**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA 3 PART A NA:Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing Umar Farouq Zango. POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷 Idan zaku iya tunawa a littafi na biyu marubucin ya tsaya a inda hirama take tunanin yadda zata iya fitar da su Uzaifat da uwar mayu da sauran yayanta daga cikin kejin da Maridi zurkas ya sa su. To Insha Allahu zamuji yadda zata kasance a cikin littafi na uku, ku biyoni muje. Marubucin yaci gaba da cewa Lokacin da Hirama ta aiyana a ranta cewa komai rintsi sa tsanani sai ta kubutar da rayuwar su lafirat sai gaba daya taji wannan abinci ya fita daga ranta don haka sai ta sa kamarta ta ture kwanon gaba daya har ya bingire. Tsam! Ta koma shimfidar ta ta kwanta tayi lami tana mai rufe idanunta tamkar barci take yi. A dai dai lokacine dan uwanta Hiram ya shigo cikin dakin. Koda ya ga hirama ta zubar da nata abincin ko rabinsa bata cinye ba, sai ya kama kyalkyala mata dariya. Nan take ya dauki ragowar naman ya cinye yana cewa, yarinya kin bar lagwada ta wuceki. Mu kam bazamu bar wannan dadi ba. Lallai zamu kwana biyu muna walima. Gama fadin hakan ke da wuya sai shima Hiram ya koma kan shimfidar sa ya kishinguda. Ba dade da kwamciya ba kuwa shima barci ya kwasheshi. Hirama dake kwance a can gefe daya tayi lami duk tana kallon sa kawai tana ta sake saken zuciya da kuma tunani da fargaba sun cika mata rai. Abinda ya fara fadowa ran hirama a rai shine ta yaya zata iya ceton rayuwar su lafirat alhalin zurkas da maziba na nan. Kai bama su na ko dan uwanta Hiram ba zai barta ba. Wata zuciyar tace da ita, to me zai hana ki bari sai dare ya raba sunyi bacci sannan ki sadada Kije ki bude kejin da aka zuba wadannan biladama da aljanu ki kubutar da rayuwar su ina taso ki bisu ku tafi tare kema ki hakura da rayuwa da iyayenki da yan uwanki har abada. Koda aiyana haka sai zuciyar hirama ta buga da karfi sosai sakamakon tunowa da yanayin yadda kofar kejin take. Ita dai kofar kejin ko tabbata kayi sao tayi kara, saurin Karar ya cika codon kunne don haka duk irin bacci da zurkas da maziba ke yi da zarar an taba kofar wannna keji sai sun farka. Hirama ta tuna cewa shi kansa dan uwanta Hiram ba karamin matsala bane a gareta domin idan dare yayi ana rufe kofar wannan daki da suje kwance kuma ko yaya ta mike tace zata je ta bude kofar dakin sai tai motsinta da zarar yaji motsin kuwa sai ya tina mata asiri. Lokacin da Hirama tazo nan a tunaninta sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya, nan fa ta sake afkawa cikin sabon kogin tunani. Bayan ta jima tana tunani sai hawaye ya sake zubo mata sakamakon mugun nufin da ya fado mata arai wanda shine kadai mafitarta idan har tanaso ta cimma wannan buri nata na kubutar da rayuwar su Uzaifat. Ha dare ya fara rabawa hirama idanunta a bushe suke bata rintsa ba kuma zuciyarta sai faman sake sake take. Tana cikin wannan hali ne Zurkas da maziba suka shigo cikin dakin suna magana sai tayi sauri ta ruf da ciki kuma ta rufe idanunta tayi kamar ta dade da yin bacci har da Jan dogon munshari kamar yadda dan uwanta Hiram ke yi. Dama zurkas ne akan gaba rike da fitilar. Maziba na biye da shi. Kai tsaye zurkas yaje kan Hirama ya tsaya ya dallare fuskar ta da fitila domin ya tabbatar da baccin take ko kuwa lamo tayi. Bisa mamaki sai yaga idanunta basu motsa ba kuma gashi tana Jan dogon munshari. Kawai sai yayi murmushi ya dubi maziba yace, nifa ban yarda da wannan yar taki ba domin gani nake zata iya haintarmu a ko yaushe tayi mana nasarar wannan da muka damu. Kodajin wannan batu sai Maziba ta bushe da dariya ta dubeshi tace, Haba mai gida ta yaya Maziba zata iya kubutar da wadannan fursunoni namu ba tare da muji motsinta ba. Kai kafin ma ta bude kofar wannan daki nasu ta fita na tabbata dan uwanta Hiram yaji motsinta. Ka san kuwa yana jin motsinta zai tona mata asiri. Kai koda ma baiji motsinta ba tayaya zata iya bude kofar wannan keji ba tare da mu muji motsinta ba. Na rantse da darajar auren mu idan kuwa tayi wannan ganganci ni da kaina zan yi mata kisan gilla sannan na dafeta tayi luguf mu cinye namanta don mu huce takaici. Zurkas yace, Haba ai idan kika kasheta farat daya Mun yi mata adalci ma. Ai tana ji tana gani da ranta zamu daurewa tamau sannan mu dinga yankar sassan jikin ta da kadan kadan muna cinyewa har akai munzalin da zata mutu a haka. Yanzu dai sai kj zo mu koma can dakin mu mu fara cin naman. Ni anya ma kuwa yau zanyi barci saboda murnar wannan garabasa da muka samu? Maziba ta bushe da dariya tace ai yau batun bacci ma babu shi kwana zamuyi muna rakashewa ni da Kai. Irin soyayya da muka yi tun a daren farkon auren mu sai mun maimaitata a yau. Koda jin wannan batu sai zurya maziba ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya kama hannunta suka fice daga cikin dakin. Sun fita sai zurkas ya rufe kofar dakin yasa wani katon kwado ta waje ya datse kofar. Cikin mamaki maziba ta dubeshi tace, saboda me zaka rufe yaran nan ta waje. Zurkas yace, nifa hankalina bai kwanta da wannan yarinya Hirama ba gani nake a koda yaushe zata iya haintarmu, gwara dai mu dauki kwakkwaran mataki akan ta. Maziba tayi murmushi tace, kaima kana da gaskiya domin kuwa riga kafi yafi magani. NAn take zurkas da maziba suka tafi izuwa nasu dakin suka Zauna suka hau cin naman su shan ruwan giya. Da suka cika cikinsu sai zurkas ya dauko wata katuwar ganga tasa ya kama koda, ita kuwa maziba ta dinga tika rawa a gabansa suna ta kyalkyala dariya cikin farin ciki da annusuhuwa. Da yaje dare ya raba sosai sai dajin gaba daya ya dinga amsa kuwwar dariyarsu da wannan koda. Al'amarin Hirama kuwa, duk irin Hirar ta wakana tsakanin zurkas da maziba taji don haka bata san Sa'adda ta fashe da kukan takaici ba. Babu abinda ya bakntamata rai face yadda taji iyayen ta suna cewa zasuyi mata kisan gilla muddin tayi yunkurin tserar da rayuwar wadannan fursunoni. Bayan hirama ta dade tana tunani da kuka sai dabara ta fado mata akan yadda zata fita daga cikin dakinsu ba tare da dan uwanta Hiram yaji motsinta ba. Nan taje ta aiyana a ranta cewa lallai a cikin wannan dare zata fita kuma ta yanke don dukkanin kauna tsakaninta da iyayenta don haka yanzu wannan fita da zatayi ta sallama ranta ne ko tayi nasara ko akasin haka, amma babu gudu kuma babu ja da baya. Ba tare da bata lokaci ba hirama ta mike tsaye tsam cikin sanda da lambo ta bude wata katuwar bakar akwatinta wadda take ajiye tarkacen ta a ciki ta fiddo wat yar karamar kwalba mai dauke da wani Jan gari a ciki. Hirama ta bude kwalbar ta zazzaga garin kadan akan tafin hannunta. Kawai sai taje kan hiram ta sa bakinta ta hurawa garin iska ya vade fuskar Hiram. Faruwar hakan ke da wuya sai Hiram yaja dogon numfashi, bisa dalilin shakar wannan hodar gari sannan yaci gaba da bacci mai nauyi. Koda ganin haka sai farin ciki ya lullube hirama ta juya tanufi bakin kofar dakin nasu tasa hannunta ta zare sakatu biyu ta janyo kofar da nufin ta bude, sai taji kofar ta ko budewa. Al'amarin da ya mutukar girgiza ta kenan kuma ya bata tsoro ta fahimci cewar an kulle kofar ta waje. Nan fa hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ta shiga sabon tunani bisa neman mafita. Tana cikin haka ne dabara biyu ta fado mata ta kama bangon dakin ta hau tana tafiya akansa kamar kadangaruwa har ta USA inda rufin dakin yaje wanda aka yishi da itatuwa da manyan ganyayen bishiya mai fadi. Kawai sai ta sa hannunta ta zare itatuwa shida a hankali, sai ga wawakekiyar hanya a saman rufin daki. Kawai sai ta zuro kanta cikin hanyar ta dubi gabas da yamma kudu da arewa bata ga kowa ba. A wannan lokaci tana iya hango zurkas da maziba daga can nesa suna ta sharholoyarsu ta kida da rawa. Cikin sanda hirama ta hau kan rufin saman dakin tana tafiya da ruf fa ciki har ta biyo saman katangar dakin ta sauko kasa tamkar kadangaruwa. Tana dira kasa ta ruga bayanta wata bishiyar ta labe ta ci gaba da hangen iyayenta a wannan lokaci ne jikinta ya kama Bari saboda tsananin tsoro da fargaba saboda tasan cewa ko yaya asirinta ya tonu tata ta kare kam. A rayuwar Hirama babu abinda jikinta baya so irin sanyi, kuma gashi a wannan lokaci ana wata irin iska mai sanyin gaske. Nan da nan jikinta ya kama bari, bakinta ya kama rawa har hakoranta na sama suka gogi na kasa. Karar haduwar hakoran nata ne ya baiyana a fili kuma a kunnuwan zurkas da maziba don haka sai suka tsaya cak! Ga barin kida da rawar suka kura idanuwansu suna kallon kowacce kusurwa. Ita kuwa Hirama sai tayi sauri ta datse bakinta ta rukeshi GAM da hannunta a lokacin da taji tsoro ya kara dabaibayeta fiye da kowanne lokaci. A wannan lokaci inda wani abu kanka ni zai dungureta ta baya zata iya sakin fitsari saboda tsananin razana. Tsawon dakika sittin maziba da zurkas sun tsaya cak! Suna sauraro da kalle kalle basu ga komai ba kuma basu ji motsin komai ba face sautin gyare da ya cika dajin gaba daya. Zurkas yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi maziba yace, nifa naji kamar motsin wank wani abu, bari naje na bude dakin yaran can na gani ko Hirama ce ke kokarin fitowa don ceton fursunonimu. Koda gama fadin haka sai zurkas ya yunkura zai Mike tsaye. Caraf! Sai maziba ta cafo hannunsa ta zaunar da shi tace, Haba maigida ai amfani hankali aiki dashi. In banda abinka ta yaya Hirama zata iya fitowa daga cikin dakinsu alhalin muna hango kofar dakin nasu daga nan. Ai yau anan zamu zauna mu ci gaba da hirarmu domin mu tabbatar da tsaro kuma mu Kawar da zargi har gari ya waye ko barci ba zamuyi ba. Koda jin wannan batu sai zurkas ya bushe da dariya sannan ya rungume maziba suka kishingida a kasa ta kwanta bisa kirjinsa yana mai cewa, madallah da ke matata ma'abociyar jikina da basira. Lallai kuwa yau ko rintsawa ba zamuyi ba, kawai mu ci gaba da hirarmu. Sa'adda hirama taji wannan batu sai hankalinta ya kara dugunzuma ainun ta tabbatar da cewa Yaufa tashi ga TSAKA MAI WUYA, domin bata isa ta sake motsawa ba daga inda take labe domin ko yaya ta motsa sai zurkas sunji motsinta tunda yanzu sun daina kisa da rawa bare wani abu ya dauke musu hankali, duk da cewa kuwa akwai yar tazara a tsakaninsu. Haka dai hirama taci gaba da hangen su zurkas zuciyarta cike da tsoro da fargaba kuma tana ta tunanin mafita, amma babu har tsawon sa'a guda ya zamana cewa bata da sauran buri akan rayuwarta kawai sai ta rungumi kaddara ta ci gaba da jiran gari ya waye asirinta ya tonu iyayenta su hallaka ta. Allah sarki, hakika ita hikima baiwa ce, kuma komai na duniya rabone. Shikuwa rabin kwado baya hawa sama, koda ya hau kuwa sai ya fado. Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace mai rabon ganin badi sai ya gani. Kwatsam! Bazata ba tsammanin sai hirama ta tuni da wannan garin hodar bacci dake cikin karamar kwalbar dake tare da ita. **DAKARUN MUSULUNCI** Littafi Na Uku 3 Part B ✍️ Na: Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing Umar Farouq Zango Posting: Najibullah Muhammad 🥷🥷 Nana take ta dauko kwalbar ta budeta zazzaha hodar akan tafin hannunta sannan ta dauke numfashinta ta hira hodar da iskar bakinta. Nan take hodar taji iska, kamshinta ya tafi har zuwa inda zurkas suke albarka cin iska mai karfi da take kadawa a cikin daren. Koda zurkas da maziba suka shaku wannan hoda sai suka fara lumshe idanu suna cikin wannan hira tasu. Basu ankara ba kuwa sai duk su biyun suka bingire suka kana bacci mai nauyi. Kafin ajima munsharinsu ya cika dajin gaba daya. A wannan lokaci ne gagarumin farin ciki ya lullube Hirama ta fito daga inda take a labe ta ruga izuwa inda wannan keji yake ta bude kejin. Koda ta ga fursunoni gaba dayansu a kwance suje suna ta shara baccin tsafi., sai hankalinta ya dugunzuma domin ba zata iya daukar su gaba daya ba. Ta san dai zata iya daukar biladama guda uku amma bazata iya daukar uwar mayu da sauran yayanta ba. Nan fa ta tsaya tana tunanin mafita nan take kuwa dabara ta fado mata ta ruga da gudu izuwa dakin mahaifinta zurkas inda yaje ajiye kayan tsafe tsafensa. Da shigarta cikin dakin ta zubawa tarkacen tsafin idanu wadanda adadinau yafi dubu. Wasu daga cikin kayan tsafin ma sari suke dole ta rinka tashen hancinta. Kawai sai idanunta suka kai kan wata farar siririyar kwalba mai dauke da shurin gari a ciki. Hirama ta kurawa kwalbar idanu nan take ta tuni da wata rana Sa'adda zurkas ke yiwa maziba bayanin amfamin wannan shurin gari, a lokacin hirama na labe a kofar dakin tana kallon su da sauraronsu basu sani ba. Abinda hirama ta iya tunowa kawai shine, taji zurkas yana cewa. Wannan hodar tana yin aiki casain da tara amma fa idan akayi aiki da ita bisa kuskure za'a iya asarar rayuka da duk wani abu mai tsiro daga cikin kasa a cikin dajin gaba daya. Sa'adda Hirama ta gama wannan tunani sai kawai taje ta dauki wannan kwalbar ta fita da gudu ta koma can inda kejin yake. Da zuwa sai ta fara dauko lafirat, Uzaifat da Abul shaja'a ta sabasu a kafada tamkar ta saba gawa sannan ta busawa su uwar mayu wannan sbudin garin tsafi cikin yanayin tsoro domin duk jikinta kyarma yaje domin gani take kamar zata iya sauya musu kammani ko ta zamo sanadin ajalinasu. Koda garin hodar ya basu akan uwar mayu da ragowar yayanta sai duk suka farka daga bacci a firgice suka yunkura zasu rafka ihu sai hirama ta zazzare musu idanu tana mai yi musu nuni da su nutsu. Dama ita uwar mayun a nutse ta mike zaune tayi nazarin abinda ke faruwa. Hirama ta dubi uwar mayu tace, abinda nake so daku shine, Yanzu zamuyi gudu iyakar marfinmu har tsawon sa'a shida, idan ba muyi haka ba lalli dayanmu ba zai tsira ba daga sharrin iyayena ba. Koda gama fadin haka sai Hirama ta juya ta falfala da azababben gudu izuwa cikin daji tana dauke da Uzaifat. Koda ganin haka sai uwar mayu da yayanta suka firfito daga cikin kejin suka yi koyi da hirama wato suma suka ZAGE DANTSE wajen yin gurin mutuwa, musamman ma da suka ga Hirama ta basu rata mai yawa wacce koda karfin tsafi ba su isa su cimmata ba. Tun da uwar mayu tazo duniya bata taba gamin wata halitta nai karfin gudu ba kamar Hirama. Iat ma uwar mayu ta zage damtse iya karfinta tana gudu har ta wuce dukkan yayanta da tazarar zira'i arbain amma da kyar take iya hango kurar uwar Hirama. Kamar yadda hirama tayi bayani haja al'amarin ya kasance, wato sai da suka shafe sa'a shida suna tsala gudu amma har alfijir ya keto, rana ta fara budewa basu tsaya ba. Uwar mayu da yayanta suna gudu suna haki kamar ransu zai fita, wani lokacin ma sai kaga yayan uwar mayu suna faduwa kasa amma saboda tsoron mutuwa sai kaga sun mike zumbur sun ci gaba da tafiya. Lokacin da hirama ta iso karshen dajin huzurul has dai dai inda yayi iyaka da dajin cikin birnin shumbul, sai Hirama ta fadi kasa tana haki ta dauke Lafirat, Uzaifat da Abul shaja'a a kasa a hankali ta zuba ido akan hanya domin ta ga isowar uwar mayu da yayanta. Sai da ta shafe rabin sa'a a zaune tana kallon hanya amma ko alamun su bata hango ba. Al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinta kenan ta fara tunani cewa lallai iyayenta sun farka daga barcin sun biyo bayansu har sun cimma uwar mayu da yayanta. Ba kamai ne yasa Hirama tayi wannan tunani ba ba face sanin cewa iyayenta da tsananin karfin gudu ninkin nata sau uku. A Yanzu dai da ta iso wannan iyaka ta dajin huzurul has ta san cewa ita da su Uzaifat sun tsira daga sharrin iyayenta domin basu isa su ketara wannan iyaka ba saboda haja dokar tsafin zurkas ta shirya masa shi da matarsa maziba, amma banda yayansa. Idan kuwa har suka yi gangancin haura iyakar nan take jikinsu zai kama da wuta gaba daya ya babbake sai dai kashi yayi saura. Rabin sa'a na cika sai hirama ta jiyo ihun uwar mayu da wadansu dai daikun yayanta daga can nesa. Hirama ta tsaya cak! A inda take bata motsa ba bare tayi yunkurin komawa da baya don kai dauki, amma sai ta mike tsaye ta ci gaba da kallon hanya. Jim kadan sai ga uwar mayu da ragowar yayanta su goma sha biyar kacal sun kasa uban tsere da zurkas da maziba. Uwar mayu da yayanta suna ihu suna waige. A duk Sa'adda suka wai ga suka ga tazararsu da su maziba bata wuce taku uku ba. A haka ne kuna maziba da zurkas suka ci gaba da cafke yayan uwar mayu suna tsintsinkasu tamkar suna kakkarya kara suna cinyewa danyi akan hanya ana cikin gudun. Kaico! Nan fa uwar mayu taga inda aka fita maita domin maziba domin da mijinta zurkas suna cin naman yayanta ne da jini. Kai hatta kashinsu basa zubarwa taunewa suke. Daga cikin yayan uwar mayun duk wanda ya waigo yaga ana walima da dan uwansa sai ka ga ya kara firgicewa kuma ya kara karfin gudunsa, amma duk ya zama a banza domin kuwa zurkas da maziba kure musu gudu suke yi sna cafkeau suna cinyewa. Kafin akai iyakar dajin huzurul has tuni zurkas da maziysun cinye gaba daya yayan Uwar mayu saura daya JAL da ita kanta uwar mayun. Koda uwar mayuda danta suka tsallaka karshen dajin suka dira a cikin dajin birnin shumbul suka fadi a gaban Hirama sai uwar mayu ta rungume dan ta ta fashe da matsanaicin kuka. Ba shiri zurkas da maziba sukayi turjiya basu yarda kafarsu sun taka kasanr dajin birnin shumbul ba. Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin Hirama da su zurkas kallo na tsananin Kiyayya da takaici. Cikin tsananin fushi da takaici fuskar sa ta kama yatsina kamar zata zazzago kasa yace, ya ke yata hakika kin ci amanarmu ni da mahaifiyar ki kuma in badon saarki tayi yawa ba da baki isa ki tsallake sharrinmu ba. Ni yanzu abinda nake rokonki shine ki bamu wadannan biladama guda uku dake gabanki da kuma uwar mayu da danta guda daya wanda ya rage mu cinye su yanzu taje a gabanki idan kikayi haka kin wanke dukkan laifi ki a wajenmu kuma zamu yafe miki bisa alkawarin ba zamu cutar dake ba inyaso sai ki bimu mu koma gida. Ina so ki fahimta cewa ba yar Adam bace ke ba dodo bace, kuma ba aljana bace. Babu inda zakije ki yi rayuwa mai dadi a fadin duniyar nan face tare da mu, domin duk inda kikaji za'a kyamaceki a dinga tsoronki. Koda zurkas yazo nan a zancensa sai hirama ta bushe da dariyar mugunta, lokaci guda kuna ta turbine fuska, a lokacin da hawaye ya zubo mata ta dubi zurkas tace, ya kai abbana ina son ka sani cewa an dade ana ruwa kasa na tsotsewa don haka ba zaku iya yaudarata ba da daina bakinku kai da uwata. Na sanku kuma na san Ma'anar ko wanne motsi naku. Na yarda na fuskanci kowanne irin yanayi da zan tsinci kaina a ciki. Kalmata ta karshe a gareki itace karshen zalincinku ga sauran halittu yazo. Ku saurari ranar da ajalinkh zai riskeni a cikin wannan dajin huzurul has. Wannan shine bankwana nawa a gareku. Gama fadin hakan ke da wuya sai Uzaifat Lafirat da Abul shaja'a suka farka daga dogon barcin da sukeyi. Cikin tsananin mamaki duk su ukun suka mike tsaye, suka kama kallon su zurkas da Hirama. Nan take Lafirat ta gane abinda yafaru saboda haka sai ta dubi Hirama tace, ta yaya kika zabemu kika guji iyayenki har kika kubutar daga sharrinsu? Koda jin wannan tambaya sai Hirama tayi murmushi tace, iyayena azzalumaine wadanda suka shafe daruruwan shekaru suna zalunci a doron kasa, ni kaina za su iya salwantar da rayuwata don kada na hanasu zaluncinsu. Tuni na yanke kauna tsakanina da su bisa wannna daliline na yanke shawarar na kubutar da rayuwarku kuma na bimu izuwa inda zakuje domin naje na fara sabuwar rayuwa a wani bangare dabam. Kafin Hirama ta gama rufe bakinta tuni maziba ta tsandara ihu sannan ta yunkura zata daka tsalle ta fada kanta sai zurkas yayi sauri ya riketa tamau da hannayensa biyu ya daka mata tsawa yace, baki da hankalina ko kuwa kin manta cewa idan ni ko ke dayansu ya shiga dajin gaba take zai hallaka? Koda jin haka sai maziba ta fashe da kukan bakin ciki tace, yanzu ni menene amfanin wannan bakar haihuwa da mukayi? Gwara ka kyakeni na kasheta koda kuwa nima zan hallaka. Hawayen takaici ya zubowa zurkas yace, rabu da ita amma su abokan tafiyar ta idan sun isa su tako izuwa nan inda muke mana. Koda jin haka sai Uzaifat ya fusata ya zare takobinsa zai afkawa su zurkas sai Lafirat tayi caraf! Ta rukoshi ta dawo da shi baya ta dubeshi tace, aikin dake gabanmu gagarumin akan wannan. Kayi hakuri muje mu dawo babu mamaki ajalinsa a wuyanka zai rataya. Gama fadin hakan ke da wuya sai Lafirat ta kama hannun Uzaifat ta jashi suka juya suka ci gaba da tafiya. Abul shaja'a uwar mayu da danta guda daya da garage suka take musu baya. Zurkas da maziba kuwa suka bisu da kallo kawai suna ciza yarda cikin tsananin takaici domin suna ji suna gani babu wata illah da zasu iya yi musu. Ba tare da wai waye ko tsayawa ba su Uzaifat suka ci gaba da tafiya suka durfafi birnin shumbul kai tsaye. Da yake Lafirat ce ta san hanya itace akan gaba. ************* ******* Najibullah Muhammad ************ ********** Koda ta ga su Uzaifat sun zare takubbansu suna waige waige da hange hange sai ta yi murmushi tace, ku kwantar da hankalinku ai muna da sauran daoguwar tafiya kafin mu isa birninmu, domin a kalla nan gaba sai mun tafiyar sa'a bakwai sannan zamu isa kofar birnin shumbul. Kuma ina tabbatar muku da cewa daga nan har izuwa birnin shumbul ba zamu sake haduwa da wani mugun tarko na mahaifina ba face tsirarun yan fashi, muggan dabbobin daji da muggan aljanu. Koda jin haka sai Uzaifat da Abul shaja'a suka fara mayar da takubbansu cikin kufe suka ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali. Haka dai suka wanzu suna ta keta daji har izuwa kusan sa'a uku, a sannane magriba ta kunno kai. Koda Uzaifat ya ga magriba ta kusa sai ya dubi Abul shaja'a da uwar mayu tare da danta yace, ina ganin zaifi kyau mu yada zango tunda magriba ta kusa, in yazo bayan munyi sallar ishai kuma munck abinci sai mu ci gaba da tafiya. Cikin hadin baki Abul shaja'a uwar da danta suka ce, lallai haka ya kamata ayi. Ba tare da neman shawarar Lafirat da hirama ba aka tsai da tafiya, Uzaifat ya kafa tanti sannan yayi alwala. Cikin sauri Abul shaja'a da uwar mayu suna sukayi alwala suka bishi yayi musu sallah. A wannan lokaci Lafirat na zaune a gefe daya ta kurawa su Uzaifat idanu tana kallon Yadda suke yin ibadarsu, abin na birgeta tana ta murmushi. Sa'adda Hirama taga yadda su Uzaifat suke wannan ibada sai ta cika da tsananin mamaki domin ita bata taba sanin cewa akwai wani ubangiji da ake bautawa ba face aljanu. Hirama ta mike tsam daga inda take zaune ta koma daf da Lafirat ta zauna sannan ta dubeta tace, wadannan kuma wane irin sihiri ne su Uzaifat sukeyi? Koda jin Wannan tambaya sai Lafirat tayi dariya sannan tace, ai wannan abinda kika ga suna yi ba sihiri bane, aikine na bauta ga ubangijin su, wato abin dogaronsu wanda ni kaina na aminta dashi kuma ako yaushe zan iya karbar wannan addinin nasu. A Yanzu haka uwar mayu ma da kike gani ta karbi addinin nasu. Cikin mamaki Hirama tace, to menene yaja hankalin uwar mayu ta karbi wannan addini alhalin bata sanshi ba bata san komai a kansa ba? Lafirat tace, babu bukatar na baki amsar wannan tambaya domin ance gani ya kori ji. Lallai idan kina tare damu zaki ga amsar wannan tambaya da kika min da idanun ki. Bayan su Uzaifat sun gabatar da sallar ishai sai aka ci abinci, sannan Uzaifat, Abul shaja'a da Lafirat sukayi shimfida kowanne ya kishingida domin ya huta. Dama an kunna wuta a tsakiyarsu don jin dumi sakamakon sanyin da ke kadawa a cikin dajin, kuma sun yiwa wutar kawanya suna daf sa juna. Duk Sa'adda Uzaifat ya dago kai ya sai ya hada ido da Lafirat, sai suyiwa junansu murmushi kawai kowa ya sunkui da kai. Babu wanda ya lura da wannan hali da suke ciki face Hirama don haka sai tayi dariyar ciki kawai tayi shiru ba tace komai ba. Ana cikin haka ne Hirama ta taso daga inda take zaune ta zo daf da Uzaifat lokacin da yadaga kansa sama yana kallon taurari, nan take ya shiga tunani mai zurfi sai ga hawaye na zubo masa. Babu wanda ya lura da wannan sabon yanayi sa Uzaifat ya shiga face Hirama don haka sai ta dubeshi cikin mamaki tace, ya kai wannan jarumi mai kirar sadaukai Ina dalilin zubar wannan hawaye a idanunka? Kodajin wannan tambaya sai Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, yake wannan ma'abociyar taimako a garemu kiyi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da hawaye ba face tunowa da irin halin da dan uwana Ukashat ya jefa kansa a ciki na bijirewa ubanhijinmu, kuma ya hada kai da makiyanmu su sarki shaaran domin ya rushe birninmu saboda kwadayin duniya kawai. Ashe dan uwa na iya barin dan uwansa na jini saboda abin duniya? Sa'adda Uzaifat yazo nan a zancensa sai ya ga itama Hirama hawaye ya zubo mata. Hirama ta dubi Uzaifat cikin yanayin ban tausayi tace, ni fa ma tuna cewa iyayena na bari da dan uwana saboda bambancin rarayinmu bisa mugayen dabiun da muka dade munyi wadanda na gabe cewa basu dace ba. Koda jin haka sai Uzaifat yaji ya kamu da tsananin tausayinta don haka sai ya dubeta yace, ya ke hirama inayi miki fatan samun babban rabo na karbar addininmu domin da zarar ki karbeshi zaki sami nutsuwa da kwanciyar hankali kuma mune zamu maye miki gurbin iyayenki da dan uwanki da kika rasa. Saboda dukkanin musulmi na kwari yana kaunar dan uwansa musulmi kamar yadda yake kaunar kansa. Kafin Hirama ta kara cewa wani abu sai kawai suka ga Lafirat ma ta so daga inda take kishingide ta dawo daf da Uzaifat ta zauna a gefen shimfidar sa sannan ta dubi hirama tace, ya ke wannan ma'abociyar kyautayi da taimako a garemu hakika na tausaya miki bisa yadda kika danne zuciyar ki kika sabawa kyayenki domin ki tserar sa rayuwa mu. Amma ki sani cewa nice abar tausayi fiye da ke, domin ni na tsani iyayen nawa kamar yadda nasani mutuwa ta kuma bani da burin da yafi na ga na hallaka su da hannuna don kawar da bakin ciki da takaicin da suka dasa min a zuciyata. Kafin wani a cikinsu ya kara cewa wani abu sai suka fara jiyo wani irin gurnani mai ban tsoro acikin duuwar dajin. Ba shiri dukkanin su suka mike tsaye Uzaifat, Lafirat da Abul shaja'a suka zare takubbansu. Hirama da Uwar mayu suka gyara tsayuwa gami da bude hannayensu masu dauke da manyan yan yatsu da farata cako cako suna jiran ko takwana. Ba zato ba tsammani sai ga wasu murguza murguzan kuraye masu tsananin kwarjini da ban tsoro sama da guda dubu sun firfito daga cikin duhuwar bishiyoyi da ciyayi suka yi musu kawanya kuma suka rinka matsowa a hankali. A iya rayuwar Uzaifat da ta Abul shaja'a ko a labari basu taba jin irin wadannan kuraye ba. Uzaifat ya dubi Hirama da Uwar mayu yace me kuka sani dangane da wadannan kuraye. Duk su biyun sai suka gyada kai alamar cewa basusan komai ba akansu. Uzaifa ya dubi Lafirat yace, ke kuma fa kin san wani abu akan wadannan kuraye? Lafirat ta jinjina kai tace kwarai kuwa na sansu. Wadannan kuraye tsafaffune kuma mahaifina ne yayi musu kiwo na musamman kuma ya tsafance su ya zamana cewa ya killacesu. Nataba ji yace ba zai taba fito da su b sai ya gama fita yakin karshe tsakanin birninmu da birninku na darul husuf. Duk yadda akayi mahaifina da dakarunsa suna nan Musa da inda muke. Koda jin wannan batu sai uwar mayu da hirama suka firgita ainun domin su Kansu sun san masifar sarki sha'aran da matsayin sa a fagen yaki da yadda yake da karfi akan dukkanin halittun dake cikin dazuzzukan da suka kwaye kasasrsu. Lokacin da Uzaifat da Abul shaja'a suka a saura kiris wadannan kuraye su cimmusu sai sukayi kabbara cikin hadin baki suka afkawa kurayen suka hausu da sara da suka, suma kurayen sai sukayi musu rubdugu. Nan take wurin ya yamutse aka kacame da azababben yaki ya zamana cewa Uzaifat da Abul shaja'a sun fara samu nasara akan kurayen domin duk wacce suka sara ko suka soka sai dai kaga jikinta ya dare ko ya bule jini na zuba. Amma a bangaren Lafirat da hirama da uwar mayu abin ba haka yake ba domin ko kadan sun a kasa cutar da kurayen saboda duk Sa'adda suka karci jikin kuraye ko suka saresu sai kaga ko kwarzanewa basa yi, suma kurayen sun kasa yiwa su Lafirat lahani da kaifin faratnsu da na hakoransu, amma kuma duk Sa'adda suka bangajesu sai kaga sun kaisu kas wani lokacin ma har turmushesu suke yi suna dudufniya a Kansu. Lokacin da Uzaifat ya lura da halin da su Lafirat suka shiga sai ya daka tsalle daga inda yake yana mai kwalla kabbara da karfi fiye da ko yaushe ya tarwatsa kurayen yaci gaba da ragargazarsu, kafin a jima Uzaifat ya kashe sama da kuraye dari biyu. Shikuwa Abul shaja'a ya kashe dari. Ganin wannan nasara da suke sanine itama uwar mayu tayi koyi da su ta rinka kwalla kabbara sai gashi tana guda cikin kurayen da tsinin faratan hannayenta suna zubewa kasa matattu. Kafin kace wani abu itama ta kashe sama da guda hamsin. Kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji an busa wani irin kaho mai karfin sauti wanda ya cika dajin gaba daya. Dajin sautin kahon sai sauran suka daina gumurzun dasu suka ja da baya suka tsaya cak tamkar basu da rai a jikinsu. Kawai sai su Uzaifat suka jiyo motsin sawayen dawakai a can samansu bisa wani dogon tsauni da yayiwa dajin gaba daya kawanya. Koda su Uzaifat sukayi arba da rundunar mayakan birnin shumbul wadanda adadinsu ya wuce miliyan biyar. Sarki sha'aran, Ukashat da sazirat ne akan gaba bisa wadansu ingarmun dawakai sunyi gagarumar shigar yaki. Nan taje aka fara kallon kallo tsakanin sarki sha'aran da su Uzaifat. Sazirat da Lafirat suka fara hararar junansu, haja ma Uzaifat da Ukashat kowannesu zuciyarsa na tafarfasa kamar su ruga su afkawa juna. Shi kuwa sarki sha'aran koda ya dubi au Uzaifat ya gansu yan kalilan sai ya bushe da dariyar mugunta. Lokaci guda ya murtuke fuska tamkar an aiki masa da sakon mutuwa ya dubi Lafirat a fusace yace, kaiconki yata, hakika kin bani kunya kuma kin ci amanar kulawar da na vakj a matsayina na mahaifinki Tun kina jaririya. Tabbas yanzubne zaki yi nadamar butulcin da kika yi mini. Kafin sarki sha'aran ya gama rufe bakinsa sai Lafirat ta tari numfashin sa tace, Kai tsohon banza annamimi mai abin kunya, kayi sani cewa har abada ba zan yi nadamar butulcin da nayi maka ba, domin na tsaneka kamar yadda na tsani mutuwa ta. Nayi kuka da bakin ciki matsanaici da ya zamo kaine mahaifina, tabbas inda ina da ikon sauyawa kaina asali da suna da tuni na sauya. Har abada tsakanina da kai da duk wani mai goyon bayan ka babu kauna kuma babu abinda zai rabamu face kaifin takobi. Koda ji haka sai sarki sha'aran ya bushe da mahaukaciyar dariya wacce amsa kuwwarta ta cika dajin gaba daya. A wanna lokaci ne sarki sha'aran ya lura da kurayensa na tsafi wadanda su Uzaifat suka karkashe. Nan take jikinsa ya kama tsuma, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone. *DAKARUN MUSULUNCI* Littafi Na 3 Part C ✍️ Na:Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing Muhammad Umar Zango. Posting Najibullah Muhammad 🥷🥷 Marubucin yaci gaba da cewa.. Kawai sai ya dubi sazirat da ukashat yace, ku sauka izuwa kasan tsaunin nan ku gama da abokan gwaminku. Ya sake dubdan sarkin yakinsa yace, kai kuma ka sauka ka kashe Abul shaja'a dama yana daga cikin manyan mayakan birnin Darul husuf masu ci mana tuwo ak w arya. Ni ku kyaleni da hirama da uwar mayu zanyi maganin su. Koda jin wannan umarni sai ukashat sazirat da sarkin yaki suka saki linzami dawakansu suka fara saukowa kasa dgaga kan tsaunin sannayan shima sarki shaaran ya biyo bayan su ya juya ya dubi sauran miliyoyin dakarunsa yace, kada dayan ku ya sauko nan kasa ba tare da kunji umarni daga gareni ba. A dai dai wannan lokacine uzaifat, lafirat da Abul shajaa da hirama da uwar mayu suka dunkuke guri daya suna masu hada bayansu suna kallon kowanne gefe nasu. Cikin alamun karayar zuciya hirama ta dubi uzaifat tace, ya kai wannan jarumi tayaya kake zaton zamu iya ceto kanmu a wajen sarki shaaran? Ka dubi miliyoyin dakarunsa dake tsaitsaye a saman mu. Su kansu su sarki shaaran din sun ishemu balai da masifa. Saada uzaifat yaji wannan tambaya sai ya dubi hirama yace, kash inda ace kema kin yi imani da ubangijina da ko kadan ba zaki ji shakkar kimai ba a zuciyar ki. Kuma ina tabbatar miki da cewa albarkacin ubangijina a yau si mun ga bayan wadannan majiya namu. Kedai abinda nake so dake shine kada ki yarda kiyi nisa da ni ko lafirat ko uwar mayu domin duk saadda kika shiga halin kaka ni kayi zamu iya baki kariya da maimakon ubangijina. Wannan shine abinda su uzaifat suka tattauna. Alamarin su sarki shaaran kiwa, lokacin da suke sakkowa kasan daga kan tsaunin kiwa sai sarki shaaran ya dubi ukashat yace duk yadda zakayi ka tabbata ka kashe danuwanka a wannan lokaci tunda yanzu kana da abinda shi bashi da shi. Ka sani cewa dukan burina akanka yake. Kai kadai ne zaka iya zuwa ka tono wadannan layu guda hudu wadanda aka binne a kasan katangun birninku kuma idan har baka tono wadannan layu ba har abada ba zamu iya cin birnin da yaki ba, kaga kenan har abada ba zaka zami sarkin Darul husuf ba. Shirina shine da zarar mun ci birnin da yaki sai a daura maka Aure da yata sazirat ka co gaba da mulkin kasar ya zamana cewa mun rushe dakunan bautarsu mun Kawar da addinin nasu. Wanda duk ya bijirewa umarnin mu daga cikin talakawansu mu take wuyansa muyi masa yankan rago. Ina son ka sani cewa dan uwanka uzaifat ne kadai zai iya ruguza mana wannan lissafi ta hanyar hanaka zuwa hako wadannan layu amma idan ka sami nasarar hallakashi a yanzu shikenan. Idan ka kasa hallakashi lallai ni da kaina zan kawo maka dauki mu gama dashi. Lallai wannan karon sun fado hannun mu kuma vasu da mafita gaba da baya dole ne su dandana mutuwa. Tabbasa lokacin cikar burina yazo. Sarki shaaran ya dubi sazirat yace, ke kuma ta kowanne hali ki tabbatar dacewa kin kashe yar uwarki lafirat domin itace kadai ta san sirrin mu da sirrin birnumu. Idan har kika bari ta rayu zata iya giwa abokan gabarmu jagora su shiga har cikin birnjnmu su cimu da yaki. Tabbas kema yanzu kina da abinda ba ta da shi,don haka ina da yakinin cewa zaki iya gamawa da ita cikin kankanin lokaci. Gama wannan jawabi ke da wuya suka gama sauko wa daga kan dogon tsaunin su hudu suka tsaya cak a gabanku uzaifat aka ci gaba da kallon kallon ya zamana cewa tazara dake tsakaninsu bata wuce taku goma ba. Daga can sai sazirat ta zare takobinta ta sauko daga kan dokin ta ta fuskanci lafirat tace da ita, ke nake jira mu raba gardama. Yauce ranar karshen tina tiki tsakanina dake. Na rantse da karagar mahaifina yau sai na cire miki kai da wannan takobin tawa. Koda jin wannan batu sai lafirat ta fusata ainun ta daga tata takobin da hannu biyu ta riketa da kyua tana mai fuskantar ta tace, ai ranar wanka ba a boye cibi. Ya ke yar uwata kiyi sani cewa bani da sauran buri wanda yafi na gana kasheku d a hannuna ke da mahifinmu. Tabbas naji a jikina cewa lokacin cika wannan buri nawa yazo. Da jin haka sai sazirat ta tuntsire da dariyar mugunta tace, hakika wannan sambatu da kike dai dai yake da mafarkin karya. Kafin lafirat ta sake budar baki tace wani abu sai sazirat tayi kukan kura ta ruga kanta suka kacame da azababben yaki. A bangaren uzaiat da ukashat kuwa dayan su baice uffan ba, kawai dai sun kurawa juna idone suna giwa kansu kallon KAR TA SAN KAR Ukashat ya tuntsire da dariya yace, ya kai dan uwana kayi sani cewa karshnku yazo kai da sarki, domin dole ne wannan karon katangar Darul husuf ta fadi, dole ne a zubar da jini a cikin birnin kuma nine zvgan yau karagar mulki. Saadda ukashat yazo nan a zancensa sai takaici ya kama uzaifat har kwalla tazo masa ya dakawa ukashat tsawa yana mai cewa, tur da wannan mugun hali naka. Hakika ka cuci rayuwarka da ka baiwa makiya Allah hadinkai don ganin an Kawar da dan uwanka musulmi. Ka sank cewa ni yanzu bana san nayi yaki da kai a cikin duhu. Maana ina son na san matsayinka shin kai musulmine ko kafiri? Ina da labarin kayi zina kuma ka sha giya. Wadannan duk manyan kaifuka ne a wajen Allah wadanda suna da hukunci, amma ka aikatasu duk da cewa hakan baya nufin wai ka fita daga addinin musulunci, face ka aikata babban laifi a matsayinka na musulmi. Ina mai yin umarni gareka da ka gaggauta sanar da ni matsayinka na sani. Koda jin wannan batu sai ukashat yayi murmushi yace, ina nan a cikin addinina kawai dai na saki hanya ne domin na sami biyan bukatata. Shawarar da zan baka itace, ka san hanyar da zakabi ka sulale ka bar wajen nan domin ni bazan iya kashe ka ba amma duk yadda zan yi bukatata ta biya sai nayi. Ya kamata ka mika domin bazaku taba samun nasara ba. Koda jin haka sai uzaifat ya daga takobinsa sama yace, tsakanina da makiya Allah babu gudu kuma babu ja dabaya. Nima bazaniya kashe ka ba amma zan iya illataka. Kuma da izinin Allah sai na kamaka da hannuna na damkaka ga mahaifinmu anyi maka hukunci dai dai da binda ka aikata. Gama fadin hakan ke dawuya sai uzaifat ya afkawa ukashat suma suka kacame da azababbane yaki ya zamana cewa suka kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da zafin nama da bajinta. Kai da gani babu tambaya ka san cewa sadukantaka ce ta hadi da takwarar ta kuma kowanne na ji dan kansa. Shikuwa sarki shaaran sai yaki saukowa daga kan cikinsa ya dubi uwar mayu da hirama a fusace ya daka musu tsawa yace, tur da wannan aiki da kuka aikata. Ke uwar mayu hakika kin bani kunya kuma kimin bani mamaki yadda kananan yara sauya miki raayi cikin kankanin lokaci. Ki tuna cewa shekara da shekaru kina zaune lafiya da yayanki a cikin gidanki ba a taba kashe miki kiwa ba, yau gashi an wayi gari kin rasa gaba dayan yayanki face guda daya JAL wanda ke goye a bayanki. Yanzu wacce tina kika samu bisa karbar wannan addini na musulunci face kin rasa gidan ki mai kama da aljannar duniya kuma kin rasa yayanki, ina Zakije ki cigaba da rayuwa ma dadi a duniya. Uwar mayu tayi murmuahi tace gaba dayan duniyar na ta ubangijin musulunci ce, don haka duk inda yaso zanje nayi rayuwata domin shine zai bani tsaro da kariya. Babbar ribar dana samu bisa karbar addinin musulunci itace, na gane gakiya na saki karya. Na fahimci cewa tsafi karya ne kuma zalunci haramune. Abu ma biyu shine, na sani cewa idan na mutu anan duniya ubangijin musulunci zai kasheni nan gaba a Wata rayuwar daban, kuma zai yi min sakayya da gidan aljanna, idan har na bishi na kiyaye cikinsa. Kaifa wane tanadi ne da a ban rayuwa ta nan duniya? Kodajin wannan batu sai sarki shaaran ya bushe da dariyar mugunta yace, kece kika yi imani da wannan batu amma ni banyi ba kuma tabbas zan nuna miki kuskurenki kuma zan ga ta yadda ubangijin naku zai iya tserar daku daga masifata. Shaaran ya dubi hirama yace, ke kuma kinyi babban gori ga rayuwar ki tunda har kika guji iyayenki kika jefa su cikin matsanaicin bakin ciki na har abada. Koda jin haka sai hirama tayi murmushi tace, ai ba nice na fara yin abin gori ba yarka ce ta lafirat tafara tunda ta gujeka kuma ta tsaneka harma bata da burin da yafi ta kashe ka da hannunta, shin akwai abin da yafi wannan abin kunya da takaici. Saadda sarki shaaran yaji wannan batu sai jikinsa ya kama tsuma zuciyarsa ta kufula. Cikin tsananin shammata ya daka tsalle sama daga kan dokinsa tamkar daga cikin baka aka cillashi. Ya na a saman ya zare takobinsa ya kawai hirama mummunan sara a wuya da nufin ya filke nata kai. Cikin tsananin zafin nama uwar mayu ta sure hirama daga inda taje tsaye, takobin sarki shaaran ta sari iska. Uwar mayu ta ajiye hirama a bayanta ta ce da ita duk gumurzun da za'ayi kada ki sake ki ce zakiyi gaba da gaba da sarki shaaran. Ban hanaki taimako na ba wajen yakarsa, amma dai kiyi taka tsantsan, nima zan tunkareahine da taimakon ubangijina, amma bani da karfin da zan iya tunkararsa. Nan take uwar mayu ta daga kanta sama tace, ya ubangijin komai da kiwa ka sani cewa ni mai raunice akan sarki shaaran saboda haka ina mai neman taimakon ka da saarka akan wannan azzalumi mai sabonka a doronkasa. A dai dai wannan lokacine sarki shaaran ya juyo ya sake fuskantar su cikin murmushi kuma ya kara rike takobinsa da hannu Baiyi yace, na gaisheki uwar mayu. Tabbas kina da zafin nama, domin ban tana kai hari ba an tsallake sai wannan karon. Yanzu zan yakeku da dukan karfina da dukka dabarata sai na ga ta yadda zaku kubuta. Kafin uwar mayu ta budi baki tace wani abu sai sarki shaaran ya sake afka musu ya rinka kai musu sara da suka cikin zafin nama da karfin. Uwar mayu ta wanzu ta mai karewa da hannayenta. Duk saadda takobin sarki shaaran ta hadu da hannun nata sai kaji kamar karfe da karfe ne suka hadi, har tartsatsin wutane ke tashi. Alamarin da ya mutukar baiwa sarki shaaran mamaki kenan domin ya san cewa babu wani abu da zai sara da wannan takobi bai rabe biyu ba ko da kuwa karfe ne ko dutse. ********************* Najibullah Muhammad 🥷🥷 ************************ Haka kuma ya san cewa a halin yanzu gaba daya sihirin tsafin uwar mayu ya karye tunda ta karbi addinin musulunci yaya akayi yanzu takobinsa ta kasa yi mata illa. Haka dai suka ci gaba da gumurzu su sazirat da nasu sarki shaaran. Kura ta turnuke sararin samaniya. Karafkiyar karafa ta cika dodon kunne su kuwa sauran dakarun sarki shaaran suna sama kan tsauni sunyi cirko cirko suna more kallo kawai, kuma sun giwa filin yakin kawanya dayansu baiyi yunkurin sauko wa kasa ba. Sazirat da lafirat sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna kaiwa junansu sara da suka, dayansu bai sami nasarar komai ba. Koda ganin haka sai sazirat ta fara amfani da karfin sihirinta ta rinka watsa mata kibiyoyim tsafi masu da wuta. Amma duk abinda ya doshi lafirat sai ka ga ya narke ya zama ruwa. Ita kanta sazirat sai abin ya bata mamaki domin a saninta lafirat bata da karfin sihirin da zata iya kare kanta daga wadannan miganyen makamai. Abinda bata sani ba shine, karfin addua ne yaje aiki. Haka dai suka ci gaba da gumurzu har tsawon wata rabin saar ya zamana cewa duk takubbansu sun dakushe, Shima sarki shaaran sai tsafaffiyar takobin nasa ta karye. Cikin fushi yayi wurgi da takobin tasa. Uzaifat da ukashat ma nasu takubban duk sun kakkarye sukayi watsi dasu. Nanfa akayi cirko cirko ana kallon juna. Daga can sai sarki shaaran ya koma kusa da ukashat da sazirat ya tsaya. A wannan lokaci Abul shajaa ne da sarkin yaki ne kadai ya rage suna fafatawa har ma kowannesu yayi nasarar yankar jikin dan uwansa. Shidai Abul shajaa a kirjinsa aka sareshi wajen ya dare jini na zuba. Amma saboda juriya sai yayi sauri ya daure kirjin da rawaninsa ya gyara tsayuwa. Shikuwa sarkin yaki a cinyarsa aka dankara masa saran. Shima wajen yayi rami sosai jini na shatata amma sai yayi sauri ya yage rigarsa ya daure cinyar tamu ya tsaya yana dingishi cikin juriya da bajinta. Kawai sai suka sake kacamewa da sanin artabu. Ya zamana cewa wannan karon yaki suke mai ban tsoro domin kowa iya karfinsa yake yi. Kuma suna neman rayuwar junane. Har ukashat ya yunkura zai kai masa dauki sai sarki shaaran ya tareshi yace, ai abin kunyane mutum biyu su rufarwa mutu daya shiyasa ma na hana dakaruna tayamu wannan yaki. Yanzu mu zuba ido muga waye zai nasara namune ko nasu. Bayan an kashe daya daga cikinsu sai kuma mu gwanda yar kashi tsakanin mu da abokan gwaminmu, tunda makami da tsafi yaki yayi tasiri. Tabbas yanzu ne na gane sai munyi da gaske zamu iya samun nasara akan wadannan mutane domin sihirinsu yana da matukar karfi. Koda gama fadin haka sai sarki shaaran yayi shiru ya zuba ido akan gumurzun da su Abul shajaa suke. Filin yakin yayi tsit bakajin komai face ihun Abul shajaa da na sarki yaki da kuma karar haduwar takubbansu. Nan fa suka ci gaba da mugun artabu ya zamana cewa karfi yazo daya suka ci gaba da yiwa junan su muggan raunika. Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda yanayin yakin nasu yake kasancewa. Da zarar daya yasamu nasarar yankan daya sai kaga dayan ma ya samu. Nan da nan jikinsu yai kaca kaca da raunika, jini ya rinka zuba a jikinsu. Tun suna tsaye sai da suka durkusa kasa suna ci gaba da saran juna. A karshe sai kowannensu ya cakawa kowa takobi a ciki. Takubbansu suka faso ta bayan su. Sarkin yaki ya tsandara uban ihu ya fara kakarin mutuwa. Shikuwa Abul shajaa sai ya fara Kalmar shahada. Cikin gudu uzaifat ya ruga ya dora Abul shajaa akan cinyarsa. A hannunsa ya karasa cikawa ya rasu. Nan take hawaye ya zubowa uzaifat ya rungume gawar Abul shajaa a kirjinsa. A wannan lokaci ne shima sarki shaaran ya rugo fa gudu izuwa wajen sarkin yakinsa ya kankameshi yana girgizashi amma sai ya ga ko motsi bayayi. Harshensa ya zazzago kasa, idanunsa suka Kafe. Koda ganin haka sai sarki shaaran ya takarkare ya kwada uban ihu mai tsananin firgitarwa. Ihun nasa ya cika dajin gaba daura yana mai amsa kuwwa. Nan take uzaifat ya dauke Abul shajaa ya koma can da baya ya ajiyeshi sannan ya dawo ya tsaya kusa da lafirat. Shima sarki shaaran sai ya dauke gawar sarkin yaki ya kaita can gefe daya ya ajiyeta sannan ya dawo filin daga ya kanannade rigar hannunsa sannan ya cire dukan sauran makaman dake jikinsa ya watsar dasu gefe daya, kawai sai ya dunkule hannunsa biyu ya dagasu sama ya fuskanci uwar mayu da hirama yace, yanzu sai kuzo mu fidda raini ko. Koda uwar mayu da hirama suka ga yadda kwanjin sarki shaaran ya kumbura kuma suka ga kirare jikinsa, suka ga duk jijiyoyin jikinsa sun kumbura, sai suka razana, jikinsu yayi sanyi zuciyar su ta karaya domin sun tabbatar da cewa ruwa ba saan kwando bane. Shima ukashat sai ya dunkule hannunsa ya fuskanci uzaifat. Sazirat ma ta dunkule nata hannun ta fuskanci lafirat. Sarki shaaran ya dubi uzaifat yace, yanzu ne zami yakin gakiya da gakiya. Na rantse da girman karagata dayanku ba zai tsira da rayuwar sa ba. Gama fadin hakan ke da wuya sai shima sarki shaaran ya ruga kan uwar mayu da hirama ya rufesu da duka. Naushin farko da yayiwa uwar mayu a fuska sai da gudan jini yayi fitar burgu daga bakinta, idanunta suka lumshe taga taurarin wuya. Tayi baya taga taga ta baje a kasa. Ita kuwa hirama da kafa sarki shaaran ya nausheta a ciki, sai da tayi tsalle sama da baya ta fado kasa tana aman jini ta baki da hanci. Kafin uwar mayu ta mike tsaye sai sarki shaaran ya ruga inda hirama ke kwance ya cafi wuyanta ya daga ta sama da hannu daya ya shaketa. Nan da nan idanunta suka yi lubu lubu suka kada sukayi jawur, kafafunta suka kama wutsil wutsil. A wannan lokaci uzaifat da ukashat suna mugun gumurzu suna ta naushin juna da bugun juna,duk sun hadawa junan su jini da majina. Wani lokacin ma sai kaga sun kacame da kokawa sun rukunkume juna. Wani lokacin kaga sun fadi kasa suna birgima wannan ya danne wancan wancan ya danne wannan, sukayi busu busu da kasa. A bangaren sazirat da lafirat ma kuwa irin abinda ke faruwa da su uzaifat suma shi sukeyi, wato karfi yazo daya sun ragargazar juna, fuskokinsu duk sun kumbura saboda tsabar naushin juna, kuma kowaccensu jikinta yayi tsami har suma sun fara kokawa a kasa. Lokacin da uwar mayu ta dawo cikin haiyacinta ta mike tsaye zumbur ta hango sarki shaaran rike da wuyan hirama ya shaketa tamau har kumfar wuya ta fara fita daga cikin bakinta. Sai ta sake mikewa tsaye ta ruga kansa ta rufeshi da duka da dukan karfita. Ai tamkar yarone ke dukansa ko juyowa baiyi ba ya kalleta, kawai sai yaci gaba da kyalkyala dariyar mugunta, kuma ya dada shake wuyan hirama da karfi, ya zamana cewa hirama da kyar take iya motsa kafarta guda, ta wuce mutuwa sai dai ace suma suma. Koda uwar mayu taga haka sai ta daga hannayenta sama ta kwala kabbara da karfin tsiya tana mai neman taimakon Allah, kawai sai ta karci bayan sarki shaaran da faratanta. Take wajen ya dare gida takwas jini yayi tsartuwa. Sarki shaaran ya kwala ihu ya dimauce. Bai san saadda ya saki hirama ta fadi kasa ba. Shima sai tsugunna kasa bisa gwiwoyinsa ya rintse idanunsa ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi. Nan take wannan rauni na bayansa ya fara warkewa da kansa da kadan kadan, daga ya na sama raunin na bacewa tamkar bai taba wanzuba a wajen. Cikin hanzari uwar mayu ta ruga da gudu izuwa inda hirama ke kwance ta fara yi mata firfita da hannayenta domin ta farfado daga dogon suman da tayi. Kafin sarki shaaran ya mike tsaye daga inda yake durkushe ya sake kawo musu wani harin. Ai kuwa a dai dai wannan lokacin da saunin sarki shaaran ya gama bacewa ne hirama ta farfado daga sogon suman da tayi. Cikin zafin nama uwar mayu ta sunkuceta ta goya a bayanta ta daureta tamau da jelar jikinta sannan ta juya ta fuskanci sarki shaaran a lokacin da ya mike tsaye ya juya suka dubi juna. Kawai sai sarki shaaran ya rugo da gudu izuwa kan uwar mayu cikin mugun mufi. Kafin uwar mayu ta budi baki tayi wata addua ka ta nemi taimakon Allah sai kawai ta ga sarki shaaran ya baiyana a gabanta tsulum kawai sai ya sa hannunsa UA gabza mata nashi a fuska. Saboda karfin naushin sai da ta yi katantanwa sau uku a tsaye sannan ta sukale kasa a sume. Hirama ta subuce daga bayanta itama ta baje a kasa. Sarki shaaran ya sunkuyo da nufin ya kama kan uwar mayu da na hirama ya murde, kawai sai ya juyo ihun dakarunsa dake saman tsaunin. Nan take yaga ana jeho dakarun nasa daga kan dawakansu suna gangarowa kasan tsaunin. Wasunsu da kibiyoyi ake harbosu, wasu kuwa sai dai kaga an fille kawunansu. Nan da nan saman tsaunin ya kacame da azababben yaki. Ba wani bane yake wannan barnar ba face sarki uwaisul karni da dakarunsa na yaki wadanda suma adadinsu ya kai miliyan uku da dubu dari bakwai. Da karfin tsiya sarki uwaisul karni ya tarwatsa dakarun sarki shaaran dake gabanta yana ragargazarsu har ya iso karshe tsaunin ya leka kasa. Nan take yayi arba da sarki shaaran, suka kalli juna sannan taga yayansa uzaifat da ukashat suna ta tumurmusar juna. Kuma ya hango lafirat da sazirat suna kwamarzuwa. Kana ya hango gawar Abul shajaa a can gefe daya a kwance. Koda ganin wannan alamari sai sarki uwaisul karni ya fusata ainun, zuciyar sa ta kama tafarfasa kamar zata kone. **DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA 3 PART D✍️✍️ NA;ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING UMAR FAROUQ ZANGO. POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷 Bai san saadda yayi kundunbala ba ya dako tsalle daga saman tsaunin ya duro izuwa kasansa yana mai kwala kabbara duk da cewa nisan kasan tsaunin ya kai zirai arbain. Ai kuwa kafafunsa na dira bisa kasa sai ya ruga izuwa kan sarki shaaran rike da takobinsa a sama. Koda sarki shaaran ya hangoshi sai yayi alkafira a kasa izuwa inda ya watsar da wasu gajerun addunansa guda biyu ya suresu sannan ya tari sarki uwaisul karni suka kacame da sanin masifaffen yaki. Sai gashi ana yaki a saman tsaunin a kasa ma anayi. Yanzu dai gashi manyan kuraye biyu ne a kasa suke fafatawa wadanda suka kasance tsofaffin abokan gaba da suka zamana cewa KAR TA SAN KAR, kuma a shekara da shekaru kowannensu na son ganin bayan kowa amma lamarin ya taazzara. Sarki shaaran da sarki uwaisul karni suka wanzu suna kaiwa junansu sara da suka cikin nuna kwarewa da sanin makama har tsawon sa'a daya da rabi, amma dayansu bai sami nasarar komai ba. Sarki shaaran ya fara amfani da karfin sihirinsa domin ya hallaka sarki uwaisul karni amma sai abu ya gagara. Haka dai suka ci gaba da artabu har wata rabin sa'ar ta sake shudewa ya zamana cewa duk sun gaji. Da kansu suka rabu suka ja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru. A sannane sarki shaaran ya dubi uwaisul karni ya bushe da dariyar mugunta sannan ya murtuke fuska yace, ya kai abokin gabata kayi sani cewa kk yanzu rasuwa tatashi dan koli ya ci riba. Na haddasa rashin kwanciyar hankali a gareka da jamaarka. Na raba zumuncin dake tsakanin yayanka. Kuma na sa dankara guda daya akan mugun TAFARKI na sabawa ubangijin ku. Kuma ina tabbatar maka da cewa babu yadda za'ayi ku sami nasara a wannan yaki da mukeyi. Kodai mu musami nasara akanku ko kuma ayi RAGAS. saadda sarki shaaran yazo nan a zancensa sai sarki uwaisul karni ya yi murmushi yace,ya kai abokin gabanta kayi sami cewa zuciyata a wanke take tas babu wani takaici a cikinta bisa illar da kaimin. Dana da ya bijire min ya hada kai da ku domin aga bayanmu yayi hakance saboda kwadayin duniya kawai domin baya son dan uwansa ya samu mulkin birnina. Nayi sani cewa ya aikata babban laifi huda biyu na karya dokokin ubangijina. Kuma akwai hukuncinsu da ya dace da wadannan laifuka. Na sani cewa yanzu baka da wani buri wanda yafi kai da jamaarka kun dangana izuwa birnina har ukashat ya sami damar tono wadannan layu guda gudu da aka binne a karkashin katangunhudu na birnina. To ina Tabbatar maka dacewa kaine abin tausayi a ganina tunda gashi yar cikinka bata d wani buri wanda yafi ta kasheka da hannunta. Ina tabbatar maka dacewa ko yanzu ka umarci dana ukashat ya kasheni da hannunsa ba zai iya ba duk da cewa baya kaunata a zuciyar sa. Idan kuma kana musu ne to ka jarraba ka gani. Saadda sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa ne ukashat da uzaifat suka baje a kasa suka daina gadan saboda tsananin gajiya suka kama haki da numfashi kamar tansu zai fita. Sazirat da lafirat ma haka alamarin y kasance a garesu. Koda ganin abinda ya faru sai sarki uwaisul karni ya daga hannunsa yana mai nuni ga jamaarsa da su janye daga filin yakin. Nan take kuwa aka Busa kahon tsaida yaki sai dakarun suka fara guduwa daga filin yakin suna barin gawarwakin yan uwansu suka nufi can bakin wani kogin. Har dakarun sarki uwaisul karni sun fara binsu suna rafkewa sai sarki uwaisul karni ya daka musu tsawa suka daina. Shikuwa sarki shaaran sai yayi nuni da hannunsa izuwa ga ukashat da sazirat da kuma gawar sarkin yakinsa. Nan take suka bace daga filin yakin. Har uzaifat ya yi yunkurin yin addua domin Allah ya baiyana su, sai sarki uwaisul karni ya hanashi ya dubi lafirat yace, tashi kuzo muje can kusa da inda su mahaifinki suka tsaya muma mu kafa namu san sanin wannan yaki bai kare ba sharar fage kawai akayi. Ba tare da fargabar komai ba kuwa uzaifat da lafirat ta mike tsaye tazo kusa da uzaifat ta tsaya. Sarki uwaisul karni ya kama hawa kan wannan tsaunin uzaifat da lafirat na biye dashi. A sannane uwar mayu ta mike tsaye da kyar dama ta dade da farfado sannan taje ta dauki hirama ta sake goya ta a bayanta tabi su uzaifat. Koda suka hau kan tsaunin gaba dayansu inda sauran dakarun yaki suke sai sarki uwaisul karni yasa aka baiwa uzaifat da lafirat dawakai suka hau. A sannane hankalinsu ya kai kan uwar mayu da hirama. Har uzaifat ya bude baki zai ambaci wani abu sai yaji uwar mayu ta ambaci sunan Allah kuma tayi godiya a gareshi bisa ceto rayuwar su da yayi ita da hirama daga hannun azzalumin sarki shaaran. Kod jin haka sai sarki uwaisul karni yayi shiru baice komai ba. Su kuwa sauran dakarun koda suka hango uwar mayu goye da hirama ta durfafo inda suke sai suka firgice suka hau dana kibiyoyi akan baka suka saitata. Take uzaifat ya daka musu tsawa yace, akul dayanku ya harbeta domin yar uwarmu ce musulma. Koda jin haka sai dakarun suka sauke bakansu kas suka cika da tsananin mamakin yadda wannan shirgegiyar aljanar ta karbi musulunci. Ba tare da bata lokaci ba sarki uwaisul karni ya bada umarni a tafi can kusa da inda wannan kogin ya ke inda su sarki shaaran suka je suka tsaitsaya yace, ake a kafa tantuna. Amma a sami tazara ta a kalla zirai sabain a tsakani yadda dai suna iya hangosu suma haka. Nan take kuwa aka bi umarni. Da izuwa aka iske tuni jamaar sarki shaaran sun gama kafa nasu tantunan. Don haka suma dakarun sarki uwaisul karni sai suka hau aikin kafa nasu tantunan. Cikin kankanin lokaci suka kammal. Gashi dai kowacce runduna tana hango kowanne bangare an zuba dakarun tsaro sun kewaye sansaninsu don gudun kada akawo farmakin sumame na bazato. Lokacin da sarki shaaran ya shiga tantinsa ya zauna ya huta aka kawo masa abinci da giya yayi hanian sai ya tura aka kirawo masa ukashat da sazirat amma kafin su zo tuni yayi bincike a cikin hallarar tsafinsa. Da shigowar ukashat da sazirat sai suka zauna a gefe daya suka fuskanceshi sukayi shiru. Sarki shaaran ya dubesu cikin nutsuwa tamkar bai sha wani abu na maye ba yace, abinda nakeso da ku shine ku saurara da kyau kiji abinda zan gaya muku domin idan kukayi kuskure guda daya a cikin aikin da zan baku yanzu shikenan dukkanin shirin mu ya ruguje babu wanda burimsa zai cika daa cikinmu. Da farko dai ina so ku sani cewa ba wani abu bane yasa na tsaida wannan yaki ba face gano cewa idan aka ci gaba dashi bamu da nasara. Domin sai an kasheni gaba dayanmu a wannan karon. A yanzu haka daa cikin dakaruna mutum miliyan gudu an kashe mutum miliyan daya da dabi saura miliyan uku cif. Ba komaine yasa suka sami wannan nasara ba face farmakin sumamen da suka kawo mana lokacin da jamaata ke bisa kan wannan tsauni ashe tuntuni suna labe a cikin dajin a kwance cikin duhuwa suna kallon mu sai bayan mun hau kan tsaunin sannan suka sadado suka afka mana. A cikin binciken da nayi yanzu na ga duk wannan alamari a mudubin tsafina. Idan har muna son mu cisu da yaki kuma muje har can birnin Darul husuf mu karya katangarasu ya zamana cewa ki ukashat ka hau karagar mulki dole ne muyi abu uku. Abu ma farko dolene muyi abinda zai dauke musu hankali anan dajin sannan mu sulale basu sani ba mu tafi izuwa birninsu koda kuwa mu ukun nanne Jal domin mu kadai zamu iya cin garin da yaki. Abu na biyu dole ne mu sati yata gimbiya lafirat daa sansanin su domin idan har tana tare dasu zata iya musu jagora izuwa can birninmu suje su kubutar da rayuwar dakarun nan nasu wadanda muka tsare da kuma luhaira yar likita abu sharhaz a cikin gidan gonata inda aka killaceta tsawon shekara da shekaru. Kun sani cewa bani da wani buri wanda yafi na tara da wannan yarinya luhaira amma ba zan taba samun damar hakan na sai bayan kunci birnin Darul husuf da yaki mun Kawar da musulunci mun shimfida kafirci da addininmu na tsafi. Lokacin da sarki shaaran yazo nana a zancensa sai hankalin ukashat da sazirat ya dugunzuma ainun. Ukashat ya dubi sarki shaaran cikin damuwa yace, ya kai wannan babban sarki yanzu ta ya ya kake ganin zamu iya sato lafirat da daga cikin wancan sansanin na su uzaifat? Tayaya kake ganin zamu sulale mu tafi izuwa can birnin Darul husuf ba tare da su sarki uwaisul karni sun sani ba? Wane abune na uku wanda dolene muyi shi idan har munason musami wannan nasara akan abokan gabanmu? Domin baka baiyana mana shi ba. Saadda sarki shaaran yaji wadannan tambayoyi sai ya bushe da mahaukaciyar dariya harda bingirewa kasa tamkar nazai daina ba. Daga can sai ya tsuke bakinsa ya hade fuska yace, dangane da abu na uku wanda ban baiyan muku shiba, abune wanda bakune zaku aikatashi ba. Ba komai bane wannan abu face sato muzaira matar sarki uwaisul karni mahaifiyarka wadda yanzu haka antsareta a kurkuku sakamakon yunkurin kashe sarki uwaisul karni da tayi. Dole ne mu satota kafin ma ka tono wadannan layu guda gudu domin itace kadai zata iya sanar dani abinda zanyi na iya hallaka sarki uwaisul karni a filin yaki. Lallai ni da kaina zam sulale naje birnin Darul Husuf na sato muzaura. Yanzu sai ku sake nutsuwa kiji bayanin da zan ya muku akan yadda zaku sami nasarar yin abubuwan biyu. Na farko wato sato lafirat da tafiya izuwa birnin Darul husuf wanda a rana daya zamuyi su. Dafarko a gobe idan gari ya waye zamu fito filin yaki na bukaci da aci gaba da yaki, amma ta hanyar zabar gwanayen sadaukanmu da nasu guda goma shabibbiyu su kara. A gobe kuma sai a zabi mutum dari dari. A jibi kuma sai a zabi mutum dari biyar biyar. A rana ta gudu kuma mutum dubu dubu muyi yarjejeniya akan cewa haka zaaci gaba da yakin har mu karar dasu ko su sukarar da mu. *********************** Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷 ************************ A wannan rana ta uku da za'ayi yakin mutum dari biyar daya daga cikinmu zai yi bad kama ya shiga yakin yadda ba zaa ganeshi ba. Abinda nake bukata kawai shine ya yi iya kokarinsa ya sato gawar daya daga cikin abokam gabar ya kawo ta sansanin mu a boye ba tare da wani ya ganshi ba. Tufafin badakaren muke so zamuyi amfani da shi idan dare yayi. Wannan tufafi shi daya daga cikinku zai sanya a cikin daren yaje har sansanin nasu ya sato gimbiya lafirat ta kowanne hali ta hanyar amfani da dukan hikimarsa domin tsafi bazaiyo tasiri ba a cikin wannan alamari. Idan har aka sami wannan nasara to a daren zan kirawo wani aljanina wanda zai daukemu yayi sama damu ya keta tacikin samaniya ba tare da makiya sun ganmu ba ya kaimu hat can kusa da kofar birnin Darul husuf. A cikin daren zamu afkawa mutanen birnin mu cisu da yaki da karfin tsiya mu kafa gwamantain mu. Su kuwa su sarki uwaisul suna nan filin yaki suna jira gari ya waye a ci gaba da yaki basu san tabargazara da muka tafka musu ba. Yanzu a cikinku wane zai iya samo mana gawar badakaren abokan gaba kuma ya sati lafirat? Koda jin wannan tambaya sai gardama tasarke tsakanin sazirat da ukashat kowannensu na cewa shine zai iya wannan aiki cikin nasara ba tare d an sami kuskure ba. Koda ganin haka sai sarki shaaran ya shiga tsakanin suka yi shiru sannan ya dubi sazirat yace, ke mecece hujjarki ta ganin cewa lallai zaki fi ukashat samun nasara yin wannan aiki? Sazirat ta yi gyaran murya tac, ya kai abbana kasani cewa ni ya mace ce saboda haka mata sunfi maza iya makirci da iya shirya tuggu. Koda jin haka sai sarki shaaran yayi murmushi yace, naji taki hikimar. Kai kuma fa? Ukashat yayi gyaran murya yace, ya shugabana ni babbar hujjata itace ni na fito ne daba cikin wadannan mutane don haka ni nafi sanin dukkan dakarunsu na tsaro kuma ni ne nasan dukkan sirrin su na dana tarkon kama abokan gaba. A takai ce dai da dan gari akanci gari. Koda jin wannan batu sai sarki shaaran ya bushe da dariya tace, Tabbasa nafi samun nutsuwa d naka jawabi don haka kaine zaka yi wannan aiki nan da cikar kwana uku. * * * * * * A can tantin sarki uwaisul karni kuwa, kamar yadda sarki shaaran ya zauna ya gana da sazirat da ukashat haka Shima sarki uwaisul karni ya zauna tare da uzaifat da lafirat domin su tattauna danagane da yadda zasu bullowa wannan yaki domin basu san manufar sarki shaaran bisa dalilin tsayar da yakin ba, kuma idan gari ya waye basu san abinda zai zo dashi ba. Sarki uwaisul karni ya dubi uzaifat da lafirat yace, yanzu ku a tunanin ku da kuma hangen nesanku me kuka fahimta dan gane da tsayar da wannan yaki da sarki shaaran yayi ya gudu shida jamaarsa izuwa bakin wannan kogi, kuma me kuke tunanin zai iya shiryawa anan gaba wanda zai iya cutar damu? Yayin da uzaifat sukaji wannan tambaya sai duk suka kara nutsuwa suka yi shiru. Daga can sau lafirat tanumfasa tadubi sarki uwaisul karni cikin niyaiyya tace, ya shugabana ni a ganina mahaifina ya janye wannan yaki ne domin ya ga alamar cewa basu da nasara akanmu kuma abin da nake hange shine zai iya kokarin kawo mana farmakin sumame a cikin dare don haka dole ne kasa dakarunka su kara karfin tsaro a wannan sansanin namu ya zamana cewa ko yaushe a cikin shirin yaki muke. Kuma ko yaya muka ji wani motsi mu kai hari wajen babu sassauci. Ya yinda sarki uwaisul karni yaji wannan batu sai ya jinjina kai yace, tabbas kinyi tunani mai kyau, kuma lallai zamu yi amfani da wannan shawara taki. Sarki uwaisul karni ya dubi uzaifat yace, kai kuma fa me kayi tunani akan wannan alamari kafin nima ubangijina ya nusar da ni bisa abinda yazo a cikin mafarkina? Koda jin wannan tambaya sai uzaifat yayi ajiyar zuciya sannan yace, ya kai abbana ni a tunanina da hangena lallai ruwa baya tsami banza. Tabbas masu iya magana sunce shi yaki dan zambane don haka lallai akwai wata yaudara da sarki shaaran ke kakarin shirya mana a cikin wannan yaki. Abu ne mawuyaci ya kawo mana harin sumame a cikin dare tunda muna dag da juna ido na kallon ido. Ku dubi sansanin su ko ina a haska ke yake da fitilun itatuwa haka muma namu don haka babu wani bangare da zai yi wani yunkuri ba tare da daya bangaren ya gani ba. Idan harzai shirya wata dabarako wani tuggu dole sai idan a lokacin da aka ci gaba da yaki. Abinda nake so damu shine, da zarar an ci gaba da yaki lallai mu sa ido akan abokan gaba kuma ta kowanne hali kada mu bari mutum daya cikinsu ya shigo cikin wannan sansanin namu kuma duk yadda zamuyi lallaine mu yi kokarin kwato yarima ukashat daga hannunsu ta kowanne hali a matsayin fursunan yakin mu domin shine kadai ya san sirrin birninmu kuma shine kadai zai iya shiga birnin ya cutar da jamaarmu ko kuma Ya tono wadannan layu daga karkashin katangun birnin namu. Abu na uku da ya kamata muyi shine, lallai da zarar an fara ci gana da wannan yaki mu sami wani daga cikinmu wanda zai sulale ba tare da anganshi ba ya tafi can birnin shumbul yaje har inda aka boye mutanen mu da inda aka boye luhaira yar likita abu sharaz yaceto rayuwar su. Ina ganin idan muka sami nasarar aikata haka bukatarmu zata biya kuna zamu sami cikakkiyar nasara akan abokan gaba. Saadda uzaifat yazo dai dai nan a jawabinsa sai sarki uwaisul karni ya jinjina kai yayi shiru yana nazarin alamarin har izuwa lokaci mai dan tsawo. Daga can kuma sai yai ajiyar zuciya yace, ya kai dana hakika ka zo da shawara mafi kyau. To amma yanzu tsakanin kai da lafirat wanene zai iya izuwa can sansanin shumbul ya ceto rayuwar jamaaramu a cikin nasara ba tare da an sami matsala ba. Kuma wane ne zai tayamu tabbatar da tsaro a wannan sansanin yaki namu? Koda jin wannan tambaya sai uzaifat da lafirat suka dubi juna sukayi shiru. Daga can sai uzaifat yace, ni ina ganin cewa dole sai da dan gari akanci gari. Lallai lafirat ce ya kamata ta tafi birninsu ta ceto mana rayuwar jamaarmu da ta luhaira tunda ta san a inda suke kuma ta san duk irin matakan tsaron dake wajen. Ni kuwa sai na tsaya anan filin yaki na tabbatar da tsaro kuma na tayamu yaki har Allah ya baku nasara akan abokan gaba. Koda jin wannan batu sai hankalin gimbiya lafirat ya dugunzuma tace, ai idan akayi haka ni burina bazai cika ba na ganin cewa na kashe mahaifina da yar uwata da hannuna tunda wata kula bana nan za'ayi yakin. Ku tuna cewa nayi alkawarin ba zan karbi addininku ba har sai na ga na cika wannan buri nawa. Shin bakwason na karbi addinin naku ne? Saadda sarki uwaisul karni da uzaifat sukaji wannan tambaya sai jikinsu yayi sanyi, suka sunkui da kawunanzu kas suka yi shiru basu ce kala ba. Daga can sai sarki uwaisul karni ya dago kai ya dubi lafirat yace, ya ke yata hakika kinyi babban ganganci da kika daukarwa kanki wannan alkawari mai nauyi kuna mai wuyar cikawa tunda ako yaushe zaki iya rasa rayuwar ki. Kinga kuwa idan har kika mutu baki karbi addininmu ba kin mutu kafira baki da rabo gobe kiyama. Ni a yanzu tawa shawarar kuma bisa hangena ke da uzaifat zaku tafi izuwa can birnin shumbul domin a hangena ke kadai ba zaki iya wannan aiki ba na ceto rayuwar jamaarmu da ta luhaira saboda babu wani abu da kike takama dashi sama da tsagwaron iyakar karfin dantsenki da sihirin tsafi. Na tabbata mahaifinki ya fiki karfin sihiri don haka ba zaki iya datea hijaban da ya sanya ba na bayar da tsaro da a wuraren da ya boye jamaarmu shi kuwa uzaifat zai iya keta hijaban da karfin addua kinga kenan kuna bukatar juna ku biyun tunda ke kin san wuraren da zaaje, shi kuma zai iya shigo ko ina. A gaba daya dakarun babu wanda zai iya tarar sarki shaaran face ni. Haka kuma na yarda da sauran dakaruna a cikinsu akwai wadanda zasi iya taka muhimmiyar rawa a wannan yaki. Zan yi iya kokari na na ga na hallaka sarki shaaran sannan na fuskanci yar sa sazirat. Babbar matsalar mu itace ta yaya zamu iya sato yarima ukashat daga cikin sansanin yakinsu a lokacin da ba a yin yaki musamman cikin dare? Koda jin wannan tambaya sai yarima uzaifat da lafirat suka sake kallon juna a kari na biyu sukayi shiru. Lafirat tayi ajiyar zuciya tace, ni kadaice zan iya wannan aiki tunda na fiku sanin dukkan matakan tsaron da ke sansanin mutanen mu kuma zan iya amfani da makirci irin namu na mata. Amma ina bukatar kwana biyu rak nayi nazari akan wannan alamari. Sarki uwaisul karni yayi murmushi yace, na baki wannan dana amma ki sani cewa lallai a ranar kwana na nake son ki cika wannan aiki in yaso kashe gari sai kusan yadda zakuyi ku sulale ku tafi can birnin shumbul ba tare da kowa ya sani ba. Lafirat ta maida wa sarki martanin murmushi sannan ta ce, an gama ya shugabana. Kashe gari da safe bayan jamaar kowanne bangaren sun kintsa sai sarki shaaran yasa aka Busa kahon ci gaba da yaki. Nan take dakaru suka hau sahu sahu akan layi akan fuskanci juna. Mahaya layinsu da ban, mayakan kasa ma layin su daban. Bayan kowanne bangare ya gama shiri tsafi sai sarki shaaran ya zaburi dokinsa izuwa tsakiyar filin yakin ya tsaya. Koda ganin haka sai shima sarki uwaisul karni ya zaburi nasa dokin ya tunkareshi har yana shirin zare takobinsa domin a zatonsa sune zasi fara bude fagen yakin sai sarki shaaran ya dubeshi yayi masa murmushi yace, ai ba fitowa nayi ba domin mu yi yaki da kai ba. Nafitone domin kaima ka fito mu tsara yadda zaaci gaba da wannan yaki domin mu gaggauta kawo karshen yakin kuma mu kece raina a tsakanin mu. Idan har ka yarda da kanka kuma ka yarda da mayakan ka. Ina son mu fara fito na fito da mutum goma sha bibbiyu daga cikin jamaarmu su yaki juna a yau. Gobe kuma sai mu fito da mutum dari dari, jibi mutum dubu dubu. A ranar kwana ma uku mu ninka sau goma. A haka za acigana da yakin har mu karshi. Koda jin wannan batu sai sarki uwaisul karni yayi shiru yana nazari, kawai sai yayi addua a cikin zuciyar sa yace, Allah ka bamu saa a cikin wannan sabone sako da wannan makiya namu yazo dashi kuma idan wani makircin yaki ya shirya mana kada ka bashi nasara akanmu. Koda gama wannan addua sai sarki uwaisul karni ya dubi sarki shaaran ya ce, na yarda da kaina kuma na yadda dakaruna. Nayi imani cewa ubangiji na zai bamu sa'a akanku don haka na amince da wannan tsaru da kazo dashi. Koda jin haka sai sarki shaaran ya tuntsire da dariyar mugunta irin tasu ta kafirai sannan yace, muje izuwa mahaukaci ya hau kura. **DAKARUN MUSULUNCI* Littafi Na 3 Part E ♥️✍️ NA: Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing Umar Farouq Zango POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ A wannan rana ta uku da za'ayi yakin mutum dari biyar daya daga cikinmu zai yi bad kama ya shiga yakin yadda ba zaa ganeshi ba. Abinda nake bukata kawai shine ya yi iya kokarinsa ya sato gawar daya daga cikin abokam gabar ya kawo ta sansanin mu a boye ba tare da wani ya ganshi ba. Tufafin badakaren muke so zamuyi amfani da shi idan dare yayi. Wannan tufafi shi daya daga cikinku zai sanya a cikin daren yaje har sansanin nasu ya sato gimbiya lafirat ta kowanne hali ta hanyar amfani da dukan hikimarsa domin tsafi bazaiyo tasiri ba a cikin wannan alamari. Idan har aka sami wannan nasara to a daren zan kirawo wani aljanina wanda zai daukemu yayi sama damu ya keta tacikin samaniya ba tare da makiya sun ganmu ba ya kaimu hat can kusa da kofar birnin Darul husuf. A cikin daren zamu afkawa mutanen birnin mu cisu da yaki da karfin tsiya mu kafa gwamantain mu. Su kuwa su sarki uwaisul suna nan filin yaki suna jira gari ya waye a ci gaba da yaki basu san tabargazara da muka tafka musu ba. Yanzu a cikinku wane zai iya samo mana gawar badakaren abokan gaba kuma ya sati lafirat? Koda jin wannan tambaya sai gardama tasarke tsakanin sazirat da ukashat kowannensu na cewa shine zai iya wannan aiki cikin nasara ba tare d an sami kuskure ba. Koda ganin haka sai sarki shaaran ya shiga tsakanin suka yi shiru sannan ya dubi sazirat yace, ke mecece hujjarki ta ganin cewa lallai zaki fi ukashat samun nasara yin wannan aiki? Sazirat ta yi gyaran murya tac, ya kai abbana kasani cewa ni ya mace ce saboda haka mata sunfi maza iya makirci da iya shirya tuggu. Koda jin haka sai sarki shaaran yayi murmushi yace, naji taki hikimar. Kai kuma fa? Ukashat yayi gyaran murya yace, ya shugabana ni babbar hujjata itace ni na fito ne daba cikin wadannan mutane don haka ni nafi sanin dukkan dakarunsu na tsaro kuma ni ne nasan dukkan sirrin su na dana tarkon kama abokan gaba. A takai ce dai da dan gari akanci gari. Koda jin wannan batu sai sarki shaaran ya bushe da dariya tace, Tabbasa nafi samun nutsuwa d naka jawabi don haka kaine zaka yi wannan aiki nan da cikar kwana uku. * * * * * * A can tantin sarki uwaisul karni kuwa, kamar yadda sarki shaaran ya zauna ya gana da sazirat da ukashat haka Shima sarki uwaisul karni ya zauna tare da uzaifat da lafirat domin su tattauna danagane da yadda zasu bullowa wannan yaki domin basu san manufar sarki shaaran bisa dalilin tsayar da yakin ba, kuma idan gari ya waye basu san abinda zai zo dashi ba. Sarki uwaisul karni ya dubi uzaifat da lafirat yace, yanzu ku a tunanin ku da kuma hangen nesanku me kuka fahimta dan gane da tsayar da wannan yaki da sarki shaaran yayi ya gudu shida jamaarsa izuwa bakin wannan kogi, kuma me kuke tunanin zai iya shiryawa anan gaba wanda zai iya cutar damu? Yayin da uzaifat sukaji wannan tambaya sai duk suka kara nutsuwa suka yi shiru. Daga can sau lafirat tanumfasa tadubi sarki uwaisul karni cikin niyaiyya tace, ya shugabana ni a ganina mahaifina ya janye wannan yaki ne domin ya ga alamar cewa basu da nasara akanmu kuma abin da nake hange shine zai iya kokarin kawo mana farmakin sumame a cikin dare don haka dole ne kasa dakarunka su kara karfin tsaro a wannan sansanin namu ya zamana cewa ko yaushe a cikin shirin yaki muke. Kuma ko yaya muka ji wani motsi mu kai hari wajen babu sassauci. Ya yinda sarki uwaisul karni yaji wannan batu sai ya jinjina kai yace, tabbas kinyi tunani mai kyau, kuma lallai zamu yi amfani da wannan shawara taki. Sarki uwaisul karni ya dubi uzaifat yace, kai kuma fa me kayi tunani akan wannan alamari kafin nima ubangijina ya nusar da ni bisa abinda yazo a cikin mafarkina? Koda jin wannan tambaya sai uzaifat yayi ajiyar zuciya sannan yace, ya kai abbana ni a tunanina da hangena lallai ruwa baya tsami banza. Tabbas masu iya magana sunce shi yaki dan zambane don haka lallai akwai wata yaudara da sarki shaaran ke kakarin shirya mana a cikin wannan yaki. Abu ne mawuyaci ya kawo mana harin sumame a cikin dare tunda muna dag da juna ido na kallon ido. Ku dubi sansanin su ko ina a haska ke yake da fitilun itatuwa haka muma namu don haka babu wani bangare da zai yi wani yunkuri ba tare da daya bangaren ya gani ba. Idan harzai shirya wata dabarako wani tuggu dole sai idan a lokacin da aka ci gaba da yaki. Abinda nake so damu shine, da zarar an ci gaba da yaki lallai mu sa ido akan abokan gaba kuma ta kowanne hali kada mu bari mutum daya cikinsu ya shigo cikin wannan sansanin namu kuma duk yadda zamuyi lallaine mu yi kokarin kwato yarima ukashat daga hannunsu ta kowanne hali a matsayin fursunan yakin mu domin shine kadai ya san sirrin birninmu kuma shine kadai zai iya shiga birnin ya cutar da jamaarmu ko kuma Ya tono wadannan layu daga karkashin katangun birnin namu. Abu na uku da ya kamata muyi shine, lallai da zarar an fara ci gana da wannan yaki mu sami wani daga cikinmu wanda zai sulale ba tare da anganshi ba ya tafi can birnin shumbul yaje har inda aka boye mutanen mu da inda aka boye luhaira yar likita abu sharaz yaceto rayuwar su. Ina ganin idan muka sami nasarar aikata haka bukatarmu zata biya kuna zamu sami cikakkiyar nasara akan abokan gaba. Saadda uzaifat yazo dai dai nan a jawabinsa sai sarki uwaisul karni ya jinjina kai yayi shiru yana nazarin alamarin har izuwa lokaci mai dan tsawo. Daga can kuma sai yai ajiyar zuciya yace, ya kai dana hakika ka zo da shawara mafi kyau. To amma yanzu tsakanin kai da lafirat wanene zai iya izuwa can sansanin shumbul ya ceto rayuwar jamaaramu a cikin nasara ba tare da an sami matsala ba. Kuma wane ne zai tayamu tabbatar da tsaro a wannan sansanin yaki namu? Koda jin wannan tambaya sai uzaifat da lafirat suka dubi juna sukayi shiru. Daga can sai uzaifat yace, ni ina ganin cewa dole sai da dan gari akanci gari. Lallai lafirat ce ya kamata ta tafi birninsu ta ceto mana rayuwar jamaarmu da ta luhaira tunda ta san a inda suke kuma ta san duk irin matakan tsaron dake wajen. Ni kuwa sai na tsaya anan filin yaki na tabbatar da tsaro kuma na tayamu yaki har Allah ya baku nasara akan abokan gaba. Koda jin wannan batu sai hankalin gimbiya lafirat ya dugunzuma tace, ai idan akayi haka ni burina bazai cika ba na ganin cewa na kashe mahaifina da yar uwata da hannuna tunda wata kula bana nan za'ayi yakin. Ku tuna cewa nayi alkawarin ba zan karbi addininku ba har sai na ga na cika wannan buri nawa. Shin bakwason na karbi addinin naku ne? Saadda sarki uwaisul karni da uzaifat sukaji wannan tambaya sai jikinsu yayi sanyi, suka sunkui da kawunanzu kas suka yi shiru basu ce kala ba. Daga can sai sarki uwaisul karni ya dago kai ya dubi lafirat yace, ya ke yata hakika kinyi babban ganganci da kika daukarwa kanki wannan alkawari mai nauyi kuna mai wuyar cikawa tunda ako yaushe zaki iya rasa rayuwar ki. Kinga kuwa idan har kika mutu baki karbi addininmu ba kin mutu kafira baki da rabo gobe kiyama. Ni a yanzu tawa shawarar kuma bisa hangena ke da uzaifat zaku tafi izuwa can birnin shumbul domin a hangena ke kadai ba zaki iya wannan aiki ba na ceto rayuwar jamaarmu da ta luhaira saboda babu wani abu da kike takama dashi sama da tsagwaron iyakar karfin dantsenki da sihirin tsafi. Na tabbata mahaifinki ya fiki karfin sihiri don haka ba zaki iya datea hijaban da ya sanya ba na bayar da tsaro da a wuraren da ya boye jamaarmu shi kuwa uzaifat zai iya keta hijaban da karfin addua kinga kenan kuna bukatar juna ku biyun tunda ke kin san wuraren da zaaje, shi kuma zai iya shigo ko ina. A gaba daya dakarun babu wanda zai iya tarar sarki shaaran face ni. Haka kuma na yarda da sauran dakaruna a cikinsu akwai wadanda zasi iya taka muhimmiyar rawa a wannan yaki. Zan yi iya kokari na na ga na hallaka sarki shaaran sannan na fuskanci yar sa sazirat. Babbar matsalar mu itace ta yaya zamu iya sato yarima ukashat daga cikin sansanin yakinsu a lokacin da ba a yin yaki musamman cikin dare? Koda jin wannan tambaya sai yarima uzaifat da lafirat suka sake kallon juna a kari na biyu sukayi shiru. Lafirat tayi ajiyar zuciya tace, ni kadaice zan iya wannan aiki tunda na fiku sanin dukkan matakan tsaron da ke sansanin mutanen mu kuma zan iya amfani da makirci irin namu na mata. Amma ina bukatar kwana biyu rak nayi nazari akan wannan alamari. Sarki uwaisul karni yayi murmushi yace, na baki wannan dana amma ki sani cewa lallai a ranar kwana na nake son ki cika wannan aiki in yaso kashe gari sai kusan yadda zakuyi ku sulale ku tafi can birnin shumbul ba tare da kowa ya sani ba. Lafirat ta maida wa sarki martanin murmushi sannan ta ce, an gama ya shugabana. Kashe gari da safe bayan jamaar kowanne bangaren sun kintsa sai sarki shaaran yasa aka Busa kahon ci gaba da yaki. Nan take dakaru suka hau sahu sahu akan layi akan fuskanci juna. Mahaya layinsu da ban, mayakan kasa ma layin su daban. Bayan kowanne bangare ya gama shiri tsafi sai sarki shaaran ya zaburi dokinsa izuwa tsakiyar filin yakin ya tsaya. Koda ganin haka sai shima sarki uwaisul karni ya zaburi nasa dokin ya tunkareshi har yana shirin zare takobinsa domin a zatonsa sune zasi fara bude fagen yakin sai sarki shaaran ya dubeshi yayi masa murmushi yace, ai ba fitowa nayi ba domin mu yi yaki da kai ba. Nafitone domin kaima ka fito mu tsara yadda zaaci gaba da wannan yaki domin mu gaggauta kawo karshen yakin kuma mu kece raina a tsakanin mu. Idan har ka yarda da kanka kuma ka yarda da mayakan ka. Ina son mu fara fito na fito da mutum goma sha bibbiyu daga cikin jamaarmu su yaki juna a yau. Gobe kuma sai mu fito da mutum dari dari, jibi mutum dubu dubu. A ranar kwana ma uku mu ninka sau goma. A haka za acigana da yakin har mu karshi. Koda jin wannan batu sai sarki uwaisul karni yayi shiru yana nazari, kawai sai yayi addua a cikin zuciyar sa yace, Allah ka bamu saa a cikin wannan sabone sako da wannan makiya namu yazo dashi kuma idan wani makircin yaki ya shirya mana kada ka bashi nasara akanmu. Koda gama wannan addua sai sarki uwaisul karni ya dubi sarki shaaran ya ce, na yarda da kaina kuma na yadda dakaruna. Nayi imani cewa ubangiji na zai bamu sa'a akanku don haka na amince da wannan tsaru da kazo dashi. Koda jin haka sai sarki shaaran ya tuntsire da dariyar mugunta irin tasu ta kafirai sannan yace, muje izuwa mahaukaci ya hau kura. *********************** Najibullah Muhammad *********************** Kawai sai ya kada linzami dokinsa ya juya da baya ya koma cikin jamaarsa. Shima sarki uwaisul karni ya koma cikin tasa rundunar. Jim kadan sai ga dakaru goma sha biyu daga kowanne bangare sun fito sun nufi tsakiyar filin yakin. Su dai wadannan dakaru goma sha bibbiyu kwararru ne masana yaki kuna abin kamar hadin baki domin kowanne bangare ya zabi dakaru mafiya sa'a a wajen yaki wadanda a tarihin yake yakensu ko rauni ba a tana ji musu ba. A bangaren mayakan sarki uwaisul karni kuwa, cikin wadannan mutane sha biyu akwau wani saurayin sadaukin gaske mai suna aba Huraira. Aba Huraira ya kasance kyakkyawan saurayi maabocin hidimar addini kuma yana da tarin ilimi na alkurani da sauran litattafai na addini. Shekarunsa gaba daya ba zasi fi ashirin da uku ba. Ya kasance makusancin sarki uwaisul karni domin kusan kullum ko yaushe suna tare dare da rana basa rabuwa face idan lokacin bacci yayi. A kullum aba Huraira ne ke kuka da shimfidar sarki uwaisul karni ya aminta dashi ainun yana matukar kaunarsa shima haka. A takai ce dai sun shaki da juna. Tun aba Huraira yana shekara goma sha daya yakewa sarki uwaisul karni wannan hidima ta kuka da shimfidarsa kuma tun a sannan aba Huraira ya taso da tsananin Farin jini a wajen yan matan birninsu amma har ya cika saurayi bai taba yin soyayya ba kuma bai yi tunanin yin Aure ba. Bisa wannan daliline wata rana sarki uwaisul karni ya kirawo shi suka kadaita a cikin turakarsa ya dubeshi yace, ya kai babban masoyina aba Huraira kayi sani cewa Allah ya yi maka gagarumar baiwa guda biyu. Ka kasance kyakkyawan saurayi kuma sadauki abin kwarance domin a duk fadin garin nan babu gaba da kai face yaya na uzaifat da ukashat. Abu ma biyu Allah ya baka tarin ilimi mai yawan gaske tun shekarunka basu kai haka ba. Me zai hana kayi aure da wuri ko Allah ya sa ka haifa mana wadansu yayaye irinka? Saadda aba Huraira yaji wannan batu na sarki sai ya sunkui da kansa kas cikin alamun kunya yana yake yace, ya shugabana kaine mafi sanina a duk fadin wannan gari namu. Ni maraya ne kuma tun ina da shekara bakwai a duniya suka mutu a wani yaki da akayi da mutanen birnin shumbul. Tun daga sannan nadawo hannunka ma zamo uwata d ubana. Bani da wani abokin shawara sama da kai. Ya shugabana wallahi ban isa ma zabawa kaina matar aure ba kuna duk zabin da ka bani shi zan karba. Koda jin haka sai hankalin sarki ya dugunzuma yace, haba ya kai aba Huraira kayi sani cewa kowacce zuciya akwai abinda yakan kawatu a cikinta. Blallai bane zabina yayi maka dadi ba. Dajin haka sai aba Huraira ya numfasa yace, ai kuwa har abada ni bazan iya yiwa kaina wannan zabi ba domin tutuni na dauki wannan alkawari a zuciyata cewar babu abinda zan gudanar da shi na rayuwata face bisa kan umarninka. Ya shugabana na sani cewa Allah ya baka baiwa ta ganin alamura da zasi faru a gaba cikin mafarkinka saboda haka kayi mini istihara bisa wannan alamari duk abinda da Allah ya nuna maka a kaina a cikin mafarkin ka zartar dashi a gareni amma ina rokonka alfarma guda daya. Lallai kadaka ka sanar dani abinda ka gani a cikin mafarkinka har sai ranarda alamarin ya faru. Kod jin wannan batu sai jikin sarki uwaisul karni yayi sanyi domin bai sao faruwar hakan ba don gudun kafata hango abinda bashi yaje son gani ba, amma sai ya yi ajiyar zuciya yace, to shikenan ya kai babban masoyina Allah ya za'a mana alherinsa. Aba Huraira yace, amin Sannan suka ci gaba hira har dare ya raba sosai. Koda aba Huraira yaga sarki uwaisul karni ya fara gyan gyadi daga zaune sai yayi masa sallama ya tafi izuwa nasa dakin. Fitarsa ke dawuya sai sarki uwaisul karni ya mike tsaye yayi alwala sannan yazo ya gabatar da nafila rakaa biyu. Bayan yayi sallama sai yadaga hannayenasa sama ya roki Allah yana maicewa, Allah ka nuna min matar da aba Huraira zai aura a cikin baccina kuna ka nuna mini dukkan abubuwan alheri da kishiyarsa masu kusantar jamaata da birninmu gaba daya. Koda gama wanna addua sai sarki uwaisul karni ya kwanta. Kwanciyarsa ke wuya sai bacci ya daukesbi bai farkawa a sai daf da asuba. Yana farkawa kuwa ya tashi yaje yayi alwala ya tafi masallaci aka yi sallah da tare da shi. Bayan an idar da sallar ne ana cikin yin addua sai sarki uwaisul karni ya tuno da mafarkin da yayi a jiya daddare. Nan take alamarin mafarkin gaba daya ya dunga zuwar masa a cikin ransa tamkar a sannane yake mafarkin. Kawai sai aka ga hawaye ba zubowa sarki uwaisul karni daki daki kuma ya kasa daina zubar da hawayen. Alamarin da ya dugunzuma hankalin Lima da sauran jamaar dake masallacin kenan. Lima ya kasa hakuri ya dubi sarki uwaisul karni yace, ya shugabana me ya faru gareka kake ta faman zubar da hawaye haka?. Koda jin wannan tambaya sai sarki uwaisul karni ya sunkui da kansa kas yace, babu komai Liman. Kawai sai ya mike tsaye ya fita daa masallacin ya nufi gida. Daga wannan rana sai sarki uwaisul karni ya kwana bakwai yana kuka dare da rana kuma a tsawon bakwai bai sake yarda sun hada idanu da aba Huraira ba. Duk saadda aba Huraira yazo wajen sa sai ya sunkui da kansa kas ya dauki alkurani ya ta karatu har sai shi kansa aba Huraira ya tashi ya tafi don kansa sannan sai sarki uwana karni ya ci gaba da kuka abinsa. Shi kansa aba Huraira da ya ga sauyin yanayi a tare da sarki uwaisul karni a gareahi sai hankalinsa ya dugunzuma to amma da yaga sarki uwaisul karni ya saki ransa bayan kwana bakwai sunci gaba da hulda kamar yadda suka saba sai hankalinsa ya kwanta bai kara jin wata damuwa ba a ransa. Tun daga wannan lokaci kawo izuwa wannan rana da aba Huraira ya fito wannan yaki a cikin mutane gona sha biyu da aka zabo sarki uwaisul karni bai baiwa aba Huraira labarin wannan mafarkin da yayi ba akansa kuma shima bai tambayeshi ba. Lokacin da aba Huraira ya gyara damararsa kuna ya zare takobinsa cikin kuzari da yarda da akai sai yazo zai gifta ta gaban sarki uwaisul karni. Koda suka hada idanu sai sarki uwaisul karni yayi sauri ya sunkui da kansa kasa bai yarda ya dago sun hada idanu ba har aba Huraira ya isa tsakiyar filin yakin tare da sauran yan uwansa mutum sha daya. Bayan dakarun kafirai mutum sha biyu sun fuskanci DAKARUN MUSULUNCI sha biyu ana shirin Busa kaho don basu umarnin fara yaki, sai aba Huraira ya juyo da fuskarsa baya ya dubi inda sarki uwaisul karni ke tsaye sai kuwa suka hada idanu. Nan take sarki uwaisul karni ya ga kwalla a idanunsa amma kuma yana yi masa murmushi da wani irin kallo mai nuna alamun bankwana. Alamarin da ya mutukar baiwa sarki uwaisul karni mamaki kenan kuna ya karya masa zuciya bai san saadda hawaye y subuto masa ba har aba Huraira ya ga hawayen. A dai dai wannan lokaci ne aka busa kahon fara yaki, mayakan guda ashirin da gudu suka kacame kowa ya zabi abokin gwaminsa aka soma kwabsa azababben yaki, kura ta turnuke filin yakinn, karar karafliyar karafa ta da tartsatsin wutana tashi. Maza suka soma cakuduwa da kirazan damakansu na bangazar juna. Sai da aka shafe sa'a uku cur ana wannan gumurzu ya zamana cewa mutum ashirin da buyi duk sunyi ragas saura mutum biyu kacal suna fafatawa. Wadannan mutane biyu ba wadansu bane face aba Huraira da wani babban hadimin sarki shaaran wanda Shima a shekaru ba zai fi aba Huraira ba kuma ya kasance kyakkyawan saurayi mai kirar sadaukai ana kiransa da suna salhaf. Kamar yadda aba Huraira ya shaku da sarki uwaisul karni haka shima salhaf ya shaki da sarki shaaran harm shakuwar taci wacce ke tsakanin tasu aba Huraira da sarki uwaisul karni domin duk duniya babu mutumin da us isa ya baiwa sarki shaaran abinci ko abin sha yayi amfani da shi face salhaf. Babu wani sirri na sarki shaaran wanda salhaf bai sani ba, kuma bashi da wani abokin shawara sama dashi. Kai saboda tsananin yarda da kauna irin wacce sarki shaaran ke yiwa salhaf sai ya zamana cewa ya bashi gaba dayan sirrikan tsafinsa ba tare da lafirat da sazirat sun sani ba. Lokacin da gumurzu ya kai gumurzu tsakanin aba Huraira da salhaf ya zamana cewa karfinsu yazo daya sun kasa cutar da juna sai salhaf ya fara amfani da sihirinsa domin cutarda aba Huraira shikuwa aba Huraira sai kama karanta adduoin nema tsari don haka sai tsafin yaki tasiri a haka suka shafe sa'a guda a banza. Da kansu suka yarda takubbansu suka kacame da kokawa suka hau naushi da bugun juna. A wannan lokaci ne fa gadan ya sauya salo domin nan da nan suka hadawa junansu jini da majina kuma a sannane hankalin sarki uwaisul karni da na sarki shaaran ya dugunzuma ainun har suka kasa ci gaba da zama akan dawakansu ya zamana cewa sun sauko sun matsa daf da su aba Huraira kowanne na karawa nasa matayakin kwarin gwiwa da baki suna yi masu kirare da yi zuga. Nan ga samarin biyu suka kara kaimi wajen ragargazar juna. Har ta kaisu fmda cewa sun yiwa juna jina jina, jiri na dibarsu suna faduwa amma sai kaga sun sake mikewa sun kacame da sabon gumurzu. Wani lokacin kaga sun rukunkume juna da kokawa su fadi suna birgima su fadi nam su tashi can suka rinka birgima a kas. A wannan lokaci ne sarki shaaran d sarki uwaisul suka far kuka saboda ganin cewa kowannensu zai rasa masoyinsa, sukaji kamar su raba fadan amma da zarar sun dubi jamaarsu wadanda ke kallon gumurzun sai su kasa. Bayan aba Huraira da salhaf sun galabaitar da juna ainun har takai cewa basa iya mikewa tsaye a durkushe suke naushi da bugun juna sai kawai sarki shaaran ya zare wat wuka a jikinsa ya salhaf. Salhaf yayi sauri ya cafe wukar ta cakawa aba Huraira a tsakiyar cikinsa. Wukar ta nutse a cikinsa, aba Huraira ya kwada kabbara da karf. DAKARUN MUSULUNCI Littafi Na Uku 3 Part F 💯👌 Marubuci Abdul Aziz Sani Madakin Gini✍️ Typing Umar Farouq Zango🤝 Posting Najibullah Muhammad 🥷🥷 Note: Ina yiwa dukkan jama'ar wannan gida masu bibiyar littatafan da muke kawowa barka da Sallah, tare da fatan kowannenmu yayi sallah lafiya Kuma cikin aminci Allah yasa haka Amin🙏 Bayan haka Ina Mai Kara Baku hakuri sakamakon dakatar da kowane posting da mukayi na kwana biyu, hakan ya faru ne a dalilin watan Ramadan Mai albarka da muka tsinci kanmu ciki, shiyasa muka zubar da gaba dayan makamanmu domin Neman yardar Allah ♥️💯🙏 Kuma Muna Fatan Allah yasa Muna daga cikin yardaddunsa, Allah Kuma ya tattara mu a cikin gidan Aljannah kusa da MUHAMMADAN RASULULLAHI SALLALAHU ALAIHI WASALLAM ♥️💯💯🙏🙏🙏 Muna yiwa kowa fatan Alkhairi. Naku har kullum wato Najibullahi Muhammad 🥷🥷🥷 Marubucin ya ci gaba da cewa:- Kawai sai aka ga salhaf ya kama kyalkyala dariyar mugunta. Ya mike tsaye da kyar yana dariyar. Bazato ba tsammani sai kuma aka ga Aba Huraira ya zare wukar daga cikinsa ya daka stalle daga inda yake durkushe tamkar biri ya dira akan salhaf kawai sai yasa wukar aka wuyansa yayi masa yankan rago. Nan take salhaf ya kife kasa matacce shima Abta Huraira ya fado kasa ya baje yana kakarin mutuwa. Lokaci guda sarki shaaran da sarki uwaisul karni suka ruga garesu kowa ya rungume nasa a kirjinsa suna matsanaicin kuka. Cikin matukar karfin hali Aba Huraira ya dubi sarki uwaisul karni yace, ya shugabana kayi sani cewa tuntuni Allah ya nuna mini a cikin mafarkina cewa ba zanyi aure ba har na mutu kuma a filin yaki zan samu shahada. Naji a jikina cewa kaima abinda ka gani ke nan a cikin mafarkin ka shi yasa ka kasa sanar dani. Shin abinda na fada gaskiya ne ? Ma za ka sanar dani kafin rai yayi halinsa domin kuwa dama alkawarin dake tsakaninmu cewar baza ka sanar dani mafarkina ba sai ranar da abin da ka gani a mafarkin ya faru. Koda jin wannan batu sai sarki uwaisul karni ya sake fashewa da kuka kuma ya dada kankame Aba Huraira a kirjinsa ya ce, Ya kai masoyina tabbas zamcenka dutsene, abinda kaga ni shi na gani a cikin nawa mafarkin. Gama fadin hakan ke da wuya sai Aba Huraira ya biya Kalmar shahada ya rasu. Nan take uwaisul karni ya kasa sakin gawar Aba Huraira yayi ta kuka kamar ba zai taba dainawa ba. Shima sarki shaaran haka yaci gaba rungumar gawar salhaf ya kasa tashi har sai da kowannensu jamaar sa suka daukeshi kuma suka da dauke gawarwawkin dake filin yakin A wannan rana sai da kowa yayi bakin cikin mutuwar wadannan kyawawan samari biyu. Uzaifat da Lafirat ma sun sha kuka mai yawa. Haka ma a can bangaren sai da ukashat da sazirat suka sha faman nasu kukan. Kai gaba dayan mayakan dake wannna sansanin yaki babu wanda bai zubar da hawaye ba saboda wannan gagarumin rashi da akayi. Kashe gari da safe kuwa aka sake ta busa kawon ci gana da yaki. Sai da aka fito da mutane dari dari daga kowanne bangare kamar yadda akayi alkawari. Ba tare da bata lokaci ba aka bada umarni wadannan mayaka dari biyu suka kacame da azababben yaki. Sa'a daya akayi ana wannan gumurzu sai gashi an kashe mutum tamanin daga cikin dakarun kafirai. Mutum ashirin sun raunana ainun yadda bazasu iya moruwa ba. Watakila ma anan gaba su rasa rayuwar su. A bangaren dakarun musulunci kuwa, mutum talatin kacal aka kashe aka raunana saba'in, kuma ba Irin raunin da zai zama sanadin ajalinsu ba. Dama anyi kaida cewa sa'a daya na cika za a tsaida yakin, walau anyi nasara ko baayi nasara ba. Don haka lokaci na cika aka busa kahon tsaida yaki kowanne bangare ya rugo ya kwashe gawarwakinsa da raunatattunsa. Lokacin da sarki shaaran yaga cewa wannan yakin an fisu rinjaye, gashi kuma na jiya ragas akayi, sai ya cika da tsananin bakin ciki mara misaltuwa, don haka sai ya sake kadaita da ukashat da sazirat cikin tantinsa yace dasu, ina mai yi muku tini da cewa gobe fa itace damarmu ta karshe bisa abinda muka shirya domin samun nasara akan wannan abokan gaba. Kun sani cewa a gobe mutum dari biyar biyar zasu fafata wannan yaki, don haka lallai a cikin su ne daya daga cikinku zaiyi badda kama ya sato mana gawar abokan gana guda daya yazo da ita ba tare da kowa ya ganshi ba. Kai ukashat lallai kaine zaka yi wannan aiki. Kuma kaine zaka sa tufafin gawar kaje can sansanin abokan gaba ka sato mana gimbiya Lafirat. Koda jin wannan batu sai ukashat yayi murmushi yace, ya shugabana na ka kwantar da hankalinka tamkar tsumma a randa. Na rantse da darajar burin zuciyata sai na sai na sami nasara bisa wannan aiki a gobe kuma sai na sato Lafirat na kawota nan gabanka. Da jin wannan batu sai sarki shaaran ya cika da Farin ciki ya kama kyalkyla dariyar mugunta. Daga can kuma sai dariya ta juye izuwa kuka har da hawaye. Alamarin da ya matukar baiwa ukashat da sazirat mamaki kenan. Cikin matukar damuwa sazirat ta dubi sarki shaaran tace ya kai Abbana ina dalilin wannan kuka naka ? Sarki shaaran yayi ajiyar zuciya, sannan ya sa hannu ya share hawayen idanunsa yace, ya ke yata kiyi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da wannan kuka ba face tunowa da masoyina salhaf. Na rantse da darajar tsafi idan muka sami nasarar wannan yaki sai anyiwa sarki uwaisul karni da duk iyalansa kisan gilla irin wanda ba a taba yiwa wani bil adama ba a duniya. Koda jin wannan batun sai ukashat yaji ransa ya baci saboda jin cewa za'ayi wa mahaifinsa kisan gilla duk da cewa ko kadan baya kaunar mahaifin nasa a cikin zuciyar sa, amma kuma sai ya danne damuwarsa a cikin ransa bai nuna na a fuskar sa. Nan dai sazirat ta shiga rarrashin sarki shaaran tana bashi baki. Shikuwa ukashat sai ya mike tsaye ya fita daga cikin tantin ya barsu su biyu. A can sansanin mayakan sarki uwaisul karni, a cikin tantinsa hankalin uzaifat dana Lafirat a tashe yake domin tun daga lokacin da aka kashe Aba Huraira sai sarki uwaisul karni yashiga cikin wani irin hali na rashin ci da sha da kuma rashin baccin dare ida rana ya zamana cewa bashi da aikin yi sao jan carbi, tunani da zubar hawaye. Da kyar da Sidin goshi uzaifat ke lallabashi yaci dabino guda biyu rak, kuma ya karbi ruwa sau daya a tsawon rana guda. Alamarin da ya jefa kowa cikin damuwa kenan saboda sanin cewa rashin yin baccin sarki uwaisul karni ba karamar ila bace akan samun nasarar yakin. Dama idan har sarki uwaisul karni zaiyi bacci, to tabbas Allah zai nuna masa duk irin kaifin abokan gaba da zasu shirya a yakin da za'ayi kashe gari. Yanzu gashi kowa yasan cewa abu ne mawuyaci sarki uwaisul karni yayi bacci a daren yau saboda alhinin masoyinsa Aba Huraira kuma gashi yakin da za'ayi gobe mai zafine tunda mutum dari biyar biyar ne. Bisa wannan daliline uwaisul da lafirat suka tafi izuwa tantin da uwar mayu da hirama suke suka zauna tare da domin suyi shawara bisa irin matakin da ya kamata su dauka a yakin da za'ayi gobe. Kafin kowa ya fara magana sai Hirama tai gyaran murya tace, ina da uzuri guda daya. Cikin mamaki uzaifat ya dubeta yace, fadi uzurinki muji yake Hirama. Hirama tayi ajiyar zuciya tace, ina mai rokon alfarma guda biyu rak a wajenku. Alfarmar ta farko itace, ina so ku shigar dani cikin wannan addini naku yanzu take. Alfarma ta biyu ina so koda bayan wannan yaki ne mu koma can dajin Huzurul Has mu yaki iyayena mu kawar da su domin indai suna nan a raye ba zasu daina cin naman mutane ba dana aljanu kuma ba zasu bari a rinka ratsa dajin ba. Saãd uzaifat da lafirat sukaji wannan batu sai suka cika da tsananin Farin ciki. Uzaifat ya dubi Hirama yace, ke kuwa menene ya janyo hankalinki har kikaji kina son ki karbi addininmu? Hirama tace, ai na ga abubuwan alajabi da yawa a cikin tafiyata da ku. Duk balain da muka shiga sai na ga mun kubuta da zarar dayanku ya nemi taimakon ubangijin musulunci. Hakance tasa na tabbatar da cewa lallai wannan addinin shine addinin gaskiya domin babu wani tsafi ko wata dabara da ta isa ta cecemu. Koda jin haka sai uzaifat yayi kabbara, nan take uwar mayu ta biyawa Hirama Kalmar shahada ta maimaita sannan suka rungume juna. Uwar mayu na cewa, tabbas yanzu kin zamo cikakkiyar yar uwar mu. Da ni dake da uzaifat mun zama tamkar jini daya. Cikin alamun matukar damuwa uwar mayu ta dubi Lafirat tace, yake wannan jaruma me yasa kema bazaki karbi addinin Allah ba yanzu take domin ki zamo cikakkiyar yar uwarmu tunda dai kin aminta dashi? Kodajin haka sai lafirat tayi murmushi ta ce, kada ki damu yake kawata tabbas nima ina daf da samun wannan babbar rabo. Yanzu dai sai muyi shawara bisa abinda ke gabanmu, wato dangane da yakin da za'ayi gobe na mutum dari biyar. Koda jin haka sai uzaifat yayi murmushi yace, to yanzu sai ku fadi taku shawarar naji domin nima ina da tawa shawarar a zuciyata. Uwar mayu tayi gyaran murya tace, ni dai a ganina babu abin da ya kamata muyi face muje mu sami mahaiimu sanar da shi cewa ya dakatar da wannan salon yakin da ake yi yanzu. Gwara kawai ayi fito na fito gaba daya a karar da yakin kowa yasan makomarsa a huta da fargaba. Koda jin haka sai uzaifat yayi murmushi yace, ai wannan shawarar taki ba abar karba bace, ina tabbatar miki da cewa shi kansa sarki bazai aminta da hakan ba, domin akwai dabarun da muka shirya a sirrance don ganin mun sami nasarar da muke nema. Idan kuwa muka katse yakin da wuri bukatarmu bazata biya ba. Ke kuma fa Hirama fadi taki hikimar muji, domin na gamsu da cewa ke mai hikima ce tunda har kika iya kubutar damu a lokacin da mahaifinki ya jefamu a cikin kejinsa da nufin ya cinyemu. Saadda Hirama taji haka sai tayi murmushi tace, ai ba hikimata bace ta kubutar daku ba, kawai dai saace da kuma taimakon ubangijin musulunci. Ni a ganina yakin da za'ayi gobe mai hadarin gaske ne, saboda kun ga yakin da akayi yau mune da nasara kuma abokan gaba sunyi matukar bakin ciki dole ne suyi babban tanadi na ramuwa. Abinda za'ayi shine, ya kamata kai ko Lafirat daya daga cikinku yayi bad da kama gobe ya shiga cikin dakaru dari biyar din da za'a fafata dasu domin ya ragargaji kafirai saboda babu mamaki suma sunyi irin wannan tunani. Kodajin wannan batu sai uzaifat da lafirat suka jinjina kai da suka gamsu da wannan shawara uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, wallahi nima nayi irin wannan tunanin naki don haka tabbas nine zan bad da kamannina na shiga cikin dakarun dari biyar din amma abinda nake so da ku shine kuyi shiru da bakinku kada ku fadawa kowa wannan shawara da muka yanke domin idan sarki yaji ba Zak yarda na shiga ba saboda bai yarda da hainci ba koda a cikin yaki. Shi mutum ne laifi daya mai magana daya. Cikin hadin baki Hirama, Lafirat da uwar mayu su kace tabbas ba zamu bari kowa yaji wannan zancen ba. Lafirat ta dubi uzaifat tace, abu na karshe da nake so da kai shine, ka zuba ido da kyau kuma ka lura da dukkan abubuwan da kowanne abokin gaba keyi a lokacin da kuke yakin a gobe saboda a cikin wannan yamutsin na mutum dubu za'a iya shirya makirci wanda ba lallai bane wani ya gani ba. Uzaifat yayi ajiyar numfashi yace, tabbas wannan batu naki gaskiya ne don haka da izinin Allah zan kuma sosai. **DAKARUN MUSULUNCI** Littafi Na Uku 3 Part G Marubuci :- Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing:- Umar Farouq Zango Posting:- Najibullahi Muhammad 🥷🥷🥷 Marubucin Ya ci gaba da cewa Kashe gari, wato rana ra uku dakurn musulunci da dakarun kafirci suka sake fitowa filin daga kamar yadda aka saba. Nan take dakarun kafirai suka fito su dari biyar sanye da bakaken kaya kuma dukkanin su sun rufe fuskokin su da bakaken rawani idanunsu kadai ake gani. Wani abin mamakin kuma kowannensu ya sanya katuwar bakar alkyabba a jikinsa sannan suna haye akan bakaken dawakai. Al'amarin da ya bawa dakarun musulunci mamakin kenan domin basu taba ganin an fita yaku da irin wannan shiga ba. Lokacin da sarki uwaisul karni yaga dakarun kafirai su dari biyar sun fito filin daga, amma dakarun musulunci sun yi jinkiri basu fito ba sai ya fusata ya dakawa sarkin yakinsa na wannan runduna tsawa yace, ya Kai habinullahi ina dakarun da nace ka waresu ne tun jiya, me suka tsaya yi haryanzu basu fito ba. Cikin rawar baki habinullahi ya budi baki da nufin ya ba da amsa kawai sai ya ga dakarun musulunci su dari biyar dukkanin su sanye da fararen tufafi da kjam fararen alkyabbu, kuma bisa fararen dawakai. Dukkanin su sun rufe fuskokinsu da fararen rawuna. Al'amarin da ya mutukar bawa habinullahi mamaki kenan domin shi akansa bai san da wannan tufafi ba da fararen dawakai. Abinda yazamo kamar hadin baki, sai dai shigar da dakarun musulunci sukayi tafi ta dakarun kafirci ban shaawa da birgewa. Koda sarki uwaisul karni ya ga dakarunsa a cikin wannan shiga sai ya cika da tsananin farin ciki ya rinka yiwa habinullahi kirari harma ya yi masa alkawarin bashi kyauta ta musamman saboda wannan hikima da basira da ya baje a filin yakin a wannan rana. Nan dai dakarun musulunci suka iso tsakiyar filin daga suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya suna fusknatar abokan gaba. Yarima ukasha ne akan gaba a cikin dakarun kafirci. Haka ma yarima uzaifat ne akan gaba a cikin dakarun musulunci. Duk da cewa kowannensu ya rufe fuskarsa da rawani suna yin arba da idanunsu suka shaida juna. Nan take ukashat yaji zuciyar sa ta buga da karfi domin ya san cewa uzaifa zai iya hanashi aiwatar da babban shirin da yazo aiwatarwa yanzu. Amma da ya tuna cewa ai cikin gwamutsi suke na mutum dubu, kuma da zarar an fara yakin kowa zai rasa nutsuwa. Sai hankalinsa ya kwanta ya gamsu cewa lallai sai ya sami nasarar abinda yazo aiwatarwa. Bayan an yi kallon kallo tsakanin bangaren biyu sai aka busa kahon fara yaki. Nan take aka ruguntsume da masifaffen yaki, kura ta turnuke sararin samaniya. Ihun mazaje da haniniyar dawakai da Karar karafa ta cika dodon kunne. Nan fa aka fara turmutsi da yamutsi. Jim kadan kuma aka fara sarki ya hana dawa tsaiwa. Wani lakacin sai dai kaga an safe kan mutum ya yi sama jini ya yi tsartuwa da feshi gangar jikin ta rikito kasa ana tattakata. Abin da Ya firgita kowa shine, an kasa gano bangaren da ke samun nasara domin musulmai na zubewa suna shahada, kafirai na zubewa suna mutuwar banza. Ana cikin wannan gumurzu ne uzaifa ya fara kokarin zuwa ya hadu da ukasha, amma da zarar ukasha ya ga uzaifa Ya tunkaroshi sai ya sulale ya bar wajen. Haka ya yi masa zulliya ya ki yarda su yi gaba da gaba. Kuma a hakan ci gaba suke da yaki kowannensu yana mummunar barna. Yayin da aka sami kudan rabin Saa ana wannan bakin gumurzu sai rabin dakarun dake filin suka zamo gawa. Koda ukasha ya fahimci hakan sai hankalinsa ya dugunzuma domin ya san cewa idan baiyi da gaske ba abin da yake son yi ba zai sami damar yi ba. Kawai yana cikin yin yakin sai yayi wuf! Ya duro kasa akan wata gawa ta musulmi, ya lullube gawar da bakar alkyabbarsa. Cikin tsananin zafin nama ya cure gawar tamkar an dunkule kayan wanki ya cafota da hannu daya ya dafa kasa da daya hannun nasa ya yi tsalle sama ya dira akan dokinsa ya na lullube da gawar Ya ci gaba da yakin a haka har ya tarwatsa dakarun musulunci dake gabansa da karfin tsiya, ya ratsa ta tsakiyar su ya sukwani dokinsa izuwa inda sansaninsu ya ke. Ashe uzaifa ya ga saadda ukasha ya duro daga kan dokinsa amma bai ga abinda ya dauka ba a kasan amma tabbas zuciyar sa ta raya masa cewa lallai wani abu ya dauka. Cikin hanzari uzaifa ya tambayi kansa menene a filin yaki wanda ukasha zai dauka ? Ai babu komai face gawa ko makamai. Ya bawa kansa amsa. Nan take ya aiyana a aransa kawai nima na sci gawar daya daga cikin gawarsu na tafi da ita tunda dai ban ga amfanin da makamin wani zaiyi ba. Daga baya idan nayi nazarin gawar wakin da suka rage a filin yakin da dakarun da suka tsira da rayuwarsu zan iya ganowa idan ma gawar dayanmu ya sace. Gama aiyana hakan ke da wuya sai shima uzaifa ya duro kasa daga kan dokinsa ya lullube gawar kafiri guda daya ya cureta kamar yadda ukasha yayi, ya daka tsalle sama ya dira akan dokinsa ya tarwatsa abokan gaba shima ya durfafi inda nasu sansanin yake. Koda ganin haja sai sauran mayakan da ke faman yakin suka daina yakin kowa ya ruga da baya izuwa sansanin su. Al'amarin da ya mutukar baiwa sarki uwaisul karni mamakin kenan kuma ya fusatshi ya dubi habinullahi a fusakce yace, wannan wane irin shirine na banza da wofi? Cikin biyayya habinullahi ya dukar da kansa kasa yace, ka gafarceni ya shugabana, hakika nayi kuskure. Gama fadin hakan ke da wuya suka ji an busa kahon tsaida yaki. Cikin fushi sarki uwaisul karni ya kada dokinsa ya nufi can sansanin su inda tantinsa yake. A sannane kowanne bangare ya ruga ya debo gawarwakin jamaarasa. Kafin a binne gawarwakin musulman da aka kashe sai da uzaifat yazo ya kirgasu sannan yaje ya kirga wadanda basu mutu ba, take ya gane cewa ba aga gawa daya ba. Kawai sai yayi murmushi domin ya tabbatar da abinda yake zargi. Bayan magriba tayi anci abinci. A can bangaren dakarun kafirci sai sarki shaaran ya rungume ukashat cikin tsananin Farin ciki sannan ya janye jikinsa daga cikin nasa yace, da kyau sadaukin sadaukai, aikinka yayi kyau, ka samo nasarar matakin farko. Yanzu idan dare ya raba sai ka cire tufafin dake jikin wannan gawa da ka sato kasa a jikina ka sadada kaje har can sansanin mayakan su ba tare da an ganka ba ka binciko tantin da lafirat ke ciki ka satita ta kowanne hali ka kawota nan. Koda jin wannan batu sai ukashat yayi murmushi yace, ya shugabana ai shan ruwa yafi wannan aiki sauki a wajena. Lallai zaka sameni nai cika umarninka. Wannan shine abinda ya faru tsakanin yarima ukashat da sarki shaaran bayan an gama yaki. * * * * * * Alamarin yarima uzaifat kuwa, bayan ya Kai wannan gawar ta abokin gaba cikin tantinsa ya lullubeta da alkyabbarsa sai ya zauna ya kurawa gawar idanu ya shiga tunanin mai zurfi bisa abinda ya kamata yayi da gawar, amma babu wata dabara data fado masa. Yana cikim wannan hali ne Lafirat ta shigo cikin tantin ta sareshi. Koda taga yayi tagumi kuna ya kurawa kunshin kaya idanu yana tunani sai ta cika da mamaki. Kawai sai ta wuce kai tsaye izuwa inda kunshin kayan suke ta yaye alkyabbar, nan take tayi arba da gawar badakaren mahaifita Cikin kasuwa da mamaki ta dubi uzaifat tace, me zakayi da gawar abokan gaba? Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, abinda dan uwana ukashat zaiyi da gawar bamu badakaren shi nake son yi da gawar tasu badakaren. Lafirat ta sake dukansa cikin mamaki a karo na biyu tace, ni fa ban gane abinda kake nufi ba. Uzaifat ya dubeta a nutse itace, lokacin da muke wannan yakin na fahimci cewa ukashat ya saci daya daga cikin gawarwakin mutanen mu ya tafi da ita izuwa sansanin su. Saboda haka nima sai na sati gawar nasu badakaren na taho da ita. Wannan tunanin da kika ga na shiga ba ta komai bace face ta kasa gano abinda ukashat zaiyi da gawar da ya sata, wanda shine nima abinda ya kamata nayi. Saadda uzaifat yazo nan a zancensa sai lafirat ta bushe da dariya, sannan tace hakika kai bakon fita yaki ne. Inda ace ka saba fita yaki da dole ne ka gano abinda zaiyi da gawar. Abinda zai yi da ita shine, tufafin gawar zai cire yasa a nasa jikin domin ya sami damar shigowa nan sansanin a cikin dare, ko domin leken asiri ko kuma domin ya saci wani abin. Don haka sai mu san matakin da zamu dauka akansa. Koda jin wannan batu sai uzaifat yayi murmushi wannna ya dubi Lafirat yace, kada kk damu yake Lafirat, ki tafi izuwa tantinki ki kwanta kiyi bacci har da munshari babu abinda zai faru. Na san dan uwana ukashat kuma na san duk irin motsinsa zan kuka da shi. Dajin haka sai Lafirat tayi murmushi tace, na yarda da kai gwarzona dari bisa dari. Na san zaka iya yin abinda yafi haka. Sai da safe, Allah ya tashemu lafiya. Koda gama fadin haka sai Lafirat ta juya tafi ce daga cikin tantin ta tafi nata tantin ta kwanta. Fitarta ke da wuya sai uzaifat ya mike tsaye ya cire tufafin dake jikin wannan gawa ya adanansu a cikin akwatinsa na karfe. Wanda ya zubo wasu makamansa na yaki, sannan ya kwalawa wasu dakaru biyu kira dake tsaye a kofar tantinsa suka shigo da sauri. Uzaifat ya dubi dakarun yace, maza ku dauki wannan gawar ku fita da ita waje ku binneta. Cikin biyayya dakarun suka dauki gawar suka fice da ita, a zuciyar su suna mamakin yadda akayi gawar ta shigo cikin tantin yarima uzaifat. Uzaifat bai kwanta bacci ba sai da dare ya fara rabawa bayan ya gabatar da nafilfilinsa da adduoi sannan ya kashe fitilar tantin nasa ya kwanta yayi lamo kamar yana bacci. * * * * * * A can sansanin su ukashat kuwa lokacin da dare ya raba sai ukashat ya mike tsaye ya dauki tufafin gawar da yasato ya sanya a jikinsa sannan ya daukko wata sharbebiyar wuka ya baiyeta a cikin rigarsa ya fita daga cikin tantinsa. Da fitarsa ya banga can inda sansanin muslmai yake yaga gaba daya nahiyar wajen a haskake yake sakamakon fitilun itatuwa da aka kukkuna masu yawa. Sai ya tabbatar da cewa babu yadda za'ayi yaje wannan wuri batare da an ganshi ba. Haka kuma ya tuna cewa sarki shaaran ya gaya masa cewa sihirin tsafi ba zai yi tasiri ba ballatana ya bace bat ya baiyana a can kawai. Nan fa hankalinsa ya dugunzuma yayi shiru yana tunani. **DAKARUN MUSULUNCI** Littafi na Uku 3 Part H ( Last ) Marubuci :- Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing- Umar Farouq Zango Posting Najibullah Muhammad legends 🥷🥷 Marubucin ya ci gaba da cewa... Daga can sai ya dubi kasa ya ga ai kariyar ciyawace a wajen tun daga bakin sansanin su hat izuwa can sansanin musulmi. Kuma ciyawar tana da dan tsawo har ta haifar da yar karamar duhuwa. Nan take dabara ta fado masa yaje ya tsinko koriyar ciyawar da yawa ya manne ta a jikinsa gaba daya da ita sannan ya kwanta a kas yai ruf da jiki ya dinga tafiya da ina ciki a kas a hankali har ya durfafi sansanin musulmi. Haka yaci gaba da jan ciki, da zarar ya ga wani motsi a gabansa ko giftawar wani sai yayi luf a cikin ciyawa, sai kaga ya saje da ciyawar ko alamarsa ba a gani. Sannu a hankali har ya isa har cikin sansanin musulmi ba tare da wani ya ganshiba. Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda ukashat ke ratsawa ta tsakiyar kafafun dakarun musulunci yana wucesu amma basu ganshi ba kuma basu ki motsinsa ba. Akwai lokacin da ma wani badakare ya taka masa yatsun hannunsa na hagu yaji mugun zafi da zogi saboda takalimin karfe ne mai nauyi a kafar badakaren. Har ukashat yaji kamar ya tsandara ihu amma sai yayi ta maza ya daure ya dauke numfashinsa har sai da badakaren ya dauke kafarsa daga kan hannun nasa ya kara gaba, sannan shima yaci GBA da jan ciki ya durfafi tantin farko dake gabansa. Da zuwansa bayan tantin yana daga kwancen a cikin ciyawar sai ya zaro wannan sharbebiyar wuka tasa ya tsaga tantin ya leka ciki. Ai kuwa sai yaga ashe sarki uwaisul karni ne. A lokacin sarki uwaisul karni na zaune bisa buzu ya idar da nafila yana lazimi. Kawai sai ukashat ya bar wajen ya matsa gaba izuwa tanti na biyu, shima yasa wukarsa ya tsagashi ya leka. Duk da cewar fitilar cikin tantin a kashe take ukashat ya gane cewa uzaifat ne a ciki a kwance domin ya karewa siffar jikinsa kallo ya shaidashi. Ukashat ya kara wucewa gaba izuwa tanti na uku wanda Lafirat ke ciki. Ukashat na barin wannan tantin na biyu sai uzaifat ya mike zumbur ashe yana ganin saadda ukashat ya tsaga tantin nasa da wuka ya leko ya kare masa kallo. Shi ukashat bai san cewa kallon kallo akayi ba. Cikin sanda uzait ya dauki wannan tufafi na gawar daya dauko yasa a jikinsa sannan shima ya cisgi ciyayi ya lullube jikinsa gaba daya da su kamar yadda ukashat yayi ya kwanta a kas yai ruf da ciki ya bi ukashat a baya ba tare da ya sani ba. Lokacin da ukashat ya isa tanti na uku yasa wukarsa ya tsaya tantin sai yai arba da Lafirat kwance tana ta sharar barci abinta har da munshari. Cikin sanda ukashat ya mike tsaye ya shiga cikin tantin ta cikin wannan kafar tsaga da yayi yaje kan Lafirat ya tsaya. Kawai sai yasa hannunsa a cikin aljihu ya dauko banji ya shaka mata a hanci. Nan take barcinta ya kara nauyi. Duk da wannan abu dake faruwa uzaifat na labe a kasa bayan tantin yana lekensa. Ukashat ya juyo da baya ya nufi inda ya shigo cikin tantin. Sai uzaifat yai sauri ya matsa gaba ya kwanta a cikin ciyawa yai lamfo. Kawai sai ya ga ukashat ya fito ya cisgi ciyayi da yawa sannan ya koma cikin tantin ya lullube Lafirat da ciyawar sannan ya janyo ta a kas shima ya kwanta a kas ya ci gaba sa jan ciki kuma yana jan hannun Lafirat da hannu daya. Koda ganin haka sai uzaifat ya bishi a baya a hankali ba tare da ukashat ya ankara ba. Sannu a hankali suka isa har can sansanin. Da zuwa sai ukashat ya mike tsaye ya saba Lafirat a kafadarsa ya shiga da ita cikin tantinsa ya kwantar da ita bisa shimfida. Nan take ya cika da tsananin Farin ciki bisa wannan gagarumar nasara da ya yi ta sato gimbiya Lafirat. Kawai sai ya juya da sauri da nufin ya tafi izuwa tantin sarki shaaran domin ya sanar dashi cewa ya cika umarninsa cikin nasara. Juyowar da zaiyi haka sai yaji biri ya debeshi ya kama tangadi, bai Sam saadda ya sulale kasa ba ya kama barcin dole. Ba komai ne ya haddasa hakanba face banji da uzaifat ya watsa masa a fuska ya shaka. Koda uzaifat ya ga ukashat ya baje a kasa yana barci sai yai sauri ya janyeshi izuwa wajen tantin yayi ruf da ciki ya ci gaba da jansa a kas har ya isa can tantin musulmai janye da shi. Ita kuwa Lafirat sai ya barta a can tantin ukashat dake sansanin kafirai. Lokacin da gari ya waye sai mayaka suka fito sansanin yaki na kowanne bangare suka yi sahu sahu ana kallon juna. Wannan karon dai mutum dubu ne zasu kara da mutum dubu. * * * * * * A can bangaren sarki uwaisul karni babu uzaifat kuma babu Lafisai Habibullah, Hirama da uwar mayu da sauran dakaru, kuma ko kadan sarki uwaisul karni bai damu ba domin tun a daren jiya uzaifat ya dankara masa ukashat a hannunsa. Nan take sarki uwaisul karni yasa aka daure ukashat da murtukekiyar ankwa kafa da hannu a jikin katon turke na karfe. A daren uzaifat ya yai bankwana da sarki uwaisul karni ya sanar da shi cewa shi kam Yanzu zai durfafi can birnin shumbul domin yaje ya kubutarda rayuwar lahira da sauran mutanen su da aka tsare a kurkuku. Nan take sarki uwaisul karni yacika da tsananin Farin ciki yayi ta sawa uzaifat albarka. Kuma ya bukaci sa ya bashi dakaru wadanda zasi masa rakiya. Amma sai uzaifat yace dashi baya bukatar rakiyar kowa face ta Lafirat, don haka shi da ita zasu tafi. Nan dai suka yi sallama uzaifat ya tafi ba tare da ya sanar da sarki uwaisul karni gaskiya lamarin ba cewar yabaro Lafirat a can sansanin kafirai. Abinda yasa yaki gaya masa gaskiyar kuwa shine baya son hankalinsa ya tashi kuma akwai hikimar sa tasa ya barta a can din. * * * * * * A can sansanin kafirai kuwa,lokacin da dare ya tsala da yawa sarki shaaran yaji shiru wato har a sannan baiji dawowar yarima ukashat ba sai hankalinsa ya dugunzuma ya muje zumbur daga zaune ya ruga izuwa tantin ukashat. Da zuwa sai ya iske Lafirat a kwance akan shimfidar sa ta na shara barci, amma babu ukashat a wajen. Nan take sarki shaaran ya cika da mutukar Farin ciki bisa ganin ya sami nasarar sato Lafirat. Amma kuma sai yayi mamakin rashin ganin ukashat a lokaci. Kawai sai ya ga wata yar karamar takarda akan akwatin ukashat. Cikin sauri ya dauki takarda ya warwareta ya ga ashe sako ne aka rubuta waiska. Nan take ya fara karanta bayanin dake cikin takarda kamar haka :- Takarda daga hannun ukashat zuwa ga shugabana kuma sarki na sarki shaaran na birnin shumbul. Dalilin rubuta naka wannan wasika shine, domin na sanar da kai cewa na samu nasarar sato Lafirat wacce ita kadai ce zata iya yiwa makiyanmu jagora izuwa cikin birninka. Ni yanzu tini na tafi izuwa birnin Darul Husuf domin naje na tono wadannan layu guda hudu don haka zan jiraku a can sai ku taho da sauri domin mu aiwatar da abinda ke gaban mu. Koda sarki shaaran ya gana karanta wannan wasila sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya. Karfin dariyar ne yasa Lafirat ta farka da ga barcin da take mai nauyi sakamakon banjun da ta shaka. Koda tayi arba da sarki shaaran a gabanta kyalkyala dariya sai ta firgita ainun ta bude baki da nufin ta kira sunan Allah, amma sai sarki shaaran ya gabza mata naushi a wuya ta sulale kasa sumammiya. Nan take yayi nuni da hannunsa izuwa kanta ta sake cigaba da barci mai gaske, sannan kuma wata sarka ta tsafi ta kanannade jikinta gaba daya. Cikin sauri sarki shaaran ya kira sunan wani aljani waishi muruzul kurbaz. Kawai sai kasa ta stage aljanin ya Faso ta ciki ya baiyana a gaban shaaran yana mai sujjuda a gareshi. Girman aljani muruzul Kurabz ya kai a cure giwaye goma a wajen guda sannan ya na da fuka fukai goma sha hudu manya manya a jikinsa. Baiyanar aljani muruzul kurbaz ke da wuya sai ga sazirat ta shigo cikim tantin. Koda taga yar uwarta Lafirat kwance a gefe daya, kuma a daure cikin sarka sai ta cika da tsananin Farin ciki ita da mahaifinta. Sarki shaaran ya dubi aljani muruzul kurbaz yace maza ka daukemu ni da yata sazirat ka kaimu can kusa da kofar birnin Darul husuf domin mi cisu da yaki kuma mu sato muzaira. Koda jin wannan umarni sai aljani muruzul kurbaz ya risina cikin biyaiyya yace, an gama ya shugabana. Nan take ya rankwafa sarki shaaran da sazirat suka hau kansa suka zauna. Kawai sai ya bude fuka fukansa y luluka izuwa can kololuwar samaniya ya bace bat, a cikin gajimare. Sarki shaaran da sazirat na kyalkyala dariyar Farin ciki. Abinda basu sani ba shine, ukashat bai tafi can birnin Darul Husuf ba domin tono layun nan guda hudu. Yanzu haka yana can a tsare a hannunsu sarki uwaisul karni. Kuma wannan wasila bashi ya rubutata ba uzaifat ne domin kawai yaja hankalinsu su zata cewa ukashat na kan cikinsa. A halin yanzu tini uzaifat ya tunkari birnin shumbul domin yaje ya kubutar da rayuwar jamaar su da a tsare a kurkuku da kuma rayuwar Luhaira yar likita abu sharhaz. A dai-dai Nan littafi na uku ya kare, marubucin ya ce mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI na hudu don Jin yadda zata kaya tsakanin Uzaifat a birnin Shumbul..