[25/01, 1:56 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI littafi na daya 1A Marubuci:- ABDUL AZIZI SANI MADAKIN GINI Typing:- UMAR FAROUQ ZANGO Marubucin ya fara da... A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude, anyi wan shararren sarkin musulunci wanda ya shekara dari da sittin akan karagar mulki, ana kiransa da suna Uwaisul Karni. Har tsufa ya riski sarki uwaisul karni matansa biyu kacal, kuma 'ya'yansa biyu dukkansu mazane kuma sa'annin juna. Ana kiran wadannan 'yaya nasa da UKASHAT da UZAIFAT. Mahaifiyar Ukashat itace uwar gida. Ukashat da Uzaifat sun taso da tarin ilimi, hankali da sanin yakamata, sannan kuma kowannesu ya kasance sadauki kuma Barde dodon maza a filin yaki, wanda har ta kai cewa an kasa banbance wanda yafi wani karfi da jarumta a tsakanin su. Ya yin da tsufa ya riski sarki uwaisul Karni sai matansa shulaifa da muzaira suka fara kisha akan kowacce tafi son danta ya gaji sarki. A dalilin haka ne suka dukufa wajen ziyartar malamai domin bukatarsu ta biya. * * * * * * A can nesa da birnin Darul husuf, wato birnin sarki uwaisul karni, akwai wata babbar kasa ta kafirai wacce ta gagari uwaisul karni, domin sau tara yana yaki da su amma sai dai ayi KARE JINI BIRI JINI. Sunan kasar SHUMBUL, kuma sunan sarkin su SHARAN IBINI NUKAIB. Lokacin da sarki uwaisul karni ya fahimci cewa ukashat da uzaifat sun tada hankalin su akan su gajeshi saboda kowanne ya dauki zugar mahaifiyarsa sai ya kirasu yace dasu. "Ya ku 'ya'yana kiyi sani cewa bani da wani buri wanda yafi naga naci birnin shumbul da yaki kafin cikar ajalina, bisa wannan dalili ne na umarceku da kije kowanneku ya shirya DAKARUN MUSULUNCI nasa mataimakansa wadanda basa yin aiki da alfasha basa shan giya, basa yin zina, wadanda basu taba sabon Allah ubangijin Muslinci ba, kowannenku ya taro nasa mataimakan, duk wanda ya sami nasarar wannan yaki akan kasar shumbul daga cikinku shi zai gajeni". Koda jin wannan batu sai uzaifat da ukashat sukayi murna, suka yi farin ciki da jin wannan batu. Domin lokacin yayi da zasu nunawa duniya cewa musulunci ba kanwar lasa bane. Anan suka yi alkawarin lallai sai sun cikawa mahaifinsu burinsa. Nana take kowannensu ya fara shirye shirye, suna masu shirya dakarun yaki kuma DAKARUN MUSULUNCI. Dama kuma sarki uwaisul karni ya basu izinin kowannesu ya tara Dakaru dudu dari uku kadai. Ukashat ne ya fara hada tasa rundunar inda yayi Saudi ya zabe dukkan in manyan Dakarun kasar wadanda ake takama dasu a fagen fama, wato wadanda suka fi jarumta, juriya da jajircewa. Lokacin da ukashat ke zabo wadannan zaratan dakaru bai yi la'akari da bayanin mahaifinsu ba na cewa lallai su zabo daga masu kwatanta gaskiya da tsoron Allah. In dai kawai ya fahimci cewa mutum Barde ne kawai sai ya zabeshi. A lokacin da uzaifat yazo zai zabi nasa dakarun sai ya ga Ashe ukashat yayi masa shigar sauri, ya kwashe manyan baraden kasar. Hatta sarkin yakin kasar kuwa salhaddeen ayubi. Al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan, har yaji gwuiwarsa tayi sanyi, amma duk dahaka bai fasa zabo nasa dakarun ba wadanda basu kasance zakwakurai ba, amma kuma suna da karfin imani gami da tsoron Allah. Ya fitar da shugaba a cikinsu wanda babu kamarsa a jarumta ana kiransa da suna Abuk shaja'a. Bayan uzaifat ya gama hada wadannan runduna wadda Abul shaja'a ke jagoranta sai suka fara fita bayan gari kullum suna bawa Kansu horon yaki domin su tabbatar da cewa anyi kyakkyawan shiri kafin zuwan ranar da zasu fara fita sutari abokan gaba. A can bangaren dakarun ukashat kuwa, ko sau daya basu taba tunanin su fita yin horo ba saboda sun yarda da Kansu, sun san cewa ko daga barci suka tashi zasu iya tarar yaki. A ranar da su uzaifat suka cika kwana bakwai suna bawa Kansu horon yakan ne labari ya riski su ukashat. Al'amarin daya basu dariya kenan. Ukashat ya dubi sarkin yaki salahuddeen ayubi cikin murmushi yace, "ya kai dirkar Darul husuf kaji cewa su uzaifat sun dukufa wajen baiwa Kansu horon yaki har tsawon kwana bakwai kenan yau. An ya kuwa ba ma kai musu ziyarar ba zato ba, domin mu auna iyakar kokarinsu da namu. Ka san fa ance dan hakin da ka raina shike tsone maka ido. Kada fa muyi sakaki su bamu mamaki, wato su sami nasarar wannan yaki da za'ayi da mutanen birnin shumbul". Koda jin wannan batu sai sarkin yaki salahuddeen ayubi ya bushe da dariya yace, 'Ranka ya dade in banda abinka yaya gara zatayi da zago? Shin ka manta da yawan mayakan birnin shumbul ne da Kuma yawan zakwakuran dakarunsu ne, ai duk irin horon da su Abul shaja'a zasu samu ba zasu taba samun nasara ba a Kansu. Mu kanmu sai munyi da gaske, munyi tunanin sabbin dabarun da yakamata muyi amfani da su. Ka sani cewa a cikin mayakan birnin shumbul akwai wani gawurtaccen barde daya fara fitowa a yaki a shekara uku baya. Wannan barden shi nafi shakka fiye da kowa, kuma babu yadda za'ayi mu sami nasara akan mutanen shumbul face mun gama da bareden". Ya yin da ukashat yaji wannan batu sai ya jinjina kai yace, "Mene ne sunan barden, kuma ya za'ayi na shaidashi idan muka fita yakinin? Inaso ka barni da shi, ina tabbatar maka da cewa ni zan kashe shi komai karfin jarumtar sa". Dajin wannan batu sai salahuddeen ayubi yai dariya yace, Ya kai yarima ukashat ka sani cewa sau uku ina tarar wannan barde fa muna yin ragas, ban taba samun nasara akansa ba, Shima haka. Tayaya kake tsammanin cewa kai zaka iya da shi?. Ukashat yayi murmushi yace, ina da tabbacin cewa zan iya samun nasara akanka, ka ga kenan idan har zan samu nasara akanka lallai zan sami a kansa. Na fuskanci cewa saboda bamu taba fita yaki ba ni da uzaifat shi yasa ba a san iyakar jarumatarmu ba, sai iya wadda aka ga mun nuna anan gida. Idan kana da shakkar abin da na fada yanzu mu jarraba fidda raini yanzu ni da kai. Sa'adda sarkin yaki salahuddeen ayubi yaji haka, sai ransa ya baci, zuciyar sa ta kama tafarfasa yace a ransa, Yanzu wannan karamin taron ukashat da ya girma a gabana shine yaje gamin cewa zai iya karo dani? Lallai kuwa yau zan nuna masa cewa bakin Rijiya ba wajen wasan yaro bane. Koda gama aiyana hakan aransa sai ya zare takobinsa ya sauko daga kan dokinsa a fusace ya nufi ukashat. Abinda ya daurewa sauran dakarun kai shine, ukashat bai zare tasa takobin ba bare ma ya sauko daga dokinsa, kawai sai ya ci gaba da zamansa yana mai sauraron isowar salahuddeen. Ai kuwa salahuddeen na isowa sai ya kai masa wawan sara a wuya. Cikin mutukar zafin nama ukashat ya sunkuya takobin ta sari iska. Kafin salahuddeen ya sake kai wani saran tuni ukashat yayi tsalle sama daga kan dokinsa tamkar an janyeshi da kugiya kawai sai ya jerawa salahuddeen duka da kafa a kirji sau uku yana a Daman kamar tsuntsu. Duk da cewa salahuddeen murjejen kato ne mai kirar sadaukantaka sai da yayi baya taga taga zai fadi, amma saboda taurin rai da zuciya sai da yadage ya tsaya cak a waje guda. A sannane fa gaba daya dakarun suka kaure da kabbara bisa mamaki ganin jarumtar da ukashat yayi. Shi kansa salahuddeen yayi mamaki, duk da cewa ya sha ganin yadda ukashat da uzaifat ke dafawa maza gumba a hannu a cikin gari, amma da yake suna shakkarsa sai yayi tsammanin cewa ba zasu iya karawa da shi ba. Abinda bai sani ba shine kawai suna girmama shine a matsayin sa na sarkin yaji kuma basa san su kunya tashi. Ukashat ya diro kasa a bayan salahuddeen ya zare tasa takobin suka fara zagaya juna ana kallon kallo tamkar zaki da zaki zasu fafata. Kawai sai suka kacame da azababben yaji suna masu kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama, juriya da bajinta masu jikin karfe saboda sauri. Nan fa dakaru suka zuba ido suna kallon ikon Allah suna alajabi, domin a tarihin sadaukantakar salahuddeen ba a taba samun mutumin da ya fafata da shi ba tsawon dakika Dari da tamanin ba tare da ya kishi kasa ba, sai wannan bakon barde na birnin shambul, amma yanzu gashi ukashat na neman gagararsa. Abu dai kamar wasa sai gashi an sake shafe rabin sa'a ana fafatawa amma duk a tsawon lokacin ko sai daya salahuddeen bai samu damar yankar jikin ukashat ba ko sukarsa. Alamarin da ya kara fusatashi kenan ya kara kaimi. Yayin da ukashat yaga haka sai yayi wata irin alkafira da baya baya ya nisanta da salahuddeen ya tsaya daga nesa kadan fuskarsa cike da murmushi yace, ya kai sarkin yaki kayi sani cewa na baka dama har tsawon sama da rabin sa'a baka iya cutat dani ba, to yanzu ganinan nisa kanka nima zan yi amfani da tawa damar. Alhamdulillahi zamu dakata anan Insha Allahu zaku jini da ci gaban wannan littafi. Na barku lafiya, naku a kullum dako da yaushe UMAR FAROUQ ZANGO Ina muku fatan alkhairi. [25/01, 9:04 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI Littafi na daya 1B MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI. TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO Marubucin ya cigaba da cewa. Kafin sarkin salahuddeen yayi wani yunkuri tuni ukashat ya daka tsalle ya dira a gabansa kamar dau koshi akayi aka ajiye. Banga ya shiga kaiwa salahuddeen mummunan sara da suka. Tsakanin karfin harin yasa salahuddeen ya kasa maida martani, sai kawai yaci gaba da kare kai. A duk sa'adda ukashat ya samu damar cutar da salahuddeen sai yaji cutar dashi dan yayi dariya kawai. A haka suka cigaba da artabu har ukashat ya kaishi kasa kuma ya huge takobin sa ta fadi kasa ya tsirashi da tasa. kawai sai sauran dakarun suka rude da kabbara suna yiwa ukashat jinjina cikin matukar alajabi. Ukashat ya juyawa salahuddeen baya ya tafi izuwa dokinsa ya kama ya hau, sannan ya juyo ya dubeshi yace, ku biyoni a baya mutafi izuwa bayan gari inda su uzaifat ke baiwa Kansu horo. Gama fadin hakan ke da wuya sai ukashat ya sakarwa dokinsa linzami ya sukwaneshi da gudu ya bar harabar gidan sarautar. Cikin alamun kunya da matukar takaici sarkin yaki salahuddeen ya mike tsaye ya hadu kan nasa dokin a lokacin da kwallar takaici ta ciko idanunsa, amma kuma da yaga sauran dakaru sun tsaitsaya a bayansa sai daya hau dokinsa yayi gaba sannan suka take masa baya sai yaji dadi a ransa, domin ya fahinci cewar haryazu yana da sauran kina da martaba a idanunsu duk da cewa yarima ukashat ya kaskantar dashi a gabansu. Sarkin yaki salahuddeen da sauran dakaru suka zaburi dawakansu a guje har suka cimma ukashat, ha zamana cewa ukashat da salahuddeen sun kusan hada kafada. A sannane ukashat ya dubi salahuddeen yace Ka gafarceni ya dirkar darul husuf, kayi sani cewa bani da niyyar kaskantar da kai akan idanun kowa. Koda jin wannan batu sai salahuddeen yaji zuciyarsa tayi sanyi ya maida masa martanin murmushin sannan yace, ya shugabana ai kome kamin bazai taba zama laifi ba, domin kaine sarkin gobe. Fatana shine idan har bukata ta biya nazamo makusanci a gareka. Sa'adda ukashat yaji haka sai ya bushe da dariya daga can kuma sai ya hade fuska yace, idan har Ka taimaka min wannan runduna tamu ta ci birnin shumbul da yaki nayi maka alkawarin kaine zaka zama wazirina yayin da na zama sarkin darul husuf. Koda jina haka sai salahuddeen ya cika da tsananin Farin ciki, ya kara bakinsa daf da na yarima yace ukashat yace, ai kuwa koda zan kace hanya saina kace muddin bukatar mu zata biya, saboda haka ka Kwantar da hankalika komai rintsi da tsanani kaine zaka hau karagar sarki, ba dai uzaifat ba sai dai idan bana numfashi a doron kasa. Dajin haka sai shima ukashat ya cika da murna suka ci gaba da hira cikin nishadi har suka iso bayan gari inda su yarima uzaifat suka yada sansani suka kafa tantuna. Da zuwa kuwa sai suka iske uzaifat tare da dakarunsa yana tsaye a tsakiyarsu sunyi masa da'ira yana koya musu yadda ake sarrafa takobi a tsakiyar abokan gaba, harma yana umartar wasu daga cikinsu da su afka masa. Da zarar sun afka masa sai su ga ya tarwatsasu nan da nan. Suna cikin wannan hali ne kawai sai suka hango Karar dawakan su ukashat daga nesa kadan don haka sai suka tsaya suna jiran isowarsu don su ga ko su waye. In ba don ma sunga cewa daga cikin gari suka fito ba da sai suyi tsammanin ko abokan gabane suka kawo musu farmakin sumame. Lokacin da su ukashat suka karaso aka ga juna sai mamaki ya kama uzaifat ya dubi ukashat yace, lale marhabun da dan uwa rabin jiki. Shin kunzo ne ku bamu gudunmawa bisa kokarin da mukeyi?. Ukashat ya kada kai alamar cewa ba wannan ce ta kawo su ba, sannan yace munzone muyi leken asirinku mu saci irin salon halin da kuka tanada. Koda gama fadin haka sai mamaki ya kama uzaifat da jama'arsa, domin sun san cewa basu fi su ukashat iya yaki ba, asalima ko tafin hannunsu basu kai ba. Ukashat da jama'arsa suka bushe da dariya, al'amarin da ya Sosa zuciyar uzaifat kenan, amma sai ya dubi ukashat yace, ya kai dan uwana ina son kubar wajen nan kau da jama'arka ku kyalemu muyi abinda ke gabanmu mu da ku kiwa tasa ta fishsheshi. Ukashat ya gyada kai yana mai yin murmushin mugunta yace, Bazai yiwu muzo har nan kuma mu tafi a banza ba . munzone domin a bambance tsakanin Yaya da tsakuwa, asan wadanda ya kamata a tura yaki ba sai an tsaya bata lokack ba. Ciki. Fushi uzaifat ya dakawa ukashat tsawa yace, wannan ai zancen banza kakeyi, domin kuwa ba haka Abbanmu ya shirya ba. Cewa yayi ni da kai kowa yashirya dakarun sa daban, kuma dukkaninmu zamune wannan yaki bai zaba ba. Ukashat yayi dariya sannan yace wannan gaskiyane haka abbanmu ya tsara amma kuma nima yanzu nazo da nawa tsarin kuma dole haka za'ayi. Koda gama fadin hakan sai ukashat ya dubi su sarkin yaki salahuddeen yace, ku afka musu ku maishesu nakasassu yadda bazasu iya fita yaki ba. Koda jina wannan umarni sai su salahuddeen suka zare makamnsu da nufin au afkawa su uzaifat, amma sai uzaifat yayi wuf ya sha gabansu yace, ku fara gamawa dani kafin su. Da jin haka sai su salahuddeen suka dan ja baya domin sun san cewa abune mai hadarin gaske idan dayansu ya kuskura ya taba lafiyar yarima uzaifat. Ukashat ya dafawa su salahuddeen tsawa ya ce, me kuke jirane da shi? Ku afka masa kawai, umarnina ne ba umarnin kowa ba. Cikin sanyin jiki da alamar karayar zuciya sarkin yaki salahuddeen ya dubi ukashat yace, ya shugabana kai ma ka san cewa duk wanda ya taba yarima daga cikinmu zai fuskanci fushin sarki. Ina ganin cewa zai fi kyau muhakura da wannan shiri mu koma cikin gari. Koda jin wannan furuci sai ukashat ya fusata, ya zare takobinsa ya nufi uzaifat gadan gadan yana mai cewa ni bari na nuna muku misali kuga zahiri, don ku san cewa babu wargi a cikin lamarina. Lokacin da uzaifat yaga dan uwansa ukashat ya taho kansa rike da takobi tsirara cikin mugun nufi sai shima ya zare tasa takobin ya tare shi a lokacin da gaba daya dakarun dake wajen suka nutsu suka tattare hankalinsu kowa a akan su. Yan uwa biyun na haduwa suka kaure da azababben artabu, ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka ciki zafin, juriya da bajinta. Wohoho! Idan sadaukantaka ta hadu da takwararta dole ne idanu su more kallo. Lokacin da wannan gumurzu ya dan yi nisa sai hankalin gaba daya dakarun dake wajen ya dugunzuma ainun, domin tsananin ya kai tsanani, ga dukkan alamu ba za a gama lafiya ba ba tare da an salwantar da rayuwar daya ba. Domin yadda suke kaiwa juna gari tamkar kafiri da musulmi sun hadu, kowannensu bil hakki yaje fadan kuma a fusace suna kokarin ganin bayan juna. Koda aka kara shafe rabin sa'a ana wannan fafatawa sai sukaja da baya a lokaci guda suka ba da tazarar taku biyar biyar, sannan suka rugo ga juna cikin mugun nufi. Tun kafin su hadu hankalin kowa dake wajen ya kara dugunzuma, domin an san cewa in dai aka hadu karon ba zaiyi kyauba. Koda ya rage saura taku daya su hadu sai suka daka tsalle suka yi sama a lokaci guda suka kaiwa juna sara da takobi. Kowa sai ya sami nasara suka yanki damatsan hannayensu, jikinsu ya dare jini ya zuba suka rikito kasa suna masu dage raunikan. Amma saboda juriya da jarumataka basu nuna wata gazawa ba, sai kawai suka sake yunkurawa suka ruva ga juna. Cikin zafin nama sarkin yaki salahuddeen ya daka tsalle ya dira a tsakiyarsu, bai bari sun hadu ba. Cikin fushi ukashat ya dakawa salahuddeen tsawa yace, saboda me zaka katse mana wannan fadan?. Salahuddeen ya risina yace ka gafarceni ya shugabana, kayi sani cewa idan muka bari kuka lahanta junanku sosai fushin mahaifinku zai tabbata akanmj. Idan ka ga munbarku Kunci gaba da wannan fada sai dai idan bama numfashi a doron kasa. Sa'adda ukashat yaji wannan batu sai takaici ya Ka mashi ya rasa abinda ke masa dadi a duniya, kawai sai yayi tsaki ya juya ya tafi ga adokinsa ya Kamashi ya hau ya sukqaneshi a guje. * * * * * * Da magriba yarima uzaifat ya shiga cikin gidan sarautar ya nufi bangaren mahaifiyarsa gimbiya shulaifa. Dashigarsa cikin tura karta sai ya isketa a zaune ta idar da sallah taba nafila. Cikin biyayya uzaifat ya sani wuri ya zana a gefe daya. Koda ta idar da sallah ta juyi sai tayi arba da raunin dake jikin hannun uzaifat. Nan taje hankalinta ya tashi, ta mike tsaye ta karaso gareshi ta rike kafadunsa tace, yaya akayi kajika wannan raunin? Ai wannan ma da gani saranka akayi da takobi?. Ya yin da uzaifat yaji wannan tambayar sai ya yi murmushi yace, karki damu ya ummina, wannan ba komai bane, kin san muna fita hoton yaki ni da dakaruna, to a can ne na sami wannan raunin. Shulaifa tayi ajiyar zuciya tace, Haba dana yau kwana nawa kuna fita wannan horon? Me yasa tsawon kwanankin nan bakayi wannan raunin ba sai yau? Na san irin jarumtakarka duk garin nan mutum dayane za ka kafsa dashi har ya sani nasarar yi maka rauni. Koda jin wannan batu sai jikin uzaifat yaya sanyi, ya tabbatar da cewa ta gano cewa ukashat ne yayi masa wannan rauni. Cikin alamun damuwa ya dubeta yace yake ummina kiyi sani cewa shima wanda yayi min wannan rauni nima haka nayi masa. Na rokeki dan girman Allah kibar wannan zance a tsakanin mu, domin idan maganar taje ga kunnen sarki gurina zai wargatse zai iya fasa gasar da yasa mana tsakanina da dan uwana. Sa'adda shulaifa taji haka sai itama jikinta yayi sanyi tace, shikenan na bar Maganar. Yanzu wane irin ci gaba ka samu a bangaren horon daku ke yi kai Dakarunka?. Uzaifat yace Alhamdulillahi muna samun ci gaba sosai. Yake ummina abin danake so shine, ki cigaba da yin min addu'a bisa nasara da nake nema a wannan ganin dazamu yi da birnin shumbul. Shulaifa tace, kullum a cikin yi maka addu'a nake, kuma da izinin Allah zaka sami wannan nasara, domin alherine a zuciyarka ba sharru ba. Ina tabbatar maka da cewa bazan daina yi maka addu'a ba daga yau har izuwa ranar da zaka tafi wannan yaki. Nasihata a gareka itace, ka rike abu uku, in dai kana rike da su dukabinda daka sa a gabanka zakayi nasara. Wadannan abubuwa guda uku ba komai bane face duk abinda zaka fadi ka tabbatar cewar ka fadi gaskiya, idan aka baka Amana ka riketa, kuma idan ka dauki alkawari ka tabbatar cewar ka cikashi, indai ka kiyaye wadannan abubuwan uku to tabbas makiya bazasu ga bayanka ba. Lokacin da shulaifa tazo nan a zancenta sai yarima uzaifat ya jinjina kai yace, Insha Allahu kuwa zan kiyaye wadannan abubuwa uku. Nan take yayi mata sallama ya fita daga cikin turakar. * * * * * * Al'amarin yarima ukashat kuwa, lokacin da ya shiga turakar mahaifiyarsa muzaira taga wannan rauni na hannunsa sai hankalinta ya dugunzuma, ta dubeshi tace, ya kau dana, yaya akayi ka sami wannan rauni?. Ukashat ya kashe labarin duk abinda ya faru tsakanisa da dan uwansa uzaifat ya shaida mata. Koda jin haka sai ranta ya baci, kishi ya turnuketa ta sunkui da kanta kasa ta shiga tunani mai zurfi. Daga can sai ta dago kai ta dubeshi tace, yaki dana kayi sani cewa a duniya bani da wani buri wanda yafi naga ka gaji mahaifinka, wato ya zamana cewa kaine ka hau karagar mulkinsa. A shirye nake na fansar da raina don cika wannan buri, kuma duk abinda baka zato zan iya yi don samun biyan bukata. A yanzu haka akwai kulle kullen da nake yi akan hakan. Yayin da yarima ukashat yaji wannan batu sai ya cika da murna. Daga can kuma sai ya dubeta cikin damuwa yace, yake ummina kiyi sani cewa ni a ganina da ni da dan uwana uzaifat babu wanda zaici wannan gasa da yashirya mana domin naje wajen malamai sama da guda bakwai sunyi istihara akan hakan. Abinda suke gaya min shine zamuje wannan yaki, kuma zamu sha bakar wahala, da kyar ma zamu tsira da rayuwar mu. Yanzu wane matakin kike ganin ya kamata mu dauka akan wannan al'amarin?. Yayin da muzaira taji wannan batu sai ta bushe da dariya sannan tace, yaro man kaza, hakika ba ka san rana ba sai ka shigeta, ka nake tukunna. Ai na gaya maka cewa tuni na yi kulle kullena don haka ka Kwanar da hankalika, duk wuya duk rintsi komai gumu kai ne zaka gaji sarki. Abinda malamanka suka gaya maka gaskiya ne, zaku sha bakar wahala a wannan yaki, amma ina tabbatar maka da cewa kai bazaka mutuba. Abinda nake so da kai shine, duk umarnin da na baka kabishi kada ka kuskara ka kereshi indai kayi hakan zamu cika burinmu. Mahaifinku yace a gobe ne zai yi bayanin yadda tafi wannan yaki da yadda zaku gabatar da yakin, kuma a goben ne zakuyi shiri ku tunkari birnin shumbul. Kafin ku tafi ne idan zamu yi bankwana zan gaya maka umarnin da zaka bi. Cikin mamaki ukashat ya dubi muzaira yace, wai shin ya ke ummina wane irin kulle kulle kika yine akan wannan bukata tamu? Muzaira tayi murmushi tace, lokacin sanjnka bai yiba, idan yayi lallai zaka fahimaci komai bayan an kammala wanan yaki. Ukashat ya matsawa muzaira akan sai ta gaya masa irin shirin da tayi, ita kuwa taki. A karshe dole ya hakura ya tashi ya tafi izuwa bangaren da turakarsa take. A daren wannan rana sarki uwaisul karni a dakin muzaira zai kwana, amma a ka'ida kullum sai ya shiga dakin wadda bata da kwanan sa ya tambayeta ko tana da wata matsala kafin yaje daya dakin ya kwanta. Bisa wanann al'ada sarki uwaisul karni ya shiga dakin shulaifa inda ya isketa a zaune tayi tagumi kuma ta zurfafa a cikin tunani. Koda Yau sallama sai ga amsa, kuma ta mike da sauri ta taho gareshi ta tsaya daf dashi a bakin kofa suka fuskanci juna ya yin da fuskarta ke nuna alamun tsoro da damuwa karara. Kafin ma ya budi baki ya tambayeta abinda ke damunta sai ta fashe da kuka, al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya dubeta yace, yake matata ina dalilin wanann kuka naki? Maimakon ta bashi amsa sai ya rungumeshi ta sake fashewa da sabon kuka. Da kyar ya rarrasheta tayi shiru , sannan ya cire ji kinsa daga cikin nata ya rike kafadunta yace, yanzu idan baki gaya min abinda ke damunki ba to wa zaki dayawa. Cikin sanyin murya shulaifa tace, yakai mijina kayi sani cewa jiya da daddare nayi wani mafarki mai ban tsoro wanda ya tsaya min a zuciya har izuwa daren yau ya hanani sukuni, domin a jiya yadda naga rana haka naga dare. A cikin mafarkin an nuna mini cewar ka shiga cikin wank irin mugun hali, wato rayuwar ka na tsakanin mutuwa da jinya. Sannan kuma an nuna mini yarima uzaifat a cikin tsakanin halin shan wuya tamkar shima zai rasa rayuwarsa. Tun da na farka daga barci sakamakon wanann mugun mafarki da tsakar dare sai nayi ta addu'o'i har gari ya waye ban rintsa ba. Ya kai mijina ka sani cewa mafi akasarin mafarkina yana zama gaskiya, bisa wanann daliline na shiga mugun tashin hankali. Shima baka tsammanin cewa wannan yaki da su uzaifat zasu tafi yana da nasaba da wanann mafarkin nawa? Sa'adda shulaifa ta zo nan a zanceta sai sarki uwaisul karni yayi murmushi a gareta yace, yaje matata kiyi Sani cewa dukkan wani mahaluki rayuwar sa ta kasance rubutaccen al'amari tun kafin ya zo duniya, saboda haka abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalin ki kuma ki ci gaba da tayamu da addu'a bisa aikin alherin da muka sa a gabanmu. Ni yanzu tsufa ya riskeni, fatan kawai shine na cika da imani. Shulaifa ta dago kai ta dubi uwaisul karni a lokacin da hawaye ke sartu bisa kumatunta tace, ya kai mijina, to wai shin me yasa tun tuni baka zabi halifanka ba a tsakanin uzaifat da ukashat har zaka sanya wanann gasa a tsakaninsu mai tsananin hadaki? Kai da kanka ka yaki kasar shumbul yafi sau a kirga baka taba samun nasara akan su ba. Ta yaya kake tsammanin cewa 'ya 'yanka zasu iya samun nasara?. Koda jin wannan tambaya sai sarki uwaisul karni ya sunkui da kansa kasa yayi shiru baice komai ba. Daga can saiya dago kai ya dubeta, bisa mamaki sai taga hawaye na zuba a idanunsa. Al'amarin daya mutukar bata mamaki kenan ta dubshe cikin mutukar damuwa tace, ka gafarceni ya kai mijina idan wannan tambayar da nayi maka ta Sosa naka zuciya. Sarki uwaisul karni yasa hannu ya share hawayen sa, Sanna yace,yake matata kiyi sani cewa tambayar ki bata bata min rai ba face ta tuno min da qani kuskure da na tafka guda daya sa'adda na gaji ubana akan wanann karagar mulki, sa'adda nake da shekara talatin da Shifa a duniya. Ina so ki saurari labarin da zam baki da kyau domin ki fahimci kuskuren da nayi rauywata da kuma illar da kuskuren ya haifar a garenj wanda gashi har na mutu bazan iya magance matsalar ba face 'ya'yana sunci birnin shumbul da yaki. Nan zamu dakata sai mun hadu lokaci na gaba. Ina muku fatan alkhairi. Naku a kullum da ko yaushe UMAR FAROUQ ZANGO. [26/01, 12:14 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA DAYA:- 1C MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO. MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA:- Kimanin shekaru dari da ashirin baya, mahiafina sarki Hurusul karni ya kasance shahararren a wannan nahiya, babu wani sarki mai daukakarsa da karfin mulkinsa faceahaifin sarki sharan na birnin shumbul wato sarki Nukaib. Duk da cewa mahaifina musulmine shi kuma sarki Nukaib kafirine ma'abocin bautar gunki, akwai kyakkyawar alaka a tsakaninsu, ba don komai ba sai domin tun suna yara kanana iyayensu suka kaisu wata makaranta ta koyon yaki a birnin rum. A can suka hadu kuma suka zamo abokai. Sai da suka shekara tara a wannan makaranta sannan suka rabuwa kowannensu ya koma kasarsa. A wannan zama da sukayi ne na tsawon shekaru tara a wannan makaranta yasa suka shaku ainun har sukayi alkaqarin cewa zasu tabbatar da abotarsu har abada kuma zasu tabbatar da zaman lafiya a tsakanin kasashen gajiyar duk da cewa a wannan lokaci ma duk shekara sai anyi yaki a tsakanin kasashen masu kuma duk Sa'adda akayi yakin RAGAS akeyi. Mahaifina sarki Hurusul karni da mahaifin sarki Nukaib basu san cewa 'ya'yansu sun hadu a wannan makaranta ba har suka shaku da juna, kuma basu san wannan alkawari da suka daukarwa juna ba. A wannan shekara da su sarki Hurusul karni suka kammala wannan makaranta ne yaki ya taso, kuma sai aka sami akasi cewa Hurusul karni shine zai jagoranci mayakan birnin Darul Husuf, shikuma Naukib shine zai jagiranci mayakan kasar Shumbul. A wanna lokaci duk iyayensu sun tsufa ainun baza su iya fita yaki ba, suna kwance a cikin ciwon ajali, kuma kowannensu burinsa shine yaga kafin ya mutu yaci wannan yaki. A lokacin malamai sun tabbatarwa da kakana cewa wannan ciwo nasa bana tashi bane, lallai shine ajalinsa. Shima sarki Nukaib bokayensa sun tabbatar masa da cewa mutuwa zaiyi. Bisa wanann daliki ne kowannensu ya gaba da dansa kafin ya fita yakin. Suka roki 'ya'yan masu akan duk yadda za suyi su tabbatar da cewa sunci wanann yaki. Sarki Hurusul karni da sarki Nukaib suka yiwa iyayensu alkawarin cewa wanann karon kk dukkannin mayakansu zasu kare sai sun Karar da abokan gaba. Babban kuskuren da Hurusul karni da Nukaib sukayi shine, har suka rabuwa a makaranta babu wanda gadan sunan garin kowa, asalima basu san cewa a nahiya daya suke ba, kuma duk shekara kasashen su ma yakar juna. Lokacin da rundunar biyu ta baiyyana a filin daga ya zamana cewa Hurusul karni ma jagirantar mutanen Darul Husuf, shu kuma Naukib na jagorantar mutanen shumbul sai aka sami duk su biyun sunyi wata irin shiga ta rufe fuskokinsu, don haka babu wanda ya shaida kowa. Tazarar dake tsakanin rundunar biyu ta kai zira'i dari, don haka daga nesa ake kallon kallo. Kowanne zuciyarsa cike da mugun nufi. Ba tare da bata lokaci ba sarki Nukaib ya daga takobinsa sama yayi wa jama'arsa inkiya a afkawa abokan gaba. Ai kuwa duk sai suka zare takubbansu suka sakarwa dawakansu linzami suka nufi inda rundunar su Hurusul karni suke. Koda aka hangosu sai shima Hurusul karni ya baiwa nasa jama'ar umarni suka sukwano da gudu suna kabbara, takobin kowa a sama, wato arna na ihu musulmai na kabbara. Yayin da aka hadu a tsakiya sai wuri ya yamutse da kuwwar mazaje, Karar karafa da haniniyra dawakai ta yawaita, aka garkame da azababben yaki ya zamana cewa duk indasu sarki Nukaib da suka sa gaba sai dai kaga musulmai na zubewa kasa suna shahada. Haka shima sarki Hurusul karni duk inda ya durfafa sai da kaga arba na zubewa kasa matattu. Yayain da shugabannin biyu suka ga suna yiwa junan mummanar barna sai suka yi kokari suka tari juna suna masu warewa gefe guda suka bar jama'arsu suna masu ci gaba da kafsawa. Wohoho! Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce fadan manya babu mai shiga, idan kuwa mutum ya shiga zaiyi nadama. Nan zamu dakata sai Allah ya kara hadamu a wani lokacin nan gaba. Ina godiya bisa nuna soyayyarku gareni. Ina muku fatan alkhairi, naku a kullum da ko da yaushe, UMAR FAROUQ ZANGO [26/01, 8:16 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA DAYA 1C. ( !! ) MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO. MARUBUCIN yakara da:- Lokacin da sarki Nukaib da sarki Hurusul karni suka ware gefe daya suka fara fafata yaki sai da suka shafe sa'a guda cur! Suna kaiwa juna sara da suka akan dawakai, amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba. Al'amarin da ya basu mamaki kenan, kuma ya fusata su. Bisa dole sai suka sauko daga kan dawakan nasu suka fara sabon yaki a kasa. Nan ma sai da suka sake shafe wata sa'a guda babu wanda ya sami nasara komai. Babban abinda da ya daure musu kai shi ne, karfi yazo daya, kuma dabatun yakinsu iri dayane. Nan kowannensu ya fusata ainun ya kara zage dantse suka ci gaba da fafatawa da dukkanin karfin su. A lokacin ne kowa ya sami nasarar yankar kowa. Sarki Nukaib ya yanki Hurusul karni a kafada, shi kuma ya yankeshi a cinya. Lokacin guda kowannensu ya dafe raunin sa gami da gyara tsayuwa. Kamar hadin baki sai kowannensu ya yagi rigar jikinsa ya daure raunin jikinsa, sannan suka sake kacamewa da sabon azababben yaki. Wannan karon sai da suka shafe sa'a uku cur!. Suna fafatawa amma dayansu bai gajiya ba, kuma basu fasa fi gaba da yakin ba. Ganin yadda suke wannan mugun artabune duk jama'ar tasu suka tsaya da yakin suka Kewaye su suna kallonsu, don aga wanda zai samu nasara akan wani. Hakika a wannan rana an ga jaruma taka da sadaukantaka gami da juriya irin wadanda ba'ataba gani ba a tarihin jaruman nahiyar gaba daya. Bayan jaruman biyu sun shafe sa'a uku ne suna wannan artabu, sannan suka fara samun nasarar ci gaba da yiwa juna rauni, har ta kai cewa kowannensu ya sami rauni goma sha uku a jikinsa, ya zamana cewa dukkanin su jikinsu yayi fata fata da jini har jiri na dibarsu, amma an rasa wanda zai je kasa. Kuma wani babban abin mamaki shine, a lokaci guda suke yiwa juna rauni, wato da zarar daya ya sami nasara akan dayan sai shima dayan ya sami nasara. Kai tun suna tsaye sai da suka durkushe kasa amma basu fasa kaiwa juna hadi ba. Abu dai har ta kai cewa makaman hannunsu sun lalace sun zubar da su suka kacame da kokawa, a hakan ne kowanne su rawaninsa ya tube fuskokinsu suka baiyana a fili. Koda suka yi arba da fuskokin juna sai suka kame kamar humaka suka kurawa juna ido cikin tsakanin takaici da nadama, daga can kuma sai aka ga sun fashe da kuka, suka rungume juna. Al'amarin da yayi mutukar baiwa kowa mamaki a wajen kenan, jikin jama'ar yayi sanyi aka kara marmatsowa kusa da su. Sarkin Naukib ya dubi Hurusul karni a lokacin da hawaye ke zuba a idanunsa yace, ya kai abokina ya ya akayi muka yi wannan babban kuskure, yanzu Ashe da kai nake yin wanann yakin ban saniba?. Cikin matukar karfin hali Hurusul karni ya share nasa hawayen sannan ya kara kankame Nukaib a kirjinsa yace, Hakika munyi babban kuskure da har muka rabu a makaranta bamu sanar da junanmu ainahin kasashenmu ba. Tabbas rashin sani yafi dare duhu, yanzu gashi abune mawuyaci mu rayu bare mu kawo karshen wannan yaki a tsakanin alummarmu, alhalin tun a baya munyi alkawarin tabbata da zaman lafiya a nahiyoyinmu gami da tsayar da yake yake a duk Sa'adda muka zamo shugabanni. Yanzu gashi mun kawo matsayin shugabancin amma kuna burinmu ya yanke anan. Sa'adda sarki Hurusul karni yazo dai dai man a jawabinsa sai shima sarki Nukaib ya sake kankameshi a kirjinsa duk su biyun suka sake fashewa da kuka, sannan Nukaib yace, ya kai abokina kayi sami cewa duk da cewa mutuwa zamuyi a yanzu ina matakur Farin ciki da zan mutu ina kan kirjinka, domin a ko yaushe burin masoyi shine ya kasance tare da masoyinsa. In da ace ka kadai ne zaka tafi ka barni da tabbas sai bakin ciki ya sa na kashe kaina, domin kaine abokina na farko a duniya kuma kaine na karshe, domin tun da muka rabu ban sake yin wani abokin ba. Kayi sani cewa kaine mutumin da na shaku da shi ainun fiye da iyayena da suka haifeni, amma idan baka manta ba mun rabu a makaranta ba tare da sanin cewa zamu rabu ba, domin mahaifina ne yazo a rana daya ya daukeni daga makarantar saboda kawai ya sami labarin cewa ni da kai mun shaku ainun. Lokacin da muka isa gida sai ya rufeni da da matsanaicin fada yana mai cewa saboda me zan yi abota da ma'abocin addinin musulunci? A wannan lokaci yayi ta nuna min illolin jama'ar ku da addininku da irin gabar dake tsakanin mu da ku tun iyaye da kakanni. Nan dai kawai ina sauraronsa ne kawai amma ko kadan a zuciyata ban gamsu cewa ku mutanen banza bane domin a zaman da nayi da kai ban taba ganin mutum mai kyawun hali ba kamarka da sanin yakamata da kuma tausayi da taimako. Ya kai masoyina kayi sane cewa tun a bayan rabuwarmu nake ta bincike a sirrince domin na gano sunan kasarku na kawo maka ziyarar ba zato, amma sai na kasa samun wanda yasan a inda kake. Ni kam tuntuni na gamsu da addininku, don haka a yanzu take inason ka shigar dani cikin wannan addini mai albarka. Koda jin wannan batun sai Hurusul karni ya cika da tsananin farin ciki. Na taje ya soma bi yawa sarki Nukaib Kalmar shahada. Allah sarki! Hakika idan mutum yana da rabo to fa komai rintsi sai rabonsa ya riskeshi. A dai dai lokacin da Hurusul karni ke biyawa Nukaib Kalmar shahada yana maimaitawa ne Allah ya karbi rayukansu a lokaci guda. Koda gainin abinda ya faru sai gardama ta kare a tsakanin rundunar biyu. Mutanen Hurusul karni suka ce ai duka gawar biyu ta zama tasu tinda sarki Nukaib ya karbi musulunci. Su kuwa mutanen birnin shumbul suka ce A'a Sam Sam basu yarda ba, sia dai a basu gawar Nukaib su tafi da abarsu. Al'amarin da yajanyo akaci gaba da yaki kenan, yakin ya zamo mai tsananin gaske, jar sai da kowa ya mutuba wajen, mutum daya bai tsira da rayuwarsa ba bare a sami wanda zai kai labarin hakikanin abinda ya faru a filin yakin. Sai bayan kwana guda da faruwar yakin ne iyayen su sarki Hurusul karni suka yi shiri suka zo filin yakin saboda sun ji shiru babu wanda jama'arsa ta koma gida. Koda aka da iso filin yakin kowa yaga dukkanin mayakansa sun zama gawa, haka ma 'ya'yayensu sai suka cika da tsananin bakin ciki suka kama kuka kamar bazasu daina ba. Tsananin bakin cikin rashin yayan nasu ne ya hanasu yin wani sabon yakin a wajen, don haka kowa sai ya dauki gawar dansa yabtafi da ita izuwa kasarsa akan cewa daga baya za a sake yin sabon shirin yakin. A wanann lokaci ne sarki uwaisul karni bai fi shekara bakwai ba a duniya. Alhamdulillahi nan zamu dakata sai Allah ya kaimu gobe zaku jimu da ci gaban wannan littafi. Ina fatan yana nishadantar ku. Ina muku fatan alkhairi UMAR FAROUQ ZANGO. [27/01, 11:57 am] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA DAYA MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI. TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO. YACI GABA DA CEWA:- Lokacin da kakana ya dawo gida dauke dagawar mahaifina rungume a kirjinsa yana ta faman rusa kuka muna tsaye a harabar nan gidan ni da uwata muna ya wasan birin birin ta daure min fuskata da yanki. Koda uwata ta hango gawar mijinta a hannun ubansa sai ta tafka salati da karfi. Nan take zuciyarta ta buga ta sulale kasa matacciya. Cikin hanzari na cire yankim dake fuskata. Koda naga mahaifiyata a kasa ta zama gawa kuma naga mahaifina a kirjinsa kakana shima ya zama gawa sai na fada kan gawar uwata na fashe da matsanaicin kuka. Duk mutum mai imani dole ne ya tausaya min a wannan lokaci, domin bani da kowa face kakana. Kuma na shaku matuka da mahaifina domin a kullum shi ke koya mini yaki kafin su fita wannan yakin da aka kashe shi. Lokacin dana fashe da matsanaicin kuka sai shima kakana ya kama mikan aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakanin mu. Sai da muka jima a hakan sannan ya ajiye gawar mahaifina yazo gareni ya kamani ya rungumeni a kirjinsa ya shiga karfafa min gwiwa yana cewa. Ya kai jikana kayi sani cewa ni tsufa ya riskeni don haka a koda yaushe ta Allah zata iya kasancewa a kaina. Idan ka gajeni ka tabbata cewa ka ci gaba da yaki da birnin shumbul har sai izuwa ranar da ka rushe birnin su ka kashe dukkanin mazansu da matansu. Lallai inaso ka daukar min wannan alkawari. Koda naji wannan batu sai na shiga rantsuwa da girman Allah ina mai cewa, ya kai kakana na dauki alkawari komai dadewa kamar yadda na ga gawar uwata da ubana yanzu sai naga gawar duk abinda ke da rai a cikin birnin shumbul kuma sai na naje birnin su. Idan kuwa abin ya gagareni ba zan mutuba face na dora 'ya'yana akan wannan turba. Sa'adda sarki uwaisul karni yazo dai dai nan a labarinsa sai hawaye ya zubo masa ya dubi shulaifa yace, kinji asalin abinda ya haddasa yaki tsakanina da kasar shumbul kuma har kwanan gobe ina son na cika alkawarin da na daukarwa kakana duk da cewa na san kuskure be yin hakan tunda mahaifina da sarki Nukaib bai mutuba ba face sai da ya karbi musulunci. Koda jin wannan batu sai shulaifa ta cika da tsananin mamaki tace, ya kai mijina lg akayi kasan cewa sarki Nukaib ya karbi musulunci alhalin kowa ya mutu a filin yakin ba a sami wanda ya kawo labarin abinda ya faru ba?. Uwaisul karni yayi ajiyar zuciya sannan yace, yake matata hakika kinyi tambaya mai matukar mahinmmanci kuma mai Ma'ana. Ina son ki sani cewa bayan kimanin shekaru arbain da mutuwar mahaifina na tsinci wata wasika a cikin irin tufafinsa da na gada wadanda ban taba sauyawa ba. Wannan wasika na kunshe da wasiyya ce ta mahaifina a gareni. Ashe kafin ya mutu a wannan filin yaki ya sami damar rubuta wannan wasiya, domin ya kawo karshen yakin a tsakanin kasashen biyu. A cikin wasikar ne ya bukaci da nayi tallan addinin musulunci ga mutanen kasar shumbul, kuma a cikin wasikar ne yayi min bayanin dangantakarsa da sarki Nukaib bisa abotarsu a makaranta da kuma duk abinda ya faru a tsakaninsu a filin yaki. Lokacin da na gama kiranta wannan wasika sai na fashe da kuka domin bakin alkalami ya Riga da ya bushe babu abinda zan iya yi a kan al'amarin. Bazan iya tsaida yakin ba tsakanina da birnin shumbul saboda na rigaya na dauki alkawarin ci gaba da yaki ga kakana, kuma har a ranar da kakana zai mutum yana kan cinyata babu abinda yaje maimaita min face na cika alkawarin da ke tsakaninmu. Yake matata tabbas bazan taba janye wannan alkawari ba, don haka dolene naci gaba da karfafawa su uzaifat gwiwa akan wannan yaki kuma duk wanda ya sami nasarar cin birnin shumbul da yaki shinea zai gajeni. Wannan itace wasiyyatr da zan bari kuma ko a bayan raina da ita za'ayi amfani. Koda gama wannan jawabi sai uwaisul karni yayiwa shulaifa sallama ya tafi izuwa dakin muzaira domin ya bata kwananta. * * * * * * Kashe gari bayan an yi kalacin safe sarki uwaisul karni ya tura aka kirawo yarima uzaifat da yarima ukashat suka gabata gareshi. Bayan sun durkusa a gabansa sun kwashi gaisuwa sai ya dube su a nutse yace yaku 'Ya'yana ina son nayi muku nasiha guda daya kafin nayi muku bayanin yadda zaku gabatar da wannan yaki da mutanen shumbul. Nasihar da zan muku itace, duk abinda zaku yi kada kuyi gaggawa, domin ita gaggawa taba kai mutum izuwa ga nadama. Sannan kuma ku kasance masu bincike bisa duk al'amarin da yazo muku saboda bincike na iya haifar da fahimtar juna gami da samun zaman lafiya ba tare da kun aikata abin da zaizo ya dameku ba. Dan gane da batun yakin da zaku tafi, ina son kuyi shiri kowannenku ya jagoranci rundunar dakarunsa a lokacin guda ku tafi yakin inda aka saba fafatawa muda mutanen birnin shumbul a gobe. A yanzu zan yi muku kacici kacici domin fitar da rundunar da zata fara tarar abokan gaba. Koda gama fadin haka sai sarki uwaisul karni ya sanya hannunsa a cikin aljihun rigarsa ya fiddo wadansu takardu dunkulallu biyu ya ajiye a gabansu yace kowannenku ya zabi takarda guda. Wanda ya dauki takardar da aka rubuta daya a cikinta dakarunsa ne zasu fara fita filin daga. Koda jin wannan batu sai uzaifat da ukashat suka tsirawa takardun biyu idanu aka rasa wanda zai fara dauka. Sarki uwaisul karni ya daka musu tsawa yace, me kuke jirane. Koda jin tsawar sai jikin su ya kama kyarma, cikin sauri uzaifat ya kai hannunsa ya dauki takardar dake gabansa sannan ukashat ya dauki dayar, sarki yace to ku warware takardun don muga abinda ke ciki. Ba tare da fargabar komai ba uzaifat yayi bisimillah ya bude tasa shi kuwa shi kuwa ukashat sai ya kama nuku nuku da kyar ya bude tasa. Sarki uwaisul karni ya karbi ta uzaifat ya duba sai ga lamba biyu a rubuce, kawai sai ya nunawa ukashat yace, to kaine zaka fara tarar abokan gaba. Nan take bakin ciki ya turnuke ukashat saboda shi a tunaninsa idan su uzaifat ne suka fara yin yakin nan da nan za a fara cin lagonsu uzaifat sai su kasa samun nasara inyaso daga baya sai su tsinci dami a kala. Yayin da sarki uwaisul karni yaga alamun damuwa karara a fuskar ukashat sai ya dubeshi yace, ya kai dana kayi sani cewa komai na duniya rabone. Babu wanda ya isa ya hanaka samun nasara a wannan yaki idan kana da rabo, haka kuma babu wanda ya isa ya sa samu idan baka da rabo. Koda sarki uwaisul karni ya zo nan a zancesa sai tari ya sarkeshi. Abu kamar wasa sai tarin yaki tsayawa, sai kuma ya fara aman jini. Nan da nan hankalin uzaifat da na ukashat ya dugunzuma suka dimauce. Cikin karaji uzaifat ya kwalawa wani hadimi kira wai shi amzabu. A guje Amazabu ya shigo cikin turakar, uzaifat ya umarci amzabu daya ruga gidan likitan sarki abu sharaz ya ki rashi yanzu yanzu. Koda jin wannan umarni sai amzabu ya sake juya wa wajen ya kama dokin ya haye ya zabureshi. Jima kadan sai ga amzabu tare da abu sharaz sun shigo cikin turakar sarki. Da shigowar su abu sharaz ya ga halin da sarki ke ciki, a wannan lokaci sarki na numfashi sama sama kuma idanunsa sun kada sunyi jawur babu kyan gani, sai shima hankalinsa ya dugunzuma nan take ya bude jakarsa ya fiddo wadansu magunguna ya hadasu a cikin kofi sannan ya durawa sarki a baki. Alhamdulillahi nan zamu dakata sai Allah ya kaimu lokaci na gaba zaku jimu da ci gaban wannan littafi. [28/01, 8:25 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI Haryanzu muna cikin LITTAFI NA DAYA MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO Yaci gaba da cewa Koda sarki uwaisul karni ya sha wannan maganin sai ya sake yin wani sabon kumallon mai dauke da wani irin bakin abu. Likita abu sharaz yayi nazarin wannan bakin abu kuma sai yayi nazarin kumallon da sarki yayi sai kawai ya sunkui sa kai cikin takaici ya kwantar da sarki akan gadonsa ya lullubeshi da mayafi sabo da jikinsa na karkarwar dari. Cikin dimauta uzaifat da ukashat suka dubi sharaz suka ce likita sarki zai sami lafiya ko? Kafin abu sharaz ya budi baki ya basu amsa sai kawai sukaji sarki uwaisul karni yayi ajiyar zuciya yace, ku fita ku bamu wuri ni da abu sharaz zamuyi sirri. Koda jin sarki yayi magana sai murna ta kama uzaifat da ukashat domin suna ganin cewa ya sami lafiya kenan. Ba tare da wata gardama ba uzaifat da ukashat suka mike suka fita daga cikin turakar. Fitarsu ke da wuya sai sarki uwaisul karni Ya dubi Abu sharaz yace, tashi ka rufe kofa da tagogin dakin nan domin bana son kowa yaji abinda zamu zanta. Cikin sauri Abu shares ya mike ya cika wannan umarni, sannan ya dawo kusa da sarki ya zauna daf da shi a gefen fadin suka kurawa juna idanu tsawon dakiku biyar dayansu baice uffan ba. Daga can sai sarki uwaisul karni ya yi kakin jini ya tofar sannan ya dubi Abu sharaz cikin alamun takaici da karayar zuciya yace, ya kai amintaccen likitana fada mini gaskiyar al'amari bisa abinda ka fahimta akan wannan rashin lafiya data sameni. Sa'adda likita Abu sharaz yaji wannan batu sai yayi ajiyar numfashi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan yace, ya shugabana hakika a cikin abincin da kaci na karshe ko a yau ko ajiya an zuba guba a ciki. Tuni wannan guba ta gama zagaya jinin jikin ka. Maganin da na baka zai kwantar da gubarne kawai amma abune mawuyace ka hate illar wannan guba sai dai idan kana da sauran kwana a duniya. Koda Abu sharaz yazo nan a zancensa sai ya ga hawaye ya zubo a idanun sarki uwaisul karni, al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan, yayi na damar sanar dashi gaskiyar al'amarin. Yayin da sarki uwaisul karni ya fahimci halin da Abu sharaz ya shiga sai ya dubeshi a nutse yace, yakai amintaccen likitana kayi sani cewa wannan hawaye nawa daka ga ya zuba ba na tsoro bane kuma bana takaici bane face na takaicin rashin daukar shawarar mahaifiyata, domin kuwa in da nayi amfani da shawararta da banshiga wannan hali da na shiga ba. Tabbas yanzu na gano cewa ba wani bane ya zuba mini guba a abincina ba face muzaira mahaifiyar ukashat. Tun kafin na auri muzaira mahaifiyata ta shawarceni akan kada na aureta domin bani take so ba, mulkin da nake ciki take sha'awa wannan lokacin soyayya tasa idanuna sun rufe bana ganin laifin muzaira ko kadan don haka sai naki amfani da shawarar mahaifiyata. Tabbas a yau na gane cewa duk wanda ya ketare maganar manya sai ya ga ba dai dai ba. Yanzu gashi muzaira ta nemi rayuwata saboda kawai ta mallaki mulkina. Ma'ana ta karbe karagata ta baiwa danta.ya kai amintaccen likitana yanzu a kiyasce kana ganin cewa tsawon wane lokayzan iya rayuwa tare da wannan guba da ke jikina? Koda jin wannan tambaya sai tausayin sarki uwaisul karni ya turnukeshi har kwalla tazo masa yace, ya shugabana ka sani cewa mutuwa lokaci ce, indai lokacin yazo baza a kara ba, kuma ba za a rage ba. Amma a kiyasi irin namu ba likitoci indai mutum ya sha irin wannan guba da kasha duk irin taimakon daza a bashi ba zai wuce kwana bakwai a duniya ba. Koda jin wannan batu sai fuskar sarki uwaisul karni ta fadada sa murmushi yace, Alhamdulillahi! Abinda na ke so da kai shine, ina so ka tafi izuwa gidan Malam abdulwahab ka gaya masa cewa ya tara sauran jama'ar sa su shiga halwa bisa rokawa kasata sarkin da zaifi zama alkhairi ga jama'ata bayan mutuwa ta. Wannan shine kadai sakon da nake son ka Isar min da shi, kuma a yanzu idan ka fita ka sanar da 'ya'yana su uzaifat cewa bana bukatar kowa ya kara shigowa cikin turakata, hatta iyayensu mata kuwa sai lokacin da na bukacesu da kaina. Koda jin wannan batu sai likita abu sharaz ya dubi sarki uwaisul karni cikin mamaki yace, ya shugabana yanzu tun da kana da tabbacin cewa muzaira ce ta saka maka guba a cikin abincin ka me zai hana kayi mata hukunci. Koda jin wannan tambaya sai sarki uwaisul karni yayi yake yace, ai baa fafe gora ranar tafiya, shi zunubi matane in dai ka daukeahi baka isa ka ajiye shi ba face asirinka ya tonu, domin sai nauyinsa yasa ka gajiya. Da sannu gaskiya zatayi halinta kowa ya ganta a fili karara. Yanzu na sallameka sai naje ka cika wannan umarni. Yayain da sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa sai likita abu sharaz ya mike tsaye cikin sanyin jiki ya fita daga turkar yana waigen sarki yana zubar da hawaye saboda tausayi da kuma sabonda sukayi tsawon shekara da shekaru. Da fitowar abu sharaz daga turakar sarki sai ya iske uzaifat da ukashat a tsaitsaye a cikin alamun tashin hankali. Koda suka ga ya fito daga cikin turakar sarki uwaisul karni sai suka taho gareshi da sauri da nufin shi shiga cikin turakar. Abu sharaz ya sha gabansu yace, sarki yace na gaya muku cewa daga yau kada kowa ya sake shiga cikin turkarsa face bawansa mai yi masa hidima a kullum har sai yabukaci ganinki. Koda jin wannan batu sai su uzaifat suka cika da mamaki, kuma hankalin su ya dugunzuma ainun. Nan dai abu sharaz ya tafi ya barsu a tsaye cikin mutukar damuwa da tunani. Bisa dole suma suka tafi suka bat kofar turakar sarki. * * * * * * Lokacin da ukashat ya koma turakar mahaifiyarsa muzaira ya sanar da ita duk abinda ya faru tskaninsu da sarki sai ta bushe da dariyar farin ciki har kwalla ta zubo mata, sannan ta hade fuska tace, ya kai dana kayi sani cewa tabbas yanzu sarki ya gane cewa nice na zuba masa guba taci, kuma a shirye nake na fuskanci kowanne irin hukunci daga gareshi, koda kuwa na kusane, domin bukatata ta biya tun da babu maka wa sai ya mutu domin gubar da na bashi taci ta gama ratsa jinin jikinsa, babu yadda za'ayi ya rayu. Koda jin wannan batu sai ukashat ya zazzaro idanu cikin firgici sannan yace, ya ke ummina yanzu kina da tabbacin cewa sarki mutuwa zai yi? Yayin da muzaira taji wannan tambaya sai ta bushe da dariya sannan tace, ai ina tabbatar maka da cewa sarki ba zai wuce nan da kwana bakwai ba, kaga kenan kafin ku dawo daga yaki anbinne sarki a kabarinsa. Abu na biyu sa zan sanar da kai shine, idan kuka tafi wannan yaki duk gumun da da zaku shiga kai zaka dawo a Raye, shi kuwa dan uwanka uzaifat sai dai a dauko gawarsa, amma dole ne ka kiyaye abinda zan gaya maka a yanzu. Abu na farko, ka tabbatar dagewa baka rufe fuskarka ba a cikin hular yaki. Abu na biyu, kayi shigar jajayen tufafi maimakon farare. Indai kayi haka zaka tsira da rayuwar ka,kuma zaka dawo gida cikin koshin lafiya. Kayi sani cewa daga cikin mayakan birnin shumbul akwai wani sadauki mai bakaken kaya kada ka kuskura kace sai kaga bayansa, domin yafi karfin ku duk ku biyun kai da dan uwanka don haka kada ka matsa yayin da kuna hadu dashi a filin daga. Sa'adda muzaira tazo nan a zancenta sai ukashat ya cika da tsananin mamaki, don haka sai ya dubeta cikin rashin gamsuwa yace, ya ke ummina wai shin menene dogaronki bisa samun tabbacin nasara akan abinda muka sa gaba? Muzaira ta bushe da dariya a karo na biyu tace, ya kai dana ka zuba ido kawai kasha mamaki, amma ina tabbatar maka da cewa komai zai tafi dai dai kuma sai bayan mun sami nasara sannan zan yi maka bayanin komai yadda akayi duk na tsara shirina. Koda jin wannan batun sai ukashat yayi murmushi yace, na yarda dake ya ummina tabbas na san cewa zaki iya domin duk abinda kika sa gabanki sai kin cimma gaci. Koda jin haka sai farin ciki ya lullube muzaira ta rugume ukashat tana mai cewa, in mai alfahari da kai ya dana. * * * * * * A can bangaren yarima uzaifat da mahaifiyarsa kuwa, lokacin da ya labartama halin da sarki ya shiga sai ta rude ta dimauce ta mike tsaye zumbur d nufin ta ruga izuwa turakar sarki, amma sai ya rikota da sauri yace, yake ummina kiyi sani cewa koda kinje kofar turakar sarki baza a barki ki shiga ciki ba, domin sarki ya kafa doka cewar bai yarda kowa ya shiga wajen sa ba hatta mu din kuwa sai ya bukacemu da kansa. Koda jin wannan batu sai shulaifa ta cika da tsananin mamaki, na take idanunta suka ciko da kwalla, hawaye ya fara zuba. Al'amarin da ya kefa uzaifat cikin mamaki kenan, ya dubeta yace yake ummina ina dalilin zubar wannan hawaye naki alhalin sarki na nan a Raye bai mutuba?. Shulaifa ta dubi uzaifat cikin alamun karayar zuciya tace yakai dana kayi sani cewa tun daga ranar da na auri mahaifinka kawo i yanzu ban tana ganin yayi rashin tafiyar da ta kaishi kwanciya ba sai wannan karon. Koda naji sarki ya bada wannan doka sai jikina ya bani cewa lallai ba karamin ciwo ne ya sameshi ba. Lallai bayason ma ganshi a cikin wannan hali shi yasa ya kafa dokar shiga wajen sa. Bugu da kari a cikin wadannan 'yan kwanaki nayi mafarki mai ban tsoro wanda aka dinga nuna mini sarki uwaisul karni a cikin mawuyacin halo wanda ban taba ganinsa a ciki ba. Duk sa'adda na tuno wadannan mafarkai sai tsoro ya baibayeni zuciya ta ta kama daka da karfi. Ga yadda kayi min bayani cewa a lokaci guda sarki ya kama kumallon jini na gasgata mafarkina. A cikin mafarkina nawa an nuna min cewa guba aka baiwa sarki a cikon abinci. Hannun da ya baiwa sarki wannan guba makusancinsa ne, in ba don zargi haramun ne ba ni kain na san wannan hannu. Shin baka zargin cewa tabbas guba ce sarki yasha? Uzaifat ya sunkui da kansa kasa yace, ko shakka babu akwai alamun haka, domin acikin aman jinin da sarki yayi akwai wani bakin abu mara kyan gani. Kafin uzaifat ya gama rufe ba kinsa sai ya ga shulaifa ta yanke jiki ta fadi sumammiya. A tude ya nemo ruwa ya yyafa mata sannan ta farfado, ya dubta yace yaje ummina ki sani ta da mutuwa duk a hannun Allah suke saboda haka guba bata isa ta kashe sarki ba face idan kwanansa ya kare. Abin da nake so dake kawai shine, kici gaba da yi masa addu'a akan Allah ya bashi lafiya, ni kuma Allah ya bani sa'a a wannan yaki da zamu fita gobe. Sannan ya karemu daga sharrin dukkan sharrin abokan gaba da makiyanmu. Koda jin haka sai shulaifa tayi ajiyar zuciya sannan tace, madallah da wannan da nawa na gari mai tunasar da ni kadaitar Allah. Alhamdulillahi, anan zamu dakata sai kuma gobe Insha Allahu zamu dora daga inda muka tsaya. Ina muku Fatan alkhairi b [29/01, 3:20 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA DAYA 1. MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO Kashe gari kuwa tun da duku dukun safiya bayan any isar da sallah asuba, rundunar biyu ta DAKARUN MUSULUNCI suka yi sahu sahu a kofar fada bisa dawakai kuma cikin shigar yaki mai kwarjini da ban tsoro. Al'amarin da ya janyo hankalin jamaa kenan aka firfito daga cikin gidaje aka tari ana yi musu kabbara, don kara musu kwarin gwiwa saboda sanin cewa JIHADI za su fita. Sai da dakarun biyu suka shafe kusan rabin sa'a a tsaitsaye sannan masu jagorantarsu suka fito daga gidan sarauta. Ba wasu bane face yarima uzaifat da yarima ukashat. Koda ganin iri shigar da jaruman biyu sukayi sai gaba daya jama'ar gari suka cika da tsananin mamaki. Suka zuba musu idanu kawai a lokacin da fadar tayi tsit tamakar babu mai rai a wajen. Ba komai ne ya janyo hakan ba face ganin irin shigar da yarima ukashat yayi wadda ta saba da al'adar dakarun yakin kasar. A ka'idar wannan dakarun musulunci na wannan birni duk sa'adda za'a fita yaki kowa na sanya fararen tufafi ne ba'a taba ganin wanda sanya wani kamar ba daban, amma yau sai aka ga yarima ukashat shi kadai ya sanya jajayen tufafi. Nan fa fadar ta rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa. Uzaifat ya tafi izuwa gaban dakarunsa ya tsaya, sannan Shima ukashat ya tafi izuwa gaban tasa rundunar. Faruwar hakan ke da quya sai ga wazirin sarki uwaisul karni ya fito daga cikin fada, sauran 'yan majalisa na boye da shi. Koda juma'a suka hangosu sai filin fadar yayi tsit aka zuba musu idanu har suka zo gaban juma'a suka tsaya. Bayan waziri ya wuce gaba sai ya tsaya cak ya fuskanci alumma a cikin nutsuwa sannan yayi sallama iri ta addinin musulunci. Cikin hadin baki gaba daya gaba daya jama'ar gari suka amsa sallamar sannan yayi gyaran murya yace, yaku 'yan uwana musulmi kuyi sani cewa ni wakili ne na sarkinmu mai girma sarki uwaisul karni, kuma na tsaya ne a gaban ku domin na isar da sakonsa a gareku bisa kasan cewar ba zai iya fitowa ba a yau ya fuskanceku sakamakon 'yar lalurar rashin lafiya data riskeshi a jiya. Koda jin wannan batu sai fadar ta sake rudewa da hayaniya, masu salati nayi masu yin addu'o'i nayi. Wasu kuwa sai hankalisu ya dugunzuma. Bakomaine ya haddasa hakan ba face mamaki da kima fargaba, domin a tarihin rayuwar sarki tun da ya hau kan mulki bai taba yin tashi lafiyar da ta hanashi fitowa ba sai yau. Koda waziri yaga fadar ta rude sai ya daga hannunsa sama, take kuwa juma'a suka yi shiru kamar mutuwa ta gifta waziri taci gaba da bayani yana maicewa. Yaku 'yan uwana musulmi, kuyi sani cewa babu wani abu dauwamamme face Allah da kansa, kuma ciwo ba shine ajali ba. Kada ku tayar da hankalin ku bisa lalurar data samu sarkinmu mai adalci, domin babu mai yaye masa face ubangijin daya dora masa. Abinda ya kamacemu shine muci gaba da yi masa addu'a akan Allah ya yaye masa wannan lalura. Koda gama fadin haka sai fadar ta rude da amin!! Nan take waziri yace a karantawa sarki falaki da nasi da ayatul kuriyyu. Aka rufe da sirril fatiha. Cikin hadin baki kuwa aka kammala wannan addu'a. In da mutum na kusa sa'adda ake wannan addu'a sai gaba daya tsigar jikin sa ta tashi saboda jin dadin sautin addu'ar a bakin jama'a wacce ta cika dodon kunne, kuma ta sanyaya zukata. Koda mutum kafirine in dai ya jiyo wannan sauti sai zuciyarsa ta karaya. Bayan am idar da wannan addu'a sai waziri yavi gaba da jawabi yana mai cewa. Yaku jama'ar wannan birni, kuyi sani cewa sarki yace a sanar daku ana bukatar gudunmawar ku ta addu'a bisa wannan yaki wanda 'ya'yansa zasu jagoranta izuwa birnin shumbul. Kamar yadda kuka sani shekara da shekaru muna fafata yaki da wadannan mutanen kasar shumbul amma bamu taba samun nasara akansu ba, suma haka. To fa a wannan karon anyi shiri na musamman wanda ake sa ran cewa lallai za a sami nasara akan abokan gaba, don haka ana bukatar jajircewar gudunmawarku ta addu'a daga yanzu har zuwa lokacin da za a dawo daga wannan yaki. Wannan shine iyakar sakon da sarki ya bayar a shaida muku. Idan akwai wani mai korafi yayi bayani. Idan kuma babu yanzu mu yi bankwana da mayakanmu domin su kama hanya izuwa filin daga. Koda waziri yazo nan a zancensa sai yayi shiri ya kurawa jama'ar gari idanu ko zai ji wanda zai zo da korafi. Tsawon 'yan dakiku fadar ta sake yin tsit. Daga can sai wani Dattijo mai yawan shekaru ya dogara sandarsa a hankali yana mai rantsowa ta tsakiyar jama'a ya ido gaban waziri ya tsaya sannan yayi sallama irin ta addinin musulunci ya ce, ya kai wazirin sarkinmu, kayi sami cewa mi dai a garin nan Allah yayi baiwar kwana domin a halin yanzu bana tsammanin cewa akwai mai yawn shekaru na, domin da wayona aka haigi kakan sarki na ukj. A iya taso wata a wannan birni namu mai albarka ban taba ganin bakon al'amari ba irin na yau. Wannan bakon al'amari kuwa ba komai bane face irin shigar tufafin da yarima ukashat yayi a yau. A iya sanina tun daga kafa wannan birni kawo I yau duk sa'adda za'a fita yaki kowa fararen tufafi yake saw a jikinsa, ba'a taba ganin wani ya sanya sabanin haka ba, shin ko yarima zai iya yi mana bayanin da yasa yazo da wannan sabone tsari a yau? Yayin da waziri yaji wannan tambaya daga bakin Dattijo sai ya gyara murya yace, to masu iya magana sunce waka a bakin mai ita tafi dadi, saboda haka yanzu zan bukaci yarima ukashat da ya fito gaban jama'a ya kare kansa in da hali domin ni kaina ban san hujjar sa ta sanya jajayen tufafi ba a yau. Kafin waziri ya gama rufe bakinsa tuni ukashat ya sauko daga kan dokinsa yazo gaban jama'ar ya tsaya yana mai murmushi ba da fargabar komai ba. Nan take ukashat yayi sallama jama'a suka amsa masa, sannan yace. Yaku 'yan uwana musulmai, da farko dai ina son kusani cewa a har kullum ana son musulmi yayi aiki da kyakkyawar niyya. Al'ada bata gaban farilla ko sunana. Sanya fararen tufafi yayin fita yaki a wannan birnin namu al'ada ce ta iyaye da kakanninmu ba wai farilla bace a cikin addinin Allah, don haka sabanin haka baya nufin an kauce hanya ko an sabi Allah. Ina son kowa ya fahimat cewa na bambanta suttura ta da ta sauran abokan tafi yane domin kawai na darsa shakku a cikin zuciyar abokan gaba kuma na firgitasu suyi tunanin wani abun Daban wanda zai iya kawo musu nakasu a cikin wannan yaki. Wata kila yin hakan yazamo sanadin samun nasara akansu. Abu na biyu da nake son jama'a su fahimta shine, mahaifinmu ya tura mu wanann yaki ne akan babban hujja guda daya. Wanna hujja itace, ya raba mayakanmu izuwa kaso biyu, naso na farko na Karkashin jagorancin dan uwana uzaifat, daya kason kuwa a Kar kashin nawa jagorancin yake. Za'a fara wannan yaki ne da tawa rundunar sannan daga baya rundunar dan uwana su kafsa da abokan gaba. Duk wanda rndunarsa ta samu nasara shine zaigaji karagar sarki. Shin ba kwa tunanin cewa wannan gasa wadda sarki ya shirya mana bata dace ba? Shin ba kwa ganin cewa akwai son zuciya a cikinta? Koda jin wannan batu sai fadar ta rude da hayaniya, al'amarin da ya dugunzuma hankalin 'yan majalisar sarki kenan ga dayansu suka ware gefe guda suka tattauna. Daga bisani sai waziri yace shi kenan an yarda yarima ukashat ya tafi wannan yaki a cikin shigarsa ta jajayen tufafi. Ba tare da bata lokaci ba aka buga tambarin yaki dukkanin dakaru suka yi bankwana da iyalinsu wasu na kwalla, wasu kuma na yiwa dakarun murna akan zasu tafi neman shahada. Daga nan sai dukkanin dakarun suka hau dawakansu. A lokacin ne shulaifa ta zo gaban yarima uzaifat domin suyi sallamar karshe. Ta dubeshi cikin yanayin damuwa tace, ya kai dana kada ka mance da nasihata a gareka bisa abubuwa uku nan da nace ka kiyaye su. Abu na farko shine, gaskiya, sai amana, sai cika alkawari. Uzaifat yayi murmushi yace, ya ke ummina ki kwantar da hankalin ki da izinin Allah zan kiyaye bisa wadannan abubuwa uku, ni dai bukatata a wajenki kawai itace ki tayani da addu'a. Koda jin haka sai idanun shulaifa suka ciko da kwalla tafara zubar da hawaye, al'amarin daya dugunzuma hankalin uzaifat kenan ya dubeta cikin matsanaiciyar damuwa yace ina dalilin zubar wannan hawaye naki ya ummina Shulaifa ta share hawayenta sannna tace, ya kai dana kayi sani cewa dolene nayi kuka domin ina cikin tsaka mai wuya. Katuna halin da mahaifinka ke ciki yana kwance cikin jinya babu tabbacin zai tashi, kai kuma gashi yanzu zaka tafi jihadi ba lallai bane ka dawo ba, kaga kenan zan iya zama bazawara kuma mara da, idan na rasaku duk ku biyun. Sa'adda shulaifa tazo nan a zancenta sai tausayinta ya kama yarima uzaifat har shima ya kama hawaye, kawai sai ya sauka daga kan dokinsa suka rungume juna. Tsawon 'yan dakiku suna Jade sannan ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna yace. Yake ummina ina son ki kasance mai yin tawakkali bisa kaddara, ki tuna cewa RAI DA MUTUWA duk na Allah ne, kuma Allah baya barin wani domin wani. Idan sarki na da sauran shnaruwa a duniya dole ne ya tashi daga wannan cuta. Ni kan takaicina daya ne da ya hanamj ganawa da shi. Yanzu gashi zan tafi wannan yaki ba tare da nayi masa bankwana ba wata kila kuma shikenan har abada ba zamu sake ganin fuskar juna ba. Yayin da uzaifat yazo nan a zancensa sai itama shulaifa ta kamu da tsananin tausayinsa ta rungumeshi tana kuka shima yana kuka kamar ba zai daina ba. * * * * * * A can bangaren yarima ukashat da mahaifiyar sa muzaira kuwa, lokacin da suka zo yin bankwana ko kadan babu alamar wata damuwa a tare da fuskokinsu face Farin ciki. Kalma daya muzaira ta dubi ukashat tace dashi. Nasara na garemu ya dana. Ukashat yayi murmushi yace, Tabbas maganar ki dutse ce. Gama fadin hakan ke da wuya sai sukaji an sake buga tambarin tafiya. Nan take uzaifat ya sako mahaifiyar sa ya kama dokinsa ya hate. Dam ukashat da dakarunsa ne akan gaba don haka sai suka wuce izuwa kofar fita daga cikin birnin, sannan uzaifat da nasa dakarun suka take musu baya a lokacin da jama'ar gari da 'yan majalisar sarki suka busu da kallo har aka daina hangosu, sannan waziri ya sallama kowa fada ta watse ya zamana cewa babu kowa a wajen face mutum biyu rak. Ba wasu bane face muzaira da shulaifa. Koda suka dubi juna sai muzaira tayi murmushin mugunta a gareta sannna ta taho daf da ita ta tsaya suka kurawa juna idanu. Muzaira tace, to babban abokiyar gabata kiyi sani cewa lokaci yayi da zan dauki fansa akanki da mijinmu. Ina tabbatar miki da cewa nan da kwana bakwai rak sarki zai mutu, domin ba zai tsufa daga sharrin gubar dana bashi ya ci ba. Wannan yaki da 'ya'yan mu suka tafi ina tabbatar miki da cewa sanki ba zai dawo a raye ba, dana ne zai dawo cikin koshin lafiya, kuma kafin ya dawo sarki ya mutu, kin ga kenan dana ya zama sarki, Darul Husuf ta zama tamu. Idan babu sarki babu uzaifat ta ya ya zakiji dadin rayuwa da mu? Lallai a sannane zaki ga wulakanci da tozarci irin wanda baki taba gani ba a rayuwarki. Ko magen gidan sarautarmu sai ta fiki jin daraja. Lokacin da muzaira tazo nan a zancenta sai kawai raga shulaifa ta dubeta tayi murmushi tace, ka jahila wadda bata san fari da baki ba! Shin kin matane cewa RAI DA MUTUWA duk a hannun Allah suke? Ina mai tabbatar miki da cewar gubar da ki kabawa sarki yaci bata isa ta kasheshi ba face idan kwanan sa ya kare. Haka kuma duk irin gumun da za'ayi a filin yaki bai zama dole dana ya hallaka ba, zai iya tsira da rayuwar sa tinda Allah ne mai kashe wa da rayawa ba mutum mai najasa ba. Furucin karshe da zan miki shine, kiji tsoran karshen rayuwarki, domin duk wanda ya shika sharri dole ya girbi sharri. Koda gama fadin haka sai shulaifa ta juya ta nufi gidan sarautar tabar muzaira a tsaye tana kyalkyala dariya, domin ta tabbatar da cewa babu abinda zai han hakant ya cimma ruwa. Wannan shine abinda ya faru a birnin Darul Husuf bayan yarima uzaifat da yarima ukashat sun tafi yaki tare da DAKARUN MUSULUNCI rukuni biyu. Masha Allah nan zamu tsaya sai Allah ya kaimu gobe zamu ci gaba. Bayan haka ina mai baku hakuri bisa rashin sakar littafin sau biyu a yini daya, hakan ya farune saboda wasu dalilai amma Insha Allahu zanyi kokari naga na saita ta yadda zai cigaba da zuwan muku yadda aka fara da farko na nagode da nuna kauna da goyon bayanku gareni. Naku a kullum da ko da yaushe UMAR FAROUQ ZANGO. Na barku lafiya [30/01, 11:04 am] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA 1 MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO Lokacin da rundunar DAKARUN MUSULUNCI rukuni biyu ta dau hanya sai suka wanzu suna ta tafiya ba tare da sassauci ba har sai da rana ta fadi. Babu abinda ke tsai dasu face sallah da cin abincin rana da sukeyi sau daya. Sa'adda rana ta fadi sai suka yada zango a cikin wani daji mai yawan sarkakiya, duhuwa da dogayen bishiyoyi. Shi dai wannan daji yana da mutukar kwarjini da ban tsoro, domin sai da kowa ya sha jinin jikinsa. Tabbas ba za a rasa mugayen abubuwa ba a cikin wannan daji fiye da shekaru arba'in baya fatake ma basa yarda su yada zango a bakin wannan daji, amma yau sai gashi DAKARUN MUSULUNCI sun tsaya a wannan waje. Watakila ko don sun ga yawansu ne ko kuma don sun yarda da Kansu ne? Amma a zihir dosowar magriba ce ta sa suka yada zango a wajen domin su gabatar da sallar magriba. Nan take salahuddeen da Abul shaja'a suka baiwa dakarun su umarnin a sassabe ciyayi masu tsawo, sannan a kunna fitilun itace kuma a kafa tantuna. Nan da nan kuwa aka cika wannan umarni, cikin kankanin lokaci. Bayan an tabbatar da cewa babu wani mugun abu a kusa sai aka tayarda sallar magriba. Da aka idar aka shafa addu'a sai aka shiga kokarin cin abincin dare. A wannan lokaci ne Abul shaja'a da yarima uzaifat suka shiga cikin tanti suka zauna aka kawo musu nasu abincin. Koda uzaifat yayi loma daya sai ya kasa ci gaba da cin abincin, ya sunkui da kansa kasa ya shiga tunani. Cikin alamun damuwa Abu shaja'a ya dafa kafadar uzaifat yace, ya Shugabana lafiya, tunanin me kakeyi haka? Uzaifat yayi gyaran murya yace, ya kai Abul shaja'a kayi sani cewa ina cikin tsananin damuwa bisa halin da na baro mahaifina a ciki na rashin lafiya, har ina jin kamar na koma da baya a sirrance na shiga har cikin turakar sa na ganshi. Koda jin haka sai Abul shaja'a yace, haba ya shugabana ai tunda sarki ya kafa dokar cewa kada dayan ku ya sake ya shiga cikin turakar sa face da izininsa ai bai kamata ka karya dokarsa ba, tunda ka kasance mai biyayya a gareshi tun daga kuruciyarka kawo izuwa girmanka. Ina son kasani cewa sarki na da babbar hujja wadda tasa ya kafa wannan doka babu mamaki idan ka karya dokar ka wargatsa masa wank shiri nasa. Sa'adda uzaifat yaji wannan batu sai idanunsa suka ciko da kwalla, ya ce, Wane shiri ne ga mutumin da ke kwance cikin jinyar ajali? Ya kai Abul shaja'a kayi sani cewa ban sa ran sarki zai kara kwana bakwai a duniya. Cikin mamaki Abul shaja'a ya dubi shi yace ya ya akayi kasan haka? Take hawaye ya zubowa uzaifat yace, ya kai Abul shaja'a ka sani cewa mahaifiyata tayi mafarki an ciyar da sarki guba tun data bani wannan labari sai nayi istihara aka nuna min abinda ta gani. Abinciken da nayi wajen likitoci sun tabbatar min da cewa in dai mutum yaci guba a cikin abinci abune mawuyaci ya wuce kwana bakwai a duniya. Abul shaja'a ya kawo gwauron numfashi ya ajiye, sannan ya dubi uzaifat cikin matukar mamaki yace, wane ne ya baiwa sarki guba yaci. Uzaifat yace, a gaskiya bazan iya cewa komai ba sai dai mu jira izuwa lokacin da asirinsa zai tonu. Wai shin yanzu tafiyar kwana nawa zamuyi mu isa filin daga inda za'a kafsa wannan yaki tsakanin mu da mutanen birnin shumbul? Abul shaja'a yace, a Kalla sai munyi tafiyar kwana goma sha biyar sannan zamu isa. Ya kai yarima ka sani cewa karo da mayakan birnin shumbul ba karamin aiki bane, domin duk sa'adda muka gwabza yaki dasu muna shan tsananin wuya... In ba domin karfin addu'a ba zasu iya samun nasara akanmu. Tabbas a wannan karonina shakkar gamuwarmu da mutanen birnin shumbul saboda matsala biyu. Matsala ta farko itace, babu gwarzon mayakin mu wanda yafi kowa jarumataka a Darul Husuf, wato sarki da kansa. Matsala ta biyu itace, wannan karon adadin mayakan da muka fito da su rundunar ka data ukashat gaba daya basu fi rabin rundunar da muka saba fitowa da su ba a duk sa'adda zamu yi yaki da birnin shumbul. Alhamdulillahi zamu tsaya anan sai Allah ya kaimu anjima zamu ci gaba. [30/01, 8:04 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA DAYA 1 MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, wai shin wace irin sadaukantaka sarki ke da ita ne? Kasan cewa ban taba ganin yakinsa ba. Abul shaja'a ya jinjina kai yace, ai ni a rayuwata ban taba ganin sadauki mai zafin nama da jarumataka ba kamar Mahaifinku face mai bakaken kaya na birnin shumbul, wanda a ko yaushe suke RAGAS! Cikin mamaki uzaifat yace, to wai shin shi Wannna mai bakaken kaya wane ne shi, menene matsayinsa a birnin shumbul? Abul shaja'a yace, yau shekara takwas kenan da fara fitowar mai bakaken kaya filin yaki, babu wanda ya taba ganin fuskar sa kuma baya daya daga cikin manyan mayakan kasar. Ina tabbatar maka da cewa koda kai da ukashat zaku taru akan mai bakaken kaya bazaku iya hallakashiba, saboda yana da mutukar karfin damtse na gaban kwatance. Uzaifat ya sunkui da kansa kasa yace, ai kuwa ko zan hallaka zai natari wannan mai bakaken kaya koda zan halaka. Haka dai uzaifat d Abul shaja'a suka ci gaba da hira har lokacin sallar isha yayi, suka fito daga tantin suka iske tuni su ukashat sunyi alwala. Koda aka zo za a tayar da sallah sai ukashat yayi sauri ya shige gaba da nufin yayi limanci alhalin ko a gida uzaifat ne yaci gaba da limanci a lokacin da sarki ya sami lalurar rashin lafiya. Koda salahuddeen yaga ukashat ya wuce gaba zai yi limanci sai ya matsa daf dashi yace, ya shugabana sarki fa ya nada uzaifat a matsayin limaminmu na sallah a cikin wannan tafiya. Koda jin wannan batu sai ukashat ya dakaw salahuddeen harara yace, nan ba gida bane, don haka da ni da uzaifat anan kowa sarki ne. Koda gama fadin haka sai ukashat ya juyo ya dubi mai tayar da ikama yace da shi Bismillah, nan take kuwa aka tada sallah. Ko kadan uzaifat bai nuna wata damuwa ba. Bayan an idar da sallar sai uzaifat yaje ga ukashat yace, ya kai dan uwana ka sani cewa yana da kyau mu zauna ni da kai mu tattauna akan yadda zamu bullowa mai bakaken kaya na birnin shumbul, domin na sami labarin cewa ni da kaima bazamu iya da shiba. Haka kuma yana da kyau mu tattauna akan yadda zamu bullowa tsarin yakin, domin adadin da abokan gaba ya ninka mu sau biyu ko ma fiye da haka. Yayin da ukashat yaji wannan batu sai ya yi irin murmushin mugunta da ya saba yi, sannan yace. Ya kai dan uwana shin ka manta ne cewa wannan yaki da muka fito gasane a tsakanina ni da kai? Ya za'ayi mu hada kai wajen neman nasara? Ai sai dai kowa tasa ta fishsheshi! Ka sank cewa a halin yanzu duk sa'adda na dubi fuskarka sai naga kamar bakin kumurci nake kallo. Nifa ban daukeka a matsayin dan uwa ba face makiyi wanda ke kokarin dakusar min da burin rayuwa. Ni yanzu abin da nake so da kai shine, ka manta da cewa akwai wata nasaba ta jini tsakanina da kai, idan ma kana ganin zaka iya Kawar da ni ka jarraba, domin rayuwata hadarice ga taka. Koda ukashat yazo nan a zancensa sai uzaifat yace, subahanallahi! Yanzu matsayin da ka daukeni kenan? To in dk saboda ka mallaki karagar mahaifinmu ne ka tsaneni har kake son Kawar da ni daga yau na janye wannan gasa na bar maka. Na yarda ka zamo sarki Darul Husuf! Koda jin haka sai ukashat yayi tsaki yace, ai bakin alkalami ya bushe tunda ka Riga ma amsa cewa zaka yi wannan gasa a gaban sarki. Inda bakason muyi gaba da tun sa sannan zaka janye ka bar min. Daga yau ina mai shawartarka da ka fita daga harkata, idan da hali ma ka daina yi min magana. Bazai ga Uzaifat yace, wa'iyazubillahi! Ai a matsayina na musulmi haramun ne na daina maka magana. Ya ya kake zance kamar wNj jahili? Ukashat yace, ai ni akan wannan sarautar na makance, kuma na kurmance. Gaba daya tinanina ya gushe, babu komai a gabana face nasara ta kowanne hali. Koda jin wannan batu sai uzaifat ya gyada kai yace, ai kuwa sai dai nace Allah ya shirye ka. Ukashat yayi tsaki a karo na biyu ya tafi ya bar uzaifat a tsaye yana binsa da kallo kawai cikin mamaki, domin bai taba zaton zai ji kalaman da yayi ba daga bakinsa. Lokacin da uzaifat ya koma cikin tantinsa ya kwanta don yayi bacci sai ya kasa saboda tunani da mamakin kalmonin da dan uwansa ukashat ya gaya masa a yau. Yana cikin wannan haline Abul shaja'a ya shigo cikin tantin. Koda yaga uzaifat a cikin wannan hali sai ya zauna kusa da shi yayi gyaran murya, hankalin uzaifat ya dawo jikinsa. Abul shaja'a ya sake dubansa cikin mamaki yace dashi. Ya shugabana me kuka tattauna ne da dan uwanka ukashat? Ga dukkan alamu abin da ya hanaka bacci kenan. Koda jin wannan batu sai uzaifat ya kurawa Abul shaja'a idanu na dan wani lokaci, daga bisani ya kau da kai gefe yace. Tsakanin dan uwa sirrine, bazan iya gayawa kowa ba. Koda jin haka sai Abul shaja'a yayi shiru bai kara cewa komai ba. Kawai sai ya koma kan shimfidarsa ya kwanta. Uzaifat ya juyo ya dubeshi yace, yaya ka tsara harkar tsaro anan? Abul shaja'a yace, rabin dakarunmu ne zasu yi bacci, rabi suyi gadi. Muzaira Uzaifat yace, da kyau, kayi tsari mai kyau. Daga nan duk su biyun suka yi shiru basu kara cewa komai ba har bacci ya kwashesu basu sani ba. Asuba na yi dai dai lokacin sallah sai Abul shaja'a ya farka. Koda ya bude idanunsa yaga uzaiu bai farka ba sai ya mike da hanzari ya fita wajen tantin. Koda fitowa sai yaga babu dakarun ukashat ko mutum daya daga cikin masu aikin tsaro. Nan take hankalin Abul shaja'a ya dugunzuma, yakoma cikin tantin nasu da gudu a dimauce ya taso uzaifat. Koda suka fito daga cikin tantin sai suka shiga duba cikin tantuna. Bisa mamaki sai suka ga babu kowa a cikin tantunan. Hatta tantin yarima kuwa. A dimauce suka duba sawu lo zasu ga sawun 'yan uwansu ko wani wuri suka tafi amma ko alamar sawunsu basu gani ba. Al'amarin daya jefasu cikin tsananin mamaki kenan, hankalinsu ya kara dugunzuma ainun, suka tsaya suna tunanin mafita. Daga can sai uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, mu fara gabatar neman 'yan uwanmu. Ba tare da bata lokaci ba kuwa suka yi alwala sukayi sallah, sannan suka roki Allah akan ya baiyanar musu da 'yan uwasu. Nan take suka nufi inda aka daure dawakai bisa mamaki kuwa sai suka iske dawakan rututu a daure kamar yadda aka barsu jiya, Ma'ana ko guda daya ba a daukaba. Cikin hanzari suka kama dawakansu suka zaburesu izuwa cikin dajin suna tafiya a hankali suna waige waige ko zasu ga alamar inda 'yan uwansu suke. Abu kamar wasa sai da suka shafe sa'a uku suna yawo a cikin dajin basu ga duriyar abokan tafiyar su ba. Babban abin da yafi tayar musu da hankali shine, yayin sa suka kara nutsawa a cikin dajin suna shiga cikin muguwar sarkakiya don ratsawa, kwatsam! Sai suka ji sun fada cikin wani irin mugun tabo. Kafin suyi wani yunkuri tuni tabon yarike dawakansu suka kasa gaba ko baya, sannan kuma dawakan na nutsawa kasa. Uzaifat da Abul shaja'a suka daga kai sama suka yi nazarin wajen gaba daya, suka ga ba zasu iya yin tsalle ba daga kan dawakan nasu subar harabar da tabon yake, domin tabon ya mamaye ko ina, gabas da yamma, kudu da arewa. Koda suka fuskanci hakan sai hankalinsu ya kara dugunzuma ainun, domin sun tabbatar da cewa in ba wani ikon Allah ba babu yadda za suyi su tsira da rayuwarsu. Babban tashin hankalin shine , tuni tabon ya shanye gangar jikin dawakan nasu, yazo musu iya wuya. Cikin karayar zuciya Abul shaja'a ya dubi uzaifat yace, ya shugabana bamu da abinyi face mu fara shahada, domin tabbas mutuwa za muyi a cikin wannan tabon, domin ban ga yadda zamu iya kubutar da kanmu ba. Koda jin wannan batu sai uzaifat ya dakawa Abul shaja'a tsawa yace, akul ka kara irin wannan furuci, domin dukkan mai rai baya cire tsammanin rahamar Allah a irin yanayin da ya tsinci kansa. Koda gama wannan jawabi sai uzaifat ya fada karanto wata addu'a bisa neman taimakon ubangiji. Haja dai wannan tabo ya ci gaba da shanye jikin su uzaifat har ya zamana cewa gangar jikinsu ta nutse a ciki, ya kawo musu iya habarsu. Har a sannan uzaifat bai cire tsammanin samun taimakon Allah ba, kuma bai fasa yin addu'a ba. Shi kuwa Abul shaja'a ban da Kalmar shahada babu abinda yake yi. Ba zato ba tsammani sai suka hango wani mutum daga can saman wani tsauni mai tsawon gaske bisa dole ya taho izuwa karshen tsaunin. Mutumin na sanye da bakaken kaya, fuskar sa ma a rufe take ruf cikin hanzari mutumin ya sauko daga kan dokinsa ya debo wasu dogayen igiyoyi guda biyu yayi musu zarge, sannan ya jeho su kasa daga saman tsaunin. A lokaci guda igiyoyin suka fada kawunan su uzaifat da Abul shaja'a, sukayi musu kawanya a wuyansu. Kawai sai mutumin yaja igiyoyin. Sai gashi yana janyosu daga cikin tabon, amma saboda igiyoyin sun shake wuyan su nan da nan suka fita haiyacinsu. Kafin ya gama fito da su daga cikin tabon duk su biyun sun suma. Koda mutumin yaga ya samu nasarar janyosu izuwa gareshi jikin tsaunin da yake kai saiya dauko battar ruwa ya budeta ya sako ruwan daga sama ya zuba a kansu. Faruwar Hakan ke da wuya sai uzaifat da Abul shaja'a suka farfado suna taron wahala a matukar galabaice. Alhamdulillahi nan zamu dakata sai Allah ya kaimu gobe Insha Allahu zamu dora daga inda muka tsaya. DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA DAYA 1 MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO Mai rubutun ya ci gaba da cewa, Koda suka daga kai sukayi arba da Wannan mutum wanda ya ceci rayuwar su sai ya bude baki yace dasu, ku cire igiyoyin daga wuyanku ku rikesu, ni kuma zan taimaka muku na hawo da ku izuwa saman wannan tsauni inda nake. Yayin da uzaifat da Abul shaja'a suka ji muryar wannan mutumi sai suka cika da tsananin mamaki, suka daga kai suna kallonsa a cikin rashin yarda. Ba komaine ya janyo hakan ba face sunji muryar tasa ce irin ta mata mai zakk tamkar sarewa. Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, anya kuwa wannan mutumin da ya cecemu ba shibane mai bakaken kaya na birnin shumbul wanda aka bamu labari? Wata kila wata muguntar ya ke son ya shirya mana shine ya ke son ya yaudaremu. Sa'adda Abul shaja'a yaji wannan batu sai yace, anya kuwa hakane? Ai inda shine ba zai cecemu ba. Ai kawai mubi umarnin sa mu ga abinda zai faru tunda dai bamu da wani zabi, babu yadda zamu iya fita daga nan face mun hau kan wannan tsauni. Cikin gaggawa uzaifat da Abul shaja'a suka cire igiyoyin daga wuyansu sannan suka kama igiyoyin suna hawa izuwa saman tsaunin. Babu abinda ya basu mamaki face ganin irin tsabar karfin wannan mutum mai bakaken kaya, domin shine ya rike igiyoyin da hannayensa har suna lilo a kai ba tare da nauyinsu ya rinjayeshi ba. Shi dai wannan tsauni ya kai zira'i dari da arba'in. Amma mutumin nan mai bakaken kaya bai gajiya ba har su uzaifat suka gama hawa saman tsaunin suka riskeshi. A sannane yayi haki guda daya yayi watsi da igiyoyin kawai sai ya kwaye rawanin da ya rufe fuskar sa. Take uzaifat da Abul shaja'a suka dimauce, bisa yin arba da fuskar. Ba komai suka gani ba face wata tsaleliyar budurwa mai tsananin kyawun na gaban kwatance. Gashin kanta ya zubo har kasan kwankwasonta. A bayanta tana goye da wata jibgegiyar takobi. Budurwar ta dubesu tayi musu murmushi tace, lale marhabun da yarima uzaifat dan sarki uwaisul karni. Kayi sani cewa akwai labari mai yawa a bakina, domin na san komai akanku. Hatta abokan tafiyar ku da suka bace na san da inda suke. Koda jin wannan batu sai uzaifat da Abul shaja'a suka sake cika da tsananin mamaki. Uzaifat ya dubeta cikin mamaki yace, ya akayi duk kika san wannan al'amari? Kuma wacece ke ? Sannan saboda me kika ceci rayuwar mu? Koda jin wadannan tambayoyi sai budurwar ta sake yin murmushi tace, duk za kuji amsar tambayoyina, amma sai kun nutsu tukunna. Abin da nake so daku shine, ku kwantar da hankalinsu ku bani yarda, na rantse da girman uwata ba zan cutar daku ba, domin kuna da mutukar amfani a gareni. Ku biyoni izuwa cikin gidana domin mu zauna mu tattauna a cikin nutsuwa. Koda gama fadin hakan sai budurwar ta kama dokita ta hau tayi gaba tana mai tafiya a hankalin, su kuwa sai suka bita da sauri don kada tayi musu nisa ta bace. Sannu a hankali suka gangara kasa tsaunin, sannan suka iso bakin wani katon mulmulallen dutse fari fat, irin wanda basu taba gani ba a rayuwarsu. Koda isowar wannan budurwa gaban farin dutsen sai ta sauka daga kan dokinta ta shafi dutsen da hannunta na hagu, kawai sai suka ga wata kofa ta zinare ta baiyana akan dutsen, ta bude kanta suka hango kayataccen gida a cikin dutsen. Budurwar ta waiga ta dubi uzaifat da Abul shaja'a cikin murmushi irin wanda ke ruda dukkanin da namiji tace, ku biyoni izuwa ciki. Nan take ta kunna kai cikin gidan, shi kuwa wannan doki na ta sai ya raba jikinsa da wannan farin dutse, take ya shige cikin dutsen ya bace bat! Tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen. Abul shaja'a da uzaifat suka dubi juna. Abul shaja'a yace, ya shugabana anya kuwa ma shiga cikin gidan nan? Na fuskanci cewa wannan budurwa ma'abociyar tsafi ce, bai kamata muyi Hulda da. ita ba. Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, ai akwai hulda ta lalura, don haka ba laifi bane. Mu shiga cikin wannan gida, amma dole ne mu kiyaye ga barin duk abinda zayasa mu sabi Allah. Koda gama fadin haka sai uzaifat ya bi bayan wannan budurwa, shima Abul shaja'a sai ya bi bayan sa yana tafiya a cikien dari dari. Gaba daya kasan gidan an malaleshi da lu'ulu'u ne, kuma komai na amfanin gidan da zinare aka yi shi. Babu abinda ya baiwa su uzaifat mamaki face yadda gidan ke da girman gaske, sannan an tsarashi wuri wuri, kuna ko ina an zuba kayan alatu na gaban kwatance. A takaice dai wannan gida aljannar duniya ce a cikin sa. Nan dai suka yi ta wuce barori da kuyangi suna ta hidima, har suka isa wata kasaitacciyar fada mai dauke da shimfidu da kujeru na alfarma iri iri. Da Isar su wannan fada sai budurwar ta hau kan wata karagar mulki ta zamu, sannan ta yiwa su uzaifat nuni da wasu kujeru tace su zauna. Zamansu ke da wuya sai aka kawo musu abinci iri iri da ababan shaye shaye kala kala da kuma 'ya 'yan itatuwa. Kyakkyawar budurwar ta dubi uzaifat da Abul shaja'a tayi musu tayi. Kawai sai uzaifat ya dauki tuffa guda daya ya soma ci. Ganin hakan ne shima Abul shaja'a ya dauki tuffa ne sai uzaifat ya dauki tambulan na kayan shaye shaye yana shinshinasu har sai da yaji wanda ke kanshin ruwan inibi sannan ya dan dana kadan ya tabbatar da cewa babu giya a cikina, ya sha. Shima Abul shaja'a sai yayi koyi dashi. Sai da suka sha ruwan inibin suka koshi sannan suka yi hamdala suka zubawa Wannna kyakkyawar budurwa idanu. Budurwar ta bushe da dariya tace, hakika ku dai ma'abota addinin musulunci kuna da tsantseni akan alamuran duniya. To ku sani cewa na san duk irin dokokin cin abinicinku, don haka na zan taba cigar da ku abin da addininku ya haramta ba. Ina mai sanar daku cewa na zauna da ma'abota addinin addininku har tsawon shekaru shida, babu abinda ban iya ba na dangane da yadda ake bautar ubangijin ku. Nayi ilimi dai dai gwargwado, kuma nayi nazarin addinin naku da kyau, na gano shine addinin gaskiya, amma na ki karbarsa saboda in na karbeshi ba zan taba cika burina ba na duniya. Wannan wank darasine Daban a cikin tarihin rayuwata. Yanzu dai ina mai sanar daku cewa sunana Lafirat, kuma na kasance 'ya ga sarki sha'aran ibn Nukaib mai mulkin birnin shumbul, wato birnin abokan gabarku. Ina son ku sani cewa ba nice kadai 'yar sarki shaaran ba, akwai 'yar uwata mai suna sazirat, wacce aka haifemu tare. Ma'ana Hassana da Hussain's muke, wato uwa daya uba daya. Ni da ita kamarmu daya tamkar an tsaga kara, komai Kular mutum ba zai iya bambancemu ba , to amma akwai bambancin, kuma duk duniya babu mai iya tantancemu face mahaifinmu. Tun da aka haifemu muka taso da tsagwaron sadaukantaka, wato karfin damtse na tsiya tsiya, sannan kuma sai mahaifinmu ya rinka tsumamu da tsumin tsafi har izuwa sa'adda muka zama cikakkun mata. A sannane na fara samun sabani da 'yar uwata sazirat, bisa burinta na son ta gaji mahaifinmu, watota zamo sarauniyar birnin shumbul kamar yadda a yanzu kaima ka sami sabani da dan uwanka ukashat. Kafin wannan lokaci daga kuruciyarmu zuwa gairmanmu ni da sazirat bamu taba yin koda sa inda ba, amma sai gashi a ta kaimu ga zagin juna, harma da yin kazamkn fada. Idan muka fara kwamarzuwa sai mu kwana uku muna yaki bamu saurara ba har mu rushe wurare da dama a gidan sarautar mu, mutuwa junanmu mugayen raunika. Babu wanda ya isa ya rabamu wannan fada face Mahaifinmu, amma kuma sai yaki rabamun sai dai ta kaimu ga sumar da juna. Bisa wannan halaiya ne watarana sarki shaaran ya taramu a gabansa yace, a cikin ku duk wadda take son ta gajeni dolene tayi abu uku. Abu na farko dole ne ta bani kanta na kwanta da ita. Abu na biyu dolene ta yanka jariri a gabana ta shanye jikinsa. Abu na uku kuwa dole ne ta hakura dayin aure har abada. Koda naji wannan batu sai na kwalla ihu mai firgitarwa na rushe da kuka, sannan na dubi mahaifinmu nace. Tur da wannan bakar al'ada taka. In dai sai nayi wannan abubuwan uku sannan zan gajeka na hakura da mulkin kasar nan har abada. Ni kan da na aikata wadannan abubuwa uku gwara ma na rasa rayuwata. Na dubi 'yar uwata sazirat nace, yake 'yar uwata kada kwadayin mulki ya rudeki ki bata rayuwar ki. Lallai kema ki hakura da wannan bukata. Yayin da sazirat taji wannan shawara tawa, sai ta bushe da dariya, daga can kuma sai ta murtuke fuska tace, Ni kan na sami hanyar da zan cika burin a cikin ruwan sanyi. Don haka dole na aikata wadannan abubuwa uku. Koda jin wannan batu sai hankalina ya dugunzuma ainun, na sake fashewa da kuka na shiga rokon sazirat, ina maicewa da ita. Kada ta yarda ta aikata wadannan mummunan aiki. Koda na ga ta nufi inda mahaifinmu ke tsaye, sai na duga da gudu da nufin na riketa na hanata zuwa gareshi. Kawai sai mahaifinmu ya nunani da hannunsa na hagu, taje wata irin murtukekiyar sarkar tsafi ta nannade jikina gaba daya tayi min mugun dauri ya zamana cewa na kasa koda motsa hannayena. Nan fa ma shiga amfani da karfin sihirna don na kwance kaina, amma sai tsafina yaki yin tasiri. Mahaifinmu ya sake dubana ya kyalkyale da dariya yace, yake 'yata ki hakura kawai, domin baki isa ki iya hanamu aikata wannan aiki ba. Yin wannan aiki ne kadai zai sa ki samu cikakken tsafin sihirin tsafi dai dai da nawa. Nan take sarki shaaran ya farwa 'yar uwata sazirat ya santa 'ya mace a gaban idanuna, a lokacin da na ke ta faman rusa ihu da kuka saboda tsananin takaici. Bayan sun gama aikata lalatarsu sai sarki yasa aka je aka nemo jariri sabon haihuwa aka kawo. Nan take sazirat ta yanka jaririn da wuka akan makogwaronsa, ta kafa bakina ta sha jinin jaririn. DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA DAYA 1 MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO LAFIRAT ta ci gaba da cewa. Koda na gama ganin wannan mugun aiki na rashin imani da batanci, sai nan take naji na tsani mahaifina da 'yar uwata sazirat kamar yadda na tsani mutuwa ta. A sannane sarki ya sake nuna ni da hannunsa na hagu, wannan sarka data daure ni ta bace bat. Kawai sai na dubi sarki da sazirat a lokacin da hawaye ke zuba a idanuna nace, Hakika daga yau bani baku! Wannan gidan ya haramta a gareni, zamana daku ya kare har abada, tsakanina da ku sai yaki! Kiyayya ta a gareku ba zata gushe ba face na ga na zare muku ruhin numfashi saboda mugun aikin da kuka aikata. Ya kai Abbana hakika ka cika kazami wanda yayi amai ya lashe abinda. Wannna abu da ka aikata ya shafe matsayinka na uba a gareni. Kuma ka cusa mini bakin ciki wanda har abada ba zai kankaru ba a cikin zuciyata face ajali ya riskeni. Ina nadama da na zamo tsatsonka.... Gwara ace na kasance ba 'yar kowa ba sai 'yar talakan da babu kamarsa a talauci a fadin duniya. Da wannan furuci nake yi muku bankwana na karshe... Duk ranar da kuka fa na dawo gidan nan, to ku tabbata cewa wannan rana itace ranar mutuwarku. Koda gama wannan jawabi sai na juya na fice daga cikin fadar. Sarki sha'arn da 'yar uwata sazirat kuwa, suka yi ta kyalkyala dariya kamar bazasu taba dainawa ba har abada." Lokacin da Lafirat tazo dai dai nan a labarinta, sai ga hawaye na sartu akan kumatunta. Al'amarin da ya sa uzaifat da Abul shaja'a suka kamu da mutukar tausayinta kenan. Uzaifat ya dubeta a nutse yace, " Hakika kina da babbar hujja wadda ta sa kika rabu da mahaifinki da kuma'yar uwarki. Yake wannan kyakkyawar budurwa, yanzu una batun abokan tafiyar da kika ce kin san inda suke, amma haryanzu baki sanar da mu ba. Haka kuma baki fada mana dalilin da yasa kika ceci rayuwar mu ba, kamar yadda na bukata a baya?". Lafirat tayi gyaran murya tace, "A jiya da daddare, lokacin da kuka yada zango a cikin dajin nan, mai sarkakiya har kuka kafa tantuna kuka kwanta a ciki. Dukkanin ku kunyi barci face wadanda ke tsaitsaye a wajen tantin suna gadi. Sa'adda dare ya raba ne, sarki sha'aran ya turo wadansu zakwakuran aljanu dai dai adadinku suka zo suka kwashe mutanen ku gaba daya face ku biyun nan kawai. Abin da ya hana kuma a dauke ku shine, kafin kuyi barci kai Uzaifat ka tofa addu'a a cikin tantin naku a gabas da yamma kudu da arewa da kuma sama da kasa. Karfin wannan addu'a da kayi ne tasa duk aljanin da ya doshi tantunku sai yaji kamar zai babbake. Bisa dole suka hakura suka tafi suka barku a cikin tantin. Bayan aljanun sun kwashe jama'ar taku sun yi sama da su, basu zame ko ina ba sai fadar mahaifina sarki sha'aran ta birnin shumbul. Tsananin ganin munin wadannan aljanu ne yasa jama'arku suka dimauce har suka kasa yin addu'ar daza su kubuta daga hannunsu. Suna ji suna gani aka kaisu har cikin fadar aka kuma daddauresu da sarkokin tsafi, kuma aka kukkulle bakunansu yadda bazasu iya motsa harsunansu ba bare suyi addu'a. Dayawa daga cikinsu ma sun haukace, wasu sun suma saboda yin arba da wadannan aljanu. Mutum dayane daga cikin jama'ar taku ba a daureshi ba da wannan sarkar tsafi. Wannan mutum ba kuwa ba kowa bane face mai jajayen tufafi, wato dan uwanka Ukashat. Lokacin da Ukashat yaga shi kadaine ba daureshi ba sai ya cika da mamaki, kuma ya zama dan kauye ya kama kalle kalle a cikin fadar mahaifina saboda ganin irin aljannar duniyar da aka shirya a cikinta. Ba zato ba tsammanin sai Ukashat yaga sarki sha'aran da sazirat sun baiyana a gabansa suna kyalkyala masa dariya. Cikin tsoro ya kura musu idanu ya kasa yunkurin komai. Sarki sha'aran ya dubeshi yace, "Ya kai Ukashat dan sarki uwaisul karni wanda ke burin zamowa sarkin Darul Husufa, ka kwantar da hankalinka ka sani cewa mu ba zamu cutar da kai ba shiyasa ma muka tura aka daukkoku tun gabannin ku iso filin daga inda zamu fafata yaki daku. Ina mai tabbatar maka sa cewa koda an fafata wannan yaki, dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba, domin munfi karfin ku nesa ba kusa ba. Sarkinkune kadai ya zame mana matsala. Yanzu gashi mahifiyarka tayi mana maganin sarkinku, ta ciyar da shi guba wacce zata zamo sanadiyyar ajalinsa. Babban sirrin da baka sani ba shine, asalin mahaifiyar ka 'yar mu ce, run tana jaririya muka shayar da ita komai na al'adarmu, amma sai muka Kaita cikin birnin ku ta taso a hannun wani aminin sarkin ku a matsayin 'yarsa. Abinda bai sani ba shine, a ranar da matarsa ta haifi 'ya mace sai muka yi masa musanya da tamu ya ci gaba sa renonta a matsayin 'yar cikinsa. Tasa 'yar kuwa sai muka kawota nan muka ci gaba da renonta ta girma a matsayin mafita 'yar uwarmu. Wannan amini na Mahaifinku ba wani bane face likita Abu sharaz, wato kakana". Sa'adda sarki sha'aran ya zo nan a jawabinsa sai Ukashat ya cika da tsananin mamaki. Koda ganin haja sai sarki sha'aran ya sake tuntsurewa da dariya yace, Ai na san za kayi matukar mamaki bisa jin wannan labari, amma duk abinda nake so ka fahimta shine, abokin gaba yana iya bata shekara da shekaru wajen neman hanyar da zaibi yaga ya samu nasara akan abokin gabarsa. Ya kai wannan dan sarki kasani cewa na dade ina aika dakarun aljanu domin suje su baje birninku, amma ba dayansu da yake dawowa a raye. Lokacin da nayi bincike sai na gano cewa akwai wasu layu da aka binne a Kar kashin katangun da suka kewaye birnin ku guda hudu, tunda aka kafa ganuwar wannan birin wadannan layun suke, a cikin bincikena an tabbatar min da cewa indai ina so naci birninku da yaki har nasamu basarar shiga cikin birnin to dole ne sai an tone wadannan layu, sau shida ina tura dakarun aljanu domin su tone wadannan layu shima duk wa'yanda suka tafi basa dawowa. Daga baya sai na sake shiga halarar tsafi ta kwana bakwai, a sannan na gano cewa ba wanda ya isa ya tone wadannan layu face tsatson gidan sarautar birnin, Ma'ana sai jinin sarautar birnin. Tunda na fahimci haka na dukufa wajen ganin ya za'ayi na samu nasara samun tsatson jinin gidan sarautar, ina cikin bincike na ne aka nuna min fitowarku yaki zuwa filin daga inda aka saba gwabza yaki tsakanin mu. Nayi amfani da wannan dama bayan kunya da zango a cikin wancan daji nasa zakwakuran dakarun aljanuna suka je suka deboku. Kasani ya kai yarima na dade ina jiran irin wannan dama amma bansameta ba sai yanzu. Tabbas indai ka yadda muka hada hannu ka hada kai damu muka ci birninku da yaki kuma muka samu nasarar kashe Mahaifinku da dan uwanka to tabbas duk abinda ke cikin fadar nan ya hallata a gareka. Abu na biyu da ban fada maka shine duk wannan abinda ke faruwa da sanin mahaifiyar ka domin muna tura wasu aljanu suna sanar da ita ilimin tsafi a sirrance ba tare ya kowa ya sani ba, haka kuma mu muka tsara mata yadda zata kawo mana karshen sarkinku, kuma muka umarceta da lallai idan lokacin fita yaki yayi ta sa ka kasa jajayen tufafi. Kuma mun mata alkawari indai burinmu ya cika to kaine zaka zama sarkin darul husuf. Koda ji wannan batu sai Ukashat ya dubi sarki sha'aran yace, "Yanzu ina labarin 'yar likita abu sharaz koda jin wannan tambaya sai sarki ya dubi Ukashat yace, " Yar likita abu sharaz tana gidan gonata a cikin tsaro babu wanda ya isa yaje inda take face ni. Abinda nake so da kai shine ka kwantar da hankalinka ka kall daular nan duk takace duk abinda kake so kayi amfani dashi, ga kyawawan kuyangi da 'yan mata duk wanda kakeso ka kwanta da ita zata baka hadinkai ko da kuwa 'yata ce Sazirat. Koda jin wannan batu sai Ukashat ya daga kai ya dubi irin daular dake cikin fadar da irin kayan alatun dake cikinta, sannan ya daga kai ya dubi sazirat kawai sai ya duma wawa akan kayan abinci da abinsha da aka ajiye a gefen fadar a kan tebur, daga bisani kuma ya farwa sazirat suka aikata lalata. Wannan shine abinda ya faru ga dan uwanka sa abokan tafiyarku. Koda Lafirat tazo nan a zancenta sai hawayen takaici ya zubowa Uzaifat yace, yanzu kina nufin dan uwana ya gujemu ya hada kai da kafirai makiya Allah akan kawai ya gaji karagar mulki, kuma ya yadda ya aikata zina kuma yasha giya a matsayin sa na dan sarkin musulmi me mulkin babbar kasa. Tabbas sharrin zuciya yafi fa haka, to yanzu munji bayanin inda abokan tafiyarmu suke, amma kuma haryanzu baki fada mana dalilin da yasa kika ceci rayuwar mu ba. Koda Lafirat taji wannan tambaya sai tace, ai nafada muku bukatata da kuma dalilin da yasa na ceci rayuwrku tun a cikin labarin da na baku ni da 'yar uwata. Bukatar kuwa itace ina so ku taimaka min na samu damar da zan iya hallaka mahaifina wato sarki sha'aran da kuma yar uwata sazirat, domin a binciken da nayi dole sai na hada kai da ku domin samun wannan nasara na cika burina. Sa'adda Uzaifat ya ji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya yace damu dake duk bukatar mu irin daya ce bambancin dake tsakani kawai shine, ke kina sone ki kashe sarki da Sazirat don sun aikata wancan aikin, mukuma muna so ne muyi jihadi mu kafa turar musulunci a kasar. Abinda nake so dake shine zamu taimaka miki amma bisa sharadi guda daya, sharadin shine zaki mana rakiya izuwa kurkukun birninku inda aka kai abokan tafiyamu domin na ceto rayuwarsu, kuma na dauko 'yar likita Abu sharaz a cikin wannan gidan gona inda aka tsareta, inyaso sai mu koma can kasarmu domin muyi sabon shirin yaki. Kuma naje na ga halin mahaifina ke ciki, yana rayene ko ya mutu?. Koda jin wannan batu sai Lafirat ta kwalla ihu mai razanarwa, sannan tace, ai kazo min da abinda yafi karfina. Idan har na bika izuwa cikin birnin mu tabbas hallaka zanyi, burina bazai cika ba, domin ban gama shirye shiryena ba na tunkarar ubana da 'yar uwata, A kalla ina bukatar wata uku nan gaba kafin na kammala shirina. Shawarata agareku itace, ku koma da baya zuwa birninku kuje ku sanar da jama'ar ku abin da ya faru, domin kuyi gagarumin shiri kafin su sarki Sha'aran su iso birninku don yakar ku. Nima zan kawo gudunmawata idan yakin ya taso. Koda jin haka sai Uzaifat ya dubi Lafirat a cikin fushi yace, yake wannan basadaukiya kiyi sani cewa ni bazan koma da bayaba, ba tare da na kaiwa 'yan uwana dauki ba! Da dai na koma na tare da cikakken labarin su ba gwara na sara rayuwata. Idan har ba zaki iya yi mana jagora ba izuwa birnin shumbul to ki samu a hanya, in kuma ba haka ba sai dai mu ma mu warware alkawarinmu na baki had in kai. Yayin da Lafirat taji haka, sai hankalinta ya dugunzuma, tarasa abinda ke mata dadi a duniya, don haka sai ta kasa zaune ko tsaye. Tayi ta kai kawo a cikin fadar tana tunani. Alhamdulillahi nan zamu dakata sai kuma Allah ya kaimu gobe zamu ci gaba fatan kuna jin farin ciki bisa sharhin wannan littafi, na barku lafiya. UMAR FAROUQ ZANGO