DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA BIYU 2 Marubuci:- Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing:- Umar Farouq Zango. A can birnin Darul Husuf kuwa, lokacin da kwanaki bakwai suka cika sai mutanen birnin suka taru a fada domin ganin yadda za'a fito da gawar sarki a masa jana'iza, a wanna lokaci gidan sarautar yayi tsit ba'a jin komai face sautin iskar dake kadawa. A can kofar turakar sarki kuwa shulaifa da muzaira ne a gefe daya a tsaye yayinda sauran bayi da kuyangin gidan suma sukayi sahu sahu, kowa kansa a sunkuye, a gefe guda kuma sauran yan majalisar sarki ne suma sunyi sahu sahu kowa kansa a sunkuye. Bayan wasu wani lokaci sai kawai akaji karar bude kofar turakar sarki, sai kowa ya dago kai domin ganin yadda za'a fito da gawar sarki. Kwatsam ba zato ba tsammani sai aka ga sarki ya fito yana takawa da kafafunsa cikin koshin lafiya, bai doshi ko ina ba sai inda matansa suke, wato inda mulaifa da shulaifa ke tsaye. Yana zuwa gaban su ya tsaya sannan ya dubi muzaira yace kinyi mamakin ganina a raye ko, wannan kadan daga ikon Allah kenan, gubar da kika bani gashi bata kasheni ba. Koda gama fadin haka sai muzaira ta sulale kasa sumammiya. Lokacin da sarki uwaisul karni yada matarsa muzaira ta sulale kasa sumammiya, sai ya dubi dakaru ya ce, ku dauketa ku kaita kurkuku ku kulleta. Nan take kuwa wasu dakaru biyu suka cika wannan umarni. Faruwar hakan ke da wuya, sai shulaifa ta ruga ga sarki uwaisul karni ta rungumeshi cikin farin ciki, tana mai godiya ga Allah da ya tserar da rayuwarsa. Sarki uwaisul karni ya janye jikinsa daga cikin na shulaifa, sannan ya dubi wani hadiminsa yace, kaje kayi shela a gari cewar kowa ya hallara a fada yau da yamma bayan sallar la'asar. Hadimin ya risina yace, an gama ya shugabana. Bayan anyi sallar la'asar kuwa, sai fadar ta cika ta batse da jama'a, ya zamana cewa duk inda mutum ya duba babu abinda zai gani face kawunan bil adama rututu, babu masak tsinke. Jim kadan da gama taruwar jama'a, sai ga sarki uwaisul karni ya fito Fes da shi yaci ado yana takawa a cikin koshin lafiya, a wannan lokaci yana sanye ne da fararen tufafi, farin rawami da farin takalmi fade, ya shafe gemunsa da sajensa da kunshi, sai kyalli suke tamkar matashin saurayi. Duk da cewa sarki uwaisul karni ya fara manyanta idan mutum ya ganshi a wannan lokaci, sai yayi zaton cewa, saurayine saboda kyan jikinsa da kuma koshin lafiya. Koda jama'ar gari suka ga sarkinsu ya fito da karfinsa cikin koshin lafiya, sai sika cika da tsananin farin ciki suka rude da kabbara. Har sarki uwaisul karni yaje ya zauna akan karagar mulki basu daina kabbara ba. Jim kadan sai sarki uwaisul karni ya mike tsaye ya fuskanci alumma. Nan take fadar tayi tsit tamkar babu wani abu mai rai a wajen. Uwaisul Karin yayi gyaran murya, sannan yayi sallama irin ta addinin musulunci, ya fara bayani kamar haka... "Yaku jama'ar wannan birni namu mai albarka, kuyi sani cewa, abinda ya faru gareni ishara ce babba garemu baki daya, domin Allah ya nuna ikonsa cewa, rai da mutuwa duk a hannunsa suke. Matata muzaira ta zuba min guba a cikin abincina na ci, amma si gashi ban mutum ba, duk da cewa na sha bakar wahala tamkar zan mutu. Wannan ya isa hujja a garemu da zamu sake jajurcewa akan addinin Allah, mucire tsoron abokan gaba daga cikin zukatanmu, mu tare su da dukkan karfin mu. Ina son ku sani cewa, a lokacin da na kwanta jinyar rashin lafiya bisa wannan lalura data sameni nayi wani mummunan mafarki da ya tayar min da hankli. Ba wani abu na gani ba a cikin mafarkina, face an nuna mini cewa, dakarun da muka tura yaki izuwa birnin shumbul suna cikin mugun hali, domin makiya sun kamasu, mutum biyune kacal ba a kamasu ba, wato Uzaifat da Abul shaja'a. Ukashat kuwa an nuna mini cewa ya guji 'yan uwansa ya sabi Allah, kuma ya hada kai da makiyan mu. Kun sani cewa, a rayuwata ban taba yin mafarkin da bai zamo gaskiya ba, saboda haka bani da wata tantama akan wannan mafarki don haka zama bai samemu ba m. Dolene muyi gagarumin shiri mu kaiwa 'yan uwanmu dauki, tun gabanin su hallaka. Bisa wannan dalilin yanzu na bada umarni ga dukkanin mayakan wannan kasa tawa, su yi shiri daga nan zuwa kwana uku domin mu je mu yakin karshe da wadannan abokan gaba namu. Lallai ba zamu dawo ba face mu ko su. Yayin da sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa, sai fadar ta sake rudewa da kabbara. Nan take sarki yayi addu'a tare da gaba dayan jama'ar dake fadar suka nemi sa'a da taimako a wajen Allah. Bayan an shaga adduar ne fadar ta watse kowa ya kama gaban sa. Lokacin da sarki uwaisul karni ya shiga cikin gida, sai ya wuce kai tsaye izuwa dakin shulaifa. Da shigarsa cikin dakin saiya isketa a zaune tana ta zubda hawaye. Koda ganinta a cikin wannan hali sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya karasa gareta da sauri ya zauna daf da ita, ya kama kafadunta suka fuskanci juna, yace, yake matata me ya faru kike faman kuka? Shin na bata miki rai ne, ko kuwa wani ya bata miki ne gidan nan. Koda jin wannan tambaya sai ta dubeshi ta ce, ba wanine ya bata min rai ba kuma ba kai bane, abinda ya sa kaga ina zubar da wannan hawaye ba komai bane, facw bakin labarin da na ji daga bakin ka, wanda kayi dazu fada cewar, dana ukashat ya hada kai da makiya Allah. Ina jin wannan batu sai na kaimu da tsananin bakin ciki, kuma na tausaya masa matuka domin abin tausayine shine a matsayin musulmi kuma dan sarkin musulmi na wannan babban birni ace ya kauce hanyar gaskiya ya kama ta karya. Ni babban abinda yafi damuna ma a yanzu shine, rashin sanin matsayinsa a wajen Allah. Lokacin da sarki uwaisul karni yaji wannan tambaya, sai yayi ajiyar zuciya, sannan yace, idan har Ukashat bai yi ridda ba, har yanzu shi musulmi ne, amma akwai hukunci a kansa bisa laifin daya aikata wanda aka nuna min a mafarki. Abu na farko sai an nuna mini cewa yasha giya, kuna sannan yayi zina. Koda jin haka sai shulaifa tayi salati ta sake fashewa da kuka cikin matukar bakin ciki. Uwaisul karni ya mike tsaye yace, mene ne abin kuka? Ai kawai zainfuskanci hukuncine kamar yadda Allah ya shar'anta muddin na sameshi a raye, saboda haka ina mai shawartarki da ki daina zubar da hawayen ki a banza domin tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ke duka. Koda gama fadin haka, sai sarki uwaisul karni ya mike tsaye ya fice daga cikin dakin yabar shulaifa tana mai ci gaba da kukanta, ko waigota bai sake yi ba. Kamar yadda sarki uwaisul karni yayi bayani, haka alamura suka kasance, domin sai da aka shafe kwana uku cur ana ta shirye shiryen yaki sannan aka gama kimtsawa. A ranar kwana na ukunne da yammaci dakarun kasar gaba daya suka gama hallara a fada. Nan take sarki uwaisul karni ya fuskancesu yayi musu nasihohi da wa'azi kamar yadda ya saba yi musu a duk sa'adda za'a fita yaki, sannan ya dubi waziri yace, ya kai waziri ga amanar kasata nan a hannunka, mu zamu tafi yaki, sai Allah ya dawo damu. Ka ji tsoron Allah, ka tafi da mulkinka bisa adalci da gaskiya kwatan kwatankwacin yadda zaka iya kuma kuci gaba da tayamu da addu'a akan Allah ya bamu sa'a da nasara. Sa'adda sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa, sai waziri ya numfasa, yace, da izinin Allah zan kasance mai rike wannan amana bisa gaskiya da tsoron Allah, kuma ni da sauran jama'a zamu kasance cikin yi muku addu'a daga yau, har izuwa ranar da Allah zai dawo daku, idan kuma kun sami shahadane a can, to muna yi muku fatan samun rahamar Allah. Koda jin wannan batu, sai murna ta kama sarki uwaisul karni, ya rungume waziri, sannan suka yi bankwana. Sarki yaje ya kama dokinsa ya hau, har ya kada linzamin dokin sai yi gaba, sai waziri ya kira sunansa yace, ya shugabana ya za'ayi da matarka muzaira wacce kasa aka kaita kurkuku. Baka yanke mata hukuncin komai ba, har yanzu bisa laifinta? Sa'adda sarki uwaisul karni yaji wannan batu, sai ya gyada kai, kuma yayi ajiyar numfashi yace, kuci gaba da ajiye ta har izuwa lokacin da zan dawo daga wannan yaki idan kuma ajalina ya riskeni a can wajen yaki, wanda duk ya gajeni shine zai yanke mata hukunci dai dai da laifinta. Koda gama fadin hakan, sai sarki uwaisul karni ya sakar wa dokinsa linzami yayi gaba. Nan take dakaru sama da guda dubu arba'in bisa dawakai, alfadarai da rakuma suka bishi a baya du.... tamkar kaza da 'ya'yanta suka nufi kofar fita daga harabar gidan gaba daya. A wannan lokaci gaba daya jama'ar gari sunyi cincirundo a kofar fadar suna yi musu jinjina, gami da addu'ar nasara, sai kabbara suke tayi musu. Allahu Akbar! Musulunci da dai yake. Hakika in da mutum na tsaye a wannan lokaci yana ganin yadda dakarun suka sa niyyar wannan tafiya da zuciya daya, bisa dogaro da Allah ba tare da shakkar mutuwa ba, da kuma yadda iyalansu suke tayasu da addu'a ba tare da bakin cikin rabuwa ba, ko kuka ba, dole ne zuciyarsa ta sosu koda kuwa ya kasance Arne. Haka dai wannan tawaga taci gaba da tafiya, jama'a na yi musu rakiya a baya, har suka isa can bayan gari. Anan ne masu iyali suka rinka bankwanan karshe da iyalansu suna rungumar juna da sumbata, amma dayansu bai rushe da kuka ba, sai dai kaga kwalla a idanu. Nan dai aka gama yin sallama, sarki ya jagoranci dakarun suka nausa cikin dajin. Tun ana hangensu, har suka bace bat. Wannan shine abinda ya faru a birnin sarki uwaisul karni, bayan ya tashi daga jinyar cutar da ya kwanta sakamakon gubar da matarsa muzaira ta zuba masa a abinci yaci. * * * * * * Al'amarin Uzaifat, Abul shaja'a da Lafirat kuwa, lokacin da Lafirat tahau kan dokinta na tsafi taci gaba sa tafiya, su kuma suka bita a baya suna tafiya da kafafunsu cikin sauri sauri, gudu gudu sai da suka yi tafiyar sa'a uku cur, amma basu iso dajin mashharul kais ba. A dai dai wannan lokacine Uzaifat da Abul shaja'a suka fara gajiya, suka fara tafiyar sarsarfa. Kamar Lafirat tasan abinda ke faruwa garesu sai ta tsaida dokinta ta juyo taga halin da suke ciki. Koda ganin haka, sai ta sauka daga kan dokin ta jashi izuwa Kar kashin wata bishiyata tsaya daf da ita, Uzaifat yace, me yasa kika tsaya a nan? Koda jin wannan tambaya sai Lafirat tayi murmushi tace, ai koda mun ci gaba da tafiya, sarewa zakuyi domin yanzune ma muka ci rabin tafiyar, nan gaba sai munyi kamarta sannan zamu isa dajin na daya, wato dajin mashharul kais inda muggan tsuntsaye suke, ga shi kuma tun yanzu naga kun gaji. Lallai akwai bukatar mu yada zango domin ku huta kuma muci abinci, tunda rana na daf da faduwa sai mu bare idan dare yayi, sannan mu ci gaba da tafiya tunda dai za'a sami hasken farin wata a wannan lokacin. Ba tare da gaddamar komai ba, su uzaifat suka amince da wannan shawara. Nan take suka kwance jakunkunansu sukayi shimfida suka zauna. Ita ma Lafirat sai tayi tata shimfidar a can gefe daya ta zauna kuma ta dauko soyayyen nama ta ajiye a gabanta. Maimakon ta fara ci, sai ta dubi su uzaifat ta ce, Bismillanku fa ha nama. Cikin tsananin mamaki Uzaifat ya dubeta, kawai sai yayi murmushi, yace Mun gode. Nan take Uzaifat da Abul shaja'a suka fiddo dabino suka kama ci. Lafirat ta dubesu tayi murmushi, sannan ta budi baki tayi bismillah ta fara cin wannan soyayyen nama dake gaban ta. Al'amarin da ya mutukar baiwa Uzaifat mamaki kenan, har suka kasa cin dabinan nasu suka tsaya suna kallonta kawai. Koda Lafirat taga sun zuba mata idanu, sai tace, lafiya naga kun kura min ido haka, shin ba kwajin kunyata ne a matsayina na 'ya mace? Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, ki gafarcemu yaje wannan 'yar sarki, kiyi sani cewa tsananin mamaki ne yasa muka kura miki idanu. Manene dalilin da yasa kika yi bismillah a lokacin da zaki ci wannan nama alhalin baki kasance musulma ba? Sa'adda Lafirat taji wannan tambaya, sai tayi murmushi tace, ai na gaya muku na koyi yadda duk aladar ku take ta musulmi kuma aladace wadda take mutukar burgeni duk da cewa ban karbi addininku ba amma ai nayi imani dashi a cikin zuciyata, kawai dai ina jiran lokaci ne dazan karbeshi, don haka bai kamata kuyi mamaki ba, saboda kunga ina yin wasu abubuwa cikinsa. Ina tabbatar muki da cewa, na iya salloli biyar da kuje a rana, kuma nayi zurfi a cikin karatun littafi mai tsaki, amma saboda sanin cewa, ina taammali da tsafi shi yasa bana yinsa. Sa'adda Lafirat tazo nan a zancenta sai yarima uzaifat yace, ai gwara da bakya yinsa, domin baki da tsaki, kuma ina mai shawartarki da kada ki sake yunkurin yin wani abu makamancin hakan face kin karbi addininmu, saboda kin san cewa ruwa da wuta basa haduwa. Lafirat tayi murmushi, tace, na karbi shawarar ka, kuma zanyi aiki da ita. Haka dai suka ci gaba da hira suna cin abincin har suka kammala. Basu bar wajen ba sai da su Uzaifat sukayi sallar isha sannan suka mike suka ci gaba da tafiya a cikin daren domin an sami hasken farin wata a wannan lokaci kamar yadda Lafirat da fada. Basu gushe ba suna tatafiya har tsawon sa'a biyu, a wannan lokaci dajin yayi tsit ba ajin komai face kukan kananan tsuntsaye da kwari. In banda hasken farin watan da Ya gauraye dajin gaba daya ba dole ne mutum ya razana da dajin, saboda yawan duhuwarsa gami da dogayen bishiyoyi da manyan duwatsu da tsaunika. Suna cikin tafiya ne kwatsam sukaga wani katon shuri a gabansu mai girman gaske, tamkar katon dutse aka ajiye. Shurin ya cika hanyar gaba daya babu ta inda za'a wuce face anji ta kansa. A jikin shurin akwai wasu manyan hudoji wadanda mutum na iya shigewa cikinsu, hudojin na da yawa babu adadi. Koda sukayi arba da wannan shuri sai suka ja suka tsaitsaya, kamar hadin baki, ai duk su ukun suka zare takubbansu suka kura idanu ga shurin suna jira suga ko wani abu zai fito daga cikinsa. Tsawon dakika dari da a shirin basu ga komai ba. Uzaifat ya dubi Lafirat yace, me kika sani dan gane da wannan shuri? Lafirat ta gyada kai tace, ban san komai ba, asalima ban taba ganinsa ba anan, ma'ana bai taba wanzuwa ba sai yanzu da muka ganshi. Abinda naje zargi shine, duk yadda akayi mahaifina yasan da zuwan mu don haka shine ya turo mana wannan shuri, lallai ba a rasa wani mugun abu ba a cikinsa mai mugun hadari. Kafin Lafirat ta gama rufe bakin ta kuwa, sai sukaga wadansu irin aljanu kanana masu suffar bil adama suna fitowa daga cikin hudojin shurin suna shawagi a saman shurin, tamkar anan ruwan fari. Banbancinsu da bil adama shine, rafkeken kai mai surar shanty, sai kuma wadansu irin fuka fukai irin na jemage sannan kowannensu yana da hannaye hudu, kafafu hudu. Bakunansu dogayene ga tsini tamkar allura. A dai dai wannan lokacine tsautsayi ya biyo da wani shawo zai gifta ta saman shurin kawai sai daya daga cikin aljanu yayi sama ya cakeshi da tsinin bakinsa. Taje ya zuke jinin jikin shagon ya fado kasa tim sa sandare tamkar gawar da ta kumbura take shirin yin bundiga. Koda Lafirat, Uzaifat da Abul shaja'a suka ga abinda ya faru ga wannan shaho, sai hankalinsu ya dugunzuma ya tashi, domin sun san cewa, suma abinda zai samesu kenan da zarar miyagun aljanun sun farmusu. Babban abin tashin hankalin shine, yawan aljanun ya wuce daruruwan dubbunai, sai dai ace miliyoyi, sannan suna ta wani irin kara mara dadin ji, wacce ka iya dodar da kunne, ba shiri su uzaifat suka fara to she kunnuwansu kuma suka dimauce basu san sa'adda suka rikito kasa ba daga kan dawakansu. Koda aljanun suka ga haka, sai suka taho da gudu izuwa Kansu suka yanyamesu suna kawo musu suka da tsinin bakinsu ta ko ina, cikin tsananin zafin nama Uzaifat, Abul shaja'a da Lafirat suka shiga kare harin da aljanun suke kawo musu da takubbansu. A duk lokacin da takubbansu suka hadu da bakin aljanun, sai kaji kamar karfe da karfe ne suka hadu, kuma har tartsatin wutane ke tashi. Tsananin zafin naman aljanun be yasa su uzaifat suka kasa saran jikinsu. Ana cikin wannan gumurzu ne daya daga cikin aljanun ya cakawa Abul shaja'a tsinin bakinsa a cinya. Abul shaja'a bai san sa'adda ya kurma uban ihu ba ya sulale kasa sumamme. Kafin aljanin ya zuke jinin Abul shaja'a tuni Uzaifat ya kwalla kabbara ya tsargeshi gida biyu. Nan take aljanin yayi bindiga tamkar mushen gawa ya fashe kuma ya kone kurmus, ya zama toka. A dai dai wannan lokacune, wani aljanin dabamya make Lafiratda jelarsa yayi mata mugun rauni a gadon bayanta, ita ma ta sulale kasa sumammiya. Koda ganin abinda ya faru sai Uzaifat ya ci gaba da kwalla kabbara yana sarana aljanun, suna babbakewa da tarwatsewa a sama. Koda aka jima a haka, sai aljanun suka ga cewa m, Uzaifat ya zame musu alakakai, kuma indai aka ci gaba da wannan gumurzu a haka, sai ya karar dasu gaba daya duk da cewar, yawansu ya wuce kima, domin lokaci guda yana saran guda dari. Da yaga yana samun wannan nasara, sai ya sunkuci takobin Abul shaja'a wato ya hada guda biyu ya ci gaba da ragargazar aljanun. Fa dai aljanun suka ga Uzaifat ya Karar da sama da rabinsu, sai suka juya gaba dayansu da gudu suka koma wannan shuri sukayi ta shigewa cikinsa. Kafin Uzaifat ya ruga inda shurin yake sun gama shigewa cikinsa gaba dayansu. Ai kuwa Uzaifat na zuwa kan shurin sai ya daga takobinsa guda biyu sama yana mai yin kabbara har sau uku, sannan ya sari shurin da dukkan takunban biyu. Faruwar haka ke da wuya sai gaba daya shurin ya kama da gagarumar wuta, sai ga wadannan aljanu da ke cikin sa suna narkewa tamkar an dafa dalma. Nan da nan duk suka zagwanye dayansu bai tsira da rayuwarsa ba. A wannan lokacine hankalin Uzaifat yakoma kan Abul shaja'a da Lafirat ya yarda takubban hannunsa ya ruga garesu. Koda ya je Kansu ya tsaya sai ya ga haryanzu duk su biyun a sume suke, babu wanda ya farfado, al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinsa kenan. Kuma ya rude ya rasa wanda zai fara baiwa agajin gaggawa daga cikinsu. Cikin hanzari ya ruga ya dauko sallar ruwan sa ya zuba musu aka a tare. Faruwar hakan ke dawuya, sai duk su biyun suka farfado suna masu yin numfashi sama sama kamar zasu mutu. Uzaifat ya dubi raunin dake jinyar Abul shaja'a ya ga wajen ya fafe yayi rami mai zurfi da fadi kuma har yanzu jini bai dai na bulbulowa daga ciki ba, sannan kuma ya dubi raunin dake bayan Lafirat yaga shima ya dare yayi tsawo, amma bai kai na Abul shaja'a muni ba, amma kuma ita ta fishi jin jiki, don tunda ta kofa tayi rufe da ciki ko motsawa bata sake yi ba, sai ci gaba take da numfashi sama sama. Cikin matukar karfin hali Abul shaja'a ya dubi Uzaifat yace, maza ka fara baiwa Lafirat again gaggawa kada ka damu dani, domin zan iya yiwa kaina wani abun. Koda gama fadin hakan, sai Abul shaja'a ya cire rawanin kansa ya daure raunin jinyar tasa tamau don tsaida jini. Cikin gaggawa Uzaifat ya dauko jakar guzurinsanya budeta ya fiddo wani garin magani ya zuba a cikin raunin Lafirat, koda maganin ya shiga cikin raunin taji wani irin zugi da radadi ya shigeta, sai ta kankame jikin Uzaifat ta rafka ihu. Da kyar ta iya jurewa ya gama sa mata maganin, Uzaifat ya umarceta da kada ta motsa, taci gaba da rub da ciki. A sannane Uzaifat yaga hawayen wuya ya zubo daga Lafirat, nan take yaji ya kamu da tsanannin tausayinta. Uzaifat ya mike tsaye ya koma wajen Abul shaja'a ya kwance rawanin da ya daure wannan raunin nasa, sannan ya debo garin wannan magani zai zuba a cikin raunin amma sai hannunsa ya kama karkarwa ya kasa zuba maganin saboda sanin irin mugun zafin da zaiji. Koda gamin haka sai Abul shaja'a ya kama hannun Uzaifat ya ruje da kyau yace, Haba ya shugabana bai kamata kaji tausayinta ba, Ashe inda dates kafar tawa ne ya kamata ba zaka iya ba? Maza kasa mini wannan magani domin mu yi maganin zafin ake cikinsa. DAKARUN MUSULUNCI LITYAFI MA BIYU MARUBUCI ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING UMAR FAROUQ ZANGO. Koda gama fadin hakan, sai Abul shaja'a ya rungume Uzaifat shi kuma sai ya sa masa garin maganin a cikin raunin. Ai kuwa Abul shaja'a bai san sa'adda ya kwada kabbara da karfin gaske ba, muryarsa ta amsa kuwwa ta cikin dajin gaba daya, al'amarin da ya janyo gaba daya tsuntsayen dake dajin suka firgice suka tashi daga kan bishiyoyi suka kama guje guje a sama ba tare da sanin inda suka dosa ba. Kai hatta dabbobin dake kwance a cikin ramukansu sai da suka farka daga barci a firgice, suka kama fitowa suna gudu da neman matsera. Faruwar hakan ke da wuya sai Lafirat ta juyo da kanta ta dubi Uzaifat cikin karfin hali tace, nagode yakai wannan gwarzom jarumi, hakika ka ceci rayuwata a karo na biyu, ban san dame zan saka maka ba. Yanzu gashi ni da abokin tagiyarka mun samu wannan lalura ina mai baka shawara daka hakura da ci gaba da yin wannan tafiya, inyaso mu koma can baya izuwa gidana domin muyi jinya, inyaso bayan mun sami lafiya sai mu sake fitowa. Abinda yasa na baka wannan shawara shine, lallai kana bukatar gudunmawarmu a cikin wannan tafiya, yinta kai kadai abune mai hadari. A yanzu idan kace zamu ci gaba da wannan tafiya a haka, wahala zata maka yawa domin jinyar mutum biyu zaka yi a lokaci guda, kuma idan wata masifa ta afko maka ba zamu iya kare ka da komai ba face ma mu zamo maka matsala. Yayinda Lafirat tazo nan a zancenta, sai Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, yake wannan 'yar sarki ki tuna cewa, bata lokacina a cikin wannan tafiya dai dai yake da salwantar rayuwar 'yan uwana da kuma tarwatsewar birninmu, domin kuwa su sarki Sha'aran suna nan akan shirin zuwa su yakemu, kuma muddin dan uwana ukashat zai tona wadannan layu da aka binne a jikin katangar birninmu sai sun sami nasara a kanmu, kinga kenan banga ta zama ba. Ba zamu koma da baya ba, kuma bazan barku a ko ina ba, har sai mun isa dajin karshe tare da ke kamar yadda mukayi alkawari da farko. Na dogara da ubangijina, kuma nasan tabbas nasan zai taimakeni har na sami nasarar abinda nasa a gabana. Koda gama wannan furuci sai Lafirat ta kira dokinta na tsafi, yazo daf da ita ya tsaya sannan ta dubi Uzaifat tace, taimaka min ka dorani akan dokina. Uzaifat yace indai kina so na ci gaba da taimakonki bisa halin da kike ciki, sai dai ki ajiye komai na harkar tsafinki. Koda jin haka, sai Lafirat tayi murmushi tace na amince da hakan. Nan take tayi nuni da hannunta na hagu ga wannan doki nata, ya bace bat. Faruwar hakan ke da wuya sai Uzaifat ya sunkuya ya dauki Lafirat ya goyata a bayansa ya daureta da rawaninsa tamkar uwa ta goya danta. Abul shaja'a dake zaune akas sai ya dubeshi yayi murmushi yace, to ni kuma ya zakayi da ni yanzu? Ka goya Lafirat a bayanka, ni kuma akan wuyanka zaka dorani? Maimakon Uzaifat ya bashi amsa, sai ya tafi izuwa ga wata bishiya ya karyo reshenta daya dan dogo ya dawo wajen Abul shaja'a ya mika masa, yace, ungo wannan ka dogarashi ka yi tafiya da kafarka domin kai namijine, cikin tsananin mamaki Abul shaja'a ya dubi Uzaifat yace, haba yarima ya za'ayi kace na mike na taka kafata ina da wannan sabon raunin? Uzaifat yace ai kashinka bai tabu ba zaka iya takawa. Koda gama fadin haka sai Uzaifat ya juya yaci gaba da tafiya yabar Abul shaja'a a zaune a wajen, kawai sai Abul shaja'a yaga Lafirat ta waigo tana yi masa dariya. Nan take Abul shaja'a ya fusata ya kama wannan ice dake hannunsa da kyau cikin tsananin juriya ya yunkura ya tashi tsaye da kyar, sannan ya fara dogara sandar yana dogarawa da kyar yana cijewa, a wannan lokaci ji yakeyi kamar kafar zata gutsure saboda tsananin zafi da zugin da yake ji. Haka dai ya jure ya ci gaba da dogarawa yana bin Uzaifat a baya har hawayen wahala na zubo masa. Koda Uzaifat ya juyo yaga halin da yake ciki, sai da tausaya masa, amma sai ya dake bai nuna ya ji tausayin nasa ba. Haka dai suka ci gaba da tafiya, bayan 'yan sa'o'i sai suka tsaya su huta, sannan su ci gaba da tafiya, har dai suka iso bakin dajin masaharul kais. Da zuwansu sai Lafirat tace, ya kai gwarzon jarumi kada ka shiga cikin wannan daji yanzu, mu zauna anan tsawon kwana uku, domin ni da Abul shaja'a mu kara samun sauki. Komai kankantar taimakon da zami iya baka yana da muhimmanci. Na tabbata cewa, nan sa kwana ukun zamu iya samun karfin jikinmu, mu iya agazawa da wani abin. Sa'adda Uzaifat yaji wannan batu, sai ya yi shiru baice komai ba, ya dubi Abul shaja'a. Abul shaja'a ya jinjina kai yana mai yi masa nuni da cewa ya karbi wannan shawara ta Lafirat. Ba tare da gardamar komai ba Uzaifat ya je jikin wani dutse ya tsugunna ya sauke bayanta ya dubi raunin nata yaga ya fara kamewa, amma kuma akwai bukatar tayi mata addu'a ya tofa akan ciwan. Har ya yunkura zai fara adduar sai ya tuna cewa, ai Lafirat ba musulma bace, don haka sai ya fasa, ya dawo wajen Abul shaja'a ya tsugunna ya kwance raunin yaga shima nasa ya fara kamewa harma yafina Lafirat warkewa. Cikin mamaki Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace yaya akayi raunin naka naga yayi saurin warkewa haka. Abul shaja'a yayi murmushi yace, albarka cin addu'a ne ya kawo haka. Me yasa ka fasawa yiwa Lafirat addu'a dazu alhalin da naga kayi niyyar yin haka? Koda jin wannan tambaya, sai Uzaifat yayi shiru bai ce komai ba, kuma ya juya ya dubi Lafirat wacce ke can gefe daya a zaune, tsakanin su akwai tazara bata jiyo abinda suke tattaunawa. Uzaifat ya juya ya sake fuskantar Abul shaja'a yace, kasan cewa Lafirat ba musulma nace, don haka banga dalilin da zai sa nayi mata addu'a ba. Abul shaja'a yace, wannan gaskiya ne, amma ina Fatan ta samu lafiya da wuri, domin tana da mutukar muhimmanci a cikin wannan tafiya tamu. A dai dai wannan lokacine Lafirat tayi tati ta kira sunan Uzaifat. Cikin sauri Uzaifat ya mike tsaye ya ruga gareta yace, me kike bukata? Lafirat tace, ina mutukar jin kinshirwa, kuma na duba salka ta naga babu komai a ciki. Uzaifat na jin haka, sai ya duba tasa salkar ya ga itama ko digon ruwa babu a cikinta, kawai sai ya sake rugawa wajen Abul shaja'a ya duba tasa salkar, ita ma babubkomai a ciki. Nan fa hankalinsa ya dugunzuma ya rasa me zaiyi. Kawai sai ya dubi Abul shaja'a yace, ya zama dole na shiga cikin wannan daji na mashaarul kais domin neman ruwan sha tunda wajen dake da ruwa a bayanmu yana da nisa sosai. Zan tafi na barka a nan tare da Lafirat. Ka sani cewa, Lafirat ba zata iya yiwa kanta komai ba, amma kai da sauran kwarinka. Koda wani abu zai taso muku kayi iya kokarinka wajen kare lafiyar ku, kafin na dawo. Koda gama fadin haka, sai Uzaifat ya koma wajen Lafirat ya tsugunna a gabanta, ya ce, zan shiga cikin dajin mashaarul kais domin na samo mina ruwan sha, zaku ci gaba da zama a nan har dawo. Koda jin wannan batu, sai idanun Lafirat suka zazzaro ta dubi Uzaifat cikin tsananin damuwa da fargaba tace, in dai saboda ni zan tafi neman wannan ruwa ka barshi zan iya jure kishirwata har tsawon kwana ukjn da zamuyi anan. Uzaifat yayi murmushi yace, haba Lafirat yaya za'ayi ki rayuwa tsawon kwana uku cikin kishi, ai bazaiyiwu ba. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai sameni, da izinin ubangijina. Na yi miki alkawarin zam dawo nan da sa'a uku. Ga Abul shaja'a nan zai debe miki kewa kafin na dawo, kuma na tabbata cewa, zai iya baki kariya dai dai gwargwado. Sa'adda lafirat taji haka, sai ta yi yake tace, bazai iya debe min kewar da zaka iya debe min ba, kuma bazai iya bani kariyar da zaka iya bani ba. Babu abinda zan iya cewa tunda nasan cewa bazan iya hanaka tafiya ba, amma zan kasance a cikin tsananin bakin ciki idan har baka dawo ba kariskeni a raye ba. Koda jin wannan bayi, sai Uzaifat ya cika da tsananin mamaki, yace ni fa ban fahimci komai ba dan gane da duk wannan bayani naki ba. Lafirat tayi murmushin yake tace, ai bazaka fahimta ba, domin lokacin fahimtar baiyiba. Fatana kawai shine, ni da Kai mu sake saduwa, kuma mu rayu har zuwa lokacin da zamu cika burikan zukatanmu. Maza ka tafi neman wannan ruwa domin ka dawo da wuri, kasan cewa yanzu fa lokaci abune mai mutukar muhimmanci a garumu. Uzaifat yace, kwarai kuwa, nan take ya mike tsaye ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi cikin dajin mashaarul kais. Koda ya juyo ya hada ido da Lafirat, sau yaga idanunta sun ciko da kwalla sannan fuskarta na nuna tsananin damuwa karara. Kuma tana yi masa kallo mai dauke da alamar tambaya. Kawai sai Uzaifat ya ji tsikar jikinsa ta tashi gaba daya, zuciyarsa ta buga da karfi, ya kaimu da was wasu gami da jimami a ransa, nan take yaji kamar bazai iya tafiya baya bar lafirat a cikin wannan hali ba, amma sai ya daure ya juya ya kunna kai cikin wannan dajin na mashaarul kais, bai yarda ya sake juyowa sun hada idanu da Lafirat ba, kada zuciyarsa ta karye. Bayan kamar dakika dari uku da sittin da tafiyar Uzaifat, Abul d Lafirat na zaune shiru dayansu baice kala ba, sai dai su kalli juna su kau da kai, kuma ga shi akwai tazara a tsakanin su, koda zakuyi magana da juna sai dai su daga murya. Kawai sai Lafirat ta yafito Abul shaja'a da hannunta tana mai nufin ya taso ya dawo inda take. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Abul shaja'a ya dauki wannan dogon icen da yake dogarawa ya mike tsaye da kyar ya dogara yana tafiya a hankali har ya isa inda Lafirat take, ya zauna daf da ita. Lafirat ta dubeshi cikin murmushi tace, hakika mutanen birninku sunyi babbar sa'a. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Abul shaja'a yace, ke kuwa saboda me kika fadi haka? Lafirat tayi murmushi ta ce, saboda kun sami magajin sarkinku yarima uzaifat domin na fuskanci cewar, yana da dakakkiyar zuciya ta rashin tsoro irin ta mahaifinsa, kuma sannan yana da tausayi da adalci ga tsagwaron jarumta. Akwai alamun cewa, nan gaba zai iya yin shahara a duniya, idan har ajali bai yi masa gaggawaba. Uzaifat mutumne irin wanda kowace 'ya mace lo son ta mallaka domin zai share mata hawayenta a duk sa'adda yaga yana zuba. Wai shin kuwa Uzaifat na da macen da yake son aura a rayuwarsa? Koda Jin wannan tambaya, sai Abul shaja'a yayi murmushi yace, ai Uzaifat bai taba yin soyayya ba, duk cewa 'yan matan garin mu da yawa sun shiga mugun hali bisa kamawa da sonsa. Abinda ya kan gaya musu shine, bazai taba yin soyayyaba, ko Aure face yacika burin mahaifinsa, wato yaci birnin shumbul da yaki. Koda jin wannan batu, sai Lafirat ta cika da farin ciki ta kama murmushi, kuna ta yi shiru batace komai ba. Shi kansa Abul shaja'a da ya ga tana wannan murmushi sai da ya tsargu yace a ransa, anya kuwa babu soyayyar Uzaifat a cikin zuciyar Lafirat? Idan ma akwai zan gane nan gaba, domin an ce somi somin hauka zuba da yawu ne. Ga ma aiyana hakan ke dawuya a cikin zuciyar Abul shaja'a sai kawai sukayi gaba daya dajin ya kama girgiza kasa na neman darewa ta rufta dasu ciki, al'amarin da ya mutukar dugunzuma hankalin Lafirat da da Abul shaja'a kenan suka kama kalle kalle da hange hange ko zasu ga abinda ke shirin aflo musu amma shiru basu ga komai ba. Cikin karfin hali Abul shaja'a ya mike tsaye yan dogara wannan ice da hannun hagu, sannan ya zare takobinsa da hannun dama ya tsaya yana saurare. Ita kuwa Lafirat da tasan cewa bazata iya komai ba, sai ta zuba idanu kawai tana sauraron abinda zai wakana. Doke dai tasan cewa, cikin biyu sai abu daya ya faru. Ko su hallaka, ko kuma su tsira da rayuwar su. Kwatsam ba zato ba tsammani sai ga wani garjejen maridi ya durfafosu, wanda hucin isar bakinsa ta haddasa karamar guguwa, ashe karfin takun sawayensa ne ya haddasa wannan girgizar kasa. Girman kansa kuwa ya kai na wani dan babban dutse wanda karti shirin bazasu iya rabashi da kasa ba. Maridin yana da manyan idanuwa kwala kwala guda hudu, biyu a kwan girar ido, biyu kuma a daman girar. Yana da wawakeken baki tamkar an fafe ganga, gami da dan mitsitsin hanci, wanda ko karamin dan yatsa bazai shiga ba. Fuskarsa gaba daya a cike take da gashi, babu kyan gani. Hakika munin wannan maridi ya wuce misali, sai abinda ido ya gani. Koda Lafirat tayi arba da wannan maridi sai ta figita ainun, ta kamu da tsananin tsoro, domin duk iya saninta da sirrin wadannan dazuka ba ta taba sanin cewa akwai ba. Kai ko a labari nata taba jin cewa irinasa ya taba wanzuwa ba. Inda tasan dashi wata kika tasan hanyar da za a bi a hallakashi. Lokacin da Abul shaja'a yaga wannan maridi ya taho kansu gadan gadan da nufin ya hallakasu, sai yayi jifa da sandar hannunsa ya take kafar tamkar bai taba samun rauni ba, ya ruga ga maridin da dukkan karfinsa, yana kururwa irin wacce ke firgita mazaje a filin daga, ya kaiwa maridin sara da takobinsa a ciki. Take maridin yasa hannuna ya kare saran, ai kuwa sai takobin Abul shaja'a tayi tsalle sama ta fadi can gefe daya, kafin Abul shaja'a yayi wani yunkuri tuni maridin ya mangareshi da daya hannun nasa. Saboda karfin mangarar sai da Abul shaja'a yayi sama tamkar an janyeshi da kugiya yaje ya gwara Kai d wani dutse, kansa ya fashe jini yayi tsartuwa ya fado kasa magashiyan tamkar gawa, ko motsawa bai sake yi ba. A sannane maridin ya tunkari Lafirat. Koda taga ya yo kanta sai ta tsandara ihu tana mai kwalawa Uzaifat kira. Sautin ihun nata ya cika dajin gaba daya, yana mai amsa kuwwa. Wannan shine abinda ya faru ga Lafirat da Abul shaja'a, bayan yarima Uzaifat ya barsu a bakin dajin mashaarul kais ya tafi neman ruwa sha. * * * * * * * A can birnin shumbul kuwa, a cikin masarautar, sarki shaaran ya ga duk abubuwan da suka faru ga su Uzaifat a cikin madubin tsafinsa, wato yaga lokacin da yarima Uzaifat ya afka cikin dajin mashaarul kais don neman ruwan sha, kuma ya ga lokacin da wannan garjejen maridi ya mangare Abul shaja'a yayo kan Lafirat, tana ta kwala ihu. Koda ganin wannan al'amari sai sarki shaaran ya kyalkyale da dariyar farin ciki kamar bazai daina ba. A wannan lokaci ukashat da gimbiya sazirat na zaune a gefe daya bisa kujerun daraja suna kallosa kawai. Bayan sarki shaaran yayi dariya har ya gaji sai ya hade fuskanci ya dubi sazirat da ukashat yace, ku tashi kuke kuyi shiri yanzunnan zamu kama hanya mu tafi izuwa birnin Darul husuf domin cika burinmu. Tabbas dan uwanka Uzaifat sai ya hallaka a cikin wannan daji na mashaarul kais, ita ma Lafirat nasan cewa tuni wannan maridi ya gama da ita. Hakika yanzu ne muje da cikakkiyar dama, wacce zamu iya tafiya mu ci birninsu da yaki ba tare da mun fuskanci wata matsala ba. Koda jin wannan batu, sai ukashat da sazirat suka mike zumbur cikin murna suka nufi hanyar fita daga cikin fadar. Har sunje bakin kofar sai ukashat ya juyo ya dubi sarki shaaran yace, ya shugabana me zai hana yanzu ka duba mana a cikin madubin tsarin ka mu ga halin da birnin Darul husuf ke ciki. Nasan halin mahaifina yana da wata irin baiwa tayin mafarki bisa duk irin abinda zai same shi. Babu mamaki a halin yanzu tasan da zuwanmu, kuma ya dauki mataki akan hakan. Koda jin wannan batu, sai sarki shaaran ya tuntsire da dariyar mugunta, sannan ya tako kafafunsa yazo daf da ukashat ya tsaya ya dafa kafardarsa, yace, kwantar da hankalika ya kai sarkin Darul husuf na gobe. Ina tabbatar maka dacewa, duk irin sihirin da sarki uwaisul karni zaiyi, sai mun sami nasara a kansa domin abin dogarona ya bani sa'a. Abinda nakeso da kai kawai shine ka tabbatar da cewa ka tone wadannan layu guda hudu da aka binne a kasar katangun birninku kafin mu fara Yaki dasu. Ka sani cewa a duk sa'adda na yi yunkurin ganin abinda ke faruwa a birninku, sai mudubin tsafina ya fashe nayi asararsa saboda karfin sihirin mahaifinka. Sa'adda ukashat yaji wannan batu, sai yayi shiru bai ce komai ba, ita kuwa sazirat sau ta kama hannunsa ta jashi suka fice daga cikin fadar da sauri suka wuce izuwa can harabar gidanta, inda suka shiga shiri da kimtsawa domin gagarumin yakin da zasu tafi. Shi ma sarki shaaran sai ya shiga hada dakarunsa aka rinka fito da makaman yaki iri iri ana rabawa dakarun, sannan aka yi ta shirya dawakai da guzuri ba adadi. Idan mutum ya ga yawan dakarun sarki shaaran wadanda zasu tafi wannan yaki da kuma yawan dawakan da aka ta Nada da guzuri, dole ne ya cika da mamaki, domin an kashe dukiya mai tsananin yawan gaske. Wannan shine mugun tanadin da sarki shaaran sukayi, abinda basu sani ba shine abokan gabar tasu ma sunyi shiri, sun taho gareku saboda haka sai dai a hadu akan hanya a gwabza kazamin yaki da za a fidda raini mai sa'a ya cika burin sa. * * * * * * Al'amarin yarima Uzaifat kuwa, lokacin da ya kunna kai cikin dajin mashaarul kais yana neman ruwa, sai ya shafe sa'a guda bai ga wani tafki ko koramaba, al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ainun, saboda tunanin halin da ya Bari Lafirat a ciki, don haka sai ya kara kaimin tafiya, har ma yana gudu gudu yana waige waige ko zai hango rafi ko korama. A wannan lokaci Uzaifat ya ma manta da cewa a cikin dajin mashaarul kais yake, dajin da Lafirat ta basu labari cewa, akwai wadan su muggan tsuntsaye a cikinsa manya manya masu tsananin karfi da hikimar kai hari. Uzaifat yaci gaba da gudu yana waige waige har tsawon wata rabin Saar. Kwatsam ba zato ba tsammani sai ya hango wata babbar fadama a gabansa ruwa na ta gudu a cikinta. Cikin tsananin farin ciki ya karasa cikin fadamar wacce ruwanta ke kwararowa daga sama takan duwatsu. Da shigar Uzaifat fadamar sai ya tsuma salkarsa a cikin fadamar da nufin ya cikata taf da ruwa, sannan shima yasha ya koshi. Kwatsam uzaifat yaji wata irin gagarumar iska kafin ya dago kai yaga ko menene sai kawai yaga wadansu irin jibga jibga tsuntsaye guda biyu dai dai kansa. Tun da Uzaifat ya zo duniya bai taba ganin irin su ba. Kafin Uzaifat yayi wani yunkuri tuni tsuntsayen sun cafi kafadunsa sunyi sama da shi, sun luluka. Uzaifat ya yunkura da nufin ya zare takobinsa daga cikin kufenta, amma sai yaji ya kasa motsa hannayensa duka biyun, sakamakon mugun rikon da tsuntsayen suka yi Masa da kafafunsa, kawai sai ji yayi yana ta wutsil wutsil da da kafafunsa, amma babu mafita ko dabara. Koda ganin haka, sai Uzaifat ya saduda ya zubawa sarautar Allah ido kawai yana jira yaga inda tsuntsaye zasu kaishi. Sai da tsuntsayen suka yi doguwar tafiya da Uzaifat a sama, har gaji likis yaji kamar kafadunsa zasu gutsure, sannan tsuntsayen suna ido kan wani dogon katon tsaunin wanda akan sama akwai wadansu manyan duwatsu. Kwatsam sai Uzaifat ya hango wata babbar sheka ta tsuntsayen cike da jira jiran 'ya'yansu. Alhamdulillahi nan zamu diga aya sai Allah ya kaimu gobe zaku jimu da ci gabansa. Ni UMAR FAROUQ ZANGO nake cewa mu kwana lafiya. [11/02, 6:23 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA BIYU MARUBUCI ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING UMAR FAROUQ ZANGO Suna kansu 'ya'yan tsuntsayen girman su abin mamaki ne, domin ko wanne dayansu ya kai girman katuwar damisa. Koda 'ya'yan tsuntsayen suka hango iyayensu dauke da Uzaifat a sama sai suka kama tsalle suna kokarin cafko Uzaifat tun gabanin a sauki masu da shi kasa. Nan taje Uzaifat ya gane cewa wadannan yayan tsuntsayen yunwa suke ji, don haka da zarar anjefashi cikin wannan Sheka zasu dasa masa wawa su cinyeshi. Koda fahimtar haka sai hankalin Uzaifat ya dugunzuma bai san sa'adda ya kwarara kabbara ba yana mai neman taimakon Allah. Faruwar hakan ke dawuya sai tsuntsayen suka saki kafadun Uzaifat ya rikito daga sama zai fado cikin shekarsu. Cikin hanzari Uzaifat ya zare takobinsa, ai kuwa yana fadowa cikin shekar sai yayan tsuntsayen suka yanyameshi zasu cinyeshi. Shi kuwa sai ya hausu da sara da suka ba kakkautawa, ya zame musu alakakai suka kasa cinyeshi, shi ma kuma ya kasa hallakasu domin duk sa'adda ya sari jikinsu sai ya ji kamar dutse yake karta har tartsatsin wuta ne ke tashi. Su kuwa iyayen tsuntsayen da ke sama koda suka ga abinda ke faruwa tsakanin Uzaifat da yayansu sai suma suka yo kasa suka rinka kaiwa Uzaifat mugun farmaki don yayyagashi. Nanfa Uzaifat ya shiga cikin mugun hali, domin ana kawo masa hari ne ta sama da kasa, ya rasa inda ya kamata yafi bada karfinsa, domin duk ta bangaren daya sakwa sakwa nan da nan zai hallaka. Haka dai aka ci gaba da wannan gumurzu har tsawon sa'a guda tsuntsayen kai masa hari da bakunansu da kafafunsu yana gocewa, kuma shi ma yana kai musu sara da suka da takobinsa. Nan fa gajiya ta fara riskarsa har tsuntsayen suka fara samun lagons ya zamana cewa sun fara masa raunika a jiki, jini na zuba. Tun Uzaifat na tsaye sai da ya fara durkushewa kasa yana mikewa, a sannane jiri ya fara dibarsa. Baiyi aune ba, daya daga cikin su yayi masa wata muguwar mangara da fukafukinsa nan taje ya fadi kasa magashiyan yana mai ganin dishi dishi, kawai sai yayan tsuntsayen suka sake yo kansa gaba dayansu cikin wani irin zafin nama Uzaifat ya kwalla kabbara ya sake mikewa ya kuma tararsu aka ci gaba da fafatawa, wannan karon sai ya fara karanta wata addu'a a cikin zuciyarsa cikin ikon Allah kuwa ya fara samun nasara akan su ya fara yi musu rauni a wannan karon duk wanda ya sara sai dai kaji karar ballewar kashi kasss! Koda ganin wannan nasara da ya fara samu sai ya kara zage dantse ya ci gaba da kabbara yana saransu da takobinsa, koda ganin irin barnar da Uzaifat yaje musu sai suka tsorata da shi suka fara baya baya amma kuma duk da haka basu fasa kawo masa hariba. Ana cikin wannan gumurzu ne Uzaifat yayi wani irin yunkuri cikin shammace na bazata ya daka tsalle sama ya sare kawunan iyayen tsuntsayen atare a lokaci guda suka fado kasa suka kife matattu, tamkar giwaye biyu sun fadi. Koda ragowar yayan nasu suka ga abinda ya faru ga iyayensu, sai suka nutsu suka koma gefe daya a cikin shekar tasu suka noke aka cigaba da kallon kallo tsakanin su da Uzaifat, ya zamana cewa, su basu afka masa ba, shi ma bai afka musu ba. Jima kadan sai Uzaifat ya koma gefe daya ya zauna yana haki, sakamakon tsananin gajiyar dake tare da shi. A sannane kuma ya bude jakarsa ya fiddo magani ya shafa a jikin raunikansa. Bayan ya sami nutsuwa, sai ya mike tsaye ya leka kasan shekar da yake ciki. Koda ya ga nisan dake tsakanin saman tsaunin zuwa kasa sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi, domin bai ga ta yadda zai iya sauka kasan ba, do ko igiya zai daunra ya bi sai ya shafe sama da sa'a goma ya na sauka kasa, tabbas bazai iya jure hakan ba, ba tare da ya gaji ba ya saki igiyar ya hallaka a banza ba. Duk wannan nazari da Uzaifat ke yi yana lura da wadannan ragowar yayan tsuntsayen kuma yana ruke da takobinsa, jira yake kawai yaga sun yunkuro masa ya gama dasu. Uzaifat ya sake komawa ya zauna ya shiga tunani mai zurfi cikin tsanani damuwa da tashin hankali. Abu na faro dai yanzu bai dan dabarar da zaiyi ba ya sauka kasan wannan tsauni ba. Abu na biyu, bai san halin da Lafirat da Abul shaja'a suke ciki ba a yanzu. Shin kinshirwa ta zamo ajalinsu ko kuwa wani balai ya afko musu? Koda gama aiyana haka, sai zuciyar sa ta karaya, ya tabbatar da cewa, yana cikin tsaka mai wuya . idan ya ci gaba da zama a cikin wannan shekar tsuntsaye har ya kuskura barci ya sace shi, to tabbas wannan tsuntsaye cinyeshi zauyi, tunda suma a cikin balain yunwa suke. Me ya kamata yayi? Shin zai karasa kashe ne? Idan ya ka shesu ya zaiyi da gawarwakinsu? A yanzu haka ma gawar iyayensu da ta sauran yan uwansu ta kusan cike shekar, samun inda zai mike ma ya kwanta aikine, kuma tabbas bazai iya ture wadannan gawarwaki ba. Koda gama aiyana haka yaga bashi da mafita kawai sai ya shiga rokon Allah akan ya fitar da shi daga cikin wannan hali na kaka ni kayi da yake ciki. Kafin Uzaifat ya gama shafa addu'a sai kawai ya ga wadannan ragowar yayan tsuntsayen sun afkawa yan uwansu matattu suna cin namansu, al'amarin da ya mutukar bashi mamaki kenan, yace a ransa, lallai yunwa balai ce, domin in ba masifar yaunwa ba, me zai sa wadannan tsuntsaye su afkawa mushe yan uwansu da ci? Babban abinda yafi daurewa Uzaifat kai shine, yadda tsuntsayen suka kusan cinye naman yan uwana nasu gaba daya a cikin kankanin lokaci, wato suka gwaguye kafa naman jikinsu sai kasusuwa suka bari. Uzaifat ya gama shafa adduar, sai ga wani narkeken tsuntsu ya taho a sama zai gifta ta saman tsaunin. Koda ya hango Uzaifat a durkushe sai yayi kasa kasa ya sureshi yayi sama da shi da nufin Shima ya samowa nasa yayan abin tabawa. Sa'ar sa Uzaifat yayi a wannan karon shine, tsuntsun ba jikinsa ya cafka ba, rigarsa ya cafka. Tsuntsun yaci gaba da tsala azababben gudu a sama, har ya iso saman fadamar nan wacce Uzaifat ya so ya debe ruwan ta ya cika salkar sa, bai sami dama ba. Koda Uzaifat ya leko kasa yaga zasu gifta ta kan koramar sai ya zare takobinsa yana mai yin kabbara ya dan karawa tsuntsun sara a kafa.take kafar ta guntule, bai san sa'adda yayi wata irin kara ba abin firgitarwa ya saki Uzaifat ya rikito kasa. Sai da Uzaifat yaji kamar iskar sama zata yayyagashi saboda nisan da ke tsakaninsa da kasa, sannan ya fado cikin wannan fadama. Ji kake tinjim... Uzaifat ya nutse izuwa can kasan fadamar sannan yayi linkaya ya taso sama. Cikin sauri Uzaifat ya cika salkar sa da ruwa ya rufeta ruf sannan ya fito daga cikin fadamar ya daga hannunsa sama yayiwa Allah godiya bisa saukar dashi kasa kasa da yayi daga kan wannan dogon tsauni, inda shekar tsuntsaye take, kuma ya tareshi daga sharrin tsuntsayen. Bayan ya gama wannan godiya ga Allah ne ya shiga farautar abinda zaicu dokin yunwa ta sashi yafara ganin dishi dishi. Cikin ikon Allah kuwa bai dade yana nemana, ya yi kicibus da wani maciji wanda ya hango abisa wata bishiya yana shirin hawa can saman bishiyar, kawai sai Uzaifat ya zare wata yar wuka da ke daure a cinyarsa ya cillawa maciji. Take wukar ta huda idon dama kuma ta cake macijin a jikin bishiyar, nan take macijin ya zama gawa. Cikin farin ciki Uzaifat ya ruga ya cire macijin daga jikin bishiyar sannan ya nemi duwatsu kanana guda biyu yayi kyastu da su ya kunna wuta bisa kan wadansu kirare, bayan ya fede macijin kenan. Ba tare da lokaci ba ya gasa macijin, Sannan ya ci namansa ya koshi ya zuba ragowar a cikin jakarsa a matsayin guzuri, sannan ya mike tsaye yana mai hamdala ga ubangiji ya falfala da gudu ya koma can baya inda Lafirat da Abul shaja'a. Lokacin da Uzaifat ya ido dai dai wajen da ya bar su Lafirat, sai ya isje wajen wayam babu su Lafirat babu alamun su. Ya duba gabas da yamma kudu da arewa babu alamar inda suka taka da sawayensu suka wuce. Uzaifat ya budi baki ya kwala musu kira har sau uku a lokacin da muryarsa ta cika dajin gaba daya da amsa kuwwa, amma shiru baiji sun amsa ba. A sannane hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tabbatar da cewa lallaiba lafiya ba. Uzaifat ya sami wuri ya zauna yana tunani, yace a ransa, to wai shin menene ya faru dasu Lafirat? Inda wata dabbarce tadaukesu ko kuma wata halitta mai kafafun tafiya da tabbas ya ga sawunta. Idan kuwa ba dabba bace, kuma ba halitta bace mai tafiya a kasa bisa kafafunta, to sai dai idan mai fuka fukai ce, wato mai iya tashi sama. Bayan Uzaifat yayi dan dogon tunani akan lamarin, saiya mike tsaye ya fara yawo a cikin dajin yana mai karanta wadansu adduoi yana mai rokon Allah ya bayyana masa inda su lafirat suke. Ya na wannan hali ne ya ido gaban wata katuwar bishiyar kuka, mai tsananin girman gaske. Koda Uzaifat yayi arba da wannan bishiya sai ya tsaya cak! A gabanta yana nazarinta cikin matukar mamaki. Uzaifat ya daga kansa sama don ya ga iyakar tsawon bishiyar, amma sai ya ga ashe bata da karshe. Zagaye da bishiyar tun daga kasanta har izuwa inda ido ka iya gani wata matattakala ce, yace a ransa, to wai shin wane ne ya gidan wannan matattakala haka, kuma a yaushe akayi wannan gagarumin aiki? Duk yadda akayi dai ba aikin bane na mutane sai dai aljanu. Koda gama aiyana haka, sai Uzaifat ya haukan matattakalar benen a jikin bishiyar ya fara hawa yana yin Sama batare da sanin inda zai je ba. Haka dai ya ci gaba da hawa matattakalar yana kara yin sama, har tsawon sa'a biyu, amma kuma sai ya ga ya kasa kure matattakalar, kuma har a sannan bai je karshen bishiyar ba, al'amarin da ya kara bashi mamaki kenan. Haka dai Uzaifat yaci gaba da hawa matattakalar dake jikin bishiyar har ya sake shafe wata sa'a biyun. Kwatsam sai ya tsinci kansa a gaban kofar wani makeken gida, a sannane ya gane cewa, ashe gidana akan saman bishiyar. Abin mamakin shine, gidan an ginashi ne da zallan duwatsun wuta, kuma ya kasance mai girman gaske. Yaya akayi wannan gida ya zauna daram akan bishiya? Amsar da Uzaifat ya kasa baiwa kansa kenan. Alhamdulillahi nan zan dakata sai Allah ya kaimu gobe. Zanyi amfani da wannan dama dan sanar muku da cewa Insha Allahu gobe za'ayi sadakar bakwai ta yayata. Ina mai gode a gareku kuma ina muku Fatan alkhairi. UMAR FAROUQ ZANGO [12/02, 7:57 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA BIYU MARUBUCI ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING UMAR FAROUQ ZANGO Uzaifat ya kasa kunnensa a jikin kofar, amma sai yaji shiru tamkar babu kowa a cikin gidan, ko sautin gyare baiji na. Ya dubi kofar gidan da kyau wadda aka yita da zallan karfe mai kaurin gaske, ya tabbatar da cewa ba zata ballu ba da karfin tsiya, sai kawai ya sa hannunsa ya kwankwasa kofar. Shiru baiji ance komai ba, sai ya kara kwankwasawa da kotar takobinsa. Wannan karon sai yaji ance, wanene nan yake kwankwasa mana koda haka da sanyin safiya? Muryar Sam irin ta mutane ba ta aljanu ba. Batare da fargabar komai ba Uzaifat yace, nine bakon ku Uzaifat dan sarki uwaisul karni. Na zo ne ku bani abokan tafiyata Abul shaja'a da Lafirat. Idan kuwa kun taba lafiyar su, sai na kashe duk wani mahaluki da ke cikin gidannan, sannan na ruguje gidan naku gaba daya na konashi. Koda jin wannan batu, sai aka kyalkyale da dariya. Dariyar dai ta matace wadda ta kasance sirirya mai dadin sauraro. Nan take kofar ta bude da kanta, shi kuwa gogan naka, sai ya ruke takobinsa tsirara a hannu ya kunna kai ciki. Da shigar Uzaifat cikin wannan gida, sai ya tsinci kansa a cikin wata makekiyar fada kasaitacciya, wadda ko a labari bai taba jin mai kawatuwarta ba. Wadansu kyawawan 'yan mata ya gani kimanin su dubu uku a tsaitsaye, sunyi sahu biyu dama da hagu sun ci ado da wani Korean tufafi duk iri daya mai gaske da kyalkyali, kuma mai daukar ido sai kamshi suke. Wani abin mamaki shine, gaba dayan 'yan matan kammaminsu iri dayane Sak, tamkar an tsaga kara. A nan saman wani gini mai tudu an ajiye wata luntsumemiyar karagar mulki. Zaune akan karagar wata kyakkyawar budurwa wace ta gaban kwatance wadda kyawunta ya ninka na ragowar 'yan matan sau goma. Tana da cika haiba da matukar kyawun dirin jiki da kyawun sura. Babu wani da namini da zai ga wannan budurwa bai kamu da sha'awarta ba, amma bisa mamaki tana hada ido da Uzaifat, sai ta ga ya daka mata harara bai na damu da kyanta ba, bare taka hankalinsa ta rudeshi. Koda ganin haka, sai kyakkyawar budurwar ta mike tsaye daga kan karagarta ta taho ga Uzaifat a lokacin da wadannan kuyangi nata suka dare suka bata hanya. Koda ta zo daf Uzaifat sai ta tsaya ta kura masa idanu tana murmushi, kuma tana kallonsa sama da kasa sannan ta kewayashi tana mai dada yi masa wani irin kallo, wanda za'a iya fassarashi da kallo ne na sha awa ko na hilata. Asannane ta dawo gaban Uzaifat suka fuskanci juna ta dubeshi cikin tattausan murmushi mai karya zuciya tace, haba gwarzo uban sadauka, haba jaurmin jatumai saboda me zaka shigo fadar sarauniyar kyau ta matan duniya, kana turbine fuska alhalin ba a bakin ciki a fadata, kuma ba a yunwa da kishirwa anan, sannan ba a rashin lafiya ko wata lalura da ka iya kefa mutum cikin damuwa? Ka sani cewa, wannan gidana nawa aljannar duniya ce, babu wani abu na jin dadin duniya da babu shi, duk wanda ya dace ya shigo nan bazai tsufa ba kuma bazai mutuba har abada. Koda sarauniyar tazo nan a zancenta, sai Uzaifat ya daka mata tsawa, yace, ke munafukar Allah karya kike yi, babu wannan rayuwa da kika siffanta a wannan duniya tamu. Ubangijin musulunci shi kadai ne ya shirya wannan rayuwa ga bayinsa, wadanda suka bishi a bayan rayuwar su ta duniya, wato a can makomarsu aljanna. Ina so ki sani cewa, duk wannan kawar taku da kyawunnan naki bai burgeni ba, kuma ban yarda cewa ku mutane ne ba. Maza ki fito min da abokan tafiyata su Lafirat don tabbas kune mini kuka daukko su daga can inda na barosu, ko kuma yanzunnan na hallakaku ke da kuyangin naki. Koda gana fadin haka, sai Uzaifat ya daga takobinsa sama, sannan ya budi baki da nufin zai kwala kabbara, kawai sai yaga wanna kyakkyawar sarauniya ta fashe da kuka. Nan take ta dauki Wata 'yar karamar wuka da ke cake a jikin tuffa bisa wani teburi ta yanki damtsen hannunta. Take wajen ya dare jini ya zubo cikin fusata ta dubi Uzaifat, tace, shin yanzu ka yarda cewa ni bil adama ce kamarka? Jikina irin nakane, zuciyata irin takace. Ina son ka sani cewa asalina na kasance 'ya ga sarkin birnin hindu, aljanune suka satoni suka kawonj nan saboda a duniya babu Wata 'ya mace mai kyawuna. Ka saki jikina ka yarda dani a sannane zan iya gaya maka yadda zaka iya saduwa da abokan tafiyar ka, ka ceto rayuwar su domin suna can a cikin halin tsaka mai wuya. Sa'adda sarauniya tazo dai dai nan a zancenta, sai jikin Uzaifat yayi sanyi, yaji kamar abinda ta fada gaskiyane, amma duk da haka sai yaji zuciyar sa tana wasuwasi akan hakan. Nan dai sarauniyar ta baiwa kuyanginta umarni da akai Uzaifat izuwa masaukinsa ya huta. Nan take wasu kuyangi hudu suka kama Uzaifat suka ja shi suka kai shi izuwa cikin wani kasaitaccen daki daban mai dauke da wani luntsumemen gado, suka zaunar dashi akan gadon, sannan suka fita suka barshi. Jim kadan sai ga wasu kuyangin biyu daban, sun shigo da manyan farantan abinci guda biyu. Farantin farko a cike yake da nama kaji kala uku soyayyu gasassu da kuma farfesu. Shikuwa faranti na a cike yake da 'ya 'yan itatuwa kamar su, tuffa lemon zaki ayaba baure da fasadabur. Bayan kuyangi biyu sun ajiye farantan biyu a gaban Uzaifat sai suka fice daga cikin dakin suka barshi shi kadai. Uzaifat ya dubi wannan abinci yaji yana shaawar ci, amma kuma sai yaji hankalinsa bai kwanta ba da abincin, kawai sai yayi bismillah gami da karanta wata addu'a ya hau abincin da ci, hat sai da yakoshi. Wani abu da Uzaifat ya lura da shi shine, lokacin da ya fara wannan adduar sai ya jiyo kamar ana ihu a can wajen dakin da yake ciki, amma kuma da ya kammala addu'ar sai ya dai na jiyo ihun. Bayan Uzaifat ya kimtsa cikinsa sai ya sake yin wata adduar ya tofa a gabas da yamma kudu da arewa da sama da kasa, sannan ya mike kafafunsa akan luntsumemen gadon yayi kwanciyarsa. Abinka da gajiyayye, kuma ga shi ya ci ya koshi, nan da nan barci ya kwasheshi bai sani ba. A can fadar wannan sarauniya kuwa tana zaune tare da kuyangin ta sai ga wata kuyangarta ta taho daga bangaren dakin da aka kai Uzaifat. Da zuwan kuyangar sai ta zube kasa gaban sarauniyar tace, ya ke uwar mayi ta aljanu ai hakanmj ya cimma ruwa, tuni wannan bako yaci wannan abincin da muka kai masa, don haka dafin dake cikin abincin yayi tasiri a jikinsa, ya zama gawa akan gado. Koda jin wannan batu sai uwar mayi ta bushe da dariya, sannan tayi girgiza ta juye izuwa wata mummunar halitta mai kama da ta dodanniya, ba kyan gani. Suma sauran kuyanginnata sai duka suka zama irinta. Uwar mayu ta dubi wadansu daga cikin kuyangin ta tace dasu, kuje ku dauko wannan bakon ku kaishi can dakin da muka kulle abokan tafiyar sa dayazo yana nema, si da daddare za'a hadasu su ukun ayi mini romonsu na sha lagwada. Koda jin wannan umarni sai wadannan kuyangi suka ce, an gama ya shugabarmu. Nan take mayun aljanun su uku suka bude duka fukansu suka tashi sama suka nufi inda wannan faki yaje, wanda Uzaifat ke kwance a ciki. Mai makon su shiga dakin ta cikin kofa sai suka ratsa ta cikin gini tamkar danshi ya tsattsafo daga cikin kasa. Take suka baiyana a gaban gadon da Uzaifat ke kwance. Koda suka durfafi Uzaifat sai sukaji wani irin gagarumin zafin wuta na fesowa. Ba shiri suka ja da baya cikin alajabi. Daga can sai suka sake yunkurawa a karo na biyu don su daukko Uzaifat ai kuwa sai suka kara jin wannan zafi ya feso musu tamkar jikinsu zai narke. A dimauce suka sake rugawa da baya, ba tare da sun kara jarrabawa ba a karo na uku suka fice daga cikin wannan dakin da gudu suka je gaban uwar mayu suka zube suna gaki. Sarauniyar mayu ta daka musu tsawa tace, wannan kuma wane irin shashancin banza ne haka? Ina bakon naman da nace ku dauko a hada da wadancan a dafa mini don suyu luguf da wuri kafin dare yayi? Koda jin wannan tambaya sai daya daga cikinsu ta dubeta tace, ya shugabata ai al'amarin yafi karfin mu domin sau biyu muna kokarin dauko shi, amma da mun kusanceshi si muji mugun turirin wuta na fesowa zai narkar damu. Koda jin haka, sai uwar mayu ta buga tsaki ta dubi wasu zakwakuran kuyangin nata guda biyu tace, maza kuke ko daukko shi tunda wadannan ragwayen sun kasa. Nan take kuyangin suka tafi cika umarni. Jim kadan sai ga su suma sun dawo a guje suna haki kamar ransu zai fita suka fadi gaban sarauniya suka yi bayani kamar yadda na farko sukayi. Koda jin wannan batu sai uwar mayu ta mike zumbur a fusace a bude fuka fukanta ta nufi wannan daki inda Uzaifat ke kwance. Ai kuwa sai gaba dayan kuyangin nata suka bita a bata du domin su ga abinda zai faru. Da shigarta cikin dakin, sai suka iske Uzaifat a kwance yana ta shara bacci abinda, bai ma san abinda ke faruwa ba. Kai tsaye uwar mayu ta durfafi Uzaifat tana karanta wasu dalasiman tsafi. Sai da yarage saura bai fi taku uku ba ta isa daf da shi, sai taji wani irin mugun hucin zafi gami da wata iska mai karfin gaske sun buso mata sai gani akayi an watsota baya tamkar an janyo ta da kugiya sannan aka fyada ta da bango ta fado kasa a mutukar galabaice, kuma rabin fuskarta UA kone. Koda ganin wannan abu da ya faru, sai gaba dayansu suka firgice ainun, ba shiri suka dauke sarauniyar tasu suka fice da ita daga cikin dakin, suka maida ita can fadartata suka zaunar da ita akan karagar mulkinta. Sarauniyar mayu ba ta dawo cikin haiyyacinta ba, sai bayan dakika dari uku. Koda ta bude idanunta taga kanta a raye, sai ta yi ajiyar zuciya ta hau kallon kuyangin nata daya bayan daya, dagacan sai ta numfasa tace. Yanzu ya zamu yi da wannan shaidanin bako? Tabbas idan har ya farka daga barcin da yake yi bamu hallaka shi ba. Shi zai hallakamu, kuma ya dauki 'yan uwansa. Alhamdulillahi nan zan dakata sai Allah ya kaimu gobe. [13/02, 8:50 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA BIYU MARUBUCI ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING UMAR FAROUQ ZANGO Sa'adda kuyangin suka ji wannan tambaya sai duk sukayi shiru suna nazari. Daga can sai mafi shekaru daga cikinsu wata tsohuwa yar shekara dubu biyu da dari shida tayi murmushi tace, ya shugabata ina da dabara. Abinda ya kamata muyi shine, mu banka wuta aikin dakin da wannan bako yake ya zamana cewa ko da ya farka daga barcin ba zai iya fitowaba face wutar ta babbakeshi. Su kuwa sauran yan uwan nasa guda biyu sai mu daukesu tun yanzu mu yayyakasu mu zuba a tukunya a fara dafasu. Koda jin wannan shawara sai uwar mayu ta cika da farin ciki tace, an gaisheki tsohuwa jalziba hakika kinzo da shawarar da zata fisshemu, in ba dan keba bamusan yadda zami da wannan shaidanin bako ba. Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce duk wanda ya rigaka kwana dole ne ya riga ka tashi. Nan take uwar mayu taba da umarni aje a dauko Abul shaja'a da Lafirat daga cikin wani daki mai duhun gaske wanda ko tafin hannu mutum baya iya gani a cikinsa. Nab take kuwa aka je aka fiddo Lafirat da Abul shaja'a sai gasu a daure tamau da wasu irin sarkoki na tsafi wadanda ko yaushe juya wa suke a jikinsu suna kanannadesu. Kallo daya mutum zaiyi wa Abul shaja'a da Lafirat a wannan lokaci ya gane cewa basa cikin haiyacinsu domin idanunsu ma a lumshe suke kuma suna tangadi kamar zasu fadi kasa tamkar wadanda suka sha giya suka bugu. Bayan an zo dasu Lafirat gaban sarauniyar mayu an watsar da su, sai aka dauko wata katuwar tukunya aka dorata bisa murhu aka zuba ruwa a cikin tukunyar aka watsa cefane a ciki, sannan aka kunna wuta ana dafa cefanen. A sannane uwar mayu ta dubi sarkin fawarta wata garjejiyar aljana tace, yanzu kece da aiki, sai ki je ki debo kayan aikinki ki fara. Kafin uwar mayu ta rufe bakinta tuni sarkin fawa ta bace bat ta sake baiyana dauke da wata katuwar akwatin karfe. Koda ta bude akwatin sai ga wukake da adduna da gatari iri iri a ciki sama da kala dari, amma gaba dayan wadannan makamai a dakushe suke, saboda tsabar yawan saran kasusuwan aljanu da dabbobi da akayi da su. Koda uwar mayu ta lura da dakushewar makaman sai ta dakawa sarkin fawa tsawa tace me yasa kika bar kayan aikinki babu washi haka? Sarkin fawa tace, ki gafarceni ya shugabata ki tuna cewa rabonda mu sami abinci afarutar da muke fita yau shekara guda Kenan, shiyasa na shaafa bam wasosu ba. Sarauniyar mayu tace maza ki wasosu yanzu da sauri. Nan take sarkin fawa ta shiga aikin wasa makaman ta cikin gidan gaba daya ya cika da Karar karafa kai kace a makera kake. Duk da cewar Abul shaja'a da Lafirat na cikin gushewar hankali a wannan lokaci da sukaga ana wasa wadannan muggan makamai za'a yankasu, a daddatsasu sai da hankalinsu ya dugunzuma suka kamu da tsananin tsoro. Dama tuntuni Lafirat ta karaya tun a Sa'adda aljanu suka shammacesu sukayi musu surar shirwa sukayi sama da su lokacin da suke zaune acan dajin da Uzaifat ya tafi ya barsu. A wannan lokaci babu irin kokarin da Lafirat batayi ba, don ta cecesu da karfin sihirinta amma sai sihirin nata yaki yayi tasiri saboda karfin sihirin aljanun yafi nata, bisa dole ta rungumi kaddara ta zuba ido kawai. Shakuwa Abul shaja'a tun Sa'adda aljanu suka sokeshi sukayi sama dashi sai yaji bakinsa ya rufe ruf ya kasa yin addu'a kuma yaji wata irin muguwar kasala ta baibayeshi idanunsa ma dakyar yake iya bude wa. Suna j suna gani akayi ta tafiya dasu a sama, har aka iso dasu wannan isa aka jefasu cikin dakin duhu aka kullesu. A dai dai wannan lokaci da sarkin fawa ke wasa wukakenta ne Uzaifat dake barci acan daki yake wani mummunan mafarki mai ban tsoro. A cikin mafarkin ne aka nuna masa cewa sun shiga cikin wani bala'i na halin tsaka mai wuya suna daf da rasa rayuwarsu. Kawai sai Uzaifat ya kama mutsu mutsu da jikinsa. Tuni a wannan lokaci an baka gagarumar wuta a cikin wannan daki da Uzaifat ke kwance ta kama ko ina saura kiris ta kama gadon dayake kwance akai. Tiririn hayaki da zafin wuta ne yasa ya farka a firgice ya mike tsaye zumbur kawai saiya ga babu ta inda zai wuce ya fita daga cikin wannan dakin face ta cikin wutar, gashi kuma wutar ta fara kama gadon da yake har tana kawowa kafarsa barazana. Al'amarin da ya mutukar dugunzuma hankalinsa kenan ya fara tunanin dole ne yasan abinyi cikin gaggawa don ceto rayuwarsu. A can fadar uwar mayu kuwa a wannan lokaci sarkin fawa ta gama wasa wukakenta na saran nama don haka sai aka fara dauko Lafirat aka dorata akan wani katon teburin karfe, aka kwance sarkar da aka daureta da ita. Lafirat ta dubi Abul shaja'a suka hada idanu a Lokacin da hawayen takaici ya subuto mata bisa cewa zata mutu bata cika burinta ba na duniya. Koda Abul shaja'a yaga zubar wannan hawaye a idanun Lafirat sai yaji ya kamu da tsananin tausayinta inda yana da ikon ceton rayuwarta da yayi. Sarkin fawa ta dauki wani faskeken gatari mai fadin kai ta daga sama da nufin ta fara datse kan Lafirat kawai sai akaga jarumi Uzaifat ya taho da gudu a sama tamkar an harboshi daga cikin baka ya doki kirjin sarkin fawa da kafarsa. Take sarkin fawa ta yi sama ta naku da gini ta fado kasa, jini na zuba ta cikin hancinta da bakinta, ko shurawa batayi ba. Koda ganin haka sai gaba dayan kuyangin uwar mayu suka kwashi wukaken sarkin fawa suka fakwa Uzaifat aka ruguntsume da a azababben yaki. Ita kuwa uwar mayu o motsawa batayi ba daga kan karagarta ta mulki. Maimkon ta razana da ganin Uzaifat ma sai harde kafafu ta zuba ido domin taga iya Kar jarumtakarsa. Lafirat kuwa sai ta fado kasa daga kan wannan tebur da aka dorata sakamakon hautsinin yakin da ke afkuwa a fadar, shi kuwa Abul shaja'a har a sannan yana daure cikin sarkar tsafi. Uzaifat ya ci gaba da kaiwa kuyangin sarauniyar mayu sara da suka da takobinsa suma suna kai masa, ya zama tamkar shaidani a tsakiyarsu. Duk Sa'adda takobinsa ta hadu d makamansa sai dai kaga tartsatsin wuta na tashi gami da hayaki. Nan fa suka kasa yi masa illah, shima ya kasa kashe ko da guda daya daga cikinsu ne. A wannan lokaci ne hankalin Uzaifat ya dugunzuma domin yasan cewa muddin aka ci gaba da wannan fafatawa a haka zai gaji su kuwa kuyangin sarauniyar mayu ba zasu gaji ba, tunda su ba mutane bane. Da zarar ya gaji kwa yasan cewa sai sun sami nasara akansa sun hallakashi. Hakika lokacin da sarauniyar mayu dakuyamginta suka ga Uzaifat tsulum ya fito da ga cikin wannan daki a sama kamar tsunsu sai da suka cika da tsananin mamaki yadda akayi ya kubuta daga sharrin wutarda suka banka wa dakin. Abinda basu sani ba shine, karfin addu'a ce kawai ta kubutar dashi. Lokacin da Uzaifat ya tabbatar da cewa lallai idan ya gaji kuyangin uwar mayu zasu sami nasara a kansa, sai ya farakaranta wata addu'a ta musamman a cikin zuciyarsa yana mai neman taimakon Allah. Nan take kuwa yaji wani irin sabon karfi da zafin nama suna shigarsa. Ita kanta takobinsa sai ta sauya launi ta zama ja jajir tamkar an gasa ta a wuta. Da zarar ya makamansu sai ka ga makaman nasu sun guntule duk aljanar da ya sari jikinta kuwa sai ya ga ta kama da wuta ta soye kurmus ta zana toka, sabanin da idan ya sari jikinsu basa jin komai tamkar ya sari karfe. Kuyi min hakuri nan zan dakata Insha Allahu zan dora gobe. Naku a kullum da koda yaushe UMAR FAROUQ ZANGO [14/02, 9:09 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA BIYU MARUBUCI. ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING UMAR FAROUQ ZANGO Kafin kuyangin uwar mayu su ankara tuni Uzaifat ya kashe sama da rabin su. Koda uwar mayu taga abinda ke faruwa, sai ta kwalla uban ihu ta mike tsaye zumbur daga kan karagarta, Al'amarin yasa ragowar kuyangin nata suka ja da baya kenan. Shi ma Uzaifat sai ya juyo ya fuskanci uwar mayu, bisa mamaki sai yaga hawaye na zuba a idanunta. Cikin tsananin takaici da bakin ciki uwar mayu ta dakawa Uzaifat tsawa, duk da kasancewar sa jarumi mai dakakkiyar zuciya sai da hantar cikinsa ta kada, domin bai taba jin kakkausar murya mai among ba tamkar uwar mayu. Uwar mayu tadubi Uzaifat tace, yakai wannna hatsabibin biladama kayi sani cewa, yau ka yanke min burin rayuwa, kuma ka haddasa min bakin cikin zuciya. Kasani cewa wadannan kuyangi nawa da kashe gaba dayansu ya'yana ne na cikina wadanda ban sami damar haihuwarsu na sai bayan shekara dubu da dari daya ina faman neman haihuwa. Ba wani bane ya samo min magani haihuwar ba, face sarki sha'aran ibini Naukib na birnin shumbul bisa sharadin cewa, zan zauna a wannan dajin nayi masa gadon hanya na tsawon shekara sittin, sannan ya yantani na koma can ainahin kasata ta haihuwa inda na baro iyayena da kakannina. A tsawon shekara sittin da zanyi a cikin wannan daji, sarki sha'aran ya tabbatar min da cewa zan haifi yaya dubu uku kuma daya zan tafi dolene na bar masa guda dubu daya da dari biyar, yanzu gashi ka kashe dubu daya daya da dari biyar din, kaga kenan koda na hallaka ka idan zantafi, sai dai na tafi ni kadai ba tare da da ko daya ba. Daga cikin yayan nawa yanzu ka kashe mafi soyuwa a raina, wadda itace yata ta farko mafi shekaru daga cikinsu, mai bani shawara bisa dukkan alamurana. Ni kam yanzu da na koma kasarmu ba tare da dan da na haifa ba, gwara ma nima na rasa rayuwata, domin yau shekara ta dubu uku kenan da yin aure ban taba haihuwaba, har na gaji da gorin dangin miji, sannan na samu haihuwar kuna na rasa. Ya zama dole a gareni yanzu na yi maka kisan gilla domin na huce wannan takaici daka jefani a ciki. Koda gama fadin haka, sai uwar mayu ta zare wata sharbebeyar takobin tsafi dake rataye a bayanta. Ita dai wannan takobi sauya launi take yi ita kadai tana zama kala kala kuma tartsatsin wuta gami da hayaki na tashi a jikinta, tun gabanin ayi sara da ita. Nana take uwar mayu ta daka wawan tsalle a sama tadira a gaban Uzaifat. Saboda nauyinta sai da gidan gaba daya yayi girgiza tamkar zai ruguje. Kawai sai ta kaiwa Uzaifat mummunan sara da nufin ta fille masa kai cikin zafin nama shi ma ya sa ta sa takobin ya tare saran. Koda takubban biyu suka hadu sai akayi wata irin gagarumar tsawa, wacce ta firgita sauran yayan uwar mayu suka dimauce suka kama guje guje a cikin fadar. Tartsatsin wutar da ya zubo kasa kuwa sakamakon haduwar takubban sai ya haddasa gobara a fadar ko ina wuta ta kama ci ganga ganga. Nan fa suka ci gaba da kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta babu sassauci. Nan da nan fadar ta yamutse gaba daya dirkokin gini suka rinka karyewa suna ruguzowa kasa. Duwatsu da aka yi ginin gidan da su suka rinka farfashewa suna ruburbushewa. Kai shi kansa Uzaifat bai taba ganin tashin hankali irin na wannan rana ba. Sai da aka shafe sa'a uku cur ana wannan gumurzu dayansu bai sami nasarar illata daya ba. A sannane Uzaifat ya tuna cewa ya shaafa dayin addu'a don haka sai ya fara kiran sunayen ubangiji tsarkaka yana mai neman taimakon sa. Faruwa hakan ke dawuya sai yaga ya raba takobin uwar mayu gida biyu bata san Sa'adda ta saki takobin ta fadi kasa ba, sannan ta ja da baya a tsorace. uzaifat ya tsaya cak rike da tasa takobin yana kallonta kawai. Ita ba tayi yunkurin gudu ba ko afka masa shima haka. Cikin fushi uwar mayu ta dubi Uzaifat tace, idan ka isa ka yarda wannan takobi tana mu gwada yar kashi ni da kai. Nan rantse da ababan dogarona Saina karairaya ka, nayi gutsin gutsin da sassan jikinka. Yayin da Uzaifat yaji wannan batu, sai ya yi murmushi, sannan yace, yake wannan muguwar aljana kiyi sani cewa koda wannan takobi ko babu sai na yi nasara akanki da izinin ubangiji na, domin kuwa kina kan bata mabaiyani. Koda gama wannan batu sai Uzaifat yayi nifa da takobinsa ya karanta wata addu'a ya tunkari uwar mayu b tare da shakkar komaiba. Koda ganin haka, sai uwar mayu tafara murmushin mugunta domin tasan cewa ta farat daya zata gama da Uzaifat, don haka sai ita ma ta tunkareshi. Suna haduwa ta kai masa wawan naushi da hannuna guda a fuska, cikin matukar zafin nama na ban alajabi ya sunkuya kasa bata sameshi ba, sai ta naushi dirkar gini mai kaurin kamu ashirin. Take dirkar ta rushe, fadi kasa kafin uwar mayu ta sake kaiwa Uzaifat wani naushi tun Uzaifat ya dunkule hannunsa ya gabza mata naushi a cikin ta tadurkushe kasa tana mai kurma ihu sakamakon tsananin zafin da taji tamkar yayan hanjinta sun karkatse. Shi kansa Uzaifat sai ya cika da tsananin mamaki bisa yadda ya sami wannan gagarumin karfi. Uzaifat ya sa kafarsa ya sake gabzawa uwar mayu naushi a fuska ta kuga da baya. Nana take Uzaifat ya take wuyan uwar mayu da kafarsa tafara kokarin mutuwa bata san Sa'adda ta budi baki ba tace kayi min rai ya shugabana. Ina son ka amsa mini tambaya guda daya kafin ka kashe ni. Koda jin haka, sai Uzaifat ya dauke kafarsa daga kan wuyanta a lokacin da ta dawo gwauron numfashi tamkar wadda ta farfado daga suma. Uwar mayu ta dubi Uzaifat a lokacin da idanunta suka kada sukayi jawur tamkar an gasa dan buda a wuta, ta ce, kai kuwa yaya akayi ka sami wannan gagarumin karfi haka? Shin kana tsafine ko kuwa kana da wani boyayyen sihirin? Yayinda Uzaifat yaji wannan tambaya sai ya yi murmushi sannan yace, ni bana tsafi, kuma bani da sihiri. Wannan karfi da kika ga na samu yazone daga ubangijina, domin ya nuna fifikon gaskiya akan karya. Sa'adda uwar mayu taji haka, sai tayi ajiyar zuciya tace, Hakika ubangiji da ya baka wannan karfi shine ubangijin gaskiya, domin yau shekara ta arba'in da biyar a wannan daji duk biladaman da yayi karo da ni, sai na ga bayansa domin ina da karfin sihirin tsafin da babu mai irinsa a duniya face sarki sha'aran. Koda jin wannan batu sai jikin Uzaifat yayi sanyi da kansa ya kama Ka fadar uwar mayu ya tasheta tsaye suka fuskanci juna, sannan yace ki karbi addinina yanzu ni kuma na yi miki alkawarin zaki koma kasarki tare da ragowar yayanki, domin ki huta da gorin fangin miji. Uwar mayu tayi murmushi tace bani addinin naka ina marhaba dashi. Nana take Uzaifat ya biya mata Kalmar shahada ta mai mai ta. Duk wannan abu dake faruwa ragowar yayan uwar mayu na durkushe a can gefe daya kuma a takure suna kallo tamkar ace kyat su fita da gudu. Abul shaja'a da Lafirat ma suna kallon duk abinda ke Faruwa, suna alajabi. Uwar mayu na gama karanta Kalmar shahada sai wannan sarkar tsafi data daure Abul shaja'a ta bace bat, duk abubuwan tsafin dake cikin fadar suka bace tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen. Uzaifat ya dubi uwar mayu yace, yake wannan aljana kiyi sani cewa daga kin zama yar uwar mu musulma, don haka ina maiyi miki nasiha da kada ki sake cin naman mutum ko na dan uwanka aljan. Ki sani cewa, wannan maita da Allah ya baki ba don kiyi barna bane, sai domin ki zamo tamkar likita ga jama'ar ki tunda kinada baiwar ganin abinda su basu da ikon gani a cikin jikinsu. Yanzu abinda nake so dake shine ki musuluntar da yayanki kamar yadda na musuluntar dake. Kafin uwar mayu ta budi baki gaba dayansu suka karanta Kalmar shahada, al'amarin daya jefa Uzaifat Abul shaja'a cikin matukar farin ciki kenan. Ita kanta Lafirat sai da ta ji ta kamu da farin ciki duk dacewar itaba musulma bace. Uwar mayu ta dubi Uzaifat tace, yanzu menene dalilinku na ratsowa ta ciki wadannan muggan dazuzzuka alhalin shekara da shekaru biladama sun dai na shigo wa saboda sanin masifun dake cikin su? Dajin wannan tambaya sai Uzaifat ya kwashe labarin su tsaf ya zaiyanewa uwar mayu dan gane da tsohuwar gabar dake tsakanin birnin shumbul da birnin Darul Husuf da kuma duk abubuwan da suka faru garesu tun daga lokacinda suka fito yakishi da dan uwansa Ukashat da kuma labarin da Lafirat ta basu na hadin kan da Ukashat ya baiwa sarki sha'aran don aje aci birnin su da yaki. A karshe ya sana da ita cewa yanzu suna sone suje can birnin shumbul domin ceto rayuwar yan uwansu da kuma rayuwar luhaira yar likita abu sharaz sannan su sato yarima Ukashat don kada yaje ya tono wadannan layu guda hudu da aka binne akasan katangun birnin Darul Husuf. Lokacin da uwar mayu ta gama jin wannan bayani, sai tayi shiru kuma ta sunkui da kanta kas, tana jin jina al'amarin cikin damuwa. Daga can sai ta dago kai ta dubi Uzaifat tace, hakika akwai gagarumin aiki agabanku domin ita Lafirat tasan irin masifun dake cikin sauran dazuzzukan da zaku ratsa ku isa birnin shumbul. Shidai dajin mashaarul kais ka gama da shi tunda ka shigeshi harka fafata yaki dawasu daga cikin muggan tsuntsayen cikinsa harka hallakasu. Tabbas yanzu wadannan tsuntsayen duk inda suka ganka bazasu kasance ka ba, domin sun tsorata ainun, lafiya kalau zaku wuce ta cikin dajin. Inda zaku fuskanci matsala shine, aicikin dajin zarsus inda muggan kunamai da macizai suke da kuma dajin Huzurul Has inda tsafaffen maridi yake tare da matarsa da yayansa biyu. Bisa tarihi sama da shekaru hamsin baya babu wani mahaluki da ya taba ratsa wadannan dazuzzuka biyu ya wuce a raye, walau mutum ko aljan, face da izinin sarki shaaran bin Naukib. Koda uwar mayu tazonan a zancenta, sai Lafirat ta taso daga inda take zauneta taho gaban Uzaifat tatsaya tace, tabbas abinda uwar mayu ta fadi yanzu gaskiya ne. Uzaifat yace babu komai mu zamu ratsa ta cikin dazuzzukan biyu, kuma mu wuce a raye da izinin Allah. Uwar mayu tace, ya kai wannan gwarzon jarumi kayi sani cewa yau shekara arba'in da biyar kenan ina tare da mutane da aljanu a wanann daji ina kashesu da cinyesu. Lallai wannan aiki dana ai nata ba karamin zunubi bane don haka inaso na share zunubina da aikata aikin alkhairi saboda haka nima yanzu na sallama rayuwata bisa yi muku rakiya a cikin wannan tafiya har mu isa birnin shumbul. Idan Allah yasa kun sami nasara akansu kuma ni da ya'yana rayuwar mu, shikenan sai na cika burina. Idan kuma muka hallaka, ina fata mutuwarmu ta zamo sanadin samun rahama a wajen ubangijin musulunci. Koda jin wannan batu sai Uzaifat yaji kaunar uwar mayu ta shiga zuciyarsa, abu san Sa'adda ya rungume ta ba. Alhamdulillahi nan zamu dakata sai Allah ya kaimu gobe zamu dora. Zanyi amfani da wannan dama domin na mka sakon godiya dafatam alkhairi ga dukkan mutanen gidanna, muna godiya bisa nuna hadin kai da goyon baya da kuma kara mana kwarin gwiwa da kuke da wadanda suke bin mu ta DM da kuma kira duka muna godiua. Muna jin korafe korafen ku kuma Insha Allahu zamu ci gaba da gyara domin ganin kun samu nishadi da farincki. Haka zalika kuma ina mai neman afuwarku a duk lokacin da kuka ga nayi karamin typing to bawai da gangan nayi bane, akwai uzurin da yake zuwane ni kuma sai naga da naki yin postin gwara nayi ko yaya yake don ganin duka kun samu nishadi da farin cikin. Na barku lafiya naku a kullum da ko da yaushe UMAR FAROUQ ZANGO [16/02, 9:25 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA BIYU MARUBUCI ADBUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING UMAR FAROUQ ZANGO Nan dai Uzaifat Abul shaja'a Lafirat da Uwar mayu da yayanta suka fice daga cikin gidan suka yi ta sauka kasan bishiyar da gidan ke kai, ta kan wannan matattakala. Koda fara saukarsu sai gidan yaci gaba da rushewa yana neman zubowa kasa. Cikin hanzari suka ci gaba da saukko wa da gudu, aikuwa suna gama sauka kasan bishiyar da gidan ke kai, sai ta nutse izuwa cikin karkashin kasa ta bace bat. Ba tare da bata lokaci ba kuwa suka afka cikin dajin mashaarul Kais suka kama tafiya ba kakkautawa. Ai kuwa suna cikin tafiyar ne suka ga irin wadannan manyan tsuntsaye na ta shawagi a samansu, amma da zarar sunyi kasa kasa sunyi arba da Uzaifat sai suke yin sama su lulaka ba sa sake dawowa. Haka dai su Uzaifat suka ci gaba da tafiya, har tsawon kwana uku a cikin dajin mashaarul kais, duk inda dare ya riskesu, sai su yada zango zai gari ya waye, sannan suci gaba da tafiya. Da yake har yanzu Lafirat na fama da lalurar wannna rauni dake bayanta Uzaifat ne ya dinga goyata a bayansa a tsawon kwanaki ukun kuma wani iko na Allah, sai ta kamu da zazzabi mai zafi, har da kumallo, al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa kenan, musamman ma shi Uzaifat domin tattara hankalinsa yayi gaba daya akanta ya rinka jinyarta yana bata magunguna tana sha, kuma ya dinga dura mata abinci da hannunsa. Da yammacin kwana na uku ne zazzabin Lafirat yayi zafi ainun, har numfashinta ya dinga sarkewa, al'amarin da ya dimauta Uzaifat kenan, bai san Sa'adda ya fara a addu'a yana rokon Allah ya baiwa Lafirat lafiya ba. Ai kuwabai dade ba da fara addu'ar, sai Lafirat ta samu sauki, har ta bude idanunta ta dubeshi tayi masa murmushi. Nan take farin ciki ya lullune Uzaifat yaji kamar ya rungume Lafirat, amma sai ya kasa. Bisa mamaki sai Uzaifat yaga hawaye na zuba a idanun lafirat al'amarin daya mutukar bashi mamaki kenan, ya dubeta cikin karayar zuciya yace, yake Lafirat ina dalilin zubar wannan hawaye naki? A lokacin da Uzaifat yayiwa lafirat wannan tambaya babu kowa a kusa da su, domin Abul shaja'a uwar mayu da yayanta na can gefe daya. Abul shaja'a yana koya musu karatun alkur'ani. Yayin da Lafirat taji tambayar da Uzaifat yayi mata, sai tayi ajiyar numfashi sannan tace, ya kai gwarzona kayi sami cewa a rayuwata babu wani mahaluki daya taba nuna damuwa da kulawa a kaina sama da kai. Tsananin farin cikine yasa kaga ina zubar da wannan hawaye bisa ganin nuna kulawarka a gareni. Kai kuwa mai ya sa ka damu da rayuwata lhakin kasan cewa bazan iya yi muku komai ba acikin wannan tafiya? Aikina kawai shine na nuna muku hanya, to yanzu ma ga uwar mayu da yayanta ko babu ni su zasu iya nuna muku hanyar. Lokacin da Lafirat tazo nan a zancenta, sai Uzaifat yayi shiru yana kallonta kawai ya rasa amsar da zai bata. Lafirat tace ya naga kayi shiru baka ce komai ba? Uzaifat yayi murmushi yace kiyi hakuri yake Lafirat domin a gaskiya yanzu bazan iya baki amsar wannan tambaya ba, amma idan lokaci yayi zan amsa tambayar, idan muna tare kuma muna raye. Koda gama fadin haka sai Uzaifat ya mike tsaye ya kara gaba ya bar Lafirat a zaune tana mai binsa da kallo kawai cikin mamaki da wasu wasi. Ba komai taje wasu wasi ba, face wai shin wannan kulawar da Uzaifat ke nuna mata SO ne kk tausayi? Amsar da ta kasa baiwa kanta kenan. Yayin da Uzaifat ya baro wajen Lafirat sai yaje wajen su Abul shaja'a ya zauna yaci gaba da tayasu karatun alkurani izuwa wani lokaci. Bayan sun hatatama ne Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, Yanzu ya kakejin raunin kafarka? Abul shaja'a yace, ai na warke sumul, shin baka yadda na ke takawa ba sosai yanzu, ga shi ma na daina dogara ice. Uzaifat yayi murmushi yace, gaskiya ne amma ina neman alfarma mu kara kwana uku a nan domin ku kara samun lafiya sosai, kai da Lafirat. Koda jin haka, sai Abul shaja'a ya dubi Uzaifat cikin matukar mamaki, yace aini ma warke bana bukatar karin bata lokaci, sai dai saboda ita Lafirat din. Kuma ka tuna cewa, ita Lafirat babu wani abu da zata iya yi mana a cikin wannan tafiya face nuna mana hanya, ko babu ita Yanzu akwai uwar mayu da yayanta. Uzaifat yace nasan da hk, amma lallai nafi son sai Lafirat ta warke sumul sannan zamu rabu da ita a dajin karshe, bana son mu rabu da ita tana cikin lalura. Ka tuna cewa, ba don ita ba da tuni mun hallaka tun a baya albarka cin ta ne muka kawo izuwa matsayin da muke kai yanzu. Sa'adda Uzaifat yazo nan a zancensa, sai jikin Abul shaja'a yayi sanyi, bai kara cewa komai ba. Kamar yadda Uzaifat ya tsara haka al'amari ya kasance, wato sai da suka kara kwana uku a wannan wuri, sannan suka ci gaba da tafiya suka durfafi dajin zarsus. A wannan lokaci kuwa Lafirat ta warke sumul, karfin jikinta ya dawo sosai tamkar ma bata taba yin wata lalura ba. Sai da suka yi tafiyar sa'a shida sannan suka iso farkon dajin zarsus. Da zuwansu bakin dajin, sai uwar mayu da ke kan gaba ta daina kada fuka fukanta da karfi ta sauko kasa, kuma ta daga hannuna tana mai yiwa su Uzaifat nuni da su tsaya. Ba tare da gardamar komai ba kuwa suka tsaya cak! Uwar mayu ta dubi gabas da yamma kudu da arewa, sannan ta shauki kamshi da hancinta, kawai sai ta juyo ta dubi su Uzaifat tace, akwai mugayen kunamai anan gabanmu kadan, don haka sai kowa yayi shirin tukararsu. Ina mai gargadinku dacewa, kada ku bi hanyar da kika ga babu sabar macizai akanta a cikin wannan daji, domin itace kadai hanyar da kunamai basa bi saboda a kaidar dajin kunaman da macizan basa faduwa a waje guda. Tunda dai yanzu banjiyo kamshi macizai ba, sai na kunamai, to mu ratse hanyar su mu bi ta macizai shine kadai hanyar da zamu it tsira daga sharrin su. Koda gama fadin haka, sai uwar mayu ta wuce gaba, yayata nabiye da ita sannan Lafirat ta bisu sai Abul shaja'a, Uzaifat ne a karshen baya. Dafara tafiyar tasu a cikin dajin na zarsus sukayi kicibus da wata katuwar sabar maciji wadda za'a iya nannade gaba dayansu a cikinta saboda girmanta. Koda ganin wannan sabar maciji, sai dukkaninsu suka cika da mamaki. Abul shaja'a ya dubi Lafirat yace, yake wannan yar sarki shu kuwa wannan maciji mai wannan saba wane irin girma ne da shi haka? Lafirat tayi murmushi tace ai girmansa ya wuce misali, da kamantawa sai abinda idanun ya gani. Na taba ji mahaifina yace, a duniya kaf irin wannan macijin guda uku ne rak, yanzu daya na can karshen bangon duniya, bangaren kudu. Dayan kuma a bayan birnin sin yake a cikin wani teku, baya fitowa saman tekun sai bayan kowace shekara goma, don ya shaki numfashi kawai. Ina jiye mana yin arba da wannan maciji domin karfin damtsen dana sihir ba zai kwacemu ba. Gama fadin hakan ke dawuya sai suka fara jiyo wani irin numfashi mai karfin gaske tamkar an yanka shanu dubu a lokaci guda suna kakarin mutuwa. Sannan suka rinka jiyo wani irin huci yana buso musu. Al'amarin da ya matukar razana su kenan, uwar mayu ce tafara juyawa da baya kamat zata ruga da gudu suma yayanta sai suka a da baya, haka ma Lafirat da Abul shaja'a. Uzaifat ne kawai bai firgita ba, kuma ko gezau Baiyi ba. Kawai sai ya zare takobinsa ya ci gaba da tafiya ya durfafi inda wannan huci ke fitowa. Nan dazuka rasa wanda zai bi bayan Uzaifat, duk sai suka tsaya sukayi cirko cirko suna kallon juna. Daga can sai Lafirat tayi kundunbala ta bi bayan Uzaifat. Koda ganin haka, sai Abul shaja'a ya bita, sannan ne uwar mayu da yayanta suka biyosu. Sai dai Uzaifat yayi yar doguwar tafiya sannan ya tsaya yayi gurus bisa abin mamakin da ya gani a gabanku. Ba wani abu ya gani ba face wani narkeken maciji wanda tsawon sa da kaurinsa ya wuce kamu dari biyu. A wannan lokaci macijin ya hadiye wata narkekiyar kunama wacce girmanta yakai na babbar giwa. Kawai macijin yayi lamo a kasa ko kyakkyawan motsi baya iya wa saboda hadiyar da ya fara. Uzaifat ya tsaya cak! Yana kallon ikon Allah. Jim kadan sai ga Lafirat ta iso wajen, sannan Abul shaja'a da su uwar mayu. Da isowar uwar mayu ta ga saura kadan macijin ya gama hadiye kunamar, sai ta dakawa su Uzaifat tsawa tace, maza ku ruga da gudu mu bar wajen nan kafin ya gama hadiye wannan kunamar dan kanmu zai juyo ya yi loma daya damu. Dajin haka sai Lafirat, Abul shaja'a da yayan uwar mayu suka falfala da gudun kara gaba. Shikuwa Uzaifat sai ya daka tsalle ya hau kan jelar macijin ya fara tafiya a kansa tamkar ya hau kan katon tsauni. Sannan ya waigo ya dubi uwar mayu yace, idan ba zaki iya tsaya wa ba, ki kallo abinda zai faru ba kuma kiyi takanki. Koda jin haka sai uwar mayu ta dan ruga gaba kadan ta buya a cikin wata yar duhuwa tana leken a abinda zai faru. Uzaifat ya ci gaba da tafiya akan macijin har ya iso tsakiyar kansa. A dai dai wannan lokacine macijin ya gama hadiye wannan katuwar kunama, kuma a sannane Uzaifat ya daga takobinsa ya cakata a tsakiyar kan macijin. Kawai sai yaji kamar akan dutse ya cakata takobin, take ta karye gida biyu, macijin ya yunkura ya girgiza kansa yayi cilli da uzaifat tabayansa can gefe daya tamkar yafado daga kan dutse mai tsawon gaske. Kafin Uzaifat ya yunkura ya mike tsaye tuni macijin ya juyo da kansa baya ya kawo masa cafka baki bude zai hadiye shi. Cikin matukar zafin nama Uzaifat ya goce yana mai mirgina jikinsa gefe guda macijin ya hadiyi iska. Uzaifat ya mike tsaye da sauri ya falfala da gudu, aikuwa sai macijin ya sako kansa ya biyoshi suka kasa tsere. Babu abinda zai mamaki face tazarar da ke tsakanin kan macijin da Uzaifat bai wuce kamu uku ba, kuma a sannan fa karshen jelar macijin a tsaye take a waje daya bai ma fara gudu ba. Uwar mayu dake labe a cikin duhuwa koda ta ga an kasa mugun tsere tsakanin macijin da Uzaifat sai ta firgita ainun tayi fitar burgu daga cikin maboyarta ta falfala da matsanancin gudu har ta zo ta wuce macijin da Uzaifat ta basu tazara mai yawa, saboda kasan cewar ita a sama taje gudun tana kada fuka fukanta. Tsananin tsoro ne ya Janata ta juyo ta sure Uzaifat tayi Sam da shi don ta tserar da rayuwarsa domin gani take cewa, idan hartayi kuskuren haka tamkar ta sayi ajalinta ne, saboda sanin cewa macijin yana da zafin nama na gaban kwatance. Bayam macijin ya kure iya tsawon sa yana bin Uzaifat da gudu bai cafkoshi ba, sai ya fara gudu a kasa tamkar doki ne ke sukuwa, a sannane fa tazararsa da Uzaifat ta zamo bata wuce kamu daya ba. A duk sa'adda Uzaifat ya waigo baya sai yaga macijin na bude baki daf da shi zai hadiye shi duk da cewa yana falfala azababben gudu. Al'amarin daya mutukar baiwa Uzaifat mamaki kenan domin shi as saninsa a gaba daya birnin Darul husuf ma babu maguji tamkarsa. Duk sa'adda akayi tseren gudu shi yake zuwa na daya, kuma yana gudu ba tare da ya gaji ba. Kai saboda tsananin baiwar gudun Uzaifat ma ko da dawakai ya kasa tsere basu tazara yake, amma sai gashi yanzu wannan maciji yana gudun ban alajabi fiye da saninsa. Jim kadan sai Uzaifat yaji macijin ya fara dungurar bayansa, bai aune ba ma sai yaji ya ce rabin rifarsabta bayabda kaifin hakoramsa al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar da cewa, gudu fa ba zai cecishi ba, don haka sai ya fara zulliya yana kauce kauce yana ratsawa ta cikin duwatsu da bishiyoyi ya shia nan ya can ya jurda nan, shi kuwa macijin yaci gaba da binsa a cikin naci. Sai da suka shafe sa'a guda suna wannan tseren, amma macijin ya kasa kama Uzaifat kuma sakamakon shige da fice da suke yi ta cikin duwatsu macijin ya gabgabje kansa har ya sami raunika, al'amarin da ya kara fusata macijin kenan ya kara kaimi dadagewa don tabbatar da cewa ya lamo Uzaifat, amma sai abu ya faskara. Haka dai suka ci gaba da wannan tsere har tsawon sa'a shida a wannan lokacine duk su biyun suka jigata ainun, sai ga shi macijin baya iya gudu da karfi, shima Uzaifat haka. Dukkaninsu sai fama haki suke amma saboda naci sunki su daina gudun. Kwatsam sai suka iso bakin wani matin kogi. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin uzaifat Uzaifat kenan, domin ya san cewa muddin suka shiga cikin wannan koni sai macijin ya hallaka shi, domin ba zai iya gudu ba acikin ruwa. Yayinda macijin yaga sun iso bakin wannan kogi, sai ya dai na gudun yaci gaba sa bin Uzaifat a hankli domin yasan cewa anzo inda zai sami nasara. Babu damar Uzaifat ya juyo da baya kuma babu damar ya shiga cikin kogin don bazai kubuta ba. Cikin karayar zuciya Uzaifat ya tsaya a gaban kogin ya juyo ya fuskanci macijin ba tare da nufin yakarsa ba, don yasan cewa babu abinda zai iya. Macijin yaci gaba da tunkaro Uzaifat maimakon macijin ya wangame bakinsa ya hadiye Uzaifat, sai ya cillo jelarsa ta kanannade kafafun Uzaifat ya daga shi sama ya dinga makashi a cikin wannan ruwan kogi. Sai Uzaifat ya nutse can kasan kogin sannan macijin ya dagoshi sama ya sake makashi ciki. Nan da Uzaifat ya fara fita daga cikin haiyacinsa, ya fara jiyo kamshi mutuwa muraran. Al'amarin su lafirat kuwa, lokacinda suka yi ta gudu a cikin daji har suka yi nisasosai da inda suka Bari wannan maciji, sai Lafirat ta tsaya cak! Ta daina gudun ta juyo ta kallo baya, amma ko duriyar Uzaifat bata ji ba, sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta fara shawarar ta koma sa baya. Ganin Lafirat ta tsayane yasa Abul shaja'a da uwarmayu da yayanta ma suka tsaya. Abul shaja'a ya dawo da wajen Lafirat ya dubeta yace, saboda me kika tsaya anan ki zo muci gaba da gudu domin macinjinan bazai daina binmj ba, face muje karshen wannan daji. Koda jin wannan batu, sai Lafirat ta harzuka ta dubi Abul shaja'a cikin fushi tace, amma ka bani mamaki, yanzu kana nufin kenan mu gudumu bar Uzaifat a can baya bamu san meke faruwa da shiba? Ka tuna fa cewa Uzaifat dan uwanka ne musulmi , ni kuma ba musulma bace, amma na ga bai kamata mu gudu mu barshi ba cikin balai. Ni kam dolene na koma na kai masa dauki koda zan rasa rayuwata, tunda shi ma yaceci rayuwata a baya, har sau biyu. Idan ma gujeshi a wannan lokacin nayi butulci. Koda gama fadin hakan, sai Lafirat tafalfala da gudu izuwa baya. Abul shaja'a da su uwar mayu suka tsaya suka yi tsuru tsuru suna kallon junansu suka rasa abinda zauyi tsakanin ci gaba dagudu da komawa baya. Lafirat taji gaba da gudu iya karfinta, harta iso bakin wannan katon kogi. Tun daga nesa ta hango wannan katuwar macijiya tana ta tsoma uwa a cikin koginnan har ya suma bata sani ba. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Lafirat kenan, kuma ya cire dukkan tsoro daga zuciyarta, don haka sai ta daka tsalle ta dane jikinsa ta ci gaba da hawa samansa tamkar kadanfare na hawa bango, har ta iso inda kansa yake bai saniba. Kawai sai ta zare wani karamin gatari da ke cinyarta ta saribidon macijin. Taje ruwan idon ya fashe jini ya kama kwararowa kasa kamar idaniyar ruwa ra balle. Macijin yayi wani irin ruri bai san sa'adda ya saki Uzaifat ba ya kama matagungun a kasa. Uzaifat ya nutse izuwa kasan koginnan. Koda ganin haka sai Lafirat ta daka tsalle ta fada cikin kogin ta yi nutso kasa tana laluben Uzaifat. Cikin sa'a kuwa sai ta ji ta rukoshi. Lafirat tadago saman kogin ruke da Uzaifat tamkar taruko gawa tana ninkaya. Har izuwa wannan lokaci wannan maciji na ta birgima da matagungun a gefen kogin, kuma ya haddasa gagarumar kura sakamakon birgimar da yakeyi akan rairayi. Da kyar Lafirat ta fito daga cikin kogin ruke da Uzaifat ta kaishi can gefe daya bakin gaba. Cikin dimaucewa ta shiga danna kirjin Uzaifat sai ga ruwa na fitowa tacikin bakinsa da hancinsa, amma ko motsawa baiyiba, Sam Sam babu alamar numfashi ajikinsa. Koda ganin haka sai Lafirat ta fada kan Uzaifat tafashe da matsanancin kuka cikin tsananin bakin ciki. Tsawon yan dakiku tana faman kuka, kawai sai taji Uzaifat ya kama kafadarta. Saboda tsabar farin ciki sai ta tasheshi zaune ta rungumeshi kuma ta bushe dadariya, tana mai kankameshi a kirjinta. A dai dai wannan lokacine Uzaifat ya hango wannan katon maciji ya sandare jikinsa gaba daya ya zama gawa. Uzaifat ya janye jikinsa daga cikin na Lafirat suka fuskanci juna, duk su biyun suna murmushi, yace menene dalilin da ya sa kike zubar da hawayen ki saboda tsammanin cewa na mutu? Yayinda lafirat taji tambaya sai ta ce dalilin da yasa kaji ka damu da tafiyata da rayuwata sa'adda na kamu da ciwo shine ya sani zubar da hawaye da kuka a lokacin da nake zaton ka mutu. Koda jin haka sai shima Uzaifat ya bushe da dariya ya rungume Lafirat yace, tabbas kinyi gaskiya, kuma yanzu ne na tabbatar da cewa akwai so da kauna tsakanina da ke. Gama fadin hakan ke da wuya sai ga uwar mayu da yayanta da kuma Abul shaja'a sun rugo wajen. Cikin sauri gami da alamun jin kunya Uzaifat ya cire jikinsa da ga cikin na Lafirat ya mike tsaye domin a sannane ya dawo cikin haiyacinsa ya tuna cewa haramun ne a gareshi ya rungumi Lafirat a matsayinta na mace, wadda ba muharramarsaba. Uzaifat yace a ransa tabbas, Hakika sharrin soyayya yafi ga haka kuma tabbas idan mace da namiji suka kasaita shedanne na ukunsu. Alhamdulillahi nan zan dakata sai kuma gobe Insha Allahu zaku jini da cigaba nagode. [17/02, 9:31 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI Littafi na BIYU Matubuci Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing Umar Farouq Zango Cikin tsananin mamaki su Abul shaja'a suka karaso gaban su Uzaifat suka tsaya suna kallon gawar wannan narkeke maciji. Uwar mayu ta dubi Uzaifat tace, tayaya ka sami nasara kashe wannan macijin? Koda ji wannan tambaya, sai Uzaifat ya nuna Lafirat da hannusa yace, ba nine na kashe wannan maciji ba, ga wadda takasheshi, kuma ina badon ita ba da tuni nima wannna macinjn ya hallakani. Itace ta kawo min agajjn gaggawa. Dan jin haka, sai Abul shaja'a, uwar mayu da yayanta suka sake cika da mamaki, suka kura mata idanu. uzaifat yayi murmushi yace, mamakin me kukeyi? Ai dama dujk tafimu jarumataka, kawai dai don ta sami rauni ne a jikinta saboda haka daga yanzu sau u daina tunanin cewa bata da amfani a cikin wannan tafiya tunda gashi tayi abinda ya gagareni. Abul shaja'a ya dubi Uzaifat yayi murmushi yace, kaima ba gagararka yayiba, shaafa kayi baka nemi taimakon ubangijinka ba, wanda ya halicceka, kuma ya halicci wannan macinj da Lafirat ta kashe. Koda jin wannan batu, sai Uzaifat yayi murmushi yace, amma fa kaima ka shaafa da neman taimakon Allah domin bai kamata ka gudu kabarni ba a lokacin da nake artabu da wannan maciji. Abul shaja'a ya sunkui da kansa kasa cikin alamun kunya. Yace kayi gaskiya ya shugabana. Ina fatan zaka yafeni domin na yi babban laifi. Nan dai suka zauna gaba dayansu a bakin wannan kofi suka huta, a nan suka kwana sai da gari ya waye sannan suka muke suka ci gaba da tafiya suka durfafi dajin huzurhas inda tsafaffen maridi ke zaune tare da matarsa da yayansa guda biyu. Tafiya sannu sannu kwana nesa, sai da suka cika kwanaki goma sha bakwai daga ranar da suka fara tafiya sannan suka iso dajin huzurul has. Da isowar farkon dajin, sai uwar mayu ta daga hannuna tana mai nuni da cewa a tsaya dama itace akan gaba. Ba tare da gardamar komai ba kuwa kowa yabi umarnin ta aka tsaitsaya. Uwar mayu ta kalli gabasa da yamma kudu da arewa ta shaki numfashi, so tayi ajiyar zuciya, kuma tayi shiru ba tare da tace komai ba. Koda ganin haka, sai Uzaifat ya dubeta yace, ya ke yar uwata yaya kika yi shiru baki ce damu komaiba? Uwar mayu ta sake yin ajiyar zuciya sannan tace, ya kai wannan dan sarki kayi sank cewa, wannan daji da zamu shiga shine mafi hadari daga cikin dazuzzukan uku daomjn a cikinsa ne tsafaffen maridi yake, wanda ake kira da suna zurkas. Maridi zurkas ya kasance narkeken katon da bazai kwatantu ba da baki, sannan yanada masifaffen karfi na Allah ya isa domin komai kwarin dutse idan ya nausheshi da hannu sai ya dagwargwaje. Kaifin ko tsinin basa tasiri a jikinsa. Zurkas na da karfin sihirin da idan ya bace babu bokan da zai iya ganinsa. Komai yawan rundunar mayaka shi kadai yana iya tarwatsa su. Shi ma shekararsa hamsin kenan a cikin wannan daji na huzurul has, tunda ya baiyana ya hana shiga da fita. Duk mahalukin da tsautsayi ya kawoshi walau mutum ko aljan ya zama gawa kenan. Lokacin da uwar mayu ta zo nan a zancenta, sai Uzaifat yayi murmushi yace, ya ke yar uwata ki yi sani cewa, babu wani abintsoro da zai figitani a cikin wannan tafiya, domin koyaushe ina sa ran cewa ubangiji zai fitar da ni daga cikin kowane hali. Shin ki manta ne cewa baya ma kin figitamu da labarin dazuzzukan da muka ratsa kafin mu shigesu, amma sai ga shi mun shige ta cikinsu, kuma sha gumurzu tamkar na zamu Kai labari ba. Uwar mayu tace, tabbas zancenka dutsena, kuma ina alfahari da irin wadannan makamai nan, domin suna karamin kwarin gwiwa gami da Karin tsoron ubangijin musulunci da dadin imani a gareshi. Gama fadin hakan ke da wuya, sai uwar mayu ta wuce gaba, sannna yayanta suka bita baya. Abul shaja'a ne ke biye musu, sannan Uzaifat da Lafirat suka jera tare. Abu kamar wasa sai da suka shafe sa'a tara suna tafiya a cikin dajin huzurul has basu hadu da wani mugun abu ba, face kanan kwari da daidaikun tsuntsaye masu shawagi a sararin samaniya. Al'amarin da ya daurewa su uwar mayu kai kenan suka cika da mamaki, domin ta taba ni a bakin sarki shaaran cewa duk halkitar da ta shiga cikin dajin huzurul has ba zata yi sa'a ba a raye, amma ga shi su yanzu sunyi sa'a tara cif abin da ya samesu. A dai dai wannan lokaci ne rana ke daf sa faduwa, kuna dukkaninsu akwai alamun gajiya a tare sa su. Koda Uzaifat ya lura da hakan sai banga can gabansu ya hango wani wuri mai cike da bishiyoyin masu yawan rassa sannan ga ciyayi masu taushi a wajen tamkar kilishi aka shimfida. Cikin farin ciki Uzaifat ya bada umarni a karasa wannan wuri a yada zango. A guje suka karasa wajen gaba dayansu. Da zuwa sai Abul shaja'a ya kwance a kansa. Ita ma Lafirat ta fiddo wata babbar fatar damisa ta shimfida, ta dubi Uzaifat cikin murmushi mai nuna tsantsar kauna ta ce, zo ka shingida anan ya gwarzona, ina son mu yi yar hira. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Uzaifat yaje ya zauna akan farar damisar itama Lafirat sai ta zauna daf dashi a lokacin da uwar mayu da yayanta suka baje akan ciyawar mai taushi a gefe guda suna hutawa. Lafirat ta dubi Uzaifat tace, ba ni labarin yadda ake bikin aure a aladarku da addininku. Koda jin wannan tambaya sai Uzaifat ya kyalkyale da dariya, yace ke kuwa saboda me kikayi mini wannan tambaya? Lafirat tace, saboda ina son na sami ilimi ne akan al'amarin kafin ya tabbata a kaina, domin a halin yanzu shine burina na biyu a duniya. Fatana na farko shine, na kashe ubana da yar uwata sazirat da hannuna bisa mugun aikin da suka aikata, kuma na dakatar da dukkan barna da suke shukawa a doron kasa. Fatana na biyu shine, na ha na karbi addinina, kuma na zamo abokiyar rayuwarka Koda lafirat tazo nan a zancenta sai Uzaifat ya tari numfashinta yace, Haba ai sai Yanzu nagane dalilin da yasa kika ki karbar addinina da wuri. Ina tabbatar miki da cewa, zamu iya samun nasarar hallaka mahaifinki da yar uwar ki ba tare da kinyi amfani da karfin sihiri ba. Ki tuna cewa, duk sihirin da kike takama sa shi mahaifinki ya fiki, to taya kike tsammanin cewa zaki iya hallakashi? Lokacin da Lafirat taji wannan batu sai zuciyarta ta karaya, tayi shiru ba tace komai ba, tsawon yan dakiku daga can kuma sai ta dago kai ta dubi Uzaifat tace, mahaifina ya taba gaya mini cewa hr abada babu abin da zai iya hallakashi face sihiri. Nayi imani da wannan furuci na mahaifina, shi yasa na sa a raina cewa bazan iya hallakashi ba face da karfin sihiri. Uzaifat yayi dariya yace, amma dai kin yarda cewa, karfin ubangijin musulunci ya tafi kowane karfi ko? Lafirat tace kwarai kuwa domin na ga zahiri da idanuna, ni ganauce ba jiyauba. To tunda haka ne ina mai baki shawara da ki karbi addinin musulunci tun gabanin dama ta wuceki, domin rayuwa bata da tabbas, in mune yau ba mune gobe ba. Ko yanzu idan kika mutu kin mutu ne a matsayin mafita, kuna Allah bazaiyi miki uzuri ba. Lafirat ta gyada kai tace, tabbas maganarka gaskiya ce, kuma na karbi wannan shawara taka, ina fatan nayi amfani da ita cikin gaggawa. Koda gama fadin hak, sai Lafirat ta bude salkarta ta kama shan ruwa. Gama shan ruwan ke fa wuya ta dubi Uzaifat, sai ta ga Ashe har ya fara bacci. Kawai sai tayi dariya ta mike tsaye tsam ta koma can gefe daya tayi wat shimfidar dabam ita ma ta kwanta. Kafin cikar sa'a daya gaba dayansu sun bige da bacci, saboda gajiyar da suka sha a baya. Kash! Rashin sani yafi dare duhu, hakika wannan bacci da su Uzaifat sukayi a wannan wuri shi ne babban kuskurensu. Shi dai wannan wuri da suka kwanta Ashe wajen shakatawar maridi zurkas ne da iyalansa, kuma kullum sai sun zo wajen su zauna sun huta bayan sun yini suna farauta a adaji. Har magriba ta kusa yi dayansu daga cikinsu Uzaifat bai farka ba. Kwatsam sai ga maridi zurkas tare da matarsa maziba da kuma yayansa hiram da hirama, sun durfafo wannan wuri. Tun daga nesa maziba ta kyallara ido ta hango su Uzaifat a kwance sai ta kama hannun Zurkas da hannun su hirama ta tsai dasu suka tsaya cak! Sannan tace, yau fa mun tsinci tsuntsu daga sama gasasshe. Cikin mamaki da fushi zurkas ya dubeta ya ce, wannan kuma wace irin maganar banza kikayi haka, ina gasasshen tsuntsun yake? Maziba tace, dubi can wajen hutawarmu da kyau ka gani. Wasu biladama ne kwance suna shara bacci abinsu. Zurkas yace, hana maziba shin kin fara makancewa ne? Yaya za'ayi biladama su shigo wannan daji alhalin sama da shekaru talatin suka daina ratsawa ta nan, ba ma biladama ba, hatta aljanu ma sun kauracewa dazuzzukan nan guda uku. Koda jin wannan batu sai ran maziba ya baci tace, ai idan ni ban makance ba, to kuwa tabbas kai ka makance. Ka tambaya yayanka ka ji ai su yara ne masu kuruciya suna da lafiyar idanu. Kafin zurkas ya bude baki tuni Hiram yace, ya kai abbana hakika maganar Umma gaskiya ne, akwai biladama a kwance a can wajen hutawarmu, har ma da wadansu aljanu kimanin su dubi daya da doriya. Biladama kuwa basu wuce su uku ba. Tabbas yau zamu sha romo mu more, wai yaushe rabonmu da cin naman biladama da na aljanu? Ai munfi shekara talatin. Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube zurkas ya dubi maziba, Hiram da hirama yace, ku tsaya anan kada ku biyoni, sai bayan na gama kamasu. Koda gama fadin haka, sai zurkas yayi girgiza ya bace bat. Bai baiyana a ko ina ba, sai gaban su Uzaifat suna ta shara barcinsu. Nan take zurkas yayi nuni sa hannunsa a garesu sai ga su a cikin wani katon keji na bakin karfe. Zurkas ya ci gaba da kallon su Uzaifat daya bayan daya. Koda ya zo kan Uzaifat, Abul shaja'a da uwar mayu sai ya gane cewa, sun kasance maabota addinin da bai sani ba, ita kuwa Lafirat saibya gane cewa matsafiyace. Nan take ya nisa wata iska daga cikin bakinsa sai barcin Uzaifat, Abul shaja'a da na su uwar mayu ya kara nauyi, ita kuwa Lafirat sai ta farka. Koda ta gansu a cikin keji a kulle, sai ta mike zumbur a firgice a Sanna ne tayi arba da maridi zurkas. Nan take ta sulale kasa sumammiya saboda tsananin da tayi domin a rayuwarta bata taba ganin halitta mai matukar kwarjini ban tsoro da muni kamarsa ba. yayinda zurkas yaga Lafirat ta suma sai ya bushe da dariyar mugunta, wadda aminta ya haifar da girgizar bishiyoyin dajin gaba daya. Nan take ya dauki kejin da yatsa daya ya juya don ya tafi, sai ga maziba da su Hiram sun rugo da gudu izuwa gareshi suna tsalle da murna, amma ita Hirama ba ta farin ciki sosai, domin a rayuwarta babu abinda taje tausayi, sama d biladama. Ko a shekarun baya idan an kama biladama an bata, Sam bata cin namansu, amma tana cin na aljanu. Lokacin da zurkas ya lura da fuskata Hirama yaga bata farin ciki da wannan garabasa da aka samu, sai ya dubeta ya data mata tsawa yace, ya ke hirama ina mai yi miki gargadi da kada ki kuskura kice zaki kubutarda daya daga cikin wadannan biladama da muka kamo. Ki tuna irin muguwar azabar da nayi miki a shekaru baya, Sa'adda kika kubutar da wadansu biladama daga cikin kejina. Ki sani cewa, wannan karon idan kika sake aikata hakan ba azaba zan miki ba, zan murder miki wuya ne ki mutu, sannan na dafaki, na cinye namankk domin na huce takaici. Kinji abinda na fada ko bakijiba? Jikin hirama na karkarwa tace, na ji baya ninka ya abbana. Nan take suka dunguma su hudun suka nufi gida. Sai da sukayi tafiyar saa hudu, sannan suka iso gidan nasu, wanda ke can sama bisa wani dogon tsauni da ake wa lakabi da hulasul maut. Ba komai ne yasa ake kiran wannan tsauni da suna hulasul maut ba, face tsananin tsawon sa da fadinsa, domin tua ninka tsaunin dajin mashaarul kais sau uku. Wani abin alajabi da ya faru shine, a cikin rabin saa maridi zurkas da iyalansa suka gama hawa kan tsaunin suka shige cikin wani katon gida, wanda aka ginashi da zallan itatuwa. Da shigarsu cikin gidan, sai zurkas ya ajiye wannan keji a kasa gefe daya da yake duhu ya soma sai maziba ta kunna fitilun da ke gidan ya haska ke gaba daya. Su hudun suka zo suka zauna bisa wadansu kujeru domin su huta, dama tun kafin su tafi maziba ta tanadi abinci da ruwan shansu. Man take suka ci suka sha sannan aka shiga tattaunawa akan yadda za a cinye wadannan bakin biladama da aljanu da aka tsinto tamkar dami a kala. Zurkas ne ya fara magana, ya dubi maziba yace, yake matata Yanzu yaya kike zamu farada wannan naman da muka sami. Shin biladaman zamu farka cinyewa, ko kuwa aljanu? Kinga dai aljanu ne masu yawa zamu iya yin kwana uku muna cinsu, idan muka rabasu gida uku, su kuwa biladama su ukune rak, ko ni kadai aka bar min su kwadayi zasu tayar min. Kafin maziba ta budi baki ta bada amsa, sai Hirama ta tari numfashinta tace, ai kuwa a fara yi mana dabge da wadannan aljanu kowa yaci ya more, kusan munci nama sosai, inyaso bayan kwana ukun ku dafa biladama kuci abinkj ku uku ku raba dai dai tunda dai ni bana ci. Koda jin haka, sai zurkas yace, gafara can shashasha, ya za ai mu fara cin nama mara dadi, sannan muzo muci mai dadin da ga baya? Maziba tace, A'a maigida yarinya fa tana da gaskiya. Ai idan muka fara cin mai dadin, to daga baya muna fara cin mara dadin sai muji ya gunduremu. Shawararta ya kamata mu dauka. Zurkas yayi tsaki cikin alamun rashin jin dadi yace, to ai shikenan tunda kema kin yarda da hakan. Duk wannan hira da ake tsakanin zurkas da iyalansa ashe Lafirat tana ji, domin tuni ta dade da farfadowa daga dogon suman da tayi. Koda taji shirin da akayi a Kansu, sai hankalinta ya dugunzuma ta fara kokarin amfani da karfin sihirinta domin ta bude kejin su fita, amma sai sihirin yaki yayi tasiri. Lafirat taci gaba da kokarin tashinsu Uzaifat daga baccin amma sai ta ga sun ki motsawa tamkar sun zama gawa. Al'amarin da ya mutukar kara dugunzuma hankalinta kenan, ta tabbatar da cewa suna cikin mugun yanayi. A wannan rana dai har dare ya raba sosai Lafirat batayi bacci ba saboda tsananin tsoro, fargaba da tunani, kuma har a sannan babu wanda ya farka daga bacci daga cikjn su Uzaifat basu san ma halin da ake cikiba. Ita kadai ce a cikin tashin hankali. A wannan lokaci ne nadama tazowa Lafirat, tace Kash! Ina ma na karbi addinin musulunci tuntuni, da yanzu na nemi taimako a wajen ubangijin musulunci ya tserar da mu daga cikin wannan mugun hali. Kawai sai wata zuciyar tace da ita, to ai karbar addinin musulunci ba wani abu bane face ki biya Kalmar shahada. Har Lafirat ta yumkura zata budi baki ta karanta Kalmar shahada, sai taji wata irin iska mai sanyi ta bugeta takaita kas. Nan take ita ma ta kama barcin dole. Ashe maridi zurkas ne ya buso mata wannan iska kawai sai ya dubeta ya tuntsire da dariyar mugunta yace, wane ke ki ce zaki katse min shirin? Ai tabbas sai mun cinye ku da dai dai kamar yadda muka tsara. Kashe gari kuwa da sassafe, maridi zurkas ya bude kejin ya debo yayan uwar mayu guda dari biyar ya daddatsa su kamar yadda ake gididdiba nama a mahauta, sannan ya zuba su duka a cikin wat katuwar tukunya K hau dafasu. Sai da aka shafe sa'a ukucur ana dafa nama ya zamana cewa, yayi luguf luguf sannan maziba ta raba nama izuwa kashi hudu kowa aka bashi nasa rabon. Koda aka bawa hirama nata rabin, sai ta karba ta mike tsaye ta koma can cikin dakin ta zauna ta faraci. Tana cikin cin abincin sau idanunta suka ciko da kwalla ta farazubar da hawaye. Ba komai ne yasa hirama zubar da hawaye ba, face tsananin tausayi da takaici. Nan take zuciyar hirama ta kama tafarfasa kamar zata kone , kawai sai ta aiyana a ranta cewa, komai rintsi da tsanani, kuma koda zata rasa rayuwarta sai taceci wadannan halittu aje cikin wannan keji a daren yau, lallai bazata bari a sake cinye daya daga cikinsu ba. Alhamdulillahi nan muka kawo karshen wanann littafi na DAKARUN MUSULUNCI littafi na biyu Insha allahu ba da dadewa na zaku jimu da ci ga a cikin littafi na uku. Ina godiya ga duk wani leadership na wannan gida da kuma sauran members bisa bani kwarin gwiwa tare da fatan alkhairi da nake samu ta ko ina wasu suna kirana suna min fatan alkhairi wasu kuma ta DM dina wasu kuma ta hanyar yin liking da sauran hanyoyi, gaskiya ina jin dadin haka, kuma nima ina muku fatan alkhairi. Zan cigaba da yi dominku kuma saboda ku, saboda idan babu ku babu ni, tabbas kuna bani kwarin gwiwa sosai kuma saboda jin dadin da kuke da nishadantuwar da kike nima sanadin Wannna ina shiga cikin farin ciki, abinda nake nufi anan shine inayin farin ciki da farin cikinku kuma ina jin dadi da jin dadinku. Ina muku fatan alkhairi Allah ya bar kauna ya bar zumunci. Na gode naku a kullum da ko da yaushe UMAR FAROUQ ZANGO.