[11/12 11:59] MRS SADAUKI: *MAFARKI*🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` SADAUKARWA: Ga mata ma'abotan saka hijabi.🤗 01 Yau ma kamar kullum tun safe na yi wanka na shirya cikin uniform ɗin makaranta,na fesa turare marar ƙamshi kafin na ɗauki jakata mai ɗauke da Alkur'ani da sauran littafai da ake koya mana.Cike da nutsuwa na sauko ƙasa,da Momy idona ya yi tozali matar kirki wacce daular da muke ciki ba ta saka ta zama raguwa ko mai ƙiwar aiki ba kullum a tsaye take domin farin cikin ahalinta. Duk wata sangartata ce na ji ta motsa,na tattare zumbulelen hijabina wanda tsabar girmansa har jan ƙasa yake yi.Da ɗan guduna kamar zan faɗi na je na rungume ta ina mai yi mata sallama madadin na ce ina kwana,saboda haka Daddynmu ya koyar da mu yin sallama kafin kowacce gaisuwa. “Wa'aleyki salam autar Momy” ta amsa mini. Na turo baki don na tsani a ce mini auta ina mugun ƙaunar yara wannan yasa kullum fatana Momy ta haihu.Na ce “ni dai ba auta ba Momy,kin ga Mamarsu Mujahida ma ta haihu” Ta yi ɗan murmushi mai sauti kafin ta ja hancina ta ce “wuce dai ki je direba na jiranki,ki aje hankalinki ki yi karatu banda surutu” Na ce “to Momy ki haɗa mini lemun zoɓo da kanki ,in an kusa shan ruwa kuma a yi mini salade na fruits” “In sha Allah auta, Allah ya tsare ki ya maido mini ke lafiya” “Amin Momy ” na amsa ina mai ɗaura niƙaf a fuskata kafin na fita harabar gidanmu wacce take ɗauke da shuke-shuke gwanin sha'awa.Da sallama na ƙarasa wurinsa ina mai buɗe baya na zauna,shi kuma ya shiga ya yi wa motar key. Muna hawa babban titi na ciro wayata na saka ta silence ,sai kuma na shiga gallery tare da danna kundin da nake ajiye hotunansa.Kamar wacce ta zauce haka nake kallon sajensa wanda ya haɗe da dogon gemunsa mai cikar gargasa baƙa ƙirin sai ɗaiɗaiku daga tsakiya da suka fitar da fari.Idona ya ciko da ruwan hawaye ina jin kuma wani murmushi na sauko mini wanda ba komai ya haifar da shi ba sai zuciyata da ta raya mini ‘ saura ƙiris ki cimma burinki’ Tsayawar da motar ta yi shi ya fargar da ni mun kawo,a hankali na buɗe murfin motar na fita wanda hakan yayi daidai da tahowar motarsa.Haka na yi tsaye ina bin motar da ido har ta tsaya inda malamai ke ajiye motocinsu,ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya fito.Kamar kullum yau ma sanye yake cikin fararen kaya sai ya ɗora alkyabar nan da malaman Saudiya ke sakawa,ita kuma baƙa ce haka ma hiramin kansa baƙi ne yayin da gilashinsa kuma ya kasance fari.Da sauri na ɗauke dubana daga gare shi na tunkari ajinmu zuciyata na dokawa,ina yin sallama ƴan matan ajin waɗanda suka zo duk suka juyo yayin da Mujahida ta wani zo da sauri ta rungume ni tare da yi mini raɗa a kunne wacce ta ƙara tsananta bugun zuciyata. Ta janye daga jikina tana dariya,na riƙo hannunta ina mai cewa “wai da gaske? ” “Wallahi kuwa ni ma yanzu da na je can ofishin shugaban makaranta na ji ana zancen” ta bani amsa. Na ce “amma kuma ba a yi sanarwa ba” Ta ce “ƙila sun canza tsari” Daga haka na je na zauna ,kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na yi sukuku duk hirar da Mujahida ke yi mini ta yadda bikin gidansu zai kasance haka-haka nake jin ta a haka har ajin ya cika.Ƙarfe takwas na bugawa kuma malaminmu ya shigo da sallama,bayan mun amsa sai ya zauna yana fuskantarmu kafin ya fara da cewa “yau za a fara zana jarabawa, binciken karatun Alkur'ani shi ne farko waɗanda ba su da gyara da yawa iya su kaɗai ne za su tafi aji na gaba wanda ya kasance ajin ƙarshe” Malam na gama wannan jawabin Mujahida ta kalle ni tana murmushi ta ce “yanzu kin yarda?” Na ce “ƙawata tsoro nake ji” Ta ja tsaki ƙasa-ƙasa kafin ta ce “na me kuma? Bayan duk lokacin da kika ɗauka kina burin ganin wannan lokacin? Ko dai kin daina sonsa?” Na dube ta da sauri ina mai cewa “na daina? Kuma kika ganni a raye” Ta ɗan bangaje ni tana dariya,kafin kuma duk mu nutsu saboda buga teburi da malam ya yi alamun a nutsu.Bai wani ɓata lokaci ba kuwa ya soma binciken karatun,kasancewar da tsarin ABCD aka bi wannan yasa har aka fita shan iska ba a kawo sunana ba. Muna fitowa Mujahida ta ce “ni kam Khadeeja na tambaye ki,yanzu in mun gama jarabawa muka shiga ajin ƙarshe wace kalma ce ta farko da za ki furtawa Sheikh Rayyadeen?” Na yi ɗan murmushi kafin na ce “to ai kin bari ki ga in mun ci exam ɗin ko?” Ta ce “na ma san za mu ci ai” “To Allah yasa” “Amin! Ina jinki me za ki ce masa?” “Zan faɗa masa ina sonsa fiye da rayuw...” sauran maganar ce ta maƙale mini a maƙoshi sakamakon ido huɗu da muka yi da Sheikh Rayyadeen duk da yana ɗan nesa da ni amma kallon da ya yi mini kamar mai nuni ne da ya ji abin da na furta,wani abin mamaki kuma sai na kasa ɗauke idona daga cikin nasa ɗin yayin da shi kuma ya fara tunkaro inda muke.Yana dab da isowa na ji Mujahida na cewa “kamar fa wurinmu zai zo” furicinta ya ida hautsana cikina kawai na yi baya da mugun sauri na koma cikin aji. “Khadeeja” na ji Malam Ibrahim ya furta,na juyo da sauri ina mai cewa “ka yi haƙuri malam ” “Bai komai kin ga dama ina ta son yi miki magana,har yanzu ba ki gama tunanin ba ?” Cike da kunyar abin da zan faɗa masa na ɗan kawar da kai gefe na ce “shi so abu ne da ke da alaƙa da zuciya...” shiru na yi saboda lura da inuwar mutum a bakin ƙofa. “Sheikh !”malam Ibrahim ya faɗa da ƙarfi muryarsa na fitar da amon tsoro.Kamar wacce aka yi wa allurar hauka haka na ruga a guje domin na fita,ina dab na kai gare shi na ji wani abu lummm ya disashe ganina.Kan ƙirjinsa na tsinci kaina wanda hakan ya yi daidai da tsayawar bugun zuciyata,ban sani ba suma ne na yi ko kuwa mene ne oho abin da na sani shi ne kawai bayan na dawo hayyacina na samu kaina a can wani wuri da aka ware domin malamai su huta. Zaune na yi ina kallon ɗakin ina jin kaina na ɗan sara mini,na yi tunanin ni ɗaya ce a wurin sai da Mujahida ta shigo ne da sallama na ji an amsa mata daga can bayana.Da wani matsanancin sauri na juya idona kuwa ya sauka cikin nasa,yanzu babu gilashi a fuskarsa wanda hakan ya ƙara tona asirin kyawun manyan fararen idonsa.Wannan karon kasa jurewa na yi kawai sai na yi juyo kaina tare da sunne shi, Mujahida ta ƙarasa ta miƙa masa gorar ruwa. Murya cike da nutsuwa ya ce “kuna iya tafiya” Sai ta zo ta kama hannuna ta miƙar da ni tsaye,sai da muka kai bakin ƙofar fita sannan na juyo na saci kallonsa wannan karon idonsa a lumshe suke ya ɗaga gorar ruwan yana sha har suna ɗiga a gemunsa wanda hakan ya nuna a matuƙar buƙace yake da su. Muna fitowa Mujahida ke cewa “yau na ga ikon Allah kin ga yadda ki ka sandare a jikin Sheikh Rayyadeen? Kamar mai cutar sanƙarau,wajen mu huɗu muka ɗauke ki zuwa ajin malamai bawan Allah shi kuwa Sheikh sai hankalinsa ya tashi shi ne ya tsaya kanki yana ta yi miki karatu har sai da numfashinki ya dawo normal ” Tun da ta fara magana nake kallonta amma ban ce komai ba a haka muka ƙarasa can ajinmu.Yadda duk suka zubo mini idonsu ya saka na ji duk na tsargu,hatta shi kansa malam Ibrahim kallon nawa yake yi.Zaune na yi kawai,ina sauraren yadda yake bincikar karatun sauran ɗalibai tuni ma an wuce sunana.Kwance na yi jikin table na lumshe idona nan take hoton yadda na faɗa jikin Sheikh ya shigo tunanina,yadda ya wani riƙo ni da mugun ƙarfi da hannuwansa masu taushi duk ina tune daga nan ban tuna komai ba.Ina a haka har lokacin tashi yayi muka fito,sai a lokacin kuma na tuna babu niƙaf a fuskata. “Mujahida ina niƙaf ɗina?” na tambaye ta ina mai kamo hannunta.Ta ce “oho ni ma ban sani ba,ko ƙila tana can ajin malamai” Ban ƙara ce mata komai ba haka muka nufi wurin da ake cin abinci,gefe kawai na zauna har ta gama ci muka fito zuwa masjid na mata wanda yake babba ne akwai kuma banɗakuna.Sai da muka yi alwala kafin mu shiga mu zauna,saboda na ture tunaninsa daga cikin kwanyata na ɗauko hirar bikin gidansu nan fa muka ta zantawa muna dariya.Lokacin sallah na gabatowa masjid ɗin ya soma cika,kafin kuma mu miƙe mu fara daidaita sahu.Yau ma Sheikh Rayyadeen ne ya bamu sallah,har aka gama idona na lumshe don ji na yi ƙira'arsa ta yau ta fi ta kullum daɗi.Bayan mun gama kwantawa na yi domin na rumtsa kafin lokacin shiga aji yayi. Ban san iya lokacin da na ɗauka ina hutawa ba amma ko da na tashi na hangi Mujahida ita ma tana baccin.Fita na yi na shiga banɗaki bayan na yi addu'a,ko ina tsaf yake babu datti don har wanka ma wasu na yi amma ni dai ban taɓa yi ba in ba yau da nake jin zafi na rufe ni ba. Wankan na yi na ɗaura alwala na mayar da kayana kafin na fito,fitowar tawa ta yi daidai da fitowar Mujahida ita ma cikin kiɗima take cewa “ƙarfe uku ta buga fa har da minti wajen biyar bari na yi alwala kawai” Na ce “da yake da na tashi ban duba lokaci ba”ciki na shiga na fiddo mai na shafa da turare sannan na ɗauko jakakunanmu na fito na tsaya.Tana fitowa na miƙa mata tata kafin mu wuce aji, Allah yayi sa'a ma Malam bai shiga ba.Ko da ya shigo kuma sai aka raba mana takardu muka zana jarabawa wacce ta ƙunshi abubuwa da dama,ba mu yi awa ɗaya ba kuma duk aka lashe amshe saboda lokacin sallah da ya yi ina ta jiran jin muryar abincin ruhi amma sai na ji ta wani malami daban.Bayan mun dawo aka ƙara bamu muka ƙarasa duk wanda ya ida sai ya fita wannan yasa da na gama na fito na ciro wayata na soma lalubo wayar direba amma a kashe. Ji na yi kamar na mutu tsabar takaici,haka na yi ta tafiya har na fita daga cikin makarantar ga shi fuskata a buɗe mutane sai kallona suke yi ga abin hawa ya yi wuyar samu.Abinka da ƴar Daddy kawai sai na ji hawaye sun cika mini ido,ina nan tsaye na ga motar gidanmu.A gabana ya tsaya tare fitowa ya buɗe mini murfi yana bani haƙuri kan ya manta ne bai taho da wuri ba.Ji na yi takaici ya ƙara rufe ni kukan da nake ta riƙo ya kubce mini a hankali na fara magana ba cikin hayaniya ba,“ta yaya mutum zai manta da haƙin da ya rataya a wuyansa? Dama ana manta aikin wajibi ne?” Ya haɗe hannuwansa biyu yana bani haƙuri,ban ƙara cewa komai ba na shiga na zauna ina shafar hawaye.Ina ɗaga kai na hangi Sheikh Rayyadeen a tsaye kuma da dukkan alamu ya ga komai don idonsa na kan motarmu ne,zuciyata ce na ji tana bugawa a haka dai ya ja mu zuwa gida. Ina shiga yadda na ga an cika dianing da kayan lambu da na motsa baki na ji a raina Daddy zai dawo sai dai falon tsit yake.Ina shirin nufar ɗakina na ji tambaya daga sama “ina niƙaf ɗinki?” muryar Daddy ce ,cak na tsaya ina kallonsa yana cikin shiga ta manyan kaya har da hulla ya ɗora.Ban basa amsar tambayar ba sai nufarsa na yi na je na rungume shi ina kukan farin cikin ganinsa. Ya tallabo fuskata yana goge mini hawayen kafin ya ce “Ummita ba na hana ki fita babu niƙafi ba? ” Na kwaɓe baki na ce “ai da zan fita na tafi da ita faɗuwa ta yi ban sani ba” “Ta ya ta faɗi har ba ki sani ba?” shiru na yi ban basa amsa ba,sai kuma can na canza akalar zancen “Daddy shi ne ba ka sanar da ni za ka dawo ba” “Na cewa Momynki ta sanar da ke,kenan ba ta faɗa miki ba?” Na turo baki gaba na ce “Daddy ai ka san Momy na kishina so take ta fara ganinka kafin ni shi yasa ta ƙi faɗa mini” Yayi murmushi mai ɗan sauti kafin ya ce “ƙila tana tsoron ki ƙi zuwa makaranta ne shi yasa” “Da dukkan alamu gulmata ake yi ƴa da uba” Momy ta faɗa tana mai fitowa daga ɗakinta ta saka wani rantsatsen less,dariya kawai na yi na wuce can ɗakina da ke hawa na farko. Uniform ɗin na cire na shiga wanka,a gaggauce na shirya cikin doguwar riga ta atamfa.Ko da na fito tuni Daddy na zaune yana addu'a saboda gabatowar lokacin shan ruwa,ni ma kujera na ja na zauna na fara nawa addu'o'in idona na lumshe nake roƙon Allah ya mallaka mini Sheikh Rayyadeen matsayin miji. ★SHEIKH RAYYADEEN Matashin malami ne wanda har yanzu yake cikin ganiyar samartaka,duk da shekarunsa sun ɗan ja amma fatar jikinsa ba ta nuna hakan ba.Shekarunsa arba'in da ɗaya a duniya yana dab da cika da biyu,fari ne sol yana da ƴar ƙiba amma ba sosai ba.Shi ɗin ya fito daga ƙabilu biyu,mahaifinsa kanuri ne ɗan asalin garin Diffa da ke nan ƙasar Nijar yayin da Mahaifiyarsa ita kuma ta kasance Balarabar Nijar ce suna rayuwa a babban birnin Yamai. Wannan yasa kyawunsa ya fito da wani fasali na daban,wanda hatta shi da kansa ya san shi kyakkyawa ne don yana ɗaya daga cikin abin da yasa mata ke tururuwa suna kawo masa tayin soyayya amma bai karɓa a bisa wani dalili nasa da ya ɓoyewa kansa. Malamta kusan gadon gidansu ne don kusan kowa yana da ilimin addini,sai dai banbancinsu da shi kawai ita ce aƙida duk da tun farko karatun allo ya yi amma daga ƙarshe da ya canza akalarsa zuwa karatun habsi wannan kuma ya samo asali ne saboda keta ƙasashen Larabawa da ya yi ya ƙara samun gogewa ta fanni daban-daban. Shi ne da kansa ya buɗe makarantar NOOR-RULLAH sannan kuma ya zuba malamai daban-daban ya kuma bai wa wani matsayin jagoranci yayin da shi kuma ya zo a matsayin malami.In banda mahaifiyarsa babu wata halitta da ta san sirrinsa,komai zai yi yana ɓoyewa bai son bayyanawa. Yana ɗaya daga cikin tabi'unsa shi ne baiwa sirri da amana muhimmanci,yana son turare saboda mutum ne mai musulmar tsabta.Ya tsani yawan surutu,bai cika son shishigi ba wannan yasa kusan bai da abokai barkatai sai dai in na karatu wannan kenan; Bayan ya gama haɗa komai ya mayar da komai kan fasali sai ya ɗauki key ɗin motarsa ya fito.Kusan makarantar ta yi tsit saboda lokacin tashi tuni ya kusa,a hankali yake driving lokaci zuwa lokaci fuskarta na faɗo masa a rai da kuma irin yadda ta yi shure-shure da yana yi mata karatu,yadda take kuka tana ƙanƙame shi gaban ɗaliban da yasa suka kai ta can.Ya ɗan ja tsuki yana jin wani irin takaicin yarinyar da ya ji suna kira da Khadeeja,kamar mahaukaci haka shi kaɗai ya soma yin magana “ni da ba haka Ammyna take ba,ban ma san wane ne ya zaɓa mata suna mafi daraja ba” ya ƙara jan wani tsaki yana mai karyar hancin motarsa tare da yin Horne,babu jimawa aka buɗe ƙaton get ɗin ya shiga a hankali ya je ya parker motar ya fito. Tun kafin ya shiga falon yake jin masifar Grand-Maa ,yana yin sallama ta ja baki ta yi shiru tana mai cewa “to ga ustazu nan” Ammy wacce ke tsaye kanta a sukunye ta ja numfashin samun ƴanci tare da ɗagowa ta dubi Sheikh da ya yi tsaye ransa na ɗan susa, Ammy ta yi masa alama da kar ya ce komai haka ya daure ya gaishe da Grand-Maa cikin sakin fuska ta ce “ustazu sannu da zuwa ya na ga ranka duk a dagule ko yau ɗin ma ka samu wasiƙar soyayya daga shashun ƴan mata?” Ya ɗan murmusa ya ce “Grand-Maa ke kullum ba ki rasa abin dariya,ke da kin san ban ko sakin fuska ta ya za a kawo mini wasiƙa?” Tsakiyar idonsa ta kalla tare da yin shiru,tun yana jiran ta ce wani abu har ya juya ya kamo hannun Ammy ya ja ta can sashensu.Suna shiga ta ce “duk abin da ka ga Grand-Maa na yi tsufa ne sheikh Rayyadeen,kar ka taɓa damuwa” Ya ce “haba Ammy ta ya ba zan damu ba alhalin tana yi miki abubuwan da suke sosa mini rai” Ammy ta ɓata fuska ta ce “tun da ta haifa mini miji ina da wata ne? Yadda kake mugun jina a zuciyarka haka shi ma Abih ɗinka ke son mahaifiyarsa,ko za ka ji daɗi in matarka ta yi ba daidai ba in na yi mata faɗa sai ɗanka ya zo shigar mata?” Ya marairaice fuska yana mai cewa “haba dai Ammy ta ya ma zan auro matar da za ta raina ki?” Ta yi ƴar dariya tana mai cewa “to ai misali ne na buga maka,kuma ma ma fi akasarin ustazan yanzu matansu duk shegiyar tsiwa ce da su da sangarta ka ga kuwa ni ba zan juri na ga ba a kula mini da kai yadda ya kamata ba” Bai san dalili ba haka kawai fuskar Khadeeja ta faɗo masa a rai,ya wani tamke fuska yana cewa “ni ma na tsane ta Ammy,ba ki ga yadda ta ɓare baki tana kuka ba kawai daga direba ya jinkirta zuwa ya ɗauke ta” “Wace ce?” Ammy ta tambaya,sai Sheikh Rayyadeen yayi tsuru-tsuru kamar wani ƙaramin yaro.Shi sam bai farga da abin da ya yi ba sai yanzu,cike da jin nauyi yayi saurin nufar step yana hawa bibbiyu don tserewa kallon tuhumar da Ammy ke yi masa.Ita kuwa ta ɗaga murya tana mai cewa “in ka yi wanka ka fito da wuri don yau a part ɗina za mu sha ruwa” ya tsaya cak tare da juyowa ya kalle ta,ya san dalilinta na yin haka wato so take yi ta yi masa tambayoyi game da yarinyar da yayi suɓutar baki ya yi maganarta..... [11/12 11:59] MRS SADAUKI: *MAFARKI*🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 02 Yana shiga ɗakinsa ya wuce can bedroom ,kan bed ya haye yana tunanin me zai cewa Ammy shi da tuni ya ajiye azuminsa a bisa larurarsa da ta motsa .Ji yayi ya ƙara jin tsanar Khadeeja saboda a kanta zai yi wa Ammy ƙarya ya je su yi buɗa baki tare,don bai ji zai iya sanar mata ya aje azumin ba duk da cewa kuwa bayan ya sha ruwan babu wani abu da ya ƙara sakawa bakinsa.Ya miƙe dakyar ya rage kayan jikinsa sannan ya shiga toilet,wanka yayi haɗi da alwala da ya fito jallabiya ya saka ya fesa turare kafin ya sauka ya nufi can falon Ammy,yayi sallama ta amsa sai faman haɗa Lipton take yi a kofi biyu. Gefenta ya zauna tare da yin shiru,ta ɗan dube shi kafin ta ce “yau ba za ka yi addu'o'in ba? Saura ƙiris lokaci ya cika” ya ɗan murmusa kafin ya soma yin istigfar“Ya Allah ka yafe mini a bisa kuskuren da na yi, sannan ka kawo mini sauƙin wannan larrurar da nake fama da ita , in aure bai cikin ƙaddarar da shimfiɗa mini Ya Rabb ka cire mini sha'awa gaba ɗaya” Tamkar Ammy ta san abin da yake ransa sai cewa ta yi ,“Allah dai ya nuna mini aurenka Sheikh Rayyadeen ɗina” murya can ƙasan moƙoshi ya amsa da “amin!” amma fa tuni ya ji a ransa kawai yana cikin mutanen da Allah ya jarabta da hanawa aure .Ana yin kiran sallah suka fara buɗa bakin har suka kammala shi ya wuce masjid ita kuma ta miƙe ta yi sallarta a nan. Sai bayan sallar isha'i sannan ya dawo gida , lokacin tuni ahalin gidan duk sun hallara falo domin cin abincin dare kamar yadda tsarin yake. A mutumce duk suka gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska yana mai tambayar Aliya,“me yasa yau ba ki je makaranta ba?” Ta sunkuye kai kafin ta ce “na tafi can babban gida ne ” wato gidan kakarta ta wajen uwa tana rufe bakinta Mama wacce ta kasance ƙishiyar Ammy ta yi caraf ta ce “ni ce na aike ta” Ya dube ta kafin ya ce “amma ai da bari kika yi sai ranar da babu makaranta Mama” Ta ɗan washe baki kafin ta ce “gaba za a kiyaye” Abba wanda yake fitowa daga ɗakinsa duk ya ji abin da suke tattauna wa,har ƙasan ransa yake jin daɗin yadda ahalinsa ke mu'amulantar junansu amma duk da haka yana jin babu daɗi in ya tuna wani sa'in Grand-Maa na yin ƴar tsama da babban ɗansa mafi soyuwa a kaf ƴaƴan nasa. Da sallama ya iso wurin,duk ƴar rige-rigen gaishe shi suka fara in ka cire Sheikh Rayyadeen da ya miƙe tsaye yana mai zuwa gun Abban ya amsa masa sallamar tasa tare da miƙa masa hannu suka yi musafaha. Grand-Maa wacce ke zaune kan kujera ta ja tsuki tana mai cewa “in ba zuwan ƙarshen zamani ba da lalacewa ta ina ɗa zai tunkari ubansa ya miƙa masa hannu suna gaisawa sai ka ce wasu turawa,in kuma ka yi magana a ce ma ai shi ma addini ne” Abba ne ya tanka ta don shi Sheikh ko kallon inda take bai yi ba. “Maa wannan fa ba wani abu ba ne,ya ƙarfin jikin naki?” Abba ya tambaye ta cike da kulawa. Kamar wata ƙaramar yarinya haka ta kwaɓe baki tana kukan dole haɗi matso ƙwalla.“Ta ya zan ji sauƙi alhalin kullum a gidan nan ni ce mai laifi,ka ga haka ɗazu uwarsa ta hana ni abinci wai ya kamata na dinga yin azumi tun da ban wani tsufa ba” Abba ya dubi Ammy ransa a ɗan ɓace,ita kuma baiwar Allah sai ta fara ƙoƙarin kare kanta. “Abban yara wallahi ban faɗa da wata manufa ba,gani na yi tun safe ba ta ci komai ba sai ruwan shayi shi ne na ce inda ma azumi ta yi ya fi ta zauna da yunwar nan ” “Khadi a gidan nan wa yake sayen abinci?” Abba ya tambaye ta,idonta suka ciko da ƙwalla murya na ɗan rawa ta ce “kai ne” “A kaf gidan nan wa yake da iko a kaina yayi mini faɗa har duka ma in ta kama?” Ta basa amsa da “Grand-Maa” “A ƙarƙashin wa kike a gidan nan?” Kafin ta amsa masa tambayar Sheikh Rayyadeen ya tari numfashinta ,cike da nutsuwa ya ce “Abba don Allah ku bar maganar girma da ikon nan,cin abinci ya tara mu a nan amma kuma kuna shirin saka abincin ya fita ranmu ” Abba ya ja numfashi tare da kawar da kai, Grand-Maa ta harari Sheikh kamar idonta za su faɗo yayin da ta yi wa Ammy mugun kallo sai dai suna haɗa ido da Mama sai ta sha jinin jikinta.Duk Sheikh na kallon komai ,har zuwa yanzu ya rasa dalilin da yasa Grand-Maa ke shakkar Mama amma kuma ta tsani mahaifiyarsa. Ammy ce ta zuba wa kowa kamar yadda tsarin yake ranar girkinka kaina za ka yi haka. Sheikh ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce “Aliya ke sai yaushe ne za ki fara taya iyayenmu aiki? Ko sai an kai ki gidanki ba ki iya komai ba?” Duk sai suka kalle ta,Aliyu wanda ya kasance Yayanta uwarsu guda sai cewa yayi “wai wannan ce za ta yi girki mu ci? Allah ya tsari gawa da dariya” Ammy ta yi ƴar dariya ta ce “Gadanga kar fa ka zo kana santi ” Ya ce “haba dai Ammy wannan yarinyar ce za ta yi abinci mu ci? Ku dai barta da kwalliya da saka jan baki” Ammy ta ce “in sha Allah duk ranar weekend tare da ita za mu dinga shiga kitchen ,zan sa kuma Saude ta koya miki girke-girken gargajiya” Grand-Maa ta yi caraf ta ce “to sannu ƴar boko,ai gara na gargajiyar kan uwar fulawar da kike bamu kullum muna ci” Ammy ta ce “yi haƙuri Ammy in sha Allah za a dinga yi miki girkinki daban,sai ki dinga faɗar abin da kike so” Mama ta ce “haba dai Khadi wasa fa Grand-Maa ke yi miki amma tana son abubuwan da suka shafi fulawa ko Maa?” ta ƙarashe faɗa tana mai tsura mata ido, Grand-Maa duk da ranta ya ɓace haka ta daure ta yi murmushin yaƙe, Sheikh ya tsure ta da ido yana nazarinta kafin kuma ya ture plate ɗin gabansa ya ce “sai da safenku ” “Tun yanzu za ka kwanta?” Ammy ta tambaye shi,sanin dalilin da yasa take tambayar tasa yasa ya ce “ban jin daɗin jikina ne Ammy,yau na gaji sosai” “To ka sha maganinka kafin ka kwanta,in na tashi zan shiga na duba ka” Ammy ta faɗa cike da kulawa. Ya ce “to Ammyna” sai yayi gaba,Abba ya dube ta ita kuma ta sunne kai tana jin fa ita ba ta ga dalilin da zai sa ta bar nunawa ɗanta kulawa ba.Duk shekarunsa ita a yaro take ganinsa,sauran ne suka tashi Aliyu da Aliya sai wurin ya yi saura Abba, Grand-Maa da Mama da Ammy. “Mahmuda ya kamata ka yi wa matarka faɗa,shishigin da take yi wa mai gemu(cewa da Sheikh Rayyadeen) ya fara yin yawa,yanzu mene ne na tafiya duba shi? Ƙaramin yaro ne da za ta shayar ko me ? ”wannan ƙorafin na Grand-Maa ya fi shuren masaki da ta yi shi,don haka ba wani baƙon abu ba ne gun Ammy shi yasa ma ba ta wani damu ba. Mama ce ta amsa mata madadin shi Abban,ta ce “Grand-Maa kin san tsakanin uwa da ɗa sai Allah,kamar ke ce da Abban yara kin ga duk da ya tsufa da ƴaƴansa haka wani zubin kike basa kulawa kamar ƙaramin yaro,in ba ki manta ba in ya jinkirta zuwa har cewa kike a kira miki shi a waya” Cike da jin haushin katsalandan ɗin da take yi mata a lammuranta Grand-Maa ta ce “amma ai ni tsohuwa ce,ita kuma fa ba ki da sauran ƙurciyarta” Mama ta ce “to mene ne aibu a ciki?” Idon Grand-Maa ma suka kaɗa suka yi ja tsabar takaici,daga ƙarshe ta miƙe ta bar wurin.Mama ta ita ma ta miƙe da sauri tana cewa “ku jira kar dai a ce fushi Maa ta yi da ni ” sai kuma ta tafi da sauri,tana dab da shiga ɗakinta Mama ta ƙaraso tana mai cewa “wane sabon abu ne kuma kika tsiro Maa?” Ta juyo cike da takaici ta ce “Ramma ki fita daga idona na rufe” Mama ta zo ta ida tura Maa cikin ɗakin ita ma ta shiga ta dantse ƙofar kafin ta ce “me kike nufi? Kar dai ki ce mini zuciyar ƙurciya Sheikh Rayyadeen take so? Ke yanzu ba ki jin kunya cewa jikanki kike so? Wannan kuma wane irin salon tsafi ne?” Grand-Maa ba ta bata amsa ba,sai shaƙe wuyan Mama da ta yi tana wani juya idonta suka rikiɗe kamar garwashin wuta yayin da akaifunta suka ƙara tsayi zaƙo-zaƙo. Mama ta fiddo nata kayan aikin,wata ƴar siririyar tsutsa ce da ke cikin jijiyar wuyanta tana fitowa idon Grand-Maa ta cabka,babu shiri kuwa ta saki wuyan Mama ta yi baya tana dafe gun. Mama ta shafi wuyanta tsutsar ta koma kafin ta ce “har abada ba zan bari ki cutar da Sheikh ba” Ita kuwa Grand-Maa sai cewa ta yi “da ni da ke shege ka fasa” ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta fice,ko da ta koma can falo tuni kowa ya watse. Sheikh Rayyadeen na zuwa part ɗinsa sai ya shiga toilet ya haɗa ruwan wanka masu ɗumi ya shiga cikin bahon ya kwanta tare da ɗan lumshe idonsa.Wata irin kasala yake ji ga wani yanayi kamar wanda zazzaɓi zai damƙa,a duk lokacin da fuskar Khadeeja ta faɗo cikin magijin ganinsa sai ya ji wani abu ya tsarga masa wanda hakan yake ƙara hura wutar kasalar da ta aure shi.Dakyar ya fito ya ɗauro towel ya fito,yanayin ɗakin ya fara canzawa ya kunna na'urar ɗumama guri sannan ya tsane jikinsa tare da saka kayan bacci masu ɗan nauyi.Kan bed ya kwanta amma bai kashe fitila ba saboda sanin Ammy ta yi masa alƙawarin za ta zo ta duba shi. Babu jimawa kuwa ta buga ƙofa ya ce ta shigo,ta tura ƙofar da sallama da sauri shi kuma ya tashi zaune yana mai daɗa jan blanket ɗin sama yana rufe jikinsa. Tana zuwa gefen wuyansa ta taɓa ta ji da zafi,cikin muryar tausayi take cewa “jikinka da zazzaɓi shi ne ka yi wanka? Ka sha maganin da na baka?” Ido ya tsura mata na wani lokaci kafin ya girgiza kai,ta ce “ don me? Ai ko addini bai hana a sha maganin gargajiya ba,me yasa ba za ka sha ba tun da har ka ga na baka bai kamata ka yi sakaci da shi ba.A ina ka ajiye shi?” Ya shagwaɓe fuska kafin ya ce “Ammy ba fa abin da ke damuna kawai ɗan zazzaɓi ne” “Shi mugu da kake ganinsa wayo ne da shi,a sannu a hankali yake kama ka har ya damƙe ka duka” ta faɗa tare da soma duba inda za ta ga maganin. Can kuwa ta gansa,da kanta ta kaɗa madara sannan ta zuba maganin ta basa ya sha ba don ya so ba sai don yi mata biyayya.Yana gama sha ya koma ya kwanta yana mai lumshe ido,nan take kuma yadda Khadeeja ta faɗa ƙirjinsa a bisa kuskure ya faɗo masa,da sauri ya cije leɓe yana jin kamar ya ƙurma ihu . “Me sunan yarinyar ta ɗazu da ka fara yi mini magana?” ya tsinkayo muryar Ammy,a hankali ya ɗan buɗe idonsa da suka yi masa nauyi yana kallonta kafin ya mayar da su ya rufe ruf. “Deeni!” Ammy ta kira sunansa,wanda wannan sunayen ya kasance keɓaɓe ba ta kiransa da shi sai in tana son nuna masa shi ɗin yaro ne ƙarami a idonta har yanzu bai wuce ta yi masa duka ko kuma wani abu da uwa ce kawai za ta iya yi wa ɗanta shi. Kamar zai yi kuka ya ce “Ammy ba fa sonta nake yi ba” “Na sani,amma ai ita ce silar ciwonka ” “Wane ciwo kuma Ammy?” “Deeni ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce,kar ka manta ni na ɗauki cikinka na tsawon wata tara,na haife ka sannan na raine ka.Babu wani hali naka da ban sani ba,hatta Maa da ke kakarka ta gane da yau ka haɗu da wata budurwa sai ni ce ba zan fahimta ba?” Shiru ya yi kafin ya ce “Ammy na faɗa miki ba sonta nake yi ba,kawai tsautsayi ne yasa ta shigo hanyata” “Na ji ba ka sonta mene sunanta?” “Sunan mai darajata ne da ita” ya faɗa kamar zai fasa ihu,Ammy ta yi ɗan murmushi ta ce “takwarata ce kenan?” “Eh!” ya bata amsa,idon Ammy suka ciko da ƙwalla tana mai yin addu'a a zuciya ‘ Allah yasa wannan ɗin ita ce abokiyar rayuwarka’ sai kuma ta fice ta barsa cikin duniyar tunani. ★KHADEEJA Muna gaba buɗa baki na wuce sashena,sallar magarib na yi sannan na soma yin azkhar na maraice ina zaune kan sallaya lokacin isha'i yayi na miƙe na gabatar.Bayan na gama na yi wanka na saka kayan bacci pink riga da wando ne masu hulla,sai na ɗora ɗan madaidain hijabi a sama na fita zuwa falo.Soyayyen dankali na zauna na ci ina kallon Arewa24 da suke nuna shirin rayuwata,duk abin da jaruman ke yi sai nake hango kanmu ni da Sheikh wannan yasa na zauna ni ɗaya ina ta murmushi. “Ke lafiyarki?” na ji muryar Yaya Hamza,da sauri na nutsu ina mai cewa “lafiya lau Yaya Barka da shan ruwa ka ga Daddy? Yau ba ka zo muka yi buɗa baki tare ba halan gidansu Mujahida ka sha ruwa?” Ya ja dogon tsaki yana mai cewa “ke me yasa kin cika surutun tsiya ne,a yi mutum kamar Aku cacacaaa babu hutu sai zubo shi kike yi” Na turo baki na ce “ai Mujahida ta koya mini” ya banko mini harara kafin ya ce “ba Mujahid ba?” Na tuntsire da dariya kafin na ce “ka san kuwa haka ƙawata ta ce mini wai inda ma Yayanta Mujahid na aura shikenan mun yi masayar yayyu ” Ya ɗan murmusa kafin ya ɗan dungure mini kai ya ce “ina mai tabbatar miki da cikin sati biyu kacal zai maido ki gida saboda ya tsani surutu” Na sheƙe da dariya na ce “ai kuwa saurayina ma shi ma shiru-shiru yake kullum bakinsa a rufe kamar mai ciwon haƙori” Yaya Hamza ya shiga yin dariya kafin ya ce “Allah ya shirye ki auta,kullum har tambayar kaina nake ko wane bawan Allah zai auri shirmamar ƙanwata?” Na yi murmushi mai fiddo tsantsar farin cikin da ya fito daga zuciya sannan na basa amsa da “wani mai ilimi ne,mai nutsuwa, kyakkyawa ɗan gayu ,yana da cikar haiba da ƙwarjini.Bari na faɗa maka Yaya Hamza kaf makarantarmu kowa tsoronsa yake ji,hatta malamai fa ” sai kuma na tuntsire da dariya kafin na ci gaba da cewa “ɗazu fa malamin saura ƙiris zuciyarsa ta buga da Sheikh ya shigo ajinmu ” sai kuma na yi shiru ina tuna irin yadda ƙirjinmu ya haɗu da na juna. Kamar wacce aka tsikara sai kuma na miƙe na nufi ɗakina ba tare da na yi wa yaya Hamza sallama ba.Ina shiga kawai na haye bed tare da jawo pilow na ƙanƙame na soma yin hawaye tuna cewa babu tabbas ya karɓi soyayyata.Ba tare da na shirya yin bacci ba na ji wani abu mai kamar rumfa ya luluɓe ni,kawai kwatsam sai na tsinci kaina a duniyar mafarki sai dai ba irin mafarkin da mutane suke yi ba a'a nawa na daban ne. Cikin wani babban gida ne na tsinci kaina mai hoton ahali,ɗaya bayan ɗaya haka nake kallon hoton har idona ya sauka kan na Sheikh da na yi gaba kuma sai ya na ci karo da na wata mata,sosai suke kama da Sheikh tamkar ƴan biyu sai dai za ta girme masa.Ina shirin janye idona sai hoton ya soma yi mini magana. “Kar ki tafi ba ki ji labarina ba” tana faɗa mini haka sai kuma na ƙara tsintar kaina wani wurin,sai dai wannan tare nake da ita. “Ina ne nan?” na tambaye ta. Ta bani amsa da “maƙabartar rayayyu ce” “Rayayyu kuma?” “Eh! Ni ma saura ƙiris na bi ayarin waɗanda za a binne da ransu” ta bani amsa tana goge hawayen jini.Kafin ta ci gaba da cewa “ni mace ce mai addini,na taso gidan malamai duk da ba su suka haife ni ba amma a can na girma tun ina ƴar shekara uku a duniya ƙanwar Mamana ta ɗauke ni riƙo.A can gidan aka yi mini aure,sai dai ban taɓa haihuwa ba.Farkon matsalata ta soma ne a wata rana da na bincika wayar mijina na samu shaidar yana cin amanata shi da wata mace a waje,da na tunkare shi da zancen sam bai yi mini gardama ba ya karɓi laifinsa tare da neman yafiya ni ma sai na haƙura na yafe masa.Sai dai a bisa tsautsayi ko na ce ƙaddara,sai na ƙara duba wayar tasa na ga dai ashe har yanzu bai goge komai nata ba sai na je can facebook na binciko sunanta tare da following nata.Na ɗauki tsawon sati biyu ina bibiyar duk wani abu da za ta yi posting a page ɗinta amma ko sau ɗaya ban ga mijina yayi comments ba,duk da cewa mafi akasari hotunanta ne masu bayyana tsaraici.Kwatsam wata rana sai ta wallafa zancen fyaɗe na wata yarinya da aka tozarta,kawai sai na yi mata magana pc na ƙirƙiro zancen ƙarya na ce ni ma da ina yarinya an taɓa yi mini fyaɗe,daga nan ne muka fara gaisawa fa har ta kai da mun yi masayar lambobin juna muka soma yin WhatsApp.Wata rana sai ta shirya mana haɗuwa a wani gidan cin abinci haka na kwashi jiki na je,a fili har ta fi kyau kan a zahiri tabbas ta yi haɗuwar da duk wani namiji mai lafiya zai so ya kasance da ita,tuni kishi ya turnuƙe ni amma na daure muka gaisa aka gabatar mana da abin sha da kuma abin motsa baki bayan nan kowacce ta kama gabanta.A wannan daren ne na ga ta saka video ɗinta a status jikinta babu wata suturar kirki,haka na kalla na sake kallo da na ji ban gaji da kallo ba kawai sai na yi saving nata.Tsabar yadda ta shiga raina yasa duk hankalina ya tashi,maimakon na je gun mijina a'a sai na ji tamkar wani baƙin ruhi na zuga ni a haka na yi amfani da kaina na biya wa kaina buƙata wacce a zahiri ni ɗaya ce amma a baɗini akwai sheɗani a tare da ni ” tana kawowa nan sai kuma ta dafe mararta tana cije haƙora,ina shirin yi mata magana alarm wanda ke tashina sallar dare ya soma ruri,na buɗe idona da suka yi mini nauyi kafin na miƙe dakyar na shiga toilet.Kan WC na hau na soma yin fitsari amma kamar abin tsiya haka na ji wani baccin na ƙara jana daga zaune.... [11/12 11:59] MRS SADAUKI: *MAFARKI*🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 03 Da sauri na kamo ta,sai ta ɗago ta dube ni da idonta da suka soma canza launi suna komawa kore kamar na maciji.Murya na ɗan rawa ta ci gaba da cewa “tun da nake ban taɓa yin auren hannu ba sai wannan ranar,abin mamaki kuma shi ne gamsuwar da na samu ta sha banban da irin wacce nake samu a wurin mijina sam ban fahimci abin da yake faru da ni ba.Sai na yi istigfari har da ma azumi uku ina ɗauke da na huɗun ne kwatsam ta aiko mini video a WhatsApp wannan karon babu sutura ko ɗaya a jikinta ko ɗan kamfai,fuskarta kuwa duk ta ɓace da dukkan alamu sun gama mu'amula ne da namiji sai ta yi tabi'arsu ta ƴan kwalta.In taƙaice miki dai nan take azumina ya zama gurgu,na mance da istigfarin da na yi na ƙara biyawa kaina buƙata a karo na biyu.Sai bayan na gama ne na yi ta kuka tare da goge video na kuma ja mata kunne kar ta sake in kuma ta ƙara zan yi blocking nata.Ta bani haƙuri muka wuce wurin,sai dai ba a wani ɗauki lokaci ba kamar abin tsafi haka na ƙara tsintar videon a wayata alhalin na goge ta.Sai kuma na sake komawa ruwa duk da kuwa na yi ƙoƙarin hana kaina ƙara kallon videaon amma yadda kika san akwai wani baƙin ruhi mai zuga ni haka na buɗe na kalla .Na riga da na hallaka,karuwar mijina tuni ta yi galaba a kaina don har da link ɗin groupe ɗinta ta aiko mini na shiga ba tare da na san wannan shi ne takun farkona a cikin duniyar matsafa.Duka-duka mu bakwai ne cikin groupe ɗin,babu wata hira da muke yi sai ta sex da kuma videon batsa wani sa'in ma video call muke yi muna biya wa juna buƙata,a cikin irin wannan shiriritar ce muka fara yin gasar mazajen bogi ta hanyoyin biyawa juna buƙata da kanmu.Wata daga cikinmu ta bani wani abu wanda ba zan ce miki mene ne ba,ta ƙalubalance ni muddin na yi amfani da shi matsayin mijin tarayya na kwana ɗaya kacal to za ta bani 500k.Haka na yi ɗin duk da ina jinsa har cikin marata yana tokare ni haka na haƙura na cuci kaina akan kuɗi,yayin da su kuma suke tsaye a zahiri suna kallona.Bayan na gama kuwa ta bani kuɗin,ba tare da na san cewa duk don su ƙara kwaɗaita mini zama cikinsu ba ne mu ci gaba da sheƙewa” sai ta yi shiru tana mai ɗan lumshe idonta. Na ce “mijinki fa ya sani?” Kai ta girgiza mini kafin ta ci gaba da cewa “da na samu kuɗin dai na saya masa agogo sabuwa yayi murna sosai,ɓangaren auratayyarmu kuwa sai abubuwa suka canza na soma tsiro da abubuwan sheɗanci ina yi masa da sunan gamsar da shi,abin mamaki kuwa sosai yake jin daɗin haka ya kuma ƙara sona har yake mamakin yadda ban ƙyanƙyaminsa da nake kai bakina a wurin da yake bahaya” sai ta buɗe ido tana murmushi mai ciwo.Can ta ɗora da “wata rana kamar a MAFARKI haka na tsinci kaina wata duniya.Ƙawayen sharholiya suka ja ni wani gun don mu huta mu cashe,sai kuma tsari ya canza muka soma shiririta kafin kuma duk su tsaya cak suna masu haɗin baki su ce “lokaci yayi” duk sai suka zube ƙasa suka kuma roƙe ni na yi yadda suka yi ɗin,haka ni ma na zube gwiwana ƙasa ba tare da na san dalili ba.Babu jimawa wata tsohuwa ta bayyana,sanye take da baƙaƙen kaya,gashin kanta a buɗe yake wanda yayi fari ƙal,idonta kuwa sun shige sosai can cikin gurbi ko ƙyaftawa ba ta yi haka ta kafe ni da su tana kallona,ni kuwa zuciyata sai matsanancin bugawa take yi kamar zan mutuwa. Cikin masifa take yi wa sauran faɗa tana zaginsu don me yasa ba su samo wasu members dayawa ba alhalin ta faɗa musu wannan karon mutane sosai take so.Kafin kuma ta juya ga karuwar mijina wacce ita ce shugabar groupe ɗinmu,ta tozarta ta sannan ta ce “me yasa ba ki sanar da ita tun farko ba? ” ba ta iya cewa komai ba,sai tsohuwar ta dawo kaina tana mai tambaya ta “me sunan mahaifiyarki?” na shaida mata sai kawai ta rufe ido tana kiran sunan Mamana,babu jimawa na soma jin kukanta haɗi da kakari.Ko da na koma gida kiran farko da na samu shi ne don a sanar da ni mutuwar Mamana,tun daga wannan lokacin kuma na yi alƙawarin ko mutuwa zan yi ba zan yi musu biyayya ba kin ji kuma inda farkon wata izayar ta soma yanzu haka ina jin motsinta za ta kawo mini ziyara domin amsa mata tambayarta a karo na ƙarshe na yarda na yi wa baƙin ruhi hidima ko kuwa na zaɓi ta binne ni da raina kamar sauran da suka bijire” tana gama bani labarin na farka. Yadda na tsinci kaina a toilet yayi matuƙar bani mamaki,haka na yi tsarki na je kusan pampo na yi alwala.Da na fito na duba agogo sai na ga tuni lokacin sallar asubah ma ya yi,haka na yi nafila tare da farillar kafin na zauna ina lazumi ina kuma tunanin mafarkin da na yi. Bayan na gama sai na fita,ɗakin Momy na je na gaishe ta tare da tambayarta abin da za a yi na breakfast ta faɗa mini sai na wuce kitchen.Tare da taimakon ƴar aikinmu na haɗa komai , lokacin da na gama tuni ƙarfe bakwai da rabi ta gota.A gaggauce na je na yi wanka na yi shirin makaranta,abicina ma sai cikin kula na zuba shi na wuce direba ya kai ni. Ina sauka abu na farko da na fara yi shi ne duba inda yake parking motarsa,wurin wayam yake babu motar sai na ji babu daɗi.Haka na wuce ajinmu,bayan mun gaisa da Mujahida ne nake bata labarin mafarkin da na yi kafin na ƙara da cewa “ sosai fa na ji tsoro,kar ki so ki ga yadda na yi ta murna tare da yi wa Allah godiya da yasa mafarki ne” “Amma abin da mamaki yake,kuma duk da kin farka bayan kin koma wani baccin matar ta sake dawowa ta baki ci gaban labarin?” Mujahida ta tambaya. Na ja numfashi kafin na ce “shi ne abin da ya fi bani tsoro,kuma fa ina zaune cikin toilet.Haka kawai nake ji a raina wannan ba kawai MAFARKI ne ba” Ta ɗan bangaje ni ta ce “dalla can matsoraciya wa ya sani ma ko Film ne kika kalla kawai kin manta ne kin yi dubin mafarki ne” Na yi ƴar dariya ina mai cewa “in akwai wanda ya raina ni duniyar nan bayanki yake” ba ta kai ga cewa komai ba malam Ibrahim ya shigo.Abu na farko da ya ce mu yi shi ne raba mana takardun da zamu zana jarabawa haɗi questions ɗin. Haka muka soma yi,duk wanda ya gama sai ya kai masa.Ina kammalawa na miƙe na kai masa,sai ya ƙi karɓa tare da cewa “ya jikin naki?” “Alhamdullah!” na basa amsa tare da ajiye takardar kan teburi na fice.Idona na ƙara kaiwa wurin parking special amma har yanzu dai babu motarsa,haka kawai na ji hankalina ya tashi. Ina nan tsaye Mujahida ta fito tana mitar cewa ta gaji,ban kula ta ba sai ma zancen Sheikh da na ɗauko mata.“Yau mutumin bai zo ba Allah sa dai lafiya” “Wane mutum?” “Ke banza dubi babu motarsa” na faɗa tare da bangazarta. Ta ja tsaki tana cewa “uban ƴan takura za ki ce,ashe bai zo ba shi yasa na ji makarantar ko ina hayaniya” Na ɗan murmusa kafin na bata labarin abin da Yaya Hamza ya ce,sai da ta ci dariya kafin ta ce “kuma fa zamanku zai yi wuya kin ga dai shi bai son yawan magana,ke kuma ga ki kamar Akun kuturu” na dake ta na ce “ni ce Akun kuturun?” ita ma ta rama ta tabke ni sosai tare da rugawa tana cewa “eh ke ɗin” da gudu na bi ta don na rama ɗin wanda ya yi daidai da shigowar Sheikh Rayyadeen a ƙafa yake babu mota.Cak na tsaya ina mai kallon tsakiyar idonsa da suka yi ɗan ja,shi ne ya fara ɗauke kansa kafin ni kuma na juya masa baya ina dafe saitin zuciyata. Daga bayana na ji Mujahida na cewa “to sai ki juyo don kuwa tuni ya tafi da dukkan alamu dai bai da lafiya don na ga abin ƙarin ruwa a hannunsa” Na juyo ,na fara rama dukan da ta yi mini ina mai cewa “babu wani nan,so kike yi dai ki ɗaga mini hankali” “Wallahi gaske don me zan yi miki wannan wasar,kin ga waccan ita ce ƙanwarsa” Mujahida ta faɗa tana yi mini nuni da wata budurwa wacce za mu iya yin sa'anni ko kuma ta girme mini da kaɗan. “Amma ya na ganta ita baƙa?” “Oho ni za ki tambaya,bari in Sheikh ya kai ki gidansu sai ki tambaye ta” ta faɗa tare da yin gaba,na tsayar da ita ina mai cewa “na fa kawo abinci daga gida yana can aji” “Na sani ai,ruwa zan nemo” ta bani amsa,sai na take mata baya muka je ta samo ruwa muka dawo.Bayan kowa ya gama zana jarabawa muka shiga aji don cin abinci amma sam na kasa cin na kirki saboda tunanin abin da ke damun Sheikh .Wunin nan dai haka nan na yi shi duk babu daɗi,da na je gida ma haka sai da aka ga canji. Abu kamar wasa sai ga shi wajen kwana uku Sheikh bai ƙara takowa makaranta ba,ga shi kuwa tuni an kai mu aji na gaba wanda ya kasance ajinsa.Ga baƙunta ga kuma tunani sai duk suka taru suka ramar da ni,yau ta kama Lahadi bayan mun fito shan iska tsoffin ƴan ajin Sheikh suka yanke shawarar zuwa duba shi haka ɗaiɗaiku daga cikinmu mu ma muka runguɗa muka bi ayari kasancewar da ƙanwarsa a ajin wannan yasa ba mu da damuwa ta fannin sanin gidansu. Babu wani nisa sosai,tafiyar minti goma sha muka isa ƙaton gidan wanda ya ninka namu sau biyu.Tun da na ɗora ƙafa a ƙasar gidan jikina ya ɗau rawa zuciyata ta soma bugawa kamar za ta faɗo tsabar lugude. Ita ƙanwar tasa mai suna Aliya ita ta yi mana iso zuwa babban falon gidan,kan lafiyayyen capet duk muka zubo sai wasu su biyu ne wanda alamu ya nuna ƙawayen Aliyar ne suka hau kujeru. Babu jimawa ta sa aka fara kawo mana lemu mai sanyi,kafin ta ce “bari na je na kira shi” wani irin dam na ji zuciyata ta buga . Can kuma ta dawo ita da wata mata wacce kallo ɗaya na yi mata na gano inda Sheikh ya samo kyawunsa,wato daga gare ta ne.Cike da girmamawa duk muka shiga gaishe ta,ita kuma tana amsawa cikin kulawa kafin ta ce “ku taso ku ƙaraso” haka duk muka miƙe muka take mata baya,wani falon muka ƙara ratsawa kafin kuma ta ƙara kai mu can cikin wani.Ido na lumshe jin yadda duk ƙamshinsa ya cika ɗakin,sai da Mujahida ta ɗan bangaje ni sannan na buɗe idona sai na ga tuni har sun zauna sai ni ce a tsaye kamar haure .Jikina ne ya hau rawa saura ƙiris na faɗi Allah ya gyara na samu wuri na zauna, Ammy ɗin ce ta kira sunansa “Sheikh Rayyadeen? Tashi ga su nan sun shigo” Ta ƙasan ido na kalle shi,yana kwance kan kujera mai zaman mutum uku ya luluɓe da blanket.A hankali ya tashi ya zauna yana mai yi mana sallama,ni dai ban amsa ba sai ɗan kallon fuskarsa da na yi wacce ta ƙara yin haske . Ƴar rige-rigen yi masa ya jiki suke yi shi kuma yana amsawa,tare da tambayar sabbin fuskokin da bai sani ba su kuma suna yi masa bayani ɗaliban da aka kawo ne sabbin zuwa. A bisa tsautsa yi na ɗaga kai da niyyar satar kallonsa,karaf idonmu ya sarƙe cikin na juna da wani irin mugun sauri na sunne kai ina mai kama yatsuna ina wasa da zobena. Ammy wacce ke tsaye duk tana kallon komai,dama burinta bai wuce ta ga wacce ta jefa ɗanta cikin wannan halin ba.Amma don sake tabbatarwa sai cewa ta yi “ma sha Allah nan dukkanku ajinsa kuke ?” Cikin murna suka amsa da eh,Ammy ta ce “ina ga dai tun da shi malamin naku bai da lafiya ni zan je na ci gaba da koyar da ku” duk sai aka soma murna tare da nunawa eh ana so ta koya ɗin,ita kuwa Ammy sai cewa yi“ke ya sunanki?” “Sadiya” ta bata amsa tana wani sunne kai,na dube ta ina mai cewa a zuci ‘ kina da kunya amma shi ne kika haye kujera daga zuwa gidan mutane’ haka Ammy ta dinga tambayar sunaye har ta kawo kaina ta ce “ke kuma me sunanki?” Na ɗan dubi Sheikh kamar ba zan yi magana ba sai kuma na ce “Nana Khadeejatu” ina ganin lokacin da ya kawar da kai kamar na ambaci sunan kashi.Bayan ta gama jin sunayenmu cikin tsokana ta cewa Aliya “ke kuma fa?” duk sai aka sa dariya,nan dai ta fita Aliyar na take mata baya. Sheikh Rayyadeen kuwa tambayoyi ya soma yi wa ɗaliban nasa suna basa amsa yadda ajin ya kasance bayan tafiyarsa .Duk da kaina na sunkuye amma lokaci zuwa lokaci ina jin kaifin idonsa a kaina,a hankali na kai hannu na taɓa Mujahida ta juyo ta dube ni tana mai tambayar “ya dai?” “Ki tashi mu tafi” na furta kamar zan yi kuka,don wani irin yanayi ne nake ji yana ratsa ni ga kuma kallon Sheikh da nake ji a jikina.Hararar wasa ta yi mini tana shirin juyawa na ce “please ki zo mu fita waje to” kanzil ba ta ce mini ba sai ma yadda kusan kowa ya maido dubansa kaina sai na ji duk na tsargu,cikin ikon Allah Aliya ta sake shigo wa hannunta riƙe da faranti an yanka ƴaƴan fruits sai ta soma tsokanarsu tana cewa “yau dai za ku ci abinci a gidan malaminku duk wacce ta ƙi ci kuma bulala goma” hakan da ta yi ne yasa sai hankalinsu ya koma can. Uwar iya yi Sadiya wacce na lura kamar kanta na rawa sai cewa ta yi “duk wanda ya yi habaici dai a kasuwa ya san da wanda yake” ɗayar ce wacce suka hau kujera a ɗazu ta karɓe da cewa “ai ban so kika kula ta ba Diya ” Yadda suke raha a gabansa abin yayi matuƙar bani mamaki,ko da yake kawar da kai yayi gefe yana latsa waya.Ko kunya ba su ji haka wasu daga cikinsu suka sa hannu a faranti suna ɗauko fruit suna ci. Aka yi sallama, Ammy ce da tare da wani mai farar rigar likitoci.Gaishe shi aka fara yi kafin shi kuma ya tambayi jikin Sheikh ɗin kamar wanda bai son yin magana ya ce “alhamdullah!” Hannunsa ya kama don saka masa sabon tiyon ƙarin ruwa amma samun jijiya ya gagara sai sokarsa yake yi jini na zuba.Duk in ya tsake shi sai na rumtse ido don takaici,da na ji na kasa haƙuri ban san ina na samo jarumtar miƙewa ba na ce “kawo ka gani” Ba Sheikh ba alamun mamaki ne ya bayyana a fuskokin kowa,duk yadda kuwa Mujahida ta so riƙe mini ƙafa ina tuni har na isa gabansa na karɓe allurar .Sai kuma a lokacin na dawo hayyacina,yadda Sheikh Rayyadeen ya kafe ni da ido shi ya saka jikina soma rawa. Mahaifiyarsa ce ta matso tana cewa “bari kallonsa yi aikinki” sai da na ƙara kallon tsakiyar idonsa kafin na sunne kai,a cikin ledar magunguna na zaro safar hannu kafin a hankali hannu na yi mini rawa na soma jan hannun jallabiyarsa sama.Ɗaure damtsensa na yi gam ba a ɗauki lokaci ba kuwa jijiyarsa kore ta bayyana,da Bismillah na soka allurar ina mai ɗan ɗagowa na dube shi idonmu ya sarƙe cikin na juna kafin kuma ya kawar da kai gefe.Na ja numfashi ina mai kwance ɗaurin da na yi masa tare da cewa likitan “na nemo jijiyar” Ya saki ɗan murmushi kafin ya zo ya ƙarasa aikinsa,ni kuwa ji na yi ban iya zama cikin ɗakin na nufi ƙofar fita ina shirin ficewa muka yi kaure ni da wata,da sauri ta yi baya ni ma haka kafin kuma mu ɗago muna kallon juna.Zuciyata ce ta wani buga darammm sakamakon ganin fuskarta,ba kowa ba ce sai matar da ta zo mini jiya cikin mafarki..... [12/12 18:35] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 04 Da wani sauri na ƙara ja da baya ina mai ci gaba da kallon matar wacce idon nata suka ke kore kamar dai yadda na gani a mafarki.Ita kuwa ban sani ba ko ba ta gane ni ba ne oho,haka ta bi ta gabana ta ƙarasa shiga falon.Na bi bayanta da kallo sai dai kafin ta ida sa wurin Ammy ta zube nan tana wani abu kamar wacce ta aka yi wa allurar hauka.Duk aka kwashi salalami kafin Ammy ta zo tana kiran sunanta haɗi da jijiga ta,“Rashida? Rashida?” sai dai babu wani canji zai ma ƙara hauhawa ciwon yake,tuni ɗaliban suka fara fita a bisa umarnin Sheikh Rayyadeen da ya miƙe tsaye kamar ba shi ne ke yin ciwo ba.Duk kowa ya fita hatta likitan da ya zo yi masa magani,Mujahida ta zo ta kama hannuna amma kamar gunki haka na ƙi motsawa.Sheikh wanda ke tsaye ya zubo mini idonsa kafin cikin wata murya ya ce “fita” Na ɗan girgiza masa kai saboda wani furici da zuciyata ke jadadda mini ‘ Khadeeja ba banza ba ne Allah ya nuna miki matar nan a cikin mafarki ƙila ke ce za ki cece ta’ haka Mujahida ta fita ta bar ni saboda yadda Sheikh ke banko mana wani mugun kallo kamar idonsa za su faɗo. Daga nan inda nake tsaye na ce “a yi mata turaren habbatu sauda ” Ammy ta ɗago ta dube ni kafin ta cewa Sheikh “je ka ɗauko,ke kuma je ki nemo garwashi ” sai a lokacin kawai na fita zuwa can falo,babu kowa da dukkan alamu ɗaliban sun tafi. Waige-waige na fara don duba ina ne kitchen,kwatsam idona ya sauka kan hoton ahali shi ma sak irin yadda na gansa a mafarki ne.A hankali na soma takawa na isa gare shi,abu biyu ne suka ɗaure mini kai yadda na ga kaf mutanen cikin hoton an yi musu wani mugun ɗauri daidai wuyansu in aka cire Sheikh da kuma wata tsohuwa wacce nake kyautata zaton kakarsa ce. Hannu na kai na shafi hotonsa,ina taɓa na tsohuwar na ji wata murya a bayana. “Wace ce ke?” ita ce tambayar da aka yi mini cikin wata baƙar murya mai tarwatsa hankali.Da mugun sauri na juyo nan na yi arba da tsohuwar,ina shirin yin magana sai ga Aliya tana mai cewa “Grand-Maa tun ɗazu fa ke nake nema kin Rashida can ta zo babu lafiya” ta faɗa tana mai kama hannun wacce na ji ta kira Grand-Maa.Take musu baya na yi,su ke gaba wannan yasa suka rige ni shiga da wani mugun sauri na ga Grand-Maa ta fito tana tari kamar ranta zai fita. Wani kallo da ta yi mini da jajayen idonta kamar na tsohuwar mayya shi ya tsorata ni ,da gudu na baro wurin na kama hanyar fita daga gidan gaba ɗaya.Ko da na fito ƙofar gida sai na hangi Mujahida can gaba tana zaune kan dakali tana waya.Na ƙarasa ina mai zama kusa da ita,da sauri ta yi sallama ta kashe wayar kafin ta zuba mini na mujiya. “Me?” na tambaye ta. Ta waro ido ta ce “yaushe kika koyi ƙarfin hali Khadeeja? Kin ga kuwa yadda ran Sheikh ya ɓace amma ke oho ko a kwalar rigarki,kuma a haka ne kike so ya amince ya karɓi soyayyarki” Na ce “ni fa ban ga abin laifi ba” “To a wane dalili za ki tsaya alhalin kowa ya fita?” Sai da na kamo dukkan hannuwanta sannan na ce “Mujahida matar nan da ta shigo ita ce wacce nake baki labari na yi mafarki da ita,kuma wallahi yanzu ma idonta sak irin na macijin na gansu” Mujahida ta ƙwace hannuwanta kafin ta ce “kin ga tafiyata babu ni cikin hikayar nan,ta ya daga ganin mata yau ki ce wai ita ce ta zo miki a mafarki” Na ce “ki yarda da ni,wallahi hatta hoton da na ce miki na ahali to yau ɗin nan ma sai da na gansa” Shiru Mujahida ta yi kamar mai nazari kafin ta ja numfashi ta ce “ni ma na ga hoton amma sai na yi tunanin ko dai ƙila kin taɓa ganinsa ne Sheikh ya ɗora” Na girgiza kai kawai ina jin wani tsoro na luluɓe ni,haka muka runguɗa zuwa makaranta. Yadda ajin ya kancame da hirar Sheikh Rayyadeen ana haɗa sunansa da na Sadiya sai abin yayi mugun ɓata mini rai.Mujahida wacce ita kaɗai ta san sirrin da ke ƙunshe a birnin zuciyata sai cewa ta yi “kar ki wani damu kanki wai don tana rawar kai, wallahi ina da yaƙinin ita kaɗai ke kiɗanta take rawarta.Ke yanzu ki dube ta kin ga ta yi kama da macen da Sheikh Rayyadeen zai so?” Idona ya ciko da wasu hawaye kafin na ce “na sha ji a labarai cewa baƙar mace na ɗauke da wata irin baiwa Mujahida,kuma malamai sun fi kowa sanin sirrikan da ke tattare da mata to ƙila ita ma Sadiyar tana da shi” Ta ja tsaki kafin ta ce “waccan fa da kike gani tsohuwa ce don ta haura shekaru talatin da biyar yanzu kuma yayin ƴan shila ake yi” sai kuma ta yi shiru tare da yin wata muguwar dariya kafin ta kawo bakinta daidai kunnena ta raɗa mini “amma fa ƙawata za a sha gwagwarmaya don an ce tuzurai sun fi kowa zalamar mata kuma alƙur'an yadda Sheikh yake da ilimi na san akwai kallo duk ranar da kuka keɓe” Wani irin yammm na ji a jikina,na ɗan bangaje ta tare da yi mata hararar wasa na ce “ta ya aka yi ma har tunaninki ya kai can? Ni fa ko sau ɗaya ban taɓa hango mu a wannan matakin ba” Ta yi wani ƙayatacen murmushi kafin ta ce “ Khadeeja ko kin san da ina sonki ne domin Allah? Ganinki cikin farin ciki shi ne abu mafi tsada a rayuwata,silar ƙaunar da nake yi miki shi ne dalilin da yasa har na karɓi Yaya Hamza matsayin wanda zan aura amma kin san ba irin kalar namijin da nake so ba ne” Na ja numfashi na ce “amma Mujahida a wane dalili ne ba ki son farin namiji?” “Ni dai bai yi min ba” ta bani amsa a takaice. “Yaya Hamza fa shi ya yi miki?” na jefo mata tambayar. Ta yi murmushi ta ce “jininki ne fa ai ke ma kin san dole na so shi” Na kama hannunta na ce “don Allah kar ki yi wasa da zuciyar ɗan uwana yana mugun sonki” “Na sani,don yana faɗa mini kusan kullum ” Ina shirin yin magana amma ɗaya daga cikin manyan ɗaliban ajinmu ta yi magana kan a yi shiru sai ta soma jawabi “da farko ina yi muku sallama irin ta addinin musulunci,abin da yasa na buƙaci na yi magana shi ne dama don na ce mu yi wa kanmu faɗa .Don Sheikh bai da lafiya ba shi zai sa a ce an ƙi ci gaba da karatu ba,a cikin ajin nan akwai mahadatan Alkur'ani har biyu Sadiya da kuma A'isha da wannan nake kira a gare su don Allah su taimaki sauran wurin koyon karatu na san in kun yi haka sosai Sheikh zai ji daɗi in ya dawo” wannan shawarar da ta bayar duk kowa sai yayi amanna da ita,yayin da kuma aka fara zuwa suna koyar da karatun haka kawai na ji kishin Sadiya duk da tana yin karatu mai daɗi sai dai ba ta fi ni iya ƙira'a ba. Ko motsi ban yi ba ballantana na je ta koyar da ni kasancewar ita A'isha ɗin an tsara waɗanda suke yin hadda take yi wa gyara.A gabana Mujahida ta je aka koya mata tana zaunawa ita Sadiyar ta ɗago kai tana kallona,na kawar da kai gefe ina kallon Mujahida wacce zungurar mini ƙafa. “Ke?” ta furta duk da na san da ni take amma ban ko waiga ba,“ke kin iya karatun ne?” wannan karon a gabana ta zo ta tsaya tare da buga table.Na ɗaga kai na dube ta,a girme ta girme mini don ta kusa ninka shekaruna biyu amma da yake shi kishi babu ruwansa da shekaru sai cewa na yi “ai masu ra'ayi ne za a koyar to ni banda shi” Tana shirin yin magana malam Ibrahim ya shigo da sallama,aka amsa masa cikin ladabi kafin shi kuma cike da murna ya ce “na ji daɗi sosai yadda na ga kun mayar da hankali kuna karatu masha Allah ” “Malam ita wannan ta ce ba a isa a koyar da ita ba” cewar Sadiya tana mai nuna ni da yatsa. Malam Ibrahim ya dube ni da kyau kafin ya ce “Khadeeja yaushe kuma kika ɗauki wannan hali?” Na turo baki gaba ina cewa “ni ban so ta koya mini ne don ban saba yin karatu wajen mace ba in ba Momyna ba” Kusan ajin dariya aka shiga yi mini wasu na tsokanata da sunan ƴar Momy,sai da malam ya tsawata musu kafin ya cewa Sadiya “tun da ba ta so ki bar ta kawai,ci gaba da koyar da sauran” Sai da ta banka mini mugun kallo kafin ta gusa daga inda nake.Mujahida ta ce “ban so kika yi haka ba yanzu sai ki sa ki yi baƙin jini wurin mutane a yi dubin girman kai ne gare ki” “To sai me? Su suka sani” na faɗi haka ina mai ɗaukar jakata na fice daga ajin,wayata na fiddo na kira direba na ce ya zo ya ɗauke ni.Kusan mintin sha biyar kafin ya iso,na shiga baya na zauna kafin na ci gaba da latsa wayata ina aikin da na saba.Shafinsa na facebook na shiga na duba ai kuwa na ci karo da wani sabon hotonsa da ya ɗora.Kamar wata mahaukaciya sabon kamu haka na yi ta dariya ni ɗaya har sai da direba ya juyo ya tambaye ni sai a lokacin na nutsu. Ina isa gida na tarar Daddy na nan,sallama kawai ya amsa mini ya jefo mini tambayar “me kika dawo yi gida?” “Malaminmu a bai da lafiya shi yasa,yau muka je ganinsa har na saka masa ƙarin ruwa.Wallahi Daddy sai na ji na matsu a koma Makarantar boko don na ƙara ci gaba da karatuna daga inda na tsaya,ka ga shi kenan in Sheikh bai da lafiya ni ce zan dinga duba shi” yadda Daddy ya kafe ni da ido ko ƙyaftawa bai yi shi ya fargar da ni kan kwabsawar da na yi. Sai na rufe bakina da hannu ina mai waro ido.Ya ce “kafin ki amsa mini tambayoyin da zan jero miki da farko fara bani amsar me yasa yanzu kika bar saka niƙafi?” Na ɗan kwaɓe fuska kafin na ce “Daddy ta ɓata ni ma ban san inda take ba,kuma ita kaɗai gare ni duk na yi kyauta da sauran saboda na yi wa Momy alƙawari wacce ta saya mini kawai zan dinga sakawa” “Na ji! Yanzu yaushe kika zama likitar malaminku?” “Daddy ba fa abin da kake tunani ba ne,kawai mun je ganinsa ne sai likitansa ya gagara samun jijiya shi ne na nemo” na basa amsa ina mai sunne kai ƙasa zuciyata na dakan uku-uku saboda ganin kamar ran Daddy ya ɓace. “Wane Sheikh ne za ki dinga yi wa magani in bai da lafiya?” “Ƙanena wanda Momy za ta haifa mini” na basa amsa ina mai yin wani murmushi duk a tunanina zan iya yi wa Daddy wayo,shi ma martanin murmushin ya maido mini kafin ya ce “to je ki in kin huta ki gyarawa Umma ɗaki yau da maraice in sha Allah za ta zo” Wani irin tsallen murna na yi ina mai cewa “a ɗakina za ta sauka Daddy” Ya ce “kin sani sarai da Ummah ba ta iya hawan sama ciwon ƙafa take” Na soma kukan sangarta kafin na ce “a'a Daddy kar ka bari ta ji haka please ka bari na sauke ta a ɗakina” Kai kawai ya girgiza,ni kuwa ina haurawa sama na ƙara gyara ko ina duk da kuwa mai aiki ta gyara shi.Toilet na shiga,ina cire sutura ta sai na samu kaina da tsayuwa gaban mirror ɗin da ke manne a bango.Na yi murmushi ina jin wata irin kunya ganin surata a ciki,sai nake ganin tamkar mirror ɗin idon Sheikh ne.Da sauri na gusa na je na yi wanka na ɗaura towel na fito,kafin na kimtsa sai da na ƙara shiga shafin Sheikh Rayyadeen na yi bincike a nan ne na ga nan da sati biyu yake birthday na cika shekara arba'in da biyu. Ina shafa mai ina tunanin irin gift ɗin da zan basa,a haka har na shirya na sauko ƙasa.Daddy tuni ya tashi,motsin da nake ji a kitchen yasa na nufi can yau ma kamar kullum Momy ce ke a tsaye tana girki Baba Laure na taimaka mata. Kusa da ita na ƙarasa ina mai jingina kaina a kafaɗarta tare da kallon abin da take dafawa cikin tukunya. “Momy kan rago za mu ci?” na faɗa ina haɗiyar yawu. “Na Ummah ne” ta bani amsa tana yin murmushi mai sauti,na ce “to ai tare za mu ci” “Na sani! Je ki ma ki dama fura na can kan dinning ” “Momy na gaji please ki saka Baba Laure ” na faɗa a shagwaɓe ashe rabon a yi mini faɗa ne,nan ta soma balbale ni da masifa har da su cewa “wato duk yadda na tsaya kai da fata ina yi wa ahalina hidima ke ba za ki iya yin koyi da ni ba? Dama furar shi ne kin gaji? An faɗa miki zama mace raggonci yake nufi? To gara ma ki jajirce don in kin yi aure babu wanda zai yi miki aikin gida ke za ki yi abinki ” Ina turo baki ina ƙari na fita na je na ɗauki furar na dama,bayan na gama na saka ta a frigo don ta yi sanyi.Sai kuma na koma kitchen na soma kama mata aikin,ina kallon yadda Ammy ke sakin murmushi.Bayan mun gama komai muka jera a dinning kafin mu yi sallah,duk yadda Momy ta matsa mini kan na ci abinci ƙin ci na yi don na yi alƙawari tare da Kakata za mu ci. Sai yamma lis sannan Ummah ta zo,tuni lokacin yunwa ta gama galabaitar da ni amma ina ganinta na neme ta na rasa na je da guduna na rungume ta. “Haba Deeje ya isa haka kar ki kayar da ni ” Ummah ta faɗa tana dariya,na yi baya ina turo baki ina mai cewa “ni dai wallahi ba Deeje ba ke dai ce sunanki ke haka” Ta yi dariya ta ce “ ai sunan dai nawa ne ubanki ya ara ya maƙala miki”duk aka yi dariya,bayan gaishe-gaishensu ita da Momy aka gabatar da abinci har za ta je ta yi wanka amma na hana ta ina mai cewa “ƙawali wallahi in har sai kin yi wanka mutuwa zan yi kafin ki fito” na faɗi haka ina mai riƙe ciki. Da sauri kuwa ta zauna muka ci abinci,sai dai kamar abin tsiya ina ci zazzaɓi ya rufe ni saboda jimawar da na yi ban ci ba haka na yi ta yin amai wanda hakan ya galabaitar da ni sosai.Ni da na so na sauke Ummah a ɗakina a ƙarshe dai can sashen da ake sauke ta kullum in ta zo muka tare ni da ita. ★SHEIKH RAYYADEEN Yana cikin mazan da ba kasafai sha'awarsu ke motsawa ba,amma in abin ya taso masa kamar zai yi hauka.A daren da Ammy ta barsa bayan ya faɗa mata sunan Khadeeja ikon Allah ne kawai da kuma sauran shan ruwa gaba yasa bai mutu ba.Kamar yadda in gobara ta kama take ci bal-bal haka dukkanin illahirin gaɓansa ke kukan a kawo musu ɗauki.Bai da wani buri in banda ya samu mace a gadonsa sai dai hakan ba mai yiyuwa ba ne saboda bai taɓa yin aure ba.Ƴan matan da ma aka taɓa yunƙurin aura masa su ko da shi bai so to ɗaya bayan ɗaya haka suke mutuwa ba tare da ya san dalili ba. Muguwar kasala ce ta ci karo baƙin cikin da ya daɗe yana cin ransa har suka yi galabar kwantar da shi jinya.A ranar da ya je makaranta domin saka hannu a takardar da za ta bada damar turo sabbin ɗalibai ajinsa jikinsa yayi ɗan dama-dama sai kuma aka yi rashin sa'a ya ci karo da Khadeeja tana gudu a filin makaranta dukkan jikinta na motsawa duk da kuwa tana sanye da hijabi.Ba tare da yayi abin da ya kawo shi ba ya juya ya koma,nan ne ciwon ya ƙara rikice masa. Yau kuma da suka zo duba shi yadda ta taɓa hannunsa sai da ya shiga wani yanayi,dauriya kawai yayi saboda a gaban ɗalibansa ne. Abin da ya ɗan mantar da shi wannan yanayi shi ne shigowar Rashida cikin mawuyacin hali. Ko da ya dawo daga ɗaukar habbatu sauda sai ya biyo da gawayin zamanin nan da ake kunna shi da ashana.Hannunsa har rawa yake yi ya kunna tare da zuba ta ciki,nan fa Rashida ta soma yin tari yayin da shi kuma ya soma yi mata karatu.Dakyar aka samu ta dawo hayyacinta,Ammy ta ƙanƙame tana wani irin kuka kafin ta ce “don Allah ki yafe mini” “Laifin me kika yi mini da za ki nemi yafiyata? Ai ko ma kin taɓa yi na yafe miki ” Ammy ta faɗa . Rashida ta girgiza kai tana mai cewa “a'a na yi miki laifi mai girma Ammy,na ci amanarki na rogaza tarbiyyar da kika yi mini”jikin Ammy ya yi sanyi sosai ta ƙara rungume Rashida tana kallo Sheikh wanda haka kawai ya ji zuciyarsa na bugawa. Rashida ta buɗe baki za ta yi wa Ammy bayanin dalilin ciwonta amma Sheikh ya dakatar da ita yana mai cewa “Ammy tana buƙatar hutu don haka a bata magani ta sha” Ammy ta jinjina kai ta ja ta zuwa can sashenta ,garin tafarnuwa na habbatu sauda da zuma ta haɗa ta bata ta sha babu jimawa kuwa ta soma yin bacci wanda ba a ɗauki lokaci ba ta tsinci kanta wani wurin sai dai kuma ta shaida ɗakin da take ba kowane ne ba sai na Grand-Maa. Babu jimawa fuskarta ta bayyana a gare ta tana mai cewa “wato kin zo ki sanarwa da Ammynki abin da ke damunki? Wato asirina za ki tona? To ki sani wannan baccin shi ne za ki yi ta yi har ƙarshen rayuwarki don ba zan bari ki farka ba” Grand-Maa ta faɗa tana mai buɗe bakin Rashida ta zuba mata wani rubuta da aka rubuta kalmomin tsafi,tana gama zuba mata shi kuwa Rashida ta soma fizge-fizge wanda hakan ya jawo hankalin Ammy ita kuma ta kira Sheikh.Babu jimawa suka kwashe ta zuwa asibiti ba tare da sun san cewa ba a uƙuba suka jefa ta ba....... [13/12 09:05] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 05 An kwantar da Rashida kan gadon asibiti da tunanin za ta samu lafiya sai dai abin da Ammy ba ta sani asibitin cike take da miyagu don kusan maguna/ƙuliyoyin da ke yawo mutane ne a cikin siffar mage.Sheikh bai wani jima ba wannan yasa lokacin da wata mage ta shigo sam babu wani mai jarumtar da zai hana ta,ita Ammy ta yi tunanin normal mage ce har da cilla mata guntun burodi amma maimakon ta ci a'a sai suka da ta yi ta haye gadon da Rashida ke kwance tana mai yagarta a fuska har sai sawun akaifunta suka fito raɗau tare da jini. “Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un !” Ammy ta faɗa tare da zuwa ta cabko magen,sai dai madadin ta ji tsoka a'a wani irin abu ta ji kamar lagwami kafin ta ƙyafta ido sai ga mage ta koma tsumma.Ammy ta yi wurgi da shi tare da komawa gefe tana zarar ido haɗi da yin duk addu'ar da ta zo bakinta.Babu jimawa wata nurse ta shigo,babbar mace ce don za ta kai sa'an Ammyn.Kicin-kicin da fuska ta shigo tare da miƙawa Ammy takarda ta ce “wannan maganin muke so ki je ki nemo” Da ɗan mamaki ta dube ta sannan ta ce “kafin yarona ya tafi ai ya bada kuɗi masu yawa ya ce ko buƙatar wani abu ya tashi ku cire ciki” “To ban yi niyyar cira a ciki ba,ungo ki sayo ko kuma ku fita ku bamu asibitinmu ” ta faɗa tana wani ƙanƙance ido tana yi wa Ammy wani irin kallo wanda ba baƙo ba ne a wurinta,kusan kullum Grand-Maa na yi mata shi,kuma sosai take tsoronsa. Ba tare da ta ce komai ba ta jawo waya ta kira Sheikh ,sai dai har ta yanke bai ɗaga ba.Sam Ammy ji ta yi ba ta iya fita ta bar ƴarta ita ɗaya,kawai sai ta tura gadon da kanta har ta fito waje.Mai tsaron get ne ya je ya taro mata mai taxi,haka shi ya taimaka mata ta saka Rashidar.Ammy na shirin shiga taxi ya dakatar da ita tare yi mata magana can ƙasan maƙoshi “ciwonta ba na asibiti ba ne Hajiya,in son samu ne ki mayar da ita gida don ina mai baki tabbaci kusan duk asibitocin yanzu irin wannan ce duk miyagu sun fi yawa.Da zarar kuma kun shiga akwai wani dafi a cikin ruhinta da zai jawo hankalin sauran miyagun zuwa gare ta” Ammy na jin haka ta yi masa godiya har da basa kuɗi kafin ta shiga,har sun ɗauki titin wata asibiti amma ta ce ya kai ta can gida,ta kwatanta masa unguwar.Tun kafin su isa ta kira Mama a waya ta shaida mata, wannan yasa taxi na tsayawa ta zo ita da Aliya suka kama mata suka shigar da Rashida ciki.Baiwar Allah numfashi ma dakyar take yinsa,kallo ɗaya Mama ta yi mata ta fahimci damuwar hakan yasa cikin dauriyar zuciya ta ce “Khadi ina neman alfarma ki kai Rashida ɗakina na yi jinyarta” Zaman amana suke yi da kwanciyar hankali wannan yasa Ammy ko tunani ba ta yi ba ta amince suka kai ta can.Mama ba ta ɓata lokaci ba ta soma yi wa Rashidar hayaƙin turaren Mayu,duk ɗakin ya turniƙe da hayaƙi.A hankali ta soma yin tari alamun ta sake dawowa duniya a karo na biyu,ta buɗe idonta wasu hawaye na yi mata zuba.Maƙoshinta take jin an riƙe shi gam an yi masa mugun ƙulli wanda ba ta ɓatawa kanta lokaci wurin gwada yin magana ba tuni ta fahimci abin da ke faruwa da ita,babban tashin hankalinta kuma bai wuce sanin ashe Grand-Maa ce wannan tsohuwar da ta taɓa bayyana a gabansu ga shi kuma ba ta da bakin da za ta iya yin bayani. Ɗakin ne ya dawo normal duk hayaƙin ya ɓace,sai a lokacin Mama ta ga idon Rashidar a buɗe sosai ta ji daɗi duk da dama ta san da wuya mutum ya shaƙi turaren nan bai farfaɗo ba. “Ya jikin naki?” ta tambaye ta ,da kai ta amsa mata kafin ta ja fatun idonta ta rufe tana tunanin duk wannan tashin hankalin ya faru ne silar binciken wayar miji. A can ɓangaren Sheikh Rayyadeen kuwa tun bayan da ya dawo daga asibiti ya shige ɗakinsa,wani irin tuƙiƙin baƙin ciki ne ke rufe shi yadda ƙanƙanuwar yarinya ta raina shi ta nuna masa taurin kai.Ji ya yi ya matsu gobe ta yi don ya je makaranta,yana son yi mata hukunci mai tsauri domin ta shiga hayyacinta. Zama ya yi ya ɗauko system ɗinsa yayi bincike,yana nan zaune Ammy ta shigo ta sanar da shi halin da ake ciki kafin ta ƙara da cewa “Sheikh ina ga lokaci ya yi da zan koma ƙauyen nan da na taɓa faɗa maka zan je na karɓowa Rashida magani wurin tsohuwar nan” Ya ɗan ja numfashi kafin ya ce “amma Ammy kin tabbata ba shirka ba ce ?” “Magani ne kawai fa take bayarwa,ba ta yin dibo kai ne da kanka za ka faɗa mata matsalolinka sai ta baka maganin da ya dace.Shekarun da suka shuɗe ita ce ta bani magani na sha har na samu cikinka ya tsaya ban yi ɓari ba” “Yaushe za mu tafi?” yayi tambayar don ya san tun da ta ce za ta je to in ba zuwan suka yi ba to ba zai samu kanta ba. “Yanzu!” ta basa amsa tare da miƙewa ta fita wanda tuni ya fahimci me take nufi, wannan yasa ya miƙe ya kimtsa.Ba su wani ɗauki lokaci ba suka fito ,direba ne ya ja su sannan babu wanda ya san sun fita.Tafiya ce ta awanni wajen biyar, Sheikh na baya zaune kusa da Ammynsa wacce ba sai an faɗa maka hankalinta ba kwance yake ba. Sallah kawai ke tsayar da su,abinci ma iya direban ne kawai ya ci har suka isa ƙauyen wanda iya idonka kawai sun isa su yi maka fassararsa.Kirarin da suke yi wa ƙauyen BABU RABON MUGU A CIKI,ko ta ina ka duba wasu alamomi ne masu nuni da kariya a haka Ammy ta dinga nuna masa hanya har suka isa ƙofar gidan tsohuwar sai dai aka samu akasi a rufe yake. Duk fitowa suka yi, Sheikh ya ce “ga shi gidan a ƙargame ba ki da lambarta?” “A'a bani da,ga wani yaro can tambayo mana shi ka ji ƙila tana nan kusa ” Da hannu Sheikh ya kira yaron, Ammy ta ce“ ina tsohuwa mai wannan gidan don Allah?” “Ta tafi birni yau ɗin nan” ya bata amsa. “Amma ko ka san yaushe za ta dawo?” kai ya girgiza,ba su da wani zaɓi a dole suka koma cikin mota.Cike da takaicin rashin ganin tsohuwar suka juyo mota,ba su kawo gida ba sai cikin dare suna shiga suka ƙara tarar da wani tashin hankalin Rashida ta farka sai dai ba ta cikin hankalinta har yawu ke yi mata zuba.Haka Ammy ta sa kuka tana yi,yayin da Mama ke cewa “wallahi ban san abin da ya faru ba ni dai na bar ta a ɗaki ta buɗe idonta daga in shiga kitchen in fito ne na same ta tana ƙyalƙyata dariya” Sheikh dai bai ce komai ba sai kofi ya samu ya zuba ruwa ya yi mata addu'a,wurin fa shan ruwan ne aka yi daga don sai da aka dadanne ta aka ɗura mata su.Baiwar Allah sai ta soma jan ajiyar zuciya tana kallon Sheikh Rayyadeen,a cikin ƙwayar idonta yake hango wani duba wanda ba nata ba sai dai sam bai ba hakan muhimmanci ba. Sashen Ammy aka mayar da Rashida,da lokaci yayi haka aka haɗu wurin cin abinci a nan ne Abba ya samu labarin abin da ke faruwa.Faɗa ya soma yi musu me yasa ba a kira shi a waya an sanar da shi ba, Grand-Maa ta yi caraf ta ce “saboda ba kai ka haifi Rashidar ba,inda ƴarka ce akwai ƴar isk...” yadda Sheikh ya buga table da mugun ƙarfi har kwanukan sama sai da suka motsa,shi ya katse hanzarin Grand-Maa ta kasa ƙarasa abin da take da niyyar faɗa.Idonsa sun kaɗa sun yi ja,duk safiyar yau in banda baƙin ciki babu abin da yake cin karo da shi,duk zafin ran sai ya soma zube shi kan Grand-Maa wacce ta yi tsuru-tsuru kamar an rutsa kwarto. Muryarsa har wani sarƙewa take yi wurin cewa “ ba zan taɓa ɗaukar cin mutumcin mahaifiyata ba a gurin ko ma wane ne,a kullum ina yawan nusar da kai Abih ka dinga faɗawa Grand-Maa darajar aurenka ce da ke kan Ammy yasa take yi mata abubuwa har nake yin shiru,amma ba ta gani.Ta yaya ne za ka bari tana zagin Ammyna a gabanka amma ba ka cewa komai?” Ran Abba ne shi ma ya ɓace ya ce “Rayyadeen ni kake yi wa faɗa? Ai da haɗe mu ka yi ka yi mana duka sai mu san kana son mahaifiyarka,wato uwarka ta fi tawa uwar kenan? Kai me yasa ba za ka yi wa mahaifiyarka magana ba? Ka faɗa mata ta tsarkake bakinta kafin ta yi magana” Sheikh har ya buɗe baki amma Ammy ta dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa,“Deeni yi shiru” ba don ya so ba ya ja bakinsa yana mai tsure Grand-Maa da ido don tun da ya fito daga ƙauyen can yake jin tsanarta tun bisa hanya ba tare da ya san dalili ba. Tsam ya tashi zai tafi amma Abba ya dakatar da shi yana mai ce masa “ka nemo malamin ruƙiya ya dinga zuwa nan gida yana yi mata karatu” Grand-Maa ta ce “da dai asibiti aka kai ta Mahmuda saboda alamomin hauka duk sun tabbata” Mama ta karɓe da “babu wani hauka iskokai ne ga kanta” Grand-Maa ta fiddo idonta na mugunta wanda iya Mama ce kawai ke iya ganinsu,ita kuma sam hakan bai bata tsoro ba sai ma gefen wuyanta da ta soma shafawa inda take ajiyar nata makamin muguntar.Dole dangin naƙi yasa Grand-Maa ta tsuke shegen bakinta,shi kuwa Sheikh sashensu ya wuce sai da ya fara shiga wurin Rashida ya tofa mata“ As'alullahul azima rabal arshil azimi an yashfiyaki ” ƙafa bakwai kamar yadda Manzon tsirai ya umarce mu da mu yi in mun je duba marar lafiya. Daga nan ɗakinsa ya wuce,wanka yayi ya canza kaya ya ɗauko Alkur'ani kenan zai fara yin karatu Ammy ta yi sallama.Ya amsa,sai ta shigo hannunta ɗauke da tray, Sheikh ya wani langaɓe kai kamar ƙaramin yaro yayin da Ammy ta soma haɗa masa abincin da bai ci ba a can.Haka ta zauna sai bayan ya gama ci sannan ta fita,shi kuma karatun yayi bayan ya gama ya yi dogayen addu'o'i yana roƙon Allah lafiya da kuma kyautar aure da sauransu. Lokacin da ya kwanta ƙarfe biyu saura ,hakan yasa bai wani jima ba bacci ya ɗauke shi. Washegari bayan ya dawo daga masjid ma sai da ya je ya duba Rashida ya yi mata addu'o'i sannan ya je ya fara shirin zuwa makaranta. Tun da safe ya shaidawa shugaban zai zo yau , wannan ya sa aka ƙara tsabtace makarantar fiye da kullum. Tsit kake jin ɗalibai babu haniya saboda kawai an ga motarsa,shi Sheikh ya banbanta da sauran malamai duk girman ɗalibi in yayi laifi tsaf zai zane shi.Ya sha dukan ƴan mata sai su turo samarinsu wasu su yi masa kashedi wasu kuma da niyyar ramawa suka zo.Amma kuma hakan bai sa ya canza ba,kusan kuma hakan ne yasa duk ake tsoronsa don bulalarsa ma in ka kalle ta sai gabanka ya faɗi. Yana shiga ajin wani ƙamshi ya bugi hancinsa,bayan sun amsa sallamar da yayi musu sai ya samu wuri ya zauna kafin ya ɗago a hankali ya maido dubansa gare su. Kowacce ta saka uniform,nan babu matsala sai ya soma kiran sunan ɗalibai bayan ya gama ne ya ce “sabbin zuwa su koma wannan layin” ai kuwa duk tashi suka yi ɗin,ɗaya bayan ɗaya haka yake kiran sunansu yana binciken karatunsu da ya zo kan Khadeeja sai ya lura ita sam ba ta ma yi karatun Alkur'ani ba amma aka ƙetara ta zuwa aji na gaba,ransa ne ya ɓace duk da ya lura ta yi kaf ɗaliban maki a karatun litattafai. “Nana Khadeeja Abdullahi” ya kira sunan nata tare da ɗaga kai,Mujahida ce ta basa amsa da “ba ta zo ba malam ba ta da lafiya” “Ita ta faɗa miki ko kuwa ƙarya kika yi don ki kare ta?” ya tambaya yana haɗe rai, Mujahida ta sunne kai tare da yin shiru sai ya ji ita ma tana basa haushi.Ya ce “tashi tsaye” ai kuwa jikinta na yin rawa ta miƙe,shi kuwa babu tausayi haka yayi mata bulala uku saboda ƙaryar da ta yi sai ga Mujahida da guntuwar ƙwalla. Bayan ya gama bincikar karatun nasu,sai ya fara tambayar manyan ajin abubuwan da suka faru nan ne fa Sadiya uwar kauɗi ta shaida masa abin da ya faru jiya sai maƙe murya take yi tana yin ƙalƙala duk don ta burge Sheikh Rayyadeen.Sai dai bai ce komai ba ya soma yin karatu har lokacin shan iska yayi, Mujahida yau sam ba ta da walwala haka ta yi ta jaraba kiran Khadeeja amma ba a ɗauka ga kuma lambar Hamza ita ba ma ta shiga. Bayan sun dawo aji ne ya tura sabbin ɗalibai gun waɗanda ya yarda da iliminsu domin su sauƙaƙa musu karatun wanda kuma hakan sabon tsari ne ya ɓullo,don ya rantse dole Khadeeja wurin Sadiya zai tura ta duk ranar da ta zo. ★KHADEEJA Sam kasa rumtsawa na yi ita kuwa Ummah sai faman shafa mini maganin aboniki take yi kafin can mu haɗa ido da ita.Da dafe ƙirji tana mai cewa “mu ga idonki” sai ta gwale mini su kamar wata doctor haka ta sa fitila ta duba,wani kwalli ta ɗauko ta rambaɗa mini mai mugun yaji tana mai cewa “dama na san Allah ba zai ɗauki raina ba har sai ya nuna mini wanda zai gaje ni ” sai ta soma shafa mini wani maganin a goshi,sannu a hankali na soma jin bacci na surata har na tsinci kaina a duniyar MAFARKI.Yau ma kamar wancan lokacin a gidansu Sheikh na tsinci ruhina,duk abin da ya faru ga Rashida bayan tafiyata haka aka yi mini wahayinsa.Hatta zuwan Sheikh Rayyadeen ƙauye duk an nuna mini da kuma abin da zai faru a futur,wato ya bugi ƙawata Mujahida daga nan kuma sai aka cilla ni wani wurin.Da na ƙarewa wurin kallo sai na gano farfajiyar gidansu Sheikh ce, waige-waige na fara yi har idona ya sauka ka wani tsohon toilet duk ya gurɓace daga can cikin ƙasar.Da wani sauri na ƙarasa na isa wurin na zube tare da soma yin tono,na yi rame mai zurfi kafin na cimma wata baƙar tukunya mai murfi haka na ciro ta.Na buɗe ta,hoton Sheikh ne a ciki yana ɗan matashi bai fi shekara ashirin da bakwai ba,a hoton an zagaye wasu gaɓoɓinsa,na farko idonsa,na biyu kunnuwansa,na uku bakinsa,na ƙarshe kuma al'aurarsa sam ban san me hakan ke nufi ba kawai dai na samu kaina da ɗauko tukunyar na bi ta ƙofa na fita.Tafiyar ƙasa na yi har na iso gidanmu,cikin furanni na ɓoye tukunyar yayin da hotonsa kuma na riƙe shi a hannuna na zo na shiga ɗakina na kwanta ina bacci,kuma duk hakan ya faru ne a MAFARKI. Washegari da sarawar kai na tashi,idona har wani zafi suke yi mini.Na tashi dakyar na zauna kan katifar,tuni gari yayi haske babu Ummah sai ƙullin kayanta.Na zira ƙafata kenan don zuwa banɗaki na ji na taka wani abu mai sulɓi kamar leda,amma ban wani duba ba na je na shiga toilet sai kuma na samu baƙon watana ya zo.Wanka na yi da ruwan ɗumi na fito,cak na tsaya ina kallon yadda iska ke tunkuɗo wani kwali har ya iso gabana,na duƙa na ɗauka ina birkito shi sai na ga hoton Sheikh a nan take kuma mafarkin da na yi ya faɗo mini a rai sak irin hoton banbancinsa da na cikin MAFARKI shi ne wannan bai da zagayen nan da aka kewaye gaɓoɓinsa. Mamaki kamar zai kashe ni haka na zumbula hijabina na fita zuwa ɗakina,falon tsit yake babu kowa sai masifar Ummah da nake jiyowa ita da ƴar aiki.Sama na haura ,na ɗauki pad da pant na saka sannan na zira doguwar riga ta kanti na fesa turare na shafa mai.Kan bed na haye tare da riƙe hoton Sheikh ina kallo sai yanzu ma idea wanko hotunansa ta zo mini,tsam na manna shi a ƙirji kafin na lumshe ido zuciyata na ɗan dokawa a haka bacci ɓarawo ya kwashe ni sai wuraren ƙarfe sha ɗaya na rana na farka shi ma Ummah ce ta zo kaina tana balbale ni. Na turo baki gaba ina cewa “ƙawali ya za ki tashe ni ina hutawa?” “Tashi maza ki ci abinci babu ruwa da sakarci,kin ga jiya haka kika jigata da kika zauna da yunwa” Tashi na yi na yi brush na wanke fuskata ko da na fito sai na samu hoton Sheikh Rayyadeen a hannun Ummah tana kallo.A kunyace na karɓe hoton,yayin da ita kuma ta tsuro mini na mujiya kafin ta ce “wane ne?” “Saurayina mana” na bata amsa ina mai fesa turare. “A ina kika samu hoton?” ta jefo mini tambayar. Na ce “ni da saurayina shi ne za ki tambaya ina na same shi? To shi ne ya bani da kansa” “Ke da shi halan duk makafi ne shi yasa ba ku ga matsalolin da ke tattare da hoton ba?” Ummah ta faɗa cikin ɗaga murya,da sauri na juyo ina kallonta zuciyata na ɗan bugawa.Na san Ummah na bayar da magani,wani sa'in ma ba sai ka tambaye ta ba a'a haka kawai a hanya ma in ta haɗu da kai sai ta baka magani amma ban taɓa sanin cewa iliminta har ya kai iya ta hoto ma tana iya hango matsala. Na zo dab da ita ina mai cewa “halan meke da hoton ?” “Zo mu sauka ƙasa ki ci abinci ” ta sauya zancen,haka na ajiye hoton ƙasan pilow na take mata baya.Ammy na zaune a falo,gaishe ta na yi sannan na zuba abinci na soma ci ta miƙo mini wayata sai na ga miss call ɗin Mujahida.Sanin yanzu tana cikin aji yasa ban maida mata ba sai text na yi mata,ai kuwa ta maido mini har take shaida mini cewa Sheikh Rayyadeen ya bulalaye ta saboda ta yi ƙaryar banda lafiya,dariya na shiga yi kafin kuma na yi tsit sakamakon zuciyata da ta raya mini ‘ jiya ai na yi wannan mafarkin ’ babu shiri na ajiye plate ɗin na haura sama,ina jin Ummah na tambayar lafiya amma ban juya ba.Zaune na yi na soma rubutawa Mujahida kaf irin mafarkin da na yi a daren jiya,ita kuma ta tabbatar mini da za ta zo gidanmu in an tashi daga makaranta. Haka kuwa aka yi,ta cika alƙawari bayan ta zo ɗakina muka shige na ciro hoton Sheikh Rayyadeen na miƙa mata ina mai cewa “kin gansa” Shiru ta yi tare da karɓa tana dubawa kafin ta ce “kuma kin tabbata ba wani ne ya baki hoton nan ba?” Na ce “wani wa? Mujahida ni fa na fara jin tsoro kar dai a ce ni ma Rashida ta saka ni cikin group ɗinsu na Mayu ” Sai da ta sheƙe da wata dariya kafin ta ce “ke fa matsala ta da ke hauka,yanzu dai abin da za a yi kawai mu shirya mu je gidansu Sheikh ɗin sai mu kaiwa mahaifiyarsa hoton” ba tare da wani tunani ba kuwa na amince,muka fito lokacin har duhun magarib ya fara shigowa wannan yasa Ammy da Ummah duk ba su falo. Muna fita na karɓi key ɗin mota ga direba,haka na tuƙa mu har zuwa gidansu Sheikh Rayyadeen.A bakin ƙofa na yi parking,na cewa Mujahida “yanzu in muka shiga me za mu ce?” “Wurin Ammy muka zo ” ta bani amsa sai muka fito,ni ke gaba ita kuma tana baya bakin get ɗin babu kowa hakan yasa muka shiga kai tsaye.Ina shirin shiga falon na ci karo da shi har kaina na dukan ƙirjinsa,ruwan gemunsa suka ɗiga kan fuskata da wani matsanancin bugawar zuciya na yi baya saura ƙiris na faɗi Mujahida ta taro ni sai muka yi cirko-cirko muna ƴar kallon mu da Sheikh Rayyadeen..... Group biyu ne normal 300 , VIP kuma 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 .Kamar tun a talla na faɗa muku wannan sabon salo ne sabuwar sheƙa to haka take,nan duk shimfiɗa ce ba mu ma fara labarin ba. [14/12 15:15] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 06 Ban san me yasa yake yi mini ƙwarjini ba a duk lokacin da babu gilashi a idonsa,sai na dinga ganinsu tsirararsu girma da kyawunsu ya ƙara fitowa uwa uba wani abu da nake gani kwance a cikinsu mai ɗaga mini hankali da kaɗa hantar cikina. Mujahida ce ta yi ƙarfin halin gaishe shi “barka da warhaka Sheikh ” Bai amsa ba sai ni da yake kallo,ƙila gaisuwar tawa yake jira.Kai na sunne ina mai ƙara jimƙe hotonsa da ke hannuna.Bai ce mana kanzil ba saboda kiran sallar da aka ƙwala a masjid ɗin gidansu,yayi gaba yana jifata da mugun kallo yayin da ni kuma na ja wata ajiyar zuciya ta murna ina mai shigewa cikin falon . Ko ina tsaf yake sai ƙamshi ke tashi,kamar wacce ta san gidan haka na bi na tafi wancan sashen na jiya sai a lokacin ma na farga da Mujahida ba ta biyo ni ba.Zan juya kenan Ammy ta fito tana cewa “wa ke nan?” da sauri na juyo ina kallonta,a kunyace na gaishe ta ita kuma ta amsa mini da murmushinta tana ambaton sunana daga ƙarshe,babu wata magana don duk a daburce nake na ciro hoton Sheikh ɗin na miƙa mata.Sai ta karɓa ta duba tare da kallona da mamaki,“ina kika samu wannan hoton?” ta jefo mini tambayar. Shiru na yi,sai ma a wannan lokacin na ga wautata.Kame-kame na fara kafin daga ƙarshe na shaida mata mafarkin da na yi,duk illahirin jikinta ne na ga yana kyarma kafin ta ce “ MAFARKI?” Na jinjina mata kai,sai ta ja hannuna ta kai ni ɗakinta ta zaunar da ni tana mai cewa “zauna na yi sallah” banda wani zaɓin haka na zauna,yadda ta jima a sujidar ƙarshe yasa na ji ina ƙaunarta don na tabbata addu'a ce take yi. “Ammy?” na ji muryar Sheikh daga can falo,bai tsaya da kiran sunan nata ba yadda na ji amon muryarsa na tunkaro nan shi yasa na tashi da mugun sauri na buɗe wata ƙofa na shige ina dafe zuciya da tunanin na tsira sai dai nan ɗin ma wani tashin hankali na ci karo da shi .Fuskar tsohuwar nan Grand-Maa ce zaune raɗam a mirror ɗin toilet,babban tashin hankalin shi ne iya kanta ne kawai ya bayyana kuma a gundile babu gangar jiki. “Yiiiii!” ta girgiza gashin kanta tana bani tsoro na fasa ihu tare da banko ƙofar na fito,sam idona sun rufe da tsoro ban gansa ba haka na je na faɗa jikinsa tare da ƙanƙame shi gam ina kuka tare da rumtse idona ina cewa “aljana! Aljana!“ Kiciniyar hakice ni yake yi,sai dai sam na ƙi basa wannan damar don ba mugun riƙo na yi masa.Sai da Ammy ta yi magana ne sannan nutsuwata ta fara dawowa,“Khadeejatu?” ta furta tana mai jawo ni ta baya,na ɗan jan numfashi kafin a hankali na buɗe idona akan gemun Sheikh suka sauka,zuciyata na ɗan bugawa na soma sassauta riƙon da na yi masa ina mai ɗaga kai na dube shi.Idonsa ne na ga sun kaɗa sun yi ja,sai na ƙara ruɗe na ƙi sakin gefen cikinsa da na cikuikuye,kamar wani wanda bai da hankali haka yasa tafukan hannuwansa kan ƙirjina ya wani tura ni baya,saura ƙiris na faɗi amma Ammy ta tare ni.A zuciye ya fita ko sakan biyu bai ƙara ba,wani kuka ne ya zo mini wanda ban san na mene ne ba. Ammy ta fara rarrashina sai bayan na yi shiru sannan ta kamo hannuna ta ce “zo mu je ki nuna mini daidai ina ne kika tukunyar ” haka na bi bayanta muka je can bayan ɗakunansu na nuna mata wurin.Ta ja numfashi tana mai cewa “ Khadeejatu kin san wani mafarkin gaskiya ne,ta hanyarsa ce Allah subhanahu wata'ala yake nunawa muminai abin da ke faruwa a rayuwarsu.Ban san me lokaci ya tanadar muku ke da Deeni ba da har ƙaddararsa ta faɗo a tafin hannunki,ga shi ke ce za ki zamo silar warware wani baƙin ƙulli na rayuwarsa” Saurarenta kawai na yi amma ban ce komai ba,sai ta ci gaba da cewa “ki tsaya nan bari na je na dawo” kai na jinjina mata ta tafi ta bar ni nan. Tuna wa na yi yadda hannuwan Sheikh suka sauka a ƙirjina,duk da na san a bisa kuskure ne amma haka nake jin haushi .Ina nan tsaye Ammy ta dawo da abin haka rame,da sauri na karɓa na buga daidai wurin da aka nuna mini a mafarki.Bugu guda ne na yi amma sai ƙasar ta soma buɗewa da kanta, Ammy ta duƙa ta sa hannu ta soma janye sauran ƙasar da ke bakin rame cm.Hannunta na rawa ta ciro tukunyar tana mai ambaton sunan Ubangiji ,a gabana ta buɗe ta a ciki mun samu wandon Sheikh tun yana ɗan yaro sai kuma wani ƙwai mai kamar na jimina sai wasu tarkacen. Ƴar kallon-kallon muka soma yi ni da Ammy kafin na ji wata idea haka kawai ban san daga ina ta fito ba,“ki ƙona komai ni kuma ki bani tukunyar da kuma ƙwan na tafi da su” wani abin mamaki shi ne ko kaɗan Ammy ba ta yi gardama ba hakan kuwa ta yi ta miƙo mini tukunyar wacce ƙwai ke ciki na ɓoye ta a hijabi ,a haka muka rabu na fita waje sai dai babu key ɗin mota a hannuna kuma ban san inda yake ba. Don dole na koma can cikin gida,falon Ammy na shiga na kuwa same ta tuni ta zuba tarkacen a cikin kasko ta ƙyarta musu ashana. “Ammy makullin motata” na furta,haka aka ta bincikensa amma ba a gani ba. Ta ce “bari na kira Sheikh ya sauke ki” ba ta ma bari na furta wata kalma ba ta fita. Ammy na shiga ɗakinsa ta same shi a kwance gorar ruwan sanyi a hannunsa,yana jan numfashi duk da ta san abin da ke saka shi a wannan halin amma wannan karon sai ta ƙi nuna damuwarta ta ce “ka taso ka sauke Khadeejatu gida” Ya ɗago da sauri yana kallon Ammyn wacce ta haɗe rai ,kamar wani maraya cike da tausayin kansa ya ce “to” Sai ta fita ta barsa yana jin kamar ya kama da wuta ko kuma ya fasa ihu ƙila zai ji sassauci.Ya miƙe yana masifa yana cewa “ke ɗin ba masifa ba ce a gare ni a'a ke kanki matsala ce,a kullum banda fitina babu abin da kike kawowa a rayuwata duk in mun haɗu daga kina gudu sai kin faɗo jikina mtswww!” ya ja dogon tsaki kafin ya ci gaba da cewa “na tsane ki!” haka ya fita can farfajiya ya buɗe motarsa ya shiga yana jiran fitowarta. Ina nan tsaye Ammy ta shigo ta kama hannuna muka fito,sai ta sa key ta rufe ɗakinta kafin mu fito babban falo.Karo muka ci da Grand-Maa,cike da girmamawa Ammy ta gaishe ta amma tsabar munafurci irin nata sai cewa ta yi “Khadi wannan fa wace ce?” “Ƴata ce Maa ta kawo mini ziyara ne za ta koma gida” Ammy ta bata amsa. “Amma kamar na ganta a jiya” Ammy ta dube ni kafin ta ce “eh ta zo” “Tun da ta zo jiya ,yanzu kuma me ya maido ta? Munafurci ko me?” Ammy na jin haka ba ta ƙara tankata ba ta ja ni zuwa waje,idon Grand-Maa ƙur kaina tana kallon hijabina da dukkan alamu so take yi ta san mene ne ciki. Muna zuwa kusan motarsa Ammy ta buɗe mini gidan gaba,kasa shiga na yi na girgiza mata kai tare da buɗe baya na zauna.Ta yi murmushi ta ce “sai da safe Deejar Ammy ki gaishe mini da mamarki” A hankali na ce “to Ammyna” wata irin waigowa Sheikh yayi da sauri yana yi mini kallon mamaki mai cike da tsana kafin ya soma jan motar. Sai da muka hau kan titi ya ce “wace unguwa?” maimakon na basa amsa sai na soma leƙen fuskarsa,rai a ɗan ɓace ya sake tambayata sai a lokacin na shaida masa.Da muka shigo layin kuma na soma nuna masa har muka iso ƙofar gida,gabana ne ya faɗi rasss ganin duk ahalin gidan a waje har da masu gadi. Murya na rawa na cewa Sheikh “don girman Allah ka fita ka yi wa Daddyna bayani ko ƙarya ce ka yi masa ka ce daga makaranta nake motata ce ta lalace shi yasa ka ɗauko mu ni da Mujahida ” Wani irin rumtse ido Sheikh yayi yana jin zuciyarsa na azalzala,shi da yake hukunta ɗalibai akan in sun yi ƙarya amma yau shi ne ɗalibarsa ke son ya yi ƙarya.Fita ya yi ya je ya gaishe da su Daddy,ban san me ya faɗa musu ba sai na ga duk sun shiga cikin gida.Sai a lokacin ya buɗe mini na fito,na yi tsaye ina kallonsa yadda haiba da ƙwarjininsa suka fito.Motarsa ya rufe sannan ya yi gaba na dinga take masa baya,cike da mamaki nake kallon yadda yake sa kai ciki.Muna shiga falo sai na ga Momy har wani rawar jiki take yi wurin kawo ruwan sha,yayin da shi kuma Daddy ya nunawa Sheikh wurin zama .Ban wani jinkirta ba na haura can sama inda ɗakina yake,ƙarƙashin bed na ajiye tukunyar kafin na cire hijabina.Toilet na shiga na haɗa ruwan ɗumi na yi wanka na canza pad,yunwa nake ji amma kasa fita na yi ƙasa don na san bai tafi ba,har yanzu kuma ban bar mamakin dalilin da yasa Daddy bai ce mini komai ba alhalin yana da zafi sosai. A can falo kuwa cike da mutunta wa suke kula da Sheikh Rayyadeen,wanda shi ɗin ba ɓoyayye ba ne a wurinsu musamman ma Daddy wanda suke cikin association Islamic ta ƙasar Nijar shi da Sheikh ɗin.Ammy ita kuwa ta san shi a tv da kuma bakin mijinta in yana yi mata hirar addini,ko kaɗan Daddy hankalinsa bai tashi ba da Sheikh Rayyadeen ya fito ya shaida musu cewa ya kawo Khadeejatu ne gida a bisa umarnin mahaifiyarsa,sai dai yana mamakin meke haɗin Deejar da Ammy ɗin. Ummah dai na zaune tana kallon Sheikh Rayyadeen don ita ba ta san shi ba,amma sosai take mamakin ta ya babban malami kamar shi yake ɗauke da ƙulli-ƙulli na asiri a jikinsa.Hirar addini kawai suke yi kafin ya miƙe ya ce “ni zan koma” Daddy ne ya yi masa rakiya har zuwa ƙofar gida sannan ya dawo ciki, ya dubi Momy ya ce “je ki kirawo mini Ummita” Ina kwance ina wasiƙar jaki Momy ta shigo,da sauri na sunne kai ina jin gabana na faɗuwa.“Ki taso Daddynki na kira” shi ne kawai abin da ta faɗa ta fice,jiki babu ƙwari na zumbula hijabi na sauka.Kusa da Ummah na zauna ina mai kwantawa a jikinta,“daga ina kike? ” Daddy ya watso mini tambayar da ta tabbatar mini cewa Sheikh bai sanar da su komai ba.Wannan yasa na gyara zama na shararo ƙarya,“daga makaranta muke Daddy,motar da na ɗauka ce ta lalace ka san an kai mu ajin ƙarshe shi ne Mujahida ta zo muka tafi can don mu yi exercises ” “Amma shi Sheikh ce mini yayi Ammynsa tasa ya kawo ki gida” “Eh suna tare ne lokacin da suka haɗu da mu a hanya,ka san wani abu Daddy Ammynsa nada kirki sosai ” na faɗa ina murmushin ƙarfin hali don zuciyata cike take da fargaba. “Ina motar take yanzu?” “An kira mai gyara ya tafi da ita ,Ammy ta ce in an gyara za a kawo mini har gida” na basa amsa.A yadda na ga Daddy ya gamsu da hujjojina shi ya kwantar mini da hankali har na nemi abinci na ci. Ummah ta miƙe ta nufi ɗakinta tana mai cewa “ƙawali ki zo ki yi mini tausar ƙafa” Sarai na san halin Ummah babu wata tausa da zan yi mata ,tambayoyi ne za ta yi mini amma saboda ban jin tsoro ko shakkar sanar da ita sirrina kawai na miƙe na bi bayanta. Ina shiga kuwa ta jawo ni ta zaunar tare da tsura mini ido,na ja ɗan numfashi kafin na ce “gidansu ne na tafi Ummah ,kin san kusan shekara uku kenan nake ciwon son Sheikh Rayyadeen amma ban taɓa furta masa ba.Jiya kuma na yi wani mafarki da ya tsorata ni shi ne na je na shaidawa Ammynsa ” Ta ja numfashi kafin ta ce “ƙawali ba ki ganin mutumin nan yayi miki girma? Dube shi fa gudan dattijo da me Daddynki ya girme masa?” Na turo baki na ce “to ni ina ruwana da girmansa tun da ba goya shi zan yi ba na yi yawo?” Ta yi ƴar dariya kafin ta ce “lokaci yayi za ki fahimci abin da nake nufi.Matansa nawa?” “Bai taɓa aure ba” na bata amsa,ta ce “amma hotonsa ne na gani a hannunki ko?” na jinjina mata kai,ba ta ce komai ba sai jakarta da ta jawo.Magani ta kaɗa mini ta bani na sha,kafin na fita na koma ɗakina.Wayata na ɗauka na kira Mujahida,tana ɗauka na soma yi mata masifa.Ta sheƙe da dariya ta ce “ke ba fa zan tsaya ba Sheikh yayi dambuna ah to,kin ga yadda yake hararenmu kuwa?” Na ja tsuki ina mai cewa “to ai shi ya kawo ni gida” cike da mamaki ta ce “da gaske?” nan fa na bata labarin duk abin da ya faru. Ta ja numfashi ta ce “yanzu tukunyar na nan wurinki?” “Eh bari duk ranar da kika zo zan nuna miki ” na faɗa ina mai jingina jikin pilowe da na ɗora a baya,haka muka yi waya sosai ni da ita kafin mu yi sallama.Na cije leɓena na ƙasa ina mamakin maganar da na furtawa babban malami kamar Sheikh Rayyadeen,sai yanzu ma na ji kunya na rufe fuskata da tafin hannu ina mai cewa “ oh Khadeeja me ya shiga kanki da har za ki cewa Sheikh ya furta kalaman ƙarya?” sai kuma na ji tsoro kar ya ɗauke ni wata iri wacce ba ta da tarbiyya.Karon farko da na ji cewa ya zama dole na samu lambarsa,sai dai duk iya binciken shafinsa ban ga inda ya taɓa ɗora lambar ba a dole na haƙura na shiga rungume pilow ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba ya kai ni duniyata ta MAFARKI. Yau kuma cikin wata asibiti ce na tsinci ruhina,ina tafe ina dube-dube kamar wacce ta ɓata kafin kuma na soma shiga ɗaki bayan ɗaki har na isa wani mai lamba uku.A can ƙarshen gado na hango ta tana kuka,gashin kanta duk ya cunkushe haka ma kayan jikinta duk sun yage,yayin da fatarta ke fitar da jini saboda yagar kanta da take yi da manyan akaifunta. Ina yin tsaye bakin ƙofar ta tsaya cak da kukan da take yi tana kallona,a zahiri mahaukaciya ce amma a baɗini da hankalinta rasss. “Me yasa ki ke zaune a asibitin mahaukata alhalin da hankalinki?” ita ce tambayar da na jefo mata. Jikinta ta ƙanƙame tana mai cewa “alhaki ne! ” tako biyu na yi kawai amma na ganni a gabanta,hannunta na kama na jimƙe sosai sai ta soma magana kamar an kunna rediyo. “Ƴar talakawa ce ni,na auri talaka na rayu da shi na tsawon shekaru har na haifa masa ƴan mata biyu.Amma rayuwarmu na nan a talauce,ƙarfin babu ta sa na soma yin aikatau don ciyar da yarana saboda mijina ya koma cima zaune.Yawan aikin da nake yi yasa cikina ɓarewa ina tsaka da gugar tiles,nan na zube jini na bin ƙafafuna ina murƙususu.Na ɗan fita hayyacina na wani lokaci kafin na dawo normal,nan na yi tozali da abu ma fi girman ɗaga hankali.Uwar mai gidan da nake yi wa aiki ce na yi tozali da ita ta kwashe ɓarin da na yi ta saka shi a kwalba tana siɗar yatsunta da suka yi kace-kace da jini.Ƙwala-ƙwalan idonta kuma suna juyawa babu sirki kamar na ƴar tsanar roba,wagegen bakinta ta buɗe mini tana wani irin murmushin ajali kafin ta ce “ni da mai ciki ba mu iya zama wuri guda,yawuna tsinkewa suke yi ” wani tashin hankalin ne ya sake rufe ni,don kuwa na fahimci ita ɗin mayya ce na yunƙura da niyyar maƙure mata wuya shi ne ta cire igiyar da ke saita tunanina ta haɗiye a bakinta,kin ji dalilin zuwana a nan ɗin ” ta ƙarashe faɗa tana mai janye hannunta yayin da kuma idonta suke canza kala zuwa kore kamar dai na Rashida. Ina gama jin labarinta na fito daga cikin ɗakin,cikin wani lungu mai tsananin duhu wata mata ta bayyana a gare ni tana mai yi mini wani jawabi mai kamar bushara.“Duk wasu matsalolin da muke faɗa miki a MAFARKI don su nusar da ke ne gidan da kike son kutsa kanki ciki.Hadiza(cewa da Ummah mahaifiyar Daddy) ta yi wa duniyarmu hidima wannan yasa muka yi alƙawarin kare bayanta, wannan ɗin haƙinmu ne.Ungo wannan ruwan ki zuba su a cikin baƙar tukunyar da kika ɓoye a ƙarƙashin gado” ta ƙarashe tare da miƙo mini wata ƴar mitsitsiyar kwalba na karɓa tare da jimƙe ta gam cikin tafin hannuna.Daidai nan na farka,wata irin ƙirshiwa ce nake ji ina shirin dirowa daga kan gado na ji wani abu cikin hannuna ko da na duba sai na yi tozali da kwalba.Nan take kuma mafarkin da na yi ya dawo mini cikin kai,sauka na yi na jawo tukunyar na buɗe ta tare da zuba ruwan ciki wani abin mamaki shi ne yadda ɗigon ruwan da ba su wuce biyar ba amma suka kusan cika tukunyar .A sannu a hankali na ga ƙwan na ƙara girma yana yin motsi,kafin kuma ya soma tsagewa .Ido kawai na zuba ina kallo har ida buɗewa duka,wata ƴar jaririyar halitta ta fito mai kamar mutum kamar kuma aljana,tana da manyan ido da kunnuwa faka-faka sai ɗan ƙaramin hanci.Wani tsalle ta yi tare da yin suka kan jikina,na buɗe murya cincin ƙarfina na ƙwala razananiyar ƙara da mugun sauri ta sauka daga gare ni ta yi suka ta haye gadona tana mai zubo mini idonta da suke wasar canza launi.... Normal group 300, VIP 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [15/12 09:13] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 07 Ban taɓa shiga tashin hankali ba irin na yanzu,kuka nake yi na rashin mafita.Ga shi dai ni ce da kaina na binciko wannan baƙin sirri amma kuma sam ban ji zan iya zama tare da aljana ba a ɗaki guda,ita kuwa shegiyar halittar sai ci gaba take da kallona tana juya ido kafin ta ce “ sunana Nina halittar prophecy,na rayu a wasu ƙarnikan baya,yanzu kuma kin sake haifata kin raya ni ” Jikin ƙofar toilet na ƙara matsawa na riƙe ta gam,jin kuma wata lukutar masifa wai ni na haife ta.Wani tsallen ta sake ta diro ƙasa kafin ta ci gaba da cewa “kar ki ji tsorona,aikina shi ne nusar da ke hanyar da za ki bi don cimma burinki na samu Sheikh Rayyadeen ” Ambaton sunansa da ta yi shi ya ɓarar mini da dukkan tsoronta da nake ji,kan gwiwaina na zube ina mai cewa “da gaske za ki taimaka mini na samu Sheikh Rayyadeen?” Ta jinjina kai kafin ta ce “bani hannunki na dama” a tsorace na miƙa mata su,caraf ta saka yatsana manuniya a baki ta dantse da haƙoranta wani abu ya shige ni mai kamar lantarki ya soma caza ni kafin wani lokaci na tsinci kaina kwance a kan capet Daddy da Momy da kuma Ummah kewaye da ni.Ɗaya bayan ɗaya na kalle su kafin na ja numfashi na ce “meke faruwa da ni kamar ni kamar ba ni ba?” “Alhamdullah tun da kin farka,je ki haɗa mata wani abu ta samu ta ci” cewar Daddy yana mai kallon Momy,amma Ummah ta yi karaf ta ce “a'a bari na haɗa mata” sai ta fita. Tashi na yi zaune ina mai ɗan lumshe ido haɗi da sauraren yadda jijiyar gefen wuyana ke wani bala'in harbawa.Babu jimawa Ummah ta kawo mini abinci,amma kallo guda na yi masa na san da ta saka magani amma haka na ci kafin in shiga toilet na yi wanka da ruwan ɗumi.Ko da na fito babu kowa ɗakin,kimtsawa na yi na saka sabuwar pad tare da uniform ɗin makaranta.Ina saukowa ƙasa duk sai suka yi murnar ganina,sai a lokacin na gaishe su Daddy ya ce “mu je na sauke ki makarantar a motata ” cike da jin daɗi na yi masa godiya kafin mu fita,yau a gaba na zauna kusan Daddyna sai da ya fara tuƙi a babban titi sannan ya miƙo mini wayata wacce ban san yaushe ya ɗauke ta ba kuma ni kaina da na tashi ban ma neme ta ba. Ina karɓarta sai na ga an ɗora mini hoton Sheikh Rayyadeen kan fuskar wayar,hakan ya tabbatar mini yanzu Daddy ya san mene ne burina wata irin kunya ce ta kama ni,sai kawai na sunne kai ina shafar screen ɗin da ke ɗauke da haske yana nuno mini abincin ruhina. “Tun yaushe kuka fara soyayya Ummita?” Daddy ya jefo mini tambayar. A kunyace na ce “Daddy ba soyayya muke yi ba,hasali ma bai san ina sonsa ba” “Don me? Ai sai ki sanar da shi” da sauri na ɗago kai na dube shi jin abin da yake cewa,ya jinjina mini kai kafin ya ce “manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kansa ya yi mana nuni da hakan,ya ce duk wanda muka ji muna so mu faɗa masa” Na rufe fuska na ce “ni dai Daddy kunya nake ji” yayi ƴar dariya kafin ya ce “duk da cewa ba zubar da aji ba ne mace ta furtawa namiji kalmar so,amma kuma na ji daɗin haka daga gare ki .Na san ba ke ce ta farko da kike sonsa ba,ƙila ma har wasu sun taɓa furta masa to ke ina so ki zama daban da sauran.Duk namiji in dai malami ne shi to yana ƙaunar ɗalibarsa ko ɗalibi mai ƙwazo,to ke yi ƙoƙarin kasancewa haka” A shagwaɓe na ce “Daddy tun tuni fa nake ta ƙoƙarin hakan,amma a cikin ajinmu fa har da mahadatan Alkur'ani akwai” “Ke ma ki haddace Ummita ” “In sha Allah Daddy” na furta daidai nan kuma muka kawo makarantar,har ciki ya shigar da ni na yi masa sallama na fita.Daddy na tafiya na kai dubana inda ake parking amma ban ga motarsa ba,jiki a sanyaye na nufi sabon ajinmu sai na tarar da wani sabon tsari wai layin da za mu zauna daban.A gaba na zauna,babu jimawa Mujahida ta zo ita ma bayan mun gaisa take cewa “yau kuma mafarkin me kika yi?” shiru na yi kafin na tuna matar da na gani a gadon asibiti,bayan na gama labarta mata ta ce “ko mu je can asibitin mahaukata ɗin mu gani?” Na ce “har mu tashi daga makarantar safe,amma kin san muddin na ganta har azahiri to wallahi zan sa a raina ba wai kawai MAFARKI ba ne akwai wani ɓoyayyen lamari da ke faruwa da ni” Shiru duk muka yi sakamakon shigowar malam Hafiz wanda ya kasance shugaban makarantar. “Ku fitar da littattafai ko kuma alƙur'ani ku yi karatu yanzu Sheikh ya kira ya ce zai zo a makare a shaida muku ku fara yin karatu kamar yadda ya tsara muku” yana gama faɗar haka kuwa aka fara yin karatun sai dai yau ɗin ma Sadiya ce ke son lallai sai ta koyar da ni amma na ƙi. ★SHEIKH RAYYADEEN Tun bayan da ya fito daga gidansu Khadeeja ya nufi wata makaranta da yake bada karatun dare zuciyarsa fal takaici da haushin Deeja.Ya hau ya zauna kan cewa raina shi ne ta yi shi yasa har take basa umarni,umarnin ma na ya saɓawa Ubangijinsa yayi ƙarya.Sosai ma yayi mamakin cewa ƴar malam Ben Abdullahi ce,don su haka suke kiransa .Ya ja tsaki ya fi shuren masaki,yana jin inda ma da ta ce yayi ƙaryar kwashe ta yayi da mari.Yana isa makarantar kafin ya shiga ciki sai da yayi sallar isha'i sannan ya wuce ya koya musu bayan nan ya dawo gida.Yau ba tare da shi aka ci abincin dare ba wannan yasa bai san abin da ke faruwa ba sai da ya shiga babban falon sashensu ya tarar Ammy na zaune tana kuka idonta sun kaɗa sun yi ja sosai. Tun kafin ya ji dalilin kukan nata hankalinsa yayi matuƙar tashi,da sauri ya ƙarasa yana mai yi mata sallama tare da tambayar “Ammy lafiya me kuma ya faru?” Kamar wata ƙaramar yarinya haka ta jimƙe hannunsa gam tana mai ci gaba da yin hawayen da yake ɗaga masa hankali. Jijiyoyin kansa ne duk suka fito,ya ce “na sani yau ma Grand-Maa ce ta taɓa ki babu komai ni na san abin da zan yi, Please Ammy ki bar kuka” Ya faɗi haka tare da goge mata hawaye,ita kuma ta jinjina masa kai.Dakyar ya samu kanta ta shaida masa abin da ya faru,“Maa ta baiwa mahaifinka zaɓi ko dai ya sake ni ko kuma ita ta bar masa gidansa sai ya je ya canza uwa,shi ne shi kuma sam babu uzuri ko tambayar dalili ya hau ni da masifa har da cewa asiri na yi masa” ran Sheikh ne ya ƙara ɓaci sosai.Sai dai bai sanar da ita matakin da ya ɗauka ba,ɗakinsa ya shiga ya ɗauko mata maganin ciwon kai da na bacci ya bata ta sha babu jimawa kuwa bacci ya ɗauke ta. Babban falo ya fita ya je buga ƙofar ɗakin Saude mai aiki,bayan ta fito ya shaida mata yana son a yi masa aiki ne.Haka ya ja ta can zuwa sashen Ammy ta soma jera kayanta a trolly yayin da shi kuma ya kira amininsa Sheikh Laminu yana son a kawo masa babbar mota wacce za ta kwasar masa kaya,duk da shi ɗin bai ƙasar amma motocinsa ne haka yasa aka aiko mota biyu har da ma masu kwasar kaya.Sai ga shi abu kamar a mafarki ana kwashe kayan Ammy,hankalin Mama ne ya tashi duk da ta san abin da ya faru amma ba ta yi tsammanin gaske Abban yara zai iya sakin abokiyar zaman nata ba.Tambayar duniya ta yi wa Sheikh ya ƙi yi mata magana,ga Ammy sai bacci take yi sai bayan an kwashe abubuwan amfaninta kawai, ya tashe ta shi ma ba wai ta wartsake ba ne garas haka ya taimaka ya riƙe ta suka fita ya saka ta a motarsa,Rashida haka ya kai ta mota ita dama kayanta suna can gidan mijinta.A nasa ɓangaren ma kaf kayansa ya kwashe,motarsa ce a gaba yayin da na kayansu ke bin bayansa har suka isa babbar palace ɗinsa wacce ya gina domin matarsa da kuma ahalin gidansu sai dai kuma a dare ɗaya an rushe masa plan ɗin surprise ɗin da yake son yi musu. Duk wani abu da za a buƙata a cikin rayuwar ɗanAdam duk ya saka su.Lokacin da suka iso gidan ƙarfe ɗaya saura,amma tsabar yadda zuciyarsa ke tafasa haka cikin wannan daren ya narka musu kuɗi suka shiga jera masa abubuwansa da kayan jikinsa,na Ammy kuwa Saude ce ta fara shimfiɗa zanen gado suka kwantar da ita kafin ta soma aikin amma yadda bacci ya fi ƙarfinta haka ta haƙura ba ta yi shi ba. A ɓangaren Sheikh kasa baccin yayi,baƙin ciki ne iri-iri ke taso masa dakyar ya iya tashi ya nufi danƙareren benen saman da yasa aka gina masa duk don domin shi da matarsa ,amma ga shi an dawo babu ita a ciki.Haka ya soma ƙarewa ɗakin kallo tun daga kujeru har labulaye da capet sun machin,ba kuma sai an faɗa maka ba miliyoyin kuɗi ne aka kashe ba.A hankali ya taka ya shiga ƙaton bedroom ɗin wanda shi ma tsabar girmansa yasa sai da aka zuba masa kujeru sai dai wannan ɗin ɗaya ce mai katafaren girma kai kace ma wani gadon ne,a gabanta an ɗora capet mai taushi da ƙaramin banci na gilas .Shi kuwa gadon wasu labulaye ne farare tasss sun kai goma aka yi masa wata kwalliya da su ta yadda in mutum na ciki ba za ka sani ba. Wanka ya yi sannan ya shimfiɗa dadduma ya shiga jero nafiloli sam bai rumtsa ba ko kaɗan har aka kira sallah ya fita yayi,sai bayan ya dawo ne ya soma jin baccin kafin ya kwanta sai ya turawa shugaban makaranta saƙo.Sosai ya samu bacci mai daɗi ya ɗauke shi,ƴan magana na cewa abin da ka kwanta da shi a rai to shi kake mafarki hakan ce ta faru da Sheikh Rayyadeen ya yi mafarkin yayi aure sun tare a wannan gidan har da ma haihuwar yara biyu.Ko da ya farka kusan ƙarfe takwas na safe,wanka ya fara yi ya saka jallabiya ya sauko ƙasa amma da mamakinsa Ammy ya tarar a falon ita da mai aiki Saude. A hankali ya ƙarasa yayi musu sallama tare da gaishe su,yana zaunawa ita Sauden sai ta tashi yayin da shi kuma ya sunne kai yana mai cewa “yi haƙuri Ammy na san ranki ya ɓace da kika tashi kika ganki a wannan gidan” “Ko kaɗan raina bai ɓace ba Deeni,in akwai abin da ban ji daɗinsa ba shi ne ta yadda silata ka rushe plan ɗinka na sai ranar da za a kawo matar aurenka za ka shaidawa ahali su ma nan ɗin gidansu ne” Yayi wani ɗan murmushi wanda a cikinsa za ka iya hango damuwa ya ce “Ammy lokacin ina da burin auren Safara'u ne,na yi tunanin ita za ta ƙetarewa baƙar ƙaddarata sai dai ashe ita ce ma za ta rufe babin kwaɗayin yin aure a rayuwata” Ammy ta yi ɗan shiru kamar mai nazari kafin ta ce “ina yi maka kwaɗayin yin aure Sheikh Rayyadeen ɗina,kar ka taɓa yanke zuwan tsammani daga Ubangijin rahama”' Ya ce “na sani Ammy,ba wai na fidda rai ba ne a'a banda burin son ƴar kowa gudun kar na shafa mata kashin kaji ” “To ka auri Khadeeja” Ya wani dube ta da sauri kafin ya ce “Ammy ban sonta ” Ta ce “su ma ai sauran waɗanda ka yi burin aure babu wacce ka taɓa so Deeni” “Yunwa nake ji Ammyna,duk jiya ban ci komai ba” ya faɗa tare da jingina jikin kujera yana jin zuciyarsa na dokawa,tsoronsa guda ɗaya ne tak kar Ammy ta ɗaukin dogon buri ta ɗora kan sai ya auri Khadeeja.Bai so hakan ya kasance abu na farko da zai bijire wa umarninta,don shi kaɗai ya san matakin tsanar da yake yi wa Khadeejar.Sam zuciyarsa ba ta yarda cewa wannan za ta iya ma mata tagari ga mijinta ba ballantana uwar kirki ga ƴaƴanta,to ita kanta yarinya ce tana buƙatar a yi mata tarbiyya da kuma horon girmama manya,in son samu ne a bulalaye ta domin ta cire rashin kunya da tsaurin ido.Ya ja tsaki a fili tuna yadda jiya ta wani tsure shi da ido ko kunyarsa ba ta ji ba,tsabar iskanci kuma ko gaishe shi ba ta yi ba sai ma dai ƙawarta ce mai hankali ta yi haka. Ammy wacce ta zuba masa ido jin lokaci guda ya canza musu akalar zance,tana shirin tashi kuma ta ji yayi tsaki ita kuwa murmushi ta yi don tana ji a ranta tunanin Khadeejatu ne yake yi. Kitchen ta shiga ta haɗo masa abin da suka ɗan girka ta kawo masa,da mamaki ya ce “Ammy ina kuka samu gas ?” “Na mai gadi ne Saude ta karɓo ,shi kuma na aika ya sayo mini komai” ta basa amsa . Ya ce “in sha Allah zuwa an jima duk za a kawo komai na dangin abinci har da butalin gas ɗin” Ammy ta ce “Allah yi maka albarka ya kare ka,ta tsare ma dukiyarka ya kuma ƙara buɗi na alkhairi ” Ya amsa da “amin Ammyna na gode sosai” Bayan ya gama yin breakfast ɗin ya koma ciki,sai da ya sake yin wani wanka yayi brush ya fesa turaren baki sannan ya fito.Cike da nutsuwa ya shafa mai ya gyara saje da guminsa da kuma sumar kansa wacce take kwance luf irin ta larabawa.Yau ma fararen kaya ya saka,sai ya ɗora alkyabar maza mai ruwan ƙasa ya saka hirami ja.Tsadadiyar agogo ya ɗaura a hannun dama,ya saka takalmi ƙafa ciki irin rigarsa wani turaren ya ƙara feshe jikinsa da gemu kafin ya ɗora farin gilashi ya sauko ƙasa. A falo ya tarar da Ammy tana baiwa Rashida abinci,kusa da ita ya je ya tofa mata addu'a kafin ya yi wa Ammy sallama ya tafi.Tuni kuwa an wanke motarsa,ya shiga ya zauna bayan ya yi addu'a yana shirin tuƙawa Ammy ta fito tana tsayar da shi . Ta ƙaraso tana mai cewa “ga key ɗin motar Deeja ka kai mata” yadda ta game fuska babu hanyar yi mata gardama yasa shi ya karɓa kafin ya wuce. Ko da ya isa makaranta ƙarfe tara saura,sai da ya fara zuwa suka gaisa shi da malam Hafiz kafin ya je ya buɗe keɓaɓen ajin da yake tara malaman dukkan makarantar in yana son yin magana da su wanda su kuma ɗalibai suke yi wa lakaɓi da ajin hutun malamai. Yana buɗewa ya ga wani baƙin abu yashe a ƙasa,ya duƙa ya dauƙa sai ya ga niƙafi ce.Da mamakin ta ya aka yi ta zo nan ya je ya ƙarasa ciki,shaf ya manta da an kawo masa Khadeeja har na cikin babu lafiya.Cikin wata jakarsa ya cilla niƙafin sannan ya soma bincike har ya nemo littafin da yake so. ★KHADEEJA Ni ɗaya na buɗe alƙur'ani ina yin hadda,ban damu ba sam da ƙin zuwa a koyar da ni don ni ban ga wani aibun yin haka ba.Mujahidah kam an tafi ana ta yi mata gyara,sauran ɗaliban ma haka.A hankali na miƙe saboda yadda na ji zuciyata na tashi,bakin ƙofa na fito na tofar da yawu sai dai aka yi rashin sa'a suka sauka kan rigar Sheikh Rayyadeen wanda yake dab da ya shigo ajin,sam ban gansa ba .Na waro ido a tsorace ina kallon yadda ya wani ja burki yana kallon inda yawun nawa suka sauka...... Normal group 300, VIP 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 🚫 Waɗanda suka yi payment su yi mini magana na saka su group Please [16/12 07:55] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 08 Dukkan illahirin jikina rawa yake,yadda Sheikh Rayyadeen ya wani haɗe fuska kai ka ce bai taɓa yin dariya ba. “Biyo ni ” ya faɗa cikin tsananin fushi kafin ya juya,kamar zan faɗuwa haka na take masa baya har zuwa ajin malamai.Ya buɗe ya shiga ,kamar ba zan bisa ba sai kuma na ɗan shiga tare da tsayawa bakin ƙofa. “Ban san wane sheɗani ne a kanki ba da har yake yi miki huɗuba ki yi mini abubuwa iri-iri,to ko ma uban waye ya tsaya iya kanki saboda in kuka shigo gonata sai na yi mugun baki mamaki.Ban son rashin kunya da tsaurin ido,duk wanda ya yi mini ɗaya daga cikinsu zane shi nake yi” ya ida furicin tare da juyowa rai ɓace hannunsa na gani riƙe da bulala. Ko kaɗan ban taɓa tunanin zai doke ni ba,shauɗar da ya yi mini ita ta maido ni daga duniyar mamakin da na tsunduma.Na ƙara tare da sosa wurin,cike da masifar da ban san yana da ita ba ya ce “wato don kin ma raina ni ina yi miki magana hankalinki na wani wuri ,zaunaaa ” ya ƙarashe tare da sake shaɗa mini bulalar a karo na biyu.Babu shiri na zube kan gwiwaina,ya ɗaga zai yi mini ta uku na yi saurin kamo ƙafarsa cikin kuka na ce “don Allah Sheikh ka yi haƙuri ba zan sake ba,amma kar ka doke ni ban so” hannuwan nawa da na riƙe masa ƙafa ya shaɗe na sake shi da mugun sauri ina jin wani zafi yayin da shi kuma ya wani ja da baya yana jan numfashi kamar zai mutu.Ba tare da ya bani damar fita ba na tashi a guje na bar ajin na nufi namu inda muke karatu.Kamar an jefo ni haka na faɗa ciki ina matsanancin kuka, Mujahida da ke kusa da ni ce take cewa “a kullum ina faɗa miki ki rage wannan shagwaɓar taki nan makaranta ce ba komai ne za ki nuna ke ƴar Daddy ce ba amma ba ki saurarena.Waɗanda ke kusan window sun ga duk abin da ya faru,tun bayan fitarki ake cece-kuce don ma malam Hafiz ya shigo ya tsawatar ne da ƙila sun ta yi miki dariya” Kanzil ban ce mata ba don baƙin ciki,ita da ya kamata ta yi rarrashina amma ta zo tana yi mini surutu.Na ɗauki kamar minti biyar kafin na ji sallamarsa,duk aka amsa masa kuwa.Gudun kar na yi wani laifin na gyara zamana ina shafar ido,tambayoyi ya fara nan uwar iya yi Sadiya ta shaida masa ni kaɗai ce na ƙi zuwa a koyar da ni. Idonsa masu masifar tsoratar ni ya zubo mini,kamar daga sama na ji ya ce “zo ” kasa motsi na yi don duk a tunanina dukana zai yi.Duk ƴan ajin suka zubo mini ido,ina jin Mujahida na salalami “innalillahi!” Wani abin mamaki yana cewa na je ɗin ya ɗauke idonsa a kaina ya soma buɗe alƙur'ani.Zuciyata na ɗan dokawa na tashi ,kamar mai koyon tafiya haka na ƙarasa kusa da babban teburin gabansa na ja na tsaya. “Me yasa ba ki son yin karatun Alkur'ani? Ko ba ki iya komai ba kawai turo ki aka yi aji na gaba?” ya tambaye ni tare da ɗago kai,ni kuwa kayan jikinsa nake kallo yadda ya wani cire rigar sama kawai don na tofa masa yawu. “Kwashi kayanki ki koma tsohon ajinku ” ya faɗa a hankali amma kana iya jin feshin wutar da zuciyarsa ke yi. Sai a lokacin na yi magana “ka yi haƙuri na iya karatun ne” Hannuwansa ya game wuri guda ya ɗora haɓarsa tare da tsura mini na mujiya kafin ya ce “ina jinki Malama koyar da ni” Da sauri na sunne kai ina murmushi don na fahimci me yake nufi.Ya turo mini Alkur'ani wanda shi ne da kansa ya buɗe mini shafin,idona cikin nasa na jawo alƙur'anin tare da juyo shi gabana na soma karantawa cikin ƙira'ar da Daddyna ya koyar ni,sam ban taɓa sanin ainahinta ta Sheikh Rayyadeen ɗin ce ba saboda in banda cikin sallah ban taɓa jin yana koyar da karatu ba. Daga can baya na ji muryar A'isha tana cewa “ma sha Allah! Yau dai mun ji wacce ta iya bin ƙira'ar Sheikh ” duk sai wasu suka shiga yin murmushi mai sauti. Ni kuwa shi na kalla sai na ga ya ƙara haɗe rai kuma ko arzikin kallo ban ƙara samu ba haka ya dinga yi mini binciken karatun kamar wani makaho har ya kammala ya ce na je na zauna. Ƙin tafiya na yi na sake cewa “don Allah malam ka yi haƙuri ka bar fushi da ni, wallahi muddin ka ci gaba da yi to ba zan samu sukuni ba har abinci ba zan ci ba” Yadda duk mutane suka zubo masa ido suna kallo yasa shi cewa “na ji to tafi ki zauna” Na ɗan yi murmushi na ce “da gaske ka haƙura?” ya jinjina mini kai cike da murna na je na koma wurina na ci gaba da kallonsa cike da so.Shi kuwa Sheikh Rayyadeen karatu ya soma koyar mana, lokaci zuwa lokaci haka nake tsintar idonsa cikin nawa a haka har aka fita shan iska. Muna fita na rungume Mujahida tare da bata labarin yadda muka kwashi adashen tsiya ni da Sheikh bayan na tofa masa yawu daga ƙarshe na ƙara da cewa “wannan dukan da ya yi mini sosai na ji daɗinsa,kin ga yau zai wuni da tunanin abin” Ta ja tsuki tana mai cewa “ni dai wuce mu tafi mu yi sauri mu dawo kar lokacin dawowa aji ya yi mu kuma muna can” “Ina za mu tafi?” na tambaye ta,sai ta waro ido tana mai cewa “asibitin mahaukata ko kin manta?” ina shirin yin magana wani abu ya ɗauki hankalina yadda Sadiya da ƙawayenta suka tunkari aji alhalin Sheikh na ciki. Da wani mugun sauri na ja hannun Mujahida muka zagaya bayan aji don ta can ne zan fi jin abin da za su yi wurin nasa. Kunne na kasa ina saurare,ina jin lokacin da Sheikh ya ce “ina jinku me kuka zo yi?” Kame-kame suka fara kafin ɗaya ta ce “dama...dama mun zo ne mu sanar da kai ɗaya daga cikinmu ce ke sonka shi ne kawai” Na yi tunanin zai balbale su da masifa,zuciyata har wani bugawa ta yi jin ya ce “ita wacce ke son nawa ba ta da baki ne sai ke? ” “A'a malam ba haka ba ne kunya take ji” “To ku fita ku bani wuri” ya faɗa . “Sadiya ki faɗa masa mana” na ƙara jin wata ta faɗa ,ƙiri-ƙiri Sadiya ta canza harshe zuwa larabci ta shaidawa Sheikh Rayyadeen tana sonsa har da su cewa in bai aure ta ba mutuwa za ta yi. Ban san matakin fushi da kuma tashin hankalin da na tsinci kaina ba,sai da na ji ƙusoshin kaina na kwancewa yayin da wani abu ya soma yi mini motsi da mugun ƙarfi na ƙwala wata razananiyar ƙara wacce ta karaɗe dukkan makarantar.Duk wata bishiya da ke da kwai sai da ta kaɗa cike da razani, wannan karon hankalina bai gushe ba duka ina jin lokacin da Sheikh ya leƙo ta window yana tambayar Mujahida wacce ke faman riƙona. Can kuma suka zagayo su duka huɗun,cikin bayar da umarni yasa aka kai ni ajin malamai.Karatu ya soma yi mini su kuma suna tsaye a kaina, Mujahida kawai ce ta riƙe ni.Kamar zan mutuwa haka nake ji,shigowar malam Ibrahim ce yasa sauran suka fita iya ƙawata ce kawai ta tsaya. Wani abu ya shaƙa mini a hanci wanda ya kusa kai ni lahira ban shirya ba,wani irin ƙarfi ne ya zo mini na turo Mujahida zan gudu.Sheikh Rayyadeen ya riƙo ni da hannu ɗaya tare da mini wani riƙaƙen kamu wanda na kasa kubcewa,ci gaba yayi da karatun yana bugun tsakiyar bayana da hannunsa. Kamar ana ruwa haka na soma jin wani sanyi na rufe ni,yayin da wani abu mai zafi da ke cikin jikina ke yin ƙasa.Kamar wata ƴarsa haka yake ganin Khadeeja,shi sam bai ma taɓa ganinta matsayin cikakkiyar budurwa ba duk in Ammy na yi masa zancen ya aure ta har mamaki yake ji. “Khadeejatu?” muryar malam Ibrahim ta daki kunnena, lokacin tuni na ida samun cikakken hankalina.A hankali na sa hannuna kan na Sheikh Rayyadeen don cire nasa da yayi mini mugun riƙo don har wani zafi nake ji.Sai da ya kalli tsakiyar idona kafin ya sake ni,a hankali na miƙe kamar zan faɗi Mujahida ma ta tashi tana mai kamo hannuna. “Ya jikin naki?” ya sake tambaya ta,ban basa amsa ba sai ma ƙeya da na sa na fice. Sheikh Rayyadeen ji ya yi kamar ya haɗiye zuciya ya mutu don takaicin abin da ta yi wa malam Ibrahim shi kuwa da wani irin kallon so ya bi bayanta har ta fice. Yana maido hankalinsa ga Sheikh ya sha jinin jikinsa saboda irin mugun kallon da ya ga yana yi masa. “Khadeeja har yanzu yarinya ce,sai a hankali ” ya furta don ya ga da alamu ran Sheikh ɗin ya ɓace yadda ta tafi ba ta yi musu sallama ba haka kuma babu godiya. “Kana iya tafiya” Sheikh ya faɗa a takaice. Malam Ibrahim ya ce “don Allah ina neman alfarma ne,a yi haƙuri da ni son Khadeeja ya daɗe a zuciyata ne shi yasa na kasa controling kaina,na san haramun ne a bisa dokar makaranta yin soyayya da ɗaliba muddin dai ba a wajen nan ba ne za ku yi ta.Amma ina so ni dai a bani wannan damar zan dinga koyawa Khadeeja karatu duk in lokacin shan iska ya yi ta haka ne ƙila za ta yarda da ina sonta” Tun da ya fara zuba Sheikh ya tsura masa na mujiya har ya dire,da sauri ya juyar da kai yana mai cewa “ka tambayi mahaifinta ni malaminta ne kawai,sannan wurin shugaban makaranta ya kamata ka nemi izini ba wurina ba” Jikin malam Ibrahim ya yi sanyi kafin ya ce “to in sha Allah! ” sai ya juya ya fita, Sheikh ya bisa da wani mugun kallo kafin shi ma ya fita don lokaci ma tuni yayi. Muna fita direct aji muka nufa,yau ɗin ma haka mutane suka yi mini caaa suna kallo yayin da Sadiya ke hararena kamar idonta za su faɗo.Samun kaina na yi da mayar mata da martani tare da jan tsuki,na furta “marar aji kawai” yadda ta waro ido shi ya tabbatar mini ta canki abin da bakina ya furta.Ni kuma raina sai yayi fari ƙal kafin na ɗauki ruwa na leƙa ta window na wanke fuskata juyowar ga da zan yi muka yi ido huɗu da Sheikh.Da wani mugun sauri na je wurina na zauna,shi kuma rubutu ya soma yi jikin babban allon aji kafin ya soma yi mana bayani kan tarihin rayuwar Annabi.Tsawon lokaci kafin ya tsaya a wani wurin sakamakon lokacin tashi da ya yi,haka aka fara fita amma ni da ke a gaba ko motsi ban yi ba. “Tashi mu tafi Malama ni nan yunwa nake ji ban ci komai ba” cewar Mujahida. Na ce “to sannu acici uwar sakawa ciki abinci,ni me ki ga na ci?” “Na tafi don wallahi ba a gabana za ki sake yin wata tijarar ba” ta furta tare da ficewa,haka kowa ya fita aka bar ni a zaune ina kallon Sheikh Rayyadeen da ke faman latsa waya da dukkan alamu bai ma san ina nan ba. Murmushi na ga yana yi wanda ya fito tsantsar kyawunsa,muryar Ammynsa na ji tana cewa “yau yarona ya yi kewata har haka ne shi yasa ya kira ni video call?” A shagwaɓe ya ce “Ammy please kafin na iso a haɗa mini ruwan wanka kuma a sake gyara ɗakina don yau ina son na huta sosai” Ta ce “tuni fa Saude ta yi komai,sai ka zo” Ya shafi sajensa ya ce “ina jin yunwa kuma” “Oh! Ni Khadi Allah ya nuna mini dai ranar da za ka kawo mai yi ma girki don ni na kusa gajiya.Yawwa ka baiwa Khadeeja key ɗin motarta ” Ya dafe kai ya ce “ciwon kai dai,don Allah Ammy ki bar mini maganarta zuciyata ta tafasa take yi.Yanzu dai gani nan tafe yanzu in sha Allah ” yana gama faɗa haka ya kashe kiran,ni kuma da mugun sauri na yi kwance jikin table ina mai rera kuka a hankali. Inuwarsa da na gani a tsaye yasa na fahimci ya farga da mutum a ajin.“Ke?” ya furta,a hankali na ɗan ɗago kai na dube shi.Ya haɗe fuska tamau kamar ba shi ba ne ya gama zuba shagwaɓa,“me kike yi nan?” Ya tambaye ni,wani haushi ya rufe ni wato bai ma ga kukan da nake yi ba ballantana ya rarrashe ni.Ban ce masa komai ba,shi ma bai ƙara ba sai key ɗin motata da ya ajiye mini ya fice na bi bayansa da kallon mamaki kafin na tashi da mugun sauri na fita. Sadiya na tsinkayo can nesa kusan inda yake ajiye mota,da sauri na ga ta nufe shi tare da karɓar jakarsa ta kai masa har mota.Bayan ya buɗe ya shiga ya zauna,ita ta yi tsaye ta riƙe murfi yayin da kuma suke yin maganar da ban san me suke cewa ba.Gudun kar baƙin ciki ya kashe ni na nufi masjid ɗin mata,ai kuwa a can na samu Mujahida tana waya ita da Yaya Hamza ko da muka haɗa ido taɓe baki ta yi tare da juya mini baya. “Taso mu tafi ga key ɗin motata ya bani” na furta,ta juyo da sauri kafin ta kashe wayar ta ce “ da gaske?” Nuna mata na yi,sai ta miƙe da sauri tana murmushi muka fito.Bakin hanya muka tsaya muka samu abin hawa ,duk da babu nisa haka muka je a taxi ɗin.Muna sauka kuwa na hangi motata,sai kuma na yi mamakin ta yaya aka yi har yanzu Sheikh bai zo ba. Kasancewar a hanya duk na baiwa Mujahida abin da ya faru sai cewa ta yi “ko ya tafi kai matsiyaciyar nan ?” Na yi shiru kafin na ce “ban iya na sani,amma tana yi yiwa motarsa na cikin gida” Mujahida ta ce “to sai dai in ke ɗaya za ki je amma wallahi ni ba zan shiga ba” haka na je na gaishe da mai tsaron get na shaida masa motar da ke ƙofa tawa ce tun jiya na bar ta a nan sannan kuma ina son ganin Aliya saboda yau ba ta je makaranta ba.Ƙofar ya buɗe mini na shiga,sai dai a farfajiyar gidan ma babu motar Sheikh.Maimakon na juyo a'a sai wata zuciyar ta ce mini na shiga na gaida Ammy,ina dab da shiga falon na soma jin hayaniya da alamun kuma faɗa suke yi. “Ba zan taɓa tafiya na maido Khadi ba saboda ba ni ne na ce ta tafi ba,ɗanta ne ya kwashe ta suka koma can saboda ya nuna mini isasshe ne shi sannan ya fi son mahaifiyarsa da ni.Ke kuma da ba ki kishin mijinki shi ne kike goya musu baya” murya babban mutum ce wacce nake kyautata zaton mahaifin su Sheikh ne. “Abban yara sam wannan ba adalci ba ne,yadda Maa ke da haƙi a kanka mu ma matanka haka.Amma babu komai ni ma gidanka zan bar maka sai uwa da ɗa su zauna su kaɗai” “Mahmuda in dai ni na haife ka to kar ka dakatar da Ramma ta yi ta tafiya,ai ba su kaɗai ba ne mata ni nan zan auro maka yarinyar ɗanyar sharrr” wannan karon kuma muryar wannan tsohuwar ce na ji wacce suke kira da Grand-Maa. Da sauri na yi baya jin kamar za a taho,ina fita na buɗe mota muka shiga ni da Mujahida sai da muka hau titi ne ta tambaye ba'asi na kuwa labarta mata kafin na ce “kakarsu Sheikh ba ƙaramar sheɗaniya ba ce” “Yanzu asibitin za mu je?” “Eh saboda ina son ganin mahaukaciyar nan,ina ji a raina kamar akwai abin da ta ɓoye mini a cikin labarinta sannan a wajenta ne kawai za mu samu tarihin gidansu Sheikh ” haka muka ta yin hira har muka isa asibitin. Kamar yadda tsarin yake sai ka je ka nemi izini sannan ka je wurin mutum,sai da muka je can muka nemi izini sunanta aka tambaye ni. Na ce “gaskiya na manta sunanta sai dai wancan lokacin da muka zo ni da Kakata a ɗaki mai lamba uku ne take” Shiru ya yi yana kallona na wani lokaci kafin ya miƙa mini wata ƴar guntuwar takarda na karɓa sannan muka fito.Kamar a MAFARKI haka na dinga bin hanyoyin har muka kawo ɗakin,ina yin tsaye ƙofar ta bada ƙiiii tare da buɗe kanta ban san ta ya aka yi ba ƙafata ce ta dama ta yi mini nauyi wannan yasa a dole na shiga da ƙafar hagu,wanda ya yi daidai da tashinta tana yin ihu.Da sauri na ƙarasa na kamo hannunta,shiru ta yi tana kallona da idonta da suke son canza siffa suna ɗaukar na tsohuwa kafin na kai ga furta wani abu fuskar Grand-Maa ta bayyana madadin ta mahaukaciyar,da wata irin murya ta maƙetata take cewa “wane ruhi ne ya zo wanda idona suka kasa ganinsa?” Shiru na yi ina nazari kafin na kai yatsana cikin idon nata na tsokane,muryar Grand-Maa na ji tana ihu kafin kuma fuskar baiwar Allah ta dawo normal.Ƙanƙame ni ta yi tana mai cewa “ki tafi da ni don Allah kar ki bar ni a nan” Wani likita ne ya shigo yana cewa “lokacin yi mata magani ya yi ku fita” sai ya matsa ya yi mata allurar bacci.... Normal group 300 ne, VIP 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBANK DM +22795045822 [17/12 09:25] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 09 Haka muka fito ba don mun so ba,makaranta muka koma don a can muke wuni kullum har sai an yi karatun maraice kafin mu koma gida. Mujahida ce ta nufi toilet,sai dai ba ta jima da shiga ba na ji ta fasa ihu.Da saurina na isa wurin ko ƙofa ba ta rufe ba tana tsaye kamar gunki. “Me aka yi?” na tambaye ta,da idonta masu zubar da hawaye ta yi mini alama.Ina dubawa na ga wani ƙadangare ne babba a kwance yana maida numfashi shi ma alamun duk a gajiye yake. A kallon farko da na yi masa na fahimci ba wannan ba ce ainahin siffarsa,ina son jin daga gare shi amma ganin Mujahida cikin wannan halin yasa na ce masa “ka fita daga toilet ka koma kan bishiyoyi tun da akwai su dayawa a cikin makarantar nan amma a nan za ka iya tsorata mutane ” ina gama rufe bakina ya soma jan ciki tare da nufo ƙofa Mujahida ta yi tsalle ta ɗale kan jikina wanda ya haifar mana faɗuwa don ba zan iya ɗaukar nauyinta ba.Ko da muka miƙe tuni ƙadangaren ya fice,ga kuma kayanmu sun ɓace da ruwan toilet duk da dai a tsabtace take . Cikin masifa nake cewa “ja can matsoraciya kin sa duk kayanmu sun ɓace” haka na cire zumbulelen hijabina na wanke shi Allah ya yi sa'a banda riga ta. Can wajen masjid na nufa don shanyan hijabin nawa amma sai na sake shi ya ƙara kwasar wata dauɗar sakamakon ido huɗu da muka yi da Sheikh Rayyadeen wanda ban san uwar me ta maido shi makarantar ba. Jikina na rawa na ɗauko hijabin tare da rufe ƙirjina kasancewar rigar da na saka mai ƙananun hannuwa ce.Kai ya kawar tare da yin gaba abinsa,hijabin da ban shanya ba na dawo da abina na ƙara wankewa na saka shi a haka nan.Sosai hankalina yake a tashe,na ji kunya sosai da ya ganni a haka.Mujahida ma ta lura da canjina amma kuma sai na ɓoye mata ban sanar da ita ba. Har aka yi sallah muka shiga aji hijabina bai bushe ba,duk da sanyin da ya kwasa na damuna haka na zauna da shi. ★SHEIKH RAYYADEEN Sosai yayi mamakin yadda Sadiya ta yi fatali da kunyarsu ta ƴa mata take wani zuba masa kalaman soyayya har da wani cewa tana iya rasa rayuwarta muddin bai karɓi soyayyarta ba,shi dai kallonta yayi kafin ya ce ta ja ya rufe motarsa.A hanya ma haka ya yi ta tunani har yake jin tsoron kar dai zuciyarsa ta aminta da zancen soyayyar.Yana isa gida da Ammynsa ya ci karo a farfajiya tana yi wa sabbin ƴan aikin da shi ne ya bada umarnin a kawo su bayani.Tana ganinsa ta saki murmushi tare da sallamarsu,yau jinsa yake matsayin Deeni wannan yasa yana zuwa kusa da ita ya kamo kafaɗarta ya soma janta ciki yana mai gaishe ta da tambayarta ya baƙunta. Sai da suka isa tsakiyar falo ne take cewa “ɗazu Mamarku ta kira ta ce ita ma za ta dawo nan” Ya ce “babu damuwa Ammy dama ai na tsara dukkan ahalin ne za su tare a nan” “Allah yi maka albarka” Ya amsa da “amin” har zai wuce ta ce “ina rigarka ta sama don ba haka ka fita ba,kuma ba ka saba rabuwa da ita ba” A nan take yadda Khadeeja ta tofa masa yawu ya faɗo masa,ransa ne ya ji ya ɓace amma ya daure ya ce “tana can makaranta Ammy ” “Ko yau ma kun yi faɗa?” “Haba dai Ammy sai ka ce wata babbar mace da har zan tsaya yin faɗa da ita,ɗalibata ce fa ƙaramar yarinya ko yau sai da na zane ta” yadda yake magana za ka iya cankar cewa zuciyarsa cike da zafi take. Ammy ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “je ka yi wanka,zan haɗa ma abincinka kafin ka fito” Haka ya wuce can sama, Ammy ta bi bayansa da kallo ita kaɗai take hango masa irin tarin kulawar da zai samu a wurin macen da yake ganin yarinya ce. Yana shiga ya rage kayansa sannan ya shiga toilet ya sakarwa kansa,shower ruwan na ratsa gashinsa suna sauka a duk illahirin jikinsa.Tunani yake yi ta yaya ne ma zai fallasa sirrinsa ga ƙanƙanuwar yarinya irin Khadeeja wacce ba ta wuce a yi rainonta ba,don ya lura akwai ƙurciya a tattare da ita in ba haka ba me zai sa ta dinga gudu a cikin makarantar duk jikinta na motsawa in ba don Allah yasa ma tsit wurin yake ba duk ɗalibai na cikin aji.Kansa ya kalla shi kansa ba kasafai yake son duban jikinsa ba to ballantana ya bari wata ta kalle shi.Babban towel ya jawo ya ɗaura a ƙugu sannan ya ɗauki ƙarami ya fita yana tsane jikinsa.Cike da nutsuwa ya shirya cikin jallabiya fara ya fesa turare sannan ya sauka ƙasa.Tuni kuwa Ammy ta kawo komai tsakiyar falo,ya zauna kan capet ya tanƙwashe ƙafafu da kasan ya zuba yayi Bismillah ya soma ci sai ga Ammy ta fito. Kan kujera ta zauna suna taɓa hira wacce rabinta ita ce ke yi don shi Sheikh Rayyadeen bai cika yin magana ba,don ma wai Ammyn ce shi yasa har yake kama mata amma haka a cikin abokai shi ɗan kallo ne in kuwa ka yawaita jin muryarsa hirar addini ce. Bayan ya gama aka kira ƴar aiki ta zo ta kwashe,ya miƙe ya haura sama yayi brush sannan ya sake fitowa.Kan kujera ya kwanta yana lumshe ido so yake ya ɗan yi bacci amma Ammy ta tsiro masa da hirar Khadeeja. “Me ta yi ka dake ta?” Duk da ya gane amma sai ya nuna bai san wace ce take magana akai ba.Ya ce “Wa fa?” “Deeja mana” ta basa amsa tana wani yin murmushi mai sauti, Sheikh ya ɗan ware idonsa ya ga yadda fuskar Ammy ta cika da annuri . “Tana da tsiwa ne yarinyar, ga taurin kai kamar rainon aljanu” ya faɗa yana cije jan leɓensa na ƙasa. Ammy ta yi dariya ta ce “ni ma lokacin da ina daidai gaɓar shekarunta haka nake,kusan Abuh sai ya dake ni musamman a fagen yawan yin faɗa da rigima” Sheikh ya ce “Ammy ki bar faɗar haka don goya mata baya,ni dai na san Mummyna ba haka take ba” Ammy ta kama kunnensa ta ja tana mai cewa “kai ma da kana yaro ai haka kake,kullum cikin yin faɗa kana damun Rashida ” Ambaton sunanta yasa Sheikh cewa “tana ina ma? Ya aka yi ban gan ta ba?” “Tana ɗakinta,na bata magani ne sai ya saka ta bacci ” “Mijinta ya kira?” “A'a bai kira ba,dama ina jiranka ne har ka dawo na sa ka kira mini shi” Sheikh Rayyadeen ya ce “a'a don me za mu kira shi? Kawai ki barsa ƙila ya bar sonta ne” “Kamar ya na bari? A'a ban so aurenta ya samu tangarɗa ka ga in sha Allah tana samun lafiya zan mayar da ita ɗakinta” Sheikh bai ƙara cewa komai ba,ganin haka Ammy ta dasa daga inda ta tsaya ta ce “ka bai wa Khadeejatun makullin?” “Na bata Ammy ” “To tashi ka dubo mini ka gani ko ta ɗauki motar” Sheikh ya ce “haba dai Ammy sai ka ce dai ita ce ƴarki ba ni ba,motsi kaɗan sai kin kira sunanta ko dai kin bar sona ne ban sani ba?” “Soyayyar taka ce ta saka nake yawan ambatonta tashi ka tafi Deenina” Ya turo baki gaba kamar wani ƙaramin yaro, Ammy ta gumtse dariyarta tana mai cewa in ka ganta kuma ka kira ni a waya ka bani ita . Bai ce komai ba ya je sama ya ɗauko key,shi takaicin ɗaya yadda zai tafi unguwar can har yayi tozali da gidan Abba .Amma haka ya daure ya tafi,bai ga motarta ba kawai sai ya yanke shawarar bari ya je makaranta yana zuwa kuwa ya tarar da motar.A hankali ya fita,sanin babu inda take tsayawa sai cikin masjid na mata yasa ya nufi can.Yana tsaka da tunanin me ma zai ce mata har ya samu su yi wayar da Ammy kwatsam ya ga abin da ya ɗaga masa hankali.Khadeeja ya gani babu hijabi ga shi rigar jikinta ƙarama babu wani tudu da kware da ba ta bayyana ba,tashin hankalin bai tsaya iya nan ba shi ne kama shi da ta yi yana kallonta ido cikin ido suka kalli juna.Da sauri ya kawar da kai tare da juyawa ,idonsa har wani rufewa suke bai gani sosai.Dakyar ya isa bakin motarsa ya shiga ya zauna yana wani haƙi kamar wanda ya yi ƴar tsere. Jikinsa na rawa ya soma lalube ya yi sa'ar ɗauko gorar ruwa guda,ya buɗe murfin kafin ya kafa ta a baki ya soma sha, numfashinsa na kokowa da magudanar jininsa. A hankali ya soma jin dama, sai ya jingina jikin kujera yana maida numfashi cikin ikon Allah larurar tasa ta lafa ba kamar wancan lokacin ba da ta saukar masa da zazzaɓi.Motarsa ya ja ya tafi gida,bai samu Ammy a falo ba kawai ya wuce ɗakinsa yana shirin kwanciya Sheikh Laminu ya kira shi don yi masa barka da tarewa cikin sabon gida . Har sai da kiran ya yanke wani ya shigo sannan ya ɗauka,shiru yayi sai ma abokin nasa ne ya fara gabatar masa da sallama.Sheikh ya amsa a sanyaye wanda tuni shi Sheikh Laminu ya fahimci damuwar saboda shi ɗin amininsa ne ba su ɓoyewa juna sirrinsu. “Aboki lafiyarka kuwa?” “Da dai dama,ya kake ya iyali?” “Lafiyarsu lau sai mitar dai ta kullum da ba ta barin bakinta” ya basa amsa. Sheikh ya ce “aboki ku je asibiti a yi muku gwaji don a gano matsalar daga wurin wa take” “Ina jin tsoro ne a ce daga gare ni ne,a zo Mardiya ta guje ni.Ya naka ɓangaren ka samu matar auren ne na ji ka cikin wani hali,na tabbata kuma in ba zancen aurenka aka fara ba to ba za ka shige shi ba” Sheikh Rayyadeen ya ɗan murmusa yana mai cewa “aboki ban san ranar da za ka rage surutu ba, wannan duk ranar da ka haɗu da mace daidai kai ai an shiga uku sai dai ku haifi rediyo” Sheikh Laminu ya tuntsire da dariya yana mai cewa “ka san kuwa ina son mace mai surutu,saboda yawancinsu za ka same su da tsiwa” Sheikh Rayyadeen ya ja tsuki saboda yana furta haka Khadeeja ta faɗo masa a rai.Cike da jin haushi ya ce “kai dama duk inda wani abin shirme yake to can kake,ina wani abin burge wa ga mace mai tsiwa? Na san dai Mardiya ba haka take ba ita mace ce mai hankali ” “Aboki a kullum ina yi maka addu'ar Allah ya baka mace mai tsiwa don ita ce daidai da kai,ita kaɗai ce za ta ture miskilancinka” Sheikh ya ɗan gyara kwanciya yana mai cewa “in kuma aka zo fannin shimfiɗa fa?” Murmushi mai sauti yayi yana mai cewa “shi ne kawai damuwarka shimfiɗar aurenku?” “To aboki mene ne auren? Duk macen da ba za ta iya ji da nauyina ba mene ne amfanin auro ta? Shi yasa nake son mace mai nutsuwa wacce ta mallaki hankalinta amma ka ga yaran nan sai a hankali banda shirme babu abin da suka iya” Dariya Sheikh Laminu yayi har da ƙyalƙyatawa kafin ya tsagaita ya ce “in dai irin matar nan kake so ina da wata cousin wallahi dama ta dame ni da na yi mata addu'a Allah ya bata aure shekararta talatin da uku,tana hadda Alkur'ani amma ba ta yi karatun boko mai zurfi ba zan turo ma hotonta in ta yi maka sai mu yi tuwona maina ” Shiru Sheikh Rayyadeen yayi Allah ya gani yana son aure amma kuma yana jin tsoro kar wani abu ya samu ƴar mutane.Kafin ya kai ga cewa wani abu kuma kiran ya katse,ya ajiye wayar yana mai lumshe ido tare da jan numfashi yana.Hoton Khadeeja ne ya faɗo masa a rai,duniyar Allah duk da bai taɓa yin aure ba amma yana mugun son dukiyar Fulani .Juyi ya sake yi yana jin tsoron sake shiga wani hali,ƙarar shigowar saƙo ne ya ji a wayarsa.Ya jawo ya duba sai ya ga hoton ne Sheikh Laminu ya turo masa,haka ya ƙure hoton da kallo babu laifi Kyakkyawa ce sannan tana da zubin halitta mai kyau don babu hijabi a jikinta kayan atamfa ne ta saka amma sosai suka karɓe ta. “Ta yi?” ya ga wani saƙon ya shigo. Ya basa amsa “aboki in dai ka yarda da tarbiyyarta na karɓi tayinka ” sosai Sheikh Laminu ya yi murna nan take ya aiko masa lambarta sai a lokacin ya tambayi sunanta ya ce “Maryama” sai yayi saving kafin ya tashi yayi wanka ya tafi masjid yana dawowa kuma yayi shirin zuwa makaranta. Yana saukowa ƙasa ya je ya duba Rashida ya tofa mata addu'o'i sannan ya yi wa Ammy sallama.Yana isa makarantar yayi tsinke ajinsa,yana shiga idonsa a kanta ya fara sauka tana kwance a takure sai rawar sanyi take ga kuma fankar aji a kunne.Saurin ɗauke idonsa yayi ya je ya zauna ya soma koya karatunsa,amma lokaci zuwa lokaci yana ɗan satar kallonta da dukkan alamu ma bacci ne take yi. Lokacin sallar la'asar na yi duk kowa ya soma fita. Cikin baccin da ya shure ni ban shirya ba na ji muryar Mujahida na cewa “ki tashi lokacin sallah yayi” sai da na ɗan jinkirta kafin na buɗe idona maimakon Mujahida Sheikh Rayyadeen na gani a tsaye.A hankali nake kallonsa,shi kuwa hannunsa na dama yasa ya kamo kaina tare da soma yi mini karatu. Yadda nake jin ana yin motsi a cikin jijiyoyin kaina shi yasa na fara kiciniyar ƙwatar kaina.Hannuna na ɗora kan nasa da niyyar janye shi amma ya ƙi saki,haka na dinga yin hawaye har sai da ya gaji don kansa sannan ya sake ni.Ina tafiya toilet domin yin alwala na ga jinin period ɗin ya dawo a dole na haƙura da yin sallar na koma cikin aji na kwanta.Ina nan suka fara dawowa daga masjid,ajin na gama cika Sheikh Rayyadeen ya shigo yanzu ma idon muka haɗa na yi saurin ƙanƙame jikina shi kuma ya kawar da kai tare da matsawa ya kashe dukkan fankonin ajin.A sannu a hankali zafi ya fara ziyarta ajin,hakan sosai yayi mini daɗi wanda kuma ina da yaƙinin sauran ɗaliban za su cutu. Ba a fi minti biyar ba na ɗan gyara zamana ina sauraren darasin da yake yi game da wajabcin sallah ga Musulmi har aka zo babin abin da ke hana sallah daga ƙarshe ya koya mana yadda ake wankan janaba da na haila.Ɗaya daga cikinmu wato sabon shigowa ta ce “malam mene ne banbancin wankan hailar da shi janabar? Mene ne su?” Duk ƙarancin shekaruna na girme mata,irin yaran nan ne waɗandan iliminsu ne ke sa a kai su ajin manya.Tambayar tata sai ta saka manyan ajin jin kunya,amma shi kuwa Sheikh Rayyadeen tiryan-tiryan ya soma fayyace komai,abubuwan da ke kawo janaba dukkansu sai da ya faɗa ni kaina sai da na sunne kai duk da dai sai ya faɗa da larabci sannan ya fassara. Abin takaici duk bayanin da yayi daga ƙarshe ita wacce ya yi wa ɗin ba ta fahimci komai ba. Shi kuwa Sheikh Rayyadeen ganin suna sunne kai yasa shi cewa “tambaya ce ta yi mai muhimmanci,a fagen neman ilimi babu kunya ya kamata duk abin da ba ka sani ba ka yi tambaya a kai” A hankali na ɗago na dube shi,bawan Allah sai na ga yana goge gumi da tissu alamun zafi yake ji.Mujahida ta yi ƙasa da murya tana mai cewa “dubi saboda ke ya wani kashe fanka sai gumi yake fitarwa mu kuma ya bar mu da jin zafi cikin hijabi” Kwantawa na yi jikinta ina mai yi mata raɗa,“ina ma a ce cikin ƙirjinsa ne ya rungume ni na ji ɗumin jikinsa ya kike gani?” Mujahida ta ce “innalillahi!” da ɗan ƙarfi ta faɗa wannan yasa waɗanda suka ji duk suka zubo mana ido.Da sauri na sunne kai ganin kallon da Sheikh ke yi mini sai nake ganin kamar ya ji abin da na ce ɗin ne. Har lokacin tashi ya yi ban ɗago kai ba,don da zarar na yi yunƙurin haka sai na ga idonsa na kaina.Mutane na soma fita amma ya dakatar da mu ni da Mujahida,haka aka fita aka bar mu . Gilashin idonsa ya cire yana mai kafe mu da ido,tuni Mujahida ta soma yin hawaye cikin tsare gida ya ce “mene ne take raɗa miki a kunne?” “Komi!” ta faɗa tana shafar hawaye . “Mene ne kike faɗa mata?” ni ma ya tambaye ni.Na ce “ban ce mata komai ba” kawai sai ya miƙe tsaye ya ɗauko bulalarsa yana mai cewa “zaɓi uku zan baku,na farko ku sanar da ni cikin lalama,na biyu zan dake ku in jikinku yayi tsami sai ku sanar da ni,na ukun kuma zan kira iyayenku na basu takardunku na ce kun fi ƙarfinmu mun sallame ku” Kallon juna muka yi ni da Mujahida,ina ganin ta buɗe baki za ta yi magana na yi saurin girgiza mata kai ina cewa “don Allah Mujahida ki rufa mini asiri kar ki ce komai” ban rufe bakina ba kuwa ya shiga zuba mana bulalarsa,in yayi mini biyu sai ita ma ya yi mata can ya tsaya ya ce “za ku sanar mini ko kuwa?” Mujahida wacce dukan da yake yi mata ya fi ƙarfi saboda ya san ita ce kawai za ta yi magana don taurin kan Khadeeja shi ne shaida ba za ta saduda ba ko kashe ta zai yi.Cikin tsanani fitar hayyaci ta shaidawa Sheikh Rayyadeen abin da na faɗa mata ɗin,idonsa ne suka yi ja sosai jijiyoyin kansa suka fito raɗo-raɗo rai ɓace ya cewa Mujahida “ke ki tafi” da gudunta kuwa ta fice.Ina ganin haka na zube gwiwaina ƙasa na soma yin kuka kamar raina zai fita,sam ban ji zan iya haɗa ido da shi ba haka kuma ba zan taɓa yafewa Mujahida ba. Kujera ya jawo ya zauna yana mai cewa “ina jinki,ki maimaita abin da ƙawarki ta faɗa yanzu da bakinki ko kuma in kira mahaifinki ki sanar da mu abin da kike nufi”..... Saura page guda free page ya ida,zaɓi group ɗin da za ki yi karatu ƴar uwa normal group only 300, VIP kuma 500 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBANK DM +22795045822 [18/12 12:58] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 10 Idona na shatatar da hawaye na ɗan ɗago kaina dakyar ina duban Sheikh Rayyadeen wanda ya yi kicin-kicin da rai kamar mai shirin fasa kuka. “Don Allah ka rufa mini asiri ka yi haƙuri wallahi ba zan sake ba” na furta cikin muryar kuka. “Kenan kin faɗa ɗin dai ko? Faɗa mini rashin ingantacciyar tarbiyya ne? Ko kuwa tsaurin ido ne na yaran yanzu? Ni sa'anki ne? Ko ina wasa da ke?” Duk tambayoyin da ya jero mini babu ɗaya da na amsa,kuka kawai nake yi ina roƙon Allah a zuci kar ya taɓa bai wa Sheikh ikon kiran Daddyna. “Tun da aure kike so zan sanar da shi Bin Abdullahi ɗin ya nemo miki miji” ya furta yana mai miƙe wa ya fita ya bar ni cikin ɗumbin tashin hankali.Dakyar na samu jarumtar tashi,zuciyata a cunkushe na je na shiga mota dakyar nake driving ikon Allah ne kawai ya kai ni gida.Ina fita na shige ciki,Daddy da Momy duk suna falo amma ban gaishe su ba.Kan bed na zube ina mai fashewa da sabon kuka,a haka Momy ta shigo ta same ni. “Auta lafiya meke damunki?” ita ce tambayar da ta yi mini tana mai zaunawa bakin gado.Rungume ta na yi gammm kafin na ce “wata ƙawarmu ce ta rasu” “Ayya! Allah ya jiƙanta ,ke kuma addu'a ya kamata ki yi mata mamaci bai son ana yi masa kuka” Momy ta faɗa tana shafar fuskata,kai na jinjina mata kafin na miƙe na shiga toilet.Iya hijabi kawai na cire na je na tsaya ƙarƙashin shower na sakarwa da kaina ruwa,na lumshe ido ina jin zuciyata duk babu daɗi. Kalaman Sheikh Rayyadeen tamkar cida haka suka dinga kutso kwanyata suna firgita ni.Na toshe kunnuwana kafin na zube ƙasa dirshen ina yi wa kaina tambayoyin da babu mai bani amsarsu “shin mene ne laifina don kawai ina sonsa? Ni kaɗai ce nake da irin gurɓataccen tunanin na kasancewa da wanda nake so ko kuwa duka masoya haka suke ji?” ganin wannan ba za ta fishe ni ba na miƙe na cire kayan jikina,tsarkake jikina na yi sannan kuma na haɗa ruwan ɗumi na shiga na kwanta kamar daga sama haka na soma jin yanayin nan yana fizgata na son lulawa duniyar da ban san taƙaimaimai ina ne ba amma na bata suna kawai MAFARKI domin a cikinsa ne kawai nake tsintar kaina. Yau kuma cikin wata ƴar ƙaramar buka ce nake mai ɗauke da wasu tarkace irinsu;ƙaho,ƙaton kan bijimin sa,fatun namomin daji daban-daban,kwari da baka na ƙashi,wasu abubuwan ma ban san sunansu ba. A kwance nake kan baƙar fatar akuya,an yi wani circle da kyandir duk sun zagaye ni.Kusan kaina Nina ce a tsaye sai manyan idonta take juyawa,can kusan ƙafafuna kuwa Ummah ce Kakata riƙe da wata ƙwarya. “Lokaci yayi” cewar ita Nina ɗin.Sai kawai Ummah ta soma zuba mini ruwan da ke cikin ƙwaryar tana bin duk illahirin jikina tana zubawa duk ɗigo ɗaya in sun taɓa fatata wani irin shock ne nake ji kamar lantarki ya kama ni.Ana zuwa daidai kaina ji na yi kamar raina zai fita ,ana gama wankan kuma sai aka kunna wani turare wanda bai da hayaƙi sai dai ƙamshinsa wasu kalamai Ummah ke furtawa waɗanda ban san mene ne ma'anarsu ba. “Barka da shigowa wannan duniya!” Nina ta furta tana mai kwantowa jikina,kamar yadda ruwa ke shiga ƙarƙashin ƙasa haka Nina ta ɓata a cikin ɓargona.Na ja wani dogon numfashi wanda ya yi daidai da wanzuwata a wani wurin,ƙofar wani gida ce ina tsaye daga gefe ina kallon abincin ruhina Sheikh Rayyadeen tare da wata budurwa .Na ƙarasa kusa da su ina mai ɗauke budurwa da mari tare da yi mata kashedi “ Sheikh Rayyadeen nawa ne ni ɗaya,ba kuma zan yi sharing nasa da wata ba” “Ni kuma ba ni sonki,kuma ba zan taɓa aurenki ba” Sheikh ya furta mini yana jifata da kallon tsana,hawaye suka soma bin kumatuna daidai nan na farka .Wani abin mamaki kuma da kuka na tashi kamar wata yarinyar goye,na yi saurin tashi na fito daga cikin ruwan na yi alwala kafin na ɗaura towel na fita. Kayan bacci na saka,na yi sallar magarib da isha'i sannan na sauka.Falon babu kowa sai Ummah a zaune ta saka tv a gaba tana kallon India Film ,na ɗan yi murmushi ina mai cewa “ƙawali kallo ne ake yi?” Ta dube ni kafin ta ce “sai yaushe za ki sanar da shi kina sonsa?” Mai shirin kuka an jefe shi da kashin awaki,kawai sai na faɗa jikinta ina hawaye.“Akwai wacce take so tun tuni” “Shi ya faɗa miki hakan ?” “A'a a gabana ta sanar da shi” “Je ki ci abinci to” ta furta tare da miƙewa tsaye tana yi mini wani irin kallo,da sauri na kamo hannunta ina mai cewa “na yi miki alƙawari gobe zan sanar da shi” sai ta yi wani murmushi tana shafar kaina,sai dai fa ba normal shafa ba ce a'a ina jin wani ɓoyayyen sirri na ratsa ni wanda ya mantar da ni duk wata damuwata. Da hannunta ta bani abinci mai magani,a ɗakinta kuma na kwana a wannan daren.Wanda a cikinsa abubuwa da dama sun faru,Ummah ta koya mini abubuwa da dama duk da cewa cikin MAFARKI ne amma gaskiyar magana ita ce komai reality ne. Washegari da wani irin ciwon kai na tashi,sai dai ban san dalili ba don duk mafarkan da na yi na manta su. Bayan na yi sallar asubah kitchen na shiga na taya ƴar aiki girka abin da za a yi breakfast kafin kuma na haura sama na yi wanka tare da shirin makaranta,karon farko a rayuwata da na ɗauki turare mai ƙamshi na fesa a jikina shi ma ɗin ina son bar wa Sheikh Rayyadeen aiki ne ina son ya riƙe ƙamshin turarena ta yadda ko ina zai ji shi sai ya tuna da inda ya fara jinsa kamar dai yadda ni ma ya zautar da ni da nasa turaren. Ko da na fito sai Ummah kawai a falon tana tsaye tana kallon saman ɗakina da alamun ni take jira.Ina zuwa ta jawo ni tare da dangwala mini wani abu a tsakiyar goshi sai kuma baƙin kwalli da ya kasance ban ɗauke shi abin ado ba ban saba shafa shi fa.Wannan yasa sai da aka sha daga sannan na bari ta shafa mini shi,na turo baki gaba ina cewa “haba dai ƙawali kamar dai abin tsafi” “Soyayyarki tsabtatacciya ce ƙawali babu wani tsafi da zai shigo ciki, wannan fa kwallin Momynki ne na karɓo .Kuma tsaya ki gani yadda zai yi matuƙar tasiri kin san ido na ɗaya daga cikin abin da ake amfani da su don isar da saƙon so” Ummah ta faɗa . Na ce “kenan ba da baki zan furta masa ba?” Ummah ta ɓata rai tana mai cewa “au da kin zata ki furta masa nake nufi?” Ban ce komai ba na wuce,yau dai direba ya sauke ni .Na kai dubana a parking special,babu motarsa duk sai na ji babu daɗi.Da na shiga aji Mujahida na gani,ta taso kamar kullum za ta rungume ni amma na ture ta tare da yin gaba na bar ta tsaye. Zaune na yi tare da fiddo littafi na soma dubawa amma a zahiri ba karatun nake yi ba. “Ki yi haƙuri don Allah wallahi banda wani zaɓi ne shi yasa na sanar da shi” Mujahida ta faɗa tana mai yin zaune kusa da ni .Ban ɗago ba haka kuma ban ce mata komai ba sai ita ce ta ci gaba da cewa,“wallahi tun jiya da na tafi gida na kasa sukuni na so ma kira ki sai kuma aka yi katari banda kuɗi a layina ga kuma Ya Hamza bai kira ni ba ballantana na sanar da shi” Miƙewa na yi a hankali na fita na bar mata ajin,can wajen wasu shuke-shuke na nufa na zauna ina kallon yadda ruwa ke faltsa suna zuba kan ciyayi. ★SHEIKH RAYYADEEN A ɓangarensa kuwa sosai ya ji zafin yadda ƙanƙanuwar yarinya irin Khadeeja har za ta iya yin gurɓataccen tunani a kansa.Zuciyarsa har azalza take yi yana jin kamar ya kama da wuta don baƙin ciki,yana isa gida yayi parking tare da bai wa masu kula da gidansa key ya ce a wanke motar. Yana shiga falo da kukan Rashida ya soma cin karo, wannan yasa ya nufi ɗakinta da sauri.A takure ya same ta wuri guda tana ƙanƙame jikinta ga Ammy a tsaye riƙe da kofin ruwa. “Malamin da Abbanku ya ce zai yi mata karatu yanzun nan ya fita,shi ya bada ruwan nan a bata ta sha” Ammy ta faɗa kamar za ta yi kuka. Sheikh ya karɓi kofin,ya je a gabanta ya tsaya kanta ya kamo yayi Bismillah ya soma bata ruwan idonta ta zuba masa waɗanda da a ce ya lura da kyau da zai gane sak na Grand-Maa ne don ba su bar komai daga siffarsu ba. Abin da Sheikh Rayyadeen ɗin kawai ya iya tsinta cikinsu shi ne zallar sonsa,ya yi saurin kawar da kai kafin ya janye kofin daga bakinta don tuni ta shanye.A nan ta ɓingiri ta shiga yin baccin wahala. Sai a lokacin suka gaisa da Ammy kafin su fito,ta ce “ɗazu Mamarku ta zo nan har sun fara kawo kaya” Ya ce “babu damuwa zan shiga daga ciki” Ammy ta yi saurin tsayar da shi tana mai cewa “amma ya na ga kamar ranka a ɓace?” “Babu komai Ammy kawai gajiya ce” ya bata amsa kafin ya wuce sama.Kayan jikinsa ya rage ya shiga toilet don yin wanka saboda magarib ta gabato.Bayan ya gama wankan gaban mirror ɗin da ke cikin toilet ya ja ya tsaya yana ƙarewa faffaɗan ƙirjinsa kallo,yayin da kuma rashin kunyar Khadeeja ke keta tunaninsa.Da ya ji ransa na shirin ƙara ɓaci sai kawai ya fita,ya shirya cikin jallabiya ya fesa turare tare kuma da ɗaukar dadduma ya fita don tuni an soma kiran sallah .Ba shi ya dawo ba sai bayan isha'i,yau kwata-kwata bai da ra'ayin cin abinci abu mai ɗan sanyi yake so hakan yasa iya zoɓo kawai ya sha ya wuce ɗakinsa,ita ma Ammy ba ta wani takura masa ba sai kallon tausayi da ta bi ɗan nata da shi. Kan bed ya hau tare da kunna system ya soma yin bincike kan madu'in da zai yi wa'azi a wannan juma'ar.Duk yadda yake son ajiye hankali wuri guda abu ya cuttura kalaman Khadeeja ne kawai ke yi masa yawo,can kuma saƙon text ya shigo sai ya ga sunan Maryama.Sallama ce ta yi masa tare da gaishe shi,a duniya ya tsani mace marar aji shi yasa kaf ƴan matan da ke kawo masa tallar kansu yake jin ba zai iya soyayya da su ba. Ya ja tsuki a fili kafin ya danna kiran Sheikh Laminu,ringung biyu ya ɗaga yana mai yi masa sallama.Bayan ya amsa ne yake cewa “aboki kenan sai da ka bai wa yarinyar can lambata?” Sheikh Laminu ya tuntsire da dariya ya ce “Maryama ce yarinya? Fatan dai ba shirme ta yi maka ba? Ɗazu na shaida mata yadda muka yi da kai shi ne na tura mata hotonka da kuma lambarka ” Sheikh Rayyadeen ya yi shiru kafin kuma ya ce “okay!” sai ya kashe kiran,bai yi mata reply ba sai aikinsa da ya ci gaba da yi har kusan ƙarfe biyun dare kafin ya rufe system ɗin ya je yayi alwala yayi nafiloli.A nan kan dadduma yayi bacci mai cike da mafarkin Khadeeja,abin da ta faɗa ɗin dai ne ya faru wato yana rungume da ita ya saka ta a ƙirjinsa suna kwance kan bed sai faman manne masa take yi tana ƙara dagula masa lissafi wanda hakan ta kai shi da raba su da suturar jikinsu har suka raya daren da soyayyar baki da kuma ta gangar jiki. Da ya farka ji yayi kamar ya kama da wuta,ga lokacin sallah tuni yayi don wasu masallatai har sun fara ga kuma yadda wanka ya hau kansa.Duk da sosai ya ji daɗin mafarkin amma kuma bai hana takaici kama shi ba yana daɗa jin tsanar fitinaniyar yarinyar wacce ta addabi rayuwarsa. Cikin woshin mashin ya saka kayansa da dadduma kafin ya tsabtataccen jikinsa,ko da ya tafi masjid iya raka'a ɗaya ya samu sai bayan an salamce ya miƙe ya kawo cikon sannan ya zauna yayi azkhar.Bai dawo gida ba sai da rana ta fito sosai,jikinsa duk a sanyaye don rabon da ya rasa sallar asubah tun yana ganiyar ƙurciyarsa. Sai da ya shiga kitchen ya gaishe da Ammy sannan ya je ya dubo Rashida yau tana zaune kan dadduma da alamu kamar hankalinta ya ɗan dawo jikinta. Sallamar da yayi ta amsa kafin ta ɗago ta dube shi cike da rauni,shi kuwa Sheikh sosai ya ji daɗin ganinta haka. “Ya jikin naki?” ya tambaye ta. Ta ce “da sauƙi Ya Sheikh ” kasancewar haka take kiransa saboda tun suna yara ta bar masa girman. Ya ɗan murmusa ya ce “Allah ya ƙara miki lafiya ƙanwata” Ita ma murmushin ta yi kafin ta ce “amin!” addu'o'in da ya saba yi mata ya yi kafin ya juya,har ya kai bakin ƙofa ya ji muryarta tana cewa “ina ɗalibarka wacce na gani ranar nan?” Da wani irin sauri ya juyo ya dube ta,kafin ya ce “wace ɗaliba? Ai suna da yawa” Ta girgiza kai ta ce “ka san wacce nake nufi Ya Sheikh ” ta ida furicin tana mai yin kwanciya,kafin ma ya kai ga yin magana tuni Rashida ta yi bacci. Da wannan abin al'ajabin Sheikh ya nufi ɗakinsa,sai da ya sake yin wanka sannan ya shirya cikin fararen kaya yau kuma baƙar alkyaba ya saka da jan hirami ya feshe jikinsa da turare sannan ya sauko. Ammy ta tarbe shi tana mai cewa “ga abincinka nan na kawo ma tsakiyar falo ” “Azumi nake yi Ammy ” ya bata amsa. “Yau fa Laraba ce” ta faɗa da ɗan mamaki. Ya ce “eh na sani Ammy,na tafi sai na dawo” “Amma Deeni...” yayi saurin katse ta da cewa “Ammy na makara ƙarfe takwas saura kuma sabbin ɗalibai ne da ni ” “To a dawo lafiya” “Amin” Haka ya fice ya shiga motarsa,yana gudu yana ta nazarin maganar Rashida sai mamaki yake yi kan cewa da ta yi wai ya san wace ɗaliba ce yake nufi.Yana shigowa harabar makarantar ya ga yadda ruwa suka fara ɓullo shuke-shuken suna shigowa har inda babu su.Sai da ya fara yin parking ɗin motar kafin ya fito ya nufi can. ★ Ruwa na ɗaya daga cikin abin da ke bani sha'awa,yadda suke faltsar ba ƙaramin burge ni hakan ke yi ba.Wannan yasa da mai gadi ya kashe pampon sai na ji haushi,yana gusawa na je na sake kunnawa tare da tsayuwa ina kallo daga ƙarshe ma jakata na ajiye na je ina saka hannuwana a ruwan ina wasa. Ba zan iya ƙa'ide lokacin da na ɗauka a wurin ba,na shagala sosai a wasar kafin na soma ganin wata narkekiyar tsutsa tana fitowa na miƙe da sauri ina mai yin wata irin razananiyar ƙara na yi tako ɗaya ƙafata ta zame na yi tuntuɓe tare da yin gaba,sai dai ban faɗi a ko ina ba sai kan ƙirjin Sheikh Rayyadeen wanda ban san me ya zo yi kuma a nan ba .Tsabar ruɗewar da na yi shi ya mantar da ni tsoronsa da nake yi,ƙanƙame shi na yi gam igiyar numfashina na soma cirewa,“maci..ma .cijiii!” na furta,ina jin lokacin da yake bubuga fuskata cikin ɗimuwa yana cewa “kar ki rufe idonki! Kar ki some mini” idon nawa na soma ƙoƙarin buɗewa ina ɗan juya su,sai dai firgicin da ya kame mini zuciya shi ya hana ni yin yadda yake so ɗin.Ba zan ce na suma ba,haka kuma ba zan ce ɗari bisa ɗari ina cikin hayyacina ba sai dai ina ɗan tsintar maganar mutanen da tuni hankalinsu ya kawo gare mu. Ina jin lokacin da yake cewa “ku zo ku kama ta kuka wani tsaya kallona” sai kuma na ji an ciciɓe ni ana tafiya da ni yayin da kuma amon muryar Sheikh ke ratsa kunnena yana yin masifa.Daga nan ne na ji ɗif,ban san kuma wane lokaci aka sake ɗauka ba kafin na ja ajiyar zuciya na buɗe idona Sheikh Rayyadeen na gani riƙe da kaina yana yi mini karatu. “Ta buɗe idonta” muryar Mujahida ce wannan karon,sai ya saki kan nawa tare da tashi ya wani juya mana baya.Na tashi a hankali ina kallon ƙawata wacce idonta suka yi ja da alamun ta sha kuka,hannuna ta kama ta miƙar da ni sannan muka nufi ƙofa na ɗan juya domin satar kallonsa daidai shi ma ya juyo idonmu suka sarƙe cikin na juna.Daidai nan free page ya ida duk mai son ci gaba zai iya biyan 300 kuɗin normal group,ko kuma 500 na VIP group via 2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBANK DM +22795045822 *NB:* Yanzu nake rubuta shi banda complete ɗinsa,in kina da niyyar shiga group ki tura kuɗinki kai tsaye ki bani receip Ni kuma zan saka ki group.Daga lokacin da book ya kammala zai koma 1k. 18 Disamba 2025. [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 01 Sakacin iyaye na ɗaya daga cikin abin da ke jefa rayuwar yara yin mu'amala da aljanu tun suna ƙananu ba tare da an ankara cewa wannan illa ne ba. Sunana David,ɗan farko gun wasu shagalalun iyaye waɗanda suka mayar da sa'insa abin ado,cin amanar juna ruwan sha,wasa da tarbiyyar ƴaƴansu tabi'arsu.Shekaruna ashirin da biyar kacal a duniya amma in aka ganni za a iya bani shekaru talatin saboda yadda ƙwanjina ya buɗe silar aikin wahala.Tun ina ɗan yaro mahaifiyata ta rataya mini nauyin kula da ƙannaina,tun daga yi musu tsarki,wanka da kuma basu abinci a baki madadin ita ta yi.Komai tsawon dare in ƙanena yayi bahaya ni ne ke zuwa na wanke masa na kuma kai banɗaki na zubar,babu wata addu'ar neman kariya ko wani furici da zan furta domin gusar da wani abin cutar wa a irin haka ne na haɗu da wata baƙar siffa wacce duk da ƙanƙantar shekaruna bai hana na fahimci wannan ba bil'adama ba ce. A tsaye nake tsakiyar banɗaki hannuna riƙe da fo ,yayin da kuma siffar ke tsugunne kan inda mutum ke hawa don yin buƙatarsa.A lokacin wani irin tsoro ya ziyarce ni,sai dai tamkar itaciya haka na kasa motsi sai ma ido da na ƙanƙance ina ƙarewa siffar kallo.Mace ce a zubin halitta don ga dogon gashinta nan ya zubo har yana jan ƙasa,fuskarta baƙa ƙirin ce mai ɗauke da wasu ƴan ƙananun ƙahonni daidai gefe da gefen hanci,bakinta a buɗe yake wanda hakan zai iya baka damar ganin dogayen haƙoranta biyu da suka zarce sauran.Duk a cikin duhun daren idanuwana suka bani ikon ganin wannan ikon Allahn,a hankali na ga ta taso ta zo gare ni ba tare da ta ce komai ba ta karɓi fo ɗin hannuna sai ta ɗora babban yatsanta a tsakiyar goshina wani irin abu na ji mai mugun zafi ya ratsa ni wanda yasa na fita hayyacina.Ko da na farka Ummah na gani gefena tana jiƙa wani zane a ruwa tana ɗora mini yayin da kuma idonta suka yi ja alamun ta yi kuka.Muna haɗa ido da ita ta ce “Davido?” a cikin muryarta na tsinto tsantsar tausayina,a bakinta kuma na ji cewa an same ni a yashe ga ƙasa daidai ƙofar banɗaki . Mahaifina ya matso yana cewa “har yanzu jikin nasa da zafi?” “Eh kamar gawarshi har wani tiriri ke tashi,dubi hatta ruwan da nake tsoma zanen sun ɗauki gumi” Ummah ta faɗa tana matsar ƙwalla. Abba ya ce “ki goya Joy mu tafi mu kai shi gidan mai magani” ba ta ce komai ba haka ta ɗauki ƙanena Joy wanda bai rufe murfin shekara biyu ba,ni kuma Abba ne ya saɓe ni zuwa gidan mai magani. Tun da muka shigo farfajiyar gidan idona suka soma yi mini gane-gane.Abin da ido bai kamata ya gani ba ni ras nake ganinsa,duk mutanen da suka zo babu lafiya kallo ɗaya na yi wa kowanne daga ciki na hango matsalarsa.A bisa bangunan gidan mai magani kuwa kamar yadda ƙadangaru ke yawo haka ko ta ina aljanu ne ƙanana da manyansu.Lokacin da muka shiga cikin ƴar bukarsa kuwa muna haɗa ido da shi na ga ya ɗan tsorata,amma sai ya ɓoye tsoron tare da bada umarnin a kwantar da ni kan tabarmar da ake shimfiɗe majinyata.A ido tabarma ce,amma a baɗini bijinmi wani dodo ne,bai tambayi iyayena abin da ya faru ba amma sai ni ya tambaya shi ɗin ma ba ta baki ba a'a ta ido. “Wane ne kai? Me kake so a gare ni har ka bari aka kawo ka wurina alhalin ka fi ƙarfina?” su ne tambayoyin da idonsa suka watso mini amma ni sam ban basa amsa ba,kuma ban san dalilina na yin haka ba.Ƙila shi kuma ya fahimci har zuwa lokacin ƙarfin ikon da ke jikina ban fara yin aiki da shi ba ne ko kuwa tasirinsa bai bi jikina ba ne oho,sai ya ɗauko wata ƙatuwar laya ya ɗaura ta a damtsena tare da cewa “zuwa saukowar zazzaɓin rana duk wannan zafin jikin nasa zai sauka zai kuma samu lafiya” Abba ya basa kuɗi amma ya ƙi karɓa a haka muka dawo gida.Kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa haka ta faru,ina warware wa kawai sai na fara walwala tare da mantawa da wannan siffar da na gani .Yayin da kuma Abba da Ummah suka dasa rashin mutumcinsu daga inda suka tsaya,dama iya na ɗaya rana ne ba su yi masifar da suka saba ba da yi wa juna gori wasu kalaman sam ba su dace ba. A lokacin da na shiga zangon shekara goma sha biyar a duniya na soma yin aikin ƙarfi don ciyar da ƙannaina biyu Joy da kuma Joyel wacce ta kasance autarmu.Tamkar mahaifi haka suka ɗauke ni,da zarar na shigo haka suke zuwa da gudu su tarbe ni da murna iya wannan annushuwar da nake gani a tattare da su shi ke wanzar da nawa farin cikin har izuwa yanzu da nake ganiyar shekara ashirin da biyar. “Ba ka da aikin yi kullum sai shan giya da bin mata a hakan wai kai miji ne” “In ba miji ba ne ni ai ba zan baki yara har uku ba” “Uwar me kake yi wa yaran ? ” “In ban yi musu komai ke da ke uwarsu ai ina yi miki wata tsiyar da har ta sa kika kasa barina kika manne mini” “Zancen banza yo kar ka sake yi,ka zata kai kaɗai ne namiji a duniya?” “Kenan dama abin da nake zargi gaskiya ne kina cin amanata?” Wannan ita ce sa'insar da iyayenmu suka tashi da ita a safiyar yau duk sun cika mana gida da surutunsu da babu daɗin ji.Cike da ɓacin rai na tashi daga kwancen da nake ,tun ina haƙurin saurarensu har na kasa jura na tunkari ɗakinsu.Ban ɗaga labule ba,a bakin ƙofa na ce “don Allah ko za ku iya yi mana shiru ko mun samu mu yi bacci cikin salama?” Daga can cikin ɗaki Ummah ta ce “kan ubanka! Haifarmu ka yi da za ka bamu umarni?” Shi kuwa Abba wata irin dariya ya yi kafin ya ce “ai shi ne daidai ke tun da ke ma ɗin ba mutumci ne da ke ba ga shi nan kin haifi ɗan daba ” “Ko ma dai mene ne babu ruwanka da ɗana ” “Ni ma ai nawa ne ina ce ni ne ubansa ko?” “Wa ya sani abu cikin duhu!” Ummah na faɗar haka na gusa daga gurin.Ƙofar gida na fita na zauna kan dakali ina jin zuciyata duk babu daɗi. Wani irin yammm! Yammm! Na soma jin ƙafata na yi mini ko da na duba sai na ga tururuwa ce duk ta yaɓe mini ƙafa kamar ta samu wani suga.Girgiza ƙafar na yi amma ko ɗaya ba ta faɗi ba kamar ma an sa super glue ne a manne su.Da sauri na kai hannu don kakaɓe su sai dai wani abun mamaki bayan na shafa ƙafata sai na ga wayam babu komai kuma ba su zuba a ƙasa ba.Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya ziyarce ni,dole na miƙe na koma cikin gida na cika bokiti da ruwa na kai banɗaki .Ina tsaka da yin wanka na soma jin wani irin yanayi wanda tun da nake zan iya cewa sau ɗaya tak na taɓa samun kaina a cikinsa shi ɗin ma a mafarki a lokacin da na shiga zangon balaga. Idona a rufe suke na goga sabulu ban wanke ba,yayin da kuma nake jin tamkar ana shafar duk illahirin jikina ana yi mini abin da ban taɓa jin makamancinsa ba.A wannan lokaci ba zan iya tantance ina cikin hayyacina ne ba ko kuwa ya gushe,abu ɗaya zan tuna shi ne na samu kaina a matsayin namiji har na samu nutsuwa,sai dai da wa? Ban sani ba.Ina dawowa cikin tunanina na ida yin wanka,na fito na je ɗakina na shirya .Ciwon kan da ya sauko mini tuni na neme shi na rasa,na fito kenan zan fita neman kuɗi sai ga su Joy sun fito su ma cikin shirin zuwa makaranta. Da turanci suka gaishe ni na amsa musu ni ma da turancin,Joy ya ci gaba da yin magana don yana ɗaya daga cikin abin da yake yi mini wani sa'in yayi mini magana da turanci kasancewar tawa makarantar ba ta yi nisa ba na fita.Amma wani abin mamaki sai na samu kaina da iya turancin, Joy ya ce “amma Yaya ya aka yi ka iya turanci haka?” shiru na yi ina kallonsa,ni ma ban sani ba amma sai na share na miƙa musu kuɗin da za su ci abinci na fice. Direct inda muke haɗuwa ni da abokaina na tafi,duk sun hallara kuwa da alamu ni suke jira.Hannu na basu duk muka gaisa kafin na samu wuri na zauna a daidai tsakiyarsu wanda kuma kusan kullum muddin za mu haɗu ni a tsakiya nake zama ,in suna son tsokanata suna cewa ni ne shugabansu. “Yau dai in mun tafi aiki sai dare na dawo saboda ina son kuɗi sosai zan fara tara kuɗin aurena ” Isa ya faɗa yana wani jan gemu. Abdul ya karɓe da “ai kuwa kamar ka shiga zuciyata ni ma haka na yi tunani ya kamata a ce mun fara tara kuɗin aure tun yanzu kafin ƙarshen shekara ta zo tun da layi ya kawo kanmu” Isa ya ce “a'a yanzu fa layinsu David ne masu shekara ashirin da biyar” “To ai ba wani girme mana ya yi ba kawai ƴan watanni ne” Da na ga za su ɓata mini lokaci na miƙe na tsaye na ce “ko za mu iya tafiya?” duk suka miƙe suna dariya kafin mu tafi can wurin aikinmu na dako.A nan ɗin ma wani abin mamaki ya faru da ni,a yayin da abokaina ke ta aiki tuƙuru don samun kuɗi masu yawa ni kuma kamar wani shashasha haka na samu wani lungu na ɓingire ina bacci wanda ban san dalili ba.Sai yamma lis na farka,duk wata kasala ce nake ji ta rufe ni amma a haka na samu ruwa na wanke fuskata. “Ina ka tafi tun ɗazu?” Isa ne ya yi mini tambayar ,yayin da kuma Abdul ke tsaye yana kallona.Dakyar na buɗe baki na ce “ina can kwance ina bacci tun safe” “Amma kuma babu inda ba mu duba ba kuma har can ɗin mun je ba mu ganka ba” cewar Abdul yana mai ci gaba da tsure ni da ido .Shiru na yi don ban san taƙamaimai abin da zan ce ba,Isa ya ja ajiyar zuciya ya ce “tashi mu ƙarasa aikin to” haka na miƙe muka yi aikin a tare da aka zo raba kuɗi nasu sun ninka nawa biyar amma da yake abokan ƙwarai gare ni sai suka ƙara mini cikin nasu kafin mu koma. Ina shiga gida da Ummah na fara cin karo,lissafin bashin da ta ciyo mini ta soma yi mini daga ƙarshe ta tara hannunta alamun na bata kuɗin.Hannu na saka aljihu na ciro dukkan kuɗin na miƙa mata,har zan tafi amma wani abu ya ja hankalina.Zanen kunamar da ke hannun Ummah na ga yana motsi har da wani buɗe baki kunamar take yi,cak na tsaya ina mai ci gaba da kallon zanen yayin da ita kuma Ummah ke ƙirga kuɗin. “Lafiya me aka yi kake kallona?” ta tambaya,ba tare da na bata amsa ba na wuce ɗakina.Tsaye na yi bakin ƙofa na riƙe ƙugu tare da yi wa kaina tambaya “wai shin meke faruwa da ni ne? Ko na haukace ne? ” tamkar bugawar guduma haka na ji kunnuwana sun bada wani sauti duummm! Sai kuma na ji tamkar ana kiran sunana a wani wurin da ni kaina ban san ina ne ba.Kamar zararre haka na fito,a lokacin tuni gari ya ƙara yin duhu .Tafiya kawai nake yi ba tare da na san inda zan je ba,har yanzu kuma ina jin sautin nan na kamar ana kiran sunana.A haka na yi nisa sosai a tafiya har na iso cikin wani wuri mai ciyayi da kuma dogayen bishiyoyi,haka nake ratsa wa ta cikinsu ba tare da wani tunani ba a haka har na iso gaban wani kabari.Haske na ga yana ɓulɓulowa ta cikinsa,ina zube gwiwaina ƙasa muka samu contact da ƙasar wurin sai yanayin tafiyar kaɗawar iska ya canza,ƙamshi wurin ya ɗauki yanayin damshi kamar irin an yi ruwa an ɗauke.A kan kabarin wasu irin ƙananun baƙaƙen duwatsu ne a zube kamar shara,sai kuma wani farin kyandir daga tsakiya wanda ya fara ci da wuta da kansa,wani irin abu nake ji kamar ana fizgo ruhina tamkar dai akwai wani ɓoyayyen ruhi da ke jawo ni izuwa gare shi.Ba tare da tunanin komai ba na soma ture ƙasar kabarin ina buɗe shi,sama da minti talatin na ɗauka kafin yi nasarar buɗe shi duka.Wani ƙyalle ne na ci karo da shi a shimfiɗe a samansa wani ƙaton littafi ne akai,an yi masa cover da wata fatar dabba tamkar mai motsin rai,a ƙasa an yi wani rubutu wanda ba da Yaren da na taɓa ji ko gani ba ne,amma sai na ji rubutun da kansa yana yi mini magana. Ina sa hannu na ɗauki littafin sai wani irin shock ya ziyarci yatsun hannuna suka fitar da wani hasken wuta irin kamar waya ta ƙone.Bishiyoyin da ke zagaye da ni ne suka soma yin wata irin rawa har kana jin suna kai wa juna karo,yayin da kuma wani huci wanda kana ji ba na bil'adama ba ne ya soma karo da juna yana fitar da wani iska da ya saka furanni faɗowa suna mutuwa murus.Page ɗin farko na buɗe,nan take na soma jin ana yi mini wankin ido na soma gane-gane ina ganin abubuwan da suka faru lokacin baya a cikin littafin tamkar an kunna tv.Abubuwa ne waɗanda hankali ba zai ɗauka ba,mata da maza suna bayar da jininsu domin ƙaddamar da yarjejeniyar a tsakaninsu da Aljanai ,lamarin da muke ta tunanin tatsuniya ce ashe gaske ne an yi su a ƙarnin baya .Littafin na riƙe a hannuna yayin da kuma kukan ƙananun yaran da aka sayar da ruhikansu ko kuma aka bayar da jininsu matsayin hadaya na ta kawowa dodon kunnena farmaki,gefe guda kuma dubban ahali ne tsundum cikin rayuwar ƙunci saboda tun kakanni da iyaye sun yi harƙalla da Aljanu a yanzu kuma suna biyan bashin ƙarfin ikon da aka basu. Duk page ɗin da zan buɗa tana ɗauke da wani baƙin sirri da ya gabata.Na ga ahali da dama waɗanda suka yi ƙaurin suna a zube gaban baƙaƙen ruhikan da ido bai isa ya gani ba amma sun yi harƙalla da su don samun dauɗar duniya ko iko.Wata page ɗin kuma magana take yi kan ƙungiyoyin asiri waɗanda aka ƙulla ta hanyar jini da kuma sassan jikin ɗan Adam ,yayin da kuma wata ke magana kan mutanen da aka jefa wa ƙunci a zukata ta hanyar tsafi wasu kuma an haukata su ,yayin da wasu aka ɓatar da su daga duniyar bil'adama zuwa ta ruhaniya saboda sun gwada tonawa azzalumai asiri. Numfashina ne na ji yana son ɗaukewa,littafin kamar yana son koyar da ni,ya canza tunanina,ko kuma ya gwada imanina.Ji na yi ruhina yana kimsa mini wasu kalamai,yana cika mini ƙwaƙwalwata da ilimin da aka yi hani,a kuma wannan lokacin ne na ji wani irin tsoro mai tsanani ya ya daskarar da ni,sai kuma idona suka ci karo da wani rubutun da aka yi da manyan harufa. “DUK WANDA YA TAƁA WANNAN LITTAFI SHI NE SHAIDAR INUWARMU.WANDA YA KARANTA SHI KUMA YA ZAMA *INUWAR ALJAN*” kalmar ƙarshe ta inuwar aljan wacce rubutunta yake da jan jini na ƙara maimaita a zuci,sai kuma na fahimci cewa wannan littafi ba wai iya kundi ne mai ɗauke da sirri ba,a'a shi kansa yana rayuwa ne yana tattare da motsin rai.Yana ankare da ni tun tuni,ko kuma dai yana amayar da wani sirrina da nake ɗauke da shi tun tuni.Ji nake ana kallona,ana ankare da ni ana kuma gwada ni da kuma tsare ni da ido waɗanda ba a iya gani.A nan take kuma na fahimci wani abu ,na canza har abada kuma ba zan dawo yadda nake ba tun farko ....... [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 02 Banda wani zaɓi wanda ya wuce na taho gida da wannan littafin sirrin wanda nake jinsa tamkar wani jigo na rayuwata.Wuri mai kyau na yi masa a cikin akwatin kayana na ajiye shi,abincin dare sam ban ma yi tunanin ci ba don dama duk wunin yau ba zan ce ga abin da na ci ba. A wannan daren sam ban yi baccin kirki ba,da zarar na samu na ɗan tsunduma cikin bacci sai na soma ganin baƙaƙen inuwoyi masu jajayen idanuwa suna ambaton sunana suna kuma nuna mini yadda ake gudanar da baƙin tsafi da wasu dangin asirai.Yadda ake yin hadaya da jinin bil'adama,da kuma yadda ake ƙulla harƙalla tsakanin jinsi biyu.Cikin firgici na farka jikina duk ya jiƙe da gumi,idona kan littafin da na ɓoye a cikin kayana ya sauka amma a yanzu kan table na gansa kuma a buɗe.Da na ɗauke shi sai na ga sak irin abin da na gani cikin mafarki ne,wato ya buɗe kansa da kansa yana karanto mini labarin da ke ƙumshe a ciki ne.Waje na fita na yi rame can bayan ɗaki na binne shi da tunanin hakan shi ne kawai mafita,ina komawa ɗaki na sake tarar da littafin ya buɗe shafi na gaba.Zaman ƴan bori na yi tare da yin tagumi,wata murya na ji tana cewa “littafi ya zaɓi wanda zai karanta shi,tun da kuma ya zaɓe ka to har abada ba zai taɓa barinka ba” kamar wani mahaukaci haka na matsa kusa da shi na ce “to na ji ni ne ka zaɓa amma sai ka bari har lokacin da na buƙaci karanta ka ni ne da kaina zan ɗauko ka na karanta don haka yanzu ka koma ma'ajiyarka ta farko” abin mamaki ina gama rufe bakina na ga ya ɓata kamar walƙiya yayin da kuma jakar kayana ta yi wani motsi tana rawa alamun dai ya shiga ciki ya zauna. Kan shimfiɗata na kwanta na shiga yin wasiƙar jaki,ƴan magana na cewa bacci ɓarawo ne to shi ne yayi nasara sace ni a karo na biyu sai dai sam ban yi mugayen mafarkai ba a wannan karon. Ina tsaka da yin baccin da ban samu na yi ba na ji muryar Abba kaina yana kuma jijiga ni alamun na tashi,ina buɗe ido na ga sai yaƙar haƙora yake kamar gonar auduga. “David tashi! Tashi ka ga waɗanda suka zo gidanmu.Taso suna son ganinka” Abba ya faɗa cikin murna,yadda ya riƙe mini hannu gam shi ya sa na tashi don dole na biyo bayansa.A cikin rumfarmu ta kara na hangi dattawan garinmu a zaune ko wannensu ya ƙure ƙofar ɗakina da kallo,cike da mamakin abin da ya kawo su na ƙarasa na gaishe su.Bakunansu har rawa suke wurin amsawa kafin ɗaya daga cikinsu ya ce “Jakob ka ɗan bamu wuri muna son yin magana da ɗanmu” Abba ya washe baki yana kallona kafin ya ce “David wannan shi ne pasto ɗin Cochinmu ka saurare shi da kyau,su kuma waɗannan ai ka san su tun da kana shiga gari” yana gama faɗa ya tafi. Tambayoyi ne suka fara yi mini waɗanda sam ban san mene ne alaƙata da su ba,amma da na ajiye hankali sai nake ganin kamar sun san na taɓa littafin nan na sirri.Shiru kawai na yi ban iya ce musu komai ba,da suka gaji don kansu suka yi wa Abba sallama suka yi tafiyarsu. Ina shirin shiga ɗaki Ummah ta fito kamar wata munafuka ta ce “Davido wacce maganar ce waɗan can mutanen suka yi da kai?” kallonta na yi da kyau,sai na ga duk wasu alamomin rashin gaskiya sun bayyana a fuskarta. “Babu komai Ummah” na bata amsa tare da yin gaba.A tsakiyar ɗakina na yi tsaye ina kallon akwatin kayana ina son ɗauko littafin sirri ina kuma jin tsoron kar wani ya shigo ya ganni da shi. Daga nan inda nake a tsaye na soma jin wani irin yanayi kamar kasala kamar gajiya,idona na ɗan rufewa na soma jan ƙafata na je na kwanta kan shimfiɗata.Ba bacci nake ba kuma ba idona biyu ba,ina cikin wani lamari ne mai wuyar fassarawa.Adaidai nan wata kyakkyawar mace ta bayyana a gare ni cikin shigar fararen kaya,tsawon lokaci tana yi mini wani kallo kafin ta zumbule suturarta nan siffar jikinta ta bayyana a gare ni,haka na ci gaba da kallonta kafin ta tako zuwa gare ni.Abubuwan da suka faru a tsakaninmu,ba zan iya furta su ba saboda yadda ta shagaltar da ni ta saka ni cikin wani hali da babu shi a duniyata ta zahiri.Sai bayan ta gama mu'amalantata sannan ta bi ta jikin bango ta fice daidai nan kuma control ɗin kaina ya dawo.Yadda na samu duk na ɓata jikina shi ya tursasa mini zuwa na cika bokiti na yi wanka,bayan na fito na ɗauki tsintsiya na share ɗakina wanda kuma hakan sam ba tabi'ata ba ce Jowel ce ke yi mini gyaran ɗaki amma yau dai haka na ji ina ra'ayin yin kayana. Ba tare da na yi wa kowa sallama ba na fice,wurin da muke haɗuwa na je a yau ni ne na zauna domin jiransu.Ina nan zaune sai ga wata tsohuwa ta zo wucewa,sunana ta ambata wanda kuma ba iyayena ne suka raɗa mini shi ba a'a hasali ma ba na wannan duniyar ne ba amma a hakan na fahimci sunana ne. “Mikiya!” ta sake furtawa a karo na biyu,sai a lokacin kuma na saka idona cikin nata wanda hakan ya bani damar yin kutse a cikin ruhinta.Babbar matsafiya ce wacce ta laƙanci aikinta na bokanci da tsafi,ta kwashe kusan ƙarni biyu a doron duniya tana rayuwa ta hanyar fatalwar ruhinta. “Ba sunana Mikiya ba! David ne sunana” na faɗa murya a ɗan dake.Ta yi wani murmushi wanda ya ida fito da sauran muguntarta ta ce “sai yaushe ne za ka yarda? Sai zuwa yaushe ne za ka ɗauki ƙaddararka a hannu? Kai Mikiya ce mai yi wa dukkan abin da ya tunkaro ka dirar sauri,kar ka hana ikonka yin aiki akan nauyin da ke kanka” ba tare da na fahimci abin da take nufi ba na ce “na ji na yarda! Za ki iya tafiya” “Wannan salo naka ya burge ni sak irin jarumtar mahaifinka sarki Alfanso”tana gama faɗar haka ta ɓace cikin iska, maimakon na ɗauki ƙarshen furicinta da muhimmanci sai na watsar.Ina nan zaune sai abokaina suka zo a tare lokaci guda,yanayinsu kawai na duba na fahimci yau ba su fito da niyyar yin dako ba. “Ina za ku je haka?” na tambaye su ba tare da na yi nauyin baki ba. Isa ya bani amsa da “za mu je mu kai takardunmu ne ko Allah zai sa mu dace a ɗauke mu aiki ka ga shikenan sai mu huta da yin dako” “Yaushe aka yanke wannan shawarar ba tare da sanina ba?” na faɗa ina jin wani iri alamun babu daɗi don duk abin da ɗaya zai yi to dole ya shawarci sauran. “Saboda mun ga ba ka yi wani dogon karatu ba ne shi yasa,amma ba wai da wata manufa ba” Abdul ya faɗa . “Okay!” shi ne abin da na faɗa kafin na miƙe na kama hanyar kasuwa,tafiya nake cike da ɓacin rai ina jin ya zama dole ma na yi karatun boko tun da har an fara yi mini gori sai dai ta ina zan fara ? Ban sani ba.Da isata kasuwa na soma yin dako cikin zafin rai,wanda sam ban san na yi aikin mai yawa ba da Alhajin ya zo biyana sai ya bani kuɗi na ban mamaki.Cike da murna na koma gida,sai kuma ta koma ciki tarar da mutane da na yi a tsakar gidanmu fuskokinsu cike da alhini haka na ratsa na isa gaban Ummah wacce ke ta gumurzun kuka. “Ummah?” shi ne kawai abin da na iya cewa,ta ɗago kanta ta dube ni da idonta da suka yi mugun ja kafin kuma ta sake rushewa da wani kukan. “Meke faruwa ne wai?” na sake tambaya,da hannu ta yi mini nuni da ɗaki haka na tunkari ɗakin zuciyata na yi mini matsanancin bugawa.Cak na yi tsaye ina kallon tashin hankalin da na ci karo da shi,gangar jikin Joy ce a kwance cikin ɗaki babu numfashi .Fuskarsa babu ido an cire su haka ma daidai wuyansa an yi masa wani rame da dukkan alamu wani abu aka cire daga jikinsa. Ta maza na yi na ƙarasa na zube gwiwaina ƙasa tare da tallabo kansa,wani abu na ji ya caki idona mai bala'in zafi da raɗaɗi a dole ban shirya ba na rumtse ido gam.Kamar magiji haka aka nuno mini ta yadda aka yi abin ya faru da shi.Yana zaune cikin ajinsu aka aiko kiransa,bayan ya fito sai ya ga su Isa ne da Abdul.A mutumce suka gaisa kafin su ja hankalinsa sosai ta hanyar yi masa ƙaryar cewa ya zo ni ne ke nemansa cikin gaggawa .Suna fitowa daga cikin makaranta wata mota suka shiga da shi suka saka shi a tsakiya,suna tsaka da yin gudu suka shaƙa masa hodar bacci a haka suka isa wani gida inda suka yi masa kisan gilla,da farko wuyansa suka caka da wuƙa wanda zafi da raɗaɗi yasa ya dawo hayyacinsa kafin kuma su cire masa idanuwa duka biyun. Daidai nan kuma wasu mutane masu baƙaƙen kaya suka shigo suka zagaye Joy,wata hoda ce ɗaya daga cikinsu ya zuba a jikin Joy ɗin yana yin wasu kalamai waɗanda ba na wannan duniyar ba ne amma sarai na fahimce su.Nan take gawar Joy ta ɓata ta zo nan inda yake kwance a tsakiyar ɗaki,sai kuma na ga lokacin da Ummah ta shigo ɗakin da kuma yadda ta tsorata saboda cin karo da ta yi da wannan lukutar masifar. Idona na buɗe waɗanda nake jin sun yi mini wani mugun nauyi da zafi,har wani yaji nake ji suna yi mini feshi. Jiki na ɗan rawa na miƙe tsaye da niyyar fita sai dai wani jiri ne na ji ya soma kwasa ta,da sauri na dafa bango ina jan numfashina da ke barazanar ɗaukewa gaba ɗaya.Amma da yake ina da ƙarfin hali haka na ƙoƙarta na fito ina rangaji,wata irin runguma Ummah ta zo ta yi mini tana mai kiran sunana tashin hankalin da nake tsinkayowa a cikin amonta kamar ma ya fi na mutuwar Joy. Damtsena na ji shigar wani abu kamar mashi,amma ba shi ne ba yatsan Ummah ne.Wani furici take yi mai shige da wancan ɗin wanda ya kasance na ƙarnin baya sai dai wannan sam ban fahimta.Kamar yadda in an zuba wa wuta ruwa take mutuwa murus,to haka na ji duk zafin kaina da ɓacin raina sun sauka.Baya na ɗan yi ina kallon Ummah wacce take yi mini wani kallo ita ma,kafin cikin ɓacin rai ta ce “mene ne wannan Davido? Ina za ka je da wannan ɓacin ran? Wuce ka tafi ɗakinka,yanzun nan Abbanku zai zo” ‘Wace ce ke?’ ita ce tambayar da zuciyata ke son yi mata amma kamar wanda aka tsafe na kasa furtawa,ɗakina na koma na yi tsaye ina kallon akwatin kayana inda na ajiye littafin sirri.Ina son yin bincike a cikinsa sai dai shock ɗin mutuwar Joy ya ƙi barina dole na haƙura,babu jimawa kuwa Abba ya shigo ya kira ni da kansa.Gawar Joy muka ɗauka muka kai can gidan gawa kafin mu fara shirya yadda jana'izar za ta kasance don sai an yi bikin binne shi,domin yin haka kuma muna buƙatar kuɗi masu ɗan yawa .Na sayen akwatin gawa,da kuma abincin da mutane za su ci da kuma kuɗin da za a bai wa makaɗa da pastocin da za su yi masa addu'o'i. Tun a hanyar komawa gida Abba ya ce mini “ David ya kake gani game da bikin binne Joy? Ka ga dai ni banda kuɗi kai ne za ka yi komai,kana ganin sai mun yi gayyata dayawa ko kuwa?” Na dubi Abba cike da takaici na ce “kai ba ka damu da irin yadda ka samu gawar ɗanka ba a'a ta yadda za a rufe shi kake ? Abba ka cire ran zan bari a rufe Joy ba tare da na binciko su wane ne suka yi masa wannan kisan gillar ba suka raba shi da sassan gangar jikinsa” Sake da baki Abba ke kallona kafin ya ce “wane irin sassan jiki kuma? Ciwon ciki ne fa ya kashe shi ko?” Ni ma da mamakin na dube shi,kafin na yi wa kaina tambayar ‘ kenan shi Abba bai ga gawar Joy an cire mata ido ba?’ amma don sake tabbatarwa haka na buƙaci mu koma can mutuware. Da muka je muka shiga ciki na buɗe gawar Joy tare da tsure Abba da ido kafin na ce “ka gani ko?” “Me?” ya tambaye ni,“ba ka ga komai ba?” na tambaye shi ni ma.Ya ce “ka ga David mu je gida” ba tare da na ce komai ba na rufe gawar muka fito.Ko da muka dawo gida mun tarar da Joyel na yin kuka kamar ranta zai fita ,tana ganina ta zo ta faɗa jikina.Ban iya rarrashinta ba kawai na bar ta tana ta yin kukan har ta gaji don kanta ta je ta zube kan tabarma.Mutane sai shigowa suke yi suna taya mu jaje har cikin dare kuwa,sai da daren ya tsananta sannan ƙafa ta ɗaga.Na je na rufe ɗaki tare da shiga ɗakinsu Ummah na yi zaune kamar yadda su ma ɗin suke zaune in aka cire Joyel da ke bacci. So nake mu haɗa ido da Ummah amma ta ƙi yarda da hakan,da na gaji don kaina na miƙe na fita.Sai da na watsa ruwa na ɗan ji sanyi kafin na shige ɗakina,bayan na rufe ƙofa na ɗauko littafin sirri na ajiye kan table. A hankali ya soma buɗe kansa har aka zo a page ɗin da na tsaya,idona ya sauka kan rubutun da ya shafi nasabata. “BABU WANDA ZAI IYA MALLAKAR LITTAFIN NAN SAI SARKI KO KUMA MAI SHIRIN ZAMA SARKI! DOMIN SANIN DALILI KA BUƊE PAGE TA GABA” shi ne abin da yake a rubuce, wannan karon da kaina na buɗe page ɗin ta gaba sai dai wayam take babu rubutun komai a cikinta haushi na ji kawai na rufe shi na mayar. Na ja tsuki kafin na kwanta ina shirin lumshe idona na soma jin yanayin iskan ɗakin na canzawa.A nan take na fahimci ta zo,babu jimawa kuwa na soma jin ana shafar jikina tare da sarrafa ni kafin ta mu'amulance ni bayan nan sai na ji wata irin gajiya da ciwon jiki amma ban iya ko da motsi ba ne a haka bacci ya ɗauke ni. Wannan karon a wata unguwar nakassu duniyar mafarkin tawa ta kai ni,ko ta ina makafi ne da kurame da guragu da duk wata irin nakasa.Cike da ƙyanƙyami nake ratsa wurin wanda yake cike da datti da ƙanzata iri-iri,daga bayana na ji an dafa ni.Na juyo da sauri nan na yi arba da wata yarinya wacce ba za ta wuce shekara goma ba a duniya ,fara ce tasss ban taɓa ganin mutum mai irin farinta ba.Gashin kanta kuma wani iri ne kamar na gingiya,idanuwanta blue ne masu ɗan girma duk da kuwa yadda take ta ƙoƙarin ƙanƙantar da su,laɓanta jajaye ne sirara. “Ina ne nan?” na tambaye ta. “Daular Alfanso !” ta bani amsa tare da miƙo mini wani ɗan itaciya wanda shi ma ban taɓa ganinsa ba,hannunta na bi da kallo wanda yake da datti duk laka ta ɓata shi .Na girgiza mata kai na ce “a'a ban ci” “Ka karɓa dai za ka ji daɗinsa” ta faɗa tana yi mini dariya wacce ta bank damar ganin haƙoranta waɗanda suka sha banban da na mutane don kuwa ba farare ba ne a'a kamar chocolat haka suke da duhu amma wani abin mamaki sosai suka yi mata kyau ƙila don saboda kalar fatarta.Na kai hannu kenan zan karɓa na ji muryar Ummah “Davido?” kamar tsawa haka na ji sautin,da mugun sauri na tashi ina ware ido a kallon farko sai na ga Ummah da wata siffa kanta kamar na Tinkiya amma da na murje idona sai na ga ta dawo normal. Kafin na kai ga cewa wani abu ta ce “ka tashi ka yi mini rakiya can mutuware ina son ganin gawar ɗana kafin a rufe shi” Na ce “an samo kuɗin bikin jana'izar ne? ” “Ka same ni a ƙofar gida” ta faɗa tare da ficewa,a dole na fita na yi wanka na zo na shirya.Sai da na shiga ɗakinsu,a zaune na hango Joyel ta rakuɓe kamar wata marainiya,tausayinta ne na ji ya ratsa ni amma ban iya yi mata magana ba na fice na samu Ummah a ƙofar gida.Gaishe ta na yi amma ba ta amsa ba,taxi na samo mana muka shiga.Har muka isa babu wanda ya yi magana,sai da na nuna takardar shaida sannan aka buɗe mana mutuwaren.Wani irin iska ne mai haɗe da hucin ruhika ya tarbe mu,da sauri muka kalli juna ni da Ummah kafin kuma mu ida shiga. Gawar Joy na nuna mata,ta buɗe tana shafar fuskarsa.A yanayinta kawai na fahimci ita idonta suna gane mata abin da ni ma na gani a tattare da gawar saɓanin Abba. “Je ka biya kuɗin wanka a zo a yi masa mu wuce da shi,ba zan bari ya ƙara kwana ɗaya ba a nan” Ummah ta faɗa . Na ce “akwatin gawa fa? Ina za a samu?” “Ka yi abin da na ce” ta faɗa cikin ƙaraji,wani irin tsoron Ummah ne na ji ya ɗarsar mini a ƙahon zuciya wanda ban taɓa jin makamancinsa ba,da sauri kuwa na je na nemi mai gadi na sanar da shi tare kuma da biyan kuɗi. Wani matashin saurayi ne aka turo domin yi masa wankan,Ummah ta fita yayin da ni kuma na tsaya.Almakashi yasa ya yage suturar Joy sannan ya luluɓa masa wani zanen,ya ɗago da niyyar yi mini magana sai kuma na ga ya yi shiru tare da kafe ni da ido har sai da na tsargu na ce “Me?” “Babu komai! Ammm.. na ce ka taɓa ganin an yi wankan gawa irin wannan ko kuwa yau ne farko?” ya faɗa . Na ce “ban gane irin wannan ba?” Sai da ya sake dubana da kyau kafin ya ce “kar ka nuna kamar ba ka san abin da nake nufi ba, alhalin ga alamun baiwar da ke tattare da kai nan a bayyane” Na ja ajiyar zuciya don na fahimci abin da yake nufi, wannan yasa na basa amsar tambayar tasa na ce “yau ne farko” Ina faɗar haka sai ya miƙo mini auduga ya ce “ka cusa wannan a ƙofofin hancinka ” na dube shi har zan yi tambaya amma kuma sai na karɓa tare da yin yadda ya ce ɗin ,yana fara zuba ruwa a gawar Joy sai na ga gawar ta yi motsi.Murya na ɗan rawa na ce “kamar fa ya motsa” ya ce “ba kama ba ce motsin ne ya yi” sai kuma ya ci gaba da yin wankan,can sai ga gawar Joy ta tashi zaune kan ƙugunsa.Matashin sai ya ciro wani abu daga aljihunsa ya shayar da Joy,nan take sai ya soma aman wani baƙin abu ana cikin haka sai kuwa wasu baƙaƙen inuwoyi suka fara bayyana a cikin gidan gawar..... [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 03 Yadda baƙaƙen inuwoyin suka zagaye wurin shi ya haifar da dissashewar ƙwan lantarkin mutuwaren.A daidai wannan lokacin ne matashin mai wankan gawa wanda har zuwa yanzu ban san sunansa ba ya soma yin magana. “Kar ku yi kuskuren taɓa patient ɗina,kun yi naku aikin kun kashe shi yanzu kuma ku bari na yi nawa aikin” ya faɗa cikin muryar gargaɗi.Sai kuma na ga duk sun nutsu sun bar motsi,wani abu ya ƙara cirowa daga aljihu ya shafa a goshin Joy nan take gurbin idonsa wanda babu komai a ciki ya soma ɓulɓulowa da jini can sai ga dukkan idanuwansa biyu sun dawo.Kamar yadda mutum mai rai ke kallo haka Joy ya dube ni da idonsa kafin ya yi baya ya kwanta ya lumshe ido,gefen wuyansa wanda yake a ɓurme nan ma sai da ya zuba maganin da ban san na mine ne ba shi ma ya dawo daidai . Inuwoyin da suka kawo mana caffa? Tuni sun ɓace kamar walƙiya.Na ja ajiyar zuciya na dubi matashin na ce “kana da baiwa ! Haifarka aka yi da ita ?” “Sunana Nelson ɗa ga Sarkin yaƙin Daular Uganda ” ya bani amsar da ba ita na tambaye shi ba yana mai ci gaba da gyara gawar Joy har ya kammala. Ƙofa aka buɗe,mai gadi ne da wani suka shigo suka kawo akwatin gawa sai muka haɗu mu duka huɗun muka saka gawar a ciki. Tare da fito da ita aka saka a mota,Ummah na duba sai na ga tana kallon Nelson na ɗan matsa kusa da ita na ce “ko kin san shi ne?” “Mutane na can gida suna jiranmu mu je” shi ne abin da ta faɗa tare da yin gaba,na juya na kalli Nelson wanda shi ma na ga yana kallon Ummah wani iri.Na ce “na gode ” ya jinjina kai.Sai na wuce na shiga mota,kusa da ita na zauna kafin na ce “a ina kika samu kuɗi?” Ko kallona ba ta yi ba,a haka muka ƙarasa gida.Tun da muka shigo layinmu na soma jin ƙarar sautin ganguna ana kiɗe-kiɗe,muna isa aka zo aka sauke gawa aka ajiye ta a wurin da aka yi mata tanadi aka ci gaba da yin kiɗa da rawa da waƙe-waƙe. Hannuwana na harɗe ina kallon akwatin da ke ɗauke da Joy,duk wasu tsoffin moments ɗinmu ne suka ta kawowa ƙwaƙwalwata ziyara ina tuna yadda yake mugun sona da girmama ni.Wasu hawaye masu ɗumi ne suka zubo mini,daga bayana na ji muryar Isa yana cewa “David ashe rasuwa ƙanenmu ya yi? To Allah ya jiƙansa ya yi masa gafara,yanzun nan muka dawo daga wurin interview tun jiya da muka tafi” Na ida juyowa ina kallonsu,tsabar yadda hankalina ya ɗan gushe sam ban san mene ne shi Abdul ke faɗa ba kawai dai na ga bakinsa na yin motsi. Ji nake yi kamar na shaƙe musu wuya na kashe su kamar yadda suka yi wa ɗan uwana,amma wani sashe na zuciyata na bani wata irin shawara mai muhimmanci wacce nake ganin ita ce daidai da rayuwarsu.Rungume su na yi a tare na soma kuka biyu,ɗaya na rashin ƙanena ɗayan kuma takaicin rungumar da na yi wa abokana kuma manyan maƙiyana.Rarrashina suka fara,ina jin yadda suke sauke ajiyar zuciya mai nuni da sun samu salamar ruhi,ƙila suna tsoron kar a ce na fahimci suna da hannu a mutuwar Joy. Keɓaɓen wuri muka zauna har zuwa lokacin da manyan pastoci suka ƙaraso duk kowa ya miƙe.Addu'o'i suka fara yi kafin a buɗe akwatin gawa aka cewa Abba da Ummah su zo su yi masa kallon ƙarshe,sai dai wani abin mamaki Isa da Abdul ƙoƙarin kutsawa suke yi ban san mene ne nufinsu ba amma dai ina da tabbacin ba mai kyau ne ba wannan yasa na kasa na tsare na ƙi bari su gusa daga kusa da ni. Abdul ya shiga matso ƙwallar munafurci yana mai cewa “bari na matsa na ga ƙanenmu shikenan mun rabu da shi yaro mai kirki” hannunsa na yi saurin riƙewa na ce “kar ka tafi” sam ban yi tunanin furicina zai yi babban tasiri ba,kamar wani dutse haka Abdul ya kasa motsi da Isa ya so matsawa kuwa iya kallo na yi masa shi ma ya kasa wani kataɓus har aka rufe akwatin gawar aka ɗauke shi domin kai shi makwancinsa.Muna tafe ana waƙa har aka isa maƙabarta aka binne shi sannan muka dawo gida ,abinci aka rarraba da abun sha daga nan mutane suka ɓage da yin hirarrakin duniya. Su Isa kuwa kasa zama suka yi haka suka yi mini sallama suka tafi,ni ma wuraren ƙarfe shidda haka na silale na tafi can mutuware na kuwa ci sa'a na ga Nelson.A zaune na tarar da shi yana shayi,muna haɗa ido ya sakar mini irin murmushin nan na dama na san za ka dawo.Gefensa na samu na zauna kan banci kafin na ce “barka da warhaka” Ba tare da ya amsa ganuwar da na yi masa ba ya ce “ka yi nasarar hana su jefa ƙwayar cutar tsafi a cikin akwatin gawar ƙanenka amma hakan ba shi ke nufin yaƙi ya ƙare ba,akwai sauran rina a kaba” Na dube shi da kyau na ce “me zai faru kuma?” sai da ya miƙo mini kofin shayi sannan ya ce “za su sake yunƙurin cikar burinsu ta hanyar farmakar kabarinsa tabbas za su je” Hankali tashe na ce “mene ne mafita?” sai da Nelson ya yi mini wani kallon tsakiyar ido kafin ya ce “ka tambayi littafin sirrinka ” Ƙyaf-ƙyaf na yi da ido ina mamakin ta ya aka yi ya san ina da littafin sirri,amma sai kuma na ƙi yarda na nuna na san abin da ma yake nufi don ƙila shi ma aiko shi ne aka yi.Na ce “wane littafi kuma?” Wata dariya ya yi kafin ya ce “kar ka nuna kamar ba ka san abin da nake magana akai ba,za ka iya yi wa kowa ƙarya amma banda ni don haka ka bar ɓoye-ɓoye littafin sirrin Ruhaniya yana hannunka” “Kai ta ya aka yi ka sani?” na tambaye shi. “Saboda mahaifina ne mawallafin littafin ” ya bani amsa kai tsaye,na ce “kenan ba Aljanu ne suka rubuta shi ba?” “Akwai wani banbanci ne tsakanin matsafi da Aljanu?”shi ma ya tambaye ni. “Wane ne matsafi?” na sake yi masa sabuwar tambaya,ya bani amsa da “ni da kai” “Ni ba matsafi ba ne” “Da ace zancenka gaskiya ne to da littafin sirri bai zaɓe ka ba matsayin wanda zai karanta shi ya kuma maido tarihin ƙarnin baya” Nelson ya faɗa yana kallon kofin shayin da ya bani wanda har zuwa yanzu ban sha ba,saurin shanye wa na yi na miƙa masa kofin ina shirin yin magana na ji wani irin rau da idona kamar an watsa mini yaji.Bibbiyu nake ganin Nelson wanda ya soma karanto wasu ɗalasiman tsafi yana mai jimƙe hannuna,kamar wata leda haka ƙafafuwanmu suka bar ƙasa muka yi sama muna shawagi cikin sararin samaniya.Tun ina kallon duniya cikin hayyacina har na neme shi na rasa,ko da na dawo normal a wani ruɓaɓen ɗaki na tsinci kaina a kwance kan gadon kara irin na ƙarnin farko.Da sauri na tashi zaune ina dafe kaina da ke mugun sara mini,daidai nan aka buɗo ƙofa wani tsoho ne ya shigo hannunsa riƙe da sandar tsafi sai wani sheƙin baƙar azaba take. “Ka tashi? Barka da zuwa fadar Jacki! Ungo wannan na san ba za ka rasa jin yunwa ba” tsohon ya faɗa yana mai miƙo mini wata guntuwar gurasa da ya ciro daga aljihunsa. “Wane ne kai? Me nake yi a nan?” na tambaye shi a harzuƙe ina mai miƙewa tsaye,kafin ya bani amsa Nelson ya shigo a hasale na yi cikinsa zan kai masa naushi amma abin mamaki tsohon nan na nuna sandarsa kawai na yi baya cikin iska na dawo na faɗa kan gado. Cikin bayar da umarni ya ce “ka nutsu da kyau don za ka fi fahimtar dalilin zuwanka nan” nutsuwar na yi don ban ga hanyar ɓulle mini ba muddin na kawo gardama. Ya saki ɗan murmushi kafin ya ci gaba da cewa “wannan ɗana ne,na san ya baka labarin cewa ni ne Sarkin yaƙin wannan Daular ta Uganda.Ni ne babban abokin mahaifinka,duk wata shawara da za a zartar a masarauta ni ne nan ne basa ita a ƙarshe dai ina son ka ɗauki ɗana Nelson matsayin mai baka shawara” Wata dariya na yi kafin na ce “ni kuma meke haɗina da Uganda da kuma sarauta?” Bai ce komai ba sai sandarsa da ya nuna a kusurwar ɗakin nan take wani haske ya fito mai kamar madubi kafin kuma wata madaidaiciyar ƙofa ta bayyana.Na waro ido ina mai miƙewa tsaye,a hankali na taka na isa can na yi tsaye.Wata masarauta ce idona yayi tozali da ita,kamar dai a mafarkina kusan duk al'ummar yankin suna da nakasa ɗaiɗaiku masu lafiya.Ina cikin baza ido kuwa kallona ya sauka kan yarinyar nan,tabbas ita ce na gani ko shakka babu yarinyar da ta bani ƴaƴan itaciyar.Tana tsaye tana kallon wani gun idonta na zubar da ruwan hawaye,inda ta tsure da ido na duba sai na hangi wani babban mutum cikin naɗin sarauta da na ƙare masa kallo da kyau sai na ga sak irin fuskata ce da shi,banbancinmu shi ne tasa ta fi manyanta. “Wannan shi ne Sarki Alfanso, adalin Sarki kuma gwarzon yaƙi,shugaba ɗaya tamkar dubu,wanda bai jin tsoro ko shakkar faɗar gaskiya ko da zai rasa ransa.Shi ne mahaifinka!” tsohon ya faɗa yana dadaɓa kafaɗata,kasa cewa komai na yi tsabar shock.Duk tsiyata bai yiyuwa na ƙaryata cewa ni ɗin jinin wancan mutumin ne,sai dai ta ya aka yi hakan ta faru? Ban sani ba. “Nan ina ne muke?” na tambaya. “Kana cikin masarautarku ne wato Uganda ” tsoho Jacki ya bani amsa. “Ita waccan kukan mene ne take yi?” na tambaye shi tare da nuna yarinyar. Ya bani amsa kai tsaye da cewa “ita ɗin ta fito Albino girl,rayuwarsu nada matuƙar haɗari a duniya saboda a kullum matsafa cikin nemansu suke yi.A irin hare-haren da ake kawo mana ne aka tafi da mahaifiyarta shi ne mafarin kukanta ” Na maida dubana da kyau a gare ta na ce “to amma me yasa take kallon Sarki?” “Saboda ya ce babu wata hanya da za a san a wacce masarauta ce aka kai mahaifiyarta” “Kenan Masarautu ne ke kawo farmakin?” bai bani amsa ba sai sandarsa ya dangane da ƙasa,magijin da ke bani damar ganin yarinyar mafarkina ya ɓace.Tsoho Jacki ya dube ni ya ce “mabuɗin littafinka shi ne ka rubuta cikkaken sunanka a jikin takardar littafin sirri” sai kuma ya juya ya dubi Nelson ya ce “ku koma can inda kuka fito” ya jinjina kai kafin ya zo ya kama hannu ko kafin na furta wata kalma sai tsintar kanmu na yi a kan bancin da ke bakin mutuware. “Ya kamata ka koma gida don yau muna da aikin dare” Nelson ya faɗa . “Ta ya aka yi duk ka yi wannan? Ina nufin muka bar wannan ƙasar zuwa Uganda?” na tambaye shi. “Babu wuya ai kai ma za ka iya yi,fiye da wannan ma”ya bani amsa,ban ƙara cewa komai ba na miƙe tsaye,ta ido na yi masa sallama kafin na fito bakin ƙofar asibitin. Ina nan tsaye motoci na ta bi suna wucewa kamar wanda bai san ciwon kansa ba haka na ƙi gusawa har dare ya shigo ,iska haɗi da ruwan sama suka fara sauka sai a lokacin na motsa don neman abin da zai kai ni gida sai dai kamar an yi ruwan an ɗauke haka taxi ta bar wucewa. Ina tsaka da tafiyar ƙasa na hangi wata baƙar mota tana gudu a tsiyace,idona tamkar na mage haka suke fitar da haske suke zuƙo mini abin da ke cikin duhu.A irin haka ne na hangi Joyel a bayan mota tana ta shure-shure,tana zaune tsakiyar Isa da Abdul .Kamar wanda aka yi wa allurar ƙarfin doki haka na soma yin gudu ina bin motar har muka fita daga cikin gari .Titi motar ta saki ta ratsa jan yashi ni kuma ina bayansu,a haka har suka yi parking daidai ƙofar wani gida . Cak na yi tsaye ina kallon yadda suka ɗauke ta suka shiga da ita cikin wani gida wanda kaf wurin shi ɗaya ne,suna shiga aka rufe ƙofar sai dai ina isa bakin ƙofar wani abin mamaki na ratsa ta cikinta na wuce.Sai kuma na yi tsaye muna ƴar kallon-kallon tsakanin wasu baƙin fuska da kuma su Isa waɗanda tsabar shock yasa suka saki Joyel ba su shirya ba.Da wani matsananci gudu ta zo ta rungume ni tana kuka,ɗaya daga ciki ya ce “wane ne kuma wannan?” Ni na basa amsa da kaina da kuma amon muryar da ba tawa ba,“mutuwarka ce!” rufe bakina ke da wuya ya faɗi warwas kansa na fita daga gangar jikinsa wanda sanadiyar haka Joyel ta suma a jikina..... [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 04 Cikin rigar rashin mutumcin da na aro na yaɓawa kaina na ce “ku sanar da ni abin da Joyel ke yi a wannan gidan tare da ku” Cikin rikicewar tunani Abdul ya fara yi mini bayani daki-daki,“ka yi haƙuri David wallahi su pasto ne suka saka mu wannan aikin,su ne suka yi mana alƙawarin bamu aikin gwamnati da kuma arziki mai ɗumbin yawa muddin za mu kashe Joy bayan mun aiwatar da abin da suka ce sai kuma suka bamu maganin da za mu zuba a cikin akwatin gawar amma ka hana faruwar haka shi ne kuma suka buƙaci mu kawo Joyel ” Zuciyata na tafasa na ce “ita kuma me za ku yi mata?” “Budurcinta kawai za mu cire” ya bani amsa . Na maimaita kalmar kawai a zuci kafin na ƙure Abdul da rikitatun idona,ba tare da na furta komai ko wani motsi ba jikin Abdul ya soma yin rawa harshensa na zazzalowa kafin kuma ya yanke ya faɗi kamar yadda ake datsa nama to haka wata ƙara ta ziyarci wurin harshen Abdul na guntsirewa ƙasa ya faɗi. Isa ya saki wani mahaukacin ciwo kafin ya soma suratai na alamun hauka ya aure shi.Wani irin daɗi ne na ji a raina ganin ya haukace,ɗayan kuma na nakasa shi.Kan kafaɗata na saɓi Joyel na tashi sama cikin iska ,kamar leda haka nake shawagi a sama har na isa ƙofar gidanmu . Ina tura ƙofa na ci karo da Ummah a tsaye tsakar gida tana yin tsafi ido rufe,jikinta babu kaya daga ita sai ɗaurin ƙirji na wani jan zane.A gabanta kuwa wata ƴar madaidaiciyar tukunyar ƙasa ce cike da ruwa,muna haɗa ido da ita ta yi saurin lumshe nata waɗanda suke a juye sak irin na tumakai.Ban ce mata komai ba na shiga ɗakinta na shimfiɗe Joyel ,ina nan tsaye na ji motsi bayana. “Daga ina kuke? Me ya samu Joyel ɗin?” na ji muryar Ummah,share tambayoyin nata na yi na ce “ki zo ki taimaka mata ta farfaɗo” sai kuma na fice muna yi wa juna wani irin kallo.Ɗakina na shiga,kayan jikina da suka jiƙe na cire na rataye su jikin ƙarfen da nake aje sakale kaya. Ba tare da na juya ba na yi wani furici nan take ƙofar ɗakin ta sakawa kanta sakata,na ja wani dogon numfashi kafin na buɗe akwati na ciro littafin sirri na ajiye kan teburi.Pages suka fara ƙarrr na buɗe kansu har suka tsaya a daidai farar page ɗin da babu komai a cikinta.Nan ne na ji wata murya cikin ƙwaƙwalwata na yi mini magana “jinin jikinka shi ne tawadar rubutu” ban ɓata lokaci ba kuwa na samu allurar da nake yin ɗinki na tsaki yatsana,jini ya soma ɓulɓulowa wani kare na ɗauka na rubuta sunan David Jakob amma sai ban ga komai ba.Iskan bakina na hura daidai saitin sunan Abba nan take ya goge na maye gurbinsa da na Alfanso nan take rubutu ya soma bayyana jikin takardar kamar ana ƙyanƙyasarsa. Ina fara karanta farkon abin da ke rubuce kamar magic sai ga shi abin da na karanto ɗin ya soma bayyana a gare ni kamar na kunna magiji ko tv sai na soma ganin video ɗin shuɗaɗen zamanin da ya wuce na can wasu ƙarni da kuma na shekaru baya. Wata Masarauta ce mai girma da tsari wacce ta dace da zaratan dakarun yaƙi.Wani sarki ne mai jini a jiki ya fito,kallo ɗaya za ka yi masa za ka fahimci shi da imani da tausayi sun yi hannun riga.Wata magana ce ya yi mai kama da raini da kuma cin fuska,“duk wani mai nakasa na ƙasar nan,daga yau ina mai bada umarni da ya koma can keɓaɓen wurin da na sa aka gina .Ban son ganin nakasshe ko ɗaya na yawo a doron masarautata, wannan shi ne adalcin da ƴata tilo ta yanke wanda ya saɓawa nawa wanda na faɗa a jiya na cewa za a kashe duk wani mai nakasa in kuma nan gaba aka haifo yaro da ita za mu sadaukar da shi matsayin hadaya ga ababen bautarmu masu inganta gobenmu ” Sarkin ya faɗa yana kallon wata matashiyar budurwa wacce ba kowa ce ba illa Ummana.Wani irin kafirin murmushi ta yi tana mai bai wa sojojin yaƙin damar aiwatar da abin da mahaifinta ya ce. Daga can cikin duban al'ummar wani matashin gurgu ya matso a gaba cikin ɗaga murya ya ce “ya sarkinmu mai adalci a sake duba wannan hukunci,ta ya za a ce a mayar da mu bayan gari kamar dai wasu dabbobi? Shin nakasasshe shi ya halicci kansa?” yana gama rufe baki sai masu nakasa suka fara yin shewa haɗi da taɓa masa, wannan ba ƙaramin abu ba ne.Lamari ne mai nuni da cewa shi ɗin jarumi ne tun da har ya iya yin magana a gaban Sarkin da ba ka isa ka ɗaga kai ka kalle shi ba muddin ba shi ya lamunce da hakan ba. Cike da takaici da baƙin cikin da ya rufe Sarki ya ɗaga hannu,nan take aka sauko da tutar rashin mutumci mai nuni da za a kashe matashin wanda ba kowa ne ba sai wannan mutumin nan da tsoho Jacki ya ce shi ne mahaifina. Wasu dakaru biyu majiya ƙarfi suka zo suka ja matashi Alfanso suka tafi da shi,shi kuwa cike da ƙwarewa a aikinsa ya saka idonsa cikin na gimbiya Janaki ya jefa mata ƙwayar sonsa da kuma tausayinsa.Wani baƙin kurkuku ne aka tura Alfanso,yayin da kuma ta ɗaya gefen kuma sarki ya cika umarninsa aka soma kwashe nakassu aka kai su keɓaɓen wurin da ya yi musu tanadi. Ina kawowa nan page ɗin ta ida sai na rufe littafin na mayar da shi ma'ajiyarsa,ina shirin fara tunani na soma jin yanayin kaɗawar iska na canzawa.Ko tantama babu ruhin matar nan wacce zan iya cewa matar da ta mayar da ni mijinta shi ne zai ziyarce ni.Ban yi ƙarya ba don kuwa kamar ƙyaftawar ido haka ta bayyana gabana,a madadin ta zo ta mu'amulance ni kamar yadda ta saba a'a yau tsaye ta yi muna kallon juna. “Ban san ke wace ce ba,amma abu ɗaya na sani ba za ki taɓa yin nasarar hana zuciyata son albino girl ba” shi ne abin da na samu kaina da furtawa,furicin nawa ba ƙaramin harzuƙata ya yi ba sai na ga ta wani cije haƙora gashin kanta ya watse cikin iska yayin da fuskarta ta yi ja kamar wuta. Wani irin tsalle ta yi ta faɗo jikina,babu ɓata lokaci ta soma yin abin da ya kawo ta.Sai da komai ya lafa sannan na samu hankalina ya dawo jikina,na ja wani dogon tsaki ina jin takaicin lamarin kafin na buɗe ƙofar ɗakina.Har zuwa yanzu ana ruwan sama,amma haka na fita na cika bokiti na yi wanka.Ina dawowa na tarar an canza mini zanen shimfiɗa,an kuma kunna turaren wuta sai dai ƙamshin ba irin na bil'adama ba ne.Ina jin motsin ruhinta a cikin ɗakin alamun ba ta tafi ba,yi na yi kamar ban fahimci komai ba na shirya cikin kaya marar nauyi na kwanta.Wata murya na ji ana rera waƙa mai bala'in daɗi,sai dai sam hatta waƙar tsohuwar yayi ce ta ƙarnin baya.Amma sosai nake jin daɗinta,ido na soma lumshewa a daidai nan ne na ji motsi a bayana da kuma yanayin nan in an kwanta gefenka sai dai ban iya yin komai ba saboda fin ƙarfin ruhina da aka yi. A can ɓangaren Ummah kuwa David na barin ɗakin ta matsa kusan Joyel ta dafa kanta ta soma yi mata wasu surkulle tana jin ranta na azalzala saboda abin da bincikenta ya bada.Joyel ta ja wani dogon numfashi tana cewa “Yaya David me yasa ka kashe mutum? Wayyo ! Wayyo!” sai kuma ta buɗe idonta taram kan fuskar Ummah wacce take ta Tinkiya amma idon Joyel ba su isa su ga hakan ba kasancewarta normal mutum. “Tashi ki sha magani” Ummah ta faɗa . “Ina David Ummah?” Joyel ta tambaya. “Yana ɗakinsa” ta bata amsa tana mai tashi ta shige uwar ɗaka.Wani irin motsi ne zuciyarta ke yi mata,ganin David a cikin yanayin ɓacin rai da kuma yadda zubin jarumtarsa ya bayyana yau a fili sai ta tuno da tsohon mikin da zuciyarta ke ɗauke da shi.A fili ta furta “ina sonka Alfanso” karaf a kunnen Abba wanda yake shigowa,cikin kaɗuwar zuciya ya ce “uban wane ne Alfanso?” Ummah ta juyo a firgice sai dai ko kafin ta kai ga yi masa bayani ya rufe ta da duka,tun tana kaucewa har ta soma mayar da martani,ran Abba ya ɓace sosai ya fito waje ya ɗauki wuƙa yana ɓaɓatu “wato ni za ki dinga cin amana kina bin mazan banza sai na kashe ki yau” ita ma Ummah fitowa ta yi waje, Abba ya je zai caka mata wuƙa amma ta juya tsinin wuƙar zuwa ga Abba ta hanyar furta kalmar tsafi. Ihun Abba shi ya fito da ni daga cikin ɗakina,ban ida fita daga cikin mawuyacin hali ba na kuma shiga wani shock ɗin.Na ga lokacin da bakin Ummah ya motsa na kuma ji sarai abin da ta furta duk da kuwa kamar mai yin raɗa ta yi furicin.Babban tashin hankali a ciki kuma shi ne huda cikin Abba da wuƙar ta yi,nan take kuma jini ya soma yi masa zuba kafin ya faɗi warwas a ƙasa. Shigowar maƙwabta kuma kamar ƙyaftawar ido ce,ni ma wani furicin na yi wanda ya fito tun daga ƙasan zuciyata sai ga ni kusan Abba hannuna riƙe da wuƙar da ke soke a cikinsa har zuwa yanzu. Kururuwar Ummah cikin tashin hankali tana ambaton sunana shi ya ida jawo hankulan sauran maƙwabtan da ba su shigo ba.Raina ne nake jin yana ɓaci yayin da kunnuwana ke zuƙo mini munanan kalamai daga bakunan mutanen da suka shigo,babu jimawa kuma jiniyar motar ƴan sanda ta cika wurin.Sai da suka zo suka janye ni ne kawai na cire hannuna daga jikin wuƙar,tsakiyar ido na dubi Ummah ina yi mata wani kallo da ni kaina ban san ma'anarsa yayin da kuma ƴansanda suka maƙala mini ankwa suka fita da ni. Kamar wani kare haka wasu ɗaiɗaikun mutane suka fara jifata da duwatsu sai dai rasss nake kallon kowanne daga cikinsu .Har muka kai babban ofishin ƴansanda ban ce uffan ba,tun kafin a sauko ni daga cikin mota wani babban jami'i ya fito ya ce a wuce da ni kurkuku tun da dai an kama ni dumu-dumu cikin laifin kisan kai kenan babu buƙatar sai an shari'a. Ido kawai na rumtse tun da aka canza akalar motar zuwa kurkukun ƴan ta'adda.Motarmu na tsayawa suka fito da ni,sai da aka kai ni wani ɗaki aka canza mini kayan jikina zuwa na ƴan kaso aka kuma saka mini sarƙar ƙafa da ta hannu sannan aka kai ni masaukina.Wurin ko ta ina ƙwayaƙwayin lantarki ne manya-manya sun haska wurin kai ka ce rana ce,idanun mutane ƙur a kaina har aka buɗe ƙaton kejin da aka tunkuɗa ni na faɗi ƙasa warwas nan aka shiga yi mini dariya waɗanda suke masifafu suka shiga tsokanata suna yi mini waƙa.Cike da takaici na miƙe tsaye ina kallon kowanne sai na ga duk sun shiga hankalinsu suna wani ja da baya,daga can gefe na ji wasu masifafun IDON SHARRI(MRS SADAUKI) suna kallona ina waiga wa na ci karo da mamallakinsu,wani matashin saurayi ne da ba zai wuce shekara ashirin da bakwai ba.A kallon farko da na yi masa na ji a raina na samu aboki ,a hankali na cira ƙafata na fara tunkararsa kacar da aka ɗaure mini ƙafafu na fitar da wani irin sauti mai ƙarfi har na isa gare shi.Ina shirin zama ya dakatar da ni,“kar ka take mini yaro” wurin na duba sai dai ban ga komai ba,sai na ga ya kai hannu ya gusar da wani jaririn maciji ,tozali da idona suka yi da macijin shi ya bayyanar mini da wannan tururuwar da na taɓa gani a ƙafata,kamar ƙuda haka suka yaɓe macijin ba su barsa ba har sai da ya mutu.Nan take wanda na yi wa ɗaukar aboki na ga ya ɓingire ya faɗi babu numfashi,yayin da sauran cikin kejin suka fara yin ihun na kashe shi....... [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 05 Cikin ikon Allah ni ma nake kallon gawar mutumin da ake ikirarin ni ne na kashe shi alhalin ko yatsansa ban taɓa ba.Tuni kururuwar mutane ta jawo hankali ƴansanda,suka shigo wasu suka fitar da gawar yayin da wasu ke tambayar ba'asi daga ƙarshe dai aka fito da ni aka kai ni wani keɓaɓen wuri wanda iskan shaƙa ma wuya yake yi tsabar matsatsi kuma ni ɗaya ne a ciki. Kamar wani kumurcin zaki haka nake hargowa ina jin wani abu daga can cikin ɓargon ruhina kamar yana son farkawa wanda hakan ba komai ba ne sai baƙin makamin iko da ke gudana yana rikiɗewa cikin jinina.Adadin fusatata iya adadin yadda inuwar ke daɗa luluɓe raunatacen ruhina mai ɗauke da ƙunci tun na yarinta.Kan kace wani abu na ji abun ya ɗauki mallakar komai nawa,tun daga gangar jikina,ruhina da kuma tunanina.Wani irin ɓacin rai da rashin imani ne nake jin yana tafasa ni yana fitar da tiririn zallar son yin kisa a duk mutumin da ya yi kuskuren shiga gonata. Ina nan a tsaye cikin sabon al'amarin da ya aure ni aka buɗe ƙofa haɗi da kunna hasken ɗakin.Wani babban jami'i ne ya shigo,kana kallon fuskarsa ka san bai da tausayi ko wasa a cikin aikinsa. “Ku cire masa wannan kacocin da kuka ɗaure shi da su” shi ne abin da ya faɗa yana mai kallona,ƴansandar da suka rako shi izuwa nan cike da tsoro suka ƙaraso jiki na yi musu rawa suka buɗe makullin da aka rufe kacar kafin su yi baya da sauri su ɓuya a bayan jami'in. Sai da ya yi mini kallon ƙurilla kafin ya ce “biyo bayana ” sai ya juya ni kuma na take masa baya har zuwa wani ofishi. Duk ƙamewa suka yi yayin da shi kuma cikin bayar da umarni ya ce “ku rubuta bayanin bogi ku ce an tura shi izuwa babban kurkuku don yanke masa hukuncin kisa,daga ɓangarena zan fitar da nawa jawaban” babu wanda ya yi masa gardama haka suka ƙame tare da yin biyayya ga umarninsa.Sai da aka bani wasu sabbin kaya na saka na cire na gidan yari. Cike da girmamawa kuma aka yi mana rakiya ni da shi zuwa bakin wata zuƙeƙiyar mota.A baya muka shiga ni da shi aka dinga sharara gudu da mu,har muka isa wani tabkeken wuri ban ce masa kanzil ba ina can cikin kogin tunanin dalilin da yasa Ummah ta kashe Abba da kuma shi nasa dalilin da ya so kashe ta. Hannuna ya riƙe,wani girrr ya ziyarce ni kamar na taɓa lantarki.Na juya na kai dubana gare shi,ya sakar mini murmushi kafin ya ce “mu fita” ban yi masa muso ba na buɗe ƙofa na fita nan na yi tozali da babbar hotel,ciki muka shiga yana mai yi mini magana “za mu kwana a nan zuwa ƙarfe uku na dare sai mu wuce” kai kawai na jinjina masa kafin mu shiga daga ciki,a reception aka bamu makullin ɗakunan da ya kama mana.Makullin hannuna na shiga juyawa ina jin wani abu na daban na ratsa ni,na ɗaga kai na kalli wanda ya bani key ɗin wato mai kula da hotel ɗin .A tattare da shi na hango zallar tsoro amma ban damu ba na share tare da yin gaba don nemo ɗakin da aka bani.Ina tsayuwa bakin ƙofar na ji wani irin iska na daban ya wuce shuuu,amma a haka na zura makullin ko kafin na juya shi sai na ji ƙofar na buɗe kanta handle na yin motsi kafin ƙiiii ƙofar ta buɗe mini ta bani hanya.Ƙafata ta hagu ita ce ta fara shiga,kamar na shiga wuta haka na ji jikina yayi tsammm wanda hakan yasa don dole na rumtse ido.Kamar walƙiya haka wani haske ya feso mini fuskar wata budurwa,sanye take da doguwar riga kanti kanta babu kallabi hakan ya bai wa doguwar sumar gashin dokin da ta saka bazuwa a kafaɗunta. Ba za ta wuce shekara ashirin da uku ba,tana da matuƙar kyawu.Yadda take tafiya cike da yanga shi ya ɗauki hankalin mutane da dama da suka zo wani wuri da ban san ina ne ba kawai dai na ganta tsakiyar taro.Kan kujera ta zauna,daga nan ne ta hangi wani mutum yana sanye da suit baƙaƙe tun na mutanen ƙarnin baya,ƙamshin jikinsa kamar na gawar da ta shekare a cikin rana madadin gidan sanyi.Kallonta yake yi cike da zallar maita,yayin da ita kuma ke jin tsikar jikinta na tashi wani irin sanyi na rufe ta maimakon kuma ta gudu a'a sai ma hakan ya tafi da imaninta.Miƙewa yayi daga inda yake ya zo ya miƙa mata hannu tare da yi mata magana ƙasan maƙoshi “taso mu tafi,na jima ina dakon zuwanki na tsawon shekaru masu yawa” ba tare da ta san dalili ba haka miƙe ta bi bayansa suka shiga wata mota har zuwa wannan hotel ɗin da muka zo ni da jami'i da aka basu key ɗin ɗaki kuwa wannan ɗakin nawa shi ne suka shigo. Da wani irin mugun ƙarfi na ja numfashi tare da yin baya na fito daga ɗakin ina fitar da gumi.Daga bayana na ji muryar jami'in yana cewa “zo mu je ɗakina” na juya na dube shi,ban yi masa muso ba nan ɗin ma na take masa baya. Muna shiga kamar wanda ya san irin abin da na gani sai cewa ya yi “Nadiya ƙaramar yarinya ce,ƴa ga shugaban ƴansanda wanda yayi ƙaurin suna wurin maƙiya.Duk duniyar nan babu abin da ya fi so irin Nadiya, wannan yasa ya killace ta ya haɗa ta da littatafai don ɗebe mata kewa.A wani dare ƙaddarar Nadiya ta canza ,bayan ta wuni tana karatu haka ta shirya ta tafi bikin shagalin ƙarin shekarar ƙawarta a nan ne ta haɗu da wani mutum wanda yayi daban da mutane.Duk da ta san haka amma ta bi bayansa,kaf ƙawayenta babu wanda ya iya ganin mutumin sun ce ita ɗaya ta fita.Hatta wannan hotel da suka zo masu kula da ita sun ce ita ɗaya ta shigo ta kama ɗaki,kuma da aka duba camara tsaro ta nuna iya ita ɗaya ce . Lokacin da suka shiga ɗaki sai ta kunna ƙwan lantarki,amma lokaci guda ya ɗauke daga nan babu abin da hoton bidiyon ya sake nunawa sai kukanta da kururuwarta haɗi kuma da wani yanayi marar daɗin ji da dukkan alamu tarayya ɓoyayyar siffar ke yi da ita.Sai bayan sati ɗaya sannan aka farga da mutuwarta saboda wari da ɗoyin da hotel ɗin ta ɗauka.An same ta a cikin toilet,jikinta babu sutura fatarta duk ta zagwanye.Fuskarta ta ɗauki wata irin mummunar siffa kamar ta zombie,babban tashin hankalin da aka fuskanta tattare da gawarta shi ne a cikin madubin banɗaki an hangi gangar jikinta na yin motsi wanda ke nuni da ba ta mutu ba tana raye.Can kuma aka ga bakinta ya motsa da aka bi didigin motsi laɓanta sai aka gane cewa ta furta kalmar “ga shi nan zuwa” wasu daga cikin ma'aikata suka gudu yayin da masu ƙarfin hali suka fito da gawar Nadiya aka binne ta.Tun daga wannan rana aka rufe wannan ɗakin ba a sake buɗe shi ba,amma ma'aikatan hotel ɗin sun tabbatar cewa duk dare suna jin sauti na fitowa daga cikin ɗakin wani sa'in kuma amon muryarta ne ke neman agaji ” yana kawowa nan sai yayi shiru. Na ce “to ni mene ne haɗina da duk wannan ɗin?” Ya bani amsa da “akwai haɗi sosai ma,yau bayan na kalli video ɗin da aka ɗauka a yayin kai ka can cikin kurkuku sai na ga shigen abin da ya faru ne da Nadiya ,sam babu wata alama ko shaida cewa kai ne ka kashe saurayin nan sai dai na ce wani abu da ke ƙunshe a ruhinka” ya faɗi haka tare da kunna mini video ɗin Nadiyar ta cikin ƴar ƙaramar system ɗinsa sai dai me zan gani? Fuskar Nelson ce shi ne wanda yayi tarayya da ƴar mutane.Sam ban san dalilinsa na yin haka ba,muryar jami'in na ji yana cewa “har zuwa yanzu da nake yi maka magana ba mu samo asalin wanda yayi wannan zaluncin ba,amma kai tabbas na san za ka iya gano wane ne saboda baiwar da kake tattare da ita” Idona na ɗauke daga kallon video ɗin Nadiyar na mayar da su kan fuskar jami'in,na haɗiye wasu yawu kafin na ce “wace irin baiwa?” “Je ka kwanta zuwa da safe za mu wuce” ya faɗa yana mai rufe system ɗin tare da nuna mini gado,wani kallo na yi masa mai cike da shakka kafin na je na kwanta ɗin.Ina lumshe ido na ji wani sabon al'amari kuma wanda ban yi zato ba,ruhina ne ke yin magana da esprit ɗina kan na kai ga tantance taƙamaimai abin da ke faruwa tunanina ya ɗan gushe sai tsintar kaina na yi a mutuware.Kamar kullum a zaune na tarar da Nelson kan banci yana shayi,gefensa na samu na zauna amma abin mamaki ya gane da wanzuwata har ma yana iya ganin ruhina. “Tun ɗazu nake zaman jiran ka ” shi ne abin da Nelson ya furta yayin da kuma ruhina ya ce “ni ma na zo ne mu yi wata magana ” “Abin da nake son sanar da kai ya fi muhimmanci kan wanda kai za ka faɗa mini” ya furta tare da miƙewa tsaye,sai na ga ya rabu gida biyu waninsa tsaye yayin da kuma waninsa ke zaune a take kuma na fahimci cewa shi ma yayi balaguron ruhi ne... ★UGANDA Tsugune take gaban wata ƴar ƙaramar rijiya tana leƙon baƙaƙen tafasasshen ruwan da ke ta zafir.Ba ta buɗe bakinta ba,iya idonta ne take juyawa wanda hakan shi ke ƙara hautsana baƙaƙen ruwan masu mugun kauri kamar narkakar dalma.Daga bayanta ta ji muryar Abbanta na kiran sunanta “ EZRA!” ba ta juyo ba sai da ta daidaita saitin idonta ya dawo normal,cikin wani irin rauni ta ga mahaifin nata na kallonta. Idonta ya kawo ruwa cikin amon muryartar wanda ya kasance da i'ina cikinsa wanda tun asalin haihuwarta da shi ta zo ta ce “Abiiih..kakkkar ka damu na ci alwaaa...shin zan nemo Ummi a duk inda take a faɗin duniyar nan” Abih ya kawar da kai kafin ya ce “ki tashi ki yi shirin makaranta kar ki makara ƙarfe bakwai ta kusa ” Cike da takaicin yadda mahaifinta a kullum yake ƙoƙarin ƙaryata abin da ke ƙunshe a zuciyarsa ta miƙe tsaye wanda hakan ya bai wa baƙar doguwar rigarta damar zubewa tana jan ƙasa.Kamar wata macijiya haka take tafiya sululu ba ka ma jin sawun takonta haka kuma kamar wata inuwa sam ido bai ganin lokacin da take cira ƙafarta. Tana shiga ɗaki ta buɗe wani akwati ta fiddo Bible wanda tsabar tsufansa har wasu takardun sun cire.Biro ta ɗauka da takarda ta rubuta wasu bayanai kafin ta rufe shi ,wani baƙin mayafi ta ɗauka ta yane dogon gashinta wanda ya zubo har gadon baya sannan ta fito. Har ta kai bakin ƙofa ta kuma cin karo da muryar mahaifinta yana cewa “ga wannan baƙin tabarau ki saka domin luluɓe idonki” Ta juya da mugun sauri tana kallonsa,sai ta ga sam Abih bai so suna haɗa ido yana kauce wa dubanta.Cikin saurin fushin da ya zama ɗabi'arta yasa ta yi amfani da idon nata ta fizgo tabarau ɗin ba tare da ta motsa ko da yatsan ƙafarta ba ne.Tana gama daidaita zaman tabarau ɗin ta fice cikin sauri,tana tafe tana furta wasu ɗalasimai da ita kaɗai ta san ma'anarsu har ta isa makarantarsu . Tun a bakin ƙofa kunnuwanta suka zuƙo mata gulmarta da ake yi a can ofis ɗin shugaban makarantar,cak ta yi tsaye tana mai kaɗa kunnuwan nata suna yin wani irin motsin rai haɗi da ɗan ƙara girma. “Ɗalibai da dama suna cutuwa saboda ita ,a ƙaf makarantar nan ita ɗaya ce Albino ta banbanta da students abin da ya fi shi ne kawai a sharanɗa mata saka safar hannu da kuma niƙaf ko kuma dai abin da zai rufe wannan ƙonanniyar fuskartata mai kamar zazzaɓin faɗuwar rana” shi ne abin da muryar wata mata ke faɗa kafin muryar wani mutum ta ɗora da “ya kamata kuma a lura da kyau a zuba mata ido,makin da take samu a kowace jarabawa ya wuce hankali duk ta ƙare tana amfani da baƙin tsafin gidansu ne”..... Yadda wani jinjirin Jemage yayi mata tsuwa a kunne ne ya janye hankalinta daga sauraren masu hana ruwa gudu.Ta ɗaga kanta sama tana mai kallonsa,babu shiri wani murmushi ya bayyana a fuskarta wanda haka ya bayyanar da haƙoranta masu kalar chocolat. A zahiri za ka ji kuka ne Jemagen ke yi,amma a baɗini magana ce yake yi mata.Idonta kawai take juyawa suna fitar da wani kalar haske kamar na wutar kyandir,tana a haka ta ji daga bayanta a rungume ta. “Koojal !” ta furta tana murmushi mai sauti,Jemagen ya ɓace kamar walƙiya yayin da kuma EZRA ta juyo tana facing ƙawarta Koojal wacce ta kasance makauniya ce ba ta gani. Cike da zumuɗi ta ce “EZRA yau dai za ki cika alƙawarin da ki ka yi mini” EZRA ta sake yin wani murmushin kafin ta ce “Yesu ya albarkaci rayuwarki Koojal ,da dukkan alamu kin ƙagu ki ga duniyar nan mai cike da ababen tsoro” Koojal ta ce “Ameine!(Tana nufin Amin kamar yadda in an yi wa musulmi addu'a yake cewa Amin !) Amma dai yau za ki buɗe mini ido ko?” “Ta buɗe miki ido kamar yaya? ” Malama Sharly ta faɗa wacce fitowarta kenan daga ofis ɗin shugaban makaranta.EZRA ta ƙure ta da ido tana mai juya su suka canza kala,cike da mugunta take haɗe fuska tana yi tana motsa bakinta sai ga Malama Sharly ta zube ƙasa,wanda ya yi daidai da tasowar guguwa iya inda suke ta luluɓe su tana wani laulaye su tana yin sama da su.Ita dai Kajool ba gani take yi ba kawai dai tana jin wani canji ne.EZRA ba ta tsayar da wannan guguwar ba sai da suka isa wani keɓaɓen wuri wanda ita kaɗai ta san ina ne. Cikin i'ina take kallon Madam Sharly tana cewa “tambaya kike ba? Ta ya zan yi na buɗe wa ƙawata Kajool ido? To idonki zan cire na saka mata” Kajool wacce ke tsaye kamar itaciya ta waro makafin idonta,yayin da kuma Madam Sharly ta yunƙura za ta gudu don kuwa tuni ta dawo hayyacinta.EZRA ta lumshe idonta ta fara karanta ɗalasima “akasubamatahe! Janukohiii! Jangooo! Jangooo! Jan...jan...jango!” wasu irin ƙananun baƙaƙen macizai suka ɓulɓulowa daga cikin ƙasa suka yi wa Madam Sharly sarƙa ta ko ina....... [18/12 13:06] MRS SADAUKI: https://chat.whatsapp.com/DINOgJaFqZuCh9dFNLLmp8?mode=ems_copy_t *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 06 Wani irin murmushi ne EZRA ta yi wanda ba ka ganinsa sai ɗayan biyu,ko dai tana magana da masoyanta irinsu Jemagu,macizai ,kifaye da kuma ƙawarta Koojal, ko kuma in ta yi nasara ne akan wani abu da ta ƙudirta. Takardar da ta yi rubutu a kai ta fiddo kafin ta dubi Koojal ta ce “kar ki ji tsoro ƙawata,yanzu nan zan yi miki aiki idonki su buɗe” Kooljal ta yi ƙyaf-ƙyaf da idonta waɗanda suke farare tasss babu ɗigon baƙi ko ɗaya kafin ta ce “da gaske kuma na Madam Sharly ne za ki saka mini?” ba ta bata amsa ba,sai aikinta da ta fara tana karanto ɗalasimai kamar haka“marmaid nakhily bahee eyes! Kuncutacu habkur eyes ! Eyes” wata irin ƙara Madam Sharly ta soma yi ,yayin da kuma EZRA ta canza siffa daga mutum zuwa kifanyar ruwa,cikin zafin rai ta matsa kusa da ita tana mai sa hannu ta ciro idon Malama Sharly ɗin sannan ta dawo kusan Koojal ta shafi fuskarta nan take makafin idonta suka faɗo ƙasa kai ka ce dama na roba ne.Cike da ƙwarewa wurin tsafi EZRA ta ciro sanadarin ganin ta saka cikin gurbin idon Koojal sannan ta maida mata nata ɗin da suka zube ita ma Malama Sharly ta mayar mata da nata sai dai fa ba su da amfani. Tsaye ta yi gaban Koojal ta yi wani furicin a take ita kuma ta buɗe idon ta yi tozali da ƙawarta wacce tun tana makauniya take yawan shafar fuskarta sannan wani sa'in EZRA ɗin da kanta take siffanta mata yadda take wannan yasa ba ta yi mamakin ganin fuskarta fara ƙal ba irin ta Albino. “EZ..RA! ” ta furta murmushi mai haɗe da kuka yana kubce mata,rungume juna suka yi cike da murna kafin ta shiga yi mata godiya. “Ina Malama Sharly?” Koojal ta tambaya. EZRA ta ce“an mayar da ita makaranta” Koojal ta fara dube-dube ta ga manyan duwatsu ne ta ko ina ta ce “nan kuma ina ne?” “Farfajiyar Mermaid ce,an keɓance wannan wurin ne domin halittun ruwa masu rayuwa a doron duniyar bil'adama” EZRA ta bata amsa. Koojal ta ce “ko za ki iya zagayawa da ni? ” “A'a ba dai yau ba sai dai wani lokacin,yanzu za mu koma makaranta ne kafin a farga ba mu nan” ta faɗi haka tana mai kamo hannun ƙawarta,kamar tuntuɓe haka suka tsinci kansu a makaranta cikin kuma ajinsu.Wannan lamari ba ƙaramin burge Koojal ya yi ba,don ita a duniya tana son abin almara sai kuma Allah ya haɗa ta da matsafiya. Cikin ƙasa-ƙasa da murya ta ce “yanzu da nake gani mutane suna iya ganewa ?” EZRA ta girgiza mata kai,daidai nan malaminsu ya shigo ajin wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi gulmarta. Darasi ya fara yana tambayoyi amma babu wanda ya sani sai EZRA,duk da ya ga tana ɗaga hannu amma ƙin saka ta yayi ya juya ya ci gaba da rubutunsa. Koojal ta dubi littafinta irin wanda makafi ke aiki da shi mai kamar na'ura,shafa shi ta fara yi tana mai kallon rubutun sai ta ji tamkar wata murya na karanto mata abin da ke rubuce ba tare da ta san idanuwanta ke karatun ba. “Koojal?” malamin ya kira sunanta,cikin sauri ta ce “na'am malam” “In kin ga matsafi a gabanki mene ne farkon abin da za ki? Shin za ki guduwa ne ko yaya?” ita ce tambayar da malam ya jefo mata. Koojal ta basa amsa da “zan gaishe shi cike da girmamawa saboda babu abin da ya fi burge ni a duniya kamar tsafi da matsafi” Duk da ya ji haushin amsar haka ya ƙara jefo mata wata tambayar,“in ya yi ƙoƙarin cutar da ke fa wane mataki za ki ɗauka?” “Zan karanto addu'o'in kongosa na neman kariya Yesu ya taimake ni ” ta basa amsa.Sai ya saki murmushin jin daɗi ya ce “ta ya ake gane matsafi? Ina tambaya ne ga duk ƴan aji” Duk kowa shiru ya yi,can ya ci gaba da cewa “Maraton babban malamin Kiristanci ya ce duk wani matsafi ya tsani Bible da kuma Cross wannan ne yasa za ku ga da yawan mabiya addinin ke maƙale da Cross ko kuma ɗan ƙaramin icce mai hoton inda aka maƙala abin bauta Yesu Almasihu wannan babbar kariya ce.Sannan ya ƙara da cewa addu'ar Yesu Almasihu ka cece mu ta yi nauyi a bakin matsafi.Ku maimaita YESU KA CECE MU!” duk ƴan ajin suka furta amma banda EZRA sai kuma ya ci gaba da kawo wasu addu'o'in waɗanda suka saka kanta fara juyawa tana jin tamkar suna ƙona ta ne. Daga nan inda take zaune ta soma jin jijiyoyin jikinta suna wata irin kumbura suna ƙara girma,ta ware idonta waɗanda hucin azabar halin da take ciki ne ya haddasa suka rine suka zama kamar nunannen tumatur.Kan malam Rohan ta sauke su wanda shi kuma tsabar kaɗuwa da ganin lukutar masifa ya soma yin fitsari a wando ji kake shaaa kamar raƙumi na fitsari.Duk ƴan aji suka sa dariya,babu wanda kuma ya lura da halin da EZRA take ciki in banda shi wanda ya yi sanadiyar shigarta. Kamar wanda lantarki ya damƙe haka ya kasa yin motsi yana mai ci gaba da kallonta don dole don ita ce da kanta ta hana jijiyoyin jikinsa ci gaba da aiki.Cikin ƙaraji ta yi amfani da wata guragurbin murya mai matuƙar firgitarwa ta ce “wato so kake yi a lalle dole sai ka murƙushe baiwar tsafi da ke gudana a jinina da kuma ire-irena? Ka makaro domin kuwa na da ɗan lokaci tutar tsafi ce za ta dinga kaɗawa a kaf Daular Alfanso” Malam Rohan wanda yake cikin halin ƙaƙanikayi ya soma motsa baki yana son yin magana amma babu dama,ta hanyar tunaninsa ta bankaɗo abin da ke ƙunshe a ruhinsa.“Duk yadda kike son cikar wannan buri naki har abada ba zai taɓa cika ba ƙasƙantaciyar matsafiya,ba tun yau ba na daɗe da fahimtar cewa laifin ƙazamai nakassu ire-irenki ne suka hassala gimbiya Janaki ta yanke wa iyayenmu hukuncin mayar da su a keɓaɓen wuri ” Ambaton sunan gimbiya Janaki shi ya ƙara tunzura EZRA ,saboda duk wani mai rai da ke rayuwa a Daular Alfanso ya tsane ta saboda silarta ne suke a bayan gari ba tare da an basu damar cuɗanya da sauran al'ummar yankin Uganda ba . Daidai saitin zuciyar malam Rohan EZRA ta aika masa da wata kibiyar tsafi ta cake shi nan take ya saki wata irin razananiyar ƙara wacce ta jawo hankulan mutane da dama ciki kuwa har da shugaban makaranta. Duk students ɗin suka miƙe tsaye cike da tsoro ganin malaminsu yashe a ƙasa yana fitar da wani baƙin hayaƙi kamar tsohon batiri haka fatarsa ke zagwanyewa.Shigowar shugaban makaranta ya yi daidai da dawowar EZRA normal,ita ma sai ta miƙe tsaye kamar sauran ɗaliban tana waro idonta da suke sak irin na mage don ita madadin baƙi wani blue mai ratsin kore ke juya duniyar ganinta. Kallon tsaf shugaban ya soma yi wa students yayin da sauran malaman da suka samu damar zuwa nan ɗin suka fara ƙoƙarin ceton ɗan uwansu sai dai sun kasa saboda lamari ne na tsafi. “Kowa ya tafi gida an tashi!” shi ne kawai abin da ya faɗa kowa ya soma fita.EZRA na riƙe da hannun Koojal suka fito,direct kuma can wajen banɗakunan makaranta ta kai ta. “Me za mu yi a nan?” Koojal ta tambaya,EZRA ta ƙara ƙanƙame ta sosai kafin ta ce “ki jira kaɗan yana zuwa” ko gama rufe bakinta ba ta yi ba kuwa sautin iskan fukafukinsa ya soma kawo musu farmaki.Kamar saukar jirgin sama haka Jemagen ya dira a gabansu,babba ne sosai don ya fi girman Giwa wannan ya tsoratar da Koojal ta ɓuya a bayan EZRA ita kuwa ce mata ta yi “kar ki ji tsoro mana,zo mu hau ya kai mu fadar Mermaid zan nuna miki abubuwan da ban taɓa faɗa miki su ba” Koojal dai a tsorace ta yarda ta hau bayan Jemagen, EZRA ke gaba ita tana baya a haka ya tashi da su sama.Cikin abin da bai fi minti biyar ba ya kai su wata duniya wacce ba ta bil'adama ba. Farkon wurin ya soma ne da wani abu mai kamar bakan Gizo,yayin da hotonsa yake kamar madubi.Sauka suka yi suka ratsa ƙofar,nan suka ɓulla a daidai wurin nan da suka zo ɗazu da Malama Sharly. EZRA ta ce “nan ne tushenmu,ni ɗin jinsi biyu ce .Ba koyon tsafi na yi ba,haifata aka yi da shi sai dai ban taɓa sanin mene ne ba sai da Ummi ta ilmantar da ni.Wannan Jemagen da kika gani shi ne abin hawata,duk inda zan je muddin yana da nisa to da shi nake amfani” Koojal ta ja ajiyar zuciya ta ce “amma ta ya aka kika san da zamansa?” kafin ta bata amsa wata kifanyar ruwa ta ɓullo ta cikin wani ɗan ƙaramin gurbin ruwa.Ta yi ihu ta ce “ EZRA???” ambaton sunan nata yasa ruwa suka dinga ɓulɓulowa ta ko ina kafin ƙyaftawar ido sai ga su a ƙasan ruwa.Ido Koojal ta buɗe tana kallon halittun ruwa,wasu rabi mutum rabi kifi ko kuma rabi mutum rabi maciji.Tsaye ta yi tana kallon ƙawarta wacce a duniya in aka cire iyayenta babu wacce take so bayan EZRA,yadda ta ga jelar kifi madadin ƙafafu yasa ta waro ido ta matsa da sauri don fargar da ƙawartata sai dai ita ma sai ta ashe ita ma ta zama Siren ɗin.Wani irin kuka ne ya zo mata ba ta shirya ba,wanda ya jawo hankalin EZRA da sauri ta zo ta kama hannunta.Kamar ƙyaftawar ido sai ga su wajen ruwa a saman wata ƙatuwar bishiya.... ★ DAVIDO Ruhina da ruhin Nelson ne suka ɗingiza esprit ɗinmu izuwa maƙabartar da aka binne ƙanena Joy.A tsaye suke suna ta shawarar yadda za su haƙo gawar Joy,na dubi Nelson kafin na ce “mene ne zan yi a yanzu?” “Ka yi musu magana,ka kuma basu damar ganin ruhinka ” ya bani amsa,sai dai ko kaɗan wannan karon ban tambaye shi ƙarin bayani na game da yadda zan yi hakan ta tabbata.Ƙarasawa na yi na tsaya kai ga kabarin,abu na farko da na yi shi ne bayyana musu hasken ruhina.Sai duk suka ja baya,sai kuma na soma gaggaɓa dariya kafin na soma yi musu magana cikin gargaɗi “tona wannan kabarin shi ne babban kuskuren da za ku aikata a rayuwarku,ina mai baku shawara da ku juya ku koma inda kuka fito” Ɗaya daga cikinsu wanda yake da ƙarfin hali sai cewa yayi “ba za mu taɓa matsawa daga nan ba sai mun tabbatar da abin da muke zargi,don haka kar ku wani ji tsoro ku tuna cewa littafin sirri ya fi komai muhimmanci a rayuwar kowanne daga cikinmu” ya yi furicin ne tare da duƙawa ya soma ture ƙasar kabarin.Kamar yadda ake ɓalle hannun ƴar tsanar roba haka na yi wa dukkan hannuwansa a lokaci guda suka fita suka yi sama.Cikin iya shege irin nawa na yi amfani da hannuwan na soma ɓalla musu maruka ji kake fauuu,tun suna daurewa har suka soma yin ihu sai dai babu damar guduwa na riƙe ƙafafun. Koke-kokensu ya jawo hankalin mai gadin maƙabartar,shi kuma babu wani tunani ya kira jami'an tsaro.Ko da suka iso wurin tuni na canza musu kamanni. “David? David?” na ji muryar Jami'i na tashe ne,dakyar na fizgo ruhina daga waccan duniyar na maido shi gangar jikina.Na ware ido dakyar na sune shi,da sauri na ga ya ɗan ja baya yana haɗiyar yawu.Duk da ban san dalili ba haka na ja fatun idona na rufe,kafin can ƙasan maƙoshi na ce “har gari ya waye ne?” “Wai don Allah wane ne kai?” na ji ya yi mini wata tambayar rainin hankali sai ka ce ba shi ne ya je ya ɗauko ni ba. Ni ma cikin rainin wayon na ce “David Jakob,Mama kuma ta ce Davido” Ya ja dogon tsuki kafin ta bugi gefen cinyata ya ce “banza ba wannan nake nufi ba,a duniyar ruhaniya nake tambaya wane ne kai?” Zumbur na miƙe tsaye ina mai yi masa wani kallo kafin ni ma na aiko masa da tawa tambayar“ wa ya aiko ka wurina ?” bai ce mini komai ba illa juya mini ƙeya da yayi ya fice. Ina nan tsaye na ji wata irin ƙara haɗi da buguwar abu kan madubin window.Da sauri na juya sai dai wayam babu kowa,ƙarasawa na yi na buɗe window ɗin ban ida daidaita tsayuwata ba na ji wani irin iska wanda ba zan iya kamanta shi ba ya bugi fuskata.Na lumshe ido ina shaƙarsa ina jin wani irin yanayi kamar ana lilo da ni,ko da na buɗe idona sai na fahimci tuni ƙafafuna sun rabu ga ƙasa wato ina tsaye ne cikin iska.Ban gama fita daga wannan mamaki ba na soma jin ƙasusuwan jikina na fitar da wata irin ƙara kafin kuma a sannu a hankali wani gashin tsuntsuwa ya soma tsiro mini a jiki can kuma ɓoyayyar siffata ta ida fito na rikiɗe na zama Mikiya daidai nan kuma jami'in ya shigo idonsa ƙurrr a kaina...... Ga masu son fara payment,Waɗanda ba su da hali su tura 300 ,masu shi 500, hajiyoyi kuma 1k🌚 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +2279505822 [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 07 Cikin siffata ta tsuntsu nake kallon jami'i kamar yadda shi ma yake kallona cike da tsoro da firgici.Murya na ɗan rawa ,ya nuna ni da yatsa ya ce “David kai ne ka koma Mikiya?” ban basa amsa ba sai tashi da na yi sama ina kaɗa fukafukaina kafin na bugi gilashin window ya tarwatse haka na fita a guje ina shawagi a sararin samaniya.Cikin abin da bai fi minti biyar biyar na isa gidanmu wanda yake ɗauke da masu zaman jana'izar Abba.Kan wata bishiya da ke cikin gidanmu na sauka ina kallon kowa da ke wurin kafin idona ya sauka kan Ummah wacce ita ma ban sani ba ta ji a jikinta ne da akwai idon sharri a ankare da ita ko me,sai gani na yi ta ɗago kanta sama ta sauke idonta cikin nawa tana wani ƙanƙance su. “Me ka dawo yi?” ita ce tambayar da ta jefo mini ta ido da dukkan alamu ta gane ni,kai tsaye na bata amsa da “wurinki na zo ,ina son mu yi magana ne” “Ba ka ganin jama'a ne? Ka koma ka bari zuwa dare” “Inda zan komawa can ɗin yanzu dare ne,na yi tunanin nan ɗin ma haka ne.A takaice dai dole ki saurare ni” na faɗa ina mai ɗaga kaina sama tare da yin wata irin cara sai ga kowa da ke wurin ya ɓingire bacci in ka fidda Ummah.Ban kuma ɓata lokaci ba na sauko ƙasa,direct ɗakina na yi tsinke Ummah ta take mini sawu.A gabanta na canza siffata na dawo normal mutum,kamar wani ƙaramin yaro haka ta zo ta ci kwalar rigata tana cewa “Davido ba ka da hankali ne? Me ya maido ka nan bayan ka samu ka kuɓuce?” Na sa dukkan hannuwana na cire nata kafin na kalle ta tsakiyar ido na ce “ki faɗa mini gaskiya wace ce ke? Mene ne dalilinki na kashe Abba?” Cikin ƙaraji ta ce “ba Abbanka ba ne!” ni ma na tari numfashinta na ce “ko ma dai mene ne ai shi ya raine ni ya kuma yi ɗawainiya da ni” Wani gigitacen mari ta ɗauke ni da shi kafin cikin wani yare da ba na Hausa ba ta ce “ ni ce na haife ka don haka dole ka saurare ni kuma ka yi abin da na ce” tana gama faɗar haka ta soma harhaɗa mini kayana tana buɗe akwatina nan ta yi kiciɓis da littafin sirri ta kai hannu za ta ɗauko shi amma na hana ta hanyar yin furucin tsafi littafin ya tashi sama ya zo hannuna. Jikin Ummah na ɗan rawa ta ce “tun yaushe ka samu littafin sirri? Davido dama kana mafarkin samun prophecy amma shi ne ba ka taɓa sanar da ni ba? Faɗa mini ya siffarta take?” Ido kawai na tsurawa Ummah jin tana magana kamar dama tun can asali ta san abin da ke faruwa a rayuwata ko kuma zai faru,amma daidai ɗaya rana ba mu taɓa zama ni da ita mun yi maganar fahimta ba. Ganin na yi shiru sai ta ci gaba da cewa “haukan da abokinka ke yi kenan kai ne sila? Mutuwar Joy fa?” ta ƙarashe idonta na cikowa da ruwan hawaye. Na yi wani murmushin gefen baki kafin na ce “Ummah me yasa kike son nuna mini kina da ƙawa zuci? Kar ki yi ɓarnar hawayenki don zuwa yanzu ban san wani abu wai shi tausayi ba,zuciyata ta ida ƙeƙashe na ɗauki alƙawarin yin rayuwata a salon yadda na gani ta dace da ni.Ban damu da sai kin sanar da ni wane ne mahaifina ba saboda na riga da na san shi ” ina gama faɗar haka na nufi ƙofar fita ina mai rungume da littafina. “Ka kula da kanka, sannan ka yarda cewa Ummarka na ƙaunarka fiye da komai na duniya da ta mallaka” shi ne abin da ta furta ,duk da kalaman sun dake ni amma ban juya ba haka na fita tsakar gida a kuma take na ƙara ɗaukar siffar Mikiya na yi sama ina mai sakin carar da ta dawo da kowa cikin hayyacinsa sannan na yi gaba abina. Sai da na yi shawagi sosai wanda ya ishe ni kafin juya idona ta hanyar tsafi na dira a Uganda wannan karon a karan kaina a kuma hayyacina.Gidan Sarki Alfanso na dira a bayan wata ƙatuwar bishiyar kuka wacce Hausawa ke yi mata laƙabi da uwar Aljanu .Ƙafafuwana na sauka ƙasa kamar tarko haka wata raga ta dabaibaye ni wacce ƙaryar idon mutum normal ya ganta saboda ta tsafi ce. Sawun tawowar runduna da ya fara kawo mini farmaki yasa na yi saurin ɗaukar siffar bil'adama sai dai fa kash sam ƙafafuwa sun ƙi bani haɗin kai suna nan dai irin na tsuntsu. Yadda inuwoyin siffofin mutanen suka kewaye ni yasa na ɗaga kai domin ganin su wane ne,sai dai sam kawunansu sumul suke babu ido,babu hanci babu baki .Cikin nasu kalar siddabarun suka cilla ni wata haɗaɗɗiyar fada,sai ga ni zube kan gwiwaina a gaban Sarki Alfanso wanda ke zaune daram kan kujerar sarauta. Kaina a sunne yake hakan ya hana shi damar ganin fuskata sai ƙafafuwana waɗanda duk nake jin idanuwan dakarun a kansu. “David?” na ji muryarsa cike da nutsuwa ta ambaci sunana yayin da kuma wurin ya ɗauki wata irin guɗa wacce kana ji ba matan bil'adama ne ke yinta ba sai dai na mutanen ɓoye. Na ɗaga kaina muka yi ido huɗu da dattijon,ya sakar mini murmushi.Sam ban ga tahowarsa ba kawai dai na gansa tsudum a gabana,rungume ni yayi ƙam a ƙirjinsa nan take hasken idona ya ɗauke ban ƙara sanin abin da ya faru da ni ba sai tashi na yi na tsinci kaina kan gado na alfarma,a gefena kuma littafina ne na sirri. “Barka da tashin asubah Yarima!” wata sanyayyar murya ta daki kunnena,a hankali na juya ɓangaren da na ji ta.Nan na yi tozali da wata baƙar yarinya mai masifar kyau da kyawun fasali,a ta cikin idonta kawai ka kalla za ka iya hango farin ruhinta mai cike da tausayi da kuma rauni. Ta sakar mini murmushi wanda ya bayyana fararen haƙoranta masu ɗauke da ƴar siririya wushirya,ta ce “sunana Izzatu baiwarka ce ni wacce za ta dinga yi maka hidima” Tana gama rufen bakinta aka buga wata irin ƙarar rawa mai mugun ƙara wacce ta karaɗe kaf illahirin masarautar.Wata irin zabura na ga ta yi haɗi kuma da tsorata,na ce “ƙarar mece ce wannan?” Murya na ɗan rawa ta ce “in ka ji an buga ƙarar rawar nan to an samu wani hatsabin matsafi ko matsafi a daular nan ne” A hankali na sauko daga kan gadon ina gyaran zaman wata rigar bacci da ban san yaushe aka saka mini ita ba.Kusan window na tsaya tare da yin tsaye na ɗan ɗaga labule ina kallon yadda aka jawo wani tsoho a tsiyace,“in an kama su wane irin hukunci ake yi musu?” na samu kaina da tambayarta. Daga can inda take a tsaye ta ce “ana killace su ne domin yin hidima ga Masarauta ” Na ɗan juyo na dube ta na ce “amma ya na ga kin tsorata?” Ta yi ƙasa da kai ta kasa furta komai sai jikinta ne da ke ɗan yin rawa,tambayar tawa na sake maimaita wa hakan yasa ta ɗago fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce “ana yanka Musulmi guda ne matsayin hadaya ga ababen bautar Masarauta ” “Musulmai? Su wane ne su?” na tambaya. Cikin kuka ta ce “Addini ne da ya sha banban da sauran addinai, wannan dalili ne yasa ake yanka ɗaya daga cikinmu a cewarsu jinin musulmi tsarkake ne bai da wani rauni ko datti” Ƙarar buɗe ƙofar ɗakin yasa na mayar da idona can,wa zan gani? Nelson ne cikin shigar dakaru.Ya shigo yana mai sakar mini murmushi,kallo guda ya yi wa baiwa Izzatu ta fita da sauri. Zuwa ya yi ya rungume ni kafin ya ce “barka da shigowa Masarauta ! Ya kamata ka shiga ka yi wanka,a karo na farko za ka fita zuwa faɗa domin ƙaddamar da ƙarfin iko kan sabon matsafin da aka samu” “Ta ya aka yi ka san har na zo nan?” na tambaye shi.Ya yi mini wani kallo kafin ya ce “ka san kuwa tun yaushe kake cikin masarautar nan? Kimanin awa takwas kenan,tun da ka zo ruhinka ya fita zuwa dajin ɗaukaka, kai dai mu je ka yi wanka daga baya za mu yi magana ” Da taimakon Nelson na samu na yi wanka na shirya cikin kayan sarauta waɗanda ba a kawo su ɗakina ba sai da aka tsafe su ta yadda za su tafasa jinina . Tun kafin na fita aka fara shelar Yarima David zai fito,ɗa ɗaya tilo ga Sarki Alfanso.Ba ka jin komai sai busar sarewa,a haka na ratso cikin dubban mutanen da suka hallara wurin taron bayyana ni da kuma na hukuncin da zan yanke.Kujera ta musamman aka ware mini na zauna yayin da kuma Nelson ya yi tsaye gefen damana. Bayan kirari da sauran abubuwan da al'adu suka tanada mahaifin Nelson wanda ya kasance Sarkin yaƙi da kuma babban abokin sarki ya gabatar da ni.Kafin kuma a fito da tsohon da aka ce matsafi ne,ana gurfanar da shi ƴarsa ta rugo da gudu tana kururuwa sai dai ba a bata damar isa wurinsa ba aka dakatar da ita.A hankali na sauke idona kanta,yarinyar mafarkina ce wacce nake gani nake kuma jin ƙaunarta har ƙasan raina. Daga can inda take tirjiya kan sai an sake ta domin zuwa ga mahaifinta,a inda take tsayen ta saka idonta cikin nawa tana yi mini wani irin kallo wanda na hango tsantsar ƙarfin baƙin tsafi da kuma muguntar da ruhinta ke ɗauke da shi. Ban san lokacin da bakina ya furta “ku barta ta ƙaraso!” sakinta suka yi sai kuma ta yi tsaye tana mai ci gaba da kallona, wannan karon da ɗan tsoro a tattare da ita. Ganin ba za ta iya ƙarasowar ba na mayar da dubana ga mahaifin nata cikin bayar da umarni na ce “maida siffarka daidai shekarunka” idonsa cike da nadama ya dawo normal don a zahiri bai wani tsufa ba. Na miƙe tsaye ina mai kallon dubban mutanen da ke wurin na ce “daga rana irin ta yau,duk wanda aka kama yana gudanar da tsafi ba tare da neman izini ba,za a kashe shi yayin da kuma iyalansa za su zama bayin Masarauta.Wannan dokar za ta soma ne daga yau,dakaru ku ɗauki wannan matsafin ku kai shi kurkuku sannan ku je ku kwaso iyalansa ku maido su nan” ina gama faɗar haka na dubi Nelson shi kuma ya buga wata guduma kafin kuma ya ja ragamar tafiyata zuwa wani wurin. Wani sashe ne mai ɗauke da symbol na tsafi da kuma wasu hotuna masu motsin rai.Sarki Alfanso na ganina ya yi saurin tashi cikin iska ya zo ya tsaya gabana yana mai cewa “ya za ka yanke wannan hukunci? Shin ba ka san cewa matsafa sun fi kowa daraja a wannan Daular ba? In an kashe su ta yaya za mu haɗa ƙarfin ikon da za mu tunkari abokan hamayya?” Na yi wani guntun murmushi kafin na yi masa raɗa a kunne,ya ja numfashi tare da yin baya ya zauna .“Ka tabbata?” ya tambaye ni,na jinjina masa kai.Sai ya dubi Nelson ya ce “ka yi wa Yarima rakiya zuwa sashensa, sannan ka yi masa duk wani abu da ya kamata” “An gama shugaba!” Nelson ya amsa tare da juyawa na take masa baya muka fito.Muna tafe muna hira har muka isa sashen nawa,shi ya taimaka mini na rage kayan jikina kafin kuma na zauna shi kuma ya fita.Can ba da jimawa ba baiwa Izzatu ta shigo hannunta ɗauke da wani ɗan madaidaicin baho,ƙasa ta ajiye shi kusa da ƙafafuna tana mai cewa “ranka shi daɗe za a yi ma wankin ƙafa ne” ba tare da na ce mata komai ba na ɗauki ƙafafun nawa na saka cikin ruwan sai na ga kamar tana jin tsoron saka hannun nata a ruwan ta wanke mini ƙafafun ba tare da na san dalili ba. “Ni zan wanke da kaina?” na samu bakina da furtawa,da sauri ta girgiza kai ta ce “a'a ranka shi daɗe” sai kuma ta ɗago ta dube ni da manyan idonta masu kamar hasken gold har ta motsa baki kamar za ta yi magana sai kuma na ga yi shiru ta saka hannun nata cikin ruwan ta fara motsa su kamar mai yin wasa kafin na je ta kama tafin ƙafata.Wani yammm na ji haɗi da tsirgawar wani abu tun daga babban yatsana har tsakar kaina,yayin da kuma zuciyata ta soma matsanancin dokawa kamar wanda yayi gudun fanfalaƙi,babu shiri na ja fatun idona na rufe.Can kuma na tsinkayi muryartar na cewa “na ji daɗin hukuncin da ka yanke ranka shi daɗe,hakan da ka yi sai yasa na ji a raina wata rana mafarkina zai zama gaskiya” A hankali na ɗan ware idona ina kallon yadda take murmushi har dimple ɗinta na lotsawa ,yadda kuma ta ci gaba da wanke ƙafafun ya kusa saka ni na suma don har wani tausa mini ƙafafun take tana cuɗa su kamar mai yi mini susa.Da wani bala'in sauri na ciro ƙafafun nawa sama wanda hakan ya haifar da faltsar ruwan suka shigar mata ido ,ta saki wani irin ihu tana kuka kamar wata yarinyar goye ni kuma na saki baki ina kallonta kamar na sheƙe da dariya..... Waɗanda ba su da hali su tura 300 ,masu shi 500 hajiyoyi kuma 1k🌚 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 08 A hankali na miƙe na yi tsaye gabanta sai na ga na kere ta tsayi sosai.Fuskarta na tallabo tare da gwale idonta na kai bakina ina bushe mata ruwan,sai ta ɗan ware idon alamun tana son ganin ko ya fita kafin ta ƙara rufe su gam tana yarfa hannu.Wani irin tausayi ta bani sai na ga kamar ƙanwata ce Joyel wannan yasa na ƙara mayar da hankali wurin bushe mata idon,sai kuma reshe ya juye da mujiya ta yi mini wani ƙwaƙwaran riƙo wanda ya kusan sumar da ni don kusan jikinta duk yana kan nawa.Wanda kuma shi ne karon farko da na taɓa samun kusanci da wata mace wacce ba muharamata ba. Da sauri na ɗan ture ta saboda sam ba zan juri lantarki da nake jin yana jana ba,ita kuwa da wani mugun gudu ta nufi toilet har dogon mayafinta na faɗuwa wanda ya bani damar ganin baƙar sumarta wacce aka yi wa saƙar kitso .Ina nan tsaye nake jin ƙarar zubar ruwa,sama da minti biyar amma ta ƙi fitowa sai na ji kuma na damu a hankali kamar mai tsoron taka ƙasa na je na buɗe ƙofar.Cak na yi tsaye kamar wanda aka zubawa ruwa masu mugun sanyi ,yayin da ita kuma ta ƙara sunne kai tana wasa da yatsun hannunta.Cikin abin da bai fi sakan biyar ba na ƙarewa zubin halittar kallo ta saman jiƙaƙiyar rigarta wacce ta kwanta luf jikinta ta lafe,dakyar na iya yin baya na koma na duƙa na ɗauko mata mayafin nata wanda na yi imani rashinsa ne ya hana ta fitowa. Ban ƙara shiga toilet ɗin ba,na dai miƙa mata shi ni kuma ina daga waje.“Ungo ki saka” na faɗa cikin wani irin sauti wanda ya fito daga ƙasan zuciyata ji nake kamar ina son kare mata wata daraja ce wacce ni kaina ban san dalili ba. Ban sani ba ko har zuwa yanzu ba ta ɗago kan nata ba ne wannan yasa ta ɗan haɗa da hannuna ko mene ne,amma haka nake kyauta zato.Da sauri na sakar mata shi na nufi kujera na je na zauna,zuciyata na ɗan dokawa ta fito sululu kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Fuskarta nake son gani wannan yasa na ce “sabulun ya fita?” Murya kamar ta yaro mai koyon magana ta ce “ba sabulu ba ne sinadarin tattalin lafiyar ƙafafu ne” sai kuma ta kai gefen mayafinta ta goge ƙwalla. Raina ne na ji babu daɗi na ce “zo zauna bari na fita na ga Nelson ko zai samu wanda zai duba miki idon” da wani irin sauri ta ɗago tana girgiza kai ta ce “ka rufa mini asiri ni ɗin baiwa ce kawai,in na je gida Kakata za ta duba mini ita ɗin likitar gargajiya ce” Cike da jin haushin kaina na ce “ok” sai ta zo ta ɗauki bahon ta fice,yayin da ni kuma na shiga jan tsuki ina jin wani irin takaici na rufe ni amma Nelson na shigowa sai na wani manta da wata baiwa Izzatu. Masarauta muka zagaya Nelson na nuna mini komai da ke cikinta da kuma yadda ake gudanar da lamurra har muka zo kurkuku.Nelson ya ce “wannan shi ne kurkukun sirri wanda ake ɓoye wasu daga cikin matsafan da ake shakku akan tsafinsu ” yana furucin ne tare da kamo hannuna yasa wuƙa ya tsaga shi,jini ya soma zuba sai ya ɗora shi jikin ƙofar yana mai ci gaba da cewa “manyan Aljanai ne suka tsafe ƙofar nan ta yadda babu wanda zai iya buɗe ƙofar nan sai jinin mutum uku,na farko mahaifinka na biyun kuma mahaifina sai kuma kai” Ba tare da na ce komai ba na ratsa baƙar ƙofar wacce ba irin normal ƙofa ba ce,Nelson ya take mini baya.Kejin farko idona ya fara sauka,wata mata ce fara sol idonta na tsiyayar da ruwan hawaye yayin da kuma gundulalun yatsunta ke share su.Muna haɗa ido da ita ta wani zabura irin kamar Kare ya ga mutum yana son cizonsa,da ido kawai na kalli Nelson ya bani jawabinta. “Matar matsafin nan ce ta ɗazu,an samu nasarar cabko ta ne a wani dare da bokayen Masarauta suka gano ita ce matsafiya ta farko da ta fara yin nasarar gurɓata ruwan da mutane ke sha ta silar haka ne adadin makafi ya yawaita a wannan Daular ” Raina ne na ji yana azalzala sai na ce “kenan ita ce ta haifi Albino girl ɗin nan?” “Eh ƴarta ce!” ya bani amsa. Na ce “me ake jira to da ba a kashe ta ba?” “Lokaci na zuwa” Tafin hannuna na ji yana motsi wanda ko tantama babu tururuwa ce ke fitowa,ƙwaya biyu na jefa mata cikin kejin suka fara cizonta ta soma gurnanin wahala.Sai kuma muka yi gaba inda na samu wani tsoho mai ɗauke da ƙusumbi wanda kuma ba komai ne cikinsa ba sai macizan tsafinsa. “Shi kuma wannan fa?” na tambaya. “Shi ne farkon wanda ya taɓa shiga wannan kurkukun,shi ne ya yi silar ƙetarar da sarauniya Janaki daga wannan Daular zuwa wata ƙasar ya kuma rufe duk wata ƙofa da za ta sa ta ƙara shigowa nan saboda gallazawa sarkinmu” Da ido na tsure shi nan take na fahimci shi ne bafaɗen wancan Sarkin mahaifin Ummana,na yunƙura zan kashe shi amma Nelson ya dakatar da ni ya rarrashe ni sannan muka fito. Ko da dare yayi zama na musamman muka yi ni da sarki Alfanso wanda har zuwa wannan lokacin ban furta masa kalmar da ke nuni shi ne mahaifina ba.Bayan mun gama cin abinci muka tattauna game da abin da na gani a Masarauta kafin kuma mu yi sallama kowa ya tafi sashensa. Cikin kayan bacci na alfarma na shirya ,na rage hasken ɗaki kafin na jawo littafin sirrina.A daidai page ɗin da na tsaya ya buɗe sannan ya ci gaba da nuno mini abubuwan da suka shuɗe. Ta ƙarfin tsafi ne a wancan lokaci Alfanso ya jawo ragamar hankalin gimbiya Janaki ta zo har a nan cikin kurkuku ta kawo masa kanta ya yi tarayya da ita wacce ta sauya ƙaddararsu shi da ita. Ina kawowa nan na yi wa littafin magana cikin sigar raɗa na ce “ka bani wani tarihin ban son wannan,in lokaci ya yi iyayena da kansu za su bani gwagwarmayar da suka sha” ai kuwa ina gama rufe bakina sai pages ɗin suka fara yin ƙarrrr suna ta gudu haɗi da buɗe kansu,har aka zo kan wata page mai ɗauke da wasu ahali.Uba mahaifi ,uwa da kuma wata ƴar babynsu a hannu ita ma tana riƙe da ƴar tsanar roba. Na kai hannu na shafi hoton babyn,girrr na ji wani shock ya kama ni da sauri na rufe littafin ina jin kamar na taɓa jin makamancinsa abin da na ji sai dai ko da wasa ban kawo a kaina wai moments ɗinmu ne na ɗazu ni da baiwa Izzatu. Ina shirin kwanciya bacci na soma jin yanayin iskan nan na kaɗawa,wato matar mafarkina ce za ta bayyana.Wani irin sanyi ne ya soma luluɓe ni yana saukar mini da kasala,idanuwana sun yi mini nauyin da yasa dole na soma rufe su a daidai kuma wannan lokacin ne ta bayyana a gare ni cikin shigar tsaraici.Tana shirin kai hannu jikina wani irin haske da ban san daga ina ya fito ba ya taso ya luluɓe ni tare da yi mini iyaka da ita.Na ja wani numfashin farin ciki kafin wani daddaɗan bacci ya ɗauke ni mai ɗauke da mafarkin prophecy ɗina wanda ababen bauta suka zaɓe ni matsayin wanda zai cika musu wani buri wanda tun lokacin baya suka fara gina shi. ★IZZATU Ko da ta fita daga sashen Yarima David direct can ɓangarensu na bayi ta nufa.Tana shiga ta soma cire kayan jikinta ta jawo wani tsohon zane ta yi ɗaurin ƙirji kafin ta fara kiran sunan Kakarta “Dadda? Dadda?” daga can cikin wani ɗan ɗaki mai kamar akurkin kaji wata dattijuwa ta fito tana cewa “shalele har kin dawo?” da mugun sauri Izzatu ta ƙarasa wurinta tana cewa “kin ga Dadda ruwan wankin ƙafafun Yarima sun shigar mini ido kuma an zuba musu sanadarai dayawa” Wani irin kallo ne Dadda ke yi wa Izzatun mai cike da tsoro,shakku da kuma zargi kafin can ta nisa ta ce “je ki kwanta kan gado na duba idon” ba tare da ta musa ba ta je ta kwanta ɗin,Dadda ta ɗauko wata ƴar ƙaramar fitilar hannu wacce a baɗininta wani busashen maciji ne da ya yi zamani wajen ƙarni uku. Idon Izzatu ta soma dubawa bugun zuciyarta na sake tsananta tana jiye wa ƴar jikarta tsoron abin da tarihi ya tanadar mata.Yadda take gumi ya saka Izzatu cikin damuwa ta ce “Dadda ko dai makancewa zan yi ?” Dadda ta ajiye fitilar tana mai cewa “a'a zan saka miki magani sai a ɗaure idon” Izzatu ta ce “to bari na yi alwala tukun ” sai da ta je ta yi alwala ta dawo sannan Dadda ta saka mata maganin ta ɗaure idon sai ta zauna gefenta tana kallon face ɗinta sannan ta ce “ya yariman yake a zubin halitta? Ɗazu na ji gangami amma ban fita ba ballantana na gansa” Izzatu ta saki wani murmushi wanda kana jin sautinsa za ka fahimci tun daga ƙasan zuciyarta yake,ta ce “dogo ne mai cikar zati,yana da manyan idanuwa da ɗan madaidaicin saje,fuskarsa babu walwala amma yana da kirki” Dadda dai ido kawai ta tsura mata can ta miƙe ba tare da ta ce komai ba ta shiga haɗa wasu magunguna tana yi tana yin wasu siddabaru tana zuba wasu kalolin ruwa da aka tatso daga jikin wasu dabbobin masu dafi. Bayan ta gama sai ta zuba maganin cikin kofi ta bai wa Izzatun da kanta,duk da babu daɗi haka ta daure ta sha.Magungunan sai suka saka ta bacci wanda hakan ya bai wa Dadda yin wani tsafi wanda ta jawo wasu tsoffin ruhika da zamaninsu ya shuɗe.Kamar wasu likitoci haka suka zagaye Izzatu kowanne yana nasa aikin sai dai sam sun ƙi yin nasara game da abin da suke buri a dole suka haƙura. Lokacin sallar azahar na yi Izzatu ta farka ta je ta yi,haka ta wuni tana tunanin irin yadda Yarima David ya bushe mata ido ita ɗaya kuma sai ta yi ta murmushi a haka dare ya same ta.Bayan ta gama shafa'i da witiri sai ta yi zaune kan sallaya idonta na rufe da bandejin da Dadda ta saka mata.Tasbihi ne take ta jerowa haɗi da kirari ga Ubangijin talikai tana jin wata nutsuwa na ratsa ta,a daidai lokacin ne kuma aljanar Yarima David ta yi ƙoƙarin kusantarsa sai dai kash addu'ar kariya da neman Allah ya saka hannu a lamurran sarkin daularsu na gobe yasa ta kasa mu'amulantarsa. A wannan daren sam Izzatu ba ta yi bacci ba,wani irin sabon yanayi take ji yana bijiro mata wanda ba taɓa sanin kanta da shi ba.A hankali ta tashi kamar makauniya ta soma yin lalube sai kuma wani abin mamaki sai ta ga wani haske ya fito mata a tsakiyar goshi wanda ke bata damar gani duk da idonta a rufe suke.Sam ko kaɗan tunaninta bai bata cewa ido uku ne gare ta ba,biyu na normal mutum ɗayan kuma wanda ababen bautar kakanni da iyayenta ne suka tsaga mata ita wacce za ta dinga bata damar ganin abin da mayafin sirri ya ɓoye.Cak ta yi tsaye tana kallon Dadda wacce ta sharar baccinta da gibjejen kanta irin na Saniya,yadda zuciyarta ta soma bugawa a tsiyace shi ya bai wa masu kula da idon goshin saurin rufe mata ita sai ta bar ganin komai.Ji ta yi wani abu ya matsar da ita shuuu ya kai ta dab da ɗan madaidaicin gadonta na itace,babu shiri ta kwanta tare da soma karanta “hasbunallahu wa ni'imal wakil!” cikin ikon Ubangiji ta samu salamar ruhi ta yi baccinta. ★A can ɓangaren EZRA kuwa duk da Yarima David ya bada umarnin a damƙo ahalin gidansu hakan bai sa dakaru sun rufe ta ba. Gida ta koma ta je ta yi tsaye gaban baƙar rijiyar tsafin da mahaifiyarta ta nuna mata ita da kuma yadda ake amfani da ita.Cikin ƙwarewa a wurin tsafi ta soma kiran baƙaƙen ruwan da ke kwance a rijiyar,nan suka fara yin zillo suna tumbatsa sai dai fa sam ta kasa taɓuka komai game da Yarima David saboda shi ne zaɓin ababen bautarsu. Duk da haka EZRA ba ta karaya ba da dare ya yi sai da ta ƙara gwada sa'arta sai dai wannan karon garkuwar da ke bai wa Yarima kariya ta sha banban don kuwa wannan garkuwar hasken rahama ce .Cike da tsoro da firgici ta soma kiran ruhin Goggoji wato aljanarsu babu jimawa wata baƙar siffa marar kyawun gani ta fito daga can ƙasan rijiyar tana mai bata amsar abin da take son sanin cikin wata irin murya ce marar daɗin amo sannan a Yaren mutanen farko take cewa “garkuwar Yarima tana cikin Daular Alfanso,ba iya garkuwa ba ce ita ce sarauniyar gobe muddin ba ki yi wani abu ba to za ta hana ki cikar burinki da na mahaifiyarki” Cikin ɓacin rai EZRA ta yi wani ihu wanda ya haifar da rikiɗewar harshenta ya koma wani baƙin maciji,idonta ma suka juye suka dawo wasu kore kafin ta fara aman furicin ɗaukar fansa tare da alwashin ko wace ce mai bai wa Yarima kariya ita ce za ta zamo ajalinta...... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ BONUS Daga yau Laraba bonus zai tsaya da zarar na saki page 10 to 500 ne,yanzu kuma bonus za ki tura 300 VIA 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 . 09 #Yarima David Tsawon kwana biyu ban saka baiwa Izzatu a idona ba,tun ranar da ta zo wanke mini ƙafafuwa sabulu ya shigar mata a ido.Duk yadda na so kuma na watsar da zancen nata sai na ji na kasa ina son jin labarinta.Yau rana ta uku kamar yadda na samu canjin wacce ke zuwa tana yin ayyukan da baiwa Izzatu ke yi,tana shigowa ta gaishe ni cike da ladabi tana shirin kwasar kayan wanki na ce “ina waccan baiwar?” Ba tare da ta ɗago ba ta bani amsa da “ba ta da lafiya,idonta ya samu matsala ” Haka kawai na ji ƙirjina ya buga,na ce “makancewa ta yi ko me?” “Eh to hakan dai na ji ana faɗa amma ban tabbatar ba” ta bani amsa kanta na ƙasa har yanzu. “Okay! Ki yi mata jagora zuwa nan ɗin” na faɗa cikin wata irin izza da ban san yaushe ta ratsa jinina ba.Sai da ta ɗan rusuna kafin ta ce “an gama ranka shi daɗe ” sai ta fice. Bakin window na je na yi tsaye ina kallon yadda bayi ke ta kai komo a cikin katafariyar farfajiyar masarautar.Yadda nakasa ba ta hana wasu daga cikin bayin aiki ba shi ya fi komai burge ni,saboda ina son mutum mai jarumta.Ina nan tsaye na ji suna neman izini,ba tare da na juyo ba na ce “ku shigo!” Da sauri kuma na lumshe ido jin amon muryartar na furta kalmomin amincin Ubangijinta a gare ni,duk da cewa ni ɗin ba musulmi ne ba amma na ji daɗin haka sosai.A hankali na juyo,idona suka yi tozali da ita tana sanye cikin wani pink ɗin hijabi har ƙasa idonta na naɗe da wani jan ƙyalle.Ɗayar baiwar na kalla,da mugun sauri ta fice har tana tuntuɓe. “Ga ni ranka shi daɗe ” ta furta cikin wata irin sanyin murya tana ƙanƙame jikinta da alamu kamar sanyi take ji,a hankali na soma takawa zuwa gare ta har na isa gabanta na tsaya.Ba tare da na ce mata komai ba na kai hannu zan cire bandejin sai dai ya ƙi fita ba tare da wani tunani ba na ja wuyan hijabinta baya kanta ya fito.Na ɗan ranƙwafa tare kai hannuwana baya ina kuma kallo na kwance ƙullin tare da cire ƙyallen duka. “Buɗe idon na gani!” na furta cikin bayar da umarni,kai ta girgiza wanda ya bai wa baƙar sumar kanta damar motsawa.Zuciyata na ɗan dokawa na soma motsa bakina ina karanto wasu ɗalasima haɗi da hura mata iskan bakina a fuska.Babu shiri ta buɗe idon,sai dai a tashin farko sun canza daga na normal mutum saboda wata irin kalar haske da suke fitarwa.Ɗayan idon ya zama kamar hasken rana yayin da kuma ɗayan ya ɗauki siffar na mage yana fitar da wani blue haske. A hankali kuma ta ƙara mayar da su ta rufe,da sauri ni kuma na sa hannu ina ƙoƙarin buɗe su sai ga Nelson ya turo ƙofa ya shigo.Cak ya yi tsaye yana kallon mu kafin yayi gyaran murya,baiwa Izzatu ta nufi ƙofa za ta fita amma na dakatar da ita “ke!” cak ta tsaya ba tare da juyo ba. “Kina iya tafiya ke ɗaya ne ba tare da ƴar jagoro ba?” na tambaye ta ina kallon yadda hijabinta ke jan ƙasa.“Eh ranka shi daɗe zan iya” “Okay!” na furta,tana fita Nelson ya matso yana cewa “meke tsakaninka da wannan baiwar? Ka rasa wacce za ka ƙulla alaƙa sai wacce ba ta da wasu taurari masu haske?” Wani irin kallo na yi masa kafin na ce “na yi maka kama da wanda zai yi mu'amalar banza da mace ? Yawwa dama ina son yi maka wata magana,me yasa ka kusanci Nadiya sannan kuma ka kashe ta?” Babu wata kunya Nelson ya bani amsa da “saboda ina son samun ƙarfin power,ita ɗin ƴa ce ga wani matsafi ya saka mata abubuwan tsafi sosai su ne na sace sai kuma aka samu akasi ajalinta ya yi” Na taɓe baki kawai tare da komawa bakin window na yi tsaye. “Yarima faɗa mini mana shin namiji ne kai?” na ji wata tambayar rainin hankali Nelson ya jefo mini. A zuciye na ce “a'a mace ce ni ! Ai ka ɗan kwali a kaina” Ya yi wata irin dariya sannan ya zo kusa da ni ya tsaya yana mai cewa “ba haka nake nufi ba,tambaya nake yi in ka taɓa jin feeling akan mace” Da sauri na kalle shi ina jin bugun zuciyata na canza sheƙa,na haɗiye wasu yawu ina mai ci gaba da kallonsa.Yayin da shi kuma ya ɗora da cewa “kar ka ji kunyata,ni abokinka ne sannan kuma mataimakinka ban yi maka wannan tambayar don rainin wayo ba a'a sai don ina son isar maka da wani saƙo mai muhimmanci ” “Wane irin saƙo?” na tambaye shi. Ya ce “duk wanda ke ɗauke da rigar prophecy ana killace masa sha'awa har zuwa wani tsaunin nasara,ba zai kasance namiji ba har sai in ya haɗu da macen da ababen bauta suka zaɓa masa wacce ita kanta ba normal mutum ba ce tana ɗauke da wani muƙamin ƙarfin iko ne wanda zai taimaka maka ka tura motar burinka ga ci” Na kawar da kai gefe ina mai cewa “sam ban fahimci abin da kake son faɗa ba” Nelson ya ce “ka fahimta sarai Yarima kawai ba ka son sanar da ni amsar tambayata ta farko,sai dai ka sani nan kaɗan zan samo ta ba ni ɗaya ba har da mai girma sarki Alfanso ” Na juyo da sauri ina kallonsa,ya jinjina kai yana mai ci gaba da cewa “a ranar da ka zo masarautar nan in ba ka manta ba ka suma,a lokacin ne kuma aka gudanar da bikin ƙaddamar da kai.Aka yi maka wankan ruwan tsafi wanda ba a samu damar yi maka shi ba lokacin da aka haife ka, sannan an yi maka sabon shayi wanda za a tabbatar da ingancinsa nan da kwana uku ” “Shayi? Ni ɗin ne aka yi wa sabuwar kaciya? Hahaha” na yi wata irin dariya saboda maganar tasa ta fi kama da rainin wayo. Ya ɗaga gira ya ce “tabbas an yi maka sabon shayi Yarima.Kuma ƴan matan lorori ne za su tabbatar in kai namiji ne ko kuwa dai...” mugun kallon da na watso masa ya saka shi yin shiru . “Kana iya tafiya!” na furta ina jin wani nauyi a zuciyata.Nelson ya ɗan bubuga kafaɗata ya ce “ka huta lafiya sarkinmu na gobe” har zai fice na dakatar da shi ta hanyar cewa “an kawo iyalan wannan matsafin?” “Matarsa na rufe a kurkuku ko ka manta? Sai ƴarsa ce kawai EZRA Albino girl ” “A je a tawo da ita” na faɗa cikin bayar da umarni,ya ce “an gama” sai ya fice na bi bayansa da kallo ina maimaita kalaman da ya furta mini a game da nagartata ta ɗa namiji.In da akwai wacce zan gwada sanin ni ɗin a wane sahu nake cikin jerin maza to EZRA ce,yarinyar mafarkina matar da zuciyata ta zaɓa. Ina nan a tsaye bakin window na tsinkayi Nelson shi da wasu dakarun sun haɗu wuri guda suna yin wasu alamo na tsafi,kafin ƙyaftawar ido suka ɓata cikin wata ƙura da ta turniƙe wurin ta haifar da guguwa. Ba a kuma ɗauki lokaci ba suka bayyana suna riƙe da EZRA,sai ƙoƙarin ƙwacewa take .Nelson ya ɗago kansa saitin benen da nake,duk nisan tazararmu kuma bai hana mu ganin ƙwayar idon juna ba har muka yi magana irin tamu ta matsafa. Cikin sauri na je ƙara kimtsawa na ɗora babbar rigar ƴaƴan sarakai kafin na fita.Ina tafe wasu ɓoyayyun ruhika na take mini sawu har na isa wani sashen sirri wanda aka ware domin ni,ban jima a cikinsa ba aka kawo mini EZRA hannuwanta ɗaure da kacocin tsafi waɗanda nata tsafin ya gagara ya kwance su. A gabana suka gurfanar da ita kafin su fice su bar Nelson shi kaɗai yana kallona. “Zan neme ka daga baya” na furta,ya jinjina kai kafin ya fice. Na maida dukkan hankalina a kanta ina jin wutar sonta na ƙara ruruwa a birnin zuciyata. “Mene ne sunanki?” na tambaye ta. Cikin zafin kai na matsafiya ta ce “ka juya ƴaƴan wurinka domin samo sunan” “Ni ba boka ba ne matsafi ne!” na bata amsa ina mai ɗauke ta da wani gigitacen mari wanda ainahinsa ba daga gare ni ya fito ba a'a kawai na samu kaina da yinsa ne. Ta goge bakinta da ke fitar da jini kafin ta ɗago tana kallona da idon sharri,kunnuwanta kuma suna daɗa yin tsayi sosai har suna mai hudu dogon gashin kanta wanda yake kamar zaren kwakwa. “Ki yi ƙoƙarin mayar da waɗannan siffofin naki kafin raina ya ƙara ɓaci na sauke miki waɗannan kunnuwan masu kamar na Zomo ” na furta tare da kallon tsakiyar idonta da nawa idon muguntar. Ta saki wata razananiyar ƙara tana mai rumtse idonta gam,nan take kuma suka fara shatatar da jini.Rai a ɓace na ce “dakaru!” suka wani buɗo ƙofa da ƙarfi suka shigo,“ku ɗauke ta ku kai ta can inda aka ajiye mahaifinta ƙila in ta ga irin azabar da ake yi masa ta yi hankali ta saurare ni a nutse ” na furta cikin amon ɗaga murya. Ƙiiii suka ja ta suka fice da ita,ni ma fita na yi na koma sashena na fiddo littafin sirrina.Hoton nan dai ne na ƴar babyn nan mai ɗauke da ƴar tsanar roba.Zama na gyara na soma gwada yin siddabaru don nuna mini abin da babyn ta zama a yanzu sai dai kashhh iya wani zane kawai na iya gani da ke manne gefen wuyanta. ★ BAIWA IZZATU A daren ranar da ta ga Dadda da kan Saniya a wannan daren ne prophecy ɗinta ta soma.A washegari sam ba ta tada wa Dadda zancen ba ita kuma a nata ɓangaren sai ƙoƙarin ganin ta rufewa Izzatun idanuwanta take don kar ta ƙara yin tozali da Yarima David sai dai kuma aka samu akasi yau Yariman da kansa ya turo wata baiwa kan ta zo ta tafi da ita.Duk yadda Dadda ta so hana Izzatun tafiya amma kasa samun ƙwarin gwiwar yin haka ta yi a dole ta bar ta suka tafi. Ita kuwa IZZATU banda bugawar zuci babu abin da take yi har lokacin da suka isa can ɗin.A sa'ilin da Yarima ya samu kusanci da ita sosai ji ta yi numfashinta na ƙoƙorin ɗaukewa,don haka ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba da Nelson ya shigo ya same su wanda hakan yasa ta samu damar silalewa. Tana tafe tana gwada buɗe idon nata amma ta kasa,yau ɗin ma ji ta yi wani abu na yi mata motsi a tsakiyar goshi kafin kuma ta samu damar ganin duk abin da ke gabanta.Sam ba ta yi tunanin idonta ne na uku ya buɗe ba,a haka ta ƙarasa gida tana buɗe ƙofa Dadda ta saki ƴar tukunyar ƙasar da ke hannunta tana mai kallon idon da ke tsakiyar goshin IZZATU wanda kuma da idon ne take kallonta. “Dadda lafiya kika saki tukunya haka kamar kin ga aljana?” IZZATU ta tambaya. Dadda ta haɗiye wasu yawu kafin ta zo da sauri kamar za ta faɗi ta kamo hannun Izzatun .Jikinta na ɗan rawa ta fiddo wani tandun kwalli cikin aljihun rigarta,ta shafa wa kanta sannan ita ma Izzatun ta shafa mata.Kamar ƙuda haka suka dawo ƴan ƙananu da su,Dadda ce ta kama hannun Izzatun suka shiga wannan tandun kwalli wanda ya kasance wata duniya ce ta daban da wasu al'ummar ke rayuwa a cikinsa. IZZATU wacce take ganin komai kamar a mafarki ta soma ƙoƙarin toshe hancinta da yake shaƙo mata wani irin wari kamar na ruɓaɓen kifi,ga wani irin duhu da ya mamaye ko ina.A cikinsa Dadda ke ci gaba da jan hannunta suna tako cikin caɓo har suka isa wani tabkeken Teku sai duk suka ja suka tsaya.A wannan lokacin duka idanun IZZATU uku a buɗe suke,murya na ɗan rawa ta ce “Dadda ina ne nan kuma kika kawo ni?” Idon Dadda suna fitar da wasu ruwan hawaye ta ce “asalinki shalele zo mu je” sai ta ƙara janta suka fara ratsa ruwan har suka je tsakiya .Wasu mata ne suka fara yin da'ira suna fitowa daga ƙasan ruwan suna zagaye su. A tsorace IZZATU ta riƙe Dadda gam,ɗaya daga cikin matan ce ta matso tana cewa “kar ki ji tsoro ƴata,ba ki zo nan don a cutar da ke ba sai don nuna miki hanyar da ya kamata ki ɗauka sannan kuma mu buɗe miki taurarinki” sai ta kamo hannun Izzatun nan take ruwan suka yi wani irin juyawa kamar walƙiya suna fitar da wani irin sautin wuluuuk.Jiri ne ya soma ɗibar ta,ganinta ya dinga dissashewa , kunnuwanta suka fara jiyo mata waƙe-waƙen kwaɗo,wani ɓangaren kuma dariyar mutane ce ke fitowa daga can nesa da su garwaye da maganganun wasu mutanen daban suna magana kamar a lokaci guda.Can kuma komai ya tsaya cak,tunaninta ya yi duhu,igiyar da ke saita numfashinta ta katse.Ba ta ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi ta yi ta ganta kwance a kan gadonta wanda aka yi masa ƙawa da manyan kyandir sun zagaye shi suna ci da wuta.Izzatu ta yunƙura za ta miƙe ta ji wani abu mai taushi da santsi a cikin tafin hannunta,tana buɗewa ta ga wani jibgegen Kwaɗo ne kore sharrr da shi ya zubo mata manyan idonsa.... *Da zarar na saki last free page shikenan book ya dawo 500 ,don haka wanda ke buƙatar discount ya yi niyya ya yi payment 300 Via* 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +27795045822 🚫Ga détail nan na bada Please ki tura kawai kai tsaye ki bani shaidar biya ta WhatsApp, yan Nijar carte Moov ko airtel ta 300f [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 10 Wani irin matsanancin dokawa ƙirjinta ya yi,kamar kuma wacce aka yi wa dole ta ƙi jefar da Kwaɗon sai ma kallonsa da take yi ita ma kamar yadda ya zuba mata manyan idonsa. “Barka da safiya Queen!” ta ji wata siririyar murya irin ta maza,bakinsa ta ƙure da duba sai ta fahimci yana motsi kuma daga nan ne maganar ta fito. “Kar ki ji tsoro ni ne abokin ɗebe miki kewa ” ya sake faɗa . Ba tare da ta buɗe baki ba ta jefo masa tambaya ta idonta na tsakiyar goshi “wane ne kai? Mene ne haɗina da kai? Mafarki nake yi ko gaske?” Tana gama jero tambayoyin ya yi tsul ya sauka daga cikin tafin hannunta ya sauka kan ƙirjinta,kamar wani mutum haka ya ɗora tannuwansa kan haɓarta kafin ya ce “na kasance tsawon ƙarni biyu da wasu ƴan shekaru ina wanzuwa a wannan doron duniyar ta bil'adama,ba don komai ba sai don yi wa masu jinin prophecy jagora zuwa tsoffin asirai da wasu ɗaiɗaikun musulmi suka yi amfani da su waɗanda suka sha banban da sauran waɗanda ki ka sani.Ba mafarki ki ke yi ba,a zahiri ne ki ke tare da protector ɗinki,babbar alaƙata da ke ita ce jagora” yana gama faɗar haka ya wani turo bakinsa gaba sannan ya tsirta mata yawunsa masu yauƙi,da wani mugun sauri ta rufe ido tana mai yin wata irin ƙara saboda zafi da raɗaɗin abin da ta ji ya game mata fuskar kamar wuta. A hankali fuskarta ta soma canza launi tana rikiɗa zuwa kore kamar dai jikin kwaɗo,tsawon lokaci kafin ta dawo normal . Ta buɗe idonta tana mai jan numfashin wahala kafin ta tashi zaune, wannan karon kuma cike da murna ta ɗauko Kwaɗon ta ɗora a tafin hannunta kiss ta yi masa a goshi kafin ta sauka ta ɗauko ƴar ƙaramar jakarta wacce a duk inda za ta je tana maƙale da abarta a ciki ta jefa shi kafin ta shiga wanka.Sai bayan ta fito ta yi sallah tana tsaka da shirya wa Dadda ta shigo hannunta riƙe da ganyen bishiyar floris. “Daga ina haka tun da safe?” Izzatu ta tambaya tana mai saka doguwar riga. Dadda ta ce “ke ya kamata na tambaya ina zuwa da farar safiya?” “Na warware zan koma bakin aikina,saura ke ki faɗa mini ina ki ka je?” Dadda ta ɗan ja baki kafin ta ce “dajin tsira na je,ungo wannan itaciyar sirri ce ki dinga tafasa ta kina zuba ruwan a cikin shayin Yarima ” Wani kallo Izzatu ta soma yi mata,Dadda ta dungure mata kai ta ce “yana da muhimmancin ne a rayuwarsa kin ga ke ma in kina so za ki iya sha” Izzatu ta turo baki kafin a shagwaɓe ta ce “shi ne tun can ba ki taɓa bani ba sai yanzu da Yarima ya zo? To na ƙi na sha ɗin shi kaɗai zan saka ma tun da kin fi sonsa fiye da ni ” Dadda ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “haba shalelena!” Izzatu ta mayar mata da martani kafin ta fice,tana tafe tana rangaji har ta isa sashen Yarima. Falonsa ta soma sharewa ta goge ta saka turare sannan ta shiga kitchen ta soma haɗa masa breakfast kamar yadda aka ɗora mata nauyin dukkan abin da ya shafe shi.Tana aiki tana karatun Alkur'ani cikin taushin murya da daɗin amo. ★YARIMA Bayan na gama bincike akan babyn littafin sirri ban samu komai ba haka na kwanta lamo ina tunanin abubuwan da suka ƙunshi rayuwata a haka bacci mai ya ɗauke ni ban shirya ba sai kuma na tsinci kaina a wata duniyar wacce ba ta bil'adama ba. A gaban idona babyn littafin sirri ta fito ta daga cikin page ɗin ta zo ta yi tsaye a gabana,a hankali take daɗa girma har ta zama matashiyar budurwa sai dai baƙin dogon gashin kanta ya rufe mata fuska hakan ya hana ni ganin ainahin face ɗin nata .Wasu fitinanun kayan bacci ne a jikinta waɗanda suka fallasa ni'imar da baiwar da Allah ya zuba mata.Cikin abin da bai fi minti biyu ba casbin hankalina ya katse ,nutsuwata ta gushe jikina na ɗan rawa na jawo ta gare ni ta faɗo kan ƙirjina ina shirin yaye gashin gaban goshinta ɗakin ya ɗauki duhu sai hannuwanta da na ji suna yawo a duk illahirin jikina.Cike da tsimin abin da ban taɓa jinsa ba a siffar normal ni ma na dinga mayar mata da martani har ta kai na kusance ta.Ba wai iya cikin baccin ba ne na samu gamsuwa a'a har a zahiri ina jin daɗin mu'amulantar juna da muka yi. Ina gama samun kaina na farka daga baccin,da baiwa Izzatu na ci karo ta juya kenan za ta fita da sauri duk illahirin jikinta kuma rawa yake.Da na dubi jikina sai na ga ko albarkar blanket ɗin rufa babu,ƙila kuma ta ga yanayina ya canza ne a yayin da nake bacci.Ko kaɗan ban yi ƙoƙarin tsayar da ita ba,tana fita na miƙe cike da ƙyanƙyami ina jan tsuki na shiga toilet na cire kayan jikina na yi wanka na ɗauro towel na fito. Gaban makeken madubina na yi tsaye wanda aka cika da mayukan gyaran fata da Kuma turaruruka.Ina tsane jikina ina kuma kallon siffata ta madubin,duk da ina baƙi amma ina da kyau da kuma nagartar da duk wata ƴa mace za ta so mijinta ya kasance da ita.Amma duk da haka wani irin tsoro ne nake ji kar na je wa da EZRA da buƙatata amma ta watsa mini ƙasa a ido duba da yadda na hango zallar ƙiyayyata a ƙwayar idonta.Na ja dogon numfashi kafin na soma shafa mai da turare,bayan na gama na je gaban drower na zaɓi kayan da zan saka da kaina saɓanin kullum baiwa Izzatu ce ke fitar mini da su.Ina gama kimtsawa na fita falo,can rakuɓe jikin kitchen na hange ta tana magana ita ɗaya don babu kowa kusa da ita.Ba tare da na ɗauke idona a kanta ba na je na yi zaune,sai kuma a lokacin ta farga da wanzuwata.Ta sunne kai ƙasa kafin ta fara takowa inda nake,ta ɗan tsaya nesa da ni kaɗan kafin ta ce “barka da fitowa ranka shi daɗe ” “Sunana David in kuma ba za ki iya faɗa ba kawai ki ce Yarima ” na faɗa ina mai kallon yatsun ƙafafuwanta,wani irin yarrr na ji sakamakon ganin wani sirri a tattare da baiwa wanda ba kowacce mace ke da shi ba. “To yallaɓai!” ta furta tare da juyawa ta shiga kitchen na bi bayanta da kallo a zuci ina cewa ‘bawan da zai samu wannan baiwar ya ji daɗinsa ya samu macen zinare ’ Ba ta wani jima ba ta fito hannunta riƙe da babban faranti,akan table ɗin gabana ta dire shi kafin ta soma haɗa mini shayi mai kyau sai dai aka samu akasi wajen rawar jikinta shayin ya zube mini a ƙirji.Ido kawai na rumtse yayin da kuma nake jin shashekar kukanta haɗi da hannunta yana goge mini rigar. Cikin kiɗima da tsantsar tashin hankali take cewa “yi haƙuri don Allah, wallahi ba da niyya na yi ba.Hankalina ne ba ya jikina amma na yi maka alƙawarin ba zan sake aikata wannan kuskuren ba,don Allah kar ka hukunta ni ” Ba tare da na buɗe idona ba na ji wani sashe na zuciyata na bani wata shawara da ta dace da halin da nake ciki ,ba tare da wani dogon tunani ba na buɗe ido ina mai haɗe rai na yi mata wata uwar tsawa wacce ta saka ta yin baya ta faɗi ƙasa kanta ya bugu a jikin table nan take kuma jini ya soma yi mata zuba. Ba tare da ɓata lokaci ba ta ɓare baki ta shiga yin kuka,wanda zan ce shi ne raunina a game da ita don duk lokacin da na ganta cikin yanayin nan tana tuna mini ne da Joyel. A hankali na sauko na soma ƙoƙarin tsaya da jinin ,sai dai ɗan kusanci da na samu da ita yasa na soma jin wata irin kasala na rufe ni.Na ɗan ja baya kaɗan na ce “je ki toilet ki wanke kayanki duk sun ɓace da jini,ki kuma wanke jikinki ” Ba tare da ta ce komai ba ta miƙe za ta nufar waje,na dakatar da ita na ce “ki je can ɗakina” ta yo baya tare da nufar bedroom.Ta kai kamar minti biyar da tafiya kafin na take mata sawu,tsaye na yi ina jin motsin ruwa kafin na ƙarasa a bakin ƙofar zuciyata na ɗan dokawa. A hankali na duƙa na soma leƙa ƴar hudar jikin handle,kusan suman tsaye na yi ganin baiwa Izzatu a tsaye gaban madubi daga ita sai pant ko bra babu amma ta juya wa ƙofa baya. Das ! Das! Das! Haka bugun zuciyata ke tafiya ina Allah-Allah ta juyo don in ga abin da nake kwaɗayin ganin.Sai dai da dukkan alamu ciwon goshinta take ƙoƙarin rufewa,ƙugunta na duba wanda ya sha duwatsu ƙananu masu masifar kyau sai wani walwali suke yi. Kamar wacce ke yi da gayya haka take ɗan motsawa sai ta yi kamar za ta juyo sai kuma ta koma daidai,a haka na shiririce ina kallonta ina haɗiyar yawu ina jin kamar na shiga ciki na same ta. Yadda ƙafafuwana suka yi mini mugun sanyi yasa na lalaɓa na jawo blanket tare da kwanciya kan doguwar kujera na yi wa ƙofar toilet ƙuri da ido.Har sai da na fidda tsammani sannan ta fito da jiƙaƙun kaya,amma da dukkan alamu ma ba ta ankare da ni ba. Fanka ta kunna ta yi tsaye daidai saitinta,ɗan juyawa ta soma yi tana yarfa ɗan maidaicin hijabinta ruwan ne suka soma feso mini a fuska,na lumshe ido ina jin ƙamshin turarenta na ƙara saukar mini da kasala.Ina cikin wannan hali sai ji na yi an faɗo mini ana kiran sunan. “Wai Allah jiri nake gani!” ta furta tare da ƙanƙame ni,yadda ni da ita ɗin duk jikinmu bai da ƙwari yasa muka mirgino muka faɗo ita ke ƙasa ni kuma a kanta.Kusan a tare muka buɗe ido da ita sai dai ta yi saurin mayar da nata ta rufe ƙila ko jirin take ji,yayin da ni kuma muradina ya fi ƙarfin nagartata kawai na sauke bakina kan nata. Yau ne karon farko da na taɓa jin son sumbatar mace,kuma yau ne farko da na fara.Babu wani tunani a cikin kwanyata banda na gusar da ƙishin da nake ji, wannan yasa kamar mayunwacin zaki haka nake kissing nata.Sam banda wata saurar nutsuwar da za ta sa na farga halin da take ciki, burina kawai na sani.Ina dab da cire mata sutura na ji wani masifaffen zafi ya ratsa gefen wuyana,babu shiri na mirgina gefe na dafe wurin da ke yi mini zugi. Sinadarin ganina yana daf da rufewa na ga baiwa Izzatu ta kwasa a guje ta fita.Cikin dauriya da kuma jarumta na soma motsa bakina ina karanto ɗalasiman tsafi nan take na yi balaguron ruhi,na fitar da ruhina na bar gangar jikin nan kwance yayin da kuma na yi azamar tare baiwa Izzatu da ke dab da ta fita da katafaren sashena.Daidai nan free page ta ida duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 ko kuma a turo katin mtn na 500.Don Allah duk wacce ke buƙata ga detail nan kawai ta tura sai ta bani shaidar biya. *NB:* yanzu nake rubuta shi ,da zarar kuma ya zama complete 1k ne farashinsa.