Assalamu Alaikum بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ Page 1️⃣ ⏩2️⃣ *ABUJA* _Sardauna crescent City_ ________Mota ce ta shiga wani babban gida, wanda kaf layin shine maƙura a haɗuwa, gidan mai bene ne, ya haɗu ma sha Allah, black gate ne wanda desire ɗin sa abin tsayawa ne kallo ko in ce background ne ma musamman. Ciki kuwa hmmmm interlock ne a zube ya malale cikin gidan, ga flawers da aka zagaye haraban gidan da shi, sannan daga can gefe akwai garden wanda ke ɗauke da bishiyoyi na fruits daban-daban, sai wani gefe guda parking lot ne In da motoci uku harda wanda aka shigo yanzu, ƙiran Sport blue da ƙiran BMW ash, sai wanda aka yi parking Rolls-Royce white ƙal, take aka buɗe ƙofan motan tare da fitowo, tsayawa na yi cak dan ganin wa zai fito, sai ga wani haɗaɗaɗdan Handsome guy, a ƙalla ba zai wuce 27yrs ba, saurayi mai jini a jika, ba ƙarya daga sama har ƙasa ƙyakkyawa ne, haka kuma maji ƙarfi, ba fari bane irin choculate colour ne, irin aikin ɗin nan mai garesa da ƙyalli, yana da tsayi haka kuma faɗi ma, sai masha Allah, tafiya ya fara yi cikin gidan cike da natsuwan da ya zama mai abokin rayuwa. __________Ma sha Allah, ma sha Allah, wani irin gidan ko ina ce aljannar duniya, baban falo ne irin wanda nake gani a finafinan ƙetare, komai na ciki royal blue ne da fari, komai na wal-wal, an zuba kujeru a babban parlour in da ya ci set huɗu, sannan ga wata arniyar tv mai rai da lafiya. Ga wani labulaye masu matuƙar ƙyau. Ba makusa a falon, sannan da ga ba na zaman mutum ɗaya ba ne, domin tsaf family guda za su sauna a wadace. A hankali saurayin nan ke bin ko ina da kallo, take ya saki wani murmushi mai sanyi, sannan ya buɗe baki cike da taushin murya ya ce. “Soon buri na zai cika, a wannan gidan” ya faɗa yana zama kan ɗaya daga cikin kujerun parlour. ************** ****************** ************* ********** *_KADUNA_* _POLYTECHNIC_ _____________ Mota ce ta shigo cikin makarantar ƙiran buggati da uban gudu, wanda ya sanya mutane kaucewa daga hanya, parking lot ta nufa sannan ta ci uban burki, an ɗau kaman minti uku kafin aka buɗe mazaunin driver, ƙafarta ce ta fara saukowa cikin takalmin Snickers black, sannan sai da ta ɗauki ɗan lokaci kafin ta fito gaba ɗayan ta. _________Wow ma sha Allah, budurwa ce ta sauke cikin shigar Abaya Black sai ta yafa Vail ɗin a kanta, kana iya hangen yadda kashin kanta ya kwanta ya yi kyau sosai, eyes glass ta cire tana danna car key ɗin, tafiya ta fara yi cikin natsuwa da aji, kowa Binta yake da ido dan yadda shigan ya hauta tamkar ba school ta zo ba. ____________Direct department ɗin su ta shiga kai tsaye, tana shiga aka hau ihu sauran students ɗin, ɗaya daga cikin kujerun cikin ajin ta nufa ba tare da ta ce komai ba, ta na zama sauran ƴam matan da ke gun suka ɗan yi murmushi da ganin shugabar su ta iso, ɗaya daga cikin ladies ɗin ce ta ce. "Mymoon, kina kashemu da wanka fa." sai a lokacin ta kallesu sannan ta buɗe baki a hankali ta ce. "Hmmm Ladies, a gajiye na zo school, da badan akwai text ba, da ban zo ba, kuma gashi yau na makara sosai." ƴar dariya suka kwashe sannan wata ma ta ce. "Daɗi na dake Mymoon akwai ɗaukan serious, yanzu fa kika zo, ko gaisuwa ai ma yi." Mymoon ta kalla friends ɗin ta su uku, suma ƴam mata ne masu ji da class - kyau - da ƙuruciya. "Merry kenan, bansan carryover and kuma level na ƙarshe ne, dole mu mai da hankali." "Ma'esh ga guy ɗinki can ya iso." wacce ke gefan Merry ta faɗa ta na kallo wani ɗan saurayi da ya shigo. "Muheey ina yawan faɗa miki ki dena haɗani da waccan yaron. Uhmmmm ladies ku tashi muɗan zagaya mana, tunda an sanar Sir Kashim ba lafiya." ba musu suka miƙe kowa cikin shigar da ta hau ta, suna fara tafiya kowa na class ɗin ya na binsu da idanu, dan suna burge jama'a da yawa hatta lecturers ma in sun ga wanna tawagan sai sun bi su da idanuwa. _________Sune ake ma take da M - Ladies, domin dukka su huɗu sunan su da letter M suka fara. Mymoon - wato Maimuna Tahir ƴar shekara 22, yarinya mai ji da dukiya - kyau - da ilimi, kyakkyawa ce ta ta gaban kwatance, ita kaɗai iyayenta suka haifa, shi yasa take wadaƙa da dukiya yadda ya taso dan Babanta baban attajiri ne wanda ke sahun gaba a masu kuɗin Nigeria gaba ɗaya. Ta ɗauki ƙawayenta da daraja dan haka take sakar musu kuɗi dan su fito gari kamar Ita. Ita kuma Merry wato Maryam Nuraddeen mai kimanin shekara 21, ita kuma ita ce kaɗai mace a gidan su, Babanta babban soja ne ya mutu tun tana ƙarama, tana da yayyani maza huɗu wanda suka maye mata gurbin mahaifinsu, ita ce ƙarama kuma dukkan su sojoji ne su ma, duk suna ji da ita hakan ya sa take wadaƙa da abin da suke ba ta, haka kuma Mahaifarta babba likita ce. Ma'esh wato Ma'ishat Muhammad Sani, shekarunta 21, yarinya mai ji da ƙwalisa da ƙyau, iyayenta sun rasu tana zaune ne a gidan yayarta wacce ta yi aure, mijin yayar ne ya ke ɗaukan ɗawainiyar karatunta, akwai dai rufin asiri na Ubangiji, amma rayuwar Ma'isha daban ne tana son ƙarya da harkar manya. Sai Muheey wato Muhibbat Yaƙub mai shekara 22, yarinya ce ita mai son duniya da shiga cikin manya, mahaifinta malamin islamiyya ne, haka dukkan yaran gidan duk sun yi saukan alƙurani kuma suna koyarwa a islamiyya, ita ma ba baya ba wajen ƙyua da wanka, ita ce kaɗai a gidan ta dage sai ta yi karatu mai zufi, da taimakon mahaifiyarta ta shiga daga nan kuma Mymoon take biya mata, kusan koda yaushe cikin aro sutura take dan ita ma ta cinye wankan, ba tai musu ƙarya ba ta nuna musu ita talakace, sai suke bata kuɗaɗe dan maganar kuɗi ba damuwar su ba ne jiƙakƙune sosai balle Mymoon, dan ita ma Ma'isha tana ji da Naira. Mymoon da Merry sun mallaka motoci manya-manyan dan haka suma Ma'isha da Muhibbat ke neman su mallaka ko ta wani fanni ne. *Tafiya suke kaman ba zasu taka ƙasa ba, tsayin kusan ɗaya, kuma dukkan su ma sha Allah ƙyawawa ne na bugawa a jarida, Mymoon - Muheey da Ma'esh farare ne sosai, duk da hasken kowa da ban ne, Merry ce mai duhu amma duhun mai ɗaukan ido, choculate ce mai sheƙi. Sannan suna da body shape mai kyau na ɗaukar hankali, ko wacce ɗauke take da babban wayarta, gaba ɗayan su I-phone 16 ne suka riƙe wa. * Zama suka yi a wani ƙawattacan waje da hutawa. "Nan da 25mnt Sir Umar zai mana text ɗin Sir Kashim, fatan kun yi karatu, kun san ba sauƙi cost ɗin shi." Mymoon ta faɗa tana bin su da kallo. "Ba ki da case, wai ya maganar........." Muhibbat ta katse maganar sakamakon tsayawan samari huɗu a kansu. "M-Ladies, Amicin Allah su tabbata agareku." Ba wanda ya amsa duk da Shamo ya yi maganar cikin sanyin murya da natsuwa. "Ladies muje class." Mymoon ta furta tana miƙa wa, a cikin rai Muheey ta ɗan yi ƙwafa dan tana jin haushi yadda suke share zafafan gayu kamar su Shamo. suna barin gun, sai mazan suka zauna a gun suna ɗan dariya ƙasa-ƙasa. "Shamo wallahi a wanna rayuwa kar kasha wiya, kawai kayi wuff da ɗaya daga cikin wa'incan shike nan, ka huta da komai ka zama mijin Hajiya mai capacity." Dariya suka sanya sai ɗaya shima ya ce. "Haka ne Abdul, ni Muheey ta fi tafiya da imani na, ina ma ta amince min, na aureta kaga shike nan naja ƴan canji sosai." "Uhmmm narasa mai ya shiga tinanin ku, ni wallahi da gaske na ke son Maryam, badan kuɗin ta ba, sannan ina son na mallaka nawa kuɗin da inganta rayuwar ta." "Abbas kenan, ana maganar capacity, kana shirme, wani inganta rayuwarta bayan a ingance take, rayuwar yanzu sai a hankali, Nigeria ba aikin yi, ni ba zan tsaya ɓata ma kaina lokaci ba gurin neman aiki, to mu matasa ya za mu yi?, Wallahi mace irin su kawai nake nema mai dukita.” dariya suka kuma yi dan Shamo akwai son duniya da son hutu gashi ɗan talaka. " Wait........ Abbas kai Merry - Shamo kai Muheey - Abdul kai kuma Ma'esh, ni kuma jagaba, shugabar tawaga (Mymoon).” "I.b shegen ƙura, kaine ai ka kwashe duka ganimar, kowa yasan irin dukiyar mahaifin Mymoon, gashi ita kaɗai ce, kana aurenta kai za ka maye dukiyar sannan ka yi karatu ba maganar raini mutuminaaaaa." Shamo yakai maganar yana imagine wannan lokacin ya zo musu. "Ba ƙarya wallahi, yanzu muje class, zuwa gobe za mu fara takun ɗana soyaya, dan babban tarko za muyi musu." Abdul ya faɗa suna tafawa da Shamo, jerawa suka yi suna tsara yadda salon tafiyar zai kama, shi dai Abbas sai jinsu yake kawai. __________ Samari ne su, irin handsome guys ɗin nan, suna ɗaya daga cikin matasa masu ji da wanka a kaf school ɗin, abokai ne tin secondary school, kuma layin su ɗaya, dukkan su shekarun su 26 ne, abota mai tsafta suke yi, gasu da brain, idan suna speaking English sai ka za ci ba a Nigeria suke karatu ba, hakan ya sa suka ɗauka ka, dan kusan komai suna kan gaba. ________Babu wanda yake sana'ar annu a cikin su duk dun dogara ne da karatu, amma a yanzu Shamo - Abdul da I.b sun can za kota yayane so suke su aura mace mai dukiya domin su huta, Abbas ne ya ƙi biye musu amma duk da haka suna tare, ba tawagar da Shamo yaga sun cancanta da su sai M- ladies, duba da yadda suke ji da dukiya.......... **************************************** *KANO* * Wani madaidaicin gida ne a cikin wani gajeren layi, ba laifi gidan ko ina a gyare yake tsaf duk da na masu ƙaramin ƙarfi ne, wata budurwa na hanga tsaye a tsakar gidan, tana sanye ne doguwar riga ban iya tantance yanayin ɗinkin dan ta sanya hijab wanda yake dai-dai gwiwarta, ma sha Allah, yarinya ce ƙara ma wacce ba za ta wuce 20yrs ba, fara ce ƙal dan ko tabo babu a fuskarta, niƙaf din dake kan igiya ta ɗauka tare da ɗaurawa. wow babu abin da ake gani a jikinta, dan ƙafarta sanye cikin safa haka hannunta ma, hatta ƙwayen idanunta a baka tantance ya suke dan niƙaf ɗin ma ɗinkinsa daban ne. Jakkarta wanda yana kan kujera ta ɗauka tare da riƙewa sannan ta haɗa hannu ta tafa da ƙarfi, jin shuru yasa ta kaɗa kai dan ta tina mahaifiyar ta na barci, fita ta yi tana mai addu'a fita daga gida. Tafiya take a hankali cikin takatsantsan, har ta isa bakin titi, hannu ta sa ta tari nepep ɗin da ya tawo, take ya tsaya dai-dai ita, sai ta buɗe jakkatar sannan ta bashi wani paper, amma ya yi ya duba, sai ɗan Dattijon ya ce. “Kurma ce ke?.” sai ta ɗaga mai kai. “Babban titi, dari biyu da hamsin ne, amma ko ban dari biyu.” ya faɗa yana miƙa mata parper, ta amsa tana mai alaman godiya sannan ta shiga cikin, bayan sun hau titi da ƙyau, ta lumshe idanunta tana magana a cikin ranta har suka isa wajen, kuɗin ta bashi ya ba ta canji, sannan ta kalla babban wajen da ya ajiye ta, a hankali ta sauke ajiyan zuciya sannan ta fara tafiya cikin wajen. Driver ne ya bita da idanu dan ta bashi tausayi. A tsakiyar cikin filin gidan TV na GOODNESS TV, gidan Tv ne da yake taka babbar rawa a hajar Kaduna. Ta tsaya tana mai bin mutane da kallo, dan akwai mutane ba laifi kowa na harkokinsa. A cikin ranta ne ta furta. “Ya Allah badan ni ba, badan halina ba, dan soyayyar da kake ma Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ❤️, kasa a yau na haɗu da CEO, ya min interview sannan na ci tare da fara aikin nan. Ya Allah ka cika min burina.” ta kai nan tana jin hawaye a cikin idanunta sai ci gaba da tafiya ta na mai ta ambaton Allah..........✍️ > Hmmmmm ✍️✍️✍️✍️ ba wasa *HASASHE KO BURI* tafiyar wannan na daban ne domin akwai abubuwan ban mamaki, taɓa zuciya, ruɗani da zalama irin na ɗan adam. Mu daihe zuwa.......... PAID BOOK ne 😏 by PRETTY SK NOVERLIST 🥰 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖 https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t *_HASASHE KO BURI_* _SADAUKARWA_ *🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).* You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! 💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍 🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️ Page3️⃣⏩4️⃣ *KADUNA* *Bayan an kammala text, suka aka yi lecture sannna aka tashi, a parking lot suka tsaya suna ɗan tattauna daga baya Mymoon da Ma'ishat suka hau motan Mymoon suka bar school ɗin, sannna ita ma Muhibbat ta shiga motar Maryam dan sunfi kusa suka bar school ɗin. Da idanuwa suka bi motan Maryam da ya bar makaranta, wani ɗan sanyi ne ke ratsa zuciyar Abbas in dai a ga wani abu na Maryam balle da ya hangi fuskantar ta. Trekking suka sha har gida duk da akwai nisa sosai, bayan sun shiga layin nasu, wani gida suka shiga ina da ba za ka yi tsammanin ganin su ba, ɗakin dake zaunen gidan suka zazzuna kan katifa. Gidan su Abbas ne da Shamo dan su gidansu ɗaya imfact yaran kishiyoyine amma babu mai ganewa dan wata muguwar shakuwace tsakaninsu, Ibrahim da Abdul kuma duk maƙotane amma ana suke ƙwana in da suka yi ƙofa ta waje, da yake ɗakin ba laifi akwai girma, katifar biyu suke amfani da shi sannan ga tsohuwar wardrobe ɗin su, wanda ana suka sanya kayansu, sai kuma renting da suke yi wajen Ado mai wanki. “Na samo Numbers ɗin M-Ladies, na tura muku ta whatsApp.” Shamo ya faɗa tare da ciro arniyar wayansa. “Wow mutumina, a gun Zubaida ka samu ko?.” “Eh mana, sai ku fara gina love tin yanzu, balle kai I.B kasan Mymoon akwai ji da kai.” dariya suka yi sannna Abbas ya ce. “Hmmmm Allah ya ganar da ku, dan wannna hanyar akwai matsala.....” “Kul, kar ka mana mugun baki, yadda kake son Maryam haka muke son namu.” “Dena tada jijiyan wuya, ni kunga na fita dan yau zan fara zuwa gareji.” dariya suka kwashe suna mai a dawo lafiya. Shikam ko a jikinsa ya yi waje tare da nufan gajeri dan fara aikin da ya sha wuya aka bashi dan wai ya girma sosai. *Ma'esh* A ƙofar gidan su Ma'esh ta faka, sannan suka yi sallama tare da rabuwa, ba ƙwarya, gidan su Ma'esh ya haɗu sosai, ciki ta shiga a in da ta hangi mota baƙa a harban gidan tana mai cin burin ta fara zuwa school da ita. Wani parlour ta shiga wanda ya gaji da haɗuwa, a kujera ta zauna tana kallon TVn dake aiki, ta jima babu motsin kowa sai daga bisani wata mata ta fito daga ɗaki. “Ma'esh kin dawo?.” matar da a kallo ɗaya za ka ga mugun kaman da suke yi, sai dai shekaru su banbance. “Aunty na dawo.” ta faɗa da kyar. “Lafiya!? Me aka miki?.” wacce ta kira da Aunty ta nufeta da sauri, dafata ta yi tare da sanya hannu ta share mata hawayen idanunta. “Faɗa min, what's wrong?.” Aunty ta faɗa. “Na faɗa miki I need my own car but.....” sai wasu hawayen, da sauri ta miƙe tare da barin parlour, da idanu Aunty ta bi ta, tana mai jin zafi a ranta, dan idan kana so ka kanta a wani hali ka taɓa mata Ma'ishat. “Bara Alhaji ya dawo dole yasan abin yi, domin buri na shine faranta miki rai.” Tana shiga ɗakin ta kulle tare da hawa kan gadonta, wanda ya gaji da tsaruwa. Tasan dole Aunty ta ɗau mataki. *Merry* Merry tana yin horn aka buɗe mata, sannan ta shiga, tana yin parkinga ta nufi cikin parlour su, masu aiki ne kawai ta tadda dan har lokacin Mom ɗin ta ba ta dawo ba. Ba laifi nan ma gida ne mai sunan gida, dan a kwai komai na more rayuwa, kuma ko ina ya ji kuɗi, kana isowa za ka gane gidan sojoji ne dan uku suna gadi ta waje haka ciki akwai mutane biyar, manyan sojoji masu ƙarfi. *Muheey* *Kwance take kan kujera tana latsa waya cikin nishaɗi, dan tin bayan da ta shigo daga school ta haye kujera tana chart da wani wanda ba ta san waye ba, murmushi ne kwance a kan fuskarta. Sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa a kallo ɗaya za ka ma gidan ka fahimci akwai rashin wadata kaman na sauran amma akwai rufin asirin Allah, kiran sunanta a ka kuma yi dan haka ta miƙe da nufi ƙaramin tsakar gida amma a ɗan gyare yake. “Haj. gani.” ta faɗa tana isa gaban matar dake zaune kan tabarma tana yankan kabeji. “Na faɗa miki ki sha gari ki zo ki amsa girkin nan, kafin ki fice, yau Allah ya yi kin leƙo mu.” wani abu ne ya tsaya mata a rai, amma ta kasa magana, ganin haka bai da amfani shi yasa ta koma ɗaki dan shan gari ta amsa aikin kafin ta bar gidan zuwa in da take ƙwana. *Mymoon* Wani haɗaɗɗen place ne mai matukar haɗuwa, yana bene haka kuma ya tsari, stairs Mymoon ta fara takawa zuwa bedroom ɗinta, bayan ya shiga aljannar duniyar ta, ta shiga bayi ta yi wanka sannan ta fito ɗaure da towel tana tsane dogon gashin dake kanta. Zama ta yi tana mai kallon chocolate ɗin da ke kan bed, da sauri ta dauka tare da yaga ledan ta kai baki, dan ita akwai son kayan zaƙi. ************************************* *KANO* Bayan ta shiga wajen direct in da jiya ta shiga nan ta nufa tana da maimaita addu'oi a cikin ranta. Ta riga ta saba duk in da ta bi sai an zuba mata saboda irin shigarta, dan a yanzu ko a jikinta dan an bi ta da kallo. Bayan ta shiga wajen da kai ta gaishe su, sannan ta hau layi, in da mutane huɗu ne gabanta. Daga kallon wajen ta fahimci wanda ake jira yana nan. Wayarta ta ciro tare da rubutu sai ta miƙa ma wacce ke gefanta, da yake jiya sun haɗu to tasan ba ta magana dan haka ta amsa ta karanta sai ta ce. “Hmmmm Sister, wai ce wa ya yi da baki zai mana tambayar kuma mutane biyar zasu ɗauka dan suna da mutane.” da jinjina kai tana kuma wani typing ɗin, bayan ɗayar ta duba ta ce. “A ƙalla mutane 15, sun shiga kuma gamu mu huɗu.” alaman godiya ta mata tana mai da wayan tare da tsare ƙofan da kallo har wanda ke ciki ta fito, sannan wani ya shiga, haka haka har wacce ke kusa da ita ta fito rai ɓa ce, a kallo ɗaya ta fahimci akwai matsala, dan haka ta dafata tana ɗaga mata kai. “Na haƙura nikam, ki shiga Allah ya sa ki da ce.” daga haka ta wuce, take jikinta ya yi sanyi, sannan ta nufi ƙafan ta tura a hankali, tana sallama a cikin ranta. Duk da tana cikin niƙaf amma sai da lafiyyan ƙamshi ya dake ta, lumshe idanunta ta yi, sannan ta kalla officer ɗin, ba laifi ya haɗu, duk da akwai abubuwa da ko ina na da ga na'urori, cameras da dai sauransu. Namiji ne ta hanga tsaye jikin glass yana kallon haraban gidan tvn, matsawa ta yi ta zauna tunda ya ji ya tashi. Tsaye yake cikin manyan kaya, hannusa riƙe da flask tea yana sha a tsaye, juyowa ya yi tare da nufo in da take tsaye sannan ya mata alama da ta zauna, a ɗan daburce ta zauna dan ya mata ƙwarjini. Guy ɗin ya haɗu ma sha Allah, dogo mai cikar kamala. Shima zama ya yi. Yana mai kallonta dan ko ƙyayar idanunta ba ya gani. Take wayarsa ta kuma yin ringing sai ya ɗaya. “Darling still mace ce......” take ta jiyo muryan mace ta cikin wayar tana cewa. “Ta yi waje, na faɗa maka maza zalla.” “Wanan matar aure ce fa.” ya faɗa yana kuma kallon yarinyar da ke zaune. “Juya cameras kanta ya yi.” kafin ya yi magana ta katse, sannan ya yi latse-latse a System, ba'a jin ba ma wayar ta kuma yin ringing. “Ka mata interview ɗin.” “Okh my Darling.” daga haka ya sauke ajiyan zuciya yana mai faɗin. “Takaddu.” da yake ta ciro sai ta miƙa mai ba tare da ta falle rubutun ba, ya amsa yana dubawa. “Uhmmm your full name.” da sauri ta miƙa mai wani paper ya amsa ya kalla. (My name is Ameeratulkhairi. Sa'adatu Jibril) shine a rubuce sai ya ɗago da ɗan faɗa. “Ba ki da baki ne, dan kina matar aure, ba za ki yi magana ba?.” da sauri ta kuma miƙa mai wani, kamar ba zai amsa ba sai ya amsa. (Bana magana, Bebiya ce.) Take ya ji wani abu ya tsirga a zuciyar sa. Sannan yaji tausayinta sai ya aje. “Na fahimta, kinsan kafin na baki aiki dole kiban labarin ki, da dalilin son aikin journalist, da kuma irin gudummawar da za ki ba da sai kuma wani fanni dan na ga ba ki yi zurfi a karatu ba.” ɗaga mai kai ta yi sannna ta cori wani littafi tana miƙa mai. Ya amsa yana mai buɗe wa. ( Buri na shine zama ƴar jarida) shine ya fara cin karo da shi sannan ya ɗago ya kalleta. “Ki je gobe ki dawo, misalin 1:30pm, in dai labarin ki ya gamsar shike nan.” godiya ta mai da hannu sannna ta yi fara tafiya, sai ya samu kansa da bin bayanta da kallo da sauri ya ɗauke kai yana cewa. “Ki gaidamin mijinki, bangan shi ba amma ya burgeni da yake sa ki yi wannan shigar.” murmushi ta yi tana mai ɗaga kai tafice. Take ya hasaso Darling cikin shigar nan za ta yi ƙyau amma ko mutuwa zai yi ba za ta sanya ba, yara sa maike yawo a kansa ne, da zarar ya bar gida yakan ta jin wani yanayi akan ta da kuma abubuwan da baya so ta na yi, amma da ya ji muryanta ko ya koma gida shike nan sai ya mance. Kallon rubutun ya yi da ya yi mai mugun ƙyau, ita ce ta ƙarshe dan haka ya buɗe shafin gaba. (Labari na mai ɗauke da darasi da haƙuri.) Sai ya yi murmushi ganin rubutun da yawa ya sa ya miƙe sannan ya hau kan sopa ya hau karatu............. *ABUJA* Office ne wanda yake cike da takkadu, zaune yake kan kujera yana latsa system sannan yana kallon screen ɗin, knocking aka yi ya ba da umarnin shigowa. Take aka shigo, wani saurayi ne sa'ar shi, yana rike da laptop ya ce. “Aboki na kammala.” sai ya kalla abokin na sa ya ce. “Good job, yau za ka raka ni wani waje.” “Hmmmm na san yanzu burinka kawai kake so ka cika, amma a ganina Ukasha ka sauya shawara please.” sai ya bar latsa system ɗin ya zuba ma abokin na sa idanun. “Umar, dole na cimma wannan burin na wa, a yanzu biyu na ƙasa saura biyu, na tambayeka, burina zan fasa? ko na Hussain ɗina?.” “Haka ne, shike nan, Allah ya cika maka burin na ka.” “Ameen Umar, nan da watan biyu nake so na yi auren.” sai Umar ya ja numfashi yana kallon Ukasha take magana a cikin ransa..... 'Shin kunsan waye Ukasha?, Kunsan labarin rayuwarsa? Kusan ya halinsa? Kunsan ya nake haƙuri da rayuwa da shi? Kunsan ya yake ɗaukan Burinsa? Wai ma kunsan menene Burin? To Bara na baku labarin a kan Ukasha da kuma Burinsa...........✍️ > To Umar za mu haɗu next page. Still C.E.O muna jiran labarin Ameeratulkhairi. Sai jama'ata kunsan ina yin Ladies kuwa, haka su Abbas ma..........hmmmmm......akwai aiki...... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️🥰🤗. https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t *_HASASHE KO BURI_* _SADAUKARWA_ *🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).* You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! 💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍 🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️ Page5️⃣⏩6️⃣ *KANO* ______Bayan ta koma gida, a parlour ta iske mahaifiyarta zaune tana kallon TV, zama ta yi kusa da ita tana mai cire niƙaf ɗin. Mahaifiyar da ke zaune hancin su ne iri ɗaya, amma ba sa kama sai haske duk da hasken Ameeratulkhairi na daban ne, tana cire niƙaf ni ƙyakyawan fuskarta ta bayya. Hmmmmm haske har kashe ido yake yi, murmushi ta saki wanda fararen haƙora ta suka bayya tare da dimple ɗin ta da suka lotsa, kusa da ita ta zauna tana magana da hannu wanda mahaifiyar ta gane sannan nima na gane saboda Allah ya min baiwar hakan. “Insha Allah komai zai yi dai-dai, ance gobe na koma, ki ta ya ni da addu'a.” shine abin da ta furta sai mahaifiyar ta ɗaga mata kai. Sun jima a nan suna kallo dan shirin da ake haskawa akwai daɗi. Su biyu suke rayuwa a gidan wanda shine kaɗai suka mallaka daga uban dukiyar mahaifinta wanda ya rasu. Kuma Alhamdulillah suna cikin godiyan ubangiji. Ɗan ƙaramin ɗakin ta shiga in da ta ga wani littafi akan ƙaramin gadonta, ta sauri ta ƙara da tana ɗauka, take da dafe ƙirji tana fita riƙe da littafin, maihifiyar ta juyi da sauri dan jin yadda Ameeratulkhairi ta buƙa ƙofa , kai ta ɗaga mata alaman tamabaya (Lafiya). Ƙwatance ta shiga yi wa Mamar tana haɗawa da hannun tare da nuna littafin. Da sauri Maman ta waro ido tana wani irin salo da hannunta. ( Sai da na jima kafin na gane mai ta ce) “Garin ya?.” sai naga Ameeratulkhairi ta zauna daɓas. “Kar ki damu, insha Allah ba zai karanta wancan ba, ko kuma alhaki na ne, nai ta ki ban na karanta littafi sirrinki mai suna SIRRI ki hanani. Hmmm ai shike nan ga wani ya samu a sama.” Mahaifiyar ta buɗi baki ta koro wannan zancen da hausarta wacce ba ta wani zauna ba. Take hawaye suka gangaro a cikin idanunta, a yau ta yi dana sanin rubuta gajeren labarinta a irin littafin SIRRI, littafin iri ɗaya ne, dan na Sirrin ya cika shine take so ga fara a sabo, sai ta rubuta gajeran labarin a shafin farko, saboda kar ya ɓaci shine ta bari idan ga je can ta falle, to gaba ɗaya hankalinta ya yi gaba. Kuma jiya duk ta yi rubutu a ciki, hasali ma a gu ɗaya suke, yanzu idan ya karanta wannan shike nan ya gama sanin komai aka ta. Ta sha ainiyin ko wanda za ta aura ba za ta so ya gani ba. Akwai abubuwa da ita kaɗai take son gani, wani ta rubuta dan nishaɗi, wani tana kuka tana rubutawa, wani kuwa duk wanda ya karanta dole ya ta ya ta kukan. Ji take kaman ta fita ta koma sai dai tasan Amma ba za ta barta ba......... *ABUJA* Umar ne ya lumshe idanunsa tare da fara karanto min waye Ukasha?. *Ukash wato Hassan Muhammad, haifaffen Abuja ne, Mahaifinsa baban attajiri ne, maihifiyarsa kuwa baturiya ce, a America Alhaji Muhammad ya auro ta, bayan sun yi ɗan rayuwa a can sai suka dawo Nigeria saboda business ɗin sa. Alhamdulillah yana samun kuɗi fiye da tinin mai tunani, sannan yana da alheri sosai, a Nijer yake, haifaffen can ne, shi kaɗai ne ya yi rai a wani gobara ta ta cinye ƴan gidan su, sannna ba wani zumunci ake ba da ɗangiba dan wasu ko saninsu bai yi ba, Kasuwanci ya baro da shi daga ƙasarsa, ya gina sabuwar rayuwa a nan. Bayan ya yi kuɗi mai sunan kuɗi, shine wasu daga danginsa ke waiwayansa, ba laifi yana ƙyautata musu fiye da misali. Sun ɗau lokaci shi da Rose kafin ta samu ciki, a gun haihuwa ta mutu, dan ko musulunta ba tai ba, ya yi iya yinsa Alhaji ganin ta musulunta amma ta ƙi. Tweens ta haifa masu matuƙar kama da shi. Ya ƙi wani auren dan haka ya neman musu wata tana rainan mai su, har zuwa fara tafiyan su, Hassan - Ukasha da kuma Hussain - Sadik, sun taso kansu ɗaya matasa masu jini a jika ga wayau da fasaha, ba yadda za ka yi ka banbance dan komai na su iri ɗaya ne, hatta mood ɗin su sauyawa yake, in yau wannan ne yake da fara'a ko gobe ɗayan ne, abu ɗaya zaka banbance su shima sai kuna tare shine idan suka yi magana domin Hassan ya fi taushin murya shi kuma Hussain muryansa na da sauti. Haka rayuwa taita tafiya har suka kai shekara 24, a wata rana kuwa aka wayi gari babu Alhaji Muhammad, wanda hakan ya yi sanadiyar bugawa zuciyar Hassan dan akwai shi da rauni sosai. Tabbas a lokacin saura kaɗan Hassan shima ya mutu dan har ƙasar waje aka kaisa, ya jima yana jinya kafin ya dawo dai-dai, Ni Umar nine abokinsa na layi, dan haka ni ya mayar ɗan uwana, komai da ni yake tattauan. Sai dai me Ukasha wani irin mutum ne wanda mai tsatsauran ra'ayi, in ya ce abu to babu fashi. Yakan zo min da tambaya na bashi shawara, haka zan zauna na jero mai sai da ƙarshe ya ce nasa ya fi. Yana da halaye masu ƙyau shi yasa har yanzu nake tare da shi, akwai mutumci, sai dai baya ɗaukan raini da wasa, haka baya son yawan magana, shi dai a yi shuru kawai ayi shuru, ba ya yawan magana, hmmmmm karna jaku da yawa, bara dai na faɗa muku burin sa. Yana da buri biyu haka marigayi Hussain ma, burin na su ko na ce hasashensu suna ɗan kama sai dai akwai banbanci. Ukasa Burinsa na farko shine cimma wannan matsayin da yake kai yanzu kenan, ya sha wiya sosai amma sai da ya ga ya cimma mallakan kamfanonin da ya yi niyya, baya damuwa da ko nawa ne zai ɓatar in dai ya cimma Burinsa, Sai na biyu shine Aure, yana son ya aure mata biyu a rana ɗaya, Bahaushiya da Bafullatana. Hussain ma ya cimma Burinsa na farko, wanda sai da ya zageye ƙasashe 15 na duniya, na biyun kuma shine auren Yoruba da Igala, domin yana son al'adar yare. In da abun yake shine; Ukasha ya ƙulla aniyar cika ma Hussain *Burinsa* dan haka ya yi *Hasashen* auren mata huɗu a rana ɗaya kuma kowacce da na ta yaren......... “Umar! Umar!! Umar!!!.” take ya buɗe idanunsa ya zuba ma Ukasha yana faɗin. “Na'am.” “Tinanin me kake yi?.” “Babu komai, Bara na koma office ɗina.” ɗaga haka Umar ya miƙa tare da fice, da idanu ya bi abokinsa har ya fice. Yana fita ya shiga nasa office ɗin sannan ya zauna yana mai faɗin. “Yau ko wani duniyar Ukasha zai kaimu neman yarinya oho........” sai ya lumshe idanunsa yana faɗi a cikin zuciyarsa “Ni yake sanya na bincika mai mace, sai na sha wiya na nemo irin macen da yake so, da munje sai ya ce ba tai ba, a ƙalla mun kai wata biyu amma mace ɗaya ce ta yi mai wata Bahaushiya, saura mata ukun........... *KADUNA* _Ma'esh_ haka ta hora kanta da ƙin cin abinci badan komai ba sai dan Aunty ta fahimci irin son da take ma mota, sam ta ƙi fitowa ma, har dare, tana jin lokacin da Uncle ya shigo wato mijin yayarta, aikam da shigorwa ko minti 10 ba'a yi ba yarinyar Aunty Rumaisa ta shigo ɗakin na ta. “Aunty Ma'eh, Momyna tana kiranki.” daga haka ta yi waje, hijab ta zura sanna ta yi waje, babu kowa a babban parlour sai ta nufa ƙaramin, bayan ta shiga ta zauna daga gefe tana gaida Uncle cikin ladabi. “Lafiya lau, Alhamdulillah, zauna a sama.” sai ta zauna tana facing Aunty, take Aunty ta sakar mata murmushi. “Maman Ruma na ji ta ce, kina son mota dan zuwa school.... To ai ba ki iya mota ba kuma kinga ita nake so na fara siya ma wa dan ta dinga kai Ruma school. Ki bari da na fara siya mata sai ke kuma duk a cikin shekarar nan insha Allah.” ya kai maganar yana kallon Aunty, sai ya ga ta haɗe rai, tare da miƙe wa ta nufi babban parlour. Ma'isha tasan yau dole a baka carkey, ba a jima ba Uncle shima ya miƙe ya barsu. A tsaye ya tadda da jikin fridge. “Hayathy......” “Dan Allah ka yi shuru Habiby, yanzu a ce Ruma ta girma ta nema abu kuma akwai amma a hanata." “Haba Hayathy, wallahi ba haka bane, yanzu kinsan banda wani kuɗi, shike nan zan fara siya mata.” “A'a ni banso, na haƙura." Sai ta fara tafiya da sauri ya riƙo hannunta yana zagayawa gabanta ya ce. “Kinsan na tsana na ganki cikin wani hali. Me kike so?." Murmushi ta saki tana mai cewa. “Kaba Ma'isha aron prado kafin ka siya mata." “Shike nan.” sai ta ɗaga mai kai. Tare suka koma ɗayan parlour, a idan Ma'esh ta saki wani murmushi dan ta san a yau dole burinta ya cika. “Na bar miki motata prado.” Uncle ya faɗa yana miƙa ma Ma'esh car key, da uban tsalle ta isa gabansa ta na amsa tare da mai godiya kaman za ta shige ƙasa, da yake ta iya mota sosai, da gudu ta bar ɗakin, Aunty da Uncle suka tintsire da dariya. *Muheey* * Misalin 4:12pm na rana ta zura hijab ɗin ta sannan ta fita a gidan, sai da ta ɗan yi tafiya mai tsayi domin kuwa layin na su akwai tsayo, wani gidane me gate black ta shiga, ba laifi gidan mai ƙyau ne, knocking ta yi ba'a jima ba aka buɗe, matar da ke tsaye ta kalla Muheey tana faɗaɗa murmushi tare da faɗin. “Na kira wayanki not reachable.” sai bayan da ta shiga harabn gidan tukun Muheey ta ce. “Network, na leƙa gida ne.” “Ni dai in ce.” A ƙawataccen parlour suka zauna, take muhibbat ta nufi wani ɗaki in da take ƙwana tana mai cire hijab ɗin ta, sannan ta zauna kan wani gado mai shegen ƙyau. Tana fatan Alhaji Ahmed kar ya dawo nan kusa, dan ko ya dawo baya fin sati ɗaya, yake koma wa aiki, in da a chine yake aiki a wani Company, yakanfi wata biyu a can. Ya auro ƴar uwarsa ce ya aje ta a wannnan layin, in da ya haɗa shegen gida, Mariya ba ta iya zama ita kaɗai a gidan kuma gashi su a salin ƴar Kebbi ne, shine Alhaji Ahmed ya nema da ɗaya daga cikin yaran Malam Yaƙin da a dinga ta ya Mariya kwana shine Muheey ta tare abinta, takan kwana biyu ba ta leƙaba, dan anan tana jin daɗin rayuwar gida kuma take fatan ta samu mijin kamann Alhaji Ahmed. Parlour ta dawo ta zauna gefen Mariya. Mariya ba wata babba ba ce dan da kaɗan za ta girma Muheey. “Aunty Mariya ina son na roƙe ki wani abu.” Muheey ta faɗa tana kallon Mariya. Ɗaga mata kai ta yi alaman ta na ji, take da dasa da faɗin. “Kinsan group ɗina na school M-Ladies koh?.” “Eh kina ban labarin su.” “To dukka suna da mota, wallahi suna cinye wankan, kina yawon faɗa min ina da ƙyau da iya jan hankali namiji, to wallahi a school sai kana filawa, hatta wasu daga kayanki in nasa sai na je ina jin nakai sai na ga sun kereni." Ta kai maganar tana mai da idanunta ga tv, hannu Mariya ta sa tana dafe kafaɗarta. “Wallahi Muheey, kina da ƙyau sosai, kuma insha Allah mai kuɗin dai za ki aura, yanzu dai ki bari zuwa gobe duk yadda muka yi da Alhaji, sai na faɗa miki, sai ki dinga aron motata tunda ni yanzu na bar zuwa aiki saboda ciwona.” takai maganar tana ɗan tari. Take tausayin Mariya ya kamata saboda ita sikila ce, yau lafiya gobe rashin lafiya a haka dai take lallaɓawa shi yasa tabar aikin da ta fara yi anan...........✍️ END. > Hmmmmm ✍️✍️✍️✍️ ba wasa *HASASHE KO BURI* tafiyar wannan na daban ne domin akwai abubuwan ban mamaki, taɓa zuciya, ruɗani da zalama irin na ɗan adam. Mu daihe zuwa.......... PAID BOOK ne 😏 by PRETTY SK NOVERLIST 🥰 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 Part 7️⃣⏩8️⃣ *ABUJA* _____Sun jima suna tafiya a mota kafin Ukasha ya yi parking a gefen wani gida sai a lokacin ya buɗe baki ya ce. “Common ƴam mata huɗu sun gagara ka samo min, ji bi wadda ka kai ni wajen ta last hmmmm.” “Ukasha, kai fa kace mace ta kasance da abubuwa biyar na farko mai natsuwa, siririya, mai sakin fuska sannan wacce tsayinta kar ya wuce ƙirjinka, sannan mai addini. Amma ba ya maka duk wacce na kawo maka.” “Kai ne ba ka iya tsaɓe ba sam, Murja - Bahaushiya, wata ƴar lukuta da ita, sam ba ta min ba.” Fita suka yi yana mai kiran wata number, bayan ya yi magana ya ce ma Umar. “A facebook muka haɗu, kuma hotonta ya min shine na zo na ganta, Fulani ce.” kai kawai Umar ya ɗaga yana tsanar wanna burin na Ukasha. Basu jima ba wata ta fito daga wanna gidan. Budurwa ce amma mai irin garin jikin nan dan za ka sa ci ta haihu ma, bayan sun gaisa, Umar ya shiga mota yana matse dariyarsa, domin kuwa wannna sam ba za ta yi ba, ta na da ƙiba sosai, haka kuma daga ganinta akwai rawar kai. Bai jima ba ya shigo motar tare da figarta da uban gudu. “Malam ban shirya mutuwa ba.” Umar ya faɗa yana murmushi sai Ukasha ya ce. “Wallahi ba haka hotan yake ba, gaskiya Umar ka ci gaba da neman min maybe na dace.” Haka suka ɗan yi hira har suka isa, wanda kusan dukkan hirar akan sauran ƴam matan ne. Wani gida suka nufa, bayan sun isa, a parlour Suka zauna sai ga wata mata ta fito daga ɗaya daga cikin rooms ɗin ciki. A kallo ɗaya za ka ga kamarsu da Umar, gaishe ta suka yi, ta amsa tana mai zama. “Kun dawo lafiya?.” “Alhamdulillah Hajja." Ukasha ya faɗa, bayan sun ɗan jima suka bar ɗakin, wani ɓangaren suka nufa, ba laifi gidan ya haɗu, dan wannan ma gidan Ukasha ne ya dawo da abokinsa tare da iyayensu gidan, tare suke rayuwa dan shi kaɗai ke rayuwarsa. Zama Umar ya yi akan bed ɗin su, shi kuma Ukasha ya nufa toilet dan yin wanka; har lokacin Umar bai bar dariya ba, dan Ukasha ya shaƙa sosai. A hankali ya ce. “Allah ka nunamin ranar da burin Ukasha zai cika..... Hmmmm akwai drama sosai." Sai ya ɗan haɗe rai tare lumshe idanunsa yana faɗi a cikin ransa. “Ni kaina ina da wani Buri. Wanda shine ya hanani aure, ya hanani kula kowace mace, hmmmm wani lokacin ni kaina burin nawa na ban dariya, amma ina yawon hasashen lokaci na nan zuwa da zan cimma wannan burin nawa. Za ku yi mamaki idan na faɗa muku nawa burin domin ba sauƙin sam.”.......... *KADUNA* Su huɗu ke tafiya cikin ƙananun kaya masu ƙyau, duk da na Abbas bai kai na su ba domin shi na sa ne, amma su renting suka yi, daga class suke dan haka suka nufi in da suka tabbar da M-Ladies suna can. A hanya Shamo ya ke faɗin. “Ku zauna wasa, ni harna shiga ran Muheey, domin jiya munsha love, gashi yau da wata arniyar mota na ga ta shigo.” “Ba ka da wasa fa, ni kam ina ɗan shakka Mymoon ne, da na kira ta ko ma ta text." “Ka dai zauna wasa, ai yi ba kai, dan ni ma na yi ma Ma'esh magana, sai dai ba reply amma nasan za ta yi.” dariya suka dan yi Shamo na kallon Abbas ya ce. “Kai fa?.” “Tukuna dai.” daga haka suka hangesu zaune suna ɗan hira cikin raha. Ba ƙyarya sun haɗu iya haɗawa, sannan kowacce da irin ƙyauwun da Allah ya yi mata, kuma kowa akwai abin da ta fi wata. Bayan sun isa suka yi musu sallama, da yake yau Mymoon na cikin farin ciki sai ba ta ce su tashi ba. Amsa sallamar suka yi, tana mai jin annashuwa a cikin ranta domin Ma'esh da Muheey sun yi motoci, kuma har ta tsara class party da zasu yi a yau, dan tasa ansanar da kowa ya ɗan jinkirta. “In badamuwa zan iya magana da ke, Maryam.” suka tsinkayi Abbas ya faɗa, sai dai ba musu Maryam ta miƙa tana gyara gyalenta, ɗan gefe guda suka zauna sai Abbas ya ce. “I'm sorry in na dameki......” “No karka damu.” ta faɗa tana faɗaɗa murmushin da ke kan fuskarta. “Maryam, bansani ko za ki fahimci ni, domin ni ba maye ɗin ki bane, kuma ta yu kimin wata fassara, a gaskiya tun dana shigo school ɗin nan na ganki, na ji kin shiga rai na. Hmmmmm ina ta so na bayya na miki duk da ina da numbers ɗin ki amma ina jin nauyi, yanzu haka na faɗa miki ne saboda ki bayyani eh ko a'a duk da nasan a'a ne, in na ji daga gunki zan maybe na shiga hankalina........” dafiyar da Maryam ta yi shine ya katse mai maganar. “Abbas, ci gaba ina jinka.” daga haka ya dasa yana ji a ransa harya haƙura ma. “Idan maganata ba ta miki ba, to dan Allah ki ya ƙuri.” sai ya miƙe take ta ce. “Zauna ka ji.” ba musu ya zauna sannan ta dasa da ce. “Nasan kana sona tin ba yauba, nakan gane mai ƙyauta daga cikin idanun mutum. Hulaƙanta mutum baya tsarani na, sai dai zan ma albishir da cewa kana birge Merry tin ba yau ba, amma ka dage dan samun soyyayarta, kuma na zallar gaskiya.” daga haka ta barshi zaune baki buɗe, wajen Ladies ta koma in da ta tarda suna hira ne da su Shamo. Zama ta yi aka da sa da ita. Su da suke da confidence sai yau suka musu kwarjini, amma Abbas gashi har ya isar da na sa saƙon zuciyar zuwa ga burin ransa. Da misalin 2:30pm suka sha shagali, Maymoon ta yi wasan kuɗin, domin musamman aka yi order abinci mai rai da lafiya, aka kawo drinks da wasu abubuwan. A na cikin shagalin a filin ball in da aka musu decorating ya yi ƙyau. Hatta case Muheey da Ma'esh sun yanka, Wayar Mymoon ne ya hau ringing, ganin mahaifiyarta sai ta amsa tana fara tafiya saboda hayaniya. Kusa da department ɗin su ta tsaya tana faɗin. “Alright, thank you so much my dear.” ta faɗa tana kissing wayar, tana juyowa ta ga I.B tsaye ya haɗa hannaye waje ɗaya. “Lafiya?.” sai ya kalleta tare da faɗin. “Wannan adalci ne?, A ce ina kiyon abin da ya zama mallakina sai na fahimci wani yana so ya siya.” cikin rashin gane maganarsa ta ce. “Ka ce mai ba na siyarwa ba ne, ko ya jira ina zaka siyar sai ya siya.” “Bazan ta ɓa sai da wa ba.” sai ta fara tafiya, da yake ta gefe ne ba wani mutane sai ya shamma ce ta ya tsugunna gabanta tare da miƙa mata flawerr mai launin ja da green. “Wannan ba iya flawers ba ce, zuciya ta ce, dan Allah ki amsa tare da mai muhalli a cikin zuciyaki.” amsa ta yi sai ta ce. “Da gaske wannan zuciyar ka ne?.” ya ɗaga mata kai, sai ta saki murmushin mugunta sannan ta saki flawers take ta sanya ƙafarsa ta murje a jikin korayen ƙananan abubuwa dake tsirowa. Take I.B ya dafe zuciyarsa bai damu ba zuɓe ƙasa, dan shi a rayuwarsa yana son fina-finan soyayya to ya ƙare ta wannan fannin. Sai dai me faɗin da ya yi yana dafe zuciya, ya sa ci za ta yo kansa ne yana da gudu tana mai cillar da komai da ke hannunsa tare da ɗagoshi tana mai kalamai masu daɗi. Sai dai mai da ƙasan idanunsa ya ke kallon fuskarta, dariya ta yi sannan ta kaɗa kai ta yi gaba, ta barshi ƙwace dafe da zuciya................ *KANO* * Shafi na gaba ya buɗe tare da bin zanen da aka rubuta da *SIRRI* , mamaki ne ya kamasa sannan ya kulle littafin yana faɗin. “Anya wannan matar ba ta yi mistake ba, oho dai ni kam ina son na karanta ko dan handwriting ɗin ciki.” sai ya kuma buɗe wa, tare da fara karantawa. _Wannan littafin nawa ne Ni kaɗai, sirrina ne a ciki. Sunana Ameeratulkhairi, wato Fatima Abdullahi, na ta so cikin gata da jin daɗi, sai dai rayuwar bai min tsayi ba, haka kuma ban karaya ba na dage na jure. Hmmmm ni ina mamaki da wannan duniyar amma ina alfahari da cewa gidan biyu, akwai nan akwai can. Ina ma kaina nasiha da na dinga tina wa da wannan, gaskiya ina son kai na, kalla-kalla, uhmmm Bara na yi shafi-shafi dan sauyaƙe ma kaina_ Ƙarshen shafin kenan, sai ya furzar da iskan baki yana faɗin. “Anya ba mistake ba ne!.” buɗe gana ɗaya shafin ya yi kowanne da Tittle, Amma akan samu shafi huɗu-biyar kafin wani heading ɗin. na farko *Matsalata* , *Damuwata* , *Mafarkina* , *Burina* *Hashashena* *Farin cikina* sai na ƙarshe *Zuciyata* . Tashi ya yi ya zauna yana mai mamakin ko dan ita ba ta magana ne take rubuce-rubuce haka. Take ya buɗe sannna ya nufa *Burina*. *BURINA* _Zama ƴar jarida mai ɗaukan rahotonni, na so a ce mai jawabi ce sai dai matsalata ta rashin magana. Sai na sauya burin da zama mai ɗaukan rahotonni guri-guri, na dage sosai na yi karatu duk dan haka. Allah ka cika min burina, dana dinga yawo a duniya ina ɗauko rahotonni_ sai ta yi zanen hannu. Bai san murmushi ya ƙwace mai sai ya kulle yana ajiyewa akan desk tare da nufan cikin Tv station ɗin..... Sai yamma ya ta nufi gidansa dake G.R.A, Wani tsararren gida ya shiga, sannna ya fama motarsa Ferari ya nufa aljanar duniyarsa. Ƙofar mai numfashi ne, yana kusanto ta buɗe dan haka ya shiga ƙawataccen parlour wanda ya haɗu iya haɗuwa. Tsayawa muku bayanin zuɓin parlour ɓa ta lokaci ne. Tsayawa ya yi daga in da yake yana kallo macen dake saukowa daga stairs tana taƙu tare da girgiza, ba laifi ƴarinyar akwai ƙyau, a ƙalla ba za ta wuce 23yrs ba, ba fara ba ce tana da duhu, sannan tsiririya ce, sai dai akwai shape, dan rigar da ta sanya ya kamata sosai, tafiya take har ta ido gabansa yana kallonsa, ya fita tsayi sosai duk da tana sanye heal shoe ne. Akwai ta ƙananun ido amma akwai hanci mai tsini. Hancin ta kai jikin rigarsa ta shinahina sannan ta ɗago hannusa ta kalla sai kuma ta sanya yatsanta mai shengen ƙumba ta danna saitin zuciyarsa tana faɗin. “Fatan babu wata ƴar iskan da ta shiga nan?.” shikan wanna tambaya ya ishesa a ƙalla daga aurensu 1ye kenan amma kullum ya dawo sai an gaba duba shi da tambayarsa. “Darling Ni na kine ke kaɗai, har abada.” sai a lokacin ta saki murmushi sannan ta rungumesa ta na faɗin. “Your welcome Baby.” hannunsa cikin nata suka jera har bedroom ɗin sa sannna ta fita tabar mai ɗakin dan ya yi wanka, dafe kansa ya yi yana zama gefan bed, yana mai dafe kansa. A hankali ya nufa restroom, sai da ya sakan ma kansa ruwan zafi tukun ya furta abin da ke mai yawo a cikin zuciyarsa. “Waye Ni? Meyasa na ke ji kaman ba dai-dai ba! Kaman na manta abubuwa a cikin kaina, to ina dangi na suke?.” take ya ji yadda yake jin kaman an buga mai guduma, sai ya dafe kansa, yarasa da ya fara tunanin waye shi sai ya ji haka tare da ciwon kai. Da ƙyar ya kammala ya fito tare da sanya P.J-mask yana mai kallon kansa a mirrow ...............✍️ END. > Ko a iya haka kunsan tafiyar akwai ƙura, shin su waye burinsu ko na ce hasahsensu zai cika. Yanzu muka soma, domin har yanzu wasu burin ba su gama bayyana mana ba. Still na ƙaƙu na ji na Umar😜. > Hmmmmm ✍️✍️✍️✍️ ba wasa *HASASHE KO BURI* tafiyar wannan na daban ne domin akwai abubuwan ban mamaki, taɓa zuciya, ruɗani da zalama irin na ɗan adam. Mu daihe zuwa.......... PAID BOOK ne 😏 by PRETTY SK NOVERLIST 🥰 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t *_HASASHE KO BURI_* _SADAUKARWA_ *🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).* You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! 💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍 🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️ Page9️⃣⏩🔟.. *KADUNA* Misalin karfe huɗu suka kammala sa'an nan sukari loads tafiya suke suna yi ga tsakaninsu cikin raha da nishaɗi a bakin mota mai musu ka tsaya gaba dayansu suna tattaunawa r basu jinha ba kowa ya hau motansa tare da barin makaranta mai murna isa gidansu ka tadda mahaifinta ya zo tare da wani dansa na cikinsa bane amma kamar dansa yake domin a wajen sa yake rayuwa bayan ta zauna a falo suka gaisa sa'an nan ta nufi dakin ta na shiga ta watsa ruwa tare da gabatar da sallah dama tayi alwala kwanciya tayi akan gadon tana mai fidda wayanta da su ba adadi a kan screen din wayau murmushi kawai ya saki tana mai latsa massage din ner ce wa tasan na waye don haka shekarar ta saƙonnin soyayya da ta gani birjik wani tai dariya wani tai mamaki kira numban ya shiga wayanta ba musu ta ɗaga Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu allah ya tabbata a garekiya ki kyakkyawa da ke haska taurari cikin dare, ina ji a cikin raina cikin koshin lafiya sai dai ni da masoyanki na nan kwance ina fama da ciwon zuciyar soyayyakin amsa soyayyata a gare ki don allah kin ji na san kina sauraro na nge laifinki ba don kinki furta komai domin wannan zazzaka muryar jaki bai kamata in jita-jita a alha kawai ba yanzu ki faɗa min nawa zan biya domin in saurari wannan dadin muryan naki ne kama da busassarewa Ba shi da kyalkyali da dariya domin ya matukar bata dariya bata so yin magana ba amma dole ta amsa mai Wannan iya zance haka to sannunka daga kokari tom ni kwanciya zanyi sai anjima da sauri ya katseta da cewar shin baki a kauna na ne don allah ki tausayawa marayan allah zuciya na kona yake min zaka da zaki taba saitin zuciya nakiji jwe tamkar ana yakin badalme na biyu tamkar kuma gidan mai ya ƙone da wuta wani gadadi da zafi duka nakeji a guri daya bawan allah kar ya mutu maraya Ibrahim kenan ni ba komai yasa ban sakamaka fuska ba sabida inaji son ginamijiya da colleges guda biyu suke burge ni so kai naga kana da guda daya tana da maida hankali a karatu kuma gaskiya kina da interesting akan ka so na biyu ne gaskiya baka da shi inda ace kana da shi to gaskiya zamu iya bari ka so ni Shine menene wannan? Ina son ya zamana saurayi na ya dinga sanya manyan kaya kullum.” An gama My Love ” dariya ta yi daga kuma I.b ya shiga jera mata kalaman soyayya masu narka zuciya, aikam babu ɓata lokaci ta yi accepting soyayarsa. Bayan sati uku kuwa, gaba ɗaya M-Ladies sun faɗa soyayya da su Abbas, sai dai soyayyar Abbas da Maryam ita ce kaɗai aka gina akan gaskiya saɓanin na sauran. A yanzu I.b ya fara jiƙa da kuɗi, dan da gaske Mymoon na da hannun ƙyauta fiye da misali, komai ita ta ke bai ba tare da ta damu ba tinda ya ce mata da sun kammala karatu zai ne ba babban aiki shike nan. Haka Shamo da Muheey, ta so ya na da kuɗi a yanzu domin ta fantama amma sai dai tana target da idan sun kammala ya ce mata a Dubai zai fara aiki, hakan yasa ta sake maj sosai, kuma in ta samu kuɗi wajen wasu samarin ta shi take bawa. Ma'esh da na ta wato Abdul, suma ba ƙyar soyayya suke sha. Kaf cikin su, su Merry ne suk gina tasu akan gaskiya. Sau da dama takan yi mai ƙyauta amma baya amma saman, dai-dai da katin waya sai ta dawo mata da shi, har sabuwar waya ta siya mai amma yaƙi amsa. *Merry* Zaune take tana kallon wani Nigeria Film, take wayarta dage gefe ta yi saƙan saƙo, da ta basar amma jin na biyu yasa ta ɗauka tana kallo. Sauƙon farko na kuɗi ne, 3k sai saƙon Abbasa. “My patner ba yawa, my first gift to you." Murmushi ne ya ƙwace mata sannan ta kira number na sa, sai dai kaman kullum ba yi pecking ba har ya katse, take na sa kiran ya shigo wayan ta amsa. Bayan sun gaisa. “Nagode sosai.” ta faɗa tana jin wani shauƙi na mamaye ta, ita ko dubu darin da yayanta ya saman tama ɗazu ba ta yi wannan farin cikin ba. Maganar minti uku suka yi katinsa ya ƙare, ajiye wayar ta yi dan tasan ko kira nawa za ta mai bazai ɗaga...... *KANO* A gurguje ta shirya, ko wani lafiyayyan breakfast ba ta yi ba, bayan ta isa Goodness Tv, sanna in da suka zauna jiya, tambaya ta yi akan c.e.o, aka ce mata yakusa iso wa. Zama ta yi dan gaba ɗaya tin jiya ba wani natsuwa ta samu ba, littafin sirrin ta ne, ba za ta so kowa ya gani ba, fatan dai ɗaya bai karanta ba. Tana zaune ta ga wuce wansa, da idanunwa dake cikin niƙaf take kallonsa. Shigen dressing ɗin jiya ta yi, sai dai na yau hijabi ɗin dogone har ƙasa, haka kuma ɗaurin niƙaf ɗin a ciki ta yi kafin ta ɗauka hijab. Yana zama ya runtse idanuwa, tare da kifa kansa jikin desk. Har ga Allah in ya ce ba ya cikin damuwa ya yi ƙarya, Darling na neman kashesa. A ce matarsa, matar aure, haka take yawo cikin maza balagaggun da sunan suna mata aiki, dan ta ƙi yadda da mace ta dinga mata aiki. Shi tunda yake bai taɓa ganinta da kayan mutumci ba sai ranar aurensu, amma a washegari tin da safe ta sanya wasu tsinannun kaya, shi kansa mamaki take basa, domin in ta yi wani abun sai shi ya ji kunya. Yana so ya dinga taka mata burki amma. Baya iyawa sam, yanzu haka ya baro gidan ne tana sanye da wasu sleeping dress, kuma a parlour take zaune, yasan dole Musa mai shara ya shiga cikin. A karo na ba adadi ya kuma jan tsaki, take ya buɗe idanuna, sai aka yi sa'a suka sauka akan littafin jiya, take ya tuna ya hangenta ɗazu. Bayan ya ba da umarnin da a taura ta. Ta shiga a gabansa ta tsaya tana ɗan tsugunna mai kai, tare da basa wani paper. Amsa ya yi yana mai karantawa. “Assalamu alaikum, sir good morning, I'm sorry, jiya na yi mistake, ba wannan book ya dace na dauko ba, fatan ba'a duba ba?.” sai ya ɗago ya kalleta yana ɗaga mata kai. Sannan ya ba ta wancan, tare da amsa ɗayan bayan ya duba ya ce. “Sa'adatu jibreel.. Right?." Sai ta ɗaga mai kai. Bayan ya kuma ɗan ɗau lokaci ya ce. “Gobe ki dawo akwai interview, wanda da kinci zai fara aiki Monday.” wani irin farin cikin ne ya kamata, take ta kalla gefe guda da yi sujuddur-shukrh, sannan ta ɗago tana mai godiya da hannu har ta fice. Samun kansa ya yi da murmushi, sannan ya kalla CCTV cameran gidan Tv, sai ya tsinci kansa da bin ta da idanu, duk in da ta yi, har ta bar gidan Tvn. A ransa ya ke aiyana “Yanzu wannan halittan dake naɗe cikin shigar mutum, ta taɓamin zuciya....... Anya matar aure ce ma?." Ganin babu mai bashi amsa, ya sa ya fita dan duba ma'aika. Ɓangaren masu ɗauko rahoto ya yi, komai na tafiya dai-dai, yanzu abin da yake hari shine, gasar da aka sanar za'a yi a gaba Nigeria, akan ɗauko rahotonni, kuma nan da wata uku ne, sannan Goodness Tv yana ɗaya daga cikin gidan Tv goma da za'a yi wannan gasar da su. Gobe zai tantance masu tafiya dan mutum biyu kawai ya ke so. Yama san dole ya sanya Haidar, dan a kashi 100 na ci gaban gidan tv shi ya samo musu kashi 50, yaron akwai hazaƙa, kuma yana ji da shi, duk in da rahoto take to Haidar na wajen, shi yasa gidan Tvn su ya zama the best a Kaduna state. “Sir Abubakar, Alhaji Banbo ya iso.” jin an kira sunan sa ya kalla yarinyar da ta yi magana, ita ma ɗaya daga cikin masu aikin gidan ne, dan dukka suna sanye riga mai tambarin gidan Tvn wato wasu na'urori na zamani, sannan an rubuta *GOODNESS TV* _taken mu ƴan cin mu_ . Bayan ya ga Alhaji Banbo da za su yi hira da shi aka irin nasarorin da yake samu a cikin ɗan shekarau. Wani Senior shine suka gabatar da shirin shi yana gefe ne. Sai misalin 2:30 ya koma office. Wayarsa ya ciro yana shiga contact gani 10 missed call, kuma dukka na Darling. Bin kiran ya yi, take ta ɗauka ta hau mai faɗa kaman wani yaronta. “Ina ka ake wayan? Sai ai ta kiranka ba za ka ɗaga ba, kana can kana washe ma ƴamma haƙora koh?.” ji ya yi kaman ya jefar da wayan amma sai ya ce. “Dear da zan shiga masjeed ne na sanya wayar a mute......” “Ya isheni, ka dai kula, kuma wallahi in ka kalla wata mace ban yafe ba.” ƙit ta kashe wayan. Dafe kansa ya yi, shi dai kullum wannan Darling ɗin neman haukata sa take. Take kuma ya ɗauki wayan yana shiga Gallery lock, bayan ya fito da shi daga freezer (wani wajen na ɓoye app) take ya cire password ɗin yana kallon hotunan wajen. Murmushi ne ya ƙwace mai, dan jiya da zai wuce sai da ya yi snapping littafin dukka, dan har ga Allah so yake ya karanta komai dake ciki............. *ABUJA* Bayan ukasha ya fito daga wanka, shima Umar ya shiga, ya jima yana gasa jiki sannan ya fito, bayan sun sanya kayan barci, tare suka ci abincin da suka yi order sannan suka kwanta suna hira. Wayan Ukasha ne ya yi ƙara ganin. Amira ya sa ya kira bayan na ta ya katse. Suna gaisawa ta ce. “Masoyi, wai yaushe burin na ka zai cika ne?, Baba ya ce ka turo gobe, in ya wuce zai ba wa ɗan uwansa ni, kuma Ni kai na ke so." Shuru ya yi yana kallon Umar sai ya ce mata. “1mnt." Kafin ta ce wani abu, ya kashe. “Umar menene abin yi?.” “Ai tin ba yau ba na ce maka, ka aure su daban-daban, amma kaƙi ji.” “A'a, na haƙura da ita ɗin." “Amma......” sai kuma Umar ya yi shuru, dan wallahi ya sha wahala kafin Amira ta a toh amince ta amince da kyar domin kuwa yarinya ciwon da samun ta yana wahala gashi kuma a yau missing na wannan yarinyar yana ji yana fada mata cewa allah ya hada kowa da rabonsa ya gode da kulawar ta ga haka idanuwansa suka kulle ya fada duniyar tunani na rayuwarsa Na fada muku nima ina da wani buri kunda a kullum da shi nake kwana nake tashi a kuma bane wannan burin illa a kan wata yarinya zakuyi mamaki ku ji nace wata yarinya sai dai nawa ba irin nauka shi ba ne burin a kan lamba kwara daya tak wimu nake shan wahala kasa gano ta bari dai in baku taƙaitaccen labarin shekaru biyu baya, a wata rana laraba bayan na dawo gida sai na koma office saboda na yi mantuwa. Bayan na juyo, ina cikin tafiy bayan na jiyo ina cikin tafiya sa na paka daga gefen hanya sabida hadari ya hade sosai kuma libana son tafiya ana ruwan sama r kyakkyawan yarinya na gani daga gefe guda lalami ita mahalalin ne tsai da ita cikin yini cikin uniform din islamiyya h tsaya take makama nta mai yiwuwa jiran mota take wani ta jima a tsaye kuma hadari ya hadu sosai kuma ake da saukar da ruwa yasa na buɗe motan ina mata magana da ta shigo ngo ta jima tana tunanin shigowan ko kadda shigo ngo sai daga baya ta shigo cikin zama dai tana cemin ta gode mata kai kawai nayi take kuwa aka tsuge da wani ruwa mai matukar kara da karfi mai iska an jima ana zubga wannan ruwan daga bisani ya dan sassauta sa'an nan na tambayeta ina son kaita ce a badamuwa zata sauka a nan da muka dinga musu har dai ta iya mun kwatancen inda zata sauka ba musu na ku dauki hanya zuwa gwara da ta mun kwatance za ta fita kenan na buɗe bakina nace mata baki fada mun sunanki ba en mata sai tayi murmushi sa'an nan tace mun sunan mai tsada ne sai nace to dan allah ban numban wayanki ba musu ta dauko pepper ta bani numban tare da ficewa cikin farin ciki da murna na dawo gida na daukefan zan kira number sai naga lambar bai cika ba i mamaki sosai ganin number guda goma ne kasa kuma ta rubuta ka nemi ɗayan da kanka sai ka kirani tafa in fada muku daga wannan ranar likita faman haɗa lambobi don in kira ta sai dai kullum cikin rashin sa'a nake har yau ban same ta ba shekara biyu kenan ban santa ba ba za su sunanta ba kuma na koma inda na sauke ta a mota ance ba wanda ya santawa unguwa har ya ban fidda rai ba ina nan ina bincike a kan lambobin ba daya zan saka to dayan a wani bangare tambayan da nake wa kaina ko da yaushe kenan kasa gano ɗayan nan a ina yake. “ Mun gama magana, Umar ni yanzu a lokaci guda nake son samunsu.” Amma shiru umar yayi kamar yana bacci shima ya kwanta yana mai tunani n yaushe wannan burin nashi zai cika ke ya hada su a lokaci daya kuma har ga allah ba zai ɓoye ma kowa ba, domin shi auren gaskiya zai yi ba na yaudara ba............ END. > Page1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣ *KANO* Bayan ta isa gida, ta tadda ƙanwar mahaifiyar ta ta zo, da yake a nan take ita ma, ta yi tafiya ne zuwa Abuja dan kasuwancin ta, business take yi kuma ita ke rufa musu asiri kamar yadda suka rufa mata ita ma, domin mijinta ya rasu, kuma ba ta haihuba, danginsa suna ƙi ba ta komai, shine ta dawo gidan na su. “Na yi kewarki.” ta faɗa amma ta hannuwa, matar ta fahimta sai ta rungume Ameeratulkhairi ɗin tana faɗin. “Ni ma haka, wallahi duk lokacin da na kalle ki, sai na ji wani tausayinki na taso min, insha Allah maƙiyanki sai dai su mutu, sun rabaki da abin da ya ke na ki, wanda Allah ma ya baki suna so su ƙwace.” “Ke dai bari, yanzu haka daga gidan Tvn take, wai za ta yi ɓangaren ɗauko rahoto.” “Mubarta, idan suna tsammanin ta nakasa kenan to akwai wani baiwar ai. Ƴata ko ina ne ni zan tsaya miki sai dai karki kuskura duk rintsi ki bayya wa duniya jikinki, hatta fuskarki bansan ta bayya wa kowa.” Ameeratulkhair ta ɗaga mata kai tana mai ɗauko abinci dan yunwa take ji, farin ciki ne fal ranta dan tana da yaƙinin wannan ƙyakkawan bai karanta littafin ta ba. “Yanzu wannan ne ake nuna kishinsa haka, tab ni kuma sam bai mun ba......uhm shan koko kwanciyan rai.” ta faɗa a zuciyarta dan tina matar da ta kira C.E.O, shi kuma har da rawar jiki ana ce mata Darling. Murmushi take tana mai bar wannan tunanin a cikin ranta........ Babu page ɗin da ya tsaya sai *Zuciyata* , murmushi ya saki yana mai fara karantawa. “Ban tsammanin zan yi aure a rayuwata amma idan har zanyi, ina buƙatar don wasu abubuwa akan mijin. Bayan ilimi, nagarta, hali mai ƙyau, akwai wasu abubwan da na ke so. Misali Namiji mai suna Namiji, natsana Mata-maza, ban san namiji ya zama kaman yaro, na juya sa yadda na ke so, a'a na fison namiji mai izza, mai cika ido, mai zafi, mai ƙarfi (ba wai dan mu yi faɗa ba, dan in na taro faɗa ina da shi.)” Ajiye wayan ya yi yana mai jin abubuwa biyu na taso mai, na farko tamkar da shi take magana, kamar dai yadda Darling ke juyasa. “Dama ni Mata-maza ne?.” ya tambaya kansa, wani zuciyar nasa ya ce masa 'Eh' tsaki ja yana mai miƙa wa, ta ku biyu ya yi sai ya tsaya cak, yana duban jikinsa, ko zai ga duk abin take faɗa, ya jima a tsaye sannan ya ƙara karanta sauran layikan. “Ƙyau, sanyi-sanyi, taushin murya, tafiya a natse, fara'a mai yawa, da kuma iya soyayya, *Duk bansan namiji da su* wallahi banso.” daga nan shafin ya ƙare, sai ya kasa motsi, dan da fari komai ta faɗa, sai ya auna kuma yaga yana dashi amma at end wai ta tsana hakan. “To ya take son Namiji?.” ya tambaya kansa, dan akwai aikin da zai yi da ya zauna karanta shafin gaba, ɗan uwan wannan. *ABUJA* Washegari tare suka je office, bayan sun shiga kowa ya shiga nasa office ɗin dan yin aiki, basu suka tashi ba sai misalin 6. Haka suka juyo dan dawowa gida, ta cikin motan ne, Ukasha dake gefe ya hanga wata budurwa tsaye daga tsallake tana siyan abu a sago, da yake utone ne, sai suka zagayo ta gafen da take, take yarinya ya bar shagon tare da shiga wani layi. “Umar bi wancan yarinya.” ba musu ya karya kwanan motan tare da bin ta a hankali, wani gida ta shiga dan haka suka faka, take wani yaro ɗan saurayi ya fito daga ciki, da sauri Ukasha ya fito yana ma yaron magana. Bayan sun gaisa ya ce. “Dan Allah yarinyar da ta shiga yanzu, kasanta?.” “Eh yayata ce.” “Ma sha Allah, in ba damuwa ina son na ɗan tambayeka a kanta.” bayan saurayin da ba zai wuce 20yrs ba ya ɗaga mai kai sannan Ukasha ya dasa magana. “Ya sunanta? Kuma dan Allah an mata miji ne?.” “Sunanta Fillo, ko ka ce Fatima, da yanzu an yi auren amma aka fasa saboda ko kwanji ne, ko menene.... Na dai manta.” sai ya ɗan yi murmushi, yana maimaita sunanta Fillo, ba ƙyarya daga nesa ya hangi haksenta, kuma ga wannan ƙanin nata shima fari ne. “Ka mana sallama da ita.” bayan yaron ya shiga sai can ya fito tare da faɗin. “Ta ce sai ka fara samun Baba am(Baba), in ya ba ku izini sai ta fito.” number Baba am ya amsa tare da wuce wa. “To Allah ya sa, munyi da cen ɗaya, dan ga alamu, akwai tarbiyya a gidan.” Umar ya faɗa yana fita daga layin, shi kuma Ukasha yana ta maimaita sunan ta *Fillo* . *****Omo ta siyo, dan haka wanke-wanke ta shiga yi, ko da ƙaninta ya faɗa mata wasu na neman ta sai ta mai magana cikin fillanci. “Kace su nema Baba am, in ya amince to.” aikinta ta ci gaba da yi, can sai ya dawo yana murna an bashi dubi biyar. Bafullatanar da ke wanke-wanke ta kalla ƙaninta da suke kama da juna sosai, kafin ta ce komai sai ga wata mata ta fito tana magana da fillancin. “Ban kuɗin.” yaron ya kalleta tare da juyawa ya fice, yana ji tana kiran sunan sa 'Moddi.' amma ya shareta. Budurwa da ba za ta wuce shekara 20 ba ta yi murmush. Take ta wani haska, dan a lokacin na mata kallon tsab. Ƙyaƙƙyawace ajin farko, tana haske mai sosai, sannan ga uban hanci ma sha Allah, duk da ta ɗauka ɗan kwalli amma gashin mai uban tsayi ya sauka har gadon baya. “Dada am (Mama) ya gudu ai, kinsan Moddi da son kuɗi.” “Zai dawo ai.” matar ta wuja ta koma ciki. Su huɗu suke rayuwa, Ita Fillo, Dada am wato mama amma ba ita ga haifesu ba, kishiyar Mamarsu ce, mahaifiyarsu ta rasu tin suka yara, Dada am ce ta raine su, ita ma ta haihu amma yaron ya ɓace tin yana ƙarami, ko ita Fillo lokacin tana jaririya ya ɓa ce, an dai ce lokacin shekarunsa 6 ne. Alhamdulillah domin suna rayuwa cikin ni'imar Allah, ba sa samun matsala da Dada am, domin Fillo yarinya ce natsatstsa shuru-shuru. Da dai shiga wani hali sosai da aka fasa aurenta da wani da take mutuwar so, saboda ƙwajin jini dukka 'AS' ne, daga lokacin ta ɗaura aniyar ba za ta ƙara soyayya ba sai bayan ta yi aure, da faruwan al'amarin wata na uku kenan, sannan kusan kullum sai anyi sallama da ita amma ba ta fita sam. Sai ta ce su nema Baba am................. *KADUNA* Su uku ne suke zaune suna raha kwanin sha'awa, sam babu mai damuwa a cikin, dan a yanzu suka ƙara tabbatar da Allah yana matuƙar ƙyaunarsu. A yanzu I.B ya riga ya rikita Mymoon da zazzafar soyayyarsa. Yadda kasan asiri koma ya ce sai ta yi, domin kuwa ya iya sarrafa mace fiye da lissafi, hatta mota ta mallaka mai. Shi dai yana cikin alheri dumu-dumu. Sun zama wasu manyan mutane, dan ko su Shamo suna jan kuɗi ba wasa suna target ɗin su mallakar mota. A dai-dai lokacin Abbas ya dawo daga garaji dan alhamdulillah yanzu yana samu ba laifi, wata rana dubu uku ko biyu. Kuma yana jin daɗi in ya samu, kuma yana fatan nan gaba ya fi haka dan haɗama Merry lefe. Bai manta ba a lokacin da ya faɗan masu Abdul ba, dariya suka sa mai suna ganin wautarsa ƙarara amma ya share su dan shi yasan mai ya taka, kuma ya dogara ga Allah. “Assalamu Alaikum.” suka haɗa baki suna amsawa. Shamo ne ya kalla kayan jikin Abbas ya yi murmushi yana faɗin. “Aboki, kana wahalar da kanka wallahi, dan Allah ji yadda ka kamo duk ka yi ɓaki ma........... Ka bar wahala Merry nasan za ta taimaka maka amma kai dan aci da Gumi ka ƙi......” “Shamo bar ɓata miyanka, kasan Abbas, in ya faɗa abu baya sauyawan mu dai mu tayasa da addu'a. Ga wannan wallahi bansan ganinka cikin kayan nan, kuma wannan aikin.....” da sauri Abbas ya fizge rigar da I.B ke miƙa mai yana faɗin. “Good da ka san ban sauya ra'ayi. Kuma in addu'a ce ku zan yi ma wa.” “Abbas wallahi muna sonka, bamu son ganin kana aikin mai wahala, kafimu haske amma jibi yadda ka koma, mukan sai wani fresh muke yi.” sai dai ya kalla Abdul da ƙyau, kaman zai ce abu amma ya fasa tare da shigewa bayi dan yin wanka. Yasani ba sai sun faɗa mai ba, suna sonsa sosai, kuma ba sa son aikin da yake yi, suna yawan faɗa mai, su za su nema amma shi ya wuta sai suba shi amma ya ƙi sam. Kuma ba ƙarya wani fresh suke dan kuwa ba ƙaramin daɗi suke ci ba. Haka zai dawo ya tadda uban leda tsire, balango, drinks, marada kuwa hmmmm, sannan komai suka ci sai sun aje mai, wani lokacin ya ci in sun matsa. Bayan ya fito wanka ya samu suna shirya wa tare da cika ɗakin da ƙamshi. “Ka shirya mu ajeka a ƙofar gidan su Merry.” I.B ya faɗa yana taje ɗan gemunsa. Dayake yana son zuwa, aikuwa suka shirya dukkansu. Sun yi ƙyau kaman za su wani taro, Abbas ne ya zura wata jallabiyarsa, sun mai tsiya da ya cire amma ya yi banza da su. Mota suka hau, a hanya Abbas ya ce su tsaya bayan Abdul ya faka dan duk sun iya mota hatta Abbas ya iya. Bai jima ba ya dawo riƙe da leda baki. “Mutumina me aka siyo ne?.” “Merry na son awara shine na siya mata.” dariya suka kwashe suna kallon Abbas da hankalinsa ƙwance kuma ya yi banza da su. Shamo da ke gefensa ya dafa kafaɗarsa yana faɗin. “Abbas, da baka siya ba, taya mace kaman Merry ta ci awaran bakin hanya.” “Hmmmm za ta ci.” ya faɗa da confidence ɗin sa dan yasan duk abin da ya ba ta cike da nishaɗi yake amsa kuma bai ta ɓa ganin sauyin yanayin a fuskarta ba, shiyasa ko ba yawa yake siya mata abu in dai yasan tana so. Yanzu haka awaran dari biyar ya siya mata............✍️ END. > Tab akwai ƙura fa, hmmmmm mudai na mu ido, 🥱🙄🙄🙄🙄🙄 > Hmmmmm ✍️✍️✍️✍️ ba wasa *HASASHE KO BURI* tafiyar wannan na daban ne domin akwai abubuwan ban mamaki, taɓa zuciya, ruɗani da zalama irin na ɗan adam. Mu daihe zuwa.......... PAID BOOK ne 😏 by PRETTY SK NOVERLIST 🥰 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t *_HASASHE KO BURI_* _SADAUKARWA_ *🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).* You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! 💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍 🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️ PAGE1️⃣3️⃣⏩1️⃣4️⃣ *ABUJA* Misalin ƙarfe 8:30pm, Ukasha ya kira wannan numbern, sai da ya yi kira uku tukun aka ɗauka, wani dakakkiyar murya ce da mai amsakuwa a cikin kunnansa, bayan sun gaisa Ukasha da duk da bai ga mutum ya mai ƙwarji ya ce. “Baba am, ɗazu ne na ga Fillo, shine na nemi ta fito na gabatar da kaina gareta, sai ta aiko sai na fara magana da kai, shine na ke neman izini.” yana ji mutum ya ja dogon numfashi. Shigowarsa kenan ya zauna a parlour, Kallon Fillo ya yi take ci abinci tana kallo, shi ya ƙosa ya aurar da ita, saboda ya gaji, a ƙalla a yau wannan shine na shida a kiransa. “Gobe ka zo na ganka.” take ya mai kwantance tare kashe bayan dan ko godiyan Ukashan bai amsa ba. Shuru ya yi dan a yanzu Fillo ce damuwansa akan wanda zai aura mata, ba wai ba ta masu bin ta bane, sai dai da yawa sha'awarta ke kawo su, kuma yana gane haka, so yake Allah ya haɗa shi da wanda zai ya amsa da ya mai da amanar Allah zuwa garesa. Babban abin farin cikin shine Fillo duk abin da suka za ɓa mata ba musu shi take accepting. “Bingel am ( Ƴata ko ɗana) waye aka kuma ba wa numberta?.” da ya faɗa da Hausa dan shi ya ƙware da Hausa sosai. “Baba am, bansan shi ba nikam.” ta mai da mai da fillanci. “Voɗi ( yayi kyau).” take Dada an ta fito dan ba tasan ya shigo ba. “Jabɓama ( sannu dazuwa), Awarti?( Ka dawo?).” ya ɗaga mata kai. Sai ta nufa kitchen Dan haɗo mai abinci. *Barcin ya ɗauke da da wuri, shi kam Umar ya dage, sai haɗa numbers yake amma number ɗaya yake so ya kuma jarrabawa sai dai daga kira an ɗaga ya yi magana an kuma kashewa, yanzu ya yi kira na huɗu kenan, take na biyar na shiga aka ɗauka. “Assalamu Alaikum” “Uban wa ke magana." Muryan gardi ya dakeesa. Sai ya ma ze dan ba yau ya saba kiran maza ba a haɗe-haɗen number. “Ka ya ƙuri, mistake ne, wata nake nema.” “Ka kira number mata ta kace mistake ne, dama zargi ta na ke yi, to Allah ya tona muku asiriiiii.” ƙit Umar ya kashe kiran tare da sanya wayar a fightmood tare da kwanciya yana faɗin. “Zargin uban me, ka mannamin hauka.” daga haka ya shafa addu'ar barcin yana rufa da duvet................ *KADUNA* A bakin get ɗin gidan su Muheey suka faka, wannan shine karo na biyu da ya zo, bayan sun ɗan jima sai ga ta tafito cikin wata arniyar less maroon, ta yi mugun ƙyau haka kuma sai wal-wal take yi, tana isowa ta sakar mai murmushi tana mai bismillah da ya shiga. A cikin motan suke hanke yadda ake kallon love, sannan suka riga mota, a ɗayan layin suka sauke Abbas, dan ko kusa da gidan ba su ƙarasa ba saboda hango masu bindiga. Dariya Abbas ya musu sanan ya sauka, su kuma suka bar area dan a ɗan kwai nisa tsakanin su da Mymoon. Mymoon duk ta fi nisa dan haka still, Abdul ya fara sauka sannan I.B ya amsa tuƙin motarsa ya nufi gidan su Mymoon. A waje ya faka, sannan ya ɗan ɗau lokaci sai ga ta tafito cikin wasu riga ta da wando Pakistan, sai babban gyalen da ta yafa. Ta haɗe rai sosai. Take ya sausauta nishaɗinsa, amma ya danne bai tambayeta ba. Shiga babban gidan ya yi, a wannan Gazibon ta kuma saukansa, ba ƙarya ko ina cike yake da abinci iri-iri, tare suka zauna tana mai ce mai tana zuwa, sannan ta fice. *Shamo* A falo ta sauke sa, yana ta bin ko ina da kallon dan yau ya fara shiga ciki, fatansa shima Allah ya ba shi ikon mallakan irin gidan nan. Abinci ta jera mai sannan ta zauna suna hira, abincin ya ci kaɗan yana so ya tambayeke ina sauran ƴan gidan amma ya yi shuru. Hira suka sha sosai, hankalin su a kwance. *Abdul* Kuwa yaga ƙauna, domin Auntyn Ma'esh da kanta ta haɗa mai lafiyayyen abinci, sannan ya ci, ya ji daɗin yadda suka ƙarɓe sa, hatta Ruma ta dinga hira dashi kaman ta san sa. Bayan sun gama, a falon suka zauna, su biyu sai soyayya suke sha, ga Ma'esh akwai iya narka mutu, dan ta iya soyayya balle ta so mutum da zuciya ɗaya. *Abbas* Wayanta ya kira sannan ta fito tare da tarensa. Tsayawa ya yi yana bin ta da kallo, hijab ne ta sanya har ƙasa, fuskarta babu komai sai wani ƙwarji da sheƙi da suke mai. A tsakar gidan ya tsaya dan ya ƙi yadda su shiga ciki, har sai da ranta ya soma ɓa ci sai ya ce. “Ki bari idan zan wuce.” daga haka suka zauna daga gefan gafan garden ɗin. Ledan hannunsa ya miƙa mata, ba musu ta amsa tana mai buɗe wa. Sai kuma ta miƙa mai tana barin wajen da sauri. Da idanu ya bi ta dan bai fahimci yanayin ta ba. Har ya miƙa sai ga ta ta dawo, fuskarta ya kalla sai yaga tana murmushi hakan ya sa ya ɗan saki ransa. “Na za ci amai kika je yi, ai sai kice min kina zuwa, da wucewa zan yi.” “Ayya My Ƙwanƙwaso.” murmushi ya ɗanyi sai ta ce. “Ga abin da na je ɗaukowa nan.” sai ya hannunta da ta fito da shi daga hijab. Plate ne da sai goran ruwa da wani ɗan roba. “Zuba min, wallahi yunwa nake ji, yau na kasa cin komai, gaskiya na gode sosai da sosai." Ta faɗa, yana gama juye mata awaran, sannan ta zazzaga yaji akai dan shine a roban. “Malam ɗan kalla can zan ci abinci, kuma sai dai kai haƙuri dan ko bismillah bazan yi ma ba.” dariya ya yi yana mai kallon gefe ita kam ta hau ci tana ta santi. Wani farin ciki ne ya kamashi tare da mamaye zuciyarsa. Har ga Allah ba zai iya misalta yadda Merry take a cikin zuciyarsa dan ita ta daban ce...... *KANO* Ita ka ɗai ce zaune a wannan ƙaton parlour tana kallon tv, take wayarta ta fara ringing, ganin yayarta ya sanya ta ɗauka tana kai kunni. Bayan sun gaisa sai ta cikin wayar ta ce. “Mama ta ce tana son ganin ki, yaushe za ki zo, ina so samune ki zo gobe idan Abubakar zai barki.” “Hmmmm yama isa ya hanani zuwa!, Ko a yanzu na so sai ki ganni a Abuja......” “Rahma ke sam ba kisan haƙƙin aure ba ko? Ina raba ki da azabar Allah......” ita ta yi saurin katse ta. “Aunty Aisha kenan, me na yi? Mallaka mijina na yi, sannan na yi mai iyaka da duk mai son shiga tsakanin mu.” “Har da danginsa?.” “Ƙwarai da gaske, nifa duk wanda yake cikin zuciyarsa dole na rabasu, zuciyarsa danni kaɗai take bugawa, babu wanda yasan wannan sai ke da Aminiya.” “Ai nasan wannan Ƴar iskan ce, ta ruɗa miki tinani, hala ma son Abubakar take yi." “Hmmm har yanzu ba kusan irin ƙawance mu bane, kuma ita ma soon za ta yi aure, lokaci muke jira tare da wani target." take yayar ta kashe kiran, murmushi Darling ta yi tana gyara zaman. Sanye take cikin wani matsiyacin riga, dan da ita da babu duk ɗaya, sharashara ce, kuma iya gwiwa, gaba ɗaya dai rigar ba ta yi ba. A dai-dai lokacin Abubakar ya shigo. Gaba ɗaya hankalinta ta mai da a kansa, har ya iso in da take. “Darling wannan kallo fa?.” sai ta miƙe tsaye tana girgiza kai tare da faɗin. “Da zarar ka ci wannan gasar, za ka bar zuwa aiki, sai dai a sati ka leƙa sau ɗaya, amma daga nan za ka dinga aikin.” ta kai maganar da dukka gaskiyar ta. “To shike nan, Allah ya sa mu ci.” “Ameen, na ce ma ka rage yawan murmushi, banso yanzu Allah ka ɗai yasan matan da suka kalleka.” ta faɗa tana jan tsaki sannan ta zare wayarsa dake ajiyu. “In ka gama wankan ka zo ka amsa.” sai ya rintse idanusa yana mai dannar zuciyar sa, haka ya bar parlourn ta bi bayansa da ido. Tana maƙutar don Abubakar fiye da misali, kuma tana ji dan ita kaɗai aka yi sa har abada. Wayar babu password, haka ta gama bincike ta tsab sannan ta ajiye. Wanka ya yi sannan ya sauya shiga yana sai sakin murmushi dan yasan ba za ta taɓa ganin in da ya ɓoye hoton littafin nan ba, kuma zumuɗi yake an jima ya ɗan duba ko shafi ɗaya ne. *** Facebook ta hau in da take kallon wata budurwa dake zaune tana koro rahoto, akan nan da wata uku za'a yi wannan gasar na gidan tv, yarinyar kawai take kallo cike da burgewa, take wasu hawaye suka gangaro daga idanunta, ta sanya hannu ta share, abubuwa da yawa suke mata yawo a ciki, da sauri ta ɗauki biri tare da buɗe littafin amma sai ta rufe saboda ta rubuta shi. A cikin zuciyarta take faɗin. “Allah ka sakamin, Allah ka isar min, kamin sakayya.....” sai kuka ya ƙwace mata amma babu sauti. Haka ta shafa tsawon dare gaban Allah tana kuka. Akan daddumar barcin ya yi gaba da ita. **Barci ne ya yi gaba da Darling, sai a lokacin ya samu ya janye jikinsa a na ta, sannan ya miƙa yana mai da maɓallen rigarsa, sauka ya yi daga gadon yana barin ɗakin, ɗakinsa ya koma tare da ƙwanciya, yasan dole shi zai tashe ta, dan ta iya uban barci, kashe hasken ɗakin ya yi yana mai ƙwanciya tare da kunna wayar, har ga Allah in bai ga ragowar ɗaya shafin ba, bai jin zai iya barci, tsabar sa wa rai. “Ina son naga Namiji mai cikan haiba, mai ɗan haɗe fuska, ba wai ba ya dariya ba amma ya zama mai tsaɗa ga kowa, sannan in yana tafiya ya zama ƙasa na amsawa, wato mai ƙarfi, bansan ya dinga slow ko wani tafiya a natse, no cike da izza da ƙarfi, sai kuma ya zama mai faɗin girji mai ɗauke da yalwaccen gashi, Ina son gemu mai yawa, sannan ko da yaushe cikin manyan kaya yake. Eh to irin wannan na ke so, amma Allah duk wanda kaban, sai dai nasan babu mai auren bebiya duk da ba'a haka ka yi ni ba, mugunta ne irin na wasu ɗan Adam.” daga haka shafin ya ƙare, shuru ya yi yana mai kuma karantawa sannan ya furzar da iska daga bakinsa. Wani yanayi yake ji a cikin zuciyarsa na daban haka, sai ya ajiye wayan yana kulle idanun, take ya buɗe dan yarinyar nan yake hange cikin wannan shigar, murmushi ya saki yana mai jan duvet..............✍️ END. > Hmmmmm ✍️✍️✍️✍️ ba wasa *HASASHE KO BURI* tafiyar wannan na daban ne domin akwai abubuwan ban mamaki, taɓa zuciya, ruɗani da zalama irin na ɗan adam. Mu daihe zuwa.......... PAID BOOK (500) 😏 by PRETTY SK NOVERLIST 🥰 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t *_HASASHE KO BURI_* _SADAUKARWA_ *🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).* You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! 💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍 🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️ PAGE 1️⃣5️⃣⏩1️⃣6️⃣ *KADUNA* _______Ya ƙi cin komai har ta dawo, sai a lokacin ta ɗan saka fuska tana faɗin. “Laaa Baby ba ka ci ba wai?.” “Eh ta ya zanci na ga ranki a haka, meke damunki Please." Ya kai managar yana ƙara kallonta da ƙyau. Take hawaye suka gangaro daga cikin idanunta tana mai miƙa wa tace. “Baby ka ta fi da abincin dukka, in ka koma za mu yi waya.” sai ta yi hanyar fita, da sauri ya ɗan riƙo gefan gyalenta yana magana cikin da taushin murya. “Beb, why are you crying? Ki faɗa min please.” sai ta girgiza mai kai tana faɗin. “Baby wai ni Dad zai ma haka, wallahi bazan yadda ba sam, ina jiran shi Taj ɗin ya dawo ne.” “Ban fahimta ba.” take ta roko mai zancen da take zuciyarsa ta tsaya cak, tana mahana tare da haɗawa da hawaye, jikinsa ya yi sanyi, dan haka bai ce komai ba ya yi waje tare da barin gida, haka ya biya ya ɗauki sauran duk suna cikin farin amma banda shi. Duk sun fahimci akwai abin da ke damunsa. “Meke faruwa ne?.” sai ya yi parking, Abbas kuma ya kama tuƙin, har suka kai gida bai ce komai ba. Zama ya yi akan gadonsu take wani murmushi ya ƙwace mai dan yasan ta ina zai bi, sai kuma a lokacin ya buɗe baki tare da ce musu. “Mahaifin Mymoon ne ya yi mata miji, yaron aikin sane Taj, shine ita Mymoon ɗin tace sam ni take so, har dai faɗa suka yi da Dad, a kan haka kuma shi Taj ɗin bai ma san da maganar ba.” ya kai maganar yana mai jin babu daɗi. “To yanzu menene abin yi?.” faɗin Shamo “Karku damu, ba sai an ce muku ba kunsan waye I.B.” sai suka ɗaga mai kai, sun san tsab zai ji da komai. *Ma'esh* Bayan fitar Abdul, Ta koma cikin gida murna fal ranta, Maman Ruma ta samu zaune a babban falonsu sai ta ƙarasa tana faɗin. “Ruma an samu na cin bisciut.” Ruma dake kwance kan cinyar Mamarta ta ɗago tana kallonta. 10k ne ya Abdul ya ba ta da ta bawa Ruma duk da ita ce ta tura mai 20k daren jiya. “To Allah ya biya, ki ce ƙanwata kin ɗauko mana babban mutum, Ai Alhamdulillah, yana da ƙyau haka kuma ga alamun za mu huta da shi, Allah ya taimake sa da kun kammala karatun ya ta fi aikin a U.S.” “Aunty ai aiki na ƙasa, takaddun suke jira kawai.” cike da alfahari da faɗa. Aunty ta yi murmushi, sannan ta kwashe kuɗin da Ruma ta ajiye a gefen Auntyn. *Muheey* Bayan ya wuce, tattare komai ta yi, sai a lokacin matar gidan ta fito wato Aunty Mariya. “Na ganshi ta window lokaci da kuke shigowa, gaskiya ma sha Allah kawai.” murmushi ta ɗan yi sannan suka ɗan hau hira sama-sama. *Merry* Farin ciki fal ranta, domin yadda Abbas ya shiga parlour na su, ya dinga ɓoye-ɓoye akan kunya yake ji, haka suka gaisa da Hajiya da Babban yayanta kuma Alhamdulillah bayan ta fiyansu sun ce ya musu, sai dai za su bincika halinsa. Daga haka ta koma ɗakinta dan wani nishaɗi take yi saboda haka. Sannan awaran ɗazu ya mata daɗi. Wayarta ta ciro tare da tura mai kuɗi 20k amma ta san zai dawo mata dasu...... *KANO* Washegari misalin 11:30am, yana shiga wani office in da ya tabbatar mutanen da ya umartar suna ciki, sai bayan da ya shiga suka gaisa da kowa sannan ya zauna, take aka buɗo ƙofa aka shigo, wani matashin saurayi ne da bai huce 26yrs ba, yana sanye ne da ƙananan kaya wanda suka ƙara bayyana jikinsa na ƙarfaffen namiji, hannunsa na ɗauke da system da kuma wayarsa sai wiyansa da ya ke ɗauke da igiyan da ya riƙe camera, yana duhun fata kaman baƙin balaraɓe, Allah ya mai ƙyau sosai. Faɗaɗa murmushi ya yi yana magana cike da dakewa, bayan sallaman da ya yi suka amsa. “Sir Good morning, a min uzuri da arean mu ana gyaran titi, to motata ma ta maƙale na barta a can.” daga mai kai Abubakar ya yi yana mai kallan ƙofa, da aka kuma shigowa. Ita ce ta shigo, kamar kullum haka yau ma shigan na ta, dogon hijabi dari blue, niƙaf ɗin ta ciki ta ɗaura haka kuma hannunta suna sanye da handglobe, ƙafanta kuwa ko hangensa ba ya'a yi balle a san me ta sanya amma daga gani shima a rufe yake. Kowa na ciki kallonta suke da mamaki ganin ta shigo hannu kawai ta ɗaga musu sannan ta zauna. Haidar dake tsaye jikinsa babu laka, dan daga ganinta zuciyarsa ta tsaya cak, take ya kuma tina ɗazu. ****Motarsa bayan ta maƙale, shine ya fita tare da canza hanya, napep ya samu ya ko hau, a ciki ya same ta zaune tana latsa wayanta. Sun ɗan jima suna tafiya sai ya buɗe baki ya ce.* *“Baiwar Allah a ina za ki sauka?.” sai ta yi shuru, rufe idanunsa ya yi sannan ya buɗe, ya manta sharp ya fito babu kuɗi, kuma akwai wasu a mota shima ya manta da ya ɗau ko 5k ne, kuma mai Napep ya ce ya fi son cash, abin haushin har ATM ɗin na mota. Ƙara kallonta ya yi yana kuma ce wa.* *“Zan iya miki transfer ki ban aron ₦500 naira.” shuru ta yi dan yau sam ba ta san rubutu da ta rubuta mai. Take mai nepep ya faka, ganin a dai-dai in da yake aikin ne yasa ya ce mai yana zuwa, ko bayan da ya dawo, sai mai nepep ɗin ya ce.* *“Ai matar nan ta biya ma, dan ma kayanka na ciki ne da na wuce.” murmushi ya yi yana kuma bashi 1k ɗin ya ce.* *“To ka ƙara Nagode.” cike da nishaɗi ya wuce, shima ya shige cikin station ɗin.****** Zama ya yi yana mai ayyana ta ya ya zai mata godiya, amma sam bai ji daɗin sharesa da ta yi ba, haka kuma yanzu ya ga tashigo amma ba ta yi magana ba. “Ta burgeni sosai.” ya faɗa dan yana da yaƙinin ba matar aure ba ce. Take Sir Abubakar ya fara abin da ya haɗa su, duk motsi sai ya sata kallon, kuma har ga Allah wani yanayi na musamman yake ji akan ta. Bayan ya ɗau 20mnt yana bayanin sannan ya jero musu tambayoyi tare da ce wa kowa ya rubuta yanzu, take mutanen da ba za su ce 15 ba suka hau note, ciki har da ita. Bayan lokacin amsa ya yi ya amsa ya yi tare da ba Haidar daya duba dan shi bai yi ba saboda yadda yake da ƙwarewa sosai. A take ya duba sannan ya fitar ma kowa da marks, a na ƙarshe ya tsaya, ya rasa ganewa shin da rubutun da abin da aka rubuta wanne ya fi sanya sa mamaki, rubutu kaman zanen inji, haka kuma duk abin da yake tinani akan in da an ce ya rubuta to su zai rubuta to a wannan har da ƙari. Domin a abin da aka yi da wanda aka kalla za ka fitar da tambayoyi tare da amsa su. 100% ya sanya mata yana kallon sunan Ameeratulkhair. Kamar kar ya ba da dan ya shagala da kallon sai da ya ji murya Sir Abubakar. “Are you done?.” sai ya miƙa mai. Take ya duk wanda ya kira sai ya bashi har aka kira Ameeratulkhair, cike da natsuwa ta miƙe ta isa gabansa amsa ta yi, ta koma ta zauna. “Duk wanda ke da mark sama da 80% ya zauna sauran kuwa ku je zan nemeku anjima. Take duk aka watse sai ita kaɗai. Mamakine ya kamata dan ita ba ma komai ta rubuta ba amma wai ta ci 100%, ganin su uku suka rage sai Sir ya mata alama da ta dawo gaba, ba musu ga dawo set ɗin dake gefen na Haidar. “Bara na ɗauko abu a office.” daga haka ya yi waje, ajiyan zuciya ta sauke tana ta karanto addu'oin dake kan leɓanta. “Madam nagode da biya min kuɗin mota da ki ka yi.” sai ta ɗaga mai kai, ganin haka ya kama kansa, ko da Abubakar ya shigo, wani video ya kunna musu suka mai da hankali sosai. Bayan ya ƙare ya ce. “Muna da gurare 8 na musamman wanda kuma in muka samu ɗaya a ciki to zamu iya cin wannan gasar, sai dai a yanzu wasu gidan tv sun diran ma wasu.” take ya ɗan basu labarin yadda tsarin yake. “Hakane in babu damuwa zuwa gobe sai mu fara namu binciken.” “Shike nan Haidar, Ameeratulkhair kin yi sa'a daga zuwanki za ki hau aiki, fatan a gida za'a barki?.” sai ga ɗaga mai kai. “Yauwa, to Haidar ka ƙara mata explain akan yadda tafiyan yake.” sai ta ɗaga hannu, kallonta suka yi dukkansu. “Kina da magana?.” ta kuma ɗaga kai. Whiteboard ɗin dake gefe ta nufa tana ɗaukan maka ta fara rubutu. “Na yi bincike akan gasar nan, kar mu tsaya a iya wa'innan saboda kowa da su suka dogara, gurare 8 ne, kuma abubuwan wajen suna kamanceceniya dan haka a ciki akwai masu ɗaukan iri ɗaya, ina babu damuwa a nema a wani waje na daban wanda hankalin mutane ba zai kai wannan ba, kuma na wannan gidan Tvn zai zama na daban thanks." Daga haka ta koma ta zauna. Abu ne ya ishe Haidar kuma shi baya ɓoye duk abin da ke ransa. “Baƙya magana ne?.” ta ɗaga mai kai, sai suka kalla juna amma ko kaɗan ba ya ganin idanunta. “Haidar bebiya ce ita.” Abubakar ya faɗa yana ɗan jin wani abu a ransa. “Ayya shi yasa na miki magana ɗazu baki kulani ba kenan.” ta kuma ɗaga mai kai, lumshe idanunsa ya yi yana mai jin wani yanayi na daban. Abubakar kuma waya ya ɗaga yana faɗin. “Alhamdulillah Darling, ya gidan?.” basu ji mai a ke ce ba sai dai take fuskarsa ya sauya sannan ya ce. “Shike nan sai kin dawo?.” ya kashe kiran wai ace sai da ta isa Abuja take kiransa akan ta je gidansu.......... END. > Hmmmm soyayya, toh fa da alamun Haidar ya kamu, kuma shima Sir Abubakar ya harbul..... Ko yaya tafiyar za ta kasance oho...... > I.B sannu da ƙokari. hmmm wato ke Maman Ruma, Abdul ya muku za ku huta 👍🤗.. Mai kunya kai ma sannau *Abbas* . Sai ku ma sauran sannunku. Jama'a akwai ƙura muje zuwa....... By PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️. 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t *_HASASHE KO BURI_* _SADAUKARWA_ *🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).* You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪 🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.* Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! PAGE1️⃣7️⃣⏩1️⃣8️⃣ *ABUJA* Ukasha yau cikin farin yake sosai, domin kuwa Baba am ya amince da shi, sai dai bai san ko ita Fillo za ta yadda da burin sa ba, ya ji daɗin yadda yaga Baba am ya sakar mai fuska, sai dai yasha tambayoyi sosai, kuma dukka ya amsa. Parking ɗin da Umar ya yi yane yasa ya kalla Umar ɗin ya ce. “Ya mun iso ne?.” “A'a, a yanzu idan na samo wacce ta yi, to sai ka fara ganinta, to na samu wata Yaruba, dan haka zuwa za ka yi ka ganta, na yi bincike akan ta sosai, sunan ta Ashake amma na ainiyi, Bilkisu, shekarunta 21, ta kammala HND wanna shekaran, ana suke sai da abinci sannna gidansu na farkon layin dake bayan namu." Sai Ukasha ya jinjina kai. “Ka yi aiki me ƙyau, bara na ganta, akwai tuƙwicin da zan ba ka." Numfashi Umar ya sauke dan shi har ga Allah komai da yake ma Ukasha tsakani da Allah ne. Sauka Ukasha ya yi yana mai isa wajen da ake siyar da abinci, kafin ya isa ƙamshin fatan wake ya cika sa, sai a lokacin ya tina bai san ma mai suke siyarwa ba. Yana isa wajen ya yi sallama, sai wata wacce ke gefe ta amsa tana miƙe wa daga gaban murhu, a kallo ɗaya yasan ba ita ba ce Asheka dan wannan za ta girmesa ma. “Alhaji, mi za ki siya ne." Ta faɗa da hausarta mara ma'ana. “Wake da bread.” sai ta ɗaga mai kai. “Ashake Ṣe o fi ounjẹ sí (Zuba mai abincin)." Take wata budurwa ta miƙa daga zaunen da take, hannuta na ɗauke da huƙa alaman yankan wani abu take yi. Kallon tsab Ukasha ya shiga mata, daga in da take tsaye ya kimanata tsayinta, dai-dai wadaida take, ba ta haske sai dai colour ɗin ta mai sheƙi ne, sannan tana da jiki ba laifi. Tabur dake wajen ta buga, sai ya dawo duniyar nan yabar kallon ta. “ To, bani take away. (Ó dájú, fún mi ní take away).” ta fa ɗa cikin yaren, matar ta miƙa mata. “Sir, for how much?.” sai ya sosai kai sanna ya ce. “Beans for 1k than 1 bread." Zuba mai ta yi a babban take away sanna ta kalla shi tace. “Sir, which bread? Choose one?." Sai ya ɗauka Jovard bread. “₦220." Sai ya ciro a pocket ɗin sa. 3k ya ba ta sannan ya ce. “Please can i have your digit." Ɗago idanunwa ta yi ta wurga mai kallo, sannan ta miƙa mai canjin sa. “Please." Ya kuma faɗa yana rage murya. “Sorry Sir, me za ki yi da shi?." Sai ya yi murmushi. “I want." “See you next time." Ta faɗa tana zama bayan ta aje mai canjin kan table. Wucewa ya yi, yana shiga mota ya kalla Umar ya ce. “Insha Allah, Burina yana gab da cika, ta yi min sosai, amma ba ta ban number ta ba." “Zuwa dare zan samo maka domin nasan yayanta." Rumgumesa ya yi yana cewa. “Kai Umar ka biya ni, gaskiya nima zan taimaka maka akan wannan number, zamu samo ta insha Allah." Da mamaki yake kallon Ukasha dan bai faɗa mai ba sam. “Hmmm, an faɗa ma kai kaɗai ne kasan ni sosai, nima nasan naka kuma nasan irin gwagwarmayar da kake yi akan ta." Sai Umar ya yi murmushi suna barin layin. **** “Gakiya yaron ya yi, me yasa ba ki ba shi ba number ba?, (Ọmọkùnrin náà ti pe, kí ló dé tí o kò dáhùn nùmbà rẹ?).” “Uhmmm Hausa ba abin yadda bane. (Uhmmm, èdè Hausa kò rọrùn.)” Sai matar ta yi murmushi tana cewa. “Wannan ne bahaushe? Ai da Balarabe yake kama. (Ṣé èyí ni Bahaushe? Ó dàbí Bàláràbì gan-an.)” ta ɓe baki Ashake ta yi tana canza hirar. “Ni dai barni, aramin wayarki. (Èmi, jẹ́ kí n gba fóònù rẹ.).” “Amsa. (Dáhùn.).” ta miƙa mata, amsa ta yi, tana zama tare da ci gaba aikin da take yi tana kallo a wayar matar Yayanta, ita wayanta ya ɗauke......✍️ *KANO* Driver ya ɗauke ta har zuwa Abuja, gidansu ta shiga, wanda ta kwana biyu ba ta zo ba, ba ƙarya gidan ya ƙara jan kuɗi, fitowa ta yi tana mai gyara vail ɗin kimono wanda ta sanya, ta yi ƙyau sosai, dan gida ta zo shi yasa ta yi wannan shigar amma har ta gaji da shi, shiga baban parlourn ta yi wanda ya ƙawatu sosai kaman ba ɗakin iyayen ta ba. “Aunty Aisha, kin iso ashe?.” sai ta ɗaga mata kai, kusa da ita ga zo ta zauna tana faɗin. “Ya hanya?.” “Lafiya lau, ina Boy yake?.” “Ya tafi makarantar.” a kallo ɗaya za ka ga suna kama sosai, sai dai akwai shekaru a tsakanin su, Aunty Aisha ita ce babba a ɗakin sai ƙanin Umar sai ƙaramar su Rahma, sam Rahma ta fita zakka a cikin su, domin kuwa tana da wani irin halaye marasa ƙyau, A'isha ita ce kaɗai tasan halayen ta na ɓoye, da fari zargi take amma a yanzu ta yadda. Rahma tun lokacin da ta kammala karatu ta haɗu da Abubakar, shike nan duk ta haukace musu, cikin ikon Allah kuma ya aure ta sai dai me Rahma ta rabasa da kowa, shi kansa yanzu ya mance su waye dangin sa, rayuwa yake duk yadda ta juyasa kaman motar da ake control, a haka ma auren dududu shekara ɗaya ne da ɗan watanni. “Rahma kin iso." Su ka ji muryan Hajja, da sauri ta miƙe tana isa kusa Hajja sannan ta rungume ta. “Hajja ya kike?.” “Lau, ya Baba? Ya fita ne?.” “Eh.” daga haka suka dawo cikin parlourn, gaisawa suka kuma yi sosai, hmmmm karkuso kuga yadda Rahma ke ƙanƙan da kai, tamakar ba Rahma mai isa da fariya ba. Jikinta ya mutu dan tana tunanin Aunty Aisha za ta tona mata asiri ne, sai dai a'a, amma cikin hikima ta isar ma Hajja da cewan sam Rahma ba ta jan ƴan uwan mijinta a jiki. “Rahma, a wanna duniyar dangi sune komai, muddin mutum ya yi wasa da su to tamkar ya yi wasa wani babban dama ce da Allah ya bashi, ki riƙe dangin mijinki kaman naki, ki so su, ki ƙauna ce.” “Insha Allah Hajja.” daga haka ta ƙara mata nasiha sosai sai dai me yana shiga ne ya fita dan ko ɗaya ba ɗauka ba. Bayan Hajja ta gama sai Rahma ta shiga ɗakin ta na da, tana shiga ta kira number ƙawarta. “Ke Ina Abuja, zuwa anjima ki shigo mana.” “Ai dole na leƙo, zan shigo, fatan kin zo min da tsaraban." “Sosai ma kuwa ƙawata, ki zo sannan ki sha ado, domin kuwa a yau insha Allah za ki yi kasuwa, wani matashi uhmmmn ki dai zo." Ta faɗa tana kallon Aunty Aisha da ta shigo. “Ba dai Zuby ce za ta zo ba?.” “Aunty ita ce, ni fa dan Allah ki dena shiga rayuwata please.” sam A'isha ba tai mamakin jin haka daga bakin Rahma ba sai ta ce. “Insha Allah, bazan kuma shiga abin da ya shafe ki ba, amma a duk lokacin da ƙwaɓarki ta yi ruwa karki nuna kin sanni." Daga haka ta juya ta fita. “Khairan insha Allah.” ta faɗa har da murguɗa baki......✍️ END. > Hmmmmmm lalle kam Rahma kina ruwa, kin raba mutum da danginsa, ke wai a haka soyayya ce. Fatan sa'a Ukasha 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 PAGE 1️⃣9️⃣⏩2️⃣0️⃣ *KADUNA* Washegarin ranar, tare suka shiga makaranta, yau suna da lecture, bayan an tashi, a haraban da suke zama suka zauna su uku, dan I.B yana can class suna magana da Mymoon. “Baby a ina shi yake Taj ɗin?.” “Yanzu yana Dubai ne, tamkar yaro haka Dad ya ɗaukesa, marayane, yaron abokin sa ne." “Hmmm har na harbo jirkin.” I.B ya faɗa yana ɗan murmushi. “Me ka gane.” ta faɗa tana ƙare mai kallo, ya yi ƙyau sosai, yana sanye ne da ƙananun kaya sun mai ƙyau sosai, ba ƙyarya Ibrahim ƙyakkwane. “So yake ya aure ki, ya mallaka duk abin da yake na ki, wasa yake so ya yi da hankalin ki da na Dad, shin idan kun haɗu yana sake miki sosai.” “Ina ɗan ɗacin rai ne, rabon sa da Nigeria ina ga 3yrs kenan, amma Dad ya ce soon zan dawo.” “Okh, to bara kiji, kuɗinki yake so, so yake ya mallaka duk abin da yake naki, na tsana naga namiji a haka, mutum ya dage da guminsa, ya fi. Hmmm ina da shawara in za ki yadda.” sai ta kalla ƙasa saboda irin kallon da ya cilla mata na soyayya, a zahiri ne yake a natse amma daga ta ciki, wani mugun razana yake, domin yaga samu kuma samun na neman ƙwace mai. “Baby ina jinka?.” sai da ya ƙara gyara zama, amma ba su mannu ba duk da kujera ɗaya suke kuma gaba da juna, sannan ya ce. “Ki buɗe kunnuwanki da ƙyau, ki ji duk mai na ce, sannna ki yi shawara duk abin da zuciyarki ta yanke miki, shawara shine, account ɗin ki nawa?.” “Guda biyu ne.” “To zan buɗe miki wani, amma da sunana za'a yi komai, kuɗi kawai za ki dinga tarawa, domin goben ki, domin kuwa nan gaba zai iya bijirowa da mallakar kuɗin ki, to a lokacin sai ki nuna kema fa kina da madafa, hatta filaye lokaci ya yi da za ki mallaka abubuwa da yawa.” murmushi ta saki dan shawararsa ta yi mata. “Haka za'a yi, hatta su filayen duk sunan ka zamu sanya, idan nan gaba Dad yaƙi ɗaura mana aure, sai mu nema wasu su wakillce mu.” wani farin cikin ya mamaye zuciyarsa sannan suka miƙa, da motarta suka bar school ɗin, dan a ranan sai da suka buɗe bank a access, sanna ta tura dubu ɗari uku, sai misalin 3:30pm ta kaisa unguwar su, yau kam ta biya sa dan wani farin cike ne fiye da za to. “Ka fara neman filaye dan zuwa next week kuɗin za su iya haɗuwa.” “To shike nan, Baby kin yi tinani mai ƙyau sosai, kuma nan gaba za ki ga amfanin haka." “Hmmmm, ina alfahari da kai, na gode, ka nuna min hanya mai ƙyau.” “Baby ai ke tawa ce, sannna wannan ya zama secret domin kuwa in Dad ya ji zai miki iyaka da wasu abubuwan." “Insha Allah Baby.” daga haka suka yi sallama sannna ya fita ita kuma ta tada motar tana barin layin. *ABUJA* Sai dare Baba am, ya shigo gidan, da yake har sallan isha'i ya yi, sai ya kulle gidan, yana shiga parlourn aka kawo nepa, sai ya sanya wayansa a caji yana nufan ɗakinsu. A ciki ya tarda Dada am na salla, bayan ta isar ta mai sannu da zuwa sai ya amsa. Watsa ruwa ya fara yi sannna ya dawo parlour, a lokacin har Dada am ta haɗa mai abinci sannan Fillo ta dama mai fura da nono, sai bayan da ya ƙoshi sannan ya kalla Fillo ya ce mata. “Ƴata, na amince idan wannan saurayin ya zo da ki fita, sunansa Ukasa. (miɗo acci so gorko on wi’i Ukasa ardataa, so mo yahi ardataa.)...........Na ya ba da hankalinsa sosai, sai dai ya faɗa min wani abu wanda da ƙyar za ki yadda. (Mo ɗaɗi mo waawi yeddu, kono mo wi’i min koɗɗo mo jogii, tee ko on woodani ɗum, miɗo tuugii on)." “Baba am, miɗo naati. ( Babana, Ina jinka).” sai da ya sauke ajiyan zuciya sannan ya ce. “Mo wi'i: gorko ɗum yiɗi ammbude rewɓe nayi ɗiɗi e jam. A acci sabu don ɗum walla a woodani? Mi yaafa ɗum wi'i min goonga, tee gorko ɗum naatata mi. (Yaron yana da burin auren mata huɗu lokaci guda. Shin na amince da hakan ko kuwa ba zan iya ba? Na ji daɗin gaskiyar da ya faɗa min, kuma yaron ya shiga raina).” sai ta saki murmushi, ta yi mamakin jin haka amma ita za ta yadda, domin a aladarsu ta fulani yarinya na kai shekara 13/16 ake mata aure amma ita ta kai 20, duk da ba ta haɗa ba dukka. “Shike nan na amince.” ta faɗa tana miƙewa tare da barin wajen da sauri. "Fillo akwai kunya. (Fillo ena heɓɓude semteende).” "Aikam, ai ta gado jinin mu. (Ato, ko mo lootii ɗuum ndiyam.)” "Da fa Yayansu na raye, da shima ya yi aure ko ya kusa. (So rewɓe mawni ɗum woni, mo ɗuum kadi yoo mbaɗi ngam jooni.).” ta faɗa tana mai jin kewan yaronta, shi kaɗai ne gudan jininta, amma ta rasa tin daga zuwa makaranta a can Allah ya yi sanadin, dan jin shuru shine suka je school ɗin amma babu shi, da yake wasu a layin ke tawo da shi to a ranar su an koresu school fees, shine da aka tashi yaron ya kama kansa shima. "Eh, daya kusa Allah dai ya jiƙan Jauro. (Ee, mo jooni, Alla yo yaaru Jauro).” "Ameen." *****Bayan sun koma gida aikin gida suka yi, sannan suka ɗaura girki, ba laifi gidan madaidaici ne, gidan zaman mutum ɗaya, amma two bedroom ne, ɗaya na Ashake da yarinyar da Uncle ɗin ta suka haifa. Bayan isha'i suka zauna suna hira a parlourn, su biyu ne amma Amira ta yi barci. “Yóò kam, sáákí Hamdalah, we made some sales today, not bad at all.” Maman Amira ta faɗa tana ƙirga kuɗin hannunta. “Rárá o, weekend is tomorrow — no work, Insha Allah I go wake up do laundry." "Okay, do you even know your brother said someone talked to him? And he said the guy will come tomorrow to greet you." Take ta haɗe fuska "Uhmm, I just hope it’s not one Hausa guy o, because me I no fit marry Hausa guy abeg." "Ashake, seek God's will o, look at me now — I married your brother and I’m Igbo!" "True, but Hausas can be wahala sha." "Uhm, that’s it. This your shirt fit me small sha." Ta faɗa tana cilla mata sata doguwar rigarta, dan ya matseta sosai “Wow, I like it — thanks!" Ta faɗa dan rigar na burgeta sosai.......✍️ END. > Kun fara hasashen me zai faru kuwa. Ukasha dai buri ya kusa cika tunda ga Fillo da Ashake a hannu, ko ya zasu yadda da wannan haɗin oho..... *SHAMO* anya kana da imani, ke kuma so ya rufe miki eyes ko! Hmmmmm tafiyar yanzu aka fara, na faɗa muku labarin mai tsawo ne...... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️ 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! PAGE 2️⃣1️⃣⏩2️⃣2️⃣ *KANO* Bayanin komai ya musu sannan ya musu fatan sa'a dan zuwa gobe zasu tafi, a ƙalla sati ɗaya za su ɗauka sannan da sun dawo za su shiga tace hotohutana tare da gyarasu. Barin su ya yi yana mai nufan office ɗin sa. “Yanzu ƴan gidan ku, za su yadda ki yi sati ɗaya a wajen aiki, gashi yau kika fara zuwa." Ajiyan zuciya ta sauke sannan ɗaga mai kai. “Shike nan, gobe misalin 10:30am za mu ɗau hanya." Nan ma ɗaga mai kai ta yi sannan ta miƙe, da sauri ya bi bayan ta yana faɗin. “Ameeratulkhairi, ki zo da wuri saboda harda I.D card zamu baki sannan ki tawo da passport.” sai ta tsaya cak, sannan ta ci gaba da tafiya, tare suka hau Napep, sai magana yake mata amma ta yi banza da shi, shi ya fara sauka sai a lokacin ya tina bai da kuɗi dan haka ya koma cikin Napep ɗin, sanna mai Napep ya ci gaba da tafiya, a dai-dai in da ta buƙata aka sauke ta, bashi kuɗin ta yi sannan ta wuce, da idanu yake bin ta har mai Napep ɗin ya juya, har gida aka kaishi, wani babban gida mai ƙyau, wajen mai gadi ya amsa 5k sannan ya ba mai Napep ɗin, aikam ya dinga godiya dan kuɗin 2k ne. Transfer ya yi ma Sule mai gadi na 10k, aikam shima shima ya yi mai godiya sosai, motarsa ya hanga har an dawo da ita, da sallama ya shiga babban parlourn gidan, amma ganin mata ne zaune kawai kuma kishiyoyin Ummin sa sai ya haɗe rai, a rayuwar nan ya tsan ya shigo ya taddda su domin munafukai ne, sannan suna yawan sanya Ummarsa zubda hawaye, da dai yasan kishi suke yi da Ummi amma yanzu ya fahimci tsabar hassada ce, dan shi kaɗai ne namiji a gidan, gashi mahaifinsu ya tara maƙudan kuɗaɗe, sai dai ba su san shi kuɗin Alhaji ba ya gaban sa ne. “Barkan ki da gida, ina wunin ku.” ya gaishesa cikin jimla, sai dai me babu wacce ta amsa sai ma bi shi da suke yi da wani irin kallo, shikam a banza dan kuwa ko a jikinsa, part ɗin Ummi ya wuce direct. “Kinga wannan tsinannan yaron kullum ƙara ci gaba yake, hmm na tsanesa wallahi.” wacce ta ke farko ce ta faɗa haka. “Maman Sumayya kenan, ai ni dan kin ƙi yadda ne, gobe muje wajen sabon malamin nan Mai sittin goma, a kashe mana shi daga doran duniya.” “Ba haka za mu yi ba, kinga dai yanzu mun fara ciresa a zuciyar yaran mu, kuma a hankali gidan nan zai gagaresa zama, sai dai mun kasa ciresa a cikin zuciyoyi iyayensa, kullum mukaje sa'a ce 'hakan ba zai yuhuba saboda akwai wai abu da yake gani a tare da yaron, kuma ya kasa gane menene shi, yanzu kashe Haidar ba shine mafita ba, kashe Abban Haidar shine mafita, lokacin mallakan komai ya yi Maman Safna.” “Hana ne, kuma insha Allah da munje wajen Mai sittin goma, komai zai yi dai-dai, ance aikinsa kaman yankan wuƙa ne.” “Kinga abu na farko, a cire mai wannan zarran in munce abu to shine dole, so muke ya dawo mana biyayya kaman uwarshi." sai suka yi shewa suna tafa hannu, gaba ɗaya su babu mai imani a cikinsu, ƙawaye tin daga makaranta, kuma basu da buri sai auren miji ɗaya mai tarin dukiya, shine wata rana suka yi arba da Mahaifin Haidar, wanda suke cema Abu Haidar. aikam daga wannan lokacin, Boka ya musu aiki, Maman Sumayya ita ya fara aure, sai Maman safna, wanda tsiransu kaɗan ne dan wata biyu ne tsakanin bikin, tin shigowarsu wannan daular suke wadaƙa da kwasan kuɗi suke tarawa, babu wacce ta shige musu gaba sai Ummin Haidar, sunyi sunyi a haukatar da ita amma hakan ya ƙi cimmawa saboda kullum cikin azkar take yi, gashi Abban Haidar yana mata wani mugun so, domin kuwa auren haɗi ne tsakanin su jinin su ɗaya. Haidar shi kaɗai ta haifa, suma yaransu ɗai ɗaya ne. Sun manyanta babu aure dan sun kai 28yrs dukka kafin suka yi aure, haka kuma daga shikan su sun haifa yara mata, daga nan kuma shuru har yanzu, yaran shekarun su 20 amma ita Safna ba ta gama haɗa wa. Suma sun taso sak halin iyayensu na maitar kuɗi, da rashin ganin Uwar gidan Abban Haidar da ƙima, yanzu haka yaran sun fara jami'a dake cikin gari, kuma suna more wa da kuɗin ubansu. “Assalamu alaikum.” ya shiga ɗakin Ummin, sai dai babu komai a wannan parlourn sai ƙaran tv, tashar Africa tv, ɗaga kitchen ta fito, dan ita ya kanyi wiya ka ganta a babban parlour. Babbar macece mai cike da haiba da kalama, matar akwai ta da cika ido sosai, hannunta yana ɗauke ne da break, murmushi ta saki tana kallon tilon yaron na ta. “Wassalamu Alaikum, My son ka dawo.” “Eh Ummi, ya gida?.” ta zauna tana faɗin. “Alhamdullah.” “Ba dai yanzu za ki ci abincin rana ba?.” ya faɗa dan yasan halin Ummi ba ta son cin abinci gashi tana da ulcer. Ganin ta yi wani murmushin yasa ya ce. “Haba dan Allah, Ummi me yasa, na faɗa miki banso, sau nawa ina kawo masu aiki, sai dai su dena zuwa, ni ko aikin da kike yi banso, kuma Abbana ya umarci da a dinga kawo miki abinci har nan.” “Kai ma kasan wannan zance ne kawai, iyayenka ne za su min girki.....?.” sai ya katseta. “A'a mai girki Zarha mana.” “Haidar share kawai, tin da Allah ya ban lafiya bar ni, da masu aikin sun zo sai su kuresu kuma ni banshiga harkan su, ina raunin zuciya sosai abu kaɗan ke tsayamin a zuciya, haka su Sumayya ɗazu suka shigo nan karka yadda suka zage ni, ban faɗa ma ɗan ka rama min sai dai komai Lokacine.” ta faɗa tana kai bread ba kun ta, murmushi ya yi, inda ya gode Allah Ummi ba ta fita wancan parlour, kuma suma an musu iyaka da na ta parlour, sai da ya danna zuciyarsa sosai sannan ya kalla Ummi wacce kwata-kwata ba sa kama. “Gobe wannan tafiyar.” addu'a ta mai sosai dan ta san da maganar, daga haka ya bar part ɗin, a lokacin su Maman Safna ba sa nan, part ɗin sa ne a farko dan haka can ya nufa tare da yin tunanuka barkatai........ *(Hmmmm har yanzu wasa muke yi, domin kuwa wannan littafin mai dogon zango ne, na kusa koma wa kiran sunaye dan Kano da Abuja da Kaduna ya kusa zama labari ɗaya.) _Abubakar_ Bayan ya koma gida suka ƙara waya da Darling akan sai gobe za ta dawo, bai mu sa ba, ya kashe wayan, abincin da mai girki ya girka shi ya ci, yana ci yana ƙwaɗayin ranar da zai ga matarsa ta girka mai abinci sannan ta ba shi a baki, sam ita Darling ba ta san wani tarairaya ba sai tsabar tuhuma, yana so ya ƙara aure amma yana tsoron ya faɗa ma ta dan ba za ta yadda ba. Wayarsa ya ciro tare da shiga wannan wajen, so yake ya ɗan yi karatun *littafin sirrin Ameeratulkhair*. Bai tsaya ɓa ta lokaci ba ya shiga na gaba *MATSALA TA* . “Toh fa, Allah ya sa yana da daɗi." Ya faɗa yana shiga. ( Yauwa bara na dasa, kafin na rubuta komai bara na ɗan rubuta labarina kaɗan, Ni ce dai da nake rubutu wato Ameeratulkhair, shekaruna 20, hmmmm matsala ɗaya tak, sume Family na, da fari sun rabani da uban na, sannan sun raba ni da iya magana, sai dai ni da Allah na dogora, ina rayuwa ne bisa yadda ya tsaɓarmin, tin Ina ƙarama na zama mai fuska biyu, domin kuwa babu wanda yasanni, ban bayya fuskata domin cikin tsoron ƴan uwan nake, gani nake kaman da sun ganni za su sanya a kashe ni, neman rai na suke kaman yaƙi, sune kawai matsala amma su jira ina nan bayya a lokacin da *BURINA* yan cika, lokacin na zama tauraruwa, zan bayya ga duniya hmmmm ina tsimayen wannan lokacin, banda mugun nufi akan su amma wallahi wallahi ban yafe ba, da sun barni da muryata amma ina me naaaa naaaaa naaaa). Ƙarshen kenan sai Emoji na kuka, tabbas yasan a lokcin kuka ta yi ita ma, shi kansa ya ji wani iri haka sai ya ce. “Yanzu tana magana shine wasu suka mai da ta haka!?, Innalillah wa'inna ilaiyi raji'un', duniya ina za ki kaimu, yau kam sai na gama karanta dukkan wannan bara na kammala cin abinci." Ya faɗa yana ci gaba da cin abinci duk da sam girkin ba ya mai daɗi.........✍️ END. > Tab 😳😳😳😳 ku kuma kun ƙulle kenan team ɗin Mai sittin goma, hmmm Allah ya shirya mu. Toh fa kunfara jin ɓangaren *Haidar* shima dai ba sauƙin. Hajiya Ameeratulkhair 👂 yau fa Abubakar ya ce sai ya kai ƙarshen littafin sirrinki 🤣🤣. I'm sorry gaskiya ƴan uwanki sun cuceki, sun rabaki da Magana da Mahaifin ki 😭😭. Mu dai je zuwa Guys .........HASASHE KO BURI✍️ PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️. 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! PAGE 2️⃣3️⃣⏩2️⃣4️⃣ *ABUJA* Cike da nishaɗi suka koma gida, har ga Allah yana ji a ransa saura kaɗan ya mallake mata huɗu, so yake ya cika sunna, abin jin daɗi, biyu an bashi dama kuma yana ji da yardan Allah komai zai ta fi yadda yake so. Part ɗin Hajja suka shiga, aikam nan sun ka ga, Aunty Aisha, gaisheta suka yi ta amsa cike da walwala, da yake ta shirya za ta wuce, aikuwa Ukasha ya sanya Driver ya kaita har gida, kuma ya ba ta maƙudan kuɗaɗe, godiya ta yi mai sosai, sannan ya dawo ciki, take Rahma da wata yarinya suka fito, kallo ɗaya Ukasha ya musu ya ɗauke kansa dan shi bai son kallan mace, yanzu ne dai da aure ya saka sa gaba. “Yaya Umar sannu da dawo wa, Laaa Uncle Ukasha ana ganinka da ma?.” Rahma ta faɗa suna zama a gefe, da ta so Ukasha fiye da tunani, har an fara maganar aurensu, sai aka fasa da ta ji burin sa, tabbas a lokacin akwai mata uku da suke ƙasa amma ta zame kanta daga nan zance ya ruguje, cikin ikon Allah ta haɗu Abubakar wanda ya fi Ukasha komai sai dai ba lalle ya fi Ukashan kuɗi ba dan shi ma mugun mai kuɗi ne. “Ina nan, ya Kano ɗin da Abubakar?." Ukasha ya faɗa sai ta ce. “Alhamdulillah." Dun ƙafar ƙawarta ta ta ka, take ta buɗe baki ta ce. “Ina wunin ku?.” suka amsa atare. “Uncle Ukasha dama na yi ma wannan ƙawar tawa magana ne akan ka, to ta yadda ta amince, dama Yaya Umar ya ce na ta ya shi bincike, kuma an dace dan Kanuri ce." Ta faɗa da ɗan ɗar-ɗar. Ukasha kallon Umar ya yi dan ƙarin bayi, sai yaga Umar ya basar. Ƙwafa ya yi ya kalla yarinyar da ƙyau, bai ta ɓa ganinta ba sai yau, ba laifi ba mummunan ba ce, kuma dai-dai take, akwai dai dogon hanci sosai, ba ta haske sosai amma ta ƙara da bleaching. “Ta faɗa miki komai akai na?." Ya faɗa yana karantar natsuwarta. “Eh, kuma na amince, dan Burinka mai ƙyau ne.” “Ma sha Allah, kai gaskiya na yi murna." Umar ya faɗa sai Ukasha ya ce. “A ina kike da zama?, Ban ta ɓa ganin ki ba?." “A barno iyayena suke amma ni a nan na girma wajen yayan bababmu, karatu ne ya haɗa ni da Rahma, kuma ina yawan zuwa gidan nan amma ɓantaɓa ganin ka ba.” ta faɗa harda wani ranƙwaɗa murya. “Eh ban wani zama, ban numberki zan nema magabatanki dan jin ta bakinsu." Take suka yi exchanging number. “Ya sunan Hajiyar?.” Ukasha ya faɗa sai ta ɗan yi murmushi sannan ta ce. “Zuby, wato zubaida.” sai ya yi saving da haka sannan ya bar ɗakin. Yana fita Umar ya ce. “Ke da muka yi magana a sirri, ai da sai ki min magana, yanzu ji yadda kika ɓa ta komai." “Uhmmm ai shike nan, ƙawata zo mu shiga ciki.” “Yamma na yi yaushe za ki wuce?.” ya kuma tamabaya ganin ko shiryawa ba ta yi ba. “Sai gobe zan wuce, Baba nake jira.” ta faɗa tana shigewa ɗakin tare da kulle ƙofar. “Ƙawata ya kika ganshi?.” “Gaskiya Guy ɗin ya yi, ƙawata ina godiya.” “Kinfi ƙarfi haka a wajena, yanzu dai da biyu na zo Abuja, dole muje wajen Mai sittin goma kafin na wuce." “Gaskiya kam, nima ko kwalli ya ban dan na janyo hankalinsa." “Sosai ma kuwa, ai wani bura-uban sai bayan auren, duk ki yi waje da sauran ki mallesa kaman yadda na mallake Abubakar, kinsa tin daga wancan lokaci har yau bai sake waiwayen familynsa ba, kuma suna can cikin wahala.” tafawa suka yi, dan tin da Zuby ta shigo hirar da suke yi kenan akan Ukasha, balle yanzu da Zuby ta gansa sai ta yi ya yi mata 100%..... *KADUNA* _Muheey_ Yau a gidan su ta wuni, ta sha faɗa sosai wajen mahaifiyarta akan rashin leƙosu da ba ta yi, dan rabon da su haɗu da Mahaifinsu ta manta. “An ce ana ganin kina fita a motar Hajiya (Mariya), haka ne?." Mama ta faɗa tana kafe Muhibbat da idanu, haɗe fuska ta yi tana faɗin. “Mama ashe har gulmata ake kawo miki, to dan ta a ramin menene a ciki, har mijin na ta ya sani ai." “Hmmm ina raba ki dai, bansan wannan halin wallahi, ka tsaya in da Allah ya ajeka ya fi, amma ke tin kina ƙara akwai son rayuwar ƙarya, gidan nan dai babu abin da muka rasa amma ke sam mafiyinsa kike so." “Mama dan Allah ya ba ka bashi kenan ba ka nema ƙari da mafiyinsa." Ta faɗa tana miƙa wa, ɗakinsu ta koma, a lokacin duk ƙanenta na Islamiyya, dama ita ta yi sauka, to ci gaban ne ya gagara. *Merry* Kamar yadda ta yi tsammani sai da Abbas ya dawo mata da wannan kuɗin, murmushi ta yi dan ganin alert ɗin sannan ta yi accepting kiran da yake mata. “Babyna me yasa in na maka alheri kake dawomin da shi?.” ta faɗa tana zama kan fridge dan shigarta kitchen kenan. “Malamata kenan, ni ya dace na miki ba ke ba, yanzu dai ba wannan ba, kinci abinci kuwa?." “Gani a Kitchen dai, zan haɗa custard ne." “To shike nan, haɗa zan ta ya ki sha.” murmushi ta yi sannan ta sauka, kashe wayan ta yi sai bayan da ta gama haɗawa sannan ta koma room ɗin ta, video call ta kirasa, duk da ɗakin nasu da haske amma ya yi dishi-shishi dan haka ya koma waje dan ya fi haske, hira suka sha sosai. Ita dai tana zaune ne kan babban gadonta, ɗakin komai pink colour ne dan shine favourite ɗin ta. “Ustaz ɗina, yanzu da mun kammala karatu sai ka bar ƙasar nan! Gaskiya banso.” sai ya yi murmushi. “Aikin ba tabbas domin wani Alhaji ne ya yi mana alƙawari, balle ni a gaskiya na fasa zuwa, insha Allah zuwa lokacin aikin hannuna ya yi ƙwari kuma ina samu, zai fimin da barin county.” “Haka ne, domin a can ɗin bakusan wani aiki za ku yi ba." “Aikin company ne." “Okh, ni da kana son aikin soja dana neman maka." “Soja a'a, nafison aikin hannu, amma Malamata in shi ɗin nasamu zanyi.." “Zan ma hanya." “Na gode, ki barshi kawa.” “Baka so na ko kaɗan, komai na ce kai bai maka ba, shike nan sai da safe." Kafin ya ce komai ta kashe kiran, take yi offline, kiran wayan ya yi _witch up_ sai ya yi murmushi sannna ya koma cikin ɗakin na su. “Ɗan soyaya an gama ƙonewar kenan?.” Shamo ya faɗa da sigar tsokana. “Na lura kaf cikin mu babu wanda ya kai Abbas iya soyayya, mu na mu duk wasan yara ne." “In na fika (I.B) iya soyayya ai sai an bugani a jarida, ni Bara na matso mu yi sirri, dan kuwa ina so ka ƙara koyamin kalamai sosai, na lura Ma'esh sai da haka." Abdul ya kai maganar yana dariya, sai a lokacin Abbas ya ɗan dafa kafaɗar Abdul yana faɗin. “Hmmm Allah ya shirye ku, yauwa shamo ya maganar mu ne?." Sai Shamo ya ce. “Don't worry mutumina, zamu ja maka attendance." “Gobe hala akwai aiki sosai ne a gareji?.” “Eh Abdul, akwai motar da za mu kai Kano, da asuba zan fita." Hira suka sha kamar kullum, wani suyi dariya wani kuwa su yi hayani akai, haka har suka yi barci.......✍️ END. > Hmmmmm na yi shuru kawai. 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! PAGE2️⃣5️⃣⏩2️⃣6️⃣. *KANO* _Abubkar_ Yana kammala cin abinci sai ya tattara komai sannan ya koma ɗakinsa, kwanciya ya yi sannan ya ɗauki wayan nasa ya dasa karatun, shafin gaba ya shiga tare da ganin *FARIN CIKINA* “Uwata ita ce farin ciki ta, idan har mutum na son faranta min to ya so ta, murmushin ta shine ƙwanciyar hankali na, sai dai kash, ƴan uwan na, na jini sun ruguza wannan farin cikin dake zuciyar Mahaifiyarta, sai dai ina fatan Allah ya isar mana tin a nan duniyar ba sai munje can ba, ya saka mana, da gatanmu amma muke rayuwa a wahale, amma muna cikin farin ciki sosai da sosai.......” daga haka ya ƙare sai ya sauke a jiyan zuciya yana mai ci gaba da duba na gaba....... _Ameeratulkhairi_ Shuru parlour ya ratsa na tsawon lokaci mai yawa, sai a lokacin Mahaifiyarta ta saki wani ajiyan zuciya mai ɗauke da manufofi, kallo Ameeratulkhair ta yi sannan ta mata magana da hannu. “Shike nan, amma ki kula sosai, ni dai banso daga fara aikin ki, ki bar gida ba, amma wannan ne burin ki ba zan shiga haƙƙin ki ba.” hawaye suka idanun Ameeratulkhair, sai ta rungumeta, take ita ma mahaifiyar ta fara kuka, sun jima a haka, daga bisani suka tsagaita sannan Ameeratulkhair ta wuce ɗakinta dan fara shiryawa........... _Haidar_ Sallah magrib da Isha ne kawai suka fitar da shi daga gida, sai misalin 9:20pm ya fito daga ɗakin dan gaishe da Abban Haidar dan ya ji dawowarsa. A babban parlour ta riske Abban Haidar ya zauna yana shan ruwan da Maman Sumayya ta ba shi, bayan ya musu sallama ya zauna daga ƙasa yana faɗin. “Abbana an dawo lafiya?.” sai ya yi murmushi Abban Haidar har haƙorin makansa na bayyana. “Yarona lafiya lau lau, yana ga kaman ka rame?.” dan dattijon mai cike da haiba da kamala ya kuma faɗin haka, sai Haidar ya yi murmushi. “Abbana ƙi ba ma na yi fa.” kafin ya ce komai sai ga wasu ƴam mata sun iso cikin parlour, sai wani yauƙi suke yi, akan kujera suka zauna suna gaida Abban Haidar. “Abban Haidar an dawo lafiya?.” Take fuskar ɗan dattijon nan ya haɗe, sam su Safna ba su da tarbiyya shi yana sama suma haka. Safna da Sumayya taunar cwing gum suke yi. su dai suna kama a fizge amma ba da Abban Haidar suke kama ba, haka kuma shima Haidar ɗin sam ba sa yanayi, sai dai Haidar ya fi kowa na gidan ƙyau, daga shi sai Mahaifiyarsa. “Uban wa kuke gaisarwa daga a gadarance?.” Haidar ya daka musu tsawa, dama sun sa ba basa zama inuwa ɗaya da shi. Miƙa wa suka yi maimakon su zauna a ƙara sai suka bar parlour suna ƙunƙunai. “Abban Haidar (Haka ya yi umarnin kowa ya dinga kiransa.) ka ja ma wannan yaron ka mai kama da baƙin balaraɓe kunne, ya dena koran mana yara, sun zo su ji dubin mahaifinsu amma sai ya koresu." Maman Sumayya ta faɗa tana ɗan jijjiga. “Ke ba ki ga abin da suka yi ba.” Abban Haidar ya faɗa, tsaki ta ja tabar parlour, sai ya girgiza kansa sannan ya ce. “Yaro na, gobe ne tafiyan ko?.” “Eh." Ya faɗa yana jin zafin tsakin da ta ja ma Abbansa. “Shike nan, ka je ka huta, da safe kafin ka tafi kazo na ganka, sannan na turo maka da wasu kuɗaɗe, salan ka dawomin da shi, dan mai kai sam baka ɗaukan shaware ne da aikin companynka ka dawo yi, ka bar wannan aiki.” “Abbana ai nama alƙawarin zan amsa sai bayan wannan aikin, Aikin jarida buri na ne, sannan aikin da kake magana akai wannan burin Abban na ne, kuma duk zan cika." “Shi yasa nake alfahari da kai, yanzu kar na jaka da magana, je ka kwanta." Rabuwa suka yi kowanne cike da soyayyar juna. Yana shiga ɗakinsa ya kwanta akan babban gadonsa, Company haɗa motoci na H - Halal Company na Abbansa ne wanda a zahiri Abban ya mallaka mai, zai fara zuwa soon, dan sanya Abban Haidar farin ciki. Amma kafin ya fara ya so a nemo mai abokin aiki amintacce sosai. “Gobe zan ma Abba magana insha Allah.” ya faɗa dan ya tina ya so ya faɗa mai amma yake mantawa..........✍️ *ABUJA* _Ukasha_ Washegari weekend babu office, dan haka da misalin 4:30pm ya nufi gidan su Fillo, yau shi kaɗai ne dan Umar ya fita zuwa kasuwa. Bayan ya aika wani ya kirata, ba ta ɓa ta lokaci sosai ba, ta fito sanya take cikin hijabi har kasa ɗan kaɗan ake iya hango zanin amatamfar da ke jikinta, baƙi ne hijab ɗin sai ya ƙara haska fatar da sosai, fuskar ta ba ta bayyana ba sosai saboda ta jawo hijab ya rufa rabin fuskar, bayan ta yi sallama ya amsa sannan cikin yaran fullancin ta fara gaishe da shi sai kuma ta sauya harshen ta dawo hausa amma hausar a gurbaci take. “Ina yini?.” sai dai bai amsa ba, kawai kallonta yake yi, a karo na farko ya ji wani iri dangane da ita, shi bai ta ɓa jin irin wannan yanayin da game da mace sai yau, kuma ya ji zuciyar sa ta buga, karo na farko kenan a rayuwarsa da ya ji mace ta shiga ransa, ba wai dan cika burin sa ba, sai da ya ɗan ja lokaci kafin ya ce. “Ina lafiya lau. Ke fa?.” “Alhamdulillah." daga haka bai ƙara cewa komai ba ita ma haka, karantar natsuwar ta ya ke yi sosai kuma ya fahimta tana dashi, can sai ta ce. “To zan koma gida ka gaida su Mama.” da sauri ya ce. “To shike nan na gode da lokacin ki amma kin amince za ki aure ni a haka?.” sai ta dago take fuskanta ya bayyana sosai, ƙandarewa ya yi da kallon fuskarta, wani murmushi ta ɗan sakar mai, sannan ta nufi cikin gida har da haɗawa da sauri-sauri, sai ya saki murmushi dan ya lura kunya ce ta mata yawa, motan ya shiga sa'annan ya nufa hanyar gidan su ƴar yarbawa dan a jikinsa yake jin watan aurensa ya matso. Tana shiga ta ga Dada am na wanki da sauri ta amsa tana ce wa. “Laa ba na faɗa maka zan dinga yi ba.” ta kai maganar ta zama daga gefe tare da ɗaukan sabulu ta fara. “Ya kun sasanta? (On waɗi laawol?).” Dada am fa tambaye ta. Sai ta yi murmushi. “To masha Allah, Allah ya nuna mana lafiya? (Masha Allah, Alla hokki no fayde e jam?).” da sauri Fillo ta miƙa tana shigewa ɗakin, girgiza kai Dada am ya yi tana faɗin. “Ameen, yaro sai kunya, kai Fillo fito nan mu yi magana." Tasan ba ma za ta fito ba sai anjima kuwa. *****Bayan ya sauka a mota nan ma aka mai sallama da Ashake, ya jima a tsaye kafin ta fito, ta haɗe fuska sosai, dan wani zani ma ta yafa, kun dai san yaruba, Allah ya so dan ta gama wanki da ba za ta fito ba. Sallama ya mata ta amsa tana ɗan sakin fuskarta. “My name is Ukasa. I came because I love you. Please… will you accept my love? (Suna na Ukasa ne. Na zo ne saboda ina sonki. Don Allah, za ki amince da soyayyata?).” sai ta ɗan yi murmushi, ta yi soyayya da maza uku hausawa kuma duk sun yaudareta. “Sir, I don’t even know you. And honestly, I can’t marry a Hausa man — you people have attitude. (Ranka ya daɗe, ban san ka ba. Kuma gaskiya ni ba zan iya auren Bahaushe ba — ba ku da hali).” “But I’m not Hausa. (Amma ni ba Bahaushe bane.)." Sai ta kallesa tabbas bai yi kama da bahaushe ba. “Oh really? Then who are you? (Da gaske? To, kai wane ne?).” “I’m Djerma." “Hmm, okay… I’ve heard you. I’ll think about it. (Hmm, to shikenan… na ji. Zan yi tunani).” sai ya ji daɗi a ransa sannan ya kuma faɗin. “Uhmm, but there’s just one thing — something small I need to say first. (Uhmm, amma akwai ƙaramin abu guda da nake so in faɗa.).” ya faɗa yana mai jin da ƙar ta yadda. “ Alright, I’m listening. (To, ina sauraronka).” sai da ya sauke ajiyan zuciya sannan ya ce. “I believe in marrying four wives. May Allah make it easy. But I’m telling you the truth — if that’s a problem for you, I understand. (Ni ina da burin auren mata huɗu. Allah ya sauƙaƙa. Amma na faɗa miki gaskiya — idan hakan zai yi miki wahala, zan fahimta.” zaro idanuwa ta yi tana cewa. “Four wives?! Hmm... May God guide you. Honestly, go find someone else. I’m the jealous type — I can’t handle that. (Mata huɗu?! Hmm… Allah ya shiryar da kai. Gaskiya, ka nema wata. Ina da kishi — ba zan iya ba.)” sai ya marairaice fuska. “Please, My Ashake, help me reconsider. (Don Allah Ashake, ki taimaka ki sake tunani).” furzar da iskan bakinta ta yi ta ce. “Okay… I accept. But just to be clear, the other things — no hidden issues, right? (To… na amince. Amma fa dai sauran abubuwan babu wata matsala, ko?) “No, everything is fine. A’a, komai lafiya.)" “ Then go and speak to my uncle. Bye. (To, ka je ka yi magana da ƙanwata/uncle ɗina. Sai an jima.)" Wani nishaɗi ya ji sannan ya ce. “Thank you so much for your time. (Na gode sosai da lokacinki.)." Hannu kawai ta ɗaga mai tana shigewa gidan nasu, saboda murna har buga jikin motarsa ya yi, yanzu mace ɗaya ta rage Bahaushiya, kuma yana fatan ya yi dace, domin kuwa watan gobe insha Allah zai auresu dukkan. Mota ya data yana mai barin layin......✍️ END. > Ukasha Fatan nasara, saura Bahaushiya hmmm akwai bura-uba, ga dukkan alamu Asheka ƴar Yoruba akwia masifa, Fillo bafullatana akwia kunya, ita kuma Zuby Kanuri 🥺 bin Boka,hmmmm ko wacece bahaushiyar oho?. > Haidar kai kuma haka gidan naku yake, toh Allah ya ƙyauta wasu dai akwai hassada. > Abubakar sannunfa Darling ba ta gida ka zamu yadda kake so, amma fa Darling ba ta ƙyauta maka. Mu dai zuwa. Daga littafin *HASASHE KO BURI* by PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️. 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕 PAGE2️⃣7️⃣⏩2️⃣8️⃣ *KADUNA* _Abbas_ Abbas da ogansu suka nufi Kano dan kai wata mota, tin asuba suka fita saboda mai motar na jira, dan Alhajin ya shigo Kaduna ne motar ta samu matsala, sun isa da wuri dan kuwa motar lafiyayya ce sosai. Da isarsu gidan Alhajin, aka umarci su jira yana zuwa, a dai-dai lokacin Haidar ya fito daga part ɗin sa cikin shigar manyan kaya ya yi ƙyau sosai, sannan ya ɗauko trolley wanda ya zuba abubuwan da zai buƙata. Har ƙasa suka gaishe da Haidar sai ya yi murmushi yana dafa su da faɗin. “Injin miya (Haka yake kiran Ogan Abbas) ban so, ko Abbana bason wannan gaisauwar yake ba, ya Kaduna?” “Alhamdullilah.” “Sir good Morning." Abbas ya faɗa sai Haidar ya miƙa mai hannu suka gaisa. “Morning, kai ma Injin miya ne koh?.” sai ya yi murmushi ya ce. “Eh muna ta ɓa wa.” “Allah ya ƙara jagora, bara na shiga zan fito da Abbana ɗin.” daga haka ya yi ciki, su kuma suka bishi da idanu. “Kasan waye me wannan gidan?.” Ogan Abbas ya faɗa. “A'a Oga.” “Kasan H - Halal Nigeria Motors?.” “Oga waye bai san wannan Company ba, ai yawancin daga can ake kawo mana kayan aiki.” “Haka ne, to wanda muka zo wajensa shine mai wajen, wannan kuma da ya wuce shine babban ɗan sa, kuma ma'anar H- Haidar Halal Motors.” zaro idanunwa ya yi, yana ƙare ma gidan kallo, tabbas tin shogowanshi ya san mai gidan nan ya tara sosai, dan motocin dake gidan baya iya ƙirgawa. “Ashe yau zanga wannan Attajirin." “Aikuwa, shi yasa na tawo da kai, na aminta da kai sosai, kuma na yadda da kai, shi Alhajin yana neman na turo mai yaron aiki na guda 1 tak, amma bansan dalili ba, sai dai kai na za ɓa, duk da ba komai ka iya ba, amma hazaƙanka ya na min sosai.” “Ogaaaaa na gode.” Abbas ya faɗa yana rungume Ogan sa. “Kai sake ni, ka bari ya fito dai, tare zamu koma sai bayan wata biyu zaka dawo domin zuwa lokacin ka kammala karatun ka.” “Haka ne, dan yanzu shirye-shiryen exam muke yi." Tare suka fito suna tafiya a tare cike da nishaɗi, yadda kasan wasu abokai, haka suka jero har wajensu. “Ina kwana Alhaji.” suka haɗa baki wajen gaisasa, da murmushi ya amsa. “Har kun kawo kenan, da yake wani zan ba mota kuma yau yake so, shi yasa na ta doku." “Allah sarki, yanzu dai mota ta gyaru sosai.” “Yauwa haka ake so, ina ɗayan maganar na mu?.” “Alhaji gashi nan, sunnan sa Abbas." “Haidar ga wanda na maka.” Haidar ya saki murmushi yana kallon Abbas sai ya ce. “Masha Allah kaman kasan ina so na ƙara maka magana.” “Ya yi maka?.” “Eh, Abba tunda Injin miya ne ya kawosa na amince, amma sai nan da wata uku zuwa lokacin mun kammala wannan aikin har result ya fito, amma kafin nan ya fara zuwa dan sanin komai kafin na zo." “Alhaji dama shima yana so ya kammala karatunsa gashi shirin exam suke yi ma.” “Ma sha Allah, ai hakan ya yi, da ka kammala kawai ya zo nan.” godiya suka mai sosai. “Abbana sai na dawo.” Haidar ya faɗa yana raba hannuwansu. “Da kun isa ka tabbatar ka kira ni.” “Insha Allah, Abokina zo muyi wata magana mana.” daga haka ya ja hannun Abbas, tare suka jera har gaban wata arniyar mota wanda ya shiga cikin ya ajiye abubuwan hannunsa sannan ya ce. “Za mu yi magana, dan Allah ka riƙe amana, domin kuwa ni ba wani zama zan dinga yi ba, ina yin wasu ayyukan, amma karka damu zan ki raka, number ya yi?.” ya miƙa mai wayansa yana faɗin. “Eh Sir, sai na jika, Na gode sosai.” murmushi Haidar ya yi yana faɗin. “Injin miya zai baka saƙo." Daga haka ya tada motar yana fita. Murmushi ne kwance a kan fuskarsa ya iso wajensu Alhaji. “To muje." “Injin miya ai ƙwayi breakfast, mu shiga ciki." Hmmmm ai ba'a magana kawai, Ogan Abbas da Abbas sai bin ko ina suke yi da kallo, dan gidan ba magana, a parlour suka zauna. “Maman Safna, a haɗa musu breakfast, wai har kin shirya ne?.” Maman Safna da take sanye da hijab har ƙasa ta faɗaɗa murmushi tana faɗin. “Eh Abban Haidar, muna so mu dawo da wuri ne." “Okay, karku daɗe, kuma kuja ma Driver ku ja mai kunne ya bi da ku a hankali.” “To Abban Haidar." “Ku bi Flight kawai, zan miki transfer.” “To muna godiya, daga haka ya yi part ɗin Ummin Haidar, wani harara ta dalla mai, dan kuwa duk buru-uba yau sai sun shiga tsakanin su. Abinci masu rai da lafiya Zahra mai girki ta haɗa musu, aikam suka ja daɗi, bayan sun gama Alhaji ya basu dubu hamsin ladan aiki, sannan ya biya su kuɗin aiki. Aikam sun mai godiya sosai. “Abbas sai mun ganka." “Insha Allah.” a dai-dai lokacin ƴam mata biyu suka fito suna ta ranƙwaɗa, gaishe da Abban Haidar suka yi, sannan har sun ɗaga ƙafa sai Abban Haidar ya ce. “Ni kaɗai kuka gani?.” da sauri suka gaida sauran, sai dai me da sauri Sumayya ta kuma kallon Abbas tana faɗin. “A....A...Ab...Abbas.” ba shi kaɗai ba dukkansu suka kalleta, dan yadda ta kira sunan nasa. “Abbas ni ce fa Sumayya Abu Haidar." (haka sunan su yake har a school, komai Abu Haidar ko Abban Haidar, shi yasa suka tsanar Haidar sosai). “Bangane ki ba.” Abbas ya faɗa yana mamakin a in da ta sanshi. “Yanzu school za ni, ban numberka za mu yi magana." Ganin kamar ba ta san Abban Haidar na wajen ba, yasa ya koma ciki, sam bai son ɗaga musu murya dan kanshi yana sarawa in ya yi hakan. Yana wucewa Ogan Abbas shi ya ba ta number sanann suka wuce. “Ai da ba ka ba ta ba, sam ba ta da ɗa'a." “A'a fa, kasan ko hakan wani alkairi ne." Suka ci gaba da hira har suka fita a babban haraban gidan. Tana shiga mota ta rungume Safna tana faɗin. “Finally na samu number Abbas." “A Ina kika san shi?." “Hmmmm a facebook, guy ɗin ya min, ke in kika bibiye page na shi ko, za ki kwasa ilimi, ɗan boko ne sosai, ina yawan ganin videos na shi yawanci friends dinsa ke daura, ke kinji speech, hmmm su 4 ne gaba ɗaya Poly na Kaduna ke ji da su.” “Okay amma dai ba sonsa kike ba?.” “Kina wasa ne, ai ni na haukace a soyayyar Abbas." “Kina ruwa kinsan dai Mom ba za ta yadda ba." Ta figa motar tana wani sakin murmushi. “Ni dai na gani kuma ya min.” girgiza kai kawai Safna ta yi dan tasan hauka kawai Sumayya ke yi............✍️ > Hmmmmm 🤐 yanzu wasan zai fara kun faji wata sabuwa Sumayya ƙanwar Haidar da son Abbas, gefe guda ga Merry ♥️, hmmm haɗin biza kenan....✍️ FREE PAGE'S ya kusa ƙare wa, ai munyi da waya, akwai point ɗin da nake so ku kai ne..... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️. 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! PAGE 2️⃣9️⃣⏩3️⃣0️⃣ *ABUJA* Su biyu ke tafiya a cikin mota suna hira, a hankali ta faka daga gefe dan ganin wasu mata sun tare motar, Zuby da ke driving ta sauke glass tana kallon mata biyun wanda a ƙalla za su iya haifa su. Bayan sun gaisa ɗaya ta ce. “Dan Allah Filin Bora muke tambaya." Tana faɗin haka sai Darling ta ɗago ta kalle su. “Ku shigo can zamu.” ba musu suka shiga cikin motan, dan kuwa ba kowa ke zuwa wajen ba, saboda hanyar babu ƙyau. “Mama kuma wajen Mai sittin goma za ku?.” “Ƴar nan eh.” Maman Safna ta faɗa tana jin sanyi a ranta dan yadda ake koɗa wannan malamin. “Muma can zamu, gaskiya aikinsa ba wasa sai shi akwai tsaɗa.” cewan Zuby “In da biyan buƙatar ai kuɗi ba matsala bane, munan daga Kano muke, flight muka biyo, to me motar da muka hau shine ya sauke a in da kuka same mu.” faɗin Maman Sumayya. “Hala kuma an saku a gaba ne?.” Maman Safna ta tambayesu, sai da Darling ta yi murmushi sannan ta ce. “A'a Mama, mijina zan sa a ƙara mallake min sa, sai ita ƙawata ya janyo hankalin sa wajensa.” “Na ku da sauƙi, mukam kishiya ce matsalarmu, ta cike mana gida, ga yaronta shima duk sun hana mu jin daɗin gidan. Maganinsu za'a yi mana.” haka suka dinga hira kaman wasu sa'anni. A wani tsohuwar Fili suka faka sannan suka fito, ba yawaitan gidaje a wajen sai wani ƙarami guda ɗaya. Suna isa jikin wajen suka bi layi dan mata ne a wajen sosai. Ba su jima ma ba Maman Safna suka fara shiga. Sannan bayan sun fito su Darling Suka shiga. Mutum ne zaune cikin jajayen kaya, sannan fuskarta an shafe ta da farin fenti sai kuma zanen baƙi abu. Mummunan ne sosai, sai washe jajayen haƙoransa yake. Wani abune a hannusa yana jinjigawa sannan ya watsa akan wani ƙyalle. Magana ya fara cikin amon murya da cika kunni. “Za ki aure Ukasha, kuma za ki juyasa yadda kike so, sai dai ki bi a hankalin domin jininsa na da ƙarfi, amma ki fara sanya wannan ƙwallin, sai kuma wannan garin ki jiƙa ana saura sati ɗaya bikinku kullum ki dinga sha da ruwa, sai dai ki tabbarar ke ce Uwar gida, da kuma ke ya fara mu'amala." Jiki na rawa Sumayya ta amsa wani ƙullin magani da ƙwalli. “Ke kuma, karki damu mijinki na cikin kariyar mu, ku ta fi, kuje.” Darling ta aje mai uban kuɗi sannan suka fita. A airport suka sauke su Maman Sumayya, sun musu godiya sosai, Darling harda alƙawarin in ta samu lokaci za taso gidansu tinda ita ma a nan Kano ɗin take............. _Ashake_ Yayan Ashake bai jima da dawo wa daga aiki ba, Asheke kawai ya samu tana kallo a waya, bayan ta gaidashi ya amsa sannan ya shiga room ɗin sa can ya fito ya zauna sannan ya kalla Ashake da ƙyau ya ce. “Àbúrò mi níyàwó sọ pé ọ̀la ló máa lọ sílé ìdílé láti dá ọrọ ìgbéyàwó dúró, ní oṣù tó ń bọ́ ni ó fẹ́ kí ìgbéyàwó náà wáyé. (Ƙanwata saurayin nan ya ce gobe zai je family house Dan tsaida maganar aure, a watan gobe yake so auren ya kasance.)" “Ó dájú níyá. (Shike nan Uncle.)” “Ṣùgbọ́n ọkùnrin náà ti ní fún ẹ̀ ni? (Amma yaron ya miki ko?)." “Bẹ́ẹ̀ ni, níyá.(Eh Uncle.).” ta faɗa tan aiyana irin yaɗuwar Ukasha amma ba ya gabanta sam. “Ó dára, fún mi nǹkan àmì, inú mi ń rẹ̀, níbo ni ìyá àbúrò rẹ lọ? (Yauwa, miƙo min Alama na ci yunwa nake ji, ina Auntynki ta je.).” “Ó lọ rà àwọn ohun ìjẹun, ní báyìí ló máa wá.(Kayan miya taje siya, yanzu za ta shigo.)” da haka ta kawo mai abinci, a lokcin Maman Amira ta shigo, bayan a ajiye kayan miyan, Ashake ta ɗauki roba ta fita dan su wanke, gobe akwai aikin abinci. "Surprisingly, it’s only you he loves, or maybe he has plenty money. (Da mamaki ace daga ke sai ke yake so, ko kuma yana da kuɗi ne sosai)” “Yes o, I hope after marriage he will leave me to start working, because next week our results will be out. (Haka ne, fatan ɗaya bayan auren ya barni na fara aiki, dan next week result din mu zai fito.)” “Okay, ask him for us, but about love, he just wants marriage, isn’t marriage supposed to be love? (To ki tambaye sa mana, amma ya maganar soyayya, shi aure kawai yake so, dama ana aure ba soyayya ne?)” “Eh, maybe he wants love after marriage, only he knows. (Eh to maybe she bayan aure yakeson soyayyar, shi ya sani.)” “Hmmmm, God should grant us good health, then let’s hear what the Alfas will say. (Hmmmm Allah ya nuna mana lafiya, sai ma munji me su Alfa za su ce.)” ta yi murmushi dan tunawa da Alfa, ƙanin mahaifin ta ne shima, yana da faɗa sosai, shima mai dai sam ba ya son hausawa....... _Abubkar_ Kiran sallan farko ya farka, barcin ne ya ɗauke dat nan take, bayan ya yi alwala ya tafi masjeed, yana dawowa ya ɗan shingiɗa akan sopa, ba wani aiki ya yi ba jiya amma ya gaji sosai. Wayansa ya sake dubawa yana mai tuna ya karanta *Farin cikina* daga nan ya barcin ya ɗauke sa. *Mafarkina* shi ya shiga sannan ya fara karantawa. ( *MAFARKI NA* KIYaruwar ƴanci, rayuwa kaman kowa, ina so na shaƙar iskan ƴan ci, hmmmm sai dai Mahaifiya ta ce mun komai lokaci ne, kuma na haƙura ina nan ina jiran wannan lokacin, da zan zama tamkar tantabara, na yi shawagi kamar kowa.) Nunfashi ha sauke sannan ya shiga na gaba. *Damuwarta* (Damuwata ɗaya ne tak shine ƙyau, wasu na nema ruwa a jallo, amma Allah bai basu ba, sai dai ni kam Allah ya jarrabeni da ƙyau wanda shine ya yi silar duk halin da nake ci, ƙyawuna ya yi wayan da ya zama min masifa, amma na ɗauka hakan a matsayin ƙaddarata, ina da ƙyau wanda ni kaina ina mamakin kallon kai na a mirrow, Alhamdulillah kawai, shi yasa na zaɓa ɓoye kai na har zuwa ga cikon *Hasashe na*.) Shafin a hanɗe yake dan haka ya dasa. (Hasashe na, samun mamallakin zuciyata, wanda ya zai zama min gata, da na Mahaifiyata, ya zama min wani bango wanda zan dinga jingina a kodayaushe, ina fatan na Hasashe na ya faru ya tabbata ga duk wanda Allah ya zaɓa min, ina son muyi rayuwa bisa ta farkin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ❤️, ina son na koyar da yarana addini da kai na kafin su shiga makaranta, ina son na koya musu karatu amma kash ba ni da wannan ikon, ban da ikon rere musu karatun Alkur'ani, kai alkur'ani ya yi, sauti mai sanyi ga daɗi sannan ga riba, ni sai dai na yi a zuciya. Hmmmmm Hasashe na Maybe ya zama gaskiya......) Bai san hawaye ya ɗan gangaro daga idon saba sai da ya ji lema, tabbas kanshi ya yi nauyi, ya manta rabon da ya ɗauki alƙurani, da sauri ya miƙe amma me kaf gidan nan babu Alqur'ani, haka a cikin wayansa, download ya yi yana shiga har jikinsa na rawa. Suratul baƙara ya fara shiga bayan ya karanta fatiha, karatu ya fara yana mai kulle idanunsa hawaye na zuba, rero ayoyin kawai yake yi cikin fitar da hukuncin kowani harafi, ji yake tamkar an fara yaye mai wani abu a cikin zuciyarsa, ya jima yana kuka da karatun, take ya ji wani iska na ratsa shi sosai, shuru ya yi yana mai ƙura ma littafin Allah ido take yakai bakinsa ya sumbata. “Yaushe rabon da na karanta wannan littafin? Me yasa na dena? Ya akai ban samu ko da Alqur'ani ɗaya ba a gidan nan? Me yasa har na wayana babu?.....” kiran da ya shigo wayarsa ne ya tsaida shi, dan Haidar ba ne ba yadda za'a yi ya ɗau wannan kiran. Bayan ya yi sallama a hankali, sannan shi Haidar ɗin ya amsa. “Sir zamu ta fi, mun jira ko zamu ganka amma shuru, fatan lafiya?.” “Eh Haidar, kuje kawai, kai na yana ciwo, Allah ya tsare kuma fatan sa'a." Ya faɗa da ƙyar, yana jin shi yana mai addu'a amma bai amsa ba. Sai ya ajiye wayan yana miƙewa sannan ya nufa cikin room ɗin sa, zama ya yi yana mai dafa kansa sai kuma ya miƙe ya fara Safa da marwa. Wani ihu yaji anyi a cikin kansa take ya zube a kan carpet ya suma....... END. > Hmmmm kunji wata sabuwa, Matan Abban Haidar sun haɗe da Darling wato Abubakar, sannan ga Zuby Kanuri ita ma, kuma wai duk a wajen *Malam Mai sittin goma* . Hmmmm ko ya ya tafiyar za ta kasance, mu je zuwa dai...... > Yau dai tsab mun karanta littafin *Ameeratulkhair* gaskiya ni kai na zan so sanin wacece ita, su waye suka ruguza komai na rayuwarta?, Su waye suka sa ta fara rayuwar rashin ƴan ci? Waye mahaifinta? Ko farcenta babu mai gani sai mahaifiyarta ashe dai wani lu'ulune a ɓoye....... Tabbas wani ƙyau ɗin masifa ne. > *Abubakar* yau dai ka kai ƙarshe, sai Ameeratulkhair ta tinama waye *Allah* hmmmm kai dai Darling ta gama da kai wlh, a ce kaf gidan ka babu Alqur'ani, ka yi download ka karanta gashi daga ƙarshe ka faɗi, Suma ka yi ko barci 😓....... Mun dai HASASHE KO BURI✍️ 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! PAGE 3️⃣1️⃣⏩3️⃣2️⃣ *KADUNA* Su biyar ne a zaune a cikin ɗakinsu, Alhajin dake sanye da babban riga ya kuma yin murmushi sannan ya ce. “Zuwa jibi zasu wuce, na so ace da ku a ciki, amma ku kammala karatun sai ku bisu, kar ku yi wasa da aikin nan domin sai an biya makuɗan kuɗi ake samu, amma saboda ina son taiamaka ku ne, farashin kaɗan na nema, gashi ana samu fiye da tina.” ya kai maganar yana ɗaukar pure water sannan ya kai bakinsa. “Alhaji, insha Allah da mun gama zamu yi maka magana, gaskiya muna godiya.” faɗin Shamo sai I.B shima ya ce. “Haka ne Alhaji, muma muna buƙatar wannan aiki.” sai ya duba wayansa alert ne da 800k ya shigo daga Mymoon. “Zan biya mana kuɗin jirgin in lokaci ya yi." I.B ya kuma faɗa sai Alhajin ya ce. “Shike nan.....” “Gaskiya ni na fasa, saboda na samu wani aikin hannu kuma ya min sosai, dan kuwa nan da two month zan koma aikin a Abuja ƙarƙashin Company H - Halal Nigeria Motors.” Da mamaki suke kalla Abbas, sai ya ɗaga musu kai alaman tabbatarwa. “Mene? Wai ba za ka U.S ba? Akan me Abbas?." “Kawai dai Abdul.” yana faɗin haka ya yi waje. “Aiki ne ai ba dole ba ne, akwai masu so zan musu magana, ku dai shirya.” daga haka Alhajin ya yi waje. Shuru ya ratsa ɗakin. “Meyasa Abbas yake son tarwatsa mune?." Sai ga Abbas ya shigo. “Abbas ya wuce su ɗauke ka a mai wanke mota, ni dai gaskiya ban yadda ba da kai zamu.” sai Abbas ya yi murmushi sannan ya dafa kafaɗar Shamo ya ce. “Karka damu mutumina, muna tare har abada, kawai zan ci gaba da aikin hannuna kawai.” haka suka jima suna bashi baki amma ina ya kafe sosai. Daga haka suka bar maganar. Haka dai rayuwa ta ɗan fara gangarawa suna shirin exam, Mymoon na ta narka ma I.B kuɗi masu yawa har sun siya filaye huɗu duk da sunansa sannan a cikin ɓakin ta zuba kuɗaɗen kaman yaƙi. “Mymoon, ina kike kai kuɗi ne, kashe kuɗin ya yi waya." Dad ya faɗa yana kallon Mymoon da ta haɗe rai. “Dad, bansan ya kake so na yi ba, shike nan na dena ta ɓa komai a ciki shike nan.” “Ni bance, domin kuwa duk dukiyata na kune ke da Taj......” sai ta miƙe. “Dad wani Taj ɗin?, Ta ya kuɗin ka ya zama na sa, ohhhh na gane.” daga haka ta bar Dining ɗin, girgiza kai ya yi yana kallon Mom da ke cin arish ya ce. “Yarinyar nan duk ta sauya, bansan me ya shiga kanta ba sam, kallona take tana mai faɗa min magana.” “To Ni Dad me zance, ba ka son Ina mata faɗa, ga kuma lokacin yin faɗan ya yi amma ba ka saba ma ta ba." Sai suka yi shuru. “Hmmm duk me ke kanta zan sauke ma shi, Taj zan kira ya shigo ƙasar nan domin aurensu, in na mata auren sai na ga ƙaryan tsiya.” murmushi Mom ta yi tana faɗin. “Ban shiga tsakanin ku, zan iya jin kunya nan gaba.” sai shima ya yi murmushi. *** Dariya ta yi sosai dan jin abin da Abdul ya ce. “Kai Honey, yanzu dai mubar wannan zancen, nawa ne kuɗin da kake buƙata.” “Uhmmm 500k ne haka.” “Shike nan karka damu, zuwa gobe za ka ji saƙon.” sai ta miƙe daga kan gadonta tana kuma cewa. “Zan yi ma Uncle magana, yanzu dai da mun kammala exam sai tafiya.” hira suka sha sosai sannan ta kashe wayan. *KANO* _Haidar_ Yana isa haraban gidan tv na GOODNESS TV, ya riske mutane duk sun shirya, har Bus ɗin ɗaukarsu ta iso. Hatta Ameeratulkhair an ba ta I.d card, daga in da yake ya ke karantar natsuwarta, a takure take sosai dan ta kasa sakin jiki, kamar dai kullum irin wannan shigar ta yi. Sun jima sai Haidar ya kira Sir Abubakar, jin abin da ya ce aikam ya ce. “Duk mu tafi, C.E.O ba zai shigo da wuri ba.” da mamakin take kallon mutanen dake shiga dan a ƙalla sun kai kusan 15 haka. Sai ta saki ranta dan ta za ci ita da Haidar kawai za su. A layin na uku ta zauna sannan mota ta hau titi, take Haidar ya dawo kusa da ita yana faɗin. “Fatan ban takura ki ba?.” sai ta ɗaya mai kai, zaman sa ya gyara sannan ya ciro wayansa yana ɗan latsawa, sun ɗan jima a haka kafin ya ce. “Ameeratulkhair, gaskiya kina burge ni sosai, jiya na soma ganinki amma kin shiga raina, ban ta ɓa soyaya kuma bansan yadda ake yi ba amma akan ki na ji wani abu na daban haka." Ya kai maganar cikin sanyin murya, ita kuwa murmushi kawai take saki, a karo na farko wani yace yana son ta ba tare da yasan wacece ba. “Naso ace a yanzu muna magana da ke sai sai babu dama, sanya min numberki sai mu yi chat, Please." Ba musu ta sanya mai number sannan suka hau online suka fara chat. “Na miki?.” sai ta tura mai Emoji na thinking, can sai ta rubuta 'No' shuru ya yi sannna ya yi typing. “Why?.” “Ka fiye surutu.” “Na dena.” sai ta yi murmushi sannan ta ce. “Zan yi tinani to.” kaman sun san juna haka dinga shan hira sosai, dujuka huɗu za su wanda duk an tsara tafiyan na su. “Na ji daɗi na ga muna da yawa, mu 15." Sai ya mata reply. “Eh, kinsan aikin babbane shi yasa, kuma kowa da aikinsa, kinsan dai naki.” “Ɗaukan rahoto, rubuce-rubuce." “Eh ni kuma photo.” ba ta san lokacin da ta sake da shi ba, sai faman hira suke yi sosai, sai wajen yamma suka isa wani daji, gaba da baya bishiyoyi ne sosai, haka kuma wajen akwai ƙyau sosai. Kafa runfuna suka yi, dan harda masu gadi suka zo, su uku ne masu aiki, Haidar mai ɗukan hoto, Ameeratulkhair mai rubuce-rubuce sai wani mai jawabi, sauran daga masu girki sai masu gadi. Huta suka kunna a tsakiya , anan duk suka yi alwala sannan suka yi salla cikin jam'i, gaba ɗaya a hau hira cikin nishaɗi, ko wa zafi yake ji amma banda Ameeratulkhair dan ko niyyar cire nikaf ba ta da shi sam. Duk sun ci abinci amma banda ita ta dai ajiye agefenta, kuma tana da ga nesa da su. “Barka." Haidar ya faɗa yana zama tare da kai goran faro bakinsa. “Ba ƙyajin yunwa ne?.” sai ta girgiza. “To ki ci mana.” ta kuma kaɗa kai kaman ƙaɗangare. ”Tashi na rakaki cikin can sai ki ci.” ba musu ta bi bayansa har zuwa ɗaya daga cikin rumfan nasu, zama ta yi a ciki shi kuma ya zauna a waje, ya fahimci ba ta so a ga fuskarta ne. “Aganinka ya za ta kasance? Ƙyaƙƙyawa ko mummunan? Fara ko baƙa?." Zuciyarsa ta tambayesa. Sai ya yi saurin faɗin. “Koma ya take Ni kam zuciyata ta ya ba gaskiya.......” END. > Hmmmm masu tafiya U.S Allah ya sa aikin yadda kuke tsammani ne. Amma I.B kana bura uba, sai kace tsafi kabi sai jidan kuɗin Mymoon kake🙄🙄🙄. > Finally dai Dad ya ce Taj zai dawo..... Ko Mymoon za ta iya rabuwa da I.B oho, kuma ga dukkan alamu ba ta don Taj..... > Hmmm Soyayya ruwan zuma, Haidar ka rufta amma ka ji daɗi dan ta na biye maka, karfa amanta da Abubakar tab......😳🥱🥱🥱 💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔 > 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny! Page 3️⃣3️⃣⏩3️⃣4️⃣ *KANO* Kamar kullum wayarta ce ƙiran techno ce a hannunta tana junjuyawa, da sauri ta kuma juya miyar dake kan gas, wayar ta kalla tana faɗin. “Ko sai yaushe zan cire rai da kiran wannan mutumin oho, na ma kai na alƙawarin in dai ya kirani, to na mallaka mai zuciyata na har abada.” kallon wacce ta shigo Kitchen ta yi. “Zahra, ba ki ga min miyan ba?.” “Aunty Safna yanzu zan gama." Daga haka Safna ta yi waje, a zuciya ta ja tsaki, dan tana zamanta wai Safna ba za ta ci abin da aka dafa fa sai taliya da miya shine yake yi. Tana gamawa ta kai mata kan dining sannan ta nufa wani ɗan ɗaki dake gefen kitchen, a nan take kwana. Shiga ta yi tana mai hayewa kan babban katifar ɗakin dan sabuwa ce fil. Tabbas ta gaji da rayuwar wannan gidan amma in ba ta yi ba ya za ta yi, dole ce ga kawo ta aikatau wannan gidan mai hargitsi, tasan komai da ake yi a cikin gidan har da abubuwan da matan gidan ke ƙullawa akan Ummin Haidar, ko da tana aikine sai wani sanadi ya kaita in da za ta ji sirrinsu.. A parlour kuwa, Safna ke cin abincin tana latsa waya da hannu ɗaya, sai Sumayya dake kallo a I.G (Instagram). “Kalla Abbas, ji karatun da yake yi, lokacin da suka kammala ND1.” Safna ta kalla ba ƙyarya magana Abbas yake a video kaman wani bature, sannan Abbas yana da kyau da cikan haiba. A kan stage yake yana koro zance. “Gaskiya Guy ɗin ya haɗu, amma ina rabaki da su Mom.” “Karki damu, banda case da su." Ci gaba da cin taliyar ta yi hankali kwance. A fusge Sumayya da Safna suna ya yi, duba da hasken fatansu, mai haske ne ba can ba, sannan kusan tsayinsu tsaya, a na dai ganinsu anga jini ɗaya. “Yanzu sai mu jira dawowan shi, musan yadda za mu yi ya ci abinci da wannan garin." sai ta mai da garin ciki jakka. “Maman Safna yau Abban Haidar na wajenki, zuwa anjima sai ki goga a in da Mai sittin goma ya ce.” ta amsa ɗan ƙwalba mai ɗauke da ruwa kalan blue. Ya ce ta shafa a wiyarta, ƙasanta, da ƙasan brest ɗinta. Tina wa ta yi da abin da ya ce. “Dole Ummin Haidar ta fuskanci tsana daga wajen Abban Haidar in dai ku biyu kuka yi aiki da su, sannan shi Haidar ɗin da ya ci abinci sau uku da garin nan shike nan, za ku juyasa yadda ya muku, sannan ku yi wasa da dukiyar Alhaji.” ajiyan zuciya ta sauke.... *ABUJA* _Ukasha_ Ya rasa ina zai sanya kansa dan farin ciki, Ashake yoruba familynta sun amince, haka na Fillo Fulani ance a tsaida lokaci, sannan jiya yaje Borno nan ma alhamdulillah ya samu tarba mai ƙyau, dan nan ma ance a tsaida bikinsu da na Zuby Kunuri, ji yake kaman ya sha ruwa a ƙasa, yanzu haka kuma an bashi wata Maryam Bahaushiya, bai ganta ha amma shi kam ya amince, tinda wani amintaccen sa ne a wajen aiki ya bashi ita. Anan ba maganar ɓa ta lokacin dan an bashi, farin ciki kawai yake yi, take kuma ya yi ma Umar ƙyautan sabon gida, Umar godiya ya yi ba tare da ya yi zumuɗi ba. “Umaruna menene?.” Ukasha ya faɗa tana kashe system ɗin sa. “Aboki, da matsala, gaskiya banjin daɗin yadda kake neman aure haka, ba soyayya ba shaƙuwa, sannan kai aure kawai ba zaɓin Allah, sam banjin kana Allah ya ba ka ta gari.” sai ya dafa Umar. “Wallahi duk sallar dare, sai na roƙa mace ta gari, mai ibada da sanin ya kamata. Shi yasa na ce inason mai addini, domin kuwa kishinsu ba zai huce yadda addini ya tsara ba.” “Haka ne, Allah ya kaimu wannan lokacin?.” “Ameen, hmmm akwai abu fa, ban wayarka.” ba musu ya ba Ukasha, contact ya shiga, sai ya karanto number ya na faɗin. “Shine ko?.” Kai Umar ya ɗaga mai, sai yaga Ukasha na murmushi. “Da ace washegarin ranar ka faɗa min, to da yanzu kun haifa min yaro, amma ka wani ɓoye min, toh wannna number ne abu mai sauƙi ne dab ba sai na yi amfani da system ba, yarinyar akwai basira tasan cewa number ta da cire za ka iya samu domin Code ta cire, kuma na Mtn ne, dan haka number biyu zan baka ka kira a ciki dole a samu ɗaya, bayan 070, sanan 3 ko 6.” ba musu Umar ya fara sanya 6, sai dai number ba ta aiki, sai ya sanya 3 amma ya kira har sau huɗu ba'a ɗauka ba. “Karka damu, a ciki tabbas akwai, ni yanzu so na ke na leƙa Zuby dan mu gaisa.” “Okh, hope ka kammala fitar da taswiran asibitin." “Eh, yanzu zan turo maka ta Email, ka ƙarasa komai sai ka kira mutumin.” daga haka Ukasha ya ɗauki car key yana barin office ɗin. Company biyu garesa ɗaya _ARCHITECT / CIVIL ENGINEERING SERVICES._ Sai kuma _REAL ESTATE DEVOLOPER. Yana Gina gidaje, offices, estate da haya da siyarwa, yana samun kuɗi ba ƙarya..... Gaisawa suka yi cikin sakin fuskarka, ita dai Zuby akwai ta da fara'a sosai. “Ba ki ji sosai?.” “Eh bawani can ba amma na iya.” “To yi mana inji.” sai ta ɗan jingina da motarsa tana ce wa. “Sunana Zuby, Ni Kanuri ce, kuma ina alfahari da yaren na, akwai mu da tsafta, ga ƙamshi, uhmmm kuma muna da tsafta sosai. (Inji Zuby, In Kanuri mana, kuma inji togo na, wa so gaji, wa lahi, uhmmm wa so tsatfa sosai.) Sai ya yi dariya. “Eh kaɗan-kaɗan dai haka, (E, kaɗan kaɗan, dewa wo.).” “Yaren akwai daɗi, bara na gudu sai zuwa wani lokacin.” Daga haka suka yi sallama yana barin wajen, murmushi ta saki dan sun haɗe idanu kuma ta sanya wannan kwallin. *KADUNA* Yau ma wani filin suka ƙara siya, ko bayan da suka koma ciki school, suka riski har an gama lecture, dan haka suka zauna suna hira. _Shamo da Muheey_ “Yanzu ni da so samu ne, a ɗaura mana aure, da munje in aikin ya kama ƙasa sai ku biyo mu.” ya faɗa da sigan jan hankali, sai ta yi wani murmushin. “Why not! Ai hakan ya yi sosai.” ta faɗa tana imagine ganinta a jirgi. _Maryam_ Ita kaɗai ce zaune akan a sit ɗin ta, yau ma Abbas yana je gareji, murmushi ne yalwaccen akan fuskarta, dan baya gajiya da mata ƙyauta ko ya ye, kuma hakan na faranta mata rai sosai, yanzu haka kati ya sama mata na 1k, shine ta ke jin daɗi. Lumshe idanunta ta yi dan jiya ta ji daɗin labarin da ya zo mata na aiki a Abuja, ita ya fiye mata barin ƙasa sau dubu.... _Abbas_ Kamar kullum sanye yake da kayan aikin sa, hannusa duk ya ɓa ci da ɓaƙin mai, dan yanzu ya fito daga ƙasan wata mota, sai ya shiga dan kwada aikin ya yi. Aikam motar ta tashi, sai da zagaye garejin sannan ya dawo. “Oga komai normal.” sai Ogan ya jinjina kai dan akwai wani spaner da ya riƙe da baki dan shima ƙarƙashin wani motan zai shiga. Sauke ajiyan zuciya ya yi dan wannan motar ta hawalar da shi sosai, amma gashi ta tashi. Bayan Ogan ya gaji ya fito dan motar ta ƙi yin yadda yake so, Abbas ne ya shiga take motar ta tashi, aikam Ogan ya dinga sa mai albarka, yanzu kusan Abbas an yayesa dan abu ɗaya daya gani shike nan, sai ma in ya yi yafi na wanda ya koya mai. Bayan sun yi sallar Azahar suka zauna cin abinci, bread da Pepsi mai sanyi suka siya, suna ci suna korawa, sannan ana hira........... END. > Kuna tinanin me nake tinani kuwa..... Anya ba Zahra mai girkin gidan su Haidar ita ce wacce Umar ke na ma ba, mu je zuwa..... > Ukasha an kusa dai, Ni ma dai bara na kuma faɗin maganar Umar, Allah ya kai mu dai...ameen. 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖 [9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t ❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._ Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_ 🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟 *📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!* 💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍 PAGE 3️⃣5️⃣⏩3️⃣6️⃣ _KANO_ A kwance ta riske Abubakar a kan carpect, sai ta fita masu shara ta kira, wasu matasa, Usman mai shara, Nuhu mai cefane da Adam mai girki. Su suka kama shi suka mai da shi kan kadon. “Adam me aka girka ne?.” Adam da ba zai wuce sa'arta ba ya ce. “Madam, Doya da ƙwai.” “Okh, Nuhu zan tura ma kuɗi kaje kasuwa dan yin siyayya, daya dawo Adam ka min dambu.” “To Madam.” suka amsa tare sannan suka yi waje. Sai ta koma ɗakin, ruwa ta samu ta yayyafa mai amma bai farka ba, sai dai barci mai nauyi ya ɗauke sa. “Ka yi wani tunanin da ya motsa aljanun da Mai sittin goma ya aiko kenan, dole haka ya same ka, na ce ka dena ta kura wa kanka da sanin kai waye amma ka ƙi ji, shike nan.” daga haka ta nufi part ɗin ta.......... _Washegari_ A ranar suka fara aiki, kuma cikin ikon Allah a waje ɗaya sun samu abubuwa masu yawa. Komai Ameeratulkhair ta gani sai ta rubuta, shi kuma Haidar ya ɗauka, haka dai suka wuni, shi har mamaki yake dan da handglobe take rubutu, a ransa ya ce 'Ameeratulkhairi, ko hannu ba a so mu gani kenan hmmmmm.' A wani wajen suka kuma kafa tantina, sai dai Ameeratulkhair ta fara gajiya da kayan jikin ta domin kuwa, hijab ne four yeard, sannan ta sanya atamfa doguwar riga a ciki, gaba ɗaya iska ba ya ratsa da kuma niƙaf ɗin ɗaurin cikin hijabi ta yi, ga safa hannu da ƙafa. Shuru ta yi tana mai kallon yadda kowa ke raha daga gefe can, wayarta ta ɗauka sannan ta tura ma Haidar saƙo, dan a iya wunin yau sun wani shaƙu sosai. “I need your help." Shi ya gani ta tura mai, sai ya miƙe ya isa wajenta. “Khair, meke faruwa ne?.” sai ta yi mai alamana da ya zauna, zama ya yi, sai ta kuma mai typing. “Sai zuwa gobe ne zamu isa masauƙin koh?.” “Eh.” ta kallesa. “Gaskiya ba zan iya tsallake yau banyi wanka ba.” sai ya yi murmushi. “Dole sai dai gobe, Ni kaina haƙuri na yi, dan na iya wanka kaman ƙwaɗo.” ta tura mai Emoji na dariya, sai kuma na damuwa. “Menene, Gimbiya ta.” “Mamamki nake yi, kai baka sanni ba, ba kasan ya nake ba amma wai kana sona.” “Zuciyata ta gani kuma ta yaba ne.” “Zaka iya min alfarma ɗaya dan Allah.” sai ya ɗaga mata kai yana kallonta, so yake ko ƙwayan idanunta ya gani, amma babu dama. Jin saƙo ya shigo ya kalla wayan. “Minti 30 nake so na yi a cikin nan, dan Allah kar wani ya zo, ina son na sauya tufafi kuma na ɗan sha iska." “Yadda kika ce, zan miki gadi, a huta lafiya.” ya faɗa yana barinta a wajen. Zip ta zuge na Tintin ɗin sannan ta buɗe na sama yadda iska zai dinga shiga. Hijab ta fara cirewa sannan niƙafa da safa hannu. Lumshe idanunta ta yi tana ɗan kwanciya akan ƙaramin tabarma mai kama da katifa. Fuskar fayau take, haka kuma gashin idanunta sun kwanta sosai baƙaƙe dogaye, yadda kasan dai wata balarabiya, akwai ƙyau fiye da misali, sai ma da ta miƙe, hmmmm mace iya mace mai cikar halitta, akwai jiki dai-dai, sannan Allah ya ba ta dukiyar Fulani masu cika da ɗaukan idanu, doguwar rigar ta cire sannan ta sanya wasu riga da wando marasa nauyi, haka ma hijab ɗin ta sanya mai saukin nauyi, sai ta zauna, ta jima a haka kafin ta kuma rufe fuskarta ta sanya safar ƙafa da hannu, fitowa ta yi ta nufesu dan yanzu tana jin iska sosai. “Sir Haidar, wannan matar aure ce ko?.” wani ya faɗa yana kallon Ameeratulkhair take nufi su. “A'a amma soon zan yi wuff da ita.” “Gaskiya ka yi sa'a akwia kamun kai.” “Haka ne, iya su sun wadata zuciyata akan ta.” ya faɗa yana kallon taba zama kusa da masu yin girki, hannu kawai ta ɗan ɗaga musu......... _Abubkar_ Cikin dare ya farka da sunan Allah, kallon kansa yake da mugun tsoro dan yadda jikinsa ya jiƙe da zufa, da ƙyar ya watsa ruwa sannan ya fito sallolin dare da ya manta rabon da ya yi shi ya raye daren dashi, daga nan ya dasa karatun Alqur'ani har asuba ta yi, wani iska ne ya ji na daban na shiga jikinsa. Misalin 7:30am na safe ya bar gidan lokacin ko Daling ba ta farka ba, abubuwa da ya ne ke masa mugun yawo a cikin kansa. Haka dai ya kusan wuni babu abin da ya iya yi a gidan Tvn. Files ne ya shiga dubawa bayan ya ga wanda yake so ya duba sannan ya yi waje tare da nufin wani address da ya bincika, ya sha wuya sosai kafin ya gane gidan domin bai taɓa zuwa unguwar ba, ya ɗan ƙarasa yana kwankwaso kofar gidan, anjima sosai kafin aka buɗe gani namiji tsaye yasa ta tsaya tana kallonsa da mamaki, sai ya gaisheta yana cewa. “Na zo gurin mahaifiyar Ameeratulkhair ne, dan Allah tana nan.” sai ta ƙara jigun take ta ɗan saki fuska sanan ta mai iso bayan ta sanarwa mahaifiyar Ameeratulkhair ɗin. A falo ya zauna, ƙanwar Adda ta ɗibo mishi ruwa, bai sha ba sai ya kuma ƙara gaishe da su cikin girmamawa, suka amsa sai Adda ta ce. “Th bawan Allah daga ina? Me yasa kake nemana ta fatan dai lafiya.” sai ya fadyada murmushin sa yana faɗin. “Sunana Abubakar ni ne mai gidan tv godness tv inda ƴar ki ta fara aiki jiya........” da sauyi ƙanwar Adda mau suna Aunty Saratu ta ce. ”Innaliillahi me ya sami Amiran? fatan tana lafiya?.” ta faɗa da sauri sai ya ce. “Alhamdulillah, ni bama wannan ne ya kawo ni ba don tuntuni suka tafi, kuma munyi waya ma, kusan sun yi rabin tafiyar.” Sai Adda ta ce. “Hmmm to me ya faru?.’ “Gaskiya Mama ba zan ɓoye miki ba, wallahi wallahi Ameeratulkhair tashiga raina, ban iya ɓoye-ɓoye ba shi yasa na zo nan direct domin in faɗa miki ke da kika haife ta, ban santa ba ban taba ganinta ba sai a dan kwanakin nan amma ta shiga raina fiye da yadda kuke tsammani, jiya na kasa barci saboda tunanin ta sa yau na ce zanyi shawarar in zo wajenki, abu na gaba na karanta littafin sirrinta wanda anan na fahimci wasu abubuwa dangane da rayuwarta, ina babu damuwa ina so in zama wannan bangon da take so ta dinga jingina da ita da mahaifiyarta, dan Allah ki faɗa.” ya kai nan yana mai jiran ya ji abin da mahaifiyarta za ta ce. Ta shiga ransa fiye da tsammani me zai ji ya dawo ba ya tina wannan, abinda ke gaba kawai yake tinkara, shuru ɗakin ya ɗauka na lokaci mai tsawo, ta jima Adda na ƙare mai kallonsa sa'annan ta ce. “Ban ta ɓa karanta littafin na, hmmmm amma ina da yaƙinin ta rubuta wasu abubuwa ne dangane da rayuwar mu dai, rayuwar mu na baya sai dai na ce maka, kayi haƙuri, baka san wacece ba, kada ka shiga inda ba za ka iya fita ba, Ameeratulkhair ba yariya ba ce da kasafai mutum zai gani yace yana santa, tana da tarin matsaloli a rayuwarta, mun dawo nan ne domin tsiratar da rayuwarta da kuma ranar da za ta bayyana ga duniya, sai dai me ina tabbatar maka a ranar sai an rabani da ganinta na har abada, mutane uku suna neman ta ruwa a jallo tun ba yanzu ba, tin daga shekara biyar baya muke rayuwa kaman wasu dabbibi, daga nan sai nan, cikin jin daɗi da wahala. dan Allah kar ka kawo wani zance aure a ciki domin kuwa akwai matsala.” sai ta yi shuru, take ya ce. “Ni kawai ina so na zamo bango a rayuwarta ne, ban damu da ko suwa ke neman ta ba, ni dai ki bani wannan damar.” sai ta kuma yin murmushi. “Kasan wacece Ameertulkhair?.” sai ya girgiza kai. “Ban sa ni ba amma wallahi ko ya take ni dai ina son ta.” “Hmmm zan baka labarita idan na gama sai ka tantance shin za ka iya zama da ita ko a'a, domin rayuwarta ba irin rayuwar kowace ƴa mace bace tun daga haihuwa ta fara samun kalubale na rayuwa har izuwa yanzu da kake gani, tana da juriya ba ta bayyana komai hakan yasa ina farin ciki da hakan, a yanzu zan faɗa maka wacece *AMEERATULKHAIRI* da cikakken tarihin rayuwarta, ita kanta wacece, zan faɗa maka amma kafin in ce komai na gode sosai bakasan ƴa ta ba, kake sonta baka ta ɓa ganinta ba amma ta shiga ranka, baka ta ɓa jin sautin muryar ta ba amma ka ce kana sonta. “Daga zuciya na ke jin ta, ban samu da sanin ko wacece ba." sai Adda ta kalla Sararu murmushi ta sakar mata sannan ta ce. “Idan har za ka ji za ka iya auren ta to ni nan a matsayina na mahaifiyar ta na baka ita halak malak indai za ka iya rayuwa da ita, sai sai nasan hakan ba zai yiwu ba ko kadan.” A hankali ya furzar da iskan bakin sa yana mai ritsa idanuwansa domin a wunin yau kaɗai ya fahimci akwai abubuwa da dama na rayuwar sa da ya yi missing, daga nan in ya tashi babu in da zai nufa sai wani gidan da yake tsammanin ganin ƴan uwansa a ciki, ya manta su amma a yau ya tina da su, a karo na farko da yaji Darling ba ta gabansa, ta mai kira har sa huɗu sai dai ya dinga yankewa abin da bai taɓa yi ba kenan, jiya ke a yanzu ya dawo mutum cikakke ba da ba da yake rabi mutum, muryan Adda ce ta dawo da shi duniyar nan. “Ka shirya jin cikekken labarin AMEERATULKHAIR?." Sai ya ɗaya mata kai. Take hawaye ya fara gangaro daga idanun sai kuma kuka mai sauti ya ƙwace mata, sam labarin Ameera babu daɗi, sam ba ta son tunawa da komai, amma a yau za ta tina, za ta ba da labari, za ta tuna wasu mugayen mutane dake addabar rayuwar Ameera........... END. > Toh fa wai jama'a wacece AMEERATULKHAIR ne, sannan ko dai asirin Darling ya karye ne....... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️ 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖 [9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t ❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._ Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_ 🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟 *📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!* 💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍 PAGE3️⃣7️⃣⏩3️⃣8️⃣ _ABUJA_ “Tinda ki ka ji na amince da auren nan to kawai ki yadda, kinsan waye Ukashe kuwa? ki dai bari ayi auren nan a nan ne za mu fara target din mu, yanzu baki ga yanda nake mulkin babanki ko akwai wani matsala a cikin gidan nan babu, dan haka ki mai da hankali, mahaifinki shi yace ya miki a mijin aure Ukasha, ki amince domin kuwa in Ukashe ba ƙaramin mutumin ba ne, mai mugun kuɗi ne kuma haka nake fatan ki aure mai kuɗi, to gashi Allah ya kashe ya bamu, yanda nake Hasashe ma duk yafi samarin ki kuɗi, don haka ni nan mahaifiyar ki na amince da auren nan ki, bayan aure zamu mallaka gidan da shi kansa, sannan ki dinga juya sa da sauran matayen gidan, ke za ki zamo sarauniya idan ma ba kya son su sai muyi waje da su ki mallake sa ki mallaki gidansa.” murmushi budawar yarinyar dake zaune ta yi tana karka ƙafarta. “Wo ke Mamanaaaaa, gaskiya ina son ki Allah ya bar min ke, gaskiya ne naga Guy ɗin ya haɗu ba laifi amma Mama, ina da kishi fa gaskiya ina da kishi bazan iya sharing mijina da mata har uku ba, Mama kuma ƙabilu daban-daban." “Hmmm ki bi komai a hankali, ina ji dai ko da wani yare aka zo, bahaushiya ita ce gaba dan haka Maryam ki natsu ki jini da ƙyau, kina ji na?.” *Eh ina jin ki Mamana." “In bakya son kishiyoyin duk zanyi waje da su idan kina so kuma su zama miki ƴan aiki duk sai su zama miki, ba ki da case yarta.” tashi ta yi da sauri tana runguma mahaifiyar ta cike da jin daɗi da annashuwa, da sauri kuma ta nufa ɗakin ta na mai tafiya ta na haɗawa da rawa da ɗan ihu. Ba laifi Maryam budurwa ce wacce ba za ta wuce shekara ashirin da biyu ba, tana da duhu fata amma kyakkyawa ce ga jiki dan ba za'a ce mata siriya ba ko kaɗan, ita ce tilo a wajen mahaifiyarta, sannan ga samu tarairaya sosai domin komai kuwa ita kaɗai Allah ya ba ta. Maryam ta taso ne cikin gata da jin daɗi, haka mahaifiyar ke fatan ta huta a gidan mijinta, dan ita ta shigo gidan mijinta ne yana da mata biyu, amma sai da ta kora kowacce ta mulki gidan ta mulka mijin in zan faɗa kalma ɗaya bai isa ya sauya mata shi. Fatan ta ɗaya shine Maryam ta aura mai shaken ƙudi yanda zasu juya shi yadda take so sai gashi Allah ya basu, Mahaifin Maryam shi ya bashi ita kyautar domin a ƙarƙashin sa yake aiki a kamfaninsa ta yi farin ciki da jin haka sosai kuma tana fatan ayi bikin lafiya daga nan za su fara ba za mulki a cikin gidan Ukasha, za ta sanya Maryam ta mallake gidan gaba daya sai abin da Maryam tace shi za'a cikin gidan, za ta nunawa kowace yariya cewa bahaushiya ba sa'ar su ba ce ba kuma sa'ar kishin su ba ce haka. sai ta saki wani murmushi na mugunta tana mai cewa. “Mu je zuwa, Ƴa ga sai kin zama sarauniya a gidan mijinki da yardar ubangiji, kuma babu mai juya min ke.”.......... *KANO* Haidar da Ameeratulkhair su wani kulle sosai, dan a cikin kwana 7 da suka yi saoyayya mai zafi tashiga tsakaninsu wadda dukansu sun makance a soyayyar, abu na Allah har suka cikin kwana bakwai babu wanda iya ganin ko da farcin Ameeratulkhair ne, dan akwai da taka tsan-tsan sosai. Yau ce ranar ƙarshe sun shirya tsab dan dawowa, su gama haɗa komai da hujjojin suna mai farin ciki dan kuwa abin da suka zo nema sun samu ninkinsa, dajuka huɗun nan da suka zaɓa kuma Alhamdulillah basu samu matsala a dukka, kuma duk suna cikin koshin lafiya. Farin ciki ne kwance akan fuskar Haidar dan kuwa a yanzu Amira jinta yake a jikin jikinsa. Kuma ina suna tare sai ya ji tamkar ya shiga wani sabon duniya ne, ya ara wayanta ya kai sau ba adadi domin ko zai ga hoton ta amma sai dai babu komai a ciki sai hotunan aiki da wasu abubuwa amma babu hoton ta a ciki, yayi-yayi ya ga fuskar ta amma taki sam, ina kuma ya matsa sai tayi fushi tare da rubuta mai kawai su haƙura da soyayya amma da ta faɗa haka sai ya ruɗe sannan ya ba ta haƙuri. A kwana bakwai nan yanda kasan sun tafi yawon shakatawa ne dan kuwa kullum suna tare, suna yin chat, da yake sun ta fi da power bank kusan guda huɗu manya-manya wadanda har ila yau basu kare ba. Ta cikin niƙaf ta sakar mai wani murmushi, tana jin san Haidar a cikin zuciyar. Ta tina chart ɗinsu na ƙarshe. “Wace irin mace kake so?.” “Sak ke." Murmushi ta yi sannan ta ce. “Eh, amma a ra'ayinka ya kake son mace.” a lokacin ya jima kafin ya ce. “Ina son mace mai juriya, mau baki dan ta dinga ƙwatar kanta a wajen kishiyoyin ta.” “Wai kana da aure ne." Sai kawai ya fizge wayanta dan yana kusa da ita sannan ya ce. “A'a ba mata na bane, matan Abba na ne, ba su da sauƙi, mace dai-dai su suke buƙata." Ta so ta ce wani abu amma sai ta fasa. Numfashi ta ja, tabbas ta yi kuskuren faɗa wa soyayya da wanda ba ta sani ba, hakan ba shine illa ba, shin wanda suke nemanta ba za su bar Haidar da rai kuwa muddin suka sani, ta yi kuskure sosai da ta faɗa wa tarkon Haidar na soyayya. dogon ajiyan numfashi ta kuma sake wa sa'annan ta rinsa idanun da nake cikin nikaf ta buɗe su, sun ja sosai. Mamakin yadda ta sake da shi take, dole ta nisanci kalmar soyayya domin duk wanda ya yi gangancin kusantar rayuwarta, to kuwa ya na kira ma kansa matsala ne, domin ɗayan-biyu ne ko mutum ya rasa ransa ko mutum ya zaucewa. Ba ƙaramin abu bane a wajen su hake mutum, sai dai ta dogara da Allah kuma shi ne majibancin al'amura, shi zai mata tsari ga ku duk masu ganin bayanta, mutum uku sun hata natsuwa, sun jakula mata lissafi.............. END. > Cab Maryam Bahaushiya 🙄🙄🙄🙄🙄. Hmmm akwai abu fa. Ku kuma masoya sannunku *Haidar da Ameeratulkhair* ka ga Abubakar a gefe, sannan har yanzu ba musan wacce ita ba.......muje zuwa dai✍️ 🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚 ✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖 [9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t ❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._ Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_ 🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟 *📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!* 💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍 PAGE3️⃣9️⃣⏩4️⃣0️⃣ _Bayan wata biyu, abubuwa sun faru da dama wasu na daɗi wasu marasa daɗi, bari mu garzaya kowane bangare dan ji me ya faru a cikin wata biyu._ *UKASHA* Wani aiki ne babba ya taso mai, dole ta sa yabar ƙasa, dan haka aka sa bikinsa saura wata biyu ta kuma kowane bangare suna ta shirye-shirye gadan-gadan, duk da yace shi ba ya buƙatar komai daga mace sai mace kawai yake so a kai cikin gidansa a yanzu haka ya washegari ne ɗaurin auren Ukasha, dan haka gaba ɗaya ba shi da wani natsuwa, duk da komai kuɗi kwai yake turawa, ba ƙarya ya saki kuɗaɗe domin kowace sai da aka mata akwati guda sha biyu, kuma ya yi ma kowace kaya irin na al'adar su, ya yi ƙoƙari fiye da misali, dan ko ina sai maganar wannan auren ake yi. Sannan duk ya samu fahimta mai kyau ga dukka matan, kuma yana fatan babu mai bashi matsala a ciki, sai dai tun kafin auren, Fillo ta gama mamaye mai zuciya, abun har mamaki yake yi sai dai ba'a mamaki da ikon Allah, sannan baisan dalili ba yana son ganin Ashake, ita kuma masifarta da rashin hakurinta na burge sa, yana son zuwa wajenta hira dan kuwa yana sha sosai, sau ran biyun kuwa suna girmamasa sosai kuma yana jin daɗin haka. *SAMARI* Su Shamo kuwa sun gama shirye-shiryen tafiya US domin kuwa sun kammala jarrabawan su, basu ji sakamako ba, sun c daya fito sai a tura musu. Yau ne tafiyar kuma sun gama shiri tsaf, washegari ne tafiya US, hankalin su a ƙwance dan sun gaba biyan kuɗin komai, ba karamin kuɗi suka kashe ba amma da yake a yanzu kuɗi ba komai bane a wajen su, suna wasa da kuɗi, dan dai can ɗin aikin za'a fi samu da ba in da za su, so domin ƴan matan su sun tsaya musu especially ma I.B dan a yanzu ba ƙaramin kuɗi yake da shi ba, sai dai duk ya sun siya filayen kuma ta hannun Alhaji, sannan ya a dana takaddun sosai. Shamo da Abdul sai da suka san yadda suka yi aka ɗaura musu aure da ƴan matan su kafin su tafi, da cewa aiki yakan kama ƙasa sai a turo su kawai, Muheey ce da kyar mahaifinta ya yarda da hakan dan shi bai kamata mace ta yi aure kuma ta ci gaba da zama a gidansa amma ba yadda ya iya, dan Muheey ta nace, dan a tinanita kar ya je can, ina ya ga fararen fata ya ce ya fasa da ita. Bayan hargitsin aka ko ɗaya musu aure, ita dai Ma'esh ba'a samu matsala ba ta bangarenta domin kuwa yana magana aka ɗaura auren da cewa bayan wata biyu za ta bi shi ita ma, karya ba'a yi taro sosai ba amma fa an kashe kuɗi. I.B ma yaso haka amma shi babu dama sai dai shi daya dawo ko ta tsiya sai sun aure juna. *Mymoon* Tun bayan kammala jarrabawarta Dad ya hanata fita ko'ina, sannan ya mata tambayar akan ina take kai kuɗaɗe dan wasan kuɗin na ta ya yi mugun yawa, haka motocin ta guda biyu duk babu yanzu, da ya tambaye ta sai ta ce. “Ai tana da hankali, tasan me take yi da shi, ita ba yarinyar ba ce." Dad ya gaji, shi yasa ya kulle gaba ɗaya account ɗin ta, sai dai ba tasan Dad ya gane I.B ke hure mata kunne ba, kawai ya share zancen ne, abin da yafi damun shi bai wuce number Taj da baya shiga kullum. Zauna yake a kan kujera idonsa na kan tv amma sam baya gane me ake yi a cikin tv domin gabaɗaya kwana biyu ne yana cikin damuwa, saboda sauyawan Mymoon, bayan kuɗaɗe da take wasa da su yanzu haka kamfaninsa guda ɗaya ya ruguje duk saboda hannun jari ya karye a ciki kuma ita ke rike da wannan kamfanin, a yanzu abin ya ishesa ne shiyasa ya zuba mata ido tare da ɗaukan tsattsauran mataki akan ta. wayarsa ya ƙara ɗauka sanana ya kuma kiran numbar nan sai dai kamar kodayaushe in ya kira ba ta shiga, sai dai mai yana kira na biyu wayar ta fara ringing, da sauri ya gyara zaman sa yana mai fatan Taj ya ɗauki wannan, kiran sai dai katse har sau uku, sai ya ajiye wayan yana mai tunanin gobe dole ya tafi dubai domin dubo shin lafiya yake, shurin ya yi yawa, baya kwana biyu ba tare daya kira su ba, amma tun sati biyu baya bai kira shi ba, take wayarsa ta hau ringing da sauri ya ɗauka ganin number Taj ne, picking ya yi yana kai kunnensa take wani dakakkiyar muryar mai cike da amu ta doki kunnensa, gaishesa ya fara yi cikin ladabi, sa'annan ya amsa yana mai ce wa. “Taj ina ka shiga ne, me ya samu number ka baya aiki, ai da zuwa gobe nan zan shigo dubai ɗin, shirun ya yi yawa meke faruwa ne." Ya kai maganar cikin ɗan damuwa, sai wannan murya ya yi murmushi wanda yake jiyo sautin ta ta cikin wayar sa'annan yace. “Haba Dad ina cikin koshin lafiya, abubuwa ne suka min yawa sosai, so nake ma in kiraka in ce maka gobe zan dawo Nigeria."" Baisan lokacin da murmushi ya kwace masa ba, sai ya ce. "Kamar kasan neman ka, nake yi ruwa a jallo, goben dai zaka dawo." ” Eh insha Allah Dad, zuwa goben nan za ka ganni na dawo, fatan duk kuna lafiya lafiya?." “Alhamdulillah, sai dai akwai yar matsala amma sai in ka iso ɗin.” “Toh shike nan Dad, ina godiya Allah ya saka da alkhairi.” “Ameen yarona.” “A huta lafiya." daga haka ya kashe kira yana mai jin wani nishaɗi da jin daɗin gobe Taj zai shigo, ji yake kamar ya zubar ruwa a ƙasa ya sha dan murna. Fitowar ta kenan daga kitchen, ta ji wannan hirar Dad yake yi, take ta kuma haɗe fuskan, dan dama ba ta cikin walwala kwana biyun nan, tsaki ta ja tana mai ayyana cewa. "Ya zo din wallahi wallahi bazan aure Taj ba, gaskiyar I.B gashi ina gani wani zai aureni saboda kuɗi. “Toh Alhaji mu dai zamu tafi.” Faɗin Abdul yana saba jakkan. “Shike nan Allah ya tsare hanyar da ku isa ku tabbatar kun samu kun kira ni domin V.I.P ne ba za'a haɗa ku da sauran mutanen da kuka gani ba." Alhaji ya faɗa yana ƙara gyara babban rigarsa. “Allah ya tsare min ku, fatan sa'a." Faɗin Abbas jiki a mace, wannan shine karo na farko da zasu yi tafiya ba dukkansu ba, daga haka Shamo da Abdul da kuma I.B suka shiga wannan babbar motar dake ɗauke da samarin maza kusan guda goma a ciki, Abbas in da yake ya ɗaga musu hannu jikin sa babu laka domin bai son suyi tafiyan nan ji yake kaman ya bisu amma ina yanzu haka ya kammala shiri ne na tafi aybuja, sai da motar nan tashi ta bar wajen sa'annan ya kaɗa kansa tare da jakan bayan sa, tasha zai nufa daga can zai nufa Abuja, Alhaji na kallon Abbas ya wuce sai ya girgiza kai tare da faɗin. “Allah sarki Abbas, baka da rabon wahala, Allah ya soka, Allah kuma ya ce ce ka, kai mai sa'a ne kuwa, abokanka kuwa ka musu kallo na karshe kenan, dan har abada abadan ba za ka kuma ƙara ganin su ba.” Ya faɗa hakan yana mai murmushi, sai ya ciro wayarsa yana mai kai kunne. “Hello, motan ta tashi sun tawo, to shike nan ina godiya, a miƙa min godiya wajen *Giji Zulƙu* ina matukar godiya kafin zuwa dare na zo, kuma ina farin cikin da Mamba a cikin ƙungiyar halaka.” daga haka ya kashe wayan yana fada yana wai wani murmushi, ya tabbatar ba mutane kusa da shi shiyasa ya saki jiki yake magana a haka, shiga mota ya yi yana mai barin wajen cike da annashuwa. *ABUJA* Gabaɗaya Sumayya ba ta cikin nutsuwar ta, tana cikin wani hali, ta ji haushi abin da ya faru, a ce kamar ita mai aji ƴar kwalisa, cikakkiyar mace budurwa mai ji da dukiya tana neman wani amma yake wulakanta, da ba ya ɗaukar number ta, sai dai ta yi mai saƙo ta whatsApp, sai dai ya yi ta gani amma baya reply, daga ƙarshe blocking ɗin ta yi a shekaran juya, tin daga haka take cikin wani yanayi dan ta rasa makama, ba ta san me za ta yi ba, ji take kamar ta je har kaduna ta samu Abbas ta ci mai mutunci ta ji dalilin da yasa yake wulakanta ba kamar ita mai aji tana kula shi dan talaka amma baya ga ta gabansa, ta fara bin abin a hankali amma ta ga abun ƙi yiwuwa, yanzu gashi an ɗauka kusan wata biyu da fara kulawa da ta yi, ba ta manta kalma na karshe da ya ta ɓa shiga tsakanin su ba, ce mata ya yi. “Sumayya ina da wacce nake so kuma na mata alkawarin zan aure ta, dan haka dan Allah ki fita daga sabgata, in tasan da wannan maganar za ta yi fushi dani sosai, kuma fushinta tamkar ana zuba min garwashin wuta ne a jikina, dan Allah ki rabu da ni." abin da ya faɗa mata kenan ta kasa mai reply domin voice ya mata take kuma ya yi blocking ɗin ta, ta yi kiran duniyar nan bai ɗauka, saboda shi ka canza lambobi da dama amma duka a banza, sai dai me ta kai karshe so take ta faɗa wa mahaifiyar ta, koda kuwa ba za ta so ta ji tana son ɗan talaka amma ta taimaka ta yi mata hanya, rayuwarta na gaba da rugujewa in dai ba ta auri Abbas ba, ji take tamkar ta samu attack na zuciya. Da sauri Safna ta faɗo ɗakin tana cewa. “Sumayya! Sumayya!! Sumayya!!!, albishirinki.” gaba ɗaya zazzabi ya rufe ta, dan ko tana ji a yau ɗin nan dole sai ta je asibiti an duba lafiyar ta, a hankali ta budye bakinta ta ce. “Ke da Allah banda lafiya, ki ƙyaleni ke Please.” “Na kawo miki maganin zazzaɓin.” idanu ta buɗe a hankali, tana kallon Safna dake tsaye akanta. “Ina wannan tsinanen yaron da kika haukace ma wa, yanzu na gan shi a cikin haraban gidan nan, yana tsaye da jakan bayinsa ya zo yana neman Abban Haidar.......” ai ba ta ƙarasa maganar ba ta zabura da sauri tana cewa. “Ab......Ab....Abbas wai.” “Eh Abbas, yana cikin gidan nan a yanzu haka.” ba ta damu da shigar dake jikinta ba, ta yi waje saboda girgiza kai tana cewa. “Wai Sumayya ta haukace da yawa.” sa'annan ta ɗauki mata hijab ta bi bayanta. Tana tafiya tana haɗawa sauri har da haɗawa da gudu-gudu ta fita haraban gidan, tsaye ta hangi Abbas yana mai latsa wayarsa gefen gate, shi ga nufa da sauri-sauri har ta isa gaban sa, ta isa tana haki, kallonsu take yi tana mai yi mai kallon tuhuma, shi kuwa sai a lokacin ya ju ya kalleta, kallo ɗaya ya yi mata sannan ya ɗauke kansa, domin kuwa rigar bacci ne a jikinta mai ragaraga wanda aka ganin kalan kayan da ke cikin jikin ta, tsaki ya ja a cikin zuciyarsa, yana faɗin. “Wannan yarinyar sam ba fa da hankali, jibi yadda ta fito daga cikin gidan nan.” kafin ya yi wani maganar har Safna ta karasu sannan ta miƙa mata hijabi, ta amsa tana mai sanyawa sai a lokacin ta lura da kayan da ke hukunta, a hankali ta buɗe bakinta ta fara cewa. “Ab......Ab..........Abbas." take ta yanke jiki a wajen, da sauri Safna ta yi kanta ta na mai cewa. “Sumayya! Sumayya!! sumayya!!!.” amma ina ta yi nisan kiwo domin kuwa suma ta yi take. *ABUJA* Babban Masallacin jumma'a ne wanda ya cika sosai, a yanzu a ka gama ɗaura auren Ukasha da ƴam mata huɗu, abin da ya ma wa mutane da yawa mamaki kenan. Tsaye yake cikin babban riga sai faman murmushi yake yi, ba ƙyarya ya yi ƙyau fiye da misali, farin shadda ce ƙal a jikinsa an mai aiki da golding colour. Gefansa kuwa Umar ne shima ya sha wani shadda, matsawa ya yi kusa da shi ya ce. “Ango, Ango Allah ya yi dai.” hannusa ya riƙe yana faɗin. “Wallahi wani farin ciki nake yi sosai, alhamdulillah buri na ya cika.....” “Saura Hasashen burin....” sai ya kuma sakin wani murmushi. END. BOOK ONE is done. *To jama'a a nan na kawo karshe, kowani cakwakiya za'a warware shi a book 2, dan labarin zai fi ɗaukan zafin duk wannan wasan yara ne, zallan yana tafe.* Akan darasin ₦500 ne kacal 😎 Ga dukka mai so ya fara booking, sannsn ya min mgn 07038436703 *HASASHE KO BURI* by PRETTYN JAJIRTATTU [10/3, 22:59] Mrs I ♥️💔: *TEAM OF UKASHA* _Burin sa dai ya cika ya malla mata huɗu daga differents culture 😁, Shin HASASHE sa sai cika kuwa? Sai a book 2 za mu ji ya zaman gidan zai kaya._ > Fillo Bafullatana : ba ruwanta, mace mai natsuwa da sanin ya kamata ❤️. > Ashake Yoruba: akwai da ta masifa, sannan ita ma ba ruwanta, amma akwai kishi , kuma ta tsana Hausawa 😁. > Zuby Kanuri : Mai burin mallakan Ukasha da koran gaba ɗaya sauran, tana da mugun ƙudiri akansa, domin Mai sittin goma ya dafa mata 🔥, shin za ta yi nasara?. > Maryam Bahaushiya : mai ɓakin buri, da san kai, mai uwa mai dasa ta akan keken ɓera, ita ma burinta mallakan Ukasha dan ba za ta sharing miji da kowa ba.. > Tsakin Zuby Kanuri da Maryam Bahaushiya wacce za ta Malla UKASA. A BOOK TWO ne zamu ji yadda zaman gidan zai kaya......✍️ [10/3, 22:59] Mrs I ♥️💔: *AMEERATULKHAIRI* _Da wa kuke fatan ganinta da shi?._ > Haidar : soyayya ta shiga tsakanin su mai zufi. Sannan yana da matsala a gidan su, haka kuma mace wacce za ta yi zaman kishiyoyin da kishiyar Ummisa ya ke so 😁. Boom 🔥 > Abubakar : Adda ta bashi Ameeratul Khairy, haka hankalinsa ya dawo jikinsa, hmmmm waye shi ma oho Ina *Darling* wai .....🔥. > Suwa ke neman ran AMEERATULKHAIR? > Wacece ita? [10/3, 22:59] Mrs I ♥️💔: *Capacity 💃* *Ƴan US sun ɗau hanya, Shamo ya aura Muheey, Abdul ya aura Ma'eh da cewan da sun kwana biyu za su bi su, sai bangane wannne Alhaji ba?* > Ya ce ya turosu, kuma yan mai godiya ga ƙungiyar su ta halaka hmmmmm 🔥🔥 > Ba musan ina Alhji zai kai ku ba..... Book 2. > Mymoon : Taj yana hanya, ko ya zasu ƙarge oho, ga dai I.B gefe guda....... > Abbas ka shiga wani jalIy ainun, ka tafi Abuja, dan aiki ga Sumayya ta suma saboda kai, hmmmm ko ya kuma zaku sanye oho..... book 2, can fa ga Gimbiya Merry. BOOK TWO for ₦500 only. Darajar littafin ya fi kuɗin. [10/3, 23:11] Mrs I ♥️💔: ``` *📢 Albishir Jama'a!* *Assalamu Alaikum* Ina farin cikin sanar da ku cewa mun kammala *HASASHE KO BURI — Book One* 🎉 *Book Two* zai kasance a kan *₦500 kacal*. Ku shirya domin jin ƙarshen wannan zazzafan labari mai cike da rikici, soyayya, kishi da burin zuciya. > Buri duk ya cika saura Hasashen burin, shin na kowa ne zai cika. Kar ku manta na yi jawabi akan kalaman *Buri* aba ce wanda kowa yake da shi, na wasu alkhairi ne, wasu kuma na su sharri ne, wasu yana cika amma sai ansha siya sosai, wasu kuma har abada baya tabbata. > *Daga ni — PRETTYN JAJIRTATTU 💪* Wallafa ce daga zuciya, don ku masoyan karatu 😁🔥✍️✍️✍️✍️✍️✍️