jawabansa, sannan ne ta fara da bashi hakuri kafin ta ɗaura mashi da sauran bayanai. Da yake mai ilimi ne shi ɗin sai ya fahimceta ya kuma yi mata uzuri, suka yi hira cikin mutunci da mutunta juna, ta yi ta bashi hakuri yana ce mata ba komai wlh, ai bai sani ba ne, da ya san tana da wanda take so ma ba zai zo ba, dan haka ita ma ta yi hakuri. Cikin fara'a da girmama juna suka rabu abin gwanin birgewa saɓanin Sarina da nata saurayin. ______________________🦋💘 Har cikin ɗaki ta bisa tana faɗin Allah ba zata rabu da shi ba, sai dai ko da ta shigo cikin room ɗin baya nan, babu shi a ɗakin. Duba shi ta fara yi dan dai ita tasan taga shigowarsa, yana shigowa ta biyo bayansa, sannan ace baya ciki, to ina ya shiga?. Balconynsa ta fara leƙawa, wayam baya nan, a hanzarce ta zo ta nufi toilet dan wauta. Wayam baya ciki, yanzu da yana ciki ma haka zata shiga dan yarinta na mata gizo a kai. Bincikarsa ta fara yi babu kakkautawa, tsabar shiririta har da leƙa kasar gado, tana yi tana hawaye, ni kam na ce Jawad mage ne da zai shiga kasar gado ya ɓuya fisabilillahi idan ba shirme irin ma Chuchun ba. Ta ko'ina sai da ta leƙa except bayan curtains kawai, ta sha wahala bata gansa ba, sai ta haye saman gadonsa, ta kwanta tare da rungumo pillow tana cigaba da kukanta tamkar wadda aka daka. Kamar daga sama taga an kashe wutar ɗakin, ai a fujaje ta miƙe zaune a tsakiyar gadon tana rarraba idanu kamar an tare ɓera ga tarko, ɗakin ya yi duhu sosai saboda curtains gabaɗaya a sake suke. Zaro idanu ta fara yi, kumatu a kumbure ansha kuka a ƙoshi ta furta. "Yah Jawad bana so, dan Allah ka kunna wutar, ka dai san duhu tsoro yake bani ko?". Tana magana hawaye suna kara tsananta gudu a saman face ɗinta. Muguwar matsoraciyar duhu ce, bata kaunar rashin haske ko kaɗan! Tana iya sumewa ma idan duhu ya yawaita. Shiru bata ji motsin kowa ba, kamar zata saki fitsari a wandonta ta sake faɗin. "Yah Jawad dan Allah ka bari ka ji, wlh ina jin tso........." Bata kai karshen maganar ba sai ji ta yi ya rungumeta ta baya, ta tsorata sosai sai ta wage baki zata fasa mashi ihu. Da sauri ya rufe mata shi da hannunsa, a kunne ya raɗa mata kalmar sarkin tsoro yi mun shiru. Ƙoƙarin kai mashi dukan wasa ta yi tana ƙoƙarin kwace kanta daga riƙon da ya yi mata. Jawota mai gabaɗaya ya yi ta faɗa jikinsa yana faɗin. "Sorry my beb kin ji?". Harara a duhu ta banka mashi, tana shasshekar kuka ta furta. "Dan Allah ya Jawad ko wutar lamp ne ka kunna, kaga ina jin tsoron duhu sosai, ko dai ka manta ne?". Kai ya girgiza mata alamar a'a bai manta ba, ƙasa ƙasa ya ce. "Tun da kina jikina bai kamata ki ji tsoro ba". Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar haka ne, amma bata furta kalma ba, ta yi shiru tare da kwantar da kanta a kirjinsa. "My beb kin san me nake tunani kuwa?". Ba tare da ta ɗago ko ta yi magana ba ta girgiza mashi kai kawai alamar a'a bata sani ba. "Tunani nake yi ko dai na yi wa dad batun aurenmu ne? Wlh na gaji da ɓuye masu da nake yi, ina buƙatar kasancewa da ke a kullum ba tare da wani shamaki ba". Tana dai lafe, kasa kasa a shagwaɓe ta ce. "Da zanfi kowa farinciki kam my melody". Da sauri ya ce. "Da gaske kike yi? Kin yarda na bayyanar da soyayyarmu na kuma nemi aurenki?". Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e, wani irin farincikin da ya ji ne har bai san lokacin da ya matseta a jikinsa sosai ba, har sai da ta furta washe ne ya farga ya ɗan sassauta mata riƙon yana sauke ajiyar zuciya. Shiru suka yi na ɗan lokacin, shi ya afka tunanin ɗan uwansa Jaish wanda da shi yake kwana da shi yake tashi a cikin ransa, kullum tunaninsa ina ɗan uwan nasa ya tafi? Ga shi har yana shirin yin aure bai dawo ba, yau tsawon watanni kenan. Abin ya yi mugu mugun taɓasa, dik ya zabge sosai, dan ma Momma tana tsawatar mashi haɗe da rarrashinsa a kan ya kwantar da hankalinsa ɗan uwansa yana nan dawowa nan ba da jimawa ba, amma dik da hakan ya kasa samun nutsuwa, kullum yana cikin fargabar labarin da zai ji a kan ɗan uwan nasa. Ita kuwa rufe idanu ta yi babu jimawa barci ɓarawo ya saceta, dan daren jiya ta biye mashi, bata yi barci ba suka rinka zuba hira, da safe kuma ta tafi school, shi ne yasa barci ya tarun mata sosai. Saukar numfashinta irin na mai barci da ya ji ne ya fargar da shi tare da dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka. Ajiyar zuciya ya sauke tare da matsawa kaɗan, a hankali ya kwantar da ita, ya janyo pillow ya sanya mata a wajen kanta, ya kuma janyo bargo ya lulluɓeta. A gefenta ya kwanta shiru, jikinsa dik a mace na tuna Jaish da ya yi, ji yake yi tamkar ya sanya hannu bisa kansa ya zunduma ihu ko zai ji sassauci a ransa. A ɓangaren Auta da uncle Taheer da suke cikin gonar dad kuwa, sai janta da hira uncle Taheer yake ta faman yi, yana son su saba da ita sosai, ita kuwa ta tasa waya a gaba tana ta danne danne. Wani irin sako aka turo mata ta nutsa ciki take ta aikin karantawa, abin ya bata mamaki kuma ya taɓata sosai, sai take ganin kamar wannan yarinman ne da ya nemi izinin neman aurenta dad yaki yarda, kamar shi ya turo mata da saƙon, dan taga saƙo ne na zallar madarar kalaman soyayya masu ratsa zuciya. Gabaɗaya sai ta ji wani irin yanayi haɗe da nutsuwa ya ratsata, dik da bata son shi sai da ta ji sakon nasa ya yi matuƙar birgeta, ya zuba kalaman da zasu kwantar da hankalin mai karantawa, da alama ya iya tsara zance sosai, ga wani irin yaba kyanta na daban da ya rinƙa yi, addu'oi sosai ya rinƙa kwaranya mata. My people's kun ga ta in da yarima zai ɓullo wa Autarmu kuma ko? Ko waye ya bashi numberta? Wai ana so dole ne ma?. Muje dai zuwa, kowa ya iya allonsa ya wanke, iya ruwa fidda kai! Ni dai ina gefe ina shan maltina mai sanyi!. Yar tahaliƙar nan bata san lokacin da ta fara sakin murmushi tana karantawa ba, lokacin da ta zo karshen rubutun sam bata so ya kare ba, bata gaji da karanta yabonsa a gareta ba, ya tsara zance iya zance. Haka kawai saboda daɗin kalamai sai ta tsinci kanta da yi mashi reply, mutumin da tana ji dad ɗinta ya ce ya dakatar da shi daga zuwa in da take, amma sai ga shi tana yi mashi reply a what'sapp, har da murmushinta. Aikuwa tana tura mashi reply tamkar jira yake yi ya sake maido mata da sakonni masu zafin gaske, kalamai masu zafi da suka fi na baya. Tuni ta nutsa cikin karantasu, ya ja hankalinta matuƙa, sai surutunsa uncle Taheer yake yi bata ma san da yana yi ɗinba. Idan muka waiwaya muma waiwayo gidansu Khadija kuwa. __________________________🦋💘 GIDANSU KHADIJAH 😥 💔 Kwance take saman gadonsu ita kaɗai a cikin ɗakin, Zee bata nan, da alama akwai in da ta je ne. Ta yi nisa cikin barcin da take yi, ta kudundune a cikin bargo saboda sanyin safiyar, jiya da ruwan sama suka kwana, ruwa tamkar da bakin kwarya haka ya rinƙa zuba, kun san irin wannan barci na sanyin ruwan saman daɗi ne da shi ga nauyi. Dan haka barcinta ya yi nauyi matuƙa, ga cikinta a yanzu ya kara girma sosai, ya bayyana, a cikin fari dai tamkar zata haihu yau ko gobe, sai dai cikin nata watansa bakwai ne, da sauran two months. A hankali Hauwa ta turo kofar ɗakin nasu ta shigo, tafiya take yi tamkar sabuwar ɓarauniya, kamar bata son taƙa ƙasa, tana sanye da wani shegen hijabi har yana jan ƙasa na munafurci, ita fa Hauwa wlh ko takaba matar nan bata yi ba, baban Zainab yana rasuwa da sati biyu ta shiga yawon zawarcinta abinta. Wai shin ina Sadiq? Ina hajiyarsa? Ina maman Haidar? Mu je dai zuwa. Ɗakin nasu da ɗan duhu kasancewar dukkannin labulaye ɗakin a sake, haka ta rinƙa lallaɓawa a cikin wannan duhu ta nufi wajen drawers na gadon, Khadija tana ta barci bata sani ba. Cikin sanɗo ta fara bubbuɗe drawers ɗin, ko tsoro bata ji ba, bata fargabar Zee ta shigo ta kamata, haka ta bubbuɗesu dikka ta caje ko'ina a cikinsu tsab, sai dai bata ga jakar kuɗin ba. Miƙewa ta yi ta koma wajen wardrobe ɗinsu, a hankali ta buɗe kofarta, sai dai ga mamakinta sai ta ga cikin wayam babu komai, ko ɗan'kwalinsu babu a ciki, ina suka kai kayan sakawar tasu kenan? Ta jefawa kanta tambaya. Waigowa ta yi ta nufi wajen bayan gado, matar nan tsabar kwarin gwiwa har da hayewa saman bed ɗin ta leƙa ta baya ko Allah zai sa ta gani. Wayam babu komai, saboda tsabar karfin hali har da saukowa ta nufi toilet dan ta duba ta gani. Babu in da bata bincika a cikin toilet ɗin nan ba, har da buɗe cikin wc tsabar kanta famko ne babu komai a ciki, tsab ta bincike ko'ina, ita fa bata tunanin ga wajen da ya dace ace abu makamancin haka ya kasance, idan ba rashin basira ba fisabilillahi me zai kai jaka cikin wc idan ba tunanin dabobi irin na Hauwa ba!. Fitowa ta yi sumomoi sumomoi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, tamkar zata rusa ihu na rashin samun biyan buƙatarta. Khadijah kuwa har lokacin bata farka ba, Allah sarki abin ku da barcin mai ciki. Har ta kai bakin kofa zata fita kenan sai tunanin ta ji sun ce yau zasu tafi Kaduna ya faɗo mata a cikin ranta, cikin sauri ta juyo ta dawo cikin ɗakin, tabbas ta ji suna hira daren jiya a kan yau zasu ta fi wajen kakarsu a Kd, to da yiwuwar shiyasa suka kwashe kayansu dake cikin wardrobe ɗin dikka suka sanya a akwaiti kenan, to dik yadda aka yi wannan jakar kuɗin ma tana cikin akwatin. Ai kuwa jin wannan tunani nata ya yi mata daɗi ne yasa taji tamkar ta kurma ihun daɗi, har da yar tsallenta, kamar har ta ga kuɗin ta gama take ji a ranta. A hanzarce ta fara neman ta ina akwatin kayan nasu yake? Ta sake duba cikin wardrobe babu, ta duba wajen gado nan ma babu, nan take ta fara ɗaure fuska dan ta ga alamar murna zai koma ciki, tsabar shegen son abin duniya har toilet sai da ta sake komawa ta duba, nan ma babu komai. Kamar zata yi kuka ta nufi hanyar fita daga ɗakin, har ta kai kusa da bakin kofa sai kuma ta juyo da sauri ta nufin gefen wardrobe ɗin ta wajen jikin bango kusa da mirror. Aikuwa tana zuwa ta isko jakar kuɗin a saman akwatinsu da suka gama shiryata tsab saura tafiya, bayin Allah sun shirya komai nasu tsab, jiran Zee kawai Khadija take yi ta dawo su tafi, ta je kwaso masu sauran wasu abubuwan da zasu buƙata ne a tsohon gidansu, shi ne Khadija ɗin ta ce bari ta ɗan kishingiɗa ta huta kafin ta zawo su wuce tasha in da zasu hau mota, shiyasa Hauwa ta tashi hankalinta sosai ta ƙasa hakuri har sai da ta shigo masu ɗaki neman kuɗin, dan tasan yau zasu tafi, idan suka tafi kuma shikenan ta rasa wannan kuɗi. Wannan kuɗi na Khadija fa idan za'a canza shi a kuɗin Nigeria to ba za'ayi maganar millions of naira ba, sai dai billions of naira, da alama wanda ya bata wannan kuɗi a gaskiya yana ɗaya daga cikin manyan masu kuɗin kasarsu, kuma a haka take tunanin buga shari'a da shi ta ɓata mashi suna idan ta haihu! My people's thinks about that fa da kyau, mutumin da zai kwashi kuɗi makudai irin waɗan nan ya baka ai kasan ya wuci tunaninka, kuma a hakan fa kaɗan ya ɗan tsakura daga cikin dukiyar tasa ya bata, a haka zata ja da shi? Ni dai a ganina gaskiya Khadija zata yi ganganci in ta ce zata yi hakan, kuma wlh zata iya janyo matsalar da zai sa ta rasa ranta, kai bama ita kaɗai ba harta Zainab idan abin ya kwaɓe ba tsira zata yi ba! Ku dai duba mun wannan lamari fa. Akwai matsala gaskiya, da ta yi hakuri ta barwa Allah komai, ko ba ji ma ko ba daɗe gaskiya zata yi halinta, domin kuwa Allah bai yi alkawarin tallafawa azzalumai ba, mu je dai zuwa. Wani irin uban tsalle da ta daka tare da kware baki zata yi ihu ne sai ta tuna ashe a cikin ɗakinsu take, jikinta na kerma ta kai hannu a kan jakar kuɗin, idanunta garau ta waro a kansa. Mu koma baya kaɗan, kwanaki huɗu da suka wuce maman Haidar ta dawo Kano, dik ta rame ta kwanjame, tamkar ƙashi da rai haka ya zama, abin tausayi kuma shi ne har wa yau bata sami damar ganin Haidar ɗin ba. Wasu ma idan ta je wajensu cemata suke yi an kashe su Haidar ɗin ai, dan haka ta dai'na wahalar da kanta, an rufe babinsu yanzu ta koma gida. Sam taki yarda Haidar ya mutu, tana ta shan wahalar bibiyar manya dan ta samu sahihin ainahin labarin in da yake ko da ba zata samu damar ganinsa ba. Yanzu haka karewan da kuɗin hannunta ya yi ne yasa ta dawo gida ba dan ta so ba, babu mai bata abinci bare abin sha, a ƙasan gada ma take kwana, ba ta da wata mafaka, ganin yunwa yana ƙoƙarin yi mata illah ne yasa ta gudu ta dawo domin ta ɗan harhaɗa wasu kuɗaɗen ta sake komawa. Sai dai kuma tana dawowa ta iske mummunar labari na rasuwar mahaifiyarsu, aikuwa wani ihun da ta kurma ta yanke jiki ta faɗi ne har yau ba'a sake gane kanta ba, tana gadon asibiti tare da maman Hanif dake jinyarta, ko leƙa asibitin Hauwa bakar munafuka taki yi, kuma ko naira biyar taki basu su yi jinya, sai dai maman Hanif ɗin ce yar albarka take ta ɗawainiya, baiwar Allah ita ma ba karfi ne da ita ba, abinci ma da kyar suke iya samun cin sau biyu a rana, amma dik da hakan bai sa ta juyawa ƴan uwan nata baya ba, dik wanda ya shiga matsala dai ita ɗin ce kawai take tsaya mashi. Wannan a takaice kenan abin da yake faruwa, su Khadija sun je asibitin har sau biyu suna dubata, a lokacin bata farfaɗo ba, yanzu da ta farfaɗo kuma ko magana bata iya yi, sai shiru kawai tana bin mutane da ido, sannan ta samu cutar mutuwar ɓarin jiki wato paralyze, ɓarin hagunta ya mutu gabaɗaya daga hannun har kafa, bata iya motsa shi, innalillahi wa inna ilahir rajiun, ya Allah mun tuba, mun tuba ya Allah, Allah ka rabamu da mummunar ƙaddara, kasa mufi karfin zuƙatanmu, ya Allah ka karemu daga zalintar wani da har alhakinsa zai bibiyemu, hasbunallahu wani'imal wakil. Kun ji abin da yake faruwa a halin yanzu, to mu koma kan labarinmu!. STORY cikin hanzari Hauwa ta dauke jakar kuɗin nan ta fice da shi, kai tsaye room ɗinta ta nufa. Tana shiga ta datse kofa, tana shigewa kuma ɗakinta Zee na shigowa cikin parlourn hannunta ɗauke da jakar school ɗinta mai shake da wasu kayan sakawansu da litattafansu. Bata san da Hauwa ta shiga ɗakinsu ba, dan bata ganta ba, ta shige ɗakinta. Kai tsaye nasu ɗakin ta nufa, tana zuwa ta haye gado tana kiran suna Khadija da ta tashi su tafi kada rana ta yi. Da kyar ta iya samu Khadijar ta farka tana wani yin uban miƙa haɗe da hamma. "Aunty khadina ki tashi mu tafi rana tana yi". Idanu jajir saboda barci, murya irin na mai barci ta furta. "To kin ɗauka mana kayan ne?". Kai ta gyaɗa haɗe da cewa e. Miƙewa zaune a tsakiyar gadon ta yi, jikinta sanye da hijabi har ƙasa, saukowa kasa ta yi suka nufi wajen akwatin, Zee ce ta janyoshi ta fito da shi tsakar ɗakin. "Zee ina kamar jakar dake kan akwatin? Ko dai kin sanyata a ciki ne?". Har lokacin muryarta irin na masu barci ta yi tambayar. Zee ɗin kuwa cike da zumuɗin son ganin Sadiq, burinta kawai su tafi, a ƙage take da son ganin sun bar gidan, sai kawai ta ce. "E ina ga na haɗesu a ciki kawai, yanzu ke aunty kadina ki ɗauki jakar school ɗin nan naki ki goya a baya bari na ja akwatin nan mu tafi ko?". Da to Khadija ta amsa, ba tare da sun duba jakar kuɗin sun tabbatar tana cikin akwatin ko bata ciki ba kawai suka ja suka fice daga gidan ba tare da sun bi ta kan Hauwa ba, suka rufe kofar room ɗinsu da key suka kuma sanya key ɗin a aljihun jakar bayan Khadija ɗin. Dama already Zee ta fitar da kuɗin motarsu a gefe kafin su shirya kaya, dollars dubu ɗaya ɗaya guda huɗu ta fitar, wai kuɗin mota da kuɗin cin abinci, a hakan ma fa dan wani ɗan islamiyansu da ya zo kawo masu ziyara tare da tambayar lafiya kwana biyu basu je islamiya ba ya gaya masu cewa dollar dubu ɗaya ta fi karfin dubu ɗayan Nigeria, dan yaga dubu ɗayan a hannun Zee zata je saya masu kayan tea ranar da maman Hanif ta daki Hauwa, idan baku manta ba a ranar ciwon Zee ya tashi, shi ne Khadija ta ce ta sayo kayan tea ta zo ta sha abu mai zafi sai ta sha maganinta da daddare kenan, kun ji dalilin da yasa kuɗin ya sake fita. So ya gaya masu kuɗin ya fi na Nigeria, dan haka su kai kasuwar canji a canza masu ko su kai bank, shi ne fa kuka ga yanzu suna ɗan daraja kuɗin har suke ganin dubu huɗu zai iya kaisu Kaduna daga Kano har su ci abinci. Ko da suka hau mashin suka je suka sauka a tasha sai suka bashi dubu ɗaya ta dala, basu tsaya ɓata lokaci ba suka shiga cikin tashar, kun san tasha dama idan ka je har rububin kwatar kayanka ake yi a sanyasu a mota, to haka suma aka yi masu. Mai mashin ɗin kuwa, ganin hankalinsu baya a kansa, basu tambayi canji ba sai ya buga mashin ɗinsa ya gudu abinsa, gaskiya ta yi ƙaranci over a duniyar yanzu, jama'a bin haramun suke yi da gudu suna ƙoƙarin kamata su ci, Allah ka kiyashemu cin haramun. Motar saura passenger huɗu dama, da zuwansu yanzu saura mutun biyu, zama Khadija ta yi a cikin motar ita kuma Zee ta ce bari ta je ta tambayi in da ake canza kuɗi zuwa kuɗin Nigeria ta canzo masu su samu su biya kuɗin mota. Mai motan da zai ɗaukesu ɗin ta nema, Allah ya taimaketa sai ta nuna mashi dollars dubu ɗaya ta ce tana son ta je ta canza ta izuwa kuɗin Nigeria ne dan ta biya kuɗin mota ya nuna mata wajen da ake canzawa, Allah ya rufa mata asiri bata nuna mashi dikka ukun ba, kamar tasan kuɗin darajarsu ya wuci tunani, kuma bata sani ba, kawai dai ta zaɓi ta nuna mashi guda ɗayan ne. Aikuwa zaro idanu ya yi waje, cikin kaɗuwa ya tambayeta shin tasan nawa ne a hannunta kuwa?. Girgiza mashi kai ta yi alamar bata sani ba. Ganin e da gaske bata san darajan kuɗin bane yasa ya ce mata zai canza mata to, duniya babu gaskiya, gaskiya ta yi ƙaranci, zalinci ta yi yawa, ba amana, bawan Allahn nan bai ji tsoron Allah ba ya ɗauki dubu goma ya bata ya karɓi dallar da darajarta ya kai almost 1.5m da dauriya. Da yake bata san darajarta ba sai ta karɓi dubu goman ta yi mashi godiya, sai ta sake tanbayarsa nawa ne kuɗin motarsa, ko tsoron Allah babu har da wani cewa ba damuwa ya yafe mata, wannan kuɗin da ya bata su yi kuɗin mashi idan sun sauƙa a Kd. Ko da yake ya fi wasu fa, da wani ne ma a duniyar yanzu wlh da kwace kuɗin zai yi ya gudu, gara shi ya basu 10k dan a tunaninsa iya kuɗin hannunsu kenan, ya ɗan ji tausayinsu kada ace basu da wani kuɗi su sauƙa a tasha su rasa ya zasu yi, shi ko tsoron kada gaskiya ta bayyana ko kuma ƴan uwansu su zo ɗaukarsu a tasha su gane gaskiya a kamasa ma bai yi ba, shi dai yana jin daɗi ya yi cuta mugu, shi dai ya samu kuɗi a tunaninsa. My people's wani fata zaku yi wa Zainab and Khadija a halin yanzu? Ga su dai zasu ɗauki hanyar Kaduna, me kuke tunanin zai faru? Shin zasu haɗu da Sadiq ɗin nasu kuwa? Zasu kai labari ko yaya? Mu dai je zuwa. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/11/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 __________38 In short haka mota ta tashi da su suka nufi Kaduna, har a lokacin babu wadda ta yi tunanin ina jakar kuɗinsu yake? Da gaske yana cikin akwatin ne ko babu, su dai kawai sun tafi. _______________________________💘🦋 _______________ JIMETA YOLA🦋🕊️ Tsab bappa da Jaish suka haɗa bukkar da shi Jaish bai san ta mecece bace, shi dai ya taya bappa aiki kawai. Suna kammalawa ana kiran sallar azahar, alwala bappa ya yi tare da ce mashi ya yi alwalar shi ma su je masallaci. Kin yi ya yi ya samu waje saman dutsen goge kafarsu ya zauna, kamar dai mai jiran wani abin, bappa kuma da ya kammala alwalar sai ya nufi masallaci a zuwa idan Jaish ɗin ya kammala ya same shi a masal. Zamansa ya yi saman dutsen da ya zauna da Mahnoor ɗazun, kamar mai tunanin wani abin ya buga uban tagumi a tsakiyar rana, ya yi shiru. Tana ɗingisa kafa ta fito daga cikin ɗakin na bappa, yana zaune ta zo zata wucesa, da idanunsa ya yi mata alamar ina zata je a tsakar ranar nan haka? Ga shi rana ta take sosai. Kitchen ta nuna mashi tare da ce mashi. "Ruwan wanka zan ɗaura maka hamma". Alama ya yi mata da hannu a kan ta koma ɗaki kada ta kara jin wani ciwo a kafan nata, kada ta fama ciwon nata. "To hamma idan na koma waye zai sa maka ruwan wanka?. Ka gani dai kai baka iya sakawa ba, ga shi ko masallaci kaki zuwa saboda baka yi wankan ba, bari zan iya ɗaurawa ai sai kai kuma ka juye to idan ya yi zafi". Tambayarta ta hanyar alama da hannnu ya sake yi a kan ina Mahreen ne take? Ita bata iya aikin komai ba face barci, yanzu ma tana can tana zuba barci ne. "Mahreen tana barci, kuma koda idanunta biyu ma bata iya hura wuta ba, bari dai na ɗaura maka ɗin". Kai kawai ya jinjina mata ba tare da ya sake yin wani motsi ba. Wucewa ta yi izuwa cikin kitchen ɗin, kafarta sai zogi yake yi mata, haka ta tsugunna ta hura wutar, ta ɗauko tukunya ta zuba ruwa izuwa rabi a ciki, sannan ta yunkura zata ɗauka ta ɗaura a saman wuta, sai kuma ta ƙasa, saboda a kan yatsun kafafunta take tsaye, idan ta ce zata ɗauki tukunyar yatsun nata suna iya karyewa ma, dan kun san dai ba zasu iya ɗaukar gangan jikinta cikin sauki bama bare kuma ace ta sake nauyinta sosai zata ɗaga abu mai nauyi, akwai wahala. Duƙawa ta yi a karo na biyu zata ɗauka, kamar daga sama taga farar hannunsa yasa ya karɓi tukunyar, a saman wutar ya ɗaura mata ba tare da ya yi mata wata alama ba, ya juya ya nufi waje abinsa. Da kallo ta bi bayansa tana tunano zantukan Jumman Inna Rabi, ita kanta yanzu sai ta fara ganin kamar ya fi Hamma Faisal ɗinta sosai, da soyayyar Faisal ya rufe mata idanu yasa bata ganin kowa da wani fasali idan ba shi ba. Komawa ɗaki ta yi ta kwanta, tana jinsa lokacin da ruwan ya yi zafi ya juye da kansa ya ɗebo na sanyi ya surka. Wanka ya je ya yi abinsa, yanzu fa shi ma ya saba da abubuwa dayawa nasu, yana cin irin abincinsu, yana kuma shan nono da fura, rayuwa kenan, kana naka Allah na nasa, dik wanda kuka ga yana ihun shi bai iya abu kaza ba bai iya abu kaza ba, hmmmm bai je in da zai iya dan dolensa bane. Bappa kuwa tun da ya yi sallah bai dawo gidan ba, kasuwar kauyen gabansu nan ya nufa, kauyen tafi nasu girma, har ɗan primary school suna da shi, so akwai kasuwa mai dan girma, a nan suke sayen abubuwa. Abubuwan amfanin gida irin nasu na kauye ya je sayawa Mahnoor ɗin kamar yadda yake a al'adance, har da su samiru dikka, ya saya masu katifa da dik abin da za'a buƙata. Ko da ya dawo gidan Jaish baya nan, ya tafi yawonsa cikin kauye. Cikin sabuwar bukkar da suka haɗa ɗin ya shigar da kayan, Mahreen ta tashi barci a lokacin, ita ta taya shi aiki, ƴan uwansa dik sun ki zuwa in da yake, saboda ya hana Faisal Mahnoor ya bawa wani, abin ku da kauye wai gaba suke yi da shi, da yake su basa raina abin yin gaba, ga basa manta gabar komai daren daɗewa. Shi ne yasa suka ki zuwa taya shi murnar auren, bawan Allah ko a jikinsa, a cikin zuciyarsa abin ta yi mashi zafi, amma a fuska sam bai nuna hakan ba. Haka suka shirya komai tsab shi da Mahreen, Mahnoor tana barci. A daren ranar dai a ɗakin bappa Jaish ya kwana kamar yadda suka saba, ita ma Mahnoor a ɗakinsu ta kwana, dik da an haɗa masu ɗakinsu bappa ya ce sai anyi biki an gama za'a kaita ɗakin nata. Washegari da safe suka tashi da shirin yin biki, sai hidima Mahreen take yi, tana ta up and down, shige da fice, ba zama busyn body, abin yi ya samu Addarta da Hamma aljaninta suna aure. Bappa kuwa sai lallaɓa Jaish yake yi yana rarashinsa haɗe da rokonsa da ya yarda ya je wajen bikin nan ya kuma karɓi al'adunsu hannun bibbiyu. Ba dan ya so ba ya amince da hakan, sai dan yana matuƙar ganin girman bappan sosai, yana kuma jin kunyarsa!. Kuɗi sosai da a kallah zasu kai 100k bappa ya damƙawa Inna Rabi da ta je cikin gari ta yi wa Mahnoor sayayyar kayan kwalliyar da za'ayi mata kwalliya a wajen bikin, da kuma kayan sakawa, sannan ta sayawa Jaish ɗin ma kayan sakawa da dai dik abin da ya dace. Bawan Allahn nan shanunsa har guda uku ya sayar yau da safe dan ayi hidiman bikin nan cikin gata da birgewa. Kun san bappa fa yana yawace yawace, so ya ɗan waye abinsa. After some hours. Bayan sun yi sallar la'asar, zaune take ita da Mahreen a cikin ɗakinsu, sun yi wanka, ita Mahnoor tana shafa mai a fatarta, ita kuma Mahreen tana zabga powder a fuska kamar dai yadda ta saba. Sallama aka yi masu a kofar ɗakin nasu, kallon juna suka yi suna mamakin jin muryar Inna Rabi yau a gidansu, dan bata zuwa saboda masifar Nenne, kuma su sun mancema yau ake bikin. Mahnoor ce ta danne mamakin nata tare da amsa mata sallamar, cikin ɗakin ta shigo kai tsaye, sai kallonta suke yi har cikin ido, Mahreen ta zaci ma ta biyota ne har gida ta zaneta dan yau basu je islamiyyar ba, dan tasan ita ɗin uwar yin laifi ce acewarta. "Inna ina wuni". Cewar Mahnoor. Fuskarta cike tab da fara'a ta amsa da. "Lafiya lou Noor". Mahreen ma ɗaga mata gaisuwa ta yi tana cigaba da labtaka powder dai. "Mahreen a rage powder nan haka mana". Inna ta faɗa tana kallonta. "Ai sai ki ƙarisar maku da shi a tashi ɗaya, ke baki san kaɗan kaɗan ake shafawa bane? In ma kika shafa dayawa ai ba zaki yi kyau ba". Ta kai karshen maganar tana maido da kallonta a kan Mahnoor. Baki ta turo gaba. "Inna dandali fa zan je, bappa ya ce in je in same shi a can, kin ga kuma yau auren Adda Mahnoor ɗina za'ayi, dole na fi kowa kyau". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar. Sai a lokacin Mahnoor ta tuna ashe wai bikinta ake yi yau. "Dik da haka a dai rage powder, idan kina son ki yi kyau ma ai kaɗan zaki saka, sai ki fi kyau haka". To kawai ta amsa kumatu a kumbure, ita a dole bata ji daɗi ba za'a rage mata make up ɗinta. Dawo da kallonta a kan Mahnoor da ta takure waje guda Innar ta yi, ta wani haɗe jikinta waje guda, saboda daga ita sai ɗaurin kirji, mai take son ƙarisa shafawa ta sanya kaya, amma Inna tazo tasa ta jin kunya, sai ta kasa iya ƙarisa shafa mai ɗin ma, ta zauna shiru kanta a ƙasa. "Mahnoor ki karisa shafa man mana, jiranki fa muke yi mu tafi". Cewar Innar. To ta amsa kanta a ƙasa, ta kasa iya ɗagowa, tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta kai hannu ta ɗebo man ta cigaba da murzawa a jikinta kunya kamar ta shige cikin ƙasa, ita da kullum ba dare ba rana tana tare da hijabi a jikinta, yau kawai Inna ta zo ta sani kalleta da ɗaurin kirji, dik sai ta ji babu daɗi. Ni kam na ce Jaish dai ya ji daɗi wlh, ya samu matar da bappanta ma rabonsa da ya kalli iya wuyarta ma tun da ta fara wayo, kullum cikin hijabi, ta killace jikinta, ko mata ƴan uwanta bata yarda su gani ba bare maza, ko Mahreen bata samun ganinta babu hijabi, yau ɗin ma ta wanke hijabin ne ta shanya yasa Inna ta shigo ta sameta a haka. Ledar hannunta da ta shigo da shi Innar ta miƙa mata tana faɗin. "Karɓi wannan kaya ne da bappanki ya bani kuɗi a kan naje cikin gari na saya maki, ki sanyasu, akwai na Mahreen a ciki........". Jin akwai na Mahreen a ciki yasa ta yi zafin namar kwace ledar daga hannun Innar, Mahnoor da ake miƙawa bata kai ga karɓa ba ta rigata, tuni ta miƙe tsaye tana sakin uban murmushi. A hanzarce ta fito da kayan, blouse ne masu kyau, dogayen riguna ne, dikkansu kala uku uku ta saya masu, rigunar da gyalensu, kayan suna da kyau, sai dai kayan takaici Inna ta tashi ta je ta ɗauko masu kaloli marasa kyau kamar mutun ya kurma ihu, wani irin yellow irin mai paw ɗin nan, da kuma wani ja jaw haka, sai kuma ruwan omo ta ɗauko masu, wai a haka tana gani ba kalar da ya kaisu kyau, ga shi iri ɗaya ta saya masu, haka takalmar da ta saya masu ɗin ma, yellow da baki, irin takalmar masu high kaɗan ɗin nan, ba abin da ya fi bakanta mun rai ma kamar wannan yellow doguwar rigar, ga riga har riga amma kamar ka kurma ihu saboda rashin kyan kala. A haka su kam suka rinƙa murna, wai kayan ya yi masu kyau, tuni Mahreen ta fito da wannan yellow ɗin ta zurmuƙa ga jikinta, da alama dama sun fi son abu paw mai haske haka. Ai kuwa tana sanyawa sai ta zama kamar aljana albojel, dama ga uban powder da kwalli a fuska, idanun nan sun ji kwalli marau, abin sai wanda ya gani. Wannan idan ka ganta da daddare ka yi gudu ne har da zawo a wando, dan ba abin da zai hana baka ce aljana bace, da alam yau Jaish ba zai ganeta ba, dik wannan kauna da shakuwa dake tsakaninsu ina ga yau sai ya gudu idan ya ganta. Ita kanta Inna sai da ta ce. "Mahreen ki cire wannan riga ki saka ɗaya mai kalar omon nan, ita ce zata fi dacewa da kwaliyar nan taki tun da tana da ɗan duhu, ke kuma kwalliyar taki ta yi paw". Inna tana son ta cire yellow ne ba dan komai ba sai dan ita kanta taga ya yi wani paw, ga fuskarta kamar jan ƙosai ya ji kayan alatun bature. Aikuwa make kafaɗa ta yi. "Ni Inna wannan nake so gaskiya, yafi kyau da haskakawa". Bata da zaɓin da ya wuce ta kyaleta, idan ba haka ba yanzu sai ta tsayar masu da iyashege da kukan banza, gara kawai ta rabu da ita taje a kamar aljanar sai ya fi mata. Ita kuwa Mahnoor da ko ta kan Mahreen ɗin bata bi ba, dan tasan Mahreen dai ba canzawa zata yi ba. Miƙewa ta yi abinta ta ɗauki riga mai ruwan omon ta nufi bayan kofa, ɓuye ta yi ta sanya kayan, ba laifi sun yi mata kyau, dan ita bata yi pente penten komai a face ɗinta ba, hakan yasa kayan suka zauna mata dai'dai. A takaice dai haka suka shirya, Inna ta yafa mata gyalen rigar a kanta, ta riƙo hannunta suka fito waje. Cincirindon mata ne sosai a wajen, dik makota da abokan arziki haɗe da kawayen mamanta, ƴan uwan Inna kakarta dik sun zo daukarta zuwa wajen taron, ƴan uwan bappanta ne kawai ko mutun ɗaya bai zo ba, sun ki zuwa dan an hana Faisal ita. Inna Rabi ita ce malama shiyasa aka ce ta shiga ta fito da ita. A can wajen da za'ayi taran bikin kuwa, kasan wata katuwar dutsen dake kauyen ne, gabaɗaya an gama shirya komai, matasa da ƴan'mata a cike ta ko'ina, ga dattawa da sa'anin juna, ta ko'ina mutane, an kafa runfuna manya manyan, sannan an shinfiɗa tabarmu manya a cikin runfar, runfar dattawa maza daban, runfar mata daban. Biki fa gagaru suke shiryawa idan ma baku sani ba, dare suke ɓatawa suna shagali, kowa da irin al'adarsu a duniya, su kuma kunga irin nasu, kuma kowani al'ada ba wai suna yin shi ne dan nishaɗi kawai ba, a'a, kowanne da nufinsu a kansa. An ƙawata wajen sosai, harda kwalliya irin nasu dai na kauye suka yi wa wajen. Abin ya ƙayatar matuƙa. Daga can gefe akwai wata rami babba a in da ake ta aikin hura wuta a cikinta, dama ramin saboda bukukuwansu suka tonasa, dan aji daɗin yin shagali da kyau ana cin nama. Shanu manya manya guda biyu babba ya bada aka yanka, dama a al'adar yadda suke bikinsu, za'a yanka shanu a wajen, sannan a wajen za'ayi ta gasa namar kowa yana zuwa yana yanka ya ci yadda yake so, cikin wannan rami da suka hura wuta a saman ramin ake ɗaura karafunar gashin namar, mata masu yi wa namar haɗin kayan miya suna aikinsu, masu gasawa ma suna aikinsu, dik yadda ƴan kauye ke son dabbobin sun nan dai haka suke yin wannan al'adar, kun san fulani da masifar son dabbobinsu, amma dik da haka in dai za'ayi biki sai sun yi wannan al'adun ta iyaye da kakannin. Aci nama har a ƙoshi, sai dai ba'a taɓa yanka shanu biyu ba sai a wannan biki ta Mahnoor, kowa shanu ɗaya yake yankawa ƴarsa, shi bappa ya nuna masu da banbanci ya yanka biyu!. Yanzu ma haka aka yi, matasa majiya karfi ne suka kayar da shanun, aka ɗauresu Arɗo ya yanka, Jaish kam sai ganinsu kawai yake yi, shi fa wani lokaci idan suna yin wani abin wlh kallon tantiran mahaukata yake yi masu bawan Allahn nan, dan bai saba ba. Bappa yana ƙoƙarin sosai, dik kayan da Jaish ɗin yake sakawa fa bappan ne yake shiga gari ya saya mashi, shi dai bappan yana da kirki sosai, amma yakamata mu ɗan ji labarin bappan nan kaɗan dan mu san daga ina ya samo wannan kirkin nasa. To shi dai mutun ne ba mazauni ba, yanzu ma ba dan Jaish ba da ba zai zauna a garin har ya ɗauki tsawon lokaci har haka ba, baya wuce wata ɗaya zuwa biyu idan ya dawo, idan kuma ya tafi yana iya kai 6 month up haka, to a baya dai bappa mafaɗacin mutun ne sosai, dik da akwai ɗan wayewa a tattare da shi, sannan yana da ilimin addini, amma haka yake da faɗa sosai, auren soyayya suka yi da mahaifiyar Mahnoor, yana sonta sosai, amma saboda bakar zuciya da iya faɗa yasa yake gallaza mata. Ya wahalar da ita sosai har ta kai ta ce ba zata iya zama da shi ba, mafaɗaci ne sosai fiye da tunaninku, ga saurin fushi, abu kaɗan idan ta yi mashi haka zai hauta da faɗa, kun san maman Mahnoor ɗin yar uwarsa ce, so yana ganin kanwarsa ce, wani lokaci har hannunsa yake ɗaurawa a jikinta da sunan duka, a lokacin da take da cikin Mahnoor ɗin ya taɓa dukanta da har cikin ya kusa zubewa, daga haka ta gudu ta koma gida. Amma dik da haka arɗo ya datse idanunsa ya sake dawo da ita, kun san iyayenmu sai ayi ta kai masu karan miji suna cewa mutun ya yi hakuri ya yi hakuri, ba bincike ba bibiyar lamuran mutun, haka dai sai ayi ta ce mata ta yi hakuri komai zai wuce, watarana sai labari, ina mai tabbatar maku da bakincikin bappa maman Mahnoor ta bar duniya, a lokacin Nenne tana ƴar matashiya. Kai in takaice maku zance an haifi Mahnoor da kwana uku ma sai da ya daddallah mata marika a kan dan ta ɗauka mashi wasu magunguna da ya ajiye ta yi amfani da su bata tamnayesa ba, kuma a hakan fa ba wai baya sonta bane, yana sonta, kawai dai zafin zuciya garesa da rashin hakuri, ga shegen saurin fushi. Wani lokaci sai ya yi mata wani abin idan ya fita wajen kiwo sai ya yi ta faman danasani maras amfani, idan ya dawo kuma ba zai hana shi in ta yi laifi kaɗan ya wawwaka mata marika ba, aikin kenan kullum. In takaice maku labari dalilin mutuwar maman Mahnoor ɗin ya sanya zuciyarsa ta ladabta, tun daga lokacin da ta kwanta dama ya shiga damuwa mara misiltuwa, har jinya sai da ya yi, daga wannan lokaci ya rinƙa neman gafara a wajen Allah, ya kuma roki Allah da ya sassauta mashi wannan zuciya tasa, yasa a masallaci aka yi mashi addu'a, so a lokaci ne Allah ta karɓi addu'ar tasa zafin zuciyar ta tafi, ya zama so silent, dama can mutumin kirki ne, zuciyar ce matsalar. A takaice shi ne kuka ga ya zama haka, dik abin da yake yi wa mutane na kyautatawa a yanzu zaku ji yana cewa Allah ya kai ladar wa maman Mahnoor, ita yake yi wa hidima, wannan dalilin yasa yake yiwa Mahnoor ɗin kauna ta daban, a takaice kenan yadda aka yi ya zama na kirki kuma na daban a cikin kauyen nasu, sannan mai ɗan wayewa dai'dai gwargwado, dan haka mu koma kan labarinmu. Saman wani benci irin dogayen nan Inna Rabi ta zaunar da Mahnoor da kanta a ƙasa, shi ma bappa ya sha sabon ɗinkin kayan sallarsa da ya ɗinka, dama ya ɗinka ya ajiye sai sallah ta zo ya yi amfani da ita, haka yake yi kowace shekara, yana ɗinkin sallah da wuri ya ajiye, to a wannan karon dai sara ta zo a kan gaɓa, ya samu na shagalin biki. Kowa a wajen ya yi kwalliya sosai, wasu dan cin nama suka zo, wasu dan ganin gulma, wasu dan Allah, wasu dan suga aljani Jaish, wasu kuma dan suga shin mijin Mahnoor zai yi nasara ne ko zai faɗi, wasu dan kaunar da suke yi wa bappa da kyautatawar da yake yi masu. Kowa dai da abin da ya kawowa. Sai gutsiri tsomi ake ta yi a kan Jaish ɗin. Kada ku so ku ga Mahreen kanwar amarya, idan kuka ganta na tabbata sai cikinku ya yi ciwo saboda dariya, sai hidima take yi, ga shi ta je kusa da wuta zata ɗauko namar da ake gasawa, dan ita tana son abincin wajen biki hajiya mandiya ba. Aikuwa tana zuwa ta haɗa uban zufa, kada ku so ku ga yadda power face ɗinta ya zama, abin na manya ne, kawalliyar faɗarta wato Zainabu Abu ce ta matso kusa da ita tana rokarta nama. "Ki je ki ce in jini a baki". Ta faɗa cikin nuna isa, irin ita ce fa kanwar amaryar nan ta bada umarni dole abi. Ga shegen son girma kamar wata gembu. Labarina yana da tsawo, ba zan tsaya ɓata lokaci a wajen shirirtar ƴan kauyen nan ba, dan wlh akwai labarai a gaba, yanzu wasan zai fara, ba'ayi komai ba, dan jiga jigan shegun ma basu bayyana ba, akwai sauran tafiya kafin mu kai kansu, sai a fara buga wasan, dan haka ba zan tsaya cinye space da nake da shi a nan ba, so bari mu duba al'adun nan nasu in short, dan ma akwai abin da idan naje book 3 zan dawo dubawa a wajen bikin ne ya sa zan tsaya bada labarin, dan in mun je gaba in na tuna maku da wajen biki anyi kaza ku gane!!. Sai da suka ci suka sha, nama kamar hauka, masu kwasa suna kaiwa gida sun kwasa, anyi gashi sosai. Jaish dai yana zaune kusa da bappa, kansa na kallon ƙasa, dan ya gaji da kallonsu ya ce, ga shi kuma ya yi wa bappa alkawarin zai yi hakuri ayi komai da shi tsab a gama, dama tun kafin so zo wajen sai da bappa ya rokesa da ya yi hakuri ya cika al'adunsu, shi kuwa ya ce babu abin da bappa zai nema a wajensa ya gagara yi mashi, dan haka ya yi alkawarin tabbas zai yi iya ƙoƙarinsa ya yi abin da ya dace, shiyasa yanzu da ya gaji da kallonsu ɗin ma haka ya jure ya yi ƙasa da kai bai tashi ya bar wajen ba. Mahreen tana zaune kusa da Mahnoor, Jumma da ta ci kwalliyarta sosai ita ma tana zaune a ɗayan gefenta, sun sakata a tsakiya kenan, dan bata da ƙawaye, Jumma ce kawai kawarta, ita ma saboda tana zuwa Islamiya a gidansu yasa suka saba sosai har haka. Su Inna Rabi suna kan tabarmar a cikin runfa, jama'a suna zazzaune shiru. Kun san fa yanzu android phone ta ratsa har kauye, so a nan ma akwai ƴan gayu masu vivo, ga wani ɗan iskan Mp ɗinsu kato mai kama da irin manya manyan Radion nan na masu tallar maganin basir a kasuwan nin nan.........😂 Mp suka kunna, suka sanya wakar sauta fasitaka waɗata mivima ta metu, wai kun san fassarar abin da ake faɗa a waƙar nan kuwa?.....🤔 Sai chashewa ake yi, ga matasan mata da maza sai rawa suke yi a gefe, kun san sun iya cakuɗuwa mata da maza su yi ta chaskale rawa abinsu, wlh yadda suke rawar tamkar waɗan da aka sanyawa battery, kalan ƴan tsana masu magana, sai wani kaɗa kayuka da dogayen wuyoyi suke yi. Ai Mahreen ta ce baku iya ba ku bani waje, wani irin yawan da yarinyar nan take yi yadda kuka san rawan shegun karuwai, sai Allah kaɗai ya san mata daga ina ta koyo irin wannan rawa haka, yadda kuka san indiyawa masu rawa a club, har da wani girgiza tamkar wata mai cutar farfaɗiya, dama tasa jan power ta zama irinsu.........😂 Abin ba'a magana, a tsakiya suka sakata sai tikar uban rawa take yi, Mahnoor kuwa sai satar kallon angon nata take yi, yadda ta ga ya yi ƙasa da kai sai ta gane a dame yake, an takura shi dayawa, shi baya son hayaniya, dik sai ta ji tausayinsa ya kamata. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A..✍️🔥🕊️ Da misalin karfe 5 dai'dai Inna Rabi ta ce a dakatar da wannan kiɗan, dan lokaci gudanar da abubuwa ya yi, ai anci an sha, kuma an ɗan watsa jini wajen raƙashewa, dan haka yanzu saura a nutsu ayi kallon amarya da ango, a kallah yadda zasu kula da junansu. Bisa al'adar dama a halin yanzu yan uwan miji ne zasu fara bawa amaryar umarnin da ta ɗauki kwano ta ɗebowa mijinta namar da aka gasa ta zo ta bashi a baki, su kuma nasu kenan, to kun ga shi Jaish bashi da ƴan uwa a wajen, dan haka sai Inna Rabi ta wakilci yan uwan nasa a in da ta yi wa Mahnoor wannan umarnin. Dama bappa ne ya ce mata ta zama uwa kuma ƴan uwan Jaish ɗin a wajen taron. Baiwar Allah kunya kamar ƙasa ya buɗe ta nutse ciki, haka ta miƙe tsaye, idanun gabaɗaya jama'a a kanta, tamkar zata kurma ihu, Jumma ya ɗan riƙota suka nufi wajen da Inna Rabin take zaune cikin mata a ƙarƙashin runfar da aka kafa saman tabarma. Sabuwar plate dal a ledarta Innar ta basu, da yake bappa yasan al'adun nasu sai ya shirya komai da kansa, har plate ɗin dik shi ya saya, dozen ya sayo, sai ya ajiye mata sauran a cikin bukkarta. Dik wannan bidiri da ake yi Nenne bata nan, ko leƙau taki leƙowa, harda Arɗo yana wajen saman kujerar sarautarsa na musamman, amma ina bakar zuciyar Nenne ya hanata zuwa. Kun san yan uwan Arɗo su ne ƴan uwan bappa, dan shi ne kawunsa, ƴan uwan maman Mahnoor da nace maku sun zo yan uwan Inna kakarta ce. So shi Arɗo ya zo, ƴan uwansa ne suka ki zuwa. Wajen gasa namar ta nufa, a tare da Jumma suka je, gabaɗaya masu gashin namar matsawa suka yi suka bata wajen, dan da kanta zata zuba mashi, da ƴan uwansa suna nan zasu gani ne tasan abu mai kyau ne ko bata sani ba, idan ta zaɓo tsokoki masu kyau da laushi to tasan abu mai kyau kenan, ana sa ran abubuwa masu kyau zata rinƙa bashi idan suka tare a gidansu, idan kuma ta zaɓo irinsu hanji da huhu tun daga nan ƴan uwansa zasu fara jefanta da maganganu ace ya yi zaɓen tumun dare, bata san abu mai kyau ba. Yo Mahnoor da take nutsestsiya mai hankali yaushe zata ɗauko abu maras kyau?. Dama dai Mahreen ce kila ta zaɓo mashi ra'ayinta, amma Mahnoor jajayen tsokoki masu kyau da laushi ta zaɓo mashi, da zafinsu, sai titirin hayaki yake yi, ga shi sun gasu sosai. Tun da ta fara zaɓar namar bappa ya tashi ya bar wajen, dan kunya ba zata barshi ya iya kallonsu ba, dama saboda Jaish ɗin ya zauna a wajen, a gefensu Arɗo yakamata ya zauna, shi kuma Jaish dama da abokansa zai zauna, amma da yake bashi da aboki ne sai yasa bappa da kawu Ibrahim kanin maman Mahnoor ɗin suka zauna a tare da shi, to kunga a matsayin bappa na uba ai ba ya zauna ayi wannan abin da ake yi tare da abokan ango ayi da shi ba ko?. Shi ne yasa ya bar wajen, ya bar Jaish ɗin da Ibrahim, shi ma Ibrahim ɗin yaso barin wajen a matsayinsa na kawunta, amma bappa ya ce mashi ya daure ya zauna tun da Jaish dai bashi da kowa........ Wayyo wai ina Yah Jawad, ya zo ya ga ikon god yau, ina ga da idan Jawad ya fara dariyar mugunta sai ya suma saboda dariya, dan ɗan duniya ne, yana can yana cin amanar Yah Rizwan, ya sanya Chuchu a ɗaki har da kashe wuta....😂 A gabansa tazo ta tsugunna ita da Jumma, kansa ya ɗago ya kalleta, dik sai ta ji tsoro da shakkarsa ya kamata, kasa ɗaukar wukar ta yi ta yanko ta sa mashi a baki. Sai jira jama'a suke yi su ga kwakwaf. Mahreen sarkin wutar ciki ne ta ce. "Adda Mahnoor ki bashi mana". Wato ita Mahreen an katse mata jin daɗi ne, ayi maza ayi dan a sakar mata kiɗa ta cigaba da taka rawanta, ta cire gyalen kayan nata ta ɗaura a kunkuminta, rawa ne ya yi daɗi, sam kada ku ga laifinta. Yaufa wani ɗagun kai na daban take ji da shi, dan ta saka sabon kaya kuma mai kyau na yan birni, sai kallon ƙaskanci take yi wa kowa. Mahreen manyan ƙasa. Dafa shoulder ɗinta Jumma ta yi alamar ta daure ta bashi, shi kuwa kallon face ɗinta kawai yake yi, tabbas yana jin daɗin kallonta, saboda yanayin da yake shiga na kokarin tunano Zunaira da yake yi. Kamar zata yi kuka ta sanya hannu ta ɗauki wukar, ɗan ƙarami ta yanka mashi, sai tiriri yake yi, ji take yi kamar ba zai karɓa ba ko ta bashi, kamar zai yarfata a cikin mutane, shiyasa ta kasa iya fara bashi da wuri. Aikuwa ta gudu bata tsira ba, dan kuwa ko da ta kawo mashi saitin bakinsa sai yaki buɗe bakin, ya tsareta da idanu yana ta kallonta. Sai kallonsu jama'an suke yi suna jira su ji dalilinsa nakin karbar nama. Kamar zata mutu saboda kunya, ga shi ya ki karɓa abin ya kara kunyatata sosai. Ɗan taɓa shoulder ɗinsa Ibrahim ya yi, nisawa ya yi tare da dawo da kallonsa a kan Ibrahim ɗin, alama ya yi mashi da ido a kan ya karɓi namar da take bashi, kallon namar ya yi da kyau, kamar ba zai karɓa ba, sai kuma ya tuna yadda suka yi da bappa kafin su zo wajen, hakan yasa ba dan ya so ba ya buɗe baki. Lokacin da ta zo saka mashi a bakin sai da ta ji duniya ya yi wani irin juya mata, saboda a lokacin ta matso sosai ta kuma kalli face ɗinsa da kyau, hakan yasa ta ji kamar wadda aka jonawa shocking a jiki. Karɓa ya yi ya fara taunawa a hankali cikin nutsuwa. A ƙa'ida sai ta bashi namar ya ci ya ƙoshi, amma ina shi ya karya masu doka tun a karon farko, dan kuwa da ta yunƙura zata yanko mashi na biyu, hannu ya ɗaga mata alamar baya da buƙata. Abin ya yi matuƙar bawa jama'ar wajen mamaki, ba'a taɓa yin angon da ya yi irin abin da ya yi ɗin ba. Bappa kam da yasan halin kayansa sai bai wani damu ba. Nan take aka fara tsegumin anya angon nan yana sonta kuwa? Anya ba kawai bashi ita aka yi ba? Kun san jama'a da dama burinsu suga laifinka ko kaɗan ne su yi ta ririta shi wa duniya, aikuwa haka aka yi, su Nenne dake gida ma har sun samu labarin abin da Jaish ya yi a wajen bikin, ya ce ba zai ci abin hannun amaryarsa ba, wannan ai cin mutunci ne. Da yake a yanzu yana jin fulatancin sai yake tsinkayo maganganun mutane ɗaiɗai a cikin kunnensa, ya ji sai aibata abin suke yi, har da masu cewa anya wannan ba zaluntar Mahnoor ɗin zai yi idan aka damƙa mashi ita ba kuwa?. Hakan ta ɗan sosa mashi rai, da farko bai yi niyar yin al'adun nasu ba, amma jin yadda jama'a suke ta faman ririta kin karɓar namar da ya yi har suka sanya Mahnoor ɗin kuka sosai ne yasa ya kuduri niyar zai yi ko dan ita Mahnoor ɗin da take marainiyar Allah. Tana tsugunne a gaban nasa ta kasa miƙewa saboda tsananin kunya, kuka ta fara yi jin yadda jama'a ke tufa albarkacin bakinsu a kanta, wasu sun yi mata dariya, ƴan uwan bappa da basu a wajen, tsintar labarin ma suka yi har da cewa Allah ya kara Allah yasa angon ma ya azabtar da ita dan kawai Allah ya ƙaddara ba rabon Faisal bace ita ɗin shikenan daga samun labari suka hau banka munanan fata. Sam ran bappa bai ji daɗin yadda jama'a suke ta zagin ba, ba'a taɓa yin amaryar da aka zaga haka kamar ita ba, abin ya sosa mashi rai!. Kwatsam suna tsaka da surutansu sai ya gwada masu shi ma ɗan duniya ne, ya yi abin da ya ja suka rufe bakunansu tsit. Abin da ya yi kuwa shi ne yadda take tsugunne a gaban nan nasa tana kuka sai ya kai hannu ya riƙo shoulder ɗinta, ɗagota ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi in da bappan nata ya tashi kenan, dama shi zamansu a kusa da shi ba bakon abu bane a wajensa, kada ku manta shi ɗin aljanin Mahreen ne, abin da har saman cikyarsa Mahreen ɗin tana zama. So bai ji wani shakkar zaunar da ita a kusa da shi ba!. Karɓar plate ɗin namar dake hannunta ya yi ya miƙawa Jumma dake tsugunne a gabansu ta miƙe da shi ta mayarwa Inna. Sannan ya hau share mata hawaye da kyawawan fararen tafukan hannunsa tare da nuna alamar rarrashi. Daga karshe ma sai ya ɗan jawota jikinsa, ya kwantar mata da kanta a saman gefen kirjinsa yana ɗan bubbuga bayanta da hannunsa ɗaya alamar rarrashi. Habawa ji kake tsit ya kashe bakin masu cewa baya sonta, ba'a taɓa yin irin angon da ya yi hakan a kauyen ba, harda runguma e lallai a cewarsu ya tabbata kula na daban zai bata. Bappa ransa fes, ya ji matuƙar daɗi hakan, dama shi bai ji haushin abin da Jaish ɗin ya yi da farko ba, haushin jama'ar kawai ya ji, dan in baku manta ba shi yana ganin kamar suna son junansu, so yasan Jaish yana sonta, shiyasa bai damu ba. Yanzu kuma da ya rarrasheta sai abin ta ƙara faranta mashi rai. Shiru ta kwanta a kirjin nasa tana shesshekar kuka a hankali hankali, gabaɗaya ta rasa a wani duniya take, ta rasa farinciki take ji ne ko bakinciki. Ihu jama'a suka fara yi suna yi masu tafi suna faɗin wai ya kai namiji. Inna Rabi ce ta katse masu ihun nasu ta hanyar kawowa Jaish ɗin kayan kwalliya cikin tray a gabansa, wai ya yi mata kwalliya su hau dutse, dan bappa ya cire batun girki a ciki, saboda shi da kansa yasan Jaish kam ba zai iya yin girki ba gaskiya, dan haka kada su wahalar da shari'a. Ba musu ya karɓi kayan kwalliyar, irin kayan kwalliya ce dai ta kauye. Shiru ya zubawa kayan kwalliyar idanu yana kallonsu, shi da bai san me ma ake yi da su ba, bai san a ina ake sanyasu ba. Muryarta cikin kuka ƙasa ƙasa ne ya katse mashi tunani da cewa. "Hamma zan taimaka maka". Tana daga kwance a jikin nasa ta yi maganar....... Eye su Mahnoor an fara sanin daɗin duniya, har da wani zata taimaka mashi, eye amarya ta angonta kenan, da gaskiyarki taimaka mashi kada ayi mashi dariya. Kawo mata kayan kwalliyar ya yi gabanta alamar to ta taimaka mashi ɗin, dama a cikin tray ɗin silver aka zuba su. A hankali ta ɗan ɗago kanta, hannunsa ɗaya yana ta bayanta yadda yake dan bubbugata a hankali, jama'a sai kallonsu suke suna mamaki, dan su dai sun san ba haka ake wannan al'adar ba, Jaish ya kawo masu sabon salo, komai sai ya canza da nasa salon, su fa amarya tana zaune saman kujera ango zai tsugunna a gabanta ya hau yi mata kwalliya babu mai taya shi suke yi, amma shi da yake nasa na daban ne amaryar har taya shi zata yi, abin nasu ya bada kala. Powder ta ɗauko daga cikin kayan, kasa ƙasa yadda ko kawunta dake gefensu ma bai ji me take faɗa ba ta fara yi mashi bayani a kan me powder da yadda zai sanya mata. Tana kai karshen maganar ta ɗago ido dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, dan ita yake kallo. Da sauri ta yunƙura zata sunkuyar da kanta, ɗaura tray ɗin ya yi a saman cinyarta, sannan ya riƙo haɓarta da hannun nasa, ya ɗagota suna fuskantar juna, ya iyahi me jama'a zasu yi banda ihu, sun ga salon Jaish ɗin ma ya fi nasu bada kala............ Sosan powder ya ɗauko da hannunsa dake saman bayanta, kurawa face ɗinta idanu sosai ya yi, har wani irin yar ya ji a jikinsa, tsikar jikinsa gabaɗaya sai da ya tashi, ji ya yi kamar bashi da lafiya, amma haka ya daure ya fara shafa mata powder. Tafi jama'a suka fara yi suna ihuuu alamar jin daɗi. Kaɗan ya shafa mata, sannan ta nuna mashi yadda zai sanya mata kwalli. Ɗaukowa ya yi da nufin yasa mata, a wannan lokaci ya zamar mata dole ta buɗe idanu su kalli juna ido cikin ido dan ya iya saka mata. Da kyar ta iya buɗe idanun nata, sai kuma me? Sai ga Mahnoor ta mace da kallon face ɗinsa, ta mance da kunya, shi ma macewa ya yi da kallonta, ya mance da cewa kwalli zai sanya mata, idanunsu suka sarƙafe juna...... Da alama waɗan nan ma'auratan sun afka duniyar sama jannati, waye ya ce soyayya karya ce? To koma me dai ina da Maltina ta mai sanyi ni dai🤔 (Sai dai matsalar angon baya cikin hayyacinsa, ko ya zai kasance idan ya dawo dai'dai?🤔 Shin zai karɓeta a matsayin mata ko a'a? Mu je dai zuwa, lokaci zai warware mana komai.) Sun macewa kallon juna har sai da Mahreen ta ce masu. "Hamma ka saka mata kwallin mana, ni fa ina so ne ku gama ku haura saman dutsen nan mu kuma a saka mana waƙa mu cigaba da rawanmu har ku dawo, amma kun tsaya kuna ta wani kallon kanku, to ba kun san juna ba dama?". Miƙewa shi kuma bappa ya yi ya bar wajen ma mai gabaɗaya, ya nufi gida abinsa, ya yafe murnar da za'ayi idan Jaish ya gama cike waɗan nan al'adun nasu, dama idan ango da amarya suka cike al'adun, akwai wata murna na musamman da iyayensu zasu yi dan ƴaƴansu sun cancaci zama a tare kenan, to shi dai ya yafe wannan murna, kunya tasa ya bar wajen da sauri. Shi ma Arɗo dik da yake matsayin kakansu yau Jaish yasa kunya tasa ya bar wajen, da sauri, dikka manyan iyayen dake wajen sai da suka watse, dan kunya, su a yadda suke yin nasu al'adar ba wata soyayya da ango zai nuna bare har aje ga batun kallon juna da runguma, suna yin nasu ne tamkar dai yaya da kanwa haka amarya da angon zasu kasance, kawai shi ya zo ya goge masu hadda ya wani tsare yar mutane da ido, ai dole iyaye su matsa su basu waje. Sai dai kuma da bappa ya tafi manyan dattawa ma suka tafi sai yan kallon suka fara tsoron Jaish ɗin, su dama dan bappa suka tsaya, suna ganin kamar idan bappan yana nan ba abin da zai same su. Amma dai saboda tsabar soyayyar Jaish da salonsa ya burgesu sai basu gudu ba, suka tsaya ganin gulma. Maganar Mahreen yasa ya farga tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya kai tsinken kwallin cikin idanun nata, ɗan kyaftasu ta yi saboda idanu basa son bako. Ɗan tsuke fuskarsa kaɗan ya yi dan a tunaninsa ya ji mata ciwo ne yasa ta kyafta idanun, shi ne ya ɗan tsuke fuska alamar sorry kenan. Sosai ta ji daɗi yadda har alamar tausayinta ya bayyana a saman face ɗinsa kowa yana iya gane hakan, godiya ta yi wa Allah. Jumma uwar soyayya and lecture ai antashi kanta, Jaish ya goge mata hadda, tuni ta karisa wajen saurayin nata da shi ma yana wajen, ba ko kunya ta gaya mashi haka zasu yi a ranar nasu bikin. Ni ko nace ai dama babu wanda ya kaiku iya iyashege idan kuka ga abin da ya yi dai'dai da ra'ayinku. Cikin nutsuwa, salo mai jan hankali haɗe da kula da tausayawa ya sanya mata kwallin. Shi kansa sai da ya kara shagala da kallon idanun nata, yaki sakar mata haɓa, saboda kwallin ya kara fito da hasken idanun nata suka yi tas, ta ƙara kyau sosai. Inna Rabi ma fa ta gudu, Jaish ya ja ta ji kunya ta ware, yanzu matasa ne kawai suka rage a wajen, yara sun gogewa iyayensu hadda, sun ja iyayen sun ji kunya sun gudu. "Hamma saura janbaki fa". Ta faɗa tana rufe idanunta, dan kallon da yake yi mata ya yi mata yawa. Yadda ta motsa lips ɗinta a kusa da shi sosai ta furta saura janbakin nan ba ƙaramin tafiya da imaninsa ta yi ba, sai ya dawo da kallonsa a kan ɗan bakin nata. Mahreen dai sun fara shiga hakkinta, ita dai ayi a haura dutse su tafi a sakar mata kiɗa, kun san dama idan suka haura dutsen ma ba wacewa jama'a zasu yi ba, cigaba da bidirin bikin za'ayi ana abubuwa har sai sun dawo. "Hamma ka saka mata jan bakin mana da wuri, sai kallon bakinta kake yi kamar zaka cinye shi". Cewar Mahreen sarkin azarɓaɗi, yarinyar nan taki bari soyayya ta kullu, ta saka masu idanu. Hannu ya miƙawa amaryar tasa a kan ta bashi janbakin dan shi bai san me shi ba. Idanunta a rufe har sai da ya taɓa kumatunta sannan ta buɗesu, a hanzarce ta miƙo mashi janbakin. Ai irin wannan al'adun ma ko mutun baya son yarinya in dai kyakkyawa ce sai ya fara sonta, bare ma idan ya zo yi mata kwalliya yana kallon face ɗin nan nata, ai dole ya afka duniyar lovayya, uhmmm dama ga Mahnoor da shegen kyau, Jaish ka shiga tarko, ni kuma princess Teema ba zan yarda ba, sai na raba wannan al'amari, dik wadda ta ji haushi ina gidanmu ta zo ta sameni.......🥱😂 A hankali ya buɗe janbakin ya fara goga mata a ɗan lips ɗin nata, dik sai ya nemi sukuninsa ya rasa, wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ce take ratsa shi, bare ma idan ta ɗan motsa lips ɗin nata, dik sai ya rasa gane kansa. Da kyar bawan Allahn nan ya iya ƙarisa saka wannan janbakin, ta yi kyau sosai, dan bai cika mata abubuwan a face ɗin nata ba, kaɗan kaɗan ya saka, ba'a taɓa yin amaryar da aka yi wa kwalliya mai kyan nata ba, kyanta ya ƙara bayyana. Haba me zai faru? Ai tsalle Mahreen ta yi ta dire, ta ce allan baram daga yau Jaish ne zai rinƙa yi mata kwalliya, wato dama ya iya kenan ko? Shi ne baya yi mata. Ita kanta Mahnoor ɗin ta yi mamakin yadda ake ta yaban kwalliyar tata, Jumma sai santin hakan take ta yi. Shi dai kawu Ibrahim kunya ta kusa nutsar da shi cikin ƙasa, ni kuwa nace ai wlh da Jaish yana ainahin Jaish ɗinsa, kuma yana son mace za'ayi wannan biki ai da bama zaku iya zuwa ba saboda kunyar da zaku sha na abin da zai yi. Yau da alama yaron Mommarsa ya mance da yana jin kunyar bappa ya wani tsare mashi ƴa da kallon kauna!. In takaice maku labari haka ya miƙe ya saɓeta cak a saman shoulder ɗinsa, ya karɓi wutar torch light da kawu Ibrahim ya miƙo mashi. Shi ana goyon amarya dan kar a gaji da wuri, shi kuwa yana ɗaukarta a saman shoulder ɗinsa, komai na al'adun nan sai da ya canza masu da nasa salon mai ƙayatarwa. Dutsen ya rinkara gadan gadan, tana fa da tsawo da faɗin sosai dutsen, ga bishiyoyi da ciyayi sosai a sama, kun san haka duwatsu manyan nan suke, akwai bishiyoyi a kansu. Haurawa ya farayi jama'a suna yi masu addu'ar adawo lafiya, ga mangariba ta fara kawo kai, ni kam nace Allah yasa ya ci angwancinsa a saman dutsen kafin ya sauko ba shikenan biki ya kare ba? Daga nan sai su wuce gida ya yi jinyarta, idan suka ga ya sauko sa ita bata da lafiya ai dole a dakatar da dik wasu tsarfa na al'adun nan a barshi ya wuce da ita gida, haba al'adu ne haka kala kala kamar ba gobe!! Ko ya kuka ce my people's? To mu dai bisu saman dutsen muga ya suke tafiya ato, dan mu sai mun leƙa komai dallah dallah!!......😂 Suna haurawa aka saki kiɗar nan nasu dai na yaren fillanci, habawa Mahreen ta ce ku bani waje, tuni ta afka cikin ƴan'mata da samari aka fara raƙashewa. Su kuwa Jaish sun yi tafiya mai nisa kafin nan ya fuskanci lokacin sallar mangariba ta yi, da yake saman dutsen akwai ƴan ramukan da zaku tarar da ruwan sama da ya taru a cikinsu, sai ya sauketa kasan wani bishiya da nufin ya ɗauro alwala ya yi sallah, ya kunna wutar tocin da suka bashi ya miƙa mata a kan ta zauna ta jirasa bari ya yi alwala ya zo. Ga garin akwai hadari sosai alamar ruwan sama za'ayi, da rabon ruwa zai yi wa wasu duka. "Hamma nima zan bika na yi alwalar!". Ta faɗa a sanyaye. Da yake safiya a saman dutsen sai anbi a hankali, idan ba haka ba in mutun ya yi garaje ƙasa zai faɗa, sai ya miƙa mata hannunsa a kan ta zo ya riƙeta su tafi a hankali, dan kada ta je ta faɗi ƙasa. Cikin ɗari ɗarin jiki ta miƙe ta ƙarisa garesa, hannunta tasa cikin nasa, gabaɗayansu sai da suka ji wani irin yanayi na musamman da basu taɓa jin irinsa ba tana ratsasu. Riƙeta da kyau ya yi suka fara tattakawa zuwa wajen da yake zaton zai samu ruwan. "Hamma ina jin................ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2024-11-18.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 39 "Hamma ina jin kamar zan faɗi". A tsorace ta yi maganar, dan ita bata taɓa hawa wannan dutse ba, da dai Mahreen ce sun taɓa hawa ita da Jummar Inna Rabi. Riƙe hannunta da kyau ya yi, har suka ƙarisa wajen da suka yi alwala, suka dawo ƙasar wannan bishiya. Sallah suka gabatar ya limancesu, bayan sun idar a maimakon ya tashi su cigaba da tafiya, sai ya zauna a wajen yana naɗe yatsun hannunsa ya sake waresu, da alama askar yake yi, shiru ta zauna tana ta satar kallonsa, ya lankwashe ƙafafunsa a yayin da ya zauna a kansu. Shiru shiru har tsawon minti ashirin yana zaune, yadda kuka san jikinta dik ta damu sosai, saboda yanda ya lankwashe kafafun nasa ya yi zaman sallah a kan dutse ya yi wani iri, ta tabbata dole zai ji zafin hakan, kawai dai ya zauna ne. Dik tabi ta damu, hankalinta na'a kan kafafun nasa, sai ta ji kamar ta kai hannu ta ware mashi su, tana son yi mashi magana tana kuma jin tsoro, idan ta tuna cewa ai jikinsa ne, dan haka yafita jin zafin hakan sai taga to ai bai kamata ta yi mashi magana ko ta damu ba, idan kuma ta waiga taga yadda zaman nasa ya kasance sai ta ji kai ta damu. Daga karshe dai kasa hakura ta yi har sai da ta ce. "Hamma kai kam baka jin zafin irin zaman nan da ka yi ne?". Shiru bai motsa ba na almost 3 mins, kamar bai jita ba, sai da ta cire tsammanin zai tankata sai kawai taga ya ware kafafun nasa ya yi zaman cin abinci irin na manzon Allah, wato ya dawo da kafafun nasa ta gaba ya naɗesu kenan. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke wanda yasa har sai da ya ɗan juyo da gefen face ɗinsa ya kalleta ta wutsiyar ido, bata yi tunanin zai kulata ba, shahada kawai ta yi dama ta yi maganar, sai kuma ga shi ya kula ɗin, ta ji matuƙar daɗin hakan. Cigaba da zama ya yi har lokacin sallar Isha'i ta yi, a nan ne ya miƙe suka gabatar da sallah, bayan sun idar ta ɗaga hannunta sama ta gabatar da addu'oi sosai, sannan ta shafa. Miƙewa tsaye ya yi tare da miƙo mata hannu a kan ta kama ta miƙe ya ɗauketa su tafi. Da sauri ta riƙo hannun nasa, tana miƙewa ya ɗauketa kamar yar jaririya, hannu tasa ta saƙalo wuyarsa, ɗayan hannun nata kuma ta ɗaura saman shoulder ɗinsa, yanzu ba saɓata ya yi a kafaɗa ba kenan. Haurawa saman suka fara yi garin yana kara duhu, hadari na cigaba da haɗuwa. Ita take rike masu da light ɗin suna tafiya. Ta shiga damuwa sosai da tashin hankali na ganin sun yi tafiya mai nisa bai sauketa dan su huta ba, ɗago kanta ta yi daga saman kirjin nasa tana satar kallon face ɗinsa, in da yasa gaba kawai yake kallo, zuciyarsa tana harbawa da karfi karfi da har take iya jiyo sautin. Jin sautin zuciyarsa yadda take harbawa ne yasa ta yi tunanin ko ya gaji sosai ne yasa hakan, sam bata yi tunanin kawai yana cikin wani yanayi bane, hakan yasa ta yi ƙasa da murya sosai, cikin girmamawa ta ce. "Hamma ka saukeni ƙasa na ɗan yi tafiya da kafafuna". Tana kai karshen maganar ta mayar da kanta saman kirjin nasa ta kwantar, dan tasan dole zai dawo da kallonsa kanta, so bata san su haɗa idanu, dan akwai hasken wata dake tsakiya, hadarin kuma ta gabas yake. Aikuwa hakance ta faru, dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, ta datse idanu kamar maras gaskiya. Dakatawa da tafiyar ya yi yana mai kallonta da kyau. Jin ya dakata yasa ta ɗan buɗe idanunta a hankali, ta kuma fara ƙoƙarin sauka daga jikin nasa, dan a tunaninta ya tsaya ne ta sauka kamar yadda ta buƙata. Kara ƙanƙameta sosai ya yi. "Hamma sauka zan yi sai mu tafi". Ta faɗa a hankali, taki yarda kuma su haɗa idanu, sai ta ƙaƙalo kallon saman dole, ta wani ɗaga fararen idanun tana kallon wata. Hakan ba ƙaramin kyau ta kara yi mashi ba, yadda ta ɗaga fararen idanun nan nata sama sai ta kara tafiya da imaninsa sosai. Shiru bai sauketa ba bai kuma yi wani motsi ba, ya dai tsareta da kallo kuma bai cigaba da tafiyar tasa ba. Dawo da kallonta a kansa ta yi dan ta saci kallon nasa, ta ji ya tsaya shiru ne, aikuwa tana sauke idanunta suka sarkafe cikin nasa, ita kanta bata san time ɗin da abin ya sanyata murmushi ba, ɗan siririn murmushi ta saki, bata san ta sake shi ba. Kwatsam ba zato ba tsammani tana tsaka da murmushi sai jin voice ta yi ya furta. "Murmushin me kike yi?". Bata yarda shi ya yi maganar ba, dan ita tasan baya magana, a dubu ta ɗago kanta tare da fara waige waige, ga shi cikin harshen fillanci aka yi maganar, daɗin muryarma yasa take tunanin ko dai aljani ne ya yi maganar ba mutun ba, nan take sai ta ji tsoro ya dira a ranta. Ƙanƙame shi ta yi tana zaro idanu tare da jujjuyasu dan neman ta ina aka yi maganar. Tabbas shi ya yi maganar, dama bappa ya jima yana yi mashi magani tare da addu'ar Allah yasa bakinsa ta buɗe, sai kuma ga shi anyi sa'a ta buɗe a ranar aurensa. Sai dai har yanzu ba wai ya dawo cikin hankalinsa bane, no, maganarce kawai Allah ya buɗe mashi bakin, sauki tana samuwa a hankali hankali, dan harta idanunsa da suke jajir kamar wuta ma yanzu suna washewa izuwa yadda suke. Dawo da kallonta a kansa ta yi tana jiran taga reaction dinsa. "Hamma na fasa, dan Allah kada ka sauke ni, ina jin tsoro, na ji kamar wata murya ta yi magana ne". Murya cike da tsoro ta yi maganar. "Bayan ni babu wanda ya yi magana a nan sarkin tsoro". Ya sake faɗa a hankali. Ai a dubu ɗari ta waro idanunta waje tare da ɗago kanta daga saman kirjin nasa, tamkar kwayar idanunta zasu faɗo ƙasa saboda zarosu da ta yi. Nan take jikinta ya fara ɓari kamar mai rawar sanyin zazzaɓi, kasa yin magana ta yi, ta rasa shin a duniya take ne ko dai a duniyar mafarki, ita dai tasan bata yi barci ba bare ta yi mafarki, hammansu da yin magana abin da mamaki sosai gaskiya!. Ganin ta kasa yin magana ne yasa ya kureta da kallon kurillah sosai, can ƙasa ƙasa ya furta. "Lafiya jikinki yake kerma haka?". Dik maganar da yake yi cikin harshen fillanci yake yinta, zazzakar voice ɗin nan nasa ya fita sosai, yadda kuka san dama yarensa ne ba ara ya yi ba, abin ta yi maruƙar ƙayatarwa. Har lokacin ƙasa yin magana ta yi, sai ma datse idanunta gam da ta yi, dik da cewa tasan bappa ya ce kowani lokaci bakinsa zata iya buɗuwa, amma abin ya bata tsoro gaskiya. "Noor lafiyarki kuwa?". Da mamaki sosai a saman face ɗinsa ya yi maganar, yaga ne jikinta sai kerma yake yi. Wani irin walkiya ta ruwan sama ce ta haskasu sosai a yadda suke tsaye a wajen, tsawa mai karfin gaske ne ya biyo bayan walkiyar. A dubu ɗari ta ƙanƙameshi sosai, hannunta dake sakale da wuyarsa ce ta ƙara ƙanƙame wuyar da shi, tamkar zata fashe idanunta saboda yadda ta matsesu, tsananta kerma jikinta ya yi, tsawar ta tsoratata da tsawar ya yi sosai. Shi kuwa da yake tsaye ko gezau bai yi ba, ko kawar da kallonsa daga saman face ɗinta ma bai iya yi ba, ya shagala da kallonta, ni kuma da tsabar tsokanata na ce anya ba garɗi da manɗo haɗe da daɗin auren nan yasa bakin Prince Jaish namu na amana ya buɗe ba kuwa? Mun fa san komai shiru muke yi! Mu zai renawa hankali! To ni ba zan bari arena maku hankali ba, in gaya maku gaskiya ga dikkan alamu Jaish ya jima da soyayyarta a ransa, tsabar ikkanci yana cikin ciwon ma sai ya nuna mana halin miskilanci da iyashege, to mun gano komai! Idan baya sonta dai kun san ko da baya cikin hayyacinsa ba zai yarda ya karɓi auren ba, zai ce baya so, amma tun da aka fara maganar har aka gama bai ce ko uppan ba, daga nan ni princess Teema na fara zarginsa, yanzu babban tashin hankali na a nan shi ne ya zata kasance idan ya dawo cikin hankalinsa? Zai yarda da ita kuwa? A yanzu dai da baya cikin hayyacin nasa alamu sun nuna yana sonta, ko ya zata kaya idan ya dawo dai'dai? Allah sarki ƴar marainiyar Allah........😥💔 A hankali yayyafin saukar ruwan sama ta fara ɗiga mashi a saman kumatun matar tasa wanda ya tsare da kallo. Ganin saukar ruwan yasa ya dawo daga duniyar shagala da kallonta da ya afaka. Nisawa ya ɗanyi tare da ɗago da kallonsa ya fara bin sama da kallo. A hankali ita ma ta ɗan waro idanunta domin ta samu damar kallon duniya, saboda ta ji saukar ruwa a saman face ɗinta. Jin da gaske ruwan ne yake kokarin kecewa yasa ta yi hanzarin danne tsoronta haɗe da mamakinta ta furta. "Hamma mu tafi ruwan sama yana zuwa". Murya na rawa ta yi maganar. Sauko da kallonsa a kanta ya yi, can ƙasar maƙoshi ya furta. "Yau kece da tsoron ruwa? Kin manta a rafi kike wanke mana kayanmu ne?". Ita dai ta kasa yarda da cewa shi yake magana, dan bata taɓa jin murya mai zaki da daɗin nasa ba, ni kam na ce dan ma baki ji muryan Guyson nawa ba, ai da kin ruɗe saboda daɗi. Kasa haƙura ta yi har sai da tamkar zata yi kuka ta ce. "Hamma da gaske kai ne kake yin magana?". Yadda ta yi maganar ba ƙaramin burgesa ta yi ba. "Kina tantama ne?". Kai kawai ta iya gyaɗa mashi alamar e, ta ƙasa sake yin magana. Shiru ya yi bai sake magana ba shi ma, yayyafin da ya kara tsananta ne yasa ya cigaba da tafiya da ita, ya mayar da kallonsa a kan in da yake takawa. Tun da ya cigaba da tafiya idanunta suke a kansa, ta dai rasa ya zata yi da mamakin da yake son kasheta. Wasa ruwan saman ya rinƙa yi kamar zai zubo kamar kuma ba zai zuba ba, har suka ƙarisa hayewa sama gabaɗaya, around karfe 11 na dare suka isa. A ƙasan wani katan dutse mai cike da zane zanen sunaye da larabci haɗe da abubuwan hannu ya sauketa, idan amarya da ango suka hau wannan dutse suna iya kaiwa karfe 2 kafin su isa sama, saboda su tafi kaɗan su hutu su tafi kaɗan su huta, amma shi kunga ai bai wani ɓata lokaci wajen tsayawa hutu ba, shi ne yasa suka isa da wuri. Tun da ya zaunar da ita take ta aikin bin shi da kallo, shi kuma ya juya ya bata baya a in da yake kallon ƙasa yana hango garuruwa da ƙauyuka, waje ya yi clean daga saman, shiru ya tsaya yana jin kansa tana ɗan jujjuya mashi tamkar mai san tuna wani abin, yana dai ji kamar ba shi ba. Miƙewa tsaye ta yi, wani ɗan ƙaramin karfe ta hango a jikin dutsen wanda kamar ɗan keji aka yisa, dama Inna Rabi ta yi mata bayanin abin da zasu yi idan suka haura saman, wanna ɗan kejin ta nufa, tun iyaye da kakanni aka buga shi a saman dan ajiyar kifiyar da suke rubutu a ciki. Jin motsin ta miƙe yasa ya saci kallonta ta wutsiyar idanunsa. A hankali ta tattaka ta je ta buɗe ɗan kejin, kifiyar ta ɗauko ta dawo wajen dutsen, yana ta kallonta shi dai yana jiran ya ga me zata yi. Ita ma satar kallonsa take yi, da yake ita take riƙe masu da light ɗin sai hakan yasa bai gane tana satar kallonsa ba. Jikin dutsen ta sanya kifiyar, yana da tsinin baki sosai, karfinta tasa ta zana design of heart a ɗan karkace saboda rashin sabo, hannunta na rawa. Juyowa ya yi da kyau dan ya kalli me zata yi, sai a lokacin kuma ya lura da sunayen mutane dayawa a jikin dutsen, an zanasu ta yadda ruwa ba zai wankesu ba, ba zasu taɓa gogewa ba har abada, sai yanzu ya gane wato dik amarya da angon da suka zo sai sun rubuta sunansu da yadda suka iya, in ma da arabic or da boko, su killace shi a cikin design of heart. Ita fa bata ma san menene ma'anar design of heart ɗin ba, kawai taga dik waɗan da suka rubuta sunansu a cikin irin design ɗin suka rubuta ne yasa ita ma ta zana design ɗin. Da karfi ta fara zanen sunansa wato Hamma a sama, ta rubuta sunanta Mahnoor kuma a ƙasan nasa sunan, tana yi tana kallon design da mutane suka yiyyi tana kofa, da larabci ta yi masu zanen sunayen nasu, bata iya karatun boko ba, amma ta iya Arabic sosai. Bayan ta gama sai ta kallah a sauran zanen sunayen dake wajen ai an sake zana karamin heart a tsakiyan sunan ango da amaryar, dan haka ita ma sai ta sake zana masu heart ɗin kamar yadda ta gani, sai Allah kaɗai yasan waye ya fara zana wannan design ɗin da kowa ya zo sai ya kofa, abin ya ƙayatar sosai. Shiru ta yi tana kallon zanen nata ta kuma kalli na mutanen dake wajen dan ta kara dubawa shin ta yi dai'dai ko da sauran gyara?. A ƙaida angon ne zai zana sunayen, amma ita tana ganin kamar ko ta ce ya yi ba zai yi bane yasa ta yi da kanta. Tana tsaka da ganin zanen kamar daga sama ta ji shi a bayanta, a hanzarce ta yi yunƙurin juyawa dan ta ga shi ɗin ne? Ko ba shi bane?. Bata kai ga juyawa ba sai taga hannunsa ya sauka a saman nata da take riƙe da kifiyar, riƙo kifiyar ya yi haɗe da hannun nata ya mayar jikin zanen. Dogon mashin kauna ya zana a tsakiyar sunayen nasu har ya ɗan fi heart ɗin tsawo, kamar yasan haka ake zanawa, a dai dikka al'adun nan nasu sai da ya kawo masu sabon salo, dik cikin zanen da jama'a suka yi a wajen babu mai zanen mashin kauna sai nasu da ya wani zana masu, kuma abin ya yi matuƙar kyau da ɗaukar hankali sosai. Zaro idanu ta yi tana kallon yadda abin ya yi mugun kyau ba kaɗan ba, a hankali ta ɗago kai ta kallesa. Ita yake kallo shi ma, hakan yasa idanunsu suka sarƙafe cikin na juna.............. Wasa wasa fa wato Jaish ma taƙadari ne.😂 10 mins suka ɗauka a wajen a haka, sannan ya sanya hannunsa ɗaya ya juyo da ita garesa, har lokacin ɗayan hannunsa na saman nata dake riƙe da kifiyar. Ƙasa ta yi da kai kamar mai ɗaukar darasi a islamiyar Inna Rabi. "Muje ko?". Can ƙasan maƙoshinsa ya furta hakan, daga jin yanayin muryarsa akwai alamar tanbaya, dan ta sauya......... Ni ko nace shi soyayya da sha'awa ina ruwansa da baka cikin hayyacinka? Sai dai idan bata taso ba, cap zai capkeka ba ruwansa, to gara ma ka sani ato!!... Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa cak, kai tsaye wajen ajiye kifiyar ya nufa da ita, yana ɗauke da ita ta buɗe ɗan kejin ta mayar da kifiyar ta rufe. Saƙalo wuyarsa da hannunta ɗaya ta yi tare da kwantar da kanta a saman kirjinsa, har lokacin ana yin ɗan yafyaf na ruwan sama. "Hamma naga kai baka huta ba, ko zamafa baka yi ba". A raunace ta yi maganar, baiwar Allah ta damu sosai, sai take ganin kamar tana gajiyar da shi, bata san cewa shi ɗin jinin Modarawa jinin Akka bane, jarumta a jininsu yake. Hannunsa ɗaya yasa ya ɗan shafi face ɗinta kaɗan ba tare da ya furta uppan ba, alama dai ya yi mata a kan kada ta damu sam bai gaji ba. Cigaba da gangarowa suka yi, a hankali yake tafiya gudun kada su gangara su faɗi, saboda gangarace sosai. Akwai lokacin da wani ango ya yi ganganci wajen gangarar nan, ai a dubu ɗari ya gangaro kasa, bai tsaya ko'ina ba sai a kusan karshen garin ya afka cikin wani rami, badan wannan ramin bama ina ga sai ya fita garin saboda gudu, tuni ya yi wurgi da amaryar tasa ya rinƙa gudu kamar wanda birkinsa ta tsinke, sai da ya kai wata yana jinyar jikinsa, dan ma Allah yasa jama'a sun biyo bayansa da gudu, hakan yasa yana faɗawa cikin ramin aka yi maza aka cirosa, badan haka ba ai da sai dai wani ba shi ba, so sai da kulawa wajen wannan gangara. (Tab wayaga Jaish yaro ɗan Mommarsa an samu akasi ya gangaro a miliyan? Birkinsa ta tsinke bata kamuwa, ai ina ga daga nan har ƙasar Tunisia zai tsaya, sai Akka ta taresa😂 ba ruwana kada kuce ni na faɗa.) Sai da suka kai kusan sauƙa da misalin karfe 2:30, sannan ne ruwan saman ta kece kamar da bakin kwarya, hakan yasa ya ɗan ƙara saurin tafiyar tasa, ita kuma ta ƙanƙameshi sosai tare da kwantar da kanta ta ɗan saman kirjin nasa. Su Mahreen kuwa har wajaje shabiyu da rabi tukun nan suka dai'na rawa, wannan ma sai da bappa da ya dawo wajen ne ya tsawatar masu a kan su kashe mpn nasu dare ta yi sosai, ba dan haka ba da kwana zasu yi suna yi, bappa misalin karfe 10 ya dawo wajen domin yana son su Mahnoor su sauƙo a gaban idanunsa ya tabbatar da babu abin da ya sameta, shiyasa ya dawo. Gari ya yi shiru sai tashin hiran jama'ar dake wajen bikin kawai zaka ji, sai hira suke yi kamar ba dare ba, sai da aka fara ruwan sama ne suka shige cikin runfunar nasu suka tsaya tsit suna ganin zubar ruwa. Tun da ruwan nan ya fara a kansu ya fara, ga shi zuba yake tamkar da bakin kwarya, ga iska mai karfi, ta manne da jikinsa tana jin wani irin sanyi na ratsata, ga sanyin fitowar alfijir ya keto, sai ya haɗe masu. Around karfe 4 daidai suka sauko daga ƙasa saman, sun jiƙe sharkaf da ruwa, har lokacin kuma ruwan ake zubawa kamar me. Tun da aka fara ruwan Mahreen ta fara yi wa bappa kuka a kan ruwa zai jiƙa mata ƴar uwa da kuma Hammanta, shi kansa bappan ya shiga damuwa, sai dai ya danne ya rinƙa rarrashinta, da kyar ya samu ta yi shiru. Idan ran Jaish ya kai dubu a wannan lokacin to ya ɓaci, a ransa yake faɗi ko uban waye ya kafa waɗan nan al'adu to lokacin rusheta ya yi, bai ga uban da zai sake yin wannan al'adar a wannan kauye ba idan har yana nan, wannan ai sai su kashe ƴaƴan nasu da hannunsu, dan kuwa ba kowa ne zai iya hawa wannan dutse ba, musamman waje saukowa ba karamar kasada ake ɗauka ba, idan ka yi wargi kaɗan wajen saukowa to faɗowa zaka yi ko ka gangaro a miliyan ka yi gudun wuce ƙaidar ɗan adam. Idan ka faɗo a wannan waje kuwa idan baka mutuba to ba zaka sake moruwa ba, shirmen banza da wofi, haka ya rinƙa faɗa a ransa. Bai san cewa su wannan al'adar ta iyaye da kakannin ganinsa suke yi kamar bauta ba, bama su taɓa yarda ayi biki ba'ayi shi ba, ai wannan aure bai cika ba. Ko kallon in da su bappan suke bai yi ba a lokacin da ya sauko, su kuwa sun kasa yarda da cewa shi ne, saboda gani suke yi lokacin da kowa yake saukowa idan ya hau bai yi ba, ya aka yi shi ya yi sauri, sun ɗan tsorata sun kuma yi mamakin ganinsa. Baiwar Allah Mahreen ta kasa yin barci, tunaninsu kawai take yi ta kwanta a jikin bappa shiru. Tana ganinsu da gudu ta bar jikinsa ta nufesu. Yana ƙoƙarin riƙota saboda ruwan sama, amma ina tuni ta nufesu while shi kuma Jaish ɗin bai dakata a wajen ba, hanyar gida kawai ya nufa, dan wani irin haushinsu na musamman ma yake ji na wannan abin. (Ni kuwa nace anya Jaish ba haushi yake ji dan ruwa ya jiƙa mashi mata ba kuwa? Ɗan ƙaniya meyasa tun farko bai ji haushin al'adun ba sai da ruwa ya sauƙo? Ni fa ban yarda da kai ba Jaish, ato!) Da gudu ta bi bayansu tana yi masu sannu da saukowa. Bisa al'ada fa idan ya sauko daga saman dutsen a wajen zasu zauna a cigaba da gudanar da bikin, amma shi ya wani wuce da ita, a nan ma sai da ya sake yi masu tsarinsa. Ganin sun wuce gida ne yasa bappa ya fita a cikin ruwan shi ma ya bi bayansu, dan hankalinsa a tashe na ganin halin da suke ciki, ruwa ya yi masu duka. Kusan a tare suka shiga gida, a tsakiyar gidan ya sauƙeta yana sauke numfashi a hankali hankali, fuskar nan a ɗaure tamau. Da gudu Mahreen ta zo ta faɗa jikinsa tana yi mashi sannu da dawowa. Ƙasa ƙasa kamar mai ciwon baki ta furta. "Meyasa kika fito a cikin ruwan nan?". A fujaje ta ɗago kanta daga saman jikin nasa ta kalli face ɗinsa. "Hamma yaushe ka iya yin magana?". A ruɗe ta yi tambayar. Dai'dai lokacin bappa ya ƙariso wajen, shi ma ya ji maganar, da yake yana sa ran hakan sai ya fara zabga godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya nuna mashi wannan rana da ya ji sautin muryar bakon nasa a kunnensa. A ransa yake faɗin lokacin ya yi da zasu san wanenen bakon nasu, Allah sarki basu san bai gama samun sauki ba, dan baya a hayyacinsa har yanzu. Ganin ta dunkule jikinta waje guda tana aikin rawan sanyi ne yasa Jaish ya nuna mata hanyar ɗakinsu da hannu a in da ya ce ta tafi ɗaki. Bappa ne ya tari numfashinsa da cewa. "Ga naku ɗakin ai ta je can kayanta suna ciki sai ta canza, kai ma yakamata ka je ka canza kaya kada mura ta kamaku, kaga sanyin asba tana gabatowa". Tun da bappan ya fara magana ya tsare shi da ido bai ce komai ba, sai dai ba ido cikin ido yake kallonsa ba, ji yake kamar ma ya dallah wa bappan mari, dan dik waye ya ja masu wannan wahalar idan ba shi ba, da wani zancensa na banza wai tun iyaye da kakanni al'adar take, kayan takaicin..... Jaish fa ya fara samun sauki, hali ta fara dawowa, akwai aiki kenan. Ganin bai motsa ba sai kallon in da yake yake yi ne yasa bappan ya gane haushin bikin nasu yake ji, dan ya iya karantar yanayinsa a yanzu, kuma dai kun san dole su iya karantarsa tsab, saboda iya maganar kurame da mutun ba ƙaramin abu bane, dole su iya gane ma'anar shirun da kowace motsinsa. Hakan yasa bappan ya fara rarrashinsa a kan ya yi hakuri komai ya wuce, kuma ya yi mashi alkawarin ba za'a ƙarisa sauran waɗan nan al'adu ba, ya yi babban ai. Wani irin kallon da ya wurga mashi mai cike da takaici ne yasa bappan juyawa ya nufi nasa room ɗin, dan yasan halin mutumin nasa, wannan kallo ba komai bace face na bakinciki, so gara ma ya kama kansa, dan yasan Jaish baya jin rarrashi, tun baya magana abin da ya yi niya kawai yake yi, bare yanzu ya fara yin magana, ai sai a slow. Wucewa da sauri Mahnoor ta yi ta shige cikin ɗakin da bappan ya ce ta shiga, dan wani irin bala'in sanyi take ji na daban. Ɗan rage tsawonsa ya yi tare da raba jikinsa da Mahreen da ta ƙanƙame shi. "Jeki ki canza kaya kada sanyi ya kamaki ko?". Yana magana yana kara rage tsawonsa har yazamana ya sunkuyo sosai suna fuskantar juna. "Hamma yanzu ka iya yin magana?". Kamar zata yi kuka ta yi maganar, tana jin wani irin tsantsar farincikin na musamman. Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce. "E ina magana, yanzu jeki ki canza kaya ki ɗan kwanta kaɗan zuwa asuba". Ya yi maganar suna kallon juna har cikin ido. "Hamma muryarka tana da daɗi sosai, idan kana magana kamar ba mutun ne yake yi ba". "Da gaske?". Ya yi tambayar ba tare da yasan ya ɗaga mata gera ɗaya ba, da yake hakan kusan ɗabiarsa ce a da, sai ya yi ta bai san ya yi ba. A hankali dai wasu ɗabi'un nasa suna dawowa jikinsa. Mamaki ne ya kamata na ganin ya ɗaga gera guda, miƙewa tsaye ya yi tare da karɓar torch light dake hannunta, ya riƙe hannunta har izuwa cikin ɗakin nasu, a lokacin Mahnoor ta canza kaya, sai kuma ta zauna a ƙasa bata hau saman mattress ɗin nasu ba, ta takure jikinta waje guda, hakan zai tabbatar maka da sanyi take ji sosai. Mamaki ne ya kamashi lokacin da ya shigo cikin ɗakin, kayansa gabaɗaya bappa ya dawo mashi da su nan, ita ma gabaɗaya kayanta ya dawo da su, lallai ma bappa akwai kokari sosai. Wucewa da ita ya yi, cikin sanyin murya ya ce da Mahnoor ina kayan Mahreen suke?. "Kayan ta baya nan, ina ga yana ɗakinmu ko ɗakin bappa". Da kyar ta iya bashi amsar, saboda yadda jikinta ke kerma haka hakwaranta suke garuwa da na juna. "Jeki ki ɗauko kayan naki kizo ki canza kin ji?". Ya faɗa yana sakin hannun nata. Da gudu ta juya ta fita. Shi kuma ya nufi wajen kayansa. Kayan da yake da buƙata ya ɗauka ya fice daga ɗakin. After 30 mins ya dawo bakinsa a ɗauke da sallama. Shiru bata amsa mashi ba, ciki ya shigo. Saman mattress ɗin ya nufa, dan ya ɗan kwanta ko da na 20 mins ne sai ya tashi ya yi raƙatainil fajir sannan su tafi masallaci. Har ya karkata zai kwanta sai kuma idanunsa suka sauƙa a kanta, Allah sarki ta yi barci a yadda take zaune, ga wani irin rawar sanyi da take yi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya kariso in da take ɗin, ɗan rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa cak, barcin nata mai nauyi ne sosai, saboda gajiya ga dukan ruwan saman da ta sha, hakan yasa bata farka ba da ya ɗauketa. A saman mattress ɗin ya kwantar da ita, sannan ya janyo bargon da Inna Rabi ta shinfiɗa masu a karshen mattress ɗin irin kwalliyar nan, ya janyo ya rufeta har zuwa saman kirjinta, ya juya mata baya ya kwanta, shiru ya ɗan yi kaman mai wani tunani. Sai kuma ya juyo da jikinsa ta in da take, ya zamana suna fuskantar juna, zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take sauke numfashin barci a hankali hankali irin na gajiya. Ji ya yi tsikar jikinsa tana tashi tamkar wanda rayuwarsa ta baya take ƙoƙarin dawo mashi, ɗan kawar da kallonsa daga face ɗin nata ya yi izuwa gangan jikinta. Kamar wanda aka tsikara ya wani miƙe zaune tare da kawar da kallonsa daga kanta. A hankali ya sauko da kafafunsa ƙasa, sannan ya miƙe ya nufi waje. Ita kuwa sai ta ƙara kudundunewa a cikin bargon da bata san da shi ba, baiwar Allah ta ji ɗumi mai ni'ima yana ratsa har cikin ƙashin jikinta ne, hakan yasa ta kara shigewa bargo sosai. Yana fita bappa na fitowa, sam yaki kallon in da yake, sai yanzu yake kara jin wani sabon kunyan bappan tana ratsa shi, alwalarsa kawai ya ɗauro ya wuce ya dawo cikin ɗakin, bappan ma alwalarsa ya yi ya koma ciki, Mahreen tana kwnace a saman gadonsa, shi ya hanata komawa wajen su Jaish ɗin, da ta canza kaya sai ya ce ta hau gadonsa ta kwanta, kuma daga yau kada ta rinƙa shiga masu ɗaki idan har basu suka kirata ko suka aiketa ciki ba. Ai kuwa nan ta yi tsalle ta dire ta ce bata yarda ba, ya za'ayi ɗakin addarta da Hammanta kuma ace ba zata shiga ba? Ai ita ma ɗakin zata koma kwana. Da kyar ya samu ya yi mata dabara ya shawo kanta ta yarda da hakan, shi ne ta kwanta ta yi barci. Akwai komai da zasu buƙata a cikin ɗakin, harta dadduma an kai masu, yana shinfiɗe a ta gabas. Raƙatainil fajir suka gabatar kusan a tare shi da bappan da yake ɗakinsa, sannan suka fito suka nufi masallaci, a tare suka tafi, Jaish kansa a ƙasa, kamar ma ba zai jera da bappan ba, amma ba yadda zai yi, bappan ya rigada ya fito, ga shi an fara tada sallah ba halin ya ce bappa ya je yana zuwa dan ya je shi kaɗai daga baya, hakan zai sa sallah ta wucesa, dole kawai su jera kaman wani yaya da ƙani, sai dai Jaish ya fisa tsawo gaskiya, amma shi ma dogon mutun ne. Bayan sun idar da sallah, suka yi askar kafin su dawo gida, sai dai bappa ya rigasa dawowa, da gangan ya ki tashi su dawo a tare, dan baya son su jera, kunya sosai yake ji, sai ya ƙaƙalo askar ɗin karya har bappa ya wuce gida. Har lokacin da ya dawo tana kwance bata ko motsa ba a yadda ya ganta. Ɗan zuba mata idanu kaɗan ya yi kafin ya ƙariso gefenta ya kwanta, ji yake yi kamar ya tasheta ta yi sallah, sai kuma ya tuna irin wahalar da ta sha, hakan yasa ya kyaleta tare da gyara kwanciyarsa. A hankali ya lumshe idanunsa, dan shi ma barci yake ji, agajiye yake sosai. A fujaje ta miƙe tana ƙoƙarin barin gadon, kamar wata zararriya ko wadda aka tsoratar, ashe kenan ta farka idanunta biyu, kwarai ta farka ta yi sallah ne ta sake kwanciya. Idanunsa a lumshe amma ya ji yadda ta miƙe daga kwanciyarsa kamar shi ɗin dodo ne, hannu yasa zai kamata idanunsa a rufe. A guje ta yunkura zata sauka ƙasa, ya yi sa'a ya dapko shoulder ɗinta, a hankali ya waro idanunsa, caraf suka haɗa ido, dan kuwa shi take kallo da ya riƙota, ɗakin akwai ɗan duhu duhu, gari bai gama waye ba, amma kuma iya ganin juna. A hankali ya mayar da idanunsa da suka yi ja saboda barci ya lumshesu ba tare da ya saketa ba. "Ina zaki je da sanyin nan?". Kamar baya son yin magana ya yi ta. "Zan je in yi wa Nenne aiki ne, shara da wanke wanke da........." Ɗaukewa ta yi diff da yin maganar saboda waro idanun nasa sosai da ya yi a kanta, dawo da kallonsa a kan hannnunta da ya riƙe dake ta fama kerma ya yi, slowly kuma ya dawo da kallon nasa saman tsoratacciyar face ɗin nan nata, ya sani sarai tsoronsa take ji, kuma ba zata iya kwanciya da shi a mattress ɗaya bane yasa zata sauka ta gudu waje, ga sanyi kamar me ko me zata je ta yi a wajen, har yanzu yayyafi ake ɗan yi ko ta yaya zata yi shara? Ya jefawa kansa questions. "Daga yau kada na sake ganin kin fita daga ɗakin nan da sassafe, sai karfe 8 dai'dai zaki rinƙa fita". Kamar wanda yake cikin maye ya yi maganar, dama ya jima yana bakincikin yadda take fitowa da sanyin safiya tana yi wa Nenne aiki kamar wata jaka, to yau dai Allah ya bashi damar hanata, a ransa ya kuduri niyar ba zama ta sake yi wa Nenne aiki a gidan nan ba, idan ya wuce aikin gyaran ɗakin bappanta da sharar tsakar gida ba zata sake yin komai ba, idan Nennen ba zaman aure ta zo yi ba sai ta kara gaba bappan ya auro wadda zata zo ta yi zaman aure, ta kula da gidan da abin da zai ci. To fa akwai cakwakiya, Jaish zai hana Mahnoor yi wa Nenne aiki! Kuna ganin akwai zaman lafiya kuwa idan ya yi hakan? Dan dai kunsan Nenne dole ta dawo gidan, dole Arɗo zai kaɗota ta dawo, me kuke tunanin zai faru? Akwai rikici fa my people's, abubuwa zasu ɗauki zafi kenan. Shiru ta yi kirjinta yana dukan uku uku, tara tara. "Koma ki kwanta". Ya yi maganar tare da sakin shoulder ɗin nata ya juya ya bata baya. Kamar zata yi kuka, cike da tsoro ta koma ta takure jikinta waje guda, Allah tsoron kwanciya a saman mattress ɗin take ji, dan ma ɗan kwana biyun nan ta ɗan saba da shi, ai da ko kallonsa ba zata iya yi ba. Shi kuwa barci sosai kamar zai yi yaya, amma hakan yana iya jiyo dik wani motsinta, ta manne da jikin bango kamar ance zai cinyeta,.sai mutsu mutsu take yi, dik ta ishe shi ta hana shi runtsawa, ba abin ya juya ya dallah mata mari ba, amma tana mugun bashi tausayi sosai. Cikin muryar barci ta furta. "Noor ki dai'na mutsu mutsun nan kina damuna, barci nake ji". Yadda ya yi maganar sai ka rantse da Allah shagwaɓa yake yi mata, dan barcin dake kansa. Ai bata san lokacin da ta saki baki, ido da kuma hanci tana kallon bayan wuyarsa ba, tunani take yi akan ya aka yi ya yi shagwaɓa irin na Mahreen? Ko dai dama shi ma ya iya ne? Bata san barci yasa shi yin hakan ba. Wani irin daɗi na musamman ta ji na cewa ya yi mata magana cikin nuna kauna da kulawa. Hakan yasa ta kwanta shiru dan kada ta takura mashi, kafin wani ɗan lokaci barci ya yi awon gaba da su. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ FRANCE🔥🌹 Zaune yake a tsakiyar bed ɗinsa ya tasa wata haɗaɗɗiyar tsadaddiyar laptop ɗinsa a gabansa, ya kura mata idanu tamkar mai nazarin wani abin. Shirye shiryen tafiya duniyar wata yake yi saboda wani binciken nasa a kan aikinsa da zai je, da farko yaransa biyu zai tura, sai kuma ya fasa zai tafi da kansa. Tun last week ya tashi launch rocket, so yanzu lokaci ya yi da ya kamata ya tura life support system, kun san kafin ka tafi duniyar wata kana da buƙatar fara bincikar yanayin sararin samani first, sannan a tashi launch rocket ita ce hanya ta farko da zata fara yi maka clearing hanya, sai system da zai duba maka yanayin yadda karfin hazo, karfin sanyin da yake sararin samaniyar duniyar watar da dai sauransu, sannan sai ka tura life support system wannan zai tantance rai zai iya dinfarar wajen a wannan lokacin ne ko kuwa zai iya samun matsala idan ya je?. Idan ya tabbata zaka iya zuwa a wannan lokacin to ba tafiya kai tsaye zaka yi ba, sai ka sake tura navigation system mai karfi wanda zai duba maka yanayin motsin abubuwan da suke sararin samaniyar. Kun san sararin samaniya fa sai Ubangijin da ya halicceta ne kawai yasan adadin abubuwan dake wajen, so unexpect zaka iya cin karo da wani abin da baka raɓa zata ba, shiyasa ake tsawaita bincike kafin mutun ya tafi, aiki ne fa babban zuwa duniyar watar nan, ba wai ɗaga jirgi kawai za'ayi a tafi ba, planet ɗin zuwa can ma na daban yake. Daga nan sai ka haɗa energy generation, amfaninsa shi kuma shi ne zai taimaka maka wajen tare maka karfin hasken rana ta yadda ba zai yi maka illah ba, haka zalika yana ɗan taimakawa wajen tare maka sanyin dake duniyar watar, kun san fa wata bala'in sanyi ne mai ratsa ƙashi da ɓargo na wuce misali a wajen. Mataki na gaba shi ne safety and emergency za'a haɗa, wato irinsu medical supplies, domin kula da lafiyarka idan Allah ya nufa ka sauka a duniyar watar, ana iya samun mura ko wata ciwon ta kamaka saboda tsananin sanyin dake wajen da kuma sauyin yanayi, kun san dai dik wasu system da za'a sanya dan su tare maka sanyin wata ba zai taɓa yiwuwa ba sai dai su rage maka, dan ba wanda ya isa ya tare abin da Allah ya kaddamar da shi, so akwai sanyi sosai dik da waɗan nan systems ɗin. Sai kuma su oxygen dan babu iska a sama ko kaɗan, ainahin sama duniyar wata ake magana, babu iska a wajen, dole sai da irinsu oxygen ɗin nan dan shaƙar numfashi a rayu. Sannan yazama wajibi a bawa wanda zai je wajen ƙwaƙƙwaran training na musamman, dan ya iya kare kansa da dik abin da zai iya cin karo da shi, dole ya cire tsoro a ransa, abin fa ba ƙaramin aiki bane wlh, sai masu dakiya, juriya da kwarin gwiwa. So ya nutsa cikin dube duben da yake yi a kan abubuwan da suka tura ɗin, daga wajen aikin nasu yaransa dake kula da wannan ɓangaren suka turo shi rahoton da system ɗin da suka tura sararin samaniyar ta basu, shi ne yake dubawa, ya ce yau ba zai fita ba sai dare, shi ne ya buƙaci da su turo mashi ta nan ya duba. Door room ɗin nasa ne ta buɗe kanta da kanta, bai ɗago ya kalli door ɗin ba, dan yasan guarantee familnsa ne. Daddynsa ne ya shigo, yana cikin shigar cargon short and singlet fara tas, hannunsa ɗauke da two cup of cortado, dik dangin su coffee ne, sai dai shi cortadon zaku ga suna yi mashi design of heart a saman shi, shi ma wanda dad ya kawo yanzu har da design ɗin, kamar wasu masoya, ya zo ya ɗaura cup ɗaya a saman bed kusa da Smart, ya zago ta ɗayan side ɗin, ya haye saman bed ɗin ya zauna tare da janyo pillows ya ɗaura saman laps ɗinsa, a bayansa ma ya sanya pillow ɗaya. Tun da ya shigo room ɗin idanunsa a saman laptop na Smart, da alama yasan aikin da yake yi. Sipping na cortadon nasa kaɗan ya yi tare da cirewa. "Son take urs". Ya faɗa yana kara sipping, still idanunsa a kan laptop ɗin. "Daddy who told you that I woke up from sleep?". Calmly ya furta hakan. "My heart! you forget that our hearts are connected?". Shiru ya yi yana jin kaunar daddyn nasa tana kara ratsa shi sosai, wato har yasan ya farka ma tsabar soyayyar dake tsakaninmu. Kai mashi cup cortadonsa sai tin ɗan bakinsa daddyn ya yi, a hankali ya buɗe ya ɗan yi sipping kaɗan, yana cigaba da latsa madannan laptop ɗin. Mayar da cup ɗin bakinsa dad ɗin ya yi ya cigaba da sipping a hankali cike da class, shi kuwa cup ɗin Smart yana gefe bai ko kalli in da yake ba suka cigaba da shan na dad ɗin, idan ya yi sipping ɗaya sai ya kawowa Smart ɗin ma ya ɗan yi. Suna yi suna hira cike da so da kauna yana kuma yin aikinsa har suka shanye cortadon dad tas ba tare da sun sani ba, ganin ya kare yasa da gangan dad ɗin ya kawo mashi saitin ɗan bakinsa da nufin ya yi sipping. Dama kun san hankalinsa yana a kan aikinsa, dan haka sai ya yi sipping na iska babu komai a ciki cup ɗin. Ɗan turɓune fuska ya yi tare da juyowa ga daddyn nasa. "Daddy!". Ya faɗa yana binsa da kallon kauna. "Son". Shi ma ya faɗa yana binsa da hararar wasa. Ɗan ɗaga voice kaɗan ya yi ta furta. "Mum c.......". Da sauri dad ya rufe mashi baki da tafin hannunsa, aikuwa ya yi daidai da ita ma tana nufo ɗakin, hakan yasa da ta shigo sai suke ganin kamar ta ji kiran da ɗan nata ya yi mata ne yasa tazo. Da sauri dad ya zame hannunsa yana hararan ɗan nasa. Ƙarisowa ciki ta yi tana tambayar ta ji ya kira sunanta tana gab da shigowa ko lafiya?. A ɗan takaice ya ce. "Mum daddy prevented me from resting, he came to restrain me". Da sauri dad ya fara girgiza kai alamar a'a ba haka bane, aikuwa mum bata bashi wani damar yin magana dan kare kansa ba ta yi kansa da sauri. Jajir ɗin kunnensa ta kama ta murɗe da karfi har sai da ya furta wash da karfi, sannan ta ja tana faɗin. "Let's go, you come and restrict my son for what reason? You don't have something to do, you will not let him rest?". Dan dole ya miƙe, saboda ta murɗe mashi kunne, shi da ya zo domin ya lallaɓa Smart ɗin ya bashi cortado, idan suka gama sha sai ya ce mashi ya yi hakuri ya je su gaisa da iyayen Heleena, amma ta zo ta ja shi sun wuce. Har sun kai bakin kofa zasu fita ya juyo tare da sauke kallonsa a kan ɗan nasu. "We will meet later, I have to take revenge". Yana magana yana wurga mashi harara. Shi ma Smart ɗin harara ya wurga mashi tare da sanya yatsunsa guda biyu a gaban goshinsa irin sai mun haɗu anjuman kenan, tun da kace zaka ɗauki fansa, har da yi mashi alama da anjuman ma shi zai yi nasara tun da shi yake da mom. Wato idan kana da mom a gidan ka more, shi dai yanzu yafi karfin dad tun da yana da goyon bayanta. Jan kunnensa da karfi da ta yi ne yasa ya juya dan dole suka cigaba da tafiya har suka fice daga room ɗin. Suna fita ya duƙa ya ɗauki mom ɗin cak yana sakar mata ƙayatattcen murmushi, ita ma murmushin take sakar mashi suna zubawa juna kallon soyayya, a hankali ta fara luguiguta mashi kunnen nasa da ta ja, daga jan mashi da murɗewa ya koma luguigutawa haɗe da rareshi, wato su dai turawan nan ba su tsufanwa soyayya, ko da yake su ai basu wani tsufa ba, Smart kawai suke da shi, dan haka su sha sharholiyarsu ni na goya masu baya. Haɗaɗɗen sumbata ya kai mata a saman jajir ɗin lallausan kumatun nan nata, ita kuma ta sumbaci ɗan bakinsa, daga haka suka wuce room nasu cike da kaunar juna, iyayen Heleena sam basu san me yake faruwa ba, suna nasu ɗakin da aka basu. Dad ya samu kira saman da 10 mins daga kingdom of england, a kan ɗaure yarima da ya yi, amma yaki ɗaga ko kira ɗaya, domin kuwa nan kasarsa ce, shi ne da power da kuma iko ba su ba, basu isa su ce zasu ɗaga mashi murya ba, idan sun bi ta lalama zai iya dubawa ya gani, idan kuma suka nuna mashi ɗan yatsa to tabbas ya ci alwashin sai ya karyeta ta hanyar ladabtar da yariman har sai sun miƙa wuya, shi ma irin ɗan nasa ne, ba'a kawo mashi wargi, kamar ba shi ne yanzu mom ta murɗewa kunne yana wani faɗin wash kamar ƙaramin yaro ba, mu dai mata sai sam barka lamuranmu ato, a waje namiji zaki, ana tsoronsa ana shakkarsa, idan ya dawo gida kuma mun fi jin tsoron ɓera a kansa. Smart tiger kuwa, iyayen nasa suna fita ya sanya hannu a saman saitin bed drawer ɗinsa, yana sanya hannu drawer ta buɗe, dan da na'ura take aiki, door remote ɗin ya ɗauko, dan baya son miƙewa daga in da yake bare ya je ya rufe kofar with password, amma da Allah yasa apart from fingering and password tana da remote and card, sai ya saita remote ɗin ya danna gabaɗaya lock na door ɗin. Tana rufewa ya mayar da remote ɗin tare da cigaba da yin aikinsa. Yana rufe kofar Heleena tana ƙarisowa wajen, hannunta ɗauke da ƙayatattcen luxury plate mai shake da small chop masu bala'in kyau a idanu, da gani zasu yi masifar daɗi a baki. A cewarta ta kawo mashi ne, dan ta samu damar ganinsa, dik da ba shiri suke yi ba tana son ganin face ɗinsa a koda yaushe, ta tsantsara kwalliyarta cikin athletic wear da suka matseta, cibiya a waje, iya breast ɗinta rigar ta rufe, da wani ɗan iskan shafaffen cikinta dake manne da baya, kugunta kamar zai ɓalle tsabar babu auki, bayanta a shafe kamar allan mayu, sai ɗan banzan shape kamar zata karye, kafafu kamar na belbela, fuskarn nan kam ba dai kyau ba, kyakkyawa ce gaskiya, kirar jikin ne sai dai sam barka, ba'a faɗin dayan. Ni takalmar da ta wani kwama a kafafunta ne ma ya bani dariya, kamar wadda ta kwato daga dawau namu na nan Nigeria, irin takalmar nan ne na yawo a cikin gida, sai dai ita nata dai kamar na mahaukata ta ɗauko, har saman singalalin ƙafafunta fa yakai, ga uban gashi gashi a jikinsa, su a dole sun yi mashi kwalliya masu buga takalman. Ta saki gashin nan har baya, idanu kamar na mujiya. Yana tsaka da aikinsa ta wutsiyar ido yaga alamar na taɓa kofar. Door ɗin nasa ba irin local kofofin nan masu handle bane, shi wannan kofa da ka cire password ɗinta ko ka sanya fingerprint ɗinka or remote, da dai ka cire lock ɗinta zata buɗe maka kanta da kanta ka shige kawai, kana shiga zata kuma ta rude kanta, so no need of handle a wajen. To ta taɓa jikin kofar ne tana wasi wasin shin ta yi knocking ne ko dai ta koma? Dan bata san password ɗinsa ba, tana tsoron yin knocking kada ya zamana yana barci ta tashesa, tasan me zai biyo baya idan hakan ya faru. Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli katafaren tv dake ta yamma maso gabas a cikin ɗakin. Hangota ya yi tana tsaye a jikin door ɗin tana ta wasi wasi, wani irin kallon tsana ya jefa mata, ya tsani ganinta, ba komai yasa hakan na kuma face irin wannan dressing ɗin nata, dama ace tana sanya kayan mutunci ta rufe kugun nan nata kamar allon mayun nan ne ma to da ta ɗan yi kyan gani, amma abu ne kamar sandar snowkar, har wani amai ya ji ya yunkuro mashi da ganinta da ya yi. Kawar da kallonsa ya yi izuwan kan laptop ɗinsa yana jan tsaki haɗe da kara ɗaure fuska kamar tana kallonsa. (Kun san me nake tunani ne my people's? A samu wani shafaffe da mai fisabilillah ya ɗaurawa Smart auren dole da Heleena naga karshen tsiya😂 saura kuce na iya mugunta, yo tun da ya tsaneta ai sai mu haɗasu dole ko ya kuka ce?) Ita kuwa ta ɗauki a kallah 10 mins tana tsaye tana tunanin mafita, daga karshe kawai ta hakura ta juya da kayan cimartata. Ni kam tana bani tausayi idan tana tafiya, sai naga kamar zata karye.........😥😂 Kun dai sai kirar turawa dama sai hamdala kawai za'a ce, su ba welcome ba bare good bye, ta ko'ina dai'dai yake ɗan battin nan. Cigaba da yin aikinsa ya yi yana tunanin rayuwarsu da iyayen nasa, gwanin ɗaukar hankali. Ita kuma ta koma room ɗinta. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A..✍️🔥🕊️ DARK WORLD💔😥💔 Matasane masu gigin tasowa, a kallah zasu iya kai 15 to 18 years haka, dik wanda ka ɗaga idanu ka kallesa sai ya baka sha'awa yanayin kirar jikinsa, sun horu sosai a hannun master Devil, sai gwajin karfi suke yi a tsakaninsu, dik wanda ya kayar da ɗan uwansa sai su ɗaga shi sama suna ihun murna, a kallah adadin yawansu zasu kai 80 haka, da alama suna cikin nishaɗi matuƙa yau. Sai dai dik wanda ka kalli face ɗinsa zakaga babu alamar annuri ko kaɗan, babu dariya ko ɗigo a saman face ɗinsu, suna tuɓune kamar ba mutane ba, ga shi dai suna tare cikin ƴan uwansu suna wasannin, amma babu ko irin ɗan murmushin nan wa junansu babu, ko da yake dama ai ba zasu yi murmushi ba, saboda master ma ai bai san wannan ba, su ɗin kuma hotonsa ne, so mai tsayawa jiran ganin murmushinsu ma yana ɓatawa kansa lokaci ne kawai a banza. Wani matashin ne lafiyayye fari tas ya miƙe tsaye yana faɗin babu wanda ya isa ya yi abin da zai yi, dan yana jin kamar yafisu karfi. Wani daga cikin nasu ne ya sake miƙewa tsaye, bugun kirjinsa ya yi da karfi da hannunsa yana faɗin ga shi nan zai iya komai su gwada a gani. Biyu daga cikin su ne suka sake miƙewa tare da buga kirazansu da karfi suma suna faɗin zasu iya, yadda suka bugi kirjin sai sun burgeka, saboda yadda kirarsu yake, ga su da kyau irin na mutanen birnin. Da alama suna ji da lafiya. Master da yake zaune saman wata chair yana fuskarsu ne ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, a zahiri zaka yi zaton ƴan training da suke yi a gabansa yake kallo, amma a baɗini kwata kwata hankalinsa bayaa kansu ma bare kan matasan gefensa, ya afka duniyar tunanin ta yadda zai yi ya raba Ronnie da Black Tiger, rabawa ta har abada! Dan tun da Ronnie ya dake shi ya ci alwashin ba zai taɓa kyalesa ba. Idan bai rabashi da Black Tiger ba kuma bai isa ya ce zai ɗauki fansa ba, yasan a iya training da ya bawa Ronnie bai isa ya iya dukansa ba, dole Black Tiger ne ya kara mashi power, yasa ya tozarta shi, ya zubar mashi da girma da kimansa a idanun gabaɗaya yaran da yake horarwa, ya ci mutuncinsa matuƙa, ya ja ya ji matuƙar kunya, dan haka ba zai taɓa kyalesa ba, dole ya mutu, kuma da hannunsa zai kashe shi, sai dai ta yaya? Ta wani hanya yakamata ya bi? Bai isa ko yatsa ya ɗaga mashi ba matuƙar yana a tare da Black Tiger, kuma yasan Black Tiger ɗin yana kaunarsa sama da komai a duniya, yanzu tunani yake yi ta yadda zai yi ya rabasu, ya ɗauke hankalin Black Tiger ya ɓatar da Ronnie daga empeir ɗin, idan ya so sai ya ja shi zuwa wata ƙasa ta daban cikin daji ya hallaka shi ba tare da sanin kowa ba, a tunaninsa kenan. Yau tun safe da ya shigo wajen training ɗin tunanin da yake ta yi kenan, ya kasa bawa yara horo, ya zauna saman kujera shiru kamar mai tilawar karatun Alkur'ani mai girma a cikin zuciyarsa, alhalin mugun abu yake ƙullawa, kowa dai yasan master bakin mugune, sannan idan yasa kai tsab zai iya yin abin da ya fi haka, to masoyan Ronnie sai ku tayasa addu'a, zamu ga tsakanin master and black tiger wanene ainahin shegen shu'umin a cikinsu, shin master zai iya wasa da hankalin Black Tiger har ya sace Ronnien kuwa ko yaya? Akwai game babba a tsakaninsu gaskiya, mu je dai zuwa. Wannan matashi da ya fara miƙewa mai suna Udesh ne ya nufi saman wata iriyar step mai shegen kyau, haurawa ya fara yi cikin jarumta, gini ne aka yi mai tsawo kuma ɗan siriri haka, sai aka yi step na hawansa, a can nesa ma aka yi irinsa, sai aka sanya wani irin murɗaɗɗen sarka mai karfi dogo kamar igiya, dik wanda ya iya hawa saman sarkar daga wannan ginin ya yi tafiya a kan sarkar har zuwa wancan ginin bai faɗo kasa ya ji ciwo ba to fa ya gama haye matakin farko na horo, sai mataki na biyu. Tun da suka ga Udesh ya nufi wannan gini zai hau wannan sarka suka karaya, da kuwa su a yanzu suke koyar tafiya a kanta, suna tsoron su faɗo su karya wuya ko wani sassa na jikinsu. Sai a lokacin hankalin master ya dawo kansu, wani irin tsawa ya dakawa Udesh ɗin wanda ya sanya shi saukowa a dubu. Master yasan basu kai ga iya tafiya a kanta ba, kada su je su faɗo su mutu yawan mayakansu masu tasowa su ragu, shi fa bama ransu yake yi wa ba, damuwarsa yawan mayakansu zasu ragu ku kunji mun bakar zuciya fisabilillahi!. Cikin hanzari ya dawo cikin ƴan uwansa jikinsa na kerma, dan suna bala'in tsoron master, yana zuwa ya zauna shiru, saura matasan kuma kowa ya kama abokinsa suka cigaba da gwada gwanji da karfi ta hanyar faɗa da juna, dama abin da master ya sakasu kenan. Sake sauke ajiyar zuciya ya yi a in da ya cigaba da tunanin ta yadda zai ɓatar da Ronnien. A can cikin Black Tiger empire kuma, zaune Floris take a parlour tana buga game ɗin triangle ita da ɗaya daga cikin ƴan'mata marayu da Black Tiger yake rai'na, yarinyar ita ma kyakkyawace jinin Dark world. Ko ina Ronnien yau kuma Floris take buga game da wata ba shi ba? Da alama ya tafi school. Ainahin Black Tiger empire, fitowa Sweetie ta yi daga cikin wani haɗaɗɗen luxury bedroom mai bala'in kyau, rufeta dama aka yi a cikin room ɗin, kullum sai ta gwada buɗe kofar amma sai ta jishi a rufe, yau dai tana gwadawa sai ta yi sa'a taga ya buɗe. Sanye take cikin jelly dressing, sai dai rigar ya ɗan yi kata tsawo sosai, dan ya sauka har kasar gwiwanta a maimakon ya tsaya a saman gwiwan wajen cinya, haka zalika wandon ma ya ɗan yi mata yawa, ya fi tsawonta. Kanta babu ɗan kwali, saboda kayan basu da shi, golden white hairnta a watse kamar wata mahaukaciya, da alama tana cikin damuwa sosai, dan sexy eyes ɗin nan nata a kumbure alama ta ci kuka sosai, ta rame matuƙa kamar ba ita ba, idanun nan sun kara kwala kwala kamar ball, olive eyes ɗinta sun ƙara ratsa olive green sosai, lokacin da suke jarirai idanunta forest green ne, Pretty ce ke da olive, a hankali hankali suma girma idanun nata suna riƙiɗewa har suka koma sak na Prettyn ba maraba. Dark purple lips ɗinta suna bushe karau tamkar bata shan ruwa, sun zama kamar basu ne masu sheki da ɗaukar hankali idan Kamran ya ga na Pretty ba, dik ta canza tamkar wadda aka ɗauki lokaci ana azabtarwa. Kana ganinta zaka fahimci a ruɗe take, ga tsantsar tsoro a face ɗinta, kamar wata zararriya haka ta fara waige waige tana neman hanyar fita daga wajen, tsarin ginin ya sha gaban tunanin wayayyun mutun ma bare ita girman forest, komai wayenwan mutun idan ya shigo wannan waje sai ya ɓata hanya ya kuma zama cikakken ɗan kauye, ga ɗakuna da a kallah zasu kai biyar a wajen, dik kuma design na komai iri ɗaya a cikin wajen, hanyoyi har huɗu ne a ciki, tashin hankalin ma bata san a hawa na nawa take ba, abin da baku sani ba hanyar da Ronnie yake shiga idan zai je wajen Black Tiger sai ya hau elevator sannan ya kai ga babban parlournsa, daga nan sai bedroom ɗinsa, so bata san a wani hawa ma take ba. Zubawa kujerun dake parlourn idanu ta yi, da zallar madarar gold aka yi su, gabaɗaya kujerun design of ɗawisu aka yi head ɗinsu, yanayin kayin kujerun ne sak gashin bindin ɗawisu, sun yi matuƙar tsaruwa sosai. Wajen zama kuma luntsuma luntsuman sofa foam ne masu lumar da mutum. Ganin cewa tsayawa ganin kujerun nan da tsaruwan parlourn ba zai kai ta ko'ina bane yasa ta nufi hanyar da ta gani yana fuskantar in da take tsaye. Sauri sauri gudu gudu ta nufe shi. Wani irin haɗaɗɗen door room ta gani a wajen, bata yi wani tunanin ba kawai ta tura ta afaka ciki, a tunaninta kofar fita ce. Wani irin juyi da kanta ya yi mata ne yasa ta sunkuyar da shi ƙasa ba shiri, ji ta yi tamkar wadda aka kwaɗawa katon guduma a tsakiyar kanta, dum ta ji duniya ya yi mata. A hankali ta fara ɗago sexy eyes ɗin nan nata ta fara kallon tun daga kan tafukan kafafunsa da suke farare tas tamkar madara, from his legs fingers ta fara kallo, gasu dogaye masu bala'in kyau, wani bakin gashi siɗif kwance saman kowani yatsarsa zuwa kusa da faratunansa. Bata san lokacin da ta fara ɗago idanunta izuwa sama ba, skin ɗinsa sak Koreans guys skin, ba karamin girgiza ta yi ba na ganin har ta kai kallonta saman santala santalan cinyoyinsa da wani siɗif ɗin gashi ke kwance luf bata ga kaya a jikin nasa ba. Ƙoƙarin kawar da kallonta ta yi daga kansa dan gudun kada ta ga abin da kanta ba zai iya ɗauka ba, amma ta ƙasa, haka idanunta ya cigaba da kallonsa har izuwa saman denim short white color dake jikin nasa. Bata daddara ba ta cigaba da ɗaga idanunta tana kallonsa, ƙara zaro idanun waje sosai ta yi a lokacin da ta sauke su a saman gurayen layukan dake zane a saman plat tummynsa. Bata ƙarisa tsinkewa ba sai da ta kai kallonta saman lion chest ɗinsa mai bala'in faɗi kamar wani zaki, ga ɓul ɓul ɗin breast ɗinsa a cike, babu riga a jikinsa, tamkar shi ya yi wa kansa halittar jikin nan nasa, gorgeous, sexy body ne da shi. Wani irin bala'in tsoro ne ya dira mata a ranta, sai ta ji anya zata iya ganin face ɗin mai wannan jikin kuwa? Dan kuwa master Devil da take jin tsoron gani saboda murɗewar jikinsa da kuma tsawonsa ma to bai kai wannan jikin ba, da alama wannan shi ne ubansu a kyan jiki a gabaɗaya kingdom ɗin. Abin mamakin kuma dik wannan murɗewar tasa wuyarsa tana da tsawo, bata yi tsawo zalau ba, tana da kauri sosai, har wasu gurayen layuka ne a wajen masu kyau da ɗaukar hankali, tun daga kan jikinsa zaka gane mamallakin jikin makura ne wajen haɗuwa. Wani irin ja da baya ta yi har sai da ta yi tangal tangal zata faɗi ƙasa a lokacin da ta ƙarisar da kallonta a saman face ɗinsa, ya subhanallah, ni kai'na sai da na ja da baya, saboda ban taɓa ganin halitta mai kyansa ba, wow nace, na kara cewa Masha Allah, na sake haɗawa da kam balai'n can, Allah mai yin halitta a duk yadda ya so, amma dai wannan guy ɗin makura ne. Kamar wani rafani za'ace ne ko me, ban ma san da ya zan kwatanta maku kyan guy ɗin nan ba. Namiji iya namiji, ga tsawo da cikar halitta. Pink lips yake da shi kamar na mace, yana yin tsarin lips ɗinsa kawai abin kallone ga ɗaukar hankali, ga idanu nan dara dara, farin ciki idanun nasa ya yi milk milk haka, kwayar kuwa olive ne irin na su Sweetien, sai dai shi nasa ya ɗan yi wani iri kamar anyi mashi mix da hazel haka, kumatun nan nasa sai dai muce masha Allah, ɓul ɓul, a haka bai yi magana ba, bai motsa kumatun nasa ba ma zaku iya ganin alamun kyawawan dimple a kumatun nasa, dik yadda zan gaya maku haɗuwar guy ɗin nan ba zaku gane ba, dan baki ma ya yi kaɗan ya bayyana kyansa, wane alƙalamina a wannan gaɓar. Lafiyayyen matashi mai shekaru 30 a duniya, handsome! Sexy! Gorgeous, end of discussion a kyau, sai dai kuma his heart is totally bad, fine guy with black heart!!. Yana tsaye a tsakin bedroom ɗin, daga shi sai danim short, hannunsa na riƙe da king scepter ɗinsa da kuma wani ɗan karamin circle abu mai haske kamar madubi, ba kuma madubi bane, idanunsa suna a kan wannan hasken, ya saita scepter ɗin nasa a saman abin, ya bada wani irin haske na musamman, da alama magic yake yi. Kasa tantance a wani irin duniya ko yanayi take ciki ta yi, gani take yi ba'a duniya take ba, dama tun daga kan yanayin tsarin part ɗin nasa ta ji a ranta ba'a duniya take ba, gani take yi a duniyarsu babu kyakkyawan halittata irin Ronnien ma, to yau kuma taga wanda ya ci uban Ronnie a kyau, mutum kamar bai taɓa taka kasa ba, kamar bai taɓa fita waje ba, jiki kamar na jariri, sai kawai ta sallama shikenan ita kam kawai ta bar duniya, an rabata da su Prettynta. Tunanin Pretty da ya faɗo mata a ranta ne yasa ta ji wani irin kwarin gwiwa ya diro mata lokaci guda, sake ɗago kaifafan idanun nan nata ta yi ta kara kallon face ɗinsa a karo na biyu, tamkar bai san da wata halitta ta shigo mashi ɗaki ba. Nasan zaku so sanin wanenen wannan sexy guy ɗin! To ba kowa bane face Black Tiger a ainahin siffarsa ba tare da tsafi ya canza shi ba, ainahin siffarsa ce wannan...........Na san a dai'dai wannan gaɓar na jijjige teburin dayawan jama'u, musamman ƴan comments section grp ɗina, tsammaci abin da baka tsamata ba kenan shi ne wannan, Black Tiger matashi mai shekaru 30 a duniya, abin dai da mamaki ko? My people's, kada ku manta ni dama na iya surprising ɗinku, to yau ma ga shi na yi, mu je dai zuwa, akwai kura over mai tashin kai!!. Wlh guy ɗin nan yadda kuka san bai san da shigowarta ba, abin da yake gabansa kawai yake yi. Ganin hakan yasa ta juya a guje, da iya karfinta ta watsa a gujen ta nufi waje. King scepter ɗin nasa ya nuna kofar room ɗin da ita, a take ta rufe kanta, wasu irin mahaukatan locks ne ke jikinta, dik suka datse kansu, dama kullum a rufe suke, akasi aka samu yau, Ronnie ne ya fita cikin fushi ya bar kofar a buɗe, shi kuma Black Tigern bai rufe ba yana jiran Ronnien ya dawo, dan yasa definitely zai dawo, fushinsa ga yayan nasa na ɗan lokaci ne. Wani irin juya magic eyes ɗin nan nasa ya yi, gani kake walwal kamar walkiya, bata yi aune ba sai ganinta ta yi a gabansa, ita da take ƙoƙarin guduwa ta fita, bata san ta ya aka yi ta zo gabansa ba. Ita ma dai ta yi gangancin yunkuri guduwa, domin kuwa tasan ba zata tsira ba, in baku manta ba Ronnie ya gaya mata already cewa dik wanda ya taɓa kallon face ɗin yayansa to baya rayuwa, kashesa yake yi! Kuma ya gaya mata kada ta yarda ta yi crossing wannan kofar, dan dik wanda ya shiga baya fitowa, ya tafi kenan har abada, dan ko gawarsa ba za'a gani na, amma tsabar rashin ji irin nata ta fito daga in da ya ajiyeta ta je afaka nan, ai ga shi yanzu zata gane kurenta, ta ɗebowa kanta bala'i. Sai dai kuma ta ciri tuta, dan ko shi Ronnie bai taɓa ganin ainahin face ɗinsa ba, karo na farko ba zato ba tsammani taga ainahin face ɗinsa a shegen shisshiginta da rashin ji, ta wani afka mashi cikin ɗaki babu ko excuse kamar gidan Kamran ne aka ce mata, yo ko gidan Kamran ai sai ta yi mashi excuse tun da ƴar uwarta yake so ba ita ba. Wayyo my people's, kuna tunanin Black Tiger zai barta kuwa? Ido cikin ido fa yau taga ainahin face ɗinsa? Ai yau ina ga ko RONNIE zai mutu ba abin da zai hana Black Tiger kasheta, na yi nan ni dai. Ganinta gata ga shi kusa kusa ne yasa tsoro yasata kandarewa a wajen, kamar wadda rai ya yi halinsa, da alama tsafin da ya yi mata ta zo gaban nasa ya taɓata ne yasa ta samdare haka. Tashin sense yau ina RONNIE? Black Tiger zai cinye mashi second beb ɗinsa. My people's idan kunji ana cakwakiya ma to abu mai iya kwatantuwa ne, rikicin da za'ayi a cikin empeir ɗin nan ba'a magana, dan ya wuce misali, ni dai na wuce sai mun haɗu gobe a kingdom of power idan mai dukka ya kai mu. ________________________ KINGDOM OF POWER💪🔥💘 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2024-11-19.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 40 KINGDOM OF POWER. Yau fada a cike yake da manyan cikinsa, su waziri and Galadima dik suna wajen, ga su commander, Akka and su uncle Abbas da yake son komawa bakin aikinsa, shi uncle Abbas ɗin nan sam baya son zaman Tunisia, ya fison ya yi waje abinsa, uncle Jahiz kamar a kan ƙaya yake, shi ma baya son ƙasar, Aunty miemie da mijinta sadauki Suhail dik suna cikin fadan. King yana zaune saman kujerarsa na sarauta, yana dake cikin alkyabbarsa, ya sha naɗin rawani kam, ya yi shiru yana jin cecekucen da suke yi dan ya basu damar su faɗi albarkacin bakinsu a kan yakin da suke shirin tafiya, shi ne ya basu damar zuba surutu har haka, da alama yana cikin damuwa sosai, haka zalika Akka, sam bata sanya bakinta a cikin maganar ba, ta yi shiru kamar wadda ta rasa abin faɗe. Aunty miemie da yake ita fa ta gaji King ɗin da gaske, jinin jikin shi yana yawo a jikinta, ko in ce jinin Akka ya ringayi jinin mom ɗinta da ya yi mix, in baku manta ba ita mom ba jinin modarawa bace, jinin Nigeria ce, iya momma ce kawai jinin modarawa a cikin matan King, shiyasa su Jaish suka fi saura zafin zuciya da shegen faɗa kamar me, dan su ta ko'ina jinin ne a jikinsu babu mix. Cike da nuna isa da izza ta furta. "Amma daddy ni fa ina ganin mu fara yakar Zarina kafin nan mu nemo Spender, dan ni gaskiya Zarina ta tsaya mun a wuya, tana hanani yin barci saboda takaici". Aunty miemie ba sauki, tafi son da an kawo masu hari su mayar da martani dan su nuna da banbanci, kada su ɗaga kafa. Commander ne ya ce. "Allah ya baki tsawon rai, amma ni sai nake ganin neman Spender ya fi, mu fara nemansa tukun nan, saboda haɗarin da yake tattare da shi abu ne wanda ya shafi jama'a dayawa, Zarina daga baya zamu ji da ita". Galadima ne ya tari numfashi commander da cewa. "Commander gaskiya ranki ya daɗe Queen miemie ta fika gaskiya, mu fara ladaptar da Zarina first, dan ta gane shayi ruwa ne, ka sanine ma ko Spender ɗin yana a hannunta?". Uncle Jahiz ne ya amsa da cewa. "Spender baya hannunta, idan da yana hannunta yanzu wani zance ake yi ba wannan ba, dole Spender yana ta wani wajen in da ba'a san amfaninsa ba". Cike da class and izza ya yi maganar. Uncle Jahiz akwai kaifin basirarsa, kamar kuwa yasan Spender dai yana can wajen da ba'a san amfaninsa ba, wadda take riƙe da shi ɗin ma ba'a san ina tayi ba a yanzu, ta je can ta ajiye shi dan rashin sanin illarsa........ Wai menene haɗarin da yake a tattare da shi ne wai? Mu je dai zuwa. Uncle Abbas ne ya ce. "Jahiz ka yi gaskiya a nan kam, haka ne kuma, tabbas Spender yana ta wani wajen da ba'a san amfaninsa ba, da yana hannun waɗan da suke nemansa misali kamar Zarina ai da yanzu mu kammu ba kyalemu zata yi ba, da ta fara ruguje dauloli!!" cikin nutsuwa da dattaku ya yi maganar, yana magana one after the other. Ita dai Akka da idanu kawai take binsu kamar yadda King yake aikin binsu da kallo. Kowa sai faɗar ra'ayinsa yake yi. CIKIN GIDA. ______________________________💘 Auta sai biyewa wannan guy ɗin take yi tana yi mashi reply yana sake mai do mata, uncle Taheer dai ya yi magana har ta gaji yaga bata amsa mashi, sai ya lura da hankalinta kacokam yana a kan wayarta, hakan yasa ya nemi karɓar wayar, nan fa ta yi saurin fita daga what'sapp ɗin tana sanya mashi kuka a kan ya kyale mata wayarta. Dan dole ya kyale ɗin ba da ya so ba, sai dan yasan idan ya sake ya sanyata kuka shi kansa zuciyarsa ba zata yafe mashi ba bare ƴan uwanta, zai haɗu da fushin King, ga su uncle Abbas suna nan, ai sai sun saɓa mashi, hakan yasa ya kyaleta da wayar. Sai ma ya ce to ta tashi su wuce cikin gida tun da ba hira zata taya shi ba. Ba musu kuwa ta miƙe, alamar ba hiran take so ba dama. Sam bai ji daɗin hakan ba, amma ya ya iya to? Dole sai hakuri ya cigaba da lallaɓata tun da shi yake so. Miƙewa shima ya yi tare da miƙa mata hannunsa a kan ta kama su tafi, ba musu ta bashi hannunta ɗaya while ɗayan yana kan wayarta tana karanta sakon yarimanta. Suna fitowa daga cikin wajen suka ci karo da Hoorain da yake tsaye a kusa da wajen shi da abokinsa Ansar suna tattaunawa. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa, yadda ya kawar da kan sai ya baku mamaki, tamkar gaba yake yi da ita, dik da yana cikin hular kayan yakinsu hakan ba zai hana ka iya gane cewa ransa a matuƙar ɓace yake ba, sai ma ya yi ƙasa da kansa, da alama baya son haɗa idanu da Ansar ɗin ma a wanann lokacin. Ita kuwa tana ganinsa ta saki murmushi tare da furta. "Hoorain yau tun safe ban ganka ba, ina ka shiga ne wai?". Kamar ba zai tanka mata ba saboda ɓacin ran da yake ciki, sai kuma yaga rashin dacewar amsa mata da yake ƙoƙarin kin yi ɗin, hakan yasa ya danne ba tare da ya juyo ya sake kallon in da take ba ya yunƙura zai buɗe baki ya amsa kenan muryar uncle Taheer ta katse shi da cewa. "To ina ruwanki da shi da zaki nemi ganinsa? Har da cewa tun safe baki ganshi ba! To me zaki bashi idan kin ganshi ɗin?". Ya yi maganar da alama ransa a matuƙar ɓace shi ma, kamar dai kishi shi ma yake yi dan ta tambayi ina Hoorain ya shiga tun safe. Jin wannan magana na uncle Taheer ɗin ne yasa ya fasa amsa maganar tata, sai ma ya nufi hanyar barin wajen. A takaice ta ce. "Hoorain ka dakata ka ji". Ta kai karshen maganar tare da juyowa ga uncle Taheer da yake ta kallon face ɗinta cike da jin haushin kula mayaki ƙasƙantace mai bata kariya da take yi, amma fa a cewarsa ne Hoorain ƙasƙantacen bawa ne mai bata kariya, sam bai ɗauke shi da wata daraja ba, bai san cewa idan ba dan su Hoorain ɗin ba shi kansa kingdom ɗin ba zata zaunun mashi ba, da ayake yaken da ake yi ai da an jima da kashe shi, su Hoorain ai sune jarumai, kowa a kingdom ɗin nan da bazarsu yake taka rawa, sune ainahin mazajen. "Uncle Taheer dole zan tambayesa ina yaje mana yau tun safe, kada ka manta fa kula da ni yake yi, meyasa ni ma ba zan kula da shi in damu idan ban ji motsinsa ba?............" Tun time ɗin da ta ce ya dakata ya dakata da tafiyar kamar yadda ta buƙata, sai dai yaki juyowa ya kalli in da suke, sai ya juya gefe guda. "Katseta uncle Taheer ya yi da cewa. "Baby yana da kyau ki san cewa ke fa daban kike da su, akan me zaki nemi sanin ko yana lafiya? Kin manta karen farauta ne shi ɗin? Baki da wata hujja na neman sanin ya lafiyarsa take!!". Cikin ɓacin rai sosai ya yi maganar. "No uncle Taheer, ba haka bane gaskiya, dikkan mutane abu guda ne, da ni da shi dik ɗaya ne a wajen Allah, babu wani bawa da Allah ya ƙaskantar ko ya wulakanta, dikkan bayin Allan masu daraja ne, wanda Allah zai fiso kuma shi ne wanda yafi jin tsoronsa, bani da wani banbanci da Hoorain, kuma yana kyautata mun dole ni ma na............". "Ki mun shiru!!". Tsawan da ya daka mata ne yasa ta haɗiye sauran maganganun nata ba tare da ta ƙarisa amayar da su ba, dan ta ɗan tsorata gaskiyar. "Ranki ya daɗe zan iya tafiya?". Cewar Hoorain da takaici ya gama cika mashi cikinsa, so yake yi kawai ya bar wajen, dan yasan idan ya tsaya tsab zai iya sumar da uncle Taheer ɗin nan, so gara mashi ya tafi, sai dai ba zai yiwu ya tafi ba tare da ta bashi izini ba, dole ya jira izininta koma me zai faru ya faru. Allah sarki shi dai kam Ansar sai binsu da ido yake yi yana mamakin hali irin na Hoorain, tunani yake yi da shi ne ya samu wannan dama da har Gimbiya mafi soyuwa a cikin kingdom ɗin take damuwa da shi har haka ai da ya more ya kuma saki jiki, amma shi Hoorain ya samu dama yana wasa da ita. "A'a Hoorain kada ka tafi, ina son yin magana da kai". Ta faɗa a tsorace, tana kuma ɗagowa ta saci kallon uncle Taheer wanda ya gama zuwa wuya da takaici, kishi kamar zata kashe shi. Cikin tsawa haɗe da bada umarni uncle Taheer ya ce da Hoorain ɗin. "Daga yau na haramta maka sake yi mata magana! Sannan na soke bata gariya da kake yi! Na haramta maka ɗaga idanu ka sake kallonta! Kada ka yarda ku sake haɗa hanya da ita, ka wuce ka bani waje yanzun nan bana son sake ganin ko mai kama da kai!". Kamar zata yi kuka ta ce. "Uncle Taheer a kan............" Bata iya ƙarisa maganar ba sabo wani irin fusata da ya yi har bai san lokacin da ya cire hannu zai dallah mata mari ba. Aikuwa kamar wani walkiya haka Hoorain ya iso wajen ya riƙe hannun nasa ya hanasa sauke mata marin, shi a dole ransa ya ɓaci yana kuma kishi har da ƙoƙarin kai mata mari. Ta datse idanu tana jiran saukar marin, sai ta ji shiru, tuni jaruminmu Hoorain ya riƙe hannun nasa. Ƙoƙarin kwace hannun nasa ya fara yi, amma ina ya kasa, da hannu ɗaya kuma Hoorain ɗin ya riƙesa amma ya gaza kwatar kansa. A hankali ta waro idanun nata dan taga ya aka yi marin bai sauka a kumatunta ba. Ai bata san lokacin da ta saki cool ajiyar zuciya ba, wani irin sanyi ta ji a ranta na ganin jaruminta ya tare mata faɗa, dama tasan da wuya idan yana wajen ya bari ayi mata wani abin, sai dai idan Jaish ne zai daketa, wanna babu yadda ya iya dole ya kawar da kansa, amma irin su uncle Taheer gaskiya ba zai bari ba, idan sun daketa a cikin gida wannan fine bai gani ba, amma a wajen kam a'a gaskiya. "Ka sakar mun hanu!". Ya faɗa cikin tsawa, dan ya kasa iya kwatar kansa, shi ne zai nuna mashi jan ido ya sakesa. Calmly haɗe da kwamciyar hankali ya furta. "Zaka iya kwatar hannun naka ai!". Zaro idanu sosai Ansar ya yi, ya tsorata na ganin Hoorain ya mayarwa da ɗan cikin family amsa, tashin hankali. Ita kam Auta ranta fes abinta, dan Hoorain take so ba Uncle Taheer ba!. "Ba zan daina kula da ita ba har sai ranar da mai girma King ya faɗi hakan da bakinsa, ba kai ka bani aikin kula da ita ba! Kasani wannan riƙe hannun naka ma da nayi dik a cikin aikina yake, kuma ba yau ba dik ranar da ka yi kuskuren hannunka ya taɓa jikinta, na yi maka alkawarin sai na datse maka shi!!". Yadda yake maganar one after the other sai ya yi matuƙar burgeku, ga maganar tasa cikin sanyin murya da nutsuwa, babu hayani, ga zallar madarar jarumta a kowace word da zata fita daga bakinsa, yau karo na farko a rayuwarsa da ya taɓa yin makamancin hakan, baya shiga shirgin kowa, amma uncle Taheer ya kuresa ne, dan ma ya yi sa'a yana matsayin ɗan cikin family ne yasa ya raga mashi, bada ban haka ba da babu abin da zai hana bai karya mashi hannun ba!!. Matsawa kusa da shi a tsorace Ansar ya yi tare da riƙo damtsen ɗayan hannun nasa yana faɗin. "Hoorain let's go, ka bari haka". Wani irin kallo ta wutsiyar ido da ya wurgawa Ansar ɗin ne yasa ya sake mashi dantsen hannun nasa tare da ja da baya, dan shi yasan wanenen Hoorain, idan ya zuciya karo da shi babu daɗi, so karya jawa kansa cin jibga. Uncle Taheer ɗin kuwa irin shi kada ya bada kansa a gaban Auta ta ce da Hoorain ya rikesa ya kasa kwacewa, sai ya yi ƙoƙarin saka dikkanin karfinsa zai kwaci hannun nasa, har da ƙoƙarin yadda zai yi ya kaiwa Hoorain ɗin duka. Shi kuwa tun yadda ya rikesa da farko ko motsawa bai kara yi ba, da hannu ɗayan dai uncle Taheer ya kasa kwatar kan nasa, ta wutsiyar ido ya kalleta, ta zuba masu ido irin like wow ɗin nan tana kallonsu, wani irin daɗi take ji, tana son ganin Hoorain a cikin irin wannan fusata, shiyasa ranar da aka kawo masu hari a masarautar ta rinƙa kallonsa da yana yakin cike da jarumta. Ajiyar zuciya ya sauke ganin alamar murmushi a saman face ɗinta. Dawo da kallonsa a kan uncle Taheer ɗin ya yi, sannan ya ce. "Bana magana biyu, amma yau zan sake maimaita maka abin da nace, in har ka kuskura shaiɗan ya ruɗeka ka kai hannunka a jikinta da sunan duka na yi maka alkawarin datse maka hannu! Na rantse da girman Allah!!". Yana kai karshen maganar da ɗan karfi ya watsar da hannun uncle Taheer ɗin, wani irin baya baya ya yi kamar zai faɗi kasa saboda wurgi da hannun nasa da ya yi, a haka ma fa bai saka karfinsa wajen wurgar da hannun ba, da ya saka karfi kam ina ga uncle Taheer sai ya faɗi ƙasa. Yana wurgi da hannun uncle Taheer bai tsaya wani ɓata lokaci ba ya juya cikin taku mai cike da tsantsar jarumta ya bar wajen. Bayansa ta bi da kallo just like wow ɗin nan, sam bai sake juyowa garesu ba har ya fice daga wajen. Da sauri Ansar ya rufa mashi baya. Ji ta yi ita ma kamar ta bi bayansa ta je ta bashi hakuri, dan tana ganin ransa ya ɓaci sai dik bata ji daɗin hakan ba. Uncle Taheer dai ya kwashi kunya da kayan takaici a idanun Auta, an yarfa shi, kuma shi kansa ya san Hoorain dai ba tsaransa bane, idan ya ce zai yi mashi wani wargi tsab zai ɓaɓɓallasa, dan fa zama assistant commander ba karamin jarumi bane yake iya kai wannan mataki, so shiyasa kuka ga ya shafawa kansa ruwan sanyi bai bi bayan Hoorain ɗin ya ce zai yi faɗa da shi ko wani abin makamancin hakan ba, shi dama karfinsa kawai dan ɗan cikin family ne, da wannan power yake amfani yasa dik mayakan su yi mashi biyayyar dole, kurinsa dikka shi family ne, dole su bi umarninsa, amma batun faɗa ku kanku kun san idan kuka cire commander Zafar caf cikin kingdom ɗin nan babu mai iya taɓa kwalar rigar sadauki Hoorain kuma ya sha, karya ne wlh, babu wannan a cikin gabaɗaya mayakan, kawai dai shi shiru shiru ne yasa ake ganin like ko an sanya mashi yatsa a baki ba zai ciza ba. Dik jikin uncle Taheer ya yi la'asar ya ji kunya sosai, haka ya wuce cikin gida fuuuuu ya barta tsaye a wajen, a cewarsa zai je ya gayawa mama ta gayawa King dole Hoorain ya daina tsaron Auta daga yau. Ganin ya tafi ne yasa ta yi yunkurin bin bayan jaruminta, sai dai ko da ta bi hanyar bata gansa ba, ta ɗan yi tafiya mai nisa har ta kusa shan kwana amma ko mai kama da shi bata gani ba. Zata juya ta dawo kenan daga bayanta ta ji ance. "Ranki ya daɗe wani kike nema ne?". A hanzarce ta juyo, cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Abbo ina wuni?". Ɗan yaƙe ya yi kafin ya amsa da. "Lafiya lou gimbiya, wani kike nema ne?". Kara faɗaɗa murmushinta yi. "Abbo Hoorain nake nema, yanzu ya biyo ta nan shi ne na zo duba shi". Kallon hanyar da ya fito ta wutsiyar idanu ya yi, Hoorain ɗin yana zaune kasan wata bishiya shi da Ansar dake ta faman tayasa tausan zuciyarsa, sai huci yake yi, dan uncle Taheer ya bakanta mashi sosai, ace a gaban idanunsa ya yi yunkurin marin Auta? Ai ganganci da rayuwarsa ma yake wannan, ya ji takaicin da ya kasance ba wani bare can bane ya yi wannan gigin, da yau sai ya gane annabi ba ɗan Allah bane manzon Allah ne. "Ki koma ciki kawai gimbiya Hoorain baya nan, ya tafi cikin ɗakinsa, amma idan na koma zan gaya mashi kina nemansa". Da yake in da Hoorain ɗin yake a ta kwana ne bata iya ganinsa idan har ba ta yanki kwanar ba. Amma meyasa commander zai ɓoye mata Hoorain ɗin? Da alama shi ma baya son wani abin ya rinƙa haɗasu kenan! To me dalili? Muje dai zuwa, kowa dai sai ya fito mana da manufarsa ato. Kamar zata yi kuka ta ce. "To dan Allah Abbo ka ce anjuma ya zo lambun dad ya sameni, magana nake son yi da shi". "In Sha Allah zan sanar da shi". Ya bata amsa yadda kuka san wanda yake kulla wani abin. Juyawa ta yi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi hanyar komawa cikin gidan. Tsayawa commander ya yi yana kallonta har ta kurewa ganinsa, sannan ya sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, a hanzarce ya juya ya koma wajen ɗan nasa. Abin da baku sani ba shi ne, shi Abbo ya ga tahowarta a lokacin da yake ƙarisawa wajen su Hoorain ɗin, shi ne ya zo ya tareta dan kada ta ƙarisa wajen kwanar ta gansu. Yana komawa wajen su Hoorain ɗin ya zauna kusa da ɗan nasa. Tare da fara tambayarsa meyasa me shi yaga kamar ransa a ɓace. Ansar ne ya kwashi dik abin da ya faru ya zanta mashi. Shiru ya yi yana tunanin ta yadda zai ɓullowa lamarin, ta yadda zai yi ya raba ɗansa da ita, dan yana gudun abin da zai je ya zo, yasan ko mutuwa Hoorain yake yi ba zasu bashi auren Auta ba, so is better a matsayinsa na uba kada ma ya bari wata alaƙa ta soyayya ta shiga tsakaninsu har ɗan nasa ya wahala.. Gmmm suma nasu part ɗin akwai gwarama dai kam, dan ga dikkan alamu Auta dai son Hoorain take yi, dama ance kowace zuciya tana son mai kyautata mata, to yana kyautata mata, yana kula da lafiyarta, yana bata kariya fiye da kansa, ai dole ta so shi! Ko ba haka ba my people's?. Kuma ita nata soyayyar ta gaskiya ce, domin kuwa ko face ɗinsa bata taɓa gani ba, amma a haka take son kayanta baiwar Allah. ________________________________💘 Luv bird 💘🕊️🦋 A hankali ya waro idanunsa da suka yi mashi nauyi saboda barci, ya mance da ya kashe wutar ɗakin, yana ganin duhu ya yi hanzarin miƙewa zaune, dan a tunaninsa dare ta yi, hannu yasa ya fara laluɓar wayarsa domin ya kunna haskenta, sai dai bai jita ba. Laluɓar side drewer ya yi, remote ya ɗauko a ciki. Lamp ya fara kunnawa kafin ya miƙe tsaye, gaban switch ya je. Wutar ɗakin ya kunna nan take haske ta gauraye ko'ina. A hanzarce ya juyo da kallonsa izuwa saman bed ɗin, wayam bata ba labarinta, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya koma bakin bed ɗin. Can kusa da pillown da ya kwantar da ita ya hango wayarsa. Ɗaukota ya yi ya kunne screen light ɗinta. 6:05 a lokacin, mangariba ta kawo kai. Nisawa ya yi yana ƙoƙarin yunkurawa ya miƙe ya shiga toilet kenan aka turo kofar room ɗin. Dakatawa ya yi tare da kai kallonsa wajen dan yaga waye mai shigowar. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya ga wanda ya shigo ɗin. "Welcome daddy". Ya faɗa yana kallon uncle Abbas cike da kauna. Gefen bed ɗin uncle Abbas ya zauna, tun da ya sako kafafunsa a cikin ɗakin idanunsa suke a kan ɗan nasa kamar mai zargin wani abin. Shi kansa ya ɗan yi mamakin irin kallon da dad ɗin nasa yake yi mashi, kamar yana tuhumansa, dik sai ya tsargu, dan kunsan maras gaskiya fa kullum a tsarge yake, ba da shi ake abu bama idan bashi da gaskiya sai yaga kamar da shi ake yi, yasan ya kawo Chuchunsa cikin ɗakin sun kuma yi barci a tare, to sai yake ganin kamar uncle Abbas ya gane komai ne yasa yake yi mashi irin wannan kallon. "E lallai son ya tabbata dole a cikin wannan satin na yi maka aure, iyeee gaskiya ka nuna mun kana buƙatar hakan". Uncle Abbas ya faɗa cike da zolaya. Tuni ya kara tsarguwa jin abin da daddyn nasa ya faɗa, ɗan zaro idanu ya yi, a ɗan ruɗe ya ce. "Daddy me kuma ka gani da zaka ce zaka mun aure? Ko ka ganni da wata ne? Ni fa bani da budurwa!". Yadda yake maganar ma sai ya baka dariya, tsantsar tsarguwa da rashin gaskiya ne a tattare da shi. Uncle Abbas kuwa da yake shi ma ha iya tsiya sai ya ce. "Malam ya da tsarguwa ne? Daga magana ka fara jero mun tambayoyin da kai kanka kake kama kanka a cikin tambayoyin naka! Wato kenan ya tabbata kana tare da watan ko? Shi ne ka ruɗe kake tambayata ko na ganka da wata ko? To ina take?". Ƙaƙalo murmushin dole ya yi. "Kai daddy ni bana a tare da kowa, sai dai idan aure dole zaka mun, sai ka zaɓa mun budurwa a cikin ƴaƴan dad". Ɗan ɗaure fuska uncle Abbas ya yi irin ba wasan nan san ya ce. "Ba shakka zan yi maka auren dole, amma kuma da kai da mamallakiyar jambakin nan dake saman kumatunka, da ita zan haɗaka, maza gaya mun wacece cikin satin nan ayi komai dan ba zan yarda a lalata mun kai ba". Ya kai karshen maganar yana danne dariyar da ta so kubce mashi dan ma kada Jawad ya zaci wasa yake yi. A fujaje ya kai hannunsa saman kumatunsa, ganin ba zai iya gani bane yasa ya yi saurin miƙewa ya ƙarisa gaban mirror dan ya gani. Aikuwa yana isa gaban miror ya kallesa kuwa, ga shatin ɗan bakinta a kumatunsa, da alama sumbatarsa ta yi da ya barci kafin ta bar ɗakin, kallon kansa da kyau ya yi yana imagine yadda ta matso yana barci ta sumbacesa, lallai Chuchu ta iya tsiya ashe ita ma, ga zanen ɗan bankin nata ya fito sosai, saboda jan janbaki ne, skin ɗinsa kuma kunga arabs skin ne, yana da haske sosai, dole yafito ɓaro ɓaro. Ta cikin mirror suka haɗa ido da uncle Abbas dake ta kallonsa, gera guda uncle Abbas ɗin ya ɗaga mashi, ai bai san lokacin da murmushi ta kubce mashi ba, wani irin daɗi ya ji tamkar a lokacin ta sumbace shi ko kuma idanunsa biyu ya ji saukar ɗan bakin nata. Har wani imagine yake yi yana jin kamar a lokacin take kai mashi sumbatar. "Sai kazo ka gaya mun wacece mamallakiyar jambakin dan na yi saurin ɗaukar mataki". Muryar uncle Abbas ta daki dodan kunnensa. "Kai daddy, ni ka bari mana, Allah bana so, ni babu kowa, kuma wannan ba jan baki bane, ni na zanawa kaina". Ya kai karshen maganar yana juyowa gabaɗaya. Wani irin kallon da ya wurga mashi ne yasa shi sake cewa. "Kai daddy zaka fara ko? Da gaske babu kowa". Yana magana yana wani sakin murmushi kamar ance mashi an bashi ita, dik daɗin sunbatar da ta yi mashi ɗin ne fa. "Ni dai azo a gaya mun wacece tun wuri, idan ba haka ba in ɗauki mataki a kanka". Ya yi maganar idanunsa a kansa. "Ni dai wlh daddy kun saka mun ido kuma kun matsa mun, ni fa Allah zan kaura na bi uncle Jahiz mu tafi ina bar maku gidan". "Da gaske?". Ya yi tambayar yana ɗaga mashi gera. Zama ya yi saman bed ɗin yana janyo pillow ya rungume, dan wani irin nishaɗin da yake ji dole ya rungume pillown ko zai ji kamar ita ya runguma. "Da gaske mana daddy, ni kun takura mun". "Tom shikenan tun da ba zaka faɗa mun ba bari naje na samu daddynku na gaya mashi na baka auren Aneesa jummar nan a ɗaura........". Ai bai bari ya kai karshen maganar ba a dubu ya ce. "Daddy Aneesa ko kuma Jannat?". Ai uncle Abbas bai san time da dariya ta kwace mashi ba, cikin dariya ya ce. "Ina kace baka ji? Ni zaka ɓoyewa ko son? Idan baka gaya mun ba kana da wanda ya fini da zaka gayawa ne? To dik wani take takenka dai na gama gano ka". Ƙasa ya ɗan yi da kai zai fara kunyar rashin kunya, cikin sanyin murya ya ce. "Gaskiya daddy ina da wanda ya fika da zan gayawa, dad kawai na yi niyar gayawa, dan shi ne zai nemomin aurenta a hannunka, kuma dole ka bashi idan ya nema". Murmushi tamkar bakin uncle Abbas ba zai rufu ba ya amsa da. "Aikuwa ba zan baka ƴata ba sai kun yi biyayya". "Kai daddy wani irin biyayya kuma ya rage? Ko dai wahalar da ni kake son yi ne........?". Tarar numfashinsa ya yi da cewa. "Kamar yadda ka wahalar da zuciyata wajen kin bayyana mun wannan daddaɗar labarin da zai sanyani tsananin farinciki ba, kasa ina ta tunanin kana sonta da gaske ne ko dai kawai zargi nake yi". Cikin girmamawa ya ce. "Ka yi hakuri daddyna, tuba nake yi, kunyarka nake ji yasa na ɓoye, to amma ba ga shi yanzu na gaya maka ba?". "Yanzun ma ai sai da na ritsaka ne ka gaya mun". Ya yi maganar yana wurga mashi hararar wasa. "To daddy sorry, dan Allah a bani ita kada a wahalar da ni, kuma daddy kamar yadda ka ce ayi mana aure a satin nan ɗin na yarda ka ji my hero?". Yana magana yana ɗan turɓune fuska zai yi wa daddy shagwaɓa. Hannu uncle Abbas ɗin yasa a gefen cikin ɗan nasa ya fara yi mashi cakulkuli yana faɗin. "Eyeee my son ya girma zai zama ango". Dariya sosai ya fara yi yana faɗin. "Kai daddy ka bari mana, zaka sa cikina ya yi ciwo". Cigaba da yi mashi ya yi yana ta dariya har da hawaye, da yaga ba zai dai'na yi mashi ba sai ya kwanto jikinsa ya rukunkume shi ta ko'ina ya hana shi yin wani motsi, dan dole ya dakata taga yi mashi cakulkulin ya rungumeshi suna ta dariya gwanin birgewa. Sai da uncle Abbas ya tabbatar ɗan nasa ya yi farinciki sosai sannan ya miƙe ya nufi waje yana faɗin zai yi magana da King a kan batun kafin su sanar da Akka halin da ake ciki. Cike da tsantsar farinciki babu ko kunya ya hau zubawa daddyn nasa godiya ba adadi, har tsokanarsa uncle Abbas ya yi a kan wato baya jin kunyarsa ko?. Yana fita ya miƙe ya faɗa cikin toilet, dan an fara kiraye kirayen sallar mangariba. A gaban mirror dake kusa da wash hand base ya tsaya yana kara kallon zanen janbakin dake saman kumatun nasa, hannu ya kai ya shafa wajen yana jin matuƙar farinciki sosai. Uncle Abbas kuwa yana fitowa ya nufi part ɗin King, a hanya suka ci karo da Chuchu da ta fito daga part ɗin ita ma zata je wajen Auta a ɗakin momma ta bata labarin soyayyarta da Yah Jawad ɗinta. Tsabar sun samu tarbiya wajen momma har ƙasa ta tsugunna zata kwashi gaiwa kanta a ƙasa. Ai tsabar farincikin da uncle Abbas yake ciki na ganewa da ya yi suna soyayya da ɗansa bai san lokacin da ya ɗagota ya rungumeta yana murmushi ba. Ya sha rungumarsu sosai, amma sai ta ji na yau ya yi daban, dan wani irin rungumar farinciki ya yi mata, ji yake kamar ya mayar da su cikin jikinsa saboda farinciki, bai san lokacin da ya hau zuba mata ruwan albarkoki ba adadi ba, tun tana amsawa da amin har ta kwanta shiru a jikinsa tana mamakin meyasa yau ya tsawaita addu'arsa a gareta? Bata san ya san komai ba. Ya ɗauki tsawon mintuna 5 yana zuba mata addu'a kafin ya saketa yana shafa kanta. Ƙasa ta yi da kai ta yi shiru kamar wata amaryar da ake yi wa nasiha. Wucewa ya yi baki yaki rufuwa ya shiga part ɗin King, ita kuma ta wuce ta nufi na Momma. Momma kawai ta samu a ɗakin, zama ta yi kusa da ita suka ɗan yi hira kamar na 30 mins haka, sannan ta miƙe tare da cewa Mommar bari ta je ta duba Auta a part ɗin Akka, da okey momma ta amsa mata. A lokacin kuma Auta suna tare da Hoorain da uncle Taheer wajen da suka samu wancan miss understanding ɗin nan. Part ɗin Akka ta nufa, yau dai kaya marasa nauyi ne a jikinta, doguwar riga ce mai karamar hannu, bata da wata kwalliya sosai a jikinta, ta sanya malesian cap a kanta mai shegen kyau, irin waɗan nan ƴan huluna marasa nauyin, masu mannewa da kan mutun. Kai tsaye room ɗin Akka ta nufa. Sai dai bata kai ga shiga room ɗin ba ya rufe mata idanu ta baya tare da ɗaukarta cak sai cikin room nata dake cikin part ɗin. A tsakiyar ɗakin ya sauketa tare da zagowa ta gabanta. Ya yi wanka ya shirya cikin arab jallabiyar fara tas, da alama massalaci ya fito, sai tashin kamshi yake yi, ya yi kyau sosai. A tare suka sauke ajiyar zuciya na ganin juna da suka yi. Ƙasa ƙasa ta ce. "Yah Jawad ina wuni". A ɗan takaice ya ce. "Ban wuni ba". Ɗan zaro idanu ta yi, kamar zata yi kuka ta ce. "Kai Yah Jawad me kuma na yi maka?". Ɗan rage tsawonsa kaɗan ya yi. "Mema baki mun ba?". Turo baki ta yi. "Me na yi to?". Hannunsa ɗaya ya ɗaura a bayanta tare da matso da ita jikinsa, ya kara rage tsawonsa ya rankwafo kanta kenan, ƙasa ƙasa ya ce. "Waye ya ce ki sumbaci kumatu na? Ga shi yanzu kinsa daddy ya gani kin sa na ji kunya ko?". Zaro idanun ta yi tare da ɗago kallonta a kansa, kashe juna da kallon kauna suka yi. "Yanzu Yah Jawad da gaske daddy ya gani? Kuma me ya ce maka?". Tana magana tana kara zaro ido ga shi tana kallonsa. "In gaya maki abin da ya ce?". Kai ta gyaɗa da sauri. Iskar bakinsa ya hura mata a face ɗinta, hakan yasa ba shiri ta datse idanunta gam, matso da face ɗinsa daf da tata ya yi, ya haɗesu, kamar kai raɗa ya furta. "Cewa ya yi sai na gaya mashi wacece mamallakiyar wannan jambakin?". A ɗari ta waro idanunta waje. "Amma dai Yah Jawad baka ce mashi ni ce ba ko?...........". Ƙasa ƙarisa maganar ta yi jin yadda ya sauke ɗan bakinsa a saman nata. "Waye ya koya maki sumbtar mutun ma tukun nan?". Ya yi maganar lips ɗinsa suna saman tata. "A wajenka na koya". Yadda ta yi maganar sai ka rantse da Allah battery aka sakawa yar tsana, idanunta a buɗe garau tana kallon nasa, kamar dai wadda ta yi suman tsaye kuma, ba zaka taɓa cewa ita ta yi maganar ba kamar wata Robbot ta koma. "A yaushe na koya maki ni kuma? Ko yaushe kika taɓa ganin na sumbaci wani?". Yana magana suna kallon cikin idon juna babu ko kyaftawa. "Ba kai ne ranar da na yi barci a room naka ka dawo dani room nawa ka kwantar da ni kafin ka fita sai ka sumbaceni a goshi ba? Daga ranar na koya, shi ne nima na yi maka yau". Ɗan zaro idanu shi ma ya yi. "Kenan baki yi barci ba ranan?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Okey bari in yi maganinki yanzun nan, wato idanunki biyu kina jina ko? Kin ga komai ko?A haka kuma kika wahalar da ni wajen nunawa kamar baki san ina sonki ba ko? Allah ba zan kyaleki ba". Ɗan raba jikinta da nasa ta yi, ta sanya hannu ta riƙo waist ɗinta, tana jujjuya fararen idanunta ta ce. "Ni dai babu yadda zaka yi dani! Kuma kai Yah Jawad dama so kake yi in ce na gane kana sona tun baka furta mun ba? To ai idan na yi haka ban cika mace mai aji ba! A'a ni ina da ajina dole na ja class, na san komai kawai wahalar da kai nake son yi kamar yadda ka yi ta bani punishment a baya". Tana magana tana ɗan girgiza weist ɗin nata. Ai mutuwar tsaye ya yi, ta kwance mashi notikan ƙwaƙwalwa, iyee ashe ita ma tasan komai kawai tsiya ce irin tata. Cigaba da jujjuya fararen idanun nan nata sama ta yi tana faɗin. "Allah Yah Jawad nima ai ka wahalar da ni da kaki bayyana mun soyayyarka da wuri, ka azabtar da zuciyata........". Bata kai karshen maganar ba ta yunƙura zata kwasa a guje, sakamakon capka da ya kai hannunsa zai yi mata. Ai kuwa ta gudu bata tsira ba, dan kuwa a dubu ya capkota tare da jawota jikinsa, yarinyar nan ta wahalar da shi, wato dama dik wasu take takensa tana sane da su, tsabar iyashege ne ta bar shi ya wahala wai ita tana jan aji, to wlh yau sai ya tsinke ajinan ƴar kaniya kawai, har da wani girgiza mashi weist da wani yin fari da ido, ta sanya ya faɗa cikin yanayi dan iyashege. "Wayyo my melody ka yi hakuri ka ji? Na tuba ba zan sake na". Tana maganar da ɗan ihu. Mannata da jikinsa sosai ya yi, ya ƙanƙameta ƙasa ƙasa ya ce. "Nutsu in gaya maki wata magana". Jin haka yasa ta nutsu tsit ɗin. "Meyasa kika wahalar da ni to?". Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman weist ɗinsa ta baya, ta rungumo shi da kyau, ɗayan hannun kuma ta ɗaura saman kirjinsa, cike da so da kaunarsa, cikin salo mai ɗaukar hankali ta ce. "Saboda na ja ajina mana Yah Jawad, yanzu kaga ai zaka soni sosai". Murmushi ya sakar mata tare da kai hannunsa ya riƙo hannunta dake saman kirjin nasa, ya ɗan matse hannun nata kaɗan kafin ya rankwafo kanta. "I really love Jannat, ke ɗin ta daban ce a rayuwata, please ki so ni ko da rabin wanda nake yi maki ne kin ji?". "Yah Jawad a gaskiya son da nake yi maka yafi wanda kake yi mun, kasan yadda nake sonka kuwa?". Ƙasa sosai ya yi da murya. "Da gaske?". Yadda ya yi maganar zaka gane da kyar ya iya yinta, idanunsa a kan lips ɗinta. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Tana yi tana jujjuya idanun nan nata sama. Ai kasa jurewa ya yi, yadda take magana a kusa da shi, yadda take juya waɗan nan fararen idanun nata sama tana rikita shi, yadda take motsa kyawawan lips ɗin nan nata ya ji ba zai iya gani ya kawar da kai ba, ba zai iya hakura ba, ya zo har wuya yau Shammatarta ya yi ba zato ba tsammani sai ji ta yi ya capki lips ɗinta na ƙasa ya fara bata hot kiss. Zaro idanu ta yi tamkar kwayar idanun nata zasu faɗi ƙasa, hannu yasa ya rufe mata idanun nata da shi saboda kada ma ya kallesu ya ji zai dai'na. E Jawad ya fi karfina gaskiya, my people's ina zuwa🥱😂. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2024-11-20....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 41 KINGDOM OF POWER A ɓangaren uncle Abbas kuwa, wajen King ya nufa, bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ne uncle Abbas ya buƙaci da yana son su yi magana da yayan nasa. Uncle Jahiz yana cikin parlourn shi ma a lokacin, yana kwance saman doguwar sofa, sanye yake da arabs jallabiyar shi ma, ya tasa waya a gaba suna hira da wani shararren abokinsa, shi ma shararren ɗan kwallone wanda suke bugawa a team guda, sai hira suke yi cikin kaunar juna. Saman sofa mai zaman mutun biyu King ya zauna, shi kuma uncle Abbas mai zaman mutun uku, Akka tana part ɗinta, bata jin daɗi, zazzaɓi take yi, sai da aka kira nurses daga hospital na cikin Kingdom ɗin suka zo suka hau dubata. Uncle Jahiz ne ya kira number momma. Tana ɗauka ya ce. "Hello kanwata a kawo mana cappuccino mana". Harararsa King ya yi kafin ya ce. "Ka raina mun mata ko Jahiz?". Ba tare da ya katse kiran ba ya amsa da. "A'a yaya ni fa da kanwata nake yi ba matarka ba". "Ba cinya ba kafar baya". In ji uncle Abbas da shi ma yake wurga mashi harara. Dik abin da suka faɗa momma tana jinsu, dan bai katse kiran ba. "Yaya na zo mu yi magana ne fa". Uncle Abbas ya sake faɗa. Katse kiran uncle Jahiz ya yi domin ya samu damar saurarawa ya ji me ɗan uwan nasa ya zo da shi. "Okey ina jinka". King ya faɗa a nutse. Gyara zamansa uncle Abbas ya yi tare da ɗan jingina bayansa da jikin head na sofar, sannan ya fara magana a nutse cikin girmamawa, da alama suna girmama King sosai, ko da yake babban yaya ai ba wasa ba. "Yaya dama batu ne a kan Jannat da Jawad". Tattara hankalinsa King ya yi gabaɗaya a kan kanin nasa, dan ya ji kamar ya zo mashi da sabon magana. Cigaba uncle Abbas ya yi da cewa. "Jawad ya gaya mun yana son Jannat, ko in ce maka suna son junansu, sannan ya nemi da a nema mashi aurenta". Ɗan dakatawa ya yi da maganar ganin yadda face ɗin yayan nasa ta ɗan sauya, sai ya dakata ya ji me zai ce kafin ya ɗaura. Uncle Jahiz da ya ji zancen sai ya ɗan taɓe baki yana mamakin wai su me ya haɗasu da yi wa yara auren wuri ne? Nawa Jawad yake da zai ce zai yi aure? Baga yayyunsa su Ramish da suke manya ma ko batun aure basa yi ba, sai shi yaro? Su ma ai basu gama wani girman da za'a ce su yi aure...... Hmmm uncle Jahiz dai baya son batun auren wuri, su Ramish kuma ai ba yara bane, sun kai almost 30 years a yanzu fa, amma yake ce masu yara, ko da yake shi da yake da 35 to 40 years ma ga shi bai yi aure ba, gani yake yi har yanzu bai kai ace ya yi auren ba, rayuwa cikin turawa ya lalata shi, kun san su basa auren wuri sai aukin zinace zinace suka iya, to da irin wannan zinace zinacen ba gara auren wurin sau dubu miliyan ba? Amma shi ina, gara mashi a yi rayuwa kawai, tun yana kyamar al'adunsu da ɗabi'unsu har ya zo ya saba abin ya zame mashi jiki, ya koyi wasu al'adun nasu ma abinsa. Jin King bai ce uppan bane yasa uncle Abbas cewa. "Yaya yanaga kamar face ɗinka ta sauya?". Nisawa ya yi kafin ya ce. "No ka gama maganar naka sai na yi tawa". Jinjina kai ya yi tare da cigaba da cewa. "Cikin satin nan da zamu shiga nake son a ɗaura aure, idan Sarina da Fanan sun aminta da waɗan can prince's ɗin sai a haɗa auren gabaɗaya, babu abin da za'a jira ko a tsaya ɓata lokaci a kansa, gara kawai mu aurar da su a wuce wajen". Dakatawa ya yi yana sauke numfashi a hankali hankali. "Yaya wai meyasa kuke son dole dole sai kun aurar da yaran nan da wuri ne? Nawa Jannat take da kuke batun aurenta? Wai me suka tare maku ne? Ku bar yara su girma su san ƴancinsu da kuma menene rayuwa, sannan sai ku aurar da su, yanzu sun yi yara, idan kuka aurar da su Allah cutar su za'ayi, dan kwata kwata basu san me rayuwa ba, basu gama yin wayo ba". Cewar uncle Jahiz, yana magana yana ɗaure face ɗinsa irin bada wasa yake yin nan ba. "Jahiz kai baka san me duniya take ciki bane, a rayuwar nan na yanzu aurar da yara da wuri shi ne mafi a'ala a garemu mu iyaye, dan yaran yanzu da wayonsu ake haifarsu, so ba wani wayon da zasu kara, already da shi aka haifesu, zaka ga yarinya tun tana ƴar 11 years tasan komai, kaga yara tun basu kai ko'ina ba suna soyayya, gara auren a kan zinace zinace". Shi dai uncle Jahiz he didn't not green with this season da uncle Abbas ya faɗa, sam bai yarda ba, dan haka sai ya sake cewa. "Yaya to why su Jannat? Gara ma Sarina ta ɗan fara girma amma ba sosai ba, Fanan da su Jannat fisabilillah me suka sani? Cutarsu kawai za'ayi, shi ma Jawad he's to yong, ga su Ramish da suka fara girma ba'a ce su yi aure ba sai shi? Ko da yake su Ramish ɗin ma da sauransu su ma". Ɗan girgiza kai uncle Abbas ya yi tare da buɗe baki zai yi magana King ya rigasa da cewa. "Ba su Ramish zaka ce ba, ka fara da kanka katan gwauro, gaka a zaune 35 years ne ko up to 35 ne ba mata bare yara, kake kwantance da su Ramish waɗan da bama su gama cika 30 ba! Ai dik kai ka lalatasu, halinka suka ɗauko" "Yauwa gaya mashi dai yaya". Cewar uncle Abbas. "A'a yaya, ni ai ban girma bane, sai na kai 40 or 45 haka zan duba batun auren, yanzu dai a'a, ai shiyasa nace maku su Ramish ma basu girma ba, yara ne, basu kai aure ba, dan Allah a barsu sai sun cika 40 years haka, ku bar yara su shana mana!". "To idan ka kai 40 years kuma sai ka auri yarinya mai shekaru nawa?". Cewar uncle Abbas. "Mai shekaru 25 haka is okay, 25 years tasan me take yi, ta yi wayo, ba zata sanya maka ciwon kai ba, amma ƴan under 20 nan dik wahala ne, ciwon kai zasu saka maka, ai ni nama wuce auren irinsu, Allah ma ya kikaye". Ya kai karshen maganar yana ɗaure fuska irin ba da wasa yake yi ba, shi yafi karfin ƴan under 20. Girgiza kai kawai King ya yi, dan ya lura uncle Jahiz fa ya yi nisa ba zai ji kira ba, dan bashi da ƴaƴa ne yasa yake wannan magana, amma dik uba na gari wanda yake da ƴaƴa mata to yana cikin tashin hankali da fargaba har sai ranar da ya aurar da su zai samu sukuni. "Yaya kaga rabu da Jahiz, bai san me duniya take ciki ba, mu cigaba da maganarmu". Cewar uncle Abbas. Wani irin ajiyar zuciya King ya sauke kafin ya ce. "Abbas Rizwan ne yake son Jannat ba Jawad ba, ina ga kayi kuskuren fahimta ne!". Tashin hankali. Zaro idanu uncle Abbas ya yi, a ruɗe ya furta. "A'a yaya Jawad ne yake sonta ba Rizwan ba, kai ne dai watakila baka fahimci maganar da kyau ba". Gyara zama uncle Jahiz ya yi tare da fara bin brothers ɗin nasa da kallo, dik wanda zai yi magana sai ya bisa da ido, yaga abin yana neman kawo ruɗani a tsakaninsu. "No Abbas, kai ne ka yi kuskuren fahimta, ko daren jiya mun yi maganar da Akka da kuma Jannat ɗin, Akka ce ma ta fara samuna da maganar, nima nace mata kamar Jawad yana son Jannat fa, kuma ita ma Jannat ɗin kamar Jawad take so ba Rizwan ba, shi ne Akka ta ce a'a da Rizwan suke soyayya, kawar da ruɗani yasa muka kirasu dikkansu biyu, na tambayi Rizwan shi yake son Jannat ya ce mun e, na sake tambayar Jannat da Jawad take soyayya ko da Rizwan? Sannan wanenen take so a cikinsu". Ɗan yin shiru ya yi yana sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗaura da cewa. "Buɗar bakin Jannat ta ce mun ita Rizwan take so, da shi kuma suke soyayya ba da Jawad ba, to kaga a nan kai ne kake cikin ruɗani ba mu ba"....... Tashin hankali. Abin da baku sani ba, idan baku manta ba ita Chuchu dik wanda take tare da shi a lokacin to da shi take yi, idan tana tare da Rizwan tana mantawa da Jawad, idan kuma tana tare da Jawad mantawa da Rizwan take yi, a lokacin da Akka da king suka tambayeta waye take so Rizwan ne a wajen, so dole shi zata ce, dan a lokacin ta manta da Jawad.... Akwai tashin hankali sosai da ruɗani a wannan al'amari, ta ya aka yi dik son da take yi wa Jawad zata rinƙa mantawa da shi idan ta haɗu da Rizwan? Wannan ruɗani dayawa yake wlh, ita dai Chuchu gatanan gata nan ne kawai, mutun mutumi. Shiru uncle Abbas ya yi, kansa ta ɗaure, ya shiga ruɗani dayawa, ya za'ayi ace Rizwan Jannat take so bayan ya sha ganinta a tare da Jawad ciki nishaɗi! Sannan ga shi Jawad ya tabbatar mashi da soyayya suke yi! Kai gaskiya abin ya ɗaure mashi kai sosai. Shi dai uncle Jahiz har yanzu bai yanke hukunci ba, yana ta binsu da kallo kawai, yana jiran su gama tattaunawa ya faɗi nasa albarkacin bakin. "Dan haka tun a daren jiya na bawa Rizwan aurenta, zai koma Dubai next week, so ya buƙaci da a ɗaura auren kafin ya koma, na kuma yi mashi alkawarin this coming friday za'a ɗaura ya wuce da matarsa". Cewar King, cikin nutsuwa yake yin maganar, ga izza ta jinin sarauta. "Amma yaya Jawad ya tabbatar mun da cewa soyayya yake yi da Jannat ya abin zai kasance haka kuma?". Cewar uncle Abbas. Jiki a mace ya yi maganar, muryarsa ta canza sosai, da alama ya shiga damuwa matuƙa, kuma dama dole ya damu, dan kuwa ace mace ɗaya yaya da kani suke matuƙar so abin akwai taɓa zuciya, kuma dik suna yi mata wani irin soyayya ne wanda rabuwa da ita ba kamar cutuwa zasu yi ba, barema shi Jawad ai da wuya ma ya rayu yadda ya ɗauki son duniyar nan ya ɗaura mata, wlh abin akwai taɓa zuciya sosai, ga shi ita kuma an rasa me ya shiga kanta, idan tana tare da Jawad aka ce waye take so zata ce Jawad, haka zalika in suna tare da Rizwan, abin dai akwai mugun ɗaure kai. Sosai jikin uncle Abbas ta yi la'asar, ya shiga tashin hankali da damuwa, yanzu ya zai yi da Jawad kenan? Ga shi ya hango tsantsar madarar soyayyar Chuchun a cikin kwayar idanunsa, waye za'a bawa waye za'a hana?. Muryar king ne ta katsesu da cewa. "Ni ma lokacin da Akka ta gaya mun Rizwan yana son Jannat sai da na sake tambayarta Rizwan ko Jawad? Ta ce mun Rizwan, sam a lokacin zuciyata bata yarda ta karɓi hakan ba har sai da na kira Jannat da Rizwan ɗin, sai da suka gaya mun da bakinsu sannan na gamsu, kuma a baya na sha tambayar Jawad ɗin yana son Jannat ne sai ya ce a'a kawai yana kaunarta ne a matsayin kanwa, kullum haka yake ce mun, to kaga kenan shaƙuwace ta yaya da kanwa kawai a tsakaninsu ba soyayya ba, mune muke zargin kamar soyayya ce". Ya kai karshen maganar yana dawo da kallonsa a kan uncle Jahiz da ya tsaresu da ido yana sauraron wannan ruɗanin. Uncle Abbas ya rasa bakin magana, ya rasa tacewa, tabbas in kuwa haka ne da gaske Jannat Rizwan ta ce take so, to kenan Jawad shi ne yake dakon makauniyar soyayyarta ba tare da saninta ba,? Yanzu ya zai ji idan aka ce mashi ɗan uwansa aka bawa ita? Innalilahi wa Inna ilahir rajiun!. Sallamar mommar ce ta katse masu dik tunanin da suka afka, ƙarisowa ta yi cikin parlourn kuyanga mama Haulat na biye da ita a bayanta hannunta ɗauke da katon tray mai ɗauke da luxury cups na cappuccino. Kusa da King ta zauna tana hararar uncle Jahiz da yake binta da kallon zolaya. A gabansu kuyanga mama Haulat ta zube ƙasa domin kwasar gaisuwa, da alama momma ta yarda da mama Haulat sosai gaskiya, dan bayan kuyanga Zubaida mai yin serving ɗinsu abinci babu wata kuyanga da ta taɓa shiga parlon King sai ita. Dikkansu uncle Abbas ne ya ari bakinsu ya amsa masu gaisuwar da ta ɗaga masu ɗin. Sannu da hutawa momma ta yi wa King, cike da so da kauna ya amsa mata, sannan uncle Abbas and uncle Jahiz ma suka yi mata sannu da zuwa. Miƙewa kuyanga mama Haulat ta yi ta fara kawo masu trayn cappuccinon gabansu suna ɗauka, King ta fara bawa sai uncle Abbas sannan uncle Jahiz, suna gama ɗauka momma ta miƙe tare da yi masu sallama sannan ta wuce gaba mama Haulat ta take mata baya, alkyabbar yana jan kasa fuuuuuuuuuuuuuu suka nufi waje. Uncle Abbas dai ya kasa shan cappuccinonsa, saboda damuwa da tashin hankalin da ya shiga na halin da Jawad zai shiga idan ya samu wannan bakin labari, King and Uncle Jahiz kuwa shan abinsu suka fara yi cikin nutsuwa. _____________________________🔥🤍🕊️ "Yah Jawad tunanin me kake yi ne?". Muryarta ta daki dodan kunnensa. Yar firgita ya yi tare da dawowa daga duniyar tunanin da ya afka, dama tunani ya afaka yi yana imagine ga shi ya capki lips ɗinta yana kissing, a zahiri ba da gaske bane, tana dai kwance a jikinsa tana jiran jin wasu zafafan kalaman daga bakinsa, ashe shi kuma ya afka duniyar tunanin yana shanye mata baki. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Tunanin me zan yi kuma da ya wuce tunaninki my Jannat? Kenake tunawa". Ɗan waro ido ta yi like wow ɗin nan, sannan ta ce. "To tunani na na me kake yi?". Shiru ya ɗan yi, sai yaki gaya mata cewa ya yi tunanin ga shi yana yi mata kiss ne, ya canza izuwa wani topic daban, ya ce. "Tunanin yadda zamu rayu bayan aurenmu nake yi". Ba zai iya gaya mata har yana imagine na kissing ɗinta ba, dan hakan zai janyo raini a tsakaninsu, gara ma sai sun yi auren, shiyasa dik yadda zuciyarsa take ingiza shi ya yi kissing ɗinta baya yarda ya yi, dan yana da ilimin addini na farko, yasan hakan kuskure ne, na biyu ita ɗin kanwarsa ce har yanzu, sai ranar da aka ɗaura masu aure ne zancen zai canza, shiyasa yake kame kansa, rungumar juna kuma sun saba ne tun kafin natun soyayya. "Yah Jawad ina mamaki sosai, wai yau ni ce nake soyayya da yayana da nafi kauna a duniya! Kasan daɗin da nake ji kuwa?". Kai ya girgiza mata yana ƙoƙarin yin magana kenan wayarsa ta fara ƙara. Wani irin faɗuwar gaba ya ji ta dira mashi kamar ba lafiya ba. Hasbunallahu wani'imal wakil ya furta lokacin da ya ji hakan, sannan ya zura hannu a aljihunsa ya ciro wayar. Ganin sunan my daddy wato uncle Abbas ne yake yawo a saman screen ɗin yasa ya yi saurin raba jikinsa da nata, ya ɗan yi one step sannan ya ɗauki call ɗin. Ya sha mamakin ganin kiran, saboda yanzu suka rabu babu jimawa, meyasa yake sake kiransa?. "Hello daddy". Ya faɗa a sanyaye, kirjinsa sai dukan uku uku yake yi kaman wanda ya yi wani laifin aka kama shi. "Jawad ka sameni a part ɗina nan da 20 mins". Shi ne abin da uncle Abbas ya faɗa, daga haka ya katse kiran. Dum dum ya ji kirjinsa ta yi da karfi, a hanzarce ya nufi hanyar fita, dan yadda ya ji muryan daddyn nasa sai yake ganin kamar yana cikin damuwa da tashin hankali, hakan yasa ya ce gara ya je tun yanzu ya ji menene, sai ya alaƙanta sauyin sautin muryan daddyn nasa da faɗuwar gaban da yake ji. "Yah Jawad ina zaka je?". Ta faɗa a ɗan ruɗe kuma da mamaki, dan taga irin saurin da ya kwaso. "Ina zuwa Jannat". Abin da ya faɗa kenan, daga haka ya fice da sauri. Shiru ta ɗan tsaya na ƴan mintoci kafin ta wuce ta haye saman bed ɗinta ta kwanta tana tunanin soyayyarsu da shi yadda zata kasance bayan aure....... Hmmm akwai gagarumin matsala kam, to ni dai bari na leƙa su Khadija mutanen Kaduna mu ji ya suka isa, zamu dawo daga baya mu ji kiran me uncle Abbas yake yi wa Jawad?. Sorry my people's, da babu gwara babu daɗi sai mun haɗu gb. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2024-11-21....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 _____42 SU KHADIJAH. Karfe ɗaya dai'dai na rana suka sauƙa a kawo Kaduna, Khadija ta ce Zee ta nemo masu aran waya su yi kira, su sake gwada number kawu Sadiq ko tana shiga, abinku da yarinta da shiririta, tun suna gida fa suke gwada number a kashe, amma sai suke ganin kamar idan suka zo Kd suka kira zata shiga. Da okey Zee ta amsa, Khadija ta samu waje saman irin bencin da ake ajiyewa na zaman jama'a haka, nan ta zauna tare da matso da akwatin nasu kusa da ita, Zee ta wuce zuwa neman masu aran waya. Sai kalle kalle Khadija take yi, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana cikin damuwa, da alama ma kuka take son yi, sai a yanzu tunanin basu sanar da maman Hanif ba ya faɗo mata, sai ta ji babu daɗi, dan kuwa ko ba komai maman Hanif ta yi ɗawayniya da su, ta fita zakka a cikin familyn baban nasu. Wani matashi ne ya zo ya zauna a kusa da ita yana faɗin. "Sannunki ƴan'matan". Bata kula shi ba, bama ta ɗago ta kalle shi ba, ta cigaba da tunanin da take yi abinta, dan ita yanzu duniyar nan binta da kallo kawai take yi, bata da wani sauran kataɓus. "Wani kike jira ne ko wani wajen zaki je ne?". Ya sake tambayarta kamar dole sai ta tanka shi. Shiru kamar babu ita a wajen, ko motsawa bata yi ba. "Idan akwai in da zaki je ki yi magana sai a kaiki! Ni fa mai keken napep ne". Jin haka yasa ta ɗan ɗago ta kallesa, a ɗan takaice ta ce. "Kasan unguwar Rimi?". A hanzarce ya ce mata e yasani kawai ta tashi su tafi, to dama ita already tasan sunan unguwar su Sadiq, mamanta tana yawan kama sunan unguwar, gidan ne dai tun da suka yi wayo basu taɓa zuwa ba, amma idan ba'a canza yanayin tsarin unguwar ba tabbas idan taga kofar gidan zata iya ganesa, dan tana da shekaru 6 sun je da mamanta, tasan ya kalar gate ɗin gidan yake da yanayin tsarin ginin. "To can zaka kaini bari kanwata ta zo mu tafi". Ta faɗa a takaice. Da shegen shisshiginsa yana ganin yadda take magana sai ya ce. "Amma wani abin ne yake damunki ƴan'mata? Dik da ban sanki ba ban taɓa ganinki ba sai yau, tabbas naga damuwa a saman face ɗinki, in ba damuwa ko zaki iya gaya mun kila in iya taimaka maki". Jin maganar nan tasa yasa ta ji tamkar ta fashe da ihu mai sautin gaske, ta yi ta yi kada ta dakata watakila zata ɗan samu sassauci a cikin zuciyarta, dama kamar jira take yi a ce mata Khadija fashe da kuka kawai ta fashe. Ƙarisowar Zee wajen ne yasa ta danne kukan da ya zo mata ɗin. "Aunty Khadijah ni ban samu waya ba, kowa sai ya ce mun bashi da shi, jama'a basu son bani dan basu yarda da ni ba, yanzu babu yarda sam a duniya!". Ta faɗa kamar zata yi kuka. "Me zaku yi da waya?". Cewar wannan mai napep ɗin. Wani kallon uku saura kwata Zee ta watsa mashi, kun san ita fa ba sauki, ƙaddarar da ya faru da sune yasa ta yi laushi. Haka kawai sai ta ji bata yarda da guy ɗin ba, ta ji kamar bashi da gaskiya, dan haka sai ta ɗaure fuska irin ba wasan nan tana binsa da kallon rainin wayo. "Kawunmu da muka zo wajensan ne zamu kirasa, dan mu bamu san gidan nasu ba". Khadijah ta bashi amsa. Kamar zata fashe da kuka ta yi maganar. "Ayya Allah sarki, to shikenan ku zo muje na kaiku unguwar, sai na baku wayata ku kirasa ko?". Khadijah na ƙoƙarin yin maganar Zee ta rigata da cewa. "Baza'aje ɗin ba, ka je zamu sami wani abin hawan". Cikin tsiwa ta yi maganar, Zee fa kamar mai aljanu a kai wlh, idan bata son abu fa sai a hankali. "Ke Zee baki da hankali ne wai? Ke baki ga taimaka mana zai yi ba? Ki gaya mun idan ya tafi yaushe zamu samu wani da zai san unguwar har ma ya ɗaukemu zuwa can ya kuma ara mana wayarsa mu kira kawu Sadiq?". Tun da ta fara magana yake ta aikin girgiza kai irin shine fa ɗin nan, wato Khadijah tana yabashi shi ne yake wani kaɗa kai. "Aunty Khadijah na Allah basa karewa a duniya, ɗik min lalacewan duniya ba zaki taɓa rasa na Allah ba, dan haka tabbas zamu samu waɗan da suka fishi kyan zuciya, ni wannan bai kwanta mun a rai ba sam". Oh Zee sarkin faɗa, to dai kinyi kuskure a nan, ko ya kake jin ɗan adam a zuciyarka ba'a fitowa karara a bayyana mashi, in ma sonsa kake tsananin yi ko kinsa, idan ka bayyanawa mutun tsananin sonsa da kake yi is very very hardly ya ɗaukeka da wata daraja, idan kuma kinsa kake yi nan ma ka bayyana mashi, to wlh da matuƙar wahala ya iya mantawa, zai riƙeka a zuciya ne sosai, zuciya kuma bata da ƙashi, ya kan iya yi maka wata muguntarma a sanadin haka. Sai mu kiyaye Sosai guy ɗin ya ji ɗacin maganganun Zee, har ya miƙe zai bar wajen Khadijah ta fara bashi hakuri, saboda ita ya dawo ya hakura, ya kuma ja akwatin nasu ya ce su ƙarisa wajen keken napep ɗin nasa. Haka kuwa aka yi, suka je suka shiga ciki ya ɗaukesu suka bar tashan. Abinku da basu san unguwar ba, dik ta hanyar da aka bi da su sai su kalli kamar unguwar ya nufa. Shi kuwa ya yi tafiya mai mugun nisan da a kallah ya kusa awa guda da su, yana tafiya har da ce masu ya yi unguwar a kusan karshen gari yake, Khadijah dai ta yi shiru ta kifa kai da jikin karfen napep ɗin tana tunanin duniya, ita kuwa Zee da already dama bata yarda da shi ba sai take ganin kamar ba unguwar ya nufa da su ba. Hakan yasa ta shiga damuwa take ta aikin tambayarsa wai har yanzu basu iso bane? Sai ya ce mata ai sun kusa isowa. Har Khadijah tana yi mata faɗa a kan ta barsa ya yi aikinsa mana, zata wani tasa shi a gaba tana tambayarsa, ya ji da tuki ne ko da amsa tambayoyinta? Sai ta je tasa sun faɗi ko?. Turo baki take yi ta yi shiru, hakan kuma ba shi ne zai sa anjuma kaɗan ta fada tambayarsa wai har yanzu basu iso bane?. Bawan Allahn nan da yake babu Allah a ransa sai da ya fitar da su gefen gari, sun bar cikin mutane sannan ya dakatar da tafiya, Khadijah ta afka duniyar tunani bata ji ya tsaya ba. A hanzarce ya juyo in da suke, Zee tana ƙoƙarin tambayarsa akan meyasa ya tsayar da su a wannan waje mai kama da dajin, sai dai bata kai ga buɗe baki ta yi magana ba ya yi hanzarin fito da sleeping power ya fesa masu a face ɗinsu. Da yake Khadijah kanta na kife a jikin karfen mashin ɗin sai power ya sauƙa a jikinta ta bayan wuyarta, ita kuwa Zee tuni ta yanke jiki ta sume, ta kwanta a jikin head na kujerar mashin ɗin. Jin abu ya zuba mata a bayan wuyarta ne yasa ta ɗago kai, tana ɗagowa ita ma ya watsa mata rabonta, kan ta yi wani motsi ta sume. Wani irin farinciki ne ya bayyana a saman face ɗinsa, kunna mashin ɗin ya yi ya kara kutsawa cikin dajin da kyau da su, sannan ya ciro wayarsa tare da fita daga cikin napep ɗin ya ɗan yi gaba kaɗan. Dama kuskure ne ka sauka a kawo Kaduna ka hau kowani irin mashin da ka gani, hakan babban kuskure ne sosai, domin ba kalar fuskar da babu a wajen, akwai na Allah haka zalika masu taya kidnappers aikin suna nan. PRINCESS TEEMA 🔥 A can Kano kuwa, su Khadijah suna barin gidan bai fi da awa ɗaya ba wasu irin jiga jigan motoci masu kama da jirgin sama suka keto cikin unguwar tasu, jama'ar unguwa tun suna ƙirga yawan adadin motocin har suka hakura kawai, saboda yawansu ya wuci tunani, yadda motocin nan suke tafiya kai kanka kasan ko shugaban kasan Nigeria ba za'ayi mashi irin wannan ba, a jere suke cikin nutsuwa, gabaɗaya motocin daga villa suka fito. Kai tsaye kofar gidan nasu suka nufa, a lokacin Hauwa tana shirin fita domin ta je ta canza wannan kuɗi nasu Khadija, har ta gama lissafin kasashen da zata je hutawa. Ta kammala shiri ta fito tsakar gida kenan wasu irin mahaukatan bodyguards suka danno kai cikin gidan babu ko excuse, kana ganin face ɗinsu sai ka tsorata, dan kuwa babu alamar mutunci ko imani a tattare da su, shiyasa suka shigo babu ko excuse, dan ma a san ba mutunci ne da su ba kuma ba shi suka zo yi ba. Ga su wasu katti da su, ga sawo da ƙiba, dik suna cikin black shiga, bakin kayan yasa hasken fatarsu ta ƙara bayyana sosai, gabaɗayansu turawa ne, babu bakin fata ko larabawa a cikinsu, dikkansu suna riƙe da manya manyan bindigu kamar zasu tashi gari, sai wani zaro jajeyen idanun nan nasu suke yi kamar mutun ya ruga a guje. Sun kai su 20 suka shigo cikin gidan, ta kowani lungu da tsako a cikin gidan sai da bodyguard guda ɗaya ya je ya tsaya, a guje suka kewaye ta ko'ina suna wani leke leke domin su tabbatar da ba wata motsi na cutarwa. Ji kake yi dip dip dip wasu security jami'an fararen kaya sun sake kutsowa cikin gidan su shidda. Ai a miliyan Hauwa ta juya zata gudu ta koma cikin parlour, wani security farin kaya da suka shigo daga baya ne ya tare gabanta, ya tareta, ya hanata shigewa cikin parlourn, dan an basu umarnin in sun shigo cikin gidan kada su bar ko tsinke ya motsa, komai ya tsaya a yadda yake kenan. Tuni ta hau kerman jiki, tsabar tasan bata da gaskiya har faɗi take. "Wlh ba gidana bane, mai gidan baya nan, kuma wlh matarsa ce ta kashesa, dan Allah kada ku yi mun komai, wlh bani ma aikata laifin ba, idan ma kuɗin su Khadija ne ga shi can a ɗaki ban ɗauki ko biyar daga ciki ba, dan Allah ku yi hakuri". Ko sannu babu wanda ya ce mata, kamar wasu saƙaguna haka suka tsaya irin tsayuwar jarumai suna kallonta da jajayen idanun nan nasu. Wasu dakakkun maza madaka katti ne suka sake shigowa cikin gidan suna shinfiɗa wani irin haɗaɗɗen white carpet, tun daga waje jikin motocinsu suka shinfiɗa shi har izuwa cikin gidan, har bakin kofar parlour tsawonsa ya kai. Bayan sun kammala shinfiɗawa ne suka tsaitsaya a gefe gefen carpet ɗin, suma hannunsu riƙe yake da wasu mahaukatan bindigu na ƙasashen ketare. Shiru suka tsaitsaya tamkar ba mutane ba, sai ka rantse da Allah basa numfashi, saboda irin tsayuwar da suka yi, sun ƙame waje guda. Wani irin ƙara ƙamewa gabaɗayansu suka yi a lokacin da wata kafa ta tako saman carpet ɗin ta nufo cikin gidan. Tun daga kan luxury hiking boots shoe mai bala'in kyau da tsada launin milk color dake kafarsa, tun daga kan takalmar kafar tasa ta ji tsoron ɗaga idanu ta kalli face ɗinsa, cikin nutsuwa, isa da izza yake takowa har izuwa in da take tsaye. Matashin ne da ba zai wuci 35 years ba, cikakken namiji ne da dik in da ake neman namiji to ya kai, yana sanye da white face mask a face ɗinsa, tsadadden haɗaɗɗen Jessy wato kayan ƴan kwallo ne a jikinsa, daga yanayinsa zaka fahimci wannan kuɗi sun jiƙasa over, dik da yana sanye da face mask hakan ba zai hana ka gane bashi da mutunci ba, dama tun daga kan yadda yaransa suka watso cikin gidan zaka fahimci wannan ya bawa mutunci baya, sam basu haɗa hanya ba. Ko waye shi? Ni kai'na ina son sani, dan irin wannan isa da taƙama dole mu so sanin wanene shi. Tamkar baya son motsa laɓɓansa ya furta. "Where's Khadijah?". Cikin harshen turanci ya yi maganar. Hauwa da bata jin turanci tuni ta kara tsurewa tana muzurai kamar an tare ɓera a tarko, jikinta na kerma kamar mazari. Da ido guy ɗin ya kalli wannan jami'in da ya tare gaban nata, bai furta komai ba jami'in ya wani daka mata tsawa mai sauti a in da ya maimaita tambayar da guy ɗin ya yi da farko wato ina Khadija?. Tsabar tsorata da wannan tsawa da ta yi har bata san lokacin da ta saki fitsari a wajen ba, ta tsorata sosai da jin katuwar muryar jami'in. Ita ga shi bata jin turanci bare tasan me suka faɗa, kan fanko ne, ɓata kuɗin makaranta kawai kawunta ya yi, ko kaɗan babu abin da ta sani. Jin ta yi shiru tana muzurai ne yasa ransa ya ɓaci, dan sai yaga kamar rai'nin wayo ne, bai santa ba, bai san wacece ita ba kawai ya cire hannunsa dage cikin aljihun wandonsa ya ɗauketa da wani irin gigitattacen marin da ya sanyata ganin taurari. Haba wani irin baya baya ta yi kafin ta zube ƙasa, ji ta yi duniya ya ɗauke mata cak. Dawo da kallonsa a kan securitys ɗin nasa ya yi, cikin magana ɗaya a takaice ya ce masu su shiga ko'ina a cikin gidan nan su fito mashi da Khadija. Yadda suka amsa da to haɗe da sara mashi ne yasa Hauwa dawowa cikin hanyacinta, dan kunnuwanta sun ji muryoyin maza. Zaro idanu ta yi tana kallonsu, tama kasa kuka, dama idan kun ji abin da ake yi wa kuka to bai kai abin tashin hankali bane, idan bala'i ta yi balai neman kukan ma ake yi a rasa, ita dai yau Hauwa ta ji marin namijin gaske hegiya ta nemi kuka ta rasa. Ko waye shi hegen kuma?🤔 Ko uban neman me yake yi wa Khadija? Anya ma ba shi ne uban cikin jikin nan nata ba kuwa? Da alama ya ji labarin cikin bai zube bane ya zo karasa shi kome? Dan naga basu shigo gidan da mutunci bane! Dik yadda aka yi ba mutunci ne ya kawosu ba, to koma dai me ai Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai bawa ya zalinci kansa, kila addu'ar da suke yi ne ya karɓu yasa Allah ya basu ikon guduwa Kaduna kafin hegun nan su iso, Allah sarki bayin Allan. A guje gabaɗaya securitys ɗin suka danna cikin parlourn, ta ko'ina suka fara nemanta, shi kuwa yana tsaye kekam kamar wani gunki. After some minutes suka dawo tare da isar mashi da saƙon babu Khadija a cikin gidan. Cikin harshen turancin dai ya yi masu umarnin da su ɗauko mashi Hauwa su wurgata a bayan boot na motarsa su wuce da ita, daga haka ya juya ya nufi waje........... Koma wanene wannan ya cika shafaffe da mai, wato kasar ce ma ba zai taka ba sai an shinfiɗa mashi carpet ya bi ta kanta, hmmmm akwai hegu fa a RAWANIN ZALINCI ba kaɗan ba yaseen, kowa da kalar iskancinsa da iyashegensa, shi kuma ga nasa, to mu ai munga Black Tiger ma a iya mulki, shi babu wanda ya taɓa ganin face ɗinsa ma amma bala'in tsoronsa ake ji tamkar mutuwa, shi da tsabar bala'insa da ya azawa ƴan birninsa ma, gara mutuwa a kan jin komai ƙanƙantar motsinsa ko kuma maganarsa a kansu, to dan haka mu munga Black Tiger ma, ba wani sauran abin da za'a nuna mana kuma, dik wanda zai zo da nasa iskancin dik ya biyo bayan Black Tiger, ko kafarsa ma baku kama ba!!. Da hannu ɗaya ɗaya daga cikin securitys ɗin ya zo ya ɗaga Hauwa sama sai cikin boot ya watsa hegiya, cikin takun isa ya juya ya bar gidan, a guje gabaɗaya securitys ɗin suma suka bar gidan, suka shiga motocinsu suka tafi. Sun bar ko'ina na gidan a wangale basu rufe ba, ni kam nace Allah yasa kada ɓarayi su shigo su ɗauke jakar kuɗin Khadija, wayyo wannan kuɗi yana ganin rayuwa, ko me yasa suke neman Khadijan? Allah yasa su yi ta jibgar Hauwa har sai ta koyi turanci a ranar ta gaya masu ina su Khadijah suka je.....🤸😂 Kai tsaye hanyar Kaduna motocin suka nufa domin komawa villah Abuja kenan. Allah da ikonsa kuwa, suna shiga Kaduna a tsakiyar gari suka samu saɓani da motar da ta ɗauki su Khadija dake sume kamar gawarwaki, har saura kaɗan ma su ɗan yi karo motar su Khadija ɗin ta kauce ta basu hanya, a takaice dai an sace su Khadijah sun kuma yi saɓani da motocin da suka ɗauko hauwa dan nemansu. Ko su waye suka sace su Khadijah? Ina kuma zasu kai su? Su kuma waɗan can ina zasu kai Hauwa?! Hmmm akwai dai cakwakiya, Allah sarki su Khadija bayin Allan, mai keken napep ɗin nan ne ya cucesu, ashe mugu ne mai safaran mutane, dama Zee bata yarda da shi ba Khadijah taki jin maganarta. To yanzu dai ga shi ya cucesu, Allah yasa ma ba sayar da su ya yi ba. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ JIMETA A hankali ta waro idanunta da suke cike da barci, bata taɓa yin barci mai daɗi irin wannan ba a gabaɗaya tsawon rayuwarta, kullum tana tsaka da barci Nenne take tashinta, ta katse mata farincikinta, sai ga shi yau ta yi barci cike da annashuwa kuma mai tsawo, ya lulluɓeta da bargo mai ɗumin gaske, ta ji matuƙar daɗin hakan. Barcin ma bai isheta ba, kawai ta farka ne saboda rashin sabo, bata saba rana ta tsala tana barci ba, shiyasa ta gaza iya cigaba da yi ta farka. Saman ɗakin nasu ta fara bi da kallo, kamar wadda aka tsikara, ko me ta tuna ta yi hanzarin miƙewa zaune a dubu tana kai kallonta wajen da ya kwanta. Wayam babu shi babu labarinsa a ɗakin, tuni ya fice abinsa, dan ya ƙasa yin barci bawan Allah, ya zuba mata idanu yana ta kallonta tana barci, hakan yasa shi ya kasa rintsawa, da ya gaji da kallon nata sai ya miƙe ya fita abinsa. Wani irin ajiyar zuciya na musamman ta sauke ganin baya nan, hannu ta ɗan ɗaura a saman kirjinta tana sauke numfashi a hankali hankali. Ta ji daɗi da baya nan, a hankali ta sauƙo ƙasa, jikinta dik a mace ta nufo waje. Ga mamakinta sai taga babu kowa a gidan nasu. To ina bappa da Mahreen? Ta jefawa kanta tambaya. Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta wuce ta nufi ɗakin bappa. Wayam babu kowa, dawowa cikin ɗakinsu ta yi, bargon nasu ta fara naɗewa kafin ta hau gyaran ɗakin. Ta ɗauko tsintsiya ta share fes, ta fito ta share waje, abinku da jiki ya saba da aiki, ta gyara ɗakin bappa dana Nenne tsab, sannan ta fito ta gyara ɗakinsu wanda ya zama mallakin Mahreen ita kaɗai a yanzu. Sai da ta gama da sharan gidan tsab sannan ta shiga kitchen, wuta ta hura ta ɗaura ruwa a katon tukunya, ta haɗa kwanikan wanke wanke ta kaisu wajen wankewa. A hanzarce take yin aikin nata, da yake ta saba sai yazamana cikin ƙanƙanin lokaci ta gama wanke wanke, ta share wajen ta gyara bayan ta kwashi kwanikan ta kai cikin kitchen. Sannan ta zo ta ɗebi ruwan zafin dai'dai wanda zai isheta wanka, sauran kuma ta yi talgen garin masara zata tuƙa masu tuwo. Surka ruwan ta yi tare da ɗauka ta wuce banɗaki dan ta yi wanka. Kafin ta fito talgenta ya nuna, dan haka sai ta zura hijabinta kawai ba tare da ta sanya kaya ba ta zo ta tuƙa tuwon. Bayan ta tuƙa ta ɗan sanya mashi ruwa kaɗan ta bar shi ya ɗan silala na ƴan mintuna, sannan ta fito ta shiga ɗakinsu domin ta shirya. Ɗaya daga cikin sabbin dogayen rigunar da bappa ya saya masu ta sanya jan, ta ɗan yi kwalliyarta sama sama sannan ta fito ta shiga ɗakin bappa, ta yi kyau abinta, sai dai a jikinta tana jin zazzaɓi da ciwon kai, ba komai bane ya ja mata hakan kuma face wannan ruwan saman da ya yi masu dukan tsiya. Naman zabo da man shanu ta ɗauko a ɗakin bappa ta wuce kitchen da shi. Tukunyar miya ta ɗauko ta fara haɗa kayan miya a ciki, sannan ta sauke tuwon ta ɗaura miyar. Ta sake tuƙa tuwon ta kawo kwanika ta kwashewa kowa nasa, ta ɗebo daddawa ta daka ta zuba a miya, sannan ta saka maggi. Ta miƙe ta ɗauki tuwon kowa ta fara kai mashi ɗaki kafin miya ya nuna ta raba ta kaiwa kowa. Ko da ta zo ɗaukan na Jaish sai ta rasa a wani ɗaki zata kai mashi, wani zuciya ya ce ta kai mashi ɗakinsu wani kuma ya ce mata ta kai ɗakin bappa. Daga karshe dai ta ce bari ta kai mashi ɗakin nasu tun da jiya a nan ya kwana, kila ya dawo ɗakin kenan. Can ta kai mashi ta dawo ta zauna a kusa da murhun tana aikin hura wuta har tsawon awa ɗaya miyan na tafasa, ruwa ya kare ta kara wani, sannan ta kaɗa garin kuka ta sauke, ta kwaso kwanikan miya ta fara zubawa kowa nasa, naman zabo da miyar kuka sai a girkin Mahnoor manya, ba'a iya miyar kuka kawai ba, ita idan bappa ya yanka nama a koma wani irin girki idan zata yi banka shi ciki take yi abinta, ba dai nama nama bane? Ai shikenan kuma. Ɗaki ta kaiwa kowa miyarsa kusa da abincinsa, sannan ta zo ta ɗauki wani karon kula da ta kwashe ragowar abincin a ciki ta fito da shi waje, ta zuba miya a kular miyan, daga kasar Niger bappa ya sawo masu wannan kula, suna ji da shi sosai. Ta ɗauki kwanikan ƴan madaidita guda uku ta haɗa, ta haɗo da maran kwasan tuwon dik ta ajiye a sakar gidan, alwala ta je ta ɗauro dan azahar ta yi. Sai da ta gabatar da sallarta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sannan ta fito ta ɗauki wannan kular abinci da kwanikan da ta ajiye ta nufi waje, da nufin zata kaiwa su bappa abinci a gonarsa. Su dai kauye sun huta, babu ruwansu da garƙame gida da kwaɗo or key, haka zasu yi ficewarsu su bar ko'ina a wangale abinsu. Dab zata fita waje ita kuma Jumma tana shigowa, saura kaɗan su yi karo Jumma ta ja birki. "Kai amarya da fita waje? Ina zaki je to?". Jumma ta jefa mata tambaya cike da mamaki tana taɓe baki. "Su bappa zan kaiwa abinci". Ta bata amsa a sanyaye. "Waye ya ce maki amarya tana fita? Ki kawo in kai masu". Cike da mamaki ta yi maganar, dan dai ita tasan amarya sai ta yi wata bakwai a al'adarsu kafin ta fara ɗan kaiwa iyayenta kawai ziyara, sai ta yi shekara guda zata fara zuwa gidan sauran ƴan uwa kuma, amma ita kwana uku kenan yau da auren nata ta wani ce zata fita, abin dole ya bawa Jumma mamaki, dan bata saba gani ba. "A'a Jumma ki bari zan kai masu da kai'na". Ta faɗa a ɗan takaice. Ɗan zaro idanu Jumma ta yi kafin ta ce. "Mahnoor ko dai baki son na je na kalle maki angonki ne? Baki son na kai mashi abinci ko?". Dan turɓune fuska kaɗan ta yi. "Ni Jumma baki ji na faɗi hakan ba, kada ki zo ki mun sharri, kuma ni ce maki aka yi shi zan kaiwa abinci ne ma........?". Ai bata gama rufe baki ba Jumma ta hau kirga kwanikan da suke hannunta. Ganin guda uku ne yasa ta ce. "Mahnoor, yanzu idan zaki ɓoyewa kowa komai a garin nan har da ni zaki ɓoyewa?" "Me na ɓoye maki ɗin?". "Ba ga shi kwanika uku kika ɗauka ba, bappa ɗaya, Mahreen ɗaya sai shi kuma ɗaya, amma kike ɓoye mun ko?". "Ni ba abin da na ɓoye maki Jumma, ɗayan kwanon nawa ne ba na Hamma ba, ai nima ban ci abinci ba". Ta faɗa tana ƙara turɓune fuska. Dariya sosai Jumma ta kwashe da shi. "Amma Mahnoor Allah ya nuna mun ranar da zaki canza hali ki dai'na wannan kunya taki maras amfani, gara maki ma ki saki jiki ki ware ki kula da mijinki, idan ba haka ba kina ji kina gani zaki rasa shi!". Wani irin zaro idanu ta yi. "Zan rasa shi kuma Jumma? To meyasa zan rasashi? A kan wani dalili?". Dariya ne mai ɗan sauti ya sake kubcewa Jumman, kun san ita fa ta ɗan waye, dan haka bata kunbiya kunbiya, komai gar take yinsa a faranti, amma tana ɗan sakayawa idan a gaban Inna Rabi ce, sai kun ganta a cikin kawayenta ne zaku gane Jumma ƴar air ce. "Su Mahnoor kenan, wato jin zaki rasa shi har kin tsorata ko? Eyes soyayya ruwan zuma, to dai shikenan ni dai na gaya maki in dai baki kula da shi tsab zaki rasa shi, dan kuwa ƴan'matan kauyen nan dik yanzu sun fara yarda shi ba aljani bane kuma ba maye bane, shi ɗan adam ne kamar mu, dan haka yanzu har gona suke binsa su je suna leƙansa suna jin daɗi, ni kai'na a da na yi tashen zuwa kallon kyansa, amma yanzu da ya zama mijinki gaskiya na dai'na, da ina fatan samunsa a matsayin miji, amma yanzu gaskiya na daina, kuma bana fatan na rinka haɗuwa da shi ma, dan haka idan kin saki jiki kin kula da shi kina iya cin riba, idan kuma kinki kula da shi to wlh zaki rasa shi, dan dai kinsan tu Fatu kam ba kanwar lasa bace, suna ji da kansu sun waye a birni, kina ganin yadda nima da nake zuwa birnin suke yiwa kallon ƙasƙanci da rai'nin wayo, to wlh tun wuri gara ki riƙe mijinki hannu bibbiyu". Ta kai karshen maganar tana jan numfashi. Kamar zata yi kuka ta ce. "To yanzu ni Jumma ya zan yi?". Kamar zata yi mata dariya sai kuma ta fasa, yadda ta marairace murya sai abin ya so bata dariya. "Sai kin gaya mun da gaske kina sonshi ne ko bako son shi? Idan kika gaya mun ni kuma zan gaya maki yadda zaki kula da shi sosai ta yadda ba zai taɓa kula kowace mace a garin nan ba, dik da nasan ma da wuya hakan ta faru, saboda yanayinsa dama baya kula kowa, amma fa ki sani zuciya bata da ƙashi, yana iya canzawa bana yi maki fatan hakan". Narai narai ta yi da ido kamar zata sa kuka. "Jumma ni ban sani ba, abin da nasani kawai shi ne ina son Hamma Faisal, shi kuma Hamma ina jin dai kamar bana son ya tafi, bana son ya rabu damu, kuma yana bani tausayi haka kawai". Sosai Jumma ta fahimci akwai soyayyar Faisal sosai a cikin zuciyarta, amma da alama soyayyar Jaish da yake samun gurbi a zuciyar tata a yanzu zai iya tunkuɗe soyayyar Faisal ɗin. Ita Jumma tana sonta a tare da Jaish ɗin ne, ba dan komai take sonta a tare da shi ba kuma face tana zargin Jaish ɗan birni ne, kuma tsayayen namiji ne mai karfi, tana fatan ya cetota daga ukuban da Nenne take gana mata, dan har ga Allah Jumma tana jin ciwon cutar da ita da Nenne take yi, sau da dama tana yi mata kuka, shiyasa ta kafe take son yi mata wayo ta sanyata yin wasu abubuwan da zai sanya soyayyar Jaish ɗin zai shiga ranta ba tare da ta sani ba, dan a ganinta ko ba jima ko ba daɗe Jaish zai koma in da ya fito, sai take tunanin idan zai koma tabbas in suna son juna zai tafi da Mahnoor ɗin, daga nan kuma ta huta da bala'in Nenne, shiyasa take son koyawa Mahnoor ɗin yadda zata sanya shi kansa Jaish ɗin in baya sonta ya fara dan dolensa, Jumma akwai ƙoƙari, lallai kin ɗauko aiki kuwa, baiwar Allah bata son ganin Mahnoor a cikin damuwa. "Mahnoor Allah ina gaya maki wannan Hamman naki ko in ce mijin naki sau miliyan yafi Hamma Faisal, dan haka ki manta da shi ki rungumi mijinki, kuma ina gaya maki ki dai'na tunanin Hamma Faisal, dan ke ɗin yanzu matar aure ce, idan kuma kina son shiga cikin tsinuwar Mala'iku kuma tom shikenan ki cigaba da zancen Hamma Faisal". Ta kai karshen maganar tana ɗaure fuska sosai, irin Mahnoor ta ɗauki zancenta serious. "In Sha Allah daga yau na dai'na zancen Hamma Faisal, kuma na dai'na tunaninsa, ki tayani da addu'ar jure hakan kin ji?". Murya a marairaice ta yi maganar, gwanin ban tausayi!. "In Sha Allah zan tayaki da addu'a, da izinin Allah daga yanzu da muke tsayen nan ma alfarman Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama kin dai'na tunaninsa kenan". Da Allah yasa ta amsa mata, sannan ta ce. "To Jumma ki gaya mun ta yadda zan yi da Hamma ɗin". Hannu ta kai ta karɓa mata kwanikan dake hannunta tare da cewa. "Muje in ɗan rakaki kaɗan sai in yi maki hiran a hanya, amma dai banso ace kin fita a yanzu ba, mutane zasu yi ta surutu idan suka ganki, sai dai ni a wajena ba komai bane tun da wajen mijinki zaki je kai mashi abinci, kuma yanzu zaki yi yaki ne a kansa". "Yaki kuma Jumma?". Ta faɗa tana miƙa mata kwanikan. Karɓa ta yi suka jera a tare tana faɗin. "E yaki mana, ai yanzu dole ki yi yaki a kansa dan kada a kwace maki shi, kuma kema dan kin san ba zaki taɓa samun irinsa ba". Jinjina kai ta yi suna mai cigaba da tafiya. Wasu irin shawarwari masu kyau da amfani Jumma ta rinƙa bata irin na ƴan birni ƴan gayu. Ƙawa ta gari kenan, su yayin cin amanar juna bai shigo garesu ba tukun nan. Sai da suka kusa isa gonar ne ta miƙa mata kwanikan tare da faɗin. "Dan Allah Mahnoor ki daure ki yi amfani da shawarwarin nan da na baki, sannan ki kula sosai kin ji?". Da to ta amsa mata tare da karɓar kwanikan tana zuba mata godiya, ta wuce izuwa gonar ita kuma Jumma ta juyo izuwa gida. Tun daga nesa Mahreen ta hangota, da gudu ta taso ta nufota dan ta karɓa mata kwanikan. Da farko bappa ya ce ba zasu fita kiwo ba yau, sai bayan kwanaki, sai yaga dabobin suna jin yunwa, sun yi yawan da ba'a isa a ciyar da su a gida ba, dole a fita neman masu abinci, hakan yasa suka fita. Bappa baya wajen, daga Mahreen sai Jaish ɗin ne suke zaune a wajen zaman nasu, shi bappa ya fita da dabbobin dan su ɗan yi kewaye su samu wadatatcen abinci. Karɓa mata kwanikan Mahreen ta zo ta yi tana bata labarin Hamma ya ciro mata gwaiva da mangoro ta sha, kuma ya ajiye mata nata ita ma, Mahreen sarkin labari, wato faɗi ba'a tambayeka ba kenan. Da to kawai Mahnoor ta bita sa shi har suka ƙarisa wajen da yake. A saman tabarman nasu ta ajiye abincin tare da tsugunnawa da kyau ta ce. "Hamma ina wuni". Yana kallon face ɗinta ya amsa da. "Lafiya lou Alhdulillah". Wani ajiyar zuciya ta sauke wanda yasa shi cigaba da kallonta, dama zai kawar da kallon nasa ne, jin wannan ajiyar zuciya da ya sauke yasa ya fasa kawarwan. "Lafiya?". Ya tamnayeta. "Babu komai". Ta faɗa cike da fargabar abin da zata aikata wanda Jumma ta bata shawara a yanzu, shi ne ya tsaya mata a ranta sosai. "Adda Mahnoor me kika dafa mana?". Cewar Mahreen. Shiru ta yi bata amsa mata ba, dan ita ba wani juriyar biye surutun Mahreen ta ke da shi ba. "Me kika dafa mana?". Jaish ya jefa mata tambayar idanunsa a kanta, ta wani sunkuyar da kai kamar tana gaban malaminta zata kai haddan Alqur'ani mai girma. Jin shi ya yi tambayar yasa ta yi saurin ɗago kai ta kallesa, wato ganin taki amsawa yar rigimarsa Mahreen yasa shi ya tambaya ko? Wato yana son sanyata bawa Mahreen amsa ne. A ranta ta ce dama haka yake? Dama dan baya magana ne yasa bai cika shigarwa Mahreen surutunta na banzan nan ba! Wato shi ma baya iya jure maganar kurma kurman nan bawan Allah, shiyasa baya biyewa Mahreen sosai, yanzu kuma yana da bakin magana, Allah sarki. "Ba zaki gaya mana me kika dafa bane?". Ya sake jefa mata tambayar. Ɗan tsorata ta yi na jin sake tambayar tasa da ya yi, sai kuma a lokacin ta farga ashe ta tsaresa da idanu ta afka duniyar tunani bata sani ba, a hanzarce ta zare idanunta daga cikin nasa tare da yin ƙasa da kai. "Tuwo da miyar kuka na yi". Ta bashi amsa ƙasa ƙasa. Mahreen ce ta ce. "To ki zuba mana ni da Hamma mu ci a tare, yunwa nake ji". Wani irin faɗuwar gaba ta ji lokacin da ta ji Mahreen ta faɗi hakan, domin kuwa cin abinci a tare da shi yana ɗaya daga cikin shawarin da Jumma bata, ta ce mata ta rinƙa ci a tare da shi, cin abincinsu kwano guda zai sa su kara jin kaunar juna sosai da sosai, yana kara dankon soyayya......... Ni kuwa nace ashe Jumma ma hegiya ce tasan kauna, a lallai zuwanta birni ya yi amfani........😂 "A'a Mahreen zan saka maki naki ke kaɗai dai ni kuma zanci a tare da Hamma". Ta yi maganar tana kara yin ƙasa da kai sosai, sam bata fatan yau su sake haɗa ido, saboda kunyarsa kamar zata nutse cikin ƙasa. Turo baki hajiya Mahreen tamu ta zamani ta yi kafin ta ce. "Wato dan mijinki ne shi ne zaki ce ke zaki ci tare da shi ko? Tom shikenan ni ma nawa mijin zai zo, kuma kema ba zaki ci a tare da mijina ba". Aka ce kuruci dangin hauka, to idan ba hauka ba ina ruwan Mahnoor da wani cin abinci da mijinki, ita fa bama ta san me ma'anar mijin ba, ita dai kawai ace mata ana biki a saki kiɗa ta ci uwar sabada da rawa ta sani, shikenan abin da ta ɗauki aure kenan, hmmmm kila da ta san menene auren bazata ce mijinta yana nan zuwa ba, ko daga ina zai zo? Ni dai da bappa zai bi shawarata da ya haɗa ƴar ƙaniya aure da Hamma Faisal, su je can su kashe kansu in sun gadama, idan ya bata baby ai zata nutsu ne, haba yarinyar ce sai iya tsaro maganar da ita kanta bata san ma ina ya dosa ba, kawai a kwasosa a sharɓa. Tabbas Jaish ya yi mamakin jin abin da ta faɗa, saboda yasan halinta da shegen kunya kamar dai shi ɗin, dik da baya a cikin hayyacinsa kaifin ƙwaƙwalwarsa tana nan, hakan yasa ya fahimci wannan magana da ta yi tabbas watace ta koya mata, dan ita bata da kwarin gwiwar cewa zata ci abinci a tare da shi. Taki ɗago kai tasa hannu ta buɗe kular, ta zubawa Mahreen nata daban ta zuba masu nasu su biyu, ta matso mashi da shi gabansa, ta miƙawa Mahreen kuma nata, ta rufe sauran na bappa ne, kuma baya nan, dan haka sai ta rufe mashi ta matsar gefe guda. Sai kuma me? Ai kasa motsawa daga in da take ta yi bare ma ta matso su ci abincin a tare, shi kuwa ya zuba ido yana son ganin zata iya hakan ne ko dai da gaske wata ce ta tsara mata maganar ba daga bakinta ya fito ba. Mahreen kam tuni ta ja abincinta ta fara kaiwa baki, dama yunwa take ji, dan haka hannu baka hannu kwarya ta fara yi. Shiru shiru har almost 10 mins tana tsugunne a wajen bata motsa ba, shi ma kuma bai motsa ba, bai fara cin abincin ba, yana ta kallonta kawai, ga Mahreen har ta kusa cinyewa, sun yi sa'a Mahreen idan tana cin abinci bata kula kowane, da sun sha mamakin abin da zata yi masu, ina ga da sai ta ciyar da su a baki ma, sa'ansu dai ba ruwanta da kowa idan ga abinci a waje, hankalinta gushewa yake yi nake gaya maku, bare ma idan abincin ya ji man shanu, habawa, girkin Adda Mahnoor ba wasa ba jama'a, shiyasa Jaish yake iya cin abincin nasu, dan fa Mahnoor ta kware a girki, so Mahreen tana tafiya dubiyar santi ne idan tana ci, kai har wani lumshe idanu fa take yi abinta.......😂 Ganin kai ba zata iya cin abincin a tare da shi bane yasa ta yunkura zata miƙe ta gudu ta bar wajen. Cap ya kai hannu ya capko nata hannun, hakan kuma ya yi dai'dai da ƴar karar da ta saki sakamakon yunkurawa da gudu da ta yi yasa ta fama ciwon da ta ji shekaran jiya da kwalba. Jini wajen ya fara yi. Ganin jinin yasa ya miƙe tsaye daga zaunen da yake, ya saki hannun nata tare da riƙo shoulder ɗinta. A saman tabarman ya zaunar da ita, sai ya ɗan tsugunna a gabanta wajen kafafun nata. Slippers ɗin kafarta ya cire, ta taka kan yatsun nata ne yasa ciwon ya buɗe, dama ya ɗan haɗe, ya buɗe kuma ai kunga dole jini ya zuba. "Da kika tashi zaki gudu ina zaki je?". Ya jefa mata tambayar yana ɗauko ruwa a galon wanda bappa yake ajiyewa a wajen dan shan su. Tana ciza laɓɓanta saboda zafi ta ce. "Babu". Idanunta sun cika da kwallah. Bai sake tanka mata ba ya wanke mata kafar tas, sanan ya koma wajen zamansa ya zauna, ya janyo abincin ya fara ci. Shiru ta ɗan yi tana tunanin meyakamata ta yi? Anya zata iya bin shawarin Jumma kuwa?. "Juyo ki sa hannu muci". Muryarsa ta katse mata tunanin da take yi. A miliyan ta zaro idanunta waje, ko me ta tuna kuma sai ta ɗan saisaita nutsuwarta. A hankali ta juyo kanta a kasa, tamkar kasa ta shage ta shige ciki haka take ji a lokacin da ta kai hannunta cikin kwanon. Da kyar ta iya fara cin abincin, a lokacin ita kuma Mahreen ta gama cin nata ta miƙe tsaye, tana wani gyatsa ta nufi rafi dan ta wanke kwanon nata ta sha ruwa mai sanyi, bata son shan wanda bappa yake ajiye masu. Shi kansa Jaish ɗin kunyar cin abinci a tare da ita yake yi, amma haka kawai ya ji yana sha'awar su ci taren, ba komai ne yasa hakan ba kuma face nunawa da ta yi tana son ci a tare da shi, yana tausayinta matuƙa shiyasa yake son abin da take so, dan ta yi farinciki yasa ya danne kunyar tasa suka fara cin abincin a tare. Sun yi nisa cikin ci babu wanda ya ce da wani uppan, babu kuma wanda ya iya ɗago idanu ya kalli ɗan uwansa, haka kaman wasu kurame kuma makafi suke cin abincin, ba zato ba tsammani kwatsam sukaga bappa yana tunkaro in da suke. Ai a fujaje har suna rige rigen cire hannun daga cikin kwanon, abin nasu ma gwanin ban dariya, dik suna tsananin kunyar bappan ne. Da sauri Jaish ya miƙe ya bar wajen, ya bi ta bayan itacen da suke karkashin nasa. Sarai bappan ya gansu, tun daga nesa ya hangosu, su kuma basu gansa ba sai da ya iso kusa, amma sai ya yi kamar bai gani ba, da ya ƙariso wajen ma har da tambayarta ina hammansu ya yi? Irin shi bai gansun nan ba. Kanta a ƙasa ta ce ya tafi yanzun nan, kamar bappan zai ce mata to ta ƙarisar da cin abincin mana, sai kuma ya fasa ya ce ta zuba mashi nasa. Bayason tasan ya gansu ne. A hanzarce ta zuba mashi ta miƙa mashi. "To ku koma gida kinga ke Mahnoor bai kamata ma ki fito ba, ban ma san me ya kawoki ba! Ki tashi ku koma ke da Mahreen, ita ta shirya ta tafi islamiyya idan lokacin ya yi, ke kuma ki yi zamanki a gida ko nan da kofar gida kada ki sake takawa". Cewar bappa da ya wanke hannu zai fara cin abincinsa kenan. Kai a ƙasa ta amsa da to, sannan ta miƙe tana ɗan ɗingisa kafa ta nufi wajen rafi. Nan ta isko Mahreen tana aikin shirirta, wato wasa da ruwa, kiranta ta yi a kan ta zo su tafi. Da sauri ta fito suka nufi hanyar gida Mahnoor ɗin tana gaya mata bappa ya ce kada ta je islamiya yau. Suna tafiya suna hira gwanin birgewa. Abin mamaki baya karewa, suna isa gida suka isko Nenne ta dawo, Arɗo ne ya ce ta wuce ta koma gidanta, kuma ita ma izuwa yanzu ta yarda Jaish mutun ne ba aljani ba tun da aka aura mashi Mahnoor bai yi mata komai ba, sai dai ni princess Teema ban yarda da dawowan nan nata ba, ban yarda ta tuba ba, munahika da walaƙin goro a miya, sun kullah wani abin ne idan aka bibiya. Ga mamakinsu kuma shi ne yadda Nenne bata kulasu ba, bata ce masu ko sannu ba, suka zauna a tsakar gida suka sha hiransu har la'asar, sannan suka ɗaura ruwan wanka a wuta, Mahreen ta fara yin wanka ta je ta yi shirin tafiya islamiyya, ita kuma Mahnoor sai ta sake ɗaura wani ruwan bayan ta juyewa Mahreen ɗin. Nenne kuma ta fito ta shiga maƙota, dama shegen kafar gantali gareta, bata son zama waje guda. Sallah Mahreen ta yi lokacin da ta gama shirin nata, sannan ta fito riƙe da Alqur'aninta hizbu 10, a lokacin Mahnoor ta fito daga wanka ta zauna saman dutse zata yi alwala. "Adda Mahnoor na tafi islamiyya". Cewar Mahreen. "Tom sai kin dawo". Ta bata amsa tana fara alwalar. Da to ta amsa mata sannan ta wuce. Ita kuma ta ɗauro alwalar sai ta shiga kitchen, ta ɗaura tukunya a kan wuta tasa ruwa fin rabi, a cewarta ta ɗaurawa Jaish da bappa ruwan wanka idan suka dawo, sannan ta wuce ta nufi ɗakinta dan ta shirya ta yi sallah. Tana shiga kai tsaye wajen kwallar kayanta ta nufa, hijabin jikinta ta fara cirewa ta ajiye a gefe, daga ita sai ɗaurin kirji, ta ciro ɗayan dogon rigarta wannan yellown kenan, ta ɗauko ɗan kwandon kayan kwalliyarta da zata ɗan yi, ta ɗauki pant haɗe da wani hijabin, ta dai haɗa dik abin da zata buƙata, tana juyowa da nufin ta je bakin mattress ɗinsu ta zauna ta yi kwalliya ta shirya kenan suka yi ido huɗu da shi, yana kwance a saman mattress ɗin yana kallonta dik abin da take yi, tun lokacin da bappa ya zo gona ya samesu suna cin abinci da ya bar wajen gida ya dawo, shi ne ma yasa kuka ga Nenne bata kulasu ba, dan tasan yana cikin ɗakin yana kwance, in ta yi mata wani abin zai ji, kuma tsoronsa take ji sosai, ita kuma Mahnoor da ta shigo sam bata lura da shi a ɗakin ba. Saura kaɗan ta saki fitsari a wando saboda tsorata da ta yi, ga shi irin yana yin kallon da yake yi mata na daban ne, irin like wow ɗin nan, bai taɓa ganinta babu hijabi ba sai yau, da tasan yana cikin ɗakin ko shigowa ma ba zata yi ba bare har a kai ga cire kaya zata canza ya kalle mata jiki, ita da ko Mahreen bata yarda ta kalle mata jiki ba, ɓoye kayanta take yi. Ƙasa motsawa daga in da take ta yi, dan kuwa ta rasa ya zata yi, ba zata iya fita waje babu hijabi ba, dan bata san wanenen zai iya shigowa gidan unexpect ba, da ta fita waje a haka gara mata shi ya kalleta ɗin tun da mijinta ne. Kunya kamar ta shige cikin ƙasa, ta kuma kasa iya warware kayan dake hannun nata ta sanya ta rufe jikin nata, ta dai yi ƙasa da kai kamar wadda aka sankarar a wajen. Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa zaune yana cigaba da kallonta, ba komai ya ja hankalinsa har yake binta da kallo haka ba face gurun wuyarta, tsoka ne cike a wuyar nata gwanin birgewa, har wani irin guru guru mai matukar ɗaukar ya yi, ba ƙaramin kyau ya kara mata ba, ga fatarta har wani yellow yellow ya yi. A ransa ya ce ashe ta.......... P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2024-11-22...✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 ________43 Yaseen keyboard ɗina ta haukace 💔😥 sai na yi rubutu na tsab babu typing errors, ina bada space yake canza mun abin da na rubuta, idan ban lura ba haka zan wuce na barsa, sai na rubuta where's tsabar iskanci ina bada space sai ya koma mun why's 🤔 ni sai na danna abu ma yaki dannuwa ta daɗi, na rasa me yake so keyboard ɗin nan, na yi refreshing ɗinsa ma dik yaki komawa dai'dai, ina ga shima hutu yakeso, dan ya rubutu gaskiya wlh, mun wahala! To dai idan kuka ga typing errors haka zaku karanta abinku yauwa. Isn't my fault 😥💔 A ransa ya ce ashe ta tana da cika masha Allah, idan ka ganta a cikin hijabi ne baka gane mata, ashe dai ƴat ɓul ɓul ce. Shi ya manta ma da wai kunyarsa take ji, ya wani tsareta da ido, bai ankaraba sai ganin hawaye ya yi ya wanke mata fuska yana kuma gudun ƴar tsere daga idanunta zuwa saman kumatunta. Ɗan waro idanu waje ya yi haɗe da mamakin meya sanyata kuka kuma? Baiwar Allah ta ƙasa motsawa daga wajen kuma tana son sanya kayanta, shi ne yasa ta fara hawaye. Shi kam da ta burgesa ai kunga har da wani tashi zaune dan ya kare mata kallo da kyau kamar ba shi ne yanzu ya gudunwa bappa saboda kunya ba. _________________________________🕊️🌹 "Noor". Ya ambaci sunanta a hankali. Da na'am ta amsa cikin kuka, taki ɗago kai kuma. Ya so ta ɗago kai ta kallesa ne sai ya yi mata alama da hannu a kan ta zo, amma sai taki ɗago kan nata ta amsa kawai. "Zo". Ya sake faɗa har lokacin kallonsa a kanta. Kasa motsawa ta yi, dan ji take yi kamar zigidir take babu kayan a jikinta, dan haka sai ta gaza motsawa daga wajen. Ganin bafa zata iya zuwa ba ne yasa ya miƙe ya nufeta. Har ya ƙariso gabanta bata motsa ba, yana zuwa ya riƙo hannunta suka koma wajen mattress ɗin. Da kyar take iya ɗaga kafafunta ta bi bayansa. A bakin mattress ɗin ya zaunar da ita tare da zama a gefenta, sannan ya kai hannunsa ya karɓi kayan dake hannunta ya ajiye a gefe guda. ____________________________ "Kukan me kike yi? Meya faru?". Ƙasa ƙasa ya yi maganar kamar mai ciwon baki. Kasa iya amsa mashi ta yi, tana ta aikin murje ƴan yatsunta cikin na juna. A karo na biyu ya sake tambayarta, nan ma shiru, ban da kuka babu abin da take yi. Hannunsa ya sanya ya riko hannayenta da take murjewa cikin juna, ya ɗan dunkule hannun nata a cikin nasa, ƙasa ya kara yi da murya. "To ya isa haka kukan, ki gaya mun me ya faru kike kuka?". Tana wani irin shesshekar kuka irin zuciyar mutum tana kusan nan ta ce. "Babu komai". Da kyar maganar ta fita har ya iya gane me ta ce. "Saboda na kalleki ne kike kuka? Ko dan saboda ina cikin ɗakin ne?". Ya sake jefa mata. Kai ta fara girgizawa alamar ko ɗaya babu a ciki. Har lokacin hawaye marasa dalili suna ƴar tsare a saman face ɗin nata. Sake hannayen nata ya yi tare da janyota jikinsa mai gabaɗaya. Lokaci guda dukkansu biyu suka yi wani irin shiru kamar an kashe engine, shi dai wani irin duniya na daban ya afka, ita kuma tsoro da fargaba yasa ta ji numfashinta ya dai'na fita sosai, dik sai ta rasa a wani mataki take. Tuni ta luluƙa duniyar tunanin zantunkan Jumma na ɗazun, musamman yadda Jumma ta takura mata a kan Hamman nan nata ya fi Faisal komai da komai sai yanzu ta fara yarda da hakan da jikinsu ya haɗe waje guda, sai ta ji ina da banbanci. "Noor". Sautin muryarsa a tsananin kasale tamkar mai jin barci ya daki godan kunnenta. Bata iya amsa mashi ba, saboda yau ya goge mata haddarta da Inna Rabi ta ɗauki tsawon shekaru tana karantar da ita, tashi ɗaya ya sanya ƙwaƙwalwata ta washe ta yi wani fresh. "Yanzu gaya mun dalilin kukan to? Saboda na ganki ne ko?". Da kyar a wannan karon ta iya gyaɗa mashi kai alamar e hakan ne, saboda ya ganta ne take kuka. Hannunsa ya ɗaura a saman kanta, ba ƙaramin burgesa gashin kanta ya yi ba, ga shin nata ya yi dark brown, ga tsantsi, Jumma ta gyara mata shi da bikin nan nasu. A hankali ya ɗan shafa gashin nata, can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Meyasa dan na ganki zaki yi kuka? Baki son in kalleki ɗin ne?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a ba wai bata son ya kalle ta bane. "To meyasa kika yi kuka dan na gankin?". Shiru ta ɗan yi tana tunanin amsan da yakamata ta bashi, dan bata son ta ce ya dai'na kallonta, sannan tana son ta yi amfani da shawarar Jumma, sai dai tana tsoro sosai. Hannunta ɗaya ya riko cikin nasa, cikin salo ya ɗan matse hannun nata a hankali har sai da ta ji wani irin abu ya soki zuciyarta, har ta ji zazzaɓinta na ɗazun ya dawo mata, nan take ta ɗan fara rawan sanni, zazzaɓi ya dawo sabo. Shi kuwa ba dan komai ya sa ya yi mata hakan na face rarrashi, a ɓangarensa hakan rarrashi ne. "Kin manta ke matata ce ko?". Ya faɗa yana cigaba da ɗan mammatse mata hannun nata........ Ni kam nace ina ma bappa ya yi ɓatar hanya ya faɗo cikin ɗakin, me kuke tunanin zai faru? Ni dai ina ganin daga yau Jaish ya dai'na fita kenan, ko kuma ya bar gidan mai gabaɗaya saboda kunyan sake haɗa ido da bappa. "A'a ban manta ba hamma". Muryarta na rawa ta bada amsar, da alama wannan matse mata hannun da yake yi tana rikitata matuƙa, shi kuma bai gane hakan ba. "Meyasa to zaki damu saboda na ga matata? Baki san kawu Ibrahim ya ce na kula dake sosai ba ko?". Kai ta gyaɗa mashi alama e bata sani na, ɗan sama sama ya bata labarin abin da kawunta Ibrahim ya ce mashi dangane da ita, wato abin da baku sani ba shi ne, nasihar aure da ake yi wa miji fa to shi kawu Ibrahim ɗinta ne ya fara yi mashi kafin Arɗo ya ajiye shi ya fere mashi daga biri har witsiya, bappa dai yaki yarda ya furta mashi ko uppan, yo ya za'ayi ya koyawa wani yadda zai ci amarci da yarsa? Tab ai ba wannan zancen, ya dai rakasa har gidan Arɗo, sai ya shiga wajensu Inna dan su gaisa, ya bar Jaish ɗin da Arɗo yana gaya mashi yadda aure take da dai sauransu, to kun ji yadda aka yi, wato ya ɗauki maganganun su Arɗo har da wani cewa ita ɗin matanshi ce dan ya kalleta ai matarsa ya gani, lallai ma Jaish ka shahara gaskiya, ashe su Arɗo sun koya mashi komai ni princess Teema bani da labari, kai ana al'amurra a wannan gari na su Mahnoor wlh!. "Kawu Ibrahim ya ce na dubi girman Allah na riƙe ki da amana, kada na bari ki yi kuka, kuma na ɗauka mashi alkawarin zan yi hakan, amma shi ne a maimakon ki tayani cika alkawarin da na ɗaukan sai kike ƙoƙarin sakani saɓawa ko?". A hankali ta fara girgiza mashi kai tana faɗin. "A'a Hamma, ka yi hakuri, ban sani bane da na san ka ɗauki alkawari tabbas da ba zan yi kukan ba kome zai faru, da zan taya ka cikawa". "Da gaske?". Cikin salo ya yi maganar. Kai ta gyada mashi alamar e. "To zaki taya ni cika wannan alkawari dana ɗauka?". A wannan karon ma kai ta gyaɗa mashi alamar e tare da faɗin. "In Sha Allah". "Okey ki mun alkawarin ba zaki sake zubar da hawayenki ba?". "Nayi maka". Ta faɗa tana kai ɗayan hannunta da bai riƙe ba saman face ɗin nata da nufin ta goge hawayen nata. Hanata ya yi a in da ya sanya tafin hannunsa da kansa ya share mata fes. "Idan kina murmushi kin fi kyau, ko zaki mun murmushi a yanzu? Dan ina son gani". Yadda ya yi maganar ai bata san lokacin da cool murmushi ya kubce mata ba, sai dai kuma ta juyar da kanta tana ƙoƙarin ɓoyewa a cikin faffaɗar chest ɗinsa. Hannunsa dikka biyu yasa ya rabata da jikin nasa dan ya samu damar ganinta da kyau. Kin yarda ta yi ta fara tirje mashi ita ala dole ba zai kalleta ba. Ba dan ya so ba ya barta ta ɓoye face ɗin nata a kirjinsa. Dikkansu biyu wani irin daɗi na musamman suka ji yana ratsasu, sun samu farinciki matuƙa. "Kawo kayan na sanya maki na sake yi maki kwalliya irin na jiya". Ya faɗa a hankali. "A'a Hamma zan sanya da kaina". Cikin girmamawa ta yi maganar. "Bakiso na sanyawa matata kaya kenan?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Allah sarki a yanzu dai Jaish yana da ƙoƙarin rama alkhari da alkhari, domin kuwa dik ƴan uwan Mahnoor harda kakarta Inna sai da suka rinƙa haɗa shi da Allah a kan ya kula da ita, shi kuma ya ɗauka masu alkawarin yin hakan, shiyasa yake iya ka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin bai karyar masu da zuciya ba, ya cika alkawari. "To tashi kisa bari na je na yi wanka ko?". Da to ta amsa mashi, sannan ta raba jikinta da nasa. "Bari na zo na surka maka ruwan Hamma". Ta faɗa tana ɗago kallonta a kansa. Jinjina mata kai kawai ya yi idanunsa a kan gurun wuyarta, ya yi matuƙar burgesa sosai gaskiya. Tana miƙewa tsaye da nufin ta ɗauki kayanta ta sanya hijabi ta shige ɗakin Mahreen ta sanya kayan a wajen ba zato ba tsammani zanin jikinta ya zame ƙasa, kwanciyar da ta yi a jikinsa yasa zanin ya kwance ba tare da ta ankara ba. Kawar da kansa ya yi kamar bai ganta ba, dan yasan kuka zata sake yi mashi idan ya kalleta, shi kuma baya son kukan, dan ya yi wa bappa alkawarin ba zai barta ta yi kuka ba. A miliyan ta kama zanin nata idanunta a kansa, tana son gane ya ganta ne ko bai ganta ba. Ganin yana kallon ƙasa yasa ta yi saurin ɗaura zanin nata, sannan ta ɗauki hijabinta ta zura, a hanzarce ta wuce izuwa ɗakin Mahreen dan ta sanya kayan. Bayanta ya bi da kallon yana jin wani irin daɗi, weist beat dake ɗaure a weist ɗin nan nata ba ƙaramin burgesa ya yi ba, ta tafi da imaninsa sosai, sai ya ji tamkar ya kai hannunsa ya taɓa a lokacin da ya gani, dannewa kawai ya yi ya kawar da kallonsa dan gudun kukanta, amma bai so dai'na kallon weist beat ɗin nan ba gaskiya. Weist beat ne da mamanta ta bar mata su wajen guda 20, sai ta ɗaura guda 5 ta ajiye saura, da Mahreen ta ɗan girma sai ta ɗaura mata 3 ta ajiye sauran 12 ɗin, sun yi matuƙar haskaka weist ɗinta sosai, sun ƙara fito mata da shape ɗinta sosai, ga duwatsu beat ɗin sai wani irin sheki suke yi tamkar sabbi, kuma ya kai shekaru 3 a ɗaure a weist ɗinta fa, kawai suna da kyau ne da quality. Haƙiƙa surar jikinta ya tsaya mashi a ransa, dik da yau ne karo na farko da ya fara gani, amma ba shakka ya kwaɗaitu ya kuma so shagaltuwa da kallonta kada ya daina, ashe tasan meyasa take ɓoye jikinta, ta tara abubuwan da zasu ɗauke hankalin dik wanda ya kalleta ne yasa take ɓoyewa. Ya nisanta cikin tunanin dik wani motsinta tun ranar da ya fara ɗaura idanunsa a kanta har izuwa yau, zazzakar voice ɗinta ne ta katse shi a in da ta ce. "Hamma na juye maka ruwan saura ka je ka yi wankan kawai". Nisawa ya yi tare da ɗaura idanunsa a kanta. "Bappa yana waje?". Ya tambaya tamkar ba shi ya yi maganar ba, saboda yadda ya motsa lips ɗin nasa a hankali. "A'a bai dawo ba tukun nan". Tana magana tana satar kallonsa ta kasan ido. "To zo ki zauna a nan kada ki fita waje bari na yi wanka na zo". Ƙarisowa ciki ta yi tana amsawa da to. Miƙewa shi kuma ya yi ya nufi waje. Saman mattress ɗin ta haye ta kwanta tana tunanin yadda ta ji jikinsa a karo na biyu, abin ya tsaya mata a rai, ita kaɗai kamar ba lafiya ba sai ku ga ta saki murmushi, idan kuma ta tunano yadda zaninta ya kwance a gabansa sai ta ɗan ɗaure fuska a fili ta ce Allah yasa bai ganta ba, in ta tuna yadda ya rarrasheta kuma sai ta ji wani irin farinciki na musamman yana ratsata. Da yake akwai ɗan zazzaɓi a jikinta sai yasa barci ya ɗauketa a ɗan wannan kwanciya shiru da ta yi tana tunanin, kun san zazzaɓi da iya saka mutun barci, musamman ma idan ya haɗu da mura. Sosai barci ya ɗauketa kafin ya fito wankan, ko da ya gama wankan ya dawo cikin ɗakin barcin nata ma har ya ɗan yi nauyi. Ɗan zuba mata idanu ya yi yana jin tamkar ya kai hannu ya ɗage rigar nata ya kara kallon weist beat ɗin nata, sun yi mugu mugun tafiya da imaninsa, da gurun wuyarta da kyansa ya ratsa zuciyarsa matuƙa, abu biyun nan sun tsaya mashi a rai. A gefen bed ɗin ya zauna ya kasa cire idanunsa a kanta, zuga shi kawai zuciyarsa take yi tana ingiza shi da ya ɗage hijab and rigar nata ya ga beat ɗin. Daga karshe dai kasa hakura ya yi ya kai hannunsa, haka kawai yau karo na farko a rayuwarsa hannunsa ta fara kerma dan zai taɓa wani abin, kamar wani maras gaskiya. Kamar zai fasa, sai dai kuma zuciyarsa taki aminta da ya fasa ɗin, da kyar ya iya kai hannu nasa ya ɗage mata hijabin a hankali, yau fa zuciyar maza sai harbawa da karfi take yi kamar dai wanda yake cikin tsananin tsoro, ashe akwai abin da zai bawa Jaish tsoro? To tsoron me ma yake ji? Ya yi babban sa'a riga da sket ce a jikinta ba doguwar riga ba, kunga ya samu damar ɗaga rigar ba tare da wata wahala sosai ba. Wani irin faɗuwar gaba ya ji a lokacin da ya kama gefen rigar nata zai ɗaga..... Ni kam na ce su Jaish ana satar kallewa yarinya weist, kai anya yaran King Zuhair akwai mai ta ido kuwa? Dan naga kunyar Jaish ɗin ma yana neman komawa sai kan wanda ya zaɓa zai ji ta, ko da yake Mahnoor kanwarsa ce.........😂 (Maman Sultan kina zagin Yah Jawad kullum to ga Jaish ɗinki zai yi satar kallon jigidan yar mutane 🤔 ku kuma haka kuke kenan da satar kallo ko? Gara shi Yah Jawad kai tsaye ya tafi ɗoɗar, to wlh ku canza hali, ku canza hali maman Sultan, ki zo ki koyawa Jaish lamura ato, idan ba haka ba mu miki.............. Na dai yi shiru.) Yana yi yana fargabar kada ta farka ta kama shi ya ji kunya, kamar mai ɗaga kwai a saman bajajjen faranti haka ya ɗage rigar tata. Aikuwa yana ɗagewa ta firgita ta miƙe zubur a tsakiyar mattress ɗin. Tana miƙewa ta waro idanunta da suka yi ja saboda barci. Kai tsaye suka yi ido huɗu da shi. Allah sarki tsabar tana killace jikinta ma har ga kai ga tana cikin barci ma in aka buɗe mata sai ta farka. Ganin shi ne yasa ta yi ƙasa da kai jiki dik a mace, shi ma wani irin kunyarta ne ya ji ta kama shi, sai ya ji dama bai yi ba. "Ka yi hakuri Hamma, na tsorata ne shiyasa". Muryarta ta daki dodan kunnensa. Shiru ya kasa furta uppan, saboda bai san me zai ce mata ba. Sallar la'asar ma fa zai yi ya biyewa ruɗun zuciyarsa na son ganin beat ɗin, yanzu ga shi ta ja mashi jin kunya. "Noor ina son wannan beat dake kwankwason naki, sun mun kyau sosai". Ya faɗi hakan yana ɗago da kallonsa a kanta. "Ina da wasu a ɗakin bappa, in ɗauko maka ne?". Kai ya girgiza mata tare da juyowa gareta da kyau. "Wannan da yake jikinki ne ya burgeni ba wanda yake ɗakin bappa ba". Ƙasa sosai ta yi da kai, cike da kunya ta ce. "To bari na je ɗakin Mahreen in ciro shi na kawo maka shi". Ajiyar zuciya ya sauke. "Ba amfani zan yi da su ba, in gansu a jikinki shi ne kyan, sun yi matuƙar dacewar da ke, ki yi hakuri na tasheki daga barcinki". Shiru ta yi ta rasa abin faɗa. Ganin bata yi magana ba yasa ya miƙe ya nufi saman dadduma. Hiƙama ya tayar tare da kabbara ya fara sallah. Zuba mashi idanu sosai ta yi, dik yadda zai motsa a sallan idanunta na'a kansa babu ko kyaftawa. Cikin nutsuwa yake gabatar da sallarsa. Sai dai yana idarwa ta yi saurin kawar da kallonta daga kansa. Addu'oinsa ya gabatar kafin ya miƙe ya nufeta. Tana zaune kamar yadda ya barta bata motsa ba. Gefenta ya zauna ƙasa kasa ya ce. "Ki kwanta ki cigaba da barcinki mana". "Barcin ya watse ai, kuma kaga babu kyau yin barcin bayan la'asar, yanzu ma ban sani bane barcin ta ɗauke ni". A nutse ta yi maganar. Jinjina kansa ya yi tare da cewa. "Nima da kwanciya zan yi amma na fasa bari na je waje". Da to ta amsa mashi, miƙewa ya yi ya fita waje. Ita ma miƙewa ta yi ta bi bayansa. A tsakar gida ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin abin da ya faru a yanzu na ɗage mata riga da ta kamasa ya yi. Wani irin bakon yanayi mai wuyar ganewa ta ji yana shigarta. A haka har Mahreen ta dawo daga islamiyya ta sameta, goshin mangariba kenan. A lokacin kuma Nenne ta dawo cikin gidan. Kamar wata munafuka ta yi ƙasa da murya ta ce. "Ke Mahnoor mijin kin nan yana nan?". Kai ta girgiza mata alamar a'a baya nan ya fita. Ajiyar zuciya ta sauke. "To tashi ki zo ki mun wanki, kayana dik sun yi datti, kin fi sati rabonki da yi mun wanki, dan haka tashi maza ki yi mun da sauri". Ba musu ya amsa da to, fuska ba yabo ba fallasa ta miƙe ta bita izuwa cikin ɗakinta. Uban lodin kaya ta haɗo mata tare da omo ta bata, kwasowa ta yi ta nufo waje da su, kayan yin waki wato su bokiti ta ɗauko ta fara tikar aiki. Gab da mangariba bappa ya dawo daga kiwo, da sauri ta ɗaura mashi ruwan wanka, dan mangariba ta kawo kai, ya so ya hanata yin wankin da take yi a matsayinta na amarya, amma sai kuma ya kasa, yana ji yana gani ya kyaleta tana yi. Har bayan sallar isha'i baiwar Allah tana wannan aikin, ga zazzaɓi dama a jikinta, Nennen kuwa ta kara tafiya gantalinta, already idan baku manta ba da rana ta yi abincin nata ne har da dare, dan ya kwasa a kwanika ta kaiwa kowa ɗakinsa, so a daren nan babu wani girki da zata sake yi yar albarka. Bata yi sallar mangariba ba bare isha'i, tana ta aikin wanke kayan Nenne, Mahreen kuma bata iya wanke kayan manya ba bare ta tayata, sai ta zauna kusa da ita kawai tana binta da surutai. Shi kuwa Jaish tun da ya fita waje ya samu waje a karkashin bishiyar kofar gidan nasu ya yi zamansa, har aka kira sallar mangariba ya wuce masallaci, a can ya yi alwala. Ba shi ya dawo gidan ba sai da aka yi sallar Isha'i, ya riga bappa shigowa gida, yaki yarda ne su haɗa hanya. A lokacin da ya dawo ta kammala wankin ta shige ɗaki, ta yi sallar mangariba da isha'i, tana kundundune cikin hijabinta a saman dadduma saboda sanyin zazzaɓi da take ji, jikinta ya yi zafi jau kamar wuta, kuma dik zama da ta yi a waje tana wanki iskar yamma ya bugeta ne yasa zazzaɓin ya kara tsananta. Ɗakinsu kai tsaye ya nufo, dan sai azalzalarsa zuciyarsa take yi a kan ya zo ya ganta. Ya sha mamakin ganin tana kudundune a saman dadduma, ta kwanta shiru, da alama ma barci ya ɗauketa, ga fitillar da ta kunna ya haske ɗakin da haske tas, so yana iya ganinta da kyau. A gabanta ya zo ya duƙa, a hankali ya kai hannu zai ɗauketa kenan ya ji jikinta da zafi sosai. Har kaman zai ɗauke hannun nasa ya fasa ɗaukarta ɗin sai kuma ya danne ya ɗauketa cak suka nufi saman mattress ɗin, cikin magagin zazzaɓi ta fara sambatu jin and ɗauketa, surutu take yi wanda ba zaka iya gane me take faɗe ba. "Noor lafiya kuwa? Meyasameki?". Ya jefa mata tambayar cike da mamaki a ransa, dan shi dai yasan sun rabu da ita tana cikin ƙoshin lafiyarta, yanzu ya dawo ya sameta haka abin da mamaki, sannan ya yi maganar yana kwantar da ita a saman mattress ɗin. "Hamma jikina ciwo yake yi mun". Ta faɗa cikin magagin ciwo kamar zata sa kuka. Harta iskan dake fita daga bakinta mai zafi ne sosai. Sosai ya ji tausayinta ya kara ratsa shi har jijiyoyin jikinsa, a sanyaye ya ce. "Sannu kin ji? Bari na kawo ruwa na ɗan sa maki a jikinki ya rage zafin ko?." Shiru bata iya amsa mashi ba, saboda wani irin sara mata da kanta yake yi. Gyara mata kwanciya ya yi, ya jango bargon da ta naɗe ɗazun ya warware, lulluɓa mata ya yi kafin ya fice daga cikin ɗakin. Yana fita tsakar gidan bappa yana shigowa, da sauri ya wuce kitchen dan ma kada wani abin ya haɗasu. Kwano ya ɗauka ya ɗebo ruwa mai sanyi, sannan ya koma cikin ɗakin, shi ma bappa ya wuce cikin nasa ɗakin. A saman mattress ɗin ya ɗaura ruwan, ya je ya ɗauko ɗankwalinta daga cikin kayanta, yanzu fa shima zama da bappa yasa ya iya jinyar marasa lafiya ya yi masu magani, ya ga haka bappa yake yi wa masu zazzaɓi kafin ya basu magani, shi ma ya zama likita, wato Jaish fa ɗan baiwa ne, yana cikin hayyacinsa shi ɗan jarida, baya cikin hayyacinsa kuma likita!......😂 A saman mattress ɗin ya zauna tare da tallabota da hannunsa ɗaya, a hankali ya zare hijabin jikinta, jikinta dik a sake saboda ciwo, sam bata san ya cire mata hijabin ba, dan bata ji lokacin ba, ciwo ya yi tsanani. A gefe ya ajiye hijabin, a hankali ya fara ƙoƙarin cire mata riga dan ya sanya mata ruwan sanyin a jiki. Dik bata yi wani yunkurin ba. Haka ya cire tsab, sai kuma me? Ya subhanallah. Sai kuma shi ya kasa yin abin da ya yi niya, ya zuba idanu kawai yana kallon abin da bai taɓa gani ba tun da mommarsa ta haifesa ya yi wayo, bai taɓa ganinsu hakansu muraran ba. Ji ya yi ɗakin nasu ma gabaɗaya tana juya mashi, ai bai san lokacin da ya kawar da hasken fitillar dake haskasu ba, ya sanya paipain da ta rufe masu abincinsu da shi ya ƙare hasken ta gefensu. Ya ruɗe sosai kamar ba shi ba, ya nemi dik wani sukuninsa ya rasa, ba zai iya cigaba da gani bane yasa ya kare, ji ya yi anya ma zai iya sanya mata ruwan nan a jiki kuwa? Ko dai ya je ya kira bappa ne?. Wata zuciya ne ta amsa mashi da ina bai kamata ya kira bappa ba, ai abin kunya ne ma wani ya duba mashi lafiyarta. Kai shi kuma ba zai iya dubata ba, to yake kenan, Jaish fa ya karaya, ya ga tula tula ya ruɗe, ko dama waye ya aikesa ya kai idanunsa can? To shi dai ya sani, ni bari na leƙa wani wajen na dawo, amma me kuke tunanin zai faru? Shin zai iya yi mata wannan treatment ɗin kuwa? Bari dai mu je mu dawo sai mu gani shin zai iya ko ba zai iya ba!. ____________________________________ 🫀🪴EVIL KINGDOM😈🔥 A gabaɗaya tarihi bayan Dark world da ta zo ta yi breaking record da babu wata masarauta da ta kai wannan zalinci, suna mulki ne bisa ga juyin turawa, azzalumi ne King Abdul raof, yana mulkar mutane ne bisa zalinci da rashin daraja halitta ta dan adam, cin zarafi, mugunta, hainci, nuna wariyar launin fata, kullum cikin azabtar da bayi, tsabar zalincinsa ga motoci ga dawakai, ga duk wasu abin haka da kuka sani masu kyau da tsada, amma idan muguntarsa ta motsa wlh ta kan bayi yake bi ya taka tamkar stair case, bayi zasu jerun masa tun daga farkon part ɗinsa har izuwa cikin hamshakiyar fadarsa, ya tattaka ta kansu da wani shegen gold shoes ɗinsa mai kama da cover, ya bi kansu har izuwa cikin fadarsa. Haka zalika tsabar bakar mugunta sai ya ce motar da bayi zasu ɗauka a kansu zai hau, ba gaira babu dalili a fara azabtar da mutum, ga shi baka isa ka fita daga garin or masarautar ba, rashin adalci zallarta ake gudanarwa, zaluntar mutane shi ne abin da yake sanyashi nishaɗi saboda bakar zuciya. Yana da mata biyu yara huɗu, wannan bakar zaluncin nasu yasa King Zuhair ya taɓa yakarsu, saboda ya samawa ƴan ƙasar ƴancinsu, a wannan yakin ne su commander Zafar suka kashe King Abdul raof wanda daga baya aka naɗa kaninsa mai suna Abdul Aziz. Abin mamaki baya karewa, ashe kanin ma ya fi yayansa iya zalinci, to a yanzu dai duk zalincin da yake yi hankalin kingdom of power bata a kansu, suna can suna pama da Queen Zarina bakar azzaluma bakar matsafiya, kun san a tarihi labaran masarautu akwaisu da iya tsafi, to ita dai Queen Zarina bata yasar ba, ba tayar baya bace, bakar matsafiya ce ta gasken gaske, ita ta sako kingdom of power a gaba da yasa hankalin King bai koma a kan kanin King Abdul raof, da tun yaushe zai fara shirin gwagwarmayar nemawa ƴan kasar damar shaƙar iskar ƴanci. Dan Evil kingdom ta kai munzalin a yake ta sosai ma, saboda King Zuhair ya daka masu warning ba sau ɗaya ba sau biyu ba, kunga a matsayinsa na babban sarki ana tabka zalinci ya yi warning ba'a dai'na ba me yakamata ya yi? Ai dolensa a matsayinsa na babba ya samawa ƴan cikin masarautar ƴanci mai girma. Sai dai kuma King Zuhair yana can yana ƙoƙarin yadda zai kifar da Queen Zarina, su kuma King Abdul Aziz suna ta ƙoƙarin yadda zasu yi su yakesa su kwaci Spender daga hannunsa. Evil kingdom ita ce masarauta ta uku bayan Black Tiger empire da Kingdom of justice wato masarautar Queen Zarina kenan, sai evil ita ce ta uku a masu neman Spender ido a rufe. Kada ku damu, dik wata masarauta da kuka ga sunanta a cikin littafin RAWANIN ZALINCI to fa tana da tushe da kuma nata labarin, san haka shi ma evil kingdom ba haka ɗai yake ba, dayawa daga cikin jiga jigan labarin daga cikinsa suka fito, amma mu je dai zuwa, mun kusa kamo bakin zaren labarin mur warwareta. In short ta ko'ina dai ƙoƙarin yakar King Zuhair ake yi, saboda kujerarsa ta fi ta kowa karfin ikon faɗa aji a duniya, na biyu ya fi su tarin mayaƙa masu haɗari, na uku shi ne mamallakin Spender, kun ga ai yana tsaka mai wuya, bashi da nutsuwa tukunan. Amma mu kutsa cikin masarautar mugani. Masarauta ce mai girma kamar dai yadda kuka san sauran masarautu, suna da komai na daga abin da ya shafi sarauta, mayaka da bayinsu hazikai ne wajen sake jikinsu su jibgi aiki, a yanzu haka bayi sama da gudu ɗari biyar ne aka kaisu bayan kingdom ɗin suna aikin fasa duwatsun dake wajen domin su samu filin King Abdul Aziz ya kara girman kingdom ɗinsa, burinsa masarautar ta yi girma kamar dai Kingdom of power or masarautar su Zarina. Gabaɗaya bayin nan sun jigata, sun ga ji sosai, wasu suna sare itatuwa, wasu suna fasa duwatsu, daji ne mai girman gaske fa. Amma a haka King Abdul Aziz yake azabtar dasu wajen saran dajin. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 ❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2024-11-25...✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥 44 EVIL KINGDOM😈🔥 Gabaɗaya bayin nan sun jigata, sun ga ji sosai, wasu suna sare itatuwa, wasu suna fasa duwatsu, daji ne mai girman gaske fa. Amma a haka King Abdul Aziz yake azabtar dasu wajen saran dajin. Cikin familynsa kuwa ba karamar dirama ake bugawa ba, domin kuwa kamar yadda kuka ji na ce maku matansa biyu ƴaƴansa huɗu to hakansu ke, sai dai fa matarsa ɗaya wato amaryarsa matar marigayi yayansa ne King Abdul Raof, bari dai na fayyace maku, amaryarsa matar yayansa ne, suna kuma da yaya maza biyu da suka haifa da yayan nasa kafin King Zuhair ya kashe shi, dukkansu kuma manya ne ƴaƴan, dan dik sun haura 25 years, nasan zaku sha mamaki a lokacin da zan ce maku Adam wato yarinman Gimbiya Sarina da ya je naman aurenta ɗa ne ga King Abdul Raof, makirci suka shiryawa King Zuhair domin su ɗauki fansa, batu na gaskiya shi Adam ba auren Sarina ya zo yi ba, leƙen asiri ya zo yi, sun yi amfani da sunan kingdom daban daban ne suka shigo cikin kingdom of power, a karo na biyu nasan zaku yi mamaki idan nace maku Yusuf saurayin Sarina na farko wanda ya yi yunkurin yi mata fyaɗe yaya ne ga Adam! Ainahin Yusuf ɗa ga abokin uncle Abbas ba shi ne ya zo wajenta ba, amfani suka yi da tsafi suka yi irin siffan wancan Yusuf ɗin, suka juyawa uncle Abbas ƙwaƙwalwa ba tare da ya sani ba, kunga dikkansu Sarina ta shuka masu rashin mutunci ba tare da ta san makiyansu bane. A nan dai ta kyauta sosai. Yanzu dai kila ba zaku fahimci komai ba sai gaba, to in short dai da Yusuf da Adam uwarsu ɗa ubansu ɗaya, kuma wutar fansar kashe masu mahaifi da King Zuhair ya yi ne take ruruwa a cikin zuƙatansu, ta kowacce hanya so suke suga sun kai King Zuhair kasa. Shiyasa suke bin dik wata motsin kingdom of power, sun samu labarin akwai yariman da zai je ganin Sarina, shiyasa suka garzayo izuwa kusa da Kingdom ɗin, da yariman ya doso wajen sai suka yi amfani da tsafi suka gusar mashi da tunanin Sarinan, suka kuma sanya ya juya ya koma, sai Adam ya rikiɗa ya koma siffar wannan yariman ya je wajenta, shi ma Yusuf haka suka yi mashi a lokacin. Abin da baku sani ba shi ne, aka ce idan zaka gina ramin mugunta ka ginasa dai'dai kai, da gangan Yusuf ya bari su commander Zafar suka wahalar da shi har aka ɗaure shi a cikin gidan yarin cikin masarautar, dik cikin taku ne, dama so yake a kawo wani abin da zai sa ya ɗauki lokaci a cikin kingdom ɗin dan ya samu damar bincike yadda yake so, amfani yake yi da tsafinsa idan dare ya yi ya fice daga cikin gidan yarin, ya shiga cikin kingdom ɗin ya tafi leƙe leƙen asirinsu, sai dai bai kai ga gama bincikensa bane King Zuhair ya ce a sakesu su tafi, shi ne yasa yanzu Adam ya sake dawowa dan ya karasa binciken da kyau kafin su fara shirin ruguje King Zuhair. Akwai gagarumim yaki fa, King Zuhair ya tara uban makiya kam ba'a magana. Ta ko'ina so ake yi a kaisa ƙasa. Amma kuna tunanin shu'umai Yusuf da Adam zasu rabu da Sarina kuwa? Dan dikkansu biyu ta ci masu mutunci ba kaɗan ba. Akwai matsala kuwa, shiyasa koya ɗan adam yake kada ka walaƙanta shi, dan baka san wanenen shi ba, baka san a ina zaku haɗu gaba ba, Allah baya shawara da wani kafin ya aiwatar da abin da zai aiwatar, hmmmm bugu da ƙari gasu riƙaƙƙun matsaya, sai dai mu ce Allah ya ceci uncle Abbas bawan Allah, dan kuwa dik abin da ya sami Sarina kamar shi ya sama.........😥 To kun ji diramar waje, daga cikin gida kuma da mahaifiyarsu Yusuf sharariyar mushirikar nan, da kuma uwargidan King Abdul Aziz sam basa shiri, tamkar wuta da audiga haka suke, saboda kunga yanzu Abdul Aziz ne a kan mulki, so uwargidansa tana sa ran ƴaƴanta su karɓi mulki bayansa, sai dai kuma kash ƴaƴanta basu kai su Yusuf girma ba, ɗa namiji ɗaya da mace ɗaya take da su, kuma yara ne, namijin bai wuce 19 to 20 years haka ba ,ita kuma mace 15 years, shi ne yasa suke faɗa da mahaifiyar su Yusuf a kan mulki. Amma kuma fa dik tsafin mamarsu Yusuf bata iya cutar da ko ɗan yatsar uwar gidan King Abdul Aziz, saboda ita ɗin baiwar Allah ce, tana da riƙo da addini, matsalarta ɗaya son da take yi yaranta su gaji babansu, ba komai yasa take son hakan ba kuma face dan ayi adalci, tana danasanin auren babansu, dan bata san bakin mugu bane sai da suka yi aure, to shiyasa ta tsaya ta bawa ƴaƴanta tarbiya irin na addinin musulunci dan su yi mulki bisa adalci da tausayawa bayin Allah talakawa, wannan ne dalilinta na son su yi mulki. Ta tsani su Yusuf su hau kan wannan karaga, dan tasan sun fi ubansu ma iya zalinci, to my people's wani fata zaku yi wa gimbiya Zahra uwar gidan King Abdul Aziz a halin yanzu? Mu je dai zuwa. Sai dai fa dik kudurin ɗaukar fansa da su Yasuf suke yi shi King Abdul Aziz ba shi ne a gabansa ba, shi Spender ce a gabansa, ya yarda da kudurinsu ne kawai dan dikkaninsu makiyinsu ɗaya ne wato King Zuhair, shi ne mamallakin Spender shi ne kuma ya kashe King Abdul Raof, kunga makiyin nasu ɗaya. ___________________________🔥😈 Rana ta yi sanyi, yanayin gari ta canza, yalwar iska ya yawaita a gari, motsin mutane ya ragu, hayani babu, iska na ƙaɗa dogayen bishiyoyin dake cikin lanbun, sanyi mai daɗi na ratsa fata har izuwa cikin ƙashi na gimbiya Zahra uwargidan King Abdul Aziz dake zaune a cikin lambu saman wani haɗaɗɗen shinfiɗa na alfarma, ta ɗan yi rigingine a saman ɗaya daga cikin manya manyan throw pillows da aka ƙawata saman shinfiɗar da su. Ta haɗe cikin alkyabbar nan nata mai bala'in kyau da tsada, daga ita sai wasu kuyangu guda huɗu dake yi mata hidima ne a wajen, ƴan'mata ne masu tasowa masu jini a jiki, sune kewaye da ita sun zube gwiwowinsu a ƙasa. Ga wasu irin nau'i na cima daban daban a gabanta masu bala'in daɗin ɗanɗano, fresh fruit ga su nan nau'ika daban daban birjik a wajen. Wata yar kyakkyawar matashiyar yarinya da bata wuci 15 years bace ta ƙariso wajen cikin shiga ta alfarma ta ƴaƴan sarakuna, fara tas da ita. A jikin maman nata ta zauna tana ɗan turo baki. "Lafiya Suhaima?". Gimbiya ta faɗa tana kallon face ɗinta. Shiru ta yi bata yi magana be, yarinyar akwai riƙo da addini, ga tarbiya sosai da ta samu daga wajen mahaifiyarta, tana da son mutane da saukin kai, sai dai bata son hayaniya. Yayanta wanda warriors guda biyu suke aikin take mashi baya ne ya shigo cikin wajen, shima yana cikin shiga ta kowani irin yarima mai ji da kansa. A kusa da ita ya zauna shi ma tare da yin ƙasa da kansa. "Lafiya Suhail naga kamar ranƙa a ɓace?". Cewar mahaifiyar tasu, ta yi maganar tare da miƙewa daga kishingiɗar da ta yi. "Babu komai Ammie". Ya bata amsa voice ɗinsa akwai sanyi alamar yana da nutsuwa sosai, ya kuma samu tarbiya. "Ammie in faɗa maki me yake damunsa?". Cewar Suhaima da yarinta yake ɗawainiya da ita, tana magana tana murmushi. "E faɗa mun me yake damunsa mamana". Ɗan ɗago kai ya yi ya kalleta. "Ni nace maki hakan? Na ce ki faɗa mata". Ya jefa mata tambayar yana kallonta. Kai ta fara girgizawa alamar a'a ba shi ya ce ba. "Tom kada na ƙara jin bakinki a nan wajen". "Kai Yah Suhail zaka fara ko?". Cikin shagwaɓa ta yi maganar. Da yake yau baya cikin mood na wasa sai bai amsa mata ba, ya kawar da kansa, damuwa yake ciki sosai a kan haɗuwarsa da mahaifiyar su Yusuf da ya yi a yanzu a kan hanyarsa ta zuwa wajen Ammien tasu, dama a tare suke tahowa da Suhaima, da suka haɗu da ita da Adam ne sai ta dakatar da su, Suhaima kam ta gudu taki tsayawa, shi kuma da yake Ammiensu ta hanasa raina babba sai ya tsaya ya saurareta. Zaginsa fes ta yi kamar an aikota, ta tsanesu ne kamar ta kashesu, dan ma ta gaza iya hallakasun ne da ta jima da yin hakan, su sun fi mahaifiyarsu ma riƙo da addinin Islama, shiyasa ta gaza iya aikata masu komai, sai dai ta ƙare a zagi da hantararsu kawai. Bayin Allah dik zagin da zata yi masu basa ce mata ko uppan. Sai dai su tsaya shiru, idan ta kammala zagin nata sai su bata hakuri su wuce abinsu, ta so yin tsafi da jinin Suhaima, amma ina ta kasa, sun riƙe Allah sun fi karfin mushirikai dama kowa na duniya. Yanzu haka tana can ita da Adam suna shirya yadda zasu yi su hallaka King Zuhair, Adam ya sake gano masu wasu sirrika dangane da kingdom of power a wannan zuwan da ya yi wajen Sarina, shi kuma Yusuf baya nan, yana can yana ƙoƙarin yadda zai yi su haɗa kai da Queen Zarina dan su shafe babin kingdom of power a doron duniya, shi ne ya tafi zaman meeting da Zarina ɗin, idan kuma suka yi sa'ar haɗa kai fa to wlh Allah ne kawai zai iya kwatar King Zuhair, saboda dikkansu shu'umai ne na bugawa a jarida, ga Black Tiger baban sheɗani na karshe ma yana shirin murƙushe King Zuhair, kuma dik bawan Allah King Zuhair namu na amana bai san suna shirya mashi wannan gagarumin abin ba, Allah sarki shi ta Spender ma yake yi, bai tsare masu komai ba, bai hana su jin daɗi ba, bai takura masu ba amma suke neman ɓatar da shi a doron duniya. To sai dai mu ce Allah ya kwacesa daga hannunsu. Ammafa akwai matsala ba ƴar karama ba, abin da baku sani ba a nan shi ne, ita kuma Ammien su Suhail burinta kawai su King Zuhair su kashe Yusuf, Adam, mamansu da kuma mijinta King Abdul Aziz, a kan hakan kuma ta shirya bada gudunmawa ko da hakan shine zai zama sanadiyar rayuwarta, burinta kawai a kawar da waɗan nan azzaluman daga doron duniya. Abin da zai baku mamaki kuma ya yi matuƙar girgiza ku a nan shi ne Mammien su gimbiya Sarina tana ɗaya daga cikin membobi masu leƙen asirin na Queen Zarina, idan baku manta ba commander Zafar a lokacin da aka kawo masu wannan unexpect harin, in baku manta ba yace a yadda mayakan suka shammacesu suka shigo har ta kofofin baya na kingdom ɗin dole dole suna samu masaniya ne yasa hakan, dole akwai ɗan leƙen asirinsu a cikinsu, har ya ƙara da cewa ɗan leƙen asirin nasu kuma na kusa da su ne, to ba kowa bane face Mammie, bayan ita ma akwai wasu na kusa ɗin. Ita take bawa Zarina information a kan dik wani motsin kingdom of power, dik wasu kofofin sirri na cikin masarautar sai da ta gaya masu shi, ita tace masu Spender yana cikin kingdom ɗin, a lokacin bata san an canza mashi mazauni ba, yanzu haka tana nan tana binciken in da Spender yake ta gaya masu. Ita fa ba wai son auren King Zuhair ma take yi ba a yanzu, da farko dai tana son auren nasa, amma yanzu da Queen Zarina ta ce mata in ta tallafa masu suka kashe King Zuhair da ahalinsa to tabbas ita Mammien za'a bawa mulkin Kingdom of power, dan tsabar rashin hankali da jahilci kuma wai sai ta yarda da alkawarin mushirika, mutumin da zai saɓawa mahaliccinsa wanda ya kawosa duniyar da yake jin daɗinta har baya son barinta yaushe kai kuma zaka yi tunanin ba zai saɓa maka naka alkawarin ba? Kai ɗin banza!. Kuna tunanin a yadda Kingdom of power ta fi dikkan masarautun da suke kewaye da ita girma da komai ɗin nan kuna tunanin Zarina zata barwa Mammie ta mulke masarautar ne idan suka kashe King? Ku dai yi tunani, dan ita kam Mammie babu wannan tunanin a kanta, ta yarda da Zarina, tana jin daɗi za'a shafe mata babin su King a bata karagar mulki a haukarta, wato cin amana ne kan cin amana, yanzu zamu taɓo game ɗin cin amana, amma batu na gaskiya Mammie ta ci amanarsu mafi muni ma kuwa, bama kamar yadda take ɗaukar dik wani sirrinsu ta kaiwa su Zarina. Abin takaicin kuma a nan shi ne, dik wani hira da suka yi ko a fada ne sai uncle Abbas ya faɗa mata, Allah sarki dan bata taɓa muna mashi mummunar dabi'a ba, tana nuna tana tare da shi, ita ce sirrrinsa, aka ce rashin sani yafi dare duhu, bai san ita ɗin makashiyarsu bace, kunga a sauki tana samun dik wani sirrin fadan King ta bakin uncle Abbas tana gayawa Queen Zarina, ashe ba a banza uncle Jahiz ya tsaneta basa shiri ba. Yanzu dai Kingdom of power dik wasu sirrikansu da motsinsu Queen Zarina tana sani bayin Allah. Amma mammie ta gama dasu ta cucesu. Yanzu haka shirye shiryen yakar Queen Zarina da suke yi dik uncle Abbas ya gaya mata ita kuma ta gayawa Zarina ɗin, dik wasu tsare tsaren da suka yi da hanyar da zasu shiga kai tsaye dik ta gayawa Zarina, dan haka ita kuma Zarina tasa an kafawa su Hoorain zakunan mayaƙa tarko a dik wasu hanyoyin da zasu bi, tasa an tona ramuka tare da caccaka kifiyoyi a cikin ramukan, dik wanda ya faɗa sai dai gawarsa, in short ta dai shirya masu gagarumin shiri na tarwatsasu komai yawasu idan suka zo, sannan ta shirya sai sun kamo hanyar zuwa kai mata farmaki, ita kuma nata mayaƙan su biyo ta bayan fage, su mamayesu, su shigo kingdom of power su kashe King Zuhair da familynsa, su cinyesu da yaki kenan. My people's ya kuke tunanin wannan bakar cakwakiyar zata kasance?. Wlh Mammie ta gama da King Zuhair azzaluma, ta masu cutar da idan suka gane ba zasu taɓa mantawa ba, ta masu tabo gaskiya, ace matar kaninka da kuke uwa ɗaya uba ɗaya, ya uncle Abbas zai ji shi da ya yarda da ita sosai? Ga shi suna da yara har biyu da ita, ace matarsa ta cutar da ɗan uwansa mai kaunansu, kai akwai ciwo matuƙa wlh. Ni kuwa nace Aliyah tana can yana haukar yadda zata auri King Zuhair bata san shirin ƴar uwarta ya wuci tunaninta ba, akwai cakwakiya gaskiya. To bari dai mu leƙa wani wajen tun da su waɗan nan cakwakiyarsu ya wuci tunani, kowa kawai duniya yake so, wayaga Mammie a kan karagar mulkin Kingdom of power? Wannan ina ga zalincin da zata yi ba'a taɓa yin irinsa ba! Zuciyarta a bushe yake babu ɗigon imani ko kaɗan gaskiya, ta wuci tunanin mai tunani. Ku baku yi mamakin tsafin da take yi bane? Ai Queen Zarina ta bata kambun tsafin hegiya. Izuwa yanzu na san kun ɗan fahimci wasu abubuwa game da sarkakiyoyin da ban kai ga fara warware maku su ba!.. let's go dai, akwai game matuƙa a gaba. __________________________💘 JIMETA Ya ruɗe sosai kamar ba shi ba, ya nemi dik wani sukuninsa ya rasa, ba zai iya cigaba da gani bane yasa ya kare, ji ya yi anya ma zai iya sanya mata ruwan nan a jiki kuwa? Ko dai ya je ya kira bappa ne?. Wata zuciya ne ta amsa mashi da ina bai kamata ya kira bappa ba, ai abin kunya ne ma wani ya duba mashi lafiyarta. Ƙasa ya yi da kai tare da ɗan runtse idanunsa yana jin wani irin yanayi da bai taɓa ji ba a jikinsa, shi ya rasa meyakamata ya yi kuma a yanzu. Numfashi da ɗan karfi ta ja, a hankali ta huro iska mai zafi daga bakinta, a saman face ɗinsa ta hura wannan iska, saboda ya sunkuyar da kansa a dai'dai saitin face ɗinta. Jin yadda zazzaɓi nata ya tsananta har iskar bakinta yake da zafi sosai ne yasa shi ɗan ɗago kansa, a hankali ya waro idanunsa a saman face ɗinta. Wani irin tausayinta ne ya kara shigarsa, ya ɗan kura mata idanu kaman mai tunanin wani abin. Can kuma ya kai hannu ya ɗauko ruwan da ya ajiye a gefe, jikinsa dik tamkar wanda aka zarewa laka, a hankali ya fara sanya ɗan'kwalin nata yana matse ruwan, hannunsa har kerma take yi wajen sanya mata ɗan'kwalin a saman goshinta. Jin abu mai sanyi ya taɓata ne yasa bata san lokacin da ta kai hannu tana ƙoƙarin kankame dik abin da yake kusa da ita ba. Kun san idan mutun yana zazzaɓi baya son abu mai sanyi ta taɓa mashi jiki, to hakance tasa ta ƙanƙame shi. Rigarsa ta ƙanƙame ta wajen kirjinsa. Ƙasa ƙasa a hankali hankali ta fara kuka, sannu ya rinƙa yi mata muryarsa tana sarkewa kamar ba shi ba. Haka ya rinƙa bin jikinta yana sanya mata wannan ruwan har sai da ya ji jikin nata ya yi sanyi sosai, sai dai kuma yaki yarda sam ya nufi kirjinta da wannan ruwan, sai ya yi kamar bai gani ba, amma kuma na zuci tana zuci. Sai da ya kammala ya sauke kwanon ruwan ƙasa, sannan ya ɗan tallabota, a kunne ya fara ambatar sunanta. A yanzu ta fara gare kanta, dan jikin nata ya ɗan sassauta mata. Barci ne ya ɗan ɗauketa irin wannan barci na ƴan mintunan. Zuba mata idanu ya yi yana ta karewa gurun wuyarta kallo, shi dai wannan abin ya tafi da imaninsa sosai, amma kuma abin dariya abin mamaki shi ne sai satar kallon tula tulanta yake yi kamar wani mara gaskiya, ya kalli abin da bai taɓa kallo ba, ji yake kamar ya kai hannunsa ya taɓa, sai kuma ya ji ba zai iya ba, kunnyarta yake ji...... Ni fa idan Jaish ya yi wata tsiya ya sake cewa kunya yake ji sai na ji kamar abani bulala na zane ɗan rainin wayo, ashe Jawad yasan kayansa da ya ce kunyar rashin kunya ne, to idan ba kunyar rashin kunya ba yaushe zaka gama sanyayawa yarinya jiki da tsumma da ruwan sanyi, sannan yanzu tsabar ikkanci ka wani ce kana jin kunyar tula tula? Yau ga tsiya da iyashege wajen Jaish. Ya shagala da kalle mata su sai gani ya yi ta waro idanunta da suka rikiɗe suka yi jajir. A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta. Mamaki ne ya kamata na ganinsa a kusa da ita, sai take jin kamar mafarki take yi, dik sai ta ji jikinta kamar ba ita ba, dan ta tabbatar da cewa shi ne sai ta ambaci sunansa. "Hamma". Ɗan dawo da kallonsa a saman face ɗinta ya yi, can ƙasan maƙoshinsa da kyar murya na sarkewa ya amsa da na'am, yaga tula tula har voice ɗinsa ta daina fita sosai, bawan Allah yaron Mommarsa........😅 Jin ya amsa yasa ta tabbatar da cewa e shi ne ba gizo ba, dan haka sai ta yunkura zata tashi, sai a lokacin ta lura babu riga a jikinta. Ai a miliyan ta wani irin zabura tare da miƙewa a hanzarce, jikinta nan take ya fara kerma, sai ta rasa ina zata sanya ranta, ga shi babu abin da zata rufe jikinta a kusa, sai kawai ta zauna shiru tare da fashe mashi da kuka kanta a ƙasa. Dik da yasan me take yi wa kukan, amma abin ya ɗan bashi mamaki na ganin yadda ta zabura ta kuma tsorata har haka, sai kace bata taɓa zanin ko alif a makaranta ba, kuma tasani sarai, kawai dai kunya ce ta yi mata yawa, amma tsab tasan komai, sannan kuma bayan auren nan nasu ma Inna Rabi ta kara fayyace mata komai. Gyara zamansa ya yi tare da ɗan janyota jikinsa, takurewa ta yi waje guda kamar wadda aka watsawa ruwan kankara a lokacin hunturu. Kuka take yi ƙasa ƙasa, a cikin kunnuwanta ta tsinkayo sanyayyar voice ɗinsa yana faɗin. "So kike yi zazzaɓin ya dawo ko?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a. "To meyasa kike kuka? Ko dai baki san idan kina kuka sake dawowa zai yi bane?". Shiru bata amsa mashi ba, saboda bata da abin sake faɗa. "Kin manta ni mijinki ne da dan na ganki sai ki rinƙa yi mun kuka?". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "A'a ban manta ba". "To meyasa kike kukan?". "Babu komai". Ta bashi amsa da kyar. "Kin manta ɗazun kin ce ba zaki sake zubar da hawayenki ba? Kin manta zaki tayani cika alkawarin da na ɗauka?". Sake rigar tasa da ta riƙe ta yi ta fara goge hawayen face ɗinta, cikin sanyin murya ta ce. "Ka yi hakuri ba zan sake ba, na tuba". Hannunsa dikka biyu yasa ya rungumeta da kyau. "Tom shikenan ki yi murmushi". Sam ta rasa dalilin da yasa idan ya ce ta yi murmushi ba zato ba tsammani take jin murmushin ya kwace mata, yanzu ma haka ne bata san lokacin da murmushin ya kubce mata ba Zuba mata idanu ya yi yana kallonta, cikin dabara ya kai hannu ya cire paipan da ya rufe hasken fitillar yasa basu ganin juna sosai. Nan take haske ya haskata sosai, ta yi wani irin kyau sosai yadda take murmushin ga guntun hawaye a face ɗinta, haba kafeta da ido ya yi shi kansa ya rasa a wani matsayi zai ajiye kansa a wannan hali. Har cikin ransa yake jin tula tulanta da suke mashi kwalele a jikinsa na kwanciya da ta yi a jikin nasa, ji yake yi kamar ya kai hannu ya taɓa, amma kuma ba zai iya yin hakan suna kallon juna ba, sai dai in baya kallonta bata kallon shi, ni dai PRINCESS TEEMA ina ganin sabon iskanci wajen Jaish wlh, wannan kalar salon tasa fa hmmmm bari dai na yi shiru. Yadda take murmushi ba ƙaramin tafiya da imaninsa ta yi ba, matsowa ya yi daf da face ɗinta, hakan yasa ta ɗan yi kasa da kanta. "Murmushi yana yi maki kyau sosai.........." Ɗan dakatawa ya yi da maganar ba shiri, haka kawai hawansu dutse ya faɗo mashi a ransa a dai'dai wannan lokacin, zanen sunayen mutanen dake saman dutsen ne ya faɗo mashi a ransa, wani irin shock ya ji a jikinsa kamar wadda wutar lantarki ta ja, ƙoƙari ya yi ya iya furta wata suna da ya gani a rubuce a wajen sai kuma ya kasa, ya ji kamar ya manta wasu harufan sunan. Ɗan dafe kansa ya yi yana jin ɗan jiri jiri haka, a idanunsa ya fara ganin motsin abubuwa da dama, kunnuwansa ne suka tsinkayo mashi muryan Jawad in da zasu rabu a airport yana faɗin. "In ka sauka ka kirani, saura ka manta da ni. Da ɗan karfi ya dafe kan nasa, sai kuma muryarsa ta yi mashi gizo a in da yake cewa Jawad ɗin. "Ka kula mun da Auta ni dai, kuma kira dai sai na yi barci na tashi". Amma ku my people's me kuke tunanin ya kawo Jaish Nigeria? Akwai matsala fa. Da ɗan karfi ya furta wash yana dafe da kansa. Da sauri ta ɗago kanta, ganin ya dafe kansa ne yasa ta kai hannunta saman kan nasa ba tare da ta san ta yi hakan ba, ta ruɗe ne, a tunaninta kan nasa ne yake yi mashi ciwo. "Sannu hamma". Ta faɗa tana taɓa goshinsa. Jin muryarta yasa ya dawo da kallonsa a kanta, sai kuma dik wasu tunanin da suke yi mashi gizo ɗin suka kau, ya koma normal Hamman nasu ba Jaish ba, kan nasa ma ta daina juya mashi. Ajiyar zuciya ya sauke, da alama ƙwaƙwalwa tasa tana yi mashi wasa ne, kamar zai dawo cikin hankalinsa sai kuma abin ya sake gagara, da alama idan ya cikaro da abu mai karfi wanda ya saba da shi sosai a baya kamar dai gimbiya Zunaira ko King Zuhair or mommarsa haka zai iya komawa normal, yanzu haka kunga yana kallon Mahnoor ce kamar Zunaira yasa ƙwaƙwalwar tasa take yi mashi wasa haka, kunga idan yaga Zunairan ainahi dole ma ya koma daidai. Kun san cewa tsawon Mahnoor da Zunaira ɗaya ne, sannan yanayin face ɗinsu ya ɗan yi shige kaɗan, ita ma Mahnoor bata da kiɓa kamar Zunaira, suna dai ɗan cike ɓul ɓul ne, in short dai yanayin jikinsu guda ne yasa yake yi mata kallon Auta. Sannan maganarta a sanyaye kamar Auta, wlh dikka yaran Mommar haka maganansu yake, voice ɗinsu a sanyaye, to haka ita ma Mahnoor voice ɗinta yake. "Hamma kanka ne yake ciwo?". Ta faɗa a ɗan ruɗe. Ɗan sake fuska kaɗan ya yi. "A'a babu komai". Wani irin ajiyar zuciya da ta sauke ne yasa ya ɗan kara waro idanunsa a kanta, mamaki ne ya kama shi, meyasa take yawan damuwa da damuwarsa ne? Ya jefawa kansa tambaya, idan abu ya samesa sai ta fi kowa nuna damuwanta. "Muje kici abinci ko?". Ya yi mata raɗa a kunne idanunsa a kan gurun wuyarta. "A'a hamma ni na ƙoshi". "Da gaske?". Ya yi tambayar cikin zolaya. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Hannu ya kai saman wuyarta, dan ya kasa hakuri bai taɓa gurun nan nata ba. "Wuyar nan naki ya mun kyau". Ya faɗa kamar mai raɗa. Sai a lokacin rashin riga a jikinta ya faɗo mata a rai, ɗan mutsu mutsu ta fara yi a jikinsa, tana son kara shigewa jikin nasa ta ɓoye kayanta. Shi kuwa sai satar kallonsu yake yi dama tun ɗazun, kawai ya yi mata dabara ne ya yi kamar baya kallonsu, amma yana ankare da su yana baiwa idanunsa abinci. "Meyafaru? Ina kuma zaki je?". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kan idanunta. "Zan je in ci abincin ne". Ta faɗa daga ji ba daga zuciyarta maganar ta fito ba, dan ta samu hanyar guduwa ne kawai. Yatsarsa ɗaya ya ɗaura a layin gurun wuyarta, daga shi har ita sai da gabaɗaya jikinsu ya amsa. Nisawa ya yi tare da ɗan jan yatsar tasa kamar yana zana mata layi ya bi layin gurun nata. Ji ta yi tamkar wanda ake zarewa wasu abubuwa a cikin jikinta, har cikin ɓargon ƙashinta ta ji hakan. "Wato saboda na taɓa wuyarki ne zaki ce zaki ci abinci ko? Ba ɗazun kin ce kin ƙoshi ba? So kike ki gudu ko?". Yadda ya yi maganar kamar wanda yake cikin maye zai sa ku fahimci lallai shi kansa saƙon ta ratsa shi. Zancen Jumma ne kawai ya faɗo mata a ranta, bata san lokacin da murmushi ya kubce mata ba, a tsakiyar kirjinsa ta cusa kanta tana kara sakin murmushi, shi kansa ta so sanya shi murmushin a yadda take gwada tsantsar yarintarta a fili. Wai tana kunya kuma ta kara shigewa jikinsa, daga shi har ita sai ka rasa gane shin rashin kunya ne ta yi masu yawa ko dai kunya!. Amma shi dai su Arɗo ne suka ɓata shi, su suka koya mashi wannan abin dikka, time da yake wajen Mommarsa ai kunga babu ruwansa, bai san komai ba...........😅 Ganin ta kara shigewa cikin jikinsa ne yasa ya ji daɗi ta kara ratsa shi hakan kuma ya bashi damar cigaba da shafa mata tsokar wuyarta mai daɗin taɓawa. Hannayenta ta zura ta baya ta ƙara kwanciya a jikinsa da kyau, Jumma ta ce mata kwanciya a jikinsa zai sa ya kara sonta, shi ne ta gwada, ni kuwa na ce in kuwa kika ɗauki hakan in kinyi na yau kin ci banza to kika kara dai da wuya ya kyaleki ato, dan fa jinin King Zuhair mai mata har uku ne.......🤣 Yo in banda shegen jaraba irin na King fisabilillahi mata har uku fa, amma dai na yi shiru kada ace bani da kunya na sakawa surukina baban Guyson ɗina ido.......🙄🌝 Aa su more rayuwarsu, ƴaƴansu ma su gada su more nasu rayuwar, mu kuma muna binsu da addu'ar samu ƴaƴa irin na King Zuhair dozen dozen, yo me zai dame mu?. Da alama Mahnoor bata son zaman lafiya ne, cigaba da kwanciya a jikinsa ta yi, Jumma zata kai ki ta baro a tashar jambutu Jimeta. A hankali ya kai ɗayan hannunsa saman waist beat ɗinta da suke ɗaukar hankalinsa. Ai bata san lokacin da ta zabura a miliyan zata miƙe ba, da hannunsa dake saman wuyarta ya maida ita jikin nasa ba tare da ya furta uppan ba. Shiru ta kwanta tana jin yadda yake taɓa mata beat ɗin, sai ta ji kamar yana yi nata cakulkuli, hakan yasa ta fara mutsu mutsu tana kara nutsewa cikin jikinsa da kyau. Shi kuwa ba ƙaramin daɗin hakan yake ji ba, sai ma ya sa ya cigaba da wasa da beat ɗin. Ai bata san lokacin da ta saki yar ƙara ba jin ya taɓa mata flat tummynta. Bawan Allah shi bai ma san ya taɓa wajen ba har sai da ya ji yar kararta, ya shagala ne da taɓa beat ɗin, bai san hannunsa ta gangara ba. Da sauri ya cire hannunsa yana kawar da kallonsa daga kanta, irin ya ji kunyar nan, wayyo yau ina neman Yah Jawad a wannan al'amari gaskiya, ya zo mu yi wa Jaish dariya over a tare. "Muje ki ci abinci to". Ya faɗa yana dakewa, irin yana son kawar da kunyar tasa. "Ni Hamma bana jin yunwa". Ta yi maganar muryarta a sarke. Shiru ya yi ba dan ya rasa abin faɗa ba, sai dai muryarsa da ta sarkafe ta kasa iya cigaba da yin magana, bashi da zaɓin da ya wuce ya yi shirun. Ita ma shiru ta yi tana jiran ta ji me zai sake cewa. Tsawon 10 mins suna a hakan, sai kuma can kamar wanda yake cikin maye ya furta. "Meya jawo maki wannan zazzaɓin nema haka? Lafiyarki lou muka rabu da yamma fa". Cikin rashin damuwa da amsar da zata bayar me zai iya haifarwa ta furta. "Dama tun da yamma ina ɗan jin ciwon kai da zazzaɓin kaɗan kaɗan, da Nenne ta sanyani na yi mata wanki ne iskan yamma ya bugeni sai zazzaɓin ta.........." Bata kai karshen maganar ba ta dakata sakamakon ido da ya zaro mata. Sam bai san lokacin da ya furta. "Dikka kayan da suke shanye a wajen nan dama ke kika wanke su?". A tsorace ta amsa mashi da e, ta tsorata sosai na ganin ya zaro mata idanu, dan ma yanzu idanun nasa suna washewa, sun rage ja sosai. Ai bai san lokacin da ya rabata da jikinsa da nufin ya miƙe tsaye ya je ya samu Nennen ba, saboda ransa in ya kai miliyan to ya ɓaci, ai wannan rashin imani ne, wannan uban kayan har da zanin gado zata sakata wanki, shi a ganinsa ma kamar Mahnoor bai kamata ace ta iya koda shara bane a yanzu, a ganinsa yarinya ce sosai, rashin imanin ya yi yawa, to shi dai yanzu ba zai ɗauki hakan ba tun da ta zama mallakinsa. A tsorace ta riƙo hannunsa, idanunta sun ciko da kwallah sosai, sai dai bata bari sun zuboba saboda alkawarin da ta yi mashi zata dai'na yin kuka. A ruɗe ta ce. "Hamma ina zaka je? Dan Allah kada ka je ka gayawa bappana, wlh Nenne zata kasheni da duka, ta ce idan na gayawa bappa tana sakani aiki in bappa ya yi tafiya sai ta kwantar dani tasa wuƙa ta yanka mun wuya". Tana magana tana ƙoƙarin yadda zata yi ta hana hawayen idanunta zuba, bata son ta saɓa maganarsa. Allah sarki ya fahimci tana matuwar tsoron Nenne, ga idanunta sun nuna razana da firgici a kan hakan, dik sai ya ji ya kara tausaya mata, ya kuma kara jin tsanar Nennen nan, dama ashe ba iya tashinta da sassafe kawai take yi ta yi ta mata aiki kamar jaka ba, ashe muguntarta ya wuce haka, har da yi mata duka da kuma yi mata barazanar yanka ta da wuƙa, kai Nenne yar duniya ce wlh. Jikinta har kerma yake yi. Ganin hakan yasa ya zauna da kyau ya juyo suna fuskantar juna. Hannunsa dikka biyu yasa ya ɗan rufe mata idanu, nan take hawayen da suka cika mata idanun suka zubo, da tafukan hannunsa ya goge mata su, ta yi ƙasa da kai tana jiran ta ji me zai ce. Jawota jikinsa ya yi na ganin jikin nata na kerma. "Noor". Ya ambaci sunanta. Bata iya amsawa ba saboda tana cikin halin razana. "Menene ni a gareki?". Tambayar tasa yasa ta ɗago kai ta kallesa. Jaddada mata tambayar tasa ya yi ta hanyar amfani da idanunsa. Ba tare da ta kawar da kallonta daga kan nasa ba ta amsa da. "Kai Hammana ne kuma mijina". "A yanzu da ni da bappa or Nenne waye yake da iko dake?". "Kai ne kafisu iko da ni". Ta bada amsa a dame, burinta kawai kada ya gayawa bappa Nenne na wahalar da ita, baiwar Allah tana tsoron a yankata da wuƙa. Jinjina kansa ya yi kafin ya ce. "Daga yau ko tsinke kada ki sake kawarwa a cikin gidan nan idan ba kin tamnayeni ba, zan yi magana da bappa a kan hakan, dik wanda ya sanyaki aiki ki ce ya jirani sai na dawo idan ma bana nan, ki ce sai na dawo zan baki izinin yi in ya mun, idan ya sa hannu a jikinki zai dakeki ki bar masu gidan ki zo in da nake ki sameni, kada ki sake tsayawa wani ko wata yasa hannu a jikinki da sunan duka, ban yarda ba kuma ba zan yarda ba!". Cike da ɓacin rai sosai ya yi maganar. Da to ta amsa mashi, ta lura sarai yana cikin ɓacin rai, ta ji daɗi sosai na yadda ya nuna matuƙar damuwarsa a kanta, har da nuna ɓacin ransa har haka a kanta, abin ya yi mata daɗi sosai. "Hamma ka yi hakuri ka ji?". Ta faɗa kamar zata yi kuka. "Laifin me kika yi mun da zaki bani hakuri sarkin bada hakuri? Ke baki gajiya da bada hakuri ne?". "Hamma ai dik mai bada hakuri Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce ba zai taɓa taɓewa ba, ko ka yi laifi ko baka yi ba idan ance ka yi ka bada hakuri kawai a wuce wajen, manzon Allah ya albarkaci masu irin wannan ɗabi'ar, kuma yana yi masu kyakkyawar zato, to kaga nima dole na yi ƙoƙarin koyan bada hakuri ko dan na samu albarkan Manzon Allah". Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ji zuciyarsa ta yi sanyi na kiran mashi sunan Manzon Allah da ta yi, a ransa ya ji cewa shi kam ya yi dace gaskiya, har wani irin kifiyar sonta ne ya caki farfajiyar zuciyarsa, jawota jikinsa ya yi tsabar farinciki, ya rungumeta da kyau yana sanya mata albarka. Ita ma ta ji matuƙar daɗi sosai na ganin cewa maganganunta sun sanya zuciyarsa ta yi sanyi ta kuma sa ya fita daga cikin farinciki, lallai ya cika cikakken musulmi, domin kuwa dik musulmin da za'a ambaci manzon Allah bai ji zuciyarsa ta yi sanyi ta kuma shiga wani irin yanayi mai daɗi ba to gaskiya ya binciki imaninsa wlh, musulmin kwarai ko a wani hali yake aka ambaci fiyayyen halitta dole ya ji wani irin daɗi kamar wanda aka tsoma a cikin gidan aljanna, habawa ai manzon Allah ya yi ne, kai ni fa ko ni na kira sunansa da kai'na wani irin shaukin nishaɗi na musamman nake ji, sai na rasa ma ya zan kwatanta wannan farinciki nake shiga, wlh ina son Manzon Allah, Allah dai ya kara mana kaunarsa over to over. Tsab zamu sadaukar da ranmu a kansa, jininmu fansa ne a kansa wlh. Ita ma rungumesa ta yi tana murna yau ta sanya ya fita daga cikin ɓacin rai cikin ƙanƙanin lokaci, sai take jin kamar ta yi kuka saboda daɗi. Gyarawa ya yi ya kwanta tare da ita a jikinsa, ya jawo masu bargonsu ya lulluɓa masu, ya manta da ya ce tazo ta ci abinci. Farinciki samun mace ta gari mai addini ga iya magana da sanyin hali yasa ya manta da batun cin abinci, dama can shi baya jin yunwa. Shiru ta kwanta a jikinsa, hannu ya ɗaura a saman waist beat ɗin nan nata yana taɓasu kamar an aikesa. Ita barci ya fara ɗauka saboda rashin isasshen lafiya, shi kuma ya jima yana jinta a ransa, yana jin kamar ya kai hannu ya taɓa tula tulanta dake damunsa a saman kirjinsa, dik ya gama shafe mata beat, bai san ta yi barci ba, da tuni ya yi abin da ya yi niya wato taɓa mata tula tulanta. A tunaninsa idonta biyu, sai da ya ambaci sunanta zai ce ta tashi su ci abinci ne sai ya jita shiru. Sai a lokacin ya ji sautin saukar numfashinta a hankali hankali irin na mai barci. Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, a hankali kamar mai juya kyau a saman tray ya ɗan juya da ita. A saman mattress ya kwantar da ita, sai yazamana suna fuskantar juna, kamar wani ɓarawo yake yin sanɗo a abu. Hannunsa ya kai ya kashe fitilar tasu, dan ko da ta yi barci kunyar taɓa mata tula tulanta ya ji. Wai ni kam anya Jaish bashi da alaƙa da jinin mu ƴan arewacin Nigeria kuwa? Ni dai nasan mune muke da kunya sosai haka.......🌝😅🤭 Kai Jaish yana goge mun hadda har da wani kashe fitillah ɗan ikka. Abin dariya abin tausayi, hannunsa sai kerma suke yi, shi kuma ya zage sai ya taɓa, zuciyarsa sai ingiza shi take yi. Kamar mai kakkarwar zazzaɓi haka hannunsa suke yi a lokacin da ya nufi tula tulanta da su, sai zuba barcinta take yi cikin kwanciyar hankali. Wani irin azabbabben shock ya ji lokacin da ya sauke hannunsa a kansu, bai ma san lokacin da ya ɗan yunkura zai miƙe zaune ba, sai kuma ya kasa yin hakan, dan dole ya koma ya kwanta, bai kuma cire hannunsa daga kansu ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan datse idanunsa, a cikin duhunma bai yarda ba sai da ya kara da datse idanu saboda kunya. Shafasu ya fara yi a hankali hankali kamar mai tsoron taɓasu. Wani irin duniya na daban ya afka, jinsa yake yi yana shawagi a sararin samaniya. Ya afka duniyar sama jannati. A hankali ta waro idanunta waje, ta tsorata lokacin da ta ji an taɓa mata su, sai dai bata nuna tsoron nata ba, dan tasan shi ne, kunya ne sosai ya kamata, da farko bata yi niyar nuna alamar ta farka ba, amma sai ta kasa, dan shafasu da yake yi yasa tana jin shock har cikin ranta, ya hanata sukuni ne yasa ta waro idanunta waje, ta rasa ina zata sanya ranta, sai ta ji kamar yana yi mata cakulkuli ne. Shi kuwa ya shagala da shafesu yana jin daɗi bai ma san ta farka ba, ni kuwa zan ga da safe da wani ido zasu ga juna har ma su ga bappa. Ana show a Jimeta Yola yaseen. Kasa hakura ta yi, ta kasa dannewa har sai da ta yi motsin da ya fahimci ta farka, a hanzarce ya cire hannunsa ya kuma juya mata baya a dubu, abin gwanin ban dariya. Ganin ta katse mashi jin daɗinsa ne sai yasa dik ta ji babu daɗi, ta ji ta damu sosai, tunani ta fara yi meyakamata ta yi mashi a halin yanzu. Bangaren zuciyarta ne ya amsa mata da. "Ki mayar mashi da jin daɗin nasa kawai, idan ba haka ba kuma zaki shiga tsinuwan Mala'iku". Shiru ta yi tana saƙa maganar a ranta, sai taga babu wani hanya face hakan, amma tana jin kamar ba zata iya ba, tunawa da ta yi Jumma ta ce mata zata iya yin komai sai dai idan bata fara bane yasa ta yardanwa kanta zata iya, dama ta ce wa Jumam ba zata iya bane yasa ta gaya mata hakan. A hankali ta ambaci sunansa Hamma. Ba tare da ya juyo gareta ba ya amsa mata da na'am. Shiru ta yi tana tunanin meyakamata ta yi? Da ta yi tunanin idan ta ambaci sunansa zai juyo gareta ne, sai taga bai juyo ba, ba haka ta so ba sam. Shi kuwa dik kunya ce ta isheshi yasa yaki juyowa. Shahada ta yi ta matso ta kwantar da kanta a saman faffaɗar bayansa, jikinta har yana ɗan kerma saboda tsoron me zai je ya zo. Tamkar mai ciwon baki ta sake ambatar sunansa. Kada kuso ku ji wani irin ajiyar zuciya mai shegen daɗin da ya sauke jin ta kwanto a jikinsa, hakan yasa ya juyo gareta tare da amsa kiransa da ta sake yi. "Kayi hakuri hamma". Ta faɗa kamar mai tsoron yin magana. Shiru bai iya amsa mata ba saboda wani irin daɗi da yake ji, ya kasa yin magana, sai dai ya rungumeta tare da kai hannunsa saman ƙugunta, ya cigaba da wasa da beat ɗin idanunsa a lumshe. Biye mashi ta yi ta hanyar kwamciya shiru a jikinsa tana sauraro dik abin da yake yi mata. My people's nasan kuma zaku so ganin yadda za'a kalli juna da safe ko? Mata kunya miji kunya, wlh suna bani joy, to bari dai mu je wani ɓangaren mu dawo, watakila kafin mu dawo garinsu ya waye. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A..✍️🔥🕊️ ABUJA. Bayan wasu lokuta!!. Wani ɗan madaidaicin restaurant ne irin wanda matafiya suke tsayawa su ci abinci a wajen, daga ta cikin restaurant ɗin akwai ɗakin mamallakiyar wajen, wato in da take kwana kenan, jama'a sai hada hada suke yi, suna shiga suna kuma sake fita, masu cin abinci suna ci masu aikin suna yi. A ta bakin hanya restaurant ɗin yake. Ɗauke take da tray mai ɗauke da plate ɗin abinci har kala uku take ta nufi teburin abinci dake fuskantar kofar shigowa, daga ganin yanayin yadda take tafiya zaka iya fahimtar tana cikin tsananin damuwa da rashin lafiya. Maza biyu da mace guda ɗaya ne a zaune a saman teburin, su tazo ta zubewa abincin, kamar zata kifa a kansu ma haka ta ji. Daga bayanta wata yar lukutar mata gajeriya kakkarfa ta ce. "Zainab amma nace ki bar aikin nan sai kin samu karin lafiya ko? Ki je wajen ƴar uwarki ku kwanta ku huta". Juyowa ta yi idanunta jajir da su. "Ai na samu lafiya Aunty". Ta yi maganar tana tinkarar matar. "Dik da haka ni dai ki je ki huta". Da to ta amsa mata tare da wucewa can cikin ɗakin matar. A nan ta isko Khadija tana kwance saman ƴar katifar dake a ɗakin, ta tada kai da jakar kayansu, ta tasa wani hoto da kallo, rike take da hoton a hannunta. Zee tana zuwa ta leƙa hoton ai bata san lokacin da ta ce. "Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Hasbunallahu wani'imal wakil, Aunty Khadijah a ina kika samo hoton Balarabe ne ko Bature ne wannan? Kai kin gansa kaman shi ya yi kansa saboda kyau, kamar na san face ɗin nan nasa kuma, sai dai na manta a ina na taɓa ganinsa". Tun da ta shigo ɗakin Khadija bata lura da ita ba har ta yi wannan maganar dikka bata jita ba, ta luluƙa duniyar tunanin wanda take gani a jikin hoton, tana ganinsa tana hawaye, ko daga ina ta samo hoton? Allah masani sai kuma alkalamina. "Yauwa Aunty Khadijah kaman wannan shi ne wannan Jahiz ɗan kwallo da baba yake kallon wasansu kullum har yasa nima na fara supporting guy ɗin, kamar sun yi kama fa, anya ba shi bane kuwa? Kai dik da kullum cikin kayan ƴan kwallo nake ganinsa hakan ba zai sa na gaza ganesa dan yana cikin wasu shiga na daban ba, Allah ni dai nasan fuskarsa a cikin ƴan kwallon da baba yake gani, Allah yasa Jahiz ɗin ne, ina son guy ɗin nan over". Ta kai karshen maganar tana taɓa Khadija da ta yi nisa a wata duniya ta daban. Tun tasowansu suka san babansu da kallon kwallo, yana mugu mugun kaunar uncle Jahiz namu dai nasu King Zuhair, saboda tsabar kaunarsa da yake yi yasa yake da tarin jaridu masu ɗauke da sunansa, ko ban maimaita ba nasan kun san baban Zee dai yafi yawan kasancewa a tare da Zee, hakan yasa ita ma ta kamu da kaunar guy ɗin, idan baku manta ba a baya nace maku tana son kallon kingdom of power ko a tv ne, to saboda uncle Jahiz take son kallon su King Zuhair. Ta kaunacesa sosai kamar yadda babanta yake sonsa, kullum in dai wasansu ne sai sun kallah a tare da baban nata. Wani irin firgita Khadija ta yi, a miliyan ta yunkura zata ɓoye hoton wai dan kada Zee ta gani, bata san ma ta riga ta gani har ta gama surutan da zata yi a kansa ba. "Aunty khadina me kuma abin ɓoyewa? Dan Allah ki gaya mun kin san shi ne? A ina kika samu real hotonsa ba'a jarida ba kuma ba sanye da kayan kwallo ba? Wlh ya yi kama da Jahiz namu ni da baba". Tashin hankali uncle Jahiz namu kuma?. Rai a ɗan dakile ta ce. "Wannan ba Jahiz bane". Shiru Zee ta ɗan yi tana ƙoƙarin tunano fuskar Jahiz ɗinsu ita da babanta, sai kuma tunanin baban nata ya faɗo mata, nan take idanunta suka ciko da kwallah. Ita kuma Khadija ta yi maza ta ɓoye hotonta a cikin jakar da ta tada kai da shi. Wai shin mema ya kawo su Khadija Abuja? Ya aka yi suka kuɓuta daga hannun waɗan can mutanen, da gaske uncle Jahiz ɗinmu ne a jikin hoton dake hannun Khadija ko dai mai kama da shi ne? Hmmm akwai tashe tashen hankula fa. To sai mun haɗo gobe idan mai dukka ya kaimu ma ji dikka waɗan nan amsoshin, love u all guy's 💘 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 45 ABUJA. "Kai Aunty Khadijah wlh ya yi mun kama fa da Jahiz ɗinmu ni da baba, dan Allah ki gaya mun idan shi ne! Na yi iya tunanin da zan yi a kan kamanin Jahiz ni dai wlh ban ga wani canji ba, kaman shi ne". Ta yi maganar cikin ƙaguwa da son jin shin da gaske shi ɗin ne ko dai Khadijah ta fita gaskiya ba shi bane kama ce kawai?. "Zee wannan ba Jahiz bane ba, ki daina wahalar da kanki, kuma ni ban ga kamanin Jahiz a tattare da wannan guy ɗin ba, kece dai kika gani". Da kyar ta idasa maganar, saboda wani irin kululum bakinciki da ya tokare mata maƙoshinta, ta tuna da abubuwan da suka faru da ita a baya. "Shikenan Aunty Khadijah na yarda, amma meyasa kike ɓoye mun abubuwanki? Shin ni ba yar uwarki bace? Ko kina tunanin zan iya cutar dake kamar yadda Hauwa ta yi wa mama ne?". Tun da ta fara magana idanunta suka karo kwallah. Shiru Khadijah ta ɗan yi, dik jikinta sai ta ji ya yi mata mugun sanyi, tunani ta fara yi a kan idan ta cigaba da ɓoyewa Zee gaskiya to fa za'a iya samun matsala sosai a tsakaninsu, bata da biyun Zee yanzu a duniya, idan ta sa ƴar uwar tata ta fara zargin bata sonta ko bata ɗauketa da mahimmanci ba hakan zai sa ita ma ta fara ɓoye mata nata sirrin, ta kuma ja baya da ita sosai, sanadin hakan za'a iya samun rabuwar kai a tsakaninsu, a gaskiya ko zata ɓoyewa kowa bai kamata ta ɓoyewa Zee ba, yana da kyau ta gaya mata gaskiyar abin da yake faruwa. "Aunty Khadijah ki yi hakuri da abin da na faɗa idan ya ɓata maki rai, amma ni a nawa tunanin tun da ke kika tashi na kwanta, ke kika sha kika sake na kama, ke kike fara sa kaya idan sun yi maki kaɗan ki cire na saka, komai kace a gaba ina biye dake, dik in da kika saka kafa kika cire next nawa kafan ne a wajen, sai nake ganin kamar na wuci ki ɓoye mun wani abin da ya shafi rayuwarki, amma tun da baki son na sani ba zan sake tambayarki komai ba". Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka, har ga Allah tana matukar jin ciwon ɓoye mata da Khadijah take yi...... Amma fa a nan wajen wlh Zee ta yi magana mai ma'ana, wato ita ta kwanta a ciki da ta fito sai ita kuma ta kwanta, ita ta sha nono ta sake ta kama, gaskiya ta yi magana a wannan waje, dik mai hankali kuma zai san tana da nutsuwa da iya magana. Tun da ta fara magana Khadijah take binta da kallon tausayi da kuma so da kauna, har ta idasa zata miƙe ta fita ne Khadijah ta riƙo hannunta. "Zauna mu yi magana". Ta faɗi hakan ita ma kamar zata yi kuka. Ba musu ta koma ta zauna kanta a ƙasa, yau ta tuna da rayuwarsu ta baya, Jahiz yasa ta tuna da babanta, dik jikinta ya yi la'asar. "Zee ina son ki sani ba wai ina ɓoye maki abu bane dan bana kaunarki ko ba ki kaina faɗa maki ba, zancen bana kaunarki ma ai bata taso ba, kin fi kowa sanin kece farinciki na, kuma idan da babu ke kin san da shaiɗan ya jima da cin galaba a kaina wajen zugani na hallaka kaina da kaina..............". Dakatawa da yin maganar tayi tana ƙoƙarin share kwallar da take zubo mata, ta kuma sauke ajiyar zuciya. "Kiyi hakuri, ni dama ina ɓoye maki wasu abubuwa ne dan ina ganin kamar baki yi girman da zaki iya rike wasu maganganu ba, amma ki yi hakuri, na miki alkawarin zan faɗa maki komai, kuma daga yau ba zan sake ɓoye maki komai da ya shafeni ba". Tun da ta fara magana idanun Zee yake a kanta, ta ma kasa iya rarrashinta, so kawai take yi ta faɗa mata gaskiyar al'amari. "Wannan hoto da kika ga na ajiye a yanzu tabbas shi ne wan da ya mun wannan ciki, shi ne uban cikina, and then kamar yadda na faɗa maku ranar da ke da maman Hanif a parlon to gaskiya ne, sai dai ban faɗawa maman Hanif cewa bayan mun yi rayuwa da shi a gida daga ni sai shi ya kaini wani gida wanda ina zaton familynsa ne a ciki ba, ni ban san su waye su ba, amma a yadda naga hotonsa da wani babban mutun yana manne a jikin bangon parlonsu to ina zaton daddynsa ne, dan sun yi kama da na jikin hoton sosai, ni kaina na yi mamakin ganin yana mugun kama da Jahiz ɗinku, ina ji a jikina ba Jahiz bane, amma idanuna sun gaza iya karyata mun hakan.....". Shiru ta ɗan dakata tana cigaba da goge kwallan dake zubo mata, abu ɗaya take tunawa ya sanyata irin wannan kukan, ba komai bane kuma face disvirjin ɗinta da ya yi, ba zata taɓa manta wannan azaban da ta sha ba, shiyasa a dik lokacin da ta tunasa sai ta yi kuka dan sai ta tuna wannan ranan. "Aunty Khadijah da ya kaiki gidan me ya faru?". Zee da hawaye suka gama wanke mata fuska ne ta jefa mata wannan tambayar. Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗan yin gyaran murya dan ta samu damar cigaba da yin magana da kyau. "Akwai wata mata wadda ita ce ya sanya ta zubar mun da cikina, ina tunanin mom ɗinsa ce, basa kama da ita kam sam, amma a nawa tunanin ne mom ɗinsa ce, baturiya ce fara tas da ita, ita ta kawo likitoci kala daban daban suka yi yunkurin zubar mun da cikin, bana son in gaya maki irin azaban da na sha, bana son ki ji bakar wahalar da na ɗanɗana a sanadin ƙoƙarin zubar da wannan ciki da wannan mata ta yi mun........." Dakatawa ta yi a wannan gaɓa ta rushe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Matsowa kusa da ita sosai Zee ta yi, ita ma tana kukan amma hakan bai hanata ta rarrashi ƴar uwar tata ba. "Zee dan Allah ki barni na yi kuka sosai, zuciyata zafi take yi mun, idan ban yi kuka ba zata iya buga mun". Ta yi maganar cikin muryar kuka da yake fita haɗe da shessheƙa. "A'a Aunty Khadijah, ba dan ni ba, ba dan kowa ba, dan babynmu dan Allah ki yi shiru kuma ki daina damuwa kin ji? Wlh tallahi ina son koma menene a cikin cikin nan naki, ina kaunarsa fiye da kaina, dan Allah kada ki yi sanadiyar salwartansa". Still tana kukan ta ce. "Zee tun da kika ga dik wannan wahala da na sha, dik wannan azaban da na ɗanɗana, dik waɗan nan turawan likitoci da aka kira domin cire wannan cikin sun kasa iya fitar da shi, har jini na zubar amma cikin bai fita ba, daga nan yakamata ki san cewa ta Allah bata mutun ba, ba a haifi wanda Allah zai ce e shi kuma ya ce a'a ta yi wu ba, ba haifa ba kuma ba za'a haifa ba, Allah ya ce ɗana sai ya zo duniya, ba'a yi abin da zai tare shi ya hanasa zuwa ba, dan haka ki kwantar da hankalinki, idan namiji ne a cikina to Ahmad sai ya zo duniya, idan macece kuma to Zainab sai ta zo duniya da izinin Allah, kuma wlh sai Allah ya saka mun ya kuma nunawa duniya waye su". Ta kai karshen maganar tana kifa kanta a saman gwiwonta saboda wani irin kululun bakincikin da ya tokare ta. (My peoples kun san me nake tunani?🤔😅 Idan da gaske cikin uncle Jahiz ɗinmu ne me kuke tunanin Akka zata yi ma ɗan autan nan nata?😅 Ni dai ina tunanin yaseen sai ta yanke bananarsa🤣🤭 a yanketa kawai muga ta tsiya ato🤸) "Haka ne Aunty Khadijah, amma dan Allah ki daina damuwa kin ji?". "Hmmmm Zee dole na yi bakinciki na kuma damu, sun cutar dani sun kuma wahalar da ni, mom ɗinsa ta azabtar dani wajen yunkurin cire mun ciki, tasa aka daina bani abinci a gidan, ta tsaneni kamar ta kasheni, kuma dik abin da take yi ba mai ce mata uppan a cikin gidan, shi ma yana sane da komai amma bai tanka ba saboda baya son na haifa mashi cikin, baya son ɗan shege". "To Aunty Khadijah kin manta da akwai Allah ne da har kike ɓarnar hawayenki a banza?". Kai ta ɗago tare da fara girgizawa. "Ban manta ba Zee, amma kukance ta gaza dakatawa, na gaza iya mantawa da su a rayuwata!!". "To amma ya aka yi kika samu hotonsa mai kyau haka?". Zee sarkin tambaya da son ta ji komai dallah dallah. "Ba iya hoto ɗaya nake da shi ba, ina da su dayawa, kuma a ɗakinsa na ɗaukesu". Ta bata amsa tana aikin goge hawayen da suka ki dakatawa daga zuban da suke yi. Janyo jakar Zee ta yi tare da buɗesa, ciro hotunan ta yi wajen kala shidda, dik hotunan sanye yake da kayan ƴan kwallo a jikinsa, guda biyu ne kawai yake sanye da kananan kaya. Zuba mashi idanu Zee ta yi tana mamakin irin kyansa da zubin kyakkyawar halittarsa, a yadda ta ga face ɗinsa tabbas za'ayi mutun mafaɗaci mai kuma kafiyar balain, sai dai kuma a yadda yake ɗin nan da wuya ya yi rashin imani har haka, to meyasa yake son zubar da cikin nasa? Yasan baya son cikin ya bari ta ɗauka? A jikin ɗayan hoton nasa ga shi nan riƙe da wani ɗan matashin yaro da ba zai wuci 7 years ba mai balain kama da shi, ko dai shi ma ɗan sa ne?. Ta jefawa kanta tambaya. Da wuya ma in wajen iyayensa ya kaita! Kila wani waje ya kaita dan a zubar mata da cikin, idan baya son asirinsa ya tunu to dama meyasa bai ɗauki matakin hana cikin shiga ba?! Kai gaskiya akwai matsala, kila labarin nan sun yi wa Khadijah hauhauwa ne yasa watakila bata fahimci ainahin kan abubuwan da suka faru ba, ita dai Zee a nata tunani dole akwai abin da ya tsaɓa ba daidai ba a cikin wannan al'amari. Amma kuma tasan yanzu ko ta gayawa Khadija ba yarda da ita zata yi ba, ba zata taɓa yarda akwai abin da ya saɓa ba, dan ta yi nisa a son ɗaukar fansa, wutar fansa ce kawai take ruruwa a cikin zuciyarta. Wai taya ma aka yi suka zo Abuja? Mu koma baya na kwanaki da suka suɗe. Kamar da na gaya maku wannan restaurant ɗin yana ta farko farkon shigowa cikin garin Abuja ne. To wannan mota da ta ɗaukesu dai garin Abuja ta nufa da su, sai dai bai kai ga shiga cikin gari ba cikinsa ya fara murɗa mashi, hakan yasa ya yi parking a bakin hanya ya fito daga cikin motar, cikin daji ya nufa dan a tunaninsa bayan gari zai yi, bai san cewa mai sama ne ya yi kira ba, kuma dole a amsa. Allah mai iko mai yin yadda ya so, dik abin da zai yi kuma baya shawara da kowa, zai karɓi rayuwar bawa a lokacin da ya so, idan ya ga dama a rana ɗaya zai iya bawa uwa wani yaron ya kuma karɓi wani daga cikin ƴaƴan nata, mutuwa bata sallama, wani ma yana cin abinci yake tafiya, akoma ina a koma yaushe mu rinƙa tunanin ba zamu bar wajen da muke a raye ba, yawan tunan mutuwa zai sa mu yi aikin alkhairi sosai, Allah baya kuskure, komai ya yi dai'dai ne, mutuwa baya sallama. Shi dai wannan bawan Allah yana shiga cikin daji da nufin ya yi bayan gari kawai rai ta yi halinta, babu ciwo babu komai, su Khadijah kuwa ya barsu cikin mota suna ta zuba barci, kafin ya fita motar kuma dama sai da ya kulle ko'ina, rashin samun wadatatcen iskan numfashin ya farkar da su daga barci, dama kuma da alama maganin da aka shaƙa masu ɗin karfinsa ya kai time na karewa. Hakan yasa suka farka, sai suka rasa ta yadda zasu yi su fita, kun san rashin samu iska ba karamin cutar da rai yake yi ba, dan haka sai suka fara rasa ina zasu sanya ransu, suka fara neman mafita ido rufe. Wani abin suka samu suka fara bubbuga glass ɗin motar da shi, amma abin ya gaza fasa glass ɗin. In short dai har Zee ta fara galabaita tana ƙoƙarin sumewa, ita kuma Khadija da alama jinin cikin jikinta yana da karfin da yasa ta iya juriya fiye da Zee. A takaice dai suna cikin halin mutuwa ko rayuwa Allah ya kaɗo masu wani bafulati mai kiwon shanu, Allah yasa kuma ya zo ya jingina da jikin motar tasu yana jiran dabobin nasa su gama sallaka titin. Dama ance mutuwar wani tashin wani. Bubbuga glass ɗin da karfi Khadija ta yi hakan yasa ya ja hankalinsa a in da ya juyo garesu, da alama ya saba ganin irin haka, dan kuwa yana ganinsu bai yi mamaki ba, bai kuma ɗaga hankalinsa ba, sai ma ɗaga sandarsa da ya yi ya makawa glass ɗin motar ta gaba, nan take glass ɗin ta tarwatse, dik yadda aka yi ya saba da irin hakan. Yana fasa masu glass ɗin iska ya risƙesu suka fara jan numfashi da karfi karfi. Bai bar wajen ba har sai da ya taimaka masu suka fito daga cikin motar, sai dai kash baya jin Hausa su kuma basa jin fillanci, hakan yasa basu iya sanin komai dan gane da shi ba, shi ma kuma bai iya sanin komai dangane da yadda aka yi suka zo nan ba, ya so ya gaya masu cewa ai irin wannan satar mutane suke yi su shigar da su kudu su sayar da su, amma sai ya rasa ta ina zai gaya masu su yi taka tsantsan, sun yi sa'a ba'a kai ga fita arewa gabaɗaya da su ba. Bashi da wata zaɓin da ya wuce ya kama hanya ya bi bayan shanunsa su cigaba da tafiyarsu, haka kuwa aka yi, ya bi bayansu suka tafi ya barosu tsaye a wajen a galabaice, ga kishin ruwa da yunwa, ga kuma mangariba ta kawo kai. Bawan Allah ya so ya faɗa masu su gudu su bar wajen, amma ba halin yin hakan. Da yake suma a yanzu sun fahimci satosu aka yi sai suka fara ƙoƙarin barin wajen, amma saboda ƙoƙari irin na Khadija sai da ta fito masu da akwatin kayansu daga cikin motar, sannan suka nufi barin wajen. Wannan shi ne sanadiyar rashin lafiyar Zee da kuka ji wannan mata mai restaurant ɗin tana ce mata ta je ta kwanta ta huta har sai ta kara samun lafiya, to wannan shi ne silar rashin lafiyar. Cikin garin Abuja suka nufa, dan babu nisa da su. Sai dai basu iya ƙarisawa ba suka samu waje a bakin hanya suka zauna suna mai da numfashin, yunwa da ƙishirwa ya fi karfin. A nan Allah ya jefo masu wannan mata ta zo wulgawa ta wajen, shi ne ta ga sun, ta tausayi masu yasa ta tsaya ta tambayesu me suke yi a nan, Khadija ce ta iya faɗa mata abin da yake faruwa da su. Baiwar Allah da yake ita ma ƴar arewa ce, yar Kano ce sai ta tausaya masu, ta kuma ji daɗin ta ga ƴan uwanta yan Kano, kun san kanawa fa akwai halacci batu na Allah wlh, suna da halaccin sosai. Wannan shi ne a takaice yadda aka yi suka koma hannun matar nan mai restaurant, ta kula da su tamkar ta sansu, ta yi masu halacci da kyautatawa, ta yi jinyar Zee har da saya mata magunguna, akace na Allah basa karewa a duniya, Zee tana son tayata aiki ma ta hanata wai sai ta samu lafiya, to kunji abin da ya faru. Mu koma kan labarinmu. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ KINGDOM OF POWER. Kwance yake a saman bed ɗin mommarsa, ya yi nisa a cikin barcin da yake yi, da alama barcin ta yi mashi daɗi sosai, yana lume cikin lallausan bargo mai jikin mage, kyakkyawan arab hairn nan nasa ta sauko har ta rufe mashi idanu, kamar dai kullum ya yayyanke bakin gashin ya dai'daita, kai guyson dai kyau iya kyau ne, madaran kyau babu sirki. A kunne Mummyn Gimbiya Chuchu ta fara faɗa mashi. "Happy birthday to you our Guyson, happy birthday to you". Auta dake saman bed ɗin ita ma ta ɗayan gefensa ne ta karɓi zancen mummyn da cewa. "Happy birthday my yah Omar, ka tashi yau ranarka ce". Su Mommar dik suna cikin ɗakin, idan baku manta ba dama shi guyson ai ɗan ɗakin mummyn Chuchu ne, so ita ta fara yi mashi celebrate ɗin, ta shirya mashi small party a part ɗinta wanda family ne kawai zasu hallata, ta so a lokacin birthday ɗin nan nasa su shirya gagarumin party, amma sanin kanku ne yanzu kingdom of power babu kwanciyar hankali, so dole dik abin da zasu yi su rinƙa takaitawa ko dan Akka da take cikin damuwa, wannan dalilin yasa ba'a shirya gagarumin party kamar yadda ta so ba. A hankali ya fara motsa idanunsa, bai kai ga warosu waje ba ya saki wani irin ƙayataccen murmushi wanda ya kara fito mashi da tsantsar kyansa, dimple ɗinsa dikka suka lotsa. Auta da Chuchu har suna rige rigen sanya hannunsu a ramin dimple ɗin nasa, gabaɗaya ƴan'matan King suna a cikin ɗakin, dik sun zo tayasa murnar birthday. "My mummy yaushe wai na kara shekara ne?". Ya faɗi hakan ba tare da ya waro idanunsa ba, yana magana yana turo baki. "Wake up my son, today is ur day". Ta faɗa tana sanya hannu ta ɗagosa. Yana turo baki ya miƙe, sai kuma ya kwantar da kansa a jikinta yana waro idanunsa waje. Ganin gabaɗaya ƴan uwansa a cikin ɗakin ba karamin sanyaya mashi zuciya ya yi ba, a hanzarce ya kara waro idanunsa waje, yalwar murmushi ne ta kara mamaye face ɗinsa. Cikin tsantsar farinciki ya ce. "Momma all of u kun zo ne saboda yau it is my birthday day?". Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbatarwa, wani irin daɗi ne ya karara mamayesa. Ɗago kansa ya yi ya kalli uwar gayya wato mummy. "Mummy tun ina Dubai kullun ke kike fara yi mun celebrate na Birthday ɗina, baki taɓa yin missing ba, i really love u my Mummy". "Love u too my son". Ta kai karshen maganar tare da manna mashi sumbata a goshi, kara sakar mata murmushi na musamman ya yi kafin shi ma ya bata hot sumbata a kumatu. Mommarsa har mamaki irin kaunar dake tsananin mummyn Chuchu da Guyson take yi. Tun yana jariri take bala'in sonsa, daga nan har Dubai take tafiya dan ta je ganinsa, ko da yake dama da shi da Auta sun fi sauran yaran momma dikka farinjini, ba komai ne yasa hakan ba kuma face yadda suke karrama ɗan adam, suna son mutane, kun ga dai yadda Auta take girmama har warriors ɗin cikin kingdom ɗin. Mommarsa ce ta ƙariso wajen tare da miƙa mashi hannu. "Zo mu je kayi wanka ka shirya". Ɗan make kafaɗa ya yi. "Momma ni dai a'a, sai dai idan ke zaki yi mun wankan". Ɗan zaro idanu ta yi. "Omar baka canza hali ba ko? Kana da 17 to 18 years ɗin ne zan yi maka wanka?". Kai ya gyaɗa mata tare da karawa da cewa. "Ni momma in dai ba zaki mun ba yau ba zan yi wanka ba da datti zan zauna". Mummy ce ta ce. "A'a kwantar da hankali ɗan lelena, Rahilarh maza haɗa ruwa ki wanke mun shi fes bari na kawo mashi kayan da nake son ya sa". "Good my mummy, that's why i really love u". Ya yi magana tare da rungumarta. Ɗan siririn hararar wasa Mommarsa ta watsa mashi kafin ta nufi toilet, bata isa ta yi wa mummy musu ba, dan zaman amana suke yi, kuma mummy ita ce babba da ita wato uwargida kenan, bada ban ita ba aikuwa ba zata yi wa Guyson wanka ba, babba da shi ɗin, amma fa ita momma bata sani ba wlh a Dubai Ramish yi mashi wanka yake yi, sai ma idan bashi da lafiya har su Dr Raj wanka suke yi mashi, to shi ya saba shiyasa baya ma jin kamar ya girma, su suka saba mashi, kun san idan ciwon nan nasa ta tashi fa jariri yake koma masu, su Ramish su yi ta fama kamar masu jego sabbin haihuwa.........😅 Sai yi mashi congratulations su Fanan suke yi, Allah ya gani Fanan tana kaunarsa sosai har cikin ranta, sai ta rinƙa ganinsa kamar Jaish ɗinta, shi ma dik yana balai'n kaunarsu. "Mummyna ina Yah Jaish da Yah Jawad su basu zo yi mun congrats ba? Kuma shi Yah Jaish ma tun da na zo bamu haɗu ba, idan na tambayi momma ina yake sai ta ce mun zai zo mu haɗu, na je part ɗinsa ya fi a kirga bana samunsa, shi ma Yah Jawad bana wani ganinsa sosai". Kamar zai yi mata kuka ya yi maganar. Allah sarki ya sosawa Fanan in da yake yi mata kaikayi, nan take face ɗinta ya sauya, wani kuka ta ji ya zo mata, sabon kewar Jaish ɗinta ne ya dawo mata, sabon tunaninsa ya dawo mata, dik sai ta shiga babin sabon damuwa. "My son Jaish ya yi tafiya ne, amma soon zai dawo, shi kuma Jawad ina ga aiki ne ya yi mashi yawa yasa baka ganinsa, amma ka yi hakuri zasu zo su yi maka ko da zuwa gobe ne". Cewar Mummyn Chuchu. "Mummyna kin san fa last year a lokacin da nake school da Birthday ɗina ya zo Yah Jaish baya Dubai, yana kasar China, yana tsaka da aiki ma ya dakatar ya zo mun congrats a Dubai, ya zo da safe ya koma da yamma, ni gaskiya ina jin dai akwai wani abin, dan ni nasan babu abin da yake hana ƴan uwana zuwa gareni dik wuya dik daɗi". Kamar zai yi mata kuka ya yi maganar. Auta ce ta ce. "To Yah Omar baka yi korafi a kan saura ba sai a kan Yah Jaish ɗina? Ai su Yah Ramish ma basu zo ba". Ta kai karshen maganar ita ma kamar zata yi kuka. Bata son ta ji za'a kawo laifin Jaish a waje, yanzu sai ta karesa. "To waye ya ce maki su Yah Ramish ba zasu zo ba? Ki jira mana ki gan......" Bai idasa maganar ba idanunsa suka sauƙa a kan Ramish and Bilal dake tsaye a bakin door room ɗin suna kallonsa. Ai bai san lokacin da ya miƙe daga jikin mummy a miliyan ya diro ƙasa daga saman gadon ba, da gudu ya tafi wajensu, yana zuwa ya daka wani uban tsalle ya haye jikin Ramish da ya buɗe mashi hannayensa. Ai ita ma Auta a miliyan ta miƙe ta nufesu, bakin unexpect kenan, ko King bai san da zuwansu ba, sun yi masu bazata, murna a wajen kanne da iyayen nasu ba'a magana. "Yah Ramish is that u?". Ya faɗa cike da murna sosai. Shi kuwa Dr Raj yana parlourn a zaune, ya ce su fito su same shi a wajen, murnar birthday suka zo taya Guyson sai su halacci ɗaurin auren Yah Rizwan and Chuchu. Kash ba dan wannan matsala da kingdom of power take ciki ba ai da kunga birthday da ba'a taɓa shirya party irinsa ba, da an tashi kan jama'a, amma ba komai akwai gaba ai. Momma da ta fito daga cikin toilet a yanzu ne ta saki wani irin haɗaɗɗen murmushi kafin ta ce. "Ramish da gaske ku nake gani?". Jinjina mata kai ya yi. "Mune our Momma". Ya faɗa ƙasa ƙasa cikin nutsuwa. Mummy ce ta sauko daga saman bed ɗin ita ma. "Wow wannan shi ne ainahin surprised ɗinmu, ina Dr Raj?". Baku tanbayeni ina su Sarina ba? Tuni sun nutsu tsit tamkar babu su a cikin ɗakin, sun saki baki suna aikin kallonsu Ramish da basu taɓa gani a zahiri da wayonsu ba, sai dai a hoto da kuma lokacin da suke yara, basu taɓa yin expert ɗin ganinsu ba, wow abin ya ƙayatar matuƙa. Ramish ransa ya ɗan sosu ganin kowa yana nan banda mamarsa, ita kaɗai ce taki zuwa, dama dai kun san ba shiri take yi da momma ba, so bata leƙo ba, ya ji babu daɗin hakan, ya so ace kamar yadda momma da mummy suke zaune cikin girmama juna da mutunta juna ita ma haka take da su, amma masifarta ya yi yawa. Ɗunguma suka yi gabaɗayansu Ramish yana ɗauke da guyson suka koma parlon, a nan suka isko Dr Raj, Bilal kuma ya ɗauki Auta, King Zuhair bai san sun zo ba, yana can suna ta aikin shirya tafiya yakin da su Hoorain zasu yi masarautar Queen Zarina, Allah sarki ni dai fatana Allah tasa kada Hoorain ya faɗa tarkon Queen Zarina da ta kafa masu. Dik in da Ramish ya motsa sai Sarina ta bishi da ido, ashe a hoto ma bashi da kyau sosai, hoto ta rage mashi kayansa, ashe a zahiri ya fi kyau, haka take ta faɗe a ranta. Fanan kuwa tunanin Jaish ne ya addabama rayuwarta, faɗin take yi da yananan yanzu da shi ma yana cikin ƴan uwansa. Aneesa kuwa da kamar aljana take sarai ta san da labarin zuwan su Ramish da ko King bai sani ba, wai ko a ina take samun waɗan nan labaran da ko iyayensu basu sani ba sai kuga ita ta sani? Anya mamarta bata tsafi kuwa? Anya basu da aljanun gado kuwa? Yarinya kamar wata yar ruwa!. Sannu da zuwa ta yi wa yayyun nata cikin girmamawa, sannan ta tafi shirin Birthday ɗin guyson ɗinsu. Ita kuwa Sarina da murna ya hanata yi masu sannu da zuwan ma guduwa ta yi izuwa wajen Mammiensu dan ta kai mata labarin abin da yake faruwa. A nan ta isko uncle Abbas yana gayawa Mammie aftar ɗaurin auren Rizwan da chuchun ranar Friday on Sunday tawagar mayaƙansu zasu dinfari masarautar Zarina domin shafe babinta a doron duniya. Allah sarki bai san tamkar a kunne Zarina yake wannan magana ba. Sai addu'a da fatan nasara take yi masu a zahiri, daga ta cikin zuciyarta kuma addu'ar rugujewarsu kawai take yi. Cike da murna Sarina ta shigo cikin room ɗin, daidai lokacin uncle Abbas zai fita kenan bayan sun kammala yin magana. Cike da so ya dubeta tare da cewa. "Daughter murnar me kike yi ne haka?". Bakinta da yaki rufuwa ne saboda murmushi ta ce. "Daddy murna nake yi su Yah Ramish sun zo". Ɗan zaro idanu ya yi. "Ramish kuma? Kai inaga dai baki ji da kyau ba, nasan baki sansu ba, so baki ji sunanyen waɗan da suka zo ɗin da kyau bane, amma ba su bane". "Allah daddy su ne, ai na san su a hoto". Fuskarsa ɗauke da mamaki ya ce. "Su Ramish dai? Kai abin da mamaki, jiya fa na yi waya da shi har nake ce mashi yaushe zasu zo ya ce mun babu rana, har ce mashi na yi Akka bata da lafiya dik dan ya zo, amma ya kekashe ya ce mun kila nan da one year haka idan yaga yana da lokaci zai zo, shi ne yanzu zaki ce mun shi ne? Kai basu bane". "Wlh daddy shi ne, ka je part na momma zaka gansu, harda Yah Bilal da Yah Raj". Kallon mammie dake tsaye a gaban mirror ya yi. Ita ma shi take kallo. "To ka je ka duba mana ko dai su ɗin ne da gaske". Cewar Mammie. Jinjina mata kai ya yi tare da wucewa ya fice. Da gudu Sarina ta kariso gabanta tana faɗin. "Mammie yau kam mijina ya zo, yau kam na gansa ido da ido, sai dai kuma fa ko kallona bai yi ba, kuma Aneesa da take kanwarsa ma ta yi mashi sannu da zuwa bai amsa ba, wai Mammie kin gansa kuwa? Allah ya haɗu sosai like wow, ya yi kama da dad fa, kai ni ban ma san me zan ce ba". Dik tana ruɗe yau ta gansa, dik ta rikice sai surutai take yi. "Ke waye ya gaya maki Ramish ne na ajiyewa ke? Waye ya ce maki shi ne mijinki?". Cewar Mammie dake binta da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa. Cak ta dakata da murmushin da take yi, sai ta ji maganar wani irin, ba Ramish aka ajiyewa ita ba to me Mammie take nufi?. Ta jefawa kanta tambayar da bata da amsarsa. "Ni ki wuce ki bani waje zan yi wani abin ne". Mammaien ta sake faɗa, da alama ranta bai so zuwan su Ramish gidan ba sam. Kamar zasu katse mata wani abin ne. "Mammie ba kin ce babban yayanmu zan aura ba? To ai Yah Ramish shi ne babba, ko dai Yah Bilal ya fishi ne?". Cike da damuwa ta yi tambayar, dan ita fa a gaskiya ta faɗa daga kallon farko da ta yi wa Ramish, ta ji sonsa a ranta. "E haka nace, amma ba Ramish bane, ki fice mun a ɗaki da wuri zan yi aiki". Ɗan zaro idanu ta yi. "Mammien babban yayanmu kika ce zan aura, sannan kuma kika ce ba Yah Ramish ba, to wanene? Dad yana da wani yaro ne bayan Yah Ramish?". "Bashi da wani yaro bayan Ramish, amma ba shi zaki aura ba, ni bai yi mun ba, zaki iya fita yanzu". Cikin faɗa ta yi maganar. Ɗan tsuke fuska ta yi tare da buɗe baki da nufin ta sake tamnayarta, hannu ta ɗaga mata alamar bata son sake jin wani magana kuma. Dan dole ya hakura ta nufi waje sake sake cike tab a ranta, ta rasa ma me zata tuna dan nemanwa kanta mafita, ta dai kamu da son Ramish daga kallon farko. A ɓangaren su Momma kuwa, Yah Ramish ne ya yi wa guyson wanka kaman yadda ya saba, dan kuwa Momma ta ce tun da sun zo ba zata yi mashi ba, sai dai su da suka shagwaɓa shi da hakan su karita da shi, part ɗinsa Ramish ya wuce da shi har da cewa Mommar e sun ji a basu kayansu su je su yi mashi wanka dama sun saba. Mummy kuma ta fito mashi da sabbin haɗaɗɗun kayan da ta saya mashi, kyautar birthday ɗinsa ma kayayyakin wanka na gayu masu bala'in tsada ta saya mashi, ta ce ya cigaba da ɗaukar wanka yana tashin kan kowa, komai dozen dozen ta saya mashi. In short sun kammala shirya shi, shi fa kowani irin wanka ya ɗauka tashin kai yake yi, ya yi masifar kyau, su Chuchu dik sun ɗauki wanka, sai da aka gama haɗuwa a part ɗin mummy za'a fara gudanar da abubuwa ya saka masu kuka a kan babu Yah Jawad, Yah Rizwan, and Yah Jaish a wajen, shi ba zai yanka cake ba har sai sun zo. Kallon su Ramish momma ta yi, domin kuwa aikin neman Jaish yanzu ya koma hannunsu, ya rataya a wuyansu, ɗan duƙawa Ramish ya yi ya mashi raɗa a kunne, nan take ya ɗan saki murmushi sannan ya ce. "To ina Yah Jawad and Yah Rizwan kuma?". Kallon room ɗin Ramish ya yi, ganin babu su a wajen ne yasa ya kalli Bilal dake kusa da shi. Shi ma Bilal ɗin kallon Dr Raj ya yi ba tare da ya furta uppan ba. "Momma ina Jawad da Yah Rizwan?". Cewar Dr Raj. "Jannat jeki ki kira Jawad yana room ɗinsa, ke kuma Zunaira jeki ki kira Rizwan a part ɗin uncle Abbas". Cewar mommar. Da sauri suka miƙe, Chuchu ta sha kwalliya sosai, ta yi kyau cikin doguwar rigarta Turkish gown. Part ɗinsa ta nufa, sallama ta yi ti a parlonsa, babu kowa sai kuyangun da suke yi mashi hidima, suna ta aikin gyaran parlourn. Suna ganinta suka zube ƙasa domin kwasan gaisuwa. "Yah Jawad yana ciki?". Ta gefa masu tambayar ba tare da ta amsa gaisuwar tasu ba. "E yana ciki". Suka bata amsa har suna haɗe baki wajen magana, cikin girmamawa suka yi maganar. Wucewa ciki ta yi ba tare da ta sake bi ta kansu ba. A bakin door room ɗin ta yi sallama. Shiru ba'a amsa ba, sake kwala sallama ta yi, shiru. Sau uku tana yi ba'a amsa ba, kamar zata juya ta koma, dan in baku manta ba ya ce ta dai'na shigo mashi cikin ɗaki, ta rinƙa tsayawa a iya parlour, to sai take jin kamar ta juya. Har ta juya sai kuma ta ji wani irin nishi kamar gurnanin zaki, tamkar wanda aka shakewa numfashi bata fita, bata taɓa jin irin wanann nishin ba, hakan yasa ta yi saurin juyowa, a ɗan tsorace ta tura kofar ɗakin, fargaba kamar zai kasheta, a tsorace take da abin da idanunta zasu gane mata. Kara tsorata sosai ta yi a lokacin da ta hangosa kwance a saman bed ɗinsa yana wani irin numfashin da karfi karfi, ya kudundune cikin bargo gabaɗaya har kansa, ba zaka ce akwai mutun a gadon bama idan ba ka ji numfashin nasa ba. Ai a miliyan ta ƙarisa wajen, bama ta san lokacin da ta haura saman gadon ba, tuni ta ruɗe, sunansa kawai take ambata Yah Jawad, Yah Jawad. Amma ina bayan wannan numfashin babu wani abin da yake yi kuma. Hannu tasa da karfi ta yaye bargon. Wani irin baya baya ta yi a razane na ganin irin yadda yake kwance, kamar babu rai a jikinsa, ga kuma wani irin numfashi da yake fita wanda sai ka yi zaton ba daga jikinsa yake fita ba. Ai bata san lokacin da ta kurma ihu tare da dirowa kasa daga saman gadon ba, da gudu ta nufi waje. Allah sarki tun lokacin da uncle Abbas ya gaya mashi cewa jumma'ar nan za'a ɗaura auren Jannat da Rizwan shikenan ya dawo ɗaki ya kwanta, ya ƙasa iya furtawa uncle Abbas ɗin ma ko uppan, tin daga lokacin bai iya furta ko uppan ba, tun da ya kwanta a kan gadon nan nasa kuma bai tashi ba, ko sallar asuba bai yi ba, haka zalika bai ci abincin daren jiya ba, babu wanda yasan halin da yake a ciki. Part ɗin momma Chuchu ta koma, tana zuwa ta gaya masu halin da ta gansa a ciki, ai ba wanda ya riga guyson da ya ce lallai a kirasa riga kowa miƙewa a cikin waɗan da suke zaune. Ramish dake tsaye shi da Bilal a tsakiyar parlourn su suka riga kowa nufar hanyar fita, da sauri Dr Raj ya bi bayansu, momma ta riga Mummy bin bayansu. Chuchu da hawaye ya gama wankewa fuska ne ta bi bayan momma da gudu, yau dai an ɓatawa guyson murnar Birthday ɗinsa, tuni ya watsar da batun ya bi bayan brothers ɗin nasa. Suna shiga cikin ɗakin Ramish ya yi kansa a ɗari, Dr Raj ya riga Bilal ƙarisawa wajen, dan yadda suka ji numfashinsa yake fita tamkar wanda zuciyarsa take son bugawa, hankulansu ya yi mugun tashi, tuni momma ta ce guyson ya je ya kira masu King, ai kasa tafiya ya yi a in da ya tsaya ya fara yi masu ruwan hawaye, da yake shi hawaye sun mashi yawa, abu na faruwa kaɗan zai fara ruwan hawaye. A tare su mummy suka ƙariso ɗakin ita da Yah Rizwan da Auta, sun je part ɗin nata tana ƙoƙarin fitowa ne ta ce masu su zo su je part ɗin Jawad bashi da lafiya. Ai suna shigowa a miliyan ɗari Rizwan ya yi kansa yana ambatar sunansa, har bai san lokacin da ya kai hannu zai karɓesa daga hannun Ramish ba, da alama ya fita daga cikin hayyacinsa, ya manta su ɗin dik abu guda ne, tuni ya manta da hakan yana ƙoƙarin kwacesa daga hannunsu. Dr Raj ne ya ce. "Rizwan calm down please, zan duba shi yanzu, In Sha Allah babu abin da zai faru". Ramish ne ya ce da Bilal. "Kama shi Bilal". A hanzarce Bilal ya kai hannu ya riƙoshi da nufin ya ja shi su fita waje, amma ina tirgewa ya yi yana cigaba da kiran sunan ɗan uwan nasa, ga dai numfashinsa na fita da karfi karfi amma kuma baya motsi kamar wanda ya mutu. Momma ce ta ce Auta ta je ta kira King tun da Guyson ya kasa zuwa, ya ƙanƙame mummy yana ruwan hawaye, sai faɗi yake yi dan Allah a ce Yah Jawad ɗinsa ya tashi kada ya mutu. Ita ma Autar dai kuka ta fara yi, amma ta fi guyson kwarin jiki, dan haka tana hawaye ta nufi fada wajen King. King yana tare da uncle Abbas, dan wajensa uncle Abbas ya nufa dan ya tambayesa batun da gaske ne su Ramish sun zo?. Sai dai ko da ya tamnayesa sai ya ce a'a basu zo ba, dan shi ma bai san da zuwan nasu ba, dan haka sai uncle Abbas ɗin ya yi zamansa kawai a zuwan ai Sarina bata sansu bane, watakila wasu baki ta gani ta ce su ne, so sai ya shashantar da maganar. Chuchu kuwa hauka ta kusa yi masu, ta manta da family dik suna waje, ta manta ma cewa tana jin tsoron brothers ɗin nata, tuni ta haye saman gadon tana kuka tana ambatar sunansa. Kowa ya ɗauka saboda shakuwar dake tsakaninsu yasa take wannan kuka, momma ce kawai tasan dalili, dan haka ita ce ta zo da nufin ta kamata su fita. Ina ai kin yarda Chuchu ta yi, ihu kawai take yi tana faɗin. "Dan Allah Yah Jawad ɗina ka tashi, Momma ki ce ya tashi, wayyo na shiga ukuna!!". Harta mummynta bata san da batun soyayyarsu ba, ita dai tasan King ya sameta da batun jibi Jummaa kenan zai ɗaura auren Jannat da Rizwan, a matsayinta na uwa tana da abin faɗe, sai ta ce Allah ya bada zaman lafiya kawai tun da Jannat ɗin tana son shi, bata da wani abin faɗe illah ta tayasu da addu'ar zaman lafiya. Mammien su Sarina kuwa, dik abin da yake faruwa a cikin family tana tsaye a gaban wannan mirror nata ga wani kwarya mai ɗauke da ruwan tsafi a gabanta tana kallon dik abin da yake faruwa, tsabar mugunta sai ta yi amfani da tsafin nata ta rufe bakin Jawad ɗin dan ma kada ya farka ya fara kiran sunan Jannat har a fahimci da wani abin a tsakaninsu, ta kuma rufewa ita ma Chuchun baki ta hanata kiransa da sunayen soyayya da take kiransa, sai dai ta yi ta ihun Yah Jawad ka tashi kawai. Yau ranta fes, sai daɗi take ji burinta ya kusa cika, wani irin daɗi na musamman take ji, musamman ma da ta ga Rizwan ya kusa zarewa, sai kiran sunan ɗan uwan nasa yake yi, dama tasan Rizwan ba zai iya jure rashin Jawad ba, shiyasa bata damuba ta barshi zancen soyayarsa da Jannat ya isa gaban iyaye, saboda a cewarta shi mutuwarsa mai sauki ne a kan Jawad, amfani ta yi da raunin kowannesun. Tasan Jawad zai yi wuya ya rayu idan ya rasa Chuchu, tasan idan Jawad ɗin ya mutu shi ma Rizwan da wuya ya sha, shiyasa ta yi masu haka, har wani irin shu'umin murmushi take saki a lokacin da idanunta suke kallon ƴan uwan a cikin tashin hankali, tsabar mugunta ta kara iza wutar soyayyar Chuchun a cikin zuƙatarsu dikkansu biyu da tsafinta. A tare uncle Abbas, uncle Jahiz, and King suka shigo cikin room ɗin. A lokacin kuma Rizwan yana ƙoƙarin yi masu karamar hauka, dan gani yake kamar Jawad baya raye, saboda anyi kiran duniyar nan dik yaki motsawa, sun zuba mashi ruwa ma amma shiru bai motsa ba, kuma dai ga numfashi fa yanayi, abin akwai mamaki da ɗaure kai matuƙa. Karfi Bilal ya sanya ya cicciɓi Rizwan sama suka nufi waje, dan ba zai barsu su yi abin da ya dace ba, ita ma Chuchun sai da momma tasa karfi ta jata suka nufi waje, mummy ma waje ta yi yunkurin fita da guyson dake aikin kuka, amma sai ya tirje yaki yarda, ya kankame King da hannunsa ɗaya, rabin jikinsa yana jikinta yana ƙoƙarin gudu ya bar jikin nata ya koma wajen King da suka shigo yanzu. Ramish ne ya ce da mummy ta fita da shi ko ta karfi ne, idan ta je kuma ta tabbatar ta rarrashe shi ya yi shiru, kada ya yi kuka sosai ciwonsa ta tashi. Haka kuwa aka yi, sai dai uncle Abbas ne ya fita da shi, mummy ta kasa jansa, saboda ya tirje yana boƙarewa shi ba zai fita ba sai yaga Yah Jawad ɗinsa ya farka. Uncle Abbas ya sa karfi ya ɗaukesa suka fita, sai ihu yake yi yana wiwwintsila kafafu shi ba zai fita ba. Auta ma bin bayan Mommarta ta yi dan ta je ta lallashi Chuchu. Ɗakin ya rage daga Ramish dake tallafe da Jawad ɗin, sai Dr Raj da yake ƙoƙarin cire rigan jikin Jawad ɗin, sai King Zuhair, dama ita Sarina bata dawo cikin part ɗin ba, Aneesa da Fanan ma bin bayan momma suka yi dan su je su rarrashi Chuchu, sai uncle Jahiz da ya kara cewa uppan. Ai King ya manta ma da cewa su Ramish ya gani unexpect, tuni ya nufi Jawad, sai bai yi mashi kaman bakin da bai san da zuwansu ya gani ba, ciwon Jawad ya ɗaga hankalinsa yasa ya mance da ya gansu a wajen. Bilal ne ya dawo cikin ɗakin hannunsa ɗauke da boxes na magunguna da allurai, ya je ne ya rufe Rizwan a cikin ɗakinsa, sannan ya kwaso kayan magunguna dan su ceto rayuwar Jawad ɗin. To quickly recovery our Yah Jawad, Allah ya baka Jannat idan alkhari ce a gareka, Allah ya kuɓutar daku daga makircin mammie, Allah kuma ya bawa dik wanda ya rasa Jannat hakurin rashi da iya juriya. Bari mu leƙa wani wajen, watakila kafin mudawo zaƙwaƙwurin doctornmu wato Dr Raj zai iya shawo kan matsalar. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ JIMETA. Sanyin safiya ne ya ratsa shi yasa ya farka da daddaɗar barcin da ya ɗaukesa, a hankali ya waro idanunsa da suke jajir. Gefensa ya fara juyawa domin ganinta, sai dai kash bata nan, cikin nutsuwa ya juyar da kallonsa ya fara bin ɗakin da kallo, mamaki ne ya yi matuƙar kamasa na ganin gari ya yi haske kamar asuba ta ɗan gota. A hanzarce ya miƙe zaune, aikuwa da gaske ne asuba ta gota, lallai yau yaron Mommarsa ya yi barci mai daɗin da har ya makara ba tare da ya sani ba. Ɗan dafe kansa ya yi yana mamakin hakan, jikinsa dik a mace haka ya miƙe ya nufo waje. A tunaninsa zai ganta a tsakar gida, sai dai wayam bata nan. Abin dariya baya karewa a kauyen su Mahnoor, sai da ya tsaya ta cikin ɗakin ya leƙa waje ya gani bappa na nan a tsakar gida ne ko baya nan, abin kunya su haɗa idanu da bappa bai je masallaci ba, to me ya hanasa zuwa zai ce wa bappan kenan? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsarta, dan haka ya yi godiya ga Allah na ganin bappa baya nan a tsakar gidan. Da sauri ya fito ya ɗauki buta, ruwa yasa ya shiga toilet dan yin tsarki. A gaggauce ya fito ya yi alwala ya komo cikin ɗakin, zuciyarsa cike tab da tunanin ina ta tafi da sassafiyar nan, ko wayewa gari bai gama yi ba. Sallarsa ya gabatar cikin nutsuwa tare da zama saman daddumar ya fara gabatar da addu'oi. Ya ɗauki a kallah 1h a saman daddumar kafin ya miƙe ya koma saman mattress ɗin nasu. Shiru ya zauna yana tunanin ina ta yi? Yana son zuwa ya dubata yana kuma jin kunyar shiga ɗakin bappa tambayar ina take, yasan bazata wuce tana can ba. Addu'a ya yi Allah ya kawo dalilin da zai sa ta shigo cikin ɗakin domin ɗaukar wani abin ya kamata. Aikuwa bai gama rufe baki ba sai gata ta shigo jikinta sanye da hijabi, daga wajen dabbobinsu ta fito, ta je tatsan nono ne suka tsaya hira ita Jumma da ta fito samo kara da itace zata hura wuta. Sai faɗa Jumma take yi mata a kan fitowar da ta yi da sassafe, ta yi mata faɗa sosai ta ce maza ta koma, baiwar Allah ba ƙaramin daɗi ta ji ba da Mahnoor ɗin ta gaya mata Jaish ya hanata yi wa Nenne aiki, ta tayata murna matuƙa har take kara gaya mata cewa ba ga shi nan yanzu taga banbancin Jaish da Faisal ɗin ba, ai da Faisal aura bai isa ya hanata yi wa Nenne aiki ba, ƙaramin aikin Nenne ne ma ta haɗata ita da Faisal ɗin dik ta zaga, ko ta kamata a gaban Faisal ɗin ta yi mata duka bai isa ya yi magana ba, dan gwaggonsa ce Nenne, amma shi Jaish ai bata isa ba, dan haka ta kara riƙe mijinta da kyau in ba haka ba ta koma cikin azabtarwar Nenne. Ta ji daɗi shawarin Jumma sosai a wannan karon, dan ta ankarar da ita abin da bata ankara da shi ba wato gaya mata da ta yi idan Faisal ta aura ba zai hana Nenne azabtar da ita ba, amma Jaish kuwa bata isa ba, hakan yasa ta ji wlh bari ta koma ta kula da mijinta sosai, yanzu ta yarda zata daina son Hamma Faisal, kuruci dangin hauka, yaro dai yanzu zaka yi mashi dabara ka juya shi ta yadda kake so, ji fa kalma ɗaya tasa wai ta dai'na son Faisal, sai kace soyayyar wasa ce, dama can bata san me ake cewa son soyayya da son ƴan uwantaka ba, ita dai tana son Hamma Faisal kawai. Ba ƙaramin daɗi ya ji ba na ganinta ta shigo cikin ɗakin, sai dai kuma wani irin kunyarta ne ta lulluɓesa na tuna abin da ya faru a dare jiya da ya yi, sai ya ji ba zai iya haɗa idanu da ita ba, ya yi ƙasa da kai yana faɗin. "Ina kika je da sassafen nan?". Ita ma kanta a ƙasa, kunya kamar ta juya ta fice daga cikin ɗakin, amma ba dama, tana son kashe shi da soyayya kamar yadda Jumma ta gaya mata, wato Jumma fa ƴar air ce, ce mata ta yi ta je ta kashe shi da soyayya da sanyin safiyar nan, shi ne ta zo aikatawa..............😅 "Waje na je?". Ta faɗa a sanyaye. "Kin tamnayeni ne?". Ya jefa mata tambayar ba tare ya kalli in da take ba. Kai ta girgiza mashi alamar a'a tana amsawa da a'a ɗin. "Bana ce kada ki sake yin abu ba tare da kin tambayeni ba?". "Ka faɗa, ka yi hakuri ba zan sake ba". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. Ɗago kai ya yi da nufin ya sace kallonta, sai kuma aka yi dace ita ma ta ɗago dan ta saci kallonsa, ai kuwa suka yi ido huɗu, da sauri ta kawar da nata kallon shi kuma ya cigaba da kallonta. "Zoki kwanta". Ya faɗa yana gyarawa shi ma ya kwanta. Wani irin daɗi ne ta ji ya kamata, da yanzu fa zata tafi cikin sanyin nan ta kama yi wa Nenne aiki, amma Allah ya kawo mata sauki, yau waye zai yi wa Nenne aiki? Idan bata fito da kanta ta yi ba asirinta zai tonu wajen bappa cewa dama ba ita take yin aikin ba kullum. Cike da farinciki ta nufi mattress ɗin, can gefe ta kwanta tana tunanin yadda zata yi ta kashe shi da soyayya da safiyar nan. Shi kuwa da yake ya ji daɗin kwanciya a jikinsa da ta yi jiya, ya ji daɗin da bai taɓa jin irinsa ba har da makara sallar asuba, sai ya juyo gareta. Abin dariya a miliyan ta datse idanunta, shi fa take ta kallo da ya bata baya, amma yana juyowa ta wani datse idanu. Shiru ya zuba mata idanu yana tunanin ta yadda zai yi ta dawo jikinsa, ita ma tunanin hakan take yi, dan ta ji matukar daɗin kwanciya a jikinsa da ta yi jiya. Sai dai kuma ba zai iya ce mata ta zo garesa ba, yana jin kunyar yin hakan, addu'a yake yi Allah ya kawo mashi dalilin da zai sa ta dawo jikinsa ta kwanta, ita ma addu'a take yi Allah yasa ya ce ta zo garesa ta kwanta. Ita dai Mahreen hankalinta a kwance tana ɗakin bappanta tana barci, shi kuma bappa yana ɗakin Nenne suna diramar da suka saba, ya baro Mahreen tana zuba barci. Kasa hakura shi fa ya yi, a hankali ya nufi saman wuyarta da hannunta dake ta faman kerma, ta datse idanu gam tana tunanin yadda ta ti barci cikin farinciki a daren jiya. Ɗan taɓa wuyarta ya yi tammar bai jin tsoronta. Wani irin ajiyar zuciya da suka sauke a tare ne yasa ya fahimci ita ma tana kewar jikinsa, dan haka sai ya matso kusa da ita tare da sanya hannunsa dikka biyu ya janyota jikinsa. My people's ba zan bari kuga irin farincikin da suka shiga yau ba🤸 sai gobe idan mai dukka ya kaimu zaku gani 🤪 idan kun ji haushi kuzo na baku Maltina mai sanyin sanyaya zuciya ku kora zuciya ta ɗan yi sanyi🌝😅🤸 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 46 JIMETA A ɓangaren Nenne kuwa sam bata yi zaton Mahnoor ba zata fito ta yi mata aiki ba, hakan yasa ta koma ta yi kwanciyar kamar yadda ta saba. Sai dai kuma sam bata ji motsin kowa a tsakar gidan ba, hakan ba ƙaramin damunta ya yi ba, ya kuma ɗaga hankalinta sosai, dan ita fa ba iya jure aikin da Mahnoor take yi zata yi na. Hmmm rayuwa kenan ita ma da take uwa ba iya jure aikin Mahnoor da take yi zata yi ba, amma saboda tsabar mugunta take sakata yi, har ma ta kara mata da wasu miscellaneous, minus aiki da baya a cikin lissafi, Allah dai ya kyauta ya rabamu da sharrin zuciya yasa mufi karfinta. Har around karfe 7 bata ji motsin kowa a waje ba, hakan ya bata tabbacin Mahnoor bata fito ba, cike da tashin hankali ta miƙe ta nufo wajen dan ta tabbatarwa da kanta shin da gaske ne ko dai kunnuwanta ne basu jiyo mata da kyau ba!. Bappa bawan Allah shi kuwa tuni ya fice ya tafi gidansu Faisal duba jikinsa, a yanzu ya fara samun sauki har yana ɗan fita, sai dai kuma fushi yake yi da bappan, ko bappa ya yi mashi magana baya amsawa, akwai zuciya ne sosai, ya zuciya ya yi fushi. Amma dik da haka baya hana bappa zuwa duba shi, saboda yasan cewa shi ne ya zama silar rashin lafiyarsa. Ba karamar girgiza ta yi ba a lokacin da ta fito taga tsakar gidan kamar yadda suka barshi a daren jiya, baa kawar da komai ba, ya tabbata dai Mahnoor bata fito ba, ta jefawa kanta wannan tambayar. Tattare tsakar gidan ta fara yi tana wani uban ɗaure fuska tamkar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa. Haɗa kwanikan wanke wanke ta yi ta kaisu mawanki, ta dawo ta shiga ɗakin bappa domin ta taso Mahreen ta zo ta yi mata koda wanke wanke ne, dan ba iya yin aikin nan gabaɗaya zata yi ita kaɗai ba. Tana son shiga ɗakin Mahnoor ɗin ta dubata ko Jaish ya fita ita kaɗai ce a ciki take barci sai ta tasota ta zo ta yi mata aiki, amma kuma tana bala'in tsoron ace yana nan su yi arba, ai da ta shiga uku. Kiran sunan Mahreen ɗin ta fara yi a kan ta tashi, amma ina Mahreen sarkin barci kin tashi ta yi, sai ma sa ta matsa mata ta saka mata kuka cikin magagin barci ta fara faɗin. "Wai Nenne kekam meyasa baki son ganin mutane suna jin daɗin duniyarsu ne? Ni wlh ba zan iya tashi yanzu ba". "Tashi zaki yi ki je ki mun wanke wanke". Nenne ta faɗa. Turo bakin nan ta yi, cikin tsiwa da magagin barci ta ce. "Nenne ni kuma? Gaskiya ni ban iya ba, ina Adda Mahnoor? Ba ita ce take yi maki kullum ba?". "Yau ba ita zata yi ba, ni zan yi aikin, dan haka ki taso mu je ki tayani!". Ta faɗa cikin tsiwa da ɗaga murya ita ma, da alama ranta ya fara ɓaci. "Nenne ita Adda Mahnoor fa bata tashina na tayata aiki, dikka aikin ita kaɗai take yin abinta, kema ki je ki yi aikinki keɗai ni dan ban iya ba". Tana kai karshen maganar ta juya mata baya dan ta cigaba da yin barcinta. Ranta ne ya kara ɓaci, sai yau ta yi nadamar hana Mahreen ɗin da take yi ta taya Mahnoor aiki, ai ga shi nan yanzu ko wanke wanke bata iya ba bare ta fara taimaka mata, Allah sarki baiwar Allah Mahnoor dikka aikin ita kaɗai take yi har ta dafa masu abin da zasu ci da safe, dik kuma kafin karfe 8 ta gama komai, baiwar Allah tun karfe 5 idan ta yi sallah take fitowa ta hau yin aiki kamar wata jaka maras gata wanda ba'a so. Yau dai ga shi muguntarta ya juyo kanta, Mahreen dai bata iya komai ba face taya Mahnoor surutu idan tana aiki, sai cin abinci da wanka da barci, wankar ma fa idan tsiyanta ya motso sai ta ce lallai Mahnoor ce zata yi mata ko kuma bappa, kaso 70 cikin ɗari na wankanta su suke yi mata, ko bappa ko Mahnoor, kaso 30 ne take yi da kanta. Dan dole ba dan ta so ba ta fito ta baro Mahreen ɗin, dan ko ta tashi ba wani abin da zata iya taɓuka mata ba. Wajen wanke wanken ta koma, ruwa ta ɗebo ta fara yi, tana yi tana tsinewa Jaish a cikin zuciyarta, tana ta kwashe mashi albarka da ya hana Mahnoor fitowa.... Ni kuwa nace ki kwana kina tsine masa idan kin ga dama, ai tun da mommarsa ta ce ɗan albarka jeka Allah ya yi maka albarka ai sai dai yaga cigaba, ke tsinuwarki ta haɗuwar titi rabuwar gate me zata yi mashi in banda ma ta kara mashi lafiya da kwarin gwiwar cigaba da zuba love ɗinsa da ƴar matarsa hankalinsu a kwance, aiki ne dai ya hana kuma ta hanu sai dai ayi wacce za'ayi ato, kuma mu ya yi mana dai'dai!!. Ta ɗauki almost 1h a wajen wanke wanken nan, tsabar san jiki irin nata ma ta gaza iya tattare wajen wanke wanken ta share ta gyara kamar yadda Mahnoor take yi, ta dai ɗauke kwanikan daga wajen ta yi komai sama sama, sharar gidan ma sharar gongoloso ta yi, iya in da idanu suke gani kawai ta share saɓanin Mahnoor dake ɗage komai ta bi lungu da tsako ta kwakulo datti ta share tsab. Ita kam sai ta zuba abinta fisha kawai aka wuce wajen. Haka ta hura wuta ta ɗaura ruwan girki, kada ku so kuga abincin shafshuta, a take ta jajjaɓa komai, miyarma sai da ta gama haɗa komai a ƙasa, cikin ruwan sanyi ta zuba maggin da su gishiri kafin ya ɗaura a wuta, ta ɗauko nama ta banka, yana tafasowa ɗaya ta kaɗe hege, rabonta da yin girki yau a kallah ya kai shekaru 6 zuwa 7, tun Mahnoor tana yar shekaru 8 take girki da sauran aikace aikace, har ta fara manta yadda ake hura wuta, shiyasa ta sha bakar wahala kafin wutan ya kama, sai ta shirya itacen wutar ta kama daga baya itacen su sake watsewa wutar ta mutu, hegiya har murar dole ta yi saboda hayaki. Haka ta kwasawa kowa abincinsa ta kai masa, a lokacin karfe 9:30 ya yi, dan dole ba dan ta so ba ta kwasawa su Mahnoor, dan tana tsoron Jaish yasa ta yi hakan, ɗakin bappa ta kai masu ta ajiye, dan tana tsoron shiga room ɗinsu. Bayan ta gama ba tattare kitchen ɗin ta gyara ba bare a kai ga wanka a tsabtace jiki, sai haɗa zufa take yi ta jawo mayafi fuuuu ta fice sai gidan Arɗo dan ta je ta gayawa gwaggonta, ta ce da sake, ba zata saɓuba bindiga a ruwa, ba zata iya wahalar nan ba, dole gwaggonta ta samo mata mafitar da zai sa Mahnoor ta koma yi mata aiki. ________________💘🌹_____________ Shigewa jikinsa ita ma ta yi, dukkansu biyu wani irin farinciki na musamman suka tsinci kansu a ciki. Saman waist beat ɗinta ya ɗaura hannunsa yana cigaba da wasa da su kamar dai jiya. Shiru ta kwanta, kafin wani ɗan lokaci barci mai daɗi ya ɗauketa. Shi ma bai wani jima ba ya mayar da barci. Baiwar Allah da yake bata saba barci haka ba, kun san iwar haka tana fama da aiki, sai barcin nata ya gaza nisa, ta gaza yinsa mai nauyi, sai ta rinƙa zabura tana farkawa, idan ta ganta a kwance a jikinsa sai ta sauke ajiyar zuciya ta sake mayar da kanta ta mayar da barcinta. Dik abin da take yi yana jinta, dan barcinsa bata yi nauyi ba, yana da ɗabi'ar jin dik motsin mutun a cikin barci. Ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, dik in ta zabura zata miƙe sai ya ji hakan har cikin ransa, wato ta saba da tashi a wahalce, a ransa yake faɗin ai wlh ko tsinke ta dai'na ɗagawa a gidan nan, harta gyaran ɗakin nasu ma dole Mahreen ta koya yi dan ta rinƙa yi masu, at least ta huta ko da na one year haka bata yi aikin komai ba. Around karfe 8 da ta farka daga barcin ne ta fara ƙoƙarin barin jikinsa, a cewarta zata je ta duba ko Nenne ta fito, in bata fito ba sai ta yi aikin, har ta manta da ya ce kada ta sake yin komai sai da izininsa, Allah sarki ba laifinta bane, sabo ne ya ja hakan. Tana ƙoƙarin lallaɓawa ta bar jikinsa idanunsa a lumshe yasa hannu ya mayar da ita, can kasan maƙoshinsa da murya irin na mai barci ya ce. "Ina zaki je?". "Aiki zan je na yi hamma". Ta bashi amsa cikin nitsuwa. Waro idanunsa ya yi a kanta. Kallon face ɗinta da kyau ya yi kafin ya mayar da su ya limshe da alama barci bata ishashi ba. "Babu in da zaki je" . Shi ne kawai abin da ya furta, daga haka ya kara ja masu bargo suka cigaba da yin barci. Hajiya Mahreen tamu kuwa, sai karfe 10 ta tashi daga barci, nan fa suka saka sabon dirama ita da Nenne, dan kuwa ita Nenne bata ɗaura mata ruwan wanka kamar yadda Mahnoor take yi ba, har gidan Arɗo ta bi Nennen nata dan ta tambayeta ina ruwan wankanta. Nan fa Nenne ta ce ta je ta hura wuta da kanta ta ɗaura, aikuwa ta ce ita wlh ba zata iya ba, ai kullum Mahnoor ce take ɗaura mata, dan haka wlh ba zata iya hura wuta ba. Ta saka masu kuka tana birgima a ƙasa kamar mai aljanu. Gwaggo kakarta ce ta ce. "Taso kizo muje na ɗaura maki ruwan sai ki yi wankan a nan". Make kafaɗa ta yi, ta ce Allahn baram ba zata yadda ba, domin bappanta ya hanata cire kaya a koma ina ne in ba a gidansu ba, saboda haka ita ba zata yi wanka a wannan gidan ba, sai dai gwaggon ta biyota gidansu ta ɗaura mata tuwan wanka a can. Tashin hankali kenan, Mahreen duniya, wai gwaggo ta bita gida ta ɗaura mata ruwan, wlh mugunta babu kyau jama'a, yanzu dai da Nenne da Mahnoor waye yafi wani cin riba? A tunaninta ta cuta mata, to ku yi masu alkalanci! Ai ko da bata auri Jaish ba ita ta ci riba a kan Nenne tun da ta iya aikin komai!. Taɓe baki gwaggo ta yi tana salati ta ce. "Ke bappan naki ma ya ci gidansu, wuce muje nayi maki wanka a nan, da zai ce kada ki cire kaya a ko'ina nan ba gidan da uwarki ta yi wasan kasa bane?". Cewar gwaggo da haushin bappa ya kamata, a ganinta ai nan gidan ya wuce ya yi wani magana a kai, bata san yana da gaskiya ba, idan zaka hana yaro abu tofa ka hana shi gabaɗaya ne, kada ka kuskura kace mashi a nan zai iya yi a nan ne karya kuskura ya yi, in ka yi haka wlh in mai yi ne tsab zai yi a koma ina, dan kuwa sai ya ce ai baka son waɗan nan ne yasa zaka ce ya yi a nan kada ya yi a nan, so the best way kawai ka hana shi gabaɗaya shi ne zaka ci riba ya kuma hanu ɗin, misali kaman dai Mahreen ɗin, kun dai san gidan Arɗo gidan baffan bappn ne, sannan gidan surukansa ne, mata biyu Arɗo ya bashi a cikin gidan, amma kunga da yake ya hanata gabaɗaya har nan ta ki yarda. Gwaggo ta kara jin haushin bappa sosai, dama yanzu ma haushinsa kamar ta shakesa, saboda ya bawa Mahnoor bango majigina ya zama garkuwa a gareta ya hanata yin komai sun bar mata ƴa Nenne tana wahala. "Ni fa gwaggo ba zan yi wanka a nan ba, koma me zaki ce bappana ya hanani cire kayana a gidan koma waye, kuma ni ba zan cire ba, sai dai ki bini gida ki ɗaura mun ruwan a can, idan ya yi zafi ki juye ki kai mun banɗaki kamar yadda Adda Mahnoor ɗina take mun, in ba haka ba ni ba zan yi wankan ba". Cikin tsiwa take maganar, tsabar kwarewa a masifa yarinyar nan har da rufe idanu. Tun da ta fara surutan nata gwaggo ta taɓe baki tana kallonta har ta kai aya, dama ta san Mahreen ba kunya ce da ita ba, to yanzu kuma bappa ya kara mata wasu huɗuba ai kuma shikenan. "Eyeeee to sannu uwata, wato na biki gida na ɗaura maki ruwan ko? To dan uwarki sai dai kada ki yi wankan, ke dama baki da kunya ai na sani ba sai kin kara jaddada mun ba, sai ki wuce uwraki Mahnoor ɗin ta ɗaura maki!!". Cewar gwaggo masifa, cikin faɗa ta yi maganar Miƙewa tsaye ta yi tana yi wa kakar tata kallon uku goma. "Ke dama gwaggo waye ya ce ma ki ce zaki ɗaura mun ruwan? Ni ai ba wajenki na zo ba da zaki ce kada na yi wanka, so kike na zauna da datti jikina ya nannaɗe kamar taki ko?". Mahreen duniya ita a tunaninta tamu tamun da jikin gwaggo ya yi na tsufar nan datti ne yasa hakan ba komai ba, yarinta akwai daɗi, Allah na tuba idan datti ne ina mutun zai tsaya da wari? Kai Mahreen akwai iya goge hadda wlh. "Dama ba sai kin mun haka zan gane rashin kunyarki ta karu ba, shegen ido kamar na ubanki, ni zo ki wuce ki bar mun gida ko na zaneki". Cewar goggo. (Yau kaka da jikarta an ɓata fa jama'a ku zo ku yi sulhu.) "Wlh idanuna sun fi naki kyau goggo, kuma bappana dai ya fiku kyau dikkanku gidan nan, kuma dama ni me zan yi da wannan gidan naki da dik datti baki share kofarki da ɗakinki?". Tana magana tana murguɗa baki. Hannu goggo ta kai zata capkota da zaneta kamar yadda ta faɗa, ina ai tana da kafar da me taci bata bashi ba, tuni ta watsa a miliyan ta nufi hanyar gida tana faɗin ba zata sake zuwa in da suke ba. Salati Nenne ta sa tana mamakin hali irin na ƴar tata, yarinyar tana kara girma bushewar idanu na karuwa mata? Sam babu ragawa kowa a idanunta, dik wanda ya ce mata kule sau ɗaya kafin maganar ta faɗi kasa sai ta ce mashi cass sau hamsin. Me kuke tunani da Mahreen girman birnice ga wayewa ga komai? Ya kuke tunanin bushewar idanunta zai kai? Amma fa ta wani ɓangaren alhakin Mahnoor ce ta kamasu suka samu dai'dai su, har Arɗo bata bari ba sai dai in bai taɓota ba, ta yi mashi pes ta gudu gida abinta. Tana shiga cikin gida ta isko bappa a tsakar gida yana ƙoƙarin fita zai je ya kaɗa dabbobinsa ya tafi ciwo rana ta yi mashi, ya kammala cin abincinsa, sai dai fa yana fara cin abincin ya ji da banbanci da wanda ya saba ci, amma bai yi magana ba, dan shi baya complain a kan abinci, saboda ya ce manzon Allah bai taɓa cewa abu kaza bai ji a abinci ba ko abu kaza ya yi yawa, bai taɓa yin complain ba, dan haka shi ma ba zai taɓa yin hakan ba In Sha Allah, kuskure ne kuma babba a kan korafi a kan abinci, musamman maza masu shegen korafi idan matansu sun yi iyaka bakin ƙoƙarinsu, kasan dai ba za'a ce tana da ƙoƙarin da ya fi wannan a girki kuma ace bata yi maka amfani da shi dan ta kyautata maka ba, so iya ƙoƙarinta na karshe ta yi kenan, sai ka yi mata uzuri, idan baka sa mata albarka ba ai baka tsine mata ba, babu wanda ya kai Manzon Allah jin tausayin mata da kyautata masu haɗe da bada umarnin a ji tausayinsu a kula da su, wlh har yana kan gaɓar yin wafati nasiha yake yi wa Sahabbai a kan su ji kan mata da yara su tausaya masu su kuma kula da su sosai. Hakan yasa Manzon Allah yake da hikimar rashin korafi a kan girkin da zai ci dikka, dan ya gwadawa maza irin ƙoƙarin da mata suke yi. Allah ka barmu da son shugaba kawai zamu ce, dan ya yi mana komai!💘 So shi dai bappa baya complain a kan abinci, haka ya ci kayassa bata da daɗin ɗanɗano, ya gama ya fito zai fita kenan Mahreen ta shigo. Tana ganinsa ta sa kuka. A dame ya ce. "Lafiya gajin bappa? Waye ya taɓaki? Ina ma kika je?". Zama ta yi a ƙasa ta hau zazzage mashi dik yadda suka yi da gwaggo a kan wanka. Murmushi ya sakar mata tare da ƙarisowa in da take ya tsugunna. "Kai gajina ba gwaggonki bace? Ki dai'na ce mata haka, ai tana sonki ne yasa ta ce zata yi maki wanka ko?". Abin da yake cikin zuciyarsa daban da abin da ya faɗa a bakinsa, shi kansa yasan goggo ba mace mai kyan hali bace, amma kuma ba zai so ace jikarta ta fahimci hakan ba, kuskure! Shiyasa yake ƙoƙarin nuna mata darajarsu, ya kankaro masu ƙima. "Ni bappa ba wani sona da take yi, ka ji har da zagin idona ta yi wai irin naka ne, kuma ba kai ka ce kada na yarda na cire kayana a wani waje ba?". "Haka ne ni nace, kuma ina kan bakata, kaya kam kada ki yarda a koma ina ne ki cire, kuma ai gaskiya ta gaya maki, idon naki irin nawan ne ai, yanzu to mu je na saka ruwan na yi maki wankan". Miƙewa ta yi tana jin haushin Nenne da goggon gabaɗaya ta bi bayansa suka shiga cikin kitchen, zuciyarsa cike da bakinciki, yanzu yaushe gari ya waye har Nenne ta fice ta bar gidan? Gaskiya da sake, dole ya nemawa kansa mafita, comond ƴarta ba zata iya kula da ita ba bare miji, kai wannan abin da sake gaskiya, tunani ya fara yi ko dai ya kara yin wani aure ne? Dan shi ba babba bane ai, bai manyanta ba, Mahnoor ce fa yar farinsa, kuma kun san fulani daji da auren wuri, tun yana da 19 to 20 years suka yi aure da maman Mahnoor, da wuri Allah ya albarkacesu da ita, kun ga kuwa shi ɗin ba wani babba bane, da shekaru ƙalilan ya girmi Jaish, dan haka sai yake tunanin ko dai aure zai kara ne domin ya samawa kansa mafita. Wannan tunanin ne a ransa har ya kammala abin da zai yi, ya yi wa Mahreen wanka ya fito ya nufi wajen dabobinsa. Sai da ya tasi nono a ɗan bokitin da suke zubawa, ya kai ɗakinsa ya ajiyewa su Mahnoor a kan idan sun tashi su yi amfani da shi, sannan ya kwance iyayen shanun da suke ɗaurewa da daddare, ya haɗa kan dabobin ya baro Mahreen tana wannan haɗaɗɗen kwalliyar tata na juye powder full gora a fuskarta rana guda, shi ya barota tana yi ya kaɗa kan dabobin ya tafi ciwonsa. A kan hanyarsa na tafiya ya ci karo da Mairo yar kanwar Inna kakar Mahnoor, wato kanwar maman Mahnoor ta gefen Innarta kenan, har ƙasa ta tsugunna ta gaishe da shi, cikin mutunci ya amsa yana ta kallonta, sai ya ji kamar maman Mahnoor yake kallo, ta wuce ya wuce, amma har da sake juyowa ya kalleta da kyau, rayuwarsa ta baya ne ta sake dawo masa, sai ya ji mamakin kansa ta kamasa, shi kansa ya rasa meyasa ya yi sanyi haka. Tunanika kala kala cike a ransa ya kaɗa dabobinsa suka wuce. _____________💘🌹_____________ Kusan a tare suka farka daga barcin nasu, yama rigata farkawa, ya zuba mata idanu yana ta kallonta, kamar wanda aka tsikara ya yi saurin ɗago kai yana bin ɗakin da kallo. Ɗan zabura ya yi ya mike da ita a jikinsa, kara waro idanu ya yi yana kallon yadda rana ta tsala, ko ba'a faɗa mashi lokaci ba yasan karfe 9 ta wuce, tunani ya fara yi a kan bappa ya tafi kiwo yanzu, to fa yau bai je sallar asuba ba, sannan kuma ga shi har bappa ya fita kiwo ya basu tashi ba, yau da wani ido zai ga bappan?. Ya jefawa kansa tambaya, mikewa da ya yi da ita ne yasa ita ma ta farka daga barcin nata, tana waro idanunta sai a cikin nasa. Wani irin kunya ne ya kamasu dikkansu biyu, ga hannunsa a saman ƙugunta ta baya daidai beat ɗinta. Ɗan kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana muku muku. Ƙasa ƙasa ya ce. "Menene kuma?". "Babu komai". Ta bashi amsa tana ɗan ɗaura hannunta a kan bayansa. Wani irin shock ya ji ya kamasa, hakan yasa ya ɗan juyo da face ɗinsa gareta, kasancewar kanta na saman shoulder ɗinsa sai ya zama fuskokinsu sun samu kusanci da juna sosai. Kasa furta uppan ya yi, sai ya kura mata idanu shiru kamar mai nazarin wani abin, zara zaran eyelashes ɗinta dake ta faman motsawa ne suma ja hankalinsa sosai, da yake ba barci take yi ba kun san in ta rufe ido dole idanun nata su yi ta motsawa, sosai suka yi matukar birgesa. "Noor". Ya ambaci sunanta kamar mai raɗa. A maimakon ta amsa da na'am sai ta ce ummmm kamar mai shagwaɓa, har cikin ransa ya ji hakan. "Yau kin yi kyau sosai da safiyar nan, fuskarki ta yi fresh sosai". Ya yi maganar yana kai hannunsa saman lallausan kumatun nata. "Hamma ai babu wanda ya kai ka kyau dikka garin nan". Hannunta dake ta bayansa ya kai nasa hannu ya riƙo, sai ya zagayo da shi ya yadda zata kara riƙesa da kyau, da alama yaron Mommarsa ya ji daɗin rikon da ta yi mashi, alamu sun nuna rungimarsa yake son ta yi amma yana jin kunyar nuna hakan, Allah nake roko yasa naga ranar da zasu angwace in ga karshen tsiya da kunya..........😅🤭 "Baki ci abincin dare ba fa". Idanunsa a kan ɗan bakinta ya yi maganar. "Kai ma ai baka ci ba". Kamar mai shagwaɓa haka voice ɗinta ya yi. Bai san lokacin da ya tsinci kansa da kara matso da face ɗinsa dab da tata ba. Jin tana iya jiyo numfashinsa yasa ta ɗan tsorata tare da waro idanu dan ta tabbatar da abin da take tunani. Ai kuwa shiɗin ne, hakan yasa ta yi saurin mayar da idanunta ta datsesu tana jin jikinta yana mata wani irin kamar mai jin sanyi. A hankali ya koma baya baya ya kwanta da ita a saman mattress ɗin tare da juyowa gareta da kyau, tana kwance saman mattress ɗin ya ɗan kwanto kanta kaɗan face ɗinsa a daidai sai tin tata. Tsoro ta ji ya kamata, tana son buɗe idanu taga wenenen zai yi mata amma kuma tana tsoron yin hakan, dan kada su haɗa idanu. Ya kasa iya furta uppan ya kai ɗan bakinsa saman tata, da alama a wannan gaɓar ya manta da yana jin kunya. Lips ɗinta na ƙasa ya kama ya fara bata hot kiss da shi kansa bai san ta ya aka yi ya iya yin hakan ba, lips ɗin nata ne sun tafi da imaninsa sosai. Mutuwar kwance ta yi, ta gaza iya gane mema yake yi mata, ta rasa a wani duniya ma take, ji ta yi kanta na jujjuya mata. Shi kuwa da daɗin kiss ta ɗebesa bai san lokacin da ya kai hannunsa saman tula tulanta ya fara matse mata su ba. Haba ai jin haka yasa bata san lokacin da ta kai hannu tana ƙoƙarin ture shi ba, ta fara ƙoƙarin raba bakinta da nasa, hakan ce ta fargar da shi tasa ya yi saurin zame hannunsa daga kansu ya kuma raba bakinsa da nata ya miƙe daga kanta zubur kamar wanda aka razana. Kamar maras gaskiya ya miƙe tsaye ya nufi waje, ita kuma kasa motsawa ta yi daga wajen, ta yi shiru kamar wadda ruwa ya cinye. Yana fita ya bar gidan mai gabaɗaya, dan baya son su haɗa ido a yanzu. Yana fita kuma suka haɗu da Ibrahim kanin maman Mahnoor ɗin. Jerawa a tare suka yi suka nufi hanyar gona. Ita kuma ta jima a kwance a saman mattress ɗin kafin daga bisani ta miƙe, kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta lallaɓo ta fito waje, yau ta jita a sabuwar duniya ta musamman, har wani ɗan munafikin jiri jiri take gani. Waje ta nufo, dik da tana cikin hijabi ya taɓa mata tula tulan nata har yanzu ji take yi kamar hannunsa yana a kansu, sai ta ji kamar yana matsa mata su, abin ku da bata saba ba. Tana fitowa waje Nenne na shigowa cikin gidan, katari suka yi a in da ta tsaya a tsakar gidan tare da yin ƙasa da kai, dik sai ta ji kamar tsirara take, kunya kamar ta shige cikin ƙasa, sai take ganin kamar Nennen tasan me ya faru, kamar ta ga kiss da Jaish ya yi mata. Ita kuwa Nenne wani irin ɗan iskan matsiyacin kallo ta fara binta da shi, so take ta fahimci wani abin, sai take ganin kamar Jaish ya cika aiki shiyasa take wani rakuɓe rakuɓe. Ƙasa ta yi da murya kamar kishiyoyin da suka haɗa kai suna gulmar uwar mijinsu. "Ke mijinki yana ciki?". Ta faɗa cike da fargabar amsar da zata bata, tana tsoron ace tana nan. Kai ta fara girgiza mata alamar a'a baya nan, kanta a ƙasa taki ɗagowa. Haba jin baya nan yasa ta ɗaga murya. "Dan ubanki meyahanaki fitowa ki yi mun aikin da kika saba yi". Ƙasa iya bata amsa ta yi, dan ba zata iya yin magana ba, Jaish ya kwance mata notikan ƙwaƙwalwa, abin da bata taɓa saninsa ba, bata yi tsammani ko tunanin makamancinsa ba da rana tsaka suna ganin juna ya wani kama ya sha mata ɗan bakinta dan tabbatar rashin kunya irin nasa. "Ina magana ba zaki bani amsa ba sai na taka ruwan cikinki a wajen har sai kin mutu ne?". Jikinta ne ya fara kerma, sai ta fara ruwan hawaye, domin kuwa bakinta yaki iya buɗuwa ta bata amsa, sai kawai ta fara kuka. Nufota gadan gadan ta yi da nufin ta daketa, sai da ta isota gab da ita kome ta tuna sai kuma ta fasa, a cikin ranta ta ce kenan ya tabbata mijin nata ya cika aiki, tun da ga shi ko magana ma ta kasa iya yi. "Wuce ki zo ki gyara mun ɗakina, dama ban sharesa ba". Ta faɗa a gadarance, irin ta isa da ita ɗin nan. Ba komai yasa ta fasa dukanta ba kuma face tana tunanin a kowani lokaci Jaish zai iya shigowa cikin gidan, kada ya shigo ya sameta tana ruwan hawaye ya zamar mata matsala, shi ne yasa ta dakata bata kai mata jibgar da ta yi niya ba. Da kyar ta iya buɗe baki ta ce. "Kiyi hakuri amma ni hamma ya hanani yin aikin komai sai na tambayesa". Eyeee zaro idanu waje sosai ta yi, bata taɓa expect ɗin irin wannan amsa daga gareta ba, ba ƙaramin fusata ta yi ba, cikin fushi ta ɗaga hannu da nufin ta yi mata duka har sai ta kasa miƙewa, a wannan gaɓar ɓacin rai yasa ta manta da cewa Jaish ne mijinta fa, sai ta yi yunkurin jibgarta. Ina ai bata tsaya ba, gudu ta yi ta bar mata gida, dan kuwa zancen mijinta yana a ranta na kada ta tsaya wani ya daketa, sai ta watsa a guje ta barwa Nennen gidan. Baki galala Nenne ta buɗe tana bin bayanta da kallo har ta fice ta bar gidan, dama ita Mahreen tun da ta gama cin abincinta ta wuce wajen bappanta. Tana fita gidan ta dakata da yin gudun ta fara tafiya cikin nutsuwa, yunwa take ji baiwar Allah, ta fito da nufin ta nemi abincin da zata sa a bakin salatinta amma Nenne ta hanata yin hakan ma. Kai tsaye wajen bappa ta nufa. Tana tafiya tana waige waige, dan a tunaninta Nenne zata biyo bayanta. Tana tsaka da waige waige bata ankara ba sai ji ta yi ta bugu mutun. Baya baya ta yi kamar zata faɗi, a ɗari ta ɗago kanta domin ta ga wanene. Ba ƙaramin razana ta yi ba na ganin yadda ya ɗaure fuska yake binta da wani irin mugun fusatatcen kallo. Murya na kerma ta ce. "Hamma....... Hamma Faisal ina......... Ina kwana". Tana magana maganar yana rarrabewa. Ko uppan bai furta ba, sai ma wani irin harara na musamman da ya bita da shi, dan a cewarsa ita ce nan ta ci amanarsa, dan da ta ce fir bata son Jaish bappa ba zai yi mata dole ba, dan haka yanzu ya tsaneta kuma har da cin alwashin ba zai rabu da ita ba sai ya ɗauki fansa. Takowa ya fara yi tana tinkarota da nufin ya aikata mata dik abin da ya zo cikin ransa. Baya baya ta farayi tana zaro idanunta. Ganin da gaske yake kara tinkarota yasa ta juya ta watsa a guje. Sai dai bata yi nisa a gudun ba ta ci karo da su Salisun Inna Rabi dake nemanta dan ɗaukar fansa su ma. Ga kuma Faisal ɗin ma ya biyo bayanta, kai jahilci dai bata yi ba a rayuwa wlh. Ihu su Salisu suka saka suna murnar yau sun kamata, ga shi kuma a cikin gonaki ne su yi mata duka su gudu babu wanda zai san su suka yi, amma fa a cewarsu. Salis shi ne a gaba ya nufota yana faɗin. "Yau ai gudun naki ya kare ko akwai saur.............". Bai ƙarisar da maganar ba ya dakata, ya zaro idanun nan waje kamar zasu faɗin ƙasa yana kallon Faisal dake bayanta wanda ya iso wajen ba jimawa. Ita ma zaro idanu ta yi tana kallonsa tana mamaki me ya gani yake zaro idanun. A miliyan ya juya kamar kafarsa zata tsinke saboda gudu ya bar wajen. A hanzarce ta juya domin ta ga wenenen a bayan nata. Tana juyowa sai taga Faisal ya ɗaga sandar hannunsa zai buga mata Jaish dake bayansa ya riƙe sandar, wannan dalilin yasa Salis suka bar wajen a guje, su ƴan uwansa ma sun rigasa barin wajen, dan su tun Jaish bai iso wajen ba suka hangosa, hakan yasa suka gudu. A tunanin Faisal bappa ne ya riƙe mashi sandarsa hakan yasa ya juyo da karfi dan ya gaggaya mashi maganganu son ransa. Sai dai kuma yana juyowa suka yi ido biyu da namijin gaske, ai bai san time ɗin da ya saki sandar ba, ya koma gefe yadda zai ji daɗin ganin Jaish ɗin da kyau. Jefar da sandar a gefe ya yi tare da miƙa mata hannu a kan ta zo. Ba musu ta nufesa dan a tsorace take da Faisal. Kamar zai yi wa Faisal ɗin magana sai kuma ya fasa, saboda yasan in ya ce zai yi magana ransa ne zata kara ɓaci yaja ya karya Faisal a banza, shiyasa ya wuce, amma ba wai dan ya barsu bane, so yake ya haɗasu da su Salis ɗin dikka ya ɗauki kwakkwaran kataki a kansu wanda gobe ko da kuɗi aka basu ba zasu nufeta ba, ko ganinta ma bazasu so su sake yi ba. Cikin gonar bappa ya nufa hannunsa riƙe da nata, suka bar Faisal tsaye yana binsu da kallon takaici kamar zai haɗiyi zuciya ya mutu. Suna shiga cikin gonar akwai wani faffaɗar bishiyar gwaiva mai wani irin faɗi ta tsakiya kamar kujerar zama, a kasan bishiyar suka tsaya, sannan ya sanya hannunsa dukka biyu a saman waist ɗinta ya ɗaga ta sama, ya ɗaurata a saman bishiyar ta zauna kamar kujera, sai ya zama tana daga zaunen tsawonsu ya yi daidai. Ai bata san lokacin da murmushi ya subce mata ba, ta manta da tana jin yunwa, bappa yana can wajen kiwo sun zo gonarsa zasu kashe juna da love su shuka flowers ɗin kaunarsu bai sani ba. "Meya fito dake daga gida?". Muryarsa ce ta katse mata murmushin da take yi. "Nenne ce zata dakeni shiyasa na gudu". Ta bashi amsa tana sunkuyar da kai ƙasa. Jinjina kai ya yi har cikin ransa ya ji daɗin hakan, kuma ya kudurta dole yau ba sai gobe ba ya yi mata tsakani da Nennen nan in ba haka ba ta kuskura ta sake taɓa mashi lafiyar jikinta to fa zasu ga abin da basu taɓa zato ba, shi yanzu ya ji daɗin duniya a tattare da ita, dan haka jikinta nasa ne ba nata ba, jiya ya yi barci cikin nishaɗi har da makara saboda daɗin kasakcewarta a jikinsa, dan haka babu wanda zai sake taɓa mashi jikinta ya zauna lafiya..... (To fa. Maman Sultan kina ina? Jaish dai ya ɗanɗani daɗin duniya za'a fara ɗaukar fansar dik wanda ya taɓa mashi jikinta😅🤭 eyee su Malam Jaish, aa ban ga laifinka ba, ai jikinka ne ma daman, oh ni Bintu ɗiyar babana, ina ganin al'amura a wajen Jaish namu na gargajiya 🤭) Ganin ya luluƙa duniyar tunani ne yasa ta sanya hannunta a saman shoulder ɗinsa dan ji take yi kamar zata faɗi ƙasa shi kuma bai ankara ba ya afka tunani ya barta. Ajiyar zuciya ya sauke ya jin hannunta a jikinsa, ɗago kai ya yi ya kalleta da kyau, ga yanayin wajen akwai ɗan sanyi madaidaici, dan a bayan wannan bishiyar gwaiva fadamar nomar shinkafa ce a wajen, a nan bappa yake nomar shinkafa, kun san kuma dik in da fadama take to fa akwai yalwar sanyi a arear. Yanayin wajen akwai daɗi ga masoya, ga iska mai daɗi ta ganyen bishiyoyi suna kaɗawa, sosai ya ji wani irin tsumin soyayya na tsuma shi, ga tsumin sha'awa dake addaba mashi. Ɗago kai da ya yi ya kalleta babu abin da ya zo ransa face kiss da ya yi mata ɗazun, ba ƙaramin daɗin abin ya ji bafa, bai ki ya yi ta shanye mata baki daga nan har dare ba, abin akwai sugar amma fa in ji shi tom. Zubawa laɓɓan nata idanu ya yi yana wani kallonsu cike da kwaɗayin ya sake sha. "Hamma jiya Mahreen ta ce ka cire mun gwaiva ka ajiye mun to ina yake?". Kai Mahnoor akwai nutsuwa yarinyar, dole idan tana magana ta sa ka bita da kallo, wannan nutsuwa tata tana kara jan hankalinsa sosai. Da kyar ya iya cewa. "Sai dai in ciro maki wannan, na jiya na barsa a wajen da muka ci abinci ai". "Tom ka ciro mun". Ta faɗa tana ɗan sake shoulder ɗin nasa dan ta bashi damar ciro mata. Hannu ya miƙa ya tsinko guda biyu dake kusa da su, sannan ya ƙarisa wajen fadamar ya wanko mata su ya dawo. Sun kuwa nuna sosai, saboda ba mai zuwa ya cirosu, dama shi yake cire masu sai kuma bappa idan ya shigo cikin gonar. Wajen da ya tashi ya koma ya tsaya, miƙo mata su ya yi, sai ta ɗauki karamin ciki ta bar mashi babban. Kallonta kawai yake yi bai ce komai ba. Kasa iya kai gwaivar bakinta ta gutsira ta yi saboda kunyarsa, ya kafeta da kallo, sarai yasan ba zata iya ci a gabansa ba, amma yana son hakan ne yasa ya tsareta da kallo, dan in ta motsa lips ɗin nan nata ba ƙaramin rikita shi take kara yi ba. Shiru shiru ta ki ci kanta s ƙasa, shi kuwa da ya kasa hakuri bai ma san lokacin da ya kai nasa baki ya gutsira ba, sai ya kai mata ragowar saitin ɗan bakinta a kan ta gutsira. Ki ta yi tana wani muku muku, wani tunani ne ya faɗo mashi a ransa wanda ya yi matukar yi mashi daɗi, ya kuma ji zai iya aikatawa, kara kai ragowar gwaivar da ta ki karɓar bakinsa ya yi, ya sake gutsira kaɗan, sai ya shammaceta ya matso kusa da ita sosai ya haɗe bakinsu waje guda. Subhanallah wani shock da ta ji ne yasa bata san lokacin da ta ƙanƙame shoulder ɗinsa ba, shi kuma yasa hannunsa ɗaya ya riƙo waist ɗinta ta baya, ɗayan kuma ya tallaɓo bayan wuyarta da kyau dan ya ji daɗin yin abin da yake yi. A hankali hankali yake tura mata gwaivar da ya fara tauna cikin bakinta, kuma dan tsabar tabbatar rashin kunya wai sai ya rufe idanu kada ma su haɗa ido kenan. Yana tura mata gwaiva yana tsotse mata lips na ƙasa cikin dabara, sai wani sauke ajiyar zuciya take yi yana ɗan shafa waist ɗinta. Daga karshe ma sai ya janyota ta dawo saman kirjinsa mai gabaɗaya, dik sai ya ji ma da ace a ɗakinsu suke mana, amma a nan ɗin ma ya more ai. Hannu bibbiyu tasa ta riƙosa da kyau dan kada ta faɗi, ta datse idanu gam kamar zata fasasu, dik wani kofa a jikinta sai da ya buɗe, ya sanyata cin gwaivar dole, dan kuwa dan dole ta karɓi wanda ya turo mata da tongue ɗinsa. Tsabar rashin kunya har da wani sanya harshensa yana wasa da gwaivan da yake tura mata ɗin, jin sa yake yi a wata iriyar duniya ta daban, kwata kwata ya mance da in da yake. Kai my people's Jaish ya iya goge hadda, amma mu leƙa KINGDOM OF POWER mu dawo, dan lokacin da na ɗeba maku ya kusa karewa kuma ban son na yi rubutun page ɗungurungum a part ɗaya ba tare da na leƙa wani part ɗin ba, dan haka mu je mu leƙa mu dawo sai mu ji daɗin ganin soyayyar tasu da kyau. ______________🌹💘_____________ KINGDOM OF POWER💪🔥 King and his first love ne zaune a cikin room ɗinsa, King yana zaune a saman bed ya jingina bayansa da jikin headboard na bed din. Shi kuma Ramish yana kwance a saman bed ɗin, ga two cup of cappuccino a saman table kusa da bed ɗin Momma ta kawo masu ta fita. Ramish ya tada kai da laps ɗin daddyn nasa kamar wani ƙaramin yaro, sai shafa arab hairnsa King yake yi yana jin wani irin tsantsar farinciki. Ba jimawa suka dawo daga ɗakin Jawad da yake ta zuba barci sakamakon alluran da Dr Raj ya yi mashi, sun samu bugun zuciyarsa ta daidaita, komai ya fara tafiya normal shi ne Dr ya ɗirka mashi alluran barci dan su samu ya samu wadatatcen hutu, yanzu haka yana ta zuba barci Rizwan na zaune a kusa da shi yana ta kallonsa kamar zai yi mashi numfashi saboda so da kauna, dik yana firgice bawan Allah. _____________🌹💘🔥______________ "Son baka ce mun komai bafa". Cewar King. Ramish dake kwance ne ya ce. "Dad dama tunani nace maka zan yi, to yanzu na yanke matsaya". Cikin nutsuwa kamar baya son yin magana ya yi ta, word by word, character by character. "To me ka yanke my son?". "Na yanke babu batun zuwa wani yaki a yanzu, kaga jibi za'a ɗaura auren Rizwan, so kada ka yi wani yunkuri, ka bari kuma kada ka gayawa kowa ka barin, ka bari makiyanka su yi ta tsammaninka a yayin da kai kuma zaka ki zuwa, ka shanyasu su yi ta jira har su gaji su cire tsammanin, a lokacin da zasu cire tsammani su manta da batun a lokacin kai kuma zaka mamayesu ya cinma burinka, hakan sai ya fi maka".. Jama'a nace ku tafawa Ramish, akwai kaifin ƙwaƙwalwa, kamar yasan akwai abin da ake shirya masu na tuggu, like wow tunaninsa ya ƙayatar. "E son ka kawo shawara my kyau, zamu tattaunata da Abbas da kuma sauran wakilan fada sai mu ji me su kuma zasu yanke a kanta". Miƙewa zaune Ramish ya yi. "No dad, kada ka gayawa kowa, kullum fa muka yi waya sai na ce maka ba'a yarda da kowa a duniyar nan, ka dai'na yarda da kowa". Droopy nose ɗinsa King ya ɗan ja kafin ya ce. "Son a naka yanayin aikin ne zaka ga kamar ba'a yarda da kowa, amma shikenan tun da ka ce kada na gayawa kowa, ba zan faɗa ba, amma zamu tatauna da iya Abbas and Jahiz kawai". Ɗan ciza Heart shaped lips ɗinsa ya yi kafin ya ce. "Dad even uncles ɗin ma i didn't agree ka gaya masu, just ka bar zancen iya mu biyu, idan ranar Sunday ta zo sai ka ce da commander ka ɗaga bayun tafiya yakin nan, in suka tambayeka sai yaushe kuma kada ka gayawa kowa, ai tsammaci abin da baka tsammata ba ya fi, ka dai'na gayawa kowa shirinka sai ranar aiwatarwa kawai a gani a ƙasa". Ya kai karshen maganar yana komawa ya kwanta. "Ni dai zan yi magana da Abbas and Jahiz, son uncles ɗinka ne fa, do you mean su ma baka yarda da su ba or kada na yarda da su kenan?". Girgiza kai ya yi. "No dad, tom shikenan kana iya faɗa masu ɗin, amma bayansu don't tell anybody". Jinjina kai ya yi yana cigaba da shafa mashi kai. "I really missed u my son". "Missed u more my dad, kullum kana rai'na, da kai nake kwana nake tashi". Sumbata a goshi King ya kai mashi yana mai jin tsananin kaunar ɗan nasa. "Tashi mu sha cappuccino". Cewar King. "No dad bari Bilal ya zo sai mu sha a tare". Jinjina mashi kai ya yi, daga nan ya ɗauko mashi hiran duniya, a nan yake tambayarsa shi kuma sai yaushe zai fito da mata ya yi aure tun da ga Rizwan nan zai yi auren. "Kai dad zaka fata ko? Ni ai bani da ko budurwa, ban ma taɓa yi ba, kuma ba yanzu zan yi ba, sai na kara girma, dan nifa har yanzu son kake ce mun". Harararsa King ya yi kafin ya ce. "Ai ni ina da ƴan'matan da zan iya bawa kowannenku idan ma baku da budurwa, da safe ka duba Sarina mana zata dace da kai, kaga ba sai mun fita waje nema ba, dikka ranon mommarku ce, zaka ji daɗin zama da ita In Sha........." Rufe mashi baki ya yi da tafukan hannunsa. "Kai daddy is okey please, who's Sarina? Ni fa bana rayin auren ne yanzu dad, please ka kawo wani hira, ni ban girma ba, sai ranar da ka dai'na ce mun son zan girma". Ɗan cizan hannun nasa King ya yi har sai da ya zameta daga bakin nasa yana ɗan ɗaure fuska. "Ni kuma maganar auren nake so, ba kun biyewa Jahiz da wata banzar tunaninsa wai sai ya kai 40 years zai yi aure ba ko? To ni ban yarda ba, kawai ka je ka duba Sarina da safe sai a haɗa aurenka da Rizwan tun da dikka abu ne na gida, batun son kuma daga nan har jikokinka in ban mutu ba a son kake a bakina". Miƙewa zaune ya yi tare da matsowa zai sauƙa daga saman bed ɗin. A hanzarce King ya janyosa yana faɗin. "To sarkin zuciya dawo mana, haba my son to mu bar maganar zo ka gaya mun labarin wajen aiki". Juyowa ya yi ya dawo jikinsa ya kwanta. "My dad on Friday after ɗaurin auren Rizwan or Saturday zan............ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ No editing 47 Juyowa ya yi ya dawo jikinsa ya kwanta. "My dad on Friday after ɗaurin auren Rizwan or Saturday zan yi tafiya, i have a beautiful surprise for u". Ya faɗa fox-s eyes ɗinsa masu kama da sleeping eyes ɗin nan a kan daddyn nasa, idan ka kallesa in the first place zaka yi zaton idanun nasa sleeping eyes ne, amma fox-s ne, suna da banbanci da sleeping eyes, sun fi sleeping eyes kyau da ɗaukar hankali, sannan yana yawan lumshesu yasa suka kara rikiɗewa izuwa sleeping eyes ɗin da kyau. "Okey i wouldn't ask which surprise, but I will ask one question on that". "No please daddy don't ask". Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa da kyau dan ya ji daɗin tumurmushe jikin dad ɗin nasa. "But why?". King ya faɗa yana kallonsa. "Daddy it's a surprise I told you, meyasa zaka yi tambayi question again? If I tell you what's the surprise now, it won't be a surprise again" Sake jan doopy nose ɗinsa King ya yi. "Son u want me to sleep with thinking something in my mind?". Girgiza kai ya yi. "No dad". "Okey tell me where you are going and what you are going to do there?". Sallamar Bilal ce ta katse masu hiran nasu da suke yi. Dawo da kallon gabaɗayansu suka yi a kansa. "Kai Ramish Mama tana can tana nemanka kai kana nan ko?". Cewar Bilal. "Nemana kuma? A kan me to?". "I don't know, amma nasan in kaje u will know the reason". Ya kai karshen maganar tare da hayewa saman bed ɗin. "Dad i really missed so much". Ya faɗa yana matsowa kusa da King da yake ta binsa da kallo kauna. "Dad lafiya kake ta kallona haka?". Ya sake jefa mashi tambaya bayan ya iso kusa da shi kenan. "What's wrong with u Bilal?". King ya faɗa. "Nothing dad". Ya bada amsa a taƙaice. Kallon Ramish wanda shi yake kallo shi ma dad ya yi. "What's wrong with my love Son?". Juyowa Ramish ya yi yana kare mashi kallo, ba shakka ya ɗan yi rama, kai King har ya ganosa, ni kuwa na ce anya Bilal ba son Leesharh yake yi ba kuwa? Ko dai kewarta ce ta sako shi a gaba har ya fara ramewa haka. Dr Raj ne ya shigo cikin ɗakin bakinsa a ɗauke da sallama, hannunsa na riƙe da cup of coffee, ɗayan hannun nasa kuma wayarsa ce a riƙe, kayan barcice a jikinsa wando dogo da riga mai ɗan madaidaicin hannu launin coffee brown, ya yi matuƙar kyau a cikinsu. Saman bedside drawer ya zauna yana faɗin. "Our hero barka da dare". Sai binsa da kallon tsab King yake yi dan ya ga ko akwai wata abar zargi a jikinsa. Chuchu da Guyson a tare suka shigo cikin ɗakin suma. Ganin yayyunta maza a ciki yasa ta ji kamar ta koma, dama Guyson ne ya sakota gaba a kan ta zo su je wajen dad, ya lura tana cikin damuwa sosai ne yasa ya ce ta zo su je dan su taya dad hira su rage mashi kewa. Saman gado Guyson ya haye tare da shigewa tsakanin Bilal da Ramish ya yi kwanciyarsa. Ita kuma ta tsaya tana kallon yayanta wato Bilal, yana kama da ita sosai, jini ba wasa ba. King ne ya yi mata alama da hannu a kan ta zago ta gefensa ta zo. Ba musu ta ƙarisa da hanzari, ɗan rungumota ya yi yana faɗin ina autarsa?. Shi dai a jikinsa yana jin lallai Chuchunsa Jawad take so na Rizwan ba, sai dai kuma tun da ita da bakinta tace Rizwan ɗin takeso ba sa tirsasa mata ba ai. Miƙewa Ramish ya yi ya nufi waje domin amsa kiran mamarsa, ya bawa Guyson damar komar da kansa saman laps ɗin King da kyau, shi dama Bilal a gefe ya kwanta yana aikin taɓa waya, yana son yin chat da Leesharh bashi kuma da numberta, ji yake yi kuma ya fi karfin tambayar Sharifat. Shi ne yasa dik ya shiga damuwa. ______________🌹💘____________ A ɓangaren Auta kuwa, mu ɗan koma baya kaɗan, da yamma kamar yadda ta faɗawa commander Zafar tana son haɗuwa da Hoorain a lambun daddy hakan aka yi, ta yi wanka ta tsara kwalliya ta nufi lambun nasa, ta zauna saman sofa tana jiransa, shi kuma in baku manta ba ai commander bai gaya mashi ba, ya ki sanar da shi. So bai san tana jiransa na, yana can suna gardama da Ansar. Ansar ya ce mashi. "Hoorain batu na gaskiya son Gimbiya Zunaira kake yi, ko ka fito ka faɗi gaskiya ko kuma ka cutar da kanka, kuma ita ma wlh tana sonka sosai, naga hakan a tattare da ita". Kansa yana ƙasa ba tare da ya ɗago ba ya ce. "Wacece kuma gimbiya Zunaira?". Kai Hoorain ma wato ɗan duniya sosai, wai wacece Zunaira? To koma dai wacece ai zamu gani dan gidanku idan zuciyarka ta kusa bugawa ɗan ikka kawe. Taɓe baki Ansar ya yi, mamaki kamar me, shi har yanzu ya kasa haddace ainahin wanene Hoorain, dan kullum da sabon hali yake ganinsa, sun fi shekaru 10 suna a tare, amma wlh kullum da kalar halin da yake kallon Hoorain da shi, yau kuma ga wata sabowa wai bai san Zunaira ba, Allah mai iko. "Hoorain a matsayina na aminin da baka da biyunsa, ɗan uwanka kuma, wlh zan baka shawarar da ko ba zaka gayawa kowa kana sonta ba ita ka sanar da ita, ka sani Zunaira kowa sonta yake yi a............." Ƙasa ƙarisa maganar ya yi sakamakon wani irin kallo mai kama da harara da Hoorain ɗin ya ɗago idanu ya watsa mashi wanda bai ma san ya watsa mashi ɗin ba. Ɗan siririn murmushi ya saki kafin ya cigaba da cewa. "Mayar da wukar sarkin kishi da zuciya, ai ba wai irin wancan soyayya nake nufin kowa yake yi mata ba, ina nufin ƴan uwanta har da mai martaba sun fi sonta sama da kowa, dan haka idan ta ce kai take so babu mai hanata dan suna son farincikinta, kada ka cutar da kanka a banza ɗan uwana". Kawar da kallonsa ya yi ya cigaba da kallon kasa, cikin sanyin murya ya ce. "Wai Ansar lafiyarka kuwa yau? Ko dai ka sha wani abin ne?". "Ni babu abin da na sha, me ka gani da zaka ce na sha wani abin?". Harara ya ɗan watsa mashi ta witsiyar ido kafin ya ce. "Kazo ka dameni da batun wanda ban santa ba, na tambayeka wacece ita baka gaya mun ba, ni ban san wata Zunaira ba, haka zalika ban san wani abu wai shi soyayya ba!!". With his full confidence ya yi maganar kamar da gaske, in baka san shi a tare da Auta ba wlh zaka rantse da gaske yake yi bai santa ba. "Baka san wacece Zunaira ba then me hotonta yake yi a wayarka? Me hotunanta suke yi a room ɗinka?". Shiru ya yi bai amsa mashi ba, dan a yanzu dai bashi da abin cewa. "Har da nuna madaran kishi a kanta ka wani ce baka santa ba, meyasa ɗazun zaka ɓata rai har da shiga damuwa dan ka ganta riƙe da hannun wani wanda kasan ya fika kusanci da ita? Allah Hoorain zaka cusawa kanka wani cutan in baka kiyaye ba". Nan ma dai shiru bai tanka ba kuma bashi da niyar tankawa, dan shi kaɗai yasan me a cikin zuciyarsa baya kuma neman wani ya sani koda kuwa Abbonsa ne, idan akwai wanda ya kamata ya sani cikin gaggawa ma to bai wuce ita dake cikin zuciyar tasa ba. "Hoorain wlh zan baka shawara, ka sami gimbiya ka gaya mata gaskiyar abin da yake a ranka, wlh ba zan yi kaffara ba ita ma tana sonka, naga hakan a cikin idanunta ɗazun............" Shiru ya dakata da yin maganar sakamakon sake ɗagowa a karo na biyu da Hoorain ya yi ya dallah mashi harara. Sai a lokacin kuma ya buɗi baki yana a harararsa ya ce. "Awww dama kallonta kake yi kenan?". Ai Ansar bai san lokacin da dariya ta kubce mashi ba. "Wato Hoorain ni ka rai'na ko? Yanzu kenan kasan wacece gimbiya ko?". "Wato kallonta kake yi ko?". Ya sake jefa mashi tambaya yana ƙara ɗaure fuska irin shi fa ba da wasa yake yi ba. "E kusan haka, amma kuma ai matar abokina nake kallah ko? Ko nace maka da wata manufa nake kallonta? Ni kawai dan na tabbatar da zargina a kanku nake hakan, kuma na tabbatar.........." Bugun da Hoorain ɗin ya yi niyar kaimasa a damatsan hannunsa ne yasa ya dakata da maganar ya kuma kaucewa bugun da sauri. Har cikin ransa ya ji daɗin da Ansar ya ce matar abokinsa yake kallah, sai ya ji dama Allah ya amsa bakin Ansar ɗin. "Allah Hoorain baka da dama, ni yanzu to me na wani kai mun bugu? Daga faɗar gaskiya, look, sonka fa nake yi yasa nake maka faɗar soyayyarta kada wani ya rigaka, kai kanka kasan da ace zaratan samarin gidan nan ba mahaifinsu ɗaya da ita ba da tuni sun kacame da faɗa a kanta, amma kai ka samu dama kana son wahalar da ƴar tahaliƙa ko?". "Ni wai Ansar me ka sha ne yau? Hala ka je ka sha wannan abin da baba dattijo yake yawan girkawan ko?". "Wani abu ne kuma baba dattijo yake girkawa?". Harararsa ya cigaba da yi. "Allah ka fita idona bana son shiririta, ni nace maka ban san maganar da kake yi ba". Yana magana yana ƙara ɗaure fuska. "Hoorain mu yi magana serious please, bar wasa, tsakaninka da Allah kana son gimbiya ko baka sonta?". Ya yi maganar shi ma yana ɗan ɗaure fuska irin da gaske yake yin nan. Wani irin nisawa ya yi, ya ɗan lumshe idanunsa ya sake warosu, cikin sanyin murya ya fara magana kamar haka. "To Ansar menene amfanin in na gaya maka gaskiyan? Me zata kara maka in banda bakinciki?". "No Hoorain, kada ka ce haka, babu wata bakinciki da zata kara mun, sai dai ma mu nemowa kanmu mafita, Please answer my question, kana son gimbiya ko a'a?". Shiru ya ɗan yi na a akallah 2 mins haka, ya mayar da kansa yana kallon ƙasa, kamar mai nazarin wani abin sai kuma ya ce. "Tun tana da shekaru 5 a duniya ma nake sonta, in takaice maka labarin tun ranar da na fara ganinta Prince Jaish yana ɗauke da ita, a lokacin tafiya mai kyau ma bata iya ba, amma kuma soyayyar ai bata da wani amfani, babu abin da zata yi mun da ya wuce cutar da ni, dan nasan ba zan taɓa samunta ba........" Ƙasa idasa maganar ya yi ya dakata yana jin zuciyarsa tana yi mashi zogi, wannan dalilin yasa baya son yin magana a kanta, ko kuma su haɗa ido da ita yana cutuwa. Dik ranar da suka haɗu kwana yake yi baya barci, tun farkom dare har karshenta tunaninta zai kasance yana yi, sai idan ya ji zuciyarsa na neman azabtuwa sosai ne sai ya miƙe ya ɗauro alwala ya zo ya fara nafilfili domin ya rage tsawon dare, amma barci kam sam baya rintsawa, tana ransa a kullum, da ita yake wuni ya kuma kwana ya tashi, ya yi mafarkinta a duniya babu adadi, baki ba zai iya zayyana yadda yake ji a kanta ba. "A lokacin da King ya sanyani kula da ita sai da na ji tankar na zuba ruwa a ƙasa na sha saboda daɗi, ban taɓa son wani abu a duniya kamar yadda nake sonta ba, amma dik nasan a banza ne, nasan sai dai na mutu da soyayyarta a cikin zuciyata". Ya kai karshen maganar yana ɗago da idanunsa da suka rikiɗe a take suka yi jajir. Sam Ansar bai yi mamakin ganin idanunsa sun rikiɗe sun yi jajir ba, saboda yasan wanenen shi, akwai taurin zuciya da iya shanye abu, sai dai kaga alamarta a cikin idanun nasa. Matsowa Ansar ya yi ya dafa saman shoulders ɗinsa dikka biyu, cike da tausaya mashi ya fara magana kamar haka. "Hoorain ka dai'na cewa soyayyar da kake yi wa gimbiya maras amfani ce........". "Ansar idan ban kirata da maras amfani ba me kake son na kirata da shi kenan?". "Hoorain wlh soyayyarka a gareta ba maras amfani bace". "Saboda me zakace hakan?". "Saboda kasani kuma kasan nasan kasani gimbiya ita ma tana sonka, tana sonka kamar yadda kake sonta". Girgiza kai ya fara yi. "No Ansar, tana dai sona, amma ba kamar yadda nake sonta ba, badan iyaye iyaye bane da sai nace nama fi King sonta, amma ina da tabbacin nafi su Prince Jaish sonta". "Sannan soyayyar da take mun shima dik na banza ne, ita ma wahala zata sha kawai kamar yadda nake sha, dan sanin kankame dik cikin masarautar nan ita kaɗai ce ma take daga idanu ta kallemu". Zuciya babu daɗi ya kai karshen maganar. "Hoorain zaka yi nasara, wlh trust me, ka ɗauki shawarata ka bayyana mata soyayyarka, in har soyayyar gaskiya ƴan uwanta suke yi mata to dole su baka aurenta a lokacin da zata ce masu babu wanda take so sai kai, idan har baka gaya mata kana sonta ba to ka sani tabbas za'a yi mata miji ne a cikin gida, in kuma hakan ya faru babu abin da zata iya cewa dan bata san kana sonta ba, baka bayyana soyayyarka a gareta ba ba ta yadda za'ayi ta fito cikin ƴan uwa tace bata son wani sai kai, think about it". Shiru ya ɗan yi yana nazarin maganganun Ansar ɗin, sai dai kuma baya jin kamar zai iya aikata hakan, saboda shi ya fi Ansar sanin su wanenen Jaish, ba zasu taɓa yarda ko da sunan wasa a bashi ita ba. "Trust me Hoorain, yanzu haka tana lambun daddynsu, tun ɗazun naganta a can, ka je wajenta, kada ka ɓoye mata gaskiya, ka bayyana mata kana sonta, da izinin Allah zamu yi nasara". Wani irin daɗi ya ji na jin cewa tana lambu, dama tuntuni yake ta fama da kewarta a cikin ransa, yana son sanyata a idanunsa, dama ce kawai bai samu ba, amma kuma dik da haka fa bai ɗauki shawarar Ansar ba, ya yarda zai je lambun dan yana son sanyata a idanunsa, amma ba wai zai je ya bayyana mata soyayyarsa a gareta ba. "Gimbiya bata da dalilin kinka Hoorain, dik in da ake neman namiji cikakke ka kai nan har ma ka wuce, kyan fuska Allah ya baka, kyan zuciya Allah ya baka, kyan jiki Allah ya baka, jarumta da jajircewa, ina ga baya Abbo a kaf cikin kingdom ɗin nan babu wanda ya kaika jarunta, zama assistant commander ba karamin abu bane, na duba gabas da yamma gudu da arewa ban ga wani abin da zai sa a kiƙa ba". Cewar Ansar. Hmmmmm jinjina kai kawai ya yi, shi kaɗai yasan me yake hangowa. Dafa shoulders ɗin Ansar ya yi. "My brother kai dai pray for me kawai, am coming bari in je ko ganinta ne na yi zan ji daɗi a rai'na". "By the grace of god zaka mallaki gimbiya, ina yi maka wannan addu'ar our Lion amount the Lions". "Thank you block brother". Ya yi magana tare da sake shi, cikin takun jarumta ya wuce ya nufi lambun. A lokacin ta fi awa tana zaune a wajen tana jiransa, har ta fidda rai da zai zo gareta sai kuma kwatsam ta hangosa ya shigo cikin lambun. Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya a lokacin da idanuwansu suka sauƙa a kan face ɗin juna, shi ma ya ji daɗin ganinta, ita kuwa ji ta yi tamkar ta tashi ta je ta rungumesa saboda tsabar farinciki. Idan ta kallesa sai taga kamar baya ganinta, amma tin da ya shigo idanunsa suke a kanta, sai dai ya ji babu daɗi a cikin zuciyarsa na ganin kamar tana a ciki damuwa sosai. Ita kuwa tana mutuwar son ganin yadda yake tafiya, yanayin tafiyarsa akwai ɗaukar hankali, sai ka yi zaton baya taka kafafunsa gabaɗaya a ƙasa, in ka kallesa a fisge zaka yi zaton da iya yatsun kafafun nasa kawai yake tafiya, amma sam ba haka bane, kawai jarumta ce da zafi wajen saurin tafiya yasa hakan. Tun bai gama ƙarisowa gabanta ba ta shagwaɓe fuska tana faɗin. "Hoorain tun ɗazun fa nake jiranka, sai yanzu zaka zo?". Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin jin cewa tun ɗazun shi take jira, to ai shi bai san da tana jiransa na. Amma sai bai nuna mata bai san shi take jira ba, sai ya ce. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe". "To zauna mu yi magana". Ta yi maganar tana nuna mashi saman sofa. Sanin cewa yau brothers ɗinta dik suna nan yasa ya ɗan girgiza kai. "A'a ranki ya daɗe mu yi maganar a haka ina tsaye". "Kana tsoron su Yah Ramish ne?". Ta jefa mashi tambayar idanunta a kansa. "Wani abu makamancin hakan dai". Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. "E sai dai wani abin makamancin hakan, amma dai ba tsoro ba, dan kuwa ni nasan my hero baya jin tsoron komai". Shiru ya yi kansa a ƙasa bai furta uppan ba. Shiru ita ma ta ɗan yi tana ta kallonsa. Sarai yasan shi take kallo, har ga Allah tausayi take bashi, yana jin kamar ya zubar mata da kwalla, yasan ta kamu da sonsa sarai, amma kuma yana ji a jikinsa ba zasu taɓa mallakar juna ba. "Hoorain Yah Jawad ɗina bashi da lafiya, na rasa ina zan je na ji daɗin rayuwata shi ne nace kazo mu yi hira dan nasan tabbas zan samu farinciki da nutsuwa idan ina tare da kai, amma kuma shi ne zaka ce ba zaka zauna mu yi hira ba ko?". Ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka. Ai bai san lokacin da ya juyo saitinta da kyau ya kuma ɗago ido ya kalleta ba, bai taɓa tunanin tana ɗaukarsa a matsayin mai sakata farinciki ba, shi dai ya san tana son shi, bai san soyayyar tasa ta kai har haka a ranta ba, Allah sarki wai bari ta zo wajensa tasan zata samu farinciki, bai yi zaton muhimmancinsa ya kai haka a gareta ba, ai kuwa bai kamata ace ta tafi bai sakata wannan farinciki da ta fito nema ba, sai dai kuma baya son ƴan uwnata su samesu a haka, yasan nan lambun daddynsu ne, kowa yana iya zuwa a kowani lokaci. Amma da ya tuna cewa farincikinta ya fi mashi komai sai ya matso ya zauna saman sofa. Kasa ya ɗan yi da kai yana tunanin to shi me zai ce mata ta yi farinciki ne wai?...... Yau ake yinta, masu abin fa suna magana, wayyo Allah shi da bai san komai ba face sare kawunan mutane a yaki ne zai sata farinciki, ina ga sai dai ya bata labarin kalar takobin da ya fi kaifi da kuma yadda ake sare wuyar mutane, yo in ba shi ba shi me ya sani? Dik tsawon rayuwarsa ya bata ta a yaki, bashi da wata abin da ta fi wannan. Ya ɗauki almost 10 mins shiru kansa a ƙasa, ita ma ta yi shiru tana ta kallonsa, ko ba komai ta ji daɗi ya zauna, sai bata furta mashi uppan ba. "Kiyi hakuri gimbiya, In Sha Allah Yah Jawad zai sami lafiya nan ba da jimawa ba". Ya faɗa kamar mai raɗa, kun san cewa abin da ya faɗa ɗin nan ita yake ta tunawa har na wannan tsawon 10 mins da ya zauna shirun? Kurma kenan, sam bai iya magana ba. "Allah yasa, amma kasan me ya sa Yah Jawad rashin lafiya kuwa?". Kai ya girgiza mata ba tare da furta uppan ba. "Yah Jawad yana son Aunty Chuchu, ita kuma ta fara soyayya da Yah Rizwan kafin Yah Jawad ya gaya mata yana sonta, to da dad ya tanbayeta waye take so sai ta ce Yah Rizwan alhalin ita ɗin ma Yah Jawad take so ba Yah Rizwan ba, ni kai'na na rasa dalilinta na zaɓar Yah Rizwan, bayan kuma ni da ita ta ce mun Yah Jawad take so, Yah Jawad fa tun tana ƙarama ya ce mun yake sonta, shi kuma Yah Rizwan sai da ta girma, jibi za'a ɗaura aurenta da Yah Rizwan to shi ne Yah Jawad ya fara rashin lafiya da ya ji hakan, ita kuma Aunty Chuchu na ce mata ta je ta gayawa daddy ita Yah Jawad take so ba Yah Rizwan ba, amma ta ce mun ba zata iya ba, ni yanzu ma na rasa me zan yi, shiyasa ina cikin damuwa sosai, dan Aunty Chuchuna ma bata da lafiya kamar dai Yah Jawad". Ta kai karshen maganar idanunta cike tab da kwallar. Tun da ta fara magana yake kallonta ta kasar ido, kansa kawai ya tuna, ashe a tare suka yi dakon soyayya shi da Yah Jawad, a gaskiya ya tausayawa Jawad ma bare kansa da bai san matsaya ba bai san a wani mataki yake ba a yanzu, dik sai ya ji ya karaya. Rasa abin faɗa ya yi sai kawai ya yi ƙasa da kai, sarai tasan bai san ta ce wa bane yasa ya yi hakan, dan dik wani halinsa babu wanda bata sani ba. "Ka taya mu da addu'a ka ji? Ka yi mana addu'a Allah ya barmu da masu sonmu na gaskiya". Ɗagowa ya yi ya kalleta, kamar tana karanta me a ransa, a sanyaye ya ce. "Allah ya baku mazaje na gari waɗan da zasu kasance alkhari a gareku". Da amin ta amsa idanunta a kansa. Tana son su yi hira amma ba hali, haka ta hakura suka cigaba da zama kamar kurame, sai aikin kallon juna. _____________🌹💘____________ JIMETA YOLA. Sosai ya yi kissing ɗinta kafin zame ɗan bakinsa, sai kuma ya rungumeta yaki bari ta ɗago bare su haɗa idanu, ita ma kwanciya shiru ta yi a jikinsa tana jin zuciyarta na harbawa da sauri sauri. Sai da rana ta ɗaga around karfe 11, sannan ne ya ce su je gida. Ba musu ta ce to, tana wani ɓoye fuska, shi kuwa da alama yanzu ya dai'na kunyarta, dan kuwa idanunsa a kanta har suka nufi hanyar gida, yana riƙe da hannunta, saboda tsabar kunya har ce mashi ta yi ya ɗan saketa sai ya yi gaba ko ita ta yi gaba kada su jera, amma ina yaki yarda, ya ƙanƙame suka nufi gidan. Ko da suka koma Nenne na tsakar gida tana shirye shiryen girkin rana, ko kallon in da take bai yi ba ya ja hannunta suka wuce cikin ɗakinsu. Suna shiga ya sake rungumota kamar wani ya ce zai rabasu, shi fa yanzu ya ji daɗin jikinta sai ku abin da hali ya yi. "Hamma bari na je na ɗumama mana abincinmu ma daren jiya da bamu ci ba?". Ta faɗa ƙasa ƙasa. Da to kawai ya amsa tare da saketa. Da sauri ta nufi waje, shi kuma ya karisa bakin mattress ya zauna, arab hairnsa yanzu ta yi tsawo saidai, yaki yin aski kuma, dan su askin reza suke yi, a cire gashi dikka, shi ne yaki yarda bappa ya yi mashi............😅 Ko da ta fito tsakar gida Nenne bata kulata ba, dan tasan yana nan, in ta kulata tasan me zai biyo baya. Kitchen ta shiga abinta, ta hura wuta ta dawo cikin ɗakin, abincin nasu ta ɗauka ta fita, ɗumame mai daɗi ta yi masu, ta shiga ɗakin bappa zata ɗauki man shanu ne ta ga Nenne ta ajiye masu abincin safe, kamar zata ɗauka ta kai mashi sabon tuwon sai kuma ta ce bari ta fara zuwa ta sanar da shi tukun nan. Wanke kwanikan nasu ta yi ta kwashe ɗumamen a ciki, ta zuba man shanu ta ɗauka ta nufi ɗakin su, ajiyewa ta je ta yi sannan ta fito ta ɗaura ruwan wankarta, ta koma ɗakin ta same shi. Yana zaune kamar yadda ta barshi, a gabansa ta tsugunna cikin ladabi da biyayya ta ce. Hamma Nenne ta ajiye mana abinci in ɗauko maka tun da shi sabon tuwo ne ba ɗumame ba?". Ɗan kwaɓe fuska ya yi kafin ya amsa da. "Bana buƙata, abinci in ya wuce naki ba zan iya cin na kowa ba". Wani irin sanyi ta ji a ranta, hakika ta ji daɗi sosai, wani irin ƙayataccen murmushi ne ya kubce mata, sai kallonta yake yi. Cike da farinciki ta miƙe ta nufi waje, ruwan zanfin ta juye a bokiti tare da surkawa ta ɗauka ta nufi banɗaki dan ta yi wanka, shi kuma bai ci abincin ba yana jiran ta dawo su ci. Bayan ta yi wanka sai ta ɗauro alwala azahar dik da lokaci bai cika ba, sannan ta nufi cikin ɗakin. Still dai yana zaune in da ta barsa. Ta yi mamakin ganin yana zaune a wajen, dan haka sai ta ce. "Hamma ya baka ci abincin ba?". "Ke nike jira". Ya bata amsa idanunsa a kanta babu ko kyaftawa. Murmushi ta ɗan yi kafin ta wuce ta ɗauki kayan da zata saka, sannan ta nufi hanyar fita dan ya je ɗakin Mahreen ta shirya. "Zo nan". Ya faɗa kamar ba shi ya yi maganar ba. Ba musu ta juyo ta nufosa. Zata tsugunna a gabansa kenan ya yi saurin riƙo hannunta ya jawota ta faɗa jikinsa, daga ita sai ɗaurin kirji sai kuma hijabin dake jikinta. Hijabin ya yaye ya ajiye shi a gefe, shiru bata ce mashi komai ba. Ya kai hannu ya karɓi ɗan basken ɗin kayan kwalliyar tata, gyara mata zama da kyau a jikinsa ya yi kafin ya ɗauko powder ya zuba a soson. Cikin nutsuwa ya fara goga mata a face ɗinta, dan tun da ya yi mata shi a wajen bikinsu ya haddace komai. Kwalliya mai kyau ya tsantsara mata, yana yi idanunsa suna a kan gurun wuyarta, sai da ya gama yi mata komai sai ya kai ɗan bakinsa saman gurun wuyar tata. Iya sumbatarta ya so ya yi, sai ga shi ya fitar da tongue ɗinsa yana yi mata tafiyar tsutsa a wajen. Ji ta yi mamar cakulkuli yake yi mata hakan yasa ta fara dariya tana muku muku, ta ƙanƙame shi. Cigaba da yi mata hakan ya yi har sai da ta saki jiki sosai tana dariya mai ɗan sauti, tun da yake da su a gidan bai taɓa ganin ta yi dariya mai sauti na sai yau, murmushi ma ba kasafai ta cigaba yi ba, sai Mahreen ta zage sosai take iya sanya murmushi, yau sai ga shi tana dariya mai sauti. Sosai ya ji daɗin hakan, ya kuma rungumeta a jikinsa, ta yi matuƙar kyau a simple make up da ya yi mata. Sallamar Mahreen a bakin kofar ɗakin nasu ne yasa ya yi saurin sakinta tare da cire tongue ɗin nasa, ya miƙa mata hijabinta yana kallonta. A hanzarce ta sanya hijabin kafin ta miƙe daga jikinsa tana amsa sallamar. "In shigo". Cewar Mahreen, bappa ne ya ce lallai kada ta kuskura ta shiga masu ɗaki kai tsaye, dole sai ta tambayesu ta shigo, idan suka ce mata e sai ta shiga, to shi ne fa kuka ji tana faɗin ta shigo. "E shigo" Mahnoor ta bata amsa. Sake yin wani sallamar ta yi kafin ta sa kai ta shige ciki, ashe kasuwan kauyen dake gaban nasun nan Mahreen ɗin ta je ita da Inna Rabi, bappa ya basu kuɗi su sayawa su Mahnoor wasu abubuwan buƙata har da sugar da lip tom da dai sauransu, shi ne ta kawo masu. Tana miƙawa Mahnoor kayan ta nufi Jaish dake ta kallonta, daga jiya zuwa yau da basu kasance a tare ba ya yi kewarta sosai. Tana zuwa ta faɗa jikinsa tana dariya tana faɗin. "Hamma yanzu baka fitowa mu je wajen bappa mu yi hira". A shagwaɓe ta yi maganar. Satar kallon Mahnoor ya yi kafin ya ce. "Ba laifina bane, amma zan rinƙa fitowa, na yi kewarki ai nima". Labarin kasuwa ta fara bashi tana yi mashi wasa da gashin kansa, biye mata ya fara yi daga karshe suka sauko saman dadduma suka ci abinci a tare su ukun, su Mahnoor yanzu ta rage jin kunyarsa. After some times. Bayan wani lokaci. In short yanzu dai shaƙuwa sosai ta shiga tsakaninsu, kunya ta ragu sosai, Mahreen bata takura masu, dan bata ma shiga room ɗinsu kwata kwata, iyaka su haɗu da ita a waje, bappa ma baya takura masu, yana basu waje, sai dai har yau har gobe dikkansu kunyar bappan suke ji sosai, basa yarda su haɗa ido da shi, idan ma yana nan basa fitowa, in sun shiga ɗaki su kashe junansu da soyayya, idan suka fito waje kuma sai kaga kamar waɗan da basa yi wa juna magana. A satin da ya wuce aka sha bikin Jumma, sai dai ita Mahnoor bata je ba, Jaish ya hanata zuwa, sosai Jumma ta ji babu daɗi, amma ya ta iya to? Yanzu Jaish ɗin ne sai addu'a, ya samu tula tulan yar mutane yana matse mata, tin da ya matsa sau ɗaya ya ji da daɗi shikenan kuma ya dai'na barinsu su huta, amma har yau har gobe a iya matsesu ya tsaya, baya taɓa yarda ta fita ko nan ca kofar gida, ya yi mata iyaka da Nenne kuma, yanzu bata shiga harkarta. Bappa kuma ya ɗauko maganar karin aurensa gadan gadan, nan fa Nenne ta ce idan ya isa shegiya take, bare kuma da ya kasance kanwar maman Mahnoor zai aura, yanda basa shiri iyayensu ma basa shirin nan ai ba ƙaramin ɗagawa Nenne hankali suka yi ba, nan fa gwaggo ta ce zama bai gansu ba, dole su fita naman mafita, dan idan wannan Mairon ta shigo gidan bappa fa akwai gagarumin matsala, dan haka ba zasu bari hakan ya faru na. Gaskiya akwai case a gidan bappa wlh, dan kuwa za'a buga game tsakanin Nenne da Mairo, mu dai namu ido, kuma muna da Maltina mai sanyi, ana yi muna sha, dik wadda aka sumar sai mu yayyafa mata maltina ko ya kuka ce?. Ga Nenne yanzu dan dole take aikin gida, ita kuma Mahnoor tana yi masu girki ita da mijinta, dan baya cin abin hannun Nenne, abin dariya baya karewa Jaish, idan bappa yana cikin gidan har Mahnoor ta yi girki ta gama ba zaku ga kafarsa a waje ba. Idan kuma bappa baya nan iya Nenne ne wlh har kitchen yake shiga ya tayata aiki, suna yi suna hira. Yau ta kama ranar Sunday, tsaye take a bakin ruwan kogin nan da suke wanke kaya, wanke kafarta ta yi ta fito, daga saman dutsen ta tsaya tana kallon ruwan kogin yadda yake tafiya, bappa ta kawowa abinci zata koma. Bappa kuma yana ta kusa da ita yana ɗan tsistsige ciyayin da suke takuwa wakensa da ya shuka. Kamar daga sama ta hangosa yana nufosu, kasa ta yi da kanta tana guntse dariyar da ya ciyota, ai ma taki guntsuwa bata san ko da ta kwashe da dariyar ba, sai dai ta yi ƙasa da kai tana toshe baki. Shi kansa bappa bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba na ganin Jaish ɗin da ya yi ya iso wajen nasu. Abin yayi matukar bawa Jaish mamaki yadda kowa yake kallonsa yana dariya, shi ya kasa gane komai, ganin bappa ma ya yi mashi dariya ne yasa ya juyo da kallonsa a kanta, tun a hanya yana tahowa jama'a suke yi mashi dariya, dik wanda suka haɗu da shi sai sun yi mashi dariya. A fujaje ta kawar da kallonta daga kansa ta juya tamkar tun ainahi ruwan take kallo ba shi ba. Tunani ya shiga yi a kan to me kenan ta yi mashi da yasa jama'a suke kallonsa suna dariya? Dan shi yasan daga ita sai shi a cikin ɗaki ta fito ta barsa da nufin bari ta kawowa bappa abinci, kuma tana fita bai ɓata lokaci ba wajen tashi ya bi bayanta, dan ma lokacin da ta fito barci bai gama sakinsa bane yasa ya bari ta yi gaba, shi yasan babu in da ya je daga gida sai nan bare ya ce ya je wani wajen wani abin ya ɓata mashi jiki da yasa ake yi mashi dariya. Shi ba zai iya tambayar bappa ba saboda yana jin kunyarsa, ga shi Mahreen bata nan bare ta fasa kwai wajen gaya mashi menene, ita kuma Mahnoor ƴar rainin wayo yasan ma ba samun amsa zai yi ba ko ya tambaye ta, dan ta saba yi mashi tsiya idan bappa na waje ya yi magana taki amsawa. Duk sun ruɗar da bawan Allah sun sa yana ta aikin kallon jikinsa daga sama har ƙasa ko zai ga dalilin yin dariyar tasu, kasancewar bappa yana tare da su ne yasa bai yi yunƙurin titsiyeta sai ta gaya mashi dariyar me ake yi mashi ba. Idan ya ce zai kawar da zancen ya cigaba da aikinsa to dik wanda ya zo wucewa sai ya kallesa ta tuntsire da dariya, wasu ma har da riƙe ciki a hanya da yana zuwa, ba zai iya jurar hakan ba, to meyakamata ya yi kenan?. Ya jefawa kansa tambaya yana kara dawo da kallonsa a kanta. A fujaje ta sake kawar da kallonta yadda zaku san alamar tsagwaran maras gaskiya ne a tattare da ita ƴar ƙaniya, tasan me ta yi mashi, ta jefa bawan Allah cikin damuwa. Shi dai bappa da ya yi dariyarsa har da hawaye yana rike ciki mai isarsa, sai ya koma ya duƙa ya cigaba da nomarsa, dik in ya ɗago ya kallesa kuma sai wata sabuwar dariya kamar zararre ta kubce mashi. Wow bappa angon Mairo yau ya sha dariya sosai. Wlh Mahnoor wasa wasa ta kuyi iyashege fiye da tunanin mutum, ji yanzu cikin minti ɗaya ta rikita bawan Allah. Shiru ya taya yana son su haɗa ido ya harareta amma taki yarda su kalli junan, sai ma ta juya ga kogin mai gabaɗaya. My people's a tunaninku me ta yi mashi yasa ake yi mashi dariya haka?. Ganin kamar suna buƙatar samun waje su biyu ne yasa bappa ya bar wajen da ya basu dama su yi magana, har lokacin dariya kamar wani zautatce, da kyar ya iya danne dariyar tasa dan kada ɗan nasa ya ɓata rai, ya kutsa cikin gona ya basu waje. Ai bappa na barin waje ta kwasa a guje ta sauƙa ƙasan dutsen. Ai a miliyan yabi bayanta dan ya gaya mashi me ta yi mashi. Gudu ta fara yi a bakin kogin tana kewaye dan neman hanyar da zata samu ta gudu ta ɓuyan mashi. Shi kuwa yaki bata dama, dik ta in da ta bi sai ya tarota, ga uban dariyar da take yi mashi kamar cikinta zai fashe........... Wai me kuke tunanin ta yi mashi ne? Waɗan nan luv bird ɗin suna sha'aninsu wlh. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 48 Gudu ta fara yi a bakin kogin tana kewaye dan neman hanyar da zata samu ta gudu ta ɓuyan mashi. Shi kuwa yaki bata dama, dik ta in da ta bi sai ya tarota, ga uban dariyar da take yi mashi kamar cikinta zai fashe. Wai me kuke tunanin ta yi mashi ne? Waɗan nan luv bird ɗin suna sha'aninsu wlh. Mu koma baya kaɗan. Yau ta kama Sunday, tun da sassafe bappa ya fita da dabobinsa ba tare da ya karya kumallo ba, dan ya lura yanzu dabbobin nasa basa samun ishasshen abinci, wasu daga ciki sai rama suke yi, sun kuma yi yawan da za'a ce lallai a kula da su a gida. Dan haka sai ya zaɓi ya rinƙa fita da su tun wuri domin su samu wadatatcen abubuwan da suke buƙata. Tin kafin kowa ya tashi daga barci ya fice, harta Mahreen tana barci. Nenne kuwa tana cikin kitchen tana aikin tsinewa Jaish tana kuma yin aikin girki, ga takaicin bappa zai kara aure, ta kai kukanta ga Arɗo ya ce ta wuce ta bashi waje namiji ai dan mata huɗu aka yi sa ba ɗaya ba, ita ɗin mata nawa ta buɗe ido ta gani a gidansu da zata wani ɗebo jiki ta zo ta ce mashi ya hana bappa kara aure? To ta sani shi ne ma zai shigewa bappa gaba wajen neman auren Mairo, kuma nan ba da jimawa ba za'ayi shi tun da dai abin dik na gida ne. Wai nace ni kam ina iyayen bappa ne da komai Arɗo ne yake tsaya mashi? Mu je zuwa. Takaici Nenne kamar ta mutu, ta wuce cikin gida ta gayawa gwaggonta. A nan gwaggonta ta rarrashe ta kuma ce wlh ba zata bar irin abin da ya faru da ƴar uwarta ya sake faruwa da ita ba, kada ta damu zasu ɗauki mataki. To shi ne fa ta dawo gidan bappa tana jiran gwaggonta a kan matakin da zasu ɗauka. ______________🌹💘____________ A hankali ta waro idanunta da suka yi mata nauyi sosai saboda barci, sun sha barci da shi da ita yau, tun da suka yi sallar asuba suke barci har karfe 8, a lokacin Mahreen ta wuce gidan Inna Rabin haddar weekend da suke zuwa. Kasancewar a saman kirjinsa take kwance sai hakan ya bata damar ganin face ɗinsa da kyau, barcinsa ta yi nauyi sosai saboda ya sha aiki jiya sosai, ya ƙara masu faɗin bukkar tasu da itatuwa, ya dai sha aiki har karfe taran dare sannan ya yi wanka ya kwanta, shiyasa barcinsa ta yi nauyi, da kyar ya iya tashi ya yi sallar asuba ma saboda barci. Zuba mashi idanu ta yi tana jin wani irin kaunarsa yana shigarta, a fili ta furta. "Kai hammana kyakkyawa ne sosai wlh". Ta yi maganar tare da manna mashi sumbata a goshinsa kamar yadda yake yawan yi mata. A hankali ta raba jikinta da nasa ta sauƙo daga gadon. Hijabinta ta ɗauko ta sanya a jikinta ta nufi waje, yanzu fa Jaish ya hanata kwana da hijabi, yarinyar da kullum da hijabinta take amma yanzu gabaɗaya ya mayar da ita sai sorry, ba hijabi take kwana ya yi ta aikin latse mata tula tulanta kamar wanda ya samu aiki ana biyansa. Kitchen ta shiga ta ɗaura ruwan wanka tare da fitowa ta shiga ɗakin bappa dan ta duba ko yana nan. Ganin baya nan ne yasa ta fito, kiciɓis suka yi da Nenne a tsakar gida. "Ina kwana Nenne?". Ta faɗa ba tare da ta dakata daga tafiyar da take yi ba, da alama yanzu Jaish ya canzata sosai, dan kuwa wlh kaso sittin cikin ɗari na tsoron Nenne da take ji yanzu ya kau, kuna dai gani ta ɗaga mata gaisuwa ma ba tare da ta tsaya ba tana cigaba da nufar in da take son zuwa, ai daga nan ma zaku gane huɗubar Jaish ta yi tasiri a ranta. Kullum cikin karfafa mata gwiwa yake yi yana kara mata karfi. Taɓe baki Nenne ta yi mamaki kamar zai kasheta, in a lower voice ta ce. "Daga yau kada ki sake shiga mun cikin ɗakin miji kai tsaye haka! Dole ki nemi umarni daga wajena". Nenne dai da alama ta rasa abin faɗa ne yasa zata wani kawo banzan sharaɗinta. Yo banzan sharaɗi mana, yarinya da ɗakin babanta ki ce kada ta kuskura ta shiga maki ɗakin miji? Sai yau ta san da mijin ta ne kenan? Yau ga ikon Allah. Ko sannu Mahnoor bata ce mata ba, ta cigaba da abin da take yi, dan kuwa Jaish ya ce mata ba komai ake bi ta kansa ba. Da alama Mahnoor tamu ta zama ƴar air yanzu, Jaish ya koya mata duniyanci fa. Baki galala Nenne ta saki na ganin Mahnoor bata amsata ba, abin ya yi mugun bata mamaki, wlh bata taɓa expect ɗin haka daga gareta ba. Ga shi ba halin ta daketa, dan kuwa Jaish ya daka mata Capital warning a kan taɓa mashi jikin mata, dole dai ta sake yin hakuri ta bisu da kallon takaici wanda gara kuka da shi. Nenne ta yi mutuwar tsaye a wajen tana al'ajabi har Mahnoor ta juye ruwan wankanta a bokiti ta ɗebo na sanyi ta dai'dai ta zafinsa da shi, sannan ta ɗaura wani a saman wuta ta fito ta shiga cikin toilet. Nenne dai baki a sake tana binta da kallo, ita kuwa ko in da Nennen take bata sake ɗaga idanu ta kallah ba. Sai ta yi wucewarta kawai. Har ta fito daga wanka Nenne na tsaye, al'ajabi ya hanata motsawa. Kitchen Mahnoor ta koma ta sauke ruwan dake saman wutar ta yi masu ɗumamen abincinsu, ta kwasa a kwanikan silver ta sake mayar da ruwan dan na wankan Jaish ne. Sannan ta ɗauki abincin ta nufi ɗakinsu, wlh har lokacin Nenne na tsaye, dan gani take yi abin kamar a mafarki, yau Mahnoor ce da yi mata haka? Duniya kenan. A in da ta saba ajiye masu abinci a nan ta ajiye, sannan ta kwaso kayan da zata sanya a jikinta da kuma kayan kwalliyarta, ta zo saman mattress a gefensa ta zauna tare da fara aikin shiryawa. Simple make up ta yi wanda ya kara tsatso kyanta sosai, sannan ta miƙe ta sanya kayan a jikinta, doguwar rigar atamfa ce mai kyan gaske. Ɗinki ya yi kyau sosai a dai yanayin garin nan nasu. A kusa da shi ta koma ta zauna yana ta sharara barcinsa cikin kwanciyar hankali. Cikin nutsuwa ta kai ɗan bakinta sai tin kunnensa. "Hamma ka tashi rana ya yi fa". Ta faɗa. Ko motsawa bai yi ba, saboda barci ne a kansa sosai. Sake faɗin hakan a karo na biyu ta yi, nan ma bai motsa ba. Sai a karo na uku ne ya motsa tare da ɗan juyowa unexpect ya ɗaura hannunsa a saman mazaunanta. Wani irin faɗuwar gaba ta ji wanda ya sanyata ɗan tsorata, a hanzarce ta ɗan juya tana ganin hannun nasa. "Noor ki kyani barci nake ji sosai". Ya faɗa cikin muryar barci. "To shikenan na kyaleka". Ta faɗa tare da kai hannunta a hankali ta janye hannunsa dake saman mazaunan nata. Tashi ta yi ta tattare kayan da ta cire ta kai wajen kayan wanki, sannan ta zo zata tattare kayan kwalliyar tata kenan shaiɗan ya jefo mata wani tunani, wai ta yi mashi kwalliya taga ya kyansa zai kara yi. Wannan tunanin yasa ta koma ta zauna kusa da shi. A hankali ta ɗauko bakin gazal ta feƙe shi, to kun san idanunsa a rufe yana barci, hakan yasa ta zana mashi gazal ɗin a wajen idanunsa instead of a ciki, a hankali take yin komai kuma bata yarda ta taɓa face ɗinsa da hannunta ba. Hannunta sai kerma yake yi tana addu'ar Allah yasa kada ya farka ya sameta, tsabar kerman da hannunta yake yi ne yasa ta sanya mashi janbakin a karkace, ga janbakin irin wannan 24 hours ɗin ne da baya goguwa ta daɗi, kasancewar laɓɓansa ƴan kanana ne yasa janbakin da ta tabka mashi ya fi lips ɗin yawa har kusan kyakkyawar gemunsa. Tabbas yana jin kamar tana taɓa mashi face dinsa, sai dai kuma barcin da ta sha kansa ya hanasa buɗe idanu. Idan kuka ga yadda face ɗinsa ta zama kamar tsohon aljanin da ya rikiɗe ya zama matashi sai kun yi dariya kamar zaku mutu, sai ma kunga gazal da ta zana mashi a kasan idanunsa, ita kanta taga abin ya munana ga abin dariya shi ne yasa ta fara tunanin ta yadda zata goge mashi ba tare da ya farka ba. Kunsan gogewa da zanawa akwai banbanci, in dai zata goge mashi fa dole ya farka. Hakan yasa ta fara tunanin mafita. Ta kwashi kayan kwalliyar ta mayar mazauninsu, da sauri ta ɗauko ɗankwalinta dan ta zo ta goge mashi. A kusa da shi ta zauna, a hankali ta kai ɗan'kwalin ta fara ƙoƙarin goge janbakin. instead of ya gogu sai ya kara kwaɓe mashi face ɗin nasa, ga shi tana a tsorace da kada ya farka, sai hakan yasa hannunta na kerma dik ta kara kwaɓe mashi fuska. Cikin barci yasa hannu ya jawota jikinsa, dan ta takura mashi da taɓa mashi face ɗinsa. Idanunsa a lumshe murya can ƙasa ƙasa ya ce. "Noor ba zaki barni na yi barci ba ko? Me kike so da kike ta taɓani tun ɗazun?" Muryarta na rawa saboda tsoron abin da ta aikata mashi ta amsa da. "Babu komai hamma, ka yi hakuri na dai'na". Tana magana tana ɗan goge mashi janbakin ta rarragesa dan ya yi dai'dai da ɗan bakinsa, da yake yanzu tana jikinsa gabaɗaya sai ya zama ba zai ji dan ta taɓa face ɗinsa ba, ba zai yi zaton wani abin take zana mashi or take gogewa ba. "Waye ya ce ki saka doguwar riga?". Ya faɗa ba tare da ya buɗe idanu ba. "Ka yi hakuri bappa zan je kaiwa abinci, naga abincinsa a ɗaki bai ci ba, nasan ya yi sammako fita ne kafin a gama girki, wani lokaci haka yake yi". Da kyar ya iya waro idanunsa a kanta, idanun jajir da su saboda barci. Like wow ya ɗan warosu waje yana kallonta, ta yi kyau. Yau safiyarsa zata yi kyau yadda ya fara ganin face ɗin kyakkyawar matarsa. "Kin yi kyau sosai Noor ɗita". Ya faɗa yana ɗage mata doguwar rigar tata, ya samu damar yaye rigar har izuwa saman waist ɗinta ya fara wasa da beats ɗinta dake mugun tafiya da tunaninsa. Hannunta ta ɗaura a saman arab hairnsa ta fara wasa da shi tana faɗin. "Hamma ai ka fi kowa kyan a garin nan". "Wash". Ya furta yana kallonta. Da sauri ta zame hannunta daga kan nasa dan a tunaninta taɓa arab hairn nasa ne yasa ya furta wash ɗin. Kama hannunta ya yi ya mayar saman kan nasa yana lumshe idanu alamar ta cigaba da wasa da shi. "Hamma in je in kaiwa bappa abinci?". Tana magana tana watsa gashin nasa. Sai wani lumshe idanu yake yi alamar yana jin daɗi tana ratsa shi. Sai da ta sake tambayarsa a karo na biyu batun kaiwa bappa abinci, sannan ne ya ce e ta je. Da sauri ta yunƙura zata bar jikinsa, riƙota ya yi yana kallon face ɗinta. Ɗan rufe idanunta ta yi tana sakin ɗan siririn murmushi, da alama tasan me zai yi maka, kuma ga dikkan alamu ita ma tana son hakan. Matso da face ɗinsa dab da tata ya yi. Kamar zai yi maka kiss sai kuma ya fasa, ya ɗan kura mata ido na ƴan mintuna kafin ya saketa tare da miƙewa zaune, ya sanyata ta kawo masu abincinsu kusa da shi, ya miƙe ya fita waje domin ya wanke fuska da bakinsa dik da da asuba ya yi. Ko da ya wanke fuskar tasa kwalliyar bai fita ba, dan kunsan wannan janbaki mai suna 24 hours ɗin nan ruwa bata wankesa, baya fita ta daɗi, sai dai kwallin nasa ne ya ɗan kara ganganrowa kaɗan, amma babu abin da ya sami kwalliyarsa. Jikinsa dik a mace haka ya zo ya tasata a gaba sai da ta ci abincin nan ta ƙoshi, sannan shi ma ya ci, sai ya miƙe ya kwanta a saman mattress, sai ɓoye dariya take yi tana kawar da kai dan kada su haɗa idanu. Sam bai lura da ita ba, hankalinsa yana wajen tunanin bappa, so bai gane tana ɓoye dariya ba. Tattare wajen ta yi da sauri, tin da ta fita kai kwanika kitchen sai ta wuce wajen bappa abinta, taki dawowa cikin ɗakin, sai karfe 2 Mahreen zasu tashi daga haddar weekend, karfe 4 kuma su sake tafiya islamiyya, haka tsarin karatun yake, weekend basu da hutu sam......... Wannan shi ne abin da ta yi mashi, kuma abin dariyar ta watsa mashi Arabs hairnsa, sai abin ya kara bada dariya, shi kuma bai yi wanka ba da kwalliyar zata ragu, dan kuwa lokacin da ya jita shiru bata dawo ba sai ya fito domin ya dubata. A nan ne ya fahimci ta tafi kaiwa bappa abinci, sai ya bi bayanta da wuri shiyasa bai shiga wanka ba. Tun da mun ji me ya faru mu koma kan labarinmu. STORY🌹 Dakatawa ya yi da binta ya tsaya yana kallonta, ita ma tsayawa ta yi tana cigaba da dariya kamar wata zararriya, sai ma ya ɗaure fuska idan ta gansa sai ta ji wani irin mahaukacin dariya ya kara kamata, ta mayar da shi kamar wani kakanta. Shi kam bappa ba ƙaramin farinciki ya ji ba na ganin su haka, saboda yasan Mahnoor ce ta yi mashi wannan tsiyar, idan babu soyayya da shaƙuwa kuma me zai ja Mahnoor ta yi mashi kwalliyar? Ai ba zai yiwu ba, ita da a baya ma tsoronsa take ji, ai yanzu bappa sai hamdala, ya ji daɗi ƴar marainiyarsa tana samun farinciki. Ɗaure fuska sosai ya yi tare da ce mata. "Zo nan". Irin tun da ya kasa kamata bari ya gwada powersa.........😂 Ɗan tsuke fuska ta yi irin Allah sarkin nan. "Kai Hamma ni to me nayi maka?". Shiru bai ce uppan ba. Ganin hakan yasa ta yi zaton da gaske yake yi ba wasa ba, dan haka sai ta nufosa, nan take ta yi mashi narai narai da idanu tana ƙoƙarin saka mashi kuka!. "Kada ki kuskura ku mun kuka!". Ya faɗa da ɗan daga murya kaɗan, irin shi fa ba da wasa yake yi ba. Gabansa ta ƙariso tana sunkuyar da kai ƙasa. Tana zuwa ya capkota yana faɗin. "Yanzu waye na kama?". Kumatu ta kumbura ta ce. "Ni Hamma baka kamani ba da kai'na na zo". Da yake ta baya ya riƙota ya zamana bayanta ne ta kwantar a jikinsa, sai ya rage tsawonsa a in da ya kwanto da kansa a saman shoulders ɗinta, kamar mai raɗa ya ce. "To yanzu dai gaya mun me kika mun da yasa ake ta yi mun dariya? Nasan kece kika yi mun wani abin". "Ni fa Hamma babu abin da na yi maka, ka tambayi bappa ka ji". Tongue ɗinsa ya zuro waje tare da fara yi mata tafiyar tsutsa a gurun wuyarta. Murmushi ta fara yi, a hankali hankali yana cigaba da yi mata har ta fara dariya sosai tana mutsu mutsu tana son kwace kanta. Ƙanƙameta da kyau ya yi yana jin tsananin farinciki na wannan dariya da take yi. "Kai Hamma ka bari mana dan Allah, Allah kana mun cakulkuli ne fa". Cikin dariya ta yi maganar. Ɗan mayar da tongue ɗin nasa cikin baki ya yi kafin ya ce. "Har sai kin gaya mun me kika mun sannan zan rabu dake". "To ka tsaya zan faɗa". Ta faɗa tana ɗan turo baki. Dakatawa ya yi yana jiran ya ji amsa. "Kwalliya fa na yi maka ba wani abin ba". Zaro idanu waje ya yi tare da juyo da ita suna fuskantar juna da sauri. "Mene?". Ya faɗa kamar wanda ta ce ta yi mashi wani mugun abu. "Kwalliya na yi maka". Kumatu a kumbure ta yi maganar. A hanzarce ya saketa ya fara kai hannu yana taɓa kumatun nasa, ai kuwa ya ji janbakin a saman laɓbansa, zaro idanu ya karayi tare da yin yunkurin kamata. Ai a miliyan ta watsa zata gudu. Hannunta ya capko da karfi ya janyota ta faɗo saman faffaɗar chest ɗinsa. A ruɗe ta fara faɗin. "Wayyo bappana, dan Allah Hamma ka yi hakuri ba zan kara ba, wayyo na tuba kada kace zaka yi mun komai, wlh sharrin shaiɗan ne". Ba tare da furta uppan ba ya fara ƙoƙarin haɗe hannayenta dikka biyu dan ya samu damar yin abin da zai yi mata ba tare da ta hana shi ba. Sai hakuri take bashi amma yaki kulata. Kamar daga sama suka ji muryar Mahreen a saman dutsen tana faɗin. "Hamma kada ka rabu da ita koma me ta yi maka, dan jiya da daddare ta zagan mun idona". Wai me idon Mahreen ya tarewa mutane ne da kowa idan ya tashi zaginta sai ya zagi idanun? Ga dai gwaggo ma idan ta tashi bata da abin zagi a jikinta face ido, ku gaya mun me idanunta ya yi maku?. Jin muryarta yasa suka ɗago a tare suka kai kallonsu a kanta, sai kuma ya saki Mahnoor ɗin yana juyowa. Subhanallah wani irin ja da baya Mahreen ta yi tana zaro gulu gulun idanun nata. Zuba mata idanu ya yi yana jiran yaga ita kuma kalar rashin mutuncin da zata yi mashi dan matarsa ta yi mashi kwalliyar kauna. "Hamma yau kam ya tabbata kai aljani ne da gaske, ni ma yau kam na yarda, innalilahi Adda Mahnoor kina ganin fuskarsa kuwa?". Ta faɗa tana kara zaro idanu. Juyo da kallonsa a kan Mahnoor ya yi, ya watsa mata irin kallon nan na ai kinga abin da kika jawo mun. Kawar da kanta ta yi tana guntse dariya. "Mahreen ba aljani bane kwalliya ne fa". Tana kai karshen maganar ta kwashe da dariya kamar zararriya. Ai ita ma Mahreen me zata yi idan ba dariya ba. Bata san lokacin da dariyar ya kubce mata ba, Hamma ya zama kamar mayaudaran bokaye, subhanallah. Da gudu ta sauƙo izuwa wajensu. "Hamma kaga face ɗinka kuwa? Wlh kamar warthrog". Tun bata ƙarisa isowa wajensu ba ta faɗi hakan. (Sorry ban san sunan warthrog da hausa ba, amma wata dabbace mai fuska yana ɗan yanayi da dorinar ruwa haka, yana da kananan kawo ta wajen kumatu za'ace ne ko baki ne oho dai😂) Ɗaure fuska ya yi, yau har da Mahreen ɗinsa ma ta juya mashi baya, ita da bayan bappa ita ce mutun na biyu da ta fara karɓarsa a garin, ta yarda da shi ba maye bane kuma ba aljani bane, amma yau ta juya mashi baya, to gaskiya wannan kwalliyar da Noor ɗinsa ta yi mashi ya munana. "Hamma wlh yau ni ban san ma da me zan ce ka yi kama ba, amma dai idan mutun ya ganka da daddare hasken farin wata na haskaka zai iya yin fitsari a wando saboda tsoro". Cewar Mahreen. Tana magana dariya kamar zai kasheta. Shiru ya yi yana mamakinta, ita fa wato bata san idan ta yi nata kwalliyar tana fin wanda matarsa ta yi mashi muni da razana bayin Allah ba, amma ta tsaya tana yi mashi dariya dan rashin kunya. Amma kuma fa wlh Jaish ya yi kyau da kwalliyar........😂 (Nima na ɗana dariyar ne, yo hauka ake da ba zan yi dariya ba?😂 Irin wannan kwalliyar?🤔 Kwallin mafa a kasar ido aka saka mashi 🤔 😂 ina ma ace akwai wanda zai yi masu video ya kaiwa Yah Jawad ya ga abin da yake faruwa😂) "Wai ke Mahreen mema ya dawo dake daga hadda yanzu? Lokaci ya yi ne?". Ya faɗa babu wasa a tattare da shi. Tana ta tikar dariya ta ce. "Inna Rabi ce ta ce mu tafi gida kanta na ciwo yau shi ne na dawo". "Amma ni fa daɗi na ji da Inna Rabi ta ce mu tafi gida, ba ga shi na zo na ganka na sha dariya ba, amma waye ya yi maka kwalliyar?". Da sauri Mahnoor ta juya zata bar wajen, dan ta ji Mahreen ta tambayi waye ya yi mashi kwalliyar, so tasan zai tuno da ashe punishing ɗinta zai yi. Capko hannunta ya yi yana faɗin. "Zo nan, ina zaki je?". Katsesu Mahreen ta yi da cewa. "Hamma ita ce ta yi maka kwalliyar ko?". Jinjina mata kai ya yi alamar e. "Wlh Hamma kada ka kyaleta, dama jiya da daddare ta yi mun laifi, ka zaneta bari na je na ɗauko maka bulala mai kyau da zai shiga jikinta sosai ka zaneta da shi, daga nan na je na ɗauko maka sabulu na zo na wanke maka fuskar". Jama'ar kun ji mun Mahreen da ƙoƙari, matar mutun tana tsaye a gabansa ki ce zaki kawo sabulu ki wanke mashi face? Kai amma yar nan sai shirin Allah. "A'a gajin bappa, ke dai jeki ki kawo sabulun kawai". Ya faɗa yana hararar Mahnoor dake ta ƙoƙarin guntse dariya. "Hamma bulalar fa? Ko ka fasa dukanta ne?". Yadda kuka san wata ta Allah haka ta yi maganar, irin ta damu a zanen Mahnoor ɗin. Kai ya girgiza mata kafin ya ce. "A'a ban fasa zaneta ba, amma ba sai kin kawo mun bulala ba, ina da bulala a gida a ɗakinmu, in mu koma zan zaneta a can". A hanzarce ta ce. "To in ɗauko maka bulalan ɗakin naku sai ka zaneta a nan?". Nan ma girgiza kai ya yi. "A'a ki bari sai mun koma zan zaneta". Turo baki ta yi. "To Hamma ai lokacin da zaku koma kila na tafi islamiyyar yamma, kuma ni ina son in ga ka zaneta a gabana ne". "A'a ke baki san matar aure iya mijinta ne kawai yake zaneta kuma shi kaɗai zai gani ba? Ke ba zaki gani ba, amma dai zan zaneta har da rabonki na zagin maki ido da ta yi". Shiru ta ɗan yi kamar mai mazarin wani abin, a fili ta maimaita ba'a zane matar aure sai iya mijinta kawai, wani side na heart ɗinta ne ya ce mata to kenan kema yakamata ki yi aure ko dan Inna Rabi ta daina zaneki idan baki iya karatu ba, tuna haka yasa ta ce dole ta gayawa bappa ita ma ya yi mata aure. Ganin ta luluƙa duniyar tunani ne yasa ya sake ce mata. "Jeki ki kawo mun sabulun ko?". To ta amsa tare da wucewa. Da kallo suka bita har ta bar wajen, tana ɓacewa ganinsu a tare suka dawo da kallonsu a kan juna. "Kin ga abin da kika ja mun ko?". Ya faɗa yana janyota jikinsa. "To Hamma ba sonka nake yi ba yasa na yi maka?". "Da gaske?". Yadda ya yi maganar sai ya burgeka, kamar ba shi ya yi ta ba. Kai ta gyaɗa mashi alamar e tana zura hannayenta ta baya ta rungumosa da kyau, Allah sarki yanzu fa ya koya mata sonsa sosai, ta mance da wani soyayyar hamma Faisal, shi kawai take gani ta ji daɗi. "To ni dai gaskiya wannan son bai mun adalci ba, kawai sai ki saka ana yi mun dariya". "Ka yi hakuri ba zan sake ba, amma kuma ai da na yi maka mai kyau zaka yi kyau sosai". "Allah ko?". Yadda ya faɗi hakan tasan da biyu, hakan yasa ta ɗago ta kallesa. Aikuwa tana ɗagowa ya sake waist ɗinta ya kamo jajir ɗin kumatunta ya kai ɗan bakinsa samansu ya fara goge mata janbakin a samansu. Gata fara tas sai janbakin ta fito sosai, ƙoƙari kwace kanta ta fara yi, amma ina sai da ya bi ya ɓata mata ko'ina na face ɗinta, ta yi wani jajir da ita. Ɗan saketa ya yi yau karo na farko a rayuwarsa ya ɗan saki ɗan siririn murmushi yana kallonta. Da farko taso ta saka mashi kuka, amma ganin murmushinsa a karo na farko yasa ta mutu da kallonsa ta manta da cewa kuka zata yi. Ya ilahi ya lilliahi jama'a madarar kyau na zuba a time da Jaish ya yi murmushi, dole ma ta tsaya tana kallonsa, sai yau ta ga tsantsar kyan dimple ɗinsa, wani irin tsantsar sonsa ne ya ƙara ratsa dikkanin ilahirin jikinta har izuwa cikin farfajiyar zuciyarta. Bata san lokacin da ta matso ta faɗa jikinsa tana kai ɗan latsarta saman dimple ɗinsa ba. Sai a lokacin shi ma ya farga da ashe ta saka shi murmushi, riƙo hannunta ya yi ya manna a ɗan bakinsa ya sumbata. Ƙasa ƙasa ya furta. "Ina sonki sosai Noor". "Nima ina sonka Hammana". Sai a lokacin tunanin bappa fa yana kusa bai yi nisa ba ya faɗo mashi a rai, hakan yasa ya ɗan saketa yana jin wani irin sanyin daɗi na ratsa shi na kaunarta. A haka Mahreen ta dawo ta samesu. Hannunta na riƙe da sabulu, tana isowa wajen ta ce. "Hamma zo na wanke maka fuskarka da ruwan kogin nan". Miƙa mata hannu ya yi a kan ta bashi sabulun. Ba musu ta miƙa mashi tana jiran ya karisa bakin ruwa ta wanke mashi. "Jeki wajen bappa bari zan wanke da kaina". Ya faɗa idanunsa a kan Mahnoor dake ta sakin murmushi saboda daɗin dake ratsata, yau taga murmushinsa. "Hamma to meyasa ba zaka kawo in wanke maka ba?". A shagwaɓe ta faɗa. Girgiza kai ya yi. "Zan wanke da kaina, ke dai jeki bappa na kiranki". Oh ni har da yi wa bappa karya, ko yaushe ya kirata? Jaish fa ya canza, garinsu Mahnoor ya canza yaron Mommarsa har da karya saboda soyayya ta rufe mashi ido, kai jama'a. To ta amsa da shi tare da wucewa, amma bata so ace bata wanke mashi ba kam, sai dai kiran da bappa ya mata ya fi mahimmanci, sai bata tsaya ja da shi ba ta wuce kawai. Sai da ta ɓacewa ganinsu sannan ya miƙa mata sabulun. "Wuce ki wanke abin da kika zana". Cike da kaunarta ya yi maganar. Karɓa ta yi still tana murmushi. Ɗan rungumota ya yi. "Murmushi yana yi maki kyau sosai Noor". Yana kai karshen maganar ya saketa. "Hamma ban taɓa tunanin murmushi yana da kyau ba a duniya sai da naga naka yau, kai ni nama rasa ta ya ya zan kwatanta maka". Hannunta ya riƙo suka karisa bakin kogin yana faɗa mata nata murmushi yafi nasa kyau. Tsugunawa ya yi a bakin ruwan, a kusa da shi ta tsugunna sai ya juyo suna fuskantar juna. A hankali ta ɗebo ruwa a hannunta ta shafa mashi a fuska, wani daddaɗar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanu, da alama kauna tana ratsa shi, giyar soyayyarta na ɗebansa. Cikin nutsuwa tasa sabulun a face ɗinsa, a hankali hankali ta fara goge mashi tana wanke dik baki da jan tana kuma latse mashi lallausan kumatunsa. Ita kuwa Mahreen da ta je ta ce wa bappan gata nan Hamma ya ce yana kiranta, sai bai musa ba ya ce e tazo ta taya shi hira, dan yasan takura masu ta je tana yi yasa suka yi mata hakan. Taso ki ta ce wa bappa ita dai bata son yin hira da shi wajensu hamma zata koma, da kyar ya shawo kanta ta hanyar ce mata tazo su yi hira zuwa anjuma kaɗan zata raka shi wani wajen. Jin za'a je yawo ne yasa ta yarda ta zauna. Luv bird kuwa, tas ta wanke mashi face ɗinsa, shi ma ya karɓi sabulun ya wanke mata jaja jajan janbakin da ya goga mata. Bayan ya gama wanke mata ne ya ɗabo ruwa a hannunsa ya watsa mata a kirji saman tula tulanta. Da sauri ta kalli wajen, sai kuma ta ji kunya ya kamata, zata yi kasa da kai ya yi saurin yallabo haɓarta. Ɗago ido ta yi suka kalli juna. Girgiza mata kai ya yi alamar bai yarda ta sunkuyar da kai ba. Murmushi ta sakar mashi ba tare da ta furta uppan ba. Sake haɓar tata ya yi yana kallonta. Hannunta tasa cikin ruwan tana ɗan wasa da shi. Matsowa ya fara yi da face ɗinsa izuwa saitin tata, dan ya jika mata fuska lips ɗinta sun yi pink sun tafi da imaninsa, ya ji ba zai iya hakura ba sai ya ɗan shasu. Sai da ta bari ya iso dab da ita sai ta watsa mashi ruwa a fuska ta miƙe da gudu zata bar wajen. A miliyan ya miƙe ya riƙota, dama kamar yasan zata yi mashi hakan, shiyasa ya yi timing ɗin kamata. Sama ya ɗagata sai saman shoulder ɗinsa. Bubbuga bayansa ta fara yi tana faɗin. "Hamma dan Allah ka saukeni kada bappa ya ganmu, Allah ba zan sake ba". Ina bai kulata ba ya haura sama da ita, dan yasan bappa dai ba zai zo ba. Cikin daji ya kutsa da ita, da alama cikin gonar shinkafa zasu tafi, dan fa soyayyarsu a wajen bishiyar gwaivar nan tana muguwar tafiya da imaninsa, wannan shi ne akuya ta ji daɗin manda, Mahnoor na Hamma hamma na Mahnoor, suna sha'aninsu nima ina nawa sha'anin da Maltina ta mai sanyi....😂 To kuzo mu je mu leƙo su Khadija bayin Allah, watakila kafin mu dawo Hamma ya isa in da yake da nufin zuwa, sai muga me za'ayi kuma tun da shi baya gajiya da................ ________________🌹💘___________ ABUJA.🌹 Zee ta kara samun lafiya sosai masha Allah, kullum na Allah sai sun ari wayar wannan Auntyn tasu sun gwada kiran number Sadiq, amma ina bata shiga, kullm magana ɗaya dai tana a kashe, tun suna damuwa da hakan har suka daina bayin Allah. Wai ina Sadiq ne my people's, kun dai san haka kawai wlh ba zai yi shiru bai nemi ƴaƴan nan nasa ba, dan yasan halin da ya barosu, dole dai akwai wani dalili bawan Allah. Zee tana taya wannan mata aiki sosai, matar yanzu bata hanata, dan ta samu lafiya. Sun ki su gaya mata labarinsu, dan a cewasu gara masu zama a wajenta da su koma gidansu wajen Hauwa hakan yasa suka ɓoye mata asalinsu, Allah sarki basu san Hauwa kam bata nan bama, bata kasar ma, dan kuwa Kasar Brazil suka wuce da ita, sun ce dai sai ta faɗi in da su Khadija suke ko kuma ayi ta azabtar da ita har sai ta faɗa, Allah sarki ba turanci hakan yasa ta yi shiru ba magana, su kuma sun ɗauka taurin kai take yi masu ba zata buɗi baki ta yi magana ba, shiyasa shi gogan ya ce a wahalar da ita har sai bakinta ya buɗe. Ni kuma sai ihu nake yi ina gaya masu bata jin turanci ne yasa ta yi shiru ba taurin kai bane, amma ina sunki saurarona dan nima da Hausa na gaya masu........😂 Cikin Khadija a yanzu ya shiga watansa tara, daga yanzu zuwa kowani lokaci zata iya haihuwa, saboda haka lafiyarta dai sai a hankali, yau zazzaɓi gobe ciwon kai jibi ciwon baya, haka take ta fama baiwar Allah, fatarta ya ɗan kara duhu yanzu. Zee tana iya bakin kokarinta wajen taimakawa yar uwar tata, ita ma wannan mata tana iya kokarinta wajen taimakawa Khadija ɗin, dan ta ce tausayi suke bata, sai dai Khadijah ta ki gaya mata cikin jikinta bashi da uba, bata sheganta shi ba, sun ɓoye suka ce mata ai ɓarayi sun kashe baban nasa, hakan yasa ta kara tausaya masu. Amma Khadija tana da iya shege wlh, wai ɓarayi sun kashe baban, wato dai tasan shi ɗin ɓarawo mutane ne yana zuwa yana yi masu ciki shi ne aka ce masu aiki irin nasa ne suka kashe shi, to baban cikin ina kake? Da ranka da lafiyarka kana ji da mulki isa da izzar zuwa ka ɗauki dik ƴar da ka ga dama ka yi mata ciki amma Khadija ta ce ka mutu. Zee ta ɗan mayar da jikinta kaɗan, ta ɗan murmure saboda tana samun kulawa, kullun fuskarta a ɗaure tamau, ko baki sun zo cin abinci bata ɗaga idanu ta kalli mutun, zata kai masu abincin amma fuska kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa. Yaran aikin da suke taya Hajiyar aiki tun kafin zuwansu Zee wajen, yanzu suna mugun respect ɗin Zee, dan kuwa ta riƙe mutuncinta basu ga fuskar wasa ba, ta ja ajinta, dama ita Khadija ba fitowa take yi ba, tana kwance a ɗaki, idan ta gaji da kwanciya ne sai ta fito ta koma ta baya ba ta idanun mutane ba, ta zauna ta buga uban tagumi tana tunanin duniya, kullum aikin kenan. Kun san halin Zee dama bata ɗaukar raini ko wargi, shiyasa a dik in da take take kama mutuncinta take kuma girmama kanta. Yau Sunday babu kasuwa sosai, jama'a ɗaiɗai ne suke shige da fice a wajen, hayaniya ya ragu saboda weekend kowa yana gida. Zee ta yi wankarta tana sanye cikin doguwar rigarta, daga cikin kayan da suka zo da shi ne. Wajen Khadijah ta nufa, tana zaune saman stool tana cin yalo da Auntyn tasu ta saya mata a kasuwa da ta je cefene............. Na ce anya kuwa kirkin wannan mata haka kawai take yi masu kuwa? My people's ku duba fa ku gani, mun san na Allah basa karewa, amma a irin wannan yanayi da duniyarmu ta lalace anya kuwa? Har da saya masu tsaraba fa take yi idan ta je kasuwa, anya bata buƙatar wani abin daga garesu kuwa? Haka kawai kam akwai dai wahala gaskiya, ni dai na ɗiga ayar tuhuma a kanta gaskiya, mugu bashi da kama, su Khadijah ku kula dan Allah, kada dai ku saki jiki. Plastic chair Zee ta ɗauko ta zo ta zauna a kusa da ita, miƙo mata yalon ta yi tana faɗin. "Tun ɗasun ina kika shiga? Na san dai yau babu aiki sosai". Ɗan turɓune fuska ta kara yi. "Ina wajen Aunty ne mana tana bani labarin rayuwarta na baya, ni bama wannan ba, wai Aunty Khadijah yaushe zamu bar gidan nan ne? Dan wlh ni banson zama a nan". Ɗan zaro idanu Khadija ta yi. "Zee mu bar nan fa kika ce?". Tana magana tana miƙo mata plate ɗin yalon. Kai ta gyaɗa mata alamar e hakan yake nufi, sannan ta ɗaura da cewa. "Ni ba zanci yalon ba". "To idan muka bar nan ina kike son mu je?". Tana magana tana gutsiran yalon nata, bayan ta mayar da plate ɗin saman laps ɗinta. "Wajen kawu Sadiq mana". A takaice ta bada amsa tana kara turɓune fuska. "To ai sai ki bari mu cigaba da gwada number tasa sai randa Allah ya yi muka samu wayarsa sai ya yi mana kwantance mu je ko kuma ya zo ya ɗaukemu ko?". Shiru ta ɗan yi kamar mai wani tunani, tasan dai ba zasu iya komawa gidan babansu ba, dan idan akwai in da suka tsani zama a duniya bai wuce wannan gida ba, idan suna ciki kullum a cikin kunci suke suna tuna rayuwarsu ta baya, ba zasu samu farinciki da walwala ba, so ba zasu koma can ba, gidan su Sadiq kuma tasan dole sai sun same shi a waya ya gaya masu in da zasu je su samesa ko ya zo ya ɗaukesu dan gudun kada su sake faɗawa irin wancan tsautsayin da suka faɗa. "Zee ki rinƙa ɗan sakin fuskar taki mana, aka ko saurayi ai kya samu, amma yadda kike kamar wata basawan nan yaushe zaki samu saurayi? Baki san razana masu kallonki kike yi bane? Wasu fa zaki tarar ba abinci suka zo ci ba, ke suke son samun damar gani, amma sai ki rinƙa ɗaure fuska haka?". Cewar Khadija, cikin zolaya ta yi maganar. Kara cukule fuska ta yi. "Ni Aunty Khadijah bana so, ce maki aka yi ina neman saurayi ko kuma zan yi aure ne?". Zaro idanu ta yi. "Ba zaki yi aure ba ya zan yi dake to?". "Ki yi yadda kike so dani, amma ni da aure kam babu wannan zancen". "Meyasa to?". Tana magana tana cin yalo. "Saboda yawancin maza mugayene, azzalumai kuma mayaudara, ki kalli irin zaluntarki da aka yi mana, amma kike cewa na yi aure?". Cike da damuwa sosai ta yi maganar. "A'a Zee, kada ki kafa hujja dani wajen faɗar ra'ayinki, ke dai kawai ki roƙi Allah da ya baki na gari". A sanyaye ta yi maganar. "Ni fa Aunty Khadijah wlh babu aure a tsarina, kuma banga namijin da ya isa in sake mashi fuskata ba, ke ni in takaice maki ma na tsani maza". Tana kai karshen maganar ta miƙe da alama ranta ya ɓaci, bata son batun maza ne tun da namiji ya cutar mata da ƴar uwa. Khadijah na ƙoƙarin kwala mata kira a kan ta dawo ne sai ta ji cikinta ya yi wani irin murɗa mata, a take mararta ta amsa wajen murɗawa da karfi ta kuma riƙe gam tana yi mata ciwo. Kara ta saki na jin wannan azaban, hakan yasa Zee ta juyo da sauri ta kalleta. Sake sakin wani karar ta yi tana sakin plate ɗin yalon dake hannunta. Da gudu Zee ta dawo wajen tana ambatar sunanta tare da tambayar ko lafiya take?. Cikin azaba ta ce. "Zee help me, cikina ciwo yake yi". Tana magana ta cakumo Zee ɗin saboda zafin da farar tata take yi mata. "Bari dai na kira Aunty sai mu je asibiti". Ta faɗa tare da kwace kanta daga riƙon da Khadija ta yi mata ta nufi ciki da gudu. Murkutsotso ta fara yi a hankali tana karanto dik addu'ar da ya zo bakinta. A hankali ta ji ciwon ya fara lafa mata, godiya ta fara yi wa Ubangiji tana miƙewa ta koma ya zauna da kyau. Kafin Zee da Aunty su ƙariso wajen ciwon ya lafa mata ta koma ta zauna da kyau tana ƙoƙarin ɗauko yalonta dan ta cigaba da ci. Suna karisowa ita kuma bata kai ga ɗauko yalon ba sabon ciwo ya ce salamu alaikum, habawa ihu ta saki tare da dafe cikin nata an fasa ɗaukar yalon. Da sauri Aunty tasu ta tallafota tana faɗin. "Zee ina ga haihuwa zata yi maza jeki ki nemo mana mai adaidaita sahu tun da kinga Kb ya fita da mota". Da gudu Zee ta nufi hanyar fita ba tare da ta amsa ba, hankalinta ya tashi har idanunta suka ciko da kwallah. Abin da zai baku mamaki a nan shi ne wannan Auntyn tasu ta fi Zee nuna damuwa da tashin hankalinta a kan Khadijah, ta zage sosai har da ruwan hawaye ya cika mata idanu, sai sannu take yi mata. Ta yi sa'a tana fitowa ta samu mai adaidaita zai gifta, cikin sauri ta tsayar da shi, Allah ya taimaketa ya tsaya, ciki ta ce ya shigo da yake wajen a wangale yake, ba iya restauren ɗin bane kawai a wajen, akwai masu sayar da drinks, masu gasa nama, masallaci, toilet na haya da dai sauransu, kun dai gane irin wajen da matafiya suke tsayawa dan yin sallah a ci abinci ai? To kamar dai haka wajen yake. Da kyar Auntyn ta tallafa mata ta miƙe, ko mayafinta basu ɗauka mata ba suka shiga cikin adaidaitan. Amma sai da suka ɗan yi ja in ja da Zee, Auntyn tasu ta ce Zee ta zauna kada ta bisu, ita kuma ta ce a'a ba zai yiwu ba, ita ce kawai ƴar uwar Khadija dole ta bita dan komai zai faru ya faru a kan idonta! Kin yarda Auntyn ta yi har sai da mai adaidaitan ya sa baki a in da ya ce to ta kyale Zee ɗin su tafi da ita mana. A nan ta yi shiru ta ce su tafi to. Allah sarki mai adaidaitan yana da kirki, ganin halin da Khadija take ciki yasa ya taka mashin ɗin da gudu suka nufi asibiti. To Khadija Allah ya saukeki lafiya idan haihuwar ce, bari mu leƙa KINGDOM OF POWER watakila kafin mu dawo kin sauƙa. ____________🌹💘______________ KINGDOM OF POWER. A daren ranar aka sanya amarya Chuchu a wani ɗaki na musamman in da ake ajiye matan da Princes zasu aura dan girkasu da kuma gyarasu, a tsumasu da kayan gyaran ciki da waje, tun ana saura wata guda biki ake kawo amaryar, a ɗaukota daga gidan iyayenta a kawota cikin masarautar, to a wannan ɗakin ake ajiyeta, a sanya tsofaffi su yi ta kula da ita ana zuba mata gyara, ba'a bari kowa ya ganta, ita ma kuma bata fitowa ko nan da kofar ɗakin, sai a shafe tsawon wata ana gyarata, ko ango baa bari ya ganta sai an ɗaura, gara ma kawayenta idan tana da su ana bari su ganta. Ango kuma sai dai su yi waya. So ita Chuchu aurenta ya zo unexpect shiyasa saura kwana biyu bikin aka sakata a cikin ɗakin. Momma da ta ji labarin ba karamin girgiza ta yi ba, dan ita dai tasan Jawad ne ke son Jannat ba Rizwan ba, amma tun da King ya rigada ya yanke hukunci dolen Jawad ya ɗauki dangana, dan haka sai ta wuce gaba wajen gyaran amarya, tana kuma taya Jawad da addu'ar Allah ya bashi ikon cinye jarabarwarsa, sai a yanzu ta gane dalilin yin rashin lafiyarsa, haƙiƙa ta tausaya mashi matuƙa. A ɓangaren Rizwan kuwa, sai da su Ramish suka sanya shi a gaba sannan ya fara shiri kamar ango, da ya ce a ɗaga bikin zuwa kaninsa ya samu lafiya, King ne yaki, ya ce already ya gayyaci mutane, manya manyan sarakuna daga ƙasashe daban daban, ƴan siyasa, ƴan kasuwansu da dai sauransu dik ya gayyacesu, ya gaya masu jibi za'a ɗaura auren, dan haka ba wani ɗagawa da za'ayi, ba zai iya cewa jama'arsa su fasa zuwa ba. Su Ramish ma suka ce su basu ga dalilin ɗaga wannan aure ba, ayi kawai a wuce wajen, uncle Jahiz kuwa ya kafe a kan shi fa Allah baya son wannan aure, dan Chuchu ta yi ƙanƙanta, har da wani cewa shi ma Rizwan ɗin nawa yake? Bai fa gama cika 30 years ba. Uncle Abbas ya ce wlh idan uncle Jahiz bai kiyayesa da wani banzan zancensa na basu girma ba a cikin satin nan shi ma za'a ɗaura mashi auren dole da dik wadda suka yi katari da ita a cikin bakin da zasu zo ɗaurin auren nan. Yasan uncle Abbas zai aikata sarai, sai ya koma gefe ya yi shiru yana binsu da ido dan kada ayi mashi auren dole. Biki dai sai kara shirya mata ake yi, manya manyan baki sai zuwa suke yi, matan uncle Rahab ma sun zo, Ummien Sharifat ma ta zo, baki daga Dubai sosai sun zo, Abu Abdussalam zai zo ɗaurin aure, abin dai ba'a cewa komai, taro ya yi taro jama'a. Chuchu kuwa tana cikin wannan ɗaki tana aikin kuka, sai tayata auta take yi, ita ma tana jinyar soyayyar Hoorain a ranta. Wannan shi ne kaɗan daga cikin abin da yake faruwa a KINGDOM OF POWER. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 49 Chuchu, Auta, Aneesa and Fanan ne zaune a cikin wannan ɗaki da Chuchu take ciki suna hira, Sarina ce kawai bata a wajen. Suna zaune a tsakiyar katafaren bed dake cikin room ɗin, bayan gadon babu komai a ciki sai dressing room, dan ɗakin gyara ne ba'a buƙatar wasu tarukuce irinsu kayan make up da sauransu, iya mirror da amarya zata rinƙa kallon kanta ta tabbata ta ji gyara ya wadatar. Allah sarki ta haɗa kai da gwiwowinta ta yi shiru, ita kaɗai tasan raɗaɗin da take ji a cikin zuciyarta, ji take yi kamar ta sanya hannu a kai ta yi ta zabga ihu ko zata samu sassauci, ba abin da take so a yanzu fa ce ta je ta dubasa, tun safe take son zuwa dubasa amma ina tsofaffin kuyangun dake kula da ita sun hata fita, ta shiga damuwa sosai. A gefe guda ita kuma Fanan ta buga uban tagumi tana ta faman tunanin Yah Jaish ɗinta, yau kowa na family yana nan amma ban da shi, abin ya yi mugun taɓata, kewarsa take yi over. A ɗayan gefen kuma Aneesa ce ta buga nata uban tagumi, tun ranar da ta fara ganin Yah Rizwan ta kamu da sonsa, Allah Allah take su samu hutun school ta ce wa King zata je Dubai dik dan ta je ta gansa, da sonsa take kwana take kuma tashi, hotunansa kala kala ya fi 50 a wayarta, ba randa bata kallon hoton nasa sama da sau 20. Aka ce idan baka yi wa wani ba wani kuma yana can yana mutuwa a kanka wata kila ma baka san yana yi ba, haka rayuwa take, shiyasa ka tsaya a yadda Allah ya ajiyeka sai ya fi maka, babu wata halitta na jikinka da zaka canza ya yi maka kyau sama da yadda Allah ya yi ka, Ubangijinmu ya fimu sanin dai'dai, ya fimu sanin abin da zai dace da mu shiyasa ya yi mu a haka, ba wai baya sonmu ko wani abin makamancin hakan ba ne. Ki sani dik yadda Ubangijinmu ya yi ki hakan ita ce alkhairi a gareki, kin karɓar hakan hannu bibbiyu babban kuskure ne da zai jefaki danasani ko ba a yanzu ba. Fatan zaku fahimci hakan. Ta shiga matsanancin tashin hankali na jin labarin aurensa da chuchun, Allah sarki hakan yasa ta danne sonsa ta karɓi kaddararta hannun bibbiyu ta zo taya yar uwarta murna har ma ta tayata zama a wannan ɗakin. A ɗayan gefen kuma Auta ce ta buga uban nata tagumin ita ma tana tunanin Heronta da ya tsaya mata a rai, ganin shi take yi a idonta kawai yana yi mata gizo, zuciyarta zafi yake yi mata sosai, ingizata kawai yake yi a kan ta tashi ta je ta dubasa, a lokacin kuma karfe 9 na dare ya yi, dik ta shiga damuwa. Allah sarki ƴan'matan King fa kowacce da nata damuwar a yanzu ba tare iyayen nasu sun sani ba. Rashin sani ya fi dare duhu, Aneesa bata san cewa ita Chuchu ba Rizwan take so ba Jawad take so, amma ta sadaukar da soyayyar da take yi mashi ga ƴar uwar tata, ita ma Chuchun bata san Aneesa na mutuwar sonsa ba. Ita kuma Fanan bata san Jaish yana can yana shuka flowers ɗinsa da ƴar matarsa ba, har ma flowers da yake shukawa sun kusa girma su yi su haifi ƴaƴa kun gane ai?. Ita kuma Auta bata san cewa ita ma Hoorain yana mutuwar sonta ba, nata son ma ai wasa ne a gaban nasa, dik dai suna cikin rashin sani bayin Allah, haka zalika iyayen nasu ma suna cikin rashin sani, suna ƙoƙarin kwaɓe abubuwa dik a rashin sani. Komai na ƙoƙarin kwaɓewar da daga baya sai anyi danasani. Miƙewa Auta ta yi jikinta dik a mace, da kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa. Kayan barci ne a jikinta wando da riga pink color, ta yi matukar kyau, ta ɗaura silk scarves a kanta. Bedroom sillpers ta zura a ƴan kyawawan kafafunta zata nufi waje. "Ina zaki je Auta?". Cewar gimbiya Chuchu. "Aunty Chuchu zan je shuka flowers nawa ne". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe kamar zata yi kuka. Ɗan zaro idanu Chuchu ta yi, dan tasan wannan kalma ta shuka flowers suna amfani ne da shi idan sun ga masoya, haka suke gulmar Sarina da samarinta a waya, haka suke gulmar King and momma ma, dan tsabar rashin kunya, idan King ya zo part ɗin Momma da daddare in dai Auta bata yi barci ba sai ta gudo wajen Chuchu, idan Chuchu ta ce me ya kawota ɗakinta a wannan lokacin, sai ta ce daddy ne ya zo suna shuka flowers ɗinsa mana, wato daddy ne ya zo zuba love da momma, kuma dik kalle kalle fina finan turawa ya lallata Auta da Chuchu har suka yi wa soyayya farin sani haka, har da bashi wani suna wai shi shuka flowers, dik dan kada a gane sun san love kenan, da sun ce shuka flowers wa junansu sun san me suke nufi. Hmmmm wai a haka uncle Jahiz yake cewa Auta da Chuchu basu san komai ba, sai ya samesu a tare suna magana a nan ne zai gane wanene su. Sai ma idan sun kalli love film, sai su zauna suna faɗin haka zasu yi wa mazajensu idan suka yi aure, ba abin da basu sani ba yara biyun nan da kuke gani. "Auta wani flower kika shuka da har kike zuwa bashi ruwa ni ban sani ba?". Cewar Chuchu. Tana magana yana kara zaro idanunta da suke jajir saboda kukan rashin lafiyar Jawad da take fama da shi. Wlh ƴaƴan King sun san kan duniya, kai ka ji wai wani flower ta shuka har take zuwa bashi ruwa? Kai jama'a ana abubuwa a RAWANIN ZALINCIN wlh. "Kai Aunty Chuchu zan gaya maki idan na je na dawo". Allah sarki Aneesa da Fanan sun yi nisa cikin kogin tunanin masoyansu da suke dakon soyayya basu jin me su Auta suke faɗa, wlh son maso wani akwa wahala matuƙa, su kaɗai suka san raɗaɗin dake a cikim zuƙatansu a halin yanzu, kai Allah dai ka barmu da masu son mu, amma wlh ina tausayawa Fanan da Aneesa, especially ma Fanan..........😥💔 "Dan Allah Auta kada ki tafi ki barni ba tare da kin taimaka mun na gansa ba, in har ban sanyasa a idanuna yau ba zan iya mutuwa kafin da safe". Tana magana idanunta na cikowa da zafafan hawayen da suka fi wuta ƙuna. Nan take Autar ta ji wani irin muguwar tausayin ƴar uwar tata ya kara kamata, ita ma sai da idanunta suka kawo kwallah, dan tasan zafin so ita ma tun da flowers ɗin Hoorain yana shuke a cikin zuciyarta, sai dai Hoorain ɗin yaki yarda ya rinƙa bawa flowers ɗin ruwa ya ginasa da kalamai masu zafi. "Aunty Chuchu ba zan bari ki cutu ba, In Sha Allah a daren nan zaki gansa, bari na tuna mafita, idan wani abin ya sameki ni ya zan yi kenan?". Ɗan sunkuyar da kai Chuchu ta yi tana kokarin shanye waɗan nan zafafan hawayen nata kada su zubo. Wayarta dake gefenta ne ya fara ruri yana neman agaji. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kai kallonta a kan wayar. Yah Rizwan shi ne sunan da bayyana a saman screen ɗin. Da sauri ta yi picking dik dan ta ji a wani hali Jawad yake ciki, tun jiya rabonta da shi. Da kyar ta iya saita nutsuwarta haɗe da gyara voice ɗinta, a sanyayye ta ce. "Hello Yah Rizwan". Daga ɗayan ɓangaren ya amsa da. "My Jannaty barka da dare". Yadda ya yi maganar zaka iya fahimtar yana cikin tsananin damuwa matuƙa, da alama jikin Jawad bata yi sauki ba, bawan Allah ya shiga tashin hankali na wuce misali, Allah sarki dik suna kan rashin sani, kuna tunanin da Rizwan yasan dalilin rashin lafiyar ɗan uwansa ko zai mutu ba zai hakura da ita bane? Wlh sai dai sonta ya kashe shi amma tabbas zai hakura ya bar mashi, amma kash ba daman sanin hakan domin kuwa Mammie ta datse dik wannan hanya, ba ta yadda zasu sani sai bayan aure haka ta tsara masu hegiya. "Yah Rizwan ya jikin Yah Jawad?". Ta faɗa waɗan nan hawaye suna gangaro mata a guje kamar ruwa ya fasowa kansa hanya. A hanzarce ta kai hannunta ta toshe bakinta dan kada sautin kukanta ya fita. Da sauri Auta dake tsaye tana kallonta ta koma ta zauna a bakin bed ɗin tare da sanya hannu ta fara goge mata hawaye tana girgiza mata kai alamar ta yi shiru. Sai a lokacin su Fanan suka farga da abin da yake faruwa, a ruɗe suka kewayeta suna tambayar ko lafiya take kuka. Daga ɗayan ɓangaren ya ce. "Jannat jikin ɗan uwana sai dai nace maki Alhamdulillah kawai, dan Allah ki tayani da addu'a, idan wani abin ya same shi bana jin zuciyata zata iya ɗaukar hakan, ba zan iya jurar ganin ko ciwon kansa ba bare har ya kwanta irin wannan ciwo mai tsanani haka da ko motsi baya yi, wlh ji nake kamar ana caka mun wuƙa a kahon zuciya". Ya kai karshen maganar yana huci tare da furzar da iska mai zafin gaske kamar dai iskan bakin mai fama da tsananin zazzaɓi, da alama akwai zazzaɓin a jikinsa bawan Allah. Ai kasa yi mashi magana ta yi, ta ji batun da ya ƙara ɗaga hankalinta matuƙa, sai take jin kamar ba fa a duniya ta ji wannan zancen ba, a take ta ji ta kasa iya tantance a duniya take ko akasin haka, kanta da ya yi wani irin sara mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wayar ya yi ƙasa zai faɗi ba. Da sauri Auta ta tare wayar tare da katse kiran ta ajiye a gefe. Hankalinsu idan ya yi miliyan to ya tashi, a ruɗe Fanan da Aneesa suke jera mata tambayoyin me yake faruwa ko dai wani ne ya mutu?. Ta kasa iya buɗan baki ta furta uppan. Suna goge mata hawaye wani yana sake ɓulɓulowa kamar indororon ruwan sama. Auta ce ta riƙo hannunta ta miƙar da ita tsaye, dan ita ce kaɗai tasan matsalar. "Aunty Fanan, Aunty Aneesa muna zuwa, idan mun dawo zata gaya maku menene yake faruwa, amma dai ku sani ba wani abin bane da ya wuce tana damuwa ne a kan rashin lafiyar Yah Jawad, dan haka kada ku ɗaga hankulanku, bari dai mu dawo sai ta gaya maku da bakinta". Tana kai karshen maganar ta ja hannunta suka nufi hanyar fita. Kafin su Fanan su yi wata magana tuni ta fice da sauri, da alama da gangan ta yi wannan sauri dan kada su dakatar da ita, ta kuwa yi sa'a har ta fita basu kai ga yin magana ba. Suna kaiwa wajen ɗan corridor dake tsakanin room ɗin da parlourn sai Auta ta dakata tare da juyowa suna fuskantar juna. "Aunty Chuchu ki yi shiru ki goge hawayenki, yanzu ki laɓe a nan zan shiga cikin parlourn mu gaisa da su Inno sai nace masu ina zuwa, idan na zo fita zan shammacesu in kashe wutar parlourn, kina ganin duhu ki yi sauri ki fita, bayan minti ɗaya zan sake kunna wutar, da yar dan Allah sai kin kalli Yah Jawad yau. Zaro idanu Chuchu ta yi, a ruɗe ta ce. "Idan suka tuhumeki a kan wani dalili zaki kashe wutan fa me zaki ce? Kin dai san halinsu da bin kokkofi". Da kyar ta iya faɗar hakan saboda kukan da ta sha. "Ke dai Aunty Chuchuna kada ki damu, na san yadda zan yi da su, ke dai ki tabbatar kina ganin duhu kin laluɓa kin fita da sauri". Hmmm Auta da ta yi wa King da kansa ma wayo ta je ta kalli Hoorain da daddare waye ba zata yi wa wayo ba? Dik wani fitar sirri dan kada a ganota yarinyar nan ta san hanyar yinsa, dik dan zuwa ganin Hoorain a sace, kunga kuwa ai fin haka ma zata aikata, yaran King dik sun shuka flowers ɗinsu har suna zuwa bashi ruwa King bai da labari, shi uncle Jahiz ma har da wani cewa basu girma na, bai san manyan ƴan love bane, sai ranar da dubu ya cika akwai zare idanun kam. "Tom shikenan Auta ta my lovely baby, Allah ya bar mun ke yar kanwata rabin rai'na ". Yadda take Maganar zai nuna maka tsabar farincikin da take ciki ne yasa har ta ruɗe take ta surutai, Allah sarki zata je ta ga flowernta ta zuba mashi ruwa. Wucewa gaba Auta ta yi tana faɗin. "Ke dai yanzu ba lokacin godiya bane, bari idan mun dawo zamu yi murna a tare, yanzu dai ki shirya". Da okey ta amsa kawai. Da sauri Auta ta fito cikin parlourn. Dattawa kuyangu mata guda biyu ne a cikin parlourn, ɗaya tana zaune a saman sofa tana kallon tv, ɗayar kuma tana ta aikin haɗe haɗen magungunan gyara a cikin kwarya. "Barkanku da dare Inno mariya". Cewar Auta ƴar basaja. Inno mariya dake zaune a saman sofa ne ta fara faɗin. "Farar mace lantarkin gida, takawarki lafiya sanyin idaniyar ahalin mai girma Abdul Malik, bangon sugari kowa ya jingina dake sai ya sha zaki, kaga mace mai zuciyar zinari, mace mai kyau kamar ɗawisu, kaf familyn mai girma Abdul Malik babu mai kyanki, tauraruwa mai haska gabaɗaya kingdom of power, murmushinki tamkar hasken wata...........". Tana kirarin tana jinjina hannunta alamar girma. Ɗaga mata hannu Auta ta yi kafin ta ce. "Inno ya isa haka! Meyasa kuke son wahalar da kanku da buɗe muryan ku ne wajen jero waɗan nan kirarin?". Kara dunkule hannun Inno mariya ta yi ta jinjina mata kafin ta ce. "Ranki ya daɗe ƴar Autar familyn King Abdul Malik, tauraruwan kasar Tunisia, muna yin haka ne dan mu sanyaki farinciki, domin farincikin farincikin kowa ne dake cikin wannan masarautan". Tana magana kuyanga Inno Raliya dake haɗa magunguna tana jinjina kai alamar irin gaskiya ne, gaskiya ne, wato irin gaskiya Inno mariya take faɗe kenan. "To amma Inno in dai kuwa haka ne daga yau na baku dama a wannan yawun bakin naku da zaku ɓata wajen yi mun kirari to ku mun istigifari ku nema mun yafiyar laifukana a wajen mahaliccinmu sai na fi jin farincikin hakan". Jinjina kai Inno mariya ta yi kafin ta ce. "Ai ranki ya daɗe muna neman maki gafara wajen Allah a koda yaushe, da dai an barmu mun yi kirarin ma ai ko?". "Wannan gaske ne". Cewar Inno Raliya. "A'a ni dai na yafe wannan kirarin ai mun istigifari sai ya fi mun, a kara a kan wanda ake mun, in dai kun ganni daga yau ba kirari zaku yi ba, istigifari zaku yi". Cike da ƙaguwar ta bar wajen ta yi maganar, dan ta ƙotsa ta kashe wutar chuchunta ta samu hanyar zuwa wajen flowernta ta zuba mashi ruwa ko zai farfaɗo. "To shikenan tun da haka kikeso daga yau hakan za'ayi In Sha Allah". Cewar Inno Raliya. Jinjina masu kai ta yi tare da ɗan sakar masu murmushi. "Inno zan je wajen Mommana amma zan dawo dan a nan zan kwana tare da Aunty Chuchuna". Jinjina kai Inno ta yi tare da yi mata fatan a dawo lafiya. Yadda kuka san a kan ƙaya take ta yi maza ta wuce, tsabar sauri har kamar zata kifa, sai da su Inno suka yi mamakin irin wannan uban sauri haka. Ita kuwa Chuchu baiwar Allah tana tsaye a corridor tana aikin sharar kwallah, a ƙage take da a kashe wutar kawai ta fice da sauri, ta matsu da ta ganshi. Shammatarsu Auta ta yi basu ankara ba sai gani suka yi duhu ya gauraye ko'ina, ta yi switching off na wutar ɗakin. Ai a miliyan Chuchu ta laluɓa ta fita, kafin Inno ta kai ga yin magana a kan dalilin ɗaukewar wutar ma har Chuchu ta fice, ita kuma Auta ta sake kunna wutar. "Ranki ya daɗe lafiya kika kashe mana wutan?". Inno Raliya ce ta yi maganar. "Lafiya lou Inno, mistake ne zan wuce hannu ya taɓa wajen, kunga saurin da nake yi ya ja". Sun gamsu da zancenta, dan sun san bata yi masu karya, bata ma taɓa yi sun san karya ɗin bane, sai suka yarda. Da sauri ta sa kai ta fita dan ma kada su jefo mata wata tambayar. Tana fita ta nufi ɗakinta. Felix ɗinta yana ta barci a saman bed ɗinta, ya shige cikin bargo, tana matukar kaunar wannan wolf ɗin nata, ga shi fari kal gwanin birgewa, ko baka son jinsin karnika in dai aka baka Felix sai ka ji kana sonsa. Shafa jikinsa ta ɗan yi kafin ta wuce a hanzarce ta ɗauko ɗan please call me abaya hijab ɗinta ta sanya a saman kayan barcin jikinta. Sai da ta dawo wajen bed ɗin ta sumbaci Felix ɗinta a kan lallausan gashin kansa, sannan ta fice da sauri. ______________🌹😥🔥_____________ CHUCHU. Kai tsaye part ɗinsa ta nufa, sai sauri take bugawa gudun kada wani ya ganta. A yadda ta afaka cikin part ɗin nasa sai da ta sanya kuyangun da suke yi mashi hidima tsorata, saura kaɗan su zura a guje, basu expect za'a shigo ba. Bata bi ta kansu ba ta wuce can cikin ɗakinsa. Suna ƙoƙarin ɗaga mata gaisuwa tare da zubewa kasa amma ina tuni ta wuce ciki. Sai da ta tura kofar bedroom ɗin zata shiga sai tunanin Rizwan ya faɗo mata a ranta, yanzu idan yana ciki fa? Ta jefawa kanta tambaya, zafafan hawayene suka cigaba da bin ƙuncinta, idanunta har sun kumbura saboda uban kukan da ta sha. Tuna cewa ganinsa shi ne zai ceci numfashinta daga tsayawa da fita yasa ta kai hannunta ta goge hawayen nata tare da afkawa cikin ɗakin. Ta yi babban sa'a Rizwan baya a ciki, iya Jawad ɗin ne kawai kwance a saman bed ɗin, lulluɓe yake da bargo mai laushi har izuwa kirjinsa, yana kwance shiru kamar wanda ba rai a jikinsa, yanzu ba jimawa King, Uncle, uncle Jahiz and uncle Taheer suka fita daga cikin ɗakin, sun zo sun duba shi ne. A guje ta tafi ta haye saman bed ɗin, wasu zafafan hawayen ne suka cigaba da keto mata a guje. Daidai saitin face ɗinsa ta matso, kuka ya ci karfinta sosai, amma a haka ta daure take ambatar sunansa. Shiru bai amsa ba, kara rankwafowa kansa ta yi tana cigaba da kuka, kamar wadda ta rasa hankalinta ta fara zuba sambatu kamar haka. "Yah Jawad ka tashi dan Allah, idan har ka mutu ni ya kake son in yi? Ka manta ka ce zamu rayu a gidan auren mu a tare ne? Dan Allah kada ka bari soyayyata ta zama ajilinka, wlh idan hakan ta faru ba zan taɓa yafewa kaina ba, na shiga uku, dan Allah ka tashi". Tana yi tana kara rankwafowa kansa, hawayenta ne suka fara zuba a saman lallausan kumatunsa. Ta san cewa saboda ita yake wannan ciwon, dan tana da tabbacin ya ji labarin aurensu da Rizwan ne yasa ta fara ciwo. Still dai bai motsa ba, dan alluran barci Dr Raj ya kara yi mashi domin lokacin da ya farka ya tashi ne da wani irin razana da kuma azababben zazzaɓi, shi ne Ramish ya ce har yanzu yana bukatar karin hutu, dalilin kara yi mashi alluran bayan sun yi treating ɗinsa kenan. Dik abin da Chuchu take yi Mammie tana kallonta, domin kuwa ta sakawa room ɗin Jawad idanu a yanzu, dik abin da yake faruwa tana sane da su, da alama ita ce ma nan ta danne Jawad ɗin da tsafinta, ita ta hana shi ja in ja da uncle Abbas, ta hana shi buɗe baki ya gayawa King or ɗan uwansa gaskiyar abin da yake faruwa. Ganin bai motsa bane yasa ta fara ɗan bubbuga kirjinsa tana mai cigaba da ambatar sunansa, amma ina ko motsi bai yi ba. Tun tana kuka da daɗin rai har ta fara fita hayyacinta ta fara tari mai kwazure zuciya ya tayar da hankalin mai sauraro. A hankali ta sulale ta kwantar da kanta a saman kirjinsa dake harbawa da karfi, karfi, sauri, sauri, ta kwanta tana cigaba da hawaye suna jika mashi jiki. Har lokacin kuma Rizwan bai dawo cikin ɗakin ba, da alama akwai abin da ya riƙesa ko kuma makircin mammie, dan shi yake jinyar ɗan uwan nasa, kuma baya taɓa yin nisa ya barsa, ɗazun da ya kira Chuchu ma yana a cikin ɗakin, so kamar ansan tana zuwa aka ja hankalinsa ya fita. A hankali barcin wahala ya kwasheta kwance a saman kirji nasa, ta sha kuka ne har muryarta ya dashe ya dai'na fita, ta ƙanƙame rigarsa gam kamar nace zan rabasu. Sai sauke wahalallen ajiyar zuciyar a cikin barcin take yi. ________________🔥💘🌹_______________ RAMISH. Tsaye yake a gaban bed ɗinsa hannunsa riƙe da cup mai ɗauke da cappuccino da bai samu ya sha ɗazun a wajen King ba, dawowarsa daga wajen mamarsa kenan, ya ɗaura kafarsa ɗaya a saman bedside drawer ɗayan kuma yana ƙasa, ya ɗaura hannayensa a saman gwiwarsa na kafarsa dake saman bedside drawer, Bluetooth mai bala'in kyau da tsada ne manne a kunnensa guda ɗaya yana amsa kira. Kwance Bilal and Dr Raj da suka baro wajen King a yanzu suke a saman bed na Ramish ɗin, Bilal ya tada kai da lallausan pillow ya kuma rungumo pillow ɗaya a chest ɗinsa, shi kuma Dr Raj ya yi kwanciyar ruf da ciki yana latsa waya. Bilal kuma ya zubawa Ramish idanu yana sauraron maganar da yake yi a waje cikin kwararriyar larabcinsa ga wannan sexy voice ɗin nasa mai kwantar da hankali masu sauraro, magana one by one cike da class. "Lallai dole sai ranar Sunday za'ayi taron ne?". Ya yi maganar cikin mutunci, dik yadda aka yi da Abu Abdussalam yake waya, dan shi ne cikon mutun na uku da Ramish yake girmamawa yake kuma yi masu magana cikin mutunci da natsuwa a rayuwarsa. Shiru ya yi yana sauraron abin da ake faɗa a cikin wayan na ƴan mintuna da basu fi biyu ba, da alama bayani ake yi mashi. "Okey for sure za'ayi, on Sunday by 3pm dai'dai zan yi leading a airport". Ya faɗa yana latsa wayarsa dake hannunsa, kamar mai rubuta saƙo zai turawa wani. Miƙewa zaune Bilal ya yi yana mai cigaba da kallonsa da kyau. "Okey Abbie In Sha Allah". Ya faɗa tare da juyo da kallonsa a kan Bilal. Katse kiran ya yi kafin ya sauke kafarsa daga saman drawer ya nufi wani haɗaɗɗen set of rocking chair dake kusa da mirror ya zauna saman guda ɗaya yana ɗaura cup ɗin hannunsa a saman table dake center wajen. "Yah Ramish on Sunday fa ka ce?". Bilal ya jefa mashi tambayar yana tsaresa da ido. Ɗan lumshe fox-s eyes ɗinsa ya yi tare da sauke ajiyar zuciya. "To ya zanyi Bilal?" Ya faɗa. "A'a ai abin ne ya yi maka yawa, kada ka manta a massages da muka samu an buƙa ci da lallai ranar Sunday zamu yi wannan tafiya, how comes zaka cewa Abbie zaka yi attending taron nan a ranar kuma? Why not a ɗaga taron sai zuwa Monday". "Zan iya Bilal". Shi ne abin da ya furta yana ɗan ɗaga kansa sama kamar mai tunanin wani abin. Tun da Bilal ya ji ya furta kalmar zai iya sai ya yi shiru, dan dik san da kuka ji Ramish ya ce zai iya to fa sai dai ayi shiru, dan kuwa komai wahalarta sai ya yi ta ko da kuwa zata iya yin barazana da rayuwarsa sai ya aikata. "Amma ka yi tunani a kan wanda ya turo mana wannan sakon kuwa?". Cewar Bilal. Kai ya girgiza alamar a'a ba tare da ya furta uppan ba. Dr Raj dake aikin latsa waya ne ya ce. "But the guy is very very smart and talented wlh, na sha madarar mamakin ganin Yah Ramish ya jinjina mashi, koma wanenen ya turo sakon nan shegen kwaro ne, ya kware a aiki over". Sirrin tsaki Bilal ya ja kafin ya ce. "Shirmen banza, ni ba shi nake magana a kai ba, so nake mu yi tracking ɗinsa ta koma wace hanya mukamashi, daga nan ya gaya mana ya akayi ya sanmu ya kuma san komai da ya shafe mu da har yake ƙoƙarin taimaka mana! For what reason?". Juyowa garesa Dr Raj ya yi tare da dai'na latsa wayar tasa ya ce. "Yah Bilal kai dai akwai saurin hawa wlh, kawai ku kyalesa tun da ya taimaka mana ba cutar da mu ya yi ba". Miƙewar da Ramish ya yi tsaye ne yasa suka yi shiru tare da mayar da kallonsu a kansa dan su ji me zai ce. Hannaye ya zura cikin aljihun wandon sleeping dress ɗin jikinsa, calmly ya furta. "Akwai wanda nake zargi, but kada ku tara mun aiki a brain ɗina, let me finish what I started first, zan kama koma wanene". Ya kai karshen maganar tare da hayewa saman bed ɗin. "Wai me kuke yi a room ɗin nan ne? Kowa ya wuce nasa mana, i want to sleep". Cewar Ramish again. Harara Bilal ya wurga mashi kafin ya gyara kwanciyarsa yana faɗin. "Dr idan ka fita ka rufo mana kofa ni kum maga kwanciyata good night". Alamar ba zai bar ɗakin ba kenan. Wani harara na musamman Ramish ya wurga mashi da idanunsa da suka koma sleeping eyes sosai saboda barci da yake ji. Bai ce ko uppan ba ya kwanta tare da janyo bargo. Cikin zolaya Dr ya ce. "Ko aure kuka yi ai ni ina tsakaninku da matan naku babu mai rabani daku, dan haka bari ma na kashe mana wuta ku gani sai da safe". Ko sannu Ramish bai ce masu ba ya kara gudun Ac tare da janyo bargon har kansa ya rufe. Dr Raj ya kashe wuta tare da juya masu baya ya cigaba da latsa wayarsa, shi ma Bilal bargon ya ja kawai ya rufe jikinsa. Ba'afi 10 mins Ramish and Bilal suka yi barci, shi kuwa Dr ya jima yana taɓa waya kafin barci ta kwashesa. Asuba ta gari zakunan King Zuhair. _______________🌹💘______________ AUTA ZUNAIRA. A hankali ta lallaɓa ta fita ta kofar baya, da yake gidan nasu yanzu a cike yake da manyan baki saboda bikin nan sai ya zamana busy ya kara yi wa iyayen nasu yawa, kowa hankalinsa yana kan ɓangaren da ya riƙe, ita dai Momma an barta da dik wasu bakin da zasu zo alhakin kula da su yana a kanta, so kowa da abin da yake yi, su Auta kuma an barsu a hannun Aunty MieMie. Kai tsaye part of warriors ta nufa ko tsoro bata ji ba, sai dai tana tafiya tana ɓuya idan ta ga warriors zasu gifta, bata bari kowa ya ganta ba, da yake yanzu ta san room nasa sai kai tsaye ta nufi wajen. Sai dai bata kai ga ƙarisawa wajen ba ta tsinkayo muryan Ansar a ɗan jefe can wajen wasu wishbone chairs da aka ƙawata kewayayyen wajen da su, ga wasu flowers masu kamshi cike a wajen, sannan akwai dogayen bishiyoyi da suka kewaye wajen, kamar small garden haka, yawancin lokuta Hoorain da Ansar suna yawan zama a wajen. Lallaɓawa ta yi ta matsa kusa domin ta ji me suke faɗa, dik da bata ji voice ɗinsa a wajen ba hakika tasan yana a wajen, dan ta ji zuciyarta ta amsa sunansa a kisa. Su uku ne a wajen yau kam, zaune suke saman kujerun suna hira cike da shaƙuwa da juna. Cike da zolaya Anwar ya ce. "Hoorain ina gimbiyarka take?". Ɗago kai ya yi cike da mamaki ya ce. "Wacece kuma Gimbiya?". Wato dai kowa ya gane cewa Hoorain yana son Auta fa, saboda ba so ne na wasa yake yi mata ba, hakan yasa dik abokan da suke tare suka ganosa. Kallon Ansar Anwar ya yi kafin ya ce. "Ansar ka ji mum mutumin wai ni yake tambaya wace gimbiya kuma?". Yana magana yana murmushi kyakkyawan balarabe da shi. Kara matsowa kusa ta yi dan ta ji me suke faɗa da kyau sosai. Ganin Hoorain ba kayan mayakan bane a jikinsa ba ƙaramin mamaki ya bata ba, sai dai kuma daga in da yake zaune ya bata baya ta yadda ba zata iya kallon face ɗinsa ba, tunani ta fara yi a kan wato dama yana cire holar yakin nan a cikin mutane? Kenan su Ansar sun san ainahin face ɗinsa? To meyasa ita yake ɓoye mata fuskarsa? Anya ba wani dalili mai karfi kuwa?. Ta jefawa kanta waɗan nan tambayoyin wanda a wajensa ne kawai zata samesu. Sosai ta ƙagu da son ta ga face ɗinsa, ga shi tana son jin hiran da suke yi, ya zamar mata dole ta laɓe ta gama jin hiran nasu sannan ta shiga wajen taga face ɗinsa, dan tana son ta ji me zasu ce a kanta tun da zancenta suke yi. Zubawa halittar jikinsa ido cikin shigar wandon jeans milk milk color and t-shirt ash ta yi, hakika kayan warriors sun fi yi mashi kyau matuƙa. __________________________ "Kai Anwar ka dai'na ɓata bakinka a kansa, dan ko me zaka ce mashi sai dai ma ya ce maka bai santa ba". Cewar Ansar. Ɗan zaro idanu Anwar ya yi tare da cewa. "Kai Ansar yama isa ya ce bai san gimbiya ba? Mun fa san komai shiru kawai muke yi, kawai malam ka gaya mana ya take?". Shiru bai tanka masu ba, hannunsa riƙe da wayarsa yana latsawa, hasken kwayayen fitillun dake wajen sun haska face ɗinsa dake sanye da face mask da kyau. Ya fake da iska mai sanyi ya yi yawa ya sanya face mask a face ɗinsa. Sake maimaita mashi tambayar ina gimbiya Zunairansa take Anwar ya yi cikin zolaya. A kule ya ce. "Anwar kada ka sake mun maganar wata a nan, na ce maka ni ban san wacece wata Zunaira ba, dan haka kada ku ɓata mata daɗin hiran da muke yi da hiran wata can daban, in hiran ƴan'matanku ma zaku yi ni bari na shige ciki sai da safe kawai". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye. Wani irin faɗuwar gaban da ya ji ne yasa shi fara ɗan waige waige kamar mai neman wani abin. Kallo suka bishi da shi Ansar yana faɗin. "Kai our Lion matsalata da kai saurin hasala da fusata, wai a haka kuma zaka yi aure? An gaya maka mata zasu iya ɗaukar wannan uban saurin fushin naka ne? Daga maga sai ka wani fusata kace zaka tafi ciki?". Ko kallon in da suke bai yi ba, bai ma ji me suke faɗe ba, saboda hankalinsa ya yi wani wajen, zuciyarsa ta buga ta amsa da sunanta, tabbas ya ji a zuciyarsa tana kusa da su, shiyasa ya fara waige waige, lallai ya tabbata ba son wasa yake yi mata ba tun da har in ta matso kusa da shi sai ya ji hakan a cikin zuciyarsa koda bai ganta ba, sonsa na daban ne wlh. Ita kuwa idan ranta ya kai miliyan to ya ɓaci, bata ji daɗin yadda ya furta da bakinsa cewa bai santa ba, har da wani bai san wata Zunaira ba, wato itace ma wata, abin ya bakanta mata rai da har wayarta dake hannunta ya zame ya faɗi kasa ba tare da ta farga ba, abin da taɓa zuciya ace wanda kake mutuwar so ne zai tsaya a gaban abokansa yana cewa bai ma sanka ba, abin da ciwo gaskiya, zuciya bata da kashi!!. Ganin yana nufo ta in da take yana waige waige kamar mai neman wani abi ne yasa ta bar wajen da sauri domin ta koma cikin gida, ta fasa haɗuwa da shi ɗin ma dan ya bakanta mata. Wucewa ta yi ta bar wayarta a ƙasa a wajen ba tare da ta sani ba. Tana barin wajen ba jimawa ya iso daidai in da ta bar wayar tata, dik ta in da take da ya matso zuciyarsa take kara amsa mashi da tana wajen, shiyasa ya nufo wajen kai tsaye, ya yi mamakin meya fito da ita a daren nan?. Yana ƙoƙarin bin hanyar da ta bi ne ya hango waya a ƙasa, da farko bai san wayarta bane har sai da ya ɗauko tukun nan ya gane nata ne, dan ya saba gani a hannunta. Wannan waya ta kara sawa ya tabbatar da zarginsa a kan tana kusa da shi, sai dai kuma ya ji zuciyarsa ta sosu sosai, dan yana da yakinin ta ji maganganunsu ne yasa ta gudu, dik sai ya ji babu daɗi, a ransa ya ce lallai yakamata su haɗu tun kafin ta koma cikin gida domin ya bata hakuri, yasan halinta sama da kowa, yasan zata iya kwana yin kuka a kan hakan, idan hakan ya faru kuma ba zai taɓa samun nutsuwa ba shi. Cikin zafi ya fara takun jarumta yabi bayanta dan ya cin mata. Dik ƙaguwa da son ganin face ɗinsa da take yi a yau ta samu dama amma ya ɓata mata rai yasa ta ji bata da buƙatar hakan. Da yake takunsa ɗaya ta ninka nata uku sai ya yi saurin cin mata, ya hangota tana ƙoƙarin komawa cikin gida. Ƙara zafafa tafiyar tasa ya yi dan ya cin mata ya samu ya bata hakuri, sai dai bai kai ga hakan ba ya hango guyson yana nufota. Dakatawa da bin nata ya yi yana danasanin kalaman da ya furta na cewa bai san wata Zunaira ba. Jiki a mace ya juya da sauri ya bar wajen dan ma kada guyson ya kalle shi. Bai zame ko'ina ba sai cikin ɗakinsa. Yana shiga ya turo kofa ya rufe har da sa key dan ma kada su Ansar su biyosa, yasan sarai sai sun zo bashi hakuri dan a tunaninsu fushi ya yi ya tafi, basu san bayan masoyiya rabin rai ya bi ba. Kifa kansa da jikin kofar ɗakin ya yi yana jin kamar ya koma ya yi mata magana koda a gaban guyson ɗin ne, zuciyarsa ta ɗacaca ainun. Burinsa kawai a yanzu ya sanyaya mata rai koda kuwa bayyana mata soyayyarsa ce zai sa hakan to zai yi, zai bayyana mata. Call ne ya shigo cikin wayarta dake hannunsa hakan yasa ya ɗaga kansa daga jikin kofar. Kawo wayar saitin face ɗinsa ya yi dan yaga wanene mai kira. Uncle Taheer shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Wani irin ɗaure fuska sosai ya yi tamkar akwai mai ganinsa, nan take kishin maza ya motsa, har zai buga wayar da ƙasa saboda kishi sai kuma ya danne ya fasa dan kada ya kara laifi a kan laifi, yanzu ma flower tasa fushi ta yi. Call ɗin ta yanke wata ta sake shigowa, dogon tsaki ya ja tare da wucewa ya nufi saman bed ɗinsa dake shinfiɗe tsab gwanin birgewa. Kwanciya ya yi a lokacin call ɗin ya yanke, sai ya fara ƙoƙarin yi mata bincike a waya kamar ta aikesa, wayar babu password ba komai, hakan ya bashi damar shiga ciki. Sai dai wasu sassa daga cikin wayar ta sanya masu password, da alama akwai abin da take ɓoyewa. _____________🌹💘_____________ A nata ɓangaren kuma ta sha madarar mamakin ganin Guyson ya biyo bayanta, daga shi sai short na Jessy and singlet a jikinsa, kamar dai wanda ya kwanta ya fara barci ma, yadda yake tafiya zaka fahimci jikinsa a mace. Nan take ta fara ƴan kame kame tana tunanin me zata ce mashi, sai dai bata wani ɗaga hankalinta sosai ba, dan tasan Guyson mutun ne mai saukin kan da a tunaninta ko da ya san gaskiyar abin da ya fito da ita ma ba zai ɗaga hankalinsa ko ya yi mata faɗa ba. "Zunaira me ya fito dake waje a cikin dare nan?". Ya jefa mata tambayar yana ɗaure fuska. Zaro idanun waje ta yi, da mamaki ta ce. "Yah Omar yau kuma kai ne kake kirana Zunaira?". "Meya fito dake waje a daren nan nace?". On a serious note ya yi maganar, babu wasa a tattare da shi. "Babu komai". Ta faɗa a tsorace, dan bata taɓa ganin ɓacin ransa haka ba, shi kullum cikin murmushi yake. Tsawa ya daka mata cikin ɗaga murya ya ce. "Meya kawoki ɓangaren warriors?! Mama kika fita yi?!" Yadda ya yi maganar ya ɗaga hankalinta sosai, har ta ji zuciyarta ya karaya da son Hoorain, wannan ma guyson mai bala'in saukin kai ne ya ganta a hanyar part na warriors ma kawai ku dubi yadda yake yi mata tsawa abin da bai taɓa yi ba, to ina ga kuma yasan abin da ya fito da ita? Kuna tunanin ba zai ɗauketa da mari ba kafin ya san hukuncin da zai yi mata?. Guyson ma ya yi haka ina kuma ga su Ramish, Jaish da su Bilal? Me kuke tunanin zai faru in suka sani?. Ganin ta yi shiru bata amsa mashi bane yasa ransa ya ƙara ɓaci da har ya ɗaga hannu zai dalla mata mari. Kuka ta saka mashi tare da zurawa a guje ta nufi cikin gida, da sauri ya juya ya bi bayanta. Tana shiga part na Akka ta gudu ta ɓuya, shi kuma ya wuce part na Momma, dama daga nan ɗin ya fito, yaga lokacin da ta shigo part ɗin ta ɗauki hijabi a room ɗinta, a lokacin yana tsaye a parlourn reast area yana waya da su Omaid, shiyasa har ta fita bai dakatar da ita ba, da ya gama wayar kuma ya manta da batun sai ya koma cikin bedroom ya kwanta a saman bed ɗin Momma, har ya fara barci sai ya tuna da yaga ta fita ta kofar baya, hakan yasa ya bi bayanta. Nemanta ya fara yi a dikka ɗaku nan dake cikin part ɗin Momma, shiru bai ganta ba, part na mummyn Chuchu ya nufa, nan ma tsab ya bincike ko'ina bata ciki. Wayarsa ya dawo ya ɗauka a cikin room na Momma ya fara kiran numberta. 3 miss calls ya yi mata Hoorain bai yi picking ba, hakan yasa ya fita ya nifi part ɗin Akka dan ya duba wajen, in bata nan sai ya dubata wajen King. Kwance ya iskota saman bed ɗin Akka ta shige cikin bargo ta yi barcin karya. Ajiyar zuciya ya sauke alamar ya ji sanyi a ransa na ganinta da ya yi, da a tunaninsa bata dawo ciki bane. Kamar zai tasheta dan ta gaya mashi abin da ya fito da ita, sai kuma ya fasa a zuwan da safe zai tambayeta ta faɗa mashi. Sumbatarta ya yi a goshi kafin ya juya ya bar ɗakin. Yana fita ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya tare da gyara kwanciyarta, sai tunanin maganganun jarumin nata ya dawo mata cikin kwakwalwata, Allah sarki bata san lokacin da hawaye suka fara gangaro mata ba, sai take ganin kamar ita kaɗai ce take dakon sonsa. Hawaye sharɓa sharɓa a face ɗinta barci ya yi awon gaba da ita. ASUBA TA GARI. Washe gari da safe wasu zaƙwaƙuran masu iya lalle sosai daga kasar Sudan suka yi diran mikiya a kingdom of power domin yiwa amarya da ƴan uwanta lalle. Su ƙawatasu da kyau. Abin mamaki shi ne a ɗakik Jawad Chuchu ta kwana kwance a saman jikinsa amma babu wanda ya sani, Rizwan dake jinyarsa tun da ya fita a daren jiya bai jara dawowa ba, dan ya shiga cikin ɗakinsa da nufin ya yi wanka ya canza kaya, sai ya ji gajiya ta ka mashi ya ce bari ya kwanta ya huta, daga kwanciya wani irin barci mai azabbabben nauyi ya yi awon gaba da shi, har yanzu kuma wajen karfe 9 bai farka ba. Cakwakiya kenan baku tunanin da sa hannun mammie a wannan barcin kuwa?. Sannan abin mamaki shi ne su Aneesa basu nemi Chuchun ba, suka kwanta suka yi barcinsu, su Inno mariya kuma dama basu san ta fita ba, abin dai da mamaki gaskiya. ___________________🌹💘____________ Zaune Aunty MieMie take a saman egg chair dake cikin ɗakin King, yanayin chair ɗin design of egg aka yi su, sun yi matuƙar haɗuwa ga wani lallausan sofa a cikinsu mai daɗin zama. King yana zaune a bakin bed ɗinsa yana shan coffee ɗin da momma ta kawo mashi, ya dake a cikin alkyabbarsa ga haɗaɗɗen naɗin rawanin da ya sha, ya fito a balarabensa sak, madaran kyau iya kyau Hankalinsa a kan Aunty MieMie da ta tsaresa da ido alamar damuwa a face ɗinta, fada zai fita amma ta tsayar da shi wai tana son yi magana da shi, dole ya bata lokacinsa dan yana ji da ita. Sai dai kuma ya zauna ta kasa yin magana, ta tsaresa da kallo kawai tana tunanin ta ina zata fara yin magana. Gajiya da shirun nata ya yi ya ce. "Daughter wai lafiya? Maganar me kike son mu yi kika tsayar da ni?". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa, cikin girmamawa ta fara magana kamar haka. "Daddy maganar Jawad da Jannat nake son mu yi da kai dama, amma ka gama shan coffee ɗin sai ya fi". P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 50 "Daddy maganar Jawad da Jannat nake son mu yi da kai dama, amma ka gama shan coffee ɗin sai ya fi". Shiru ya ɗan yi yana kallonta, damuwa ce sosai a tarrare da ita, dan in baku manta ba da ita da Chuchu mamarsu ɗaya, so kunga ai ba zata so kaunarta ta auri wanda bata so ba, zata so farinciki har karshen rayuwar ƴar uwartata, sannan ita ta yi auren nan tasan ya yake, ba abu ne na rana ɗaya ko biyu ba, tamkar rai ne da shi shi ma, sai randa kwanakinsa ya kare yake katsewa. Rayuwa da wanda baka so akwai ciwo matuƙa. "Daughter just tell me kawai is better, coz ba zan iya cigaba da shan coffee ɗin ba bama until i know what's wrong with u i saw ur face like you're in a bad mood". Nisawa ta yi tana jin wani irin ɗaci a ranta, ita da take matsayin sistersu ma kenan ina ga su kuma masoyan? Ai sai Allah ne kawai zai iya sanin me suke ji a cikin ransu, dan baki kam ya yi kaɗan ya bayyana yadda suke ji. "No my dad, take the coffee first sai na fi samun farincikin yin maganar da kai". "Really?". Ya faɗa cikin zolaya yana ɗaga mata gera. Dan dole yasa murmushi ya subce mata ba tare da ta shirya ba, dama kuma abin da yake son gani a face ɗin nata kenan yasa ya ce really haɗe da ɗaga mata gera. Ajiyar zuciya ya sauke alamar ya ji daɗin murmushi nata, sannan ya yi continue take his coffee. Kasa ta ɗan yi da kai tana jin zuciyarta ya ɗan sanyaya. Ga dikkan alamu ba iya Jaish bane yake da kunya a ƴaƴan King, har da Aunty MieMie ma tana da shi, dik yadda aka yi tsakanin Akka da King Abdul Malik akwai wanda kunya take yawo a jinin jikinsa, sai dai idan da ga baya ya yaye kunyar ya jefar saboda yanayin rayuwa, to kun san idan abu tun ainahi a jininka yake ko ka yayesa ka jefar dole a jininka asamu masu gado, ga dai Jaish da Aunty MieMie sun yi gadon kunya. Ramish ne ya shigo cikin room ɗin bakinsa ɗauke da ɗan siririn sallama ƙasa ƙasa. Har suna haɗa baki ita da King wajen amsa mashi sallamar. Yanzu tashinsa daga barci ya yi wanka kenan ya nufo wajen daddyn nasa, dan fa bashi da burin da ya wuce ya gansa a tare da mahaifinsa, dan suna jimawa basu haɗuwa sai dai a video call. Gefen bed ɗin ya zauna yana faɗin. "Good morning our dad". Kallon tsab Aunty MieMie ta yi mashi tun daga kan arab hairnsa har izuwa kan kyawawa kafafunsa, sanye yake da white arabs jallabiya mai bala'in kyau, sai ya yi wa kayan kyau over kamar dan shi aka yi jallabiyas, ga arabs hairnsa da ta sha gyara matuƙa, sai tashin daddaɗar kamshi yake yi. "Big bro good morning". Aunty MieMie ta faɗa cikin zolaya tana ɗan murmushi. King ne ya amsa da. "Morning my son how was your night?". Alhamdulillah ya amsa da shi sannan ya dubi Aunty MieMie ya ce. "Morning big Aunty". Harara ta ɗan watsa mashi kafin ta ce. "Kai baka ji kunyar haɗa ido da ni ba ko?". "For what kuma kunyar?". Ya faɗa idanunsa a kanta babu ko gezau, da alama dai babu wanann kunyar a tattare da shi. "Tun yaushe kake cikin gidan nan da ba ka nemi in da nake ba? Sannan kace baka ji kunyar haɗa ido da ni ba? And last two months na je Dubai baka nan i know they told u, kuma baka kirani ba, ka fa yi mun laifuka dayawa". Ta kai karshen maganar tana ɗaure fuska irin ba da wasa take yi ba. Ɗan shafa Arabs hairnsa ya yi ya ɗan yi shiru yana tuna ta yadda zai tsarata su rabu lafiya, yasan dik cikin ƴan uwansu babu wanda ya kai Aunty MieMie and uncle Abbas tsananin madarar kaunarsu kauna ta haƙiƙa, haka kawai zata tashi ta ɗaga jirgi ta nufi Dubai dan kawai ta je ta gansu face to face ba a video call ba, haka shi ma uncle Abbas yake ɗaga jirgi ya je wajensu, so ba zai so ace ya ɓatawa su biyun nan rai ba. "Don't think anything da zaka wanke kanka, dan ba wani excuse da zan yi accepting, see ur big eyes a wajen". Ta faɗa tana harararsa. Hannu ya kai ya karɓi cup na coffee da dad yake sha ya ɗan kai saitin bakinsa ya yi sipping, dara daran idanun nan nasa a kanta ya rasa abin cewa, ta riga ta ganosa. King ne ya ce. "Idan ya zo part ɗinki sai ki titsiyesa dan kun fi kusa, now dai gaya mun damuwarki, dan shi ne a cikin rai'na, ko dai son ya fita ya bamu waje ne". Kawar da kallonta daga kan Ramish ta yi izuwa kan dad ɗin, a sanyayye ta ce. "Ya fita kuma dad?". Kai King ya gyaɗa alamar e. Girgiza kai ta yi kafin ta ce. "A'a ai babu wani abin da zan iya ɓoyewa our big bro, so na ma ji daɗin zuwansa saboda zai tayani fighting a kan abin da na zo nema". "Aunty MieMie karfi da ya ji fa kin mayar da ni babba ko?". Ramish ya faɗa idanunsa a kanta. Siririn murmushi ta saki tana faɗin. "To ai dik in da namiji yake shi ne babba, na baka girman ne, ni yanzu ma harta Jaish ni kanwarsa ce". Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya sake furta uppan ba, dan yanzu ma idan ba ita da King ba ko uncle Abbas baya hira da shi haka, gara ma Bilal idan tsiyar Bilal ɗin ta motso yana sanya shi biye mashi su ɗan yi hira, amma ko da Dr Raj baya maganar wuce 1 mins, sai dai ya yi shiru yana sauraronsu idan suna hira da su Rizwan, ba zai dai yi magana ba, amma zai saurari dik abin da suke faɗe. "Okey to faɗa mun menene yake damunki da har kike fatan ɗan uwanki ya tayaki faɗa a kai'na?". Cewar King. Ɗan gyaran murya ta ɗan yi haɗe da gyara zamanta kafin ta fara magana a nutse kamar haka. "Dad dama magana ce a kan Jannat da Jawad, wlh dad ba Rizwan ne yake son Jannat ba, Jawad ne yake sonta, ni shaida ce a kan hakan, dad please ka fahimceni kuma ka fahimcesu, kasan da cewa saboda auren Jannat da ka bawa Rizwan shi ya kwantar da Jawad ciwo?" "What!!". King ya faɗa yana zaro idanu, dan shi kanshi ya yi zargin hakan, ganin bashi da wata hujja yasa ya watsar da batun, bugu da kari shi fa dama Jawad yake son bawa ƴar tasa ba Rizwan ba, amma amsawa da Chuchu ta yi da bakinta cewa Rizwan take so ba Jawad bane yasa ya ja baya da kudurin nasa, idan baku manta ba akwai ranar da ya cewa Jawad tun da ba zaka gaya mun gaskiya ba nasan maganinka, da safe zan ɗauki mataki, to dama niyarsa a wannan lokaci da safe ya samu Akka da batun haɗa Jawad da Chuchu aure ne, sai wani abin ya ɗauke mashi hankali har Rizwan ya rigasa. ___________________________🌹 "Kwarai dad, saboda Jannat Jawad yake kwance rai a hannun Allah a yanzu, ita kanta Jannat ɗin ba lafiya ce da ita ba, tun around karfe 7 take part ɗina, ta tasani a gaba sai kuka take yi mun, na yi maganar duniyar nan amma taki amsani, idan na matsa mata sai ta ce mun Jawad ɗinta har yanzu bai tashi ba, shi ne kawai abin da take iya faɗa, dan Allah dad ka duba wannan lamari da kyau, ka kallesu da idanun basira dikkansu, kada mu yi abin da daga baya zamu yi danasani". A marairace ta kai karshen maganar, alamar damuwa sosai ne ya kara bayyana a saman face ɗinta. Zuba masu idanu Ramish ya yi yana ta kallonta ita da King ɗin dikka bai furta uppan ba, yana dai shan coffee ɗinsa a hankali hankali. "Amma Daughter how comes hakan zai kasance?". King ya tambaya. "Dad i don't know nima, what i know here's Jannat Jawad take so, and shi ma Jawad Jannat yake so". "No daughter, in kin ce Jawad yana son Jannat ba zan musa maki na, saboda nima ina zargin hakan, amma ki ce mun Jannat tana son Jawad ba zan yarda da wannan ba, saboda baki da baki ni da ita na tambayeta tsananin Rizwan and Jawad waye take so ta ce mun Rizwan, maybe saboda shakuwar dake tsakaninsu ita da Jawad ne yasa take kukan ciwon nasa". Shiru Aunty MieMie ta ɗan yi kamar mai nazarin wani abin, can kuma sai ta ce. "Okey dad, amma ina ganin ka duba lamarin Jawad ɗin, ka bashi aurenta tun da kaga saboda sonta ya faɗa cikin wannan hali". Jiki a mace ta yi wannan magana, dan bata taɓa tsammanin Chuchu Rizwan take so ba Jawad ba, abin ya ɗaure mata kai ita ma, bata yi tunanin Rizwan Chuchu ta zaɓa ta bar Jawad ba, da tasan haka ne ba zata tinkari King da zancen nasu ba. Ita ma dai Aunty MieMie an ruɗar da ita, kanta ya shiga duhu, a gaskiya Mammie hegiya ce, ji ta ruɗa mutane cikin ƙanƙanin lokaci!. "Kin zaɓi na yi wa Jannat aure da wanda bashi ne a ranta ba? Wanda ba shi ta zaɓa take so ba? Na ɗauketa na bawa wani dan shi yana sonta? Shi Rizwan ɗin ce maki aka yi baya sonta? Ko shi ba mutum bane?". King ne ya jera mata waɗan nan tambayoyi masu wuyar amsawar. Shi dai Ramish ko uppan bai ce ba amma idanunsa a kansu. King ya ɗaureta da tambaya, a nan ta rasa amsa gaskiya, saboda ba ta yadda za'ayi ta amsa magana ɗaya daga ciki, haƙiƙa ba zata so kanwarta ta auri wanda ba shi ta zaɓa ba, baka san cikin zuciyar bawa ba, watakila da gaske shakuwa ce tasa Jannat take yi wa Jawad kuka, watakila da gaske ba son Jawad ɗin take yi ba Rizwan take so, so idan ta matsa a bawa Jawad aurenta ya zamana Rizwan take so kunga da waye zata yi kuka? Ai kunga da Aunty MieMie zata yi kuka ko? Sannan kuma uncle Abbas ya tabbatar mata shi ma Rizwan yana son Chuchu sosai, kuma King ya karyar mata da zuciya a lokacin da ya ce shi Rizwan ɗin ba mutun bane. Babbar magana! Ruɗu iya ruɗu sun shiga!. "Daughter ina son ki sani shaƙuwa tasa Jannat yi wa Jawad kuka ba komai ba, ita Rizwan take so, kuma idan kin bibiya ma ita bata taɓa sanin cewa Jawad yana sonta ba, dik laifin Jawad ɗin ne da ya yi nauyin bakin kin gaya mana tun wuri yana sonta, dan haka dole ya karɓi kaddararsa ya hakuri da Jannat, ina son yanzu idan kin fita ki faɗawa mommarku nace ta shirya Aneesa gobe a tare za'a ɗaura auren Jawad da Aneesa danasu Rizwan, na bashi Aneesa a madadin Jannat tun da ya yi nauyin bakin faɗa mana gaskiya". Ɗan zaro idanu waje Aunty MieMie ta yi, cike da damuwa da tashin hankali ta ce. "Dad, ka bawa Jawad Aneesa kuma?". Kai ya jinjina mata kafin ya ce. "Ko Jannat da Aneesa suna da banbanci ne?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a, ta zo da nufin gyara abu komai ya sake lalacewa, ta ya za'ayi ya ɗauki Aneesa a bawa Jawad fisabilillahi? Ba a tambayi yarinya ko tana da wanda take so ba, sam ran Aunty MieMie bai yi daɗi ba kuma bai so hukuncin da King ya yanke ba, domin kuwa tasan dole Aneesa zata yi kuka da ita ta ja an aura mata wanda bata so, ya ilahi wannan abu sam bai yi mata daɗi ba!. "Zan iya tafiya fada ko dai akwai wani sauran magana da kike da shi?". King ya jefa mata tambaya. Sai a lokacin Ramish ya yi ɗan gyaran murya tare da ajiye cup ɗin dake hannunsa a saman bedside drawer, ya ɗan jingina bayansa da jikin headboard na bed ɗin, shi yana da ɗabi'ar karanta ya mutun yake ji a cikin zuciyarsa idan ya kalli face ɗinsa, so ya fahimci damuwar da Aunty MieMie take ciki matuƙa wanda King ya gaza fahimta, cike da so da kauna ya kalleta cikin sanyin murya ya fara magana ƙasa ƙasa a nutse. "Big Aunty, jeki abinki, jeki yi abin da dad ya umarceki zan yi magana da shi". Ɗan zaro mashi idanu ta yi, ita dai tasan King yana kaunarsu, yana kuma nuna masu soyayya a fili, sannan yana basu dama sosai a rayuwarsu, sai dai shi kaifi ɗaya ne da in ya yi magana tankwarasa ya juya maganar abu ne mai matuƙar wahalar gaske, kai abu ne ma da ba zai yiwu ba, ita ma ta gwada sa'arta ce kawai, abin kuma ya ki aiki. "Trust me big Aunty, jeki kawai". Cewar Ramish again. Jinjina mashi kai ta yi tare da miƙewa tana yi wa dad ɗinta addu'a da fatan alkhairi haɗe da fatan isa fada lafiya ya kuma dawo lafiya. Da amin ya amsa yana mai sanya mata albarka har ta fice daga cikin ɗakin. Miƙewa Ramish ya yi yana faɗin. "Dad let me escort u". Jinjina kai King ya yi kafin ya miƙe yana faɗin. "Dama ina buƙatar shawararka a fada". "Shawara kuma dad?". Jinjina kai ya yi alamar yeah shawara. "So for what kenan?". Yana magana ya riƙo hannun dad ɗin nasa. "A kan kuɗin shiga ne, tunani nake yi kamar mu kara yawan ma'aikatu domin a kara rage matasa masu zaman banza marasa aikin yi, sannan kuma kaga za'a kara samu kuɗin shiga again tun da ma'aikatar zata rinƙa fitar da kaya zuwa makotan ƙasashe, ko ya kace?". Shiru ya ɗan yi yana tunani. Can sai ya ce. "Yeah dad shawara ce mai kyau, za'a rage masu zaman banza and akwai amfani daban daban apart from that". Jinjina kai King ya yi. "To amma wani irin ma'aikata kake ganin yakamata mu buɗe?". Kai tsaye ya ce. "Ma'aikatar karafuna, i means karafunar mota hakan, ba karamin cigaba zai kawo maku ba, sannan zai kara ɗaga kasar sosai musamman idan kayanku yana da saukin kaso ashirin cikin ɗaki fiye da kowacce kasa". Jinjina Kai King ya yi alamar ya gamsu da maganar ɗan nasa. A haka suna tafiya suna hira har suka isa fada. ____________________________😥 A ɓangaren Chuchu kuwa, lokacin da ta farka ta ganta a room ɗin Jawad sai ta ji sanyi a ranta, da face ɗinsa ta fara cin karo da sassafiyar nan. Wayarsa ta ɗauka ta duba time karfe bakwai saura minti goma, a hanzarce ta diro kasa daga saman bed ɗin. Da sauri ta fice ta nufi part ɗin Aunty MieMie tana kwallah tana waigosa, to kun ji yadda aka yi ta tafi wajen Aunty MieMie ta gaya mata abin da yake faruwa. Tana barin ɗakin Rizwan yana shigowa kamar wani shiri. Ya sha madarar mamakin ganin kansa a room ɗinsa part din uncle Abbas a lokacin da ya tashi daga barcin nasa, jikinsa dik ciwo yake yi mashi lokacin da ya farka, da kyar ya iya tashi ya yi wanka, Jawad ne kawai a ransa a lokacin, shiyasa yana yin wanka ya yi maza ya shirya ya nufo ɗakin nasa. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da ya sauke idanunsa a kan ɗan uwan nasa, ya ji matuƙar daɗin ganinsa, a hanzarce ya nufesa dan ya duba lafiyarsa. Still yana nan dai kamar yadda suka barshi, ko motsawa bai yi ba, a gefensa Rizwan ya zauna yana tunanin kalaman mamarsu na karshe a kunnuwansu. "Rizwan na baka amanan Jawad, ka kula da shi tamkar yadda zaka kula da kanka, sannan ka tabbatar kana kulawa da dik wanda zaku yi tarayya da shi, domin ni ban yarda da gidan nan ba, ban sani ba ko ina da rabon sake sanya Rahilarh a idanuna, wata kila kuma kafin ta zo rai zai yi halinsa, dan Allah idan ma bata zo ta sameni da rai ba ka ce mata na bata Jawad duniya da lahira ta kula mun da shi, ban yarda ya girma a hannun babanku ko matarsa ba, ya girma a hannun Rahilarh shi ne wasiyata a gareka, ka zama mai biyayya ga manyanka, ka zama mai hakuri sai dai ba irin hakurina ba, ni kai'na nasan hakurina ya yi yawan da shi ya cutar da ni har haka, bana yi maku fatan hakuri mai yawa irin nawa, ina yi maku fatan wani lokaci idan anyi maku abu ku yi magana dan ku samu sassauci a cikin zuƙatanku, rashin amayar da magana ya jefani cikin wannan hali da nike ciki.............". Dakatawa da yin maganar ta yi tana wani irin tari mai sanya dik mai sauraro ya ji zuciyarsa ta karaya. Kuka sosai Rizwan yake yi yana faɗin. "Mommy ba zaki mutu ba, In Sha Allah zaki rayu damu, ki dai'na faɗin batun mutuwan nan". Sosai ta yi tari kafin ta samu ya ɗan tsagaita mata, sai ta cigaba da cewa. "Rizwan mutuwa tana a kan kowa, ni dai nasan lokacin nawa ne ya yi, ka dai'na kuka komai zai wuce, lokacin kaɗan zaka dai'na jin ciwon rabuwa dani ka fara mantawa dani, wasiya ta karshe da zan yi maka shi ne ka zama mai manta baya ka kula da abin da zai zo gaba, ka tsaya tsayin daka wajen ganin baka maimaita abin da ya faru a bayanka ba koma me shi...........". Rufe mata baki ya yi da tafin hannunsa yana cigaba da kuka yana girgiza kai, cikin kuka ya ce. "A'a mommy, har duniya ta tashi ba zan dai'na jin zafin rabuwa dake ba, In Sha kuma sai mun rigaki mutuwa, ki dai'na faɗin hakan, dan Allah ki yi shiru". __________________________ Ƴar firgita ya yi tare da dawowa daga duniyar tunain da ya afka. A fili ya furta. "Ba zan taɓa dai'na jin raɗaɗin rabuwa dake ba mommy, wannan ciwon ba zata taɓa warkewa ba! A kullum tana a cikin zuciyata, da ita nike kwana nike kuma tashi! Allah ya jikanƙi da rahma ya gafarta maki yasa mutuwa hutuce a gareki". Yana magana idanunsa suna a kan face ɗin Jawad, zafafan hawaye ne suka cika idanun nasa tab, ya fama ciwon dake zuciyarsa na rashin uwa na tsawon shekaru. Dr Raj and Bilal ne suka shigo cikin ɗakin domin duba jikin Jawad ɗin. A kusa da Rizwan Bilal ya zauna tare da kai hannu yana share mashi kwallar da ta zubo mashi a yanzu. "Be a strong man please my bro, by the grace of god babu abin da zai samu kaninmu, continue pray for him, very soon zai tashi". Cewar Bilal. Jinjina kai Rizwan ya yi ba tare da furta uppan ba, shi kaɗai yasan raɗaɗin da yake ji a ransa, tabbas rashin uwa babbar musifa ce ga ƴaƴanta komai girma da mulkinsu kuwa, ba zaka taɓa gane hakan ba sai idan bata tare da kai, ita ɗin bango ce ga dukkanin ƴaƴanta, waɗan da iyayensu suka riga mu gidan gaskiya Allah ya yi masu rahma ya gafarta masu, waɗan da nasu kuma suke raye Allah Ubangiji ya kara masu lafiya ya kuma bamu ikon yi masu biyayya haɗe da kyautata masu mu sanyasu farinciki a rayuwarsu ko Allah zai jiƙanmu. Dr Raj ma hakuri ya bashi kafin ya fara duba lafiyar Jawad ɗin. Sosai abin ya ɗaurewa Dr kai ganin yadda yanayin komai na jikin Jawad ɗin ya koma yake tafiya dai'dai, amma da zarar ya farka daga barcin alluran da suka yi mashi gabaɗaya sai jikin ta rikice ya fara yin wasu abubuwa kamar mai fama da tsananin zazzaɓin typhoid, kun san zazzaɓin typhoid idan ta tsananta tana da shegen saka mutun surutai har ma da ƴar fisge fisge kamar mai aljanu, idan ma ba'a sani ba sai a zaci aljanu sabon kamu ne da shi, domin zazzaɓin tana saukarwa da bawa gizon tsoro ne a cikin kwakwalwarsa, sai ya rinƙa ganin kamar abu zai bugesa ko wani abin makamancin haka, tana rikita jinin mutun ne sosai. A nan wajen dai dik kwarewan Dr a iya aiki sai da abin ya yi mugun ɗaure mashi kai, Allah sarki basu san tsafi ce take aiki a wajen ba ba wani abin ba. Sai dai bai gayawa Rizwan abin da ya gani ba, sai ya fake da ce masu gara a karawa Jawad alluran dan har yanzu jikinsa bata karɓi hutun nan yadda yakamata ba, yana buƙatar karin hutu sosai, ya dai yi masu dabara basu gane komai ba. ________________🌹💘________________ A ɓangaren cikin gida kuwa, sai shirye shirye ake yi gobe za'a ɗaura aure, ƴan uwan maman Jawad sun zo daga kasar Saudiya, su suka ɗauki nauyin haɗawa Rizwan ɗin kayan lefe, sun nuna bajinta kam, tun da Rizwan ya sanar da su dama Auntynsa babba ƴar mamarsa wadda suke uwa ɗaya uba ɗaya ta ce ita zata yi kayan lefe, ba yadda bai yi da ita ba a kan ta bari taki, har ma sai da ta haɗa mashi da zagi wai ya ci gidansu, sannan ne ya yi shiru ya kyaleta ta yi, su biyu iyayensu suka haifa, daga wannan Auntyn tasu sai mamarsu, shiyasa suke bala'in son Auntyn tasu, sai dai ba'a Saudiya take da zama ba ita, a kasar America take, dan bature ta aura ba balarabe ba, yanzu daga America ta wuce Saudiya suka taho tare da sauran ƴan uwansu. Kingdom of power taga manyan baki, dan kuwa ba kananan mutune ne suka zo ba, familyn mamarsu Jawad mutane ne masu tarin arziki da ji da kansu, basu ɗaukar wasa, jiga jigan hajiyoyi ne. Kai jama'a! Wato sun yi wani abin da ake cewa lefe, ya ilahi ya lillahi, kun san su ba lefe suke yi kamar namu na gargajiya ba............🌝🙄 Abin da ake kira lefe shi suke yi ba muna lefe ba, sai da suka shirge akwaitina ɗaiɗaiɗai har gudu 36 wato dozen mai goma sha bibbiyu har dozen uku, dikka shake suke da kaya irin su jinsin Abayas kawai, dama Rizwan ya gaya Auntyn tasa matarsa ƴar wanka ce mai shegen san kwalliya, ai kuwa sun zuba mata kayan gayu iya gayu, dik son gayun Chuchu fa sai ta gaji da canzawa bata gama sakasu ba, ga ƙananan kaya suma nasu akwaitin dozen guda mai goma sha biyu, kayan wanka irin na cikin ɗaki ma da nashi dozen ɗin, abin dai sai wanda ya gani, dan baki ya yi kaɗan ya faɗesa, sannan Aunty ta kara wa Chuchun da makullin dankareriyar mota kirar *PININFARINA BATTISTA* wadda a kallah kuɗinta ya kai kimani 2.9 million dollars. Dik isa da izzar kingdom of power sai da suka jinjinawa kayan da familyn mamarsu Jawad suka kawo, sun tashi kai matuƙa gaya. Chuchu kuwa Aunty MieMie ta je ta rarrasheta da kyar ta ce su je ta mayar da ita wanann ɗakin da ake yi mata gyara dan masu lalle sun zo zasu yi mata. Da kyar ta yarda suke tafi, sai dai fa Auntynsu Jawad ta tashi kansu Aunty MieMie, dan kuwa da tawagar masu lalle nata na musamman ta zo da su, ta ce su zasu ɗauki nauyin yi wa amaryarsu komai, dan haka masu lallen da Aunty MieMie ta kira su yi hakuri kawai waɗan da Aunty ta kawo su zasu yi wa amaryarsu lalle. Haka ta ciro makudan dollars ta miƙawa masu lallen Aunty MieMie ta ce su koma kawai. Maga ake ta dollars ta manyan kai jama'a! Babu harkar wasa ko harkar karanta, dollars ne kawai suke amshi a cikin kingdom of power my people's, wacece zata je bikin ta shirya mu tafi a tare? Sai dai Aunty ta shiga tashin hankali na ganin Jawad a kwance babu lafiya, ta shiga damuwa matuƙa da har ta kasa samun nutsuwa, dan ta fi son Jawad ma a kan Rizwan, saboda shi yafi zuwa wajenta, in dai ya shiga united state to fa a wajenta yake sauka shi da Jaish, Rizwan kuwa sau ɗaya ya taɓa zuwa in da take saboda kun san halinsa ɗaya da su Ramish, gidan iyayensu kingdom of power ma basu zo ba bare wani wajen, ba in da suke zuwa, Abu Abdussalam ya mallakesu, suna tare da shi kawai. Shiryawa masu lalle suka fara yi Aunty MieMie ta sanya Chuchu ta shirya cikin wando short zuwa gwiwowinta, da kuma riga mai ƙaramin hannu dan za'ayi mata lalle. A lokacin da Auntynsu Jawad ta ɗaura idanunta a kan Chuchu ai bata san lokacin da ta ce. "Ashe Rizwan yana rage maki kyau ne a hotunan da ya ɗaukeki ya tura mun, wow Masha Allah, Jannat wutar kyau, kai ai waɗan nan kaya da muka kawo ma sun yi kaɗan, kin cancanci fin haka, ba shakka Rizwan bai yi karya ba da ya ce ke ƴar wanka ce, gaskiya ya faɗa, yama rage ashe kin fi haka a zahiri, a gaskiya mun karɓi wannan amrya hannu goma goma ba bibbiyu ba, bibbiyu ya yi kaɗan, sai dai kuma Raeesa (Aunty MieMie) me ya samu amaryar tamu idanunta suka yi ja suka kumbura haka?". Fuska a ɗauke da fara'a ta yi maganar. Nasan dayawa daga cikinku kun manta sunan Aunty MieMie na gaskiya, shiyasa da ta ce Raeesa na sanya maku Aunty MieMie yadda zaku fi ganewa, Raeesa shi ne sunanta na gaskiya MieMie inkiya ce. Auntynsu Jawad fa irin wayayyun matan nan ne da suke very friendly, bata da wata damuwa a rayuwarsu, ga fara'a da iya zama da mutane, ga shi ta iya wa'azin zama da miji da shegen iya soyayya, dan masu miƙo flowers ta aura, wato bature sarakan iya soyayya ba, hakan yasa ta zama malamar soyayya, dik wata amaryar da zata fita ko zata shigo cikin familynsu ita ce nan take yi mata wa'azin zama da miji, ta kuma koya mata dik wasu abubuwan da bata iya ba, sam bata da girman kai dik da wannan uban arziki da suke da shi, yanzu haka ta tsaya haikam a kan bikin Rizwan ɗin nan, sai dai kuma dik da wannan Allah bai taɓa bata haihuwa ba, shiyasa take son ƴaƴan ƴar uwar tata sosai wato su Jawad, ta so ɗaukar Jawad da mommynsu ta rasu, Momma ce taki yarda, ta ce ita aka bawa amanarsa dan haka zata haɗa shi da Jaish ta yi renonsu, dan dole ta hakura baiwar Allah, tun tana sa rai da samun haihuwa har ta cire rai gabaɗaya tana addu'ar Allah yasa ta cika da imani kawai. ____________________________🕊️ Shiru Aunty MieMie ta ɗan yi kafin ta ce. "Babu komai Aunty, kukan rabuwa da su momma and su Auta take yi". Matsowa Aunty ta yi ta rungumeta tana faɗin. "Sorry my daughter, In Sha Allah babu wanda zai rabaki da ƴan uwanki, ai kina a tare da su, dan haka ki dai'na kuka kin ji ko?". Wani irin kuka mai karfi ne Chuchu ta ji ya kubce mata, ba zasu gane me take ji bane, da sam ba zasu yi ƙoƙarin bata hakuri ba. Ganin haka yasa Aunty MieMie ta matso ta karɓeta daga jikin Aunty tana faɗin. "Ya isa haka Jannat, ki yi shiru kin ji?". Kasa iya motsa laɓɓanta ma ta yi bare ta yi magana, sai dai ta kwantar da kanta a jikin Aunty MieMie tana kuka ƙasa ƙasa. Chuchu na kuka a nan, Aneesa ma tana nata kukan a cikin ɗaki Fanan tana tayata, tun daga sa'ar da Aunty MieMie ta isar mata da saƙon gobe za'a ɗaura aurenta da Jawad tare da na su Rizwan, tun daga lokacin ta rasa nutsuwarta, sosai take kuka kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, saboda Rizwan take so ba Jawad ba, babu soyayyar Jawad a ranta ko kaɗan face kauna ta tsakanin yaya da kanwa, how comes za'a ce mata ta auresa fisabilillahi? Wlh ita dai ba'ayi mata adalci ba take faɗe. Su Aunty basu san da batun auren Jawad da Aneesa ba sai da suka iso ne suka samu labari, dan haka Aunty ta ce yazamar mata dole ta ɗaga jirgi zuwa Dubai ta je ta sayowa Aneesa ɗin ma kaya kamar yadda ta sayawa Chuchu, hanata su momma suka yi, suka ce ta bari idan ya so sai bayan auren tun da dai abin ya zo unexpect haka. Da farko kin yarda ta yi, sai daga baya da King ya sanya baki sannan ta yi shiru ta hakura, amma da nufin idan an ɗaura aure gobe jibi ita kuma zata wuce Dubai ɗin. Su momma sun yi na'am da hakan. Rakuma manya manya guda goma, shanu goma aka yanka saboda wannan biki, hidima dai babu kama hannun yaro, amarya kuma tana can tana faman kuka ana zuba mata lallen. Sun kuwa iya tsara lalle ba'a magana, har saman singalalin ƙafafunta aka zuba mata lallen. Ita kuwa Aneesa da farko cewa ta yi a barta haka ba zata yi lallen ba, sai da Aunty MieMie ta ɓata rai sannan ta yarda aka shirya yi mata. Dik wannan sharholiya da ake yi fa ba Sarina a cikinsu, tana can tana ƙoƙarin binciken waye mammiensu ta zaɓa mata a matsayin miji, ita bama ta su Chuchu take yi ba, ta kanta take yi a halin yanzu, sai dai kuma da kamar wuya ta iya gano shirin mammmien tasu a kanta, dan kuwa ta buga ta raya, har Aunty Aliyarsu sai da ta tambaya amma ta ce mata ita fa wlh bata san shirin Mammien nan tasu ba, har da kara mata da cewa Mammie kun nan kamar Aljana take ba'a taɓa gane ina ta dosa. A can wani ɓangaren kuwa Adam ne yake ta ƙoƙarin yadda zai yi ya sace Sarinar ya dawo da ita EVIL KINGDOM, domin ya kwaɗaitu da surar jikinta, tun da ya koma ya gaza samun sukuni, dik hankalinsa a tashe burinsa kawai ya ɗanɗaneta, idan baku manta bama yana ɗaura idanunsa a kanta ya ce zazzafa, so gaskiya ta tafi da shi ainun, in baku manta ba na gaya maku tana da surar jiki mai ɗaga hankalin dik namijin da zai kalleta. Sai saƙa ta yadda zai shigo cikin kingdom of power ya ɗauketa yake yi, shi kansa Yusuf har yau akwai kwaɗayin surar jikinta a cikin zuciyarsa, burinsa kawai ya sameta ya biya buƙatursa da ita....... Ni kuwa nace Allah ya ceci uncle Abbas, dan kuwa dik abin da zai sami Sarina tamkar shi ya sama bawan Allah, dik abin da suka yi mata tamkar kingdom of power gabaɗaya suka yi wa, familyn Akka zasu zubarwa da mutumci, hegiyar yariya bata jin magana, ana tausaya mata ita kuma bata tausayawa kanta. One sweet thing shi ne, hidimar bikin Chuchu ya ɗauke hankali King Zuhair bai yi wa uncle Abbas hiran da suka yi da Ramish a kan yaki ba, yana ta busy da manya manyan bakinsa da suka fara dira a cikin masarautar daga jiya, har yanzu kuma baki ne suke ta tururuwan zuwa, abin dai ba'a magana. _________________🌹💘______________ JIMETA YOLA🦋🕊️🌹 "Hamma lafiya ka tsareni da idanu haka kana ta kallona". Ta faɗa kanta a ƙasa, tana zaune saman wannan itaciyar gwaiva da yake zaunar da ita. "Da wani ido kika kalleni har kika san ina kallonki?". Ya jefa mata tambayar yana riƙo ƴan hannayenta. "Ni ai ban ganka ba, kawai a jikina nike jin kana kallo na". Tana magana tana ɗan turo baki kamar Mahreen. "Da gaske?". Cikin zolaya ya yi maganar. "Kai hamma da gaske fa nike yi". "Faɗa mun meya ja hankalinki kika mun kwalliya da kika yi mun?". Girgiza kai ta ɗan yi tare da sake ƙayataccen murmushi, ya tuna mata da batun kwalliya. "Babu komai". Ta bada amsa tana wani kara yin ƙasa da kai kamar wata saliha. Matsawa kusa da ita sosai ya yi, ya ɗaura hannunsa a saman waist ɗinta ta baya, a hankali ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, idanunsa a saman face ɗinta babu ko kyaftawa. Juyo da face ɗinta ta yi saitin nasa, sai dai bata yarda sun haɗa idanu ba, sai ta ɗan lumshe idanun nata tana satar kallonsa. "My Noor ke karshe ce a kyau, kuma kin iya satar kallon mutun, sai aga kamar baki kallon abu". Ya faɗa can ƙasa ƙasa. Bata san yana kallonta tana satar kallonsa ba. Zaro idanu waje ta yi, kafin ta yi magana sai ya rigata da cewa. "Ko dai so kike yi ki haifa mun yaro mai kama da nine da kullum kike aikin satar kallona?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Da sauri ya ɗago kan nasa daga saman shoulder ɗin nata. "Noor da gaske kina son yaronmu ya yi kama da ni?". Ya faɗa cikin nutsuwa. Kai ta sake gyaɗa mashi alamar e. "No Noor, ki buɗi baki ki yi magana kin ji? Zan fi jin daɗin hakan". "Ni Hamma kunyar yin magana nike ji". A ɗan shagwaɓe ta yi magana. Hannayensa dikka biyu yasa ya tallafo kyawawan kumatunta. Ya zamana suna fuskantar juna, a hankali ya haɗe fuskokinsu, idanunsa a kanta ya ce. "Kina son mu haifi yara ko baki so?". Idanunta a datse ta amsa da. "Ina so mu haifa". Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ya sauke, ga dikkan alamu ya ji daɗin amsar tata, ransa ta sanyaya sosai. Cike da zumuɗi ya ce. "In Sha Allah nan ba da jimawa ba zamu haifa, zo mu koma gida ki yi mana abinci ko?" Da to ta amsa mashi tare da saƙalo neck ɗinsa da hannayenta dikka biyu. Shi kuma ya kai hannayensa dikka biyu saman waist ɗinta ya dagota sama sai saman chest ɗinsa, da haka ya nufi hanyar fita daga cikin gonar. "Hamma dan Allah ka saukeni zan tafi da kafafuna ka ji?". Ba musu ya sauketa tare da riƙo hannunta suka fice. Suna fita ta shammacesa ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata, da ɗan gudu ta yi gaba ta barosa a baya. Binta da kallo kawai ya yi, ita a dole tana jin kunyar jerawa da shi su nufi gida, dan tasan zasu yi ta haɗuwa da iyaye da dattawan kauyen, shiyasa ta gudu abinta. __________________________🤸 Tun daga nesa ta hango cincirindon yara a kusa da gidan nasu, kamar dai faɗa ake yi, sanin cewa Mahreen bata islamiya yasa ta yi saurin nufar wajen dan taga su wanene da kuma abin da yake faruwa suka taru haka a wajen. Ai tun daga ɗan nesa ta tsinkayo muryar Mahreen tana zazzage kwandon masifa. Haba ai a miliyan ta ƙarisa wajen dan tun da ta ji muryar Mahreen tasan faɗa ake yi. Aikuwa faɗa ake gwabza kamar ba gobe, Mahreen ta cire hijabin dake jikinta ta ɗaure shi a waist ɗinta, ta sha ɗamara kenan, kafafun nan nata sun yi futu futu da kuran ƙasa kamar wadda aka tono daga cikin rami, kayan jikinta a cukurkuɗe kamar wadda aka kwatota daga bakin kura, alamar andoku ne ba karya a wannan faɗa. Ga wasu ƴan'matan da basu kai Mahnoor ba su biyu a kewaye da ita, sai wata yar yarinya da ba zata wuce kamarta ba tsaye a kusa da ƴan'matan tana kuka hawaye sharɓa sharɓa ga baki a kumbure kamar an naushi rubaɓɓen alala. Suma waɗan nan ƴan'mata biyun sun ci uwar ɗamara kamar zasu tafi yakin duniya na uku, dik kayan jikinsu a cukurkuɗe, da alama da su fa ake gwabza wannan dambe. Oh Allah mai iko, Mahreen gidan dirama, Mahreen duniya mai zaman kanta, Mahreen gidan rina idan ka taɓo ta sai ka sha arbi, kabewan kan kabari take bakincikin mai taushe, dik kafiyarka nan zaka ganta ka barta, yanzu banda neman bala'i fisabilillahi ina Mahreen ina faɗa da ƴan'mata har biyu? Ku gane mun hanya, da alamu kuma wlh ta jibgesu dukkansu biyu, dan sun ci wahala sai nishi sama sama suke yi suna haki, ita kuwa da Allah yasa ba kiba gareta ba sakayau take jin jikinta tamkar ta kwasa a juye ta tashi sama, su kuwa ba laifi suna da garin jiki. A ruɗe Mahnoor ta ambaci sunanta tana zaro idanun, jikinta har kerma yake yi na ganin ƴan'mata biyu sun kewaye mata kanwa, fatan ta kawai kada a dakar mata ƴar uwa, shi ne hankalinta ya tashi. Tamkar Mahreen bata san da ita a wajen ba, ta cigaba da girgiza kugu tana wani bin ƴan'matan da kallon uku goma, da yake dikka yara ne a wajen sai suke ihun. "Dik wanda ta fasa Allah ya tsine mata". Mahreen kuwa da dama shi ne best abin da ta fi iyawa a rayuwarta wato faɗa, sai ta ji tsumin jikinta ya kara tashi da aka ce dik wanda ta fasa Allah ya tsine mata, dan haka nan take ta yi salle ta dire tare da buka kafarta a kasa, sannan cikin tsiwa ta ce. "Idan ba tsoro ba yarinya ta matso taga yadda zan gurji bakin shegiya". Ni kuwa princess Teema nace ko wace ƙaddara ya haɗa waɗan nan ƴanmata da Mahreen? Ai kowa wace ƙaddara ce yau zasu gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah ne tun da suka faɗo hannun Mahreen, sai ta Allah kuma. Dik cikin ƴan'matan babu wadda ta yi gigin matso Mahreen, da alama sun jibgu iya jibguwa ne yasa suke shakkarta a yanzu, kada su gudu ne dai a ishesu a kauyen da sunan sun ji tsoro, da wlh babu abin da zai hanasu cikawa zannuwansu iska, dan Mahreen ta basu tsoro, kamar wata mai karfin aljanu ta hau jibgarsu, kun san meyasa Mahreen take cin galaba a faɗa ne? To bari na baku sirrinta, saboda bata da kiba ne, da zarar sun fara faɗa da mutun zata daka tsalle kamar biranya ta haye saman shoulders ɗin mutun ta hau jibgarsa kamar me, wannan rashin kibar tata da iya daka tsalle yasa take more abokan faɗar tata............😂 Ganin babu wadda ta yi gigin matsota yasa ta sake buga kasa da ƴan kafafunta ta ce. "Sun ji tsoro a basu kunun maɗaci su sha su yi wanke wanke, kuma na faɗa ƴaƴan Boɗejo bugaza kawai, in kun isa ku zo kuga ikon mai sama, wlh in murje yarinya a cikin kasa". Yadda take masifar wlh sai ta baku dariya, dan tana yi dikan ilahirin jikinta yana motsawa, hannu na yi kafa nayi, ido da hanci dik suna yi. Hasbunallahu wani'imal wakil, ko wacece Boɗejo bogaza kuma? Kai Mahreen duniya, ƴaƴanta sun ja mata zagi koma wacece. Ma'anar bogaza dai irin mata masu kama da Hajiya two seater nan ne, wato masu kiba sosai kenan, shiyasa ƴaƴan nata suke da garin jiki suma, Mahreen akwai iya shege, wato bogaza take ce mamar yaran. A ruɗe baiwar Allah Mahnoor ta sake cewa. "Ki yi wa Allah Mahreen ki rabuwa da faɗar nan ki zo mu tafi gida". Ai ina ko kallon in da Mahnoor ɗin take bata yi ba bare ta tankata, cigaba da zazzaga masifa ta yi ba kama hannun yaro, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, har da datse idanu ta yi yanzu kam, so take ta zugo yaran su matso ta kara jibgarsu kafin ta tafi gida. Ita da ta kama yar mutane ta daka yayyunta sun biyo jin ba'asin me kanwarsu ta yi mata ta daketa sai ta haɗe da yayyun dik tana surfa masu surfen da nikar balainta, kuma fa wlh suna da manyan yayyun da tsab ɗaya daga cikinsu zata iya yi mata dukan mutuwa, amma da yake tana da baki kuma bata da tsoro sai bata wani damu ba. Abin da ya faru shi ne ta baro wajen bappa zata je gida kenan a daidai wajen ta haɗu da wannan karamar yarinya dake tsaye kusa da ƴanmatan nan mai suna Bintu tana wucewa. Ke Bintu da neman bala'i kin san halin Mahreen sarai ba wai baki sani ba sai tsautsayi ya ɗebeta ta ce. "Ke Mahreen ƴar gidan Nenne mai siririn kafa ina zaki je?". Aikuwa Mahreen bata bari maganar ya faɗi ƙasa ba ta amsa mata da. "Allah sarki Bintu ƴar gidan Boɗejo bogaza wajen ubanki malam Sani mai katon kafa zan je". Nan fa Bintu ta ji zafin Mahreen ta zagar mata iyaye, shi ne ranta ya ɓaci, cikin fushi ta ce. "Iyayena fa ba abin wasanki bane Mahreen, banaso kada ki sake cewa mamana bogaza ko ki cewa babana mai katon kafa!". Tana cigaba da tafiyarta bata ma tsaya ba ta ce. "Kai ashe iyayenki ne? Ai ni dik ɗaukata daga sama suka faɗo". Cike da shakiyanci da iyashege ta yi maganar. Hegiya Mahreen akwai mannin hauka yarinyar wlh, dik wani salo na faɗa da bakar magana ta iyasa, in faɗar cacan baki ne tsab zata yi nasara, haka zalika idan na duka da hannu ne ma, bata taɓa bari a taɓa lafiyar jikinta, idan kuna neman abin da zai ɗaga hankalin Mahreen to ku kawo mata batun taɓa lafiyar jikinta, ta tsani wannan kamar yadda ta tsani mutuwarta, amma ita kuma zata jibji ƴaƴan mutane fa. "Mahreen wasa wasa ban da dungurar uwar miji da taɓarya, na gaya maki kada ki sake saka iyayena a cikin maganarmu". Bintu da karfin hali take, ita fa ta fara cewa Mahreen ƴar Nenne mai siririn kafa, amma take cewa kada a sako iyayenta a magana yau ga ikon god. Dakatawa da tafiya Mahreen ta yi, sai da ta watsa mata kallon uku goma da waɗan nan idanun nata irin na bappanta sannan ta ce. "Wa ma kike da suna? Boɗejo bogaza kike ko Bintu? To na faɗa malam Sani mai katon kafa, in kin isa ki kira wanda zai likeni ya mayar da ni ta bakin allura". Cikin fusata Bintu ta amsa da. "Ni ma na faɗa Nenne mai siririn kafa kamar burugalin burga fura da nono........." Aikuwa bata dire zancenta ba Mahreen ta yi kukan kura ta yi kanta, shi ne fa farkon fadar. Ta gurji bakin Bintu har sai da ta kumbura, ta lillisa ƴar mutane, sannan ta samu waje ta zauna wai Bintu ta je ta kirawo dik uban da zai tare mata faɗa tana nan tana jiran koma waye ne, ai uwa bata fi uwa ba. Shi ne Bintu ta je ta kirawo yayyunta mata biyun nan, suma da suka zo tsabar dikka yarinta ce a kansu a maimakon su ce sun zo ramawa Bintu dukan da ta yi mata, sai suka ce idan Mahreen ta isa ta sake zagin iyayensu ta ga ikon Allah, sai sun canza mata kama da duka. Aikuwa ta tashi tsaye, sai da ma ta karkarɗe kuran kasan da ya hau zaninta wajen dukan Bintu, sannan ta ce. "Nafaɗa Boɗejo bogaza da kuma malam Sani mai katon kafa, duk uban da zaku yi bismillah ku yi". Tana magana tana binsu da kallon uku goma. Kai Innalillahi, wai malam Sani mai katon kafa, bama mai katon kai ba mai katon kafa, wlh Mahreeh duniya ce yarinyar nan, dik ta sakawa iyayen Bintu suna cikin ƙanƙanin lokaci. Ran waɗan nan ƴanmata ne ya ɓaci suka kamata da faɗa, aikuwa Allah ya bata sa'a ta samu tsokar mazaunansu ta rinƙa daga masu naushi a wajen tana haɗawa da yagushi a fuskarsu, kafin su kai mata duka ɗaya ta kai masu biyar, duk ta lallasa masu mazaunai suka yi jajir saboda suna da hasken fata, ta ya gushe masu fuska har sai da na ɗayar ya yi jini. Dik da haka fa bai isheta ba sai da ta ja gyalen jikin ɗayar ta daure mata wuya ta jata da karfi ta baya sai ga ƴar mutane tim a ƙasa ta faɗi gwanin ban dariya gwanin ban tausayi, da ta faɗi ma bata barta ba sai da ta ɗebo yashin kasan wajen ta danna mata a baki, ga shi kuwa ta yi sa'a yarinyar ta wage baki tana ihun faɗuwar da ta yi wajen ya yi mata zafi, aikuwa babu tsoron Allah Mahreen ta tiɗɗa mata kasa a baki ta sanya ta yin shirun dole. Ita kuwa ɗayar Allah ya bata saa ta kayar da Mahreen a ƙasa, tana jin daɗin ta yi galaba aikuwa bata ankara ba sai jinta ta yi ita ce a kasar, dan Mahreen ta janyo kafarta ta zube wanwar. Da sauri Mahreen ta haye kan ruwan cikinta tare da sanya gyalen yarinyar ta rufe mata fuska ta hau kai mata naushi a kirjinta, ga shi yarinya ta fara kirgan dangi, dik ta lallasa mata ƴan abubuwan, sai ihun azaba take yi hakan ya janyo hankalin sauran yara masu wucewa a kansu. Shi ne fa suka taru haka kuke ganin nan, babu wadda ta yi gigin rabasu faɗar, dan sun san in suka rabasu wlh kansu Mahreen zata koma da faɗar, dan haka sai suka zama ƴan kallo suna kara zuga al'amari ta hanyar wake wakensu na kauye. Kun ji daga in da faɗar ta samo asali, to yanzu mu koma kan labari. Babu irin maganar da Mahnoor bata yi ba a kan Mahreen ta rabu da su ta zo su tafi, aikuwa ta ki fir, ta ce yau sai waɗan nan ƴan'mata sun gudu da kafafunsu, in ba haka ba ita kuma yanzu tayi karin kumallon wannan faɗa, bata ga mai dakatar da ita ba. Tana tsaka da zazzaga wannan masifa kamar daga sama ta bayanta ta ji an ɗauketa cak, ko bata juyo ta ganshi ba tasan Hammanta ne, dan shi ne kaɗai mai iya ɗauketa a waje idan tana faɗa. Kuka ta saka mashi tana faɗin. "Dan Allah Hamma ka saukeni na karisa aikin da na fara". Sam bai kulata ba ya miƙawa Mahnoor hannu a kan ya kama su wuce gida. Da sauri ta wuce gaba ba tare da ta riƙo hannun nasa ba. Su kuwa ƴan'matan ganin Jaish ya ɗauketa ne yasa suka fara faɗin. "Ki dawo mana ki ga yadda zamu yi fata fata da bakinki". Kun gane irin cika bakin nan ai? Haka suka fara yi. Habawa tamkar Mahreen zata yi hauka ta fara ƙoƙarin kwatar kanta daga hannun Jaish dan ta diro ƙasa ta je ta karisa rugurguza masu baki, amma ina ta kasa iya kwatar kanta. A kule ta ce. "Wlh sai dai idan ba zan sake gamuwa da yarinya ba, Allah tun yanzu ku fara gina hanyar da zaku rinƙa bi dan kada ku haɗu da ni, in ba haka ba dik sai ba kunbura maku laɓɓa ku rasa na cin abinci. Shi kansa Jaish Mahreen tana goge mashi hadda wajen zaƙewa a faɗa bare ni kuma princess Teema, ai sai shiru kawai. Bai direta a ko'ina ba sai a tsakar gida. Yana sauketa ta yunkura zata yi waje da gudu ya daka mata tsawa a kan ta dawo kokuma yau ya zaneta. Dan dole ta dawo tana kumbure kumburen kumatu ita a dole ya ɓata mata rai, ɗakin bappa ta shige ta haye gado ta fara murzan kuka. Bai kulata ba ya ce Mahnoor ta ɗaura masu abinci yana cikin ɗaki. Da to ta masa. Ya nufi cikin ɗaki ita kuma ta nufi kitchen, Nenne kuma bata nan, ta tafi gidansu Mairo matar da bappa zai aura ta yi masu ɗibar albarka da tijara..... Bari dai mu waiwaya kingdom of power mu je mu dawo mu ga kalar ɗebar albarkar da Nenne zata yi wa su Mairo. ______________😥🌹_____________ Yau ta kama Friday, tun safe ake ta shirye shiryen bikin nan, komai ya kankama, masarauta ta ci tab da manya manyan baki, da kyar Rizwan ya yarda ya yi shiri ango cikin tsadaddiyar three-piece suit ɗinsa mai bala'in kyau da tsada, nan ma sai da su Ramish suka takura mashi da magana sannan ya shirya. Amare sun sha tsantsarerren lalle, gasu da hasken fata da aka yi masu maroon ɗin flowers ɗin ba ƙaramin haskawa suka yi ba. Chuchu dama ta sha gyara su dilka da halawa, ga Auntynsu Jawad ta ƙara gyarata da nasu kayan gyaran, dama ita skin ɗinta very smooth yake, hakan yasa wani irin sihirtatcen kyanta ya kara bayyana, kamar ka saceta ka gudu, jikinta sai glowing yake yi tana wani shining. Ita ma Aneesa ba laifi, dik da jiya aka fara yi mata gyaran ta yi kyau sosai. Jawad ya farfaɗo daga barcin, sai dai ko uppan baya iya furtawa sai dai bin mutane da ido kawai, King ya ce ba sai sun sanar mashi za'a ɗaura aurensa da Aneesa ba, tun da bashi da lafiya su kyalesa har bayan biki idan ya warware sai ayi mashi bayani. A katafaren masallacin King dake cikin kingdom ɗin za'a ɗaura auren, hakan yasa dik wasu bakin da zasu halarci ɗaurin auren suka yi cincirindon isa wajen, ko'ina a cikin masallacin nan ka juya jama'ar annabi ne, dan ma masallacin yana da girman gaske ne, da jama'ar da suka halarta ba zasu samu isasshen waje ba. A gaskiya babu karya King Zuhair yana ɗinbin tarin masoya, dan kuwa sun yi mashi kara, sun cika masallaci, manya manyan suwagabannin ƙasashe da dama sun zo, manya manyan sarakuna da ahalinsu dik sun zo, jiga jigan ƙusoshin gwamnati dik sun zo, biki ya yi biki. A tare suka gabatar da sallar jumma'a, ana idarwa liman ya gabatar da batun ɗaurin aurarrakin da za'ayi. Gabaɗaya Rizwan hankalinsa baya'a jikinsa har liman ya gabatar da ɗaurin auren kamar yadda yake a shari'ance. Nan jama'a suka shaida, wajen uncle Abbas aka karɓi auren, King ne kuma ya karɓa, sannan King ɗin shi ya biya sadaki da wani dallelen gold mai bala'in tsadar gaske, uncle Abbas shi ya karɓa. Rizwan ya yi nisa cikin tunanin ɗan uwansa da yake yi sai ji ya yi ana ambatar sunansa, Dr Raj ne yake kiran sunan nasa yana gaya mashi aure ya ɗauru. Gabaɗayansu sun yi shiga iri ɗaya na three-piece suit masu bala'in tsada, sai dai Ramish bai halarci ɗaurin auren ba, ana idar da sallah ya bar masallacin izuwa wajen aunty miemie, dan baya son tsayawa a wajen taron. Kan kace me murna ya karaɗe ko'ina a cikin masarautar, bawan Allah har aka gama dik abin da ake yi bai sani na yana can duniyar tunani, sai da ya ji uncle Abbas yana kiransa a kan ya tashi su yi hotuna ne hankalinsa ya dawo jikinsa. A razane ya miƙe tsaye yana faɗin........... P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 51 A razane ya miƙe tsaye yana faɗin. "Ina Ramish?". Dafa shoulders ɗinsa uncle Abbas ya yi, cike da tausayin yaran nasa ya ce. "Rizwan ka nutsu mana, ga manyan baki can suna son yin hotuna da ku, ka zo kuɗauki hoton". Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya furta uppan ba, ya wuce gaba Dr Raj ya rufa mashi baya suka ƙarisa wajen jama'a, King ta ko'ina jama'a ne suka kewayesa, kowa hoto yake son yi da shi, dik sun saka bawan Allah busy. ____________________________ A can cikin gida kuwa, Ramish ne kwance a saman doguwar dake parlourn ƙasa na Aunty MieMie, call ɗin Sharifat ce ta shigo cikin wayarsa, bin screen ɗin da kallo ya yi. Har call ɗin ya katse bai ɗaga ba. Sallama Aunty MieMie ta yi a cikin parlour. Hankalinsa na'a kan wayarsa so bai samu damar amsawa ba, hannunta ɗauke da tray mai shake da kayan cima kala kala, sam bata bawa ƴan aiki daman su kawo mashi abinci ba, dan ta san shi da murɗaɗɗen hali, ga shegen kyankyani, shiyasa ta kawo mashi da kanta kada ƴan aiki su kawo ya ce ba zai ci ba. A saman center table ta ajiye mashi tare da matso mashi da table ɗin gabansa. "Big Bro ka dai ki halartan ɗaurin auren nan ko?". Ta faɗa tana ɗan komawa baya Daga bakin kofar shigowa parlourn Bilal da ya shigo a yanzu ne ya amsa da. "Hayaniyar mutane ne bama so yasa bamu je ba, ai ba laifinmu bane". Ya kai karshen maganar tare da shigowa ciki. Hararar wasa ta watsa mashi kafin ta koma saman sofa ta zaune. "Kai Yah Bilal wato badan big bro yana part ɗin nan ba da ba zan ganka ba ko?". Saman sofar kusa da Ramish ya zauna, dik suna cikin shiga iri guda, sai suka haɗe kamar wasu twin's. "Kai Big Aunty, ni ban san da Yah Ramish yana nan ba, kawai zuwa na na yi dan na dubaki fa". Ta wutsiyar idanu Ramish ya kallesa, dan yasan karya yake yi, ya duba shi ne ta location ɗin wayoyinsu yasan yana part ɗinta shi ne ya biyosa, amma yanzu zai wani waske wai ita ya zo gani. "Amma Aunty MieMie me yake damunki na ga fuskarki a haka kamar kina da damuwa?". Cewar Bilal again. Ajiyar zuciya Ramish ya sauke, domin kamar Bilal ya shiga cikin zuciyarsa yaga tambayar da yake shirin yi mata kenan. Fuskarta ne ya sauya izuwa ta damuwa sosai, cike da rashin jin daɗin abin da ya faru ta ce. "Nayi kuskure ne Bilal". "Kuskure kuma?". Ya tambaya yana kai hannu ya ɗauki cup dake cikin tray ɗin da ta kawowa Ramish. Bottle watar ya ɗauko tare da ɓalle bakinta, ruwa ya zuba a cup ɗin, cikin nutsuwa ya kai bakinsa. Jinjina mashi kai ta yi alamar kwarai kuwa kuskure. Shanye ruwan tas ya yi tare da mayar da cup ɗin ya ajiye, sannan ya ce. "Kuskuren me kenan?". Ramish da yake kwance ne ya miƙe zaune yana binta da kallo, dan kuwa abin da zai saka Aunty MieMie a damuwa ba karamin abu bane, in baku manta ba jajirtatciyar jaruma ce, so sai suka zuba mata idanu suna sauraron su ji me ya ɗaga hankalin jarumar tasu. "Na yi kuskure na ja dad ya haɗa Aneesa da Jawad aure yanzu haka rikicin dake faruwa a cikin gida ya hanani zuwa cikin, dik ƴan uwana da su momma suna nan, mutanen Dubai dik suna nan, amma ni na kasa zuwa". "Meyasa to?". Bilal ya sake tambaya. "Aneesa ta sanar da mama cewa ni nasa dad ya yi mata aure da Jawad, ita bata son shi, yanzu haka mama ta ɗaga hankalin kowa a cikin gida a kan ita ba zata yarda ba dole a warware wannan aure, bata ga wanda ya isa ya yi wa yarta auren dole ba, sai zagin mummy take yi wai ni muguwa ce meyasa ba zan sa a bawa Jawad Chuchu ba sai Aneesa? Wai dan ba uwa ɗaya muke da Aneesa ba shiyasa zan cutar da ita, meyasa ban yi wa Chuchun da muke uwa ɗaya uba ɗaya irin haka ba? Dik hankalin kowa a tashe a cikin gida, shiyasa na yi zamana a nan kawai". Ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka, dan ita sam bata son wannan faɗa da iyayen nasu suke yi, kuma dik matsalar mamansu Ramish ce, ita ce bata da hakuri kuma bata da kawaici, ga shi yaran suna son junansu, kunga Bilal da Ramish kamar twin's suke, yanzu bayan waye zasu bi kenan? Ai kunga wannan faɗa sai dai su koma gefe su yi shiru kawai, dan basu da ta cewa, dik wanda ya ji zafin an zagi mahaifiyarsa sai dai ya sha Maltina mai sanyi dan zuciya ta sanyaya ya kawar da kai kamar bai gani ba kawai. Shiru dikkansu suka yi, shi Ramish ma sunkuyar da kansa ƙasa ya yi, dan yasan mamarsa ce mai wannan matsala dikka, shi kuwa Bilal da ya ji mama tana can tana kwashewa mummynsa albarka dan Aunty MieMie ta yi laifi sai aka sauke a kan uwarsu sai ya ji ransa ta sosu, amma sai ya danne ya ce. "To amma kema Aunty MieMie meyasa zaki ce dad ya bawa Jawad auren Aneesa? Baki yi shawara da ita ko tana da wanda take so ba kawai ki yanke mata hukunci". Yana magana yana satar kallon Ramish da ya yi ƙasa da kai ya rasa ta cewa. "Bilal ba laifina bane wlh, bani na ce dad ya bawa Jawad Aneesa ba, ni Jannat ma naje rokan a basa ba Aneesa ba, abin ne ya juye mun ta yadda ban zata ba". Cike da damuwa sosai ta yi maganar, ga damuwar an bawa kanwarta wadda bata so, ga damuwar Aneesa na kuka da ita, sannan ga bala'in da ake yi a cikin gida, mama bata duba bakin da suka zo ba ta nemi ta zubarwa da King mutunci a gabansu, ta kafe dole a raba wannan auren ita bata bayar ba, ƴarta wanda take so zata aura, kuma ita ƴarta ba zata yi auren gida ba, bare zata aura. A nan ne mummynsu Aunty MieMie ɗin ta ce. "Kenan baki son haɗa jini da Abbas ɗin ne?". Nan fa ta fara sabon sababi a kan mummy na binta da sharri, Momma dai da bata son abin kunya sai ta wuce part ɗin King, dik da baki suna cike a part ɗin nasa dai tasan babu wanda zai shiga mashi uwarɗaki, dan haka sai ta wuce master room ɗinsa ta yi kwanciyar a saman bed ɗinsa ranta cike da damuwa, dan har ga Allah ranta ya sosu a kan yadda mama ta ke ƙoƙarin zubar masu da mutunci, sannan ta ji takaici yadda mamar ta nuna tana kyamar Jawad ya auri Aneesa, bata son haɗa jini da shi, ko me dalilinta?. Dik fa wannan bidiri da ake yi a cikin gidan King or uncle Abbas basu da labari, bama su dawo daga wajen ɗaurin auren ba, suna can mama na bidirinta a nan............GIDAN SARAUTA KAGA ABUBUWA DAYAWA WLH, KOWANI RIKICI BA ZAKA RASA A CIKI BA, MUNAFURCI, MUGUNTA, CIN AMANA, ADALCI, RASHIN MUTUNCI, MUTUNCI, TIJARA, ƳAN ISKA, ƳAN ALBARKA, KAI KOMAI SAI KA GANI. __________________________ "Aunty MieMie ni fa ban gane ba, ki mun dallah dallah, da farko kin ce kin yi kuskure, yanzu kuma kin ce bake kika ce dad ya aurawa Jawad Aneesa ba, ban gane ba". Cewar Bilal da ta ruɗar da shi. Nan fa ta fara gaya mashi dallah dallah a kan ita ta je rokarwa Jawad Jannat ne sai dad ya ce ya bashi Aneesa. "Tab lallai kuwa, e a nan gaskiya ba'ayiwa mama adalci ba, kuma ita ma Aneesa ba'ayi mata adalci ba, ta ya za'ayi ba'a tambayi yarinya da mamarta ba kawai a yanke masu hukunci? Gaskiya ba'a kyauta masu ba, dole mama ta ji babu daɗi". Cewar Bilal. Sarai Ramish yasan saboda shi yasa Bilal yake ƙoƙarin kawar da cewa mamarsa ta yi laifi, amma shi kansa yasan ta yi abin da bai dace ba, domin kuwa ko da King bai kyauta mata ba ai tasan in da zata samesa ba sai ta tsaya tana zazzagawa mummy masifa a idanun baki ba, wannan ai rashin mutunci ne, amma saboda ganin idonsa ne suke ƙoƙari nuna mamarsa ta yi dai'dai. Shiru dai ya yi yana addu'ar Allah ya canza mashi halin mamar nan tasa, masifarta ya yi yawa. Shiru suka yi a parlourn, Aunty MieMie tana son gayawa Bilal irin zagin cin mutuncin da mama take yi wa mummynsu, amma kuma ta kasa yin hakan saboda Ramish dake wajen. Sun yi mashi kara suka danne. Kada ku manta da Aunty MieMie da Bilal and Chuchu sune yara Mummy. Ramish and Dr Raj sai Aneesa su ne Yaran mama. _____________🌹💘_____________ Sarina a hankali take lallaɓawa kamar wata ɓarauniya, daga gani bata kullo alkhairi ba, daga part ɗin mummy in da ake ta zuba uban dirama ta fito, sanye take da silk gown wanda ya bi shape ɗin jikinta, kunsan halinta da shegen son kaya mai fitar mata da dik wani surar jikinta. Ganin hankalin su mummy dik yana a kan diramar maman ne ya bata damar gudowa part ɗin momma ba wanda ya ganta. Can uwarɗakan momma ta shiga. Babu kowa a part ɗin dik suna part na mummyn Chuchu. Mama da neman bala'i har part ɗin mummyn ta je ta sameta, dama kuma kunsan a ƙaida idan irin wannan biki ya zo to baki sun fi sauka a part ɗin uwar gida, hakan yasa bakin suka fi yawaita a part ɗin mummyn, sannan kuma yarta ake aurarwa. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba a lokacin da taga babu kowa a cikin ɗakin Mommar, a hanzarce ta ƙarisa ciki har da rufo kofa, wlh Sarina bata da tsoro, ko me ya kawota room ɗin momma kuma? Anata hidimar biki ita tana can tana faman kulle kulle, ko me suke kullawa kuma?. Dik wasu drawers dake cikin ɗakin ta hau bubbuɗewa tana bincike a ciki, tana yi tana zaro idanu, zuciyarta sai bugawa yake yi da karfi karfi, har hannayenta na kerma alamar zallar rashin gaskiya. Sosai ta hau bincike cikin ɗakin, har da kasan gado ta leƙa, momma kuma tana part ɗin King, kuyanga mama Haulat tana cikin gida wajen masu girki ta can baya kenan, momma ta wakiltata ta jagorancesu. Dik wardrobe dake cikin dressing room sai da ta bubbuɗe kofofinsu, ba abin da bata buɗeba a cikin dressing room ɗin, ganin bata samu abin da take nema bane yasa ta dawo cikin room ɗin, jiki dik a mace ta juya ta nufi kofar fita, ranta dik a jagule alamar bata ji daɗin rashin nasararta ba. Har ta kai tsakiyar ɗakin sai kuma ta juyo da gudu ta dawo wajen mattress na bed, a hanzarce ta ɗaga mattress ɗin ta wajen pillows. Nan take wasu envelope har guda uku masu ɗan matsakaicin girma suka bayyana. Wani irin murmushi ta saki mai wuyar fassaruwa, jikinta har rawa yake yi wajen kai hannu ta kwashi envelope ɗin dikka. A hanzarce ta saki mattress ɗin ta ruga da gudu ta nufi waje, tsabar ta kware a sanya high heel haka ta kwasa a guje da shi a kafafunta a saman wannan tiles mai uban smooth ɗin, kun san zai yi tsantsi ai, amma haka ta kwasa da gudu saboda buri ya cika, da alama aikota aka yi fa. Tana barin part ɗin kai tsaye part ɗinsu ta nufa, wato side ɗin uncle Abbas kenan, amma kafin ta bar part ɗin momma sai da ta tsaya ta ɗaga rigarta sama ta cuta envelope ɗin dikka a cikinta, ta ɓoyesu, da yake tana da dogon wando a ciki, sai ta cusasu ta wajen waist ɗinta ta kuma sanya waist beads ɗinta a kansu dan kada a gani. Ita da murmushi bai dameta ba, bata yi sai na mugunta sai ga shi yau sai sakin uban murmushi take yi kamar baki ba zai rufu ba, da sauri ta shige cikin side ɗinsu har tana haki. ________________🌹💘_____________ Sai lokacin da aka ɗaura auren Chuchu ne Auta ta fahimci wayarta baya a tare da ita, dan haka sai ta fara nemansa, dan zasu yi hotuna, kowa ta fito da wayarta, ga su Jannat ƴaƴan uncle Rahab dik sun zo, kowa sai ɗaukar hotuna da ƴan uwa yake yi da wayarsa banda ita. Room ɗinta ta nufa domin ta nemi wayar tata, yau gabaɗaya haka take wata sukuku da ita, dan daren jiya jaruminta wato Hoorain ya bakanta mata, da abin ta kwana a ranta, shiyasa ko kwalliya ta gaza yi wa kanta sai da Aunty Ummi babban ƴar uncle Rahab ta yi mata, ba dan haka ba da yau ba zata yi kwalliya ba. Gabaɗaya ƴan'matan sun shirya cikin wasu irin haɗadɗun Turkish gown mai kama da wedding gown, kasa a buɗe sosai daga ta sama kuma ya ɗan kamasu zuwa waist ɗinsu. Sun yi kyau over, ga shi sun sha lalle, ba ƙaramin kyau suka yi ba, sai kamshi ne yake tashi ta ko'ina. Aunty MieMie ce ta kira masu masu gyaran gashin familyn nasu suka zo suka gyara masu wanan kyakkyawan Arabs hairn nasu. Binciken ɗakin nata ta fara yi tana neman wayar, sam ta manta jiya ta fita da shi. Da sauri ta aro wayar gimbiya Fanan ta fara gwada number tata. Wayar tana ta ringing ba'a ɗaga ba. Tana hannunsa kuma, yana kwance a saman bed ɗinsa yana ta ƙoƙarin gwada buɗe wasu folders ɗin da ta sanyawa password dan ya ga me ta ɓoye a ciki, akwai wajen hotuna ta rufe shi shi ma, sannan ta rufe Whatsapp ɗinta, ta kuma rufe wajen videos na wayar, to me take ɓoyewa?. Shi ne abin da ya dame shi yake son buɗewa. Ita kuwa idan hankalinta ya kai dubu to ya tashi na rashin ganin wayar nan tata, ta ruɗe kamar wata maras gaskiya ko wadda take da wani abin da bata son a gani cikin wayar, da sauri ta hau wargaza bed ɗinta, dik pillows ɗin ta yi watsi da su kasa. Sai da ta gama watsa ɗakin caf sai ta tuna ashe jiya bama a ɗakin ta kwana ba, sai a lokacin tunanin ta fita da wayar zuwa wajen Hoorain ai ya faɗo mata, kuma kamar bata dawo da shi ba. Tuna hakan yasa a hanzarce ta shigar da number Hoorain da ta haddace shi a kanta a cikin wayar Fanan, da sauri ta fara kira. Lokacin da call ɗin ta shigo ya ɗaga yaga sabuwar number ce sai ya mayar ya ajiye bai yi picking ba. Ganin bai ɗaga bane yasa ta hau rubuta sako dan ta tura mashi. Salam Zunaira ce ka ɗaga please, shi ne abin da ta rubuta ta numbersa ta tura mashi. Yana ganin sakon sai da ya miƙe zaune a tsakiyar gadon, wani irin daɗi ya ji a ransa ya samu hanyar da zai bata hakuri, da alama shi ma da tunaninta ya kwana, ya gaza samun sukuni. Yana ƙoƙarin fita daga sms ɗin sai ga kiran nata ya sake shigowa. Cikin nutsuwa ya yi picking tare da kara wayar a kunnensa. "Assalamu alaikum". Ya faɗa a sanyayye. Ta saba idan sun haɗu ta ɗaga mashi gaisuwa, yau kam sai ya ji bata ɗaga mashi gaisuwar ba, da alama dai da gaske fushi take yi da shi, sai ya ji abin ya kara taɓa zuciyarsa. "Hoorain dan Allah wayata tana hannunka ne? Ka ganta?". Shi ne abin da ta ce mashi kawai. Bawan Allah bai iya bada hakuri ba, sai ya rasa ta ina zai fara, hakan yasa ya yi shiru yana tunanin meyakamata ya faɗa. "Hoorain baka ji nane?". Ta sake faɗa tana ɗan ɗaure fuska. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yi kasa da murya sosai, a hankali ya ce. "Am so so sorryyyyyyy ranki ya daɗe, ina tuba kuma ina fatan zaki mun afuwa". "Tuba a kan me kuma Hoorain?". Ta jefa mashi tambaya. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Idan ba zaki damu ba zamu iya haɗuwa yanzu?". To fa yau da kansa yake neman su haɗu?. "Meyafaru kake neman mu haɗu? Ko dai yanzu kam ka san wacece Zunaira ɗin ne?". Ɗan dafe forehead ɗinsa ya yi, wato dai bata manta ba, lallai yanzu ya tabbatar da maganar ta yi mata zafi ashe. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe kuskure aka samu, amma tuba nike". Allah sarki soyayya, zuciya bata da ƙashi, ai bata san lokacin da murmushi ya kubce mata ba, amma da yake ta yi degree a sanin ilimin soyayya sai ta danne ta ce. "Ni kam ka dai'na bani hakuri dan baka yi mun laifin komai ba, wayata tana hannunka ne in turo a karɓa mun?". "E wayar tana hannuna, amma dan Allah kada ki turo kowa, ki zo da kanki kin ji? Magana nike son yi dake please, ba dan ni ba, saboda nasan ni ban kai na kiraki ki zo ba".. Sosai ta ji daɗin da yau shi ya nemi da su haɗu, bayan tsawon lokaci da ita take zuwa dan ta gansa, abin ya yi mata daɗi, sam bata duba matsayinta da girmanta ba, ita dai tun da zuciyarta na son shi ai shikenan kuma. "Ni gaskiya Hoorain ba zan iya zuwa ko'ina a yanzu ba, bani da lokaci, zan turo a karɓa mun wayar kawai ka gaya mun in da kake". Wai ita ma zata ja ajin nan, har da wani dake murya irin ya san da gaske take yi. Bai ji daɗin hakan ba, ya so su haɗu da ita ne, amma ba yadda zai yi, sai ya ce. "Tom shikenan ranki ya daɗe, ina ɗaki amma zan fito wajen garden ɗin da muke zama ta zo wajen ta karɓa maki wayar". "Tom gata nan zuwa". Ta kai karshen maganar tare da ciro wayar daga kunnenta tana ƙoƙarin katse call ɗin tana sakin murmushi dan ta ji daɗi, dama tun safe take kewarsa sosai, yanzu ta ji voice ɗinsa zuciya ta sanyaya. Sai dai kuma burgagin banza ne take yi na nuna cewa tana son katse kiran, amma har ga Allah ba call ɗin take son katsewa ba, bataki su yi ta wayar daga nan har gobe da safe ba, amma nauyin jansa da hira take ji yasa ta yi kamar zata katse. "Dan Allah kada ki katse kiran ranki ya daɗe". Shi ne abin da ta ji ya sake faɗa. Ai bata san lokacin da ta saki wani irin cool murmushi haɗe da sanyayyar ajiyar zuciya ba, abin da take so me dama. Wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta, fasa katsewan ta yi tare da mayar da ita kunnenta. "To me kake so kuma? Ko da sauran wani magana ne?". Ta jefa mashi tambayar tana murmushi, irin kada ya gane ta damu ɗin nan ne yasa ta yi mashi wannan tambaya. Girgiza kai ya yi kamar yana a gabanta, bai san lokacin da ya ce. "Kawai ban gaji da jin voice ɗinki bane, yau nayi kewarki sosai, na kuma shiga damuwa a kan hakan sosai, meyasa zaki yi fushi dani? Kin san cewa ba zan iya juran fushinki ba? Kin san cewa jiya kwana na yi ban rintsa ba? Dan Allah ki yi hakuri, yanayi ce tasa nike cewa ban sanki ba bawai da gaske bane, bana son su gayawa Abbona wani maganar ne yasa nike faɗan dik abin da na faɗa, amma in har baki son hakan ba zan ƙara ba". Tun da ya fara magana ta samu wajen bakin bed ɗinta da ta gama watsawa ta zauna tana sakin murmushi. Yana kai karshen maganar ta sauke wani irin daddaɗar ajiyar zuciya wanda har cikin ransa ya ji hakan, shi kansa bai san lokacin da ya sauke nasa ajiyar zuciyar ba. "Okey na yarda da dik abin da ka faɗa, kuma zan hakura, amma yanzu ka gaya mun ka san wacece Zunaira?". A hanzarce ya ce mata. "Sosai ma na santa". "Wacece ita to?". Ta sake jefa mashi tambaya. Shiru ya yi yana tunanin wacece zai ce to? muryarta ce ta katse shi da cewa. "Zan hakura amma har sai ka gaya mun wacece Zunaira a zuciyarka? Sannan ya ka ɗauketa?". Ɗan shafa kansa ya yi yana mamakin wayo irin nata, wato so take ta ji sirrin zuciyarsa kenan, wai ita ma ta yi girman da zata yi mashi wayo, ita da ko soyayyar da take yi mashi ta kasa iya ɓoyewa kada a gane ne take son yi mashi wayo, shi da tsawon shekaru goma kenan yanzu sonta yana ɗawainiya da shi amma ba wanda ya iya gane hakan har sai yanzu da ta fara girma ta kai 13 years, kyanta yana ta kara bayyana abin ya matsawa zuciyarsa ne yasa su Ansar suka iya ɗagosa, amma a haka wai zata yi mashi wayo. Amma jin yadda ta yi mashi tambayar dik da baya ganinta ya iya gane cewa tana cikin farinciki sosai, dan haka ba zai iya karyar mata da zuciya ya gaya mata akasin abin dake cikin zuciyarsa ba, amma kuma yana tunanin me amsar shi zata haifar? Baya son tashin hankalin Abbonsa. "Sai ka yi tunanin wacece Zunaira a gareka kafin ka gaya mun ko? Tsabar Zunaira bata da amfani a wajenka ko?". Siririn muryarta ce ta katse mashi tunanin da yake yi da faɗin hakan. Ta faɗa kamar zata yi mashi kuka. Da sauri ya fara girgiza kai yana faɗin. "A'a ranki ya daɗe, tsabar girman Zunaira a cikin zuciyata yasa nike tunanin ta ina zan fara bayyanata, girmanta ya wuci tunanin dik mai tunani, amma in ba damuwa zan fi so mu haɗu sai na bayyana maki ya take ko?". Wayyo soyayya, wani irin daɗin da bata taɓa jin irinsa bane ta ji ya ziyarceta, cikin sanyin murya ta ce. "Da gaske Hoorain ina da girma da kima a cikin zuciyarka?". Kai ya jinjina haɗe da faɗin. "Sosai kuma, fiye da tunaninki, baki ma ya yi kaɗan ya zayyana girmanki, sai dai kawai na faɗi iya abin da zan iya faɗa na bar sauran". Bata san lokacin da idanunta suka ciko da kwallah ba, miƙewa tsaye ta yi, a hanzarce ta fara ƙoƙarin danne hawayen firincikin nata, ƙasa ƙasa ta ce. "Hoorain mu haɗu a bayan side ɗin uncle Abbas, na tabbata babu mutane a wajen kuma babu wanda zai ganmu ko yasan muna tare a wajen". Cike da farincikin hakan ya amsa da to, sannan ya miƙe da sauri ya sauko ƙasa daga saman gadon. Hular kayan yakinsa ya ɗauka ya sanya tare da ɗaukar wayarta. Ita kuma ta katse kiran ta nufi waje da sauri, yau ranta fes Hoorain ya ce tana da girma da kima a idanunsa, wannan ma bai bayyana mata cewa yana sonta ba, idan ta ji haka ya kenan?. Kai tsaye bayan side na uncle Abbas ta nufa, dik wanda ya ga face ɗinta sai ya tabbatar da yau tana cikin farinciki na musamman, ta baro su mama suna ta kai ruwa rana a kan dole fa sai mummy ta yarda cewa ƴarta MieMie azzaluma ce kuma ba tsakani da Allah take son su Aneesa ba, tana nuna banbanci, ita kuma mummy dik hakurinta yau sai da ta yi faɗa, ta ce wlh MieMie ba muguwa bace, ku kun san mama fa tsabar masifa ce ta yi mata yawa da shegen son rashin zaman lafiya, amma Aunty MieMie ba munafuka bace. ________________________________ Ta rigasa ƙarisawa wajen, dan haka tana zuwa sai ta tsaya tare da harɗe hannayenta a saman kirjinta tana jiran isowarsa, dik ta zaƙu da ya iso suga juna a cikin ido. Ga wajen babu kowa, very clear, silent and ventilation, ba wanda yake zuwa ta wajen ma, dan ba zaka taɓa tunanin akwai wajen tsayawa a yi hira a nan ba. Cike da jarumta yake takowa ya nufo wajen, tun daga nesa ta hangosa yana nufota, wani irin sanyi take ji yana ta kara ratsa mata zuciya, sai ta ji kamar ta ruga ta je ta rungumesa su ƙariso a tare. Amma sai ta danne ta zuba mashi ido yana tahowa. A gabanta ya kariso ya tsaya, cikin girmamawa ya ce. "Sannunki da isowa ranki ya daɗe". Fuska a ɗauke da ƙayatattcen murmushi ta amsa da. "Yauwa kai ma sannunka da zuwa". Jinjina kai ya yi yana ta kallonta kamar zai cinyeta da ido. Cike da zaƙuwa ta katse masu shirun da suka yi da cewa. "Faɗa mun ya ka ɗauki Zunaira a cikin zuciyarka". Nisawa ya yi, haƙiƙa ya ga zaƙuwa da son jin amsarsa a cikin idanunta, murmushi da take saki yasa ya ji wani abin a ransa tamkar ya fasa abin da ya yi niya, ya ji tausayin innocent face ɗinta kaɗan, yarinya yar baruwanta mai farar zuciya. A hankali ya tako two step ya matso kusa dab da ita sosai kamar zai rungumuta, har sai da abin ya ɗan bata mamaki. Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Yadda na ɗauki Zunaira a cikin zuciyata shi ne in ɗauki fansa a kanta, in kuma kasheta har lahira!!,". Tashin hankali!!. Yana kai karshen maganar ya sa hannu ya janyota jikinsa tare da rufe mata bakinta da hannunsa ɗaya, tana ƙoƙarin ce mashi bata gane bane ya janyo waist ɗinta ta faɗa jikin nasa, zaro idanu ta yi ba halin ta yi magana dan ya rufe mata baki, ƙoƙarin kwatar kanta ta fara yi dan ta tsorata, amma ina ta kasa. Matsawa da iya ya yi a in da ya mannata da jikin last wall na uncle Abbas, ya matse mata baki sosai ya haɗeta da bangon da karfi, sannan ya zaro wani ɗan madaidaicin wuƙa daga waist ɗinsa, babu tausayi babu imani ya caka mata a cikinta, ya kuma kara mannata da bangon da karfi dan ya ji daɗi wukar ta shiga cikinta sosai, ya toshe mata baki da kyau ta yadda wane ita ta iya fitar da komai kanƙantar sauti daga bakinta. Zaro idanu ta yi tana kallonsa har cikin ido, while shi ma kallonta yake yi har cikin ido babu ko kyaftawa. Nan take idanunta suka rikiɗe suka yi jajir kamar jini, wasu irin hawaye masu zafi kamar wuta ne suka fara bin ƙuncinta, dik jikinta ɓari yake yi, da alama ba ƙaramar azaba take ji ba, dan daga yanayin hawayen dake fita daga idanunta sai ya ɗaga hankalin mutun. Babu ko ɗigon tausayi a idanunsa, yana kallon cikin idonta yasa hannun ya kara murza wukar a cikinta da kyau ta yadda zata kara shan azaba kafin rai ya yi halinsa. Kamar yadda yake murza wukar a cikinta haka yake kara matse mata baki haɗe da matseta a bangon............Tashin hankali, innalilahi wa inna ilahir rajiun. For what reason Hoorain zai kashe Auta? Meta yi mashi? Fansar wa zai ɗauka a kanta? Laifin me ta yi mashi da har zai ɗauki fansa?. Ko tausayinta bai ji ba ya cigaba da matseta tun tana iya fitar da numfashi kaɗan kaɗan har sautin numfashin ya daina fita daga kofofin hancinta, idanunta dake tsaye cikin nasa ne suka fara rufewa a hankali hankali har suka rufe gabaɗaya, nan take jikinta dikka ya saki alamar rai ya yi halinsa, innalilahi wa inna ilahir rajiun. Ganin ta mutu da gaske ne yasa ya saki bakin nata tare da sanya hannu ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa, jini ne yake zuba daga jikinta tamkar ruwa ya faso hanya, ga kayan jikinta white color ne hakan ya yi sanadiyar bayyanar jinin sosai. Wani ɗan siririn hanya dake ta wajen ya bi da ita, da yake in baku manta ba na gaya maku yasan dik wata hanyar sirri dake cikin masarautar, hakan yasa ya fita da ita ta kofar da babu wanda ya gansa. Dik in da ya wuce jininta ne yake ta zuba, hanyar da ya bi ya fita kuma babu wanda yake zuwa ta wajen, ba zama ka taɓa zaton da akwai kofa a can ba, Allah sarki King yana can yana fama da jama'a an kashe mashi bugun zuciyarsa a nan bai sani ba. Amma batu na gaskiya Hoorain ya cuci Auta, ina da tabbacin da tana raye sai ta yi fatan da wani ne ya kasheta ba shi ba sai ya fi mata daɗi, na tabbata ba zata ji zafin wukar da ya caka mata har ta mutun nan ba kamar yadda zata ji zafin kasancewar shi ya yi mata hakan, tana ganin cikin kwanciyar idanunsa har ya yi halinsa, kai abin ya yi muni over, mutumin da take mutuwar so fa? Innalilahi wa Inna ilahir rajiun, ya ta ji a ranta lokacin da ya caka mata wannan wuƙa?.............I cant stop my tears wlh, abin ya taɓa zuciyata matuƙa. Cikin daji ya kutsa da gawarta, babu ko tunanin ya ƴan uwanta zasu ji? Ya iyayenta zasu ji? Ya Chuchu zata ji? Bare ma Guyson ya zai ji a ransa bawan Allah? Haka ya bar cikin mutane, ya yi nisa da in da za'a iya jin ɗuriar mutane ma, sannan ya samu kogi ya jefa gawar tata a ciki, ya cire kayan jikinsa ya wanke jininta da ya taɓa shi gabaɗaya a wajen, sannan ya shanyasu, sai da suka bushe ya mayar jikinsa ya kuma koma cikin kingdom of power, da alama fa Hoorain he come for taking revenge ne or something like that. Baku tunanin idan Hoorain ya aikata hakan kenan commander Zafar ma amanarsu King yake ci tun da dai Hoorain ɗansa ne? Yanzu lokacin gwabzawa ne, yanzu fa zamu shiga ainahin cakwakiyar, kada ku bari book 3 ya wuceku, a nan zamu damalmale dik wani rikita rikita da cakwakiya. Yana dawowa cikin masarautar ya koma cikin ɗakinsa ya kwanta tamkar bai fita ko'ina ba, zuciyarsa fes, sai farinciki yake yi da alama burinsa na farko ya cika. Ni ce dai princess Teema taku ta amana mai abin ban mamaki, yanzu zamu fara buɗe babin surprise, zan bawa kwakwalenku caji fa..........😂 _______________🌹💘________________ A can cikin gida kuwa, sai hidima ake yi, Chuchu dake kwance a saman gadon Akka ta ci kuka har ta ƙoshi ne ta ji wayarta dake kusa da ita ya yi kara alamar shigowar sako. Akka ta rarrasheta har ta gaji amma taki yin shiru, kunsan yanzu ba lafiya ce da Akka ba, so komai a hankali take binsa, da taga Chuchu taki ta yi shiru ne sai ta ce to bari ta je ta kira King ko mummyn Chuchun su zo zu rarrasheta kila zata yi shiru, shi ne ta fita. Kamar ba zata duba wayar ba sai kuma ta jawosa, ganin sunan Auta a saman screen ɗin wayar ta turo sakon ne yasa ta buɗe tana cigaba da hawaye. Da kyar ma ta iya cire password na wayar ta fara karanta saƙon kamar haka. "Aunty Chuchu ki zo ki sameni a wajen back side na uncle Abbas akwai maganar da zamu yi". Shi ne abin da aka rubuta a sakon. Kai my people's Auta kuma? Da ni da ku dai mun san Auta ta mutu ko ba haka ba? Kuma mun san wayarta baya a hannunta time da Hoorain ya kasheta, wayar tana hannunsa, kenan shi ya rubutawa Chuchu sako ko waye? In shi ne me zai yi wa Chuchu ɗin da ya buƙaci yana son ganinta? Tashin hankali kenan! Ko ita ma kasheta yake son yi?. Kun san idan ana biki a waje ana samun damarmaki daban daban, ina ga shi ne yasa ya yi amfani da wannan dama domin ya yi abin da zai yi kunga ba za'a zargesa ba, za'ace akwai baki sabbin fuska da suka zo sai dai in a cikinsu ne wani mugun ya aikata hakan, kunga shi ba za'a zargesa ba saboda ya jima a cikin kingdom ɗin bai taɓa nuna wani mugun hali ba, shiyasa yake son yi wa ƴaƴan King ɗauki ɗaiɗai kenan? Tab akwai matsala kuwa. Ajiye wayar ta yi tana tunanin meyasa Auta zata ce su haɗu a wannan waje? Ita dai tasan wannan fili sam mutane basa zuwa wajen, to me ya kai Auta can?. Ta jefawa kanta tambaya. Da farko kamar ba zata je ba, sai kuma ta tuna Autar tana jiranta a can, dan haka sai ta miƙe zaune tare da zuro kafafunta kasan gadon ta miƙe tsaye, jiki ba kwari ta ɗauki wayarta ta nufi waje. Tab zata fita part ɗin Akka kira ya shigo cikin wayar tata, har lokacin bata daina kwallah ba, daga ita sai kayan barci daren jiya a jikinta, ko wanka taki yi, da Auntynsu Jawad ta matsa mata da tazo ta yi mata wanka ne ma ta gudo part ɗin Akka ta kwanta ta cigaba da rera kukanta, silk scarves ne ɗaure a kanta, ta rufe arabs hairnta da ya sha gyara sosai. Wani irin dum dum ta ji zuciyarta ya buga a lokacin da taga sunan my melody a saman screen ɗin wayar yana yawo, Yah Jawad ɗinta kenan. Zaro idanu ta yi, jikinta na kerma ta yi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnenta. Kasa yin magana ya yi yana daga zaune a bakin bed ɗinsa, dik ya rame bawan Allah, sai ido gulu gulu farare tas zaka gani. Kuka mai sauti ne ya kwace mata jin yaki ya yi magana, cikin kuka ta ce. "Yah Jawad ka yi magana dan Allah". Shiru bai iya furta uppan ba, sai ma kara shiga tashin hankali da ya yi na jin tana kuka, yana son ya ce mata tazo ya ganta amma ya kasa iya buɗe baki, tongue ɗinsa ta yi mashi wani irin tsananin nauyin gaske. A karo na biyu ta sake cewa. "Yah Jawad dan girman Allah ka yi magana ka ji?". Nan ma dai shiru bai motsa ba, jin ba zai iya jurar sauraron kukanta ba ga shi ya kasa yin magana ne yasa ya katse kiran tare da yin jifa da wayar gefe guda, idanunsa sun cika da zafafan hawaye sosai. Ai tana jin ya katse kiran ta watsa a guje ta nufi part ɗinsa, ta fasa zuwa su haɗu da Autar da mu munsa ba ita bace dan bata raye. Akka ta je ya kira uncle Abbas dan ya zo ya rarrashinta, sai suka zo suka tarar da bata nan, zama Akka ta yi tana mitan yaran zamani da iyashege suke, shi kuma uncle Abbas ya juya ya koma wajen jama'arsu. Ko sallama babu tana kuka ta afka cikin part ɗin nasa, still dai waɗan nan kuyangu masu yi mashi hidima ne kaɗai a cikin parlourn nasa, bata bi ta kan kowa ba ta afka cikin bedroom ɗin. Tana turo kofa ta afaka ciki, sai ta tsaya a bakin kofar ta ciki tana haki sama sama idanunta a kansa. Miƙewa tsaye ya yi na ganin da ya yi, idanunsa shi ma a kanta amma ya kasa yin magana har lokacin, ya kuma kasa takawa izuwa in da take. Sai ya tsaya kawai bawan Allah. Da gudu ta watsa ta je ta faɗa jikinsa tana sakin kuka mai sautin gaske. Rungumeta sosai ya yi tamkar zai mayar da ita cikin jikinsa gabaɗaya, sai a lokacin shi ma kwallar da suka cika mashi idanu suka samu damar zubowa, wani irin raɗaɗi suke ji a cikin zuƙatansu. Cikin kuka ta fara faɗin. "Yah Jawad meyasa zaka bari a rabani da kai? Meyasa baka gayawa dad ba zamu iya rabuwa ba? Meyasa ka yi shiru? Ni ba zan iya zama da kowa ba sai kai? Ba zan iya rayuwa da kowa ba sai kai? Dan Allah kacewa dad ya warware aurenmu da Yah Rizwan dan bana sonsa, Aunty Fanan ta ce mun an ɗaura!". Can ƙasan maƙoshinsa da kyar, voice ɗinsa sam bata fita ya furta. "Amma Jannat kece kika cewa dad Yah Rizwan kike so ba ni ba! Meyasa zaki yi mun haka? Meyasa kin san Yah Rizwan kike so tun farko baki sanar da ni shi kike so ba ni ba? Meyasa kika bari nayi zurfi a sonki? Ko so kike yi ki kashe ni ne? Kin san me nike ji kuwa? Kin san ya zuciyata take a yanzu kuwa, tamkar ana gasa mun zuciyata da wuta haka nike ji Jannat..........." Kasa iya cigaba da maganar ya yi a in da ya dakata yana wani irin jan numfashi mai ban tausayi. "Yah Jawad nasan kai ne kaɗai zaka yarda da ni, na gayawa su Aunty MieMie dukkansu cewa bani nacewa daddy ina son Yah Rizwan ba amma sunki yarda dani, har cewa suka yi daddyn zai yi musu karya ne? Wlh ni ban ce ina son Yah Rizwan ba, kai nike so, ni dai nasan daddy ya kirani, kuma na amsa kiransa na je, tabbas kuma naga Yah Rizwan a wajen, ban san me suka tattauna ba, ni dai sai ji na yi daddy ya ce to in tashi in tafi ya ji zaɓina, kamar zan ce mashi wani zaɓi sai kuma na yi shiru, dan Allah kar ka gaza yarda da ni ka ji?". Tana magana tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Kasa iya magana ya yi, sai kawai ya kara rungumeta sosai ya yi shiru, tabbas har cikin zuciyarsa ya yarda da ita, dan bata yi mashi karya, sai dai kuma tambayar da yake yi wa kansa a nan shi ne ya aka yi su dad zasu ce ita ta amsa masu da bakinta cewar Rizwan take so? Abin akwai ɗaure kai matuƙa wlh. A hankali aka turo kofar ɗakin, a tsorace gabaɗayansu biyu suka kai kallonsu wajen. Ai Chuchu bata san lokacin da ta saki Jawad tana zaro idanu ba, ganin wanda ya shigo cikin ɗakin ya ɗaga hankalinta, shi kansa Jawad ɗin zaro idanu waje ya yi ga hawaye ya wanke dikka fuskokin masoyan biyu. Mekuke tunanin zai faru my people's, waye kuke tunanin ya shigo ya samesu a haka? Ya kuke tunanin family zasu yi a lokacin da zasu farga ankashe Auta bata a tare da su? Waye kuke tunanin zai kasance Hoorain? Shin fansa yazo ɗauka ne ko dai menene? Meyasa ya kashe Auta?. Mu je dai zuwa, yanzu wasan zai fara fa, ku gyara zama. _________________🌹💘_____________ Busoshin yaki da ake bugawa ne ya karaɗe ko'ina a cikin kingdom ɗin, nan take hankulan al'umma ya tashi, ga jama'a sosai da suka zo biki, babu wanda ya shiryawa yaki dan basu yi tunanin za'a kawo masu hari ba, ba su shriya yaki ba hakan ba ƙaramin ɗaga hankulansu ya yi ba. Mayakan cikin Kingdom ɗin ne gabaɗaya suka fara gudu suna haɗa kan al'umma waje guda dan kada a samu asaran rayuka sosai. Dama a sama wajen bakin gate na farko akwai wasu warriors guda huɗu da suke zama a round wall dake wajen, can sama suke, aikinsu kawai dubawa da camera suga menene yake kusanto masarautar, so sune suke bada masaniya idan sunga zugan mayakan wata masarauta ta dinfarosu, suna bada masaniya kuma warriors masu kula da wajen busoshin yaki zasu bawa na ƙasa dasu umarnin da su buga bososhin domin kowa yasan halin da ake ci, dik wanda ya ji wannan kara fa to yasan babu zaman lafiya, wannan shi ne. Waye kuke tunanin ya kawowa kingdom of power hari ana tsaka da biki basu shriya ba? Shin evil kingdom ne? Or kingdom of justice su Queen Zarina kenan? Ko dai mai gayya mai aiki ne wato babban hege Black Tiger? Waye daga cikin waɗan nan? Gaskiya in dai black world ne to suka kawo wannan hari fa sai dai muce Allah ya jiƙan kingdom of power ya kwacesu, dan bana jin ko sun shriya zasu iya kwatar kansu a hannun Black Tiger bare kuma basu shirya ba basu san da yakin ba. To koma dai me ina yiwa kingdom of power fatan alkhairi tare da fatan nasara. Mu damalmale daku a asibiti Kasar Nigeria garin Abuja wajen Khadija mu leƙo meyake wakana kafin mu dawo muga wannan zazzafar cakwakiyar. _________________🌹💘______________ NIGERIA..............ABUJA🌹💘 Naƙuda gadan gadan ne ya tasanwa Khadija, tamkar zata haihu a cikin wannan keken napep ɗin, da kyar suka iya karisawa asibitin. Cikin gaggawa nurse suka karɓeta, tamkar sun san wannan mata, dan cikin mutunci suka tarbesu. Kai tsaye labour room aka wuce da Khadija da bata san in da kanta yake ba. Zee da Auntynsu ne suka tsaya a bakin labour room ɗin suna ta kai koma haɗe da yi wa Khadijah addu'ar sauka lafiya. "Zainab tashin hankali yasa mun manta bamu taho da kaya ba, ko zani bamu ɗauko ba, dama kinga bamu bawa mai wannan keken napep ɗin kuɗinsa ba, dan haka ki je ya mayar dake gida ya ɗauko akwatin kayanku dan bamu san tsawon lokacin da zamu ɗauka a nan na". Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce. "Kenan in tafi in bar ƴar uwata ita kaɗai a nan?". Cike da damuwa sosai a tattare da ita ta yi maganar. "Ban gane ki tafi ki bar ƴar uwarki ita kaɗai ba? Ni ba mutun bace ko so kike ki nunawa jama'a bani da wata alaƙa daku?". Cikin ɓacin rai ta yi maganar, da alama maganganun Zee sun sosa ranta. Kai Zee ta girgiza alamar a'a kafin ta ce. "Allah ya baki hakuri Aunty ni ba haka nike nufi ba, bari na je to". Jinjina mata kai kawai Auntyn ta yi. A ruɗe take baiwar Allah har ta manta hanyar fita ta je tana ƙoƙarin buɗe kofar labour room ta afaka ciki, sai da Aunty ta riƙeta tana faɗin. "Lafiyarki kuwa Zainab? Baga hanyar can ba". To kawai ta amsa mata da shi tare da wucewa kamar zata faɗi ƙasa. Tana fita ta samu bai keken napep ɗin yana tsaye yana jiran kuɗinsa. Yana ganinta ya ce. "Ta haihu ne?". Kai kawai ta girgiza mashi bata furta uppan ba, dama kun san ita ba kowa take kulawa ba har ta sakar mashi fuska. Cikin keken napep ɗin ta shiga gidan baya ta zauna. "Muje ka kaini gida bari na ɗauko kaya". Shi ne abin da ta ce da shi kawai. Da okey ya amsa mata tare da komawa cikin napep ɗin, sai da ya kunnata sannan ya ce. "Ai naga hankalinku a tashe ne yasa ban tsayar daku tambayar kuɗi na ba nace bari na jira abin ya ɗan lafa ko ta haihu sai in shiga in karɓi kuɗina". Tamkar da karafunan mashin ɗinsa yake yi bada Zee ba, kamar bata ji me ya ce ba taki tanka shi, kuma wlh sarai ta ji abin da ya ce, maganar ce dai ba zata yi ba, hankalinta kacokam yana a kan Khadijah, zuciyarta sai harbawa yake yi da karfi karfi tana ta addu'ar Allah ya jiƙai ɗinta yasa kada ta rasa ƴar uwarta ɗaya ɗaya a duniya. Tsabar ta afaka duniyar tunani har bata san lokacin da suka iso restauran ɗin ba sai dai ta tsinkayo muryarsa yana gaya mata sun iso. Ai a ɗari da sittin ta fito daga cikin napep ɗin ta nufi ciki, tana zuwa bata tsaya ɓata lokaci ba ta janyo akwatinsu da school bag ɗinsu, jikinta har rawa yake yi wajen fitowa. Sauran masu taya matar aiki sai tambayarta ya jikin Khadija suke yi, amma ina hankalinta baya a kansu, burinta kawai ta koma hospital ɗin. Tana zuwa ta faɗa cikin napep ɗin ya ja da gudun gaske suka nufi hanyar komawa hospital. Sai dai a hanya go slow ya yi ta tsayar da su da a kallah sai da suka ɓata almost 1 hour, su da bai wuce su ɓata 30 mins a zuwa da komawan ba sai ga shi sun ɓata 1h saboda go slow. Allah dai yasa sun isa hospital ɗin lafiya, yana kashe mashin ɗin ta fito da sauri har tana haɗawa da gudu ta ja akwatin nasu tare da goya school bag a bayanta ta nufi ciki. Tana zuwa bata ga Auntynsu a bakin labour room ɗin na, ga shi mangariba ta kawo kai, hakan yasa ta ɗan zauna a saman kujerar dake wajen tana tunanin ina Auntyn tasu ta je? Shiru shiru ta yi zaman 10 mins bata ga motsinta ba kuma bata ga alamar zata ganta ba, hanan yasa ta ce bari ya shiga cikin labour room ɗin ta duba ta gani ko an bada damar shiga ciki ne Auntyn tasu ta shige ciki. Jan akwatin ta yi, a hankali ta tura kofar ta shiga. Wayam babu kowa a cikin ɗakin sai Khadija dake kwance tamkar gawa bata motsi. Da gudu Zee ta saki akwatin a bakin kofa ta ƙarisa wajenta. Babu ciki a jikinta alamar ta haife shi, waige waige Zee ta fara yi tana neman ta ina zata ga jaririn tun da taga babu ciki. Sai dai kash babu kowa a cikin ɗakin. Hannu tasa tana ɗan bubbuga gefen fuskar Khadija tana ambatar sunanta, ina shiru kake ji bata motsa ba, ga dikkan alamu babu rai a jikinta. Ɗago kai da Zee zata yi domin ta kara kallon cikin ɗakin da kyau ko idanunta ne suka daina gane mata mai kyau yasa bata ga jarir ba!. Tana ɗago kai sai ta hango giftawar mutun da gudu ta wajen windown ɗakin da suke ɗin, a idanunta sai taga kamar mai keken napep ɗin da ya kawosu ne ya gifta da gudu, zuciya da sake sake sai ya saƙo mata tabbas ba lafiya ba, kuma kunga ai an sha cutarsu ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, dalilin wannan cutar da aka yi masu ma yasa Zee ta dai'na yarda da kowa. Dan haka a yanzu ma sai ta ji cutarsu za'a sake yi, a ranta ta ji lallai wannan mata ita ta ɗauke abin da Khadijah ta haifa kuma bakinsu ɗaya da wannan mai keken napep ɗin. Tuna haka yasa ta shiga wani irin tashin hankali mara misiltuwa, wani irin jiri ta ji ya debeta, ga shi bata da tabbacin Khadija tana raye ko ta mutu, daddagewa ta yi ta haɗa iya karfin da ya rage mata ta ja kafafunta da suka yi mata nauyi domin ta bi bayan wanda ta gani ya gifta ta wajen wannan window ta gani ko zata iya kamosu. Innalilahi wa inna ilahir rajiun, my people's me kuke tunanin zai faru, Khadija tana raye ko ta mutu? Shin da gaske wannan mata ce ta ɗauki abin da Khadijah ta haifa? In ita ce me zata yi da shi? Zee zata ci nasara ganinsu kuwa? Idan ta gansu tana da karfin iya kwatan babyn ne? Me kuke tunanin zai iya faruwa a cikin littafin RAWANIN ZALINCI, sai dai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu, akwai cakwakiya over to over!!!. a page full of pity that touches the heart🥲 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ 2024-12-05 52 Da kyar Zee ta iya fitowa tsakar hospital ɗin, a lokacin aka fara kiraye kirayen sallar mangariba, kanta ne ta ji yana juya mata, duhu duhu ta rinka gani a idanunta ga wani irin jirin wahala da yake ƙoƙarin ɗibarta, ba komai ya haifar mata da hakan ba face ɓacin rai. Waje ta nufa tana jan kafafu da kyar da kyar ta nufi waje dan ta duba mai napep ɗin yana nan ko baya nan. Tana fitowa tun daga nesa ta hangosa yana tsaye jikin mashin ɗin nasa, da alama ita yake jira ta kawo mashi kuɗinsa ya wuce. Aikuwa tana ganinsa bata san lokacin da wani irin karfi ya zo mata ba, da wani irin sauri ta taka ta nufesa. Yana ganinta shi ma ya ɗan matso kaɗan dan shi fa a cewarsa yaga mata, batu na gaskiya ma shi ba kuɗinsa ya tsayar da shi ba, Zee ta tsayar da shi, ta yi matuƙar tafiya da imaninsa ne yadda take da shariya halin ko in kula da rashin magana, abin ya yi matukar birgesa, kuma dani da ku dik mun san dik wanda ya ga Zee da Khadija sai ya ji yana sonsu sai dai idan yasan ba samu zai yi bane sai ya kama kansa, amma kyau iya kyau Allah ya yi masu ga diri mai ɗaukar hankali. Tun bata gama ƙarisowa wajen nasa ba ya tare ta da faɗin. "Auntyn tamu ta haihu ko? Ai na rigaki sanin hakan". Yana magana yana ɗan murmushi, alamar yana tayata murna bawan Allah. Tana ƙarisowa wajen cikin tsawa ta ce mashi. "Ina babynmu? Ka fito mun da shi kawai". Mamaki ne ya bayyana a saman face ɗinsa, a ɗan rikice ya ce. "Babynku kuma? Me zan yi da baby ni kuma da zan ɗauka? Kuma ai ni ban ma iya rike baby ba, baki ga ma babu shi a hannuna bane?". Ya kai karshen maganar yana ɓuɗa mata tafukan hannunsa da babu komai ciki. Ɗan dafe kanta dake barazanar tarwatse mata ta yi, komai ya rikice, rikicewar da ta yi yasa ta jefesa da wannan magana, yau hawayen Zee fa sun kasa zubowa ma saboda tsabar tashin hankali. "Ka yi hakuri, so nike in ce maka baka ga wannan mata da muka zo a tare da ita ba?". Ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, da har ya tsorata ya zaro idanu, cikin nuna rashin damuwa a kan tambayar tata da ta sake jefa mashi ya amsa da. "E naganta ta fito ɗauke da baby a hannunta yanzun nan ba jimawa, kina shiga ciki tana fitowa, a tunani ma irin scanning ɗin nan zata kai babyn ayi mashi tun da nasan ba kowani hospital ne suke yin scanning ba, sai dai ban san ana yi wa jariri scanning ko ba'ayi mashi ba". Tun da ya fara magana idanun Zee yake a kansa babu ko kyaftawa, jira take yi kawai ya dasa aya ita kuma ta ɗaura, ta kara shi ga tashin hankali na jin cewa da gaske ƴar uwarta ta haihu kuma wannan mata ce ta ɗauke yaron ta gudu da shi. "Dan girma Allah malam ka taimaka mun, wlh sace mana babyn ta yi ta gudu da shi!". Yadda ta yi maganar wlh kamar ba ita ta yi shi ba, saboda jikinta a tsananin mace yake, muryarta a kasale baya fita sosai. Wani irin zaro idanu waje ya yi, a razane ya ce. "Dama ba ƴar uwarku bace matar?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e ta ƙasa iya furta uppan. "To shiga cikin mashin mubi bayanta, ai naga hanyar da ta bi, ki yi sauri". Cewar guy ɗin, hankalinsa a tsananin tashe ya yi maganar. Yau dai Zee bata tsaya har sai zuciyarta ta aminta da shi ba, kawai ta yi saurin afkawa cikin mashin ɗin. Da gudu ya shiga ya ja suka bar wajen suka bi bayan mata, a lokacin har anfara gabatar da sallar mangariba. Abin fa da mamaki yadda wannan mata ta saci jaririn nan, sai ka ce babu nurses a cikin hospital ɗin, ko da yake mai san abinka ya fika wayo, tun da ta yi acting like ƴar uwarsu ta jini ne kunga babu wata nurse da ta isa ta yi mata shamaki da babyn, Allah dai ka rabamu da mugu, dan wlh idan mutun ya shirya yi maka mugunta babu wanda zai iya tseratar da kai daga sharrinsa face Allah. Ni anya ma wannan mata ba rufa ido ta yi masu ba kuwa? To me zata yi da jaririn? Muje dai zuwa. Sosai wannan mai keken napep yake tsala gudu suna neman wannan mata, a hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauƙa gari yana kara duhu sosai, amma har e wannan lokaci Zee bata cire rai da samun nasaran ganin wannan mata ba, ta dafe kanta da yake barazanar tarwatsewa tana karanto dikkan addu'oin da suka zo bakinta, shi kansa mai mashin ɗin addu'a yake tayata da shi yana aikin tsinewa wancan mata albarka, shi ma bahaushe ne ɗan Kano, neman na halaliyarsa ya kawosa Abj. Basu yi wani tafiya sosai tsakaninsu da asibitin ba suka tsinkayo hanyoyin biyu sun rabe a wajen, ɗaya ya yi ta cikin daji ɗayan kuma ya ƙarisa kutsawa cikin gari. Shi kansa mai keken napep ɗin hankalinsa a tashe ta yadda baya gane me yakamata bare kuma ita Zee, sai dai dik da halin da take ciki bata bari kaifin ƙwaƙwalwarta ya dishashe ba, wannan guy ɗin zai wuce da su ta hanyar da ya kutsa cikin gari sosai ne ta ce mashi. "A'a mu bi wannan hanyar da ta bi cikin dajin nan". "Meyasa zamu bi nan?". Ya jefa mata tambayar yana ɗan rage gudun mashin ɗin dan kada su nisanta da wannan hanya. "Saboda babu wani mai gaskiya da zai bi hanyar dajin nan a irin wannan lokaci, haka zakila babu wani mai hali irin na matar nan da zai saci yaro a irin wannan lokaci ya bi hanyar cikin gari da shi, bata da gaskiya, so ƙoƙarin ɓoye kanta zata yi, dan haka mu bi nan in da rabo sai kaga Allah ya haɗa mu". Ya gamsu da maganganunta da hujojinta ya kuma jinjinawa kaifin tunaninta da hangen nesanta, dik da tana cikin damuwa bata bari hakan yasa ta rasa nutsuwar da zata fiddawa kanta mafita ba, haka ake son mumini mai zuciyar imani, a dik lokacin da wata ƙaddara ta faɗowa bawa so ake ya nutsu ya koma ga Allah dan gudun kada ya sake tabka asara a cikin asara. A hanzarce ya juya kan mashin ɗin suka bi wannan hanyar, a lokacin ruwan saman ya kara yawaita irin wannan ruwa wanda babu iska babu tsawa, sai dai ku ji yana zuba shaaaaaaa haka. Basu yi nisa a kan wannan hanya ba tun daga nesa suka ga ansanya hannu a saman hanyar alamar ana son tare abin hawa. Sam bai sanya alamar tsayawa ba ya yi niyar wucewa. Ita kuwa Zee idanunta suna a kan wadda ke ƙoƙarin tsaidasu ɗin dan taga wanene or wacece a cikin ruwan saman nan ga dare kuma take neman abin hawa. Gab zasu wuce ba tare da sun tsaya ba Zee ta yi ihun cewa wlh wannan mata ce ya tsaya ita ce. Ai matar tana jin haka ta bar bakin hanyar a guje ta shiga ta cikin dogayen ciyayin dake gefe gefen wajen. Wani irin mahaukacin birki mai mashin ɗin ya ja, a miliyan ya fito ya bi bayan matar, haba Zee ma a miliyan ta bi bayansa tanata faɗin Alhdulillah babu iyaka. Kun san ba zaku haɗa gudun mace da namiji ba, hakan yasa ya yi saurin cin mata, yana gab da zai kamata ta jefar masu da babyn a kasa ta kara karfin gudu da iya karfinta ta kutsa cikin daji, dan tasan me zai biyo baya idan asirinta ya tonu, a tunaninta gara ta rasa wannan jariri da ta tsaya su kamata su yi mata ihu jama'a su taru asirinta ya tonu. Allah sarki bai bi bayanta ba ya dakata a miliyan ya ɗauki jaririn dake kuka kamar maƙoshinsa zai ɓalle, bawan Allah ya ji wuya, farkon zuwansa duniya ya fara da shiga ruwan sama mai sanyi, ga shi dan bakar mugunta matar ta jefar da shi a ƙasa, kila ya buge ne ko ya ji ciwo yasa yake ihu haka. Dai'dai lokacin Zee ta ƙariso wajen tana haki sama sama. Jikinta har ɓari yake yi wajen kai hannu ta karɓi jaririn. Guy ɗin ne ya ce. "Ki yi sauri mu bar cikin ruwan nan da shi". Ai tun bai ƙarisa magana ba ta wuce gaba da sauri ta, tana zuwa ta afaka cikin napep ɗin da sauri. Yana zuwa shi ma ya shiga da gudun gaske ya ja mashin ɗin, basu zame ko'ina ba sai asibiti in da Khadija take. Suna isa yana kashe mashin ɗin Zee ta fito da sauri ta koma cikin hospital ɗin, bayanta ya bi shi ma domin ya ce mata ta zo su canza asibiti kada wani matsalar ta sake faruwa. Ɗakin da Khadija take ta koma, har lokacin Khadija bata motsa ba kamar dai da gaske babu rai a jikinta. Mai napep yana zuwa bai ɓata lokaci wajen shiga cikin ɗakin ba. A gefen Khadija ta kwantar da babyn, zanin da matar ta kudundune shi a ciki ya jike, yaron ma ya dai'na kuka sam, kamar dai ya yi barci ne ko ya suma. A gaggauce ta janyo akwatin kayansu dake a cikin ɗakin. Sauri sauri ta buɗe akwatin ta ciro zanin Khadija, jikinta har rawa yake yi wajen miƙewa ta karisa wajen babyn. Sauri sauri ta cirosa daga cikin wannan jikakken zanin ta sanya na Khadijah da ta ciro ta kudundunesa a ciki. Guy ɗin yana ƙoƙarin yi mata magana suka ga anturo kofar ɗakin an shigo. Wata nurse ce ta shigo, sai a lokacin Zee ta lura ashe ba'a labour room aka kawo Khadija ba, wani ɗaki ne na daban. Ƙarisowa ciki nurse ɗin ta yi, tana ƙoƙarin yin magana guy ɗin nan ya rigata da cewa. "Madan muna da buƙatar canza hospital". Kallonsa ta yi kafin ta ce. "Anyi maku laifi a nan ne?". "Ko anyi mana laifi ko ba'ayi mana ba mu dai canza hospital zamu yi, ko bamu da ra'ayin zaɓar asibitin da dik muke so ne?". Yana magana yana buɗe mata ido irin ta san shi fa ba da wasa yake yi ba kuma ba zai ɗauki wani iskanci ba!!. Ɗan siririn harara ta wurga mashi kafin ta ce. "To umma ta gaida A'isha, kufi ruwa tafiya in kunga dama, amma ai sai kun biyamu kuɗin aikin da muka yi maku da gado, haihuwa da muka karɓa da sauran abubuwa". "Nawa ne kuɗin naku?". Ya faɗa shi ma yana harararta. Guy ɗin idanunsa a buɗe suke, da alama wayayyene sosai. Zee dai ba ta su take yi ba, bata ma ko jinsu, hankalinta yana kan yadda zata kudundune wannan baby ya ji dumi, shi ne a gabanta, bama ta bi ta kan Khadija ba tukun nan, sai a yanzu kuma idanunta suka ciko da kwallah tab. "Dubu shabiyar ne kuɗinmu". Ta faɗa a gadarance. Bawan Allahn nan da yake yana da zuciyar kirki sai ya ciro atm card daga aljihunsa ya ce da Zee yana zuwa bari ya je waje ya nemi mai pos ya cire masu kuɗinsu su basu sai su karɓi sallama su tafi wani hospital ɗin. Zee da hankalinta baya jikinta ai ko amsa mashi bata iya yi ba, sai da ta sanya zannuwa har uku ta kudundune yaron nan da kyau, sannan ta mayar da sauran kayan nasu cikin akwati, ta matso kusa da Khadija tana cigaba da ambatar sunanta. Shiru bata motsa ba, shi ma babynta bai motsa ba har wannan mai keken napep ya je ya ciro kuɗi ya dawo, nurse ta yi mashi jagoranci zuwa in da zai biya kuɗi ya karɓi sallama su zo su haɗa kayansu su tafi. Sosai Zee ta zauna a gefen gado tana ruwan hawaye, wani na bin wani zafafa da su, har wa lokacin jikinta kerma yake yi. Baiwar Allah taga wahala taga bone!!. Ba ƙaramin tausaya masu wannan mai napep ɗin ya yi ba, wannan ma bai san ainahin labarinsu ba, bai san tashin hankalin da suka shiga a baya ya wuci na yanzu ba. "Baiwar Allah ki ta shi ƴar uwar taki mu je na kaiku wani asibitin mai kyau da tsaro wan da ya fi wanna, dan kada makamancin abin da ya faru sake faruwa da ku". A tunaninsa Khadija barci take yi. Cikin kuka murya a marairaice ta ce. "Ai taki tashi, tun da nazo nike ta ƙoƙarin tashinta amma taki". Matsowa kusa da su ya yi dan ya gani ko dai suma ta yi. Da yake dai ya fi Zee shekaru kuma namiji ne shi ɗan gwagwarmaya, anga jiya anga yau yana ganinta sai ya gane ba barci take yi ba suma ta yi ko kuma mutuwa. Hakan yasa ya ce bari ya nemo ruwa a waje ko pure water ne su zuba mata su gani suma ne ko dai rai ne ya yi halinsa. Zee dai bata ce ko uppan ba ta bishi da kallo tana tunanin ko dai shi ma cutar da su zai yi ne, dan ita a yanzu dik wanda ya nuna zai taimaka masu gani take yi shi ma kawai wani abin ya biyo a tattare da su, kwata kwata yanzu babu yarda da ko leda ce bare dabba bare mutun a zuciyar Zee, sai dai ta bi kowa kawai da ido. A hankali baby ya fara motsawa. Da sauri Zee ta kai kallonta a kansa. Cikin gaggawa ta sa hannu ta ɗaukesa tana ƙoƙarin ɗan buɗe mashi fuska ya shaki iska, dan ita da taga kamar yana jin sanyi over sai ta kudundunesa har da rufe mashi fuska ta bar iya yadda numfashinsa zata iya fita kawai. Tana buɗe fuskar tasa miƙa babyn ya yi tare da zabga hamma sannan ya waro idanunsa waje. Ya subhanallah, idan baka sani ba ko kwana za'ayi ana gaya maka Khadija chocolate colorn nan ce ta haifo wannan babyn ba zaka taɓa yarda ba, saboda yadda ya fito a bature sak babu mix, fari tas da shi, yanayin skin ɗinsa ma ya fi kama da Koreans ne ba ainahin turawa ba, gashin kan nan nasa golden white ne irin na Sweetie, ga lips ɗinsa dark purple, gashin kansa ya sauko mashi har gaban goshi yana rufe mashi idanu, ɗan fuskar nan dan daidai, kai kace bashi da baki saboda kankantarsa, idanunsa manya manya a waje, ga su launin ash colar mai haske hakan yasa suke kyalli sosai. Wlh sai da Zee ta yi muguwar tsorata har ta kwantar da yaron a saman bed kusa da mamarsa a zabure ta miƙe tsaye lokacin da ta ga face ɗinsa, ɗazun tana cikin tashin hankali burinta kawai ta raba shi da wannan zani da ruwa ya ɗan taɓa, bata lura da face ɗinsa ba sai yanzu. Dafe saitin zuciyarta ta yi tana karanto dik addu'ar da tazo bakinta, a tunaninta aljani suka karɓo ba babyn da Khadija ta haifa masu ba. A haka wannan mai keken napep ya shigo ya sameta. Ya yi mamakin ganinta a can gefe ta manne da bango ta kuma dafe kirji ga bakinta na motsi na addu'ar da take karantowa. "Lafiya baiwar Allah?". Ya tambaye yana kallonta face ɗinta. A razane ta fara faɗin. "Wlh ba babyn Aunty Khadijah muka karɓo ba, wannan aljani ne, ba mutun bane". Tana magana tana nuna babyn da hannunta ɗaya. Abinku da namiji, da sauri ya ƙarisa gaban gadon dan ya ganewa idanunsa. Ai shi ma sai da ya ɗan ja baya kaɗan a lokacin da ya sauke idanunsa a kan yaron, ga shi babyn ya waro idanunsa waje yana ta zuba hamma alamar yunwa yake ji. Zuba mashi idanu guy ɗin nan ya yi a cikin zuciyarsa yana faɗin tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya yi wannan kyakkyawar halitta, dan shi bai yarda aljanin bane, saboda yana kalle kalle turawa a TV, ita ma Zee tana kallo, kawai dai abin ya rikitata ne sakamakon bata taɓa ganin irin hasken fatarsu a zahiri ba, dan wlh camera tana ɗan dishashe haskensu, idan ka gansu a zahiri in dai baka taɓa ganinsu ba sai ka ɗan tsorata, wasu ma wani faw zaka gansu hasken ya yi yawa har ya munana, to gaskiya babyn Khadija farine sosai, shiyasa Zee ta tsure. Ƙoƙarin kuka babyn ya fara yi. Da sauri guy ɗin ya ce. "Zo ki ɗaukesa bari na zubawa mamarsa ruwa, ba aljani bane, ɗan korea ta haifa mana, ke baki ganin Koreans film ne? Dik yadda aka yi babansa Korean ne ko?". Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, sai a yanzu ta ji zuciyarta ya ɗan nutsu, jiki ba kwari ta zo ta ɗauki yaron tana kallonsa, wani irin kaunarsa ta ji yana ratsata, sai a yanzu ta gane ashe mutun ne, madarar kyau ne ya rikitata, dik da bata dariya ga kuma halin da take ciki bata san lokacin da ta saki murmushi ba a lokacin da take kallon fuskarsa, a fili ta furta. "Allah ya rayaka bisa sunnah Ahmad babana". Idan baku manta ba sunan babansu Ahmad, dama kuma Khadija ta ce idan namiji ne to Ahmad ne sunansa, idan kuma mace ce Zainab, to Allah ya yi Ahmad ne, baban Zee ya tafi baban Zee ya dawo, fatan mu dai Allah ya rayasa bisa sunnah. In short mai napep ya zubawa Khadija ruwa amma bata farfaɗo ba, abin ya ɗaga hankalinsa sosai, amma sai ya danne ya ce da Zee bari ya ɗauki Khadija zuwa cikin mashi sai su je wani asibitin ko za'ayi mata magani a can ta farfaɗo. Zee da ta samu baby hankalinta ya koma kansa da okey kawai ta amsa. Karfi guy ɗin yasa da kyar ya iya ɗaukar Khadija ya nufi waje da ita. Bayansa Zee ta bi bayan ta vakka baby a saman should ɗinta, sai ta ja akwatin nasu da jakar da hannu ɗaya suka nufi keken napep ɗin. A gidan baya ya kwantar da Khadija sai ya ce Zee ta shiga gaba su tafi. Akwatin ma a gidan baya suka saka. A lokacin har anyi sallar isha'i, gari ya yi duhu sosai saboda hadarin ruwan sama. Haka wannan bawan Allah ya ja mashin ɗinsa suka nufi ainahin cikin garin Abj. Allah sarki, dan Allah ya taimaka masu dan kuma ya ga mata a wajensu wato Zee, sonta ya yi mashi mugun kamu lokaci guda. Gudu ya fara shararawa sakamakon ruwan saman dake kara yawaita daga yayyafi izuwa babban ruwa. Sun miƙi hanyar da zai sadasu da cikin gari, basu yi nisa da tafiya ba ba zato ba tsammani suka tabka mummunar accident da wasu uban shirga shirgan jerin gwanon motocin da suka danno kan hanyar. Wajen motoci uku dikka sun daki juna glasses ɗinsu ya yi watsa watsa, gudun da mai napep ɗin yake tsalawa kuma ga ruwan sama ne ya haifar da wannan matsala, bai lura da gabansa sosai ba, hankalinsa na'a kan Zee kuma dai Allah ya ƙaddara hakan sai ya faru. Gabaɗaya napep ɗinsa ta yi watsa watsa a kan hanyar, dikkansu sun faɗi gefe gefe, Zee ta yi gefe sai dai Allah da ikonsa babyn yana hannunta, Khadija da dama ita da gawa dik ɗaya suke ta yi gefe kanta na zubar da jini, shi ma mai mashin ya yi gefe, jini ne shi ma ke bulbulowa daga kansa, da alama ya ji ciwo sosai shi da Khadija, dikkansu babu wanda yake numfashin a cikinsu banda kukan baby dake tashi, da alama shi bugewa ya yi yasa yake wannan ihu. Ganaɗaya sauran jerin gwanon motocin ne suka dakata da tafiya. A guje a ka bubbuɗe kofofin motocin a tare, wasu jiga jigan securitys ne suka fito da gudu daga cikin motocin, gabaɗayansu sanye suke da long coat a jikkunansu, sun kai su 10 suka yi kansu su Zee a cikin wannan ruwan sama. Ɗaya daga cikin securitys ɗin ne ya sa hannu ya ɗauki babyn dake ta faman tsala ihu yake hannun Zee, securitys uku kuma suka nufi wajen motocinsu da glasses ɗin ya farfashe domin suga waɗan da suke ciki sun rayu ko sun mutu? Sauran securitys ɗin kuma suka yi kansu Zee a in da suka fara ɗaukarsu izuwa cikin mota domin su ceci rayuwarsu idan suna da sauran numfashi kenan. Har da mai keken napep ɗin dik suka ɗauka, a cikin mota ɗaya suka sanya Zee da Khadija, shi kuma mai napep suka sanya shi a mota dake gaban nasu Zee, babyn kuwa yana hannun securityn da ya ɗaukesa tin farko ya shiga gaban mota da shi, Allah sarki wannan babyn ya ga duniya, tun diga faɗowarsa duniya ya fara shiga haɗarurruka, dan ma kun san Allah yana kare jarirai sosai ne, ai da abin sai dai shiru kawai. A cikin motocinsu da suka lalace mutun biyu sun saunata sosai, saura kuma alhamdulillah, ɗan jijjiga suka yi. Motocinsu uku daga cikinsu ne suka juya suka nufi cikin gari da gawa su Khadija, sauran motoci 15 kuma suka wuce in da suka nufa tun farko. Motoci uku kuma sun lalace sai suka barsu a wajen. To my people's me kuke tunani zai faru? Wani irin darasi kuka ɗauka a labarinsu Khadija? Zasu rayu ko sun mutu? Waye uban wannan kyakkyawan babyn na Khadija? Ya makomar mahaifiyarsu dake gidan yari? Idan Zee tana da sauran rayuwa a gaba me kuke tunanin zai faru a cikin rayuwarta? Ina Sadiq kawunsu yake? Ya batun mahaifiyarsa da aka ce ta suma saboda labarin halin da maman Zee take ciki da ta ji? Kuna tunanin haka kawai da gangan Sadiq zai iya mancewa da ƴaƴansan nan? To mu je dai zuwa. Fatana dai idan su Zee suna raye Allah ya basu lafiya ya kuma takaita masu wannan jarabawa, ya jiƙainasu ya sauya masu rayuwa, Allah ya raya mata baby Ahmad a kan Sunnah...... A jikina ina jin kamar Khadija bata raye.......😥 Dama tana yawan gayawa Zee da wuya ta rayu da ɗanta ko ƴarta da zata haifa, ta jima tana kariyar mun da zuciya da kalamanta.........😥💔 Mu je dai zuwa dan muga yacce abin zai kaya, akwai cakwakiya da tarin tambayoyin da nasan kuke dakon samun amsarsu wanda a alkalamina kawai zaku sami amsarsu, to ku kwantar da hankulanku alkalamina yana tare da ku zai kuma warware maku komai cikin sauki, fata na dai shi ne kada ku bari book 3 ya wuce ku, dan a nan asalin cakwakiyar take. ______________________________🌹🕊️ .....................JIMETA YOLA🔥 Ihun da yara suke yi a wajen ne yaja hankalinsu Jaish a kansu, bama yara ba harda manya, dik ƴan ƙauyen sai firfitowa suke yi daga gidajensu suna ihu. Mahreen dake cikin ɗakin bappa tana kuka ne ta tsinkayo ihun mutane a kunnenta, ai da gudu ta watso waje, tuni ta manta da tana kuka. Tana fitowa tsakar gida suka fara jin karan kukan jirage a sararin samaniya, Nenne uwar bala'i tuni ta kasa ƙarisawa gidansu Mairo ta juyo da gudu ta dawo, dan taga abin da bata taɓa gani ba, basu taɓa ganin jirgi a kauyen ba, sai yau ga shi jirgi ba ɗaya ba biyu ba, jirage goma cif ne suka doso cikin kauyen. Da gudu Mahnoor ta fito daga cikin kitchen, shi ma Jaish fitowa ya yi daga cikin ɗakinsu domin yaga ihun me ake yi kuma karan me yake ji?. Yana fitowa suka ci karo da Mahnoor dake ƙoƙari shiga cikin ɗakin nasu, hannunta ya riko suka nufi waje ba tare da ya yi magana ba. Gabaɗaya dattawan kauyen sun firfito waje, iyaye, yara da matasa, kowa ya ɗaga kai sai kallon jiragen suke yi, manya manyan fighter jet guda biyu ne a cikin jiragen, da F-15E Strike Eagle, da kuma F-16 Fighting Falcon, domin tabbatar da tsaro yasa fighter jet ɗin suka kasance a gaban, sauran jiragen kuma suna nan daban daban, akwai B-55 da su F-25. Shawagi suka fara yi a dai'dai sararin samaniyar kauyen kamar wasu eagle, da alama kauyen suka zo, dan basu matsa ko kaɗan daga wajen ba. Gabaɗaya idanun ƴan kauye a kansu, Mahreen sarkin rashin tsoro ita ce a gaba wajen kallo, tuni ta share hawayenta, bappa yana gona yana barci bashi da labarin abin da yake faruwa. Wani irin jiniya ne tamkar zasu tashi gari ya dinfarosu, jiga jigan motocin jami'ai ne suka keto cikin dajin suka danno cikin ƙauyen. Suna danno kai gabaɗaya ƴan kauyen suka fara watsewa suna gudu suka shiga cikin gidajensu, dan fa motoci ne masu kama da jirage. Manya manya. Jaish, Mahnoor and Mahreen ne kawai basu gudu ba, Mahnoor abin da ya hanata gudu cikin gida saboda Jaish yana tsaye ne, ita kuwa Mahreen dama can bata yi niyar gudu ba, ta tsaya ne ta kalli abin da zai turewa buzu naɗi. Motoci masu tashin jini shidda ne a gaba suka dira a kofar gidan bappan, still Jaish yana tsaye yana kallonsu, wasu jiga jigan jami'an sojoji ne suka fara firfitowa daga cikin motocin, waɗan da suke baya ma suka diro ƙasa. Da gudun gaske suka kewaye ko'ina a arear gidan bappa, hannunsu rike da manyan bindigu sai wani muzurai suke yi da idanunsu jajir kamar gauta. Tsorata iya tsorata Mahnoor ta yi, da sauri ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata zata gudu cikin gida kenan ya ce ta dawo. Ba musu ta dawo ta tsaya ta bayansa, ita kuwa Mahreen sai kallonsu take yi tana karawa, a albarka irin nata ma wai kyau suka yi mata, Wasu tsala tsalan motoci sabbi dal dal ne suka biyo bayan motocin sojojin nan, motoci huɗu ne cif dikkaninsu kirar PININFARINA BATTISTA, bakake kirin sai kyalli suke yi. Sai wasu motocin sojoji da ƴan'sanda uku suna take masu baya. Har daf gaban Jaish waɗan nan motoci suka kariso, kun san da yake ƙauye akwai fili, sai yazama dik motocin nan kofar gidan bappa ya ɗaukesu. Still Jaish yana tsaye idanunsa a kansu ko motsawa bai yi ba, kaman wanda ruwa ta cinyesa. Motocin suna tsayawa wani katon soja ya zo ya fara ɓalle kofofinsu yana buɗewa. Kusan a tare Ramish da Bilal and uncle Jahiz suka fito daga cikin motocin, kowa da nasa. Gabaɗayansu suna sanye cikin shigar three-piece suit irin wanda suka kalarci taron ɗaurin auren Rizwan da shi, sun yi matuƙar kyau sosai. Ai razana Mahreen ta yi, kun san jini ba wasa ba, sai taga sun saje mata da Jaish, taga sun zama mamarsu ɗaya, ta kalli Jaish ta juyo ta kallesu, dik ta rikice. Ita kanta Mahnoor ta rikice kuma ta tsorata, ta kalli Jaish ta sake kallon Ramish, ta kasa gane komai. Still jirage nata shawagi a sararin samaniya. A miliyan Jaish ya zaro idanunsa waje yana kallon Ramish, nan take ya ji kansa ya yi wani irin mugun sara mashi, da karfi ya datse idanunsa tare da dafe forehead ɗinsa da hannu bibbiyu yana jin wani irin jiri mai karfi tana ɗibansa. Kafin su Ramish su ƙariso gabansa ya yanke jiki zai faɗi ƙasa Ramish ya yi zafin naman isa garesa ya taresa, ai Mahnoor bata san lokacin da ta juya a guje zata gudu cikin gida ba. Mahreen ce ta riƙo hannunta har da ce mata ta tsaya su kalli kyawawa masu kama da Hamma, ita fa yarinyar nan sai addu'a. Mahnoor ta tsorata da su amma ita ko a jikinta, kyau ma Ramish ya yi mata dan yana cikin kaya matsu tsada, dik sai ta rikice a kansa. A saman shoulder ɗinsa Ramish ya saɓi Jaish sai cikin motarsu, basu yi wa kowa magana a kauyen ba, basu nemi kowa ba kuma basu taɓa kowa ba, Jaish kawai suka ɗauka suka taga motocinsu suka bar ƙauyen. Suna tafiya jiragen dake sama suka take masu baya har ma suka wucesu. Tashin hankali, kallon kallo Mahreen da Mahnoor suka fara yi wa junansu, kuka zasu yi ne ko ihu sun rasa, barema Mahnoor da ta kamu da son Jaish ga shi an ɗaukesa, ita kuma Mahreen an ɗauke bata abin kauna mai tare mata faɗa, ya kuke tunanin makoman Mahnoor?. Da gudun gaske Mahreen ta watsa ta nufi wajen bappa a gona dan ta sanar da shi wasu sun zo sun ɗauki hamma, ita kuma Mahnoor ta shige cikin gida da gudu tana sakin kuka mai sauti. Su kuwa su Ramish kai tsaye airport suka nufa, dama ba zama suka zo yi ba, barema shi Ramish da yau yana da taro da misalin karfe 5 na yamma a Dubai, so ba zasu wani ɓata lokaci ba. Suna airport suka hau jirgin Abuja, dama already sun yi bukking, jet da suka zo da ita kuma a Abj ɗin suka barota saboda wani dalili nasu na kansu da basu bayyana ba, motocin da suka ƙarisa da su cikin kauyen kuma dama daga gidan gwamnati ana turo masu da shi. Amma my people's me kuke tunanin dangane da yadda aka yi su Ramish suka iya zaƙulo Jaish? Hmmmm akwai matsala fa. Suna sauka a Abj suka nufi hotel ɗin da suka sauka, a nan suka raba hanya, Bilal and Ramish zasu ɗauki jet ɗinsu su wuce Dubai kai tsaye, su uncle Jahiz kuma zasu wuce da Jaish Tunisia, hakan ma yasa Ramish ya zo da uncle Jahiz domin ya koma da Jaish. Baku tunanin ya aka yi suka tsallake rikicin dake Kingdom of power suka zo ɗaukar Jaish?🤔 Ramish and Bilal ne suka fara yin gaba suka bar uncle Jahiz a hotel ɗin tare da Jaish da bai farfaɗo ba. Kamar yadda Ramish ya faɗa karfe uku dai'dai suka yi wa Dubai dirar mikiya, sosai Abu Abdussalam ya ji matuƙar daɗin hakan. Abin da banku sani ba ban gaya maku ba shi ne, Ramish, Bilal, Dr Raj, uncle Jahiz tun ranar Jumma'a bayan ɗaurin auren Rizwan da misalin karfe 3 na rana suka baro kingdom of power suka nufo kasar Nigeria, so su dik rikicin da yake faruwa a kingdom of power basu sani ba, ga shi uncle Jahiz zai koma can yanzu, me kuke tunanin zai faru? Kada ku manta ankawo masu hari watakila ma suna can suna gwabza yaki waya sani!. Abu Abdussalam bai samu damar ziyartar ɗaurin auren Rizwan da ya ce zai je ba, saboda wannan taro da suke da shi na karawa Ramish and Bilal girma da za'ayi ga kuma walimar da Abbie ɗin nasu ya shirya masu. Lokacin da su Ramish suka dira a Dubai har an fara gabatar da taron, gabaɗaya family sun hallara a cikin hall ɗin, ba'a gidansu za'a gabatar da taron ba, ba kuma a wajen aikinsu ko a gidan gwamnati ba, Abu Abdussalam ya buƙaci da su kama tampatsetsan hall saboda dubban baki da za su zamu halatta. Mu koma baya kaɗan, a tsawon kwanaki da suka shuɗe bamu leƙo Dubai ba abubuwa da dama sun faru, ciki harda amsawa masu nikaf da Leesharh ta yi a kan zata yi masu last aikin da suka buƙata, sun canza mata wayar da yake hannunta, ana saura kwana biyu wannan taro Leesharh bata san daga ina ko ya aka yi aka kawo mata waya ba, sai dai taga waya kawai a cikin akwatinta, ta sha madarar mamaki sosai, amma sai ta danne ta cigaba da bin umarninsu dan sun ce mata shi ne last mission. Alakarta da Ummie ya kara tsananta, Ummien ta tsaneta sosai, sam bata son ganinta, Abu Abdussalam kuma kullum cikin ƙara janta a jiki yake yi, yana kaunarta saboda Allah sosai. Sun sha samun saɓani ita da Ramish and Dr Raj tana shan marika a hannunsu, Bilal ne kawai bai taɓa marinta ba, shi tausaya mata ma yake yi hakan yasa yake kyautata mata sosai, in kuma yana nan baya barin su Ramish su taɓata ko da ta samu saɓani da su. Tamkar Ramish yasan akwai abin da ya kawota gidansu, haka kawai ya tsani ganinta, ya kuma dakawa Sharrifat warning a kan kada ta kuskura ta sake zuwa mashi da Leesharh part ɗinsu, dan baya son ganin mai kama da inuwarta a arear wajen, Bilal ya yi ƙoƙarin bashi hakuri amma ya nuna a kan hakan zasu iya samu matsala da Bilal ɗin ma, hakan yasa suka kyalesa Leesharh ta dai'na zuwa part ɗin. Wannan dalilin yasa ta dai'na samun information da take bawa masu nikaf a kansa, amma dik da haka tana samun wasu bayanai nasa ta bakin Sharifat ƴar soyayya, zuwansu Kingdom of power dik ta samu labarin wajen Sharrifat kuma ta sanar da masu nikaf, sannan Leesharh ta fara zuwa school kamar yadda Abu Abdussalam ya faɗa, wani lokaci ma Bilal da kansa yake kaita, sai dai fa malaman sun gane takardun karya ne takardun nan na Leesharh, amma basu yi wani magana ba dan a tunaninsu Abu Abdussalam ne ya buga mata takardun karyan da ta tsallake, kunga kuwa idan shi ne ai basu da bakin magana, Allah sarki basu san ba shi bane bai ma san na karya bane. Wannan shi ne kaɗan daga cikin abubuwan da suka faru a baya. To mu koma kan labarinmu. Ko da suka zo gida dan su yi wanka su shirya babu kowa daga cikin family, dik suna wajen taron da Abu Abdussalam ya shirya, taron kara masu girma kuma sai sha biyun dare za'a gabatar da shi a can headquartersu. Hall ɗin nan shake yake da jama'a ga uban securitys ta ko'ina, kada ku manta Abu Abdussalam fa hukuma ce mai zaman kansa, dik wata kaki a karkashinsa take, ba iya ƴan'sanda ko sojoji ba, dik wasu kaki da kuka sani a kasansa suke, so hakan yasa tsaro ya yawaita sosai a wajen, gabaɗaya hall ɗin a kewaye yake da jiga jigan tsaron da ko guda idan da dama ba zasu bari ya gifta ya shiga cikin hall ɗin ba tare da saninsu ba. Ga manya manyan Cameras ta ko'ina, amma fa dik da wannan gabaɗaya hall ɗin kewaye yake da bomb ba tare da saninsu ba. Suna ta shagalinsu dai su kam. Sai around 5 dai'dai Ramish and Bilal suka ƙariso cikin hall ɗik, sun sha gayu cikin two-piece suit mai bala'in tsada. Dama already gabaɗaya familyn Abu Abdussalam da manyan bakinsa kujerun zamansu yana a saman stage, an kawata hall iya ƙawatuwa. Abu Abdussalam yana a tare da Ummie, Sharifat dai tana tare da Leesharh, suna zaune kusa da kusa. Ga wani haɗaɗen mic da aka kawata wajensa domin yin magana. Dikka manyan kai ne a cikin hall ɗin babu yara. Albarkarcin Abu Abdussalam da su Leesharh ai ko a mafarki ba zata taka matsayin kusantar wannan taro ba, amma yau sai gata a cikinsu kuma saman stage waje na musamman, abin gaskiya abin a jinjinawa Abu Abdussalam ne. Manya manyan jami'an Swat sun kai goma me a kewaye da wannan stage da familyn Abu Abdussalam suke a kai, Ramish ya zauna yana ta ƙoƙarin gwada number King domin ya sanar da shi sun wuce Dubai, amma wayar bata shiga, dama tun kwana biyu da suka wuce tun yana Nigeria yake gwada number bata shiga, so sai abin ya fara damunsa yanzu, idan ya kira nasu Momma kuma sai ya yi ringing ba'a ɗagawa, to daga ƙarshe ma network na Tunisia gabaɗaya ta yanke. Sau uku ana kiran sunan Ramish da ya taso ya zo ya nuna tsantsar farincikin da yake ciki amma hankalinsa na kan wayarsa yana ta gwada number ƴan gida. Sai da Abu Abdussalam ya taɓasa sannan ne ya ɗan farga. Tun da suka zauna a wajen Sharifat ta tsaresa da idanu, Sharifat fa ta je bikin Rizwan, amma a ranar Friday ɗin bayan ɗaurin aure suka dawo da Ummienta, dan idan baku manta ba Ummie ita ce uwar su Rizwan a nan Dubai, so ita za'a kawowa amarya, shiyasa ta dawo dan ya shirya masu tarba, da Sharifat ta ce ba zata bita su dawo ba zata biyo tawagar amarya, Abu Abdussalam ne ya kira waya ya ce maza ta bi Ummie su dawo, da suma yanzu suna can yaki ya ritsa da su, wato idan baka da rabon shan wahala fa sai kaga Allah ya fito maka da hanyar da baka zata ba ka kuɓuta da wannan wahala, Allah dai ya cigaba da dafa mana. Miƙewa Ramish ya yi ya nufi wajen mic dake saman stage ɗin, Abu Abdussalam ne ya miƙe ya rakasa har izuwa wajen, suka tsaya a tare, da sauri jami'ai huɗu suka haura saman stage ɗin suka tsaitsaya biyu a ta gabansu biyu a ta bayansu. Ƴan jaridun dake cike a hall ɗin ne suka fara ɗaukarsu hotuna da rahotanni, masu waya ma ba'a barsu a baya ba suka fara ɗaukarsa video da hotuna, a kallah mutane da suke cikin hall ɗin nan zasu fi 500, dan hall ɗin yana da girma sosai kuma sai da ya cika makil, dik tsadaddun kujerun da aka zuba sai da wasu suka rasa wajen zama, Abbie yana da jama'a over. Wani jami'i ne ya taso daga kasan stage ɗin ya hauro sama domin ya tsaya a ta gabansu Ramish ɗin a tsakiya kenan, katon balarabene mai tsawo da kiɓa, faffaɗa da shi. Leesharh da Sharifat sai kallon mutane suke yi suna gulma kasa kasa, suna cikin dressing iri ɗaya na riga da wando arabs dressing. Sun sanya ƙaramin hijabi a kansu, sai dai rigar wandon ya saukar masu har gwiwa, sun fa yi kyau matuƙa musamman ma Leesharh da idanun kowa yake a kanta, tana rike da wayar da masu nikaf suka canza mata, sak irin wayar da Bilal ya saya masu suka bata dan ma su ɓatar da hankalin Sharifat da ƴan gidan kada su ga ne ba wayar da Bilal ya bata bane. To wai wani aiki ne last mission da zata yi masu? Muje dai zuwa. Dai'dai lokacin da wannan jami'in ya iso tsakanin Ramish da Abu Abdussalam da nufin ya ƙarisa ga dai'dai saitin minister Abu Abdussalam. Yana a dai'dai saitin Ramish kamar daka sama aka saki harbi da suka yi saitinta da kyau already, wannan security ya yi masu shigan sauri, gaban goshin Ramish suka saita babu saɓawa, amma sai ga shi sun tarwatsa kan wannan jami'in, nan take wani irin jini jajir ya fallatsa har saman fuskar Ramish, ya kuma wankewa Abu Abdussalam farar alkyabbar dake jikinsa. Kafin sauran securitys dake wajen su yi wani motsi mai harbin ya sake yin harbi a karo na biyu, sai dai a wannan karon ya yi harbin ne a in da ya tarwatsa mirror dake bayansu Ramish, ya yi hakane kuma domin yasan tabbas mirror zata ɗauki hoton daga ina aka yi harbin. Ba mirror ce kamar kowacce ba, akwai camera a jikinta ne, to camerar ya tarwatsa. Kan kace me wasu irin jiga jigan securitys kaki daban daban ne suka wani irin zaro mahaukatan bindigunsu da basa saɓa saiti, nan take securitys sama da guda 20 suka saita bindigunsu tare da kewaye gabaɗaya familyn Abu Abdussalam dake saman stage ɗin. Cikin ƙanƙannin lokaci hall ɗin ya rikice, jama'a kowa ya mimmike yana faman neman ta in da zai gudu, securitys jiga jigai dayawa ne suka nufi gate ɗin hall ɗin domin su hana kowa fita. Wayar hannun Leesharh dake tsaye kusa da Sharifat ce ta fara vibrate, cike da tsananin tashin hankali ta fara bin wayar da kallo. Sai dai a maimakon taga full number, sai taga numbers guda huɗu ne kawai suka bayyana a saman screen ɗin wayar. Tana ƙoƙarin yin picking na call ɗin Sharifat ta jawo hannunta tana faɗin. "Leesharh kizo mu wuce sojoji da ƴan'sandan zasu mayar damu gida". Binta ta yi ba musu amma tana ƙoƙarin yin picking na wannan call ɗin wadda bata san da cewa makunnan wannan nakiya bomb dake kewaye da wannan hall ɗin bane, nakiya ce mai girman tank 900, wadda kuma tana yin picking wannan call ɗin to fa ko tokar gawar mutun ɗaya ba za'a samu a fitar ba, har ita kanta mutuwa zata yi bata sani ba, dan wani irin tashin da hall ɗin zai yi ma wlh ko karfe ne sai ya narke bare ɗan adam, aka ce rashin sani yafi dare duhu, da farko a rashin sani ita da kanta ta shirya yadda za'a sami damar ganin Ramish ɗin har a harbesa bata sani ba, ranar ma ita da kanta a cikin rashin sani tasa aka yi masa wannan harbi na hannu da ciki wannan Billa ya cecesa, yau kuma ita da kanta zata ɗauki nauyin alhakin mutuwar mutane sama da dubu a rashin sani, wannan shi ne bala'i, ana ta amfani da yarintarta da ƙwaƙwalwata ana kashe wanda ake so a kuma cutar ba tare da ta gane ba, ba zama ta iya ganewa ba, domin kuwa ai kunga a kullum a matsayin taimako take yi ake nuna mata, batu na gaskiya sun cuci Leesharh iya cuta, sun saka ta zama the most wanted criminals da familyn Abu Abdussalam suke nema ido a rufe a yanzu. Dan tun lokacin da aka harbi Ramish suke neman su waye suka yi wannan aiki, idan baku manta ba har sun kama mutane biyu waɗan da su Omaid suka hukunta, so tun lokacin suke binciken wanene? Kun ga kuma idan suka yi bincike ita zasu gano, dan masu nikaf kam babu hanyar da zasu kamasu, dan nasu bar wata dama na. (Ko ya zasu yi da ita idan suka kamata🤔💔😥 wlh sunanta sorry, dan tabbas su bisho wato karnikan Ramish ne zasu cinyeta a ɗanyarta) My people's me kuke tunanin zai faru idan Leesharh ta yi picking wannan call ɗin? Akwai gujegujen cakwakiya. Tammat bi hamdillah, a nan na kawo ƙarshen littafin RAWANIN ZALINCI book 2 sai mun haɗu a book 3 nan da ɗan lokacin ƙankani, amma kafin na tafi bari na baki ɗan taɓa ka lashe daga cikin book 3, bari na fara da jera maku tambayoyi. Mekuke tunanin zai faru a kingdom of power? Waye zai mallaki Chuchu na har abada? Waye zai rasata? Waye ya kawo masu hari? Zasu yi nasa ko kuwa a'a? Shikenan Auta ta mutu? Me ta yi wa Hoorain da ta cancanci irin wannan hukunci? A cikin waɗan nan masarautu guda biyar ɗin wani masarauta kuke tunanin zasu yi nasara? Ya Sweetie zata kaya da Black Tiger? Zata fito ko dai ita ma ta tafi kenan kamar yadda kowa in ya shiga baya fitowa? Ya Ronnie zai iya barin Black Tiger ya kasheta ko akasin haka? Ya makomarsu Khadija? Ta mutu ko tana raye? Waye uban wannan baby nata? Zata ɗauki fansa ko akasinsa? Ya makomar Hauwa? Ya makoman maman Zainab?. Jigeta ya makomar Mahnoor da su Ramish suka ɗauke mata miji? Ya zata yi da sonsa da take yi? Shin idan ya dawo dai'dai zai iya tuna rayuwar da suka yi a baya ko akasin hakan? Idan bai tuna rayuwar da suka yi a baya ba dai kun san ba zai waiwayi jigeta ba, dan zai manta da ya taɓa zuwa wajen, ya su Mahreen zasu yi? Ina Pretty and Kamran? Ina mom twins? Waye babansu Pretty? Da gaske Leesharh ta kashe mamarta da kanta? Ya Jasrah take? Ankasheta ko yaya? Waye baban Kamran? Wacece Mammarsa? Meya zaunar da su a forest? Waye wannan jarumi dake taimakon su Pretty a forest? Bayan mammie da cin amanarta ya bayyana idan baku manta ba nace maku akwai wasu maciya amana na kusa da King wa kuke tunanin zasu kasance? Shin mammie zata cinwa birninta? Me Sarina ta ɗauko a ɗakin Momma? Waye Mammie take sonwa Sarina? Tsakanin Aliyah da Mammie wace zata mallaki King? Shin su Yusuf zasu cinwa burinsu? Ina mahaifiyar Hoorain matar Commander Zafar? Kai tambayoyin nan fa ba zasu kare ba, sai dai mun haɗu a book 3 kawai, a nan zamu ragargaje komai, wlh kada ki bari ayi tafiyar book 3 babu ke. TAƁA KA LASHE. *DARK WORLD* "Ronnie get out!". Lion voice ɗinsa ta daki kunnuwan Ronnie dake tsaye a kan ƙafafunsa sam bashi da niyar motsawa daga in da yake, idanun nan nasa sun yi jajir kamar wuta, sai wani uban zufa yake haɗawa kamar wanda aka watsawa ruwa a fuska, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin tsananin tashin hankali na wuce misali. Ko motsawa bai yi ba tamkar ba ƴaƴan nasa bane ya yi mashi magana, ga dikkan alamu suman tsaye ya yi, dan bai taɓa tsammanin kamanin Black Tiger haka yake ba, bai taɓa tsammanin ƴaƴan nasa king of beauty bane. Magic eyes ɗinsa ya juya, idan ya juyasu kuma alamar zallar madarar rashin imani zai aikata, Ronnie yasan da haka amma yana tsaye bai motsa ba. Wasu irin dogaye dogayen...................... Kai taɓa ka lashen nan ma ba zata yi maku a nan ba, ku dai mu haɗu a book 3, dan zan kara rikita maku ƙwaƙwalwa ne kawai, gara na bari. Yau dai na kai kashen book 2, zan ɗan ɗauki hutu in huta ƙwaƙwalwa ta yi fresh ta karo walaƙanci in zo in cigaba sauke maku su da zafinsu. Ba wani jimawa sosai zan yi a hutun ba, kada ku damu. Alhdulillah ala kulli hali, todya no more typing, no more editing, no kore posting, princess Teema taku ta amana zan yi barci har da minshari🥱 much love my people's. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, game buƙata kuɗin karanta shi naira 500 ne normal grp. For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍