WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE... AKAN NERA DARI BIYAR KACHAL.TUNTUBENI TA 09134848107 DON MALLAKAR NA KU... *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO:_* بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai..... Assalamu Alaikum Wa Rahamatullahi Wa Barakatuh!!_ _Barkan mu da dawowa daga hutun Ibadah!! Allah yasa munyi ibada karbabbiya, Allah yasa muna daga cikin yantuttun bayin sa. Allah kuma ya biya mana dukkanin bukatun mu. ya kuma yafe mana kurakuren mu. Aameen. Fatan anyi sallah lafiya? Toh Allah ya karba mana Amin... Zafafa na miko gaisuwa da dinbin fatan alkhairi agare ku😍🎀_ _PAGE 1:_ °•°•°•°• **Tamkar* a mafarki, tana jin kamar zuciyarta ta fada cikin wani irin nauyi da ba ta taba jin irinsa ba. Kalaman Fawaaz sun kasance kamar wani sako daga duniyar da ba ta taba tsammani ba, amma a lokaci guda, suna da karfi fiye da yadda take iya dannewa. Hannunta yana rawa, ta sauke ajiyar zuciya, amma kafin ta samu damar kara tunani, karar kararrawar motar yan fashin dake gefe ya katse ta. Ta dago kai da sauri, zuciyarta tana dukan uku-uku, tana kallon yadda daya daga cikin 'yan fashin ya matsa kusa da su da wata matsananciyar fusata a fuskarsa. "Nace maki kiyi shiru, ko kuwa kina bukatar a koya maki darasi?" Ya fadi cikin tsawa, yana daga hannunsa da wata sanda kamar zai buga musu. Nabeeha ta razana, ta rufe idonta a firgice, amma kafin ma ta iya tunanin yin wani abu, Hajiya Zaytunah ta tare ta da jikinta, tana cewa da murya mai sanyi, "Don Allah, ku yi hakuri. Ta dan razane ne, amma ba zata sake ba." Nabeeha tana jin kamar ana karanta mata labari ne daga wani littafi na soyayya. Amma wannan ba labari bane, Fawaaz ne, mutum mai rai da numfashi, wanda bai taba nuna wani irin motsi na soyayya a kanta ba, sai yau. Tana jin bugun zuciyarta yana karuwa, amma a lokaci guda tana cikin wani hali mai wahala. Wani bangare na zuciyarta yana son amsa sakon nan take, yana son fadin abin da ke zuciyarta,. Amma wani bangare kuma yana ji kamar ba wannan ne lokacin da ya dace ba. Yanzu haka suna hannun 'yan fashi, cikin yanayi na tsoro da fargaba, kuma har yanzu ba su san yadda za su kubuta ba. A hankali ta dauke idonta daga kan hannunta da aka daure da igiya, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Idanunta suka sauka kan Hajiya Zaytunah wacce ke kokarin kwantar musu da hankali.. Ta dan kakaro murmushi tana kokarin danne hawayen dake kokarin zuba daga idanun tah... A zuciyarta, Nabeeha tana jinjina irin tashin hankalin da suke ciki. Amma zuciyarta ba za ta iya musun yadda sakon Fawaaz ya shigeta ba. Tun farkon haduwarsu, ya kasance mutum mai nisa, miskili wanda bai fiye magana da ita ba sai idan ya zama dole. Musanman da shi din magana ta fatar baki ma bata dame shi ba. Ki cikin yan uwansa da suke ciki daya baka Jin bakinsa..Amma yau… yau ne rana ta farko da ya furta wani abu mai kama da soyayya a gare ta. Hannunta na rawa, sai ta sake duban hannun ta..Tamkar wayar ce agabanta. Idanunta da kwakwalwar ta suna tariyo mata sakonnin fawaaz, “Ki min alkawari cewa za ki tsaya min, Nabeeha. Ko bayan wannan wahala, kar ki guje ni.” Sai ta runtse idonta, ta jin cunkoso a KIRJIN ta. Me zai hana ta amsa? Idan har akwai lokacin da zata fara tunanin Fawaaz da gaske, ba a cikin irin wannan hali ba. Amma zuciyarta ta riga ta furta amsa tun kafin kwakwalwarta ta tantance. Kafin ta iya cigaba da dulmiya a duniyar fawaaz data lula, Razananniyar karar sautin muryar wani daga cikin yan fashin ya kurma kururuwa yana cewa, "Lokacin lallasa yazo.." Yan fashin sukayi kansu, Suka sake tamke daurin hannayensu da kafafuwansu, sai suka fara azabtar da su ta hanyoyi daban-daban. Hajiya Zaytunah, wacce take da jiki da nauyi, an rike ta da karfi yayin da take kokarin kare 'ya'yanta Nabeeha da Hammad. Wani daga cikin 'yan fashin ya watsa mata mari mai karfi da ya gigita ta. Idanunta sun yi jajir saboda zafin dukan da ta sha. Kafin ta farfado daga girgizar marin, wani daga cikinsu ya fizgo gashinta da karfi, yana jan kanta zuwa gefe. Nabeeha kuwa, duk da kokarin karfafa zuciyarta, ta kasa jurewa azabar da take sha. Wani dan fashi ya dunkule hannunsa ya kwada mata naushi a gefen cikinta, wanda ya sa ta zube a kasa da radadin ciwo. Ta narke, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Hawayen da ta kasa shanye wa sun zubo kan kumatunta. Ya yinda wani daga cikin 'yan fashin ya rike hannun Hammad, wanda bai cika girma sosai ba, ya yi kokarin daga shi sama yana mai tsoratar da shi. Hammad ya yi kururuwa da murya mai tsanani, yana rokon su su sake shi. Amma maimakon su tausaya masa, sai suka dinga dukansa da sanduna a cinyoyi da hannayensa. A cikin wannan halin, Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa. Ta durkushe tana rokon su, “Don Allah, ku yi hakuri! Ku bar yaran nan haka, ku duke ni a madadin su!” Amma 'yan fashin sai suka fashe da dariya, daya daga cikinsu yana cewa "Ai ba mu dauko ku don sauki ba! Za ku dandana bakin ciki kafin mu raba ku da iska" Duk azabar da suke sha, babu wanda ya kawo musu dauki. Duhu ya lullube su, tsoro ya cika zukatansu, kuma babu alamun kubuta a gaban su… A yayin da azabar ta kara tsananta, Nabeeha ta kasa motsi, jikinta yana karkarwa saboda radadi da tsananin tsoro. Idanunta sun cika da kwalla, amma ta runtse su da karfi, tana fatan mafarki ne kawai, ko kuma wata rana mai kyau za ta farka ta ga komai ya wuce. Hajiya Zaytunah ta kokarta ta tashi, amma wani dan fashi mai dogon gemu da idanu masu kaushi ya yi birgima da ita gefe, yana dariyar mugunta. Ya kama mata hannu, yana matsawa da karfi, har sai da ta saki wata kara mai tsanani. “Ai yau ne ranar ku! Babu wanda zai cece ku!” ya fada da wata murya mai cike da izgilanci. Hammad ya ci gaba da kiran mahaifiyarsa, yana kuka da karfi. Amma maimakon jin tausayinsa, daya daga cikin ‘yan fashin ya rike shi da karfi ya wurgar da shi gefe, har sai da ya bugi bango, Hammad ya saki wata kara, jikinsa yana rawar sanyi. Daya daga cikin ‘yan fashin, wanda yake kamar su ne shugabansu, ya matso kusa da Hajiya Zaytunah yana kallonta da mugunta yace, "Meyasa ake son aga bayan ku? Ku din su wanene? Kuna da babban daraja a wajen wadanda suka turo mu!” ya fada, yana gyara bindigar da ke rataye a kafadarsa. Hajiya Zaytunah ta kasa magana. Hankalinta yana kan yaranta da ke kuka da radadi. Sai dai kafin ta iya cewa wani abu, sai daya daga cikinsu ya zaro waya ya fara daukar bidiyo. “Muna so ki amsa mana tambayoyi!” ya fada yana zungurin Nabeeha da gefen takobinsa. Sai da Nabeeha ta saki kara, jikinta yana karkarwa. Sannan daya daga cikinsu ya matso kusa da ita yana fadin, "Da alama ke ce kadara a cikin ku! Domin an ja mana kunne akan ki sosai, Wannan ne zai sa mu ci gaba da azabtar da ku har sai mun ji daga gare su" "Dan Allah kuyi hakuri. Wallahi mu ba kowa bane." Nabeeha ta fada cikin muryar ban roko da lallashi "Bude muryar ki sosai kiyi magana..." "Wallahi mu ba kowa bane. Dan Allah kuyi hakuri ku sake mu" Ta karasa fada tana fashewa da matsanancin Kuka.. Tsoro ya sake lullube su. Wane irin hali ne sukatsinci kansu? Shin akwai mai ceton su?... _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09032345899_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ MX🎀 *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:2_ Azaba da tsoro sun cika sararin da suke ciki. Numfashin Nabeeha yana fita da kyar, jikinta yana karkarwa yayin da yan fashin ke ci gaba da azabtar da su. Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa ganin yadda suke dukan 'yarta da danta. Ta yi kokarin tashi amma wani daga cikin yan fashin ya hankada ta da karfi, ta fadi a kasa. "Ke dai ba kya jin magana, ko?" Shugaban yan fashin ya fada da murya mai cike da tsawa. "Ki gaya mana gaskiya! Wacece ke? Kuma menene SIRRIN da wasu ke kokarin karewa game da ke?" Hajiya Zaytunah ta dan kalli Nabeeha da Hammad da ke kuka da radadi. Ta san cewa ba zata iya bayyana komai ba, amma azabar da ake yi musu na neman ya tilasta ta yin magana. Sai dai kafin ta iya cewa komai, daya daga cikin yan fashin ya janyo gashinta da karfi. "Idan baki gaya mana ba, kiyi tunanin abin da zai faru da 'ya'yanki!" Ya fadi yana daga wuka. Hammad ya kara fashewa da kuka. "Don Allah ku kyale mu! Ba mu da laifi!" Nabeeha kuwa ta kasa cewa komai. Kawai idanunta ne suka cika da kwalla, tana kallon mahaifiyarta cikin tausayi. Baki daya tausayin mahaifiyar tasu take bata. Taga rayuwar tsanani a baya. Yanzun da rayuwa take kokarin sauyawa musu sun fara Jin dadi kuma ga abunda ya biyo baya... A wannan lokacin, wata yarinya daga cikin yan fashin ta matso kusa da su, tana kallon su da alama kamar tana jin tausayinsu. Amma kafin ta iya cewa wani abu, shugabansu ya daka mata tsawa. "Ke kuma me kike Shirin yi? Idan baki da zuciyar cigaba da aiki, sai ki bar nan yanzu!" "Sorry sir.... " Yarinyar fashin ta fada tana juyawa baya ta koma... Zuciyar Hajiya Zaytunah ta buga da karfi. Shin akwai wanda zai taimaka musu daga cikin su? Shin akwai wata hanyar tsira? A wani sashe na daban, cikin wani katafaren gida mai dauke da kayan alatu, Hajiya Rumanah zaune take akan wata kujerar alfarma, hannunta rike da kofin shayi. Idanunta sun kada sun cika da tunani., Hajiya Karama da Hajiya Ladi suna zaune atare da ita , Da juice a hannayen su. kowacce na da fuskar da ba ta bayyana yarda ko damuwa. Hajiya Karama ce ta fara magana, tana dube-dube kamar mai son tabbatar da cewa ba wanda ke leken su. "Yanzu dai an kama su. Kuma an tafi da su wurin da ba wanda zai iya samun su." Ta fada da murya mai cike da kwanciyar hankali. Hajiya Ladi ta gyara zaman mayafinta, ta kada kai tana murmushin jin dadi. "Wannan ai babban nasara ne. Har yanzu ba wanda ya fahimci cewa mu muka tsara komai." Hajiya Rumanah ta ajiye kofin shayinta a hankali, sannan ta dago kai, idanunta sun cika da wani irin kallo mai cike da natsuwa amma har yanzu ba ta nuna wata alama ta farin ciki ba. "Ku tabbata cewa babu wata matsala. Ban yarda da waɗancan mutane ba sosai. Ko sun tabbatar mana da cewa sun yi abin da ya kamata?" Hajiya Karama ta yi murmushi, sannan ta dan rankwafa kadan cikin muryar rada mai cakude da munafurci tace, "Kada ki damu, Rumanah. Yan fashin nan sun fi kowa kwarewa. Mun tabbatar da cewa ba wanda zai iya kubutar da su." Hajiya Ladi ta sake gyara mayafinta dake zumewa, ta dube su tana dariya. "Yanzu dai abin da ya rage shine mu jira jin yadda za a yi. Idan dai komai ya tafi daidai, wannan maganar ta kare." Hajiya Rumanah ta runtse idanu na wani lokaci, tana tunani mai zurfi. Daga bisani ta bude su, ta numfasa. "Idan har suka samu damar kubuta, kun san abin da zai faru, ko?" Dukansu suka yi shiru na dan lokaci. Sai Hajiya Karama ta gyara zaman rigarta, ta ce da murmushi, "Ba za su kubuta ba." "Aameen..Dan akwai babbar matsala idan hakan ta kasance..." Haka dai suka cigaba da tattauna irin sake 'damarar shirin muguntar da zasu cigaba da yiwa Hajia Zaytunah da yaranta Nabeeha da Hammad... 🎀🎀🎀🎀 Hankalin Gwaggo Hafsatu gaba ɗaya ya tashi, tana a zaune a kan gadon asibitin da aka kwantar da ita. Duk da irin ciwon da kanta ya soma yi, zuciyarta na a tare da Zaytunah da 'ya'yanta. Major General Dawud yana zaune gefenta, hannunsa rungume da wayarsa. Zuciyarsa na cike da damuwa, amma bai nuna sosai ba. Tun da aka kwantar da Gwaggo, yake jiran su Hajiya Zaytunah su iso. Basu iso ba. Tun dazu Kuma ya sanarwa mai dakin sa Hajiya Maijiddah kanta sanarwa Hajia Zaytunah .. Ya ɗaga kai ya dubi matarsa, Hajiya Hauwa Maijidda, da ke tsaye a gefe tana gyara zaman hijabinta. "Hauwa, kin tabbatar da kin sanar da su su taho?" Ta gyada kai da tabbaci. Tana duban screen din wayarta.. "Eh, na tura mata sako tun dazu." Ya gyara zama, zuciyarsa na raya masa wani abu. Ya ɗauki wayarsa, ya kira lambar Hajiya Zaytunah da kansa. Wayar ta yi ƙarar bata shiga.. Ya sake gwadawa, amma sai aka nuna "number not reachable." Ya tsagaita, yana kallon wayar da jajayen idanu. Sai ya sake gwada lambar Nabeeha. A kashe. Damuwa ta fara shigar masa da kyau. Hammad fa? Shi ma aka kashe tasa. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa. Ya dubi Hajia Hauwa da jajayen idanu. "Ki sake gwadawa mana, ko ta karanta sakon?" Hajiya Hauwa Maijidda ta sake duba wayarta, ta shiga sakon da ta tura. Ta karanta.. Batare da bata lokaci ba, ta kira lambobin gida. Daya bayan daya, babu wanda ya daga. Kamar yadda ya zata, babu wanda ke kusa da waya. Sai ya kira lambobin ma’aikatan gidan domin jin halin da ake ciki. Babu wanda ke ɗauka. Nan take zuciyarsa ta buga! Gwaggo Hafsatu ta lura da yanayin fuskarsa. "Dawuda, me ke faruwa?" Ta tambaya cikin raunanniyar murya. Ya buɗe baki da ƙyar yana kokarin daidaita kansa yace "Ba ma iya samun su." "Me kake nufi da hakan?" "Bakomai gwaggo. Kwantar da HANKALIn ki.." Bayan yace da gwaggon haka, Ya tashi tsaye da sauri, yana kiran daya daga cikin masu gadin sa . Ya ɗauka a take. Bayan sun gaysa, Mai gadin ya tanbayi jikin gwaggon .. Major general yace da shi, "Kana gida?" "A'a, ranka ya daɗe, ni da wasu daga cikin ma'aikata mun fita siye-siye." "Kana da masaniya kan inda su Hajiya Zaytunah da sauran yaran suke?" "Eh, ranka ya daɗe. Ai sun fita tun dazu da motar Hammad. Sun ce zasu taho asibiti." "Amma har yanzu basu iso ba!" Mai gadin ya yi shiru na wasu dakiku..kafin yace, "Allah Sarki, ranka ya daɗe. To ban san inda suka wuce ba. Ko sun samu cunkosu a titi" Major General ya kashe wayar a fusace... Gwaggo Hafsatu ta dafe KIRJIN ta. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Dawuda, kar ka ce an samu matsala!" Hajiya Hauwa Maijidda ta dube shi da tsananin tashin hankali. "Ko dai hatsari suka yi?" "Haba Hauwa. For heaven sake. " Ya karasa bata amsa yana narka mata uwar harara. A wani yanayi mai cike da firgici, Major General Dawud ya sake duban wayarsa, ya fara kiran lambobin da suka dace don a fara bincike. Zuciyarsa na bugawa da sauri. Bai taɓa jin irin wannan tsoron ba. Wannan ba al'ada ba ce.. Gwaggo Hafsatu ta rungume kanta da tafin hannayenta, idanuwanta sun kada. "Allah Ka tsare su! Allah Ka kawo su lafiya!" Major General ya furta da ƙarfi, "Ba zan zauna ba har sai an gano inda suke. Inshaaa Allah gwaggo ba matsala." Ya shiga cewa da ita haka yana kokarin karfafa mata gwiwa.. "Tohm dawuda..." Ta fada tana sauke nannauyar ajiyar zuciya. Hade da rarumar carbinta ta cigaba da lazimi tana rokon Allah ya kawo musu mafita. _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09032345899_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:3_ Gabanta ya shiga dukan tara tara, yayin da ilahirin gabobin jikinta suka soma yi mata sanyi. Ganin an sake daukar wasu lokutan shiru ba alamar su ba labarin su.. Gashi su Raudah har sun taho asibitin daga gidah.. Gwaggo Hafsatu ta fashe da kuka mai ban tausayi, jikinta na karkarwa. Duk dakiyar da take da ita da kauda kai a abubuwa da kokarin boye damuwa.. kasancewar ta tsohuwa mai kamun kai da jan girmanta..Amman a ranar ta gaza boye dukkanin damuwarta. Tashiga tsananin dimuwa mai wuyar fassarawa. Domin tana jin kaunar Hajiya Zaytunah tamkar yar data haifa daga cikin cikinta. Hakama su Nabeeha tamkar su Raudah suke awajen ta. Ma'ana jikokin ta. Takance hajia zaytunah da yaranta amanace Allah ya damka a hannayen su itada major general dawud. "Dawuda, Kada ka bari wani abu ya same su! Wallahi zuciyata tana kara nauyi!" Major General Dawud ya daure, amma a ciki jikinsa shi kansa ya gama sanyi.. Duk makota, da sauran shagunan sayayya da aka san zasu iya biyawa anje basa nan... Don haka major general ba shida wasu sauran zantukan kwantar da HANKALI da zai fadawa mahaifiyar sa gwaggo Hafsatu akansu hajia zaytunah.. Ya numfasa kawai yana kada kai cikin girmamawa yace, "Inshaa Allah Gwaggo..Allah ya datar da mu.. Kiyi hakuri" Ya sake ɗaukar waya ya kira Brigadier General Mukhtar dake military intelligence unit. abokin aikin same wanda yake a karkashin sa yake a baya kafin yayi retire, Bayan sun gaysa ne. Brigd Gen.. Mukhtar ya numfasa, "Yallabai!" Brigadier General Mukhtar ya amsa da girmamawa. "An samu matsala! Ana buƙatar gaggawar bincike kan bacewar kanwata da yayanta daga gidana. Duk hanyoyin sadarwa sun katse, Kaganmu atare da Gwaggo ma a asibiti. Munyi iyaa mai yiwuwa wajen tattambayar makota, shaguna da wuraren da akasan zasu iya biyawa. Yes asibitin zasu zo...Ah Alhamdulillah da sauki. Okay zataji.. No gaskia basa zuwa ko'ina. Ba masu fita bane. Dan yarinya daya cema ke zuwa jami'a tare da daya yarinyata. To kuma driver ne ke kai su ya dawo dasu ko yayan su idan yana gari. Eh su uku ne. Ita Zaytunah, sai Nabeeha. Sai Hammad. Hammad din shi bama anan yake karatu ba a oversea ne. Eh tabbas, muna tunanin yiwuwar an yi garkuwa da su." A ɗaya ɓangaren, Brigadier General Mukhtar ya farka gaba ɗaya. Jin labarin ban mamaki da tu'ajjabi.. "Ranka ya daɗe! Za mu fara aiki nan take! Ko akwai wani bayani na ƙarin haske?" Major General ya runtse idanuwansa yana kokarin dakile wani abu dake kokarin taso masa daga ciki mai zafi, "No, Muna jiran su nema su zo nan asibitin alfirdaus specialist dinnan na outskirt of cikin gari dinnan.amma tun ɗazun ba su iso ba. Duk wayoyin su a kashe, Kaga kuwa. Wannan ba karamun abu bane, akwai wani abun a kasa" "Mun fahimta! Bari mu tara jami’anmu don a fara bincike nan take!" "Godia nake..." Ya katse wayar bayan sunyi sallama.. "Inshaa Allah yanzu zasu fara aiki Gwaggo... Yana ma duba jikin ki kafin ya iso yace" "Toh Allah yasa mu dache... Ina amsawa nagode kwarai" Major general baiyi kasa a gwiwa ba. Ya sake danno kiran wani yaron sa, Bayan sun gaysa ne yake tambayar yaron inda yake, "Ina barracks yallabai!" "Inaso ka jagoranci bincike kan motar number motar nan da zan turo maka, Daga nan ka yi coordination da Intelligence Unit don mu gano inda aka kwashe su." "Za a fara aiki nan take, ranka ya daɗe!" Major General Dawud ya sauke ajiyar zuciya. Amma har yanzu, zuciyarsa na bugawa da tsanani. Ya juya ga Gwaggo Hafsatu da Hajiya Hauwa Maijidda. "Inshaa Allah, Duk yadda za a yi, sai mun gano inda suke..Allah ya shige mana gaba yasa mu dache Amin" "Toh Allah ya amince" "Aameen" suka amsa baki daya... Ranar dai a dole likitan ya sallame su. Don gwaggo Hafsatu ta matsa kan ba zata kwana a asibitin nan ba. HANKALIn ta baya jikin ta. Nutsuwar ta da kwanciyar hankalin ta baki daya ya tattara ne awajen su hajia zaytunahh na rashin sanin takamaimai halin da suke ciki.. Hankalin Major General ya ƙara tashi fiye da yadda zai iya bayyanawa. Bai taɓa jin zuciyarsa ta yi nauyi haka ba. Hannunsa ya fara gumi, ya sake duba wayarsa. Bai san sanda ya miƙe tsaye da sauri ba. Ganin lokaci ya sake zartawa.. Amman ba wani labari daga dukkanin wadanda ya saka aikin bincike... Gwaggo Hafsatu ta dubi dan nata, idanuwanta cike da tsoro. "Dawuda, ka ce wani abu! Ka ce ba wata matsala!" Hajiya Hauwa Maijidda ta dan matsa kusa da shi. "Kayi shiru! Me ke faruwa?" Muryarsa ta ɗauka da ƙarfi. Bai masan ya furta, "Wannan abu ba daidai bane! Ba abu ne na hatsari ba. Ba daidai bane gaba ɗaya!" hajiya Hauwa Maijidda ta ɗaga wayarta da sauri, tana sake ƙoƙarin kiran Hajiya Zaytunah, Nabeeha, da Hammad. Amma duk wayoyin a kashe suke. "Subhanallah!" Ta furta, jikinta na rawa. Major General Dawud ya haɗa fuska, ya danna wata lamba a wayarsa. Cikin daƙiƙa biyu kacal aka ɗauka. "Captain!" Ya kira da kakkausar murya. "Na’am, ranka ya daɗe!" "A gaggauce ka bi sawun brid. Gen. Mukhtar, Ka temaka musu ku tsananta binciken nan da gaggawa" "Ina nan a kan hakan, ranka ya daɗe." Ya kashe wayar batare da wata magana ba. Gwaggo Hafsatu tasake fashewa da kuka. Wannan karon muryarta har wani rawa takeyi, "Dawuda, ka taimake ni! Kar dai wani abu ya same su!" Zuciyar Major General tana bugawa, amma ya daure kansa. Ya kalli mahaifiyar sa, gwaggo Hafsatu cikin muryar ban tausayi da rarrashi yace, "Inshaa Allahu zasu kubuta, Za'a ceto su gwaggo, Zaa gansu. Ki bar zubar da hawayen ki dan Allah.." Major General ya rufe idanuwansa na wasu dakiku, yana shakar iska mai nauyi. Nan take ya ɗauki waya, ya kira Control Room na sojoji. "Ina so a fara bincike! A duba ko an samu wani rahoto na motar da ta bar gida tun dazun!" A ɗaya ɓangaren, wani yaron sa ya kira shi. "Tracking ɗin motar yana nuna an bar hanya mai tsaro. Motar ta shiga cikin wani yanki da ba a saba wucewa da ita ba!" Kamar an caka wa Major General ƙwalla da wuka, haka zuciyarsa ta ji. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!" Ya dafe goshinsa, hannunsa na rawa. Gwaggo Hafsatu ta kama rigarsa. "Ka ce ba a sace su ba, Dawuda! Kar dai yan fashi ne!" Zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Bai iya cewa komai ba. Amma zuciyarsa na jin 'An sace su!' Ya dan kakaro murmushin kwantar da gwaggon HANKALI yace, "No akan na'urar aiki ne ta katse. Inshaa Allah komai zai daidaita Gwaggo..ki kwantar da HANKALIn ki" 🎀🎀🎀 Duk da an jima ana tafiya, babu wata gajiyar da Fawaaz ke ji. HANKALIn sa gaba ɗaya yana kan abu ɗaya wato Nabeehan sa... Tunda suka fara tafiya daga base, tunaninsa ya kasa barin fuskar Nabeeha, Yanayin tsarin halittar jikin ta, sanyayyar muryarta, Kai komai nata ma, Yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa da soyayyarta, yana jin yadda zuciyarsa ke harbawa da son ya ganta a zahiri, ya fuskance ta, ya faɗa mata abin da ke ransa. Ya gama yanke hukunci, yau ba zai kwanta ba tare da ya fuskance ta ba. Duk da miskilancinsa da kamun kansa, ya yanke shawarar faɗa mata gaskiyar zuciyarsa. 😂 Sai ga direban nasa yana sanar da shi, "Yallaɓai, yanzu zamu hau babban titi har cikin gari" Yana shirin bayar da umarni, sai wayarsa ta fara ringing. Mahaifinsa ne. Wato, Major General Dawud. Nan take bugun zuciyarsa ya sauya. Ya duba fuskar wayar, yana jin kamar numfashinsa na ɗaukewa, Mahaifinsa ba mutum ne mai yawan kiran sa ba, sai dai idan da wani lamari mai muhimmanci. Ya ɗaga wayar da sauri. "Morning sir! Barka da war haka Baba!" Muryar mahaifinsa ta fito da ƙarfi da girmamawa, amma kuma da wani yanayi na tashin hankali da bai saba jin sa da shi ba. "Fawaaz! Ba lokaci, muna da matsala! An sace su Hajiya Zaytunah, Nabeeha da Hammad!" Zuciyarsa ta tsaya cak. Duk duniya tamkar ta tsaya cak a kunnensa. "M... menene?" "An sace su akan hanyar zuwa asibiti! Gwaggo an kwantar da ita as of then , su kuma an sace su! Duk wayoyinsu a kashe! Babu wanda ya san inda suke!" A wani lokaci dabam, Fawaaz zai iya sarrafa kansa, amma yanzu zuciyarsa ta gama harbawa da tashin hankali! Ya ji wani sanyi yana ratsashi daga ƙasa har sama. Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi. "Nabeeha..." ya furta a hankali, yana jin yadda wani abu mai tsananin zafi ke ciwo a KIRJIN sa. Tunanin cewa Nabeeha tana hannun wasu mutane ya kusa gigita shi. Ita da ke ransa da zuciyarsa, ita da yake shirin faɗa wa gaskiyar zuciyarsa, ita ce aka sace? "Kana jina kuwa, Fawaaz?!" Mahaifinsa ya ɗaka masa tsawa. Ya rufe idanunsa, yana kokarin daidaita numfashinsa. Ya sanya hannunsa yana dafe kansa. "Sorry sir. Yes sir! I'm all ears..Ina sauraron ka... gashinan zan dawo gidan yanzu! Babu wanda zai kwana ba tare da an san inda suke ba inshaa Allah !" Major General Dawud ya sauke ajiyar zuciya. "Godiya nake, Fawaaz. Mun baza jami’an bincike, amma kana da ilimi da kwarewa wajen gano abubuwa. Sauran jami’ai na kan aikinsu, amma ina bukatar ka waiwayo gidah yanzu don taimakawa wajen gano su." Fawaaz ya sunkuyar da kansa, yana jin yadda zuciyarsa ke ƙuna da damuwa. "Inshaa Allah baba...." Major general ya katse wayar.. Cikin muryar sa mai cike da damuwa yace da direban, "Kara gudu ! Please... I beg you!" _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:4_ Gaba daya tunda Captain Fawaaz Dawud ya karɓi kiran mahaifinsa, Major General Dawud, hankalinsa ya yi matuƙar tashi, amma a zahiri ba a iya karanta komai a fuskarsa. Yana daga cikin mota tare da direbansa lokacin da kiran ya shigo. Duk da cewa tunaninsa yana kan Nabeeh.. masoyiyar da bai furtawa kalaman yana kaunarta ba a zahiri. Sai gashi labari mafi muni ya riskesa alokacin daya gama tsarawa zuciyarsa da labbansa yanayin yarda zai furta mata komai na kaunar da yake mata. Mummunan labarin an sace su ya doki kofofin kunnuwan sa.. “An sace su Hajiya Zaytunah akan hanyar su ta zuwa asibiti duba gwaggo,” Ya tuno mahaifinsa ya sanar da shi da kakkausar murya... Fawaaz ya ɗauki sakanni kaɗan yana nazari, ba tare da wata hayaniya ko wata alama ta firgici ba. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Gabansa na tsananta bugawa, Ahankali ya zura hannu ya zare katin kuɗi mai nauyi daga aljihunsa, ya miƙawa direban nasa, sannan ya ce, “gashi ba yawa, ka tafi gida ka huta, Na gode.” Direban ya ji mamakin yadda Fawaaz bai nuna wata damuwa ko firgici ba. Lalle wannan shi ne Captain Fawaaz Dawud Mafia. Soja mai cikakken ikon sarrafa kansa... Direban ya sauka ahankali yana yana sake yiwa captain fawaaz godia. Idanuwansa sun cika da ruwan hawayen kyautar kudi masu yawa da fawaaz din ya masa, "Nagode ranka ya dade. Allah ya saka maka da alkhairi. Ya yi riko da hannuwan ka. Allah kuma ya shiga cikin lamuran ku Kai da zuriyar ka. Ya kawo karshen dukkanin matsaloli" "Aameen, Ni ne da godiya" captain fawaaz, Bai jira komai ba, ya shiga cikin motarsa ya ja da gudun wuce kima, har sai da tayoyin suka yi ƙara akan titin. Hannunsa yana kan sitiyari, idonsa yana kan hanyar da ke gabansa, amma zuciyarsa tana can waje guda kawai., Nabeeha. Sai yanzu ya fahimci cewa damuwar da yake ciki ba saboda kowane mutum ba ne sai ita. Duk da kasancewarsa mutum mai natsuwa da miskilanci, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi saboda ita. Amma ba lokacin tunani ba ne. Yanzu aiki ya rage masa. Yana tafe yana amfani da na’urorin binciken sojoji na zamani, yana tuntuɓar abokan aikinsa ta SIRRI. A matsayin soja, ya san hanyoyin gano mafakar masu aikata laifi, kuma ya san yadda ake bibiyar mutum ta hanyoyin zamani. Yana tuki da gudu fiye da kima, yana kauce wa motocin da ke kan titin, yana kwana cikin gaggawa. Da wani irin zafi yake tuƙi, tamkar idan har ba zai isa ba nan take, zai iya karya ƙa'idojin duniya gaba ɗaya don kawai ya isa. Wani lokaci ne da bai taba jin kansa a haka ba cikin tsananin gaggawa da tsoro mai yawa. "Waye ya sace su? Me suke nufi? Me yasa?!" A yanzu, babu wani abu a duniyarsa da ya fi muhimmanci fiye da gano inda Nabeeha take. A zuciyarsa, yana jin wani sabon irin fushi da ba kasafai yake jin sa ba. Idan har wani ne ya kuskura ya cutar da ita... to wannan zai kasance babban kuskuren rayuwarsa. Fawaaz ya cigaba da tuƙi da gudun tsiya, tamkar zai tarwatse da zuciya. Bai damu da harbin hanyoyi ko ƙa'idojin hanya ba, burinsa guda ɗaya ne isa gida cikin gaggawa! A lokacin da ya kusa isa, ya hango daya daga cikin masu gadin gidan yana buɗe babbar ƙofar shiga. Wani saurin fakin ya yi, motar na kusan sulalewa ta tsaya cak! Bai ko kashe injin ba, ya fice da matuƙar sauri. Da sauri da gudu gudu yana shigewa cikin gida da hanzari. Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. Yana shiga cikin babban falo, ya hango mahaifinsa, Major General Dawud, tsaye cikin damuwa, yana waya da wasu mutane. A gefe kuma Gwaggo Hafsatu zaune, hannayenta a dage a sama, kamar tana addu’a. Damuwa ta bayyana a fuskarta, "Baba! Sir! " Fawaaz ya furta, zuciyarsa na harbawa. Major General Dawud ya waiwaya da sauri, idanunsa sun nuna yawan tunani da damuwa. "Fawaaz, an sace su! An sace su akan hanyar zuwa asibiti!" "Subhan'Allah!" Fawaaz ya kusan faɗuwa saboda girgiza da tashin hankali. "Who did this?! Waye yayi haka?!" Gwaggo Hafsatu ta dago idanunta da suka cika da hawaye. "Ya Allah, ka tsare su! Ka kubutar da su cikin aminci!" Major General Dawud ya ajiye wayarsa, yana jan numfashi. "Ba mu san su waye ba, amma tun dazun muna kokarin bincike. Har yanzu babu wani sahihin labari daga jami'an tsaro." Fawaaz ya runtse idanunsa da ƙarfi, numfashinsa yana ƙara nauyi. "Father... Su Nabeeha fa? Ta ina suka tafi da su?" Major General ya gyara tsayuwarsa, yana daidaita muryarsa da ƙyar. "Bamu san inda aka tafi da su ba, amma mun tabbatar an sace su a kan hanyar zuwa asibiti. Mun kira wayoyinsu, duk a kashe." Fawaaz ya dafe kansa, yana jin ƙarar zuciyarsa na bugawa kamar zata faso kirjinsa ta fito. "Ba zai yuwu ba! Oh no no no no..!" Ya juya da sauri, yana lalubo wayarsa. "Ba za su iya ɓacewa haka kawai ba! Dole akwai mafita!" Fawaaz ya riƙe wayarsa da ƙarfi, numfashinsa yana saurin hawa da sauka kamar wanda ya yi gudun fanfalaki. Tashin hankali ya cika zuciyarsa, tunaninsa ya rabu biyu, Ina Nabeeha? Me ke faruwa da ita a wannan lokacin? An sace su a yanayin da yake matukar bukatar ta don sanar mata labarin zuciyar sa.. Ya sa hannu ya share gumin da ya taru a goshinsa, ya danna lambar wasu daga cikin ma'aikatan sa domin tabbatar da wani abu, amma babu wanda ya ɗaga. "Damn it!" Ya furta, yana jan numfashi mai nauyi. Major General Dawud yana tsaye kusa da shi, hannunsa cikin aljihun wandonsa, fuskarsa cike da kaffara da damuwa. "Fawaaz, ka kwantar da hankalinka." Muryarsa ta fito da nutsuwa mai cike da umarni. Fawaaz ya juyo da sauri, idanunsa sun kada kamar wutar lantarki. "Baba, Ta yaya zan iya wani kwantar da hankalina? Nabeeha na hannun wasu mutane da bamu san ko su wanene ba! Wannan ba lokaci bane na nutsuwa!" Fawaaz ya fada acikin zuciyar sa.. "Allah ka kubutar da Nabeeha" ya fada batare da yasan subatar bakin da yayi ba. Major general ya lura dashi yana dan bubbuga kafadar sa yache "It shall be well inn shaa' Allah" Gwaggo Hafsatu ta sauke numfashi mai nauyi, tana girgiza kai. "Ya Allah! Ka tsare mana su. Allah ka dawo mana da su lafiya!" Major General ya ɗauki wayarsa, ya sake kiran sauran jami’an tsaro domin a tura jami’ai don bincike da gaggawa. Captain Fawaaz ya tsaya cak, idanuwansa sun ɗauki wani irin kalar tsananin tunani. Cikin ƙanƙanin lokaci, kwakwalwarsa ta fara hango hanyoyin da zai bi don gano su Hajiya Zaytunah, Nabeeha, da Hammad. Ya juya ga mahaifinsa, Major General Dawud, cikin cikakkiyar murya mai ƙarfi. "Sir, ina buƙatar cikakken bayani. Wa ya san tafiyarsu? Wani lokaci suka bar gida? Wane irin shiri aka yi don tsaron su?" Major General Dawud ya gyara tsayuwarsa, yana jin alfahari da yadda ɗansa ya saba da aiki ba tare da ɓata lokaci ba. "Mun san dai sun taho asibiti ne, amma ba su iso ba. Wayoyinsu duk a kashe. Motarsu ba a gani a asibiti ba basu iso ba. Ba kuma ta gidah alamar sun bar gidah kenan. Sannan bata dukkanin inda ake tunanin zasu je. Muna da sakon da mahaifiyar ku ta aika musu kafin tafiyarsu, amma bayan haka babu wani bayani daga gare su." Gwaggo Hafsatu, da hawaye ke ƙoƙarin taruwa a idanunta, ta ce cikin shashsheƙar murya, "Fawaaz, Ku tsananta bincike,... Nabeeha... Hammad... Zaytunah... har yanzu ba a san inda suke ba. Ka yi wani abu, dan Allah." Fawaaz ya kalli kakarsa da idanunsa masu ƙayatarwa, sannan ya rankwafa a gabanta "Gwaggo, zan dawo da su. Inn shaa' Allah na miki alƙawari." Bai ƙara bata lokaci ba, ya fice da sauri zuwa sashen sa ya ɗauko wata na'urar gano siginar wayoyi ta sojoji daga cikin akwatinsa. Nan take, ya fara aiki. "First step, gano waje karshe da aka yi amfani da wayoyin su." Ya ce a hankali, yana duba bayanan da suka fara bayyana a na'urar. Ya latsa wani maballi, na'urar ta yi ƙarar ɗan motsi, sannan ya fara samun sakonni, Last known signal: kusa da hanyar asibiti. Next movement: ba a iya gano shi. Possible jamming detected: wani abu yana toshe siginar wayoyin su. Fawaaz ya rufe idanunsa na sakanni kaɗan, yana ƙoƙarin fahimtar abinda ke faruwa. Duk alamu na nuna cewa wannan ba kawai batan hanya ba nez tabbas an sace su. Ya buɗe idanunsa a take, yana jan numfashi da zurfi. Sannan ya juyo yana fuskantar mahaifinsa. "Sir, ba hatsari suka yi ba. Wannan shiri ne aka yi don a sace su. Ina buƙatar izinin amfani da dukkan hanyoyin tsaro don gano su." Major General Dawud ya gyada kai ba tare da wata gardama ba. "Permission granted. Ka yi duk abinda zai dace, Captain." A nan Fawaaz ya danna wani maballi a na'urar hannunsa, yana aika da bayanai zuwa wata runduna ta musamman da ke taimakawa a irin waɗannan lokuta. A lokaci guda kuma, ya ɗauki wayarsa yana dailing wata lamba, wanda zai iya taimaka masa fiye da kowa a wannan yanayi. Yanzu dai lokaci ya fara ƙurewa,duk wani mataki da za su ɗauka dole su ɗauka da gaggawa.A cikin zafin nama, Fawaaz ya fice ya nufi parking lodge tuni har masu gadin sun shigar masa da motar, Ya karbi makullin motar tasa yana musu godiya.. Ya buɗe motarsa ya shiga da sauri, zuciyarsa cike da tsananin tashin hankali da fargaba. Bai tsaya tunani ba, ya danna motar da gudun tsiya. Takalminsa ya danna kan accelerator da ƙarfin tsiya, yana tukin cikin fushi da tsoro. "Nabeeha! Kar ki bari wani abu ya same ki!" Ya furta cikin sauti mai ƙarfi, zuciyarsa na bugawa da mugun sauri. _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 5_ Captain Fawaaz Dawud ya naɗe hannayensa da ƙarfi akan sitiyarin motarsa, idanunsa sun cika da girmamamman al'amarin da ke gabansa. Hankalinsa ya ƙara tashi lokacin da ya duba taswirar wayarsa, ya ga cewa siginar tracking na inda akai amfani da wayar karshe tana motsi yanaa nufin an wuce da su! Ya danna kira ga tawagar bincikensa. "Bravo Team, target yana motsi! Sigina yana nuna suna tafiya cikin wani yanki da ba a fiye amfani da hanyarsa ba. Dole mu gaggauta kafin su kauce daga tracking range!" Wani daga cikin sojojinsa ya amsa, "Roger that, Captain! Muna bin sawun coordinates da ka aika. Muna shirye don ɗaukar mataki." "Thank you" Fawaaz ya fada yana katse kiran... Airpods ya zura a kunnuwansa saboda saukin amsa kira ba sai yata latsa wayar sa ba. Gabansa na tsananta bugawa ayayinda yaketa kokarin kiran sauran maaikatan dake gudanar da bincike. Wani bangaren na zuciyar sa yana samun saukin radadi ganin tracking devices sun fara aikin kokarin gano inda su Nabeehan sa suke... 🎀🎀🎀 A wajen da suke a tsare , Nabeeha, da Hammad da Hajiya Zaytunah da ta daidaita tana addu’a cikin shiru. Zuciyarta ta cika da fargaba, amma ta yi ƙoƙarin ƙarfafa ƙwarai domin ba 'ya'yanta damar samun kwanciyar hankali. A wannan lokacin, Hajiya Zaytunah a cikin ɗakin da aka tsare su, ta fara kallon sama cikin dogon nazari. "Allah ya tsare mu, ya kawo mana agaji," ta yi ta addu’a, tana fatan cewa Allah zai kawo musu sauki ba tare da bata lokaci ba. Daya daga cikin tawagar binciken Fawaaz ta fara motsawa cikin dazukan, suna amfani da kayan zamani na bincike da fasahar tauraron dan adam, tare da makamin CCTV da na'urorin sa ido. Daga cikin wannan tsari, Captain Fawaaz ya kasance cikin cikakken natsuwa... ko da yake zuciyarsa na bugawa da karfi a cikin rufin jikinsa, ba ya bari damuwarsa ta bayyana a fili. "Mu tashi, mu shiga aikin ceto. Ba zan bari wannan muguntar ta kare ba," in ji shi a cikin murya mai kwarin gwiwa. A nan, lokacin ya fara ƙurewa, kowane sakan na tafiya yana nuni da muhimmancin daukar mataki cikin gaggawa. Fawaaz ya kafa hannunsa a kan na'urar, yana tura bayanai zuwa rundunar musamman da aka kebe domin irin waɗannan lamurra. Yayin da tawagar binciken ke matsowa cikin ƙaramar ƙofar daji, Captain Fawaaz ya ƙara jaddada umarni, "Ku kasance masu faɗakarwa, duk wani motsi mara kyau, ku sanar da ni kai tsaye. Mu tabbatar babu wata hanyar da za su iya ɓoye mu a ciki." Duk da kasancewarsa mutum mai ƙarfi da rashin bayyana jin zafi, cikin zuciyarsa ya cika da kishi da ƙwazo na ganin su Nabeeha sun dawo lafiya. Duk abin da ya faru, shi ba zai yarda da wannan mugunta ta ci gaba ba, daga nan zai tashi don daukar duk wani mataki mai tsauri. Tsohon gidan da ke tsakiyar dajin ya fara bayyana a nesa, kamar wani guri mai shakku da duhu. Wannan shi ne wurin da na'urar tracking ta nuna, kuma tawagar binciken ta fara shiryawa tsaf don shiga cikin aikin ceto. Captain Fawaaz Dawud ya ɗauki numfashinsa da zurfi, ya tsayar da tafiyarsa a wani wuri mai nisa, yana auna kowane alamun motsi a taswirar digital. "Mu shirya. Lokaci yayi da za mu tunkari wannan wuri," in ji shi cikin muryar soja mai cike da umarni, yayin da zuciyarsa ta ci gaba da bugawa ba don bayyana damuwa ba, amma saboda kishi da kwarin gwiwa na son ganin su Hajiya Zaytunah sun dawo lafiya cikin koshin lafiya. Sai dai lokacin da suka karasa shiga cikin dokar dajin..sun Sha tsananin mamakin ganin wuta tanaci da bukkoki tamkar da mutane acikinta. Amman ba kowa awajen wayam. Kenan yan fashin backup sukayi musu don su zata suna nan da su Hajiya Zaytunah a tsare.. "God damn it! " Captain fawaaz ya fada yana cijan yatsansa. "Roger that, captain yanzu ya zamuyi what's next? " "Muyi grouping into 4,. Ku nan ku yanki dajin kudu, ku kuma dajin yamma, Ku Kuma nan haka gabas zakuyi. Kai da Kai da Kai muyi arewa. Let's go.no time ...move it soldiers.." "Aye aye captain" suka amsa shi cikeda zafin nama da Kuma girmamawa. Motocin su suka shisshiga suka fara barbazuwa cikin dazukan don neman su Hajiya Zaytunah.. Captain fawaaz suna tafiya acikin mota yana jera tsaki ba adadi. Ya sauke numfashi Mai zafi yana dartse lebensa. Mahaifinsa ya kira a awaya ya sanar masa yadda suke ciki ya karkare da, "Amma mun rabu wings hudu sir, yanzu haka Muna mota ma zamuyi arewa. Inshaa Allah su aunty, Hammad da Nabeeha zasu dawo gidah cikin koshin lafiya in Allah ya yarda" "Allah ya amince captain. Sannu ku da kokari" major general ya amsa a sanyaye a nasa bangaren.. Gwaggo Hafsatu da tunda suka fara wayar take dubansa ganin sun kammala wayar bai ce komai ba ya sata cewa, "Wani abune ya faru?" "Aa inshaa Allah kalau Gwaggo. Ai sun barbazu ma cikin dazukan kudu da arewa, gabas da yamma. Su Hajiya Zaytunah zasu dawo gidah cikin koshin lafiya inshaa Allah" "Toh Allah ya amince dawuda. Allah ya yarda dawuda. Allah ya kawo karshen wannan mummunan labari Amin" "Aameen Gwaggo.. Aameen" Yana rufe bakinsa. Wayar sa ta fara Kara. Ya dauka ganin chief judge Abdulfatah ne. Bayan sun gaysa yake sanar dashi dazu jikin Gwaggo ne ba lafiya. Ankwantar da ita a asibiti ma amma sun dawo gidah.. "Toh shikenan babu damuwa... Allah ya kawo su lafiya. Okay kai baka nan ma? Ayyah ehh. Supreme court. Toh Allah ya bada saa. Alright sai munyi magana. Nagode. Zataji inshaa Allah yauwa sai ka dawo" Ya katse Kiran yana hurar da iskar bakinsa Mai tsananin zafi..ya dubi gwaggo yache, "Abdulfatah ne. Yana duba jikin naki. Yana miki sannu yace na gayshe ki idan ya dawo zai zo ya dubaki inshaa Allah. Wai shugaban kasa ne yake neman su da gaggawa kan shari'ar nan ta supreme court." "Allah sarki... Nagode kwarai. Allah yabada saa" "Aameen gwaggo. Sai Kuma yake sheda mun mahaifan Muhammad mai neman Nabeeha sun taho suna kan hanya zasu karaso gidah" Ya karasa fada yana duban gwaggon da itama shi take kalla. Allah yaso su biyu ne a parlorn. Daga ita sai shi. Hajiya Hauwa ta tashi. "Tohh fa... Allah ka kawo mana sauki... " "Aameen Gwaggo. Yanzu ya zamuyi kenan?" "Dawuda ni kaina banida abun cewa.. Bamuda wani abun fada. Kaga dai halin da muka tsinci kanmu aciki ma. " "Ko ca za'ai musu sunyi tafiya basa nan? Nabeehan" "Toh kadai san me zaka sanar musu... Allah zai shiga cikin lamuran namu in Allah ya yarda" "Aameen gwaggo. In shaa Allah" Bai karasa rufe baki bayan maganar da yayi. Horn din dake jikin gate din gidan mai bada sauti ga bakin motocin da suka dososhi ne zasu shigo ya farayi ba kakkautawa. Inda masu gadin kafin su danna permit button sai da suka kira intercom na sashen major general dawud suka sanar masa. Nan yace abude musu bakin sane... A lokacin da su Alhaji Amiru, Alhaji Uzairu, Muhammad, Gwaggo Zainabu, da mai aikinta suka iso gidan Major General Dawud, an shigo da su ta babban kofar gidan, inda masu gadin gidan suka gaishe su cikin ladabi. A nan ne suka zarce zuwa cikin babban parlour, inda aka sauke su domin jiran Major General Dawud. A yayin da suke zaune, ma’aikatan gidan suka shiga da kayayyakin da suka kawo. Manya manyan ledoji shake da kaya. Da kwalaye. Harda Karin wasu akwati guda biyu... Akwatinan da suka ƙunshi kayan kyauta da wasu kayayyakin alatu, da manyan kwalaye.. Akwai ma wasu ledodi na kaya da aka mika wa wata daga cikin masu aikin, wadda ta shigar da su zuwa ɗakin da Gwaggo Hafsatu ke amfani da shi. A hankali, an gama sauke komai, sannan aka tabbatar da cewa babu wani abu da aka bari a waje. Duk da cewa ma’aikatan ba su fahimci dalilin kawo kayan ba, sun kasance cikin girmamawa da kwarewa, suna kokarin yin komai ba tare da hayaniya ba... Bayan ma’aikatan gidan sun gama shigar da kayan cikin tsari, daya daga cikinsu ya iso kusa da Alhaji Amiru cikin ladabi, yana sanar da su cewa an kammala jera kayayyakin a inda ya dace. Gwaggo Zainabu ta ɗan zubawa parlourn ido, tana nazarin yadda gidan yake. Ita kanta ta san cewa gidan ba ƙaramin gida ba ne, kuma tsarinsa yana nuna cewa yana ɗauke da duk abubuwan jin daɗi. Sai dai hakan bai hana ta jin wani ɗan ɗaci a ranta ba, saboda tunani da damuwar da take ciki. Muhammad ya matsa kusa da mahaifinsa, yana dan shafa KIRJIN sa da hannunsa kamar mai son yin magana amma yana kokarin kame kansa. Alhaji Uzairu kuwa, ya ɗan lumshe ido na wani lokaci, yana jin shiru da yanayin gidan ya lullubesu. Gwaggo Zainabu ta kalli mai aikinta, wadda ke tsaye cikin nutsuwa kusa da ita, sannan ta ce da ita da sassanyan murya, "Samu waje ki zauna kema.. sannu da kokari" "To Hajiya," mai aikin ta amsa a ladabce, sannan ta juya zuwa hanyar wani dan corridor da kujera a wajen ta zauna tana nazarin kawataccen parlorn dayaci kayan kudi ya lashe.. A dai-dai wannan lokacin, wata daga cikin masu aikin gidan ta iso kusa da su cikin nutsuwa, sannan ta rusuna cikin girmamawa tana cewa, "Barkan ku da zuwa. Yallabai yana zuwa yanzu." Alhaji Amiru ya jinjina kai kawai ba tare da ya ce komai ba. Amma yana cikin zurfafa tunani. Ya san cewa wannan zama ba sauki ba ne, kuma ya shirya yin duk abin da zai yi don tabbatar da cewa an warware matsalar da ya kawo su. Gidan ya kasance cikin tsananin shiru, kowannensu yana cikin tunaninsa, har sai da aka fara jin alamun takun mutum yana matsowa daga waje... _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI* *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 6_   A hankali, cikin kasaita da nutsuwa, Major General Dawud ya taka zuwa cikin babban falon gidan nasa, inda bakin suka hallara. Yana ɗauke da wani irin kwarjini da kamun kai da suka dace da mutumin da ya saba da shugabanci. Da zarar idonsa yana sauka kan Gwaggo Zainabu, wadda ke zaune cikin kamala da haiba, sai ya taka da girmamawa, yana sunkuyawa kaɗan cikin dattako. A matsayinta na babbar macen data Isa ta haife shi, kuma dattijuwa mai cikakken daraja, ya san dole ya gaisheta da irin gaisuwar da ta dace da ita. A nutse, cikin ladabi da haiba, ya ɗan rusuna kaɗan, yana faɗin da murya mai zurfi da cike da girmamawa, “Ranki ya daɗe, Hajiya barka da wannan lokaci. Kun zo kalau?. Allah Ya ƙara lafiya da nisan kwana. Allah Ya ƙara girma da daraja.” Gwaggo Zainabu ta kalle shi da murmushin jin daɗi, tana jin daɗin yadda ya girmamata kamar yadda ya kamata. Ta amsa cikin kulawa da jin daɗi, “Alhamdulillah! Sannu da kokari. Yaya aiki? Allah Ya ƙara maka nasara da rufin asiri.” Ya ɗaga kai cikin girmamawa, yana amsawa, “Amin, Hajiya. Mun gode da addu’a. Allah Ya bar mana ke.” Bayan ya gama gaisheta da mutuntaka, sai ya juya zuwa sauran da suka zo. Ya miƙa wa Alhaji Amiru hannu, yana kallonsa ido cikin ido da cikakken mutuntaka. “Sannu da zuwa, Alhaji Amiru. Da fatan an zo kuma hanya lafiya?” Alhaji Amiru ya kama hannun nasa da ɗan murmushi, yana gyada kai. “Lafiya kalau, Major General. Mun gode da kulawa.” Bayan haka, ya miƙa wa Alhaji Uzairu hannu, suma suka gaisa cikin mutuntaka da ladabi. A ƙarshe, idonsa ya sauka kan Muhammad, matashin saurayin da ke zaune kusa da mahaifinsa. Muhammad Hammad, da zarar idonsa ya haɗu da Major General Dawud, sai ya ji wata irin kunya da girmamawa sun mamaye shi. A matsayinsa na mutum mai natsuwa da kamun kai, Muhammad ya san yadda ake mutunta manya, musamman irin su Major General Dawud, wanda shahararsa da mutuncinsa sun bazu a ko’ina. Uwa uba kuma mai babban matsayi ga zuciyar da yake kaunar kasancewa da ita wato Nabeeha.. A hankali, ya miƙa masa hannu cikin girmamawa, yana faɗin da wata murya mai cike da girmamawa, “Ina wuni, Baba barka da war haka.” Major General Dawud ya karɓi hannunsa da kulawa, yana kallonsa da idanu masu zurfi, amma ba tare da ya nuna wani abu a fili ba. Ya fahimci yadda Muhammad ke ji a lokacin, kuma bai da niyyar tsorata shi ko sanyaya masa guiwa. “Lafiya lau, Muhammad. Ya wajen su mama?” Muhammad ya gyada kai cikin girmamawa, yana cewa, “Alhamdulillah, suna lafiya.” Bayan haka, Major General ya matsa kaɗan ya zauna cikin kwanciyar hankali, fuskarsa na bayyana cikakken nutsuwa da sanin ya kamata. Duk da cewa kasancewarsa mutum mai ƙwarewa a lamurran tsaro ya sa yana da natsuwa da ƙarfin zuciya, yana da kyakkyawar dabi’ar girmama mutane, musamman waɗanda suka girme shi da shekaru ko matsayi. A cikin falon, an ɗan yi shiru na wasu ‘yan dakiku, kowa yana duba yadda yanayin zaman zai kasance. Kafin a soma tattaunawa kan batun da ya kawo su, Major General Dawud ya ɗauki lokaci yana duban fuskokinsu, yana nazarin yadda kowannensu ke kallon sa. Wannan shiru da nutsuwa da ya nuna, ya ƙara tabbatar wa da su cewa mutumin da ke gabansu ba mai sake-sake bane. Sai dai duk da haka, yana da halin yin biyayya da girmama waɗanda suka cancanta. Tuni maaikatan suka cika gaban su da abinci da sauran abubuwan motsa baki.. Bayan ɗan lokaci, Ya ɗan gyara zamansa, yana kallon Gwaggo Zainabu da sauran bakin da ke falon, yana jiran jin dalilin zuwansu da abinda suke da bukatar tattaunawa a kai. "Ranka ya dade... Nasan wata kila chief judge ya sanar maka da zuwan mu ko?" "Eh anyi haka. Yace zaku zo da yardar Allah..Dazu ma ya kirawo ni yake duba jikin mahaifiyata yake kuma sheda mun cewar shugaban kasa yana neman su kan wata shariah da.. yace idan ya dawo daga tafiyar zai shigo inshaa Allah" "Allah sarki. Shi yasa nayita kiran wayar sa bata shiga?" Cewar Alhaji Amiru "Zai iya yiwuwa kam. Kila suna cikin meeting. Allah yasa adace" "Aameen Yaa Rabbi. Ya jikin Hajian? " Suka shiga tanbayar jikin Gwaggo Hafsatu "Da sauki Alhamdulillah.... Zata karaso nan din yanzu Inshaa Allah.." major general ya fada yana murmushi. Bai rufe baki ba kuwa... Gwaggo Hafsatu ta shiga parlorn. Hajia Hauwa tana biye da ita a baya. Bakunan su dauke da sallama suka karasa shiga Suka amsa sallamar ta su... Gwaggo Hafsatu ta zauna akan kujera yayinda hajia Hauwa take daga kasanta. Gaisuwa suka farayi. Gwaggo Hafsatu da gwaggo zainabu sun gaysa sosai. Har suna tuno abubuwan da suka faru a baya lokacin da suka fara haduwa a asibitin dake birnin mawii. Alhaji Uzairu ya zauna cikin kamewa da dattako, ya gyara zamansa sannan ya fara magana da ladabi, "Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Yan uwa da iyayena mun zo gare ku ne a yau da farin ciki da girmamawa, domin mu gabatar da bukatar mu ta musamman. Da farko, muna mika gaisuwa da fatan alheri gare ku baki daya. Mun zo ne domin neman izinin ku da yardar ku, wajen neman auren 'yar ku, Nabeeha, ga ɗan mu, Muhammad. Mun yi imani cewa wannan haɗin zai kawo farin ciki da ɗorewar zumunci tsakanin iyalanmu. "Muhammad, ɗanmu, matashi ne mai tarbiyya da kyawawan halaye. Ya kammala karatunsa tare da samun nasarori masu yawa, kuma yana da kyakkyawan aiki da ke ba shi damar kula da iyali yadda ya kamata. Wato matukin jirgin sama ne, Air captain Muhammad, Har ila yau, yana da kyakkyawar mu'amala da mutane, kuma yana da kishi da kishin al'umma. Mun yi imani cewa zai zama miji nagari ga 'yar ku, Kuma yar mu, Nabeeha. "Mun kuma ji labarin kyawawan halayen Nabeeha, Mun yaba kwarai matuka, Yadda take da ilimi, Tana karatun likita, Ga tarbiyya, da kuma kwarewa a fannoni daban-daban. Mun yi imani cewa tare da Muhammad, za su kafa gida nagari mai cike da soyayya, fahimta, da kuma goyon bayan juna. "Muna fatan Allah ya sa wannan haɗin ya zama alheri ga dukkanmu, ya kuma ba mu ikon cika dukkan hakkokin da ke kanmu wajen wannan aure. Muna kuma fatan za mu ci gaba da ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin iyalanmu, domin amfaninmu da kuma al'ummar da muke ciki. "Aameen" suka amsa baki daya... Bayan Alhaji Uzairu ya kammala bayani, Gwaggo Zainabu ta gyara zamanta cikin nutsuwa, ta kalli iyayen Nabeeha da murmushi, sannan ta fara magana, "Assalamu alaikum.... Masha Allah, Ya gama fadan kusan daya daga cikin abunda ya kawo mu...Na zo tare da su ne domin nuna goyon baya ga wannan kyakkyawar manufa. Ina fatan wannan ziyara za ta taimaka wajen ƙara sanin juna, ƙarfafa zumunci, da gina kyakkyawar alaƙa tsakanin iyalanmu. Har ila yau, ina son in ga yarinyar da jikata, Muhammad, yake so ya aura. Wato kishiyata Nabeeha, don in fara Shirin damarar zama da wadda zaa kawo" Suka Saka dariya baki daya... na Jin gwaggo zainabu tana wasan kaka da jika.. Gwaggo zainabu ta dan murmusa sannan ta cigaba da cewa, "Ina fatan Allah ya sa wannan haɗin ya zama sanadin samun zaman lafiya, farin ciki, da ci gaba ga iyalanmu baki ɗaya.muna fatan za mu yi aiki tare wajen shirye-shiryen wannan aure, idan har an amince mana, tare da yin duk mai yiwuwa domin ganin an gudanar da komai cikin nasara da yardar Allah. Allah ya sa a yi aure lafiya, ya ba su zuri'a dayyiba, ya kuma sa zaman aurensu ya kasance cike da farin ciki da albarka. "Da fatan za mu ci gaba da haɗin kai da fahimtar juna a duk matakan da za a bi domin cimma wannan manufa ta alheri. Muna godiya da lokacinku da kuma karɓar mu da kuka yi da hannu biyu. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu." "Wa'alaykumm Salam Wa rahamatullahi Wa barakatuh. Sannu ku da kokari Gwaggo. Muna godia kwarai da gaske. Hadi da kambamawa da wannan dattako irin naku. Harda wahala. Ga kayanan fal? Mungode Allah ya Saka da alkhairi " major general ya fada yana nuni da kayayyakin da suka kawo.. "Sai yanzu na lura da su... Aa harda kokari haka? Toh Allah ya Saka da alkhairi ya bar zumunci har gaban abadan. Sai dai ban sheda ka sosai ba" gwaggo Hafsatu ta karasa magana tana duban Alhaji Uzairu. Alhaji Uzairu ya dubi Gwaggo Hafsatu da murmushi a kwance a fuskar sa yace, "Laa Gwaggo kin manta uzairu? Ni ne ke zama da gwaggo a asibiti da safe zuwa da yamma kafin a kawo abinci." "Oh haka haka. Allah sarki ai dake shekarun da yawa. Jikin tsufa. Toh Allah yayi muku albarka" "Aameen gwaggo Aameen" "Alhaji Uzairu ne. Kani ga Alhaji Amiru " major general ya dubi gwaggo Hafsatu yana gaya mata.. gabansa na bugawa.. Gwaggo Hafsatu mahaifiyar sa ta lura ta dube shi cikin idanu tana murmushin da zai kwantar masa da hankali. Gwaggo zainabu ta dan numfasa tana kurbar ruwan gorar da ke hannunta tache, Bayan Gwaggo Zainabu ta kammala jawabin ta na farko, ta ɗan yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta numfasa cikin nutsuwa, ta kalli Major General Dawud da iyalansa, ta ci gaba da magana cikin tausayawa, "Abin da ya sa na zo tare da su a yau, ba wai kawai don neman auren Nabeeha ga Muhammad ba ne, har ila yau akwai wata muhimmiyar magana da take damuna sosai. Na san cewa kai, Major General Dawud, kana iyaka ƙoƙarinka wajen ganin an samu nasara a dukkan al'amuran tsaro da suka shafi ƙasarmu. Amma ina roƙonka da Allah, a sake tsananta bincike domin gano halin da Zaytunah da 'ya'yanta biyu suke ciki..shekaru matukar yawa bamu sake Saka su a idanun mu ba. Ko suna raye ko kuma sun rasu. "Zaytunah tana da matuƙar muhimmanci a gare mu. Matar da na ce uzairu gashi nan., kuma tun lokacin da muka rasa labarinta tare da 'ya'yanta biyu, Zainab da Muhammad . Wanda suna daya suka ci da wannan manemun Nabeeha. zuciyata tana cikin tsananin damuwa da rashin tabbas. Mun yi ƙoƙari da dama wajen gano inda suke, amma har yanzu ba mu sami wani sahihin labari ba. Na san cewa kana da damar da za ta iya taimaka mana wajen gano gaskiyar al'amarin. Don Allah, ka taimaka mana a wannan lamari, ka yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gano ko suna raye ko kuma sun rasu, domin mu samu nutsuwar zuciya. "Rashin sanin halin da suke ciki ya kasance wani babban ƙunci a zuciyarmu. Idan har suna raye, muna fatan Allah ya sa mu sake haɗuwa da su cikin koshin lafiya. Idan kuma akasin haka ne, to muna so mu san gaskiya domin mu yi musu addu'a yadda ya kamata, kuma mu ci gaba da rayuwarmu tare da karɓar ƙaddara. Amma wannan rashin tabbas yana ci gaba da damunmu, kuma muna fatan za ka taimaka mana wajen kawo ƙarshen wannan yanayi. "Na san cewa kana da nauyi mai yawa a kan ka, kuma kana aiki tukuru wajen tabbatar da tsaron ƙasa da walwalar jama'a. Amma ina roƙonka da ka ɗauki wannan lamari a matsayin wani abu na musamman, ka ba shi muhimmanci, domin taimaka mana mu samu kwanciyar hankali. Ina fatan Allah ya taimaka maka a aikinka, ya ba ka nasara a dukkan al'amuranka, ya kuma saka maka da alheri bisa taimakon da za ka yi mana. "Muna godiya sosai da lokacinka da kuma kulawarka. Allah ya saka da alheri, ya kuma sa mu ji labari mai daɗi nan ba da jimawa ba." Bayan ta kammala wannan jawabi, Gwaggo Zainabu ta share hawaye daga idonta, tana fatan cewa wannan roƙo nata zai samu karɓuwa, kuma za a ɗauki matakan da suka dace wajen gano halin da Zaytunah da 'ya'yanta suke ciki. Duk jikin su sai yayi sanyi gaba ki dayan su. Musanman yadda kalaman gwaggo suke futa daga bakinta da tausayawa matuka... _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:7_ Bayan Gwaggo Zainabu ta kammala bayani kan bukatar a tsananta bincike don gano halin da Zaytunah da 'ya'yanta biyu suke ciki, Major General Dawud ya gyara zamansa cikin tawali'u, ya dubi Gwaggo Zainabu da kulawa, sannan ya fara magana cikin nutsuwa, "Gaskiya, Gwaggo Zainabu, na yi matukar jin dadin zuwanku da kuma wannan muhimmiyar bukata da kuka gabatar. Ina mai tabbatar muku cewa muna daukar wannan al'amari da matukar muhimmanci, kuma za mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an gano halin da Zaytunah da 'ya'yanta suke ciki. Za mu kara kaimi wajen bincike, tare da amfani da dukkan hanyoyin da suka dace domin samun bayanai masu inganci kan wannan batu...." Ya numfasa ainun yana jujjuya yadda zai furta zancen. Don a zahirin gaskiya a halin da suke ciki shi kansa ba shida masaniyar inda su hajia zaytunahh suke a yanzu kenan. A baya suna gidansa ne tabbas. Amma yanzu an sace su bai san inda suke ba. Yanadai iya kokarin wajen gano inda suke don haka ya dubi gwaggo Hafsatu cikin kwarin gwiwa hadi da mayarda dubansa ga Gwaggo zainabu ya cigaba da cewa, "Wallahi a yanzu haka ma... Babban da na Fawaaz suna can shida matemaka suna iyakar kokarin binciken inda su zaytunah suke. Wallahi tallahi billahi gwaggo bamusan inda su Zaytunah suke ba. Ko suna a raye? Ko akasin haka..Amman inshaa Allahu. Da yardar Allah zamu tsaurara tsananta bincike don gano halin da suke ciki..." Yakarasa yana duban gwaggo Hafsatu. Da tayi murmushi sosai tana dubansa. Don duk a maganganun da yayi babu na karya. Da gaske basusan inda su zaytunah suke ba.. Kuma fawaaz yana bakin kokarinsa shida matemaka suna kokarin gano inda suke... Duk kuwa da su su Gwaggo zainabu suna magana ne akan tun Zaytunah tana goyan baby Muhammad Wanda yake Hammad a yanzu. Yayinda take rike da Zainab wadda itama karama ce alokacin. A yanzu kuma take Nabeeha. Shekarun baya kenan... Yayinda su Kuma su major general suna amsa su ne abisa abunda yake faruwa a yanzu. A wannan shekarar da suke ciki.. Major general ya cigaba da cewa, "Game da batun Nabeeha kuwa, ina mai baku hakuri cewa ba ta nan a halin yanzu. Sun tafi wani shirin makaranta na yawon koyo (excursion) tare da sauran dalibai, kuma suna cikin wani yankin da babu isasshen layin sadarwa. Amma da zarar sun dawo, insha Allah, za mu tabbatar kun hadu da ita domin ku gaisa a zahiri. Idan kuma kuna so, za mu iya shirya wata hira ta wayar tarho ko ta bidiyo da zarar ta samu damar yin hakan, kafin ta dawo gida. "Ina kara baku hakuri kan wannan jinkiri, kuma muna fatan Allah ya sa a yi komai cikin sauki da alheri. Muna godiya da fahimtar ku da kuma goyon bayan da kuke nunawa a wannan lokaci mai muhimmanci." Bayan ya kammala wannan jawabi, Major General Dawud ya dauki wayarsa don kiran Nabeeha, Duk kuwa da yasan halin da ake ciki. Wato faduwa tazo dai dai da zama. Nan da nan ya shiga kiran number Nabeeha ya Saka a handsfre. 'The number you're calling is switched off... " Ya sake kira not available. "Bara na gwada ta sauran yan uwan ta da suka je... " Nanma ya shiga Kiran number Hammad da Hajia Zaytunah. Duka dai zancen daya ne.. "The number you're calling is not available to pick your call at the moment. Dayar number Kuma akace The number youre calling is not reachable at the moment please try again later" "Kunji ta sauran ma ko? Sun tafi excursion ne. Amma inshaa Allah da zarar sun dawo ko idan an same su a waya. Da yardar Allah" Ya kara jaddada alkawarin cewa za su tuntube ta da zarar ta samu damar yin hakan, domin ta gaisa da Gwaggo Zainabu da sauran iyalan da suka zo tare. Bayan Major General Dawud ya bayyana halin da ake ciki game da Nabeeha, Gwaggo Zainabu ta dube shi da murmushi mai cike da jin ƙai, ta ce, "Alhamdulillah, mun gode ƙwarai da wannan bayani. Mun fahimci cewa Nabeeha tana cikin wani shirin makaranta, kuma muna fatan Allah ya kiyaye ta tare da sauran ɗalibai, ya kuma dawo da su gida lafiya. Muna godiya da yadda kuka nuna kulawa wajen tabbatar da cewa za mu sami damar haɗuwa da ita da zarar ta dawo. Hakan ya nuna mana yadda kuke daraja wannan alaƙa da muke son kafawa.... Sannan mungode kwarai da yadda kuke cigaba da bibiya don tsawaita bincike akan zaytunah da iyalanta. Allah ya Saka da alkhairi yasa mu dache" Alhaji Uzairu, wanda ke zaune kusa da Gwaggo Zainabu, ya gyara zamansa sannan ya ƙara da cewa, "Hakika, muna matuƙar godiya da yadda kuka karɓe mu hannu biyu, da kuma yadda kuka saurari buƙatunmu da kulawa. Mun ji daɗin ganin yadda kuke da kyakkyawar zuciya da kuma yadda kuke ɗaukar wannan lamari da muhimmanci. Muna fatan Allah ya sa wannan zama ya zama farkon kyakkyawar alaƙa mai ɗorewa tsakanin iyalanmu." Gwaggo Zainabu ta sake duban Major General Dawud, ta ce, "Muna roƙon Allah ya ci gaba da ba ku nasara a aikinku, ya kuma ba ku ƙarfin guiwa wajen ci gaba da hidima ga al'umma. Muna fatan za mu ci gaba da wannan zumunci da muka Kara kullawa a yau, kuma Allah ya sa ya zama alheri ga kowa da kowa." Alhaji Amiru yana daga gefe yana nazartar komai. Musanman maganganun major general. Sai gaba daya ya rasa madafa ma. Tukukwin maganar data tsaya masa a wuya yana kallon major general da wata fuska ta daban sai yaji komai ya wuce. Ya sauke katuwar ajiyar zuciya.. Bayan Gwaggo Zainabu da Alhaji Uzairu sun nuna godiyarsu ga Major General Dawud, Alhaji Amiru, wanda shi ma ya kasance tare da su, ya gyara zamansa cikin tawali'u, ya dubi Major General Dawud da murmushi, sannan ya fara magana cikin ladabi, "Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Hakika, muna matuƙar godiya da yadda kuka karɓe mu hannu biyu, da kulawa da girmamawa. Mun ji daɗin yadda kuka saurari buƙatunmu da kuma yadda kuka nuna ƙwazo wajen taimaka mana, musamman kan batun Zaytunah da 'ya'yanta. Allah ya saka da alheri, ya kuma ƙara muku nasara a aikinku." Duk da wannan furuci na godiya, a zuciyar Alhaji Amiru akwai ɗan ƙaramin ƙwaƙwƙwafi kan saƙon da aka turo masa a baya. Ya cigaba da tunanin ko wannan saƙo makirci ne ko kuma sharri.. Bayan Alhaji Amiru ya nuna godiyarsa ga Major General Dawud, zuciyarsa ta shiga cikin yanayin tunani mai zurfi. A baya, ya karɓi wani saƙo ta hanyar text message da ya ƙunsa wasu bayanai masu tayar da hankali game da Zaytunah da 'ya'yanta biyu da usulin su . a Yanzu, bayan jin bayanan da Major General Dawud ya bayar, Alhaji Amiru ya fara tunanin ko wannan saƙo da ya karɓa makirci ne ko kuma sharrin wasu da ke son kawo ruɗani. Don tabbatar da gaskiyar lamarin, da muhimmancin yin hattara wajen yarda da duk wani saƙo da aka tura masa akan wannan yanayi, Alhaji Amiru sai ya yanke shawarar tambayar Major General Dawud kai tsaye don samun ƙarin bayani kan halin da ake ciki, tare da neman ƙarin haske kan saƙon da ya karɓa. Domin aganinsa hakan zai taimaka masa wajen fahimtar gaskiyar lamarin, da kuma kauce wa yarda da bayanan da ba su da tabbataccen tushe... Daga nan, suka ci gaba da tattaunawa cikin annashuwa, suna musayar labarai da dariya, tare da ƙara fahimtar juna da gina kyakkyawar alaƙa tsakanin iyalan biyu. Sai bayan da sukayi sallah suka fara Shirin haramar komawa garin su wato gidah. Gwaggo Hafsatu ta rokesu da su kwana mana..Amman dake sunada abubuwan yi sai suka dan kawo musu nasu uzurin da doriyar zasu dawo inshaa Allah.. Bayan sun firfita harabar gidan ne suna cigaba da magana. Major general shima ya hada tagomashin arziki ya basu. Muhammad dai duk jikinsa yayi sanyi baiji dadi ba. Don idanuwansa basuyi tozali da bugun zuciyar sa ba wato Nabeeha.. Murmushin yake kawai yake amman a zuciyar sa kuka na yake sharara da hawaye.. Bayan tattaunawar da suka yi a gaban kowa, Alhaji Amiru ya sake maimaiata muhimmin batu da yake buƙatar magana ta SIRRI da Major General Dawud. Cikin ladabi, ya nemi izinin yin magana da shi a gefe. Suna samun wuri mai nisa da sauran jama'a, Alhaji Amiru ya fara da cewa, "Yallabai, da farko ina so in nemi afuwarka kan wani abu da ya faru. Na karɓi wani saƙo ta text message da private number. Sakonnya ƙunshi wasu bayanai masu tayar da hankali game da Zaytunah da 'ya'yanta biyu. Kan kasan masaniyar inda suke . Sannan Nabeeha ba yar ka bace yar zaytunah ce. A lokacin, na yi zaton cewa dagaske kai ne ka aikata hakan, Ma'ana kanada masaniya akai. Kuma na yi maka zargin da bai dace ba. Amma bayan jin bayaninka a yau, na fahimci cewa wannan saƙo makirci ne da sharri daga wasu masu nufin ɓata. Don haka, ina roƙon ka da ka yafe mini bisa wannan kuskuren da na yi." Major General Dawud ya dubi Alhaji Amiru da murmushi, Gabansa na tsananta bugawa yana neman afuwar Allah ya ce, "Alhaji Amiru, babu komai. Kowa na iya yin kuskure, kuma ina godiya da ka zo ka bayyana min wannan. Na yafe maka daga zuciyata, Ina Kuma fatan ka yafemun kai ma. Dagaske Nabeeha 'yar 'yar uwata ce. A hannuna take tun tana karama..ni ne tamkar mahaifin ta. Tare suka tashi da yayan wajena. Kamar yadda bansan masaniya akan Muhammad ba dan wajen chief judge bane sai daga baya, Duk munyi kuskure. Ina fatan zaka yafemun kai ma, kuma mu ci gaba da haɗin kai wajen ganin an gano Zaytunah da 'ya'yanta." Alhaji Amiru ya numfasa da sauƙi, sannan ya ƙara da cewa, "Mashaa Allah! Wannan batu haka yake, Na gode ƙwarai, Yallabai. Haka zalika, muna matuƙar godiya da yadda ka amince da buƙatar ɗanmu Muhammad ya auri 'yarka Nabeeha.. Ai da na kowa ne. Don haka da Kai da kaya duk mallakar wuya ne. Yar yar uwarka yar ka ce. Mashaa Allah! Muhammd Kuma har Sako na turo nima akan hakan inaga baka gani ba matsalar network.. Muna fatan Allah ya sa wannan haɗin ya zama alheri ga iyalanmu baki ɗaya." Major General Dawud ya amsa da cewa, "Zahiri kam. Network. Ai komai ya wuce. Abdulfatah amini nane. Kowa wani ya kawo na daban yace ya bawa ya ta zan aminta bare dan wajen ka.. Allah yasa mu dache, Muna fatan Allah ya sa a yi komai cikin nasara da farin ciki." Daga nan, suka koma cikin taron tare, zuciyoyinsu cike da farin ciki da kuma kyakkyawar fahimta... Su gwaggo zainabu suka shisshiga mota.. motocin su suka fita daga gidan zukatan su cike da farin cikin wannan rana mai tarin dimbin alkhairi.. Hajia Hauwa ta ciji yatsa ... Bataso haakn ta faru ba. Taso sun tabbatar sa su Zaytunah suna gidan. Amman ta ya ya? Bayan anyi garkuwa da su. Ta numfasa tana adduar Allah ya watsa komai su zaytunah su tattara su tafi. Idan kuma rai yayi halinsa ma shikenan. Yayinda gwaggo Hafsatu ta major general suka sauke numfashi mai tattare da hamdalar yadda komai ya kasance a tsare. Suka koma godewa Allah da ba abunda ya taso na tashin hankali. Major general ya sanarwa mahaifiyar sa gwaggo Hafsatu yadda sukayi da Alhaji Amiru... "Toh Alhamdulillah... Allah abun godiya. Ubangiji Allah Kuma ya bayyana su zaytunah yasa suna cikin koshin lafiya. Komai yazo ya wuce. Dukkanin abunda akayi mata da yaranta Allah yasa ya karye. Suma su waiwayi yan uwa. Allah ya datar damu" "Aameen Gwaggo. Allah bakiji gabana yadda yake faduwa ba. Amman yadda komai ya wuce na yau da mike tunanin zai faru komai yazo da sauki. Sai na samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Ina Kuma fatan Allah ya bayyana su zaytunah da gaggawa yasa suna cikin aminci. Wannan munafiki ko munafaka da suke turawa Alhaji Amiru wannan Sako Kuma Allah ya bayyana mana su. Ya tarwatsa Shirin su duk me hannu aciki" "Aameen Yaa Rabbi dawuda, Allah yayi maka albarka, Allah yayi maka albarka , Allah ya maka albarka" "Aameen gwaggo na.. Ubangiji Allah ya Kara miki tsawon kwana da yalwar afuwa, lafiya mai inganci, ya yi riko da hannuwan ki. Yasa ki gama da duniya lafiya" "Aameen dawuda. Tare da Kai da sauran musulmai baki daya" Da wannan suka koma cikin gidah su na kambama mutunci da dattako na zuriyar gwaggo zainabu da gwaggo zainabun kan ta... _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:8_ Hajiya Rumanah ta jingina da kujerarta, zuciyarta na bugawa da sauri. Idanunta sun kada, cikinta kamar yana kuna da wutar da ba ta da iyaka. Tunani ne ya cika zuciyarta, yana tsunduma ta cikin rudani mai tsanani. Shin da gaske Muhammad yaron nan yana son auren Nabeeha? Kuma wai ita Nabeeha ‘yar waye a hakikanin gaskiya? Ta saki numfashi a hankali, sannan ta mika hannu ta dauki wayarta daga gefenta. Ta dade tana kallon fuskar wayar kamar wacce ke shirin daukar matakin da ba ta da tabbas a kansa. Sai kuma ta bude sabon sakon rubutu, ta danna lambar da take bukata. Hannunta yana kadawa yayin da take danna rubutun, “Muhammad dan wajen Amiru, wacece yarinyar da yake son aura dagaske? Nabeeha ce?” Ta yi shiru na dan lokaci, tana kallon sakon da ta rubuta. Sai ta kara danna wasu kalmomi, “Kuma ina so na tabbatar, wacece ita a hakikanin gaskiya? Ita ‘yar Major General Dawud ce?” Bayan ta gama, ta danna send. Wayarta ta koma hannunta, amma zuciyarta ta kasa samun kwanciyar hankali. Bata dade da aika sakon ba, sai ga amsa ta shigo. Ta yi saurin dannawa, zuciyarta na bugawa da sauri. "Nabeeha 'yar Hajiya Zaytunah ce, dake gidan Major General Dawud. Amma ba 'yar Major General Dawud bace." Hajiya Rumanah ta zaro ido, wani irin jiri ya kwasheta. Gabanta ya fadi, hannunta ya soma rawa, ta saki wayar tana duban su Hajiya Karama da Hajiya Ladi da ido waje. “Subhanallah! Kenan…” Ta kasa karasawa, sai ta dafe kanta, zuciyarta kamar zata faso kirjinta ta fito. Hajiya Karama ta matso kusa da ita, tana kokarin lallashinta. “Rumanah, ki kwantar da hankalinki. Me ya faru? Me suka ce?” Hajiya Ladi ta dan matsa kusa da ita itama, fuskarta dauke da damuwa. “Ki fada mana! Me ya sa kike cikin wannan tashin hankalin?” Hajiya Rumanah ta runtse idanu, ta dafe goshinta da hannu daya, sannan ta furta da kyar, “Nabeeha ba ‘yar Major General Dawud bace…” Hajiya Karama da Hajiya Ladi suka zaro ido a tare. "Me kike nufi?" Hajiya Rumanah ta bude idanu, tana kallon su da tsananin firgici. “’Yar Hajiya Zaytunah ce! Kuma tana gidan Major General Dawud ne… Amma ba ‘yar sa bace!” Shiru ya biyo baya. Zuciyoyinsu sun cika da mamaki da firgici. Hajiya Ladi ta yi saurin fadin: “Haba Rumanah! Wannan ba zai yiwu ba. Kin tabbata? Wannan bayanin ba kuskure bane?” Hajiya Rumanah ta kada kai, hawaye na taruwa a idonta. "Ban san me ke faruwa ba… Amma idan haka ne, to lamarin ya fi yadda muke tunani. Wannan matsala ce babba!" Hajiya Karama ta dafe kirjinta, tana kokarin kwantar da nutsuwarta. “Dole ne mu samo mafita da wuri. Kada mu bari wannan ya bata mana shiri.” Amma Hajiya Rumanah ta kasa samun nutsuwa. Duk yadda suka so su lallasheta, tunaninta ya tafi nesa. Idan har Nabeeha ba ‘yar Major General Dawud bace, Toh ta tabbata yar Hajiya Zaytunah ce kenan... Zuciyarta ta sake harbawa da karfi… Hajiya Rumanah ta kasa zama. Ta tashi tsaye, tana safa da marwa a cikin dakin, zuciyarta tana tafasa kamar ruwan dafawa. Idanunta sun kada, tana huci kamar wacce aka yi wa dukan tsiya. "Wannan ba zai yiwu ba! Nabeeha 'yar Zaytunah ce? Amma me hakan ke nufi? Me yasa take gidan Major General Dawud? Yaki ya fito da ita. Shine gaskiar lamarin ne ko kuwa?" Hajiya Ladi ta gyara zaman mayafinta, ta dubi Hajiya Karama da fuskar da ke bayyana damuwa. "Yanzu, Rumanah, yaya za a yi?" Ta tambaya da karyayyen murya. Hajiya Karama ta numfasa, ta saki wani murmushin dole. "Ba mu da wata mafita illa mu sake duba lamarin da kyau. Mu tabbatar da gaskiyar al’amarin kafin mu dauki wani mataki." Amma Hajiya Rumanah ta juyo da sauri, ta daga murya. "Karama! Da me za mu sake duba lamarin? Ai an riga an tabbatar! Idan har Nabeeha 'yar Zaytunah ce, to tabbas muna cikin matsala! Me ya sa ba wanda ya gaya mana? Me yasa har yanzu Muhammad yake bibiyarta?" Ta dafe goshinta da hannu daya, tana girgiza kai. "Haka kawai na ji ba dadi! Na ji kamar muna cin amanar kanmu! Don kuwa lamarin backfiring zeyi. Komai tsawon lokaci sai gaskia ta fito mun kwashi kashin mu a hannu" Hajiya Ladi ta yi gyaran murya, tana kokarin dan shawo kanta. "Rumanah, ki kwantar da hankalinki. Muna da damar da za mu iya gyara komai." "Yaya?" Hajiya Rumanah ta yi tsawa. "Za mu ci gaba da bincike. Sai mun tabbatar da komai kafin mu dauki mataki." Hajiya Karama ta jinjina kai. "Eh, dole ne wannan" Shiru ya ratsa dakin na wasu ‘yan dakiku. Sai dai zuciyar Hajiya Rumanah ta kasa samun natsuwa. Ta sake kallon wayarta, zuciyarta na bugawa da sauri. "Dole in sake aika sakon tambaya! Ina so in tabbatar da abu daya..." "To me yasa Muhammad ke son aurenta. Bashi ita akai ko ganinta yayi yana so?" Hajiya Rumanah ta danna sakon cikin sauri, zuciyarta na dokawa da karfi. Hannunta na rawa, ta zuba ido kan wayar tana jiran amsa. Hajiya Ladi ta lura da hakan, ta kalli Karama kafin ta dubi Rumanah da kulawa. "Rumanah, ki kwantar da hankalinki. Kina acting kamar kin san komai, alhali ba mu gama fahimtar lamarin ba." Hajiya Rumanah ta juyo, idonta cike da bacin rai. "Ladi, wannan ai ba wasa ba ne! Idan har Nabeeha 'yar Zaytunah ce, kuma take tare da Major General Dawud, muna cikin matsala!" Hajiya Karama ta yi ajiyar zuciya, ta gyara zaman hijabinta. "Kin ce haka, amma har yanzu ba ki tabbatar da komai ba. Idan har Muhammad ita din yake so Kuma an tabbatar , ya kamata mu gano me yasa." Hajiya Rumanah ta sake duban wayarta, tana huci. Kafin su samu damar ci gaba da tattaunawa, amsar sakon ya shigo. "Nabeeha ba 'yar Major General Dawud bace. 'Yar Hajiya Zaytunah ce, wadda ke zaune a gidan Major General Dawud." Wayar ta sulale daga hannun Hajiya Rumanah, zuciyarta ta buga da karfi. Kamar an tsikare ta, ta dafe kirjinta, zuciyarta na bugawa da mugun sauri. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!" Hajiya Ladi da Hajiya Karama suka matso da sauri, suka tsare ta da ido. "Me ya faru?" Karama ta tambaya da damuwa. Hajiya Rumanah ta nuna wayar da yatsa, idanunta sun ciko da matsanancin tashin hankali. "Kun ga? Nabeeha 'yar Zaytunah ce! Kuma suna gidan major general dagaske" Shiru ya ratsa tsakani na wasu dakiku, kowacce daga cikinsu tana kokarin fahimtar wannan ruɗanin da ya kunno kai. "Ko dai akwai wani abu da ba mu sani ba?" Hajiya Ladi ta furta a hankali, tana mai jin gabanta yana faɗuwa. Hajiya Karama ta share gumin da ya keto mata. "Rumanah, muna bukatar karin bayani! Me yasa take a gidan Major General Dawud? Kuma me yasa har yanzu ba mu san hakan ba. Shin su alhaji sunada masaniya ko kuwa?" Hajiya Rumanah ta jingina jikin kujera, zuciyarta tana ci gaba da tafasa. Wannan batu ya fi ƙarfin yadda take zato! Tana jin kamar zuciyarta zata tarwatse. Abin da ta fi tsoro yana kokarin zama gaskiya!.. 🎀🎀🎀🎀 A cikin wani tsohon gida da ke tsakiyar daji, an ajiye su Hajiya Zaytunah, Nabeeha, da Hammad a ɗaki mai duhu. Hannayensu da ƙafafunsu an ɗaure su da igiya mai ƙarfi, yayin da wasu daga cikin yan fashin suka tsaya a bakin ƙofa suna gadinsu. Nabeeha ta kalli mahaifiyarta da damuwa, hawaye na kokarin cika idanunta. “Ammi, su wanene waɗannan mutanen? Me su ke so da mu?” Hajia Zaytunah ta sauke ajiyar zuciya, tana kallon ɗiyarta da ƙoƙarin kwantar mata da hankali. "Ban sani ba, amma abin da na sani shi ne dole mu ci gaba da yin addu’a.” Hammad ya runtse idanu, zuciyarsa na tafasa da takaici. Bai iya jure ganin mahaifiyarsa da yayar sa cikin wannan hali ba. Ya ce da ƙasa da murya, "Su wane ne suka aikosu? Wane irin mugunta ce wannan?” A dai-dai lokacin, kofar ɗakin ta bude da karfi, daya daga cikin yan fashin ya shigo. Fuskar sa a tamke, idonsa na cike da ƙeta. Ya kalli su hajia zaytunah da wani irin murmushin mugunta. “Kuna bukatar ruwa ko abinci?” Ya tambaya da wata murya mai cike da zolaya. Hajiya Zaytunah ta ɗago idonta, tana kallon sa da tsananin tsoro amma ba tare da ta nuna rauni ba. Ta ce da ƙarfi, “Me kuka ke so da mu? Ku gaya mana, me muka muku?” Dan fashin ya bushe da dariya. "Ba ke ce matsalar ba. Amma fa idan ba a bi umarnin mu ba, sai mun koya muku darasi.” Sai ya juya ya fice, ya bar su cikin damuwa da rashin tabbas. Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah da Hammad, zuciyarta na bugawa da karfi. “Ya Allah, ka kawo mana agaji.” Ta furta cikin sanyin murya... _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ * *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 9_ Hajiya Zaytunah ta runtse idanuwanta da ƙarfi, zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi. Kamar yadda ta taɓa jin irin wannan firgici a baya, haka take ji yanzu, amma wannan ya fi komai muni. Ta dubi gefenta, tana kallon Nabeeha da Hammad da ke a daure kamar yadda ita ma take. Sun yi shiru ba tare da sun furta uffan ba, amma idanuwansu sun bayyana tsananin tsoro da damuwa. Ta juya idanunta cikin ƙwaryar ɗakin da ake tsare da su. An ajiyesu ne a wani wuri da ya yi kama da tsohon daki, katako ne ke rufe jikin bangon, kuma kowane lungu cike yake da ƙura. Abin da ya fi damunta shine sanin cewa har yanzu ba su san waye ke da alhakin wannan Kamen nasu ba, kuma ba su san me suka yi da har hakan ta faru da su ba. Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, zuciyarta cike da addu’a. Shin wannan tashin hankalin zai ƙare lafiya kuwa? A daidai wani dare mai tsananin duhu, cikin wani lungu da baƙin duhu a wani yanki na barikin da suka fake, wani guntun mutumi dake cikin yan fashin ya taho da waya a hannunsa, daya hannun nasa rike da torchlight. Ya mikawa daya daga cikin 'yan fashin da suka kama Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha. Takardar da aka rubuta da dogayen kalmomi masu nauyi, wato in bold letters ta turo text message din Suna ɗauke da umarni daga wacce ta fi kowa kula da lamarin - Hajiya Rumanah. Kuna cikin bakin aiki, kuma babu wani kuskure da zan lamunta daga gareku. Haka nan, babu wasa a cikin wannan danyen aiki da aka damka muku. Zan yi muku magana ta gaskiya, kuma dole ne ku aikata abin da nake so cikin gaggawa. Ga umarni na a gareku, Na farko, Za ku yanke gashin wannan annamimiyar (Hajiya Zaytunah) ku aiko mini da shi. Gashin kanta dole ne ya iso hannuna. Babu buƙatar yawan tambayoyi ko ɓata lokaci. Idan har ta ƙi yarda, ku tabbatar kun yanke shi da karfi da yaji. Idan ta yi ihu, to ku ƙara mata azaba! Na biyu, Kada ku sake a bar wannan ƴar wulakancin (Nabeeha) ta kubuta cikin salama. Idan har za ta rayu bayan wannan dare, to dole ne a ɗauke mata mutuncinta! Ku tabbatar an shanye duk wani alamar mutunci daga jikinta kafin ku bar ta ta numfasa. Idan ta mutu cikin tsananin azaba, to hakan ma zai zama alheri. Babu wani kuskure da zan yarda da shi! Idan kun yi sakaci, ku sani cewa rayuwarku ce za ta biyo baya. Ku sanar da ni idan kun kammala. Mutumin ya gama karanta sakon, zuciyarsa ta cika da kasala. Duk da ya saba da aikata muggan laifuka, ya san cewa wannan umarni ya wuce gona da iri. Kallon wasu daga cikin abokan aikinsa ya yi, kowanne yana jiran a ce komai. Daga ƙarshe ya kalli wanda ya kawo sakon ya ce: "Wannan matar ba zata taɓa yin imani da ƙwaƙwalwarmu ba. Ita ba ta kula da komai sai mugun nufinta!" Daga gefe, wani daga cikin 'yan fashin da ke jin maganar ya murmusa, yana kaɗa kai, "Dama mun san cewa akwai wani abu da ke ƙasa da wannan lamarin. Ba so kawai ake su mutu ba, ana son a bar musu tarihi da abin da zai ruguza su tsawon rayuwarsu." Duk da haka, babu wanda ya ce uffan na tsawon lokaci. Shirun ya yi yawa, sai ƙarar wata tsuntsuwa da ta ketara ta wuce cikin duhun dare. Daga bisani, babban shugaban 'yan fashin ya gyara zamansa, ya saki numfashi mai nauyi sannan ya ce, "Za mu bi umarninta. Amma idan wata matsala ta taso, sai mu yi tunani kafin mu dauki mataki." Suka yi shiru na wani lokaci, kafin wani daga cikinsu ya tashi tsaye ya ɗauki wani almakashi, yana kallon shi da kyau kamar yana nazari. A cikin duhun dare, aka fara tsarawa domin aiwatar da mugun aikin da Hajiya Rumanah ta bayar... A cikin dakin da aka kulle Hajiya Zaytunah da Nabeeha, ana iya jin numfashinsu yana fita cikin sauri da tsoro. Wutar fitila guda daya ce ke haskaka dakin, tana bayyanar da inuwa a bangon da ke nuna yanayin tsoron da ke tattare da su. Hajiya Zaytunah tana zaune a gefe, hannayenta daure da igiya, idanunta sun kada saboda tsananin damuwa. Nabeeha kuma tana a gefenta, jikinta yana rawa, zuciyarta cike da tsoron abin da zai biyo baya. A waje kuwa, daya daga cikin 'yan fashin ya dubi shugabansu, yana girgiza kai cikin shakku. "Mun san aikinmu ne, amma wannan ai ya yi yawa." Shugaban ya kalle shi da idanun da suka cika da rashin jin tausayin komai. "Hajiya Rumanah ba za ta ji daɗin jin cewa ba mu aikata abin da ta umurce mu ba. Kuma ba na son jin bayanin kowa. Za mu aiwatar da umarnin nan da aka bayar!" Ya juya yana duban wani daga cikinsu, wanda aka fi sani da Gora, ya ce da shi, "Kai ne za ka shiga ka yanke mata gashi." Gora ya haɗiye yawu, yana jin wani irin sanyi yana ratsa zuciyarsa. Duk da kasancewarsa da ƙwarewa a aikata laifi, wannan lamarin ya ɗauke shi a matsayin wani mummunan aiki da zai bar tarihi mai muni. Ya ɗauki almakashin da aka ba shi, sannan ya sa hannu ya tura ƙofar dakin. Kamar yadda ya zata, idanun Hajiya Zaytunah sun zazzaro da ganinsa, tana kallon almakashin hannunsa. "Mene ne kake shirin yi?" Ta tambaya da muryar da ke rawa. Gora bai ce komai ba. Ya matsa kusa, zuciyarsa na dukan uku-uku. Ya tsugunna a gabanta, yana kallon gashinta da ke nade cikin mayafi. Ya san cewa wannan ba abu ne mai sauki ba, amma ya san cewa idan bai aikata ba, rayuwarsa tana cikin hatsari. Hajiya Zaytunah ta fahimci manufarsa nan take. Ta motsa a inda take daure, tana kokarin janye kanta. "Kada ka kuskura!" Ta ce, idanunta sun cicciko da hawaye. Gora ya runtse ido yana shirin saka almakashin a cikin gashinta, amma zuciyarsa ta gaza. Sai ya sauke almakashin a kasa, yana jan numfashi mai nauyi. A waje, sauran 'yan fashin suna jiran jin motsin da zai tabbatar da an yi aikin. Shugaban ya daka tsawa: "Meye ya tsaida ka?" Gora ya goge zufar da ta bayyana a goshinsa, sannan ya dubi shugabansu da fuskar da ke nuna rashin yarda da lamarin. "Ba zan iya ba," Ya ce cikin sauti mai ƙasa. Shugaban ya fusata, yana matsowa kusa da shi. "Kana nufin kana ƙin yin abin da aka umurce mu?" "Ba haka bane," Gora ya amsa, yana kokarin kare kansa. "Amma wannan abu ya wuce gona da iri. Wannan matar ta riga ta wuce wahala. Me yasa ba za mu yanke kanta gaba daya mu huta ba?" Shugaban ya kara harzuka, sai ya finciki almakashin daga hannun Gora. "Ka matsa gefe!" Ya ce da tsawa. Ya shiga dakin cikin sauri, ya kama gashin Hajiya Zaytunah da karfi, yana kokarin yankewa. A take, Nabeeha ta tashi tsaye, tana kiran cikin kuka, "Don Allah, kada ku yi haka, Dan Allah !" Shugaban bai saurare ta ba, sai kawai ya ci gaba da yankewa. Gashin da ya faɗi daga kanta ya shiga cikin wani farin leda da aka tanada, sannan ya kalli wasu daga cikin 'yan fashin. "Ku shirya, za a aika da sakon nan zuwa wajen su." Da wannan umarni, wani daga cikin 'yan fashin ya ɗauki ledar, ya fice daga dakin, yana shirin aika da sakon. A waje kuwa, wata matsala mai girma ta taso saboda wasu daga cikin 'yan fashin sun fara nuna shakku akan abu na biyu da aka umurce su da su aikata… _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 10_ A cikin dakin da aka kulle su, Hajiya Zaytunah ta kasa motsi yayin da idanunta ke zub da hawaye. Numfashinta ya tsananta, zuciyarta tana harbawa da sauri. Duk da azabar da aka yi mata da yankar gashinta, wani abu mafi muni ya fi tada hankalinta, wato abin da zai biyo baya... Nabeeha ta kankame jikinta, tana jin gabanta yana faduwa da wani irin tsoro da ba ta taba jin irinsa ba. A zuciyarta, tana rokon Allah ya kawo mata mafita. Idanunta sun cika da hawaye, amma ta kasa kukan da zai sa su nuna rauni. A waje kuwa, shugabansu ya sake duban sauran ‘yan fashin, yana furta abin da ya fi rudani. “Ku tabbata an aiwatar da abu na biyu da Hajiya Rumanah ta bukata.” Da jin haka, gaba daya ‘yan fashin suka yi shiru. Wasu sun zuba masa ido, wasu kuma suka dauke kai. Ko da sun saba da aikata miyagun ayyuka, hakan ba zai sa su yi wannan aikin da ya zama wulakanci ba. Wani daga cikinsu, mai suna Bala, ya kalli shugaban da ido kamar yana tunani. “mu dan dakata mu dauki lokaci kafin mu aiwatar da wannan,” Bala ya ce, yana kokarin kaucewa matsalar. Shugaban ya dube shi da harara. “Wane lokaci kake nufi? Ko dai mu aiwatar da shi ko kuma mu kashe ta gaba daya.” Gora, wanda ya riga ya nuna rashin yarda tun da farko, ya sake matsowa. “Wannan ba abu ne da zan iya aikatawa ba,” ya furta da karfi. Shugaban ya kalle shi da fuska mai nuna rashin hakuri. “Kai ne zaka zaba, ko dai ka aikata, ko kuma kai ma ka fuskanci hukuncin Hajiya Rumanah.” Gora ya kara hararar shugaban, zuciyarsa cike da bacin rai. Ya jima yana rayuwa da laifi, amma bai taba zuwa inda aka ce ya wulakanta mace ba. Bai taba yi ba, kuma ba zai fara da wannan ba. Ya sauke numfashi, sannan ya ce, “Idan wannan shine abin da kuka shirya, to ni ba zan kasance da ku ba.” Shugaban ya yi dariyar takaici, yana girgiza kai. “Dama nasan kana da wata zuciya mai laushi. Ba ka dace da wannan aiki ba.” Daga cikin sauran ‘yan fashin, wasu suka fara hada ido da juna, kamar suna tunanin cewa Gora yana da gaskiya. A wannan lokaci, an samu rarrabuwar kawuna. A gefe guda kuma, Bala ya kalli dakin da aka kulle su Hajiya Zaytunah da Nabeeha. Yana jin zuciyarsa tana bugawa da wani irin yanayi da bai taba ji ba. “Idan muka aikata hakan, me zai rage mana?” Bala ya fada a hankali. “Mu ‘yan fashi ne, amma ba azzalumai ba.” Shugaban ya yi fuska, yana kallon Bala da Gora da mamaki. Bai zata cewa matsalar zata yi girma haka ba. “Ina jin dai kun manta cewa mun karbi kudi a wannan aiki,” ya fada cikin bacin rai. “Kuma duk wanda ya ki aikatawa, to shi da kansa zai fuskanci hukunci.” A wannan lokaci, Bala ya dauki mataki na rashin zato ya zaro bindigarsa! Gaba daya ‘yan fashin suka ja da baya, sai wasu suka zaro makamai suma. Rikici ya fara tasowa, kamar tafasasshen ruwa. Bala ya kalli shugabansu ido cikin ido, sannan ya ce da kakkausar murya:l, “Ba zan bari ka wulakanta su ba. Idan haka ne, to sai dai ka kashe ni.” Hakan ya tada hankalin sauran ‘yan fashin. Gora ma ya janye daga gefe, yana goyon bayan Bala. Sauran suka fara yin tunani. Shugaban ya gane cewa idan har zai cigaba da tilasta su, to zai iya rasa hannun wasu daga cikin nasa. Ya hura hanci, sannan ya girgiza kai. “To, tunda haka ne, sai dai mu mayar da ita ga Hajiya Rumanah ta yi da ita yadda take so.” Ya juya yana fita daga wajen, yana huci da takaici. Sauran ‘yan fashin suka bi shi, amma akwai wadanda suka yanke shawarar cewa wannan shine lokacin da za su daina wannan aiki. Bala ya dubi Gora, sannan ya ce cikin sassanyar murya: “Mun ceci rayuwar su, amma ba mu san makomarsu ba.” Bayan shugabansu ya bar wajen da fuskar rashin jin daɗi, Bala da Gora suka kalli juna, kowanne yana nazarin abinda ke zuciyar ɗan uwansa. Sun san cewa sun yi kuskuren yin adawa da shugabansu, kuma hakan na iya jawo musu matsala. Amma sun yanke hukunci rayuwar Hajiya Zaytunah da Nabeeha ta fi komai muhimmanci. Daga can gefe, wasu daga cikin ‘yan fashin suka ja baya, ba sa so su tsoma kansu cikin lamarin. Wasu kuwa sun riga sun yanke shawarar cewa wannan aiki ba zai ci gaba ba. Bala ya lumshe ido, yana jin zuciyarsa tana dukan uku-uku. Ya san cewa idan aka mayar da Hajiya Zaytunah da Nabeeha ga Hajiya Rumanah, to babu shakka za su fuskanci matsananciyar azaba. Dole ne su yi wani abu da wuri. “Gora,” ya ce da ƙasa da murya. “Dole mu ceci su kafin a kai su wajen Hajiya Rumanah.” Gora ya gyada kai, yana jin wani irin karfin gwiwa na ratsawa cikin zuciyarsa. “Amma yaya za mu yi hakan?” Gora ya tambaya. “Shugabanmu yana da ido a ko’ina. Idan muka yi kuskure, mu da kanmu za mu rasa rayukanmu.” Bala ya dube shi, yana murmushi mai cike da rashin tsoro. “Idan muka tsaya muna tunani sosai, lokaci zai kure mana. Mu aiwatar da shirinmu kafin su kai su wajen waccan muguwar mata.” Bala ya sake duba dakin da aka daure Hajiya Zaytunah dasubNabeeha. Idanunta sun cika da hawaye, sai dai yanzu ta fahimci cewa akwai wani abu da ke faruwa tsakanin ‘yan fashin. A ganinta, kamar dai ba dukkansu ne suka amince da azabar da aka bukaci a yi mata da ‘yayanta ba. Bala ya juya ya dube Gora. “Zan nemo wata mota, sai mu fita da su cikin dare.” Gora ya sauke numfashi. “Kana nufin mu fitar da su ba tare da wani ya gane ba?” Bala ya gyada kai. “Haka nake nufi. Idan muka yi hakan cikin sauri, kafin shugabanmu ya dawo daga shirin aikawa da Hajiya Rumanah sakon cewa an kama su, to za mu iya fitar da su lafiya.” Gora ya sake duban sauran ‘yan fashin da ke gefe. “Me kuke tunani?” Daya daga cikin su ya numfasa. “Ni dai na san cewa idan suka koma wajen waccan mata, za su fi shan wahala fiye da yadda aka yi musu a nan.” Wani daga cikinsu ya ce: “Ina tare da ku. Idan dai zamu cece su, dole ne mu yi hakan yanzu.” Da dare sosai, Bala da Gora suka shiga cikin dakin. A hankali, suka warware igiyoyin da ke daure Hajiya Zaytunah da Nabeeha da Hammad. “Ku yi shiru,” Bala ya ce da su, yana duban kofa don tabbatar da cewa babu wanda ya lura da su. “Za mu fitar da ku daga nan, amma dole ne ku bi umarninmu.” Hajiya Zaytunah ta kasa magana, zuciyarta cike da tsoro da fargaba. Ita dai ba ta fahimci dalilin da yasa wasu daga cikin ‘yan fashin suka canja ra’ayi ba, amma duk da haka, ta san cewa wannan shi ne damar da zasu iya samu don su tsira. Nabeeha ta kalli Bala da Gora, tana jin wani irin fargaba. Amma lokacin da ta kalli idon Gora, ta ga baƙon abu a ciki, ba irin mugunta ba ne da ta saba gani daga sauran ‘yan fashin, sai dai Bala ya riko mayafin hannun Nabeeha , Hammad da Hajiya Zaytunah yana matsawa cikin duhun dare. A hankali suke tafiya a gefen shinge mai katanga da ke kewaye da sansanin ‘yan fashin. Gora kuma ya tsaya yana saurarawa, yana jiran lokacin da zai tayar da hankali don jawo hankalin sauran ‘yan fashin zuwa wani wuri daban. Hajiya Zaytunah tana jin jikinta yana rawa, ba don sanyi ba, sai don tsananin fargaba. Idan har suka yi kuskure, to ba shakka za a kama su kuma wannan wata babbar matsala ce da ba za ta iya fatan tsira daga gare ta ba. Nabeeha kuwa ta kasa gane yanda ake tafiyar da lamarin, zuciyarta cike da addu’a da fatan samun mafita. Duk tsawon rayuwarta ba ta taba jin tsoro irin wanda take ji a wannan lokaci ba. “Ku ci gaba da tafiya a hankali,” Bala ya rada musu a kunne. “Muna kusa da inda na ajiye wata mota da za ta fitar da mu daga nan.” A cikin wannan lokaci, Gora ya matsa zuwa wani wuri da yake kusa da wani babban gangare. Ya dauki wata babbar duwatsu, ya jefar da ita a wani bangare na sansanin da ke kusa da inda wasu daga cikin ‘yan fashin suke gadin shinge. A take, hayaniya ta tashi! “Wane ne a can?” Wani daga cikin masu gadi ya daka tsawa, yana juyawa da bindiga a hannunsa. “Wata kila wani abu ya fado,” wani ya ce. “Sai dai mu duba don tabbatarwa,” wani daga cikinsu ya kara da cewa. Suna tafiya don duba wajen, hakan ya samar da dama ga Bala da su Hajiya Zaytunah su ci gaba da tafiyarsu ba tare da an gano su ba. Bala ya kai su zuwa wata tsohuwar mota da ke kusa da wata hanya da ke gefen daji. Ya bude kofar motar cikin hanzari, yana duban Hajiya Zaytunah da Nabeeha. “ku shiga cikin mota,” ya umarce su. Ba tare da bata lokaci ba, suka shige motar, zuciyarsu na bugawa da sauri. Bala ya kunna motar, sai dai a lokacin da ya fara juyawa don fita daga wurin, wani mummunan abu ya faru. Daya daga cikin ‘yan fashin ya lura da motsin motar, sai ya daka wata tsawa da karfi. “Waye ke cikin waccan mota?!” A take, karar harbi ta biyo baya! “Sun gano mu!” Nabeeha ta furta cikin tsananin firgici. Bala ya cije lebe, yana danna motar da karfi don ya fice daga wurin. Motar ta yi kara, sai ya ja birki da karfi, yana kokarin kaucewa harsashin da ke shigowa. Wani daga cikin ‘yan fashin ya ruga zuwa inda suke, yana kokarin harbawa, amma kafin ya samu damar yin hakan, Gora ya bayyana daga gefe, yana rike da bindiga! “Ka ajiye makamin nan ko kuma na harbe ka!” Gora ya daka masa tsawa. Mutumin ya tsaya cak, yana kallon Gora da mamaki. Bai taba tunanin cewa daya daga cikin ‘yan uwansa zai yi masa haka ba. Kafin ya samu damar yin wani abu, Gora ya kwada masa kwallo da hannu, ya fadi a kasa sumamme! Bala ya kalli Gora, yana jin zuciyarsa tana bugawa da sauri. “Shiga mota!” Bala ya ce da Gora. Ba tare da bata lokaci ba, Gora ya bude kofar motar, ya shiga cikin hanzari. Bala ya danne motar da karfi, suka fice daga sansanin da gudu. ‘Yan fashin da suka lura da abin da ke faruwa sun ruga da gudu suna kokarin bin su da harsasai, amma Bala ya ci gaba da tafiya da sauri, yana kaucewa harsashin da ake harbawa. Bayan tafiya da gudu har na tsawon mintuna, Bala ya shiga wata hanya da ke cikin daji, ya rinka bi da hankali don kada su bar wata alama da za a iya binsu da ita. Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah, tana jin hawayen da suka cika mata idanu. “Mun tsira, Ammi?” Ta tambaya cikin rawar murya. Hajiya Zaytunah ta rungume ta da karfi, tana jin wani irin sanyi a zuciyarta. Daya hannunta Kuma takamo na hammad tana damtsewa Bala da Gora kuwa suna jin nauyin da ke kan zuciyarsu yana raguwa. Sun san cewa ba su gama ba tukuna, amma sun san abu daya sun ceci rayuka, kuma hakan shi ne babban nasara. Daga nesa, fitilun wasu motoci suka bayyana a bayan su, alamar cewa akwai wadanda suke kokarin bin sawu. Sai suka ci gaba da tafiya cikin duhun dare, rayukansu suna hannun lokaci… _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 11_ A dai-dai lokacin da Bala da Gora suka tsere da Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha, wani sakon gaggawa ya isa wajen Hajiya Rumanah. Wani daga cikin mutanenta ya durƙusa gabanta yana sauke numfashi, alamar gajiya da hanzarin isowa. “Hajiya, akwai matsala!” Hajiya Rumanah ta ɗago daga inda take zaune a cikin wani falo mai ɗauke da kayan alfarma. Idanunta suka kaɗa, alamar ba ta da niyyar karɓar wata matsala a wannan lokacin. “Wace irin matsala?!” Ta tambaya, muryarta cike da ƙwarin gwiwa. Mutumin ya haɗiye yawu. “‘Yan fashin da aka ba aikin sun yi kuskure. Wataƙila wasu daga cikinsu sun canza ra’ayi, suka fitar da matar da yaranta daga hannunsu.” Hajiya Rumanah ta tsinci kanta tana matse mayafinta da ƙarfi, zuciyarta na bugawa da sauri. “Ba abu ne mai yiyuwa ba! Me kake nufi?!” Mutumin ya sunkuyar da kansa. “Har yanzu ba mu da cikakken bayani, amma an ga wata mota da ta tsere daga sansanin. Shugaban ‘yan fashin yana kokarin bin sawu.” Hajiya Rumanah ta tashi daga kujerarta cikin zafin rai. "Ina bukatar su dawo hannuna da wuri! Ku nemo su, ku kamota, ko da kuwa za a kashe wanda ya aikata wannan cin amanar.” Ta juyo ta kalle shi tana ɗaga hannu. “Kira Shugaban ‘yan fashin! Ina son jin bayaninsa.” A can gefen Bala da Gora kuwa, motarsu na cigaba da tafiya da sauri, suna kokarin kauce wa duk wata barazana. Amma duk da haka, suna jin tsoron cewa ba su gama da matsalar ba. “Mun tsira daga sansanin, amma har yanzu ba mu fita daga haɗari ba, saboda manyan dazuka ne. Sanda Wanda muke cikinsa babban dajine mai zurfin kilomitoci” Bala ya faɗi, yana tsananta riƙon sitiyari. Nabeeha ta cije leɓe, tana jin tsoron irin makomar da ke gabansu. Hajiya Zaytunah kuwa tana ta yi addu’a a cikin zuciyarta. A can bayan su, fitilun motoci sun bayyana, alamar cewa suna bin sawu! Gora ya juya da sauri ya duba ta bayan gilashin mota. ** Bala ya yi kokarin tsayar da motar da sauri a bayan wani tsohon gini mai fashe-fashe. Wurin ya yi shiru sosai, kamar ba a taba zama a cikinsa ba. Ya juyo ya dubi Gora, yana busar da iska cikin gajiya. “Muna bukatar mu ɓuya a nan har sai mun san inda suke.” Gora ya duba kewayen wurin, zuciyarsa tana bugawa da sauri. “Amma idan sun same mu nan fa? Za su iya harbe mu kafin mu yi wani yunƙuri.” Bala ya sauke ajiyar zuciya. “Muna da zabin da ya fi haka? Idan muka cigaba da tafiya cikin dare, za su iya bin sawun mu.” Hajiya Zaytunah ta kalli su cikin damuwa. “Kun tabbata wurin nan zai iya kare mu?” Bala ya juyo ya dubeta. “In Allah Ya yarda, muna da damar tsira. Amma dole ne ku bi umarninmu.” Nabeeha ta kalli kewayen ginin, zuciyarta na dukan uku-uku. Wurin ya yi tsit, sai dai shure-shuren namun daji da iska mai kaɗawa. Ta kama hannun Hajiya Zaytunah, tana jin fargaba. “Ammi, me zai faru da mu?” Ta tambaya a hankali. Hajiya Zaytunah ta dafa kanta, tana murmushin da ke boye tsoro. “Za mu tsira, In Sha Allah.” Bala da Gora suka fita daga motar suna lekawa don ganin ko akwai wata hanyar guduwa idan har abin ya tashi. Sun san cewa idan ‘yan fashin suka iso, ba za su tsaya da sunan neman bayani ba za su iya harbinsu a take. A can gefe, hayakin tayar motoci ya bayyana daga nesa. Fitilun su na haskawa cikin duhun dare, alamar cewa ‘yan fashin sun kusa isowa. Gora ya runtse ido. “Bala, ba su yi kasa a gwiwa ba. Har yanzu suna binmu.” Bala ya furzar da iska mai zafi. “Idan sun shigo nan, za mu yi yunkurin juyar da hankalinsu. Idan na ce ku gudu, ku gudu babu ja da baya.” Hajiya Zaytunah ta dubi Bala cikin damuwa. “Ya kuke tunanin za mu tsira daga gare su?” Bala ya numfasa. “Ina da wani shiri, amma dole ne mu kasance cikin shiri.” Gora ya kalli Bala cikin shakku. “Kana nufin za mu ƙaddamar da hari?” Bala ya lumshe ido, yana jin nauyin kalmomin da zai faɗa. “Ba mu da wata dama. Ko dai su kama mu su kai mu hannun wadda tasa aka kawo ku, ko kuma mu yi kokarin tsira da kanmu.” Nabeeha ta ji jikinta yana rawa. Wannan shi ne karo na farko da take jin yadda rayuwa ke iya canzawa cikin ƙanƙanin lokaci. Kafin su samu damar ci gaba da magana, karar harbi ta tashi! “Sun gano mu!” Gora ya faɗi da murya mai ƙarfi. Bala ya yi sauri ya ja Hajiya Zaytunah da Nabeeha zuwa bayan ginin don su kauce wa harbin. ‘Yan fashin sun riga sun kewaye yankin. Muryar shugabansu ta tashi cikin tsawa. “Kun zata za ku tsere daga gare mu? Ku fito ko kuma mu cinna wuta a wurin nan!” Bala ya matse hakora. “Dole ne mu yi wani abu yanzu ko kuma su kama mu!” Gora ya janyo wata tsohuwar sanda da ke kusa, yana duban Bala. “Ko da zan mutu, ba zan bar su su kama su ba!” Bala ya dubi Gora, sannan ya dube su Hajiya Zaytunah da Nabeeha. Lokaci ya yi da za su yanke hukunci, zai zama ko dai tsira ko shan wahala a hannun Hajiya Rumanah. “Mu shirya. Komai zai iya faruwa a wannan daren.” 🎀🎀 A daidai lokacin da harbin ya lafa, Bala da Gora suka sami damar janye Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha daga wajen. Sun fice daga ginin da suka buya, suka samu wani wuri mai tsaro inda za su huta kadan. Duk da cewa har yanzu suna cikin fargaba, sun san cewa sun tsira daga hannun ‘yan fashin, amma har yanzu akwai tambayoyi da ke bukatar amsoshi. Hajiya Zaytunah tana dafe da kirjinta, zuciyarta na bugawa da sauri. Bata fahimci dalilin da yasa aka kama su ba, balle kuma wanda ya kitsa wannan sharrin. Ta kalli Gora, murya na rawa. “Don Allah, ku gaya min, waye ya sa aka kama mu? Me muka yi da har za a dauki hayar ‘yan fashi don su tsare mu kamar wasu ‘yan ta’adda?” Gora ya lumshe ido, ya sauke ajiyar zuciya. Ya san cewa dole ne su fada gaskiya, domin babu wani dalili da zai hana hakan. Ya dube ta, fuskar nan tasa cike da alamar tausayi. “Hajiya…” Ya furta a hankali. “Wata mata ce mai kudi ce ta biya mu don mu kama ku. Ita ce ta sa a kawo ku sansanin ‘yan fashi.” Hajiya Zaytunah ta kara matse mayafinta, zuciyarta na tsananta bugawa. “Wacece wannan mata? Wacece take da wannan azancin da za ta iya yin haka a kaina?” Gora ya yi shiru na dan lokaci, yana tunanin ko zai iya fadin hakan. Bala ya jefa masa harara, yana nuni da cewa lokaci ya kure, kuma bai kamata su boye komai ba. A karshe, Gora ya numfasa, sannan ya ce da karfi, “Sunanta Hajiya Rumanah.” Wani irin razana ya bayyana a fuskar Hajiya Zaytunah. Ta ji kamar an jefata a wata duniya da ba ta da alaka da ita. Kafafuwanta sun yi sanyi, zuciyarta ta yi nauyi. “Me… me kace?” Ta tambaya, kamar bata ji abin da Gora ya fada ba. Gora ya sake numfasa, yana jin tausayin yadda fuskar Hajiya Zaytunah ta rikice. “wasu mata ne, Amman babbar ciki Hajiya Rumanah ce ta biya mu don mu kamo ku. Itace Kuma duk ta tsara dukkanin nau'ikan azabobin da akai mu ku." Hajiya Zaytunah ta ja da baya, hannunta yana rawa. “Hajiya Rumanah?” Ta sake maimaitawa da murya kasa-kasa. Wata zufa ta fara keto mata a goshinta. Kamar yadda take tsaye haka ne zuciyarta ta dauki nauyi, numfashinta ya soma hauhawa. Matar yayan mijin… ‘yar uwarta ta jini… . Yar wan mahaifin ta. Da aka haife su rana daya, akai auren su rana daya, Suka Kuma auri mazaje yan gidah daya. Ita ce ta jefa su cikin wannan azaba? “Ba zai yuwu ba… Rumanah ba za ta iya min haka ba!” Hajia Zaytunah ta fada tana girgiza Kai cikin tabbatarwa.. Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah cikin mamaki. Ita ma bata fahimta ba. “Wacece Hajiya Rumanah, Ammi?” Hajiya Zaytunah ta ji zuciyarta kamar zata fashe. Ta runtse ido, tana jin yadda wannan gaskiya take cin ranta. Tana jin tamkar ba ainihin duniyarta take ba...Sam bata samu damar amsa tambayar Nabeeha ba. Ta kara kallon Gora, zuciyarta cike da shakku da rashin yarda. "Don Allah, ku fada min, me ya sa ta aikata haka? Me yasa ta dauki hayar ‘yan fashi don su kama ni? Me nayi mata?” hajia zaytunah ta tanbaye su don baki daya kwakwalwar ta da tunanin ta sun ki amincewa da Hajia rumanah ce tayi haka. Bala ne ya amsa wannan karon. “Ba mu da cikakken bayani, amma daga abin da muka ji daga bakin shugaban ‘yan fashin, Hajiya Rumanah tana so ta wulakanta ku, a yi muku wani abu da ba zai taba mantuwa ba...a Kuma kashe ku a sanda ta umarta. " Idanun Hajiya Zaytunah suka ciko da hawaye. “Na amince da ita… Na dauke ta tamkar uwar mu daya ubanmu daya. mijinta yayan mijina ne, Mahaifin ta yayan mahaifi nane. Rana daya aka haife mu. Tare muka tashi tun yarinta. Karewarta rana daya aka daura auren mu. Kai komai namu iri daya ne. … yaya za ta iya min haka?” Nabeeha ta matso kusa da ita, ta rike hannunta. “Ammi…” Ta kira sunanta da murya mai rauni. Hajiya Zaytunah ta girgiza kai, tana jin zuciyarta tana karyewa. “Hakan ba zai yuwu ba… Rumanah ba za ta iya min haka ba…” Amma zuciyarta ta sani, Idan har Gora da Bala sun fadi haka, to akwai gaskiya. Kuma hakan yana nufin akwai wani abu da take bukatar sani. Bayan ‘yan dakiku, Hajiya Zaytunah ta dago kanta. Idanunta sun canza, sun yi ja. Ba hawaye take ba yanzu, Ba tsoro take ji ba, sai fushi da ƙudurin gano dalilin da yasa Hajiya Rumanah ta aikata wannan danyen aiki. “Dole ne in san gaskiya.” Ta juyo ta kalli Bala da Gora. “Ina son jin komai. Ina son sanin dalilin da ya sa ta aikata hakan.” Bala ya lumshe ido, sannan ya furta: “Za ki ji komai, Hajiya. Amma dole ne mu fice daga nan da farko.” Hajiya Zaytunah ta gyada kai, tana jin zuciyarta cike da zafi. Duk da cewa har yanzu ba ta gama fahimtar dalilin da yasa ‘yar uwarta za ta aikata hakan ba, ta san abu daya, ba za ta kyale wannan lamari haka kawai ba. Da wannan kuduri a zuciyarta, Hajiya Zaytunah ta tsaya da ƙarfi. Babu gudu, babu ja da baya. “lokaci yayi da AKWATI zai bude, SIRRI ka zasu bayyana. Fargaaba zata cika KIRJI, HANKALIn mutane da dama zai hauhawa.." Haka dai suka dauki matakin barin wurin, yayin da zuciyar Hajiya Zaytunah ke tafasa da zafi, tana jira ta hadu da Hajiya Rumanah domin jin dalilin wannan mugunyar makarkashiya… A cikin dare, motarsu na tafiya da sauri yayin da Bala ke kokarin kauce wa duk wata barazana. Gora yana zaune a baya tare da Hajiya Zaytunah da Nabeeha, amma duk zuciyarsu cike take da damuwa. Hajiya Zaytunah ta kasa hakura. Ta sake duban Bala da Gora, zuciyarta na tafasa da fushi. "Don Allah, ku gaya min komai. Ku daina ɓoye min gaskiya!" Bala ya yi shiru, yana tunanin yadda zai bayyana abin da ya sani. Amma kafin ya iya magana, Gora ya riga shi. "Hajiya, ba mu san ainihin dalilin da ya sa ta aikata hakan ba, amma shugabanmu ya ce Hajiya Rumanah ta fi son mu cutar da ku sosai kafin wai akai gashin kan ki da aka aske gareta, Ta bada umarni cewa a azabtar da ku a wulakanta ku, A tozarta ku. A Kuma raba wannan budurwar yar ta ki da mutuncin ta... Tamafi jaddada sunan yarinyar nan ta ki. Tace a tabbatar an rabata da martabarta.." Jikin Hajiya Zaytunah ya yi sanyi. Ta jinjina kai, tana jin wani irin raɗaɗi a cikin zuciyarta. "Ta yaya za ta iya yin haka? Me nayi mata?" Bala ya gyada kai. "Wataƙila ta gaji da kasancewarki a duniya. Wataƙila tana jin tsoron wani abu a kanki." Nabeeha, wadda ke shiru tun tuni, ta juyo tana kallon Ammin ta. "Me hakan ke nufi, Ammi? Me yasa za ta yi hakan?" Hajiya Zaytunah ta numfasa, hawaye na taruwa a idanunta. "Nabeeha, Hajiya Rumanah matar yayan mahaifin kuce kamar yadda na fada, sannan yayata ce. Yar wan mahaifi na ce..gidan mu daya. Mun daɗe tare da ita, mun rayu a gida daya. Ban taɓa tunanin cewa wata rana za ta nemi hallakani ba." Nabeeha ta ji jikin ta na rawa. "Matar yayan baba na ce?!" "Eh," Hajiya Zaytunah ta tabbatar da hakan. "Ta kasance kamar ‘yar uwa a gare ni, amma yanzu ta juyawa rayuwata baya." Bala ya kalli Gora, sannan ya sake fuskantar Hajiya Zaytunah. "Hajiya, akwai abu daya da ya kamata ki sani. A lokacin da aka ba mu aikin, an ce mana cewa dole ne mu tabbata cewa babu wanda zai sake jin labarinki ko ‘yar ki da danki. Kuma mun fahimci cewa tana matukar tsoron wani abu." Hajiya Zaytunah ta jinjina kai, zuciyarta na tambayar kanta me hakan ke nufi. Me Rumanah ke tsoro har ta kai ga neman rayuwarta? Bala ya ci gaba da magana, yana bayyana abinda ya ji daga bakin shugaban ‘yan fashin. "Wani abu ne da ke tsakanin ki da ita. Wani abu da ya shafi rayuwar mijinta ko yayanta ne ko danta na dai manta" Hajiya Zaytunah ta runtse ido. Ta san cewa akwai abubuwa da yawa da suka faru a baya, amma ko daya daga cikinsu bai yi mata kama da dalilin da zai sa Hajiya Rumanah ta nemi hallakawa ba. "Dole ne in samu amsar tambayoyi na," ta furta a hankali, amma da ƙuduri mai karfi. "Ba zan bar wannan lamari haka ba." Duk da cewa sun tsira daga wannan haɗari, hakan bai nufin cewa sun gama da barazana ba. Har yanzu akwai Hajiya Rumanah a can, mai cike da makirci da sharrinta. Kuma har yanzu ba su san menene ainihin dalilinta na yin haka ba. Hajiya Zaytunah ta matse hannun Nabeeha, sannan ta dube su Bala da Gora. "Babu komai, Allah yana tare da mu. Yadda ya kubutar da mu daga sansanin yan fashi. Da yardar Allah zai karasa warware duk wani tuggu da makirci, sharri da ma sihiri da ake aikatawa da yardar Allah. Komai nisan dare gari zai waye..Allah zai bayyana gaskiya.. Kuma shi sharri dan aike ne..idan ka turashi karka rufe kofa zai dawo maka..." _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 11_ A dai-dai lokacin da Bala da Gora suka tsere da Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha, wani sakon gaggawa ya isa wajen Hajiya Rumanah. Wani daga cikin mutanenta ya durƙusa gabanta yana sauke numfashi, alamar gajiya da hanzarin isowa. “Hajiya, akwai matsala!” Hajiya Rumanah ta ɗago daga inda take zaune a cikin wani falo mai ɗauke da kayan alfarma. Idanunta suka kaɗa, alamar ba ta da niyyar karɓar wata matsala a wannan lokacin. “Wace irin matsala?!” Ta tambaya, muryarta cike da ƙwarin gwiwa. Mutumin ya haɗiye yawu. “‘Yan fashin da aka ba aikin sun yi kuskure. Wataƙila wasu daga cikinsu sun canza ra’ayi, suka fitar da matar da yaranta daga hannunsu.” Hajiya Rumanah ta tsinci kanta tana matse mayafinta da ƙarfi, zuciyarta na bugawa da sauri. “Ba abu ne mai yiyuwa ba! Me kake nufi?!” Mutumin ya sunkuyar da kansa. “Har yanzu ba mu da cikakken bayani, amma an ga wata mota da ta tsere daga sansanin. Shugaban ‘yan fashin yana kokarin bin sawu.” Hajiya Rumanah ta tashi daga kujerarta cikin zafin rai. "Ina bukatar su dawo hannuna da wuri! Ku nemo su, ku kamota, ko da kuwa za a kashe wanda ya aikata wannan cin amanar.” Ta juyo ta kalle shi tana ɗaga hannu. “Kira Shugaban ‘yan fashin! Ina son jin bayaninsa.” A can gefen Bala da Gora kuwa, motarsu na cigaba da tafiya da sauri, suna kokarin kauce wa duk wata barazana. Amma duk da haka, suna jin tsoron cewa ba su gama da matsalar ba. “Mun tsira daga sansanin, amma har yanzu ba mu fita daga haɗari ba, saboda manyan dazuka ne. Sanda Wanda muke cikinsa babban dajine mai zurfin kilomitoci” Bala ya faɗi, yana tsananta riƙon sitiyari. Nabeeha ta cije leɓe, tana jin tsoron irin makomar da ke gabansu. Hajiya Zaytunah kuwa tana ta yi addu’a a cikin zuciyarta. A can bayan su, fitilun motoci sun bayyana, alamar cewa suna bin sawu! Gora ya juya da sauri ya duba ta bayan gilashin mota. ** Bala ya yi kokarin tsayar da motar da sauri a bayan wani tsohon gini mai fashe-fashe. Wurin ya yi shiru sosai, kamar ba a taba zama a cikinsa ba. Ya juyo ya dubi Gora, yana busar da iska cikin gajiya. “Muna bukatar mu ɓuya a nan har sai mun san inda suke.” Gora ya duba kewayen wurin, zuciyarsa tana bugawa da sauri. “Amma idan sun same mu nan fa? Za su iya harbe mu kafin mu yi wani yunƙuri.” Bala ya sauke ajiyar zuciya. “Muna da zabin da ya fi haka? Idan muka cigaba da tafiya cikin dare, za su iya bin sawun mu.” Hajiya Zaytunah ta kalli su cikin damuwa. “Kun tabbata wurin nan zai iya kare mu?” Bala ya juyo ya dubeta. “In Allah Ya yarda, muna da damar tsira. Amma dole ne ku bi umarninmu.” Nabeeha ta kalli kewayen ginin, zuciyarta na dukan uku-uku. Wurin ya yi tsit, sai dai shure-shuren namun daji da iska mai kaɗawa. Ta kama hannun Hajiya Zaytunah, tana jin fargaba. “Ammi, me zai faru da mu?” Ta tambaya a hankali. Hajiya Zaytunah ta dafa kanta, tana murmushin da ke boye tsoro. “Za mu tsira, In Sha Allah.” Bala da Gora suka fita daga motar suna lekawa don ganin ko akwai wata hanyar guduwa idan har abin ya tashi. Sun san cewa idan ‘yan fashin suka iso, ba za su tsaya da sunan neman bayani ba za su iya harbinsu a take. A can gefe, hayakin tayar motoci ya bayyana daga nesa. Fitilun su na haskawa cikin duhun dare, alamar cewa ‘yan fashin sun kusa isowa. Gora ya runtse ido. “Bala, ba su yi kasa a gwiwa ba. Har yanzu suna binmu.” Bala ya furzar da iska mai zafi. “Idan sun shigo nan, za mu yi yunkurin juyar da hankalinsu. Idan na ce ku gudu, ku gudu babu ja da baya.” Hajiya Zaytunah ta dubi Bala cikin damuwa. “Ya kuke tunanin za mu tsira daga gare su?” Bala ya numfasa. “Ina da wani shiri, amma dole ne mu kasance cikin shiri.” Gora ya kalli Bala cikin shakku. “Kana nufin za mu ƙaddamar da hari?” Bala ya lumshe ido, yana jin nauyin kalmomin da zai faɗa. “Ba mu da wata dama. Ko dai su kama mu su kai mu hannun wadda tasa aka kawo ku, ko kuma mu yi kokarin tsira da kanmu.” Nabeeha ta ji jikinta yana rawa. Wannan shi ne karo na farko da take jin yadda rayuwa ke iya canzawa cikin ƙanƙanin lokaci. Kafin su samu damar ci gaba da magana, karar harbi ta tashi! “Sun gano mu!” Gora ya faɗi da murya mai ƙarfi. Bala ya yi sauri ya ja Hajiya Zaytunah da Nabeeha zuwa bayan ginin don su kauce wa harbin. ‘Yan fashin sun riga sun kewaye yankin. Muryar shugabansu ta tashi cikin tsawa. “Kun zata za ku tsere daga gare mu? Ku fito ko kuma mu cinna wuta a wurin nan!” Bala ya matse hakora. “Dole ne mu yi wani abu yanzu ko kuma su kama mu!” Gora ya janyo wata tsohuwar sanda da ke kusa, yana duban Bala. “Ko da zan mutu, ba zan bar su su kama su ba!” Bala ya dubi Gora, sannan ya dube su Hajiya Zaytunah da Nabeeha. Lokaci ya yi da za su yanke hukunci, zai zama ko dai tsira ko shan wahala a hannun Hajiya Rumanah. “Mu shirya. Komai zai iya faruwa a wannan daren.” 🎀🎀 A daidai lokacin da harbin ya lafa, Bala da Gora suka sami damar janye Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha daga wajen. Sun fice daga ginin da suka buya, suka samu wani wuri mai tsaro inda za su huta kadan. Duk da cewa har yanzu suna cikin fargaba, sun san cewa sun tsira daga hannun ‘yan fashin, amma har yanzu akwai tambayoyi da ke bukatar amsoshi. Hajiya Zaytunah tana dafe da kirjinta, zuciyarta na bugawa da sauri. Bata fahimci dalilin da yasa aka kama su ba, balle kuma wanda ya kitsa wannan sharrin. Ta kalli Gora, murya na rawa. “Don Allah, ku gaya min, waye ya sa aka kama mu? Me muka yi da har za a dauki hayar ‘yan fashi don su tsare mu kamar wasu ‘yan ta’adda?” Gora ya lumshe ido, ya sauke ajiyar zuciya. Ya san cewa dole ne su fada gaskiya, domin babu wani dalili da zai hana hakan. Ya dube ta, fuskar nan tasa cike da alamar tausayi. “Hajiya…” Ya furta a hankali. “Wata mata ce mai kudi ce ta biya mu don mu kama ku. Ita ce ta sa a kawo ku sansanin ‘yan fashi.” Hajiya Zaytunah ta kara matse mayafinta, zuciyarta na tsananta bugawa. “Wacece wannan mata? Wacece take da wannan azancin da za ta iya yin haka a kaina?” Gora ya yi shiru na dan lokaci, yana tunanin ko zai iya fadin hakan. Bala ya jefa masa harara, yana nuni da cewa lokaci ya kure, kuma bai kamata su boye komai ba. A karshe, Gora ya numfasa, sannan ya ce da karfi, “Sunanta Hajiya Rumanah.” Wani irin razana ya bayyana a fuskar Hajiya Zaytunah. Ta ji kamar an jefata a wata duniya da ba ta da alaka da ita. Kafafuwanta sun yi sanyi, zuciyarta ta yi nauyi. “Me… me kace?” Ta tambaya, kamar bata ji abin da Gora ya fada ba. Gora ya sake numfasa, yana jin tausayin yadda fuskar Hajiya Zaytunah ta rikice. “wasu mata ne, Amman babbar ciki Hajiya Rumanah ce ta biya mu don mu kamo ku. Itace Kuma duk ta tsara dukkanin nau'ikan azabobin da akai mu ku." Hajiya Zaytunah ta ja da baya, hannunta yana rawa. “Hajiya Rumanah?” Ta sake maimaitawa da murya kasa-kasa. Wata zufa ta fara keto mata a goshinta. Kamar yadda take tsaye haka ne zuciyarta ta dauki nauyi, numfashinta ya soma hauhawa. Matar yayan mijin… ‘yar uwarta ta jini… . Yar wan mahaifin ta. Da aka haife su rana daya, akai auren su rana daya, Suka Kuma auri mazaje yan gidah daya. Ita ce ta jefa su cikin wannan azaba? “Ba zai yuwu ba… Rumanah ba za ta iya min haka ba!” Hajia Zaytunah ta fada tana girgiza Kai cikin tabbatarwa.. Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah cikin mamaki. Ita ma bata fahimta ba. “Wacece Hajiya Rumanah, Ammi?” Hajiya Zaytunah ta ji zuciyarta kamar zata fashe. Ta runtse ido, tana jin yadda wannan gaskiya take cin ranta. Tana jin tamkar ba ainihin duniyarta take ba...Sam bata samu damar amsa tambayar Nabeeha ba. Ta kara kallon Gora, zuciyarta cike da shakku da rashin yarda. "Don Allah, ku fada min, me ya sa ta aikata haka? Me yasa ta dauki hayar ‘yan fashi don su kama ni? Me nayi mata?” hajia zaytunah ta tanbaye su don baki daya kwakwalwar ta da tunanin ta sun ki amincewa da Hajia rumanah ce tayi haka. Bala ne ya amsa wannan karon. “Ba mu da cikakken bayani, amma daga abin da muka ji daga bakin shugaban ‘yan fashin, Hajiya Rumanah tana so ta wulakanta ku, a yi muku wani abu da ba zai taba mantuwa ba...a Kuma kashe ku a sanda ta umarta. " Idanun Hajiya Zaytunah suka ciko da hawaye. “Na amince da ita… Na dauke ta tamkar uwar mu daya ubanmu daya. mijinta yayan mijina ne, Mahaifin ta yayan mahaifi nane. Rana daya aka haife mu. Tare muka tashi tun yarinta. Karewarta rana daya aka daura auren mu. Kai komai namu iri daya ne. … yaya za ta iya min haka?” Nabeeha ta matso kusa da ita, ta rike hannunta. “Ammi…” Ta kira sunanta da murya mai rauni. Hajiya Zaytunah ta girgiza kai, tana jin zuciyarta tana karyewa. “Hakan ba zai yuwu ba… Rumanah ba za ta iya min haka ba…” Amma zuciyarta ta sani, Idan har Gora da Bala sun fadi haka, to akwai gaskiya. Kuma hakan yana nufin akwai wani abu da take bukatar sani. Bayan ‘yan dakiku, Hajiya Zaytunah ta dago kanta. Idanunta sun canza, sun yi ja. Ba hawaye take ba yanzu, Ba tsoro take ji ba, sai fushi da ƙudurin gano dalilin da yasa Hajiya Rumanah ta aikata wannan danyen aiki. “Dole ne in san gaskiya.” Ta juyo ta kalli Bala da Gora. “Ina son jin komai. Ina son sanin dalilin da ya sa ta aikata hakan.” Bala ya lumshe ido, sannan ya furta: “Za ki ji komai, Hajiya. Amma dole ne mu fice daga nan da farko.” Hajiya Zaytunah ta gyada kai, tana jin zuciyarta cike da zafi. Duk da cewa har yanzu ba ta gama fahimtar dalilin da yasa ‘yar uwarta za ta aikata hakan ba, ta san abu daya, ba za ta kyale wannan lamari haka kawai ba. Da wannan kuduri a zuciyarta, Hajiya Zaytunah ta tsaya da ƙarfi. Babu gudu, babu ja da baya. “lokaci yayi da AKWATI zai bude, SIRRI ka zasu bayyana. Fargaaba zata cika KIRJI, HANKALIn mutane da dama zai hauhawa.." Haka dai suka dauki matakin barin wurin, yayin da zuciyar Hajiya Zaytunah ke tafasa da zafi, tana jira ta hadu da Hajiya Rumanah domin jin dalilin wannan mugunyar makarkashiya… A cikin dare, motarsu na tafiya da sauri yayin da Bala ke kokarin kauce wa duk wata barazana. Gora yana zaune a baya tare da Hajiya Zaytunah da Nabeeha, amma duk zuciyarsu cike take da damuwa. Hajiya Zaytunah ta kasa hakura. Ta sake duban Bala da Gora, zuciyarta na tafasa da fushi. "Don Allah, ku gaya min komai. Ku daina ɓoye min gaskiya!" Bala ya yi shiru, yana tunanin yadda zai bayyana abin da ya sani. Amma kafin ya iya magana, Gora ya riga shi. "Hajiya, ba mu san ainihin dalilin da ya sa ta aikata hakan ba, amma shugabanmu ya ce Hajiya Rumanah ta fi son mu cutar da ku sosai kafin wai akai gashin kan ki da aka aske gareta, Ta bada umarni cewa a azabtar da ku a wulakanta ku, A tozarta ku. A Kuma raba wannan budurwar yar ta ki da mutuncin ta... Tamafi jaddada sunan yarinyar nan ta ki. Tace a tabbatar an rabata da martabarta.." Jikin Hajiya Zaytunah ya yi sanyi. Ta jinjina kai, tana jin wani irin raɗaɗi a cikin zuciyarta. "Ta yaya za ta iya yin haka? Me nayi mata?" Bala ya gyada kai. "Wataƙila ta gaji da kasancewarki a duniya. Wataƙila tana jin tsoron wani abu a kanki." Nabeeha, wadda ke shiru tun tuni, ta juyo tana kallon Ammin ta. "Me hakan ke nufi, Ammi? Me yasa za ta yi hakan?" Hajiya Zaytunah ta numfasa, hawaye na taruwa a idanunta. "Nabeeha, Hajiya Rumanah matar yayan mahaifin kuce kamar yadda na fada, sannan yayata ce. Yar wan mahaifi na ce..gidan mu daya. Mun daɗe tare da ita, mun rayu a gida daya. Ban taɓa tunanin cewa wata rana za ta nemi hallakani ba." Nabeeha ta ji jikin ta na rawa. "Matar yayan baba na ce?!" "Eh," Hajiya Zaytunah ta tabbatar da hakan. "Ta kasance kamar ‘yar uwa a gare ni, amma yanzu ta juyawa rayuwata baya." Bala ya kalli Gora, sannan ya sake fuskantar Hajiya Zaytunah. "Hajiya, akwai abu daya da ya kamata ki sani. A lokacin da aka ba mu aikin, an ce mana cewa dole ne mu tabbata cewa babu wanda zai sake jin labarinki ko ‘yar ki da danki. Kuma mun fahimci cewa tana matukar tsoron wani abu." Hajiya Zaytunah ta jinjina kai, zuciyarta na tambayar kanta me hakan ke nufi. Me Rumanah ke tsoro har ta kai ga neman rayuwarta? Bala ya ci gaba da magana, yana bayyana abinda ya ji daga bakin shugaban ‘yan fashin. "Wani abu ne da ke tsakanin ki da ita. Wani abu da ya shafi rayuwar mijinta ko yayanta ne ko danta na dai manta" Hajiya Zaytunah ta runtse ido. Ta san cewa akwai abubuwa da yawa da suka faru a baya, amma ko daya daga cikinsu bai yi mata kama da dalilin da zai sa Hajiya Rumanah ta nemi hallakawa ba. "Dole ne in samu amsar tambayoyi na," ta furta a hankali, amma da ƙuduri mai karfi. "Ba zan bar wannan lamari haka ba." Duk da cewa sun tsira daga wannan haɗari, hakan bai nufin cewa sun gama da barazana ba. Har yanzu akwai Hajiya Rumanah a can, mai cike da makirci da sharrinta. Kuma har yanzu ba su san menene ainihin dalilinta na yin haka ba. Hajiya Zaytunah ta matse hannun Nabeeha, sannan ta dube su Bala da Gora. "Babu komai, Allah yana tare da mu. Yadda ya kubutar da mu daga sansanin yan fashi. Da yardar Allah zai karasa warware duk wani tuggu da makirci, sharri da ma sihiri da ake aikatawa da yardar Allah. Komai nisan dare gari zai waye..Allah zai bayyana gaskiya.. Kuma shi sharri dan aike ne..idan ka turashi karka rufe kofa zai dawo maka..." _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI* *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 12_ Suna isa wani wuri da ke da nisa da inda aka tsare su, inda Bala da Gora suka tanadi wani tsohon gida mai matukar kango. A nan suka tsaya domin su huta, kuma su tattauna gaba ɗaya a kan matakin da ya kamata su ɗauka. Hajiya Zaytunah ta kalli su Bala da Gora, zuciyarta na tafasa da mamaki da kuma fushi. Duk da cewa sun kubuta daga sansanin yan fashin suna dai cikin dajin. har yanzu ba ta iya fahimtar dalilin da yasa Hajiya Rumanah za ta nemi hallakata ba... “Bala, me yasa? Me nayi mata da har ta tsaneni haka ita wadda ta turo ku?” Bala ya yi shiru na ɗan lokaci, yana nazarin yadda zai bayyana gaskiyar. Gora ya jefa masa harara, yana son ya yi magana kawai. A karshe, Bala ya numfasa sannan ya ce, “Akwai wata magana da na ji daga bakin shugabanmu kafin a kawo ku. Yana cewa Hajiya Rumanah tana tsoron cewa idan kika ci gaba da rayuwa, to akwai wani babbar SIRRI da zai tonu.” Hajiya Zaytunah ta runtse ido, zuciyarta na kara harbawa da sauri. SIRRI i? Wane irin SIRRI ne hakan? Nabeeha, wadda ke zaune a kusa da ita, ta dafa hannunta. “Ammi, ko da wasa ban taba tunanin cewa yar uwarki ta jini za ta iya yin haka ba... shine dalilin daya sa bamu san su ba kenan? ” Hajiya Zaytunah ta girgiza kai. “Ni ma haka. Amma yanzu dole ne mu san komai... Dalilai da yawa Nabeeha. Amma kwata kwata bana Saka rumanah aciki. Nasan akwai zazaafar gaba da take yi akai na..Amma bansan ta tsananta haka ba" Bala ya kalli Hajiya Zaytunah kai tsaye. "Hajiya, kin taɓa jin wani abu game da wata mata da ta bata a baya?" Hajiya Zaytunah ta cika da mamaki. "Yarinya? Wacece kuma?" Gora ne ya amsa da wata irin murya kamar yana kokarin kauce wa wata masifa. " A cewar shugabanmu, akwai wani SIRRI da ke tsakanin ku da Alhaji Uzairu wanda ya shafi wata mata da ta bata shekaru da suka wuce. Kuma ana zargin cewa idan kika ci gaba da rayuwa, akwai yiwuwar gaskiya ta bayyana." Hajiya Zaytunah ta runtse ido, zuciyarta na dukan uku-uku. Yarinya? Ko dai babbar mace...Hmm Me ya faru? Sai dai wani abu yana dawowa cikin tunaninta, tsohuwar rayuwarta a gidan Alhaji Uzairu. Shekaru da suka wuce, akwai abubuwa da suka faru da ba ta taba tunanin za su iya dawowa gare ta ba. Nabeeha ta kalli Ammin ta da damuwa. "Ammi, ko akwai wani abu da kike tunawa?" Hajiya Zaytunah ta dago kai, idanunta na cike da ruɗani. "Ban da tabbas... amma ina jin cewa akwai wata babbar magana da ban sani ba." "Shin wannan wane SIRRI ne haka ammi?" Hammad ya tanbayi mahaifiyar sa yana jujjuya zancen a fatar bakin sa... "Tarin SIRRI ka ne da yawa Hammad. Wanda ni kaina bazan iya gaya maka takamaimai yadda suke ba. Amman nasan akwai boyayyen lamarin dake faruwa Wanda yasa ta hauhawa haka" "Kaico rayuwar duniya kenan. Da ya yi kokarin kashe mahaifinnsa ko mahaifiyar sa. Yan uwa su cinye gadon marayu.. Sannan dangi su nemi kashe dayan su saboda abunda suka qudirar na daga dukiya da sauran su" gora ya fada yana furzar da iskar bakinsa. 🎀🎀 A cikin dakin shakatawarta, Hajiya Rumanah tana tafiya a zage-zage, zuciyarta cike da tsana da fushi. Ta kasa zama, ta kasa natsuwa. Labarin da ta samu a safiyar yau ya dagula mata lissafi, ya ruguza duk wata kwanciyar hankali da take da ita. "Suka tsira?😂!" Ta furta cikin matuƙar mamaki da takaici, tana watsa kwanon shayi da ke gabanta. "Su suka tsira?! Me kuke nufi da hakan?" A gefe, Hajiya Karama da Ladi suna tsaye cikin nutsuwa, suna kallonta da mamaki. Sun san cewa yau Hajiya Rumanah tana cikin wata irin damuwa da ba ta taɓa shiga ba. "Wallahi ba zan taba bari su tsira ba! Ba zan bari wannan masifar ta cigaba ba!" Ta ja tsaki mai karfi, ta dafe kanta kamar wacce ke jin zafi kwakwalwarta. "Me yasa ita ce kullum ke ci min buri?!" Hajiya Karama ta dan rankwafa. "Hajiya, ki kwantar da hankalinki. Me zai hana mu sake daukar mataki?" Hajiya Rumanah ta juyo da mugun kallo. "Mataki? Mataki?! Me kika san game da mataki? Kin san tun daga ina wannan masifar ta fara?" Ta ja kujera ta zauna, amma har yanzu jikinta yana bari saboda takaici. Ta dubi su da idanuwan da suka cika da tsana. "Kullum ita ce matsalata tun farkon rayuwata! Mahaifiyarta ta aure min mahaifi! Babana wanda ya fi kowa so, mahaifiyarta ce.. Tun daga ranar muka dena zaman lafiya." Ladi ta waro ido. "Anya kuwa?" "Eh! Zahiri! Da mahaifiyarta ta zo, sai mahaifiyata ta koma kaskiya! Komai ya canza, babana baya shiri da mahaifiyataa, sai dai ita!" Ta numfasa da karfi, kamar wacce ke jin zuciyarta tana kuna. "Mahaifiyar ta. Shegiya la'ananniya data haifo mana dangin jaraba da kulafici. Kanin mahaifina ne mahaifin ta. Bayan rasuwar sa sai mahaifiyar ta aure babanmu..a baya bakuga mutuncin da ake ba. Gidanmu daya ashe ashe jira take dama tana sonsam mijinta na rasu ta aure babanmu. Kunji cin amana daya?" Hajiya Karama ta dafe baki. "To amma menene hakan ya shafe ki?" Hajiya Rumanah ta yi dariyar takaici. "Me yasa ba zai shafe ni ba?! Dole ne nai kishi, dole ne na tsane su! Mahaifiyarta ta aure min mahaifi, ita kuma ta aure min miji!" Ta runtse ido, ta kaɗa kanta da sauri kamar wacce ke jin wani abu mai zafi a kanta. "Na rasa saurayi na saboda ita! Alhaji Uzairu ni zai aura a baya, amma sai gashi ita ya aura. Ni da nake jin shi ne kad’ai nawa, amma sai aka ɗauke shi aka miƙa mata!" Ladi ta dan girgiza kai. "To yanzu ai duk ya wuce." "Ya wuce?!" Hajiya Rumanah ta dauke mata kafa, ta watsa mata harara. "Kika ce ya wuce? Ai wannan shine babbar matsalar! Tun da na haifi Muhammad, na dauki alkawarin cewa shi zai fi kowa a gidannan. Sai gashi yanzu, dan cikina, jinina, shi ma yana bibiyar ‘yar Zaytunah?! Wacce iriyar bakar lukutar masifar kaddara ce wannan?" Ta tashi tsaye da sauri, ta fara tafiya a cikin dakin, tana girgiza kai da takaici. "Na rasa uba a hannunta. Na rasa miji a hannunta. Kuma yanzu har da dana? Har da Muhammad? Ku duba fa! Muhammad yana so ya auri ‘yar waccan munafukar? Wannan ai cin fuska ne! Baiwa ne aka raina!" Hajiya Karama ta numfasa, tana kokarin kwantar da ita. "To ki yi hakuri. Muhammad ba zai aure ta ba." "Da gaske kike?" Hajiya Rumanah ta watsa mata wani kallo mai cike da hauka. "Da gaske kike? Idan ban dauki mataki ba, Muhammad zai aure ta! Zai zama surikin Zaytunah, ni kuwa me zan zama?! Wai ni ce za a kira da uwar surikin yarinyar da mahaifiyarta ta kwace min rayuwa?" Ta dafe KIRJIN ta, zuciyarta na bugawa da sauri. Tsananta, haushi, kishi, bakin ciki,duk sun taru suka mamaye ta. "Wallahi bazan yarda ba. Bazan taba yarda ba! Ba za ta ci gaba da samun nasara a kaina ba!" Ta dauki waya, zuciyarta na tafasa. "Dole a nemo su, kuma a wannan karon ba zan yarda a yi wasa ba. Idan har suka ci gaba da rayuwa, to hakan yana nufin cewa ni na gaza. Kuma bazan yarda da hakan ba!" Sai a lokacin ta tuna yadda labarin ya zo gare ta. Akwai wanda ya sanar da ita cewa su Hajiya Zaytunah sun tsira daga hannun Gora da Bala. Wata zuciyarta na gaya mata cewa wani daga cikin mutanenta ne ya yi sakaci. Ta kalli Hajiya Karama da Ladi da idanuwanta da suka yi jajir. "Ku saurara! Ba zan yarda da shirme ba. Duk wanda ya saba umarnina, zai gamu da fushina!" Ta matse wayarta a hannunta, zuciyarta tana tafarfasa. "Na tsani Zaytunah! Na tsani iyalanta! Kuma ko da wane hali, ba zan bar Muhammad ya aure Nabeeha ba! Ko da kuwa hakan na nufin... dole ne in dauki babban mataki!" Ladi ta kalli Hajiya Karama da mamaki. "Kin fahimci inda zaytunah ke shirin dosa?" Hajiya Karama ta jinjina kai, ta lumshe ido. "Eh... Kuma ina jin tsoron hakan." Hajiya Rumanah ta ja numfashi, idanuwanta na dauke da mugun ƙuduri. "Wannan karon, Zaytunah ba za ta tsira ba." Hajiya Rumanah ta zura ido cikin wayarta, zuciyarta na tafasa da tsana da bakin ciki. Ta san cewa idan har ta zauna kawai tana magana ba tare da ta dauki mataki ba, to hakan na iya zama dalilin da zai sa komai ya rushe mata. Dole ne ta dauki matakin da zai tabbatar da cewa wannan masifa ta kare nan take. Ta latsa lambar daya daga cikin abokan huldarta a boye, tana jiran a dauka. Da zarar an daga, ta numfasa sannan ta furta cikin wata murya da ke cike da hadari, “Ina son ku nemo min su. Ku kama su, amma a wannan karon, ba na son kuskure.” A dayan bangaren, muryar wani namiji mai karfi ta amsa. "Kiyi hakuri hajiya" Hajiya Rumanah ta cije lebenta. "Kun yi sakaci ne! Kuma wallahi ba zan yarda da hakan ba. Ku nemo su, a kawo min su da rayuwarsu, ko kuma ku tabbatar da cewa ba za su kara zama a doron kasa ba!" "Za a yi aiki, Hajiya." Ta kashe wayar tana mai huci. Idanunta sun kada suka yi jajir kamar wacce ke shirin fashewa da kuka saboda takaici. Hajiya Karama da Ladi suna zaune a gefe, suna kallonta da damuwa. Hajiya Karama ta yi gyaran murya. "Hajiya, kin tabbata wannan ne mafita? Balle kuma yanzu ana cewa Major General Dawud yana kokarin gano inda suke..." Kafin ta karasa, Hajiya Rumanah ta juyo da wawan tsawa. "Kada ki sake ambaton sunan wannan mutumin! Kada ki kuskura ki ce min yana kokarin gano su! Ko da kuwa zai shiga tsakaninmu, wallahi ba zan bari ya hana ni cimma burina ba." Ladi ta hadiye yawu, ta dafe habarta. "Hajiya, amma ai su Major General ba kanwar lasa ba ne... idan suka sa baki a wannan al’amari, to kuwa zamu shiga matsala." Hajiya Rumanah ta busar da iska mai karfi. "Ni ce Rumanah! Ni ce uwar wannan gida! Me kuke tunani? Ku na zaton zan bar wata matsiyata da yaranta su cinye min duniya a ido?! Na rasa uba a hannun su! Na rasa miji a hannun su! Kuma yanzu ina da niyyar rasa dana? Ba zan taba bari hakan ta faru ba! Ba zan bari Muhammad ya auri waccan yarinyar ba!" Ta koma kusa da Hajiya Karama da Ladi, ta kafa musu ido. "Ku saurara, wannan karon ba zan tsaya da hannaye a kunne ba. Dole ne a dauki mataki. Idan har ba za a iya hallaka su gaba daya ba, to sai an ga yadda za a wargaza su. Sai an raba Nabeeha da Muhammad, koda kuwa hakan na nufin a bata ta!. Maganar dana yanke kenan dazu ban sanar muku na" Ladi ta zaro ido cikin tsoro. "Hajiya! Kina nufin..." "Kwarai kuwa! Idan har aka ci gaba da barin Nabeeha a matsayin budurwa, Muhammad zai dage sai ya aure ta. Amma idan aka bata ta, to ba zai kara kallo a kanta ba!" Hajiya Karama ta girgiza kai. "Amma Hajiya, wannan ai..." "Shiru!" Hajiya Rumanah ta katse ta da tsawa. "Babu wani abu da zai hana ni cimma burina. Ba na fatan ganin wannan matsala ta ci gaba! Idan har aka bar Zaytunah da yaranta su cigaba da rayuwa, wata rana su ne za su zama shugabanni, ni kuma in koma bakin ciki! Ni fa ba raini na ke ba!" Ta dafe goshinta, tana jin zuciyarta na tafarfasa. Ta riga ta gama yanke shawara. Dole ne ta dauki mataki kafin lokaci ya kure mata. "Ku jira. Zaku ga yadda zan sauya wannan al’amari. Idan har akwai wanda zai ci gaba da rayuwa a cikin wannan gida, to tabbas ba Zaytunah da yaranta ba!" Ta daga wayarta, ta kira wani sabon mutum. Lokacin da aka daga wayar, ta furta, "Kana buƙatar aiki?" A dayan bangaren, wata muguwar dariya ce ta amsa mata. "Hajiya Rumanah, ke dai kin san me kike so. Ba ki da wasa da mugunta. Ina sauraronki." Shin Hajiya Rumanah za ta iya cimma mugun nufinta? Ko kuwa zata gamu da fushin Major General Dawud da mutanensa? Kuma shin Muhammad zai gano cewa mahaifiyarsa ce ke kokarin ruguza masa rayuwa? Tirqashi🤭 _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 13_ Hajiya Rumanah ta kashe wayar tare da wani murmushin mugunta. Idanunta sun cika da ƙuduri, kudurin ganin cewa babu wata hanya da za ta bari su Hajiya Zaytunah su tsira. Hajiya Karama da Ladi sun kalle ta da mamaki, har yanzu sun kasa yarda da irin wannan matakin da take shirin ɗauka. "Hajiya, ko kin tabbata wannan ne mafi dacewa?" Hajiya Karama ta tambaya cikin nutsuwa. Hajiya Rumanah ta juyo da wani mugun kallo. "Da me kike nufi? Me kike tunani? Wannan karon ba na wasa! Babu wani 'hakuri' ko 'ji da mutane' a cikin lamarin nan!" Ta ɗauki kofin shayi da ke gabanta, ta kafa kai, amma ba ta gama ba ta watsar da shi gefe. "Dole ne suyi nadamar zuwa duniya. Dole ne su fuskanci hukunci!" Baki daya a hautsine take..ta birkice tamkar mahaukaciya.. Ta ɗauki wayarta ta sake latsa wata lamba. Bayan an ɗaga, ta yi shiru na ƴan dakiku kafin ta ce, "Dan Allah, A yanzu ina son ku sanya ido kan su Hajiya Zaytunah da yaranta. Ba na son a sake yin sakaci irin wanda aka yi da farko." Muryar namijin a daya bangaren ta ce: "Ba matsala, Hajiya. Kawai ki bamu umarni." "Dole ne ku kawo min wani abu da zai ruguza rayuwarsu! Idan har Nabeeha ta rasa mutuncinta, Muhammad zai ji kunyar kallon ta! Kuma idan hakan ta faru, da hannunsa zai gujeta!" Hajiya Karama ta yi saurin kallonta. "Hajiya, wannan ai babban zunubi ne. Ko kin manta cewa Muhammad da kansa zai iya gano hakan kuma ya tsane ki?" Hajiya Rumanah ta yi dariyar takaici. "Ke da kike tunani kamar mai hankali, tunani nawa kika taba yi da ya yi tasiri? Idan har hakan ya faru, ba za a san ni da hannu a ciki ba!" Duk fa tare muke shirya abubuwan nan da ku..kada ku manta dai kishiyar kuce tare kuke a zaune. Kuma mijin ku yafi kaunarta kamar ransa. Kawai dai saboda ku ba danku bane zai auri yar ta shisya abun baya damun ku. Allah ya kyauta" "To idan kuwa haka ne, me zai hana mu bi hanyar da ta fi sauki?" Ladi ta tambaya, tana neman hanya mafi dacewa da zata iya hana Muhammad auren Nabeeha ba tare da tashe-tashen hankula ba. Hajiya Rumanah ta girgiza kai. "Ba zan tsaya jiran lokaci ba. Ba zan ƙyale ta ta auri ɗana ba! Babu wata dabara da ta fi wannan! Idan kuwa hakan bai samu ba, to sai dai a kawar da ita gaba ɗaya!" Hajiya Karama ta shiga tunani. "Amma fa Hajiya, idan har za a aiwatar da hakan, dole ne a tsara komai da kyau." Ta fada a sanyaye. Don kasurguman mugaye ne suma na kata'i. Amman a zahirin gaskia suna matukar tsoron hajia rumanah Kuma shakkarta. Komai tace binta sukeyi tamkar uwar data tsugunna ta haife su.. Hajiya Rumanah ta ja tsaki. "Ke dai ku jira. Ku gani yadda zan aikata hakan ba tare da an iya gano ni ba." A zuciyarta, tana jin wani irin sanyi. Tana jin cewa wannan ne mafi dacewa. Wannan ne abin da zai saka ta samu nasara. Wannan ne zai tabbatar da cewa Zaytunah da Nabeeha ba su taba ruguza mata rayuwa ba. "Za ku gani. Zan tabbatar da cewa babu wata hanya da za su sake tsira!" Shin Hajiya Rumanah za ta iya aiwatar da shirinta? Ko kuwa wannan ne zai zama dalilin da zai kai ta ga halakar da kanta? Kuma shin Muhammad zai gano gaskiyar abin da mahaifiyar sa take aikatawa? 🤭 🎀🎀 Hajiya Zaytunah ta kasa motsi. Kamar wacce aka yi wa dukan gwiwa, ta zube a kasa, zuciyarta na harbawa da sauri. Idanunta sun kada suka yi ja, hawayen bakin ciki na cika su. “Rumanah?” Ta furta a hankali, tamkar wacce ba ta jin abin da ta fada. Rumanah? Yar uwarta ta jini. Yar yayan mahaifina. Matar Yaya Amiru . Aminiya ta tun muna yara. A rana daya aka haife mu, aka taso da mu tamkar yan biyu. A duk lokacin da aka tambaya wace ce Rumanah, sai a ce “wannan ce Zaytunah,wannan Rumanah.” Sun raba dariya, sun raba kuka, sun raba SIRRI ka har da burinsu na rayuwa. Amma yau? Ita ce ta bayar da umarnin a kama ta? Ita ce ta so a nakasta Hammad? Ita ce ta nemi a cire wa Nabeeha mutuncinta? Hajiya Zaytunah ta rike kanta da hannaye biyu. Kamar zuciyarta za ta faso KIRJIN ta. Hawaye suka tsinke daga idanunta, suka gangaro kan fuskarta. “Wai Rumanah ce? Ita ce ke kokarin ganin an kashe ni da ‘ya’yana?” Ta girgiza kai cikin matsanancin firgici. Kamar mafarki take ji. Mafarki mai cike da tsoro da tashin hankali. Idan aka ce ta fada mafarkin da zai firgita ta, wallahi ba ta taba tunanin wannan ba. Hajiya Zaytunah ta runtse ido, ta fashe da wani sabon kuka mai tsananin radadi. “Rumanah, me na miki?” Sai a lokacin ta fara tuna wasu abubuwa da suka faru a baya. Kodai tun tuni take ginin kiyayya a zuciyarta? Ta cika da tsananin mamaki! Wata zuciya ta ce mata “Idan har Rumanah ta kai ga bayar da umarnin a bata Nabeeha, hakan na nufin babu wani abu da ba za ta iya yi ba.” Zaytunah ta dago, idanunta sun yi jajir. “Dole ne a dauki mataki!” Hajiya Zaytunah ta yi shiru na tsawon lokaci, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi, tamkar zata faso kirjinta. Hawaye suka ci gaba da gangarowa daga idanunta, hannayenta sun yi sanyi, jikinta ya dauki rawa. "Rumanah?" Ta sake maimaitawa cikin rauni. "Ashe ke ce kika kulla wannan makircin? Ke ce kika so a bata Nabeeha? Ke ce kika so a nakasta Hammad?" Wani irin sanyi da radadi ya ratsa ta. Babu abinda ke kara huda zuciyarta kamar tunanin yadda ita da Rumanah suka taso tare, suka raba komai, suka rayu tamkar yan biyu. "Wai har kin kai matsayin da ba kya jin tausayin jinin ki? Har kin kai matsayin da zuciyarki ta zama kamar dutse, babu tausayi ko kadan?" Ta runtse ido, tana jin yadda numfashinta ke fita da kyar. A zuciyarta, tambayoyi sun yi mata caa. Zaytunah ta dago kai, ta share hawayen da ya cika fuskarta. Duk da bakin cikinta, zuciyarta ta fara kallon wannan matsala a wani sabon salo. Idan har Rumanah ta aikata haka, hakan yana nufin cewa akwai wani abu a zuciyarta tun tuni da ba su fahimta ba. Me ya sa ta tsane su haka? Me yasa take ganin su a matsayin abokan gaba? "Ina jin akwai wani abu da zan gano." Ta furta a hankali. Dole ne ta fahimci SIRRIN Rumanah, ta gano dalilin kiyayyar da take yi musu. Kuma kafin ta dauki mataki, dole ta tabbatar da cewa komai a fayace. Ta numfasa da kyar, ta juyo ta kalli su Gora da suka gama sanar da ita SIRRIN da suka samu. Ta yi shiru na dan lokaci, sannan ta ce da su cikin murya mai tsanani, "Kun ce min Rumanah ce ta dauke ku aiki?" Gora ya gyada kai cikin girmamawa. "Eh, Hajiya. Ita ce ta biya mu, ta ce mu tabbata mun bata miki rai. Ta ce mu yi duk mai yiwuwa domin mu tabbatar da cewa kin yi nadamar rayuwa." Wani takaici ya sake turnuke zuciyar Hajiya Zaytunah. Ta numfasa a hankali, sannan ta ce: "Ba damuwa. Na gode da gaskiyar da kuka gaya min." Ta juya tana kallon kofar da ke gabanta, zuciyarta na cike da sabbin tunani. Wannan abu ba zai kare haka ba. Dole ne ta dauki mataki. _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ **KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 14_ Captain Fawaaz ya jinjina kai, bai ce komai ba. Idanunsa sun sauka kan na’urar tracking da ke gabansa, ya tuno da sakonnin daya turawa Nabeeha, Wannan yana nufin cewa a wannan lokacin layinta yana bisa sabis, kuma hakan na iya basu damar gano inda suke. Ya matsa wani maballi a kan na'urar, ya duba taswirar da ke gabansa. Hanyar da suka bi tana da wahala, sai dai a haka ma ba zai yi kasa a gwiwa ba. Yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Ko da yake ya saba da irin wannan aiki, wannan yana da bambanci , Yana nufin ceto most beloved love of his life, Wato Nabeeha. "Kayi tracking ɗin network ɗin nata?" Lieutenant Ibrahim ya tambaya. "Eh," Fawaaz ya amsa, yana duba wani karamin screen a gefen dashboard. Ya kara danna wasu maballan sannan ya ce, "Anan sakon ya shiga, daga nan zuwa wani wuri a kusa da gabar rafin Chida." "To, akwai wata gada kusa da wannan rafi, amma an ce tana da matsala, babu wanda ke amfani da ita," Warrant Officer Suleiman ya kara da furtawa, yana duba bayanai a cikin wata ƙaramar kwamfuta. "To lallai sun bi waccan hanyar," Fawaaz ya yanke hukunci. Sai ya kara gudun motarsa a hankali, yana bin alamar da suka samu. Sauran motocin biyu da ke biye da su suma suka kara saurin tafiya, dukkansu cikin shiri. Su na ci gaba da tafiya cikin dajin, tayoyin motocin su na dannan ciyayi da ƙurar dajin. Kusan mintuna talatin suna tafiya, sai na’urar tracking ɗin ta soma nuna wani matsayi kusa da su. Zuciyar Fawaaz ta buga da sauri. "Alhamdulillah suna nan kusa," ya furta da wata murya mai ƙarfi. Yana tsayar da motarsa a hankali, sauran motocin suma suka tsaya. Dukkaninsu suka kama bindigoginsu suna shirin fuskantar duk wani haɗari. "Mu fita a hankali. Kar mu yi saurin motsi har sai mun tabbatar da yanayin da muke ciki," Fawaaz ya umarta, yana kokarin danne tsananin kwadayin da yake ji na ganin Nabeeha. Sai suka rarrafa cikin dajin da taka-tsantsan, kowannensu yana duban gefen daji. Bayan kusan minti goma da shiru-shiru, sai suka jiyo wata murya daga baya, "Da alama su ne can!" Fawaaz ya zura zooming tool. Ya na ware ido, zuciyarsa na dukan uku-uku. A cikin wata ruguwar kwantaccen ciyayi da wasu tsofaffin bishiyoyi, ya hangi wasu mutane suna zaune kusa da wata karamar bukka. A tsakiyarsu, su Nabeehan sa ce! Haj. Zaytunah tana zaune a gefe, tana rike da hannun Hammad da ke jin tsoro sosai. Nabeeha kuma tana a gefe, idonta cike da damuwa. Sai kuma wasu mutum biyu, Gora da Bala, waɗanda suke kallon gefe-gefe, suna jin wani irin damuwa. Fawaaz ya dan zaro iska daga bakinsa, yana kokarin nutsuwa. Amma a zuciyarsa, yana jin wani irin ƙarfi da ƙwazo sun lullube shi. "A shirya!" ya furta cikin sassanyar murya. "Zamu yi aiki mai tsabta. Nabeeha da sauran su na bukatar mu." Babu wanda ya musa. Sun san cewa wannan aiki ne da ba za su bari ya gaza ba. Fawaaz ya gyara rike bindigarsa, idonsa ya fi komawa kan Nabeeha. Ko da yake ba ta ganshi ba tukunna, amma ya san cewa cikin 'yan dakikoki, zai yi duk mai yiwuwa don ganin sun fita daga wannan wuri lafiya! Fawaaz ya dan sunkuya yana lura da yanayin wurin. Binciken idanuwansa ya nuna masa cewa mutanen da suka yi garkuwa da su Nabeeha ba su da yawan makamai, amma hakan ba yana nufin ba su da hatsari ba. Ya san cewa su Gora da Bala mutane ne masu dabara, kuma ba zai yi ƙasa a gwiwa wajen yaƙar su ba. Ya yi alama ga abokan aikinsa su zagaya ta bangarori daban-daban domin su mamaye yankin da dazukan uku da suka rage, kudu, gabas dana yamma, Lieutenant Ibrahim da Warrant Officer Suleiman sun kama hagu, yayin da sauran suka kama dama. Fawaaz ya cigaba da lurawa da yadda ake tafiyar da abubuwa daga inda suke.. Nabeeha tana zaune a gefen Hajiya Zaytunah, idanunta cike da damuwa. Hammad yana nan rike da hannunta, yana ta kallon gefe cike da tsoro. Gora yana tsaye kusa da Bala, yana magana da wani karamin walkie-talkie, yana kokarin tuntubar wani a waje. "Hello...." Daidai lokacin, Nabeeha ta ji zuciyarta tana wani irin bugawa. Ta rufe idanuwanta na wasu dakiku, tana jin kamar numfashinta zai dauke. Amma cikin wannan yanayi na tsoro, sai wani tunani ya fado mata… Fawaaz! Bata ankara ba, sai kawai ta ji karar wani abu yana kara kusa da su ,kamar motsin mutane cikin daji. Idanunta suka kai kan Gora, wanda shima ya ji motsin. "Me ke faruwa?" Bala ya tambaya yana kai hannu kan bindigarsa. A daidai wannan lokacin, Fawaaz ya bayar da umarni cikin walkie-talkie, "Roger that soldiers..Yanzu! Mu Shiga!" Cikin gaggawa, sojojin suka fantsama daga bangarori daban-daban! Wani dan karamin fashewar hayaki ya biyo baya, wanda ya sa Bala da Gora suka rude, suna kokarin zaro makamai. Fawaaz bai bata lokaci ba, ya shiga ta babban kofar bukkar cikin matsanancin sauri, bindigarsa a hannu, idanunsa suna kan Gora da Bala. "Kada ku motsa!" ya daka musu tsawa. Bala ya yi kokarin daga bindigarsa, amma kafin ya ankara, sai Lieutenant Ibrahim ya karbe bindigar daga hannunsa. Gora kuwa ya yi kokarin tserewa ta bayan bukkar, amma kafin ya iya, Warrant Officer Suleiman ya cafke shi da karfi, ya buga shi kasa. Fawaaz bai damu da su ba, idanunsa sun sauka kai tsaye kan Nabeeha! Zuciyarta ta buga da karfi, tana jin kamar numfashinta zai tsaya. A karo na farko, ta ji wani irin kwanciyar hankali da ta dade tana jira. Fawaaz ya taka kusa da ita, yana kallonta ido cikin ido. Babu wanda ya ce uffan. Ya mika mata hannu a hankali, idanunsa cike da nutsuwa. "Kin ji tsoro?" ya tambaye ta da murya mai laushi. Nabeeha ta girgiza kai, amma idanuwanta sun nuna cewa ta ji tsoro fiye da yadda zata iya furtawa. Ba tare da wata shakka ba, ya kama hannunta ya rike da kyau. "Don't be...Ssshhh is okayy" ya furta. A gefe guda, Hajiya Zaytunah ta runtse idanuwa, tana fitar da ajiyar zuciya. Hammad kuwa ya ruga ya rungume Captain Fawaaz da karfi, yana kuka da murna. Fawaaz ya dan matsa daga gefe, yana tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai. Sauran sojojin sun riga sun kama Gora da Bala, sun daure hannayensu da igiya, sannan suka rufe musu baki domin su guji yin hayaniya. A gefe guda, Lieutenant Ibrahim yana duba motar da masu garkuwar suka kawo, yana tabbatar da cewa babu wani abin fashewa ko tarkon da zai iya kawo hatsari. Nabeeha har yanzu tana tsaye a wurin, zuciyarta na harbawa da karfi. Idanunta sun cika da ruwaye, ba wai saboda tsoro ba, amma saboda yawan damuwar da ta sha. Har yanzu tana jin yadda hannun Fawaaz ke rike da nata , rikon da ya tabbatar mata cewa yanzu tana cikin aminci. Fawaaz ya dan sunkuya yana shafa kansa, sannan ya ce, "Su daina damunki, Zamu mika su hannun hukuma, za su fuskanci hukuncin da ya dace da su." Hammad ya dan yi shiru na wasu dakiku, sai daga baya ya jinjina kai. "Mungode, Captain brother!" Fawaaz bai ce komai ba, sai ya mike tsaye, ya nuna musu hanyar da za su bi zuwa motocin su. Sauran sojojin sun bi sawu, suna rike da Gora da Bala da aka daure su. A daidai lokacin da suka fara tafiya, sai Fawaaz ya lura da yadda Nabeeha ke tafiya a hankali, kamar wacce ba ta da kwari sosai. Bai yi wata-wata ba, ya dan riko hannunta, yana tafiya tare da ita. "Kin gaji?" ya tambaya, amma yana kallonta cikin ido. Ta dan yi murmushi kadan, sannan ta ce, "Kadan dai." Sai da suka soma tafiya kafin Nabeeha ta iya furta wani abu. Fawaaz bai ce komai ba. Amma a zuciyarsa, ya san cewa zai iya yin komai don ganin cewa ba ta sake fuskantar irin wannan hatsari ba har abada. Zuciyar Fawaaz tana daka da sauri fiye da yadda ya saba ji. Hannunsa yana rike da nata, amma har yanzu ba ya jin hakan ya wadatar. Idanunsa na tafiya a fuskarta, yana nazarin ta, yana neman wani alamun ciwo ko wahala. Idonta ya lumshe na wani lokaci, sannan ta bude su a hankali, tana jin yadda dumin hannunsa ke ratsata. A duk tsawon rayuwarta, bata taba ganin Fawaaz a irin wannan yanayin ba. Idonsa na bayyana damuwa da tsananin kauna, amma duk da haka yana kokarin boye hakan a karkashin miskilancinsa. Ya dan tsugunna kadan gabanta, yana kallonta sosai. “Nabeeha…” ya kira sunanta da wata murya da bata saba ji ba, murya mai cike da soyayya da fargabar rasa ta. Ta dago idonta ta kalle shi. “Yaya Fawaaz…” Ya dan rufe idonsa na dan lokaci, yana kokarin daidaita numfashinsa, saboda yadda sanyayyar muryarta Mai kama da ana busa sarewa ta doki kofofin kunnuwansa. sannan ya bude su da karfi, kamar wanda ya yanke shawarar cewa ba zai kara boye abin da yake ji ba. “Ban taba jin tsoro irin na yau ba.”Ya fada a hankali, amma tare da zurfi..''Ban taba tunanin za a dauke ki ba, ban taba jin fargabar rasa wani kamar yadda na ji akan ki ba.” Nabeeha ta kalle shi da sauri, zuciyarta na bugawa da karfi. Tana iya jin gaskiyar da ke cikin muryarsa. Bata taba jin Fawaaz yana magana da irin wannan zafin rai ba. Ya dan sosa keyarsa yana jin yadda zuciyarsa ke tashi da wani irin yanayi da bai saba ba. “Kin san me yasa na san daidai inda kike?” Ya tambaya, yana kallon cikin idanunta. Ta girgiza kai a hankali. Ya dan sauke ajiyar zuciya, sannan ya saki murmushi kadan, “Saboda na riga na turawa zuciyarki saƙo.” ya fada cikin zuciyarsa. Sai Kuma yace, "Tracking device" a fili.. Idanunta suka cika da mamaki. “Saƙon dama turo fa?”ta furta a kasan zuciyar ta "Ohh" tace a fili.. Ya gyada kai. “Eh. Na san da cewa idan har da gaske akwai soyayya a zuciyarki, to da zarar kin karanta sakon nan, sai zuciyata ta ja ni zuwa inda kike.”ya furta a kasan makoshi .. "You're loved..." Hawaye suka cika idon Nabeeha. Bai taɓa furta mata soyayya a fili ba, amma wannan maganar ta fi duk wata soyayya da take zato. Fawaaz ya zare safar hannunsa a hankali, ya cusa mata acikin hannunta. Saboda yadda sanyi ke kadata. Ya zare coat din jikinsa ya dora mata akan kafadarta yana dubanta cikeda kulawa yace, “Nabeeha…” ya furta sunanta da wata irin murya mai daɗi. “Kin ji wani rauni a jikinki? Sun miki wani abu?” Ta girgiza kai cikin sanyin jiki. “A’a… Ni lafiya lau nake.” Amma Fawaaz bai yarda da hakan ba. Ya matsa kusa da ita, yana dubanta sosai, yana nazarin yadda jikinta yake. “Babu inda kike jin ciwo?” Ya sake tambaya, yana kiran sunanta cikin kwantar da murya. Nabeeha ta dan lumshe idonta, sannan ta ce, “Kai ne kake bani ciwo, Fawaaz.” ta furta batare da ta sani ba.. Ya dan zaro ido kadan, zuciyarsa na harbawa. “Me kike nufi?” Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta bude idanunta ta kalle shi. "Babu.” Fawaaz ya dan yi shiru, yana jin kalmomin nata na ratsa zuciyarsa. A koyaushe yana miskilanci, yana boye abubuwan da yake ji. Amma yau, ba zai iya musanta gaskiya ba. Ya dan yi murmushi a hankali, sannan ya ce, “Kin san wani abu?” Ta girgiza kai, tana jiran jin me zai fada. Ya dan matsa kusa da ita sosai, har numfashinsa yana haduwa da nata. “A duk tsawon lokacin da nake boye abin da ke raina, sai da aka zo kusa da dauke ki ne na fahimci cewa… Babu sauran boyewa.” Ta lumshe ido, tana jin nauyin kalmomin nasa a zuciyarta. “Da gaske kake,Yaa Fawaaz?” ta tambaya cikin wata murya mai taushi. Ya murmusa, yana dubanta da wani irin so da babu wanda ya taba gani a idanunsa. “Ba zan taba barinki ba, Nabeeha.” Ya furta da karfi. “Koda zai zame min zunubi, 🤭koda zai haifar min da matsala, koda duniya za ta juya min baya, ba zan taba barinki ba.” A lokacin, wani hawayen farin ciki ya sulale daga idon Nabeeha. Tana kallon Fawaaz, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin shauki da bata taba ji ba. Bata taba sanin cewa shi ma yana jin haka ba. Bata taba sanin cewa kaunar da take masa na da girman haka ba. A hankali, ta daga hannunta, ta matse yatsunta tana jin yadda dumin tafin hannunta ke bata kwanciyar hankali. “Nagode, Yaa Fawaaz.” Ya dan lumshe ido, yana jin yadda wadannan kalmomi suka bugi zuciyarsa fiye da komai. Bai taba jin farin ciki irin wannan ba. A yanzu, ba shi da shakka. Nabeeha ita ce ransa. Ita ce zuciyarsa. Ita ce rayuwarsa.kuma daga yau, ba zai taba barinta ba. _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 14_ Captain Fawaaz ya jinjina kai, bai ce komai ba. Idanunsa sun sauka kan na’urar tracking da ke gabansa, ya tuno da sakonnin daya turawa Nabeeha, Wannan yana nufin cewa a wannan lokacin layinta yana bisa sabis, kuma hakan na iya basu damar gano inda suke. Ya matsa wani maballi a kan na'urar, ya duba taswirar da ke gabansa. Hanyar da suka bi tana da wahala, sai dai a haka ma ba zai yi kasa a gwiwa ba. Yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Ko da yake ya saba da irin wannan aiki, wannan yana da bambanci , Yana nufin ceto most beloved love of his life, Wato Nabeeha. "Kayi tracking ɗin network ɗin nata?" Lieutenant Ibrahim ya tambaya. "Eh," Fawaaz ya amsa, yana duba wani karamin screen a gefen dashboard. Ya kara danna wasu maballan sannan ya ce, "Anan sakon ya shiga, daga nan zuwa wani wuri a kusa da gabar rafin Chida." "To, akwai wata gada kusa da wannan rafi, amma an ce tana da matsala, babu wanda ke amfani da ita," Warrant Officer Suleiman ya kara da furtawa, yana duba bayanai a cikin wata ƙaramar kwamfuta. "To lallai sun bi waccan hanyar," Fawaaz ya yanke hukunci. Sai ya kara gudun motarsa a hankali, yana bin alamar da suka samu. Sauran motocin biyu da ke biye da su suma suka kara saurin tafiya, dukkansu cikin shiri. Su na ci gaba da tafiya cikin dajin, tayoyin motocin su na dannan ciyayi da ƙurar dajin. Kusan mintuna talatin suna tafiya, sai na’urar tracking ɗin ta soma nuna wani matsayi kusa da su. Zuciyar Fawaaz ta buga da sauri. "Alhamdulillah suna nan kusa," ya furta da wata murya mai ƙarfi. Yana tsayar da motarsa a hankali, sauran motocin suma suka tsaya. Dukkaninsu suka kama bindigoginsu suna shirin fuskantar duk wani haɗari. "Mu fita a hankali. Kar mu yi saurin motsi har sai mun tabbatar da yanayin da muke ciki," Fawaaz ya umarta, yana kokarin danne tsananin kwadayin da yake ji na ganin Nabeeha. Sai suka rarrafa cikin dajin da taka-tsantsan, kowannensu yana duban gefen daji. Bayan kusan minti goma da shiru-shiru, sai suka jiyo wata murya daga baya, "Da alama su ne can!" Fawaaz ya zura zooming tool. Ya na ware ido, zuciyarsa na dukan uku-uku. A cikin wata ruguwar kwantaccen ciyayi da wasu tsofaffin bishiyoyi, ya hangi wasu mutane suna zaune kusa da wata karamar bukka. A tsakiyarsu, su Nabeehan sa ce! Haj. Zaytunah tana zaune a gefe, tana rike da hannun Hammad da ke jin tsoro sosai. Nabeeha kuma tana a gefe, idonta cike da damuwa. Sai kuma wasu mutum biyu, Gora da Bala, waɗanda suke kallon gefe-gefe, suna jin wani irin damuwa. Fawaaz ya dan zaro iska daga bakinsa, yana kokarin nutsuwa. Amma a zuciyarsa, yana jin wani irin ƙarfi da ƙwazo sun lullube shi. "A shirya!" ya furta cikin sassanyar murya. "Zamu yi aiki mai tsabta. Nabeeha da sauran su na bukatar mu." Babu wanda ya musa. Sun san cewa wannan aiki ne da ba za su bari ya gaza ba. Fawaaz ya gyara rike bindigarsa, idonsa ya fi komawa kan Nabeeha. Ko da yake ba ta ganshi ba tukunna, amma ya san cewa cikin 'yan dakikoki, zai yi duk mai yiwuwa don ganin sun fita daga wannan wuri lafiya! Fawaaz ya dan sunkuya yana lura da yanayin wurin. Binciken idanuwansa ya nuna masa cewa mutanen da suka yi garkuwa da su Nabeeha ba su da yawan makamai, amma hakan ba yana nufin ba su da hatsari ba. Ya san cewa su Gora da Bala mutane ne masu dabara, kuma ba zai yi ƙasa a gwiwa wajen yaƙar su ba. Ya yi alama ga abokan aikinsa su zagaya ta bangarori daban-daban domin su mamaye yankin da dazukan uku da suka rage, kudu, gabas dana yamma, Lieutenant Ibrahim da Warrant Officer Suleiman sun kama hagu, yayin da sauran suka kama dama. Fawaaz ya cigaba da lurawa da yadda ake tafiyar da abubuwa daga inda suke.. Nabeeha tana zaune a gefen Hajiya Zaytunah, idanunta cike da damuwa. Hammad yana nan rike da hannunta, yana ta kallon gefe cike da tsoro. Gora yana tsaye kusa da Bala, yana magana da wani karamin walkie-talkie, yana kokarin tuntubar wani a waje. "Hello...." Daidai lokacin, Nabeeha ta ji zuciyarta tana wani irin bugawa. Ta rufe idanuwanta na wasu dakiku, tana jin kamar numfashinta zai dauke. Amma cikin wannan yanayi na tsoro, sai wani tunani ya fado mata… Fawaaz! Bata ankara ba, sai kawai ta ji karar wani abu yana kara kusa da su ,kamar motsin mutane cikin daji. Idanunta suka kai kan Gora, wanda shima ya ji motsin. "Me ke faruwa?" Bala ya tambaya yana kai hannu kan bindigarsa. A daidai wannan lokacin, Fawaaz ya bayar da umarni cikin walkie-talkie, "Roger that soldiers..Yanzu! Mu Shiga!" Cikin gaggawa, sojojin suka fantsama daga bangarori daban-daban! Wani dan karamin fashewar hayaki ya biyo baya, wanda ya sa Bala da Gora suka rude, suna kokarin zaro makamai. Fawaaz bai bata lokaci ba, ya shiga ta babban kofar bukkar cikin matsanancin sauri, bindigarsa a hannu, idanunsa suna kan Gora da Bala. "Kada ku motsa!" ya daka musu tsawa. Bala ya yi kokarin daga bindigarsa, amma kafin ya ankara, sai Lieutenant Ibrahim ya karbe bindigar daga hannunsa. Gora kuwa ya yi kokarin tserewa ta bayan bukkar, amma kafin ya iya, Warrant Officer Suleiman ya cafke shi da karfi, ya buga shi kasa. Fawaaz bai damu da su ba, idanunsa sun sauka kai tsaye kan Nabeeha! Zuciyarta ta buga da karfi, tana jin kamar numfashinta zai tsaya. A karo na farko, ta ji wani irin kwanciyar hankali da ta dade tana jira. Fawaaz ya taka kusa da ita, yana kallonta ido cikin ido. Babu wanda ya ce uffan. Ya mika mata hannu a hankali, idanunsa cike da nutsuwa. "Kin ji tsoro?" ya tambaye ta da murya mai laushi. Nabeeha ta girgiza kai, amma idanuwanta sun nuna cewa ta ji tsoro fiye da yadda zata iya furtawa. Ba tare da wata shakka ba, ya kama hannunta ya rike da kyau. "Don't be...Ssshhh is okayy" ya furta. A gefe guda, Hajiya Zaytunah ta runtse idanuwa, tana fitar da ajiyar zuciya. Hammad kuwa ya ruga ya rungume Captain Fawaaz da karfi, yana kuka da murna. Fawaaz ya dan matsa daga gefe, yana tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai. Sauran sojojin sun riga sun kama Gora da Bala, sun daure hannayensu da igiya, sannan suka rufe musu baki domin su guji yin hayaniya. A gefe guda, Lieutenant Ibrahim yana duba motar da masu garkuwar suka kawo, yana tabbatar da cewa babu wani abin fashewa ko tarkon da zai iya kawo hatsari. Nabeeha har yanzu tana tsaye a wurin, zuciyarta na harbawa da karfi. Idanunta sun cika da ruwaye, ba wai saboda tsoro ba, amma saboda yawan damuwar da ta sha. Har yanzu tana jin yadda hannun Fawaaz ke rike da nata , rikon da ya tabbatar mata cewa yanzu tana cikin aminci. Fawaaz ya dan sunkuya yana shafa kansa, sannan ya ce, "Su daina damunki, Zamu mika su hannun hukuma, za su fuskanci hukuncin da ya dace da su." Hammad ya dan yi shiru na wasu dakiku, sai daga baya ya jinjina kai. "Mungode, Captain brother!" Fawaaz bai ce komai ba, sai ya mike tsaye, ya nuna musu hanyar da za su bi zuwa motocin su. Sauran sojojin sun bi sawu, suna rike da Gora da Bala da aka daure su. A daidai lokacin da suka fara tafiya, sai Fawaaz ya lura da yadda Nabeeha ke tafiya a hankali, kamar wacce ba ta da kwari sosai. Bai yi wata-wata ba, ya dan riko hannunta, yana tafiya tare da ita. "Kin gaji?" ya tambaya, amma yana kallonta cikin ido. Ta dan yi murmushi kadan, sannan ta ce, "Kadan dai." Sai da suka soma tafiya kafin Nabeeha ta iya furta wani abu. Fawaaz bai ce komai ba. Amma a zuciyarsa, ya san cewa zai iya yin komai don ganin cewa ba ta sake fuskantar irin wannan hatsari ba har abada. Zuciyar Fawaaz tana daka da sauri fiye da yadda ya saba ji. Hannunsa yana rike da nata, amma har yanzu ba ya jin hakan ya wadatar. Idanunsa na tafiya a fuskarta, yana nazarin ta, yana neman wani alamun ciwo ko wahala. Idonta ya lumshe na wani lokaci, sannan ta bude su a hankali, tana jin yadda dumin hannunsa ke ratsata. A duk tsawon rayuwarta, bata taba ganin Fawaaz a irin wannan yanayin ba. Idonsa na bayyana damuwa da tsananin kauna, amma duk da haka yana kokarin boye hakan a karkashin miskilancinsa. Ya dan tsugunna kadan gabanta, yana kallonta sosai. “Nabeeha…” ya kira sunanta da wata murya da bata saba ji ba, murya mai cike da soyayya da fargabar rasa ta. Ta dago idonta ta kalle shi. “Yaya Fawaaz…” Ya dan rufe idonsa na dan lokaci, yana kokarin daidaita numfashinsa, saboda yadda sanyayyar muryarta Mai kama da ana busa sarewa ta doki kofofin kunnuwansa. sannan ya bude su da karfi, kamar wanda ya yanke shawarar cewa ba zai kara boye abin da yake ji ba. “Ban taba jin tsoro irin na yau ba.”Ya fada a hankali, amma tare da zurfi..''Ban taba tunanin za a dauke ki ba, ban taba jin fargabar rasa wani kamar yadda na ji akan ki ba.” Nabeeha ta kalle shi da sauri, zuciyarta na bugawa da karfi. Tana iya jin gaskiyar da ke cikin muryarsa. Bata taba jin Fawaaz yana magana da irin wannan zafin rai ba. Ya dan sosa keyarsa yana jin yadda zuciyarsa ke tashi da wani irin yanayi da bai saba ba. “Kin san me yasa na san daidai inda kike?” Ya tambaya, yana kallon cikin idanunta. Ta girgiza kai a hankali. Ya dan sauke ajiyar zuciya, sannan ya saki murmushi kadan, “Saboda na riga na turawa zuciyarki saƙo.” ya fada cikin zuciyarsa. Sai Kuma yace, "Tracking device" a fili.. Idanunta suka cika da mamaki. “Saƙon dama turo fa?”ta furta a kasan zuciyar ta "Ohh" tace a fili.. Ya gyada kai. “Eh. Na san da cewa idan har da gaske akwai soyayya a zuciyarki, to da zarar kin karanta sakon nan, sai zuciyata ta ja ni zuwa inda kike.”ya furta a kasan makoshi .. "You're loved..." Hawaye suka cika idon Nabeeha. Bai taɓa furta mata soyayya a fili ba, amma wannan maganar ta fi duk wata soyayya da take zato. Fawaaz ya zare safar hannunsa a hankali, ya cusa mata acikin hannunta. Saboda yadda sanyi ke kadata. Ya zare coat din jikinsa ya dora mata akan kafadarta yana dubanta cikeda kulawa yace, “Nabeeha…” ya furta sunanta da wata irin murya mai daɗi. “Kin ji wani rauni a jikinki? Sun miki wani abu?” Ta girgiza kai cikin sanyin jiki. “A’a… Ni lafiya lau nake.” Amma Fawaaz bai yarda da hakan ba. Ya matsa kusa da ita, yana dubanta sosai, yana nazarin yadda jikinta yake. “Babu inda kike jin ciwo?” Ya sake tambaya, yana kiran sunanta cikin kwantar da murya. Nabeeha ta dan lumshe idonta, sannan ta ce, “Kai ne kake bani ciwo, Fawaaz.” ta furta batare da ta sani ba.. Ya dan zaro ido kadan, zuciyarsa na harbawa. “Me kike nufi?” Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta bude idanunta ta kalle shi. "Babu.” Fawaaz ya dan yi shiru, yana jin kalmomin nata na ratsa zuciyarsa. A koyaushe yana miskilanci, yana boye abubuwan da yake ji. Amma yau, ba zai iya musanta gaskiya ba. Ya dan yi murmushi a hankali, sannan ya ce, “Kin san wani abu?” Ta girgiza kai, tana jiran jin me zai fada. Ya dan matsa kusa da ita sosai, har numfashinsa yana haduwa da nata. “A duk tsawon lokacin da nake boye abin da ke raina, sai da aka zo kusa da dauke ki ne na fahimci cewa… Babu sauran boyewa.” Ta lumshe ido, tana jin nauyin kalmomin nasa a zuciyarta. “Da gaske kake,Yaa Fawaaz?” ta tambaya cikin wata murya mai taushi. Ya murmusa, yana dubanta da wani irin so da babu wanda ya taba gani a idanunsa. “Ba zan taba barinki ba, Nabeeha.” Ya furta da karfi. “Koda zai zame min zunubi, 🤭koda zai haifar min da matsala, koda duniya za ta juya min baya, ba zan taba barinki ba.” A lokacin, wani hawayen farin ciki ya sulale daga idon Nabeeha. Tana kallon Fawaaz, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin shauki da bata taba ji ba. Bata taba sanin cewa shi ma yana jin haka ba. Bata taba sanin cewa kaunar da take masa na da girman haka ba. A hankali, ta daga hannunta, ta matse yatsunta tana jin yadda dumin tafin hannunta ke bata kwanciyar hankali. “Nagode, Yaa Fawaaz.” Ya dan lumshe ido, yana jin yadda wadannan kalmomi suka bugi zuciyarsa fiye da komai. Bai taba jin farin ciki irin wannan ba. A yanzu, ba shi da shakka. Nabeeha ita ce ransa. Ita ce zuciyarsa. Ita ce rayuwarsa.kuma daga yau, ba zai taba barinta ba. _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 15_ Fawaaz ya kura wa Nabeeha ido, kamar zai tsotse ta da kallon kauna. Duk da sojojin nasa na tsaye a gefe suna jiran umarninsa, duk da akwai sauran aikinsa na tabbatar da tsaro, babu komai a duniyarsa a wannan lokacin face ita. Zuciyarsa na bugawa da sauri, ya shafi kumatunsa hankali, yana jin yadda dumin fatarsa ke ratsa tafin hannunsa. “You don’t know how much I was scared, Nabeeha,” ya furta da wata murya mai cike da zurfin shauki. Idanunta suka dan kakkalo kwalla. “I knew you would come for me,” ta furta a hankali, murya na rawa. Ya dan lumshe ido, sannan ya bude su da sauri. “Even if the whole world stood against me, I would have still come for you.” Ta runtse ido, tana jin yadda nauyin kalmomin nasa ke shigarta, suna watsa mata dumin da ba ta taba ji ba. Ya matse hannunsa , yana jin yadda zuciyarsa ke harbawa da soyayya. “I thought I had lost you…” ya karasa cikin wata murya mai nauyi, kamar wanda yake kokarin hadiye damuwa. Ta girgiza kai a hankali. “No, Yaa Fawaaz. I was waiting for you.” Ya saki ajiyar zuciya, yana jin wani irin sanyi yana lullube shi. Bai taba jin irin wannan soyayya ba. Bai taba jin cewa yana bukatar wani a rayuwarsa haka ba. Amma yau, a gabanta, yana jin komai a gare shi ita ce. A hankali, sai ya lumshe ido na dan wani lokaci, yana kokarin danne fushin da yake ji akan mutanen da suka dauketa.. Ya bude idonsa, sai ya dan matsa gefe, ya gyara tsayuwarsa. A hankali ya waiwayo ya kalli Hajiya Zaytunah, wadda take tsaye tana kallonsa da wani irin yanayi na mamaki. Bai ce komai ba, sai ya sunkuya kadan cikin girmamawa... Da kunyar data gama dabaibaye shi. Sai a lokacin ya tuna da baranbaramar da yayi. Na rike mata hannun 'ya gam sai kache zaa kwace masa ita. Ya sosa keyarsa yana sake sunkuyawa. “Ina wuni, Aunty..” Ta kalle shi, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da mamaki. A lokacin da ta tuno wannan yaron a baya, sai ta dauka mutum ne mai yawan fushi da fadin kai da rashin kulawa. Amma a yau, sai ta fahimci cewa akwai wani zurfi mai girma a halayensa. “Lafiya lau, Captain Fawaaz. Allah ya saka da alheri.” Ya dan gyada kai a hankali, sannan ya juya ya kalli Hammad, wanda ke tsaye yana kallonsa da murmushi. “senior man. Da fatan kalau kake?” Ya tambaye shi da wata murya mai laushi. Hammad ya gyada kai, yana murmushi. “Eh, Yaya.. Ba wani abu.. mungode Allah ya saka da alkhairi.” Fawaaz ya dan shafi kansa a hankali, yana jin wani irin yanayi na tausayin su duka. Sun shafe lokaci cikin tsoro da damuwa, amma yanzu suna nan cikin kwanciyar hankali. Ya dubi duka mutanen fashin da aka kamo na sauran dazukan. Ya sauke katuwar ajiyar zuciya, ya tabbatar da cewa babu wanda ke da wata gagarumar matsala. Sai ya kara wa Nabeeha kallon ƙarshe, kafin ya juya zuwa ga abokan aikinsa. “Mission accomplished.” Ya furta da kwarin gwiwa. “Let’s go home.... Soldiers. Weldone" Hajiya Zaytunah ta kalli Fawaaz da idanu masu cike da gaskiya da nauyin abin da take shirin furtawa. Ta numfasa, sannan ta ce da murya mai taushi tana Mai Saka hannu tana nuni da gora da bala.. "Fawaaz, akwai wani abu da nake son ka sani. Wadannan mutanen nan guda biyu, Gora da Bala—tabbas sun kasance cikin waɗanda suka yi fashin da suka kama mu tun farko. Amma daga baya, su ne suka taimaka mana muka kubuta. Sune suka cire mu daga hannun ‘yan fashin, suka dawo da mu inda kuka same mu a cikin dajin nan. Da awata bukka aka ajiye mu ana azabtar da mu." Ta kalli Gora da Bala, wadanda ke tsugunne, fuskokinsu a kasa cike da fargaba da shakku. Daga bisani ta ci gaba, "Tabbas sun yi mana adalci. Duk wasu munanan ayyukan azabtarwa da aka bukaci su aikata mana, sun ki aikata su. A zahiri, sun butulce wa shugaban su ne don su taimake mu. Da ba don su ba, da har yanzu muna hannun ‘yan fashin, ko ma fiye da haka..." Ta yi shiru na wani lokaci, tana kallon Fawaaz kamar tana neman karbuwa daga gare shi. Sannan ta ce da murya mai tausayawa, "Don haka, ina rokonka, a kyale su. Na san cewa ba mugaye bane. Sun yi abin da za a iya kira da sadaukarwa domin su ceto mu. Ina neman afuwarka a bar su su tafi, domin sun riga sun zabi kyakkyawan hanya a lokacin da suka yanke shawarar taimakonmu." Fawaaz ya saurara ba tare da ya ce uffan ba. Idanunsa sun kada, yana nazari. Daga can gefe, Bala da Gora suka ji zuciyarsu na bugawa da karfi, suna jiran hukuncin da zai biyo baya... Don fawaaz din bana wasa bane. Fuskar sa yadda ya hade rai yana duban su goran zakasan soja ne mai cikakken Iko.. Fawaaz ya dauki lokaci yana nazari, yana kallon yadda Hajiya Zaytunah ke magana da cikakkiyar gamsuwa. Idanunsa sun sauka kan Gora da Bala, wadanda suka kasa hada ido da shi, kamar suna jiran kaddarar su. Daga can gefe, Hammad ya matsa kadan ya ce da rauni, "Kuyi tunani sosai. Idan suka ci gaba da zama a hannun mu, me zai faru da su? Shugaban yan fashin har basu sako yayi yace an bashi umarni a raba sister Nabeeha da mutuncin ta..Kuma goran ya saka da bala amma ba wanda ya amince yayi acikin su. Da kansa shugaban ya yanke gashin Ammi..... " "What? A raba nabeeha da me?" Fawaaz ya fada yana cakumo wuyan Hammad tamkar shi yayi masa lefin. Can ya sake shi ya juya yana naushin mota. Hajia zaytunah tayi kansa tana bashi hakuri tare da kwantar masa da hankali, "Ai Allah bai basu dama ba. Allah bai amince ba. Ba abunda ya faru da ita. Basu kai ga cinma burin su ba. Waɗannan yara gora da bala sune suka kubutar da mu." Fawaaz bai ce komai ba. Sai dai yana jin zuciyarsa na yarda da bayanan Hajiya Zaytunah. Idan da gaske wadannan mutanen sun butulcewa ‘yan fashin domin ceton su, hakan na nufin akwai ragowar mutunci a zuciyarsu. "Alhamdulillah..." Ya ambata yana sauke zuciya.. Ya dago kai ya dubi Bala, sannan ya watsa wa Gora kallon bincike. "Kun san abin da kuka aikata. Ku ne kuka taimake su, amma kuma kun kasance tare da su tun farko. Me yasa?" Bala ya gyada kai, yana kokarin samun karfin guiwa. "Mun shiga rayuwar fashi da makami ne saboda rayuwa ta tilasta mana. Ba mu da mafita a baya. Amma bayan mun ga irin wahalar da mutane ke sha a hannun manyan mu, zuciyarmu ta girgiza. Ba mu iya ci gaba da kallon hakan ba. Mun san cewa abu ne mai hadari, amma mun zabi taimakon su." Gora ya daga kai da sauri ya kara da cewa, "Kuma da mun so mu tafi tare da ku, amma kun san cewa idan muka bayyana kanmu a wancan lokacin, ba wanda zai yarda da mu. Mun yanke shawarar bin bayanku daga nesa, domin mu tabbatar kun tsira lafiya." Fawaaz ya sake duban Hajiya Zaytunah, sannan ya dauki tsawon minti yana tunani. A karshe, ya numfasa ya ce, "Ku tafi. Get lost.." Gora da Bala suka dago da mamaki. "Ka yafe mana?" Fawaaz ya girgiza kai, yana kallon su da tsananin natsuwa. "Ba wai an yafe muku ba ne, amma kun nuna cewa kuna da damar gyarawa. Ku fita daga nan kafin wasunmu su canza shawara." Hajiya Zaytunah ta yi murmushi a hankali, zuciyarta ta saki da jin dadin yadda lamarin ya kaya. Bala da Gora suka mike da sauri, suna mai godiya, kafin su ruga cikin daji da sauri, suna fatan samun sabuwar rayuwa. Hajiya Zaytunah ta kalli Fawaaz ta ce, "Ka dauki babban mataki yau. Ka nuna halin jagora." Fawaaz bai amsa ba, sai dai ya ci gaba da kallo cikin nesa, zuciyarsa cike da tunani.ya juya yayi mata murmushi kawai yana Jan kasan leban sa.. domin wata gagarumar kunyar ta ce take dimauta shi.. Bayan Gora da Bala sun bar wurin, shiru ya ratsa tsakanin su Hajiya Zaytunah da Fawaaz. Kowa na nazarin abin da ya faru. Hammad ya numfasa da nauyi, sannan ya ce, "Da ace wasu ne, ba za su taba barinsu su tafi ba. Amma gaskiya sun cancanci a basu wannan damar." Hajiya Zaytunah ta gyada kai cikin gamsuwa. "Hakane. Rayuwa ba ta da tabbas. Watakila wata rana, su ma su ga damar taimakon wani." Fawaaz ya mike tsaye, yana yamutsa gira kamar wanda ke jin wani abu a zuciyarsa. "Ba wai na basu dama ne saboda sun cancanta ba. Na basu dama ne domin sun fi wasu mutanen da muka hadu da su kyau. Kuma na fi son su yi tafiyarsu fiye da barinsu a nan suna ci mana zarafi ko su zama barazana." Hajiya Zaytunah ta fahimci cewa ko da yake Fawaaz bai furta kai tsaye ba, amma zuciyarsa ta karaya da yanayin da Gora da Bala suka shiga. Idan da Fawaaz ne a matsayinsu, da watakila shima ya dauki irin matakin da suka dauka. Hammad ya kada kai yana murmushi. "Ko dai yaya ne, ai hakan ya nuna kai mutum ne mai tunani da adalci." Fawaaz bai ce komai ba. Ya dan matsa gefe yana duba yanayin wurin. "Muna bukatar mu koma cikin gari da wuri. Wannan wurin bai da aminci sosai." Hajiya Zaytunah ta gyada kai. "Hakane. Allah yasa mu dache" Fawaaz ya yi shiru, yana nazari. Yana jin yadda tsananin gajiya ya lulluɓe shi, amma bai so ya bayyana hakan. Duk da haka, yana fahimtar cewa hakan ne kawai mafita. Daga can gefe, Hammad ya dago yana kallon sararin samaniya. "Da alama, gobe zata kasance wata sabon kamawa." Hajiya Zaytunah ta murmusa. "Allah ya sa hakan ya zama mafi alkhairi." Su Fawaaz suka shirya don barin dajin. Hajiya Zaytunah ta daura gyale a kanta, fuskarta cike da nutsuwa, yayin da Hammad ya ja tsaki yana yamutsa fuska. "Ba zan ce komai ba, amma daji bai dace da ni ba," ya fada yana shafa wuyansa. " idan na koma gida, sai na kwana rana biyu ina barci inshaa Allah.. God I'm soo tired." Fawaaz ya dan kalle shi daga gefen ido. "Ka ce ka fi so a bar ka a hannun ‘yan fashin?" Hammad ya girgiza kai da sauri. "What? Noo! Omo.. A’a fa! Na gode wa Allah da muka tsira. Amma dai... gaskiya sai nayi sati ina cin abinci mai kyau don dawo da kuzari. " Hajiya Zaytunah ta yi murmushi. "Allah ya kai mu lafiya." Ba tare da bata lokaci ba, suka fara tafiya cikin dajin, suna bin hanyar da za ta mayar da su cikin gari. Duk da cewa ba su san ko wani hadari zai sake zuwa ba, sun yarda cewa komai zai tafi daidai... _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ * *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 16_ A lokacin da motocin suka soma tafiya cikin dajin, an samu nutsuwa sosai fiye da daa. Hasken fitilar motocin na haskaka hanya, yana bayyana ƙurar da take tashi a kan titin ƙasa. Kowa a cikin motar ya yi shiru, kowanne da tunanin da yake yi a zuciyarsa. Fawaaz yana riƙe da sitiyari, amma hankalinsa ya kasa kwanciya. Duk da cewa sun samu Nasara, har yanzu zuciyarsa ba ta bar jin wani irin nauyi ba. Idanunsa sun dan kalle ta cikin madubin motar, yana kallon Nabeeha da ke zaune a baya kusa da Hajiya Zaytunah. Ta jingina kanta da jikin kujera, idonta a rufe, amma Fawaaz ya fahimci ba barci take ba. Sai dai ko kawai tana kokarin dan hutawa ne ko tunani. Hajiya Zaytunah ta juyo ta dubi Fawaaz, idonta cike da godiya. "Allah ya saka da alkhairi, Captain. Da baku zo da wuri ba, da ko me zai faru damu, Allah ne kadai ya sani... Don mun kasa tsarewarwa waɗannan mugayen mutanen da ke ta bibiyarmu" Fawaaz ya dan sauke numfashi, yana jin nauyin wannan magana. Ba don wani abu ba, sai don yasan irin hatsarin da su Nabeeha suka tsallake. "Mun gode wa Allah,.. Inshaa Allah su Kuma waɗannan da muka kama duka zasu Sha tambayoyi bayan mun hora su." ya amsa a taƙaice. Bayan wani lokaci, sai Nabeeha ta bude idonta a hankali. Duk da cewa idonta yana nuna alamun gajiya, amma akwai wani irin natsuwa a fuskarta. Ta juyo tana kallon Fawaaz, yana tuƙi hankalinsa kwance. "Da gaske ka yi tracking din wayata ne har ka gano inda muke?" ta tambaya da wata murya mai rauni, amma da alamun sha’awa. Fawaaz bai juyo ba, amma ya gyada kai. "Eh." Nabeeha ta dan yi murmushi, sannan ta ce, "Mashaa Allah ." Ya ɗan danne numfashinsa, bai san dalilin da yasa zuciyarsa ta daka da karfi ba a lokacin da ta fadi hakan. Amma sai ya ce, "Dole ne na tuna da ke, domin nasan kina cikin hatsari." Ya furta a zuciyar sa.. "Kasan sun kwace wayoyin mu sun Kona su duka?" ta kara tambaya, tana so ta ji ko zai kara wani abu. Ya dan yi shiru, yana tunanin amsar da zai bayar. Bai saba bayyana abubuwan da yake ji ba, ko yawan amsa tambayoyi musanman game da ita, kuma yanzu ba shi da niyyar yin hakan. "Allah ya kyauta , abu mafi muhimmanci shine mun same ku lafiya." Nabeeha ta dan tabe baki, amma bata ce komai ba. Ta san halinsa , miskili ne. Sai dai yadda ya zo domin cetonsu, yadda ya damu da ita fiye da kowa, hakan kadai ya ishe ta sanin cewa akwai wani abu mai girma a zuciyarsa. Tafiyar su ta cigaba cikin shiru na wani lokaci, har suka fara fita daga cikin dajin. Lokacin ya kusa wayewa, iskar safiya tana kadawa cikin sanyin daren da ya kusa karewa. Hammad ya juyo yana duban Captain Fawaaz, yana murmushi. "Captain, ka zama jarumin labarina!" ya fada da dariya. Duk wanda ke cikin motar ya dara, har da su Lieutenant Ibrahim da ke gaba. Fawaaz ya girgiza kai, yana murmushi a hankali. Nabeeha kuwa sai ta lumshe ido, zuciyarta cike da natsuwa. Wannan daren ba zai taba goguwa daga zuciyarta ba. Kuma ko da Fawaaz ba zai iya furtawa ba, amma ta san cewa akwai wani abu a tsakaninsu da babu wanda zai iya musantawa. Motocin sojojin suka ci gaba da tsula gudu a kan titin ƙasa, suna barin dajin Arewa a baya. Ana iya jin sautin gurnanin tayoyin motar suna neman nutsuwa a ƙasa mai laushi. Iskar safiya tana kadawa, tana ɗauke da dumin farkon rana. Nabeeha ta jingina da kujerar motar, tana kallon yadda titin ke ratsa ta cikin duhun da ya rage a sararin samaniya. Kowane numfashinta yana ɗauke da jin daɗin tsira, amma a lokaci guda, zuciyarta ta cika da tunani. Idanunta sun kai ga Captain Fawaaz, wanda ke riƙe da sitiyari da kwanciyar hankali kamar yadda ya saba. A zuciyarta, tana tambayar kanta, shin wannan shi ne Fawaaz ɗin da ta sani? Miskilin da ke guje mata? Amma yau, ya tsaya tsayin daka ya cetota. Hakan ya sa zuciyarta cika da wani yanayi da ba ta iya bayyanawa ba. A gefe guda, Hajiya Zaytunah ta juya tana duban Fawaaz, sannan ta sauke ajiyar zuciya. "Allah ya saka muku da alheri, Captain," ta furta cikin gamsuwa. "Kai da mutanenka kun cika jarumai. Allah ya biya ku da gidan aljanna" "Aameen" su lieutenants suka amsa.. Fawaaz bai ce komai ba, sai ya gyada kai kaɗan, yana mai mayar da hankali kan tuƙinsa. Amma idan aka kalli fuskarshi da kyau, za a iya hango wani irin natsuwa a cikinta. A baya, Hammad yana kallon sojojin da suka jera a motocin baya ta cikin taga. Cikin farin ciki, ya ce, "Kai! Kamar a fim! Captain Fawaaz da sojojinsa sun zo sun ceci talakawa daga hannun azzalumai!" Duk wanda ke cikin motar ya dara. Nabeeha ta ɗan yi dariya, amma ta lura da cewa Fawaaz bai ce komai ba. A hankali, ta matsa kusa da shi, ta ɗan sassauta muryarta. "Yaya jikinne??" Ya ɗan kalleta ta cikin madubi, sannan ya maida dubansa gaba. "Lafiya lau." Nabeeha ta taɓe baki . "Kamar ba ka da lafiya." Fawaaz ya sauke numfashi, ya ɗan rage gudun motar. Yana jin tambayarta tana tasiri a zuciyarsa, amma bai so ya bayyana hakan ba. A ƙarshe, ya furta cikin wata murya mai taushi fiye da yadda ta zata, "Wani lokaci, akwai abubuwan da mutum bai taɓa tunanin zai yi ba, amma sai gobe ta zo da nata labarin." Nabeeha ta yi shiru tana kallonsa, tana ƙoƙarin fahimtar abin da yake nufi. "Me kake nufi?" ta tambaya. Fawaaz ya ɗan yi shiru kafin ya ce, "nothing much, Babu komai." Nabeeha ta dan murmusa. Tana jin cewa akwai wani abu da yake ji a zuciyarsa, amma kamar kullum, Fawaaz na ɓoye komai. Amma hakan ba zai hana ta fahimtar cewa akwai abu mai ƙarfi da ke tattare da shi ba. "Na sani." Ta furta a hankali. Ya ɗan kalleta, alamar tambaya a fuskarsa. "Na sani cewa ka damu da ni." Ta fada cikin zuciyar ta., Fawaaz bai ce uffan ba. Amma yadda ya kalleta da yadda numfashinsa ya sauya, hakan kadai ya tabbatar mata da cewa ta fadi gaskiya. A hankali, motar ta ci gaba da tafiya, har sai da suka soma shiga birni. Rana ta fara fitowa a sararin samaniya, tana bayyana sabon safiya, amma a gare su, wannan safiya sabuwa ce ta rayuwa, ta fahimta, da kuma ƙaddara da ba su san yadda za ta kaya ba. Fawaaz ya kalli titin gaba, yana tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai. An dade ana tafiya, amma yanzu gida yana kusa. Ya ji wani nauyi yana sauka daga zuciyarsa, kamar wanda aka daga masa wata babbar kaya da ta dade tana damunsa. Ya zaro wayarsa daga aljihunsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa a hankali. Lokaci ne na kiran mahaifinsa, Major General Dawud, don sanar da shi cewa suna kan hanya, kuma suna nan kusa da isowa. A lokacin da ya danna lambar, ba a dauka ba sai da aka buga sau biyu. Yana cikin shirin sake kira, sai ga amsa daga dayan bangaren. "Fawaaz?" Muryar mahaifinsa ta fito da karfi, cike da zurfin tunani da kulawa. Akwai wani nauyi a cikin sautin sa, wanda ya tabbatar da irin damuwar da yake ciki tun lokacin da aka fara wannan abu. Fawaaz ya dan lumshe idanu, yana jin yadda numfashinsa ke fita da sauki. "Morning sir!! gamunan muna hanya, za mu iso gida yanzu, Insha Allah." Shiru ya biyo bayan hakan, kamar Major General Dawud yana kokarin fahimtar cikakken abinda ya ji. Bayan wasu ‘yan dakiku, sai ya sauke wata ajiyar zuciya. "Kun iso gari... Sun kubuta? " "Eh,Baba. Mun tsira, babu wata matsala. Su Aunty Zaytunah dasu Hammad suna lafiya. Muna cikin motocin mu yanzu, kuma muna gab da shigowa cikin anguwa." A daya bangaren, an sake yin shiru. Sai daga baya aka ji muryar Major General Dawud yana cewa, "Allah ya muku albarka.. ka gayawa lieutenants Ina godia kwarai. Akwai gwaggwabar tagomashi da zai biyo musu da yardar Allah. Tell them I say weldone...." Fawaaz yayi murmushi yana duban su lieutenants yace da mahaifin sa, "Inshaa Allah sir. Allah ya Kara maka lafiya da nisan kwana mai albarka. Aameen.." "Aameen muna jiran ku," Major General Dawud ya kara fada, muryarsa na nuna cewa yana cikin tsananin shirin ganin su.. "Zamu iso cikin mintuna goma zuwa sha biyar," Fawaaz ya fada. "Allah ya kiyaye hanya," Major General Dawud ya kara fada, kafin ya katse. "Aameen" kit major general ya katse Kiran. Fawaaz ya dubi su lieutenants yana sanar musu abunda mahaifinnsa yace ya gaya musu. Nan da nan Kuma wayoyin kowannen su Sako ya shigo masa daga major general dawud mafia. "Weldone soldier! Your Legacy Will Live Forever, Long after the battles are won, your bravery and dedication will be remembered. You are not just a soldier, you are a hero, a protector, and a symbol of strength. Stand tall, keep the fire of duty burning, and never forget the difference you make. Check your account balance. Allah ya Saka da alkhairi" Suka fara murna baki daya da farin ciki... Fawaaz yayi murmushi bayan lieutenant ya karanto masa sakon.. sai murna sukeyi sunata godiya. Don tuni har wasunsu sun fara Jin alerts na kudi daya tuttura musu.. Fawaaz ya lumshe idanu na dan lokaci, yana jin yadda gajiyarsa ke sauka a hankali. Ya san cewa komai bai kare ba, amma akalla sun tsira daga wani babban hatsari. Ya juyo yana duban Hajiya Zaytunah, wadda ke zaune cikin motar da kwanciyar hankali. Duk da alamun gajiya a fuskarta, akwai murmushi mai cike da natsuwa a saman lebbanta. "Su baba suna jiranmu," Fawaaz ya fada mata. Hajiya Zaytunah ta gyada kai a hankali. "Allah ya nuna mana lokacin da za mu samu kwanciyar hankali bayan wannan wahala." Hammad ya dan ja numfashi mai zurfi yana gyara zamansa. "Wai ma gida dai ya kusa kenan?" Fawaaz ya kalle shi daga gefe. "Idan ba canzawa akayi ba, eh, mun kusa isa gida.... Senior man" Hammad ya sake gyara zamansa yana fadin, "Toh, idan muka iso, sai a samo min abinci mai kyau. Na gaji da wannan yunwar!" Suka sake Saka dariya baki daya... Banda Fawaaz da bai ce komai ba, sai ya juyo ya kalli titin gaba. Motar na cigaba da tafiya a hankali, tana ratse cikin titunan da suka saba bi. Yanzu dai, ko menene zai biyo baya, sun kusa isa gida........ _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 17_ MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RESIDENCE: Tunda motocin suka ratsa kofar shigowa gidan, farin ciki ya bayyana a fuskar kowa. Wutar fitilu masu launi na musamman sun haska ko'ina, suna bai wa ginin kamannin gata da martaba. Dawakan tsaro suna ta kai-komo, kowannensu cikin shirin ko-ta-kwana, amma a wannan rana komai ya sauya, dukansu suna murmushi, wani ma har yana daga hannu yana gaisawa da su. A lokacin da motocin suka tsaya, kafin ma kowa ya fito, Gwaggo Hafsatu ta riga ta fito da sauri daga cikin gida, ba tare da la’akari da shekarunta ko nauyin da ke kanta ba. Har lokacin da suke bude kofar mota, ta riga ta tarbe su da hawaye a idanuwanta, na farin ciki da godiya ga Ubangiji... Ta durkusa tana yin sujjadar godiya ga Allah madaukakin sarki da ya kubutar dasu hajiya Zaytunah.. Da kyar ta iya jira har suka fito daga cikin motar. Da zarar Hajia Zaytunah ta fito, sai Gwaggo Hafsatu ta rungume ta da karfi, kamar ba za ta sake ta ba. Ta dinga shafa kanta tana duban fuskarta cike da tausayawa da kaunar da ke cikin zuciyarta. "Ina godiya ga Allah! Allah mai iko ne, Allah mai taimako ne!" Ta fada tana sharar hawaye, hannuwanta biyu na rike da hannun Hajia Zaytunah. Idanunta sun cika da soyayya lokacin da ta juyo ta rungume Nabeeha da Hammad. "Ya Allah, Alhamdulillah! Kun dawo lafiya, ko? Babu ciwo? Babu komai, ko?" "Eh, Gwaggo, mun dawo lafiya," Nabeeha ta fada a hankali, muryarta cike da kauna. "Allah mai iko! Allah mai cikakken iko!" Gwaggo Hafsatu ta sake nanatawa, tana jin kamar zuciyarta za ta fashe da farin ciki. Daga gefe, Fawaaz ya tsaya cikin nutsuwarsa, kamar kullum, yana kallonsu da ido mai cike da kulawa. Duk da rashin sakewarsa, akwai wani yanayi na kwanciyar hankali a tattare da shi. Bai yi wani yunƙurin shiga cikin tarbar ba, amma idanunsa sun bayyanar da yadda zuciyarsa ke farin ciki da ganin sun dawo lafiya. Gwaggo Hafsatu ta juyo da murmushi tana kallonsa. "Fawaaz, Na gode maka sosai. Na gode da komai, da kulawa, da fahimta, da jarumtarka." Maimakon ya amsa da kalmomi, sai ya kada kai yana mai nuna cewa babu komai. Sai dai idanunsa sun furta abin da bakinsa ya kasa fadi. Gaba daya gidan ya kaure da murna. 'Yan gidan, masu aiki, hatta ma'aikatan tsaro sun yi tattaki zuwa bakin babban falon don nuna farin cikinsu. Ga kamshin abinci daga cikin gidan, alamar an dafa girki na musamman don tarbar su. A falon, kowa ya zauna cike da nishadi. Hammad ya dinga yawo da fara’a yana gaisawa da kowa, shi kadai yana cikin karamin nishadi. Nabeeha kuwa ta zauna kusa da mahaifiyarta, tana dubanta da kulawa. Gwaggo Hafsatu tana ta duban Hajia Zaytunah da kulawa. "Ya jikinki? Yana ciwo? Me kike bukata?" Zaytunah ta yi murmushi mai rauni. "Alhamdulillah, Gwaggo. Sai dai radadi kadan ne." "Allah ya sawwake, kin ji?" Gwaggo Hafsatu ta fada tana shafa bayanta da kuncinta. Cikin shafar bayan zaytunah sai ga dan kwali ya fadi cike da tsananin tashin hankali gwaggo Hafsatu ta hango keyar da aka saisaye da gashi.. hawaye suka cika idanunta. Gwaggo Hafsatu ta dago tana duban Fawaaz. "Subhan'Allah... Dawuda, Kaga Zaytunah an aske gashin ta. Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Waɗannan mutane da sukai wannan abu Ubangiji Allah ya saka muku Allah ya bi muku hakkin ku.. Gwara mu tashi mu tafi asibiti kafin gabatar da komai...Har a tabbatar da lafiyar su. Ina so mu rankaya asibiti, ko da babu wata matsala, A dai tabbatar." Fawaaz ya kada kai yana amincewa. "Tohm gwaggo . Hakan yayi" ya fada a takaice. "Subhan'Allah. Ai a hakan ma gwaggo an auna arziki. Ubangiji Allah yasa karshen wahalar kenan ... Bayaga haka babu wani abun na daban ko?" Cewar major general dawud. Yana duban hajia zaytunah. Hajiya Zaytunah tayi hanzarin girgiza kanta da sauri ta Kuma ce, "Babu wani abu na daga labari marar dadi. Sai dai duka da sukayi mana sun azabtar da mu sosai.. Duk kuwa da umarni ne daga wadanda suka turo su acewar su. Don dayan umarnin nema Allah ya tsare bai faru ba. Kusan akansa nema wasu daga cikin yan fashin suka bijere maganar shugaban su. Suka ketare suka kubutar da mu" "Subhan'Allah Subhan'Allah..ai idan Allah yarda duk masu hannu acikin wannan abu zamu kamasu red handed. Shin wani abu ne wannan da basu kaiga aikatawa ba Allah ya takaita ku ka kubata?" Hajia Zaytunah ta dubi major general dawud tana tunanin yadda zata fada. Don maganar batasan fadar tama saboda tsananin muninta, Falo ya ɗauki shiru bayan da Major General Dawud ya yi tambaya mai nauyi, "Zaytunah, me ya faru da ku?" Gwaggo Hafsatu ta gyara zama a kujerarta, zuciyarta tana tafasa da fargaba. Nabeeha da Hammad kuwa sun natsu a gefen mahaifiyarsu, suna jiran jin yadda zata bayyana abin da suka fuskanta. Fawaaz yana gefe, yana kallon fuskar Hajia Zaytunah da idanun da ke cike da zurfin nazari. A farkon fara magana, Hajia Zaytunah ta runtse idonta na dan lokaci, kamar wadda take kokarin tattara karfin gwiwa. Zuciyarta tana bugawa da karfi, wani irin tsoro da ba ta san yana ciki ba yana neman turnuke ta. Sai ta bude idanu, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta soma magana da muryar da ke sanyi, amma mai nauyi. "Sun kama mu... sun yi mana azaba fiye da tunanin dan adam," ta fara, tana jin yadda muryarta ke rawar jiki. "Sun daure hannuwanmu da kafafuwan mu da igiya mai karfi... kamar wata dabba da ba ta da iko da jikinta. Sun toshe mana baki da zani don kada mu iya kiran wani." Duk wanda ke cikin falon ya zura mata idanu, babu wanda ya motsa. Ta ɗauki wani numfashi mai nauyi, hawaye na taruwa a idonta. "Sun... sun aske min gashi. Ba don......" Sai Kuma tayi shiruh ta kalli Gwaggo Hafsatu da Major General Dawud, idanunta cike da hawaye. Kamar tana sake jin raɗaɗin abin da suka fuskanta a hannun miyagun mutanen da suka kama su. Ta ɗan tsaya na wani lokaci, kamar mai tattara ƙarfin gwiwa, sannan ta ci gaba da magana. "Sun kama mu a dare, babu wanda ya san inda aka kai mu. Sun daure hannuwan mu da kafafuwan mu da igiya mai ƙarfi, kamar wasu dabbobi da ba su da iko da jikin su. Sun toshe mana baki da zani don kada mu iya kiran wani. Munyi ƙoƙarin tserewa, amma igiyar da suka ɗaure mu da ita tana matse ƙasusuwanmu har ba ma iya motsawa. "A lokacin da suka kawo Nabeeha da Hammad a gabana, zuciyata ta karye. Na ga yadda suka dinga dukansu. Hammad yana ihu yana kiran sunana, yana kuka, amma babu wanda ya ji shi. Idanunsa sun kumbura saboda dukan da suka masa. Nabeeha kuwa, ba zan taɓa mantawa da yadda wani daga cikin su ba ya taka ruwan cikinta..Sun yi ƙoƙarin raba ta da mutuncinta! Amma Allah bai nufa hakan ya faru ba! Ta runtse idanu, hawayenta na sauka "Nabeeha ta yi ta kokawa da karfinta, tana kuka tana ihu. A karshe, daya daga cikinsu ya daga hannu zai mare ta, amma wani daga cikinsu ya hana shi. Har yanzu, ban san dalilin da yasa ya hana ba, amma yana daya daga cikin dalilan da yasa bata fuskanci mafi munin abin da suka nufa ba." Fawaaz ya matse hannayensa, jijiyoyin wuyansa sun fito. Idanunsa sun kada da tsananin fushi, amma bai ce uffan ba. Kawai yana saurara, zuciyarsa na tafasa. Hajia Zaytunah ta ci gaba, "Sun ci mutuncinmu da kalmomi, sun dinga zaginmu suna dariya. Sun ce babu mai kubutar pda mu, sun ce za su kashe mu a ranar da suke so. Amma Allah ya kawo mana agaji a hannun wasu da ba mu yi tsammani ba, wasu daga cikin su, wato su Gora da Bala." Tana ambaton sunayen, sai Gwaggo Hafsatu ta ɗago kai da sauri. "Gora da Bala?" "Eh, su ne suka taimaka mana. Duk da cewa suna cikin 'yan ta'adda, amma sun nuna jinƙai. Sun nemo mana abinci da ruwa. Suna boye mu daga sauran miyagun. A ƙarshe, su ne suka sassauta igiyoyin da suka ɗaure mu da su, har suka samar mana hanya muka tsere daga hannunsu." Tana gama faɗin haka, sai ta sunkuyar da kai, tana jin kamar duk tsawon lokacin da suka shafe a hannun miyagun ya dawo da ita cikin wannan dakin. Shiru ya biyo baya, amma shiru mai cike da nauyi. Kowa yana jin girman azabar da suka sha. Fawaaz ne ya fara magana, cikin muryar da ke cike da ƙarar zuciya. "Wadanda suka aikata wannan azaba ba za su tsira ba." Major General Dawud bai ce komai ba, amma idanunsa sun nuna alamar hukunci. Ba zai bari su tsira ba. Gwaggo Hafsatu kuwa ta rungume Hajia Zaytunah cikin kulawa da ƙauna. "Alhamdullillah, Kun tsira da ran ku, Sannan baa yi Wa nabeeha wannan danyen aiki ba. kuma wannan shine abu mafi muhimmanci." Haka dai suka cigaba da tattaunawa. Kafin daga bisani sukayiyyi wanka bayan sunci abinci suka dauro tsarki. Suka rama sallolin da basuyi ba .. sannan suka rankaya zuwa asibiti kamar yadda gwaggo tabada shawara. A cikin motocin soja da ke rakiyarsu, suka isa asibitin cikin girmamawa. Likitoci da nas-nas sun riga sun shirya don karbar su, saboda Fawaaz da Major General Dawud sun tabbatar an sanar da su kafin isowarsu. An fara da gwaje-gwaje na cikakken lafiya. An duba Hajia Zaytunah sosai, aka tabbatar babu wata matsala babba, sai dai radadin da ta ke ji a wurin da aka yanke mata gashin kanta. Don haka, likitocin suka yi mata karin ruwa don karfafa jikinta, sannan suka bata magungunan rage radadi. Nabeeha da Hammad suma an yi musu gwaje-gwaje, aka tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya. Sai dai an musu allurori na kariya da magungunan antibiotics don hana kamuwa da wata cuta sakamakon wahalar da suka sha. Gwaggo Hafsatu ta cigaba da nuna damuwarta har sai da likita ya tabbatar mata da cewa babu wata matsala. Bayan an kammala komai, suka fito daga asibitin, kowa cikin kwanciyar hankali da godiya ga Allah. A cikin motocin da ke tafiya a nutsuwa, ana jin saukar zuciya a tare da kowa. A zuciyar kowa, sun san cewa rayuwa za ta cigaba, kuma a wannan lokaci, sun san cewa akwai sabuwar fata da sabuwar soyayya da ke ci gaba da bayyana a zuciyoyinsu. Duk da SIRRIN da ke tsakaninsu, akwai haske a gaban su. Da zarar da motocinsu suka iso gida daga asibiti, sabuwar rayuwa ta soma fantsama cikin zuciyar kowa. Daga yanayin yadda Gwaggo Hafsatu ta sake rungume Hajia Zaytunah a lokacin da suka fito daga mota, har zuwa murmushin da ke fuskarta, ya nuna yadda take jin daɗin dawowarta gida cikin kwanciyar hankali. "A yanzu, sai dai mu gode wa Allah," Gwaggo Hafsatu ta furta, tana kallon su Nabeeha da ke gefenta. "Kun ga, kowa ya dawo gida lafiya." Wannan kalma ta sa Hammad ya saki murmushi yana jin wani irin nutsuwa yana ratsa shi. Duk wahalar da suka sha, sun samu nasarar komawa cikin iyalansu. Nabeeha kuwa tana gefen mahaifiyarta, tana ta duba ta da kulawa. Tun daga asibiti har zuwa gida, ba ta dena tambayarta yadda take ji ba. Fawaaz kuwa daga gefe yake, kamar kullum, yana kallon komai cikin nutsuwa da kamun kai. Bai ce komai ba, amma idanunsa sun nuna yadda zuciyarsa ke jin daɗin ganin kowa cikin farin ciki. Da suka shiga falon, an sake jin daɗi a zuciyar kowa. Wurin ya cika da haske da kamshin turaren gida na kamfanin YERWA INCENSE AND MORE.. A gefen babban falon, manyan kujeru ne masu taushi da sanyin fata, suna ba da kwanciyar hankali ga wanda ya zauna a kansu. Masu aiki sun taru suna murna, kowannensu na nuna farin ciki. Sun shirya kayan marmari da shayi mai zafi, don su samu nutsuwa bayan dawowarsu daga tafiya. Daga nesa, motsin shigowar Major General Dawud. Da alama ya dade yana jiransu su dawo, saboda yana sanye da kaya masu sauki fiye da na jikinsa dazu, yana nuna cewa ya fi mayar da hankali ga tarbarsu a yau fiye da komai. Da ya karaso, idanunsa suka fara sauka kan mahaifiyarsa. Daga nan sai ya dubi Hajia Zaytunah, wadda ke zaune kusa da 'ya'yanta. Kallon da ya yi mata ya nuna cewa yana jin tausayinta, amma ya fi jin daɗin ganin ta cikin koshin lafiya. Ya numfasa kadan, sannan ya kalli su gaba ɗaya. "Mun gode wa Allah. Dukkanin ku kun sha wahala, amma Allah ya kawo mana sauki." Hajia Zaytunah ta gyaɗa kai cikin jin daɗi. "Allah ya bar zumunci." Gwaggo Hafsatu ta yi murmushi tana duban ɗanta. "Dawuda, zan sake cewa, mun gode maka. Kai da Fawaaz, da dukkan sojojin da suka bada gudunmawa wajen kubutar da yaran nan da mahaifiyarsu." Ya girgiza kai cikin girmamawa. "Gwaggo na.., wannan aikina ne. Kuma na san duk wanda ke cikin wannan gida zai yi hakan idan da dama ta samu... Sannan sauran yan fashin da aka kama su da yardar Allah zamubi diddigin gano Wanda yasa suka aikata wannan abu. Sannan zamu hora su sosai zasu sha dukan sojoji sannan zamu dauki tsattsauran mataki akan su inn shaa' Allah" Fawaaz ya gyada kai kadan. Duk da cewa bai fiye magana ba, yana jin irin godiyar da kowa ke yi a ransa. 🎀🎀 Bayan wannan rana, gidansu ya cika da kwanciyar hankali da farin ciki. Duk da cewa akwai abubuwan da ba a gama fahimtarsu ba, amma babu shakka, sun shiga wani sabon mataki na rayuwa. Daga bangaren Fawaaz kuwa, da sauran sojoji karkashin Dawud Mafia suna ci gaba da aiki don tabbatar da cewa babu wata barazana da ka iya sake samun su. A gefe guda kuwa, akwai sabbin soyayyar da ke tasowa a hankali. Duk da cewa Fawaaz bai taɓa furta wani abu ba, amma yadda yake kulawa da Nabeeha ba boyayyen abu ba ne. A wasu lokuta, idan Nabeeha ta tashi daga zaune, idanunsa kan bita har ta fita daga falo. Idan kuma tana kusa da mahaifiyarta, yana lura da yadda take yi mata kulawa da so. A ranar da Gwaggo Hafsatu ta lura da hakan, sai ta saki murmushi tana gyara zaninta. Ta kalli Nabeeha da ke gefen mahaifiyarta sannan ta kalli Fawaaz. "Allah ya shiga cikin lamuran mu. Ya zaba mana abunda yafi alkhairi ," ta furta a hankali, tana jin cewa lokaci ne kawai zai nuna yadda za a shirya kaddarar da ke tafe. _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ ** *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 18_ Koda suka koma gidan su bayan sun bar gidan alhaji Uzairu , Hajiya Rumanah ta ajiye hijabinta sannan ta nufi sashen Alhaji Amiru. A tsaye ta tarar da shi a kan sallaya, yana karanta azkar cikin nutsuwa. Ta dan tsaya daga nesa tana kallonsa, sannan ta nisa da kyau kafin ta karasa kusa da shi. "Alhaji," ta kira shi da wata murya mai rauni. Ya dago ya dubeta, ba tare da ya ce komai ba. Sai da ta sunkuya ta zauna a gefen kujerar dake sashen nasa, sannan ta ci gaba da magana cikin kissa da kisisina. "Gabana yana ta tsananta bugawa. Har yanzu ba mu da wani bayani a kan Hajiya Zaytunah da yaranta?" Ta dan yi shiru kadan, tana nazarin fuskarsa. Alhaji Amiru ya ajiye tesbihinsa, yana me gyara zamansa. Fuskar nan tasa da ba a cika fassara ainihin abinda ke cikinta ba, ya dauki lokaci kafin ya dago ya kalleta. "Me ya sa kike tambayar hakan a yanzu, eh rumanah?" Ya tambaya cikin yanayi mai cike da taka tsantsan. Hajiya Rumanah ta dan gyara zama, tana wasa da zoben hannunta. "Alhaji, shekara da shekaru muka dauka ba tare da sanin inda suka shiga ba. Kuma kai da kanka ka ce a lokacin ba sai mun ci gaba da bincike ba. Amma yanzu... yanzu abubuwa sun fara daure min kai. Ba ka ganin lokaci yayi da ya kamata mu san halin da suke ciki?" Alhaji Amiru ya zuba mata ido, yana nazarin ta da kyau. A fili yana jin tsananin nauyin wannan tambaya, domin kuwa akwai SIRRIN da bai son ya bude. Ya daure fuska, sannan ya ce cikin kakkausar murya, "Rumanah, ki daina yawo da tunani mara amfani. Idan lokaci yayi, Allah zai bayyana komai." Hajiya Rumanah ta runtse idanu, tana jin wani yanayi na takaici yana ratsa zuciyarta. A ranta, ta san akwai wani abu da Alhaji Amiru bai fada mata ba, amma ba ta da ikon matsa masa don jin ainihin gaskiyar lamarin. Bayan Hajiya Rumanah ta tashi ta bar sashen nasa, Alhaji Amiru ya jingina da kujerarsa, yana kallon sararin dakin kamar mai neman amsar wata tambaya. Ya lumshe idanu, yana jin nauyin tunanin da maganganunta suka jefa shi ciki. "Har yanzu ba mu da labarin Hajiya Zaytunah da 'ya'yanta?" Wannan tambaya tana da nauyi a zuciyarsa. Tun kafin ta tambaye shi, wannan batu yana damunsa, amma yana kokarin rufe shi da tunanin cewa lokaci ne kawai bai kai ba. Amma me yasa Hajiya Rumanah ta kawo maganar yanzu? Shin tana jin wani abu ne? Ya sauke ajiyar zuciya. Idan har za a waiwaya baya, babu shakka, Hajiya Zaytunah da 'ya'yanta sun bace a duniya kamar ba su taɓa wanzuwa ba. Bai taba ganin wata alama da ke nuna inda suka shiga ba, kuma babu wanda ya taba kawo musu wata kwakkwarar magana a kansu. Amma zuciyarsa tana tsananta bugawa a duk lokacin da aka ambaci sunanta. A wani bangaren zuciyarsa, yana jin wani mugun nauyi. Yana sane da irin matsin da Zaytunah ta shiga kafin tafiyarta. Yana sane da halin da ta bar gidan kanin nasa a ciki, da irin yadda abubuwa suka rikice mata. Amma ko da yake, hakan ba ya nufin yana son ci gaba da wannan bincike da Hajiya Rumanah ke kokarin tunzura shi akai. Ya dafe goshinsa, yana jin wani iri. Idan har Zaytunah tana raye, ina take? Shin tana can tana rayuwa cikin kunci da wahala, ko kuwa lokaci ne kawai ya jefa ta cikin duhun da babu mai iya ganinta? Kuma idan har tana raye, shin za ta taba yafe musu abin da ya faru? Ya gyara zamansa, zuciyarsa na sake nauyaya. Idan da akwai wani abu daya ke tsoro a rayuwarsa, to yana tsoron wani lokaci ya zo da ahalin zasu fuskanci Zaytunah. Ya san idan hakan ta faru, ba zai iya boye duk wata damuwarsa ba. 🎀🎀🎀🎀 A tsakar dare, dakin Hajiya Rumanah ya dauki shiru, sai karan AC da ke busa iska a hankali. Ta juyi a kan gadonta, zuciyarta cike da damuwa, amma har yanzu barci ya gagara daukarta. Wayarta ta fara vibration, sai karar shigowar kira ta ratsa cikin dakin. A firgice ta bude idanu, zuciyarta na harbawa da sauri kamar mai shirin tsallake KIRJIN ta. Ta kai hannu ta dauki wayar daga gefen filo, ba tare da ta duba sunan mai kiran ba, ta amsa cikin murya mai sanyi, kamar wadda aka taso daga mafarki. "Waye?" Ta tambaya, muryarta na nuna alamun rashin kwanciyar hankali. A dayan bangaren, an dan yi shiru na ‘yan dakiku kafin wata murya mai cike da tsoro da gaggawa ta karanto mata, "Hajiya... Nine! Na tsere! Su duka sun shiga hannu! Tawagar fashi an tarwatsa su, kuma wadanda kika saka a sace, sojoji sun kubutar da su!" Zuciyarta ta harba da karfi, hannunta na tsananta zufa. Ta dan daka tsalle daga kwanciyarta, tana jin wani irin jiri na neman dibarta. "Me kake nufi? Su waye suka shiga hannu?" Ta tambaya, cikin wata irin murya da ta kasa boye gigicewarta. "Yan uwana, duka an kama su! Ni kadai ne na tsira, kuma na bar garin gaba daya. Hajiya, na yanke shawarar sanar da ke, don ki san cewa shirin ya rushe. Mutanen da kika saka a sace, sun kubuta!" Wayar ta kubce daga hannunta, ta fado a kan gadon. Idanunta suka firfito waje, zuciyarta na bugawa kamar za ta tsage KIRJIN ta ta fito. Ji take tamkar iska ta daina ratsawa cikin huhunta. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un...!" Ta furta a hankali, hannunta na kerma. Ta kama kanta da duka hannayenta, tana jin yadda gumi ke keto mata kamar wadda aka tsoma cikin ruwa. Asirinta yana kokarin tonuwa! Idan har sojoji sun kama su, babu shakka za su tona mata asiri! Ta dauki wayarta da sauri, tana kokarin sake jin cikakken bayani, amma sai ta fahimci cewa mutumin ya kashe wayarsa. Ta danna lambar a gaggauce, amma ba ta shiga. Cikin tashin hankali, ta mike daga gadon, zuciyarta na lugude kamar ana dukan ganga a cikinta. Ta fara tafiya a rude a cikin dakin, tana rikita kanta da tunani. "Me zan yi? Ya Allah, me zan yi?" Hannu ta daura a kanta, tana jin tamkar duniyar ta ruguzo mata. Idan aka kama ta, menene makomarta? Me Alhaji Amiru zai ce? Ya za a yi idan wannan magana ta fito fili? Ta durkushe a kan kafafunta, jikinta na kerma tamkar wadda zazzabi ya rufe. Idan wani ya ganta a wannan lokaci, babu shakka zai dauka cewa ta haukace! Tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi, yana kokarin tarwatsewa. Ashe, yau ce ranar da asirinta zai tonu? Wayar ta ta Kara dubawa tana Kiran ainihin number mutumin daya hadasu da yan fashin... Ta sanar masa komai tamkar suna ganin juna yadda take labarta masa. Shiru ya ratsa tsakanin su. Duk da cewa ba ta ganin fuskar wanda take magana da shi, amma ta san cewa wannan labari ya razana shi. Hannunta na kerma, zuciyarta na cigaba da bugawa da karfi. "Me kike nufi, Hajiya?" Muryar namijin ta sauya, akwai tsoro da damuwa a cikinta. "Na ce sojoji sun kama su! Mutumin da ya kira ni yanzu ya ce tawagar fashi an tarwatsa su! Idan har sojoji sun kama su, ba shakka za su tona asirina! Dole ne mu dauki mataki kafin lokaci ya kure!" Wani guntun shiru ya sake shiga tsakaninsu, sannan murya mai cike da taka tsantsan ta ce: "Hajiya Rumanah, kina nufin ba a samu wanda ya kubuta ba?" "Mutum daya ne ya tsira! Kuma ya ce ya bar garin gaba daya. Amma ka san me hakan ke nufi? Idan sojoji suka matsa wa wadanda aka kama, ba shakka za su fadi komai!" Ta sake matsa wayar a kunnenta, zuciyarta na ci gaba da harbawa. Idan sojoji suka kama shi, kuma suka matsa masa, zai iya tona sunanta da duk wata alaka da take da wannan shiri. "Dole mu nemi hanyar dakatar da binciken nan." Muryarta ta fito da karfi fiye da yadda ta zata. "Hajiya, ai kin san wannan abu ba mai sauki bane. Idan har su sojoji sun riga sun kama su, to kuwa abu ya fi karfinmu." "Baka gane bane?! Idan aka bincike su, kuma suka fadi sunana fa? Ka san me hakan ke nufi? Na gama, na mutu! Kuma ba ni kadai ba, hatta kai ma wannan abu zai shafe ka!" Tayi tsit na ‘yan dakiku, tana kokarin daidaita tunaninta. "Yanzu haka Alhaji Amiru bai san komai ba," ta furta a hankali, kamar tana magana da kanta. "Idan kuwa ya gano...!" Sai ta dafe kanta, zuciyarta na lugude. Tun daga wannan rana, komai zai iya sauyawa. Ta san halin Mai gidan nata Alhaji Amiru, mutum ne mai tsananin taka tsantsan da mutunci, kuma yana da karfin iko. Idan ya gano cewa ita ce ta shirya sace mutanen da aka cece, me zai faru? A lokaci guda, ta ji wani irin faduwar gaba. Idan ta gaza hana wannan bincike cigaba, to kuwa za ta iya rasa komai! "Dole ne mu dauki mataki yanzu!" Ta kara nanatawa, da muryar da ta nuna ba za ta amince da wani shiru ba. "Me kike so muyi, Hajiya?" Muryar namijin ta dawo da taka tsantsan. Ta dan yi shiru na ‘yan dakiku, sannan ta furta cikin murya mai cike da karfin hali, "Dole ne mu dauki matakin da zai hana wannan bincike kaiwa garemu. Kuma dole ne a gaggauta!" Jikinta yana kerma, zuciyarta na bugawa, amma yanzu ta san cewa ba ta da wani zabi. Asirinta yana kokarin tonuwa, kuma dole ne ta dauki matakin da zai hana hakan faruwa. Tirqashi!!! _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ * *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:19_ Jin shiru daga dayan bangaren ya tabbatar mata da cewa maganarta ta yi tasiri. Dole su dauki mataki, kuma dole su gaggauta kafin lokaci ya kure. "Hajiya, ina jin tsoron cewa..." "Kada ka ce min haka! Idan muka tsaya muna tsoro, to fa kowa zai sha da kansa!" Ta katse shi da wata irin kasala a muryarta. Ta tashi daga inda take zaune, ta soma yawo a dakin, kafafunta suna bugawa da sauri a kan falon dakin kamar wadda take kokarin watsa duk wata damuwa da ke zuciyarta. "Mun riga mun shiga, babu hanyar janyewa. Idan mun yi sake, sai dai mu shirya da kanmu zuwa gidan yari!" A dayan bangaren, namijin ya sauke ajiyar zuciya. Sai can ya ce, "To me kike ganin za a yi?" "Binciken dole ne ya tsaya! Kamar yadda muka saba, dole ne mu hada hannu da wanda zai iya murkushe wannan magana kafin ta fita waje." "Amma Hajiya, wannan binciken ba karamin abu bane. Idan har su sojoji ne suka sa hannu, ai kinsan ba lallai ne a iya hana su ba." "Ba su ne matsalata a yanzu ba" Ta katse shi, tana kokarin hadiye tashin hankalinta. "Babban abin da ke gabana shi ne, ina fargabar cewa mai gidah na zai iya jin wani abu! Idan ya fara bincike, to kuwa babu shakka zai gane komai!" Da zarar ta ambaci sunan Alhaji Amiru, sai shiru ya sake biyo bayan su. Kamar kowane lokaci, wannan sunan yana da nauyi, domin duk wanda ya san shi, ya san cewa ba mutum ne da za a iya yaudara da sauki ba. Idan ya gano cewa matarsa tana da hannu a cikin wannan danyen aiki, babu shakka zai dauki mataki. Kuma ita ta san cewa matakin ba zai zama mai kyau ba! "Hajiya," murya mai cike da taka tsantsan ta sake bayyana, "ko kin tabbata babu wani da ya riga ya sanar da shi wani abu?" Wani irin sanyi ya ratsa ta. Ta ji wani irin jiri yana neman daukarta. Idan har akwai wanda ya riga ya sanar da shi, to lamarin ya fi ta karfin tunani. Ta hadiye yawu da kyar, ta ce, "Ba zan iya cewa da tabbaci ba, amma zan tabbatar kafin gari ya waye. Ka tafi ka kula da abin da na fada maka. Idan wani daga cikin wadanda aka kama ya fara magana, dole mu samu labari kafin sauran mutane!" "Hajiya, na fahimta. Amma fa wannan lamari yana bukatar shiri sosai." "Ni zan shirya abin da ya kamata a bangarena. Kai kuma ka kula da naku." Ta kashe wayar a fusace, sannan ta jefa ta a kan gado. Ta zura ido a cikin dakin, zuciyarta tana tafarfasa. Kawai lokaci ne yake tsakanin ta da faduwar asiri! Idan ba ta yi gaggawa ba, rayuwarta za ta shiga ruftawa kamar gida mai tushe mai rauni. Ta dubi agogon da ke gefen gadonta karfe uku da rabi na dare. Tana jin zuciyarta na tafarfasa da damuwa. " dole ne na fara binciken sa!" Wannan tunanin ya tsaya a zuciyarta kamar dutsen da aka kafa. Idan har yana da wani bayani da zai kai shi ga gano abin da take boyewa, to dole ne ta dakatar da shi, kafin lokaci ya kure! Hajiya Rumanah ta kasa zama. Hankalinta ya gama tashi, zuciyarta na tafarfasa da tsoro da fargaba. Ta san cewa idan ta yi sake, komai zai fita hannunta. Ba tare da bata lokaci ba, ta dauki wayarta, ta fara laluben lambar Hajiya Karama. Hannunta yana kerma yayin da ta danna kiran. Wayar ta fara ringin, zuciyarta na bugawa da karfi. Bugu na uku, aka dauka. "Hajiya Rumanah?!" Muryar Hajiya Karama ta fito da alamun bacci a cikinta. "Lafiya kuwa kike kirana a wannan dare?" "Karama!" Hajiya Rumanah ta furta da wata irin murya da ba ta saba da ita ba,muryar mace mai cike da damuwa da fargaba. "Mun shiga matsala! Babbar matsala!" "Subhanallah! Me ya faru?" Hajiya Karama ta tambaya, yanzu hankalinta ya fara dawowa hayyacinsa. "Dan daban nan da muka tura... ya kira ni yanzu!" Ta sha jinin jikinta, sannan ta cigaba. "Karama, sojoji sun tarwatsa su! Duk an kama su, shi kadai ne ya tsira!" "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Hajiya Karama ta furta, zuciyarta na harbawa. "Me kike nufi da an kama su?! Kin tabbata?!" "Na tabbata, Karama! Kuma kin san me hakan ke nufi?! Idan suka fara magana, to fa...!" Shiru ya ratsa tsakaninsu. Kowannensu ya fahimci girman abin da ke tafe. Idan har ‘yan fashin suka fadi hakikanin wanda ya dauke su aiki, to babu makawa SIRRIN su zai tonu! A can bangaren, Hajiya Karama ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce, "To yanzu me za mu yi?" "Dole mu dauki mataki kafin su fara magana!" "Wane irin mataki?" "Abu na farko shi ne dole mu tabbatar da cewa Alhaji Amiru bai ji wani abu ba. Abu na biyu, dole mu san yadda binciken nan ke tafiya ko sun riga sun samu wata hujja da zata iya kai su gare mu!" "Tabbas!" Hajiya Karama ta ce cikin wata irin murya mai nuna damuwa. "Yanzu haka ya kamata ki kira Hajiya Ladi mu sanar da ita. Wannan magana fa ba karamin abu bane! Dare yayi ballantana naje wajenta.." Hajiya Rumanah ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta koma cikin lissafi. Ta san cewa Hajiya Ladi tana da muhimmanci a cikin wannan shiri. Ita ce ta fi sanin yadda za a yi da wannan lamarin, domin ta saba da irin wadannan dabaru. Ba tare da bata lokaci ba, ta lalubi lambar Hajiya Ladi, ta danna kira. Bugu biyu kacal aka dauka. "Rumanah?" Muryar Hajiya Ladi ta fito da karfi, kamar wadda take cikin bacci. "Lafiya kuwa? Me ya faru?" "Ladi, mun shiga matsala!" "Matsala kuma?!" "Eh! Sojoji sun kama su!" A nan take, Hajiya Ladi ta mike a zaune. "Me kike nufi da sun kama su?" "Na ce an kama ‘yan fashin nan baki daya! Daya ne kadai ya tsira, kuma ya bar garin gaba daya. Ya kira ni yanzu, yana cewa mutanen da muka saka a sace, sojoji sun kubutar da su!" "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!" Hajiya Ladi ta furta, zuciyarta tana bugawa da sauri. "Rumanah, wannan abu yana da hadari sosai!" "Na sani!" Hajiya Rumanah ta ce cikin tsawa. "Shi yasa na kira ku, don mu san matakin da za mu dauka kafin komai ya rikide!" "To yanzu me kike ganin za a yi?" Hajiya Rumanah ta lumshe idanu, tana kokarin tara duk wata dabara da zata iya amfani da ita. "Na farko, dole mu samu cikakken bayani kan abin da ya faru. Dole ne mu san inda aka kai wadanda aka kama, su waye ke da alhakin binciken, sannan mu san ko akwai wanda ya riga ya fadawa Alhaji Amiru." "Kwarai kuwa!" Hajiya Ladi ta ce, tana tunani. "Dole ne mu dauki mataki cikin gaggawa." "Ba shakka!" Hajiya Karama ta katse su. "Ba za mu zauna muna jiran abin ya zo mana ba. Idan aka gano mu, to mu duka mun shiga uku!" Hajiya Rumanah ta numfasa a hankali, tana jin zuciyarta tana tafarfasa. Ta san cewa daga wannan dare, dole ne ta tashi tsaye. Komai ya kusa rugujewa, kuma idan ba ta yi taka tsantsan ba, to babu shakka za ta iya rasa komai! Hajiya Rumanah ta lumshe idanu, zuciyarta na tafarfasa. Hankalinta ya gama tashi, saboda tasirin wannan labari ya fi karfin yadda ta zata. Idan har sojoji sun kama su, kuma aka matsa musu da tambayoyi, babu makawa za su tona asirin ta! Muryar Hajiya Ladi ce ta katse shirun da ya biyo bayan hirar su. "Rumanah, lokaci ya kure! Dole mu dauki mataki yanzu kafin komai ya fita hannun mu." Hajiya Karama ta gyada kai kamar tana kallonta, duk da cewa suna waya. "Kwarai kuwa! Amma menene mafita? A ina aka ajiye su yanzu?" Hajiya Rumanah ta dafe goshi, sannan ta ce cikin in'ina, "Ban sani ba har yanzu, amma na aika wani yaronmu da ya binciko. Da zarar ya dawo da bayani, zan sanar da ku." "Ya kamata mu nemo wanda zai iya dakatar da wannan bincike tun kafin ya zurfafa," Hajiya Ladi ta ce da wata murya mai nuna karfin hali. Hajiya Rumanah ta gyada kai. "Hakane. Idan muka samu wanda ke da karfi a wannan lamarin, zai iya hana maganar ta fita. Amma fa..." Ta yi shiru na dan lokaci. "Me fa?" Hajiya Karama ta tambaya. "Idan har Alhaji ya samu labari, ko kuma wani daga cikin su ya fadi sunana, to ko mene ne sai dai mu fuskanci hukunci." Wani irin shiru ya ratsa tsakanin su. Kowannensu yana jin nauyin wannan magana. Hajiya Ladi ce ta daka tsawa. "Ba zai yiwu hakan ba! Babu wanda zai tona mana asiri! Dole mu dauki matakin hana hakan faruwa." "To yaya za mu yi?" Hajiya Karama ta tambaya, muryarta na nuna damuwa. Hajiya Rumanah ta dube su cikin tunani. "Dole mu raba kan wadanda aka kama! Dole mu hana su yin magana tare, ko su hadu da wanda zai tunzura su su tona asirinmu." Hajiya Ladi ta ja dogon numfashi. "Hakane. Amma har yanzu ba mu san wanda ke da alhakin binciken ba. Idan sojoji ne suka karbe shi gaba daya, to kuwa abu ya fi karfinmu." "Zan bincika. Dole mu san da wa muke yi," Hajiya Rumanah ta ce, sannan ta kara da cewa, "Duk da haka, akwai abin da nake so ku kula da shi." "Muna jinki," suka ce a tare. Ta rage murya, kamar tana tsoron wani na sauraren su. "Dole mu yi taka-tsan-tsan da yadda muke mu'amala da Alhaji Idan muka nuna wata alama da zai sa ya fara tunani, zai iya gane komai." Hajiya Karama ta gyada kai. "Hakane. Amma fa ya kamata mu shirya yadda za mu hana shi samun labarin nan gaba daya." "Zan dauki matakin hana hakan faruwa," Hajiya Rumanah ta ce da wata murya mai cike da kaushin azama. "Idan har akwai wanda ya fara bincike ko ya samu wata shaida, dole mu dakatar da shi kafin ya kai labari wajen Alhaji" Hajiya Ladi ta gyada kai, zuciyarta na bugawa da karfi. "Idan dai haka ne, to dole mu hada kai. Komai zai iya faruwa nan gaba kadan." "Tabbas," Hajiya Rumanah ta ce. "Tun daga wannan dare, dole mu tashi tsaye! Dole mu yi komai don ganin ba a gano mu ba!" Sun yi shiru na dan lokaci, kowannensu yana tunanin irin hadarin da ke gabansu. Wannan ba karamin aiki ba ne. Idan suka yi kuskure, to komai zai iya rikidewa zuwa masifa! _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_ 🧳➿💞 *PG :20* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb ___ Bayan sun kammala waya, Hajiya Rumanah ta sake komawa gefen gadonta, zuciyarta na bugawa da karfi. Dole ta yanke shawarar da zata kare ta kafin komai ya rikide. Ta janyo wayarta, ta kira wani lambobi da ba kasafai take amfani da su ba. Tana danna kira, numfashinta ya sauya, hannunta yana kerma. Bugu daya kacal aka dauka. "Hajiya Rumanah," wata murya mai zurfi ta karanto sunanta, kamar wanda ya san dalilin kiran nata. "Abubakar," ta furta cikin nutsuwa, "muna da matsala!" "Na riga da na samu labari," ya ce, yana mai shafar gashinsa da ke gefe. "Meye kike so in yi?" "Ina bukatar ka binciko min cikakken bayani, wa ke da alhakin binciken nan? Ina aka kai wadanda aka kama? Kuma ina so in san ko wani abu ya riga ya isa kunnen Alhaji Amiru." "Zan yi hakan," ya ce ba tare da wata jinkiri ba. "Amma fa Hajiya, yana da kyau ki rage motsi a yanzu. Idan kika yi gaggawa da yawa, zai iya jawo hankali." "Ba na bukatar shawararka!" ta katse shi da takaici. "Ina so ka yi abin da na ce, kuma ka tabbatar da cewa na samu bayani kafin gari ya waye!" Ya yi shiru na dan lokaci, sannan ya ce, "Zan tuntuɓi mutanena." "Kuma," ta kara da cewa, "idan akwai wanda ya fara magana, ko ake shirin tuhumarsa dole a dauki mataki kafin su tona asirinmu!" Muryarsa ta koma mai nauyi. "Kin san me hakan ke nufi, ko?" "Na sani!" ta furta da karfi. "Idan har muna son mu tsira, dole mu yi komai da zai hana mu faduwa!" Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Zan yi abin da zan iya." "Kar ka bari wani abu ya kubuce mana," ta fadi, sannan ta kashe wayar batare da ta jira amsarsa ba. A wannan lokacin, Alhaji Amiru yana zaune a falo, yana tunanin maganganun da Hajiya Rumanah ta fada masa da daddare. Wani irin matsanancin tunani ya lullube shi. Me yasa take jin tsoro haka? Me yasa take ta matsawa da jin ko ya samu labari game da Hajiya Zaytunah da yaranta? Ya dafa goshinsa, yana jin zuciyarsa na bugawa da karfi. Bai taba tunanin cewa wata rana zai fara zargin matarsa ba, amma yanzu yana jin kamar akwai wani abu da take boyewa! Sai kawai ya dauki wayarsa, ya kira daya daga cikin mutanensa masu SIRRI. "Baffa, ina bukatar ka bincika min wani abu." "Ina sauraron ka ranka ya dade..." "Ina so ka binciko min game da harin da aka kai kwanakin baya... na sace mutanen nan da aka ce sojoji sun ceto." A dayan bangaren, Baffa ya dan yi shiru, sannan ya ce, "Alhaji, kana nufin garkuwa da mutanen nan? An ce fa an tarwatsa ‘yan fashin gaba daya." "Eh," Alhaji Amiru ya ce, yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa. "Ina so in san wa ke da alhakin wannan aika-aika. Kuma ina so a binciko min wanda ke da hannu a bayan fage." Baffa ya numfasa. "Zan bincika, Alhaji. Amma fa wannan batu yana da sarkakiya." "Kawai ka yi min bincike. Ina bukatar cikakken bayani cikin gaggawa." Ya kashe wayar, sannan ya jingina da kujerarsa. Zuciyarsa na bugawa... Idan har akwai wanda ya shigo da Hajiya Zaytunah cikin matsala, dole ya gano! Kuma idan har wannan abu yana da alaka da wani daga cikin iyalinsa… to, babu shakka, hakan ba zai wuce ba tare da hukunci ba! Hajiya Rumanah ta gama fidda umarni, amma zuciyarta har yanzu bata samun nutsuwa. Wata zuciya na gaya mata ta bar komai haka nan, amma tsoron abin da zai iya biyo baya ya hana ta yin watsi da lamarin. Sai da ta tabbatar da cewa komai ya kankama, sannan ta koma dakinta ta zauna akan gado. Amma ko da ta rufe idanu, ba ta iya barci. Maganar Abubakar na daukar mata hankali—"Idan har muna son mu tsira, dole mu yi komai da zai hana mu faduwa!" Ko me hakan ke nufi, ta shirya tsaf! A daidai wannan lokacin, wayarta ta dauki kara. Ta daga da sauri, tana sa ran jin labari daga Abubakar ko daya daga cikin mutanenta. Amma lambar da ta bayyana a fuskar wayar ba ita bace. Gaba daya jikinta ya dauki rawa lokacin da ta ga sunan da ke kan allon wayar. Baban Hammad! Wato Alhaji Amiru, Numfashinta ya kusa tsaya wa. Me yasa yake kiranta cikin dare haka? Ko dai ya fara jin wani abu ne?! Ta gyara murya, sannan ta danna amsa. "Assalamu alaikum." Ta fadi da murya mai sanyin jiki. "Wa alaikum salam," muryar Alhaji Amiru ta amsa, mai cike da kasala. Duk da haka, ta fahimci cewa yana cikin wani hali. "Ya dai, Alhaji? Lafiya kuwa?" Ya dan yi shiru na wasu 'yan dakiku, sannan ya ce, "Rumanah, akwai wata tambaya da nake so in yi miki." Zuciyarta ta buga da karfi. "Tambaya?" Ta maimaita a hankali. "Eh," ya fadi, yana jan numfashi. "Jiya da dare, kin tambaye ni ko na samu labarin Hajiya Zaytunah da 'ya'yanta. Me yasa kika yi wannan tambaya?" Jikinta ya dauki matsanancin zufa. Ta zaci cewa ta rufe komai a natse, amma yana iya yuwuwa ya fara shakku? "Eh... Alhaji, ai kawai ina tambaya ne, saboda..." Ta yi shiru, tana kokarin tsara abin da zata fada. "Saboda me?" Ya katse ta, yana kara matsa mata lamba. "Saboda... ai ai..." Ta dan yi dariya kadan, tana kokarin boye fargabarta. "Kawai ina jin labarai ne daga wasu mutane, kuma na zata kila kai ma ka sani." Alhaji Amiru ya sake yin shiru. Wani abu yana gaya masa cewa ba gaskiya take fada ba. "Wane irin labari kika ji?" Hajiya Rumanah ta ciza lebe. "Ba fa komai Alhaji. Kawai dai ." "Kawai dai me?" "Ina fatan suna cikin lafiya" "Daga ina kika samu wannan bayani?" Zuciyarta ta doka kamar ana busa ganguna a cikin kirjinta. Wannan tambaya bata yi tsammani ba! "Eh... eh... ai dai. Fata na ce .." Ta sunkuyar da kanta, tana kokarin nemo wata amsa da zata rufe komai da ita. Amma kafin ta samu bakin magana, Alhaji Amiru ya ce, "Kin san me, Rumanah?" "Naam?" Ta amsa da wata irin murya mai sanyi. "Na tabbata akwai wani SIRRI da kike boye min wani abu!" Ta firgita matuka! Kawai sai ta mike tsaye a kan gadonta, jikinta yana rawa. "B-boye maka wani abu? Me yasa zan boye maka wani abu, Alhaji?" Ya yi ajiyar zuciya mai nauyi. "Wannan shine abinda zan gano!" Ya kashe wayar batare da ya jira amsarta ba! Hajiya Rumanah ta kasa motsi, wayar a hannunta. Numfashinta yana fita da wahala. Haka kawai, ta san cewa abu ya fara baci. Idan har Alhaji Amiru ya shiga bincike da kansa, to komai zai iya tonuwa! Dole ta dauki mataki kafin lokaci ya kure! Hajiya Rumanah ta zube a kan gadonta, zuciyarta na bugawa kamar zata faso kirjinta. Gabanta ya gama faduwa, Alhaji Amiru ya fara zargin ta! Idan har ya ci gaba da bincikensa, babu shakka zai gano komai. A firgice ta sake daukar wayarta, ta kira Hajiya Karama da gaggawa. "Karama, muna cikin matsala!" Ta furta da rawar murya, hannunta na kerma. "Meye kuma?" Hajiya Karama ta tambaya, jin yadda muryar Rumanah ta sauya. "Alhaji ya fara bincike! Ya fara zargin cewa ina boye wani abu! Na tabbata idan bai samu amsa mai gamsarwa ba, zai zurfafa bincike har sai ya gano gaskiya!" Hajiya Karama ta runtse idanu, zuciyarta na tsananta bugawa. "Wannan fa bala’i ne! Kin tabbata ba wani abu kika fada da zai sa ya shiga shakku?" "Wallahi ban ce komai mai hadari ba! Amma dai na fahimci cewa yana da shakku! Kuma idan ba mu dauki mataki ba, to fa..." "Ke dai ki nutsu! Ba lokacin firgici bane yanzu," Hajiya Karama ta katse ta. "Abin da ya kamata mu mayar da hankali akai shine, ya za mu dakatar da shi kafin komai ya fito fili." "Yaya za mu yi?" Shiru ya ratsa tsakanin su. Kowannensu na jin nauyin wannan matsala. Hajiya Karama ta numfasa sannan ta ce, "Dole ne mu karkatar da hankalinsa. Dole mu jefa masa wani sabon tunani da zai sa ya bar binciken nan. Idan hakan bai yi aiki ba, to sai dai mu dauki matakin karshe!" _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_ 🧳➿💞 *PG :21* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb __ Idanun Alhaji Amiru suka kada yayin da ya karanta wani sashi na bayanin da aka rubuta a cikin takardar binciken, "A cewar wanda aka kama, akwai wani babban mutum da ke daukar nauyin ayyukan su. Sun ce ana basu umarni daga wata mata mai karfin iko, wadda take amfani da wasu mutane domin kare kanta daga tonuwa." Hannunsa ya soma kerma, zuciyarsa na bugawa da karfi. Ya sake duban hotunan da aka turo masa, duk sun kasance mutane da bai taba ganin su ba, amma abin da ya fi daukar hankalinsa shine yanda wani daga cikinsu ya fadi cewa "ba wata shakka, akwai wani da ya fi kowa sanin gaskiya, amma yana boye komai saboda tsoron tonuwa." A wannan lokacin, numfashinsa ya sauya. Wane ne wannan babban mutum? Kuma wacece wannan matar da suke magana akai? Zuciyarsa ta tsananta bugawa. Ko akwai wata alaka tsakanin wannan bayani da tambayoyin da Hajiya Rumanah ke masa kwanan nan? "Ba zan yi gaggawa ba," ya furta a hankali, yana jingina da kujerarsa. "Dole ne in yi bincike na kaina." Ya dauki wayarsa ya kira Baffa. "Baffa, kana ina?" "Ina nan, Alhaji." "Ina so ka samu min cikakken bayani akan wannan binciken. Ina son in san ko akwai wata alaka tsakanin barayin nan da wasu daga cikin mutanen gida." "Na gane, Alhaji. Zan ci gaba da bincike, amma kana bukatar yin taka tsantsan. Idan da gaske akwai wata babbar fuska da ke bayan wannan lamarin, to yana da hadari." "Ba matsala," Alhaji Amiru ya ce da kwarin gwiwa. "Bari mu fara gano gaskiya." __________ Bayan ta gama waya da Hajiya Karama, zuciyarta ta kasa samun natsuwa. Hankalinta ya fi karkata zuwa kan abubuwan da suka faru kwanan nan. Shin Alhaji Amiru ya riga da gano wani abu? Ko dai yana kan hanya ne? Tana cikin wannan tunani ne wayarta ta sake daukar kara. Ta dauka da sauri. "Waye?" "Ni ne," Abubakar ya ce da wata murya mai cike da tsoro. "Muna cikin matsala." Gabanta ya fadi. "Meye kuma?!" "Sojoji sun riga sun kama wasu daga cikin mutanen mu! Kuma daya daga cikinsu ya fara magana!" Hajiya Rumanah ta zaro ido. "Mene ya ce?!" "Ya furta cewa suna da wata babbar fuska da ke basu umarni!" Hajiya Rumanah ta mike tsaye, jikinta yana kerma. Idan har hakan ya ci gaba, yana nufin cewa suna dab da gane cewa ita ce ta shirya komai! Ta rufe idonta, zuciyarta na suya. "Abubakar, dole ne mu dauki mataki!" "Me kike so mu yi?" Ta dauki numfashi mai zurfi. "Dole ne mu tabbatar da cewa mutumin da ya fara magana ya yi shiru har abada!" Abubakar ya yi shiru na ‘yan dakiku, sannan ya ce da murya mai nauyi, "Kin tabbata da hakan?" "Ba mu da zabi," ta fadi a tsawace. "Idan ba haka ba, to fa komai zai ruguje!" A wannan lokaci, Alhaji Amiru yana tsaye a gefen tagar ofishinsa, yana kallon nesa, zuciyarsa cike da nauyin tunani. Ya fahimci cewa akwai wani abu mai girma da ke faruwa, kuma yana da alaka da mutanen da ke kusa da shi. Sai kawai ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya dauki waya ya kira Baffa. "Baffa, yanzu na yanke shawara. Dole ne a ci gaba da binciken nan ba tare da wata fargaba ba. Duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan lamari, dole ne ya fuskanci hukunci, ko waye ne!" A can bayan fage kuwa, Hajiya Rumanah ta gama yanke hukuncin da zata dauka. Idan har tana so ta tsira, dole ne ta dauki matakin karshe kafin lokaci ya kure. MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RESIDENCE: Daren yana lullube da wani irin sanyi mai dadi, iska tana kaɗawa cikin nutsuwa, tana kadawa da daddawa cikin lambun gidan Major General Dawud. Wata ya bayyana a sararin sama, yana haska filin gidan da haske mai taushi. A cikin babban falonsa mai yalwa, Major General Dawud yana zaune tare da mahaifiyarsa, Gwaggo Hafsatu. Wani kwanon kwadon rama Da tacaccen lemo na abarba yana a gaban su, mai aiki ce ta kawo musu kafin ta fice. Gwaggo Hafsatu ta dube shi da murmushi. "Dawuda, kanason kwado kamar yadda ka saba tun kana yaro." Major General ya girgiza kai yana dariya. "Ai kwado abinci ne na musamman, Gwaggo. Yana karfafa jiki, kuma yana kara kuzari." Duk suka yi murmushi, suka ci gaba da shan lemo cikin nutsuwa. Sai dai a hankali hirar su ta fara sauyawa. "Dawuda," Gwaggo Hafsatu ta furta, tana gyara zamanta. "Ni dai har yanzu zuciyata na kasa samun sukuni Yakamata mu sanar da Hajiya Zaytunah halin da ake ciki." Major General Dawud ya gyada kai. "Hakane, Gwaggo. Ya kamata ta san cewa Muhammad shi ɗan gidan Alhaji Amiru ne. Kuma Alhaji Amiru, shi ne yayan mijinta, Alhaji Uzairu." Gwaggo Hafsatu ta dubeshi da takaici. "Kila wannan shine dalilin da yasa aka sace su tun farko. Duk alama akwai wata babbar makarkashiya a bayan lamarin nan." "Da alama haka ne," Major General ya ce. Sai ya miƙa hannunsa ya dauki intercom daga saman teburin kusa da shi, ya danna lambar dakin Hajiya Zaytunah. "Assalamu Alaikum," muryarta ta fito daga cikin intercom. "Wa Alaikum Salam, Hajiya Zaytunah. Muna son ganin ki a nan falon Gwaggo." "Tohm gani nan zuwa." Bayan dan gajeren lokaci, ta shigo cikin falon. Kallo daya za a yi mata, a fahimci tana cikin tunani. Ta zauna a kasan kujerar da ke kusa da Gwaggo Hafsatu, tana kallon su da nutsuwa. "Barkan ku da war haka?" Ta karasa tana gayshe su cike da girmamawa. Major General Dawud ya gyara zamansa, yana kallonta da kulawa. "Hajiya Zaytunah, muna son mu sanar da ke wani abu mai muhimmanci." Ta kalle su da mamaki. "Ina sauraren ku. Gwaggo" "Mun tabbatar da cewa muhammd manemin Nabeeha yar mu. Da ne ga yayan mijinki, wato, Alhaji Amiru." "Ehh" Ta furta, jikinta na daukar wani irin shauki. Tabbas ta tabbata Muhammad jinin hajia rumanah ne. Numfashinta ya dauke na wasu dakiku. Ta dubi Major General da Gwaggo Hafsatu kamar mai son jin karin bayani. "Subhan'Allah.... Dama gwaggo Ina san sanar daku nima na daga abunda su gora da bala suka sanar da mu a lokacin da aka kamamu... " "Eh, babu shakka," Major General ya tabbatar. "Hajiya Rumanah ce mahaifiyarsa. Ita ce matar Alhaji Amiru." Hajiya Zaytunah ta zaro ido, numfashinta na sarkewa. "Muhammad... ɗan gidan Alhaji Amiru ne. Yayan mahaifin su Nabeeha" A hankali, wani abu ya soma fitowa daga cikin zuciyarta. Wata ƙwaƙƙwarar fahimta ce take fado mata. Ta dafa goshinta, tana kokarin daidaita numfashinta. "Gwaggo.... e?" Ta ce da wata murya mai nauyi. "Ina da wani abu mai muhimmanci da zan fada muku." Major General Dawud da Gwaggo Hafsatu suka kara nutsuwa, suna sauraro. "Hajiya Rumanah," ta fara bayani, "ita 'yar uwata ce, kuma ita ce matar Alhaji Amiru.. " Gwaggo Hafsatu ta zaro ido. "Me kike nufi?" "Itace yar wan mahaifina. Wadda aka haife mu rana daya. Aka aurar damu ma rana daya. Saa tace Kuma kawata ta kut da kut alokacin yarinta. Zumuncin mu ya fara warewa ne alokacin da mahaifinta ya auri mahaifiyata bayan rasuwar mahaifin mu. Sannan manemin ta shine Wanda aka aura mun aure dashi amainakon Amiru sai aka samu sabani aka aura mun uzairu ita Kuma Amiru. Amman sai manya suka ce abar auren a haka tunda dama na Hadi ne bana nagani inaso ba. To yanzu Kuma kaddara tasa dan cikinta yazo yana neman ya ta... atakaice dai kar na cika ku da surutu, Ina nufin cewa ita ce ta bada umarni a dauke mu! Ita ce ta hada baki da wasu, ta turo ‘yan fashin da suka kama ni da yaran nan! Ita ce ta bada duk umarnin azabar da aka yi mana!" Major General Dawud ya runtse idanu, zuciyarsa na tafasa. "Wannan lamari yana kara zama mai hadari." Gwaggo Hafsatu ta numfasa. "Zaytunah, kin tabbata da wannan magana?" "Eh, babu tantama," ta ce, hawaye na taruwa a idanunta. "Gora da Bala sun sanar da ni da bakinsu. Sun gaya min cewa ita ce ta bada duk umarni. Duk abin da aka yi mana, umarninta ne!" A wannan lokaci, Major General Dawud ya mike tsaye. "Wannan abu ba za a kyale shi ba! Idan har haka ne, to lallai dole ne mu dauki mataki!" Gwaggo Hafsatu ta gyara zamanta. "Dawuda, wannan magana ba a yi ta da gaggawa ba. Idan har da gaske Hajiya Rumanah ce ta shirya wannan danyen aiki, to akwai babban shiri a bayanta. Bamu san iya sharrinta ba tukunna." Major General ya gyada kai. "Hakane, Gwaggo. Amma fa ba za mu zura ido muna kallon zalunci yana cigaba ba." A can bangaren Hajiya Zaytunah, zuciyarta cike take da bakin ciki. Ta rufe idonta, ta furta cikin tsanani, "Ya Allah, ka tona asirin duk wanda yake cikin wannan mummunan shiri! Allah ka nuna mana gaskiya, ka tona asirin azzalumai!" A wannan dare, wata sabuwar makoma ta fara bayyana. Lamarin ya kara zama mai hatsari, domin yanzu an fara bankado manyan sirruka. _____ A BANGAREN HAJIYA RUMANAH A ranar, bayan ta samu wannan kiran da ya firgitata, Hajiya Rumanah ta kasa samun sukuni. Ta sha kwanciya tana tashi, zuciyarta tana tsananta bugawa. Kamar wadda aka tsunduma cikin matsanancin firgici, ta kirawo abokan muguntar su Hajiya Karama, da kuma kishiyar ta Hajiya Ladi. Lokacin da suka iso gidanta, suka same ta zaune a kan kujera, tana jijjiga kanta da damuwa. "Rumanah, lafiya kuwa?" Hajiya Karama ta tambaya, tana dubanta da kulawa. Hajiya Rumanah ta dube su, idonta cike da tashin hankali. "Muna cikin matsala." Hajiya Ladi ta hade girar sama da kasa. "Mene ne kuma? Ke me ya same ki haka?" Hajiya Rumanah ta numfasa, sannan ta furta da raunin murya: "Asirina yana gab da tonuwa. Sojoji sun ceci su zaytunah da muka bada umarnin a sace. Sannan sun kama kusan dukkansu, sai guda daya da ya tsere. Kuma kun san me ya faru?" Suka girgiza kai. "Wannan daya da ya tsere, sai ya kira ni, ya sanar da ni cewa shirinmu ya gaza, kuma yanzu an kama abokan aikinsa." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Hajiya Karama ta furta. Hajiya Karama ta zuba tagumi. Ta Kara da cewar "Yanzu me kike tunani? Dole ne mu san matakin da za a dauka kafin abubuwa su kara dagulewa." Hajiya Rumanah ta dafe goshinta. "Yanzu haka Major General Dawud yana bincike. Idan har ya gano cewa ni ce nake bayan lamarin, to zan shiga matsala." Hajiya Ladi ta numfasa, tana girgiza kai. "Ke dai kin jefa kanki cikin babbar matsala. Idan hakan ta fito fili, ba zaki iya shiryawa ba." "Don Allah, ku taimaka min!" Hajiya Rumanah ta ce da muryar kuka. "Dole ne mu sami mafita kafin lamarin ya fi kamari! Kada ku manta harda ku acikin komai" Hajiya Karama ta kalli Hajiya Ladi. "Wannan abu yana bukatar dabaru. Idan har muna so mu ceci Rumanah, to dole ne mu yi tunani mai zurfi." Hajiya Ladi ta sake daidaita zaman mayafinta. "Da alama dole ne ki fara tunanin yadda za ki karyata wannan zargi tun kafin su fara bincike sosai." Hajiya Rumanah ta dafe kirjinta, zuciyarta na dokawa da tsananin tashin hankali. ____ A wannan dare, bayan dawowa daga ofishinsa, Major General Dawud ya sake komawa sashen mahaifiyarsa. Gwaggo Hafsatu tana zaune akan kujera, tana juyawa cikin Azkar. Ya zauna a gefenta, sannan ya furta cikin kwanciyar hankali. "Gwaggo, zamu iya samun babbar matsala nan gaba." Ta dago ta kalle shi. "Me ya faru?" "Duk alama Hajiya Rumanah tana kokarin boye hannunta a wannan lamari. Amma ina da tabbacin cewa akwai karin sirruka da ba mu sani ba tukuna." Gwaggo Hafsatu ta numfasa. "Allah ya tona asirin wanda yake da laifi." Major General Dawud ya gyada kai. "Babu shakka, lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan." A wannan dare, zuciyoyi sun kagara. Wasu suna firgita da tsoron abinda zai biyo baya, wasu kuma suna shirin tonon silili. Shin Hajiya Rumanah za ta iya kare kanta? Ko kuwa gaskiya za ta bayyana? Lokaci ne kawai zai tabbatar! _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_ 🧳➿💞 *PG :22* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb __ Dare ya ja, amma Nabeeha ba ta jin barci. Barci ya kauracewa manyan idanunta da suke dauke da gashin idanu Zara Zara tubarkAllah ..Iskar sanyi tana kadawa daga kofar tagar da aka bude kadan, tana motsa labulen siliki da ke lullube da gilashin. Tana kwance a gadonta, tana kallon rufin dakin, amma zuciyarta na can... a wani wuri daban. Zuciyarta cike take da tunanin captain Fawaaz.... A zahiri, yana da kamewa. Mutum ne mai miskilanci da ba ya nuna damuwarsa ko ra’ayinsa kai tsaye. Babu wanda ke iya gane abin da ke ransa – ko da shi ne yake shirin bayyana shi. Amma duk da haka… yana aika mata sakonnin soyayya! Tun farko, ta yi zaton ba da gaske ba ne. Ta ce, watakila wani ne ya yi amfani da wayarsa. Ko kuma wasa ne kawai. Amma sakonni na ci gaba da zuwa, kowanne cike da kalmomin da ke bayyana yadda zuciyarsa ke a kulle. "Nabeeha, ki yarda da zuciyata… ko da ba zan iya furtawa a baki ba." "Idan har akwai wanda zuciyata ke muradi, to ke ce…" "Soyayya ba wai da baki kawai ake furtawa ba. Amma idan har kina bukatar jin hakan daga bakina, to wata rana zan samu karfin gwiwa." Ta rufe idanunta da karfi. Me yasa yake hakan? Me yasa yake aikata abin da ba zai iya bayyana wa duniya ba? Idan har yana sonta, me yasa yake yin nesa da ita? Me yasa ya kasa furtawa kai tsaye? Zuciyarta na dauke da amsar da ba ta iya fahimta.. Ana cikin haka, sai aka turo kofar dakin da sauri. "Nabeeha!" Nabeeha ta zabura kadan, tana kallon kofar. "Lafiya?" "Yi hakuri, ‘yar uwa!" Humayrah ta ce, fuskarta dauke da murmushi. "Muhammad ne ke son yin magana da ke." Nabeeha ta yamutsa fuska kadan. "Muhammad?" "Eh mana, kin san ba ki da waya, sai ya kira ta tawa.. dalla malama karbi" Nabeeha ta dan yi shiru. Ba ta da wani tunani a kai. A yanzu, zuciyarta na wajen wani daban – Fawaaz. Ta dan yi kasa da idanu tana dankarawa humyrah hararar wasa, "Gashi nan, ki karba," Humayrah ta ce, tana mika mata wayar. A hankali ta karba, ta kara a kunne. "Assalamu alaikum." A daya bangaren, muryar Muhammad ta amsa cikin nutsuwa. "Wa alaikumus salam, Nabeeha. Ya kike?" "Ina wuni ? Alhamdulillah!Lafiya lau." Sai shiru ya biyo baya na wasu sakanni. Muhammad yana kokarin samun kalmomin da zai fara da su. Ita kuwa Nabeeha, hankalinta ba kan wayar yake ba – tana can tana sake tunanin Fawaaz da sakonnin da ya turo mata. Muhammad ya numfasa. "Nabeeha... I love and miss you soo much" Ta dan runtse idanu. Ta san abin da zai fada. "Nabeeha, ina kaunarki." Zuciyarta ta buga, amma ba don maganar Muhammad ba – sai don tunanin yadda Fawaaz ya kasa furtawa haka. "Kullum dada kewarki. Nake, tamkar na janyo ranar bikin mu haka nakeji, Ban san me yasa ba, amma tun farkon haduwarmu, na ji wani abu na daban a kanki. Ina son ki, Nabeeha, da gaske nake." Shiru ta yi, ba ta ce komai ba. A zahiri, ta ji kalmomin Muhammad, amma ba su shiga zuciyarta ba. Tunani kawai take—da ace Fawaaz ne ke furta mata hakan a baki, ba kawai a rubuce ba… Yar wahalaaaaa🤭😏 Muhammad ya dan yi murmushi. "Kin yi shiru?" Ta numfasa. "Ba komai." "Ba ki ce komai ba akan abin da na fada." Ta dafa goshinta. "Muhammad… Kai na ke ciwo. Yi.hakuri" Ya yi shiru na wani lokaci. "Babu matsala. Amma a kalla ki san cewa na fadi abin da zuciyata ke ji. Kuma ba zan yi nadamar fada ba...Allah yakara miki lafiya da nisan kwana mai albarka amin" Ta dan yi murmushi kadan. "Nagode." Sun dan kara hira kadan, sannan suka yi sallama. Ta mika wa Humayrah wayarta, sannan ta koma ta kwanta, zuciyarta na kara cike da tunanin Fawaaz. "Me yasa ya kasa furtawa a baki?" "Me yasa ya ke boye abin da yake ji?" "Ko kuwa yana fargabar abinda zai biyo baya?" Watan wata rana… wata rana zai iya furtawa? Bayan tattaunawarta da Muhammad, Nabeeha ta ajiye mikawa humyrah wayarta,. Sai dai, ko da suka yi sallama, ba kalmomin Muhammad take tunani ba—sai Fawaaz. "Me yasa ya kasa furtawa a baki?" Tana kwance kan gadonta, hannayenta sun dunkule a kirjinta, zuciyarta tana gudu da sauri. Ta rufe idanuwanta da karfi, tana kokarin korar tunanin da ya mamaye ta. Amma hakan bai yiwu ba. Tunanin Fawaaz ya ci gaba da dawowa. Idanunta na kulle, ta fara tuno lokacin da ta fara lura da sauyin da ya faru da shi—lokacin da ya fara kallonta da wata irin kallo mai nauyi, lokacin da ta fara samun sakonninsa masu dauke da kalmomin da suka fi yadda yake iya furtawa. "Ba zan iya furtawa a baki ba… amma ki sani, zuciyata ta yarda da ke." "Ke ce abin da nake bukata, ko da kuwa duniya ba ta fahimta." Tana da tabbacin cewa Fawaaz yana da wata irin soyayya a gare ta, amma ya kasa furtawa a fili. Me yasa? Shin miskilancinsa ne ke hana shi? Ko kuwa wani abu ne da ba ta sani ba? Ta bude idonta, tana duban rufin dakin. "Idan har yana sona da gaske, me zai hana ya fada?" Tana cikin wannan tunani ne sai aka turo kofar dakin. "Nabeeha!" Ta dago da sauri. Humayrah ce ke kokarin shigowa, fuskarta cike da murmushi. "Mene ne kuma?" Nabeeha ta tambaya, tana zuba mata harara. Humayrah ta zauna a gefen gadon, tana yatsina fuska. "Haba dai, ke kam. Me yasa kika yi kamar ba kya son magana da Muhammad?" "Ban ce ba na son magana da shi ba." "Amma ba ki nuna sha'awar tattaunawar ba." Nabeeha ta dube ta da murmushin gefen baki. "Ke dai bari kawai, ina cikin tunani ne." Humayrah ta mike tana kallonta. "Tunanin wani kike ko?" Nabeeha ta zabura. "Me yasa kika ce haka?" Humayrah ta harare ta. "Ai a yanzu haka, koda ace wani zai baka labari mai dadi, amma kana da wani abu a zuciyarka, ba za ka ji dadin labarin ba." Ta yi shiru, tana nazarin maganar Humayrah. Ko da yake ba ta son yarda da hakan, amma akwai gaskiya a ciki. "Ke dai bari kawai," ta ce, tana kokarin kawar da batun. Humayrah ta yi dariya. "To Allah ya kyauta. Amma dai Muhammad na nan, yana jiranki ki yanke hukunci." ____ A gefe guda, Fawaaz yana zaune a kofar falonsa, cikin duhun dare. Ya jingina da kujerar da yake zaune a kai, hannunsa rike da wayarsa. Ya kafe screen din wayar da idanu, yana nazarin sakonnin da ya tura wa Nabeeha. Ya sani. Ya sani cewa bai dace ya ci gaba da boye soyayyarsa ba. Ya sani cewa ba zai iya ci gaba da kamewa ba, amma me zai yi? Zuciyarsa na cike da tsoro. Ba tsoron soyayya ba—tsoron abin da zai biyo baya. Yana jin zuciyarsa na dukan abu guda. Idanunsa sun kada kadan saboda tunani da damuwa. A can can, zuciyarsa na tambayarsa, "Za ka ci gaba da ɓoye gaskiyar zuciyarka?" "Ko kuwa lokaci ya yi da za ka bayyana?" Ya sauke ajiyar zuciya, yana jin daren yana yi masa nauyi. Numfashin Nabeeha ya tsaya cak. "Yaa Fawaaz?" Muryarta ta fita da sanyi, tamkar ba ita ta yi magana ba. A daya bangaren, shiru ne. Sai daga baya ta ji numfashinsa ya sauka kadan. "Eh, .. Zan iya ganinki?" Wata irin kasala ta shige ta. Hannunta ya yi sanyi, zuciyarta na bugawa kamar zata fado daga kirjinta. Me zai fada mata? Meyasa yake neman ganinta a wannan dare ta intercom din dakin ta? Tayi shiru, zuciyarta na kokarin tattaro amsar da zata bashi. "Ina kusa da balcony. Idan har ba damuwa, ki fito." Zuciyarta ta tsananta bugawa. Shin ta fita? Shin da gaske zai iya furtawa a yau? Tana cikin wannan tunani ne sai aka turo kofar dakin. Humayrah ce. "Ke! Waye haka yake magana da ke da daddare?" Ta tambaya, tana kokarin karbar wayar. Da sauri Nabeeha ta kashe kiran, zuciyarta na harbawa. "Ba kowa." Humayrah ta kalle ta da mamaki. "Ba kowa kuma? To me yasa kika kashe wayar da sauri?" Nabeeha ta girgiza kai, tana kokarin boye rikicin zuciyarta. "Ki daina bincike mana." Humayrah ta tabe baki. "To ai da gani akwai abu. Ko dai Muhammad ne ya kira?" "A'a kuma ta intercom? ." Nabeeha ta fada da sauri, tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da dukan abu guda. Humayrah ta yi shiru, sannan ta kalli gefenta. "Da gaske dai babu matsala?" Nabeeha ta yi kokarin murmushi. "Eh, ki kwantar da hankalinki." Amma ita kanta ta san cewa hankalinta ya tashi. Ta mike daga gadon, zuciyarta na tafasa. Shin ta fita ta hadu da Fawaaz? Ko kuwa ta share shi kamar yadda yake son boye soyayyarsa? Fawaaz yana tsaye a jikin motarsa, hannayensa a cikin aljihu. Zuciyarsa na tafasa, yana jiran amsar Nabeeha. Me zai ce idan ta fito? Meyasa bai iya furtawa a da ba? Ya sauke numfashi. "Yau, dole zan fada." Idan har ba zai iya furtawa a yau ba, to zai iya rasa ta har abada. _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ **KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_ 🧳➿💞 *PG :23* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb __ A tsakar dare, Fawaaz yana zaune a kan kujerar barandar gidan, hannunsa na jingine da gefen kujera, yana kallon sararin samaniya. Hasken wata yana haska filin gidan, yana ba da nutsuwa, amma zuciyarsa ba ta da nutsuwa ko kadan. Me yake yi da zuciyarsa haka? Ya rike goshinsa a hankali. Duk yadda ya so ya boye abin da ke ransa, ya kasa. Yana son Nabeeha. Bai san yadda zai iya rayuwa ba tare da ita ba. Yana shakar numfashinta idan tana kusa. Idan ta wuce ta gefensa, wani kamshi na musamman ke ratsa shi. Bai san ko menene ba, amma yana tabbatar da cewa ko a cikin taron mutane dari, zai iya gane Nabeeha. Komai nata daban ne. Tana da nutsuwa, tana da sanin ya kamata, tana da ilimi, tana da hankali fiye da yadda yawancin mata ke da shi. Ba kawai kyawunta ba ne ya ke ja shi gare ta, dabi'arta ce, hankalinta, tausasawarta. Ya yi murmushi a hankali. Ta na da tausayi. Yana iya tuna yadda take tausaya wa kowa, har da wadanda ba su san tausayin wasu ba. Ya kan ga yadda take rike da addininta, yadda take nisantar abin da bai dace ba. Ba wai tana takura wa kanta ba, amma tana da tsoron Allah. Wacce mace ce kamar haka? Duk da cewa tana da karancin shekaru, ta fi kowace mace da ya sani. Yana sonta. Yana son ta fiye da yadda ya taba son wani abu a rayuwarsa.🥹 Amma yana tsoron furtawa. Ya jima yana tunanin hakan. Idan ya fada mata, me zai faru? Shin zata karba? Shin zata fahimce shi? Shin zata yi dariya kawai ta bar shi yana jin zuciyarsa na kuncewa? Ya sauke ajiyar zuciya, yana jin bugun zuciyarsa na tsananta. Nabeeha tana zaune a gefen gadonta, tana rike da wayar Humayrah da ta ajiye a gefenta. Hannunta da sanyi, zuciyarta na bugawa da sauri. "Ya fawaaz..." Shin da gaske yana son ganinta? Me zai ce? Meyasa yake ta ɓoye abu a zuciyarsa? Tun da ya fara turo mata sakonni a rubuce, zuciyarta ta daina samun sukuni. Tana son sanin dalilin da yasa yake haka. Idan har yana da abin da yake ji a zuciyarsa, me zai hana ya fada? Tayi shiru, tana jin zuciyarta na kokarin bata amsa, "Ko kuwa miskilancinsa ne ke hana shi furtawa?" Ta rike hannunta da hannu guda, tana jin yadda jikinta ke daukar zafi. Tana jin dadin yadda Fawaaz yake kula da ita, duk da cewa bai taba cewa tana da muhimmanci a gare shi ba. Sai dai zuciyarta tana jin hakan. Tana jin yadda idanunsa ke magana idan suka hada ido. Tana jin yadda shiru yake da ma'ana idan suna tare. Tana jin yadda kalmominsa ke bayyana da sauri a rubuce, amma ba zai iya fada da baki ba. Tana jin yadda yake tsoron furta abu a bakinsa. Tana jin yadda ya rasa yadda zai fada mata abin da zuciyarsa ke rayawa.. Ta lumshe idonta a hankali. Ta fahimci abu daya. Fawaaz yana sonta. Amma ya kasa furtawa. Fawaaz ya tsaya yana kallon wayar da ke hannunsa. Sabuwar waya ce mai kyau da tsada, kirar zamani, wadda ya siya da sabon SIM a ciki. Tun kafin ya karɓi wannan matsaya, ya sha gwagwarmaya da zuciyarsa. Ya dade yana tunani, yana shan shakkar ko hakan daidai ne. Amma a ƙarshe, ya yanke shawara, yanzu lokaci ne na aikatawa, ba tunani ba. Ya ɗan gyara zaman rigarsa, ya kalli agogo. Wajibi ne ya kammala wannan lamari cikin nutsuwa, batare da wani yayi tunanin akwai wani abu daban ba. A hankali ya kira Nabeeha, murya a daidai misali. "Ina son ganinki a waje," kawai ya ce mata, ba tare da wata sharhi ba. **A lokacin da ta fito, ya jingina da motarsa, hannayensa a cikin aljihu, idanunsa na kallon gefe tamkar ba shi ya kira ta ba. Nabeeha ta dan yi jinkiri tana nazarinsa, sannan ta karasa kusa da shi. Tana gayshe da shi.. "Ga wannan." Bai iya kallonta ba yayin da ya miƙa mata wayar. Murya a dakile, kamar yana bayar da wani abu mara muhimmanci.😂 Nabeeha ta kalli wayar da mamaki. Idanunta sun cika da alamar tambaya. "Wannan fa?" Fawaaz bai amsa ba. Ya ɗan juya gefen fuskarsa, yana kallon wata hanya kamar wanda ba ruwansa da abin da ke faruwa. "Ta waye.. ko tawa ce?" Ta tambaya a hankali, tana jin kamar mafarki take yi. Ya numfasa kadan, yana cigaba da kallon gefe. "Ee." Shiru ya biyo baya na ƴan dakiku. Sai da zuciyarta ta harba da wani yanayi mai rikitarwa. "Nagode Allah ya Saka maka da alkhairi amin," ta ce cikin sanyin murya. Bai amsa ba. Bai ce komai ba. Kawai ya jinjina kai kaɗan, sannan ya juya ya buɗe motarsa ya shiga fice daga gidan. Yana barin wajen, zuciyarsa na bugawa da karfi. Bai ce mata komai ba. Bai iya furtawa ba. Amma ya san, daga yanzu, zai iya jin ta kusa da shi... ko da kuwa ta hanyar sakonni ne kawai. Nabeeha ta tsaya a wajen, hannunta rike da wayar da ya bata. Kamar mafarki ne, kamar ba gaske ba. Idanunta sun cika da tambayoyi, amma wanda ya dace ya amsa su, tuni ya tafi. Ta lumshe idanu, zuciyarta na harbawa. Ba wai sayen wayar bane matsalar amma yadda ya bayar. Yadda bai ce komai ba, yadda ko murmushi bai yi ba, yadda ya maze kamar ba wani abu mai muhimmanci ya aikata ba. Wayar ta rike a tafin hannunta, tana jin nauyinta fiye da yadda ta kamata. A hankali ta shaka iska, sannan ta juya zuwa cikin gida, zuciyarta na ji kamar tana tafiya da wani SIRRI. *** Fawaaz yana tuƙi, amma hankalinsa ba a kan titi yake ba. Bai masan dalilin futar sa daga gida ba, Ba don yana da horo ba, da tuni ya samu matsala. Yana ta kici-kicin tunanin abinda ya aikata. Me yasa bai iya cewa komai ba? Me yasa ba zai iya cewa "na siya miki ne domin dubun kaunar ki danake da tsananin kwadaituwa da son jin muryar ki.." ba? Bai gama amsa wa kansa wadannan tambayoyin ba, sai wayarsa ta fara ƙara. Ya duba—Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad. Zuciyarsa ta harba. Sai dai ko da haka, ya tsare fuska kamar ba komai. A hankali ya ɗaga, yana kokarin tabbatar da cewa muryarsa ba zata nuna wani motsin rai ba. "Hello," ya ce a dakile. Shiru daga dayan bangaren. "Yaa Fawaaz..." Ta ambaci sunansa a hankali, kamar mai jin nauyin magana. "Na'am," ya amsa, har yanzu ba tare da ya nuna wata alama ba. "Ba ka gaya min me yasa ka siya min waya ba." Sai da ya lumshe idanu kafin ya bude su a hankali. Bai san me zai ce ba. "Saboda ina so ki dinga samun damar magana da kowa cikin sauki," ya ce, ba tare da ya yi tunani sosai ba. Shiru. "Yaa Fawaaz," ta sake kiran sunansa, murya a kasalance. Ya ji kamar tana son tace wani abu. Kawai sai ya danyi ajiyar zuciya. "Nabeeha, ki yi amfani da ita. Hakanan." Daga nan ya katse kiran. Ya ajiye wayarsa a gefen kujera, ya dan tsare numfashinsa na ƴan dakiku. Bai san dalili ba, amma zuciyarsa na bugawa da wani iri. Ya riga ya aikata. Kuma ko da kuwa bai fadi ba, ya san zata fahimta... ko ba yanzu ba, wata rana. _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ * *KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_ 🧳➿💞 *PG :24* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb __ Nabeeha ta kalli wayar a hannunta, zuciyarta cike da tunani. Kalaman Fawaaz sun sake dawo mata da karfi, "Nabeeha, ki yi amfani da ita. Hakanan." Hakanan? Ta girgiza kai a hankali. Duk da miskilancinsa da kamun kansa, Fawaaz ba mutum bane da zai bada kyauta haka kawai. Wani abu ya sa shi yin haka, amma bai iya furtawa ba. Ta lumshe ido, zuciyarta na bugawa da wani iri. Me yasa Fawaaz yake haka? Me yasa bai iya cewa komai kai tsaye ba? Me yasa yake boye komai a karkashin miskilancinsa? *** Bayan kwana biyu, Nabeeha ta saba da sabuwar wayarta. Sai dai har yanzu, bata daina mamakin Fawaaz ba. Tun daga lokacin da ya bata wayar, bai sake magana da ita ba. Kamar yadda ya saba, sai dai idanunshi da take ji kamar suna bin ta a duk lokacin da suke tare da kowa. Wannan dare, tana dakin ta tana duba wayar. Bata san dalili ba, amma sai da ta shiga sakon ta na WhatsApp ta fara neman lambarsa. Sai ta tsinci kanta da kallon chat dinsu. Kusan duk sakon da ya taba turawa yana da kamewa. "OK." "Na gani." "Zan duba." Ko da wasa bai taba cewa wani abu mai yawa ba. Sai dai a tsakanin wadannan sakonnin masu takaitaccen lafazi, tana jin akwai abu da yake boyewa. A hankali ta zura yatsarta ta rubuta, "Yaa Fawaaz, nagode." Ta aika, tana jin bugun zuciyarta yana karuwa. Tana shirin kashe wayar, sai ta ga alamar typing. Zuciyarta ta tsaya cak. Daga nan, sai sakonsa ya shigo. "Ba komai." Saukakken kalma ce. Amma tana jin kamar akwai wani nauyi tattare da ita. Ta cije leɓe. Hannunta na rawa kaɗan, ta sake rubuta wani sako. "Me yasa ka siya min ita?" Sai shiru. Babu alamar typing. Babu komai. Duk da haka, ta tabbata ya gani. Kuma ta tabbata yana ji kamar yadda take ji. Tana ajiye wayar a kan filo, zuciyarta cike da tambayoyi da ba ta da amsarsu. Fawaaz yana son boye kansa. Amma ita, tana jin kamar lokaci na zuwa da zai fuskanci zuciyarsa, ko da kuwa da kalmomi masu sauki ne. Zuciyar da Ba Ta Magana Fawaaz yana kwance a gadonsa, wayarsa a hannu, yana kallon sakon Nabeeha. "Me yasa ka siya min ita?" Zuciyarsa ta harba, amma bai motsa ba. Bai rubuta komai ba. Bai san me zai ce ba. Me zai ce? "Saboda ina son ki"? Hakan ba zai taba fita daga bakinsa ba. Ko "Saboda ina kaunarki"? Ai ma ya kasa furtawa ga kansa, balle kuma gareta. Hannunsa ya kara matse wayar. Bai taba jin kansa haka ba. Bai taba jin tsoron furta abu ba kamar haka. Amma ita, ta sanya shi jin wani yanayi da bai saba da shi ba. Sai ya kashe wayar, ya ajiye a gefensa, yana jin nauyin zuciyarsa. *** A rana ta gaba, sun hadu a farfajiyar gidan. Kamar yadda aka saba, Fawaaz yana zaune ne yana duba laptop dinsa, yana duba wasu bayanai na aikin sa. Nabeeha ta karaso, hannunta rike da wayar da ya bata. A hankali ta tsaya a gabansa, tana kallonsa. "Fawaaz." Ya dago ido, fuskarsa kamar ba shi ya jiya sakonta ba jiya. "Me yasa ka siya min ita?" Ta sake tambaya, kamar yadda ta rubuta a sakon WhatsApp. Shiru. Ya kalleta, amma ba tare da ya furta komai ba. Ta sauke ajiyar zuciya. "Idan ba ka son fada, ba komai. Amma na gode." Ta juya da niyyar barin wajen. Amma kafin ta taka mataki na biyu, sai ta ji muryarsa—mai sanyi, mai nauyi, wadda ta sa numfashinta tsayawa. "Saboda na san wata rana, zan so jin muryarki... ko da kuwa ba za ki taba ji na na magana ba." Ta tsaya cak, ta juyo da sauri. Idanunta suka sauka a kansa, amma har ya riga ya sunkuyar da kai, yana sake maida hankalinsa kan laptop dinsa, kamar ba shi ya furta kalmomin ba. Zuciyarta ta harba. Ta bude baki da niyyar cewa wani abu, amma ba ta san me zata ce ba. A karo na farko, Fawaaz ya bar zuciyarsa ta yi magana. Ko da kuwa a takaice ne. Kuma ita ta fahimta. Ta fahimci komai. ______ Dakin shiru ne. Babu komai sai kiran iskar dare daga waje da kukan agogon bango yana tafiya a hankali. Fawaaz yana kwance a gadonsa, hannunsa daya a dunkule, dayan kuma yana shafa gashin kansa a hankali, tamkar wanda yake tunanin matsala mai wuyar warwarewa. Idanunsa a rufe, amma zuciyarsa ba ta huta ba. Duk da shiru da duhun dakin, tunaninta yana nan da shi. Yana jin numfashinta a cikin tunaninsa, yana ganin murmushinta a cikin duhun da ke rufe idanuwansa. Ya juyo da gefen jikinsa, yana jin nauyin zuciyarsa kamar tana cike da wani abu da ba zai iya furtawa ba. Yana son ta. Ya san hakan. Ya tabbatar da hakan fiye da yadda yake tabbatar da komai a rayuwarsa. Amma yana gudu. Yana gudun furta abin da zuciyarsa ke ji. Yana tsoron idan ya fadi, idan ya bayyana, me zai faru? Me zai faru idan zuciyarsa ta bayyana sirrinta? *** A cikin duhun dakin, idanunsa a rufe, yana iya hango ta kamar tana kusa da shi. Yadda idanunta ke haskakawa idan tana magana. Yadda take dan taɓa hancinta idan tana tunani. Yadda take murmushi har dimples dinta su bayyana. Ya tuno yadda take kokarin hana dariyarta fita idan wani abu ya bata dariya. Yadda idan tayi murmushi, zuciyarsa ke tafasa da wani yanayi da ya kasa misaltawa. Kamar yana jin kamshin turarenta a kusa da shi. Wannan turaren da ya saba jin kamshinsa idan ta wuce kusa da shi, ko idan tana kusa da shi a dakin gaisuwa. Ya runtse idanu da karfi. Me yasa bai iya barin tunaninta ya fita daga zuciyarsa ba? Ko zai yi bacci, da ita yake kwana. Ko zai farka, tana nan cikin tunaninsa. Ko yana aiki, yana jin kamar zata fito daga wani wuri ta sake ce masa, "Yaa Fawaaz." Muryarta tana da laushi, tana da wani irin sauti da ke sanya shi tsayawa tunani ko da kuwa yana cikin gagarumin aiki. *** Ya kai hannu ya dauki wayarsa, yana kallon fuskar wayar na tsawon lokaci. Bai san dalili ba, amma sai da ya bude chat dinsu. "Me yasa ka siya min ita?" Tun jiya take jiran amsa. Tun jiya take son jin dalilin da yasa ya bata kyauta. Shiru yayi yana kallon rubutun. Zuciyarsa na bugawa da karfi. Yana da abubuwa da yawa da zai ce. "Saboda kina da muhimmanci a wajena." "Saboda na riga da na saba da kasancewarki kusa da zuciyata." "Saboda... ina son ki, Nabeeha." Sai ya dafe goshinsa a hankali. Zai iya cewa haka? Zai iya bude zuciyarsa da kansa? Wani sashe na zuciyarsa yana son rubutawa. Yana son furta gaskiyar da yake boyewa tun farko. Amma wani sashen yana hana shi. Fawaaz ya kashe wayar, ya sake kwanciya, yana jin zuciyarsa tana bugawa kamar zai ji kalmomin da bai iya furtawa suna fitowa da kansu. Zai iya boye zuciyarsa daga mutane. Amma ba zai iya boye ta daga kansa ba. Kuma babu shakka—wata rana, watakila daga bakin ta ko daga nashi, amma wata rana, wannan gaskiya da yake gujewa za ta fito fili. .... Yana tsaye a cikin duhun bishiyoyi, yana boye jikinsa da kyau domin kada su gan shi. Daga inda yake, yana iya hango su Hajia Karama, Hajia Ladi, da Hajia Rumanah suna tsaye a gaban wani tsoho mai dogon gemu da jajayen idanun da ke cike da alamun sihiri. A hankali ya matso da kunensa domin jin abin da suke fadi. "Ba mu son kuskure wannan karon," cewar Hajia Karama, tana hadiye yawu. "Dole a tabbata an shafe su gaba daya," Hajia Ladi ta ce tana girgiza kai. "Idan Zaytunah da yaranta sun wanzu, to wallahi, mu za mu zama matsala a idanun duniya." Bokan ya kada sandarsa mai bakin ƙaho. "Kun tabbata ba wanda ya biyo ku?" Hajia Rumanah ta dan saki murmushi. "Babu. Mun fito a hankalce sosai. Muna son a yi aikin da babu wanda zai taba sanin mu ne muka aikata." "Toh ai na gaya muku," cewar bokan yana mai kada kansa. "Idan za a yi aikin, sai kun kawo mini wani abu da ke jikin wannan Zaytunah. Na biyu, dole a samo wani abu da zai shafi yaranta—wanda suka fi amfani da shi kullum." Hajia Karama ta kalli Hajia Ladi, sai ta ce, "Zan samu mayafinta. Ni na san yadda zan yi hakan." "Ina da kofin shan shayi da take amfani da shi kullum a baya" Hajia Rumanah ta kara da cewa. Bokan ya kada kansa. "Duk wannan yana da kyau. Amma ku sani, idan har kuka biya kudin da ake bukata, to babu komai. Za a shafe su daga doron kasa." Hajia Ladi ta zaro kudade masu yawa ta aje a gabansa. "Idan kudin ne, babu matsala. A tabbata aikin an yi shi yadda ya kamata." Suka tsaya suna ci gaba da tsara yadda za a aikata abin da suke shiryawa. Amma Haruna, daya daga cikin ma’aikatan gidan Alhaji Uzairu, yana jin komai daga inda yake laɓe. Sun manta cewa idanun wani yana kansu. Suna gamawa, suka fice cikin dare. Haruna ya saki ajiyar zuciya, yana jin yadda gumi ya lulluɓe shi. A cikin zuciyarsa, ya san wannan lamari yana da matukar hatsari. Idan har bai yi abu akai ba, to ba zai yafe wa kansa ba. Dole ne ya sanar da Alhaji Amiru... *** Alhaji Amiru yana zaune a cikin falonsa, yana nazarin wasu takardu, lokacin da Haruna ya shigo da sauri. Da yake ya san shi a matsayin ma’aikacin gidan Alhaji Uzairu, sai ya kalle shi da mamaki. "Haruna, lafiya kuwa?" Haruna ya duka a gaban sa, yana kokarin daidaita numfashinsa. "Alhaji... akwai matsala babba! Wata babbar fitina ake shiryawa!" Alhaji Amiru ya jingina da kujera, yana jiran karin bayani. "Alhaji," Haruna ya ci gaba da cewa, "Ni ne da idona na ji, da kunnuwana na saurara. Su Hajia Karama, Hajia Ladi, da Hajia Rumanah... sun je wajen boka domin a kashe su Zaytunah gaba daya! Sun bada kudi, sun kuma tsara yadda za a aikata hakan." Zuciyar Alhaji Amiru ta buga da karfi. Ya kafe Haruna da ido na sakanni da dama. "Wani irin abu kake fada haka?" Ya tambaya, yana jin wani abu yana taso masa a KIRJI. "Wallahi da gaskiya nake magana, Alhaji!" Haruna ya kara tabbatar da cewa ba karya yake ba. "Sun ce za su kawo wani abu da ke jikin Hajiya Zaytunah da yaranta domin a kammala aikin." Alhaji Amiru ya shafa fuska da hannunsa, zuciyarsa na tafasa. Ya san cewa su Hajia Karama suna da tsananin kiyayya, amma bai taba zaton za su kai ga irin wannan mummunan nufi ba. Dole ne ya dauki mataki. Bai tsaya wata-wata ba, ya dauki waya ya kira Alhaji Uzairu, sannan ya kira mahaifiyarsu, Gwaggo Zainabu. *** A lokacin da suka zauna a babban falon gidan Alhaji Uzairu, shiru ne ya ratsa bayan Alhaji Amiru ya bayyana musu duk abin da ke faruwa. Alhaji Uzairu ya girgiza kai, yana jin kamar ba a duniya yake ba. "Babu yadda za a ce matana sun je wajen boka saboda su kashe Zaytunah!" Ya ce da karfi. Alhaji Amiru ya kafe shi da ido. "Uzairu, ka tabbata da hakan? Ka tabbata da cewa su Hajia Karama ba su da irin wannan niyyar?" Shiru ya biyo baya. Gwaggo Zainabu ta sauke ajiyar zuciya. "Idan da gaske ne wannan magana," ta ce cikin yanayi mai nauyi, "to dole ne mu dauki mataki kafin su aikata abin da suke so." Alhaji Amiru ya mike tsaye, yana jin zuciyarsa na harbawa da karfi. Idan har matan gidan suna da wannan mugun nufi, to dole a dakatar da su. Domin ko ba komai, Zaytunah da ‘ya’yanta suna da hakkin rayuwa. Ba za a bari wani ya shafe su daga doron kasa ba! _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_             🧳➿💞 *PG :25* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb ___ Shiru ya ratsa falon, kowanne daga cikinsu zuciyarsa tana tafasa. Alhaji Uzairu ya jingina da kujera, yana girgiza kai tamkar wanda ya kasa yarda da abinda kunnuwansa suka ji. "Subhan'Allah, Yaya Amiru," ya furta a hankali, yana dafe goshi. "An tabbatar da gaske Ladi da karama sune suka je wajen boka domin kashe Zaytunah?" Alhaji Amiru ya cije lebe, yana kafe shi da ido. "Uzairu, ya kamata ka gane cewa kai ba ka san matanka ba. Kawai kana zaune kana tunanin komai lafiya kalau, alhalin wasu suna neman shafe daya daga cikin matan ka da ya’yan ka daga doron kasa!" Gwaggo Zainabu ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. "Yanzu me za a yi?" Ta tambaya, tana kallon Alhaji Amiru. Alhaji Amiru ya kalli Haruna, wanda ya yi ta bayani a baya, ya kuma tabbatar da cewa abin da ya ji da kunnensa ba karya ba ne. Daga bisani, ya kalli Alhaji Uzairu. "Uzairu, ya kamata ka dauki mataki kafin lokaci ya kure," ya fada da kakkausar murya. Alhaji Uzairu ya numfasa, zuciyarsa na tafasa da tunani iri-iri. Bai san cewa haka matansa suke ba. Bai taba tunanin cewa za su iya aikata irin wannan mummunan abu ba. "Amma... ina bukatar hujja," ya ce cikin kasala. "Kana bukatar hujja?" Alhaji Amiru ya tambaya yana kallonsa da mamaki. "Shin har yanzu baka yarda da abinda aka fada ba?" "Ba wai ban yarda ba bane," Alhaji Uzairu ya ce, yana shafa fuskarsa. "Amma dole ne a tabbatar da komai kafin a dauki mataki." Haruna ya gyara zama, yana fuskantar Alhaji Uzairu. "Alhaji, wallahi da idona na gani, da kunnuwana na ji," ya fada cikin tabbaci. "Idan kuwa kuna bukatar wani shaida, zan iya komawa har wajen bokan domin a tabbatar." "Ba dole sai ka koma ba," in ji Alhaji Amiru. "Dole ne mu dauki mataki tun kafin lokaci ya kure." Gwaggo Zainabu ta jinjina kai. "Amma su kansu ba su san an tona musu asiri ba, ko?" "A’a," Haruna ya amsa. "Babu wanda ya san cewa na bi su, babu wanda ya san na ji komai." Shiru ya sake ratsa falon. Alhaji Uzairu ya dafe kansa, yana jin yadda zuciyarsa ke karyewa. Shin haka matansa suka zama? Su ne da suka daɗe suna tare da shi? Gwaggo Zainabu ta yi gyaran murya, sannan ta kalli Alhaji Amiru. "Yanzu me za ku yi?" Alhaji Amiru ya sauke ajiyar zuciya. "Muna bukatar mu fara da kare su Zaytunah," ya ce. "Dole ne mu tabbatar cewa sun fi kowane lokaci a cikin kariya." "Ta yaya?" Gwaggo Zainabu ta tambaya. Alhaji Amiru ya gyara zama. "Za mu samu Major General Dawud," ya ce. "Shi kadai ne zai iya tabbatar da cewa ba za a cutar da su ba. Idan har akwai wanda zai iya daukar mataki cikin gaggawa, to shi ne." Gwaggo Zainabu ta gyada kai. "Hakan yayi. Amma fa, ba za mu bari su Karama su fahimci cewa an tona musu asiri ba." "Tabbas," in ji Alhaji Amiru. Sannan ya juyo ga Alhaji Uzairu. "Uzairu, dole ne ka kara lura da matanka," ya ce cikin tsananin takaici. "Idan har ka barsu da wannan mugun nufi, to za su iya aikata abinda ba za ka taba yarda da shi ba." Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin tamkar kansa zai fashe. Bai san cewa matsalar ta kai haka ba. Amma yanzu, babu abin da ya rage face daukar mataki.... Shiru ya sake ratsa falon, kowanne daga cikinsu zuciyarsa cike da tunani mai nauyi. Gwaggo Zainabu ta dafa gefen kujera, ta dubi Alhaji Uzairu da idanuwanta da ke dauke da damuwa. "Uzairu, lokaci ya yi da za ka tsayu ka fuskanci gaskiya," ta fada cikin nutsuwa. "Idan ka yi sakaci, abin da zai biyo baya ka iya zama mafi muni fiye da yadda kake tunani." Alhaji Uzairu ya bude ido, yana kallonta. Har yanzu zuciyarsa ba ta gama karbar gaskiyar abin da ake fada masa ba. Sai dai yana jin nauyinsa sosai. Alhaji Amiru ya yi gyaran murya. "Maganar gaskiya, ba zamu jira har su sake kokarin cutar da Zaytunah ba," ya ce da kwarin gwiwa. "Dole ne mu kai rahoto wajen Major General Dawud. Shi ne kadai zai iya magance wannan matsala cikin gaggawa." Gwaggo Zainabu ta jinjina kai. "Hakan daidai ne," ta ce. "Amma kada mu manta cewa idan suka fahimci cewa an gano su, to ba abin da ba za su iya aikatawa ba domin su kare kansu." Haruna ya gyada kai. "Tabbas, su Karama da kishiyoyinta ba za su yi kasa a gwiwa ba idan suka ji cewa an bankado SIRRIN su," ya ce. "Wannan shine dalilin da ya sa dole a yi komai a hankali, ba tare da sun fahimta ba." Alhaji Uzairu ya gyara zamansa, ya dubi Alhaji Amiru da Gwaggo Zainabu. "To yanzu, ya za ayi?" ya tambaya cikin damuwa. Alhaji Amiru ya yi shiru na dan lokaci, kafin ya kalli Haruna. "Ka shirya ka sake tafiya wajen boka?" ya tambaya. Haruna ya yi ajiyar zuciya, ya kalli su duka. "Idan hakan zai tabbatar da cewa muna da cikakken shaida, zan sake komawa," ya ce cikin karfin hali. "Sai dai, dole a yi HANKALI kada su fahimci cewa ana bincikensu." Gwaggo Zainabu ta dubi Alhaji Uzairu. "Uzairu, kana da tabbacin cewa za ka iya hada kai da mu wajen ganin an yi adalci?" Alhaji Uzairu ya dago idanuwansa, yana kallon kowa daya bayan daya. A zuciyarsa, yana jin radadin cewa iyalinsa sun fi kowa cutar da shi. Bai taba tunanin cewa akwai wata rana da za a gaya masa irin wannan abu ba. Ya numfasa, sannan ya gyada kai. "Na amince," ya ce a hankali. "Ba zan bari su kashe min iyali ba." Alhaji Amiru ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. "To, lokaci bai yi ba da za mu tafi wajen Major General Dawud ba?" Gwaggo Zainabu ta gyada kai. "Yanzu ne lokaci. Ba za mu jira har sai wani abu ya faru ba." Alhaji Amiru ya mike tsaye. A nan suka yanke shawarar tafiya wajen Major General Dawud, don a dauki matakin kare Zaytunah daga mummunar makarkashiya da kishiyoyinta suka kitsa... Suna fitowa daga falon, kowanne daga cikinsu zuciyarsa cike da tunani. Alhaji Uzairu yana bin su da baya, har yanzu kansa a kulle yake da abubuwan da suka faru. Bai taba tunanin cewa wata rana zai fuskanci wannan matsala daga matansa ba. Haruna ne ya dauki nauyin tukin motar, yayin da Alhaji Amiru da Alhaji Uzairu suka zauna a bayan mota, kowanne cikin nitsuwa. A lokacin da motar ta bar harabar sashen Gwaggo Zainabu, shiru ya ratsa cikin su. Alhaji Uzairu ya lumshe idanu, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi. Abin da ke faruwa ya girgiza shi matuka. “Uzairu, ka tabbatar cewa kana da ƙarfin zuciyar fuskantar abin da zai biyo baya?” Alhaji Amiru ya tambaya, yana dubansa. Alhaji Uzairu ya bude idanu, ya dubi dan uwansa. “Dole na yi hakan, Yaya Amiru,” ya ce da karfin hali. “Ba zan iya bari su hallaka min ‘ya’ya ba.” Haruna ya cigaba da tuƙi cikin nutsuwa, yana bin titin da zai kaisu gidan Major General Dawud. MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RES: A lokacin da suka isa, an shigo da su kai tsaye zuwa falon ba tare da wata matsala ba. Major General Dawud yana sanye da kayan gida, yana zaune bisa kujerar da ke gefen babban falonsa. Da gani, yana cikin shirin hutawa ne kafin su shigo. Ya kalli su daya bayan daya, kafin ya maida kallonsa ga Alhaji Amiru. “Kun zo da gaggawa, Amiru,” ya fada a hankali. “Ina sauraronku.” Alhaji Amiru ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara bayanin komai dalla-dalla. Ya fada masa yadda Haruna ya bi matan Alhaji Uzairu har wajen boka, yadda ya ji su da kunnuwansa suna tsara kashe Zaytunah, da yadda Alhaji Uzairu ya kasa yarda da hakan har sai an kawo hujja mai karfi. A lokacin da Alhaji Amiru ya kai karshe, fuskar Major General Dawud ta nuna tsananin ɓacin rai. “Kun tabbatar da cewa wannan maganar gaskiya ce?” ya tambaya, yana duban Haruna da tsananin ido. Haruna ya gyada kai. “Wallahi, babu shakka akan haka, ranka ya dade,” ya ce da tabbaci. Major General Dawud ya jingina da kujera, yana tunani na wani lokaci. “Idan haka ne, lamarin yana bukatar gaggawa,” ya ce a hankali. “Ba zan bari komai ya same su Zaytunah ba. Fata dai a same sun..” Ya dubi Alhaji Uzairu da kyau. “Uzairu,” ya kira sunansa da kakkausar murya. “Kana da tabbacin cewa ba za ka yi wata-wata wajen daukar mataki akan wannan lamari ba?” Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin nauyin kalmomin Major General Dawud. Da farko, yana jin kamar abin kamar mafarki ne, amma yanzu ya san babu gudu ba ja da baya. “Na tabbatar,” ya amsa cikin muryar da ke nuna yanke shawara. Major General Dawud ya mike tsaye. “To, ku jira ni,” ya fada. Ya yi gaba zuwa wani daki, sannan ya fito cikin uniform dinsa, yana daure da damara. Fuskar sa a daure take, alamun ya gama yanke shawara akan abin da zai yi. “Za a tsaurara tsaro Inn shaa' Allah" Ya kalli su duka, sannan ya dauki wayarsa. “Kuma ba zan tsaya nan ba. Sai mun tabbatar da cewa an hukunta duk wanda ke da hannu a wannan makirci.” Alhaji Uzairu ya runtse ido, zuciyarsa cike da nauyi. Ya san cewa daga wannan rana, rayuwar sa ba za ta kara zama kamar yadda take a da ba... _1-KALBIM:MAMUH GEE_ _2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_ _3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_ _4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_ °° _1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_ _2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_ _3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_ _4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_ _5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_ _ku tura receipt zuwa ga 09033181070_ *IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:* *09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!* ____ *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:26_ Da Alhaji Uzairu ya iso gida, bai wuce kai tsaye zuwa dakinsa ba. Maimakon haka, ya tsaya a babban falon gida inda matansa, Hajiya da Hajiya Karama, suke zaune suna tattauna wasu batutuwa a tsakaninsu. A ganinsa, kamar dai suna magana ne da nutsuwa, amma da zarar suka hango shi, sai suka yi shiru tamkar wadanda aka kama da laifi. Ya zuba musu ido na dan lokaci ba tare da ya ce komai ba. Sai da ya zauna a kujera ya dora kafa daya kan daya, sannan ya gyara zama, yana jin nauyin da ke cikin zuciyarsa. "Hajiya," ya kira sunan matar sa ta farko, "yau na wuni a gidan Ya Amiru." Hajiya ta kalle shi cikin kulawa. "Lafiya dai? Ka dawo da wuri yau." "Eh, ai ba wani abu," ya fada, yana juyawa zuwa ga Hajiya Karama. "Mun yi doguwar hira da Alhaji Amiru da Gwaggo Zainabu. Sun yi tambayoyi da yawa game da rayuwar mu." A take, Hajiya Karama ta hadiye yawu. "Tambayoyi irin na menene kuma?" Alhaji Uzairu ya girgiza kai. "Kawai dai wasu tsofaffin batutuwa ne… da kuma wasu abubuwan da suka shafi rayuwar mu a baya." Hajiya ta dube shi da dan tsoro. "Rayuwa ta baya fa?" Sai ya gyada kai a hankali, yana kallonsu dukkansu. "Kusan shekara goma kenan da wasu abubuwa suka faru… kuma sai yanzu suke tambayata su kansu. Abin mamaki, ko ba haka ba?" Hajiya Karama ta shiga girgiza kai. "To, me ya sa sai yanzu suka tuna? Ai da ace wani abu ne mai muhimmanci, da tuni sun yi magana da kai a baya." Alhaji Uzairu ya dan saki murmushi mara dadi. "Hakan nake tunani. Amma kin san wani abu? Na fara jin kamar akwai wani abu da ba a gaya min ba. Kuma hakan yana bani mamaki sosai." Hajiya karama ta dan yi dariya. "Me kake nufi da wani abu da ba a gaya maka ba? Me ya sa kake tunanin haka?" Sai ya jingina da kujera, yana dubansu dukkansu da idon bincike... "Hakane," ya ce yana kallonsu da ido mai zurfi, "amma abin da ya faru bai shuɗe haka kawai ba. Ko dai wani ne ya sa hannu, ko kuma akwai wani SIRRI da ake boyewa." Hajiya da Hajiya Karama suka kalli juna a lokaci guda, tamkar suna kokarin jin wace za ta fara magana. Sai dai dukkansu sun kasa cewa komai nan take. Alhaji Uzairu ya gyara zama, yana nazarinsu. "Kun san abinda ya fi bani mamaki?" Hajiya Karama ta yi saurin girgiza kai. "A’a." Ya sake dubansu duka, sannan ya furta a hankali: "Yadda duk sanda aka ambaci sunan Zaytunah, sai ku dinga kokarin gujewa maganar." A take, Hajiya ta ɗan ja numfashi. "Ba haka bane, Alhaji. Ai ba wai muna gujewa bane, kawai dai... ba mu ga amfanin tada wannan batu ba." "Ba ku ga amfaninsa ba?" Ya jinjina kansa, yana kallonsu da kyau. "Matar aure ce, Mahaifiya ga yayanta. Yara biyu. , baƙar rana daya ta ɓace, har yau ba a san inda take ba da iyalanta, ba a san ko tana raye ba ko kuma..." Ya dan dakata, yana son ganin yadda za su karɓi kalmomin nasa. Hajiya Karama ta sake gyara zama, ta lumshe ido na ɗan lokaci, kamar tana tunanin wani abu. Da ta buɗe su, sai ta ce da ƙasa-ƙasa: "Ai Allah kadai yasan inda take, Alhaji." Alhaji Uzairu ya haɗiye yawu. Yanzu ya fara jin wata irin hujja a cikin muryarta. "Kun tabbata?" Ya tambaya, yana jefa musu wani irin kallo da ya sa dukansu suka rasa yadda za su mayar masa da martani. Hajiya ta ɗauke kanta gefe, yayin da Hajiya Karama ta sunkuyar da kai. Wannan ne karon farko da ya tabbatar da cewa akwai wani abu da suke ɓoyewa. SIRRI ne da suka daɗe suna rufewa, amma yanzu lokaci ya kusa da za a tona komai. Alhaji Uzairu ya jima yana kallon matansa, zuciyarsa na harbawa da sauri. Sun kasa sake kallo da shi kai tsaye, wanda hakan ya tabbatar masa da cewa akwai wani abu da suke ɓoyewa. Ya numfasa a hankali, sannan ya ce da murya mai cike da tuhuma, “Da alama akwai wani abu da ba a gaya min ba.” Hajiya ta ɗan ɗago kai cikin gaggawa. “Me kake nufi da haka, Alhaji?” Ya gyara zama, yana mai haɗa yatsun hannunsa. “Ina nufin, tun shekaru da yawa da suka wuce, na lura da yadda kuke kaucewa batun Zaytunah. Kullum idan na kawo maganarta, sai ku canza zancen. Kuma a yau ma, abin da kuka faɗa ya kara bani mamaki.” Hajiya Karama ta yi saurin girgiza kai. “Ai ba haka bane, Alhaji. Muna tsoron kada wannan maganar ta dawo da maka damuwa ne. Ka san dai yadda rayuwa take…” Alhaji Uzairu ya saki wani murmushin da bai kai idonsa ba. “Rayuwa ko kuwa wani abu daban?” Hajiya Karama ta shiga ƙara haɗiye yawu, alamar damuwa. Ita kuwa Hajiya, sai ta cije leɓenta na ƙasa, kamar mai tunanin wani abu. Sai ya jingina da kujera, yana dubansu da kyau. “Ko da ace an manta da duk abin da ya faru, to me zai hana ku gaya min gaskiya yanzu? Ku faɗa min abin da kuka sani game da batan Hajiya Zaytunah.” A take, fuskar Hajiya Karama ta ɗan chanza launi, sai dai ta yi kokarin boyewa. “Ai... ai bamu san komai ba, Alhaji.” Alhaji Uzairu ya daka tsaki, yana jin zafin yadda suke ƙoƙarin ɓoye wani abu. Ya dafe goshinsa sannan ya dubi Hajiya da idanu masu ƙayatarwa. “Na faɗa muku gaskiya za ta bayyana, ko da ba daga gare ku ba. Amma idan har wani abu ya fito daga bakin wani, ba daga wurin ku ba, to wallahi ba zan taɓa yafewa ba.” A take, Hajiya Karama ta yi saurin kallon Hajiya, fargaba na bayyana a fuskarta. Hajiya ta matse hannunta tare da jan numfashi. “Alhaji…” Ta kira sunansa da wata irin murya. “Na ji,” ya katseta da kakkausar murya. “Sai dai in faɗi haka kawai, amma na san tabbas kuna da hannu a cikin batan Hajiya Zaytunah.” Hajiya Karama ta shiga girgiza kai da sauri. “A’a, Alhaji, ba haka bane…” Ya tashi tsaye da sauri, yana mai jefa musu wani kallo mai tsananin tuhuma. “Kada ku ƙara ƙoƙarin raina min hankali. Gaskiya tana nan kusa, kuma da izinin Allah, zan gano komai.” Ya juya yana barin falon, zuciyarsa na tafasa. A yanzu, ya tabbatar da abu guda—matansa sun san wani SIRRI mai girma, kuma lokaci ya kusa da dukkan komai zai fito fili! MX *KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_ 🧳➿💞 *PG :27* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb Nabeeha ta goge hawayen da suka wanke mata fuska. Har yanzu zuciyarta tana dukan da ba ta saba ba. Komai yana yawo a kwakwalwarta tamkar mafarki. "Ammi, me kike nufi da cewa har yanzu ba kya so wasu su san kina raye?" Hajiya Zaytunah ta dafe zuciya, tana jin yadda kalmar da Nabeeha ta furta ke da nauyi. Ta san cewa dole ne ta karasa bayyana komai, amma ba ta so ta daga hankalin ‘yarta fiye da haka. "Nabeeha, akwai abubuwan da suka faru a baya da suka tilasta min boyewa," ta fara da murya mai rauni. "Ba wai kawai kishiyoyina suka yi min sharri ba, har da wasu daga cikin dangin mahaifinki sun hada baki." Idanun Nabeeha suka kara girma. "Dangin Abba?" Hajiya Zaytunah ta gyada kai. "Eh, Nabeeha. Ba kowa ne a dangin mahaifinki ke kaunata ba. Wasu sun yi kokarin ganin cewa na rasa komai, har da rayuwata." Nabeeha ta hadiye wani yawu mai daci. " Nabeeha ta ji wani irin nauyi a zuciyarta, kamar ana kokarin murkushe ta. "Ammi, wa ke da alhakin rabamu da ke? Ban da kishiyoyin ki, wane daga cikin dangin Abba ke da hannu?" Hajiya Zaytunah ta yi shiru na tsawon lokaci, tana tunanin yadda za ta fassara wa ‘yarta matsalar da ta jima tana gujewa. "Akwai mutanen da ba za su so ki san gaskiya ba, Nabeeha," ta fada a hankali. "Ba wai kishiyoyina kadai suka so su hallaka ni ba, akwai wasu daga cikin ‘yan uwan mahaifinki da suka dauka cewa kasancewa ta a cikin gidan na zama barazana gare su."ta karasa fada tana boye lamarin game da ainihin babun rumanah yar uwarta Kuma matar wan mijin tah.. Nabeeha ta dafe kanta. "Ammi, menene hakan ke nufi?" Hajiya Zaytunah ta gyara zama, tana mai tattara natsuwarta. "Na kasance a matsayin matata biyu ga mahaifinki, kuma hakan ya sa na samu kulawa da girmamawa sosai daga bangaren danginsa," ta fara bayani. "Kishiyoyina ba su taba jin dadi da hakan ba. Sun san cewa idan zan zauna a gidan, ina da damar yin tasiri, kuma ina iya tabbatar da cewa yaran da na haifa su ne za su gaji mahaifinsu fiye da kowa." Nabeeha ta lumshe ido. Ta san irin takun saka da ke tsakanin mata da kishiyoyinsu, amma ba ta taba tunanin cewa hakan zai kai ga irin wannan makircin ba. "Kishiyoyina sun hada baki da wasu daga cikin mutanen su suka yanke shawarar kawar da ni," Hajiya Zaytunah ta cigaba. "Sun fara da haddasa matsala a tsakanina da mahaifinki, ta yadda zai fara jin cewa ni ce matsalar gidan. A lokaci guda kuma, suna aiki a bayan fage domin ganin na fada cikin wani hali da ba zan iya dawowa daga ciki ba." Nabeeha ta kasa hakuri. "Shin mahaifin mu ya san da wannan makirci?" Hajiya Zaytunah ta numfasa. "Ba zan iya cewa ya sani gaba daya ba, amma yana da laifin kasa gane gaskiya. Sun rufe masa ido da makirci, suka sa shi ya fara kallona a matsayin matsala maimakon matar da yake so. Hakan ya sa na shiga wani hali da ba zan iya fita daga cikinsa ba." Shiru ya ratsa dakin. Nabeeha ta ji wani irin zafi a zuciyarta. Kamar zuciyarta tana tafasa da wani abu mai radadi. "Ammi, don Allah ki gaya min gaskiya, shin mahaifin mu yana da hannu a abin da ya faru da ke?" Hajiya Zaytunah ta kalli ‘yarta a hankali. "Ba zan ce yana da hannu kai tsaye ba, amma laifinsa shi ne kasa fahimtar gaskiya. Idan da ya tsaya ya bincika, da ba zan shiga wannan hali ba. Idan da ya tsaya ya kare ni kamar yadda ya kamata, da ba zan shiga cikin wahalar da na shiga ba." Hawayen Nabeeha suka cika idonta. Tana jin wani irin takaici a zuciyarta. Ashe mahaifinta ya bar mahaifiyarta cikin hali mara dadi? Ashe ya bari wasu suka yi mata sharrin da ya raba su? "Ammi, menene ya faru da ke bayan kin bar gidan?" Hajiya Zaytunah ta lumshe ido. "Bayan an yi min asiri, na yanke shawarar barin gidan, amma ba da sanin mahaifinki ba. Na san cewa idan har ya san inda nake, zai iya sa a dawo da ni, kuma hakan na iya jawo wani mummunan abu. Gwaggo Hafsatu ce kadai ta san gaskiyar lamarin. Ita ce ta dauke ni ta kawo ni gidan nan, ta rufa min asiri....duk da lokacin Dana bar cikin gidan mahaifin ki. Gaskia magana bansan inda Kai na yake ba a lokacin. Na ji dai tamkar ana ingiza wutar kiyayyar san barin cikin gidan a zuciyata. Na kasa nutsuwa da sukuni har sai Dana bar cikin gidan. Kai tsaye bansan inda Kai na yake ba. Har na bar garin. Da temakon Allah da dattijuwar arzikin da muka hadu da ita. Allah ya sanya albarka a yadda na kawo a yanzu . Ciki harda ku. Ke da Hammad" Nabeeha ta goge hawayenta. "To, me ya sa har yanzu ba ki yi kokarin sanar wa mahaifin mu gaskiya ba? Ba kya so ya san cewa kina raye?" Hajiya Zaytunah ta girgiza kai. "Ba haka kawai zan iya komawa rayuwarsa ba, Nabeeha. Abubuwa da yawa sun faru. Ba zan so komawa rayuwarsa ba tare da tabbacin cewa zan iya kare kaina daga masu son ganin bayana ba." Nabeeha ta gyada kai, tana jin yadda zuciyarta ke cike da damuwa. "Ammi, me zai faru idan Abba ya gano gaskiya? Idan ya san cewa kina raye?" Hajiya Zaytunah ta dafa hannun ‘yarta. "Zan fuskance shi idan lokaci ya yi. Amma har yanzu, ba na son hakan ta faru ba tare da nayi shiri ba." Shiru ya ratsa dakin. Nabeeha ta ji wani irin nauyi a zuciyarta. A yau, ta gano cewa rayuwarta ba kamar yadda take tunani ba ce. Ashe ita ‘yar wata halitta ce da aka ci da sharri? Ashe ita ce ‘yar matar da aka aikata mugunta a kanta? Daga karshe, ta kalli Ammi da idanu masu cike da alamar tambaya. "Ammi, yanzu me kike so in yi da wannan gaskiya?" Hajiya Zaytunah ta sauke numfashi. "Ina so ki yi hakuri, Nabeeha. Kuma ina so ki ci gaba da rayuwarki da tsantsar HANKALI. Kada ki bari wannan gaskiya ta rude ki har ki dauki matakin da ba a shirya ba." Nabeeha ta runtse ido. Ta san cewa daga yau, babu komai da zai kara zama kamar da.. Duk da fadin hajia zaytunah cewa kada ta bari wannan gaskiya ta rudeta, zuciyar Nabeeha ta kasa daukar hakan. Ta kwana tana juyi akan gado, zuciyarta tana yawo daga abu zuwa abu. Tunani daban-daban suka cunkushe mata kwakwalwa—abin da ya fi ci mata tuwo a kwarya shine mahaifinta, Alhaji Uzairu. Idan har Ammi ba ta so ya sani, to me ya kamata ta yi? Ta ci gaba da rayuwa tamkar babu komai? Ta rike wannan sirrin a ranta har abada? Da safe, har ta gama shiri ba ta ga Ammi ba. Wannan ya dada dagula mata lissafi, don haka sai ta nemi Hammad a waya. “hammad, kana ina?” Muryar Hammad ta amsa da kasala. “Ina gida. Kina bukatata?” “Kana da lokacin magana?” “Eh, menene?” Nabeeha ta hadiye yawu. Duk da cewa Hammad yana cikin wannan al’amari, har yanzu bai fahimci nauyinsa ba kamar yadda take ji Shiru daga dayan bangaren na dan lokaci, sannan Hammad ya ce, “Tun kafin na zo nan.” Nabeeha ta runtse idom A bangaren Ammi kuwa, tana cikin falonta tana tunanin irin kallon da Nabeeha ke yi mata tun jiya. Duk da cewa ta gama shari’ar da kanta cewa Nabeeha za ta dauki lokaci kafin ta gama karbar gaskiya, ta san cewa yarinyar nan tana da son sanin hakikanin gaskiya. A ranar, tana zaune tare da Gwaggo Hafsatu a dakin. Bayan dogon shiru, sai Gwaggo Hafsatu ta kalle ta. “Zaytunah, ya kamata ki shirya kanki.” Hajiya Zaytunah ta dago ido. “Meye hakan ke nufi, Gwaggo?” Gwaggo Hafsatu ta dan ja dogon numfashi. “Nabeeha za ta iya tunkarar mahaifinta da kanta. Idan har hakan ta faru, ba zai kasance da sauki ba.” Hajiya Zaytunah ta dafe kanta. “Gwaggo, har yanzu ban shirya fuskantar sa ba. Ban shirya fuskantar dukkan su ba.” Gwaggo Hafsatu ta kalli Zaytunah da kulawa. “Dole ne ki shirya. Idan har Nabeeha ta tunkare shi da kanta, ba zai kasance da sauki gare ki ba. Idan har gaskiya ta fito, ba za ki so a same ki cikin rashin shiri ba.” Shiru ya ratsa dakin. Hajiya Zaytunah ta san cewa Gwaggo Hafsatu na da gaskiya, amma har yanzu zuciyarta tana tafasa da fargaba. --- A ranar, da yamma, Nabeeha ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta. Idanunta sun cike da damuwa, zuciyarta tana bugawa da sauri. . MX *KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_ 🧳➿💞 *PG :28* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb ×××Alhaji Uzairu ya ja dogon numfashi a daya bangaren wayar, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri. "Nabeeha, menene wannan magana?" Nabeeha ta rufe idonta da karfi, zuciyarta tana tsananta bugawa. Wannan shi ne lokaci mafi wahala da ta taba fuskanta. "Abba na,Ashe inada rabon ganawa da ku a doron duniyar nan? Ashe muma munada mahaifi da yake a raye kamar su Humayrah? zan zo wajenka in gaya maka da kaina abba," ta fada a hankali. Shiru ya ratsa tsakanin su na tsawon dakika goma. Sannan sai Alhaji Uzairu ya furta, "Eh mana diyar albarka, wannan batu haka yake. To shikenan, ina jiranki." Nabeeha ta kashe wayar, sannan ta dafe KIRJIN ta. Har yanzu, zuciyarta ba ta dai-daita ba. Shin ta yanke shawarar da ta dace? Shin hakan ba zai jefa Ammi cikin matsala ba? Firgigit tajiyo karar sautin maganar Hammad ya shigo dakin yana kallonta. "Me kike yi haka?" Na beeha ta dago ido, tana jin yadda jikinta ya yi sanyi.ashe mafarki take yi? "Na kira Abba. Zan je in gaya masa komai." Hammad ya runtse ido yana girgiza kai. "Wane Abba kuma dear sis? Me zaki fada masa? Mafarki kike ne?" Nabeeha ta numfasa tana sauke katuwar ajiyar zuciya tace, "Ina jin tsoron ci gaba da rayuwa cikin wannan duhun, Hammad" ta fada da shesshekar kuka. "Ya kamata mu waiwaya dangin mahaifin mu. Tabbas ammi taga rayuwa tana kuma cikin jarabawar wannan kaddarori da taketa fuskanta..!" Hammad ya dafe kansa, yana jin tsantsar tashin hankali. Bai san me zai ce ba, domin yasan cewa komai ya kusa fashewa. "Inshaa Allah khair... Dear sis.... Kowani tsanani yanatare da sauki. Da yardar Allah lokacin warwarar komai ne yazo gangara..." "Allah ya amince" "Aameen" 🎀🎀🎀🎀 Cikin sanyin jiki da girmamawa, Gwaggo Hafsatu ta dubi fuskokin dake gabanta. Babban parlorn nata ya cika da nutsuwa, sai murmushin hikima dake kwance a gefen lebenta. Kowa ya zauna bisa kujera, duk da a kasa suka fara zama dukansu gwaggon taki kememe kan kowa ya koma kan kujera saboda sanyin ac dake busawa ko'ina na marbles din ya dauka da sanyi... amma babu wanda ya iya fadin uffan. Fuskokin su Nabeeha da Hammad cike suke da tambayoyi, yayin da Hajiya Zaytunah ke daure fuska, tana kokarin kwantar da hankali. A gefen dama Major General Dawud ne, yana zaune da kamewa. Kamar kullum, dattako ya rufe fuskarsa, sai idanunsa da ke bin komai a parlorn da kulawa. Hajiya Zaytunah na kusa da Gwaggo Hafsatu, tana dafe da mayafinta kamar mai jin sanyi. Nabeeha da Hammad kuwa, suna gefenta suna jiran jin abin da zai fito daga bakin Gwaggo Hafsatu. Gwaggo Hafsatu ta numfasa a hankali, sannan ta dube su duka. "Nasan kun dade kuna tunanin wanene ku, daga inda kuka fito. Lokaci yayi da ya kamata ku san asalin usulin ku," ta fara magana cikin muryarta mai nutsuwa. Ta kalli Nabeeha da Hammad kai tsaye. "Mahafiyarku, Hajiya Zaytunah, 'yar gidan kirki ce. Ta taso cikin jin dadi da kulawa, amma hakan bai hana rayuwa tura mata jarabawarta ba. Kafin a haife ku, ta yi aure da mutum mai tarin nutsuwa da hikima, sunansa Alhaji Uzairu Muhammad, mijin ta na sunnah. Shi da yayansa, Alhaji Amiru Muhammad, su ne suka gaji dukiyar gidan su. Sai dai fa wannan aure bai kasance cikin kwanciyar hankali ba, domin kishiyoyinta biyu, Hajiya Ladi da Hajiya Karama, sun mayar da ita kamar baiwar da ta shigo gidan da kafafunta." Gwaggo Hafsatu ta dan ja numfashi. "Hajiya Ladi da Hajiya Karama sun yi iyakar bakin kokarinsu wajen ganin cewa mahaifiyarku ba ta sami kwanciyar hankali a gidan ba. Sun hada baki da wata uwa 'yar uwarta, Hajiya Rumanah, wadda ke da tsantsar tsana da kyashi gare ta tun suna yara. Hajiya Rumanah ba wai kishiyar mahaifiyarku bace da dai da ita zaa daura auren ta da Alhaji uzairu sai Allah yayi ikon sa aka daura aurenta da Alhaji Amiru.Wato yayan mahaifinku." Gwaggo Hafsatu ta girgiza kai, sannan ta cigaba, "Bayan mahaifiyarku ta haifi Nabeeha, ke kenan .. sannan ta dauki ciki na biyu,wanda ke cikinta shine kai, Hammad, aka shirya wata mummunar makarkashiya. Asiri aka mata! An hada baki da bokaye, aka tsara makircin da zai sa mahaifiyarku ta bar gidan ba tare da tunanin dawowa ba. Kuma hakan ya faru." Nabeeha ta saki numfashi, tana kallon mahaifiyarta da idanun da suka cicciko da kwalla. "Ammi, me yasa kika bar gidanmu? Me yasa baki koma ba?" Hajiya Zaytunah ta rintse ido, ta dafa hannun Nabeeha. "Ba zan iya komawa ba, Nabeeha. Na rasa komai. Ba ni da mafita, kuma a lokacin, Hajiya Ladi da Hajiya Karama sun makantar da Alhaji Uzairu da zargin karya akaina. Na san idan na tsaya, da za a kashe ni ko kuma na rasa hankalina." Hammad ya dafa hannun mahaifiyarsa. "Ammi, na fahimta. Amma me yasa sai yanzu ake sanar mana?" Gwaggo Hafsatu ta gyara zamanta. "Saboda lokaci yayi. Har yanzu ana neman mahaifiyarku. Duk wanda ya mata wannan asiri, ba ya so ta dawo cikin iyalinta. Sai dai hakan ba zai canza gaskiyar lamarin ba." Nabeeha ta runtse ido, zuciyarta cike da mamaki. Hammad kuma ya dafe goshinsa. Amma abu mafi tayar musu da hankali shine kalmomin da Gwaggo Hafsatu ta kara fadi, "Sai Muhammad manemin ki Nabeeha, Da ne ga Alhaji amiru. Wato dan gidan hajia rumanah. Hajia rumanah Kuma da mahaifin ta da mahaifin mahaifiyar ku uwar su daya uban su daya, sannan rana daya aka haifi hajia rumanah da hajiya Zaytunah... atakaice dai Muhammad Hammad dan Alhaji Amiru Muhammad ne dan yayan mahaifin ku Alhaji uzairu!" Wani mugun shock ya saukarwa Hammad da Nabeeha. Idanunsa suka firfito, yana kallon su duka. "Dan Hajiya Rumanah ne?"suka hada baki wajen tambaya idanuwan su sun furfuto waje cike da mamaki .. Gwaggo Hafsatu ta gyada kai. "Eh, dan Alhaji Amiru da Hajiya Rumanah ne. " Wani irin nauyi ya saukarwa Hammad da Nabeeha. Don Nabeeha kuwa, numfashinta ya fara hawa da sauka. .. Major general dawud mafia yana daga gefen da yake zaune yana hankalce da komai gefe daya dinbin mamaki da sanyin jiki sun dabaibaye shi... Yana tausayin su sosai . "To yanzu me zai faru?" Hammad ya tambaya, yana kokarin daidaita kansa. Gwaggo Hafsatu ta dube shi da kulawa. "Atakaice dai mahaifiyarku Hajiya Zaytunah tana son ku. Ta yarda da kaddara, kuma tana rokon Allah ya bayyana gaskiya. Abin da ya fi shine ku cigaba da rayuwar ku da hakuri da biyayya." A wannan lokaci, dakin yayi shiru. Idanun Nabeeha da Hammad sun cika da kwalla, zuciyoyinsu suna cike da rudani. Rayuwarsu ta canza a cikin dare daya. Sun san iyayensu, sun san asalin su. Kuma sun san cewa komai da suka sani a baya—ya canza... MX🧕 *KIRJIN MAI HANKALI* _(AKWATIN SIRRIN SA)_ 🧳➿💞 *PG :29* *AREWABOOKS VVIP:👇* https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb Tashin motar Fawaaz kadai ke karan kunne a kofar gidan Major General Dawud. Baba . Wato Major general dawud ne yace ya dauki nabeeha ya kaita workshop din da sukeyi na wani course na su na makaranta. Yana jingine da kujerar motar, hannayensa rike da sitiyari, yayin da zuciyarsa ke tafasa da tunanin wacce zai dauka a yau.... Nabeeha. Ya lumshe ido a hankali, yana jin bugun zuciyarsa na karuwa da wani irin salo da ba kasafai yake jin sa ba. Bai san me ke damunsa ba, amma abu daya ne yake a fili—ya makara. Ta dade a shirye, kuma shi ke bata lokaci. Daga cikin gidan, Nabeeha ta fito a nutse, sanye da riga da siket na atamfa mai launin royal blue, wanda ya kara fidda kyawun fatarta. Dogon gyalen kanta ya tsaya tsaf akan kafadunta, yana sauka daidai gadon bayanta. Fawaaz ya dago idonsa daga sitiyari, idanuwansa suka sauka a kanta. Ya hadiye yawu. Ya san cewa Nabeeha kyakkyawa ce. Amma a yau, akwai wani abu a tare da ita da ya kasa fassara. "Sorry na bata lokaci," ta fada a hankali, tana kokarin bude kofar mota. Fawaaz bai ce komai ba. Sai kawai ya juya yana kallon gaban motar, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da wani irin nauyi. Tana shiga, ya danna wani button, motar ta rufe da kanta. Ya daidaita sitiyari, sannan ya kunna motar, suka fara tafiya. Shiru ya ratsa tsakanin su. Kamar kullum. Nabeeha ta dan matsa jikinta gefe, tana kokarin tsaida zuciyarta daga bugun da take yi. Tunanin cewa yau Fawaaz ne zai kaita makaranta kadai ya ishi zuciyarta gamsuwa. Amma a lokaci guda, ya tuno mata da yadda shi mutum ne da ba ya taba magana da ita. Ya kwana biyu yana wani iri. Yana kamar yana da damuwa, amma ba zai taba fada ba. Sannu a hankali, karar kidan da ke fitowa daga stereo ya fara cika motar. "Can’t help falling in love with you…" Muryar Elvis Presley ta ratsa cikin motar a hankali, tana karawa yanayin shurun dake tsakaninsu nauyi. "Wise men say… only fools rush in… but I can’t help… falling in love with you." Fawaaz ya murza sitiyari da hannunsa, yana jin yadda kida ke mamaye zuciyarsa. "Like a river flows… surely to the sea… darling so it goes… some things are meant to be." Ya cije lebe, yana kallon titi amma tunaninsa yana kan wacce ke kusa da shi. Nabeeha. Yana jin dadin kasancewarta kusa da shi. Yana jin shaukinta. Amma ba zai taba iya furta hakan ba. Wakar dake fita itake bada sautin labarin dimbin kaunar da yake mata a birnin zuciyar sa.. Nabeeha ta juyo a hankali ta kalle shi. Idanunta sun sauka a kan hannayensa da suke kam da na soja, cike da layukan karfi. Sai kuma fuskarsa, wacce ke cike da natsuwa da miskilanci. Hawaye ne suka taho mata, amma ta mayar. Kamar yadda ya saba mata miskilanci, shima zata saba. "Take my hand… take my whole life too…" Sai dai bata san cewa a zuciyarsa, Fawaaz yana juyawa kalmomin wannan waka ne a kansa. "For I can’t help… falling in love with you." Ya dauke numfashi a hankali, yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa. Ba zai iya cewa komai ba. Kuma ba zai iya dakatar da zuciyarsa daga jin abinda take ji ba. Ya san abu daya ne kawai. Shi fawaaz Dawud mafia yana son Nabeeha. Amma zai iya furta hakan? Fawaaz ya dan gyara zama, hannunsa na dama yana murza sitiyari a hankali. Wakar da ke tashi a cikin motar na dada saukar da wani irin shauki a zuciyarsa. "Take my hand… take my whole life too… for I can’t help falling in love with you." Yana jin wakar tamkar ita ce ke fassara zuciyarsa. Duk da miskilancinsa, zuciyarsa na cike da zafi—zafin soyayyar da ya kasa furtawa. Idanunsa sun dan sauka a kan Nabeeha, wacce ke kallon titi ta window, hannayenta suna rungume da juna. Duk da bata ce komai ba, ya san tana jin wani abu. Da alama ita ma tana kokarin boye abin da take ji, kamar yadda shima yake yi. Hannunsa ya kara murza sitiyari. "Kin shirya test ɗin?" Ya tambaya a hankali, muryarsa na fita da natsuwa. Nabeeha ta juyo tana kallonsa da mamaki. Bai taba tambayarta wani abu makamancin hakan ba. Ta dan saki murmushi, sai dai yana dauke da alamun damuwa. "Eh, ina kokarin karatu sosai." Fawaaz ya gyada kai, sannan ya cigaba da tuki a shiru. Shi kadai ya san yadda yake jin dadin jin muryarta. Amma me zai yi? Idan har yana jin wannan kauna mai tsanani a zuciyarsa, me yasa yake jin tsoron furtawa? Kayi shiru! Ya fada a zuciyarsa. Kar ka sake. Ba dole sai ka fada ba. Amma a lokaci guda, zuciyarsa na fada masa cewa yana makara. Nabeeha ta dauke kai, zuciyarta na bugawa da sauri. Idanunsa sunyi mata kyau sosai yau. Tana son yadda uniform dinsa na yan sanda ke sake fidda kyawunsa. Iya kyan mutum! Ta lumshe ido a hankali. "Ina jin wani shiru," ta ce a hankali, bata san ta fada ba. Fawaaz ya juyo da dan mamaki, sannan ya dauke kansa daga kanta. "Me kika ce?" Nabeeha ta girgiza kai, tana murmushi. "Ba komai." Shi ma ya dan saki murmushi, amma cikin zuciyarsa yana jin abinda ta fada. Eh, yana jin shiru. Shiru ne ke tsakanin su, shiru ne ke bayyanawa zuciyarsa dukkan abin da yake ji. Amma zai iya furta hakan? "Like a river flows… surely to the sea… darling so it goes… some things are meant to be…" Wakar na cigaba da tashi a hankali, tana bayyanawa zuciyarsa abin da bai da karfin furtawa. Ya lumshe ido na dakika daya, sannan ya bude. Bari ya cigaba da yi shiru. Zuciyarsa kadai zata fassara abin da take ji. Sai dai, har zuwa yaushe? Motar Fawaaz na tafiya cikin nutsuwa, tana yanke iskar titin da ke cike da shuke-shuke masu kyan gaske. An makara sosai, hasken rana ya fara dusashewa, yana barin wani launin orange mai kyau a sararin samaniya. Nabeeha ta lumshe idanu a hankali, tana jin sanyin A.C na motar yana ratsa fuskarta. Sai dai, ba sanyin ne ya fi shigar ta ba—yana nan kusa da ita. Duk da shiru ne tsakaninsu, tana jin wani nauyi yana cika zuciyarta. Fawaaz. Idanunta sun sauka a kan hannayensa, wadanda ke rike da sitiyari da cikakken control, kamar yadda ya saba. Miskili ne, amma yana da nutsuwa. Kuma yana da wani abu da yake jan hankali ba tare da yana kokarin hakan ba. Ta dauke kanta da sauri, saboda tsoron kada idanunta su bayyana abin da take ji. Fawaaz a nasa bangaren, yana kallon titi amma zuciyarsa na wani irin tafasa. Bai saba da wannan yanayin ba. Me yasa yake jin wannan abu a jikinta? Me yasa shaukinta ke shigar sa sosai, har ma ya fi yadda ya zata? Ya dan murza sitiyari, yana jin yadda numfashinsa ke sauka da nauyi. Sai dai duk da haka, ya ki bude baki. Ya ki furta wani abu. A zuciyarsa, yana jin kalmomin da bai da karfin furtawa, "Nabeeha, ina matukar kaunar ki. Har tana yi min yawa. Amma ba zan iya furtawa ba." Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta dafa glass din motar. "Zan yi kokari in gama wannan course din cikin lokaci." Fawaaz ya dan juyo, ya kalle ta a gefe. "Kin san sai an yi kokari." Ta gyada kai. "Ina kokari." Ya dan lumshe ido na dakikoki biyu. Ta na kokari, amma shi fa? Shima yana kokarin boye soyayyarsa? Shiru ya sake cika motar, yayinda wakar da ke fitowa daga speakers take dada shiga zuciyarsu, "For I can’t help… falling in love with you…" Kamar wanda ya saba da hakan, Fawaaz ya daidaita mirror din motar, yana dan gyara gefen hularsa ta soja( beret/military cap). Nabeeha ta juyo da sauri tana kallonsa. Idanuwanta sun tsaya cak a kan shi. Ya kara kyau fiye da yadda ta zata. Wannan shigar tasa ta sojoji ta kara masa wani irin kamala da take jin zuciyarta tana tsalle idan ta kalle shi. Sai dai, sai ta sunkuyar da kai cikin sauri. Bata son yayi tunanin wani abu daban. Amma kuma, me zai yi idan ya gano? Fawaaz bai kula da kallon da take masa ba. Bai san cewa yana kara burgeta da miskilancinsa ba. Abinda ya sani kawai shine, zuciyarsa na tafasa. Yayi kokari ya cigaba da tukinsa, amma ya kasa. A hankali ya sake rage gudun motar, zuciyarsa na bugawa da sauri. Da alama yana makara. Ya san cewa idan bai furta ba, zuciyarsa za ta iya fashewa. Sai dai, me zai ce? Fawaaz Dawud ya saba da jan aji. Amma yana iya cigaba da jan aji akan soyayya? Nabeeha ta juyo tana kallonsa. Yana daure fuska, amma hakan bai hana shi kyau ba. Ya san cewa idan ya ci gaba da yi shiru, soyayyar za ta yi nauyi fiye da yadda yake zato. Da wannan tunanin, ya dan gyara murya. "Ina fatan test din zai tafi daidai," ya ce, ba tare da ya kalle ta ba. Nabeeha ta dan zaro ido da mamaki. Wannan shi ne karo na farko da Fawaaz yake nuna mata wata alama ta kulawa, ko da kuwa kadan ne. Sai ta saki murmushi, zuciyarta na bugawa da sauri. "Ina fata haka," ta amsa a hankali. Fawaaz bai sake cewa komai ba. Bai san me zai ce ba. Bai san ko yana da karfin fadin abinda zuciyarsa take fada ba. Sai dai abu daya yana a fili. Shi captain fawaaz yana son Dr. Nabeeha. Kuma yana jin hakan yana yi masa nauyi fiye da yadda ya zata.... MX *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:30_ Motar na cigaba da tafiya a nutse, iskar dake fitowa daga A.C na motar na yawo cikin cikinta, yana ratsa jikinsu da sanyin da bai kai ya isa ya rage zafin da zuciyarsu ke ciki ba. Fawaaz ya lumshe ido na wuni dakikoki kadan, sannan ya budesu, yana sauke numfashi a hankali. Ya dade yana kokarin hana zuciyarsa bayyana soyayyar da take da ita. Ya dade yana kokarin boyewa, amma yanzu ya fara jin kamar yana makara. Kamar dai yadda wakar da ke fitowa daga speakers take fada masa: "Wise men say… only fools rush in… but I can’t help falling in love with you." Ya dan matsa hannunsa a kan sitiyari, yana ji kamar yana jin zafin da zuciyarsa ke yi a fatar tafin hannunsa. Nabeeha a daya bangaren, ta kara daidaita zamanta. Duk da sanyin dake cikin motar, tana jin wani irin dumin shauki yana ratsa zuciyarta. Tana jin kamshin turarensa yana kara hadewa da sanyin da ke fitowa daga motar, yana sakata jin wani irin natsuwa mai dauke da tsananin shauki. Sannu a hankali, zuciyarta na tafiya da wani irin salo da ta kasa fassarawa. Ta dago a hankali, tana kallonsa daga gefe. Ya kyau… Sai dai ta sunkuyar da kai da sauri, zuciyarta na dokawa da sauri. Meye haka, Nabeeha? Sai dai a cikin zuciyarta, bata da amsar tambayar. Fawaaz kuwa, sai ya cigaba da tukinsa, yana ji kamar zuciyarsa na kokarin doke duk wata ka’ida da ya gindayawa kansa. A hankali, ya dan juyo yana kallonta. Ta bace cikin tunani, hakan ya bashi damar kare mata kallo. Ya lura da yadda fuskarta ke da annuri, ko da yake idanuwanta cike suke da tunani. Ya san cewa tana burgesa fiye da yadda ya zata. Ya san cewa yana jin zuciyarsa tana tafasa a duk lokacin da yake kusa da ita. Amma hakan ya isa ya furta mata? Sai ya dauke kai, yana hadiye wani nauyin da yake ji a KIRJI. Kai, Fawaaz! Ba dole sai ka fada ba! Sai dai zuciyarsa na sake fada masa akasin haka. Nabeeha a nata bangaren, ta kasa dauke zuciyarta daga kansa. Wannan shine karo na farko da take tafiya tare da shi, babu kowa sai su kadai, a cikin wannan yanayi na shiru mai cike da ma’ana. Kuma yana kyau fiye da yadda ta zata. Ta kalli hannayensa da ke rike da sitiyari. Me yasa suke burgeta haka? Sai ta rufe ido, tana jin kamar tana kokarin kaucewa soyayyar da take ji. Sai dai, shin yana yiwuwa? Wakar dake fitowa daga motar ta sake mamaye zuciyarsu: "Take my hand… take my whole life too… for I can’t help falling in love with you." Fawaaz ya lumshe ido a hankali. Nabeeha, me kike so na yi? Ina jin ki. Ina jin ki fiye da yadda na zata. Amma ba zan iya furtawa ba. Ya gyara zaman hularsa ta soja (Beret/Military cap), yana jin yadda soyayyar ke kara cika zuciyarsa da nauyi. Nabeeha ta dago da sauri, tana kallon sa. Shigarsa ta kara burgeta fiye da yadda take zato. Ba ta san lokacin da murmushi ya subuce mata ba. Fawaaz kuwa, ya lura da murmushin, amma sai ya dauke kai. Idan ya ci gaba da kallo, zai iya furta abin da zuciyarsa take fada. Sai dai a zuciyarsa, yana jin kamar yana makara. Yana makara kafin soyayyarsa ta fishe shi, har ta gagara ɓoyuwa. Fawaaz ya kafe idanunsa a kan titin da ke gabansa, hannayensa na riƙe da sitiyari da cikakken iko. Motar na tafiya cikin nutsuwa, iska na tashi daga A.C, tana ratsa su da sanyin da bai iya kashe wutar zuciyarsu ba.. Yana sanye da kayan sojoji—khaki mai kyau da tsari, da hular soja (beret) da ya gyara a gefen kansa. Dogon hannun rigarsa ya bayyana ƙwarewa da ƙa’ida irin ta sojoji, lambar sunansa ta manne a gefen ƙirjinsa. Nabeeha ta ji zuciyarta ta buga da sauri da ta sake kallonsa. Yana da kyau sosai a haka… Amma hakan bai dame shi ba. Yana tukinsa cikin shiru, fuska a daure kamar yadda ya saba. Sai dai ta lura da yadda jaw-line dinsa ke motsi—alamar yana taƙure wani abu da bai so ya bayyana ba. Shiru ya fi magana sau dubu. Sai dai ita kanta tana cikin tunani. Ba ta san me yasa zuciyarta ke dukan wata irin guda ba. Ba ta son ya fahimta. Sai dai, shin yana yiwuwa ya riga ya fahimta? Wakar da ke tashi a hankali daga motar (Slow Love Song) ta cika zuciyarta da wani irin nutsuwa mai sanyi, amma da sauƙin da ke ɗauke da nauyi.. "I don’t wanna say goodbye… Even when the night is over… I just wanna hold you close… Even if we’re lost forever…" Ta dan lumshe idanu a hankali. Tana jin shaukinsa na ratsa ta. Hankalinsa na kan titi, amma zuciyarsa na wani wuri daban. Wurin da aka kulle shi da soyayyar da ba zai iya furta wa ba. Fawaaz ya gyara zamansa a kujerar direba, yana matsa yatsunsa a kan sitiyari. Numfashinsa na fita a hankali, amma zuciyarsa na tafasa. A gefensa, Nabeeha ta sake gyara zaman mayafinta, tana ƙoƙarin kwantar da zuciyarta. Sai dai hakan ya gagara. Kafin ta fito daga gida, ta yanke shawarar cewa ba za ta sake kallonsa da wani irin kallo ba. Ba za ta bari zuciyarta ta bayyana abin da take ji ba. Amma yanzu… Yana da kyau… Yadda kayan sojoji suka zauna masa daidai, sun bayyana cikakken ƙuruciya da ƙwarewarsa. Beret ɗinsa na gefen kansa, yana ƙara masa kwarjini. Idanunsa kuwa, ko da bai kalleta kai tsaye ba, akwai wani irin zurfi da take ji idan ta kalle su. Zuciyarta ta ja da baya da sauri. Wani sanyi ne ya ratsa ta lokacin da ta sake jin wakar da ke tashi a hankali daga speakers ɗin motar. "I will always, always love you…" Wata irin zufa ta keto mata a goshinta. Ta san cewa ba kawai kalmomin waka ba ne ke ratsa ta. Soyayyar da take jin yana ɓoye wa ne ke ratsata. Fawaaz ya juyo da dan kallo, a hankali. Bai yi magana ba, amma idanunsa sun fada mata duk abin da bakinsa ya gaza furtawa. Ta yi saurin dauke kai. Zuciyarta na tsalle tamkar za ta fito waje. Me yasa ba zai yi magana ba? Me yasa ba zai furta abin da yake ji ba? Ya jima da sanin cewa soyayyarta ta mamaye shi. Ya jima da sanin cewa yana cikin matsala idan bai gaggauta daukar mataki ba. Sai dai… yana jin tsoron furta hakan. Hannunsa na dama ya dan dunkule sama da sitiyari, yana jin wani irin nauyi a KIRJI. Fawaaz, kai soja ne. Kai namiji ne. Amma kuma me yasa soyayyarta ke galaba da kai? Sai ya sake kallonta da gefen ido. Sai dai ta kau da kanta, kamar yadda shima yake ƙoƙarin kau da zuciyarsa daga shaukinta. Zuciyarta ta furta abu guda. Duk da shiru ya yi yawa, zuciyoyinsu sun san gaskiya. A haka ya karasar da ita zuwa inda zasuyi aikin... Ya jirata har suka kammala sannan ya dakkota suka koma hanyar gidah.. Motar ta tsaya a harabar gidan a hankali, amma babu wanda ya yi yunƙurin fita daga ciki. Shiru ya ratsa tsakanin su, sai dai sautin numfashinsu da aka kasa ɓoyewa.🤭 Fawaaz ya kafe idanunsa a kan gaban motar, amma zuciyarsa na wani wuri. A zuciyarsa, yana jin tamkar bai so su koma gida ba. In da za a ce lokacin zai tsaya cak, ya kasance tare da ita har abada, babu shakka da ya yi hakan. Sai dai rayuwa ba haka take ba. Ya juyo a hankali, idanunsa suka sauka a kanta. Nabeeha tana zaune da mayafinta da ya zame a gefe, yana bayyana fuskar da ya daɗe yana gujewa kallon kai tsaye. Amma yau… Yau zuciyarsa ba ta iya daurewa ba. “Nabeeha.” Muryarsa ta fito a kasalance, amma cike da nauyin da bai saba da shi ba. Ta dago idanunta a hankali, idanunta masu launin hazel sun ratsa nasa. Duk wani ƙoƙarin da take yi na guje wa kallonsa ya gagara, saboda yadda idanunsa suka kulle nata gaba ɗaya. Fawaaz ya dan matsa, yana jin wani abu na fisgarsa da ƙarfi. Bai san lokacin da hannunsa ya kai ya riƙo nata ba. Hannunta ƙanƙani ne cikin nasa, amma dumin da ya ji ya fi duka sojojinsa cusa masa jini a cikin gangar jikinsa. Nabeeha ta runtse ido. Ta san cewa idan har ta sake kallonsa, tabbas za ta nutse a cikin abin da take ƙoƙarin guje wa. Sai dai hakan bai hana ta jin yadda zuciyarta ke bugu da sauri ba. A hankali, Fawaaz ya ɗago da ɗayan hannunsa, ya sanya yatsansa a gefen fuskarta. Bai sani ba, amma yana jin tamkar zuciyarsa ta ɓarke da wani irin shauƙi da bai taɓa fuskanta a rayuwa ba. Ta buɗe idanunta a hankali. Idanunsu sun haɗu, zuciyoyinsu suka yi shiru, amma jikin nasu na furta dukkan abin da suke ji. Fawaaz ya saki ajiyar zuciya mai nauyi. Ina ma ita ce tasa. Ina ma yana da ita tamkar yadda yake buƙatar ta. A hankali ya matsa, yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa. Yana jin yadda idanunta ke kiran nasa, ba tare da wata kalma ba. Labbanta sun jike da ɗan sauƙin numfashi. Suka kasance jajaye kamar furannin wardi, suna kiran nasa da wani irin nutsuwa da tsoron zuciya. Tamkar Ya kai karamin sumba a hankali. Sai da ya ji yadda duk wani zafin da zuciyarsa ke ji ya narke a take. Nabeeha ta lumshe ido. Bai da ƙarfin ja da baya. Bai da ƙarfin barin abin da zuciyarsa ta riga ta aminta da shi. Fawaaz yaji tamkar ya jingina goshinsa da nata, yana mai jin tamkar wannan ne farkon tafiyar da bai san inda za ta tsaya ba. Yana jin zuciyarsa na bugawa, amma ba da tsoron soja ba—da tsoron so. Soyayyar da ba zai iya furtawa ba. Fawaaz ya kashe motar, amma bai yi yunƙurin buɗe ƙofa ba. Hannayensa suna kan sitiyari, amma zuciyarsa tana wani wuri. Zuciyarsa tana tare da ita. Nabeeha tana gefensa, zaune kamar yadda ta kasance tun farkon tafiyar. Sai dai yanzu, shiru ya mamaye tsakanin su. Wani irin sanyi ya ratsashi. Bai san dalili ba, amma zuciyarsa na faɗin abu ɗaya, "Ina ma halaliyata ce, inama tawa ce mallaki na ce.." "Ina ma zan iya riƙe ta cikin kaina, ba tare da wata shakka ba.inama ace matata ce" Ya dan juyo, idanunsa suka sauka a kanta. Ta daɗe da sunkuyar da kai, tana wasa da yatsunta cikin nutsuwa. Fawaaz ya kafe ta da ido, yana jin wani nauyi a zuciyarsa. Wani ƙarfi ne ya lulluɓe shi, yana ƙoƙarin fisgarsa. Ya ma rasa dalilin da ya sa hakan ke faruwa. Hannunsa ya dan motsa, yana so ya kai ga nata. Amma ya dakata. Ba ta tashi ba. Ba ta yi magana ba. Haka shima bai ce komai ba. Bai san yaushe ya juyo da fuskar sa sosai ba, yana kallon yadda hasken fitilar gidan ke sauka saman fuskarta. Ta haɗiye yawu a hankali, tana jin idonsa akan ta kamar wuta. Fawaaz ya sake numfasa, yana jin yadda zuciyarsa ke faɗin abu ɗaya, "Ina ma zan iya rungumarta a kaina." "Ina ma zata iya jin yadda zuciyata ke bugawa saboda ita." Sai dai… Ba halaliyar sa bace. Ba mallakinsa ba ce. Zuciyarsa ta amince da hakan, amma gangar jikinsa ta ƙi. Ya lumshe ido, yana mai jin yadda wannan tunanin ke ƙara masa raɗaɗi. Ya ɗauki lokaci kafin ya matsa baya kadan, ya jingina da kujera, yana mai kakkabe duk wani tunani da ke ransa. Soja ne shi. Dole ne ya riƙe kansa. A hankali ya ce, “Mun iso.” Muryarsa ta fita da sanyi, ba tare da ƙarfin da ya saba da shi ba. Nabeeha ta daga kai a hankali, suka yi ido biyu. Sai dai kafin ta samu damar cewa komai, ya riga ya buɗe ƙofar motar ya fita. Ya riga ya rufe komai cikin zuciyarsa.... Dan wahala 😂🤭🧑‍🦯 MX🧕 *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:31_ A cikin babban falon gidan Major General Dawud, kowa ya hallara. Gwaggo Hafsatu na zaune a tsakiyar kujerar da take da alfarma, tana daura tafukan hannunta a saman cinyoyinta. Fuskar ta na bayyana alamar tunani mai zurfi, tamkar tana jin nauyin wani babban yanke hukunci. Major general dawud mafia na daga gefen ta yana kallon kasa da shiru. Duk da cewa shi mutum ne da ke da karfi da iko, yau ya kasa daukar mataki ba tare da jin ra’ayin Gwaggo Hafsatu ba. Yana jin nauyin amanar da ta rataya a wuyansa—amanar Zaytunah da ‘ya’yanta. A gefe guda, Hajiya Zaytunah na zaune da kai a kasa, zuciyarta cike da tunani. Shekaru da yawa da suka shude, ta san ba za ta iya komawa gidan Alhaji Uzairu ba a tunanintaa, kuma yanzu da aka buɗe sabon shafi a rayuwarta, dole ta yanke shawarar da ta dace. Nabeeha da Hammad kuwa suna zaune kusa da ita, suna kallon kowa da kowa a falon, ba tare da sanin abin da ke tafe ba. Gwaggo Hafsatu ce ta katse shiru da wata kakkausar murya, “wannan hutun mai dogon zango. Inshaa Allah a birnin mawii zamuyi shi.” Kowa ya kalleta. Major general yadan gyara zamansa, yana jiran jin dalilinta. "Dawuda yana da katafaren gida a can, gida ne da zai iya daukar su Zaytunah da ‘ya’yanta cikin kwanciyar hankali. Babu wanda zai takura musu ko ya binciko su, babu wanda zai dinga bibiyar rayuwarsu. Idan muna so su sami sabuwar rayuwa, to Mawii shine mafita.” " hakan zai fi dacewa,” ya fada a hankali. “Ni kaina ba na so su zauna a nan, saboda idan SIRRIN ya tonu, za mu shiga matsala.” Hajiya zaytunah ta dago kai a hankali. "Gwaggo, kina nufin mu bar noka gaba daya?” “Eh, Zaytunah,” Gwaggo Hafsatu ta fada da karfin gwiwa. “Dole mu fice, saboda noka ba wurin da zai ba ki kariya bane. Na gama magana da Dawuda, ya shirya mana komai.” Nabeeha ta kalli mahaifiyarta da mamaki. Komawa wani gari daban? Wata sabuwar rayuwa? Ta kalli Hammad, shima yana kallon ta, tamkar yana jiran jin ra’ayinta. "Tohm gwaggo abunda kika yanke shi za'ai. Allah dai ya Saka muku da alkhairi. Yasa komawar tamu canne mabudin alkhairan mu gaba daya Amin" "Aameen" suka hada baki wajen amsa ta. ___-----____ Bayan kwana biyu da tunani da shawarwari, Major General Dawud ya yanke shawarar kira Alhaji Amiru domin su yi wata muhimmiyar ganawa. A lokacin yana zaune a cikin ofishinsa, cikin tsanaki ya dauki wayarsa ya danna lambobin Alhaji Amiru. Da alama yana jiran kiran, domin kuwa cikin ‘yan kara-kaushe Alhaji Amiru ya daga wayar. "Salamu alaikum, Major General." Muryarsa da karfin gwiwa kamar yadda aka santa, sai dai akwai dan nutsuwa cikin ta. "Wa’alaikumus salam, Alhaji Amiru. Ina fata kana lafiya?" "Alhamdulillah. Yaya aiki?" "Alhamdulillah. Akwai magana da nake so mu yi, idan baka da wani uzuri, acikin tsukukun nan. Zan neme ka" Shiru na dan lokaci ya biyo baya. Alhaji Amiru ya fahimci cewa maganar dole ce, kuma ba zai yi mata rikon sakainar kashi ba. "Babu matsala, Major General. in Allah Ya yarda." "Shikenan.sai ka jini." Bayan kammala kiran, Major General Dawud ya sauke numfashi. Yana da tabbacin cewa wannan ganawar za ta tsayar da shawarwarin da suka dauka a gida game da Zaytunah da ‘ya’yanta. .... A yini biyu da suka gabata, an yi zaman shawarwari mai tsawo a gidan Major General Dawud. Gwaggo Hafsatu ce ta sake kira zaman, inda ta bukaci a zauna a sake tattauna batun komawar Hajiya Zaytunah da iyalanta zuwa wani wuri mafi tsaro da kwanciyar hankali. "Na dade ina addu’ar Allah Ya yi mana jagora," cewar Gwaggo Hafsatu, tana kallon Major General Dawud da Hajiya Zaytunah. "Duk da haka, ba zan yanke hukunci ba sai da amincewarki, Zaytunah." Hajiya Zaytunah ta sauke numfashi, tana dan gyara zamanta. "Gwaggo, ni babu abin da nake so sama da kwanciyar hankali ga ‘ya’yana. Amma har yanzu ba zan iya komawa gidan Alhaji Uzairu ba. Komai yana nan yadda na bari." "Mun fahimta," Major General Dawud ya katse shurun da ya biyo bayan maganarta. "Akwai wani wuri da muke son mu kaisu, Birnin Mawii. Gida ne da aka tanada tun tuni kamar yadda aka fada a baya, amma yanzu ne zai fi dacewa da su." Hajiya Zaytunah ta daga ido tana kallonsa. "Birnin Mawii?" "Eh. Gida ne mai tsaro da kwanciyar hankali. Ba kowa zai iya gane su can ba, kuma za su sami damar sake farawa da sabuwar rayuwa." Shiru ya sake ratsa dakin, kafin daga bisani Hajiya Zaytunah ta gyada kai a hankali. "Idan hakan ne mafi alheri gare mu, to na amince." Washegari kuwa, aka fara shiri don fice wa cikin SIRRI da kwanciyar hankali. 🎀🎀🎀 Major General Dawud mutum ne mai kamun kai, wanda ya fi so abubuwa su tafi yadda ya tsara su. Bai cika barin wayarsa a ko’ina ba, domin yana da matukar kula da SIRRIN SA. Amma yau, kwatsam, yana dawowa daga sashen mahaifiyarsa, Gwaggo Hafsatu, ya shiga dakinsa ne ba tare da tsammani ba, sai ya ci karo da wani abin da ya kada masa gwiwa. A kusa da gadonsa, Hajiya Hawwa Maijiddah na zaune da wayarsa a hannunta. Ba wai tana kallonta ba ne kawai, a’a, Tana rubuta wata lamba a nata wayar! Da farko, bai ce komai ba. Ya tsaya a bakin kofa, yana nazarin lamarin. Ya lura yadda ta mayar da hankali sosai, tana ta dannawa cikin hanzari kamar wacce ke tsaka da wata gaggawar aiki. Da sauri ya kutsa cikin dakin, zuciyarsa na bugawa. "Hawwa!" Ya kira da murya mai karfi, amma ba tare da hayaniya ba. Da sauri ta daga kai, idonta cike da firgici. Kafin ta samu damar ɓoye abin da take yi, ya karaso ya kwace wayarta. "Meye haka?" Ya tambaya da karfi, yana kallon wayarta. Tana kokarin mayar da nutsuwa, amma jikinta ya nuna cewa an kamata. "Uh… Ni dai kawai… na duba wani abu ne." "Duba wani abu?" Ya maimaita, yana duba fuskar wayarta. ya duba fuskar wayar Hajiya Hawwa Maijiddah, idonsa ya tsime kan jerin sakonni da ta tura. Bai tsaya bata lokaci ba, ya danna kiran baya (recent messages). Cikin ikon Allah, sakon da ta tura bai riga ya goge ba. A yayin da ya karanta, fuskar sa ta nuna tsananin bacin rai. Har gaban zuciyarsa yaji wani irin daci. "Wannan shine babban shirin su. Za a mayar da ita da ‘ya’yanta wani area dake garin ku na mawi.. Gida ne na SIRRI da aka tanada tun tuni, amma yanzu ne za a kaisu. Za a yi tafiya cikin SIRRI." Hannunsa ya fara matse wayar da karfi, idanuwansa suka kada. Ya dago kai a hankali, yana kallon Hajiya Hawwa Maijiddah da take kokarin boye firgicinta. "Hawwa, wa kike tura wa wannan sakon?" Muryarsa cike da tsawa, da wata irin natsuwa mai hade da fushin da ba kasafai ake ganin shi da shi ba. "Ni… Ni… Wallahi… Ba wani abu bane" Ta fara kokarin magana, amma muryarta na rawa. "Ba wani abu bane? Kina fadawa wani SIRRIn da ni da Gwagggo muka dauki tsawon lokaci muna kiyaye shi, sannan kice ba wani abu bane?!" Ya nuna mata wayarta da ke hannunsa, yana mai nuna mata sakon da ta tura. "Daga ina kika samu wannan number.. shinma Wa kike turawa, Two face?? Fuska biyu hauwa?!" Tayi shiru. Jikinta har rawa yake yi. Idanuwanta sun cika da ruɗani. A yadda ta san shi, idan yana cikin fushi irin wannan, babu mai iya hanashi daukar mataki. Ya dauki tsawon lokaci yana kallonta, zuciyarsa na tafasa. Wata zuciyar tana gaya masa ya mata tambayoyi da ladabi, wata kuma tana gaya masa cewa babu sauran lokacin sassauci. Ya kai hannu ya dauki wayarsa, yana dubawa don ganin ko ta duba wasu bayanai a cikinta. Bai jima ba, ya gano cewa ta shiga cikin saƙon wayarsa, tana duba sakonninsa da kuma lambobin da suka shafi Zaytunah da iyalanta. "Whattttttt!" Ya furta a hankali, amma muryarsa ta kara tsananta. Yayi kokarin bin lambobin da ke cikin wayarta, yana nazari kan wanda take tura wa wadannan sakonni. Amma hakan bai samu ba cikin sauki. Amma abu daya ya bayyana, wannan lambar ba sabuwa bace. Wani mutum ne da take da alaƙa da shi tun baya. Da sauri ya kalle ta, yana kokarin gano amsar tambayoyin da zuciyarsa ke yi. "Waye wannan? Waye kike turawa wannan bayanai?" Hajiya Hawwa Maijiddah ta sunkuyar da kanta, tana kokarin kaucewa kallon idanunsa. "Daga yau, kada ki kuskura ki kara taba wayata!" Ya furta da kakkausar murya, yana jefar da wayarta akan gadonta. "Duk wani abu da kike shiryawa, na tabbatar ba zai yiwu ba." Ya juya, zuciyarsa cike da tunani. Wannan abu ba zai wuce haka kawai ba. Zai bincika komai ko da kuwa hakan yana nufin zai bankado wani SIRRI mafi muni fiye da wanda ya gani yanzu. Shi ya Saka ma ba zai dauki hukunci ba anan take. Sai ya gama bincike ya futarda sakamakon bincikensa... ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:32_ Major General Dawud ya yi numfashi mai nauyi, zuciyarsa na tafasa da tunani. Bai taba zaton Hajiya Hawwa Maijiddah zata iya aikata irin wannan ba. Ya san cewa ba ta cika jin dadin zaman Zaytunah a gidan ba, amma bai yi tsammanin cewa za ta kai ga tona SIRRIN da aka dauki lokaci ana boyewa ba. Yana tsaye a tsakiyar dakin, yana kallonta da idanuwansa masu nuna tsananin takaici. Hajiya Hawwa Maijiddah ta sunkuyar da kai, tana kokarin kauce wa kallonsa. Duk da cewa a zuciyarta ta san cewa bata da wata hujja mai kwari da zata iya kare kanta da ita, har yanzu tana kokarin boye gaskiyar lamarin. "Hawwa," ya kira sunanta da murya mai cike da natsuwa, amma hakan bai sa zuciyarta ta daina bugawa da karfi ba. "Daga ina kika samu wannan bayanin? Waye yake ba ki shi? Waye kike tura wa wannan sakon?" Ta dinga hadiye yawu, tana jin tsoron bayyana gaskiya. Idan har ta fada masa komai, tabbas hakan zai kara dagula al’amura. "Dawud, wallahi ba wani abu bane… Ni dai kawai… kawai ina son sanin abubuwan da ke faruwa ne. Na tsinci labari ne daga inda ba zan iya bayyanawa ba." Ya saki murmushin takaici, yana jin yadda zuciyarsa ke kara tafasa. "Kin san mene?" Ya kalle ta kai tsaye. "Bani da bukatar jin wani karin bayani daga gare ki, domin abinda nake gani ya ishe ni." Ya juya, ya dauki wayarta yana sake duba sakonnin da ta tura. Yayi mamakin yadda ta samu cikakken bayani game da shirin komawar Zaytunah da ‘ya’yanta. Wannan ya tabbatar masa da cewa dibar rahotan komai take tana barbadawa.. "Hawwa, ni da ke muka zauna a wannan gidan tsawon shekaru, amma ban taba tunanin cewa wata rana za ki iya cin amanata haka ba." Hajiya Hawwa Maijiddah ta dago kanta a hankali, idanunta cike da hawaye. "Wallahi ba hakan bane, Dawud… Ni dai kawai—" "Ya isa!" Ya katseta da muryar da ta firgita ta. "Na ce ki bani amsa, ba na son jin wata ‘yar magana maras amfani." Ta yi shiru. Idanunta sun kada da tashin hankali, amma ta kasa furta komai. Major General Dawud ya runtse idonsa na wani lokaci, yana kokarin kwantar da fushinsa. Amma hakan ba abu ne mai sauki ba. A zuciyarsa, ya fara tunanin duk wata hanya da zata iya fallasa bayanan SIRRIN da suka dade suna kokarin rufewa. Idan Hajiya Hawwa Maijiddah ta iya sanin wannan labari, hakan na nufin cewa akwai wanda ke ba ta bayanai a cikin gidan. Ko kuma ta samo su daga wajen wani da ke da masaniya game da lamarin. Ya dauki wayarta, yana kokarin ganin idan zai iya gano wanda take turawa sakonni. Amma abin mamaki, lambar da ta aika wa sakonnin ba ta da suna. Wata lamba ce da ba a rubuta mata suna ba, wata sabuwa ko wata da aka boye. Wannan ya kara tabbatar masa da cewa akwai wani abu mai girman gaske da ke faruwa. A take ya juya, ya dubi Hajiya Hawwa Maijiddah da idanuwansa masu nuna bacin rai. "Na dauki alkawari, babu wanda zai taba Zaytunah da ‘ya’yanta ba tare da sunan Allah ya tabbata akai ba. Idan har kina da hannu a cikin wani shiri na cutar da su, to ki sani, ba zan taba lamunta ba." Ya wuce zuwa kofar fita, amma kafin ya fita, ya tsaya ya sake dubanta. "Ki tanadi amsa, domin zan dawo." Ya fice daga dakin, zuciyarsa na cike da tunani. Wannan batu ba zai tsaya nan ba. Dole sai ya gano wanda ke bayan wannan al’amari—da kuma abinda ya kawo hakan. Major General Dawud yana fita daga dakin, zuciyarsa cike da tunani. Bai yi kokarin rufe kofa da karfi ba, amma Hajiya Hawwa Maijiddah ta san cewa hakan ya fi komai nuna tsananin fushinsa. A karo na farko cikin shekaru da suka yi tare, ta fahimci cewa tana gab da rasa amanarsa gaba daya. Ya nufi dakin sa na aiki, inda ya zauna a kan kujerarsa yana sake nazarin sakonnin da ya gani. Bai so ya dauki hukunci cikin fushi, amma dole ne ya san gaskiyar al’amari kafin lamarin ya fi kamari. Ya sake duba lambobin da Hajiya Hawwa Maijiddah ta tura wa saƙonni. Lambar da ba ta da suna ta fi daukar hankalinsa. A matsayinsa na soja mai kwarewa da bincike, ba zai bar wannan lamari haka nan ba. Major General Dawud ya dan jinkirta kafin ya kira Captain deen, domin ya san cewa idan ya dauki wannan mataki, komai zai sauya. Wannan ba matsala ce ta iyali kawai ba, matsala ce ta tsaro—wacce dole sai an dauki matakin gaggawa. Ya latsa kiran, yana sauraron karar ringi. A lokaci guda, yana ta faman dannawa cikin wayarsa domin gano wata hanya da zai iya bin diddigin lambar da Hajiya Hawwa Maijiddah ta tura wa sakonnin sirri. "Sir!" Muryar Captain Deen ta karade kunnensa, cike da girmamawa. "Deen, ina bukatar bincike cikin gaggawa. Akwai lambar waya da zan tura maka yanzu—dole ne ka gano wa take da ita da kuma inda take aiki. Hakanan, ina bukatar ka bincika ko akwai wani shiri da ake kullawa da SIRRIN gidan nan." "An gama, Sir!" Deen ya amsa ba tare da bata lokaci ba. "Zan tura bayanai cikin kankanin lokaci." Major General Dawud ya katse kiran, sannan ya aika da lambar wayar. Yana gama hakan, sai ya lumshe idanuwansa, yana kokarin nazarin duk abin da ke faruwa. Ya san cewa Hajiya Hawwa Maijiddah ba ita kadai ce ke da masaniyar SIRRIN Zaytunah da ‘ya’yanta ba. Idan har ta samu bayanai da yawa haka, hakan na nufin akwai wanda ke mata bayanai daga cikin gidan ko kuma daga wajen sa. Wannan ya kara masa damuwa. Bai dauki lokaci mai tsawo ba, Captain Deen ya sake kiran sa. "Sir, mun fara samun bayani akan lambar da aka tura sakonnin nan." "Muna sauraron ka." "Lambar tana da alaka da wata mace da ake kira Hajiya Rumanah. Matar da ke da dangantaka da wasu mutane masu tasiri a birnin mawii da Fubu. Tana kasuwanci, amma kuma ana kyautata zaton tana da alaka da wasu mutane da ke tattara bayanai na SIRRI." Major General Dawud ya lumshe ido, yana jin yadda zuciyarsa ta kara tafasa. "Kana nufin akwai yiwuwar Hajiya Rumanah na tattara bayanai akan Zaytunah da iyalanta?" "Hakan yayi kama da gaskiya, Sir. Kuma abu mafi hadari shine, tana da alaka da wata mata, Hajiya Zaytunah... Gwaggo Zainabu... " Dawud ya dan runtse ido. Wannan batu yana kara rikicewa. Gwaggo Zainabu? Me take da niyyar yi da Zaytunah? Kuma me yasa Hajiya Hawwa Maijiddah ke kokarin tona SIRRIN gidan? Dole ne a dauki mataki cikin gaggawa. "Deen, ina bukatar ka ci gaba da bincike cikin nutsuwa. Kada a bari wani ya gane muna kokarin gano gaskiya." "An gama, Sir!" Bayan kiran ya kare, Major General Dawud ya dauki lokaci yana nazari. Yanzu ya tabbatar da cewa Hajiya Hawwa Maijiddah na da alaka da Hajiya Rumanah, kuma hakan na iya nufin cewa tana da wani shiri da bata bayyana masa ba. Ya mike tsaye a hankali, yana tafiya zuwa dakin da ya bar Hajiya Hawwa Maijiddah. Lokacin da ya isa, ya tarar da ita zaune akan gado, amma a bayyane take cewa hankalinta a tashe yake. Ba tare da bata lokaci ba, ya zauna a gefen kujerar dake kusa da ita, yana kallonta kai tsaye. "Ki gaya min gaskiya, Hawwa. Me kike nema?" Tayi shiru. Ta ji nauyin furta komai, domin ta san cewa duk abin da zata fada, zai iya kara tsananta lamarin. "Me yasa kike tura bayanai akan Zaytunah da iyalanta? Wace alaka kike da Hajiya Rumanah?" A wannan lokacin, jikinta ya fara rawa. Idanunta suka kada, sai ta dan ja numfashi kafin tace: "Dawud, ni ba nufina na cutar da kai bane. Ni dai kawai ina kokarin kare martabarka ne." "Kare martabata?" Ya maimaita, yana kallonta da mamaki. "Ta yaya yin cin amana zai kare martabata?" Hajiya Hawwa Maijiddah ta sunkuyar da kanta. "Ina jin tsoro. Ina tsoron cewa wata rana, Zaytunah da ‘ya’yanta za su kwace maka hankalinka har ka manta da ni da ‘ya’yanmu." A wannan lokacin, Dawud ya yi shiru. Wani irin takaici da ba zai iya misaltawa ba ya lullube shi. Ashe saboda kishin duniya ne yasa Hajiya Hawwa Maijiddah ke aikata haka? Tamkar ya sharara mata uban Mari ya lakada mata duka yakeji. Cike da takaici yache, "Ke kin san cewa tun farko ba ke kika kawo Zaytunah gidan nan ba. Kin san cewa mahaifiyata ce ta bukaci hakan. Ni na tsaya domin ganin cewa babu wanda zai cutar da ita, saboda sanin cewa ba laifinta bane aka jefa ta cikin wannan hali." Ya girgiza kai. "Kuma ki sani, idan har ina da amana, babu wanda zai iya kwace martabarki a idona sai dai ke da kanki." Hajiya Hawwa Maijiddah ta dan rusuna, zuciyarta na tafasa da tunani. "Kiyi kokarin tunani, Hawwa. Idan har kika ci gaba da wannan makircin, ba ke kadai zai shafa ba. Idan aka gano cewa ke kika tona SIRRIN gidan nan, kin san me hakan ke nufi?" Ta runtse ido, tana jin yadda maganganunsa ke sauka akanta kamar toka mai zafi. "Da na fi so ki zo ki gaya min matsalarki, ba ki shiga wannan lamarin ba. Amma yanzu dole ne a dauki mataki. Kuma dole ne ki daina duk wani alaka da Hajiya Rumanah. Bayan barin dakin, Major General Dawud ya nufi ofishinsa. Ya kira Captain Deen a waya. Domin ya kyale hajia hauwa Maijidda ne batare da ya sake mata wata barazanar ba so yake ya gama gano dukkanin kullalliyar da suke shiryawa itada mutanenta na cikin waya... "Deen, akwai bukatar a ci gaba da sanya ido akan Hajiya Rumanah. Kuma ina so a san takamaiman abin da take nema da wannan bayanan." "An gama, Sir!" Yana katse kiran, ya mike tsaye yana nazari. Wani sabon shiri zai dauka. Domin yanzu ya fahimci cewa akwai wata babbar makarkashiya da ake kokarin kullawa a kan Zaytunah da iyalanta. Kuma ba zai bari hakan ya faru ba. Ba tare da bata lokaci ba, ya fara tsara matakin gaba—wanda zai tabbatar da cewa ba wanda zai iya cutar da Zaytunah da ‘ya’yanta, ko da kuwa hakan na nufin yin abin da bai taba yi ba a rayuwarsa. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:33_ Daren ya yi shiru, sai iska mai laushi da ke kadawa cikin lambun gidan. Wutar fitilun da ke zagaye da falon shakatawa sun haskaka fuskar Captain Fawaaz Dawud, wanda ke tsaye a cikin duhu, yana kallon sama kamar yana nazarin taurari. A zuciyarsa, yana jin wani irin nauyi da bai taba jin irinsa ba. Nabeeha da iyalanta za su bar garin zuwa wani lokaci.. Wannan yana nufin cewa ba zai sake ganinta ba har sai Allah ya kawo wata dama. Ya lumshe ido na wani lokaci, kafin ya juyo ya kalli hanyar da take tahowa. A kwance fuskar Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad take, ba tare da wata damuwa ba. Amma idan aka kalli cikin idanuwanta, sai a ga wani irin soyayya da ke boye a zuciyarta, soyayyar da ta kasa furtawa da bakinta. Bata gama karasowa ba, Fawaaz ya ji wani abu na taso masa daga zuciyarsa. Kafin ya ankara, sai da ya tsugunna a gabanta, yana kokarin saukar da idanuwansa cikin nata. He kneeled down on his knees .. begging for her love 🥹 Nabeeha ta tsaya cak, tana kallonsa da mamaki. Idanunta suka zaro da dan razana. "Yaa fawaaz?" Ya kasa magana na wasu dakiku. Hannunsa ya dan taba cinyarsa, yana jin yadda gwiwoyinsa suka daskare akan simintin. "Nabeeha," ya furta da murya mai sanyi, amma wacce ke cike da nauyi. "Ba zan iya barinki ki tafi ba tare da kin san gaskiyar zuciyata ba." Zuciyarta ta buga da karfi. "Gaskiya?" Ta furta a hankali. Fawaaz ya saki wata ajiyar zuciya, yana kokarin danne nauyin da ke kansa. "Yes. I love you, Nabeeha. Ina sonki fiye da yadda kike tunani." Hawaye ya cika idanuwansa. Duk da miskilancinsa, ya san cewa babu wata dabara da zai iya amfani da ita a wannan lokaci. Wannan ba fagen yin taurare bane, ba lokaci bane da zai boye soyayyarsa a karkashin kamun kai. "Kiyi hakuri," ya ci gaba da magana, muryarsa na rawa. "Na jima da fahimtar cewa ke ce kadai mace da zuciyata take bukata, amma na ki furta hakan."🤭 Ya runtse idanuwansa kamar mai jin radadi. "Na ki bari ki san yadda kike da muhimmanci a rayuwata. Amma a yau, ba zan bari ki tafi ba tare da kin san cewa ina matukar son ki ba." Nabeeha ta saki numfashi, zuciyarta na kokarin daukar nauyin kalmomin da ta ji. Ba ta taba tunanin cewa Fawaaz, mutumin da ke da kamun kai da miskilanci, zai iya furta irin wadannan kalmomi ba. "Yaa fawaaz… ka tabbata da abinda kake fada?" Ta tambaya cikin rawar murya. Ya bude idanuwansa a hankali, yana kallonta da soyayya mai cike da tsafta. "Yes, Nabeeha. I am sure. I have never been more sure about anything in my life." Ta dauke kai a hankali, hawaye na taruwa a gefen idanuwanta. "Amma me yasa yanzu, Yaa Fawaaz? Me yasa sai a daren da zan tafi?" Yayi murmushi, murmushin da ya fi kama da radadi fiye da jin dadi. "Saboda na ki amincewa da zuciyata tun farko. Saboda na dade ina kokarin danne soyayyarki a raina, amma sai gashi yanzu tana neman tarwatsa zuciyata." Ya kara matsowa kusa da ita, yana kallonta da wani irin yanayi da ya sanya ta kasa dauke idonta daga nasa. "Nabeeha," ya sake furta sunanta, yana shafar hancinsa da hannunsa. "Ba na so ki tafi ba tare da kin san cewa babu wanda yake son ki kamar yadda nake son ki ba. Ko da kuwa ba zan taba samun ki ba, na fi so ki tafi da sanin gaskiyar zuciyata." Hawaye ya gangaro daga gefen idanuwansa. "I love you, Nabeeha." Ta dan rusuna, zuciyarta cike da shauki da soyayya. Bata san lokacin da hawaye ya wanke fuskarta ba. "Na jima ina jin hakan, Ya Fawaaz. Amma ba na son yin kuskure. Ka yi min alkawari cewa ba ka da wata mace da kake so kamar yadda kake so na." Ya daga hannayensa sama kamar yana yin rantsuwa. "I swear by Allah, ke kadai nake so, Nabeeha." Ta shafi fuskarta da tafin hannunta, tana kokarin boye jin dadinta. "Na amince da kai, Yaa Fawaaz." Wani irin sanyi ya sauka a zuciyarsa. Ya lumshe idanuwansa na wani lokaci, kafin ya bude su a hankali. "Thank you, Nabeeha. Thank you for trusting me." Suka tsaya suna kallon juna, kowannensu yana jin irin soyayyar da ba su taba bayyanawa da fadar magana ba. Daren nan ya dauke su a cikin shaukin da ba za su taba mantawa da shi ba. Iskar dare ta ci gaba da kadawa cikin lambun gidan, tana tayar da sassanyar ƙamshin furannin da ke kewaye da su. Fawaaz har yanzu yana tsugunne a gaban Nabeeha, yana kallonta da idanuwansa masu cike da so da buƙatar ta fahimce shi. She was standing still, her heart pounding wildly in her chest. Never had she imagined that Captain Fawaaz Dawud, the ever-mysterious, ever-distant man, would kneel before her and pour out his heart like this.🥹 Hannayensa sun yi sanyi a gefensa, yana kallonta da idanuwansa masu tsananin zurfi. "Nabeeha," he whispered, his voice laced with raw emotion. "I can’t let you go without telling you what’s in my heart." A cikin zuciyarta, tana jin kamar zata daina numfashi. "Yaa Fawaaz..." Ta kira sunansa da murya mai sanyi, idanuwanta cike da jin ƙauna da tsoro. "Why now? Why tell me this on the night I’m leaving?" Yayi shiru na wasu dakiku, kafin ya saki wata ajiyar zuciya mai nauyi. "Because I have been a fool," he admitted. "Because for too long, I let my pride and my fears stop me from saying what my heart has always known—I love you, Nabeeha. I love you more than I ever thought possible." Hawayen da take ƙoƙarin hana su zuba sun gangaro a kumatunta. "Fawaaz, you don’t know what you’re asking of me." Ya girgiza kai a hankali, yana kallonta da kulawa. "I know exactly what I’m asking. I am asking you to believe me. To know that I have never felt this way about anyone before. And I don’t think I ever will." Zuciyarta ta buga da ƙarfi. Tana jin cewa idan har zata amince da kowa a duniya, to Fawaaz ne. "But what if fate separates us? Idan kaddarar mu bata haduwa bace ba fa?" Ta tambaya da murya mai sanyi. Fawaaz ya ɗan saki wani murmushi mai cike da zafi. "Then I will fight for us. I will find you. I will prove to you that what we have is real. Ina matukar kaunar ki" Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta ɗaga hannunta ta kama nasa. Wannan shi ne karo na farko da ta taɓa yin hakan, kuma jin sa a tafin hannunta ya sanyaya zuciyarta fiye da duk wani abu da ta taɓa ji. "I won’t make promises, Yaa Fawaaz," she whispered. "But if we are meant to be, I believe fate will bring us together again." He closed his eyes for a moment, as if letting her words sink deep into his soul. Then, slowly, he nodded. "That’s enough for me, Nabeeha. That’s all I need to hear." She smiled through her tears. "Take care of yourself, Yaa Fawaaz." A hankali, ta janye hannunta daga nasa, sannan ta juya. She walked away without looking back—because she knew that if she did, her heart would never let her go. Fawaaz remained on his knees, watching her disappear into the night. His heart ached with longing, but deep down, he knew one thing—what they shared was not something time or distance could ever break.🥹🤭 Fawaaz ya ci gaba da kallon Nabeeha har sai da ta bace cikin duhun dare. Wani irin sanyi da daci suka gauraya a zuciyarsa, yana jin kamar ba zai iya motsawa ba. Ajiyar zuciya ya sauke, ya runtse idanuwansa na ɗan lokaci, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi. "Ko da kuwa za ki tafi, Nabeeha," ya furta a hankali, "na riga na ajiye soyayyarki a zuciyata." A can gefe, Nabeeha ta tsaya a bakin kofa, tana kallon sama. Ta lumshe ido, tana jin kalmomin Fawaaz na ci gaba da karade zuciyarta. "I love you, Nabeeha." Wani irin shauƙi ya ziyarci zuciyarta. Bai kamata ta yi tunanin cewa wannan rabuwa ce ta har abada ba, saboda zuciyarta ta riga ta gamsu da cewa Fawaaz yana sonta da gaske. Amma har yanzu, akwai abubuwa da yawa da ba ta fahimta ba. Ta dan runtse ido, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. "Idan kaddara ta so, Fawaaz," ta furta a hankali, "to wata rana, za mu sake haduwa." A can bayan ta, Fawaaz yana tsaye yana kallonta daga nesa, ba tare da ta sani ba. Bai san lokacin da ya runtse ido ba, yana jin wani nauyi yana danne zuciyarsa. "I will wait for that day, Nabeeha," ya furta da wata murya mai sanyi. "No matter how long it takes." Daren yana da shiru, amma zuciyoyinsu na cike da kalmomin da ba su fada ba. Wannan ba dare ne na rabuwa ba, dare ne na alkawari, na fata, da kuma soyayyar da lokaci ba zai iya rushewa ba. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:34_ Daren ya yi nisa, iska tana kadawa a hankali, tana haifar da wani irin shiru mai cike da natsuwa da zurfin tunani. Fawaaz har yanzu yana tsaye a inda ya tsaya, hannayensa a cikin aljihunsa, zuciyarsa cike da tunani. Bai san tsawon lokacin da ya tsaya a wurin ba, amma abu ɗaya yake ji azuciyarsa ta makale a daren nan, a kalmomin Nabeeha, a yadda hawaye suka cika idonta lokacin da take fadin, "Idan kaddara ta so, Fawaaz, to wata rana, za mu sake haɗuwa." Ya sauke ajiyar zuciya, yana jin wani abu na fizgarsa daga ciki. Tun farkon saninsa da ita, bai taɓa tsammanin cewa wata rana zai iya tsugunawa a gaban mace ba, ya furta kalmomin da suka fito daga zuciyarsa ba tare da shakku ba. Amma yau, ya yi hakan. Kuma a karon farko a rayuwarsa, yana jin tsoro, tsoron rasa ta, tsoron kada lokaci ya mayar da shi wani baƙo a wajenta. "Fate will bring us together, Nabeeha," ya furta a hankali, yana jin kamar yana magana da iska. "I will find you again." Nabeeha ta kwanta a gadonta, amma bacci ya gagara zuwa. Ta jujjuya, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Idanunta sun cika da ƙwalla, tunanin Fawaaz na yawo a kwakwalwarta. "Why did he wait until now?" Ta tambayi kanta, amma babu amsa. Duk da cewa ta ji ƙaunar da yake mata, har yanzu akwai abubuwa da dama da ba ta fahimta ba. Ta san cewa Fawaaz mutum ne mai kamun kai, mutum ne da ba ya bayyana soyayyarsa da sauƙi. Amma hakan bai hana ta jin cewa yana ɓoye abu mai zurfi a zuciyarsa ba. Hannunta ta daura saman KIRJIN ta, tana jin yadda bugun zuciyarta ke sauri. "Wata rana, idan lokaci da kaddara sun amince, zan san menene a zuciyarka da gaske, Fawaaz." A washegari, garin ya waye da wani irin sanyi mai daɗi, alamar cewa hunturu na gab da ƙarewa. Shirye-shiryen tafiya sun kankama, kaya sun cika akwatuna,su na ta faman bankwana da juna. Fawaaz bai fito daga sashensa ba, amma zuciyarsa na tare da su Nabeeha. Bai jin zai iya kallonta tana tafiya ba, domin yana tsoron kada idon su ya haɗu kuma ta ga SIRRIN da yake ƙoƙarin ɓoyewa. Amma kafin su shiga mota, zuciyarsa ta kasa jurewa. Kamar wanda aka fizgo da ƙarfi, ya fito daga sashensa, ya tsaya daga nesa yana kallonta. Nabeeha ta ji motsinsa, sai ta juyo. Idanunsu suka haɗu. A nan ne Fawaaz ya fahimci abu ɗaya—ko da kuwa zata tafi yau, akwai wata rana a gaba da ke jiransu. Wata rana da kaddara za ta sake haɗa su, domin soyayyar da take tsakaninsu, ba ta cikin irin waɗanda lokaci da nisa ke iya rushewa. 🎀🎀🎀 A cikin falon katafaren gidan Major General Dawud, an hallara da martabarsu. Alhaji Amiru, Alhaji Uzairu, Gwaggo Hafsatu, da Gwaggo Zainabu sun iso, kowa da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa. Falon yana da yalwa, an kawata shi da kujeru masu kyau, hasken fitilu yana ba wa dakin wani irin kyan da ke kara girmamawa ga wadanda ke zaune a ciki. Kamar yadda ya kamata, an fara taron da gaisuwa da hirar duniya, domin kowa ya samu nutsuwa kafin a shigo da maganar da ta kawo su. "Allah ya kara lafiya," cewar Alhaji Amiru, yana mai gyara zamansa. " "Eh, Allah ya taimaka," major ya amsa da murmushi....." Duk suka hada baki wajen cewa, "Aameen" Gwaggo Zainabu ta dan bubbuga cinyarta.. "Lokaci na tafiya" Gwaggo Hafsatu ta yi murmushi. "Haka rayuwa take. Allah ya sanya zaman lafiya." Major General Dawud yana zaune cikin shiru, yana sauraron tattaunawar tare da jan numfashi a hankali. Yana jiran su samu nutsuwa kafin ya shigo da maganar da ta kawo su. Bayan ƴan mintuna na dariya da tuno abubuwan da suka gabata, hirar ta dan lafa. Sai Major General Dawud ya gyara zamansa, ya dube su da nutsuwa. "Mun gayyace ku a nan ne," ya fara da murya mai kwarjini, "saboda akwai wani abu mai muhimmanci da ya kamata mu bayyana muku. Shiru ya baci. Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru suka kalli juna, sannan suka mayar da hankalinsu kansa. Gwaggo Zainabu kuwa ta gyara zama, zuciyarta cike da tuhuma. "Ba wani abu ba ne illa dangane da Hajiya Zaytunah da iyalanta," ya ci gaba. "Mun kira ku ne domin mu gaya muku cewa tun tsawon shekarun nan, suna a karkashin kulawar gidanmu." Wani irin shiru ya sake baci. Alhaji Uzairu ya dan zabura, yana kallon Major General da ido waje. "Kana nufin cewa... Zaytunah tana gidanka tsawon wannan lokaci gaba ɗaya?" Major General Dawud ya gyada kai a hankali. "Eh." Gwaggo Zainabu ta dan dafe KIRJIN ta, tana kallon Gwaggo Hafsatu da mamaki. "Haj Hafsatu, kin san da wannan har na tsawon wannan lokaci?" Gwaggo Hafsatu ta sauke ajiyar zuciya. "Na sani, Zainabu. Kuma ina fata zaku fahimta bayan kunji dalili." Alhaji Amiru ya dafe gemunsa, yana mai sake gyara zama. "Wannan lamari yana bukatar karin bayani. Me ya sa aka boye mana ita? Me ya hana ta komawa gidanta?" Gwaggo Hafsatu ta dubi dukkansu, sannan ta gyara mayafinta. Ta bude baki a hankali. "Asiri aka yi mata." Wani irin shiru ya sake ratsa falon. Alhaji Uzairu ya girgiza kai, alamar bai fahimta ba. "Asiri?" Alhaji Amiru ya maimaita, yana mai fidda numfashi. "Eh, asiri," ta tabbatar da murya mai nauyi. "Ba wai kawai an yi mata asiri ba, a'a, makirci ne aka yi mata da tsibbu aka rabata da gidanta da iyalanta. Ba don ta guje ku ba, don kuwa tana so ta dawo, amma kurciya aka yi mata har sai da ta kasa komawa. Har sai da ta zama kamar ba ita ba." Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Bai taɓa sanin cewa akwai wani abu mai muni irin wannan da ya faru da ita ba. Gwaggo Zainabu ta gyara zama, muryarta na nuna alamar damuwa. "To yanzu ya take? Da wanne hali take ciki?" Major General Dawud ya amsa. "Alhamdulillah, tana cikin kulawa, kuma an yi mata addu'o’i da magunguna da yawa. Amma har yanzu akwai tasirin abin da aka yi mata." Alhaji Amiru ya sauke ajiyar zuciya. "Allah ya kiyaye gaba. Wannan abu da muka ji yana da nauyi sosai." Alhaji Uzairu ya dafe kansa, zuciyarsa cike da damuwa. Ya dubi Gwaggo Hafsatu, yana mai furta da wata murya mai rauni, "Duk tsawon wannan lokaci, ni da dangi muna tunanin cewa ta tafi ne don ta fice daga rayuwarmu. Ba mu taɓa sanin cewa akwai wani abu mai muni da ya hana ta komawa ba." Gwaggo Hafsatu ta girgiza kai. "Ba don ta so ba, Uzairu. Amma ka san halin duniya. Allah ya kiyaye gaba." Shiru ya sake baci. Kowannensu na tunani. Wannan dai ba taron banza ba ne—taro ne da zai sauya komai. A cikin falon da shiru ya lullube, kowanne daga cikin manyan da suka hallara yana nazarin abin da ya ji. Alhaji Uzairu ya dafe kansa da hannunsa biyu, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Duk shekarun nan, yana zargin cewa Hajiya Zaytunah ce ta guje su, bai taɓa tunanin akwai wani abu da ya fi karfinta ba. "Wato haka al’amarin yake?" ya furta a hankali, yana mai duban Gwaggo Hafsatu. "Kenan duk waɗannan shekarun, tana cikin ƙunci ne ba don ranta ba?" Gwaggo Hafsatu ta gyada kai a hankali. "Hakika, Uzairu. An yi mata asiri mai tsananin gaske, har sai da ta rasa ikon komawa gidanka. Kuma ba wai kawai hakan ya faru ba, an yi mata kurciya—wato tunani da firgici da tsoro, har sai da ta ji ba za ta iya komawa ba. Wannan shine dalilin da yasa take nan." Alhaji Amiru ya gyara zama, yana mai fidda numfashi. "To yanzu menene matakin gaba?" Major General Dawud ya dube shi da idanu masu ƙarfi. "Mun kawo wannan taro ne domin mu sanar da ku gaskiya, kuma mu ɗauki matakin da ya dace. Ku sani, Hajiya Zaytunah ba ta da wata matsala da ku. Tana kaunarku, tana son yaran ta tana Kuma kula da su, amma maganin da aka yi mata ya hana ta komawa." Alhaji Uzairu ya lumshe ido na wasu dakiku, yana mai jin wani irin zafi a zuciyarsa. A matsayin sa na miji, bai kamata a ce bai fahimci halin da matarsa take ciki ba. Gwaggo Zainabu ta gyara mayafinta, tana mai kallon Gwaggo Hafsatu da alamar tambaya. "To yanzu, Hafsatu, kina ganin akwai mafita? Ko dai haka al’amarin zai ci gaba da kasancewa?" Gwaggo Hafsatu ta yi shiru na dan lokaci kafin ta girgiza kai. "Mafita akwai, amma dole ne a bi HANKALI. Har yanzu ba mu san su waye suka aikata wannan mummunan aiki ba. Idan ba mu dauki mataki mai kyau ba, hakan na iya zama barazana gare ta da iyalanta." Alhaji Amiru ya gyada kai. "Hakan gaskiya ne. To amma, Zaytunah ta san da wannan taro?" Major General Dawud ya gyada kai. "Eh, ta sani. Kuma a shirye take don ta fuskanci wannan matsalar. Amma sai an yi HANKALI." Alhaji Uzairu ya dago kansa, yana kallon Major General Dawud kai tsaye. "Ina son ganin ta." Shiru ya sake baci a falon. Wannan kalma daya ce kacal, amma tana ɗauke da nauyin shekaru da yawa da suka shuɗe. Gwaggo Hafsatu ta dubi Major General Dawud, sannan ta sauke numfashi. "Zai fi kyau a yi hakan a hankali. Akwai abubuwan da za a shirya kafin hakan ta faru." Gwaggo Zainabu ta kara da cewa, "Gaskiya ne. Muna bukatar tabbatar da cewa ba za a samu matsala ba idan suka hadu." Alhaji Uzairu ya gyada kai a hankali, amma idanuwansa sun cika da damuwa. "Ba zan gajiya ba har sai na ganta." Duk wanda ke wurin ya fahimci cewa wannan taro ba zai ƙare a yau ba. Wannan dai hanya ce ta bude sabon babi a rayuwar Zaytunah da iyalanta. Kuma abu guda ya tabbata—komai zai canza daga yau. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:35_ Bayan wani shiru da ya dauki kusan mintuna biyu, Alhaji Amiru ya gyara zama, yana mai duban Major General Dawud da Gwaggo Hafsatu. "Tun da dai yanzu mun samu tabbacin cewa Hajiya Zaytunah tana nan cikin kulawarku, akwai bukatar a dauki matakin da ya dace don dinke wannan barakar shekaru da suka shude." Alhaji Uzairu ya gyada kai da karfi. "Hakan ne! Dole ne mu hadu da ita, mu ganta da ido, mu tabbatar da halin da take ciki. Ban yarda da jin kawai ba, dole na ganta da kaina." Gwaggo Zainabu ta dubi Alhaji Uzairu da tausayi. "Na fahimce ka, Uzairu. Ka jima kana rayuwa da tunanin cewa matarka ta guje ku, ba tare da sanin abinda ya faru ba. Amma dole ne mu bi komai a hankali. Idan da gaske asiri aka mata, to hakan na nufin akwai hatsari idan ba a bi da lamarin da hankali ba." Major General Dawud ya jinjina kai. "Mun riga mun tsara yadda komai zai kasance. Za mu tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai. Amma kafin hakan, akwai bukatar mu san cewa wane hali take ciki yanzu. Har yanzu tana fama da tasirin abin da aka yi mata." Alhaji Amiru ya lumshe ido, yana mai nazari. "Wato yanzu dai kuna nufin har yanzu ba ta gama dawowa hayyacinta dari bisa dari ba?" Gwaggo Hafsatu ta gyada kai a hankali. "Ba wai bata da lafiya ba, amma akwai wasu abubuwan da ke damunta. Duk da cewa ta san da mu, ta san da ‘ya’yanta, har yanzu tana da wani irin tsoro da rashin kwanciyar hankali idan aka ambaci komawa gidan mijinta." Alhaji Uzairu ya dan sake numfashi, yana mai jin wani irin nauyi a zuciyarsa. "Ba zan matsa mata ba. Amma dole ne na ganta." Major General Dawud ya dubi Gwaggo Hafsatu, kafin ya maida kallonsa kan duka mutanen da ke falon. "Za a iya hakan, amma dole ne mu tabbatar da cewa ba za ta samu wata damuwa ba. Idan aka matsa mata sosai, hakan na iya kawo wani sabon tashin hankali." Alhaji Amiru ya gyada kai. "To menene mafita?" Gwaggo Hafsatu ta gyara zama, sannan ta dubi kowa cikin falon. "Zan fara magana da ita a hankali. Zan sanar da ita cewa kun san inda take. Idan ta nuna cewa tana da karfin zuciya don haduwa da ku, to za mu shirya haduwar cikin nutsuwa." Alhaji Uzairu ya gyada kai, kallo a idonsa yana nuna cewa yana fatan hakan ta tabbata ba tare da wata matsala ba. Gwaggo Zainabu kuwa ta dafe hannayenta, tana mai jin wani irin tausayin matar Dan nata. Shekaru da dama ba su hadu ba, amma yanzu da yake suna daf da haduwa, zuciyarta cike take da fargaba. Major General Dawud ya mike tsaye a hankali, yana mai da kallo ga mutanen da ke falon. "Zan dauki alhakin tabbatar da cewa an samu mafita mai kyau. Amma sai an bi komai a hankali. Na amince da shawarwarin Gwaggo za ta fara magana da ita. Idan ta shirya, sai mu shirya haduwar da ba za ta cutar da ita ba." Alhaji Uzairu ya numfasa a hankali. A zuciyarsa, yana so ya rungume matarsa a take. Amma dole ne ya hakura. Duk da cewa zuciyarsa na masa ruri, dole ya jira har sai lokacin da ya dace. Kowa a falon ya fahimci cewa wannan dai ba shi ne karshen maganar ba. Amma abu guda ya tabbata akwai fata. ..... Gwaggo Hafsatu ta dan murmusa, amma cikin zuciyarta akwai nauyin da take jin zai iya girgiza zuciyar Hajiya Zaytunah. Ta zauna a gefenta, tana mai dubanta da kulawa. "Zaytunah, akwai wani abu da nake so muyi magana a kai." Hajiya Zaytunah ta ajiye littafin hannunta, tana mai dubanta da kulawa. "Ina sauraronki, Gwaggo. Menene?" Gwaggo Hafsatu ta sauke numfashi a hankali, sannan ta dubeta da ido mai dauke da hakuri da tsantsar soyayya. "Akwai mutanen da suka zo gidan nan, kuma sun zo ne domin su gan ki. Sun dad’e suna neman ki, amma sai yau Allah Ya hada ku." Wani irin kakkarwar zuciya ya kama Hajiya Zaytunah, numfashinta ya dauke na wasu ‘yan dakiku kafin ta iya tambaya. "Su waye suka zo?" Gwaggo Hafsatu ta dafa hannunta cikin kwantar da murya. "Alhaji Uzairu, Alhaji Amiru, Gwaggo Zainabu… duk sun zo." Cikin sauri zuciyarta ta buga. Idanunta suka fara cikowa da hawaye, hannunta ya dan yi sanyi kamar ba jini a ciki. Ta dafa KIRJIN ta, tana jin nauyin kalmomin da ta ji. "Uzairu?" Ta maimaita cikin wata irin murya mai rauni. Gwaggo Hafsatu ta gyada kai. "Eh, Zaytunah. Sun zo ne domin su san halin da kike ciki. Sun dauka cewa ke ce kika guje su, ba tare da sun san abin da ya faru da ke ba." Hajiya Zaytunah ta runtse ido, hawaye suka zubo mata. Tun shekarun da suka shude, bata taɓa tunanin cewa wani lokaci za ta sake ganin su ba. Shekaru da dama na rashin sanin me ya faru da su, na jin cewa wataƙila sun manta da ita, ko kuma sun yanke hukunci a kanta ba tare da sanin gaskiya ba. "Zaytunah," Gwaggo Hafsatu ta kira sunanta a hankali. "Mun shirya yadda za ku hadu, amma sai da amincewarki." Hajiya Zaytunah ta goge hawayenta, zuciyarta tana harbawa da nauyin tunani. "Gwaggo... Ban san me zan ce ba. Zan iya fuskantar su? Shin zasu yarda da ni? Shin har yanzu suna ganin ni a matsayin matar da suka sani?" Gwaggo Hafsatu ta rike hannunta, tana mai gyada kai. "Sun zo ne domin jin gaskiya. Sun zo ne domin su fahimta. Idan kina da karfin zuciya, to lokaci ya yi da za ki hadu da su." Hajiya Zaytunah ta dauki lokaci kafin ta iya furta kalma. Ta dubi Gwaggo Hafsatu da idanu masu cike da tausayi da tsoron ciwon zuciya. "Gwaggo, ina bukatar lokaci. Ba zan iya haduwa da su haka nan ba." Gwaggo Hafsatu ta shafa kanta cikin kwantar da hankali. "Babu matsala, Zaytunah. Lokacin da kike bukata zai kasance a gare ki. Amma ina so ki sani babu wanda ya manta da ke. Babu wanda ke jin haushin ki. Sun zo ne domin ki, domin su sake jin dumin ki." Hajiya Zaytunah ta rufe fuska da tafukan hannayenta, tana jin wani irin zafi a zuciyarta. Idan har hakan gaskiya ne, to watakila lokaci ya yi da za ta fuskanci abin da ta tserewa shekaru da dama. A gefe guda, Alhaji Uzairu yana can a dakin da aka kebe shi, yana jiran amsa daga Gwaggo Hafsatu. Hankalinsa a tashe yake, zuciyarsa tana bugawa da sauri. Shin Zaytunah za ta amince su hadu? Shin har yanzu tana tunaninsa? Ko kuwa ta manta da shi? Duk wadannan tambayoyi suna masa yawo a zuciya. Kuma babu amsar da zai iya samu sai dai har sai lokacin da ta amince su hadu. A wancan dare, zuciyoyi da dama suna juyawa. Kuma duk da fargaba da ke akwai, akwai fata—fata na cewa wata rana, komai zai koma daidai. ..... A cikin dare mai cike da natsuwa, Hajiya Zaytunah ta kwana tana juyi akan gadonta. Idanunta sun ki rufuwa, zuciyarta tana ta kai da kawowa. Wani bangare na zuciyarta yana so ta hadu da su Alhaji Uzairu, ta fuskance su, ta bayyana gaskiyar abin da ya faru da ita. Amma wani bangare yana cike da tsoro—tsoron abin da zai biyo baya, tsoron ko za su yarda da ita, tsoron yadda zata iya fuskantar wanda ta dauka cewa ta rasa har abada. Washegari da safe, bayan ta gama shiryawa, ta zauna a gefen gadonta tana tunani. Gwaggo Hafsatu ta shigo, ta zauna kusa da ita tana murmushi. "Kin yi barci?" Hajiya Zaytunah ta girgiza kai a hankali. "Wallahi, Gwaggo, zuciyata ba ta bani damar yin barci ba. Hankalina yana a tashe." Gwaggo Hafsatu ta dafa hannunta cikin kulawa. *Zaytunah, wannan ba lokaci ba ne na tsoro. Wannan lokaci ne na dinke barakar da aka jima ana fuskanta. Idan kika bari tsoro ya hana ki fuskantar su, hakan na iya jawo bakin ciki har karshen rayuwarki Hajiya Zaytunah ta sauke ajiyar zuciya, tana wasa da yatsun hannunta. A hankali ta dago kai ta dubi Gwaggo Hafsatu, idanunta cike da ruɓaɓɓen tunani. "Gwaggo, me zai faru idan ba su fahimce ni ba? Me zai faru idan suka yanke hukunci cewa ni ce na watsar da su?" Gwaggo Hafsatu ta murmusa, tana shafa hannunta cikin kwantar da hankali. "Zaytunah, su Alhaji Uzairu da sauran su ba yara ba ne. Sun yi shekaru suna neman ki, da basa kaunar sake sanya ki a idanuwan su ai duk tarin shekarun nan da ba zasu dinga neman ki ba.., suna neman hakikanin abin da ya faru. Wannan shi ne lokacin da za su ji gaskiya daga bakin ki. Babu wanda zai zarge ki idan suka fahimci matsalar da kika shiga." Hajiya Zaytunah ta jinjina kai a hankali, tana jin wani sanyi a zuciyarta. Duk da haka, fargaba ba ta gushe ba. A wancan lokacin, a gefen Alhaji Uzairu, zuciyarsa tana tafasa. Tun bayan da suka bar falon Major General Dawud jiya, ya kasa samun natsuwa. Tunani ya hana shi barci. Shin zai sake ganin Zaytunah? Shin zata gane shi? Shin zata yarda ta dawo da komai kamar da? "Uzairu," murya ta katse masa tunani. Alhaji Amiru ne ke magana, yana dubansa da kulawa. "Kana da yakinin cewa kana shirye ka fuskance ta?" Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin zuciyarsa na harbawa. "Ya Amiru, ba wai tambayar ko na shirya ba ce. Tambayar ita ce—shin zata yarda da ni? Shin zata fahimce ni?" Alhaji Amiru ya dan murmusa, yana dafa kafadar shi. "Zaytunah ba matar da zata manta da kai haka kawai ba. Idan da hakan ne, da tuni ba ta damu da ciwon da take fama da shi ba. Ka yi hakuri, ka bari lokaci ya yi aiki." A can gefe, Major General Dawud ya fito daga sashensa yana kallon su duka. A yau ne suka shirya haduwar da suka jima suna jira. Ya kalli Gwaggo Hafsatu, wadda ta jinjina kai, tana nufar su Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru. "Lokaci ya yi." Ta fada a hankali. Alhaji Uzairu ya mike, ya gyara rigarsa. Zuciyarsa na bugawa da sauri. Wannan haduwar ba zai taba mantawa da ita ba. Duk da sanyin gari, idanun Alhaji Uzairu sun cika da zufa. Yayi nisa a tunani har sai da suka iso bakin kofar dakin da Hajiya Zaytunah take. Gwaggo Hafsatu ta ja numfashi sannan ta tura kofar a hankali. Cikin nutsuwa, Hajiya Zaytunah ta dago daga inda take zaune, idanunta cike da tsoro da fargaba. Kamar dai yadda take a daren jiya, zuciyarta ta kasa natsuwa. A hankali, Alhaji Uzairu ya taka zuwa ciki, yana kallonta da ido. Tsawon shekaru bai ganta ba, amma yau, gashi a gabansa. "Zaytunah..." Muryarsa ta fito cikin karyewa. Hajiya Zaytunah ta sake kakkarwa, zuciyarta na bugawa. Ta dauke kanta gefe, tana jin yadda numfashinta ke rikicewa. Alhaji Uzairu ya matsa kusa, amma ba tare da matsawa fiye da kima ba. Ya lura da yadda take a tsorace, hakan yasa ya daidaita kansa. "Zaytunah, ni ne. Uzairu. Ki kalleni." Idanunta sun cika da kwalla, amma ta kasa dago su. Babu abin da take ji sai bugun zuciyarta da wani irin sanyi a gabanta. "Ban taɓa mantawa da ke ba." Ya fada a hankali, hawaye suna taruwa a idonsa. "Ban san me ya faru da ke ba. Ban san inda kika shiga ba. Amma ban taɓa dena tunaninki ba." Hawayenta sun gangaro, amma har yanzu bata iya motsi ba. "Idan har da gaske kika manta da ni, idan har da gaske kika manta da rayuwarmu..." Ya runtse ido, yana jin yadda zuciyarsa ke suya. "To zan tafi. Amma da fatan za ki gaya min gaskiya, menene ya faru?" A wannan lokacin ne zuciyar Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa. Kamar wacce ta sha ruwa mai sanyi, ta fashe da kuka. "Uzairu..." Muryarta na rawa. "Ban guje ku ba. Ban manta da kai ba. Ban manta da komai ba." Alhaji Uzairu ya kafe ta da ido, zuciyarsa na suya da karaya. "To me ya faru? Menene ya hana ki dawowa?" Hajiya Zaytunah ta runtse ido, tana jin yadda hawayenta ke bin fuskarta. Cikin wani irin shesshekar kuka, ta furta kalmomin da suka kasa fita tsawon shekaru. "Asiri aka min, Uzairu. An rabani da ku da sihiri da tsibbu. An tursasa min tafiya, aka hana ni dawowa. Ban yi hakan da kaina ba!" A take zuciyar Alhaji Uzairu ta buga, ya dafe kirjinsa kamar wanda aka caka wa mashi. Idanunsa suka firfito da mamaki. "Asiri?" Ya tambaya cikin rawar murya. Hajiya Zaytunah ta gyada kai, tana jin yadda zuciyarta ke kunshe da zafi. "Kurciya aka yi min, Uzairu. An kulle ni cikin wani hali da bai barni na koma gare ku ba. An sace rayuwata." Shiru ya ratsa dakin. Alhaji Uzairu ya dafa goshinsa, yana jin yadda nauyin abu ya hau kansa. Idan har wannan gaskiya ne, to hakan na nufin shekaru da dama na rashin sanin hakikanin abin da ya faru. Bai san lokacin da hawaye suka gangaro daga idonsa ba. Bai san lokacin da zuciyarsa ta fashe da raɗaɗi ba. A hankali, ya matsa kusa da ita. Babu kalma da zai iya furtawa, sai ya tsugunna gabanta, yana kallonta da ido. "Zaytunah..." Ya kira sunanta cikin rawar murya. A hankali, ta dago ta kalle shi. Idanun su cike da hawaye. "Kin dawo gare ni?" A wannan lokacin ne zuciyarta ta fashe, ta sunkuya, ta boye fuskarta cikin tafukan hannunta, tana kuka mai karfi. A wannan lokacin ne Alhaji Uzairu ya fahimta duk tsawon shekarun da suka shude, duk radadin da suka sha, wataƙila wannan ce ranar da za a fara farfaɗowa daga ciki. Ranar da komai zai fara gyaruwa... MX🧕 *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:36_ Hawaye suka ci gaba da sintiri a fuskar Hajiya Zaytunah. Hannunta yana rawa, zuciyarta na bugawa da karfi. Ta kasa motsawa, ta kasa yarda da cewa yau, gashi da gaske Alhaji Uzairu na a gabanta. "Yaya uzairu..." Ta sake furta sunansa cikin raunaniyar murya, kamar mai neman tabbaci. Alhaji Uzairu ya gyada kai, yana kallonta da ido mai cike da tausayi. "Eh, ni ne, Zaytunah. Na zo, na zo gare ki. Amma kina nufin shekaru duka wadannan ba ki san yadda za ki dawo ba? Ko da sandar sako?" Hajiya Zaytunah ta runtse ido, wani sabon hawaye na gangarowa. "Ba ku fahimta ba, Uzairu. Ba wai kawai an rabani da ku ba ne. An tsare ni a wani hali na kurciya da ba zan iya bayyana ba. Wataƙila har yanzu ba ku san cewa har cikin barcin ku an danƙa min tsinuwa da tunzuri akan kin waiwayar gidah ba" Alhaji Uzairu ya dafe goshinsa, zuciyarsa na kuna. Wani irin tausayin Zaytunah ya lulluɓe shi, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi. Duk da shekara da shekaru da suka shude, ba zai iya musanta cewa wannan matar da ke gabansa ita ce zuciyarsa, soyayyarsa, iyalinsa da ya dade yana nema. A hankali ya kalli cikin idanunta da suka cika da hawaye. "Zaytunah..." Ya kira sunanta da wani irin sanyin murya, yana jin yanda kalmomin suka makale masa a makoshi. "Kina nufin duk wannan lokaci kina raye da kike fama da wannan hali?" Zaytunah ta lumshe ido, tana jin zuciyarta na rawa. "Uzairu, ba abu ne mai sauƙi ba. Wallahi ba zan iya bayyana azabar da na sha ba. A kowace rana ina jin kaina a cikin duhu. Akwai lokutan da nake jin kamar na salwanta, kamar rayuwata ta kare." Ta runtse ido, hawaye suna sintiri a kumatunta. "Ban san yadda zan iya komawa gare ku ba. Ko da na so, ba zan iya ba. Duk hanyoyin da zan bi an toshe min su." A can gefe, Gwaggo Hafsatu ta dafa hannun Zaytunah, tana girgiza kai. "Ai mun san hakan, Zaytunah. Mun san cewa ba da kanki kika bar su ba. Muna tare da ke, mun sha wahala wurin fahimtar abin da ya faru." Alhaji Amiru ya dubi Major General Dawud, yana dan gyara zamansa. "Wannan abu da aka yi mata ba ƙaramin zalunci ba ne. Na sha bincike a baya, amma ban taɓa tunanin cewa har tsibbu da asiri ne aka yi mata ba." Gwaggo Zainabu, wadda tun farkon maganar take kallonsu da damuwa, ta numfasa. "Wai shin waye ya yi wannan asirin? Su waye suka shirya wannan makircin?" Shiru ya ratsa falon. Kowa ya juya yana kallon Zaytunah, amma sai ta kauda kai gefe. Akwai abubuwan da ba za ta iya faɗa yanzu ba. Major General Dawud ne ya dubeta da kulawa. "Zaytunah, babu abinda zai faru idan kika faɗa gaskiya. Wannan lokaci ne na yanke hukunci akan abin da ya faru da ke. Idan har akwai wanda yake da alhakin hakan, to dole ne mu san shi." Zaytunah ta dan lumshe ido, ta sake jan numfashi. Sannan cikin wata irin murya mai rauni, ta furta: "Kishiyoyi hadi da wasu daga cikin yan uwana na ne suka yi min wannan asirin. Sun haɗa kai da wasu bokaye suka kulle ni da tsibbu da kurciya, suka hana ni komawa gidana... ." Wata irin faduwar gaba ta kama Alhaji Uzairu. Ya kafe ta da ido, yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi. "Wannan gaskiya ne, Zaytunah?" Ta gyada kai, hawaye suna cika mata ido. "Yaya Uzairu, wallahi gaskiya nake faɗa. Su ne suka yi min haka. Su suka raba ni da kai, suka sa na bar gidan da Muhammad wanda yake Hammad a yanzu da mai sunan Gwaggo da muke kira da Nabeeha a yanzu." Alhaji Uzairu ya rintse ido, yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. Bai taba tunanin cewa matan sa za su iya aikata hakan ba. Bai taba zaton cewa makircinsu zai kai haka ba. "Allah ya isa!" Ya furta cikin zafin rai. Gwaggo zainabu ta dafa kafadar sa, tana kokarin kwantar masa da hankali. "Uzairu, ba fushi za mu yi ba. Abinda ya fi dacewa shi ne mu yi tunanin matakin da za mu ɗauka a yanzu." Major General Dawud ya gyara zama, yana kallon su gaba ɗaya. "Tabbas dole ne a yi abu akan wannan lamari. Amma kafin komai, dole ne mu tabbatar da cewa Zaytunah da iyalinta sun samu kariya daga duk wani abu da ka iya faruwa nan gaba." Gwaggo Zainabu ta jinjina kai. "Eh, haka ya kamata. Mun dade muna neman ta, amma yanzu da Allah ya kawo mu gare ta, ba za mu ƙyale ta sake shan wahala ba." A hankali, Alhaji Uzairu ya sauke ajiyar zuciya. Ya kalli Zaytunah, zuciyarsa na cike da raɗaɗi da kauna a lokaci guda. "Ba zan taɓa barin ki sake fuskantar irin wannan ba, Zaytunah." Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, hawaye suka sake gangarowa daga idanunta. A karo na farko tun shekaru da dama, ta ji wata irin nutsuwa a cikin zuciyarta. Wataƙila, wannan ce ranar da za ta fara dawowa da kanta. Shiru ne ya sake ratsa falon, kowa cikin dogon tunani. Wani irin nauyi ne ya danne zuciyar Alhaji Uzairu, amma dauriya kawai yake yi. A gefe guda yana ji kamar ya fusata, amma a dayan bangaren kuma zuciyarsa na cike da shauƙi da ƙauna, saboda a gaban sa ne matar da ya dade yana mafarkin ganin ta. A hankali ya numfasa, ya kalli Zaytunah da idanunta suka cika da hawaye. A shekarun da suka wuce, ya yi tunanin cewa watakila ta manta da shi, watakila ta samu wani rayuwar daban, amma a yau, gashi da idanunsa yana jin labarin abin da ya raba su. "Zaytunah..." Ya kira sunanta a hankali, kamar wanda ke jin tsoron ta ɓace masa. Ta ɗan juyo, amma ba ta iya kallonsa kai tsaye ba. Numfashinta na fita a hankali, tana jin zuciyarta kamar zata fito waje. "Kin dade a cikin duhu. Kin sha wahala. Amma na rantse da Allah, daga yau ba zan ƙyale wani ya sake cutar da ke ba." Muryarsa na nuna yadda zuciyarsa ta gama cika da alhini. Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, tana jin yadda kalamansa suka saukar mata da wani irin sanyi a zuciya. Daga lokacin da ta bar gidansa zuwa yanzu, ba ta taba jin irin wannan nutsuwa ba. Gwaggo Hafsatu ta numfasa, ta kalli su duka da kulawa. "A yanzu, abin da yafi dacewa shi ne mu yanke shawarar yadda za a ci gaba. Zaytunah, ke dai kin shirya komawa gidan mijinki?" Shiru ya ratsa falon. A hankali, Zaytunah ta dago kai, ta kalli Gwaggo Hafsatu. "Ba wai ba na so ba, Gwaggo, amma ina jin tsoro. Ina jin tsoron komawa cikin wannan rayuwar, saboda har yanzu ba mu san abin da zai biyo baya ba." Major General Dawud ya gyara zama, yana kallonta da kulawa. "Ba ke kadai kike jin hakan ba, Zaytunah. Amma muna tare da ke. Duk wanda ya sake kokarin cutar da ke, zai gamu da hukuncin da ya dace da shi." Alhaji Amiru ya jinjina kai. "Haka ne. Kuma ba za mu tsaya a nan ba. Dole ne a bi wannan lamari a shari'ance. Mutanen da suka yi miki haka dole ne su fuskanci hukunci." Alhaji Uzairu, wanda ya kasa jurewa, ya kalli Major General Dawud. "Ina bukatar taimakon ka, Janar. Ina so a yi bincike sosai a gano wadanda suka hada baki akan wannan mugun nufi." Gwaggo Zainabu ta gyada kai cikin goyon baya. "Haka ya dace. Wannan ba abu ne da za a kyale ya wuce haka ba. Mun dade muna cikin duhu, amma yanzu gaskiya ta bayyana." Hajiya Zaytunah ta sauke ajiyar zuciya, tana kallon su daya bayan daya. A karo na farko, ta fahimci cewa ba ita kadai ce. Tana da mutanen da suke tare da ita, wadanda za su kare ta, za su tsaya mata. Ta juya, ta kalli Alhaji Uzairu. A karon farko tun bayan shigowarsa, ta kalle shi da tsananin kauna da tausayawa. "Yaya uzairu..." Ta kira sunansa da wata irin nutsuwa. "Ina so ka fahimta cewa ba na manta da kai ba. Ban manta da kauna da zaman mu ba. Amma ina bukatar lokaci… Na shirya dawo wa, amma ina bukatar in tabbatar cewa babu hatsari." Alhaji Uzairu ya fahimci tsoronta. Ya matso kusa da ita, yana dubanta da tsantsar soyayya. "Zaytunah, na amince da komai. Ba na matsa miki dole. Amma zan jira ki. Na jima ina jira, don haka babu matsala idan zan jira ki har sai da kika shirya." Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, ta dago cikin nutsuwa. "Nagode, Yaya Uzairu." A gefen Gwaggo Hafsatu, Major General Dawud ya numfasa, yana jin wani nauyi ya sauka daga zuciyarsa. A yau, an warware wata babbar matsala da ta daɗe tana hana su sukuni. Sai dai, wannan ba ƙarshen al’amari ba ne. Wannan ne farkon sabon babi a rayuwar su. Sabon babi da ba za a iya hasashen yadda zai kaya ba.... ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:37_ Duhu ne ya mamaye dajin, iska mai sanyi na busawa yana tayar da ganyaye suna faduwa bisa kasa. Tsuntsaye sun daina rerawa, kamar sun san wani abu mai girma zai faru. A tsakiyar dajin, akwai wata bukka, daga gefe wuta tana tashi a cikin kwanon karfe, tana daukar wani irin hayaƙi mai wari. A cikin wannan bukkah ne Haruna ya hangi su Hajiya Rumanah, Hajiya Ladi, da Hajiya Karama zaune, suna fuskantar wani dattijo da ke rike da babban bokiti mai cike da ruwa. Haruna ya dan tsuguna a bayan wata bishiya, zuciyarsa na bugawa da karfi. Bai taba zaton haka ba. Ya zo dajin ne don ya duba irin ayyukan da boka yake yi wa mutane, sai gashi ya hangi matan gidan Alhaji Uzairu cikin tsananin tawaya, suna rokon boka da yayi musu aiki. “Me kuke so na yi muku?” Bokan ya tambaya da wata murya mai sautin tsoro. Hajiya Rumanah ta dubi sauran matan, sannan ta ce, “Muna son ka kashe Hajiya Zaytunah da 'ya'yanta,Muhammad da Zainab. Wanda sunansu ya koma Nabeeha da Hammad! Ba mu son su dawo gidan Alhaji Uzairu, ba mu son su rayu ko kadan!” Hajiya Ladi ta gyara zamanta, ta matsa kusa da boka. “Muna son ka hana ta komawa gidan. Idan har ta yi niyyar dawowa, sai ka kashe ta da wani mummunan ciwo.” Hajiya Karama ta kara da cewa, “Dole ka tabbatar da cewa Nabeeha da Hammad ba su rayu ba. Muna bukatar su bace daga doron kasa.” Bokan ya yi dariya, wacce ta girgiza zuciyar Haruna. “Aiki ne mai sauki,” ya ce yana hada wasu magunguna cikin bokitinsa. “Zan musu tsibbu da kurciya. Matar ba za ta taba dawowa gidan mijinta ba, kuma idan har ta kuskura ta yi niyyar dawowa, to za ta halaka da kanta. Iyalanta kuwa, za su gamu da masifar da ba za su taba tsira da ita ba!” Ya dauko wani farin foda ya yayyafa cikin ruwan da ke cikin bokiti. Wata irin hayaki mai duhu ya tashi, yana zagaye bukkarsa. Sai ya dauki wata kwarya ya dora a kan wutar. Daga nan ya fara karanta wasu munanan surkulle, yana hura iska cikin hayakin. Haruna ya runtse idanuwansa, zuciyarsa na tafasa. Ya san cewa wannan bayani yana da matukar mahimmanci, dole ne a dauki mataki akai. Bai yi wata-wata ba, ya juya a hankali, yana kokarin barin wurin ba tare da sun gano shi ba. Bayan Haruna ya sanar da Alhaji Amiru abin da ya gani, cikin sauri suka hada mutane suka shirya tafiya dajin. Sun san cewa dole ne a cafke wannan boka domin a gano gaskiyar lamari. Suna isa bakin dajin, jami’an tsaro su goma sun rufe gefuna. Alhaji Amiru na gaba tare da Haruna, a gefensa akwai wasu manyan dattawa masu fada a ji. Kafin su karasa, sai suka hangi boka yana kokarin arcewa da wata kwarya a hannunsa. “Kama shi!” Wani dan sanda ya daka tsawa, nan take wasu jami’ai suka danne shi suka daure hannayensa. “Ku bar ni! Ku bar ni! Me kuke so ne da ni?” Bokan ya kurma ihu, yana kokarin kwace kansa. Alhaji Amiru ya matso kusa, fuskarsa cike da tsananin takaici. “Za mu tafi da kai don ka fadi gaskiya! Za ka fadi wa duniya irin munanan ayyukan da kake aikatawa.” Boka ya yi dariya, amma da ya hangi jami’an tsaro sun hada baki, sai ya sunkuyar da kansa. “To, zan fadi komai!” A cikin babban dakin taro na gidan Gwaggo Zainabu, an daura boka a kujera, an daure hannayensa da igiya. A gabansa, su Alhaji Amiru, Alhaji Uzairu, Gwaggo Zainabu, da wasu manyan mutane sun yi shiru, suna jiran jin bayaninsa. Gwaggo Zainabu ta matso kusa, idanunta cike da zafin rai. “Me yasa ka yarda ka karbi aikinsu?” Ta tambaya cikin daga murya. Boka ya dubi kowa sannan ya saki ajiyar zuciya. “Ba laifina ba ne,” ya fara bayani. “Su Hajiya Rumanah ne suka zo wajena. Sun kawo min kudi masu yawa, sun ce ba sa son Zaytunah da ‘ya’yanta su dawo gidan Alhaji Uzairu. Sun ce idan na hana ta dawowa, za su kara min kudi.” “Me ka yi musu?” Alhaji Uzairu ya tambaya, yana runtse idanu. Bokan ya gyara zamansa, yana kallon su daya bayan daya. “Na yi wa Zaytunah tsibbu na mantuwa. Na sanya ta zama kamar mara tunani, ta manta duk abin da zai sa ta dawo gidan nan. Na yi mata kurciya, na hana ta nutsuwa. Idan har ta yi niyyar dawowa, to zuciyarta za ta kasa jurewa, ta shiga cikin wani yanayi na hauka ko tsananin tsoro.” Ya kara da cewa, “Nabeeha da Hammad kuwa, na sanya musu masifar da za ta bi su har karshen rayuwarsu. Duk inda suka tafi, za su hadu da bala’i.” Kowa ya yi shiru. An rasa abin cewa. Sai dai daga gefe, Gwaggo Zainabu ta fashe da kuka. “Wato haka suka yi wa zaytunah baiwar Allah! Sun so su hallakata da ‘ya’yanta!” Alhaji Amiru ya kalli ‘yan sanda. “Ku tabbatar kun gurfanar da wannan boka da su Hajiya Rumanah a gaban hukuma. Dole a yi musu hukunci!” Kafin a tafi da boka, sai ya daga kansa ya dubi Alhaji Uzairu. “Matar ka tana bukatar addu’a. Idan kana so ta dawo hayyacinta, sai ka nemi wanda ya fi ni karfi ya fitar da abin da na saka a jikinta.” An yi shiru. Kowa ya cika da firgici. Wannan al’amari ya wuce tunanin kowa. Wannan shine karshen mugunta da zalunci. Daga wannan rana, dole a dauki mataki don kare Zaytunah da iyalanta daga makiyan su!.. A fadar Gwaggo Zainabu, shiru ya lullube dakin bayan boka ya fadi munanan ayyukan da ya aikata wa Zaytunah da 'ya'yanta. Kowa ya yi shiru, zuciya cike da fargaba da takaici. Sai dai Gwaggo Zainabu ce ta katse wannan shiru da wata zabura da ta yi, tana nunin boka da yatsa. "Wato har haka kake da mugunta? Ka hada kai da matan nan don hallaka zaytunah da jikokina? To, wallahi ba za mu kyale ka ba!" Jikin boka ya yi sanyi, ya sunkuyar da kai, yana girgiza kansa. "Ba laifina ba ne. Kudinsu ne ya rude ni." Alhaji Uzairu ya nisa, ya dafe goshinsa. A yau ya fahimci cewa muguntar matansa ta kai matakin da ba zai iya jurewa ba. Sun so halakar da iyalinsa ne kawai don girman kai da hassada? Ya dago yana kallon Gwaggo Zainabu, idanunsa cike da nadama. "Gwaggo, ni ma ba zan yafe musu ba. Sun fiye munafunci da zalunci!" "Ba magana kawai za ka yi ba!" Gwaggo Zainabu ta fada da fushi. "Dole ne a dauki mataki! Wallahi yau sai an hukunta su!" Alhaji Amiru ya kalli ‘yan sanda da ke tsaye kusa da boka, yana girgiza kai. “Ku tabbatar an kai wannan boka da su Hajiya Rumanah gaban hukuma. Dole a yi musu shari’a ta gaskiya.” Nan take ‘yan sanda suka ja boka, suka fitar da shi daga dakin. Daga nan ne Gwaggo Zainabu ta dubi Alhaji Uzairu da idanu masu cike da tsantsar takaici. "Yanzu ka tabbatar da maganganun su hajia Hafsatu ko? Bayan shekaru da yawa da Zaytunah ta sha wahala saboda matanka? Idan ba don Allah ya kubutar da ita ba, da yanzu ba ma san halin da take ciki ba." Alhaji Uzairu ya girgiza kai, yana jin zafi a ransa. "Gaskiya kike faɗa, Gwaggo. Ban taba tunanin cewa mugunta ta kai haka ba. Amma yanzu, dole a nemo hanyar da za a wanke wannan asiri da aka yi mata." Alhaji Amiru ya gyara zamansa, yana kallon Gwaggo Zainabu. "Ya kamata mu tuntubu masana, wato malaman fiqhu su duba lamarin. Idan ba a cire wannan tsibbu ba, to, Zaytunah ba za ta taba samun kwanciyar hankali ba." ... A bangaren su Hajiya Rumanah, kukan da suka tsunduma yana karaji a cikin dakinsu. Sun ji labarin cewa boka ya shiga hannu, kuma ya bayyana duk abubuwan da suka faru. Hajiya Ladi ta zube a kasa, tana rike kanta. "Mun shiga uku! Wannan boka wallahi zai jawo mana matsala." Hajiya Karama ta rungume jikinta, tana karkarwa. "Kun san cewa idan aka dauki mataki, to ba za mu fita ba! A shirye kuke da ku shiga gidan yari?" Hajiya Rumanah ta miƙe tsaye cikin hargowa. "Wallahi ba zan bari a kama ni haka nan ba! Ya kamata mu nemi mafita kafin su zo su kama mu." Hajiya Ladi ta yi shiru na dan lokaci, sai kuma ta girgiza kai. "Babu wata mafita, Rumanah. Mun shiga tarkon da ba za mu iya fita ba. Idan kuwa aka kamamu, to fa ba za mu taba samun 'yanci ba." A daidai wannan lokacin, sai ga wasu jami’an tsaro sun shigo gidan. "Ku fito!" wani daga cikinsu ya daka musu tsawa. "Mun zo daukarku bisa umarnin kotu!" Kamar an tsikare su, nan take suka rude. Hajiya Rumanah ta juya kamar za ta gudu, amma wani dan sanda ya rike hannunta. "Ba gudu ba tsira! Kun gama aikata mugunta, yanzu lokaci ne na sakamako!" Kafin su ankara, har an daure su da sarka, aka tafi da su. .. A bangaren su Alhaji Amiru, an riga an fara kokarin nemo malamai domin cire asirin da aka yi wa Zaytunah. An kai ta wani wuri na musamman, inda wani malami mai ilimi ya fara addu’o’i domin wanke ta daga wannan kurciya da aka mata. Bayan an bata ruwan tofi na ayoyi da aka yu na ganyen magarta.. Sai dai abin mamaki, da zarar malamin ya fara karanta ayoyi masu karfi, sai Zaytunah ta fara karkarwa. Hawaye suka fara kwarara daga idanuwanta, tana jin wani irin nauyi yana sauka daga zuciyarta. Wani daga cikin malamai ya kalli Alhaji Uzairu. "Gaskiya ne, an yi wa wannan mata asiri mai karfi. Amma in sha Allah, za mu cire shi." A lokacin da aka ci gaba da addu’a, Zaytunah ta fara jin sauki. A hankali, tana bude idanuwanta, tana kallon mutanen da ke kewaye da ita. "Na... na ji kamar wani abu ya sauka daga kaina," ta furta cikin raunanniyar murya. Gwaggo Hafsat ta matso kusa, hawaye suna cika idanuwanta. "Alhamdulillah! Allah ya wanke ki daga muguntar su!" A gefe guda, Nabeeha da Hammad suna kuka, suna kallon mahaifiyarsu da farin ciki. Sun san cewa daga wannan rana, rayuwarsu ba za ta sake kasancewa kamar da ba. Sun sha wahala mai yawa, amma yanzu sun samu haske. Sai dai tambaya daya ta rage: shin Alhaji Uzairu zai iya gyara abin da ya faru? Ko kuwa kaddara za ta ci gaba da gwada su? ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE: 38_ Bayan doguwar addu’a da azancin malamai, a hankali Zaytunah ta soma dawowa cikin hayyacinta. Kamar wadda aka cire wa kaya masu nauyi, ta ji wani irin saukin da bata taba jin irinsa ba. Tana daga kwance, idanunta sun kada saboda dogon shan wahala, amma yanzu tana iya kallon mutanen da ke gefenta da cikakken tunani. Gwaggo Hafsat ta kama hannunta cikin kulawa. “Zaytunah, ya kike ji yanzu?” Zaytunah ta motsa bakinta cikin wahala. “Ina jin... sauki... amma zuciyata cike take da abubuwa da ba zan iya tuna komai ba sosai.” Malamin da ya jagoranci addu’o’in ya yi murmushi. “Wannan al’amarin na tsibbu ba abu ne mai sauki ba. Amma da ikon Allah, kin samu ‘yanci daga wannan mugunta. Za ki fara tuna abubuwan da suka faru a hankali.” A gefe, Nabeeha da Hammad sun rungume juna suna kuka. Ba wai kuka na bakin ciki ba, sai na farin ciki da fargabar irin halin da mahaifiyarsu ta tsinci kanta a ciki. Hammad ya matso kusa da ita, yana kallon fuskarta cikin tausayi. “Ammi, kin san ni ne?” Zaytunah ta dubi yaron nata, hawaye suka cika idonta. Ta daga hannunta tana shafa sumar kansa, kamar wadda ke jin labarinsa ne a karon farko. “Hammad…” Ta kalli Nabeeha wadda ke durkushe a kusa da ita, ita ma idonta cike da kwalla. “Nabeeha…” Nan take kuka ya kara karfi a dakin. Gwaggo Hafsat ta shafa kanta, tana murmushi mai cike da godiya. “Alhamdulillah! Wannan ne abu mafi muhimmanci.” Alhaji Amiru ya kalli Alhaji Uzairu, wanda tun dazu ya kasa cewa uffan. Idanunsa sun cika da nadama, sai dai bai san ta ina zai fara fadin abin da ke zuciyarsa ba. Yana jin kamar ya zube ya roki gafarar Zaytunah, amma yana shakkar cewa za ta iya yafe masa. Dakin ya dauki shiru na wasu sakanni, kafin a hankali Alhaji Uzairu ya karasa kusa da gadon da Zaytunah ke kwance. Ya durkusa a gabanta, yana fuskantar ta kai tsaye. “Zaytunah… nasan babu wani abu da zan iya cewa da zai goge munanan abubuwan da suka faru. Amma ki sani, ban taba sanin cewa matana sun yi miki haka ba.” Ya runtse idanuwansa, yana jin nauyin abin da zai fada. “Na yi kuskure… Babban kuskure… Na bar ki cikin wahala, na kasa kare ki. Kuma har yau ina jin wannan nauyin a zuciyata.” Zaytunah ta yi shiru, tana kallonsa. Kusan shekaru goma sha biyu kenan da suka rabu, kuma ko da yake bata tuna komai duka ba tukuna, ta san cewa rayuwarta ba ta kasance mai sauki ba. Ta san cewa ta sha wahala, kuma hakan ya faru ne saboda rashin adalcin da aka yi mata. Sai dai zuciyarta bata da tsanani kamar yadda take tsammani. Ta dade tana rayuwa cikin duhu da rashin masaniya, amma yanzu komai yana dawo mata a hankali. Ta rufe idonta na wani dan lokaci, sannan ta bude su tana duban shi. “yaya Uzairu… ka san me ya fi komai ciwo?” Ta tambaya da murya mai sanyi. “Ba wai sharrin su Hajiya Rumanah ba ne kadai, sai yadda ka bar ni ba tare da kayi kokarin fahimtar abin da ya faru ba. Ka yarda da su fiye da ni, har ka bari su mayar da ni ba komai a idonka.” Alhaji Uzairu ya runtse idanu, yana jin nauyin kalmomin ta kamar duwatsu a kansa. Zaytunah ta sauke ajiyar zuciya, ta dube shi ido cikin ido. “Na yafe maka.” Kowa a dakin ya yi shiru da mamaki. Alhaji Amiru ya dafe KIRJI, yana kallon Zaytunah cikin mamaki. Gwaggo Hafsat ta saki murmushi mai sanyi, sai dai har yanzu tana fuskantar Uzairu da tuhuma a idonta. “Amma,” Zaytunah ta kara da cewa, “yafe wa ba yana nufin komai ya dawo daidai ba. Idan kana so ka gyara abin da ya faru, sai ka tabbatar da cewa ba za a sake faruwa ba. Ba domin kai ba, ba domin ni ba, amma domin ‘ya’yanmu.” Alhaji Uzairu ya dago kai, yana kallonta da hawaye a idonsa. “Zan yi duk abin da zan iya don in gyara kura-kurai na, Zaytunah. Zan tabbatar da cewa babu wanda zai sake cutar da ke ko da su Nabeeha da Hammad.” Nabeeha ta goge hawayenta, tana kallon mahaifinta cikin tunani. Ashe suma sunada mahaifi tamkar sauran yara.... A can bangare daban, a gaban kotu, shari’ar su Hajiya Rumanah da sauran matan Alhaji Uzairu ta fara. An gabatar da hujjoji, kuma shaida irin na Haruna da su Alhaji Amiru ya tabbatar da cewa sun aikata laifi. Boka ma ya fadi irin ayyukan da suka sa shi, kuma alkali ya tabbatar da cewa an aikata babban laifi. Bayan doguwar shari’a, an yanke musu hukuncin daurin shekaru a gidan yari. Hajiya Rumanah da sauran matan sun firgita, suna kuka da rokon gafara, amma hakan bai canza komai ba. Kowa ya san cewa sun cancanci wannan hukunci. A lokacin da aka tafi da su zuwa kurkuku, Gwaggo Zainabu ta sauke ajiyar zuciya. "Da sannu gaskiya zata yi halinta." Bayan ‘yan makonni, bayan an tabbatar da cewa Zaytunah ta samu lafiya gaba daya, Alhaji Uzairu ya roki Gwaggo Hafsat da su Zaytunah da su dawo gida. Sai dai Zaytunah bata da niyyar yin haka nan take. "Ban san ko zan iya komawa ba," ta fada yayin da take zaune tare da Gwaggo Hafsat da Alhaji Amiru. "Akwai abubuwa da yawa da suka faru. Ba zan iya mayar da rayuwata kamar da ba." Gwaggo Hafsat ta kama hannunta. "Komai yana bukatar lokaci, Zaytunah. Ba dole bane ki yanke shawara nan take, amma ina so ki san cewa rayuwar ki tana da muhimmanci fiye da komai." A gefe guda, Nabeeha da Hammad suna sauraron su, zuciyarsu cike da tambayoyi. Shin su ma za su koma gidan Alhaji Uzairu? Shin mahaifinsu zai iya gyara kuskuren da ya yi? Alhaji Uzairu ya dubi su. "Ko da kuwa ba za ku dawo yanzu ba, zan jira. Zan ci gaba da kokarin gyara abin da na lalata." Kowa ya yi shiru. Tambayoyin sun yi yawa, amsoshi kuma sun yi kadan. Amma abu daya da kowa ya sani shine, daga wannan rana, rayuwa ba za ta kara kasancewa kamar da ba. Zaytunah ta sunkuyar da kanta, tana nazarin kalmomin da suka fita daga bakin Alhaji Uzairu. Shin da gaske zai iya gyara abin da ya faru? Shin zai iya zama uban da ‘ya’yanta suka rasa tsawon shekaru? Ko kuwa hakan duk alkawari ne kawai da ba zai cika ba? Nabeeha ta kalli mahaifiyarta, tana son jin matsayinta. “Ammi, kina so mu koma?” Zaytunah ta kalli ‘yarta da idanu masu cike da tausayi. “Ba zan tilasta muku ba, Nabeeha. Wannan shawara ce da ya kamata mu dauka a hankali.” A gefe guda, Hammad ya dan buga kafarsa kasa. “Ammi, ni dai ina so in san iyalina. Amma ba na son mu koma gidan da za mu sake fuskantar matsala.” Gwaggo Hafsat ta gyara zama, tana kallon su duka. “Hammad yana da gaskiya. Komawa gidan ba matsala ba ce idan za a samu sauyi na gaske. Amma sai an tabbatar da cewa babu wata barazana.” Alhaji Uzairu ya dafe KIRJI. “Wallahi zan tabbatar da cewa komai ya canza. Ba zan sake bari wani abu ya cutar da ku ba.” Sai dai duk da irin wadannan maganganu, Zaytunah ba ta da tabbacin hakan. Ta san cewa wasu abubuwa ba su da saukin mantuwa. Ta dade cikin duhu da wahala, kuma ko da ta gafarta, hakan ba yana nufin cewa zata manta da abinda ya faru ba. ... A can bangaren su Fawaaz, yana zaune a falon gidan Major General Dawud, yana nazarin abubuwan da suka faru. Tun da aka kwantar da Zaytunah, ya lura da yadda damuwa ta shige Nabeeha. Ya san cewa yana son ya taimaka mata, amma ba ya son nuna hakan a fili. Ya dauki wayarsa, yana nazarin ko zai kira ta. Amma sai ya girgiza kai, ya ajiye wayar. “Me yasa zan kirata? Ina da wata magana da zan fada?” Ya tambayi kansa. Duk da haka, zuciyarsa ba ta bar shi ya zauna lafiya ba. Ya mike tsaye, ya yanke shawarar zuwa wajen Major General Dawud domin jin halin da ake ciki. Yana zuwa, ya samu Major General yana tattaunawa da Gwaggo Hafsat. Sun kammala magana akan shari’ar su Hajiya Rumanah, kuma yanzu suna tattauna batun komawar su Zaytunah gidan Alhaji Uzairu. Fawaaz ya gyara zamansa, yana sauraron tattaunawar. A lokaci guda, yana ta tunanin yadda abin zai shafi Nabeeha. Bayan shari’a ta kare, Nabeeha ta zauna a cikin dakinta tana tunani. Ta kasa fahimtar yadda zata ji game da mahaifinta. A da, ta dade tana mafarkin kasancewa da mahaifinta. Amma yanzu da daman ta samu, me yasa zuciyarta take jin shakku? Ta dauki wayarta, tana nazarin kira ko tura sakon ga Fawaaz. Daga karshe, ta tura masa sakon: “Ina nan.” Bayan dakika talatin, sai ga amsar Fawaaz, “Dole ne ki kasance da karfi. Na san cewa abu ne mai wahala, amma dole ne ki dauki shawarar da zata fi miki amfani.” Sai dai kafin ta amsa, sai ta ji ana kwankwasa kofarta. Ta mike tsaye, ta bude, sai taga Hammad tsaye. “Ina tunanin cewa zaki bukaci wani ya saurare ki,” ya fada yana kallonta da kulawa. Nabeeha ta dan yi murmushi. Ta san cewa ba ita kadai ke cikin wannan yanayi ba. Bayan dare ya tsala, Zaytunah ta kira ‘ya’yanta. Ta zaunar da su a daki, sannan ta ce, “Na dade ina tunani, kuma na yanke shawara. Ba zan koma gidan Alhaji Uzairu ba.” Nabeeha ta dauke numfashi. “Ammi, me yasa?” Zaytunah ta kalli ‘ya’yanta, hawaye na taruwa a idonta. “Ba wai domin ban yafe masa ba ne. Amma na san cewa idan na koma, ba zan samu kwanciyar hankali ba. Na fi son mu ci gaba da rayuwa yadda muke.” Hammad ya yi shiru, sai kuma ya ce: “Ammi, amma shi mahaifin mu ne.” “Eh, haka ne,” Zaytunah ta fada da nutsuwa. “Shi mahaifinku ne, kuma ba zan hana ku zuwa wajensa ba. Idan kuna so ku san shi, zan baku damar hakan. Amma ni, na gama rayuwata da shi.” Gwaggo Hafsat ta gyada kai. “Wannan shawara ce mai kyau. Ba dole ne ki koma ba, idan ba ki ji hakan ba.” A gefe guda, Alhaji Uzairu ya ji wannan magana, kuma zuciyarsa ta cika da nadama. Ya san cewa yana da laifi, amma hakan bai hana shi jin zafin wannan hukunci ba. Amma ya san cewa dole ne ya jure. Domin wannan shine sakamakon abin da ya aikata. A gefe guda, Fawaaz yana zaune a dakin shi, yana karanta sakon Nabeeha. Ya san cewa yana son ya kasance tare da ita, amma har yanzu bai da kwarin gwiwar bayyana abin da ke zuciyarsa. Nabeeha ta dauki lokaci tana kallon sakonsa, kafin daga karshe ta tura masa, “Duk da komai, rayuwa zata cigaba.” Fawaaz ya kalli sakon, yana murmushi. Ya san cewa akwai abu mai zurfi da ke tsakanin su, amma ba yanzu ba. Komai yana bukatar lokaci. Sai dai ko da kuwa suna boye zuciyarsu, kaddara na shirya wani abu daban a gare su. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORe *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:39_ Tun daga wannan rana, rayuwa ta ci gaba da tafiya a sabon salo. Kowa ya cigaba da shirya matakansa, amma akwai tambayoyin da har yanzu ba a samu amsarsu ba. Bayan kwanaki da yanke hukuncinta na kin komawa gidan Alhaji Uzairu, Zaytunah ta soma sabuwar rayuwarta cikin kwanciyar hankali. Duk da cewa wasu daga cikin dangin Alhaji Uzairu, musamman Gwaggo Zainabu, sun yi kokarin lallashinta ta koma, amma ta tsaya a kan matsayinta. A rana guda, tana zaune a daya daga parlorn gidan Gwaggo Hafsat tana shan shayi, sai Alhaji Amiru ya shigo da sallama. "Zaytunah, ina fata kin fara samun nutsuwa." Zaytunah ta gyada kai. "Eh, Yaya Amiru. Na gode da kulawarka." Alhaji Amiru ya gyara zamansa. "Duk da cewa ba ki koma gidan Alhaji Uzairu ba, hakan ba yana nufin rayuwar ki ta tsaya. Ina so ki sani cewa akwai mutanen da ke son ganin kin cigaba da rayuwa mai kyau." Zaytunah ta yi shiru tana nazari. Shin da gaske zata iya barin baya ya wuce gaba daya? Shin zata iya cigaba da sabuwar rayuwa ba tare da waiwaya ba? Haka dai alhaji Amiru yayita hilatar hajiya Zaytunah kan ta koma gidan kanin sa Kuma miji agareta wato gidan alhaji uzairu uban yayan ta.. A daya bangaren kuma, Alhaji Uzairu ya shiga wani hali. Tun daga yanke hukuncin kotu, ya fara jin nauyin abin da suka aikata... A cikin dare, yana zaune a falonsa shi kadai, yana tunanin yadda abubuwa suka tabarbare. Ya rasa Zaytunah, ya rasa ‘ya’yansa, kuma yanzu yana fuskantar nadama mara iyaka. Har zuwa wani dare, ya tashi tsakar dare ya dauki motarsa ya nufi gidan Gwaggo Hafsat ba tare da sanar da kowa ba. Lokacin da ya iso kofar gidan, yana shirin kwankwasa kofa, sai ya tsaya cak. Me zai ce? Ya san cewa ba zai iya tilasta Zaytunah ba, amma yana bukatar ganin ‘ya’yansa. Bai yi sallama ba, ya juya ya koma cikin motarsa, sannan ya bar wurin. ........ A bangaren Fawaaz kuwa, tunanin Nabeeha ya fara yawaita masa fiye da yadda ya saba. Duk da miskilancinsa da kamun kai, yana jin wani irin son kulawa da ita. Sai dai yana kokarin boye hakan. Wata rana, yana zaune a wajen motsa jiki, sai wayarsa ta dauki kara. Ya duba, ya ga sunan Nabeeha. Ya dauka, yana kara wayar a kunnensa. "Hello." Nabeeha ta sauke ajiyar zuciya. "Ya Fawaaz, ina bukatar magana da kai." Ya kame kansa kamar ba ya jin dadi. "Lafiya? Me ya faru?" "Ba wani abu ne mai girma ba... kawai ina son mu hadu mu yi magana." Fawaaz ya dan yi shiru na wasu mintuna, sannan ya ce, "Okay. Ki fada min inda kike so mu hadu." Da yamma, suka hadu a wani shagon shayi mai natsuwa. Nabeeha ta kalle shi cikin ido, sai ta ce, "Yaa Fawaaz, ka taba jin tsoron yanke shawara?" Ya hade gira. "Wace irin shawara?" "Shawarar da zata canza rayuwarka gaba daya." Fawaaz ya gyara zamansa. "Eh, na taba. Kuma yana da wahala." Nabeeha ta kalli kofin shayin da ke gabanta. "Ina jin tsoron cewa idan na yanke shawarar komawa rayuwar mahaifina, hakan na iya rushe rayuwata gaba daya. Kuma idan na ki, ina iya rasa damar da ba zan samu ba." Fawaaz ya dan jinjina kai, sannan ya ce, "Idan kina shakkar shawarar ki, ki saurari zuciyar ki. Kar ki bari tsoro ya hana ki yin abin da ya fi miki amfani." Nabeeha ta dube shi, tana jin wani irin sanyi a zuciyarta. Ta san cewa akwai wani abu a tare da Fawaaz da take jin nutsuwa a kansa, duk da cewa bai taba bayyana mata komai ba. A cikin ‘yan kwanaki, Gwaggo Hafsat ta yanke shawarar cewa Zaytunah ba za ta zauna haka ba. Duk da cewa ba za ta tilasta mata komai ba, amma tana so ta taimaka mata ta sake bude wani sabon shafi. Ta kira Alhaji Amiru don yin wata magana mai muhimmanci. "Alhaji Amiru, ina ganin cewa lokaci yayi da za a sami wanda zai tsaya da Zaytunah da ‘ya’yanta. Ba dole ne ta zauna a haka ba har abada." Alhaji Amiru ya fahimci inda zancen Gwaggo Hafsat ya dosa. "Kin san cewa hakan ba abu ne mai sauki ba, amma idan har hakan zai taimaka mata, ba matsala." Gwaggo Hafsat ta gyada kai. "Za mu bar lokaci ya yi aikinsa. Nabeeha da Hammad sun fara yawaita zuwa wajen mahaifinsu, duk da cewa ba su kammala sabawa da shi ba. A hankali, suna kokarin fahimtar inda suka dosa. Fawaaz yana ci gaba da kula da Nabeeha ta hanyar ba ta shawara, ko da ba ya fadin komai a fili. Amma yana jin cewa wata rana, dole ne zai bayyana abin da ke zuciyarsa ga sanin kowa .. Zaytunah kuwa, tana kokarin yanke hukunci kan rayuwarta. Shin zata iya budewa wani sabon zuciyarta? Ko kuwa za ta cigaba da rayuwarta haka, ba tare da waiwaya ba? A karshe dai, kowanne daga cikinsu yana kokarin gano matsayinsa a rayuwa. Kuma kaddara na shirya masu abin da bai zo musu a rai ba. Bayan makonni biyu da hukuncin da aka yankewa su Hajiya Rumanah, rayuwa ta fara dawowa daidai a gidan Gwaggo Hafsat. Zaytunah ta cigaba da kula da ‘ya’yanta, duk da cewa zuciyarta tana cike da tunani kala-kala. A gefe guda, Nabeeha da Hammad sun cigaba da zuwa gidan mahaifinsu a hankali. Koda yake suna jin dadin ganin Alhaji Uzairu yana kokarin gyara kura-kurensa, amma har yanzu akwai shakku a zuciyarsu. Fawaaz yana ci gaba da kula da Nabeeha ba tare da nuna hakan ba. A kullum yana kokarin hana zuciyarsa karfin gwiwar bayyana abinda ke cikinta. Wata rana, yana tsaye a bakin kofar gidan Major General Dawud yana jiran motarsa, sai ya hango Nabeeha tana fitowa daga gida. Ya kalli agogo, ya sake dubanta. “Kin fito da wuri haka?” Nabeeha ta gyada kai, tana murmushi. “Zan je gidan Abba. Hammad yana can.” Fawaaz ya dauke kansa kamar bai damu ba. “Allah ya kiyaye hanya.” Nabeeha ta tsaya na minti daya tana kallonsa, kamar tana son tace wani abu. Amma daga karshe, sai ta girgiza kai ta juya. Da zarar ta bar wurin, Fawaaz ya sauke ajiyar zuciya. Yana jin wani iri, amma bai san dalili ba. A ranar da yamma, Gwaggo Hafsat ta zaunar da Zaytunah a cikin dakinta. “Zaytunah, ba ki da niyyar komawa gidan mijin ki har yanzu?” Zaytunah ta dauke numfashi, zuciyarta ta dan buga. “Gwaggo, ba ni da wannan tunanin yanzu.” “Kin tabbata kuwa? Kin san cewa rayuwa ba za ta tsaya ba. Kuma ba zan so ki kasance a haka har abada ba.” Zaytunah ta sunkuyar da kanta. “Gwaggo, a gaskiya ban san me zai faru ba. Ban san ko zan iya sake budewa wani zuciyata ba.” Gwaggo Hafsat ta girgiza kai. “Na fahimta. Amma ina so ki sani cewa akwai mutane da ke kaunarki, kuma suna da niyyar kulawa da ke.” Zaytunah ta kalle ta, tana kokarin fahimtar inda zancen ke nufa... A can bangaren Fawaaz, yana zaune a ofishin Alhaji Amiru, inda suka soma tattaunawa kan wasu batutuwa. Bayan sun gama, sai Alhaji Amiru ya dan gyara zama. “Fawaaz, ina son in tambaye ka wata magana.” Fawaaz ya kalle shi, yana sauraro. Alhaji Amiru ya dauki lokaci kafin ya cigaba. “Me yake tsakaninka da Nabeeha?” Zuciyar Fawaaz ta buga, amma bai nuna hakan ba. “Babu komai.” Alhaji Amiru ya gyada kai. “Na fahimta. Amma ka tabbata babu abin da kake boyewa?” Fawaaz ya kame kansa. “Nabeeha kanwata ce. Ba wani abu fiye da haka.” Alhaji Amiru ya kalle shi da kulawa. “Idan har kana da wani abu a zuciyarka, kada ka bari ya kure maka lokaci.” Fawaaz ya dauke kansa, yana nazarin kalmomin Alhaji Amiru. Shin da gaske zai iya yarda da zuciyarsa? ... Wata rana, Nabeeha tana zaune a lambun gidan, tana tunani. Sai ga Fawaaz ya zo ya zauna kusa da ita. Sun yi shiru na tsawon lokaci, kafin daga karshe Fawaaz ya ce, “Kin taba jin cewa wani abu yana tsaye a gabanki, amma ba ki san yadda za ki fuskance shi ba?” Nabeeha ta kalle shi, tana murmushi. “Eh. Na taba.” Fawaaz ya gyada kai. “Kuma kin san yadda za ki fuskance shi?” Nabeeha ta girgiza kai. “Ba koyaushe ba.” Fawaaz ya yi shiru, yana nazari. Daga karshe, ya sauke numfashi. “Nabeeha, akwai wani abu da nake so in fada miki.” Nabeeha ta kalle shi da mamaki. “Mene ne?” Sai dai kafin ya iya magana, sai suka ji ana kwankwasa kofar gidan da karfi. Me ke faruwa? Wanene ke neman su da wannan gaggawa? ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:40_ A gaggauce, Nabeeha da Fawaaz suka tashi daga inda suke zaune a lambun gidan. Karan bugun kofa ya kara karfi, alamun mai bugun yana cikin gaggawa ko fushi. Nabeeha ta dubi Fawaaz da damuwa. “Waye zai iya bugun kofa haka?” Fawaaz bai amsa ba. Sai ya nufo kofar, yana kokarin ganin wanda ke waje. Da ya bude, sai ya hango wani matashi tsaye, fuskarsa cike da gumi, yana sauke numfashi. Matashin ya dubi Fawaaz da Nabeeha cikin gaggawa. “Dan Allah, ina son ganin Major General Dawud.” Fawaaz ya hade gira. “Me ke faruwa?” Matashin ya dan rankwafa. “Sun kama wani mutum da ke da alaka da abubuwan da suka faru a baya. Shi ne mutumin da ya taimaka wajen hada bokan da su Hajiya Rumanah!” Zuciyar Nabeeha ta buga. Ta kalli Fawaaz, shi ma yana kallonta da wani irin yanayi. Fawaaz ya matsa gaba. “Ina aka kama shi?” Matashin ya girgiza kai. “An kama shi ne a kusa da garin Dunaka Yana kokarin tserewa zuwa wani yanki na yankin Arewa. Amma jami’an tsaro sun gano inda yake suka cafke shi.” Nabeeha ta sauke numfashi. Wannan sabon labari yana nufin cewa har yanzu akwai wasu bayanai da ba a sani ba game da shirin da aka yi na hallaka su da mahaifiyarta. Fawaaz ya shafa kansa, sannan ya dubi matashin. “Major General Dawud yana nan ba?” “Ina tunanin yana ofishinsa.” Fawaaz ya juyo zuwa ga Nabeeha. “Ina ganin ya kamata mu sanar da shi nan da nan.” Nabeeha ta gyada kai, zuciyarta cike da tsanani. Wannan sabon labari yana nufin cewa akwai wani sabon abu da zai fito fili wataƙila wanda zai canza komai. A cikin gida, Zaytunah tana zaune tare da Gwaggo Hafsat a daki, suna tattaunawa. Gwaggo Hafsat ta gyara zamanta, sannan ta dubi Zaytunah da kulawa. “Zaytunah, akwai wata magana da nake son yi da ke.” Zaytunah ta kalle ta. “Mene ne Gwaggo?” Gwaggo Hafsat ta sauke numfashi. “Akwai wani mutum da ya zo mini da zancen ki.” Zaytunah ta bude ido da mamaki. “Mutum?” Gwaggo Hafsat ta gyada kai. “Eh. Mutumin da ya san halin da kika shiga, kuma yana son ya taimaka miki.” Zaytunah ta dan numfasa. “Gwaggo, idan maganar aure ce, ni fa har yanzu ba ni shirya ba.” Gwaggo Hafsat ta murmusa. “Na fahimta. Amma ki sani, babu wanda yake shirya a lokaci daya. Sai dai a hankali ake fahimtar cewa lokaci ya yi.” Zaytunah ta sunkuyar da kai, zuciyarta cike da tunani. Shin ta shirya budewa wani sabon zuciyarta? A bangaren Major General Dawud kuwa, yana cikin ofishinsa lokacin da sakon kama wannan mutumin ya iso gare shi. Ya kira Fawaaz da Nabeeha, sannan suka zauna a gaban sa. “Kun san wanda aka kama?” in ji Major General Dawud. Fawaaz da Nabeeha suka girgiza kai. Major General Dawud ya cigaba. “Sunan sa Malam Balarabe. Shine mutumin da ya yi wa su Hajiya Rumanah jagora zuwa wurin boka. Kuma yana da wasu bayanai da zai iya fada mana.” Zuciyar Nabeeha ta buga. “Me yasa yake kokarin guduwa?” Major General Dawud ya dan numfasa. “Saboda yana jin tsoron cewa bayanin da zai fadi zai iya jawo masa matsala.” Fawaaz ya hade gira. “Me kuke son mu yi yanzu?” Major General Dawud ya mike. “Za a yi masa tambayoyi a ofishin ‘yan sanda. Idan har yana da wasu sirrika da zai bayyana, to lokaci ya yi da za mu ji komai.” Fawaaz ya dan kalli Nabeeha, sai ya ga yadda take ta tunani. Duk da cewa ta yi kokarin boye damuwarta, amma yana iya fahimtar cewa zuciyarta cike take da rikicewar tunani. A zuciyarsa, Fawaaz ya dauki alkawari, duk abinda zai faru, zai kasance tare da ita. A daren ranar, Major General Dawud, Fawaaz, da Nabeeha sun isa ofishin ‘yan sanda don sauraron bayanan da Malam Balarabe zai bayar. A cikin dakin tambayoyi, Malam Balarabe ya zauna cikin rashin kwanciyar hankali. Idonsa a kasa, yana ta kokarin guje wa kallon kowa. Major General Dawud ya gyara zamansa, yana dubansa da tsananin kulawa. “Mun san cewa kai ne jagoran da ya hada su Hajiya Rumanah da boka. Muna so ka fada mana komai.” Malam Balarabe ya hadiye yawu. Ya san cewa babu inda zai iya tserewa daga wannan al’amari. Sai ya dauke numfashi, sannan ya soma magana. “Tabbas, ni ne na kai su Hajiya Rumanah da su Hajiya Ladi da Hajiya Karama wajen boka. Sun zo wurina ne da bukatar su kawar da Hajiya Zaytunah da ‘ya’yanta gaba daya. Sun ce idan ba ta mutu ba, to su tabbatar ba za ta taba komawa gidan Alhaji Uzairu ba.” Zuciyar Nabeeha ta buga da karfi. Fawaaz ya runtse idanuwansa, yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa. Malam Balarabe ya cigaba, “Bokan ya musu aiki, amma bai tsaya nan ba. Ya kuma saka wata kurciya a jikin Hajiya Zaytunah, wanda zai hana ta tunanin komawa gidan mijinta ko yunkurin neman hakkin ‘ya’yanta. Wannan shine dalilin da yasa ta zauna a boye tsawon shekaru, tana gudun abinda ba ta fahimta ba.” Duk wanda ke cikin dakin sai da zuciyarsu ta buga. Nabeeha ta rasa abin cewa. Tsawon rayuwarta, ba ta taba tunanin cewa akwai irin wannan mugunta a duniya ba. Major General Dawud ya gyara zamansa. “To me yasa kake kokarin guduwa?” Malam Balarabe ya sunkuyar da kai. “Boka ya fadi cewa idan aka tona asirin wannan aiki, akwai bala’i da zai bi wadanda suka aikata shi. Na san cewa da zarar an gano gaskiya, mutanen da suka ba da umarni za su yi kokarin kawar da ni. Shine yasa nake kokarin tserewa.” Major General Dawud ya kalli daya daga cikin jami’an tsaron dake tsaye a gefen dakin. “Ku tabbatar da cewa an cigaba da tsare shi. Wannan mutumin na da matukar mahimmanci a bincikenmu.” Bayan sun gama tambayoyin, Fawaaz ya fita daga dakin, zuciyarsa na tafarfasa. Nabeeha ta bi bayansa da sauri. Ya tsaya a gefen wata bishiya, yana maida numfashi da karfi. “Nabeeha,” ya fada cikin murya mai karfi. “Ina so ki san cewa ba zan taba barin wani ya cutar da ke ba. Ko da kuwa har abada ne.” Nabeeha ta kalle shi da ido cike da al’ajabi. Wannan shine karo na farko da Fawaaz ya fadi irin wannan kalma gare ta. Zuciyarta ta dan buga, amma sai ta sunkuyar da kai tana murmushi. “Nagode, Yaa Fawaaz.” Daga wannan rana, komai ya fara komawa dai-dai. Gwaggo Hafsat ta tabbatar da cewa Zaytunah ta samu cikakken lafiya. Hajiya Zaytunah ta sake farfadowa da karfinta, tana tunanin yadda zata sake gina rayuwarta da ‘ya’yanta. Alhaji Uzairu ya kara kokarin gyara kura-kurensa, yana kokarin dawo da martabar sunansa a idanun Nabeeha da Hammad. A bangaren Fawaaz kuwa, zuciyarsa ta fara karbar gaskiya, son da yake yiwa Nabeeha ba abu ne da zai iya gujewa ba. Wata rana, lokacin da rana ke faduwa, Fawaaz da Nabeeha suna zaune a harabar gidan Major General Dawud. Fawaaz ya kalleta da murmushi. “Kin taba jin cewa akwai soyayyar da ake ji a hankali, amma tana zurfi fiye da duk wata?” Nabeeha ta kalle shi da dariya kadan. “Eh, na taba.” Fawaaz ya yi murmushi, sannan ya dauke kansa daga kallonta. Zuciyarsa na bugawa, yana jin cewa wata rana, zai samu damar fada mata komai. A yau, ba lallai ba ne. Amma yana da tabbacin cewa lokaci yana tafe. Daren ya yi tsit a cikin gidan Major General Dawud. Ba kowa a lambun gidan sai Hajiya Hauwa, wadda take cikin rashin nutsuwa tana danna waya a gefe guda. Kamar yadda ta saba, tana kokarin tura sakonni ga wadanda suke tare da ita a boye. Abin da ba ta sani ba shi ne, tun kwanaki Major General Dawud ya soma zargin cewa akwai wanda yake ba da bayanai a cikin gidan nasa. Ya lura da yadda wasu abubuwa suke tafiya ba dai-dai ba. Lokacin da aka yi garkuwa da Hajiya Zaytunah da ‘ya’yanta, sai abubuwa suka soma bayyana masa a hankali. Yana tsaye a gefe yana kallonta, ba tare da ta sani ba. Idanunsa sun yi kalar takaici. A hankali ya dan matsa kusa, yana kallon yadda take rubuta wani sakon: "Idan har kuna bukatar cikakken bayani, zan tura muku. Amma ina bukatar tabbatarwar ku cewa babu wanda zai iya kamani." Gaban Major General Dawud ya fadi. Bai jira komai ba, ya karbe wayar daga hannunta da karfi. Hajiya Hauwa ta zabura, idonta cike da tsoro. “Me kake yi haka?” Major General Dawud bai kula da ita ba, ya shiga duba sakonninta. Akwai gamsassun shaidu masu nuna cewa ita ce ta sanar da mutanen da suka yi garkuwa da su Hajiya Zaytunah da iyalanta. Ita ce ta bada bayanin cewa suna cikin gidansa, wanda ya ba da damar a shirya yadda za a yi musu kisan gilla. Gaba daya jikinsa ya dauki rawa. Ya dago kai ya kalleta, idanunsa cike da takaici. “Hauwa… ke ce kika ba su bayanai?” Hajiya Hauwa ta dauke kai, tana kokarin karyata shi. “Ni kuma?” Dawud ya daga wayar yana nuna mata sakonnin da ta tura. “To me wadannan?” Hajiya Hauwa ta kasa magana. Zuciyarta ta buga da karfi. Ta san cewa wannan karon ba ta da mafaka. Major General Dawud bai bata lokaci ba. Nan take ya kama hannunta ya nufi sashen Gwaggo Hafsat, inda Hajiya Zaytunah ke zaune tare da ita. Hajiya Zaytunah na zaune da dan nutsuwa, har yanzu tana kokarin farfadowa daga matsalolin da suka addabe ta. Gwaggo Hafsat kuwa tana zaune a kusa da ita, tana lura da ita. Suna shigowa, Gwaggo Hafsat ta dubi Dawud da mamaki. “Lafiya? Me ke faruwa?” Dawud ya saki hannun Hauwa da karfi. Ta durkushe a kasa, jikinta yana rawa. “Gwaggo,” Dawud ya soma cikin muryar takaici. “Ganin da kike yi da wannan matar… tana da hannu a cikin duk abin da ya faru!” Hajiya Zaytunah ta zabura. “Subhanallah! Me kake fada haka?” Dawud ya daga wayar, yana nuna mata sakonnin da Hajiya Hauwa ta tura. “Duba wannan. Ita ce ta sanar da su inda kuke. Ita ce ta bada bayanai, kuma tana da alaka da wadanda suka yi garkuwa da ku.” Gwaggo Hafsat ta kalli Hauwa da mamaki. “Hauwa! Ashe haka kike?!” Hajiya Hauwa ta fashe da kuka. “Wallahi ba haka bane…” Dawud ya harare ta. “Kiyi shiru! Na fahimci cewa kin fi son mutanen waje fiye da mutanen gidan nan. Kina ba su SIRRIN gidan mijinki, kina ba su damar cutar da iyalansa!” Hajiya Zaytunah ta dafe KIRJI, tana jin yadda zuciyarta ke tafarfasa. “Hauwa, don me kika yi haka?” Hajiya Hauwa ta sunkuyar da kai, ba ta da bakin cewa komai. Tunanin yadda za ta kare kanta ma ya gagara. Bayan wani dan lokaci na shiru, Major General Dawud ya dubi Hauwa da tsananin fushi. “Babu wata maganar da za ta iya kare ki a wannan lamarin. Hajiya Hauwa, daga yau… na sake ki saki biyu!” Gaba daya dakin ya dauki shiru. Gwaggo Hafsat ta zabura. “Dawud! Ka yi hakuri… Ka yi tunani. Kada ka yanke hukunci cikin fushi.” Dawud ya girgiza kai, yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa. “Gwaggo, ba zan iya rayuwa da mace wacce ba ta girmama amana ba. Mace wacce ba ta kula da lafiyata da tsaron iyalina ba.” Hajiya Hauwa ta fashe da kuka, amma Dawud bai kula da ita ba. Gwaggo Hafsat ta dafa kafadarsa. “Dawud, na fahimci halin da kake ciki, amma kada ka yi sauri wajen cika saki na uku. Ka ba kanka lokaci. Ka bar wa Allah komai.” Dawud ya runtse ido, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Ya janye numfashi da karfi. “Na bar miki ita, Gwaggo. Ki yanke hukunci a kanta.” Hajiya Hauwa ta sunkuyar da kai, hawaye na kwarara daga idonta. Ta san cewa bata da wata mafita. Aminta ya kare, martabarta ta rushe. Hajiya Zaytunah ta sauke numfashi, tana jin wani irin yanayi mara dadi. Duk da cewa ta sha wahala a hannun kishiyoyinta, amma ba ta taba tunanin cewa Hajiya Hauwa za ta iya aikata hakan ba. Daga wannan rana, komai ya canza a cikin gidan Major General Dawud. Gwaggo Hafsat ta ci gaba da rarrashin danta, yana kokarin samun nutsuwa daga abin da ya faru. A gefe guda kuwa, Fawaaz da Nabeeha sun fahimci wani abu—aminci da soyayya ba kawai ana fada su suke ba. Sai an kiyaye su, sannan ake iya samun kwanciyar HANKALI. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:41_ Gidan ya dauki shiru, sai karar kukan Hajiya Hauwa kadai ke tashi. Ta durkushe a kasa, hawaye na kwarara daga idanunta, tana girgiza kanta cike da nadama. Ta rarrafa zuwa wajen Hajiya Zaytunah, ta rike kafafunta da rawar jiki. “Dan Allah, Zaytunah, ki yafe min! Ki dubi Allah ki gafarta min. Wallahi na yi kuskure!” Hajiya Zaytunah ta dauke kai, zuciyarta cike da radadi. Ba ta taba tunanin cewa hajia hauwa za ta iya cin amanarta haka ba. “hajiya hauwa, me na miki da kika yanke shawarar ba su bayanan da suka kusa hallaka ni da ‘ya’yana?” Muryarta ta bayyana rauninta da takaici. Hajiya Hauwa ta kara rushewa da kuka, tana girgiza kai. “Na yi kuskure! Na yi babban kuskure, Zaytunah. Ba na so hakan ta faru! Wallahi sharrin zuciya ne ya rufe ni.” Sai ta koma wajen Gwaggo Hafsat, ta kama hannayenta da karfi. “Gwaggo, ki yafe min! Ki tausaya min! Na san na cutar da ku, amma dan Allah, ki gafarta min.” Gwaggo Hafsat ta girgiza kai, tana jin yadda zuciyarta ke tafarfasa. “Hauwa, ba wai yafe wa ba ne matsala… matsalar ita ce, me ya sa kika aikata hakan? Kin yi aure da d’a na, amma har yanzu ba ki san darajar iyali ba?” Hajiya Hauwa ta durkushe a kasa, ta rike kafafuwan Gwaggo Hafsat, tana kuka kamar jaririya. “Na tuba, Gwaggo. Wallahi na tuba! Ku yafe min, kada ku yanke min hukunci na har abada!” Ta juyo zuwa ga Major General Dawud, wanda ke tsaye cikin rashin jin tausayinta. Idanunsa sun nuna takaicinsa. “Dawud, Alhaji… dan Allah ka yi hakuri!” Ta fashe da kuka, tana rike hannunsa. “Wallahi ban san abinda na aikata zai kai ga haka ba! Ka yafe min, kada ka rabu da ni haka.” Dawud ya sauke numfashi, yana jin wani nauyi a zuciyarsa. Ya sha wahala a aikinsa, amma bai taba tunanin cewa matsala mafi muni za ta fito daga gidansa ba. Ya dubi Hauwa, yana jin takaicin yadda ta wofintar da amana. “Hauwa, ba wai fushina kawai kika haddasa ba. Kin wargaza amana, kin jefa rayuwar mutane cikin hadari, kuma kin ci amana ta a matsayin miji.” Hajiya Hauwa ta kara fashewa da kuka. “Ka tausaya min! Na yarda da hukuncinka, amma dan Allah kada ka rabu da ni haka!” Duk wanda ke dakin ya cika da mamaki. Nadamar da Hajiya Hauwa ke ciki ta bayyana karara. Hajiya Zaytunah ta sauke numfashi, sannan ta kalli Gwaggo Hafsat. “Gwaggo, ni na yafe mata.” Hajiya Hauwa ta dago da mamaki, tana kallon Zaytunah da hawaye. “Zaytunah… kin yafe min?” Zaytunah ta girgiza kai. “Eh, na yafe miki. Amma hakan ba yana nufin zan iya mantawa da abin da kika aikata ba.” Dawud ya jinjina kai, yana jin yadda zuciyarsa ke girgiza. “Gwaggo,” ya fadi a hankali. “Zan bari komai a hannunki. Na yanke saki biyu, amma ba zan cika na ukun ba har sai na yi dogon tunani.” Hajiya Hauwa ta rushe da kuka, tana jin cewa ko da kuwa ba a sake ta yanzu ba, ta riga ta lalata amana da soyayyar da take da mijinta. A wannan dare, ta kwana cikin nadama. Ta fahimci cewa amana bata da kyan tozarta, kuma cin amana na iya wargaza rayuwar mutum. Daren ya ci gaba da shuru a cikin gidan, amma zuciyar Hajiya Hauwa na kara daukar zafi. Duk da cewa Hajiya Zaytunah ta yafe mata, har yanzu ba ta iya kallon idon kowa ba. A zuciyarta, tana jin nauyin zunubin da ta aikata, cin amana a cikin gidan da ya bata mafaka. Tana durkushe a kasa, jikinta na karkarwa, tana cigaba da kuka mai tsanani. “Gwaggo… Dan Allah… Dan Annabi, ki shawo kan Dawud kada ya rabu da ni. Wallahi na tuba. Na gane girman kuskurena!” Gwaggo Hafsat ta sauke ajiyar zuciya. Idanunta sun nuna takaici, amma a lokaci guda, tana jin tausayin Hauwa. Sai dai, cin amana ba karamin abu bane. “Idan muka yafe miki, Hauwa,” Gwaggo ta fada cikin nutsuwa, “yaya za mu sake dogaro da ke? Yaya za mu koma mu cigaba da rayuwa da ke, muna jin tsoron cewa wata rana za ki sake cin amana?” Hajiya Hauwa ta girgiza kai da sauri, hawaye na kwarara daga idonta. “Wallahi Gwaggo, ba zan sake ba! Na tuba har abada! Zan iya rantsuwa da komai mai tsarki!” Major General Dawud ya dafa goshinsa da hannu biyu, yana jin nauyin tunani. Yana son ya yi hukunci bisa adalci, amma zuciyarsa na gaya masa cewa ba abu ne mai sauki ba. Ya dauki lokaci yana tunani, sannan ya kalli mahaifiyarsa. “Gwaggo, idan ba ke ba… wacece za ta iya yanke hukunci a kan wannan lamarin?” Gwaggo Hafsat ta kalli danta. Ta jima tana nazari, sannan ta juyo ga Hauwa. “Hauwa, ki tashi.” Hajiya Hauwa ta mike da sauri, jikinta yana karkarwa. Ta sunkuyar da kai, tana jiran hukunci. Gwaggo Hafsat ta sauke numfashi. “Na ji rokonki. Kuma saboda darajar auren da kuka yi da Dawuda, zan roke shi da kada ya cika saki na uku. Amma akwai sharadi.” Hajiya Hauwa ta dago kai cikin fargaba. “Gwaggo, komai ne zan yi! Ki fada min.” Gwaggo Hafsat ta kalli Major General Dawud, sannan ta mayar da kallonta ga Hauwa. “Zaki bar gidan nan. Ba zan ce ya sake ki ba, amma dole ki bar gidan nan na wani lokaci har sai an tabbatar da cewa ba za ki sake yin irin haka ba.” Hajiya Hauwa ta bude baki da mamaki. “Gwaggo… amma ina zan je?” “Ki koma gidan iyayenki ko gidan ‘yan uwanki. Idan har da gaske kina son komawa cikin wannan gidan, sai mun tabbatar cewa kin shiryu.” Shiru ya biyo baya. Hajiya Hauwa ta yi shiru, zuciyarta tana tafarfasa. Kamar dai a yanzu aka kada ta daga rayuwarta. Ta juyo ga Dawud, tana neman sassauci. “Dawud… kai ne mijina. Ka yanke hukunci.” Dawud ya girgiza kai. “Na bar wa Gwaggo hukunci, kuma ba zan canza ra’ayi ba.” Hajiya Hauwa ta sulale a kasa, tana kuka. Ta fahimci cewa ta yi babban kuskure da ba za ta iya gyarawa ba a dare daya. Hajiya Zaytunah ta kalli yadda take kuka, ta kalli Dawud, sannan ta sauke ajiyar zuciya. Ta san cewa Hauwa ta ci amana, amma zuciyarta ba ta so a kore ta da zafi haka ba. “Gwaggo, idan zan iya magana…” Dawud ya dago kai yana kallonta. Gwaggo Hafsat kuwa ta ce, “Ki fadi.” Hajiya Zaytunah ta gyara zamanta, ta dubi Hauwa da nutsuwa. “Ina so ta bar gidan nan na wani lokaci kamar yadda kika ce, amma kada mu haramta mata dawowa gaba daya. Idan har ta gyara halinta, sai a sake tunani.” Hajiya Hauwa ta dago kai, tana kallon Zaytunah da mamaki. “Zaytunah… kina nufin har yanzu kina tunanin zan iya dawowa?” Zaytunah ta jinjina kai. “Na san cewa cin amana ba abu bane mai sauki. Amma idan har da gaske kina nadama, ba zan hana ki damar gyarawa ba.” Gwaggo Hafsat ta jinjina kai. “Shikenan. Wannan hukunci ne mai kyau.” Major General Dawud ya sauke ajiyar zuciya. “Za ki bar gidan nan gobe da safe.” Hajiya Hauwa ta lumshe ido, tana jin wani irin nauyi a zuciyarta. Ta san cewa ba ta da wata mafita da ta wuce karbar hukunci. A wannan dare, ta kwana cikin tunani. Ta fahimci cewa wasu kura-kurai suna da kudin da sai an biya su kafin a iya cigaba da rayuwa. _______ Toh haka rayuwar ta cigaba da garawa, hajia hauwa maijiddah ta bar gidan major general dawud mafia na wani dan lokaci kafin a sake nemanta. Sannan itama kotu taci tarar ta tunda tabada gudunmawa a Kamen da aka yiwa su hajia zaytunah. Sai dai kotu ta sassauta mata hukunci saboda ba ita akaje wajen boka. Batada masaniya akan Kamen su hajia zaytunah da irin azabar da aka gana musu duk batada hannu aciki. Lefinta daya. Tura sakonnin da ta yiyyi sune kawai. Amman bayaga wannan batada lefin komai... Bangaren su Alhaji Amiru da uzairu kuwa sai hamdala. Alhaji uzairu yana zuwa ya ziyarci ya'yansa ya gana dasu, haka zalika yaran nasa na zuwa su gayshe da shi suna ziyartar su... A karshe dai, an saka ranar bikin su Humayrah da Raudah. An tsaida sati biyu daga lokacin za a ɗaura aure. Amma sai aka daga bikin Nabeeha da Muhammad zuwa gaba, bayan wata guda da auren su Raudah. Dalili kuwa shine, halin da suka tsinci kansu a ciki, zancen aure na Nabeeha da Air Captain Muhammad ya zo ba zato ba tsammani, har wasu na ganin kamar al’amari ne da za a iya jinkirta don komai ya lafa. Amma wani ne bai iya fahimtar hakan ba… Fawaaz! Lokacin da ya samu tabbacin cewa idan bai yi maza ba, za a aurar da Nabeeha ga wani, hankalinsa ya gushe. Bai taba tunanin wani zai iya kasancewa mijinta ba sai shi. Bai san sanda zuciyarsa ta fara tafarfasa da tsoro ba. Rashin cin abinci, rashin samun barci, da damuwa suka fara shafar shi. Har ya soma rama! Wannan ba abu ne mai sauki ba ga shi da shi. Yana da mugun girman kai, amma kishi ya wofintar da shi. Yanzu komai ya gaza, idan bai dauki mataki ba, Nabeeha za ta zame masa tarihi… -- Bikin yayan Major General, Raudah da Wysha Humayrah Dawud, da angonta Fahad, dan gidan Chief Judge Abdulfatah, ya soma ne da tea party. Aka tsara komai cikin nutsuwa da kwalliya mai kyau. Farfajiyar gidan Major General Dawud ta sha ado da kyawawan furanni da haske na musamman. Bayan tea party, an shirya bachelorette party mai kayatarwa. Ita da Raudah Dawud Mafia, wadda za ta auri Barrister Ridwan, sun kasance cikin farin ciki. Ana tsakiyar shagalin ne aka zo da wani tsari na musamman..Black & White Party! Amaren da kawayensu duk sun sanya white gowns masu daukar hankali, yayin da mazajen suka sanya black suits da white ties. Humayrah da Raudah sun kasance cikin farin ciki... Nabeeha ta fito cikin wani black gown mai daukar hankali. Rigar ta kwanta daidai da jikinta, ta zauna a kugu, tana fidda kwarjini. Gashinta mai laushi an warware shi, yana sauka har bisa kafaɗunta. Bata saka komai a wuyanta ba face wani siririn sarka mai kyau. Hannayenta sun sha zoben azurfa, idanunta sun sha kwalliya kamar ta fito daga labarin soyayya. Sai dai Fawaaz bai so ganin hakan ba. Hankalinsa ya tashi! Ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi da bai taba shan irinsa ba. Yana jin kishi kamar zai cire ransa. Wannan kyawun fa, ba shi kadai ne zai gani ba! Yana tsaye, idanunsa sun kafa kan Nabeeha, sai dai ita ta kasa lura da shi. Ta shiga jin dadin wasan tare da sauran kawayenta, tana dariya, tana motsa jikinta cikin nishadi. Wani abu ya daki zuciyarsa. Hankalinsa ya gushe. Bai san sanda ya nufi sashensa ba. Bai san sanda ya jawo wata rigarsa ba, sannan ya dawo inda take. Lokacin da ya iso, har lokacin tana cikin wasan. Ba tare da jin kunya ba, ya ja hannunta. Nabeeha ta zabura. “Yaa Fawaaz! Me haka?” Bai bata amsa ba, sai kawai ya dauki rigarsa, ya dora mata a kafada. Ta daga idanunta da mamaki. “Lafiya?” “Ki saka,” ya fada a hankali. “Me ya faru?” Ya dube ta da idanunsa masu zurfi, sai ya matsa kusa da ita. Muryarsa ta dan murya, cikin rada, "Da gaske so kike kowa ya cigaba da kallon ki haka?" Zuciyarta ta buga. Idanunta suka fadi. Ji take tamkar yana ce mata "kin fi dacewa da idanuna kawai." Ba tare da bata lokaci ba, ya rike hannunta, ya jata daga wajen. Kowa ya tsaya da abin da yake yi, yana kallonsu da mamaki. Ya kaita motarsa. Ya bude mata, ta shiga da rashin fahimta, sannan ya zagaya ya shiga shima. Maimakon ya tada motar, sai ya kwantar da kansa a kan sitiyari. Shiru ya biyo baya. Nabeeha ta juyo ta kalle shi. “Yaa Fawaaz?” Bai ce uffan ba. Sai dai idanunsa sun rufe, yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Ta kura masa ido. A yanzu, da gaske ya rame. Ya yi duhu kamar ba Fawaaz ba. Ta dafa hannunsa. “Ka kwantar da hankalinka.” Sai ya dago, idanunsa suka hadu da nata. A karo na farko, bai iya boye damuwarsa ba. "Da gaske za ki bar ni?" Ta bude baki, amma bata san me za ta ce ba. "Da gaske za ki auri wani?" Zuciyarta ta buga da karfi. Bai taba tambayar ta haka ba. Bai taba fadin irin wadannan kalmomin da kansa ba. Sai ta runtse idonta, zuciyarta tana neman bugawa da sauri. Soyayyar Fawaaz... ta fara bayyana! ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:42_ Zuciyarta tana bugawa da sauri. Tambayar da Fawaaz ya yi mata tana yawo a kunnenta, "Da gaske za ki bar ni?" "Da gaske za ki auri wani?" Nabeeha ta kasa bude baki. Tana jin numfashinsa yana fita a hankali, amma yana da nauyi kamar yana shan wahala. Tana kallonsa, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama. Ta san Fawaaz miskili ne, ba ya fada kai tsaye, ba ya taba bayyana soyayya ko damuwarsa. Amma wannan karon… ya kasa boyewa! Ta hadiye yawun bakinta. “Yaa Fawaaz…” Ya dago idanunsa, suka hadu da nata. Idanuwansa sun canza, akwai damuwa, akwai tsoro, akwai kishi… akwai abu da ba ta taba gani a tare da shi ba. Bata taba ganin Fawaaz a haka ba. Bai da karfin yin kuka, amma idanunsa sun bayyana rashin kwanciyar hankali. Ta dafa kan giyar mota a hankali. “Ka kwantar da hankalinka.” Shiru. Bai ce komai ba. Sai dai ya lumshe idanunsa na wasu dakiku, sannan ya bude su a hankali. Ya dago hannunta daga inda take dafe da shi, ya matse cikin nasa. Jikinta ya dauki rawa. Duk da sanyin AC, amma tafin hannunsa yana da dumi. "Me yasa zuciyata ke bugawa haka?" Ta raya a ranta. A hankali, ya bude baki, muryarsa kamar mai radadi. “Nabeeha… ki fada min, da gaske ne?” Ta runtse ido, ta bude. “Menene da gaske?” Ya dan saki ajiyar zuciya. “Zaki aure shi?” Ta dauke kanta gefe. Babu abin da ta tsana irin wannan tambayar, saboda itama ba ta san me zai faru da ita ba. “Bana son ayi auren.” Muryarsa ta soma sauyawa. Ta dago da sauri. “Me kake nufi?” Fawaaz ya juyo, ya kalle ta sosai, ya bude baki, amma sai ya sake rufe shi. Bai san me zai fada ba. "Ba zan iya fadin cewa ina son ki ba. Amma ba zan iya barin wani ya same ki ba." Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. “Kiyi wani abu. Karki amince.” Ta girgiza kai. “Ya Fawaaz, aure ba wasa ba ne.” Ya dan rike kansa. “Ke kike tunanin wasa nake? Ke kike tunanin wannan abu wasa ne?” Ta yi shiru. Ya ci gaba da fadin, “Tun da kika san cewa aure ba wasa ba ne, me zai hana ki duba zuciyarki ki tabbatar ko kina son shi?” Hankalinta ya tashi. Ta furta cikin kasa da murya, “Bana son shi…” Ya dago da sauri, yana kallonta da mamaki. “Me kika ce?” “Bana son shi,” ta maimaita. Numfashinsa ya fara sauka a hankali. Ya kura mata ido. “Ina so ace na samu hanyar kubuta daga wannan matsala,” ta fada a hankali. Fawaaz ya jinjina kai. “To ki fada. Idan bakya so, ni zan fitar da ke.” Ta dago ido, tana kallonsa. “Ta yaya?” Ya shafa sumar kansa. “Ki bar wannan a kaina.” Zuciyarta ta doka. Fawaaz zai iya yin komai don ya hana ta barinsa? Don Allah, menene ma’anar hakan? Wannan ba kishi ba ne kawai… wannan soyayya ce! Ta sake kallonsa, zuciyarta cike da mamaki da ruɗani. A karon farko, zuciyarta ta fara fahimtar Fawaaz. Shiru ya biyo baya. Shiru mai nauyi. Idanun Fawaaz na kan Nabeeha, idanunta na kansa. Ba wanda ya san me ke zuciyar dayan. Da alama zuciyoyinsu na fassara abu guda, amma suna jin tsoron furtawa. Fawaaz ya sauke ajiyar zuciya, ya dauke kai gefe. Bai san me zai ce ba, kuma ba ya son cewa wani abu da zai sa ta ji kamar yana tilasta ta. Amma zuciyarsa… zuciyarsa tana barazanar fasa KIRJI ta fito. A hankali, Nabeeha ta dan gyara zamanta. “yaa Fawaaz…” Bai kalleta ba, amma ya amsa da muryar da bata saba da jin irin ta a tare da shi ba, "Na'am?" Ta dan hadiye yawu. “Me kake nufi da cewa zan bar komai a kanka?” Ya lumshe ido na wasu dakiku. Daga bisani ya bude su. “Ba sai kin damu ba.” Ta dan kalle shi da mamaki. “Ka ce haka bayan ka janyo ni daga wajen bachelorette party, ka mayar da ni kamar wata… wata—” Ya juyo da sauri. “Kamar wata me?” Ta girgiza kai. “Kamar wata wadda ba ta da ‘yancin kanta.” Idanunsa suka hade da nata. “Ba haka bane.” Tayi shiru tana kallonsa. Tana son fahimtar shi, tana son jin dalilin da yasa yake acting haka. Ya ci gaba da kallonta, sannan a hankali ya furta, “Ban san yanda zan fada miki ba.” Ta tsura masa ido. “Ka fada kawai.” Ya dauke kai gefe. Fawaaz bai taba jin wannan nauyin kalmomi a bakinsa ba. Bai taba jin wannan tsoron fadin abu ba. Bai san lokacin da ya furta ba, “Ban san yanda zan rayu ba idan har na ganki da wani ba.” Numfashinta ya tsaya cak! Hannunta ya fara rawa. Ta bude baki, amma bata san me za ta ce ba. Shi kansa yana jin kamar ya furta wani SIRRI da bai shirya bayyana ba. Amma da gaske ne! “Nabeeha.” Ya kira sunanta a hankali. Ta dago idonta da sauri. Ya kura mata ido, yana jin zuciyarsa na tafarfasa. Kamar yana gab da furta abu mafi girman da ya taba fada a rayuwarsa. Sai dai… wani bugun wayarsa ya katse shirin da zuciyarsa ta gama yanke hukunci a kai. Ya sauke numfashi, ya dauki wayarsa. "Captain Idris." Ya yi shiru, yana duban sunan da ke yawo a fuskar wayar. A hankali, ya danna answering call, muryarsa a dake. "Captain, kana ina?" Muryar can daga daya bangaren ta fada. "Muna da matsala a base" Fawaaz ya sauya fuska bayan su. Gaysa. “Wace irin matsala?” "Matsalar taron gaggawar nan da shugaban kasa zai zo." "Roger that .. okay later" ya katse Kiran yana sake duban Nabeeha. Zuciyarsa ta buga da karfi. Idan bai dauki mataki ba, Nabeeha za ta tafi! Ya bude idonsa a hankali, yana kallonta. Tana kallonsa shima. Hannunta yana cikin nata, amma ba ta san lokacin da ta rike nasa ba. Tana jin jikinta yana rawa. "Menene dalilin wannan kishi da yake nuna min?" Ta tambayi zuciyarta. "Shin hakan yana nufin Fawaaz yana sona?" "Ko kawai yana jin kishi ne don ba ya son wani namiji ya same ni?" Tayi shiru. Bai ce komai ba, ita ma bata ce komai ba. Sai dai zuciyoyinsu suna magana da juna. Shiru na wasu dakiku… Sai Fawaaz ya sauke ajiyar zuciya. Ya saki hannunta a hankali. Ya juyo da kyau ya kalle ta. “Da gaske zaki tafi?” Ta lumshe ido, ta bude. “Yaw Fawaaz… ban san me zan ce ba.” Ya kura mata ido, sannan ya furta kalmomin da suka gigita ta, “Idan har baki son tafiya, zan iya hana ki.” Idanunta suka bude da mamaki. “Me kake nufi?” Ya dago hannunsa ya dafa saitin zuciyarsa. “Zan dauki matakin da zai hana ki auren Muhammad.” Jikinta ya dauki rawa. Shin me yake nufi? "Yanzu zan je wajen su baba" Idonta ya karu. "Me zai hana?" Ya tsura mata ido. "Zan fada masa cewa ni nake son ki." Ta saki baki da mamaki! Shin Fawaaz ya fadi hakan da gaske? Numfashinta ya dauki sama. Ta ji kamar an zuba mata ruwan sanyi a zuciya. Ta kasa furta komai. Idanunsa sun kada. “Nabeeha, bana wasa. Zan je in fada masa a yau.” Tayi shiru. Tana jin kamar mafarki take yi. Kafin ta iya cewa wani abu, Fawaaz ya bude kofar motar, ya fito da sauri. Tana jin numfashinsa yana fita da nauyi. Gaskiya ne! Zai fada wa Major General cewa yana sonta. Shiru ya kara mamaye falon. Kowannensu ya tsaya da tunani, yana kokarin fahimtar abin da ke faruwa. A yau dai gaskiya ta fito fili! Major General Dawud ya jingina bayansa da kujerarsa, yana kallon Fawaaz da wani irin kallo mai zurfi. "Ka san me kake fada?" Ya sake tambaya. Fawaaz ya dan runtse ido, sannan ya bude su cikin girmamawa. A karo na farko, ba shi da niyyar boye komai! "Eh, Baba," ya fada a hankali. Gwaggo Hafsatu ta dafe KIRJIN ta. "Kai Fawaaz! Ai wannan maganar ka bata da sauki! Kasan me kake bukata daga gare mu ne kuwa?" "Dan Allah ina so ku dakata da shirin aurenta da Air Captain Muhammad." Dakin ya dauki shiru! Hajiya Zaytunah ta dubi Major General da sauri, kamar tana neman jin ra’ayinsa. "Fawaaz," inji Major General, "kai ɗana ne. Amma kayi sake mai girma." Fawaaz ya gyara tsayuwarsa, yana jin bugun zuciyarsa na karuwa. Amma ya kudurta cewa ba zai janye ba! "Baba" ya kira cikin nutsuwa, "bani da mafita da ta wuce wannan. Na san nayi sake, amma ita ce zabina." "Kai baka da hankali ne?!" Cewar Gwaggo Hafsatu, tana dubansa da mamaki. "Tun yaushe kake son ta, amma baka fada ba?" Fawaaz ya ji kunya ya lullube shi, amma hakan bai hana shi ci gaba da magana ba. "Na tsorata, Gwaggo," ya fada da gaskiya. "Na tsorata da yadda za a fahimce ni. Na tsorata da abin da Nabeeha za ta fada. Na tsorata da cewa ba za ta karbeni ba! Na fara kaunar nabeeha tun ranar dana fara dora idanuna akanta sanda suka dawo gidan nan tun muna kanana. Tun bansan meye so ba gwaggo...kaunar da nake mata batada iyaka. Bama zan iya fasaltata ba ko na bayyana adadinta" Major General ya gyada kai a HANKALI. Kamar yana jin tausayin dan sa.. "Baka da tabbacin cewa ita ma tana sonka?" Shiru ya ratsa dakin. Fawaaz ya ji zuciyarsa ta buga. Hakika bai da tabbas! Ko Nabeeha za ta amince da shi? Ko kuwa zata dauke shi a matsayin wani mai bata lokaci? Hajiya Zaytunah ta numfasa. "Fawaaz," ta kira shi a hankali. "Na’am, Aunty ." Ya amsa cike da kunyar ta mai girma... Ta kalli Major General, sannan ta kalli Gwaggo Hafsatu. "Idan har Nabeeha zata amince da shi, to ni ba ni da matsala." Gwaggo Hafsatu ta kada kai. "Ai maganar ita ce, yaushe zai fada mata?" Major General Dawud ya kura wa Fawaaz ido. "Fawaaz," ya furta, "ka shirya don fuskantar ita kanta?" Fawaaz ya hadiye yawu. Wannan ce babbar matsalarsa! Yana so ya fada wa Nabeeha. Amma yana tsoron amsar da zai samu. Ko zata amince da shi ko zata ki karbar kokon barar sa.... Don gudun kada ta badawa su gwaggo Hafsatu kasa a idanu.... Fawaaz yayi shiru kansa a kasa. Gwaggo Hafsatu da dama tasan haka zata faru don ta lura da yanayinsa ta tabbatar yana kaunar nabeeha sosai. Amman saboda tsananin fadin ransa da miskilancinsa bata taba zaton zai iya bayyanawa ba. Lalle ba karamar kauna yakewa Nabeeha ba. Don haka ta nisa kafin tache, "Wannan batu sai da amincewar kowanne bangare. Ba a neman aure akan wani neman. Ma'ana tunda Muhammad ya rigaka to fa sai da amincewar sa idan zai hakura yabar maka. Haka zalika sai idan nabeehan ta amince da karbar kaunar ka. Fata dai Allah Ubangiji yayi zabinsa na gari. Allah ya zaba mata mafificin alkhairin sa acikin ku Amin. Wannan batu sai manya sun shiga cikin sunga yiwuwar sa. Inn shaa' Allah." "Toh granny" fawaaz ya amsa a takaice ya dan dunkufa yana musu sallama. "A huta lafiya" ya Mike ya fice da sauri. Yayinda su Kuma suka cigaba da maimaita lamarin.. 🎀🎀🎀 Zaune air captain, pilot Muhammad Amiru yake akan makeken gadonsa. Kansa a saman pop. Na'urar dake tache abun kallo tana haskawa da faifon bidiyon komai da maganganun su na ranakun gaba daya. Kunya, takaici da nadama suka taru suka gauraye shi. Duk karfin halin sa sai da hawaye suka zurara daga idanuwan sa... ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:43_ Faifon bidiyon ya fara tariyo masa tun daga, Zauren babban falo ne su Gwaggo Zainabu, Alhaji Uzairu, da Alhaji Amiru suka zauna, kowanne cikin shigar mutunci, amma zuciyoyi na ruf da ciki. A gefen su kuma, a durkushe kan kafet, su Hajiya Ladi, Hajiya Karama, da Hajiya Rumanah suna zaman nasu, tamkar basu da damuwa. Muhammad, ɗan Hajiya Rumanah, yana zaune a gefen kujera, yana kallo da al'ajabi, zuciyarsa cike da shakku da mamaki. Bai taɓa tunanin mahaifiyarsa da matan kanin mahaifinsa suna da wata boyayyar magana ba, amma yau abin ya bayyana. Alhaji Amiru ne ya fara magana da muryar nutsuwa, amma a ciki akwai wata alama ta tuhuma. "Ina Zaytunah?" Gaba ɗaya suka dubi juna, sannan suka girgiza kai da ƙarfin gwiwa. "Mun ce ba mu da masaniya," cewar rumanah, tana kallon Alhaji Amiru da kyar. "Tun batan da tayi shekaru da suka wuce, ba mu sake jin labarinta ba," in ji Hajiya Rumanah. Alhaji Amiru ya kalli kowannensu ido cikin ido, sai ya sake tambaya, "Ina Zaytunah?" Gaba ɗaya suka mayar da amsa iri ɗaya, ba tare da wata alamar shakku ba, "Ba mu sani ba." Sai da ya sake tambaya karo na uku. A wannan karon ma, babu wanda ya canza furuci, "Ba mu sani ba." Sai kawai ya murmusa, yana daga kansa sama da jinjina labban sa. A take ya mike tsaye, yana mai daga dogon gyale yana gyara hularsa. Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya juya ya fita daga falon. Ba a jima ba, sai gashi ya dawo. Amma ba shi kaɗai ba, yana shigowa tare da wasu sojoji biyu, hannunsu rike da wani mutum da aka daure da ankwa. Bokan ne! Bokan da suka taɓa kaiwa don a mata asiri! Cikin tsananin firgici, suka miƙe gaba ɗaya, fuska ɗauke da fargaba. Hajiya Ladi ta dafe KIRJIN ta, tana duban bokan da tsananin tsoro. Hajiya Karama ta shiga rawa a tsaye, muryarta na kerma. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!" Hajiya Rumanah kuwa, sai ta sunkuyar da kai, jikinta na rawa. Muhammad ya daskare a kan kujerarsa, idonsa waje yana kallon mahaifiyarsa da kuma sauran matan. Bai iya cewa uffan ba. Alhaji Uzairu ya cilla musu wani kallo mai cike da takaici. Kamar wanda ya daɗe yana shakkunsu, amma yau shaidar ta bayyana. "Kun janyo wa kanku," Alhaji Amiru ya furta da kakkausar murya. "Kun janyo wa kanku!" Alhaji Uzairu ya sake kallonsu, zuciyarsa na cunkushe da ɓacin rai. "Na gama zama da ke! Na gama!!" Ya faɗa da ƙarfi, yana daga murya. A take a wajen, cikin shaidun da ke zaune da tsaye, ya dankarawa hajia rumanah saki uku.. Shiru ya ratsa falon. Kamar an ajiye dutse a cikin iska. Kowacce cikinsu ta ji tamkar an caka mata wuka a zuciya. "Allah! Uzairu, ka duba da kyau!" Hajiya Ladi ta kurma ihu, tana dafa hannunsa. "Wallahi ba laifinmu bane! Hajiya Rumanah ce ta ɗora mu a hanya!" Ta ƙara faɗi, hawaye na zubo mata. Hajiya Karama ma ta durƙusa da sauri, tana roƙo: "Wallahi ita ce ta sa mu! Ba mu da hannu cikin hakan!" Amma sai Hajiya Rumanah ta yi saurin miƙewa. Idanunta sun cika da hawaye, amma har yanzu tana da ɗan ƙarfin hali. "Karya su ke yi! Su ne suka sa ni ciki! Ni ba ruwana!" Muhammad ya cije lebensa. Wannan wane irin abu ne yake faruwa? Mahaifiyarsa ce da ta shuka irin wannan mugunta.. Da zarar suka hango shi, gaba ɗayansu suka miƙe tsaye cikin razana. "Boka?!?!" Hajiya Ladi ta furta da wata muryar da ba ta saba da ita ba. Muhammad, ɗan Hajiya Rumanah, wanda tun farko ya kasa fahimtar me ke faruwa, ya ji gabansa ya faɗi. Ya tsure da ganin mahaifiyarsa cikin wannan tashin hankali. Idanunsu sun ciko da tsantsar tsoro, yayin da boka ya kada baki cikin wata murya mai cike da mugunta, "Gaskiya ta fito! Dukan ku ne kuka haɗa baki kuka raba Zaytunah da mijinta! Ku ka raba ta da 'ya'yanta! Ku ka hana ta dawowa cikin danginta! To yau kun ƙare!" Gaba ɗayansu suka daskare, jikinsu na rawa. Kamar su yi magana, amma harsunansu sun makale. Alhaji Uzairu ya yi ajiyar zuciya mai nauyi. Babu shakka, idanun shi sun cika da takaici, kuma lokaci ne ya nuna masa gaskiya. Bai tsaya wata-wata ba, a take ya dubi su uku, da murya mai ƙarfi da ba ta buƙatar maimaitawa, "Na sake ki saki uku, saki uku... Uku! Babu sauran zaman aure tsakanina da ke" Wani irin shock ya kama su. Gaba ɗayansu suka girgiza kai, suka durƙusa suna roƙon sa, amma kamar ya gama yanke hukunci. Hajiya Karama da Hajiya Ladi sun zabura suna kuka, suna cewa ba su da laifi, wai Hajiya Rumanah ce ta jefa su cikin wannan hali. Ita kuwa Rumanah ta zabura cikin ɓacin rai, ta nunasu da yatsa tana cewa, "Karya suke yi! Sune suka ɗaura ni a ciki! Ni ba ruwana!" Duk parlorn ya cika da hayaniya, yayin da kowacce ke ƙoƙarin wanke kanta. Amma daga Alhaji Uzairu har Alhaji Amiru, babu wanda ya damu da jin bahasi. Gwaggo Zainabu, wadda tun farko ke zaune shiru, ta dafe kai tana kallonsu da takaici. Tana jin kamar zuciyarta za ta fashe. Idanun ta sun ciko da hawaye. A nan, Alhaji Amiru ya ɗaga hannu ya dakatar da hayaniyar, sannan ya dubi su da tsantsar ƙiyayya, Gaba ɗayansu suka girgiza cikin matsanancin firgici. Babu wanda ya iya cewa komai, sai dai kuka da nadama. Amma ya riga ya kure musu. Muhammad ya sunkuyar da kansa, yana jin wani irin bakin ciki a ransa. Yau ya ga wata fuskar mahaifiyarsa da bai taɓa zato ba. Yau komai ya gama tonuwa! Gaba ɗaya falon ya dauki shiru na wani lokaci. Sai kukan Hajiya Ladi da Hajiya Karama ke tashi, suna durƙushe a ƙasa, suna roƙon Alhaji Uzairu da kada ya raba su da shi. Amma a yau, ba zai saurare su ba. Ya yi ajiyar zuciya, ya dubi su da kallon takaici, sannan ya ce da kakkausar murya, "Kuka ɓata mini aure na, kuka raba ni da iyalina, kuka hana ni jin daɗin rayuwa na tsawon shekaru! To yau kun ga sakamakon abinda kuka aikata! A fitar mini da su daga gidana. Na sake ku Kuma saki uku uku!" Jin haka yasa Hajiya Rumanah ta zabura da sauri, ta dubi shi da idanunta cike da hawaye. Tana neman mafita, amma babu ko ɗaya. "Yaya Uzairu, ka saurareni! Ni ba ruwana! Ni fa su ne suka jefa ni cikin wannan fitinar! Dan Allah kabawa Yaya Amiru hakuri" Ta nuna Hajiya Karama da Hajiya Ladi da yatsa, tana kallonsu da tsantsar ƙiyayya. Su kuwa suka yi saurin juyowa suna fadin: "Karya take! Ita ce ta ja mu! Ita ce ta kitsa komai! Mu fa ba mu da hannu!" Sai dai babu wanda ke son jin uzurinsu. Muhammad yana zaune a gefe, idonsa jajir, yana kallon mahaifiyarsa da matan kanin babansa suna zagin juna. A zuciyarsa, akwai bakin ciki da takaici. Mahaifiyarsa da yake ji da ita, ita ce jagorar wannan zalunci? Bai iya gaskata hakan ba, amma abun yana a bayyane. Ya juya yana kallon Alhaji Amiru, wanda ke tsaye yana kallon su da ɗarɗar. Ya girgiza kai cikin takaici, sannan ya ce: "Tun da kun ce ba ku da hannu a cikin wannan lamarin, to menene wannan?" Ya ɗaga hannu ya nuna bokan da aka daure da ankwa, wanda ya tsaya a gefe yana kallon su da murmushin raini. "Shin bokan ma ne ya ɓullo da kansa? Ko kuwa wani ya tura shi?" Gaba ɗayansu sun toshe baki, sun kasa cewa komai. A yau, komai ya fito fili. "Bari na baku labari!" Bokan ya furta da wata murya mai nauyi, yana kallonsu da raini. "Wadannan matan nan da kuke gani, su suka zo wajena, suka nemi a raba Zaytunah da mijinta. Suka nemi a tozarta rayuwarta, suka hana ta dawowa. Kuma suka ɗauka cewa za su ci nasara har abada. To yau, kuzo ku fuskanci sakamakon abinda kuka aikata!" Hajiya Ladi da Hajiya Karama suka zabura da sauri suna girgiza kai. "Wallahi ba mu da hannu!" "Wannan boka karya yake! Bamu san shi ba!" Hajiya Rumanah ma ta yi saurin cewa, "Karya yake! Wannan sharrin ne ake son ɗaura mana!" Sai dai babu wanda ya saurare su. Alhaji Uzairu ya yi shiru na ‘yan mintuna, yana kallonsu da idanunsa jajir, yana tunanin rayuwarsa, da irin zaluncin da aka yi masa. Duk tsawon shekarun da ya shafe yana zargin Zaytunah, da tunanin cewa ita ce mai laifi, ya fahimci cewa ya yi babban kuskure. "Kuka raba ni da iyalina," ya faɗa cikin wata murya mai tsanani. "Kuka raba ni da ‘ya’yana. Kuka saka na rayu cikin ruɗu da baƙin ciki. Yau kuma kuna son ku kare kanku da ƙarya? Ai ba zan yafe ba! Kullum ina addu’a Allah ya tona asiri, kuma yau Allah ya tona!" Ya juyo ya kalli Alhaji Amiru da Major General Dawud, waɗanda suka tsaya suna kallon abin da ke faruwa. "Wallahi duk yanda kuka ga dama, ku yi da su. Ni na rabu da su har abada!" Ya juyo ga matansa, ya ɗaga murya: "Na sake ku uku, saki uku-uku! Ku fice daga gidana!" A take suka zabura, suka zube a ƙasa suna kuka, amma babu wanda ke son jin uzurinsu. Gwaggo Zainabu, wadda tun farko ke zaune shiru tana kallonsu da takaici, ta dafe kai tana jin kamar zuciyarta za ta fashe. "Ku tafi ku bar mu da rayuwarmu lafiya," Alhaji Amiru ya faɗa, yana juyawa ba tare da ya sake kallon su ba. Hajiya Rumanah ta dubi ɗanta Muhammad, tana neman taimako a idonsa, amma ya ɗauke kansa gefe. Bai san me zai yi ba. Ya girgiza kai kawai, yana jin kamar zuciyarsa ta fashe da takaici. A haka aka kori su daga gidan zuwa court.. Rayuwarsu ta rushe a take. Asirinsu ya tonu, aure ya ƙare, ƙiyayya ta girma. A yau, duniya ta sauya musu fuska. Muhammad ya yi tsaki alokacin daya karasa kallon faifon bidiyon wajen. Ya danna dakatawa. Yana cije lebensa hadi da busa numfashi mai dumi daga bakinsa. Ransa baki daya a dagule yake. Wannan abubuwa da mahaifiyar sa ta aikata don kwa itace shugabar komai baki daya ya hargitsa masa duk wani lissafin kansa.... Ita tayi abun amma baki daya shi yake jin kunya!!! Ya cigaba da kalla yana jujjuya kai cike da tsantsar takaici marar misaltuwa.... ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:44_ Hajiya Rumanah, Hajiya Ladi, da Hajiya Karama suna durƙushe a ƙasa, kuka ya cika falon. Sun rasa yadda za su yi. Fuskokin su sun cika da hawaye, amma babu wanda ya nuna tausayi a gare su. Muhammad ya dubi mahaifiyarsa da takaici. A zuciyarsa yana ƙoƙarin fahimtar yadda zata iya shiga irin wannan mugun nufi, amma babu amsar da ke da daɗi. Mahaifiyarsa ce, amma ta aikata abin da ba zai iya gafartawa ba. Alhaji Amiru ya girgiza kai cikin takaici. "Ku fice daga gidana kafin na ƙara da hukunci mafi muni!" Hajiya Karama da Hajiya Ladi sun zabura suna rarrafe suna roƙon afuwa. "Don Allah, Uzairu! Don girman Allah, ka yi mana rai!" "Wallahi ba mu da laifi! Hajiya Rumanah ce ta ja mu!" Ita kuwa Rumanah ta zabura cikin zafin rai. "Ku daina mini sharri! Ai ku kuka fara! Ku kuka ce za a hana Zaytunah dawowa! Ni fa ba ruwana!" A take suka hau musayar zargi a tsakaninsu. Kowacce tana ƙoƙarin wanke kanta, amma babu wanda ya yarda. Sun ruguza rayuwar wasu, yau kuma rayuwarsu ce take rushewa. "Ya Isa!" Alhaji Uzairu ya daka tsawa. "Ba zan saurari wata ƙarya ba! Na ce ku fice daga gidana!" Babu yadda suka iya. Da kyar suka tattara tarkacensu suna kuka, suka bar gidan kamar waɗanda aka yankewa hukuncin kisa. .... Muhammad ya tsaya a gefe yana kallon mahaifiyarsa tana barin gidan da tarin nadama. Bai san abin da zai ji ba. Bai san ko zai iya gafarta mata ba. Yana da zafi a zuciyarsa, amma ya san cewa dole ne ya cigaba da rayuwarsa. "Yaya zaka yi da ita?" Alhaji Amiru ya tambaye shi. Muhammad ya girgiza kai. "Ba zan iya cewa komai ba. Ita ta jefa kanta cikin wannan bala’in. Ba zan iya yanke hukunci akanta ba, amma gaskiya ta fito. Dole ne ta fuskanci sakamakon muguntarta." Sai ya juya ya bar falon, zuciyarsa cike da tunani. .. Bayan fitarsu, falon ya dauki shiru. Alhaji Uzairu ya zauna, yana dafe kansa da tafukan hannunsa. A yanzu, komai ya bayyana. An tona asirin mugunta, amma har yanzu yana jin nauyin zuciya. "Shekaru da dama..." ya furta a hankali. "Shekaru da dama ina tunanin Zaytunah ce ta rabu da ni, ashe ni aka yaudara?" Gwaggo Zainabu ta girgiza kai cikin tausayi. "Hakika kun shiga jarabawa, Uzairu. Amma yanzu dai komai ya fito fili. Kuma ina fata ka gane gaskiya." "Gaskiya ta fito," ya ce cikin wata irin murya mai cike da rauni. "Amma me zan yi da rayuwata yanzu?" Sai ya lumshe ido, zuciyarsa cike da nadama. .. A yanzu, Alhaji Uzairu ya san cewa dole ne ya nemi Zaytunah. Amma ina za a ganta? Shin za ta yafe masa bayan duk abin da ya faru? Ya san cewa komai ba zai dawo da sauƙi ba. Alhaji Amiru ya dube shi, ya ce: "Abin da ya rage gare ka shi ne ka nemi ‘ya’yanka. Ka nemi Zaytunah, ka nemi gafara." Uzairu ya ɗaga kai ya kalle shi, yana jin kamar duniya ta sauya. Bai san da wane ido zai kalli ‘ya’yansa ba. Duk da haka, ya san dole ne ya nemi su. A can nesa, wata rana, wata sabuwar rayuwa za ta fara. Amma yanzu, ya rage ga Uzairu da yadda zai fuskanci abin da ya shuka... Muhammad ya girgiza kai lokacin daya Kalli wajen ta faifon bidiyon da yake gani yaja dogon tsaki yana mai sake furzar da iska mai nauyi daga bakinsa.. ya cigaba da kalla.. yana saurara, Kwana biyu bayan abin da ya faru, Alhaji Uzairu ya kasa samun sukuni. Yana jin tamkar rayuwarsa ta faɗa cikin duhu. Zaytunah ce macen da ya fi so, amma saboda sharrin matansa ya zarge ta, ya bar ta.. Bayan duk wannan shekarun, yanzu ya san gaskiya. Amma ya rasa yadda zai fara. Ya zauna a cikin falonsa, yana duban hoton da ya rage masa daga aurensu—hoton da ke nuna Zaytunah tana murmushi da Nabeeha ƙarama a bayanta. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. "Dole ne in nemi Zaytunah," ya furta a fili. "Ko da kuwa ba za ta yafe mini ba, dole ne in roƙe ta gafara." Da farko, Alhaji Uzairu ya ziyarci Alhaji Amiru. Sun zauna cikin falonsa mai girma, Uzairu yana fuskantar ɗan’uwansa da tsantsar nadama a idanunsa. "Na tafka kuskure, Yaya Amiru," ya furta da wata irin murya mai rauni. "Na tafka babban kuskure da ba zan iya gafarta wa kaina ba. Amma dole ne in nemi Zaytunah. Ko da kuwa ba za ta yafe mini ba, zan roƙe ta gafara." Alhaji Amiru ya jinjina kai. "Hakika kayi babban kuskure, Uzairu. Amma ba kai kaɗai ba, ni ma ina da laifi. Lokacin da Zaytunah ta ɓace, na yi tunanin cewa kawai ta tafi ne, ba tare da neman zurfafa bincike ba. Bai kamata na bar lamarin haka ba." "Kana tunanin za ta karɓe ni?" Uzairu ya tambaya, idonsa cike da damuwa. "Ba zan iya cewa komai ba," Amiru ya amsa. "Amma abu ɗaya da na sani shi ne, dole ka nemi ta. Idan ka samu gafararta, hakan zai fi maka kwanciyar hankali fiye da komai." GANAWA DA MAJOR GENERAL DAWUD Bayan tattaunawa da Alhaji Amiru, Uzairu ya yanke shawarar cewa dole ne ya je wajen Major General Dawud, don kuwa shi ne mutumin da zai iya taimaka masa ya san inda Zaytunah take. Ya isa gidan Major General Dawud cikin matsanancin damuwa. Bayan an sanar da shi zuwan Alhaji Uzairu, Major General Dawud ya amince da ganinsa. A cikin babban falon da ya kasance mai cike da ƙamshi da ɗaukar hankali, Uzairu ya zauna yana jiran fitowar Major General Dawud. Cikin ‘yan mintuna, Dawud ya fito sanye da farin riga da wando na shan iska, yana daure fuska kamar yadda ya saba. "Ina wuni, Major General," Uzairu ya furta cikin ladabi. "Lafiya lau," Dawud ya amsa, yana kallonsa da idanu masu cike da tambaya. "Meye ya kawo ka?" Uzairu ya yi ajiyar zuciya, ya sunkuyar da kansa. "Na zo ne domin neman gafara. Ba daga gare ka ba, amma daga gare ta. Dole ne in ganta, in roƙe ta gafara. Ko da ba za ta yafe mini ba, in nemi ‘ya’yana." Major General Dawud bai ce komai ba na wani lokaci. Sai daga baya ya numfasa, ya gyara zamansa. "Zaytunah ta shafe shekaru da dama cikin damuwa. Baka san irin wahalar da ta sha ba. Kawai kana so ka je ka roƙe ta gafara, sai komai ya wuce?" Uzairu ya girgiza kai. "Ba haka nake nufi ba. Ina jin nauyin abin da ya faru. Ina son in nemi su, in roƙe su gafara, kuma in mayar da ‘ya’yana gare ni." Major General Dawud ya yi shiru, yana nazari. Bayan wasu mintuna, ya ɗaga kai ya ce: "Idan har da gaske kake, to dole ka jira. Na fahimci cewa kai ma baka san cewa ana cutar da Zaytunah ba. Amma hakan ba yana nufin cewa komai zai dawo kamar da ba. Zan fara tattaunawa da ita. Idan ta amince da ganinka, sai in sanar da kai." Uzairu ya ɗaga kai, zuciyarsa tana cike da begen samun dama. "Nagode. Ko da kuwa ba za ta yafe mini ba, zan gode idan na ganta." A cikin kwanakin da suka biyo baya, Major General Dawud ya tattauna da Hajiya Zaytunah game da bukatar Alhaji Uzairu na ganinta. A farko, ta yi shiru na dogon lokaci, tana nazarin abinda ya dace. "Bayan shekaru da dama, yanzu ne yake tunanin ganina?" Ta furta a hankali. Dawud ya kalle ta da kulawa. "Na san cewa ba abu ne mai sauƙi ba. Amma ina ganin yana cikin nadama. Yana son ‘ya’yansa, kuma yana son ya nemi gafararki." Zaytunah ta jinjina kai, zuciyarta cike da tunani. Bayan dogon tunani, ta ɗaga kai. "To, zan gan shi. Amma ba don in karɓe shi ba. Zan ji abin da zai ce." Ranar da aka shirya ganawar, Alhaji Uzairu ya kasance cikin rawar jiki. Yana fargabar yadda za a karɓe shi, amma ya san cewa dole ne ya fuskanci sakamakon abin da ya aikata. A lokacin da ya shiga falon da aka tanada don ganawar, zuciyarsa ta kusan bugawa da sauri. Ganin Zaytunah a zaune a gefen kujera, tana kallonsa da idanu masu cike da kamewa, ya ji tamkar an caka masa wuka a zuciya. Ya durƙusa a gabanta, idonsa cike da hawaye. "Zaytunah, na tafka babban kuskure. Na tafka laifi da ba zan iya gafarta wa kaina ba. Na yarda da ƙarya, na bar ku cikin wahala, Banyi kokari ba wajen fahimtar gaskiya. Na zo gare ki ba don in roƙi ki ki dawo ba, amma don in roƙi ki gafarta mini. Domin zuciyata ba za ta samu sukuni ba idan baki yafe mini ba." Zaytunah ta dubi shi, idonta cike da nauyin tunani. Tana iya ganin nadama a fuskarsa. Tana iya jin ƙaryar da aka yi masa, amma hakan ba yana nufin cewa komai zai dawo da sauƙi ba. Ta sauke ajiyar zuciya. "Uzairu, zan iya yafe maka, amma ba zan iya mantawa da abin da ya faru ba. Rayuwata ta lalace saboda laifin da baka sani ba. Amma ba zan hana ka ganin ‘ya’yanka ba." Uzairu ya ji kamar zuciyarsa ta tsinke da farin ciki. "Nagode! Wallahi nagode! Ko da ba za ki dawo gare ni ba, hakan ya isa mini." A wannan rana, duk da cewa ba a mayar da komai kamar da ba, an yi mataki na farko zuwa ga zaman lafiya. An share gaban baya, an bar gaba a hannu Allah. Kuma a yanzu, duk wanda ya aikata laifi, yana fuskantar sakamakonsa. Kamar yadda kowa ya ce… akwai sauran rina a kaba. Bayan ganawar su, zuciyar Zaytunah ta cika da ruɗani. A tsawon shekarun da suka gabata, ta koya yadda za ta rayu ba tare da Uzairu ba. Ta saba da kasancewa uwa guda ga Nabeeha da Hammad. Amma yanzu, ga shi ya dawo, yana roƙon gafara. A daren ranar, tana zaune a ɗakin ta, idonta yana kallo amma ba ta ganin komai. Tunaninta ya tafi can baya, lokacin da take matar Uzairu, da irin son da yake mata kafin a raba su. Tana tunanin yadda rayuwarta ta canza bayan fitarta daga gidansa. Major General Dawud ya shigo, ya zauna kusa da ita. "Zaytunah," ya kira sunanta a hankali. Ta ɗaga kai, tana kallonsa da idanun da suka bayyana gajiyarta. "Ba zan ce ki yafe masa ba," ya ce da natsuwa. "Ba zan ce ki manta da abin da ya faru ba. Amma ina so ki yi tunani akan kanki. Shin har abada za ki riƙe wannan zafin a zuciyarki?" Zaytunah ta numfasa. "Ban sani ba," ta furta a hankali. "Ban san ko zan iya ba." "To ki bari lokaci ya nuna," ya ce mata. "Amma kada ki ƙi yarda da zuciyarki. Idan har za ki samu sauƙin zuciya da yafiya, to ki yi. Idan kuma ba za ki iya ba, babu wanda zai matsa miki." Zaytunah ta jinjina kai, tana nazari. Bayan ganawarsa da Zaytunah, Uzairu ya koma gidansa, amma ba ya jin daɗin zama a can. Gidan ya yi shiru, ba matansa, ba ‘ya’yansa. Komai ya sauya. Ranar da ta biyo baya, ya zauna cikin falonsa, yana kallon sararin sama daga tagar da ke gefen ɗakin. Rayuwarsa ta canza gaba ɗaya. Duk abin da ya gina ya rushe. Bai san da wane ido zai kalli Nabeeha da Hammad ba. Bai san ko za su karɓe shi ba. Alhaji Amiru ya zo masa ziyarar dare, suka zauna tare a babban falo. "Ya kake ji?" Amiru ya tambaye shi. Uzairu ya yi dariyar takaici. "Ina jin tamkar mutum da aka cire masa zuciya." Amiru ya ɗan saki ajiyar zuciya. "Uzairu, an ce komai yana da dalili. Wataƙila haka Allah ya tsara. Amma yanzu da ka san gaskiya, mene ne matakin da za ka ɗauka?" Uzairu ya lumshe ido. "Zan jira. Zan jira har sai lokacin da suka shirya. Ina fatan wata rana ‘ya’yana za su yarda da ni." Amiru ya jinjina kai. "Hakan shine mafi alheri." A bangaren Nabeeha da Hammad, su ma sun samu labarin komai. Sun san cewa mahaifinsu yana neman gafara. Sun san cewa shi kansa bai san gaskiya ba. Sai dai, hakan ba yana nufin cewa komai zai dawo da sauƙi ba. Hammad ne ya fara magana lokacin da suke zaune a ɗaki. "Nabeeha, ya kika ji da jin cewa mahaifinmu yana neman gafara?" Nabeeha ta taɓe baki. "Ban san abin da zan ji ba. Abin yana da wahala. A shekaru da dama, ban taɓa tunanin zan sake ganin shi ba. Yanzu kuma gashi, yana son ya dawo cikin rayuwarmu." Hammad ya nisa. "Ni ma haka nake ji. Amma gaskiya, ina son in san shi." Nabeeha ta kalle shi. "Kana nufin za ka gan shi?" Hammad ya gyada kai. "Eh. Ko da kuwa ba zan yarda da shi ba, ina son in san mahaifina." Nabeeha ta yi shiru, tana nazari. Shin ita ma za ta iya? Shin za ta iya fuskantar mahaifinta bayan shekaru da dama? Sai ta numfasa, sannan ta ce a hankali, "Zan yi tunani akai." A cikin kwanakin da suka biyo baya, duk wanda abin ya shafa yana cikin tunani. Ko da yake an gano gaskiya, hakan bai canza komai ba cikin dare. Rayuwa tana buƙatar lokaci don ta daidaita. A wata rana, Zaytunah tana cikin shiryawa a ɗakin ta, sai ta tsaya ta dubi kanta a madubi. Ta taɓa fuskarta a hankali. Ko da yake ta sha wahala, ta tsira. Ko da yake ta rasa komai, ta sake samun sabuwar rayuwa. Kuma yanzu, tana da ‘ya’yanta, tana da mutanen da suke ƙaunarta. Shin zata iya yafiya? Shin zata iya rungumar canji? Ba ta da amsar wannan tambayar tukuna, amma ta san cewa lokaci ne kawai fada. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:45_ Bayan kwana biyu, Zaytunah ta kasa samun sukuni. A duk lokacin da ta rufe idanuwanta, sai tunanin Uzairu ya dawo mata. Kalaman sa sun tsaya a ranta, yadda ya durƙusa yana roƙonta gafara, yadda ya bayyana nadamarsa, yadda ya ce ko da ba za ta yafe masa ba, yana so ya ga ‘ya’yansa. Hakanan, ta tuna da Major General Dawud da maganganunsa masu hikima. A kowanne lokaci yana ƙarfafa ta da cewa yin gafara ba yana nufin cewa dole ne a koma da baya ba, amma yana nufin a wanke zuciya daga ɗacin rai. Ta kai hannu ta shafi fuskarta a HANKALI. Wani ɓangare na zuciyarta yana cewa ya kamata ta ƙyale shi ya ci gaba da rayuwarsa ba tare da ita ba, amma wani ɓangare kuma yana cewa ya kamata ta yi tunani akai. Da yamma, ta tafi ɗakin Gwaggo Hafsat don samun shawara. Tana jin daɗin tuntuɓarta a irin waɗannan lokutan. Ta same ta zaune bisa kujera tana lazimi, ta jira sai da ta gama sannan ta durƙusa a gabanta. "Gwaggo, ina da magana." Gwaggo Hafsat ta dubeta da kulawa. "Ina saurarenki, ‘yata." Zaytunah ta numfasa sannan ta ce, "Alhaji Uzairu yana son gafara, yana son ganin ‘ya’yansa. Kuma na san cewa yana cikin nadama. Amma ban san ko zan iya yafewa ba." Gwaggo Hafsat ta jinjina kai, tana nazari. "Zaytunah, na fahimci halin da kike ciki. Ba sauƙi a yafe wa wanda ya zalunce ki. Amma kuma idan kika riƙe fushin nan a zuciyarki, waye zai fi cutuwa? Zaytunah ta yi shiru, tana nazari. "Idan kika ba shi dama ya gan su, ba yana nufin cewa kin karɓe shi ba," Gwaggo ta ci gaba. "Kawai yana nufin cewa kina bin tafarkin da Allah ya fi so. Idan har yana cikin nadama, Allah zai hukunta shi bisa gaskiya." Zaytunah ta lumshe idanuwanta. Tana buƙatar tunani mai zurfi. .. A ɗaya ɓangaren kuma, Nabeeha tana zaune a ɗakinta tana nazarin abin da ke faruwa. Tun daga ranar da ta ji labarin gaskiya, take jin zuciyarta tana tafasa. Ba wai tana jin ƙiyayya ga mahaifinta ba, amma tana jin tsoron sake karɓarsa cikin rayuwarsu. Bayan dogon tunani, ta yanke shawarar cewa dole ne ta yi magana da wani. Ta samu Fawaaz yana zaune a cikin falon gidan yana kallon wani bayani a wayarsa. "Yaa fawaaz," ta kira shi a hankali. Ya ɗago, yana kallonta da yanayin da bai nuna komai ba. "Eh?" Ta matsa kusa, ta zauna akan kujerar kusa da shi. "Ina cikin ruɗani. Ban san yadda zan ji game da mahaifina ba." Fawaaz ya ɗora wayarsa gefe, yana mai sauraron ta sosai. "Kin san cewa ke ce za ki zaɓi yadda kike so ki ji?" Ya tambaya. Nabeeha ta kalle shi cikin rashin fahimta. "Me kake nufi?" "Ba dole bane ki karɓe shi cikin dare ba," Fawaaz ya amsa. "Idan kina jin fushi, hakan halal ne. Idan kuma kina jin tausayi, hakan ma halal ne. Amma duk yadda kika zaɓa, ki tabbatar cewa hakan ba zai zama nauyi a zuciyarki ba." Nabeeha ta yi shiru tana nazari. A gaskiya, maganarsa tana da ma’ana. "Duk yadda kike ji, dole ne ya fuskanta," ya ƙara da cewa. "Amma idan za ki gafarta, ki yi domin kanki, ba domin shi ba." Ta numfasa, ta gyada kai. "Zan yi tunani akai." Bayan kwanaki uku, an shirya wata ganawa. Wannan karon, Zaytunah, Nabeeha, Hammad, da Alhaji Uzairu za su hadu. A lokacin da suka iso cikin wani falo mai cike da nutsuwa, zuciyar kowa tana bugawa da sauri. Alhaji Uzairu ya tsaya yana kallonsu da tsantsar nadama a fuskarsa. Nabeeha da Hammad suna zaune kusa da juna, yayin da Zaytunah ke gefe. Ya numfasa, ya durƙusa a gabansu. "Na sani cewa ba zan iya gyara baya ba," ya ce da murya mai rauni. "Amma ina roƙon ku, ku bani dama. Nabeeha, Hammad… ku bani dama in san ku." Hammad ya yi shiru, yana kallon mahaifinsa. "Kana nufin kana so ka zama ɓangare na rayuwarmu?" Uzairu ya ɗaga kai. "Eh, amma ba zan matsa ba. Idan ba ku shirya ba, zan jira." Nabeeha ta dubi mahaifiyarsu. Ta san cewa ita ce ke da yanke shawara. Zaytunah ta numfasa, ta kalli Alhaji Uzairu da ido. "Ka riga ka yi barna da yawa," ta ce a hankali. "Ba za a iya gyara baya ba. Amma ba zan hana ka ganin ‘ya’yanka ba." Uzairu ya ji wani nauyi ya sauka daga zuciyarsa. Hammad ya numfasa, sannan ya ce, "Ina son na san ka. Amma zai ɗauki lokaci kafin na iya mantawa da komai." Nabeeha ta kalle shi, sannan ta dubi mahaifinsu. "Ni ma haka nake ji." Uzairu ya gyaɗa kai, hawaye na taruwa a idanuwansa. "Nagode. Wannan damar ce babba a gare ni." A wannan rana, an ɗora tushen wata sabuwar rayuwa. Ba wai komai zai dawo kamar da ba, amma a kalla, an fara mataki na gafara da fahimtar juna. Akwai sauran rina a kaba. Amma lokaci ne zai nuna yadda abubuwa za su kasance. Bayan taron da suka yi da Alhaji Uzairu, zuciyar Zaytunah ta cika da tunani. Ko da yake ta ba shi dama ya riƙa ganin ‘ya’yansa, hakan bai sauƙaƙa mata raɗaɗin abin da ya faru a baya ba. Tana zaune a ɗakinta, tana kallo daga tagar da ke fuskantar lambun gidan. Hasken yamma yana haskaka fuskar ta. Tana jin wani abu mai ƙuna yana yawo a KIRJIN ta, tunani ne, shakku ne, da kuma wasu ƙananan jin daɗi da ba ta san ta yaya suka zo ba. Major General Dawud ya shigo cikin ɗakin a hankali. Bai ce komai ba har sai da ya zauna kusa da ita. "Zaytunah, me kike tunani?" Ya tambaya da natsuwa. Ta ɗanyi jim, kafin ta amsa. "Ina tunanin ko da gaske Uzairu yanaa nadama." Major General ya lumshe ido na ɗan lokaci. "Mutum na iya yin nadama, amma hakan ba yana nufin cewa za a goge abin da ya aikata ba." Zaytunah ta kalle shi. "To yaya zan yi? Ya kamata in gafarta masa gaba ɗaya?" Ya numfasa. "Gafara ba dole ba ce. Amma idan za ki yi, ki yi don ki sami sauƙi a zuciyarki. Idan kuma ba za ki iya ba, to kada ki tilasta wa kanki." Zaytunah ta yi shiru, tana nazari. A bangaren Alhaji Uzairu, zuciyarsa ta kasa samun sukuni. Duk da cewa Zaytunah ta ba shi dama ya ga ‘ya’yansa, bai jin cewa hakan ya wadatar. A daren ranar, sai da ya tattara jikinsa, ya nufi gidan Gwaggo Hafsat. Ya san cewa ita ce wadda ta riƙe Zaytunah tsawon shekaru, kuma tana da matsayi mai muhimmanci a rayuwarta. A lokacin da ya isa, Gwaggo Hafsat tana zaune bisa darduma tana lazimi. Ya tsaya a bakin ƙofa, ya saki ajiyar zuciya. "Shigo, Uzairu," ta ce, ba tare da ta kalle shi ba. Ya matsa cikin ɗakin a hankali, ya durƙusa a gabanta. "Gwaggo Hafsat," ya kira sunanta cikin muryar nadama. "Na san cewa ba zan iya gyara abin da ya faru ba, amma ina roƙonki ki faɗa min, shin akwai wata dama da zan iya samu daga Zaytunah?" Gwaggo Hafsat ta ɗago ido ta kalle shi da tsantsar hikima. "Uzairu, kai ka fi kowa sanin irin zaman da ka yi mata a baya. Idan har za ka iya jira, ka jira. Idan kuma ka san ba za ka iya ba, to ka bar ta da zaman lafiya." Uzairu ya runtse ido. "Zan jira," ya ce da ƙarfi. "Ko da shekara nawa ne, zan jira har sai ta gafarta min." Gwaggo Hafsat ta jinjina kai. "To mu gani." A bangaren Nabeeha da Hammad, har yanzu suna kokarin fahimtar sabon yanayin da suka shiga. A wata rana, suna zaune a cikin falon gidan, kowannensu yana cikin tunani. Hammad ne ya fara magana. "Nabeeha, kin shirya haduwa da mahaifinmu nan gaba?" Ta ɗanyi jim. "Gaskiya ban sani ba. Har yanzu zuciyata tana cike da shakku." Hammad ya gyada kai. "Ni kuwa ina son in san shi, amma bana son in ji kamar muna tilasta miki." Nabeeha ta saki ajiyar zuciya. "Zan yi tunani akai." A daidai lokacin, wani saƙo ya shigo wayarta daga Muhammad (ɗan Hajiya Rumanah). Muhammad: "Ina fata kuna lafiya. Yaya kuke ji game da mahaifinku?" Nabeeha ta kalli saƙon, ta yi jim, kafin ta amsa. Nabeeha: "Ba sauƙi. Amma muna ƙoƙarin fahimta." Muhammad ya dawo da amsa da sauri. Muhammad: "Ni ma har yanzu na kasa fahimtar mahaifiyata. Abin yana da wahala." Nabeeha ta fahimci cewa ba ita kaɗai ce ke cikin matsala ba. A gefe guda, bayan sakin da Uzairu ya musu, Hajiya Rumanah, Ladi da Karama sun tsinci kansu a cikin ruɗani. Suna zaune a wani ɗaki, kowannensu da damuwa a fuska. Ladi ta ce cikin murya mai rauni. "Mun rasa komai." Karama ta gyaɗa kai. "Ba mu san inda za mu dosa ba." Rumanah ta ja dogon numfashi. "Mu muka jefa kanmu cikin wannan hali. Amma har yanzu akwai hanya guda—muna da ɗanmu Muhammad. Dole ne mu same shi, ko da kuwa yana fushi da mu." Dukkansu suka yi shiru. Tabbas, suna bukatar mafita. Amma tambaya ita ce—shin akwai wani lokaci da za a iya gyara wannan lamari? Yayin da kowa ke cikin tunani da fuskantar matsalolinsa, lokaci yana tafiya. Wata sabuwar rayuwa na tafe, amma har yanzu akwai tambayoyi da ba a samu amsarsu ba. Shin Zaytunah za ta iya gafarta wa Uzairu gaba ɗaya? Shin Nabeeha da Hammad za su iya karɓar mahaifinsu? Shin Rumanah, Ladi da Karama za su iya gyara barnarsu? Shin Muhammad zai karɓi mahaifiyarsa bayan asirin da ya tonu? ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:46_ Da dare ne Muhammad ke kallon faifon bidiyon, yana ci gaba da nazari kan abubuwan da suka gabata. Duk da kokarin sa na danne zuciyarsa, zuciyarsa ta kasa jurewa. Ya lumshe ido, hawaye suka sauko masa. A cikin ransa yana jin radadin abin da mahaifiyarsa ta aikata, amma yana ganin shi ne mai laifi. Idan aka dubi fuskar sa kadai, da alama za a iya hango wannan laifi da mahaifiyarsa ta aikata. Kunya ce ta lullube shi gaba daya. Idan kaka duba fuska, zai iya ganin laifin da mahaifiyarsa ta tafka a bayyane. Don haka, ya yanke shawarar hakura da auren Nabeeha. Yana jin faduwar zuciya, amma yana son a yafe wa mahaifiyarsa, don haka sai ya mike, ya dauro alwala, sannan ya yi sallar nafila domin neman zabin Allah. Yana mai rokon Ubangiji da ya taimaka masa ya dauki wannan mataki da ya dace. Da safe kuwa, yana gama shiri, ya wuce gidan kanin mahaifinsa, wato Alhaji Uzairu, don ya sanar masa da shawarar da ya yanke. A tare da fuskarsa da natsuwa, ya ce. Bayan sun gaysa ne yace da shi, "Kawu Uzairu, na yanke shawarar fasa auren Nabeeha. Ina jin cewa idan na auri Nabeeha, zan zama kamar mai cin amana. Ba na jin cewa zan iya jurewa idan aka tuno wannan lamari a kullum. Don haka, na yanke shawara zan janye." Alhaji Uzairu ya yi shiru na dan lokaci, yana nazarin yadda zai amsa. Daga nan ya nufi wajen yayansa, wato Alhaji Amiru, ya sanar da shi wannan batu. Alhaji Amiru ya ji mamaki, ya danne zuciyarsa kafin ya ce, "Muhammad ya riga ya dauki matakin da yake ganin ya dace, amma wannan abu ba abu ne da za a yi shiru a kansa ba. Dole ne mu tafi mu sanar da su Major General Dawud." Ba tare da bata lokaci ba, suka rankaya zuwa birnin Noka domin ganawa da Major General Dawud. ______ A wannan rana, bayan taron da suka yi a birnin Noka, Zaytunah ta yanke shawarar amincewa da komawa gidan mijinta, Alhaji Uzairu. Duk da haka, ta gindaya sharadi daya, komawarta sai bayan bikin Nabeeha. Gwaggo Hafsat ta kalli Zaytunah cike da tausayi. "Kin tabbatar da cewa kin shirya?" Zaytunah ta lumshe idanu, sannan ta numfasa cikin kwanciyar hankali. "Na riga na yanke shawara. Amma sai bayan bikin Nabeeha." A ranar dinner ɗin su Humyrah, kawayen amaryar sun shirya tsaf, kowacce ta yi ado cikin kwalliyar da ta dace da daren. An tsara cewa tawagar amarya za su shiga tare da abokan ango domin fara shagalin bikin cikin tsari. Tun da aka fara shirye-shiryen tafiya, Nabeeha ta shirya cikin lallausan less na musamman mai kyau da tsari. Kawayenta sun yi ado iri daya da ita, sun sanya kayan da suka dace da yanayin dinner. Amma tun kafin ta fita, Fawaaz ya jima yana kallonta da ido mai nuni da damuwa. Har ta kammala shiryawa, bai ce komai ba, amma idonsa sun bayyana wani abu da ya kasa furta. Da ta gama, ta ɗauki mayafinta ta sanya a kafaɗarta, sannan ta ɗauki wayarta. Dake a parlorn Gwaggo Hafsatu ne.. "Yaa Fawaaz, bari in tafi. Kawayena sun kusa isa wajen." Fawaaz bai amsa ba nan take. Ya ci gaba da kallonta, yana nazarinta tamkar yana son fahimtar wani abu. Bayan wasu ‘yan dakiku, sai ya ce cikin nutsuwa, "Ba za ki shiga tare da su ba." Nabeeha ta zaro ido cikin mamaki. "Me kake nufi? Kawayena ne fa. Kowa zai shiga tare da su." "Ke ba kowace ba ce." Fawaaz ya amsa a takaice. Nabeeha ta cije leɓenta. "To ai ba zan je ni kaɗai ba. Dukkan amaren suna shiga tare da abokan ango. Hakan ne tsarin dinner ɗin." Fawaaz ya gyara zaman rigarsa, ya ɗaura hannu kan cinyarsa, yana kallon ta da wani irin kallo mai cike da ƙarfi. "Nabeeha, na ce ba za ki shiga da su ba. Idan kin isa wajen, ki jira a yi shigar su, sannan sai ki shiga daga baya." Nabeeha ta yi shiru tana nazari. Ta san cewa Fawaaz mutum ne mai kishi, amma bata yi tsammanin zai hana ta shiga dinner tare da tawagar kawayenta ba. "To me zai hana?" Ta tambaya, tana son jin dalilinsa. Fawaaz ya numfasa a hankali, sannan ya ce, "Saboda ba zan so wata guda daga cikin su ya shiga kusa da ke ba. Idan kin shiga da su, wani daga cikinsu zai iya kallon ki da idon da ba na gaskiya ba." Nabeeha ta zaro ido cikin mamaki. "Yaa fawaaz! Me kake nufi? Ai waɗannan abokan angwaye ne!" Fawaaz ya ɗaga gira. "Ban ce kowa ne zai yi hakan ba. Amma ba zan bari wani ya sami dama ya kalle ki da idon da bai dace ba." Nabeeha ta cije baki, amma daga ƙarshe ta fahimci cewa babu fa’ida a cikin jayayya da Fawaaz. Idan ya ce abu, to ya gama yanke hukunci. "To shikenan." Ta amsa, koda ba ta ji daɗin hakan ba. Da suka isa wajen dinner, kawayenta suka shiga tare da abokan ango, amma ita sai da ta tsaya a ƙofar hall din tana jiran su gama shiga kafin ta shige ita kaɗai. Yayinda ta shiga, Fawaaz na zaune a wata kujera, yana kallonta da wani irin kallo mai cike da izza da ikon mallaka. Ta zauna kusa da shi ba tare da ta ce komai ba. Amma zuciyarta ta yi dariya. "Wannan kishi na Fawaaz dai..." Ranar da za a kai su humyrah gidajen aurensu, an shirya siyan baki na musamman. Kamar yadda aka saba, abokan ango ne za su siya bakin kawayen amarya. A lokacin da ake shirin wannan al’ada, Nabeeha tana zaune cikin ɗakin shiryawa, tana jiran lokacin da za a kira su su fito. Kawayenta sun hallara, suna dariya da raha, suna jiran lokacin da za a fara siyan baki. Amma kafin su tafi, sai Fawaaz ya shigo cikin ɗakin da wani irin yanayi na girmamawa da iko. Kallo ɗaya za ka masa ka san cewa akwai wani abu da yake so ya faɗa. Nabeeha ta kalle shi tana murmushi. "Ya fawaaz, me kake yi a nan? Ai yanzu za a fara siyan baki." Ya kalleta da ido mai zurfi. "Ba za ki zauna a wajen siyan bakin ba." Daga inda take zaune, ta ɗago tana kallonsa da mamaki. "Me kake nufi?" "Ba zan bari wani ya tsaya yana ‘yan kace-nace da ke ba. Wannan abu ba ya min daɗi." Nabeeha ta zaro ido. "Kai dai kana da matsanancin kishi! Ai hakan ya zama al’ada. Kuma dukkannin amaren suna yin hakan." Fawaaz ya ɗan matsa kusa da ita, ya zauna gefenta, yana kallonta da ido mai cike da tsaro. "Ke ba kowace kawar amarya ba ce. Ke mallaki na ce. You're mine and mine only" Nabeeha ta yi shiru tana nazarin yadda zai kaya. Ta san Fawaaz ba mutum bane mai sauƙin shawara idan ya yanke hukunci. "To amma..." Ta fara magana, amma ya katse ta. "Ba wani ‘amma.’ Ki zauna a nan har sai an kammala komai." Daga waje, an fara siyan bakin. An fara raha da zolaya tsakanin abokan ango da kawayen amarya. Sai dai Nabeeha, babbar amarar da ya kamata ta kasance a wajen, tana zaune cikin ɗakin shiryawa, tana murmushin takaici. Kawayenta suna ta nemanta, amma ana cewa ta yi shiru tana dariya kawai. Duk da haka, babu wadda ta fahimci cewa Fawaaz ne ya hana ta fitowa. Bayan an kammala komai, sai Fawaaz ya mike, . "Za mu tafi?" Ta kalle shi, tana girgiza kai cikin murmushi. "Kai fa akwai matsala." Ya ɗan kalleta a hankali. "Matsala kamar yaya?" Ta girgiza kai. "Matsalar kishi. Kishi kamar na soyayyen jan nama." Fawaaz ya ɗaga gira, yana kallonta da kallo mai ma’ana. "Kishi na wajibi ne. Idan ban miki kishi ba, wane zai miki?" Ta cije leɓe, sannan ta ce cikin raha. "Ai haka ne. Amma ka rage mana kaɗan." Ya girgiza kai yana dariya. "Ragewa ba zai yiwu ba." Da haka suka fita, suka nufi motar da za ta kai su, Nabeeha na jin cewa rayuwa da Fawaaz ba za ta kasance mai sauƙi ba, amma za ta kasance cike da so da kulawa. Fawaaz ya kalleta kafin su shiga mota. "Na gaya miki cewa zan kula da ke, ko?" Ta gyada kai. "Eh." "To ki sani, in har ina son ki, ba zan bari wani ya zo kusa da ke da wata manufa ba." Nabeeha ta yi murmushi. Ta san cewa Fawaaz ba zai taɓa canzawa ba. Kuma wata zuciyarta na jin daɗin hakan. 🎀🎀🎀 Yayin da suke zaune a babban zauren gidan Major General Dawud, an hallara gaba daya, har da Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru. Zancen da Muhammad ya fada yana ci gaba da mamaye tunanin kowa. Sai dai kafin su yanke hukunci na karshe, sai Fawaaz ya durkusa cikin mutuntawa bayan sun gaisa. Dukkan idanu suka sauka a kansa. "Ina neman alfarmar a bani auren Nabeeha." Kowa ya kalli juna da mamaki. Gwaggo Hafsat ta dan runtse ido kamar mai nazari. Major General Dawud ya jinjina kai, yana kallon dansa da basira. Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru suka kalli juna, sannan suka dubi Major General Dawud don jin ra'ayinsa. Wannan batu ya dauki hankalin kowa, don haka dole ne su dauki lokaci kafin su yanke shawara. Amma abu daya ya bayyana wannan rana rana ce mai cike da yanke manyan shawarwari! ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:47_ Wurin ya dauki shiru bayan Fawaaz ya bayyana bukatarsa. Kowa ya dauki lokaci yana nazarin kalamansa. Idan aka duba halinsa na miskilanci da kamun kai, ba kowa zai yi tunanin cewa zai fito fili ya nemi auren Nabeeha ba. Major General Dawud ya kalli dansa cike da zurfin tunani. Wannan mataki da Fawaaz ya dauka ba karamin abu ba ne. A gefe guda, Gwaggo Hafsat ta kalli Zaytunah, wadda ta dafa habarta cikin nazari. Haka ma Alhaji Amiru da Alhaji Uzairu, duk suna jiran jin ra'ayin iyayen Nabeeha. Zaytunah ta numfasa, sannan ta dubi Fawaaz. "Kana da tabbacin wannan shawarar da ka dauka?" Fawaaz ya dago idonsa, yana kallon mahaifiyar Nabeeha da mutuntaka. "Eh, aunty. Ba zan yi magana da ku ba sai da na tabbatar da cewa zuciyata ta yanke hukunci. Idan Allah ya bani dama, zan kula da ita da dukkan mutuntawa da soyayya." Gwaggo Hafsat ta kalli Major General Dawud. "Dawuda, yaronka ya fito da bukatarsa. Mene ne ra'ayinka?" Major General Dawud ya gyara zamansa, yana duban danta kai tsaye. "Na san halin Fawaaz. Ba mutum bane da yake daukar mataki cikin gaggawa. Idan har ya yanke shawara, to yana nufin ya rigaya ya yi nazari mai zurfi." Sai dai, har yanzu akwai matsala guda, yadda za a sanar da Nabeeha da kuma yanke shawarar amincewa da hakan ko akasin haka. Zaytunah ta dubi Gwaggo Hafsat, sannan ta ce, "A ganina, ya dace a ji ra'ayin Nabeeha kafin a dauki wani mataki. Wannan abu ne da ya shafi rayuwarta gaba daya." Gwaggo Hafsat ta jinjina kai. "Hakan ne dai. Bai kamata mu tilasta mata ba." --- Bayan an gama wannan zama, sai aka yi shawarar cewa za a kira Nabeeha don jin ra'ayinta. Ana so a tabbatar da cewa ba za a yi mata dole ba, kuma za a yi abu ne cikin natsuwa. A gefe guda, Muhammad da kansa yana nazarin abubuwa a zuciyarsa. Shin zai iya jurewa ganin Nabeeha da wani? Duk da cewa ya yanke shawarar hakura da ita, amma zuciyarsa ba ta da sauki. A gefe guda kuma, Fawaaz yana da natsuwa, amma yana jiran jin amsar Nabeeha. Shi kansa ya san cewa ba lallai ta amince ba, amma yana fatan Allah ya zaba masa mafi alheri. Zaytunah da kanta ta tafi sashen Nabeeha don sanar da ita wannan batu. "Nabeeha, akwai maganar da muke bukatar jin ra'ayinki a kanta." Nabeeha ta dago da mamaki. "Mene ne Ammi?" Zaytunah ta dan yi shiru na wasu sakanni, sannan ta dubi ‘yarta ido da ido. "Fawaaz ya fito da bukatar auranki." Nabeeha ta zaro ido! "Ni? Da Fawaaz?" Numfashinta ya dan tsaya na wani lokaci. Hankalinta ya tashi. Wannan abu ne da ba ta yi tsammani ba... Nabeeha ta zaro ido tana kallon Zaytunah tamkar ba ta jin daidai. Kamar dai bata fahimci abin da Ammi ta faɗa ba. "Ni? Da Fawaaz?" Ta maimaita tamkar tana son tabbatarwa idan da gaske take. Zaytunah ta numfasa, sannan ta gyara zama. "Eh, Fawaaz da kansa ya zo ya nemi auranki. Amma muna son jin ra'ayinki kafin a dauki mataki." Nabeeha ta janye hannayenta daga cinyarta tana danne cikin. Wani irin faduwar gaba ta ji, zuciyarta na bugawa da sauri. Ko da yake ta san Fawaaz mutum ne mai kamun kai da miskilanci, bata taba zato ko a mafarki cewa zai zo da irin wannan bukata ba. Ta dago idanunta tana kallon Zaytunah. "Ammi... ya aka yi hakan ya faru? Me ya sa?" Zaytunah ta yi murmushi mai taushin gaske. "Shi ne zai fi dacewa ya baki amsa. Amma kafin nan, ina so ki yi tunani sosai. Kada ki amince saboda matsin lamba, kada kuma ki ki saboda mamaki. Ki nemi zabin Allah." Hankalin Nabeeha ya cunkushe, bata san ta yaya zata ji ba. A gefe guda, tana mamakin yadda hakan ya faru. A wani bangaren kuma, zuciyarta ta soma tunanin halin da Muhammad yake ciki. Shin yana da masaniya? Ya yarda da wannan hukunci? Bata san abin da zata ce ba. A gefe guda, Muhammad yana tsaye a barandar gidan yana kallon sararin sama. Tunani yake, zuciyarsa tana cike da ruɗani. Bai taba tunanin cewa rayuwa zata juya haka ba cikin lokaci kaɗan. Kamar yadda aka saba, ba a boye wannan lamari daga Muhammad ba. Yana zaune a falo tare da Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru lokacin da suka fara tattauna cewa Fawaaz ya fito da bukatar aurar Nabeeha. Ya dan sake rike gefen kujerarsa, zuciyarsa na bugawa. Wani irin sanyi ya ratsa shi, amma bai ce komai ba. Bai daga kansa ba, kuma bai nuna wata alama cewa hakan ya dame shi ba. Alhaji Uzairu ya kalle shi a hankali. "Muhammad, baka ce komai ba." Muhammad ya dan gyara zama, yana kokarin danne abin da ke ransa. "Ba komai Kawu. Idan har hakan ne mafi alheri, to Allah ya yi zaɓi mafi kyau." Duk da cewa yana da dauriya, zuciyarsa na bugawa da raɗaɗi. Bai taba tunanin cewa wani zai nemi aurar Nabeeha ba da wuri haka. Amma ya riga ya yanke shawara, ya zabi hakuri. "Allah ya sanya alheri." Shi kadai ne kalmomin da ya iya furtawa. Bayan shiru mai tsawo, sai dai da kyar Nabeeha ta iya kwantar da zuciyarta. Idanun Zaytunah sun cika da kulawa yayin da take kallon ‘yarta. Ta shafa gefen kumatun Nabeeha cikin taushin zuciya. "Ki yi sallah ki nemi zabin Allah." Haka kuwa aka yi. Bayan dare ya yi, Nabeeha ta zauna ta yi addu'a, tana neman jagoranci daga Allah. Har zuwa lokacin da asubah ta gabato, bata da tabbas akan abin da zata yanke. Washegari kuwa, an shirya zaman da za a zauna su fuskanci juna. A cikin babban falon gidan Major General Dawud ne aka zauna, kowannensu yana a zaune cikin nutsuwa. Major General Dawud yana daga gefe, yayin da Gwaggo Hafsat ke kusa da shi. Alhaji Amiru da Alhaji Uzairu suna cikin hallarar. Nabeeha ta shigo cikin ladabi, zuciyarta na bugawa da sauri. Da kyar ta iya kallon fuskar Fawaaz. Shi kuwa yana zaune cikin kamun kai, yana kallon kasa. Duk wani motsi da ke cikin falon yana da nauyi. A ƙarshe, Gwaggo Hafsat ta gyara zamanta, sannan ta dubi Nabeeha da Fawaaz. "Mun kira ku nan don ku fuskanci juna. Saboda aure ba abu ne na wasa ba. Fawaaz, ka bayyana ra'ayinka, sannan Nabeeha ma ta bayyana nata." Fawaaz ya dago kansa a hankali. Idanunsa sun hadu da na Nabeeha na wasu sakanni kafin ya mayar da su kasa. Sannan ya fara magana cikin muryarsa mai natsuwa. "Na san ba zato ba tsammani ne a gare ki, Nabeeha. Amma da gaske nake da bukatarki a matsayin matata. Ba na so ki yanke shawara don wani matsin lamba. Ki yi tunani, ki yanke shawarar da kike jin zata fi dacewa da ke." Shiru ya biyo bayan maganarsa. Kowa ya juya ga Nabeeha don jin amsarta. Nabeeha ta runtse ido, tana jin bugun zuciyarta yana karuwa. Shin wane irin amsa zata bayar? Shiru ya mamaye falon bayan Fawaaz ya gama maganarsa. Duk wanda ke wurin yana jiran jin martanin Nabeeha. Nabeeha ta ji yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Ba ta taba tunanin cewa rayuwarta zata shiga irin wannan yanayi ba. A da, ta yi tunanin cewa komai ya karye lokacin da Muhammad ya fasa aurenta. Amma yanzu, ga wani sabon al’amari da ya taso. Ta dago a hankali, idanunta suka hadu da na Fawaaz, wanda ya kasance cikin nutsuwarsa. Da kyar ta iya hada kalmomi, amma ta daure ta furta. "Ban taba tunanin cewa Fawaaz zai zo da irin wannan bukata ba. Kuma gaskiya har yanzu ban san abin da zan ce ba." Ta numfasa, sannan ta ci gaba: "Amma, kamar yadda Ammi ta ce, aure abu ne da ake bukatar mutum ya yi tunani sosai a kansa. Don haka, ina bukatar lokaci domin na yi shawarwari da kaina, kuma na nemi zabin Allah." Fawaaz ya jinjina kai cikin fahimta. "Ina jin hakan ya fi dacewa, Nabeeha. Ki dauki lokaci ki yi tunani." Gwaggo Hafsat ta kalli sauran mutane a falon, sannan ta ce: "To, babu matsala. Zamu ba ki lokaci don ki yi tunani. Amma fa, kada ki dauki lokaci mai tsawo. Domin al’amari na bukatar yanke hukunci." Nabeeha ta girgiza kai. "In sha Allah, ba zan dauki lokaci mai yawa ba." --- A gefe guda, Muhammad yana cikin dakinsa, zuciyarsa cike da tunani. Duk da cewa ya fasa auren Nabeeha da kansa, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Shin da gaske ya hakura? Ko kuwa zuciyarsa na jin zafin ganin wani zai karɓi Nabeeha? Yana zaune a bakin gado, yana jujjuya wayarsa a hannunsa. Ya ji kamar ya kira Nabeeha, amma sai ya fasa. Bai san me zai ce mata ba, bai san yadda zata ji ba. A ƙarshe, ya dafe kansa. "Allah Ka yaye min wannan ruɗani." Bayan kwanaki biyu na addu’a da tunani, Nabeeha ta yanke shawara. Tana zaune a dakinta, zuciyarta na cikin natsuwa. Ta riga ta san abin da take so. Da yamma, ta samu Ammi a cikin dakin ta ce mata, "Ammi, na gama tunani. Na yanke shawara." Zaytunah ta dago da mamaki. "Masha Allah. Mene ne shawarar ki?" Nabeeha ta numfasa sannan ta ce: "Na amince da auren Fawaaz." Zaytunah ta kalli ‘yarta cike da farin ciki. "Kin yanke hukunci ne da zuciyarki? Ba matsin lamba ba?" "Eh, Ammi. Ba matsin lamba ba. Na yi sallah, na nemi shawarwarin zuciyata, kuma na yarda cewa Fawaaz zai iya zama abokin rayuwata." Zaytunah ta yi murmushi, sannan ta shafa kan ‘yarta. "Allah Ya sanya alheri, ya ba ku zaman lafiya mai albarka." --- An shirya zaman yanke hukunci a falon Major General Dawud. Duk dangin Nabeeha da Fawaaz sun hallara. Da kowa ya hallara, Gwaggo Hafsat ta dubi Nabeeha da kulawa. "Nabeeha, mun zo don jin amsar ki. Kin yanke shawara?" Nabeeha ta dago, ta kalli Gwaggo Hafsat, sannan ta juya tana kallon Fawaaz. Idanunta sun cike da kwanciyar hankali. A ƙarshe, ta furta cikin murya mai kwari, "Na amince da auren Yaya Fawaaz." A cikin dakin, an ji numfashin kowa ya sauka. Fawaaz ya dan lumshe ido, zuciyarsa cike da godiya. Duk da miskilancinsa, a wannan lokacin ya ji zuciyarsa tana cike da farin ciki fiye da yadda ya zata. Gwaggo Hafsat ta yi murmushi, sannan ta ce, "To, Alhamdulillah. Allah ya sanya alheri. To yanzu, sai a fara shirye-shiryen biki!" A gefe guda, Muhammad yana zaune yana jin wannan magana. Ya lumshe ido, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Yanzu da komai ya kammala, shin zai iya jurewa? Ya yi murmushin dole, sannan ya furta a ransa, "Allah ya sanya alheri." ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:48_ Bayan amincewar Nabeeha da auren Fawaaz, shirye-shiryen biki suka dauki zafi. Kowa ya shiga cikin damuwa da gudanar da abubuwan da suka kamata don ganin an yi bikin cikin nasara. Gwaggo Hafsat ce ta dauki ragamar tsara al’amura. Ta zauna da Hajiya Hawwa Maijidda, mahaifiyar Fawaaz, domin tattaunawa kan lokacin da za a yi aure da yadda za a tsara hidimar bikin. Duk da cewa a baya Hajiya Hawwa ba ta ji dadin kasancewar Zaytunah a gidan ba, sai da aka kai ga wannan mataki, ta fara sakin jiki da yanayin. Bayan tazo gidan halartar bikin dan nata. Ma'ana an gayyaceta kan shirye shiryen da zasuyi kasancewar ta uwa ga ango fawaaz. An sanya bikin cikin wata biyu. An fara shirin saya wa Nabeeha kayan daki, kayan sawa, da sauran bukatun amare. Haka kuma, Fawaaz da kansa ya fara nasa shirye shiryen ba kama hannun yaro... Bikin Nadia kawar su aka farayi, wato yar makociyar su da suka tashi tare tun suna kanana.. Ranar da aka daura auren kawarsu Nadia, Nabeeha ta shirya cikin doguwar shadda mai kyau, riga da skirt masu launin lilac da zinariya. Ta daura gyale mai launin fari wanda ya ba ta wani irin kyau na kwarai. Tana shirin fita tare da Nadia sai ta ji kira. Ta duba waya, Fawaaz ne. "Ina za ki?" Ya tambaya da wata murya mai tsauri. "Zan tafi yinin ɗaurin aure mana. Ka ce idan baka samu zuwa ba zan tafi da su" "Ba tare da ni ba? Ba ki ga matsalar hakan bane?" Nabeeha ta ja numfashi. "Yaa Fawaaz, dai-dai nake da sauran matan da za su tafi. Ba fa wani abu bane." "Babu wani ‘dai-dai.’ Kin fi su daraja a gare ni." Tayi murmushi. "To yanzu ka bani izini ko kuwa?" Ya yi shiru na ƴan sakanni. "Bari in yi tunani." Nabeeha ta dafe kanta. "Tunani? Akan fita ɗaurin aure?" A ƙarshe, ya amince, amma da sharadi. "Ki tsaya cikin mutuncinki. Kada ki yi wata mu'amala da wani namiji da ba dole ba. Ki kula da abinda kike yi. Ki turo min location." "Na ji." Ta ce tana murmushi. "Kiyi kyau sosai, amma kada ki burge kowa sai ni." Nabeeha ta yi dariya. "To ai ko da na so ba zan iya burge kowa ba sai kai." "Kin gane mana." A cikin wurin taron, an tsara komai cikin tsari. Mata sun zauna a gefe guda, maza a gefe guda. Amma a wajen siyan baki, an haɗa matan amare da abokan ango. Sajieedah ta ja hannun Nabeeha. "Mu je mu tsaya kusa da amarya. Daga baya sai a fara siyan bakin." Nabeeha ta fara tafiya da ita, amma kafin su isa, sai taji ƙarar waya. Fawaaz ne! Ta ɗaga da sauri. "Hello?" "Ina kike?" Muryarsa ta sauya, kamar yana canza yanayi. "Ina wajen bikin mana, kamar yadda na gaya maka." "Dama kuna siyan baki da abokan ango ne?" Nabeeha ta rufe ido. "Ya fawaaz… Ni ba ma cikin su fa." "Ki fita daga wajen nan. Ba na son ki zauna kusa da su." "To!" Ba tare da wata gardama ba, ta ja hannun sajieedah suka koma gefe. Sajieedah ta kalleta cike da mamaki. "Nabeeha! Wane irin saurayi me kishi ne haka?" Nabeeha ta yi murmushi. "Wannan kishi ne mai daraja. Ki barshi kawai." Bayan wani lokaci, sajieedah ta kalli gefe, sai ta hango wani mutum yana kallon Nabeeha. "wani saurayi yana kallonki!" Ta ce tana dariya. Nabeeha ta girgiza kai. "Wani kuma?" Duk da ba ta kula shi ba, sai da taji ƙarar waya. Fawaaz ne! Ta ɗaga da sauri. "Ina jin ka." "Wani ne yana kallonki?" Muryarsa ta canza gaba ɗaya. Ta haɗiye yawu. "Ban sani ba." "To koma gida." Ta zabura. "What?!" "Nace ki koma gida! Ko sai nazo na same ki yanzu?" Nabeeha ta sunkuyar da kai, ta ɗan murmusa. "Toh, zan koma." A haka dai, ta bar bikin kafin kowa ya ankara! Bayan ta koma gida, tana shiga ta tarar da Fawaaz yana zaune a falo. "Kin fiye kyau da yawa." Ya ce yana kallonta da kulawa. Ta zauna a gefensa, tana kallonsa da murmushi. "Na san dai baka barni na yi farin ciki a wajen bikin ba." Ya ɗauki hannunta. "Ba zan so wani ya kalle ki da niyya ba." Ta yi murmushi. "Kai fa akwai matsala!" Ya yi dariya, ya zuba mata ido da tsananin kulawa. "Kiyi hakuri, my queen. Kishina ne kawai." Nabeeha ta gyada kai. "Na san hakan. Kuma na yarda da kai." A haka dai rayuwa da Fawaaz ke tafiya—cike da soyayya, kulawa, da kuma matsanancin kishi! Bayan kwanaki, Nabeeha ta fara fahimtar cewa Fawaaz ba mutum ba ne mai sauƙin shawara idan har maganar kishinsa ce. A duk inda suke fita tare, yana da wani irin saurin lura da kallo ko motsi da wani namiji zai yi a kanta. Ranar da Ta Fita Ba tare da Izinin Fawaaz ba Wata rana, bayan Fawaaz ya fita zuwa aiki, Nabeeha ta kira saj don su fita zuwa boutique don yin siyayya. Tana tunanin cewa idan ta koma kafin Fawaaz ya dawo, ba zai sani ba. Ta shirya cikin doguwar riga mai kyau da hijabi. Ba ta yi wata kwalliya mai nauyi ba, amma duk da haka ta kasance cikin wani irin kyau na halitta. Suna tafiya a cikin boutique suna duba kaya, sai wani mai siyar da kaya ya kalleta da murmushi. "Madam, wannan kayan ya yi miki kyau sosai. Ya kamata ki ɗauka." Humairah ta kalle ta tana murmushi. "Lallai kuwa! Nabeeha, ki sayi wannan kayan." Nabeeha ta ɗauki rigar tana nazari, amma kafin ta ce komai, sai taji wata murya daga bayansu. "Ki ajiye kayan, ki zo mu tafi." Gabanta ya faɗi. Tana juyowa, sai ta ga Fawaaz yana tsaye a ƙofar boutique ɗin, hannuwansa a haɗe, idonsa cike da tsawa. Tayi shiru na ƴan dakiku kafin ta ce cikin sanyin murya. "Fawaaz… ka dawo kenan?" Ya ɗan tsuke fuska. "Ba ma haka ba. Me kike yi a nan?" Ta kalli saj da ke kallonsu da mamaki. Sai kuma ta ce cikin damuwa. "Na fita ne kawai don yin siyayya." Fawaaz ya kalli mai siyar da kaya, yana hura hanci kamar zai ƙone da wuta. Sannan ya dawo da kallonsa kanta. "Wato kin fita ba tare da izini na ba? Kuma wani yana yi miki murmushi yana cewa wannan kayan ya miki kyau?!" Nabeeha ta buɗe baki zata yi magana, amma sai ya ce: "Mu tafi, yanzu!" Tayi shiru, ta sauke rigar hannunta sannan ta bi shi da sauri. Saj ta bita da kallo cike da mamaki da sha’awa. A cikin mota, babu wanda ya yi magana. Sai dai Fawaaz yana tuka motar da wani irin ƙarfin hali, yana riƙe sitiyari tamkar zai balla shi. Bayan sun isa gida, sai ya tsaya yana kallonta da ido mai cike da kishi. "Wani ne ya taɓa ki?" Ta zaro ido. "A’uzu billah! Ya Fawaaz! Me kake nufi?" "Wani ne ya ce yana son ki?" Ta saki baki da mamaki. "Kai fa akwai matsala! Ba wanda ya ce haka!" Ya harare ta. "To me ya sa ya ce miki wannan kayan ya miki kyau?" Ta taɓe baki. "Ai hakan ba laifi bane. Yana siyar da kaya ne, ya kamata ya faɗi hakan." Fawaaz ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallonta da tsantsar kulawa. "Ki kula, Nabeeha. Ba zan yarda wani namiji ya kalli matata da wata manufa ba." Kai kace an shafa fatiha yadda yake nuna ikonsa akanta 🤣 Ta yi murmushi. "Fawaaz, kana da matsanancin kishi." Ya yi murmushi shima. "Ba matsananci ba, sai dai na gaskiya." 🎀🎀 A nutsuwar dare mai annuri, tsit ya lullube anguwar da ake kyalli da fitilu, iska mai laushi na kadawa kamar tana busa saƙon wata soyayya da ke ɓoye. A gaban wani babban gida, wata bakar Jeep mai kyan gaske ta faka a gefen hanya. Wani saurayi tsaye a cikin motar, hannunsa na dama na bisa steering, na hagu kuma yana jan wayarsa don kiran wata ‘yar baiwa. Captain fawaaz. Cikakken mutum ne, dogo, mai murɗaɗɗen jiki irin na sojoji. Fuskar tasa cike take da kwarjini da miskilanci, amma yau idanunsa sun zubo da wani yanayi mai cike da salo. Yana sanye da bakar riga mai nauyin gaske, wadda ta kwanta ajikinsa, sai wando jeans mai tsari da sneakers na designers. Lallausan gashinsa yana kwance a saman goshinsa, idonsa masu kauri da tsantsar baƙi suna haskawa da natsuwa, lebensa yana ɗauke da ƙanƙantar murmushi. Ya danna kiran. Daga can cikin gida, Nabeeha na zaune akan gadonta, cikin farin riga ta shadda mai tsabta, wadda ta zauna luf akan ta. Gashinta a daure cikin style mai kyau, sai ta lulluba da mayafi irin na ladabi. Idonta suka sauka kan sunan da ya bayyana akan wayarta. "Captain Fawaaz Dawud." Kamar an danna mata wutar lantarki haka ta ji, zuciyarta ta buga, amma ta ɗauki wayar cikin sanyin jiki. "Ina kika shiga?" Muryarsa mai daɗi da ƙara wa zuciya sauti ya fita daga wayar. "Uhmm… ina daki." Ta amsa a hankali. "Fito ki zo." Shiru ta ɗan yi, kafin ta tashi da natsuwa, zuciyarta na harbawa da nau’in wata soyayya da ta kasa fassara. Har ta ƙarasa bakin kofa, tana jin yadda numfashinta ke sauyawa. A hankali ta ƙarasa inda motarsa take, tana taku cikin cika alkawarin mace mai haiba da kamun kai. Fawaaz yana kallonta ta cikin madubin motarsa, yadda take tafiya da nutsuwa, yadda hasken fitilu ke bayyana kyanta, har sai da ya ɗan ja numfashi. Da isarta kusa da motar, ya buɗe ƙofar gaba, ya watsa mata wani kallo na ƙwarjini. "Shigo." Ba tare da wata gardama ba, ta shigo, numfashinta na luguden wata dabara da zuciyarta ke kokarin ɓoyewa. Ya juyo gareta, ya sauke idanunsa cikin nata, sannan ya ɗan lumshe su kafin ya ce, "Kin san ba zan kira ki na ce ki fito haka kawai ba, ko?" Ta ɗan haɗiye yawu, tana jinsa da kasala. Ya ɗan ɗaga gira, yana kallonta kamar yana nazarinta. "Nabeeha… kin taɓa jin ana soyayya da zuciya amma baka san ta ina za ka fara furta kalmomin ba?" Numfashinta ya tsinke. Ta kalli gefe. "Ba…" Muryarta ta makale. Ya saki murmushi, mai ɗan ƙanƙantar gaske, sannan ya ce, "Ina fargabar gaya miki abubuwa da yawa, domin zuciyata tana da SIRRI ka da yawa. Amma daya daga ciki shine…" Ya ɗan yi shiru, yana kallonta. "Kullum ina tunanin ki." Nabeeha ta runtse idonta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke, amma bata iya cewa komai ba. Fawaaz ya ci gaba. "Kina yi min yawa, Nabeeha. Idan kina kusa da ni, zuciyata na yin wani iri. Idan ba ki kusa, zuciyata na jin wani iri. Me kike so inyi da kaina?" Tayi shiru, tana jin yadda kalmominsa suka daki zuciyarta. Fawaaz ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon fuskarta da ido mai cike da wani sirrin soyayya. "Kin san tun farko bana tunanin zan iya cewa haka? Amma yanzu ba zan iya ɓoyewa ba." Ya sauke wani numfashi, ya ɗan yi ƙasa da murya. "I love you, Nabeeha." Wani irin abu ya tsarga a zuciyarta, idanunta suka lumshe, zuciyarta na dokawa kamar ana bugun ganga. Ya juyo sosai gareta, yana jira ta ce wani abu. Amma ta yi shiru. Fawaaz ya ɗan yi murmushi mai taushi. "Ba sai kin ce komai ba. Amma ki sani… zuciyata ta faɗa cikin wani launi da bai taɓa sanin sa ba saboda ke." Shiru ne ya mamaye motar, sai kukan zuciyoyi biyu da ke tafiyar da soyayya cikin shauki. MX 🧕 *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:49_ Shiru ne ya wanzu a cikin motar, amma zuciyoyi biyu na bugawa da wani irin kida mai nauyi. Idon Nabeeha har yanzu yana lumshe, tana jin kamar a mafarki ake furta mata kalmomin da suka gama ratsa tsokar zuciyarta. Ita ce? Ita ce wadda Fawaaz ke furtawa irin wannan zance? Ita ce zuciyarsa ke kira da son a kusa? Tayi shiru, ba don bata da amsa ba, sai don bata san da wanne zance za ta fara ba. Fawaaz ya jinjina kai kadan, yana kare mata kallo. Wani murmushi mara sauti ya sake, sannan ya ce, “Kin san me yasa na kira ki ki fito?” Ta yi saurin ɗago ido, ta kalle shi. Kallon da ya cika da tambayoyi. Ya ɗan ja numfashi, yana kallon ta kai tsaye. “Saboda bana iya kwana yau idan ban ji muryarki ba. Idan kika yi shiru kamar haka, zuciyata na jin wani iri.” Nabeeha ta sauke idanunta kasa, wani abu na tsarga a cikin zuciyarta. Fawaaz ya matsa kadan, ya jingina hannunsa kan kujera, yana fuskantar ta sosai. “Nabeeha, kin san lokacin da na fara son ki?” Ta girgiza kai a hankali. Ya saki murmushi. “Tun farko, tun lokacin da kika fara zama a cikin gidanmu. Tun lokacin da nake yi miki kallon wata yarinya da bata ma san yadda take a zuciyar wani ba.” Zuciyarta ta buga. Fawaaz ya ci gaba, murya a hankali, amma da zurfi. “Duk sanda na ganki da murmushinki na nutsuwa, zuciyata na bugawa. Duk lokacin da kika shigo inda nake, sai na tsinci kaina da jin wani abu da bana iya fassara wa.” Ta lumshe ido, tana jin yadda muryarsa ke saukar mata kamar iska mai daɗin gaske. “Kin taba ganin mutum da yake da tsananin soyayya, amma yana jin tsoron furtawa?” Ya yi murmushi, yana kallonta. “Ina jin tsoro, Nabeeha. Amma na gaji da tsoro.” Ta ɗago idonta, suka haɗa ido. Muryarsa ta yi ƙasa, “Idan zan zama maras gaskiya, to zan ci gaba da ɓoyewa. Amma idan ina so na kasance mai gaskiya… to na san cewa son ki ba abin ɓoyewa ba ne.” Numfashin Nabeeha ya ɗauke na wuni. Duk da yadda take jin zuciyarta na tafasa da wani iri, sai ta samu kanta da cewa, “ya fawaaz… baka tsoron cewa… idan muka biye wa zuciya, wata rana za ta cutar da mu?” Fawaaz ya ɗan saki murmushi mai cike da kauna. “Nabeeha… idan zuciyata zata cutar da ni saboda ke, to na amince.” HANKALIn ta ya tsaya. Idanunta suka cika da wani irin yanayi mai wuyar fassara. Shi kuwa Fawaaz, ya matsa kadan, yana kallonta kamar yana son karanta zuciyarta. “Amma kafin wannan, ki gaya min abu guda daya.” Tayi shiru. Ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya buɗe su cikin wata murya mai taushi. “Kin taɓa jin kamar zuciyarki tana da wani abu da take so ta faɗa min?” Hannunta ya matse a cikin rigarta. Sai dai bata san me za ta ce ba. Fawaaz ya ɗan matsa kaɗan, ya ɗaga hannunsa ya shafi steering, yana kallonta. “Ba sai yanzu ba. Ba sai yau ba. Amma zan jira.” Ya kai hannunsa ya danna makullin motar, sannan ya ce, “Amma kafin nan, ina so ki sani…” Ta juyo tana kallonsa, tana jiran jin abinda zai ce. Ya saki murmushi. “Zuciyata ta riga ta yanke shawarar inda take so ta tsaya. Kuma wannan wuri… shine ke, Nabeeha.” Jikinta ya yi sanyi, zuciyarta ta yi wani irin harbi. Shiru ne ya sake cika motar. Amma shiru mai cike da launin soyayya da murmushin zuciya... Shiru mai nauyi ya wanzu a cikin motar. Idanun Nabeeha suna ƙasa, zuciyarta na dokawa da ƙarfi, hannunta na lafe a kan cinyoyinta. A karon farko a rayuwarta, ta ji kalmomin da suka ɗaga mata hankali fiye da tunaninta. Kalaman soyayya ne, amma ba irin na wasanni ba. Na gaske ne. Na zuciya ce da ta tsinci kanta a cikin wani soyayyen wuri da bata taɓa sanin tana bukatar sa ba. Shi kuwa Fawaaz, bai sake cewa komai ba. Ya jingina bayansa a kujerar motar, yana kallonta a hankali. Yana nazarin yadda fuskarta ta canza, yadda idanunta ke ƙoƙarin ɓoye tsoro, da ruɗani, da kuma wani abu mai kama da yarda. A hankali, ta sauke numfashi. “ya fawaaz…” Ta kira sunansa da wata murya mai laushi. Ya amsa da kallonta da kyau, sannan ya ce, “Na’am, Nabeeha?” Ta ɗan haɗiye yawu, tana ƙoƙarin tattaro kalmomin da zuciyarta ke ƙoƙarin gaya mata. “Ba ka jin tsoro? Ka ce kana son zuciyata, amma… ba ka jin tsoron cewa wata rana soyayyar nan za ta cutar da kai?” Murmushi ya bayyana a saman fuskarsa. “Me yasa zan ji tsoro?” Ta ɗan daga ido ta kalle shi. “Domin…” Ta yi shiru. Fawaaz ya ɗan girgiza kai. “Nabeeha, soyayya ba tsoro bace. So zuciya ce, kuma zuciya bata faɗawa inda za ta faɗa ba. Idan na tsorata da soyayyarki, na fi jin tsoron rayuwa babu ke a cikinta.” Wani abu ya tsaya a makogwaronta. Ta runtse idonta na wasu ‘yan dakiku. Shi kuwa Fawaaz, ya ɗan matsa kadan, yana kallonta da kwarewa irin ta namiji da ya yanke hukunci. “Nabeeha, ban kira ki yau don in buƙaci amsar ki ba. Na kira ki ne domin na gaya miki cewa zuciyata ta riga ta faɗa, kuma ba zan taɓa cire ki daga cikinta ba. Kuma ki shirya kullum zanzo tadin zance wurin ki. Tamkar yadda ko wani saurayi yake zuwa wajen budurwar sa kafin aure.." Ta buɗe idonta, tana kallonsa. “Kana nufin… ba zaka daina ba?” Ya yi murmushi, amma murmushi mai cike da natsuwa. “Ba zan daina ba.” Ta sake numfashi, zuciyarta na tafarfasa da abubuwa da dama. Fawaaz ya duba agogon hannunsa, sannan ya ce, “Ya kamata ki koma ciki.” Duk da cewa zuciyarta na ɗauke da nauyi, sai da ta jinjina kai. Ta bude ƙofar motar a hankali, ta fito. Daidai lokacin da ta kai ga rufe ƙofar, muryarsa ta sake fitowa cikin nutsuwa. “Nabeeha?” Ta juyo, tana kallonsa. Fuskarsa cike da kwanciyar hankali. “Ko ba yau ba, wata rana zan ji muryarki na amsa.” Fawaaz ya bita da kallo, murmushi na sauka saman fuskarsa. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:50_   Shiru ne ya sake cika motar. Amma shiru mai cike da launin soyayya da murmushin zuciya. Idanun Nabeeha suna ƙasa, zuciyarta na dokawa da ƙarfi, hannunta na lafe a kan cinyoyinta. A karon farko a rayuwarta, ta ji kalmomin da suka ɗaga mata hankali fiye da tunaninta. Kalaman soyayya ne, amma ba irin na wasanni ba. Na gaske ne. Na zuciya ce da ta tsinci kanta a cikin wani soyayyen wuri da bata taɓa sanin tana bukatar sa ba. Shi kuwa Fawaaz, bai sake cewa komai ba. Ya jingina bayansa a kujerar motar, yana kallonta a hankali. Yana nazarin yadda fuskarta ta canza, yadda idanunta ke ƙoƙarin ɓoye tsoro, da ruɗani, da kuma wani abu mai kama da yarda. A hankali, ta sauke numfashi. “Ya Fawaaz…” Ta kira sunansa da wata murya mai laushi. Ya amsa da kallonta da kyau, sannan ya ce, “Na’am, Nabeeha?” Ta ɗan haɗiye yawu, tana ƙoƙarin tattaro kalmomin da zuciyarta ke ƙoƙarin gaya mata. “Ba ka jin tsoro? Ka ce kana son zuciyata, amma… ba ka jin tsoron cewa wata rana soyayyar nan za ta cutar da kai?” Murmushi ya bayyana a saman fuskarsa. “Me yasa zan ji tsoro?” Ta ɗan daga ido ta kalle shi. “Domin…” Ta yi shiru. Fawaaz ya ɗan girgiza kai. “Nabeeha, soyayya ba tsoro bace. So zuciya ce, kuma zuciya bata faɗawa inda za ta faɗa ba. Idan na tsorata da soyayyarki, na fi jin tsoron rayuwa babu ke a cikinta.” Wani abu ya tsaya a makogwaronta. Ta runtse idonta na wasu ‘yan dakiku. Shi kuwa Fawaaz, ya ɗan matsa kadan, yana kallonta da kwarewa irin ta namiji da ya yanke hukunci. “Nabeeha, ban kira ki yau don in buƙaci amsar ki ba. Na kira ki ne domin na gaya miki cewa zuciyata ta riga ta faɗa, kuma ba zan taɓa cire ki daga cikinta ba. Kuma ki shirya kullum zan zo tadin zance wurin ki. Tamkar yadda kowanne saurayi yake zuwa wajen budurwarsa kafin aure.” Ta buɗe idonta, tana kallonsa. “Kana nufin… ba zaka daina ba?” Ya yi murmushi, amma murmushi mai cike da natsuwa. “Ba zan daina ba.” Ta sake numfashi, zuciyarta na tafarfasa da abubuwa da dama. Fawaaz ya duba agogon hannunsa, sannan ya ce, “Ya kamata ki koma ciki.” Duk da cewa zuciyarta na ɗauke da nauyi, sai da ta jinjina kai. Ta bude ƙofar motar a hankali, ta fito. Daidai lokacin da ta kai ga rufe ƙofar, muryarsa ta sake fitowa cikin nutsuwa. “Nabeeha?” Ta juyo, tana kallonsa. Fuskarsa cike da kwanciyar hankali. “Ko ba yau ba, wata rana zan ji muryarki na amsa.” Fawaaz ya bita da kallo, murmushi na sauka saman fuskarsa. Ya ja numfashi, sannan ya tada motarsa, yana tafiya da zuciyarsa da ya riga ya miƙa a hannun wata ‘yar baiwa. Idanunta suka faɗa a cikin nasa. Bata ce komai ba. Sai kawai ta juya a hankali, tana tafiya zuwa cikin gida, zuciyarta na ɗauke da wani sabon yanayi da bata san yadda zata fassara shi ba. Nabeeha ta shiga cikin gidan a HANKALI, zuciyarta cike da nauyin tunani. Tana jin kamar ƙafafunta ba su taɓa jin irin wannan nauyin ba. Abinda Fawaaz ya faɗa mata na yawo a cikin zuciyarta, yana ratsa jijiyoyinta kamar wani irin sako da ba ta shirya karɓa ba. A harabar gidan, ta hango Hammad yana zaune akan kujerar filawa, yana duba wayarsa. Ya ɗago yana kallonta, sannan ya hura iska a hankali. “Kin fita da dare.” Muryarsa cike da ma’anoni da dama. Ta tsaya, ta kalle shi. Bata ce komai ba. Hammad ya cigaba da kallonta. “dear sis?” Ta jinjina kai kawai, sannan ta juya cikin gida. Hammad ya bita da kallo, yana nazarin yadda take tafiya cikin shiru da tunani. --- A ɗayan ɓangaren kuwa, Fawaaz na tafiya da mota cikin natsuwa, amma zuciyarsa tana tafarfasa da wani irin yanayi. Yana tunanin yadda Nabeeha ta kalle shi da idanunta masu cike da tambayoyi. Yana jin yadda shiru ya cika tsakaninsu, shiru mai yawa fiye da kalmomi. Ya saki numfashi a hankali, yana murmushi kaɗan. “Sai ki ji da kyau, Nabeeha,” ya furta a hankali. “Bana wasa da alkawari.” Bai kai ko ina ba, sai ga kira daga mahaifiyarsa, Hajiya Hawwa. Ya danna answering, yana ɗaga wayar zuwa kunnensa. “Fawaaz, kana ina?” “Gida zan koma, Mami.” “Akwai magana. Muna son muyi taro da kai gobe da safe.” Fawaaz ya ɗan runtsa ido. “Taro?” “Eh. Akwai wasu batutuwa da suka shafi rayuwarka da zamanka a nan.” Fawaaz ya yi shiru na ƴan sakanni. “To Mami, zan zo.” Ya kashe wayar a hankali, yana jin wani iri. Mahaifiyarsa tana da wani abu a zuciyarta, kuma yana ji a jikinsa cewa wannan magana tana da nasaba da abubuwan da ke faruwa. Ya sauke numfashi, yana sake tuƙa motarsa cikin dare, zuciyarsa na tafiya da tunani mai nauyi. --- Washe gari, tun da safe, Fawaaz ya shiga falon babansa, Major General Dawud. Akwai mahaifiyarsa Hajiya Hawwa a zaune, da kuma mahaifiyarsa ta ɓangaren uba, Hajiya Zaytunah. Hajiya Hawwa ta dubi Fawaaz, tana daidaita zaman hijabinta. “Muna son magana da kai.” Ya kalle ta cikin mutuntawa. “Ina jin ki, Mami.” Hajiya Hawwa ta gyara zama. “Kana jin dadin zaman ka a nan gidan?” Fawaaz ya ɗan kalli mahaifinsa, wanda ke zaune cikin natsuwa, sannan ya mayar da kallonsa kan mahaifiyarsa. “Eh.” Hajiya Hawwa ta ɗanyi jim. “Ba ka ganin lokaci yayi da zaka ƙara tunanin abubuwa masu muhimmanci a rayuwa? Irin su aure.” Fawaaz ya ɗan jinjina kai. “Mami…” Ta ɗaga hannu. “Fawaaz, ni ba ƙanwarka ka bace. Ni mahaifiyarka ce. Na san irin dabi’unka. Kuma na san cewa kana da abin da kake buƙata a zuciyarka.” Fawaaz ya numfasa a hankali. “Mami…” “Ka shirya, za mu tattauna da kai.” A lokacin, zuciyarsa ta fara jin wani irin nauyi. Ya san cewa batun aure ya fara matsowa kusa da shi, kuma yana da tabbacin cewa mahaifiyarsa tana da ra’ayin da ba zai dace da nasa ba. --- A ɗayan ɓangaren kuma, Nabeeha na cikin ɗakinta, tana kallon kanta a madubi. Har yanzu bata iya daina tunanin maganganun Fawaaz ba. Kalaman sa suna yawo a cikin kunnuwanta, suna sakata jin wani abu da ba ta taɓa jin sa ba a rayuwarta. "Zuciyata ta riga ta yanke shawarar inda take so ta tsaya. Kuma wannan wuri… shine ke, Nabeeha." Ta lumshe ido, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. Wani yanki a cikin zuciyarta yana gaya mata cewa wannan ba soyayyar wasa ba ce. Wannan abu ne mai zurfi, mai nisa, wanda ba zata iya watsi da shi ba. Amma fa tana da tsoro. Tsoron cewa idan ta biye wa zuciyarta, wata rana hakan zai jefa ta cikin hali da ba ta shirya ba. Ta sake bude idonta, tana kallon kanta a madubi. Sai dai abin mamaki, ba tsoro kadai take gani a fuskar ta ba. Akwai wani abu na daban. Wani abu da bata taɓa tsammanin zata gani ba. 'soyayya' Soyayya tana da wata hanya ta ɓoyewa a cikin zuciya ba tare da izinin mai ita ba. Idan ta shige, sai dai ka ji tana zagaye da jininka, tana fitar da numfashinka, tana bugawa da kowace irin motsin da zuciyarka ke yi. A haka Nabeeha ta tsinci kanta. Tana jin numfashinta yana yin nauyi a duk sanda ta tuno yadda Fawaaz ya kalleta da idanunsa masu cike da kauna. Kalaman sa sun bi jijiyoyinta, sun sauka a inda ba za ta iya goge su ba. "Bana iya kwana yau idan ban ji muryarki ba." Ta runtse idonta, zuciyarta na tsalle a KIRJIN ta. Yaya zai ce haka? Yaya zata iya fahimtar cewa Fawaaz, mai kamewa da miskilanci, yana da soyayya irin haka a cikin zuciyarsa? Ta sauke numfashi. Ita kanta, ba ta da tabbacin menene yake faruwa da ita. Sai dai abu guda ne take da tabbaci a kai— tunanin sa ya gama mamaye zuciyarta. --- A bangaren Fawaaz kuwa, yana zaune a cikin motarsa, ba tare da ya kunna ta ba. Hannunsa yana kan sitiyari, yana tunani mai zurfi. Bai taɓa jin irin soyayyar da yake ji yanzu ba. "Kin taɓa ganin mutum da yake da tsananin soyayya, amma yana jin tsoron furtawa?" Ya saki murmushi a hankali. Shi kansa bai san yaushe soyayyar Nabeeha ta fara cika ransa ba. Sai dai abu guda ne yake sani—zuciyarsa ta riga ta faɗa, kuma babu komai da zai iya janye hakan. A hankali, ya zaro wayarsa. Ya duba chat ɗin da suka yi da ita, amma babu saƙon da ya fito daga gare ta. Hakan ya sa ya danna rubutu, "Ina fatan kin isa gida lafiya?" Bayan sakanni, ya ga typing a jikin screen ɗin. Zuciyarsa ta buga. Sai dai kafin sakon ya iso, sai ya ga typing ɗin ya tsaya. Shiru ya wanzu. Bai samu komai ba. Ya sake duba wayarsa. Babu reply. Ya saki ajiyar zuciya. Wata murmushi ya bayyana saman fuskarsa. "My mystery girl.... Lokacin ki ne." --- A ɗayan ɓangaren kuwa, Nabeeha tana riƙe da wayarta a hannunta. Sakon Fawaaz ya shigo amma ta kasa rubuta komai. Numfashinta ya sauka da nauyi. Dan murmushi tayi, tana maimaita yadda yace taje gidah lafiya? Bayan gidan su daya. Kai kache kowanne unguwar sa daban... Sai da ta ɗauki lokaci tana tunani, sannan ta matso hannu. A hankali, ta danna rubutu: "Na isa lafiya. Kaima ka isa lafiya?" Ta aika. Bayan ‘yan sakanni, sai sakonsa ya dawo. "Ina lafiya, idan har ke ma kina lafiya." Ta ɗan runtse ido, tana jin yadda kalmomin suka shige mata kai. Wani murmushi ya bayyana saman fuskarta ba tare da ta sani ba. Soyayya… Tana da nauyi. Tana da sanyi. Kuma tana da kwarjini da ba za a iya kaucewa ba. Tana jin hakan a yau fiye da kullum. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:51_ Haka zuciyar Nabeeha take ji yayin da take kwance a kan gadonta, idanu a lumshe, tana tuno kowane kalma da Fawaaz ya furta. "Kin taɓa ganin mutum da yake da tsananin soyayya, amma yana jin tsoron furtawa?" Kalmomin nan sun mamaye tunaninta, sun cika kunnenta. Bata iya mantawa da yadda idanunsa suka cika da gaskiya lokacin da yake magana. Bata taɓa sanin cewa zuciyarta zata buga da irin wannan nauyin soyayya ba. Numfashinta ya yi nauyi, zuciyarta na ci gaba da bugawa. Wayarta tayi ƙara. Ta buɗe idanu a hankali, zuciyarta ta tsinke. Ta kai hannu ta ɗauka, sai ta hango sunansa a saman screen. Yaa Fawaaz. Ta tsaya, tana kallon sunan na wasu ‘yan dakiku. Me zai ce? Me yasa yake kiran ta yanzu? A yanda ta san shi, ba mutum bane mai yawan magana, balle shi da kansa ya kira da daren nan. Tayi ajiyar zuciya, sannan ta ɗaga wayar a hankali, murya a ƙasa. “Assalamu alaikum.” Muryarsa ta fito cikin taushi. “Wa alaikumus salam.” Shiru ya wanzu na wasu dakiku. Daga jin numfashinta a cikin wayar, Fawaaz ya san cewa zuciyarta na bugawa da sauri. Ya san tana jin wani abu, kamar yadda shima yake ji. A hankali, ya ɗanyi gyaran murya. “Ban so na dame ki da waya ba…” Ta lumshe idanu, zuciyarta na sake bugawa. “Ba komai.” Ya sauke numfashi. “Amma akwai abu guda da bana so na kwana da shi a zuciyata.” Ta jinjina kai a hankali, duk da cewa baya ganinta. “Mene ne?” Yayi shiru na wani lokaci. Sai daga baya ya ce, “Duk sanda na rufe idanuwa na, sai naga fuskarki.” Hannunta ya ɗan yi sanyi, zuciyarta ta yi wata irin harbi. Shi kuwa Fawaaz, yana jin kamar kalmomin sun fi ƙarfin shi, amma dole ya furta. “Bana so ki rufe idonki yau da tunanin cewa kin taɓa ji, ko kin taɓa tsammani. Ina so ki san cewa komai da na ce… gaskiya ce.” Ta kai hannu ta dafe KIRJIN ta. Soyayyar da take jin tana taso mata daga zuciyarta ta mamaye komai. Ta jinjina kai a hankali, murya na rawa. “Na sani.” Ya lumshe idanu, wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauka daga bakinsa. “Nagode, Nabeeha.” Tayi shiru. Ya sake furta cikin nutsuwa. “Nagode da kika ba zuciyata wuri.” Sai da zuciyarta ta gama tsinkewa da kalmomin sa, sannan ta samu kanta da furta abu guda daya, cikin murya mai taushi. "Kaima nagode, Ya Fawaaz." Hannunsa ya matse wayar da ƙarfi, yana jin yadda zuciyarsa ta amsa da ɗan ƙaramin bugu. Duk da cewa bata faɗi komai mai yawa ba, amma kalmomin ta sun ratsa zuciyarsa. Sun shige shi kamar iska mai daɗi, mai sanyaya rai. Ya ɗan lumshe ido. “Sai da safe, Nabeeha.” Ta sauke numfashi, sannan ta amsa da murya ƙasa. “Sai da safe.” Bayan ya ajiye wayar, ya jingina kansa da kujerar gadonsa, idanu a lumshe. Soyayya tana da wata hanya ta shigowa cikin zuciya ba tare da izinin mai ita ba. Kuma idan ta shigo, babu komai da zai iya korarta. Zuciyarsa ta riga ta faɗa, kuma a yau ya tabbatar da cewa… babu gudu, babu ja da baya. Shiru ne ya ratsa ɗakin Nabeeha bayan ta ajiye wayarta. Idanunta a lumshe, zuciyarta na tafarfasa da wani irin yanayi da ba ta taɓa fassara shi ba. Soyayya. Wata soyayya mai cike da natsuwa da zurfi. Wata soyayya da ba a furta ta da wasa ko burgewa ba. Wata soyayya da ta ji tana ratsa zuciyarta kamar iska mai laushi. Ta murza gefen filo da hannunta, sannan ta zame cikin bargo a hankali, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauƙin kalmomin Fawaaz. "Nagode da kika ba zuciyata wuri." Ta lumshe idanu, tana jin yadda kalmomin suka fi ƙarfin zuciyarta. Wata yar guntuwar murmushi ta bayyana a saman fuskarta. Shi kuwa Fawaaz, bayan ya ajiye wayar, bai iya rufe ido ba. Ya jingina kansa da jikin gadonsa, numfashinsa na fita a hankali. Tunanin Nabeeha bai daina ratsashi ba. Duk lokacin da ya rufe ido, sai ya hango idanunta. Idanu masu launin nutsuwa. Idanu masu taushin da suka daɗe suna jan zuciyarsa ba tare da ta sani ba. Ya dafe goshi da hannunsa, yana jin yadda zuciyarsa ta daɗe tana ɓoye wani abu da ba ya iya fassara wa da farko. Amma yau, babu ɓoyewa. Ya san abin da yake ji, kuma ya san cewa wannan soyayyar ba zai iya buɗe ido ya bar ta ta tafi ba. A HANKALI, ya lumshe ido, yana jin wani abu mai daɗi yana mamaye zuciyarsa. Idan ta amince da shi, idan ta bar shi ya shigo cikin zuciyarta, da gaske zai iya riƙe ta? Murmushi ya kwace masa, zuciyarsa na bugu da wata nutsuwa mai daɗi. Zai iya. Ba wai don yana so ba kawai, sai don cewa ta riga ta zama ransa. --- A cikin dare mai cike da shiru, Nabeeha ta kasa samun barci. Zuciyarta na cike da tunanin kalmomin Fawaaz, yadda muryarsa ta sauka cikin taushi, yadda idanunsa suka cika da gaskiya da ƙauna. Ta lumshe ido tana jin yadda hakan ke shigarta. Duk da ba ta taɓa tunanin soyayya da Fawaaz ba a baya, yanzu tana jin kamar wani abu ne da zuciyarta ke ɗauke da shi, amma ba ta san lokacin da ya shige ta ba. Soyayya ce ta bayyana kamar wata iska mai ɗanɗanon zuma—mai daɗi, amma mai firgitarwa. Ta janyo bargonta, ta ƙudundune jikinta, amma hakan bai hana tunaninta yawo ba. Wata zuciya da ta daɗe da sanin Fawaaz da miskilancinsa, da natsuwarsa, da yadda ba ya cika magana da ita. Amma yau… ya furta mata cewa ita ce wuri da zuciyarsa ta zaɓa! Ta bude idonta a hankali, zuciyarta na harbawa da wani sabon yanayi. Za ta iya furta cewa ita ma hakan take ji? Za ta iya amincewa da zuciyarta da ke harbawa idan ta kalle shi? Ta dafe KIRJIN ta da hannunta, tana jin yadda bugun zuciyarta ke gudu fiye da yadda ta saba. Shin da gaske soyayya ce wannan? *** A gefe guda, Fawaaz ma ba ya barci. Ya kasa rufe ido, yana jin kamar zuciyarsa ta faɗa wani sabon yanayi da ba ta saba da shi ba. Soyayya ba sabuwa ba ce a duniya, amma irin ta da yake ji… wani abu ne daban! Ya daɗe yana gudun bayyana yadda yake ji, amma yanzu ya san ba zai iya boyewa ba. Idan har akwai soyayyar da zai ƙaunata har ƙarshen rayuwarsa, to ba wata bace illa Nabeeha. Murmushi ya bayyana a saman fuskarsa, yana jin yadda zuciyarsa ke nutsuwa da tunaninta. Duk duniya, da akwai mata da yawa, amma babu wata da za ta iya maye gurbin wacce ta fi so. Duk da cewa ba ta furta komai ba, zai jira. Ko da shekaru ne, ko da kwanaki ne, ko da sa’o’i ne, zai jira har sai zuciyarta ta yarda da shi. *** Haka dare ya wuce, zuciyoyi biyu na ƙoƙarin fahimtar sabon yanayin da suka tsinci kansu a ciki… Soyayya ce mai nutsuwa, soyayya ce ta gaske. Cigaba yana tafe... PAGE: 55 Washegari da safe, Nabeeha ta tashi da wani sabon yanayi. Duk da cewa jikinta ya sauka da gajiya, zuciyarta tana cike da wani abu da ta kasa fassara wa. Ta zauna a gefen gado, ta rungume cinyoyinta, tana tunanin yanda zata fuskanci Fawaaz yau. Zata iya kallonsa ido-da-ido bayan furucinsa na jiya? Ta furzar da iska a hankali. Wata zuciyarta na gaya mata cewa ba abu ne mai sauƙi ba. Amma ta san ba zata iya gujewa ba. *** Fawaaz kuwa, yana tsaye a gaban madubi yana shirin fita. Kallon kansa yake, amma ba yadda ya saba ba. Yau idan zai kalli Nabeeha, zai ga wani sabon yanayi a tare da ita? Zai iya fahimtar abin da zuciyarta ke shirin gaya masa? Ya saki murmushi a hankali, ya dafe kugunsa. Yau… zai sake gwada sa’arsa. *** A tsakar gida, lokacin da Nabeeha ta fito daga ɗaki, zuciyarta ta harba lokacin da ta hango Fawaaz a bakin mota. Ya jingina da motar, hannunsa a cikin aljihunsa, yana kallon ta da idanun da suka cika da abin da zuciyarta ke gudu daga ciki. Soyayya. Ta ɗan tsaya na wani ‘yan dakiku, kafin ta karasa a hankali. Shi kuwa bai ce komai ba. Bai motsa ba. Sai dai idanunsa sun bi ta har sai da ta iso kusa da shi. “Barka da safiya,” ta ce, muryarta na ɗauke da launi mai sanyi. Murmushinsa ya bayyana cikin kamewa. “Barka da safiya, Nabeeha.” Sai shiru ya ratsa tsakaninsu. Zuciyarta na harbawa, taji kamar idan ta yi magana yanzu zata bayyana komai da zuciyarta ke ji. Shi kuwa Fawaaz, ya lumshe ido sannan ya buɗe su, yana kallon ta kai tsaye. A hankali ya furta, “Kin san mene ne abu mafi wahala a soyayya?” Ta ɗan dago ido tana kallonsa, tana jiran jin amsar. Muryarsa ta sauka a kasalance. “Rashin sanin yadda zuciyar wacce kake so take ji game da kai.” Numfashinta ya ɗauke. Ya ɗaga kai ya kallon ta kai tsaye, fuskar sa cike da gaskiya. “Ina fatan ni ba zan daɗe ina jiran hakan ba.” Hankalinta ya tafi gaba ɗaya. Idanunta suka tsaya a cikin nasa, tana jin zuciyarta tana tafarfasa da wani irin yanayi da bata taɓa fuskanta ba. Sai dai, kafin ta samu damar cewa komai, sai ya matso kusa da ita kadan, yana kallonta cikin nutsuwa. “Ki yi min alƙawari, Nabeeha.” Muryarta ta sarke. “Alƙawari?” Ya gyada kai a hankali. “Idan har zuciyarki ta taba tunani akaina… ki bar ni in sani.” Wani abu mai ƙarfi ya tsaya a ƙirjinta. Zuciyarta na bugu da sauri, amma bata iya cewa komai ba. Shi kuwa ya saki murmushi mai cike da kwanciyar hankali. “Ba yau ba… ba sai yanzu ba. Amma…” Ya tsaya na ‘yan dakiku, sannan cikin muryar da ta sauka kamar iska mai taushi, ya ce, “Zan jira.” --- ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:52_    Ta buɗe idanunta a hankali, suka haɗa ido da shi. Sai dai ta kasa cewa komai. Shi kuwa Fawaaz, murmushinsa bai gushe ba. A hankali ya ɗaga hannunsa, ya ɗan taɓa gefen motar da yake jingina da ita, yana kallonta da zurfi. "Ba sai kin ce komai ba, Nabeeha." Ta ɗauke idonta, amma zuciyarta ta kasa yin shiru. Sai bugawa take kamar ana danna gangar zuciya. Muryarsa ta sauka cikin sanyi, kamar iska mai sanyaya rai. "Amma ki sani... idan wata rana zuciyarki ta taɓa furta wani abu game da ni, ko da kuwa a cikin ruwan sanyi ne, zan ji shi." Wani abu ya tsaya a KIRJIN ta. Ya sake murmushi mai taushi. "Zan saurara… zan ji, har ma in amsa." Zuciyarta ta yi nauyi da wani abu mai daɗi da ban tsoro a lokaci guda. Shi kuwa ya gyara tsayuwa, yana kallonta cikin nutsuwa. "Ina so ki san cewa babu rana guda da zata wuce ba tare da na yi tunaninki ba." Ta haɗiye yawu. "Babu safiya da zata waye ba tare da zuciyata ta ambace ki ba." Ta ƙura masa ido, zuciyarta na tafarfasa. "Babu dare da zan kwanta ba tare da hotonki a cikin tunanina ba." Ta numfasa, amma numfashin da bata san yana ɗauke da nauyi ba. Shi kuwa, ya janye idonsa a hankali, yana duban sararin samaniya kamar yana magana da taurari. "Idan har akwai soyayya da zata iya riƙe mutum gaba ɗaya, to ni na san cewa kin riga kin mallake ta a wajena." Kallonta ya dawo kanta, cikin zurfin so da gaskiya. "Nabeeha… ina son ki." Hankalinta ya tsaya cak. Zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci, kafin ta cigaba da bugawa da wani irin yanayi da bata taɓa jin irinsa ba. Fawaaz ya gyara tsayuwa, yana dubanta da kwanciyar hankali. "Kuma ba zan taɓa gajiya da faɗin hakan ba." Ya numfasa a hankali, sannan ya ce, "Ko da baki ce komai ba… ko da kin ci gaba da ɓoye zuciyarki, zan tsaya har sai lokacin da kike da shirin bayyana min abinda take ji." "Har abada, zan jira." Shiru ya ratsa tsakaninsu. Amma shiru ne mai cike da nauyin soyayya da kalmomin da suka yi ƙaura a zuciya. Nabeeha ta ji ƙafafunta sun gaza ɗaukar ta. Sai ta ɗauke idonta daga nasa, zuciyarta na tafasa da abu mai wuyar fassara. Fawaaz kuwa, sai ya ja numfashi, sannan a hankali, ya matsa daga kusa da ita, yana kallonta da murmushi mai taushi. "Zan wuce yanzu. Amma zan sake dawowa." Ya juya a hankali, yana tafiya zuwa mota. Daidai lokacin da ya shiga, sai ya sake kallonta, yana gyada kai. "Ki kula da kanki, Nabeeha." Ya tada motarsa, ya fice a hankali, zuciyarsa na barin wani ɓangare a wajenta. Ita kuwa, ta tsaya a wurin, har sai da sautin motarsa ya ɓace. A hankali ta lumshe idonta, zuciyarta na tafasa da wani irin yanayi. Bata san yaya zata yi da zuciyarta ba. Bata san wane mataki zata ɗauka ba. Amma abu guda ta sani. Soyayyar Fawaaz… Tuni ta shiga jikinta, kuma bata san ko zata iya fita daga gare ta ba. Nabeeha ta tsaya daram a wajen, zuciyarta na dokawa da wani irin sauti da bata taɓa ji ba. Hannunta ta ɗaura saman KIRJIN ta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri kamar zata tsinke. Idanunta suka lumshe a hankali, kalmomin Fawaaz suna sake dawo mata a zuciya. "Nabeeha… ina son ki." Numfashinta ya ɗauke na wasu dakiku. Sai ta buɗe idanunta da sauri, ta ɗauke idonta daga inda motarsa ta ɓace. Soyayya ce? Zuciyarta ta ambace shi? A hankali ta ɗaga hannunta, ta taɓa saitin zuciyarta da laushi. Ta girgiza kai da ƙyar, tana ƙoƙarin kawar da wannan tunanin. Sai dai wani murya mai taushi ya faɗo mata a cikin zuciya. "Har abada, zan jira." Ta haɗiye yawu, zuciyarta na ƙoƙarin amincewa da wani abu da ita kanta bata gama fahimta ba. Wani ganyen bishiya ya fado ya ratsa kusa da ita yana busa iska, sai ta dawo daga duniyar tunaninta. Ta sauke numfashi a hankali, sannan ta ɗaga ƙafafunta da ƙyar, ta juya zuwa cikin gida. Tana jin kamar tana tafiya cikin wani sabon yanayi da bata taɓa sanin tana da shi ba. Kuma a karo na farko… Ta ji zuciyarta na yarda da abu guda. Soyayyar Fawaaz… Tuni ta fara ratsa tsokar zuciyarta, kuma bata da ikon tsayar da ita... 🎀🎀🎀 Gwaggo Hafsatu na zaune a kan gadonta, hannunta rike da carjib, tana jan karatu cikin nutsuwa. Hajiya Zaytunah ta shigo dakin a hankali, jikinta cike da lumana. Idanunta na bayyana natsuwa da shawara, duk da cewa zuciyarta tana bugawa da karfin gaske. “Gwaggo…” Ta kira da murya kasa, tana durkusawa gabanta. Gwaggo Hafsatu ta janye kallonta daga abunda take, ta kalli Zaytunah da idanu masu cike da hikima. “Na’am, Zaytunah.” Ta dan numfasa, sannan ta lumshe ido na wasu dakiku kafin ta bude. “Na gama istikhara, Gwaggo. Na ji kwanciyar HANKALI a raina. Na yanke shawarar komawa gidan mijina.” Shiru ya ratsa dakin na ‘yan dakiku. Gwaggo Hafsatu ta ajiye misbah dinta a hankali, tana nazarin fuskarta. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi murmushi mai cike da farin ciki. “Alhamdulillah,” ta fada da sigar godiya. “Allah Ya tabbatar da alheri.” Zaytunah ta gyada kai da girmamawa, zuciyarta tana karbar kalmomin da natsuwa. Gwaggo Hafsatu ta kai hannu ta rike nata. “Zaytunah, komawar ki gidan Alhaji Uzairu ba matsala ba ce, amma ki tabbatar kin shiga da addu’a. Duk wanda ya dogara ga Allah, ba zai tozarta ba.” Cikin sanyin murya, Zaytunah ta amsa, “Na yarda, Gwaggo. Da addu’a zan shiga.” Gwaggo Hafsatu ta dafa hannunta cikin kulawa. “Allah Ya albarkaci zaman ki.” .... Motar Fawaaz ta tsaya a gefen titi a gaban wani gida mai tsari. A cikin motar, shi da Nabeeha suna zaune, amma babu wanda ke magana. Sai shiru mai cike da nauyi. A hankali ya juyo ya kalleta, idanunsa masu zurfi da kwarjini sun ratsa ta. “Ki shigo ki gaisa da Humyrah, amma...” Ya dakata kadan, yana dauke kansa kamar ba ya so ya fadi abin da ke ransa. “Kada ki dade.” ya karasa fada ahankali.. Nabeeha ta dan saki murmushi, sai dai ba ta kalle shi ba. “Toh.” Ta bude kofar motar ta fito. Duk da sanyin dare da ke tashi, tana jin zafin bugun zuciyarta. Fawaaz ya kara gyara zaman sa, amma bai dauke idanunsa daga kanta ba har sai da ta bace cikin gidan. Humyrah ta karbi Nabeeha da murmushi mai cike da tsokana. Kafin ma su zauna da kyau, ta riga ta fara dariya. “Nabeeha, kin san me?” Ta dan dago ido tana kallonta. “Mene?” Humyrah ta dan rankwafa kadan, tana kallonta da wani kallo na tsokana. “Tun shekarun baya nake tunanin cewa Yaya Fawaaz yana kaunarki.” Nabeeha ta dan zaro ido da mamaki, sannan ta kada kai da sauri. “Ke dai Humyrah, me ya sa kike tunani haka?” Humyrah ta tabe baki. “Ai yana bayyane! Yanda yake kula da ke, tsananin tsaro da yake bamu, yadda baya barin kowa ya shiga tsakaninku…” Ta ja numfashi, sannan ta dan yamutsa fuska. “Ko da yake, miskili ne, sai da wuya ya nuna abin da ke zuciyarsa.” Nabeeha ta dan saki murmushi, zuciyarta na bugawa da sauri. Suka zauna. Ta cika gaban Nabeeha da kayan kwalam. Kafin daga bisani ta fita da kanta da drinks da snacks ta kaiwa yayan nata suka gaysa. Sannan ta dawo wajen nabeeha suka cigaba da hirar su.. Fawaaz na tsaye a gefen motarsa, hannayensa a kugu. Fuskar sa kamar yadda aka saba—ba yabo ba fallasa. Amma idanunsa sun nuna yana cikin tunani mai zurfi. A hankali, yaga Nabeeha ta fito daga gidan, tana tafiya cikin nutsuwa kamar yadda ya saba hangota. Bai ce komai ba har sai da ta karasa kusa da shi. Ta tsaya, tana kallonsa da ido masu cike da tambayoyi. Ya dan numfasa, sannan ya furta da murya mai kwarjini amma cike da saukin gaske. “Nabeeha…” Ta dago kai tana kallonsa, zuciyarta na bugawa da sauri. Shiru ya ratsa tsakaninsu, sai sanyin iska da ke kadawa a hankali. Daga nan sai ya matsa kusa da ita, yana kallon cikin idanunta kai tsaye. “Kin san abin da ke cikin KIRJIN duk wani MAI HANKALI?” Ta dan girgiza kai a hankali, idanunta na bayyana sha’awar jin amsar. Ya lumshe ido na wasu dakiku, yana dauke numfashi, kafin ya bude su da wani yanayi na soyayya mai cike da natsuwa. “AKWATIN SIRRIN SA ne,” ya furta da murya kasa kasa. Hannunta ya dan motsa, kamar tana son rikewa da gaske. Amma sai ta tsaya, tana kallonsa da wata shaukin fuska. Shi kuma ya ci gaba, “Kuma kinsan mene ne SIRRI na?” Ta sake girgiza kai, zuciyarta na neman dukan kirjin ta. Ya yi murmushin da ba kasafai ake ganinsa da shi ba. A hankali, ya rike hannunta, yana kallonta da wani yanayi na dabara. “Ke ce, Nabeeha.” ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:53_ Nabeeha ta tsaya cak, idanunta sun kasa dauke wa daga nasa. Zuciyarta na bugawa da sauri fiye da kowane lokaci. Kalmar da ya fada ta ratsa ta, ta tsaya a zuciyarta kamar an rubuta da bakin zinariya. "Ke ce, Nabeeha." Ba ta san lokacin da ta dan saki numfashi ba. A karo na farko, ta fahimci cewa Fawaaz ba kawai mai kareta ba ne, zuciyarsa na tare da ita. Fawaaz ya dan kalleta, sai kuma ya dauke kansa kamar ba shi da abin cewa. Amma hannunsa da ke rike da nata bai motsa ba. Sai ma ya kara matse shi a hankali, yana jin yadda tafin hannunta ke sanyi kamar yana jin bugun zuciyarta ta ratsa nashi. “Nabeeha…” Ya kira sunanta cikin nutsuwa. Ta amsa da ido kawai. Ya lumshe ido kadan, sannan ya bude su da wani yanayi na SIRRIN ta ne kawai zai iya fassara. “Kin taba jin yadda zuciya ke ji idan tana son abu da gaske?” Ta dan girgiza kai. “Ban sani ba.” Ya yi murmushi kadan, sai dai murmushinsa mai nauyi ne. “Zuciya ba ta da hayaniya, amma tana da karfi. Idan ta kamu da so, ko da baka fadi ba, sai duniya ta fahimta.” Tayi shiru, zuciyarta na harbawa da sauri. Ya dan matsa kusa da ita, murya a hankali. “Kin san nawa lokacin da zuciyata ta dauka tana son ki?” Ta girgiza kai. “ Yaa Fawaaz…” Ya kara matsowa kadan, idanunsa cike da gaskiya. “Tun kafin kisan meye soyayya.” Nabeeha ta kasa cewa komai. Ya sauke numfashi a hankali, yana kallonta da idanu masu cike da soyayya. “Ke ce SIRRI na, Nabeeha. AKWATIN SIRRIN da zuciyata ta rufe tsawon lokaci.” Ta lumshe idanu, zuciyarta na bugawa da sauri. Wannan kalaman da yake fada, ba yau suka taso ba. Ya dade yana ajiyesu a zuciya. Kuma yanzu, sun fito fili kamar yadda haske ke bayyanar da komai a dare mai duhu. A hankali, ta bude ido, tana kallon shi da fassara mai zurfi. “ Yaa Fawaaz…” Ya dan matse hannunta, yana jin yadda jikinta ya dauki dumi. “Ba zan bukaci komai daga gare ki ba, Nabeeha. Sai dai abu guda…” Ta kara kasa da murya. “Mene ne?” Ya yi murmushi, yana juyar da kallonsa gefe kadan. “Kada ki bar zuciyata ita kadai a cikin wannan tafiyar.” Idanunta suka kada, zuciyarta ta dauki zafi. Shin yana nufin... tana da wani matsayi da ya wuce abokiyar rayuwa a cikin zuciyarsa? Fawaaz ya dago yana kallonta da ido masu cike da soyayya, amma ba tare da ya ce wani abu ba. Sai numfashinsa da ke bayyana nauyin abin da ke zuciyarsa. Shiru ya ratsa tsakanin su. Sai dai ba irin shiru na rashin magana ba—shiru ne mai cike da fassara, mai cike da abinda kalmomi ba za su iya bayyana ba. Fawaaz ya fadi soyayyarsa. Kuma yanzu… Nabeeha ce ke da hakkin yanke hukunci. Nabeeha ta dauke numfashi a hankali, zuciyarta na harbawa da sauri. Ta kasa dauke idanunta daga nashi, kamar tana neman wani abu a ciki. Fawaaz kuwa, sai ya dan ja da baya kadan, yana kallonta da kwanciyar HANKALI, amma a ciki, akwai abu da yake kokarin boyewa. Ya san kalmomin da ya fada suna da nauyi. Ya san ya bude AKWATIN SIRRIN da ya daɗe yana adanawa a zuciyarsa. Amma ba ya da nadama. Shi kam, ba shi da wata bukata sai dai jin abin da Nabeeha ke ji. “Ina jiranki a mota,” ya fada a hankali, yana dauke kansa. Nabeeha ta yi shiru, har sai da ya juya zai bar wurin. Da sauri ta kira sunansa. “Yaa Fawaaz.” Ya tsaya cak, amma bai juyo ba. Tayi shiru na wani lokaci, sai kuma ta dan gyada kai. “Ba zan bar zuciyarka ita kadai ba.” Fawaaz ya runtse ido na wani dan lokaci. Wannan kalma ta shiga cikin zuciyarsa fiye da duk wani abu da zai ji a yau. Sai kuma ya yi murmushi—murmushin da ya saba ɓoyewa. Ya juyo a hankali, yana kallonta da ido masu cike da jin dadi. “Nagode.” Ya fadi haka kawai. Amma cikin wannan "nagode", akwai soyayya, akwai nutsuwa, akwai alƙawari. Tafiyar su gida tayi shiru. Amma ba irin shiru na damuwa ba—shiru ne na zuciyoyin da suka soma fahimtar juna ba tare da kalmomi ba. A lokacin da suka isa kofar gidan su, Nabeeha, Fawaaz bai yi kokarin bude mata kofa ba kamar yadda ya saba. Sai dai ya tsaya, yana kallonta da nutsuwa. “Ina so ki huta da kyau,” ya fada a hankali. Nabeeha ta gyada kai, zuciyarta cike da wani irin yanayi mai daɗi. “Kai ma.” Ta sauka daga motar, amma kafin ta rufe kofar, sai ta juyo. “Ya fawaaz.” Ya kalleta, yana jiran abin da za ta fada. Sai tayi murmushi. “KIRJIN MAI HANKALI—AKWATIN SIRRIN SA.” Zuciyarsa ta buga. Bati taba Jin kalamen sun masa dadi, cikin sanyin fuska mai daɗi irin haka ba. Ta rufe kofar a hankali, sannan ta juya ta shige gidan, zuciyarta tana harbawa da sauri. Fawaaz kuwa, ya jima a zaune a wurin, yana murmushin da shi kadai ya fahimta. A wannan dare, zuciyoyin su biyu sun cika da sabbin tunani. Fawaaz bai koma gida kai tsaye ba. Sai da ya dan tsaya a gefen titi, ya sauke numfashi a hankali, yana kallon dare. Bai taba tunanin cewa rana irin ta yau za ta zo ba—rana da zai furta SIRRIN da ya adana tun kafin ya fahimci cikakken ma’anarsa. A gefe guda kuwa, Nabeeha ta shige dakinta tana jin kamar kanta yana shawagi. Zuciyarta tana bugawa da wani yanayi da ba ta taba jin irinsa ba. "Ba zan bar zuciyarka ita kadai ba." Ta fada masa. Wannan kalma tana maimaita kanta a cikin kwakwalwarta. Shin menene ma’anarta a gare ta? Ta san cewa tun tuni Fawaaz ya ke kulawa da ita fiye da kowa. Ya riga da ya kafa bango mai karfi tsakanin ta da duk wani hadari. Amma yaushe ya fara ganin hakan a matsayin soyayya? Kuma ita fa? Shin ta riga ta san abin da ke zuciyarta? Tana cikin dogon tunani, sai wayarta ta dauki ringing. Humyrah. Ta dauka a hankali. “Hello.” Muryar Humyrah cike da tsokana ta doki dodon kunnenta. “Kin iso gida lafiya?” “Eh,” ta amsa a kasalance. Humyrah ta ja tsaki. “Karki min haka, Nabeeha. Na san kin shige a duniyar tunani. Amma ai babu wanda ya fi ni jin dadin abin da ya faru a yau.” Nabeeha ta dan runtse idanu. “Meye hakan?” Humyrah ta yi dariya. “Ke dai bari. Ina ganin yadda Ya fawaaz ya dade a waje bayan na fito. Wallahi idan so yana da fuska, to fuskar Ya fawaaz ce yau.” Nabeeha ta daure fuska. “Humyrah, ki bar wannan.” Humyrah ta yi dariya. “Ai ba za ki iya musantawa ba, domin yanzu kowa ya san gaskiya. Yaya Fawaaz yana son ki, Nabeeha! Kuma ba yau ya fara ba. Abin da kawai ya rage shine—ke fa?” Wannan tambaya ta tsaya a zuciyar Nabeeha, ta kasa amsawa. Da safe, Fawaaz ya fita da wuri, ba tare da ya jira kowa ya tambaye shi ba. A lokacin da ya dawo daga aiki, yana cikin mota yana kokarin shiga gidan su, sai ya hangi Nabeeha a bakin kofar gida tana jiran abu kamar mai son fita. Ya dan tsaya a gefe, yana kallonta kafin ya sauke glass na motarsa. “wani wajen zaki?” Nabeeha ta juya, ta gan shi, sai zuciyarta ta buga. Duk da jiya sun raba dare da tunani, yau kuma ganin shi a fili ya kara tayar da HANKALIn ta. “Eh,” ta amsa a hankali. Ba tare da ya yi wata-wata ba, ya bude mata kofar mota. Ta shiga, zuciyarta na bugawa da sauri. Lokacin da ya fara tafiya, babu wanda ya fara magana. Sai shiru mai cike da fassara. Daga bisani, sai Fawaaz ya kalleta da ido mai zurfi. “Nabeeha.” Ta juyo tana kallonsa. Ya dauke idanunsa daga hanya ya sauke a kanta. “Jiya na kwana ina tunani.” Ta hadiye yawu, ba tare da ta iya cewa komai ba. Ya sauke numfashi. “Kin ce ba za ki bar zuciyata ita kadai ba.” Ta gyada kai. Ya dan yi murmushi, sannan ya jefa tambaya wacce ta tsaya mata a zuciya kamar an rubuta da zinariya. “Amma kin san dalili?” Zuciyarta ta buga, amma ba ta da amsar da zata bashi. Shiru ya biyo baya. Shi kuwa Fawaaz, sai ya mayar da hankalinsa ga hanya, amma da alama zuciyarsa da tunaninsa duk suna kan ita Nabeeha. A ransa, yana jira ta gane kanta. Amma zai iya jira? Hakan ne tambayar da bai da amsar sa. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:54_ Nabeeha ta dan lumshe ido, zuciyarta na bugawa da sauri. Tambayar Fawaaz ta tsaya mata a zuciya, kamar sautin da ya tsaya a kunne ba tare da ya fita ba. “Amma kin san dalili?” Tayi shiru, ta kasa amsawa. Ba don bata da amsar ba, sai don bata san wacce ta dace da furta ba. Shin yana nufin yana son jin idan soyayyarsa tana da amsa daga zuciyarta? Ko kuwa tambayarsa wata hanya ce ta tabbatarwa kansa cewa ba shi kadai yake tafiya a cikin wannan yanayi ba? Shi kuwa, yana kallonta daga gefen ido, yana jiran ta ce wani abu. Amma babu komai. Daga karshe, sai ya sauke numfashi a hankali. “Ba sai kin amsa yanzu ba.” Ya mayar da kallonsa ga hanya, yana ci gaba da tukinsa da nutsuwa. Amma zuciyarsa bata da kwanciyar HANKALI. Ita kuwa Nabeeha, sai ta tsinci kanta cikin wani yanayi na dogon tunani. .. Bayan sun isa kofar gidan Humyrah, saboda shirye shiryen presentation na term paper da zasuyi na makaranta, Fawaaz ya tsaya yana kallon agogon hannunsa. “Kar ki daɗe,” ya fada a hankali. Nabeeha ta juya, tana kallonsa da fuskarta a dan kame. “Me zai hana ka shiga?” Ya girgiza kai. “Ba zan tsaya ba. Amma zan jiraki anan.” Ta kalli yadda ya jingina bayansa da kujerar mota, hannayensa rike da sitiyari, yana kallon hanyar gaba. Yadda yake kokarin gujewa ido da ita, ya sa ta fahimci cewa lallai yana cikin tunani mai zurfi. Da wannan tunanin a ranta, ta sauka daga motar, ta shige gidan. Humyrah na ganin Nabeeha ta shigo sai ta kama hannunta, ta ja ta cikin falon. Wani murmushi ne a fuskarta wanda ke nuna cewa tana jin daɗin abinda ke faruwa. “Ina yayana?” Ta tambaya da tsokana. Nabeeha ta daure fuska. “Yana waje, yana jirana.” Humyrah ta ja tsaki. “To shi kenan. Amma kin san me?” Nabeeha ta dan kalleta. “Meye?” Humyrah ta saki murmushi. “Tun shekaru da yawa nake da wannan zaton. Sai dai yaw Fawaaz ba mutum bane mai son bayyana zuciyarsa. Amma yadda yake kula da ke, yadda yake tsare ki fiye da kowa… hakan bai taba barin shakku a zuciyata ba.” Ta dan tsagaita, sannan ta dan matsa kusa da ita. “Kin san mene ne?” Nabeeha ta girgiza kai. “Soyayya ba wai sai an faɗa take bayyana ba. Wani lokaci, ana iya gani a cikin ayyukan mutum.” Nabeeha tayi shiru, tana jin yadda maganganun Humyrah ke ratsata. Daga nan suka dan taba hira na ‘yan lokuta, sannan Nabeeha ta mike tsaye. “Zan tafi.” Humyrah ta harare ta. “Ai nasan bazaki jima ba. Idan naji ance kin daɗe, lallai zan zo na ja kunnenki.”ta karasa tana gwada muryar fawaaz. Suka yi dariya tare, sannan Nabeeha ta fita daga gidan. Bayan ta fita, ta hango Fawaaz yana tsaye a gefen motarsa. Hannayensa sanye cikin aljihunsa, yana kallon sama kamar mai nazarin taurari. Tana isowa, ya juyo ya kalleta. Babu tambaya a idanunsa, amma akwai abu mai yawa a cikinsu. Ya bude mata kofa, ta shiga. Shima ya shiga, sannan ya tayar da motar. Sai da suka fara tafiya na wasu mintuna kafin yayi magana. “Kin yi sauri.” Nabeeha ta dan juyo tana kallonsa. “Ka ce kada in daɗe.” Ya saki murmushi, yana mayar da hankalinsa kan hanya. “Haka ne.” Shiru ya biyo baya. Amma shiru ne mai dadi—mai dauke da wata irin nutsuwa. Can cikin tafiya, sai ya dan rage gudun motar. “Nabeeha.” Ta juyo tana kallonsa. Ya dan sauke numfashi, sannan ya jefa tambaya wacce ta kara sa bugun zuciyarta ya tsananta. “Idan har ba za ki bar zuciyata ita kadai ba, shin hakan yana nufin zuciyarki tana tare da tawa?” Wannan karon, babu inda za ta buya. Wajibi ne ta fadi abin da zuciyarta ke ji. Tayi shiru na wani lokaci, kafin ta dan bude baki. “Yaa fawaaz…” Ya juyo yana kallonta, yana jiran amsar da zai adana a cikin Kirjin sa—Akwatin Sirrin Sa. Fawaaz ya tsaya da numfashinsa yana jiran amsar da Nabeeha za ta bayar. A karon farko, zuciyarsa ta kasance cikin yanayin da bai saba da shi ba—zuciyarsa a hannunta take. Shi da ya saba riƙe komai a ransa, shi da bai taba bari wani ya fahimci abin da ke zuciyarsa ba, yau shine ke jiran wata ta yanke hukunci a kansa. "Idan har ba za ki bar zuciyata ita kadai ba, shin hakan yana nufin zuciyarki tana tare da tawa?" Wannan tambaya ce mai nauyi. Tambayar da ko da yaushe yake gujewa. Amma yau, babu gudu babu ja da baya. Nabeeha tayi shiru. Ba wai don bata da amsar da zata bashi ba, sai don tana jin cewa idan ta furta hakan, abubuwa ba za su taba dawowa yadda suke ba. Ta sauke numfashi a hankali. “Yaa Fawaaz...” Ta kalli yadda idanunsa suka cika da zurfin tambaya. Sai ta dan sunkuyar da kanta, kafin ta dube shi a karo na biyu. “Ina tsoron cewa idan na fada, abubuwa ba za su taba zama kamar da ba.” Fawaaz ya gyara zamansa a kujerar motar, zuciyarsa tana bugawa. Amma bai kalli gefe ba, ya tsaya yana kallonta, yana jiran ta ci gaba. “Me kike nufi?” Nabeeha tayi shiru na wani lokaci, sannan tace, “Ka taba tunanin cewa akwai abubuwan da idan an furta su, sai zuciya ta rasa inda zata tsaya? Na tabbata kana fahimta, domin kai da kanka ka shafe shekaru da yawa ba tare da ka bayyana abin da kake ji ba.” Fawaaz ya lumshe ido, sannan ya bude su a hankali. “Idan so ne, Nabeeha, to a duk inda zuciya zata tsaya, ni zan kasance anan, tare da ke.” Kalmarsa tayi nauyi fiye da duk wata magana da ya taba yi a rayuwarsa. Nabeeha ta juyo ta kalle shi. Zuciyarta cike da wani irin dadi da tsoro a lokaci guda. Fawaaz ya gyada kai, yana murmushi kadan. “Ba zan matsa miki ba. Amma ki sani, tun kafin ki furta, zuciyata ta rigada ta gane amsar da take so.” Shiru ne ya ratsa tsakaninsu. Shiru mai cike da kauna da fahimta. Motar ta tsaya a kofar gidan su Nabeeha. Amma babu wanda yayi yunƙurin motsawa. Fawaaz ya juyo a hankali, yana kallonta da wani irin kallo mai cike da basira. “Ina son ki, Nabeeha.”🤭😍 Ya fada a hankali, ba tare da wata shakka ba. Kamar numfashinta zai tsaya, ta dan lumshe ido. Wannan kalma da ta ke tsammanin ba zata taba ji daga bakinsa ba. Ta bude ido a hankali, sannan ta ce da muryarta mai laushi, “Kirjin Mai Hankali—Akwatin Sirrin Sa.” Fawaaz ya lumshe ido, yana jin yadda kalmarta ta sauka cikin zuciyarsa kamar ruwa a kan ƙasa mai ƙishirwa. Ya bude idanunsa, yana murmushi. “Kin san abin mamaki?” Ta girgiza kai. “Ke ce SIRRIN zuciyata, amma kema kina cikin AKWATIn SIRRIN ki.” Sai ya jingina kansa da kujera, yana kallonta da murmushi. “Zan jira har sai ranar da za ki bude wannan akwatin.” Nabeeha tayi murmushi, zuciyarta na tafasa da soyayyar da ta fara fahimta, soyayyar da bata san yaushe ta shige ta ba. Ko da Nabeeha ta fito daga motar, bata iya tafiya kai tsaye ba. Ta tsaya tana kallonsa. Fawaaz ya dan sunkuya kadan yana kallon ta, kamar yana jin cewa akwai wani abu da take son furtawa. Sai ta saki murmushi, ta furta cikin wata irin murya mai sanyaya zuciya: “Yaa Fawaaz... ni ma.” Bai bukaci ta kammala maganarta ba. Domin ya rigada ya gane abinda take nufi. Ya lumshe ido yana murmushi. A wannan lokaci, babu bukatar karin kalmomi. Soyayya ta riga ta tabbatar kanta. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:55_ Tun daga wannan dare, komai ya canza a tsakanin su Nabeeha da Fawaaz. Ba wai don sun fito fili sun bayyana soyayyarsu ba, sai don zuciyoyinsu sun riga sun fahimci juna, ko da ba su daɗe suna furta kalmomin soyayya ba. Fawaaz ya sake zage damtsen kaimi wajen yawaitar kiranta a waya, yana tambayarta halin da take ciki, yana sauraronta fiye da da. Idan ta ce tana bukatar wani abu, ko kafin ta ƙarasa magana, zai yi kokari ya sameta da shi. Idan kuma suka hadu da juna, zai tsaya yana kallonta, kamar yana kokarin fahimtar SIRRIN da take ɓoyewa a cikin AKWATIn SIRRIN ta. Hakan kuwa ya sa zuciyar Nabeeha ta fara jin sabuwar soyayya. Soyayya wacce ba ta cikin surutu da nuna isa, amma tana cikin ayyuka da kulawa. 🎀 Rana ce mai kyau, babu iska mai ƙarfi, babu rana mai zafi. Nabeeha ta fito daga gidan su, tana sauri saboda tana da wani aiki da zata yi a makaranta. A lokacin da ta fito, ba ta yi tsammanin samun Fawaaz tsaye a bakin motarsa ba, yana jiranta. Ta tsaya cak, tana kallonsa. Shi kuwa, kamar bai ga mamakinta ba, sai ya bude mata kofa yana fadin, "Shiga." Nabeeha ta ɗan taɓe baki, amma ba tare da ta ce komai ba, ta shiga. Ya rufe mata kofa sannan ya zagaya, ya shiga driver's seat, ya tayar da mota. Ta gayshe shi cike da ladabi ya amsa tamkar zai hadiyeta saboda wani kallo da yake binta dashi. Ta masa kyau kwarai matuka tamkar wata baby doll.. Suna cikin tafiya, babu wanda yayi magana. Sai da suka yi tafiya mai nisa, sannan Nabeeha ta dan juyo tana kallonsa. "Ya fawaaz." Ya juyo a hankali, yana kallonta. “Me yasa wani lokaci kamar kana tsoron soyayya?” Ta tambaya, kai tsaye. Ya ɗan yi murmushi, sannan ya mayar da kallonsa ga hanyar gaba. "Ba tsoro ba ne, Nabeeha. Ina kallon soyayya ne a matsayin abu mai tsarki. Abu wanda ba a wasa da shi."😂 Shiru ya biyo baya. Ya sake cewa a hankali, kamar yana magana da kansa, “Soyayya ta gaske, ba a iya furtawa. Ana iya jin ta ne a zuciya.” Nabeeha ta kalli fuskarsa. A karon farko, ta fahimci cewa Fawaaz ba kawai mutum ne mai miskilanci ba, yana da zurfin tunani akan komai da yake yi. A ranta, sai ta furta: “KIRJIN MAI HANKALI... AKWATIN SIRRIN SA.” Babu shakka, Fawaaz yana da SIRRI. Amma ita ma tana da SIRRI a cikin zuciyarta. Sirrin da ya fara bayyana.... Tafiyar da suke yi a motar na da shiru, shiru mai cike da magana. Kowane daga cikinsu yana nazarin wanda ke gefensa. Duk da cewa babu abin da ya bambanta halayyar Fawaaz a zahiri, amma Nabeeha tana iya fahimtar cewa akwai wani abu da ya canza a tsakaninsu. Fawaaz bai sake cewa uffan ba, amma hannunsa da ke kan sitiyari yana dan motsi kamar yana tunanin wani abu mai muhimmanci. Nabeeha ta gyara zamanta. Ta sauke ajiyar zuciya. “Ya Fawaaz.” Ya juyo a HANKALI, yana kallonta, idanunsa na bayyanar da zurfin tunani. "Na’am." “Wata rana… za ka iya bude AKWATIN SIRRIN ka?” Ta fada a HANKALI, kamar tana tsoron jin amsar da zai bata. Fawaaz ya dan lumshe ido, sannan ya bude su da natsuwa. Bai amsa da sauri ba, sai da ya dauki lokaci yana kallonta, kamar yana kokarin sanin irin amsar da take bukata. A karshe, sai ya murmusa kadan. "Idan kin shirya jin gaskiyar da ke cikinsa." Nabeeha ta ji zuciyarta ta buga da sauri. Gaskiya? Shin menene gaskiyar da Fawaaz yake ɓoyewa a zuciyarsa? Da suka iso gidan Humyrah, Fawaaz bai bar Nabeeha ta fito ita kadai ba. Sai da ya fita ya zagaya ya bude mata kofa. "Kada ki dade," ya fada a hankali. "Ina nan a waje." Nabeeha ta dan zaro ido. “Kana nufin za ka jirani yau ma?” Fawaaz bai amsa ba, sai ya jingina da motarsa, yana kallonta da wani irin kallo mai nauyi. "Ki fito da wuri." Ta dan saki murmushi. “Ba zan jima ba.” Tana shiga cikin gidan, sai ta tarar da Humyrah tsaye tana jiranta da fara'arta. “Lallai kuwa! Daga ina kike da soja?” Humyrah ta fada tana dariya. Nabeeha ta dan hade rai. “Me kike nufi?” Humyrah ta matso kusa da ita tana tsokanarta. "Ai duk duniya babu wanda yake tsananta tsaro akanki kamar yayanmu Fawaaz." Ta dan kalle ta da murmushi mai ma'ana, sannan ta gyada kai. "Nima tun shekaru da yawa na fahimci cewa yana kaunarki, sai dai kawai miskilancinsa bai bari ya fada miki ba." Nabeeha ta yi shiru, zuciyarta tana bugawa. “Yana kaunata?” Humyrah ta yi dariya. "Idan har baki gane ba, to ke ce matsalar!" Fawaaz yana tsaye a gefen motarsa, yana jiran fitowar Nabeeha. Idanunsa suna kan kofar gidan, amma a zuciyarsa, yana tunanin abubuwa da dama. "Shin, Nabeeha za ta fahimci cewa zuciyata ta dade tana ajiyarta a cikin Akwatin Sirrinta?" Ya sauke ajiyar zuciya. Idan har akwai ranar da zai bude wannan akwati, to watakila, yau yana gab da hakan. Ko da Nabeeha ta fito daga gidan, ta tsaya tana kallonsa na wani lokaci. Shi ma yana kallonta, fuskar sa da natsuwa. Sai ta taka a hankali, ta tsaya a gabansa. “Yaa Fawaaz… Ni ma.” Bai bukaci ta kammala maganarta ba. Domin ya rigada ya gane abin da take nufi. Ya lumshe ido yana murmushi. A wannan lokaci, babu bukatar karin kalmomi. Soyayya ta riga ta tabbatar kanta. .... Falon gidan Gwaggo Zainabu cike yake da manyan mutane, kuma hirar da ake yi tana tafiya cikin annashuwa. Ana zaune cikin natsuwa, kowanne fuska cike da farin ciki da kwanciyar hankali. A gefe guda, manyan mazajen suna tattauna al’amura. Alhaji Uzairu, Alhaji Amiru, Major General Dawud, Muhammad, da Fawaaz, tare da Chief Judge Abdulfatah da wasu dattawa biyu suna zaune, suna tattaunawa kan rayuwa da zaman duniya. A dayan gefen kuwa, Gwaggo Hafsatu da Gwaggo Zainabu suna zaune cikin jin daɗi, suna sauraron hirar da ke gudana. Sai kuma Hajiya Zaytunah, wacce ke zaune cikin farin ciki, tana kallon sabuwar rayuwar da aka shimfiɗa mata. Gidan da aka gyara mata ba ƙaramin kyawu yake da shi ba. Komai sabo ne, kayan cikin gidan na ƙasashen waje, tamkar wata sabuwar amarya. Abin da aka yi mata ya wuce tunaninta, ya nuna karramawa da daraja. An ci, an sha, an yi nishadi. An yi hira mai cike da barkwanci da dariya. Sai dai daga bisani, hira ta sauya salo. Dattawan suka fara maganar rayuwa da al’amuran iyali, har suka shigo batun matasa da aure. Chief Judge Abdulfatah ya kalli Major General Dawud da murmushi. “Yallabai, har yanzu wannan ƙaton yaron naka yana da aure a gaba?” Ya nuna Fawaaz da sigar zolaya. Dariya ta biyo baya. Major General Dawud ya yi murmushi. “Shi ya sani. Idan ya shirya, to muna nan.” Alhaji Uzairu ya jinjina kai yana murmushi. “Mu ma muna da tamu ‘yar gidan. Idan tana da miji a gaba, to muna jiransa ya bayyana.” Ana cikin haka, Alhaji Amiru ya dubi sauran dattawan da ke zaune, yana mai dariya. “Ni dai ina ganin, tun da duk bangarorin suna da amincewa da juna, me zai hana a daura auren nan take, a nan cikin wannan falon?” Wani shiru ya biyo baya, kowa yana nazari. Sai kuma gaba ɗaya suka amince! Daurin Auren Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad da Captain Fawaaz Dawud A lokacin da aka tsara don daurin aure, yan uwan duk sun hallara a babban parlorn...Captain Fawaaz Dawud, ya kasance cikin kayan mutunci, tare da iyayensa da abokan arziki. Amarya, Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad, tana gida batasan wainar da ake toyawa ba .. bayan sun gama tanadar komai an sayo su huhun goro da alawa, limamin masallacin gidan ne ya jagoranci daurin aure. An fara ne da ambaton sunayen ma’auratan da waliyyansu. Amarya: Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad Waliyyin amarya: Alhaji Amiru (wanda ya tsaya a matsayin waliyyi) Ango: Captain Fawaaz Dawud Waliyyin ango: Major General Dawud.. Limamin ya nemi waliyyin amarya, Alhaji Amiru, ya amince da bayar da auren Nabeeha ga Fawaaz. Sai Alhaji Amiru ya ce: "Na aurar da Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad ga Captain Fawaaz Dawud bisa sadakin da aka yarda da shi." Sai limamin ya tambayi ango, Captain Fawaaz Dawud, ko ya karɓa. Fawaaz, cikin kamun kai da nutsuwa, ya ce: "Na karɓa." Daga nan sai limamin ya yi addu’a, tare da albarka ga ma’auratan. Jama’a suka yi farin ciki da yin kabbarar "Allahu Akbar!" don nuna gamsuwa da amincewa da auren. Bayan an kammala daurin aure, an yi wa ma’auratan addu’o’i. A wannan rana, Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad ta kasance a gida cikin halin rashin sani. Ba ta da masaniya cewa an riga an daura aurenta da Captain Fawaaz Dawud. Tun da safe, an hana ta fita, kuma duk wanda ta tambaya sai dai a bata amsar da ba ta fahimta sosai ba. Da yamma, bayan daurin aure, Fawaaz ya isa gidan da aka kai amarya. Ya shiga cikin gidan cikin natsuwa, kamar yadda ya saba—ba shi da hayaniya ko nuna wata alama ta farin ciki sosai. Duk da haka, a yau akwai wani salo a tare da shi—salo na wanda ya gama nasarar da bai taba zato ba. Akwai wata dakiya a cikin falon lokacin da ya zauna akan kujera, yana kallon Nabeeha da ta tsaya a gefe, cikin shigar biki, amma har yanzu tana cikin rashin tabbas. A zuciyarta tana zargin wani abu, amma ba ta da cikakken bayani. Ya janye numfashinsa a hankali, yana dubanta da idanuwansa masu zurfi. A dai-dai lokacin, Nabeeha ta kasa jure shiru. "Yaa Fawaaz, me ke faruwa?" Ta tambaya, muryarta na nuna rashin tabbas. Fawaaz ya kalli gefen gefe, sannan ya dawo da idanunsa gareta. Cikin nutsuwa, ya furta, "Kin amince da kaddara, ko?" Nabeeha ta rike hannayenta, tana nazarin fuskarsa. "Eh, amma—" Sai ya katseta da cewa: "Toh yanzu, ni ne kaddararki. An daura mana aure." Zuciyarta ta buga! Ta zaro ido, tana kokarin tabbatar da abin da ta ji. "Me?" Ya dube ta ba tare da sakewa ba. "Kin ji abinda na fada. Kin zama matata, Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad Dawud... Mrs, captain Fawaaz. ." Jikinta ya yi sanyi. Hannunta ya fara rawa a hankali, zuciyarta na dokawa da karfi. Wane irin abu ne wannan? Yaya hakan ya faru ba tare da saninta ba? Amma Fawaaz bai bar mata damar juyawa ba. Ya mike tsaye, yana kallonta kai tsaye. "Duk tambayar da kike da ita, sai mun koma gida." Shiru ya ratsa tsakaninsu. Lokaci daya, ta fahimci cewa rayuwarta ta canza gaba daya. Ya karasa kusada ita ya sakar mata sunba a gefen kumatunta. Ya sanya rigarsa yana goge mata hawayen da ke zuba daga idanun ta. Ya shiga rada mata, "Kuka....ki dena zubar mun da tsadaddun hawayen ki please. Ki adana su sai nan gaba. Ranar daren mu na masoya. Ina kaunar ki Nabeeha. Kuma inshaa Allah da yardar Allah ba zaki taba Dana sanin aure na ba.. I love you long time. Love you big." Ta masa dena kukan sai ma sake Jan sautin kukan da takeyi tana rerashi a HANKALI. Fawaaz, da yake ba mutum bane mai yawan surutu ko bayani, sai ya zauna a gaban Nabeeha, yana kallonta da idanunsa masu zurfi. Cikin nutsuwa, ya furta da murya mai nauyi da zurfi, "Nabeeha, from this moment on, you are mine. My wife. My responsibility. My peace. I know this is unexpected for you, but for me, it’s something I have long accepted. Fate has written your name next to mine, and I will honor that..I will protect you, care for you, and stand by you. Not because I have to, but because I want to. Because you are mine now, and I am yours."💜 Ya tsaya, yana kallonta cikin ido, yana jiran ta fahimci nauyin kalamansa. Daga nan ya kara da cewa, "You are no longer just Nabeeha Uzairu Muhammad. You are now Nabeeha Uzairu Muhammad Dawud. My wife." Kawai sai ta fashe da Kuka. Mutumin ku ya wawuro abarsa ya riketa gam. Tamkar zaa kwace masa ita.. ya sanya hannunsa yana shafa gadon bayanta.. "Shhhhhh my love. Kukan ya Isa haka nan. Please mana, kinji babyluv?" Haka dai yayita rokonta yana bata hakuri.. Alhamdulillahi Nabeeha ta samu gata iya gata daga danginta Kashi biyu. Dangin mahaifanta su Alhaji uzairu. Dama danginta na biyu na su major general dawud.. Anmata kaya na lefe da saka rana Wanda aka hada a rana daya . Akwatina kuwa bayyana adadin yawansu da kayan cikin su ma bata lokaci ne. Babu ce kawai babu aciki. Gidah sama da kasa gwaggo hafsatu ta bawa fawaaz kyauta. Da babban kamfaninta na sarrafa shinkafa da wani asibiti da yake mallakinta da wata gidauniya tadan itama duk ta bawa fawaaz. Acikin dukiyarta kaso uku . Kashi biyu ta barwa fawaaz. Lamarin sai Wanda yagani kawai . Mai karatu kadana cikaka da surutu. Nasan duk wannan zantukan Dana zayyana zaace shagalin biki fa? To amarya da ango dai sunce basasan kowani event sun yafe. Nabeeha dama irin kyalekyalen nan baso take ba. Tazo Kuma ta samu miji shima Mai masifar kishi bayason biki a kalle masa mata. Don haka tana cewa bataso shima ya amince. Har yafi Mai kora shafawa. Bayan an gama shagalin dan hidimar cin abinci iya su yan gidan a parlor, an tafi gida cikin farin ciki. Sai dai Fawaaz da Nabeeha ba su bi ayarin mutane zuwa wajen su Gwaggo Hafsatu ba. A maimakon haka, Fawaaz ya wuce da Nabeeha zuwa gida, inda sabuwar rayuwarsu za ta fara. Ko da suka isa, yana gama rufe ƙofa, sai ya juyo ya kalleta. Idanunsa cike da natsuwa da wani irin so mai zurfi. A hankali, ya tako har gabanta. Sai kuma ya ɗan sunkuya kaɗan, yana mai rikota da hannayensa duka Fawaaz ya janye kaɗan, yana kallonta da wani irin kallo mai cike da zurfin so. Hannayensa har yanzu suna riƙe da nata, kamar yana tabbatarwa kansa cewa hakika, ta kasance tasa, ba tare da shakka ba. "Kin san me, Nabeeha?" Ta ɗan lumshe ido, tana jin yadda numfashinsa ke busa fuskarta. Ta buɗe idanu a hankali, tana kallonsa. "Me?" Ta tambaya da wata murya mai laushi. Ya yi murmushi, yana sanya yatsansa ya shafi gefen fuskarta a hankali. "Na dade ina ɓoye SIRRI a cikin KIRJINa. HANKALI na baya sukuni akan ki.... Amma yanzu, ba SIRRI a tsakaninmu." Zuciyarta ta harba da sauri. Ta ji yadda kalmomin nasa suka gama ratsata, suka shige har cikin zuciyarta. Hannunsa ya shafi gefen kanta, yana kara matsota kusa da shi. Ta ji yadda numfashinsa ya daki fuskarta, kafin a hankali ya sanya labbansa ya sumbaci nata. Ta rufe idanuwanta a hankali, tana jin wani irin yanayi mai daɗin gaske yana ratsata. "Nabeeha…" Ya kira sunanta a hankali, yana sake shafa fuskarta. "Ba zan iya rayuwa ba ke ba." Ta buɗe idanuwanta da suka cika da ƙauna. A karon farko, ta fahimci cewa Fawaaz ba wai yana sonta bane kawai, yana jin ta a cikin jininsa. A hankali ta jingina kanta da ƙirjinsa, tana jin bugun zuciyarsa yana tafiya tare da nata. "Ni ma, Yaa Fawaaz… Ni ma." ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:56_ Fawaaz ya lumshe ido, yana jin dumin Nabeeha a jikinsa. Kamar a mafarki, yau ita ce a hannunsa, ita ce tasa. Ya dade yana ɓoye soyayyarta a Kirjin sa, yana ƙoƙarin danne zuciyarsa. Amma daga wannan dare, babu wani SIRRI a tsakaninsu. Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ɗaga hannayensa ya riƙe fuskarta, yana kallonta da kyau. “Kin san me yasa ba zan taɓa barinki ba, Nabeeha?” Ta girgiza kai a hankali, tana kallonsa cikin ido. Ya ɗan yi murmushi, sannan ya shafi kumatunta da yatsansa. “Domin kece amincina. Kece nutsuwata. Kece wacce zuciyata ta zaɓa tun kafin na san dalili.” Ta lumshe ido, zuciyarta tana harbawa da sauri. Jin kalmomin da suka gama tafiyar da ita. “Ya Fawaaz…” Ta furta a hankali. Ya sake shafa gefen fuskarta. "Nabeeha, ki sanarmun me ke zuciyarki. Na jima ina jira." Ta ɗan yi shiru, tana kallonsa. Sai ta ajiye tafin hannunta a kirjinsa, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa. "Ka san me, Ya Fawaaz?" Ya gyada kai, yana jiran jin abin da za ta faɗa. "Tunda nake, ban taɓa jin tsaro irin na kasancewa a kusa da kai ba." Ya ɗan murmusa, yana sake shigar da hannayensa ta bayanta, ya matseta a jikinsa. "Na jima ina jiran jin hakan daga gare ki." Ya sunkuya, yana sake sinsinar gefen kunnenta, sannan ya sauke ajiyar zuciya. "Ina sonki, Nabeeha." Ta rufe idanuwanta, zuciyarta tana tafasa da kauna. "Ni ma, Ya Fawaaz... Ina sonka." A wannan dare, babu wani sirri da ya rage tsakanin zuciyoyinsu. Duk wani tunani da shakku sun ɓace. Soyayya ce kaɗai ta zauna, ta cika sararin zuciyarsu. A hankali, Fawaaz ya dago fuskarta yana kallon cikin idanunta da ke cike da soyayya. Zuciyarsa tana tafasa da wani irin shauƙi da bai taɓa jin irinsa ba. Ya sanya tafin hannunsa ya rufe nata a HANKALI, yana jin dumin hannayenta da wani sanyi mai ratsa jikinsa. "Kin san me, Nabeeha?" Ya furta da murya mai ƙasa, cike da soyayya. Ta lumshe ido a hankali, sannan ta buɗe su, tana kallonsa. "Me?" Ya yi murmushi, yana shafa ƙananan yatsunta da nasa. "Soyayyarki tana da zuma. Amma akwai madaci a cikinta." Ta ɗan zaro ido, cikin rashin fahimta. "Madaci?" Ya gyada kai, yana kallonta da ƙwarewa. "Eh. Domin na jima ina ƙaunarki, amma ban iya faɗa ba. Wannan ne madacin." Nabeeha ta cije laɓɓanta, zuciyarta tana harbawa da sauri. Wata soyayya mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali tana ratsa zuciyarta. "Kuma zumar fa?" Ta tambaya tana kallonsa da idanunta masu laushi. Fawaaz ya murmusa, sannan ya kamo laɓɓanta da yatsansa. "Zumar ita ce ke yanzu a jikina. Ba SIRRI tsakaninmu." Tayi shiru, tana kallonsa da wani yanayi na zurfin soyayya. Sai ta sanya kanta a KIRJIN sa, tana jin bugun zuciyarsa. "Ya fawaaz…" Ta furta a hankali. Ya ɗan lumshe ido, yana sake shinshinar ƙamshin gashinta. "Na’am, Nabeeha?" Ta ɗago da fuskarta, idanunta cike da natsuwa. "Za ka riƙe ni har abada?" Ya murmusa, yana ɗan kifa goshi da nata. "A duniya da lahira, Nabeeha." A haka suka kasance, zuciyoyinsu a haɗe, ba tare da shakku ko jin tsoro ba. Fawaaz ya jingina goshinsa da nata, yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa. A yanzu, babu wani shakku a zuciyarsa. Ta zama tasa, har abada. Hannunsa ya sauka a fuskarta, yana shafa laushin kumatunta da yatsansa. "Nabeeha..." Ta lumshe ido, tana jin yadda muryarsa ke ratsata kamar sautin zuma. "Na'am?" Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya yi murmushi. "Kin taba jin ana yin soyayya a cikin sirri?" Ta buɗe idanuwanta, tana kallonsa. "Ban gane ba." Ya dube ta da idanunsa masu cike da zurfi. "Tun da nake, ban taɓa fadar soyayyarki ba. Amma kin zauna a cikin zuciyata, kamar wata ƙaunar da ba kowa ya san tana wanzuwa ba." Ta lumshe ido, zuciyarta na harbawa da sauri. " Ya Fawaaz..." Ya yi shiru yana kallonta, yana jiran abin da za ta ce. "Ina jin kamar ina raye ne a cikin zuciyarka, ba a duniya ba." Ya ɗan murmusa, yana riƙe hannayenta da ƙarfi. "Kin faɗi gaskiya, Nabeeha. Tunda nake, ban taɓa jin wata mace a zuciyata ba irin yadda kike ciki." Ta ɗan sunkuya, tana rufe fuskarta cikin tafin hannunta. Soyayyar da take ji a zuciyarta ta yi mata yawa. Ya kama hannayenta ya janye daga fuskarta, yana kallonta da murmushi. "Ki daina ɓoyewa, Nabeeha. Zuciyarmu ɗaya ce yanzu." A hankali ya sanya labbansa ya sumbaci goshinta, yana furta cikin siririyar murya, "A yanzu, babu wani sirri a KIRJINa, Kin zama SIRRI na, Nabeeha." Idanunta suka cika da hawaye, ba na bakin ciki ba, na farin ciki. "Ya Fawaaz... Ina sonka." Ya matseta a jikinsa, yana shinshinar ƙamshin fuskarta. "Ni ma, Nabeeha. Fiye da yadda zan iya faɗa." A yau, zuciyoyinsu sun haɗu gaba ɗaya. Kuma babu wani SIRRI da zai rabu da su. AKWATIN SIRRIN SA ya buɗe, kuma SIRRIN da ke cikinsa shi ne soyayya. A lokacin da Nabeeha har yanzu ke cikin matsananciyar mamaki, zuciyarta na harbawa da sauri, Captain Fawaaz Dawud ya yi abu da ba ta taba tsammani ba. Kafin ta fahimci me ke faruwa, ya dauke ta cak cikin hannayensa, kamar yadda ake daukar jaririya. "Ya fawaaz—" Ta yi kokarin magana, amma ya kalle ta da wata irin murya mai kwantar da hankali. "Shh… you are mine, Nabeeha. Tonight, I will make you understand what that means." Ya nufi dakin da aka kawata da hasken fitilu masu laushi, yana rike da ita kamar wata amana mai daraja. A hankali ya kwantar da ita a kan gadon da kayan shimfida masu laushi ke lullube da shi, yana kallonta da idanunsa masu cike da soyayya. Sai ya zauna kusa da ita, yana shafa fuskarta da yatsunsa cikin kwarewa. Ya sunkuya ya sumbaci goshinta, sannan kumatunta, a hankali kamar yana jin dadin jin dumin fatarta. "Nabeeha, do you know what you mean to me?" Ya tambaya, yana kallon ta cikin ido. "I don't know…" Ta furta cikin wata murya mai sanyi, zuciyarta na dokawa. Ya yi murmushi mai dauke da wata nutsuwa, sannan ya shafa gefen fuskarta. "You are the most precious gift Allah has given me. My heart, my soul, my peace. You are mine, and I will cherish you forever." Ya ci gaba da yi mata sumbata a goshinta, gefen wuyanta, sannan ya tsaya yana kallonta da idanu masu cike da shauki. Sai ya fara tambayarta wasu tambayoyi game da musulunci. "Nabeeha, tell me, what is the foundation of our faith?" Ta gyara zama, tana kallonsa da kulawa. "La ilaha illallah, Muhammadur Rasulullah." Ya yi murmushi. "Good. And what is the right of a husband upon his wife?" Ta dan yi shiru, sai ta ce, "To respect, obey, and stand by him in goodness." Ya kalli ta da wani irin so a idanunsa. "And my duty to you?" Ta sake kallonsa, tana jin wani sabon natsuwa. "To love, protect, and provide for me." Ya kama hannunta ya sumbata, sannan ya sanya hannunsa a kan kanta. "Let me bless this union." A hankali, ya fara yin addu’a, yana rokon Allah ya sanya albarka a rayuwarsu, ya sa soyayyarsu ta dore, ya sa su kasance cikin kwanciyar hankali da juna. Bayan ya gama addu’a, sai ya rage hasken fitilar dakin zuwa dim light, yana kallonta da wata irin natsuwa. A hankali, ya durkusa kusa da ita, yana shafa fuskarta da yatsunsa. Sai ya sumbaci idanunta, gefen kumatunta, sannan bakinta. "Nabeeha, I love you. And tonight, I will show you just how much." Ya fara romancing dinta sosai, yana shafa jikinta a hankali, yana jin yadda numfashinta ke sauyawa. A hankali ya rika sumbatar ko’ina na jikinta, yana gaya mata kalaman soyayya cikin murya mai dauke da shauki, "Your scent drives me crazy… your skin is like silk… your lips, your eyes, your everything—Nabeeha, you are perfect." Hannayensa suna biye da maganarsa, yana jin dadin jin yadda jikinta ke amsawa da shaukinta. A hankali, ya kara nutsuwa cikin soyayya da shauki, yana barin dare ya kasance na su biyu kawai... Hannunsa ya Saka a bayan rigarta ya balle bra dinta a hankali yana zume rigar zuwa kasa kasa... Ya sanya tattausan labbansa akan nata leben yana tsotsa ahankali tamkar ya samu alawar tsinke. Yayinda daya hannunsa ke zagaye acikin rigarta yana shafa albarkatun KIRJIN ta... Nabeeha, menene ginshikin addinin Musulunci? Nabeeha tache "Ginshikin addinin Musulunci su ne shika-shika guda biyar: 1. Shahada – yin shaidar babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (SAW) manzonSa ne. 2. Sallah – tsayar da sallah biyar a rana. 3. Azumi – azumin watan Ramadan. 4. Zakka – bayar da sadaka ga mabukata. 5. Hajji – zuwa aikin Hajji ga wanda yake da iko.* Fawaaz: Masha Allah! Kin fi karfin misali. Yanzu ki gaya min, wane hakki ne miji yake da shi a kan matarsa? Nabeeha: Miji yana da hakki a kan matarsa na biyayya, girmamawa, kula da gidansa da SIRRIN SA, da kuma tallafa masa a cikin halal. Fawaaz: To, wane hakki ne mata take da shi a kan mijinta? Nabeeha: Miji yana da alhakin kula da matarsa, ciyar da ita, tufatar da ita, kare ta, da kuma kyautata mata. Fawaaz: Hmmm... Nabeeha, idan Allah zai ba ki damar zabar wanda za ki aura, shin da ni za ki zaba? Nabeeha: (ta runtse ido, tana murmushi) Kaddara ta riga ta zo, amma... eh, zan zabe ka. Fawaaz: (yana murmushi, yana shafa fuskarta a hankali) Allah Sarki, kin sani kuwa cewa wannan shine abin da na fi jin dadinsa a yau? Nabeeha, me kike jin dadin yi a rayuwa da kike so mu rika yi tare? Nabeeha: Ina son karanta littattafai da yin addu’a da wanda nake so. Ina so mu rika karanta Al-Qur’ani tare. Fawaaz: (ya sumbaci goshinta) Wallahi kin zama arziki a rayuwata. Nabeeha, idan na rike hannunki, me kike ji a zuciyarki? Nabeeha: (ta yi shiru, tana kallon hannunsu da yake cikin nasa) Ina jin kwanciyar hankali, kamar babu abin da zai iya cutar da ni matukar ina tare da kai. Fawaaz: (ya rage hasken dakin zuwa dim light, yana shafa gashinta a hankali) Nabeeha, yau zan tabbatar miki da cewa ke ce ke kadai a raina. Sai ya ci gaba da shafa fuskarta da sumbata cikin soyayya, yana bayyana irin yadda yake kaunarta… ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:57_ Nabeeha ta dan rankwafa a kan cinyarta, tana wasa da zoben hannunta, yayin da Fawaaz ya kura mata ido cikin nutsuwa. Idanunsa sun cika da wani irin lumshin soyayya da ita kanta ba ta saba gani a tare da shi ba. A hankali, ya sanya hannunsa ya kamo nata. Jin yadda tafin hannunsa ke da dumi ya sa ta lumshe ido, zuciyarta na bugawa da sauri. “Nabeeha…” Ya kira sunanta da wata murya mai sanyi da ta sa ta dago kai a hankali. Ba tare da wata shakka ba, ya shafa gefen fuskarta da yatsunsa, yana kallon idonta da suka cika da lumana. “Kin san kuwa cewa tun farkon haduwar mu, zuciyata ta karɓe ki fiye da yadda zan iya bayyanawa?” Ta dan lumshe ido, tana jin yadda kalamansa ke shigar mata har cikin zuciya. Bai tsaya a nan ba, ya ɗauko lemon da ya siyo mata ya bude, sannan ya mika mata. “Ki sha mana, na san baki ci komai ba.” Ta karɓa a hankali, tana jin yadda kulawarsa ke ratsa ta. Bayan ta ɗan kurɓa, ya mika mata naman kajin da ya siyo, yana mai cewa, “Ki ci sosai, Nabeeha. Ba na son ki wahala ko kaɗan.” Sai da ta ɗan ci, sannan ya kura mata ido yana murmushi. “Kin san kuwa kin fi kyau idan kina murmushi?” Wani sanyi ya ratsa ta, ta kasa cewa komai. Ya kai hannunsa ya shafi gefen bayanta a hankali, yana jin yadda numfashinta ke fita cikin nutsuwa. A hankali ya kai bakinsa kusa da goshinta, ya dora wani laushi a kai. "Soyayyarki abu ne da ba zan iya misaltawa da komai ba, Nabeeha," ya furta a hankali. Fawaaz ya dan yi shiru yana kallon yadda Nabeeha ke taunar abincin da ya bata. Duk da cewa ta kasa dago ido ta kalle shi, yana iya hango yadda fuskarta ta sauya launi, tamkar wadda take jin nauyin kallonsa. Wani siririn murmushi ya bayyana a saman fuskarsa, sannan a hankali ya kai hannunsa ya riko nata. Nabeeha ta tsinke daga cikin tunaninta lokacin da ta ji dumin tafin hannunsa yana shafar nata. Ta yi kokarin janye hannun, amma ya rike cikin taushi, yana wasa da yatsunta a hankali. “Kina tsoro na ne, Nabeeha?” Ya tambaya cikin murya mai rauni. Ta girgiza kai a hankali ba tare da ta dago ba. Ya dan kifa goshinta da nasa, yana jin numfashinta yana gauraya da nasa. Hannunsa na rike da nata, yana shafar tafin hannunta a hankali. "Ina so ki fahimta, Nabeeha," ya fada cikin wata murya mai laushi, "soyayyata a gare ki ba wasa ba ce. Kullum ina tunaninki, kuma duk lokacin da na ganki, zuciyata tana bugawa da wani irin yanayi da ban saba ji ba." Ta lumshe ido, tana jin nauyin yadda yake furta kalmomin da suka shige ta har cikin zuciya. Fawaaz ya yi shiru na wasu dakiku, sannan ya sanya hannunsa ya shafi gefen fuskarta cikin kulawa. "Na dade ina kokarin boye abin da nake ji, Nabeeha," ya cigaba, yana kara matsowa kusa da ita. "Amma kullum sai da kika shige zuciyata fiye da da. Babu wani lokaci da nake tunani ba tare da kin zo cikin zuciyata ba." A hankali ya dora bakinsa a goshinta, yana shafar bayanta cikin taushi. "Kin canza min rayuwa, Nabeeha. Kin sa na fahimci abin da ban taba tunanin zan iya ji ba." Numfashinta ya dan rikice, ta kasa bude idanunta. Wani irin sanyi ya ratsa ta, musamman yadda yake shafar bayanta da hannunsa mai laushi, yana kara matse ta a jikinsa. A hankali ya dago fuskarta, yana kallon cikin idonta da ke dauke da wani irin shauki. "Ba zan taba gajiya da nuna miki soyayya ba, Nabeeha," ya fada a hankali, kafin ya dora laushi a saman lebenta. Ta lumshe ido, zuciyarta na bugawa da sauri. Wani irin shauki da ba ta taba jin irinsa ba ya ratsa ta. Hannunta ya fada cikin nasa, yana rike da ita tamkar ba zai taba sakinta ba. Daga nan, ya ja hannunta ya mike tsaye. "Mu koma ciki ki huta, Nabeeha. Ina so ki sami nutsuwa," ya fada yana riketa da kulawa. Ta kasa cewa komai, amma zuciyarta cike take da wani irin soyayya da nutsuwa da ba za ta iya misalta wa ba. Fawaaz ya kama hannunta cikin kulawa, yana tafiya da ita zuwa cikin wani daki na daban da aka kawata gadon da farin bedsheet daya Sha roses anyi Zanen zuciya wato heart . Dukkan motsinsa na nuni da soyayya da kwarewa, tamkar wanda ya dade yana jira ya bayyana abin da ke cikin ransa. Yana jin yadda tafin hannunta ke dumi a cikin nasa, hakan ya kara masa kwanciyar hankali. Bayan sun isa cikin dakin, ya zaunar da ita a gefen gadon, sannan ya durkusa a gabanta, yana kallon fuskarta cikin nutsuwa. "Nabeeha," ya kira sunanta cikin sanyi, yana shafar tafin hannunta. "Kina jin dadin zama tare da ni?" Ta dago ido a hankali, ta kalle shi, sannan ta dan yi murmushi kadan. “Eh…” Murmushi ya bayyana a saman fuskarsa. Ya mike ya dauko ruwa daga kan fridge, ya bude sannan ya mika mata. “Ga ruwan nan, ki sha ki huta.” Ta karba a hankali, ta kurɓa, sannan ta ajiye kwalbar a gefe. Fawaaz ya zauna a gefenta, yana kallon fuskarta da murmushi mai cike da so. "Kin san," ya fara magana, yana dora hannunsa kan nata, "na dade ina son ki, amma ban san yadda zan bayyana ba. Kullum sai na ga kamar in boye, amma zuciyata ta kasa." Ta lumshe ido, tana jin yadda kalmomin nasa ke shiga har cikin zuciyarta. Bai tsaya a nan ba, ya sanya yatsunsa ya shafi gefen fuskarta cikin taushi, yana kallon cikin idonta. "Ba zan taba barin ki ba, Nabeeha," ya fada cikin murya mai taushi. "Kuma ba zan bar ki da jin kadaici ba. Ni da ke, har abada." A hankali, ya rungumeta, yana shafa bayanta cikin kulawa. Yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa, sannan wani irin sanyi da farin ciki suka ratsa shi. Ya dora bakinsa a goshinta, yana dan lumshe ido. “Kin sa na fahimci menene soyayya,” ya fada a hankali. Ta kasa cewa komai, amma zuciyarta cike take da soyayyar Fawaaz, wanda a yanzu ta fara fahimtar cewa so na gaskiya ba kalmomi ba ne kawai, sai an nuna shi da aiki. . Fawaaz ya ci gaba da rungume ta a jikinsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da farin ciki mai cike da shauki. Numfashinsa yana sauka a cikin gashinta, yana jin daddadan kamshin turarenta da ke ratsa zuciyarsa. Na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE (08095215215) A hankali ya daga fuskarta ya kalli cikin idonta. “Nabeeha…” ya kira sunanta a hankali, kamar wanda yake jin tsoron rasa ta. Ta dago ta kalle shi, idonta na dauke da wani irin yanayi da bai saba gani a tare da ita ba. Bai yi wata wata ba, ya shafi gefen fuskarta cikin kulawa, yana lasar lebbensa kamar wanda yake tunanin wani abu mai muhimmanci. “Kin san kuwa cewa kin zama wani bangare na zuciyata?” Ya furta cikin wani irin salo da ya sa ta lumshe ido. Shiru ya ratsa tsakanin su na wani lokaci. Sai dai numfashinsu da ke gauraya da juna ne kawai ke ji. A hankali Fawaaz ya kai bakinsa kusa da nata, yana shafar bayanta da hannunsa. Ya furta cikin wani irin sauti mai zurfi, “Ba zan taba gajiya da nuna miki irin soyayyar da nake ji ba.” A hankali ya dora bakinsa saman goshinta, yana shafa gefen kumatunta da yatsunsa. Sai da ya ji numfashinta ya dan rikice, sannan ya koma gefe ya zauna, yana rike da hannunta. "Ki ci gaba da zama tare da ni, Nabeeha," ya fada a hankali, yana shafar tafin hannunta. "Kin fi karfin duk wani tunani da zuciyata ke yi." Ta yi shiru, amma zuciyarta cike take da nauyin irin soyayyar da yake nuna mata. Wannan ba Fawaaz din da ta saba gani bane—miskilin nan da baya magana da ita sai dai gaisuwa. Wannan wani daban ne, wanda yake shirin bayyana mata wani sabon yanayi da ba ta taba tsammani ba. Fawaaz ya ci gaba da kallonta, yana jin yadda zuciyarsa ke cike da shaukin kasancewa tare da ita. Hannunsa har yanzu na cikin nata, yana shafar tafin hannunta cikin kulawa da natsuwa. "Nabeeha," ya kira sunanta a hankali, yana matsowa kusa da ita. Ta dago ido ta kalle shi, tana jin yadda wani irin sanyi ke ratsa ta. Ya dan shafa gefen kumatunta, yana murmushi. “Kin taba tunanin cewa wata rana zan kasance haka tare da ke? Ni da ke, babu kowa, cikin lumana da natsuwa?” Ta dan yi shiru, sannan ta girgiza kai a hankali. “A’a…” ta furta cikin wata siririyar murya. Ya yi murmushi, yana shafa bayanta cikin kulawa. “Ni ma ban taba tunanin cewa wata rana zan iya bayyana irin wannan soyayyar ba.” Ya sauke ajiyar zuciya, yana kallon idonta kai tsaye. “Amma yanzu, babu abin da ya fi muhimmanci a gareni fiye da ke.” Shiru ya ratsa dakin, zuciyoyinsu suna bugawa da wani irin shauki. A hankali, Fawaaz ya kai bakinsa kusa da goshinta, yana dora wani laushi a kai. "Na dade ina fatan wannan lokacin, Nabeeha," ya fada a hankali, yana shafar bayan hannunta. "Ina so ki sani cewa ba zan taba barin ki ba. Ko da yaushe zan kasance tare da ke." Ta kasa cewa komai, amma zuciyarta cike take da soyayyar Fawaaz. A wannan lokacin, ta fahimci cewa soyayyarsa ba kalmomi kawai ba ne—abu ne da yake fitowa daga zuciya, abu ne da ke cike da gaskiya da natsuwa. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:58_ Fawaaz ya ci gaba da kallonta, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da wata irin nutsuwa da bai taba ji ba. Hannunsa har yanzu yana shafar nata, yana wasa da yatsunta a hankali, tamkar wanda ke jin tsoron su tsinke. A hankali, ya dago fuskarta, yana kallon idonta kai tsaye. “Nabeeha…” ya kira sunanta a hankali, murya mai dauke da zurfin soyayya. Ta dago ta kalle shi, idonta na dauke da wani irin shauki da ya sa numfashinsa ya dan dauke na sakanni. Bai yi wata-wata ba, ya shafa kumatunta da yatsunsa, yana jin yadda fatar jikinta ta yi laushi a hannunsa. “Ina so ki fahimta…” ya furta a hankali, yana shafar gashinta cikin kulawa. “Ni ba mutum bane mai son surutu, amma ke… kin sa na canza. Kin sa na fahimci soyayya a wata fuska da ban taba zato ba.” Nabeeha ta kasa cewa komai. Domin tunda ya fara magana tun dazu ta daskare tamkar wata kankara. Mamaki, kauna, farin ciki. Baki daya sun hautsine mata. Kalaman Fawaaz sun ratsa ta sosai, zuciyarta na harbawa da sauri. Jin yadda hannunsa ke rike da nata cikin taushi ya sa ta lumshe ido, tana jin dumin jikinsa yana ratsata. Fawaaz ya lumshe ido, yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa. Bai san lokacin da ya dan yi murmushi ba. “Ko da yaushe ina tare da ke, Nabeeha,” ya furta, yana kai hannunsa ya shafa bayan wuyanta a hankali. “Ba zan taba gajiya da nuna miki irin son da nake miki ba.” A hankali ya janye kadan, yana kallon fuskarta kamar mai nazari. “Kin san menene?” Ya tambaya cikin wata murya mai laushi. Ta girgiza kai, tana jiran jin abin da zai fada. Ya yi ajiyar zuciya, sannan ya rike tafin hannunta sosai. “Ke ce abin da zuciyata ke bukata.” Kalamansa sun ratsa ta sosai. Ta lumshe ido, zuciyarta na cike da wani irin dadi da bata taba ji ba. Ya cigaba da shafa bayanta cikin kulawa, yana jin yadda jikinta ke daukar dumin nasa. “Zan ci gaba da kula da ke har abada, Nabeeha,” ya furta a hankali, yana dora goshinnsa a nata. Ta kasa boye murmushinta. Wannan Fawaaz da ta san miskili ne. Amma a yau, yana fadin kalmomin da suka sanya zuciyarta bugawa da wani irin shauki da soyayya. Fawaaz ya ci gaba da kallonta, hannunsa har yanzu yana shafar nata cikin kulawa. Idanunsa sun cika da wani irin shauki da yake kokarin boyewa, amma yana jin ba zai iya hakan ba. A hankali ya sanya yatsunsa ya shafa gefen kumatunta, yana murmushi kadan. "Kin taba jin yadda zuciya ke bugawa da sauri saboda wani mutum?" Ta dan lumshe ido, sannan ta girgiza kai a hankali. “Ban sani ba…” ta amsa da siririyar murya. Murmushi ya bayyana saman fuskar Fawaaz. “Ni na sani,” ya fada a hankali. “Kuma a duk lokacin da nake tare da ke, haka nake ji.” Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta. Ta dan sunkuyar da kai, amma Fawaaz ya kamo tafin hannunta, yana shafar shi a hankali. "Kin san me yasa na kawo miki kaji da lemon nan?" Ya tambaya, yana matsowa kusa da ita. Ta girgiza kai. "Saboda na san ba kya son cin abinci idan kina cikin damuwa," ya amsa, yana kallonta da murmushi. "Kuma bana so ki wahala, Nabeeha." Hawayen farin ciki suka cika idonta. Bata taba jin wani yana kulawa da ita da irin wannan soyayyar ba. Fawaaz ya dan yi shiru na wasu sakanni, sannan a hankali ya matsar da gashinta daga fuskarta, yana kallonta da murmushi. "Na dade ina jiran wannan lokacin," ya fada cikin sanyin murya. "Ina so ki sani, ba zan taba gajiya da nuna miki soyayyata ba." A hankali ya riko hannunta da duka hannayensa, yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa. "Kuma ba zan taba barin ki ba." Nabeeha ta dago kai ta kalle shi, idonta cike da shauki da godiya. Ta san cewa Fawaaz ba mutum bane mai saukin furta kalmomi, amma a yau, yana gaya mata duk abin da ke cikin zuciyarsa. Zuciyarta ta cika da soyayya da nutsuwa. Wannan Fawaaz din da ke gabanta shine wanda take jin son shi ya zurfafa fiye da yadda ta taba tsammani. Fawaaz ya sauke ajiyar zuciya, yana jin yadda zuciyarsa ke cike da natsuwa. A wannan lokacin, babu wani abu da yake so sama da kasancewa tare da Nabeeha. Ya jima yana kokarin danne soyayyar da ke cikin ransa, amma a yau, ya yarda da zuciyarsa gaba daya. Ya dan riko hannunta da duka hannayensa, yana shafar tafin hannunta cikin kulawa. “Nabeeha,” ya kira sunanta a hankali, yana kallon cikin idonta. Ta dago, suka hada ido. A cikin idanunsa, ta ga soyayya da gaskiya. Ta ga natsuwa da nutsuwa da ya sa ta kasa dauke idanunta daga nasa. Ya yi murmushi kadan, sannan ya furta da wata murya mai sanyi. “Kin zama wani bangare na zuciyata.” Hawayen farin ciki suka cika idonta, amma ta dan yi murmushi, zuciyarta cike da soyayya. Fawaaz ya matsar da gashinta daga fuskarta, sannan ya dora laushi a goshinta. “Ba zan taba barin ki ba, Nabeeha. Ko da me zai faru.” Daga nan, ya ja hannunta cikin nasa, yana jin wani irin nutsuwa da bai taba ji ba. Sun zauna haka na wani lokaci, babu wanda ya ce komai, amma zuciyoyinsu na sadar da sakonnin soyayya masu karfi fiye da kowanne furuci. Wannan shi ne farkon sabon babi a cikin rayuwarsu—babi da zai kasance cike da soyayya, kulawa, da tsananin shakuwa da ba za a iya rabawa ba. Za mu ci gaba da labarin Fawaaz da Nabeeha cikin salo mai tsafta da cike da soyayya da kulawa. Bayan wannan dare mai cike da natsuwa, Fawaaz ya ji zuciyarsa ta samu kwanciyar hankali fiye da yadda ya zata. A da, miskili ne da baya son bayyana abubuwan da ke ransa, amma yanzu yana jin yana iya faɗa wa Nabeeha komai... A ranar baki daya bai mata komai ba na daga daren farko na raya sunnah. Sakamakon barinta yayi da su dan Kara hutawa tukunna. So yake sai ta saki jiki dashi sosai... Da sassafe, lokacin da hasken safiya ya fara ratsawa ta tagogin dakin, Fawaaz ya farka. Ya kalli gefensa inda Nabeeha take zaune akan karamin kujera, tana duba wayarta. Wata fara'a ta bayyana a fuskarsa, amma sai ya dan juya gefe, yana cigaba da kallonta ba tare da ta sani ba. Bayan ƴan mintuna, ta ɗago, suka hada ido. Fawaaz ya murmusa kadan, sannan ya furta da murya mai laushi, "Da asuba kike farkawa haka?" Nabeeha ta dan yi murmushi, ta gyara zamanta. “Na saba,” ta fada a hankali. “Kai fa? Bana tunanin kana da ɗawainiyar tashi da wuri.” Fawaaz ya dan lumshe ido na sakanni, kamar yana tunani. “Tashi da wuri ba matsala bane idan zan ga fuskarki da farko.” Murmushinta ya faɗaɗa, amma sai ta sunkuyar da kai, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Wannan Fawaaz ɗin da take gani ba shi da kama da wanda ta saba da shi a baya. Bai tsaya nan ba, ya mike tsaye ya kama hannunta, yana juyawa yana kallonta. “Me za ki ci da safe?” Ta girgiza kai. “Ba komai, bana jin yunwa yanzu.” Fawaaz ya kalleta da mamaki. “Duk da cewa jiya ba ki ci da yawa ba?” Nabeeha ta lumshe ido. “Ba kwa jin yunwa irin ku masu tarin damuwa.” Fawaaz ya yi shiru, yana nazarin maganarta. Bai so ta fahimci halin da yake ciki ba, amma hakan ya nuna cewa ita ma ta fahimci cewa akwai abubuwan da ke damunsa. A hankali, ya kamo tafin hannunta ya riketa da duka hannayensa. “Daga yau, zan kula da ke fiye da yadda na taba yi.” Idanunta suka cika da ruwa, zuciyarta na bugawa da sauri. Kalaman Fawaaz sun ratsa ta, don ta san cewa idan ya yi alkawari, ba ya saba. Ya kalleta ido cikin ido, sannan ya furta a hankali, “Kina da daraja a zuciyata, Nabeeha.” Hakan ya tabbatar mata da cewa wannan soyayyar nasu ta fara shiga sabon mataki—matakin da ya fi ƙarfinsa da na ita, matakin da zai cika da kulawa da soyayya fiye da yadda suka taba tsammani. Fawaaz ya ci gaba da kallon Nabeeha, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da wani irin shauki mai daɗi. Bai taɓa tsammanin cewa wata rana zai iya zama haka ba—mutum mai iya bayyana soyayyarsa da kulawa ba tare da wani shakku ba. A hankali ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon yadda ta kaɗa idanu kamar mai jin kunya. Hannunsa har yanzu yana riƙe da nata, yana jin dumin tafin hannunta kamar wani abu mai daɗin gaske. “Ina so ki ci abinci,” ya furta a hankali, murya mai laushi da cike da kulawa. “Ba zan bar ki da yunwa ba.” Nabeeha ta lumshe ido, tana jin yadda wani sanyi ke ratsa ta. A da, ita ce ke kula da kowa, ba tare da tunanin cewa wani zai damu da ita haka ba. Amma Fawaaz, yana nuna mata wata soyayya mai cike da kulawa fiye da yadda ta taɓa tsammani. "Me za ka kawo min?" ta tambaya a hankali, tana kallon shi ido cikin ido. Fawaaz ya ɗan yi murmushi, sannan ya yi tunani na sakanni. “Me za ki so?” Ta ɗan yi shiru, sai ta ce, “Ko tea kawai ma ya isa.” Ya girgiza kai. “A'a, sai dai idan zan haɗa da biredi ko wani abu.” Murmushinta ya ƙara faɗaɗa. “To shikenan, na yarda.” Ba tare da ɓata lokaci ba, Fawaaz ya miƙe tsaye, yana ɗaukar wayarsa don kiran mai kawo abinci. Duk da cewa zai iya fita da kansa ya siya, amma a yanzu bai son barin Nabeeha ita kaɗai. Bayan ya gama kiran, ya dawo ya zauna a gefenta, yana kallonta da wani irin nazari. "Nabeeha," ya kira sunanta a hankali. Ta ɗago ta kalle shi. “Na’am?” Ya dan lumshe ido kafin ya buɗe su a kanta. “Kin san cewa ina son ki?” Zuciyarta ta buga da sauri, sai ta kasa cewa komai. “Ban taɓa jin irin wannan soyayyar ba,” ya ci gaba da magana, murya mai sanyi. “Kuma ban san yadda zan bayyana shi ba. Amma na san cewa bana son na rasa ki.” Nabeeha ta ji kamar zuciyarta zata fito saboda yadda take bugawa da ƙarfi. Wannan ba Fawaaz ɗin da ta saba gani ba ne. Wannan wani sabon Fawaaz ne, wanda yake bayyana zuciyarsa kai tsaye. Ta sunkuyar da kai, tana jin yadda hawayen farin ciki ke taruwa a idonta. Fawaaz ya miƙa hannu ya ɗaga fuskarta a hankali, yana kallonta da kulawa. “Ki daina boye min duk wani abu da ke cikin zuciyarki,” ya ce. “Ko da wani abu ke damunki, ko da kina cikin farin ciki. Ina so na kasance tare da ke a kowanne lokaci.” Hawayen da take riƙe suka silalo. Ta yi murmushi, sannan ta ce a hankali, “Na san hakan, Yaa fawaaz.” Ya girgiza kai, yana share mata hawayen da yatsunsa. “Ba wai kawai ki sani ba,” ya ce, yana murmushi, “ina so ki yarda da shi.” Nabeeha ta lumshe ido, zuciyarta cike da soyayya. Tabbas, ta yarda da Fawaaz. Kuma yanzu, ta san cewa rayuwarsu za ta shiga sabon mataki—matakin da zai cika da soyayya, kulawa, da amana fiye da duk abin da suka taɓa fuskanta a baya. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:59_ Fawaaz ya ci gaba da kallonta, yana jin yadda zuciyarsa ta cika da wani irin nutsuwa. Ganin hawayenta ba ya masa daɗi, amma ya san waɗannan hawaye na farin ciki ne. Wannan ita ce Nabeeharsa, wacce ya daɗe yana ɓoye soyayyarsa gare ta. A yau, babu wani shakku ko jin tsoro. Ya bayyana komai. A hankali, ya kamo hannunta cikin nasa, yana murza tafin hannunta da yatsunsa. “Kin yarda da ni?” ya tambaya cikin wata murya mai laushi da cike da kulawa. Ta ɗago idonta da suka cika da ƙwalla, sannan ta gyada kai. “Na yarda da kai, Ya fawaaz.” Ajiyar zuciya ya sauke, yana jin kamar ya sauke wata babbar nauyi daga kirjinsa. “Wannan ita ce kawai maganar da take da mahimmanci a yanzu.” Suka yi shiru na wasu sakanni, zuciyoyinsu suna sadar da sakonnin soyayya ba tare da furuci ba. A wannan lokacin, babu wani abu da ya fi masa muhimmanci sama da kasancewa tare da ita. A can nesa, karar ƙararrawa ta katse shurun da ke tsakaninsu. Abincin da ya kawo mata ya iso. Fawaaz ya miƙe, yana murmushi. “Za mu ci tare.” Nabeeha ta murmusa, zuciyarta cike da farin ciki. A yau, soyayyar su ta wuce tunani. Sun isa matakin yarda—matakin da babu wani abu da zai iya karya shi... Fawaaz ya dubi Nabeeha da murmushi a fuskarsa. Ya ɗauki cokali, ya ɗiba mata abinci a hankali, sannan ya miƙa mata. “Ki buɗe baki.” Nabeeha ta kalle shi da mamaki, zuciyarta na bugawa da sauri. Bai taba nuna mata irin wannan kulawar kai tsaye ba. Amma yadda yake kallonta da yadda fuskarsa ke cike da kwanciyar HANKALI, sai ta ji wani irin yanayi da ta kasa bayyanawa. A hankali, ta buɗe baki. Ya saka mata abincin cikin taushin hali, yana kallon ta yadda take ci. Sai da ta haɗiye sannan ya ce, “Daga yau, zan kula da ke fiye da yadda kike zato.” Hannunsa ya ɗora saman nata, yana dan matsawa. “Nabeeha, kin san me yasa nake son ki haka?” Ta girgiza kai a hankali, idonta yana cikin nasa. “Saboda ke ce wacce zuciyata ta amince da ita tun kafin ki san hakan. Ke ce nutsuwa ta, ke ce addu’ata. Kin san yaushe na fara son ki?” Nabeeha ta ɗan lumshe idanu, tana jin wani irin sanyi na ratsata. Fawaaz ya ɗan yi murmushi, yana ci gaba, “Tunda na gane cewa ba za ki iya rayuwa da ciwon kewa ba, na rantse a raina cewa zan dinga kasancewa kusa da ke. Amma sai na lura cewa soyayyar da nake ɓoyewa ta fi ƙarfi fiye da abin da na zata.” Nabeeha ta kafe shi da idanu, tana jin yadda kalamansa ke ratsa zuciyarta. Dama ya iya kalaman magana haka? Haka ya iya tsara zance? Haka ya iya zuba soyayya tamkar a film? Ta murmusa kawai, kalaman sa na ratsa magudanar jini da tsokar jikin ta. Fawaaz ya ɗauki wani cokali na abinci, ya sake miƙa mata. “Ki ci, domin na san dole ne ki sami ƙarfi. Ba na so ki rame saboda tunani ko damuwa.” Bayan sun gama cin abinci, Fawaaz ya jasu sallah tare. Ya tsaya yana kallon yadda take yin addu’a da nutsuwa. Idanunsa sun cika da ƙauna da girmamawa. Bayan sallar, ya matsa kusa da ita, yana ɗora hannunsa saman nata. “Allah ya bar min ke, Nabeeha. Ina addu’ar alheri a gare ki, kuma ba zan daina ba.” Sai dare ya ja, suna tare cikin kwanciyar hankali, zuciyoyinsu sun haɗu da juna ba tare da wata shakka ba. Wannan shi ne matakin yarda—matakin da babu komai face soyayya da kulawa ta gaske. Daren ya tsawaita, amma Fawaaz bai damu ba. Yana kallon Nabeeha da wata irin nutsuwa da bai taɓa jin irinta ba a rayuwarsa. Idanunsa sun cika da so da kulawa, zuciyarsa tana bugawa da wani irin shauƙi da yake wahalar bayyana. Ya sake kamo hannunta cikin nasa, yana jin yadda tafin hannunta ke da ɗumi mai daɗi. "Nabeeha," ya ambaci sunanta a hankali, kamar yana jin daɗin furta shi. Ta ɗago idanuwanta da suka cika da kwanciyar hankali, tana kallonsa. "Kin san cewa zuciyata ta dade tana son ki?" Ya tambaya da muryarsa mai laushi. Ta lumshe idanuwa a hankali, tana jin wani sanyi yana ratsata. "Na sani, Ya fawaaz." Ya ɗan yi murmushi, yana jin yadda furucinta ke ƙara ƙarfafa shi. "Amma ba wai kawai son ki nake ba, Nabeeha. Ina ƙaunarki da zuciyata gaba ɗaya. Ina kallon ki, ina jin kamar kin mallake ni tun kafin ma ki sani. A yau, babu wata shakka, babu wata shinge. Na baki zuciyata gaba ɗaya." Nabeeha ta lumshe idanu, ta ɗan saki numfashi mai nauyi. "Ni ma na yarda da kai, Yaa Fawaaz. Na amince da kai fiye da kowa. Ka daɗe kana ɓoye komai, amma zuciyata tana karanta ta taka, ko da baka furta ba." Fawaaz ya murmusa, yana jin yadda furucinta suka saukar masa da natsuwa. "Kin san me yasa na daɗe ina ɓoye soyayyata?" Ta girgiza kai, tana jiran jin amsar sa. "Saboda bana son zuciyata ta takura ki. Bana son na ɗora miki damuwar da ba ki shirya da ita ba. Amma yau, ba zan iya ɓoye komai ba. Nabeeha, kin mallake ni gaba ɗaya." Hannunsa ya ɗaga ya shafi fuskarta a hankali, yana kallon yadda idanuwanta ke cike da ƙyau da kwanciyar hankali. "Duk da haka, ina son ki fiye da abin da zan iya furtawa. Ina addu'ar Allah ya tabbatar min da ke." Hannunta ya sake rikewa, yana matse shi a hankali. "Kuma daga yau, ina son na dinga kula da ke. Ba zan bar ki da yunwa ba, ba zan bar ki da damuwa ba. Ba zan bari wani abu ya taɓa ki ba, har abada." Nabeeha ta sunkuyar da kanta, zuciyarta tana bugawa da nauyin farin ciki. Fawaaz ya kalli fuskarta, sannan ya kai hannunta zuwa KIRJIN sa. "Ji yadda zuciyata take bugawa saboda ke, Nabeeha." Hannunta ya ji yadda bugun zuciyarsa ke da ƙarfi, yana tafiya da daɗin ƙauna mai tsafta. Daren yana ƙara ja, amma babu wanda ya damu da lokaci. Sun shagala cikin soyayyar da take tafiya a hankali, cikin tsafta da aminci. Fawaaz ya dubi kyawun fuskarta, sannan ya lumshe idanu. "Ina addu’a Allah ya albarkaci rayuwarki, Nabeeha. Ina addu’a ki kasance cikin farin ciki har abada." Sai ya sake kallonta da murmushi. "Kin yarda da ni?" Ta gyada kai, murmushi yana bayyana a fuskarta. "Na yarda da kai, Ya fawaaz." Daga nan, shiru ya ratsa tsakanin su, amma zuciyoyinsu suna magana fiye da furuci. Wannan matakin da suka kai ba wai kawai soyayya ba ce, aminci ne, kulawa ne, addu’a ce da ba ta yankewa. Soyayyarsu ta kai matakin da babu komai face tsarkin zuciya da yarda. Wannan matakin ne da ba zai taɓu ba, har abada. ,,,,,, A hankali Hammad ya turo kofar falon yana rike da basket dauke da warmers na abinci. Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya shiga, yana murmushi. "Assalamu Alaikum." Nabeeha ta dago daga inda take zaune tana duba wayarta. "Wa’alaikumus Salam, Hammad! Dear bro..iyye me muka samu? " Ya ajiye ledojin a kan teburi yana fadin, "Abinci daga gidan Granny. Tace a gaishe ku." Fawaaz, wanda yake zaune gefen kujera yana kallon wasan kwallon kafa a TV, ya dan kalle su, sannan ya mayar da hankalinsa ga wasan. "Nagode sosai," Nabeeha ta fada tana bude ledar don ganin me aka kawo. "Sannu da kokari ." Hammad ya yi murmushi yana zama. "Babu komai. Yanzu dai ku ci kafin yayi sanyi." A lokacin Fawaaz ya dan juya kansa ya kalli Hammad. "Ya fawaaz barka da rana" Hammad ya gyara zama, yana murmushi. "Lafiya kalau, bro" Fawaaz ya dan kada kai, ya maida kallonsa kan wasan da ake yi a TV. "Daga gani Barcelona ce take wasa da Real Madrid." Hammad ya yi dariya. "Eh mana! Kuma kaga yadda suka rike ball, ai dole su yi nasara." Fawaaz ya dan gyara zama yana kallon yadda ake buga wasan. "A ganina Real Madrid suna da damar cin kofin wannan shekarar." "Wallahi kuwa," Hammad ya amsa, yana kallon TV. "Messi dai ba wasa ba ne, amma kalli yadda Benzema ke kokari." Suka dan ci gaba da hirar kwallon kafa na tsawon mintuna kadan, kowannensu yana fadin ra’ayinsa kan wasan. Sai da suka ji sun dan gamsu, sannan Hammad ya sauke numfashi yana gyara zamansa. "Yaa Nabeeha, Yaa Fawaaz... zan koma makaranta gobe in sha Allah." Nabeeha ta dago da sauri, tana kallonsa da mamaki. “Hammad? Haka kawai? Da wuri haka?” Fawaaz bai ce komai ba, sai dai ya dan kalli Hammad. Hammad ya gyada kai. "Eh, hutuna ya kare, dole na koma." Nabeeha ta dan lumshe ido. "Allah ya kiyaye hanya." Fawaaz ya gyada kai. "Allah ya tsare." Hammad ya mike yana murmushi. "Nagode. Zan tafi yanzu, sai mun yi waya." Nabeeha ta raka shi da kallo, zuciyarta cike da kewar tafiyarsa. Fawaaz ya ci gaba da kallon wasan, amma yana sauraron yadda Hammad ke ficewa daga falon. Bayan dan lokaci, Nabeeha ta numfasa a hankali. "Zan rasa yawan damun Hammad kenan." Fawaaz bai ce komai ba, sai dai ya dauki remote ya kara volume din TV kadan, yana mai mayar da hankalinsa ga wasan da ake yi. Tuwon shinkafa da motar ganye dataji tantakwashi. Sai peppersoup na kaji da gasasshen cat fish. Sai doya da kwai da kunun gyada. Sai fruits da meat pie da samosa. Lamarin sai Wanda yagani kawai.... Fawaaz ya Mike ya dakko tray ya zuzzuba musu komai. Ya karasa wajen nabeeha batayi aune ba tajita a sama. Fawaaz ya daga chak ya dora ta akan cinyarsa.. Ya samu kansa da juyar da fuskar ta ya kamo labbanta da nasa yana tsotsar bakinta... Hannunsa daya Kuma ya zura shi rigar ta yana wasa da abubuwa Mafi soyuwa daga jikinta a zuciyar sa.. "Na...k...ko... Shi" ta fada a rarrabe tamkar zata shide saboda sabon lamarin da hannun fawaaz keyi acikin rigarta. "Sai da ruwan ciki akejan na rijiya... Beautiful Nabeeha" fawaaz ya radamata a kunne yana lasar gefen kunnen ta. Ta sauke ajiyar zuciya da kyar tana ajiye sautin numfarfashi... Ta shiga zame hannun fawaaz amma ya riketa kam. Sai dayaga ma jagulata sannan ya kyaleta yana bata abincin a baki. Sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta... ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:60_ Fawaaz ya Mike tsaye yana mikawa Nabeeha hannunsa. Dakyar ta iya kama nashi ya mikar da ita yana rarumar ta. Ya rungumeta tsam wanda zaa kwace masa ita.. "Muyi wanka mu raya daren yau ko love?" Nabeeha tayi shiru batace dashi komai ba. Gabanta ya tsananta bugawa fat fat fat. "Mu raya daren yau?" Tanbayar da yayi da muryarsa ta tariyo a dodon kunnenta. Jikinta ya dauki rawa. Inde raya dare ne. Irin Wanda humyrah ta sanar mata. To tabbas bata shirya masa ba. Don haka tayi kokarin zame jikinta. Ya sanya hannunsa yana tallabo fuskar ta. "Menene... Uhm? " "Ba.... Bakomai" "Ko zaki shiga kiyi wankan ki dauro alwala?" Ya fada mata ganin kamar kunya takeji. Kada ya takurata. Daman abunda take jira kenan. Don haka tayi hanzarin daga kai kafin da sauri tache, "Eh" "Tohm bari Nima naje" Da sauri tabar wajen ta shige cikin dakin. Fawaaz ma ya shiga dakinsa. Tayi saurin Saka mukulli ta rufe dakin. Gabanta ya tsananta bugawa. Bandaki ta fada tayi wanka, da bathe khumrah na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE. Bayan ta gama wankan ta dauraye jikinta da after bathe khumrah. Wani kamshi ya gama gauraye ta ... Kulaccam din kamfanin turaren ta dauka ta shafe jikinta dashi. Ta sanya riga da wando masu nauyi ta zura hula akanta Ita kanta yadda jikinta ke tashin kamshi yasa ta Kai hancinta tana sunsunar kamshin da fatarta ke bayarwa da kayanta da suke kamshin turaren kayan YERWA INCENSE AND MORE. Dake gab da zata tare aka Kai kayan kamfanin turaren na YERWA INCENSE AND MORE ta turara mata su... Sai kamshi ne ke tashi sai kace a kamfanin surrati.. Bayan ta kammala komai ne ta koma bakin gado ta zauna tana murza yatsunta.. Fawaaz yanata zaune a parlor shiru shiru yana juranta. Tuni har yayi wanka ya dauro alwala shima tun dazu. Ita yaketa jira shiru. Ya tashi ya nufi kofar dakin zai bude ya jita a rufe. Ganin ko bata karasa bane yasa ya koma ya zauna. Can bayan wani lokaci ya Kara komawa. Nanma dakin a rufe gam. Ya danyi murmushi yana sosa keyarsa cikin muryar lallashi yache, Fawaaz ba zai yi saurin nuna damuwarsa da son kwadaituwa da kasancewar sa da Nabeeha kai tsaye ba, amma yayi kokarin amfani da salo mai nutsuwa da kalmomi masu taushi domin ya janyo hankalinta ta fito daga dakin da ta buya. Sai aunawa yake kalaman da zai gargaya mata yace, Da sigar laushi da tausasawa, “Nabeeha… kin san cewa ba zan matsa miki ba, amma da gaske kike son barina a nan tsaye haka? Ko kadan ba kya jin tausayina?” Jin tayi shiru ya sake cewa, “Idan kin fito, zan yi miki alkawari. Alkawari da ba zan karya ba. Babu wanda zai takura miki, kuma ba zan ce komai da zai dame ki ba… sai dai idan har son damuwata kike.” Fawaaz ya tsaya a bakin kofar dakin, hannayensa sanye cikin aljihun wandonsa, idanuwansa masu kauri da karfi sun tsaya akan kofar da Nabeeha ta rufe. Ajiyar zuciya ya sauke cikin lumana, yana mai jin wani abu da bai saba ji ba yana zagaye zuciyarsa. "Nabeeha..." Ya kira sunanta a hankali, kamar yana jin nauyin furta shi. "Kin san ba na son matsawa mutane, amma yanzu na gaji da tsayuwa a nan. Za ki zo ko sai na ci gaba da jira?" Shiru. Batace komai ba. Bai samu amsa ba, amma hakan bai hana shi ci gaba da magana ba. A sanyaye ya jingina da bango, yana mai gyara sautin muryarsa ta yadda za ta lafa zuciyarta. "Kin san wani abu?" Ya yi murmushi mai rauni. "Ina son jin muryarki, koda kuwa don ki ce min, 'Fawaaz, ka tafi.' Zan fi jin dadin hakan fiye da wannan shiru da kike bani." Har yanzu shiru. Ya dafa kansa da hannunsa guda, yana mai jin yadda zuciyarsa ke bugawa fiye da kima. Sai dai bai nuna hakan ba. Ya kuma kamewa, yana kokarin shawo kanta da basirar sa. "To, idan na tafi, kin yarda na tafi da zuciyata?" Ya dan saki dariya mai nauyi. "Saboda yanzu haka, tana bakin kofa tana jiran ki fito. Ko dai ki fito ku gaisa, ko kuwa ki bar ni nan ina jiran har sai kin fito da kanki." Jin haka ya sa Nabeeha ta dan motsa a cikin dakin. Amma bata ce komai ba. Fawaaz ya gyara tsayuwarsa, yana mai kara danne zuciyarsa. Sai dai akwai wata murya a cikin ransa da ke turoshi gaba. "Idan na tsawaita magana, za ki ce ina wahalar da kaina," Ya ce a hankali, yana mai sake gyara murya. "Amma gaskiya, Nabeeha, idan har na kasance ina iya jure shiru a kowane hali, yau na kasa. Ba zan iya jure shiru daga gare ki ba." Nabeeha ta sake juyawa a cikin dakin, zuciyarta na bugawa. Tana jin sautin muryarsa yadda ta danne laushi a kasan tsantsar miskilancinsa. "Ki zo ki buɗe, idan har ba don ni ba, to don kanki," Ya sauke numfashi, yana mai sassauta murya. "Ko kuma sai na dauka kin fi so in shigo da kaina?" A wannan karon, tana jin yadda zuciyarta ke harbawa fiye da yadda ta zata. Hannunta ya taba murfin kofar. Kuma kafin ta yanke hukunci, Fawaaz ya sake magana. "Ki yi hakuri, kin ji? Ban zo nan don takurawa ba," Muryarsa ta lafa ƙwarai. "Na zo ne don jin cewa kina lafiya." Jin haka ya sa ta runtse idanuwanta. A hankali ta bude kofar. Fawaaz ya tsaya, yana mai kallonta da ido masu zurfi da suka nutse cikin nata. Bai ce komai ba, sai dai murmushin da ya yi,wanda kowa ya san cewa da gaske yake. Nabeeha ta tsaya a bakin kofar da ta buɗe rabin jiki, kanta a ƙasa, hannunta riƙe da murfin kofar kamar wadda ke shirin rufewa a duk lokacin da ta ga dama. Idanunta sun kasa kallon Fawaaz kai tsaye, sai dai tana jin nauyin kallon da yake mata. Fawaaz bai yi saurin yin magana ba. Ya tsaya kawai yana kallonta, kamar yana nazarin yadda take, yadda numfashinta ke fita a hankali, yadda ta ƙanƙance kanta cikin hijabinta data zura kamar mai son ɓuya. Sai da yayi wasu dakiku sannan ya ɗan lumshe idanu, murya ƙasa-ƙasa yace, "Kin fito." Ta ɗan tsuke labbanta ba tare da tace komai ba. Fawaaz ya gyara tsayuwarsa, ya sake nutsuwa fiye da da. "Nagode," ya furta a hankali. "Ko da ba za ki ce komai ba, nagode da kika fito." Nabeeha ta ɗan motsa, zuciyarta na bugawa da karfi. Bata san dalilin da ya sa ta kasa cewa uffan ba, sai dai yadda muryarsa ke fita cikin nutsuwa yana daga mata hankali fiye da yadda take tsammani. Shiru ya sake shiga tsakaninsu. Fawaaz ya dan lumshe ido kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Ba na son matsawa mutane, kin sani," ya ce a hankali. "Amma a yau, na kasa hakuri. Na san cewa ba kya son yin magana da ni, ko kuma ba kya jin dadi a kusa da ni, amma..." Ya tsaya, yana kallonta da idanu masu zurfi. "Amma kin san cewa ba zan tafi ba har sai na tabbatar cewa kina lafiya, ko?" Nabeeha ta lumshe ido na wucin gadi. Sannan a hankali tace, "Lafiyata kalau." Fawaaz ya dan yi shiru, sai daga baya yace, "Kin tabbata?" "Eh." Ta amsa, muryarta kamar ana tura ta. Bai ce komai ba na wasu dakiku, sai daga baya yace, "To, idan har da gaske lafiya kike, me yasa kika buya?" Nabeeha ta ji jikinta ya yi sanyi. Ta kasa cewa komai. Fawaaz ya ɗan gyara tsayuwarsa, yana mai kallonta da sigar mutum mai son jin gaskiya. "Ko kuma dai..." Ya rage muryarsa, ya matsa kaɗan, amma ba da nufin takura ba. "Kina buya ne daga gare ni?" Tayi saurin ɗaga kanta, idanuwanta cike da karyar cewa ba haka bane. Sai dai yadda suka haɗa ido, zuciyarta ta tsalle, ta sake ɗauke kanta da sauri. Fawaaz ya yi murmushi – murmushi mai ma’ana da ita kaɗai zata iya fahimtarsa. "Na fahimta." Ya sake matsawa kaɗan, yana mai rage murya fiye da da. "To, bari na sake tambaya, Nabeeha." Ta ɗan taɓe labbanta, amma bata ce komai ba. Fawaaz ya sunkuyo kaɗan, murya a matuƙar laushi, "Idan har ba ki tsorona ba..." Ya dan dakata, yana nazarin yadda zata karɓi maganar. "Me zai hana ki kalle ni a ido ki faɗi haka?" Nabeeha ta ji kamar zata rasa numfashi. "Ki kalle ni," ya sake maimaitawa cikin wata irin nutsuwa, "Ki ce min ba kya guje min." Hannunta ya ƙanƙance a kan murfin ƙofar. Tana ji tamkar numfashinta na ƙaurace mata. Idanunta suka fara kaɗa, zuciyarta tana bugawa da karfi. Fawaaz ya dan kalli yadda take, sannan cikin salo mai cike da wayo ya ɗan ja baya. "Amma idan har ba za ki iya cewa ba," ya ce da sauti mai kashe jiki, "To, kin san abin da hakan ke nufi, ko?" Nabeeha ta ɗan runtsa ido, sannan cikin sanyin murya tace, "Me kake nufi?" Fawaaz ya saki murmushi – murmushin da zai iya rikita mutum. "Kin sani," ya furta cikin lumana. "Kin san me nake nufi, Nabeeha." Ta sauke ajiyar zuciya. Hannunta ya dan yi sanyi, numfashinta ya yi nauyi. Fawaaz ya kalleta, sannan ya ce, "Ki huta." Sai kawai ya juya, ya bar wurin. Nabeeha ta tsaya, tana kallon bayansa har ya bace daga idonta. Sai dai har lokacin, zuciyarta bata daina bugawa ba. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:61_ A rikitaccen dakin karatu na gidan, inda shiru ya maye gurbin hayaniyar duniya, Fawaaz ya tsaya a bakin ƙofar yana kallon Nabeeha da ke zaune bisa kujera tana karanta wani littafi na anatomia. Fuskar ta cike da nutsuwa, amma idanunta sun nuna alamun gajiya. A hankali, ya shigo riƙe da gilashin ruwa mai sanyi, yana tafiya da kwanciyar hankali har ya iso kusa da ita. Ya ajiye gilashin a kan teburin kusa da ita, sannan ya ce da murya mai taushi, "Sha ruwa, Nabeeha… Kinsan bana so ki gaji ba tare da kin kula da kanki ba." Ta ɗago kai a hankali, tana kallonsa da mamaki. Idanunta sun sauka a kan fuskarsa, wadda ta cika da kulawa. "Na gode," ta faɗa a hankali, tana jawo gilashin. Fawaaz ya ɗan matsa kusa, yana mai kallon yadda ta sha ruwan a hankali. Sai da ta ajiye gilashin sannan ya furta, da murya mai zurfi da taushi, "Da ace zan iya zama ruwa, da sai na zamo ruwan da zai dinga sanyaya zuciyarki har abada." Nabeeha ta ɗan tsargu, zuciyarta ta bugawa da ƙarfi. Ta saki numfashi, tana jin yadda kalamansa suka shige ta. "Ya Fawaaz… me kake nufi?" Ya dan murmusa, yana kallon cikin idanunta. "Ina nufin… ke ce nutsuwata, ke ce abinda zuciyata ke bukata. Ko da ruwan da kika sha ya qare, in har ina kusa dake, to ba za ki taɓa jin ƙishirwa ba." Zuciyarta ta harba, wani irin sanyi da tsigar jiki suka ratsa ta. Ba ta iya cewa komai ba, sai kawai ta sunkuyar da kai, tana jin yadda kalamansa suka mamaye zuciyarta. Fawaaz ya danyi dariya, ya sunkuya kadan yana kallonta. "Nabeeha, idan zaki ji tsoro da soyayyata, to ki sani cewa… ni ne mafakarki." Hankalinta ya yi nauyi, zuciyarta ta fada tarkon da ba ta shirya ba. Fawaaz kuwa, ya mike a hankali, ya juya da wani murmushi mai cike da nufin zuciya, ya fita daga dakin, yana barin ta cikin wani yanayi da ba ta taba jin irinsa ba. A tsakar dare, shiru ya mamaye gidan, amma a zuciyar Fawaaz babu wani hutu. Ya dinga juye-juye akan gadonsa, amma duk da kokarinsa na kawar da tunanin Nabeeha, hakan ya gagara. Zuciyarsa na tafasa da soyayyarta, hankalinsa ya kasa samun nutsuwa. Ya sauke ajiyar zuciya, ya mike a hankali yana bin hanyar dakinta. A hankali ya tura kofar, yana kallon inda take kwance. Wata irin soyayya mai karfi ta lulluɓe shi. A hankali ya karasa gadon, ya tsaya na wasu sakanni yana kallon yadda numfashinta ke fita cikin nutsuwa. Da hankali, ya haye gadon, ya kwanta a bayanta a natse, sannan ya jingina fuskarsa da wuyanta, yana shakar daddadan kamshin fatarta. Hannunsa ya sauka a kan cikinta, yana rungumeta cikin kulawa da soyayya. "Nabeeha…" ya furta da kasalalliyar murya mai cike da shauƙi. Ta dan motsa, zuciyarta ta harba da sauri lokacin da ta ji numfashinsa a kusa da kunnenta. "Ya fawaaz… me kake yi?" ta tambaya da muryar da ke nuna alamun tashi daga barci. Ya dan matse ta kaɗan a kirjinsa, yana jin dumin jikinta yana ratsa shi. "Na kasa barci, Nabeeha… Na kasa samun nutsuwa, kuma daga gare ki nake so na samu sanyin da zuciyata ke bukata." Ta ɗan yi shiru, zuciyarta na bugawa da sauri. Shi kuwa ya dan yi murmushi, yana shafa gefen fuskarta a hankali. "Kin san me yasa?" Ta kasa cewa komai. Murmushinsa ya ƙaru kadan, sannan ya rada mata da murya mai kashe jiki, "Saboda ke ce komai a gare ni. Nabeeha, ke ce farin cikina. Babu inda zan fi jin kwanciyar hankali fiye da nan… a jikinki." Wata irin kasala ta lullube ta, wani sabon yanayi na soyayya ya dirar mata. Hannunsa ya kama nata, ya sumbaci bayan tafin hannunta a hankali. "Kin san yadda zuciyata ke bugawa a duk sanda na kasance tare da ke?" Ta runtse idanu, tana jin saukar numfashinsa a bayan kunnenta. "Yadda kike ji yanzu, shi nake ji duk sanda kike kusa da ni." Ya ɗan shafi fuskarta, yana jan numfashi a hankali. "Nabeeha, idan akwai abin da zan iya sadaukarwa domin ki, to rayuwata ce. Domin ke ce farin cikin da ba zan taba barin sa ya kufce min ba." Zuciyarta ta nitse a cikin soyayyar Fawaaz, ba ta san lokacin da ta lumshe ido tare da jingina bayanta da KIRJIn sa ba. A haka ya ci gaba da mata kalamai masu ratsa zuciya, Fawaaz ya jawo Nabeeha jikinsa sosai, yana jin yadda numfashinta ke hade da nasa. Wata irin soyayya da shauki sun cika zuciyarsa, ya dora labbansa a gefen kunnenta yana rada mata da murya mai kashe jiki. "Nabeeha… kin san kuwa irin tasirin da kike da shi a kaina? Kamar yanda iska ke bukatar sarari, haka zuciyata ke bukatarki." Ya sauke sumbatu a saman goshinta, yana shafa gefen fuskarta a hankali. "Da ace zan iya zana ki a zuciyata, da na fi kowanne mai fasaha kwarjini. Amma ai babu bukata, domin har yanzu zuciyata tana dauke da surarki." Hannunsa ya sauka a kan tafin hannunta, yana wasa da ‘yan yatsunta a hankali. "Kina jin yadda zuciyata ke bugawa? Ko kin san cewa kowanne bugunta na ambaton sunanki ne?" Ya jawo hannunta, ya dora a kan kirjinsa, inda zuciyarsa ke harbawa da karfi. "Kin jiyo? Wannan bugu ne na soyayya… domin ke kadai ce abinda zuciyata ke bukata." A hankali ya daga hannunsa ya shafa kumatunta, ya sauke sumba a gefen lebenta, sannan ya sauke numfashi. "Ke ce abinda ke ratsa jinina, Nabeeha… Kamar jini a jiki, ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba." Hannunsa ya gangaro zuwa wuyanta, yana shafa gefen wuyanta da tafin hannunsa mai dumi. "Ko kin san me yasa na fi son kasancewa kusa da ke?" Ya rada mata a kunne, muryarsa na rawa kadan da tsananin soyayya. "Saboda kin zama wani yanki na zuciyata. Babu wani wuri da zan fi jin kwanciyar hankali fiye da nan… a jikinki." Ya lumshe ido, ya kara shigewa jikinta, yana jin yadda sanyin fatarta ke ratsa nasa. "Ke ce sanyi a cikin ran zuciyata, ke ce farin ciki da nutsuwata." Hannunsa ya gangaro zuwa wuyan hannunta, yana shafa gefen tafin hannunta a hankali, yana jin yadda jikinta ke amsawa da sanyin halittarsa. "Idan akwai abin da nake bukata a rayuwata, to ke ce. Idan akwai abinda zuciyata ke so fiye da komai, to soyayyarki ce." Ya dan sauke numfashi, yana jin yadda jikinta ya yi laushi a cikin nasa. "Nabeeha… da ace zan iya zama mafakarki har abada, da na fi kowa jin dadin rayuwa." Ya kara rungumeta da karfi, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi. A haka ya ci gaba da mata kalamai masu ratsa zuciya, yana sauke sumba a dukkan gabobin jikinta... Ya sanya hannunsa yana kamo labbanta. Ya shiga zagaye labbanta da yatsansa guda daya.. Ya Kai mata sumba kan bakinta yana lalubar harshen ta hadi da cafkeshi tamkar alawa.. Ya koma kan labbanta yana tsotsar su sosai tamkar ya samu alawa. Ya koma kan Karan hancinta yana sakar mata sumba zuwa gefen kunnuwan ta. Can ya Kai hancinsa kan gashin ta yana sunsunar kamshin da gashin nata ke fitarwa na scented hair cream and spray da tayi amfani dashi na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE. Ya jima yana sunsunar gashinta. Ahankali ya sanya hannu yana unbutton din maballar rigarta. Duk yarda nabeeha taso ta kwace kanta ta kasa . Saboda fawaaz ya rikida ya zama tamkar wani dan karamun zaki dake tashen farauta a daji. Harda wani gurnani yake. Alokacin da bakinsa ya Kai kan na shanunta. Ya jima yana tsotsar su sosai. Kafin daga bisani ya sauka zuwa kasan cibiyarta ya sanya harshensa yana lasar ramin cibiyarta. Nabeeha ji tayi tamkar zata shide. Gashi kofofin jikinta sai maraba suke yi da sakon da yake Isar musu.. Ya gangara kan goshinta yana sakar mata sunba. Lungu da Sako na jikin nabeeha ba inda fawaaz bai tsotse ba. Ya lasa ya tsotse ya murza haka yayita yi.. Daga bisani ta jiyo shi yana adduar auratayya. Duk yadda tayi taso bijerewa ta kasa. Sakamakon rikon da fawaaz yayi mata tamau ba zata iya kwacewa ba... Sai numfarfashi takeyi tana damtse kasan labbanta cike da ciwo.. tana sake mamakin zubar hawayen fawaaz akan KIRJIn. Tabbas kuka yakeyi. Kukan me amma? Ita tana kukan wahala shi dai kam sai kukan farin ciki... Sai da fawaaz ya samu nutsuwa sosai sannan ya sarara mata. Ya koma gefenta ya rarumota ya riketa tamau. Yana shafa gadon bayanta. 🎀🎀🎀🎀 Fawaaz ya rungume Nabeeha a jikinsa da soyayya mai zurfi, yana jin wani irin farin ciki da nutsuwa da ba zai iya misaltawa ba. Ya lumshe ido, zuciyarsa na cike da godiya, sannan ya rada mata da murya mai cike da kauna, “Nabeeha… me zan ce da ke da zai bayyana yanda nake ji a zuciyata? Yaya zan iya godewa Allah da ya bani mace irinki, wadda ta kare mutuncinta ta kuma kawo shi gare ni ba tare da ta zubar da shi ba? Ke abar alfaharina ce, ke ce macen da zuciyata ta dade tana fata.” Ya janye kadan, yana kallon idanunta da nutsuwa. Hannunsa ya kama nata, ya dan shafa tafin hannunta cikin kulawa. “Nabeeha, na gode da kika zamo amintacciya a gare ni. Na gode da kika kawo girmanki gare ni, ba tare da kin sake shi ga kowa ba. Na gode da kika bani mutuncinki cikakke, cikin soyayya da gaskiya.” Ya lumshe ido na wani lokaci, sai kuma ya sake bude su, yana shafa gefen fuskarta. “Na gode da kika tsaya akan darajar ki, kika kare shi, kika kawo shi gare ni. Wallahi, Nabeeha, ba zan taba gajiya da godewa Allah da ya bani mace kamarki ba.” Ya sauke numfashi, zuciyarsa cike da tsananin soyayyarta. “Ya Allah, Ka albarkaci rayuwar Nabeeha. Ka kare ta daga dukkan sharri, Ka sanya farin ciki a zuciyarta a kullum. Ya Allah, Ka kara mana so da fahimta, Ka hada zukatan mu har abada.” Ya kama hannunta da duka hannayensa, yana murzawa a hankali. “Ya Allah, Ka sanya ni sanadiyyar farin cikin ta, Ka azurta ni da ikon kareta da kaunarta har karshen rayuwata.” Ya dora goshinsa a kan nata, yana rada mata da wata kasalalliyar murya mai cike da shauki, “Nabeeha, zan kare mutuncinki kamar yadda kika kawo mini shi cikakke. Zan daraja ki fiye da yadda kike tsammani. Kuma zan so ki har karshen numfashina.” Ya dago da hannunta, ya dan sumbata a hankali, yana jin kaunarta na kara ratsa shi fiye da kowane lokaci... ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:62_ Fawaaz ya ci gaba da rike hannunta a cikin nasa, yana shafa tafin hannunta da yatsunsa cikin kulawa. Idanunsa sun cika da soyayya, zuciyarsa na bugawa da nutsuwa mai dauke da farin ciki. "Nabeeha…" ya kira sunanta a hankali, kamar yana jin dadin yadda yake fitowa daga bakinsa. Ta lumshe ido, zuciyarta na jin nauyin irin kalaman da yake fada mata. Shi kuwa ya ci gaba, yana shafa bayan hannunta da murya mai cike da tsantsar soyayya, "Kin zamo wata duniya a rayuwata, wadda ba zan iya rayuwa babu ke ba. Kin zamo hasken da ke jagorantar zuciyata a cikin duhu. Kin zamo farin ciki da nutsuwata." Ya dan janye, yana kallon fuskarta, idonsa cike da tsafta da gaskiya. "Nabeeha, wallahi, ba zan taba gajiya da godiya gare ki ba. Kin kare mutuncinki, kin kawo min shi cikin daraja da girmanki. Ba zan taba iya godewa Allah da ya bani mace kamarki ba." Ya kamo kumatunta da hannunsa guda, yana shafa gefen fuskarta cikin kulawa. "Ke ce wadda na dade ina nema. Ke ce burin zuciyata. Ke ce mafarkina da ya zama gaskiya. Soyayyarki ta shige ni har jini da tsoka." Ya sumbaci goshinta a hankali, sannan ya sauke numfashi, yana jin yadda dumin jikinta ke ratsa nasa. "Kin zamo zuciyata, Nabeeha. Kin zamo numfashina. Kin zamo komai a rayuwata." Sai da ya sake jawo ta jikinsa sosai, sannan ya daga hannunsa sama, yana fadin, "Ya Allah! Ka albarkaci rayuwarmu. Ka kare mana soyayyarmu daga dukkan sharri. Ka sanya soyayyarmu ta dore har karshen rayuwarmu. Ka bani ikon kareta, kulawa da ita, da girmamata har abada." Ya sake kallonta, idonsa cike da natsuwa. "Nabeeha, na yi alkawari… ba zan taba barin ki ba. Ba zan taba bari wani abu ya kawo miki damuwa ba. Zan so ki fiye da yadda nake son kaina. Zan kare ki fiye da yadda nake kare numfashina." Ya daga hannunta zuwa kirjinsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi. "Kin jiyo?" Ya rada mata a kunne. "Wannan bugu ne da ke ambaton sunanki a duk daƙiƙa. Har karshen rayuwata, Nabeeha, ke ce zabina." Zuciyarta ta harba da karfi, wata soyayya mai karfi ta lullube ta. Ta dora kanta a kirjinsa, tana jin bugun zuciyarsa yana gauraya da nata. A haka suka kwanta, jikin juna, zuciyoyinsu na aiki da bugun soyayya daya, ba tare da wata shakka ko kokwanto ba.... Fawaaz ya ci gaba da shafa bayan kanta a hankali, yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa. Hannunsa na dama ya shafi bayanta a natse, yana jin yanda jikinta ke laushi a jikin nasa. "Nabeeha…" ya kira sunanta a kasalance, kamar wanda ke jin dadin furta shi. "Na'am," ta amsa a hankali, muryarta cike da sanyin soyayya. Ya lumshe ido, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da tsananin kaunarta. Sannan ya rada mata da murya mai laushi da shauƙi, "Kin san cewa kin zamo rayuwa a gare ni? Kin zamo jini a jikina. Idan har babu ke, to babu ni. Kin sani?" Ta kasa amsawa, kawai ta gyada kanta a hankali, tana jin yadda kalamansa ke ratsata. Ya sauke numfashi a hankali, yana shafa gefen fuskarta da yatsunsa masu laushi. "Nabeeha, ke ce mafarkina da ya zama gaskiya. Kin sani? A da, ina tunanin soyayya tamkar tatsuniya ce, amma tun da kika shigo rayuwata, na fahimci cewa soyayya tana da rai, kuma tana da zuciya—kamar yadda nake jin naki yana hadewa da nawa.You are not just my love, Nabeeha. You are my peace, my happiness, and my greatest blessing ." Ya kai bakinsa kan goshinta, ya sauke wani sumba mai laushi. "Bana jin zan iya rayuwa babu ke, Nabeeha. Kin cika wani gibi a zuciyata da ban san yana wanzuwa ba. Kin sani kuwa?" Ta lumshe ido, zuciyarta cike da shauki. Ta dan motsa kadan, tana jin dumin jikin Fawaaz yana lullube ta.. A HANKALI tace, "You are not just my husband, Ya Fawaaz. You are my best friend, my protector, and the love of my life." "Duk ran da babu ke, Nabeeha, to tamkar ba ni da numfashi. Duk da nake jin numfashina na fita, amma a zahiri zuciyata tana mutuwa a hankali...Every beat of my heart whispers your name, because you are my everything" Ya sauke wani ajiyar zuciya, sannan ya ci gaba da shafa gefen kumatunta. "Godia nake Yaya fawaaz. Allahn daya sa kake so na kamar haka. Allah ya so ka fiye da haka Amin .. ya fawaz Every moment with you is a treasure, and every day I spend with you is a blessing" "Ni gaskia adena cutata ane Kirana da wani Yaya. Ni ba yayan ki bane. Ni mijin ki ne. Gamu gado daya Muna sha'aninmu. Gaskia a temaka a canzan suna. Loving you is not a choice, Nabeeha. It is a part of my existence, just like breathing.. Nabeeha, the world may change, the stars may fade, but my love for you will never diminish. Bi'ixnillah! You are the only one who holds the key to my heart, and I pray that you never let it go...Nabeeha i don’t need paradise because I have you. And as long as you are with me, my world is complete. Ba karya ba every time I look into your eyes, I see my entire future—beautiful, peaceful, and filled with love...Nabeeha our love is the light that guides me, the warmth that comforts me, and the joy that completes me.ki sani, No matter how many years pass, I will always fall in love with you over and over again. Nabeeha, you are not just a part of my life—you are my whole life." Nabeeha tayi murmushi tana jujjuya kalaman sa. Hadi da gyara kwanciyar ta tana kokarin mayar da martanin dake cikin zuciyar ta Wanda zasu wanzu a labbanta, "Hayatim (my life in turkish)If love had a face, it would look exactly like you, your love is my strength, your presence is my comfort, and your arms are my home..no matter where life takes us, as long as I have you, I have everything I need. Ya Fawaaz, au hayatim.. you are my dream come true, my answered prayer, and my greatest gift....i fall in love with you every single day, and I will keep falling for you until my last breath...When I am in your arms, I know I am exactly where I am meant to be...hayatim you are my sun in the morning, my moon at night, and my heart every second of the day.. wallahi if love is a journey, then I want to walk every step of it with you, Yaa Fawaaz." Tana kaiwa karshe fawaaz ya rarumeta ya rungumeta tsam a faffadan KIRJIn sa.. kalamanta sun ratsa shi sosai. Cike da farin ciki ya cigaba da cewa, "Ya Allah, Ka sanya Nabeeha ta zamo rabin rayuwata har abada. Ka bani ikon kareta, girmamata, da sanyaya mata zuciya a duk lokacin da take bukata. Ka sanya zuciyata ta zamo mafakar farin cikinta, kamar yadda take mafakar tawa." Ya sake rungumeta, yana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa tare. "Nabeeha, da ace akwai wata duniya bayan wannan, to wallahi har can zan ci gaba da son ki. Har abada, soyayyarki zata kasance a zuciyata." Zuciyarta ta harba da karfi, wani irin shauki ya lullube ta. Ta kasa cewa komai, sai kawai ta kara shigewa jikinsa, tana jin dumin soyayyarsa na ratsata. Shi kuwa Fawaaz, ya lumshe ido, yana jin yadda bugun zuciyarta ke gauraya da nasa. Ya san cewa daga yau, babu abin da zai rabasu. Soyayyarsu ta kasance, kuma za ta ci gaba da wanzuwa har abada. 🎀🎀 Yau Fawaaz da Nabeeha sun shirya zuwa ziyarar Humayrah da Raudah, kannen Fawaaz kuma ‘yan uwan Nabeeha. Tun da safe Nabeeha ke cikin shiri, tana cike da farin ciki. Fawaaz kuwa yana kallonta yana murmushi, yana jin yadda farin cikinta ke ratsashi. A cikin mota suna tafiya a hankali, hannunta cikin nasa. Ya kalleta da dariya a fuskarsa. "Kin ga yadda kike murna kuwa? Kamar wata yarinya da za a kaiwa sabuwar shakatawa." Ta yi dariya, ta dan rankwafa a kafadarsa. "Kai dai bari. Ai na dade ban ga Humayrah da Raudah ba. Kuma na san sun jima suna jiranmu." Ya dan girgiza kai yana murmushi, ya cigaba da tukinsa har suka iso kofar gidan. Da jin karar horn din motarsu, sai ga Humayrah da Raudah sun fito da sauri, fuskokinsu cike da farin ciki. "Ah! Lallai yau mun sha mamaki!" Humayrah ta fada tana dariya. Raudah ta ruga ta rungume Nabeeha. "Aunty Nabeeha! Kin tuna da mu yau?" Nabeeha ta rungume ta itama tana dariya. "Ai ba zan iya mantawa da ku ba, kun fi kowa." Fawaaz ya kalli kannensa yana murmushi. "Ku dai kun fi son Nabeeha a kaina, ko?" Humayrah ta gyada kai da wasa. "Eh mana, ai ita ce ta fi sanin yanda za ta yi mana lallashi." Suka yi dariya gaba daya, sannan suka shiga gidan cikin nishadi da farin ciki.... Dake gidan Raudah Dana humyrah ba nisa sosai. A estate daya suke. Shi ya sanya humyrah taje gidan Raudah suka hadu gaba daya... _____ Tunda safe Gwaggo Hafsatu ke zaune a falonta, tana lazimi cikin nutsuwa. Koda aka sanar da ita cewa Fawaaz da Nabeeha za su kawo mata ziyara tare da Humayrah da Raudah, sai ta ji wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarta. Bata jima da idar da azkar ba, sai ga su sun iso. Mai gadi ya bude musu ƙofar, suka shigo cikin harabar gidan cikin natsuwa. A lokacin da suka sauka daga mota, suna kokarin shiga cikin gidan, sai ga Gwaggo Hafsatu ta fito zuwa zaure da fara’a a fuskarta. "Ah! Lallai yau na samu dama. Jikokina sun zo ne gaba ɗaya?!" Dariya suka yi gaba ɗaya, sannan suka karasa kusa da ita. Nabeeha ta durƙusa cikin girmamawa, tana fadin, "Granny, ina wuni?" Ta amsa da fara’a, tana shafa kanta. "Lafiya lau, Nabeeha tah. Yau nasan zan ji daɗi sosai." Humayrah da Raudah ma suka gaishe ta, sannan suka zauna kusa da ita, suna jin ɗumin soyayyarta. Daga nan sai ga Major General Dawud ya fito daga sashensa, yana kallon su da murmushi a fuskarsa. "Ah, yau an yi baƙi na musamman." Fawaaz ya sosa ƙeya yana murmushi. "Ai su suka ce sai na zo tare da su, idan ba haka ba, da an bar ni a gida." Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da wasa. "Na san dai ke ce kika sa shi ya zo." Nabeeha ta yi murmushi tana kallon ƙasa. "Ai ya dace ya zo Gwaggo, ba zai tsira ba." Suka fashe da dariya gaba ɗaya. Major General Dawud ya zauna, yana kallon su da kulawa. "Yau na samu ikon zama tare da ku, ya kamata ku kawo min labarai." Humayrah ta yi dariya, tana cewa, "Ai Baba, tunda ba ka fiye zama a gida ba, yau sai mun dame ka da hira." Raudah ta gyara zama tana cewa, "Ko da yake, Aunty Nabeeha ita ce zata fi ba da labarai, tunda ita ce ta fi shiru kullum." Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da murmushi. "Yau zan zauna na ji yanda kike jituwa da Fawaaz." Fawaaz ya yi gyaran murya, yana kallon Nabeeha da wasa. "Ai nasan za ta ce kina son jin SIRRIN mu ne." Dariya suka yi gaba ɗaya. Bayan dan lokaci, an kawo musu kayan ciye-ciye da ruwan zafi. Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da kulawa, tana cewa, "Yaya kike ji a gidan Fawaaz? Yana kula da ke sosai kuwa?" Nabeeha ta kalli Fawaaz, sai kuma ta yi murmushi tana cewa, "Eh Gwaggo, yana kula da ni. Kullum yana kokarin faranta min rai." Gwaggo Hafsatu ta kalli Fawaaz da murmushi. "Ka ga kuwa? Wannan shi ne abin da nake so." Major General Dawud ya yi murmushi yana gyara zama. "Ai Fawaaz ya gaji da jin kunya, tunda har Nabeeha ke yaba shi a fili." Suka fashe da dariya gaba ɗaya. A haka suka ci gaba da hirarsu cikin annashuwa, suna jin daɗin kasancewa tare da juna. Gwaggo Hafsatu ta yi wa Fawaaz da Nabeeha addu’a, tana rokon Allah ya kara musu soyayya da fahimta, sannan ta shafa musu albarka. Bayan sun jima, suka tafi da alkawarin cewa ba za su jima ba sosae zasu sake dawowa wata ziyarar bi'iznillah. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:63_ Tunda asuba Nabeeha ta farka tana shirin tafiya gidan iyayenta. Tun a kwanakin baya take shirin wannan ziyara, saboda ta dade ba ta ziyarce su ba. Tun kafin auren ta, Fawaaz ne ya lallaɓa ta suka ɗauki lokaci suna jira har zuwa lokacin da zai dace, don su tafi tare. A yau kuwa, babu wani uzuri. Sun shirya, suka fita da safe domin yin ziyarar gaisuwa ga mahaifiyarta, Hajiya Zaytunah, da mahaifinta, Alhaji Uzairu. A cikin mota, Nabeeha ta naɗe kanta da mayafi, tana kallon tituna cikin farin ciki. Fawaaz ya dan juyo ya kalleta yana murmushi. "Kin yi shiru, ko kina tunanin yanda za a tarbe mu?" Ta juyo tana murmushi. "A’a, kawai ina tunanin dadin ganin su ne. Na dade ba na tare da su." Ya girgiza kai yana cewa, "To yau sai an yi zaman hira mai kyau, tunda ke ma kin zo da shirin dadewa." Tafiyar ba ta dauki lokaci mai tsawo ba, suka iso kofar gidan. Mai gadi ya gansu, da sauri ya bude musu kofa da murmushi. "Sannu da zuwa, oga Fawaaz da Hajiya Nabeeha!" "Yawwa Baba Lawal, ya gida?" Fawaaz ya tambaya, yana ajiyar motarsa. "Alhamdulillah." Suna fitowa daga mota, sai ga Hajiya Zaytunah ta fito daga cikin gida da fara’a, har tana dan tafiya da sauri saboda farin ciki. "Ah! Lallai yau na sha mamaki! Nabeeha da Fawaaz a tare?" Nabeeha ta durƙusa tana gaida mahaifiyarta, tana murmushi. "Ammi, ina wuni?" Hajiya Zaytunah ta kama hannunta cikin kulawa. "Lafiya lau." Fawaaz ya gaishe ta da ladabi. "Ina kwana Hajiya?" Ta amsa da fara’a. "Lafiya, Fawaaaz. Ya aikin soja. Da na bindiga" Suka yi dariya gaba daya, sannan suka shiga cikin gida. Da suka shiga falo, Alhaji Uzairu yana zaune yana karanta jarida. Da ganin su, ya ajiye takardun yana kallonsu da kulawa. "Ah! Nabeeha da Fawaaz kenan?" Nabeeha ta durƙusa tana gaida shi cikin ladabi. "Baba, ina wuni?" Ya amsa da murmushi. "Lafiya lau, ‘yata. Ya hanya kunzo kalau" "Eh Baba, Alhamdulillah." Fawaaz ya gaishe shi da ladabi, yana zama kusa da shi. "Ina wuni, Alhaji?" Alhaji Uzairu ya amsa da murmushi. "Lafiya lau, Fawaaz. Yau kun kawo mana ziyara ko?" "Eh, baba" Nabeeha ta juyo tana kallon mahaifiyarta da murmushi. "Ammi, ya gida? Ya su Hammad?" "Lafiya lau, Hammad yana can kasar karatun sa" Suka zauna cikin natsuwa, ana tattaunawa kan abubuwan da suka faru tun daga lokacin da aka yi aure zuwa yanzu. Hajiya Zaytunah na kallon Nabeeha da kulawa, tana jin farin cikin ganin yarinyarta cikin koshin lafiya. Bayan an yi dan lokaci ana hira, Hisham dan hajia karama ya shigo parlorn. Dake duk yaran suna hannun hajiya Zaytunah itake rike da su a yanzu.. "Kai! Yau dai Aunty Nabeeha ta zo mana?" Nabeeha ta kalle shi tana murmushi. "Ai kuwa na zo. Kai ma ka dade ba ka ganni ba." Ya zauna kusa da ita, yana fadin, "Ai dama kullum muna magana da Ammi, tace za ki zo." Fawaaz ya kalle shi yana dariya. "Kana nufin ba ka yi missing dinta sosai ba kenan?" Suka yi dariya gaba daya. Bayan an sha hira, an ci abinci, sannan suka ce za su wuce gidan Alhaji Amiru da bangaren Gwaggo Zainabu. .. Da suka iso gidan Alhaji Amiru, mai gadi ya bude musu kofa, suka shigo cikin mutunci. Da zarar sun shiga falon, Gwaggo Zainabu ta fito da fara’a tana kallonsu. "Ah! Nabeeha da Fawaaz! Wannan ziyara ta musamman ce." Nabeeha ta durƙusa tana gaishe ta. "Gwaggo, ina wuni?" Ta shafa kanta da kulawa. "Lafiya lau, ‘yata. Yau kun tuno da mu kenan?" Fawaaz ya gaishe ta da girmamawa. "Mukace bara mu zo mu gaishe ku." Alhaji Amiru ya fito yana kallonsu da murmushi. "Kun kyauta. Sannun ku da kokari" Suka zauna cikin falo, ana hira mai dadi. Gwaggo Zainabu na jin daɗin ganin Nabeeha, tana tambayarta game da zamanta a gidan Fawaaz. "Kin more zaman aurenki ko?" Ta tambaya tana kallonta. Nabeeha ta yi murmushi, ta kalli Fawaaz sannan ta juyo tana cewa, "Eh Gwaggo, Alhamdulillah." Fawaaz ya sosa ƙeya yana murmushi. "Ai ko da ba ta fada ba, nasan cewa tana jin daɗi." Sukayi wasan kaka da jika da Gwaggon. Suka yi dariya gaba daya. Bayan sun jima suna tattaunawa, suka sha fura, sannan suka ce za su wuce gida. Gwaggo Zainabu ta shafa kan Nabeeha da addu’a. "Allah Ya albarkaci zaman aurenku, Ya kara mana fahimta da so." Alhaji Amiru ya kalli Fawaaz da murmushi. "Ka kula da ita sosai." "In sha Allah, Abba" A haka suka yi sallama da iyayensu, suka koma gida cikin farin ciki, suna jin daɗin ziyarar da suka kai. 🎀🎀 Bayan kwanaki da ziyarar da suka kai gidan iyayen Nabeeha da danginta, sai Fawaaz ya shirya tafiya da ita zuwa Bokezuwa – kauyen mahaifiyarta, Hajiya Zaytunah. Tun bayan da ta fara jin labarin tushenta, Nabeeha ta daɗe tana son ganin garin da mahaifiyarta ta fito, wurin da danginta suka rayu kafin rayuwa ta raba su. Tafiyar ta kasance mai nisan gaske, domin Bokezuwa yana can cikin karkara, a wata lungu da ke da nisa daga birni. Sun fita tun da sassafe, Fawaaz yana tuka motar, yayin da Nabeeha ke zaune kusa da shi, zuciyarta cike da tunani. "Fawaaz, ina jin kamar in yi kuka." Ta furta a hankali, tana lumshe idanu. Ya dan kalleta, yana murmushi. "Kuka kuma? Me ya faru?" Ta sauke ajiyar zuciya. "Tunani nake yi… A nan ne Ammi ta girma, ta rayu da danginta. Amma yanzu babu su, babu komai." Fawaaz ya dora hannunsa kan nata a hankali. "Ina jin ki, Nabeeha. Amma ki sani, zuwanmu nan wata hanya ce ta sabunta tarihin da ya shuɗe. Hakan ma babbar ni'ima ce." Ta jinjina kai, tana jin wani sanyi yana ratsata. Sun dauki kusan awa uku a hanya kafin suka iso bakin kauyen. Titin kauyen ba shi da kyau sosai, cike yake da yashi da ƙurare. Yayin da suka shiga cikin garin, sai Nabeeha ta fara karewa wuraren kallo. Kauyen yana da saukin kai, duk da cewa gine-ginen sa sun nuna cewa lokaci ya ja. Tsaffin gidaje ne a kewayensu, yawancinsu da bulo aka gina su, wasu kuma da tubali. A gefe, akwai wata babbar rijiya da ke tsakanin itatuwa, inda wasu dattawa ke zazzaune suna hira. Wasu mata kuma suna gefen wata bishiya suna yankan ganye da wasu 'yan mata ke taya su. Nabeeha ta cika da mamaki, zuciyarta na bugawa da sauri. " Yaa Fawaaz, kenan a nan ne Ammi ta girma?" "Eh, a nan ne asalinta." Wata tsohuwa da ke zaune kusa da rijiya ta lura da su, ta fara kallonsu da kyau. Ganin su a cikin mota mai kyau ya jawo hankalin mutanen kauyen da dama. Lokacin da suka yi parking a wani yanki da ake kiran "Tashar Bokezuwa," wasu yara suka fara matsowa suna kallonsu da sha’awa. Fawaaz ya fita daga mota, ya zagaya gefen Nabeeha ya bude mata kofa. Tana fita, tsohuwar da ke zaune kusa da rijiya ta miƙe, tana takowa da sandarta. "Wannan ai kamar Zainabu ce!" Ta fada da mamaki. Nabeeha ta kalleta da sauri. "Zainabu?" Tsohuwar ta karasa kusa da su, tana kare mata kallo. "Ke ‘yar Zaytunah ce ko?" Gaban Nabeeha ya fadi. "Eh, ni ce." Tsohuwar ta dafe kanta. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah mai iko! Dama har yau Zaytunah tana raye?" Hawayen da ke cike da idon Nabeeha suka silalo. "Eh, tana raye." Tsohuwar ta saki ajiyar zuciya, tana fadin, "Toh Alhamdulillah! Ai tun lokacin da aka ce ta bar garin nan, ba mu sake jin duriyarta ba." Wasu dattawa da ke zaune a wajen suka matsa kusa, suna tambayar me ke faruwa. Wani tsoho mai farin gemu ya karaso, yana tambaya. "Wai ‘yar wa ce wannan?" Tsohuwar ta kalleshi da mamaki. "Wannan ‘yar Zaytunah ce, yaran da sukayi aure . Zaytunah da rumanah. Dangin makarantar allo. Sansanin marigayi malam idi bokezuwa da malam nata'ala. " Sai murmurmurmi ya bayyana a fuskokin dattawan. "Subhanallah! Ashe dai ta rayu? Allah ya kai mu zamanin ganin ‘yarta!" Bayan dogon hira da dattawan, sai suka nufi inda tsohon gidan mahaifiyar ta ta rayu. Duk da cewa gidan yanzu ya rufta da yawa, har yanzu yana nan da sifarsa. Gidane mai bango da akayi da tubali, a kofar sa kuwa akwai wata tsohuwar bishiya mai inuwar da ke rufe rabin harabar gidan. Nabeeha ta tsaya tana kallon gidan da mamaki. "Ya fawaaz, nan ne Ammi ta taso?" Ya jinjina kai. "Eh, a nan ne gidan iyayenta." Tsohuwar ta karasa tana cewa, "Wannan gidan su dangin mahaifiyarki ne, Anan ta girma da mahaifanta kafin wannan bala'in ya raba su da juna." Nabeeha ta dan dafa bango, tana jin wani iri a zuciyarta. Tana iya hango rayuwar da mahaifiyarta ta yi a nan. Tsohuwar ta ci gaba da magana cikin taushin murya. "Mahaifiyarki yarinyace mai hankali da biyayya. Duk mutanen nan sun santa, sun san halinta." Hawaye suka cika idon Nabeeha. "Nagode da kuka gaya min. Ammi ba ta taba cewa da yawa game da rayuwarta a nan ba." Tsohuwar ta yi murmushi. "Ba abin mamaki bane. Wata rana za ku kawo ta, mu sake jin daɗin kasancewa da ita." Bayan sun jima suna tattaunawa, suka sha ruwa daga rijiya sannan suka yi sallama da dattawan. Suka dan musu alheri na kudi. Lokacin da suka shiga mota, Nabeeha ta juyo tana kallo ta taga, zuciyarta cike da tunani. "Ya fawaaz, mun taba zuwa garuruwa. amma ban taba jin irin wannan ba." Fawaaz ya kalleta, yana riko hannunta. "Wannan ne asalinki, Nabeeha. Kuma ina fatan kin ji dadin sanin shi." Ta jinjina kai, tana murmushi. "Eh, naji dadin sanin shi. Kuma zan dawo nan wata rana." Ya shafa kanta cikin kulawa. "Ko da yake, sai kin gama shan kukan tunani." Ta yi dariya cikin hawaye. "Toh ai ba zan daina jin kaunar wannan wuri ba." Daga nan suka tada mota, suka bar kauyen cikin natsuwa, zuciyar Nabeeha cike da soyayya da alfahari da tushenta. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_               _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _PAGE:64_ Dare ya zama safiya, safiya ta zama rana, rana ta zama yammaci. Lalle Allah buwayi ne gagara misali. Kwanaki nata shudewa, kowane bangare na cikin littafin rayuwar su na tafiya dai dai Alhamdulillah. Sai dan abunda ba a rasa ba na ups and downs . Wanda baki daya rayuwa tanada nata irin jarabawar kaddarar da take zuwa Wa kowane bawa... Wala kyakkyawa Wala akasin haka. Nabeeha ta runtse idanu, tana jin yadda kalmomin Fawaaz ke ratsata har cikin zuciyarta. Hannayensa da ke cikin nata sun ba ta natsuwa da kwanciyar hankali. Cikin rawar murya ta ce, "Ya fwaaz, ina jin tsoro..." Ya janye daga rungumar ta kadan, yana duban cikin idanunta. "Tsoro kuma, my love? Me ya faru?" Ta sauke ajiyar zuciya, tana murza yatsun hannunsa. "Ina jin kamar ba zan iya ba… Ina jin kamar wannan babban nauyi ne a kaina." Fawaaz ya dora goshinsa kan nata, yana murmushi cikin so da kulawa. "Ke dai bari, Habibty! Allah ne ke bayar da rabo, kuma shi ke saukakewa. Babu abin da zai same ki sai alkhairi. Ni zan kasance tare da ke a kowane mataki. Ba zan bar ki kin ji ƙunci ba, ba zan bari ki ji wahala ba. Zan dinga tare da ke, zan taimake ki da duk abinda kike bukata." Ya sake shafa bayanta, yana magana cikin murya mai taushi, "Allah ya sa ki haihu lafiya, Allah ya kiyaye ki, ya kare min ke da babyna. Allah ya sa ki zama uwar yara masu albarka. Allah ya albarkaci wannan jaririn da ke cikinki. Allah ya tsare ku, ya sa ku kasance lafiya a koda yaushe!" Ta dinga jin addu'o’insa kamar ana yayyafa mata ruwan sanyi. Hawaye suka ci gaba da gudu a fuskarta. "Ameen, Yaa Fawaaz... Na gode da kaunar da kake min. Ka sa na ji kwarin gwiwa. Ka sa na ji ina da matsuguni da masoyi na hakika." Fawaaz ya kai bakinsa gefen kunnenta, ya ce cikin radadi da kauna, "Kin kasance mafi daraja a gare ni, Nabeeha. Ko da za a bani duniya a madadin ki, ba zan karba ba. Ke ce rayuwata, kuma yanzu kin kara min wata rayuwar da zan runguma cikin ƙauna da kulawa!" Ta rufe idanunta, tana jin yadda soyayyarsa ke mamaye zuciyarta. Bayan sun bar asibiti, Fawaaz ya mai da hankali sosai wajen kula da Nabeeha. A kullum yana sa ido a kanta, yana tabbatar da cewa ba ta yi komai mai wahala ba. Duk inda za ta je, shi zai kai ta. Duk abinda take so, zai samo mata. Akwai lokacin da ta fara jin yunwa cikin dare. Tana kwance a gadonsu, tana jin yadda cikinta ke kara motsi. Sai ta yi dariya a hankali, ta shafi cikinta. Fawaaz, wanda ke zaune kusa da ita yana karanta wata takarda, ya lura da murmushinta. "Me ya faru?" Ya tambaya, yana kallonta da kulawa. Ta yi dariya a hankali. "Ina jin yunwa." Ya zaro idanu da mamaki. "Yunwa da daddare? Me kike so na samo miki?" Ta kwanta gefensa, tana kallon sa da idanuwanta masu cike da so. "Ina jin kamar zan ci lemun tsami da danyar kubewa." Ya zaro ido. "Lemun tsami da kubewa? Wannan wace irin haduwa ce?" Ta fashe da dariya. "Ni dai haka nake jin so." Ya girgiza kai, yana murmushi. "Ai ba komai! Bari na je na nemo miki. Ko da kuwa zan tashi na je wajen mai sayarwa a daren nan, zan yi domin na tabbatar kin samu abinda kike so." Ta kalleshi da so da kauna. "Nagode, masoyina." Ya matsa kusa da ita, ya dafa cikinta a hankali, yana magana cikin taushi. "Ina yi wa babyna sannu. Ina fatan yana jin dadi a cikin Ammi?" Ta lumshe idanu, tana jin wani irin farin ciki ya rufe ta. "Muna jin daɗi, ya Fawaaz. Ka sa rayuwata ta zama mafi kyan da na taba ji a duniya." Ya sanya tafin hannunsa a fuskarta, yana shafa kuncinta cikin ƙauna. "Ke ma kin sa tawa ta zama mai ma'ana, Nabeeha. Kuma zan ci gaba da ƙaunar ki da renon ki har abada." A haka suka ci gaba da soyayyarsu, cikin kula da juna da tarairaya. Kowace rana, Fawaaz yana ƙara fahimtar yadda soyayyarsa ga Nabeeha ke zurfafa, yana kara godewa Allah da Ya albarkace su da wannan kyauta. A kullum soyayya da kulawar da Fawaaz yake wa Nabeeha na ƙara girma da zurfi. Duk inda ta juya, a shirye yake don tarairayarta. Duk damuwarta, a shirye yake don share mata ita. Duk wahalarta, a shirye yake don daukar ta a kansa. Yanzu haka suna zaune a lambun gidan su, inda iskar sanyi ke kadawa, tana busa gashin kanta a hankali. Fawaaz yana zaune a gefenta, hannunsa rike da nata, yana wasa da yatsunta cikin kwanciyar hankali. "Nabeeha," ya kira sunanta da murya mai laushi, "Kin san ko?" Ta kalle shi, tana murmushi. "Me zan sani?" Ya sake matse hannunta a cikin nasa, yana kallonta da ido mai cike da kauna. "Kin san cewa ina ƙaunarki fiye da komai a duniya? Kin san cewa tun ranar da Allah ya hada mu, rayuwata ta samu ma'ana? Kin san cewa idan har za a tsaga zuciyata, babu abin da za a samu face ke?" Ta lumshe ido, tana jin yadda kalmomin sa ke ratsata kamar ana yayyafa mata zuma a zuciya. "Hayatim." ta furta cikin sanyin murya. Ya ɗora tafin hannunsa a saman cikinta, yana shafa shi cikin kulawa. "Yanzu ba ke kaɗai ba, Nabeeha. Kina da wani babban matsayi a zuciyata, amma wannan jaririn da ke cikinki… shi ne shaida ta babbar kyauta da Allah ya bani. Allah ya albarkace ni da ke, kuma yanzu Ya kara albarkata da wata ƙwarya daga gare ni. Ina son ki, Nabeeha. Kuma zan kasance tare da ke a koda yaushe." Hawaye suka cika mata ido, ta kasa furta komai. Sai kawai ta kai kanta kan kafadarsa, ta jingina a jikin sa. Fawaaz ya saki ajiyar zuciya, yana jin yadda jikin ta ke dumama nasa. Ya kwantar da kansa a gefen nata, yana jin bugun zuciyarta na tafiya da nasa. "Daga yau, Nabeeha," ya cigaba da magana cikin natsuwa, "Ba zan bari ki ji wata damuwa ba. Ba zan bari ki sha wahala ba. Zan kula da ke kamar wata sarauniya. Zan dinga sadaukar da komai don farin cikin ki. Zan yi miki hidima fiye da yadda na taba yi. Domin ke ce hasken rayuwata. Ke ce farin cikina. Ke ce mafarkin da ya zama gaskiya." Nabeeha ta dago fuskarta daga kafadarsa, tana kallon cikin idanunsa da suka cika da shauƙi. "Ya Fawaaz, na gode... Ba zan iya misalta irin godiyar da nake maka ba. Ka sa rayuwata ta zama cikakkiya. Allah ya bar ka da ni har abada." Ya sakar mata murmushi, yana shafa kumatunta da tafin hannunsa. "Allah ya sa mu rayu tare har karshen rayuwarmu. Allah ya bar mu cikin soyayya da aminci. Allah ya albarkaci wannan rabon da Ya ba mu, ya raya mana shi lafiya." Ta lumshe idanu, tana jin yadda addu’o’insa ke shigarta har cikin zuciya. Bayan kwanaki, Fawaaz ya dage da kula da Nabeeha fiye da da. Idan ta tashi, yana a gefenta. Idan ta zauna, yana bata goyon baya. Idan ta yi gajiya, shi ne mai shafa mata bayanta. Ranar da suka je ziyarar gida, Hajiya Zaytunah ta yi mamakin yadda Fawaaz ke lallashinta. Yana rike mata hannu kamar wata jaririya, yana tabbatar da cewa ba ta yi wani abu da zai gajiyar da ita ba. Hajiya Zaytunah ta dubi Alhaji Uzairu da murmushi. "Kana ganin yadda Fawaaz ke kula da ‘yar ka? Ya fi yadda kowanne uba zai yi wa diyarsa. Wannan abu sai wanda Allah ya sanya soyayya a zuciyarsa." Alhaji Uzairu ya girgiza kai cikin jin dadi. "Tabbas Nabeeha ta samu nagartaccen miji. Muna yi musu fatan alheri da zaman lafiya mai dorewa." Fawaaz ya dubi Nabeeha, ya matsa kusa da ita, yana furta cikin radadi da kulawa, "My Queen, zan iya raba jinina da ke, amma ba zan iya barin ki ki wahala ba. Ina son ki, Nabeeha. Har abada!" Hajiya Zaytunah da Alhaji Uzairu suka kalli juna da murmushi, yayin da Nabeeha ta lumshe idanu, tana jin yadda soyayyar Fawaaz ke kara ratsa zuciyarta, tana mai tabbatar da cewa shi ne kadai wanda Allah Ya aiko mata a matsayin abokin rayuwarta na hakika. Kwana-kwanan nan, rayuwar Nabeeha ta zama kamar mafarki. Fawaaz ya cika alkawarinsa na kula da ita, ba tare da ya bari ta ji wani nauyi ko damuwa ba. Idanunta sun fi koyaushe cike da farin ciki, fuskarta tana cike da annashuwa, kuma zuciyarta ta cika da kwanciyar hankali. Rana ce ta Jumu’a, inda suka shirya tafiya gida domin kai wa iyayenta ziyara. Fawaaz ya tabbatar da cewa Nabeeha ta huta sosai kafin su tafi. Ya zabi mata kaya masu laushi da dadi, sannan ya taimaka mata ta saka hijabinta yadda ba zai dameta ba. Da suka isa gidan, Hajiya Zaytunah ta tarbe su da murmushi mai cike da farin ciki. Nabeeha ta yi saurin rungume mahaifiyarta, tana jin yadda soyayyarta ke kara girma a zuciyarta. "Ammi, na yi kewar ki sosai!" Hajiya Zaytunah ta shafa kanta da kulawa. "Ni ma na yi kewar ki, ‘yata. Kina lafiya kuwa?" Kafin ta amsa, Fawaaz ya riga ta da cewa, "Ta na lafiya, Ammi. Ni na tabbatar da hakan!" Dariya suka yi gaba ɗaya, sannan suka zauna domin yin hira. A lokacin da Alhaji Uzairu ya shigo, Fawaaz ya miƙe da girmamawa, yana gaishe shi. "Ya jikin Amaryar tamu?" Alhaji Uzairu ya tambaya, yana murmushi. Fawaaz ya kalli Nabeeha da idanuwansa masu cike da ƙauna. "Lafiyarta kalau, Alhaji. Allah na tare da ita." A haka suka ci gaba da hira, suna jin daɗin kasancewa tare. Bayan sun gama gidan su Nabeeha, suka wuce gidan Alhaji Amiru, inda suka same shi tare da Gwaggo Zainabu. Gwaggo Zainabu ta ji daɗin ganin Nabeeha da cikinta yana girma cikin lafiya. "Allah ya sauke ki lafiya, jikata." "Ameen, Gwaggo. Na gode." Fawaaz ya zauna kusa da ita, yana jinjina mata don girmamawa. "Gwaggo, ina fata kin yi sallah lafiya." Ta gyada kai, tana murmushi. "Alhamdulillah, Fawaaz. Kai kuwa, ya mai kula da Nabeeha?" Ya lumshe ido da murmushi. "Ni dai granny na fara ji kamar ni ne mai dauke da shi. Domin ba zan iya ganin ta cikin wahala ba. Ita ce duniya ta gaba daya." Nabeeha ta ji yadda zuciyarta ta karye da kauna. Sai ta dan matsa kusa da shi, tana jin nutsuwa a jikinsa. Gwaggo Zainabu ta yi murmushi, tana fadin: "Allah ya bar ku tare cikin zaman lafiya da farin ciki." "Ameen," suka amsa a tare. Daga nan suka shirya tafiya zuwa kauyen Bokezuwa, tushen iyayen Nabeeha. Fawaaz ya tsara tafiyar ne saboda yana so Nabeeha ta ji farin ciki da kasancewa da danginta. Lokacin da suka isa, jama’a sun tarbe su da farin ciki. Duk da cewa shekaru sun shude, mutanen kauyen sun san su Nabeeha da labarin mahaifiyarta, Hajiya Zaytunah. Wata tsohuwa daga cikin dangin mahaifiyarta ta rike hannun Nabeeha, tana fadin: "Kin yi kama da mahaifiyarki lokacin tana yarinya. Allah ya kara miki albarka, ‘yata." Nabeeha ta jinjinawa tsohuwar, hawaye suna cika idonta. Fawaaz kuwa yana gefe yana kallon matarsa da wani irin shauki da ƙauna. "Mun gode da tarba, Inna," ya fada cikin ladabi. Tsohuwar ta dube shi, sannan ta yi murmushi. "Kai ne mijin ‘yar tawa?" "Eh, Inna." Ta dube shi da kulawa, sannan ta girgiza kai. "Allah ya albarkaci zamanku. Ka kula da ita, kamar yadda ka alkawarta." Fawaaz ya kama hannun Nabeeha, ya sumbata a saman tafin hannunta. "Zan kula da ita fiye da yadda nake kula da kaina, Inna." Mutanen kauyen suka yi dariya, suna yabawa da irin soyayyar da Fawaaz ke nunawa Nabeeha. Bayan sun dawo daga tafiya, Nabeeha ta fara jin sauyin jikinta. Cikinta yana kara girma, kuma Fawaaz ya dinga kula da ita fiye da yadda ya saba. Rana ce ya dawo daga aiki, ya same ta tana zaune a falo, tana kallon cikin ta da murmushi. Ya durkusa a gabanta, ya dafa cikinta da tafin hannunsa. "Yaya babyna?" Ta kalle shi tana murmushi. "Babynka yana cikin kwanciyar hankali. Yana jin sanyin addu’o’inka." Ya lumshe ido, yana fadin: "Allah ya sauke ki lafiya, Nabeeha. Allah ya ba mu ikon tarbiyyar wannan yaron daidai da yadda zai zama mai amfani a duniya." Ta furta cikin radadi da kauna: "Ameen, Fawaaz. Allah ya kara mana soyayya." Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta a kirjinsa. "Soyayyarmu ba zata taba raguwa ba, Nabeeha. Sai dai ta kara girma har abada!" Haka rayuwarsu ta ci gaba, cikin kulawa, addu’a, da soyayya ta gaskiya.. ADVERT👇 YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE YERWA INCENSE AND MORE (THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME) (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI) INA MA'ABOTA TURARE! Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa! 🌟 Mene ne za ku samu? Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno. Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan. Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa. Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida. Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi. Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa. 📍 Adireshi: Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare. 📞 Tuntuɓe mu: WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107 Instagram: @yerwaincense_and_more Facebook: @yerwacollection Twitter:Hafsaaat00 🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok: @besturarenwutainkano https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1 🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne! 🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE! *KIRJIN MAI HANKALI* _(Akwatin sirrin sa)_ _🧳👩‍❤️‍👨🌺_ *_The Vault Of His Secrets_* _®️NANA HAFSATU (MX)_ _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_ *_BOOK TWO_* _(Completed)_ *_PAGE:65_* _(shafin karshe/The end/Episode Finale)✅_ ______ A daren ranar, duhun dare ya lullube garin, amma zuciyar Fawaaz tana cike da fargaba da fatan alheri. A cikin asibiti yake zaune, hannunsa rike da na Nabeeha, wanda ke jin radadin nakuda. Idanunta sun lumshe, hawaye na sauka daga gefen kumatunta, amma har yanzu murmushi yana manne a fuskarta. "Ya fawaaz…" ta kirasa cikin wata murya mai rauni. Ya matsa kusa da ita, yana share mata gumi. "Nabeeha, ina nan. Ki kasance da ƙarfin zuciya. Kiyi haƙuri, kin kusa samun nasara." Idanunta suka cika da soyayya, ta furta cikin rauni, "Na gode… na gode da ka kasance tare da ni a koda yaushe. Ba zan iya misalta irin kaunar da nake maka ba." Hannunsa ya kara damke nata, yana girgiza kai. "Kada ki ce haka, Nabeeha. Ina tare da ke har abada. Allah ya sa wannan ranar ta zama mafi albarka a rayuwarmu." A wannan lokacin, likitoci suka bukaci Fawaaz ya fita domin su ci gaba da taimaka wa Nabeeha wajen haihuwa. Ya kasa matsawa daga kusa da ita, sai da aka lallashe shi sosai sannan ya yarda ya fita. Bai daina addu’a ba. Bai daina salati ba. Bai daina rokon Allah da zuciya daya ba. "Ya Allah! Ka sauke ta lafiya. Ka ba mu wannan jaririn cikin sauki. Ka raya mana shi cikin shiriya da albarka. Ya Allah, kada ka jarabceni da rashin Nabeeha. Ita ce numfashina." Lokaci yana tafiya, amma a cikin zuciyar Fawaaz kamar shekaru ne ke wucewa. Har sai da wata karamar nurse ta fito tana murmushi. "Captain Fawaaz?" Ya mike da sauri. "Na’am! Yaya matata take?" "Alhamdulillah! Allah Ya albarkace ku da ɗa namiji. Matarka ta sauka lafiya, kuma danta yana cikin koshin lafiya." Duk wani nauyi da ke kan zuciyar Fawaaz ya dauke a take. Idanunsa suka cicciko da hawaye, amma wannan ba hawaye ne na damuwa ba, sai na tsantsar farin ciki. Ya durkusa a kan guiwowinsa, ya dora goshinsa a ƙasa, yana sujjadar godiya. "Alhamdulillah! Alhamdulillah ya Rabb! Na gode maka, Ya Allah!" Bayan ya gama addu’a, ya mike da sauri, yana bin nurse ɗin da take jagoranta zuwa dakin da Nabeeha take. A lokacin da ya shiga dakin, ya tsaya yana kallonta. Nabeeha na kwance da ƙarfinta ya rage, amma duk da haka akwai murmushi a fuskarta. A gefenta ne aka ajiye jaririn da ta haifa, an nade shi cikin fararen kaya.. Hankalinsa ya fara tafiya kan Nabeeha. Ya zauna kusa da ita.. Fawaaz ya zauna a gefen gadon, zuciyarsa tana cike da tsananin kauna da godiya. Ya shafi gashinta da kulawa, yana kallonta da idanunsa masu cike da shauƙi. "Nabeeha…" ya kira sunanta da murya mai rauni. Ta bude idanunta a hankali, tana kallonsa da murmushi. Duk da gajiyar da ta sha, hakan bai hana hasken farin ciki bayyana a fuskarta ba. "Ya Fawaaz… mun samu ɗa." Ta furta a hankali, hawaye masu ɗumi suna gangarowa daga idanunta. Ya girgiza kai, yana share mata hawayen da yatsunsa. "Nabeeha, kin zama tauraruwa a rayuwata. Kin cika min burina. Na rasa yadda zan misalta irin godiyar da nake miki. Na gode da kika kawo min wannan baiwa daga Allah." A hankali ya kama hannunta, ya rike da karfi. "Na sha alwashin kare ki da shi da dukkan rayuwata. Ba zan taba bari ku shiga cikin wata wahala ba, Nabeeha. Ke da wannan jaririn duk abin da nake da shi a duniya." Ta kalli jaririn da ke gefenta, zuciyarta cike da tsantsar soyayya. "Ya Fawaaz, ka ɗauke shi." Fawaaz ya tsaya na wani lokaci, zuciyarsa tana bugawa da sauri. Wannan ne karon farko da zai ɗauki dansa a hannunsa. Ya matsa kusa, yana mika hannayensa da nutsuwa. Yana ji kamar idan ya ɗauke shi, zai ji wani yanayi na daban da bai taba jin irinsa ba. A hankali ya ɗauki jaririn, yana jin sa a hannunsa da sanyin fatar jikinsa. Yaron ya motsa kadan, sannan ya yi wani ƙaramin gyatsa. Fawaaz ya kasa tsayawa da murmushi, yana jin wani irin farin ciki da bai taba ji ba. Kamar su daya da fawaaz din sak..sai dai idanuwan sa na Nabeeha ne da sumar kansa ta fulanin usul. Ya rungume shi a kirjinsa, yana lumshe ido. "Muhammad Dawud…" ya furta da murya mai rauni. "Sunan mahaifina zan saka masa, domin ya zama jarumi irin sa." Nabeeha ta dube shi da murmushi, ta gyada kai. "Sunan ya dace da shi. Allah ya albarkace shi, ya tsare rayuwarsa." Fawaaz ya lumshe ido, yana jin yadda zuciyarsa ke cike da soyayya. "Ya Allah! Na gode maka da wannan baiwa. Ka sanya shi cikin shiriya, ka ba shi rayuwa mai albarka da tsawon kwana. Ka sa ya zama mai amfani ga addini da al’umma." Ya dawo da kallonsa kan Nabeeha, yana matseta a jikinsa tare da jaririn. "Daga yau, soyayyata gare ki ta kara ninka fiye da yadda take. Na fi kaunarki fiye da yadda zan iya furta wa." Ta lumshe ido, tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da kwanciyar hankali. "Na gode, Ya Fawaaz. Allah ya kara mana soyayya da fahimta." Nan da nan dama surprise (bazata) sukeso suyiwa dangi. Sai dai kawai aji haihuwar ta..nan da nan fawaaz ya fara Kiran dangin nasu a waya. Asibitin ya cika da dangi anata farin ciki. Likitan ya tattara ya sallame su yace su koma gidah. Ranar suna kuwa. Anyi suna hamshaki na masu farcinan susa. Babu ce kawai baa ci ba a sunan nan. Nabeeha ta koma gidan gwaggo Hafsatu bisaga jagorancin gwaggon da hukuncin data zarce... A wannan yanayi, rayuwar su ta canza gaba ɗaya. Sabuwar soyayya, sabuwar rayuwa, sabuwar nasara. Kuma daga nan ne suka fara renon jaririnsu cikin kulawa da kauna.. Bayan dawowar su gida, rayuwar Fawaaz da Nabeeha ta cika da farin ciki da sabuwar soyayya. Duk da cewa su biyun sun saba da juna tun farko, hakan bai hana sabon salo na kauna shiga tsakaninsu ba. Yanzu Nabeeha ta zama mahaifiya, kuma hakan ya kara wa Fawaaz ƙaunarta fiye da tunaninta. A kullum yana lallaba Muhammad Dawud, amma duk da haka yana da wata ‘yar kishi da ke ƙunshe cikin zolaya. Yana ganin kamar Nabeeha ta fi son danta fiye da shi. Wata rana yana zaune a gefen gado, yana kallonta yayin da take shayar da ɗan su. Ya rangwada a gefenta, yana me ƙifta ido. "Nabeeha?" ya kira sunanta da wata murya mai laushi. Ta ɗago, tana kallonsa da murmushi. "Na’am, My Captain?" Ya gyara zamansa, ya shagwabe fuska kamar yaro. "Kin daina sona, ko?" Ta zabura, ta girgiza kai. "Subhanallah! What? Me yasa kake cewa haka?" Ya nuna yaron da ke kwance a jikinta. "Tun da wannan yaron ya shigo duniya, kin daina kulawa da ni. Ko kallona ma ba kya yi da kyau." Ta fashe da dariya, ta ɗora hannunta a ƙirjinsa. "To ai wannan yaron naka ne. Ya kamata ka ji dadin yadda nake kulawa da shi." Ya sake matsawa kusa, yana matse rikon hannunta. "Ban ce bana jin dadi ba. Amma ki tuna, ni ne farkon soyayyarki." Ta kwantar da kanta a kafadarsa, tana me murmushi. "Fawaaz, kai ne ginshikin rayuwata. Kauna ta gare ka ba zata taba raguwa ba. Shi Muhammad Dawud jinina ne, amma kai ruhina ne." Ya lumshe ido, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da tsananin soyayyarta. "Na gode, Nabeeha. Har abada zan ci gaba da ƙaunarki fiye da komai a duniya." A haka suka cigaba da rayuwa, cike da soyayya da ƙaunar juna. Duk da su biyun ba masu yawan magana bane, amma sukan fahimci juna ta hanyar kallon ido da kallon zuciya. A wani dare, Fawaaz yana zaune a cikin bedroom, Nabeeha na kwance a jikinsa. A lokacin Muhammad Dawud yana barci a gadon sa. Wurin yayi tsit, sai saukar numfashin su kadai ake ji. Sai da yayi shiru na wani lokaci sannan ya kamo hannunta, yana murza yatsunta a hankali. "Kin san wani abu?" ya tambaye ta cikin wata murya mai nauyi. Ta kalle shi, tana murmushi. "Me kenan?" Ya dora hannunsa akan ƙirjin sa, ya rufe idanunsa. "Na sake tabbarwa da KIRJI ba MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA ne" Ta ƙura masa ido, tana jiran cikakken bayani. Ya ɗora hannunta a kan zuciyarsa. "AKWATIN SIRRIN na yana nan, a cikin zuciyata. Amma kin san waye SIRRIN? Ke ce. Ke ce SIRRINa, ke ce rayuwata, ke ce duk wani abu da nake da shi." Ta lumshe ido, tana jin nauyin maganarsa yana shiga cikin zuciyarta. "The vault of your secret...." "The vault of his secret indeed... Amma kawai ina so ki sani, Nabeeha. Ko da waye zan kasance a duniya, ko da menene zan samu, har abada, ke ce AKWATIN SIRRINa." A wannan dare, Fawaaz ya lumshe idanunsa, yana jin wani irin natsuwa da bai taba ji ba. Duk da yawan shekarun da suka shafe tare, soyayyarsa ga Nabeeha tana karuwa ne maimakon raguwa. Yana kallonta a kusa da shi, idanunta sun lumshe cikin barcin gajiya, amma fuskarta na bayyana nutsuwa da kwanciyar hankali. Ya dan rankwafa, yana shafar gashinta a HANKALI. "Ke ce AKWATIN SIRRINa," ya sake nanatawa a kasan makoshinsa, yana jin nauyin soyayyar da take cike da zuciyarsa. Sai da ya dan tsaya na wani lokaci, yana jin numfashinta yana tashi da sauka a hankali, sannan ya dora tafin hannunsa a saman cikinta da har yanzu bai gama komawa daidai ba bayan haihuwa. "Kin ci gaba da bani darasi, Nabeeha," ya fada murya a raunane. "A baya na dauka cewa zuciya ce ke dauke da SIRRIN mutum, sai daga baya na fahimci cewa HANKALI shi ne ginshikin komai. Amma yanzu, na kara fahimta cewa akwai wani abu da ya fi duka. Wurin da SIRRIN mutum ke boye, ba a zuciya yake ba, ba a HANKALI yake ba. AKWATIN SIRRIN mai HANKALI yana hannun wanda ya cancanta." Ya kalleta, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da matsananciyar kauna. "Kuma ke ce kikafi cancanta, Nabeeha. Kin rike SIRRINa, kin rike zuciyata, kin rike rayuwata. Ke ce mace daya tilo da zan iya mika dukkan amana ta gare ta." A hankali ta bude idanunta, kamar wadda ta jima tana jin maganarsa a mafarki. Sai ta dan turo baki, tana murmushi. "To sai me?" Ya yi dariya, yana dora goshinsa a nata. "Sai dai in ci gaba da nuna miki cewa bazan taba sauya tunani ba. Ke ce SIRRINa, kuma har abada, ke ce AKWATIN SIRRINa." Ta lumshe ido, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da nishadi. "Kuma kai ne komai nawa, Fawaaz. Ba zan taba iya rayuwa babu kai ba." Ya kama hannunta, yana dora mata kiss a bayansa. "Ko bayan rayuwa ma, soyayyata gare ki zata ci gaba da wanzuwa. Zuciyata ta kasance taki ce har abada, Nabeeha." Duk da maganar tana da nauyi, sai da ta yi murmushi. "Ka fiye soyayya, Captain. Yanzu dai ka barni in ci gaba da barci, saboda Muhammad Dawud na iya farkawa da dare." Ya jinjina kai, yana sake kwantar da ita. "To Allah ya sa mafarkin ki na da dadi." "Amin." A hankali ya rufe idanunsa, yana rungume ta da kwanciyar HANKALI. Cikin zuciyarsa, yana jin wani irin nutsuwa da bazai iya misaltawa ba. HANKALI ya kasance cikin KIRJI, amma SIRRI yana da nasa mazauni. Kuma a karshe, Fawaaz ya fahimci cewa ba KIRJI bane ke dauke da SIRRIN MAI HANKALI, ba HANKALI bane ake ajiye shi. SIRRIN mai hankali yana hannun wanda aka mallaka masa zuciya da rayuwa gaba daya. Kuma gareshi, wannan mutum daya tilo ce, Wato...Nabeeha uzair Muhammad..Mrs Fawaaz dawud mafia.. Ta rungume shi da ƙarfi, tana jin tsantsar soyayyarsa yana ratsa zuciyarta. "Kauna ta gare ka ba zata taba gushewa ba, Ya Fawaaz dina." A haka bacci mai nauyi ya dauke su... A wannan dare, soyayyarsu ta cika, zuciyoyinsu sun hadu, kuma SIRRIN su ya ƙare cikin ƙauna da aminci. °°°°° _Alhamdulillah! Duk da gajiyar tafiya, da ƙalubalen rubutu, da neman kyakkyawar mafita ga labari, a yau na kammala littafin KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA) gaba ɗaya._ _Na fara wannan tafiya da zuciya cike da burin bayar da labari mai ma’ana—wanda zai ƙunshi soyayya, sirri, hakuri, da yarda da kaddara. A ƙarshe, labarin ya zama fiye da haka. Ya zama tafiya ta soyayya da ƙaddara. Tafiya ta sirri da amana. Tafiya ta mutum da zuciyarsa, da wanda ya cancanci ya zama Akwatin Sirrinsa._ _Ina roƙon Allah Ya sa albarka a cikin wannan aiki, Ya yafe mun da ku duk wani kuskure da na rubuta, Ya kuma saka lada ga duk wanda ya karanta da niyyar neman nishaɗi ko darasi._ _Dukkan halaye da aiyuka na kyawawan jaruman wannan littafi ina fatan su zama abin koyi. Kuma kuskuren da suka aikata ya zama izina gare mu. Ina rokon Allah Ya gafarta mana, Ya sa mu zama cikin waɗanda suke koyi da alheri, su kauce wa sharri._ _Na gode da soyayya, goyon baya, da addu’o'in da aka yi mun a wannan tafiya. Sai littafi (zafafa paid books) na gaba, idan Mai Duka Ya kai mu!_ _Alhamdulillah!_ _Alhamdulillah!_ _Alhamdulillah!_ _wannan littafi na kudi ne, wato daya daga cikin jerin littattafan zafafa biyar... Nera dari biyar N500 ne ga duk mai son mallakar sa.... Domin karin bayani sai a tuntubeni ta 09134848107_ _Taku: Nana hafsatu... (Mss xoxo)_